*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* *₦500 ne, via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143* "Meyasa baka ɗau maganar mahaifiyarka da muhimmanci ba, har kake yi mini wannan barzanar a bayan idonta? Ko ba komai tana tausayina wataƙila ta san me nake ji game da sabir" ta saka idonta cikin nasa, wanda hakan ya sanya musu faɗuwar gaba a tare, cikin jarumta da ƙarfin hali ta daki motar Adam ta ce "Idan har bayan mutuwar anty aisha an yi umarnin a kashe sabir, na ɗau duk wani riski Allah ya dafa mini na kuɓutar da shi, kana tunanin bayan kuɓutarmu ne wani zai haɗa kai da ni a cutar da yaron da na ɗaukarwa babarsa alƙawarin kula da shi? Wace irin zuciya ce a jikinka?" Ma'aikatan wurin ne suka tunkarosu, amma adam ya dakatar da su, saboda rumaisa ta faɗi wani abu mai muhimmancin gaske. "Kai ka san abun da ya haɗani da kai ai tun farko, kuma ban janye abun da nace ba, ba zan taɓa janyewa ba kuma. Sabir idan ka ga dama ka kai shi bangon duniya, ka yi duk abun da kake ganin ya dace. Mara imani ban taɓa tsanar abu a duniya ba kamar kai, ko ƴan bindiga da na zauna a hannunsu wataran suna mutunta ni. saboda furucin da ka yi a kaina, wai a haɗa baki da ni a cutar maka da ɗa, na gode daga yau ba zan sake zuwar muku gida ba in sha Allah, in dai ni ƴat halak ce mama ce ta haifeni su yaya usman ne yayyena ba zan sake zuwa gidan nan ba" ta ɗauko maganar tiryan-tiryan ta ƙarasa da shirme, tana kuka ta juya ta nufi gate ɗin. Jikin Adam yayi sanyi, tabbas a abubuwan da ya faɗa sun ɗan yi tsauri. Da sauri ta fice tana kuka, ta bi hanya, dan ko za a kasheta ba zata hau motarsa ba, wata irin wutar ƙiyayyarsa ke cigaba da azalzalar zuciyarta, duk wanda zai yi yinƙurin rabata da sabir, to babban maƙiyinta ne. Sashin Mummy ya shiga yana ɗan tunani, lokaci-lokaci kuma yana murmushi. Mummy ta kalleshi ta ce "Bani labarin wannan murmushin, dawowar nan ta yi maka daɗi kenan?". Ya sake yin murmushi ya ce "Wata yarinya na haɗu da ita da zan shigo, na fita yanzu na kuma ganinta, gaba ɗaya zubinta da character ta abun dariya". Mummy ta kalleshi cikin nutsuwa ta ce "Ko ka fara soyayya ne?" Ya ce "Soyayya kuma? Yarinya ce ƴar ƙarama fa, amma abubuwan da ta faɗa ya bani mamaki, wai ita ce ta dawo da jaririn nan da ake ta surutu a kai, na aisha turaki, wai ta zo ta ga ɗan ta, ya ce idan ta zo kar a sake bari ta shigo. Yarinyar mugun ƙarfin hali ne da ita, maganganunta sam ba irin na shekarunta bane, akwai shirme a maganganunta, amma akwai hikima a cikin shirmen na ta. Ba abun da ya bani mamaki kamar yadda ta iya riƙe rigata cike da ƙwarin gwiwa take tuhumata a zaton ta wancan gayen ne". Cikin rashin fahimta Mummy ta ce "Wai kana nufin wadda ta zo da jaririn aisha a gidan nan? Ka ce yarinya ce ƙarama?". "Eh, wannan ai sai kun fi ni sani ku da kuke cikin gidan, ni ban san komai a kan zancen ba, kawai dai na san yarinya ce dan ta yi wutar duniya, ba za ta fi shekara sha uku ba, a nawa tunanin" "What! Kana nufin ƴar shekara sha uku ce ta zo da jaririn da ake cewa na adam ne? Amma rainin hankalin mutanen nan yayi yawa, ta yaya ƴar shekara sha uku za ta kuɓuto da jariri daga hannun'yan bindiga". Mahmud ya ɗage kafaɗa ya ce "I don't know". "Amma tsaya, yarinyar tana nan haryanzu ne, ina buƙatar in ganta" "Mummy ki ganta ki yi mata me? No need dan Allah ki daina shiga sabgoginsu da bin diddigin sai kin san abun da suke ciki, shiyasa suke raina ki, ki ƙyalesu su ji da matsalar su" yayi maganar yana miƙewa. Bin sa da ido mummy ta yi, amma da ta iya cewa komai ba. Sai mamaki da sake jinjina lamarin giwa da ɗanta saboda zallar goge hadda, wai ƴar shekara goma sha uku ce ta kuɓuto da jariri. Rumaisa kuwa tafiya kawai take yi tana kuka, dan ta ji zafin maganganun takawa matuƙa. Ta kusa titi kawai ta ji an danƙi hannunta, a fusace ta ɗaga kai, amma kan ta yi wani yinƙuri ya fara janta, a fusace ta fara kokowar ƙwace cikin tsiwa take cewa "Ka cikani me na yi maka?". Ba zata manta fuskar sidi ba, wanda suka taɓa kamota suka kaiwa takawa. Bai saurare ta ba, ya buɗe bayan motar takawa ya jefata, ya rufe motar, Adam ya sauke glass ɗin motarsa ya jinjinawa Sidi kai, sannan ya rufe glass ɗin motar ya fara ja. "Malam ka tsaya in sauka daga motar nan, bana son ka kaini gidan ka sauke ni bana so" banza yayi mata ya cigaba da tuƙinsa. "Na ce maka ka sauke ni, wai kai meyasa ka ke mini haka ne? Ka sauke ni" Ganin bashi da niyyar kulata, ya sanya ta fara kiciniyar buɗe motar, amma ta ji ƙofar motar a rufe gam. Adam a zuciyarsa yake jinjinawa masifa da taurin kan rumaisa, da a buɗe motar take haka za ta buɗe ta ce za ta fita. Ganin ba za ta iya buɗewa ba, ta zauna ta cigaba da kuka tana ƙanan maganganu. Bai tsaya a ko ina ba sai ƙofar gidan su, mamaki take yi a ina ya san gidansu?. Ko da yayi parking bai fita daga motar ba, sannan kuma bai buɗe motar ba, rumaisa ta hau kiciniyar buɗe ƙofar motar, amma ta ji a rufe. "Ka buɗe mini in fita" ta kai masa duka dan takaici. Danna wayarsa ya hau yi, na wani ɗan lokaci sannan ya buɗe motar ya fita. Sai dai ya kulle rumaisa a ciki, bai buɗeta ba, bubbugawa tayi ta yi, amma ya fita ya tsaya ya ƙi saurarar ta. Aliyu ne ya fito daga cikin gida, yana ganin Adam ya faɗaɗa Murmushin sa, ya ƙaraso suka gaisa, rumaisa ba ta iya jin mai suke cewa, amma sun ɗan jima suna tattaunawa sannan ya buɗeta ta fito tana wani basarwa. Wani mugun kallo Aliyu ya yi mata, sannan ya ce "Sai ki wuce ki shiga" ko a jikinta, ta yi gaba dan ita yau ko za'ayi mandaƙo da ita tun da buƙatar ta ta biya shikenan. Wani wawan burki ta yi, da ta ga mai sunan Baba a ƙofar ɗakin mama, yana gyara botirin hannun rigarsa. Wani irin mugun yawu ta haɗiye, ta fara takawa a hankali kamar hawainiya. Fuskarta ƙarara ta bayyanar da tsantsar tsoro da razanin da take ciki. Aliyu ne ya yi sallama da shi da Adam, mai sunan Baba ya amsa ba tare da ya ɗago ya kallesu ba, sai ma ja da yayi da baya ya basu hanyar shiga falon mama. Bai kula Adam ba, shi ma bai kula shi ba, suka shiga ɗakin mama da sallama, da gudu rumaisa ta bi su tana waiwayen mai sunan baba. Mama ta faɗaɗa murmushinta tana yi wa Adam barka da zuwa. Ya ce "Tuba nake mama, tun da aka bar asibiti ban samu na zo na gaisheki ba, abubuwa ne sun yi mini yawa ƙwarai da gaske" Mama ta ce "Babu komai, ya gida ya hajiyar take? Ya kuma mai gidana". "Duk suna nan lafiya, ta ce a gaishe ki" Rumaisa ta kalleshi a ranta ta ce "Kalleshi, kamar ba yanzu ya gama wulaƙanta ni ba, har da shigo mana gida ya zauna, yana washe baki dan ace masa mutumin kirki". Mama ta ce "Rumaisa duba kitchen, ki kawo masa ruwa" sai da ruma ta ji kamar ta yi fitsari, saboda kar ta fita mai sunan baba ya kamata. Sai da ta leƙa ta ga baya nan, sannan ta shiga kitchen da gudu, ta ɗauko pure water ɗaya, ta dawo ta tsaya a kan Adam ta miƙa masa. Kallon da mama ta yi mata ne ya sanya ta rasa in da za ta sanya kanta, dan gaskiya a tsorace take sosai. Da ƙyar ta sake komawa, ta zubo ruwan a wani ƙaton baho, kusan guda goma sha biyu, ta ɗauko ta zo ta dire masa. Aliyu ya ce "Wai ke wace irin taɓaɓɓiya ce ne? Ya zai yi da wannan ruwan babu plate a kitchen ki ɗoro masa ko huɗu ne, sai ki yi wannan shirmen?" Adam ya ce "Rabu da ita, yanzu zan tafi nima, daga gida nake Alhamdilillah a ƙoshe nake, dama ammi ce ta sanya na dawo da ita gida,kamar yadda na kira Aliyu a waya na yi masa bayani, maimakon ta je makaranta ta taho cikin gari ganin sabir, kuma ta tafi a ƙafa wanda akwai hatsari a hakan, mussaman da yanzu yakamata ace tana ƙarƙashin tsaro sosai, na kawota ne a ɗan ƙara sanya ido a kanta sosai, a kula da ita kar a sake bari ta zo, idan tana buƙatar ganinsa ayi waya za a kawo mata shi. Sannan makarantar su ma yakamata ce, sun bibiyi abun da ya sanya ba ta je ba yau, kamata ya yi ace sun kira gida" Aliyu ya ce "Makaranta suna iya ƙoƙarin su, ita ce dai kamar ƙanwar aljanu, saboda rashin ji da kafiya, duk abun da idan ta san za ta yi ayi magana shi take yi. Kuma makarantar ta gwamanti ce, suna da ɗalibai sosai babu lallai ma su san ba ta zo ba" Mama ta ce "Ai idan ba ta je ɗin ba suma hutunsu ne, mun gode sosai da sosai, in sha Allah za a sake kulawa, hakan ba zata sake faruwa ba". Ran rumaisa ya ɓaci, yadda su mama ke ta ce mata fitinanniya a gabansa, salon ya sake rainata. Babu wanda ya san da shigowarsa, sai gani suka yi yayi sama da rumaisa yayi waje da ita, tana ihu. Adam ya bi mai sunan baba da kallo, ganin yadda ya ɗaga rumaisan kamar ya ɗaga kara. Aliyu ya ce "Madalla, dama tun da ki ka dawo baku haɗu ba, ai gara ya tuna miki yana nan". Adam ya ce "Amma wannan ɗaukar da yayi mata, kar ƙashinta ya samu matsala, tun da ba ta gama warwarewa ba" "Da zai samu matsala, da ba ta kawo yanzu ba da hannun a jikinta, zata yi facing displine master". Da fari ruma tana ta kiran sunan mama, tana bashi haƙuri, amma da yayi mata wata irin tsawa tuni ta nutsu ta rufe bakinta. Ruwa ya saka ta janyo, ta cika wani ƙaramin bokiti, ya ɗora mata a ka, ya tsayar da ita a rana, ya sanya takalmansa ya fice. Hirarsu suka cigaba, babu wanda ya sake bi ta kan rumaisa, duk da mama a cikin ranta, ta ɗan ji tausayin ruman. Sai da suka ɗan taɓa hira, a kan abubuwan da suka din ga yawo a kansa a social media, haka nan yake yabawa da nutsuwar mama, tare da jinjina mata raino da tarbiyyar wannan zaratan mazan su bakwai itakaɗai, kuma wasunsu na karatu wasu suna sana'a a yanzu haka. Hakan ya sanya yake jin tana da wani experience na rayuwa, a ɗan haɗuwar da suka yi a asibiti, da yadda take magana yanzu, ya sanya ya fuskanci surutun rumaisa yana da nasaba da rayuwa cikin mazan nan, wanda kowa da kalar tunaninsa da kuma irin halinsa. Ga uwa uba yadda mama ke bayanin wasu abubuwan da ya shafi ƙasa, sai ka ce wata babbar mai kwalin karatu ce, amma wai kawai jin radio da bibiyar labarai ya sanya take sanin abubuwa sosai a kan lamarin ƙasa. Adam ya yinƙura ya ce zai tafi, mama ta ce "Gashi ka zo bamu ko sauke abincin rana ba, kuma ka ce wurin aiki zaka koma, Gadanga ko ka kusa sauke shinkafar?" Aliyu ya ce "A'a da saura, kuma ga miya ma, ko wani abun za a sayo maka?" Adam ya ce "Kai ka ke yin girki? Ka iya girki?" Yayi maganar cikin mamaki, dan shi ko gas tsoron kunnashi yake balle girki. Aliyu ya yi dariya ya ce "Ko in zo ammi ta ɗaukeni kuku ne? Ba abun da ban iya dafawa ba" Dariya suka yi, Adam ya tashi ya ce "Kar ku damu, a ƙoshe nake sai anjimanku". Mama ta ce "A'a tsaya" Ta shiga ɗakinta ta fito da tasar turare, da kuma dabino lubiya a leda ta ce "Ga turare ka shafa, dabino kuma a bawa hajiya" Adam yayi murmushi ya ce "To na gode sosai mama, Allah ya saka da alkhairi" Aliyu ya rako shi tsakar gida, hannun ruma sai rawa yake da bokitin ruwa a ka, ta haɗa uban gumi ga hawaye ya wanke mata fuska. Kallo ɗaya Adam yayi mata ya kawar da kansa, suka fita. Sai da suka fita sannan Adam ya kalli Aliyu ya ce "Ku sauke mata ruwan nan, za ta galabaita da yawa, ta yi tafiyar ƙafa nisa sosai" Aliyu ya ce "Ai wannan ruwan babu wanda ya isa ya sauke mata shi sai wanda ya ɗora mata, ka ƙyaleta ba jin magana take ba". Bai kuma cewa komai ba suka yi sallama ya tafi. Yana tafe a hanya yana tunani a ransa, abun da rumaisa ta faɗa ɗazu ne ya dawo masa, idan har za a ce a kashe sabir, ta tsaya ta kuɓuto da shi, mai zai sa a haɗa baki da ita a cutar da shi? Waye ya ce a kashe shi, kuma saboda me?" Ya tambayi kansa. Basar da tunanin yayi ya cigaba da tuƙinsa. Mama kuwa tun da takawa ya tafi, ta saka rumaisa a gaba da faɗa, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba. Ta kai a ƙalla awa ɗaya da rabi, sannan mai sunan baba ya kira Aliyu a waya ya ce rumaisa ta sauke ruwan nan. Ba punishment ɗin da mai sunan baba ya sakata ne ya sanyata kuka ba, idan ta tuna wulaƙanci da maganganun da takawa yayi mata a kan ɗan sa, sai ta ji ranta ya ɓaci sosai, wasu hawayen takaici su cika mata ido. A haka su Huzaifa suka dawo daga makaranta suka tarar da rumaisa, idon nan jawur dan ko abincin rana ta ƙi ci, ta koma gefe kawai tana kuka. "Ke wai me aka yi miki, meya sameki?" Huzaifa ya yi maganar yana zungurinta da ƙafarsa. Banza ta yi masa taƙi kula shi. Yasir ya ce 'Mama me aka yi mata ne? Ko ba ta da lafiya ne?" "Lafiyarta ƙalau, tsagwaron iskanci ne da rashin mutunci kawai ke ɗawainiya da ita, tun da ita har abada a rayuwarta sai ta yi abun da za a zageta ace ba ta kyauta ba take jin daɗi. Yau ba ta je makaranta ba ta wanke ƙafa ta tafi cikin gari, wai ta je ta ga Sabir, saboda rashin kan gado a ƙafa" Yasir ya ce "Kaii, yaushe na rakaki gidan ki ka ganshi yau ki ka koma musu gida, anya kan ki ɗaya kuwa?" Ganin duk sun tarar mata ya sanya ta ƙara sautin kukanta. "Zaki rufe mini baki, ko sai na jibgeki tukuna" mama ta yi maganar a matuƙar fusace. *** Ko da su iman suka dawo daga makaranta yau, gaba ɗaya sun lura da yadda ammi ba ta walwala, kamar akwai wani abu na damunta, nusaiba ma ta lura da hakan, sai dai iman ta kasa jurewa sai da ta magantu "Ammi, wata matsalar ce ta kuma tasowa ne?" Ammi ta ce "Me ki ka gani?" Gani na yi kamar wani abu na damunki, kamar jikinki duk a sanyaye yake. "To, damuwa dai ba a rasata Iman, tausayin yarinyar nan nake ji" Nusaiba ta ce "Wace yarinyar?" "Rumaisa, yarinyar da ta dawo da sabir?" Iman ta ce 'Ni dai ban taɓa ganinta ba, amma wani abun ne ya sameta?" "A'a, sai dai ina tsoron kar wani abun ya sametan a dalilinmu, son da take yi wa yaron nan har tsoro yake bani, yau tun daga gidansu har nan ta zo a ƙafa wai dan ta ga yaron nan, ina tsoron kar mu ɗau hakkinta" Nusaiba ta ce "Too ikon Allah, tana da ƙarfin hali gaskiya". Ammi ta nisa ta ce "Ashe Mahmud kuma ya dawo" Gaban iman ya faɗi, Nusaiba ta ce "Yaushe? Ganinsa ki ka yi?" "Ban ganshi ba, amma sun haɗu da rumaisa" Nusaiba ta ce "Mai ya ce mata?" "A'a ban sani ba, sun haɗu dai ta zata takawa ne, shikenan dai ina son in ɗan fita an jima, zan je gidan turaki" Iman ta ce "Ammi me zaki je ki ce masa? Ko akwai wata matsalar? Kin san mama tana ganinki za ta fara tunanin wani abu" "A'a ina buƙatar ganinsa ne kawai, kuma ai ni ba wurinta zan je ba". "To shikenan, a dawo lafiya". Kafafen sada zumunta suka cigaba da ɗaukar hazo, a kan lamarin mutuwar aisha, adam yayi iyakar ƙoƙarin sa, wurin kawar da kansa a kan abun da yake faruwa. Yana zaune a cikin motarsa, ya nutsu yana duba social media da yadda ake ta surutai a kan lamarin, kwatsam! Ya ci karo da posting ɗin Senator Usman wakili yayi posting a shafinsa yana yi wa adam ta'aziyyar mutuwar matar sa. *A madadina da iyalaina, ina miƙa saƙon ta'aziyyata ga ɗaya daga cikin jami'an tsaronmu, Adam Sharif Galadima bisa ga rashin matarsa, ina fatan Allah ya yi mata rahama ya sanya ta huta, sai dai abun mamaki ne ace matar jami'in tsaro kamar wannan, da ya tsayawa ƙasa ace matarsa ta mutu a hannun'yan bindiga, wannan babban abun kunya ne ga ƙasa baki ɗaya* Nan da nan mutane suka shiga tofa albarkacin bakinsu, in da suka dinga jinjinawa senator wakili na yi wa adam ta'aziyya duk da yadda ya sako shi a gaba, da ƙoƙarin binciko laifukansa. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya adam ya sauke, ya sake shafa fuskar wayarsa yayi sama, ya sake cin karo da gidan jaridar da suka fara wallafa cewar ya kashe matarsa, sun sake wallafa labari kamar haka. *Lauje cikin naɗi, Abun da Kamar wuya gurguwa da auren nesa, ace babban jami'in tsaro guda, ayi garkuwa da matarsa ba tare da sanin hukuma ba, a ƙaddara an ɓoyewa duniya, domin gudun abun kunya ace jami'in tsaro ya gaza bayar da kariya a gidansa balle ƙasa, me zai sa ace an ɓoyewa hukuma, idan har rayuwar matar jami'in tsaro ba ta da amfani an gaza ceto ta su kuma sauran al'ummar ƙasa su ce me?. Ayshercool.* MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* A hankali ya rufe datarsa, ya yi shiruu yana tunanin mai ya yi wa mutane haka, da har wasu suka sanya rayuwarsa a gaba suka mayar da ita hanyar su ta neman abinci. A hankali ya ajiye wayar ya kunna motarsa ya tafi. Baba uwani ce durƙushe a gaban Mummy, jikinta sai rawa yake yi, Mummy ta dubi baba uwani ta ce "Uwani me ki ke nufi ne? Ƴan kwanakin nan duk wasu ayyuka da na sakaki ba kya iya yi mini, sannan babu wani rahoto da ki ke kawo mini" "Tuba nake ranki ya daɗe, ayi mini afuwa, ayi mini aikin gafara". Ta ɗan ja numfashi ta ce "Yarinyar da aka ce ta zo da ɗan wurin Adam an ce ta na zuwa gidan nan haka ne?" Baba uwani ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Wallahi ba na ce ba uwar ɗakina, kin san yaron ko fito da shi daga sashin giwa ba ayi, babu wata hadima da aka amincewa zuwa in da yaron yake, ciki har da ni, dan haka ba na ce ba, amma akwai wata yarinya da take yawan zuwa, ban san alaƙarsu ba, amma zan iya cewa ita ce dan kuwa kwanaki na ji an ce za a kaita wurin mai girma turaki, amma abun da ya sa ban gazgata ita ce ba, yarinya ce fa sosai bana tunanin ita ce". "Ba tunaninki nake son ji ba, abu ɗaya zan saka ki, daga yau idan ki ka sake ganin ta zo, ki yi gaggawar zuwa ki sanar da ni, bana son ta zo ta bar gidan nan ba tare da na sani ba". "An gama ranki ya daɗe, in sha Allah zan sanar da ke" "Saura wannan karon ma ki tsaya shashanci, tashi ki bani wuri " jiki na rawa baba uwani ta tashi ta bar ɗakin. *** Jamil ne zaune a turakar turaki, bayan sun gaisa, ya ɗan gyara zama ya ce "Allah ya taimake ka, wata magana nake son mu tattauna idan babu damuwa" Turaki ya jinjina masa kai ya ce "Ina sauraronka". "Dama na ce game da riƙon ɗan wurin aisha, a hannun giwa yaron zai zauna kenan su cigaba da riƙonsa?". Turaki ya ce "Eh, wannan hukunci in da zai zauna mahaifinsa ne yakamata ya yanke, ya rasa matarsa bai kamata ɗan kuma a saka masa ido a kan sa ba" "Amma, ba kwa tunanin yana da kyau a sanya ido, idan maganar aure ta taso ya auri wadda za ta riƙe yaron da amana ta kula da shi?" "Adam ba ƙaramin yaro bane ba, na san zai samo mace mai mutunci da kirki, ba zai auri wadda za ta cutar da yaron ba". Jamil ya sake gyara zamansa ya ce "Amma ina ganin ku yakamata ku zaɓo wadda za ta maye gurbin aisha, kuma a ganina Samha ita yakamata ta maye gurbin aisha, a wannan karon yakamata a ba ta wannan damar" Turaki ya ɗan yi shiru yana nazarin maganarsa, ya ɗago ya ce "Ka zo da magana kai ma, amma ka bari zan yi tunani a kai, kuma zan yi magana da shi in sha Allah, Allah Ya sanya hakan ya zama alkhairi" "Amin ya rabb, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana" Turaki ya jinjina masa kai tare da ɗan yin murmushi. Duk wani ƙoƙari da dagewa, rumaisa tana yi wurin ganin ta kawar da tunanin sabir daga zuciyarta, amma abu ya ci tura, kullum sake jin ƙaunarsa take da tunanin sa a cikin zuciyarta. Idan ta tuno da maganganun adam sai ta ji ina ma za ta iya zuciya, ace ko kallon sabir ba zata sake yi ba, balle ta ɗauke shi, amma ina sai ta ji ba zata iya ba, yanzu ma kawai daurewa take yi. Gashi yanzu an ƙara mata tsaro, wataran mai sunan baba da kansa yake makaranta, islamiyya kuma tare da su huzaifa suke tafiya dan haka ba damar satar hanya. Haka za ta ɓoye ta yi kuka wasu lokutan dan tana kewar sabir sosai da sosai. Yau asabar tana ta shirin tahafiz, mama ta ƙwala mata kira tana daga ɗaki. Rumaisa ta shiga ɗakin, mama ta miƙa mata waya ta ce "Gashi Gwaggo ce za ta yi magana da ke". Rumaisa ta karɓi wayar ta kara a kunnenta ta yi shiru. "Hello rumaisa" "Na'am". "Ja'ira ki na ji na ba zaki yi magana ba" Rumaisa ta ce "Ina kwana" "Lafiya ƙalau, ya ki ke ya ƙarfin jiki?" "Na ji sauƙi ai, har na koma makaranta ma" "Ahh to Alhamdilillah, ya firgitar da ki ke yi fa cikin dare kin daina?" "A'a ina yi wataran" Gwaggo ta ce "Subhanallah, ki din ga addu'a sosai da sosai, dama zama a cikin wannan dajin ai dole ki yi gamo, wataƙila ma kin kwaso makarai. Zan saka a haɗo miki magunguna, a haɗo miki da kayanki a kawo miki". Da sauri rumaisa ta tari numfashin Gwaggo ta ce "A'a gwaggo, kar a kawo mini kayan nan yanzu, ki ɗaure mini su, ki ɓoye su sosai, kar ki bari wani abu ya same su, zan gaya miki lokacin da za'a kawo mini" "To shikenan babu damuwa in sha Allah, zuwa sati mai zuwa zan aiko miki da magunguna" "Ni fa lafiyata ƙalau, ba wasu aljanu da na kwaso" "Idan ma kin kwaso ai ke ba zaki sani ba, kuma idan aka kawo magani ki ka ƙi yi, da kaina zan zo har kanon na zane miki jikinki" Rumaisa ta yi shiru, gwaggo ta gama maganganunta, ta miƙawa mama wayarta ta ɗau jakarta ta fice zuwa makaranta. *** Ringing ɗin da wayarsa take yi ne ya sanya shi farkawa daga baccin da yake yi, a hankali ya yi miƙa ya buɗe idonsa, ɗan guntun tsaki ya ja, dan ya ji haushin katse masa barcin da aka yi. Ya miƙa hannu ya ɗau wayar, ya ɗaga ya saka a kunnensa. "Assalamu alaikum warahmatullah, barka da safiya" "Yauwa barka" ya amsa murya can ƙasa. "Ya gida ya ƙoƙari" Cikin ƙosawa ya amsa da "Alhamdilillah, waye?". "Khalifa Usman wakili ne, na kiraka ne domin yi maka ta'aziyya tare da jajanta maka abun da ya faru da kai". "To ka saɓa lamba, ba wanda yakamata ka kira ɗin ka kira ba" Khalifa ya ce "Na sani, ba Mahmud Sharif Galadima ba ne?" "Eh, Adam sharif galadima yakamata ka kira" "Ba laifi bane idan kai ma an yi maka ta'aziyya ai, abun da ya shafi adam ya shafeka" "Kai ka ga, abun da ya shafe shi shi ya shafa, ku je can ku yi abun ku, don't ever involves me, ba na son fuska biyu, wataƙila da har zuciyarka da gaske ka ke ka kirani ka yi mini ta'aziyya sai in amsa maka, amma kowa ya san abun da yake tsakaninsa da mahaifinkaa da kai kanka, jiya mahaifinka yayi masa ta'aziyya a kafafen watsa labarai, kai kuma yau ka kirani wai kana yi mini ta'aziyya bana son munafuncinku na ƴan siyasa, kar ka sake kirana" ya yi tsaki ya kashe wayar ya ajiye. Ya tashi zaune yana mamakin tsabar rashin kunya na wasu ƴan siyasar, ya san da biyu ya kira shi, ba dan Allah ba. Ya miƙe ya shiga banɗaki domin ya yi wanka. Ya gama abun da yake yi, ya fito ya shirya, ya fita falo domin karya, a falon ya tarar da Samha da Fauziyya ga ruky da Mummy sai hira suke yi, kuma da alama hirar ta su na da alaƙa da takawa. "Wai ku ba ku da wata magana sai ta mutum ɗaya? Look for something else mana, kowa adam adam ku bar shi ya ji da abubuwan da suka dame shi". Gaban Mummy ne ya faɗi, yaushe Mahmud ya fara damuwa da lamarin adam?. Fauziyya ta ce "Kawai muna ɗan yin hira ne a kan yadda abubuwa ke ta faruwa da shi, social media ma sai zancen ake yi". "Ni ma yanzu wannan yaron ya kirani, ɗan gidan wakili wai yana yi mini ta'aziyya, na ce kar ya sake kirana bana son munafunci da fuska biyu". Waro ido Samha ta yi ta ce "Khalifa wakili kuma?". "Shi fa, kar ma ya kuskura ya sakani a shirmensu ni buɗe masa aiki zan yi, rukky kawon breakfast zan karya" 'Mai wakili yake nufi da kiran Mahmud a waya wai zai yi masa ta'aziyya?' Samha ta tambayi kanta. Tashi ta yi da sauri ta ce ta na zuwa, ta fice ta bar sashin zuwa harabar gidan, ta kira Khalifa a waya. Sai da ta kira shi sau biyu sannan ya ɗaga. "Wai me kake aikatawa ne da ka ke ɓoyewa?" "Kamar me fa?" Ya tambaye ta cikin ko in kula. "Kai ka ke sponsoring ake ɓatawa adam suna a gidajen jaridu ko?" "Meye shaidarki na ni nake hakan?" Cikin fushi Samha ta ce "Waye idan ba kai ba?" "A tunaninki ni kaɗai ne maƙiyin adam? Ai ba mahaifina kaɗai yake da burin tozartawa ba, dan haka bani da lokacin sponsoring ɗin wasu gidajen jaridu su ɓata masa suna". "To me kake nufi da kiran ƙaninsa wai kana yi masa ta'aziyya, shi ma janyo shi zaka yi cikin tsiyar ta ka?" "Wow, kuna tare kenan few hours da kiransa har kin samu labari" "Ka ga, kashedi zan yi maka, kar ka kuskura ka sanya Mahmud cikin shirmenka, na san ba zai wuce an ce maka baya shiri da shi da adam ba, amma ka sani har abada jini ya fi ruwa kauri, adam jininsa ne kuma ko ba jininsa bane ba, Mahmud ba irin wanda zaka yi wasa da su ba ne ka cimma burinka". Khalifa ya yi dariya ya ce "Jini ya fi ruwa kauri, wane irin jini ne tsakanin ki adam da har ke ake wasan da ke? Ko daa yake wata kusan ta fi wata ai, and ba ke zaki gaya mini abun da yakamata na yi ba da wands ba zan yi ba, ina da abun yi yanzu, see you later" ya kashe wayar sa. Ajiyar zuciya Samha ta yi ajiyar zuciya cike da takaicin biye wa Khalifa tun a farko. *** Rumaisa ce zaune da wandon uniform ɗin islamiyya a jikinta, sai vest tana suyar wainar fulawa ita da Abdallah. Ta ce "Yaya Abdallah ka san me nake sha'awa?". "A'a sai kin faɗa" yayi maganar yana zuba ƙullin wainar a kasko. "Ina so in ji na ce basir ne da ni, ya tayar mini" Tsaki ya ja ya ce "Mahaukaciya ba zaki yi hankali ba, kin san meye basir ciwo ne fa". "Eh, kawai dai burgeni yake yi, idan na ji an ce ina da basir" "Sai ki yi ta yi ai, ba ki san masifar da ke cikin sa ba, ki je ki ji da yawon gudawarki da ki ka saba ba yau ba gobe, ya fiye miki alkhairi a kan ace basir ne da ke" Tura baki ta yi, ta saka hannu ta gutsuri gefen wainar fulawa ta saka a baki, Abdallah ya ce "Kin ci a taki" "Ƴar wannan ɗin?" "Eh, uban wa ya ce ki ci ba a raba ba?" Ta miƙa hannu ta ce"To bari na cinye guda ɗayan na ci a tawa" ya buge mata hannu ya ce "Baki isa ba uwar son zuciya" Sallama suka ji, suka amsa gaba ɗaya, maman habiba ce, rumaisa ta gaisheta ta amsa mata cikin sakin fuska, tare da tambayarta ina mama. Rumaisa ta ce "Mama tana cikin ɗaki ki shiga" Bayan ta shige, Abdallah ya kalli rumaisa ya ce "Ina fatan ba wani laifin ki ka aikata ba?" "Ni ba abun da na yi". "Wallahi idan ƙararki ta kawo sai kin daku?" Shiru ta yi masa ta hau lasar yaji. Maman su habiba ta ɗan daɗe, sannan ta fito, mama ta rakota sai dai fuskar mama babu walwala, ruma sai da ta ɗan tsorata ta yi zaton ko ƙarar ta ta maman su habiba ta kawo, amma bayan tafiyarta ta ji shiru mama ba ta yi mata faɗa ba. Amma gaba ɗaya maman ta sauya, damuwa sosai ta bayyana a kan fuskarta. Rumaisa ta ce "Mama ƙarata a ka kawo miki ne? Wallahi ban yi wa kowa komai ba" Mama ta ce "A'a ba ƙararki aka kawo ba" "To menene, na ga ba kya son yin magana" "Bakomai". Gaba ɗaya suka lura da yadda mama ba ta walwala, duk wanda ya tambayeta menene sai ta ce bakomai, mai sunan baba kawai ta iya gayawa abun da yake damunta. Washegari da safe, bayan tafiyar rumaisa makaranta, jikin mama ya tashi, sai da aka kai ta asibiti likita ya dubata, sannan suka dawo gida. Kusan kwanaki biyu kenan mama babu lafiya, babu walwala har rumaisa ta fara koke-koke. Cikin ƙarfin hali mama ta ce "Ba zaki yi mini Addu'a ba sai ki sakani a gaba kina kuka?" "To ba kin ƙi gaya mini abun da ya same ki ba?" Mama ta ce "Ai na ce miki bakomai, amma shikenan tun da ba zaki yi mini Addu'a ba". Rumaisa ta cigaba da kukanta, yayin da mama ta samu bacci. Wayar mama ce ta fara ringing rumaisa ta ɗaga sai ta ji muryar ammi. Suka gaisa ammi ta ce "Rumaisa ina maman taki?" "Bacci take ba ta da lafiya" "Subhanallah, meya sameta?" "Taƙi gaya mini" Rumaisa ta yi maganar tana fashewa da kuka. "Ya salam, yi haƙuri ki kwantar da hankalinki in sha Allah za ta ji sauƙi, ki daina kuka kin ji ko?" Rumaisa ta amsa da "To". Lokacin islamiyya ya yi aka gama girki, rumaisa ta ga abincin ba nama ba kifi, ba salak, ta ƙi ci, ta je ta shanye youghurt ɗin da aka sai wa mama ta kasa sha. Ta saka uniform ta tafi islamiyya. Da yamma ta yi suka dawo daga islamiyya, mai wanke-wanke ya kama, mai ɗora girki ya ɗora. Rumaisa na  yin sallama ta tsaya a tsakar gida ta ce "Me nake ji haka kamar warin daddawa?" Huzaifa ya ce "Mama ce ta ce tuwo take sha'awa, shi za ayi yau". "Taɓ mama ba ta da lafiya amma ta rasa mai za ta ci sai tuwo?" Abdallah ya fito daga kitchen ya ce "Uban me ya hana ki cin abincin rana?" "Abinci ba kifi ba nama, ba salak kawai tsuransa ni ba na ci" "Iyeee ashe da gaske Huzaifa yake, ɗazu mai sunan baba ya tambayi abincin waye Huzaifa ya ce naki ne kin ce ba zaki ci ba ba kifi ba nama, ya ce zai gamu da ke idan ya dawo" "Ku dai kullum burinku ku ga mai sunan baba yana tagayyara ni, ai shikenan" Ta shiga ɗakin mama da sallama, "Mama ya jikin?" "Da sauƙi, shi ne ki ka ƙi cin abinci ko ruma, ke idan baki samu abun da ki ke so ba ba zaki ci ba ko?" Rumaisa ta girgiza kai ta fara cire kayanta. Sallama aka yi mama ta amsa, rumaisa ta shiga uwar ɗakin mama da gudu, dan ta tuɓe daga ita sai phant za ta canza kaya. Ammi ce ita da iman da Nusaiba, iman na rungume da Sabir. A gurguje rumaisa ta canza kayan ta fito tana tsalle. "Oyoyo yau ammi ta zo gidanmu" Murmushi ammi ta yi tana faɗin "Ƴar gidan ammi, maman sabir" Ta durƙusa ta gaida ammi, ta amsa mata cikin sakin fuska. Mama ta ce "Bisimillah ku zauna" Suka zauna su Nusaiba suka gaida mama, mama ta amsa musu cikin sakin fuska. Ruma ta ce "Ammi ya aka yi ki ka san gidan nan?" "Baban sabir ne ya saka yaronsa ya kawo mu, na ce bari mu zo duba mara lafiya" Ruma ta fita da sauri, ta samu plate ta zubo musu ruwa, ta kawo musu tana ta murna. Mama ta bi ta da kallo, ta tuna iskancin da ta yi da adam ya zo gidan. Ammi ta ce "Ke maman sabir ya ki ka bar ƴan maza da aikin gida?" Ruma ta ce "Idan na yi gwaleni za su yi su ce bai fita ba, shiyasa nake bar musu aikin su. Ammi wannan wacece?" Ta yi maganar tana nuna iman. "Ƙanwar takawa ce, ita ce ƴar autana" "Tubarkallah mai kyau da ita" iman ta yi murmushi ta ce wa ruma "Ina wuni?" Ruma ta zaro ido ta ce "Kai ki ka gaishe ni, ni fa yarinya ce, kin ma fini tsawo". Dariya suka yi mata ammi ta ce "Ki daina gaya musu kar su raina ki, ai kin girma tun da ke maman sabir ce" ruma ta yi dariya ta ce "Eh kuma haka ne, ai kunya na ji da ta gaishe ni". Ammi ta ce "Yau ba zaki ɗau sabir ɗin ba?" "Hmm, ai da ni na yi zuciya na ce ba zan sake ɗaukar sabir ba, baki san me babansa ya yi mini ba ne" Ammi ta ce "Subhanallah, me ya yi miki?" "Ƙyaleshi kawai ammi, ai ba zan iya zuciya da sabir ba, a bani masoyina na ganshi" ta ɗauke shi a hannun iman, ya cika hannu, suma baƙa ƙirin ta cika masa kai. Suna cikin magana mai sunan baba ya yi sallama. Wata irin razana iman ta yi da ya shigo ɗakin, wanda ita kanta ba ta san dalilin razanar ba. Ya risuna ya gaida ammi, sannan ya tunkari rumaisa, ya durƙusa ya riƙe mata kunne ya ce "Abinci ba kifi ba nama ba zaki ci ba ko?" Ya ajiye mata leda a gabanta ya ce "Ki kai musu su dafa miki wani abun, dan yanzu ma sai ki ce yayi sanyi ba zaki ci ba, tuwo ma ki ce ba zaki ci ba, ki yi ta wahalar da mutane babu dalili". Ta sunkuyar da kai ta ƙi magana. Ya dungurar mata da ledar ya sanya hannu ya ɗau sabir a kan cinyarta ya yi waje. Ammi ta din ga murmushi, gaba ɗaya rayuwar rumaisa burge ammi take yi. Kifi ne manya ya kai na dubu, mai sunan baba ya kawo wa rumaisa, ta tashi cikin murna ta tafi kai wa su yasir su yi mata wani girkin bisa umarnin mai sunan baba. Ammi ta dubi mama ta ce "Amma dai kamar akwai wani abu da yake damunki, bayan rashin lafiya ma" Mama ta ce "A'a, jinina ne ya hau" "A tunanina zuwa yanzu mun zama ɗaya, dukkanninmu iyayene, masu fuskantar matsalar iyali kala-kala, dan Allah idan wani abu ne ke faruwa kar ki ɓoye mini ko ba zan yi wani abu a kai na yi addu'a" Mama ta nisa ta ce "Babar ƙawar rumaisa ce ta zo, take gaya mini maƙwabtana na ta yaɗa jita-jita, wai rumaisa ciki ta yi, na kaita garinmu ta  haihu, muka ce wai saceta aka yi, wai Allah ne kaɗai ya san yadda muka yi da ɗan" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, maƙwabta kuma?" "Wallahi kuwa shi ne abun ya dameni, wai abun ya cika unguwa, sun ɓata mini sunan ƴa, na san rumaisa ba ta ji, amma ko kusa komai zaki yi wa rumaisa ba ta san hanyar lalacewa ba, balle ta yi ciki". Ammi ta ce "Wallahi ba sai kin faɗa ba, duk wanda ya ji maganar nan ya san son rai ce, ki yi haƙuri basu isa su ɓata mata suna ba, duk wanda yake son ta da gaske jita-jita ba zata hana shi aurenta ba, ki kwantar da hankalinki kuma kar ki bari ta sani, tun da da bakinta ta ce mini duk wanda yayi mata abu sai ta rama" shigowar rumaisa ɗakin ce ya sanya ammi sauya maganar. Suka miƙe zasu tafi, rumaisa ta ce "Ammi, an ɗora mana abinci fa, ku tsaya a gama" Ammi ta ce "Tuba muke, muna sauri ne, ayi haƙuri" rumaisa dai ba haka ta so ba. Suka fito zasu tafi, mama ta ce ina ga mai sunan baba yana waje da sabir. Suka fito aikuwa yana wajen, ammi ta ce "Iman karɓo sabir" Jikinta har rawa yake yi, saboda gaba ɗaya mai sunan baba tsoro yake bata. Kamar munafuka sai sunkuyar da kai take, ta miƙa hannu za ta karɓe shi, amma shiru bai bata shi ba. Sai da ta ɗaga kai suka yi ido huɗu, gabanta ya sake faɗuwa, har numfashinta ya tsaya na wucin gadi. Ganin yadda ta tsorata ta rikice, sai da ya bawa mai sunan baba haushi, shi ba dodo ba meye na wani tsorata. Ammi ta saka sidi ya buɗe booth, ya ɗebo cartons na lemo da kayan marmari, na dubiyar mama. Ammi ba ta tsaya ba, dan ta san mama cewa za ta yi yayi yawa, suka shiga mota suna ɗaga musu hannu. Tun da suka tafi ammi take saƙawa da warwarewa a zuciyarta, dole mama ta shiga damuwa, babu uwar da za ta ji daɗin a ɓata sunan ƴa a cikin unguwa dan wannan kawai sai ya hanata auruwa. Suna tafe Nusaiba da iman na ta yi wa rumaisa dariya, yadda take gudanar da al'amuranta da yadda yayyenta ke kula da ita. Tun a hanya ammi ta kira adam a waya, ta ce idan an yi sallar magariba tana son ganinsa. Kamar yadda ta buƙata ya je ya sameta, ta idar da salla tana lazumi, bayan ta kammala ta dube shi ta ce "Mai ka yi wa rumaisa ne? Take cewa da tana da zuciya ba zata sake ɗaukar sabir ba?" Ya kalli ammi ya ce "Wani abun ta ce na yi mata ne?" "Ba ta ce ba, amma abun da ta faɗa ya tabattar mini da wani abun ka yi mata" "Ba wani abu bane ammi, na mata gargaɗi a kan zuwa gidan nan ne? Idan aka fuskanci wacece, za'a iya ƙoƙarin citar da ita ko cutar da sabir ta hanyar ta". "Na ji, yanzu ba wannan ba ma, wata shawara na yanke a matsayina na uwa na kira ka na sanar da kai, ba dan kana da hakki a kan abun ba ma sai dai ka ji na zartar". "Wane hukunci kenan?" "Ina son ka auri rumaisa!!!" Ayshercool. *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin* *5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14.  Supplement na whitening/glowing skin* *15.  Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* *Littafin kuɗi ne, ₦500 ne via 0009450228 sai shaidar biya ta 08081012143, aisha adam jaiz bank, masu buƙatar vip kuma, zasu iya zuwa arewabooks su yi searching sunan littafin* Waro ido adam yayi yana kallon ammi, yana tunanin ko haluccinations ɗin da ya saba ne ba gaskiya bane, ya tsatstsare ammi da ido. "Ba ka ji me nace bane kake kallona?" "Amm..mmm wai wace rumaisa?" "Rumaisa dai ta zo da sabir, ita nake nufi" "Amma ammi nan da shekara nawa?" Ammi ta ce "Nan da abun da bai fi watanni uku ba in Allah ya kaimu" Adam ya ma rasa me zai ce, "Amma ammi yarinya ce ƙarama, me ta sani a kan rayuwar aure? Ta yaya zan yi rayuwar aure da ita" "Saboda kai abu ɗaya ka saka a gaba a zamantakewar aure ko?" Da sauri cike da jin kunya ya ce "No, ammi ba abun da nake nufi ba kenan, amma meye manufar yin hakan?" Ammi ta numfasa ta ce "Ɗazu muka je gidan su, mahaifiyarta babu lafiya a dalilin jita-jitar da ake yaɗawa, wai ciki ta yi aka kaita ta haihu, ni uwa ce na san raɗaɗin irin wannan abun. Abu na biyu kuma a duniya na san babu wata mace da zaka aura ta riƙe sabir da imani da amana kamar rumaisa, ba zan so sabir ya yi rayuwa irin wadda mahaifiyarsa ta yi" "Amma, Ammi yarinyar nan ta daɗe a hannun ƴan bindiga, Allah ne kaɗai ya san abun da suka yi mata tsawon wannan lokaci" "Ko sun yi mata wani abu, kai yakamata ka yi shahadar aurenta, ko dan albarkacin abun da ta yi maka. Sannan ka san dole za a saka mana ido, a fara zancen ka yi aure, ko ma ace gashi an baka mata, wanda idan aka baka bamu isa mu ce a'a ba. Dan haka kafin su motsa mu zamu motsa, idan ya so ko wani auren ne ka yi daga baya, amma ina son ka auri rumaisa ka inganta rayuwarta, ta yi karatu mai kyau mai zurfi, ka ciyar da ita abinci mai kyau, ta kwana a muhalli mai kyau, ba zamu biyata abun da ta yi mana ba, amma zamu iya kyautata mata". Adam ya ja wani irin gwauron numfashi, dan ya san akwai ƙura, ita kanta rumaisan ba lallai ta amince dan ta ce a duniya ba wanda ta tsana kamarsa. "Ka yi shiru ba ka ce komai ba" "Shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi". "Amin ya Allah, Ubangiji Allah ya yi maka albarka, Allah ya sanya ta zame maka alkhairi a cikin rayuwarku" jinjina kai kawai ya yi, bai iya amsawa ba ya tashi tafi. Tun da ya fita kansa har wani zafi yake yi masa, saboda tsabar caji da zafi, kamar shi ya auri wannan fitsararriyar yarinyar da take iƙirarin ta tsane shi. Lokaci ɗaya ya tuna yadda ƴan bindiga ke cin zarafin mata a hannunsu, Allah ne kaɗai ya san meyafaru da ita, duk da likita bai faɗi wani abu da ya shafi hakan a kanta ba lokacin tana asibiti, amma duk da haka ba shi da tabbas. Har lokacin kwanciya baccinsa yayi, ya nemi wuri ya kwanta, bacci ya gagare shi, tunani kawai yake yi, tayaya zai zauna zaman aure da wannan fitsararriyar yarinyar mara kunya, wadda ko magana ba ta iya ba, shi ga saurin fushi da zuciya tsaf zai ɓallata wataran. Baya son bijirewa ammi, sai dai har ga Allah amsa matan da ya yi ba har zuciyarsa bane ba, dan shi auren rumaisa a wurinsa zai ƙwaru da yawa. Shi a rayuwarsa ba shi da sha'awar zama da mace sama da ɗaya, sakamakon irin zaman da ya tashi ya ga yana yi a gidansu, ba ya son ɗan sa ɗaya ya tashi a irin yanayin da suka tashi na makircin matar uba. Hakazalika ba zai so ya zauna da mata biyu ya ƙwari ɗaya ba, ga uwa uba kishi da tashin hankalin mata shi ba zai iya ba, abubuwan kansa sun isheshi. Auren rumaisa kuma a yanzu gara zamansa a haka ba mace, ina amfanin yayi aure da matar da babu duk ɗaya, sai ma da yayi raino, dan wannan raino ammi za ta ɗauko masa, tun da ta ce ya kula da cin ta shan ta da makarantar ta, ban da haka shi bai ga mai rumaisa za ta tsinana a gidan aure ba. A hankali ya lumshe idanunsa ya na son bacci ya ɗauke shi, saboda tarin matsalolin da suke kansa, sun sanya har wani zafi cikin kansa yake yi masa. Yayi ta karanto adduoi, a hankali bacci ya fara ƙoƙarin ɗaukarsa, cikin barcin ya ji muryar rumaisa da kan yi masa gizo tana faɗin "Sarki mai koriyar alkyabba ka ɗanani a kan doki" da ire-iren maganganun ta, suka dinga kai komo a kunnensa. A hankali ya buɗe ido, haryanzu ya kasa daina mamakin yadda rumaisa take yawan yi masa gizo. Ya canza bugiren da yake kwance yana karanto adduoi, a take wani baccin yayi awon gaba da shi, sai dai a wannan karon aisha ya din ga mafarki, mafarkin ƙarshe da yayi da ita ya ɗan razana shi, aisha ya gani tana ce masa. "Takawa, dan Allah ka bawa rumaisa ɗan ta, kar ka ɗau hakkinta, bana son wata damuwa ta sameta, ita ce maganin damuwowinka, ko ba ka aureta ba kar ka rabata da ɗanta" a razane ya sake farkawa yana wani irin gumi, ƙirjinsa na bugawa da sauri. Da sauri ya saukko daga kan gadon, ya buɗe tagar ɗakinsa, ya zubawa harabar gidan ido, ya tuna abubuwa da dama da suka wakana, shekarun da suka gabata. Ganin bashi da wata mafita, ya sanya ya shiga banɗaki yayi alwala ya fito ya ɗau alƙur'ani. Ɓangaren ammi ma tsayuwar dare take yi, tana kaiwa Allah kukanta a kan iyalanta, dan addu'arta bayan nemawa kanta gafarar ubangiji, ƴaƴanta kawai take yi addu'a. Ta haɗa da roƙon Allah ya ɗorata a kan iyayen rumaisa su yarda da auren nan da take son haɗawa, dan a jikinta take jin rumaisa alkairi ce ga ɗan ta. Yau jikin mama da ɗan sauƙi, ruma sai shirin tafiya tahfiz take yi, su Huzaifa sun goge mata uniform ɗin, ta cika tsakar gida da waƙe-waƙe kamar an yi mata bushara da wani abu mai muhimmanci. "Ruma ki rufe mini baki da waƙe-waƙen nan, ki yawaita tasbihi, wannan surutan da waƙe-waƙen ba in da za su kai ki" "Mama ina tasbihin nan fa". "A'a, ni wasu lokutan ina raina ibadar da ki ke yi, ki na da ƙarancin ibada rumaisa, idan kina cikin farinciki ki yawaita ambaton Allah, dan wasu lokutan idan kana cikin matsala ko damuwa sai addu'a ma ta gagareka, ki din ga yawaita ambaton Allah ba waƙa ba" Cikin mamaki rumaisa ta ce "Mama yanzu sai damuwa ta yi wa mutum yawa ya kasa ambaton Allah, to ko a hannun 'yan bindiga, addu'a na yi ta yi musu, Allah ya ƙwatoni, amma ni mai zai dami mutum ya kasa addu'a " Mama ta yi murmushi ta ce "Rumaisa kenan, lokaci yana nan zaki gane abun da nake nufi". "Au fata ki ke yi mini" tayi maganar cikin tura baki. "Ya za ayi in yi miki fata, faɗa nake yi miki, ki ƙara nutsuwa". "To hajiya mama, yanzu dai ki bani kuɗin makaranta zan tafi" "Ke idan babu kuɗin makarantar ba zaki ba kenan?" Huzaifa ya tambayeta yana ƙoƙarin ɗaukar agogonsa. "Ni fa ba na son katsalandan ina ruwanka" "Ni kar ku yi mini faɗa, ki ɗauka ki tafi". Rumaisa ta ɗau kuɗin, ta fice tana hararar Huzaifa. Ammi ta din ga lissafin ta ina za ta ɓullowa wannan al'amari, turaki zata fara gayawa, ko kuwa ta fara nemo iznin majaifiyar rumaisa tukuna? Daga bisani ta yanke za ta fara tuntubar ɓangaren rumaisa, idan sun amince shikenan, sai dai tana fatan su amince ɗin ma. Takawa har garin Allah ya waye bai samu ya rintsa ba, abubuwa da yawa sun dame shi, kasancewar yau weekends ne, ya sanya karyawa ma a ɗakinsa yayi bai fita ko ina ba. Dama shi ba wasu abokai ne da shi ba, daga abokan aikinsa sai su jabir. Wayarsa ta cika masa kunne, duk da gandar da yake ji, da ya gaji da jin rurin wayar, sai da ya tashi ya ɗauko wayar ya duba. Kakin rundur ƴan sanda ne cp baba habu yake kiransa, adam ya ɗaga wayar tare da yin sallama. Cp ya amsa masa suka gaisa sannan ya ɗora da cewa "Adam kana garin nan kuwa? Wai ba zaka fito ka yi magana a kan abun da yake faruwa ba, sai sharri ake yi maka kala-kala kai kuma ka ƙi magana" Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Me zan ce? Ko na faɗa ba za a yarda da ni ba, ƙanin mahaifina ya fito ya wanke ni, amma ba a fasa surutu ba, me zan ce? Su yi ta yi idan sun gaji za su daina ne" "Kana nufin ba zaka ce komai ba?" "Ko na ce ba za a daina ba, ka ga maganar ba ta da amfani" Cp ya ce "Ai shikenan, ɗazu mun yi magana da commissioner, saboda sabon posting ɗin da gidan jaridar nan ke cigaba da fitarwa, na yi magana da manema labarai, na sanar musu hukumar ƴan sanda mun san da case ɗin, sai dai abu ne na sirri da ba ya buƙatar a fito ayi ta yayatawa, shi ya sanya muka yi shiru muka yi ta bincike, kuma haryanzu muna kan yi ma." Adam ya nemi wuri ya zauna a gefen gadonsa ya ce "To shikenan yallaɓai, na gode sosai da sosai" "Kar ka damu, ai hakkinmu ne baka kariya, kuma abun da muka faɗa hakan yake ai, Allah ya tsare, wannan ba wani abu bane ba duk aikin maƙiya ne, kuma ba za su yi nasara ba" Adam ya ce "Haka ne, na gode sosai" "Masha Allah, Allah Ya ƙara tsarewa" "Amin ya rabb sir, na gode" daga haka ya kashe wayar. Yana gama wayar ya ji zaman ɗakin ya ishe shi, dan haka ya fita domin ya gaida ammi ya ɗan fita. Duk a falon sashen ammi ya tarar da su, har ammin, ana koyawa Sabir zama an shiryashi cikin wasu kaya masu kyau, an zaunar da shi a gefen kujera, cikin dabara iman tana taje masa sumar kansa, sai kai hannu yake yana turewa alamar ba ya so. Adam ya fara gaida ammi, sannan ya ɗau sabir ya zauna da shi a jikinsa. Adam ya karɓi brush ɗin hannun iman, ya cigaba da taje masa kai, amma ya cigaba da kai hannu yana turewa yana son yin kuka. "Kai rigimamme, baka son gayu?" Adam yayi maganar yana murmushi tare da kallon ɗan nasa cike da ƙauna. Sabir yayi shiru yana kallonsa. "Yi mini dariya mana, an ce kana dariya amma ba ka taɓa yi mini ba" Ammi ta ce "Kai ai wannan ɗan naka kai ya yo, babarsa kawai yake washewa baki gaba ɗaya yayi mata dariya, har mamakin irin soyayyar da ke tsakaninsa da ita nake yi, da ya ganta har wani ƙara nutsuwa yake yi". A ransa ya ce 'Aikuwa ba zan ba ta riƙonsa ba, ya tashi a sangarce da rashin kunya kamarta ba' ya ɗaga kai yana kallon ƙwayar idon sabir, take aisha ta sake faɗo masa a rai, dan suna ɗinar kama da sabir, duk da ya fi kama da shi. Ammi ta ce "Ina ta magana ka yi shiru, tunanin me ka ke yi ne?" Yana ɗago ido Ammi ta ga hawaye kwance a idonsa. Cikin damuwa ta ce "Lafiya kuwa?" Yayi murmushi ya ce "Lafiya lau ammi" Ammi za ta yi magana, hadimarta ta shigo, ta durƙusa ta ce su Samha ne suke neman iso. Ammi ta ce, ace su shigo. Samha ce da ruƙayya, suka shigo tare tana ganin adam sai da ta yi hamdala a zuciyarta, ta wani lumshe ido, wata irin ƙaunarsa da soyayyarsa na sake ratsata. Suka ƙarasa, suka gaida ammi ta amsa musu cikin fuska, samha ta kalli adam ta ce "Yaya ina kwana?" Ta yi maganar cikin rausaya. "Lafiya ƙalau, kuna lafiya?" "Lafiya ƙalau, sabir na zo gani, ammi yaushe za'a kai mana shi ne? Na gaji da jiran na kasa jurewa". Ammi ta ce "Banda abunki samha, yaron ai haryanzu jariri ne, ba a haɗaku da jego ba". "Haba ammi, tun da muka rasa fulani ai shi ne madadinta" Ta matsa kusa da adam, za ta ɗau sabir a hannunsa, sai da ta taɓa shi, wani irin kallo take masa ji take kamar ta rungume shi, ko ta samu sassauci a kan abun da take ji game da shi. Ta ɗauki sabir tana yi masa murmushi, wanda a ƙasan zuciyarta ji take kamar ta buga shi da ƙasa, dan yadda ba ta ƙaunar uwarsa shi ma ba son sa take yi ba. Miƙa sabir yayi ya hau kuka, duk yadda ta so ta rarrashe shi yaƙi yin shiru, ya cigaba da kuka ba shiri adam ya karɓe ɗan sa, ta ji tamkar ta dunƙule hannu ta daki kan yaron ko ta huce. Cikin iya siyasa ta ce "Ammi wai har ya iya ƙyuya ne?" "To gashi dai ya yi miki, ɗan na ku ne ɗan ganin dama, ko dariyarsa babarsa kawai yake yi wa" Da sauri samha ta ce "Wace babar ta sa?" "Rumaisa, yarinyar da ta zo da shi" Jin an ambaci labarin da Mummy ke son ji ya sanya ruƙayya cewa "Ai ammi haryanzu tana nan?" "Tana nan mana, ina za ta je?" "To ammi zuwa take ta ganshi?" Kan ammin ta bata amsa samha ta ce "Ai an ce mini an kai ta wurin turaki rannan ko?" Ammi ta ce "Eh" Ruƙayya ta sake cewa "To ammi gidan nan take zuwa?" Maimakon ammi ta ba ta amsa sai ta ce "Ruƙayya an ce mini Mahmud ya zo gari ko?" "Eh ya dawo" Ammi ta ce "To masha Allah" Iman ta ɗauko baby carrier ta ce "Yaya kawo na saka shi a Carrier ko zai koma barci, na ga yana ta rigima dama yau da wuri ya tashi" Adam ya ce "Zo ki ɗau abunki iman, na fuskanci duk abin da na yi iman sai kin nuna mini ban iya ba, ni ban san a ina ki ka koyi raino ba, tun da mu dai ba jariri ne da mu ba" Iman ta yi dariya ta ce "Ni na isa?" "Gashi nan kuwa" yayi maganar cikin sigar wasa. Ya bawa iman sabir ya tashi ya bar falon, a rayuwar duniya samha ba ta kishi da aisha kamar yadda take yi da iman, saboda akwai alaƙa mai kyau a tsakanin takawa da iman, ga iman da kyau tamkar ita ta yi kanta. Suka gama zamansu, daga bisani suka tashi za su tafi, Samha ta ajiye wata leda cike da kayan sawa da na wasa, wai sabir ta kawowa, ammi ta yi mata godiya sannan suka tafi. *** Ba kowa a gidansu rumaisa, kowa ya fita da masu makaranta da sauransu, sai mama itakaɗai, kasancewar ta ji sauƙi, ya sanya ta ɗora abincin rana, dan ba ta son su dawo ba ta kammala abinci ba, yanzu ƙaramarsu babbarsu za ta zo ta fara kwanciya da tura baki ita yunwa. Sai dai babu tsammani ta ga kiran ammi a waya. Ta ɗaga wayar suka gaisa, ammi ta kuna yi wa mama ya jiki. Sun ɗan taɓa hira sannan ammi ta ce "Yauwwa maman rumaisa wata magana nake son mu tattauna da ke, duk da kamata ya yi na zo ƙafa da ƙafa, ina da wasu baƙi ne da zan yi yau, kuma maganar yakamata mu yi ta" Mama ta nutsu ta ce "To ina jin ki, Allah ya sa lafiya". "Yauwwa, zuwa wannan lokaci tun da Allah ya riga ya haɗamu, mun riga mun zama ɗaya, tun bayan da na baro ku, nake ta tunani a kan maganar da ki ka yi mini a kan rumaisa, da kuma wasu dalilai na makomar jaririn nan, shine na yanke shawarar mai zai hana adam ya auri rumaisa, kin ga maganar wata gulma da ɓacin suna ya ƙare, kuma kin ga za ta samu cikakkiyar damar kula da sabir kamar yadda take buƙata, amma me ki ka ce?" Jiki a sanyaye mama ta ce "Aure kuma rumaisan? Shekararta goma sha uku fa, kina ganin yadda ake fama da ita, ga kuma karatunta". Ammi ta ce "Maman rumaisa ba zai gagara ba, mu ma duk da ƙuruciyar aka yi mana aure, kuma ba abun da zai samu karatunta, za ta cigaba idan aka yi auren nan ni da adam za a yi wa alfarma kuma ina tabattar miki in Allah ya yarda zai zama alkhairi, yanzu amsarki nake jira, zan kai maganar ga magabatansa, tun kan ace za a bashi wata matar, ban san wa za a bashi ba, ko dan makomar rayuwar marayan nan". Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce "Haka ne, amma gani nake rumaisa ba za ta iya raino ba, ita ma ba hankali ta cika ba" Ammi ta yi murmushi ta ce "Babu damuwa, ai ba sakar mata rainon za a yi ba, ya zamana dai ta samu kusanci da shi sosai yadda take so". "To, bari yayyenta su zo mu tattauna, abun da suka yanke shikenan" Ammi ta ce "To, Allah ya sanya mu ji alkhairi, ina saurarenku dan da wuri nake son ayi komai a gama" "To shikenan, duk yadda muka yi zaki ji ni" tun da suka yi sallama mama ta kashe wayar take zullumi. Ayi wa rumaisa aure ta je ta yi me a gidan auren? Yarinyar da ban da zunzurutun ƙuruciya da wauta ba abun da yake damunta. A haka mama ta ɗora girkin nan, take aikin jikinta duk a sanyaye. Rumaisa ce ta yi sallama, ta shigo da jakar makarantarta a ka, tana yamutsa fuska. Mama ta kalleta ta amsa mata, rumaisa ta jefa jakarta ɗaƙi, ta cire hijjabinta ta kalli mama ta ce "Mama ki aika aje a yi wa mai ice warning ba ruwansa da ni, me na yi masa da idan na zo wucewa zai din ga cewa gata can, sau biyu yana yi mini, kar na yi abun da ba shikenan ba a zo ace na yi tom" tana gama maganar ta ɗau buta ya wuce banɗaki. Bayan ta fito ta kalli mama a taɓare ta ce "Mama wai ba a gama abincin ba, ni fa yunwa nake ji" mama ta bi ta da kallo tana hango rumaisa da aure. Ta gama taɓararta mama ta kammala girki, ta ci ta tafi makaranta, sai da yamma da mai sunan baba ya dawo, mama ta yi masa zancen. Aikuwa ya haɗe rai ya ce "Dama na san ɗawainiyar da suke yi da ita, dole a ƙarshe su nemi wani abu, wane irin aure yaushe aka haifi rumaisan da har za a wani ce a aureta, mutumin da faɗa suke yi ba sa shiri, kawai ki ce musu ba zai yiwu ba su yi haƙuri". Kasancewar usman yana nan ya ce "A'a fa ayi tunani, yarinyar nan kuna ganin abun da take yi a kan yaron nan, me ake nema a aure ne ba mutum na gari ba, kuma in da za a iya riƙeta ba, idan ta amince kawai ayi musu fatan alkhairi a nawa ganin, mussaman yanzu da ƴan unguwa suke ta ƙananan maganganu a kanta, wataƙila ana yi mata auren ta nutsu" Wani mugun kallo mai sunan baba yayi masa, dan haka yayi shiru, kuma tun da ya kafe a kan ba ya so, ba zai canza magana ba. Gaba ɗaya hankalin mama ya rabu biyu, kowannensu yana da gaskiya, ita kanta ba ta shirya rabuwa da rumaisa yanzu ba, dan Allah ya sani rumaisa ba za ta iya ɗaukar ɗawainiyar aure a yanzu ba, dan a sangarce take, sai dai kuma tana matuƙar jin nauyin ammi ta ce mata ba zata basu auren rumaisa ba. Ayshercool. 08081012143 *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Maganar ta yi ta damun mama, ta fara tunanin ko Abubakar za ta kira a waya, dan neman shawarar sa, dan ya fi sauƙin kai da fahimta. Har zuwa dare mama kallon rumaisa kawai take yi, gashi yau ɗin kamar rumaisan ta san abun da ake ciki, sai taɓara take kala-kala da ƙuruciya. Da daddare ta gama shimfiɗarta za ta kwanta, ta ɗaga ido suka yi ido huɗu da mama. "Mama wai na ga kina ta kallona?" Mama ta ce "Mhmm, babu komai". "Ko kin ga na ƙara girma ne?" Mama ta ce "Girman ne dai yake tinkaro ki". "A ina?" "Ba ko ina, yi kwanciyarki". Rumaisa ta yi miƙa, ta shige cikin net ɗin ta. Cikin hanzari mama ta ce "Ke meye haka?" Rumaisa ta yi zumbur ta tashi ta ce "Mama a ina?" "Meye haka, daga ke sai wando da vest, ba zaki ɗaura zani ko ki saka underwear ba?" "Kaii mama, kin tsorata ni wallahi, zafi fa nake ji" "To kuma sai ki kwana tsirara dan shirme, tashi ki saka zani ko kunya ba kya ji sai yayyenki sun shigo sun ganki a haka, ba kya jin kunya ma" "To mama ba yayyena bane ba" Haushi ne ya kama mama ta ce "Ke ubanki, kin tashi ko sai na zo?" Ba dan ta so ba, ta tashi ta ɗaura zani ta nemi wuri ta kwanta. Washegari da safe bayan tafiyar runaisa makaranta, suka yi waya da Abubakar, ya tabattarwa da mama cewa da azahar zai zo gida. Mama ta ji daɗin zuwan Abubakar sosai da sosai, saboda ya fi mai sunan baba sauƙin kai, da sauƙin fahimta. Bayan ya ci abinci ya huta, mama ta gabatar wa da Abubakar halin da ake ciki na batun son auran rumaisa. Abubakar ya nisa ya ce "To mama ai babu wani laifi a ciki, wataƙila a dalilin auren ki ga ta nutsu, ni kaina ba wai ina son a aurar da ita ba ne, amma bamu san mai Allah ya ɓoye a lamarin ba. Dan haka mama ki yi ta Addu'a tare da istikhara, sannan kuma a nemi amincewar ta, idan ta yarda shikenan" "Nima abun da nake tunani kenan, bana son takurawa a lamarin nan, mussaman yadda ake surutu a kan ta, kuma ina jin nauyin matar sosai. Amma dan Allah ka shawo kan ɗan uwanka, dan shi ba ya son sabgar". Abubakar ya ce "Karki damu mama, ki rabu da shi ki yi ta addu'a, idan da alkhairi Allah ya tabbatar mana" Mama ta amsa da Amin. Ammi ta cigaba da addu'a, tare da tsumayin jiran amsar da mama za ta bata. *** Hajiya Lubabatu ce ta kawo wa mummy ziyara har gida, in da suka ƙule a ɗaki suna tattaunawa tare da shirya mugunta kamar yadda suka saba. Hajiya Lubabatu ta ce "Wai dan Allah jamila zuwa yaushe zaki samo maganin nan mu koma wurin malamin nan?" Mummy ta ce "Rabu da ni kawai, na saka wannan shashashar matar, ta kasa samo mini ranar a gabana aka fito da maganin aka yi masa amfani da shi, amma na kasa ɗaukowa saboda suna wurin". "To yanzu shikenan kin fasa cimma ƙudurin birkita shin? Tun da dai malam ya ce aikin da kika buƙata ba zai yiwu ba sai an samu maganin da ake yi masa amfani da shi" "Ba fasawa na yi ba, yanzu dai kan wani abun na mayar da hankalina" "Wane abu kenan?" "Yarinyar da ta zo da ɗansa ce, Mahmud ya ce mini ya ganta a gidan nan, tana zuwa yarinyar ce da bakinta ta gaya masa, kuma har shi adam ɗin ya ce kar a bari ta sake zuwa, idan da gaskiya mai zai saka ya ce kar a bari ta sake shigowa gidan nan? Kuma ba wannan ba kin san meya fi bani mamaki?" "Sai kin faɗa" Mummy ta gyara zama ta ce "Wai yarinyar yarinya ce ƙarama, ba babba ba ce ba, tayaya ƙaramar yarinya za ta kuɓuto da jariri, kuma ace an hanata zuwa gidan nan, ni fa ina tantama idan ɗan nan ma da gaske ɗan sa ne, da ƙyar idan ba wata ƙulalliyar suka shirya ba, na ji haushin rashin sanin yarinyar tana zuwa gidan nan tun a baya, da na san yadda zan na haɗu da yarinyar nan" Hajiya Lubabatu ta ce "Kaii jamila, to ki yi mata me? Me za ta yi miki?" "Ahh in samu bayanai mana, yadda zan kar giwa, in tona mata asiri". "Ke ai ni lamarin giwar nan yana bani tsoro, hatsabibiya ce ta gaske" Mummy ta ce "Ni zan gaya miki hatsabibiya ce ta gaske, shiyasa na yi alwashin kawo ƙarshenta" Hajiya Lubabatu ta ce "Aikuwa sai mun cigaba da zagewa dan da alama ita ma a tsaye take, bari na tashi na tafi". Suka yi sallama ta tafi. Mama gaba ɗaya ta rasa ta ina za ta ɓullowa rumaisa balle ta yi mata bayani, ta san halin kayarta, idan ba ta so ba ana gabas tana yamma. Abubakar ya samu suna tsaka da hira da shi da mai sunan baba, ya yi gyaran murya ya ce "Ni kuwa mama ce ta zo mini da wani zance" Mai sunan baba ya ƙura masa ido, alamar yana sauraron sa. "Mutanen da ta zo da yaronsu, suna son a basu aurenta" "Kana goyon bayan hakan kenan?" Mai sunan baba ya katse shi. Abubakar ya ce "Ba maganar ina goyon bayan hakan bane, makomar jaririn nan za a duba" "Ita kuma ta ta makomar fa, karatunta da sauransu, kawai sai a aureta dan ta je ta yi raino, ita ba ta da ƴanci kenan? Ni dama tun da naga ana ta yi mata ɗawainiya na san akwai wata buƙatar da za su zo da ita, kuma guda nawa rumaisan take da za ayi mata aure yanzu?" "Sunna ne a addinance ko ka manta Sheikh? Early marriage is better than early fornication, ko an gaya maka wannan tsalle-tsallem da take yana nufin jikinta ba ya jin komai na girma? Bai kamata mu yi saurin yin adawa da lamarin mu yanke hukunci ba, Addu'a yakamata mu yi. Na san ka na sane da yadda ake yi da ita a gari, da mu baki ɗaya, wanda bamu da damar hana mutane cigaba da yaɗa jita-jita wanda dole ya shafi rayuwarta. Kuma batun karatunta bana tunanin wani abu ne da zai gagara, yanzu sai ka gama zaƙewar ita kuma ta ce tana so, mu yi mata fatan alkhairi, atleast za ta shiga gida mai daraja da muke sanya ran ya zame mata alkairi a rayuwa, kar mu rarrabawa mama hankali" Har Abubakar ya yi ya gama, mai sunan baba bai kuma kulashi ba, dan shi sam baya goyon bayan lamarin. Rumaisa tana shimfiɗa tana waƙe-waƙenta, mama ta kalleta ta ce "Idan kin gama shimfiɗar zan yi magana da ke" "Innalillahi, Allah ya sa ba wani abun na yi ba" "Ni dai na ce zan yi magana da ke" Rumaisa ta ajiye abun shimfiɗar, ta tafi gaban mama ta zauna ta ce "Gaya mini kawai hankalina ya kwanta" Mama ta ɗan yi shiru tana nazarin rumaisa, sannan ta numfasa ta ce "Ki na ji na ko?" Ta jinjina kai alamar eh. "Waya muka yi da hajiya, kakar sabir" Rumaisa ta yi murmushi ta ce "Hajiya ammi". "Eh, ta zo mini da wata magana ne, da dole sai da yardarki abun zai yiwu". "Ni kuma, menene to?". "Rumaisa, ta ce tana son ki auri baban sabir, ɗanta adam" "Eyeee wai wa? Ni ko wa?" Mama ta ce "Da wa nake magana?" Rumaisa ta ce "Taɓ Ubangiji Allah ya kiyaye, haka kurum duk ƙawayena ba ayi musu aure ba sai ni, sai ka ce a ƙauye, ba sai na yi tsawo na girma za ayi mini aure ba, sai ayi mini aure ina ƴar haka, to wallahi bana son shi, ba zan aure shi ba taɓ baki san wannan mutumin ba ne". Mama ta ce "Wai meye haɗinki da shi ne me yayi miki?" "Ni bana son shi ne, haka kurum idan aka yi mini aure na daina yawo yadda nake so, kuma wai fa komai ya ce sai na yi, to wallahi ni ba zai saka ni abu na yi ba, sai dai ya kasheni" Mama ta ce "Yanzu dai a cewa hajiyarsa ba kya so kenan?" Kai tsaye rumaisa ta ce "Eh" "To shikenan, je ki kwanta sai da safe" rumaisa ta tafi wurin kwanciyarta, tana ta yatsine baki kamar takawan ne a gabanta. Ita rumaisa jin abun ma ta yi kamar almara, ita banda a ƙauye ba ta taɓa ganin amarya yarinya ba, ko ta ƙauyen ma tafi ta girma, sai ita a wani ce za ayi mata aure, auren ma da maƙoyanta a fili ta ce "Taɓ Allah ya kiyaye, wallahi ba na son shi". Mama ta ce "Ai kin gaya mini na ji ko" "Au, na zata a zuciyata na yi maganar" har ta yi bacci tsaki take yi, da ganin an raina mata hankali. Da safe ta gama shirin tafiya makaranta, ta saɓa jakarta ta fito tsakar gida, ta tarar da mai sunan baba a tsaye, ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa mata ya ce wuce mu je. Ba ta ce komai ba ta yi gaba ya bi bayanta. Suna tafe a hanya ya ce mata "Mama ta yi miki wata magana ne?" Rumaisa ta ce "Eh mana, wai aure za ta yi mini" "Ke me ki ka ce mata?". "Ni dai na ce mata bana son shi, ai ba a yi wa yara aure" Mai sunan baba ya jinjina kai ya ce "Good, zan tsaya miki duk yadda za ayi kar ki yadda da batun auren nan, ki ce ba kya so kin ji abun da na gaya miki ko?" Ta gyaɗa kai alamar eh ya ce "Good, idan kuma ki ka amsa zaki ga yadda zan yi da ke" suka cigaba da tafiya. Ammi ta ɗan fara tsorata da shirun da ta ji, dan har ga Allah tun da ta yanke shawarar ta ji abun ya shiga ranta sosai da sosai, gashi haryanzu mama ba ta ce komai ba, gashi ba ta son yawan takura musu da ta sake kiran waya. Ko da ta yi wa adam zancen haryanzu gidansu rumaisa ba su ce mata komai ba ya ce "Ina ga basu amince ba, kawai ki ƙyalesu" "A'a idan ka ga na ƙyale, to na ga ba yadda zan yi ne, ni lamarin ya shiga raina sosai, ina saka ran da alkhairi a ciki". Adam a ransa ya ce Allah ya sa su ce a'a, dan shi har wata kunya yake ji idan ya tuna wai rumaisa za a aura masa. Gidan mama kai ya rabu biyu, Aliyu yana cikin waɗanda suke murna da abun, dan dama shi yana shiri da takawa, yayin da mai sunan baba Abdalla da usman suma suka ce ba su yadda ba. Yasir da Huzaifa kuwa, ba su ce eh ba ba su ce a'a ba, yasir ya ce gara ta tattara a aurar da ita mu huta. Huzaifa ya ce "Ni babban jin daɗina, gidan masu kuɗi ne, da wani ƙojalallen wahalallen ne wallahi ba zamu yadda ba, amma nan mu je mu ci kayan daɗi, wallahi dan ubanta sai ta yadda ba zata yi mini baƙin ciki ba" Rumaisa ta ce "Oho muku, ni dai bana son shi, kome za ayi". Yasir ya ce "Ba ke ki ke son mai kuɗi mai kyau ba, gashi ya zo ki ce ba kya so, ke kin san menene son ma?" Ta yi farat ta ce "Na sani mana, yanzu ba na ji ina son ku ba, ina son zama a gidan nan ba, ai shine son" Huzaifa ya ce "Ji shashasha mara kan gado" Abubakar ya ce "Ƙanwata, zo nan ki ji wata magana" Rumaisa ta koma wurin yaya Abubakar ta zauna. Ya dubeta ya ce "Dan rumana ki girma mana, ki daina biyewa su Yasir, shi lamarin rayuwa Addu'a ake yi, Allah ya zaɓa mafi alkhairi" Mai sunan baba ya fito ya ce "Ke tashi ki bar nan wurin, ta ce ba ta so, dole sai ka tursasata ta amsa ne?" Abu ya nemi ya zama faɗa, sai da mama ta shiga tsakani. Kasa jurewa Ammi ta yi, ta kira mama a waya take tambayarta yaya. Mama ta ce "To, ni dan ta ni babu matsala, tun da kullum Addu'a da fatan alkhairi ka ke yi wa yaro, sai dai yayyenta wasu sun ƙi yadda, ita kanta ƴar ta ki ta ce ba ta so, mai sunan baba kuma ya goya mata baya". Mama ta ce "Subhanallah, lamari bai yi daɗi ba, to shikenan ba damuwa" Ammi har ta kashe wayar ta ji ta kasa jurewa. Ta cewa Iman "Idan an idar da sallar magariba, ki shirya zaki rakani unguwa" Iman ta amsa da to, ammi ta kira takawa a waya, ta ce masa idan an idar da sallar magariba ya zo zai kaita unguwa, ya amsa mata da to. Mamaki ne ya kama takawa, da Ammi ta sanar masa da cewa gidansu rumaisa zasu je, ya fara tunanin mai zai saka ta ce su je gidan ba tsammani haka? Ya din ga addu'a Allah ya sa ammi ba yarfa shi za ta yi ba saboda yarinyar nan. Rumaisa kuwa ta fita sayen maganin sauro, daga zuwa soro ta ɗau keken Huzaifa ta tafi da shi sayen maganin sauron, shagon da za ta sayo ɗin a farkon layinsu yake, amma saboda tsabar neman magana ta ɗau keke. Ta shiga gida ba ko sallama ta fara da "Waye ya ajiye mini mota a wurin da zan yi parking ɗin kekena, saboda an rainani". Huzaifa ya ce "Uban wa ya saka ki ɗaukar mini keke, ban hanaki ɗaukar mini keken nan ba?" "Huzaifa kana da damuwa, wannan kwaraɓaɓɓen keken kamar wani mota, ka kwantar da hankalinka, zan saya maka mota wataran". Dalla wuce ki bani wuri, daga tsakar gida ta zauna ta ce "Mama ga maganin sauronki, canjin kuma na sayo coc zan sha, idan yaya usy ya dawo sai ya baki" Ta ji shiru mama ba ta amsa mata ba, ta ware murya ta sake cewa "Mama ga aiken, canjin na sai coc". "Ni zan biyoki tsakar gidan na karɓi aiken kenan?" "A'a, zan ajiye miki a kan window, idan kin huce zan shigo ɗakin, na san sai kin yi mini faɗa na kashe miki canji, kuma ba laifina bane raina ne ya biya ta ɗau sanyi" Mama ta ce "Zan kama ki ne" Rumaisa ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Mama da wasa nake miki, kwata na faɗa da keken, bari na ɗauraye ƙafata na shigo". Sai kuma ta ɗaga hanci sama ta ce "Hmmm warin turaren baban sabir nake ji". Huzaifa ya ce "Malama ki nutsu, wane irin turarene mai wari kuma?" "Kai yasin turarensa ba daɗi, tayar mini da zuciya yake" Daga ɗaki mama ta ce "Idan kin gama tsokanar tawa ki zo kin yi baƙi". "Baƙi da daddaren nan kuma wurina suka zo? Anya wannan baƙin alkhairi ne da daddare? Ai sai ace bani da gaskiya" ta je ƙofar ɗakin mama tana leƙewa, ta ga Adam da ammi sai iman. "Kaii ammi ke ce da daddare, Innalillahi amma baku ji me nake cewa ba ko?" Ammi ta ce "Bamu ji komai ba, ance ba a sonmu ban ga ta zama ba, na ce bari na zo ƙafa da ƙafa". Rumaisa ta shigo ta zauna daga wajen bakin ƙofa ta ce "Ammi ina wuni?" "Lafiya ƙalau maman sabir, kina lafiya?" "Lafiya ƙalau ammi, iman ya kike ina sabir?" Iman ta yi murmushi ta ce "Yana gida, yana gaisheki". Ammi ta ce "Rumaisa, yau gani ga ki ga baban sabir, ki gaya mini meyasa ba kya son sa? Gaya mini abun da ya yi miki?" Ruma ta kalleshi ta ce "hmm mama ki rabu da shi kawai, ni dai kawai bana son sa" "Ai ba a ƙiyayya babu dalili rumaisa, gaya mini meya haɗaku?" Rumaisa ta ce "Ammi kina ganin hantarata yake yi, yayi ta hararata" Adam kuwa takaici ne ya ishe shi, kamar shi, wai ake lallaɓa wannan ƙwailar yarinya wai ta aure shi, wanda da shi mai kule-kulen ƴan mata ne, da bai san iya adadin ƴan matansa ba. Ammi ta ce "Rumaisa, bani da nufin cutar da ke, har ga Allah ina matuƙar ƙaunarki, ba zan so abun da zai cutar da ke ba. Daga yanzu zuwa kowane lokaci magabata zasu fara yi wa adam maganar aure, bana son a bashi matar da zata wahalar da sabir kamar yadda mahaifiyar sa ta fuskanta. Kin ga aisha ina da alaƙa da ita, itakaɗai mahaifiyarta ta haifa ta rasu, ta sha wahala sosai a wurin matar uba, mahaifinta yana basarake amma ta kwana ba ta ci abinci ba. A kulle ƙofa ta wuni a haraba, banda duka da cin mutumci, ta sha wahala a rayuwa sosai da sosai, zaki so sabir ya fuskanci irin haka?" "To Ammi ba sai ki riƙe shi ba" "Rumaisa dole wataran zan bar duniya, ko bana so dole sabir ya koma hannun mahaifinsa, ba ni zaki duba ba, ba baban sabir ba ɗan ki. Zaki samu cikakkiyar damar kula da shi sosai ya zama naki" Wayar iman ta fara ringing, dan haka ta tashi ta fita waje amsawa. Rumaisa ta yi shiru tana tunani, ammi ta ce "Ba zan takura miki ba rumaisa, ba zan so ayi miki auren dole ba, idan baki amince ba shikenan, ba zan takura miki ba, na so dai ki zama ɗaya daga cikin iyalaina ne, ba takuraki zan yi ba rumaisa". Shiru ruma ta yi, ba ta ce komai ba. Har ammi ta fidda ran rumaisa za ta yi magana, dan takawa ya fara ƙulewa. Mama ta ce "Rumaisa ke fa ake jira ki yi magana". "Mama tsoro nake ji, ƴan ajinmu sun ce maza mugwaye ne, wai ba ƴan goyo bane, tsoro nake ji ni yarinya ce". Ammi ta yi murmushi ta ce "Ya danganta, kuma ba haka abun yake ba, ke kin yadda ba ƴan goyon bane? Ke yanzu ba ƙanwar maza ba ce, kalli yadda suke kula da ke fa, komai yi miki suke, da kin motsa damuwarsu a kanki take, da ba ƴan goyo bane, ai ba za su yi miki haka ba, ki yanke hukunci da abun da yake ranki, ba surutun mutane ba". "Ammi na amince!" Ayshercool. *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* *Littafin kuɗi ne, ₦500 ne, via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143* Cikin tsananin farinciki ammi ta ce "Da gaske rumaisa kin amince?" Ruma ta jinjina kai, ammi ta ce "Alhamdilillah, Alhamdilillah Ubangiji Allah ya yi muku albarka, Allah ya sanya muku albarka, in sha Allah tarayyar nan za ta zame muku alkhairi, Allah ya albarkaci rayuwarku". Mama ta amsa da amin. Mai sunan baba kuwa, yana so ya shigo iman tana tsaye a hanyar da zai wuce, sai waya take cike da iyayi da shagwaɓa, ya ɗan jira ta gama ya wuce, amma ba ta da niyyar gamawa dan ba ta ma san ya zo wurin ba. Ga ƙamshin turaren da take yi duk ya cika masa hanci, yana neman ya sanya shi atishawa. A ƙarshe dai ya ƙule cikin dakakkiyar muryarsa ya ce "Ke! Bani hanya zan wuce!" A razane ta saki wayar ta ja da baya, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. Cikin hanzari ta durƙusa ta ɗau wayarta da screen ɗin ya tsatstsage. Ammi tana ta zuba addu'a, amma jikin rumaisa ya yi sanyi, sai dai duk da jikinta ya yi sanyi, bai hana ta yin dariya ba. Ammi ta ce "Rumaisa, ya na ga kina dariya kuma, meya baki dariya ne?". Rumaisa ta ce "Mai sunan baba ne ya tsorata miki ƴa da wannan muryar ta sa" Tana rufe baki sai ga iman ta shigo jikinta yana tsuma ta ce "Ammi wayata ta fashe". Ruma ta ƙunshe baki tana dariya ta ce "Sorry, haka yake, ya daɗe yana jiran ki gama waya ya wuce, baki matsa ba, shi ne yayi miki tsawa". Ammi ta ce "Subhanallah, maman rumaisa haka baban nan naki yake, daga baƙunta sai faɗa, bai san autar tawa matsoraciya ce ba, ai shikenan bari mu fita sai a sai wata wayar". Mama ta ce "Hmm mai sunan baba ai sai dai Allah ya shirya, ƴaƴa ne gasu nan kowa da halinsa, ki yi haƙuri kin ji iman, ban ji daɗi ba wallahi" Adam ya ce "Ammi lokaci fa, ina son yau zan kwana a gida, zan yi wani aiki". Ammi ta ce "Haka ne, dare ya fara yi, rumaisa, ba zan fasa godiya ba, ubangiji Allah ya saka da alkhairi, Allah ya sanya muku albarka, sauran magana duk yadda ake ciki zan yi magana in Allah ya yarda. Suka fito tsakar gida, takawa ya kalli rumaisa wani takaici ya ƙule shi, wannan fitsararriyar abar ce zai aura. Yaya Abubakar ne ya shigo, ammi ta kalleshi ta ce "Malam faruku kai ne ka razana mini ƴa ko? Kuma ka ce baka son in haɗa auren ƴaƴana haba mai sunan baba laifin me muka yi haka ne" Abubakar ya yi murmushi ya ce "Ina wuni" "Lafiya ƙalau ya gida ya ƙoƙari?" "Alhamdilillah" Iman ta ɗan ƙura masa ido, kamar ba wannan ne mai muryar nan ba. Mama ta ce "Ɗan uwan mai sunan baba ne, shi gashi can a bayanki yana jinki, wannan dattijon arziki kenan malam habu" Ammi ta ce "Au, ashe fa ƴan biyu ne ai ni duk kama suke yi mini" ta waiwaya ta kalli mai sunan baba ta ce "Mun zo neman aure gidanku ka hana, a sassauta adawar nan ba a san in da rana za ta faɗi ba, ina da tarin ƴan mata a gidana kar ka zo neman aure nima na rama". Suka yi dariya gaba ɗaya, mai sunan baba ya ɗan sunkuyar da kai be ce komai ba. Ammi ta ɗora da "Dan Allah ayi mana addu'a, na samu duk sun amince in sha Allah lamarin nan alkhairi zai zama, tun da Allah a ka nufa da lamarin, ba za aji kunya ba, karatun rumaisa da komai zamu kula da shi, kuma adam zai riƙeta cikin mutunci da kulawa, mu sanya a ranmu wannan haɗin Allah ne, a tayamu da Addu'a". Mai sunan baba ya ce "Allah ya tabattar da alkhairi " Ammi ta ce "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, yauwwa mai sunan baba ko kai fa, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarku, ya baku mataye nagari sanyin idaniya, ya tsare mana ku daga sharrin zamani". Ya amsa da amin. Abubakar ya ce "Hajiya babu wata damuwa, har kullum alkhairi muke fata, kuma dama babban burinmu bai wuce rumaisa ta yi ilimi, sannan ta samu abokin rayuwa nagari ba, Allah ya sanya haɗin nan ya zama alkhairi". "Amin ya Allah, na ji daɗi sosai na gode da karamcinku, Allah ya yi muku albarka, Allah ya yayi muku jagora". Adam har ya fara ƙulewa, gaba ɗaya ya gaji so yake su tafi, har ya je ya kunna mota, amma ammi tana ciki tana ta faman hira. Iman tuni ta bi bayan Adam ta shige cikin motar, sai sauke numfashi take, saboda ba ƙaramin razanata mai sunan baba yake yi ba. Aka yi sa'a mama ta yi musu sallama ta fito, maƙwabtan su rumaisa har sun fara surutun, yawan zuwan da mota daban-daban take yi ƙofar gidan su rumaisan. Suna tafe a hanya ammi tana faɗin "Alhamdilillah, na ji daɗi an gama da wannan babin, gobe in Allah ya yarda zan je na samu turaki, sai dai dole mu yi shiru da bakinmu, babu wanda zai ji wa za ka aura, sai Allah ya kaimu lokacin". Adam a ransa ya ce "Sai ka ce wata matar arziki, ni dan ta ni ba wanda zai san ma an yi auren, wannan har wani aure ne" Ammi ita kaɗai tayi ta hirarta da farincikinta, Adam yana saƙe-saƙensa, iman kuma na cigaba da jin wata irin fargaba da bugun zuciya, a haka suka ƙarasa gida, yana ajiye su ammi ya ja motar ya juya ya tafi. Rumaisa kuwa tun da ta amsawa ammi, abun duniya ya isheta, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, mai sunan baba ya je ya turketa a ɗakin mama ya ce "Ya muka yi da ke? Shi ne ki ka yadda ki ka amsa ko? Ki je ki yi ba dai aure ba gaki nan gashi. Meye a cikin auren gidan sarauta ban da tarin ƙalubale da tsaface-tsaface ke da ko ciwon kanki baki gama sani ba, amma kin tari aradu da ka, ke ko tausayin rayuwarki ba kya ji, ki je ki ƙarata". A take jikin rumaisa ya kuma yin sanyi, wata irin dana sani ya mamayeta, tare da tashin hankali, wani irin tsoro ya shigeta dan ita kanta tun da ta amsa gabanta yake faɗuwa. "Mai sunan baba, ka daina tsoratata, duk abun da yak cikin littafin ƙaddarar bawa bai isa ya kauce masa ba, wataƙila ba dan dalilin auren nan ba za a saceta ba, wataƙila sanadin sai an yi auren nan ne ya sanya aka yi garkuwa da ita, kar ka sake ka ce zaka zafafa, ko ka yi jayayya da ikon Allah" Mai sunan baba yayi ajiyar zuciya, ya ji mama ne kawai, amma bai ji yana son auren nan a ransa ba. *** Samha kuwa ta saka Jamil a gaba a kan ya ake ciki game da zancen da suka yi, na son maye gurbin aisha. Jamil ya ce "Mun yi magana da mai girma turaki, sai dai ya ce na ɗan bashi lokaci tukuna" "Amma har zuwa yaushe tukuna? An kusan kwana goma da zancen fa, amma babu wani feedback" "To amma ai shi ya ce in saurare shi, bai kamata na cigaba da takura masa" Samha ta ce "Ya salam, wallahi yaya Jamil bana son a kuma samun matsala a wannan karon" "Babu wata matsala ai in sha Allah, dama ita Aisha Allah ya ƙaddara sai ya fara aurenta ne" "A'a yaya Jamil, ina tsoron Allah ina tsoron ya ce zai auri wannan banzar iman ɗin, kusancinsu yayi yawa fiye da yadda ka ke zato, tsoro nake ji wallahi, tsaf ammi sai ta ce a wannan karon ya auri iman". "Amma ai ya ce idan har zai iya auren iman to zai auri su nusaiba, kin ga ya harantawa kansa auren iman kenan". Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Babu tabbas yaya, komai zai iya faruwa fa" "Ni fa na ce ki kwantar da hankalinki, in Allah ya yarda a wannan karon, zan yi duk mai yiwuwa ki auri adam" Ta ƙaƙalo murmushi ta ce "To shikenan, Allah ya sa yaya jamil". "Amin, bari na je gida, Hamida babu lafiya" "To Allah ya sauwwaƙe" Ya amsa da amin ya fita. *** Mama tana ankare da rumaisa, har garin Allah ya waye, jikinta a sanyaye yake, gaba ɗaya ba ta da karsashi yau, abinci ma da ƙyar take ci. Mama ta dubeta a tsanake ta ce "Rumaisa" Ruma ta ɗago ta kalli mama. "Meke faruwa ne? Ki ci Abincin mana" Rumaisa duk ƙaunarta da shayi, ta ture kofin, ta ce "Na ƙoshi tafiya zan yi" Mama ta ce "Zo nan" Rumaisa ta ƙarasa ta zauna a gaban mama. "Maganar auren nan ki ka saka a ranki ko?" Rumaisa ta jinjina kai alamar eh. "Ki kwantar da hankalinki, kar ki kuskura ki saka damuwa a ranki, ki yi ta Addu'a, sannan ki ja bankinki ki yi shiru, kin san abun da ƴan unguwar nan ke ya surutu a kanki, auren nan ne kawai rufin asirinmu" Ruma ta kalleta ta ce "Me suke cewa a kaina?" Mama ta tuna ashe fa rumaisa ba ma ta san zancen ba, mama ta ce "Babu komai, ki tashi ki tafi". "Dan Allah mama ki gaya mini" "Ba zan faɗa ba tashi ki tafi, karki makara" Ganin mama ba ta da niyyar faɗa mata, ya sanya ta ɗau jakarta ta fice, ta ƙudurce a ranta sai ta san ko menene. Tana tafe a hanya ta ji muryar habiba tana ƙwala mata kira, rumaisa ta tsaya ta waiwaya, habiba ta ƙaraso tana haki ta ce "Ruma, kwana biyu, kin ce zan rakaki kotu, amma baki kuma dawowa ba, lafiya kuwa?" Jiki a sanyaye rumaisa ta ce "Ke rabu da ni, na fasa zuwa kotun nan" "Amma meyasa, kin haƙura da karɓar ɗan?" "A'a, zan karɓe shi" "Hmm kin ji abun da ake ta cewa a kan ki ko, wallahi maƙociyarku munafuka ce" Cikin mamaki rumaisa ta ce "Me ake cewa?" Habiba ta ce "Au baki sani ba?" "Ban sani ba" "Taɓ, to da suka je asibiti dubaki, suka ga ɗa, suke cewa wai ɗanki ne, cikin shege ki ka yi, aka kai ki garinku ki ka haihu, yanzu an sallamoki kin dawo gida babu jaririn wataƙila kasheshi ku ka yi" Galala rumaisa ta bi habiba da kallo ta ce "Cikin shege kuma? Kamar yaya, to ai ko a gurin ƴan bindiga, bana yarda su taɓani, sai dai bisa tsautsayi ya za ayi ciki ya fito mini na haihu, na yi abun kunya fa kenan, ɗan anty aisha ne fa ta mutu ta bar mini shi" Habiba ta ce "To wallahi duk wadda aka ce ta yi cikin shege, to ƴar iska ce" Rumaisa ta yi tsaki ta ce "Sai su yi ta yi ai, na tafi kar na makara,ke ma ki tafi makaranta" Habiba ta ce "To shikenan, amma dai wallahi maƙwabciyar nan ta ku munafuka ce" Rumaisa ta yi gaba, sai dai maganar Habiba ta din ga yi mata yawo a ka. Har ta je makaranta ta dawo, ba ta cikin nutsuwar ta, mama ba ta kawo komai a ranta ba, sai rumaisa tana cikin alhini ne kawai na batun auren nan, ita kuwa rumaisa tuni zancen aure ta ajiye shi a gefe, zancen da habiba ta yi mata ya cigaba da damunta. A islamiyyar ma kasa sakin jikinta ta yi, maganar ta cigaba da ci mata zuciya. Har a yanzu rumaisa ba ta da takamaiman ajin da take zama, duk in da yayi mata kawai tafiya take zauna. Yau ma a ajin su Yasir take, ta matsa ku sa da wata ɗaliba, duk ƴan ajin mata da take mutunci da su, yayata take ce musu. Ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Yayata, duk wanda aka ce yayi cikin shege wai da gaske ɗan iska ne?" Ɗalibar ta riƙe haɓa ta ce "Ke rumaisa, meye haɗinki da wannan maganar? Duk wanda yayi cikin shege ɗan iska ne, kuma wasan banza yake da maza, yana bari suna ta ɓa shi ko taɓa al'aurarsa. A rikice rumaisa ta riƙe mararta ta ce "Wurin fitsari kenan?" "Ƙwarai kuwa" ta bata amsa. "Mama ta ce mini ba a wasa da al'aura, kuma ba a bari wani ya taɓa maka". "Sosai haka ne, dan haka kar ki kuskura wani yayi miki wasan banza, duk wanda ki ka bari ya taɓaki, to cikin shege zaki yi, a gidanku ma korarki za ayi kowa ya tsaneki, a din ga yi miki kallon mutuniyar banza ƴar iska, Allah ya yi fushi da ke, idan wani ne yake miki ki je ki faɗa a gidanku" Rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a tambayarki kawai na yi na gode". Tun da aka yi wa rumaisa wannan bayanin hankalinta ya tashi, wato kallon ƴar iska ake yi mata, mai wasan banza da maza, da aka ce ta yi cikin shege. Ita banda ƙaddara da tsautsayi da ya sanya takawa ya taɓa ƙirjinta, ita babu wani namiji, da ko da wasa yayi mata maganar banza balle ya kai hannunsa jikinta, iyaka dai ta san tana dambe da maza, amma ba wasan banza ba. Duk jarumtar rumaisa sai da ta yi kuka, tare da ganin an cuceta, yanzu duk in da ta wuce kallon da ake yi mata kenan. Malami ya shigo ajin, yayi musu ƙarin alƙur'ani, ana tsaka da ƙari rumaisa ta ce "Malam dan Allah ina da tambaya" yayi shiru sannan ya ce "Ina jinki rumaisa". "Lokacin da ka bamu addu'a, la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin, ita na yi ta biyawa, lokacin da aka yi garkuwa da ni, har na kuɓuta. Dan Allah ka bani addu'a da zan yi mutum ya zama kurma, da bebe" Ya ce "Ashsha subhanallah, me yayi zafi haka rumaisa?" "Wata mata zan yi wa, da wasu mutane" ta yi maganar har zuciyarta. Ya ce "A'a, ki yafe musu ko ki bar su da Allah, ki yafe musun ma shi ya fi, sai ke ma Allah ya yafe miki laifukanki" Ta girgiza kai ta ce "Wallahi ba zan taɓa yafewa ba, sai na yi addu'a Allah ya tattaro masifa ya jibga musu" Malam ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan ba halin mumini bane" Rumaisa ta tashi tsam tana kuka ta ce "Ni dai wallahi ba zan yafe musu ba, dama ka ce Allah ba ya juya addu'a wanda aka zalunta, in sha Allah sai matar nan ta zama kuturwa ma wallahi, dan ba zan yafe ba" Statement ɗin ta ƙarshe sai da ya bawa wasu dariya, Yasir yana kallonta ya shareta ta fice daga ajin tana kuka, zuciyarta na wani irin tafasa. Ba a tashi ba ta tafi gida, dama mai gadi ya daina tareta idan ta zo fecewa muddin an kusa tashi, tun da ta taɓa yi masa rashin hankali, ta fita da gudu garin bin ta ya faɗi yayi targaɗe, a hanya ta tsaya ta sai leda viva ta naira goma, ta cikota da manyan duwatsu, ta cika jakar makarantar ta da duwatsu, ta ɗora a ka, ta nufi gida. **" Takawa yana gidansa, yana duba wasu takardu da ya taho da su daga wurin aiki, saura sati biyu zai je lagos wani aiki, Jamil yana gefensa suna shan tea, takawa yana duba takardun. Jamil ya ɗan ajiye kofin, ya kalli adam ya ce "Takawa ya batun aure ne? Yaushe zaka yi wani auren?". Adam ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Maiyasa ka ke tambaya?" "Saboda abu ne da yakamata ka fara zancensa, ka san very soon za a fara yi maka magana a kai" Adam ya ɗan numfasa ya ce "Ba shi ne a gabana yanzu ba, cigaba da ayyukana na binciken da nake yi su suka fi damuna". "Amma kana ganin zaka iya cigaba a haka, duk yadda aka sakoka a gaba, gashi ka ƙi cewa komai" "To Jamil ya zan yi, duk mutanen da suka fito suka wankeni, ba su isa ba ba a fasa yi mini sharri ba, nima idan na yi maganar ba zai canza komai ba, kowa yayi abun da ya ga dama kawai, iyaka duk wanda ya ga ba zai iya haƙura ba ya nemi hujja ya kai ƙarata shikenan" Jamil ya ce "Lamarin ƙasar nan ai sai Addu'a, Allah ya kyauta ya bada nasara, nima akwai special assignment da zan tafi jigawa, na ji kana cikin wanda za su je Lagos ko?" Adam ya ce "Eh, aikin ma nake dubawa yanzu" Jamil ya ce "Allah ya sanya mu gama da aikin nan lafiya, kalli yadda muke wahala a kan ƙasar nan amma ba a gani, kalli aikin da muka yi a kan tsohon ministan harkokin waje, amma dan wulaƙanci wai kotu ta bayar da belinsa, amma daina maganar ni gaba ɗaya sai in ji aikin ma ya fita daga kaina" Jamil yayi maganar cikin damuwa. Adam ya ce "Haba Jamil, bai kamata mu karaya ba, ko da muna yi ba a ɗaukar mataki, wataran za a ɗauka, haƙuri zamu yi mu cigaba da yi, idan ba haka ba haka ƴaƴanmu da jikoki zasu taso su ɗaora da bauta babu ranar da talaka zai yi ƴanci" "Kana da gaskiya, amma ni fa na tsorata da batun garkuwa da aisha, anya baka tunanin shiri ne, saboda abun da muke yi?" "To ba na ce ba, zancenka zai iya zama gaskiya, kuma zai iya zama akasin hakan, duba da yadda dama ƙasarmu babu tsaro, kuma kai tsaye garin da babu tsaron ta tafi, dan haka bana zargin kowa" "To, Allah ya yi mana jagora, ya bayyana gaskiya a duk in da take". Adam ya amsa masa da Amin. Rumaisa ba ta yi burki a ko ina ba, sai a ƙofar gidan maƙwabciyarsu, tana tafe tana kuka har ta je ƙofar gidan, ta sauke kayan dutsenta, ta shirya tsaf, ta tattare hijjabinta, ta fara auna manyan duwatsu zuwa cikin gidan nan. A rikice matar gidan ta fito, a matuƙar tsorace, jikinta ko mayafi babu, domin ganin meke faruwa. Amma tana buɗe ƙofar gida, rumaisa ta sauke mata wata ƙatuwar marmara a bakinta, take bakin ya fashe, kan ta yi wani abu wani dutsen ya sauka a goshinta. Rumaisa ta cigaba da aika duwatsun nan babu ƙaƙƙautawa tana kuka, tana faɗin "Munafuka, wallahi ba zan yafe miki ba, ni ba ƴar iska ba ce". Kururwa matar ta din ga yi, tana neman agaji, mutane suka fara taruwa, aka rirriƙe rumaisa, amma ta din ga kuka tana ƙoƙarin cigaba da jifan. Gidansu rumaisa aka je aka faɗa, Allah ya sa usman yana nan, ya je ya danƙota, tana kuka. "Meye haka rumaisa, baki da kai ne? Dan me zaki din ga yi wa mutane jifa a gida?" "Ba ita ta je take gayawa mutane wai na yi cikin shege ba, tana nufin ni ƴar iska ce ina wasan banza da maza" tayi maganar tana fashewa da kuka iya ƙarfinta. Usman ya ja hannun rumaisa, ba tare da ya ce wa kowa komai ba, ya ja ta zuwa gida. Hankali a tashe mama ta ce "Rumaisa, kanki ɗaya ki ka je ki na yi wa mace jifa a cikin gida, tana ta kurma ihu wai a taimaketa zaki kasheta?" "Cikin kuka ta ce "Wallahi da zan iya sai na kashetan, dan me za ta ce mini ƴar iska? Cikin shege fa yana nufin mai wasan banza da maza". Mama jiki a sanyaye ta ce "Rumaisa rayuwar duniya haƙuri ake yi, sai ki zo ki gaya mini, ni na ɗau mataki" "Wallahi idan na gaya miki ba zaki ɗau mataki ba, cewa zaki yi na yi haƙuri, kuma wallahi ban haƙura ba, sai ta ga abun da zan yi mata" Rumaisa ta shige ɗaki tana kuka, Usman ya ce "Ai wallahi mama ban da kin hana da da kaina zan ci uban matar nan, duk yadda ki ka ɗauketa ƴa ki ke mutunta mata, amma ta yi mana wannan wulaƙancin". Mama ta ce "Dan Allah usman a rayuwarku ku koyi haƙuri, da ƙyale mutane da halinsu, wasu lokutan da kai da rumaisan duk halinku ɗaya ai". Ammi kuwa sake kiran mama ta yi, domin ta sake tabattar da rumaisa ta amince, dan ta fuskanci rumaisa ƴar buyagi ce, kar sai ta je ta kaiwa turaki maganar rumaisa ta mayar da hannun agogo baya. Ta kira wayar mama, mama ta ɗaga suka gaisa. Ammi ta ce "Ina maman sabir ne, a bani ita mu yi magana" Mama ta miƙawa rumaisa waya, ta ci kuka ta ƙoshi. Muryarta a dashe ta amsa sallamar ammi. Ammi ta ce "Rumaisa lafiya kuwa, na ji muryarki a dashe?". "Ba maƙwabciyarmu ce ta ke cewa mutane na yi cikin shege ba, ƴan unguwarmu suna yi mini kallon ƴar iska mai wasan banza da maza" Ammi ta ce "Subhanallah, ki kwantar da hankalinki, kin ga yana daga dalilin da ya sanya nake son ayi auren nan, ki yi haƙuri ki manta da su, yau zan je gidan turaki mu yi magana, dama kiranki na yi na sake tabattarwa idan kin amince, nan da watanni uku kacal za ayi in sha Allah". Ayshercool. *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Rumaisa ta yi ajiyar zuciya ta kasa cewa komai, ammi ta sake cewa "Kin dai amince ko? Idan aka yi aurenku shikenan babu wanda zai sake yi miki kallon mutuniyar banza, ni na san ke ba mutuniyar banza bace ba, kuma mijinki ma ya sani, dan haka ki rabu da su, kar ki sake kula kowa a cikin su kin ji maman sabir?" Rumaisa ta ce "To, ina sabir yake?" "Yana nan ƙalau, yanzun nan iman ta ɗauke shi ta fita da shi". "To a gaishe su" ba ta sake magana ba daga haka, ta miƙawa mama wayarta ta kwanta, zuciyarta na cigaba da ƙuna, da ta tuna kallon da ake yi mata sai ta ji ranta ya sake ɓaci fiye da da. Ammi ta kammala shirinta tsaf, ta fito falo, ta yi wa ma'aikatanta sallama, ta fita haraba, tana fita ta hangi Mahmud yana nufar in da motoci suke, ya ƙara ƙiba abun sa, kai da ka ganshi ka san hankalinsa a kwance yake ba shi da wata damuwa. Ammi ta tsaya tana hangensa, ya ɗan daɗe yana duba abu a wayarsa, daga bisani ya nufi motar da zai hau, ƙarasawa ammi ta yi, zuwa in da direba yake jiranta a tata motar, suka yi ido huɗu da Mahmud, amma sam bai kulata ba, sai ta tsinci kanta da kasa shiga motar. Mummy ta ƙaraso cikin shiri, da alama fita zasu yi ita da Mahmud, tun kan ta ƙaraso ta ga abun da ya faru, dan haka ta ƙaraso da fara'arta ta kalli ammi ta ce "Ran giwar galadima ya daɗe, fita zaki yi ne?" Jiki a sanyaye ammi ta ce "Eh". "Ok, ya Mahmud ƙarami, yakamata ko sau ɗaya a kawo mini shi sashina, ba dan halina ba". Ammi ta jinjina kai kawai ta buɗe motar da zata fita. Mummy ta ce "Mahmud ka shiga ka ga ɗan wurin Adam kuwa? Ka san sunanka ma aka saka masa" Mahmud ya haɗe rai ya ce "Me ganin nasa zai ƙara mini?" Ya buɗe motar ya shige. Wani abu ne mai ɗaci ya tsayewa ammi a ƙirjinta, ta san da gayya mummy take wasu abubuwan. Kasa sake kallon in da su Mahmud suke tayi, har motar ta fice daga gidan. Suna tafe a hanya Mummy ta ce "Mahmud, yakamata ka je ka ga yaron nan, sannan ka yi wa ɗan uwanka barka tare da gaisuwar rasuwar matarsa, kar ace ni nake zigaka" Mahmud da yake murza sitiyari ya ce "Dan Allah mummy ki ƙyaleni da sabgar mutanen nan, ina wuri ɗaya hankalina a tashe ni bana son tashin hankali da ɓacin rai, ni a kan haka sai na bar ƙasar na koma in da na fito, ba dai A'isha ce ba? Na ce Allah ya jiƙanta ya sa ta huta, shi kuma jariri Allah ya raya why sai na ta bin su ina wani gaisuwa abun da ba addini ba". Mummy ta ce "To shikenan, sarkin faɗa, ni zan saka a ɗauko yaron ka ganshi, duk da nima ɗin sai na roƙa za a kawo mini shi, sau ɗaya na taɓa ganin yaron, shi ma sai da na taka da ƙafata na je". Mahmud ya ce "Kin gani ko, Mummy meya kai ki? A wulaƙantaki a banza, dan Allah tun da ba sa sonki a sabgarsu, ki ƙyalesu su je sun cinye yaron, ina jin Samha ma na surutun wai ta je an yi mata wulaƙanci a kan yaron, sai ka ce dole ni fa bana zuwa in da ba a buƙatata" Mummy ta yi dariya ta ce "Sarkin tsari, mu bama son zumunci ya samu matsala ne" ya ɗan ɗage kafaɗa alamar ko a jikinsa. Ammi kuwa har suka je gidan turaki, ba ta hayyacinta, ta yi zurfi a tunani, sai da direban ya ce mata sun zo, sannan ta dawo hayyacinta ta sauka, ta shiga gidan. Tun da mama ta ganta take ta wani cin magani, tana hura hanci, samha ce dai ta din ga rawar jiki da ta ga ammin, tana tambayarta ya sabir. Ammi ta amsa mata cikin sakin fuska ta ce "Dan Allah samha ki aika ayi mini iso wurin mai girma turaki" Samha ta ce "To ammi" gaba ɗaya samha ta din ga tsuma, har a ranta take jin, anya ba a kan batun aurenta da takawa ammi ta zo ba, amma ai idan haka ne, da mai girma turaki ne zai yi mata zancen. Da haka ta je ta nemawa ammi iso wurin turaki, ammi ta shiga wurinsa. Cikin sakin fuska da girmamawa, suka gaisa da turaki, ya ce "Tun ɗazu muke tsumayinki da ki ka ce mana zaki zo" Ta risuna ta ce "Tuba nake, ayyukan iyali ne suka sha kaina, tuba nake Allah ya baka nasara" Turaki ya ce "To Madalla, Allah ya yi mana jagora ina abokin nawa, baki zo mini da shi ba?" Ammi ta yi murmushi ta ce "Yana gida, ka san baya son mutane, yana ƙyuya, kar mu zo ya cika maka kunne da kuka, ko yayi ta zare maka ido" tayi maganar cikin murmushi. Turaki ya ɗan yi dariya ya ce "Ai barewa ba ta gudu ɗanta yayi rarrafe, haka zalika kalar kumbo kalar ƴaƴanta, haka shi takawan yake ai ko da yana ƙarami, da aisha ya ɗauko da an ga haƙuri da fara'a, amma takawa dai kam hmmm" Ammi ta yi dariya ta ce "Kun fi kusa ranka ya daɗe, ba ruwana" suka yi dariya gaba ɗaya. Ya ce "To giwa meke tafe da ke ki ke son ganinmu da gaggawa haka? Allah ya yi zaki samemu, dan gobe in Allah ya kaimu muke sa ran tafiya umara" "Allah sarki, Ubangiji Allah ya sa ayi ibada karɓaɓɓiya" Ya amsa da amin, tare da sake tattara hankalinsa a kan ammi. "Allah ya taimake ka, dama wata muhimmiyar magana ce ke tafe da ni, wani hukunci na yanke da zartar da shi dole sai da izininka, kuma kai zaka yi mini jagora zuwa ga tabattauwar abun cikin hukuncin Allah" Ya jinjina mata kai cikin nutsuwa alamar yana sauraren ta. Ta ɗora da cewa "To bisa ga al'ada ta masauratar nan, duk cikakken ɗa a gidan nan, a kan yi masa zaɓi na matar da zai aura, ko ya kawo wadda yake so ƴar mutunci idan ta yi a aura masa. wani abu ne ya taso a kan yarinyar nan rumaisa, ƴan unguwar su suna ta yaɗa jita-jitar wai ciki ta yi aka kaita aka ɓoye ta haihu, sunanta dai ya ɓaci a unguwar su, na ga babu wata hanya da zamu bi domin wanketa face Adam ya aureta, duba da irin matsanancin son da take yi wa yaron nan da ta zo da shi, har ina ganin kamar rabata da yaron na shiga hakkinta, saboda na san ciwon abun, ga wannan abu da ya kunno kai game da rayuwarta, na ga abu ɗaya zan iya yi shi ne in sanya adam ya aureta, amma ya ka gani ranka ya daɗe?". Turaki ya ce "Ikon Allah, kin ga nan Jamil ya zo mini da zancen, akwai buƙatar Samha ta maye gurbin Fulani, duba da yadda ta daɗe tana son adam, dan har na yi na'am na so na tuntuɓeki, to sai gashi kuma kin zo da wani zance da yakamata a tsaya a duba. Tabbas! Idan har da yadda zamu yi yarinyar nan bai kamata mu bari ta wulaƙanta ba, dan haka a wannan karon ma samha sai dai ta yi haƙuri, ko kuma idan yana da ra'ayi ya haɗasu biyu, amma rumaisa ita tafi cancanta ya aura, duk da ƙanƙantarta". Ammi ta ɗan ji rasss, ba za ta yi fatan adam ya haɗa rumaisa da samha ba, duk da rumaisa yarinya ce amma ba za ta yi fatan ta zama bora ba, tun da dai haryanzu ba ta isa rayuwar aure ba, tana son ya aureta ne dan ya inganta rayuwarta, a haka idan ta ce za su cigaba da ɗawainiya da rumaisa, ƴan uwanta ba zasu harda ba, dan ta lura suna da gudun abun hannun wani. Turaki ne ya katse mata tunanin ta hanyar cewa "Sai dai wani hanzari ba gudu ba, kin san akwai ƙalubale, a ƙa'idar masarauta, ƴaƴan sarakuna ƴaƴanmu suke aure, ko ƴaƴan wasu manya, akwai gwagwarmaya idan aka kai maganar nan gaban su wambai" "Allah ya taimakeka shi ya sanya na zo wurinka, na san kai kaɗai ne zaka iya shiga lamarin nan ka tsayawa adam, jikina yana bani akwai alkhairi a game da lamarin nan, rumais alkhairi ce ga adam" Ya ɗan yi shiru ya ce "To babu laifi, in Allah ya yarda idan na dawo, zamu yi magana da su, na sanya zancen cikin addu'a idan alkhairi ne Allah ya tabattar ya kawo komai da sauƙi" "Amin ya rabb, idan komai ya daidaita bana son abun ya wuce watanni uku, kar wani abun ya kutso" Turaki ya ce "Babu damuwa, babu abun da zai gagara da ikon Allah" Ammi ta risuna, ta sake yi wa turaki godiya, sannan ta tashi ta fita. Samha ce ta raka ammi har mota, tana yi mata ta gaida gida. Ammi na tafiya samha ta koma ɗakin ta, ta ɗau wayarta ta kira jamil. Yana ɗagawa ko gaisawa ba su yi ba ta ce "Yaya jamil, yau ma ammi ta zo wurin mai girma turaki, dan Allah idan ka zo yau ka tuntuɓe shi da maganar, ka ji ko ita suka yi?" Jamila yayi tsaki ya ce "Ke kin fiye abun haushi wallahi" "Dan Allah yaya ka taimaka". Ya ce "Gaskiya bana nan, bana gari sai dai ki jirana dawo, idan na dawo kuma yana umara, na san duk abun da ake ciki dai, in dai a kan maganar ne zasu tattauna da mama" Samha ta ɗan yi shiru sannan ta ce "To shikenan, na gode " ta kashe wayar cike da fatan Allah ya sa tattaunawa suke a kan ta maye gurbin Fulani. *** Ana idar da sallar magariba, Huzaifa ya saka rumaisa a gaba yana ta mata faɗa, ta ƙi cin abinci sai mita take a kan abun da aka yi mata a unguwa. Aikowa aka yi wai ana sallama, ganin ba a faɗi da wa ake sallamar ba, ya sanya Usman tashi ya fita ya ga waye yake yin sallamar. Aikuwa yana fita ya tarar da mijin maƙwabciyarsu, ya kawo ƙarar rumaisa a kan abun da ta yi musu, na jifa a cikin gida ta yi musu ɓarna, ga uwa uba fashewa matarsa baki ada marmara da rumaisa ta yi. Usman ya ce "Malam shamsu ai ɓarnar da matarka ta yi mana ta fi wadda ruma ta yi mata, shiru kawai muka yi, duk yadda ruma take girmamata bai hanata yi mata ƙazafi a cikin unguwa ba, ba dan mama ta hana ba, ga kuma albarkacin aure, sai na yi mata wankin babban bargo a cikin unguwar nan, amma tun da abun ya zo da haka, kawai duk sai mu haɗu mu yi haƙuri". Cikin takaici malam shamsu ya ce "Au haka ma zaka ce? Ta rotse mana ƙwan lantarki na tsakar gida, ta fashe mana glass ga zubarwa da matata jini, amma ka gaya mini wannan maganar?". "To me zance maka, yanzu dai idan baka haƙura ba, kai ma ka tsinto duwatsu ka yi mana jifa a cikin gidan, ko in kirawo maka rumaisa ka daketa ko? Sai ka huce" aikuwa malam shamsu ya harzuƙa ya fara zage-zage, Usman kuwa ya zage shima yana ramawa, suka nemi bawa hammta iska. Mama har ta manta da Usman ya fita, ta jiyo zage-zagen usman, yana idan baa rufe masa baki ba, sai ya falla masa mari, kuma ya ɗaga shi ya buga da ƙasa. Cikin tsananin faɗuwar gaba mama ta taso, hankali a tashe za ta fita, Huzaifa ya ce "Mama ba zaki fita ba, yaya usman bai fiye faɗan rashin gaskiya ba, kuma yaya Abubakar yana kusa, na san zai raba" Mama ta ce "Kai dan ubanka bani hanya, kar ya janyo mini magana, na ji da malam shamsu suke yi, ba zai wuce a kan abun da rumaisa ta yi bane, usman in dai a kan rumaisa ne, ko ba ta da gaskiya goya mata baya yake yi, shi ba ya bin komai a sannu, wani fannin halinsu ɗaya da ita, zuciyarsu babu afuwa" mama na cikin maganar yaya Abubakar ya shigo hannunsa riƙe da na usman yana yi masa faɗa. Usman ya ce "Haba yaya, mu bamu suka fi yi wa illa ba, sun yi mana baƙin fenti a unguwa, bamu yi magana ba sai shi, wai shi tattabara wanda ya yankewa ƙauna cibiya, shi ga mai mata, banzar matar da fuska kamar baƙar jaka, wallahi da namiji ce sai na yi mata shegen duka". Rumaisa ta ce "Ƙazama da ita ba, mai bleaching" Mama ta dungurewa rumaisa kai, Abubakar kuma ya cigaba da yi wa usman faɗa. Usman ya ce "Da ne nake adawa da aurar da rumaisa, amma wallahi yanzu na zubar da makaman yaƙi na bi, wallahi party zamu shirya na tashin hankali a unguwar nan, mu hayo dokuna ayi ta kilisa, zamu kaita gidan manyan mutane, mu ga ƙarshen munafurci, mu rufe bakin munafukai" ya kalli rumaisa ya ce "Ke, dan ubanki na daina adawa da auren nan, ki yarda kawai, kuma daga yau daga ita har mijinta kar ki sake gaishe su, ta kuma yi miki maganar banza, zan samo miki duwatsu, daga nan har bamfai ba mai shari'a da ke yarinya ce, na tsaya miki ayi da ni". Mama ta ce "A'a babu ruwana, kai maimakon ka saita yarinyar nan, ku bi komai a sannu amma kana yi mata huɗubar tsiya, Nuraini har da kai fa kake zigata take rashin ji, babu ruwanka da mutumin nan ku fita sabgarsu, ni ba zan iya tashin hankali da mutane ba". Usman ya miƙe ya ce "Mama irin masu haƙurinki ake cuta, komai ki ce ayi haƙuri a barwa Allah, da haƙurinki muka ɗauko, muna zaune za a fille mana wuya ki ce mu yi haƙuri" Dariya rumaisa ta yi, mama kuwa ta rarumi takalmi, ta jefawa usman, ya goce tare da shigewa ɗakinsu. Ruma ta ce "Allah ya biya yaya usy nawa, Allah ya bar mini kai". "Ki cigaba rumaisa, yayi ta ɗoraki a keken ɓera ya kai ki ya baro, tun da ke dai ba namiji bace ba". *** Ko da ammi ta koma gida, Nusaiba da Iman suka tareta suna tambayarta yaya suka yi da turaki? Nan ta kwashe komai ta gaya musu, iman ta ce "Allah ya tabattar da alkhairi, ya sanya mai girma turaki ya shawo kansu komai ya tafi cikin sauƙi, ni dai ina sonta wallahi" Nusaiba ta ce "Mhmm, ni kam kawai yadda za ayi zaman nan nake hangowa, ba fa sa shiri ammi, kin ga ita tana da tsiwa, shi kuma akwai faɗa" Ammi ta ce "Ke rabu da shi, rayuwar aure ta fi ƙarfin wasa, idan suka zauna za su nutsu, sannan a rayuwarsa da ita akwai wani darasi da nake fatan ya koya, kuma kan ayi auren ai dolensa ya dinga zuwa wurinta su saba" Iman ta yi murmushi ta ce "Akwai rikici kenan?" Ammi ta ce "Ta bani tausayi ɗazu da muka yi waya, wai an ce ta yi cikin shege, ana yi mata kallon ƴar iska, saboda ta zo da sabir, idan ban saka takawa ya aureta ba, shikenan an yi mata mummunan tambari, mutane ɗa idan ba na su bane ba, sun din ga janyo masa jafa'i kenan" Nusaiba ta ce "Haka ne, Allah ya shirya, ya tabbatar da alkhairi" suka amsa da amin. Baba uwani da take laɓe ta ji hirar ta su sama-sama, sannan bakomai ta ji ba, amma a abun da ta jin, ta ƙudurce za ta je ta sanar da Mummy. Rumaisa mita a cikinta, kamar an yi mata gori, yau wuni ta yi tana cigaba da mitar abubuwan da ake yi mata a unguwar nan, mama tun tana yi mata nasiha tana cewa ta bar wa Allah, har ta yi mata banza ta ƙyaleta, Abdallah ya sakata a gaba yana cigaba da kunnata, tana mita. Bayan fitar Abdallah rumaisa ta shiga ɗakinsu, ta duba wurin da yake ajiye fensiransa na zane kasancewar sa architect. Ta zauna ta nutsu sosai, ta hau zane-zane. Mama ta ce "Uban me ki ke yi musu a ɗaki, ki ka shiga ki ka yi shiru?" Rumaisa ta ce "Bakomai" "To fito musu daga ɗaki, tun basu dawo sun tarar da ke ba" "Mama zan fito ina zuwa" Sai da ta gama abun da Allah ya nufeta da yi, sannan ta fito ta fice ba tare da sanin mama ba. Maƙwabciyarsu ta zana, kuma zanen ya fita sosai, ta yi headline da munafukar unguwa, a ƙasa ta rubuta by Rumaisa Mahmud ƙanwar maza. Ta je ta liƙe a ƙofar gidan matar, ta nausa ta tafi gidansu Habiba, ba tare da mama ta san ta fita ba ma. Ayshercool. paid book ne, ₦500 via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 *PAID BOOK NE, ₦500 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143* Jin shirun yayi yawa ya kuma sanyawa mama ta ƙwalawa rumaisa kira, amma har ta kira kusan sau uku shiru, ba ta amsa ba, mama ta kaste abun da take yi, ta fita domin duba me rumaisa take aikatawa ta ji shiru. Sai dai da ta fito tsakar gida babu rumaisa ba alamarta. Mama ta leƙa ɗakin ƴan maza, amma babu rumaisa ƙarshe ma sai shiga Maman ta yi ta kwaso kwanukan ta, da suka kai ɗakin suka bar su, ta fito ta duba banɗaki da kitchen duk babu rumaisa, tsayawa ta yi tana tunanin ina rumaisan ta tafi ba ta gaya mata ba?. Tana cikin jimamin in da rumaisa ta tafi babu izininta, shamsiyya maƙwabciyarsu ta yi sallama, ita da wata mata. Mama ta amsa musu cikin sakin fuska, ba tare da nuna mata ta san ta yi wa ƴarta ƙage ba. "Maman rumaisa ni ba zama zan yi ba, ki shiga tsakanina da yarinyar nan, kalli abun da ta yi mini jiya a fuskata, da ɓarnar da ta yi mini a cikin gida, maigidana ya kawo ƙararta, ƙarshe ba wani mataki da kuka ɗauka, sai ma cin mutumci da ya biyo baya, yau kuma ta je ta yi zane ta liƙe mini a ƙofar gidana ya ƙi fita, wai munafukar unguwa, me na yi muku haka ne?" Cikin dattaku mama ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, yaran zamani ne sai godiyar Allah, wallahi da kaina na yi niyyar shigowa na baki haƙuri, wallahi ban san ta yi ba, kin san dai ni ba zan goyi bayan ta yi wannan rashin kyautawar ba, ban san ta yi miki ba, dan Allah dan annabi ki yi haƙuri, bari ta shigo gidan, zan hukunta ta kuma zan sanya ta je ta cire, dan Allah ki yi haƙuri" "Wallahi banda ina jin nauyinki, Allah da sai na kama rumaisa na yi mata shegen duka". Mama ta ce "Ashsha, ba za ayi haka ba, ai ke ma ƴarki ce, yanzu kina taɓata komai zai ɓaci, yayyenta ba sa ganin laifinta, amma dai ina baki haƙuri, da kaina zan hukunta ta, kuma zan aikota ta baki haƙuri". Haka Jamila ta yi ta farfaɗar maganganu, mama tana bata haƙuri, da alwashin hukunta rumaisa, bayan tafiyarta mama ta dafe kai, haryanzu rumaisa babu alamar hankali a tare da ita, tuno damben da suka sha da ƴar ajinsu ta yi, abu har wurin ƴan sanda saboda wannan shegen zane-zanen da take yi, shi kansa Abdallah dan ba yadda za ta yi da shi ne, abun da yake karanta kenan, ga rumaisa na neman gadarsa, in dai zane-zanen banza da na wofi ne, a litattafan makarantar ta ma yi take. Mama ta rasa mai ma yakamata ta yi, ba ta san ta ina zata fara neman rumaisa ba. Rumaisa kuwa gidansu habiba ta tafi, suka shantake suna ta hira, ta bawa habiba labarin abun da ta yi wa maƙwabciyarsu. Habiba ta ce "Kin mini daidai, da nice ba zan iya ba, tsoro nake ji, kin ji yadda matar nan ta din ga yayata maganar nan a cikin unguwar nan, ummanmu ce ta fara taka mata burki ta ce ƙarya take yi, daga nan ta je ta gayawa mamanku" Rumaisa ta ce "Hmm, ai sai ta gane ba ta da wayo kan ma bar unguwar nan, da ina mutunta ita da mijinta, amma tun da ta taɓo ni, za ta gane bata da wayo" Cikin rashin fahimta habiba ta ce "Ki bar unguwar nan ki koma ina?" Rumaisa ta ɗan yi jimm, sannan ta ce "Ke share kawai, na san zuwa yanzu wataƙila ta je ta kai ƙarata gidanmu" "Me ki ka yi mata?" Cikin ƙwarin gwiwa rumaisa ta ce "Zanata na yi, na rubuta munafukar unguwa, na liƙe mata a ƙofar gida, na san yau za a azabtar da ni a gida, amma ba zan koma yanzu ba" Habiba ta ce "Wai ruma ba kya jin tsoro ke? Mama ba ta san kin zo nan ba?" "Ba ta sani ba, idan aka kai ƙarata ina gidan, a gabanta mama zata bani rashin gaskiya, duk da abun da ta yi mini, zuwa yanzu kuwa na san ta tafi, in koma gida a haɗani da mai sunan baba, ya bani gwale-gwale" Dariya habiba ta yi ta ce "Wato ke har ma kin san me za ayi miki, ina yaya Aliyu?" Rumaisa ta yi mata kallon ƙasan ido ta ce "Yana makaranta, in ce kina nemansa ne?" Habiba ta waro ido ta ce "Ke a'a, kawai dai tambayarsa na yi" "Meyasa duk cikin yayyena shi ki ka sani?" Habiba ta ce "Bakomai, ya na da kirki ne" Rumaisa kawai ta yi dariya, tana lissafa yadda zata wanye da mama idan ta je gida. Mama kuwa sai kallon agogo take yi, tana lissafa, ina rumaisa ta tafi haka? Ta ƙi dawowa, zuciyarta ta bata saboda abun da ta aikata ne ya sanya ta fece. Kasancewar azahar ta yi, kuma juma'a ce ya sanya ƴan samarin mama dawowa gida, domin shirin masallaci, kuma aka yi sa'a ana public holiday, rumaisa ba makaranta ta je ba. Faɗan Abdallah mama ta jiyo, yana faɗin "Uban waye ya taɓa mini kayan zanena, bana son rashin mutunci, Huzaifa ban hanaku taɓa mini kaya ba?" Huzaifa ya ce "Ni na iya amfani da wannan abubuwan naka ne? Sai dai ko Yasir" Yasir ya tari numfashin Huzaifa ta hanyar cewa "Saboda ni ka raina ba, yaushe na zauna a gidan balle na taɓa masa kaya". Mama ta fita tsakar gida ta ce "Ba aikin kowa bane, rumaisa ce ta taɓa maka, ita ta shiga ɗakin ta yi shiru, ita ce ba wani ba". "Tana ina, sai ta ci ubanta yau sai na zaneta, har da gum ɗina ta buɗe ta bar mini a buɗe" "Hmm, wannan yarinyar ai sai fatan shiriya, ina fatan Allah ya sanya auren nan ne mafi alkhairi, ko yau aka ce za ayi zance a ɗaura su tafi da ita" Abdallah ya ce "Tana ina?" Mama ta ce "Ina na sani, ta yi wata aika-aikar ta gudu, ban ma san ta fita ba". Yasir ya ce "Kai wannan yarinya, Allah ya yi mata maganin abun da yake damunta yake sanyata rashin ji". Rumaisa ba ta tashi tafiya gida ba, sai da unguwa ta yi tsit, duk an tafi masallaci, sannan ta nufo gida, cikin shirin karɓar kowane irin hukunci za a yanke mata. Da sallama ta shiga gidan, ta yi sa'a mama tana salla, ta lallaɓa ta shiga ɗakin ta zauna, tana jiran mama ta idar, ta shirga mata ƙaryar da zata kare kanta. Mama tana jin motsin rumaisa, amma ta shareta, ko da ta idar da sallar ma ta yi lazumi, ba ta tankawa rumaisa ba. Cikin tsoro rumaisa ta ce "Mama" banza tayi da ita ta shige uwar ɗaki ta bar rumaisa. Tun rumaisa tana ɗar-ɗar har ta ɗan saki jikinta, da ta ga mama ba ta da niyyar kulata. Sai dai ba ta ankara ba, mama ta shammaceta, ta janyota ta din ga ɗirka mata dundu. Ihu rumaisa take yi, tana neman agaji rabon da mama ta daketa har ta manta. Tun daga waje Yaya Abubakar ya jiyo ihun rumaisa, a soro ya yasar da sallaya, ya shiga da gudu, ya tarar da mama ta samu mafici, tana jibgar rumaisa tana yi tana haɗawa da hannunta. Ai da hanzari ya ƙwaci rumaisa yana faɗin mama lafiya. "Rabu da ni, yau yarinyar nan ta kaini bango, rumaisa a rayuwarta ba zata bari na huta ba, daga wannan sai wancan, gidan ubanwa ki ka tafi?" Cikin kuka rumaisa ta ce "Gidansu habiba" "Gidansu habiba gidan ubanki ne? Wato kin san abun da ki ka aikata ko?, To fita ki je ki bata haƙuri, ki cire takardar da ki ka liƙe mata a ƙofar gida, tun kan na murɗe miki wuya ki mutu in huta, da ɗaukar maganar da ki ke yi, kullum nike nan cikin bayar da haƙuri da faɗa da mutane saboda ke? Bari na kira babar adam ɗin a waya, idan sun shirya ko jibi su zo a ɗaura auren nan na huta na gaji" Rumaisa ta yi fici-fici da ido tana kuka. "Ba zaki fice ki je ki bata haƙuri, ki cire abun da ki ka liƙa mata ba?" Ruma ta fita da sauri, tana jin haushin sake kai ƙararta da matar ta yi. Ta je ta yi iya ƙoƙarin ta, wurin cire cardboard paper da ta yi zanen a jiki, amma gum ɗin da ta yi amfani da shi ya kama sosai, dan haka ta samo wata ƙusa, ta dinga durzawa takardar, ta haɗa da sabon fentin da aka yi wa ƙofar duk ta kankare abun ta, sannan ta shiga cikin gidan matar. Ta tsaya daga soro ta yi sallama, matar ta amsa sannan ta fito, ta sakawa bakinta da goshinta shanshanbale, in da rumaisa ta fasa mata da dutse. "Kin kai ƙarata, mama ta ce sai na zo na baki haƙuri, na cire takardar da na saka miki, na cire takarda, idan ki ka kuma kai ƙarata zan yi miki abun da baki zata ba, kuma wallahi ban yafe miki ba sharrin da ki ka yi mini, wuta balbalin bala'i, idan baki nemi yafiyata ba, sai kin ga abun da Allah zai yi miki, kayan da ki ke sayarwa ma sai an daina siya" tana gama maganar ta juya ta tafi. Da sauri ta biyo bayan rumaisa, sai dai tana zuwa ta tarar da sabuwar ta'asar da rumaisa ta ƙyanƙyasa mata a ƙofar gida, ta kankare tsakiyar ƙofar da ƙusa, duk fentin ya fita ga sauran takardar ba ta gama fita ba, gaba ɗaya ta sauya fasalin ƙofar. "Na shiga uku ni Jamila, wace irin masifa ce wannan, fentin ƙofar da bai fi sati da yi ba ki ka dirje?". Rumaisa ta waiwayo ta kalleta ta ce "Idan baki gaji ba, yanzu ma ki je ki kai ƙarata, zaki sha mamakin abun da zan yi miki next" Ta shige gida tana sunkuyar da kai, mama ta kalleta a fusace ta ce "Kin bata haƙurin ko kuwa?" "Na bata" ta amsa tana sunkuyar da kai. Aliyu ya kalli rumaisa ya ce "Allah ya shiryeki ruma, ke ko gajiya da ɗaukar magana ba kya yi, kullum ayi ta yi miki faɗa, daɗi yake yi miki ko?" Ta girgiza kai alamar a'a. "Zo ki karɓi kuɗin nan ki sayo mini milo a kantin malam lawan, zan sha shayi bana son cin abinci" kallon yaya Aliyu ta yi, kamar tana hararsa ya ce "Ni ki ke yi wa wannan kallon, ko ba zaki ba?" Ta durƙusa ta ɗauki kuɗin, ya ce "Ki taho da manja kwalba ɗaya, na ga wanda muke da shi ya kusa ƙarewa". Ita dai ba ta amsa masa ba, ta fice ko da ta fita a ƙofar gida ta hangi shamsiyya da mijinta, suna duba ƙofarsu da ta dirje, ba ta kula su ba ta tafi shagon. Malam lawan mai kanti, yana ta yi mata wasa yana tsokanarta, amma ta share shi, ya auna mata manjanta, ta fito. Sai dai tana fitowa ta yi karo da wani tantirin ɗan daba da ya addabi unguwarsu, wanda har kisan kai yayi, amma aka sake shi. Ya kalli rumaisa ya ce "Ke, karɓo mini sigari a cikin shagon nan" Tsaki ta yi, zata wuce, ya sake daka mata tsawa ya ce "Ke, na ce ki karɓo mini sigari a cikin shagon nan" "Na yi maka kama da ƴar iska, ni ce ma zan taɓa sigari saboda wulaƙanci, to ba zan karɓo ba" ware jajayen idanunsa ya yi a kan rumaisa, a hargitse malam lawan ya ce "Yi haƙuri bari na miƙo maka". Cikin muryar mashaya, ɗan daban da ake cewa ɗan kada ya ce "Ni ki ke gayawa haka?". Fitowa ta yi zata wuce shi, ta tafi, amma ya sanya ƙafarsa ya kwashe na rumaisa, a take kuwa ta faɗi ƙasa, manjan hannunta ya fashe, ta datse goshi. Idan da abun da rumaisa ta tsana, bai wuce ganin jini a jikinta ba, jiki na rawa ta tashi ta kalleshi, ya kalleta ya ce "Sai na tsarge hanjinki da wuƙa, na kashe banza ni zaki nemi ki zaga wata jagwal da ke" Cikin hanzari malam lawan da sauran mutane suka fara lallaɓa ɗan kada suna bashi haƙuri, rumaisa ta shiga cikin shagon, ta dumbuzo ƙwan da ke kan teburi, ta fito ta shiga jifan ɗan kada da shi. Rikicewa malam lawan yayi, dan yanzu aka sauke ƙwan ko lissafawa ba ayi ba, ji ta yi zuciyarta na tafasa, ta juya da gudu ta tafi gida. Aliyu na ganinta ya ƙare mata kallo ya ce "Meye haka?" Cikin kuka ta kwashe komai ta gaya masa, nan da nan ransa ya ɓaci ya ce "Mu je" mama na banɗaki tana gyaran murya, amma Aliyu ya ja rumaisa suka yi waje. A ƙofar shagon suka tarar da ɗan kada, har ya karɓi sigarinsa ya fara sha, malam lawan kuma yana ta masifa, yana sai ya je gidansu rumaisa an biya shi, shi kansa ɗan kada yayi alwashin sai ya kashe rumaisa, saboda wulaƙancin da ta yi masa,ta din ga jifansa da ƙwai. Idan da abun da samarin gidan maman suka tsana, bai wuce taɓa Wannan tilon yarinyar ba, dan haka a zafafe Aliyu ya ƙarasa, yana zuwa ba tambayar ba'asi ya ci kwalar ɗan kada, ya shiga kifa masa mari. Kokawa ta kacame, ga ɗan kada a buge, dan haka ya kasa wani abun arziki, Aliyu ya din ga haɗa masa naushi. Da ƙyar mutane suka shiga tsakani, ana rirriƙe ɗan kada yana rantsuwa sai ya kashe Aliyu. Mama kuwa a gigice ta fito daga banɗaki, jin wanda rumaisa ta tsokano, dan babu wanda bai san yadda ya addabi unguwarsu ba. Mama ta kira mai sunan baba a waya, ta ce masa duk abun da yake ya bari ya tafi shagon malam lawan, Aliyu ya fita ba ta san mai zai aikata ba. Aliyu kuwa ya kalli ɗan kada ya ce "Jinina da na zuriyar gidanmu ya fi ƙarfin mutum irinka,  duk wani hauka da iskanci da kake ji da shi a unguwar nan ƙyaleka aka yi, ƙanwata ta fi ƙarfin wawan mutum irinka su cutar da ita" Malam lawan ya ce "Wai Meye haka ne Aliyu, ina nan aka sace ƙanwar ta ku me ku ka yi, sai yanzu zaku haddasa mana masifa a cikin unguwa" "Wallahi malam lawan, duk shekarun da muka yi tare a unguwar nan, idan ka taɓa rumaisa sai na tuɓe na yi maka bugun sakwara, saceta kuma da aka yi wannan ƙaddararta ce, ba yadda muka iya" Rumaisa ta riƙe hannun Aliyu ta ce "Yaya mu tafi gida" Da ƙyar rumaisa ta riƙe hannunsa, suka juya suka fara tafiya, sai dai ana sakin mai kada, ya zare wuƙa ya nufi Aliyu da ita gadan-gadan yana ihu. Ihu rumaisa ta saka ganin wuƙa tsirarata, wuƙa ba ta wasa ba an nufo yaya Aliyunta da ita, wanda ba da tabbacin ita aka nufo ko shi. Aliyu ya hankaɗeta, ya kuma riƙe mai kada suka hau kokawa ga wuƙa tsirarta. Aliyu ya danne mai kada a ƙasa, ya ɗau wuƙar ya ce sai ya yankashi da ita a wurin. Nan aka din ga kokowa da Aliyu, aka kasa ƙwace wuƙa. Rumaisa ta ce "Yaya Aliyu kar ka yi kisan kai, amma dai ka yi masa dukan tsiya". Cikin takunsa na isa da taƙama, ya din ga ture dandazon mutane, ya ƙarasa in da Aliyu yake kan mai kada ana fama da shi, ya riƙe hannun Aliyu mai wuƙar ya murɗa, ya jefar da wuƙar, sannan ya ɗago shi daga kan mai kada ya tsayar da shi a kan ƙafafuwan sa ya Kalleshi ya ce "Meya haka? Shaye-shayen kai ma ka fara ne?" Ya kalli rumaisa ya ce "Duk saboda ke ko? Sai ku wuce mu tafi ai". Daga kwance mai kada ya ce "Na rantse da girman Allah, idan har ina yawo kana yawo a unguwar nan, sai na kasheka na kashe matsiyaciyar yarinyar nan, na ga uban waye gatanku" Aliyu ya sake tunzura, jijiyoyin kansa suka kumbura, mai sunan baba ya kalli mai kada ya ce "Idan kana zubar da jini a unguwar nan kai da yaranka, ana tsoronku, kar ka ratso ta gidanmu, wallahi duk wanda ka zubarwa da jini in dai ɗan gidanmu ne, kaima sai na zubar da naka, ka kiyaye" Ya riƙe rigar Aliyu, hannu ɗaya ya tankaɗa ƙeyar rumaisa zuwa gida. Mutane wasu har da shewa, abun ya burgesu, kaf unguwar nan babu gidan da suke da haɗin kai da nunawa juna soyayya kamar gidansu rumaisa. A gigice mama ta tashi da suka shigo, ta ga jikin Aliyu duk ƙasa, rumaisa kuma da fasashshen goshi, duk da ba ta zubar da jini da yawa ba. "Mai sunan baba, maiyafaru?" "Kar ki damu, ba abun da ya faru" Mama ta riƙe Aliyu da yake huci ta ce "Ina fatan dai ba abun da ya sameka ko?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. Mama ta ce "Duk saboda wannan jairar yarinyar ne, da ba zata bari a zauna lafiya ba? Ina ke ina faɗa da gagararren ɗan daba saboda ɗorawa kai bala'i" Mama ta yi maganar tana ƙoƙarin kai mata duka, amma mai sunan baba ya tare ya ce "Ki ƙyaleta please, baki ga ta ji rauni a goshi ba, ki yi haƙuri" Mai sunan baba ya sakata a gaba, ya kai ta chemist, aka duba goshin, Allah ya taimaketa babu ɗinki, suka dawo gida. Mama ta kai ƙarshen ƙulewa da rumaisa yau, ta din ga yi wa ƴan mazan faɗa a kan biye mata wurin tare mata faɗa. Kasancewar maƙwabcin su rumaisa malam shamsu, yana cikin ƴan kwamitin unguwa, shi ne mataimakin ƴan ƙato da gora, yana dawowa aka sanar masa da abun da ya faru a unguwar, nan da ya ji ya samu damar rama wulaƙancin da rumaisa da yayyenta suka yi masa, kai tsaye ya je ya sanar da ƴan sanda abun da ya faru. Mama har ta bar sallahun a rufe gida, ƴan sanda suka yi sallama, suka ce sun zo tafiya da Aliyu. Duk yadda aka so sasanta lamarin, abu ya gagara, ga Abubakar ya koma makaranta, Mai sunan baba da Usman suka bi bayansu, amma har wurin sha ɗayan dare, ƴan sanda suka ƙi bayar da Aliyu, ƙarshe ma suka sanar da su cewa sashin kula da manyan laifuka na bamfai zasu turasu, tun da Aliyu ya yi iƙrarin kisan kai. Haka mai sunan baba suka koma gida, jiki a sanyaye, mama ta rasa in da zata saka kanta saboda tsananin damuwa da tashin hankali, tare da ɗora zargin komai a kan rumaisa. Adam kuwa bayan ya kammala cin abinci, ya tashi ya yi wa ammi sallama, ammi ta ce "Yauwwa, na ce ba" Adam ya ɗan tsaya yana kallon ammi. "Dan Allah gobe in Allah ya kaimu, tun da da wuri zaka fita, kuma ka ce zaka je gidan gona, dama unguwar su matarka ne, zan baka saƙo ka kai wa rumaisa" Adam ya kalli Ammi ya ce "Matata kuma? Kuma ni zan kai ssƙon?" "Ban isa ba kenan?" Ya ce "A'a tare da sunkuyar da kai" "A yanzu kana da wata matar da ta wuce rumaisa ne? Zaka kai mata saƙo, kallonka kawai nake yi, har na je wurin turaki na dawo ba ka tambayi yaya muka yi ba, kuma ya zama dole ka din ga zuwa wurinta, saboda ta saki jiki da kai, kuma ka daina yi mata wannan muzuran" Adam ya jinjina kai yana wasa da yastun hannunsa. "Je ka, da safe in Allah ya kaimu kan ka wuce, ka biyo" Bai ce komai ba ya fice. Ayshercool. Chat me on what's app, to subscribes yours 08081012143 *PAID BOOK NE, ₦500 NE VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA, 08081012143* Gaba ɗaya ji yake duk wani girma da mutuncinsa sun zube, kamar shi ace wai zai je wurin wata ƴar yayyiyar yarinya yayi zance da ita, wai zai aureta, ko aurensa na fari aisha ta kammala deegree ya aureta, wannan shi ba ya tunanin ko primary ma ta gama. Mama kuwa kwana ta yi ba barci, sai addu'a kawai da take yi, ji take tamkar ta rufe rumaisan da duka, dan bayan gama ƴan koke-kokenta tuntsirewa ta yi ta hau bacci. Mama ta kalleta ta girgiza kai ta ce "Allah ya shiryeki, ya ganar da ke" Da asubar fari, bayan rumaisa ta idar salla, ta tafi ɗakin su mai sunan baba ta yi sallama, suka amsa mata. Ta leƙa ta ce "Yaya usy jiya kun dawo da yaya aliyun?" Abdallah ya ce "Wuce ki bawa mutane wuri, duk ba ke ki ka janyo ba, karfa kawai" Mai sunan baba ya kalli Abdallah ya ce "Kar ka kuma gaya mata haka, bai dawo ba a can ya kwana, duk saboda ke, gaba idan ki ka sake, ke zan kai musu in karɓo shi, dan mun fi son sa a kan ki, mara kai kawai" Sumi-sumi ta juyo za ta fito, ta fuskanci kowa haushinta yake ji yau. Usman ya ce "Wallahi yau da na ga malam shamsun nan a masallacin asuba, ji na yi kamar na ɗaga shi na wurga shi cikin kwalbati, shi ne babban munafukin da ya je ya kai wa ƴan sanda" Mai sunan baba ya ce "Ba ruwanka da shi, ku bari mu kashe wannan case ɗin tukuna". Abdallah ya ce "Ni malam lawan mai shago na kusa kifawa mari, ya biyo ni wai rumaisa ta yi masa asarar ƙwai cret huɗu, wai in zo in biya, na ce masa sai dai mu yi kokowa ya ɗiba, gaba ɗaya mutane fuska biyu ce da su". Rumaisa da take tsaye tana jin su da sauri ta ce "Wallahi ko kret ɗaya bai yi ba, bai fi guda shida ba fa" "Au laɓe ki ke yi mana ko?" Abdallah ya faɗa yana nemo abun duka. Da gudu ta shige ɗakin mama, sai dai irin kallon da maman ta yi mata, ya sanya ta rasa in da zata saka ranta. Haka ta tsuguna ta takure, da duku-dukun mama ta shiga kitchen, ta girka abinci, gari na yin haske, ta ce lallai mai sunan baba ya taso su tafi station ɗin. Mai sunan baba ya ce "Mama, idan kin je wurin nan babu abun da zaki iya a kai, ki bari zan je ni da Usman" Mama ta ce "Ni dai ka ƙyaleni na je na ga a yaya ya kwana?" "Lafiya ƙalau ya kwana, kuma in sha Allah zamu dawo miki da shi, ki yi haƙuri" da ƙyar mama ta yadda, ta basu abincin suka tafi. Rumaisa ta ce ita ba zata tafi makaranta ba, sai yaya Aliyu ya dawo. Mama ta ce "Aikuwa ba ki isa ba, sai kin shirya kin tafi, wataƙila kan ki dawo na huce, dan da na kalleki haushi nake ji, haka kurum saboda ke kin saka an kulle mini ɗa, mara jin magana" shiru rumaisa ta yi tana kallon mama, kenan yanzu mama ta daina son ta?. Jiki a sanyaye ta shirya, mama ta hanata kuɗin makaranta, ba babban abun da ya sake ƙular da mama, irin yadda rumaisan ta zauna ta naɗi abincinta, kamar abun bai dameta ba sosai. Haka ta tafi makaranta, tana tunani kala-kala, amma har ga Allah abun ya dameta. Kamar yadda ammi ta buƙata, da safe Adam ya je gidan, a lokacin su iman duk sun tafi makaranta. Ya ɗau sabir yana yi masa wasa, sai dai ƙememe yaron nan yaƙi dariya, sai bin sa da yake da kallo. Ammi ta fito suka gaisa, ta ce "Yanzu wurin aikin zaka tafi?" "Eh, na biyo na karɓi saƙon ne". Ammi ta ce "To, tun da baka tambayeni ba, ni bari na gaya maka yadda muka yi da turaki". Ya sunkuyar da kai yana wasa da hannun sabir. "Mun tattauna da shi, ya ce mini in bari ya dawo daga umara, zai yi magana da su wambai, dan na san akwai ƙalubale, tun da rumaisa ba jinin sarauta ba ce, ko ƴar wani sananne ba, dan haka zai yi muku Addu'a a can, da ya dawo aka daidaita kuɗin aure za'a kai, bayan salla idan Allah ya kaimu za ayi" "To, Allah ya wuce mana gaba". "Amin, wai da ce mini yayi, Jamil ya ce ko za'a maye gurbin Fulani da samha, ni dai ban ce komai ba na shigar da maganar rumaisa, dan ita ta fi kwanta mini" Adam har mamakin ƙaunar da Ammi take yi wa rumaisa yake yi, tabbas da so samu ne, Samha ta maye gurbin aisha, dan ita ta isa mace da hankalinta da iliminta, kuma Samha ta daɗe tana son shi, ya san hakan, amma ammi ta dage a kan wannan ƴar yayyiyar Yarinyar. Ya numfasa ya ce "Allah ya kyauta" Ammi ta miƙa masa leda ta ce "Gashi nan, sabuwar jakar makaranta ce, da litattafai da turare, ka kai mata ka ce ina gaisheta" Adam ba yadda ya iya, ya karɓa ya amsa da to. Ya fita riƙe da ledar kayan a hannunsa, ya san zuwansa wurin Yarinyar nan, ba abun da zai ƙara masa sai raini. A harabar gidan ya tarar da Mahmud, tun da ya dawo yana ganin shige da ficen motocinsa, amma basu ta ɓa haɗuwa ba sai yau, yana tsaye a wurin parking space ɗin Adam, kusa da in da zai ɗau motarsa. Adam bai kula shi ba, shi ma bai kula shi ba, ya je ya buɗe motarsa ya kunna, ya ɗan jima a ciki, amma ya ga Mahmud ba shi da niyyar matsawa, ya din ga danna horn, amma Mahmud ya yi burus, ba tare da wani ɓata lokaci ba Adam ya bawa motar wuta, yayi reverse, ai kuwa ya buge Mahmud, ko kaɗan Mahmud bai kawo Adam zai yi masa haka ba, kan ya ankara ya ga Adam yana ƙoƙarin bi ta kansa, ba shiri ya mirgina, Adam ya ja motar da gudu ya bar gidan. Ma'aikatan gidan suka yo kan Mahmud suna yi masa sannu, suna ƙoƙarin ɗaga shi, sai dai ciki gwasalewa ya nuna musu shi zai iya tashi, sai dai abu kamar wasa, da ya miƙe ɗin ƙafa taƙi takuwa. *** Rumaisa tana hanya tana addu'a, Allah ya sanya yaya Aliyu ya dawo, Allah ya sa komai ya wuce, sai dai ko da ta iso gida, ta tarar da Usman da mai sunan baba amma babu Aliyu. Cikin damuwa ta ce "Yaya usy ina yaya Aliyun yake?" "Ke, case ɗin nan fa maƙabcinmu malam shamsu, ya yi uwa yayi makarɓiya yana ta kambama abun, gaba ɗaya ma sun ƙi saurarmu a station ɗin, wai sai DPO ya zo, DPO na zaci wanda ku ka yi case ɗin nan ne kwanaki, ashe an canza wani, sun kafi wai sai an je state cid tun da aka yi iƙrarin kisan kai". Rumaisa ta ce "Na shiga uku, ba fa yaya Aliyu ne ya ce zai kashe shi ba, shi ne ya ce zai kashe shi". "Koma menene ba ke ki ka janyo ba rumaisa, duk abun da mutum zai gaya miki sai dai ya shiga ta kunnen dama ya fita ta hagu, saboda wautarki kin jefa ɗan uwanki a wahala" Usman ya ce "Dan Allah mama ki daina faɗar haka, ƙaddara ce" A fisace mama ta ce "Rufe mini baki, ko na make ka, ai duk gidan nan babu mai koya mata rashin ji irin ka" "Allah ya baki haƙuri, ba ri mu yi salla mu koma". Adam kuwa ko kaɗan bai ji babu daɗi ba abun da ya yi wa Mahmud, dan a lokacin nan yadda ya hasala, da ya samu dama sai ya taka shi da mota uban kowa ya huta, ya sauke masa wannan girman kan da rashin mutuncin da yake ji da shi. A haka yake wurin aiki, ya gama abun da yake yi ya fito, yana da niyyar zuwa gidan gona, sai dai dole ya je ya kai wannan saƙon kan mama ta ɓata ranta. Mahmud kuwa ƙarshe, sai ka shi sashin Mummy aka yi, a rikice take tambayarsu maiya same shi, suka gaya mata Adam ne ya buge shi da mota. Nan da nan ta hau ta fara bala'i "Wannan wane irin wulaƙanci ne, anya Adam bai fara shaye-shaye ba? Ko dai haryanzu haukar ce a kansa, tayaya zai taka ka da mota? Wallahi ba zan lamunta ba sai na ɗau mataki" Mahmud ya ɗan cije lips ɗin sa ya ce "Ki rabu da shi zan rama ne, yanzu ni dai ƙafata zafi take yi ki yi wani abu a kai" "Wallahi ba zan ƙyale ba, Fauziyya ɗauko key mu tafi asibiti kawai, Allah ya sa ba wani abun ne ya samu ƙafar ba" "Mummy, dan Allah ki rabu da shi, am just testing his anger, ashe yana nan a yadda yake bai canza ba" yayi maganar cikin zolayar Mummy. Cikin fushi ta ce "Ka rufe mini baki, this is an serious issue, ba zan bari ba" ganin yadda ta ɗau zafi ya sanya shi yin shiru yana kallon ƙafarsa. A ƙofar gidan su rumaisa, Adam ne a tsaye, yake kiran wayar Aliyu, amma shiru bai ɗauka ba, wayarma a rufe take, ya kira har ya gaji, ya aika yaro ya ce ace ana sallama. Usman ne ya fito, domin duba waye, ya tarar da Adam a tsaye, ya ƙarasa yana wani basarwa, suka gaisa sama-sama. Adam ya ce "Aliyu nake nema, na kira wayarsa ba ta shiga" Usman ya kalleshi, ya lura ta su ta zo ɗaya da Aliyu sosai. Ya ce "Ya ɗan haɗu da tsautsayi ne" ya bashi amsa a taƙaice. "Wane irin tsautsayi kuma?" "Eh waccan yarinyar ce ta tsokano ɗan daba, ya je tare mata, kuma dama ta yi rigima da maƙwabta, shi ne mai gidan ya saka aka kama su, tun jiya muke zuwa police station, an ƙi sakinsa, yanzu ma komawa zamu yi" Mamaki ne ya sha kan Adam, duk rumaisan ita kaɗai ta janyo wannan tarzomar. Cikin mamaki ya ce "Wai duk ita wannan Yarinyar ce ta yi faɗa da ɗan daban?" Usman yayi wani irin murmushi ya ce "Wannan ta wuce tunaninka, ka san ƙanwar maza ce, bamu raineta da tsoro ba" Adam har cikin ransa ya ji babu daɗi kama Aliyu da aka yi, ya ji da rumaisan aka kama ita da ta janyo abun. Ya ce "Ko zan iya magana da maman?" Usman ya ce "Ok, bari na yi mata magana". Bayan an yi wa Adam iso ya shiga gidan, ya tarar da rumaisa a takure a falon mama, sai rarraba ido take yi, suka gaisa da mama ya sanar mata da Usman ya gaya masa abun da ya faru" Mama ta ce "To, yakamata ka sake tunani a kan auren nan naku, ku gidan sarauta ba kwa son shirme, rumaisa kuma Allahn da yayi ta ba ta ji ko kaɗan, faɗa da maƙwabta faɗa wai har da ɗan daba, yaron da har kisan kai yake yi" Adam ya kalli in da rumaisa take, ta haɗe rai saboda yadda mama ke kwance mata zani a kasuwa, ya ce "Me ya haɗaki da ƴan daba, har aka kama Aliyu?" Shiru ta yi tana wulƙita ido, mama ta ce "Zaki yi bayani ko sai na mareki?" Ƙasa-ƙasa da murya ta faɗi abun da ya faru, ta wani fannin tana da gaskiya, a kan me zai aiketa sayen sigari. Adam ya ce "Ba damuwa mama, bari mu je a fito da shi, ba wani state CID, wani station ɗin ne?" Usman ya ce "Dama yanzu zamu koma da mai sunan baba sai mu tafi gaba ɗaya " wani mugun kallo da mai sunan baba ya yi wa Usman ya sanya yayi shiru, Sarai Adam ya ganshi, dan haka ya ce "Bari mu je da wuri, kuma dole ita ma a tafi da ita". Mama ta ce "Idan ma sun ƙi yarda, ku basu ita ku dawo mini da Aliyu" sanin ba ta da gaskiya ya sanya ta sunkuyar da kai ta yi shiru. Mama ta so bin su, amma kasancewar yanzu magana ake ta siriki, mama ba zata iya shiga motar Adam ba. Bayan tafiyarsu mai sunan baba ya ce "Amma ba kya ganin yawan shigarsu cikin al'amuranmu da yi mana alfarama, ba zai saka nan gaba su cigaba da kawo buƙatunsu ba, kuma ba yadda muka iya sai mun bi ba?" Mama ta ce "Babana ka san na fi kowa taka tsantsan da gudun duniya, bana jin hakan, shi ya sanya na amince" Ya ɗan rausayar da kai ya ce "Shikenan, bari na bi su a napep" Suna tafe Adam yana kallon rumaisa ta mudubi, sai wani gyatsine baki take yi, tana harare-harare kamar mai shirin iskokai. Cikin station ɗin suka shiga, aka yi musu iso wurin DPO, cikin sa'a suka tarar da malam shamsu a station ɗin yana ta cigaba da zigar kai su Aliyu CID. Adam ya ce "Case ɗin ƙanina na zo mu yi magana a kai, na san shi ba mai laifi ba ne" Malam shamsu ya ce "Ta ina, yana mana iƙirarin kisan kai a cikin unguwa" Usman ya ce "Wai kai malam shamsu meye yake damunka, meye ribarka idan an rufe Aliyu ne?" Mai sunan baba ne yayi sallama ya shiga, suka amsa masa ya nemi wuri ya zauna. Adam bai ko kalleshi ba ya cigaba da magana ya ce "Da ku ka caje Aliyu kun same shi da makami?" DPO ya ce "A'a" "Good, ɗayan fa, abokin rigimar ta sa" "Eh, mun kama shi da wuƙaƙe da tabar wiwi" Suna cikin maganar aka shigo da su Aliyu. DPO ya kalli rumaisa ya ce"Ni mamakina ma da wai duk a kan wannan Yarinyar ce ta haɗa faɗan, ke meye ya haɗaku?" Ta cunkusa baki ta ce "Cewa yayi na sayo masa sigari, kuma ni ba ƴar iska ba ce ba da zan taɓa sigari ina ƴa ma ce mai mutunci " Adam a ransa ya ce "Ko wa ya tambayi jinsinta kuma oho' Malam shamsu ya kada baki ya ce "Ƴar iska kum ta nawa, zance da ya cika unguwa" Zabura rumaisa ta yi ta ce "Yaya usy ka ji ko? Yanzu idan na yi magana ace ba na jin magana, da kunnenka ka ji yana ce mini ƴar iska, ni fa bar ƴar iska ba ce ba, bana wasan banza da maza, meyasa ake ce mini ƴar iska?" Ta yi maganar hawaye ya wanke mata fuska. Malam shamsu ya ce "Ke da aka ce an yi garkuwa da ke, ki ka dawo da ɗa, ai ba abun mamaki bane ba, tun da kowa ya san a unguwar nan ba ji ki ke yi b.... Mai sunan baba ya daki tebur da ƙarfi ya ce "Ya isheka malam" DPO ya ce "A gaban nawa, da rashin mutunci da rashin sanin darajar doka". Malam shamsu ya ce "Tuba muke Yallaɓai". Usman yayi ƙasa da muryarsa ya ce "Uban waye ya saka ki yi kuka a gabnsa, salon ya rainaki, idan ya kuma gaya miki ki ce kin yi ɗin" Adam ya numfasa ya ciro ID card ɗin sa ya bawa DPO ya ce "Ina son a bi tsarin doka, a bani Aliyu sannan a tura mai laifi gaba" Ware ido DPO yayi ya ce "Ranka ya daɗe dama kai ne? Ai da ko waya ka yi ya wadatar ba wani abu in sha Allah, case ya mutu daga nan" "And, shi wannan da yayi iƙirarin kashe Aliyu da wannan yarinyar, a kai mini shi state CID, sannan a kamo mini yaransa ma, zan bincika wanda ya saka aka sake shi ana tuhumarsa da kisan kai" Dpo ya ce "In sha Allah ranka ya daɗe" baki buɗe malam shamsu ya din ga bin Adam da kallo, da mamakin ina suka samo Adam. Adam ya dubi malam shamsu ya ce "Kai kuma, daga yanzu idan zaka yi gulmar, ka din ga nunawa mutanen unguwar ni, ka ce nine wanda yayi mata cikin shegen ta haifa, ta dawo ya karɓi abun sa, idan da wanda zai ɗau mataki a kan hakan ƙofa a buɗe take. A saya mini shi a ceil, sai na waiwaye shi" Cikin tashin hankali ya ce "Dan Muhammad Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama ka yi haƙuri, ka yafe mini, wallahi kuskure ne" Adam ya ce "Kai Yanzu wannan da ko magana ma ba ta iya yi ba, ba ta san ma'anar abunda ake faɗa ba, ta yi maka kama da mai cikin shege? Ƙaddara ƴar ka ce zaka je kana faɗar wannan maganar?" Ya sunkuyar da kai yana girgiza wa. "Ko da wasa, ka kuma gaya mata wannan mummunar maganar, sunana Adam Sharif Galadima, zaka ga abun da zai biyo baya" Ware ido malam shamsu ya yi, a radio yake jin sunan Adam, sai kuma ya san shi ne mamallakin katafaren gidan gonar da yake cikin unguwar, cikin tsuma ya ce "In sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, tsautsayi ne" Duk da wannan abun da Adam ya yi wa rumaisa bai burgeta ba, aka bawa Aliyu kayan sa, suka fito daga station ɗin, Adam ya rungumo Aliyu suka fito, Usman ya riƙo rumaisa, mai sunan baba ya fito shikaɗai ya kama gabansa. Cikin motar Adam suka shiga, ya kunna suka fita, suna tafe ya ce "Aliyu, dan Allah daga yau komai za ta tsoka no, ku ƙyaleta ita kaɗai ko zaneta ne ayi, ka ga yanzu haka kurum ta janyo maka kwanan ceil" Aliyu ya ce "Ba ayi haka ba babban yaya, tuba muke yi" "Ai ni ko ba a tare mini faɗa ba, ina da ƙarfi" "Rufen baki ko na cillaki ta tagar nan" Usman yayi maganar yana nuna mata taga. Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba, Adam da Aliyu kuma suna taɓa hira, rumaisa har mamaki take yadda yau Adam ya buɗe baki yana magana haka da Aliyu. A ƙofar gidan su rumaisa Adam yayi parking, Aliyu ya yi ta masa godiya, Adam ya ce "Ka daina wannan godiyar mana, kar ka saka na ji kunya, ai kai nawa ne Aliyu a gaida mama" suka yi musabaha ya fita, Usman ya buɗe motar ya fita, rumaisa har ta fita Adam ya ce "Ke tsaya, Ammi ta bani saƙo na baki" Rumaisa ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Sunana rumaisa, ba ke ba" yai kamar bai ji ta ba, ya ɗauko ledar wurin ammi ya miƙa mata, ta ƙare masa kallo ta ce "Ni ammi ba ta ce za a kawo mini wani saƙo ba, ni ba zan karɓa ba, duk wani abu da ya fito daga wurinka bana so, balle nan gaba ka ce mini kwaɗayayyiya, gidanku da nake zuwa saboda sabir ma, a dole na haƙura, saboda gorin da ka yi mini, ina ji ina gani ina ƙaunar ɗana, amma ka saka na yi zuciya na daina ganinsa, ni ba zan karɓi abunka ba" ta tsallaka ta shige gida ta bar shi da kayan a hannu. Ayshercool.ml Chat me on what's app, to subscribe yours. 08081012143 PAID BOOK NE, ₦500 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143. Sororo ya bi rumaisa da kallo, dan ba ƙaramin mamaki ta bashi ba, ba ya son mama ta fito ta ce za ta yi masa godiya, dan haka ya shige motarsa ya ja ya bar ƙofar gidan. Mama kuwa murna ta din ga yi da ta ga Aliyu, nan da nan ta ce Yasir ya ɗora masa ruwan wanka, ta kalli Usman ta ce "Ina yake, na yi masa godiya?" Rumaisa ta ce "Ai ya tafi" mama ta harareta ta yi mata shiru, dan haryanzu ba ta huce ba, da abun da rumaisan ta aikata. Usman ya ce "Ina saƙon da na ji ya ce ki tsaya ki karɓa?" Ta kwaɓe fuska ta ce "Ni ban karɓa ba, cewa na yi ya koma da abun sa ba na so" Cikin takaici ya ce "Dalla matsa ƴar baƙin ciki, ke da ba roƙarsa ki ka yi ba, kawai sai ki ƙi karɓowa" "Taɓ, haka kurum yayi mini gori wataran" "Uban waye ya ce miki wanda aka haifa a cikin arziki yana gori? Ai idan kin ga mai kuɗi yayi gori, to dama matsiyaci ne, daga baya yayi arzikin kuma wataƙila a tsiyarsa zai mutu" ba wani fahimtar abun da yake faɗa ta yi ba, ta shiga harkokin ta. Sai dai ta kasa sakin jikinta, duba da yadda mama ta haɗe rai, taƙi kulata. Aliyu ya yi ta basu labarin irin abubuwan da malam shamsu ya din ga faɗa a kansu da rumaisa, na ɓatanci da yadda ya ziga a ka kulleshi, duk ba a same shi da makami ko wani laifi ba. Usman ya ce "Gajiyayyen wahalalle, irinsu ne masu ƙarewa a tsiya, kuma idan bai yi wasa ba, sai na ɗaga shi na buga da ƙasa. Ai ni abun da gayen nan yayi masa ya burgeni wallahi, da ya ce shi ne uban ɗan kuma ya karɓi abun sa". Rumaisa ta yi farat ta ce "Yauwwa, na ji ya ce wai shi ne yayi mini cikin, to dama shi cikin yin sa ake yi, yi wa mutum ciki ake yi" Aliyu ya ce "Bismillahi, ashe haryanzu hankalin da saura". Ganin kowa ya yi mata shiru ya sanya ta ce "Yaya usy baka bani amsa ba". "To me zan ce miki, wai ke haryanzu kanki a tukunya yake, baki san meye rayuwa ba, baki san me yakamata ki din ga tambaya ba, Allah ya sa mai sunan baba ya ji ki, shi sai ya baki amsa" "To me na yi daga tambaya?" "Idan kun yi auren sai ya baki amsar" Aliyu ya kalli usman ya ce "Kai fa wasu lokutan sai a hankali, kai ba ka ji kunya ba kake gaya mata hakan?". "To yaya zan yi mata bayani, ita kai kamar computer abun da ka zuba mata kawai shi ta sani, idan suka yi auren ai aikace za ta gani" Aliyu ya ce "Kaii usman lafiyarka kuwa? Kar ka gurɓata mata tunani malam" Mama da ke ɗakin ta ce "Ke, ki taso ki zo ki kunno mini maganin sauro" mama ta kirata, dan katse waccan hirar da suke yi, dan idan aka zurafafa rumaisan ba ganewa zata yi ba, kuma wani zancen za ta ɓallo. *** Yanayin fuskar Ammi kawai ya kalla, ya san akwai matsala. A nutse ya ce "Ammi na dawo" Ta kalleshi, ta kalli ledar hannunsa ta ce "Wannan ledar fa?" Ya kalli ledar ya ce "Saƙon da ki ka bani ne, ta ƙi karɓa" "Saboda me?" Ammi ta tambayeshi cike da tuhuma. "Ta ce baku yi waya ba, baki ce mata zaki aika mata da saƙo ba, dan haka ba zata karɓi abun hannuna ba na zo daga na yi mata gori wataran" Ɗan jimm ta yi, ta wani fannin rumaisa tana da gaskiya, kuma ammi ta sake jinjina lallai rumaisa tana da tarbiyya. "Dole fa ka sauke wannan shan ƙamshin, da sarautar ka dawo dai-dai level ɗin ta, domin ku fuskanci juna kai da ita, dan ba zan lamunci ku yi aure, ku din ga zaman doya da manja ba, kamar wasu maƙiya" Adam ya ce "To in sha Allah" dan ya rasa mai zai cewa ammin. Ta sake nisawa ta ce "Sannan na ji abun da ka aikata, Jamila ta zo har falon nan ta nuna ni da yatsa, ka saka mota zaka kashe mata ɗa, adam ƙiyayyar da ka ke yi wa ɗan uwanka har ta kai haka dama? Ka yi yinƙurin kashe shi?" Adam ya yi shiru, ba tare da ƙoƙarin kare kansa ba. "Kai a rayuwarka duk yadda nake tausaya maka, da yin iya ƙoƙarina a kan ka, baka gani ko? Kullum burinka ka tsokano abun da za ayi ta yi mana surutu, saboda wannan zafin zuciyar ta ka ko? Gobe in Allah ya kaimu ka je ka yi masa sannu, sannan ka bata haƙuri, magana kuma har ta kai kunnen wambai yana nemanka" Dam ƙirjin Adam ya buga, ya je ya duba Mahmud, ya bawa Mummy haƙuri, sannan wambai yana nemansa. Cikin dakiya ya ce "To, in sha Allah duk za a yi" ya juya ya fice daga ɗakin. Ko abinci kasa ci yayi, abubuwa sun yi masa zafi sosai kwanan nan, ya tara ayyuka sosai a office, gashi duk iya binciken da yake ya gano, ko garkuwa da aisha shiri ne ya kasa samun komai, amma wasu daga cikin bayanan rumaisa, na nuni kamar da akwai wani abu a ƙasa,gata gardamammiya ya san idan jajjagenta zai yi ba zata yi magana ba, sai ta ga dama. Ga wannan batun auren nasa da ammi ta sako shi a gaba a ƴan kwanakin nan, babu damar ya motsa, sai ta yi zancen rumaisa, shi gaba ɗaya baya farin ciki da wannan auren. Ga surutan da ake ta yi a kansa a media, kullum ƙazafi kala-kala, ayyukansa da ya ɗauko kan sace Aisha hankalinsa ya rabu biyu duk yayi sanyi, bai samu sun kammalu ba, tun sa shi ne jagoran aikin. Ji yayi kansa ya fara ciwo, ga wani irin jiri da ya fara ɗibarsa daga zaune, a hankali ya ja jikinsa ya kwanta, gaba ɗaya bai san ta ina zai fara ba da matsalolin nasa. *** Yau mama ko sallar asuba ba ta tashi ruma ba, sai da Usman ya tsula mata wayar caji a ƙafa ta tashi, ta yo alwala ta yi salla, ta gaida mama, amma maman taƙi amsawa. "Mama wai dan Allah ba zaki kulani ba?" Ta yi maganar cikin damuwa. "In kulaki in ce miki me? Ai ki je ki yi rayuwarki ruma nima zan yi tawa, ƴaƴana suna buƙatar rayuwata, ɓacin ranki ba zai ƙarasani ba, na yi magana a samo langa-langa ayi miki ɗakinki, dan ba zan cigaba da zama ɗaki ɗaya da ke, kina zucguna mini ba" Ba ƙaramin mamaki mama ta bawa rumaisa ba, dan a ganinta mama ta daina sonta, ta tashi jiki a sanyaye, ta je yi shirin makaranta, ta tafi ba tare da ta sake kula mama ba, sai dai abun yayi ta damunta, ga wani irin son ganin sabir da take yi, ga kuma alwashin da ta ci a kan sa. Ita kanta wasu fitintinun da take yi, tana son ta daina amma Allah ya gani, ba za a taɓa ta ta ƙyale ba. Adam kuwa, Yau kamar wanda aka gayawa wani mummunan saƙo haka yake jin sa, komai ba ya yi masa daɗi, tasbihi kawai yake yi ko ya samu sassauci, ammi kuma ta sake nanata masa cewar ya je ya aiwatar da abun da ta ce na bawa Mummy haƙuri da duba Mahmud domin komai ya wuce. Ba a son ransa ba sai domin cika umarnin ammi, ya nufi sashin Mummy. Sai dai da ya tambayi Fauziyya, ta ce masa suna ɗakin Mahmud. Kai tsaye bai jira wani iso ba, ya shiga sashin da Mahmud yake, yana zaune a kan gado, an ɗaure ƙafarsa da bandeji, da alama ƙashin ƙafar ya taɓu, amma ba irin so serious ɗin nan ba. Mummy na gefen Mahmud tana takura shi ya ci abinci. Mummy ta wani haɗe rai, Mahmud ya yi wa Adam kallo ɗaya, ya mayar kan abincinsa, aka rasa wanda zai amsa masa sallamar da yayi. Hakan ba ƙatamkn ƙulara da shi ya yi ba , ya ji kamar yayi ficewarsa, amma ya san makircin Mummy. Ya dubi Mummy ya ce "Na ji baki ji daɗin abun da ya faru ba, am sorry for it, shi kuma Allah ya bashi lafiya" ya juya zai fita Mummy ta ce "Dan Allah Adam wace irin ƙiyayyace kake nuna mana haka? Har ka taka ɗan uwanka da mota, meyake damunka ne?" "Ba mayar da magana, ko bibiyar tarihi na zo mu yi ba, na baki haƙuri kar a sake saka mahaifiyata a duk wani abu da zan yi, ni na yi laifi ba ita ba" "Amma Adam ni kake gayawa haka? Da na isa da kai, ko giwa ta nuna maka ina da muhimmanci a wurinka ai da ban tunkareta ba, kai zan yi wa sanin yi maka maganar ba shi da amfani, ba zaka saurara ba ya sanya na sameta". "Kuma shine har da gayawa wambai? Idan haka ne maiyasa maganar ba ta tsaya iya nan ba?" "Magana ake yi ta rai fa adam, yinƙurin taka shi da mota ka yi". Mahmud ya ce "Mummy ki ƙyale shi dan Allah, kin san abnormal yake, kuma ko da ya takani da mota, za a iya ɓugewa da cewa ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa, sai dai zan sake ɗaukar nauyi, gidan jaridar fallasa su wallafa cewa ka yi yinƙirin takani da mota ka kashe ni" Mahmud yayi maganar cikin zunzurutun izgilanci. A zafafe Adam ya juyo, ya ɓarar da kayan abincin, ya shaƙe Mahmud zuciyarsa na tafasa. Mahmud ya kalli cikin idon Adam ya ce "Ka daina jin haushi idan an ce baka da lafiyar ƙwaƙwalwa, duk mutumin da bai iya sarrafa fushinsa ba, ƙwaƙwalwarsa babu lafiya ". "Kai adam, ka cika shi kar ka kashe shi mana, jama'a ba kowa a kusa ne?" Mummy ta fara kwarmato. Sanin cewa mutuncinsa zai sake zubewa, muddin aka sake zuwa aka gansu a yanayi mara daɗi shi da Mahmud, kuma ran ammi zai sake ɓaci, ya sanya shi sakin Mahmud, ya fice da sauri. *** Maƙwabta suka yi ta shigowa yi wa mama jajen abun da ya faru, na kama Aliyu, sai dai a wannan karon mama a tsorace take da mutanen, dan kar su je su yi musu wani sharrin. Rumaisa ta saba sa ta dawo, mama za ta ce mata, ga ruwan wanka ta wanke wannan gumin da ƙarin ranar, idan an gama abinci ta ci ta yi salla ta tafi islamiyya, amma yau ta dawo ba ruwan wanka, ga mama ba ta kulata ba, haka ta yi abun da zata yi ta tafi islamiyya. A ƙa'ida, ta kan ci abinci sau huɗu zuwa sama a rana, ba wai abincin take tsayar da hankalinta ta ci ba, zaɓe-zaɓe ne da ita, ga irin cin abincin yara take yi, tana ci tana wasa, ko da ta fara ta ce ta ƙoshi. Kullum ta dawo daga islamiyya sai ta ci abincin yamma, sai dai a yau ɗin ma mama ba ta ajiye mata abincin ba, gashi bata mayar da hankali ta ci na rana sosai ba, bugu da ƙari ta ga mama ta ɗora tuwo a matsayin abincin dare. Ba ta kula kowa ba, sai kukanta suka jiyo a ɗaki, Usman ya leƙa, ya tarar ta kwaso kayanta, tana ta ninkewa tana zubawa a bagco tana kuka, kamar mai shirin yin yaji. Cikin mamaki ya ce "Ke! Meye haka?" "Haɗa kayana nake yi, cikin dare idan kowa yayi bacci in bar gidan nan, tun da dai ba a ƙaunata" maimakon ya ji haushinta, wata uwar dariya ce ma ta kama shi. "Waye ba ya ƙaunar ta ki?". "Ba mama ce ba, ta daina kulani, wallahi duk faɗan da aka yi da ni nice mai gaskiya, ya za ayi ace in sayo sigari? Kuma dan meyasa wannan shamsiyyar zasu din ga ce mini ƴar iska, sai ayi ta yi mini abu ba zan rama ba" Usman cikin salon tsokana ya ce "Gaskiya babu daɗi kam, yanzu to ina zaki tafi?" "Tun da ba a sona a gidan nan, katsina zan koma wurin ƴan bindigar, wurin su barde, au ashe an kashe barde to dai daji zan koma na yi bukka na zauna a ciki" ta yi maganar cikin kuka mai tsuma zuciya. Usman kamar ya shiɗe dan dariya, Aliyu da su Huzaifa kansu dariya suke yi mata. Aliyu ya ce "Mama ki yi biko, saboda ke za ayi yaji" Mama ta ce "Idan ta tafi nima na huta, Allah ya raka taki gona, ku ƙara mata kuɗin mota". Jin furucin mama ya sanya ta sake tunzura tana kuka ta ce "Shikenan, bakomai" Ta ɗauko bagconta tana kuka, Huzaifa ya ce "Allah sarki rumaisa, zamu yi kewarki sai a darul salam" ta sake fashewa da kuka. Yasir ya ce "Rumaisa a yafi juna, Duk in da ki ka je ki zauna lafiya da mutane, koda yake ai kin ce a bukka zaki zauna ke kaɗai, Allah ya kiyaye hanya ga wannan" ya baya naira ɗari. Ta saka hannu ta karɓa, suka cigaba da tuntsra mata dariya, ita kuma bil haƙƙi da gaske barin gidan za ta yi. Ta waiwaya tana kallon mama, ta ga mama ko a jikinta, jajjagenta ma take yi, ta nufi hanyar soro. Abdallah ya ce "Yarinyar nan fa ba hankali ne ya game jikinta ba, bari na bi bayanta. Ta dafe kayanta ta fita waje, ta tsaya tana tunanin wace hanya za ta bi, kamar sama sai ga mai sunan baba. Ya kalleta ya ce "Meye haka? Ina zaki? Kukan me ki ke yi?" Ya jejjero mata tambayoyin. "Tafiya zan yi" ta faɗa tana share hawaye. A kausashe ya ce "Zuwa ina?" "Mama ba ta so na, kowa ya tsaneni shi ne na ce barin gidan zan yi, an bani kuɗin mota ma" tayi maganar tana nuna masa kuɗin hannunta. Takaici ne ya ƙule mai sunan baba, gaba ɗaya rumaisa ba ta da wayo wasu lokutan cikin takaici ya ce "Dalla wuce ko na mareki" Za ta yi Magana, ya daka mata tsawa zai kai mata duka, ta taka da gudu ta koma cikin gida. Abdallah da ya biyo bayanta kuwa, dariya kamar zai shiɗe. Mai sunan baba ya biyo bayanta zuwa gidan, su Usman ya saka a gaba ya din ga yi musu masifa, saboda sun bar rumaisa ta fita, ba sa tsoron ta yi wani wurin. Mama ta ce "Ka daina yi musu faɗa, ita ta haɗo kayanta ta ce barin gidan za ta yi" Mai sunan baba ya yi wa rumaisa wani mugun kallo ya ce "Zaki wuce ki ajiye kayan nan, ko sai na zaneki, idan ki ka bar gidan, wurin uban wa zaki je, mara wayo" sumi-sumi ta shiga ta ajiye kayan a falon mama. Har dare suna yi mata dariyar abun sa ta yi, wanda hakan ya sake tunzarata. Mama tana kallon rumaisa ta tada kai da kayanta, ta ƙi yin shimfiɗa ta kwanta, kuma ba ta ci Abincin dare ba. Mama ta girgiza kai ta ce "Ubangiji Allah ya shiryeki, ya rabaki da wannan rashin ji haka rumaisa, idan auren nan alkhairi ne Allah ya tabattar da shi, ya san silar shiriyarki ne". Ta gyara mata kwanciyar, ta lulluɓeta. *** Takawa ya ji zafin maganganun Mahmud sosai da sosai, abun yayi masa ciwo, sai dai ya bar abun a ransa, wani irin takaici ya cigaba da ci masa zuciya, a rayuwarsa ya tsani raini da wulaƙanci, amma Mahmud ya ci masa mutunci haka. Aliyu ne ya faɗo masa, dan haka ya kira shi, domin jin idan babu wata matsala. Aliyu sai da ya ɗan ji kunya, ya ce "Tuba nake babban yaya, ni yakamata na kiraka, ya ka je gida?" Adam ya ce "Lafiya ƙalau, ya mama?" "Tana lafiya, ta ce za ta yi maka godiya, amma muka tarar ka tafi" "Ahh haba, ba wannan tsakaninmu, ina fatan babu wata matsala, dan irin yaran nan, ka san suna da nasu yaran, duk da an kama su, kar su cutar da ku, ko kai ko ita da yayi iƙirarin zai kashe". "Aliyu ya ce babu wani abu, duk muna Lafiya, mutuniyar ce dai ta tatara kayanta wai barin gidan za ta yi, ba a ƙaunarta". Adam ya ce "What? Ku saka ido a kan ta sosai fa, na fuskanci za ta iya aikata duk abun da ta ce, kar ku je ta yi wani wurin" Aliyu ya yi murmushi ya ce "Babu in da zata je, mai sunan baba ya tsawatar mata". Adam ya ce "To Allah ya tsare, ka gaida mutanen gidan" "Za su ji in sha Allah, a gaishe mana da mai sunan babanmu" "Zai ji in sha Allah". Ganin yadda rumaisa ta addabi kanta, ya sanya mama sakkowa daga fushin da take yi da ita, ta yi ta mata nasiha, duk da ta san nasihar tata ba ratsa rumaisa take yi ba, dan za ta iya gama nasihar tana fita tsakar gida, ta ɗora daga in da ta tsaya. Bayan ta gama yi mata nasihar, ta dubeta ta ce "Ni kuwa rumaisa, ya batun al'ada ne? Tun da ki ka dawo baki yi ba fa, ko kin yi a can hannun ƴan bindigar?" Rumaisa ta ce "Wace al'adar?" "Jinin haila mana" Rumaisa ta ce "Taɓ, ni fa tun da na yi sau ɗaya, na fitsarin jinin nan, ban kuma yi ba, Allah ya yaye mini, shi ma dan wannan mugun mutumin ya watsa mini ruwan kwata ne na yi" mama ta ɗan yi jimm tana kallonta, dama hakan ta kan faru ga macen da ba ta saba yin al'ada ba, amma ta ƙudirce a ranta za ta kai rumaisa asibiti. Adam yana office ɗin sa, yana tsaye a jikin window yana kallon titi, hannunsa riƙe da kofin shayi, yana ta tunani daban-daban, ƙarar buɗe ƙofar office ɗin ce ta dawo da shi hayyacinsa, ya waiwaya. Jamil ya gani kamar an koro shi, Adam ya ce "Ya dai? Ya na ganka a haka kamar ba lafiya?" "Adam da gaske aure zaka yi?" Adam ya ajiye kofin hannunsa ya ce "In ji wa?" "Mai girma turaki ne ya sanar da ni" "Ba yana umara ba?" "Magana mu ka yi da shi ta video call" Ya juyo ya fuskanci jamil sosai ya ce "Haka ne, Turaki ba zai yi maka ƙarya ba" "Amma Adam idan ka yi wa Samha haka ka yi mata adalci kuwa? Meyasa zaka auri wata ba samha ba, ko dan ba ƙanwarka ba ce ba ka san zafin so ba?" Adam ya shafi sumar kansa ya ce "Ba soyayya nake dubawa ba, makomar ɗana nake dubawa, samar masa da jajirtacciyar uwar da za ta kula mini da shi" "Kana tunanin akwai wanda zai so ɗanka, ya nuna masa kulawa sama da ita da suke uba ɗaya da Aisha" "Ba za a rasa ba" ya bashi amsa cikin ko in kula. Cikin fushi Jamil ya ce "Anya kuwa kana da imani Adam, duk wahala da son da yarinyar nan take yi maka, ba zaka duba ba". "Jamil, maganar ammi zan ajiye na bi son zuciyata ne?" "Kana nufin ammi ce ta zaɓi wadda za ka aura?" Abun da Jamil ya faɗa, ya sanya Adam sanin cewa turaki bakomai ya gaya masa ba dan haka ya ce "Ina nufin ammi ma ta yi amanna da Yarinyar" "Kenan menene makomar Samha?" Adam ya numfasa ya ce "Da zan iya, da na haɗa su su biyu, sai dai ba zan so gidana ya zama irin gidanmu ba, bana son damuwa, kuma na san dole zan cutar da ɗaya a cikinsu, Samha ƙanwata ce, muna da alaƙa ta jini da ita, zan iya karkata gareta, saboda kusancin alaƙarmu, ita kuma waccan ta yi mini abun da ko duniya zan ba ta ba zan biyata ba, zan iya karkata gareta dan girman halaccin abun da ta yi mini. Sai dai a duk su biyun babu wadda zan gazgata cewar ita zuciya ta ke so, abu ɗaya na sani" ya taka gaban Jamil yayi ƙasa da muryarsa ya ce "Bana son ɗana ya yi rayuwa irin wadda mahaifiyarsa ta yi, so nake ya rayu a matsayin sa na cikakken ɗa a gidan mahaifinsa, ka san abun da nake nufi". Ayshercool. 08081012143 PAID BOOK NE, ₦500 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143. Cikin tsananin mamaki, Jamil ya kalli Adam ya ce "Me ka ke nufi?" Adam ya dafa kafaɗar Jamil ya ce "Ba sai mun zurfafa ba, ka san abun da nake nufi, kai ɗan uwana ne Jamil, Samha ma ƙanwata ce, ba na son zumuncin mu ya samu matsala saboda wani dalili, a madadina dan Allah ka bawa Samha haƙuri, ina fatan Allah ya zaɓa mana abun da ya fi alkhairi daga ni har ita" Daga haka Adam ya fice ya bar Jamil a tsaye da buɗaɗɗen baki. Ammi kuwa waya suke yi da rumaisa, rumaisa tana ba ta labarin yadda takawa ya fito da Aliyu bayan rigimar da suka yi aka rufe shi, wanda shi Adam ɗin sam bai gaya mata ba. Ammi ta jinjina al'amarin, tare da yi mata Allah ya kyauta. Gaba ɗaya rumaisa ba ta san wani abu wai kunyar suruka ba, mama na ta ƙifta mata ido, amma sosai take ta yi wa ammi surutu. Ammi ta numfasa ta ce "Rumaisa na bayar da saƙo a kawo miki ki ka ƙi karɓa ko?" Rumaisa ta ce "Laa ashe da gaske yake, na zata shi ya bani, na ce ba zan karɓa ba, bana son wataran yayi mini gori" "Ahh haba dai, ba zai taɓa yi miki gori ba, duk abun da ya baki ki karɓa ba zai cutar da ke ba, sannan ki din ga yi muku Addu'a a kan lamarin auren nan na ku, turaki na daf da dawowa". Ita gaba ɗaya ma ta manta da maganar auren, sai yanzu da ammin ta tuna mata. "To, ammi kin san wani abu?" Ammi ta ce "Sai kin faɗa" "Kewar sabir nake yi sosai, daurewa nake yi dan kar na din ga takura muku" Ammi ta ce "Subhanallah, rumaisa zan ci gidanku fa, ni akwai wani abu mai kama da takura tsakanina da ke, ba ni na ce duk lokacin da ki ke so ki gaya mini a kawo shi ba? Za'a kawo miki shi ranar da babu makaranta, na san shi ma yana kewarki". Rumaisa ta yi murmushi ta ce "To ammi, na gode sosai ki gaida kowa da kowa" "Yauwwa ko ke fa, za su ji in sha Allah" Ammi ta katse wayar tana murmushi. A can falo kuwa, Iman ce take bawa sabir abinci, an fara gwada masa abu mai ruwa-ruwa. Baba uwani na ta tsokanar iman "Ohh tsakanin uwa da ɗa sai Allah, tsakanin Sabir da iman sai Allah" Iman ta yi murmushi ta ce "Tsakanin kaka da jikarta ma sai Allah ba" Baba uwani ta ce "Uhumm kakar da yake yi wa ƙyuya, daga ke sai ammi sai babansa, sai kuma Nusaiba idan ya ga dama, yaro ba ya yadda da kowa" "Kar ki damu baba uwani, zai yadda da ke ne" "Mhmm, ni kuwa Iman, ina yarinyar da aka ce ta tsinci yaron nan, Haryanzu tana nan kuwa?" "Laa tana nan baba uwani, baki taɓa ganinta ba?" "Oho, yo ni a ina zan ganta ma" Iman ta ce "Kai haba, ta zazzo gidan nan fa sosai da sosai, ai duk ƙyuyar nan da yake yi, ba ya yi mata, dariya sosai ke ba kya ce shine ba". Baba uwani cikin son bugun ciki da gulma, ta sake ƙasa da murya ta ce "Ni kuwa wai babba ce ko yarinya?" "Gaskiya Yarinya ce sosai, dan duk mun girmeta" "Ikon Allah, ƴar nan unguwar ce kuma? Na ji kin ce tana zuwa gidan nan, ai ni fa ban zaci ma ƴar nan garin ce ba". "A'a ba unguwar nan take ba, zuwa take yi, amma kwana biyu ma ba ta zo ba". "Ikon Allah, ni kuwa dan Allah duk ranar da Allah ya kawota ki nuna mini ita" Iman ta yi murmushi ta ce "Maman sabir, to shikenan in sha Allah" Baba uwani ta yi gaba tana jin alamun nasara. Tafiyar baba uwani babu jimawa, sai ga Jabir yayi sallama, cikin sauri Iman ta rufe kanta da hula, ta gyara zamanta, tare da mayar da hankalinta sosai a kan Sabir. Murmushi Jabir yayi, ya ƙarasa kusa da ita ya zauna ya ce "Gashin ake yi mini rowar gani kuma?" Ta yi masa shiru ba ta ce komai ba. "Talk mana iman, ko miskilanci ne?" Ta yi masa shiru, ta cigaba da bawa Sabir abinci, Jabir ya miƙe hannu ya ɗauki Sabir, yana ƙure Iman da wani irin kallo, wani irin abu yana fuzgar zuciyarsa game da ita. Wuyanta yake bi da kallo, ya haɗiye wani irin yawu, ya zaunar da sabir a jikinsa, amma Sabir ya ce bai san zance ba ya sanya kuka. "Ka bani shi abinci nake ba shi". "Ba zan baki ba, sai kin kalleni kin amsa mini" Ammi ce ta fito falon, cikin fara'a ta ce "Jabir, kwana biyu ina ka ɓuya ne?" Yayi murmushi ya ce "Tuba nake ammi, ayyuka ne suka yi mini yawa sosai" Ammi ta kalli Sabir ta ce "Rigimamme, kai ba ka gane iyayenka ne, kowa ma ba zai ɗauke ka ba?" Iman ta tashi daga kan kujerar, ta karɓi Sabir ta bar falon, yadda ya ɗan shagala yana kallon iman ne ya sanya ammi jinjina kai a ranta ta ce "Yaushe wannan lamarin kuma ya kunno kai? Akwai ƙura idan Hajiya Lubabatu ta sani, amma da zan so faruwar hakan jabir ba shi da matsala' "To ya gidan ya hajiyar taka?" "Tana nan ƙalau Ammi, na je na duba Mahmud ne, na ji abun da ya faru sam bai yi mini daɗi ba ammi" Ammi ta nemi wuri ta zauna ta ce "Kai dai bari jabir, lamarin ɗan uwan nan na ku sai addu'a kawai, dan ku din ga yi masa faɗa, yanzu a garin wannan zafin zuciyar ta sa da ya yi masa illla ko ha salwantar masa da rayuwa fa?" "Kai, ai takawa sai haƙuri, iya masa sai Allan da ya yi shi, amma iya ƙoƙari muna gaya masa gaskiya, sai dai ayi ta yi masa addu'a, Allah ya yaye masa wannan azababbiyar zuciyar" "To Amin, Allah ya iya mana" Nan suka cigaba da hira da shi da ammi, sai dai hankalinsa ya fi karkata ga yadda yake jin iman a ransa. *** Cike da zullumi Samha ke cin abincin da yake gabanta, ba dan yana yi mata daɗi ba, sai domin zullumin abun da Jamil zai zo ya gaya mata, tun da ya gaya mata sun yi magana da turaki adam zai yi aure ta rasa nutsuwarta, so take ya zo ya gaya mata idan har hakan da gaske ne. "Wai Samha ba zaki kwantar da hankalinki, ki nutsu ki ci abincin nan ba, sai jagwalgwala shi ki ke yi?" Samha ta ce "Mama yaya jamil nake jira, hankalina ba zai kwanta ba sai na ji abun da nake son ji". Ƙanwar Samha, wadda daga ita sai ita mai suna Zainab ta ce "Ni wallahi Samha mamaki ki ke bani, wallahi babu yadda za a yi namiji yayi mini abun da Adam yayi mini na sake kallonsa, ke kam kamar mara zuciya, shiyasa na koma zaman hostel ma na bar miki gidan, yadda ki ke zubar da classic ɗin ki a kan gayen nan yana bani haushi, kamar wani ɗan gold" "Enough zainab, kar ki sake saka mini baki a maganata, idan ba so ki ke na yi miki rashin mutunci ba". Mama ta ce "Ya isa haka, ni bana son faɗa, daga dawowarki". "Mama kin san dai babu yadda za a yi ina ganin gaskiya in ƙi faɗa, Allah ya taimaki soyayyar wahala" ta ƙarasa maganar tana tashi ta bar dining ɗin. Samha gaba ɗaya ba ta yanayi na yin faɗa, dan haka ba ta tankawa zainba ba ta shareta. Jamil ne yayi sallama, mama ta amsa masa, Samha kuwa kasa amsa masan ta yi sai bin sa da ido da ta yi. Ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga cikin jerin kujerun falon. Samha ta taso cikin sauri, ta ce "Yaya Jamil ya ake ciki ne? Tun ɗazu nake jiranka" Yayi shiru bai ce mata komai ba, "Yaya magana nake fa" Ba tare da ya kalleta ba, ya ce "Samha ki na ji na?" "Eh ina jin ka" Ya taso ya zauna sosai ya ce "Samha, ina son ki saurareni da kyau, ki yi haƙuri ki cire Adam a ranki, a wannan karon ma ba zai aureki ba, domin kuwa ya tabattar mini da cewa mahaifiyarsa ta zaɓa masa wata matar, kuma turaki na dawowa za a kai masa kuɗin aure" Ras! Gaban Samha ya faɗi, ta dafe ƙirjinta ta ce "What, again ta sama mata? Iman ko? Iman ce na sani, wai dan Allah me na yi wa matar nan ta tsaneni haka? A wancan karon ma ita ta yi uwa da makarɓiya ban auri Adam ba, a wannan karon ma ta kuma yi mini, na san ba wadda za ta zaɓa masa sai Iman" Mama ta ce "To, ai a wannan karon sai ki kwantar da hankalinki, tun da an kuma kwatawa, sun nuna muraran ba sa ƙaunarki, sai ki ƙyale mata ɗanta ko?" Samha ba ta iya cewa komai ba kawai ta tafi ɗakint, tamkar wadda take shirin zarewa, kaiwa ta din ga yi tana komowa a ɗakin, cikin zafin rai ta furta "Giwa me na yi miki, ki ke ƙyamar haɗa zuriya da ni ne? To wallahi a wannan karon ba zan yadda ba, ko ni ko ke ko mu rasa Adam daga ni har ke, har wadda zaki aura masan" ta yi maganar tana zubewa a kan gadonta cikin ƙunar rai. *** Dukan teburin gabansa yayi, tare da tura kujerar da yake kai baya, ya ce "Aikin banza kawai, wai shi adam ɗin wanene da ganin ƙarshensa ya gagara, duk wannan abubuwan da aka yi a kansa, na gidajen jaridu da social media, yayi burus ya ƙi cewa uffan, sai ma wasu da yake turowa suna kare shi, wannan wane irin abu ne haka, ta ina kuma ya rage a ɓullo masa?" Usman wakili yayi murmushi ya ce "Yaro man kaza, kai fa ka ce da na sakar maka ragamar komai, zaka iya komai ka san ta yadda zaka ɓullowa lamarin" Khalifa ya ce "Haka ne Daddy, na yi duk iya yi na, ka sani na zaci yadda maganganun nan suka yamutsa hazo za su gigita shi, amma ya mayar da mutane mahaukata wato mu je ma mu yi ta yi kenan" Senator ya yi murmushi ya ce "Na jinjinawa ƙoƙarin ka Khalifa, ban taɓa zaton zaka iya wannan ƙoƙarin ba ma, ka bani mamaki sosai kuma na yabawa ƙoƙarin ka, labarin da yake zuwar mini, hankalin yaron nan ba ya kanmu yanzu, kuma waɗanda suke jagorantar aikin tare da su, na saye wasu daga cikinsu, sannan kuma dama shi yake jagorantar aikin, kuma hamkalinsa ba ya kan aikin yanzu, na yi magana da shugaban kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa, mun gama magana ba wani abu zasu wanke ni" "Amma daddy kana ganin hakan ya wadatar, kar fa ya kuma ɓallo mana ruwa". "Ai ba haka zan bar shi ba, ba ka da wata damuwa, na san abun da nake yi" Khalifa yayi murmushi ya ce "To shikenan daddy" *** Adam yana zaune yana aikinsa a office ɗin sa, ya ɗau wayarsa ya kira Bashir. Suka gaisa Adam ya ce "Ka je ka maƙale ka ƙi dawowa, akwai update ne?" Bashir ya ce "Babu wani update, sai dai na haɗu da barrister Sa'ad, ya ce akwai yiwuwar kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa a kan senator Usman wakili ba zai yi wani tasiri ba" Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na sani, dama ban ji a raina za su yi wani abun kirki ba, amma babu damuwa, zuwa next week ko upper in sha Allah zan shiga Abuja, ina son zuwa EFCC". Bashir ya ce "Meyasa ba zaka shigo next week ba?" "Wallahi ammi ce ta sakoni a gaba da wani batu, yanzu da na ce zan yi tafiyar nan, za ta ce ban ɗau abun da muhimmanci ba" "Eh kuma haka ne, to shikenan Allah ya kaimu upper week ɗin, ni ranar sunda in sha Allah zan shigo kano, dama da zaka zo next week ɗin ne sai na jiraka, duk yadda ake ciki dai za mu yi waya" "To shikenan Bashir, Allah ya yi mana jagora " "Amin ya rabb, a tashi lafiya". Ya ajiye wayar kenan, Jabir yayi sallama a office ɗin Adam, Adam ya kalleshi ya ce "Me ka ke yi a nan lokacin aiki?" Jabir ya harare shi ya ce "Ban sani ba, sai avoiding ɗina kake, ba na samunka a gida, gidanka ma baka nan, na ce bari na zo na ritsaka a nan" "Amma dai ka san lokacin aiki ne yanzu ko?" Jabir ya ce "Ai lokacin salla ne kawai ba zan datseka ba, kuma sai ka saurareni, ai ka san abun da ka yi ba ka kyauta ba, dole ka yi ta gudun haɗuwarmu" Adam yayi masa shiru, ya cigaba da aikinsa. "Adam, ka san yanzu kaf idon duniya a kan kan ka yake, amma na lura kai ba ka damuwa da hakan, baka gudun janyo wa kan ka magana, yanzu dan Allah da wani mummunan abu ya faru da Mahmud saboda zuciyarka me zaka ce? Yakamata ka sassauta wa zuciyarka wannan ƙiyayyar da ka ke yi masa, ko kana so ko ba ka so ɗan uwanka ne shi" Adam ya yi masa shiru, wanda wannan shirun shine halayarsa da ta fi ɓatawa makusantansa rai. "Ko ka kulani, ko kar ka kulani, na san dai kai ba kurma bane ba, kuma ka na jina, jibi in Allah ya kaimu zan je duba galadima" sai a yanzu Adam ya ɗago ya kalli Jabir ya ce "Ubangiji Allah ya tsare hanya, ka ce ina gaishe shi" Jabir ya girgiza kai ya tashi ya fice, dan halin Adam sai shi wasu lokutan. *** Tun da rumaisa suka yi waya da ammi, take ta zuba ido ta ga ta ina za a kawo mata Sabir ta ganshi, danne zuciyarta kawai take yi, mussaman idan ta tuna da alwashin dabta yi wa Adam, a akan ba zata sake zuwa gidansu ba. Ammi kuwa ta kasa ta tsare, ta ce lallai Adam ya ɗauki Sabir, da shi da Iman su je a kaiwa rumaisa shi, ko awanni su yi tare ta ganshi, tun da dai an yi mata alƙawarin yin hakan, a duk lokacin da ta buƙata. Tun da Iman ta ji za su je gidansu rumaisa, gabanta ya faɗi, saboda tana matuƙar fargabar haɗuwa da yayan rumaisa mai sunan baba, dan ita gaba ɗayansa tsoro yake bata. Adam dan dai babu yadda zai yi da ammi ne, ba zai iya bujerewa maganarta ba, amma a ganinsa tun da ya yadda da auren, wannan aika shin da ammin take, ba abun da zai janyo masa sai raini. Da la'asar suka shirya, aka shirya Sabir suka fito domin tafiya gidansu rumaisa, Adam na gaba iman na bin sa a baya da Sabir. kasancewar Mahmud ƙafarsa ta fara sauƙi, ya fara yawonsa a cikin gidan, hango Iman yayi da yaron a hannunta, wanda ko ba a gaya masa ba ya san shi ne jaririn, haka nan ya ji ya kwaɗaitu da son ganin fuskar yaron, tun da a yanzu, kansa kawai ya hango, mai ɗauke da tulin suma baƙa wuluk. Suna tafe a hanya Iman na yi wa sabir wasa, yana ta miƙa hannu yana son kamo sitiyarin motar. "Iman" Adam ya kira sunanta. "Na'am yaya". "Abubuwa sun fara yi mini zafi, na san magana zata fara yawo a kan auren nan nawa, dan Jamil ya zo ya tutsiyeni na gaya masa idan maganar gaske ne, kuma na tabattar masa da gaske ne, abun da nake so da ke, dan Allah ku yi shiru da bakinku, kar wanda ya san wa zan aura, idan an yi auren sa ganta" "Yaya kunya ka ke ji ace rumaisa ce matarka?" "Ke rabu da ni kawai, banda rigimar ammi, ina ni ina wannan Yarinyar da a rayuwarta babu wanda ta raina kamar ni, kuma bana son a cutar da ita, Samha haryanzu tana son aurena, a wannan karon ma ba zai yiwu ba, shiyasa bana son kowa ya san wacece". "In sha Allah yaya ba zan faɗawa kowa ba, ammi ma ta gargaɗemu a kan hakan" Ya ce "Good, ku shiga ki kai mata shi, ni zan je gidan gona, wancan karon ban samu na je ba, saboda wani dalili " yayi maganar lokacin da ya yi parking. Ta ce "To shikenan, sai ka dawo" ta sauka ta ɗauki kayan rumaisa da ammi ta sake bayarwa a bata, ta shiga gidansu rumaisa da sallama. Sai dai gidan shiru, babu alamar aksai mutane a gidan. Iman ta yi sallama, sai dai muryar da ta amsa mata sallamar ce ta razanata. Kasa shiga ta yi, ta kuma kasa komawa baya. Shi kuma bai kuma tankawa ba, sallama ta kuma yi, ya ce "An amsa a shigo mana" daga ɗakin mama take jiyo muryarsa, kamar mai shirin arangama da horo, ta shiga ɗakin. Mai sunan baba ne a zaune yana cin abinci, mama kuma tana salla. Cikin ɗar-ɗar, ta shiga ta zauna hannunta rungume da Sabir, kanta a ƙasa ta ce masa "Ina wuni?" Bai kalleta ba ya ce "Lafiya lau" Sabir ya ƙurawa mai sunan baba ido, "Miƙo mini shi" yayi mata maganar cikin umarni. Kai a ƙasa ta miƙa masa Sabir, ya rungume shi yana cewa "My boy, ka ƙara girma Masha Allah" bai yi masa ƙyuya ba, ya cigaba da cin abincin sa, iman ƙoƙarin satar kallon mai sunan baba take tana tsoro, shi kuma da ya lura da hakan, sai ya tsareta da idonsa tana ɗaga ido suka yi ido huɗu, aikuwa ta razana ta sunkuyar da kanta. 'Yarinyar nan tana da hankali kuwa?' mai sunan baba ya tambayi kansa. Mama ta idar da salla da addu'a, ta juyo tana yi wa iman sannj da zuwa. Iman ta gaisheta mama ta amsa mata cikin sakin fuska, Iman ta ce "Ammi ce ta ce a kawo wa Anty rumaisa Sabir" Mama ta ce "Allah sarki, yanzu za ta shigo daga islamiyya, ya babansa?" "Yana lafiya shi ya kawomu, zai dawo ya ɗaukemu ma" Mama ta kalli Sabir ta ce "Mutumin, zo mu gaisa mana" ya sake kwanciya a jikin mai sunan baba, yana cin hannunsa. "Allah ka aika munafukinmu ƙarshen nesa, mamarmamar, igiyar ƙasa ko da lafiya ko babu mamarmamar" Rumaisa ta shigo tana waƙe-waƙenta, da ƴan ciye-ciye. Tana shiga falon mama sabir ta fara gani, ta buga tsalle zata ɗauke shi, mai sunan baba ya ce "Fita ki yi sallama" sumi-sumi, ta koma ta yi sallama, sannan ta ɗau sabir tana murna. Ta kalli Iman ta ce "Anty iman sannu da zuwa, ya ammi?" "Tana lafiya tana gaishe ki" Babban abun da ya bawa mama mamaki, bai wuce yadda Sabir ya saki fuskarsa ba da ya ga rumaisa. Rumaisa ta shimfiɗa tabarma a tsakar gida ta ce "Anty Iman, dawo daga nan mu yi hirarmu, ya fi iska" Haka yayi wa iman daɗi, dan mai sunan baba ya takurata. Rumaisa ta cire wandon uniform ɗin ta, daga  ita sai rigar uniform, ba hijjabi ba ɗankwali, sai murna take yi. "Anty Iman, bari na zubo mana abinci" Iman ta ce "Wallahi a ƙoshe nake" "Ba kya cin abincin gidan talakawa dai" Da sauri Iman ta ce "A'a wallahi" Rumaisa ta ce "To kawai zan zubo ki ci". Rumaia ta zubo wa Iman jallof rice, mai kyau har da nama, ta kawo mata ruwa, ita kuma ta ɗauko tukunyar da aka yi girkin da cokali da yaji ta zo ta zauna. "Anty rumaisa me zaki yi da tukunya kuma?" "Ƙanzon shinkafa zan ci ya fi daɗi" Iman ta zuba mata ido tana dariya, rumaisa ta din ga kankarar ƙanzo ta na ci, Sabir ya din ga zura hannu yana nema ya ci shi ma. Iman ta na cin abincin tana yi wa rumaisa santin abinci yayi daɗi. "Garadan mama ne suka girka, kuma ba wani daɗi yayi ba kar su ji ki ziga su" hira suke yi sosai da iman. Suna tsaka da hirar suka ji sallamar Adam a ƙofar shigowa gidan, suka amsa masa, mama ta ce ace ya shigo, mai sunan baba ya tashi ya baro ɗakin mama, dan ya san nan zai shiga. Adam na shigowa da rumaisa ya fara tozali, ta taƙarƙare tana kankarar ƙanzon tukunya tana ci, kamar mayuwanciya, ga kuma abinci mai kyau a gaban iman, Sabir kamar zai shiga cikin tukunyar, yana son ya duntsi ƙanzon ya kai bakinsa. Ayshercool. 08081012143 PAID BOOK NE, ₦500 VIA 0009450228,AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143. Sallamar Adam bai hana rumaisa cigaba da taƙarƙarewa tana ƙwaƙwalar ƙanzo da cokali tana cin kayanta ba, ba ta da niyyar tashi ma ta saya jikinta, abun da ya dameta kawai take yi. Usman da tun zuwan iman yana cikin ɗakinsu, ya leƙa ta window, ji yayi kamar ya fito ya kifawa rumaisa mari. Adam ya wuce su, ya shiga wurin mama, Iman ta kalli rumaisa ta ce "Anty rumaisa baki gaida takawa ba?" Ruma ta kwaɓe baki ta ce "Kin ga ya kulani ne?" "Amma da kin yi masa magana zai kula ki" Rumaisa ta ce "Wallahi ba zai amsa ba" Cikin mamaki iman ta ce "Meyasa ki ka rantse" Ruma ta ce "Mufa gidan nan babu mai kalar halin da babu, dan haka ko sau ɗaya na haɗu da mutum zan gane halinsa, ni ba dan Sabir ba kuma a daina ce mini ƴar iska ba, ba abun da zai saka na aure shi, kuma dai ina son ammi ita ma ina jin maganarta, amma wannan mak faɗan da zuciyar taɓ" Iman ta ce "Wai ni, meyasa ba kwa shiri ne, wallahi takawa mutumin kirki ne sosai Anty rumaisa, ko wani abun yayi miki?" "Hmm ba ruwanki a wannan faɗan" Iman ta ce "Haka ne, faɗan masoya ne" aikuwa rumaisa ta ƙware da ƙanzo jin abun da iman ta ce, "Taɓ lallai kin tafka saɓo" Iman ta kuma cewa "Allah Anty rumaisa, yaya Adam yana da kirki sosai, ki din ga yi masa uzuri, abubuwa sun saka shi a gaba, kawai kina ganinsa a haka ne, idan ki ka ji abubuwan da yake ciki sai kin tausaya masa". Ruma ta taɓe baki ta ce "Da zai gane da ya daina ɗaukar damuwowinsa a zuciyarsa, babu abun da zasu ƙara masa sai nauyin zuciya, ya din ga ɗaukar damuwowinsa a ƙwaƙwalwarsa, ita ke da ma'aunin samar da mafita" Mamaki ne ya kama Iman, jin rumaisa na wani lissafi, da ba ta gane ba. "Ban gane me ki ke nufi ba". "Kar ki damu, manta da ni kawai, bari na ɗauko takarda da biro ki rubuta mini lambar wayarki, zan din ga kiranki muna hira". Iman ta yi murmushi ta ce "Akwai jotter a jakata, bari na rubuta miki" Aikuwa ta rubutawa rumaisa lambarta, a lokacin rumaisa ta shagala da wasa da sabir, sai dariya yake yi. A daidai lokacin Adam ya fito, mama ganin a yadda rumaisa ke zaune ba ƙaramin ƙular da ita ya yi ba. Iman ta ce "Anty rumaisa kawo shi mu tafi" a take jikin rumaisa yayi sanyi, ta sake rungume Sabir. Mama ta ce "Ke bana son shirme, ki ba ta shi su tafi" Kawai ta fara kuka, hawaye wani na bin wani, wanda a ganin adam kawai shagwaɓa ce da wulaƙanci. "Mama dan Allah a bar mini shi a nan, mu kwana tare" mama ba ta saurari rumaisa ba, ta karɓi sabir ta bawa iman. Wadda jikinta yayi sanyi, tausayin rumaisa ya mamaye mata zuciya. Kallon ruma da take kuka Sabir yake yi, Iman ta ce "Ka yi wa maminka bye-bye" Kwaɓe baki ya shiga yi, zai yi kuka, Adam ya karɓe shi ya yi waje da shi, saboda haka nan ya ji tausayin su ya kama shi, wata irin Soyayya mai ban mamaki tsakanin yaro da zuciyar da ba ta uwassa ba. Iman ta dafa kafaɗar rumaisa ta ce "Anty ruma ki yi haƙuri kin ji, da kun yi auren nan, za a dawo miki da sabir ɗinki, ki daina kuka" ruma ta jinjina mata kai ta ce "Ki gaida Ammi, da wannan ɗin nan mai kamar da baban sabir" "Tom za su ji in sha Allah" Suna tafiya mama ta dirarwa da rumaisa faɗa, mussaman a kan rashin hankalin da ta tafka, a gaban wanda zata aura ta taƙarƙare tana kankarar ƙanzo tana ci, babu ko kunya balle kawaici, ga wannan koke-koken na babu dalili da take yi, a duk lokacin da aka kawo sabir. Ita dai rumaisa a wurinta, ba ta ɗau adam wani na mussaman ba, balle idonsa ya hanata abun da take yi, tun da duk gidansu maza ne, ita ba ta ɗau abun da ta yi wani laifi ba. Maganar Sabir kuwa, ta barwa ranta cewa babu wanda ya san halin da take ciki sai Allah a kan yaron nan, dan haka ta daina damuwa a kan mitar da ake yi mata. Usman ya fito yana faɗin "Bagidajiya kawai, wannan ai yawa ne ki ka yi, to wallahi nan gaba rainaki zai yi, sai la ce wata budurwar ƙauye, ke ba wani class bakomai" Abdalla da bai daɗe da shigowa ba, ya tambayi mai ta yi, Usman ya gaya masa, ya ce "Kai yanzu har wani aji kake nema a wurin rumaisa, ai tun da suka ce za su aureta a haka, sai fatan Allah ya sanya su gama lafiya" Ko a jikinta, an mintsini tattaura, abun da ya dameta kawai shi ne a gabanta. *** Su Iman da suka koma gida kuwa, Ammi ba ta nan, Iman ba ta son ta fita ta koma gida ta tarar Ammi ba ta nan, gashi tare suka fita da Nusaiba, Kasancewar Sabir yayi bacci, da shi Adam ya tafi sashinsa ya kwantar da shi, Iman kuma ta wuce ɗakinta. Sai dai tana zuwa ɗakin, ta yi tozali da Samha a tsaye, sai da ta razana ta ce "Anty Samha lafiya kuwa?". "Ban sani ba, munafuka tsintacciyar mage da ba ta mage" cikin rashin fahimta iman take kallonta, dan ba ta san me ya kawo wannan maganar ba. "Saboda tsohuwar munafuka ce, shi ne ki ka je ki ka cewa giwa kina son Adam, za a haɗa aurensa da ke a maimakon ni, duk da irin kashedin da na yi miki ko?" Kamar zata yi kuka ta ce "Ni kuma?" "Ke ɗin fa, algunguma ni zaki yi wa pretending, to ki rubuta ki ajiye, gidan Adam kabarinki ne, yadda aisha ta shige shi ta bar duniya, duk wadda ta shiga bani ba sai ta bita, idan ba haka ba kuwa ayi babu, kowa ya rasa daga ni har ke, da ni ki ke zancen, zan yi maganinki baƙar annamimiya" Gaban Iman ya faɗi da jin furucin da Samha ta yi, tana gama zazzage mata ta yi waje. Jikin iman har rawa yake yi, saboda tsananin tashin hankali, da yadda hankalinta ya dugunzuma, a take rumaisa ta faɗo mata, wato a zaton Samha Takawa ita zai aura, tausayin rumaisa ya kamata ya ruma za ta yi da wannan manyan al'amura ta ko ina, ga maƙiyan mijinta, ga tarin ƙalubalen gidan, ga kuma masifar Samha, a kaf dangin nan babu wanda bai sarawa masifar Samha ba, an shakkarta sosai da sosai, saboda a tsaye take ba ta da kunya, yaya rumaisa za ta yi da ita, ita da take yarinya ƙanƙanuwa?. Rasa abun yi ta yi, ta saɓule ta zauna a kan gadonta, ƙirjinta na cigaba da dukan uku-uku saboda tsananin fargaba. Mintuna kusan sha biyar da fitar Samha, amma iman ta kasa kataɓus, ƙirjinta sai cigaba da bugawa yake yi. Nusaiba ce ta shigo da sallama ta ce "Ashe kun dawo, bamu zaci zaku rigamu dawowa ba, mun je sai wa Sabir kaya, kin san ya kusa 6months, Ammi sai nuna mini irin kayan da za a zubawa amaryar takawa a lefe take, ya kuka baro ta?" Sai da Nusaiba ta kai aya, sannan ta lura kamar Iman a tsorace take. "Lafiya kuwa?" Iman ta jinjina mata kai ta ce "Lafiya lau" Nusaiba ta ce "Kin ga idonki kuwa kamar mara gaskiya, ko wani abun ya faru a gidan da ku ka je ne?" Iman ta girgiza kai alamar a'a. "Tsaya, ko jikinki ne ya motsa?" Iman ta yi ajiyar zuciya ta ce "Babu ko ɗaya, cikina ne ya ɓaci zuciyata ce take tashi" Nusaiba ta sauke numfashi ta ce "Har kin tsorata ni, bari na kawo miki anti acid, ina da shi a ɗakina" iman ta jinjina mata kai. Da Nusaiba ta fita ta sanarwa da Ammi iman ba ta jin daɗi, ulcer ya tayar mata, a rikice ammin ta nufi ɗakin Iman, ta je ta tutsiyeta tana tambayar ko jikinta ne ya motsa. Kamar yadda ta yi wa Nusaiba ƙarya, haka ta dake, ta ɓoye damuwarta, ta tabattarwa da ammi, ulcer ne kawai ya tasar mata. *** Kwanciya ce ta isheshi, musamman da kwana biyun nan, a gida yake wuni saboda ƙafarsa, amma yanzu ta yi saƙi sosai, kawai dai fita ce bai yi ba, gashi ya kusa komawa makaranta. Kamar wanda aka tsikara, ya tashi ya fita falo, ya ɗau lemon kwali mai sanyin gaske, ya koma ɗakinsa, corridor ya nufa, ya buɗe tagar a hankali, wata sassanyar iska ta dake shi, ya zuƙe lemon tare da lumshe idanunsa. Dare ne sosai, manyan security lights, sun haske ko ina na gidan, kukan tsuntsye na ta tashi, da ƙanan ƙwari, ga ƙamshim furannin harabar gidan sun gauraye da sassanyar iskar da ke kaɗawa. Yanayin yayi masa daɗi sosai, sai dai babu tsammani ya ga wani abu yana dudduƙe, yana motsi ta jikin fulawoyin da zai sadaka da sashinsu. Tsayawa yayi ya ƙura ido sosai, yanayin inuwar abun, kamar mace ce, dan har da lulluɓinta. Mamaki ne ya kama Mahmud, ganin maimakon ta shigo direct ƙofa, ta kutsa can ƙarshen ginin da kai tsaye ɗakin Mummy zai kai ka. Bai yi wata-wata ba ya sauka, ya nufi sashin Mummy a hankali, sai dai bai buɗe ya shiga ba. "Kin shanya ni, tun ɗazu nake zaman jiranki, amma baki zo ba" Baba uwani ta risuna ta ce "Tuba nake Allah ya baki yawan rai, sawu ne bai gama ɗaukewa ba" Mummy ta hura hanci ta ce "Ina jinki, bani labari, meke wakana da ki ke son ganina?" "Allah ya baki yawan rai, labari ne nake tafe da shi, idan yayi miki daɗi haka nake fata, idan bai yi ba ayi mini aikin gafara" Cikin ƙosawa Mummy ta ce "Hanzarta, ina jin ki" "Takawa zai yi aure, sai dai alamu sun nuna kamar Iman zai aura, kuma zancen ya iske Samha ƴar wurin turaki, dan ɗazu ta zo har wurin Iman ɗin ta yi mata kashedi da zafafan kalmomi, dan na laɓe na ji komai" "What? Aure kuma? A wannan karon kuma ita za a liƙawa, ita ma ya cinyeta, lallai giwa ba ta tsoron Allah, amma na yi mamakin yadda aka yi Samha ta zo ba ta ƙaraso nan ba, kuma ba ta yi mini wannan bayanin ba, ko da yake ni kujera ce, ko dan zama za a neme ni, jeki na gode na ga yadda wannan lamarin zai yiwu" Baba uwani ta ce "Godiya nake, na barki lafiya". Mahmud ya so shiga ɗakin Mummy, dan ganin wacece wannan, take zuwa a tsohon daren nan, amma ya fasa, ya lallaɓa ya buɗe ƙofa ya fita harabar gidan ya laɓe. Can baba uwani ta fito tana dudduƙenta cikin duhuwar fulawoyi, ta nufi sashinsu ammi, tana buɗe ƙofar, fitila ta hasketa, dan haka ya ganeta da kayan jikinta. Hakan ya fallasa ma wacece ita, domin kuwa baba uwani kayanta ba ɓoyayyu bane ba, duk da tarin alkhairai da suturar da ammi ke bata, amma kullum cikin kaya ɗaya zuwa uku take. Kan sa ya ɗaure da mamakin me take zuwa yi sashinsu, a wannan daren cikin siga ta rashin gaskiya A hankali ya koma sashinsa, gaba ɗaya baya son wannan halin na Mummy, na bin diddigi da shiga abun da babu ruwanta, ya san ƙarshe ba zai wuce rahoton wani abun ake kawo mata ba. Amma ya sha mamaki, idan har ace hadimar ammi ta kusa da ita, za ta aikata mata haka, to duniya kowa ma ba abun yarda bane ba. *** Kwanci tashi asarar mai rai, mai girma turaki ya dawo daga aikin umara da ya tafi, duk da an riga an saba zuwa, amma ba a rasa ƴan sannu da zuwa da su kan zo, domin yi masa barka da dawowa. Ammi ba ta son takura masa, dan haka ta bashi lokaci, tare da sauraron abun da zai ce mata. Duk da a nata ɓangaren ta tsananta addu'a a kan lamarin sosai da sosai, tare da fatan tabattuwar alkhairin da yake cikin al'amarin. Ɓangaren Samha kuwa, da fari a iya tunaninta, za ta iya ji da lamarin, amma abun ya shallake tunaninta, kuma gaba ɗaya hankalinta ya karkata a kan Iman ce ake ƙoƙarin aurawa takawa, dan haka ta fara tunanin yadda za ta yi da ita, a ƙarshe dai ta koma wurin Khalifa, domin samun mafita sannan ta je ta samu Mummy da zancen. Mummy ta yi dariya ta ce "Yaro man kaza, ai na yi zaton ba zaki gaya mini ba, shi ya sanya na zuba miki ido na ga iya gudun ruwanki, ba shakka giwa wata irin murɗaɗɗiyar mace ce, mara alƙibla, dan haka dole ki zage ki san abun yi" Cikin damuwa ta ce "To ni yanzu Mummy ya zan yi?" "Duk abun da ya kama ki yi, ko dai a kan Iman ɗin, ko kuma a kan giwa ko ma adam ɗin. A baya babu abun da ba mu yi ba a kan yarinyar nan, wanda hakan ya sanya duk ta rasa manemanta manyan mutane da suke zuwa wurinta, dan haka yanzu shine giwa ta yanke shawarar ƙarshe na aura mata adam, shawara ta rage gareki, ko dai ki bari ayi auren daga baya ki san abun yi, ko kuma dai ki ɗau wani matakin" "Taɓ, ai wallahi da na bari ya aureta, gara uban kowa ma ya rasa, ni Mummy a cikin malamanki nake son ki haɗani da wani, a watsa komai ko da kuwa yana nufin in rasa ta rasa kowa ma ya huta ne" Mummy ta jinjina kai tana murmushi ta ce "To shikenan, zan yi tunani a kai kar ki damu" "Mummy ba ni da dogon lokacin da zaki yi dogon tunani, dan Allah ki taimaka". "Na ji zamu yi waya, ko zuwa sunday ne, akwia wani ƙauye da nake zuwa, sai mu tafi tare" Samha ta ce "To shikenan, na gode sosai Mummy". Kusan sati guda da dawowar mai girma turaki, giwa har ta fara ƙosawa, tana tunanin ko magana za ta yi masa, babu tsammanni ya kirata a waya ya ce zai zo. Hakan yayi mata daɗi, sai dai ta shiga fargabar da wacce zai zo, da nasara ko kuma babu?" Kasancewar baba uwani na wurin, ammi ta yi waya da turaki, baba uwani ta saci hanya, ta je ta kira mummy a waya, ta kai mata rahoton cewar turaki zai zo, kuma da alama magana mai muhimmanci zasu tattauna, dan haka Mummy tace lallai ta sanya mata ido, ta naɗo mata duk wani rahoto na abun da zai wakana. Bayan sallar azahar, mai girma turaki ya iso gidan, kai tsaye ya sauka a sashin giwar da. Hadimai suka shiga hidimar kawo kayan ciye-ciye, sai dai turaki yaƙi magana a kan haƙiƙanin abun da ya kawo shi, a lokacin da hadiman ke kaiwa suna komowa. Dama tuni ammi ta hana Adam fita, ta ce lallai koma menene ya zauna ayi a gabansa, dan haka shima yana nan. Ammi ta sallami hadimanta, Sannan ta nutsu ta fuskanci turaki. Hakan ba ƙaramin ɓatawa baba uwani rai yayi ba, dan babu damar samun rahoton da take son samu. Ammi ta dubi turaki ta ce "Ranka ya daɗe an dawo lafiya ya hanya? Ban samu shigowa ba, saboda ba na son zuwan nawa ya zama takura ko matsi a gareka, shiyasa ban yi maka sannu da dawowa ba" Turaki ya ce "Kar ko damu, da ke da abun ya shafi zuriyar marigayi, dolenmu ne, kuma babu yadda za ayi ku zama takura a garemu. Toh! Na zo da saƙonki, a can saudiyya ma na je gidan ɗan uwanki mahadi, mun tattauna da shi sosai, kuma ya bayar da amanna sosai. Sai dai da muka dawo gida da kwanaki uku, mun sami wambai, in da ya nuna rashin amincewarsa da nuna za a sake zubar da darajar masarauta, ta hanyar auro wadda ba jinin sarauta ko tushen arziki ba, sai dai na yi iya yina na nuna masa ƴar gidan daraja ce da kuma gudunmawar da ta bayar. Har ila yau ya gaya mana zancen da bamu ji daɗinsa ba, ya kawo ƙorafi sosai a kan ka takawa, ciki har da yinƙurin taka ɗan uwanka da mota, wannan lamari bai yi mana daɗi ba, ya ce ya bayar da saƙo ka je, nan ma ka yi burus. Abun bai yi mana daɗi ba, har yayi iƙirarin babu shi babu kai, sai dai mun yi ƙoƙarin kwantar masa da hankali, in da har mai ɗakinsa ta sanya baki, ta hanyar nuna masa tsaurinsa a gareka yayi yawa, shiyasa ba kwa shiri, amma dai duk da haka yakamata a din ga lura ana kiyaye wasu abubuwan, yanzu idon duniya a kan ka yake". Ammi ta ce "Wallahi ranka ya daɗe, abun da nake yawan gaya masa kenan, amma dai a cigaba da jaddada masa" Turaki ya ce "Haka ne, akwai buƙatar a din ga kai zuciya nesa, akwai abun da yarinyar nan ta faɗa mini a kan ka, wanda kuma tabbas haka ne ba ta yi ƙarya ba, yana daga dalilan da ya sanya na yi amanna da auren nan sosai, nake yi muku fatan alkhairi". Ammi ta ce "Allah sarki, Adam kuma ya sunkuyar da kai, yana murza zoben hannunsa. "To, mun dai yi ƙoƙarin shawo kan wambai da ƙyar, duk da yana nuna ba da yawunsa ba, amma ba wani abun damuwa bane ba zai sakko, illa iyaka kai takawa ka je ka same shi ka bashi haƙuri. Magana ta gaba kuma, a sanar da iyayen Yarinyar nan, ranar juma'a zamu kai kuɗin aure, kuma wata biyu zamu sanya rak, Allah ya tabbatar mana da alkhairi dan ba ma fatan a jinkirta wani abun ya zo ya gilma". Ammi ta faɗaɗa murmushin ta tana faɗin "Alhamdilillah, Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana da rai da lafiya" Yayin da adam wata irin mummunar faɗuwar gaba ta same shi, kansa ya sara da ƙarfin gaske, ya ji tamkar ɗakin yana juya masa! Ayshercool 08081012143 *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* *PAID BOOK NE, ₦500 ME VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143* Gaba ɗaya Adam bai san yadda aka ƙare zaman ba, da ƙyar ya tashi ya nufi ɗakinsa, yana neman yayi karo da bango, dan ko gabansa ba ya gani sosai, saboda matsanancin ciwo da kansa yake yi, ga juya masa da duniyar take yi, ga wata irin kururuwa da yake ji a kunnensa. Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yake ta maimaitawa. Gadonsa ya laluba ya kwanta, yana ta sauke numfashi, yana addu'a, sai dai kamar a hayaniyar yake jin muryar rumaisa, duk da baya gane me take faɗa, daga haka bai kuma sanin in da kansa yake ba. Bai san iya adadin lokacin da ya shafe a haka ba, ya ji ƙamshin turaren ammi, tana taɓa shi ta ce "Adam wai lafiya kuwa?" Ya buɗe idonsa a hankali yana kallon ammi. "Wa meyafaru da kai ne? Tun da turaki ya zo aka yi maganar nan, daga yi masa rakiya, na dawo na tarar baka nan, tun ɗazu kake bacci sallar magariba fa ake yi yanzu" Haryanzu kansa bai daina ciwo ba, ya dubi ammi ya ce "Bacci ne yayi mini nauyi, bari na tashi" "Ka hanzarta ka rama sallolinka, kar ka sake bari lokaci ya ƙure maka ba ka yi salla ba, sonake mu je gidansu rumaisa, mu sanar musu, yau asabar ka ga nan da kwanaki shida kenan za a kai kuɗin" Magana yake son yi, amma ammi ta ce "Bana son musu, ka hanzarta bana son ɓata lokaci" Kawai ya jinjina mata kai, dan shikaɗai ya san abun da yake ji, cikin dakiya ya tashi ya shiga yayi alwala, ammi kuma ta koma falo. Iman kuwa tausayin rumaisa take ji sosai da sosai, ji take kamar ta sanar musu da abun da yake faruwa, da irin furucin da Samha ta yi. Sai dai tana tsoron abun da ka iya biyo baya, mussaman yadda Samhan ta ƙware a iya fuska biyu da masifa, dan ita ba ta tausayawa kanta, yadda Samha ta yi zaton ita adam zai aura, kamar yadda take tausayawa rumaisa. Adam saboda yanayin jikinsa, ya ce wa yaronsa sidi ya kaisu gidansu rumaisa, yayi iya ƙoƙarinsa da jarumta ya danne yanayin da yake ciki, sai dai jirin ya kasa barinsa. Rumaisa kuwa, tana gida jikin mama tana ƙunƙuni, ta yi wa Huzaifa da Yasir rashin kunya, sun ce wannan satin ba za su wanke mata kaya su goge ba sai dai ta yi abun ta. Mama ta goya musu baya, ta ce "Kar ku wanke mata, tun da ba ta da ta ido, ai yakamata ta fara wanke kayanta da kanta yanzu, ke zaki wanke abunki yau" Cikin shagwaɓa ta ce "Dan Allah mama ki ce su wanke mini, idan na yi wanki rashin lafiya zan yi" Mama ta kalleta baki buɗe ta ce "Sangarta mai sanya kifi kukan wanka, samun wuri ne ya sanya ki ke wannan maganganun ma, ke ba dan Allah ya sa da su ɗin ba, ai shekara tara kin fara wankin ki, ko yaushe su suke yi miki, ba kuma dan baki iya ba, dole ki karɓi abunki" Rumaisa ta sake langaɓe kai ta ce "Dan Allah mama ki ce su wanke mini, ni fa yarinya ce" "Eh nono ma ki ke sha" ta kwanta a jikin mama tana cewa "Mama dan Allah" mama na shirin ture rumaisa, ruman ta tashi zaune da sauri, ta ɗan tsuke fuska. Mama ta ce "Lafiya kuwa?" "Kamar baban Sabir zai zo gidan nan, yana hanya" "Baban Sabir kuma?" Ruma ta jinjina kai ta ce "Haka nake ji a jikina" Huzaifa ya ce "Iyeee soyayya da ƙauna, bari zamu gani ai" Rumaisa ba ta iya yi wa Huzaifa martani ba, saboda ji ta yi ƙirjinta ya yi nauyi, jikinta kuma yayi sanyi ƙalau. A hankali ta zame ta kwanta a jikin mama, ta lumshe idonta. "Ki tashi bana son barcin la'asar, ki yi shi ki tashi da fushi ki hanamu sukuni da koke-koke da ɓacin rai" Maimakon ta tashi, sai ta sake langaɓewa, ta riƙe hannun mama. Mama ta kalli rumaisa ta ce "Ke! Lafiya kuwa?" Ruma ta jinjinawa mama kai alamar eh. Mintuna ashirin, sai ga sallamar ammi, mamaki ne ya kama mama, dan ba su yi waya ammi za ta zo ba. Ta ɓoye mamakinta, ta amsa mata cikin mutuntawa. Suka gaisa da mama, ammi ta ce "Maman sabir bacci take yi ne?" Mama ta ce "Rigima dai take ji, wai sai an yi mata wanki, na ce ma ta tashi kar ta yi mini barcin la'asar, ta tashi ta ishi mutane da kukan banza" Ammi ta yi murmushi ta ce "Haba maman rumaisa, kamar rumaisa idan ba ayi mata wanki ba, ai ba zata iya ba, kar a ramar mini da ita kan ta zo fa" Suka yi dariya, ruma daga kwancen ta ce "Ammi ina wuni" "Lafiya ƙalau rumaisa, kina lafiya?" "Lafiya ƙalau" Ammi ta ce "To masha Allah, tare muke da takawa fa" Mama ta ce "Ahh kuma ki ka bar shi a waje, Yasir ka ce ya shigo mana" Ɓoye mamakinsu suka yi, dan rumaisa ta ce ta ji a jikinta yana hanya. Tun da yayi sallama jikinta ya kuma sanyi, ta rasa menene yake yi mata daɗi. Ya shigo ɗakin mama, suka gaisa, mama ta ce wa rumaisa "Ba zaki tashi ki gaishe shi ba?" A hankali ta tashi zaune, ta kalli Adam sau ɗaya, ta kawar da kai ta sake kallonsa na biyu amma ta kasa magana. Mama ta ce "Ba magana nake yi miki ba rumaisa?" Ammi ta ce "Wannan ƴar tsamar ta su, idan da sabo sun saba". Mama ta ce "wannan rashin ɗa'a ne, ya girmeta, kuma mutumin da zaka aura ka din ga yi masa haka, iskanci ne kawai, ai ba haka take yi wa sauran mutane ba" Rirriƙe mama ta yi cikin kuka ta ɓoye fuskarta ta ce "Mama baki san me nake gani ba ne" A rikice ammi ta ce "Me ki ke gani rumaisa, yi mini bayani?" "Hararata yake yi, idan ya harareni ni tsoro yake bani" haka kawai mama ta ji rumaisa ƙarya take yi, dan ta sha faɗa ita fa ban da fuskar mai sunan baba, babu wata fuska da take bata tsoro. A zahiri kuwa, a karo na biyu yau ta ga abun da ta gani a tare da adam, kamar yadda ta taɓa gani, lokacin suna asibiti. Idonsa gaba ɗaya ya koma baƙi ƙirin, babu wannan farin, sai hayaƙi da yake fita, kamar ana kunna itace, a wannan karon har da kamar harshen wuta daga idanun nasa. Shi kansa adam, cikin jikinsa wata irin rawa yake yi, amma a zahiri yana zaune normal, jikinsa ji yake tamkar ana sassra shi, ba bu wani abu da yake muradi, banda ya shaƙe ruma ko ya riƙe ta, ya samu sassauci. Ya sunkuyar da kai, mama kuma ƙuluwa ta fara yi, da lamarin rumaisa, dan a ganinta rashin mutunci ne kawai. Ammi ta ce "Haba rumaisa, shi ne har da kuka, ba hararki yake yi ba, haka yake dai bai fiye fara'a ba, ku da kun kusa zama abu guda ma. Maman rumaisa dama zuwa na yi na gaya muku, a sanar da dangin mahaifinta, ranar Juma'a za a kawo kuɗin aure" Mama jikinta yayi sanyi ta ce "Da wuri haka?" "Kar ki ce haka maman rumaisa, jinkirin ba shi da wani amfani, kin san mu masaurata ba sa son jira, ayi musu addu'a dan Allah, in sha Allah za a kawo kuɗin aure" Har mama da ammi da suka gama tattaunawar su, babu wani ƙwarin gwiwar cewa wani abu, a tsakanin adam da rumaisa, kowannensu shi ya san halin da suke ciki. Bayan sun gama magana, suna fita rumaisa ta tubure da kuka ta ce ita fa ba ta so, ba zata aure shi ba, da fari mama ta fara rarrashin ta, ta zaci abun na ta na hankali ne, amma ta ga ba ta da niyyar nutsuwa, ita dai ba ta gaya wa mama, me take gani ba, amma ta ce ba zata aure shi ba. Shihowar mai sunan baba ce, ta sanya ta ɗan nutsu, Aikuwa tambayar da ya fara yi, shi ne meya sameta take kuka. Mama ta sanar masa da duk abun da ya faru, rumaisa ta zaci yanzu ma zai turje, sai ji ta yi ya ce "Allah ya tabattar mana da alkhairi, nan kano zasu kai, ko can katsina?" Mama ta ce "Wai da su kai wa kawunku na mandawari, ba sai an wahalr da su ba" Mai sunan baba ya ce "Babu laifi, Allah ya kaimu" Cikin kuka rumaisa ta ce "Mai sunan baba ni fa na fasa bana son shi". Wani mugun kallo ya yi mata ya ce "Suwa zaki mayar ƴan iska, ko yau suka ce a ɗaura, sai an ɗaura, ki bari na fita na dawo na tarar kina wannan kukan, ki ga yadda zan yi ƙasa-ƙasa da ke". Haka nan rumaisa ta tsinci kanta da kasa gaya musu abun da take gani a tare da adam, da alamu suka nuna mata su basa gani, ita kaɗai kawai take gani. Usman kuwa cewa yake "Wallahi ba zaki yi mana baƙin ciki ba dan ubanki, haka kurum ke fa ki ke son auren mai kuɗi, kuma Allah ya kawo, ki ce ke ba kya so, kin yi kaɗan yarinya, dole ayi auren nan, ko ba komai ma hau doki, kina kallo albarkacinsa aka fito da Aliyu, yanzu malam shamsu har gaisheni yake, saboda yadda ya kankaro mana mutunci, sai kin je". Cikin kuka ta ce "To ni bana son shi" "Uban da ya sanya, ki ka amince tun da fari, shi zai sa ki haƙura ma a yanzu" gaba ɗaya aka ƙi goya mata baya, ta din ga surutai da koke-koke suka ƙi kulata. Ammi da suka tafi gida, jikinta sanyi yayi, da ganin yadda rumaisa duk ta rikice lokaci ɗaya, kuma ta ga bai kamata ta ɓoye musu wasu abubuwan a kan Adam ba, amma tana ji a jikinta rashin lafiyar ta sa abu ne da ya shafe shi, da shi da ita rumaisan, ta din ga fatan Allah ya sanya hakan ba zai zama cutarwa ga rumaisa ba. Nusaiba ta din ga tambayar ammi yadda suka yi. Ammi ta ce "Sun amince, rumaisa ce dai take nema ta ce ta fasa, amma ina ganin rigima ce kawai irin ta ta, kuma kai takawa, kamar yadda na gaya maka a baya, dole ka sassauta ka mayar da kanka dai-dai da ƙuriciyarta, bana son ayi auren nan ya zaman tana jin tsoronka, ko tana ganin kamar ba ka da imani" Adam bai iya fahimtar abun da ammi take faɗa sosai, ya kwanta a kan 3seater, ya lumshe tabbas. Iman kuwa tausayinsa da na ita kanta rumaisan ya kamata, mussaman da ta ji cewar nan kurkusa sosai za ayi auren. Har dare yayi, ko abincin kirki rumaisa ta ƙi ci, sai koke-koke, suka shareta suka cigaba da harkokinsa, usman sai tsara yadda abubuwa za su kasance yake yi. Mama ta kira yaya Abubakar a waya, ta sanar masa da batun, ya ce zai shigo kano, Yakamata tun wuri su san me suke ciki, su san mai yakamata a fara tanada na auren rumaisa. Jin abun da yaya Abubakar ya faɗa, ya sanya rumaisa jin kome za ayi mata ba zata iya barin gidan nan ba, sai dai idan an yi auren ya dawo gidan ya zauna, ko ya barta a gida ya bata sabir kamar yadda aka yi mata alƙawari. Tashi ta yi ta nemi wuri ta yi kwanciyarta, saboda hirarrakin ɓata mata rai suke yi. Daga nesa take hango shi cikin hayaƙi, a hankali hayaƙin yake bajewa, yana ƙara kusantota, ganinsa ta yi cikin sarƙa hannu da ƙafa, ga idonsa na ci da wuta a wannan karon ba hayaƙi kawai yake yi ba, fiƙarsa duk ta fito daga bakinsa, ga faratansa sun yi zaƙo-zaƙo. Tunkarota yake yi, yayin da ita kuma take ja da baya, cikin tsoro da razani. Duk iya ƙoƙarin ta na addu'a, ta kasa dan ji ta yi tamkar an danne mata masarrafar tunaninta, zuwa maƙoshinta, ta kasa Addu'a. Tun tana ja da baya, har ta kai bango, fizgota yayi da ƙarfi, ya danna mata faratansa a maƙoshinta. "Wayyo Allahana mama na shiga uku, Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Ko sallame sallar da take mama ba ta yi ba, ta yo kan rumaisa jin tana ihu, kamar wadda za a kashe. Mama ta fizge net ɗin rumaisa, ta riƙota tana tambayarta "Lafiyarki kuwa? Menene?" Rirriƙe mama ta yi tana mayar da numfashi, hannu ɗaya kuma ta riƙe wuyanta, da take jin kamar yana yi mata zafi. Tuni Aliyu da mai sunan Baba suka taso da gudu suka yo ɗakin mama, saboda yadda kururwar rumaisa ta cika gidan. Mama ta jijjigata ta ce "Rumaisa menene ki yi magana mana" "Mama baban Sabir ne, shine" "Me yayi miki?" Numfashi take saukwa, amma ta kasa gayawa mama abun da ta gani. A fusace mai sunan baba ya ce "Wulaƙancin naki da iskancin har ya kai ki din ga yi mana ihu cikin daren nan? Kar ki kuskura ki kaini bango, na kuma jin bakinki sai na zaneki, ki yi addu'a ki kwanta, idan ma kina yi ne saboda ba kya son auren, to kin yi kaɗan" Mama gaba ɗaya jikinta yayi sanyi ta kuma cewa "Me ki gani ya razanaki haka?" Rumaisa ta yi shiru. Mai sunan baba ya ce "Ba wani abu da ya razanata, shirmenta da take yi ne yake zuwar mata har a mafarki" Aliyu ya yi tsaki ya ce "Rigimarki ba ta ƙarewa, har tausaya bawan Allah nan nake faman da zai sha" ya fice daga ɗakin, mai sunan baba ma ya fice. Duk iya rarrashin mama, da lallaɓa yaro a matsayin ta na uwa, ta yi, amma rumaisa ta ƙi gayawa mama ainihin abun da ya faru, haka mama ta ƙyaleta ta sake tayar da salla. Tsoro ya hana rumaisa ko rufe idonta, dan haka ta tashi ta je ta yi alwala, ta zo ta tayar da salla ita ma, sai dai tana yin raka'a biyu, wani nannauyan bacci ya ɗauke ta. Mama tana jin yadda rumaisa ke ta surutai a baccin, kamar tana hannun ƴan bindiga. Sai da mama ta sanyata a gaba tana ta tofa mata adduoi, har mama ta fara tunanin, ko rumaisa na da aljanu ne, maganar aure ta taso za su fara motsawa. Dan haka ta ƙudurce a ranta, dole ta nema mata maganin sheɗanu. Ta cigaba da sallolinta, tare da tsananta addu'a a kan lamarin auren nan da yake tunkarosu. *** Mamaki Samha take ba ɗan kaɗan ba, ganin irin surƙuƙin ƙauyen da suke kurɗawa, ita da Mummy da kuma Hajiya Lubabatu. Kasa ɓoye mamakin ta yi ta ce "Wai yanzu Mummy har nan ku ke zuwa? Ni fa ma fara jin tsoro" Mummy ta yi murmushi ta ce "Yaro yaro ne, ke ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake, tafiya duk nisanta da surƙuƙinta, in dai da biyan buƙata ai shikenan, tafiya ɗazu ce". Hajiya Lubabatu ta ce "Ke idan babu wannan ƴan biye-biyen mutum ya zauna lafiya, mussaman a irin gidajen sarautar nan, ai ni tun da Allah ya taimakeni, na kaɗa duk wata mata da ta raɓi gidana, na ga tsuguno ba ta ƙare mini ba, sai na dangana da mallakawa Jabir kujerar galadima," Samha ta ce "Takawan fa? Ba gidansu sarautar za ta koma ba". Mummy ta zunguri Hajiya Lubabatu, sannan ta ɗora da cewa "Yauwwa, mun kusa ƙarasawa, daɗinta kowa yake gani, idan muka je sai ya katse ya sauraremu". Samha ta ce "Ni fa idan za a kasheni, ban san hanyar komawa ainihin titi ba, gaba ɗaya kaina ya juye". Hajiya Lubabatu ta ce "Zaki zama ƴar gari ne da zarar kin waye". A cikin surƙuƙin ƙauye sosai mutumin yake, dan an fita daga gari sosai wurin kamar daji, a nan aka yi masa wani shinge, suka tarar da tarin mata da maza a wurin, da masu zubin hannu da shuni, da masu saffa-saffa, ga marasa lafiya kuma, wasu abun nasu ma dai ba kyawun gani. Ba tare da ɓata wani dogon lokaci ba, bayan an sallami na ciki, suka shiga, wurin duk an kafe ƙahuhuna da ƙwarangwal ɗin dabbobi, ga wani irin wari da tsamin turaruka da magunguna da ɗakin yake yi. Mutumin yana zaune cikin wasu tsummokaran kaya, ga wasu irin kayan tsubbu a gabansa shi kansa duƙun-duƙun da shi, kamar ba ɗan Adam ba, ga idonsa ɗaya hakiya ta rufe, ɗayan kuma a juye ga idon jawur. Sai da kan Samha ya sara, ta nemi faɗuwa, Hajiya Lubabatu ta riƙeta suka zauna. Mummy ta ce "Barka da warhaka malam, ya aiki ya ƙoƙari" "Lafiya ƙalau, kin yi nusau, ko buƙata ta biya ne, ko kuma dai kin fasa aikin da ki ka buƙata, tun da ki ka ce mana akawai maganin da ake masa amfani da shi, muke jiran ki kawo mana maganin mu yi aiki a kai, amma mun ji ki shiru". "Ai malam maganin ne yaƙi samuwa, duk wata hanya da zan bi a samu, ba a dace ba, amma ba haƙura na yi ba, ina nan zan dawo. Gamu tare da baƙuwa, ƴar facalarmu ce, da ita da shi yaron Adam, duk iyayensu ƴan uwa ne, ta daɗe tana son shi, amma ya auri ƙanwarta, yanzu ƙanwar ta mutu, amma uwarsa na son aura masa wannan ƴar tsintuwar da na taɓa baka labari, kuma wannan ɗin ta kuma rasawa, shine muke son ayi wani abu a kai". Yayi shiru, sannan ya ɗebi wata ƙasa ya zuba a wani fai-fai, ya dinga juya hannunsa, sannan ya kalli fai-fan ya ce "Tirƙashi, tabbas ga maganar aure nan, sai dai ita yarinyar tana tafe da wata irin guguwa mai ƙarfin gaske, sai kun tashi tsaye sosai" Cikin sauri Samha ta ce "Malam so nake kar auren ya yiw....." "Aure sai an yi shi, ma'aunin ƙaddarar yarinyar da zai aura ya rinjayi tasa, sai dai idan ɗayansu ne ya mutu" Kamar Samha za ta yi kuka ta ce "Dan Allah malam a kasheta, ba zan iya jurewa ba a wannan karon" Mummy ta ce "Malam, ka san yarinyar, wadda ka taɓa yi mini aiki a kanta ce shekarun baya, kawai ka yi wani abu a kai" "To ya aka yi ƙasa ba ta nuna mini ita ce ba? Ban ga taurarinta sun fito a cikin nasa ba, amma duk da haka babu damuwa, ta jiramu a waje, zan bata abun da za ta yi" Samha ta jinjina masa kai, ta yi godiya, sannan ta tashi ta fita ta bar su Mummy. Hajiya Lubabatu ta ce "Malam, ya ake ciki ne? Haryanzu galadima yana nan a raye, ga lokaci yana ƙurewa, bana son wani dalili da zai gifta, da Jabir zai gaza mallakar zunzurutun dukiyar nan da sarauta". "Allah ne mai kashewa da rayawa ba ni ba, dole ki cigaba da jira, ke kuma ya aka yi?" Yayi maganar yana kallon Mummy. "Malam, kamar aikin da yake tsakanin yaran nan ya fara sanyi, kamar mahamud ya sassauta ƙiyayyar da yake yiwa ɗan uwan, sannan malam yadda yake yinƙurin yin auren nan, a sake damalmala lamarinsa, bana ƙaunar ganin wani cigaba a tare da yaran nan". Malamin ya ce "Ina iya ɓata aiki ne, ba sauya ƙaddarar bawa ba, zan yi abun da ya dace a kai, ku tafi ta kudu, ku ajiye abun sadaka a mararraba ta uku, sannan shekara ta kusa, za a shayar da ƴar baƙa ta arewa da jini, sai dai ta daina samun jinin da take sha, dan haka za ayi mata sadaukarwa da wani abun, na sallameku". Da haka suka fita, Samha take ce musu bai faɗa mata mai za ta bashi na aiki ba, suka ce kar ta damu, suka yi abun da ya ce sannan suka tafi gida. *** Abubakar ya dawo, sun kuma tattauna sosai a tsakaninsu, a kan auren rumaisa, suka yanke shawarar a sake jarraba sayar da gonarsu, domin a samu abun yi mata kayan ɗaki. Ɓangaren rumaisa kuwa, sai koke-koke take a kan ita fa ba ta so, gashi har fargabar kwanciya bacci take yi, saboda munanan mafarkan da take yi, ta je ta samu malaminsu a islamiyya ta ce ya bata Addu'a, tana yawan yin mugun mafarki ya bata shawara da cewa "A duk lokacin da ki ka yi mummunan mafarki, ki nemi tsari sannan kar ki gayawa kowa, ki din ga kwanciya da alwala, sannan ki kwanta da ɓangaren dama, ya zamana kina Adduoi na safe da na maraice, sannan ki karanta na kwanciya barci, idan razana ki ake yi a mafarkin, ki daina tsorata, ba abun da yake samun bawa sai da iznin Ubangiji, kin riga kin yi azkar kin nemi tsari, babu abun da kuma zai cutar da ke". Rumaisata riƙe maganar malaminsu, ta dage da addu'a da alwala, shine ta ɗan samu rangwame. Rana bata ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, tun da su ammi suka tafi, sai ana gobe kai kuɗi suka yi waya da mama, ranar juma'a bayan an saukko daga Masallacin juma'a, mai girma turaki da wasu manya a masarautar kano, suka kai kuɗin auren rumaisa gidan ƙanin mahaifinsu, naira dubu ɗari biyar, suka saka wata ɗaya rak. Ƙanin mahaifin rumaisa ya nemi su ƙara musu lokaci, saboda shirin aure, ba abu ne mai sauƙi ba, amma suka ce basa buƙatar komai, rumaisa kawai suke son a kai musu, dan haka wata ɗaya suka saka. Ayshercool *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Tun da aka ce za a kawo kuɗin rumaisa wasu daga dangi suka fara surutun, rumaisan guda nawa take da har mama za ta ce zata yi mata aure, mussaman da ta fi kowa sanin halin rumaisa na rashin nutsuwa. Tun da aka kawo kuɗin nan, zance ya sake canza salo mussaman ganin manyan mutane da suka kai kuɗin, da kuma irin zunzurutun kuɗin da aka kai ɗin. Bayan tafiyar su turaki, suka tafi ɗorayi, domin suje a tattauna abun da za ayi, na game da shirin aure. Rumais kuwa ta manta da batun kuɗin aurenta aka kai, mama dai ta saka an yi soye-soye, suna ta faɗa da rumaisa tana dumbuza tana ci, dan da ta dawo daga makarantar boko, sai da ta ɗaure cin cin a leda fal, ta fita ta tafi gidansu Hauwwaliya. Ko a unguwar su rumaisa, babu wanda ya san da batun kawo kuɗin rumaisa. Gaba ɗaya yayyen rumaisa sun haɗu a falon mama, ga ƙanin mahaifinsu na kano, sai kuma yaya ɗan lami, da ya wakilci dangin mahaifinsu na katsina. Baba lawalli ya dire kuɗi ya ce "To ga kuɗin aure nan, naira dubu ɗari biyar, kuma sun saka wata ɗaya rak, na ce su ƙara mana, mu samu mu shirya a tsanake, sun ce su basa buƙatar komai daga garemu sai rumaisa kawai" Mai sunan baba ya ce "A'a ba zai yiwu ba, dole zamu yi mata kayan ɗaki, ba zai yiwu daga baya azo ana yi da ita ba, son zuciyar sai yayi yawa ai". Abubakar ya amsa da "wannan gaskiya ne" Mama kuwa a ɗan tsorace dubu ɗari biyar, sai da yarinyar zan yi? Ina laifin ko dubu hamsin ma" Usman ya ce "Haba mama, ko bazawara ai ba a bata dubu hamsin ba, sai ka ce a ƙauye? Yarinya falleliya, son kowa ƙin wanda ya rasa, ki ce dubu hamsin". Abubakar ya ce "Wai kai usman duk maganar kirki sai ka sako wasa, a mayar da hankali a yi magana sosai". Yaya ɗan lami ya ce "Kamar yadda muka fara magana, an riga an saka gonar nan a kasuwa, kuma an fara tayawa, tun da ita ba a yankinmu take ba, wurin da take da tsaro" Baba lawalli ya ce "A'a ba sai an kai ga sayar da gonarku ba, in sha Allah zamu iya, zamu fitar da rumaisa kunya" Mama ta ce "Duk da haka, ɗawainiyar aure, ba nan kusa bace ba, kuma da amincewar ƴan uwanta za a sayar". Haka suka cigaba da tattaunawa, a kan yadda abubuwa zasu wakana. Bayan sun watse, mama ta kira ammi a waya, ta yi godiya, sannan ta ɗora da ƙorafin kuɗin nan sun yi yawa. Ammi ta ce "Ni dai babu ruwana, babanta turaki ne ya bayar da kuɗin, kin ga babu mai ikon cewa a rage yayi yawa, kuma duk abun da zamu baku, ai bai yi yawa ba, mutum guda fa zaku bamu, ina musu fatan alkhairi sannan ina sake yi muku godiya da karamci. Sanan dan Allah kar ku ce zaku takurawa kanku, babu abun da zai gagara, komai za ayi in sha Allah, rumaisa kawai za a kawo mana". Mama ta ce "Babu abun da zai gagara ma in sha Allah, Allah Ya sanya alkhairi" "Amin ya Allah, zuwa jibi in Allah ya kaimu ma zai shigo wurinta, idan da abun da take buƙata na shirye-shirye sai su shirya" Mama ta ce "To babu laifi, Allah ya saka da alkhairi" da haka suka yi sallama. Mahmud kuwa, haka nan ya ji zaman garin duk ya ishe shi, Alla-Alla yake kawai ya koma, saboda haka ya haɗa kayansa ya tattara ya koma. Iman ma, haka nan ta fara ciwon kai a tsaitsaye, abu kamar wasa, sai dai ta sha magani ta basar, amma ko sauka baya yi, yau da aka kai kuɗin auren nan tana murna, sai dai a gefe guda kuma tana fargabar abun da Samha zata iya aikatawa. Da sallama ta shigo, hannunta riƙe da jarkar lemo, mama ta kalleta ta ce "Sannu, sai yanzu ki ka dawo? Haka muka yi da ke dama?" "Dan Allah mama kiyi haƙuri, wasa muke yi ne" "Wane irin wasa?" "Wasan ƴar carafke, ƴar gala-gala sai kuma na koya Habiba yadda ake faten tsaki" Mama ta ce "Ko kuma zuwa ki ka yi kina gaya mata zaki yi aure?" Ware ido rumaisa ta yi ta ce "Wallahi ni ban gayawa kowa ba, kawai wasa muka yi" Aliyu ne ya janyo hannunta yana cewa "Ke, kin kusa zama matar aure, dole ki daina wannan yawon,tun da an kawo kuɗin auren nan" Sororo ta kalleshi ta ce "Wai dama da gaske ne?" "Au, da da wasa ne? Dubu ɗari biyar aka kawo" Ta buɗe baki ta ce "Haba duka nawa ne? A sai mini keke a ciki, da akuya in din ga kiwonta" Abdallah ya tunsture da dariya ya ce "Ke tafi can, gado za a saya miki ƙato, da wardrobe da kayan kitchen" Ta ɗan yi shiru sanan ta ce "To duk a gidan nan za a zuba su? Shikenan sai mu din ga kwana da ni da mama a kai" Usman da yayi alwala zai fice masallaci ya ce "Gado bana mama bane ba, naki ne da mijinki, a gidan da zaki zauna za a saka miki" Kamar adam yana wurin ta ce "Taɓ, ai wallahi ba zai hau mini kan gadona ba, ta yaya mace da namiji zasu din ga amfani da gado ɗaya" Usman bai kuma cewa komai ba ya fice, gaba ɗaya suka watse suka bar tsakar gidan, jin zata fara rashin hankalin nata. Har bayan sallar magariba, zancen yadda biki zai gudana suke yi, ita kuwa ƙasan zuciyarta ta kasa manta, abun da take gani a game da Adam. Tashi ta yi kamar mara gaskiya, ta je kusa da mai sunan baba ta zauna, ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Mai sunan baba, dan Allah ka ara mini wayarka zan yi waya, na duba ta mama babu kuɗi a ciki" Sai da ta fitar da rai zai yi magana, sannan ya miƙa mata wayar, ta saka hannu ta karɓa, ta yi masa godiya, ta tashi ta je in da ta kwafi lambar iman ta kirata. Duk da iman tana jin jiki, amma ta dake jin muryar rumaisa ta ce "Amaryar takawa, takawarki lafiya" "Anty iman, baki da lafiya ne?" "A'a lafiyata ƙalau, ashe an kawo to Allah ya sanya alkhairi ya Kaimu lafiya" Rumaisa ba ta amsa addu'ar ba ta ce "Ina rabin ran, dama kira na yi ki saka masa wayar a kunnensa na yi masa magana" Iman ta yi murmushi ta ce "Bacci yake yi, amma idan ya farka kan ki yi barci zan kiraki in sha Allah, dan na san idan ya ji muryarki zai yi miki gwaranci" Rumaisa ta yi dariya ta ce "Ke kuwa Muryar mamansa fa, ki gaishe mini da ammi, ba zan barci da wuri ba". "To shikenan, yauwwa ki na ji na?" Rumaisa ta ce "Eh" "Dan Allah anty rumaisa ki dage da addu'a, akwai ƙalubale a wannan auren naku, kin san duk wani abun alkhairi zai fuskanci suka, ki yi ta addu'a, wannan familyn da kike shirin shigowa, akwai tarin ƙalubale da rikici, wanda su ke taka rawa wurin damuwowin da baban sabir yake ciki. Dan Allah idan kin aure shi ki din ga tausaya masa, maraya ne da ƙalubalen rayuwa ya sanya zuciyarsa yin rauni, ki yi ta yi muku Addu'a mu ma zamu tayaku in sha Allah". "Ni ma marainiyar ce ai, kuma shi ƙato ne, ni yarinya ce ni zai tausayawa, ya daina hantarata da hararata ai" tayi maganar iyakar gaskiyarta. Iman ta yi dariya ta ce "Zai tausya miki in sha Allah, sai mun yi wayar, kar ki yi bacci da wuri, na san dole zai farka da wuri" "To shikenan ina jira" sai da aka fara yi mata warning ta cinye masa kati, sannan ta mayar masa da wayar Wayar da tsoron mai ita bai sa kowa ya raɓeta, amma rumaisa ta je ta kwantar da kai ta karɓa. Gaba ɗaya batun auren nan baya kan rumaisa, ta haƙura da rigimar ba ta so, tun da mai sunan baba ya sanya baki, sai dai tana tsoron kar ta je Adam aljani ne. Mama da murnarta ta sanar da takawa, duk yadda su turaki suka yi a wurin kai kuɗin auren, da yadda ya din ga yaba dattaku da kuma kimar dangin rumaisa da yadda aka karramasu cikin mutuntawa. Ba dan Adam yana jin daɗin hirar ba ya cewa ammi "To Allah ya yi mana jagora" "Amin, ko kai fa, dan Allah ka saki ranka a kan auren nan, ba zan yi maka zaɓen tumun dare ba, in sha Allah rumaisa alkhairi ce a gareka da yaronka" Ya jinjina kai ya ce "Yauwwa, Allah ya sa" "Amin ya Allah, yauwwa ka san dama wata ɗaya aka saka, bana son ku zauna a gidanka da kuka zauna  da aisha, bana son ka din ga wani abu da zai ɓata mata rai, na san ba zan hanaka tunanin matarka ba da ka rasa, amma idan kana son samu cikakkiyar dama zama cikin kwanciyar hankali da iyalinka, ka yi iya ƙoƙarin ka, ka din ga danne tunanin aisha a gabanta, sabon gidan nan na jambulo, a sake yi masa fenti, tun da dama sabo ne sai ta zauna a ciki". Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Mhmm, bai yi mata girma ba?" Ammi ta ce "To ai gidanka na tudun yola, ya fishi girma, kuma nan gaba iyali zaku tara, kuma tana matarka dole a yalwata mata mazauninta". Ya ce "To" dan jin batun tara iyalin yayi wani banbarakwai, zuwa yaushe kenan, ta gama girman da zata tara iyali?. "Sannan jibi in Allah ya kaimu, zaka je ku tattauna, idan da wani abu da take buƙata, ko take son ka yi mata, a harkar auren. Ba ina nufin na manta da mutuwar aisha bane ba, saboda abu ne da ba zamu manta da shi ba, musamman a yadda ya zo mana, amma rumaisa yarinya ce, aure abu ne da ake fatan ya zo wa mace sau ɗaya a rayuwarta, bai kamata a tauye mata hakkinta ba, ayi aurenta kamar mara galihu ba" Baya son yi wa ammi musu, amma gaba ɗaya ba jin daɗin maganar yake yi ba, shiyasa kawai yake bin ta da to. Sai da ammi ta gama magana, sannan ya tashi ya tafi, dan gaba ɗaya yau ba a gidan yake son kwana ba. Yayi nafilfilinsa na dare, yana addu'a, ya idar zai miƙe aka kira shi a waya. Sunan Bashir ne ya bayyana a kan screen ɗin wayar, ya ɗaga tare da faɗin "Malam bashir" "Yallaɓai, ya gida ya aiki?" "Alhamdilillah, ya naka aikin" "Lafiya ƙalau, dama na kira ne na ji, ko zaka shigo ɗin?" Adam ya ɗan yamutsa fuska ya ce "Bana jin daɗi ne, sai wani lokacin kawai" Bashir ya ce "To shikenan, Allah ya ƙara afuwa, lambar nan da aka fara kiranka da ita, bayan sace madam, Sidi yayi bincike a kanta, ya turo mini bayanan wanda yayi register da layin". Da sauri Adam ya gyara zama ya ce "Tom ina jinka, ya aka yi, kun gano shi?" "Eh to, babu wata nasara dai, a gombe aka yi register da layin, na tura wakilai har wurin, abun da dai muka gano, mai wayar wani bafulatani ne, daga bisani ya bar gombe, irin fulanin nan ne na tashi, ya koma katsina, sai dai a katsinan ma da na je, na tarar an kai musu hari a rigarsu, an ƙona musu dabbobi, dan haka bana zaton shi mamallakin layin shi ne wanda yake da alhakin garkuwa da ita, akwai dai yadda aka yi". Adam ya yi wata nannauyar ajiyar zuciya, cikin sanyin jiki ya ce "To shikenan Bashir, na gode da ƙoƙarinka sosai" Bashir ya ce "Adam, dan Allah kar ka damu ko ka karaya, ba zamu daina ba in sha Allah, sai mun ga abun da ya turewa buzu naɗi, ni dai jikina ya gama bani garkuwa da Aisha plan ne kawai, amma zamu cigaba da addu'a da kuma bincike" Adam ya ce "To Allah ya iya mana". "Amin ya Allah, ina boy, da rigimammiyar babarsa?" Sai a yanzu Adam ya tuna an saka masa rana da shi da rumaisa. Haka nan ya tsinci kansa da cewa Bashir "Yana nan ƙalau, an saka mana ranar aure ni da ita" Waro ido bashir ya yi ya ce "Rumaisan?" "Mmmm" ya amsa a taƙaice. Wata dariya ce ta ƙwacewa Bashir ya ce "What a perfect match, amma kamar ta yi ƙarama da yawa fa" "To ya zan yi, biyayya ne ga umarnin ammi". "Kuma in sha Allah ba zaka taɓe ba, ni nayi maka murnar hakan wallahi, zamanku wuri guda zai sanya idan da wani abu da zai taimakawa bincikenmu da ta sani ta gaya maka" Adam kawai ya girgiza kai, dan ya san azabar taurin kai irin na rumaisa kan a kai ga faruwar hakan, aiki ne ja. "Na gode bashir, bari na ɗan kwanta" "To shikenan ango, Allah ya tashemu lafiya" Adam ya ajiye wayar, ya lumshe idanunsa, abubuwa daban daban, suka cigaba da karakaina a cikin kansa. Mai sunan baba kuwa wanka yayo, ya zo ya yi shirin kwanciya, lokacin ƙarfe goma da mintuna ashirin, har ya kwnata wayarsa ta fara haske, alamar ana kiransa. Ya kalli wayar babu suna, dan haka ya gyara kwanciyarsa, sai dai har kusan sau uku ana kiran wayar. Ya saka hannu ya ɗau wayar, ya kara a kunnensa. Ƴar siriryar muryarta, mai cike da shagwaɓa ya ji ta ce "Anty rumaisa, Allah ya sa baki yi bacci ba, gashi ya tashi" Zirrrr ya ji wani abu ya tsirga masa, tun daga kansa har ƙafafuwansa, yayi shiru bai ce komai ba. "Anty rumaisa, ko kin yi bacci ne? Ki yi magana mana". "Ta yi barci" ya faɗa a taƙaice. Babu tsammani ta ji muryar ta sa, a rikice ta ce "Innalillahi, yi haƙuri" ta kashe wayar ƙirjinta yana bugawa da sauri-sauri. Ajiye wayar yayi yana jan guntun tsaki, ya juya bayansa yana mamakin, yadda take shaƙe muryarta a iya wuyanta tana magana, wata ƴar murya kamar ƴar tsanar roba. Da asubar fari, rumaisa ta tashi ta fito, zata shiga banɗaki ta tarar da mutum a ciki, ta zuba ruwa a buta, ta zauna a gefe tana hamma. Gajiya ta yi da zama, ta ce "Wai dan Allah waye a banɗakin nan, zan yi a tsakar gida fa". Shiru aka yi ba a bata amsa ba, waɗanda suka yi alwala suka fara tafiya masallaci. Usman ne ya buɗe ƙofar ya fito, yana hararta. "Yaya usy wai dama kai ne a ciki? Wai dan Allah kai kullum sai ka yi wanka da asuba? Wankan me ka ke yi, ka yi da asuba, ka yi da safe zaka tafi makaranta, idan ka dawo da yamma ko da daddare sai ka yi, wanka da asuba ko sanyi baka...." Buɗe baki yayi ya ce "Zan ci ubanki, saka mini ido ki ke yi ina ruwanki da ni". Aliyu ne ya fito yana dariya, ya ce "Malam ka yi mata bayanin wankan uwar me kake yi da asuba?" Tsuke fuska Usman ya yi ya ce "Ba na so" "Meye ba ka so, tun da ba zai gaya miki ba, in anjima idan ya zo ɗakin mama ki tambayeta, wankan me yake yi da asuba?" "Ai ba sai ta tambaya ba, ita da zata yi aure kwanan nan, za ta yi ita ma". "Aliyu ya ce "Kai fa ba ka da hankali". "Allah ya kiyaye, wallahi ba zan wanka da asuba ba, sau ɗaya zan din ga yi a rana, lokacin sanyi ma wataran ba zan yi ba" Usman "ke dalla tashi ki bar wurin nan, munafuka cctv Camera, wuce ki je ki yi abun da zaki yi ko na karya miki wuya" tashi ta yi ta ja butar ta sum-sum ta tafi banɗaki. Yau asabar ce, dan haka bayan sallar asuba, mai sunan baba ya dawo ya kwanta barci, sai dai wajen ƙarfe takwas na safe, wayarsa ta ishe shi da vibration a ƙasan pillow. Cikin bacci ya ɗau wayar, ya saka a kunne yana lumshe ido. "Anty rumaisa, barka da safiya jiya ki ka yi bacci na kira kin yi barci". "Ke! Ba wayarta bace kar ki sake kirana wayata ce ba tata ba" a wannan karon ma ba ƙaramar razana ta yi ba, cikin rawar murya ta ce "Yi haƙuri, na zata wayar mama ce". "To ta umar ce, ki ka sake kirana ni da ke ne, an hana mutane barci tun jiya, ki yi ta wani yenyen, ba zaki buɗe baki ki yi magana ba" ya ƙarasa mitar yana kashe wayar. Nusaiba da take gefenta ta ce "Wannan wane bala'e'en ne haka?" Iman ta girgiza kai ta ce "Ba kowa, ga Sabir nan bari na je na kwanta" Nusaiba ta karɓi Sabir, ita kuma ta tashi ta tafi ɗakinta tana tunanin yadda mai sunan baba ya faɗa haka take magana. Sunansa da ya faɗa umar ta sake maimaitawa, dole yayi masifa, ta faɗa a ranta. Tana shiga ɗakinta ta ji tamkar an shaƙeta, kuma ta kasa gaba ta kasa baya, hannu ta saka tana riƙe wuyan nata, amma ta ji numfashinta yana neman ɗaukewa. Cikin fita hayyaci ta sulale Jikinta ta faɗi ƙasa. Can katsina kuwa, Gwaggo har da taka rawa saboda murna, tana faɗin Allah ya dubi ƴar marainiyarta, za ta yi a gidan daraja, gidan sarauta gidan masu abun hannu. Nan da nan ta ce ba zama, azo a kama wasu daga cikin dabbobinta a sayar, ta fara saye-sayen kayan da za a kai wa rumaisa. Iman kuwa ba a tashi sanin halin da take ciki ba, sai bayan wasu awanni, da nusaiba ta ji ta shiru, ta shiga ɗakin ta tarar da ita a ƙasa a sume. A kiɗime ta je ta sanar da ammi halin da ake ciki, ranga-ranga aka ɗauki Iman zuwa asibiti, ba tare da ta san waye a kanta ba ma. *** Gidansu ruma kuwa, mama ma ta fara shirin tafiya kasuwa, domin fara saye-sayen da za a buƙata, dan ba ta taɓa kawo wa rumaisa aure yanzu ba, amma cikin ikon Allah, sai gashi ba tare da wani shiri ba, dan ko ƴan kwanuka ba ta fara saya ba. Rumaisa na uwar ɗakan mama, tana ta zane-zanenta, mama sai mita take ba ta son zane-zanen nan, wataƙila ma zanen ne yake sanyata firgita cikin dare. Rumaisa ta yi dariya ta ce "Haba mama, zanen ne zai tsortani, kin ganni nan kin san bana tsoron kowa sai Allah, balle wani zane". "Kya ji da shi dai" ta yi maganar tana fita falo. Yaya Abubakar ya yi sallama a falon mama, mama ta amsa masa ta ce "Garbatina ya aka yi ne?" "Fita zaki yi ne?" Mama ta ce "Eh, kasuwa zan shiga na fara saye-saye". "To da magana nake son mu yi, amma idan kin dawo ma yi" "A'a, zauna ka gaya mini sai na fita" Suka zauna, Abubakar ya kalli mama ya ce "Mama, kamar yadda muka yi da ke, na je na ɗan zazzaga unguwar ina tambayar ya yanayin gidansu yake, da kuma shi kansa mu'amalarsa da mutane, to sai dai sakamakon baki ya rabu biyu. Wasu suk ce mutumin kirki ne, mai yawan kyauta, da girmama mutane kuma miskili ne, wasu kuma sun ce ba shi da kirki, yana da faɗa da zafin rai wai kwanan nan ya taka ƙaninsa da mota, ba wannan ne ya fi ɗaga mini hankali ba, wai ana kyautata zaton maye ne, kuma yana da taɓin hankali!!! Ayshercool 08081012143 *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Dafe ƙirji mama ta yi tana salati, ta ce "Ɗan nan, da gaske kake wannan maganar?" Abubakar ya ce "Wallahi da gaske nake, kuma ba a bakin mutum ɗaya ba, ni da wani abokina Abdurrahman muka je, abun da na jiyo kenan". Mama ta ce "Ya salam! Yanzu menene abun yi?" "Ba wata maita a musulunci, haka malaminmu ya gaya mana, to so suke a fasa shikenan a fasa bani Sabir ɗin, ko kuma kuɗin da aka kawo ɗin suke so a mayar, ƴan baƙin ciki ne kawai". Mama ta kalleta ta ce "Ke! Waye ya saka da ke? Da ke ake ke zaki yanke wa kanki hukunci?" "Mama ba haka bane ba, to kuɗin za a mayar, idan aka mayar kuma an fasa ba za a bani Sabir ba fa kenan" Aliyu ya shigo yana tambayar meyafaru?. Mama ta gaya masa abun da ya faru, Aliyu ya kalli ruma da ta kumbura baki ya ce "Ke ki na son sa a haka?" "Ba fa maye bane ba, ƙarya suke yi. Ni fa bana son shi, amma idan aka fasa ba fa zasu bani Sabir ɗin ba, kuma mama ba kwanan nan aka ce shi ya kashe Anty Aisha ba, kuma ƙarya ake yi masa ba? To wannan ma ina ga ƙarya ake yi masa, ni dai ko za a fasa, kar a mayar da kuɗin nan, kuma a bani Sabir". "Ke ki ka nema musu kuɗin, ido a kwabo" Yaya Abubakar yayi maganar yana dungure mata kai. Aliyu ya ce "Mama, bana tunanin wannan abun ya kai a fasa aure saboda shi, dama rumaisa na buƙatar tsayayyen namiji jajirtacce, saboda halinta, sannan shi mutum ne fitacce, irin wannan sharrin ba abun mamaki bane ba, ban ƙaryata b kai tsaye, amma ke ki ka gaya mini addu'a da ki ka din ga yi, kina jin son abun a ranki, lamarin ya kwanta miki a ranki, da bai kwanta miki ba sai mu ce babu alkhairi, dan babu hijjabi tsakanin addu'arki gareta da Allah, a ganina mu cigaba da addu'a babu ma'ana a kawo wannan zancen ma, tun da ai ita ma rumaisan tana son sa ko?" "A'a nifa ba son shi nake yi ba, kawai saboda a bani Sabir ne". "To amma ai ke ki ka ce mai kuɗi ki ke so, kuma mai kyau wanne ne bashi da shi a ciki?" "Wannan har wani kyakykyawa ne? Kullum yana wani zazzare ido" Mama ta ce "Tashi ki bar wurin nan, mara kunya, ana maganar aurenki kina tsoma baki" Aliyu ya ce "To sanin ma'anar auren ma ta yi? Amma mama ya kike gani? A kan wannan dalilin zaki saka a ɗauki kuɗin da aka kawo shekaranjiya a mayar musu ne?" Abubakar ya ce "A'a ba ayi haka ba, na gamsu da maganganunka nima, mu cigaba da addu'a dai, Allah ya zaɓa abun da ya fi alkhairi" Mama ta amsa da Amin, sannan ta tashi ta saka Yasir a gaba suka tafi kasuwa. Likitoci suka karɓi iman, kasancewar asibitin sun san matsalar Iman, nan da nan suka karɓeta. A duk lokacin da ciwon ya tashi, Asibitin ake kawota, tun tana yarinya abu kaɗan sai ta yanke jiki ta faɗi ta suma. Aka din ga binciken abun da yake damunta har ƙasar waje, ƙarshe dai aka ce zuciyarta ce ke kumbura wasu lokutan. Ammi ta alaƙanta hakan, da yawan damuwa da take yi, mussaman a lokacin yadda ake tsangwamarta, hakan ya sanya hankalin ammi ya tashi sosai. Ta din ga faɗi tashi, domin ganin iman ta samu lafiya, tayi iya ƙoƙari iman ta samu sauƙi, sai dai lokaci zuwa lokaci jikin ya kan motsa. Yanzu haka ammi hankalinta ya tashi, ba ta ƙaunar ganin wani abu ya sami iman, shiyasa kullum cikin addu'a take yi mata, Allah ya sanya iman ta samu miji nagari, wanda zai iya haƙuri da ita ya jurewa larurarta. Sai dai a wannan karon, su kansu likitocin lalube suke yi a cikin duhu, ake ta bankawa Iman ruwa da allurai, aka yi hoton zuciya, amma zuciyarta lafiya ƙalau. Hajiya Sauda ce zaune a turakar turaki, ta dube shi ta ce "Ranka ya daɗe, ni baka gaya mini ina ku ka je ba ranar juma'a, ka zo mana da abubuwa na ciye-ciye, haryanzu baka ce mini komai ba" Turaki da yake cin ayaba, ya ce "Dama dole ne duk in mu ka je sai an gaya miki?" "A'a tambaya dai kawai na yi, na zaci wani abun alkhairin ne ya samu ai" Ya ce "Eh, kusan haka, abun farincikin ne" "Kamar me fa?" "Aure muka je nemawa takawa, na gidan galadima" "A'a, neman aure kuma, yaushe Aishan ta rasu, da har za a nema masa wani auren?" Turaki ya ce "Addini ya bashi dama, Aisha ta kai watanni huɗu da rasuwa babu laifi a ciki dan yayi wani auren". Danne fushinta ta yi, ta ce "Amma wa zai aura haka da na ji ka ce, kun je nema masa aure". "Eh, wata yarinya ce, ƴar mutunci iyayenta masu dattaku sosai, su suka bamu wannan kayan duk da na zo da su". Cikin son bugun ciki ta ce "Kuma ƴar waye? Ai na zata iman zaku aura masa, ta maye gurbin aisha" "To, idan lokaci yayi zaku ga koma wacece, koma itan ce, ko ba ita bace ba" "Amma dai Allah ya baka yawan rai, ni na rasa dalilin da ya sanya, ka fi fifita ƴaƴan wasu a kan naka, na rasa me muka yi maka da ni da yarana. Tsakani da Allah duk yadda Samha take ƙaunar yaron nan a wannan karon ba zaku yi mata adalci ta maye gurbin aisha ba, taƙi auren kowa ta dage sai shi, amma ka yi burus, ku ke je waje nema masa auren wata?" Turaki ya ce "Ban fifita kowa a kan ƴaƴana ba, sai dai son da nake yi wa ƴaƴana, ba zai sanya na zaɓi son zuciya ba. Ba zai yiwu sun kawo wadda suke so ya aura na wuce masa gaba a matsayina na ubansa, na yi amfani da ƙarfin ikona, na ce sai ya auri ƴa ta ba, ki sani zan iya tursasa shi ya auri ƴa ta, amma ba zan iya tursasa shi ya so ta ya kyautata mata ba, na yi mata nasiha tun ba yau ba, a kan ta haƙura da shi, ta yi addu'a ta nemi wani ta aura, har haɗata da na yi da ɗan gidan madaki, Muhammad Sani, ya ce ya na sonta ta watsa mini ƙasa a ido, sai yanzu kuma ku ce ga abun da ku ke so sai na yi, ba zai yiwu ba, kuma ku yi haƙuri, da Samha da takawa duk ƴaƴana ne, ba wanda zan yi wa dole a kan wani abu da yake son zuciya" Ba ƙaramin ƙuluwa ta yi ba, da jin maganganun turaki, ba ta sake cewa komai ba, ta tashi ta bar ɗakin. Zainab ce ta shiga falon mama, in da Samha ke zaune tana kallon tv, hannunta riƙe da wayarta, ta zauna tana faɗin "Ohh God, ita wannan yarinyar ita kenan kullum cikin ciwo?" Samha ta kalleta ta ce "Wacece?" "A status ɗin Nusaiba na gani, wai iman babu lafiya, ba ta san waye a kanta ba ma, shikenan ita giwa kullum tana hanyar asibiti saboda ƴar tsintuwa, dama ta mutu ko sa huta gaba ɗaya" Samha ta yi ajiyar zuciya, tare da ji a Jikinta, aikin ta ya fara aiki kenan. Fuuu mama ta shigo falon,. Kamar mai tafiya a kan iska. Duk suka bita da kallo, suna tambayar ko lafiya?. "Hmm, ni da turaki mana, ya gaggaya mini magana a kan kawai na ce, meyasa bai saka adam ya auri Samha ba, wai nema masa aure suka je yi ranar juma'a. Ƙuuuu Cikin Samha ya bayar, wani irin fargaba da faɗuwar gaba ya kamata, neman aure aka je yi wa Adam?. "To kin ji, a wannan karon dai kya haƙura ko?" Zee ta yi maganar tana kallon Samha. "Mama, neman aure kuma? Ba iman za su bashi ba?". "Bana tunanin ita ce, wata ce daban gaskiya, tun da ya ce sun je nema masa ne, da ita ce ai ba sai sun yi haka ba" Wani irin gumi ne ya shiga ratsowa daga cinyar Samha, gaba ɗaya kanta ya toshe, saboda jin abun a bazata an shammaceta da yawa. "Amma mama wacece haka?" "Oho ina na sani, bai gaya mini ba, ni takaici ma bai barni na san wacece ɗin ba". Cikin hanzari, ta tashi tafi ɗakinta zuciyarta na yi mata zafi, tsabar wulaƙanci a waje ma ake je aka nema masa wata bayan ita gata a zaune an san tana san shi Zama ta yi daɓas a gefen gado, zuciyarta na ƙuna, wannan shine baba na ɗaka gemu na waje, amma mayar da ita wata sako tumaki ɓallo jakai. "Tun da naga aikin malamin nan yana aiki, Adam da ni ka ke zancen, wallahi kana ji kana gani sai an mayar da kai mace, ba zaka amfani kowacce mace a rayuwar aure ba, sai dai ta kalleka ka kalleta, amma kai da sake kwamciya da wata matar, har abada sai dai idan ni ka aura, zaka gane baka da wayo". *** Mai sunan baba yana tsaye a kitchen, yana kwashe abinci, kasancewar mama bata nan, babu kowa a gidan, mama tana kasuwa, sai shi da ya dawo gidan yanzu, yayi saurin ɗora girki, dan ya san tsaf rumaisa zata dawo a kowane lokaci idan ba a gama abinci ba, idan ta din ga kwanciya tana kuka, sai ta saka ya daketa. Ga lokaci ya riga ya ja. Mama ce ta kira shi a waya, ya ɗaga yayi sallama. Ta amsa sannan ta ce "Babana kana ina ne?". "Na dawo gida, na ɗora girki ne". "Yauwwa, dan Allah idan rumaisa ta dawo, ka saka ta yi wanka ta yi salla, ka tafi da ita asibitin da ta kwanta, an kwantar da iman ku wakilceni ku dubata, yanzu muka yi waya da hajiyar, wai an kaita asibiti ba ta san waye a kanta ba, ni kuma bana tunanin zan dawo da wuri". "Tom" ya faɗa a taƙaice ya ajiye wayar, ya cigaba da aikinsa. "Assalamu alaikum" rumaisa ta yi sallama, sai dai kan ya amsa ta fara cewa "Wani gardin ne yake yi mana abinci yau, Allah ya sa yayi daɗi, na ji ƙamshin miyar har tsakiyar kaina, Allah yasa ko shinkafa an gama, in fara rage hanya, dan yunwar da nake ji ba a cewa komai" ta ji shiru ba a amsa ba, ta nufi kitchen ɗin tana cewa "Baƙon aljani muka yi ko kurma, da nake magana aka shareni". Tozali da tayi da shi ne, ya sa ta ci wani wawan burki, rabon da yayi girki har ta manta, dan haka ba ta kawo shi ne ba. "Yi haƙuri, ban san kai ne ba, dan Allah ka yi haƙuri" Kifi yake sakawa a miyar, ba tare da ya kalleta ba, sum-sum ta bar wurin ta koma ɗaki ta kwanta. Mai sunan baba bai tashi gaya mata saƙon mama ba, sai da ta fara shirin islamiyya, ya ce "Na gaya wa shugaban makarantarku ba zaki shiga ba yau, zamu je dubiya" "Ina?" Ta tambayeshi tana kallonsa, sai dai ta manta shi mai sunan baba, idan ya ce ayi kawai ayi, ba tare da tambayoyi ba. Har suka tafi dubiyar, mamaki take yi, waye babu lafiya, ta lissafa wannan ta hango wancan, amma ta kasa gano waye babu lafiya. Sai dai ba ta ƙara sarewa da al'amarin ba, sai da ta gansu a asibitin da aka kwnatar da ita. Lambar mama ya kira, ya tambayeta wani ɗakin ne, ta sanar masa, yayi gaba rumaisa ta bishi a baya. Sai da suka je ƙofar ɗakin sannan ya tsaya, ya kalleta ya ce "Ƙwanƙwasa ki fara shiga" Ta matsa gaban ƙofar, ta ƙwanƙwasa sannan ta buɗe ta shiga da sallama babu kowa a ɗakin, sai iman da ke kwance, hannunta ɗauke da cannula, an rataye robar ruwan da aka gama saka mata a drip stand. Shiga ya yi shima, sai dai babu kowa a ɗakin sai ita kaɗai. Da sauri rumaisa ta ƙarasa gaban gadon tan faɗin "Subhanallah, Anty Iman, baki da lafiya ne?" Sai dai ta tarar bacci take yi. Ta kalli mai sunan baba ta ce "Amma ya naga babu kowa a wurinta" shirun da yayi mata ya sanya, ta tuna ta yi tambaya ba a gurbinta ba. Da sauri ta ce "Bari na duba waje, ko zan ga wanda yake zaune tare da ita". Ta juya ta fita da sauri, shi kuma ya tsaya a tsaye, ya sake kallonta tana kwance cikin doguwar rigar material, dogon gashin nan ya sha ribbon, duk da ya ɗan hargitse, ga farar fatarta gwanin sha'awa, babban abun burgewa da jikinta, bai wuce wuyanta ba, duk da ba ta da ƙiba, amma tana da irin wuyan nan, mai guru-guru. Da sauri ya sunkuyar da kansa yana a'uzubil'ahi. Zagayawa rumaisa ta shiga yi a cikin asibitin, tana mamakin waye yake zaune da iman a asibiti, ya bar ta ita kaɗai babu kowa? A hankali Iman take furta "Ammi, Ammi ruwa, ƙishirwa nake ji" yana jin ta, yayi shiru, kamar babu kowa a ɗakin. Tun bayan farfaɗowarta, kasancewar ciwon kan baya sauka, ya sanya likitocin, suka yi ta yi mata allurar barci, da sai yanzu ta saketa ta tashi. Duk da tana cikin ciwo, sai da ta razana da ta ganshi, a tsaye yana danna wayarsa. Tunani take yi ko a mafarki take, ta miƙa hannu jikinta yana rawa, tana ƙoƙarin ɗaukko robar ruwan da ke kan side bed. Sai a lokacin ya motsa, ya ƙarsa, ya ɗau kofi, ya zuba ruwan ba tare da ya kalleta ba ya ce "Tashi ki sha" Cikin tsananin tsoro ta ce "Bani in sha a kwance, ba zan iya tashi ba" Miƙa mata ruwan yayi, ya ga iya gudun ruwan ta, ta fara ƙoƙarin sha a kwance, ya karɓa kofin ya ce "Tashi!" Kamar zata fashe da kuka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri kaina ciwo yake yi" Haushi ne ya kama shi, gani yake kawai tsabar langwai ne, da iskanci. Ya saka hannu ya ɗagota gaba ɗaya, hakan yayi dai-dai da shigowar nusaiba. Wani irin ihu ta saki, ta riƙe hannunsa, hawaye na bin fuskarta, sabodaa ji ta yi, kamar kanta ya rabe biyu. Da gudu Nusaiba ta ƙaraso tana faɗin, "Wanene wannan, bawan Allah lafiya?" Tayi maganar tana yi masa kallon sani, amma ta manta a ina ta san shi. Wani mugun kallo ya yi mata ya ce "Wane irin shirme ne zaki tafi ki bar mara lafiya ita kaɗai, wace irin jinya ce haka?" Gaba ɗaya ruɗewa nusaiba ta yi, ba ta san waye ba, amma kwarjinin sa ya razanata, ta ce "Likita ne ya ce a bani jininta na kai gwaji yana buƙatar result yanzu, ammi kuma ta riga ta tafi gida ta je ta huta, shine na je lap ɗin asibiti, suka ce ba sa yi, shi ne na fita waje, da takawa nake jira ya zo ya kai, likita ya ce lallai yanzu yake so" Tsaki yayi, ya kalli iman ya ce "Ke kuma cikani" wata irin kunya ce ta kamata, dan ba ta san ta riƙe shi haka ba. Ta sakar masa riga, ta karɓi ruwan ta fara sha. "Ita kuma wannan ma shiririciyar ko ina ta tafi oho mata". Rumaisa kuwa lungu da saƙo na asibitin take ta bi, har ta gaji ta kama hanyar komawa ɗakin, kawai ta hango motar takawa, yayi parking ya fito daga motar, hannunsa riƙe da leda. Aikuwa ta nufe shi, babu tsammani ya ganta a gabansa. "Dama kai ne a wurin Anty Iman? Haka ake jinyar mutum dama, ka yi tafiyarka ka barta? Kai idan aka yi maka haka zaka ji daɗi ne?" Sororo yake bin ta da kallo, yadda take yi masa haƙilon masifa kamar babarsa. "Ya ina magana kana kallona, sai wani abun ya sameta? Kawai ka ɗau mota ka tafi yawonka, ka bar mara lafiya ita kaɗai? To wallahi sai na gaya wa ammi" banza yayi mata, ya nufi cikin asibitin, rumaisa kuma ta bishi tana cigaba da mita. Cike da shiga taitayi, Nusaiba ta bawa mai sunan baba haƙuri, ita dai ba ta san waye ba, amma ta tsinci kanta da shakkarsa. Ta kalli iman ta ce "Iman, me zan baki ki ci to, tun jiya baki ci komai ba, an ce lallai ki samu ki ci wani abun, ga abinci ga fruit wanne zaki ci?" Iman ta girgiza kai ta ce "Na ƙoshi, bana son cin komai" mai sunan baba a ransa yake jinjina halin mata, su a rayuwarsu ta duniya komai sai an lallaɓasu? Abincin ne ba zata ci ba, sai an yi ta rarrashinta, alhalin ta san kanta zata cuta idan ba ta ci ba. Takawa ne yayi sallama, ya shigo hankalinsa a kan iman, ya ƙarasa gaban gadon ta. Nusaiba ta ce "Maman sabir, yaushe ki ka zo?" "Tun ɗazu muka zo ni da mai sunan baba, ashe wannan ne yake jinyarta, ya tafi ya barta ita kaɗai" tayi maganar tana nuna Adam. Nusaiba ta ce "Eyya, ni ce tare da ita, jininta na tafi kai wa a gwada, ba yadda zan yi ne shiyasa na tafi na bar ta". Rumaisa ta ce "Au na zata shi ne ai". Ta ƙarasa ta leƙa fuskar iman ta ce "Anty Iman ya jiki?". Cikin ƙarfin hali ta ce "Da sauƙi Alhamdilillah ". Adam ma lallaɓata yake yi, ko za ta ci wani abun, amma ta ce ita ba ta cin komai, ya din ga rarrashin ta, ta ce tuffa take so, takawa ya tashi ya ce bari ya je ya duba, ya sayo mata. Daga mai sunan baba har Adam babu wanda ya kula wani, takawa na tafiya, iman ta fara ƙoƙarin kwanciya, mai sunan baba ya kalli Nusaiba ya ce "Ke, zuba mata abincin nan" gaba ɗaya suka tsaya suna kallonsa. Rumaisa ta jinjinawa Nusaiba kai, dan ba ruwansa da baƙunta yanzu sai ya balebalesu da masifa. Romon kifi ne da dankalin turawa, sai ƙamshi yake yi, idon iman ya cika da hawaye, dan ko ƙamshin abinci ba ta so, ya karɓa ya je gaban iman ya ajiye shi, ya tsaya mata ƙiƙam a ka, ba tare da ya furta komai ba, ta kama cokali, ta fara cin abincin nan, jikinta yana rawa, saboda tsoro da fargaba, ga wata irin Muguwar kunya, dan ba ta saba cin abinci a gaban maza ba, ko a taron mata ba iya ci take ba. Sai da ta ci sosai sannan cikin faɗa  ya ce "Kuna sane kuke wahalar da iyayenku, dan kun ga suna ta taku. Ke kuma tashi mu tafi" yayi maganar yana kallon rumaisa. Ta tashi, kamar ta tuntsire da dariya, daga Nusaiban har iman ɗin kamar ka ce kyet su zura da gudu, saboda tsoro. Ruma ta ce "Anty iman, Allah ya ƙara afuwa". Cikin sanyin jiki ta ce "Amin maman sabir na gode". Bayan tafiyarsu Nusaiba ta ce "Ke iman, wannan jarabbaben mutumin fa?" "Yayan rumaisa ne" ta bata amsa. "Kam bala'i, yau na ga wanda ya taka takawa iya tsare gida, daga zuwa ya hau ni da masifa" Iman ta sunkuyar da kai ta ce "Mhmm, baki ga komai ba" Babu daɗewa takawa ya dawo da tuffa, Nusaiba ta bashi labarin abun da ya faru, bai ce komai ba yayi shiru, dan shi kansa jin kan mai sunan baba yana bashi mamaki. *** Iman jikinta yayi sauƙi, mama ma ta je asibitin ta dubata, ta warware, sai dai lokaci lokaci, kan ya kan matsa mata da ciwo, aka sallameta daga asibiti. Sai dai tun da ta koma gida, washegari ta sake tashi da ciwon kan, sai dai ta yi ƙoƙari ta jure, saboda ba ta san sanya ammi a damuwa. A ranar da aka sallameta daga asibiti ranar Jabir ya dira Nigeria, daga wurin duba mahaifinsa. Hajiya Lubabatu ta yi mamakin ganinsa ya dawo, dan sun yi da shi zai yi sati uku a can kan ya dawo. "Wai kai Jabir, menene ya dawo da kai tun a yanzu?" "Bakomai, ji na yi an ce iman babu lafiya, shiyasa na dawo ita ma na dubata". Cikin rashin fahimta ta ce "Wace Iman ɗin, kai a wa? Meye haɗinka da ita?" "Bakomai zumunci kawai". "Ban gane zumunci ba? Jabir kar na zo na ji wata magana saɓanin wadda nake son ji, ka san halina dai ban da kyau" "Babu wata magana da zaki ji, kawai dai ina yi ne saboda Adam" tsaki tayi, ta shiga wata sabgar daban ta ƙyaleshi. *** Yau tun da safe ammi ta kira mama, ta sanar mata da Adam zai zo wurin rumaisa, domin idan da wani abu da take buƙata ta gaya masa na game da shirin biki. Amma mama ta ce "A'a hajiya, a ƙyaleta kawai, duk abun da aka yi Allah ya amfana" Ammi ta ce "Ai da ni da ke, babu ruwanmu, namu ido abu ne na ma'aurata, dan haka yakamata su din ga tattaunawa domin su fahimci junansu!. Ayshercool. 08081012143 *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Mama ta ce "Ai kin san masu sarauta ba sa son wauta, ita kuma ƴar taki sai fatan shiriya" Ammi ta yi dariya ta ce "Rabu da su, namu addu'a da ido, ai rumaisan ce dai-dai shi". "To, Allah ya iya mana ya jikin iman kuwa?" Ammi ta ce "Jiki yayi kyau mun gode Allah, har tana iya barci yanzu, in da nake ta yi wa Allah godiya, an ce zuciyarta lafiya ƙalau wannan karon, ciwon kai ne dai da razana take yi". Mama ta ce "Allah sarki, sai a dage da addu'a, a haɗa da na islamic, kin san kana da ido ba na ganin gari ba, mussaman ita da take tubarkallah Masha Allah, kyau kamar ita ta yi kanta, sai ana dagewa da addu'a" "Wallahi maman rumaisa ana yi dai-dai gwargwado, kin san sabgar iyali ce, sai dai ka yi iya yin ka ka bar wa Allah sauran, idan wannan ya ce wash anjima wannan ya ce wayyo, kuma duk kai kaɗai ranka, sai fatan ɗaukin Ubangiji" "Haka ne wallahi, dama shi ne mai tafiyar rayuwar gaba ɗaya, ba dan haka ba idan an kira ka, ba zaka amsa ba, ko yaya ace kula da ragamar gida a kan mace itakaɗai, akwai ƙalubale, Allah ya raya mana su yayi musu albarka". Ammi ta ce "Amin ya Allah, dan Allah maman rumaisa idan da abun da take buƙata kar a saka ta yi ƙwauron baki, duk ta gaya masa, tun da rayuwa za su yi inuwa ɗaya, a ƙyaleta ta faɗi abun da take so". Mama ta yi murmushi ta ce "Na lura son kan ku yayi yawa, kin fiye son ƴar nan taki, babu mai takurawa ɗana nima ehe". Ammi ta yi dariya, cikin jin daɗin hirar ta su, suka shiga tattauna yadda yakamata abubuwa su tafi game da auren. Kamar an jefota rumaisa ta faɗo ɗakin mama, mama ta ɗaga kai ta kalleta ta ce "To madiga, yau babu sallama?". "Na yi fa, baki ji bane ba, yunwa nake ji" "Kai rumaisa ni wannan ci naki yana bani mamaki, gidan miji zaki tafi, maza ba sa son mace mai shegen cin tsiya, kuma ba ma cin kirki ba, kina ci kina wasa ba zaki zauna ki mayar da hankali ki ci lokaci guda ki tashi ba". "Taɓ, aikuwa mama sai in din ga dawowa gida ina cin abincin, Allah ya halicci bawa da ciki, wani ya ce wai baya son mace mai ci" "Ke tafi can ki bani wuri, yauwwa sirikarki ta ce, in an jima mijinki zai zo" Rumaisa ta yatsune baki ta ce "Waye mijina kuma?" "Ban sani ba" Mama ta bata amsa. "Mama to ni kawai sai ki wani ce masa mijina" Mama ta ce "Ke, nutsu ki saurareni, bana son wannan shirmen da wautar taki, dole ki shiga hankalinki, aure ba abu ne na wasa ba, wallahi idan ya zo, ki ka sake ki ka yi wani abu na shirme ba dai-dai ba, wallahi ni da ke ne. Namiji duk in da yake, ko ba mijinki ba abun girmamawa ne, balle shi da zai aureki, ki ka sake ki ka yi masa wata wautar ko fitsarar, sai kin ga yadda zan yi da ke". Rumaisa ta yi shiru ta sunkuyar da kai, tana tunanin shi meyasa ba ayi masa faɗan ya daina yi mata abun da yake yi mata, ko dan tun farko ba a san ita me yayi mata ba?. "Yanzu me ki ke ganin za ayi masa wanda za'a tarbe shi da shi?" Kai tsaye ta ce"Ruwa" Abdallah da yake jiyo maganar ta su daga tsakar gida ya shigo, ya ce "Mama, ita fa wannan yarinyar taki, kamar namji take ba ta san komai na rayuwa ba, sai an karanta mata yadda yakamata". Ya kalleta ya ce "Ke, ki nutsu malama, aure zaku yi, so muke idan ki ka tafi kin tafi kenan, ba zaki dawo mana gida ba, dole ki din ga yi wa mutane abun da ya dace, har zancen ma zan koya miki. Yanzu mama ki kawo kuɗi, mu sayo kayan meat pie, in taya ta mu yi, sai a haɗa masa da lemon roba da abinci" "Duk shikaɗai? Gaskiya ni ba zan iya aikin wani meat pie ba, bacci zan yi, ni idan ya zo ma ban san me zance masa ba? Sai dai Huzaifa ya rakani, ko Yasir" Abdallah ya ce "Ka ga shashasha, tashi ki je ki yo cefanen meat pie ɗin nan" Gaba ɗaya rumaisa ga rasa gane dalilin da ya sanya, kowa laifinta yake gani a kan Adam, kowa so yake lallai sai ta kyautata masa, haka mama ta saka baki, aka aiketa sayen kayan meat pie da za a karɓi Adam. Abdallah da Huzaifa suka sakata a gaba, a kan aikin, amma ta ƙi mayar da hankali, ƙarshe su suka yi aikin suka ɗai. Yaya Usman ne ya dawo, ya tarar da su Abdallah suna ta kai kawo, an yi girki, kamar dai wani abu mai muhimmanci na shirin faruwa. "Wai lafiya na ga ana ta wani shiri, ko bikin aka fara tun Yanzu babu labari, abu na masu hannu da shuni" Huzaifa ya yi dariya ya ce "Yaya Usman, sirikin ne zai zo, yau zai fara zuwa zance, shi ne ake shirya masa abinci, kar azo a ji kunya. Gara mu  kankaro kanmu, sai dai ita yarinyar ce ba ta da hali, ana saita ta a hanya tana fizgewa". Usman ya nufi ɗakin mama yana faɗin, "ubanta kuwa za ta ci wallahi, dole a saita ta. ke kina ina?" Yayi maganar yana shiga ɗakin mama, rums ta yi ɗai-ɗai tana kallon Tv, tana cin kantu mai gishiri. "Ba zaki tashi ki fara shiri ba, yaushe ya ce miki zai zo?" Rumaisa ta ɗaga kai ta kalli Usman ta ce "Oho masa" "Ke ina yi miki magana, kina amsa mini a haka, tashi zaune" Rumaisa ta tashi zaune tana ɓata rai. Mama da ke gefe ta ce "Ai gara ku shiga cikin lamarin, tun da ni ba zan gaya mata ta ji ba". Usman ya ce "Aikuwa da ni take zancen, wallahi idan ya zo, ki ka sake ki yi masa rashin mutunci, ko wannan cin maganin, sai na yi miki bugun sakwara, ko ki zauna kina wannan ɓata ran, ki na kumbura baki zaki ga yadda zan yi da ke" "To ni yaya usy ya zan yi? ku fa ku ka ce mini ba ruwana da maza, ni ban taɓa zance ba ban san me ake cewa ba, sai dai Huzaifa ya rakani, ni tsoro ma nake ji". Usman ya ce "Au idan aka yi miki auren ma, huzaifa ne zai biki gidan mijin, ya tayaki zama da kula da mijin?". "Ni ba zani gidan kowa ba, sai dai shi ya dawo nan gidan ya zauna, kuma bada Sabir kawai zan kula ba, shi ƙato da shi me zan masa?" Huzaifa ya ce "Ki ce auren Bollywood za ayi, ayi aure miji ya tare a gidan su mata, yarinya sai dai kar ki yi zancen, idan ni zan rakaki". Usman ya ce "Ni bari na koya miki abun da zaki ce, ya za ayi wani huzaifa ya raka ki, ya ji kalaman soyayya ya dawo yana tsokanar ki". Ta kwaɓe baki ta ce "Soyayya kuma?" Usman ya ce "Eh mana, au da ƙiyayya?" Ta yi shiru, tana kallon Usman. Ya ce "Idan ya zo, ba ƙifi-ƙifi zaki yi da ido, kina kallonsa kamar fusatacciyar kyanwa ba, ya ga alamar girmamawa a idonki, idan ya zo sai ku gaisa, ki tambaye shi ya mamansa, da ƙannensa da Sabir. Cikin mutuntawa ba da zazzare ido ko harare-harare ba, ki na yi kina sunkuyar da kai, ban da tsyawa ki ƙure shi da ido, na sa cikin naki, duk abun da ya tambayeki ki bashi amsa, ba cikin tashin hankali da masifa ba, sai dai idan kin ga yayi miki wani abu da ya saɓa shari'a da tarbiyyar da aka baki, sai ki zo gida ki gaya mana". A ranta ta ce "Saɓa shari'a da tarbiyya na nawa kuma, dan dai kawai kar na zubar masa da mutunci ne, amma da sai na gaya wa kowa abun da ya yi mini". Muryar Usman ce ta dawo da ita hayyacinta, da ya ce "Kin ji abun da na ce ko kuwa?". "Na ji" ta amsa da ƙyar. "To tashi ki je ki yi wanka, zan din ga yi ina zagawa in ga yadda ki ke zancen, idan ki ka kuskura, ki ka aikata abun da na hanaki, a gabansa zan tuburbuɗaki". "To yaya usy, ni fa na yi wanka da safe" Huzaifa ya ce "Sokuwa, wannan wankan tarbar masoyi ne, wankan ganin baby". "Allah ya kiyaye na ce masa wani baby, kamar wata ƴar iska, sunansa Adamu" Usman ya saka hannu, ya talle mata ƙeya, sai da ta kusa kifawa. "Shashasha, ana koya miki abu kina iskanci, ki je ki yi shirme a auren, zaki gane baki da wayo, tashi ki je ki yi wanka" tashi tayi ta dafe ƙeya, ta fice daga ɗakin. Mama ji take kamar ta yi dariya, yayyen sun zauna suna koyawa ƙanwarsu, yadda ake yin zancen. Mama ta ce "Malam usman wannan lakcar, anya ba a zagaya zauruka da magariba? Ba a taɓa bani labarin sirikar tawa ba" Usman ya sosa kai ya ce "Mama a wurin abokaina nake ji". Mama ta yi murmushi ta ce "Ba zan hanaka ba, ni dai fatana aji tsoron Allah, kar a din ga zuwa rage dare wurin yaran mutane, alhalin ba aurensu za ayi ba". "Mama kar ki kawo komai a ranki ma, ba wurin da nake zuwa" "Idan ma ana zuwan dai, ai dole na yi kashedi" Usman ya din ga murmushi yana sinne kai. **** Iman tana zaune a kan gadonta, ta sunkuyar da kai, gefe Nusaiba na zaune, sai kuma jabir da ya saka Iman ɗin a gaba da kallo, kamar zai haɗiyeta. "Talk mana iman ko na ji daɗi, saboda an ce baki da lafiya ban gama abun da nake yi ba, na baro Germany, na zo na dubaki kuma kin ƙi magana, talk please" Nusaiba ta ce "Please iman, stop treating our uncle J this way, ki yi magana mana". Cikin sanyinta ta ce "Anty Nusaiba, maganar ce bana so in general, bana jin daɗi sam" "Amma duk da haka bai kamata ya yi ta magana ki yi masa shiru ba" Ta ɗan kalleshi ta ce "Am sorry". "To ya zan yi da ke jarumata, bana son yadda ki ke yi mini wulaƙanci, idan wani abun na yi miki am so sorry for it" Ta girgiza kai ta ce "A'a babu komai" "Shikenan, na ga kamar ina takura miki, bari na je gida, Nusaiba take a good care of her please" Nusaiba ta ce "To uncle J, but you have pay for the service" Yayi murmushi ya ce "Biyoni mu yi ciniki, za a biyaki ko nawa ne" ta yi murmushi ta tashi ta bi bayansa suka fita. A hankali iman ta furta "Ohh Allah, ka iya mini, Allah ka yi mini zaɓi na alkhairi, Allah kar ka saka Jabir ya gayawa wani yana sona, he has no space in my heart. Ni ba kowan kowa ba ce, duk zaɓin da ka yi mini ina so Allah, Allah ka iya mini" ta ƙarasa maganar tana kwanciya a kan pillowanta. Sai dai tana kwanciyar, ta ji tamkar an sanys igiyar ƙarfe, an ɗaɗɗaure mata jijiyoyin kanta, ta sanya hannu ta dafe kan ta fashe da wani marayan kuka, ta rasa me ma za ta yi, lamarin nan ya fara bata tsoro, dan kuwa ji take tamkar zata haukace. Jabir ya kalli Nusaiba ya ce "Nussy, see how your sister is behaving towards me, just because i have feelings on jer, me yasa ba ta so na, meye aibu na?" "Uncle J, yakamata ka yi mata uzuri, this girl suffer alot in this family, kalli yadda take samun manema, suna tafiya saboda abun da mutane basu da tabbas a kan sa, kalli saboda yarima ya ce yana son ta, kalli wulaƙncin da fulanin yola ta yi mata da cin mutunci, har a gidan nan ma ba ta tsira ba, na waje ma idan sun biyota suna so, sai a samu mai zigasu su daina zuwa. A yanzu ta riga ta ce ba ta son kowa ya raɓeta da sunan soyaya, ba ta son kowa, ka san abu na ƙarshe da ya faru a gidan nan ai, ba wanda bai ji ba, shi ma aka din ga surutu a kai. Dan haka ta ce idan har mijin aurenta ya zo ko ba soyayya, ta ce za ta yi, amma for now, tana buƙatar hutu ne". "Nusaiba, babu ɗan adam ɗin da baya faɗi tashi da gwagwarmaya da ƙaddara, amma hakan ba ya sanya wa a sare, this is not an excuse da za ta yi denying kowa ya ce yana son ta, ni da gaske ina son iman, amma wace shawara zaki bani a kan ta?" Nusaiba ta numfasa ta ce "Uncle J, ga ka da takawa, ga ka da Ammi, ai a duniya babu abun da za su ce ta yi, ta ƙi yi muddin bai saɓawa shari'a ba, ka bi ta wurinsu kawai, ina fatan idan komai yayi daidai, zaka kula mini da iman, ka kuma ji tsoron Allah a kan riƙon ta". "Nusaiba da zan cutar da iman, ba zan aureta ba, ina son ta so na gaskiya ne, abu na gaba ina ga ammi zan samu kawai, takawa zai iya yi mini wasa da hankali, kin san halinsa, bari na je kawai na gode, ki yi mata sannu" "Za ta ji, ka gaida gida" suka yi sallama ya tafi, ita kuma ta koma. *** Aiki ya samu ƴan maza fa, domin kuwa su Usman ne suka zaɓowa rumaisa kayan da za ta saka, sai cika take tana batsewa, wannan ya dungure mata ya ce "Ki yi dariya dan ubanki". Wannan ya ce "Ki ka yi mana shirme dakuwa zaki yi". Suka shiryata cikin doguwar rigar atamfa, ta sanya dogon hijjabi, Abdallah ya ce "Ina hoda a shafa miki?" "Ni bani da hoda" ta amsa masa tana ɗan hararsa. Usman ya ce "Jambaki fa?" Ta ɓata fuska ta ce "Ni fa kun san mai kawai nake shafawa, shi ma ba kullum ba, bani da komai ni". Usman ya ce "Ikon Allah, lallai kin cika deluwa, kina mace amma ba hoda ba Jambaki, kamar gardi, wallahi ki ka je gidan miji ba kya kwalliya, wahala zaki sha, to yaushe mutum zai ajiye mace, amma shi da ita ba maraba? Ai na ga mama tana da kwalli, shi zaki saka" Rumaisa ta ce "Yaya usman, idona fa yaji yake idan na saka kwalli". "Ai ko tsiyayowa zai yi sai kin saka, Abdallah ya riƙeta, Usman ya saka mata kwalli, tana kuka sai ka ce dole" Mama ta riƙe haɓa tana "Yau nake ganin ikon Allah" Abdallah har da lakato Vaseline, ya shafa mata a leɓenta. Huzaifa ya ce "Ai dole idan ya tafi, a yau ba sai gobe ba, a sayo kayan kwalliya ta din ga yaɓawa" Usman ya ce "Dolenta ma kuwaa" Aka ɗauko turare aka fesa mata, Usman ya ce "Ranar kamu ni zan kamaki, an ce da turare ake yi ko? Idan na din ga fesa miki, sai kin fara hayaƙi" "Sai ka ce wata ita ce" "Koma dai menene, ina sake jaddada miki, ki ka yi mini kwaɓa, da takalmi zan ladabtar da ke". Ta kalli kanta a mudubi, ta ce "Kalli yadda ku ka mayar mini da ido, kamar wata sheɗaniya" Yasir da yake zaune yana kallonsu yayi dariya ya ce "Koma dai wacece, idan ya zo, baby ka zo, you are welcome ya aiki? Ya family, kamar dai yadda ki ke gani a film, mussaman bollywood". Ta buɗe baki ta ce "Taɓ, Allah ya tsareni, Bollywood ba taɓa mata suke yi da maza ba, wallahi ya taɓa ni, sai na gantsara masa cizo, babu namijin da zai taɓa jikina in tsaya ina kallonsa, ko a wurin ƴan bindiga, bana yadda, wallahi faɗa ake da ni" ga mamakinta sai ta ga gaba ɗaya sun tuntsure da dariya, Usman ya ce "Wannan bawan Allah yana ruwa, mama akwai buƙatar ilimantar da yarinyar nan kan aure" Mama ta yi masa shiru, kamar ba ta ji ba, wanda a ranta tunani take yi, ta yaya za ta yi wa rumaisa bayanin wannan al'amari mai girma, yarinyar da ta tashi a kan iya abun da aka nuna mata shine dai-dai a gida, kome za ayi ba zata yadda ta canza ba, yanzu da an ce mata wani abu, tsaf za ta ce kenan da ƙarya ake yi mata. Wata zuciyar ta ce "Ko da yake, ai ina ga zai ɗan ƙyaleta ta ƙara wayo, tun da saboda karatunta ma mamansa ta ce ayi auren' 'Namiji ne fa' wata zuciyar ta tunatar da ita. Ta ɗan dafe kai ta ce "Yarinya ce, lokacin da aka yi mini aure, shekara sha biyar, na fi rumaisa girma sosai da sosai, amma lamarin aure abu ne mai faɗi" Yasir ya ce "Mama magana ki ke yi ne?" Ta ce "A'a kallonku nake yi dai". Mai sunan baba ya shigo, hakan ya sanya duk suka yi shiru suka nutsu. "Ke ki zo, ga mutumin can yazo, ki ɗau abun zama ki saka muku a soro, kar ki sake ki tsaya a waje, balle wannan iyayen saka idon su ganki". Cikin rawar murya ta ce "Mama ni fa tsoro nake ji, gabana faɗuwa yake yi" Mama ta buɗe baki tana kallonta, har idonta ya ciko da hawaye. "To cinyeki zai yi?" Mai sunan baba yayi maganar yana tsareta da ido. Ta girgiza kai alamar a'a. "To kukan uban me zaki yi? Wuce dalla, sai kin tayar mata da hankali haka kurum". Huzaifa ya ɗau turare da darduma, ya ce "Bari na yi maza, na je shimfiɗa dardumar na fesa turare a soron, sai taho kina taku kamar gimbiya, dan gidan sarauta ba sa son hauma-hauma" ya ruga yayi soron da gudu. Ya shimfiɗa, ya feffesa turare, ya dawo da sauri ya ce "To fito, ki ce masa ya shigo". Ta fito tsakar gida zari silifas, za ta yi waje, Usman ya riƙeta "Wai ke rumaisa wace irin ƴar baƙin ciki ce? Yasin gidan sarautar nan sai kin je shi, ba zaki mana buƙulun zuwa gida mai kyau ba, canza wannan ɗan iskan takalmin, ko na cire shi, na tsinke ki da mari da shi, kuma idan ya shigo mintuna biyar, ki zo ki ɗauki kayan abincin nan ki kai masa, dole mu koya miki soyayya, dan ba zaki yi aure ayi miki kishiya ba" Tana cusa baki, ta sauya wani ta fita, bagazan-bagazan ta leƙa wajen, ta ganshi a tsaye a jikin motarsa yana amsa waya. "In ka gama wayar, ka shigo" ta faɗa tana riƙe ƙugu. Kamar bai san ta yi maganar ba, ya cigaba da wayar, ita kuwa ta koma soron, ta zauna ta mimmiƙe ƙafafuwanta. Ya kai mintuna goma, kan ƙamshin turaren sa ya mamaye ilahirin soron, brown ɗin yadi ne a jikinsa, kansa babu hula, sai zuba ƙamshi yake, ta ɗaga kai ta kalleshi, kamarsa da Sabir ta sake fitowa sosai da sosai. Ya nemi wuri ya zauna a kusa da ita, ta matsa can ƙarshen sallayar, tana kaɗa ƙafa. Jin shirun yayi yawa, ba shi da niyyar magana, ya sanya ta ce "Ina wuni?" Ya kalleta ya yi shiru bai amsa ba. "Ai dama na san ba amsawa zaka yi ba, dan a gida an ce in gaisheka ne, amma idan na gaishe ka, ba amsawa kake yi ba, ai ni na riga na gama sanin halinka kaf, daga A har Z" Nan ma shiru bai amsa mata ba. "Taɓ kana da aiki wallahi" ta juya masa baya, ta kalli wani wurin. Ya kalli bayanta, yana jinjinawa tsiwa da rashin jin ta, wai ta san halin sa daga A har Z. Can aka kwashi wasu mintuna, sai ta tuna abun da Usman ya ce mata ta tashi da sauri ta ɗauko kayan abinci nan. Gaba ɗaya suka taso suna tambayarta yaya aka yi? Ta ce "ba komai" Usman ya ce "To, wallahi ki ka dawo da kayan Abincin nan, bai ci komai ba, to tabbss rashin mutunci ki ka yi masa, kuma zaki daku" ta gyaɗa kai, ta tafi soron ta tarar da shi, ta ajiye masa kayan a gabansa ta zauna ta ce "Ga abinci nan" ya ɗago ya kalleta ya cigaba da taɓa wayarsa. "To, ni dai zan juya maka baya, ka ci, dan ba zan yi wahalar banza ba, tun safe ake azabtar da ni a gidan nan saboda zaka zo, zan juya maka baya, ka ci idan ba zaka iya ci a gabana ba" Ta juya masa baya, ta ɗauko goruba tana ci. A ransa ya ce "Na ga ta kaina ni Adamu, wai wannan ce matar da zan aura?" Ta waiwayo ta ce "Wai ba zaka ci ba? To wallahi ba zaka ja mini duka ba. Ta ɗauki coca-cola, ta tsiyaya a kofi, ta shiga hijjabinta ta sha, ta buɗe meat pie, ta ɗauki ɗaya, ta  shiga hijjabinta ta ci, ta gutsuri wani ta ajiye ta ce "Yauwwa, dan ba zaka ja mini duka ba, an ce idan har na koma da shi ba ka ci ba, yaya usy zane ni zai yi" Adam ya zubawa sarautar Allah ido, ita a rayuwarta ba ta san kara ba, idan ana neman mutum kai tsaye da ba ya rufi, to kowa ya bi bayanta. Kamar wadda ta ci wani abun maye, ta takure abun ta, ta haɗa kai da gwiwa ta hau bacci, shi dai ikon Allah kawai yake kallo, wannan zance ya zo, ko kallon drama. Ya mayar da hankali kan wayarsa, yana dannawa. Usman da yake kaiwa yana komowa ya ce "Kai shirun nan yayi yawa, bari na duba" Wata irin razana rumaisa ta yi "Iman!" Ta faɗa da ƙarfi, tare da faɗawa jikin Adam gaba ɗaya jikinta yana rawa, hakan yayi dai-dai da shigowar su Usman cikin rige-rige, domin ganin abun da yake faruwa, saboda ihunta da suka ji. Ayshercool. 08081012143hi *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*. Adam bai taɓa ta ba, sai bin ta da ya yi da kallo, idanuwanta na neman su kakkafe, sai daddagewa take yi, jikinta yana cigaba da tsuma. Usman ya ce "Lafiya kuwa?" Mai sunan baba kuwa wani irin takaici ne ya mamaye shi, ganin rumaisa a jikin Adam gaba ɗaya. Takawa ya ce "Ban san meya sameta ba, gani na yi ta haɗa kai da gwiwa tana bacci, kawai ta zabura ta faɗo jikina". "Iman! Iman ba ta da lafiya fa, Iman ba ta da lafiya" ta yi maganar cikin surutu da magagi. "Wace kuma iman?" Mai sunan baba ya tambayeta a ƙule. Haushi ne ya kama Adam, saboda yadda mai sunan baba ya raina wa kansa hankali, wai wace kuma iman, ya lura da yadda yake a ƙule, dan haka ya ture rumaisa daga jikinsa, ya ja da baya. Mama tuni ta fito tsakar gida, dan jin abun da ya faru, amma ta kasa ƙarasawa soron, saboda jin nauyin adam. Sosai take kuka tana neman abun riƙewa, "Iman fa, na gaya muku ba ta da lafiya" Mai sunan baba ya saka hannu ya ɗagata tsaye, amma jikinta ya riga ya saki, tana neman ta faɗi. "Ki buɗe idonki menene?" Ta sake rintse idanunta, kamar mai tsoron ganin wani abu. Cak ya ɗagata ya shiga da ita cikin gidan, ya kwantar da ita a tsakar gida, gaba ɗaya suka rufu a kanta. Adam har yayi niyyar tafiya, sai ya ga idan yayi haka bai kyauta ba, mussaman da ya ji tana ta ambatar sunan Iman. Sallama ya yi ya shiga, ya tarar da su a kanta, mama tana girgiza ta, tana tambayarta menene. Idonta dai a rufe, tana ta zubar da hawaye, ta ce "Iman, ba ta da lafiya sosai da sosai" Mama ta ce "A'a jikinta da sauƙi ai, har an sallameta daga asibiti, tana gida". Ta ɗaga hannunta ba tare da ta buɗe idon ba, ta ɗora shi a saitin zuciyar mai sunan baba, idonta a rufe ta ɗaga kai in da yake ta ce "Mai sunan baba, ka ji bugun zuciyarka, ai kai ka yadda ba ta da lafiya ko? Ku yi mata Addu'a dan Allah kar ta mutu". Ya ce "To, kema ki yi addu'a" Takawa ya ɗan yi gyaran murya ya ce "Ni zan tafi, Allah ya bata lafiya" Mama da sai a yanzu ta lura da shi, ta ce "Yi haƙuri mai babban suna, wallahi tun da aka yi garkuwa da ita na kasa gane kanta, ina ga wani abun ta kwaso a zaman dajin da ta yi". Adam ya ce "Allah sarki, Allah ya bata lafiya, abun ya bani mamaki, lafiya take zaune, ta ce idan ban ci abincin da ta kawo ba, an ce za a zaneta, da ban ci ba sai ta ci, ta ce ba za a gane ba, sai ta haɗe kai da gwiwa tana bacci, shikenan kuma ta fara ihu" yayi maganar cikin ƙoƙarin wanke kansa, yadda gaba ɗaya ƙartan nan suka zubo masa ido,sun ga ƙanwarsu a jikinsa, ga mai sunan baba sai muzurai yake yi. Mama ta ce "Bakomai wallahi". Usman ya ce "Lallai yarinyar nan baki da mutunci, dama zuwa ki ka yi ki ka cinye abincin?" "Ba cinyewa na yi ba, dama ba na gaya muku ba zai ci ba, na san halin sa fa hmmm" ta yi maganar kamar wadda ta sha ta bugu. Duk suka tsira mata ido, ta miƙa hannu tana yi wa adam nuni da ya zo. Ba musu ya taka ya ƙarasa, ya sunkuya, ta riƙo rigarsa a hankali ta ce "Iman babu lafiya, kar ku zata da wasa nake yi, kar wani abun ya sameta. Kuma, kuma daga yau ba zan sake baka ko ruwa ba, yau haka aka din ga azabtar da ni, wai sai an yi maka girki kuma ka ƙi ci, to daga yau babu ni babu kai, tun da duka zaka janyo mini, sarki mai koriyar alkyabba " ta ƙarasa maganar tana murmushi. Sai kuma ta cigaba da zabura. Ya kalleta ya ce "To, na gode, ba za a dake ki ba, zan tafi da abincin" Ta kuma cewa "Yauwwa, wannan matar, da ta bamu ruwa ni da Sabir, ka tuna ta?" Adam ya ce "Eh, na tuna" "To ka san ta ce wai akwai gwagwarmaya a gaba, hmmm ba ka san fa me nake gani ba ko? To in gaya maka, wani abu na gani rannan a gidanku, kuma ma, wani zai je ya ɗebi turarenka baka sani ba, yauwwa har da maganin ka ma da ake shafa maka, ana nema". Gaba ɗaya surutan da take yi babu ma'ana a wurinsu. Mai sunan baba ya ce "Ya isa haka ki yi mana shiru" Takawa kuwa ya ce "To, kin gama na tafi?" "Eh ka tafi, amma fa kana tafe wannan matar tana binka, saboda tsabar taurin kanta, amma da kaina zan mayar da ita gurguwa" Adam ya ce "Eh yakamata, yanzu dai ki cigaba da baccin, dama ammi ce ta aikoni, zan kira Aliyu a waya mu yi magana" Ta ce "To" ta gyara kwanciyarta ta cigaba da barci. Gaba ɗaya abun ya ɗaure musu kai, Adam ya ce "To mama sai anjima, Allah ya ƙara afuwa" Suka amsa da amin, ban da mai sunan baba. Usman ya ce "Ka tafi da abincin nan, ka cika mata alƙawarin ta". Adam yayi murmushi, Usman ya bi bayansa. *** Ko da ya ƙarasa gida, sashin Ammi ya wuce, dan gaya mata abun da ya faru, amma ya tarar ba ta nan, ya fito ya tambayi baba uwani, ta ce "Ai suna tare da iman, tana can tana ta fizge-fizge kamar za ta haukace". What! Ya faɗa cikin tashin hankali, da sauri ya nufi ɗakin iman, sai dai ya je ya tarar da ita, a kwance tana ta Addu'a, ammi na ta shafa mata ruwa a ka, tana yi mata Addu'a, Nusaiba kuma na riƙe da hannunta. Da sauri ya ƙarasa yana faɗin "Iman, me yake faruwa?" Ta miƙa hannu ta riƙe nasa ta ce "Yaya Adam mutuwa zan yi, dan Allah ku yafe mini, nikaɗai na san me nake ji a kaina, baku san me nake ji ba, kaina kamar ana kafa mini ƙusoshi. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ya din ga maimaitawa, ya saka hannu ya janye piliown da take kai, ya kwantar da ita a kan gadon, ya din ga karanta mata duk addu'a da ta zo bakinsa, cikin ƙudirar Allah sai barci ya ɗauke ta. Adam ya ce "Ammi, wai takamaimai me yake damun iman ne?" "Takawa ina zan sani? Na ga na asibiti sam baya yi mata ma, na rasa in da zan saka kaina ma. To ya aka yi, kun tattauna ɗin, ya ka baro rumaisa? Ina son a satin nan idan iman ta warware a fara haɗa lefe, dan na turawa laila kuɗi, ta yi wasu sayayyar a can ƙasar" "Babu lafiya" ya faɗa a hankali. Ammi ta ce "Kamar yaya?" Nan ya kwashe komai ya gaya mata, ammi ta yi shiru ta ce "Ikon Allah, Adam akwai aiki ja a gabanmu, babban fatana yanzu shine in ga an yi auren nan, kuma bana fatan a ɗaga ko da rana ɗaya". Adam ya jinjina kai Sannan ya ce "Bari na je na ga sabir, daga nan na wuce masallaci". Tun da ya fita yake ta jujju *** Rumaisa sai magariba sannan suka samu kanta, ta tashi daga wannan baccin, ba ta iya tuna komai ba, ta cigaba da sabgoginta. Mama hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, saboda gani take rumaisa aljanu ne ke son su hanata aure. Babu wanda yayi yinƙurin gaya mata abun da ya faru, suka biye mata aka cigaba da harkokin gidan kamar yadda suka saba. Washegari Ammi ce ta kira mama da kanta a waya, tana tambayarta jikin rumaisa. Mama ta ce "Jiki da sauƙi hajiya, na ce ko ɗaga bikin nan za ayi, a nema mata magani, alamu sun nuna iskokai suna damunta, kar ayi aure da larura". "A'a maman rumaisa, Allah zai bata lafiya, wataƙila da an yi auren ta samu lafiya, wallahi kin ganmu nima iman haryanzu jiki yaƙi daɗi, na rasa abun da yake yi mini daɗi, ciwon kai ko sauka ba ya yi". Shiru mama ta ɗan yi, kenan maganar rumaisa gaskiya ce?. Mama ta ce "Allah ya basu lafiya baki ɗaya, in anjima zamu zo mu sake duba jikin nata" Ammi ta ce "Ba sai kun wahalar da kanku ba, ayi mata Addu'a kawai". Mama ta ce "Haba, ai babu wannan a tsakanin mu, bari ayi sallar magariba, rumaisa ta dawo daga islamiyya sai mu zo" Ammi ta ce "To shikenan, ta samu ta ga ɗanta ma". Bayan sun gama wayar, mama tayi ta Addu'a Allah ya sa ba aljanu ne suka buɗewa rumaisa ido ba, take gane-gane. Da magaribar, tare da mai sunan baba suka je gidan su takawa, rumaisa na ta murna za ta ga Sabir. Har ɗakin iman, aka yi musu izinin shiga, suka tarar da ita kamar mai shirin zarewa saboda surutai, duk suna kanta ciki har da Jabir. Rumaisa ta ƙarewa ɗakin kallo, ta ce "Mama, ɗakin nan na yi mafarki fa jiya, ku cirewa iman pillown nan, mafarki na yi wata ƴar tsana tana soka mata allurai a kanta, yauwwa ba na ce muku iman ba ta da lafiya ba jiya?" Ta yi maganar tana ƙoƙarin tuna abun da ya faru jiyan. Ammi ta ce "Rumaisa a ina ki ka ga ƴar tsanar?" "Mafarki fa na yi, ki dafa pillown, ki karanta mata bisimillah da fatiha, amma dai wata ƴar tsana na gani a mafarki" Abun sai da ya ɗaurewa kowa kai, Mai sunan baba kuwa tuni ya bar ɗakin, saboda yadda iman take, zaka san tana jin jiki ba kaɗan ba. Ammi ta dafa pillown, ta karanto adduoi, Rumaisa ta riƙe hannun iman tana yi mata sannu. Jabir ya tashi ya ce "Ammi, bari na je gida, Allah ya bata lafiya" Suka amsa da Amin ya tafi. Tattaunawa ammi da mama suka cigaba da yi, ammi tayi ta bawa mama ƙwarin gwiwa, a kan kar a fasa wannan auren. Bacci iman ta samu, mama ta kalli Adam ta ce "Takawa, kai rumaisa part ɗina, ta ga Sabir, sai ka tambayeta abun da take buƙata na bikin" Adam bai fiye yin jayayya da ammi ba, balle kuma yanzu da yake a gaban mutane ne, bai ce uffan ba, ya tashi ya fita, rumaisa ta bi bayansa tana murna, jin an ce za ta ga Sabir. A hanyar sashin ammai, suka haɗu da baba uwani, cikin girmamawa ta risuna ta ce "Takarwarka lafiya magajin galadima, baƙuwa muka yi ne?" "Eh" ya amsa a taƙaice yana fatan kar rumaisa ta yi wani shirmen, amma ga mamakinsa, ko kallon baba uwani ba ta yi ba balle ta gaishe ta. Sai da suka yi gaba sannan ya kalleta ya ce "Baki iya gaisuwa bane?" "Wa zan gaisar?" "Matar da muka wuce, meyasa baki gaisheta ba? Gidan sarauta ba wuri ne da zaki gwada rashin ɗa'a ba, akwai girmamawa da karamci, ko da kuwa kai ne kake gaba da mutum" Ba kunya ba tsoro ta ce "A hakan? Sau nawa na gaisheka a rayuwar nan baka amsawa, gidan sarautar da watarn wanda kake gaisarwa daban masu amsawa daban, ana ce maka an gaisheka ɗan talakawa, wannan ba wulaƙanci bane ba, ban kula kowa ba balle ayi mini wulaƙanci na ji haushi, ammi da wanda suke amsawa kawai zan din ga gaisarwa" Wato ya fuskanci ita dai wannan yarinyar, defeating ɗin ta, ba abu ne mai sauƙi ba. Sai da suka shiga ɗakin ammi, in da babu idon mutane, sannan ya dubeta ya ce "Idan ki ka cigaba da wannan taurin kan, ina gaya miki abu kina mayar mini da martani, zaki yi dana sanin aure a gidan sarauta, dan zai zame miki tamkar kurkuku mafi azaba, kowa zai yi ƙoƙarin yin amfani da ke wurin cimma burinsa, dole ki kiyaye". Rumaisa ta ce "Na sani, gidan sarauta ba irin normal gida bane, ina gani a film, na indiya da sauransu, daga tsafi sai munafunci, abun ban tsoro, kowa ba abun yadda bane ba, da an ga baka da wayo, sai a cuceka, da ka yadda da wani, sai ya nemi ganin bayanka. Ai ni a duniyar nan kurku mafi azaba ita ce zamana a hannun 'yan bindiga, abu mafi razani kuma ganin mutuwar matar da ta bani kulawa kamar ƴar ta a lokacin da ake yi mini ƙamshin mutuwa. Abu mafi tsayawa a rai shi ne tunanin idan har gawarta tana da muhimmancin da za a kasheta a ɗau gawarta a mota a bar wurin da ita, saɓanin sauran mutanen da ake kashewa wurin, to waye ya saka ayi garkuwa da ita a kasheta, kuma ayi umarnin kashe ɗan ta? Abu mafi ban tausayi shi ne haihuwar jaririn da bai san komai ba, na din ga wahalar da shi da sunan kulawa, har koko na bashi, ya shafe kwanaki da ƙazantar haihuwa a jikinsa, bayan mun kuɓuta a ka yi yinƙunrin rabani da shi. A tunaninka akwai wani abu mai wahalar mantawa kamar wannan? Ko wani irin ƙalubale ne, zan jure shi na rayu da sabir, kamar yadda na yi wa anty aisha alƙawari, amma ka ƙyaleni a yadda nake, ni ba ƴar sarauta bace ba, lokaci ɗaya ba zan iya zama irin ku ba". Tuni hawaye ya wanke mata fuska, ta taka a hankali ta ƙarasa gaban gadon Sabir, ya ƙara zama ƙato sosai, sai bacci yake yi. Takawa kuwa kamar an gina shi, wasu gaɓoɓi ta taɓo masu muhimmanci, amma ya san yanzu da yayi yinƙurin ya cigaba da yi mata maganar, zata koma masa ainihin rumaisanta, ta fara rashin kunya. Ta riƙe ƙafar sabir, tana kallonsa tana murmushi. Adam yayi gyaran murya ya ce "Ammi ta ce, na tambayeki idan da abun da ki ke buƙata na shirin biki" Maimakon ta amsa kawai sai ta hau dariya ta ce "Ni fa mantawa nake yi aure za ayi mini, ni bana buƙatar komai, su yaya Aliyu suna saya mini kaya, su mama kowa sai mini kaya yake yi". Ya jinjina kai ya ce "Good, that's their part, a ɓangarena nake nufi, wanda ni yakamata na yi" Ta girgiza kai ta ce "Za a saya mini komai, ni fa bana son ayi mini abu azo daga baya ana yi mini gori, komai za su saya mini, har da turmin ƙarfe" Ya ce "Shikenan, na gaya mata ba kya son komai, tashi mu tafi na san ke suke jira" Ta sumbaci goshin sabir ta ce "Ka yi mafarkina babyna" sannan ta yi gaba ta bar takawa a baya. Aikuwa ta tarar da su a falo har sun fito, Ammi ta ce Adam ya mayar da su gida, mama ta ce ba ta yadda ba, ba zata iya hawa motar siriki ba, ƙarshe aka saka direba ya mayar da su, mai sunan baba ya ce za shi wani wuri, dan haka bai bi su ba. A daren sai da baba uwani ta kai wa mummy tsaigumin zuwan su mama, tare da sanar mata ba ta san ko suwaye ba amma suna yawan zuwa gidan. Mummy ta ce lallai ta sanya ido, ta gane ko suwaye, ta zo ta gaya mata. Tun da Allah ya sa rumaisa, ta gaya wa ammi abun da ta gani a mafarki a kan iman, suka dage da addu'a, kuma cikin ikon Allah ta samu lafiya. Ɓangaren su mama shiri suke sosai da sosai, a kan bikin da yake gabato su, sai dai rumaisa ta cigaba da mafarkai barakatai, da razana, har da ganin ta a wurin ƴan bindiga. Mama ta sanarwa da Gwaggo, in za Gwaggo ta yi ta faɗa a kan ta sha cewa a nemawa rumaisa maganin tsari, amma maman tana yin burus da ita. Danginsu rumaisa kowa da abun da yake kawo wa na gudunmawarsa, sai dai ƴan unguwa basu san me ake ciki ba. Kwanci tashi asarar mai rai, ya rage saura kwanaki goma sha uku, auren rumaisa da adam, yayyen rumaisa da dangin mahaifinta, da na mama sai rawar gani suke yi. Gefe ga masu kawo gudunmawar magunguna na gyaran jiki, da gyara aure, mama ta kasa bawa rumaisa, gani take kamar idan aka bata za a cutar da ita, shekarunta basu kai ba, ba ta da tabbacin ma shi kansa mijin ya saurareta. Sai dai mussaman babar hauwwaliya, ta biya mai gyaran jiki, take zuwa gida yi wa rumaisa gyaran jiki, shi ma ta din ga tamɓele kenan tana guje-guje tana ihu, wai ana azabtar da ita, za'a rina mata fata da azaba. Tun zuwa ɗayan nan da takawa yayi zance, bai kuma zuwa ba sai yau, da dole ce ta kawo shi. Yau tun da ya zo, ba a kula shi ba, balle a gaishe shi, wasanninta ma kawai take yi, har da duwatsu. Ya lura ta yi wani kyau na musamman, fatarta ta yi haske, sai zuba ƙamshi take yi. Yayi gyaran murya ya ce "Haryanzu kina zuwa makaranta ne?". "An yi hutu" Ya numfasa, ya ɗauko wayarsa a aljihunsa ya kira iman, ya jira ta ɗaga sannan ya bawa rumaisa, suka gaisa iman na ta tsokanar ta amarya. "Yauwwa anty rumaisa, lefenki ya kammala haɗuwa, dama size ɗin undeas ɗinki zaki faɗa da za a saka" ta kalli takawa taga yana danna ɗaya wayar ta sa sannan ta yi ƙasa da muryarta ce "Ni bana saka underwear, sai gajeren wando" Iman ta ce "Ok, size ɗin phant fa?" Ruma ta buɗe baki, tana kallon fuskar Adam ko yana jin me iman ke tambayarta. "Wannan kuma mama za'a tambaya" "Brezia fa, ko ita ma a tambayeta?" Rumaisa ta ce "Amma dai anty iman kawai dai tsokanata ki ke yi, idan aka saka wannan ai sai dai yayanki ya saka, tun da da nace a bani sabir, cewa yayi bani da abun bashi nasa ma yafi nawa girma, sai dai idan shi zai saka, ni bana saka komai, bani da su" Dariya Iman ta yi ta ce "Allah ya baki haƙiri. Akwai kaya da zai baki, kalar da ki ka zaɓa ne, wanda zaki rabawa ƙawayenki, zamu saka ranar bridal shower, sai kuma na dinner, kayan lefenki na ji su mama sun yi magana sun ce kawai a kai miki gidanki, idan kin tare sai ki gani, kayan da zaki saka ma duk ya taho da su" Rumaisa ta ce "To, sabir fa wanne zai saka?" Iman ta yi murmushi ta ce "Iri ɗaya da babansa" Rumaisa ta yi murmushi ta ce "To ki gaishe mini da ammi". Ta miƙa masa wayar, ba tare da ta kalleshi ba. Mayafin kanta ne yake zamewa, gashinta baƙi ƙirin, har gaban goshinta, tamkar zai haɗe da yalwatacciyar baƙar jagirarta. "Me ki ke cewa na ce nawa yafi naki?" "Au kasa kunne ka yi ka ke jin me ake faɗa? To me ka ji iman ta tambayeni?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido. "Size ɗin brezia take tambayarki, kuma tun a gida na gaya musu, baki da abun sakawa" Buɗe baki ta yi tana kallonsa da mamaki, shi ko nauyin faɗar brezia ba ya ji a bakinsa, a haka sai ka rantse da Allah ba ya magana. Ya ce "Ba kin ce mata, na ce nawa yafi naki ba, ai ba ƙarya na yi ba, ko baki gani ba" 'Wallahi na kusa daina rufa maka asiri, zan fara faɗar maganganun da kake gaya mini na batsa, bana so ni ba ƴar iska ba ce ba" Guntun tsaki ya ja, ya tashi tsaye ya ce "Mu je ki karɓi kayan nan, ina da wurin zuwa" tashi ta yi ta bishi tana haɗe rai, saboda kar ya kuma kawo mata maganar banza. Ko da suka fito ƙofar gidan, ɗan ƙare mata kallo ya yi, mayafi ne a jikinta yau, ɗan ƙarami, siririya ce mai matsakaicin tsayi, ƙirjin nan fayau babu komai, sai dai daga ƙasa ƙugunta ya buɗa, ko ta zama cikakkiyar budurwa, zata kasance a cikin mata masu diri daga ƙasa. "I just wish you are that big enough, a kece raini tsakani na da ke, in ga ƙarshen fitsara, unfortunately look at you, ƙwaila mara jin magana, ban san ma iya adadin lokacin da za a ɗauka kan ki zama mace ba, baki da magana sai ce mini ɗan iska, ba zan manta ranar da ki ka gaya mini haka ba, amma zaki ga ɗan iska ganin idon ki, zo ki kwashi kayan nan zan tafi " What's app only please. Ayshercool 08081012143 *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Sororo ta yi tana kallon sa, sam ba ta fuskanci in da ya dosa ba, abun da ta iya ganewa kawai shine ƙwaila, wato wadda ba ta da nono. "Am talking to you kin tsaya kina kallona" Cikin tsuke fuska ta ƙarasa gaban booth ɗin, manyan ledoji ne a ciki. Ya dubeta ya ce "Gasu nan, iman ta ce yadin wanda zaki rabawa ƙawayenki, sauran bayanin ban riƙe ba, idan kun yi waya ta yi miki. Akwai invitations da wurin da za ayi events, sai kayan sawarki". Maimakon ta ce Ta gode, sai cewa ta yi "Ni ta yaya zan iya ɗaukar wannan kayan masu nauyi, kuma fa an sai mini kaya a gida, nifa kar ka zo daga baya ka din ga yi mini gori, idan ka san ba da zuciya ɗaya ka bani ba, ka riƙe abunka, ƙawayena za su saka abun da suke da shi" ɗagowa yayi ya kalli rumaisa, sai dai maimakon ya ji haushin abun da ta faɗa, sai ma ya yaba da yadda take taka tsan-tsan, ita dai kar ayi mata gori, tana da gudun abun wani. Amma a zahiri, sauke mata kayan ya yi a ƙasa, ya rufe booth ɗin motarsa, ya saka hannu ya ɗauko wata babbar ledar a motarsa, ɗora mata a kan kayanta ya ce "Idan da wani abun ki saka Aliyu ya kirani" daga haka ya shiga mota ya ja ya tafi. Gida ta shige ta ce wa su Huzaifa su je waje su kwaso kaya, idan ba haka ba a sace. Sun zata da wasa take yi, ashe da gaske take. Gwaggo tuni ta zo kano, ita da lawisa, da zaliha, aka baje kayan da takawa ya kawo wa rumaisa. Iya leshin da zata saka na dinner, ka san ba ƙarami bane ba, an ɗinka shi da jakarsa da takalmi da komai, an haɗo mata kayan fitar biki, ga kuma invitations, rumaisa ta yi ta kallon invitation ɗin tana mamakin wai sunanta ne a jiki. Ledar nan da ya bata kuwa, babbar envelope ce a ciki wata dubu ɗari biyar ɗin ce a ciki. Mama ta kalleta ta ce "Rumaisa tambayarsa ki ka yi?" "Haba mama, to ni ce masa ma na yi, idan ya san zai yi mini gori wataran, ya ɗauki kayansa, ni za a sai mini a gida". Gwaggo ta yi salati ta ce "Shi mijin naki ki ka gayawa hakan?" Rumaisa ta ce "Mijina kuma taɓ". Usman ya ce "Ke fa banza ce, yanzu ya kawo miki wannan uban kayan ki kasa yi masa godiya, saboda ke dai baki da alƙibla?" Ta yi shiru tana muzurai. "Bari Aliyu ya dawo, ya kira shi a waya, ki yi masa godiya tun da ba ke ki ka nema masa kuɗin ba" Haɗe rai ta yi, saboda zuwa yanzu yaya usy yana takura mata a kan mutumin fiye da kima. Can kuma ta hau murna, tana lissafin ƙawayenta da zata bawa ankon da zasu ɗinka, ga uban kuɗi kuma tana gani. Mama dai shiru tayi tana bin kayan da kuɗin da kallo, ita ba tarin kayan alatun ba, fatan ta Allah ya sa rumaisa ta shiga a sa'a ya sanya mata albarka. *** Bin invitations ɗin yake da kallo, yana tuna lokacin da yayi auren fari, tun saura wata guda biki ya fara ɗoki, yana murna yana rabon invitation card, a wannan karon da shi da amaryar bai san wanda ya fi wani anti serious ba. Rumaisa Mahmud, ya din ga kallon sunan nata, da kuma nasa Adam Sharif Galadima. Bashir ne yayi sallama a falon, Adam ya amsa masa, ya ƙarasa suka gaisa sannan ya zauna ya kalli Adam ya ce "An kammala komai na gidan, zasu iya kai kaya a kowane lokaci". Adam ya ce "Masha Allah, that's good ina godiya sosai, ina sidi?" "Na ajiye shi, shima ya sha aiki ya gaji" "Na gode sosai bashir, zan shiga na je na gani, daga nan sai na ɗauki ko mutum biyu a yayyenta, mu je su ga gidan". Bashir ya ce "Hakan yayi, Allah ya sanya albarka, amma haryanzu fa ba ka fara rabon invitation ba, ko a social media ba a saka ba". Adam ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Wallahi Bashir sam bana ɗokin auren nan, bana son duniya ma ta san zan yi shi, ni da za a shafa fatiha ma ba wannan events ɗin da na so hakan, rainon yarinya kawai za a kawo mini" Bashir ya yi murmushi ya ce "Ka yi haƙuri, ammi ba zata zaɓa maka abun da zai cutar da kai ba. Sannan ba zai yiwu ka ɓoyewa duniya zaka yi aure ba, idan ta fasu aka sani, za a iya yi maka wani sharrin" "Haka ne, haka zalika idan aka ga Yarinyar da zan aura, shi ma ba zan tsira ba, mussaman idan aka san ita ta zo da ɗa na daga hannun ƴan bindiga". Bashir ya ce "Mafita ɗaya ce, duk yadda zaka yi ka ɓoye wa duniya cewar ba son auren ka ke yi ba, dole a ga farinciki da ɗoki a fuskarka". Adam ya yi murmushi ya ce "Yadda za a ji daɗin cewa, saboda na auri yarinya ƙarama na kashe matata ko?" "Ai dama dole sai an faɗi wani abu, amma yafi ace ka yi amfani da ƙaramar yarinya ka ɓoye wa duniya laifinka, na kai kashe matarka, ka turasasata ta aureka, dan kar a cigaba da surutu da zargin ya za ayi yarinya ƙarama kamarta ta kuɓuta da jariri a hannun 'yan bindiga" Adam ya yi ajiyar zuciya, ya ɗan murza goshinsa ya ce "Duniya gidan rikici, Allah ya iya mana". "Amin ya Allah" Wayar takawa ce ta fara ringing, ya ɗauka ya duba ya ga sunan Aliyu. Ya ɗaga ya saka a kunnensa tare da yin sallama, Aliyu ya amsa ya ce "Barka da wannan lokaci, ya hidima?". "Alhamdilillah, ya taku hidimar?" "Mun gode Allah, dama rumaisa ce za ta yi magana da kai" Adam ya ce "Ok, ba ta". Rumaisa ta karɓi wayar, Usman ya sakata a gaba ya tsareta da ido. Ta karɓi wayar ta saka a kunneta, amma ta tsaya tana kallon Usman, ta kasa magana. Ya daki ƙafarta ya ce "Ba zaki gaishe shi ba?" "Ina wuni?" Maimakon ya amsa ya ce "Ya aka yi?" "Gaisheka fa na yi" ta yi maganar a ƙule. "Ba a yi wa basarake irin wannan gaisuwar, babu ladabi a gaisuwarki, dan haka ko sau nawa zaki yi ba zan amsa ba, riƙe kayarki, ina jin ki" Rumaisa ji ta yi kamar ta yi zagi, meye aibun gaisuwar ta, idan ba neman bala'i ba. "Idan kin shirya yin magana, sai ki sake kirana". "Su yaya ne suka ce dole sai na kiraka na yi maka godiya, na gode, kuma wai kuɗin da ka bani sun yi yawa, sannan......" "Lokacin da ki ka san abu yakamata, ba sai wani ya saka ki ba, sai ki neme ni, yayyenki na ƙoƙari wurin baki tarbiyya, Allah ya biya su, kuɗi kuma ki zubar" ya kashe wayarsa. Dungurar da wayar ta yi a ƙufule, ta ce "Yaya usy kalli abun da ka janyo mini" Dungure mata kai yayi ya ce "Ki ka jawa kanki dai, ke a rayuwar duniya baki iya siyasa ba? Ji yadda ki ke gantsara masa magana, kamar kashi ba tausasa lafazi, ba ɗan karya murya, wai ke ma namiji ce irinmu ne? to ko mu muna kashe murya, ranar da na kama malam habu yana waya, kamar ma nutse dan kunya, amma ke kina ta wani shirme. Ke, tashi mu je ɗaki, na yi miki bayanin me auren ya ƙunsa, in fayyace miki komai in gaya miki, na ga mama ba ta da niyyar gaya miki, daga ita har su gwaggon. Aliyu ya ce "Kai fa wasu lokutan baka da kamun kai, uban me zaka gaya mata?". "Komai ma gaya mata zan yi, yo haka za ta je ta zauna masa a gida kamar gardi, idan ka ga tana tausa murya to wani abun take nema, tashi mu je na fayyace biri har wutsiya". Aliyu da dariya ta ƙwace masa ya ce "Mama, wallahi usman ya zama abun da ya zama, zai juyawa yarinya tunani, saboda bashi da kamun kai". Usman ya ce "Eh, bani da kamun kan, ni ina ma ni za ayi wa auren nan, wai muna zaune ƴar da aka haifa a gabanmu za ta rigamu girma Allahu Akbar wata shekarar sai ta fara ƴa ƴa kuma". Aliyu ya ce "Wani irin ta fara ƴaƴa wata shekarar, kamar wata bishiyar lemo, wannan yarinyar ko nan da shekara biyar albarka" Wani irin kallo Usman ya yi masa ya ce "Haba, a banza za ku kaita ya din ga bata abinci, yana biya mata kuɗin makaranta ko? You don't get sense. Ko kaza dan a cinyeta ake killace ta a  sai mata dusa, kar ka yaudari kan ka". Aliyu ya ce "kai haba, she's too young for it, and the man is very decent and calm, bana tunanin haka". Usman ya yi dariya ya ce "Uban calm da decent ɗin, that thing don't get sense, don't fool yourself, if not ku fasa aurar da ita, hauka ake mutum zai kashe kuɗi ya auri ƴa ya sakata a gaba yana kallonta, Allah ya sa jaririya ce" Aliyu ya yi tsaki ya ce "Zaka ɓata mini rai " Rumaisa da ba gane kan hirar take ba, ta din ga bin su da kallo, Usman ya ce  "To Algume, sai kallon bakinmu ki ke, ƙila kin san komai, ki ka yi wani kasaƙe da kai". Aliyu ya ce "A hakan ta san komai? Tana wannan gidadancin". Usman ya ce "Kuma fa haka ne, to jeki na fasa gaya miki komai, duniya zata gaya miki, Allah ya shiryeki". "Nuraini, Allah ya baka abun yi na aurara da kai, ina ga daga rumaisa kuma sai kai, tun baka wuce in da nake tunani ba" a guje Usman ya faɗa ɗakinsu, dan sam bai san mama ta ji hirarsu ba. *** Jabir ya din ga juya invitation ɗin, sannan ya kalli Adam ya ce " da gaske Adam saura kwanaki a ɗaura maka aure, amma ban sani ba?" "Am sorry, abun ne ya zo cikin gahgawar gaske fiye da yadda na yi zato, sai haƙuri". Jabir ya sake kallon invitation ɗin, sannan ya ce "To ita kuma wacece, a ina take? Kamar na san sunan nan". Adam ya ce "Zaka ganta very soon". "Da jamil ya gaya mini maganar auren nan, na zaci da wasa yake yi, ashe da gaske ne, Allah sarki samha ina tausayin yarinyar nan sosai". Adam ya ce "Please, don't raise that issue here, ku daina ganin laifina, ƙaddara ce ta zo a haka". Jabir ya ce "Na yadda, ban ce wani abu ba, kawai dai ina jin tausayinta ne, sai dai na yi mamakin yadda har ka nemi aure, har ka samu ban sani ba, yaushe muka fara haka da kai". "Jabir, this is an arranged marriage, ku yi mini uzuri". Jabir ya ce "Arranged marriage, to Allah ya sanya alkhairi ya sa za ayi da mu". "Amin, addu'arku nake buƙata dama, yanzu ka tashi mu je gidan mai girma turaki, zan kai masa nasa katin, da zai bawa mutanensa, da na jamil da gidan gaba ɗaya". Jabir ya ce "Ok, ba damuwa bari mu yi salla tukuna" Bayan sun idar da salla, suka tafi gidan turaki, kai tsaye sashinsa suka shiga, bayan sun tarar da babu kowa a falon. Yayi murna sosai yayi addu'a da fatan alkhairi, sannan ya yi wa adam nasiha sosai mai shiga jiki. Sai dai kamar haɗin baki suka tarar da mama da Samha, har ma da zainab a falo. Samha jikinta har tsuma yake da ta ga Adam, ga soyayya ga kuma kishi, ya gaida mama ta amsa masa sama-sama, ta saki jiki ta amsa gaisuwar Jabir. Su Samha suka gaishe shi ya amsa, ya ajiye wa mama katuna, ya ce "Gashi nan, ammi ce ta ce in kawo miki, na taron wunin da za ta yi, na bawa mai girma turaki nasa". Da ƙarfi Samha ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Adam wai dama da gaske ne, ta tabatta aure zaka yi?" Ya ɗaga kai ya kalli Samha da tsoro da kishi ya bayyana a fuskarta, ya jinjina mata kai a hankali cikin tausayawa. "Shikenan, bakomai na gode " ta tashi ta bar falon. Jikin Adam ya yi sanyi, mama kawa jan tsaki ta yi ita ma, Zainab kuwa cewa ta yi Allah ya sanya alkhairi. Ɓangaren ammi ma, da ta bawa mummy katin gayyata, masifa mummyn ta din ga yi, wai har ace adam zai yi aure, amma a kasa sakata a cikin lamarin bikin, sai dai ta zo a ƴan gayya, saboda ba a mayar da ita a bakin komai ba. A gidansu rumaisa ma, shirye shirye sun yi nisa. Mai sunan baba ya buga wani invitation ɗin na ɗaurin aure, aka rubuta sunan Adam sharif, ba tare da sanya cikakken sunan Adam ba. Ba ƙaramin mamaki ƴan unguwar su rumaisa suka yi ba, jin za ayi mata aure, wasu suka din ga surutu suna cewa sai ka ce a ƙauye, wasu kuma suka ce ta tabbata rumaisa ta yi cikin shege ne, ake son a liƙawa wani, kuma aka kasa gane wanene mijin, sai dai hatta wurin da aka rubuta za ayi bukukuwan a wurin ba ƙananan wuri ba ne, nan ma aka yi ta surutun ina suka samu kuɗin kama wannan wurare. Zaman Gwaggo a gidan, ta din ga yi wa rumaisa faɗa, tare da nasiha a kan aure, da yadda za ta kula da miji, sai dai sam rumaisan ba ganewa take yi ba, yadda aka sakata a gaba ana sake koya mata girki ya fi komai ci mata rai, a ganinta ana hanata hutawa, girkin nan da karambani ta iya shi, dan tun shekara tara take gwadawa, tun mama tana hanata har ta haƙura ta rabu da ita. Samha ta yi kuka kamar zata yi hauka, gaba ɗaya ji take komai ya fita daga ranta, ko abincin kirki ba ta iya ci, sabuwar soyayyar adam ta dawo mata sabuwa fil, sai dai ta yi alwashin yadda ta zubar da hawayenta a kan sa karo na biyu, daga shi har matar ta sa sai sun ɗanɗana kuɗarsu. Fauziyya ta din ga zigata a kan ta san duk yadda za ta yi, ta cuzgunawa matar da adam zai aura, har da ba ta tabbacin cewa, ta ji an ce auren haɗi  ne ba son ta yake yi ba. Ana gobe za a yi wa rumaisa jeren kaya, Adam ya ɗauki Aliyu da Abdallah, zuwa gidan rumaisa, dan su gani daga nan ya basu mukulli. Sai dai da suka je, Aliyu ya raina kayan da suka saya, da suna ta murna sun yi wa rumaisa kaya masu kyau da yawa, sai dai gidan babba ne sosai. Sama da ƙasa ne, ƙasan akwai babban falo, da ɗakuna biyu, da kitchen da store, saman bene kuma falo biyu, bedroom uku, da kitchen da dining, kowane ɗaki da toilet. Gidan ya tsaru yayi kyau, dan an kashe kuɗi wurin yin sa sosai. Aliyu suka yi ta santin gida, suna yi wa Adam godiya. Sai dai tun da suka koma gida suka sanar da mama, gidan yafi ƙarfin abun da za a kai, jikinta yayi sanyi, dan ba dan kar ta nuna halin ƙaranta ba, cewa za ta yi idan da ƙarami a saka rumaisa a ciki. Kaf ƴan unguwa ba wanda mama ta ce su je yi wa rumaisa jere, ƴan uwanta da ƴan uwan mahaifinsu rumaisa, sai yayyenta ne suke je suka jera mata abun da ya samu a saman benen. Gado biyu aka yi mata, dangin babansa suka yi mata ƴan waje guda ɗaya, yayyenta suka yi mata ƴan gida, masu matuƙar kyau. Kitchen ɗin ta ma babu laifi, a dai ƴar talaka, iyayen rumaisa sun taka rawar gani sosai da sosai, ga kujerunta da labulaye, ga dininga komai dai-dai gwargwado. Ƴan uwa suka dawo, suka din ga santin gida, suna yi wa mama barka da arziki, rumaisa ta je gidan hutu. Da daddare Adam ya je gida da shi da su ammi, suka ga jeren da aka yi, ammi ta jinjinawa ƙoƙarin iyayen rumaisa, ba ita ba shi kansa adam, abun ya bashi mamaki, aka jere mata akwatunanta goma sha biyar a bedroom. Washegari Adam ya saka aka kawo abubuwan da babu, wanda basu ƙarasa ba. Rumaisa ba ta yadda aurenta za ayi ba sai da satin biki ya kama, dama Aliyu sun shirya football match, a nan cikin unguwa. Tun da rumaisa ta tabattar da idan aka yi auren barin gidan za ta yi, ta fara koke-koke tana fasa. Ranar da za ayi bridal shower, daga gidan su adam, aka aiko da mota, aka ɗauki rumaisa zuwa gidan kwalliya, ita da ƙawayenta, babu ko sisinsu, aka yi musu kwalliya aka wuce da ita wurin biki. Su Iman tuni suna can, sun sha kwalliya iman kamar balarabiya, da ita da wasu daga cikin famylinsu, da su ƙawayenta. Rumaisa gaba ɗaya ta kasa sakin jikinta, mussaman yadda ake kallonta, wasu suna jinjina wannan ƴar yarinyar takawa zai aura?. Su hauwwaliya kuwa, sai iyayi ake da rawar kai, su gasu ƙawayen amarya. Babu zato babu tsammani, sai ga ƴan mazan mama sun dira a wurin, da shigar ƙananan kaya, rigunansu mai kalar kayan da rumaisa ta saka maroon. Washe baki ta yi, ta nufesu da gudu tana dariya, suka rungumeta suna juyata. Yasir ya ce "Taɓ, kin ga fuskarki kamar sarauniyar aljanu?" Ta ɗan kwaɓe fuska ta ce "Na sani nima, fuskata sai ƙaiƙayi take yi, kuma an ce idan na sosa zan ɓata kwalliyar" Abdallah ya ce "Ai abun ka da ba a saba bane ba, kuma fa kin yi kyau" Mamaki ne ya kama ƴan wurin, me ya kawo maza wurin bridal shower, har da anko?. Iman ce ya fara ganinsa ya shigo wurin, sai da hankalin da yawa daga cikin 'yan matan ya koma wurinsa, ciki har da iman, da take ta ƙara gyara cake ɗin da yake kan table. Rumaisa ba ta taɓa tunanin mai sunan baba zai zo ba, zuwansa ya sanya suka cika su bakwai samarin gidan su kowa ya zo. Gaban table ɗin ya ƙarasa, kusa da iman ya ɗauki ƴar ƙaramar wuƙar yanka cake ɗin, ya yanko cake, ya kalli rumaisa ya yi mata alama da ta buɗe bakinta, ta buɗe kaɗan ya saka mata a baki sannan ya ce "Happy marriage life ƙanwar maza, Allah ya sanya albarka" tafi aka hau yi ana shewa, rumaisa ta kasa tauna cake ɗin idonta ya cika da ƙwalla. Ya girgiza mata kai, ya nuna mata mai hoto, ya ce "Smile, amarya ba ta haɗe rai ranar aurenta" Kasancewar yayyenta a wurin ne, ya sanya ta saki jikinta, suka din ga ƙoƙarin yin abun da zai kwantar mata da hankali. Sai dai mai sunan baba, ya rasa dalilin da ya sanya shi, son satar kallon iman, gaba ɗaya kamar ba bahaushiya ba, ta yi kyau sosai da sosai, a ɓangaren iman kuma, zuwansa wurin ya sanya duk ta takura, da ta motsa sai su haɗa ido, gabanta ya faɗi. Ƙarshe dai da su aka gama partyn, suka ɗauki ƙanwarsu suka yi gida. Mai sunan baba ne ya rage, zai tafi ya fito harabar wurin, in da zasu tafi shi da abokinsa, kasancewar abokin nasa yana da abun hawa. Iman ya gani a tsaye, wani matashin sauryi ya tsareta, yana ta zuba mata surutu ita kuma da alama akwai abun da take jira. Haka kurum ya tsinci kansa da tsareta da ido, wanda hakan ya sanya ta ji kamar ta fasa ihu, jikinta har rawa yake, gani take kamar ta aikata wani zunubi da bai kamata ba. "Me ki ke jira baki tafi gida ba?" A tsorace ta ce "Motocin ne suka cika, shi ne na ce su tafi zan taho". "Wuce mu tafi" yayi maganar cikin command. Babu musu ta wuce, ya sakata a gaba, zuwa motar da zasu tafi. Ayshercool 08081012143 What's app only please *Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* Bayan motar ta shiga suka tafi, sai da suka kai ta gida sannan suka wuce. Ko da mai sunan baba ya koma gida, mama ya tarar a ɗaki tana rungume da rumaisa, tana ta rarrashin ta, su Aliyu duk sun zauna sun yi jugum suna kallonsu. Ƴan uwa sai bawa rumaisa haƙuri suke yi. "Meye haka?" Ya faɗa a kausashe. Gwaggo ta ce "Ka san lamarin aure, dole za ta ji babu daɗi za ta yi kewar mahaifiyarta, kuka take yi" "Saboda shirme, ku kuma ku ka zo ku ka sakasu a gaba babu mai tsawatar mata? Tana fama da tension da hayaniya na biki, ke kuma kin zo kin sakata a gaba kina kuka? Da wanne za ta ji? Tashi ki cire wannan kayan, ki yi wanka ki nemi wurin kwanciya" Mama kasa cewa komai ta yi, rumaisa ta tashi tana kuka, ta shiga uwar ɗakan mama. Su usman daurewa kawai suke yi, dan gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi da suka ga tana kuka, ba su ba shi kansa gogan jikinsa a sanyaye yake. *** Samha har ta gaji da kuka, kowa da irin shawarar da yake bata, ta banza da ta arziki, tana kwance a kan gadonta ta yi rigingine, tana tunanin yadda za ta aiwatar da malamin da suke zuwa wurinsa ya bata, dan ta yi alwashin raba Adam da kowane irin farin ciki, in dai abun da ya shafi aure ne. Ba ta san a karo na nawa wayarta ta yi ringing ba, cika mata kunnuwan da wayar ta yi ne ya sanya ta ɗaga, ta saka a kunnenta ba tare da duba ko waye ba. "Babbar yarinya, ashe abun da ya faru kenan, yayanki zai angwance da wata ba ke ba?" "Murna ka kira ni ka yi mini, ko kuma ci mini mutunci?" "Babu ɗaya, jaje kawai na kira na yi miki, tare da mamakin abun da zai saka Adam kawar da kai a kan cikakkiyar mace mai aji kamar ki Samha, ban da so makaho ne, tuntuni nake jaddada miki, ki rufe ido a kan wannan son, mu yi duk mai yiwuwa mu ga bayan adam, amma ki ka dage a kan cewar ke ba za a cutar da shi ba, ai kina son sa, yanzu son wace ranar yayi miki?" A hasale Samha ta ce 'Look wakili, i don't have time, for all this now allow to rest" Khalifa ya ce "Ba ki da wani hutu samha, lokaci ne kuma zai cigaba da ƙure miki, kan ki farga yayi miki nisan da ko tafin ƙafarsa ba zaki hango ba, let's join hands together" Kashe wayar ta yi ta ajiye, tare da faɗin "Shashasha kawai". Iman ita kaɗai a ɗakinta, ta yi wanka ta sauya kaya, sai dai ta kasa manta fuskar mai sunan baba, yau yayi kyau sosai, sai dai yanayin muzuransa ko tunawa ta yi sai ta ji gabanta ya faɗi, dan har suka kawota gida, ban da kwatance, ko abokin nasa ba ta ji yana yi wa magana, balle ita ya kulata. Ɓangaren mai sunan baba ma, mamaki yake yi, yadda tsoronsa ke bayyana sosai a kan fuskar iman, ya san yana da kwarjini sosai, sai dai ita ya lura ba kwarjini kawai yake yi mata ba, tsoronsa take ji, tsoro kuma ba na wasa ba. Taɓe baki yayi ya cigaba da sabgoginsa. Washegari ya kama ranar da za ayi dinner, rumaisa ta tashi da ciwon kai, saboda kukan da ta sha jiya, idanunta duk sun yi ja. Ta wuni a uwar ɗakan mama, tun ƙarfe uku yayyenta suka tafi fara nasu shirin, a ƙarfe ukun kuma, aka aiko da motar kaita wurin kwalliya. Maƙwabta na ta mamakin wani hamshaƙin ne haka zai auri rumaisa, sai abu ake yi kamar wata babbar budurwa. A wurin kwalliyar ma, kuka take ta yi, Habiba da su hauwwaliya suna ta rarrashin ta, amma ta ƙi tsayawa. Mai kwalliyar ƙawar nusaiba ce, dan haka ta kirata ta sanar da ita halin da ake ciki. Nusaiba ta gaya wa takawa, ya din ga mitar shi ba ya son a tsaya wannan shafe-shafen aje a ajiye mutane su na jira. Ƙarshe dai da kansa ya tafi wurin kwalliyar da shi da bashir. Ya je ya tarar duk an yi wa ƙawayenta kwalliyar ban da ita. Ya kalleta ya ce "Zaki tsaya ayi kwalliyar ne, ko kuma mu tafi a haka?". "Ni bana son auren nan na fasa, mama ta ce wai barin gidanmu zan yi, ni na fasa" ta yi maganar cikin kuka. Bashir ya ce "Haba rumaisa, an gama tara mutane, ki bari idan aka gama sai ayi duk maganar da za ayi". Adam dai ya ƙule ƙarshe, Bashir ne yayi ta bata haƙuri, sannan ta tsaya aka yi. Mai kwalliyar ce ta fito da rumaisa reception, ta yi kyau kamar ba ita ba, kayanta iri ɗaya da na Adam. Hauwwaliya har da tsalle, tana koɗa rumaisa. Bashir ne ya din ga yi musu hotuna, sai dai daga ita har adam babu wanda yake walwala. A harabar wurin bikin, suka tarar da su Aliyu, sun haɗe cikin shadda iri ɗaya, hatta huluna da agogo iri ɗaya suka saka, motar na tsayawa, ta buɗe ta fice ta nufi wurin su Usman. Abdallah ya din ga ɗaukar rumaisa a hoto. Usman ya ce "Allah sarki lantarkin gidanmu, zaki tafi ki barmu a duhu, zaki barmu da ɗan hasken da ba zai ishemu ba" Rau-rau ta yi da ido, za ta yi kuka, ya girgiza mata kai ya ce "Yau ranar murna ce, da yi wa Allah godiya, ki bari mu je mu yi rawa mu ci kaji, idan an koma gidan kya yi kukan, dan kukanki ba zai hanani cin abinci ba na gaya miki" Bisa ga al'ada, ƙawayen amarya da ƴan uwanta ne ke shigo da ita, sai dai wannan amaryar, yayyenta maza ne suka shigo da ita, ga ta ƴar mitsitsiya a gaban angon nata, kamar ƴa da uba. Abun ba ƙaramin ƙayatar da mutane yayi ba, sai dai fa wasu surutu suka fara da raina wayon takawa, na auren ƴar mitsitsiyar yarinya. Taken gidan sarauta aka saka wa shigowar ta su, ga maroƙa da suka biyo su suna yi musu busa, tare da kirari. Rumaisa ta kalli yadda hall ɗin ya cika, dama tun daga haraba motoci ba a magana, manyan mata masu shiga ta alfarma, gaba ɗaya taga ido a kanta, ga takalmi mai tsini, take ta ji jiri na ɗibarta. Adam ne ya fuskanci haka, dan haka ya riƙe hannunta, sai da ta ɗan waro ido, ta sake kallon mutane ta ga kowa sai ƙoƙarin ɗaukarsu a hoto yake yi, ta sake sunkuyar da kanta a cikin mayafi, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga na Adam amma ya riƙeta sosai. Har kan high table suka raka rumaisa, suka zaunar da ita, kowa ya gansu sai ya ce Masha Allah, tare da jinjina rumaisa a matsayin ƙanwar zaratan maza har bakwai. Iman ce ta fito stage, ta karɓi mic, tare da gabatar da addu'a, da fatan alkhairi ga amarya da ango. Jabir ba ƙaramin mamaki ya yi ba, ganin rumaisa ita ce matar da takawa zai aura, ya din ga tunanin yaya aka yi hakan ta kasance bai sani ba?. Me Adam zai yi da wannan yarinyar ƴar talakawa mara kunya. Sai da aka yi kamu, kan a fara gabatar da dinner, duk wani abu da ƙawayen amarya za su yi, yayyen rumaisa ne suka yi shi. Dangin su Adam sun so su farfaɗi maganganu, da yin rashin mutunci a wurin, mussaman da kusan kowa ya san Samha tana son shi bai aureta ba, amma kasancewar su Abubakar da mai sunan bab a wurin, suka cika wa mutane ido, kowa ya riƙe gulmarsa. Jabir ya rasa nutsuwarsa, ga tunanin auren adam,ga iman ta ɗau ado, sai shiga take yi tana fita, yayin da ita kuma hankalinta ke kan mai sunan baba, har fata take Allah ya sa ba kallonsa ake yi ba, dan dangin nan akwai tarin ƴan mata. 'To sai me ina ruwanki?' wata zuciyar ta tambayeta. Aliyu habiba ya saka a gaba, yana yi wa dariya ƙawar amarya an sha ɗauri, ƴar baƙa kyakykyawa. Iman ta ƙarasa ta cewa Usman "Yaya ban san sunanka ba, na san dai duk sunanku yaya, kuma duk kamarku ɗaya, koda yake na san yaya Aliyu" Usman ya ce "Usman nake, ma'abocin haske, ƴar balarabiya ya aka yi ne?". Ta yi murmushi ta ce "Dama ban sani ba ko kun zo da abokanku, ga in da aka yi muku reserving can, za a fara dinner ne, gara mu fita kunyar kowa". Usman ya ce "Abokai kai, kin san mu yawa ne da mu, bari in tattaro su wuri ɗaya, dama zan zo mu zauna in baku amanar ƙamwarmu, dan Allah a kula mana da ita, ayi haƙuri da ita, idan aka taɓata zuciyar maza bakwai ce za ta girgiza " Iman ta yi dariya ta ce "Wane mu mu yi mata ba dai-dai ba ma, ai sai mu sha duka" tun da suke zuwa gidansu rumaisa, maganar kirki ba ta taɓa haɗata da yayyen rumaisa ba, sai yau da Usman yake yi mata halin na sa. Umar yana jin su, kasancewar yana kusa da su. Jabir ya ƙaraso in da Iman ke tsaye a wurin usman ya ce "Sweetheart, ina son magana da ke fa, ina aka yi wa abokan aikinsa reserving, suna daf da ƙarasowa, na ga ke ki ke ta arranging mutane". "Uncle J, ina wani aikin ne, ga uncle bashir nan, da shi muka zo wurin nan ɗazu, ya san yadda aka tsara komai fa" ta yi maganar cikin muryarta ta shagwaɓa. "Yes na ji, zo mu je dai, ko na ɗagaki yanzu na yi waje da ke, idan ya so gobe a ɗaura auren da namu" Usman dai murmushi kawai yake, iman kuwa ba a son ranta ba, ta bi bayan jabir. Suna yin gaba ya hau ta da faɗan, dan me za ta je wurin maza ta tsaya. Ba ta iya bashi amsa ba, ta tsaya tana kallon sa kamar za ta fashe da kuka, babu tsammani mai sunan baba ya gifta ta bayansu yana waya, ta ɗaga kai suka yi ido huɗu, da sauri ta koma cikin wurin dinner. Kwaɓe fuska rumaisa take yi, tana nema ta yi kuka, Adam ya ɗan sunkuyar da kansa ya ce "Meye kuma?". "Ni na gaji, sai kallona ake yi, kamar wata mara gaskiya, ni bana son kallo, kuma ma yunwa nake ji, ina jin bacci ma kaina ciwo yake yi, na gaji da hayaniyar nan" ta ƙarasa maganar bilhaƙƙi za ta yi kuka. "Yanzu a gaban mutanen zaki yi kuka ranar aurenki, salon ace auren dole za ayi miki, ko ki janyo mini zagi ko?" Tura baki ta yi ta ce "Ba auren dolen bane, ni na ce na fasa, amma aka ƙi fasawa, wayyo mama ni na gaji" A ransa ya ce na shiga uku, wannan Yarinyar tana neman ta jaza mini abun faɗa. Mc kuwa koɗasu kawai yake yi, saboda shagwaɓa rumaisa take yi, da ya sake fito da yarintarta, ba shiri adam ya din ga yaƙe, dan kar a fahimci wani abu. Abdallah ya hango, yayi masa alama da ya je, adam ya ce masa ya samo abinci ya zo ya bawa rumaisa, kar ta yi masa kuka. Sai da Abdallah ya dungure mata kai, ya ce "Wace amaryar ki ka ga tana cin abinci a wurin bikinta?" "Ni yunwa nake ji, ga su hauwwaliya can suna cin abinci, bari na je mu ci tare" "Dalla zauna na je na samo miki, wai yunwa ranar aurenki dan abun kunya" ya sauka yana mita, ta bi bayansa da harara. Da ya samo abincin, sai da su Aliyu suka raka shi, suka yi mata rumfa, ba a iya ganinta, Aliyu ya ɗebi abinci a cokali ya kai bakinta, wai ita ba abinci za ta ci ba, naman za ta ci, gani ta yi an bawa kowa abinci ita ba a bata ba. Suka din ga zaginta suna bata naman, shi dai adam jinjina kai kawai yayi, ya yi wa Allah godiya da babu wanda ya san wainar da ake toyawa. An sha hotuna kamar babu gobe, rumaisa ta ɗaga kai ta kalli Iman da ta zauna a kusa da ita, mai sunan baba yana gefenta aka yi musu hoto. Hatta ammi ta je wurin, an yi mata liƙi sosai da sosai, an ci an sha, manyan mata sun yi rawa sun yi liƙi. Yayyen rumaisa ma da abokansu, haka suka din ga yi mata liƙi, wannan ya ja ta nan ayi mata hoto, sai ka rasa waye angon ma a cikinsu. Adam ma basarwa yayi, ya din ga yi mata liƙi, kuɗi ba kaɗan ba, ta din ga kallonsa ta ga ko yana sane, amma yaƙi kallonta kar ta yi wani shirmen. Babban abun da ya fi burgeta, shi ne fareti, da kuma crossing sword ɗin da abokan aikin su Adam suka yi musu. Gajiya kam rumaisa ta yi ta, dan har gyangyaɗi ta fara, da ƙyar take iya buɗe idonta, ga takalmi mai tsinin gaske a ƙafarta. Sai sha ɗaya da rabi na dare aka tashi, rumaisa tana ta sauri ta bi su yaya Abubakar, amma takawa ya sakata a gaba zuwa motar da suka zo. Tana shiga ta zauna ce "Wayyo Allahana, na gaji" Ya kalleta yayi shiru, basu je ko ina ba ta hau bacci, gaba ɗaya ta kife masa a jiki, kai da jin yadda take sauke numfashi ka san ta gaji da yawa. Sidi ya ce "Sir amarya ta gaji da yawa" Adam ya ce "Gashi har ta yi bacci" Sidi ya ce "Allah mai iko, ba zan manta scene ɗin da ku ka yi making, ranar da ku ka fara haɗuwa ba, and she's now your wife" Adam ya ce "Shhhhh, a daina tayar da wannan maganar" "Sorry sir" Adam ya gyara mata kwanciyarta, ya ɗaukar pose ɗin ta, ya buɗe, ga sababbin kuɗi nan a ciki, fal. Ya girgiza kai ya riƙeta a hannun sa. Rumaisa kuwa jin ta take kamar a kan katifarta, har da gyara kwanciya. A ƙofar gida ya tarar da yayyenta, suna jiran su ga ta ina za su ƙaraso, ya sauke glass ɗin motar, gaba ɗaya suka ƙaraso. "Ta yi bacci fa" ya faɗa yana kallon Usman. Usman ya ce "Ai haka take, da yin magariba take bin bango, a bata ta ci ta yi bacci, kamar ƴar kaza". Adam ya ɗagata zaune da niyyar ya tasheta, amma ina baccinta kawai take yi. Mai sunan baba daga in da yake tsaye, yana hango cikin motar, rumaisa ba ta san ma me ake yi ba. Haka nan ya ji wani irin kishi ya taso masa, ƙanwarsa a kwance a jikin wani ƙato. Takawa ya ɗaga kai suka haɗa ido da shi, ya wani cukule fuska. Aliyu ya zura hannunsa, ya ɗauko rumaisa gaba ɗaya, ya nufi gida da ita,, da gayya Adam ya fito daga motar, ya ce "Kai Ali ka yi a hankali, kar ka yi mata rauni fa, a kawo mini nakasashshiyar amarya gobe, ba zan karɓa ba, da na san bacci za ta yi daga nan ai gida zamu wuce kawai" Aliyu ya ce "Tuba nake, zan kula sosai" Juyawa mai sunan baba ya yi, ya shiga gida, ƙasan zuciyarsa istigfari, da tunanin meye nasa na jin haushi kuma, bayan komai daɗewa dole wataran ta zama matar wani. Aliyu ya shimfiɗe rumaisa a katifar mama, Gwaggo cewa take "Wannan an yi shashasha amarya, haka take da wannan nauyin bacci haka, ta bar mutane da dakonta". Mama ta ce a tasheta ta yi sallar isha'i, lawisa ta ce sun yi salla a gidan kwalliya, kafin su tafi. Tana magagin, mama ta dafa ruwa, ta kaita banɗaki ta wanke mata fuska, ta yi mata wanka tas, ta lulluɓota ta kawota ɗaki, ƴan biki na ta yi mata dariya, sai dai har a cikin ranta ji take ruman ba ta wuce wankan ba, ƙaddarar aure zata rabata da ƴar da take matuƙar ƙauna. Ɗakin samarin nan kuwa, kusan kwana suka yi babu bacci, suna ta ɗan tattaunawa, a kan biki, da kuma jajanta rabuwa da tilon ƙanwarsu, kuma kallabi a cikin rawunansu. Mai sunan baba kuwa ya naɗe, ya lumshe idanunsa ya yi shiru, ba abun da yake ganowa sai kai wa da komowar iman a wurin nan, da yadda suke yawan haɗa ido. Tsaki ya ja ya nemi wuri ya kwanta, sai dai tunanin gobe dai-dai lokacin, rumaisa na gidan wani, ya hana shi bacci, ya din ga yi mata addu'ar shiga gidan miji a sa'a. Bayan idar da sallar juma'a, aka ɗaura auren rumaisa da adam, ƴan unguwar da basu san waye mijin ba a ranar suka ji. Unguwar ta cika da dawakai, da manyan motoci na alfarma, duk in da ka kalla, jami'an tsaro da kuma masu rawuna ne. Sai dai tun da aka ɗaura auren nan, rumaisa jikinta yayi sanyi, take ta uban kuka, duk yadda aka so rarrashinta abun ya gagara. Tuni hotunan biki suka zaga duniya, kowa da abun da yake tofawa, na alkhairi da akasin haka. Samha kuwa kaiwa take ta yi tana komowa a ɗakinta, tana fatan aikin da ta bayar ayi mata, ya yiwu ba tare da samun wata matsala ko akasi ba, dan ta riga ta ƙudirce wa kan ta ɗaukar fansa, ko da tsiya ko da arziki. Ammi a wani event center, ta shirya taron wunin bikin, sai dai abu ya so ya zama rigima, in da facalolinta da masu goya wa mummy baya, suka din ga ci mata mutunci, wai saboda Aisha ba ƴar ta ba ce, ta shirya irin wannan biki haka, kuma aka samo yarinya mara galihu ta aurawa mahaukacin ɗan ta. Duk yadda ammi ta so jurewa sai da ta kusa zubar da hawaye, Nusaiba ba ta da hayaniya, balle iman, Laila ce masifaffiya dama, kuma ba ta ƙasar da ita kaɗai ta ishi duk wani mai bakin magana. Da la'asar mama ta kira ammi, ta ce mata za a kawo rumaisa nan wurinta, ta gaisheta ta yi mata faɗa, sannan a wuce da ita gidanta, ammi ta ce ba sai an kawota ba, saboda wasu dalilai, zuwa magariba zata turo da waɗanda zasu ɗauki rumaisa. A yammacin aka yi kilisar dawakai, takawa ya haɗe cikin kayan sarauta, rumaisa ma aka yi mata ado da alkyabba, aka yi ta musu hotuna. Da magariba rumaisa ta yi wanka, ido duk ya kumbura saboda kuka, Yasir da ya shiga ya fita ya ga tana kuka, shi ma sai ya fashe da kuka, ta tashi ta saka kaya ma abu ya gagara mama sai daurewa take yi, amma hawaye ya cika mata ido. Jiki a sanyaye mai sunan baba ya shiga ɗakin, ya tarar da ita a zaune, tana kuka mai taɓa zuciya. "Rumaisa" ya kira sunanta, ta ɗaga kai ta kalleshi. "Tashi ki saka kayanki, kar dare yayi sosai". "Dan Allah mai sunan baba ku yi haƙuri, wallahi na fasa ni ba zan tafi na barku ba, mama dan Allah ku yafe mini ku barni na zauna a gida, ni ba zan iya rayuwa babu ku ba" tayi maganar cikin kuka. "Tom, mun ji, amma fara saka kayan" da ƙyar ya saka kaya, ya ciro turare a aljihunsa ya fesheta da shi, mata sai rangaɗa guɗa ake yi. Ta riƙe mama tana wani irin kuka. Ya saka hannu ya cire nata daga jikin mama, ya ja hannunta yayi waje da ita. Suna fita mama ta shiga ɗaki, ta fashe da kuka, dan an kai in da ba zata iya jurewa ba. Suna tafe a mota tana kwamce a jikin mai sunan baba, tana ta kuka, kamar ta shiɗe. "Am sorry, kiyi haƙuri haka lamarin aure yake, da haka kowace mace take tara nata iyalin, Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya, ya sanya alkhairi. Ban da rashin kunya da raina miji, mijinki ne ibada zaki je ki yi, ki nemi aljanna na san duk an gaya miki, ki girmama mahaifiyarsa, matar nan ina ganin mutuncinta saboda son da take yi miki. Sannan kuma Sabir ko Allah ya baki naki ɗan, kar ki canza soyayyar da ki ke yi masa, ki yi haƙuri ki saka a ranki, ƙofar sabon ƙalubale zaki buɗe ki shiga. Duk da ƙanƙantarki nauyin aure ya hau kanki sai haƙuri, kiyi haƙuri, ki yi haƙuri, ki jure ki daure duk ƙalubalen da zaki fuskanta wataran sai labari, ina yi miki addu'a Allah ya sassauta miki jarrabawar gidan aure, don babu auren da babu jarrabawa" Haka ya din ga yi mata nasiha, har suka je gidan, gida ya tsaru kamar ba na rumaisa ba, ko ina ya ji kaya. Ana kai rumaisa wata ƙanwar ammi, ta sake saka mata alkyabba a kan kayanta, suka din ga yi mata guɗa a ka, amarya ƙanwar maza, dan su suka kawota ɗakin ma. Sun daɗe tare da rumaisa, kowa da irin faɗan da yake yi mata. Sai da kowa ya watse, Tawagar angwaye suka ƙaraso, gida ba kowa sai tsirarin mutane da zabga-zabgan ƙarti. Suna zuwa mai sunan baba ya tashi ya ce su tafi. Rumaisa ta riƙe rigarsa ta tashi tana kuka "Dan Allah yaya umar, kar ku tafi ku barni, ku tafi da ni, ko ku zauna da ni a nan ɗin, dan Allah yaya. Yaya usy, yaya Abubakar, dan Allah duk ku zauna, Abdallah kar ku tafi, Yasir dan Allah" mai sunan baba duk ya kaɗa musu kai alamar su tafi. Iman tana cikin waɗanda suka rage, gaba ɗaya tausayin rumaisa ya cika mata zuciya. A hankali ya fincike rigarsa daga hannunta, ya juya, ta sake riƙo rigarsa. Ya juya a kausashe ya ce "Wuce ki je ki zauna" a razane ta saki rigar ta sa tana kuka. Yana juyawa sai hawaye, karo na farko da abu ya daki zuciyarsa ya saka shi kuka. Ya saka hanky ya goge, ya kalli Adam ya ce "Ga ta nan amana ce, marainiya ce, ko ka ci, ko kula da ita" yayi maganar wasu hawayen na cika masa ido. Adam har mamaki yake, wace irin soyayya suke nuna wa rumaisa haka. Bashir ya ce "Za a riƙe amana in sha Allah. Yallaɓai aje a rarrasheta dan Allah, tana cikin damuwa". Adam ya ce "Sai ma ka faɗa? Ba daga ni sai ita zaku tafi ku bari, wannan kuma ya rage nawa" dariya abokansa suka yi, suka yi musu addu'a sannan suka watse. Ya koma ya shiga ɗakin na ta, tana tsaye tana ta kuka, ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Yau sarki mai koriyar alkyabba, ya baki alkyabba saura ɗana ki a kan doki. Sannan ke kuma ki cika alƙawarin sanya shi durƙusa miki a kan gwiwoyinsa". What's app only please 🙏 Ayshercool. 0808101214 *Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* Wani mugun kallo rumaisa ta yi masa, ta ture hannunsa da yake gyara mata zaman alkyabbar jikinta, ta ce "Ba ruwanka da ni, kuma ka zo ka mayar da ni gidanmu". "Ni na kawo ki? Sai ki fita ki koma ai, tun da bani na ɗauko ki ba". "Kuma wallahi sai na tafi, ko ka sani ko ba ka sani ba". Hannunsa ya saka, ya matse mata kumatu, ta saka hannunta ta riƙe hannunsa, saboda azabar zafin da ta ji. Ya sake kallonta ya ce "You better behave yourself, a gidana ki ke, fita ki bar mini ɗaki, wancan ɗakunan zaki ɗauki ɗaya, da safe zan saka a kwashe miki tarkacenki, a mayar miki can" ya ƙarasa maganar yana sakar mata baki. "Ba in da zani, tun da dai na ga kayan da aka sai mini ne a ciki" "Kayanki ne, amma gidana ne, sai na kwashi kayan naki na mayar haraba, ki je can ki ƙarata" ya yi maganar yana wucewa cikin bedroom ɗin. Ya rage kayan jikinsa, ya shiga banɗaki. Har yayi abun da zai yi ya fito, rumaisa tana tsaye, tana kuka. Ya je yayi salla, ya wuce ta ya je kitchen, ya dawo amma tana tsaye. Nan ya sake sarawa taurin kan rumaisa. Har ya gama cin abun da zai ci, tana tsaye ƙyam, ta juya masa baya, ya kashe fitila, ya kunna A.C, ya kwanta, gajiyar biki da zirga-zirga ya sanya yana kwanciya bacci mai nauyi ya ɗauke shi. Rumaisa gajiya ta yi da tsayuwa, ga tsoro da ta fara ji saboda duhu, ga sanyin A.C yayi mata yawa, dan ba ta saba ba, ta nemi wuri ta kwanta a ƙasa, ta duƙunƙune a cikin alkyabbar ta hau bacci. Mama kuwa yadda ta ga rana, haka ta ga dare, dan babu wani abu mai kama da barci da yayi shirin ɗaukar ta. Haka ma ƴan mazan nan, Aliyu cewa yake "Allah ka rufa mana asiri, Allah ya sa kar yayi mata wani, abu yarinya ce ƙarama wallahi". Usman ya ce "To yanzu mu kake gaya wa ko yaya?" "A'a addu'a kawai nake yi" Mai sunan baba duk da yana cikin damuwa, amma jin abun da suka faɗa da ya haɗa ido da Abubakar, kawai Abubakar ya tuntsire da dariya, mai sunan baba kuwa murmusawa yayi, tare da basarwa kamar bai ji me suke faɗa ba, haka suka kai har wurin ƙarfe biyu, suna hira yadda biki ya gudana, da kuma jimamin ya rumaisa za ta kasance a gidan aure. Samha ma haka daren nan yayi, ta kasa rintsawa, duk da sun yi chatting da Fauziyya, tana ta rarrashinta, ta tura mata hoton bikinsu Adam. Amma kasa tsayawa ta yi ta kalla, saboda yadda zuciyarta ke matuƙar tafasa da wani irin masifaffen kishi. Ko lokacin da ya auri Aisha, ba ta shiga wannan yanayin da take ciki a yanzu ba. Sai da aka kusa idar da sallar asuba, sannan Adam ya farka, a gaggauce ya shiga banɗaki, yayi alwala, sai da ya ga ba zai samu salla ba ko ya fita, dan haka ya ce bari kawai yayi sallarsa a ɗaki. Ba tare da ya kunna fitilar ba, ya tayar da salla, bayan ya idar ya din ga jin kamar numfashin mutum, har gabansa ya faɗi, dan ya ɗauka irin razana shin da aka saba yi ne, ya tashi ya kunna swtich ɗin ɗakin, mai zai gani, madiga ce a kwance take ta uban baccinta, abun ka da a gajiye take dama, duk ta cukuikuye alkyabbarta. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ke wai a nan ki ka kwana?" Yayi maganar yana taɓa ta. Oho bata san yana yi ba, bacci kawai take yi. "Tashi, ki je ki yi salla" nan ma bata tashi ba. Toilet ya shiga ya ɗebo ruwa, ya dawo ya zuba mata a fuska. A rikice ta tashi tana faɗin "Huzaifa meye haka wai?". "Na hauzaifa bane Adam ne, ban ce miki ki bar mini ɗaki ki tafi ga naki can ba" Maimakon ta yi magana, sai ta haɗe rai tana kallonsa, kamar mafarki take yi ma ba a zahiri ba. Ganin ta tsareshi da ido, ya sanya ya tashi, ya riƙe hannunta ya yi waje da ita, ɗaya bedroom ɗin ya kai ta, ya juya ya tafi ya barta. Kallon ɗakin ta yi, wasu furnitures ɗin ne a ciki ba nata ba, amma sun yi kyau sosai da sosai. Ta cire Alkyabbar, ta shiga ta yi alwala, ta fito babu hijjabi. Ta koma ɗakin da aka fara kai ta, wato ɗakin da Adam ya ce nasa ne, ta buɗe drower ya ɗau hijjabi, yana zaune yana kallonta, sai murguɗa baki take ita kaɗai tana harare-harare. Ta koma ɗakinta, ta yi salla, ta idar ko addu'a ba ta yi ba, ta je ta haye kan gadon, ta ji katifar gadon, mai tauri, ta kalli ɗakin sai ƙamshi yake yi, ta tashi ta yi tsalle a kan katifar, amma taga ba ta lotse ba. "Allah sarki, zan cewa mama ta dawo gidan nan mu din ga kwana tare a kan katifar nan, su yaya Abubakar kuma sai su ɗauki ɗakin ƙasa, ko shi baban sabir ya koma ƙasa, su dawo saman bene, mu yi zamanmu" ta yi maganar tana kwanciya, saboda baccin da yake kanta. Sai da ta yi mai isarta, sannan ta tashi daga baccin, ta sauko daga kan gadon, tana son ta wanke bakinta, amma babu komai a toilet ɗin. Ta fito ta shiga zazzaga saman benen tana kallon yadda gidan yayi kyau, aka tsara shi. Shiru ta ɗan yi tana tunanin mama, da su Huzaifa, ba ta yi aune ba sai hawaye, wani na bin wani, ta din ga gogewa ta ce "In sha Allah sai na fita na koma gida". "Sai zuwa yaushe zaki yi wanka ki sauya wannan kayan, baƙi sun fara zuwa na ce bacci ki ke yi, na dakatar da su a ƙasa, kin tashi kuma baki san ki yi wanka ki canza wasu kayan ba". Muryarsa ta ji a bayanta, dan haka ta juya da sauri, ta sha kunu ta ce "To ina ruwanka da ni, ai ni yarinya ce, a gidanmu wanka ake yi mini, ban fara yi da kaina ba". Mamaki ne ya kama shi, baƙar magana rumaisa ta gaya masa. Wata irin fincikowa yayi mata gabansa, ya tsuke fuska sosai ya nuna ta da yatsansa ya ce "Nan gidana ne, kuma fadata, kuma dole ki bi umarnina, da duk abun da nace, ko na yi umarni, idan ina magana, kina mayar mini da abun da ki ka ga dama, zan yi miki abun da ba kya tunani, wuce mu je" "To, zan yi wanka ba soso da sabulu ne?" "Wuce mu je na ce" ya faɗa a kausashe sumi-sumi ya sakata a gaba zuwa ɗakinsa. Ya nuna mata banɗaki ya ce "Ki wuce ki shiga ki yi wanka, ki yi brush, ki fito ki karya, mutane na ƙasa suna jiranki". Sai da ta gama kalle-kallenta a banɗaki, sannan ta kalli kayan wankan, ta ga soson a jiƙe, alamar yayi amfani da shi. "Wallahi ba zan yi wanka da soson da yayi amfani da shi ba" Ta murza sabulu, ta yi wankanta, ta mayar da kayan da ta cire, ta fito. Yana zaune a gefen gado yana jiranta, ya nuna mata mai a kan mudubi ya ce ta shafa, ya buɗe wardrobe ya ɗauko, kaya ya tsaya ta gama shafa man. Ya kalleta ya ce "Ga kaya nan ki canza". Ta karɓa ta ce "To a gabanka zan canza kayan?". "Ai yarinya ce ke, ba yanzu ki ka gama cewa yi miki wanka ake a gida ba, da ban yi miki wankan ba, ai sai na saka miki kaya ko?" Zare masa ido ta yi, ya ce "Ki wuce toilet ki canza ni ba in da zani" Har mamaki rumaisa take, yadda yake ta hantararta. Riga da skirt ne na lace, har da undeas, ta canza kayan ta fito. Tana ta kakkare jikinta, kar ya kalleta. Fita ya yi yana waya, ta tsaya a gaban mudubi, tana kallon kanta, lace ɗin yayi mata kyau sosai. Ba wani iya ɗauri ta yi ba, dan haka kawai ta ɗora ɗankwalin a kanta. Dawowa yayi tare da iman, tana ganin iman ta fara murmushi. Iman ta ce "Amaryar takawa, ina kwana" Haka kurum sai ta ji kunya ta kamata, ta sunkuyar da kanta. Ya kalli iman ya ce "Ta yi a haka?" "Yes, ka san komai na ta mai kyau ne, bari ta karya, a ɗan yi kwalliya sama-sama". Rumaisa ta ce "Ni fa bana son wannan kwalliyar, haryanzu ta bikin nan jin fuskata nake a ɗaɗɗaure kamar ba ta wa ba". Iman ta ce "Ai ba da yawa za ayi ba, bari na kawo miki abinci nan ki karya". Abinci ne na alfarma, ammi ta saka aka kawo musu. Rumaisa ba ta iya ci da yawa ba, dan babu abun da yake yi mata daɗi, Adam kuwa cin abincin sa yayi, bayan sun gama, iman ta shafa mata powder, ta saka mata jambaki, ta ɗaura mata ɗankwali. Adam ya ce "Ki je ki ce musu su hawo, ta tashi" Iman ta jinjina kai ta fita. Ya kalli rumaisa ya ce "Akwai familynmu, da naku duk sun zo, idan ki ka kuskura ki ka yi making any rubbish scene, sai na rufeki a gidan nan, ba mai sake zuwa wurinki, kuma ba zaki sake fita ba". "Kidnapping ɗina zaka yi kenan?" Ta yi maganar tana kallon sa. "Eh" ya bata amsa, yana mamakin ita duk abun da aka faɗa tana da amsar bayarwa.. Ta yi shiru, tana kallon awarwaron hannunta. Mintuna kusan biyar, ta suka fara jiyo hayaniya sama-sama a falon saman benen. Iman ta shigo ta ce "Yaya ku fito". Ya ce "To, muna zuwa" Ya sake kallon rumaisa ya ce "Ina sake gaya miki, kar ki sake ki yi wani abu a gaban mutane, da zai sa kin janyo mana magana, you should behave yourself" Ta yi ƙuri da ido tana kallonsa. "Am talking to you" yayi maganar a ɗan kausashe. "To" ta amsa a hankali. Miƙa hannu yayi zai riƙo nata, ta janye a ɗan razane. Ta girgiza kai ta ce "Ka daina taɓani, ni bana son a din ga kallona, kuma kar in je su Yaya sun zo, su ga ka riƙe mini hannu". Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Ikon Allah, to mu je" da ƙyar ta yadda suka jera, suka fita. Suna fita aka din ga rafsa guɗa, ana yi masa kirari, haka nan rumaisa ta ji ta takura. Suka ƙarasa suka zauna, ya zauna a kusa da rumaisa, masu addu'a na yi, masu shewa na yi, ita dai ta yi ƙuri, ji take kamar ta tashi, ga adam ya wani matseta a kan kujerar. Wata mata da rumaisa ba ta san ko wacece ba ta miƙawa adam hannu ta ce "Ban ga ka fito da ƙyalle ba, dan mu tabattar da me ka aura". Ya ce "Haba jakadiya, wannan al'adar ai an daina ta, ko lokacin da na auri Aisha, ai ba ayi haka ba, kuma wannan sirrinmu ne kawai ko Mimi?" Yayi maganar yana kallon rumaisa. Sororo rumaisa ta bishi da kallo, tana tunanin wacece mimi kuma a wurin, ko ba da ita yake ba?. "To ai ita aisha tamu ce, kuma ka san ji muka yi an ce, ta shafe watanni shida a hannun masu garkuwa da mutane, kuma mun san ba a bawa kura ajiyar nama, shiyasa muka buƙaci gani, kar mu je saura aka kawo mana". Duk da rumaisa ba ta gane kan zancen ba, amma jikinta ya bata ci mata mutunci ake yi. Sai da ƙirjin Adam yayi wani damm, amma ya basar ya kalli rumaisa, ya ce "Kamar kowacce mace, za ta yi alfahari da daren jiya, za ta yi proud sosai da hakan" Ji ta yi kamar ta ce da ka koreni daga ɗakin, na kwana a ƙasa, meye wani abun alfahari. Ƴan uwansu rumaisa kuwa, jin zancen suka yi ba arziki, suka din ga sunkuyar da kai, Gwaggo ta ce "Dama ɗaki muka dawo mu gani, mu anjima zamu koma gida". Da sauri rumaisa ta ce "Haba dai Gwaggo, to wai ya baku taho da mama ba, ban ga su yaya bama". Adam ya ce "Bai kamata ku tafi yanzu ba, Yakamata a ɗan tayata zama" Gwaggo ta ce "A'a, ai gaka nan, mu mun tafi, ga saƙonki nan babarki tana gaishe ki" Tashi rumaisa ke ƙoƙarin yi, amma ya riƙeta, ya hanata tashi. "Gwaggo dan Allah karku tafi ku barni, dan Allah ku dawo, lawisa kema ba zaki zauna ba?" Ta yi maganar tana kuka. Adam ya zura hannu a aljihunsa, ya bawa iman, ya ce ta bawa su gwaggo. Ya ce Gwaggo mun gode sosai da sosai, sai mun zo gida yin bangajiya" Ta ce "Babu komai, Allah ya sanya alkhairi" Ya ji daɗin tafiyar su gwaggo, ko ba komai, ba za a cigaba da cin mutuncin rumaisa a gabansu ba. Ɗago fuskarta yayi, yana goge mata hawayen fuskarta, yana faɗin "Is ok, yi haƙuri kukan ya isa haka" Ƙoƙarin ture hannunsa take yi, amma yayi mata kallon kashedi, a dolenta ta ƙyaleshi. Baba uwani sai shiga take tana fita, tana koɗa yadda gida yayi kyau. Hajiya Lubabatu wato maman Jabir ta ce "Abun dai ya bawa kowa mamaki takawa, bamu taɓa zaton zaka auri ƙaramar yarinya kamar wannan ba, kuma ma dai abun da mamaki, ace wannan ƙaramar yarinyar ce ta kuɓuta da Sabir, daga hannun 'yan bindiga" "Ai babu mamaki a ikon Allah, ƙanƙantarta kuma ba zai hana a aureta ba, tun da bai saɓawa shari'a ba". Ta kalli rumaisa ta ce "Sannu ƴar nan, sannu da shigowa familyn gidan sarauta, kin zo babban gida, Allah ya baki wuyan ɗauka" Rumaisa dai ba ta kulata ba, sai kuka da take yi, na tafiyar Gwaggo da kuma rashin ganin mama. Haka Adam ya zauna tare da ita a wurin, dan kar ya tashi su ci zarafinta, ita kuma ya san ba kunya ce ta wadaceta ba, tsaf zata iya yi musu fitsara. Sai wajen azahar suka ragu, bayan sun gama faɗe-faɗen maganganun su, da yada habaici. Da azahar ɗin kuma, Nusaiba ce ta zo da kayan abincin rana. Sai dai rumaisa taƙi cin abinci, duk surutun nata kuma ta yi shiru, taƙi kula kowa, Iman sai rarrashinta take yi. Takawa baba uwani ya saka, ta kwashi akwatunan rumaisa, ta kai mata ɗakinta, da sauran kayanta, ya ce ta shirya mata wasu kayan a cikin wardrobe ɗin ta, ga su iman nan, su tayata a haɗa mata ɗakin. Sai dai Iman ta din ga bin baba uwani da kallo, har sai da ta tsargu, tana ta yi wa rumaisa surutu tana tsokanarta, amma rumaisa ba ta ce komai ba, sai kallonta kawai da take yi. Tana ƙoƙarin fara shirya mata kayan, rumaisa ta ce "Bar shi, zan yi da kaina" Kallonta suka yi gaba ɗaya,Nusaiba ta ce "Ki bari ya shirya miki, ke ga gajiyar biki, idan ya so sai ki gaya mata yadda ki ke so" Rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a, idan ma ta yi sai na sake, kawai ta bar shi". Nusaiba ta ce "To shikenan, baba uwani ƙyale mata". Adam ya shigo ɗakin, yana tambayarta ko an shirya mata kayan. Nusaiba ta ce "A'a ta ce a ƙyale mata, za ta yi abun ta da kanta". "Shikenan, ku ƙyale mata abun ta, tun da ba ta san gwaninta ba, idan an yi sallar la'asar sai ku tafi gida, ba sai an kawo abincin dare ba". "A'a dan Allah kar su tafi, shikenan sai kowa ya tafi ya barni?". Tausayinta ya kama iman, amma takawa ya tsare gida ya ce "Do as i said" Baba uwani ta yi mamakin yadda ƙiri-ƙiri rumaisa ta ce ba zata shirya mata kaya ba, ta so ta saki jiki da ita ta shigeta, saboda ta din ga samun wasu bayanan, da za ta din ga kai rahoto, amma mursisi rumaisa taƙi. Sai ta bar shi a rashin sabo ne, amma tayi alwashin shiga jikin rumaisa, tun da a ganinta yarinya ce ba ta da wayo. Sannan ta yi mamakin yadda suka haɗu da rumaisa, amma ba ta san ita ce wadda Adam zai aura ba, ta fara tunanin ko dai ammi ta ganota ne, ya sanya ta fara ɓoye mata wasu abubuwan. Kan su ƙarasa gida, ta ce a ajiyeta a hanya, za ta je wani gida, suka ajiyeta su kuma suka ƙarasa gida. Tun da suka koma, ammi ke tambayarsu, ya suka baro rumaisa, iman ta ce "Wallahi tana ta kuka ammi, gwanin ban tausayi". "Allah sarki rumaisa, za ta saba ne in sha Allah, na san dama za a sha daru". Iman ta ce "Ammi kin san me?" "A'a sai kin faɗa". "Wai jakadiya, da maman su jabir, suka saka takawa a gaba, wai ya basu ƙyalle su san me ya aura, sun samu labarin watanta shida a hannun 'yan bindiga, wai ba a bawa kura ajiyar nama" Ammi ta yi shiru ta ce "Daga kawo yarinyar jiya, shi ne za su fara wannan abun? Bakomai Allah ya fi su, kuma auren Adam da rumaisa, sai ya bawa mara ɗa kunya in sha Allah". Nusaiba ta ce "Suna da matsala, daga zuwanta jiya za su fara nuna hali, kuma wallahi wataƙila Mummy ce zata saka su, ai daɗinta maman Sabir ɗin ma ba kanwar lasa ba ce". Baba uwani kuwa, gulma na cinta kasa jurewa ta yi, but ta faɗa sashin Mummy, Aikuwa aka yi sa'a Samha tana nan, suna ta kitsa tsiya. Mummy ta kalleta ta ce "Ya aka yi?". "Daga gidan muke, aikin da aka bani dama na yi shi, ba wata matsala, amma jakadiya sun tambaye shi ƙyalle, ya ce wannan tsohuwar al'ada ce, kuma kamar kowace mace, za ta yi alfahari da daren jiya, nake tunanin ko dai ya.... Samha ta ce "Dakata, ƙarya yake yi wallahi, ai shi da ita sai kallon kallo, ƙarya yake babu abun da ya faru" Mummy ta ce "Haka ne, ke dai ki yi duk mai yiwuwa ki saka ido sosai, ki din ga kawo mana rahoton duk wani abu da yake faruwa, kuma idan muka baki aiki, ki tabattar kin yi shi yadda ya dace". Ta risuna ta ce "In sha Allah uwar ɗakina". Tun da su iman suka tafi, ya rage daga ita sai Adam a gidan ta cigaba da kukanta, ta window ɗakinta ya hangota, tana shirya kaya tana kuka, bai kulata ba ya koma falo, yana gwada kayan kallo. A haka rumaisa ta shafe kwanaki uku a gidan Adam, ko ƙasan bene bata taɓa sauka ba, sai dai ba ta gajiya da kuka, mussaman yadda ƴan gidansu babu wanda ya nemeta, gashi ko an zo mata ta ɗan rage damuwa, da yin la'asar kowa zai watse, shi kuma Adam ba abun da ya iya banda bayar da umarni, ko ya hantareta. A kwana na huɗu ya lura, tana gujewa haɗuwarsu, idan ta ji motsinsa ko falo ba za ta fito ba, ya lura abincin ma ba ci take yi ba, ta takura kanta sosai da sosai. Bayan sallar magariba ya shiga ɗakinta, ya tarar ta yi salla tana zaune a kan sallaya ta yi shiru. Ɗaga kai ta yi ta kalleshi, yayi mata alamar ta zo. Ba musu ta taso yana gaba tana bin sa a baya. Ƙasan bene ya sauka, ta bi bayansa, tun da aka kawota, yau ta fara sauka ƙasan benen. Harabar gidan suka fita, ya nufi motarsa, ya buɗe gaban motar ya ce ta shiga. Ta shiga ta zauna, tana kallon cikin motar sabuwa da ita fil, ga tsofaffin nasa da ta san shi da su a harabar. Sai a yanzu ta lura, har da burgar dawakai a gidan, da dokuna manya guda huɗu, ga wani murgujejen kare, da shi ma ba ta san da shi ba a gidan. Security light duk ta haske ko ina a gidan. Ba ta san in da zasu tafi ba, ita dai ta ga suna tafiya. Sai da suka je gidan, ta gane gidansu Adam suka je. Ammi na ganin rumaisa ta rungumeta tana murna, ta ce "Takawa, baka bari ta gama hutawa ba ka fito da ita" "Ta isheni da koke-koke, shiyasa na kawo ta" Ammi ta ce "Haba rumaisa, kukan bai isa haka ba, ai yakamta ki kwantar da hankalinki haka" Rumaisa ta sunkuyar da kai, ba ta ce komai ba. Nusaiba na ganin rumaisa ta fara murmushi "Amarya ba kya laifi, yau da kanki" Rumaisa ta ce "Shi ne baku kuma zuwa ba da ke da Iman". "Yaya ne ya ce kar mu sake zuwa ai" "To ni kaɗai nake zama a gidan fa, kuma shi ba kulani yake yi ba, sai dai in wuni ina kuka" Ammi ta kalli Adam, ya sunkuyar da kai, ta kalli rumaisa ta ce "Haba Yarinyar kirki, zai din ga kulaki kukan da ki ke yi ne baya so, gobe in Allah ya kaimu za'a baki hadimai mutum biyu, da zasu din ga yi miki aiki, sa din ga ɗebe miki kewa, abun da ma kin kusa komawa makaranta, wani satin za a koma makaranta". Ammi ta yi maganar baba uwani ta fito, ɗauke da Sabir a hannunta. Murmushi rumaisa ta yi ganin sabir, Adam ya karɓe shi, Baba uwani ta ce "Amaryarmu, sannu da zuwa ya gida, bamu san da zuwanku ba ai da an sheƙa girki na mussaman" Rumaisa ta ce "Mata ina wuni" Baba uwani ta ce "Tuba nake, ai ni yakamata na kwashi gaisuwa" Sabir kuwa rumaisa ya din ga miƙawa hannu. Adam ya ce "Kai, kwana huɗu baka ganni ba, amma baka ta tawa, Mimi zo ki ɗauke shi" Waiwayawa ta kuma yi, taga da wa yake, sai kuma ta tuna abun da ya ce washegarin kai ta. Ta tashi ta je ɗaukar Sabir, yayi ƙasa da muryarsa ya ce "For the second time, idan na ce mimi da ke nake, ba zan so Sabir ya tashi ya ji ina faɗar sunanki ba" ta jinjina masa kai, ta karɓi Sabir. Ta kalli Ammi ta ce "Ammi, sai a haɗo mini kayansa, na tafi da shi ko?" Ammi ta ce "A'a, ke da zaki koma school, za'a din ga kawo shi, juma'a da yamma, sai a ɗauko shi ranar lahadi, saboda ki samu ki yi karatunki a nutse, sannan bayan hadimai biyun nan, baba uwani za ta zauna da ku, saboda ta saka ido a kan yadda zasu din ga gudanar da aiki a gidan, idan komai ya daidaita sai ta dawo, saboda ita ce amintacciyar hadimata". Babu tsammani rumaisa ta ji gabanta ya faɗi, ba ta son baba uwani, kamar ma tsoronta take ji!. Ayshercool 08081012143 *Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* Rumaisa kasa cewa komai ta yi sai jinjinawa ammi kai, baba uwani kuwa har da shewa tana juyi, tana yi wa ammi godiya da karamcin da ta yi mata, a matsayin wadda za ta je ta yi guiding ɗin ma'aikatan gidan takawa. Ammi ta yi wa Adam alamar ya bi ta, ya tashi ya bi bayanta ɗakinta, ta kalleshi ta ce "Takawa, na san auren nan ba son ka bane, zaɓina ne amma dan Allah ina sake roƙon alfarmarka, ka yi haƙuri da yarinyar nan, komai zai wuce zaka yi alfahari da auren nan, ka ga yarinya ce ƙarama, dole za ta yi ta koke-koke na rabata da gida da ka yi, dan Allah ka yi haƙuri da ita. Ko dai wani abun ka yi mata?" Ware ido ya yi ya ce "Ba abun da na yi mata wallahi". "A'a takawa, dan Allah ayi haƙuri a bata lokaci, yarinya ce sosai sai ka yi haƙuri" Adam wata irin kunya ce ta kama shi, ya ji tamkar ƙasa ta tsage ya nutse don kunya, ya girgiza kai ya ce "Ban yi mata komai ba" "Na ji ba wai ina son jin sirrin aurenku ba ne, amma dan Allah ka kula da ita, next week idan Allah ya kai mu za a koma makaranta ko?" Ya ce "Eh, na biya komai ma, ana komawa zan kaita sai kuma na samo direban da zai din ga ɗaukota idan bana nan" Ammi ta ce "To shikenan, Allah ya ƙara buɗi" Suka fito, Ammi ta ce a zubawa su takawa abinci su tafi da shi. Ammi dai ta lura gaba ɗaya jikin rumaisa a sanyaye yake, har ta fara tunanin ko takawa dai yayi mata wani abun ne. Ammi ta zauna a kusa da ita, ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Rumaisa, ko akwai wata matsala ne?" Ruma ta girgiza kai alamar a'a. "To ki yi haƙuri kin ji, zaki saba ne haka aure yake, ki yi haƙuri, duk abun da yayi miki wanda bai yi miki ba ki gaya mini. Sannan su nusaiba sun gaya mini abun da ya faru washegarin kai ki, shi ma ki yi haƙuri ki kawar da kanki, na san zaki fuskanci ƙalubale, amma ki dake. Kar ki yadda da duk wata mata da zata nuna tafi kowa ƙaunarki ko ta shiga jikinki, kuma kar ki sake ki gaya wa wani sirrin aurenki, duk abun da zai yi miki, ba zai yi wanda zai cutar da ke ba, na ja masa kunne sosai da sosai, idan yayi miki abun da ba dai-dai ba, ki gaya mini. Kar ki saki jiki da kowa, sai mijinki ko kuma ni da ƙannensa zama a masaruta sai ka iya allonka, ki yi haƙuri kin ji rumaisana". Ruma ta ce "To Ammi, in sha Allah " Har gaban mota ammin ta rakasu, suka shiga suka tafi. Tun kan su yi nisa ta fara sana'arta ta barcci, ya taɓata ya ce "Idan ki ka yi bacci, sai dai ki kwana a mota, dan ba ɗaukar ki zan yi ba" da haka suka ƙarasa gida ta yi sallar isha'i, ko abincin ba ta ci ba ta kwanta. Washegari da safe, ta tashi tana ɗan goge gogenta, ta fito falo tana ta goge tiles ɗin. Adam ya fito cikin suits da jakarsa, da alama aiki zai tafi, ta yi masa ƙuri da ido, ba ta yi magana ba. "Baki iya gaisuwa bane?" Ta ɗauke kanta daga kallonsa ta ce "Ba amsawa ka ke yi ba" "Yes, ba kya gaisheni yadda ya dace ne, ki bar wannan aikin babu wanda ya saka ki, anjima masu aikin da ammi ta ce za su zo, idan da wani abu su gyara miki. Ga breakfast can a kan dining, in anjima zasu fara aiki, zan sayo kayan abinci, ko kina buƙatar wani abu?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "To ki zauna wuri ɗaya, banda taɓe-taɓen abun da ban saka ki ba". "To sai yaushe zaka dawo?". "Lokacin da Allah ya yi". "Ni dai ka dawo da wuri, tsoro nake ji" *** Gidansu rumaisa kuwa, mama ce ta hana kowa zuwa gidan, saboda ta san halin rumaisa, ta ce idan suka je kuka za ta yi ta ce zata biyosu. Sai dai ba a cikakken awa guda, ba ayi zancenta ba a gidan. Kasancewar bayan mai hoton da ɓangaren su Adam suka ɗauko, Abdallah ma ya ɗauko mai hoto, aka turo masa hotunan bikin rumaisa, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya tura su group ɗin su, na ƴan gidan. Mai sunan baba yana kasuwa, da yake bayan makaranta ya kan ɗan shiga kasuwa, hotunan suka shigo. Suna da yawa ya sauke su, ya fara buɗewa yana kallo, yana kallo yana murmushi yana jin yadda ya yi kewar ƙanwarsa. Babu tsammani ya ci karo da hotonsa shi da iman, rumaisa kuma a gefensu, ya wuce hoton da sauri, amma ya kuma karo da hoton iman ɗin, na ranar bridal shower, ta yi wani irin kyau na musamman. Zuciyarsa ta tsananta bugawa, kuma ya kasa wuce hoton nata, ba shiri ya rufe wayar, ya saka a aljihunsa yana ajiyar zuciya, kamar wanda ya yi gudu. *** "Wallahi Adam na yi mamaki da har ka iya ɓoye mini al'amari mai girma kamar wannan, menene a ciki idan na san wannan yarinyar zaka aura" Jabir yayi maganar cike da ƙorafi. Adam ya ce "Koma menene bai kamata ka ji haushi ba, yanzu ba gashi ka ji ba, ko da yake gara kai a kan Jamil, ni Jamil zai ɗauki gaba da ni, yaƙi zuwa wurin ɗaurin aurena, ni na karɓi ƙaddarata dan meyasa shi ba zai ɗauka ba". Jabir ya ce "A'a takawa, so so ne fa, amma son kai ya fi, Samha ƙanwarmu ce ga ta gida, amma ace ka auro wata a waje, wadda ba ta kaita komai ba, babu daɗi". "Amma har ya kai ayi gaba da ni saboda hakan? Meye aibun rumaisa idan aka kamanta shi da abun da ta yi mini na sadaukarwa, bai kamata gaba ɗayanmu idonmu ya rufe ba, idan akwai rabo a gaba sai ka ga na aureta, amma a yanzu ban zaci haka daga Jamil ba, amma zan shiga wurin aiki, zamu haɗu da shi mu yi magana" Jabir ya ce "To shikenan, har ka gama amarcin kenan ka fito, bai yi wuri ba komawarka aiki ba kuwa?" Adam ya yi murmushi ya ce "Bai yi ba, ita ma sai a bar ta ta huta. Kai ni har mamaki nake yi yadda kai  ba a saka maka ido ba, ko auren fari ba ka yi ba, amma ba ruwan wani da kai, duk mu aka sanya wa ido" Jabir ya yi dariya ya ce "Bayan ka ce ba zaka bani iman ba, ai ni na zaci kai zaka aureta" Adam ya ɗan ɓata fuska ya ce "Please mu bar wannan zancen" Jabir ya ce "Shikenan, tun da baka so" *** Rumaisa ta rasa abun da yake yi mata daɗi, zaman shirun nan duk ya isheta. Ta saman benen take kallon harabar gidan, da gidajen da ke maƙwabtaka da nata, duk manyan gidaje ne, sannan kowane gida a rufe yake, ko gilmawar mutane ba ka gani, sai dai a cikin mota. Mai gadin ta ga ya tashi ya buɗe gate, nan da nan ta fara murna ta yi baƙi. Ta koma ɗakinta da sauri, ta saka hula a kanta, ta fito, sai dai ta yi turus lokacin da ta ga baba uwani, da wasu matasan mata guda biyu. Jiki a sanyaye ta ce musu "Ina wuni?" Baba uwani ta yi murmushi ta ce "Ranki ya daɗe ai mu zamu gaisheki, barka da wannan lokaci? Mun same ki lafiya?" "Lafiya ƙalau" ta amsa a ɗan tsorace. "To kamar yadda giwa ta yi miki bayani jiya, ga ma'aikatanki nan, sannan kuma ni ce cikon ta ukun, zamu zauna tare da su a nan, na din ga lura da yadda zasu gudanar da aikin". Rumaisa ta ce "To sannunku". Baba uwani ta ce "Yauwwa, wani ɗakin zamu zauna, da kayanmu muka zo". "Ku zaɓi duk wanda ku ke so" rumaisa ta yi maganar tana kallonsu. Ta nemi wuri ta zauna a falo, baba uwani ta zaƙe ta fara dudduba ɗakunan da suke saman benen. Ta shiga ɗakin rumaisa, ta ƙare masa kallo, ta fito tana faɗin "Allah ya taimake ki, ashe an shirya miki kayan, ko takawan ne ya shirya miki su?" Rumaisa ta ce "A'a ni na yi" "Masha Allah, to bari ɗauki wancan ɗakin, tun da na ga ɗayan kamar babu kowa a ciki" Ita dai rumaisa ba ta ce komai ba, ta ƙare ta shiga kitchen tana dudduba kayan kitchen ɗin Rumaisa. Ganin sun isheta da kallo, sauran mata biyun da ko sunayensu ba ta sani ba, ya sanya ta tashi ta koma ɗakinta. Ta buɗe window ta cigaba da kalle-kallenta, ta hango baba uwani a bayan gidan, tana waya. Ba ta jin mai baba uwani take cewa, sai dai da alama kamar wayar ta ta ta sirri ce. Baba uwani kuwa cikin ladabi take waya da Samha. "Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurareni, bana son a samu kowane irin akasi a kan aikin nan, ki zuba mini ido sosai, duk abun da yake faruwa ki din ga sanar da ni, ina fatan kin gane?" "Na gane ranki ya daɗe, duk abun da ki ka ce in Allah ya yarda zan yi, zan zuba ido sosai da sosai" Samha ta ce "Yayi kyau". Da la'asar Adam ya dawo, rumaisa ma sam ba ta san ya dawo ba, saboda wunin ɗaki ta yi, ko haɗa hanya ba ta son yi da baba uwani. Gyaran murya ya yi, hakan ya sa ta waiwaya ta ganshi a tsaye. Ya shiga ɗakin ya ce "Me ki ke yi ke kaɗai a ɗaki?". "Bakomai" "Ke ki ka ce wa baba uwani su zauna a ɗakin saman nan?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya ce "To na ce su koma ƙasa, ba haka ake yi ba. Ga kayan abinci can na sayo, na zuba a kitchen ɗin ƙasa, zasu din ga girki suna kawo mana, sannan zasu din ga yin duk wani aiki na gidan nan, banda gyaran ɗakina, ke zaki din ga wannan ai kin iya ko?" Ta jinjina masa kai. "Bana son body language, amsa mini zaki yi" "Eh na iya". "Good, ki fito zan nuna miki abu". Ta tashi ta bishi, zuwa kitchen ɗin saman benen. Ya nuna mata kayan tea, manyan gwangwanayen madara da na milo, kayan biscuit na ciye-ciye da sauransu. Sai cartons na lemuka, da kayan marmari ya ce "Gashi nan, wanda zaki kai ɗaki ki kai, wanda za su saka miki a fridge kuma sai ki nuna musu". "To an gode" ta faɗa a sanyaye. Gani yake yi kamar an sauya rumaisa, duk wannan tsabar rashin jin da tsaurin ido, duk ta yi sanyi, sai dai a ransa ya ce ba a yabon ɗan kuturu. Kasancewar tun a yau su baba uwani suka fara gudanar da ayyukansu, sun yi abincin dare, suka kai wa su rumaisa sama. Ruma ko kallon abincin ba ta yi ba, ta din ga cin kayan marmari, sai da ta ji ta ƙoshi. Ta haɗa madara da milo, fal a kofi ta tafi da shi ɗaki, ta din ga sha ta gaji ta ajiye sauran ta yi bacci. Ba ta san ma Adam ya dawo ba, sai da asuba ta ji yana babbuga mata gefen gado ta tashi ta yi sallar asuba. Ta buɗe ido ta kalleshi ya ce "Ke ba kya iya tashi salla dole sai an tasheki ne? Kuma haka ki ke kwana da fitila a kunne?" Ba ta ce komai ba shi kuma ya fice. bayan ta yi sallar, ta ɗan yi baccin safe ta tashi, ta shiga banɗakinta, yanzu duk ta san yadda ake amfani da kayan toilet ɗin, da idan za ta yi alwala, sai ta kunna hot water ta fara, tana tsaka da yi, ta ji ruwan zafi yana ƙona ta, yanzu kuwa duk ta gane kansu. Wankanta ta yi a nutse, ta fito tana goge jikinta da ruwa, ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kanta. Baba uwani ta yi sallama, da kayan mopping a hannunta. Rumaisa ta razana tana neman hijjabi ta saka, kasancewar daga ita sai towel. Baba uwani ta ce "Haba ranki ya daɗe, ai na haifeki, meye na damuwa kuma, gyara miki ɗakin zan yi". Rumaisa ta girgiza kai ta ce "Ki bar shi kawai zan gyara da kaina, kaya zan saka". "Ki saka kayanki kawai, aikina zan yi". A ɗan hasale rumaisa ta ce "Ki bar shi kaya zan saka". Ta kalli rumaisa, ba wata uwa a jikin nata sai tsirfa. Ta juya sumi-sumi ta bar ɗakin. Guntun tsaki rumaisa ta ja ta ce "Wannan mata meye damuwarta ne? Bana son shishshigi", rumaisa ta saba yawonta a gidansu, babu suturar kirki ba ta damu ba, amma ba ta yadda wani na waje ya ganta ba. A gaggauce ta saka kayan, tana son ta yi magana da adam Kafin ya fita. A falo ta tarar da adam yana danna system, babu alamar zai fita yau. "Ina kwana" ta faɗa ba dan ta na tsammanin ya amsa ba, aikuwa bai amsa ɗin ba. Ta ɗora da cewar "Dama, tambayarka zan yi, yau tun da juma'a zaka ɗauko mini Sabir ɗin, ammi ta ce za a din ga kawo shi, juma'a zuwa ranar lahadi, sannan dan Allah ka kira mini yaya Aliyu a waya, dan Allah su zo". Ya kalleta ya ce "Da ni ki ke ko da system ɗi na, ko akwai wani bayan ni a nan?" kallonsa ta yi da mamakin rainin hankalin da ya yi mata ta ce "Da kai nake mana". "Bani da suna ne ko yaya?" Rumaisa ta ce "Ka na da shi". "Ok, ya sunana?" Yayi maganar yana tsareta da ido. Har ta buɗe baki za ta ce Adam, sai ta ji sunan yayi mata nauyi a bakinta, gashi ya tsareta da ido, yayi mata kwarjini sosai. "Papa" ta faɗa a hankali. Adam ya ce "Waye hakan?" "Saboda Sabir, na ji ya fara koyar faɗan sunanka" Ɗan rausayar da kai ya yi, a ransa ya ce "Ashe kina da hankali wasu lokutan '. A zahiri kuma ya ce "Me ki ka yi wa baba uwani, na ga ta fito daga ɗakinki, kamar ranta a ɓace?". Ta ɗan tura baki ta ce "Ba abun da na yi mata" "Bana son ƙarya" "Ba ƙarya nake ba, zuwa ta yi wai za ta gyara mini ɗaki, ni kuma daga wanka na fito ban saka kaya ba, kawai cewa na yi ta bar shi zan gyara da kaina shikenan fa" "Ba ta haifeki ba, me za ta gani?" Da sauri ta kalleshi ta ce "Taɓ, ni wallahi ba zata ganni ba". "To me za ta gani?" Shiru ta yi ba ta bashi amsa ba. Ya girgiza kai ya ce "Kasancewar ta na yi miki aiki, ba ya na nufin ki rainata bane, ita ce babbar hadimar ammi, muma muna girmamata. Ga abinci can sun girka, ki je ki karya". "Na ƙoshi" ta faɗa cikin jin haushi, dan ita ba ta ga abun da ta yi wa baba uwani ba. "Kin ƙoshi saboda me?" "Ni so nake na din ga girka abincina da kaina, ammi ta ce kar na yarda da kowa, kar na je ayi mini aisiri a cikin abincin" Tattara hankalinsa ya yi a kan rumaisa sanannan ya ce "Waye zai yi miki asirin?" Ta ce "An ce a gidan sarauta ana asiri, dan haka ni ba zan ci wannan abincin ba". "Ai dama me hali baya fasa halinsa, kin huta, sai dai idan ba zaki ci abinci a gidan nan ba, idan ki ka sake na ganki a kitchen da sunan zaki yi girki, sai na saɓa miki, ba zaki haɗa mini gobara a gida ba, kuma ki cigaba da ina magana ki na yi mini gatsali, zaki ga yadda zamu yi da ke" Ya mayar da hankali a kan system ɗin sa. Jin sa kawai take yi, amma ta yi wa kanta alƙawarin ba za ta ci abincin nan ba. Ya tashi ya shiga ɗakin sa, ya fito da mukullin motarsa, ya fice ba tare da ko kulata ya yi ba. Yana fita ta sauka ƙasan benen, ta tarar da su baba uwani suna aikace-aikace. Tana ganin rumaisa ta saki fuska tana faɗin "Uwar ɗakina, sannu da fitowa, kina buƙatar wani abun ne?" Rumaisa a ran ta ta ce, ji matar nan kamar ba yanzu ya ce ta fito ranta a ɓace ba. "Bakomai, Takawa ne ya ce mini, kin fita daga ɗakina ranki a ɓace, kamar baki ji daɗin abun da na yi miki ba, ki yi haƙuri dan Allah. Sannan zan din ga yin aikin saman, zan din ga gyara komai". Baba uwani ta ce "A'a ba haushi na ji ba uwar ɗakina, ai zamanki muke yi, kar ki damu dolenmu mu gyara miki, ai ke hutuwarki kawai zaki din ga yi" Ruma ta ce "A'a na iya aiki, zan din ga yi da kaina". Baba uwani ta bi rumaisa da kallo, ta shiga cikin kitchen ɗin, ta ɗebi indomie, da abubuwan da take buƙata. "Indomie zaki ci? Ko in turo barira ta dafa miki". "A'a na iya girki" ta juya ta nufi stairs. Mamaki ne ya cika baba uwani, sai a yau ta fuskanci yanayin rumaisa fetsararriya ce. Ko da rumaisa ta je kitchen ɗin ta na saman bene, babu gas a cylinder ta, dan haka a kan electric ta dafa indomie da tea ta zauna a kitchen, ta ci kayanta, ta yi wanke-wanke. "Ke amarya kina ina ne" ta ji muryar Aliyu a bazata. Da gudu ta fito falon, ta ɗane jikin Aliyu tana murna. Shi da mai sunan baba ta gani, ta saki Aliyu ta nufi mai sunan baba. Murmushi yayi ya riƙeta da hannu ɗaya ya ce "Ya kike?" Take ta fara kuka ta ce "Yaya shi ne ku ka ƙi zuwa" "To yanzu ba gamu ba, idan kuka zaki yi zamu koma". Ta share hawayen ta ce "na daina" Zama suka yi Aliyu yana ta kallonta yana "Inyee amarsu ta ango, to yanzu ma mama ba ta san zamu zo ba, wai kar mu saka ki kuka, yaya Umar ya ce mu zo mu ganki" "Aikuwa kuka na din ga yi, yau ne kawai ban yi kuka ba". Aliyu ya ce "Ke, na ga wasu mata a ƙasa su waye?". Rumaisa ta ce "Wai hadimai ne, su suke aikin gidan". "Saboda me, ke baki iya bane?". "To ya zan yi, ammi ta ce gidan yayi mini girma ba zan iya aikin nikaɗai ba". "Ke, wannan dattijuwar za ta yi saka ido, kamar mara gaskiya kin ga yadda ta din ga binmu da kallo, wai su waye mu daga ina muke?" Rumaisa ta ce "Ni ina ruwana, tun da ba a kaina suke ba". Mai sunan baba ya ce "Da ruwanki mana, ki dai kula da kan ki sosai ". Sallamar iman ce ta kaste musu hirar, rumaisa ta ce "Yeee, yau baƙina da yawa" Idonta bai sauka a na kowa ba, sai cikin na mai sunan baba. Da sauri ta durƙusa ta ce "Ina wuni" "Lafiya ƙalau " ya amsa yana kawar da kansa. Ta gaida Aliyu ma, ya amsa mata cikin sakin fuska. Rumaisa ta karɓi Sabir tana murna. Kamar kullum, tsoro da fargaba ya mamaye iman, kasancewar, mai sunan baba a wurin. "Anty iman, na zaci ba za a kawo shi ba fa". "A'a za a kawo shi, amma ba bar miki za ayi ba, sai an haɗa masa kayansa tukuna". Zuwan Iman ya sanya mai sunan baba tashi ya cewa Aliyu su tafi. Kamar rumaisa ta yi kuka ta ce "Mai sunan baba baku daɗe ba fa". "Eh, ai mun zo dai, tafiya zamu yi sauri muke yi " Iman ta ce "Idan saboda ni ne, bari in tafi, takawa ya mayar da sabir ɗin". Ta yi maganar tana tashi. "Meyasa zamu tafi dan kin zo? Nemi wuri ki zauna ba zama zamu yi ba dama" ya mayar da idonsa kan rumaisa ya ce "Take care" Daga haka yayi wa Aliyu alamar su tafi, rumaisa ta ce zata rakasu, amma ya ce ta yi zamanta, ya ajiye mata kuɗi, suka fice. Kuka rumaisa ta yi ta yi, iman tana rarrashinta, ita kan ta tana mamakin irin halina bawan Allah nan. Kasancewar iman na nan, ga kuma Sabir, ya sanya rumaisa ta haƙura, suka shiga kitchen ita da iman suka yi girki, iman ta tayata ta ɗebo wasu daga kayan abinci daga kitchen ɗin ƙasa zuwa na sama. Iman ta din ga mamakin yadda rumaisa ta iya girki. Rumaisa ta ce "Hmm, tun ba a barina na yi a gida, in yi in jagwalgwala har na iya, yaya Abdallah tare muke girki, har a YouTube yake ganin girki mu gwada, daga baya na gane girkin wahala ce, na daina". Iman har bayan la'asar tana nan, baba uwani na yi tana hawa benen, wai ko suna buƙatar wani abun. Direba har ya zo ɗaukar iman, takawa bai dawo ba, haka ita ma iman ta tafi, gidan yayi mata shiru da yawa. Sai yanzu take jin haushin tafiyar su mai sunan baba, ko a waya basu kira mata mama ba. Baba uwani ta shigo falon da sallama da kayan abinci, ta ce "Uwar ɗakina, ga abincin mai gida, da naki na dare". Rumaisa ta ce "A'a ai mun yi girki da iman, mun rage masa". "To wannan ɗin a koma da shi kenan?" Rumaisa ta ce "Eh, abincin ma a daina kawowa kawai". "Amma saboda me?". Ruma ta ce "Saboda na daina wahalar da ku, na iya girkin nima" 'Amma ai giwa ba ta ce mana haka ba". Ruma ta ce "Da gaske nake na iya, kar ki damu" Baba uwani ta fara jin haushin, rashin yaddar da rumaisa take nuna wa yadda taƙi sakin jikinta da ita. Rumaisa ba ta damu da sanin dawowa ko fitar Adam ba, idan ba wani abu take buƙata ba, dan haka har ta yi bacci ba ta san ya dawo ko be dawo ba. A cikin bacci yake jin kuka sama-sama, ya buɗe idonsa ya ji ana taɓa shi ana kuka. Ya tashi sosai ya ce "Waye wannan?" Ƴar siriryar muryarta ya ji tana cewa "Ka tashi zan mutu, dan Allah ka tashi!" A burkice ya tashi, ya kunna fitilar wayarsa ya haskata, rumaisa ce a tsaye riƙe da hannunsa, tana kuka. Ayshercool 08081012143 *Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 A gigice ya tashi zaune yana tambayar rumaisa ko lafiya. Idanuwanta duk sun yo waje, sai sauke numfashi take yi, hannunta ɗaya riƙe da cikin ta, tana kuka. "Ki yi mini bayani, menene meya same ki?". "Cikina ciwo, zan mutu dan Allah ka taimakeni, wayyo mama" a gigice ya sauka daga kan gadon, ya kunna fitila hakse ya gauraye ɗakin. Tana durƙushe ta riƙe cikinta, hankali tashe ya buɗe wardrobe ɗin sa, ya saka jallabiya, ya ɗauki mukullin motarsa, ya tafi ɗakinta da sauri, ya ɗauko mata hijjabi, ya saka mata, ya riƙo hannunta. Da ƙyar take iya takawa, sai yarfe hannu take yi tana kuka, suka saukko ƙasan benen. Baba uwani na jin motsi but kamar fitar tusa ta fito, "Ranka ya daɗe lafiya? Meya samu ƴar ta wa?". "Ba ta jin daɗi ne, zamu je asibiti". "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya sameki haka?" Rumaisa ba ta amsa mata ba, ta cigaba da kuka. "Yallaɓai ko biyoku zan yi, ko za a buƙaci wani abu, ba ka tafi asibiti kai kaɗai ba, daga kai sai ita". Adam ya ce "A'a baba uwani, ki yi zamanki dan Allah, ba sai mun wahalar da ke ba, zan iya kula da ita". Ya saka rumaisa a mota, ya kunna ya fita. A cikin motar ma, she was very restless, ta rasa in da za ta sanya kanta, ta juya nan ta juya can, sai kuka take yi. "Ko dai wani abun ki ka ci ya ɓata miki ciki? Ko kuma abincin da suka yi ne ya saki ciwon ciki, na ji da yaji abincin". "Nima ban sani ba, cikina zai haɗe da ƙafata duk ciwo fa suke yi mini, na shiga uku". "Meye wani kin shiga uku kuma, ki yi addu'a, sannu". Wani private hospital suka je da yake kusa da su, aka buɗewa rumaisa file ya shiga da ita. Suka gaisa da likitan, ya tambayi abun da yake damun rumaisa. Ta ce masa "Cikina ne da ƙafafuwana, da bayana na farka na ji suna ciwo, na kasa bacci ciwo suke sosai". Cikin tausayawa likitan ya ce "Wajen ina ne yake yi miki ciwon?" Ta nuna masa mararta, ya ce "Kin fara al'ada ne?". Cikin kuka, ta ce "Meye ma al'ada?". "Period, ko in ce jinin al'ada" Adam ya bata amsa. "Ban sani ba ko na fara, amma lokacin da ka watsa mini ruwan kwata, na yi rashin lafiya, na yi fitsari da jini, yaya Aliyu ya ce wai Al'ada ne". Takawa ya ce "To kuma ruwan kwatar ne ya saka ki ka fara?" Ta ce "Eh, tun da ai ni da ban taɓa yi ba" Likitan yayi murmushi ya ce "Za a kai wata nawa da farawar? Kuma tun daga wancan lokacin kina yi ne, har zuwa yanzu duk wata?". "Ni fa na manta, cikina ne kawai yake ciwo" tayi maganar tana rimtse idonta. Adam ya ce "Za ayi watanni takwas". Likitan ya sake tambayarta, ko da ta yi fitsari ta kuma ganin jinin, ta ce masa a'a. Yayi counseling ɗin ta a kan personal hygiene, amma ba ta san ma me yake cewa ba. Ya rubuta mata magunguna da allurai, Adam ya karɓa ya ja hannunta suka fita. Ta bashi tausayi ba kaɗan ba, lokacin yana tare da aisha, tana gaya masa irin azaba da wahalar ciwon, ita da ta san ciwon kanta ma kenan, balle rumais da hankali bai gama isarta ba. A durƙushe haka take tafiya, ya zauanr da ita, ya sayo magungunan, suka je ayi mata. Sai dai ta ce Allah karta ba za a buɗe mata jiki a ganta a gaban Adam ba. Ga ciwo na cinta, ga zunzurutun wauta, in da Allah ya taimaka, nurse ɗin da take on duty mace ce. Ƙarshe ta tsaya ayi allurar nan, ba ta tsaya ba, dai da adam ya fita, daga waje yana jiyo kukanta, sai ka ce ƴar shekara biyar, saboda an yi mata allura. Sai dai ana gama yi mata allurar ta hau amai, kasancewar tun rana rabonta da abinci. Aikuwa Adam ya din ga yi mata faɗa, na rashin cin abincin da ba ta yi ba, sai dai gaba ɗaya hankalinta ba ya tare da ita, ƙarshe sai da suka dangana da saka mata ruwa. Haka Adam ya zauna da ita, har asuba a asibitin, aka gama yi mata abun da za ayi mata, na ƙarin ruwa da allaurai ya ɗauke ta zuwa gida. Suna tafe a hanya ta samu barci, dama tun suna asibiti yayi sallar asuba. Da ƙyar ya kaisu gida, saboda barccin da yake ji. Sai da suka isa gida ya tasheta, ta fita daga motar tana takawa a hankali. Baba uwani na jin tsayuwar motar, ta fito tana yi musu maraba, tana tambayar jikin rumaisa, Adam ya ce mata da sauƙi. Suka nufi step ɗin bene, baba uwani ta sake cewa "Takawa ko zan zo na taimaka da wani abun ne?" Ya ce "A'a ta warware, ciwon ciki ne dama, yanzu bacci za ta yi" Ta ce "To shikenan babu laifi, Allah ya ƙara lafiya". Ya amsa mata da Amin. Sai da ya raka rumaisa har ɗakinta, sannan ya juya ya fita, sai dai yana fita ya ji kukanta ta na faɗin "Na shiga uku, zan mutu". Da sauri ya koma yana tambayarta menene?. Ta ɗage doguwar rigar jikinta, Jini na bin ƙafarta. "Dan Allah ki yi wa mutane shiru da wannan koke-koken, maganin me zai yi miki?" "Jinina ne zai ƙare, idan ya ƙare mutuwa zan yi". "Ai gara ki mutun in huta, ki yi mini shiru ni, bari na yi wa baba uwani magana, ta zo ko da abun da zata taimaka miki da shi". Da sauri ta girgiza kai ta ce "Dan Allah kar ka kirata, ka kirawo mini su Yaya usman a waya, dan Allah" Kallonta yake, cike da mamakin wauta da rashin hankalinta. "Ke wai ya ki ke so na yi ne?, shikenan ba zan huta ba saboda na aureki? Tun da ba za a kirata ba, sai ki wuce toilet ki gyara jikinki". "Ban san ya zan yi ba, jinina kar ya ƙare ka mayar da ni asibitin". Guntun tsaki ya ja, ya wuce banɗakinta, ruwa ya haɗa mata, ya fito ya ce "Shiga" ba musu ta taka a hankali ta wuce banɗakin. Ya nuna mata yadda za ta yi, ta wanke jikinta, ya fita daga banɗakin, ya janyo akwatin lefenta, ya ɗauko mata pad, kasancewar lokacin da aka haɗa lefen har da ita a ciki. Ya ɗauke bedsheet ɗin daga kan gadon. Ta fito sanye da doguwar rigar da ta shiga da ita banɗakin, tana ta raɓe-raɓe. Ya kalleta ya ce "ƙazamar ina ce ke? Ba ta ɓaci da jini ba ki ka kuma sakawa?". "To ba kaya zan fito?" Ta yi maganar tana kawar da kanta gefe. Ajiye mata pad ɗin yayi, ya ɗauki bedsheet ɗin ya fice. Ya je ya dawo, ya tarar da ita ta canza kaya, amma pad ɗin na  in da ya ajiyeta. "Ba zaki saka bane?". "Ban iya sakawa ba, waccan ma su yaya ne suka saka suka bani" Kallonta yayi, kuma da gaske take maganar, ba wai wasa take ba. Ya nuna mata yadda za ta yi amfani da ita, ya sanar da ita, duk awa biyar zuwa takwas, ta yi wanka, ta cire pad ɗin ta ɗaure a leda, ta canza phant ta canza wata. Ta jinjina masa kai, ya fita ya bar mata ɗakin. Ba tare da ya rintsa ba, haka ya shirya fita aiki, ko karyawa bai yi ba ya sauka domin tafiya, ya cewa baba uwani, idan rumaisa ta tashi a tabattar ta ci abinci, sannan akwai bedsheet a washing machine, a wanke a shanya, a haɗa da kayanta da ta cire suna banɗakinta. Ta amsa masa da za ayi, sannan ya fice. Ko da baba uwani ta ciro bedsheet ɗin, ta shanya, kallonsa ta din ga yi, da in da jini ya shata, ta yi shiru da ta tuna a yadda ya tafi Ruma asibiti jiya. "Anya ba wani abun ne ya faru a tsakanin su ba, babu ko tantama ya haikewa yarinyar nan, amma dai wannan akwai jarababbe wannan ƴar tatsitsiyar ƴar? Wannan ba labarin da zan gaya wa Samha ba ne, ko Hajiya Jamila ƙarshenta ma na sha zagi". Babban abun da ya yi wa rumaisa daɗi, bai wuce da ta tashi ta tarar da iman ba, ta ce "Anty Iman, meyasa baki tasheni ba?" Iman ta ce "Ni na isa? Yaya ne ya ce lallai in zo, in tayaki zama ba kya jin daɗi, karatu nake yi an kusa yi mana screening na sauka". Rumaisa ta ce "Ni dama ki dawo gidan da zama, ina jin daɗin ganinki a gidan nan, tun da aka kawoni fa, ban ga mama ba, ranar da ki ka zo, su mai sunan baba su ka zo, ko zama ba su yi ba, suka tafi" "Eyya, kar ki yi kuka, baba uwani ta ce baki karya ba, ki karya sai na baki wayata, ki kira maman". Haka kuwa aka yi, rumaisa ta karya, ta karɓi wayar Iman dan kiran mama a waya, amma ba ta shiga, sai ta saka lambar mai sunan baba ta kira shi a waya. Tun a lokacin da ta yi masa kira na farko, tana neman rumaisa, ya gane lambar, kuma lambar take cikin kansa, ko da bai ɗaga ba ya san lambar iman ce, yana kallon wayar ta ƙaraci ringing ɗin ta, ta kaste yaƙi ɗagawa. Lambar Usman ta yi trying, shi ma sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga yayi sallama. "Saboda tsabar kun tsaneni, kun kawo ni, kun ajiye ni, ba wanda yake nemana mama ma taƙi zuwa ta gannu, kuma bani da lafiya ma" "Iyee, ko amsa sallamar ma ba zaki yi ba, sai wassafo mini ƙorafi?". "Mama taƙi ta zo ta ganni, ni na gaji da zaman gidan nan, dan Allah ku zo ku tafi da ni, gida nake so, kuma bani da lafiya". Usman ya ce "Ke ban son shirme, a hakan zamu zo gidan naki, ki na yi wa mutane kuka?  Meya sameki?". "Fitsarin jinin da nake ne na kuma yi, a asibiti fa na kwana, cikina ya din ga ciwo, jini sai zuba yake mutuwa zan yi idan baku zo ba". Maimakon usman ya tausaya mata, sai ya ƙyaƙyace da dariya, ya ce "Kin ci kai, Allah sarki girma ya zo". Cikin kuka ta ce "Yaya usy da gaske nake, a asibiti na kwana wallahi" Sai kuma ya daina dariyar ya ce "Ahha haba dai?". "Tun da baka yadda ba, bani mama mu gaisa". Usman ya ce "Maganar gaskiya mama ta tafi cikin gari, yi wa mutane bangajiya, amma idan ta dawo sai a kiraki". "To ai ba wayata ba ce ba". "Aliyu yana da lambar mijinki, zamu zo ma in sha Allah, Allah ya ƙara lafiya uwar gida sarautar mata" yayi maganar cikin zolaya. Ganin ba shi da niyyar ɗaukar maganar ta ta serious ya sanya ta katse wayar. *** "Ya ake ciki da maganar yaron nan ne, kwana biyu na jika shiru, babu wani update a kan moves ɗin sa ne?". "Ranka ya daɗe, ai babu wani sabon abu, ka san yayi aure kwanan nan, kuma kamar ma hankalinsa ba ya kan aikin a kanka yanzu, ko cikin Abujanma, ya fi watanni rabonsa da zuwa". "A'a fa, ka san yaron nan da wayon tsiya, kar in je lumbu-lumbu yake yi mini, yana wani binciken ta ƙarƙashin ƙasa, ko shirya wani abu da ban sani ba". "Babu abun da yake aiwatarwa, ba tare da na san motsinsa ba, a yanzu dai haka babu ranka ya dade". Ya juya ya kalli wakili ya ce "Khalifa, kai wurinka babu wani update ɗin". Khalifa ya ɗan sauke numfashi ya ce "Babu Daddy, sai dai ina nan ina ta bin diddigin sa fiye da yadda ka ke tsammani, babu wani abu da yake yi s kanmu, sai dai wani ƙishin-ƙishin da nake ji, wai yarinyar da ya aura, ita ta tserato da ɗan sa daga wurin masu garkuwa da mutane, amma bani da tabbas, an ce in jira a samu tabbacin hakan". Senator wakili ya jinjina kai ya ce "Duk yadda ake ciki ka sanar mini, idan har ita ɗin ce, ka samo mini tabbacin hakan, a kan lokaci". "To shikenan, In sha Allah daddy" *** A duk lokacin da rumaisa ta je canza pad, cikin ƙyanƙyami take yi, kuma a tsorace take da tunanin jininta zai ƙare, har sai da iman ta fuskanci wani abu, amms ba ta takura mata da son sanin menene ba, tun da ba ta gaya mata ba. Mai sunan baba kuwa wuni yayi yana kallon missed call ɗin, iman a wayarsa, yana tunanin me za ta ce masa haka, da har ta yi masa 3missed calls, ko tana nufin ta ce Haryanzu ba ta san wayarsa ba ce ba?. Gashi dai yana sane yayi ignoring kiran, amma yana son sanin dalilin kiran. Yau sai da takawa ya dawo, sannan iman ta fara shirin tafiya gida, rumaisa ta din ga yi mata magiya a kan ta kwana, amma ta ce ba ta gaya wa ammi ba, direba ya zo ya ɗauketa ya mayar da ita. Takawa ya dubi ruma da ta haɗe rai saboda Iman ta tafi ya ce "Ya jikin naki?". "Da sauƙi" "Kin sha magungunan ko kuwa?". "Na sha" ta amsa masa a taƙaice, bai sake kulata ba ya ƙyaleta, dan yanayin fuskarta ya nuna masa a fusace take, idan ya biye mata rashin kunya za ta yi masa. Mai sunan baba kuwa, missed calls ɗin nan a ransa ya wani, zuciyarsa na ta raya masa ya bi kiran nan, ko ya manta ya cigaba da sabgoginsa, sai ya tuna, yayi iya ƙoƙarinsa ya manta, amma ya kasa, yana ta tunanin menene haka mai muhimmanci da ya sanya ta yi masa missed calls har uku. Babban abun da ya ɓatawa iman rai, bai wuce yadda ta koma gida ta tarar da Jabir ba, ya kasa ya tsare a falo, suna hira da Ammi, yana ganinta ya hau rawa jiki, ya fara yi mata hira. Iya ƙoƙarin ta take yi, kar ammi ta fuskanci wani abu, dan haka ta ke amsa masa hirar. Ammi ta tashi ta bar musu falon, ta tafi ɗakinta, iman na shirin tashi ita ma, wayarta ta fara ringing, ba ta duba ba ta ɗaga ta saka a kunnenta, tare da yin sallama. Shiru yayi bai amsa ba, sai wani numfashi da yake saukewa a hankali, yana jin yadda murayar ta ta, ta daki zuciyarsa. "Hello, ba a jina ne, Assalamu alaikum" ta yi maganar cikin ɗabi'arta ta iyayi. "Missed calls na gani" yayi maganar cikin dakakkiyar muryarsa da take razanata. Sai da ta ɗan ruɗe, amma ta yi iya yin ta, ta haɗa nutsuwar ta wuri guda ta ce "Yaya Umar ina wuni?". "Lafiya ƙalau". "Dama Anty Rumaisa ce ta karɓi aron wayata ta kiraka, kuma ba ka ɗaga ba, ba intentionally na kira ka ba, ai ka gaya mini na daina kiran wayar ba tata ba ce, ka yi haƙuri dan Allah" ta ƙarasa maganar kamar za ta saka masa kuka. Ji yayi jikinsa har wani rawa yake yi, dan shi a rayuwarsa, idan ba mama da rumaisa ba, babu wata ƴa da yake keɓewa yayi wata doguwar magana da ita, ko ita rumaisan ba shiga shirgin ta yake yi ba, amma ya tsinci kansa da jin daɗin sauran muryarta. Amma da yake namiji namiji ne, cikin basarwa ya ce "Ina rumaisan take?". "Ɗazu ne na je gidanta, ba ta jin daɗi shi ne ta karɓi wayata, ta kira ka, amma ta ji sauƙi". "Shikenan" ya katse wayar. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, duk da muryarsa na razanata, amma ta tsinci kanta da jin daɗin kasancewa da shi ta waya. Wani guntun murmushi ta yi, tana ɗaga kai ta ga Jabir da Nusaiba duk ita suke kallo. "Iman da wa ki ke waya?" Jabir yayi maganar a hasale. "Kamar yaya? Yayan Anty rumaisa ne". "To meye alaƙarki da shi" ya sake yin maganar yana tsareta da ido. Tashi ta yi tsaye ta ce "Yayan matar wa na ce, kuma ni babu wani abu tsakani na da shi, ta ari wayata ta kira shi ne kawai". "Ina fa lura da yadda ya din ga bin ki da kallo lokacin bikin nan, idan ya ganni tare da ke ya din ga hararata". Ta girgiza kai ta ce "Gaskiya kai ne ka ga haka, amma ba hakan bane" ta wuce ta nufi ɗakinta. Jabir zai kuma magana, Nusaiba ta ce "Uncle J, ka bi ta a hankali, fushi da tashin hankali ba naka bane ba, ba abun da yake tsakaninta da mutumin nan, na riga na baka shawara, ka je wurin ammi kawai, ko ka gaya wa turaki, na san komai zai zo da sauƙi" sauke numfashi ya yi, ya tashi ya fice. *** Tun da Adam ya fara hawo wa step ɗin bene, yake jin ƙauri, yana hawa falon saman, ya tarar da ya turnuƙe da hayaƙi, kuma hayaƙin daga kitchen yake fitowa. A sukwane ya nufi kitchen ɗin, ya na zuwa ya tarar da rumaisa tana suyar wainar fulawa tana tari, Saboda ƙaurin manja. "Ke meye haka? Me ki ke yi?" Ta waiwaya ta ce "Girki nake yi" Da sauri ya ƙarasa yana ƙoƙarin kashe gas ɗin, dan tuni suka haɗa baki da iman, direbanta ya ɗuro mata. Tarewa ta yi ta ce "Girki fa nake yi na iya" "Matsa, ban ce kar ki kuskura ki ce zaki yi girki ba?" Buɗe masa flask ta yi ta ce "Ka ga fa, na iya" wainar fulawa ce ta yi saƙa mai kyau, sai ƙamshin attaruhu take. Ba ƙaramin mamaki ta bashi ba, amma a fili ya ce "Idan ki ka yi mini gobara a gida, sai na casaki". Ta ce "Eh na yadda" ya gyaɗa kai ya fice. Kusan awa guda, ya ma manta da batun rumaisa ya tuna kar ta yi wata aika-aikar, ya leƙa falo, ya hangota tana ta suɗar baki tana cin yaji. Ganin tana lafiya, ba wani abu da ya faru, ya sanya ya nemi wuri ya kwanta, dan a gajiye yake sosai. Sai dai bacci ya gagare shi, tunani daban-daban ya addabi kwanyarsa, ya rungume pillown sa, ya rintse idanunsa, ba ya son tuna yana da tarin matsalolin da ya kasa soloving ɗin su. Ga wani abu da yake bijiro masa ba gaira babu dalili. Tashi ya yi ya kunna fitilar ɗakinsa, ya tafi kitchen, sai dai ya tarar da rumaisa ba ta yi bacci ba, tana ta gyara abubuwan da ta ɓata, tana tsaye a gaban sink tana wanke-wanke. Bai ce mata uffan ba, ya ɗauki heater, ya zuba ruwa ya jona, ita ma ba ta kula shi ba, ta cigaba da aikinta. A ransa yake yabawa mahaifiyar rumaisa da yayyenta, dan a ƴan kwanakin da suka yi, ya fuskanci tana da ƙoƙarin tsafta. Tea yake son haɗawa, ga ruwa ya tafasa amma sai duru-duru yake yi. Ta kalleshi ta ce "Rumaisa, dan Allah tun da na ga kin iya girki, dafa mini tea, zan sha. Shi ne abu mai wahala a wurin ka, bari dai na taimaka maka, ai tun da na ga ka ɗauko kofi na san shayi zaka sha, a gida ma kusan kullum sai su Yaya Aliyu sun sha shayi da daddare". Ta taka kujera, ta buɗe wata drower, ta ɗauko Lipton, da kayan shayi, wanda bai san a in da ta same su ba. Ta zuba a cikin ruwan zafin, ta sake tafasawa, ta ɗauki ƙaramin flask ta juye masa, ta haɗa masa da kofi a kan tray, sannan ta ce "Gashi nan, kar ka damu ba sai ka yi mini godiya ba, dan na san ba za ka yi ba, muna da irinka a gidanmu. Idan ka gama shan shayin, ga omo da soso, ka wanke kofunan, kar ka bar mini kwanuka wani abun ya bi". Kamar soko haka yake kallonta, ta ɗauki wani ɗan bowl, ta zuba uban cabin da madara da sugar, ta fice. Washegari ta tashi da safe, tana aikace-aikacen ta, barira ɗaya daga cikin hadimanta, ta kawo abinci ta ce na takawa ne. Ta karɓa ta ajiye masa, dan da baba uwani ta gaya masa rumaisa ta ce a daina kawo abinci, cewa yayi su ƙyaleta su cigaba da kaiwa. Ɗakinsa ta shiga da kayan mopping, ta tarar yana banɗaki yana wanka, ta karkaɗe masa gadon, ta gyara ta kalli gadon bai gyaru sosai yadda yakamata ba, ta ce "Oho, ni a gidanmu babu gado sai katifa, hakan ma na yi ƙoƙari ai". Idonta ne ya sauka a kan side bed, in da ya sha shayin, nan ya bar kwanukan, "Kam bala'i, Wa ya bar wa kwanukan nan a nan?" Ja ta yi ta tsaya tana jiran fitowarsa. Rigar wanka ce a jikinsa, sai dai gaban rigar a buɗe yake, gashin ƙirjinsa ya kwanta saboda ruwa, da sauri ta kawar da kanta gefe. "Ya aka yi?". Ba ta kalleshi ba ta ce "Eh kwanukan da na ce idan ka gama shan shayin ka wanke na gani a nan". Ya ce "Eh, idan kin gama ki fita da su ki wanke" "Ni na sha maka da zan fita da su in wanke?" Ya kalleta ya ce "Me ki ka ce?" Ta girgiza kai ta ce 'Bakomai". "Oya kwashe su ki fita da su, ki je ki wanke, sannan kan na gama karyawa, ki shirya, zamu je gidan turaki". Ta ji daɗi za su fita, amma babban abun da ya bata haushi, bai wuce sakata fita da kwanukan da shi ya mora ba ita ba. Wata turkey abaya ta saka, blueblack fuskar nan fayau babu ko kwalli, ta yi ta shafa turare, dan akwaisu available a kan mudubinta, dan ko a gida ta saba, dan Abdallah har ɓarauniyar turare yake ce mata. Suna tafe a hanya, tana kallon titi, tana son gane hanya, dan so take wataran ta ɓalle ta tafi gida. A gidan turaki suka tarar da Jabir, da shi da Jamil ga kuma Zainab da Mummy, Samha ce ba ta nan. Rumaisa ta gaishe su, sai dai ba wanda ya amsa mata da mutunci sai Zainab. Adam ya ce "Zainab nema mana iso wurin mai girma turaki" ba musu Zainab ta tashi. Rumaisa da sun haɗa ido da Jabir take galla masa harara, haka Jamil da yake ta kallonta a wulaƙance. Aka yi musu izinin shiga wurin turaki, turaki yana ganin rumaisa ya fara murmushi. Ita ma Murmushin ta yi ta ce "Barka da wannan lokaci ranka ya daɗe". "Barkanmu dai ƴar albarka, ya gidan ya ƙoƙari?" Ta amsa da "Alhamdilillah" Adam har leƙa fuskarta yake, ya ga ko ita ce ta nutsu haka. Shi ma suka gaisa da Adam, Adam ya ce masa sun zo su yi godiya ne, tare da yi musu bangajiya na hidima da aka yi. Turaki ya yi musu nasiha sosai, mussaman ma Adam, a nasihar rumisa ba komai take fahimta ba, mussaman da ta ga da Adam ake. Bayan turaki ya gama, yayi musu addu'a sosai, Adam yayi ta godiya, ya ce masa za su je wani wurin daga nan. Rumaisa ta ce "Babana, yaushe zaka zo gidanmu, na iya abinci in dafa maka duk abun da ka ke so?" Yayi murmushi ya ce "Za a zo ne in sha Allah". Gudun kar ta fara sakin layi kamar yadda ta saba, ya sanya adam sakata a gaba suka fita, sai dai a wannan karon sai suka fita ta ƙofar da zasu fita haraba kai tsaye, ba tare da bi ta falon gidan ba, sai dai suna fita suka yi kiciɓis da Samha! Ayshercool. 08081012143 *Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Adam yayi ta maza ya ce "Au dama kina nan? Mun wuce su mama a falo ban ganki ba ai". Cikin matsanancin takaici ta ce "Meye na borin kunya kuma? Ai ba ka so ka ganni ɗin ba ne? Tun da har ka shiga ta falo, ka biyo ta nan za ka tafi". Rumaisa ba ta kula Samha ba, dan ba zata manta fuskar ta ba, ta mayar da hankali wurin tsinkar furanni da ke wurin, sai dai tana jin duk abun da suke faɗa. "Yanzu da ma adam a kan wannan abar ka wulaƙanta ni, ka ƙi ka aureni? Yanzu wannan abar wani abu ta fi ni da shi, yarinyar da ba ta kai a kirata mace ba ma, an ya ka yi mini adalci kenan? Soyayyar da na nuna maka tsawon shekaru shikenan ba ni da wata makoma?" "To ni idan ba mace ba mace ba ce, namiji ce ni?" Rumaisa ta yi maganar tana riƙe ƙugunta. Adam ya kalli rumaisa ya ce "Wuce ki je mota ki jirani" "To saman motar zan hau ko ƙarƙashin tayoyi? Tun da a rufe take". "Duk in da ya yi miki" kallon banza ta yi wa samha ta wuce. Samha tana ta tunanin a ina ta san fuskar rumaisa ma, ta kasa tunawa, ta ma fi cika ido a hotunan bikinsu, a zahiri kuwa ƙwaila ce ta gaske. "Yanzu abun da ki ka yi kin kyauta Samha? Da auren wuri aka yi miki, ko baki haifeta ba kin kusa, wannan ai salon ki janyo wa kanki raini ne". "Ban damu ba adam, ba raini ne a gabana ko akasin haka ba, ni batun soyayyaya ta ce a gabana, wallahi ka cutar da ni Adam". Adam ya ɗan yi shiru, sannan ya ce "Ban cutar da ke ba Samha, abun da nake son ki gane shi ne, komai muƙadarri ne na Allah. Daga haɗuwata da rumaisa, zuwa lokacin da na aureta, da zan gaya miki zaki gane aurena da ita ƙaddarar Allah ce". "Ba ka son ta kenan?" "Ba zan ce eh ba, kuma ba zan ce a'a ba, ki yi haƙuri ki cigaba da addu'a, idan da rabo sai in aureki, idan kuma babu ko yi haƙuri, ki auri wani, kar ki ce zaki cigaba da zaman jirana samha". Rumaisa kuwa ranta a ɓace, ta ƙarasa in da motarsu take, tana zuwa ta ga Jamil da Jabir a tsaye a wurin suna magana, ba ta kula su ba ta tsaya, tana hura hanci. Jamil ya ƙarewa rumaisa kallo ya ce "Lallai, Adam sai ka ce makaho, dan Allah ina mamora a tare da wannan yarinyar? Me wanna za ta tsinana masa a zaman aure? Yanzu wannan ya zaɓa ya bar Samha? Saboda wannan abar?". Jabir ya ce "Kai ba ka san komai ba ai, ba ta da kunya ne yarinyar nake gaya maka, kai ka ga wahalar da ta din ga bashi, ka san ita ta dawo da jaririn fulani, kan ta faɗi fulanin ma ta rasu, sai da aka kai ruwa rana, ba ta da kunya" Zabura Jamil ya yi ya ce "Kana nufin da gaske wannan yarinyar ce, ta dawo da yaron wurin aisha?". Jabir ya ce "Tambayeta ka ji" Juya musu ƙeya rumaisa ta yi, tana wasa da ƙasa da ƙafarta. "Ke, da gaske kin ga fulani, kin ganta a hannun ƴan bindiga, suwaye? Ya aka yi suka kasheta?" Yayi maganar cikin rikicewa yana kallon rumaisa,ya na jin tamkar yanzu A'isha ta rasu. Ɗaga kai Rumaisa ta yi ta kalleshi, ta yi guntun tsaki. "Magana nake yi miki, aisha ƙanwata ce, jami'in tsaro ne ni, ki gaya mini abun da ya faru, ko kuma ƙarya ne kawai haɗin baki ne?" Yayi maganar kamar zai kaiwa rumaisa duka. Sheƙeƙe rumaisa ta ce "To mijinta ma shi Adam ɗin ban gaya masa komai ba, balle wani kai, ba ruwanka da ni kuma, wallahi ka sake ce mini wannan abar, sai na yi maka rashin mutunci, mai na yi muku, ni na ce kar ya auretan? Wannan masifaffiyar matar na na ɗauka ma babar wasu ce". Daga nesa da ya tunkaro su, ya hangi rumaisa tana zazzaga masifa, Jabir ya riƙe hannun Jamil, ya ce kar ya yi magana. Adam ya ƙaraso ya ce "Lafiya kuwa?" Rumaisa ta ce "Ce mini yayi wai wannan abar, ni na ce kar ka auri waccan matar, da za su din ga ce mini wai wannan abar, shi kuma wannan har da ce mini mara kunya, me na yi masa na rashin kunya". Adam ya buɗe motar, ya ce wa rumaisa "Shiga ki jirani" Buɗe motar ta yi ta shiga ta zauna, tana cigaba da tura baki. Adam ya kalli Jamil ya ce "Sannu Jamil, kirkin ka har ya yi yawa, shikenan ita rayuwa ba za a karɓi ƙaddara ba, ka ƙi halartar ɗaurin aurena, kuma ka ƙi yi mini Allah ya sanya alkhairi". "Allah sanya alkhairi saboda ka auri wannan abar?" Yayi maganar yana nuna motar adam. Adam ya sauke hannun Jamil ya ce "Ko dan albarkacina, yakamata ka tausasa harshe a kan ta, matata ce, kuma bana son zumuncinmu ya samu matsala saboda son zukatanmu". Jamil ya ce "Adam ka na da ƙwarin gwiwar yin wannan maganar? Dama yarinyar nan ita ce ta zo da jaririn aisha, ka ce aisha a hannun 'yan bindiga ta mutu, ya aka yi ita ta kuɓuta, wani mataki ka ɗauka, na san dole ba za a rasa wani information daga bakinta ba, menene dalilinka na ɓoye mana?". Nan da nan Adam ya hasala ya ce "Kai ma kana zargin ni na kashe fulani na yi tsafi da gawarta ko? To na yi, idan wani bayani ka ke da buƙatar ji daga bakinta, ka je ka tambayi mai girma turaki". Cikin sauri Jabir ya ce "Jamil, bai kamata ka faɗi irin wannan maganganun ba, da na san haka abun zai zama, da ban gaya maka ba, takawa dan Allah ka yi haƙuri" Bai ko tsaya ba, ya wuce mota, ya buɗe ya shiga, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi. Sai da suka ɗan yi nisa sannan ya cewa rumaisa me suka ce miki?. "Su wa?" Kallonta yayi, ta ga alamar babu wasa a idonsa, ta ce "Tambayata yayi, wai ya aka yi na san anty aisha, ni kuma na ce ban sani ba" Jinjina kai kawai ya yi, ya cigaba da tuƙinsa. Wani store yayi parking, ya ce ta fito su shiga. Ta fita ta bishi tana kallon wurin. Suka je ɓangaren jakunkuna ya ce ta zaɓi jakar makaranta. Haushi ne ya kamata, dan ko zancen makaranta ba ta so. Ya sai mata kayan karatu da rubutu, da takalma, jakar ma uku ya saya mata, sannan ya sakata a mota suka tafi. Gidajen ƴan uwansu ya din ga zagayawa da ita, suna gaishe su, sai dai rumaisa ta ƙule da yadda wasu suke karɓarta, tare da nuna ita yarinya ce, ta yi masa ƙarama da aure. Babu wanda ya sake ƙona mata rai, kamar hajiya Lubabatu, wato mahaifiyar Jabir, matar Galadima mai ci a yanzu. Ban da tana ganin girman matar, ta yi sa'ar mama, da babu abun da zai hana ta zageta, dan ma Adam yana ta kareta, amma matar ta ci zarafinta, duk da bakomai take fahimta ba. "Ragowar ƴan bindiga aka kawo mini kenan, lallai takawa, ka yi jihadi sai fatan Allah ya biya ka". Adam ya ce "Ba ragowa ba ce ba, kuma aurenta ba ni na yi jihadi ba, ita ta yi, tun da kun san waye ɗanku, amma ta amince da aurensa". Hajiya Lubabatu ta yi dariya ta ce "Yo ba dole ba, ai ko a turu kake ɗan mu yana da arziki da sarautar da za a aure shi domin sa, kuma a zauna da shi, kwaɗayin abun duniya ne kawai". Ba dan Ammi ta matsa, lallai ya zagaya da rumaisa, ya nuna mata familynsa ba, ya kuma yi musu bangajiya ba, da babu abun da zai sanya ya zo gidansu Jabir, wurin mahaifiyarsa. Adam ya ce "To Hajiya, ina ga bari mu koma, akwai in da zamu je". "Ahh haba dai, na saka a ɗora muku girki ai". "A'a Alhamdilillah, a ƙoshe muke". Hajiya Lubabatu ta ce "Gaskiya ban ji daɗin wannan zuwan ba, yakamata a kawo mana ita ta wuni, da haka tana shiga cikinmu, za ta san yadda matan sarakai suke rayuwa, dan na san ba sani ta yi ba". Adam ya ce "Bakomai ana koya mata" Wata hadimar Hajiya Lubabatu ta ƙaraso, ta bawa hajiyar wata leda. Ta karɓa ta miƙawa rumaisa ta ce "Amarya ga wannan ba yawa, kya sai tsintsiya, sai na sake kawo ziyara, tun da rabona da gidan, tun washegarin kai ki, mun ce a bamu ƙyalle mu tabattar da abun da aka auro mana, an yi mana wala wala". Rumaisa ta sha kunu, ta ƙi karɓar ledar. "Ki karɓa mana" rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a" Hajiya Lubabatu ta ce "Takawa, ba ka gaya mata, masarauta ba ma kyauta ace a'a ba, rayuwar masarauta, ba kamar ta sauran gama garin mutane ba ce". Ya kalli rumaisa da ke kusa da shi ya ce "Ki karɓa, ba a mayar da kyautar matan sarakai". "Bana so" ta faɗa yadda shi kawai zai ji. Ya saka hannu ya karɓi ledar ya ce "Godiya take, kin san amaryat ta wa akwai jan aji, da gudun raini, kyauta ko da ga ni take, sai ta tantance, gaku sarakai, amma ta fi ku sarauta" yayi maganar a baibai, cike da mayarwa da Hajiya Lubabatu martani. "Ikon Allah, da alama auren haɗi zai koma na soyayya, ai labarin zuciya a tambayi fuska takawa". Adam ya ce "Eh to, ba zan musa miki ba, amma hausawa suka ce ɗan hakin da ka raina.." Murmushi kawai hajiya Lubabatu ta yi, tana yi musu su gaida gida. Rumaisa tuni ta yi waje, dan idan ta cigaba da tsayuwa, matar nan tana washe baki, tana gaya mata magana, ba abun da zai hana ta zageta. Shi kansa adam mood ɗin rumaisa ya gani, ya san a ƙule take kamar ta fashe dan takaici, la'asar ta riga ta yi sosai, ya ga idan suka koma gida, shi ficewa zai yi, ya san zama za ta yi, tayi ta ƙunci a gidan, dan haka ya wuce da ita da ita gida. Ammi ba ta nan, sai Nusaiba da Iman, da kuma Sabir, ganin Sabir ya sanya ya manta wani ɓangare, na fushin da take yi. Ba ta fiye shiri da Nusaiba ba, ta fi yi da Iman, dan haka da ita suke ta hirarasu. Iman ta saka aka kawo musu abinci, nan iman take bata labarin, bayan ta dawo gida mai sunan baba ya kirata, ya ga missed calls ɗin ta, a lokacin take gaya mata, yadda suka yi da shi, da ta kira shi tana tambayar sa, ina take. Ruma ta din ga dariya ya ce "Baban mama, sa ba ka dariya sai hamma, kirarin da mama ke yi masa kenan, shi dai kar a raina shi". Iman ta ce "Anty rumaisa gara haka fa, ina son in ga namiji mai aji, rashin kintsi ko ga namiji bai yi ba ai". Suka cigaba da dariya, iman na nunawa rumaisa hotunan biki. Nusaiba kuwa kallon iman take, yadda fuskarta take nuna jin daɗin hirar mai sunan baba da suke yi. Nusaiba a ranta ta ce "Iman, wannan ba irin mutumin da ya dace ki so bane, ya fiye zafi, larurarki kuma tausasawa take buƙata, kuma wataƙila ba zai amince da ke ba, idan ya san ke wacece, uncle J ɗin dai, shi ya san k wacece, shi zai iya zama da ke, wannan wahalar sarrafawa zai yi miki'. Ana idar da sallar magariba, Adam ya dawo, ya ce rumaisa ta tashi su tafi, ta ce ya bari ta ga ammi, ya ce a'a so yake ya je je ya huta, haka ta tashi ta bishi, sai dai suna barin gidan, ta tuna abun da ya faru yau, ta ji ɓacin ran ya dawo mata. Ko da suka je gida, baba uwani ce ta fito tana yi musu maraba, sauran hadiman sam ba sa abun da take yi, rumaisa har mamaki take yi, kawai yau sai ta din ga ganin dariyar baba uwani, kamar dariyar hajiya Lubabatu da ta din ga yi musu ɗazu, tana yi musu dariya, kuma tana ci mata mutunci. A ƙasan benen ta bar shi, shi da baba uwani, ta hau saman benen ta wuce ɗakinta, ta shiga banɗaki, ta duba pad ɗin jikinta, tana fatan ta ga babu komai, dan ta gaji da zubar da jinin yake yi, amma ta ga ɗan kaɗan, kuma adam ya ce mata, idan ba ta saka, ta ga babu abun da ya zuba a kai ba, kar ta kuskura ta ce za ta yi salla, dan kamata yayi tana salla washegarin da period ɗin ya zo mata. Ta yi wanka, ta canza wata, ta saka kayan barcinta ƴar rigarta sai wando, ta hau kan gado ta baje, dan ta gaji. Ba ta yi tsammani ba, bacci ya yi awon gaba da ita. Washegari da safe, rumaisa da kanta ta sauka kitchen ɗin ƙasa, ta tarar da barira da Asiya, suna aikace-aikace. Suka hau gaida rumaisa ta ce "Ni fa ku daina gaishe ni dan Allah, kunya ku ke bani, doya zan ɗauka". Asiya ta ce "Wani abun za a girka miki ranki ya daɗe". Ta ce "A'a, ni zan yi da kaina. Ta ɗauki abun da take so, ta koma. Ta yi ta gyare-gyaren ta, sai dai abubuwan da suka faru jiya, suka cigaba da damunta. Ta saba Adam da wuri yake tashi ya fita, ta samu ta gyara ɗakin, amma ta ji shi shiru. Dan haka kai tsaye ta nufi ɗakinsa ta shiga babu ko sallama. Sai dai tozali ta yi da shi a tsaye, daga shi sai gajeren wando, ya ajiye towel a gefen gado alama wanka zai shiga. Ta kawar da kanta gefe ta ce "Ka saka kayanka, zan yi gyaran ɗaki, ko ka fito waje, idan kuma ka yafe shikenan". Girgiza kai kawai ya yi, ya ce "Zo ki gyara". Kanta a ƙasa ta shiga, ta fara kwashe kayan duk da ya barbaza tana mita. "Wai sai ka ce wani Sabir, komai sai ka watsar da shi" bai ce mata uffan ba, ta cigaba da mita. "Ga kuɗinki nan a kan mudubi, 100k ne, hajiya Lubabatu ta baki jiya". "Allah ya kiyaye, ba abun da zan yi da su, ka ɗauke ni ka kaini, ana ci mini mutunci, amma nayi-nayi ka ƙi ka kaini gidanmu na ga mama. Wallahi matar nan ba dan ta kusa zama tsohuwa ba, babba ce da sai na yi mata rashin mutunci, ina fa gane baƙar magana, shi ma wannan Jabiru yake da wannan ɗayan, suka din ga ce mini wannan abar. Ni na tsani wannan jabir ɗin, shi kuma ɗayan mai kama da mugwaye. Ita kuma wannan matar har da ce wa, wai ni ba mace ba ce, Hansai take ko Hasana, duk kana ji ana ci mini mutunci. Ta manta ai ni dama ƙanwar maza ce, a namiji aka haifeni, sai da ga baya da na fara girma aka lura ashe ni mace ce, ni na ce kar ka aureta da za a din ga zagina? to wallahi ba ruwana da wata masarauta, duk wanda ya yi mini, sai na rama, a wayance matar nan ita ma tana nufin, ni ƴar talakawa ce na aureka saboda kana da kuɗi fa take nufi, ba ta san taimaka wa na yi na aureka, saboda ammi ba da kuma Sabir" sosai take masifa, domin dama, dama take son ta samu ta amayar da abun da yake ranta. Takowa ya yi zuwa gabanta, tana tsaye a gaban mudubi, sai iya shege take yi, tana masifa. Sai kuma tsoro yakamata,ba yau ta saba ganin namiji ba riga ba, idan da sabo ta saba a gida, amma ganin adam a haka, ya sanya take jin, tamkar ta aikata wani jibgegen saɓo. "Ke dama mace ce nan a haka?" Ai ba ta san lokacin da ta ɗago ta kalleshi ba. Ya janyota gaban mudubin sosai ya, ya cire hular kanta, gashin nan na ta baƙi wuluk, ta yi parking ɗin sa. ya ce "Wannan ɗan gashin naki ne kawai zai sa a san ne ba namiji  ba ce ba, kamar namijin haka ki ke ai, taimakawa na yi na aureki, dan ba yadda zan iya, amma kalleki fa sosai a mudubi" yayi maganar yana nunata a cikin mudubi. Ɗaga kai ta yi tana kallonsa. Ya ce "Eh mana, ke ba kwalliya ba, ke dai gaki nan, behaviors ɗinki ma na mazan ya rinjayi na matan. Wasiƙar da ki ka rubuta mini, ki ka ce na taɓa miki nono ni ban gansu ba ai. Kawai da ma sharrinki ne, abun bai fi girman wake ba, wata ƙwaila da ke, ai ba ƙarya aka yi ba, dole kowa ya tausaya mini, look at you. Da ma na ce nawa sun  fi naki baki yadda ba, look at me, bai fi naki ba?" Yayi maganar yana shafa ƙirjinsa. Rumaisa ji ta yi tamakar ƙasa ta tsage ta nutse, sai ta nemi duk wasu kalaman rashin kunya, da fitsararta, ta rasa, ta rasa me ma za ta yi, ta saka hannu ɗaya ta rufe ƙirjinta, ɗaya kuma ta rufe fuskarta. "Meye a wurin da ki ke rufewa, abu fayau kamar filin ball, ni aure zan yi nan gaba kaɗan, dan da gaskiyarsu, ba mace ba ce ke, haryanzu dai namijin ce, ba a gama tantancewa ba, macen ce ko namiji, ga rashin kunya, ga fitsara da faɗan tsiya, duk ke kaɗai, ba zan iya ɗauka ba da wanne zan ji?". Dummmm haka rumaisa ta ji maganar, jin ya ce wai zai ƙara aure, saboda ba ta da nono, idan ba batsa ba, meye haɗin sa da wannan abu?. Gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, ta ma rasaa wani muhallin, yakamata ta ajiye wannan maganganun da adam yake yi mata, ba tare da kunya ko tsoro ba. Ya kuma haɗe rai ya ce "Wuce toilet ki haɗa mini ruwan wanka" "Ruwan wanka kuma sai ka ce wata baiwa?". "Ba zaki wuce ba kenan?" Kamar ta saka ihu, haka ta tafi tana ƙunƙuni, ya bi bayanta, ta shiga banɗakin, sai dai ba ta san yana ƙofa a tsaye ba. A Tsakiya banɗakin ta tsaya, ta riƙe ƙugu, cikin ƙwalla ta ce "Lallai ma, wai ni rumaisa ake yi wa wannan abubuwan, wallahi da sake". Idonta ya sauka a kan toothpaste ɗin da adam yake amfani da shi, a wani tube mai kyan gaske. Ta ɗauka ta buɗe, ta lakata ta saka a bakinta. "Dan mugunta ni ya bani mai yaji, shi kuma nasa mai zaƙi, saboda ga wadda dauɗa ta kashewa haƙora, ban yafe ba duk abun da yake mini". Da maganganun da take, da toothpaste ɗin da take sha, duk yana kallonta, ta ajiye ta nufi bath ɗin. Nan ma wata mitar take yi "Wato ma kawai an kawo masa baiwa, na yi gyaran ɗaki, ya ci abinci na yi wanke-wanke, kuma wai ni zan haɗa masa ruwan wanka, ga shower ya kunna ya yi wankan, amma ba zai iya ba, ko da waye yake haɗa masa ruwan  oho? Zai ga tsiya, wallahi ruwan zafi zan haɗa, idan ya ƙone gobe ba zai kuma sakani ba. Saboda tsabar wulaƙanci, mutumin nan ma bashi da kunya, kuma ammi ba ta san yana yin maganganun batsa ba, a haka kamar na Allah, kuma da alama ba ya yi wa kowa sai ni, to wallahi ni ina da tarbiyya ". Ta din ga surutu a banɗaki, kuma ko da wasa ba ta waiwaya ba, balle ta ganshi, ta kunna ruwan zafi, fiye da rabin bath ɗin nan, sannan ta kunna na sanyi, ruwan sai tururi yake yi, ta ce "Allah ya sa yana zuwa kawai ya shiga, gobe ba ya kuma sakani aiki ba, bayan ya gama ci mini mutunci". Ji ta yi an rufe ƙofar banɗakin, da sauri ta tashi ta waiwaya tana kallonsa. Ya shigo kamar zai wuce ta, ya shammaceta, ya danƙota, ya shiga cikin bath ɗin da ita. Ihu ta kurma, jin zafin ruwan, ga kayan jikinta nylon ne, ya sanya yatsansa a kan leɓensa ya ce "Shhhhh, ai gara mu ƙone tare". Kiciniyar tashi ta hau yi, amma ya riƙe ta sosai a jikinsa, ya din ga ɗibar ruwan, yana zuba mata a kanta. Ayshercool. 08081012143 *Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 "Na shiga uku, mama, dan Allah a taimakeni, ƙonewa nake yi fa" "Ai da ni ki ka yi niyyar ƙonawa, sai dai mu ƙone tare" ya haɗa hannayenta ya riƙe da hannu ɗaya, ya cigaba da zuba mata ruwan har a fuskarta. Ta dinga mutsu-mutsu ta tashi, amma abu ya gagara, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ta kasa, sai ta hau kuka, tana yi masa magiya, a kan ya ƙyaleta. "Har da sha mini toothpaste ko, saboda ke ƙazama ce". "Ni ban sha ba". "Ai ina jin duk abun da ki ke cewa, idan mu ka gama ƙonewar, sai mu yi jinya tare " Cikin kuka ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, fata ta zata kwashe, dan Allah ka yi haƙuri". "Ai baki isa ba, ni zaki ƙona da ruwan zafi ki huta ko?". "A'a ba haka nake nufi ba, dan Allah ka yi haƙuri ". "Ni sharifi ne, ba abun da ruwan zai yi mini, ke da ki ka shirya ramin muguntarki, gashi kin faɗa". Ganin ta na kuka wiwi, ya sanya ya cikata, ta tashi da sauri, ta fice daga bath ɗin, jikinta na tsuma ta tafi ɗakinta, ta tuɓe kayan a tsakar ɗakin, ta zura da gudu toilet, ta sakarwa kan ta shower, jikinta yayi ja, ta zauna a toilet ta cigaba da kuka tana faɗin "Wallahi ba zan yafe ba, wuta balbalin bala'i" Sai da ta daina jin zafi, sannan ta fito ta ɗaura towel. Duba jikinta take yi, tana duba wa ta ga, ko fatarta za ta kwashe, cikin ikon Allah ba abun da ta yi. "Wato shi ba ma ya jin zafin ruwan, amma ni ya ƙona ni, zai gane ni ya taɓa, sai na rama, har da wani rungumeni saboda tsabar rashin sanin abun da ya dace, Innalillahi Allah ya sa kar a gane idan na fita, ya kuma riƙe mini hannu na kasa guduwa". Ta saka hannu ta toshe bakinta ta ce "Astagfirullah, Allah ka yafe mini". Sai kuma ta tuna abun da ya yi mata na cewa, ba ta da nono. Ta kalli jikinta a mudubi, ta ɗan bankaɗa towel ɗin ta kalli ƙirjinta, ta ce "Saboda tsabar saka ido, wai nonona ne bai fi wake ba, mutumin nan ya cuceni, wato kallona ma yake yi haka? To saboda ba ni da su ake cewa ni ba mace ba ce? To na ga ma ba sai mutum ya haihu ba suke da amfani? Amma bakomai, Allah ya sa su fito mini, na huta da gori. Kai Astagfirullah, in rasa mai zan roƙi Allah sai wannan abun, Allah na tuba ka yafe mini. Amma wallahi sai na faɗi abun da mutumin nan yake yi mini, tun wuri ayi mini tsakani da shi, a taka masa burki, kar ya sake rungume ni". Sai da ta gama surutanta ita da mudubi, sannan ta tashi ta shafa mai ta saka kaya. Ta daɗe a ɗakinta, sannan ta fita, ta tarar shi tuni ya fice, ta kwaso kayan gyaran ɗakin, ta ce yayi wa kansa dan ba za ta gyara ba. Ba uwani ce zaune a ɗakin su, tana waya, ita da Samha. "Wai haryanzu babu sani muhimmin bayani a kan in da zamansu ya dosa, ba kya bani wani update". "Ranki ya daɗe, su suna saman bene, mu muna ƙasa, bana iya sanin me yake faruwa". "Dole ki din ga bibiya ki sani, bamu saka kin yi faɗi tashi, ta amince ki je gidan ki zauna ba domin ki je ki miƙe ƙafa ba, biyanki zamu din ga yi, dole ki yi mana aiki yadda ya dace, ba kuma iya leƙen asiri ba, ki yi iya ƙoƙarin ki, wurin haɗa husuma a cikin gidan nan, ki nuna mata kin fita daɗewa a duniya, dole ta fito ta bar gidan nan". "In sha Allah uwa ɗakina, za ayi yadda ki ka ce, kar ki damu". "Ina saurarenki" Samha ta katse wayarta. Rumaisa kuwa kitchen ɗin ƙasan ta shiga, Aisya da barira suna ta wanke-wanke. Rumaisa ta ce "Ina kwananku" Cikin sauri suka risuna suna gaisheta. Rumaisa ta ce "Dan Allah ku daina gaisheni, wai ba ku ga ni ƙarama ba ce?". Asiya ta ce "Ranki ya daɗe, ai Allah ya riga ya baki girma dole a biki, kuma ke matar basarake ce, dole a girmamaki". Rumaisa ta yi murmushi ta ce "Kunya ku ke bani ne" "Ba wani abu, ko wani abun za ayi mikk?" Ruma ta ce "A'a, girkin rana zan yi, kar ku dafa abinci da mu, ku yi daga naku, sai na sauran masu aikin". Barira ta ce "To, amma ba abun da zamu tayaki?". Rumaisa ta ce "Bakomai, Anty Asiya, dan Allah ɗauko mini mai, ki tayani na kai sama, bari na tafi da wannan kayan". Asiya ta ce to. Rumaisa na shirin fita, baba Uwani ta shigo tana tsuma, ta ce wa rumaisa "Amarya ba kya laifi, har mai gidan ya fita ne?". "Eh, ya fita". "Ina fatan dai ba wata matsala ko? Idan da wata matsalar zaki iya gaya mini, ni uwa ce a wurinki, kuma kin bar shi ya saukko shikaɗai, ai kamata ya yi ace ki na raka shi har mota" Murmushin gefen baki rumaisa ta yi, ta wuce ta bar baba uwani. A kitchen ɗin ta, Asiya ta sameta, ta ajiye mata man, har za ta tafi rumaisa ta ce "Anty Asiya, bari na baki hijjabi, da ke da Barira, a cikin kayan lefena suke, sun yi mini tsawo sosai". Asiya ta buɗe baki ta ce "Wane mu ranki ya daɗe, kayan lefenki fa". Ruma ta ce "menene a ciki, kyauta zan baku, sun yi mini tsawo".  Ta tafi ɗakinta, ta ɗaukko hijjabai a akwati ta kawowa Asiya. Asiya ta din ga godiya, ruma ta ce "Dan Allah ki daina yi mini godiya, har kin saka na ji kunya, ba fa ni na saya ba, nima bani aka yi". Asiya ta ce "Haka ne, duk da haka dole na yi godiya, sannan dan Allah ranki ya daɗe, ki din ga ɗabi'ar matan sarakuna, girmanki ne dole a biki, kuma duk hukuncin da ki ka yanke a gidan nan dole a bi shi, amma wani abu nake son gaya miki, ban san ya zaki ji ba". Rumaisa ta ce "Gaya mini bakomai". "Ki yi hankali da taka tsantsan da baba uwani, amma kar ki ce na gaya miki dan Allah". Ruma ta ce "Ai ni dama ba ruwana da ita, bana son dariyar da take yi mini, bakomai in sha Allah na gode" Asiya ta juya ta sauka tana murna, yarinya ƙarama mai halin manya, ta san ta yi kyauta. *** "Amma Jabir kana ganin abun da Adam ya yi ya kyauta, idan Fulani matarsa ce, mu kuma ƴan uwanta ne, shi jami'in tsaro ne nima haka? Dan meyasa bai ɗauki wani mataki a kan ɓatanta ba, meyasa bai gaya ba? Daga yin garkuwa da ita ya aka yi ya ɓoye wa duniya? Ya yi wa kansa adalci kenan, idan yana da gaskiya, ai tuntuni yakamata ya bayyana Yarinyar nan, ayi bincike a kanta, ko za a samu wani information ɗin". Jabir ya ce "Easy mana, haba Jamil, ina ga mun fi kowa sanin Adam, a ɓangaren taurin kai da zurfin ciki, duk familyn nan albarka, kowa ya san shi a kan haka, kai waye ya ce maka a zaune yake tun da ta ɓata? Adam ya shiga cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, tun bayan ɓatanta, kuma ba wai yana zaune ne kawai ba, da shi da gayen nan Bashir, da wasu daga ƴan sandan garin katsina, suka yi ta ƙoƙari a kan lamarin". "Amma ya aka yi kai ka sani, ni ban sani ba? Ina yayanta kuma jami'in tsaro kamar shi?" "Saboda na fi ka kusanci da shi, na san halinsa tsaf, dan haka na fika iya zama da shi, shiyasa nake sanin abun da ba ka sani ba, yanzu abun da ya kamata shi ne, kamar yadda ya ce ka tamabyai mai girma turaki, ka yi masa zancen ka ji mai zai ce?". Jamil ya ce "Ai gaba ɗaya ma kaina ya kulle ne ma, amma zan zurafafa bincike a kan lamarin nima". Jabir ya ce "Better". *** Ta window rumaisa ta leƙa, ta hango motar Adam, kusan biyar da rabi lokacin, Murmushin mugunta ta yi, ta koma ɗakinta ta yi zamanta, a sababbin litattafan da ya saya mata, na makaranta da za ta fara zuwa, ta ɗauki ɗaya da fensir, tana zane-zanenta. A gajiye yake sosai, ya tarar da abincinsa a ɗakinsa, yanayin yadda aka ajiye abincin ya bashi mamaki, har da jug, jikinsa gaba ɗaya babu daɗi, dan haka ya yanke shawarar fara yin wanka, sannan ya ci Abincin. Yayi wanka, ya sauya kaya, ya zo ya zauna, ya fara buɗe jug ɗin, yayi arba da ruwan famfo a ciki, shi da yake ajiye cartons na ruwa, da lemuka, ya buɗe abinci ya ga shinkafa fara ƙal, ga man ƙuli ga dunƙule da yaji. Wani irin ƙululun takaici, ya ƙule masa wuya, ba ƙaramar yunwa yake ji ba, kuma ba ya cin abinci da mai da yaji. A fusace ya tashi ya fita, ya sauka ƙasa yana kiran baba uwani. Ta fito a rikice tana tambayar ko lafiya?. "Meyasa za a dafa mini abinci mai da yaji a gida? Idan akwai abun da babu, ba na ce a din ga gaya mini ba, dan me za a dafa mini mai da yaji?". Ta shiga tafa hannu ta ce "Wallahi ranka ya daɗe laifin matarka ne, babu yadda ban yi da ita ba, ta ce ita za ta yi maka girki, na ce mata ba ka cin abinci da mai da yaji, amma yarinyar nan ta ƙi yarda". Asiya ta kalli baba uwani, suna ƙasa basu san ma me ruma ta girka ba, balle baba uwani ta hanata, amma ta ce ta hanata ba ta hanu ba. A fusace ya koma saman benen, baba uwani ta lallaɓa ta bi bayansa, tana cigaba da salallami. A falo ya tarar da rumaisa ta fito, cikin fushi ya kalleta ya ce "Muzuru ne ni da zaki dafa abinci da mai da yaji ki ajiye mini?". "Papa meye a ciki, abinci ne fa?". "Shut up! Na yi kama da wanda zai ci abinci da mai da yaji ne?". Baba uwani ta ce "Ayi haƙuri mai gida, ba za ta sake ba, rashin sani ne, in sha Allah zan nunnuna mata abubuwan da yakamata ta sani, duk laifina ne, yarinta ce take damunta" "Ba wani yarinta baba uwani, ai na ce girki ba huruminta bane ba, ta bari a din ga yi amma kasancewar, kunnen ƙashi ne da ita, ba za ta ji ba". Kuka rumaisa ta saka ta ce "Kuma sai na gaya wa ammi kana yi mini faɗa, idan na yi abu gwaleni ka ke yi". Taski ya yi ya , tafi ɗakinsa, yana barin falon rumaisa ta yi wa bayansa gwalo. Ya fito da mukullin motarsa, ruma ta ce "Papa ina zaka?" Banza yayi mata ya sauka, baba uwani sai bashi haƙuri take yi. Bayan ya sauka baba Uwani ta kalli rumaisa ta ce "Ranki ya daɗe, ai ba a...." Rumaisa ta kasteta ta hanyar cewa "Idan mun yi faɗa, ba sai kin nema mini afuwa ba, yarinya ce ni ba mahaukaciya ba, kuma ina sane na yi hakan, na san ba ya cin abinci da mai, an gaya mini" galala baba uwani ta bi rumaisa da kallo, dama baki ne da ita haka? Kamar ba daga bakinta maganganun suka fito ba. "Amma ƴar nan idan ki ka fusata shi, yana da larura fa". Rumaisa ta kalleta ta ce "Wace larurar?" Sai kuma ta tuna katoɓarar da ta yi ta ce "A'a bakomai". "Shikenan tun da ba zaki gaya mini ba , idan ya dawo sai na tambaye shi wace larurar ce da shi?". Baba uwani ta ce "Na shiga uku, da wasa nake yi miki, ba ya son ɓacin rai ne dai, dan Allah kar ki gaya masa". Rumaisa ta ce "Aini duk abun da aka gaya mini sai na bi diddigi, bana mantuwa" ta wuce ta bar baba uwani tana gumi da dana sanin maganar da ta yi. *** Ƙishirwar son ganin Umar faruk, ta din ga damun zuciyar iman, hotunan biki din ga shiga, tana kallon hotunan duk da ya fito a ciki. Cikakken namiji mai cikar zati kamala, duk da ba fara'a yake yi ba, son kowa ne ƙin wanda ya rasa, namiji mai matuƙar jan ajinsa da tsare gida. 'Na shigesu, me yake damuna ne?' 'son wanda bai san kina yi ba, wanda ba ki da damar ki nuna masa hakan, wands tsantseninss da kamewarsa, da matsanancin kwarjininsa ba za su bari ma ya gane hakan ba' wata zuciyar ta bata amsa. Tashi zaune ta yi ta ajiye wayar, tare da furta 'Allah ka iya mini" ga gefe guda Jabir yana ta hura wuta, wanda har Ammi ta fara ganewa. Ta sake ɗaukar wayar, ta shiga what's app ɗin ta, da ta yi saving number sa, da Yaya Omar, ta shiga chat, sai dai ta rasa mai za ta rubuta, ta buɗe hoton ka dp ɗin sa, hotonsa ne shi da hassan ɗin sa, wato yaya Abubakar. Ta sake ajiye wayar, tana ajiyar zuciya. *** Baba uwani addu'a ta din ga yi, Allah ya sa kar rumaisa, ta tambayi Adam, dan sai yanzu ta fara lura, yarinyar a tsaye take, gata dai yarinya amma alamu sun nuna ba ta ji. Sai da aka yi sallar isha'i, Adam ya dawo, sai dai abun mamaki, ya tarar da abincin a ɗakinsa, amma a wannan karon har da miya, da salad da komai aka shirya masa. Bai kula abincin ba, dan ya ciko cikinsa a gidan ammi. Ya zauna babu jimawa, sai ga rumaisa ta shigo da sallama. Ya shareta, ya fara ƙoƙarin buɗe laptop. "Sannu da zuwa" "Zo ki kwashe abincin nan, ki fita da shi". "Da miya ce fa yanzu". "Ba na ci" Ta yi dariya ta ce "Na sha gaya maka, ka daina yanke hukunci da zuciyarka, ka din ga yi da ƙwaƙwalwarka, na san ba ka cin abinci da mai da yaji, Iman ta gaya mini, to in gaya maka na yi miya, ina sane na baka da mai da yaji, na san faɗa za ka yi, ka yi zuciya, na san halinka ai tas, to ranawa na yi, soyanin da ka yi da ruwan zafi da safe" ta yi maganar tana haƙiƙancewa. Yayi mata shiru, bai ce uffan ba. "Kuma saura abubuwan da ka ke yi mini, duk sai na rama". "To, idan kin gama, ki kwashe abincin ki je ki san yadda za ki yi da shi" Ba ban haƙuri, ta kwashe ta fice abun ta Ya dafe kansa, rumaisa gaba ɗayanta danger ce, yana duba nasihar ammi ne a kan yayi haƙuri da ita, duk abun da za ta yi masa, y din ga duba girman sadaukarwar, da ta yi masa. Gefe ga shawarar da bashir ya bashi kan Ya aure ta, a kan ya bi ta a hankali su saba, dan ya samu bayanan da yake son samu a wurinta, idan ya tsananta ba zai samu ba. "Allah ka shiga lamarina" ya furta a hankali ya tashi ya bi bayanta. Ya ganta tana hawowa sama, bai san me ta je yi ƙasa ba, ya ce "Ki shirya, gobe in Allah ya kaimu da safe, zan kai ki makaranta" Ɓata fuska ta yi, dan sam ko zancen makaranta ba ta so. Ya juya ya koma ɗakinsa. Da asuba ta yi wanka, ta yi salla, tana tantama dai-dai ma ta yi wankan, ko ba daidai ba, dan ba za ta iya tunawa complete yadda mama ta koya mata ba, kuma ita ba za ta tambayi takawa ba. Haryanzu rumaisa tana ɗokin sababbin kayan kitchen, dan haka haryanzu ba ta gaji da shiga kitchen ta yi girki ba. Ta dafa tea, ta fito da biscuit, ta nufo falo, takawa ta gani a kan dining, ga kayan karyawarsa a kan dining, baba uwani kuma durƙushe a gabansa, ba ta san me take ce masa ba. Kai tsaye ta nufi dining ɗin, ba ta kula su ba, ta je ta hau saman dining table abun ta, ta fara ƙoƙarin haɗa tea. Baba uwani ta yi shiru, ta daina maganar da take yi. "Barka da safiya ranki ya daɗe". Rumaisa ta ce "Yauwwa sannu". "Meye haka, zaki hau saman dining?". "Idan na zauna a kan kujera, bana jin daɗin zama a kan tebur ɗin, gara na hau sama, ya fi daɗi, ka san babu a house". Ya girgiza kai ya ce wa baba uwani, "Je ki kawai, ma ƙarasa maganar". Tunani rumaisa take yi, me baba uwani take gaya masa, da ba za a faɗa a gabanta ba. "Haɗa mini tea zan karya, ki je ki ɗauki jakarki mu tafi" "Ni na kawo maka da zan haɗa maka, ita wadda ta kawo makan ta haɗa maka mana" Hannu ya saka ya janyo ta ta baya, ya jawota ta ƙeya tana kallo fuskarsa. Ya ce "Da ni ki ke?". "A'a da kaina nake" ya hankaɗata ta tashi zaune, tana ƙiƙƙifta id. Ta janyo kayan tean, ta fara haɗa masa, tana yi tana tura baki ta miƙa masa. Ita kuma ta yi ƙerere a kan table, tana karyawa. Ba ta gama na ta ciye-ciyen ba, ta ji ta ƙoshi, ta tashi ta kwashe kayan. Sai wurin ƙarfe tara da rabi, sannan suka fita, ya tafi kaita makaranta. Tsari da ginin makarantar, ba ƙaramin burge rumaisa ya yi ba, ta tabattar wa da kanta, akwai banbanci a tsakanin makarantarsu, da wannan, hatta ajinsu, basu da yawa, ga kujeru masu kyau, ga fankoki ko ina ga kayan wasa, ajinsu har da projector, da ake haska musu komai, duk wani abu na koyo da koyarwa akwai makarantar nan, makarantar ta burge rumaisa. Kan takawa ya tafi, sai da aka kai shi har ajin su rumaisa, ya kalli ruma ya ce "Yau ga ki a makarantar ƴaƴan ɓarayi da suke sace muku kuɗi suna karatu. Sannan ba zan lamunci ina biyan kuɗin makaranta in tarar ba kya karatu ba, kullum zan din ga tambayarki me aka koya muku. Ban da surutun banza, da ciye-ciye. Na bayar da ordern abinci a wani restaurant, za su kawo miki abincin break, tun da kin ce ke ba za a dafa a gida ki ci ba". "To, kai zaka zo ka ɗaukeni, ko gida zan tafi?". "Dama ke ki ka kawo kanki?" "Ahh na san hali ne, kar ka tafi ka barni, ka ga kayan wasa a makarantar nan, zan sha lilo, idan na din ga hawa ina sufa...." "Ba shi na kawo ki yi ba, karatu zaki yi, wuce ki shiga aji" Rumaisa ta shiga ajin, tana ƙarewa ajin na su kallo. *** Takawa kuwa da ya tafi hanya, Bashir ya kira a waya, ya ce masa zai shiga bamfai su haɗu su yi magana. Haka kuwa aka yi, ya haɗu da Bashir, sai dai bai shiga ciki ba, a shiya fito haraba, suka haɗu. "Allah ya taimake ka, ya amarya yaushe za a gayyaceni cin abincin amarya ne?" Yayi maganar cikin zolaya. Adam ya ce "Idan ma da wasa ka ke yi, to ta iya girki". "Ahha haba dai?" "Ka bari kawai bashir, yarinyar nan caza mini kai kawai take yi, Ammi ta bata masu aiki, amma ta ce kar su kuma dafa abinci su kai mata, wai kar ayi mata asiri. Jiya fa horon yunwa ta yi mini, mun samu saɓani da safe, na fita aiki ta hana ayi girki, wai ta dafa mai da yaji ta bani, na yi magana, wai ramawa ta yi. Wallahi haƙurina na daf da ƙarewa, duk maganar da ta zo bakinta, idan zan mutu haka za ta faɗa mini" "Adam, sai ka yi haƙuri, ka san yadda yarinyar nan take tun farko, kuma ka san ba shiri ku ke yi ba, dole ka yi haƙuri da ita, idan ka nuna mata halin muzurai, ba zaka samu abun da ka ke so ba". Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na gaji ne, gashi familynmu, sun fara yar mata da maganganu, ka san ba ta da kunya ba za ta yi shiru ba. Ga matar da take tare da ita tana yi mana aiki, baba Uwani na san zaka santa, ita ma sun fara faɗa, ita duk abun da yake dama to ita hagu za ta yi". Bashir ya yi dariya ya ce "A dai ƙara haƙuri, zai wuce in sha Allah". "To, Allah ya sa, gata can dai na kaita makaranta. Jabir ya gaya wa Jamil rumaisa ce yarinyar da ta tsinci sabir, ya kuma tayar da jijiyoyin wuya a kan, dan me na ɓoye masa yana jami'in tsaro kuma yayanta. Abun da nake so da kai shi ne, ko da zance zai zo, ya san tare da kai mu ke bincike, kar ka gaya masa komai". Bashir ya ce "In sha Allah, ba zan bayar da wata ƙofa na kowane bayani ba, sai mun yi nasara in sha Allah". "Allah ya amince, na gode sosai " suka yi sallama Adam ya tafi. Da daddare bayan ta dawo, tana ta murna, ta sha lilo har ta gaji, sai dai ba ta gane turancin da ake yi, dan malamansu har da turawa. Tana ɗakinta, ta baje textbooks ɗin aka bata tana kallon hotuna, Adam ya shigo hannunsa riƙe da wayarsa, rumaisa na ɗaga kai ta kalli takawa, ta yi sauri ta rufe idonta, da hannunta, saboda daga shi sai dogon wando babu ko riga a jikinsa. "Gaskiya ka daina shigo mini ɗaki tsirara" "Dalla karɓi" yayi maganar a kausashe, ta ɗan zame hannunta ɗaya ta karɓi wayar, ta duba ta ga kira ne, ta saka a kunnenta. "Ƙanwar maza, ƙanwar maza". "Yaya Aliyu, ashe baku manta da ni ba, tun ina kuka har na daina". "Saboda kin samu duniya ko?". Ruma ta ce "Ba wata duniya, ina mama? Ba za ta zo ba ko?". "Mijinki sun yi waya da mama, ta ce kar a kawo ki" "To Meyasa, bani ita". Mama ta karɓi wayar ta yi sallama ta ce "Ƴar auta". "Mama shi ne ki ka ƙi zuwa, kuma ki ka ce kar a kawoni". Mama ta ce "Ke tafi can, ba gaki nan ba abun da ya same ki ba". "Ni dai dan Allah ki zo, ko in ta yi masa kuka, tun da kin fi son sa" Mama ta ce "Shi wa?". "Mijina" ta bata amsa kai tsaye. "Sannu mara kunya, ai dama ban ce nawa ba ne naki ne". Ruma ta ce "Mama albishirinki". "Goro" "Kin ga haɗaɗiyar makarantar da ya kaini, kamar a turai, kin ga liluka kuwa? Ga fankoki har da malamai turawa, baki gani ba, baki taɓa zuwa gidana ba ma, gidana haɗaɗɗe, duk ya sai kayan daɗi ya zuba mini" Mama ta ce "Sai ki je ki same shi, ki yi masa godiya, dan na san baki yi ba" "Taɓ, mama yaushe zaki zo to?" "A'a ni ba zan zo gidanki ba, amma dai idan ya kawo ki shikenan". Za ta yi wa mama taɓara, mama ta kashe wayar. Rumasai ta share hawayenta, ta bishi ɗakinsa, ta tarar yana banɗakin, ta ajiye masa wayarsa ta fice. Kwanci tashi asarar mai rai, yau juma'a rumaisa kwana biyar da fara zuwanta makaranta, kuma wata guda cif, da ɗaura mata aure. Takawa ya ɗaukota daga makaranta, ta ga ya canza hanya, maimakon su tafi gida. "Ina kuma zamu je?". "Sayar da ke, na yi tsafi da ke, kamar yadda aka ce na yi da aisha" ya bata amsa. "To ai dai bani na faɗa ba ko?" Tana gane gidansu zai kaita ta ce "Yeee zan ga Ammi zan ga Sabir da Anty Iman". Da haka suka ƙarasa, cikin murna ta riga shi shiga sashin Ammi. "Oyoyo ga ruma" "Ammi, kin ga na fara zuwa makaranta, kin ga jakata" Ammi ta yi murmushi, ta ce "Masha Allah, Allah Ya sanya albarka" Iman ta ce "Congratulations Anty rumaisa". "Thank you anty iman" Takawa ya shigo, ya tarar da rumaisa a kusa da ammi tana nuna mata litattafanta. Wato rumaisa ko kumyar nan ta sirka ba ta da ita. "Ammi ina Sabir?". Ammi ta ce "Yayi bacci" "To bari in gama nuna miki litattafaina, sai na je na ganshi". Ammi ta dubi Adam ta ga yanayinsa, kamar mara lafiya, ta ce "Takawarka lafiya, ya aka yi ne? Na ga yanayin ka kamar akwai damuwa" Ya ce "Bakomai" tare da kashingiɗa. Ta kalli rumaisa ta ce "Rumaisa, ko akwai matsala ne?". Ruma ta gyara zamanta ta ce "Eh, dama ƙararsa zan kawo miki tun rannan, dan dai bamu zo ba ne, na ce sai na gaya miki, kin ce duk abun da yayi mini na gaya miki". Ammi ta ce "Subhanallah, meyafaru?" Ya kalli rumaisa yana jiran ya ji me za ta ce "Wai cewa yayi zai ƙara aure, saboda ba ni da nono!!!" Tirƙashi!. Ayshercool *Chat me on what's app, to subscribe yours 08081012143, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank* Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Sai da falon yayi tsit na wucin gadi, Adam bai taɓa tunanin wautar rumaisa ta tsananta har haka ba. Ji yake tamkar yayi layar zana ya ɓace daga wurin. Ta kuma cewa "Ammi, kuma yana yawo babu riga a cikin gidan nan, kuma alhalin ni ba muharammarsa ba ce, Yaya usy ya ce yayyena ne kawai muharramaina, amma yake yawo ba riga, ina kallonsa, ko kunya ba ya ji". Wani kallo ya yi wa rumaisa, amma ta share shi ta ce "Ai dama na rantse sai na faɗa mata, ammi ta ce duk abun da ka yi mini na rashin kyautawa na gaya mata. Hmm ni  ko za a shekara nawa idan aka yi abu bana mantawa, ina riƙe da shi a zuciyata, ina sane sai yau na ce bari na gaya wa ammi". Ammi ta yi murmushi cike da dattaku ta ce "Haba dai, wace irin kishiya ana zaman lafiya, tsokanarki yake yi kawai, wanda yake da wannan zuƙeƙiyar yarinya, ina ruwansa da wani ƙara aure. Kuma in dai saboda wannan abun ne, rai dai an fille wa fara kai, muna zaune Allah zai kawo su". "Ammi ai hijjabi zan koma sakawa, ya daina saka mini ido, dama na ce gara in gaya miki, ba zan gayawa mama ba, saboda na fuskanci yanzu mama ta fi son sa a kaina, cewa za ta yi ƙarya nake yi, kuma ita ta ce duk wanda ya gaya mini maganar banza, wadda ta saɓa da tarbiyyar da take yi mana, in je in gaya mata. Shiyasa nake gaya mata komai, amma na san a wannan karon da zan gaya mata abun da ya yi, ba zata yadda ba". "Da gaskiyarki kam, mama ta yi iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyyar ku, bai kamata ta rushe ba, Allah ya cigaba da dafa muku, bar mini litattafan naki na cigaba da gani, duba ɗakina, ko Sabir ɗin ya tashi, zamu yi wani sirri da ke". Rumaisa ta tashi ta nufi ɗakin Ammi, ka sa haɗa ido Adam ya yi da ammi, ji yake kamar ya zama guguwa ya bar wurin, saboda takaici da kunya. "Takawa" ya ɗan ɗaga kai amma bai kalli ammi ba. "Ka din ga sanin me zaka gaya mata, tun da ta ce ko za a shekara nawa ba ta manta abu, na ga hakan a cikin idonta, a hankali zaka nusar da ita abun da ya shafi sirrin aurenku naku ne, ta daina faɗa, na san kana haƙuri amma ka ƙara nan gaba zaka ci ribar hakan in sha Allah". Ya jinjina wa Ammi kai ya tashi ya nufi ɗakin ammi, bin bayan rumaisa. Ammi ta ce "Dan Allah kar ka yi mata wani abun, Allah ya taimake ka, daga ni sai ku ta faɗa, Iman ta riga ta tafi amsa waya, kar ka ce zaka yi mata wani abu". "Babu abun da zan yi mata, Sabir kawai zan gani, a nan za ta wuni, a haɗa masa kayansa, da shi zamu tafi, zan kaita gidansu gobe in Allah ya kaimu za su wuni a can, ba ta taɓa zuwa gida ba". Ammi ta ce "Masha Allah, babu laifi" Rumaisa tana zaune a gaban sabir, da yayi ruf da ciki a kan gado, yake ta bacci, sai shafa sumar kansa take yi tana murmushi. Da hannu ɗaya ya ɗaga rumaisa ya juyota tana fuskantar sa. "Me na yi maka?". "Ban sani ba, ke wace irin yarinya ce sai ka ce na'ura mai ƙwaƙwalwa, kanki gaba ɗaya baya gaya miki abun da ya dace, iya abun da aka zuba miki shi ne yake aiki a kanki, ammi fa sirikarki ce, ya dace ki gaya mata wannan maganar?". Ta kalleshi ta ce "Meye wani sirika kuma, ni ammi babata ce, haka mama ta gaya mini, ka ci sa'a da ba komai na gaya mata ba, har da cewa nonona bai fi girman wake ba, duk wannan rufa maka asirin da na yi ba ka gode ba, ga  gingimen asirin da na daɗe ina rufa maka" Adam ya dafe kai ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ba dai aure ba, zan ƙara aure ba zan zauna da ke ba kamar namiji ba, ba zan iya ba daga nan ki je ki cigaba da faɗa" "Ni ba zan kula ka ba baban sabir, na san haushina ka ke ji saboda na faɗi abun da ka ke yi, ni da kai idan na ce zan yi maka nasiha, ba yadda za ka yi ba, amma yanzu na san idan ammi ta yi maka faɗa zaka yadda" Rumaisa ta zubawa sabir ido, Ammi ta shigo, ta ce "Maman sabir, Haryanzu ba ki gama ganin sa ba?". "Wallahi kuwa ammi, bana gajiya da kallonsa ni ai". Ammi ta zauna a gefen gado ta ce "Zo ki zauna a kusa da ni mu yi sirri ƴar auta". Rumaisa ta tashi ta zauna a kusa da Ammi, Ammi ta ce "Kin ga dai ba kya so ya yi miki kishiya ko?" Rumaisa ta ce "Eh". "Meyasa ba kya so?". "Kai, ammi duk mata kowa sai na ji ta ce ba ta son kishiya, shiyasa nima na ce ba na so". "To ki saurareni ki ji, Abun da nake nufi da duk abun da ya yi miki na rashin kyautawa ki gaya mini, ba yana nufin ki din ga faɗar sirrin aurenku ba, ya ce mini da wasa yake yi miki, kin ga kin sa ya ji babu daɗi". Ruma ta ce "Ammi, ba dan ya ji haushi na faɗa ba, kin ga tsoro nake ji kar na yi wani abu da idan mama ta ji, ba zata ji daɗi ba, ta ce na watsar da tarbiyyar da ta yi mini". "Ba za ta ce haka ba, ai shi mijinki ne, sannan kar ki sake ki faɗi irin wannan a gaban wani kin ji?" "To ammi, in Allah ya yarda". Ammi ta dafa kafaɗarta ta ce "Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya sa kin fara makaranta a sa'a, idan aka kwana biyu mai koya miki girki zan ɗauko, har gida ta din ga koya miki ". "Ammi na iya girki fa, ki tambayi iman ki ji, har shi papa ya san na iya" Ammi ta ce "Waye papa kuma?" "Baban Sabir " Ammi ta yi murmushi, ta ce "Masha Allah, Allah Ya albarkaci aurenku" Rumaisa ta yi gum ba ta amsa ba, dan ita auren nan ya isheta. Rumaisa ta dage ta bi Iman kitchen, har da ammi a yin girki, sai dai ammin ya jinjinawa basira irin ta rumaisa, da ka ga yadda take gudanar da girkin zaka san, ta horu. Wuni ta yi tare da ammi, ga iman ga sabir, jin su take tamkar wani ɓangare na rayuwarta, da ganinsu kawai ke samar mata da nishaɗi. Da yamma, rumaisa ta silale ta fita harabar gidan, ba tare da sun sani ba, ta din ga zagaya fulawoyin gidan, da manyan bishiyu. Wani zomo ta gani, fari tas da shi, yana tsalle-tsallen sa, ga sauran tsuntsye da suke kaiwa suna komowa. Da sauri ta bi zomon, tana son ta kama shi, sai dai ta ga ta ɓullo wani wuri. Yana zaune a kan fararen kujeru, gabansa da litatafai, da system, ya tattara nutsuwarsa sosai a kan abun da yake yi. Bayansa ta gano ta ce "Papa" a hankali ya waiwayo ya kalleta, ta ɗan tsura masa ido, sai kuma ta ce "Laa ashe ba papa ba ne kai ne, na gane ka, da ka taɓa sawa na shigo gidan nan" ta yi maganar tana ƙarasawa in da yake. Ya ce "Wow, ashe zamu sake haɗuwa, sannunki, ya ki ke?" "Lafiya ƙalau" ta ƙarasa maganar tana zama a kujerar da ke facing ɗin sa. "Yau ya aka yi aka bari ki ka shigo, har ki ka zo nan?" Da ɗan mamaki ta ce "Wa zai hanani shigowa, to shi ya kawoni" Mahmud ya ce "Shi wa?" "Baban Sabir, ba ka san yanzu mijina ne ba?" Ya ɗan yi turus, sai yanzu ya gane zancen da Mummy suke yi ita da su Samha ɗazu, amma bai gane ba, kasancewar tun da ya dawo sai yau ma ya fito. "Da gaske ke adam ya aura?". Rumaisa ta ce "Hmmm, ya aka yi baka sani ba? Ba a gidan nan kake ba, ba ka zo bikinmu ba kenan?". "Ina ƙasar waje ai, can makaranta, labarin bikin kawai na ji". Cikin mamaki rumaisa ta ce "To ta yaya kuna gida ɗaya, amma ba ka sani ba, wai ku ba ƴan uwa ba ne?". "Eh, kowa babarsa daban". "To, ku ƴaƴan kishiyoyi ne?". Yayi dariya, tambayarta ta yi yawa amma ya ce "Eh". "Taɓ to ni wallahi ba za ayi mini kishiya ba, amma to dai meyasa ba ka zuwa wurin su, baka san yayi aure ba?". "Ni ma ba ya zuwa wurinmu" Ruma ta ce "Ai papa sai fatan Allah ya shirya shi". "Ke ma yana yi miki halin na sa kenan, na rashin kirki?" "Hmm, ai ba dan Sabir ba ko, ba zan aure shi ba, amma dai ya sakani a makaranta mai kyau na ji daɗi". Mahmud ya tattara nutsuwarsa a kan ta ya ce "Da gaske dai, ke ki ka dawo da jaririn nan?" "Wai meyasa ƴan dagin nan naku, suka damu da lamarin nan ne? Wato an rainani ko? To anty aisha da kanta ta bar mini jaririn nan, kuma har da zobunanta da ɗankwalinta, ta bani, ni fa bana damuwa da kowa sai ya yadda da ni a duniyar nan, malaminmu ya ce idan Allah ya yarda da kai, ka huta, shiyasa ni ban damu da kome za a ce a kaina ba". Mahmud ya yi dariya ya ce "Wow, i like your confidence " "Wai kai ya sunaka ne?". "Mahmud" ya bata amsa, ɗan turus ta yi tana kallon sa, "Dan Allah da gaske?" Ya ce "Eh" Ta ce "Innalillahi, sunan babana, sunan ɗa na" ya ce "Shikenan na yi ƴa, na zama daddynki" Ta yi dariya ta ce "yauwwa to ka taɓa zuwa ka ga ɗa na? Ranar nan na ce ka je wurin ammi ka ganshi". "Zan je wataran". Rumaisa ta ce "A'a, yanzu dai mu je in ga mamanku, ita ce ban taɓa gani ba, kai ma sai mu je ka ga ɗa na, mai sunan ka". Mahmud ya ce "mijinki ya huta kallon Tv, ke kaɗai kin isa ba shi dariya". Ta ce "Taɓ, sai ka ce wata cartoon, mu je ka nuna mini ita" ya tashi tsaye, yayi gaba, ya jagoranci rumaisa har tsakiyar falon Mummy. Ya ce "Mummy, ga amaryarku fa ta ce na kawota ta gaida babata" Gaba ɗaya suka juya suna kallon rumaisa da ke bin su da kallo. Samha ta fara ganewa a cikin su, ta kalli Fauziyya da ruƙayya, sai dai suna haɗa ido da Mummy, jikinta ya yi sanyi, gaban Mummy kuma ya yi mummunar faɗuwa. Mummy ta ce "Wace wannan?" Samha ta yi tsaki ta ce "Matar Adam ce, saboda asara, kalli abun da ya kwaso saboda ba ya gudun abun kunya". Mahmud ya kalli Samha ya ce "Ba ruwanki, ba wurinki na kawota ba" ya kalli rumaisa ya ce "Daughter, ga mamana nan" "To ya na ga ba ka kama da ita, kana kama da ammi?" Ji yayi wani irin gumi ya tsatstsafo masa ta kafar gashin jikinsa. Mummy cikin jarumta da iya duniyanci ta ce "Ikon Allah, da ba a kawo mini ita mun gaisa ba, kai ka kawo mini ita, takawan ne ya ce ka kawo ta mu gaisa?" Mahmoud ya ce "A'a, cewa ta yi zata zo ta gaida babata". Fauziyya ta ce "Tirƙashi, ashe da muka ganta a wurin dinner ta fi cika ido, ni Wallahi ban gane ta ba ma" Samha cikin ƙuluwa ta ce "Mummy wai meyasa ki ke wani sakar mata fuska, meye alaƙarta da ke, tun da ba ɗanki take aure ba, kuma ba ayi niyyar kawota ta gaishe ki ba?" A fusace rumaisa ta ce "Baiwar Allah wai me na yi miki ne? Kullum ki ka ganni sai kin zageni, ba ruwanki da ni, ni ba wurinki na zo ba". Mahmud ya ce "Samha ba ruwanki da ita please, ki ja girmanki, daughter ga mamana". Rumaisa ta kalli mummy, ta risuna kamar yadda ta ga ana yi ta ce "Barka da wannan lokaci " Mummy ta ce "Barkanmu dai, kuna lafiya?". "Lafiya ƙalau" "Ya mijin naki, ya Sabir? Ko da yake fushi nake yi da mijinki, ba ya zuwa in da nake, kuma ba ya kawo mini ɗan naki, Allah sarki fulani, ashe tare aka yi garkuwa da ku?". Rumaisa ta yi shiru, ba ta ce komai ba. Mummy ta ce "Ruƙayya, ki saka a kawo mata abinci". "A'a na ƙoshi, yanzu muka gama cin abinci da ammi". Cikin ƙarfin hali Mummy ke magana, domin wani irin bugu ƙirjinta yake yi, har hakan na neman bayyana a fuskarta. "Ni ma ai babar takawa ce, ki zauna mu yi hira mana, da takawa, da aisha, duk ƴaƴanmu ne, haka muka ji rasuwar ta, mun shiga tashin hankali da ruɗani, babban abun takaicin yadda ta haihu a hannun 'yan bindiga, abun bai yi mana daɗi ba". Maimaita rumaisa ta amsa mata, sai ta tashi ta ce wa Mahmud "Daddy mu tafi mu je ka cika mini naka alƙawarin" kallon rumaisa suke yi, da tunanin anya ma ba ta da taɓin hankali kuwa? Abun da ake tambayarta daban, abun da take yi daban. Yayi murmushi ya ce "To mu tafi, tun da kin ga mamana, kin gaisheta". Rumaisa ta ce "Eh, Mummy sai anjima " "To amarya, sai mun zo gidan naki kuma" Allah ya kawo ku. Mahmud ya nuna mata Fauziyya da ruƙayya ya ce "Wannan ƙannena, ga Fauziyya ga ruƙaiyya" Kan ya ce wani abu a kan Samha ta ce "Ita kuma wannan na santa, mai zagina ta na ce mini ƴar aba, na santa a gidan baba farin rawani, mai girma turaki, baban anty aisha, shikaɗai ya yi mini mutunci a gidansu". Yayi murmushi ya ce "To shikenan mu je" suka fita. Samha ta tashi zaune ta ce "Na shiga uku, na rasa me ma zan yi? Kaina ya gama kullewa". "Jikina ya na bani akwai wani abu ɓoyayye a game da yarinyar nan, dole zan ganta a karo na biyu, kuma ya zama dole baba uwani ta sanya mini ido sosai a kan su" Fauziyya ta ce "Ji munafuka kai, wai Mahmud ba ya kama da ke, kin ga idonta a tsaitsaye" Mummy ta ce "Na gani" nan suka cigaba da tattaunawa a kan abun da yakamata su yi a kan rumaisa. Ammi kuwa sai neman rumaisa suke yi, basu ma san in da ta yi ba, ammi har hankalinta ya ɗan fara ɗagawa. Rumaisa kuwa da suka fito harabar gidan, sai surutu take yi wa Mahmud, kamar dama can sun saba, ya fi takawa sauƙin kai da sakin fuska, a wajejen harabar sashin ammi ya tsaya ya ce "To shikenan, ki gaishe mini da takwarana". Ta kalleshi ta ce "Haka muka yi da kai, ba na gaida mamanka ba, ni ma ka zo mu je ka gaida tawa" Ya ɗan yi jimm yana kallon rumaisa, "Dan Allah haba daddy, ni fa a gidanmu ban san babana ba, sai yayyena su bakwai, komai nake so suna yi mini, dan Allah mu je ka ga Sabir". "Ki shiga ki ɗauko shi, ki kawo shi na ganshi". Ta noƙe kafaɗa, kawai ya tsinci kansa da bin rumaisa. Ba Ammi ba, har iman sai da ta razana, ganin Mahmud a filin falonta, shi kansa tsayawa ya yi yana bin su da kallo, rabonsa da falon nan, kusan shekara da wani abu, da Ammi ta neme shi, ta nemi alfarmasa kai tsaye ya ce ba zai yi ba. Ammi ta ƙure shi da ido, kamar yau ta fara ganinsa. Kallo ɗaya ya yi wa ammin, ya sunkuyar da kansa, ƙasan zuciyarsa yana tuna abun da ya yi mata na ƙarshe da ya kasa mantawa. "Ashe ka dawo, ya makarantar?" Ba tare da ya ɗago kai ba ya ce "Lafiya lau" Ruma ta ce "Ka zauna mana" ta nufi in da Sabir yake wasa da kayan wasansa, yana ta rarrafe yana ɓarna, ta ɗaukko shi ta kawo masa shi. Ya karɓi sabir, ya zauna da shi a jikinsa, ta kalli sabir ta ce "Waye wannan?" Sabir ya ƙura masa ido, Mahmud wani murmushi ya saki, ya shafa kan Sabir, wata irin ƙaunar yaron ta shiga ransa, da yake jin tamkar daga jikinsa ya fito. Har aka yi dambarwar nan aka gama, bai taɓa ganin Sabir ba. Cikin murmushi ya ce "Na yi kama da babanka ko, nima babanka ne" Su Nusaiba kamar tv, haka suke kallon Mahmud da rumaisa. Ruma ta ce "Ba papa ba ne, uncle ne wannan" Mahmud ya ce "A'a Daddy dai" ya miƙe da Sabir a hannunsa ya nufi hanyar waje yana faɗin "Allah ya bani  ɗa ba mata" Ruma ta bi bayansa tana cewa "Ai wallahi gara in bar maka takawa da in bar maka Sabir" Ammi ta ce "Kun ga ikon Allah, me rumaisa ta gaya wa yaron nan ya yarda ya zo in da nake?" Nusaiba ta ce "Wallahi ammi ni ma mamaki abun ya bani, wancan karon fa, kalli yadda aka kai ruwa rana, kan ya zo kiran da ki ka yi masa, bai kuma zuwa ba, kin ga ikon Allah yau shi ne har cikin falonki, kai lamarin baiwar Allah nan yana ɗaure mini kai" Kasa jurewa Ammi ta yi, ta fashe da kuka, nan da idonta ya yi ja. Iman ta ce "Ammi dan Allah ki yi haƙuri, ki cigaba da jurewa, jikina ya na bani komai ya kusa zuwa ƙarshe" "Allah ya sa, ina fatan hakan". Yauwwa share hawayen, iman ta yi maganar tana gogewa Ammi hawayen fuskarta. Mahmud kuwa ba abun da yake sai dariyar shirmen rumaisa. "Ka ga daga nan, ba zan ɗara ko ina ba, sai ka bani ɗa na, daga gani sai ka ce zaka tafi da shi, to in gaya maka yau gidanmu zamu tafi da shi, sai ranar Litinin za a dawo da shi". "Ta yaya zaki kula da shi? Kema baki wuce a kula da ke ba ai" "Zan iya, wanka ne dai, sai in saka ko baba uwani, ko su barira su yi masa wanka". Ya ce "Baba uwani kuma?" Ta taɓe baki ta ce "Na fasa ba ta, ni matar nan ba ta yi mini ba, dan dai kawai ammi ta ce ta zo ta zauna da ni ne, ta yi saka ido, kamar mara gaskiya". "Daughter, ki kula sosai da lamarin gidan nan kin ji ko? Sannan kar ki yadda wani ya din ga sanin abun da yake faruwa a gidanki, mussaman baba uwanin". "Kai ma ka lura ta na da saka ido ko?" Mahmud ya ce "Eh to kusan haka, sannan ki kula da takwarana sosai, da sosai" "Taɓ, ka manta ni na kula da shi ranar da aka haife shi ranar majaifiyarsa ta bar duniya, kwananmu uku muna bulayi a daji, bamu samu hanya ba, na zaci ma mutuwa zai yi " ya ɗan ware ido ya ce "Haba dai" Ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Wallahi da gaske nake, ka san yadda ake garkuwa da mutane kuwa, to in gaya maka har sunan wasu na ji, Anty Aisha fa wasu ne suka saka a saceta, saboda papa" kallon ruma yake cikin mamaki. Ta cigaba da cewa "Kuma wai ƴan gari ba su san meyafaru ba, suka ce shi ya kasheta yayi tsafi da ita, na san abubuwa da yawa, na ƙi gaya masa, ya fiye fushi da zafin zuciya, shiyasa maƙiyansa suke nasara a kansa. Ai ni na fi shi wayo fa, in gaya maka ranar da muka tafi katsina a kan bullet da bindigogi na zauna, jakunkunkunan, duk an yi musu lamba, duk na haddace lambobin. Har da wani gari da na je, an ƙona garin, na ga wani tsoho, muka yi hira da shi". "Amma Meyasa ba zaki gaya masa abubuwa da ki ka sani ba?" "Sai abu biyu ya faru, ya daina saurin fushi da zuciya, na biyun kuma ba wanda zan gaya wa" Murmushi yake yana kallon rumaisa, ta fiye surutu, but she's very talented akwai hikima, da kaifin basira a maganganunta. "Me ki ke yi a nan wurin?" Ta ji muryar takawa a kausashe. "Daddy na kawo wa Sabir, ya ga takwaransa". "Uban waye ya ce ki bashi ɗa na?" Ya tunkari Mahmud, zai karɓi Sabir, amma Mahmud ya riƙe Sabir, by force Adam ya hankaɗe shi, ya karɓi ɗan sa, har ya yi gaba ya dawo, ya fizgi hannunta ya nufin sashin Ammi da ita. Ya balbleta da bala'i "Kin san hatsarin da yake cikin abun da ki ka aikata? Kin san me gayen nan zai iya yi, da ki ka ɗauki ɗa na ki ka bashi, What if yayi amfani da hakan against me? Wani irin gargadi ne ban yi miki a kan yadda za ki zauna da mutane a gidan nan ba?" Rintse idonta ta yi, saboda yadda yake ta zazzaga mata masifa. Ammi ta taso, ganin yadda jikin Adam yake rawa, ta karɓi Sabir, ta ja Adam ta zaunar da shi, ta ce "Wannan haƙilon na meye haka? Ka kwantar da hankalinka ba abun da zai faru". "Ammi yarinyar nan ba ta jin magana, duk abun da zan gaya mata ba ta ji". "Ni dai na san ba da kunnen wani nake ji ba, kuma na san abun da na aikata dai-dai ne, ko ba komai na saka uwa ta ga ɗan ta, tun da har ammi ta ji daɗin abun da na yi, ta ga ɗan ta, na ji daɗi, Kuma ni yana yi mini kirki ina ruwana da faɗanku, ni duk wanda yake son sabir ina son sa, na ga kai har cewa ka yi kar a sake bari na shigo gidan nan, shi ya ce a bar ni na shigo, na roƙe shi ya zo ya ga Sabir, ya zo ya ganshi, ya kaini na gaida mamansa, duk da na san ba mamansa ba ce ba". Adam ya sunkuyar da kai, ya dafe kansa, me zai gaya wa wannan burkitacciyar yarinyar da zai sa ta gane, irin hatsarin da wautar ta ka iya jefasu, da ta wanke ƙafa ta tafi sashin Mummy. Ammi ta ce "Rumaisa waye ya gaya miki ɗa na ne?". "Da ke yake kama ai, ba ita ba, kuma wannan matar da zata gaya mini magana ya tare mini, to ammi ni sai in shiga faɗan da ba ruwana? Kuma ɗan uwan baban mutum babansa ne, dan haka shi ma baban Sabir ne". Ammi ta ce "Gaskiya ne, je ki ki shiryo, ki zo ku tafi, dama neman da muke miki kenan" Ruma ta wuce ta je ta haɗo kan jakarta, da kayanta, ammi ta din ga yi wa Adam faɗa tana rarrashinsa, a kan ya bi rumaisa a hankali. Ganin adam ya tashi zai tafi, ya sanya Ruma cewa Ammi Sabir ɗin fa. "Yayi fushi ne, ki yi haƙuri gobe in Allah ya kaimu, za a kawo shi, ku tafi, ki rabu da shi yau ya ɗau zafi". "Ammi, meyasa papa da ɗan uwansa suke faɗa? Ni fa a gidamu ba haka muke yi ba, ya za ayi ƴan gida ɗaya su din ga faɗa?". Ammi ta ce "Kar ki damu, zaki fahimta, bi shi, kar ya sake fushi". Rumaisa ta bi bayan takawa, suna tafe a hanya, yayi shiru fuskar nan a haɗe. Oganniyar ko a jikinta, zura kai ma ta yi taga, tana neman magana. Tun da suka koma gida, kowa ya kama gabansa, har wayewar gari, ba ta sake sanya takawa a idonta ba. Ba ta da masaniya ma a kan yana nan ko ba ya nan, dan ko ɗakinsa ba ta je ba yau. Ta gama gyaran saman benen nan, duk da yana bata wahala, saboda girman saman. Yau har da kunna turaren wuta, tana kallon yadda falon ya yi kyau. Ƴar siriryar muryar iman ta yi sallama, rumaisa ta ce "Anty iman". "Ki shirya, takawa ne ya je gida, ya ce Sidi ya zo ya kai ki gida, na ce bari na biku, na gaida mama, na wuce gidan sarki na ɗorayi, na karɓo mata saƙo. Tsalle rumaisa ta yi, ta na murna ta ce "Jirani, na shirya" Kamar za ta tashi sama ta shirya, ta fita mota suka tafi. Da gudu ta shiga gida, ta bankaɗa ɗakin mama, ta rungumeta. Mama ta ce "Kai rumaisa, babu ko sallama, wannan ai sai ki karyani" Kuka rumaisa ta saka tana cewa "Mama ba kya so na, kin ƙi zuwa gidana, kin ce kuma kar kowa ya je". Aliyu ne ya ga Iman a waje, ya karɓo sabir, ya shigo da shi gidan. Iman ta ɗauko manyan ledojin da takawa ya yi sayayya, ya ce su tafi da shi, dan da shi yayi niyyar kai rumaisa, ta ɓata masa rai. Iman suka gaisa da mama, mama ta ce "Iman tun da a kai biki, kin daina zuwar mini, maimakon tun da na baku rumaisa, ni kuma hajiya ta bani ke" Murmushi Iman ta yi, nan da nan ƴan mazan mama, suka cika ɗakin mama, cike da murnar ganin ƙanwarsu. Usman ya ce "Ke me yake baki ne ki ka fara ƙiba haka?" "Me kuwa yake bani, abinci, yaya kun ga makarantar da aka saka ni? Kullum sai na hau lilo, malamanmu, har da turawa". Aliyu ya ce "Babu a makaranta, idan ki ka faɗi daga lilon, ki ka fasa kai ba zaki koma ba". Mai sunan baba ya yi sallama a falon mama, suka amsa rumaisa ta tashi da gudu ta rungume mai sunan baba. Ya ɗan yi murmushi, ya dafa kafaɗarta. Iman ta ce "Ina wuni" "Lafiya ƙalau" ya amsa, ya saka hannu ya ɗauki sabir yana ɗaga shi sama. Iman na son ɗaga kai ta kalli mai sunan baba, amma ta kasa, shi kuma a wayance yake ƙare mata kallo. Iman ta tashi ta ce "Mama bari na tafi, zan je aiken mama, maman sabir ga kayan abincinsa nan a wannan jakar". Mama ta ce "Iman ki bari ayi azahar ki ci abinci" "A'a mama, na ƙoshi ni sai na kai yamma daga yanzu, ban ci abinci ba ma". Mai sunan baba ya kalli iman ya ce "Nemi wuri ki zauna" tsit kowa ya yi yana kallon mai sunan baba, ai ko motsin kirki ba ta yi ba,ta zauna ta na wuri-wuri da ido. Ya basar kamar bai yi komai ba, aka cigaba da hira har da shi, haka nan yau yake jin daɗin ganin rumaisa a gida. Sai dai bai ji daɗin yadda iman ta takure sosai ba. Har azahar iman ba ta samu umarnin tafiya da ga mai sunan baba ba, sai da aka gama girki. Sabir sai rarrafwa yake, kwano-kwano ya ci na wannan ya ci na wancan. Yadda rumaisa take a cikin yayyenta, ba ƙaramin burge iman yayi ba. Sai da mai sunan baba ya fita, sannan iman ta samu ta tafi. Rumaisa da yaya usy ta keɓe, suna magana. "Yaya yaushe za ka zo, akwai labari fa?" Usman ya ce "Labarin me?". "Ni dai kawai ka zo dan girman Allah" Ya ce "Kar ki damu, zan zo in sha Allah". Ana idar da sallar magariba, Adam ya zo tafiya da rumaisa, amma ta ce Alla kar ta ba in da za ta" sai da aka kai ruwa rana, sannan ta ɓanɓaru daga gidan nan, suka tafi, sai dai ta sha kuka sosai da sosai, mama ta harhaɗa mata ƴan kayayyakin amfani da za ta tafi da shi. Sam Adam bai kulata ba, har su ka je gida, dan haryanzu bai huce da abun da ta yi masa ba. Ya ajiyeta a gida, tana jiran ta ga ya fito daga motar, ta ga ya juya ya tafi da sabir. Hakan ba ƙaramin haushi ya bata ba, hakan ya sanya ta shiga ɗakinta, ta yi ta aikin kuka. Da ya dawo daga mayar da sabir, bai nemi ruma ba, sai da safe, shi ma dan yana tsoron, kar ya kawar da kai a kan ta, ta yi wani rashin jin. Sai dai ya tarar tana banɗaki, ya ƙarasa gaban gadon, ya kai hannu ya ɗau littafin da yake buɗe, da fensira a kai. "Duk wanda ya duba littafin nan, ba da izinina ba, Allah ya isa!!!" Tsaki yayi, ya buɗe shafin gaba. "Zan so ace ni marubuciya ce, da sai kun fi fahimtar abun da zan rubuta, amma gaskiya ba zan iya ba, ban sani ba ko ku gane me nake nufi, idan na zana abu mai muhimmanci da ya sameni a rayuwa, da wanda ya tsaya a zuciyata har in mutu ba zan manta ba, ina fatan ku ji irin abun da na ji, ko za a samu mafita". Zane ne tiryan-tiryan, zane mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, daga fitarsu daga gida zuwa tasha, tare da taƙaitattaun bayanai, a gefe, na abun da ya faru". Nutsuwa ya nutsu yana bi, sai dai duk da haka ta cire wasu abubuwa masu muhimmanci. Daga banɗakin ta fito, tana kokowa da towel, sai dai ta yi turus da ganinsa, saboda ba ta san ma yana gidan ba. Kallon-kallo aka shiga yi tsakaninsa da ita, kamar ɓarawo da mai kaya. "Meye wannan?" Yayi maganar yana nuna mata littafin. "Waye ya ce ka ɗaukar mini littafi? Ba ka ga gargadin da na yi a farko ba?". "Me wannan zanunnukan suke nufi, bayan kin ce mini, ke baki san komai ba? Meye ƙarashen wannan zanunnukan, kuma a wace tashar motar ku ka hau mota?" Tura baki ta yi ta kawar da kai, ya nufeta gadan-gadan, nan take ta ga idonsa ya fara wannan hayaƙin. "Yi haƙuri, ka bani zan yi maka bayani" Ya miƙa mata littafin, sai dai tana karɓar littafin, ta riƙe towel ɗin ta, ta kasa da gudu ta bar ɗakin. Ayshercool. 08081012143 Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Bai yi wata-wata ba ya rufa mata baya, tuni ta yi downstairs, tana riƙe towel ɗin ta, ko da ya sauka ƙasa ya neme ta ya rasa. Ya kalli Asiya da take mopping a falon, ya ce "Ina ta shiga?" Ta nuna masa kitchen, da sauri ya shiga kitchen ɗin, ya tarar da ita da barira, ta yi wuƙi-wuƙi da ido ta na kallon sa, sai dai ta ɓoye hannunta a bayanta. "Ina yake ina littafin? Ina ki ka ajiye shi?" Shiru ta yi masa ta na bin sa da kallo. Takowa ya fara yi, yana cigaba da tambayarta, sai dai ta fara ja da baya, ganin idonsa ya cigaba da wannan hayaƙin. Sai da ta dangana da jikin bango, ya zo ya tsaya a kanta. "Wannan abu ne da ya shafi rayuwata, kacokan da iyalina, ba na wasa da duk wani abu da ya shafi aisha, zuwa yaushe zaki cigaba da wahalar da ni ne? Ki gaya mini abun da nake buƙata, ki yi mini bayanin zane-zanen da ki ka yi?". Kawar da kanta ta yi gefe, daga kallon fuskar sa, tare da bawa kanta ƙwarin gwiwar jure duk wani abu da zai yi mata. "Am talking to you!" Yayi maganar cikin shouting. "Ni ka ƙyale ni, ai ba da iznina ka ɗau littafin ba" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin jan jikinta ta wuce. Dannata ya yi a jikin bango, ya zura hannunsa bayanta, ya banƙara hannunta, ta zunduma wani uban ihu, sai dai babu littafin a hannunta. Hayaƙin da kitchen ɗin yake yi ne, ya sanya shi ɗaga kai, kawai ya hango littafin ta tura a cikin gas, yake ƙonewa. 'Innalillahi wa Innalillahi raji'un ' ya faɗa a zuciyarsa, bai taɓa ganin halitta mai azabar taurin kai da masifa, kamar wannan yarinyar ba'. Baba uwani kuwa, magiya take yi masa a kan ya taimaka ya rabu da rumaisa, saboda yadda take kururwar zai karya mata hannu. Da sauri ya nufi gas ɗin, barira ta ja da baya, saboda gaba ɗaya fuskarsa har ta fara sauyawa, saboda azabar ɓacin rai da fushi. Sai dai kash tuni littafin ya babbake, ya zama toka. Rumaisa kuwa zubewa ta yi a wurin, tana yarfa hannunta, saboda yadda take jin sa tamkar ba a jikinta ba. A fusace ya waiwayo ya kalleta, ya zo ya sake danƙar hannunta, ya ja ta daga kitchen ɗin. Baba uwani ta bi shi tana yi masa magiyar ya rabu da rumaisa, amma ya shareta, rumaisa ta saka hannunta ɗaya, ta riƙe towel ɗin da yake barazanar faɗuwa. Duk wannan masifar da haƙilon, idon rumaisa mursisi, ba ta yi dana sanin abun da ta aikata ba. Ɗakinsa ya wuce da ita, ya rufe ƙofar gam, ya tankaɗata kan gadonsa, ta zauna daɓas, ita kokowarta kar towel ɗin ta ya faɗi ƙasa. "Ki gaya mini me ki ka sani game da mutuwar aisha, da saceta?". "Wai ya ka ke tamabyata kamar ni na sace ta? Ni ban san komai ba, ni ma fa sace ni aka yi". "Amma kin san wani abu, akwai abun da ki ke ɓoye wa, atleast a bayaninki akwai wani abu da zai taimaka, na gane idan saceta haɗin baki ne". Ta ce "Oho, ni dai ban san komai ba, zanena kawai nake yi, idan kun ji haushi, tun da ku jami'an tsaro ne ku din ga aiki tsakani da Allah, ni ka daina yi mini masifa, ba abun da na sani". Cikin matsananci fushi, ya ce "So ki ke na illataki ko? Idan ki ka bari na yi miki illa, na yi wa banza, ke zaki nakasa ba ruwana. Kin san muhimmancin aisha a wurina kuwa? She don't deserve, such kind of death, ki yi mini bayani kan na yi miki illa" A karo na biyu ta sake kawar da kai, ta na zumɓura masa baki. "Kalleni" "Ni ba zan kalleka ba, kai baka ganin abun da yake fitowa daga idonka?". Ba ta yi tsammani ba, ta ji ya riƙe gashin kanta ya ja, sai da ta kusa shiɗewa, ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin ƙwacewa. Ga mamakinta, sai ta ga fuskarsa ma ta fara baƙi, duk ya yi wani iri. A take mafarkin da ta taɓa yi, ya fara ƙoƙarin zama gaskiya, dan faratansa ya fara karta mata a wuyanta, ya kuma shaƙeta ya na wani irin kakari. Da fari su barira sun biyo bayan baba uwani, baba Uwani ta kasa kunne a jikin ƙofar, ta na jiyo abun da suke cewa, sai dai tun da rumaisa ta yi ƙara suka ji shiru. Jiki na rawa barira ta ce "Baba uwani, ko mu kira masu gadi, a ceto ta, kar ya yi mata illa". Baba uwani ta ce "Ke ina ruwan ki? Dalla ku wuce ku je ku cigaba da aikinku" Rumaisa kuwa bayan ya yi mata wannan shaƙar, sai da  ta suma, ya saketa ta faɗi ƙasa, sannan ya yanke jiki ya faɗi a gefenta, cikin yanayi mai kama da bacci. Asiya kasa nustuwa ta yi, ta ce "Barira, tsoro nake ji fa, kar ya kasheta, ko police station aka kaimu bayar da shaida an cucemu". "Bari kawai, wallahi nima a tsorace nake, ga matar nan ta hana a nemo taimako". Asiya ta ce "Bar ƴar rainin hankali mana". "Ita ma dai, ta na da azabar taurin kan tsiya, ni ina girki kawai na ga ta shigo da gudu, ta tura abu a wuta, zan yi magana ta ce in yi shiru, sai ga shi ya biyo ta, amma na ji yana magana a kan Aisha, wataƙila abu ne mai muhimmanci da ya shafe ta". "To waya sani, ni dai fatana kar ya illata kawai". Bayan sa'oi uku, Adam ne ya fara yin juyi, dan ji yake kamar barci yake yi, kawai ya ga rumaisa a kwance a ƙasa, ita daban towel ɗin ta daban, da ga ita, sai gajeren wando. Tashi ya yi zaune yana ƙoƙarin tuna abun da ya faru, kawai dai ya iya tuna yadda ya janyota har ɗakinsa, amma daga nan komai ya goge a kansa. Tsura mata ido ya ɗan yi, yana tunanin ko barcci take yi ne? Amma sai ya ga yanayinta bai yi kama da haka ba. 'Ko wani abun na yi mata?' ya tambayi kansa. Matsawa ya yi kusa da ita, ya ɗagota, ya ga jikinta a sake. A gigice ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, i lose my sense again?" Rabon da ya fita completely daga hankalinsa haka, an kai shekaru goma, ko ya yi loosing control, ya na iya tuna abun da ya faru, amma completely yau ya kasa tunawa. Wuyanta ya kalla, duk shedar an karceta da farce. Ya ɗan girgiza ta ya na kiran sunanta. "Rumaisa!" Amma shiru ba ta motsa ba, ya taɓa hannunta, ya ji zuciyarta na bugawa, numfashi da take yi a hankali. Ya kwantar da ita ya shiga banɗaki, ya ɗebo ruwa a hannunsa, ya dawo ya shafa mata a fuskarta, ya ƙure gudun Ac da na fanka. Bai ɗaura mata towel ɗin ba ya ƙyaleta, ya lulluɓe ta da shi, ya tsura mata ido yana fatan Allah ya sa ta farka, dan kuwa idan ya ɗauketa ya kai ta asibiti, asirinsa zai iya tonuwa, dan babu lallai ta yi shiru, kuma dole a tambayi mai ya sameta, ya cigaba da addu'a Allah ya sa ta tashi. Babu tsammani, kawai ya ga ta tashi zaune, tana ganinsa ta ja da baya, ta kare jikinta da hannunta. Sai a lokacin ya yi ajiyar zuciya "Ki ɗaura towel ɗin mana" ya faɗa a sanyaye. "Dole ka ce na ɗaura mana, bayan ka yi mini tsirara, za ka kasheni, wallahi gida zan gudu, ba zaka kasheni ba? A hakan zan gaya maka abun da na sani ɗin? Dama ban san komai ba ma, wallahi ba zaka kasheni a banza ba, ka shaƙeni kamar wata ɓarauniya". A hankali ya ce "Ya ilahi, i attempt to kill her?' Ta saka hannu ta ja towel ɗin, ta rufe jikinta, ta yinƙura ta tashi, ta fice daga ɗakin. A hankali ya lumshe idanunsa, ya bawa hawayen da suka taru a idonsa damar zuba, ba zai so ammi ma ta ji wannan maganar ba, iya rayuwarta a hanyar nema masa magani take, ana murna abu ya ɗan yi sauƙi sai abun da ba a rasa ba, kwatsam yau abu ya dawo kamar da. Sai ya ji tashin ciwon nan nasa, ya shafe abun da rumaisan ta aikata masa. "Mahaukaci ne ni? Ko kuma maye? Ko kuma namiji mai mutanen ɓoye, wato aljanu?" Tambayar da tun da ya shekara takwas a duniya, yake yi wa kansa da ya gaza samun amsarta. Ba shi da tabbacin rumaisa ta rufa masa asiri, haka zalika bai san ta ina zai fara yi mata bayani, ta fahimce shi ba, sai a lokacin yake ganin rashin kyautawar da aka yi, na rashin yi musu bayanin larurarsa. Madigar kuwa ta na zuwa ɗakin ta, gado ta hau ta cigaba da bacci. Baba uwani kuwa, ta fita ta zagaya, jikinta na tsuma, ta kira lambar Mummy. Aka yi sa'a mummy na kusa, ta ɗag wayar, gulma na cin ta ta ce "Allah ya taimake ki" "Ina jin ki". "Akwai abun da ya faru". "Je ki kai tsaye". Baba uwani ta waiwaya sannan ta ce "Ranki ya daɗe, muna cikin aiki muka ga ya biyota afujajan, a kan wani littafi, sai dai kan ya cimmata ta tura shi a wuta, na ji yana magana cewa, abun da ya shafi aisha ne, baki ga shaƙar da yayi mata ba, ƙarshe dai ya shiga da ita ɗakinsa, ya rufe su, sai yanzun nan ta fito". Mummy ta ce "Good, kin fuskanci ya yi mata wani abu ne?" "Ban san me yayi mata ba da ya rufe su, amma na ga ta fito tana kamar magagin bacci". "Kin sanar da samha ne?" "A'a Allah ya baki nasara". "Kar ki sanar da ita komai, sai abun da na umarce ki". "In Allah ya yarda". "Ki koma, ki cigaba da sanya mini ido a kan duk wani motsinsu". Baba uwani ta ce "An gama uwar ɗakina". Ta katse wayar ta koma. Adam kuwa ya yi sallar azahar, ya jingina da jikin gado, ya yi shiru yana tuna abubuwan da suka shuɗe, gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi. Kiraye-kirayen, sallar azahar ne ya tashi rumaisa, ta je ta yi alwala, ta saka kaya, ta tsaya a gaban mudubi, ta na kallon wuyanta, da ya shata yake mata zafi. Shiru ta yi tana tunanin tabbas ta taɓa ganin wannan abun a mafarki, ko kuma ya taɓa faruwa. "Wallahi sai na gaya wa mama, tun da kasheni zai yi, sai na gudu na bar gidan nan" Can kuma sai wata zuciyar ta tunatar da ita, muddin mama ta ji a kan meye, ya yi mata abun da yayi mata, ba zata goya mata baya ba, faɗa za su yi, a bata rashin gaskiya, kuma a kirsheta ace sai ta faɗi abun da ta sani, bayan ta riga ta ce ita ba ta san komai ba. 'Subhanallah, na fasa faɗa, bari na yafe masa, wataran ya na da kirki, amma wallahi ko zai kasheni ba zan faɗa masa komai ba, sai lokacin da na ga dama, bari na lallaɓa na san yanzu ji yake kamar ya kashe ni' sai kuma ta ɗan yi shiru ta ce "To da ya shaƙe ni kuma sai na yi bacci, oho dai? Ta gama abun da Allah ya nufe ta da yi, ta yi salla ta fito dan yunwa take ji. Adam ya tashi ya nufi ɗakinta, domin ya duba ko ta na lafiya ta gama wartsakewa, sai dai ya jiyo motsi a kitchen. Ya leƙa kitchen ɗin, ya hango ta taka kujera, tana saka ɗan wake, kamar babu abun da ya sameta. Abun har mamaki ya bashi, kamar ya yi mata magana, sai kuma ya fasa ya fita. Baba Uwani na ganin fitar Adam, ta lallaɓo ta hawo benen. "Sannu ƴar nan, ina fatan bai yi miki komai ba?" Rumaisa ta waiwayo ta kalli baba uwani ta ce "Yayi mini me?". "Ai ganin yadda ya janyo ki ɗin nan, abun ya tsoratani, ke ma da ko me yake buƙata kin bashi kin wuce wurin, idan ransa ya ɓaci hankalinsa gushewa yake wasu lokutan, zai iya yi miki illa. Ko dai hakkinsa ki ka hana shi ne?" Rumaisa ta juyo gaba ɗaya ta kalli baba uwani ta ce "Wane irin haƙƙi kuma?". "A'a haƙƙin aure mana". "Meye haƙƙin aure kuma?" Baba uwani ta ce "Ahh shikenan, bari maganar kawai". Har baba uwani za ta fita ta ce "Kenan papa da gaske maye ne?" A razane baba uwani ta waiwayo ta ce "Me ki ka ce?" "Kin ji me na ce ai". "Ke waye ya gaya miki?" Rumaisa ta ce "Ke ce ki ka gaya mini yanzu" Baba uwani ta ce "Ke, yaushe na gaya miki? Ki ji tsoron Allah" "Ke ki ka faɗa, wannan ne karo na biyu ki na gaya mini, zan kuma tambaye shi". "Dan girman Allah ki rufa mini asiri, da wasa nake yi ma fa, dan Allah kar ki gaya masa" Rumaisa ta juya ta cigaba da saka ɗan wakenta, baba uwani kuwa ta toshe baki ta na fatan, Allah ya sa kar garin neman gulma, ta janyo kwaɓarta ta yi ruwa, domin kuwa ta lura bayan ƙuriciya, har da wauta ke damun rumaisa. *** "Hajiya Lubabatu, ki na free gobe in Allah ya kaimu". Mummy ta yi maganar da waya a kunneta. "Ya aka yi ne?". Mummy ta ce "wurin malam na gidan dutse, zaki rakani, akwai case ne". Hajiya Lubabatu ta ce "Wane irin case kuma?". "Ɗan maje ne ya turo mini saƙo, wai ya ji mai martaba zai wakilta turaki, zuwa taron bunƙasa al'adu da harsunan afrika, rainon burtaniya, wai ya ɗauki mutum biyu a matasan yaran nan ya tafi da su, kuma da alama za a samu cigaba, wai ya ji turaki ya ce har da Adam za ayi tafiyar". Hajiya Lubabatu ta ce "To ba sai su yi ta yi ba" "Ina ba fa zai yiwu ba, wai ke meyasa ki ke ɗaukar al'amuran nan da sauƙi, komai sai dai shi, duk wannan miyagun fentin da suke tare da shi, komai sai dai a saka shi, ke me zai hana a tafi da Jabir, ga mahmud, ga Jamil nan, ina su yarima jikokin mai marataba, duk ba a ɗau kowa ba sai shi? A dalilin me?". "Kuma fa da gaskiyarki Jamila" "Dan Allah ki shirya, na ga da yadda zai tafi ai". "Ke dole ma, zan shigo da wuri ma yi maganar, ni Jabir ne yadda ki ka san an yi masa asiri,gaba ɗaya hankalinsa ba ya kan harkar sarautar nan, mussman idan abu da adam a ciki, sai ka ce ya yi masa asiri". "Ni ma na fuskanci kamar aikin da ake yi wa Mahmud ba kamar da ba, zamu haɗu kawai". *** Ko da Adam ya dawo da yamma, ya iske ruma, tana kwance a doguwar kujera, tana kallon cartoon. Ya kalleta ya na jiran ya ji ko za ta ce wani abu, suna haɗa ido ta galla masa harara, bai dai tanka mata ba, ya wuce ɗakinsa. Adam dai hatta abincin sa bai iya ci ba, yadda aka kawo su, haka ruma ta ɗauka ta mayar musu. bacci sai ɓarawo, kwana ya yi ya na juyi, kuma yau sai ya kasa tashi ya yi sallar dare kamar yadda ya saba, tasbihi ma sai ya kasa saɓanin da, sai ajiyar zuciya da istigfari, ji yake komai ya yi masa zafi, ba ya jin daɗin komai, ko abinci ya kasa ci, ya rasa ta ina zai fara. Sai gefin asuba barcci ya ɗauke shi, ana kiran salla shi ma ya tashi. Ko da ya dawo daga sallar asuba, neman wuri ya yi ya zauna, ya cigaba da Adduoi, sai da rana ta ɗaga, sannan ya tashi ya shiga wanka. Har ya kammala shirinsa, bai ji motsin ruma ba, gashi yau Monday. Gaba ɗaya ba shi da kuzari, balle karsashi, ya nufi ɗakinta. Ta na tsaye a gaban mudubi, yau ta fara saka uniform ɗin ta, ta saka skirt ɗin ya zauna a jikinta cif, da taimakon jigidar da ke ɗaure a ƙugun na ta. Ta saka ƴar cikin, ta ɗaga kai tana ƙarewa wuyanta kallo, ta na shafa wurin da ya yi mata rauni. Uniform ɗin sun yi mata kyau sosai. Ɗan gyaran murya ya yi ya ce "Haryanzu ba ki shirya ba, balle ki karya yau monday fa" "Na gama shiryawa, uniform nake ƙarasa sakawa". Ya juya ya tafi dining ya zauna, da niyyar ko yaya ya ci wani abu, dan ya na jin yunwa, amma ya ji bakinsa babu ɗanɗano. Ta fito ta ajiye jakarta a kan kujera, ta nufo dining ɗin. Ta buɗe food flask ɗin abincin, soyayyiyar doya ce da miyar ƙwai. Ta ce "Bari na yi bisimillah, na ci abincinka, yau ban yi girki ba, ko sallar asuba ba ka tashe ni ba, da safe na yi salla kuma alhaki a kan ka". Ta kama kujera, ta haye saman dining ta zauna. Kallon ta yake, yana jiran ta yi maganar abun da ya faru jiya, amma ya ga ba ta yi ba, ta haɗa shayi ta tura masa kofin gabansa, ta ɗau na ta. Jujjuya cokali ya din ga yi, amma ya gaza kai wa bakinsa ya sha. "Wai da zafi ne shayin?" Bai ce mata komai ba, ya cigaba da kallon shayin. "To in ƙara maka madara?" Sai a wannan karon ya girgiza mata kai alamar a'a. "To ka sha mana, ka ci abincin" A hankali ya kai kofin bakinsa, sai dai zuƙa ɗayan da ya yi, sai da yayi ta fama sannan ya haɗiye shi, ƙarshe ya tashi ya ce mata, ta same shi a mota. Kasancewar rumaisa tana son shayi, haka ta haɗe nasa da nata ta shanye abun ta, ta ɗauki jakarta, ta ga tasa jakar ma ya bar ta a wurin, ta ɗauki jakarta da tasa, ta fita. Ta tarar da shi, ya kifa kansa a sitiyarin motar, sai da ta buɗe motar, sannan ya ɗago. Idanunsa sun yi ja, kamar am zuba masa abu a cikin su, har sai da ta fara fargabar ko hayaƙin ne zai fara fitowa, amma ta ga idon ya tsaya a haka, ya fara jan motar a hankali. "Wai zazzaɓi ka ke yi ne?" Bai amsa ba, sai lumshe ido da yake ya na buɗewa. "Yauwwa papa ka san me? Na san ba zaka amsa ba, haka mai sunan baba yake yi, shiyasa bakomai ka ke yi mini na ji haushi ba, na san ka na ji na. Dan Allah ka sai mini lunch box mana, in din ga zuba abinci ina tafiya da shi makaranta". "Lunchbox na ƴan primary ne"ya faɗa a hankali. "Eh, ni shi nake so, ƙarami mai kyau" tana cikin maganar traffic ta tsayar da su, sai ga mai alawar madara, rumaisa ta tsayar da shi ta kalli Adam ta ce "Papa ɗan sai mini". Ya kawar da kansa gefe, yana kallon wajen window. Ta saka hannu ta zuge jakarsa da ke hannunta, ta ga kuɗi a ciki, ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Allah ya kama ka, ga jakarka a hannuna ai, na ranci dubu ɗaya, idan na gama makaranta, na samu aiki, salaryna na farko zan biyaka" sai da Adam ya kalleta jin abun da ta ce, ta bawa mai alwar madara, ta ce ya bata ta duka. Gaba ɗaya ba shi da kuzarin da zai biye mata, dan haka bai ce mata uffan ba. Ita kanta ta lura shirun nasa ya yi yawa, shi kuma mamaki yake yadda duk surutunta, da mitar tsiya amma ta yi shiru, ba ta ce masa komai ba, a kan abun da ya faru. Suna tafe ta cika masa kunne da waƙoƙin indiya, ga abun da yake damunsa, ga waƙarta da ta addabe shi, kuma ya san da ya kuskura ya ce ba ya so, za ta tsiri wani abun. Sai kuma ta koma waƙe-waƙe, masu kama da habaici "Idan mutum ma bashi da lafiya, shan kunu ba magani bane ba. Idan kuma wani abu ne yake damunsa, rashin cin abinci ba maganin matsala bane ba. Cikin mutum ne zai gaya masa, ulcer ta kama shi na ruwan rumaisa, lalaaalallaaa, alawar madara da daɗi". Duk ta yi ta gama ya na jin ta, ya kaita ƙofar makarantarsu, ta sauka ta ɗau jakarta, ta shiga. *** Ya na tsaye ya na saka lense ɗin rigarsa, sai kokowa yake ya saka, amma ya kasa sakawa saboda hankalinsa ba a kan abun da yake yi, yake ba, jin zuciyarsa yake tamkar a kan wuta, wata ƙishirwar baɗini ce ke addabar ruhinsa, abun da yake ji a jikinsa, zai iya rantsuwa da abun da zai kashe shi, tun da Allah ya sa mama ta kawo shi duniya, bai taɓa jin irin sa ba, duk yawon zuwa makaranta da yake yi, da yadda ƴan mata, ke kaiwa suna komowa a gabansa, bai taɓa damunsa ba, amma yau ba gaira ba dalili ƴar mutane ta tsaye masa a tunaninsa. Mussman jiya da ya ga status ɗin ta, ta yi video ita da sabir, ta ɗora, ya kalli status ɗin nan, bai san adadi ba, sai da ya fara bawa kansa haushi. Kuma ya kwanta bacci ya din ga mafarkinta, mafarkin da sai ya kai shi ga danganawa ya tsarkake jikinsa kan ya yi salla. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, ya mayar da hankali, ya gama abun da yake yi, ya fita ya yi wa mama sallama ya tafi. Sai dai a ƙasan zuciyarsa ya na jin, da zai samu dama ya ganta, wataƙila atleast, zai rage abun da yake ji a tsakanin ƙirjinsa zuwa zuciyarsa, amma ta yaya?. *** Sanin halin rumaisa na rashin isasshen saiti, ya sanya ba ya wasa da abun da ya shafeta, duk da halin da yake ciki, da lokacin tashi ya yi, haka ya tafi ɗaukota. Sai dai ya shafe mituna goma sha biyar, a tsaye, bai ganta ba bai ga alamarta ba. Sai da ya ɗan tsorata, ya fara addu'a Allah ya sa ba tafiyarta ta yi gida ba, saboda abun da ya faru. Har zai shiga mota, ya shiga cikin makarantar yana duddubawa, can ya hangota, a cikin liluka, ta ajiye ɗan ƙaramin hijjabinta, sai fama take yi kai ka ce wata ƴar primary 2. Sai da ta hango shi, sannan ta saukko, ta ɗauko jakarta da hijjabinta, ta zo ta wuce shi, ta tafi mota, ba tare da ta ce masa uffan ba. "Wallahi idan ka kuma daɗewa ba ka zo da wuri ba, sai na tafi gida, idan na ɓata a hanya shikenan" Ganin ya zame mata tamkar kurma, ya sanya ta ɗan fara tsorata, shirun na sa yayi yawa, dan kafin su yi aure ne yake da yawan shiru, da suka yi aure ta fuskanci yana da baki, amma daga jiya zuwa yau, shirun ya wuce hankali. Ta yi shiru ta zuba masa ido, damuwa kwance a fuskarsa. Duk sai jikinta ya yi sanyi, ta daina yi masa surutun, da neman magana. Har suka je gida, tana tunanin, ko dai wani abun ta yi masa, yake jin haushinta, har ya daina cin abincin?. A karo na farko tun da ya kaita makaranta, ya tarar da ita a falo, ta duƙufa ta na rubutu, bai san me take rubutawa ba, ya nufi in da take ya tsaya a kanta, takardar kifi ce, da wani math a jiki, da gani question paper ce, take ta fama sai ta yi soloving, ko a ina ta samo takardar oho mata. Ƙafarsa ya saka ya daki ƙashin bayanta, take ta banƙare tare da ɗan yin ihu, dan ta ji zafi. Ya zauna a kan kujera, ya ce "Samo mini abun da zan ci". Sai da ta ɗan tura baki, a ranta kuma ta ji daɗi da ya kulata, har ya nemi cin wani abu. Bayan ta tashi ya zauna ya na duba litatafan ta, maths dai gashi nan, ta na cin abun ta, daga assignment har classwork. Sauran subjects kuwa, har 2/10 ruma ci take. Assignment ɗin ma ba yi take yi ba, babu wanda ya fi kunna shi, har haushi ya saka shi dariya, irin subject ɗin basic technology, an basu assignment a kan cewa, a matsayin ka na matashin ɗan makaranta, wani abu ne zaka iya ƙirƙira, da ka ke ganin zai amfani al'umma da ƙasa baki ɗaya. Shafi guda ta ware, ta zana malamin nasu, riƙe da maka a hannunsa, yana bayani, sai dai a real portrait of him, kai ba ka ce ita ta yi zanen ba, very accurate, a matsayin amsar tambayar. Ya yi shiru yana shafa haɓarsa, wasu lokutan yarinyar kamar bil'adama ba. Ta dawo da plate a hannunta, ta ajiye masa a gabansa. "Meye wannan?" Yayi maganar yana nuna mata litattafanta" "Me na yi?" "Karatun ne ba kya ganewa, ko kuma meyafaru ki ke cin wannan makin". "Ni fa bana gane turancin da ake yi, kuma ba za ayi wa mutum bayani da hausa ba, wai ba a hausa a makarantar, yanzu haka kuɗin vanacula ya kai dubu uku ake bi na, wai idan ka yi hausa ɗari biyu, ina zan iya na ce idan ka zo a gaya maka zaka biya". "Saboda ke ki ke nemo mini kuɗin ko? Kin taɓa ce mini ga abu baki gane ba, in koya miki?" Ta yi shiru, ta kawar da kanta gefe, matsawa ya yi kusa da ita, yana kallon wuyanta, ciwon da ya ji mata, ya fara baƙi. Ya kai hannunsa wurin, amma ta riƙe hannun ta ce "Meye haka?". "Ciwon zan gani, haryanzu ban ji kin yi mini magana a kai ba". Ta sunkuyar da kanta ba ta ce komai ba. "Kin rantar mini dubu ɗaya, kuma kin ce zan biya kuɗin vanacula da ki ka yi, amma yaushe zaki biyani?? Ayshercool 08081012143 Ban da kira please, what's app only 🙏 masu jiran document, idan sai an kammala 1k ne document. *Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Shiru ta yi masa, ta kasa magana, saboda yadda take jin wani iri a jikinta. Ya janye hannunsa ya kalleta ya ce "Ba a bani abinci a plate". Ta kwaɓe fuska ta kalleshi, ta lura adam akwai saka aiki, ba gaira ba dalili. Ta tashi ta ɗau plate ɗin, sai da ta zubo a flask, da cokali, da ruwa ta kawo masa, ya ce mata ta kunna masa tv. Sai da ta ji kamar ta yi tsaki amma ta fasa, ta kunna ta dawo ta zauna, sai dai ta lura da yanayin sa, abincin ba wai daɗi yake yi masa ba, ci kawai yake yi. "Papa maiyasa idonka yake hayaƙi, idan ka yi fushi?" Yayi dariya ya ce "Sai ka ce generator, ko wani murhu, saboda gani jarababbe" Ganin ya mayar da maganar shirme, ya sa ta yi shiri. Kaɗan ya ci, ya rufe, a lokacin ta fara ƙoƙarin mayar da litatafan ta, ya ce "Ban gama da litattafan ba". Ya karɓa ya cigaba da duddubawa, a hankali ya din ga bi ɗaya bayan ɗaya, ya na sake yi mata bayanin darussan da aka koya mata, sai a lokacin ta ƙara ganewa ta kalleshi ta ce "Ai da za a din ga yi mini da hausa, da sai na fi ganewa". "No, da turanci suke magana, ni ma da turancin zan din ga yi miki magana". "Ashe za ayi zaman kurame, dan bai fi kalmomi, sha biyu na sani da turanci ba" Bai bata amsa ba ya cigaba da cewa "Zan saka a ki islamiyya, ko ba na nan, sidi zai din ga kai ki yana ɗauko ki, sannan wannan zanen da ki ka yi, ki goge shi, ki rubuta wani abun". "Ba ka san ma'anar zanen nan ba, duk makin da na ci zan zo na nuna maka" ta ƙarasa maganar tana tattare litattafan ta, a cikin jakarta, daga nan ta mayar da hankali kan abun da yake kallo. Film ne na Hollywood, sai dai yadda ake nuno matan, bai yi wa rumaisa ba, ta din ga kawar da kanta gefe, ba ta yi aune ba ta ga ana kiss, da sauri ta saka hannu ta rufe idanunta, ta sunkuyar da kai. Sai dai ta ɗaga kanta, ta gefen ido, ta ga takawa ko a jikinsa, ya cigaba da kallo. "Ka canza mana wannan tashar" Ya ce "Saboda me?". "Ba ka ga abun da ake yi ba?". "A ina?". Cikin ƙulewa ta ce "Ka na gani ana abun da bai kamata ba, amma ka ke kallo, mama ta ce ba kyau, a gida ba a bari mu kalli irin wannan film ɗin ma fa, ka daina gani za ka makance". Ya kalli cikin ƙwayar idonta, iya gaskiyarta take gaya masa, bai ga alamar wasa a abun da take faɗa ba. "Ko zamu gwada?" Yayi maganar yana tsareta da ido. "Waro masa ido ta yi ta ce "Mu gwada me?". "Kiss ɗin" Miƙewa tsaye ta yi, ta ce "Na shiga uku" har da haɗawa da gudu, ta bar masa falon. Shi a zahiri ma ba film ɗin yake kallo ba, yanzun ma fitowa ya yi, domin ragewa kansa damuwa, da kaɗaici, atleast ya ɗan ji releif kaɗan, ya saka a ransa zai yi mai yiwu wa, wurin bin shawarar Bashir, ya saki jiki da rumaisa su samu kusanci sosai da sosai. Har dare, ba ta sake yadda sun haɗu ba, dan ya gama ba ta kunya gaba ɗaya. Har ɗaki Asiya, ta kawo mata uniform ɗin ta, an wanke wanda ta cire an goge mata su. Ta karɓa ta yi wa Asiya godiya, ta cewa Asiya dan Allah ta dafa mata indomie, dan ba za ta fita ta haɗu da adam ba. A ɗakin ta bar kwanun, ta yi sallar isha'i, ta hau aikin nata na bacci. A cikin mafarke-mafarkenta, da ta saba yi, yau ta ga Mummy riƙe da sarƙar da take yawan ganin an ɗaɗɗaure adam da ita, yau ta ga mummy riƙe da sarƙar, ta hankaɗa adam cikin wani rami. Ba ta san ya aka ƙare ba a mafarkin, ta tsinci kanta a tsaye, tana ta haki zuciyarta na bugawa da sauri. Da sauri ta fita daga ɗakin, ta tafi na takawa, ta tarar da shi ya na bacci. Kuka take yi sosai, tana dukan pillown sa, "Ka tashi" Kasancewar baccin na sa ba nisa ya yi ba, ya farka, dan bai daɗe da yin baccin ba. Da fari ya zata ko ciwon marar ne, ya tamabaye ta lafiya?. "Ni tsoro nake ji". "Tsoron me kuma?" "Ni dai tsoro nake ji" ta yi maganar tana kuka. Ya tashi zaune ya ce "To zo ki kwanta a nan" ba musu ta haye gadon nasa, ta kwanta, ƙarshe dai har asuba bai samu ya yi bacci ba, ita ma kawai bakan ta yi, amma idonta biyu.. Sai dai tun lokacin da ya tashin, yake jin kamar an zare masa lakar jikinsa, ya fita masallaci, ta sauka daga kan gadon ta koma ɗakinta, tana ta addu'a a zuciyarta. Sai dai kamar jiya da safe, walwalarsa ta sake ɗaukewa, bai ko karya ba, ya tafi kaita makaranta, sai dai a tuƙinsa kawai, ya isa ka fuskanci lallai akwai matsala. Ta yi masa a dawo lafiya ya jinjina mata kai ya tafi. Sai dai ita ma ta shiga cikin tunani, tun da Allah ya sa ta ga Mummy, take yawan mafarkinsu tare da takawa. Ikon Allah ne kawai ya kai shi wurin aiki, dan ko gani ba ya yi sosai. Tun da ya shiga office, jiki yake nema ya rikice, ya rufe kansa a ciki, yake ta fama da matsanancin ciwon kai. Bai iya aikata komai ba, ya kunna karatun Alkur'ani a wayarsa, ya ajiye dan idan ya shiga wannan yanayin ba ya iya karanta komai. Ya daɗe a haka, kan a hankali ya fara samun nutsuwa, ya ɗau wayar, ya kira Jamil a waya, ya ce dan Allah ya zo office ɗin sa. Ko mintuna biyar ba ayu ba sai ga Jamil, ya na ganin adam ya ruɗe ya ce "Lafiya kuwa? Ba ka da lafiya ne?". "Bana jin daɗi ne, dan Allah so nake ka kaini gida wurin ammi, ba na son kowa ya san halin da nake ciki, bana son ayi ta mun sannu, ko azo a zagayeni ban san me zai iya faruwa ba". Jamil ya jinjina kai, ya ɗaukar masa wayoyinsa, ya rungume shi suka fita. Ko da suka je can gida, adam ya yi garajen buɗe ƙofa ya fita, ya faɗi a wurin. Dai-dai da shigowar motar hajiya jamila da Hajiya Lubabatu. Saukkowa suka yi, suka nufi adam tare da ma'aikatan, suna tambayar ko lafiya. Jamil ya ce "Bashi da lafiya, ya ce na dawo da shi gida, kuma ya faɗi". Haka aka kama adam, zuwa cikin gida sashin Ammi. Ammi ba ƙaramin tsorata ta yi ba, rabon da haka ta faru an kwana biyu, dan an samu kyakkyawan cigaba a lamarin lafiyar Adam. Kamar gawa haka aka kwantar da shi, a bedroom ɗin ammi, su Mummy suka je suka tsaya a kan sa suna yi masa sannu. Tamkar wanda aka mintsuna, ya fara daddagewa jikinsa ya na rawa, yana danƙar bedsheet ɗin kan gadon, yana girgiza kai. "Ammi, Ammi! Jikina ki danne ni" ya din ga maganar cikin ɗaga murya. Tuni hawaye ya cika idon ammi, ta ce "Sannu Allah ya baka lafiya". Mummy ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kai wannnan lamari, ni abun nan na rasa gane kansa, Wannan wace irin larura ce?". "Ammi! Ana kakkarya ni fa, Ki zuba mini ruwan sanyi a jikina" yayi maganar yana neman abun da zai riƙe. Jamil ya ce "Takawa, ka yi addu'a Allah ya baka lafiya". Hajiya Lubabatu ta ce "Jamil yo baya fa, kar ya yi maka illa, ko ka manta abun da yake yi, idan ciwon ya tashi haka?" Gaba ɗaya suka tsaya daga baya, sai ammi ce ta zauna a kusa da shi, tana cigaba da yi masa sannu, su iman duk suna makaranta, da ma daga ita sai sabir. Kan ka ce kwabo, sai ga samha ta shigo tare da Fauziyya, suna sashin Mummy, Mahmud ya gaya musu. Samha na zuwa ta ganshi jikinta ya yi sanyi, ta na jin labarin rashin lafiyar sa, tun suna yara, wasu lokutan abun ya kan tayar masa, amma ba ta taɓa tunanin abun ya kai haka ba. Ya na cikin wannan halin, ya koma cewa "Rumaisa! Ammi a ɗaukkota daga makaranta, kar wani abu ya sameta. Rumaisa! Ammi Rumaisa". Jamil ya ce "Ka kwnatar da hankalinka, wace makarantar ce, in je in ɗaukkota". Mummy ta ce "Takawa ka na ta kanka, kana ta wata daban, ka yi addu'a, fatanmu ka samu lafiya" "Ammi rumaisa" ya sake nanatawa. Haushi ne ya ƙule Samha, kamar ta buɗi baki, ta ce Allah ya tsinewa rumaisan. Ammi ta gaya wa Jamil makarantar, ya fita da sauri ya ɗau mota. Mahmud kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye, atleast ya na son jin ya jikin Adam, a wani situation yake, abun da bai taɓa ji ba sai yau. Rumaisa kuwa tuni aka tashi, har ta fara ƙuluwa, ta ce "Lallai papa, zaton sa ba zan iya tafiya ba kamar yadda na ce masa ko? To wallahi tafiyata zan yi, in bi hanyar da ba ta gida ba, in ɓata sai ya nemo ni". Ta na cikin mitar, ta ga motar adam, sai dai ta ga jamil a ciki, dan haka ta tsaya ta na kallonsa. Ya sauke glashin ya ce "Zo mu tafi" "Mu je ina?". "Can gida, takawa ba lafiya, ya ce na ɗaukkoki, ya na cikin gari wurin ammi". "Sai ka ce ba ni da hankali zan hau motar da ka ke tuƙawa, in je ka kasheni a banza, tun da na san ka tsaneni, saboda papa bai auri ƙanwarka ba, to ba zan hau ba". Ya kwantar da muryarsa ya ce "Da gaske nake yi miki, ni ba kasheki zan yi ba, ba dan shi ya ce na ɗaukko ki ba, ba abun da zai kawo ni". "Taɓ, ka isa ka gaya mini magana in yadda, ai ni yadda mutum yayi mini a haɗuwarmu ta farko da shi nake amfani. Ba ɗazu papan  ya kawoni ba ka ce shi ya ce ya zo ya ɗauke ni, bayan a gabana ranar ka ke yi masa rashin mutunci, ka ce wai bai gaya maka anty aisha an sace ta ba, to ba zan hau ka kasheni ba, ba kai ne yayan anty aisha ba, duk na san komai, da ku ka din ga cin zalinta, tun tana ƙarama, sai da ta mutu za ku nuna kuna son ta. To wallahi ba zan hau ba, gara na tafi da ƙafata". Baki buɗe yake kallon rumaisa, ita ba ta manta abu, waye ma ya gaya mata wannan zancen, ita aishan ce ko adam ɗin ne ya gaya mata? Kuma ai ba shi ne ya nuna wa aisha ƙiyayya ba. Ya dai-daita nutsuwarsa ya ce "ƙanwata ki na ji, shigo mota mu tafi, sai mu yi magana, duk wanda ya gaya miki zantukan nan ƙarya yake yi, na san dai aisha ba zata gaya miki ba". "Kai ni fa ba a lallaɓani, kuma ba a hantarata ko ayi mini dole, ka tambayi mijina ka ji" ta juya tayi tafiyarta, kan ya kunna motar, ya bita, ta haye a dai-daita sahu, ta ce a kaita gidan tsohon galadima. Ana zuwa ta sauka abun ta, sai masu gadi ne suka biya kuɗin napep ɗin, ta nufi sashin Ammi, a ranta ta na raya idan ƙarya Jamil yake, sai ya gane ba shi da wayo. Sai dai ga mamakinta ta ga baba uwani a falon ammi, bayan a gida suka bar ta. Ta na ganin rumaisa ta hau kuka, ta ce "Tun ɗazu aka ce a zo a ɗaukko ki daga makaranta, yanzu aka kirani a waya, takawa babu lafiya". Ruma ba ta amsa mata ba, ta fara laluben a ina adam ya ke. Ta na kaiwa bedroom ɗin ammi, ta ji tsigar jikin ta ta tashi, kanta ya wani sara. Kamar ƙwai ya fashe mata a ciki, ta shiga ɗakin. Duk ga su Mummy a gefe, har da Samha da su Fauziyya su na kuka. Rumaisa ta ƙarasa kansa ta tsaya, sai fizge-fizge yake yi, kamar zai fita hayyacin sa. Rumaisa ta waiwaya, ta ƙurawa mummy ido, a take jikin Mummy ya hau rawa, ta fara kame-kame "Rumaisa ko?, kin ga takawa ba lafiya ko?  Dama yanzu yake ta kiran sunanki ya ce a ɗaukko ki". Ammi ta ce "Rumaisa, ashe jamil ɗin ya ɗaukko ki?". Rumaisa ta girgiza kai ta ce "Ni ba shi na biyo ba, saboda ya tsaneni, haka kawai in je ya kashe ni, ai haushina yake ji saboda takawa bai auri ƙanwarsa ba, na zata ma ƙarya yake yi, lafiyar papan ƙalau, yaudarata zai yi na hau adaidaita sahu na taho". "Yaya jamil ɗin ne yake yi miki ƙarya?" Samha ta yi maganar a ƙufule. "Waye shi da ba zai yi ƙarya ba? Na faɗa na zata ƙarya yake yi, tun da a gabana yake yi wa papa rashin mutunci, wai bai gaya masa anty aisha ta ɓata ba. Sai kuma ya zo ya ce mini papa bashi da lafiya na yarda? Ai ni a ganin farko nake gane mutum". Ammi ta ce "Ruma ya isa haka, ki yi masa addu'a" "Ammi ni fa rashin adalci ne da fuska biyu ba na so". Kallonta duk suke yi, ba tare da gane in da zamcenta ya dosa ba. "Ammi ki danne ni, ƙasusuwana karyewa suke yi" maganar takawa ta sa suka mayar da hankalinsu kan shi". Iman ce ta yi sallama a bedroom ɗin, jikinta a sanyaye ita ma. Rumaisa ba tare da jin kunyar wani ba, ta zauna a gefensa, ta riƙo hannunsa da yake cikin na ammi, ta ce "Papa meye yake maka ciwo?" Ya riƙe hannunta sosai, cikin tsananin ciwo ya ce, "komai ma, Allah idan mutuwa za ta zama hutu a gareni, Allah ka sanya na mutu, da wannan azabar da nake ji" yayi maganar yana sake riƙeta tare da yin ƙara. Duk ta na jin azabar riƙon da ya yi mata, ta sunkuya dai-dai kunnensa ta ce "Papa ba kyau fatan mutuwa fa, idan ka mutu sabir fa, ammi fa? Dan Allah ka daina, ka bari in cikawa anty aisha alƙawarin da na yi mata, zaka warke gaba ɗaya har abada" ta yi maganar tana zubar da hawaye. Samha wani uban tsaki ta doka, ta tashi ta fita, abun da babu wani take gaya mata game da zamansu daban, abun da take gani yanzu daban. Mummy ma tashi ta yi ta ce "Giwa, Allah ya bashi lafiya, amma akawai buƙatar ki din ga kwaɓar sirikar ki, ta iya bakinta". Ammi ta ce "To na gode". Baba uwani ta kawo kai, suka haɗu da Mummy, Mummy ta yi mata sigina da ido, sannan ta tafi. "Ki yi mini Addu'a" ya faɗa ya na sassauta riƙon da ya yi mata. Baba uwani sai jera masa sannu take yi, iman ta kawo maganinsa, a shafa masa, ya ce ba ya so. Iya abun da Allah ya sa rumaisa ta iya, ta din ga karanta masa, sai dai ta fi nanata la'iila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin. Saboda tana da yaƙinin duk wahalar da ta shiga, idan ta karanta ta na samun mafita. Lumshe idanunsa ya yi, ya daina hargowar da yake yi, ta kalli ammi ta ce "Wallahi ammi asiri aka yi masa, wai ku ba kwa ganin abun da nake gani?". Ammi ta ce "A'a rumaisa, Allah ne ya ɗora masa, muna fatan Allah ya yaye masa". "Ammi, wai baku ga matar da take zaune tare da su Mummy ba, tana kallonsa, wata baƙa, idonta ya na ci da wuta, haka fa wataran idonsa yake yi, idan ransa ya ɓaci, kuma wallahi ni ban yadda da babar mahmud ɗin nan ba...... Kamar daɗi take ji abun da ya samu baban sabir, sai murmushi fa take yi ku......... Hannun sa ya saka ya toshe mata baki, duk da idonsa ya na rufe. Rumaisa baba uwani take kallo, idan har abun da Mahmud da kuma Asiya suka gaya mata a kan baba uwani gaske ne, to za ta yi amfani da shawarar yaya usman, dan ranar da suka je gida, ba abun da ba ta gaya masa ba, kuma shi ya bata shawarar ta faɗi wata maganar a gaban baba uwani, wadda ta san za ta iya zuwa kunnen Mummy. A zahiri rumaisa ta ga matar da take faɗa, a tare da Mummy, sai dai a wannan karon ma, ta gane ita kaɗai take ganin ta. Bacci ne ya ɗauke Adam, rumaisa ta tashi ta ce za ta yi salla. Ammi sai sannu take yi mata, saboda ta san idan har ciwon adam ya tashi, duk wanda ya yi wa wannan riƙon sai ya ji jiki, amma ta ga rumaisa ras da ita. Maimakon ta je ta yi sallar, sai ta fice harabar gidan. Lelleƙawa take yi, ko za ta gano Mahmud, dan ta na da labarin gaya masa. Bisa sa'a, ta ga yana tahowa daga waje, da alama masallaci ya je. "Daddy" ta ƙwala masa kira. Yana hangota ya yi murmushi, ya ce "Daughter, ina takwarana?". "Ya na wurin ammi, dama kai nake nema, Allah ya sa na ganka". "To gani ya aka yi? Amma ba kya tsoron kar mijinki ya ganki, ya kuma hantararki?". Ruma ta tura baki ta ce "Bashi da lafiya fa, kuma kowa ya zo duba shi, har da mamanka amma kai ba ka zo ba" "To ai kin san ba shiri muke yi ba" "Daddy meyasa?". Mahmud ya numfasa ya ce "Manta kawai, ya aka yi?". "Ka san maganar da muka yi ai ranar ko?, kuma ka ce zaka taimaka mini". Mahmud ya ce "Ko zan yi wa kowa ƙarya, ban da ƴa ta". Rumaisa ta ce "To ni fa na ce mamanka ce ta ke yi wa mijina asiri a gaban baba uwani". Ya ɗan yi shiru ya ce "Ke waye ya gaya miki haka?" "Haka nake tunani, kuma nake son tabattarwa, amma so nake na kama baba Uwani, yaya usman ne ya bani shawara. Ni fa ban yadda matar nan mamanka ba ce, jiya mafarki na yi tana tura papa rami, yau kuma na ganta da wata mata, ba wanda yake iya ganinta sai ni, baƙa mummuna, idonta sai wuta yake yi, abar tsoro kawai dai ni ba ta tsorata ni ba. Papa sai ihu yake yi, abun tausayi" Yayi zuru da ido yana kallon rumaisa, sai kuma ya ce "Da gaske ki ke ko da wasa?". "Ni ba kullum nake yin ƙarya ba" ta bashi amsa. "So, you want expose my mother daughter?". Ta yi shiru, tare da zuba masa ido. Ya ce "Shikenan, ni na yi alƙawari ai kuma zan cika in sha Allah, duk wani support da ki ke nema, i will assist in sha Allah, zan taimaka miki, ki cika alƙawarin da ki ka yi wa fulani, amma yaushe zaki bashi bayani a kan abun da yake nema na binciken? Ya na son aisha sosai, a yanzu ba shi da burin da ya wuce, ya gano wanda suka saceta". Rumaisa ta ce "Kamar ka na son takawa? Tun da har ka san abubuwa a kan sa, amma meyasa ba kwa shiri?" Jiki a sanyaye ya ce "Kar ki damu, lambar wayata na nan, na rubuta miki, a bayan sashin su mijinki, duk lokacin da ki ke buƙata ki kirani, idan har ina Nigeria" yana gama faɗa ya juya zai tafi ta ce "Idan kuma na gane ka zaɓi uwar riƙon ka, ka yaudareni, zan yi maka abun da ba ka zata ba, zan iya yin komai a kan uban ɗa na" Cak ya tsaya, ya waiwaya ya kalleta, kawai ta kwashe da dariya, ta ce "Kamar a film ko? Zan iya acting ashe, ai na san ba zaka yi mini haka ba" Tun da ya dawo ƙasar nan, suka haɗu da rumaisa, suka yi magana, yake jin kamar wani abu ya sauya a tare da shi, sosai yake jin tausayin Adam, kuma a jikinsa yake jin, lokaci ya yi, da yakamata Mummy ta tuba, shekaru sun fara ja, ko ba komai ta mutu ta samu rahamar Allah, sarautar da take yi masa ƙuzu kuma, shi ba a gabansa take ba ma. A ɗakin Iman rumaisa ta yi salla, iman ta baya doguwar rigarta ta saka, suka zauna su na ɗan taɓa hira, iman ta ɗan bata labarin, irin wahalar da yake sha, idan yana ciwon nan, da kuma wahalar neman magani da ammi take yi, ba yau ba gobe". Iman ta ɗora da cewa  "Anty rumaisa, da kin sani ba ki faɗi maganar nan ta ɗazu a gaban mutane ba, ba zan musa miki mummy ba ta asiri ba, amma idan maganar ta koma kunnenta fa? Zai iya haddasa wata rigimar". "Ai na ga duk wanda yake wurin, amintacce ne. Waye zai je ya faɗa? Ammi ce za ta gaya mata, ko kuma ke? Ko kuma baba uwani, da dama dan ita na faɗa" Iman ta kalli rumaisa da mamaki, rumaisa ta yi dariya, ta ce "Iman, ina da wayo fa, kawai dai ba na ji ne, amma dan Allah Meyasa papa suke gaba da daddyna? Ko da ba ammi ce ta haifesu duka ba, amma ai ƴan uwa ne" Iman ta ce "Duk ƴaƴan ammi ne" Rumaisa ta ce "Ai na zata kema zaki raina mini hankali ne, ai na sani, na san duk ammi ce ta haifesu, amma daddy ya dage wai waccan matar ce babarsa, amma dan Allah meyasa gaba ɗaya gidan nan naku, a hargitse yake? Kowa ba shi da gaskiya". Iman ta rausayar da kai ta ce "Ai ba abun da ki ka gani, family ne mai cike da rikici da ƙulla-ƙulla". "Ai shi ne wannan yayan anty aishan, zai raina mini hankali, ni kuma wallahi yadda mutum ya mu'amalance ni a farko, haka nake tafiya da shi, kin ga rashin mutuncin da suka yi mini ranar da muka je gidan su, da shi, da wannan masifaffiyar mai jan kaya ta ɗazu, da wannan jabir ɗin, shi ma jabir ɗin da babarsa, wadda ta riga Mummy tafiya ɗazu. Wai takawa ya turo shi ya ɗauke ni daga makaranta, na ce ba zan hau motarsa ya kashe ni ba, dan na san haushina yake ji, saboda takawa bai auri ƙanwarsa ba, wai ni zai yi wa dabara, a gabana fa ya yi wa papan wulaƙanci, wai an sace ƙanwarsa bai gaya masa ba, shi a wa? Sai ka ce son anty aishar suke yi". Iman ta ce "Ke dai kawai ki ce, an taɓa miki miji kin ji haushi. In dai yaya jamil ne sun saba, faɗa da takawa kuma daga baya su zo su shirya. Amma duk da haka na yi mamakin yadda ki ka iya kawo, yaya Mahmud sashen nan, ba ya son ammi da abun da ya shafe ta, balle adam. Lokaci na ƙarshe da ya zo, shi ne lokacin da aka fasa aurena, saboda rashin asali, ammi ta roƙe shi ya aureni, har da kukanta, ya ce ba ya so na, ba zai aureni ba". Ta yi maganar hawaye fal idonta. Rumaisa ta yi shiru, ta ce "Wane irin abu ne wannan kuma? To duk saboda me? Ban gane ba ki da asali ba" Iman ta share hawayen da ya zubo mata, ta ce "Zan yi miki bayani, yanzu mu cigaba da addu'a papan mimi ya warke" ta yi maganar cikin ƙarfin hali tana murmushi. "Shikenan, ara mini wayarki, na kira gida na gaya musu papa ba lafiya". Iman ta ce "Amma idan mai sunan baba zaki kira, ki yi masa magana ta what's app, ya hana ni kiransa a waya". Ruma ta ce "Au kuna waya ne dama?" Ta yi maganar tana dariya. Da sauri Iman ta ce "A'a, ba waya muke yi ba, ke ce da ki ka kira rannan bai ɗaga ba". Ruma ta yi dariya ta ce "Buɗe mini data mu yi magana da shi". Iman ta karɓa ta kunna mata data, ta ba ta, yaya umar ta ga iman ta yi saving number. Ruma ba ta ce komai ba, ta yi masa voice message "Mai sunan baba, ni ce, ka gaya wa mama mijina ba shi da lafiya, mu na gidan ammi, idan ka ga message ɗin dan Allah ka yi mini magana, rumaisa ce". Iman ta zare ido ta ce "Ba kya jin kunya, ki ke cewa ace da ammi mijinki babu lafiya" Rumaisa ta miƙe tsaye ta ce "To me zan ce? Ai maman ma mijina take ce masa, bari na je na gani ko ya tashi, idan mai sunan baba ya yi magana, sai ki kira ni" ta fita daga ɗakin, ta tafi na ammi. Ammi ba ta ɗakin, ta tarar da adam a zaune, sai dai ta ga samha a zaune a gefen sa, da flask ɗin abinci. Wani abu ne mai nauyi, ya daki zuciyar rumaisa, da ba za ta iya tantance ko menene ba. Iman kuwa ta cigaba da chatting ɗin ta, sai ga video call na mai sunan baba. Gudun kar ta yi laifi, kan ta kai wa ruma wayar ta katse, ya sanya ta ɗaga, gabanta ya na faɗuwa. Maimakon ya ga rumaisa, ya ga kyakywar fuskar iman, ta bayyana a kan screen ɗin wayarsa. Ta ɗan sunkuyar da kai ta ce "Barka da yamma yaya umar" Sunkuyar da kanta da ta yi ne, ya bashi damar ƙare mata kallo, ya na jin releif na abun da yake damun ruhinsa. Ayshercool 08081012143 What's app only please, ban da kira please 🙏. ₦500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank. Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Jin shirun ya yi yawa, sai da ta yi zaton, ko wayar ya katse, ta sake ɗaga kanta, ta ce "Ina wuni yaya umar?". Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ce "Lafiya ƙalau, ya mutan gidan?". Cikin jin daɗi ta ce "Suna nan lafiya, ya mama da su Yaya Aliyu" "Lafiya ƙalau, na ga message ɗin wannan Yarinyar ne, na mijinta ba shi da lafiya". Yayi maganar yana sake fatan iman ta ɗago kanta ya kalleta, ko ya cigaba da jin nutsuwa a zuciyarsa. Ba tare da ta ɗago ɗin ba ta ce "Eh, ba shi da lafiya, su na gida ita da shi". "Za su koma gidansu yau ne, ko su na nan?" "Wallahi yaya ban sani ba, amma dai ba na tunanin su koma yau, bari na kai mata wayar, yanzun nan ta tashi". "No ƙyaleta, idan ta dawo ki ce mu na yi masa sannu, Allah ya bashi lafiya, a gaida sabir". Murmushi ta yi ta ɗan ɗago ta ce "To in sha Allah zan gaya musu, mun gode sosai". "Zan shigo zuwa an jima, sai na duba shi". "To yaya umar, Allah ya kawo ka lafiya" Ji yake tamkar kar ya katse wayar, wata irin narkewa zuciyarsa take yi, da jin iya muryarta kawai. Mussman idan ta kira shi da yaya umar, ji yake tamkar ta fi kowa iya faɗar sunan. Kamar wanda aka yi wa dole, haka ya kaste kiran wayar, ya lumshe idonsa ya na haki, ya na gazgata zuciyarsa da babu tantama wannan shi ne so. Girgiza kansa ya yi ya ce "Ya salam, why? Why? Abun da ban taɓa yi ba, ni ko shirin aure ba ni da shi, ina zaman zamana meya aikeni" ya tambayi kansa. Gashi Abubakar ne abokin hirar sa, Abubakar baya nan, kuma duk da haka ma, ya san idan ya gaya masa dariya zai ta yi masa, abun da ba ya so, dan haka yake jin, zai iya jure koma menene. A ƙasan zuciyarsa ya ji kamar dama ce, da zai yi amfani da zuwa duba Adam, ko zai samu ya ga iman. Rumaisa kuwa, takawa ya ga reaction ɗin ta, ta ƙarasa wurinsa ta ce masa "Wai dama ka tashi, ina ammin?". "Ta fita ita da Nusaiba" ya bata amsa. Ta je ta zauna a kusa da shi, ta ce "To meyasa baka ce a kirawo ni ka tashi ba?" "To yanzu ba ga shi kin zo na tashi ba". "Ammi zan mutu, ki zuba mini ruwan sanyi, idan mutuwa ce hutu a gareni Allah ya sa na mutu, to ba in da za ka mutu ka tafi, sai na gama makaranta mai lilo" ta yi maganar farko tana kwaikwayon sa. Murmushi ya yi, da sai da haƙoransa suka bayyana, ya ce "Rashin lafiyar ta wa ce, ta zama abun tsokana kuma". "Wane irin wulaƙanci ne, ina magana da ɗan uwana zaki zo ki zauna ki na wasu surutan banza?" Rumaisa ta kalli Samha ta ce "Au dama ɗan uwanku ne? To ni kuma ƙarewar ƴan uwantaka gidansa a kai ni na zauna, ke meyasa ba a kai ki ba? Me ɗan uwa?" "Shut up" yayi maganar yana matse mata baki. "To ina ruwanta da ni, ba bu kyau wata ta kula mijin wata ba?" Kallonta kawai yake yi. "To ina ruwana. ka ci abinci ne?" Ya numfasa ya ce"Ammi ta bani, tun da tafiyarki ki ka yi, ki ka barni". Ɗan shiru samha ta yi, abun da take gani yanzu, ya sha ban-ban da wanda baba uwani take gaya mata, ƙarya take yi mata kenan ko kuwa? Ta ce mata ba sa wani jituwa, amma alamu sun nuna mata, kamar shaƙuwa a tsakanin su, babban tashin hankalin ta da fatanta, Allah ya sa wani abu bai taɓa faruwa tsakanin su ba, ta kuma fuskanci rumaisan tantiriyar fitsararriya ce. Ruma ta ce "To yanzu ya ka ke ji, da sauƙi jikin?" "Eh, Alhamdilillah" "To sannu, ka tashi mu tafi gida" Adam ya ce "Mu je gida ki yi yaya da ni, ba iya jinyata za ki yi ba" Miƙewa Samha ta yi, ta fice zuciyarta na zafi, a gabanta adam ya sakarwa wannan shegiyar yarinyar baki, wata banza da ita mara aji, balle mamora. "Kuma duk mai kula mijin wata, ɗan wuta ne, kuma sai ya daina magana" ta yi maganar cikin ɗaga murya. Samha ba ta ko juyo ba, ta yi gaba tana ƙwafa, ba dan Adam ya auri rumaisa ba, da duk hakan ba ta faru ba, ta ɗora zargin komai a kan sa, kuma ya kasa tsawatar mata. Samha na fita, ya rungumo rumaisa jikinsa, tare da kwantar da kansa a jikin na ta. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meye haka kuma, dan Allah ka cikani" Bai ce uffan ba, ya ƙara lafewa, yana sauke numfashi. Shiru ta yi, ba ta kuma ko motsawa ba, ta na jin bugun zuciyarsa a jikinta. "Ita ma haka ka yi mata ko?" "Ita wa?" "Wannan matar da ta fita yanzu". "Eh, tun da ba kya jin magana, ba zaki saita bakinki ba, idan ta zaneki shikenan" ya sake rungumeta sosai. Cikin tsoro ta ce "Ba kyau fa" Yayi ƴar guntuwar dariya, yanzu abubuwanta sun daina bashi haushi, akwai wayo wasu lokutan, wasu lokutan kuwa kanta a kwano yake, gashi dai ta fara girma, amma kamar ba mutum ba, har mamaki take bashi". Ya kalleta ya ce "Wani alƙawarin ki ka yi wa fulani?" Ta numfasa ta ce "Ba yanzu zan faɗa ba. Kuma gaskiya ka ɗagani, ka yi mini nauyi, na ji da matsar hannun da ka din ga yi mini ɗazu, ƙasusuwana sai ciwo suke yi". Bai ɗagata ba, ya kwanta sosai a kan cinyarta, ya lumshe idanunsa. *** A fusace Jamil yake sosai, ya dubi Jabir ya ce "Jabir, har ni wannan Yarinyar za ta yi wa fitsara, wai ba son fulani muke ba, kenan adam zuwa ya yi yana ɓata mu a wurinta, abun da ya wuce ba ya riga ya wuce ba? Shikenan ba ni da zarafin bincike a kan ƴar uwata, ni da a tunanina, na lallaɓata na samu wani abun daga bakinta, yadda ka san na harbeta na huta, ka ga iskancin da ta din ga yi mini?" Jabir ya ce "Wai kai da na gaya maka halinta baka yadda ba? Kai ka ga zaryar da jami'an tsaro suka din ga yi tana asibiti, amma ta ƙi magana, sai da aka kai ruwa rana, sannan ta yi". "Ni anya ba fulanin ce ta gaya mata wani abun ba?" Jabir ya ce "Ba tabbas, ka san halin Aisha bana tunanin ita ce, bari dai a yi sallar magariba, zan shiga na duba shi" "Ka dai yi a hankali, ciwon nan nasa ne, ya tashi, ka san kuma shaƙe mutane yake yi". Jabir yayi murmushi bai kuma cewa komai ba. Tamkar mai comedy, haka rumaisa take ta zuba, tana yi wa Adam shirme samfur -samfur. Can kuma ta ce "Tashi, in ɗauko maka filo, cimyata ta gaji, zan kuma je kitchen in yi girki". Gyara kwanciyarsa ya yi ya ce "Ina jin releif a haka, ba zan tashi ba" "Gaskiya cinyata ta gaji, duk jikina ya yi tsami". "Mimi" "Na'am basarake" "Meyasa ki ka faɗi maganar ɗazu?" Ta ɗan yi jimm, sannan ta ce "Wacce?". "A kan Mummy, kar ki sake makamanciyar wannan maganar,Idan maganar ta koma kunnenta fa? Zaki iya haddasa rigima, babu ruwanki da irin wannan abubuwan kin ji ko?". Ta numfasa ta ce "Waye zai je ya gaya mata, ni fa ba ƙarya nake yi ba, wata mata na gani tare da ita, gaba ɗaya ba kalar mutane ba, kuma da za ta tafi ta tashi ta bita k....." Ya katseta ta hanyar cewa "Wannan matar tun ina da shekara bakwai a duniya nake ganinta, take azabtar da ni, ko ta ɗaure ni tamau da sarƙa, ko ta din ga dukana da sarƙar, na yi mamaki da ka ce ki na ganinta, ban taɓa gaya wa kowa ina ganin ta ba. Rumaisa wannan shi ne ainihin adam, kin ga abun da na din ga yi jiya, kamar mahaukaci, dan ma na daina duka da cizo kamar maye, zaki iya cigaba da zama da ni a haka, abokiyar gaba?" Ga tausayi ya bata, amma hakan bai hanata yin dariya ba, ta ce "I tuntuni na sani, baba uwani ce ta gaya mini, idan ranka ya ɓaci ka na komawa kamar mahaukaci, har yaya Abubakar aka gayawa, kan ka aureni, wai kai maye ne. Sanan ban manta ba, kuma ina nan a kan baka na. Ai sai yanzu na gane ka na da ɗan kirki kaɗan, kar ka mutu sai na gama makaranta mai lilo" Shiru ya yi jikinsa a sanyaye "Ba ki damu da ni ba sai lilo ko?". "Kai fa ka gama addu'a ka mutu, kana mutuwa zan koma gida, idan na ƙara girma na auri Yaya Mahmud" ƙuri ya yi mata da ido, sai kuma ya tashi daga kan cinyarta ya koma kan gado ya kwanta. Ita kuwa madigar ko a jikinta ta yi nata wuri, dama ba ta son zaman wuri ɗaya. Abun da ya tsaye masa a rai bai wuce, yadda rumaisa ta ce Baba uwani ce ta gaya mata, ya na komawa kamar mahaukaci ba, sai ya ji kimar dattijuwar ta ragu a idonsa, sai kuma abun da rumaisa ta faɗa na ƙarshe bai yi masa daɗi ba. *** Tamkar ya janyo dare, haka yake ji, ƙasan zuciyarsa ya na fatan idan ya je gidan ya ga Iman. Iman ma sai kaiwa take ta na komowa, ta na fatan Allah ya sa mai sunan baba ya zo. Ammi kuwa da ta dawo, zuwa ta yi aka yi wa adam tofi, wurin malamin da take sawa ya na yi masa, ta karɓo masa, sai dai ta bar shi ya ɗan farfaɗo har da fara'a ta dawo ta tarar da shi sai a hankali. Sai ta yi zaton kawai jikin ne. Haka nan iman ta tsinci kanta da yin kwalliya cikin doguwar riga, har ammi ta na tsokanarta, ko siriki za ta kawo mata. Ta na nan zaune a falo, ta na danna waya, Sabir sai wasan sa yake yi a tsakar falon, gefe rumaisa ta na cin abinci, dan ba ta kuma komawa wurin takawa ba. Jabir ne ya yi sallama, duk suka amsa masa, ya shigo cikin fara'a, "Autar Ammi da sirikar Ammi, Barkanmu da wannan lokaci" Ba yabo ba fallasa, Iman ta amsa masa, rumaisa kuwa ta share shi. "Ina takawan yake ne?" Iman ta nuna masa sashin Ammi, ya ɗan tsaya ya kalli Iman ya ce "Bari in shiga in fito, zamu yi magana dear, kin yi kyau masha Allah" Iman ta yi masa shiru, rumaisa kuwa ta kwaɓe baki. Ya na shiga ciki, message ya shigo wayar iman "Na zo" message ɗin mai sunan baba. Da sauri ta tashi ta yi waje, a harabar gidan ta tarar da mai sunan baba, a cikin ƙanan kaya yake, amma yayi kyau sosai da sosai. Sai da ta furta Masha Allah, a hankali. Unexpectedly ya ɗaga kai ya ga Iman, cikin zazzaƙar muryarta ta ce "Sannu da zuwa yaya umar". "Yauwwa sannunki" daga nan ta yi masa jagora, har ciki. Ruma na ganinsa, ta tashi ta din ga tsalle ta na murna, amma ya basar da ita ya ɗauki Sabir, da ya rarrafo wurinsa da gudu. "Mai sunan baba, ba ka yi murna da ka ganni ba?" Kawai yayi mata murmushi, ya na sake rungume Sabir. Ko da suka shiga sashin Ammi, Jabir na ganin mai sunan baba ya haɗe rai, ya yin da takawa mamaki ne ya kama shi da ya ga mai sunan baba. Suka gaisa da Ammi, yake gaya mata rumaisa ce ta ce masa magidanta ba lafiya, ya zo ya duba shi kan ya sanar da mama, dan za ta iya tayar da hankalinta. Ammi ta ce "Ruma ce ita ma da abun ta, ai ya warware, dan Allah kar ka gaya mata hankalinta ya tashi, ya ji sauƙi. Mutumin da ya zo dubiya, bai fi mintuna goma ya yi ba, kuma daga takawan har jabir bayan sallama da ya yi musu, babu wanda ya sake kulawa, ya yi wa ammi sallama. Kayan ciye-ciyen ya ba wa sabir, sai dai sabir ya ƙi yarda ya ajiye shi ya maƙalƙale shi. Ya fita da shi a kafaɗarsa ya na murmushi, murmushin ba ƙaramin kyau ya yi masa ba. Jabir ne ya biyo bayan sa, ganin Iman ma ta bi bayan mai sunan baba. Ya ɗan kalleta sannan ya ce wa Sabir "Ka je wurin antynka, ko da kai zan tafi babana?" Iman ta yi murmushi ta ce "Baban mai sunan baba" Murmushi ya yi, ya miƙa mata sabir da yake ta ihu, ya na sake miƙawa umar hannu. "Ke iman zo ki wuce, ina son magana da ke, na gaya miki tun ɗazu amma kin yi banza da ni, ki ka bi wani" Jabir ya yi maganar cikin umarnin da iman ta ji ya yarfata. "Amma uncle J, ai gani na yi ka na wurin takawa ne, shiyasa". "Shut up malama" yayi maganar cikin fushi da kishi. "Meye haka? Yayana ne fa, me ta yi maka?" rumaisa ta yi maganar tana harar Jabir. Magana yake son sake yi, amma mai sunan baba ya ƙura masa ido. Sai kuma ya yi shiru, ya ji ya kasa sake magana. Rai a ɓace ta wuce, ba ƙaramin haushi  ta ji ba, dan tuni ta fara kuka. Ruma ta ce "Mai sunan baba, bari na raka ka" "No, ki je ki kula da mijinki, zan ce ki na gaishe su" ya juya ya fice, wani irin takaici ne ya kama mai sunan baba, ba ƙaramin haushi ya ji ba, abun da jabir ya yi wa Iman, kuma ya lura da yadda yake shishshige mata tun lokacin bikin rumaisa, tabbas ba dan a gidansu yake ba, zai nuna wa jabir, ba a shiga shirgin sa" A harabar gidan mai sunan baba suka haɗu da Mahmud, Mahmud ya yi masa magana, mai sunan baba ya tsaya suka yi musabaha, sai dai ya yi ta kallonsa, ya na tunanin yanzu ya baro Adam a ciki, kuma dai ya san ba shiga sabgar juna suke yi ba. Mahmud ya ce "Ba Adam ba ne, mahmud ne, amma ka na da alaƙa da rumaisa ko?". Mai sunan baba ya jinjina masa kai ya ce "Eh ƙanwata ce". "Kamannin na gani ai, sunana Mahmud" Mai sunan baba ya ce "Babban suna, ni kuma umar" Mahmud ya ce "Masha Allah, ka gaida gida, a gaida mama, duk ina jin sunanku a bakin ƴa ta, bari na zo na sauke ka a hanya, fita zan yi" Umar ya jinjina kai, dan gaba ɗaya ya ji Mahmud ya burge shi, mussaman yadda ya yi masa magana kamar sun saba. A ɗaki rumaisa ta tarar da iman, ta na kuka. Ruma ta ce "Gaskiya kin ba da ni, wai shi waye Jabir ɗin nan ne? Ya san waye mai sunan baba kuwa? Ke ma kin wani zauna ki na yi masa kuka, ni ma ina da saurin kuka amma kin ga ina yi? Meyasa ba a yi wa Nusaiba abun da ake yi miki?". Iman ta share hawayen ta, Sabir sai jijjiga iman yake yana cewa Iman, dan ya iya sunanta raɗau, kamar shi ya raɗa mata. Ruma ta ce "Gidanku, Anty zaka ce ko Mummy" Iman ta yi murmushi ta ce "Anty Nusaiba ta su ce, kuma ta na da bakin da idan aka yi mata za ta rama, ni bana son tashin hankali ne, baki ga komai ba ma, dan su Fauziyya sun daina zuwa ne, baki ga abun da suke yi mini ba". Ruma ta ce "Wallahi ko a kan bola aka haifeni, ba zan yadda da wulaƙanci ba, amma cika mini alƙawarina. Meyasa papa ba sa shiri da daddyna, meyasa kuma ba ya shiri da ammi, Meyasa ki ke cewa kan ki, ƴar tsintuwa?". Iman ta ɗan yi shiru, sannan ta numfasa, a dai-dai lokacin da wani hawayen yake zubo mata. *** ASALIN LABARI..... 1972 Kano state emirate palace, a zamanin sarki Adamu Abdullahi. Masarautar kano na ɗaya daga cikin manyan masarautu, da ake ji da su a Nigeria, ba iya Nigeria ba hatta turawan mulkin mallaka, suna ji da wannan masarauta. Sarki Adamu Abdullahi, mutum ne mai adalci, karamci da kuma yakana, kuma jarumi, hakan ya sanya soyayyarsa a zukatan al'ummarsa. Ya na da tarin dukiya, ƴaƴa, barori da sauran hadimai. Yana da tarin ƴaƴa, daga matansa da kuma ƙwarƙwarorin sa. A wannan lokacin, ya na kimanin ƴaƴa goma sha tara, maza da mata, a cikin mazan Allah ya jarrabe shi da ƙaunar ɗan sa Muhammad, da suke kira Sharif, tun ya na iya ɓoyewa har ya gaza, yake nuna masa soyayya muraran. A lokacin turawa sun kawo harkar karatun boko, wanda a lokacin dama sun tarar da hausawa da karatunsu na allo da tsangayu. Galibi ƴaƴan sarki a wannan lokacin, suna da sarautunsu, a lokacin da suke ƙallafa rai a kan sarauta, shi kuwa Sharif sam hankalinsa ba ya kan sarauta, ya fi karkata ga neman ilimi, na addini da kuma na zamani, da turawa ne suke koyar da su. Sharif ya na da zafin zuciya, Mai marataba ne da mai babban ɗaki, wato kakarsa kawai ke iya sarrafa shi, kasancewar mahaifiyar sa ta bar duniya. A wurin mai babban ɗaki yake, sai kuma mahaifiyar Jafaru, wato turaki a yanzu, dan kamar uwa ya ɗauketa ita ma. Bayan ya kammala karatun sakandare, turawa suka ba shi gurbin karatu a ƙasar Ingila, mai martaba ya ce bai san zance ba, babu mai raba shi da ɗan sa, Sharif ya ƙallafa rai a kan ya na son tafiya. Sai da mai babban ɗaki ta sanya baki, da wasu manya sannan ya amince. Sai dai mai martaba ya na tsoron rayuwa cikin turawa, ga ƙanƙanin yaro kamar Sharif a wannan lokacin. Bayan tafiyar sa, ya kammala degreensa na farko, a kan fannin tattalin arziki, ya ji daɗin zaman ƙasar waje, ba takura, babu kana tafe ana take maka baya, duk a hanaka sukuni da kaɗaici, a cewarsa. Da ƙyar mai martaba ya saka aka dawo masa da Sharif, sai dai da ya dawo duk ya yasar da wasu al'adun, harkar gabansa ce kawai ta dame shi. Ko zaman fada ba ya zuwa, idan ya shilla ya tafi na sa yawon, sai an ganshi. Hakan ya fara damun mai martaba, ya fara tunanin yi wa Sharif sarauta, ko zai nutsu, sai dai ya na cikin yaransa ƙanana. Sharif ya tsiri cewa zai tafi master's gombe, nan ma sai da aka kai ruwa rana, mai martaba ya ce ya na da sharaɗi, abokin sa wazirin daura, ya bashi ƙanwar matarsa ya aura wa ɗaya daga cikin ƴaƴansa dan ƙarfafa zumunci, dan haka ya ce Sharif ne zai aure ta. Sharif da fari ya ce "Shi ba ya son ta, daga baya saboda yana so karatu, ya amince, amma sai ya gama master's ɗin sa, mai martaba ya ce bai yadda ba, lokacin ya yi tsayi, wazirin daura ya ce a saka shekara, ba damuwa kan nan ta ƙara girma ita ma. Ko da Sharif ya tafi gombe, ya samu abokai ya cigaba da rayuwarsa, yadda yake so, duk da mai martaba ya na turowa, ana saka masa ido a kan sa, duk da akwai manyan mutane da suke bibiyar sharif, saboda karamci ga mahaifinsa. Ɗalibai ba kowa ya san Sharif ba, yayi ta kashe musu kuɗi, suna bin sa, har sabon babur ya saya, yake yawonsa a garin gombe. Ana haka yawo ya kai shi wani ɗan ƙaramin gari, nesa da cikin gari kaɗan, ya kusa buge wata yarinya, ya yi ta bata haƙuri, ya kafe babur ɗin sa ya rakata gida. Tun da ya haɗu da yarinyar nan ya samu wurin zuwa, kusan kullum suna tare, ita kuma a lokacin yarinya ce sosai, yadda yake biye mata suna shirme, yake bin ta gona ya sanya ta saba da shi sosai. Sunanta Bintu, ƴar wani babban malami ce a garin, shigaban manoma na wannan yankin, dan haka ya na da rufin asiri. Babanta ya na ƙaunar fura da nono, akwai wata riga da take zuwa sayo masa, duk juma'a, a titi suke haɗuwa da Sharif, ya ɗauke ta a babur su tafi cikin rigar nan, Bintu ta saba da su sosai, bafulatanar da take sayen nonon a wurinta, ta mayar da bintu kamar ƴar ta, haka Sharif ma sun saba sosai, dan kakar bintu ma yake ce mata. Kwatsam aka je aka gaya wa baban bintu abun da yake faruwa, ya din ga yi mata faɗa, aka hanata fita, hakan ya damu Sharif, ya kasa jurewa, ya bita har gida. Yayyen Bintu suka kore shi, amma yaƙi tafiya, sai da ya haɗu da mahaifin Bintu, ya ce masa idan har son ta yake ya turo manyansa ayi magana. Baban bintu yayi haka, dan ya kori sharif. Sharif ya koma gida ya sakawa mai martaba rigima, shi fa baya son wannan jamilar, Bintu za a aura masa an ce ya tura iyayensa. Mai martaba da fari ransa ya ɓaci, mai babban ɗaki ta taushe shi, ta ce dama ai so ake yayi auren, a fara aura masa bintun, sai ayi aurensa da Jamila, tun da dama shekara aka saka. Matan mai martaba suka din ga ƙanan maganganu, suna cewa ya na biye wa yaro, kimar sa na zubewa. Ya tashi tawaga daga Kano, aje a yi masa bincike a kan Bintu, idan ba su da wani aibu, a nema wa Sharif aurenta. Mai martaba ya ji daɗin bayanin da ya samu, a kan Bintu da iyayen ta. Da yawa sun yi mamaki, yadda kamar ɗan sarki daga kano, zai auri ƴar talaka. Aka yi shagali sosai, aka yi auren. Daga Bintu har Sharif, yarintar su kawai suke zubawa, dan a lokacin ba ta wuce shekara sha uku ba. Mai martaba ya tura mutane, da ban haƙuri a kan abun da ya faru, tare da tabattar wa waziri, idan lokaci yayi ba fashi, za ayi auren Sharif da Jamila. Jamila da yayarta, da mahaifiyarsu, ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, dan haka suka din ga bin malamai, Allah ya tabattar da auren Jamila da Sharif. Jin akwai wadda ake so Sharif ya aura, Bintu ta din ga murna, za a kawo mata ƙawa. Wasa² sai da Sharif ya shekara biyu, kan ya auri Jamila, yau ya bayar da wannan uzurin, gobe ya bayar da wancan. Ana haka Galadiman wannan lokacin ya rasu, bayan shafe zaman makoki, mai martaba ya sanar da naɗin Sharif a matsayin Galadima. Ƴaƴan mai martaba da matansa, suka ɗaga hankalinsu, saboda gani suke rashin adalci ne, a bawa wannan yaron da ba shi da cikakken kai wannan babbar sarauta, bayan ga yayyensa. Mai martaba ya yi burus, kuma bayan naɗin sarauta, aka ɗaura masa aure da Jamila. Maimakon Bintu ta damu kanta, ita murna take yi, shi uban gayyar ne yake ta takaici, dan har ga Allah ba ya son jamila, ga wannan sarautar da aka bashi, ya na da shekaru ashirin da biyar. Jamila ta ƙudiri aniyar, ɗaukar fansar abun da aka yi mata a kan Bintu. Rayuwa ta cigaba da garawa, son da Sharif yake yi wa Bintu, ya sanya mai martaba da mai babban ɗaki suma suke son ta, saboda tana da tarbiyya da nutsuwa. Hakan ya ja mata baƙin jini a cikin facalolinta. Da an yi maganar sirikai, sai mai martaba ya ce "Ƴa ta bintu". Sharif da kansa yake koyawa bintu karatu, daga baya ya sakata a makarantar boko. Sai dai ba ayi shekara da auro Jamila ba, abubuwa suka fara sauyawa a gidan. Jamila ta fi Bintu wayo sosai, dan ta ba ta shekara biyu ma, kuma ta rayu a gidan wazirin daura, hannun yayarta, dan haka ta san abubuwa, da munafunci na gidan sarauta. Saɓanin Bintu, da neman ilimi kawai ta taso ta na yi a gidansu, dan ita a gidansu ma, ba a banbance ɗan wannan ɗaki da wancan. Dan haka da bin malamai, da makirci, Jamila ta fara haɗa Sharif da Bintu faɗa, kuma ta din ga shishshigi a wurin facalolinsu, tare da nuna musu ita ta Allah ce, Bintu ba wayo sosai, sai dai ta yi ta kuka. Tsawon shekaru uku, da aure, sannan ta fara al'ada ma a gidan miji, wataran ta je garin su, ta tarar yayarta ta yaye jaririyar da ta tafi ta bari tana goyo, mai suna laila, ta saka rigima sai an bata ita. A duk lokacin da ta je gida, sai ta je rigar nan, wurin Ade, wato bafulatanar nan, idan har ta je kamar kaka da jika, za ta tarar ta ajiye mata tsintsiya, man shanu, da sauransu, kuma ita ma Bintu da na ta alkhairi take tafiya ta yi mata. Bayan ta dawo da laila, sharif bai ce mata komai ba, dan ya na son yara shi ma, mai babban ɗaki ta bata hadima, Uwani, domin ta din ga tayata kula da yarinyar. Sai dai ba Bintu ba, Jamila ma ba ta taɓa ko ɓari ba, suka kasa zaune suka tsaye ita da ƴan uwanta, Bintu kuwa ko a jikinta, sabgarta kawai take da karatun ta. Ana haka mai babban ɗaki ta rasu, wanda hakan ba ƙaramin tayarwa al'ummar masarautar hankali ya yi ba, mussaman Sharif da Bintu. Kwatsam Bintu ta din ga rashin lafiya, babu ƙaƙƙautawa, duk ta rame, Aka kaita asibiti aka tabattar ta na da juna biyu. Saboda tsabar ƙuruciya da murna, Sharif ya je ya gaya wa jamila, wai ta taya su murna. Aikuwa ta ƙwafe abun nan a ranta, da alwashin ganin bayan cikin, a cewarta tun da aka fara auren Bintu, sai t jira ta fara haihuwa. Dan muraran jamila ke nuna wa Bintu ƙiyayya. Dan haka maimakonsa bin malamai, Jamila ta fara shiga bokaye, da tsubacce-tsubacce iri-iri, domin ganin bayan cikin nan. Allah mai jarraba bawa, sai da Bintu ta yi ɓari uku a jere, kowanne sai ta sha wahala kamar ba ta rayu ba. Hankalin Sharif ya tashi sosai, ya damu, mai martaba ne ke kwantar masa da hankali, ya saka ake yi wa Bintu rubutun Alqur'ani. Sai a karo na huɗu, sannan cikin ya zauna, sai dai ta azabtu saboda laulayi, dan ƙarshe ba dan Sharif ya so ba, aka mayar da Bintu gida, ya din ga jin haushi, dan ba ya son ta yi nesa da shi, hakan ya sake ƙular da jamila, ta yi amfani da duk wata dama, ta asiri, wurin ɗauke hankalin Sharif daga kan Bintu, tun da ta je gida bai taka ya je dubata ba, sai da ta haihu, aka aiko. Jin haihuwar ya fi komai saka shi farinciki, ta haifi ɗa namiji, sai a lokacin ya din ga murna, ya je garinsu, abun ka da mutan da, ko da wasa bai ga alamar ta yi fushi da shi ba, sai dai bayan suna yaro ya ci sunan Abdullahi. Aka ɗauki soyayyar duniya aka ɗorata a kan yaron nan. Watanninsa shida, yayi zazzaɓin wuni ɗaya ya rasu. Mutuwar nan ta girgiza Sharif, da ƙyar aka shawo kansa. Still sai da Bintu ta sake ɓari, sannan ta samu ciki ya zauna. Da aka haife shi, aka saka masa Adam, wato sunan mai martaba, mahaifin Sharif. Ake kiransa da takawa, saboda gidan sarautar dabo ba a faɗar sunan saboda girmansa, sunan mai martaba ne, kuma a lokacin Sharif ya yi wa Bintu srautar giwar galadima. Jamila ba ta sake shiga tashin hankali ba, sai da ta ga, hankalin kowa ya koma kan Adam, ba a kansa aka fara yi wa mai martaba takwara ba, amma an fi nuna masa so, duk soyayyar da mai martaba yake yi wa Sharif ya mayar da ita kan Adam. Adam na da watanni bakwai, wani cikin ya ɓulla a jikin Bintu, da yanzu ake kira da ammi. A lokacin laila ta tasa, ba shi da wata ƴar raino, sai Laila da baba uwani, idan baba uwani ta zo ta gama aikace-aikacen ta, sai ta tafi gida ta bar sauran hadimai, laila kuma ta cigaba da raino, dan Ammi ba ta iya komai. Sharif duk ya shiga damuwa, yana murna zai sake samun ƙaruwa, amma yana jin tausayin Bintu. Ƙannen Jamila na yawan zuwa gidan, su yi ta faɗa da laila, ko su din ga cin zalin Adam, sai dai laila a tsaye take, ba ta da haƙuri, haka za su yi ta dambe, Ammi ta yi ta mata faɗan ta rage faɗa. Wannan cikin shi ma ya tsaya wa Jamila, ta yi duk mai yiwu wa ta salwantar da shi, amma abu ya gagara, sai da aka haife shi, shi ma namiji. Aka sakawa yaron Mahmud, sunan galadiman da ya rasu. Adam ba shi da wayo sosai lokacin, dan bai cika shekaru biyu ba, amma yana son sabon yaron da yake gani a wurin amminsa mai kyau, yana matuƙar kama da Adam da sosai da sosai, tamkar an raba kara biyu, duk kamarsu ɗaya da galadima. Zigar facaloli, da soye-soyen zuciya, ya tunzura Jamila, ta rasa in da za ta saka kanta, ta din ga jin idan ta samu dama, tsaf za ta iya raba yaran nan da rayuwarsu. A hakan, Sharif ya cigaba da tsaya musu, akan karatu, duk da ammi na fuskantar ƙalubale, kowa ya juya mata baya, an fi tausayin Jamila, shi kansa Sharif gaba ɗaya ya canza mata. Sai dai Mahmud ma, bai fi wata bakwan ba, ta sake fuskantar tana da ciki, dan idan ta haihu ta gama biƙi ba ta al'ada sai dai ta ga ciki. Ayshercool. 08081012143 Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Hankalin Jamila ya yi mummunan tashi fiye da da, kasancewar idan mutum ya na aikata abu, gani yake kowa ma haka yake, ya sanya ta ce Ammi ce take yi mata asiri, ta hanata haihuwa, dan haka ta ƙuduri aniyar wani abu a ranta, bayan yin shawara da Lubabatu, wato matar wan Sharif, wadda ta zame mata aminiya, a lokacin ita kuma mijinta ba shi da sarauta, yarima ne kawai. Sai bayan da suka bi gari-gari, yawon asiri, sannan Jamila, ta bijiro wa da Sharif cewar tun da ba ta taɓa haihuwa ba, a bata Mahmud ko Adam, tun da giwa ta na wani laulayin, ba iya kula take da yaran ba, sai dai laila da masu aiki. Babu musun komai, dan a lokacin ya na tausayin yadda take damuwa da rashin haihuwa, ya ce wanne take so a cikinsu. Cikin ragon azanci, da ganin yadda ammi ta fi son Mahmud, fiye da takawa, saboda takawa na kowa ne, Mahmud kuwa ƙarami ne, amma jamila ta ce Mahmud take so, a lokacin ko yaye shi ba ayi ba. Ammi ta yi kuka, ta yi kuka, har wurin mai martaba ta je a kan ya taimaka ya karɓar mata ɗan ta, amma ya ce ta yi haƙuri, da ita da Jamila duk ɗaya ne, ta tausaya wa jamila, tun da ita ba ta taɓa haihuwa ba. Rashin ɗan ta, ga laulayi, ya sanya duk ta jeme, ƙarshe tana ji ta na gani, sharif ya tattara ya koma wurin Jamila, saboda ita kullum babu lafiya, ta daina cin abinci duk ta rame. Da fari Jamila ta so azabtar da Mahmud ne, dan ta fara, kuma labari ya na iske Ammi, amma daga baya ta canza shawara, take ganin bari ta yi abun da har giwa ta mutu, zai fi yi mata ciwo, dan ta rama abun da aka yi mata, na fara auren Bintu maimakonta. Dan haka ta koma nuna wa Mahmud so, a gaban mutane, da mahaifinsa, hakan ya saka kowa Addu'a yake yi mata, a kan Allah ya bata na ta ita ma. Laila ce ke satar jiki, ta ɗaukko wa ammi Mahmud, ta kawo mata shi ta ganshi, duk yadda laila ta shaƙu da Sharif, sai da yayi mata rashin mutunci a kan ɗaukar Mahmud ta kai wa Ammi, ya ce kyauta halak ya bawa Jamila Mahmud. A haka Ammi ta haihu, wannan karon ta samu ƴar budurwa, ta yi ta murna, aka saka mata suna Khadija sunan mahaifiyarta, sai dai duk da haka tana kewar ɗan ta, Adam tun yana kuka, yana tambayar ammi Mahmud, har ya daina. Jamila ta toshe duk wata kafa, da zata sada Ammi da Mahmud, Ammi ta yi wa Sharif kuka, ta yi masa magiya a kan a din ga bari ta na ganin ɗan ta, amma ya ce wai Jamila za ta tambaya. Sai dai jaririyar nan ma ba ta yi tsawon rai ba, ta koma ga Allah. Abubuwa suka yi wa ammi yawa, depression ya nemi kamata, amma a lokacin ba a waye da ciwon ba, aka mayar da ita gida, wai aljanu ke damunta. Kamar wasa, Jamila ma ta samu juna biyu, wanda tun da ta same shi take iyayi, da sanabe da feleƙe, ranar kwanan Bintu, sai galadima ya bata haƙuri, wai zai kwana da Jamila ba ta da lafiya. Ammi ba ta taɓa tanka masa ba, dan a lokacin ta miƙa wa Allah lamarinta, ta rungumi laila da Adam, ta cigaba da riƙon abun ta, gefe tana zuwa makaranta. Facaloli suka din ga ziga jamila, suna ce mata uwar magaji, ai yadda aka tsallake yayyen sharif ya yi sarauta, haka  za a tsallake ƴaƴan bintu na ta su yi sarauta. Sai dai Allah mai yadda ya so, tashin farko ta haifi mace, ta din ga ƙunci tana baƙin ciki, kwanan ƴar uku ita ma ta mutu. Nan ta din ga yaɗa cewar, Bintu ce take bawa bokaye ƴaƴanta su cinye, shi ne wannan karon ta haɗa da tata ƴar, tun da dama ƴar gidan malaman tsubbu ce. Duk wannan abun da ake yi, Sharif bai daina ƙaunar ɗan sa takawa ba, sannan ya na ɗaukar Adam ya shiga da shi wurin Mummy Jamila, amma fa ba zai ɗau Mahmud ya shiga da shi wurin Ammi ba, wai kar ta tayar da rigima ta ce sai an bata ɗan ta. Shi kansa ya na mamakin yadda aka yi yake yi wa giwarsa wasu abubuwan kamar ba shi ba. Iyayen ammi suka yi ta bata haƙuri, da nuna mata dama aure, sai an yi haƙuri ibada ne, ta yi haƙuri da ɗan nan Allah ya bata wani. A kwana a tashi, ciwon ajali ya kama mai martaba, shi ma Allah ya karɓi abun sa, al'umma shi ma sun ji mutuwarsa sosai da sosai, bayan rasuwarsa maimakon a naɗa sarki a 'yaƴan sa, sai aka naɗa ƙanin sa. Hakan ba ƙaramin fitina ya ja ba, dan sai da zumunta ta taɓu. Shi kuwa Sharif, ba sarautar ce ta dame shi ba, rashin babban masoyin sa mahaifin sa ya fi damun sa, kuma wanda aka naɗa uba ne a wurin sa, dam tare suka rayu a wurin mai babban ɗaki kan ta rasu, shi yana ɗan ƙarami sosai, shi ne yake yi masa komai, kamar ɗan sa, kuma idan ya kwaso rigimar sa shi ne mai taya shi, shawo kan mai babban ɗaki da marigayi, dan haka shi duk ɗaya ne a wurinsa. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, bayan wannan haihuwar da Mummy ta yi, sai da ta shekara uku, sannan ta haifi wata ƴa macen, bayan sun gana ɓata Ammi a cikin masarautar, da zancen ta na yi mata asiri. Sai dai ba haka ta so ba. Ba wani armashi haihuwar ta ta, dan zuwa yanzu babu jinsin da giwa ba ta haifa ba. Adam ya kai shekaru biyar, Mahmud huɗu da watanni, hatta makaranta, Jamila ba ta yadda an saka su ɗaya ba da Mahmud, idan Adam da Mahmud suka haɗu kamar su cinye juna, har Mahmud ya fara fita ya je sashin Ammi wurin adam, duk da bai san ba mummy ce mamansa ba, Ammi ta kama shi ta rungume ta yi ta kuka. Baba Uwani ta yi ta bata haƙuri, ta ɗauke shi ta mayar da shi, dan kar galadima ya shigo ya gani, yayi mata faɗa. A irin haka Jamila ta fara amfani da baba uwani, ta bata kuɗi tana sakata kawo mata rahoton abun da yake faruwa a sashin Ammi, duk da ammin na iya ƙoƙarin ta wurin kyautatawa baba uwani. Wataran Adam ya shiga sashin Mummy, ya na neman Mahmud, kuma ya ga ƙanwarsu, dan yana son yara. galadima na ganinsa ya yi murmushi ya tashi tsaye daga kashingiɗen da yake yana cewa "Maraba da kai babana, abun ƙaunata kuma magajina, galadima ɗan galadima kuma jikan sarki, jikan manoma da malamai" Sai da kirarin da galadima yake yi, ya bawa Adam ɗin dariya, wani dunƙulallen baƙin ciki ya tokarewa Mummy zuciya, galadima magajin galadima? Wato ita ko oho, wato har ma ya sa ran ɗan sa zai yi sarauta, nan ta yi alwashin idan da ranta sai dai ayi biyu babu. Tun daga nan ta fara turawa Mahmud aƙidar tsanar Adam, wai babansu ba ya son sa takawa yake so, dan haka ya daina kula shi, shi ma ba son sa yake yi ba. Labari ya iske ammi cewa, fulanin nan su ade sun tashi, Ade ta bar sallahun a gaya mata tashi ya kama su ba shiri, sun bar wannan rigar sun yi gaba.', za su koma mahaifarsu. Ammi sai da ta je har rigar ta tabbatar wa da kanta, ta sha kuka sosai da sosai, yadda ta saba ta shaƙu da Ade da ƴan rigar, kamar danginta. Rayuwa ta cigaba da tafiya, Jamila ta sake haihuwa, amma still ƴa ma ce, sai da ta ji tamkar ta mayar ta ce ba ta so. A wannan lokacin sarkin da yake ci, mahaifiyarsa ta na raye, dan haka ammi a wurinta take samun sassauci. Mai babban ɗaki ta wancan lokacin da ta riƙe shi, ita ma ba ita ta haife shi ba. A wannan karon, shi ma Sharif ƙarara yake nuna son Adam, saboda soyayyar da yake yi wa mahaifinsa, da yadda mahaifin nasa, ya nuna masa ƙauna. Jamila kuma ta yi alwashin rusa soyayyar nan, da cigaba da baƙantawa giwa, domin rama abun da ta yi mata, na fara auren Galadima. Duk yadda ta so raba Mahmud da Adam, ba ta yi nasara yadda take so ba, duk da Mahmud ya fara yadda da abun da take gaya masa, sai dai duk yadda take korar Adam idan ya zo wurin Mahmud ya kasa zuciya. Tuni Mutanen masarautar, wasu sun fara ɗauka, tare da kiran Adam magajin galadima, har da masu ce masa galadima ƙarami, ko kuma magajin takawa, idan ƴan kan zagi suka yi masa wannan washin, haka galadima zai ta yi musu kyauta. Hajiya Lubabatu ta samo musu wani hatsabibin boka, malam na kan dutse, suka je wurin sa a kan suna son a nakasta Adam, yadda ba zai moru ba, kuma a saka gaba da ƙiyayya tsakaninsa da Mahmud, yadda wuta da ruwa ba zasu jitu ba, haka suma sannan a saka wa galadima tsanar Adam. Bokan ya ce "Sai an kai masa Adam, saboda ya san aikin da zai yi a kan sa, sannan a taho masa da jinin Mahmud a sirinji. Ta koma gida, ta saka galadima a gaba, wai tana son ta je garinsu, za ta tafi da Adam, galadima ya ce bai yarda ba, ta haɗa baki da malaman makarantarsu Adam, ta je ta ɗauke shi a makaranta, aka shaƙa masa wani abu ya suma, suka tafi da shi wurin boka, tare da jinin Mahmud. Bokan ya zuƙi jinin Adam, ya haɗa da na Mahmud, ya zuba wani abu a ciki, jinin ya rabu biyu ɗaya ya yi baƙi, ɗaya ya yi ja, ya mayar da jinin jikin Adam, ya bata sauran jinin, ya ce ta yi girki da shi, ta bawa Mahmud da galadima su ci, ya raba su. Ta ce ai ba iya nan take so ba, so take a haɗa shi da ciwon, da zai nakasa, nakasa ta har abada, da ba zai yi sarauta ba. Nan ya yi wani ƙulumboto, ya saka wani abu, ya huda wuyansa, ya zuƙi jinin Adam, ta wuya, ya zuba a wani abu, ya ce "Ramin da na yi a wuyansa, ta nan aljanar za ta din ga shan jininsa duk shekara, sai dai babu wanda zai iya hudat, Sannan zan yi wani abu da sauran jininsa, duk shekara za a din ga samun mahaukacin doki, ayi masa, zan haɗa laya da sunansa, wadda za a kai maƙerar da ta shekara goma, a binne, sannan zan saka wannan aljanar, ta zuba masa jinin mahaukaciyar kura a jikinsa, an nakasta shi, nakasa ta fili da zahiri, iya rayuwarsa wannan aljana za ta cigaba da kula da komai, tun da an bata jininsa, sai dai loka-lokaci, za ta din ga buƙatar wani abun" ya wassafa musu abun da za su bayar, suka bayar sannan suka tafi gida. Ammi ta kaiwa Adam, yana bacci, wai biyo ta yi ta hanyar makarantar su, ta ga an tashi shi ne ta ɗaukko shi yayi bacci a mota. Ammi ba ta kawo komai ba, ta karɓe shi, ta yi mata godiya, sai dai tun ammi ta na saka ran adam ya tashi, har tsoro ya kamata. Sai dai bayan ya tashi ba baki, sai dai kallo. Hankalin Ammi ya tashi, ta gaya wa galadima, hankalinsa ya tashi suka tafi asibiti aka ce lafiyarsa ƙalau, ya ce idan zuwa washegari, bai yi magana ba, za a kai shi babban Asibiti, ko ƙasar waje ne a akai  shi, sai da daga haka washegarin, tunanin galadima ya sauya, ya ce wai ta ƙyaleshi shakiyanci ne. Abu kamar wasa, sai da Adam ya yi wata tara, ba magana, ga wani irin bacci, mara kan gado, ammi ta dage addu'a, ta kai shi gidansu wurin mahaifinta aka dage da roƙon Allah, sannan ya dawo yake magana. Gaba ɗaya galadima ko a jikinsa, ya daina nan-nan da shi, sai dai abun ka da ɗa da uba, soyayyar ba ta dishe duka ba, wataran idan ya gan shi ya na jin daɗi. A lokacin Mummy ta haifi Fauziyya, mutane ana ta shigowa, Ammi da laila da adam, sun je ganin jaririya, Adam na ganin Mahmud, ya nufi wurin sa yana kiran sunansa. Sai dai Mahmud ya hankaɗe Adam, sai da ya faɗi ƙasa, ai yana tasowa, sai idanunsa suka koma kamar na mahaukaciyar kura, yana wani irin gurnani, ya shaƙe Mahmud. Ammi hankalinta ya tashi, duk wanda ya je raba su, sai Adam ya cije shi, kowa ya yaƙushe shi, sai jini ya fita. Da ƙyar Ammi ta riƙe shi ta na yi masa addu'a, ta ja shi ta tafi da shi sashinta, tana kuka ita da laila, tana tunanin menene ya samu adam?. Sai dai haka ya wuni yana wannan gurnanin, kamar kare. Mummy kuwa bala'i ta din ga yi, wai za a kashe mata ɗa, dama adam ɗin maye ne, ya tsotsa a wurin uwarsa, ko kuma a garin yawon bin bokaye, ɗan ta ya haukace. Magana ta din ga yawo a fada, galadima ya je har sashin Ammi, ya din ga yi mata faɗa, wai ita ta sangarta Adam, har yake yinƙurin kashe ɗan uwansa. Halin da ya tarar da Adam ɗin sam bai dame shi ba. Tun daga nan, idan faɗa ya haɗa Adam da yara, sai ya burkice, ya na gurnani, da cizo, idan kuma yayi cizo sai jini ya fita, wanda wannan jinin aljanar take sha. Wani lokacin idan ana ziga wutar maƙerar nan, haka yake jin ta a cikin jikinsa, yayi ta ihu ya na fuzgar fatarsa, ko kuma idan mahaukacin dokin nan, yana dara, sai ya ji tamkar ƙashin sa ake takawa. Idan kuwa shakara ta yi, lokacin shan jinin nan ya yi, ya din ga suma kenan, har ammi ta fitar da rai da shi. Mummy ta din ga tsorata Mahmud a kan Adam, da sai da ta kawo, ba mai kallon wani, juya masa bayan da mahaifinsu ya yi, ba ƙaramin tsaye masa ya yi ba a ransa. Sai dai ya je ya saka Ammi a gaba, ya yi ta kuka, abun da ake yi musu da tare shi da Mahmud, yanzu sai dai ayi wa Mahmud shikaɗai, hakan ya sanya ya ƙara tsanar Mahmud!. Roƙon Allah da neman magani, da Ammi ta dage a kai ne, ya sanya ya samu sassauci har ya koma makaranta. Lokacin da za su shiga jss1, Mummy ta saka aka kai Mahmud boarding, aka raba shi da gidan baki ɗaya, dan yanzu galadima baya iya ƙetare maganarta. A hankali aka ɗan fara sakin jiki da Adam, cousins ɗin sa suke wasa da shi, kasancewar makarantar su ma ɗaya. A gidan su jamil, gidan turaki wanda yake wa ga sharif, akwai ƴar sa ɗaya da ya ɗorawa so shi ma, bayan mahaifiyarta ta rasu, mai suna Aisha yake kiranta da fulani, sai dai a bayan idonsa, babar su jamil, ta tsani yarinyar, kamar ba ƴar sarauta ba, saboda azabtarwa daga yayyenta, da kuma uwar riƙonta. Tun ana yi a bayan idonsa, aka dawo yi a gaban idonsa, ba ya iya cewa komai, wasu lokutan ranar juma'a sai Ammi ta aika a ɗauko mata Aisha, a kai mata ita, ta yi mata kitso, ta saka ayi mata lalle, tana son ƴa mace, laila kuma ta riga ta balaga. Ana haka Ammi ta haifi nusaiba, ta din ga murna, ta samu ƴa mace, da wata salla suka je gombe, a nan yayan Ammi yake ce mata, ya wuce ta rigar su ade, ya ga kamar da mutane. Nan da nan Ammi ta ɗau hanya ta tafi, sai dai ta je ta tarar da wata kyakywar bafulatanar yarinya, da ciki. Suka gaisa da Ammi, take tambayarta, ina su Ade. Yarinyar ta ce "Ade kakata ce, sun yi gaba, ni daga yaye aka bar ni a wurin yayan babana, to sun tashi zasu tafi can iyaka, in da tushenmu yake, ni dai ban san sunan wurin ba, to mu ma can zamu tafi, da ni da yayan babana ne, da matarsa sai maigidana, sauran ayarin da muka taso tare sun yi gaba, ni kuma na yi nauyi, shi ne aka ce mu zauna in haihu, sai mu tafi, yayan babana ya san in da suke, ina son in ga Ade, kakata". Ammi ta ce "Allah sarki, Ade kam tana bani labarinki, ta ce mamanki ma tana wata riga tana aure ko?" Yarinyar ta jinjina mata kai. "To ina mijin naki da matar yayan baban naki?". Ta ce "Sun tafi kiwo, ita kuma ta je yin itace". Ammi ta din ga murna ta ga jikar Ade, kasancewar za su yi kwanaki a can, ya sanya kusan kullum sai ta je, har suka saba da matar yayan baban ade. Ammi ta sha mamaki, irin yawon da fulanin nan suke da shi, sun yi sanani sun hayayyafa, sun shafe shekaru a wurin, kuma su tashi su yi wani wurin kamar wasu iskokai. Mijin yarinyar ma, mairamu yana matuƙar girmama Ammi, su yi ta ɗaukar nusaiba suna yi mata wasa. Ammi kar ta tafi ta bar gida, dan ƙarfin zaman na ta ma, ayi wa Adam Addu'a ne, da nema masa magani. Bayan Ammi ta koma Kano, tana yawan yin waya, a kan aje a gano mata jikar Ade. Sai dai aka kira Ammi, daga garin su, aka gaya mata, an kashe mijin mairamu, an kore dabbobinsu, kuma an rasa yayan babanta da matarsa. Kasancewar ammi ba laifi, tana faɗa aji, ta saka aka kai report wurin ƴan sanda, amma ba wani labari, Mairamu ta tayar da hankalinta, a gidan su Ammi aka yi wa mijinta sutura, aka rufe shi. Ita ba ta san kowa ba, sai mijinta da yayan babanta, in da suka baro, duka suka taso, ayari sun yi gaba sun bar su, dan su har a lokacin ba ruwansu da abun hawa, kuma ba ta san in da za aje ba, dan ta na da ƙuruciya sosai abun da ta riƙe a in da za su je kawai shi ne kan iyaka, nan ne tushensu. Saboda tsabar damuwa, ta fara naƙudar dole, aka kwasa aka kaita asibiti, ta haifi yarinaya kyakkyawar gaske, jawur da ita. Ammi ce ta yi mata role ɗin uwa da na uba, dan ba zata manta karamcin Ade ba. Ta tambayeta sunan da za a sakawa ƴar amma ta ce ta saka mata duk sunan da take so. Ammi ta ce "Ta saka mata Khadijah, sunan mahaifiyar ta, kuma ƴar ta da ta taɓa rasuwa, amma take ce mata Iman". Ta din ga rarrashin mairamu, tana bata tabbacin, za ta yi ƙoƙari a nemo in da ƴan uwanta suke, kuma a lokacin waya sai gidan manya, balle a sameta hannun bafulatanin daji. Haka Ammi ta din ga sintiri tsakanin kano da gombe, mahaifiyar laila da ammi ta riƙe, ta cigaba da ɗawainiya da Mairamu, dan a lokacin suma iyayen duk babu. Sai dai har watanni uku, babu labari a kan in da ƴan uwan mairamu suke, ga ƙuriciya kuma ta yi ta fama da rashin lafiya, ƙarshe Allah ya yi mata rasuwa. Ammi ta yi kuka sosai da sosai, ta ce sai yayarta ta bata Iman, ya ce ba zata ba, sai ta nemo iznin mijinta. Ammi ta yi wa galadima bayani, ya ji rauswar yarinyar, kuma ya san ɗawainiyar da Ammin ke ta yi, dan haka ya ce ta ɗaukko ƴar, dan ya san soyayyar da ke tsakanin Ammi da Ade. Ta zube har ƙasa ta din ga yi masa godiya. Ta je ta ɗaukko Iman, a lokacin kuma ta riga ta yaye Nusaiba, ya ce ko magani za ta yi, da ruwan nono zai dawo ta shayar da iman, yayarta ta ce kar ta shayar da ita, ta na da ƴaƴa maza, ba ta san me gobe za ta yi ba. Haka ta haƙura, ta ɗaukko iman, ta zo tana bata madara. Kowa ya ga Iman sai ya tankata, saboda tsananin kyan da take da shi, gaya jaririya, amma gashinta irin na larabawa, mai tsawo. Nan ma mummy ta samu na yi, wai Ammi saboda jaraba, an yarda ƴar shege ta ɗaukko wai tana so, kamar ƴar jari bolan ƴaƴa, ɗan kowa ma sai ta ɗaukko ta ce za ta riƙe, da ganin kyan wannan yarinyar, an san shegiya ce. Aikuwa aka yadda, wasu lokutan ammi har mamaki take, yadda sirrikanta ke fita. Jamila ta hurawa galadima wuta, a kan lallai ya sa ammi ta mayar da ƴar nan, duk dan ta cusa wa Ammi baƙin ciki. Ya kuwa je ya samu Ammi ya ce bai yarda da riƙon ƴar ba, sai da Ammi ta dangana da wurin sarki, da mai babban ɗaki a kan su saka baki. Mai babban ɗaki ta ce "Dan Allah idan ma ƴar tsintuwar ce, ita ta na so, ƴar ta yi mata kyau Tubarkallah". Da ƙyar galadima ya amince, bayan mai martaba ya yi masa ta tas, a kan abubuwan da yake yi. Iman ta fara girma, ga fari ga kyau, ga uban gashin nan, kullum tana tare da laila da su nusaiba, ga Aisha idan ta zo, amma muddin ta sake suka haɗu da Mahmud, Fauziyya ko ruƙayya, to tabbas sai ta yi kuka, saboda cin zali. Sai dai duk da haka, ƴaƴan jamila na shiga wurin Ammi, kuma ba zaka ce ba nata bane ba, sai dai suna tsoron laila, dan suka yi mata rashin hankali ubansu take ci, duk da ana yi mata gorin ba gidan ubanta ba ne ba, ta kan ce musu, Jamila ma an riƙeta ba a gidan ubanta ba, dan ita har da Mummyn ma yi take yi, duk yadda Mummy ta so ta saka Galadima ya kori laila abu bai yiwu ba. Adam kuwa yau fari, gobe tsumma, kusan kullum cikin rashin lafiya, idan ciwon nan ya tashi kuwa, haka zai ta burgima yana ihu, yana neman abun da zai riƙe ya samu sassauci, makaranta wasu lokutan sai dai a jingine ta. Sashin Ammi ya zama wurin faɗi tashin yara, wannan ya shiga wannan ya fita, ta koya musu karatu, ta yi musu girki, mai assignment ta yi assisting ɗin sa. Mummy ta yi ta jawa iyayen yaran kunne, a kan su yi hankali da yaransu, kar mahaukacin ɗan ta ya kashe musu ƴa ƴa, amma yaran sun riga sun shaƙu da ita. Idan har Mahmoud yana hutu, Mummy ta din ga kitsa masa abun da zai je ya gaya wa galadima takawa ya yi masa, idan ya gaya masa, ba bincike haka zai hau Adam da faɗa, har ta kai ammi ta ce masa, kar ya sake hantarar mata ɗa, da wanne za su ji? Rashin lafiyarsa ko faɗan da yake yi masa. Dan haka a duk lokacin da Adam ya san Mahmud yana nan, ba shi da sukuni, saboda faragabar abun da zai je ya ce ya yi masa, kuma hakan ya sanya Adam ya tsani Mahmud sosai da sosai. Adam ba ya jin daɗin hantarar da ake yi masa, mussaman idan aka shiga da shi taro. Kasancewar da shi da Aisha, da Iman, ƙaddarasu na kamanceceniya, ya sanya ba shi da wanda yake ƙauna sama da su. Ya dai girmesu sosai, amma ya na jin daɗin rayuwa da su, a haka ɗan wani attajiri ya ce yana son laila, ba yadda Mummy ba ta yi ba, a kan kar abun ya yiwu, amma hakan ya ci tura, laila ta yi aure ta bar ƙasar. Daga baya Mahmud ya samu labarin, Ammi ce ta haife shi, amma bai taɓa jin hakan a zuciyarsa ba, a ganinsa da ita ta haife shi, Meyasa ba ta son sa sai wannan Adam ɗin. Idan ciwon Adam ya tashi, daga Ammi sai Aisha ko Iman, suke iya zuwa wurinsa, duk da ya taɓa ɗaga Iman ya yi cilli da ita, sai da ta suma, amma tana farfaɗowa ta fara kiran kakawa, lokacin ba ta gama iya faɗan sunan sa ba. A lokacin iman ta yi ta rashin lafiya, aka kasa gane me yake damunta, sai da ƙyae, wai zuciyar ta ce take kumbura, Ammi ta tashi hankalinta, tana tunanin ko tsangwama ce ta sanya ta haɗu da ciwon zuciya da ƙuruciyarta. Kwatsam rannan galadima ya yanke jiki ya faɗi, ya fara rashin lafiya, nan ma Mummy ta ce Ammi ce, ƙarshe dai Ammi ce ta yi jinyarsa, sai da ya kusa rasuwa, ya din ga neman yafiyarta, da ta takawa, dan bai san yadda aka yi, ya din ga wasu abubuwan ba. Ɗa da uba sai Allah, bayan rasuwar galadima, Adam ya yi kuka, ko ba komai mahaifinsa ya nuna masa ƙauna, a baya, Mahmud ma ya ɗimauta da wannan babban rashi da aka tafka a gidan sarautar. Mummy ta din ga dariya, dan ta san dai ba za a bawa takawa sarauta ba, na farko yaro ne, kuma ga larura. Dan haka ɗaga likkafar mahaifin jabir ya zama galadima. Tana ta murnar tun da Adam ba shi da lafiya, nan gaba ko za a bayar da sarauta, ɗan ta za a bawa Mahmud, amma aka tunatar da ita, yanzu babu Galadima, giwa za ta iya duk mai yiwuwa ta karɓe ɗan ta, dan haka ta ce dole ayi biyu babu, ya din ga kwaɗaitawa ƙawarta Lubabatu, ɗan ta jabir yayi mulki, nan gefe tana kuma turawa Mahmud ƙiyayyar Adam tare da tura masa son mulki, amma sai dai sam, shi kamar mahaifinsu ne, bai damu da sarautar ba, duk da Adam ya fi gado kamanni da murɗaɗɗen hali na mahaifin su. Adam yana girma ciwo yana ɗan raguwa, dan a haka yayi karatu, abu ne mawuyacin ciwon ya tayar masa a waje, Sai a gida. Ya shaƙu da Nusaiba da Iman sosai, musamman iman da yake ganinta kamar wata ƴar ƙaramar mage mai kyau, ya cafata nan ya cafata can, sai dai duk da hakan suna girmama shi sosai dan akwai tsare gida. Gefe guda, Samha ta ƙallafa rai, tana ta nuna masa so, amma mahaifiyarta ta dankwafeta, saboda rashin lafiyar Adam. Yayin da shi kuma ya fi karkata, ga Aisha, duk a lokacin bai san son ta yake yi ba, muraran Samha da mahaifiyarta, da kuma ƴan uwanta ke nunawa aisha ƙiyayya, ganinta suke kamar ba ƴar uwasuu ba, mussaman yadda turaki yake tausayinta, komai sai ya ce 'yar marainiya. Sanin sassauci ta sai idan Adam ya je gidan ya ɗaukkota, ko Ammi ta aika a ɗauko mata ita. Abubuwan da suke yi wa Aisha, ya sanya Adam ya fara tsanar mahaifiyar su Samha, Saboda ganinta yake muguwa kamar Mummy, saboda waɗan nan dalilan Adam yake jin ba zai iya auren mace sama da ɗaya ba, idan uwar ɗa ta mutu kuwa, ya ce majaifiyarsa zai bawa riƙon ɗan sa, babu wanda zai bawa riƙon ɗan sa. Tun Samha tana ɓoye son da take yi wa Adam, har ta fito muraran, shi kuma sam ba ta ita yake yi ba. Maman Samha ta shiga ta fita, ta na son a aurawa wani ƙaninta Aisha, Turaki ya ce ba zai bayar ba. Abun ya ƙular da ita sosai da sosai. Babu tsammani, Ammi ta je ta samu wambai, yayan Sharif ta roƙe shi ya nemawa Adam auren Aisha. Aka yi ta surutu, wai za ta aura wa mahaukacin ɗan ta marainiya, dan zalinci, Aisha ta ce ta ji ta gani. Ammi ta yi haka ne, dan Aisha ta samu sassauci, saboda azabtarwa da ake yi mata, kuma turaki ya ƙi ya mata ita gaba ɗaya. Samha tamkar za ta yi hauka, ta tsinewa Ammi da Aisha ba ta san iyaka ba, ta kuma lashi takobin ganin bayan Aisha, ta ƙuduri aniyar ko da bala'i sai ta auri Adam. Mummy ta ja ta a jiki, ta din ga rarrashin ta, tare da zigata da bata goyon baya ɗari bisa ɗari. Ayshercool. 08081012143 What's app only please Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Da fari saboda dagewa da neman magani, Adam ya ɗan samu sauƙi, dan ya kammala karatu ma, ya samu aiki a hukumar DSS, kuma ya shiga aiki da ƙafar dama. Yanayin larurar Adam, da abubuwan da suka faffaru da shi, ya sanya mai martaba yake matuƙar jan sa a jiki, da kwantar masa da hankali, haka zalika turaki da galadima, iyayen nan maza duk suna ƙaunarsa, kusan halinsa ɗaya da mahaifinsa, amma har ya fi babansa taurin kai wasu lokutan, amma akwai ɗa'a da ladabi. Hakan bai ishi Mummy ba, ta din ga bi  wurin matayensu, tana ɓata Ammi da ƴaƴanta, da har sai da wasu suka fara jin haushin Adam a cikinsu. Bayan auren sa da Aisha, ciwo ya cigaba da tashi lokaci zuwa lokaci, sannan kamar yadda ammi ta din ga yi, haka Aisha ta din ga ɓari, ciki ba ya zama a jikinta, ga ƙannensa suka sakata a gaba, su je har gida su yi mata rashin hankali, su ci zarafinta ga Samha ma a gefe ta sakata a gaba, da makirci da sharri kala. Sannan still daga can gida mahaifiyar su samha ma, ba ta ƙyaleta ba da sharri, da haɗata da Turaki, wai ba ta ɗauke ta uwa ba, komai sai dai ta yi ita da giwar galadima. Idan Aisha ta samu ciki, da zarar zai zube, sai ta yi magafrki da adam, yazo mata da dogayen haƙora, da kuma farata ya kafa kai a mararta, sai dai da safe ya tashi da zubar da jini. Adam bayan shigarsa Dss akwai cakwakiya daban-daban, sai dai ya tsaya kai da fata a kan gaskiya, ba ruwansa da cin hanci, da shi da Jamil suka shiga aikin, amma ya fi Jamil karatu, dan haka rank ɗin sa ya fi na Jamil. Akwai aiki da ƙoƙari, hakan ya sanya shi zama sannane, mussaman da yake kama da mahaifinsa sosai. Bashi da aiki bankaɗa, da tonawa mugwayen ƙasa asiri. A tone-tonensa, ya tono Usman wakili, da irin yadda yake yi wa ƙasa ɓarna, ya sako shi a gaba, a hukumar wasu suka goya masa baya wasu kuma suka ƙi. Ba ƙaramin ragewa wakili mutuncin yayi a idon mutane ba, ya cigaba da fafatawa, amma aka ƙi bashi goyon baya, a hukunta wakili. Shi kuma yaƙi sakin aikin, ya cigaba da bin diddigin sa, babu irin jan kunnen da ba a yi wa Adam ya ƙi ji. Ya koma ya bankaɗo wata tawaga, da suke yi wa kansu laƙabi da SMOKE, sai dai an kasa gano suwaye a ƙungiyar smoke, sai dai ana ganin miyagun ayyukansu, duk wani shige da fice na miyagun kwayoyi, da makamai ta hanyar da ba ta dace ba, suna da hannu a ciki, za kuma kaga tambarinsu na hayaƙi, an rubuta THE SMOKE. Bincike a kan Smoke, ya sanya ya sararawa wakili, bai kuma waiwayar wakili ba, sai da ya ji ƙishin walili zai tsayar da ɗan sa takarar senator, shi kuma za a ɗauke shi vice president, su yi takara, da ɗan takarar da zai tsaya shugabanci ƙasa. Wannan dalilin ya sanya, Adam sake saka wakili a gaba a karo na biyu. Nan da nan sunan Adam ya shahara, shi ma ya haɗa tasa tawagar, da lauyoyi, da ma'aikatan Efcc, da ƴan jarida da suke da burin yi wa ƙasa aiki saboda Allah. Iman kuwa tun kan ta kai shekaru goma, take samun masu cewa suna riƙo. Iman tana girma samari kamar me, nan ma Mummy ta ƙwafe a ranta, ya sake mayar da jita-jita a kan Iman sabuwa dal. Na cewa shegiya ce ba wanda ya san iyayenta. Saurayin babbar ƴar Mummy, Surayya, Wambai ya haɗata da wani babban mutum, amma yana ganin Iman ya ce shi nan duniya wannan jar yarinya yake so. Ƙarshe dai aka yi biyu babu, Surayyan ta yi aure, amma Mummy ta kai sunan Iman wurin bokansu. Manyan mutane duk wanda ya ce ya na so, sai ace masa shegiya ce, sai zance ya lalace, a ƴaƴan mai martaba, ɗaya shi ma ya liƙe Iman yake so, Mummy sai da ta yi dalilin da ya sanya, babar yaron ta hana zuwa da iman gidan. Yawan gorin da ake yi mata, ta daina shiga cikin mutane. Ammi tana tausayin Iman, ga larura ga tsangwama. Iman ba ta da wata ƙawa, kullum tana manne da Ammi, ko Nusaiba, sai kuma uwar ɗakinta Aisha matar takawa. Duk wannan abubuwan, Ammi ba ta taɓa nunawa Mummy wani abu ba, kuma ba ta saka wa zuciyarta wai wani ne yake yi mata wani abu, kawai ta saka wa ranta jarabta ce daga Allah. Sai dai har a lokacin Ammi ba ta daina son ɗan ta ya dawo gareta ba, ta kasa jurewa ta je ta sanar da wambai, dan Allah ya shiga lamarin gidansu, ya sasanta mata yaranta, ko Mahmud ba zai dawo hannunta ba, ya din ga zuwa in da take. Wambai ya yi ta faɗa ya ce laifin Mummy ne, da ta raine shi a haka, amma ta nuna ita ba laifinta bane, yayi musu sulhu, amma suna zuwa gida, ta sake hure masa kunne. Cikin ikon Allah, Iman kan ta yi candy, wani ƙanin abokin Adam ya fito zai auri iman, ɗan babban gida ne sosai da sosai, aka saka rana tana kammala sakandare ayi biki, ta cigaba da karatu a gidansa, dan Ammi ta fara tsorata da mazan da suke bin Iman. Adam kuma shekara huɗu da aure, ciki ya gagara zama a jikin Aisha, ciki na ƙarshe da ta samu, Ammi suka yi shawara a kan Aisha ya je ta yi rainon cikin a saudiyya, wurin wani wan Ammi da yaki zaune a can shi da matarsa. Ya ce karatu za ta tafi ƙarowa ƙasar waje, aka din ga surutu a kai, ya ce babu mai tsara masa rayuwarsa, tun da matarsa ce. Iman kuma watan da za a yi biki, wanda zai aureta ya aiko a karɓar masa kayan aurensa wai ya fasa. Hankalin ammi ya tashi, ta aika a tambaye shi dalili, iyayensa suka ce su manyan mutane ne a ƙasa, ba za su karɓi sirika da ba ta da asali ba. Ammi ta sha kuka, laila da ba ta ƙasar ma, abun ya baƙanta mata rai, ta cewa Ammi visa za ta yi wa Iman, a tura mata ita can, Ammi ta ce ba mai rabata da ƴar ta sai mutuwa ko aure. Ammi ta yi shawara da baba uwani, a kan ta bata shawara ko ta roƙi Mahmoud ya auri Iman, dan ta lura wannan mugun tabon da Mummy ya yi mata, ba zai bari ta auru ba, baba Uwani ta ce ai ita babarsa ce, dan haka bakomai. Daga nan ta kwashe ta je ta gaya wa Mummy. Ammi ta keta billenta, ta je ta samu Mummy, ta ce mata dan Allah ta na son yin magana da Mahmoud, ta ce mata za ta turo shi. Sai dai kan ya je, Mummy ta zauna ta kitsa masa, tare da sauya masa tunani. Ammi ba zata iya tuna rabonsa da sashinta ba. Ta roƙe shi Allah ma'aiki, ya auri Iman, ko ita kaɗai ce alfarmar da zai iya yi mata a rayuwa a matsayin ta na mahaifiyarsa. A take ya ƙeƙashe ƙasa, ya cewa Ammi shi ma ba zai auri ƴar da ba ta da asali ba. Baƙin cikin abun da Mahmud ya yi mata, ya sanya ta kamu da hawan jini, saboda ta yi kuka ba kaɗan ba, ta shiga damuwa. A lokacin Adam ya je umara, ya ga Aisha, cikinta ya girma sosai, ana ta addu'ar Allah ya sa ta haife shi lafiya, bayan ya dawo ya samu labarin, abun da ya faru tsakanin Mahmud da Ammi, ya din ga yi wa ammi mitar meyasa za ta roƙi Mahmoud ya auri Iman, ita kuma gani take ba ta da wata mafita sai wannan. Ammi sai da suka kwanta da Iman a asibiti, dan ta so Al'amin saurayin da ya fasa aurenta, haka zalika ta so ta samu Mahmoud, duk da yana cikin waɗanda take bala'in jin tsoro, saboda dukan da yake yi mata da hantara idan sun haɗu. Kuma zance ya fita a dangi, Giwa ta na neman kai da shegiyar ƴar ta, taƙi auruwa, kuma ta karya billenta ta nemi alfarmar ɗan ta, yaƙi yi mata. A zahiri za ka ga ammi kullum cikin fara'a take, amma ƙasan zuciyarta, tana cikin damuwa da tashin hankali a kan iyalanta. *** Gaba ɗaya jikin rumaisa ya yi sanyi, ta rungume Iman da take ta sharɓar hawaye, ta rungumeta ita ma ta fara kukan, ta kasa rarrashinta. Sai da suka yi mai isarsu, danna rumaisa ta din ga share mata hawaye ta ce "Ki yi haƙuri Anty iman, tun da dai ammi ta san iyayenki, meyasa za ki damu dan an ce miki baki da iyaye? Ki fuskanci rayuwarki kawai, kuma in Allah ya yarda zaki auri miji na gari, wanda zai kula da ke, ki daina kuka" Ta yi maganar tana sharewa iman hawaye, Nusaiba ta yi sallama a ɗakin, suka amsa, ta ɗan yi turus tana kallonsu, yanayinsu ya nuna mata akwai wani abu, amma ta share, ta ƙarasa ta ɗau Sabir da ya yi barci, ta fice daga ɗakin". Jabir kuwa rai a ɓace ya koma ɗakin Ammi, ya dubi ammi ya ce "Ammi, dan Allah idan ban takura miki ba, ina son mu yi magana ne". Ammi ta ce "To" ta tashi ta bar ɗakin, Adam ya bi su da kallo. Falonta suka koma, Ammi ta ce "Ya aka yi ne?" Ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa, sannan ya numfasa ya ce "Ammi wani abu ne ma daɗe ina son in gaya miki, amma na kasa ban sani ba ko zaki bani dama". "To ni ɗin baƙuwar ka ce? Faɗi ina jin ka". "Dama..dama game da Iman ne Ammi, dan Allah idan babu wani a ƙasa yanzu, ni a bani mana, ina son ta". Ammi ta ce "To fa! Babbar magana, ya aka yi ba ka gaya mini tun da wuri ba?". "Ina jin nauyi ne Ammi". "To meye na jin nauyin ban da abunka, ka san yanayin da take ciki, ta daina saurarar kowa ta daina bawa kowa dama tunda abubuwan nan suka faru, amma na yi mamakin da baka taɓa faɗa ba". "Ammi Iman ai ƙanwata ce, na daɗe ina ɓoyewa ne, yanzu kuma na ga yakamata na faɗa, wataƙila dama rabona ce". "Haka ne, amma ka san dai case ɗin da yake kanta, kuma babu lallai hajiyarka ta yarda, na san ba za ta amince ba". Jabir ya ce "Ammi zan shawo kan ta, in dai kin amince shikenan, idan har ba a cikinmu ba, haka zamu zauna mu cigaba da zuba ido, kowa ya zo ya fasa, Saboda wani dalili mara tushe, ina ga ni ɗin na fi dacewa, na san abun da yake faruwa da ita". Ammi ta ce "Na yi farin ciki sosai Jabir, Allah ya tabattar mana da alkhairi, ai kai ɗana ne, na gode da ƙoƙarin share mini hawaye ni da marainiyar Allah, Allah ya biya ka". "Amin Ammi, na gode sosai, ina ga zan yi wa mai girma wambai Magana, a nema mini aurenta, zan yi ƙoƙari ya shawo kan Hajiyata ma". "To, Allah ya ji she mu alkhairi, ya sanya albarka na gode sosai" Ammi ta ji tamkar ya yaye mata kaso mafi rinjaye na damuwarta. Da ta koma wurin takawa, ya kalleta ya ce "Ya dai na ga kina fara'a?" "Ina ruwanka?" Yayi murmushi ya ce "Tuba nake". Ta zauna ta ce "Kai ban gaya maka ba" Ya tattara mata hankalinsa. "Laila za ta shigo cikin sati Mai zuwa" Ya waro ido ya ce "Yanzu muka gama magana a waya, amma ba ta gaya mini ba". "Oho muku dai". "To ta koma ba ma so, ba ta zo lokacin rasuwar aisha ba, ba ta zo ta ga ɗan ta ba, na yi aure ba ta zo ba sai yanzu?" Ammi ta ce "Ai ka san yanayin aikinta a can, amma ta ce za ta daɗe sosai idan ta zo, yaran ne za su koma da wuri, tare da babansu idan ya zo, shi sai next month in Allah ya kaimu zai zo". "To Allah ya kawota lafiya, gashi ni zan yi tafiya. yauwwa Ammi, mai girma turaki ya kirani, ya ce mini mai martaba ya tura mu wakilcin taro, kuma da na dawo zan je course ɗin nan ta watanni shida, kin ga ba zan wani daɗe tare da ita ba". "To sai ta zo ɗin dai tukuna". "Ammi, ina Jamil ne? Ban ƙara ganinsa ba fa, tun da ya tafi ɗaukko Rumaisa". Ammi ta ce "Ni ma dai na yi mamaki, ka san da ta zo ta ce wai ƙin hawa motar ta yi, saboda ta san yana jin haushinta, ina ga saɓani suka samu, ya ji haushi, mukullin motar ma, Sidi ya bawa ya kawo". Yayi ajiyar zuciya ya ce "To ai ba da ni suka yi ba, ni kaina ba na son surutun nan na ta, ita ba ta iya kara ba ko kaɗan". "Ai ƙuruciyar kenan, sai dai ayi ta sakata a hanya, ni maganar da ta faɗa ne a kan Jamila, nake jin tsoron kar ta koma kunnenta, bana son tashin hankali da masifarta, in da na gode wa Allah ma, ba a gaban wani ta faɗa ba" Takawa ya ce "Ina tsoron wannan bakin na ta a cikin masarautar nan, sai dai Allah ya shirya". Can ɗaki kuwa, suka gama koke-koken su, ita da Iman, kamar wata babba haka ta yi ta rarrashin iman. Can Iman ta ce "Anty rumaisa ba zaki kira mai sunan baba ki yi masa godiya da ya ya je gida ba?". Ta yamutsa fuska ta ce "Godiyar me kuma?" "Dubiya da ya zo mana". "Ba ki san halin gayen nan ba, ba lallai ya gode, kina ganin yarfani ya yi dan na ce zan raka shi, wai na je na kula da mijina, yanzun ma zai iya yarfa ni". Iman ta ce "Ba haka bane, yakamata ki yi masa godiya, idan yana gida ma sai ki gaisa da su mama, ko yana zama yayi dare a waje?". Rumaisa ta kalleta ta ce "To mai sunan baba da mace ne, da an shigesu, ba shi da wasu abokai fa, daga makaranta sai kasuwa, sai gida, su wani ball su wani abubuwan abokai, ko yawo duk ba ya yi, da dai yaya usy ne ko gadanga na mama yaya Aliyu, mama da kanta take fita yawon nemansu wataran" Iman ta yi murmushi ta ce "Kowa da halinsa kenan, ga wayar ki kira shi" "Sai dai ke kira shi" "In kira shi in ce masa me, na gaya miki ya ce na daina kiransa". Rumaisa ta ce "Gaskiya idan na kira shi, ya yi mini wulaƙanci sai na rama a kan ki". Iman ta bata wayar ta ce "na yarda". Sai da wayar ta kusa katsewa sannan ya ɗaga, alhalin wayar na hannunsa, yana kallonta, ya din ga fatan Allah ya sa muryar iman zai ji, ba ruma ce ta kira ta dame shi ba. "Hello mai sunan baba" Sak yayi da ba Muryar iman ya ji ba. "Ya aka yi?" "Amm dama, kiranka na yi na ji ya ka je gida, na gode sosai" "Yayi" ya faɗa a taƙaice yana ƙoƙarin kashe wayar. Ruma ta ce "Dama Iman ce ta ce, na kira ka na tambayi ya ka je gida?" Da sauri Iman ta ce "Kai Anty rumaisa" ta yi maganar tana karɓe wayar ta kashe. "To me na yi kuma?". Cikin shagwaɓa iman ta ce "Meyasa zaki gaya masa haka, kar ya zaci wani abun fa". "Wani abu kamar me?" Iman ta ce "Bakomai" ta tashi tsaye ta ce "Ki kwana a kan gadon, ni sai na kwana a kan katifa a ƙasa". Rumaisa ta kwanta ta ce "Ai ba kara zan yi miki in ce a'a zan kwana a ƙasa ba" Iman ta yi dariya, ba ta sake cewa komai ba, ta yi shirin baccinta ta kwanta. Har kusan ƙarfe biyun dare, rumaisa idonta biyu, rabon da ta ci karo da abun da zai hanata bacci, tun farkon shigarta hannun kidnappers, daga baya kuwa baccinta take yi, sai lokacin da ta kuɓuta da Sabir. A hankali ta tashi zaune, ta na jin kanta duk ya yi mata nauyi, tausayin wa ma yakamata ta ji ne?. Ta kalli in da iman take barci, ta girgiza kai 'Allah sarki Iman, a yadda ki ka bani labari ke yanzu gaba ɗaya ba ki da uwa ba ki da uba, sun rasu ba zaki taɓa ganinsu ba har abada, ba a san in da za a ga dangin su ba, ba ki da wa ba kuma ki da ƙani ga larura. Ashe ni kukan daɗi nake, na ban san babana sai a hoto, wannan ke ce marainiya. Allah sarki ammi, ashe da gaske mama take da take cewa aure ɗan haƙuri ne, ni na zata kawai abinci ake ci ayi bacci, amma a ƙwace mini ɗa a bawa kishiyata, wallahi sai dai ayi masifar da za ayi kowa ya huta. Ga ɗan ta ba shi da lafiya, ɗayan kuma an raba shi da ita, kamar yadda dai mama take sonmu a ƙwace mata ɗaya daga cikinmu, ko kuma kamar ni a ƙwace Sabir ya auri ƙanwar anty aisha ya bata. Kam bala'i wallahi da sai dai kowa ya rasa'. Ta dafe kanta, abubuwan ba da ita suka faru ba, amma ta ji sun dameta, ammi tana da kirki fiye da tunani, amma meyasa aka tsaneta?. Ta tashi ta sauka daga kan gadon, ta zauna a ƙasa ta yi shiru, abun duniya duk ya dameta, ƙarshe a nan ƙasa ta yi bacci. Mai sunan ba tun da ruma ta ce masa Iman ce ta ce, a kira shi, yake jin wani irin nishaɗi a ƙasan zuciyarsa, dan ƙoƙari yake ya hana hakan tasiri a zuciyarsa, dan yaƙi yadda ya sallama cewar ya faɗa soyayya, haryanzu tantama yake yi. Da asuba bayan sun yi sallar asuba, rumaisa ta je ta gaida ammi, ta tarar da ammi na salla, ga sabir ya farka, yana kuka. Ta hau kan gadon, ta ɗauke shi, ta bashi ruwa ta kwantar da shi ta hau yi masa wasa, daga haka kuma suka yi bacci gaba ɗaya. Wajen ƙarfe bakwa, ammi ta tashi rumaisa, ta ce ta je ta yi wanka, ta shirya ta je ta duba takawa da ya kwana a ɗakinsa, ta zo a kaita makaranta. Gaba daya ba ta sanya ran zuwa makaranta ba, a zaton ta tun da bashi da lafiya, ba bu zuwa makaranta. Ta je ta yi wanka, ta karya, sannan ta tafi ɗakin nasa. Ciwon kwana ɗaya, amma idanunsa sun yi zuru-zuru. Ta ƙarasa kujerar da yake zaune, sanye da ashe ɗin jallabiya ta ce "Sannu ka warke?". Ya kalleta ya ce "Ina kwana?" Gatse yayi mata, amma cikin ko in kula ta ce "Lafiya ƙalau, ya jiki?" Jawota ya yi ya zaunar da ita, ya tsura mata ido sannan ya ce "Baki san gatse ba ko? Ban isa ki gaisheni ba?" Ta ce "Auu, wai dan ban gaishe ka ba, na ɗauka kawai gaisheni ka yi, to ina kwana?" Yayi shiru bai amsa ba yana bin ta da kallo. "Ai ka ga matsalar, mutum ya gaisheka, ka ƙi amsawa wai sai an yi maka irin taka". Bai ce mata komai ba ya cigaba da kallonta. "Barka da wannan lokaci ranka ya daɗe, na sameka lafiya?" Ta yi maganar tana risunar da kai, kamar yadda ake yi masa. "Ki tashi ki je, sidi zai kai ki makaranta". Ta tashi ta amsa masa da to, tayi waje. Sai dai a harabar gidan, ta haɗu da Mahmud, yana shirin fita. Gaisawa suka yi, ya ce "Ya mai jiki?". "Ai ba zan amsa ba, sai ka je ka duba shi" "Anya zuwa dubiyar nan kuwa? Taho mu je in kai ki makarantar, ya sunan makaranta".. Sunan kawai ta gaya masa ya gane, ta buɗe motar ta shige. Sidi ya taho da sauri, ya ce "Ranka ya daɗe, jiranta nake giwa ta ce zan kaita makaranta ne". Mahmud ya ce "Mayar musu da mukullin, zamu tafi tare" ya ja motar suka tafi. Suna tafe a hanya, tana zuba masa shirme, yana biye mata. Can ta ce "Kai ina son mama a rayuwata daddy, a duniya bayan Allah da Manzonsa, ba abun da nake so kamarta, dama ban san babana ba, amma mama dai kam, Allah ya tsundumata a aljanna. Allah ya bani abun da zan shagwaɓa ta, in ta sai mata abubuwa". Ya ce "Amin, sai ki yi ta mata biyayya da addu'a". "Ai ina yi mata, har da ammi ma dukkansu yi musu nake yi, mutane su yi ta hantarata wai ba na ji, har da yayanka ma hantarata yake yi wataran amma dai ya na da kirki wasu lokutan, idan na yi masa laifi sai ya yi mini banza. Ammi ka ga da mama da Ammi, da yayyena, da Anty Aisha da Sabir, da mai girma turaki, da gwaggo, da iya, da malam habibu na islamiyyarmu, da barde ɗan bindigar da yake bani abinci, da Bashir abokin takawa da ya tsinceni, da Iman kai duk wanda suke yi mini mutunci a rayuwa, kullum sai na yi musu addu'a da fatan alkhairi" Ya ce "wonderful, gaskiya nima a taimaka a sakani a ciki". "Eh zan saka ka, amma kai wa ka ke yi wa addu'a, tsakanin Ammi da wannan matar?" Shiru ya yi jikinsa ya yi sanyi ya kalli rumaisa. "Daddy, duk yadda nake son Sabir, da anty aisha na raye, duk wahalar nan da na sha, ba shi da kamarta, kuma dole ne ya bita, to kamar haka ne fa, kai da wannan matar, duk rashin ji na, Mama sai dai ta yi ta cewa Allah ya shiryeni, amma kai har ka saka Ammi ta yi maka kuka, kana da kirki amma ita ba ka yi mata meyasa?" A dai-dai nan, ya iso ƙofar makarantar su, bai amsa mata ba, yayi shiru. Ta ce "Yauwwa, ya batun baba uwani, ta je kuwa?" Ya girgiza mata kai ya ce "A'a, kuma ban ji mummy ta yi maganar ba, ina ga ba ta kai ga faɗa mata ba" Ta buɗe motar ta ce "Shikenan sai an jima, na gode sosai Daddy" ta nufi cikin makaranta. Sosai maganganun rumaisa suka ratsa shi, baya samun wanda zai din ga tattauna maganar nan da shi, yana ji a jikinsa abubuwan nan da suke faruwa, tamkar juya sama ne a ƙasa, gaba ɗaya abubuwa basa tafiya daidai, amma jin sa yake, tamkar an ɗora masa dutse, kuma kamar a cikin wata kurku yake da ruhinsa ya kasa samun salama. Ranar da ammi ta zubar da hawaye, saboda ya ƙi auren iman, ji yayi kamar zuciyarsa tana ci da wuta, ya daɗe yana ganin abun a idonsa, amma ya ji farincikin mummy shi ne a gaba, dan haka wannan bakomai bane ba. Sosai Adam yake masifa, jin wai mahamud ya ɗauki rumaisa zai kaita makaranta. "Takawa, ka sakawa zuciyarka salama, dan Allah ka yi haƙuri mana". "Ammi kin san ba shiri muke ba, idan ya kitsa mata wani abun fa? Ko ya bugi cikinta ta saki baki tana zuba, meye haɗinsa da matata? Yarinyar nan ba cikakken saiti ne da ita ba, kar a cutar da ita*. Ammi ta ce "Kana da gaskiya, amma na ga ta su ta zo ɗaya, in sha Allah babu wani abu da zai faru, tun da ka ji sauƙi ma, sai ku tafi amma dan Allah kar ka ce zaka yi faɗa, kaga ba ka da cikakkiyar lafiya. Kuma ka sani ko a dalilinta komai ya dai-dai ta tsakaninka da ɗan uwanaka?" Kallon idon ammi yake, tuni har hawaye sun cika mata ido. "Shikenan ammi, ba zan yi magana ba, ki yi haƙuri, amma dole in raba shi da iyalina". *** Da aka tashi daga makaranta, Adam ne ya zo ɗaukar ta, saboda ya ji sauƙi sosai, ciwon bai kuma tashi ba. Tana ganinsa ta hau dariya "Ka warke ne ka zo da kanka, da adaidaita sahu zan hau na tafi ai". Fuskar sa babu walwala, yayi mata banza, ya ja motar suka tafi, sai dai ta ga ya nufi gidansu, maimakon na Ammi, ganin ya na ta cika yana batsewa, ya sanya ba ta kula shi ba, ta cigaba da harkokinta. Ko da suka je gida, su Asiya suka din ga yi musu sannu da zuwa, suna yi wa Adam sannu, dan baba uwani ta gaya musu, maigidan ne babu lafiya. Ya wuce ɗakinsa ta wuce nata, ta yi wanka, ta kwanta baccin da ba ta samu yi jiya ba. Sai da aka yi la'asar, sannan ta tashi, taje kitchen ta haɗa shayi, ta zuba madara fal da milo, ta dafa ƙwai ta ci abunta, sannan ta ɗau littafinta, ta tafi ɗakin Adam. Yana zaune a kan kujerar ɗakin sa, yana dudduba wasu takardu, ta yi sallama ya amsa mata a ciki, ba ta damu ta je gabansa ta tsaya, ta ce "Albishirinka?" Ya kalleta ya ce "Ya aka yi?". Ta nuna masa littafinta, na assignment ɗin da ta yi, ta zana malaminsu, ta ci 10/10. Ya ɗan kalli littafin da mamaki, sannan ya kalleta, alamar yana jiran bayani. "In gaya maka har malamin ya kirani gaban allo, zai yi disgracing ɗina, ya ɗaga littafin ƴan ajin suna dariya, ya tambayeni da turanci wai meye wannan? Ni kuwa na ce ni ban iya ƙirƙirar komai ba, amma idan malamai suka yi kyau kamar zanen nan nawa, to za a samu ɗalibai masu ƙoƙari da tsara zane kamar nawa, koma fiye da nawa, Aikuwa aka dinga tafa mini,ya ka ji azancin nawa" Ɗan murmushi gefen baki ya yi, dan ya fuskanci ita fa dan kana fushi da ita, kai ta shafa. Ya ce "You try". "Yauwwa, sai ka saya mini kyauta, teddy bear nake so, da kuma ƴar tsana babba, sai lunch box ɗina" Yayi mata kallon ba zaki girma ba. "Ya naga kana kallona?" "Mahmud, Alaƙarki da shi bana so, kar ki kai ni bango a kan haka". "Wai meyasa zaka saka ni a cikin faɗa ku? Ni meye nawa yana yi mini kirki, shikenan dan kuna faɗa nima sai na din ga jin haushin sa. Jamil, Jabir, Samha alaƙar ka da su bana so, Jamil da Samha, sun wahalarsa da matarka, su meyasa ba ka gaba da su?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido. Rasa bakin magana yayi, duk yadda kake tunanin rumaisa ta wuce nan, a zahiri tana da ƙuruciya da wauta, but she have a very sharp brain, ba shi da amsar bata a yanzu dan ta ƙure shi. Amma saboda kar ta ga ta yi nasara ya ce "Ni ne shugaba, a gaba nake da ke, dan haka duk hukuncin da na yanke dole ki bi". Ta ɗau littafinta ta ce "Babu biyayya ga abokin halitta wurin saɓawa mahalicci, duk daƙiƙancina a makaranta, na san wannan, kuma Allah ya yanke rahamarsa ga mai yanke zumunta, Annabi ma ba ya tare da mai yanke zumunci, sai ka din ga jin tsoron Allah wurin yanke jiki kai ma" ta fice ta koma falo ta bar masa ɗakin. Mintuna kaɗan ya fito ya fice daga gidan gaba ɗaya, ya dafe kanta ta ce "Na shiga uku wannan wane irin abu ne, anya kuwa zan iya, ni duk na gaji" tayi tsaki, ta tashi ta je ta ciko roba da gugguru, ta ɗaukko lemo, ta zo ta saka a gaba tana ci, tana kallon cartoon. Hayaniya ta ji ana hawowa sama, ta tsaya tana jiran taga waye zai shigo? Samha ce da Fauziyya, da kuma ruƙayya sai zee ƙanwar Samha, baba uwani biye da su, hannunta riƙe da foodflask. Babu ko sallama suka zo suka zazzauna, baba uwani ta ajiye kwanukan, ta ja gefe. Samha ta kalli rumaisa ta ce "An samu duniyar da babu a gidan tsoho, an yi ɗai-ɗai a katafaren gida, da duk dangi babu irinsa" rumaisa ta yi mata banza, ya cigaba da kora lemonta. Ruƙayya ta ce "Allah wadaran naka ya lalace haryanzu ban ga technology a auren wannan busashiyar yarinyar ba, da ko rantsuwa na yi babu kaffara, ragowar masu garkuwa da mutane ce, sun gama lalata ta" ɗan shiru ruma ta yi tana tunanin, me take nufi. Fauziyya ta ce "Ba wani technology, wulaƙanci ne kawai, dan Allah dubi Samha ki dubeta, ita ta isa ta kira kanta mace ma wallahi wannan ko a mai aikin samha ba ta isa ta zo ba, kalli bakin shegiya yadda take auna madara, saboda samun wuri, ga ƙirjinta fayau kamar faifai ba wata mamora, amma wai ita ya aura". Rumaisa ta yi gyatsa ta ce "Gidan miji daɗi, mussman irin gidan papa, auren mai kuɗi daɗi ba, na samu promotion, gida babu, na samu a gidan miji" tayi maganar tana lashe madarar hannunta. Fauziyya ta ce "Ke dalla rufewa mutane baki, tashi ki kira mana ɗan uwanmu, mun zo duba shi" Cikin tsawa rumaisa ta ce"Ba zan kirawo shi ɗin ba tun da ke ba uwata ba ce" Samha ta ce "Ke, uban wa ki ke yi wa tsawa". "Uban duk wanda ya tsargu, ba sunana Aisha ba, sunana rumaisa Mahmud, ƙanwar maza, ku tambayi yayan naku wace ni, kawai ku zo ku cika mini kunne, wai ko a  ƴar aiki ba zan zo ba, ai Allhan ba naku ne ku kaɗai ba, da ban zo a ƴar aikin ba, sai na zo a matar gida, antynku ce ni, tun da matar yayanku ce ni, ke kuma da ki ke cewa ke ce mace, na ji ni namiji ce, ni duk wadda ta yi mini, wallahi sai ta ci ubanta, babu wata barazana da tashin hankali da ban gani ba, dan haka ba zaku ɗaga mini hankali ba, ke kuma da ki ke cikakkiyar macen, kin san idan ki ka gama cikar, zubewa zaki yi ki fara tsufa, kin ga ni kuma a lokacin da ki ka fara tsufa na cika ko? Banza kawai" "Ke! Kina ƴar matsiyata ni ki ke gayawa haka? Kina da hankali kuwa, waye ubanki a ƙasar nan, har ni ki ke cewa ubana zaki ci?" "Eh na faɗa, sai na ci ubanki, da ke da duk wanda ya ce zai zageni, ƴan fashin daji ma, ba su razana ni ba, balle ku shashashai, gwalagwaje, marasa mutunci, idan tunaninku gayya, ku taron mata ne, ni kaɗai dai-dai nake da tunanin maza bakwai". Ayshercool. Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Ruƙayya ta riƙe haɓa ta ce "Kan uban nan, wannan wace irin yarinya ce, mara tarbiyya Binta ta aurawa ɗan ta?" Jin maganar rumaisa ta yi wani iri, yadda ruƙayya ta ambaci sunan Ammi haka kai tsaye kamar sa'arta. Zee ta ce "Ni wallahi da na san irin wannan abun zamu tarar, da ban zo ba, kawai kun zo kuna zubar mana da mutunci a gaban wannan ƴar yarinyar". Ruma ta ce "Oho dai, in ma ƴar cikinki ce ku ta shafa, aka gaya mini cuta sai na faɗi mutuwa, haka kurum tiƙa-tiƙa da ku, ku zo kuna ci mini mutunci. Wai wani kun zo wurin ɗan uwanku, yo koma menene, duk ƴan uwantakar ta ku, tun da dai ni ta ajiye mussaman yake bani abinci, yake kula da ni, yafi so na" Samha da takaici ya ƙule, ta miƙe a hasale, tana yinƙurin ta ƙarasa ta tsinke rumaisa da mari. Fauziyya ta riƙe ta, ta ce "Ba girmanki ba ne". "Ki cikani Fauziyya, in zuba mata da haƙora na daki banza, dan ubanta" Rumaisa ta ce "Taɓ ki dakeni ki ga yadda ake ƙaramin yaƙi, wallahi sai yayyena sun yi miki bugun sakwara, bar ganin kin fini girma, ni da maza ma dambe nake ba ruwana da girmanki". Jin hayaniya ya sanya baba uwani hawowa saman, ta zo ta iskae rumaisa tana ta zazzaga musu rashin mutunci. Baba uwani ta ce "Haba ke kuwa, baƙinki ne fa, ƴan uwan mijinki, ya zaki din ga yi musu wulaƙanci haka, ai ba haka ki ke yi wa ƴan uwanki idan sun zo ba, kuma ba sa'anninki bane " "Baki san meyafaru ba, dan haka ba ruwanki da ni". Baba uwani ta dafe ƙirji ta ce "Ni ki ke gaya wa haka?" Rumaisa ta dubi dattijantar baba uwani, ta haɗiye abun da ta yi niyyar faɗa ta ce "Ba ruwanki da abun da na yi, idan ban saka ki a ciki ba, tun da baki san farkon abun ba, kuma kina goyon bayansu" Ta ɗauki kofinta, ta nufi ɗakinta, tare da ce musu "Mahukatan banza kawai" Tun da ta shige ɗakinta, ba ta sake fitowa ba, tayi zamanta tana zane-zane, har aka yi sallar magariba, sannan ta tashi ta yi alwala ta yi salla. Ta idar da salla kenan, ta jiyo takawa yana kwaɗa mata kira, yamutsa fuska ta yi, dan ya tsorata ta. Fita tayi, ta tsaya ta kalli falonta, an ci abinci an ɓata falon gaba ɗaya, har da fasa mata wasu daga cikin farantai. Kasa magana ta yi, a fusace ya kalleta ya ce "Meye wannan?" "Oho" ta bashi amsa. "Which kind of nonsense is this, ina yi miki magana?" Ya yi maganar a zafafe. Nan da nan ita ma ranta ya ɓaci, "Amma dai ka san ni ba ƙazama ba ce, kuma ba ka taɓa ganin nayi irin wannan abun ba, yadda ka gani, nima yanzu nake gani". "Wai ne ki ɗaukeni ne? Sa'anki or what, kina da hankali kuwa, kalli falon nan fa?" Takaici ne ya ƙule rumaisa ta ce "Ni ba mahaukaciya ce ba, ƙannenka da wannan Samhar su ne mahaukata, dan su suka yi haka da falon ba ni ba, tun da dai baka taɓa gani na yi haka da gidan ba" ta juya ta nufi ɗakinta, ya taka da sauri ya janyota ya mayar da ita falon. "Idan suka yi haka da wurin, ke ba zaki saka a gyara ba, ko ke ki gyara ba? Ba gidanki bane?" "Taɓ, ni zan gyara musu, to wallahi ko kai ne ba zaka yi haka in gyara ba, kai da kake ciyar da ni, balle wasu ƙartin banza" "Shut up! Ƙannen nawa ki ke cewa ƙartin banza? Ki kiyayeni, samo abun gyara ki gyara wurin nan, na baki mintuna biyar kawai. Ki gama ki zo ki gaya mini dalilin da ya sanya ki ke yi wa baba uwani rashin kunya" Wani irin malolon baƙin ciki ya cunkushe mata zuciya, ba ta taɓa tunanin Adam yana da kwarjini, da kima a idanunta ba sai yau, da ta ji tamkar an ɗaure mata harshe, ta kasa bijire masa, wasu hawayen baƙin ciki suka cika mata ido, amma ta danne, ta zo ta fara aikin gyara wurin. Ya nemi wuri ya zauna, ta gyara ta kammala, ba ta ce masa uffan ba, ta tafi ɗakinta. Bayanta ya bi, ya tarar da ita a gaban mudubi, ta cika ta batse, ba wani abu take a gaban mudubin ba, kawai tana tsaye, tana sauke numfashi. Tana ganinsa ya shigo, ta share shi ta cigaba da tsayuwa. "Me baba uwani tayi miki da ki ka yi mata rashin kunya?" Banza ta yi masa taƙi kula shi. "Ina sake gargaɗinki, duk abun da zasu zo su yi, babu ruwanki da su, sannan idan ki ka kuskura ki ka kuma yi wa baba uwani rashin kunya, sai na ɓata miki rai, kawai kin saka tsohuwar mutane kuka, saboda ke baki san abun da ya dace ba?" Yayi maganar yana son ta yi magana, dan ya ji meya haɗa su da su Fauziyya, dan ya san idan ya tambaye ta, yadda ta ƙule ɗin nan, ba zata gaya masa ba. "Wallahi duk wadda ta kuma zuwa ta zageni, sai na rama, kayi zuciya ka mayar da ni gidanmu, sai ka tattaro su su dawo gidan nan su zauna, gida zan tafi dan ni ba banza ba ce, da za su din ga zagina ina jin su ba, me na yi musu? Nima ƙanwar wasu ce, kuma suna sona, dan wallahi ko za su kasheni, suka zageni sai na rama, ita kuma baba uwani ta cigaba da yi mini sharri" ta yi maganar tare da shigewa toilet. Har dare taƙi ko sake fitowa, dan ko abincin dare ba ta nema ba, ta yi kwanciyarta. Sai da takawa ya nemi, Asiya da barira ya tambayesu abun da ya faru, amma suka ce ba su sani ba, baba Uwani ta hana su hawa saman, amma sun jiyo su Fauziyya suna zagin rumaisa tana ramawa. Daga nan gidansu ya wuce, bai ko je sashin Ammi ba, ya nufi sashin Mummy. Ya tarar da su gaba ɗayansu, har da Mahmud da Mummy, da ruƙayya da Fauziyya, sai dai babu Samha. Mummy na ganinsa ta ce "Ahh, takawa barka da wannan lokaci, ƙaraso mana, ya jikin naka, tun da na shiga ban sake zuwa ba, ashe ka samu sauƙi". Ya ce "Eh" "Sabuwa, ƙaro plates, a zubawa takawa abinci shi ma". Ya girgiza kai ya ce "Na gode, Fauziyya" Ta kalleshi ta ce "Na'am yaya" "Kun je gidana ɗazu?". "Eh yaya mun je, zamu sake dubaka ne kuma baka nan, matarka ta yi mana rashin mutunci, har da zagin baba uwani". Adam ya ce "Daga yanzu, idan har ba alkhairi ne zai kai ku gidana ba, kar ku sake zuwa, ina baku wannan saƙon ne har Samha, idan ma baku gaya mata ba, ni zan gaya mata. Kar ku sake zuwar mini gida ku ci mutuncin mata ta, ni na ajiyeta ba ita ta ajiye kanta ba, kuma ban aurota, dan ku je ku ci zarafinta ba, ita Aisha dama taku ce, kuma mai haƙuri ce. Wannan kuma tawa ce, sannan ba zata iya jure abun da Aisha ta jure ba, yarinya ce ba zan lamunci a saka mata tension depression ya kamata da ƙuruciyarta ba". Baki a sake Mummy ta ce "Yanzu matarka ka fifita a kan ƙannenka, duk da sun gaya maka ta wulaƙanta su? Bayan kai suka je dubawa?". "Mummy ko dabba na ajiye na ce nawa ne, bai kamata a je ci mutuncinsa ba, idan har ina da kima a idon su ba, balle ɗan adam na ajiye, idan banda rashin girma, me zai saka su biye mata, tun da ba sa'arsu ba ce ba, na san rigimammiya ce, amma ba ta yi haka kurum, ku kiyaye, aje a ci mata mutunci ace mata ƙwaila, ko ba mace ba ce, ni a idona mace ce kamar kowa.  Dan haka Please allow her to enjoy her marital home. Ko ba ku yi zumunci da ita ba, ni na isheta, na san yadda nake bi da ita mu zauna lafiya" Mummy ta yi murmushi ta ce "Hmm, wannan dai kashedin na samha ne, zuwa aka yi a gaya mana ana son ta kenan". Ya tashi yayi murmushi  ya ce "Ta cancanci hakan Mummy, a rashin Aisha ita ce uwar ɗana, idan na bari aka wulaƙanta ta, ni aka yi wa, dan haka a kiyaye" Mummy ta yi shiru, tana saƙa wani abu a ranta, lallai akwai ƙura ba ƴar kaɗan ba, Samha tana ruwa, dan ba ta tunanin baba uwani na abun aka sakata yadda yakamata. Mummy ta ce "Gaskiya ne, tayi rawar gani kam, ta cancanci a kula da ita. Duk da ka ɓoyewa duniya ita, da muhimmancin abun da tayi maka" "Ni ta yi wa, ba duniya ba, dan haka ni yakamata na girmama abun da tayi mini". Mahmud kuwa, ya kammala cin abincinsa, danna wayarsa kawai yake yi. Har Adam ya wuce shi, ya dawo ya zauna a kusa da shi, yayi ƙasa da muryarsa yadda shikaɗai zai ji me yake cewa ya ce "Am warning you, stay away from my family, da ɗana, da kuma matata" Mahmud ya ɗan kalli Adam ya ce "Ban ji zan iya ko ɗaya ba, ina son ɗanka, ina girmama matarka, kasancewar tana girmamani, we are having a deal together, dan haka you should stay away from us" Wani irin zafi maganganun sa, suka yi wa adam, amma ya shanye ya ce "Shikenan, idan ka ƙi ji, ba ka ƙi gani ba" ya tashi ya fice. Mummy kasa zama tayi, ta tashi ta bar falon, Fauziyya kuma suka cigaba da caccakar rumaisa, suna bawa Mahmud labari. Bayan ya bar sashin Mummy, ya je ya ga Sabir, Ammi ta yi masa ya jiki, tayi masa addu'a kamar yadda ta saba, sannan ya tashi ya tafi. Kasancewar a cikin garin, gidan Jamil yake, ya sanya ya biya gidan Jamil, sai dai ya tarar baya nan. Yau ya ji ƙwarin jikinsa sosai, dan haka ya shirya dan tafiya aiki, ya saba idan da makaranta, shida da rabi, rumaisa za ta zo gyara masa ɗaki, idak bai tashi ba ma, ta din ga ƙwale-ƙwale kenan sai ya tashi ko baya so. Amma har ya fito breakfast, ko alamunta bai gani ba. Kai tsaye ya tafi ɗakinta, tana zaune dirshen da kayan bacci, ta cika akwatu da kayanta, tana zugewa. "Ba zaki shirya tafiya makaranta ba ne?" "Eh na daina zuwa, gidan matsiyatan iyayena zan koma, in cigaba da zuwa wadda na saba zuwa, sannan in cigaba da cin irin abincin da na saba ci, ba irin wanda nake ci a nan ba ake yi mini gori" "Dalla tashi ki shirya zan makara" "Sai kuma ka yi, ni za a din ga yi wa gori, saboda rashin adalci irin naka, da son kai, ka ɗora mini laifi, kai ƙannenka ba sa laifi, wallahi ko ta katanga sai na haura na koma gida" tayi maganar cikin tsan-tsar takaici. "Na baki mintuna goma, ki yanke shawara, idan kin zaɓi mu rabu, abu ne mai sauƙi, amma ki sawa ranki, ba zaki sake ganin Sabir ba, har abada mintuna goma kawai gareki" saroro ta yi, ta bishi da kallo har ya fice. Ko mintuna bakwai yi ba, sai gata cikin uniform, kamar zata fashe. A ransa ya ce "Ni zaki yi wa zuciya, bayan na san lagonki?". Suna tafe a hanya ya saya mata alawar madara, dan ya san tana son harkar madara. Ta ce bata so, bai kulata ba ya ajiye a kusa da ita, suna zuwa ƙofar makaranta, ta buɗe ƙofar motar ta ɗau alawarta ta fice. Yayi murmushi ya ce "Su mimi ba zuciya in dai a kan kwaɗayi ne" tana jin sa a ranta ta ce "So ka ke in kulaka, kuma ba zan kula ka ba". Ana tashinsu ya je ya ɗaukkota, ya wuce da ita gidan Ammi, ya ajiyeta ya koma wurin aiki, tana jin daɗin hakan nan, saboda yana ɗebe mata kewa sosai, duk da su Iman na makaranta, ta yi ta hira da Ammi, tana wasa da Sabir. Ammi ta ce "Rumaisa, ashe su Fauziyya ne suka je gidanki jiya?" Rumaisa ta ce "Eh Ammi, sun je jiya da yamma" "Ina fatan dai ba wata matsala" Rumaisa ta ce "Eh Ammi babu komai, sun je duba shi baya nan" Ammi ta yi murmushi tana dafa kafaɗar ruma ta ce "Ashe mutuniyar tawa tana girma, da har take iya ɓoye abu. Ban san dai meyafaru ba, amma na san ba zasu je su dawo haka ba, sai sun yi miki wani rashin albarkar. Babarsu ta zo ɗazu tana ta masifa, wai takawa ya je ya ci musu mutunci a kanki, kamar ba ƴan uwansa ba". Rumaisa ta waro ido ta ce "Papan? Amma ni kuma jiya yayi mini wulaƙanci, suka ɓata ɗaki wai ni zan gyara". Ammi ta ce "Ki yi haƙuri, ki cigaba da kula da kanki, ban da surutu a gaban wani" "To Ammi in sha Allah" Ammi kuwa daɗi ne ya kamata, ganin alamun soyayya a tsakanin rumaisa da takawa, yadda suka din ga turjiya kan ayi auren, ba ta tsammaci haka ba bayan auren. "Yauwwa, Ammi dan Allah kira mini mama mu gaisa, ke da ita duk kun ƙi zuwa gidanmu". Ammi ta ce "Bari na kirata, to me zamu zo mu yi muku, ku ba gashi kuna zuwar mana ba". Ammi ta kira mata mama, ta bata wayar sannan ta tashi ta fita. Mama na yin sallama ta ji muryar ruma, mama ta ce "Ahh babar sabir, ƴar gidan amminta" Ruma ta ce "Mama na tabattar kin daina so na gaba ɗaya, baki taɓa zuwa gidana ba". "Ai na san kina lafiya ne, ya ɗan naki ya maigidan?" "Ɗana lafiya ƙalau, maigidan kuma mun yi faɗa bama magana" Mama ta ce "Kun yi faɗa ba kwa magana saboda baki da hankali?" Cikin sangarta ta ce "Mama faɗa yake yi mini a kan abun da ba laifina ba" "Yi mini shiru, dan me ba zai yi miki faɗa ba, ya fita ya nemo ya kawo ki ci, ƴan uwanki sun ce mini baki nemi komai kin rasa ba, kuma dan yayi miki faɗa sai ki daina yi masa magana? Idan ma daina yi miki maganar yayi, ke ba zaki yi masa ba? Kin ga ki kiyayeni". "To mama kawai sai na bashi haƙuri" "Kar ki bashi, zan nemo masa wata matar mai ɗa'a, tun da ke ba kya ji" Rumaisa ta ce "Mama ban gane ba, to wallahi ammi ta ce ba zai ƙara aure ba, daga ni shikenan". "Kar ki canza hali, na fasa zuwa gidan naki ma, sai kin yi hankali" Kan ta yi magana, mama ta katse wayarta, ruma ta ajiye wayar tana tura baki. Tayi shiru tana nazarin maganar mama, ba ƙarya duk abun da take so yana bata, ko bai amsa mata ba, za taga abun ya bata. Kuma ga ammi ta ce ya je ya yi wa ƙannensa faɗa. "Ai shikenan, zan daina fushin, amma ba zan bashi haƙuri ba" Har yamma tana gidan Ammi, sai magariba, sannan takawa yayi waya, ya ce Sidi ya mayar da ita gida. Yawan zuwan nan da take yi, ya sanya ba ta damu lallai, sai an bata sabir ba, saboda tana samun shaƙuwa sosai da sosai tsakaninta da Sabir ɗin, da kuma Ammi, gashi akwai fahimta sosai tsakaninta da iman, sannan a hankali take ƙara sanin kan masarautar, dan wataran idan ammi za ta fita, binta take yi. Tana tsaye tana ƙoƙarin shiga motar sidi, sai ga mahmud. "Daughter, ina ta so mu haɗu da ke" "Ai ban san kana nan ba, da sai na nemeka". "Kin san bana zuwa ko ina. Jiya mijinki ya zo sashinmu, yayi wa Mamana rashin kunya, saboda su Fauziyya sun je muku gida" Rumaisa ta ce "Ai gara shi, kishiyar mamansa ya yi wa, wanda yayi wa maman sa fa" "Ba wannan maganar muke yi ba, idan muna irin wannan maganar, raina zai iya ɓaci. Yanzu dai ina zaki?". "Sidi ne zai kai ni gida". "Duk an yi mini kashedin na fita harkarku, amma ba zan iya ba, ɗaukko mini Sabir sai na kai ki gidan, na dawo ni da shi" Rumaisa ta ce "Babu lallai ammi ta bani shi, sai da ka zo mu je tare" "Ina son yaron nan sosai daughter, mu je" Tare suka koma Ammi ta din ga kallon Mahmud, Ruma ta gaya mata abun da ya ce, ammi ta ce "Banda abun sa ai shi ma ɗan sa ne, Allah ya tsare" Ruma ta yi ta murna, ta ɗauke shi suka fita, Mahmud ya karɓe shi, suka shiga motarsa suka tafi. Nusaiba ta ce "Ammi, kina ganin babu wata, ko takawa ya zo yayi faɗa?". Ammi ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Yarinyar nan ta zarce duk yadda nake zato, ko da ba ta gaya mini ba, na san ƙoƙari take ta sasanta tsakanin Adam da Mahmud, tun da ni na gagara yi, ban sani ba ko ita Allah ya sa ta iya, dan haka ba abun da zan iya, yi mata Addu'a, tare da goyon baya ɗari bisa ɗari" Nusaiba ta ce "Ikon Allah, ammi kuma fa haka ne" "Ku tayani addu'a, a dalilinta sau biyu Mahmud yana zuwa in da nake, in sha Allah ko bai dawo wurina gaba ɗaya ba, sai an samu daidaito tsakanin iyalina". Nusaiba ta ce "Allah ya sa". Har ƙofar gida ya kai rumaisa, suna tafe suna tattaunawa a hanya, yadda za su fallasa baba uwani, domin sai an katse hanyar kaiwa Mummy saƙo, da samu hanyar dakatar da wasu ayyukan na Mummy. Rumaisa ta sauka, shikuma ya tafi da shi da Sabir. Sai wajen goma na dare, sannan takawa ya isa gida. Rumaisa tana fallo tana kallon cartoon, kamar yadda ta saba. Sallama yayi da kaya a hannunsa, ta tuna mama ta taɓa cewa, a zamaninsu idan miji ya dawo gida da kaya a hannunsa, jiki na rawa suke tashi su karɓa. Cikin basarwa, ta tashi ta miƙa hannu za ta karɓa, ya kalleta ya ce "Kin ci abinci ne?" "Na ci a gida". Ya ce "Dafo shayi cup biyu, ki sameni a ɗaki" Ta jinjina masa kai, ta tafi kitchen. Kan ta dafa ta dawo, har yayi shirin kwanciya, sai dai yana gefen gado, yana danna waya. Ta ajiye cup da flaks ɗin, za ta fita ya ce "Zauna ki haɗa mana" Su ruma da yake ba kowacce bisimillah take wucewa ba, ta zauna ta haɗa tea cup biyu. Gasashshen nama ne, da ƙaton bredi, ba kunya ta saka hannu tana ci, tana basar da shi, ita dole ba ta daina fushi ba. Hannu ya sa, ya matse kumatunta ya ce "Can't you smile, or say thank you? Kin shanye mini alawar madara, kuma kina wani kumbura baki" Tura baki tayi, ta cigaba da kora shayi, suka gama ciye-ciye, ta tashi zata kwashe kwanuka ta fita. "Zauna zamu yi magana". Ta zauna tana lashe hannu. Ya ɗaukko tissue, ya goge mata hannun. Sannan ya dubeta ya ce "Cikin satin nan zan yi tafiya in sha Allah, zan yi sati biyu, idan na dawo kuma, zan je ƙaro karatu, na tsawon watanni shida. Wannan asabar ɗin in sha Allah, za a saka ki a Makarantar islamiyya ta matan aure". "Islamiyyar matan aure, salon su rainani, ba manya ne matan auren ba? Kuma wai ka tafi ka barni nikaɗai?" Takawa ya ce "Eh, sidi zai din ga kai ki yana dawo da ke makaranta" "To sai in daina ganinka?". "Kina son ki dinga gani na ne?" Ta ce "Eh mana, nafi son ka dinga kaini makaranta da kanka" Yayi murmushi ya ce "Abokin gabar naki? Da ki ke yi wa rashin kunya?" Tayi dariya ta ce "Ai amanarka aka bani, sai na gama sauke amanar, sannan zan rama abun da ka yi mini, dan ban manta ba, kuma kai ne ka ke sawa na yi maka rashin kunya ai wataran, amma dai ka yi haƙuri. Wani irin murmushi yayi, yana jin daɗin jirar ta su. Ya ɗora hannunsa a kafaɗarta, kamar ƙawarsa ya ce "Ban haƙura ba, fitsararki ta yi yawa, haƙurina ya kusa ƙarewa" Ita ma ta ɗora hannu a kafaɗarsa ta ce "Allah ya sa kar haƙurinka ya ƙare, ai da ban taɓa sanin kana da haƙuri ba ma sai yau. Allah ya sa in yi tsawo in kamo ka a tsayi" "Ba wannan nake so ba, ki yi girma ki biyani bashina nake so" Ba tare da ta gane me yake nufi ba ta ce "Ai da na gama makaranta, na fara aiki, dubu goma ma zan baka". "Zaki ga idan kin gama makaranta, na gaji, baby nake so, ayi wa sabir ƙani ko ƙanwa" Ta ce "Eh wallahi, nima ina so" Yayi dariya ya ce "Are you sure?" Ta ce "Yes" cikin murna. Yayi dariya ya ce "zamu gani ai". Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Duk da na yi maganar a baya, amma yanzu zan sake jaddadawa, ki din ga iya bakinki, a al'amuran da suka shafi masarautar nan. Abu na gaba a duk lokacin da abu ya faru, idan nayi magana ko kina da laifi ko baki da laifi, bana son musu, idan baki da laifi, da kaina zan yi bincike in gane" "Idan bani da laifin sai ka bani haƙuri?" Ya ce "Ya danganta, ba sai lallai na fito kai tsaye na ce kiyi haƙuri ba, sannan a duk lokacin da wani daga familynmu, ya sake zuwa, idan har suka yi miki magana ta rashin kyautawa, kar ki kula su, idan na zo ni ki gaya mini. Sai kuma alaƙarki da wancan yaron Mahmud, ina sake maimaita miki bana so, ki kiyaye abun da ba na so mu zauna lafiya". Rumaisa ta ce "Gaskiya papa, ni ba kullum nake ƙarya ba, maganar gaskiya ba za aci mini mutunci nayi haƙuri ba, tun da dama can Allah bai yi ni a cikin masu haƙuri ba. Sai kuma maganar daddyna, dan Allah meyasa ba ka son alaƙarmu?" . "Ban ji na yadda da alaƙar bane, zai iya yin komai dan ya cutar da ni, dan haka ba zan so yayi involving ɗinki da Sabir ba. Mussaman da ki ka kasance abokiyar gabata" Ruma ta yi murmushi ta ce "Amma ka yadda ka yi mu'amala da su Jamil ko? Kai baka san farincikin ammi ne papa? Ba zai cutar da kai ba, idan kuma kana son mu rabu, to ka rabu da su Jamil kai ma". "Alaƙata da su daban...." "Amma duk wata alaƙa barin jini ce da ciki ɗaya, wai ba Jamil ɗin ba ne yake yekuwar sai ya bincike ka ba a kan Anty Aisha, haka son da yake makan yake? Maiyasa da tana raye basu damu da ita ba, sai bayan ranta har da barazanar zai yi bincike a kanka, wataƙila ma da saka hannunsa, shiyasa yake son ya ji ta ina kake binciken naka, ya ji ko asirinsa zai tonu, ka din ga wayo kamar ni mana" Gaban Adam ya yanke ya faɗi, kar maganar rumaisa ta zama gaske fa, gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, take ya ƙaryata maganar rumaisa a zuciyarsa, ya san abun da ba zai taɓa faruwa ba kenan. Ruma ta tashi ta ce "Papa sai da safe" ta kwashi kwanukanta, ta bar shi da tunani. Haka ya kwana wa wayi gari, maganganun rumaisa na kai komo a kansa, idan ya ƙaryata sai yaji abun bai kama zuciyarsa ba, kamar da wayo clue ta bashi, a kan binciken, idan ba rami meya kawo rami? Washegari a wurin aiki, takawa da kansa ya je office ɗin Jamil, Jamil ya wani tsuke fuska. Adam ya ce "Jamil lafiya kuwa? Tun da ka kaini gida, na ce ka ɗaukko rumaisa, ban sake ganinka ba" "Me zan zo na yi maka? Dama kana sane ka tura ni ɗaukko fitsararriyar matarka, ta yi mini rashin kunya, tun da ka gama zubar mana da mutunci a idonta, ni zata kalla ta ce wai ba ƙaunar aisha muke ba, ka je ka gama zazzage mata sirrinmu, meye amfanin dawo da abun da ya wuce? Adam turaki yaƙi gaya mini komai a kan abun da ta gaya masa, dole na cigaba da bibiyarka da tuhumar ka akan dalilin ɓatan aisha bamu sani ba". "Kuma ni ta ce maka na gaya mata?" "Idan ba kai ba waye ya gaya mata? A ina zata sani ko ta ji? Kuma dole ka gaya mini abun da kake ɓoyewa, dan na fika kusanci da Aisha, ai jini ya fi ruwa kauri. Kuma zan cigaba da bibiyar yarinyar nan, sai na san gaskiyar abun da yake faruwa. Adam ya haɗiyi yawu ya ce "To shikenan, ai matata ce, na gaya mata ɗin, kuma Jamil kar ka fasa tuhumata da bibiyata, ka yi duk abun da zaka yi" Ya daki tebur da ƙarfin gaske ya ce "Kuma ina yi maka rantsuwa da Allah, idan wani abu ya samu matata, sai dai ayi mutuwar kasko da ni da kai, ka je ka cigaba da bincike a kaina, amma idan har zaka bibiyi matata ita za ta gaya maka abun da ya faru, ka shirya cewa watan faɗuwarka ya tsaya, dan tana da ƙwaƙwalwa fiye da lissafinka, kuma gaskiya ta faɗa, a da baku damu da ita ba, kun cutar da ita meye na tayar da jijiyoyin wuya a yanzu? Idan ka matsa za ta saka ka a sarƙa, kuma muddin ka faɗo cikin suspect ɗina, aikina zai bi ta kan ka" Ayshercool 08081012143 Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 A rikice Jamil ya kalli takawa ya ce "Kana nufin ni ne ke da alhakin yin garkuwa da aisha, kai ba a zargeka ba sai ni?" Adam ya ce "Ni dama a can a cikin zargi nake, ban ce kai kayi garkuwa da aisha ba, amma abun da ka yi ya jefa ka cikin zargi, madalla da yarinya mai kaifin tunani kamar rumaisa" yana gama maganar ya fice daga office ɗin. Wani irin gumi Jamil ya yakice, yana wani irin huci. "Da ni ka ke zancen Adam, zaka gane ba ka da wayo, daga kai har wannan shegiyar yarinyar mai ƙulla mini jakar tsaba, saboda kaji su bini". A daren jiya kuwa, Mahmud yawonsa ya din ga yi da Sabir, har da zuwa yawon ciye-ciye, ya sayawa Sabir kaya ba kaɗan ba, soyayyar da  yakamata ya ji game da ɗan uwansa Adam, shi yake ji a Sabir, koma ya ce fiye . Ammi tana nan tana dakon dawowarsu, Nusaiba da Iman ma, duk suna tare da ammi, suna jiran dawowar Mahmud. Wajen ƙarfe tara da rabi, sai ga Mahmud, sidi ya biyo shi, da uban faggon kaya niƙi-niƙi, zuwa shashin Ammi, da da yake ji kamar wata baƙuwar duniya, amma yanzu the more yake shiga, the more yake zama familiar da wurin. Mahmud ya nuna masa wuri ya ajiye kayan, ba tare da ya kula kowa ba, ya ƙarasa kan kujera, ya kwantar da Sabir da yake bacci, ya durƙusa a gabansa yana ta shafa gashinsa, kamar ya tafi da shi, ya kwana a wurinsa. Ya miƙe a hankali ya juya zai fita, Ammi ta ce "Wannan kayan fa?". "Nasa ne" ya faɗa a taƙaice ya fice. A sashin Mummy ya tarar da Mummy ta rako Samha, tana ta rarrashinta, idonta yayi jawur, alamar ta sha kuka, ya san ba zai wuce ta gaya mata saƙon Adam ne ba, shiyasa take wannan kukan. Sai da Mummy ta rakata har mota, sannan ta koma sashinta. "Ina ka je ne? Tun sallar magariba baka dawo ba, baka kirani ba kuma, na san baka yawo da daddare". "Na fita da Sabir ne" A ɗan razane ta ce "Waye Sabir?" "Ɗan mu da Adam ya haifa" "Au yanzu dan rashin zuciya, har ɗan sa ka je ka ɗauka kana yawo da shi? Wurin giwar ka je kenan?". "Sirikarta na saka ta ɗaukko mini shi, ina ƙaunar yaron nan sosai da sosai" Mummy a ranta ta ce "Lallai tsuguno ba ta ƙare mini ba, akwai sauran rina a kaba, aikin malam na kan dutse ya fara sanyi" Ya ce "Mummy, ya dai na ganki wani iri, akwai damuwa ne?". "Damuwa akwaita Mahmud, ban gane maka bane kwana biyun nan, ka san dai a duniya bamu da maƙiya sama da giwa da Adam, yanzu kuma naga kamar alaƙa ce tsakanin ka da matarsa, ko ka san yarinyar nan cewa ta yi wai ina yi wa Adam asiri?" A ransa ya ce "Tom, hasashena ya tabbata, matar nan ta faɗa tarkonmu" "Na gaji da wannan rashin albarkar, nan ya zo ya gama yi mini rashin mutunci, a gabana ya ci mutuncin ƴaƴana, saboda wannan hatsabibibiyar yarinyar, kuma ta ce wai ina yi masa asiri, a gidan ubanta ta ga asirin, zai maimaita a gaban mai girma wambai, dole ayi mini iyaka da ita". Cikin ko in kula Mahmud ya ce "Amma dai idan ki ka kai ƙarar wannan Yarinyar, za ace girma ya faɗi, raƙumi da shanye ruwan ƴan tsaki". "Ba ita zan kai ƙara ba, shi Adam ɗin ita a wa, ina ruwana da ita, amma dole ayi mini iyaka da su". *** Daf da la'asar, rumaisa ta shiga ɗakin takawa, tana dudduba abun da za ta gyara. Daga toilet ta ji ya ce "Waye a nan?" Ta amsa masa da "Ni ce nan" "Rumaisa duba drowern mirror, ki bani shaver". Ta yamutsa fuska ta ce "Rumaisa kuma?" Ya ce "Eh" "Ba cewa ka yi mimi zaka din ga ce mini ba?" "Anƙi ace mimin, miƙo mini da sauri" Ta ɗaukko shaver ɗaya, ta tsaya a ƙofar banɗakin ta ce "To shigowa zan yi?". Ya ce "Eh miƙo mini" "Au kai ba ka jin kunya, to ni ba zan shigo ba, zuro hannu ka karɓa". Ya ce "To ai ba tsirara nake ba, miƙo mini abu nake yi" Ta tura ƙofar a hankali, ta ɗan leƙa, yana tsaye a gaban mudubin toilet ɗin, ya shafa wani cream a fuskarsa, da wata shaver a gabansa, ga wani towel ɗin a wuyansa. Duk da haka sai ta ji wani iri, ta ƙarasa a hankali, ta tsaya tana kallonsa. Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ya dai?" "Bakomai, so nake naga me ake yi da shaver" Ya ɗan waro ido ya ce "Baki san me ake yi da ita ba?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "Ba kya aski kenan?" Rumaisa ta ce "Ni namiji ce da zan yi aske kaina" Ya girgiza kai ya kerɓi shavern ya ce "To tsaya ki ga me ake askewa da ita". Aikuwa ta tsaya, ta zuba masa ido. Ya kammala gyaran fuskarsa da ita, sannan ya ɗebo cream a wata container, ya shafa a hammatarsa da ta fara fitar da gashi, ba sosai ba. A hankali ya sanya shaver yana cire gashin. Ta ce "Innalillahi, dama abun da ake yi kenan, to ni ya aka yi bani da shi, sai yaushe zai fito mini?" Ya ce "Da gaske baki da shi?" Rumaisa ta ce "Bai fito mini ba, kuma ina so, in ga ya fito mini da yawa, idan na ɗaga hannuna a din ga gano shi". Adam ya ce "Saboda ƙazama ce ke? Waye yake ado da gashin hammata, ƙazanta ne to" "Eh, amma dai ina son ya fito mini" "Duk ranar da ya fito, ki ka bar shi, ni da ke ne, idan kin ga ya fara fitowa ya taru, ki yi mini magana in sake koya miki yadda zaki aske shi. Amma gashin hannta ba abun so bane, ba abun ado bane. I even wonder kin fara period but still a child" Rumaisa ta ce "To ni dai Allah ya sa ya fito da wuri, sai ka sai mini shavern nima ko?". Ya ce "To, jeki zan aske ɗayan" "Me?". "Gashin" ya bata amsa kai tsaye. "A ina yake shi kuma, ko na ƙafarka, ga hannunka ma" "A'a towel ɗin ƙuguna zan kwance, nan ma akwai wani, shima ba a barinsa cirewa ake yi, idan ba haka ba mutum ya din ga wari, idan ya fito shima ki gaya mini a sayo shavern, sai in koya miki" Yatsunta ta saka, ta toshe kunnunwata ta bar toilet ɗin, saboda ta daina jin abun da yake faɗa, a tunaninta ai wannan abun kunya ne. Ta fice daga ɗakin sa, ta sauka ƙasan bene. Asiya da barira, suna ta yi mata sannu da gida, ta amsa musu tana gaishe su, sai dai ta lura da yadda baba Uwani ke ta wani kumbura fuska. Ruma ta ce "Baba uwani, me nayi miki ne?" Ta kalleta ta ce "Hmm tambayata ma ki ke yi?" "Papa yayi mini faɗa, ya ce kar na sake ai, ranar ma dan raina a ɓace yake ne". Asiya ta ce "Ranki ya daɗe, wata jita-jita na jiyo, da na je karɓo miki saƙo a wurin Ammi". Ruma ta ce "Wace jita-jitar kuma?". "Wai saƙo ya iske cewa, kin ce hajiya jamila, babar Yallaɓai Mahmud, wai tana  yi wa maigida takawa asiri" Rumaisa na jin haka, ta san mahmud ne ya bayar da wannan saƙon, yana nufin baba uwani ta kai tsegumin, kuma shi ya saka ta faɗa a gaban baba uwani. Rumaisa ta waro ido ta ce "Ni ɗin, waye ya faɗa? Ni harkar wa ma na shiga balle na faɗi wannan maganar?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Anya babu munafuki a sashin ammi? Idan ma na faɗa, ai ba a gaban wasu bare na faɗa ba, balle ma ban faɗa ba. Amma ai ba ƙarya nayi ba, idan ma na faɗa, idan ta san ba ta yi, ai ba zata tsargu ba, idan kuma yin take, A'uzu bi kalaimatillahi tammat. Tsuru-tsuru baba uwani tayi, tana ta yaƙe baki ta ce "Ai uwar ɗakina, asirin ma ba za a rasa yi ba, saboda abu ne na gidan sarauta, kowa kansa kawai ya sani, galibi ba Allah a ransu" Ruma ta ce "Yauwwa, Aisya kin ji ko, barira ma kin ji, ga baba uwani ma ta faɗa, mummy na yi wa takawa asiri, ashe bani kaɗai na fuskanci hakan ba". A rikice baba uwani ta ce "Ba haka nake nufi ba, ki yi wa Allah da ma'aiki kar ki ƙulla mini sharri". "Ba sharri bane, ai ke ki ka faɗa" Rumaisa ta nufi hanyar satairs, cikin tashin hankali, da mamakin yadda jikar cikinta, take yi mata wayo, ta bi bayan rumaisa. Ruma ta tsaya ta waiwayo ta ce "Idan ki ka biyoni sai na gaya masa" ta juya ta cigaba da hawa. Ta koma a sukwane kitchen, ta ce "Aisya, da ku za a haɗu a ƙulla mini sharri ko?" Barira ta ce "Ba wani sharri baba uwani, mu ba butulu ne irinki ba, idan baki yi wasa ba, an ƙulla miki kyakykyawan tarko kema, kamar yadda ake haɗa baki da ke, ake cin dudduniyar giwa". "In ji uban wa? Waye ya haɗa bakin da ni?". Asiya ta ce "Oho, a juri zuwa rafi da tulu...". Barira ta ce "Wataran zai fashe". Ruma kuwa daɗi take ji, ta san tana daf da tonawa baba Uwani asiri. Ta shiga kitchen ta duba fridge, taga takawa ya kawo kaji, amma bai gaya mata ba. Ga kayan miya duk ya ajiye bai gaya mata ba, balle ta yi aikin su. Tana aikin tana mita, ya zo ya tarar da ita a kitchen. "To uwar ƙorafi, menene kuma?". "To ba kaine ka kawo aiki ba, kuma ba ka gaya mini ba". Ya ce "No, su Aisya na ce idan sun gama aiki, su zo su gyara miki, sai ki ɗibi naki, ki basu na gida". Rumaisa ta ce "Saboda ni ban iya aiki ba ko? To Wallahi ina ƴar ƙaramata, na iya gyara nama, ko kaza ko kofi, ni fa tun ina shekara uku mama ta ce nake kuka, a bani ɓare maggi, da daka, na iya aiki sosai da kake ganina". "To Allah ya baki haƙuri, idan kin gama, ki dafawa mama wani abun, ko mu saya a waje, mu je ki gaishe ta, dan ni ina zuwa mu gaisa". Tsalle tayi a kitchen ɗin "Yeeee, zan ga mama, amma shine ka yi mini wayo, ka ke zauwa kai kaɗai?". "Eh, ai da yake maman tawa ce, ba taki ba, kuma a kyauta zan kai ki ba, da sharaɗi". Cikin mamaki ta ce "Sharaɗi kuma?" "Eh sharaɗi mana. Ta ce "Na me?" "Kiss zamu yi" Ta kwaɓe fuska ta ce "Kiss, iskanci fa kenan". Ko a jikinsa ya ce "Eh, shi zamu yi". "Taɓ wallahi a'a, ƙazantar?" Matsawa ya yi kusa da ita, ya sunkuyar da fuskarsa dai-dai tata, ta rintse ido ta kame jikinta. Ya ce "Wai ke haryanzu kamar robot ki ke, ba kya jin komai ne?" Ta sake kawar da kanta gefe, tana rintse ido. Ya rungumota a jikinsa, ya kai fuskarsa tata. "Wallahi idan ka yi mini zan yi ihu, kuma ma ba kullum nake yin brush ba, bakina wari yake" ba ƙaramar dariya ta bashi ba, gaba ɗaya ta tsorata sosai. Ya girgiza kai ya ce "Ki yi girki mu tafi da shi, idan an yi sallar magariba zamu tafi" yana fita, tayi ajiyar zuciya, tana ta sauke numfashi. *** Iman ce zaune a gaban Ammi, ta tattara mata hankalinta, jin ta ce mata, akwai maganar da take son su yi mai muhimmancin. Ammi ta ce "Iman, Jabir ne yazo mini da wata magana, wai yana sonki, kuma nan kusa yake son ayi komai a gama, baki ji daɗin da na ji ba, kin ga shi na gida ne, kuma ya san duk halin da ake ciki" Ras! Gaban Iman ya faɗi, mussaman ganin yadda ammi ke murna da al'amarin. "Ya ki ka yi shiru, ba ki ce komai ba?" Iman ta ce "Ammi tsoro nake ji, kin san mamansa ba za ta amince ba" Ammi ta ce "Iman addu'a zamu yi, Allah ya sa ta amince ya shige mana gaba, na san babu yadda za ayi" Jiki a sanyaye Iman ta ce "To Ammi" daga haka ta tashi ta tafi ɗakinta, ammi ta nuna goyon bayanta a kan lamarin, gashi ita ko kaɗan, ba ta ra'ayin Jabir, hasali ma zuciyarta na tare da wani daban, da bai san tana yi ba. Mai sunan baba yana ɗakinsu yana cin abinci, yana jiyo tsalle-tsallen ruma a tsakar gida, takawa kuma yana tare da mama suna hira. Haka kurum ya ji gabansa ya faɗi, har sai da ya ji tamkar abincin da ya haɗiya ba zai wuce ba. A take tunaninsa ya kai kan iman, ya janyo wayarsa, ya shiga What's app ɗin sa, sai dai ba ta online, to idan tana online ma me zai ce mata?. Ya taso ya fito tsakar gida, rumaisa ta zauna ta saka Yasir a gaba, suna magana ƙasa-ƙasa. "Yasir, kai ka san ta kan waya, na san kai gwani ne, hacker ne kai, hacking nake so ka yi mini" Ya harareta ya ce "Ni ne hacker?" "Yi haƙuri, wani abu zaka yi mini, wayarka zaka ara mini, zan haɗaka da wanda zaku yi aikin tare, sirri muke so". "Ke, bana son iskancin banza, haka kurum ki ja mini masifa, ke idan kin nemo magana mijinki zai fitar da ke, ni kuwa fa?" Ruma ta ce "Ba irin wannan aikin bane, yaya usy ya san komai, tare muke shawara ma, papa zaku tayani mu taimakawa, amma bana son ya san halin da ake ciki, bari ya usy ya dawo, zan baka lambar Mahmud ɗin, ƙanin mijina ne" gyaran murya suka ji a bayansu. Ruma ta waiwaya taga mai sunan baba a tsaye. Da sauri ta tashi ta ce "Laa mai sunan baba ina wuni, ban san kana nan ba ai" Alama yayi mata da ta je, ta ƙarasa zuwa cikin ɗakinsu, ya kalleta ya ce "Ina yarinyar nan, ta warke?" Cikin rashin fahimta ta ce "Wace yarinyar?" "Ƙanwar mijinki?" Ruma ta ce "Auu, Anty Iman, dama ba ta da lafiya ne?". Ya ce "Never mind, je ki kawai". "Tana lafiya ƙalau, shekaranjiya ma mun je gidan, kusan kullum idan muka je, sai ta ce mini ina yaya Umar, ko ta bani wayarta ta ce.... "Fita ki bani wuri" ya katseta, saboda yadda ta fara zuba. Sum-sum ta fice, ya nemi wuri ya zauna, yana tuhumar kansa meye ma na tambayar rumaisa. Tamkar mata, haka suka din ga shewa da Usman ya dawo, ta baje musu abincin da ta zo da shi, ta haɗu a cikinsu, suna ci. Idan da sabo, takawa ya riga ya saba, dan haka ba ya damuwa ma yanzu, ya riga ya fuskanci irin alaƙar da ke tsakanin su, shiyasa a rashin su, take sauke masa duk wani kwandon rashin ji da take yi musu. Sai ƙarfe goma suka bar gidan, suka tafi gida. *** "Jamila ina cikin damuwa, wai ni Jabir zai tunkara, ba tsoro ba kunya wai yana so in bashi dama ya auri ƴar da giwa ta tsinto iman?" Mummy ta ce "Ni na san wannan maganar tuni, ba wannan ne ya dameni ba, lamari ya fara jagulewa, na fuskanci kamar aikin malam na kan dutse ya fara sanyi" Cikin mamaki ta kalli Mummy ta ce "Kin sani fa ki ka ce? Amma baki gaya mini ba" "Ban zaci abun har zai kai haka ba, ban ɗauka da gaske zai yi maganar aure ba, amma na san ba wata matsala ba ce ba, zaki iya jajircewa a kan hana faruwar hakan". "Lallai ma jamila, ke kin fi kowa sanin, ba zan haɗa alaƙa da giwa ba, ya auri ƴar ta idan Allah ya sa ya samu sarauta, su mallake mini ɗa?" "Lubabatu naki fa mai sauƙi ne, nifa abubuwa sun fara sakwarkwacewa, dole a nemo sabon boka, duk da na bayar da aikin da aka bani na ƙarshen nan, amma dole na nemi abun yi, akwai matsala". Hajiya Lubabatu ta ce "Kin ga ni yanzu bana gane komai, sai anjima ma yi magana daga baya kawai" Mummy ta ce "Dole in motsa in sauya taku, ban taɓa samun matsala a abubuwan da nake ba sai a wannan karon, saboda zuwan wannan matsiyaciyar yarinyar, ƴar wannan abar daga zuwanta za ta hargitsa komai, Allah ya sa uwani ta yi abun da na sakata, yadda yakamata". Wayar Mummy ta fara ringing, ta duba taga baba Uwani ce, ta ɗaga ta ce "Ya aka yi?". Cikin kuka baba uwani ta ce "Ina cikin bala'i ranki ya daɗe, yarinyar nan wai ashe tana sane ta ce kina yi wa takawa asiri, dan ta gane idan ina kai miki maganar giwa, wallahi a sashinki ma akwai munafukinta, wallahi yarinyar nan ba yarinya ba ce aljana ce ranki ya daɗe, dan Allah kiyi wani abu a kai". A fusace Mummy ta ce 'Kuma ki ka samu ƙwarin gwiwar kirana ki gaya mini wannan shirmen? Yayi miki kyau, ki mayar da hankali ki yi mini aikin da na saka ki, na san matakin da zan ɗauka a kanki" "Na shiga uku, hajiya wani irin mataki?" Katse wayar Mummy ta yi, ta jefar a kan gado ta ce "Aikin banza" ** Kamar kullum takawa ya je gaida ammi, ya tarar da kaya a ɗakinta, har da ƙaramin keke na yara. Ya ce "Ammi, wannan kayan fa?" "Mahmud ne ya saya wa takwaransa" Har zai yi magana, da ya kalli fuskar ammi sai ya fasa. Ammi ta ce "Yauwwa, ban gaya maka wani abun arziki ba". "Wane abun arzikin?". "Ina ranar da jabir ya zo, muka fita ka ke tambayata fara'ar me nake yi?" Ya jinjina kai alamar ya tuna. "Wata magana ya zo mini da ita, da ta faranta mini rai" "Maganar me kenan?" "Cewa yayi ya na son Iman, kuma aurenta zai yi" Adam ya yi Jimmmm sannan ya ce "Yaushe kuma ya fara sonta?" Ammi ta ce "Ban sani ba, ya ce mini dai zai je ya lallaɓa hajiya Lubabatu, ba ka ji daɗin da na ji ba, idan ta amince ai na ji daɗi, tun da ɗan gida ne, kuma na yaba da shi, jabir ɗa ne a wurina" Adam jinjina kai kawai yayi, ya tashi ya ce "Bari na je wurin aiki, ina da idan na taso zan biyo, sai na dawo" Ammi ta ce "Allah ya tsare". Abun ya din ga damun Adam, baya son tonawa Jabir asiri, amma sam bai dace da auren Iman ba, salihar yarinya kamar wannan, duk da kashedi da gargaɗin da yayi masa, bai ji ba, bai kuma janye maganar son auren Iman ba. Ga wanccan batu da rumaisa ta ɗaukko masa a kan Jamil, gaba ɗaya sai abubuwan suka ƙara rikice masa. Sosai yake son saka pressure a kan Jamil, dan har yayi maganar da Bashir ma, sai dai gefe ɗaya yana tunanin anya haka zai yiwu kuwa? Kar ya ɓata zumuncinsu, tayaya Jamil zai saka hannu a ɓatan aisha, bayan babu wanda ya san ma ta zo ƙasar sai shi, kar ya biyewa shirirtar rumaisa ta rufta shi, amma duk da haka akwai ƙamshin gaskiya a maganganunta. Ƙarfe sha biyu ya kira sidi a waya, ya ce ya je ya ɗauki rumaisa, ya mayar da ita gida. Ƙarfe biyu ya tashi, daga wurin aiki, ya tafi wurin aikin su Jabir. Fuskar Jabir babu yabo babu fallasa, suka gaisa. "Jabir, zuwa na yi na ji dalilin da ya sanya ka je ka samu ammi, ka ce mata kana son iman, baya ka san yadda muka yi da kai?". "Tambayar da ka zo ka yi mini kenan Adam? Ka watsa komai kana neman ka ɓata zumunci, saboda kana auren wannan ƴar yarinyar, gaba ɗaya kanka ya juye, abun da ta ce kawai shi kake yi babu bincike? Ka je ka cewa Jamil yana da saka hannu a ɓatan matarka, ta yaya ƴar uwassa ce fa, ta yaya zai yi hakan? Ta ce Mummy tana yi maka asiri, magana ta koma kunnenta, ka je ka yi wa ƙannenka wulaƙanci dan su je gidanka duba ka, dan rashin ta ido, a gaban Mummy, yanzu kuma ka zo kana maganganu dan na ce zan auri Iman, kai ka san aurena da iman shine rufin asirinta, kuma ka sani Mummy sun kai ƙararka wurin mai girma wambai, dan yau da safe ya kira Ammi a waya, lallai yana nemanka, kuma zama za ayi na mussaman a kanka da matarka, dan da yiwuwar har gaban mai martaba, ba zai yiwu dan ka yi aure, ka hargitsa mana family ba. Duk da gaban takawa ya faɗi, amma cikin jarumta ya ce "Jabir, gaban mai martaba ba gaban Ubangiji bane ba, daga nan a kaini duk in da aka ga dama, shi ciki da gaskiya, wuƙa ba ta taɓa huda shi" ya fita ya bar office ɗin. Yanayin yadda ya zo ya wuceta a falo, ya sanya ta gane, akwai damuwa, har zata basar da shi, sai ta ji ba zata iya ba, ta bi bayansa. "Papa, yau ba cin abinci, ba magana, iya sanina ban yi wani laifi ba" Ya ɗan lumshe ido ya ce "Bakomai, ki je bacci zan yi". "Ba bacci ka ke ji ba, wani abu ne yake damunka",  ta yi maganar tana murza zoben hannunsa. A hankali ya buɗe idonsa ya kalleta. Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Bari na yi maka ta Yaya usy, ya ce gist me masoyiya ya ake ciki, to gist me aboki ya ake ciki?" Ita duk tsananin situation, ba ka rabata da wasa. Sai ya samu kansa da gaya mata halin da ake ciki. Ta kwashe da dariya ta ce "Ohh, ni ƴa su, yaro bai san wuta ba sai ya taka, to kar a fasa kaini wurin mai martaban mana, idan ban warware kowa a gabansa ba me nake, ni fa bana tsoron kowa sai Allah, kuma wallahi duk abun da na faɗa gaskiya na faɗa. Sai in faɗi komai a gaban mai martaban". Cikin rashin fahimta ya ce "Me zaki faɗa?" "Ba zan gaya maka ba, daga gaya maka abu a kan Jamil ka je ka gaya masa, dama na san zuciyarka ba zata bari ka danne ba, shiyasa bana gaya maka wasu abubuwan, sai ka ɓata mini aiki, ni bana ƙwaina sai da zakara, ka san wanda ya gaya wa Mummy na ce tana yi maka asiri?" Ya ce "A'a" "To baba uwani ce, kuma ina sane na faɗa, dan daga ita sai ammi da iman a wurin na faɗa, baba uwani na kwasar sirrin ammi, ta je ta gaya wa Mummy. Saura kuma ka faɗa so muke mu kama ta red handed, Daddy ya tabbatar mini da ya ganta sau biyu a sashin Mummy cikin dare". A sukwane ya tashi zaune, yana kallon rumaisa kamar ya ga abun tsoro, ya fara tsorata da lamarin rumaisa, kamar wata mai rauhanai. Ta tura baki ta ce "Meye kuma? Saura ka gayawa wani, idan ka faɗa ba zan sake gaya maka abu ba, yanzu in anjima mu je gida, ina son in ga Mummy, na tabattar maka da babu wanda zai wani kira ka ya tuhume ka". "Kin fara bani tsoro ne, don't make things complicated, tayaya za ki ce baba uwani tana cin amanar mu?" Rumaisa ta ce "Ai ban ce ka yarda ba dama, amma zan tabattar maka da hakan, yanzu dai zo mu ci abinci, mu yi wasan gudu a backyard, in anjima in je wurin Mummy". Ya ce "Am not in mood, je ki yi wasanki" "To buɗe mini wayarka na yi game" shiru yayi mata, ya tsunduma kogin tunani. Ta ɗau wayar, ta kama yatsansa ta buɗe, ta jingina da jikinsa tana dannawa. Shi muma ya bita da ido, kamar mai kallon abun al'ajabi. Ta gama danne-danne wayarta, ya ajiye masa ta tafi nata shagali. Sai dai da ta sauka ƙasa, ta tarar baba uwani bata nan, ta tambayi su Asiya, suka ce mata tun safe ta fita ba ta dawo ba. Ta tafi backyard, ta samu ball ta yi tayi, kamar ba matar ba sarake ba, ta window takawa yake hangota, yadda take sarrafa ball ɗin a ƙafarta ka san ƙanwar maza ce. Da la'asar bisa kasada, takawa ya ɗau ruma suka tafi gida, suna tafe yana sake tambayar ta, me za ta cewa Mummy, ita kuma taƙi faɗa masa. Ko da suka je, ya ce sai dai su shiga tare, ita kuma ta ce idan tare suka shiga, abun ba zai yiwu ba. A falo ta tarar da ruƙayya tana danna remote. Rumaisa cikin fara'a ta ce "Mummy tana nan ne?". Ruƙayya tayi tsaki ta ce "Wace Mummy?". "Jamila babarku" "Sunan Mummyn ki ke faɗa haka?" "Kin ji abun da na ji, ranar da ki ka faɗi sunan Ammi gatsal". Mummyn ce ta fito tana waya, tana ganin rumaisa ta yi turus. Ruma ta gaisheta, cike da duniyanci, ta yi murmushi ta ce "Amarya ba kya laifi, yau ke ce a sashina?" Ruma ta ce "Eh Mummy wurinki na zo". "To gani" Ruma ta ce "Sirri zamu yi" "Ba damuwa Bismillah" suka shiga wani ɗakin na daban. Ruma ta ce "Mummy, na ji kin kai ƙarar papa ne, shi ne na zo na baki haƙuri, dan Allah ki janye, kar ki saka ayi taron nan, ni nayi laifin ba shi ba". Mummy ta yi murmushi ta ce "Turo ki aka yi kenan? Gara na kai ƙararku ai, dan ban san laifin da na yi muku ba, kuma taro babu fashi, dole ku je ku wanke ni". "Mummy, tayaya zan san kina yi wa papa asiri, sharri aka yi mini, baba uwani ce fa ta gaya mini, kina yi wa papa asiri" A firgice ta ce "Baba uwani kuma?". "Ita, kuma ba ƙarya take yi ba, tun da na kamata da wannan ɗazu da safe" rumaisa ta yi maganar tana ɗagawa Mummy, wasu layoyi, da wasu irin abu a cikin leda. "Yanzu ko dai ki janye maganganun ki, ko kuma idan aka je gaban mai martabar, zan gaya masa komai, kuma mu ma muna da CID a sashinki, wadda take kawo mana rahoto. Abun da baku sani ba shi ne, na sanku tun kan na shigo cikinku, ina kuma sake maimaita muku, tunanin maza bakwai ne a cikin kaina, da kuma nawa na takwas. Mummy ina roƙonki, da ki jingine makaman nan, ki sassautawa mijina haka, wallahi a dalilinsa nima bani da kwanciyar hankali, muraran nake ganin abun da mutane ba sa gani a kansa, dan Allah ki bari ya huta haka. Ayshercool. Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Mummy ji tayi, tamkar an sanya mata dabaibayin ƙarfe an ɗaure mata ƙafafuwanta, ta kasa motsi, jikinta kuma yayi wani irin mugun sanyi, ta kasa motsa ko ina. Har rumaisa ta gama yi mata maganar, ba ta iya cewa uffan ba, mussaman ganin wannan layoyin a hannun rumaisa, kuma rumaisan ta ɓare fatar tsaf. A tsakiyar garden ɗin gidan, ta bawa baba uwani ta binne mata, shi ne cigaban aikin da ake yi mata a kan Adam, akwai irin layoyin a gidansu, akwai a gidan da ya zauna da aisha, wannan karon ma an yi ta saka a gidansa, saboda ana son ya din ga shige da fice a kai a kai, a in da layoyin suke. Kuma wannan laya ta bawa baba uwani jinin mage, da za ta din ga zubawa a ƙasar wurin sa'ai da lokaci. Da safe rumaisa na ta sauri, ta kammala abun da za ta yi kar ta makara, dan haka ana idar da sallar asuba ta hau ayyukanta, sai dai kanta ya din ga sara mata, ta din ga kamar wani sauti, daga bayan ɗakinta, kawai ta sauka ta zagaya, wanda a nan ta iske baba uwani, ta gama binnewa, ta jira ta bar wurin, ita kuma ta tone ba ta sani ba. "Ina sake roƙonki Mummy, mu rabu cikin mutunci da kwanciyar hankali, abun da aka yi a baya, Ubangiji Allah ya yafe, amma idan aka cigaba a haka zaku ji babu daɗi, na san ni yarinya ce a kan ku, da ku ke yi mini kallon mara hankali, amma zan iya abun da tunaninku bai taɓa kaiwa kai ba, kamar. Na kama baba uwani, kuma ta yi mini bayanin komai, wanda kafin in dawo daga makaranta ta bar gidanmu, amma kar ki damu, ban gayawa kowa ba, daga ni sai ita muka sani, idan kin so, sirrin zai zauna daga ni sai ke, idan kuma aka matsa mini, ki tambayi takawa yadda nake" ta mayar da ledar cikin hijjabinta, ta fita. Sai da ta fita sannan Mummy ta ji ta dawo hayyacinta. Jikin Mummy ya fara tsuma, tana zazzare ido, gaba ɗaya ta kasa tunani ma, neman wuri ta yi ta zauna daɓas a kan gado, wani irin gumi ya din ga tsatstsafo mata, har ta tsakanin cinyoyinta. "Lallai wannan uwani an yi ƴar........, ni zata tonawa asiri, mutuniyar banza da ta wofi?" Jiki na rawa ta janyo wayarta, ta kira baba uwani. Baba uwani ta fara koɗata, ta ce "Ke dalla saurara mini, ashe baki da hankali? Shi ne ki ka bari yarinyar nan ta kama ki, kina binne-binne a gidan?". "Ni kuma? Ai ba ta kamani ba, wallahi ba ta gani ba" "Ƙarya ki ke uwani, yanzu ta bar shashina, da ƙullin layoyin a hannunta, ni zaki munafunta? Ashe baki da mutunci? Tun yaushe na baki aikin, ki ka ajiye baki yi ba, har ta gani, kenan ma ke ki ka gaya mata ina yi wa Adam asiri". Kamar baba uwani ta saka kuka, ya ce "Wallahi, wallahi hajiya ba haka aka yi ba, ina iya ƙoƙarina dan Allah kiyi haƙuri". Kashe wayar mummy ta yi, tana fifita da hannunta, gaba ɗaya ta gigice. Ruƙayya ta shigo ɗakin, tana duban Mummy ta ce "Mummy ya aka yi ne, wai me ta ce miki?" "Bakomai, jeki hutawa zan yi" Ruƙayya ta ɗage kafaɗa ta fice. Rumaisa ba ta tarar da takawa a in da ta bar shi ba, dan haka ta wuce sashin Ammi. Ta tarar da shi a zaune a gaban ammi suna hira, sabir sai hawa yake wuyan takawa yana saukowa. "Ammi sannu da gida" Ammi ta ce "Yauwwa ƴar auta ta, ina ya baro mini ke ya shigo shikaɗai? Ai ban san tare ku ka zo ba" Ta zauna ta ja yatsan takawa da ƙarfi ta ce "Tafiya yayi ya barni". "Ke baki san da zafi bane" ruma ta harare shi ta ce "To waye ya ce ka tafi ka bar ni?" Ta mayar da idonta kan Ammi ta ce "Ammi ina Anty Iman ne?". Ammi ta ce "Kin san ta sarkin ɗaki, tana can ko tana bacci ko tana karatu". Rumaisa ta tashi ta nufi ɗakin Iman, Sabir ya biyota, ta tsaya ta ɗauke shi suka tafi tare. Ammi ta ce "Yaya ake ciki, ai yanzu rigimar ta ta da sauƙi ko? Kuna sabawa a hankali na ga ta rage daru sosai". Yayi murmushi ya ce "Ba zata sauya hali ba, kawai na koyi zama da ita ne kawai. She's simple at times wasu lokutan kuma ba a gane kanta" Ammi ta yi dariya ta ce "Tun da ka iya zama da ita ai Alhamdilillah, Allah ya ƙara haɗa kanku" Ya ce "Amin, sai dai Ammi akwai wani abu". "To, Allah ya sa ba matsala ba ce" "Ba matsala ba ce ba, ta ce zata gaya wa mummy abun da zai saka a fasa kirana wurin mai martaba, ban san me ta ce mata ba" Ammi ta ce "Wai yanzu daga can take?" Ya ce "Eh". "Takawa meyasa ka barta? Idan kuma ta je sake hargitsa lamuran fa?". "Ammi, am testing her thinking capacity, tama Sharp brain fiye da tunani, kuma na fara yadda da abun da ta gaya mini a kan Jamil, idan har tayi nasarar sanya Mummy, ta janye ƙarata data kai wurin su mai girma wambai, duk abubuwan da rumaisa take faɗa gaskiya ne". Ammi ta numfasa ta ce "Takawa, kaifin basirar yarinyar da tarbiyyarta, su ne suka saka na zaɓa maka ita, ni na san tana da kaifin tunani tun kan ku yi aure, tana da basira. Dan haka a ƙara haƙuri, ka bi komai a hankali, bari mu ga zuwa gobe in Allah ya kaimu zuwa kafin ka yi tafiyar nan, abun da hali zai yi" "To shikenan Ammi, in sha Allah". Ammi ta ce "Amma zan so sanin me za ta gaya wa Jamila, da har zai sanya ta janye abun da ta je ta faɗa". Takawa ya ce "Nima na so sani taƙi faɗa, kuma mun yi da ita ba zan gayawa kowa ba. Idan na cigaba da matsa mata ba zata faɗa ba". "To Ubangiji Allah ya iya mana, ya sanya ita ce sanadiyyar warwarewar matsalolin nan" "Amin Ammi". Ruma kuwa a kwance a ƙasa ta tarar da iman, a ɗan razane ta ƙarasa ta taɓa jikinta, ta ji yayi ɗumi. "Anty iman, lafiya ko baki da lafiya ne? Ciwon kan ne ya dawo?x ta jero mata tambayoyin. Iman ta tashi zaune, tare da yin yaƙe ta ce "Maman sabir, saukar yaushe?" "Ba wani saukar yaushe, baki da lafiya ne?". "A'a lafiyata ƙalau, kawai dai kwanciya nayi". Rumaisa ta zaune sosai ta ce "Ke da papa wasu lokutan halinku ɗaya ma, idan ba rashin lafiya ba, akwai damuwa fuskarki ta nuna, dan Allah anty iman menene, bana son in ga damuwa a fuskarki, gaba ɗaya raina ɓaci yake yi. Ko wani ne yayi miki wani abun? zan iya rama miki". Cikin dauriya, Iman ta ce "Maman sabir, bana son ɓacin ranki nima, kasancewarki a tare da ni, yana bani ƙwarin gwiwa. Zan gaya miki menene, amma dan Allah kar ki bari ammi ta sani, kin san bana son damuwarta". "Anty iman, duk surutun nan nawa, ina ɓoye sirri, gaya mini ko bani da maganin zan tayaki da addu'a". "Ammi ce ta ce mini, wai uncle J yayi mata maganar yana so na, wai zai je ya sanar da mai girma turaki, a zo a nema masa aurena, naga ammi tana murna, amma....." Sai kuma tayi shiru. Rumaisa ta ce "Amma ke ba kya son sa ko?" Iman ta zubawa rumaisa ido. "To wa ki ke so, dan ni ma bana son wannan jabir ɗin, babarsa ba ta da mutunci, wahalar da ke zata din ga yi" "Ba na son kowa maman sabir, bana son sake yin Soyayya, na barwa Allah lamarina, amma wallahi bana son jabir". "Kin tabattar babu wanda ki ke so, tuna dai" ruma ta yi maganar tana basarwa. Sai da gaban iman ya faɗi, tayi fatan, Allah ya sa ba ganota rumaisa ta yi ba. "Na tabattar bana son kowa ni yanzu" "Amma ya san ba kya son sa ya nace, kar ki damu ki yi ta addu'a, wannan masifaffiyar babar ta sa ma, ba bari za ta yi ba. Ko kina son wani a yayyena, amma su talakawa ne?" Iman kallon rumaisa take yi, tana son gano gaskiya, ko dai ruma ta gano ta ne. Ganin sun gaza haɗa ido, ya sanya ta ce "Kin manta nima talaka ce, ƴar fulanin tashi da aka tsinta a dokar daji, ai mutane masu asali kamar yayyenk......" "Iman bana son wannan maganar wallahi, raina ɓaci yake idan kina gayawa kanki haka" "Shikenan na daina". Ruma ta ce "Da dai yafi, yauwwa da muka je gida ranar, mai sunan baba ya tamabayeni kina ina? Na ce masa kina nan ƙalau" Murmushi ne ya bayyana a fuskar iman ta ce "Allah sarki yaya umar" ruma murmushi kawai tayi, dan tuni ta harbo jirginsu. "Kar ki damu anty iman, ba zan gayawa ammi ba kya son sa ba, amma in sha Allah ba za ki aure shi ba, dan nima haushin sa nake ji. Bari na je wurin papa" ta tashi ta koma falo, ta tarar ammi ta tashi. Ta je ta zauna a kusa da adam, ta yi ƙasa da murya ta ce "Done, na gama aiki, ka zuba ido ka gani". Adam ya ce "Amma baki gaya mini me ki ka ce mata ba". "Zan gaya maka, amma sai ta fasa ɗin tukuna" Ya ce "Shikenan, mu tafi ne, kin gama?" Ta ce "A'a sai da daddare" "Aliyu ya kirani, ya ce mini mama ta za ta yo miki aike, wannan yayan naki mara fara'a zai zo" Ruma ta ce "Da mai sunan baba ka ke ko?" "To waye mara fara'a idan ba shi ba" "Hmmm, ai kusan halinku ɗaya, ina kallonku fa ko magana ba kwa yi, kowa yana ji da kansa ko, zan gani dai " "Ke waye ya ce miki bama ma magana" Ta kai bakinta kunnensa, ta kare da hannunta ta ce "Ina kallon duk abun da ku ke yi fa, idan ku ga juna ku wani din ga basarwa, shiyasa duk na iya zama da ku, amma gara kai ka fi sauƙin kai wataran, kai baka sakani punishment kamar mai sunan baba, tsakar dare zai sani kneeldown idan na yi laifi fa". Dariya Adam yake, hannu ɗaya yana danna wayarsa. "Banbancinku, shi bai fiye magana ba, kai kuma idan ka ga dama, kana magana, wasu lokutan kana da wasa kamar yaya usy, jin kai kamar da son girma kamar yaya Aliyu, wataran sauƙin kai kamar yaya Abubakar, idan nayi wani laifin sai na zata zaka dakeni ne, amma sai na ga ka mini banza. Shiyasa wataran nake jin kunyar yi maka rashin kunya". "Ashe kina sane ki ke duk abun da ki ke mini". "Mama ta ce hali zanen dutse, ai ka ga bana tsokanarka sosai, kuma zuwa yanzu ba shiryu ba dan Allah, a makaranta fa ko ƙawaye bani da su, saboda kar a ɓata mini rai, a kawo maka ƙarata, bana son ka din ga ɓacin rai sosai, tausayinka nake ji" jiki a sanyaye ya ɗago ya kalli rumaisa, har cikin zuciyarta, take maganar. Ta cigaba da yi masa raɗa ta ce "Amma duk da haka fa, ban manta abun da ka yi mini ba, kuma zan rama". Jabir ne yayi sallama a falon, sai zuba ƙamshi yake. Ya ɗan tsaya yana kallon yadda rumaisa ta daddane kafaɗar Adam, ta dafa kafaɗarsa take yi masa raɗa, a tsakiyar falo ma'aikata na kaiwa suna komawa. Ya ƙaraso ba tare da rumaisa ta tashi ba, dan ba ta da niyya ma. "Takawa barka da yamma" Adam ya kalli Jabir ya ce "Barkanmu dai" Rumaisa ta yi saurin cewa "Papa zan ƙarasa maka idan mun je gida, bari na kira anty iman mu tafi, da daddare sai mu rako su gida ko papa?" Ta yi maganar kamar ƙaramar yarinya tana kallon fuskar sa. Ya ɗan ja hancinta ya ce "To mimi" ta tashi ta nufi ɗakin iman. Tana shiga ta ga iman na ɓoye wayarta, kasancewar hoton mai sunan baba take kallo. "Anty iman ta so mu je gidanmu, da daddare sai ku dawo" "Maman sabir kiyi haƙuri, gobe in Allah ya kaimu sai mu zo". "Mai sunan baba ne zai zo, yana son zai ga sabir idan ya zo, shiyasa na ce mu tafi tare, sai papa ya dawo da ku, kuma ga wancan jabir ɗin ya zo, idan kuma zaki zauna ne shikenan" Ba shiri iman ta tashi, ta shiga toilet, ta wanke fuskarta ta shirya a gurguje, suka fito tare har da Sabir. Jabir ya ƙare ta da ido. Ammi ta ce "Iman sai ina?" Adam ya ce "Da ita zamu tafi, anjima zamu dawo" Suka fita, Jabir ya biyo bayansu yana ƙwalawa iman kira. Adam ya waiwaya ya ce masa "Ya aka yi?" "Adam meyasa ka ke yi mini haka ne? Ka san wurinta fa na zo" "Ai ka san yadda muka yi da kai Jabir, tun da ku ka nuna mini iyakata da kai da Jamil, nima dole na tauna tsakuwa, aya ta ji tsoro. Ka fara nemo yardar mahaifiyarka tukuna, dan ba zaka auri iman ka ta wulaƙanta ba" Rumaisa kuwa tuni sun yi gaba, Adam ya biyo bayansu, suka tafi. Shiru Jabir ya yi ya tsaya yabi bayansu da kallo, ya jinjina kai tare da yin ƙwafa. *** Iman har ta ɗan wartsake, suka cigaba da sabgoginsu tare da ruma. Ta ce "Maman sabir, amma yaya umar zai ci abinci idan ya zo ko? Me za a dafa?" Ruma ta ce "To, nima dai ban sani ba, sai dai idan ki ka saka shi wataƙila ya ci" Gumm iman ta yi da bakinta, tare da gudun kar ta sake wata maganar da rumaisa za ta fahimci wani abu. Mai sunan baba bai tashi zuwa ba, sai bayan sallar magariba. Duk da ba sakin jiki zai yi ba, amma rumaisa ta yi murnar ganin sa sosai. Babban abun da ya saka shi farinciki, bai wuce ganin iman ba, sai dai kallo ɗaya yayi mata ya san tana cikin damuwa. Cikin sanyin halinta ta ce "Yaya Umar sannu da zuwa, ya mama?". "Alhamdilillah" ya bata amsa, a ganinsa yayi ƙoƙari ya amsa mata a sake, ba tare da sanin amsar ta sa ta taƙaice da yawa ba. Ya kalli rumaisa ya ce "Ga saƙonki nan, na je katsina shekaranjiya, gwaggo ta bani kaya na kawo miki iya ma haka, zaku yi waya da mama". Ruma ta kalli kayan a manyan ledar viva, ta ce "Amma na gode sosai da sosai, amma mai sunan baba ba yanzu zaka tafi ba ko?". "Me zan zauna na yi miki?" Yayi maganar yana ƙoƙarin tashi. Iman ta miƙe ta ce "Na ga kamar ni nake hana shi sakewa, maman sabir, bari in kira sidi a waya kawai, tun da takawa bai dawo ba". Umar ya ƙure ta da ido, da sai da ta kusa rasa nutsuwarta, duk da da mayafin abaya a kanta, wuyanta sai da ya fito, kuma ya nuna ramar da tayi. "Na taɓa cewa zuwanki yana hanani zama? Gidan yayanki ne, ni kuma ƙanwata me zan zauna na yi mata?" Iman ta girgiza kai alamar a'a. "Mai sunan baba, har gida na taho da ita, ina murna ta tayani muka yi girki,  kuma ka ce zaka tafi ba zamu ji daɗi ba, dan Allah ka zauna ka ci" "In zauna in ci abinci a gidanki, Allah ya kiyaye" yayi maganar yana kallon agogon hannunsa. Ruma ta ce "To bari na baka ka kaiwa mama" "Saboda ni ɗan aikenki ne?" Iman ma ta saka baki "Dan Allah yaya umar, ko ba yawa ka ci" ta faɗa a ɗan raunane. Ji yayi idan har bai ci ba ta ji ba daɗi, babu lallai ya iya yafewa kansa. Ya kalli rumaisa ya ce "Spoon biyu kawai". Iman ta miƙe da sauri, ya ce "Ba ke ba ita" Yayi maganar yana kallon rumaisa. Ruma ta tashi a zuciyarta tana cewa son kai. A zahiri wasa yake da sabir, amma a ɓoye iman yake kallo, yana jin ina ma ta zama mallakin sa, ace kullum gata yana kallonta. "Ina Mahmud" yayi mata maganar ba tare da tayi tsammanni ba. "Yana gida" ta bashi amsa duk da ba ta ɗago ba, dan ta san da ita yake. "Bai koma school ba kenan?" Iman ta ce "Eh, ina ga ya gama ai" Bai kuma ce mata komai ba, Ya cigaba da wasa da Sabir, kamar ba shi ba. Ruma ta dawo da kwano a hannunta, ta ajiye a gabansa, alkubus da miyar taushe, favorite food ɗin mai sunan baba. "Zuba na tafi da shi kawai" Rumaisa kamar ta fasa ihu, mai sunan baba akwai wulaƙanci, ba yadda ta ita, ta kwashi kwanukan, ta sake komawa kitchen, ta sake bashi damar kaɗaicewa da iman. Ya samu ya kalleta sosai yadda yake so, sannan ya yi musu sallama ya tafi. Ita kanta iman tana cikin farinciki, atleast sun yi doguwar magana da shi yau. Tafiyarsa babu daɗewa, takawa ya kira iman, ya ce su fito ya mayar da su gida. A kayan da mai sunan baba ya kawo wa rumaisa, har da uban fura da nono, kaya guda da su mazarƙwaila, sai addu'oi a rubuce, da wasu saiwoyi da ba ta san ko na menene ba. Ga su ƙuli da man ja da fari, kayan kuka da kuɓewa har da su wake abun ka da mutanen karkara. Haka ta keta kayan biyu, ta ce wa Iman ta kaiwa Ammi. A lokacin da Adam ya dawo daga kai su iman gida, ya tarar tuni ruma ta yi bacci. Ya ci abincinsa, da ya tarar a kan dining, dan yanzu idan ba makaranta ta tafi ba, shine su barira suke dafo abinci. Ya leƙa ɗakinta, ya tarar tana kwance a ɗakinta da kayan baccinta, ɗan mini skirt, da riga vest, ga jigidar da ke ƙugunta tayi mata cif. Ya taka ya ƙarasa ya tsaya a kanta, amma baccinta kawai take yi, ya zauna a kusa da ita, ya zubawa ƙafafuwanta ido, daga ƙasa dai ga ta da hips, amma sama kam, yanzu ne ma dai suka ɗan tasa. Murmushi yayi da ya tuna wasiƙar da ta aika masa, da ya yi ta yi wa Allah godiya babu wanda ya ga takardar ya karanta. Ya kai hannunsa kan jigidar, yana ɗan ja a hankali, yana zancen zuci, abu kamar wasa ya koma shafa cinyoyinta. Duk da nauyin baccinta, caraf ta riƙe hannunsa, ta buɗe ido "Meye haka?" Ko a jikinsa ya ce "A ina?" "Papa bana so" tayi maganar tana tura baki. "Ni ina so ai" yayi maganar yana janyota ya haɗata da jikinsa yana kallon idonta. Mutsu-mutsu take tana hararsa za ta ƙwace, amma ya saka hannunsa ya ɗaya ya ɗago haɓarta ya ce "Can we try it now?" Tayi masa ƙuri da ido tana kallonsa. "Are you ready for it? I want kiss you mimi". Girgiza masa kai ta yi ta ce "Dan Allah bana so" tayi maganar idonta na cikowa da hawaye. Bai kuma ce mata uffan ba, yayi abun da rumaisa ko da wasan wasa, ba ta taɓa kawo hakan ba. Kissing ɗin ta yake yi sannu a hankali. Ta rirriƙe jikinta, tare da jin abun wani banbarakwai a duniyar ta, abun da aka ginata a kan cewa abu ne da bai kamata ba, yau ta tsinci kanta dumu-dumu a cikin sa. Ba ta tsinke da lamarin ba, sai da ta ji Adam yana ƙoƙarin yin wani abu daban da ya tayar mata da hankali. Ihu ta din ga yi, tana riƙe rigarta, har da kiran su baba uwani su zo su rabata da Adam, zai yi mata abun da bai dace ba. Ba ihun rumaisa ne ya tayar masa da hankali ba, illa jin sa da yake yi kamar ba shi ba, kamar an canza shi. 'Me hakan yake nufi?' ya tambayi kansa a ɗan tsorace. Jikinsa ne yayi sanyi sosai da sosai, ga rumaisa a hannunsa na ta ƙoƙarin ƙwacewa. Kwantar da kanta yayi a ƙirjinsa, ya ɗora kansa a nata, a ransa yana maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace irin masifa ce kuma wannan ya sake tsintar kansa a ciki? Yana jin yadda rumaisa ke ta zubar da hawaye, tana alwashin sai ta gaya wa kowa na duniyar nan, ya saka mata hannu a riga. "Yi mini shiru, ni ki ke yi wa wannan ihun ko?". "To waye ya ce ka yi mini abun da ka yi mini, bayan ni a gidanmu an ce mini ba kyau. Wasan banza fa kenan, kuma saboda a daina ce mini ƴar iska na ƙara yadda muka yi aure". Halin da yake ciki bai hana shi yin murmushi ba, ya ce "Duk wani mai aure ɗan iska ne ai, wannan sirrinmu ne, ba a faɗa" Rumaisa ta tashi zaune ta ce "Sai na faɗa, kuma kowa na duniyar nan, duk wanda na sani sai na gaya masa" "Idan ki ka faɗa, cewa zan yi ke ki ka ce ayi, gara ma ki yi shiru". Share hawaye take ta ce "Wallahi ni ba ƴar iska ba ce, bani na ce ayi ba". Takawa ya ce "Oho dai, idan ki ka faɗa abun da zan ce kenan, yarinya ki adana hawayenki ma, ba yanzu yakamata ki yi kuka ba. Sai an zo making baby" Ba ta gane me yake nufi ba, ta cigaba da kuka. "Gobe in Allah ya kaimu zan fara shirin tafiya, in dai Mummy ta janye maganar ta, ina son zuwa wurin mai girma turaki ma" "Kai ta tafiya, ni ba sake shiga harkar zan yi ba, kuma sai na tambayi mama, in dai duk mai aure kallon ɗan iska ake yi masa, sai na koma gida" "To ki tambayo, idan kin tambayo sai ki bani amsa. Banda tsiwa ina abun yake, meye a rigar da ki ke mini wannan bankaɗar, da kururwar, abun da bai fi murfin jarkar faro ba" Banza tayi masa tana sake kawar da kanta gefe. Ya tashi tsaye, ya bar ɗakin. Duk son baccin rumaisa sai ɓarawo ne ya ɗauketa, tana jin tsoron ta rufe ƙofa, kuma tana tsoron takawa ya sake dawowa. Adam kuwa hankalinsa a tashe ya koma ɗakinsa yana safa da marwa, yana tunanin wa zai tunkara da wannan matsalar, matsala ce ba ƙarama ba, da take buƙatar ya samu mafita, kan rumaisa ta gama fahimtar menene aure, kar ya cutar da ita. Iman kuwa bayan ta koma gida, ammi kallonta kawai take tana son nazartar ta, za ta fita, ta ganta a damuwa, ta dawo ta ganta cikin annashuwa, ba tare da ta san menene ya sanya ta cikin farin cikin ba. Sai da ta je kwanciya sannan ta janyo wayarta, ta shiga what's app, cikin fargaba ta turawa mai sunan baba saƙo "Yaya umar ya ka je gida?" Kallon message ɗin ya din ga yi, yana shafa kan message ɗin amma yaƙi reply. Kusan mintuna talatin, tana ganinsa online, amma bai reply ba. Tunani tayi meyasa ma ta tura saƙon, sai ta yi sauri ta goge. Ta na gogewa ya yi replying da 'Me ki ka goge?' "Bakomai" ta bashi amsa. "Send it again" Tsuru-tsuru tayi kamar tana gabansa, sannan ta sake rubuta masa ya ka je gida. "Wayata yakamata ki kira, idan kin damu ki ji ya na je" Ta yi masa replying da "Yi haƙuri" "Kin yi laifi ne ki ke bayar da haƙuri?" "A'a na ga kamar ka ji haushi ne" "Ba haka nake ba, masifaffe kamar yadda waccan yarinyar take baki labari ba". Iman ta ce "Eyya ba haka ta ce mini ba wallahi" "Umar ba masifafe bane, na dawo lafiya ƙalau, na gode sosai" tashi zaune iman ta yi tana yarfe hannu cikin murna. Offline mai sunan baba shi ma yayi, ya na murmushin da bai san dalilinsa ba. Yau juma'a akwai makaranta, amma ruma ta ƙi shiryawa, ta sha baccinta. Takawa ma bai takura mata ba, bai ce sai ta je ba. Sai sha ƙarfe goma na safe, sannan runaisa ta fito, ta shiga kitchen ta haɗa abinci ta dawo falo ta zauna. Ta zauna ba jimawa, sai ga shi ya shigo, ashe ma ba ya gidan ba ta sani ba. Ta wani sake tsuke fuska, ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita ya ce "Ba gaisuwa yau?" Ta matsa daga kusa da shi. Ya sake matsawa ya ce "Mun yi faɗa ne?". "Gaskiya papa bana so, Allah ka taɓa ni sai na yi ihu da ƙarfi" "Me zan taɓa?" Yayi maganar yana kallon ta. "Oho ai ka san me kayi mini". "Ba wannan ba, tun da yau kin ƙi zuwa makaranta, zan je na ɗan yi bacci ne, an jima zaki tayani haɗa kaya, gobe in Allah ya kaimu zan tafi" Da sauri ta ce "Haba dai?" "Ba kya so na tafi ne? Ai gara na tafi, na je na yi aure, tun da ihu ki ke yi mini. And turaki ya ce mini Mummy ta samu mai girma wambai ya ce magana ta wuce, Weldon little Mimi, aikinki yayi kyau" Kallo ta bi shi da shi, har ya shiga ɗakinsa. Ta kalmashe ta kunna Tv, tana kallo, ta ji sallamar wata mata, wani irin ƙamshi ya daki hancinta. Ta ɗaga kai ta kalli matar, matar fara sol kamar ka taɓa jini ya fito, wata ƴat gayu, ta sha baƙin glass, da English wears. Ta nemi wuri ta zauna, ta kalli rumaisa ta ce "Hey, ina mutanen gidan?" Rumaisa ta kalleta, tare da jinjina rainin wayo irin na matar,  ta ce "Mutan gida kamar wa kenan?". Matar ta ce "Matar gidan, da kuma takawa" Cikin rainin hankali ruma ta ce "Matar gida ni ce, takawa kuma is not available" Ayshercool. 08081012143 Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Matar da mamaki take kallon ruma, "I don't get you, he is not available like how?". Maimakon rumaisa ta amsa, sai ta sake kashingiɗa ta ce "Elizabeth ma ta ci ubanta, haka ta gama turancin ta mutu". Cikin isa matar ta cire gilashin fuskarta ta ce "Kin san wacece ni kuwa?". "Ina ruwana da ke wacece? Ko da ban san ki ba, na san ba zai wuce kema a danginsu ki ke ba, masu zuwa su ci mini mutunci, ni kuwa dai-dai nake da kowa, wallahi duk wanda ya zageni ramawa zan yi ehe". "To yanzu zagin ki na yi?" "Ai na san tatsuniyar gizo, ba ta wuce ƙoƙi, kun saba zuwa ku yi mini wulaƙanci, na sani ko kema abun da ya kawo ki kenan, daga shigowarki sai kallon banza ki ke yi mini, kuma dan raini ki ke tambayata wai ina matar gidan. To ban sani ba ko nayi kama da ƴar shara da wanke-wanke" Matar ta riƙe haɓa, sannan ta jinjina kai ta ce "Anyway, na ji kece matar gida, kuma ban zo na ci mutuncin ki ba, i want see ma brother please" Rumaisa ta ce "Ban iya turanci ba" "Ohh ikon Allah, ina son zan ga ɗan uwana ne, wurinsa na zo". "To bacci yake yi, idan zaki jira shi to, bai daɗe da kwanciya ba, amma ina fatan ke ba ƴar uwar wannan samhan ba ce ba?" Matar ta yi murmushi ta ce "No, am not" ta saka hannu a jakarta, ta ciro waya, cikin harshen Ingilishi take magana, da accent ɗin da rumaisa ba ta iya fahimta, ta ajiye wayar. Bai fi mintuna takwas ba, sai ga takawa ya fito. Da sauri matar ta miƙe, ta nufe shi, kamar zasu rungume juna, suka yi musabaha, ta sumbaci hannunsa ta ce "Takawarka lafiya ranka ya daɗe, gaba salamun baya salamun" Adam yayi murmushi ya ce "Ke dan Allah yaushe ki ka sauka? Kuma da safen nan na je gidan mai girma turaki, na ji kasala nake ji, ban ƙarasa gidan ba, kuma jiya fa har 5pm muna gidan. "Around 11 na ne gida, na cewa ammi kar ta gaya maka, yau na ce ammi ta saka a kawoni, na zo na ganka na ga amarya, and i met this little arrogant creature, screaming at me that why should I ask for you. She even claims that she's your wife, but i doubt  she is the one in the pictures. She looks innocent and matured in picture". Takawa yayi dariya ya ce "She's the one, rumaisa kenan maman sabir". Jiki a sanyaye ta ce "Adam, na ga yaron fulani, so cute, yaron kyakykyawa da shi". Rumaisa da ba ta kula su ba, ta ce "Tubarkallah". Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ruma ya ce "Mimi, ga Anty Laila, cousin sister ɗina, da muka tashi tare, kuma uwar ɗakina. Tana aure a canada da mijinta da yaranta". "Au ai ban santa ba, kuma da ta zo ba ta gaya mini ita ce ba, na zata kawai ƴan uwanku ne masu zuwa gida, su yi mini wulaƙanci, shiyasa ban kulata ba". "To ai ba duka ƴan uwan mu ne, masu yi miki wulaƙancin ba, ku gaisa mana". "To ita kuma ya ake gaisheta, kar in yi ba dai-dai ba ta ƙi amsawa, ba zan sake gaisheta ba" Yayi murmushi ya ce "Ita wannan baturiya ce ai, kowace irin gaisuwa ki ka yi mata zata amsa". Rumaia ta sake kallon laila sannan ta yi murmushi ta ce "Sannu da zuwa, ina wuni? Ya hanya ya iyali, sannu da zuwa" Ta ce "Yauwwa thank you" Ta tashi tsaye ta je ta kawowa laila ruwa da lemo, ta kawo mata kayan shayi ta ajiye, ta haɗo da cornflakes duk ta ajiye mata. Laila ta ce "Ya zan yi da duk wannan kayan, kar ki takura kanki, na ƙoshi ni". "A'a kar ki je ki ce, kin zo gidana ba a baki abinci ba. Na san lokacin breakfast ya wuce, amma dai ki sha shayi, ko cornflakes, akwai fruit ma, yanzu zan je na ɗora girki". Laila ta ce "Girki kuma? Ba naga akwai maids ba, na ga baba uwani ma na nan, kar ki ciwo a kitchen fa". Rumaisa ta ce "Ai da yake a unguwar ɗorayi nake, na iya duk wani girki da yakamata, ni ba ƴar masu kuɗi ba ce, kar ki damu da yarinta ta, na iya abinci gidanmu ba ƴar aiki". Adam ya ƙunshe fuska yana dariya, rumaisa kuma ta nufi kitchen, tayi ƙasa da murya ta ce "Yenyenyen, ta wani shaƙe murya tana turanci, har da saka wando, babba da ita wai ita baturiya, Elizabeth ma ta gama saka wandon da mini skirt, aka haɗa da ita da turancin aka binneta". Laila kuwa ruma na barin falon ta ce "Bros yanzu da gaske this is your wife?" "Yeah, ta canza miki ne, ita ce dai ki ka gani a hoto". Laila ta ce "Taɓɗijan, amma ba ta da kunya, a tsaye take, amma tayi ƙarama takawa". "Haba dai, yanzu ai ta ciko, ta yi ƙiba, rigima kam akwai ta har da ta sayarwa ma, sai dai duk da haka bamu fi wata ɗaya ba, na fara jin daɗin zama da ita. She's very intelligent, fiye da yadda ki ke zato, wauta da ƙuruciya ne dai damuwarta". Nan ya bata labarin yadda rumaisa ta dawo da sabir, da yadda aka yi har ya aure ta, zuwa yanzu da suke tare, da abubuwan da take ta hasaka masa, a zamansu. Laila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Well, amma ba ta da kunya gaskiya, a haka ku ke zaune?". Ya ce "Ya ki ke zagar mini mata ne, zaki shiga sahun Black list ɗin mu fa". "Am serious matarka ba ta da kunya takawa" Sai ya tuna abun da ya faru jiya, ya ce "Kin san family ɗin mu sai a hankali, gida suka zo suke yi mata rashin mutunci, ta rama. Kin san ƙanwar maza ce ba tsoro. Haka nan muke lallaɓawa muke tare, ake rainonta kan Allah ya sa ta gama hankali, ko me za ta yi, ta cancanci ayi mata uzuri, kuma in kula da ita, abun da ta yi mini, ko duniya na bata ban biyata ba" "Haka ne, amma ban gane ake lallaɓawa ake rainonta ba, haka ku ke zaune kana kallonta tana kallonka" Yayi dariya ya ce "Ina ruwanki ne?" "Babu, amma tun a hotonta nayi mamakin yadda ka auri ƙaramar yarinya haka, na sam baka da ra'ayin auren ƙaramar yarinya, na san plan ɗin ammi ne, ban da haka wannan guda nawa take? Me ta sani?" "Ai fa, in dai ɓangaren zamantakewar aure ne, ba ta san komai ba, sai kaifin basirar sanya ido da gane mara gaskiya, shiyasa na yi mata registration na islamiyya matan aure, ta ce dai ba zata ba, ita yara zan sakata, ba zata shiga cikin matan aure su rainata ba, wannan kuma da ammi zan bar ta, dan sun fi kusa" Laila ta ce "Well, tun da ba tare zaku tafi ba, ka bar ta a hannuna, zaka ga canjin kafin ka dawo in sha Allah". Ya dubi laila ya ce "Like how kenan?". "Kai ina ruwanka, tun da tafiya zaka yi, ta zo mu zauna a gidan ammi tare, she needs to learn so many things, ko kuma you are taking another wife ne, wannan tayi ƙwaila da yawa". "Allah ya sa ta ji ki na ce mata ƙwaila, zaku yi faɗa da ita sosai, nikaɗai ne idan na faɗa take ƙyaleni, ni ɗin ma sai da tayi mini abun da na daɗe ina jin kunyar kallon ammi, ta gaya mata wai na ce zan ƙara aure saboda bata da nono" Rufe baki laila ta yi tana dariya, ta ce "Lallai wannan yarinyar ɗanya ce sharaf, ka bar ta a hannuna kawai". Hira suka cigaba da yi, ya din ga bata labarin abubuwan da suka din ga faruwa, tun bayan komwarta canada daga hutun ƙarshe da ta zo. Laila ta sha mamakin ganin yadda rumaisa ta kawo mata abinci da ta girka, komai nata tsaf, hatta falonta a gyare yake, dan har ƙamshin turaren wuta yake, a tunaninta ko masu aiki ne suka yi mata, sai da adam ya ce mata ita take abun ta. "Mimi ina nawa abincin?" Adam yayi maganar yana kallon ta. "Au, dama zaka ci? Ya ƙare saura ƙanzo, ko in dafa maka taliya da manja da yaji" Yayi murmushi ya ce "zan kama ki ne, da ke da taliyar. Rumaisa ta koma ɗakinta, ta bar musu falon, wanka ta yi, ta fito da nufin ta shirya, ta ga takawa a ɗakin nata. Ta ɗan tsuke fuska ta ce "Ya na ganka kuma, ina baƙuwar?". "Haka ake yi, kin yi baƙuwa kin tafi kin bar ta?". "To ba wurinka ta zo ba, ko zuwa zan yi na saka ku a gaba ina kallon bakin ku?". "To, yanzu dai ba wannan ba, dan ta tafi ma, taho mu yi magana". Rumaisa ta ce "Taɓ, kaya zan saka, ka je idan na kammala shiryawa, zan zo" Ya janyo hannunta ya zaunar da ita a kan gadon, ya ce "Yanzu zamu yi, baki da isasshen lokacin cigaba da ganina. Idan na tafi gida zaki koma wurin ammi, zuwa lokacin da zan dawo, lokaci-lokaci kuma, zaki iya zuwa gida, shima sai kin nemi iznina tukuna" Jiki a sanyaye ta ce "To meyasa ba zan koma gidanmu ba, ni fa ba zaman gidanku ne bana so ba, wannan ƴan rainin hankalin ƴan uwan naka ne ba zan juri wulaƙancinsu ba" "Rumaisa kin iya cewa bani da haƙuri, ke haƙurin ne da ke? Babu ruwanki da su, gobe in Allah ya kaimu da azahar zamu tafi, idan na kammala wakilicin mai martaba, zan wuce in da zan yi course ɗina na watanni shida. Dan Allah ki nutsu ki zauna lafiya da kowa, ban da rigima, ga Anty Laila nan, zata kula da ke tana da kirki sosai". "Wannan ɗin ce mai kirki, bayan daga zuwan ta ta fara gaya mini magana, dan dai kawai ka ce yayarka ce". "Dai-dai take da ke ai, idan ki ka yi mata rashin kunya, ta san yadda za ta yi da ke" "To yanzu idan ka tafi, wa zai cigaba da aikin binciken da kake yi?". Ya ce "Ga Bashir nan, akwai group ɗin mu da duk tare muke yin ayyukanmu, ki sanya ni a cikin addu'ar ki mimi, matsaloli sun yi mini yawa". Rumaisa ta ce "Allah yana tare da bayinsa masu tawwakali da haƙuri. Allah yana tare da mu papa, zan din ga yi maka in sha Allah" "Thank you dear" yayi maganar tare da sumbatar hannunta. Tayi dariya ta ce "Kai, sai ka ce abun indiyawa, kiss a hannu" "To muyi a baki?" Da sauri ta saka hannu ta rufe bakinta, ta tashi. Murmushi yayi ya tashi ya bar ɗakin. A ranar takawa ya je ya yi wa mama sallama, ya sanar da ita batun zai bar ruma, a wurin ammi. Cikin kara mama ta nuna bakomai, tare da yi masa fatan alkhairi, sai dai bayan tafiyarsa ƴan mazan mama, duka din ga mitar, dan me ba zata dawo gida ba, za ta tafi gidan sirikai ta zauna, kamar mara gata. Ruma ba ta ɗauki tafiyar takawa serious ba, sai da ta ga da gaske yana haɗa akwatinsa a daren yau. Tana tsaye ya ce ta miƙo masa wannan, ta ɗaukko masa wancan. "Papa, ya batun anty iman ne, ba wani abu da zaka yi a kai kan ka tafi? Kar wannan jabir ɗin ya aureta fa". "To ke ina ruwanki?" Yayi maganar yana duba wani turare. "Da ruwana mana, ni fa na bana son jabir ɗin nan". "Ita ta ce miki ba ta son sa ne? Kin fiye damuwa, ko so ki ke in tayata mu bijirewa ammi?" Rumaisa ta ce "Wallahi ba ta son sa, taɓ gaba ɗaya kalar munafukai ne jabir ɗin nan, da gani yana aikata wani laifi a ɓoye da Allah yake rufa masa asiri. Ko dan halin babarsa ma dole ya zama shaiɗani". Ƙurii yayi da ido, yana kallon rumaisa, zuwa yanzu ya daina mamakin abubuwan da take faɗa da aikatawa, dan idan ta faɗa, ko ɗari-bisa ɗari bai zama dai-dai ba, kashi saba'in dai-dai ne. "To, haka ta ce miki, kin san ba zamu zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba, mu cigaba da yi mata Addu'a, idan shi ne alkhairi...... "A'a ba alkhairi bane ba ma, kuma ba zata aure shi ba" ta katse shi. "Tun da kece waliyyinta ko? Wai ke kin fi ni son ta ne? Kin ƙwace mini ɗa, kin ƙwace mini ammi, kuma ƙanwartawa ma da nake ji da ita, kin ƙwace ta, haka ake rayuwa ne?" Rumaisa ta ce "Eh ɗin, tana da wanda take so yake son ta, amma ba wani jabir" Takawa ya ce "To wa take so? Dan bani da labari" "Ban gayawa kowa ba dai, saura ka faɗa kaima, mai sunan baba take so, kuma yana sonta shima" Da sauri takawa ya ɗago ya ce "What?! Umar ɗin gidanku?" "Eh mana". "Amma iman ba ta da da hankali, ina ita ina wannan yayan naki?". Rumaisa ta haɗe rai ta ce "Saboda talaka ne ko?". Shi ma ya ɗan tsuke fuska ya ce "Bana son bahaguwar fassara. Amma kin san halinsa dai sai dai ki gayawa wani, iman kuma is very simple and cool, ta yaya?" Rumaisa ta ce"Ta yadda aka yi ka aureni, kai ba ruwanka, sai dai idan saboda talaka ne ba zaku ba shi ba, yaya umar bai taɓa damuwa da halin da wani yake ciki ba, ko zai shekara dubu bai ga mutum ba, in dai ba mama ba ce ko ni, ba ruwansa, amma zuwan da muka yi ya ce mini ina ƙanwar mijinki, to dan Allah ba soyayya ba ce haka? Ai kai dai ka san soyyaya ko, ka san ya ake ji?". Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ke baki santa ba?" "Ina na sani, ni fa sau ɗaya wani ya taɓa cewa yana sona, su yaya Aliyu suka ce, idan suka ƙara ganinsa, sai sun zane shi. To sam ban san ya soyayyar take ba, in ta so in ga ina zance". Ya kwashe da dariya, rumaisa ba ta rabo da wauta. "Ni ba daga zuwa zance, ki ka haɗa kayan zancen ki ka cinye ba, ki ka faɗo jikina, ki ka sani neman kalaman kariya. To yanzu tun da baki taɓa saurayi ba, zan zama saurayinki, mu gani, idan na tafi sai mu din ga waya, irin na saurayi da budurwa". "Eh ayi haka, Allah ya sa na ji ya soyayya take, in din ga yi maka waƙoƙin soyayya, irin na Indiya" Dungure mata kai adam yayi yana dariya, ya ce you won't kill me. "Papa ni fa da, mai sunan baba wani tsoho zai aura mini a unguwar mu, malam ladan, mutumin nan ya taɓa zaneni da carbi, wai daga na tambayi mama wani abu, wai sai yayi mini aure, ya sai mini tabarma da buta. Wai ko a aura mini wani Ɗan ladi mai kan sirdi, kansa kamar plate, ka ga baƙinsa Astagfirullah, tsoro yake bani, gashi ɗan ƙarami, shi ba wada ba gashi nan dai, wata ƴar ajinmu ta ce wai saɓo yayi Allah ya mayar da shi biri, da ya tuba, sai ya koma haka" Takawa zai iya cewa rabonsa da dariya irin ta yau, tun kan aisha ta tafi Saudiyya, dan ruma labarai ta din ga bashi irin na ta'asar da ta din ga tafkawa. A haka ya gama haɗa kayan, kusan tun da ya aureta bai taɓa bata cikakken lokaci kamar wannan ba. Ita abun da yayi mata daɗi a ranta kawai shi take aiwatarwa a rayuwarta. Ya kammala haɗa akwatinsa, ya ajiyeta. Ya ce "To budurwata, na gode da gudunmawa, sai Allah ya kaimu da safe, zamu je na yi wa ammi sallama, daga nan mu je gidan mai girma turaki sai mu tafi". Ta ɗan yi shiru jiki babu ƙwari ta ce "Papa nan da wata shida, har ayi azumi da salla, kana can ko?" Ya ce "In sha Allah". "To wa zai din ga baka abinci, da shayin dare?". "Saya zan din ga yi". Ta gyaɗa kai ta ce "To shikenan, sai da safe". "Allah ya tashe mu lafiya, ki kashe mini fitila" har ta kashe fitilar, ya ji kamar tana kuka. "Mimi" ya kirata. "Na'am" "Zo nan". Ta koma gaban gadon ta ce "Gani". Ya tashi zaune, ya zaunar da ita a kan cinyarsa ya taɓa fuskarta ya ji hawaye. "Meyasa ki ke kuka?". Cike da rashin wayo ta ce "Dan Allah idan ka je, kar ka yi aure, bana son kishiya, kuma bana son ka tafi". Kawai ya kwashe da dariya ya ce "Ai fa dole nayi aure, tun da ni dai ba saƙago ne kamar ke ba. Ga rashin kunya da ki ke yi mini, daga taɓaki sai ihu da kururwa, ina sai dai ki yi haƙuri ". "Amma dai ka san abun da ka yi mini bai dace ba ko? Ba kyau fa" "To ai ba wanda zai gane, idan ba wannan maganannen bakin naki ne, zaki je ki faɗa ba" Cikin damuwa ta ce "To idan ina yadda, ba zaka auri kowa ba, har da wannan samhar?". Ya ce "Eh mana". Ta ce "Taɓ! Wallahi na san Allah ya na kallona, kuma zai ƙonani, mama ta ce in din ga jin tsoron Allah a duk in da nake, idan ba ta ganina Allah yana kallona, kuma idan na lalace ban yi mata adalci ba. Ka yi auren ni dai ba zan iya ba, amma ban da samhar nan, dan na tsaneta" sosai hawaye yake kwarara a fuskar rumaisa, zai iya cewa tun da suka yi aure, duk bala'in da zai faru, sai dai tayi ta wulƙita ido, tana harare-harare, amma ƙarara weakness ɗim ta ya bayyana yau. Kwantar da ita yayi a gefensa, sannan ya kwanta yana shafa kan ta ya ce "Let's make a memorable day, mu kwana tare. Amma dai zan yi shawara tun da kin ce ba kya son kishiya, idan kin canza halinki kin daina rashin ji, sai a fasa idan baki canza ba, samha zan auro. Ita ba zata din ga yi mini ihu ba, tun da tana so na". Shiru ta yi masa, tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta, to ta din ga yadda saboda ba ta san ya ƙara aure. Amma da ta tuna, idan yayi aure haka zai din ga wasa da samha, ita ma ya din ga kaita makaranta, su din ga zuwa cin abinci tare, ita ma ya din ga rungumeta kamar haka yana yi mata dariya, su din ga ball tare wataran kamar yadda suke yi. A ranta ta ce bana son kishiya, amma ba zan ci amanar mama ba. Bacci ne yayi awon gaba da ita, ba tare da ta gama tunanin ba. Adam kuwa ya rungumeta sosai yana shafa gashin ta. "Am going to miss you mimi, am feeling like am leaving my priceless asset in Nigeria. A lokacin da mutane suke yi miki kallon mara kunya, wadda ba ta ji. Ni a lokacin nake hangowa amfanin ki, a cikin al'umma, kin zo da babbar fitila mai haska hanya a cikin rayuwata, duk da kina bani wahala, am still owing you a debt" ya ƙarasa maganar a hankali tamkar tana jin sa, ya sumbaci goshin ta. Addu'a ya cigaba da yi, na Allah ya bashi lafiya, kafin ya dawo, dan wannan wani babban sirri ne mai nauyin da yake jin, ba zai iya sanarwa da wani shi ba. Ya sake ƙanƙameta, yana tuna farkon haɗuwarsu, da abubuwan da ta yi masa zuwa yanzu. Da safe tare suka karya, sai dai ta ƙi sakin jiki ta ci, sai kallonsa da take yi, tayi masa zuruuu da ido. "Kalli gabanki, zan ƙware". "Ni ba kallonka nake yi ba, gara ka tafi in huta, a daina takura mini" "To mutumin da zai je yayi sabon aure fill, cikakkiyar mace ya rabu da ƙwaila, sai me dan ƙwaila ta ce ba ruwanta da shi?" Ta haɗe rai ta ce "Ba ruwanka da ƙirjina, ka daina ce mini ƙwaila, kuma in sha Allah sai sun fito mini" Ya sakata a gaba ya din ga dariya, ita kuma ta haɗe rai tana tura baki. Bayan sun gama, da ita ta fito masa da akwatinsa, daga baya ta ce ba za ta ɗauka ba, tun da yake ce mata ƙwaila. A ƙasa ya ce wa su baba uwani, idan ya tafi, zasu tattara su koma can gida gaba ɗaya, ba zai bar rumaisa a gida ita kaɗai ba. Ƙarfe tara na safe, suka isa gidan ammi, ana ta yi wa takawa fatan alkhairi, abun mamaki sai ga Mummy ma a sashin Ammi, wai ta zo yi wa takawa Allah ya tsare, tun da bai je yi mata sallama ba. Tana yi tana satar kallon ruma, ita kuwa ruma ba ta tata take yi ba, abun da ya dameta daban. A gidan adam ya sauya kayansa zuwa shigar sarauta, ba kunya rumaisa ta ce "Masha Allah, saurayina ka yi kyau" Yayi murmushi ya miƙa mata hannu ya ce "Ban mu kashe" ta bashi nata suka tafa. Su Fauziyya da basu saba ganin taɓarar da rumaisa take yi, ko a gaban waye ba in dai suna tare da takawa, suka din ga ƙananan maganganu. Laila kuwa kallon su kawai take yi, tana observing ɗin rumaisa. Harabar gidan suka fito, hannunta na cikin na takawa, in da wasu za su raka adam gidan turaki. Sai dai ya ga Mahmud riƙe da mukulli a tsaye a jikin motar da za a ja shi a ciki, nan aka tsaya kallon kallo. Rumaisa a hankali ta ce "Papa" ya kalleta. Tayi ƙasa da murya ta ce "Dan Allah kar ka watsa mini ƙasa a ido, na yi iya ƙoƙari, kan a kawo wannan mataki, dan Allah kar ka watsa mini ƙasa a ido, ko dan ammi ta ji daɗi, sau ɗaya ta ganku tare, shi ya yarda ya ja ka a mota, dan Allah papa Please, kar ka yi wani abu da zaka sa maƙiya su ji daɗi" Kallonta yake yadda take yi masa magiya, Mummy kuwa kanta yayi bala'in ɗaurewa, ta tsaya ta ga ikon Allah, kawai ta ga takawa ya ja rumaisa sun shiga motar, Mahmud ya karɓi sabir, ya saka shi a gaban motar, ya shiga ya kunna. Motar da ammi suka hau ita da laila, kuka ammi take, tana "Laila, kin ga Mahmud da Adam tare a wuri ɗaya, Allah na gode maka, Allah ka ƙara haɗa mini kan iyalina". Laila ta ce "Is ok my dear ma, ai dama na sha gaya miki, addu'a da ki ke yi, Allah yana karɓa, lokaci ne kawai". Rumaisa a mota kuwa, sai aikin rarrashi takawa yake yi, ta kalleshi ta ce "Papa, na gode da baka watsa mini ƙasa a ido ba, daddy na gode sosai da sosai, da ka kasance cikin masu yi wa papa rakiya, ammi za ta ji daɗi sosai " Mahmud ya ce "Daughter, ba abun da ba zan iya yi miki ba, ba sai kin gode ba". Ruma ta ce "To ba zaku yi magana ba? Ku gaisa" Fuskar Adam ta kalla, yadda ya haɗe rai, ta ɗan girgiza kai ta ce "Papa, na ajiye maka saƙo a akwatinka, duk abun da ka gani, idan ka je, kar sake ka tambayeni komai a kai, kuma kar ka saka wani ya tambaye ni, har sai Allah ya dawo da kai lafiya". Ya ce "Menene abun?" "Idan ka je zaka gani" Shiru ya ɗan yi yana tunani, a dai-dai lokacin da suka shiga gidan turaki, ana ta bushe-bushe, turaki yana daf da fitowa. Takawa ya saukko daga motar, bai iya tsayawa gaisawa da kowa ba, duk da ga su jabir da Jamil, da sauran manyan mutane, sai ƙoƙarin rarrashin rumaisa da yake yi a gaban mutane. Kuka take yi sosai, yayi ƙasa da murya ya ce "Ki na so ni ma na yi kuka ne?" Ta girgiza masa kai. "Haba budurwata, a haka zamu rabu? Saurayi da budurwa fa ba haka suke yi ba, ki daina kuka, zamu din ga waya, Allah ya tsare mini ku, ya kula da ku". Su Fauziyya tuni suka dira a gidan, suka wuce wurin Samha, suna bata labarin, abubuwan da suka faru a tsakanin ruma da takawa yau, wanda hakan ba ƙaramin jefata ya yi cikin matsanancin tashin hankali yayi ba, baba uwani ta yaudareta, da ba ta sanar da ita alaƙar da ke tsakanin takawa da ruma tayi ƙarfi haka ba. Ta window ta hango takawa yana sharewa rumaisa hawaye, ya danƙa hannunta cikin na laila, ya nufi Mahmud da yake tsaye da Sabir a hannunsa, ya shafa kan sabir yayi masa kiss a goshi, ya nufi wata motar. Da sauri Samha ta koma ɗakinta, ƙafarta har rawa take saboda tashin hankali, ta kira baba uwani a waya, ta rufe ta da bala'i. Baaba uwani da ta rasa in da zata saka kanta, saboda ta ko ina, matsi da kyara take fuskanta ta ce "Ba laifina bane ba fa, Hajiya Jamila ce ta ce kar na sake sanar da ke komai, sai abun da ta yi mini izini". "What? Mummyn? Ni za ta ci amana!? Kuma ta rufe ni ba ta gaya mini ba?" Sakin wayar ta yi tare da yin ashar. "Lallai matar nan baki san wuta ba, kuma kin takata a yanzu, zan yi maganinki, da ni ki ke zancen". Mummy ma na can ƙarshen kiɗima ta shigeta, ganin Mahmud da kansa, ya ja adam a mota, lallai tsuguno ba ta ƙare ba. Ayshercool. 08081012143f Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Rumaisa na nan tsaye tana kuka, tawagar ta tashi, suka yi gaba. Ammi sai rarrashin rumaisa take yi, laila ta ce "Wai ke ba kya jin kunya ne, wa ki ka fi iya soyayya, soyayyar da ko iya ta baki yi ba, ko Kunyar ammi ba kya ji". Ammi ta ce "Babu ruwanki, mu ba ma wata kunyar sirikai". Su Jamil suka ƙaraso, suka gaida Ammi, sai dai ammi ba ta san, meke faruwa ta takawa da su Jamil ba, dan haka normally ta amsa musu, kamar yadda suka saba. Jabir ya dubi iman ya ce "Iman ko zaki zo in mayar da ke a mota ta?" Ammi ta ce "Kar ka damu, kwa haɗu a gida, laila mu shiga ciki mu gaisa da mutanen gidan, tun da matafiya sun tafi" Suka shiga wurin mama, sai wani cika take tana batsewa, sai dai duk da haka, ta shiga taitayinta ganin ammi tare da laila, dan kar ta san kar. Ta dubi laila ta ce "Ashe kin zo garin?" Cikin taƙama laila ta ce "Yeah, almost 2days" "Yayi sannu da zuwa, wannan kamar matar takawa ko? Meya sameta take kuka?". Laila ta ce "Abun mata da miji sai Allah, ga yarinta a kan ta, dole tayi kuka". Mama ta ce "Mhmmm Allah sarki Aisha, har ta kai adam ya manta da ita, ya cigaba da rayuwarsa?" Laila sarai ta gane magana matar turaki take nema, dan haka ta ce "Aka rasa iyaye ma a dangana, a cigaba da rayuwa ayi musu addu'a, rasuwar fulani ai mu aka yi wa, kuma babu yadda za ayi mu manta da ita, kuma takawa yana nan yana aiki tuƙuru a kan neman hakkinta. Kuma dan ya rasata baya nufin ba zai sake farinciki a rayuwarsa, da ya rasa soyayyar mahaifi ma bai mutu ba, dan haka dan Allah a daina kawo wannan maganar" Laila ta miƙe ta ce "Ammi mu tafi" Babu wanda ya kuma magana har suka fice. Zee da tana falon aka yi komai a gabanta, shiru ta yi, dan kaɗan da aikin laila ka yi mata rashin kunya, ta kwaɗeka, saboda masifarta. Takawa suna airport, ya kira iman, ya ce ta haɗa shi da rumaisa, ta miƙawa ruma wayar, sai dai ta yi shiru. "Hello, mimi" "Na'am" "Ki yi mini Addu'a, nan da mintuna talatin jirginmu zai tashi" "To Allah ya kai ku lafiya" "Amma dai kin daina kukan ko?" Murya can ƙasa ta ce "Na daina" "Yauwwa buruwar mijinta, da kun koma gida, ki samu ki ɗan yi bacci, jiya bamu samu isasshen bacci ba. Sannan a gida akwai key ɗin wardrobe ɗina, na bar miki kuɗi a ciki, sannan zan din ga turawa laila kuɗi ko zaki buƙaci wani abun". Ruma ta ce "To" daga haka ta bawa iman wayarta. Su Fauziyya kuwa bayan sun gama kai wa samha rahoto, silalewa suka yi, suka bar gidan, suka bar ta da tension. Zee ta tarar da Samha a zaune, abun duniya ya isheta, tamkar ta ɗora hannu a ka, ta fasa ihu saboda baƙin ciki, dan me Mummy za ta ce kar baba uwani ta din ga gaya mata abubuwa da suke faruwa a gidan Adam, sai wanda ta bayar da umarni?. "Samha!" Zainab ta kira sunanta a karo na uku. Samha ta ɗaga kai ta kalleta, "Sai magana nake kin yi shiru". Ɗan guntun tsaki ta ja ta ce "Menene?" "Labari ne mara daɗi bayan wanda su Fauziyya suka gaya miki. Laila ta dawo, sannan alamu sun nuna cewa yarinyar nan zaman lafiya suke yi da mijinta, kin ga zancen su Fauziyya ya tabatta". Samha ta ce "Babar su Fauziyya ce banbar munafuka, wato hajiya jamila" Cikin mamaki ta ce "Uwar ɗakin naki?" "Zainab saboda tsabar matar nan ta mayar da ni ƴar iska, mun bawa wannan uwanin aikin, kawo rahoto a kan abubuwan da suke faruwa a gidan adam, ni burina auren adam, ita kuma hana shi sarauta. Ni yayi sarauta ko kar ya yi bai dameni ba, ni shi nake so. Meye haɗin aikinta da nawa, da za ta ce wa baba uwan wai kar ta din ga kawo mini bayanin abin da yake faruwa sai wanda ta yi mata umarni, ni zata mayar shashasha, na shanya baki na san na yi aiki tuƙuru a kansu, amma na yi sakacin da har shaƙuwa ta shiga tsakaninsu. To bari a gama watsewa, na je har gida na sameta". "Ki sameta ki yi mata me ne? Ke kin san idan ki ka ce zaki yi fito na fito da ita, tafi ƙarfinki. Babarki ce a hatsabibanci, ki cigaba da abubuwan ki ba tare da ta sani ba, ki bita a haka, kar kuma sauya mata fuska". "Ba zan iya jurewa bane zee, kawai ji nake idan ban zageta ba zan huce ba". "Aikuwa ya zama dole ki danne, ko ta yi miki wani mummunan sharrin". Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Zainab na wuce yadda ki ke tunani, tun da ta ɓata nawa aikin, sai dai mu yi biyu babu, kuma son Adam yanzu na fara, sai na ga ƙwal uwar daka". Rumaisa kuwa wuni tayi baccin dole, saboda koke-koken da tayi, kanta ya fara ciwo, dan haka tayi ta kwanciya tana bacci, surutun ma ya gagareta, ba ta taɓa zaton akwai wani abu da zai tsaya mata ya hanata walwala ba. *** Mummy kuwa ta titsiye Mahmud a ɗaki, ta na tayi masa bala'i a ka, kamar ta ari baki, saboda tsan-tsar ɓacin rai da damuwa. "Kai yanzu Mahmud dan Allah ba ka ji kunyar abun da ka aikata ba, matar da ba ƙaunarka take yi ba, ta fifita ƴaƴanta a kan ka, kai ka san ba ƙaunarmu suke yi ba, daga ita har ɗanta, amma dan abun kunya, kana jiran sarauta yana jira, dan me zaka tuƙa shi a mota, direbansa ne kai, ko saboda rashin sanin ciwon kan ka ne? Ko kuma dan ka nuna mini iyakata, ka nuna mini bani na haifeka ba?" Yayi mata shiru yaƙi magana, hakan ya ƙara tunzurata, ta dungure masa kai da ƙarfi, amma cikin baƙin taurin kai, ko gezau bai yi ba. Sai da ta zuciya ta yi hanyar fita, sannan ta tsinkayo muryarsa ya ce "Tambayar da rumaisa ta yi mini, ta jefa ni cikin damuwa, da taradaddin neman amsar, sai dai ban sani ba ko zaki tayani samo amsar?" Cak ta tsaya, ta waiwayo tana kallonsa. Bai ɗago ba ya cigaba da cewa, bayan buɗar idona a hannunki, kin ginani a kan cewa, a duniya bani da babban maƙiyin da ya wuce giwa da kuma ɗan uwana Adam. Na ginu a kan haka, a lokacin da na san gaskiyar wacece mahaifiyata kuma, sai ki ka nuna mini bata sona ne, ta zaɓi waɗancan ƴaƴan nata a kaina, shiyasa ke ki ka karɓeni ki ka riƙeni, kuma kin ce baki da wani buri da ya wuce na gaji kujerar babanmu, marigayi galadima. Na hau kan tarbiyarki da hanyar da ki ka ɗorani a kai, na sawa zuciyata tabbas mahaifiyata ba ta ƙaunata. Sai dai ko da rumaisa ta tambaye ni sau ɗaya me giwa ta taɓa yi mini, a zahiri da ya nuna bata ƙaunata? Sai kunya ta rufeni, a lokacin da na tuna kin yi mini shamaki da zuwa in da take, kuma kin koyar da ni ƙiyayyar ɗan uwana, ƙiyayyar da ta yi tasiri a tsakanin mu. A lokacin da rumaisa ta tunatar da ni, na sanya mahaifiyata kuka a lokacin da ta nemi alfarmata, ƙarƙashin umarninki, na ƙi yi mata, sai na ji a duniya bani da wani amfani. Mummy ba ina nufin juya miki baya ba, bani da wata a duniya bayan ke, amma giwa na da hakkin haihuwata da ta yi, ba zan taɓa bari ki muzanta ba, sai dai ina fatan ganin tabattacen haɗin kai a cikin gidanmu, auro rumaisa cikin iyalinmu alkhairi ne mummy. Ban aikata hakan dan muzanta miki ba". Ya ƙarasa maganar cikin rauni. Kuka Mummy take tamkar ta aminta da abun da ya faɗa, sa dai ƙasan zuciyarta cike yake da baƙin ciki da takaici, tare da aniyar sake ɗaura ɗambar, kawo ƙarshen giwa, da adam har da wannan annamimiyar ƴar tayin da ke barazana ga harƙalarta. *** Wajen ƙarfe biyar na yamma, rumaisa na zaune zuruuu kamar mara lafiya, shi kansa sabir ba shi da karsashi, ya zo Jikinta ya kwanta, yayi shiru shi ma ko wasa baya yi. Iman ta ce "Haba Anty rumaisa, takawa zai dawo, tafiya ba mutuwa ba ce, wannan damuwar ta yi yawa ai" Iman ta ce "Hmm ba zaki gane ba, ni fa ban taɓa zaton zan damu ba, nayi-nayi kar ka damu na manta, amma na kasa". "To ba ga waya ba, idan ya kira sai ku din ga video call". Rumaisa ta ce "Ni duk ba wannan ne ya dameni ba" Iman za ta sake magana, Nusaiba ta yi sallama. Suka amsa mata, ta dubi iman ta ce "Amaryar uncle, his royal highness jabir, is waiting for you". Iman kamar ta saka kuka ta ce "In yi masa me?" "Iman me yake damunki ne? Ban gane ki yi masa me ba? Ki je ki ji mana" A daƙile ta ce "To, zan je" Nusaiba ta juya ta fita. Rumaisa ta ce "Kar ki damu, in sha Allah babu abun da zai faru sai ikon Allah, wannan masifaffiyar babar ta sa ma, na san ba zata bari ba". Rumaisa na cikin maganar, laila ta shigo, ta kalli iman ta ce "Iman, jabir fa yana jira" ta ƙarasa maganar tare da zama a kusa da rumaisa, ruma tana satar kallon fatar laila, kamar jikin tarwaɗa, gashi ko kunya ba ta ji, take tsukewa a cikin ƙananan kaya. Iman kamar ta zubar da hawaye, haka ta tashi ta bar ɗakin. Laila ta kalli ruma ta ce "Kina ji na ko?" Rumaisa ta ji kamar ta ce mata 'Da ni kurma ce?" Amma a zahiri ta ce "Eh" "Tun da yau mijinki ya tafi, dama ya bar sallahun kai ki makarantar matan aure, gobe in Allah ya kaimu za a fara kai ki, daga nan zaki kwaso kayanki na gidanki ki dawo nan. Ni na karɓi ragamar kula masa da ke kafin ya dawo, dan haka dole zaki din ga bin duk abun da na saka ki, bana son gardama ko rashin kunya, dan idan rashin kunya ce, sai dai ki koya a wurina. Idan kin dawo daga makaranta, zan din ga yi lesson da kaina, da kuma dabarun zaman aure. Abu na gaba, zamu din ga gyaran jiki, naga kina da tsabta, kuma kin iya girki ma, amma dole zamu din ga shiga kitchen tare ki koyi wasu abubuwan. Wannan fatar taki, so nake ta murje ta fi haka haske da kyau". "Taɓ wallahi ba zan bleaching ba". "Ni ma ba bleaching na ce ki yi ba, gyara za ayi, wannan gashin ma, ya ce ba kya son kitso, dole ya din ga shan gyara, ga iman nan, ita zata ja ragamar koya miki makeup" "Ni gaskiya idan na yi wannan damɓare-damɓaren, fuskata ƙaiƙayi take yi, duk in ji ta ɗaure kamar ta tsohuwa". Laila ta ce "To kar ki yi mana, kanki zaki yi wa, iyaka ya kawo wata matar mu shige masa gaba yayi wani auren, kuma dole ki koyi magana, ki daina yaɓawa mutane magana son ranki" "Na iya magana, kawai sai an yi mini ba dai-dai ba, nake yaɓa maganar". "Ke! Baki san komai ba game da rayuwa, shi kansa mijin naki, yadda ki ke yi masa magana, tun da ba sa'anki ba ne, ba haka ya dace ki din ga magana da shi ba, idan kin shirya zaman auren, sai ki bi instructions ɗin da zan din ga baki. Abu na gaba dole ki ga maman Khadija". Ruma ta yi ƙuri da ido tana kallon laila, wacecec kuma maman Khadija. Kamar laila ta shiga ran rumaisa ta ce "Na san baki santa ba, amma zaki santa yanzu. Wannan ƙwailar da yake ce miki, a kankaro ki, kema ki shiga cikin sahun manyan mata". Cikin zaƙuwa ruma ta ce "To ita maman khadijan me zata yi mini?" Dan a yanzu tana fatan su fito, a baya ne take zaton nono bashi da wani amfani a gareta, sai idan ta haihu za ta shayar, amma yadda ake gaya mata kalmar ƙwaila, yana ƙona mata rai. Laila ta ɗora da cewa "Garin kunun sabayarta zan yi miki order, ki din ga amfani da shi kafin ya dawo, dan ni idan na saya, Canada ake tura mini shi, yana da daɗi, zai gyara miki fata da jikinki baki ɗaya, kuma ki ciko ki murmure sosai, idan kuma kin shirya cigaba da zama ana yi miki gori shikenan". Ruma ta tuna iskancin da su Fauziyya suka din ga yi mata, wai a kalli ƙirjinta kamar plate, ga samha cikakkiyar mace, amma takawa ya aureta, ta gyara zama ta ce "To ita maman khadijan a ina take? Kuma yaushe zaki sai mini kokon nata". Laila ta ce "Ni ban ce miki koko take sayarwa ba, garin kunun sabaya take sayarwa, amma ba a kano take ba, a zariya take, bayan federal palladan. Na daɗe ina harka da ita, kuma na haɗa mutane da ita sosai, na san ingancin kayanta. Zan yi waya da ita, a sayo, tunda tana tura kayanta ko ina, amma ba zan baki ba, sai na ga gwargwadon biyayyarki" Rumaisa ta yi shiru tana kallonta, laila ta gama bayananta, rumaisa ba wani fahimta tayi ba, ita dai babban fatanta, a samo abun da laila ta faɗa na yin kunu, saboda ta sha ko ya fito ta huta gori. (*INA UWAR GIDA DA AMARE, INA WANDA SUKA HAIHU, KO SUKA YI YAYE, INA MASU RAMA DA SU KE SON JIKINSU YA MURMURE SU YI ƘIBA, INA MASU YARA WANDA SUKE FAMA DA MATSALAR RASHIN GIRMA? SHIN KEMA MIJI NA YI MIKI GORI, KAMAR YADDA TAKAWA YAKE YI WA RUMAISA? SHIN KINA KUNYAR SHIGA CIKIN ƳAN UWANKI MATA, SABODA RASHIN NONO, KO KUWA ƊINKI NE BA YA ZANA A JIKINKI, SAI KIN HAƊA DA CIKO? RAMA CE TAYI MIKI YAWA, KO KUWA YAYE YA SANYA NONONKI YA ZUBE KAMAR BANA MACE BA. TO ALBISHIRINKU! KUKANKU YA ƘARE, HAKA ZALIKA KAKARKU TA YANKE SAƘA. MAMAN KHADIJAH TA SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYE, DA INGANTACCEN GARIN KUNUN SABAYARTA. BAYA CUTAR DA LAFIYA KO KAƊAN, ZAI GYARA MUKU JIKI, YA CIKO DA NONO, INA WANDA SUKA YI YAYE, KO SUKE SHIRIN YI, KU JARRABA WANNAN GARIN KUNU, ZAKU BAYAR DA LABARI, MAMAN KHADIJAH NA NAN A GARIN ZARIYA, BAYAN FEDERAL PALLADAN, KO KU TUNTUƁETA KAI TSAYE TA LAMBAR WAYARTA 08033411249* Iman kuwa a sitting room ta iske jabir, ya wani hakimce yana danna wayarsa, tun da ta shigo ya kafeta da ido, kamar yadda ya saba. Ta nemi wuri ta zauna, tayi masa sbiru. "Wai dan Allah iman me na yi miki ne? Meyasa ki ka tsane ni haka?" Cikin mamaki ta ɗaga kai tana kallonsa, ganin yadda yake neman ya raina mata wayo, ya fi kowa sanin abun da ya sanya, ba ta yin sa, amma yake ta wani basarwa. "Ke shikenan abu ba ya wucewa a wurinki ne?. Son ki nake yi da gaske, aurenki zan yi, magana ta riga ta yi nisa, na samu amincewar ammi, takawa kuma kan ya dawo ma wataƙila an riga an yi". "Amincewata da ta mahaifiyarka ba ta da muhimmanci kenan?". Yayi murmushi ya ce "Amincewar hajiya wani abu ne daban, ke kuma a kowane lokaci idan mun yi aure komai zai wuce, dan Allah ki daina taurin kai, ke kanki kin san ba ki da wani rufin asiri, da ya wuce amincewa aurena, idan ba haka ba, duk wanda suka zo a baya sun tafi, sun kasa ɗaukar kasada. Ni a nawa ganin zaɓe-zaɓe ba naki bane ba iman, kamata yayi ki gode mini, da na ce ni na ji na gani" "Ko ba ka yi ɓoye-ɓoye ba, na san ni ba kowa bace ba, abun da ka ke son gaya mini kenan, amma kasancewata ba kowa ba, ba shi yake nufin zuciyata ba ta da ƴancin ta so ko ta ƙi wani abun ba, ina girmamaka a matsayin yayana, idan farincikin ammi in aureka shikenan, amma ni babu soyayya a raina". Jabir ya ce "Haka ne, ammi ta yi iya ƙoƙarin ta a kanki, har keta billenta ta yi, ta nemi alfarmar ɗan ta ya aureki, amma ya ƙi hakan, dan yana ƙyamarki, na cancanci ki gode mini ne iman, ba ki ƙi ni ba a halin yanzu ba ki da zaɓi, aure shi ne mafitarki, idan ba haka ba kuwa wannan kyawun barazana ne a gareki" Sannu a hankali jabir yake gasa mata munanan maganganu, amma ta yi iya ƙoƙarin ta, ta din ga haɗiyarsu, duk da yadda take ji, suna barazana ga zuciyarta. Jin bugun zuciyarta ya fara ƙaruwa, kuma numfashinta ya fara sama-sama, ya sanya ta tashi ta koma ɗakinta. Rumaisa na ta jin daɗi, tare da fatan, Allah ya sa laila da gaske take, za ta sai mata abun nan, Iman ta shigo, sai dai ba sai an gaya mata ba, ta san iman ɗin a cikin damuwa take. Rumaisa ta yi shiru ba ta ce mata komai ba, ita ma ba ta ce mata ba, ta je kawai ta kwanta a kan gadonta. Mintuna talatin ammi ta shigo, tana faɗin "Iman, ya ku ka yi da jabir ne, ba kya bani update?" Ta tarar da iman a kwance, kamar mai bacci. Ammi ta ce "Iman ƴan kwanankin nan baccin nan ya fara yawa, duk in da ki ka samu sai bacci? Rumaisa ko ta gaya miki wani abu ne?". Ruma ta ce "A'a ba ta ce mini komai ba". Ammi ta ce "To shikenan" Da daddare rumaisa ta ce A ɗakin iman za ta kwana, duk da ammi ta bata ɗaki, amma ta ce a wurin iman za ta kwana. Cikin dare iman ta tashi ta yi salloli, sannan ta zauna ta ɗauki wayarta tana dubawa, rumaisa na kallonta, a haka bacci ya kwasheta. Da safe rumaisa na baccin safe, laila ta shigo da system a hannunta, ta tashi rumaisa. Ruma ta buɗe ido ta kalleta, "Kin manta hau zaki fara zuwa islamiyya ne? Tashi mijinki zai yi magana da ke" Rumaisa ta kalleta ta ce "Da computer zan yi wayar?" Laila ta dungurarwa da ruma computer a gabanta, tana kalla ta ga fuskar takawa. Ta ce "Laaa video call a computer" Yayi murmushi ya ce "Hi little mimi". "Iyee daga zuwa turai har ka koma bature, irin...." Sai kuma ta kalli laila ta yi shiru. Yayi murmushi ya ce "Ba ki tashi ba ne? Yau zaki fara zuwa islamiyya fa, ki tashi kiyi breakfast, ki shirya a kai ki" Ruma ta yi miƙa ta ce "Shikenan weekends ma ba zan huta ba". "Ki yi haƙuri, ina boy, bai tashi ba ko?" "Eh, bacci yake shi da anty iman, kai har ka karya? Waye ya dafa muku abinci?" "Har ɗaki aka kawo mana, na karya" "To yaushe zaku fara taron?" "Sai Allah ya kaimu anjima" ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Mimi meyasa ki ka bani abun da zai sakani kuka?" Jiki a sanyaye ta ce "Ba dan kayi kuka na baka ba, ni ba dare ba rana, abun ci mini rai yake, amma ba na ce maka kar ka tambayeni komai a kai ba, sai anjima, bari na ɗan ƙara rage bacci". "Mimi tsaya ki ji". "A'a gaskiya sai anjima" ta ture system ɗin ta kwanta. Laila ta daki ƙafar ruma ta ce "Ke wace irin mashirirciya ce ne?" Ruma ta yamutsa fuska ta kalli ruman. "Ya tafi wata ƙasar, kuna waya ki kashe? Babu wani abu mai jan hankali, ba rausaya murya ba karairaya, wai ce miki aka yi dan kika ƙanwar maza, ki din ga abu kamar namiji, you are not romantic at all, mijinki matashi ne, kuma kema kin san yana da masu son sa, ko dai ki gyara ko ki ga abun da ba kya so. Ki tashi ki yi wanka ki zo ki karya" Ta ɗau system ɗin ta, ta bar ɗakin, rumaisa ta zumɓura baki sannan ta tashi. Laila kuwa komawa tayi, tana jinjinawa takawa. "Takawa i salute your effort, Wannan matar taka, zan iya saka bulala in zaneta wataran, she's very stubborn, beside she's much more than how i expect, ba ta ji ga taurin kan tsiya". Adam ya ce "Haba madam, duk ita kaɗai, ki yi ta haƙuri kema, halinku ne ya zo ɗaya shiyasa ba kwa jituwa, da ɗaya daga cikin ku na da haƙuri, zaku zauna lafiya, idan ku ka saba shikenan". "Anya zan iya jurewa? Ba ta ji fa" "Tuba muke, ayi haƙuri dai". Rumaisa ta shirya cikin dogon hijjabi, hatta jakar islamiyya da litattafai adam ya sai mata komai, sidi ya ɗauke ta suka tafi makarantar. Ya je ya gabatar da ita, mai makarantar ta ce ta san da zuwan rumaisa, aka kai ruma aji. Mamki ne ya cika su kansu ƴan ajin, ganinta sanye da hijjabi irin na islamiyyar, suna mamakin kar dai matar aure ce. Mai makarantar ta gabatar da rumaisa a wurin malamar da take ajin, zungu-zungui ta wuce ta je ta zauna, tana jin haushin kallon da suke yi mata. Ajin duk manyan mata ne, dan da yawa sun haifeta, wasu kuma sun yi ƙanwa da ita sosai da sosai. Aka yi lesson ɗin da za ayi a ka gama, har lokacin tashi ba ta kula kowa ba, sai da aka tashi suka din ga tambayarta ko matar aure ce ita, sai dai ta din ga bin su da ido, taƙi magana. Sidi ya zo ya ɗauketa, amma ta ce masa ita ɗorayi zai kai ta wurin mama, ya ce ai ammi ba ta sani ba, ruma ta ce ba ruwansa, idan ba zai kaita ba, ya ajiyeta ta je ta hau napep. Haka ya juya kan motar suka tafi ɗorayi. A ƙofar gidan yara suka tsatstsaya suna kallon uwar motar da aka kawota a ciki, har da maƙwabciyarsu shamsiyya a leƙowa, tana ɗagowa ruma hannu. Ruma ta ce 'Lallai matar nan, saboda ta ganni a mota, har da ɗago mini hannu, nan gaba a daidaita sahu zan din ga zuwa, in ga ko za samu masu kulani'. Ta kalli sidi ta ce "Ba sai ka dawo ɗaukata ba, zamu yi waya da uncle Mahmud" ta shige cikin gida, bakinta ɗauke da sallama. Gidan shiru, sai Aliyu da yake girki a kitchen. Ya amsa mata ya ce "Koma bamu san da zuwanki ba, daga tafiyar mijinki jiya, yau kin fara yawo". Ta ce "Ai da yake ba wurinka na zo ba ehe" ta shiga ɗakin mama, mai sunan baba yana kwance a kusa da mama, yana kallon tv. Mama ta ce "Ke daga ina?". "Makarantar matan aure wai ya saka aka kai ni, mai sunan baba ina kwana" "Lafiya ƙalau" Ba ta tsammaci wata magana sama da haka ba daga gare shi ba dama, dan haka ta zauna ta ce "Mama jiya ya tafi fa". "Haka Aliyu ya ce mini, ina mai gidan nawa, ina ƴa ta iman, ki ka zo mini ke kaɗai?" Mai sunan baba ɗan gyarawa yayi, yana jiran jin amsar da rumaisa zata bayar, a kan iman. "Mama, ni in koma kenan?" "Gaskiya dai, ba iman ba mai gidana, sai ke fitinanniya" "Ai shikenan, gara na koma wurin ammi. Sabir yana nan ƙalau, iman kuma gari ba daɗi, tsoro nake ji kar ciwonta ma ya tashi" A fuskar mai sunan baba ta ga razana, amma saboda azabar miskilanci yayi kamar bai san me suke faɗa ba. Mama ta ce "Subhanallah, me yayi zafi haka, yara ƙanana da ku, har kusa abu ya dameku a rai". "To ammi kin san familyn na su sai a hankali, sun takura mata da yawa, kin san ba ammi ce ta haifeta ba, sau kusan huɗu ana yinƙurin aurenta, wannan muguwar Mummyn tana hanawa, tana cewa mutane ba ta da uba, wai ammi ce garin tsince-tsincenta ta tsinto ta" Cikin rashin fahimta mama ta ce "Ke kin sani a duhu, kina nufin ba ita ta haifi iman ba?" "Hmm mama baki san badaƙalar da ke cikin gidan nan ba" nan ruma ta warware mata komai, sannan ta ce "Yanzu kuma wannan jabir ɗin ya ce son ta yake zai aureta, ammi tana ta murna, tun da shi ya san halin da ake ciki, ita kuma iman ba ta son shi sam, akwai wani wanda take so daban, amma ba za ta iya gayawa ammi ba, saboda ammi ta amince jabir ya nemi auren ta, ba wanda ta gayawa sai ni abun tausayi, kuma tsoro take ji kar wanda take so ɗin, ya ji labarin ga a halin da take ciki ya ce baya son ta". Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, lafiyayyiyar yarinya mai mutunci kamar wannan, babu wanda zai ce ba ita ta haifeta ba, ni cikin yaran nan, da da wanda yake da ƙwari sosai, ai da an auro mini ita, to sai dai ba matar talaka ba ce, ni dai ina ƙaunar yarinyar nan fisabilillahi". Cikin son sai ta yi pressing ɗin mai sunan baba rumanta sake cewa "Bari kawai ammi, kuma fa baki ga uban samarinta da suke sonta a haka ba, masu kuɗi ta ce ta daina soyayya, kawai ta zo ta fara son wani, amma taƙi gaya mini waye, ba ƙaramin son sa take yi ba. Amma wannan jabir ɗin, ya biyo kai tsaye ta wurin ammi, kuma yana daf da zuwa wurin mai girma wambai, shi kuma wannan wamban ba ɗaga ƙafa, dama yana ta yi wa ammi kashedi, ta aurar da ita ko ta mayar da ita in da ta ɗaukkota, cikin dare ina jin tana ta kuka". Tsaki mai sunan baba ya yi ya tashi ya bar ɗakin, rumaisa kuwa ta yi wani guntun murmushi, ta tura saƙon yadda yakamata. Aliyu ya shigo da plate ɗin indomie, ya ce "Me aka yi masa na ga ya fita yana tsaki?" Mama ta ce "Shi wannan sai an yi masa wani abu ma?". Ruma ta ce "Za mu ci indomie" "Ai ko mayya ce ke, sai dai ki ci kan ki" Tashi ta yi ta koma kusa da Aliyu, ta ce "Dan Allah zan ci". "Wai ke da mijinki yake ajiye miki komai, ki zo ki saka mini rani". Ruma ta ce "Allah sarki mijina, ya tafi ya barni, papa saurayina" Aliyu ya ce "Ke fa baki da kunya ko?" Flashing aka yi wa Aliyu, ta leƙa wayar ta ga an rubuta "Baby Hibba". "Ohhh ni ƴa su, yaya Aliyu soyayya?" Ya harareta, ya kira wayar "Hello my haidar". "Kuɗin wayar sun ƙare ne ake mini flashing?" "A'a ba su ƙare ba, bana son ka ɗaga su ƙare ne, kuma ka sake saka wasu, shiyasa na yi maka flashing" Yayi murmushi ya ce "An taso daga tahfiz ɗin ne?". "Eh, yanzu na shigo gida ma" "To shikenan, in ajima zan zo in sake jin haddar. Bari yanzu abinci zan ci" "To my haidar, ka gaida mama, ka ci ka ƙoshi da yawa". Rumaisa ta ce "A gaban maman ka ke waya da ƴan mata?" Daƙuwa ya yi wa rumaisa, ta hau tafa hannaye. "Yaya Aliyu, habiba ce ta koma sweet hibba?". "Uban wa ye ya ce miki ita ce" Rumaisa ta ce "Na rantse da Allah muryar habiba ce, munafuka, habiba take soyayya da yayana, ba tare da tana biyan subcidy ba, dole na je gidansu habiba, mama a gabanki ake soyayya?". Mama ta ce "Ya ce zuwa za ayi ma ayi masa tambaya, nan da shekara biyu" Ruma ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Su mai sunan baba ba su yi aure ba sai kai" "Uban wa ye zai bari kansa ya kulle kamar su? Yaya Abubakar ma kuɗin aure za a kai masa, yana gama service. " "Innalillahi, yaya Aliyu habiban da ka ke zanewa saboda ni" Aliyu ya doke mata ƙeya ya ce "Ƴar rainin hankali ba, duk ke ki ka ja, na daki mata ta". Mama ta ce "Too har an yi auren kenan" da sauri Aliyu ya ɗau plate ya fice daga ɗakin yana dariya. Wani irin zullumi mai sunan baba ya shiga, ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya kasa gane tausayin iman yake ji, ko tashin hankali ya shiga jin wani na neman aurenta, wani irin kishi ne ya taso masa, tabbas ya fi jabir komai, sai dai jabir ya fishi kuɗi, sannan kuma wa iman take so Yaya usy ne yayi sallama, rumaisa ta tashi da gudu ta tare shi, ta ce "Mussaman saboda kai na zo gidan nan yaya usy". Ya ce "Ƙarya ki ke yi". "Wallahi da gaske, zo mu zauna daga nan" Ba tara da ta bari ya shiga ko wurin mama ba, ta ja shi kitchen ta rufe ƙofa, sannan ta ce "Yaya usy wani abu ne yake damuna, na ga kaine abokin shawarata, na ce bari na gaya maka". Ya ce "To ina jin ki" "Yaya usy, dama...dam..mm" "Wai meye haka ne?" "Kunya nake ji ne, amma shawara nake nema. Ka ga dama takawa ne kan ya tafi, yake yi mini abun da bai dace ba, kuma" "Kuma me? Wane irin abu ne da bai dace ba". "Yaya usy kiss yayi mini kuma, ba zan iya faɗar sauran ba dai, kuma kaga bai dace ba, bana son mama ta gane, ya ce mini wai ai ba komai, in tambaya in ji, wai tun da ihu nake idan ya taɓa ni, zai ƙara aure, kuma ni bana son ya yi mini kishiya. Dan Allah yaya usy ya zan yi, bana son ɓata tarbiyya ta, idan mama ta sani za ta yi fushi da ni, kuma bana son yayi mini kishiya" Ayshercool. 08081012143 Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Usman ya yi ƙuri da ido yana kallonta. "Yaya usy ba ka ce komai ba?" "Ji nake kamar in kama ki in maƙure mini wuya ne". Cikin damuwa ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ka rufa mini asiri" "Ke dalla ware malama, ke yanzu duk zaman da ki ke yi, yake baki ci da sha, ya ɗauki nauyin karatunki, shirme kawai ki ke tafaka masa, zuwa ki ke kiyi masa ƙiri-ƙiri da ido, kamar gardi a cikin gida, ke kanki ba zaki taɓa waye ba, abun da aka koya miki baki san idan kin yi aure ki waye ba, sai kayan hauka da rashin hankali" "Ni fa yaya usy ban gane me ka ke nufi ba" Usman ya ce "Idan bai yi miki kiss ba, wata zai je ya yi wa a waje?" "Yaya usy, ku fa ku ka ce mini haramun ne, Allah zai ƙona ni idan na yi" "Kuma sai aka ce miki har da mijinki? Ai gara ya ƙara auren, kuma ba abun da zai hanamu raƙashewa da bikin, ki je ki yi ta shirmenki" Usman ya tashi ya bar kitchen ɗin. Ta yi shiru tana tunani, ta yaya haka zai yiwu? Sun ce mata abu babu kyau, yanzu kuma an dawo an ce mata ya halatta ba tare da wani cikakken bayani ba. Ta basar da zancen ta cigaba da harkokinta. Mai sunan baba kuwa rumaisa ta haɗa shi da assignment mai wahalar gaske, domin kuwa kasa sukuni yayi, maganar ta din ga damun zuciyar sa, ya din ga jin tamkar yayi tsuntuswa ya je ya ga Iman. Da wayar mama, rumaisa ta kira Mahmud a waya, ta ce ya zo ya ɗauke ta, ta bashi adress ɗin gidan. Yayyen ruma sun sha mamakin ganin Mahmud, basu san shi, ba sai dai wasu lokutan ta kan yi maganar sa. Ya fi takawa sakewa da mutane wasu lokutan, dan haka nan da nan ya shiga cikin su Aliyu kamar sun saba. Rumaisa ta ce "Daddy, ga Yasir, shi ne hacker shi ne ku ka yi waya da shi" "Ki ka kuma ce mini hacker, ba zan sake yi miki wani abu ba" Mahmud ya ce 'Rabu da ita, ai ni da kai muke aikinmu" ta nuna masa Abdallah ta ce "Ga masterna a wurin zane-zane, da shi nake koyi, duk da idan na taɓa masa kayan zane, wataran ranƙwashina yake, amma a hakan Alhamdilillah na koya, dan haka shi zai yi mana zane, sonake kan papa ya dawo, mun gama komai" Ya ce "Lallai team ɗin nan an haɗa manyan ƙwari a cikin sa, Allah ya dafa mana". Mama sam ba ta san a kan me suke magana ba, bayan la'asar sosai, sannan ya ɗau ruma suka tafi gida. Aikuwa ta sha faɗa a wurin laila, wai ta tafi gida, ba a kira takawa an tambayi izninsa ba, ruma tayi mata banza, irin kan ki ake ji ɗin nan. Kusan sati guda, laila ta saka ruma a gaba, ta hanata sukuni, gashi ta yi ta mata magana da turanci, komai ruma ta yi sai ta ci gyaranta. Ta hanata kwana tare da iman, tare suke kwana a ɗaki tare da ita, gashi ta kasa ta tsare ta hanata video call da takawa. Abu ɗaya ne yake yi mata daɗi, kunun maman Khadija na sabaya da take sha safe da yamma, wannan kam tun da batu ake na ci, ruma tana jin daɗin haka. Ban da wannan, duk wani wanke-wanke da gyaran fata rumaisa ba so take yi ba. Rumaisa na zaune tana shan kununta, ita da sabir, dan idan suna sha, kamar ya shiga cikin kofin, ko zama ba ya yi, yana tsaye ayi ta bashi yana lashe baki. Laila sai video call take da mijinta, ga mijin ya fara manyanta, amma ta shagwaggwaɓe, sai taɓara take, tana ce masa baby, suna wani abu mai kama da iskanci a wurin rumaisa. Rumaisa har leƙawa take, ta sake kallon fuskar mijin, wai wannan gundumemen mutumin ne baby, 'Taɓ sukumbiya, wai baby taɓ' laila tana jin ta, taƙi kulata, su suke wayar amma ita take jin kunya. Babu babban abun da yake bata mamaki, kullum da daddare sai sun yi video call, laila ta ɗau kwalliya kamar zata biki, ta sha ƙanan kaya, ta zauna a gaban waya ko system. Yau kam da abun ya ishi kunnuwan rumaisa, ta saka hannu ta toshe kunnenta. Sai da laila ta gama wayar, sannan ta dubi rumaisa ta ce "Ba zaki iya ba ko, ni ƴar iska ce ni da mijina, shi ne ki ka toshe kunne?" Ruma ta yi shiru. "Ban ce dole sai kin yi irin nawa ba, ni na yi shekaru a gidan aure, na saba da mijina sosai da sosai, ke nake fatan ki daina wannan shirmen, ki san me ki ke yi" ruma ba ta ji za ta iya abun da laila ke yi ba, a ganinta fitsara ce muraran, ga takura mata da take yi. Da safe kan ta tafi makaranta, ta karɓi wayar iman, ta kira Adam voice call. "Budurwata" "Papa" ta kira sunansa a shagwaɓe. "Ya aka yi?" "Ni gaskiya wannan anty lailan ta takura mini, ta yi ta mini masifa, da na motsa ta yi mini faɗa, duk ta bi ta saka mini ido". Adam ya ce "Haba mimi, baki kira ni kin ji lafiayata ba, sai kawo mini ƙara, ke ma ta ce mini ba kya ji, taurin kai ki ke yi mata". "Yi haƙuri ya kake?". "Ban sani ba, tun da baki damu da ni ba" "In ji wa? To yau saura kwana ɗari da saba'in da biyu ka dawo, calendar ce da ni, kullim sai na yi marking kwanakin da suka rage ka dawo" Adam ya ce "Wow, lallai kin damu da ni sosai, take care, kar ki makara" "Ni kar ka kashe" "So ki ke ki makara a school ko?" "Hmm ka san me?" "A'a sai kin faɗa" Ji tayi kamar ta gaya masa zancen kunun da take sha sai kuma ta fasa. Jin tayi shiru ya sanya ya ce "Akwai matsala ne?". "A'a" "To ki shirya a kai ki school kin ji budurwata, sai mu yi waya anjima" Ruma ta ce "Video call nake so mu yi in ganka, amma wannan anty lailan ta hana, duk abun da zai sani farinciki ba ta so". Ya ce "nima dokar nan ta isheni gaskiya, mutum da budurwasa a hanasu sakewa" Ruma ta yi dariya ta ce "To saurayina, sai na dawo, kun gama taron yaushe zaka wuce karatun" Ya bata amsa da "sai Allah ya kaimu jibi". Da ƙyar suka yi sallama, ta ajiye wayar ta tashi. Wata irin kewar adam ce ke sake bijirowa rumaisa, ji take kamar sun shekara ba sa tare, tayi shiru tana tuna abubuwan da suka faru a tsakanin su, daga aurensu zuwa yanzu, a hankali ta yi ajiyar zuciya, ta tashi tana shirin makaranta. Mai sunan baba kuwa tsayin lokacin nan, kullum sai ya ɗau wayarsa ya ji kamar ya turawa iman message, amma sai ya kasa, ya duba chats ɗin su, ko zai ganta online, amma ya ga sam ba ta fiye hawa online ɗin ba ma, gashi sai yana tsaka da jimami, da tunanin ya zai yi, Aliyu ya zo yana kashe murya yana waya da habiba, wanda ba ƙaramin ƙular da shi yake yi ba. Mummy ba ta sake nunawa Mahmud fushi ko damuwa a kan abun da yayi ba, hasali ma taƙi yarda su sake ɗaukko zacen, kamar babu abun da ya faru, ta ƙarƙashin ƙasa kuwa, tana cigaba da shirin, sake rusa giwa, saboda ta yi alwashin sai baƙin ciki ya kashe giwa, in dai da ranta babu wani abun alkhairi da zai sameta, babban birinta yanzu bai wuce kassara rayuwar rumaisa ba, kasancewar ita ce babbar barazanar ta. Ɓangaren Jamil ma, yana ta neman hanyar da zai yi magana da rumaisa, dan ya sha zuwa makarantar su, ya tarar da sidi yana tsaye yana jira, kuma alamu sun nuna babu wanda ya san adam yana zarginsa, dan haka so yake ya tutsiye rumaisa, ya ji me da me ta sani. Baba uwani ma kullum zaman ɗar-ɗar take yi, a kan kar rumaisa ta tona mata asiri, dan tuni mummy tayi mata fata-fata ta sallameta. Ammi na ta yi wa iman bayanin cewa Jabir ya ce mata, yana jira mai girma turaki ya dawo, wambai ne zai nema masa auren iman, kuma ya bata tabbacin cewa ya shawo kan hajiya Lubabatu ta amince masa ya nemi aure iman, kuma yayi mata zancen haɗa lefe ta ce masa wannan maganar su ce, su yakamata su tattauna. Iman da ke shan kunun sabayar maman Khadija, dan ba a bar ta a baya ba, har ita ake sha, dan kuwa kogi bai ƙi daɗi ba, ta sunkuyar da kai tana sauraren ammi, ruma kuwa tana ta game a wayar ammi, kamar ba ta san me ake faɗa ba. Ammi sai ta yi zaton kunya ce kawai irin ta iman, ya sanya taƙi magana, Nusaiba kuwa sai zaƙalƙalewa take yi, tana tsara yadda biki zai kasance. Sallamar hajiya Lubabatu ce, ta katse musu hirar, Ammi ta amsa su kuma duk suka bita da kallo. Ammi ta faɗaɗa murmushin ta, ta saka duk abubuwan da suka faru a baya, mussaman da Jabir ya ce mata ai ta amince da aurensa da iman, dan haka cikin murna ammi ta karɓeta. Sai dai ta turɓune fuska ta ce "Giwa ba zama na zo yi ba, magana zamu yi dan Allah" Ammi ta ce "To shikenan, ko zamu shiga daga ciki ne?" "A'a ba wani daga ciki, magana zamu yi a buɗe a fai-fai. Wallahi giwa ki ji tsoron Allah, idan har kina son gamawa da duniya lafiya, mace sai tsabar son kanki a zuciyarki. Kawai kin juya mini tunanin ɗa, ki rasa da wanda zaki haɗa shi, sai auren ƴar tsintuwar ki, yarinyar da ki ka ce kin san iyayenta, ki ka gaza nuna su har rana mai kamar irin ta yau, kawai dan ki cuceni, wato sarauta ta bar gidanku, idan Allah ya yi jabir ya samu sarautar galadima, kin dai aura masa ita, dan ku mallake shi sai yadda ki ka yi da shi, wato kowa ya rasa, wanccan ba lafiya ce da shi ba, kin san ba sarautar zai yi ba, Mahmud kuma tun da Jamila ce ta riƙe shi, ba zaki bari abun arziki ya same shi ba, tun da ba ke yake yi wa kallon uwa ba, sai ki ka lallaɓa zaki aura mata ɗa na, to ba zai yiwu ba wallahi" Ammi ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri Lubabatu, ki fuskance ni, Jabir fa shi ya kawo kansa, ya ce yana son iman, ba ni na takura masa sai ya auri iman ba, kuma shi ne ya bani tabbacin lallai kin amince wa auren nan" "Ni ina na san ana yi, ana ƙulla mini kitimurmura, ina ɗan sarauta ina auren shegiya da aka tsinto, wallahi ƴar tsintuwa ba zata samar mini da zuriya ba, idan ba haka ba a nemo iyayenta a nuna mini" Tuni jikin iman ya fara rawa tana kuka, rumaisa kuwa ji tayi kamar ta mari iman, ba ta da kataɓus, da an yi mata abu sai kuka saboda tsabar shagwaɓa. "Lubabatu shi ɗa na kowa ne, iman kuma ƴar ku ce, meyasa lallai sun kun nuna mini, iyakata ne?". "Ba wani ɗa na kowa ne, idan na kowa ne ki aurawa adam mana, ko dai sarautar ki ka ƙallafawa rai, sai kin mamaye komai, wallahi ɗa na yafi ƙarfin auren ƴar tsintuwa, baƙin halinki ne yake bibiyar ki da yaranki". Tuni rumaisa ta hasala ta ce "Wai jabir ɗin banza Jabir ɗin wofi, me aka yi aka yi wani Jabir munafiki da shi, ban da ƙaddara ta Allah, ki kalli iman ki kalli jabir ɗin mana, wani sololo kamar an mari ɗan akuya. Wai ku baku da wani buri sai ku zo kuna zagin ammi, me tayi muku?". "Ke rufe mini baki, ko na zo na talitseki, ƴar matsiyata ban saka da ke ba, sa'arki ce ni?" Ruma ta ce "Wallahi talitseni, dai-dai yake da taka kan ɗan maciji, baku da magana sai ta sarauta, fir'auna ma ya mutu ya bar mulki, dan abun kunya, mijinki na can na jinya, ke da ɗan ki kuna nan kuna fafutuka a kan wata sarauta, wannan ne abun alfahari dan za a aure shi? Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, wallahi jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, ai ni idan mutum babban banza ne, bana ganin girmansa, tun ranar da muka je gidanki, ki ka ci mini mutunci nake ƙullace da ke" Ammi jikinta har rawa yake, ta ce "Rumaisa ya isa haka, ku tashi ku shiga ciki" dan ammi ba ta taɓa ganin ruma tana asalin tijara ba sai yau. Laila ta ƙaraso falo ta ce "Ammi su shiga ciki su je ina? Rumaisa kin yi mini dai-dai, ai asara na ga matar da ta wofantar da mijin da ya gatantata lokacin yana da lafiya, yana ƙasar waje yana jinya, tana nan tana shirme a gari, ita da ɗan ta mara tarbiyya. Ƴar wahala, tun da na sanki Lubabatu baki da alƙibla daga ke har Mummy, shiyasa rayuwa ta ƙi yi muku yadda ku ke so, kuma albarkar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da alƙur'ani, cigaba yanzu muka fara" Ruma ta ce "Kuma in sha Allah, sai na dawowa da ammi Mahmud" Laila ta ce "Dan Allah malama kwashi banzayen ƙafafuwan ki, da aka saba bin bokaye, a bar mana part, kar a zuba mana masifa". Hajiya Lubabatu ta nuna kanta ta ce "Laila har da su kaza a cin danƙo, ni ƴar riƙo za ta gayawa magana haka". "Ƙwarai ƴar riƙo ba, ko nima zaki ce mini shegiyar ne? Ke sa'a fa ki ka ci, Jabir yana girmamani, da wallahi ashar zan ɗuɗɗura miki, zaki iya fita" Su biyun duk suka ƙureta da ido, ba wanda ya fi ɓata mata rai, irin cin mutuncin da rumaisa ta yi mata. "Giwa a gabanki sirikarki suka ci mini tuwo ko, duk saboda wannan yarinyar, na faɗa ba zan bari ɗa na ya auri wannan yarinyar ba, da ban san asalinta ba, wanda ba na raba ɗaya biyu, ƴar gaba da fatiha ce, kuma zaku ga abun da zai biyo baya" ta fice tana huci. Bayan fitarta, Ammi ta kalli laila ta ce "Laila mey....." "A'a Ammi, daga ni har rumaisa ba wanda yayi laifi, nima fa ba son aurenta da jabir ɗin nan nake yi ba, saboda duk wani abu da ya shafi mummy, bana ƙaunarsa na tsani matar nan kamar yadda na tsani mutuwata, ke kuma iman, idan aka kuma zuwa ana gaya miki magana, ki ka ɓare baki kina kuka, ubanki zan ci, sokuwa kawai komai kuka, bayan kin san larurar da ki ke ɗauke da ita". Jikin Nusaiba duk yayi sanyi, ita dai tana yi wa iman sha'awar auren jabir, amma halin mahaifiyarsa ne sai a hankali, kuma wani point da ruma ta kawo abun dubawa ne, mutumin da mahaifinsa yake ƙasar waje yana jinya, an bar shi shikaɗai sai mai kula da shi, tilon ɗan sa namiji kuma yana nan yana gararambarsa. Sai dai ba a fi mintuna arba'in, da tafiyarta ba, wambai ya kira ammi a waya. Suka gaisa, gabanta na faɗuwa, ko wani abun hajiya Lubabatu ta je ta kitsa masa, sai dai ta ji ya ce mata "Mun yi magana da jabir galadima, idan turaki ya dawo, zuwa ranar lahadi idan Allah ya kai rai, zamu kai kuɗin auren yarinyar wurinki iman wurinsa, ya ce mini kun gama magana, zamu sanya watanni biyu ne kawai auren" Gaba ɗaya sai ta ji ya ɗaureta ta da jijiyoyin jikinta, ammi ta ce "To ranka ya daɗe, Allah ya tabbatar mana da alkhairi" Laila ta ce "Lallai ma jabir munafuki ne, yana sane da uwarsa ba ta so, amma yake maganar kai kuɗi? Kodayake hakan shine dai-dai, ta auri jabir ɗin, mu ga ta tsiya, Allah ya tabbatar da alkhairi, ai Allah ya fi su" Ammi ta ce "Subhanallah, Allah ya kawo mini ƙarshen wannan fitintinu, ni abubuwan ma sun isheni, Addu'a dai nake tayi, Allah ya shiga lamarin nan, bai kamata a hukunta jabir, da laifin mahaifiyarsa ba, tun da shi mutumin kirki ne". Ruma ko sunan jabir ba ta son ji, dan haka ta bar falon gaba ɗaya, ita zaman gidan duk ya isheta, gida kullum cikin tashin hankali da bala'i, an saka mutum ɗaya a gaba da masifa. Harabar gidan ta fita shan iska, tana ta zazzagawa, tana kallon fulawoyi, ga sanyin la'asar, yanayin yayi mata daɗi sosai. Daga sashin Mummy ta hango jamil, ta tsaya tana kallon sa, su kullum suna gidan nan, kodayake ba abun mamaki bane ba, tun da ƴan uwa ne, amma ita a wurinta duk wanda ya fiye zuwa wurin Mummy ba shi da gaskiya. Ga mamakinta taga yana tunkarota, dan haka ta haɗe rai zata juya ta tafi, ya cimmata da sauri ya ce "Ɗan tsaya mana, yau Allah ya sa mun haɗu, magana zamu yi" Ta ƙare masa kallo ta ce "Maganar me?" "Magana a kan abun da ki ka cewa mjinki na kina zargina da kisan Aisha" Ruma ta ce "Ba rami meya kawo rami,? Ni ban ce ka kashe anty aisha ba, kuma da mijina ku ke magana ba ni ba, dan haka babu ruwanka da ni" "Amma ko menene ke ki ka kitsa misa, daga auroki ƴar mitsitsiya da ke, kin rikita mana zaman lafiya family" "Dama can ba zaman Allah da annabi ku ke yi ba, kuma na faɗa ɗin, idan kana da gaskiya, maiyasa a da baku damu da anty aisha ba, sai yanzu kake damun baban sabir, wataƙila ma da kai ake haɗa baki ake ɓata masa suna" Jamil ya ce "Kin san me ki ke faɗa kuwa?" "Malam danginmu babu mahaukaci, ban yi gadonsa ba, kuma babu ƴan shaye-shaye" Jamil ya ce "Ni fa jami'in tsaro ne, zan iya amfani da kakina wurin ladabtar da ke, da tursasaki a kan kiyi bayanin abun da ki ke ɓoyewa". "To meya hanaka yin hakan tuntuni? Ka yi mana, amma ka sani na san da batun saka sunan anty aisha, a matsayin magajiya da mai girma turaki ya yi, a kan filin sa, da wani kamfani da haɗin gwamnatin tarayya suka karɓa jingina, ake amfani da shi, ana bashi wani kaso, na kuɗi, wanda kai tsaye yake shiga asusun anty aisha. Ka ga idan baka kiyayeni ba, zaka tsinci talatarka a laraba" "Wa..ww..waye ya gaya miki wannan maganar? Kenan adam saboda wannan maganar, ya fara tunanin ɗora zargin sace matarsa a kaina?" Rumaisa ta ce "Kai ma kenan saboda ka wanke kanka daga zargi, ya sanya ka ƙirƙiri cewa ya kashe matarsa yayi tsafi da gangar jikinta?" Mamakin rumaisa ne ya mamaye shi, ya ce "Kuma aka ce miki ni ne na yaɗa wannan maganar? Me ki ke nufi ne?" Ruma ta yi murmushi ta ce "Ba ina nufin kai ne ba, kawai na yi tunanin, kowaye ya saka aka sace anty aisha, shi ne ya yi wa mijina sharri, ni ba ƴar sanda ba ce ba, amma ƴar baiwa ce, garkuwa da aka yi da anty aisha shiri ne, kuma idan ba ka da hannu, kar ka damu kanka, sai dai ita rayuwa, iyawa ce, abu ƙailalan zaka yi, ya jefeka cikin masifa a gaba, har ƙarshen rayuwarka, ka sani iya wuya ina bayan mijina, kuma kar ka sake tunkarata da wannan maganar" Dafe kai Jamil yayi, ya ja da baya,gaba ɗaya ya ma rasa ta ina zai fassara maganganun rumaisa ne? Ta hargitsa masa zance cikin zance wace irin yarinya ce ne haka? Kamar ana controlling ɗin ƙwaƙwalwarta da remote?. Lokacin da rumaisa ke daf da shiga sashin ammi, taga laila ta fito da sauri, ta yi wa sidi magana, akan ya kawo mota, zasu tafi asibiti iman ta suma. Da gudu ruma ta shiga sashin ammin, iman na kwance a in da ta barta ɗazu tana bacci, ashe daga haka ta suma, ammi na ta magana amma shiru. A gaggauce suka ɗauketa, tuni ammi zuciyarta ta karaya, saboda yadda jikin iman ya saki, kuma Ammi ta ɗora alhakin hakan a kan hajiya Lubabatu, da ta zo ta yi mata wannan cin mutuncin. Ammi ta ce Rumaisa da Nusaiba su zauna a gida, ita da laila suka tafi kai iman asibiti. Rumaisa ta kasa zaune ta kasa tsaye, lokaci lokaci ta din ga jan uban tsaki ta ce "Allah ya tsinewa babar jabir ɗin nan, da bata san darajar ɗan Adam ba, daga ita har shi wawan jabir ɗin, mara zuciya" Nusaiba ta ce "Ya zaki din ga zaginsa, shikuma me yayi miki?" "Ba ruwanki da ni, ai naga take-takenki, ke kike goya masa baya, ke ki aure shi mana" duk da Nusaiba ta girmi rumaisa sosai, dan ta girmi iman ma, amma haka tayi shiru ta kasa magana. Sai dare laila ta dawo, suka tashi gaba ɗaya suna tambayar laila ya jikin iman ɗin. Laila jiki a sanyaye ta ce "Da sauƙi, sai dai jini ya hau, zuciyar ta kumbura, amma ta farfaɗo ta samu bacci." Ruma ta ce "Anty laila dan Allah a fasa auren nan mana, ko dan ceto rayuwarta" "Ai ni zan fi so yi auren nan, dan nuna mata iyakarta, kuma magana tun da ta riga ta je gaban wambai, rusata ba abu ne mai sauƙi ba, mutumin nan ba ayi masa wasa". Rumaisa ta rasa abun sa yake yi mata daɗi, ji take kamar ita ce a halin da iman take ciki. Nusaiba ce ta shirya, ta tafi asibitin, dan taya Ammi kwana da iman. Yau sai ga rumaisa da tashi cikin dare tana sallar dare, tana yi wa iman da yayanta addu'a, idan da alkhairi Allah ya sa mai sunan baba ya auri Iman. Dan ta san mai sunan baba, akwai zafi, amma mutum ne mai kyautatawa da tausayi, kuma ba ta taɓa ganin abun da ya damu da shi sosai bayan ita da mama ba sai iman. Da gari ya waye, laila da rumaisa suka je duba iman, suka kai musu abinci. Iman ta farfaɗo, amma ta yi pretending, bacci take yi, saboda ba ta son magana, dan numfashinta sama-sama take yin sa. Ammi da Nusaiba suka koma gida, an yi sa'a ruma da anty laila an ɗan fara shiri, sannan laila ta sarawa tsagerancin rumaisa, mussaman jiya, da ga tsigalewa hajiya Lubabatu. Wayar iman na hannun rumaisa, dan yanzu wayar kamar ta su ce su biyu. Rumaisa ta kira mama ta ce "Mama dan Allah ki zo ki duba iman, ba ta da lafiya muna asibiti" Mama a duk lokacin da ta ji an ce iman ba ta da lafiya, hankalinta yana tashi, mussaman da ciwonta yake mai hatsari. Bayan ta gama wayar ta dubi laila ta ce "Anty laila". "Na'am". "Wai yaushe zan yi video call da papa ne?". Laila ta ce "Sai lokacin da ki ka fara bin umarnina" "Anty laila dan Allah, so nake na ganshi" "Kin fiye taurin kai ne, sai lokacin da ki ka fara yarda zaki yi abun da nace miki ba gardama" "To me ki ke so na yi?" Ta ce "Ba wannan ba ma, so nake mu bashi mamaki, sai kin fi haka kyau da cika, ke baki ga yadda jikinki ya fara yi ba ne" Ruma ta ce "Na gani, kullum idan na je wanka ina dubawa, idan sun fara girma". Laila ta yi dariya ta ce "Ashe dai kina son su fito". "Wallahi ina so" "To ki mayar da hankali da cigaba da shan kununki, bayan sabayar maman Khadija ma, akwai maganin maman ilham, shi kuma a iya fito da nono yake aiki, baya sanya ƙiba, haɗinta haɗi ne mai kyau ɗan mambila ita ma. Rumaisa daga lokacin da mace tayi aure, zama bai ganta ba, shekaruna a ƙalla talatin da huɗu, amma kalleni kamar ƴar ashirin da biyar. Bana zama, abu ba sai ya lalace ake gyara shi ba, garkuwa ake yi kafin ya faru, nan gaba kina haihuwa kina shayarwa, dole zasu ranƙwafa ko su zube, amma idan ki ka tattala su, ki ka kula da su, tsaf zaki yi ta haife-haifenki, ba tare da kin sirewa miji ba. Kuma ba ina nufin ki je ki sai abun da baki san menene ba ki sha, ba haka nake nufi ba, duk abun da na baki kiyi amfani da shi, na san kyansa da ingancinsa, kuma na san da me aka yi shi. Kin ga maman Khadija na ta haɗin kunu ne na sabaya, da yake gyara jiki, ya sanya ƙiba da gyara fata, kuma kowa na iya sha. Ita kuma maganin maman ilham, akwai matan da suna da ƙiba, basa buƙatar yin ƙibar, gyaran nonon kawai suke so, ita maganinta haɗe-haɗe ne, na natural abubuwa, ba shi da side effect kayanmu ne na islamic da saiwoyi masu kyau, ake kawo mata daga mambila ta haɗa. Ya ki ke gani, idan mutum ya haɗa garin kunun sabayar maman Khadija, da kuma maganin gyaran nono na maman ilham? Rumaisa ita mace ba ta zama ba gyara, dan haka so nake ki cika kiyi kyau, kan dawowar takawa". Ruma ta yi shiru sannan ta ce "Ni fa na zata kawai amfaninsu a shayar da ɗa, ashe mutum gori ake yi masa idan bashi da su" Laila ta ce "Sosai makuwa, shiyasa ake son gyarawar ai, kuma gori ba iya na mata ba, har na miji, wanda ya fi kowanne takaici ba, miji yayi miki gori dan baki da su, ko kin bari sun lalace" Ruma ta sake gyara zama ta ce "To ita ma na maman ilham ɗin zaki sai mini?" "Eh mana, mai ze hana? Ki din ga biyayya kawai, mun gama magana da ita ma". Cikin farinciki ta ce "Allah ya sa su fito kan papa ya dawo, kin san me? ce mini fa yake, wai nasa yafi nawa girma, wai nawa kamar girman wake, daga baya kuma wai kamar murfin jarkar faro". Ƙyalƙyalewa da dariya laila ta yi ta ce "Rabu da shi, kan ya dawo zai sha mamaki, sai ki rama. Ai tun da akwai kunun maman Khadija, da kuma haɗin maman ilham, an wuce wurin, kin wuce gori mutuniyar". "Allah ya sa anty laila, to zasu kai kamar na samha? Su Fauziyar nan, wai a dubi samha ta fini komai amma ya aureni, idan nawa suka fi nata, ai ba zai aureta ba ko?" Laila ta ce "Wannan kuma effort ɗinki ne zai sanya, ya aureta ko ya fasa" *INA MASU SON WUCE GORIN KISHIYA, DA NA MIJI, KAI HAR MA DA NA ƳAN UWANKI MATA, TO KU GARZAYA KU GWADA KUNUN SABAYAR MAMAN KHADIJAH DA KE ZAUNE A ZARIYA, BAYAN FEDERAL PALLADAN ZARIYA 08033411249, KU TUNTUƁETA KAI TSAYE TA LAMBAR WAYARTA* *HAKA ZALIKA KU HAƊA DA MAGANIN MAMAN ILHAM MAI TULA-TULA, MAGANINTA INGANTACCE NE, WURIN BIYAN BUƘATUNKU, BA TARE DA CUTAR DA LAFIYARKU BA, KU TUNTUƁETA TA LAMBAR WAYARTA 0813 561 3021 TANA NAN A KAWO ROAD KADUNA* *HAJIYATA KAR KI BARI MATA SU SHA GABANKI, SU RIGAKI MALLAKAR MAGANIN MAMAN ILHAM, DA NA MAMAN KHADIJAH, MACE SAI DA GYARA, SUNA TURA KAYANSU KO INA A FAƊIN A NIGERIA, HAR MA DA ƘASASHEN DA MUKE MAƘWABTAKA DA SU* Bayan sallar azahar, mama ta je ta duba iman, jikin da sauƙi, amma dai tana jin jiki sosai. Laila kuwa mama ce ta burgeta, saboda yadda take komai nata a nutse, gashi tun da tazo, rumaisa ke tsokanarta take son sakata magana, saboda kamar kakarta ta mayar da ita. Mai sunan baba ya dawo daga kasuwa, ya tarar mama bata nan, abun da yafi komai ɓata masa rai kenan, dan haka ko abinci yaƙi ci, ya koma ƙofar gida ya zauna. Ya kai awa guda da rabi sannan mama ta dawo. Mama kamar ƴa da uba, a wajen ta fara yi masa bayani, dan ta san ba shi ba, hatta sauran ƴaƴanta, ba sa son su dawo su ga bata nan, amma na sa yafi yawa. "Ƙanwar mijin rumaisa aka kwantar a asibiti na je dubata, daga nan na wuce mandawari na sada zumunci da ƴan uwana" "Wacce daga ciki?" Mama ta ce "Wadda ka ke tsoratawa mana, iman, ciwonta ne ya tashi, ban ma tarar da hajiyar ba, sai wannan yarinyar, da wata yayar mijin rumaisan". "To ya jikin nata?" "Jiki Alhamdilillah, amma dai har na taho bata buɗe ido ba" Mama ta ɗan yi shiru tana nazarin mai sunan baba, sannan ta shiga gida. Mama na shiga gida, umar ya ciro wayarsa ba tunanin komai ya kira wayar Iman. Sai dai rumaisa ta ɗauki wayar. "Ina me wayar?". "Mai sunan baba muna asibiti fa, ba ta da lafiya, ba ta tashi ba haryanzu" Ya katse wayar ya tashi, duk da yunwar da yake ji, ya shiga gida yayi alwalar magariba ya fito. Ya gama yanke koma menene, yau sai ya je ya ga jikinta, dan gaba ɗaya hankalinsa ya tashi. Bayan kowa ya tafi, ya rage daga iman sai nusaiba, laila ta ce za ta je gida tayi wanka ta dawo, ba sai ammi ta kwana a asibitin ba, su kwana ita da iman da Nusaiba. Tun kan ya shigo, gabanta ya tsananta faɗuwa, ba tare da ta san dalilin hakan ba, sai dai ba tare da tayi tsammani ba, ta ji an murɗa ƙofar yayi sallama. Da sauri iman ta fara kiciniyar neman hularta, dan kanta ko ɗan kwali babu, ba ta taɓa zaton mai sunan baba, ko da wasa. Nusaiba ta ce masa "Ina wuni" Ya amsa mata a taƙaice kamar yadda ya saba. Ba tare da fargabar komai ba, ya je gaban gadon, ya zauna a kan kujerar da ke gaban gadon. Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Yaya umar ina wuni" "Ban ganshi ba" ya bata amsa. Kamar yadda yayi tsammanni, ta ɗago ta kalleshi, ta mayar da kai ta sunkuyar. Ya waiwaya ya kalli nusaiba ya ce "Can you excuse us?" Ba musu Nusaiba ta tashi ta fita. Mai sunan baba ya kalli iman ya ce "Meya sameki?" Yayi maganar kamar ɗan sanda na tuhumar mai laifi. "Bani da lafiya" Jin shiru bai ce komai ba, ya sanya ta sake ɗagowa, ya zuba mata ido, yana jiran ta bashi amsa, dan wadda ta bashi ba ta gamshe shi ba. "Zuciyata ce take kumbura" "Meyasa?" "Nima ban sani ba" Ya ce "Kin sani" Shiru ta yi tana wasa da yatsunta. Ya ce "Well, Allah ya sauwwaƙe, kin san condition ɗinki, bai kamata ki din ga wasa da lafiyarki ba, and na ji rumaisa ta ce You are getting engaged very soon, Allah ya sanya alkhairi" Kawai ta fashe da kuka, yayi ƙuri da ido yana kallon ta, dan bai san me zai ce mata ba. Tayi me isarta, sannan ya ce "Auren ne ba kya so?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "Meyasa ki kai shi gidanku, idan ba kya son shi?" Iman ba ta san ya aka yi ta tsinci kanta da yi wa mai sunan baba bayani ba "Bana son shi, mamansa ta ce ba zai auri wadda ba ta da asali ba, gashi ya riga ya kai maganar wurin wambai" "Idan ba kya son shi, wa ki ke so?" Ɗagowa ta yi a hankali, suka haɗa ido, jikinta yayi sanyi yayin da mai sunan baba yaji tsigar jikinsa tana tashi. "Kuka ba ya maganin matsala, Addu'a ce magani, Allah na iya canza komai within seconds" A sanyaye ta ce "Labarina ba zai canza ba yaya umar, yarinya ƴar tsintuwa" Ya miƙe tsaye ya ce "Zai canza, put your trust on Allah, Allah Ya ƙara lafiya" tabi bayansa da kallo, wata irin ƙaunarsa na ratsa zuciyarta. Yayin da shi ma yake jin matsananciyar soyayyarta da tausayinta a nasa ran, ji yake tamkar kar ya tafi, sai ta samu cikakkiyar nutsuwa ta kwantar da hankalinta. Yana daf da kaiwa ƙofa, Jabir ya buɗe ya shigo. Ayshercool 08081012143 Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Kallon-kallo suka shiga yi, tsakanin shi da umar, sai dai babu alamar mai sunan baba zai bashi hanya, sai jabir ne ya kauce masa ya bashi hanya. Mai sunan baba na fita, ya jiyo muryar jabir yana yi wa Iman tsawa "Wai iman waye wannan, meye alƙarki da shi, uban me ya zo yi wurinki?" Cikin wata irin azababbiyar zuciya mai sunan baba ya koma ɗakin, motsin shigowarsa ya sanya jabir haɗiye sauran maganar sa. Mai sunan baba ya taka, ya je gaban jabir ya tsaya, ya ce "Ni zaka tambaya waye ni, da dalilin da ya sanya na zo wurinta" Jabir ya haɗiyi yawu cike da kishi ya ce "Na san kai yayan matar Adam ne amm.... Umar ya kaste shi ta hanyar cewa "Bani da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da ku, ƙanwata ake aure a familynku, sai dai akwai mutunci da karrama juna, albarkacin ana auren ƙanwata a familynku, ni yakamata ka yi wa duk wannan tambayoyin ba mara lafiyar da ke kwance a gadon asibiti ba, ko ba ka san abun da yakamata ba". Da ƙyar jabir ya aro jarumta, dan gani yake, da yayi kyakykyawan motsi, mai sunan baba zai iya kai masa naushi, ya ce "Amma ka san babu wata alaƙa tsakaninmu meyasa za ka zo in da take, aurenmu fa za ayi" Mai sunan baba ya ce "Amma ba ayi ba ko?" Jabir yayi shiru. Mai sunan baba yayi tsaki, ya nufi hanyar fita, a daidai lokacin laila suka shigo ita da Nusaiba, bai kula su ba ya fice. Laila ta ce "Waye wannan?" Nusaiba ta ce "Yayan rumaisa ne ya zo duba iman, shi ya korani waje ma". "Au ya koraki waje ma, wane irin abu ne zaku din ga barin ƙarti suna kaiwa suna komowa a wurin matar da zan aura, wannan ai cin amana ne" Laila ta ce "Nawa ka biyamu kuɗin gadin da zamu hana wasu zuwa wurin iman jabir? Kai ka isa kyakywar yarinya kamar iman, ka ce zaka hana masoya zuwa wurinta" Jabir ya ce "Ba haka bane ba anty laila, amma ai kun san bai kamata ba". Laila ta ce "Haba jabir, kalli fa kuka take yi, da wanne za ta ji? Kuma dai naga ai baka kai kuɗin auren ba tukuna. Kai baka san ka lallaɓata ba" Ya ce "Haka ne, Allah ya bata lafiya, kishi ne ya sanya ni yin hakan, zan dawo da safe" ya ajiye ledar hannunsa ya fita. Laila ta ƙarasa gaban gadon, ta zauna ta rungumo iman tana rarrashinta. Ta samu ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ashe rumaisa tana da wa babba kamar haka" Nusaiba ta ce "Ba ki ji ana ce mata ƘANWAR MAZA ba? Yayyenta bakwai maza, ita ta takwas" "Masha Allah" Nusaiba ta ce "Amma wanda ya fitan nan, shi da Hassan ɗin sa ne manya, masifaffe ne, ba shi da fara'a ko kaɗan, daga zuwansa fa wai na tashi na fita". Halin da take ciki, bai hanata sake lafewa a jikin laila ta ce "Ba masifaffe bane ba, yana da kirki" Laila ta shafa kanta ta ce "Ko dai ko dai? Ko akwai wata a ƙasa ne" iman tayi shiru ba ta ce komai ba. Laila ma tayi shirun, tana cigaba da shafa kan Iman. Mai sunan baba kuwa, yana kan babur ɗin sa ƙirar lifan, babu abun da yake tunani sai kukan iman, kuka mai taɓa rai, ga wannan mara hankalin a yanayin da take ciki, ya je yana yi mata masifa. Laila kuwa sai da ta ga iman ta samu bacci, sannan ta kwantar da ita. Mai sunan baba sai da ya koma gida, sannan ya samu ya ci abinci, sai dai condition ɗin iman, da kukanta ya gaza barin zuciyarsa. Tuni laila ta yi bacci, ita da Nusaiba, iman kuwa jin wayarta tayi vibrating a ƙasan fulo, ya sanya ta buɗe ido. "Ya jikin?" Da sauri ta sake mutstsuke idanunta, ba mafarki bane ba, mai sunan baba ne. What's app ɗin ta ta buɗe, ta tura masa saƙo "Yaya umar ya ka je gida, Na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi, bacci ne ya ɗaukeni, shiyasa ban tambayi ya ka je gida ba". "I don't mean you should reply now, bacci yakamata ace kina yi yanzu" Wani irin murmushi iman ta yi, a ranta ta ce 'Gane in da ka saka gaba sai Allah yaya umar' Tayi masa reply da emojin murmushi ta ce "You are a good counsellor, na ji daɗin nasiharka, but please include me in your prayers, Allah ya bani mafita" ta haɗa da emojin kuka da na magiya a ƙarshe 😭🙏. Ya sauke numfashi a hankali ya tura mata emojin kuka da cancel 😭❌. "To na daina in sha Allah" Ya tura mata alamar jinjina, sannan ya tura voice message, abun da ba ya yi, shi chatting ɗin ma ba damunsa yayi ba, amma yayi mata message "Na ga saura few weeks bikin saukar alƙur'aninki karo na uku, kamar yadda ki ka ɗora a status, wannan kawai ya isheki godiya ga Allah, babbar ni'im ce da baiwa, da ba kowa yake yi wa ba. Dan haka kar ki daina addu'a khadija, kuka baya maganin matsala kamar yadda na gaya miki ɗazu" Subhanallah, iman taji voice ɗin babu adadi, musamman jin sunanta na asali a bakinsa, yana da very deep voice irin na cikakken namiji jarumi, wanda muryarsa kawai ta isa sanya mutum shiga hankalinsa. "Alhamdilillah, yaya umar ashe kana ganin status ɗina, haka ne na kusa sauka a karo na uku, na gode sosai yaya umar, na yadda you are very simple, unlike before da kake bani tsoro" ai shi ma a nasa ɓangaren, ya saurari voice ɗin ta bai san iyaka ba, sassanyar muryarta wadda yake gauraye da sigar shagwaɓa, haɗi da iyayi mai matuƙar daɗin sauraro". Tunawa yayi da Jabir ne zai aureta, gaba ɗaya ya ji wani irin haushi ya kama shi, ba tare da yayi reply ba, ya rufe datar sa ya kwanta. Yayi shiru yana tunanin, duk wanda ya auri mace kamar iman, idan bai tausaya mata ba, sai yaushe, mai zai sanya mutum ya din ga ɗaga mata murya haka, yarinyar da gaba ɗayanta kalar tausayi ce. *** Sai da ta kwana biyu, sannan aka sallami iman suka koma gida, sai dai ammi ta shiga saƙe-saƙe a kan batun auren nan. Rumaisa ta zauna ta zana takawa a plane sheet, tare da calendar a ƙasa, wadda kullum take cancel ɗin kwanan wata, na lokacin dawowar takawa. Laila ta ce "Rumaisa meye haka? Ya zaki liƙe mini hoton gunki a ɗaki" "Papan ne gunki, wallahi ba gunki bane" "To ni a wurina gunki ne mana, kawai ki zana ɗan alajani ki kafe mini, baga hotonsa nan a waya ba" Ruma ta ce "Ni bana son na waya, na fi son wanda na zana shi da kaina, ba kin hanamu yin video call ba, kuma ke kullum sai kin ga mijinki ba, ki bar mini zanena" Lailaa kawai tayi murmushi, wasu lokutan rigimar rumaisa dariya take bata. "Kin sha kununki na yamma, da maganin maman ilham?" "Na sha mana, ai anty laila bana wasa” Ta ce "Good, yanzu dai je ki ɗaukko jakarki ta islamiyya, da ta makarantar boko muyi karatu, kin ga exams za ku fara" Ruma ta tashi ta ce "Bari in ɗaukko, amma ni gaskiya daina zuwa islamiyyar nan zan yi" Tana fita falo tayi kiciɓis da Jabir, ya ɗago a yastune ya kalleta ya ce "Yauwwa dan Allah yi mini magana da iman mana" Cikin tsiwa ta ce "Kai ka isa? Wallahi baka isa ka aikeni na je ba, ka nemi ƴar aiken ka" Jabir ya ce "Wai ke meye haka, ka kowa ma sai ki ci masa mutunci baki da kunya?" "Ina dai yi wa mutane marasa kirki, kuma wallahi ba zan bari ka auri iman ba in sha Allah, yayana zata aura yaya Umar ba, kuma zaka gani, idan kana da zuciya ka canza hali, ka fara zuwa ka kula da mahaifinka, kan ka yi tunanin auren iman" Ba ƙaramin zafi maganganunta, suka yi Ya risuna ya gaida ammi, suka gaisa yace mata wurin iman ya zo, ammi ta ce masa iman tana bacci, likita ya ce a bari ta samu hutu. Ko da jabir ya tafi, rumaisa ta din ga ziga ammi, tare da nanata mata idan har jabir bai tausayawa mahaifinsa yayi jinyarsa ba, tayaya zai tsaya ya kula da iman da ciwonta?. Daɗin daɗawa ga masifa da tijarar mahaifiyarsa, da take iƙirarin cewa ba za a auro mata wadda ba ta da asali ba. Kasancewar rumaisa tayi sara a kan gaɓa, domin zuciiyar ammi ta fara kaiwa da komowa a kan batun, ya sanya ta ji ita ma ta gamsu da maganar rumaisa. Abu kamar wasa a hankali mai sunan baba ya fara ɗan sakewa da iman, da Allahn da yayi shi ba shi da yarda ko kaɗan. Duk safiya za ta yi message ta gaishe shi, daga nan kuma sai ya tamabayeta ya jiki, sai dai tana shan fama kan ta ɗan ja shi da hira. Sai dai ta fuskanci yana son tayi zancen karatu, mussaman na addini, hakan ya kan riƙe mata shi, gaba ɗaya mai sunan baba mu'amala da shi sai mai haƙurin gaske, miskili ne na bugawa a jarida. Mai sunan baba yana lura da yadda Aliyu yake gudanar da tasa soyayyar, ba kunya yake soyewa da ƴar mitsitsiyar yarinyar da a baya yake zage gwanji ya kwaɗe Saboda rumaisa. Komai ya siyo sai ya ce tun da ba ruma wannan na sweet hibba ne. Mai sunan baba ya fara tunanin yi wa iman kyauta, amma sai ya rasa ita da ke wannan gidan mai zai bata ma? Wani irin kallo ma za ta yi masa idan ya bata abu. Unexpected ya ga Mahmud a online, suka gaisa mai sunan baba yake tambayarsa ya mai jiki? Mahmud ya ce "Wace mai jikin?" "Ƙanwarka mana, khadija" sai da Mahmud ya ɗan yi shiru sannan ya tuna sunan iman ne. Ya ce "Ohh tana lafiya, ban ma san ba ta da lafiya ba ai". Cikin mamaki yake tambayar sa ya aka yi bai san ba ta da lafiya ba. Mahmud ya ce "Labarin dogo ne, amma ina da tabbacin jikinta da sauƙi, dan na ganta ɗazu tare da daughter na a garden". Mai sunan baba ya ce "Ina so mu yi magana ne, ban taɓa shiga abun da ba ruwana ba a rayuwata, amma a wannan karon, ko sau ɗaya na ji ina son shiga, kuma ban ji zan iya maganar da kowa ba sai kai" Mahmud ya ce "Ba damuwa, lallai na ciri tuta, bari mu yi maganar ta waya". Mai sunan baba ya kira Mahmud da kansa, Mahmud ya ce "Ina shirin kiranka" Ya ce "Bakomai, ni yakamata na kira dama. A kan Khadija ne, na je asibiti na duba ta, kamar yadda ta gaya mini tana da ciwon zuciya ne, amma kun san da wanda zaku aura mata ba ta son shi? And he is even mad gayen, ba shi da hankali gaba ɗaya, tayaya zai je yana mata shouting a ka a condition ɗin da take, ba tare da ya tausayawa halin da take ciki ba?. Yakamata ku ƙara bincikarta, kar zurfin cikinta ya sa ayi abun da zata cutu" Ajiyar zuciya Mahmud yayi, shi kansa yana tausayin iman, kuma yayi dana sanin abun da ya yi wa ammi lokacin da ta roƙi ya auri iman. Yarinya ce nutsatsiya da ba ruwanta da hayaniya, ita ma ta tashi cikin tsantsar ƙalubalen rayuwa, a wannan gaɓar kan shi ma ya san za ta cutu idan ta auri jabir, dan ya fita baki, kuma ba kirki ya cika ba, ya ji ina ma zai iya yin wani abu a kan lamarin, dan jin kunnensa ya ji jabir ɗin na gayawa mummy, wambai ya san maganar, turaki zaa kaiwa kuɗin auren. Bai gama tunanin ba ya ji muryar mai sunan baba ya ce "Ban taɓa neman alfarma ayi wa wani abu ba, a karon farko na roƙe ka, ko dan lafiyarta" Mahmud ya ce "Kar ka damu, zan san abun da zan yi a kan lamarin in sha Allah". "Masha Allah na gode sosai" Mahmud yayi shiru yana kallon wayarsa, ya nunfasa ya ce "Allah ya sa rabonka ce Malam Umar, ni na yaba da dattakunka" *** Laila ce suke waya da takawa, tana gaya masa ruma ta ishe ta da rashin ji, ita da ɗan ta, yana ta dariya mussaman da ta ce wai ruma ta zana mata aljani ta ajiye a ɗaki, wai hoton takawa. "Anty laila bani shi mu yi magana" ruma tayi maganar tana ƙoƙarin karɓar wayar. Laila ta ce "Ungo ku ƙarata, ban da video call dai, bari na shiga wanka". Ya ce "Budurwar" "Mmm saurayin, ya garin? Ya karatu?". "Alhamdilillah, ya naki karatun, na ji anty laila ta ce tana yi miki lesson, kun kusa fara exams, dan Allah a dage a mayar da hankali" "To in sha Allah, amma ni gaskiya daina zuwa islamiyyar nan zan yi" "Meyasa kuma?" "Ba karatu kawai ake koya mana ba, sai a din ga faɗar wasu maganganu" Tun da ta faɗi haka ya san akwai ƙura, ya ce "Wasu maganganun kenan?" "Wai se malamar ta din ga tsayar da mu, wai za ayi lecture, ka ji abun da take cewa kuwa?, wai a din ga saka ƙanan kaya ana karairaya sai ka ce wasu karuwai, yanzu dan Allah ya dace a zaunar da mutane ana gaya musu haka?" Da ƙyar ya iya gimtse dariyarsa ya ce "Ke ya aka yi ki ka san karuwan ne suke haka?" "Ai in gaya maka, da akwai wani gida a unguwarmu, sai matan su dinga saka riga da wando, ko mini skirt, suna yawo, aka koresu, na ji ana cewa gidan karuwai ne, har da vest fa suke fitowa waje ana kallonsu, na zo ina bada labari a gida, mai sunan baba ya sakani kama kunne, aka ce mini kar in kuskura abun da suke yi ya burgeni, idan mutum yayi irin wannan ba ga muharraminsa ba ɗan wuta ne. Ni fa wani abun ba zan iya faɗa ba ne, wallahi ni duk mutuncin malamr ya zube a idona ma, ni kuwa da ta fara nake tashi na tafi. Da fa sun rainani ba su zata ina da miji ba, sai da malama ta ce musu ni matar aure ce, wai wata ta ce mini, wai zan sai maganin mata? Na ce mata ni ban san shi ba, dan Allah a chemist ana ware maganin maza da na mata?" Ya ce "A'a" "To a in gaya maka, na ce mata ni idan bani da lafiya asibiti ake kaini, kawai ta  nuna mini Wasu ƙulle-ƙulle da robobi mai hoton ƴan iska a jiki, Wai in saya, na rufe idona na ce a'uzubil'ahi, gaskiya ni dai a cireni daga makarantar nan" Maimakon ta ji ransa ya ɓaci kawai sai ya din ga tuntsura dariya, har da tari, laila ta ƙarasa ta ƙwace wayar, ta ce "Ke dai ban taɓa ganin yarinya mara kan gado kamar ki ba? Wai ke baki da ƙawaye ne?" "Nifa ƙawata ɗaya habiba, ko nayi ƙawaye mama korarsu take yi, kuma ko ba ta kore su ba, idan muka yi faɗa duka nake yi musu sai mu ɓata" "Aikuwa wannan karatun, dole na zauna na ɗora miki shi, idan kin ƙi ganewa kuma shi idan ya dawo ya karanta miki yadda zaki fuskanta. Haba ke gaba ɗaya abaibai ce ba kya gane komai kenan". "Anty laila ki daina hantarata, zamu yi faɗa" "To muyi faɗan mana, ke zaki yi wa kanki ai". Rumaisa ta kalleta ta ce "Saboda zaki daina sai mini garin kunun sabayar maman Khadija ko? Ba ita ce a zariya ba lambarta 0703777 7442. Sai maman Ilham mai magani ba da ke cikin garin kaduna kawo road ba, lambarta 08135613021, na riƙe komai tsaf a kaina saboda irin haka". Laila ta ce "Iko sai Allah, ke yanzu zaman hadda ki ka yi kenan?" "Ai Anty laila ba komai ake faɗa mini ba, in dai an yi abu a gabana, tsaf nake haddace komai tas a kan nan nawa". "To kin kyauta, tashi ki je kitchen ki haɗa mana kayan aiki, yanzu zan zo ki gwada mini girkin da na koya miki, in gani idan da gaske kina haddace komai ɗin" Rumaisa ta tashi ta ce "Yanzu kuwa". *** Iman duk ta kuma zama so silent, ba babban abun da yake sanyata farinciki, irin ƙoƙarin jan mai sunan baba da hira, da safe ta gaishe shi, daga nan yayi mata ya jiki. Mutum ne miskilin gaske, tana shan fama, amma wasu lokutan ya kan saki jiki, mussman idan tana yi masa hirar karatun addini. Wani irin matsanancin tausayinta yake ji, da ya tuna Jabir, sai gabansa ya faɗi, ya san duk wani kauce-kaucensa son iman yake yi, gashi shi bai san ta ina yakamata ya fara ba, bai san meya kamata yayi mata ta din ga farinciki ba, saboda shi ya saba da bosy life, ba wasa. Rumaisa ce a tsaye a banɗaki za ta yi wanka, tana ƙarewa kanta kallo a mudubin banɗaki, har da tsalle tana ɗan juyi, ganin abun arziki ya fara fitowa, yana cika. "Wayyo daɗi kasheni, zan wuce gori da wulaƙanci, na ga me sake ce mini ƙwaila, kai za a ga jan aji idan suka ƙara girma, wayyo ni maman Khadija da maman ilham sun kankaro ni yasin" Ta gama wankanta, ta fito ta shafa mayukan gyaran fata, ta saka kaya, ta kuma tsayawa tana kallon mudubi, ta ce "Hmmm, na ga wanda zai sake ce mini ƙwaila, mu haurata da shi, har shi papan, yanzu dai sun fi ƙarfin murfin jarkar faro" Ta ɗaga kai ta kalli zanenta, da take kansile date kullum, na kwanakin da ya rage ya dawo. A hankali ta furta "Lokaci baya sauri". Ammi fa gaba ɗaya ta ji batun auren nan na iman da jabir ya fita daga ranta, kuma ta bi maganar rumaisa cikin tsanaki, taga lallai gaskiya take faɗa, ta sanyawa ranta aure lokaci ne, bai kamata ta jefa rayuwar iman cikin hatsari ba. A wannan zullumin turaki ya kirata, ya sanar da ita, wambai ya ce masa zai kawo wa jabir kuɗin aure. Takanas ammi taje gida, ta iske turaki, ta nemi ya taimaka a janye maganar nan. Turaki ya ce "Giwa saboda ne, kin fi kowa sanin halin wambai, daga ni har ke ba zai saurara mana ba". Nan ammi ta yi masa bayanin komai, tuntuni ta so ta yiwa wambai maganar, amma ta san ba zai saurareta ba, turaki ya gamsu da maganganunta, dan ya san halin hajiya Lubabatu sarai, za ta aikata fiye da haka, ga yarinya na fama larura. Dan haka ya ce shi da ita yakamata su je wurin wamban, su yi magana da shi. Ammi kamar ta ce ba sai sun je tare ba, saboda tana fargaba wambai ba ya yinta ko kaɗan. Amma yadda ta iya, tun da suggestion ɗin turaki ne. Aikuwa kamar yadda ta tsammata, wambai ya balbalesu da faɗa ta in da ta shiga ba ta nan yake fita ba, ya din ga masifa. "Kana bani mamaki turaki, da ka ke biyewa matar nan, dan kawai tana sirikarka, ke ba abun farincikin ki bane ba, kamar jabir zai auri yarinyar da ba wanda ya san iyayenta sai ke da mijinki a da'awarku. Nagartaccen yaro mai daraja daga gidan sarauta, sau nawa ana shirin aurenta ana fasawa, saboda wannan abun kunyar?". Turaki ya ce "Allah ya baka yawan rai, ba jabir ɗin ake gudu ba, ita mahaifiyarsa da ta je har gida, ta nuna bata son abun, ta ci musu mutunci har yarinyar, wanda sai da ciwonta ya tashi, ita ma fa ƴa ce Allah ya baka yawan rai" "Ita lubabatun ce ta ce ba ta son auren, bayan mun gama magana da ita?" Da mamaki ammi ta kalleshi, sannan ta ce "eh, har gida taje ta ce mini ba ta so" Wambai ya kira wayar hajiya Lubabatu, amma cike da ƙwarewa a mugunta, ta hau salati ta ce ƙarya ne, kawai dai giwa ta ce ba zata bawa jabir auren Iman ba, amma ita ba ta ce ba ta so ba. Masifar da wambai yake yi, tuni idonta ya cika da hawaye. Turaki kansa ya san sharri ne, da tsabar mugunta, irin na hajiya Lubabatu. "Tun da abun naki haka ne, ba kara ba mutunci a cikinsa, ai dama a kwanakin baya, da ake ta surutu a kak yarinyar da takawa, na ce lallai ki aurar da ita, to zan sake jaddada miki, nan da watanni uku, ko dai ki aurar da yarinyar nan, ko kuma ki mayar da ita in da ki ka tsinto ta, kuma a wannan karon ba zan canza magana ba. Sannan abu na gaba, ƙara tayi yawa a kan wannan yarinyar sirikarki, daga zuwanta gida tana yi wa mutane sharri, tana haddass husuma, jamila ta kawo mini ƙara, na so na zauna da ku, ta ce a bar maganar, still na samu labari a kan tana yayaya cewar jamil ne ya saka aka yi garkuwa da ƙanwarsu, to ahir ɗin ta, ki ja mata kunne, gidan sarauta ba wurin wasa bane ba" Ammi ta risunar da kai sannan ta tashi ta bar ɗakin, ranta babu daɗi, yayin da tausayinta ya mamaye zuciyar turaki, tana da kyakywar zuciya, sai dai tana ta fuskantar ƙalubale kashi-kashi a rayuwarta da ta iyalanta. Yanayin yadda ammin ta dawo ne ya tabbatar musu akwai damuwa, har ruma za tayi magana, amma laila ta hanata. Yau wunin yau idon mai sunan Baba yana kan waya, ko zai ga saƙon iman, amma shiru, shikuma ya kasa yi mata magana, har dare shiru, gashi ya riga ya saba da daddare ɗan jan sa da take da hira, yana yi masa daɗi. Haushi ne ya ishe shi, jin yadda Aliyu ya cika masa kunne da surutu shi da habiba, ya saka waya a speaker sai ƙyalƙyala dariya yake yi, habiba ta karkace murya tana yi masa waƙa, murya kamar an shaƙe kuliya. "Kaga ka cika mini kunne, ko dai ka fita, ko kayi mini shiru. Aliyu ya miƙe tsam da wayarsa, ya koma tsakar gida, duk da sanyin da ake zabgawa. *** Jabir ne a zaune, hajiya Lubabatu da Mummy sun saka shi a gaba, suna ta yi masa famfo. "Na sha gaya maka giwa ba ƙaunarka take yi ba, ka din ga nane musu, to gashi ƙiri-ƙiri ta hanaka auren ƴa, saboda azabar ƙarya ta je ta ce wai ni ce bana son auren nan, mun yi haka da kai? Da na nuna bana so ka dage, cewa nayi Allah ya sanya albarka, amma da yake mukafuka ce, ba ta yi niyyar baka auren ba, ta je ta ce nice bana so". Mummy ta amshe ta hanyar cewa "Banda abun jabir, kai da ake yi wa fafutukar samun kujerar mahaifinka, ina kai ina wata ƴar tsintuwa, mara asali mata gata, kai ana ƙoƙarin ka samu kujera, amma ka nacewa Adam, shi ka san me suke yi ta ƙarƙashin ƙasa, dan ganin kujerar ta koma garesu, ga mata nan bila adadin a gari, ni ko ruƙayya ma sai na baka" Hajiya Lubabatu ta ce "A'a wace irin ruƙayya kuma? A dai cigaba da neman kujerar, shima uban nasu ban taɓa tunanin zai kai haka a raye ba, kalli shi adam ɗin da kake liƙewa, yadda yayi suna a ƙasar nan, duk gaku matasa amma aka ware shi, aka tura shi wakilci, yayi aure ya haifi ɗa, ga aikinnsa ga kasuwanci, kai kana nan kana fama daga kai har jamil ɗin uwar me ku ke da shi, duk da dukiyar iyayenku ku ke taƙama" Jabir yayi shiru tare da gazgata maganganun da tun a baya su mummy suke gaya masa bai ɗauka ba, tare da mantawa da asirin da takawa ya daɗe yana rufa masa tsawon shekaru. Mummy kuwa ƙulattar Hajiya Lubabatu ta yi, da ta ce ya auri ruƙayya ta ce a'a, wato a tunaninta ya samu mulki, aci moriyar ganga a yada kwauronta. Mummy a ranta ta ce 'Lubabatu baki da hankali, da ni ki ke zancen, lokaci yayi da zamu raba gari, kowa ya san in da ya kama'. Kasa jurewa mai sunan baba yayi, ya fara tunanin ko jikin iman ne ya dawo, dan haka da kansa ya kira iman a waya. Sallamar da yayi ta amsa cikin siriryar muryarta. "Jikin ne dai?" "A'a barka da safiya yaya umar" "Meyafaru?" "Bakomai" tayi maganar cikin sauke numfashi. "Something is going wrong, feel free to share it with me" "Yaya umar ba zan dameka da matsalolina ba?" Cikin nutsuwa ya gyara zamansa ya ce "If you are free with me, let's share it together" Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta yi ta ce "An yi cancel ɗin engagement ɗina da za ayi". "Ba abun da ki ke so kenan ba?" "Ba cancel ɗin ya dameni ba, tun da Allah ya sa na buɗe ido a hannun ammi, take bani kariya da nuna mini ita ta haifeni, amma mutanen da suke kusa da ita, basu bata goyon bayan hakan ba. Saboda ni ba irin tashin hankalin da bata shiga ba, kullum cikin damuwa take, kullum cikin sintiri kaini asibiti, kullum cikin neman abun da zai sani farinciki take,. Amma ni na kasa kawo mata farinciki ko sau ɗaya. Ban san dalilin fasa Engagement ɗin ba, mai girma wambai ya ce ko tayi mini aure nan da watanni uku, ko ta mayar da ni in ta tsinto ni, babban abunda ya dameni kukan da ammi ta sha, ta ce da ta rabu da ni, gara ta ɗauke ni mu bar gidan, ni rasa me ma zan yi, ina son ammi amma ba zan so ta bar gidanta ba". A tsakiyar zuciyarsa ya din ga jin kukan iman, ya jingina jikinsa da bango, wata irin karaya ta kama shi. A hankali ya ce "Khadija, kukan nan yana taɓani sosai, bana son jin kukan mace, ko ban santa ba, zamu yi waya anjima. Amma dan Allah bana son sake jin labarin kina asibiti, ya isa haka" A hankali take sassauta kukan, ta ce "Yaya Umar, na gode da ka bani dama ka ji abun da yake damuna, na gode sosai" "Don't mentioned, ki ci abinci ki kwanta ki yi baccinki, ki cigaba da addu'a, ba abun da zai faru sai ikon Allah khadija" shi kansa mamakin yadda ya tausasa murya sosai yake, bai taɓa zaton ya iya rarrashi haka ba. Rumaisa kuwa Mahmud ta kira a wayar Anty laila, ta ce tana son ganinsa a in da suke haɗuwa. Babu jimawa kuwa suka haɗu, sai dai cikin tsananin fushi ruma ta ce "Daddy anya mummy na son taga Annabi kuwa, daga ita har babar jabir fuska kamar an mari biri? Ya za ayi ta zo ta ce ba zata bari ɗanta ya auri Iman ba, ammi ta ce a fasa a janye, ta ce ita ƙarya aka yi mata ba ta faɗa ba? Ammi sai kuka take yi, har da masu kiranta a waya, ana bata kyauta ba, ta hana jabir iman, gashi wambai ya ce idan ba ta aurar da iman ba ta mayar da ita in da ta tsinto ta, wai ya suke so baiwar Allah nan tayi ne, daga ita har Iman ɗin sai koke-koke suke yi, wai kai ba abun da zaka iya yi a kai? To ni zan je wurin wamban sai na tonawa kowa asiri da kaina, ayi wadda za ayi ta ƙare! Ayshercool. 08081012143 *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 *TALLA! TALLA!! TALLA!!! *ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH* Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.” Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi. Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH…. (*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*) Cikin hanzari Mahmud ya ce "A'a rumaisa kar ki ce zaki yi wannan gangancin, Mummy ta fi gaban yadda ki ke tunani" "Shikenan saboda ana tsoron ta, sai a zuba mata ido ta yi ta abun da ta ga dama? Tayi ta yi wa mutane fuska biyu" "Kina da gaskiya rumaisa, amma Mummy ta wuce tunaninki, ki bi komai a sannu, kar aikin da muke tayi ya rushe, ina ƙara baki haƙuri, komai zai wuce dan Allah kar ki rusa mana aiki". Rumaisa tayi ajiyar zuciya tare da share hawayen da ya taru a idonta. Ta ce "Shikenan, akwai Allah ai". Mahmud ya numfasa ya ce "Haka ne. Ammm rumaisa" Ta ɗaga kai ta kalleshi. "Ya aka yi ki ka san zancen filin turaki, har ki yi wa jamil maganar, na ji zancen a bakin jabir, yana yi wa mummy". "Wai shi jabir ɗin nan wane irin munafuki ne?" Mahmud ya ce "Kusan duk bakinsu ɗaya, kuma Mummy ta fara saka mini ido, shiyasa nake son ki din ga haƙuri, komai zai zo ƙarshe in sha Allah" Ta jinjina masa kai, ta juya za ta tafi ya ce "Na ce ba" ta tsaya ta waiwayo. "Ya ake ciki game da iman?" "Kana da labari ai, ko ayi mata aure nan da watanni uku, ko a mayar da ita in da aka tsinto ta, haka Wambai ya ce". Mahmud ya ce"Ina ga rabon abokina ne ya rantse". "Wa kenan?" "Yayanki umar" rumaisa ta kalleshi ta ce "Kana nufin ka san yana son iman?" Ya ce "Na sani" Ta waro ido ta ce "Ya aka yi ka sani?" "Actions ɗin sa sun nuna mini, kina ganin zai iya auren iman nan da watanni uku?" Ruma ta yi shiru sannan ta ce "Daddy, rayuwa a ƙasarmu akwai wahala sosai, yaya umar ya sadaukar da rayuwarsa a kan inganta tamu, ya riga yaya Abubakar gama karatu, ya koma master's. Yanzu an kaiwa yaya Abubakar kuɗin aure, ya ce ba shi da shirin aure shi yanzu, dan haka ya mayar da hankali a kan ginin yaya Abubakar sosai, ya bar nasa, ga yaya Aliyu shima ya ce za a kai masa kuɗin gaisuwa, duk da yaya umar mutum ne mai zafi, amma kullum burinsa mu cigaba, duk wanda ya raɓe shi zai gane hakan. Sun haɗa gwiwa, sun buɗe shagon sayar da takalma, shi da wani cousin ɗin mu, yana da ƙoƙarin neman na kansa, amma duk mu muke cinye komai, ba shi da komai a sanina, daga filayensu da aka ce tun kan babanmu ya rasu ya sai musu, ya fara gina nasa ya ajiye, sai babur ɗin sa, dan ma yanzu yaya Huzaifa yana ɗinki, Yasir harkar wayoyi yake, yaya Umar ba zai iya auren iman nan da wata uku ba gaskiyar magana". "Kina ganin zai amince ayi supporting ɗin sa daga nan ɓangaren mu?" Ruma ta ce "Taɓ, ba zai yarda ba gaskiya" Mahmud ya ce "I see" "Amma ya dai rarraba takardunsa, amma dai bai samu aiki ba. Daddy dan Allah idan da yadda za ayi, ka tayani ya samu iman, yana sonta sosai, amma ban sani ba ko za a bashi ita". "Zasu bashi, zan san abun yi". "Na gode sosai Daddy" "Ni yakamata na yi miki godiya daughter" Rumaisa ta yi murmushi, ta tafi. Kamar wutar daji, haka aka cigaba da yi wa ammi surutu, na bata da halacci, duk irin ƙaunar da Jabir yake nunawa ɗanta, amma ace ta kasa bashi ƴa. Laila ta din ga bata ƙwarin gwiwar ta daure, ta kawar kai, kada ta tankawa kowa. Tsananin tausayin iman da Mai sunan baba yake yi, ya sanya kusan kullum sai ya kirata ya rarrasheta, ya bata baki, sai dai ya shiga zullumi shi dai ya san bashi da halin aure a nan da watanni uku kawai, duba da auren Abubakar suke ta shiri, kuma yana jin yadda yake ƙara so da tausayin iman, ba shi da burin da ya wuce ya ganta a kusa da shi, ya gatan ta ta, ya bata kulawa. Babu kunya babu tsoro, jabir ya kira Adam a waya, ya ce da haɗin bakinsa da na matarsa aka hana shi auren Iman. Takawa ya ce "Jabir ni da nake nan, ya za a yi na ziga cewar a hanaka iman" "Saboda tun asali da na zo maka da zancen, ka ce baka so" "And you keep going, ka dage sai ka aureta, ai Allah ba azzalumin sarki bane ba jabir, kuma shi Allah na kowa ne, tun ina nan aka fara maganar nan, sai dai bance komai ba na cigaba da yi wa iman addu'a da fatan alkhairi" Jabir ya ce "Dole ka faɗi haka Adam, a duniyar nan waye ba ya yi wa Allah laifi?" "Idan ma so kake ka ce ina aikata wani abun a ɓoye nima, ɗan adam ne ni, amma na san dai bai kai naka muni ba jabir". "Na gode sosai da sosai Adam, tukuicin ƴan uwantaka kenen, na gode ka nuna mana iyakarmu daga ni har Jamil, saboda ka auri wannan yarinyar, har ni za ta gayawa ban isa na auri iman ba, tun da yayanta yana son iman, kun kyauta" ya kashe wayar sa. Adam ya dafe goshin sa ya ce "You again mimi? Subhanallah" Ammi kuma rarrashin iman ta din ga yi, da nuna mata komai na Allah ne, kuma yana da iyaka, dan haka ta kwantar da hankalinta, a wannan karon ma kalaman Wambai barazana ce kawai. Kwanci tashi asarar mai rai, takawa ya cika watanni biyu cif da yin tafiya. Kullum idan ya kira video call zai ga kowa amma ban da rumaisa. Yau laila ta cewa rumaisa za ta yi video call da takawa, rumaisa har da tsalle tana murna, laila ta yi dariya kawai. An samu improvement sosai a game da rumaisa, dan yanzu tana iya turancin laila, tana ganewa har tana iya yi mata reply, sannan ta sakata ta rage tsalle-tsalle. Sai dai bakin nan yana nan, sai ma abun da yayi gaba, tsiwa da rashin mutunci ma ba ta fasa abun ta ba in dai an taɓa ta. Tun da ruma ta dawo gidan da zama, Samha ba ta sake zuwa sashin ammi ba, wurin Mummy ta daina zuwa gaba ɗaya. Laila da kanta ta yi wa rumaisa light makeup, suna yi suna faɗa, ita ba za ayi mata ba, dan haka a hoda da jambaki kaɗai kwalliyar ta tsaya, ta tafi amsa waya rumaisa ta gudu. Sai da ta je ta kuma nemo ta har da murɗe mata kunne, ta ce idan har ba ta daina taurin kai ba, to wayar ma za a fasa yin ta. English wears ta bawa rumaisa ta saka, wando da rigarta body hook mai kyau, ta gyara mata gashin ta sosai, sannan ta kalli ruma ta ce "Banda shirme da shiririta, kin san dai abubuwan da na koya miki ko?" "Ni wallahi kunya nake ji" Laila ta ce "Ba zaki yi ba kenan?" Ruma ta ɗan turza ƙafa ta ce "Anty laila wallahi kunya nake ji". Laila ta rufe system ɗin ta ce "To a fasa wayar" Tayi sauri ta riƙe ta, ta ce "A'a kiyi haƙuri" "Idan baki yi ba, ni da ke ne" Fuskar laila ya fara gani, ya ce "Madam haka muka yi da ke? Ina budurwata ne?" "Wai wani irin shakiyanci ne haka? Wani budurwarka?" Rumaisa sai so take ta leƙa ta hango shi, amma laila ta hanata. Ya ce "Eh, ba ta zama matar ba tukun, yanzu dai buruwata ce kamar yadda muka tsara, so muke mu ko yi soyayya mu ji me ake ji" "Papana" "Mimina" ya amsa tare da cewa "Laila hasko mini matata laila" Tura wa ruma system ɗin ta yi, hannunta riƙe da kofin kununta, ta ce "Papa, Innalillahi yaushe rabon da na ganka? Ka yi ƙiba" tayi maganar tana dariya. Ƙura mata ido yayi yana kallon ta, ta ɗan yi saroro ta ce "Ba network ne naga ka ƙame?". Tuntsirewa da dariya yayi, ya ce "Ciko ki ka fara ne?" Tayi turus tana tunanin cikon me?. "Cikon me?" Ta tamabaye shi cikin rashin fahimta. Laila ta ce "Takawa ka raina yarinyar nan da yawa, ka yi a hankali fa, kar ka zo kana mata kuka". "Anty laila dan Allah me yake nufi, cikon me na yi?" Adam ya ce "Madam ba ruwanki, ki ƙyalemu, mimi juyo sosai mu gani inyee". Ba ta san me yake nufi ba, ta ce "To ka gaya mini, cikon me?" Takawa ya ce "Don't mind me, me ki ka sha a kofi ne?" Ta ce "Hmm ka san me?" Daƙuwa laila tayi mata da hannu, tana girgiza mata kai. Ruma ta ce "To ba zan gaya maka ba, tun da dama baka gaya mini cikon me nayi ba". Wani lumshe ido yake yana dariya. "Why are you laughing at me ne?" Tayi maganar tana wani lumshe masa ido da shagwaɓa. Ba shiri ya tashi zaune, laila ta jinjina mata 👍. Ya ce "Kaii, mimi wannan turanci haka, kar ki sa in dawo yanzu, wannan kashen idon fa, ni wannan al'amarin ne kaina ya kulle, ya daga tafiyata wata biyu kawai, in ga abu unexpected gaskiya ban yadda da ku ba. Kin ƙara ƙiba kin yi kyau, boy ma naga sai wani kumatu yake yi. Kin ga yadda kayan nan suka yi miki kyau, rabon da na ga ko kwalli a idonki tun ranar biki, kamar na zuro baki nayi miki kiss" Rufe baki tayi tana kallon anty laila, dan tana zaune a ƙasa. "Daina juyawa kina kallonta, juyo sosai ni zaki kalla, so nake na tantance abun nan gaskiya ne, ko kuma yaudarata ake so ayi?" "Wai me?" Rumaisa ta yi maganar cikin rashin fahimta, dan duk ba ta san akan me yake magana ba. Ya ce "Zauna sosai, mana in ganki da kyau, juyo sosai". "To ni ka daina yi mini wannan kallon mana, Allah zan kashe". Sosai takawa yake dariya, ya ce "Laila you must explain this, you want scam me ba?". Laila ta ce "Za ka ga scam ganin idonka, time off sai wani lokacin kuma". Takawa ya ce "Wane time off kuma, laila zan kai ƙararki fa, ban gama ganinta ba, mimi look at me na" yayi maganar yana dariya. "Papa ina ta so in ganka amma ka sakani a gaba sai dariya ka ke yi, kamar kaga comedy, shikenan ba zan ƙara video call ɗin da kai ba". Ya ce "Haba little mimi, farinciki ne ya isheni na ganki, kar ki bar laila ta haɗamu, da na dawo zamu tafi honeymoon, mu yi spending so much time together, mu fanshe tsawon lokacin da muka yi bama tare, mu buga ball tare, mu yi gudu tare ko?" "Eh kuma zaka goyani ma" Dariya yake sosai ya ce "Ba zaki canza ba ai" Ta ce "yauwwa meye honeymoon, zuma da kuma wata kenan?". "Eh duniyar wata zamu je, mu sha zumar soyayya" Ta buɗe baki ta ce "Innalillahi, soyayya har na ji kunya" laila ta kashe system ɗin ta ce "Sarkin shirme, sai kuma wani lokacin". Adam kuwa dariya ya cigaba da yi ya ce "Daga tafiyata anya laila tana da gaskiya? Allah ya kaimu na dawo gidan. Mimi rigima". *** Mai sunan baba ga damuwa ta addabe shi, amma ya rasa da wa zai yi sharing ɗin ta, ya kasa gayawa kowa, sai ƙumbiya-ƙumbiya yake yi. Har gara Mahmud, ya ɗan saki jiki ya ce masa, da yana da hali da ya auri Iman. Sai dai a hankali yake ƙara shaƙuwa da iman, yake kuma sake fuskantar ta, ita a rayuwarta sam ba ta ɗauki duniya da zafi ba, komai nata simple ne. Waya yake yi da ita, zuciyarsa na azalzalarsa a kan yayi proposing ɗin ta, amma bai san yaya za ta kalli abun ba. Tana ta yi masa zancen shirin da suke yi a kan bikin saukar Alqur'ani da za ta yi. "Yaya ake ciki game da maganar aurenki, kin samu wanda zaki aura nan da 3months ɗin ne? Na ga you are calm now". Ta numfasa ta ce "A'a yaya umar, kamar yadda ka bani shawara ne, na barwa Allah komai ina ta addu'a, na san ya isar mini, na cigaba da gudanar da rayuwata" "Duk cikin samarin naki, ba wanda zaki zaɓa ya fito?" Iman ta ce "Ni bani da saurayi" "Ban yadda ba". "Yaya umar na daina soyayya, idan Allah ya kawo aure kawai zan yi, dama wasu wai an ce dan ina da kyau suke so na, idan suka ji bani da asali sai su fasa, wasu kuma dan ina gidan sarauta, idan suka ji bani da nasaba da sarauta sai su fasa". "Mhmm ke baki yadda ki na da kyan ba? You are beautiful, ban taɓa cewa abu yayi kyau ba, amma na yadda Khadija mai kyau ce" Iman ji tayi ya fasa mata kai, wani murmushi ya suɓuce mata, ba ta taɓa zaton mai sunan baba yana magana haka ba. "Khadija" "Na'am yaya umar" "Ina son ganinki, zamu yi magana" Kasa ɓoye farin cikinta tayi, ta ce "Yaya Umar yaushe zaka zo?" "Zan zo in anjima da yamma, ina fatan ba zan janyo miki matsala ba?" "A'a ba matsala, Allah ya kawo ka lafiya" bayan ya kashe wayar ta ce "Allah ya sa ya ce yana so na, am already in love with you yaya Umar". Ammi ta samu a ɗaki, ta sanar da ita cewar za tayi baƙo, ammi ta ce "To shi kuma wanene?". "Ammi wani ne" "Iman, kar dan saboda wambai ya faɗi wannan maganar, ki je ki jajubo wanda ba mutumin kirki ba, dan ke ki ka ce ba zaki sake kulawa ba". "Ba haka bane ammi, kawai dai na ji yakamata na sake bawa wani dama, ban sani ba ko za a dace" Ammi ta ce "To shikenan, Allah ya jishe mu alkhairi, na san dai za ayi surutu, ki kai muku kujera ta bayan sashin nan. Ni da kin gaya mini da wuri ma, da ba zan bari ki kawo shi gidan nan ba, kar aje a ɓata lamarin, Allah ya kawo shi lafiya. Ni dai ina sake gaya miki, ba a garaje a wurin zaɓar miji iman, kar takura da matsi, su sanya ki yi zaɓen tumun dare ". "To ammi in sha Allah" Kamar wannan ne karonta na farko da zata fara zance, murna da nishaɗi kawai take yi. Nusaiba ta kalli yadda take ta shiga tana fita, tana haɗa masa abun da za ta karɓe shi "Lallai da gani wannan baƙon na musamman ne, yayi awon gaba da zuciyarki da yawa" Iman ta yi murmushi ta ce "Anty Nusy kenan". "Iman kiyi haƙuri, a baya nayi ƙoƙarin goyon bayan uncle J, duk da ba kya son sa, sai daga baya na fuskanci lallai, akwai ƙalubale idan ki ka aure shi, na yadda da maganar rumaisa, wanda bai tausayawa mahaifinsa ba, yaushe zai tausaya miki. Kin san kodayaushe ni mai sonki ce, ban so ki da jabir, dan muzguna miki ba my Iman" Iman ta tura baki ta ce "Gaskiya i feel bad, na ga kamar yayata ta daina so na, ba ta son abun da nake so" Nusaiba ta dafata ta ce "Haba my iman, ke kin san ban da kamar ki, kawai dai wanda ki ke so ɗin ne, nake ganin kamar baku dace ba, ya fiye tsauri da jin kai. Kuma bana son mutane su yi miki dariya, ace duk wannan gwagwarmayar baki auri mutum na mussaman da zaki samu kwanciyar hankali ba, ba dan ina ƙyamar sa ba, amma kin san zaku fuskanci ƙalubale" "Anty Nusaiba ba yadda ki ke tsammani bane, mutumin kirki ne, ba wulaƙanci ne da shi ba, miskili ne, ba jin kai ne da shi ba, kama mutunci ne da rashin son raini, amma mutum ne mai tausayi sosai. A yanzu ba dukiya nake nema ba anty nusaiba, kwanciyar hankali da soyayya.ki yi mini Addu'a, idan shi ne allhairina, Allah ya tabattar mini, amma kar ki gayawa ammi tukuna, sai yazo yau na ji me zai ce mini" "Kar ki damu, ina yi miki fatan alkhairi ko yaushe ƙanwata". "Na gode yayata ta kaina" Nusaiba ta yi murmushi ta fice daga kitchen ɗin. Zaune suke a kan fararen kujeru, cikin yanayi mai daɗi, sai dai an rasa wanda zai yi magana, kasancewar shi wannan ne zuwansa na farko zance, ita kuma yayi mata kwarjinin da ya saba, ko ɗaga kai ta kasa, sai kallon wuri ɗaya kamar mara gaskiya. "Ki yi tayi mini surutu a waya, har na rasa abun cewa, amma yanzu kin sakani a gaba kina sunkuyar da kai, kamar kinga dodo, daga gaisawa kin yi shiru". Muryar nan ba ƙaramin narka mata zuciya take yi ba, murmushi ta kuma yi ta sunkuyar da kai. "Shikenan, Khadija ɗago in gaya miki dalilin zuwana wurinki" da ƙyar ta ɗan ɗaga kai. "Kallona zaki yi, bana son na yi miki dole, ko kiyi mini alfarma, dan kina jin kunyata ko ta ƙanwata, ni wannan abubuwan duk ban san kan su ba, ban taɓa gwadawa ba ma. Amma na ji ina son na aureki, zaki iya auren talaka kamata?" 'Na ji ina son na aureki, baya sona kenan, ko tausayina kawai yake ji' ta tambayi kanta. "Ba kya son talaka ko?' Ta girgiza masa kai alamar a'a. "Talk" "A'a yaya umar" tayi maganar muryarta na rawa. Umar ya ɗan tsura mata ido ya ce "Ba takura miki nake ba, tambayarki kawai na yi, idan ba zaki aurena ba, ba wani abu, ban san meyasa nake baki tsoro ba, rumaisa ma da muke faɗa, ba ta ji ne, but am good person ko?" Ta ce "Yes you are". "Zan tafi, duk hukuncin da ki ka yanke ki gaya mini, ba wani abu" Ledar hannunsa ya ajiye mata, ya tashi yayi tafiyarsa, ta daɗe a wurin tana tunani, daga baya ta yanke, ko baya son ta, ko iya tausayin nata yake ji, zata iya aurensa, tun da shi baƙin tabonta, bai hana shi cewa zai aureta ba. Ammi bata matsa mata a kan sanin lallai waye ba, sai dai rumaisa ta din ga cewa ƙamshin turaren mai sunan baba take ji. Turaruka ne masu kyau, guda uku da dabino lubiya manyan kwali guda uku. Har aka yi sallar magariba, ta kira shi ta sanar ta yi masa ya yaje gida, jikinta a sanyaye yake, ya ce mata yaje lafiya, daga nan ba wata magana suka yi sallama. Suna zaune a falon, suna kallo, suna taɓa hira, laila ta kora rumaisa ta je tayi karatu, dan jarrabawa suke yi a makaranta, ammi ta fara tambayar iman, wai waye baƙonta ya kuma suka yi da shi?. Sai dai kan iman ta kai ga yin magana, Mahmud ya shigo tare da yin Sallama. Masu gadi suka shigo da ruwa carton biyar, lemo carton biyar, ya ƙarasa gaban iman, ya bata envelope ya ce "Gashi nan in ji umar, ya ce a baki, ba yawa ki rage wani abun, na bikin saukar ki" Kallon Mahmud take, dan ba ta fuskanci wani umar ɗin yake nufi ba. Ganin kallon da take yi masa ya sanya ya ce "Wanda ya zo wurinki ɗazu" sai ta sunkuyar da kai tana jjya envelope ɗin. Laila ta ce "Iman, sai ɓoye-ɓoye ki ke yi, yakamata ayi mana ƙarin haske a kan wannan da yayi wuf da zuciyar taki" tayi maganar cikin wasa. Mahmud ya kalli Ammi ya ce "Allah ya baki yawan rai, ko zan iya magana da ke?" Jiki na rawa ammi ta ce "Ni, eh mana Mahmud mai ze hana". "Daddy ba Allah ya baki yawan rai ba, Ammi zan iya magana da ke dan Allah?" Rumaisa ta faɗa lokacin da ta fito, yake neman izinin magana da ammi. Bai ce komai ba ya ɗan murmusa, ruma ta ce "Waye ya kawo mana lemo?" Ammi ta sake mayar da hankalinta kan Mahmud ta ce "ko ciki zamu shiga ne?" Ya ce "To" Sashinta ya bita, tana gaba yana baya, zuciyarsa na yi masa wani irin ɗaci, yaushe rabonsa da taka wurin nan, har ya manta, yau gashi a dalilin rumaisa, yana ta kokowar farkawa da nannauyan baccin da yake tsawon shekaru. A ɓangaren ammi ma haka ne, dan fes take tuna lokacin da aka ƙwace mata shi, ta ƙarfin tsiya. A bedroom ɗin ta suka tsaya, ta ƙarasa ta saka hannunta, tana sake kaɗe masa makeken gadonta, da yake a ɗame da bedsheet fes da shi ta ce "Bismillah zo ka zauna" Ya nemi wuri ya zauna a ƙasan carfet, ya ce "ki zauna, ni nan ya isa" "To nima bari na zauna a nan ɗin, ai ba wani abu" ta zauna a ƙasa kusa da shi. Ya kalli fuskar Ammi, da ta rasa in da zata saka kanta dan daɗi, farincikin ta ya kasa ɓuya, sai ƙoƙarin mayar da hawaye take yi. Ya kawar da kai kamar bai ga komai ba ya ce "Dama na ji abubuwan da suke ta faruwa ne, da abun da wambai ya ce game da iman. Dama abokina ne yake son iman, kuma shi talaka ne, bai tara dukiya ba, amma ɗan mutunci ne, kuma na yadda da kirkinsa, sanin kowaye iman ɗin zata gaya miki, ya ce a tambayeku, zaku bashi ita, amma nan da watanni uku yayi masa kaɗan ya shirya, ku bashi kamar wata biyar, idan sun dai-daita, zai turo". Ammi ta ce "In dai bashi da wata matsala, kuma ya san wacece ita, ba zai wulaƙanta mini ita ba, ba damuwa, zan iya ɗaukar ɗawainiyar komai ni nayi masa". "Abu ne mawuyaci ya yarda da haka, amma na san zai yi iya ƙoƙarin sa a kan kula da ita." "Dama ni haka nake fata, Alhamdilillah, Allah ya yi maka albarka kaima, da nuna kulawa a kan abun da ya dameni. Na ji ka kammala karatun ka, Allah yayi muku albarka. Ya albarkaci abun da ka karanta, Allah ya sa ka koma bakin aikinka lafiya, Allah ya haɗa mana kanku gaba ɗaya ƴaƴan galadima". "Amin ammi na gode" ta ji ya tashi ya nufi hanyar fita, daf da zai fita ya jiyo sheshsheƙar ammi, amma ina bai juya ba, ya fita shima yana zubar hawaye. Ganin ya fito yana kuka, har rige-rigen shiga wurin ammi suka yi. Ruma ta ce "Ammi, me yayi miki me ya ce miki? Ɓata miki rai yayi?" Laila ma tambayoyin ta shiga jero mata, amma ta riƙe hannun ruma ta ce "Bayan tsawon shekaru, da fidda ran ɗa na zai sake kallona a matsayin uwa, ya kirani da ammi rumaisa, ɗa na ya kusa dawowa gareni, duk ƙoƙarin ki ne rumaisa na gode" Rumaisa kasa riƙe hawayenta tayi, ta fara sharewa ammi nata ta ce "Haba ammi, idan kina kuka mu idan mun yi wa zai rarrashemu. You are a good mother, you deserve to smile. Idan ana maganar jajurtattun iyaye a duniya, da mama da ke, bani da na biyun ku ammi" Ammi ta rungume rumaisa tana ta kwarara mata addu'a, da ita da iyayenta. "Tabbas duk wanda zai ce sirikata ba ta ji, to bashi da gaskiya ne, ina alfahari da ke ƴa ta". Laila ta ce "To, ammi abun har da wariyar launin fata? Kan dai ki samu sirikar taki, mu ki ka fara sani". Nusaiba ta ce "Muna zaune ta yi mana wayo, ta ƙwace mana ammi ba". Bisa kasada umar yayi proposing ɗin Iman, ba dan yana da abun da zai aurenta ba, sai dan son da yake mata da tausayinta da yake ji. Laila tana zaune suna hira da ammi, laila ta ce mata tana son zuwa gombe, idan zasu tafi suje tare da rumaisa da Iman, ammi ta amince da hakan. Ta ɗan numfasa ta ce "Laila ko iman ta gaya miki wani abu game da baƙonta ne? Haryanzu ba ta ce mini komai ba, waye daga ina yake da sauransu, Mahmud ya ce mini abokinsa ne, ta yarda ta amince tana son sa" Laila ta ce "Ahh ammi, ba yayan rumaisa ba ne, ni dai alamu sun nuna tana son shi, lokacin da ta kwanta a asibiti na ganshi, yana nan mai kama da ruma sosai" Ammi ta ɗan waro ido ta ce "Mai sunan baba wai?" "Eh ina ga shi ne" Ammi ta ce "Ikon Allah, abu kamar wasa, dama tsorata tan da yake yi na soyayya ne. Na yaba da tarbiyar gidansu rumaisa, mahaifiyarsu jajirtacciyar uwa ce, amma ina jinjina lamarin nan, anya iman za ta iya da shi, kamar boss haka yake, ba fara'a baya son mutane, mamansa na yawan faɗar zafin ransa". Laila ta ce "Ammi ki yi musu addu'a kawai, ke ba ga ɗanki nan ya samu dai-dai da shi ba, duk nasa zafin kan kalli yadda rumaisa ke sola shi yadda take so, tun da ya iya cewa yana son ta, ai a wuce wurin " Ammi ta ce "Haka ne, Allah ya sa kar a samu matsala daga baya, bari na ji ta bakin Iman ɗin, sai mu ga abun da yakamata ayi". Laila ta ce "To shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ya sa daga haka a samu ƙarshen wannan matsalar. Ammi ta amsa da Amin. Takawa na tsaye a valcony, hannunsa ɗaya riƙe da kofin tea, ɗaya kuma da takardar zanen da rumaisa ta saka masa a kayansa, sai dai kurman zane tayi, ba tare da bayanin komai ba, kuma da alama saƙo ne mai muhimmanci take son isar masa a zanen. Kusan kullum sai ya kalli zanen nan, kuma kamar yadda ta ce kar ya tambaye ta, yasan da zarar ya matsa, ba lallai ta yi bayani. Babban abun da ya fi ɗaukar hankalinsa, shi ne SMOKE, da ta rubuta da manyan baƙaƙe, sai daji da ta zana da dogayen bishiyu, sai aisha durƙushe a gefen bishiya ta riƙe ciki. "Mimi what's the meaning of this?" Yayu maganar yana shafa zanen, hawayen sa na ɗiga a kan zanen. *** Litattafai ne a gaban Iman, tana karatu, Ammi tayi sallama, Iman ta amsa. "Sarki littafi, ina fatan kin gama karɓo komai, da za ayi amfani da shi na bikin saukar?". "Eh ammina, everything is ready" Ammi ta miƙa mata leda ta ce "Sidi ya kawo, ya ce a baki in ji umar" Iman ta karɓa ta duba, keyholders ne, da jotter yayi mata na sauka. "Auta haryanzu baki ce mini komai a kan yadda ake ciki ba, kin amince da mai sunan baban, kina ganin babu matsala?" Iman ta ɗago da sauri, ba ta zaci ammi ta san waye ba. "Ko da baki gaya mini, na gane waye, amma iman kina ganin babu matsala? Zaki iya zama da shi?" Iman ta jinjina kai ta ce "Ammi yana da kirki" Ammi ta yi murmushi ta ce "So hana ganin laifi, amma ya san halin da ake ciki, ya amince da hakan?" "Eh ya sani". "To Alhamdilillah, Allah ya tabbatar mana da alkhairi" ammi ta tashi ta fita. Iman ta bi Ammi da kallo har ta fice. Mai sunan baba yana zaune a gaban mama, yana cin abinci, duk suna tare da su Aliyu, Abubakar yana kwance a gefen mama yana danna waya. "Babana" mama ta kira sunansa. A hankali ya ɗaga kai ya kalli mama. "Ashe neman aure ka ke ban sani ba?" Gaba ɗaya suka ɗaga kai suna kallon mai sunan baba. "Mun yi waya da hajiya, ta ce sun baka dama ka fito, sai dai ban san zancen ba sai ɗazu da ta kirani a waya". Ayshercool. *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin* *5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14.  Supplement na whitening/glowing skin* *15.  Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 *TALLA! TALLA!! TALLA!!! *ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH* Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.” Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH…. (*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*) Shiru yayi ya cigaba da kai lomar abinci bakinsa, suka tsare shi da ido suna jiran yayi magana. Yaya Abubakar ya tashi zaune ya ce "Malam magana fa ake yi maka" Mirsisi yaƙi magana, ya cigaba da cin abinci, Aliyu dama ya daɗe da gano yayan na su, ya afka kogin soyayya, magana ce kawai bai yi ba. Sai dai ya gama cin abincin, sannan ya ce "Mama, ba ɓoye miki nayi ba, komai ya zo mini a bazata ne. Hasalima tausayinta da na ji ne, ya sanya na ji zan iya aurenta, amma kin san ni dai ban taɓa kula ƴar kowa ba". Aliyu ya ce "Wai wa ce ne?". Harar da yayi masa ya sanya shi yin shiru. Mama ta ce "To, wai an ce turakin kano yana son ganinka, zai gana da kai, a kan maganar, kuma suna buƙatar ka fito ne" Mai sunan baba ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Mama bani da abun aurenta yanzu, kin san komai a kanta, dan ina wurin lokacin da rumaisa ke baki labarinta. An fasa aurenta da wani, kuma a yadda take gaya mini, shi ne karo na huɗu, duk saboda waccan matsala, dalilin haka kuma, an ce wa mariƙiyarta idan ba ta aurar da ita nan da watanni uku ba, ta mayar da ita in da ta tsinto ta. Magana ake ta shekaru goma sha tara da riƙonta, wurin wa za ta kai ta. Ban san ya aka yi na ji ina son na aureta ba". Aliyu shi tausayi ma ya bashi, har yanzu bai gama yadda soyayya ce tayi masa kamun kazar kuku ba. Mama ta ce "Na yadda da maganarka babana, kuma na goyi bayanka, dan shi ɗa na kowa ne, yadda hajiya binta ke riƙe da rumaisa kamar ba sirikarta ba, kaɗai ya isa na goyi bayanka. Kuma Allah ya sani tun kan haka ina ƙaunar yarinyar nan sosai. Amma abun da nake tunani, kaga an saka bikin Abubakar, muna ta fama, gashi ka tsayar da gininka ana nasa, yanzu meye abun yi watanni uku sun yi kaɗan". Abubakar ya ce "Ba dan halinsa ba, kuma tun da ban isa ya gaya mini abun da yake ciki ba, saboda halin da yarinyar take ciki, da kuma duba da muma muna da ƙanwa, muna fatan albarkacin wannan jihadi da zai yi, Allah ya kula mana da ita, a duk in da take, da kuma la'akari da yadda mutum ya faɗa soyayya, da har ta kai shi ga yanke hukunci, ba tare da shawara ba, ni yayansa wato hassan ɗin sa, zan yi magana da su baffa, a ɗaga bikina a fara nasa, tun da abun gasa ne, nayi sai yayi. Sai su tare a nawa gidan, ni na ƙarasa nasa". Mai sunan baba ya galla masa harara. Abdallah ya ce "Auren mai sunan baba, zama bai kama mu ba, dole mu yinƙura abu namu maganin a kwaɓe mu". Yasir ya yi murmushi ya ce "Ni zan sai akwatin kayan lefe, guda shida in sha Allah" Huzaifa ya ce "Ji banza, an gaya maka akwatin lefen ma, jagwal za a saya, kamar kayan jagwal ɗin da kake na wayoyi da computer, da hacking in ji rumaisa". "Bana son rashin mutunci, kai ka san abun da nake da shi ne? Kwanan nan daga china zan fara yin order wayoyi, kai ka sani ai, jari nake tarawa, amma ni zan sai akwatunan lefe, kai uwar me ka ajiye da zaman basir ɗin ɗinki, banda shegiyar ƙarya da saɓa alƙawari". Mama ta ce "To zakaru, ai kun ci kun ƙoshi, dole ku yi mini faɗa". Umar ya ce "Duk na ji ta bakin ku, na kuma gode sosai, amma babu wanda zai rabu da wani abun sa saboda ni, kai habu ba za a ɗaga bikinka ba in sha Allah, ina fatan nima wannan ɗin ba zai gagara ba, zan ƙara ƙoƙari". Abubakar ya ce "Wai dan an haife mu lokaci ɗaya ni sa'anka ne? Bana magana biyu kai ka sani, gidan nan ya zama naka, dama kaine ƙarfin ginin, ni ba gaggawa nake yi ba, ita ma haka in sha Allah ita da iyayenta za su fahimce ni". Mai sunan baba zai sake magana mama ta ce "Ka riga ka ɗaukki aiki babana, idan ba hakan aka yi ba, ni ban ga mafita ba, garbatina ɗan albarka, Ubangiji Allah ya ƙara haɗa mini kanku, ya kau da abun ƙi a tsakanin ku, a duk lokacin da abu ya tasowa ɗayanku, na ga kun haɗa kanku, ba ƙaramin daɗi nake ji ba". Usman da tun da ake maganar bai ce komai ba sai yanzu ya ce "Mama duk jajircewarki ce ta kawo haka, Allah dai ya ƙara miki lafiya da nisan kwana". Suka amsa da Amin, Abdallah ya ce "Mai sunan baba, idan abu ya taso maka, bamu yi maka ba, wa zamu yi wa? Sadaukarwar da kake yi domin farincikinmu ai tana da yawa, komai ka samu mu, kai ne wa, kuma kai ne uba, kowa ya kwaso matsalar sa, mai sunan baba, dan haka muna bayanka a kowane ƙadami Allah ya iya maka yayi riƙo da hannunka". Karar da ƴan uwan nasa suka nuna masa, ba ƙaramin daɗi tayi masa ba, har sai da hakan ya sanya shi murmushi, kuma ya kasa ɓoye farin cikinsa. *** Ko da labari ya iske dangin mahaifinsu Umar, sun yi murna, tare da tsokanar mai sunan baba, dama zai iya yin budurwa yayi soyayya. Wan mahaifinsu ya ce zasu yi ƙoƙari, amma abubakar ma ba za a ɗaga aurensa ba. Sai dai yayan mahaifinsu ya jinjina lamarin auro ƴar gidan sarauta yana talaka. Tare da shi da umar, da yaya Abubakar da ƙanin mahaifinsu, sai mijin iya baffa musa da ya zo daga, suka je gidan turaki bisa jagorancin Mahmud kamar yadda ya buƙata. Sai dai sun ga karramawa, da mutuntawa da basu taɓa tunani ba, turaki ya ƙara jaddadawa mai sunan baba matsayin iman, mai sunan baba ya ce ya amince. Turaki ya tambayi ƴan uwan mahaifinsa, a kan idan sun amince su ma, suka ce ai shi ne zai zauna da ita, kuma tun da ya ce ya ji ya gani, suma sun amince ai ɗa na kowa ne, a tarbiyyar da umar yake da ita, sun san ba zai kawo abun da zai cutar da shi ba. Baffa Musa wa ga mahaifinsu ya ce "Sai dai mu ma wani hanzari ba gudu ba, yaron nan maraya ne, bashi da ƙarfi saka biki nan da watanni uku yayi kusa da yawa, ga ɗan uwansa nasa bikin muke hari, muna fatan a ƙara mana ya zama watanni shida, gaba ɗaya ya mayar da hankali ne a kan auren ɗan uwansa bamu zaci nasan zai zo haka ba". Turaki ya ce "Babu laifi, kar ku damu. Ubangiji Allah ya yi mana jagora, kuma a hakan nan ma kawai, na yaba da tagwayen sosai, ba dan ance shi ma ɗan uwan aure zai yi ba, ai da sai na bashi ƴa ta, ai duk wani wanda ya fito daga tsatson ƴa ta rumaisa, duk abun da yake so, in dai ina da shi zan yi masa. Allah ya sanya musu albarka, ya nuna mana lokacin lafiya". Baffa musa ya ce "Amin, ranka ya daɗe tun da har an samu daidaito, ina ga ba sai mun ja lokaci ba kawo kuɗin aure, ga kuɗi mun taho da su" Gaba ɗaya suka kalleshi, su dai sun san ba su yi haka da shi ba. Ya karkace ya ciro kuɗi, dubu ɗari da hamsin, ya ajiye a gaban turaki. Turaki ya ce "Masha Allah, Allah ya sanya albarka, to ba dan ba a shirya ba, ai da sai a ɗaura, mu bashi gidan zama, a wuce wurin ko malam umar?". Mai sunan baba ya risuna ya ce "Ranka ya daɗe ni yakamata na yi ƙoƙarin samar da mahalli". Yayi murmushi ya ce "Babu laifi, Allah ya nuna mana" Ko da suka taho hanya, Mahmud har gida ya kai su mai sunan baba, a gida suka sanar da mama ai an bayar da kuɗin auren ma, mama ta ce daga zuwa tambaya an biya kuɗin aure? Ta ce to sai a nemo kuɗin malam musa a bashi abun sa, amma ya hau mama da faɗa, a kan dan yayi wa ƴaƴan ɗan uwansa abu, dan me za ta ce a biya shi. Turaki ma wayar ammi ya kira, ya sanar mata su mai sunan baba sun bayar da kuɗin auren iman, dubu ɗari da hamsin, sun sanya watanni shida dai-dai. Ammi ta yi mamaki, dan ita bata ta;a zaton abun a haka ba, ta ce to ba a basu komai na tukici ba, sun kawo kuɗin aure. Turaki ya ce su aika musu daga baya, amma sun zo da kuɗin aurensu sun bayar. Farincikin ammi ya kasa ɓoyuwa, ta nufi ɗakin laila, da suke tare da rumaisa, tana ta koya mata abubuwa. "Laila, rumaisa" suka ɗago suka kalli ammi. "Daga zuwa amsa kiran turaki, sun bayar da kuɗin auren iman, an saka watanni shida". Ruma tayi murmushi ganin yadda bakin ammi yaƙi rufuwa. "Au shine aka wareni, ban ma san za a kawo kuɗin aure ba, iman yanzu ta rama ta ƙwace mini yaya, dan na auri takawa" Suka yi dariya, laila ta ce "Kaii Alhamdilillah, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya sa za ayi da mu. Ni dai gayen ya burgeni ranar da na taɓa ganinsa, so gentle". Ruma ta ce "Taɓ, mai sunan baban ne gaye". Ammi ta ce "Ya Ubangiji Allah ka sanya ƙarshen matsalar nan ne ya zo, Allah ya sa kar a gaya masa wani abu da zai saka ya ce ya fasa". Ruma ta ce "Ammi, idan kin ga ba ayi auren nan ba, sai ƙudirar Allah.  Mai sunan baba ba zai taɓa cewa zai fasa ba, sai idan ku kuka fasa auren, duk rintsi kuwa" Ammi ta ce "Allah ya sa, bari ta dawo na gaya mata, Allah sarki ƴar marainiyata, Allah ya kaɗe abun ƙi". Ƙasan zuciyar ammi, tana ta yi wa iman addu'a Allah ya sa ta dace, dan yanayin nature mai sunan baba, tana bata tsoro, gani take kamar yanayin iman ya nuna tana son shi ba kaɗan ba. Da labari ya iske iman, da ta koma ɗakinta sai da tayi sujudu shukur, sujjadar godiya ga Allah, saboda tsananin farinciki, haka nan a ranta take jin, sassauci zai samu a rayuwarta. A irin kyan da Allah ya yi wa iman, zaka raina abun da aka bayar na kuɗin aurenta, amma jiki na rawa ta kira mai sunan baba. Sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. "Yaya umar" "Na'am". "Ashe kuɗin auren zaku kai, na zata kawai zuwa kayi ka amsa kiran da mai girma turaki yayi maka?". "Na yi garaje ko, na kai kuɗin auren ba tare da kim ce mini kin amince ko a'a ba. Tun da rumaisa ta ce mini, akwai wanda ki ke so". Iman a ranta ta ce 'Kai ɗin ne dai, kai nake so yaya umar'. A zahiri ta ce "Ni ba wanda nake so fa" Har cikin kansa ya ji shagwaɓar da tayi masa, ya sake gyara zaman wayar sannan ya ce "To ya aka yi?" "Bugowa na yi, na maka ya ka je gida, Allah ya ƙara buɗi". "Masha Allah, ayi haƙuri abun talaka na san kin fi ƙarfin hakan" Iman ta ce "A'a ban fi ƙarfin haka ba, Allah ya yassare maka". "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, thanks" ya katse wayar. Nothing romantic mai sunan baba ya sani, kawai ayi abun da ya dace, dan soyayya in dai irin yadda Aliyu da Abubakar suke me Jabir kuwa tamkar zai yi hauka, haka ya ji da aka ce, wai an kai kuɗin auren iman, bai taɓa tunanin da gaske yana son ta ba sai yanzu. A baya matsananciyar sha'awarta ce take addabarsa, tun ranar da ciwonta ya tashi, yana nan shi ya ɗauketa ya kaita mota. A baya bai taɓa tunanin jin son ta ba, saboda tana girmama shi a matsayin yayanta, shi kuma ƙanwarsa, tun daga ranar da ya ga jikinta, ya sanyawa ransa lallai sai ya mallaki iman, ko ba komai, idan ka samu irinta a yaranka, ka samu kadara, saboda kyakywar bafulatanar yarinya ce. Washegari, ammi ta bayar order yin girke² snacks, ta ce a kai gidansu rumaisa, ruma ta ce gida za ta je, ayi sabgar nan da ita, saboda wauta ta cewa Iman ta shirya, su tafi tare, laila ta ce ya za ayi ta je kai tukuicin kuɗin aurenta, ban da wauta irin ta ruma. Ammi ta ce laila da sidi sai su kai, sai su tafi da rumaisa, ruma ta ce ga Mahmud, ba sai sidi ya je ba. Ammi har mamakin yadda Mahmud yake yi wa rumaisa biyayya take yi, duk abun da ta ce masa yayi, ko musu baya yi yake aikatawa. Hakan kuwa aka yi, da shi da laila, da rumaisa, suka kai kayan nan, mama ta din ga mitar wannan kayan sun yi yawa, dan sun kusa kai ɗaya da kuɗin auren, banda uban lemuka da naman kaji. Laila sun gaisa da mai sunan baba, sai dai sama-sama, yaya Abubakar ne mai sakin fuska, sai usman sarkin tsokana. Laila ta daɗe a gidan, suna hira, take bawa mama labarin yanayin zamanta a canada, da iyalinta, take gaya mata a cikin watan, mijinta da yaranta suma zasu zo hutu. Laila ta yi wa mama sallama, ta cewa rumaisa, za ta je ziyarar ƙawayenta da ke Kano, idan Mahmud ne ya zo ɗaukarta, ko sidi sa biya su ɗauke ta. Rumaisa kuwa baki yaƙi rufuwa dan murna. Yasir ya samu ruma ya ce "Ke, zo mu yi shawara, nifa zan saiwa mai sunan baba akwatunan biki". Ruma ta ce "Da wani kuɗin?". "Ke baki san na kusa fara shigo da wayoyi, da computer daga china ba, ni da abokina muke tara kuɗin, yayansa ne zai tsaya mana, mama ma ta san zancen, amma a kuɗin dole ni zan saiwa mai sunan baba akwatunan lefe" Rumaisa ta din ga bayar da shawarwari, na arziki da na shirme. Bayan la'asar, Mahmud ya dawo ya ɗauki rumaisa, suka biya suka ɗauki laila, albarkacin rumaisa, duk da ko a baya, laila da Mahmud ba a ga maciji, amma suka din ga hira yau sosai, hirar da ba su taɓa yi a baya ba. Jabir kuwa, Kasa jurewa yayi, ya ɗauki mota, ya tafi gidansu takawa, wani irin kishi, da zafin zuciya yana ta azalzalarsa, ya shiga part ɗin su, sai dai kai tsaye da ya shiga babu kowa a falon, ya tafi ɗakin iman. Tana zaune a kan gadonta tana danna waya, kawai sai ganin mutum tayi a tsaye a kanta, yana huci. Sai da ta tsorata, ta ce "Uncle J, lafiya kuwa?". "Ban sani ba, tsohuwar munafuka, ni zaki yaudara? Wato dama wancan banzan talakan matsiyacin ki ke so? Ya rasa abun da zai kawo kuɗin aurenki sai dubu ɗari da hamsin, ko da yake babu mamaki, tun da kema tsatson tsiyar ce, ƴar masu kiwo ƙafa babu takalmi duk da babu wanda yake da tabbacin hakan ma, munafuka mayaudariya". "Uncle j ya zaka din ga zagina ne?, Nifa ban taɓa cewa ina sonka ba, na sha gaya maka a baya". "Dalla rufe mini baki, har ke wani zaɓi ne da ke, kina wulaƙantacciya" Iman tayi murmushi ta ce "Tun da ni wulaƙantacciya ce, sai ka bari mai sona saboda Allah, ba dan jikina ba, ya aureni". "Ni kike gayawa haka ko? To ayi auren mun gani, zaki gane kurenki ne". Ya juya ya fita fuuu, ta zuba bishi da ido, a falo yayi kaciɓis da ammi, ammi cikin tuhuma ta dube shi ta ce "Ahh jabir daga ina kuma?". "Wallahi baki yi wa kanki adalci ba, a da ne ake aibata ki, nake karewa, ashe haka kike, waccan ƴar matsiyatan ta zigaki kin hanani ƴa, ƴar ma da ba wanda ya san tushenta, balle a san daga gidan uban wa take, nayi jihadi na ce zan aureta amma aka wulaƙanta ni". Ammi ta ce "Jabir, ni ka ke gayawa haka?". "Na faɗa, ai kema kin san baki yi mini adalci ba, mun gama magana da ke, ki je ki canza magana, har da yi wa mahaifiyata sharri, saboda tsabar mugunta da son zuciya, ban sani ba ko dan ba ƴar ki ba ce ba, ya sanya kika zaɓa mata talaka matsiyaci". Ji yayi an ja shi baya da ƙarfin gaske, an sauke masa zazzafan marin da ya kasa gane daga ina marin ya fito. Mahmud ya fuskance shi sosai ya ce "Idan kana cin ƙasa ka kiyayi ta shuri, babarka ce babbar annamimiyar da ta haɗa komai, ita ta zo ta ce ba ta son auren, ta koma kuma ta ce ba haka ta ce ba, idan ka kuma yin mummunar magana a kan ta, sai na yi maka dukan tsiya wallahi". Duk kallon mamaki suke yi wa Mahmud, banda rumaisa da ta dubi Mahmud ta ce "Ai wallahi duk ɗa nagari abun da zai yi kenan daddy. Kuma mun ji, ni da yayana talakawa ne, amma masu mutunci da sanin darajar kai. Kuma idan har za a bawa mutum aure saboda nagartar da Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya faɗa, wallahi sai an bawa mai sunan baba sau dubu ba a baka ba". Jabir ya kalli Mahmud ya ce "Ni ka mara?". "Waye kai ɗin da ba zan mareka ba?" Jinjina kai yayi ya fita, yana huci, sai dai ya san ko a ido, ba zai iya dukan Mahmud ba. Kasancewar baba uwani tuni mummy tayi bikonta, domin kuwa ta gane cewa dole-dole tana buƙatar baba uwani a cikin al'amuranta, domin sai ta na sanin halin da ake ciki a sashin ammi, sannan za ta san ta ina za ta dinga ƙulle-ƙullenta. Ita ma baba uwanin Kasancewar ta rayu da mugun son abun duniya, ya sanya babu tunanin komai, ta komawa mummyn. Dan haka ko da wannan al'amarin ya faru, ita ta lallaɓa ta kira Mummy a waya ta labarta mata. Ammi kuwa ta rasa meya kamata ta yi ne? Farincikin ɗan da aka rabata da shi, aka cusa masa ƙiyayyarta ya damu da ita, har ya shigar mata faɗa? Ko kuma fargabar abun da ka iya biyo bayan abun da ya aikata ɗin? Washegarin da abun ya faru, shine lokacin da suka shirya tafiya gombe, wanda tafiyar har da ammi, har da laila da rumaisa, nusaiba iman da kuma sabir. Rumaisa taga karamci, kamar su cinyeta, ko ina ta shiga ayi ta nunata ga matar takawa, ga kuma ɗan sa ɗan marigayiya Aisha. Haka zalika sun yi murnar zancen auren iman, da yayan rumaisa, da ammi tayi musu, maman laila ta daɗe rasuwa, sai mahaifinta da ƴan uwanta, kasancewar saukar su iman an ƙara sati guda, ya sanya ammi ta kashe wayoyinta, dan kar ma a kirata a ɗaga mata hankali, a kan abubuwan gidan nan, sai da suka kwana uku, sannan suka dawo kano. Rumaisa ta samu abun arziki kashi-kashi. Mummy kuwa ta rasa in da zata saka ranta ta ji daɗi, domin kuwa alkadarinta ya tasan ma karyewa, tun da labari ya isaketa cewar Mahmud ya mari  jabir, saboda ya kare ammi, abun ya dungunzuma hankalinta ainun, me hakan yake nufi kenan? Asirin giwa ya fara cin sa? Zai karkata ya koma wurinta, domin shishshigin da yake yi a sashinta yayi yawa, dan ko kai kuɗin auren iman, labari ya isketa, shi ne ya jagoranci ƴan uwan su rumaisa har gidan turaki. Sai dai ta lura, kamar rumaisa ke taka muhimmiyar rawa, wurin rusa mata shirin da take yi, ta hanyar ziga Mahmud, sai dai ta rasa ta ina yakamata ta yi maganin rumaisa. Sannan ta ƙudiri yadda ta ƙwace Mahmud, ba zata bari ya koma ga ammi ba, dan ba zata gama wahalarsa ba, sannan rana tsaka ya koma wurin uwarsa ba, dan idan haka ne, gara ta nakasta shi yadda ba zai moru ba. Mummy na tsaka da tunanin meye abun yi, Hajiya Lubabatu tayi mata dirar mikiya, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, a kan marin da Mahmud ya yi wa jabir. Aka yi sa'a kuwa yana nan, mummy ta ce "Haba lubabatu, mutuwa ma na kunyar idon mahaifi, ya a gabana zaki zo kina zagar mini ɗa? Ai sai ki haɗa su ki yi musu nasiha, tun da duk ƴaƴanki ne". "Ba wani ƴaƴana, kema ki daina Wannan ƙumbiya-ƙumbiyar, ki fito kan ki tsaye ki daina wannan munafuncin, kina riƙon Mahmud ne da cikar naki muradin". Mummy ta ce "Ni tsakani da Allah na riƙe shi, sai ma dai tayaki da nake yi, naki muradin ya cika" "Jamila, wallahi kar nake kallonki. Kai kuma zaka ga abun da zai biyo ba, ban da tsabar wulaƙanci, uwar me uawar taka binta ta tsinana maka a rayuwar, da har zaka mari jabir saboda ita? Ƙarya yayi an kama an cuce shi, a kan wannan banzar yarinyar to wallahi ahir ɗin ka, shi da yake jiran gadon sarauta, ai mace ma sai wadda ya zaɓa". Mummy ta ce "Lubabatu yakamata ki san abubuwan da ki ke faɗa fa". "Ba wani, ni ki ƙyaleni, kashedi nayi da babbar murya, idan kallon uwa yake yi miki, to ki ja masa kunne, ya kiyayi ɗa na" Mummy tayi mamakin abun da hajiya Lubabatu ta zo tayi mata, wato hakan yana nufin ita ma tunanin da yake ranta, shine a nata ran, na lokaci yayi da kowa yakamata ya kama gabansa, tun da haryanzu kusan za a iya cewa ita hajiya Lubabatu ba wani benefits da ta samu a tafiyar nan ta su. 'Aikuwa ba zaki samu ba, a hakan zan ƙara zage damtse, ka samu kujerar nan Mahmud, kuma na kawo ƙarshen duk wannan abun, ta hanyar nisanta ka da giwa da ahalinta'. Ta kalleshi ta buɗe baki za ta yi magana, amma ya tashi tsam ya bar mata falon. Wanda a da, ko gyaran murya tayi jikinsa na tsuma, yake saurarata. Koda rumaisa suka dawo, kamar yadda ammi tayi tsammani, ana ta surutun kuɗin auren iman, wai dan ba ƴar ta ba ce, ta hanata auren jabir, za ta aura mata talaka, tun da laila ƴar yayarta ce, ai mai kuɗi ta aura mata. Ammi dai ta toshe kunnenta, kwanansu uku da dawowa, aka yi saukar Alqur'ani na su Iman, an ci an sha an yi walima sosai da sosai, sai dai mai sunan baba bai je ba, wanda hakan bai yi wa iman daɗi ba sam. Kayan saukar ma da ta ware masa, sai sidi ne ya kai masa gida. Sai daga baya yaje gida, ya ga allon saukar ta ta. A ranar ruƙayya ta ga iman tare da mai sunan baba, ta koma sashinsu, tana koɗa kyawunsa da tsananin kwarjininsa. A haka rayuwa ta cigaba da juyawa, matsaloli suka ƙara tsananta a tsakanin gidajen sarauta, kowa ya ba za komar cimma burinsa, ko ta halin ƙaƙa ko a mutu ko ayi rai, kowa burinsa ya ga ya samu abun da zuciyarsa take muradi. Mijin laila ya zo hutu da shi da yaransu, sai dai yaran gaba ɗaya hausa ba ta ishesu ba, sun fi magana da turanci, ga mijin lailan kansa wani fari sol da shi, kamar ba ya jin hausa, laila sai zuba taɓara take kala-kala, suka tattara zasu koma gidansu na Kano, laila ta ce sai rumaisa da iman sun bita gidanta, ammi ta ce ba za ta kwashe mata 'ya'ya ba za dai su din ga zuwa. Ƴaƴan laila kansu, tamkar black Americans, mata biyu sai namiji ɗaya, kyawawa sosai, ranar da Yasir suka kaiwa rumaisa ziyara gidan laila, yarinyar laila ta biyu, ta liƙewa Yasir, hira kala-kala, ta din ga yi masa tambayoyi, mussaman ganinsa da computer, har mamakin yadda yarinya ƙarama take da ilimin computer sosai haka. Haka mijin laila babu ruwansa, hirar da suka din ga yi da su huzaifa, da yasir, mijin laila ya cewa Yasir idan za a bar shi a gida, zai tafi da shi canada, ya ƙara karatu idan ya kammala diploma da yake yi a kan computer science. Ya cewa Huzaifa, "kai kuma gashi an ce tela ne, baka cika alƙawari kai ya zmu yi da kai" Huzaifa yayi dariya ya ce "Sharrin yasir ne, ina cika alƙawari, shi da yake hacking ma" Dariya suka yi, ya ce "To kaima zaka bi mu canadan ko kuwa?" Huzaifa ya girgiza kai ya ce "Mama ba zata bari a tafi da mutum biyu ba, shi dai ya tafi" Su duk basu zaci da gaske yake ba, laila take bashi labarin rumaisa kuma zane-zane take yi, nan ya dinga bayanin yadda masu zane-zane suka da muhimmanci a ƙasashen ƙetare. Rayuwarsu very simple, iya zaman da suka yi a ranar, sun ƙaru da mijin laila sosai da sosai, ya kuma cewa laila, idan har Yasir ya kammala diploma, tayi masa magana ayi wa Yasir visa. *** A ranar da rumaisa ta tsaya a gaban kalandarta, ta soke kwana na ɗari da saba'in da uku, a ranar yayi dai-dai da saura kwanank bakwai cif-cif mijinta ya dawo, ji take tamka ta zuƙo sauran kwanakin, dan gani tayi kwanakin ma sun daina yi mata sauri. Duk wani gyaran jiki da laila take yi wa iman na aure, da wanda ta saka ake yi mata, tare da rumaisa ake yi mata su. Rumaisa kuwa daga ita har iman yadda suka koma ba a magana, domin kuwa sosai ba kaɗan ba, sabayar maman Khadija ta karɓi rumaisa, da maganin girman nono na maman ilham, duk wanda ya san rumaisa a baya, ya ganta yanzu sai ya sake kallonta, ta cika abun ta dai-dai gwargwado, mujewar da ta yi, tayi ƙiba gwanin sha'awa ƴar caraf da ita, ga wani irin kyau da fatarta tayi. Dama iman ba a magana, gata fara tas, ta ƙara da kunun maman Khadija, gashi ita ma ba a barta a baya ba, wurin amfani da maganin maman ilham, abun sai wanda ya gani. (Ga mai buƙatar ya murmure, yayi kyau gwanin sha'awa kamar rumaisa, iman da kuma anty laila, sai ku garzaya inbox ɗin maman Khadija, domin mallakar na ku garin kunun sabayar, ku tuntuɓeta kai tsaye ta lambar wayarta 08033411249, tana zaune a bayan Federal Palladan Zaria, haka zalika tana aika kayanta ko ina a faɗin ƙasar nan, da kuma maman ilham mai tula-tula, domin tsantsamw jiki sa kama mutuncin nai, ga masu aure, ƴan mata zaurawa da masu yaye, suma suna iya garzayawa inbox ɗin ta ta wannan lambar 08135613021, tana nan zaune a no. Ai kawo road Kaduna, haka zalika ita ma tana aika kayanta ko ina a Nigeria) Ita kanta mama, sai da tayi mamakin yadda rumaisa ta koma, dan bar sai da ta fara tunanin ko ciki ne da ita, saboda yadda tayi kyau abun ta. Laila da kanta, da masu aiki, suka je gidan rumaisa, suka yi masa gyara sosai da sosai, aka gyara komai, ta cigaba da jaddada mata, ta riƙe abubuwan da ta koya mata, ta kula da kanta. Turarukan rumaisa na aure, ta bayar aka haɗa da na iman, aka ƙara tsuma su, sannan aka yi mata wasu.  Banda sabbin ɗinkuna na kece raini da aka yi wa rumaisa. Babu babban abun da ya ƙara birge ruman, irin yadda aka yi mata riguna masu breast cut, kuma suke zama cas a jikinta, gashi ta fara saka brezia, murna har da taka rawa, ta sha gyaran gashi, ga lallenta ja da baƙi. Ƴan makarantar bokon su na mamakin yadda wasu lokutan rumaisa ke cin karenta babu babbaka, an hana kowa yin lalle, amma rumaisa ana bari tayi abun ta. Ƙarfe goma sha ɗaya na safe, jirginsu ya sauka a aminu kano international airport. Sannu a hankali yake tafiya, yana jan akwatin sa, wayarsa yake dannawa yana neman layin laila, dan a wayarta suka yi magana da rumaisa jiya, ta ce za ta turo a ɗauke shi, so yake yaji waye zai zo ɗaukar ta sa. Sai dai yayi turus, da ya ga Mahmud a tsaye, da sabir a hannunsa. Da ƙarfi Sabir ya fara kiram "Papaaa. !paaapaaa" yana miƙe masa hannu, ya tattaka har da ɗan gudunsa na yara masu koyon dabo, ya nufi in da mahaifinsa yake!. Ayshercool. *SHIN YAR UWA KIN SAN ILLAR DAKE TARE DA INFECTION KUWA?, TO BARI KI JI KAƊAN DAGA CIKIN ILLAR DA INFECTION YAKE DA SHI? KIN SAN CEWA INFECTION YANA HANA HAIHUWA?, YANA HANA MA'AURATA JINDADIN MU'AMALA, YA NA SAKA  WARIN GABA KOWANE IRIN TURARE KI KA YI AMFANI KO GYARA KI KA YI, BA ZAI HANA WANNAN WARIN FITA DAGA JIKIN KI BA FITAR FARIN RUWA, TARE DA ƘURAJE. ƘAIƘAYIN GABA, TUSAR GABA, DUK SUNA DAGA CIKIN ILLAR DA INFECTION YAKE WA LAFIYARKI INA MASU FAMA DA ULCER, ASTHMA, SICKLA, INA MATAR DAKE FAMA DA MATSALAR FIBROID, MATSALAR RASHIN HAIHUWA KO BUSHEWAR  JIKI DA FATA, KU GARZAYO KU GWADA MAGUNGUNANMU MA GHT SUPPLEMENT, KU GANI DA  IKON ALLAH DA IZININ ALLAH, MAI BUƘATAR ƘARIN BAYANI YA NEMI WAMN 0703 527 5119* Ko ku danna wannan link ɗin, domin kasancewa da mu, ku ji yadda https://chat.whatsapp.com/COM8NE7rDs8HAG0Oqfr9wm *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin* *5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14.  Supplement na whitening/glowing skin* *15.  Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 *TALLA! TALLA!! TALLA!!! *ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH* Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.” Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH…. (*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*) Durƙsawa takawa yayi, ya ɗauki sabir yana juyi da shi, yana murmushi, ya ce "I so much miss you darling, how are you?" Yayi maganar yana sumbatar goshin sabir. "Paapa, daddy kaga" yayi maganar yana nuna masa in da Mahmud yake tsaye. Kallon in da Mahmud yake yayi, yana mamakin saurin wayon sabir, ya ɗaga kai yana dubawa ko zai ga su ammi, amma babu kowa sai Mahmud. Ya kira laila a waya, ta sanar masa da cewa Mahmud ya zo ɗaukarsa, zai fara masifa, ta kashe wayarta. Mahmud kuma yayi banza bai ce masa komai ba, bashi da wani zaɓi, illa ya je ya saka akwatinsa a boot, sannan ya buɗe bayan motar ya shiga. Har suka fara tafiya, babu wanda ya tankawa wani, sabir ne dai daɗi ya isheshi na ganin mahaifinsa, ya kasa zama wuri ɗaya, sai ya taka cinyar adam ya miƙe yana taɓo Mahmud "Daddy ka ga papa" Mahmud yayi murmushi,yana shafo kan sabir da hannu ɗaya. Takawa ya riƙe hannun sabir ya ce "Ina mimi?" "Mimi, iman, baba" ya din ga jero wa adam sunaye, adam yana ta murmushi, yana jin yadda yayi kewar ɗan nasa. Tun daga bakin gate, security suke yi wa adam barka da zuwa, aka ɗauki akwatinsa zuwa cikin gida. Cike da ɗoki da son ganin mimi ya ƙarasa sashin ammi, ammi ce ta fara taro shi, ta rungume shi, ya durƙusa ƙasa yana gaisheta. Ammi ta yi masa alamar ya tashi, ta sake rungume shi tana faɗin "Barka da sauka, ya hanya ya makaranta?" "Alhamdilillah ammi, na same ku lafiya?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah" Laila ta ce "Ƴan makarantar bokoko, sannu da zuwa" "Yauwwa big aunty" yaran laila safiya, anam da haidar, suma suka taho da gudu, suka rungume takawa suna faɗin uncle. Nusaiba da iman ma duk sannu da zuwan suke yi masa, fuskokinsu, ɗauke da tsantsar farincikin ganin dawowar ta sa, sai dai ya gama rarraba idonsa bai ga mimi ba. Ya kalli iman ya ce "Amarya ba kya laifi, ya shirye shirye? Kodayake dole a zo a sake wani shirin, tun da na dawo". Dariya suka yi gaba ɗaya, yana ta son ya tambayi rumaisa, amma kunya yake ji, kuma dai ya san suna cikin hutun makaranta. Nusaiba ta kai masa akwatinsa ɗakinsa da yake sashin ammi, takawa ya ce "Nusiaba ina mimi ne?". "Wallahi ban sani ba takawa, anty laila zaka tambaya" ya jinjina mata kai. Ya shiga yayi wanka, ya fito falo, an shirya masa abinci a dining, sai dai ammi kanta ta lura yadda yake ta leƙe-leƙe, ta san ba kowa yake nema ba sai rumaisa. Laila kuma ta zauna ta saka shi a gaba da surutu, ya dubi laila ya ce "Yanzu a gidan nan a rasa wanda zai iya zuwa a cikinku ya taro ni?" Laila ta ce "To yanzu a ƙafa ka taho? Ba ɗaukkoka aka yi ba?". "Amma shi ne yakamata ya je ya ɗaukko ni?" "Wannan kuma matarka za ka tambaya, da ta shirya hakan". Ya kalli in da ammi take, ya ga ba ta jiyo su, ya ce "Yauwwa, wai tana ina ne?" "Ita wa?" "Meye haka ne, matata mana". Laila tayi murmushi ta ce "Tana nan ƙalau tana gaisheka" Ya tsuke fuska ya ce "Wai meye haka ne? Dan Allah tana ina, ina son ganinta" "Zaka ganta ne, kai dai ka kammala cin abincin ka huta" Ya dire cokalin ya ce "ya haka ne? Watanni shida ba ma tare, na dawo kuma kin ɓoye ta". "To wai me za ta yi maka ne? Sai mun gama jan aji tukuna".  Yayi dariya ya ce "Jan aji, wane ajin kenan, ina fatan ba wata rigimar ki ka koya mata, in the name of jan aji ba?" "You will see" tayi maganar tana dariya. Mirsisi anty laila taƙi faɗa wa takawa, in da rumaisa take, sai da ta kai ga ya cire kunya ya cewa ammi "Ammi wai ina maman sabir ne?" Ammi ta ce "A'a bani zaka tambaya ba, ai dama da zaka tafi laila ka bawa riƙo, kuma da zaka dawo ta ce ba ruwana da abun ku, dan haka babu ruwana". Wasa² har la'asar, tun yana tambayar har ya haƙura, sai daf da magariba, laila ta ce masa jeka gida, zan kawota. Da fari bai yadda ba, sai da ta rantse masa tukuna, sannan ya amince. Da ya je ya tarar da gida ko ina tsaf, duk an sauya fasalin zaman furnitures ɗin, ko ranar da aka kai masa rumaisa, gidan bai haɗu har haka ba. Yana zaune a falo, yana kallon ƙwallon dole, saboda ya ma rasa abun yi. Ya ji maganganu ana hawowa sama, da sauri ya tashi tsaye, yana jiran isowarsu. Laila ce da Iman, sai nusaiba, rumaisa ta duƙunƙune da mayafin lafayarta. Murmushin sa ya faɗaɗa, suka matsa daga kusa da rumaisa, ta ɗaga kai ta kalleshi, ta sake rufe fuska tana murmushi, ƙarasawa yayi gabanta ya rungumeta, yana murmushi. Rumaisa ta rintse ido, saboda wata irin kunya da ta kamata, ganin yadda ya rungumeta a gaban su laila. Nusaiba kuwa video take yi musu, tana cewa bari muyi ƙara'i tun da bamu yi a lokacin biki ba. Ya ɗagota yana son ƙare mata kallo, amma ta hana shi damar hakan, sai cukuikuye jikinta take yi, mayafin gashi sai wani irin ƙamshi ne kala² yake tashi daga jikinta. Laila ta ce "Ku zo mu tafi, kar ya saka mini duka, saboda jan ran da na yi masa, ga ta nan ku cinye juna, ƙarewar ƙauna". Adam ya ce "Eh ɗin, Allah ya bada lada, amma an wahalar da mu haba". "Da ƙafarka zaka zo nemana, zan rama ne" tayi maganar tana dariya, su iman suka bita suka tafi. Suna tafiya, ya tsuguno dai-dai tsayinta, ya sake rungumota jikinsa, ya ce "I miss you little mimi" Kasa magana tayi, kawai taji hawaye na zubo mata, jin tana sheshsheƙar kuka, ya sanya ya ɗagota, ya ce "Yaya aka yi?" Kasa shiru tayi, ta cigaba da kukan. Ya zauna da ita a jikinsa a kan kujera, ya ce "Gaya mini menene?". "Ba kai ne ka daɗe ba, kuma kwanakin suka ƙi cika ba?" Takawa yayi dariya ya ce "To ni na hana su cikar?. Allah sarki, duk murnar ganina ce har da kuka? I so much miss you dear" Lafewa tayi a jikinsa, tana cigaba da kuka, cike da shagwaɓa, ganin dawowar ta sa take yi, tamkar a mafarki. "Mimi, meye sirrin ne? Kin ga yadda ku ka yi kyau kuwa, kalli skin ɗinki, duk da dare ne, kin yi fresh ga wani ƙamshi mai daɗi da ki ke yi, i like it baby" "Baby kuma, kamar wata mijin anty laila, gursumemen dattijo wai baby, ni in dai zaka ce mini baby, sai ka sayo mini feeder, da kayan wasa" "Ai na sani, ko shekara ɗari za ayi, ba zaki canza halinki ba mimi" Hira suka sha sosai, rumaisa ta din ga bashi labarin wasu daga abubuwan da suka faru, sai dai tafi karkata ga laabrai masu daɗi da suka faru. Haka shima ya din ga bata labarin makaranta, sai da suka raba dare a falon, ya ce suje ɗakinsa su kwana, amma ta kada baki ta ce Ba zata kwana a gado ɗaya da shi ba, sai ka ce Anty laila. "Au kina nufin laila ce mara kunya ko, sai na gaya mata. Kuma banda gulma ba sau biyu kina kwana tare da ni ba?" "To ai wannan tsautsayi ne, Anty laila dai kama rayuwar turai ta ratsata, take gaya mini ita ɗaki ɗaya take kwana da mijinta, wai tare a kan gado ya rungumeta, ni dai wannan karatun nata ba ɗauka nake yi ba. Dan ba iyawa zan yi ba" Yayi murmushi tare da shafar sumar kansa, ya ce "Shikenan a sauka lafiya, tsarabarki sai Allah ya kaimu da safe" Babu kunyar komai, ta wuce ɗakinta. Sai dai da ta tafi ɗakin, ta kasa manta rungumar da yayi mata, haka ta shirya ta kwanta bacci, tana sake ganinsu a tare a cikin idonta, yana magana yana yi mata dariya. Rungume pillown tayi, ta furta "papa a hankali" Washegari da wuri ta tashi ta hau aikace-aikace, ta gyara ko ina duk da babu datti. Ta shiga kitchen ta haɗa abincin karin kumallo, ta leƙa ɗakin Adam. Ya lulluɓe jikinsa da bargo, saura fuskarsa kawai a ya bari a waje, baccinsa yake yi hankali a kwance, kai da gani ka san a gajiye yake. Ta kalli agogon ɗakin, tara da rabi na safe, a hankali ta ce 'Papa baka jin yunwa ne?' Sai kuma ta tuna lecture malamarsu da ta laila, wai yadda ake tashin miji daga bacci. Ta rife bakinta da hannunta ta ce "Ni, haka kurum in je in wani kama shafa shi, ina cewa ya tashi, kamar wani mage, ko ɗan jariri, ai gara in daki ƙofa da ƙarfi irin yadda mama take yi wataran a gida, idan haka ne abun, meyass a gida ba a haka ake tashin su Yaya usy ba? Kai anty laila bata da kunya, zaman turai duk ya canza ta'. Ta gama soki burutsunta, ta koma kitchen tayi wanke-wanke. Daga nan ta tafi ɗakinta, yin wanka. Sai dai ko da ta fito daga wankan, bisa mamakinta adam har ya tashi, dan ya ma biyota ɗakin. "Wai daga zuwana nayi wanke -wanke har ka tashi?" Tayi maganar a ɗan tsorace tana rufe jikinta. Maimakon ya amsa, kawai ya hau dariya, ta tsaya cak ta ce "Menene?". Purple ɗin brezia da ta bari a kan gado, ta shiga banɗaki, ya ɗaga mata ya ce "Meye wannan?" Kame-kame ta fara tana son faɗar abun da zata kare kanta da shi. Ya ce "Inyeee mutuniyar, ai kamata yayi a nuna mini, ni dama tun da nayu hugging ɗinki jiya, i feel it but i thought na scam you wanta scam me, ashe na gaske ne, come let me see inyeee". Shan kunu tayi ta ce "Papa bana so" "Meye ba kya so kuma? Ganin kawai" Ƙarasowa tayi zata karɓi breziar, amma ya riƙeta yana dariya, ta saka hannu ta riƙe towel ɗin ta gam, tana ihu. "Ni wallahi da baka nan, nafi sakewa" "Abun har da sharri, kamar ba jiya ki ka gama kuka ba, saboda kin ganni. Anyway, shirya ki zo mu yi breakfast, zamu yi magana" Sai da ya bar ɗakin sannan hankalinta ya kwanta, ta shirya, ta fito tana wani haɗe rai. Shi kuma ya ƙureta da ido, har ta zauna. Taƙi kula shi, tayi serving ɗin sa, ta ja nata ta fara ci, duk yadda ya so ya maze kasawa yayi, dan yana jin daɗin tsokanar rumaisa yaga ta haɗe rai. "Papa dan Allah ka daina kallona kana dariya, Allah zan tashi". "Allah da iko yake, abun ne da mamaki, six months back, a ƙwailarki na tafi na barki, amma in just six months ace lamari ya kankama haka, kuma kin ƙi yarda na tabattar kar in je acuci ake yi mini. Abunki ras da ke, ai ni yanzu kuma na daina takara da ke, na yarda yafi nawa nesa ba kusa ba, wane ni ma? Ai ni yanzu babu suaran jayayya, zaki iya rainon baby yanzu sosai, kai congratulations mimi, kamata yayi fa mu yi party, tare da celebration, mimi is no more ƙwaila, she's now a big girl, she can bear a baby, she even wore brezia size nawa ne ma ki ke sakawa, mu je mu sayo dozens of it" ƙarshen ƙuluwa rumaisa ta ƙule, ta jefa masa guntun ƙashin da yake hannunta, ta tashi za ta tafi. Ba dan ya iya shanye dariyarsa ba, ya riƙe ta yana cigaba da ƙyaƙyatawa. Duk da tsiyatakun da yake tayi mata, ta kasa fushi da zuciya, watannin nan da yayi, ba ƙaramin missing ɗin sa tayi ba, amma dawowarsa ya sakata a gaba da tsokana kamar tayi kuka. Ta tafi kitchen yin wanke-wanke ya bita, ba abun da yake tayata, ya sakata a gaba da tsokana. Ruma ta kalleshi, kamar ba shi ne idan ya kamile ya tsuke fuska, ko fara'ar kirki ba ya yi ba, yayi ta muzurai, mussman idan yana cikin shigarsa ta sarauta, amma yadda ya sakata a gaba sai ka ce yaya usy saboda tsokana. Ya ƙaraci dariyarsa ya koma falo, ya cigaba da kallo, lokacin sallar azahar yayi, ya tashi ya fita masallaci. Sai dai da ya dawo, har ta kammala girki, ta yi salla ta canza kaya, amma ta kima uban hijjabi, tana so ta ganshi sosai, amma tsiyar da yake mata duk ya takurata. Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Budurwar, meye haka kuma?". "A ina?". "Meye na wani saka hijjabi ana zaune ƙalau, wannan abu na farinciki da ya same mu, gaskiya ban yadda ba". "Allah papa zan tafi ɗaki na daina fitowa" Ya ce "Sorry, ke kin san yadda na yi kewarku kuwa, tsokanar da na daɗe ban yi miki ba nake fanshewa. Ya ƙarasa wurinta ya cire hijjabin, tana riƙewa amma ya cire shi. Kasancewar ba a dining za su ci ba, suka zauna a ƙasan carfet. Ta janyo kwanukan abinci, da plate biyu, ya ce mata "an daina raba plate, a ɗaya zamu ci" ta tuna anty laila ta ce mata cin abinci kwano ɗaya da miji, yana ƙara soyayya, amma ita ba wannan ya dameta ba, sai tambayarta da tayi, to ba zai yi mini kishiya ba, laila ta ce sai kin kula da abubuwan da na koya miki tukuna. Ta zuba abinci ta ajiye masa spoon, ya kalleta ya ce "Ke ni fa tun farko a baki ake bani abinci, ba zaki ajiye mini cokali ki maza ba". "Ni zan baka abinci a bakin?". "Eh mana" Ta ce "Taɓ papa, ko jajjage baka yi mini ba da ina girki, ko sannu sai ma tsokanata da ka yi tayi, na gama abincin kuma sai na baka a baki, in bawa sabir abinci a baki, in bawa babansa saboda jin daɗi". Yayi dariya ya ce "To ki bari in baki, ai ni a wurina da ke da sabir, duk ɗaya, baku da wani banbanci dan abun da yake na shiririta kema yi ki ke" kan tayi magana ya ɗorata a cinyarsa, ya ɗebo abinci a cokali ya kai bakinta. Rufe fuska tayi ta ce "Ayi haka? Kunya nake ji fa" Sauke hannunta yayi, ya tura mata cokalin a baki, tun tana noƙewa ta saki jiki tana karɓa, ta ce "Da na san haka bawa mutum abinci yake a baki da daɗi, ai da na daina ci da kaina, idan na dafa sai ka bani a baki". "Ni zaki saka aiki, yanzu ki ka gama cewa saboda jin daɗi zaki bani abinci a baki, amma yanzu kina gaya mini, in din ga baki abinci a baki. Mara kunya kawai baby mimi an zama lady mimi" "Wallahi idan ka ce babyn nan kunya ka ke bani, ga abinci a baki ga baby, idan aka ga na koma yin rarrafe kai ne ka ja" Dariya Adam yake yi, rumaisa ba za ta taɓa girma tayi hankali ba. "Mimi, kin shiga kin fita kin hana auren jabir da iman, ki ka haɗa da yayanki, kin saka jabir gaba da ni, Jamil ma har na je na dawo bai yi mini magana ba, gaba ɗaya fushi suke yi da ni, duk saboda ke mimi" "A'a nifa ban hana aurensu ba, kuma can suka ƙulla soyayyar su da mai sunan baba, ban sani ba ina gefe ni ƙarfafawa kawai nayi. Kuma papa kawai fa ban gaya maka bane ba, kar na zama munafuka kai baka san me jabir yayi wa ammi ba, wai saboda ba yi auren sa da iman ba, ka ja maganganun da ya din ga gaya mata? Wallahi sai da Mahmoud ya mare shi". "Wane Mahmud ɗin?" "Daddy" ta bashi amsa. Yayi shiru yana mamaki, ya san rumaisa ba za ta yi masa ƙarya ba, yanzu har jabir zai iya kallon ammi ya ci mutuncin ta, matar da duk da abubuwan da mahaifiyar sa take yi mata, bai hana ta ɗauke shi tamkar ɗa ba. "Papa ni fa wasu lokutan ba haka kawai nake tsanar mutum ba, da jabir sonka yake tsakani da Allah, kome ammi za ta yi masa, ba zai wulaƙanta ta ba. Shi kuma jamil sake bina yayi, wai sai na gaya masa yadda aka yi anty aisha ta ɓata, da kuma in gaya masa abun da na sani a kan ta, na ce masa ban san komai ba, sai filin da gwamanti ta karɓa a hannun turaki, ake bashi percentage ya sanya anty aisha a matsayin magajiyarsa, shi ne hankalinsa ya kuma tashi, ya ce kaine ka gaya mini" Adam ya saka hannu ya juyo da fuskar rumaisa tana fuskantar sa, ya ce "Rumaisa, meyasa ba zaki daina yi mini yawo da hankali ba? Yanzu magana ake ta shekara guda da watanni, da ɓatan aisha, ba zaki tausaya mini haka ba, ki daina yi mini ɓoye-ɓoye? Kin bani zane ya ɗaga mini hankali, kuma ban gane komai a ciki ba Please rumaisa" Yayi maganar jikinsa a sanyaye. "Papa ba laifina bane, laifinka ne haryanzu, ka wuce duk wasu matakai da yakamata, kuma ina iya ƙoƙarina na tallafa maka, ɗaya ya rage haryanzu, nima ba son raina bane in ta wahalar da mijina ba, baban ɗa na" "Wani mataki ne mimi?". "Sauran ma ka tsallake su, ba tare da ka sani ba, wannan ma dan kan ka nake son ka yi surrender ka tsallake shi. Kullum ina yi maka Addu'a, duk wanda na yi wa abu yaji daɗi, sai in ce ya saka ka a addu'a, komai zai zo ƙarshe fa" Jiki a sanyaye ya ce "Shikenan mimi, Allah ya yi mana jagora" Ta ɗebo abincin ta kai bakinsa, amma ya girgiza kai ya ce "I loss my appetite, na ƙoshi". "Dan Allah ka ci papa, zan yi kuka, kar ka saka na karaya na rigaka miƙa wuya, ba haka muka yi da anty aisha ba" Cikin mamaki ya ce "You mean you set a deal with her a kaina?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "What was it?". "This is not the right time to voice it out, i have to finish it first, but am sorry papa" Idonsa fal hawaye ya ce "Shikenan miki, baki yi mini laifi ba" Tuni hawaye ya gangaro mata, ta shafa fuskarsa ta ce "Dan Allah papa kar ka yi kuka". "No mimi allow me, it really hurts me, ina jami'in tsaro na kasa bawa iyalina kulawa, har ta rasa ranta mutuwar wulaƙanci, ta haihu a dokar daji, what a mess". Ruma da tuni ta fara sheshsheƙa ta ce "Daga baya na gane is not your fault, ka daina dan Allah". Ya kwantar da rumaisa a ƙirjinsa, yana shafa bayanta da sigar rarrashi, amma hakan ya bashi damar, zubar da nasa hawayen silently. A hankali ya ce "Ashe turanci ya fara zama Inyeee". Ya zira hannu ya kamo hannun brziar ya ce "ina zamu je celebration ne? A buga cards, da  congratulations on your newly developed... Bai ƙarasa ba ta gantsara masa cizo a hannunsa ta tashi. Dariya yayi, atleast ta rage damuwar da ta shiga yanzu. *** Yasir kuwa kai da fata ya dage, ya ɗauki lambar iman a wayar mama, kasancewar mama ta kira iman da kanta, tana mata ƙorafin, ta daina zuwa gidan gaba ɗaya, wanda ba iman ba ƙaramar kunya ta ji ba. Yayi amfani da damar, ya ɗauki lambar, ya yi wa iman magana ta what's app, bayan sun gaisa yayi mata bayanin shi ne, ya tura mata akwatuna ya ce ta zaɓi wadda take so. Iman ta ce "Yasir duk abun da yaya umar ya bani ina so, ba zan zaɓi komai ba dan Allah ku ce masa kar ya wahalar da kansa yayi mini iya abun da Allah ya hore masa". Yasir ya ce "Amma dai bani ni ne zan gaya masa hakan ba ko? Ai wannan aikin sai ke ko hajiya mama, ni a suwa, dan Allah ki zaɓa amma kar ki gaya masa" Iman ba ƙaramin burgeta suke yi ba, suna matuƙar son junansu, fiye da tunani. Ƙin zaɓa tayi, ta ce kowacce aka yi ta gode. Da yamma mai sunan baba ya dawo daga kasuwa, ana ta cigaba da gini, yana tara kayan lefe, kowa ya fita ya dawo, sai ya kawo wani abun na kayan lefe, kuma ƴan uwa basu gaza ba, da cigaba da kawowa mama gudunmuwa. Turus yayi ganin wasu kyawawan akwatuna, guda shida da kid, haɗaɗɗu masu kyau. Mai sunan baba bai tanka ba, sai da mama ta ce "Babana, mutuminka fa ya cika alƙawari ga akwatunanka nan". "Meyasa Yasir ba ya jin magana ne? B jari yake tarawa ba, dan me zai kwashe kuɗinsa ya yi wannan hidimar, sonake na ga me zan samu a cika masa, amma ya kwashe kuɗinsa yayi wannan aiki, sai kuma da nace masa ya bari, yanzu kan ya mayar da kuɗin fa" Yasir da yake tsakar gida, bai ji daɗin abun da mai sunan baba yayi ba, sai dai ko menene shi ya san yaya umar ha cancanci fiye da haka. Mama ta yi ta yi wa mai sunan baba faɗa a kan bai kyauta ba. Ko da ya fita tsakar gida, ya kalli fuskar yasir, fuskarsa ta nuna bai ji daɗin abun da mai sunan baba ya yi masa ba. Har dare Yasir sabgoginsa kawai yake yi, ko ɗan shishshigin nan da suke yi wa mai sunan baba, yau bai yi masa ba. Sai dai da ya shiga ya fita, sai mama tayi ta saka masa albarka tana kwarara masa addu'a. Har ƙarfe goma na dare, yasir bai shiga gida ba, mai sunan baba ya ɗau babur ya biya shagon yasir, ya tarar da shi yana ta aikin wayoyin mutane da system, shi da yaransa. Horn ɗin da mai sunan baba yayi ne ya dawo da shi hayyacinsa, ya ajiye wayar hannunsa ya fito. Mai sunan baba ya bashi galan ɗin man fetur, ya ce "Gashi nan ka zuba a  injinka" Yasir ya karɓa ya ce "To na gode sosai" "Ka rufe shagon nan mu tafi gida, dare yayi goma tayi" Ya amsa masa da "To, bari na sallami yaran" ya wuce cikin shagon ya sallame su. Shagon da Yasir yake harkar wayoyinsa da system, har ma da POs mai sunan baba ne ya kama masa shagon, ya saya masa system. Ya ce hauzaifa kuma ya iya ɗinki, shegiyar shirirtar sa ta hana mai sunan baba bashi jari. Yasir ya rufe shagon, ya hau babur suka tafi gida, a ƙofar gida mai sunan baba ya ce "Yasir". "Na'am" "Ban yi maka faɗa a kan abun da kayi mini dan na ɓata maka rai ba? Kaga jari kake tarawa, bai kamata ace na mayar da kai baya ba". "To waye ya bani jarin?". "Duk da haka bai kamata dan na baka na dawo na cinye ba, anyway ka daina fushin na gode sosai Allah ya ƙara buɗi, ya sanya ku fi haka, ya sanya maka albarka a nemanka" yayi maganar yana musabaha da hannun yasir. Yasir yayi murmushi ya ce "Muke da godiya mai sunan baba" "Nima yakamata na gode, na san ka kashe kuɗi sosai, Allah ya mayar maka da ninkin abun da ka kashe" Ya amsa da "Amin Yaya" Suka shiga gida tare. *** Kwanan Adam huɗu da dawowa, rumaisa ta tarar da shi a ɗakinsa, da travelling bag. "Ya haka, me nake gani, wannan jakar fa? Ga breakfast can". Ya ce "Kin tashi kenan?" "Eh mana ina zaka?" "Nemana ake a abuja, zan je na yi booking Flight" "Daga dawowar taka za ka kuma tafiya?" Takawa ya ce "Kiran gaggawa ne, suna buƙata ta, ba zan fi sati ɗaya ba" Haushi ne ya kama rumaisa, kawai ta fice daga ɗakin, ta koma nata. Bin bayanta yayi yana kiran sunanta, ya tarar da ita a falo, ta cika tayi fam. Ya zauna kusa da ita ya ce "Wai mimi meyasa ki ke da matsala ne, harkar aiki ne, idan ban je ba ya zan din ga samo mana kuɗi, na biya miki kuɗin makaranta, na saya mana abubuwa" "To daga dawowarka sai ka kuma tafiya, kullum baka nan ai shikenan" "To yanzu ya ki ke so ayi?" "Kawai ka fasa" "Mimi zuwana yana da muhimmanci, ga kuma karatuna na kammala, akwai aikace-aikace a gabana sosai da sosai, kiyi haƙuri 5days kawai in sha Allah zan dawo". "Ni sai dai ka tafi da ni, idan ba haka ba zan yadda ba". "To shikenan, zan saka ayi mana booking Flight shikenan" Ta waro ido ta ce "Dan Allah jirgi zan hau?" "Ƴar ƙauye zata hau jirgi" Ruma har da tsalle ta ce "Wayyo daɗi, bani waya na kira yaya usy, na gaya masa zan riga shi hawa jirgi". Yayi murmushi ya ce "Sai mun sauka tukuna, Ki ɗaukko mana akwatinki guda ɗaya, ki haɗa mana kayanmu" Tashi tayi da sauri ta tafi tana murna yau zata hau jirgin sama. Ta waya ta sanar da mama zata raka takawa abuja, amma ba zasu fi kwana biyar ba zasu dawo. Aliyu ya ce "Yarinyar nan tana sararawa, taɓararta kawai take yi son ranta". Rumaisa bakinta yaƙi rufuwa, da ta ganta a cikin jirgi, ta ce "Papa, yanzu idan nayi tsalle a jirgin nan, ya zai yi ƙasa zai yi". "A'a sai dai idan yanzu zaki gwada tsallen". Ta ce "Haba dai su rainani" "Gaskiya dai, babbar yarinya kamar wannan mai abun arziki ai sai a rainaki" "Zaka fara ko?" Ya ce "Ban fara ba tukuna". Ko da suka sauka taxi suka hau, suka nufi hotel ɗin da zasu sauka. "Papa, to ina gidan shugaban ƙasa yake a nan?" "Me zaki yi wa shugaban ƙasar?" Rumaisa ta gyara zamanta ta ce "Zan ce masa dan Allah ya saka a daina sace mutane, wallahi wahala ake sha sosai" Murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba. Hotel ɗin yayi wa rumaisa kyau, sai dai nanata masa take yi, ko sun koma gida kar su gayawa kowa hotel suka zo a abuja, kar ayi musu kallon mutanen kawai. Da suka shiga bedroom ta ga ɗaki ɗaya tal, da toilet. Ta ce "To ina banɗaki, da kuma kitchen da nawa ɗakin?" "Babu kitchen, a nan zamu din ga kwana tare" "Kai, ni da kai a ɗaki ɗaya, kuma ba kitchen to me zamu din ga ci?". "Saya zamu din ga yi" "To waye zai din ga kwana a kan gadon?" "Ke dai kin san ba zan biya kuɗin ɗaki in kwana a ƙasa ba ko? Sai ki nemawa kanki mafita" Ya ajiye akwatin, ya nemi wuri ya zauna, ya ɗauki wayarsa yana kiraye-kirayen wayarsa, ya ce a kawo masa mota. Da daddare ya ɗauki ruma suka fita yawo, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa ruma ba, duk da dare ne fitar tayi mata daɗi sosai. Ta ɗauki wayarsa ta kira Huzaifa, tana ta bashi labarin yadda jirgi yake, da abubuwan da ya sai mata. Usman ya karɓi wayar ya ce "Ke wayar nan a handsfree take?" Ta ce "A'a" "To ki ba ya fita dake yawo ba, har kin hau jirgi kina yashe baki, ga uwar tsaraba da ya yi miki da ya dawo, idan. Ki ka kuma kawo mini ƙarar kin yi masa wani shirmen, wallahi kina zaune zai auri wata ya din ga wannan yawon da ita, gara a din ga gaya miki gaskiya". Shiru tayi daga baya ta ce sai anjima, ta kashe wayar tana tura baki. Takawa bai san me suke cewa ba, kuma bai damu da ya tambaya ba. Suka koma masaukinsu, sai nanatawa take ita fa tunda ta baro gida, ta saba da kwanan kan gado, dan haka ba zata kwana gado ɗaya da shi ba, kuma ba zata kwana a ƙasa ba. Yayi mata shiru, ya ɗaukko system yana daddanawa. Ta shiga banɗaki ta fito, ta zauna a gefen gadon tana kallo abun da yake rubutawa a system ɗin. Ya tashi ya shiga banɗaki, hakan ya bata damar tashi ta buɗe akwati, ta fara canza kaya. Ayshercool. 08081012143 **SHIN YAR UWA KIN SAN ILLAR DAKE TARE DA INFECTION KUWA?, TO BARI KI JI KAƊAN DAGA CIKIN ILLAR DA INFECTION YAKE DA SHI? KIN SAN CEWA INFECTION YANA HANA HAIHUWA?, YANA HANA MA'AURATA JINDADIN MU'AMALA, YA NA SAKA  WARIN GABA KOWANE IRIN TURARE KI KA YI AMFANI KO GYARA KI KA YI, BA ZAI HANA WANNAN WARIN FITA DAGA JIKIN KI BA FITAR FARIN RUWA, TARE DA ƘURAJE. ƘAIƘAYIN GABA, TUSAR GABA, DUK SUNA DAGA CIKIN ILLAR DA INFECTION YAKE WA LAFIYARKI INA MASU FAMA DA ULCER, ASTHMA, SICKLA, INA MATAR DAKE FAMA DA MATSALAR FIBROID, MATSALAR RASHIN HAIHUWA KO BUSHEWAR  JIKI DA FATA, KU GARZAYO KU GWADA MAGUNGUNANMU MA GHT SUPPLEMENT, KU GANI DA  IKON ALLAH DA IZININ ALLAH, MAI BUƘATAR ƘARIN BAYANI YA NEMI WAMN 0703 527 5119* Ko ku danna wannan link ɗin, domin kasancewa da mu, ku ji yadda https://chat.whatsapp.com/COM8NE7rDs8HAG0Oqfr9wm *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin* *5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14.  Supplement na whitening/glowing skin* *15.  Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 *TALLA! TALLA!! TALLA!!! *ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH* Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.” Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH…. (*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*) *Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143* Buɗe ƙofar banɗakin yayi ya fito, ta ƙwala ihu ta rufe jikinta, ko kallonta bai yi ba, ya maze kamar bai ganta ba, ya wuce ya kashe fitila ya kwanta. Ajiyar zuciya tayi, ta saka kayanta, ta nufo gadon, sai dai ya babbake gadon, kuma ya ajiye system a kan gadon. "To ka matsa mini in kwanta". Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Gado ɗaya zaki kwana da ƙaton?". "To a ina zan kwanta?" Yayi mata shiru, ya cigaba da tattaɓa system ɗin. Ta hau ta ja fulo ɗaya ta kwanta, ta ce "Papa ni fa buge-buge nake yi idan ina bacci, wurin nan yayi mini kaɗan" "Saboda gaki giwa ko? Ki ka buge ni ƙasan gado zan hankaɗa ki" "Dan Allah papa ka matsa, ga space can a bayanka fa" Ganin ba zai kulata ba, ya sanya ta kwanta, shima kashe system ɗin yayi, ya kwantar da kansa a kan pillonta, jin numfashin sa a fuskarta ya sanya ta buɗe ido. "Papa wai dan Allah idan baka takura mini ba baka jin daɗi". "Mmm" ya bata amsa. "To dai ina yawun bacci, kan gari ya waye na jiƙa fulon nan, gara ma ka tashi" dariya yayi ya ce "Ba zan fa tashi ba" Ta yinƙura zata juya masa baya, ya riƙeta. A haka wani irin nannauyan bacci yayi awon gaba da su gaba ɗaya. *** Iya ƙoƙari sosai mai sunan baba yana yi, a kan ya samu ya kammala ginin nan, duk da kusan abubakar ne yake ta aikin, gefe ga kayan lefe yana fama. Sai dai a duk lokacin da ya tambayi iman, ko ta na da buƙata kalar abun da za a saka mata a kayan lefe, sai ta ce masa ita ba ta da zaɓi, duk abun da yayi mata shikenan. Yadda laila ta tsaya a kan rumaisa, haka yanzu ma ta tsaya a kan Iman, take ta shan gyara, sai wani irin kyau take, ta ƙara ƙiba tayi fresh da ita, fatar nan ta ƙara sheƙi, saboda yadda ta kama sabayar maman Khadija, gefe kuma ga maganin maman ilham, wanda ya ƙara sawa ta cika ta yi fam da ita. Abunka da farar mace, har wani ɗaukar ido take yi, mai sunan baba duk lokacin da ya zo wurinta, sai ya ga ta ƙara yi masa kyau fiye da da, sai dai ba zai iya fitowa ya ce mata tayi kyau ba. Sai ma ji da ya din ga yi, ina ma ta daina fita, saboda kishinta. Mai sunan baba ya saki jiki da mahmud, dan har gidan da iman za ta zauna, sun je tare, ya din ga yabawa mai sunan baba sannan ya ce "Ni yakamata na ƙarasa aikin ginin nan fa". Mai sunan baba ya ce "Saboda me?" "Saboda haka ya kamata" "Ko kuma ka raina abun da nake yi ne?" Mahmud ya yi murmushi ya ce "Ni na isa? Kawai akwai buƙatar yin hakan ne, iman da mahaifiyata, da kuma rumaisa suna bina nannauyan bashin da yakamata na sauke". Mai sunan baba cikin rashin fahimta ya ce "Wane irin bashi kenan?" Mahmud ya ɗan yi shiru ya ce "Ban san a yaya zaka ɗauki abun ba? Na san zaka ji shi hagu a dama. Kamar yadda kowace uwa da ɗa, yake akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninsu, to ni saɓanin haka ne, ba wata soyayya ko shaƙuwa tsakanina da tawa uwar, hasali ma a gabana ake cutar da ita, bana iya cewa komai. A lokacin da iman ke kan ganiyar kwasar baƙin ciki na fasa aurenta a jejjere, a lokacin ammi ta nemi alfarmar na auri iman, amma na ƙeƙashe ƙasa na ce ba zan ba. Ni kaina bana gane yadda wasu abubuwan suke gudana, har sai da rumaisa ta shigo rayuwarmu, take ta ƙoƙarin haska mini hanya, da farko da ni daga nannauyan baccin da nake yi. Tana ta ƙoƙarin gyara tsakanina da mahaifiyata. Na san zaka ji labarin a wani iri ba lallai ka fahimta ba, amma ka bar shi a haka, ni dai fatana, ka bani dama ko yaya nayi wani abu a kan rayuwar iman, ko dan farantawa ammi da kuma rumaisa". Ya share hawayen da ke ƙoƙarin zubo masa, ya fita daga gidan, tabbas kamar yadda ya faɗa, umar bai gane kan wannan rikirkitaccen zancen ba, tayaya zaka rayu a cutar da mahaifiyarka a gabanka, ba tare da ka ɗauki wani mataki ba?. *** Baccinsa yayi nisa sosai, har alarm ɗin wayarsa ya dinga bugawa na sallar dare, amma bai tashi ba, sai da rumaisa tayi masa wani duka da ƙafarta a ciki, ya tashi a razane. Har ya tashi zaune, bacci kawai take yi, kuma kaɗan ya rage ba ta faɗa daga kan gadon ba, duk ta baje kamar baccin jarirai. Janyota yayi ya gyara mata kwanciyarta, ya rufeta da bargo.. Yayi shiru yana kallonta, tare da mamakin yadda Allah ya yassare mata baiwa kala-kala, a haka dai gata ba ta ji sam, amma tana da baiwa ba ƙarama ba, shi kansa yana mamakin yadda yake lallaɓata, yake bin duk abun da ta ce masa. Maybe hakan ba ya rasa nasaba da yadda yake ganin girma, da kuma darajar abun da tayi masa, wanda ko duniya zai bata ba zai biyata ba. Ya durƙusa yayi kissing ɗin goshinta, sannan ya sauka ya shiga banɗaki. Da safe kuwa yana banɗaki yana wanka, tana tsaye a gaban dressing mirror, tana kallon kanta a mudubi, tunani take maiyasa ba ta zo da sabayarta ba, dan ba ƙaramin missing ɗin kunun take yi ba. Kar fa ta je su koma yadda suke a da, gaskiya gara ayi a koma gida, ta cigaba da amfani da kayan maman Khadija da na maman ilham. Knocking aka yi a ƙofa, ta nufi ƙofar ta buɗe, ta ga wata mata a tsaye, cikin broken English matar ta ce mata abincin da aka yi order ta kawo. Rumaisa ta ce "Wannan wane irin turanci ne babata, wannan kalar turancin kamar na ƴan lagos, kenan turancin kano daban, na anty laila ƴan canada daban, na abuja da Lagos iri ɗaya?" Matar ta ce "Ban gane me ki ke faɗa ba?" Rumaisa ganin matar ba ta jin hausa, ya sanya ta samu abun yi, ta riƙe ƙugu ta ce "Na ce, wane irin turanci ki ke yi, ke baki iya hausa ba? Kuma dai papa bai fita ba, kuma bai yi waya ba, ya aka yi ki ka kawo abinci, ko na sadaka ne?" Kamar shashasha matar take kallon ruma, dan ba ta fuskanci komai ba. Takawa ya ƙaraso ya karɓi kayan hannun matar, ya yi signing ya ce mata ya gode. "Wai ni ya aka yi ka saka aka kawo abinci, naga ba wanda ka kira a waya" Ya ce "Ai na so matar nan ta zane ki, kawai kin saka mata a gaba, kina ta mata surutun banza da hausa, bayan ba ganewa take yi ba". Ta ce "Mhmm, nima fa kamar da a makarantar mu, bana gane komai, kamar dai ni da matar nan, ni babban abun da nake ganewa, a bani kuɗin makaranta na sai goriba, ko manɗo na yi tsokana da surutu na dawo gida". "Yanzu fa?" "Ina ganewa, anty laila ke koya mini sosai, kuma zaka ga result ɗina" Suka karya, yana yi mata mitar, dukan da tayi masa cikin dare. Dariya ta din ga yi masa, ta ce "Ai dama na gaya maka, Innalillahi ni fa sai da aka yi mini aure na daina fitsarin kwance, musamman idan ana sanyi, in ji fitsarin ya matseni, sai in yi mafarkin gani ina fitsari a banɗaki, wallahi ina tashi zan ga nayi a kwance" "Yanzun ma waye ya sani ko kuna abun ki?" Ta ce "Haba papa, lokacin fa ina yarinya ne fa nake baka labari" "To yanzun girma ki ka yi, ko da yake an fara girma fa, mantawa nake yi" Saboda kar ya zauna ya fara tsokanar ta, ya sanya ta tashi ta tafi window tana leƙawa. Can ya ji ta ce "Innalillahi" Ya ɗago ya ce "Lafiya?" "Papa ina ka kawo mu nan? Nan ai duk ƴan iska ne leƙo ka ga fa" Ya ƙarasa ya tsaya a bayanta, wasu mata take nuna masa, sun sha matsatsun kaya, marabarsu da tsirara kaɗan ne, sai kaiwa suke suna komowa. Ya ce "Sun yi kyau tubarkallah" ba shiri ta kalle shi ta ce "Me ka ce?". "Na ce sun yi kyau" Haɗe rai ta yi ta ce "Amma dai ka san haram ne ko?". Adam ya ce "Ke fa ki ka nuna mini" janyo window tayi ta rufe tana huci. Ya fara ƙoƙarin ture ta ya sake buɗewa ya ce "Matsa ban gama gani ba" Rumaisa ta haɗe rai ta ce "Wallahi ba zan matsa ba" Yayi murmushi dama abun da yake so kenan, ya ce "Yanzu da cewa na yi, ki saka irin kayan, cewa zaki yi ke ba ƴar iska ba ce,  tunda na ga na bati, ai sai ki barni na kalla ko?" Tayi shiru tana kallon sa. "Ko zaki saka?" Yayi maganar yana tsareta da ido, sai dai tayi shiru bata bashi amsa ba. Ya ce "Ke ba ƴar iska ba ce ko? Laila ba ta gaya miki babu kunya tsakanina da ke ba?" Shiru tayi tana tunani, tabbas laila ta gaya mata, kuma usy ma ya gaya mata, kenan da gaske suke mata?. A hankali ya ce "Shikenan, laifina ne" ya juya ya bar wurin. "Zan saka" ta furta kamar tayi zunubi. Ya tsaya ya waiwayo ya ce "Are you serious?" Ta jinjina masa kai alamar eh, dan har ga Allah saboda kar ya cigaba da kallon waɗancan matan ya sanya ta ce zata saka, kuma bata son kishiya. Ya ce "To mu je in anjima mu sayo, zaki saka?" "Eh amma zaka daina kallonsu?". "To me zai saka na kallesu? Ai na san ba kyau, in dai zaki saka ba zan sake ba" Murmushi yayi yana kallon baby face ɗin ta, ta faɗa ne kawai saboda kishi. Ya ce "To shikenan, in anjima zamu je, saura sai mun dawo ki ce baki san zance ba" Wuni suka yi tare, ya bata damar yin surutunta son ranta, ba tare da nuna mata ya gaji, ko ya ƙosa ba, suka sha dariyarsu tare ta bashi labaran ta lokacin tana gida, salla ce kawai ta din ga fitar da shi. Da zai fita sallar magariba ya ce mata "Mimi, ki zauna karki fita ko ina, idan na idar da salla zan je meeting ba daɗewa zan yi ba, zan dawo in sha Allah" "Wai ni zaka bari a ɗakin nan nikaɗai?" "Eh, ba daɗewa zan yi ba" "Wallahi tsoro nake ji, haka kurum a yankani, idan ka tafi sai dai ka tarar da ni a bakin titi, ko na ɗaukko rigima da sai an koromu daga wurin nan. Ko kuma in jiraka a wurin shigowar nan, kuma ka bani system ɗin ka da wayarka ɗaya nayi game har ka dawo". "Salon ki goge mini wani abun, idan ki ka goge mini abubuwana, sai na kai ki prison, zan baki amma a ɗaki zaki zauna". Rumaisa ta basar ta ce "Prison ai sai marasa gaskiya, dan Allah kar ka barni a nan papa, da gaske tsoro nake ji fa" tayi maganar cikin shagwaɓa. Yayi ajiyar zuciya ya ce "Bari na je nayi sallar sai mu tafi". Da misalin ƙarfe takwas da mintuna biyar na dare, takawa yayi parking a gaban harabar wata plaza, ya sanya rumaisa a gaba, suka shiga. Wani irin katafaren office ne, ƙato mai kyan gaske. A can suka tarar da bashir ma, ruma ta ce "Yaya bashir, ya aka yi ka zo nan?" Ya ce "Ɗazu na shigo ni, ai ya ce mini tun jiya ku ka zo" Suka gaggaisa da mutanen wurin, sai dai ruma ta raɓe a kusa da adam, saboda duk sai ta takura, ita kaɗai ce mace a cikinsu. "Adam wannan kuma fa?" Cewar ɗaya daga cikin su, da ya tsare rumaisa da ido. Barrister sa'ad ya ce "Madam ɗin sa ce". Ya ce "Masha Allah, amma me zata yi a nan, harkar aiki ce fa" Adam ya ce "Ba zata hanamu aikinmu ba, mu fara kawai barrister meye a ƙasa?" Barrister sa'ad ya ce "Eh to, harƙallar fasa bututun man fetur, da kullum ake yi wa ƴan ƙasa ƙarya da ita, Dss sun kama mutum uku shekaranjiya a delta, bayan sanarwar da hukumar matatar mai ta fitar cewa, man da ake samarwa a Nigeria yayi ƙarancin da kuɗin da yake kawowa ƙasa ba zai wadaceta ba, sai an ciyo bashi, sai dai mutanen sun ce SMOKE suke yi wa aiki, an sake su ba tare da kowa ya san an yi bama, Salim ne yake gaya mini" Takawa ya ce "SMOKE again?" Bashir ya ce "Adam, shirye-shirye fa sun yi nisa, wakili zai tsayar da ɗan sa Khalifa takarar ɗan majalisa, kuma ka san jam'iyyar tana da ƙarfin da ko da ƙarfin tuwo zasu ƙwata su bashi, mecece makomar al'ummar da mutumin banza zai jagoranta?" "Ba wannan ba, cire sunanka da ga jerin jami'an da za a ƙarawa matsayi bayan dawowa daga ƙaro karatu, yafi ɓata mini rai". Takawa ya ce "Ba matsayin nake buƙata ba, goyon baya ta yadda zamu yi ƙarfin da zamu iya ƙalubalantar kowa. Akwai buƙatar lawyoyin cikinmu, ƴan siyasa da sauran hukumomi masu son yin aiki domin ƙasarmu ta gyaru, ace sun ƙara yawa". "Adadin mutanen ka adadin matsalarka, adadin yadda sirrinka zai din ga fita, aikin yana tarwatsewa, ayi ta haɗaku rigima da zargin juna" Tsit suka yi suna kallonta, shi takawa a wurinsa ba abun mamaki bane ba, jin kalaman hangen nesa a bakin ruma idan ta ga dama, dan na shirirtarta sun fi yawa. Ya ce "Silent mimi, meeting fa nake yi". "Daga bayar da shawara?" Takawa ya ce "Idan ki ka kuma magana ba zan sake fita da ke ba" Barrister sa'ad ya ce "Adam, allow her please, gaskiya fa ta faɗa" Takawa ya ce "Rabu da ita, yanzu dai sa'ad, zan yi magana da salim, ya sake bin diddigin samo mana hujja da tabattar da abun da ya faɗa, zamu sanar wa da mutane. Sannan ɓangaren media, su musbahu, dole su cigaba da tattaunawa da masana tare da fahimtar da mutane illar ciyo wannan bashi, dan ba ƙasa ake ginawa ba, kansu suke azurtawa, na rasa wani asarraren ne ya zauna ya samar da dokar yi wa ƴan majalisa da tsofaffin gwamnoni hidima da kuɗin al'umma, wace irin ƙasa ce haka, a mulke ka a gasa ka, kuma a ranto kuɗi a bawa wanda ya zalunce ka ace ka biya, abubuwan nan sun fara isata, muna tufka ta gaba ta baya na warwarewa". "Wannan faɗar fa da ka ce ayi ta gayawa mutane, ƙara musu takaici ku ke yi, maganin abun yakamata ku yi musu, tayaya za a zo ace mini wane ya ɗauki kayana, mutane na kallonsa babu wanda yayi yinƙurin hana shi, balle a karɓa mini kayana, kuma azo ana bani labari, kamar haka ne fa papa" Bashir ne ya tafawa rumaisa, ya ce "Kai, rumaisa kina da brain irin sosai ɗin nan, takawa yakamata kayi mata special adviser a tafiyar nan. Amma rumaisa mun koma maganar mu ta farko, domin iya kama ɓarawon da yayi miki sata, dole wataƙila mutane na buƙatar ƙarfi da yawa, dan wataƙila ɓarawon ba ɗaya bane ba, sun ɓuya da yawa da muggan makamai" "Sai ku yi musu dabara, ta hanyar yi musu tarko, ku kama wakilin nasu, idan kuka cigaba da zuba ido ana yi mini sata, idan nawa kayan suka ƙare kan naku zasu dawo, kuma bayan sun gama idan suka rasa abun sata, ku zasu fara kamawa suna sayarwa, ana ciniki ku kamar dai yadda ake fataucin dabbobi, ayi ta ciniki kamar an kama bayi, kamar dai yadda aka sace ni, da ni da anty aisha". Maganganu rumaisa ta saƙa musu cikin hikima, da sai da ta sanya su cikin nazari, adam ya ce "Ina ga mu tashi haka, zamu biya wani wurin ne da ita, zamu haɗu gobe in Allah ya kaimu " Barrister sa'ad ya ce "Allah ya kaimu, amma lallai muna buƙatar ƙwaƙwalwa irin t madam a tafiyar nan". A ransa ya ce 'Baku san butsancinta ba, sai tayi muku wani shirmen zaku gane baku da wayo'. Adam kansa har wani ciwo yake, yana ta tunanin maganganun ta, ita kuwa ko a jikinta, har suka isa masaukinsu. Kamar yayi mata magana a kan maganganun da tayi, amma ya shareta, dan da yayi zata fara wahalar da shi. Kwanansu uku a Abuja, ya kaita yayi mata sayayya, ya kashe kuɗ sosai, banda tsarabar da ya yi mata da zai dawo, banda uban kayan lefenta da haryanzu wani abun ma bata taɓa ba, ga shirin bikin iman nan ma yana ta hidima. Suna tafe a hanya tana kallonsa, ba ƙaramin tausayinsa take ji ba yanzu, gaba ɗaya yadda ta tsammaci halinsa ba haka yake ba, duk da dai mafaɗaci ne mai zuciya, amma a zamansu ta tanƙwara shi ta ƙarfin tsiya ya tanƙwaru, dan shi kansa ya san ko bai durƙusa mata a kan gwiwoyinsa a zahiri ba, a baɗini yayi. Tana ta ɗaɗɗaga kayan da ya saya mata tana murna, wasu kayan tana tunanin anya zata iya sawa kuwa, duk da anty laila ta koya mata saka ƙanan kaya, amma wasu kayan sun yi watsewa da yawa. Yana zaune a kan gado yayi shiru, yana zancen zuci, rumaisa ta buɗe akwatinsu, ta fito da pencils ɗin ta na zane, ta ɗaukko cardboard paper, ta zube su a kan ƙaramin Centre table, da cleaner da duk abun da take buƙata. Ta tashi ta nufi takawa, ta riƙo hannunsa ta ce "Taso muyi zane papa" Ya ƙwace hannunsa ya ce "Leave me, am not in mood" Ta ce "Gaskiya ni ba zaka zauna kayi mini shiru ba, ka taso". Ya ɗaukko wayarsa ya ajiye mata, ya ce "Gata nan je ki kiyi hirar da ita". "I want de encrypted the portrait i gave you 6months ago". A hankali ya juyo yana kallonta, ta jinjina masa kai ta ce "Taso" Tashi yayi a hankali ya biyo ta, suka zauna a tsakiyar ɗakin. Ta fara da zana farin wata, irin a daren goma sha huɗu. Yayi shiru ya nutsu yana kallon ikon Allah, sannu a hankali ta yi zane iri ɗaya sak da wanda ta bashi, sai dai a wannan karon da alamomi da bayanai yadda zai gane. Ta zana kanta a zaune a cikin daren a daji, ga masu garkuwa da su riƙe da bindigogi, sai ta zana wata hanya, ta rubuta unknown distance. Tayi alamar yadda sautin ababen hawa ke kaiwa suna komowa a nesa da wurin, duk da yanayin wurin babu alamar abun hawa zai iya bi. Ta kalleshi ta ce "Papa meye ma'adanai?" Ya ce "Resources, albarkatun da Allah ya ajiye a cikin ƙasa, da ƙasa ke amfani da su, a sayar ko a sarrafa dan al'ummar ƙasa su mora" Ta ce "Ok" Sai ta koma kan zanen ƴan ta'addan, ta nuna ɗaya yayi magana ya ce "Ga mutanen SMOKE can suna aiki" Ɗaya kuma ta yi alamar ya ce "Ƴan wahala, coustom sun gama gyara musu hanya, da sun je za su wuce" Ta koma wajen da tayi alamar sauti na tasowa ta ce "Unknown resources" Ta ce  "zasu iya kasancewa ma'adanai ne kawai? Ko kuma akwai wani abu bayan ma'adanan da suke ɗauka. Ka tambayi uncle bashir, a ina ya tsinto ni, ba zan ce takamaimai in da ya ganmu nan ne  aka sace mu ba, amma daga nan zuwa in da aka ɗaukemu, kwana uku nayi ina tafiya, sannan duk wanda aka kama a wurin da ma'adanan nan suke, sun san suwaye SMOKE!" Jiki a sanyaye ya ɗauki zanen yana dubawa, rumaisa ta sake cewa "Nayi maka wannan bayanin ne, saboda naga you are curious about it. Amma still SMOKE ɗin na da nasaba da sace anty aisha, dan ita ba dan a karɓi kuɗin fansa aka kawota ba, dan a koyawa mijinta darasin da har abada ba zai manta ba aka kawota, ku kula sosai wannan aikin SMOKE ne. Shi ne abun da aka ce lokacin da aka kawota. Papa idan har babu wanda ya san anty aisha ta dawo daga kai sai ita, dole-dole akwai na kusa da ita da ya sani, aka haɗa baki da shi, ko ta gayawa wani kai baka sani ba, ko kuma ka ƙara tsananta bincike a kan yaronka da aka kashe wanda shi ya tafi kai ta garin nasu" Tamkar rumaisa ta zare masa lakar jikinsa, gaba ɗaya in da ya dasa hasashen binciken sa daban, abun da rumaisa kuma ta gaya masa dabanz to meye manufar ƙin yi masa wannan bayanan tun da wuri?. "Mimi meyasa duk baki yi mini wannan bayanin ba tuntuni, ki ka bari nake ta wahala?". "Saboda baka buƙatarsa a lokacin da ka neme shi, yanzu ka mayar da hankali ka san suwaye SMOKE ɗin dai. Saura kuma ka je ka gayawa wannan abokan aikin naka, dan ka fiye yadda da mutane da yawa, yaya bashir kawai zaka gayawa, idan ba haka ba zan sake gaya maka komai ba" Daga haka ta tashi ta bar shi da tufka da warwara. Gaba ɗaya ya rasa nutsuwarsa da walwala, kwanyar rumaisa ba duk kai ba, rashin jin ta kawai mutane ke iya gani, amma ba kowa ke iya ganin baiwar da Allah ya yi mata ba. Ita dai hankalinta kwance ta kwanta baccinta, amma adam bacci ya gagare shi, ya kasa zaune ya kasa tsaye ya kasa kwanciya yayi bacci, yama rasa me zai yi. Yayi alwala, ya tayar da salla, yayi ta addu'a. Har ya hau kan gadon zai kwanta, ya buɗe ya shiga kallon hotunan aisha. Ya kashe system ɗin ya kwanta, rumaisa duk tana kallonsa. "Papa" "Mimi". "Ka kwantar da hankalinka dan Allah, zaka yi nasara, sai dai kar ka sanya ran ko komai ya bayyana zaka samu adalci yadda ka ke tsammani" Bai ce komai ba, ya juya ya rungumeta sosai a jikinsa, yana ta jejjera numfashi. "You are brave papa". "Yanzu kin yadda ba sakaci ne ya sanya ina jami'in tsaro na kasa karɓo Aisha ba?". Ta ce "Faɗa fa nake dan na baka haushi kawai, anty aisha ta gaya mini kai mutum ne mai yi wa iyalinsa hidima sosai" Riƙe kunneta yayi ya ce "Daɗin me ki ke ji, idan kin ɓata mini rai ne?" "Daɗin da ka ke ji idan kana tsokanata" ta bashi amsa. Ya ce "Yauwwa kin tuna mini ma, bari in ɗora daga in da na tsaya, my mimi ƴan mata, budurwata ta kaina". Ƙoƙarin ƙwacewa take daga jikinsa, sai dai abu kamar wasa, Adam ya mayar da rumaisa cikakkiyar matarsa. Wanda shi kansa abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, kenan matsalar ta sa a cikin gidansa take kenan?. Bayan gama jero sunayen ƴan gidansu, har da kiran ƙawayenta, banda cizonsa da ta din ga yi, kamar ƴar damusa. Bayan shuɗewar wani lokaci, ya laluba ya ɗau wayarsa, ya kunna fitila ya haska fuskar rumaisa, da ta haɗa yawu da majina, da hawaye sai jan majina take yi tana kuka. "Amarsu ta ango, finally budurwata ta zama matata, wannan cizo kamar damusa mimi" ɓare baki tayi, ta cigaba da kuka, tana wallahi sai na faɗa. "Wa zaki gayawa? Ammi ko mama?". "Kowa na duniyar nan, kuma sai na rubuta kowa ya gani, kamar yadda na taɓa yi maka" Ya yi dariya mai isar sa, kashe murya yana kwaikwayon ta ya ce "Yaya usy, mai sunan baba. Ai ko shi mai sunan baban, bai isa hana ni karɓar sadakina ba. Inyee ni dakata ma, nawa na baki sadaki? Ciko zan yi ko wani abu zaki rago mini?" Ta ɗora hannu a ka, tana cigaba da kuka har da ta shiga uku ta lalace, shi kuma ya sakata a gaba, yana ta tuntsira dariya, bai taɓa ganin karaya ƙarara da miƙa wuya a wurin rumaisa ba sai yau. Ya ce "Dan Allah ki goge wannan majinar mana, ƙazama, kin bayar da mata gaskiya" ya janyo ta yana goge mata hawayen fuskarta. Buge hannunsa tayi ta ce "Wallahi yaya usy ne ya janyo mini, ya ce duk abun da ka yi mini ba haram ba ne, idan ban yadda ba zaka yi mini kishiya da shi da anty laila, suka ɗorani a hanyar da bata kamata ba". "Au zuwa ki ka yi ki ka gaya masa nayi miki wani abu?". Ta ce "Eh, duk abun da ka yi mini faɗa nake yi, wallahi Allah ya....." Sai kuma tayi shiru. "Allah ya isa, Usman ɗin ki ke yi wa Allah ya isa" Ta girgiza kai. Ya ce "Ni?" "Ni ban maka Allah ya isa ba" Ya sake juyo da ita ya ce "Oyaa say thank you". "Thank you for what?" Tayi maganar tana mamakin rainin hankalin da yake mata. "Thank you for everything i did, faɗi" "Wallahi ba zan faɗa ba" "Ok, naga alamar bakin ki bai mutu ba, am equal to you". "Na shiga uku, na gode Allah ya saka da alkhairi ya biya buƙata" Yayi murmushi ya ce "Kowa ya tuba dan wuya ba lada, ya cikata" ya sauka ya nufi toilet. Har ya fito tana zaune a takure, jikinta sai tsuma yake yi, tana ta tunanin ya ma za ta yi ne. Abun gaba ɗaya ta rasa a wani muhallin za ta saka shi, anty laila dama tuntuni tayi mata bayani, usman ma duk da ba kai tsaye ya gaya mata ba, amma yayi mata bayani, amma ita dai sam abun ya zarce tunaninta. Kamar zai tsayar da taxi ya ce "Sss" ta ɗago ta kalleshi. "Zo" Tayi shiru tana kallon sa. "Magana fa nake" a hankali ta tashi tana raɓe-raɓe. "Auren kenan mimi, ki daina hararata kamar zaki kai mini duka, ki shiga toilet ki yi wanka, kamar yadda ki ke na period, sai dai wannan akwai banbancin niyya". Karatun ajin su yasir ne ya faɗo mata, sai yanzu ta gane ina karatun ya dosa, a wancan lokacin kanta a doɗe yake. To idan haramun ne ai ba za a koyar a makaranta ba, duk da haka ai mama ba ta ce mini haka ba. Wata zuciyar ta tunatar da ita. A haka ta gama abun da za ta yi ta fito, sai dai still ba ta daina kuka ba. "Haba mimi, hawayen zai ƙare fa, is ok ya isa haka, zo in canza miki kayan sai ki kwanata ki yi bacci". Ta girgiza kai ta ce "Ni ba na so" Ta canza kayanta, ta kwanta a ƙasa, wai ba zata sake kwana a kan gadon ba. Ya tayar da salla, sai da tayi bacci, sannan ya ɗauke ta ya mayar kan gadon. "Allah kai ka san dalilin da ya sanya ka ɗauki Aisha, ina tsaka da ƙaunarta, ka bani rumaisa, kuma ita ma ka sanya mini son ta, Ubangiji Allah ka jagorance ni a al'amarin nan, ya sanya ta zame mini sanyin idaniya, kuma ka bani ikon kula da ita" yayi Addu'a murya ƙasa ƙasa, ya shfa kanta yayi murmushi ya ce "Ni na cancanci in ƙara sadaki mimi" Su da zasu yi kwanaki biyar, abu kamar wasa adam yayi burus da komawarsu, ya addabi rumaisa da sai da tayi dana sanin biyo shi, kuma ya hanata waya da kowa, ammi tana mita ta ce tana son ganin rumaisa suna shirin biki, ga sabir yana ta rigima  shi mimi. Adam yayi mursisi ya ce aiki ne ya riƙe shi zasu dawo. Tayi kukan, tayi rashin kunyar, tayi tsiwar amma babu wadda tayi tasiri, adam yayi burus da ita. Yau suna kwance da safe, tana jin yana waya da laila, laila tana tambayarsa rumaisa, ya ce bacci take. "Wai takawa ba zaka dawo da yarinyar nan ba?" "Honeymoon muke" ya bata amsa. "Ni ka ke gayawa haka, lallai baka da kunya, dan Allah a dawo mana da ita, wallahi we are missing her". Wata shida na barku tare da ita, dan haka a ƙyaleni. "Anty laila"  rumaisa ta yi maganar kamar za ta yi kuka. "Na'am mimi, ya kike?" "Dan Allah ki saka baki ya dawo da ni gida, na gaji" tayi maganar tana kuka. Katse kiran yayi, ya harareta ya ce "Da gaske faɗa musun zaki yi abun da nake miki? Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya hana, kuma Allah ya tsinewa mai tona asirin aurensa, sirri ne mimi ba a faɗa". "Ni wallahi a gida ba a ce mini haka ba" "Amma laila ta gaya miki ai, kuma Usman ma haka, amma tun da haka ne shikenan, ina ga kawai wani auren zan yi" Ayshercool. *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin* *5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14.  Supplement na whitening/glowing skin* *15.  Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 *TALLA! TALLA!! TALLA!!! *ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH* Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.” Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH…. (*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*) *Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143* Tuni idonta ya cika da hawaye ta ce "Haba papa, duk abun da fa ka ce in yi ina yi, kuma duk da haka sai ka yi auren?". Ya sake kashingiɗa ya ce "Yanzu ba gashi kina yi mini gardama ba". Kawai ta kifa kai ta cigaba da kuka, maimakon ya rarrasheta, sai ya kwanta a bayanta ya ce "Rigimar ki ke so, ba kuma zan kula ki ba". Ta gama kukan ta hau bacci. Da yamma ya ce ta shirya, ya kaita shan ice cream, tun da a satin za a koma makaranta, yakamata su tafi gida haka. Tayi ta murna za su koma gida, duk da ta wani fannin zamansu a abuja yayi mata daɗi, ta wani fannin kuwa zata iya cewa, ba ta ji dadin sa ba. Adam kuwa har fargabar komawa Kano yake yi gidansa, kar ya je su koma, matsalar nan ta sake dawo masa. Ita kuwa baki yaƙi rufuwa, da suka koma, gidansu ya ɗan yi ƙura, ta gyara abun ta fes, ta karɓi wayar adam ta sanarwa da mama sun dawo, zata je gida a cikin satin, mama ta ce ba sai ta zo ba, ita zata kawo mata ziyara. Rumaisa ta din ga murna kusan shekara da aurenta, sau ɗaya mama ta taɓa zuwa gidanta. Ta cewa takawa, ya ɗaukko mata sabir, dama anty laila ta ce yana ta rigima, Adam ya ce sai dai su je ta ganshi su dawo gida. Ta ce "Amma saboda me?" "Ya fara wayo, ba zai kwana a tsakaninmu ba". Cikin damuwa ta ce "Amma papa saboda me? A ɗakina zamu din ga kwana da shi". "Saboda mun daina raba ɗaki daga yanzu, sai ya shekara biyu ko uku, ya isa shiga makaranta, kan lokacin kema kin kammala makaranta, zan ɗaukko shi gaba ɗaya ya dawo gidan nan, a gyara masa ɗakin sa" Kai tsaye ta gane nufinsa, a tata wautar, da suka dawo gida, shikenan ta huta, amma taji ya kawo wata maganar daban. Kamar da wasa, taga da gaske takawa yake yi, ba zasu sake raba wurin kwana ba, babban abun da ya ƙara sa shi farinciki da bashi mamaki, bai wuce jin ya koma normal ba har a gidan. Sai washegari suka tafi gidan ammi, ana ta shirin bikin iman da mai sunan baba. Suna mota kan su sauka takawa ya cewa ruma "Kalli can" ta ɗaga kai, ta hango mai sunan baba tare da iman, tana magana yana murmushi. Ruma ta yi dariya ta ce "Manya gatan wasa, su mai sunan baba an tafi duniyar love". "Ina tausayawa iman zama da wannan yayan naki, dan dai ta nace ne kawai, amma gani nake kamar za ta sha wahala, mutum sai izza da jin kai". Ta haɗe rai ta ce "Papa abun ma ba kara, yayana ne fa" "Shi ɗin fa, kema ai kin san gaskiya, gashi dai ƙanwata yake so, amma ko zan wuce sau goma ko kallona ba zai yi ba". "To ai kaima baka kula shi" Ya ce "Oho muku dai, ki taho mini da key ɗina, kya je ku gaisa, ni ta baya zan shiga" Ya buɗe motar ya fice, duk da murmushi yake yi, iman na masa zancen su saka kaya iri ɗaya ranar dinner, yana ce mata shi kunya yake ji, ba ya son taron mutane. Tana yi masa magiya, tana ganin rumaisa ta nufeta tana murmushi suka rungume juna, ta ce "Mimi sannu da zuwa ya Abuja?" Ruma ta ce "Abuja ba daɗi". Iman ta ce "Haba dai? Baki ji daɗin garin ba ne ko yaya?" "Ke dai a bar zancen kawai" ta risuna ta gaida mai sunan baba, tamkar ba shi ne yake murmushi ba, ya amsa cikin basarwa. Sai da ya lura da yadda tayi ƙiba, ta ƙara kyau da haske, kuma daga yadda take yawan faɗan Adam, ko waya ake yi da ita, ya sake tabattar masa da tana cikin kwanciyar hankali. Sabir har da wata ƴar ƙara, saboda murnar ya ga miminsa, Ammi ta ce "Allah ya shiryeka sabir, wani ma sai ya ce ba a kula da kai, kullum sai yayi kuka mimi" Ruma ta yi dariya, tana kuma rungume shi, soyayyarta da Sabir, haɗin Allah ce kawai. Rumaisa suka koma hutun makaranta, sai dai duk ranar da takawa ya addaba mata, da safe sai ta lafke ta ce ba zata je makaranta ba. Haka zai yi ta fama da ita, sai dai ta je a makare, har makarantar suka fara complain da yawan fashinta da makara. Gefe guda kuma, yana ta fama a kan son gano, suwaye SMOKE, saboda ya san mutanen da ya addabawa da yawa, in dai aiki ya biyo ta kanka, babu ruwansa, kawai zai yi aikinsa ne, dan haka takamaimai ya kasa gano suwaye. Ranar da mama ta zo, kamar rumaisa ta shige cikin mama, ta sauketa da kayan ciye-ciye kala-kala, sai dai mama ba ta fi awa biyu ba, ta ce Aliyu ya tashi su tafi, dama shi ya kawota, rumaisa har da kuka, mama ta ce babu amfani zarya a gidan siriki, haka suka tafi. *** Magiyar da Mahmud yayi ta yi wa mai sunan baba ce, ta sanya ya bashi damar saka masa hannu a harkar gininsa, ƙofofi na alfarma, da glasses na window, haka ya saka a gidan da Iman za ta zauna, aka yi tiles mai kyau, gida yayi kyau sosai dai-dai zaman amarya. Kuma ya yiwa mai sunan baba alƙawarin cewa; ta ɓangaren sa babu wanda zai sanarwa da cewa ya taimaka masa a harkar ginin. Lokaci yana ta ƙaratowa, aka kai kayan lefen iman, Akwatuna shida da kit, dai-dai gwargwado yayi ƙoƙari iya ƙarfinsa. Sai dai da yake maƙiyi, ko ruwa ka shiga sai ya ce; ka tayar da ƙura, haka aka din ga kushe lefen nan, wai kamar iman, a rasa abun da z aa kawo mata, sai wannan kayan, babu wadda aka taɓa aurarwa a gidan, aka yi mata ƴan wannan kayan tsiyar, sai ita. Laila ta saka aka kwashe kayan lefen aka mayar gidanta, ta ce ba shegen da zai sake zuwa ya ga lefen, su sun karɓa kuma sun yaba, dan haka duk wani munafuki, ya je yayi yadda zai yi. Iman kuwa da rawar jiki ta kira mai sunan baba, tana yi masa godiya. Rumaisa sai murna take tana cewa "Amarya tawa ango nawa, wai ni ranar bikin nan ina zan je ne ma?" Takawa ya ce "Sai ki rabu biyu kawai, rabi a nan rabi a can". Shi kansa takawa, ya yaba abun da umar ɗin ya kawo, a zuciyarsa dan bai furta ba. Ammi kanta bakinta yaƙi rufuwa, dan ta yaba nesa ba kusa ba. Turaki da kansa ya yi wa iman kayan ɗaki, kamar yadda yake yi wa ƴaƴan Galadima idan za su yi aure. Wani kayan kitchen da sauransu kuwa, laila ce tayi wa iman, takawa ya sai mata kayan electronics, kuma a hakan gudunmawa ko ta ko ina kawota ake yi. Mahmud yayi sallama a falon, suka amsa masa, sabir da gudu ya nufe shi, yana kiran daddy, har yana neman ya faɗi, yayi carf ya ɗauke shi yana murmushi. Ya risuna ya gaida ammi, ta amsa masa cikin sakin fuska. Ya kalli laila da a sanadin rumaisa, suke gaisawa, saɓanin da da har ta ƙaraci zamanta a gidansu faɗa suke yi. Ya ce "Hajjaju barka da wannan lokaci?". Laila ta ce "Mamuda kana lafiya?" "Ki daina ɓata mini suna mana, daughter ashe tafiya ku ka yi?" Ruma ta ce "Wallahi kuwa daddy, ya garin, ka karɓo offer taka kuwa? Wane aikin ne kuma" "Na karɓo, an bamu ni da yayana?" Rumaisa ta ce "Papa, to ai papa yana da aiki". Ya harareta ya ce "Ba shi ba. Aikin coustom ne" Ruma jikinta ya ɗan yi sanyi sannan ta ce "Allah ya sanya albarka ya tsare muku, a kula da aiki daddy, dama na san kai me gaskiya ne, ka bawa ammi ta gani". Ya ƙarasa ya ajiyewa ammi envelope, ammi cikin jin daɗi ta karɓa ta buɗe tana dubawa ta ce "Alhamdilillah, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi, ya sa rai da lafiya su mora, Allah ya tsare maka" Ya ce "Amin na gode" Laila ma sanya albarka suka din ga yi, goga Adamu kuwa kamar bai san me suke yi ba. Iman ma ta ce "Allah ya sanya alkhairi yaya". Ya amsa da "Amin amarya. And mutum nawa zaku gayyata na wurin dinner? Zan ɗau nauyin abinci". Ammi za ta yi magana, laila ta ce "Godiya muke, Allah dai ya saka da alkhairi malam mamuda" Yayi murmushi ya miƙe ya ce "Iman, bayan biki, mijinki zai je Abuja interview, offer ni da shi ne. Kar ki gaya masa yanzu, kin san halinsa zai ce saboda zai aureki ne, an raina abun da yake da shi. Interview ɗin ma kawai zai je ne, dan kar ya gane daga nan a ka samo mana aikin, saboda link ne kawai na tura masa na ce ya cike CV ɗin sa" Rumaisa ta ce "Mai sunan baba, ya samu aiki daddy? Allah sarki baban marayu. Daddy Allah ya saka maka da alkhairi, ya biya maka buƙatunka na alkhairi, Allah ya nuna mini lokacin da zaku kalli juna kai da papa a matsayin ƴan uwa ba maƙiya ba, ku zauna a gaban ammi ta ji daɗi". Rumaisa har da kuka, dan abun ya zo mata a mugun bazata, bata taɓa tsammani ba. Laila ma kanta godiya take masa, iman kuwa kasa magana tayi, ammi na kuka rumaisa na kuka. Adam kuwa jikinsa ne yayi sanyi gaba ɗaya. Mahmud bai ce komai ba, ya rungumi sabir ya fita. Laila ta ce "Ke kuma mimi maimakon kiyi murna, sai ki hau kuka, daga ke har ammin?" Rumaisa ta ce "Anty laila ba zaki gane bane, baban marayu ne mai sunan baba, tun tasowarsa, bashi da burin da ya wuce rayuwarmu tayi kyau ta inganta, bai ajiye komai ba saboda mu, su kuma gaba ɗayansu basu da burin da ya wuce inganta rayuwata, ban taɓa kukan rasa abu na dai-dai talaka ba, komai suka samu ni. Albarkacin anty iman ya samu aikin yi, lallai sirikarmu mai albarka ce, ki sa a ranki You will marry the best husband ever in this world" tayi maganar tana murmushi. Papa ya ce "Wai best husband ever saboda son kai" Laila ta ce "Ba son kai ta faɗa ba, nima naga alamar hakan" Ruma ta ce "Ammi yi haƙuri, garin shirme na na saka ki kuka" "Bari rumaisa, da ke da familynku babu abun da zan ce muku sai godiya, Allah ya ƙara mana zumunci" Suka amsa da amin. Ammi ta ce "Rumaisa, yaushe su uwani zasu koma bakin aikinsu ne, baki ce komai ba haryanzu, aikin gidan nan yayi miki yawa fa" Ruma ta ce "Ammi Asiya ce kawai zata dawo, ta isa zamu din ga aikin tare" Ammi ta ce "Amma meyasa?" "Kawai Ammi" Adam ya ce "Ammi, nima ina goyon bayan hakan, mutum ɗaya ya isa" Ammii ta ce "To shikenan" *** Mummy kuwa abubuwa gaba ɗaya sun kwance mata, asirin ya daina ci gaba ɗaya, bata taɓa zaton akwai ranar da za ta zo, ace asirin da take yi ya daina ci ba. Gashi yanzu sosai suke rigima da Hajiya Lubabatu, wanda ta kai har hajiya Lubabatu ta ce kowa ta je ta ji da matsalarta itakaɗai. Ɓangaren Mahmud ma yanzu gaba ɗaya ta fara kasa gane kansa, gaba ɗaya yanzu ya watsar da shiga sabgoginta, sama sama suke yanzu. Abun da ya sake tayar mata da hankali, bai wuce yanzu Fauziyya da duk masu neman aurenta sun gudu, ruƙayya ma sai tarkace, dan yanzu gaba ɗaya ma ta fara kasa gane kan ruƙayyan, domin kuwa wasu abubuwa take, da ta kasa gane kanta, kamar ba ta cikin nutsuwarta. Babban abun da ya sake jefata cikin damuwa, bai wuce yadda samha ta daina zuwa ba, Fauziyya ta je har gidan turaki, sai dai fa ba a wanyeta lafiya ba, saboda yadda samha take ta cika tana batsewa. Fauziyya ta ce "Wai Samha lafiya kuwa?" Samha ta ce "Kin ga Fauziyya, ni fa ban san dalilinki na zuwa ma gidan nan ba, saboda na riga na raba gari da ku, na zaci Mummy ƴa ta ɗauke ni tsawon wannan lokaci da nake tayi mata biyayya, ashe raina mini hankali kawai take yi, amfani take da ni, ta caimma muradinta, dan haka ku je kuyi rayuwarku nayi tawa". Fauziyya ta ce "Mummyn ki ke gayawa haka, duk abubuwan da tayi miki a rayuwa". "Tayi mini uwar me? Na sakankance ta din ga cutata, muka yi da ita duk yadda za ayi, za tayi na auri adam, idan na bata haɗin kai, ƙarshe ta cewa baba uwani duk abun da ya faru kar ta din ga gaya mini, sai wanda tayi mata umarni, sa'a ta ci da ban zo har gida na zazzageta ba, na bar maganar". Cikin fusata Fauziyya ta ce "Do you really know what you are saying samha? Mummy ki ke gayawa haka?". "An gaya mata ɗin, ke sau nawa muke zama da ku aci mutuncin wasu, na faɗa ɗin, kuma ki fice ki bar mana gida, kuma wallahi tayi mini wani gangancin sai na tona mata asiri, fice ki bar mana gida". Haka suka rubu tsiya-tsiya dutse a hannun riga. *** "Khadija" mai sunan baba ya kira sunan iman da ke gabansa. "Yaya umar" "Ki yi haƙuri da abun da zan baki, na ga ana bayar da kuɗin gyaran jiki da sauransu, ina yawan gaya miki ni ba mai ƙarfi bane ba, dubu saba'in ce a hannuna, za ta ishe ki? Ina ƙoƙarin kama miki wurin da zaki yi hidimar biki ma" Ba tare da ta kalle shi ba ta ce "Yaya Umar, albarkar auren muke buƙata, anty laila na da event, a nan zamu yi taron biki, ka barsu ka yi wata hidimar da su kawai" "Kin raina ko?" Ta ce "A'a, ban raina ba wallahi, ka kashe kuɗi da yawa sosai ne" "Ko nawa zan kashe ai ba zan biya ba, mutum sukutum fa za a bani, ban faɗi ba ki karɓa da haƙuri" Kallonsa take tana jin tamkar ta gaya masa batun samun aikin nan, amma ta fasa, saboda gargaɗin da Mahmud yayi mata. *** Jabir da Jamil har mamaki suke yi, yadda adam ya tattarasu yayi watsi da su kamar basu taɓa rayuwa tare ba, ya cigaba da harkokinsa shikaɗai. Duk da takawa bai fiye samun shiga wurin aiki ba, saboda yawan tura shi assignments da ake yi, ko haɗuwa suka yi da jamil, Adam ba kula shi yake yi ba, kamar bai san shi ba. Faɗan da Mummy suka yi da Hajiya Lubabatu, ya sanya jabir daina zuwa gidan gaba ɗaya, dama ɓangaren Mummy ne ko na ammi, ammi yayi mata rashin mutunci, Mummy kuma sun samu saɓani da mahaifiyarsa, dan haka ya daina zuwa gidan gabaki ɗaya. Iman ta sha gyara yadda yakamata, kamar wata balarabiya, fatar nan tayi kyau. Nusaiba ma joining ɗin su tayi a shan sabayar maman Khadija, da maganin maman ilham mai tula-tula, ammi dai tana shan kunun sabayar, kasancewar baya cutar da lafiya, suka yi kyau abun su. Mussman Iman da ya ƙara fito da kyawun fatarta, gashi ta ƙara cika gwanin sha'awa. Abu kamar wasa Nusaiba har tallatawa ƙawayenta maganin maman ilham take yi, da maman Khadija mussman ƙwailayen nan, tare da basu cikakken adreshin su. Maman Ilham na zaune a no. A1 kawo road Kaduna state 0813 561 3021. Maman Khadija kuma, na zaune a garin zariya Bayan federal palladan08033411249 , haka zalika tana tura kayanta ko ina a faɗin Nigeria, masu shirin yaye da basa son nono yayi musu ciwo ya zube, wanda basa son bayan yaye yaransu jikinsu ya lalace, ga maman Khadija da maman ilham sun shirya tsaf domin tabattar sun gyara ku. Rumaisa tamkar amarya, takawa ya gwangwajeta da kayan fitar biki, na gani na faɗa, har da zobe da abun hannu na gwal. Yanzu baya ƙaunar dalilin da zai sanya ace masa ga tafiyar da zai bar gari, saboda rumaisa. Yau saura kwanaki huɗu a fara bikin mai sunan baba, ruma tana can tare da iman da anty laila wurin gyaran jiki. Takawa ya dawo gida, sai shikaɗai a gidan yana falo yana duba wata magazine, kawai ya ga Samha a tsakiyar falon. Mamaki ne ya kama shi, ya tashi zaune saboda ya baje sosai yana hutawa, kuma baƙi ba sa hawowa saman sai dai su tsaya a ƙasan bene, sai in ruma ce ta kawo su saman benen. "Samha lafiya ki ka shigo babu ko sallama?" "Adam zuwa nayi na ji matsayina a wurinka" "Matsayin me fa?" "Adam baka san me nake faɗa ba, ko raina mini hankali kawai ka ke yi? Ka daina ɗaga wayata kayi blocking numbers ɗina, Adam zuwa yaushe zan cigaba da jiranka?". "Samha dama ni na ce zan aureki ne? Samha meyasa ba zaki ɗauki ƙaddara ba?" Cikin fusata ta ce "Amma kai ka ce zaka aureni bayan ka auri wannan yarinyar" Adam ya ce "A'a, ni ban ce ba Samha, cewa na yi idan Allah ya ƙaddara, bana sha'awar tara mata a gida, iyalina su tashi kamar yadda tsarin rayuwar gidanmu take, dan Allah Samha ki yi haƙuri, na san kin so ni, amma Allah bai ƙaddara zan aureki ba, dan Allah kar ki haddasa mini matsala a rayuwar aurena". "Matsala Adam, shikenan bani da makoma kenan?" "Kina da makoma mana, matsayinki ba zai taɓa canzawa na ƴar uwata ba, kuma na san a manemanki ba zaki rasa mai sonki da zai aureki ba, kiyi haƙuri" Samha ta ajiye jakarta, ta saka hannu ta ɓalle botiran abayarta, matsatsiyar t-shirt ɗin jikinta ta bayyana, ƙirjinta tamkar zai yi magana. Ta ce "Adam kalleni da kyau? Me na rasa? Meye ban fi wannan ƙwailar yarinyar ba? Da me ta fi ni ne adam, shikenan wahalar banza nayi a rayuwata". "A'uzubillah" ya faɗa da sauri sannan ya ce "Samha ba iya sura ce dubawa a mace ba, qualities sannan sannu-sannu ba ta hana zuwa, ita ma ɗin za ta zo in da ki ka je. Abunda rumaisa tayi mini a rayuwa, ko meye ba ta da shi, zan iya haƙuri na jure, saboda martabarta da mutuncinta a idona, idan har kina son na aureki, sai dai ki nemi iznin rumaisa, idan har ta amince ba wani abu". Ta nuna kanta da yatsa ta ce "Adam, ni ce zan nemi iznin wannan ƴar talakawan wai ta bari ka aureni?" "Babu wata mafita idan ba hakan ba, ba abun da na nema na rasa a wurinta, dan haka dan Allah Samha ki tafi kawai, bana son yi miki wulaƙanci, amma dan Allah ki tafi". "Papa, yau ko nemana ba ka yi ko, ka sallama ni in gama gararambata, sai yanzu aka gama gyaran gas.... Sai dai rumaisa ba ta ƙarasa ba, idonta yayi mata mummunan gani, Samha a tsaye a gaban mijinta ta turo ƙirji, kamar ta rungume shi, shi kuma daga shi sai dogon wando, da riga armless. Zagaye su tayi ta wuce, yayin da ya ji wani irin abu mai kama da tsoro da rikicewa ya kama shi. "Kin ga Samha, dan Allah ki kama hanya ki fita, kar ki haddasa mini matsala a gidana tsakanina da matata muna zaman lafiya" Samha ta yi murmushi ta ce"Kamar gaske, wai matarka, ayi dai mu gani" ta figi jakarta tayi waje, tare da mamakin girman da rumaisa ta yi, ga abun arziki duk ya fito dai-dai da jikinta. Rumaisa kuwa kai tsaye ta shige ɗakinta, ta jefar da jakarta da mayafinta, kawai ta faɗa toilet ta shiga ta rufe ƙofa, tana jin yadda zuciyarta take yi mata zugi da raɗaɗi, ta dinga kokowa da wani abu mai zafi da ɗaci, da yake mata kai komo, yaƙi wucewa. A rikice Adam ya shiga ɗakin yana kiranta, amma tayi masa banza a banɗaki, yafi ƙarfin mintuna ashirin, yana yi mata magiyar ta fito, amma tayi burus da shi. Sai haƙura yayi ya tafi, tana jin fitarsa ta fashe da kuka, saboda yadda take jin zuciyarta tamkar tana ci da wuta, saboda ɓacin rai. Adam bai ga rumaisa ba sai bayan sallar magariba, ya faɗo ɗakin unexpectedly ya tarar da ita a zaune tamkar zata fashe, gashin nan ya sha gyara, ya kwanta sai ƙyallin mai yake yi. Gashi ta wani ƙara fresh, dan gyaran jiki suke sha tare, an yi mata lalle kamar ita ce amaryar, ɗakin kansa sai ƙamshin turare yake yi. Cikin sanyin jiki ya ƙarasa, ya ce "Mimi dan Allah ki saurareni, i will explain to you" "To hell with your explanations, bana son ji" ta yinƙura za ta tashi, ya sha gabanta. "Rumaisa kin fi kowa sanin ni ba mutumin banza bane ba, wallahi bani na gayyato Samha gidan nan ba, kawai ganinta nayi unexpected". "Dama na ce kai ka gayyato ta, idan ma gayyato tan kayi ina ruwana? Dan Allah ka rabu da ni, bana son jin duk wani bayani naka" "Kiyi haƙuri dan Allah" "Ai ni baka yi mini komai ba, ƙarewa saura tayi tsirara ka kalleta, shi ma duk cikin kuskure ne" Duk yadda ya so ta tsaya ta fahimta ta ƙi, tayi mursisi ta din ga yi masa rashin mutunci. Tun da ake faɗar fitsararta, bata taɓa gwada masa tijara muraran ba kamar yau, sam tayi burus taƙi fahimtar sa. Ƙarewa ma, yana fita ta kulle ƙofarta. Gaba ɗaya Adam ya rikice, ya rasa abun da yake yi masa daɗi, rarrashin duniyar nan, ruma tayi burus da shi, da sassafe ta fita ta tafi gidan ammi, aka cigaba da shirin biki, tamkar babu abun da ya faru. Rashin ganinta a gidan bayan ya tashi, ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba, ya fara zuwa gidansu, amma ya tarar da ita tamkar ba abun da ya faru, tana ta hidimominta, ƴan uwan su ammi na gombe, duk sun hallara. Daga nan gida tayi tafiyarta gidansu, nan ma gida ya cika mutanen katsina duk sun hallara. Ana ta shirin biki, da daddare su habiba suka zo ita da mamanta, idan da aikin da za a kamawa su mama, ga su Hauwwaliya, ai tuni ruma ta manta da damuwarta, ta shiga cikinsu suka cigaba da taɓararsu. Aliyu tun da yaga Habiba yake shiga yana fita. Ruma ta ce "Habiba baki da mutunci fa, ki ke soyayya da yaya Aliyu ba labari, kuma ko gaisheni ba kya zuwa yi" Habiba ta ce "Sannu mama" suka tuntsire da dariya. Habiba ta ce "Kamar in janyo lokacin candy rumaisa, ina ƙaunar Yaya Aliyu kamar me, Ruma aure da daɗi dan Allah?" Hauwwaliya ta ce "Eh ɗan gaya mana" Ruma ta ce "Eh to, ba nace babu ba, bana ce akwai ba, idan kun je kwa gani, idan ku ka yi sa'a ku ka auri irin mijina, to kun dace, ni da mijina bani da matsala, sai danginsa 'yan bala'i. Ku san kowa da kalar jarrabwarsa a gidan aure". Hauwwaliya ta ce "To, Allah ya sassauta mana" Suka amsa da Amin. Da Adam ya koma gida, aka ce masa ruma ta tafi gidansu, dan haka ya tafi yana fatan Allah ya sa ba ta faɗi wani abun ba. Wayar mama ya kira, suka gaisa ya ce mata rumaisa ta zo, zasu tafi. Ba ta son tayi musu ko wani abu da zai sanya, a gane saɓani suka samu, dan laila ta gargaɗeta sosai a kan haka, ta ce mata duk wata matsala, in dai za su iya warwarewa a tsakanin su, kar ta bari wani ya ji, balle ya shiga. Galibin aure yana samun matsa a dalilin sako mutum na uku a cikin matsalolin auren. Bayan motar ta buɗe ta shiga, ko kallonsa ba ta yi ba. Har suka je gida ba ta kula shi ba, shi ma kuma bai iya ce mata komai ba, duk da ƙasan zuciyarta har ta fara jin tausayinsa, dan a kiɗime yake sosai da sosai. Da suka je gida ma, a buɗe ta bar masa motarsa ta yi shigewarta cikin gida. Ko tayi niyyar daina fushin, da ta tuna yadda ta ga Samha a tsaye a gaban sa, ta turo ƙirji sai wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta. Wanka tayi, ta je kitchen ta damo kununta, ta koma ɗaki tana sha. Ita kanta missing ɗin sa take yi sosai da sosai, saboda sun yi wani irin sabo sosai da sosai. Kamar mara gaskiya haka yayi sallama a ɗakin, ta amsa masa ƙasa-ƙasa. Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita ya ce "Rumaisa". "Na'am" ta amsa a daƙile. "Yanzu kina tunanin zan iya aikata abun da bai kamata ba kenan? Yakamata ki fahimce ni, ya ci ace kin san halina, wallahi rumaisa babu wani abu da ya faru, abun da ki ka gani ma is not intentionally ban san me ma zan ce miki ki yarda da ni ba. Amma dan Allah kar ki kawo komai a ranki". "Amma fa tsayawa ka yi kana kallonta, fisabilillahi". "Rumaisa a rayuwata bana tunanin akwai wanda na taɓa bi ina bawa haƙuri, kamar yadda nake binki a yanzu, dan Allah ki yi haƙuri, ko sai na durƙusa ɗin a kan gwiwoyina?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "To ki dube ni mana, kiyi haƙuri Please" yayi maganar yana riƙe hannunta cikin nasa. "Na haƙura amma dan Allah kar ka sake kulata, wallahi ji na yi kamar na je kitchen na samo taɓarya na zo na rotse mata kai. Kawai ta wani tsaya ta gantsare a gabanka, wallahi na ji haushi" Ya ce "Subhanallah, duk ba ta kai ga haka ba, nima ban ji daɗi ba amma ki yadda da ni, ai ni namu sun isheni, me zan kalla a na wata" "Abun da bai fi murfin jarkar faron ba?" Yayi murmushi ya ce "Har laifukana na baya za'a tayar kenan?". "Eh ɗin, ka je ka kalli naka ko na Samha" Yayi murmushi ya ce "Allah dai ya bada haƙuri" Ta amsa da "Amin" Ya rungumeta ya ce "I so much miss you, smile please" Ta lashe cokalin hannunta ta ce "ba zan iya ba yanzu, idan na ce zan yi murmushi yanzu, yaƙe kawai zan yi. Ka ci abinci kuwa?" "A ina zan ci, tun da baki bani ba?" Ta ce "To mu je na sama maka abun da zaka ci" "Yauwwa my dear, ana so na ana kaiwa kasuwa, an damu da ni amma ana ta wahalar da ni" Ta kalleshi ta ce "Ka ke dai so na" Ya ce "Na yadda". Ta ce "To amma sai dai ka goya ni, ka kai ni kitchen ɗin" Ya durƙusa ya ce "Zo ki hau" Aikuwa ta miƙe ta hau bayansa tana dariya, ya goyata a bayansa, har kitchen. A ranar dai suka shirya, rumaisa tayi iyakar ƙoƙarin ta wurin bin shawarar da anty laila ta bata, na cewa idan har namji zai iya yi miki laifi ya baki haƙuri, to ba ƙaramin kimarki yake gani ba, ba kowann namiji ne zai yi ba dai-dai ba ya nemi afuwarki, sai ma yayi ƙoƙarin nemo wani laifin ya jingina miki, duk dan kar ya nemi afuwarki. Sosai aka shiga hidimar biki, ka'in da na'in, mai sunan baba kai ya ɗau caji sosai da sosai, abunka da wanda bai saba da hayaniya ba, nan da nan sai ciwon kai. Gidan marigayi galadima Sharif ma, ya cika ya tumbatsa, mutane sai kaiwa suke suna komowa. Mummy kuwa ba gaira ba dalili take tsinewa auren, tare da mummunan baki a kan haka. Rumaisa kuwa ba ta a nan bata a can, takawa sai mita yake a kan ta nemi wuri ta din ga hutawa, kar sai an kammala biki, ta zo tana ciwon jiki. Ranar da aka yi dinner rumaisa tayi kyau, haka amarya Iman da mai sunan baba, shi gaba ɗaya ma kunya yake ji, ko ɗaga kai baya son yi ya kalli taron jama'ar nan. Yazo wurin nan ne kawai saboda iman ta matsa. Kamar da bikin rumaisa a wannan karon ma, kaiwa da komowa zaratan samarin gidan maman suka din ga yi, sanye da kaya iri ɗaya a jikinsu gwanin sha'awa ango ba shi da wasu abokai, sai classmates sai ƙannensa. Ƙawayen ammi sun yi mata kara sosai da sosai, suka din ga liƙi suna kaiwa da komowa, duk wanda ya ga couples ɗin sai ya ce masha Allah, saboda kyau ne ya haɗu da kyau, duk da bai kai iman haske ba, amma kallo ɗaya zaka yi masa ka ce kyakkyawa ne. Bayan an kammala dinner suka taso, Mahmud ne ya ɗaukko su a motarsa, Iman sai hamma take yi, saboda ta gaji. "Kin gaji ne?" Ya tambaye ta lokacin da ta kashingiɗa da seat ɗin motar. "Eh yaya umar, ko ina ciwo yake mini" Yayi murmushi ya ce "To sannu, idan kin je gida ki kwanta ki huta sosai" Ta ce "To ango" Yayi murmushi, suka fara kaita gida, sannan suka wuce Mahmud ya kai mai sunan baba gida. Washegari aka ɗaura aure, turaki ne yayi wa Iman waliycci. Aka ɗaura auren Umar Mahmud da Khadija Muhammad Galadima. Ayshercool 08081012143 *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin* *5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14.  Supplement na whitening/glowing skin* *15.  Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 *TALLA! TALLA!! TALLA!!! *ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH* Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.” Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH…. (*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*) *Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143* Mai sunan baba jin sa yake yi tamkar ba shi ba, wai yau shi ne yayi aure, abun da bai taɓa kawowa nan kusa cikin lissafin rayuwarsa ba. Ya san iya karamci, an yi masa wurin bashi iman, sai addu'a yake yi, da fatan Allah ya bashi ikon riƙe amana. Ƴan unguwarsu suka din ga gulma, daga rumaisa ta auri basarake, sun liƙe sun nace musu, saboda tsabar kwaɗayi da son abun duniya. sun ga bushashar da aka yi, da irin manyan mutane da suka halarci taron ɗaurin auren Umar. Yayin da ƴan uwa da abokan arziki, ke ta yi wa mama barka, da cewar gidan sarauta sun ji daɗin auren ruma, shiyasa suka bawa mai sunan baba ƴa. Iman ta rasa wanne za ta yi tsakanin farinciki da akasin sa, bayan duk turka-turakar, faɗi tashi da ƙalubalen, yau Allah ya yanke mata, sai dai akwai tsananin soyayya da shaƙuwa tsakaninta a amminta da su nusaiba da rabuwa da su take jin wani babban giɓi ne a tare da ita. Manyan mutane ne suka hallaci bikin shaida auren, har da sarakunan maƙwabta, da manyan mutane masu faɗa aji. Gaba ɗaya jikin Iman yayi sanyi, tana tunanin sabuwar rayuwar da za ta shiga, ko da wane kalar ƙalubale za ta zo mata sanin gaibu sai Allah. Jin an ɗaura wa Iman aure kuwa, Jabir kamar ya haukace, saboda ya tabattar da ya riga ya gama rasata. Ƙarfe takwas na dare, anty laila ta shirya Iman cikin lafaya, aka ɗora mata alkyabba, maroƙa sun cika sashin ammi, suna ta faman koɗa ammi. Iman ta riƙe ammi tana ta uban kuka. Duk yadda ammi taso ta daure ta kasa, ta din ga kukan ita ma. Mai sunan baba kuwa shi ma kamar mace, Abubakar sai masifa yake masa ya shirya, azo a raka shi mutane su huta. Bayan yayi wanka ya shirya, jiki a sanyaye ya shiga wurin mama, ya durƙusa a gabanta, ji yake kamar ya ce ya fasa, har ga Allah bayan Allah da ma'aikinsa yana ƙaunar mahaifiyarsa matuƙa. Mama tayi murmushin ta cire hular kansa, ta shafa sumar kansa ta ce "Allah ya yi maka albarka, Allah ya albarkaci rayuwar aurenka, ya sanya ta zame maka sanyin idaniya. Na sanka babana amma zan sake jaddadawa a kula da amana, a kula da marainiya, ba a yi wa mace muzurai, mace uwa ce, abokiyar shawara ce. A kula mini da ita. Yadda ka tallafi rayuwar ƴan uwanka ka kula da su, Allah ya baka masu yi maka, mun gode mun gode Allah ya saka maka da alkhairi babana, Allah ya kula mana da ku Allah ya yi maka albarka" Ya sanya hannu ya kama hannun mama a cikin nasa, amma ya kasa magana, zuciyarsa ta kai matuƙa wurin yin rauni, yayi shiru ya sunkuyar da kai. Su hajiya Iya kuwa sai rafka guɗa suke yi, Gwaggo sai masifa take tana neman rumaisa, aka ce mata ai direbanta ya zo ya ɗauketa ya mayar da ita can gidansu mijinta. Gwaggo ta cigaba da masifa "Rumaisa ba zata nemi wuri ta nutsu ta zauna ba, wannan kyan da take yi da sheƙi, da ƙyar idan ba ciki ne da ita ba, a garin wannan rawar kan sai ta zubar da shi tukuna, nayi magana ta ce ita ba ta da ciki, manya ne suke haihuwa, wai ita kunun gaya take sha ko na sabulu? Ita dai ta sani" Hauwwaliya ta ce "Gwaggo kunun sabaya ta ce miki bana sabulu ba, ta ce ni ma zata bani na din ga sha. Ni yanzu jira nake ta ce za ta saka azo a ɗauke mu a tafi da mu gidan amarya". "Oho muku dai, daga ke har ita". Abubakar ne ya zo ya janye mai sunan baba suka fito, a mota ya kalli yadda umar ɗin yayi jugumm ya ce "Wai kuka zaka yi ne?" Yayi maganar yana dariya. Mai sunan baba yayi masa shiru. "Ango mai kuka, duk na gulma ne, da an ga Khadija za a ware, inyeee ango na mama". Ya din ga tsokanarsa, yayi shiru ya ƙi kula shi. Takawa da kansa ya saka Iman a mota laila da ƙawayen ammi a motar suka je suka kai iman. Hatta su Fauziyya sai da suka je gidan iman, domin ganin ƙwal uwar daka, sun kukkushe abubuwan da dama, sai dai duk yadda suka so gano makusa a jikin angon basu gano ba. Gidan Iman ɗan madaidaici, dai-dai zaman amarya, sai dai an zuba mata dakakkun kaya, na gani na faɗa. Zuwansu babu daɗewa, su mai sunan baba suka ƙaraso, har da Mahmud a tawagar angwaye. Aka yi adduoi, ƙawayen ammi suka yi musu nasiha sosai da sosai suka tafi. Takawa ya kalli mai sunan baba ya ce "Kamar yadda ka kawo mini taka ƙanwar ka ce amana, nima ga tawa nan, amanar marainiya ce a hannunka" Ya kalli in da ruma take zaune kusa da iman, suke ta kuka, ya kalleta ya ce "Mimi tashi mu tafi" yayi maganar yana jan hannunta, da ƙyar ta tashi, iman sai kuka take suka tafi. Takawa sai da ya zazzarewa Nusaiba ido, sannan ta tashi, saboda tare suke faɗuwa suke tashi da Iman a gida. Kowa ya watse, daga shi sai iman, sai dai sun shafe lokaci, ba tare da wani ya ce uffan ba, mai sunan baba ya tashi, ya je ya rufe gidan. Ya dawo falon, ya tarar da ita a in da ya bar ta a zaune, ya ƙarasa gabanta ya miƙa mata hannu ya ce "Ranki ya daɗe bisimillah" A hankali ta kalli hannun nasa, amma ta kasa motsi, ya ƙara miƙa mata hannu. A hankali ta miƙa masa nata hannun, ya riƙe ta, ta tashi tsaye ya ja ta zuwa ɗaya daga cikin bedroom ukun da yake falon. Ya taimaka mata ta cire Alkyabbar jikinta, ya saka hannu ya ɗago fuskarta, fuskar tayi pink saboda kuka, sai jan mayafin take, tana rufe baƙin gashinta wuluk, da ya sha gyara. Kallonta yake yi, wai wannan zuƙeƙiyar yarinyar ta sa ce, Alhamdilillah ala kulli halin. Ya ɗan lumshe idonsa sannan ya buɗe su ya ce "Kukan me ki ke yi ne?". Tayi shiru ba ta ce komai ba. "Mu je mu yi alwala" ta jinjina masa kai, toilet ɗin cikin ɗakin suka shiga, ya kunna mata famfo ya ce "Bismillah" tare suke alwalar, sai dai da ya kai hannu idan hannunsu zai haɗu, sai ta janye nata. Ya shammaceta ya ɗan watsa mata ruwan hannunsa, ta sunkuyar da kai tana murmushi. Salla suka yi raka'a biyu, yadda mai sunan baba ya din ga kwararo addu'a ba ƙaramin burge Iman yayi ba, dan a rayuwarta tana ƙaunar namiji mai addini. Bayan sun idar sun shafa, ya koma falo, ya shiga kitchen in da Mahmud ya ajiye kaji, da lemuka ya ɗaukko ya dawo ɗakin. Gaba ɗaya a takure take, sai sunkuyar da kai take kamar mara gaskiya. "Yaluwa, me zaki iya ci a nan?" Murmushi ta yi ta ce "Yaya umar yaluwa kuma?". Shima Murmushin yayi mata ya ce "Yeluwa mana, balarabiya a Nigeria". "Idan Larabawa sauka ji ka babu ruwana". Yayi murmushi ya tura plate ɗin gabanta ya ce "Bismillah" "Na ƙoshi" ta faɗa a hankali. Wata hamma ta kamata, tayi a hankali tana lumshe ido. Ya ɗan ƙare mata kallo ya ce "Bacci ki ke ji zaki kwanta ne?" Da sauri ta ce"A'a". Ya sake cewa "Bacci ko yunwa, wanne ne dalilin hammar?" "Yunwa" "Oya ci abinci" tamkar za ta nutse, haka take ɗan mintsunar naman tana kaiwa bakinta tana sunkuyar da kai. Tashi yayi ya bata wuri, ya tafi gaban wardrobe ya buɗe, an shirya mata kayan sawarta, kuma duk ciki ba wanda aka ɗauka na lefenta aka ɗin ka. Ya sauya kaya zuwa wata jallabiya, ya cire agogon hannunsa ya ajiye. Ta nannaɗe sauran da ba ta ci ba, ta ajiye, ta tashi zata fita, ya ce "Ina zaki?" "Can ɗakin zan je na kwanta" "Mhmm, Ashe da bayan ɗaurin aure, sai ki yi zamanki a wurin ammi, nima na zauna a wurin mama. Dan na kusa yin kuka nima ɗazu kamar ke, bana son yaran nan su raina ni ne" tayi gajeriyar dariya. Ya ce "wanko hannun ki zo" Ta ce "To" ta shiga ta wanko hannunta, ta fito. "Ki kwantar da hankalinki, ba abun da zan yi miki nima tsoro nake ji kamar ke, a gajiye ma nake kaina ciwo yake, i know what you are scared of, am scared too, ki shirya ki kwanta" wata irin Muguwar kunya ce ta kamata. Har ƙoƙarin tuntuɓe take yi, ta nufi gadon ta kwanta. "In baki bargo ne?" "A'a yaya umar ai zafi ake yi " "Shi hijjabin da kayan jikinki iska suke baki?" "A'a" "Trust me, ba abun da zan yi miki yanzu, nima tsoronki nake ji, ki sassauta kayan mana" Da ƙyar ta canza kaya, zuwa wata doguwar rigar bacci, mai balance, ta raɓa da ƙyar da kwanta a bayansa. Ba tare da ya waiwaiya ba ya ce "Kiyi Addu'a" Ta amsa da "To" Sai da ta tabbatar da gaske ba abun da zai yi mata, sannan ta yi bacci. *** Rumaisa a gidan ammi ta so kwana, amma takawa ya ce bai yadda ba, tun da suka koma gida tayi wanka, take mitar ta gaji sosai. "Papa ka yi mini sannu na gaji fa" "Lokacin da nake cewa ki nemi wuri ɗaya ki zauna, ai baki ji ba" "Mhmm, dan Allah kayi mini tausa to, ƙafata ciwo bayana duka jikina ma" Takawa ya ce "Maganinki kenan" "Wayyo mama na gaji, ka ce mini sannu" "Ke ni tausayin ƙanwata ne ya dameni yanzu, ta shiga sabuwar Rayuwa Allah ya bata ikon jure ibada" "Wai Iman, ai mai sunan baba ba irinka bane, na san ba zai mata abun da ka ke yi mini ba" "Allah ko, saboda ga shugaban waliyyan ƙarshen zamani ko?" Ruma har cikin zuciyarta ta ce "Allah da gaske nake, shi fa mai sunan baba babu ruwansa". Ba ƙaramar dariya ta bawa Adam ba, kuma ita har ga Allah take gaya masa iya gaskiyarta. "To ai shi idan ba ruwansa ke da ruwanki" da sauri ta ɓata fuska ta ce "Dan Allah wallahi bani da lafiya, gashi kuma na gaji". "Lokacin da nake hanaki ai ba kya ji, maganin mara ji kenan" ba yadda ta iya da papa, haka ta ƙyale shi. Bayan komawa bacci bayan sallar asuba, ringing ɗin wayarta ya sanya ta farka, murya ƙasa-ƙasa tayi sallama. Nusaiba ta ce "Amarsu ta ango, baccin gajiyar ne haryanzu baki tashi ba?" Iman ta ce "Bari Anty Nusaiba, gajiya fa akwaita" "Ko a taho da ruwan zafi" Kallon in da mai sunan baba yake kwance tayi, sai dai ya juya baya ta ce "Anty Nusaiba sai ka ce wata mai jego". "To idan ba mai jego ba ce yanzu, nan da 9months dai an zama" "Ina ammi?" "Tana can tare da sauran baƙi, ita ta ce na kira ki ma, zaki yi baƙi wanda ba su samu zuwa jiya ba, za a taho miki da abinci" Iman ta ce "To, Allah ya kawo su lafiya, ke ba zaki zo ba?" Nusaiba ta yi dariya ta ce "Ai ruwan zafi na ce zan kawo miki, tun da kuma ba kya so shikenan" Tayi dariya ta katse wayar ta ce "Allah ya shiryeki Anty Nusy" "Ai da kin gaya mata ba ayi komai ba, tun da shi take son ji" Gabanta ne ya faɗi, ba ta san idonsa biyu ba, ya juyo gaba ɗaya ya zuba mata ido, ta saka hannu ta rufe fuskarta. Yayi murmushi ya janye hannun ya ce "Da kin gaya mata, duk a tsaroce ki ke, nima haka, duk tsoron juna muke ji, amma zamu iya nemanta da ruwan zafinta nan kusa ko nesa kaɗan". Wato ba ƙaramin mamaki abun da mai sunan baban yake faɗa yake bata ba, bata taɓa zaton Wannan maganganun daga bakinsa ba. Hular kanta da ta zame, ta bawa gashinta damar bayyana, ya shafa gashin ya ce "My pretty yellow. Tashi mu kintsa kan baƙin naki su ƙaraso". Ta tashi zaune ta ce "In haɗa maka ruwan wanka ne?" "Kar ki damu da ni, yi wankan ki" Kafin Iman ta fito, cif ya ɗame gadon, gidan babu wani datti dama. Kasancewar baya ɗakin, ya sanya ta saki jikinta, ta shirya ta fito ta same shi a falo, yana ta ƴan dube-dube. "Yauwwa ƙaraso ki ga gidan naki, ɗan abun da talakan mijin naki yayi miki" Ta ƙarasa ta ce "Ni wannan gidan ya fi mini kowanne kyau da tsari". "Really?" "Yeah" "Jazakillah khair for appreciating it, Allah ya yassare mini in yi miki wanda ya fi wannan" "Amin ya Allah" tare suka zazzagaya, ta din ga yabon gidan, da yabawa ƙoƙarin sa. Aka ƙwanƙwasa gate ɗin gidan, Umar ya je ya buɗe, ya ga Usman da Abdallah, da ledar viva a hannunsu. "Mai sunan baba ko mu koma ne na ga kana kallonmu, mama ce ta bayar da abinci mu kawo" buɗe musu yayi, ya juya ya koma falon. A kujerar da iman take ya je ya zauna, cikin murna Iman ta ce "Yaya usy sannunku da zuwa" Usman ya ce "A'a ai mu yakamata mu gaishe ki, ina kwana antynmu" Iman ta ce "Kai dan Allah har ka bani kunya" Ya ce "Ai girmanki ne, dole a baki" Ta shiga yi musu bangajiya, tare da tambayarsu ya mama. Abdallah yayi ƙasa da murya ya cewa Usman "Ka tashi mu tafi, gulma ce a bakina, kar na yi misbehaving a samu akasi" Usman ya ce "To mu tafi, nima ita nake son yi" Suka tashi Abdallah ya ce "Bari mu tafi". "Haba yaya Usman, daga zuwanku, ko ruwa ban baku ba" "Bakomai ma sha a waje, tun da mai gida ya haɗe rai, baya buƙatar mu ne sai anjima" Bayan sun fita ta ce "Yaya umar ka din ga dariya mana, ko smiling ne" "Ban iya ba, tun da ke kina yi ai shikenan deejangala, bari mu karya ko, dan ni na fara jin yunwa". Tare suka karya, duk ita duk a ɗarare take, tun da suka fara baƙi ya fice ya bar gidan. Usman kuwa gulmar mai sunan baba suke yi, wai yadda ya wani zauna a kusa da Iman, wai shi mai gida. Suna tafe rumaisa ta kira Usman, ya ɗaga ya ce "Ke kuma meye zaki dame ni?". Ta ce "Daga kira me nayi maka to?" "Ke rabu da ni, nima aure nake so rumaisa, ke kin yi aure, mai sunan baba yayi, Aliyu da yaya Habu suna hanya, jiya dan abun takaici, rige-rigen katifar mai sunan baba muka din ga yi, da tsofaffin kayansa. Kin ga yadda yake wani basarwa yau da muka je, wai shi maigida. Ke ma kina ta ƙarshe a gidanmu, amma ƙiri-ƙiri daga sunanki rumaisa an mayar da ke mimi, saboda aure, kallemu ni da Abdallah aka bawa kwanukan abinci muka kai musu. Allah ka aurar da ni, ko babyn nan a din ga ce mini" Rumaisa dariya har da tuntsurawa, "Zaki yi dariya ne, wato ke kin tsallake, mijinki na ta lallaɓa ki, zuwa zan yi mu dai-daita da Hauwwaliya, daga baya mu yi kuɗi a tare, dama mutuniya ta ce, tun da yanzu mata sun fi son mai kuɗi muyi tuwona maina, kar na je na lalace" Shi har ga Allah yake maganar, takawa da yake jin su ya ce "Usman idan ka lalace ina muka kama? ka samo mata, in dai aure ne zan yi maka na baka jari" Usman ya ce "Subhanallah, Allah ya taimake ka dan Allah ka ce ba ka ji abun da na ke cewa ba, har kunya ta kama ni". Suka yi tayi masa dariya. *** Baƙi suka fara watsewa, saboda an kammala biki. Gidan Iman ma mutane suka yi ta sintirin zuwa gidan ta, mai sunan baba yayi burus da ita, har ta ɗan sake daga tsoronsa da take ji. Yau kiran sallar farko na asuba, ya tashi yayi nafilfilinsa da karatun Alkur'ani, ana daf da fara kiran sallar asuba, ya tashi da niyyar tashin Iman ta yi alwala. Sai dai zancen ya canza, maimakon first night shi first asuba yayi, ƙarshe sai da hasken rana ya hudo, sannan sallar asubar nan ta yiwu. Mai sunan baba kenan, komai nasa daban ne, sai dai kamar wanda ya yi laifi, duk ya diririce, mussaman ganin tana kuka. Bayan ta idar da sallar asuba, ta kifa kanta a kan sallaya, a hankali ya kira sunanta "Khadija" "Na'am" "Ki tashi ki kwanta mana". "A'a bakomai, ai gari ya waye ma" "A'a ki kwanta dai ki huta, kina buƙatar wani abun ne?". Ta ce "A'a" "To tashi ki kwanta" Ya ɗagata ya rakata kan gadon ta kwanta. Har zai tafi ya ce "A cewa Nusaiba ta zo tayi aikin nata, ta kawo ruwan zafin duk da ma dai na yi da kaina". Rufe fuska kawai ta yi ta, lumshe idonta tana murmushi. Ƙiri-ƙiri mama ta kira mai sunan baba, ta ce masa maƙwabta za su zo, amma ya ce kar su zo, ba ta jin daɗi. Abun da Iman tayi tsammanni, da kuma wanda mutane suke jiye mata, ba shi ta tarar a gidan mai sunan baba ba, mutum ne matuƙar kulawa. Aikace-aikacen gidan kuwa ba ruwansa, tashi yake yayi abun sa, da ta motsa sai ya ce ta zauna ta huta, shi tausayin ta yake ji. Ranar da zai koma kasuwa kuwa, shagwaɓa iri-iri a wurin Iman, kamar kar su rabu. *** Ihun da rumaisa take yi ne tana salati, ya sanya takawa fitowa daga toilet a hargitse, ya nufota. "Menene lafiya?" Ya tarar da ita bacci take yi, tana ta fizge-fizge tana son ta tashi, ta ɗaga murya tana "La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin". Da sauri ya ɗagata ya din ga karanta mata adduoi, yana tofa mata, ko da ta buɗe ido ta ganshi, ta saka ihu ta ƙwace tana haki. "Mimi lafiya kuwa? Menene?" "Ba kaine ka zo idonka na hayaƙi ba, zaka huda mini cikina da faratanka ba". Gabansa ne ya faɗi ya ce "Ni kuma mimi?". Eh mana tayi maganar hawaye sharkaf fuskarta. Jiki a sanyaye ya ce "Mafarki fa ki ka yi, ni ina banɗaki". "Da gaske mafarki ne, ba ka fasa mink cikin ba?" "Duba ki gani". Ta shafa cikin ta ta ce "Ni fa tun ina gida nake mafarkin idonka na ci da wuta, zaka soka mini farce a wuy, har a gaske fa watarn idonka yana yin hayaƙi" Ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Ki yi addu'a ki cigaba da baccinki mafarki ne" Ta ce "Ba zan iya ba tsoro nake ji" Ya rungumeta ya ce "Ki yi ta Addu'a" Yayi shiru yana tunanin kenan rumaisa ciki ne da ita? In dai Aisha tayi irin wannan mafarkin, to ɓari take yi, amma rumaisa ta ce masa tun a gida take irin mafarkin. Wata guda da auren su Iman. Mai sunan baba bai taɓa zaton zai iya zagewa ya yi soyayya haka ba, babban abun da yake ƙara masa son Iman bai wuce matuƙar biyayyarta ba, da soyayyar da take yi wa mama, da ƴan uwansa ba, dan haka yake ƙara iya ƙoƙarin sa wurin ganin ya kyautata mata. Tuni ta cigaba da zuwa makarantar ta, wasu lokutan kan ta dawo ya zo gida ya rage mata aiki, ranar kuwa da zata kai shida a makaranta, har makarantar yake zuwa kai mata abinci babu ruwansa. Ƙawayenta suna yawan faɗa mata, tayi dacen miji mai son ta. Idan za ta tafi makaranta idan ba zai samu kai ta ba, shi ne yake bata kuɗin mota. Tana zaune a falo da daddare tana shige -shigenta a system ɗin sa, tana typing ɗin wani assignment, ya fito daga bedroom ya kwanta a kan kujerar da yake, ya ɗora ƙafafuwansa a kan cinyarta ya ce "Me ki ke nema a computer ta?" Ta shagwaɓe ta ce "Dubawa nake ko zan ga hoton ƴan mata" Dariya yayi ya ce "Ni ina ruwana da wasu ƴan mata, ke ma dan kin liƙe ne ki ka same ni" "Ko kuma mun liƙe ba" tayi maganar tana tura baki. Tashi yayi zaune ya rungumota jikinsa ya ce "Na yadda ni na liƙe, tun a kallon farko da na ganki, na zata ma da aljana ce za ta aure ni, ashe ƴar autar ammi ce" Tayi dariya ta ce "Ni fa da tsoro ka ke bani my, i just felt for you, ashe duk fasa aurena da ake a baya rabonka ce ni, Alhamdilillah for having a good husband like you my faruk" tayi maganar tana shafa sajensa Murmushi yayi yana jin wata annashuwa, da soyayyarta na ratsa shi, ya sake rungumeta ya ce "Deejana, my pretty yellow girl, gaskiya kina so na da yawa". "To ka ce kana so na nima" Wata ƴar dariya ta bashi, ya ce "Ɗaukko carbi, ina faɗa kina lissafawa, har sai kin ji kin gamsu da ina son ki" Iman ta sake narke masa ta ce "Ni waƙar soyayya ma zaka yi mini" "Taɓɗijan, ai muryata ba ta waƙa ba ce, ban ma iya ba deeja" "Muryar ka ta tsorata mutane ce" tayi maganar tana yi masa dariya. "Eh ai an fi son haka, monster haka ba raini, tashi mu je mu kwanta, zaki school gobe in Allah ya kaimu" Ta ce "To, bari na kashe system ɗin" "Ahh, Baby an yi maka Gmail" Mai sunan baba ya ce "Ba zaki daina babyn nan ba ko? Baby kamar ɗan daudu, gara ki ce mini faruk ɗin ai". "Ai a waje ne ake maka kallon monster, ni a wurina babyna ne" "Daɗinta ke ma a da monster ki ke gani ai". "Eh yanzu kuma baby ba" tayi maganar tana duba Gmail ɗin. Message ne a kan ana nemansa a Lagos zai je interview. Ya ce "Anya wannan message ɗin nawa ne? Bana tunanin nawa ne" "To na waye, naka ne mana" Zai yi magana sai ga message ɗin Mahmud. "An kiramu interview lagos, ban sani ba ko ka ga message ɗin, ranar Sunday zamu tafi, za ayi interview Monday, mun samu aikin nan" Nunawa Iman yayi yana cigaba da mamakin abun, tamkar dai mafarki. Iman ta din ga murna, tana addu'a, tamkar tun farko ba ta san zancen ba. *** Duk da haryanzu bai gama komawa cikin nutsuwarsa gaba ɗaya ba, amma yayi ƙiba sosai abun sa, da gani ya samu nutsuwa sosai yanzu. Sallama da aka yi a office ɗin ce ta sanya ya ɗago, ya amsa sallamar. Jamil ne ya shigo fuskar nan babu annuri, shi ma Adam ya haɗe fuska yana jiran ya ƙaraso. "Wurinka na zo" "Ina saurarenka" "Zuwa na yi na ji ina ka tsaya" "Ina tsaye a in da ka sanni" Jamil ya ce "Magana nake so mu yi ta fahimta, zuwa yanzu yakamata ace ka kammala binciken da zaka yi, ka wanke ni daga zargi da kuma zullumin da ka jefa ni a ciki kai da matarka". "Jamil a kan me zaka yi zullumi, idan har ka na da gaskiya? Ka cigaba da harkokin ka kawai" "Ba zai yiwu ba Adam, ya zama dole ku wanke ni, kuma ku tabattarwa duniya, bani da laifi". "Jamil kana bani mamaki fa, ni da na dawo ban tayar maka da hankali na cigaab da bibiyar matata a kan lallai ka samu wasu bayanai ba, sai yanzu zaka zo ka cigaba da titsiyeni?" "Dole in titsiyeka Adam, tun kan ayi mini wani sharrin, ka je ka ce mata akwai filin mai girma turaki, da ya sanya sunan aisha a matsayin magajiyarsa, ta na nema ta fara yi mini barazana da haka, ta sake ƙulla mini sharri" "Duk da ba ka cigaba da bibiyarta ba, she won't go this far, amma duk abun da rumaia ta sanya a gaba, akwai ƙamshin gaskiya a cikin sa, dan haka ka fitar mini daga office" "Adam ni ka ke kora daga office ɗin ka?" "Na kore ka ɗin, a duniya ban taɓa tsammanin kai da Jabir zaku yi mini abun da ku ka yi mini ba, dan haka ka fitar mini daga office ". Ringing ɗin wayarsa ya dakatar da shi da cigaba da magana, ganin kira daga makarantar su rumaisa, ya ɗaga kiran yayi sallama. Shugabar makarantar su ta ce masa sun kai rumaisa asibiti tana ciwon ciki. Bai sake bi ta kan Jamil ba, ya fice daga office ɗin. Mai sunan baba kuwa har gari ya waye, yana doubting idan maganar nan gaskiya ce, sai da ya je gida ya samu Mahmud, Mahmud ya tabattar masa da hakan. Ya tafi gida ya je ya sanar da mama halin da ake ciki, suka din ga murna suna yi masa Allah ya sanya alkhairi, shi dai ganin abun yake yi kamar wasa. Laila kuwa sun fara shiri ita da yaranta da maigidanta, na komawa canada, maigindata sai nanata mata yake yi, ta je gidansu rumaisa yana nan yana jiran Yasir, zai fara laluba masa gurbin karatu a canada, da result ɗin sa ya zama ready a sanar da shi. Mama ta rasa wane ɓangaren ma yakamata ta yi wa godiya ne, duk dai a sanadin rumaisa alkhairi sai samun ƴan uwanta yake yi. Ruma kuasan tafi kowa shiga damuwa da komawar anty laila, saboda ko ba komai su yi faɗa su yi daɗi sun shaƙu ba kaɗan ba, tallafi rayuwar aurenta, ta wayar mata da sosai da sosai, ta fitar da ita daga cikin duhun da tsananin kunya da yi mata kallon yarinta, ya sanya mama kasa yi mata bayanin menene shi kansa auren. Takawa ya je har asibitin da aka ce masa an kai ruma, ya tarar da ruma an saka mata ruwa tana bacci, likitan ya ce masa yana kyautata zaton food poison ne, dan bai san matar aure ba ce ba. Ruwan yana ƙarewa, ya biya duk abun da aka kashe, ya ɗauke ta suka tafi gida. Ya din ga yi mata mita a hanya, ko ciye-ciyen ta ne ya sanya ta haɗu da ciwon ciki, dan kwanan nan ciye-ciyen ya fi na kullum. Sai dai da suka koma gida zuwa magariba, ta din ga amai ba ƙaƙƙautawa, dole ya ɗaketa ya mayar da ita asibiti. Asibitin da suke da ganin likita ne, aka basu scaning suka yi suka kai wa likita, a nan ya tabbatar da rumaisa ciki ne da ita, har wata uku. Ta rufe fuska ta ce "Na shiga uku" Farincikin Adam ya kasa ɓuya, yayi ta yi wa likitan godiya, sannan ya ɗaukkota zuwa gida. "Yanzu fisabilillahi da cikin ki ka din ga wannan hidimar da bikin nan, Allah ne ya rufa mini asiri baki watsar mini da shi ba". "Ni fa ba wannan ne ya dameni ba, kawai kuma sai a ganni da ciki? Kuma sai in din ga zuwa makaranta da ciki, Ammi da mama ma su ganni". Ya ce "Ammin da ki ka cewa na ce zan ƙara aure dan baki da nono" Ruma ta ce "To duk ba kai ka janyo na faɗa ba, lokacin ban san abubuwa ba, kai kuma ka yi ta yi mini gori, ai maman Khadija da maman ilham sun kankaro ni". "Suwaye hakan?" Nan ta kwashe komai ta gaya masa, duk yadda aka kai ga sirri da ruma, idan hira tayi daɗi ita da takawa, sai ta kwashe komai ta gaya masa. "Wannan kunun da ka ga ina sha na garin kunun sabayar maman Khadija ce, ƴar zariya ce, har kwatancen gidanta na sani bayan Federal Palladan 08033411249. Maman Khadija kuma a no. Ai kawo road Kaduna 0813 561 3021. Tun daga zariya da Kaduna anty laila take sayo mana kayansu, a kawo mana har kano, ta haɗani da su ma in gaya maka, kai zaka cigaba sa saya mini" Ya ce "Haba nifa in ce, dare ɗaya in ga abubuwa sun sauya haka, lallai madalla da wannan bayin Allah, dan ni suka kankaro ba ke ba, dole a cigba da sayabai". "Yauwwa papan, ai na san ba zaka bani kunya ba" Ya yi dariya, sannan ya din ga yi mata nasiha a kan kula da addu'a da zama da alwala, saboda irin akasin da aka din ga samu lokacin Aisha tana ɗauke da juna biyu. Ya kuma din ga lallaɓata tare da magiya a kan dan Allah kar ta bari kowa ya san da cikin nan, su yi shiru da bakin su, ta ce masa in sha Allah ba zata faɗa ba. Abu kamar wasa mai sunan baba suka je interview shi da Mahmud, suna zuwa yadda yanayin abubuwan suka kasance, kai ka san akwai sanya hannun wani babban, dan babu wata shan wahala, dan shi bai ɗauki abun serious ba, dan cike link ɗin ma kawai dai dan Mahmud ya dame shi ne. Offer sa ta fara aiki aka buga aka bashi, aka yi posting ɗin sa Lagos, with salary of 740k per month, kasancewar da phd in accounting aka ɗauke shi, Mahmud kuma aka yi posting ɗin sa port hacourt. Sai jikin mai sunan baba yayi sanyi sosai, ya shiga lissafin yadda zai baro kano, ya bar matarsa da mahaifiyarsa, auren da ko watanni biyu ba su cika ba, ga ta ba cikakkiyar lafiya ba, ya baro ta, dama ta gama makaranta ne, sai kawai su tafi shi ban da katsina ma sai service da ya yi a Naija state, ban da haka ba wani dalili da ya taɓa raba shi da kano. Rumaisa ba ta son tana cikin kallonta, takawa ya canza mata tasha, ya ce labarai zai kalla ko kuma ball. Sai dai yau ɗin ma haka ne, ya ƙwace mata remote ya canza tasha, kuma ya kwanta mata a kan cinya, ta haɗe rai tana tura baki. Hira ake yi da senator Usman wakili a tashar, a kan ayyukan da zasu yi wa al'umma, muddin aka ba su dama aka zaɓe su, da kuma tabattar wa da mutane idan aka zaɓi ɗan sa ma, akwai tarin alkhairi da kyawawan ayyuka. Tsaki yayi ya canza tashar, rumaisa ta ce "Meyasa ka canza tashar?" Nan ya shiga bata labarin, tsamar da ke tsakaninsa da wakili, da yadda yana tsaka da bincike a kan sa, incident ɗin Aisha ya faru, hakan ya ɗauke masa hankali daga cigaba da bikcikarsa, duk da shugaban ƙasa ya kafa kwamitin bincikarsa amma babu wani kyakykyawan result, ƙarshe ma aka din ga cewa siyasa ce kawai, dan an ga za su tsaya takara hukumar DSS ke ƙoƙarin tozarta shi. "Papa wakilin nan, sunan gari ne ko sunan mutum?" "Oho musu, ina ga sunan family ne, da zarar na gane suwaye SMOKE, ko ban gano ba, zan cigaba da aiki a kan sa, bai dace da jagorancin al'umma ba" A hankali ta furta "Tsakar dare, bayan anty Aisha ta fara rashin lafiya. Sha tara ya ce; wakili ko wakilin tsiya. Yakamata su yi magana a san yadda za ayi da matar nan, ban taɓa jin tausayin wani abu kamarta ba, ko dan cikin nan, ga waccan ƴar bala'in ta hana mu sukuni". Still a bayanin da mutumin nan da yayi mata, wanda ya saya mata kaza da za su katsina, lokacin da ta tambaye shi ya aka yi suke da bindigogi da yawa, bayan jami'an tsaro ne kawai suke da ikon mallakar su? ya ce 'Yadda ake ware kason kula da harkar tsaro a ƙasar nan, haka ake ware mana namu kason makaman da ake sayowa na yaƙi daga waje wanda za a bawa sojoji, mu ma a bamu namu. Ko da ta tambayeshi ya ce mata ita yarinya ce ba zata gane ba. Bayanan nasa yayi dai-dai da bayanan da dattijon bafulatanin da aka ƙona rigar su, wanda ta tarar da shi shikaɗai, ta tsitsiye shi da tambayoyi yake gaya mata wasu rikice-rikicen da ake yi a wasu yankunan, yana da alaƙa da gano ma'adanai a yankunan, domin kawar da hankalin mutane, sai a ƙirƙiri tashin hankali a yankin, wasu tsirarin mutane su din ga kwashe ma'adanan, suna azurta kansu, wanda hakan ba zai yiwu ga karabutin mutum wanda bai san kan yadda za ayi amfani da ma'adanan ba. Wanda still wannan dattijon, shi ma a kan idonta, ya kai wa su sha tara makamai. Babban abun da ya bata mamaki bai wuce yadda mutumin yake ɗibar yanayi da iman ba. 'Anya ban makara wurin sanar da takawa wasu abubuwan da na sani ba?' 'Baki makara ba, alƙawarin da ki ka yi wa aisha ki ke ƙoƙarin saukewa, wanda ko a yanzu cikin kashi ɗari, kin cika tamanin da biyar!!! *MASU BUƘATAR DOCUMENT, YOU CAN START MAKING YOUR PAYMENT, CIKIN SATIN NAN ZAI ZAMA READY IN SHA ALLAH 1K VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK BOOK2&3 KO KU TUNTUƁE NI A KAN LAMBAR WAYATA 08081012143 NA GODE* Ayshercool. O8081012143 WHAT'S APP ONLY PLEASE 🙏🥺 *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin* *5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14.  Supplement na whitening/glowing skin* *15.  Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 *TALLA! TALLA!! TALLA!!! *ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH* Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.” Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH…. (*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*) *Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143* "Ya ina ta magana kin yi shiru, me ki ke tunani ne?" Da sauri ta dawo hayyacinta ta ce "Ba koma" ba dan ya gamsu da babu komai ɗin ba ya ƙyale ta. Sai dai fa abubuwa suka din ga kai komo a zuciyar rumaisa, har ta rasa wane tunanin ma za ta yi. Kallon Adam take tana nazari, da jin cewa yakamata komai ya zo ƙarshe haka, ta gaya masa iya abubuwan da ta sani, a wuce wurin kawai. Mai sunan baba sam bai yi ɗokin aikin nan ba, mussman da ya san dolensa ya tafi ya bar Iman, sai dai ya din ga zuwa yana komawa har ta kammala karatun sa. Daga mama har sauran ƴan uwansa murna suke yi, da samun aikin da yayi, haka iman ma tana ta yi masa murna, amma ta ga shi sam ko a jikinsa. "Sweetheart, wai ya naga kamar ba ka murna da samun aikin nan ne? Meke faruwa ne?". Cikin damuwa ya ce "Kewar matata na fara, zan tafi na barki, yaushe muka yi aure? Muna buƙatar samun isasshen lokaci tare" Cikin nutsuwa ta ce "Haba my faruk, kar mu yi wa Allah butulci mana, na ɗan lokaci ne fa. Dan Allah ka kwantar da hankalinka sai na koma gida, idan ka dawo sai in dawo gida. Shikenan sai Usman ya cigaba da kula da shagonka". Mai sunan baba ya ce "Ki koma gida, idan na dawo ki dawo saboda bamu da kunya?" "Tayi dariya ta ce, to ai kamawa ta yi ne, dan Allah ka yi haƙuri, nima zan yi missing ɗin ka sosai da sosai " ta din ga rarrashin sa tare da haɗa masa da kalaman bayar da ƙwarin gwiwa. Duk yadda ake jiyewa Iman auren mai sunan baba, ya bawa mutane mamaki sosai da sosai, domin ranar da Ruma ta je gidan, ta ɗau wayar Iman tana kallon hotunan biki, ta sha mamakin yadda ya zage yake kwasar soyayya, videos kala². Ita kanta ammi tana hamdala da yi wa Allah godiya, domin kowa ya ga Iman ya san tana cikin kwanciyar hankali. Mama ta yi wa mai sunan baba nasiha sosai da sosai, a kan riƙe Addu'a, da kuma nasihar ya ji tsoron Allah a kan aikinsa. Saura kwanaki uku dukkanin su kowa ya tafi garin da aka yi posting ɗin sa, takawa ya dawo gida, ya tarar da gidan cike da yayyen ruma har da Mahmud, suka gaisa ya tafi ɗakinsa. Ruma ta bishi, ta bashi abincinsa, tare da yi masa ƙorafin rashin kula Mahmud, sai dai bai tanka mata ba, ya nemi wuri ma ya kwanta. Bikin Nusaiba ma ya fara ƙaratowa, ammi tana ta shiri, wanda ranar yayi dai-dai da saura kwana ɗaya Mahmud ya tafi shi ma. Sashin Ammi ya shiga, kasancewar ya ɗan kwana biyu bai shiga ba, saboda zuwa lagos da suka yi, Ammi ta ji daɗin ganinsa. Kansa ya risunar ya ce "Barka da wannan lokaci" Ammi ta amsa masa da "Barkanka dai, kana lafiya?" "Alhamdilillah, na ce gobe in Allah ya kaimu ne tafiyarmu zan fara zuwa aiki" Ammi ta ce "Haka Iman take gaya mini, Ubangiji Allah ya sa a fara a sa'a" Ya ce "Amin" ya kalli Nusaiba ya ce "Kira mini baba uwani" Nusaiba ta tashi, ta je ta kira baba uwani. Tana ganinsa ta washe baki za ta hau kirari ya ce "Bana buƙata, kayanki zaki kwaso ki bar gidan nan a yanzu" Gaba ɗaya suka kalleshi da mamaki, ya ce "Ke kin san me nake nufi, ni na roƙi rumaisa ta rufa miki asiri, tare da tunanin ko zaki shiryu, tun da ba zaki daina ba, sai kin bar gidan nan yanzu" Ammi ta ce "Mahmud ban gane me kake nufi ba? Me ta yi ne? Tsawon shekaru ina tare da ita rana tsaka ka ce ta tafi?" "Ke kin ɗauketa mutum, kin kula da ita da iyalinta, ita kuma tsawon shekaru tana cin dunduniyarki, duk abubuwan da suke faruwa a sashin ki, Mummy na da masaniya a kai" Gaban Ammi ya faɗi ta kalli baba uwani ta ce "Uwani, da gaske yake yi?" "Wuce ki kwaso kayanki ki bar gidan nan, ki je dan kanki, ko ba a ɗauki wani mataki a kanki ba, hakkin mutanen da ki ka ɗauka ba zai barki ba" Mahmud ya ƙi yi wa ammi cikakken bayani, ya kori baba uwani a gaban sauran hadimai, wanda ya san tilas maganar za ta watsu, ace ya yi mata korar kare ba tare da cikakken dalili ba". Baba uwani na kuka, ta kwashi tsummokaranta, ta fita. Gaba ɗaya ammi ta zama confused, Barira ta ce "Ai ni na san baba uwani ba zata sauya hali ba, nayi mamakin rashin tona mata asiri, da maman sabir ba ta yi ba". Jin abun da ta faɗa, ya sanya ammi ritsa Barira, barira kuwa ta kwashe komai ta gaya mata. Ammi sai da ƙafafuwanta suka nemi gaza ɗaukarta, saboda tashin hankali da zullumi, hadimar da ta amincewa tsayin shekaru, ita ce ta ci amanar ta. Kasa jurewa tayi, a daren ta je gidan takawa, hankali a tashe, dan kuka take suka je gidan. Wanda hakan ba ƙaramin ɗagawa ruma da takawa hankali yayi ba. Rumaisa ta tabbatar mata da ta san baba uwani muguwa ce, tun a lokacin da ta din ga gaya mata takawa mahaukaci ne, da lokacin da ta ce Mummy tana yi wa takawa asiri maganar ta koma kunnen Mummy. Rumaisa ta tabbatar mata da cewa, Mahmud ya gaya mata ya sha ganinta cikin dare a sashin Mummy, amma ya ce kar su tona mata asiri a lokacin, saboda basu da cikakkiyar hujja, yanzun ma tun da ya ce ta tafi, yana da dalilin yin hakan, kuma ko daga baya an tayar da magana, suna da cikakkiyar hujja a kan ta yanzu. Sai a lokacin ammi ta din ga tuna wasu daga cikin abubuwan da suka gabata, tabbas idan da babu munafuki a sashin ta, babu yadda za ayi wasu maganganun su din ga fita. Sai dai a hakan ma, ruma ta ɓoyewa ammi binne-binnen da baba uwanin ke yi mata a cikin gidan. Takawa ya din ga rarrashin ammi yana bata haƙuri, tare da yin faɗa dalilin da ya sanya Mahmud ya kori baba uwani kai tsaye, ba tare da girbar abun da ta shuka ba. Ammi ta daɗe abun nan yana ci mata zuciya, ta daɗe tana jinjina tsawon lokacin da baba Uwani ta yi, tana zaluntar ta, ta hanyar kwasar sirrinta tana kaiwa wajen Mummy. Baba uwani bayan ta fita cikin kuka, ta kira Mummy ta sanar da ita halin da ake ciki, wanda hakan ya faru a dalilin ritsa Mummy da yayi suna waya da baba uwani, dan sai da suka samu saɓani ma. Babu kunya Mummy ta ce "Ba abun da za ta iya yi mata, sakacinta ne ya janyo mata" Baba uwani ta sha mamaki, ba ta taɓa tunanin abun da Mummy zata gaya mata kenan ba. Sannu a hankali rumaisa ciki ke tasawa, tayi ta ɓoye-ɓoye, gashi yau da lafiya gobe babu, haka nan take zuwa makaranta. Ga koke-koken ba gaira ba dalili, wai ita rasa abun da yake yi mata daɗi. Sai dai takawa yayi ta rarrashin ta, ya san ƙuruciya ce da rashin sabo. Iman kuwa kusan awanni kaɗan sai sun yi waya da mai sunan baba, idan ta maƙale a kan waya, har mantawa Ammi take yi da ita. Ammi ta ce "Iman dan Allah ki ƙyale yaron nan yayi aikinsa mana, maƙal-maƙal a kan waya ko gajiya ba kwa yi ne?" Rufe fuska tayi tana murmushi, dan kuwa ba ta yi zaton ammi ta ɗagota da yawan wayar nan ba. Ɓangaren mai sunan baba, yanayin aikinsa yayi masa daɗi, sai dai kewar gida da yake yi sosai, sannan ya fuskanci akwai tarin kitimurmura da rashawa a aikin. Sai dai yadda yake umar ɗin sa bai canza ba, ba ruwansa da kowa aikinsa ne kawai ya dame shi. Sallama aka yi a office ɗin sa, ya amsa tare da kallon ƙofar. Wani babban mutum ne ya shigo, fari sol da shi, cikin manyan kayansa. Mai sunan baba ya yi masa ƙuri da ido, ya ƙaraso ya zauna suka yi musabuha da mai sunan baba. Ya ce "Namu ne ka na jin hausa ko da turanci zan yi" yayi maganar cikin guɓatacciyar hausarsa ta cikakken bafulatani" Mai sunan baba yayi murmushi ya ce "Ina kama da bayerabe ne?" "To ai abun naku ne, wasu lokutan ba a banbance ku hausawa". "Eh amma irin naku da kun ga junanku ku ke ganewa" Mutumin yayi dariya, duk da yau ya fara ganin mai sunan baba, kamalarsa ta burge shi. Ya ce "Masha Allah ya aiki?" "Aiki Alhamdilillah" "To da dai ba kai nake tararwa a office ɗin nan ba". "Eh, sabon ma'aikaci ne ni" Ya ce "Yauwwa ni fa in ce. Kayana ne nake ta sintiri ayi mini clearance, amma bayan gama biyan duk wani haraji sai wani hanya-hanya ake yi mini, ana dai nuna mini sai na bayar da cin hanci, sai dai ba dan babu kuɗin ba, bayarwa ne ba zan yi ba. Tun da na san kayana ba na laifi bane" Ikon Allah mai sunan baba yake gani, hatta yadda mutumin yake kallonsa, tamkar iman ce a zaune a gabansa. Ya ce "Wasu irin kaya ne? Fanta ne, buredi da ƙosai ne ko kuma shanu" Mutumin ya sake yin dariya ya ce "Ka fa dame ni fa, ko dai babarbare ne?" Cikin murmushin sa na ƙasaita ya ce "Ba ɗaya, mai ɗakina ce bafulatana, ai ni akwai amana a tsakaninmu" "Ahhh ashe ma sirikinmu ne, ina fatan ka bayar da nagge 100, kafin a baka" yayi maganar yana ciro wayarsa daga aljihu da take ringing. Ya cewa mai sunan baba "Afuwan dan Allah" Ya kara wayar a kunnensa, yana magana da fulatanci, mai sunan baba yana fahimtar wani abun, sai dai ya ji yana cewa Ade a cikin maganarsa. Ya gama wayar ya girgiza kai ya ce "Ade na da damuwa. Wai mahaifiyata na ɗaukko daga garinmu, na dawo da ita nan Lagos gabana, na din ga ganinta. Ni da matata fa ƴan uwa ne, kuma akwai wasu ƴan uwana da na ɗaukko duk muke zaune tare. Amma ta saka an kirani a waya, wai na rabota da danginta na zo na ajiyeta a nan, ita tunanin shanunta da awakinta ma take yi. Ace Allah ya yi mini rufin asiri, amma uwata na ƙauye ai lamari ya ɓaci" Mai sunan baba ba wai dan halayyarsa ce sakin jiki hira da mutane ba, sai dan son cigaba da kallon ƘUDURAR ALLAH (Kar ku manta da sabon littafin NAZEEFA SABO NASHE, da tuni ya fara zuwar muku, kar ku yi ƙasa a gwiwa wurin bin wannan ƙayattacen littafin) Mutum mai matukar kama da matarsa, ya fara tambayar kansa anya mutumin ba shi da alaƙa da Iman ɗin sa. Hira suka ɗan yi da mutumin, yana bashi labarin rigimar Ade, kuma ya ke gaya masa akwai mataimakin shugaban ƙungiyar fulani ta ƙasa a familynsu, Ade Allah ya yi wa iyalanta rufin asiri, amma ita ta dage sai zaman ƙauye. Mai sunan baba ya bashi labarin, shi nasu gidan, da ƴan uwansa, tare da tattaunawa a kan jajircewar iyaye mata idan aka mutu aka bar su da yara. Haka suka din ga hira, daga baya suka yi exchange ɗin numbern waya, mai sunan baba ya ce zai sake duba maganar kayan na sa. *** Ƴan kwanakin nan, Mummy tana ta fama da ciwon kai, ta je asibiti an yi mata teses amma bai daina ba, ko san haske ba ta yi sosai. A hankali kuma Allah ya taimaketa ya fara sauka, shiryawa tayi zata fita, tana son yin waya, amma tata ba network, dan haka ta karɓi wayar ruƙayya ta saka lambar wayar da zata kira, ta yi wayarta. Sai dai bayan kammala wayar, ta ga saƙo ya shigo wayar ruƙayya daga Jabir. "Wallahi ruƙayya idan ba ki zo kin same ni ba, mun cigaba daga in da muka tsaya ba, zan watsa videos ɗinki, duniya kowa ya gani, and i mean it" Bakin Mummy ne ya fara rawa, ƙafafuwan ta suka nemi gaza ɗaukar gangar jikinta, cikin tsananin tashin hankali da mamki, ta dawo falo in da ruƙayya ke kallo. Fauziyya na chatting. Tana zuwa ta jefa nata mata wayar, ta ce "Me wannan saƙon yake nufi?" Gaban ruƙayya ya faɗi, ta ɗauki wayar, ta karanta, a take ta fara kuka tana girgiza wa Mummy kai. "Ki gaya mini me saƙon nan yake nufi?" "Mummy zan yi miki bayani dan Allah" Danneta mummy ta yi tana hargagi ta ce "Ni zaki tonawa asiri ruƙayya, wace irin alaƙa ce a tsakanin ki da Jabir? Wallahi gara na kashe ki, na kashe banza, akuya ce ke? Da ke za a haɗa kai a janyo mini abun faɗa? Ni Lubabatu da Jabir za su haɗa kai su cuta? Ni?" Da ƙyar Fauziyya ta janye Mummy daga kan ruƙayya da tuni numfashinta ya fara sama-sama. Ruma ce zaune daga ita sai mini skirt da brezia, domin kuwa kayan ma ita yanzu damunta suke yi. Ta ƙurawa Adam ido, "Ya dai babyna, jikin ne?" "To jiki ai sai Alhamdilillah, papa baka gano smoke ɗin ba haryanzu?" "Mimi da na gano, ai da na gaya miki, bashir suna nan suna bincike a kan al'amarin, kuma an gano wurin da ki ka ce ana ɗibar ma'adanai, mun yi magana da hukumar mu ta katsina ana targeting wurin, kama su ake son yi red handed kamar yadda na gaya miki" "Papa, na san na yi maka laifi, tun haɗuwarmu yakamata ka san komai, amma na din ga yi maka wasa da hankali. Ka san dalili?" Ya ce "A'a" "A wannan lokacin da ka san komai, zaka yi aiki da zuciya ne, zaka iya ɓata aikin, saboda kana kan jin raɗaɗin abun da ya faru. Anty Aisha ta bani labarin komai, wanene kai, abubuwan da suka faru a rayuwarta da taka, rashin jituwaku tsakaninka da Mahmud, sannan a ƙarshe ta roƙi da na auri mijinta, saboda tana ji a jikinta zan iya taimakonka, idan har zan rayu a tsakanin ƴan bindigar daji marasa imani da tausayi, in zauna a cikinsu da baƙin taurin kai, har na din ga abun da nake so wasu lokutan, su ƙyaleni, to lallai zan iya tanƙwara zuciyarka da koya maka haƙuri da sassauta fushinka. Na tubure na ce ni fa ba zan aureka ba, dan ba ka yi mini ba, mussaman da ba ma jituwa, amma ta cigaba da yi miki magiya, tare da roƙon in taimaki rayuwar mijinta, ita tayi iya nata ƙoƙarin ta kasa". Rumaisa ta ɗan yi shiru sannan ta ce masa "Lokacin da anty aisha za ta mutu, ta cigaba da nanata mini, ta bar mini jaririn ta, kuma ta bar mini mijinta, dan Allah kar in bari ƴar uwatta ta aureka, kuma in tabattar an samu daidaito tsakanin ka da ɗan uwanka, domin samun farincikin ammi. Papa, wakili na da saka hannu a yin garkuwa da anty aisha, dan ƴan bindiga sun ambaci sunansa, cikin dare suna zaton duk mun yi bacci". Ƙirjinsa ya buga da saurin gaske ya kalleta. "Amanarka na karɓo papa, shiyasa nake iya ƙoƙarina da zuciyata da jikina domin baka kariya, da tabattar da cika alƙawarin da na yi wa anty aisha. Ina neman afuwarka bisa wahalar da kai da na din ga yi, but Alhamdilillah atleast na cika wasu daga cikin alwashin da na yi" Shiru yayi ya sunkuyar da kai, ya kasa cewa komai. Rumaisa ta ɗago kansa ta ce "Papa fushi ka yi?" Cikin tsananin ƙarfin hali, da hawayen idonsa ya kasa ɓoye damuwar, ya ce "Mimi ba ki yi mini komai ba, ni ya cancanci na yi miki godiya mimi, ban san da wasu kalaman zan yi amfani ba ma" yayi maganar yana kwanciya a jikin ta. Ta kalli hannunta da hawayen sa yake ɗiga a kan hannunta, ta saka hannu tana share masa hawayen, tare da shafa sumar kansa. "Mimi ba kya so na? Saboda alƙawarin aisha kawai ki ke tare da ni?" "To ai ban san me zan ji idan ina son ka ba" Yayi murmushi ya ce "Shikenan, but i already fall for you, ni ina son ki sosai rumaisa i love you, and i will surely keep loving you, to my last breath. Ina son ki rumaisa". Ji ta yi tsigar jikinta na tashi, kalamansa na ratsa ko ina na jikinta, har wani lumshe ido take yi saboda daɗin kalamansa. Ta yi ajiyar zuciya ta sake cewa "Papa, jaridar da suke wallafa ci maka mutunci, lokacin da anty aisha ta rasu, Yasir ya bi diddigin gidan jaridar, daddyna ya gano wakili ne suke ɗaukar nauyinsa, dan ya ce mini sun taɓa kiransa har aka nemi ya bayar da haɗin kan cutar da kai, ya ce ba ruwansa. Kaga dole a cikin family ba za a rasa wanda suka haɗa kai da shi ba, ake cutar da kai" Ya lumshe idanunsa ya ce "Mimi kaina ya daina ɗaukar wannan abubuwan ma, bari na samu nutsuwa" "Idan ka samu nutsuwar, ka yi bincike sosai a cikin gida. Sannan ka sani tun a yanzu ka sanya wa ranka cewar, zaka iya gano su waye, amma samun hukunci da adalci sai a wurin Allah, amma ba a wannan ƙasar ba" Ya numfasa ya ce "Ina sauraren Bashir ne, na ji me za su ce mini, nayi magana da su barrister ma, waɗan da ki ka ce mini kin yarda da su, muna kan faɗaɗa bincike" "Nima ni da ƴan team ɗina muna ta ƙoƙari, Allah ya yi mana jagora" ya jinjina kai ba tare da iya yin magana ba. Abu kamar wasa mai sunan baba yake ta ƙoƙari akan kayan Alhaji Aminu ɗan fulani, kuma kasancewar an samu sauye-sauye a wurin, cikin ikon Allah komai ya zo masa da sauƙi, dan ana daf da releasing ɗin kayan. Alhaji Aminu yana yawan kiran sa, su gaisa, shi kuma mai sunan baba, sai ya tambaye shi ina Ade, ya ce masa tana nan tana rigima. Alhaji Aminu ya matsawa mai sunan baba, a kan lallai ya zo gidansa su gaisa, dan yana bawa Ade labarin sa, ita kuma ta ce tana son ganin sa. Mai sunan baba ya ji a ransa yana son sanin ahalin Alhaji Aminu, ko zai samu abun da yake son tabattarwa, ko Alhaji Aminu yana da alaƙa da Iman. *** Tamkar za su kacame da dambe, haka suke musayar yawu, tamkar ba aminan da suka kwashi shekaru suna cin mushe ba, tamkar ba tare suke ƙullawa da kitsa duk wani hatsabibanci ba. Mummy tamkar za ta ari baki, saboda haƙilo da bala'i. Hajiya Lubabatu a fusace ta kira Jabir a waya, a kan lallai ya zo tana son ganinsa, ta ajiye wayar ta kalli hajiya jamila ta ce "Kar ki sake kiran ɗa na da mazinaci ɗan iska, idan ma hakan ne, sai ki ce mazinata ƴan iska". "Na faɗa ɗin, koda yake barewa ba ta gudu ɗan ta yayi rarrafe ba, tun da sai da ki ka yi yawon tazubar ki ka gama ki ka tuba aka yi auren. Kin yi wa mijinki asiri, kin ya da shi a Germany, kin cigaba da watsewa a gefe, ke ki yi ɗan ki yayi". "Jamila kina nufin ni ce nake biye² ni zaki yi wa sharri? Ko kin manta kema irin abubuwan da ki ka shuka, yayan giwa da ki ka din ga sadaukarwa, da ƴaƴan Adam, ai ni ban kai ga aikata kisan kai kamar ke ba" Jabir ne yayi sallama, suka yi shiru suka waiwaya. "Sannu munafukin Allah ta'ala" Jabir ya ce "Mummy lafiya kuwa?" Mummy ta ce "Saboda kai watsatstse ne, mara mutunci, na amince maka na amincewa uwarka, amma ku ka zalince ni, wace irin alaƙa ce tsakanin da ruƙayya har ka ke iƙirarin yaɗa hotunanta?" Yayi shiru yana kallon Mummy. "Wallahi lubabatu sai kun yi dana sanin abun da ku ka aikata mini, kai ba da ni ka ke zancen, dabba ɗan akuya". "Kar ki sake kiransa ɗan akuya, ruƙayya ce babbar akuyar da ba ta san ciwon kanta ba" Mummy kawai ta fice, zuciyarta na wani irin zafi, kuka take son yi amma ba ta son bayyana karayarta a fili. *** Mai sunan baba ya amsawa Alhaji Aminu cewar zai kai masa ziyara ya gaida Ade, sai dai yana fargabar kar ya ga abun da bai yi tsammanni ba, zai fi kowa farin ciki, idan aka ce a sanadinsa Iman ta samu ko wani ne a danginta, duk da rashin hakan ba ya nufin zai juya mata baya ne. Kiran Iman yake yi yana zancen zuci, ta ɗaga video call ɗin ta ce "Hi dear" "My yellow, how are you?" "Fine Alhamdilillah, ya aiki?" "Ai akwai shi, yanzu salary ya shigo, na ce let me call the person close to my heart" Tayi murmushi ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, mun godewa Allah" kallonta yake sake yi, hatta yanayin gashin girar iman, irin na Alhaji Aminu ne. "Ya naga kana kallona ne, na canza ne?" "Bakomai, yanzu ya za ayi da salaryn nan ne?" Iman ta ce "Ai zaka shigo kano ko? Ka ce fa ƙarshen wata zaka zo". Ya ce "Eh, ranar Alhamis zan shigo" Ta ce "To Allah ya kaimu, idan ka zo sai ayi shawara, ka turawa mama dubu ɗari a sai mata abun da take so kan ka zo na neman albarka". Ya ce "To ƴar mama, za ayi in sha Allah, zan cigaba da waya, zamu yi magana anjima" Ya ajiye wayar yayi shiru, yana cigaba da fatan Allah ya sa Alhaji Aminu yana da alaƙa da Iman. Har gida Alhaji Aminu ya aika da direba, aka ɗaukko mai sunan baba, yana da matuƙar karamci da son mutane, kamar ya goya mai sunan baba da ya ganshi a gidansa. Aljannar duniya, an kashe dukiya an zuba kayan alatu a gidan nan, kamar ba za a mutu ba, karen da yake gadin gidan kuwa bayan mai gadi, shi kansa ba na Nigeria bane ba. Ga iyayen motoci a parking space. Ya ce wa mai sunan baba "Mu je ka fara ganin Ade, ka gaya mata ta haƙura da tafiya ƙauye ko Allah ya sa ta yarda". Tsohuwa ce, a ƙalla zata shekara tamanin da biyar, tana zaune a ƙasan carfet, tana shan fura, sai mita take da fulatanci ita da jikokinta. Ta ɗaga kai ta ƙure mai sunan baba da ido, har ya ƙarasa gabanta ya zauna. "Ade, ga wanda yake ta yi mini ƙoƙari a kan kayana, shi ya ce a baki haƙuri, dan Allah kar ki koma ƙauye". "Au jibo gulmata ka ke yi kana yamaɗiɗi da ni kenan, yaro na bar shanu da dabbobina a ƙauye, an zo nan ƙwam an ajiyeni, sanyi na neman yi mini illa, ga wannan yaran da suka addabe ni, ai zaman ƙauye yafi daɗi". Mai sunan baba ko rantsuwa yayi ba zai yi kaffara ba, wannan matar na da alaƙa da matarsa, duk da tsufanta, tsananin kammaninta da iman ba su ɓuya ba, sai a yanzu ma ya ga Iman ba kama take da Alhaji Aminu ba. Ade ba ruwanta, ta din ga zuba tana bashi labarin yadda take son shanunta, tun da a cikinsu aka haifeta. Kayan marmarin da ya zo da su, ya din ga ɗauka yana ɓarewa yana bata, tana karɓa tana ci. Ta ce "Kaga yadda ka ke yi mini ɗin nan, shi ba ya yi mini, kullum cikin rubutu yake da lissafin kuɗi, Euro ya leƙo mun gaisa, sai ya kama hanya ya tafi yawonsa" Alhaji Aminu ya ce "Sai ka ce a ƙauyen hakan suke yi miki" "Eh amma dai idan na ga nagge, zuciyana na sanyi sosai" "Yallaɓai kai baka da ƴan uwana ne?" Alhaji Aminu ya ce "Kowa ya kama gabansa, ka san ainihi daman mu fulanin tashi ne. To ƴan uwan nawa galibi wasu suna wasu garuruwan, wasu ma wasu ƙasashen. Ni ne ɗan autan ta, ƙauyen fa a gidan wani ƙaninta take, wai an rabata da ɗan uwanta, kamar ɗan uwanta ya fimu" "Ya fika mana, shi yana zama mu yi hira, kai sai shegen son kuɗin tsiya". "Ni zaki tozarta a gaban baƙo ko, saboda ya baki ayaba, da lemo, to yasin a daina yin ƙosai a gidan nan, tun da ba kya so na" Alhaji Aminu kamar kakarsa ya ɗauki Ade, su yi ta faɗa wasu lokutan, saboda shi ne ƙaramin ɗan ta. Mai sunan baba ya ɗan jima a gidan, sannan baba ya ce zai tafi, Ade ta din ga tambayarsa yaushe zai dawo, idan bai dawo ba, za ta ƙulle takalmanta a zaninta, ko ta katanga ta bi, ta gudu ta koma ƙauye. Mai sunan baba ya ce "Ai ba za ayi haka ba" "Ka rabu da ita, karen nan zan kawo ɗakinta na ɗaure, na ga ta wurin fita" Ta galla masa harara ta ce "Tashi ke je ɗakina, ka samo masa ɗan biskit ɗin nan" Alhaji Aminu ya ce "Biskit kuma? Ade kyautar nagge zaki bashi, me zai yi da wani biskit" Mai sunan baba ya ga ƙoƙarin ta ma, rikicin taufan na ta ba na zage² bane ba. Mai sunan baba har ya koma gidan da yake, yana al'ajabi, kuma ya yanke shawarar zai yi wa Mahmud zancen, koma ya zo lagos ɗin, ya je su ganewa idonsu, su san ta in da za a ɓullowa lamarin. Dan baya son yayi gaggawa, a zo a gane cewar ba su da wata alaƙa. *** Ammi ta kasa mantawa da matsananciyar cin amanar da babu uwani ta yi mata, har ta kai ba ta iya sakin jiki tayi magana a gaban kowa yanzu, saboda tsoro da tunanin kowa ma ba son ta yake yi tsakani da Allah ba. Ranar da mai sunan baba zai koma, Iman gyara kala-kala, aka ƙalƙale ko ina, ta shirya girke² ta sha kwalliya. Dama har kirari yake yi mata da ɗawisu sarkin ado, Iman akwai ado da kwalliya. Sosai suka yi missing ɗin juna ita da shi, sai dai da ya kalleta, Alhaji Aminu yake tunawa da mahaifiyar sa. Ya din ga jin tamkar yayi mata zancen, amma ya kasa. Washegarin dawowarsa, da yamma ya shirya su ka yi wa mama siyayya, suka je gida gaisheta. Mama tayi ta yi masa faɗa a kan yanzu yana da iyali, yakamata ya mayar da hankali a kan gidansa, ƴan samarinta sun ɗauke mata komai, kuma dubu ɗarin ma da ya turo tayi yawa, jiransa take yi ya dawo dama. Ya ce "Ni fa ba ruwana, ƴar ki ce ta ce ayi haka" Mama ta ce "Kuma sai ka biye mata?" Iman ta ce "Mama idan bamu yi muku ba, wa muke da shi? Ayi ta saka mana albarka kawai". Mama ta ce "Albarka da addu'a kullum cikin su muke, amma dan mun haifeku ba ya nufin, mu takura rayuwarku, ina fatan dai kun je wurin hajiyar?" Iman ta ce "Gobe in Allah ya kaimu za mu je ammi, a can zan wuni, shekaranjiya na koma gida, idan na kuma zuwa faɗa za ta yi mini". Mama ta ce "Ai faɗan na gyara ne, mun kai ku ɗaki amma kullum ku ba kwa gajiya da zuwa gida" Iman ta yi dariya ta ce "Mama kenan". Kasancewar umar akwai kyauta, haka ya din ga bayar da kuɗi, ga bikin Abubakar saura wata ɗaya kacal ya rage. Mai sunan baba suka yi waya da Mahmud, ya tabbatar masa da shima zai shigo kano, dan haka umar ya ce idan ya shigo yana son su haɗu za su yi magana. Nusaiba har ta shirya tafiya makaranta, sun yi sallama da ammi, ammi tana ta fama Sabir, ya isheta da fitina, tana ta mita ta ce makaranta za a kai mata shi, ta huta. Barira tana mata dariya ta ce "Anya ranki ya daɗe, kin hana mamansa shi ma balle kai shi makaranta, idan aka kai shi, sai kin fi kowa damuwa" "A'a ba wata damuwa gara a kai shi, tun da yayi baki" "Ammi, ammi" Nusaiba ta shigo tana ƙwalawa ammi kira. "Lafiya baki tafi makarantar ba?" "Ammi wai yaya Mahmud ne ya dawo shekranjiya, wai ya je har gida ya yi wa Jabir dukan tsiya, ta ƙarfin tsiya ya saka shi a mota a fita da shi, ya kai shi ofishin ƴan sanda an rufe shi. Yau shi kuma ya wayi gari da ciwon ciki, a asibiti ma ya kwana bai san waye a kansa ba". Ayshercool 08081012143 *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin* *5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14.  Supplement na whitening/glowing skin* *15.  Supplement for Acne, dark spots remover* *Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah* *Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin* https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Susbcribe my YouTube channel please 🙏 *TALLA! TALLA!! TALLA!!! *ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH* Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.” Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH…. (*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*) *Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143* Miƙewa Ammi ta yi cikin sauri ta ce "A ina ki ka ji?" Nusaiba ta ce "Yanzu su musa suke faɗa, wai a asibiti ya kwana ma, tun cikin dare aka kai shi" Rikicewa ammi tayi, ta nufi ɗakinta, Nusaiba ta bita ta na cewa "Ammi me zaki yi?" "Nusaiba asibitin zan tafi, ni babu wanda ya gaya mini ai" Nusaiba ta ce "A'a Ammi, kar ki je su yi miki wani rashin mutuncin, ki fara kiran takawa ki gaya masa" "Yaron ya kwana a asibiti, ki ce sai na kira takawa na gaya masa?" "Dan Allah ammi ki bari ya zo tukuna, sai ku tafi tare ma, kar su cutar da ke" da ƙyar Nusaiba ta shawo kanta, ta amince a kira takawan tukuna". Juma'a ce, dan haka rumaisa ta ce ba zata makaranta ba, dan jikinta babu daɗi ko ina ciwo yake yi mata. Takawa sai lallaɓata yake yi, yana son ya fita aiki, sai sangarta take yi masa, da shagwaɓa kala-kala. Wayar Ammi ya gani, dan haka ya ɗaga tare da yin sallama. Cikin ruɗewa ba tare da ta iya amsa sallamar ba ta ce "Takawa, kana ina ne? Mahmud aka kwantar a asibiti, wai ya kwana yana ciwon ciki jiya, so nake na je" Takawa ya ce "Dan Allah ammi ki kwantar da hankalinki, ki bari na je wurin aiki, idan aka saukko daga masallacin juma'a zan zo na kai ki ki duba shi". "Baka da hankali ne? Ka san ciwon ciki kuwa? Yaron ya kwana a asibiti amma ka ce sai an idar sa sallar juma'a awa nawa? Idan zaka kaini ka zo yanzu, idan ba zaka zo ba zan yi tafiyata ko me za su yi zan jure tun da ni na kai kaina" "Kiyi haƙuri gani nan" rumaisa ta zuba masa ido, bayan ya kashe wayar ya ce "Duk ta rikice a kan ɗan da bai san darajarta ba, nan zai yi ciwo ta je duba shi, ta hanata ganinsa ta ce bacci yake, ko baya son hayaniya amma za  taje duba shi, ammi ba ta gudun abun da zai ɓata mata rai sam" Ruma ta ce "Dan Allah zuciyar mutum ce a jikinka? Ka san me ake nufi da uwa da ɗa kuwa? Kai banda dalilin sihiri da nake da tabbacin shi ya raba ammi da daddy, kai kana zaton akwai dalilin da zai sanya ta zuba ido ta barwa wata mata ɗan ta. To ai ko ni da abun da ke cikina bai zo duniya ba, da shi da Sabir, ban ga wanda ya isa rabani da su ba, kai idan aka ce za ayi asirin ma, sai na haɗa asirin da bokan na ci ubansu wallahi. Dan Allah papa kaima ka sassauta wannan ƙiyayyar, yanzu bari in saka kaya in bika". Ya ce "No, ki zauna a gida, zan je kawai" Ruma ta ce "Hankalina ba zai kwanta ba, ka tafi da ni dan Allah, idan ba haka ba zan biyoka idan ka fita". "Mimi kina da matsala, cikin nan ne bana son a gani". Ta kalleshi ta ce "Saboda me?" "Kin fi kowa sani ai, ba na son wani abu ya samu cikin nan naki, kullum cikin Addu'a nake yi Allah ya sa ki haihu lafiya, kin san komai ai" "Babu abun da zai faru sai ikon Allah, ka tafi da ni saboda zatin Allah, hijjabi zan saka, ba wanda zai gan shi ai" kasancewar rumaisa ta ƙware a iya magiya, tamkar ƴar maroƙa, haka ya sanyata a gaba suka tafi. Da shi da Nusaiba, da Ammi, haka suka rankaya asibitin da aka ce Mahmud yana can. Gaba ɗaya Ammi ba ta cikin nutsuwarta, takawa ya ce "Ammi dan Allah ki kwantar da hankalinki, kin San ki na da high bp". A rikicen dai Ammi ta ce "Kai ka san sani high bp, ka tambayar mini ɗakin da yake dan Allah " Ruma ta din ga kallon ammi cikin tausayawa, haka ta shafe shekaru da soyayyar nan da tausayi suna nuƙurƙusa zuciyarta, ruma ta jinjinawa mugunta irin ta mummy. Ba ƙaramin razana ammi tayi ba, ganin Mahmud a kwance ba ya motsi, ga ruwa an saka masa, ga kuma oxygen da take taimaka masa yana numfashi, gefensa kuma mummy ce a zaune. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Mahmud meya sameka haka?" Ammi ta yi maganar cikin rawar baki. Jin muryarta ya sanya shi ya motsa, ya fara yi wa ammi nuni da hannunsa ta zo. Cikin hanzari ammi ta ƙarasa, idonta na ta zubar da hawaye. Ya miƙa hannunsa ya riƙe nata, sai dai ba baki, sai hawaye da yake zuba ta gefen idonsa. Ammi ta riƙe hannunsa tana jejjera masa sannu. Ya ɗora hannun a kan cikinsa. Ruma ma ta ƙarasa gaban sa cikin kuka ta ce "Daddy meyafaru? Meya sameka?" Wata irin miƙa yayi bakin sa yana zubar da kumfa, cikin sarƙewar numfashi ya ce "Daughter mutuwa zan yi. Ammi. Amm....Ammi na faɗa yau rumaisa, Ammi ki yi mini Addu'a cikina" yayi maganar tamkar numfashin sa zai bar gangar jikinsa. Daga rumaisa har Ammi kuka kawai suke, Nusaiba ma kuka take. Cikin kiɗimewa Mummy ta tashi cikin azama, ta ce "Mahmud ciwo ba mutuwa bane ba, kar ka sake cewa zaka mutu, haba Mahmud kar ka yi mini haka dan Allah " tayi maganar tana fashewa da kuka. Ya buɗe ido a galabaice ya kalli Mummy, ya zare hannunsa daga na ammi, ya riƙo nata "Mummy na gode, na gode Mummy" Ya sake zare hannunsa daga na Mummy, ya miƙawa adam, sannan ya cewa ruma "Ki ce masa ko sau ɗaya ya riƙe hannuna Daughter" ya yi maganar yana sake mimmiƙe wa. Cikin matsanancin kuka da tashin hankali rumaisa ta kalli Adam ta ce "Papa dan Allah" Adam da tuni ya karaya, kuma ya tsorata da lamarin, A  hankali  ya tako, ya zauna a kusa da rumaisa, ya saka hannunsa a na Mahmud ya rungume shi. "Ina son ka ɗan uwana, Ƙaddara ce" Mummy ta rasa in da zata sanya kanta, dan lafiya ƙalau Mahmud ya kwanta, idan har ta ce ba ta ƙaunar Mahmud ƙarya take yi. Saboda yayi mata biyayya fiye da yaran da ta haifa, kuma ta saka an ƙwace shi an bata shi, dan mugunta, amma kuma sai ta fara son sa daga baya. Likita ne ya shigo, ya din ga yi wa Mahmud wasu allurai. Bayan fitar likita, duk sun yi shiru sun zuba masa ido, Adam yana rungume da shi, rumaisa ta miƙe zumbur, dan tamkar ana mata raɗa ta ji komai. "Me ya haɗa shi da jabir ne?" Takawa ya ce "A ina?" Duk suka tsaya suna kallonta. "Meyasa ya daki Jabir ya kulle shi?" Duk suka zubo mata ido. ganin da Mahmud yayi Mummy, tana cikin damuwa, ya sanya ya sakata a gaba, a kan ta gaya masa meke damunta, ta kasa ɓoye masa ta gaya masa komai. Ba ƙaramin girgiza yayi ba da jin abun da Jabir ɗin ya yi ba shi da ruƙayya, tun da ya fita a fusace, sai wayar Hajiya Lubabatu ta gani, ta tabattar mata da zata ga abun da za ta yi wa Mahmud muddin bai saka an sakar mata ɗa ba domin kuwa ta san muddin asirin jabir ya tonu ba zai yi sarauta ba, kuma ta fuskanci kamar yanzu Mummy ƙoƙari take taga Mahmud ne ya samu sarauta. Sai a yanzu Mummy ta tuna da furucin hajiya Lubabatu. Tashi rumaisa ta yi ta fara tashin Mahmud. Takawa ya ce "Ya samu bacci fa" "Tashe shi kawai, daddy" Ya buɗe ido a matuƙar wahale ya kalleta. "Meya haɗaka da jabir?" "Bakomai" ya furta yana numfarfashi. Ta ce "To koma me ka yi masa, babarsa ta ce zaka gani" Takawa ya ce "Mimi bana son rigima fa, ke a ina ki ka ganta?" Ruma ta ce "Ɗazu da asuba ina bacci, na gansu su na faɗa, ban san a kan menene ba, amma ita ta ce zai gani, jabir yana police station ko?" Ammi ta tashi ta kamo ruma ta zaunar da ita, ta ce "yi shiru da bakinki" shi dai takawa a iya sanin sa, suna tare da ruma, kuma ba wani wurin suka je ba, balle ace ta ji. Mummy ta hau bala'in cewar mahmud sun yi faɗa da Jabir, amma ba wani abu da Hajiya Lubabatu ta yi masa. Tayi maganar tana karewa saboda kar a gane sun samu saɓani da Hajiya Lubabatu, kuma muddin asirin lubabatu ya tonu, na ta ne ya tonu. Takawa ya ce "Mimi ba ta ƙarya a cases irin wannan, zan yi bincike a kai, duk wanda na gano da saka hannunsa wani abu ya same shi, wallahi sai ya fuskanci hukunci ko waye shi". "Matarka ba ta ƙarya ni nake yi kenan?" Ammi da sauri ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, ku yi haƙuri Takawa kar in sake jin bakin ka, rumaisa ku yi shiru mu yi masa addu'a". Ruma ta ce "To ammi, amma wallahi ba ƙarya nake yi ba" Mai sunan baba ne yayi sallama ya shigo, hankalinsa a tashe, "Subhanallah" yake ta maimaitawa saboda halin da ya ga Mahmud a ciki, dan kuwa sun yi waya jiya da safe, yake ce masa zasu haɗu yau. Bai iya yi wa kowa magana ba, ya ƙarasa gaban gadon yana ambaton sunansa. Gashi da an kira sunansa yake amsawa, ya buɗe idonsa ya kalli mai sunan baba. "Mahmud, meyafaru haka ne? Wayarka na kira wata yarinya ta ɗauka ta ce mini wai kana Asibiti" ya cewa mai sunan baba "Ɗago ni" Mai sunan baba ya sanya hannu biyu, ya ɗago shi, ya jingina da jikinsa. Ammi ta din ga ajiyar zuciya ganin Mahmud a zaune. "Ku yi haƙuri duk na tayar muku da hankali" Mai sunan baba ya ce "Kar ka damu sannu ya jikin naka?" "Da sauƙi, zan sha ruwa" Mai sunan baba ya kalli Adam, Adam ya ɗaukko roba ya tsiyaya ruwa ya bawa umar, ya karɓa ya bawa Mahmud, ya karɓa ya sha sosai. Ya ce "Alhamdilillah, ina ƙanwata tana lafiya?" "Lafiya ƙalau, bata san me ke faruwa ba, na riga na fito sannan na kira wayarka, sannu Mahmud" "Yauwwa yaya" kasancewar haka yake kiran umar. Ammi ce ta ce "Mai sunan baba ya gida?" Ya ce "Afuwan ammi, hankalina ne a tashe wallahi, ya gida ya mai jiki kuma?" Ammi ta ce "Jiki da sauƙi Alhamdilillah" Mummy kuwa sai cika take tana batsewa, Fauziyya ba ta taɓa ƙarewa mai sunan baba kallo ba sai yau, lallai Iman ta auri mai kyau, da cikar zati. "Me zaka gaya mini ne ka ke nema na?" Mai sunan baba ya ce "Ka ji da jikinka ka samu lafiya, kana tambayata me zan gaya maka" yayi maganar yana murmushi. "Am curious about it" yayi maganar yana lumshe idanunsa, saboda allurar baccin ba ta sake shi ba. "Zan gaya wa yayanka ya gaya maka" "Wai Takawa? Ba zai gaya mini ba" Mai sunan baba ya ce "Zai gaya maka mana, zaka ci abinci ne?" Ya girgiza kai ya ce "Bari sai na gama farfaɗowa, idan kuma na mutu.... "Shhhh, zaka farfaɗo in sha Allah, har aurar da kai sai na yi" Ammi bakinta ya ƙi rufuwa dan murna, ita ba ta san ya aka yi ma ta sa ta zo ɗaya da Mahmud ba, saboda Mahmud akwai taurin kai da rashin mutunci, mai sunan baba kuma akwai izza da son girma, amma yadda yake yi masa zaka gane akwai mutuntawa da girmama juna a tsakaninsu. Ya kwantar da Mahmud, ya ce "Ka yi bacci, zan je gida ƙanwarka ta yi maka girki, mu zo ta duba ka" "Kar ka wahalar da ita, ga Mummy ga Ammi ga daughter duk na wanda na samu zan ci". "Ba wata Mummy, na ammi zai ci" Rumaisa ta faɗa tana harare-harare. Fauziyya ta buɗe baki za ta yi magana, amma kwarjinin mai sunan baba ya cika mata ido, dan ta san ƙarya take, ta zagi rumaisa a gabansa ya ƙyale ta. Ya kalli Adam ya ce "Ina son yin magana da kai" Mamaki ne ya kama Adam, amma ya tashi ya bi bayan mai sunan baba suka fita. Fauziyya ce ta ɗora da rashin mutunci. "An yi magana wani ammi ce za ta bashi abinci, sai ka ce ammin wahalar sa ta sani, uwarmu ce dai ta yi masa duk wata wahala ta rayuwa". "Da tayi mata fashin ɗan? Kallon biri ku ke masa yake yi muku na ayaba fa. Uwar me ta tsinana wa rayuwar ta sa ban da masifa, uwar riƙon arziki ce za ta raba uwa da ɗan ta, ta raba jini da jininsa, ta raba shi da ɗan uwan sa, yanzu dai shi ma ya san gaskiya, gurbin ido ba ido ba ne, kuma wallahi ko bayan shekara dubu, tuwo sunan sa tuwo" Ammi sai ƙoƙarin hana magana take yi, amma rumaisa tayi mursisi ta din ga gasawa Mummy da Fauziyya magana, ita kaɗai su biyu ba tare da kunya ko tsoro ba. Duk abun nan da ake yi Mahmud yana jin su, amma yayi shiru kamsr mai bacci. Mai sunan baba ya kwashe komai ya gaya wa takawa, game da Alhaji Aminu, jikin takawa har tsuma yake yi ya ce "To yanzu Lagos ɗin zamu je, ko yaya za a yi? Mu ga shi Alhaji Aminun, idan ta kama tambayarsa zamu yi, ko ma a tafi da ammi sai ayi " Mai sunan baba ya ce "A'a ina ga gara mu mu je mu tabbatar, tun da yanzu tana cikin damuwar rashin lafiyar Mahmud, dama da shi na so mu je, to gashi ba shi da lafiya" "Bakomai, bari mu ga zuwa gobe in Allah ya kaimu, in dai ya ƙara warwarewa, sai mu je kawai, ina fatan Allah ya tabbatar ya sanya ƴan uwan iman ne " Mai sunan baba ya amsa da Amin, har takawa ya juya zai tafi mai sunan baba ya ce "Na ce ba" ya juyo ya tsaya yana sauraren sa. "Akwai buƙatar duk abun da ya faru a baya ya wuce, a fuskanci gaba. A zamana da Mahmud babu abun da yake marari da so da ya wuce ka, you have to play your role as his senior brother, babu abun da yafi ɗan uwa daɗi. Ba zaka gane hakan ba sai ranar da babu shi a duniya" Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Haka ne, na gode sosai" mai sunan baba ya jinjina masa kai ya tafi. Samha sun je duba Mahmud a asibiti, dan tuni labari ya zaga masarautar, Mahmud ba shi da lafiya, ƴan dubiya sun fara kaiwa suna komowa. Sai dai fa cacar baki taƙi tsayawa a tsakanin Fauziyya Mummy da rumaisa. Muraran yau ruma take nuna musu asalin tantirancinta. Samha za ta saka baki ruma ta ce "Yi mini shiru, ba dake nake ja gayyar mushirikai maƙiya Allah, ai wallahi a doron duniya ban ga bokan da zai yi asirin da zai kamani ba, sai dai ku yi wa wasu". "Su waye mushirikan?" "Gaku nan gaba ɗayanku, ban da yawon asiri da ƙoƙarin rusa rayuwar mutane me ku ka saka a gaba, azzalumai maƙiya Allah" A rikice ammi ta fita neman Adam, suka yi kiciɓis a hanya, ta ce masa maza ya je ya ɗau rumaisa ya mayar da ita gida. Sai dai suna shiga ɗakin, suka tarar Samha da Fauziyya tamkar za su rufe ruma da duka, ita ma ta tsaya ta riƙe ƙugu tana bala'i, Nusaiba sai ba su haƙuri take. Babu abun da ya gigita Samha sama da ganin tirtsetsen ciki a jikin rumaisa bayan ta miƙe, ta riƙe ƙugunta. Ruma ta ce "Mamaki ki ke yi ko Samha, kin ga ciki a jikina? Baba uwani ba ta gaya miki na cire layar da aka saka a cikin katifar ɗakunan mu ba?. Ai tunda Allah ya sa na ritsuta, duk wani lungu da saƙo, sai da ta tone komai, na zauna na warware abun da ki ka ƙulla mini na tsiya, masifarku sai dai ta ƙare muku". Cikin matsanancin tashin hankali Samha ta ce "Me ki ka nufi? Nima sharrin zaki yi mini?". "Wallahi na fi ƙarfin in yi miki ƙarya, rufa miki asiri kawai na yi, amma tarkacen layoyi da kayan tsubbun duk da ku ka binne mana a cikin gida an tone su, na kuma tara su wuri ɗaya saboda sheda, duk bala'inki ke da Adam sai dai ido Samha" Ba tare da sanin Adam ya shigo ba, ta yi ƙoƙarin hankaɗa Rumaisa. Amma cikin zafin nama, ya hana faruwar hakan, ya ɗauketa da mari. Tsit suka yi suna kallon Adam. "Wallahi ko da makamancin wasa, ki ka sake ki ka yi wa rumaisa wani abu, sai na taka ki, sai dai zumuncin ya watse uban kowa ya kama gabansa wallahi. Kuma na gode da abun da ki ka yi mini, na mayar da ni mara amfani a gidana, sai dai Allah ba a azzalumin sarki bane ba, kanki ki ka yi wa samha" Mahaifiyar Samha ta fara bala'i "Wane irin mutum ne kai? Duk abun da yarinya ta faɗa sai ka yarda da shi, kai ba ta laifi kenan. Saboda rashin ta ido, a gabana ka mari ƴa ta" "Saura Jamil ma, wallahi sai na warware kowane munafuki, babban algungumi mara tsoron Allah" Nurses ne suka shigo, suka ce su fa asibitinsu ba wurin hayaniya ba ne ba, dan haka a tafi a bawa mara lafiya damar hutawa. Adam ya maze ya ce kowa ya tafi Shi da Ammi za su zauna, ruma kuma anjima zai mayar da ita gida. Mummy ta ce bai isa ba. Likita ya zo da kansa, ya ce wace mahaifiyar Mahmuda ta zauna da shi, ita da mutum ɗaya, ruma ta nuna Ammi ta ce "Ga mahaifiyar sa nan" Mummy na ji tana gani aka sallame su, ya rage sai ruma Ammi Nusaiba da takawa. Mahmud ya kalli ruma ya ce "Daughter kina ganin bai yi wuri ba?" "Bai yi ba daddy, yakamata komai ya zo ƙarshe, enough is enough" Adam ya ce "Ban gane me ku ke nufi ba" "Zaka gane very soon, amma kar ka matsa Please" Ammi ta ce "Mahmud, a kawo abincin? Ya ka ke ji yanzu?" "Alhamdilillah da sauƙi, Yaya zai kawo abincin" Da azahar takawa ya tafi sallar juma'a, bayan ya dawo ne Iman suka zo tare da mai sunan baba. A lokacin Mahmud yana zaune, har yayi salla jikin da sauƙi. Iman ta din ga jera masa sannu, mai sunan baba ya ce "Deeja zuba mana abincin tare da shi, ko zai samu ya ci da yawa". "Cikina dai babu daɗi, kar a ɗura mini abinci da yawa". Mai sunan baba ya yi murmushi, ya ajiye abincin a kan gadon, ya ce "Ko a baki zan din ga baka ne? Na iya ɗura ka tambayi deeja ka ji" Iman ta sunkuyar kai, saboda ammi na wurin a zaune da nusaiba. Takawa kuwa ya cewa ruma ta tashi ya mayar da ita idan sun gama cin abincin. Iman sai tsokanar ruma take yi, wai yau abun ɓoye ya fito fili, sabir zai yi ƙani. Ta din ga tura baki, tana harar su. Ko da suka je gida gaba ɗaya takawa ya hau yi wa rumaisa faɗa. "Why are you making things complicated rumaisa?" Cikin rashin fahimta ta ce "As how?" "Ni da ke idan kin gaya mini abu ina yarda da ke, sauran mutanen fa? maganganu sun fara yawo, mahmud ya daki Jabir ya rufe shi ba wanda ya san dalili, mahaifiyarsa ta je an ƙi sakin sa an ce sai mahmud ya je. Kin ce Samha na asiri, a dalilinki na daketa, komai ya hargitse na ma rasa ya zan yi, wambai ya ce lallai in zo da ni da ke, kun hargitsa al'amura, babu wanda ya san me ku ke ciki, kina ɓoye mini wasu abubuwan" "Wait" tayi maganar tana ɗaga masa hannu. "Duk cikin wannan maganganun naka, marin Samhan da ka yi ne ya fi baka haushi kenan? To sai ka koma ka bata haƙuri ai. Ka san dai ba zan yi mata ƙarya ba, tun da lokacin da na zo gidanka ba uwar abun da na sani, balle in san an yi maka wani asiri baka da lafiya, ko in yi wa Samha ƙarya. Kuma ba wambai ba ko gaban waye idan na je ina da gaskiya kuma zan faɗeta. Ta ƙarasa ta saka mukulli, ta buɗe wata wardrobe, ta ɗaukko wata Viva bag, cike da takaici ta watsa masa. Ta ce "Ga kaɗan daga binne-binnen da aka yi a hanani zama, daga ni har kai, da yake Allah ba azzalumin sarki bane, duk in da nake rayuwa in dai da sihiri, sai na sani. Ka duba a ciki har da abun da Samha ta yi, ta saka aka sanya a cikin katifarka da tawa, banda abun da aka binne" Jikin takwa yayi sanyi, tsigar jikinsa ta tashi, saboda uban tarkacen da suka zubo daga cikin ledar, sai uban wari suke, ƙoƙarin rumaisa ya gani, da ta iya ajiye wannan tarkacen a ɗakinta. "Kuma ka sani ban ɓallo ruwa ba tukuna, dan wallahi abubuwan da zan faɗa a gaban wamban nan da yawa, dan sai dai ka sake ni ko a kashe ni, dan Jamil shi ne mutumin da anty aisha ta gaya mini ta gayawa cewar ta zo kano, za ta je dubiya. Kuma lambar ƴan bindiga suka kira, suka sanar da cewa ta rasu, na haddace ta, Yasir yayi tracking ɗin ta, Jamil ne, kuma shi ne yake haɗa kai da wakili yake ko waliyyi oho muku dai. Kuma duk abun da na faɗa ina da cikakkiyar hujjata, kuma ba wanda ya isa ya hana ni magana" A gigice cikin tsawa ya ce "Me ki ke nufi rumaisa? Me ki ke faɗa ne? Jamil fa ki ka ce" "Malam sake ni, ba gaya maka nayi dan ka yarda ba, amma ko ka so ko ka ƙi, Jamil ne ya bayar da bayanan da aka sace anty aisha, kuma har da shi aka je aka ɗauki gawarta, duk da a cikin kaya yake ya rufe fuskarsa, amma na gane shi" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un " ya din ga maimaitawa jikinsa yana rawa. Banza ruma tayi masa, ta fice daga ɗakin ta bar shi. Wata irin rawa jikin Adam yake yi, yana fatan Allah ya sa abun da ruma ta faɗa ba gaskiya bane ba. Jikinsa yana rawa, ya ɗaukko wayarsa da take vibrating, Sunan Bashir ya gani, ya ɗaga amma ya kasa magana. "Adam, maganar madam fa ta zama gaskiya, Wakili su ne Smoke, kuma ba su kaɗai ba ne ba, manyan ƙusoshin ƙasar nan SMOKE! Sai dai magana mara daɗi, DSS fa na Kano sun je Abuja sun kama Jamil, an kama shi da laifin fitar da sirrin hukumar ga marasa gaskiya, yanzu haka yana tsare" Ba tare da ya katse wayar ba, ya ajiyeta yana jin yadda kansa yake wata irin bugawa, zuciyarsa sai harbawa take yi da saurin gaske. Ruma ta dawo ɗakin ta tarar da shi ya haɗa gumi, sai tsuma yake yi. "Ka tashi ka bar mini ɗakina, ɗakin maƙaryaciya mai haddasa muku husuma a dangi, ka je ka bawa wadda ka ke so haƙuri, kuma ka kwashe wannan kayan tsubbun da aka binne mini, duk saboda kai". Kallonta yake yana sake jinjina yadda abubuwa suke gudana, tashi yayi ya bar mata wayarsa da kayan tsubbun, ya fice ya bar ɗakin. Ta kwashe kayan ta ɓoye, ta ɗauki wayar sa, ta buɗe pin ɗin, ta kira Iman. Iman na ɗagawa ta ce "Kun tafi ne?" "Eh, amma yanzu su mama suka shiga" Ta ce "Ok". Ta kira wayar mama, mama ta ɗaga "Mama ya jikin daddy, ya tashi kuwa?". "Eh, a zaune muka tarar da shi, jikinsa da sauƙi sosai". "Mama dan Allah ba shi wayar" Mama ta miƙawa Mahmud, da yake zaune yana hira da su mama da Ammi. "Hello daughter" "Jikin ka da sauƙi daddy?" Ya ce "Sosai Alhamdilillah" "Get ready, an ce gobe in Allah ya kaimu za a kawo ƙarshen wannan lamarin, zamu haɗu a gaban wambai, kuma ba zamu yi magana ba sai a gaban ƴan sanda" Ya ce "Am ready in sha Allah, ku yi magana da su Yasir, dama komai na sa ya zama ready, zai tafi Canada, next week" "Shikenan daddy, na gode sosai". Hankali kwance ruma ta sha baccinta yau, sai ƙarfe uku da rabi ta tashi, ta na sallar dare, tana roƙon Allah ya basu sa'a. Shiru tayi tana tunani, lokacin da take mamakin yadda mama ke katse bacci tana sallar dare, yau sai ga abun ya zo kanta. Takawa kuwa bacci ya gagari idonsa, yana sake nanata Kasancewar Jamil a cikin mummunan aikin nan, to idan rumaisa ƙarya take yi, binciken su Jamil da kama shi da aka yi fa?. Ammi kuwa ta wani fannin a iya cewa, rashin lafiyar Mahmud gaba ta kaita, domin kuwa sun fi ƙarfe biyu suna hira. Ta yi iya ƙoƙarin mantawa da abubuwan da suka faru a baya, ya bata labarin makaranta, da yadda ya samu kansa a wurin aiki, amma a cikin hirar ya din ga haɗawa da abubuwan alkhairin Mummy. Sai dai ga marasa gaskiya, ciki ya ɗuri ruwa, Samha ta din ga kiran wayar baba uwani, dan tabattar da abun da rumaisa ta faɗa a bakinta, amma wayarta ba ta shiga. Gashi ba tare da saninta ba, maman su, ta je ta sanarwa da turaki komai, cikin bala'i da tashin hankali, kuma ta kira wambai ta gaya masa, cewar takawa ya mari Samha, kuma ya ce a kan matarsa ba abun da ba zai yi ba, sai dai zumuncin ya watse. Ga gefe guda, Hajiya Lubabatu ta kai ƙarar Mahmud, wai Mummy ta saka shi, ya yi wa Jabir duka, ya saka an rufe shi, ba tare da ta san wani station ɗin aka kai shi ba. Samha ta san muddin aka yi zaman nan, to fa kashin su ya bushe, domin wannan matar ta takawa, ba mutunci ne da ita ba. Suna tsaka da wannan bala'in, maman ta lura da wuni guda, yau Jamil bai kira su ba, sun kira shi amma ba ta shiga, hakan ya ƙara dugunzuma hankalinsu. Dan haka marasa gaskiya, bacci sai rabi da rabi. *** Da safe ruma ko ta kan takawa ba ta bi ba, ta shiga sabgoginta, Asiya ta tayata gyara ɗaki, saboda yadda cikinta ya fara tsufa, duk da ba a gani, sai ta saka kaya ƙanana. "Rumaisa" ta ji ya kira sunanta. "Ba zamu Asibiti ba?" "Sai ka dawo, kar na je na kuma ɓata muku zumunci" "Kiyi haƙuri, na rasa yadda zan yi ne" Ta ce "Ni ba zani ba" "Dan Allah " Ruma ta ce "Ba fa zani ba, idan an shirya zama a gaban Wamban, na je kuma ba zan yi magana ba, sai da ƴan sanda a wurin". Juyin duniya ruma ta ce ba in da za ta je. Ya ƙyaleta ya fita tafi. Ya tarar da ammi, tana bawa Mahmud abinci a baki. Takawa ya samu wuri ya zauna, yayi shiru bai ce komai ba. Ammi ta ce "Takawa, ya dai?" "Bakomai" zata sake magana Mummy ta shigo, Mahmud ya ce "Mummy sai yanzu ko?" "Eh ai jiya korata aka yi, aka nuna bani na haifeka ba, ba dan kai ne ba ba abun da zai dawo da ni". Ya ce "Allah ya baki haƙuri, a cewa likita ya zo ya sallame ni, saboda ayi ta ƙare a yau" Mummy ba wanda ta kula sai mahmud, suma ba su kulata ba. "Mahmud ina ka kai Jamil ne? Kana a wannan yanayin zaka je wani wuri? Ka sa matar nan ta tayar wa da mutane hankali, sai bala'i take yi. Ta shafa mini kashin kaji, wai ni na saka ka dake shi ka kulle shi. Ga wani zancen ma wai ko an kama Jamil gaske ne ko ƙarya oho" Ammi ta ce "Kenan maganar ruma gaskiya ce" "Ba da ke nake ba, da ɗana nake malama" Mummy ta yi maganar gatse-gatse ga giwa. Ammi ta ce "Allah ya baki haƙuri" *** Katafaren falon ya cika ga Wambai, ga turaki da wasu manya daga masarautar kano. Ammi ta hallara, ga Mahmud dan ko gama warwarewa bai yi ba. Aka jima sai ga rumaisa da takawa, Bashir jami'an tsaro da wasu daga cikin yayyen rumaisa, ga Samha a wurin da mahaifiyar ta, ga Hajiya Lubabatu da duk wanda yakamata su halarci zaman. Gaban Samha sai dukan uku-uku yake yi, dan bata san mai rumaisan za ta kwatsa ba. Wambai ya ce "Su kuma waɗan nan lafiya?" Yayi maganar yana nuna jami'an tsaro, da suka shigo da jabir, a wahale. Bashir ya ce "Ranka ya daɗe, zuwanmu wannan zaman yana da matuƙar muhimmanci, zaka ji dalilin zuwanmu in sha Allah. Zuwanmu nan ayi tattaunawar da mu, sai ya fi sirri, saboda wasu abubuwan da za a bayyana, akwai kunya ace wasu laifukan daga gidan girma da daraja suka fito" Adam ya ce "Allah ya taimake ka, wannan ita ce rumaisa matata kamar yadda ka sani, waɗan nan kuma ƴan uwanta ne, wannan kuma abokan aikina ne" Wambai ya kalli rumaisa ya ce "Ke! Ke ce mai haddasa mana husuma da tashin hankali a cikin family ko? Kafin ki zo lafiya lau mu ke zaune, amma daga zuwanki kin hargitsa komai, ki ce wancan yana asiri, ki ce wannan baya son wannan saboda me?" Ya fara yi wa ruma faɗa, tayi shiru ta sunkuyar da kai. Turaki ya ce "Ina ganin, a fara bari mu ji ta bakinta tukuna ranka ya daɗe, kar a yanke mata hukunci kai tsaye" Wambai ya kalleta ya ce muna saurarenki. Ruma ta ƙulu, basarwa kawai ta yi, ta haɗiye wani abu mai ɗaci sannan ta ce "Kafin na ce komai, zan fara da bawa babana haƙuri a kan abubuwan da zasu fito daga bakina, duk da ya san wasu, na san bai san wasu ba. Ina neman afuwarka babana mai girma turakin kano" Turaki yayi murmushi mai ciwo, sannan ya ce "Kar ki damu yarinyar kirki, kamar yadda na riƙe miki alƙawari a baya, ina umartar ki da ki faɗi komai, dan fita daga zargi. Ayshercool. 08081012143 08081012143 Rumaisa ta ja numfashi, sannan ta fito da wata waya, duk ta sha jiki, screen ɗin ma duk ya tsage, ta ce "Wannan wayar, ita ta fara haɗani da takawa, kafin ƙaddara ta sake haɗa mu a karo na biyu. Silar haɗuwarmu na farko wannan abu ne da ya shafi rayuwarmu ni da shi, bai shafi abubuwan da suke faruwa a yanzu ba" Ta ɗan yi shiru sannan ta cigaba da cewa, "Kamar yadda wasu suka sani, yayyena maza ne, nice ƙarama da duk wanda ya sanni, aka yi mini shaidar rashin ji. Wannan wayar na ɗauke da wasu abubuwa da ka iya taimakawa jami'an tsaro, saboda a rashin ji na, bani da tsoro, kuma cikin ikon Allah ranar da mu ka tafi kai ziyara dangin mahaifina, muka haɗa mota da ƴan bindiga. A cikin wayar akwai hotunan wurare da abubuwa da na yi ta ɗauka, ciki har da jakar bullet mai ɗauke da wasu lambobi, da sunan SMOKE. A rashin ji na, na tattauna da ƴan bindigar, har shugaban su yake ce mini, ƙasa ta san da zaman su, dan kuwa akwai kason su, a kasafin kuɗi da ake duk shekara. Kasancewar a lokacin bakomai nake ganewa ba, amma na fuskanci wasu abubuwan. Zuwana garin su babana, wanda ƴan bindiga kusan suke mulkar garin, nan ma nayi wata tattaunawar da wani dattijo da aka ƙona rigar su, sai shi kaɗai, wanda shima yana da alaƙa da ƴan ta'adda. Daga nan har zuwa lokacin da aka yi garkuwa da ni, abubuwan dai tamkar a mafarki, duk yadda za a bawa mutum labarin yadda abun yake, sai ya je ya gani. Na sha baƙar wahala saboda ina da taurin kai da rashin jin magana, na daku kamar ba mutum ba, saboda ban daina rashin kunya ba. Kwatsam! Aka kawo matar da silarta abubuwa da dama suka faru, mace da tsohon ciki, ta din ga magiyar a bari ta tafi, ko dan cikin jikinta, aka ce a kula wannan ajiyar wakili ce". Ɗiff ɗakin yayi, Wambai ya ce "waye wakili, wane waikilin tukuna". Turaki ya ce "A daina katse ta, mu bari ta kammala tukuna". Rumaisa ta ɗora da cewa "Lokacin da ta zo ina tsaka da rashin lafiya, halin da take ciki bai dameta ba kamar ni, ta kula da ni sosai da sosai, sai dai wasu lokutan sai tayi ta kuka, idan na bata haƙuri sai ta ce; ba sace ta da aka yi ne dameta ba, mijinta, ba yadda bai yi da ita ta fasa tafiya ba amma taƙi, sai kuma sanya hannun ɗan uwanta a wurin saceta. Ta bani labarin mijinta, iyayensa, yadda suke rayuwarsu, da kuma irin rayuwar da tayi a nasu gidan. Ta gaya mini mahaifinta ya saka sunanta a kadararsa, kuma wasu kuɗinsa na shiga account ɗin ta, saboda ita bai taɓa mallaka mata wata kadara ba, saɓanin ƴan uwanta, da kowa yana da wani muhimmin abu da ya bashi. Ta gaya mini matar mahaifin ta da yayyenta, sun uzzura mata sosai a kan hakan, kuma babu wanda ya san da zuwanta Nigeria, sai yayanta da ta gayawa, ta sanar masa ga ranar da zata je dubiya.... "Ƙarya ne, me ki ke nufi, Jamil ne ya sanya aka yi garkuwa da aisha, wallahi ƙarya ki ke yi, ni za a yi wa sharri, a cuci ɗa na a ɓata mana suna" Wambai ya ɗagawa babar su Jamil hannu, ya dubi ruma ya ce "Wani tabbaci zaki bamu a kan haka, ta yaya zamu yarda da ke?". "Na yi wa anty aisha alƙwarurruka, bayan ta ce mini ta bani amanar mijinta da ɗan ta, duk da ƙarancin shekaruna, na fahimci abubuwa da dama a labarin da ta gaya mini" rumaisa ta basu labarin komai, har kan mutuwar aisha. Ta kalli Abdallah ta ce "Bismillah" Abdallah ya dawo tsakiya, ya zauna da kayan zanensa. Ruma ta ce "Wannan yayana ne, kuma ƙwararre ne wurin iya zana abubuwa, da shi nake koyi, ya sanya nima na iya zane-zane, amma kasancewata ƴar koyo, zan ba shi damar ya zana wani abu, kar ace na yi son zuciya ko sharri nake son yi wa wani, yana daga in da yake zaune, zan siffanta masa abun da zai zana ɗin, Abdallah ba ya nan aka sace ni, nikaɗai aka sace, dan haka you should be good in judgment" Kowa yayi shiru ya zuba musu ido, sannu a hankali take siffanta masa abubuwa yana zanawa, bai ja lokaci ba ya kammala zanen ya miƙa musu takardar da yayi zanen a kan ta. Ta siffanta masa Mutanen da suka je suka ɗauki gawar aisha ne, da motarsu, da yanayin da suka ɗauki gawar. A yadda rumaisa ta suffanta masa ya zana, Jamil ne a gaba cikin kayan ppe, amma yanayin tsayuwar da sashin da aka iya gani na fuskar sa, zai tabbatar maka da shi ne, idan har ka san shi. A lokacin takawa ya tuna a tsukin lokacin yayi ta fama da faɗuwar gaba, da fita hayyaci, kuma Jamil yayi balagro a lokacin. Mahaifiyarsa ta cigaba da bala'i, da iƙirarin wannan shegantakar banza ce ba Jamil ba ne ba. Mahmud ya ce "Allah ya baku yawan rai, muna da shaida ta gaba, ban sani ba kafin ni, ko ta gaya wa wani, amma ta same ni da maganar, kuma da ni da wasu daga cikin ƴan uwanta maza muka yi aikin nan. Akwai lambar waya da ta bani, lokacin tana magiyar a kai aisha asibiti kan ta rasu, ita ce lambar da aka kira, na bayar an yi tracking ɗin ta, haka zalika ɗan uwanta Yasir yayi tracking ɗin ta, an daina amfani da layin, amma Jamil ne yayi register da layin, Yasir na da tracking result ɗin sa, ni ma ina da nawa da police suka yi" Wani daga cikin ƴan sandan ya ce "Amma wannan ai aikin police ne, mu yakamata ace mun yi shi, ko shi Adam tun da jami'in tsaro ne". "Ban ji na yarda da kowa ba da zan iya ɗaukar shaidu, masu muhimmanci na bawa ƴan sanda ba, dan a lokacin na ji takaicin ace ƙasata da jami'an tsaro amma aka kasa kuɓutar da ni, daga hannun ƴan bindiga, kuma ƴan bindiga da kansu, suka tabbatar mana da kun san da kune ku ke sauƙaƙa musu aiki, ku jami'an tsaro. Takawa kuma ban gaya masa komai ba, saboda a wancan lokacin yana cikin damuwa da tashin hankali ne, da kuma fuskantar matsin lamba daga mutane, a yadda yake a zuciye zai iya ɓata komai a wannan lokacin. Maganar ina ƙoƙarin ɓata zumunci ta hanyar haɗa husuma kuma, ina da shaida babu wanda na yi wa sharri, ranka ya daɗe wannan ledar ta gabana, cike take da kayan tsubbu da na sanya baba uwani tsohuwar hadimar ammi tonewa, kuma nayi amfani da wayar ɗaya daga cikin ma'aikatana, na naɗi duk abubuwan da aka saka ta yi mini, suma suna cikin wannan wayar na tura a ciki". Adam ya tashi jiki a matuƙar sanyaye, ya ɗauki excuse ya fita amsa waya. Tun da suka shiga ake kiran wayar, sai dai da ya duba ya ga private number na. A yadda ruma suka tsara da Mahmud, shi ne zai faɗi abubuwan da suka shafi ɓangaren Mummy, kutungwilar da take shiryawa amma ya kasa. Turaki ya sunkuyar da kai zuciyarsa na yi masa raɗaɗi, saboda abun duniya yana ciki ɗaya da aisha, ubansu ɗaya, ya sanya aka saceta, kuma yake ta ƙoƙarin sanyawa a ɗora zargi a kan Adam, Adam ɗin da ya kasance abokinsa ɗan uwansa da suka tashi tare. Kuka matar turaki take yi, ta ce "Ita haryanzu ba ta yadda da cewa Jamil zai iya aikata mummunan abu irin haka ba sharri ake yi masa". Bashir ya ce "Hajiya sai dai ki yi haƙuri, domin kuwa jami'anmu sun riga sun kama shi ma" Mahmud kuwa ya dubi Jabir, sannan ya mayar da idonsa kan Hajiya Lubabatu ya ce "In faɗi me Jabir yayi, ko kuma in bari ku faɗa da kanku?" Suka yi tsit babu wanda yayi magana, Mahmud ya ce "Dole ka cigaba da zama a hannun 'yan sanda su kammala bincike" Wambai ya ce lallai a nemo masa baba uwani duk in da take, gaba ɗaya falon ya hargitse da hayaniya. Rumaisa ta ce "Babban roƙon da zan yi muku shi ne, kar wanda yayi ƙoƙarin yin wani abu a kan wakili, saboda nikaɗai ce shaida a kansa, sai dai in Jamil ne ya yi magana a kan sa, idan ba haka ba". Bashir ya ce "Haka ne, amma ban taɓa tsammanin wakili zai kai haka ba, saboda tsamar da ke tsakanin sa da Adam ba" Adam ya ɗaga wayar tare da yin sallama "Na san ko ban yi magana ba, ka san da wanda ka ke magana, Senator mai wakili ne. Ina tayaka da ƴan team ɗin ka murnar gano suwaye SMOKE. Sai dai nikaɗai ka sani a SMOKE, amma ka sani gano smoke ba shi da wani amfani, saboda su kansu wanda ka ke tunanin zasu ɗaukar maka matakin suna cikin SMOKE. ministan man fetur ke da shiyyar satar mai, Ɓangaren tsaro suna da kamasho a kasafin da ake yi, da wasu manyan mutane a ƙasar nan. Talakawan da ka ke yi domin su, basu isa su yi maka komai ba, duk wata shaida da kake tunanin kana da ita a kanmu, akwai gaɓar da idan aka kai, kai ne zaka kwana a ciki, dan na san baka isa ka yi jayayya da shugabannin rundunar tsaro ba, ba ka da wata shaida a kan sa. Dan haka kai zaka kwana a ciki, duk yaranmu da ku ka samu ku ka kama, babu wanda ya san suwaye SMOKE, kai kaɗai ka yi nasarar gano suwaye, ɗan uwanka Jamil yaron Khalifa ne, tare da shi suka yi aiki, sai dai shima bai san mune SMOKE ba, mun yi amfani da sace matarka, wurin ɗauke hankalin ka daga kanmu, kuma cikin ikon Allah ta haihu ta rasa ranta. Abu ɗaya zuwa biyu nake son gaya maka. Ka bar al'amarin nan a iya haka, idan ba haka ba zaka yi ta ranka, ko kuma ran matarka da ɗanka, dan kuwa  ita ce duk sanadin komai, dan kuwa duk motsin ku, da duk abun da take yi, muna samun labari ta ɓangaren Jamil. Dan haka sai ka zaɓi ɗaya, fito na fito da masu ƙasa, ko kuma ka rasa rayuwarka da na matarka, dan ka san ba abu ne mai wahala ba. Sai dai fa ka yi haƙuri, domin kuwa rayuwar matarka ta salwanta kamar ko wani karabutin ɗan ƙasa, duk da kasancewar ka mai kaki, kuma jinin babbar masarauta, ire-iren yaranmu ne kisan su baya tafiya a banza. Kuma duk wani abu da zai faru Jamil ba zai taɓa furta sunana ko na ɗa na ba. Dan haka gara ka watsar da duk wani yinƙurinka, ka tattala abun da yayi saura a rayuwarka, kan mu gama ɗiaɗaita ku" ya katse wayar. Duk da hatsaniyar da ta kaure a falon, yanayin da takawa ya shigo, ya sanya kowa yin shiru, wani irin gumi yake yi, jikinsa yana tsuma, kuma aka rasa mai tambayarsa meyafaru, kowa ya zuba masa ido. Ruma ce ta miƙe tsaye, ta ce "Papa lafiya kuwa?" Gabanta ya ƙarasa, jiki a matuƙar sanyaye ya zube a kan gwiwoyinsa ya furta "Na gaza, dama kin gaya mini, na gaza rumaisa ba laifina bane, na yi iya yina, abun ya fi ƙarfin yadda nake tunani, na barwa Allah, tun da a cikin gidanmu ma aka kware mini baya, ba ni da saurin ƙwarin gwiwa. Da izzar da tawa da sarautar tawa da komai na zube su a kan gwiwoyina, na gode rumaisa, na gode. Ke alkhairi ce ga rayuwata da ahalina, wataƙila ba dan ke ba, ba zan gane bara gurbin da suke rayuwata ba" Hawaye yake zubarwa kamar ƙaramin yaro, cike da ƙunar zuciya. Lallai faɗa da aljani ba daɗi, shiya san bai isa cigaba da fito na fito da wannan mutanen ba, in dai a Nigeria ne, mutane sun san ta'addancin Smoke, sai dai basu san suwaye ba, kuma wani abun shaidar rumaisa kawai ba zata wadatar ba, hakazalika da rayuwar rumaisa ta salwanta gara ko menene ya haƙura da shi, yarinyar tayi sacrificing alot". Rumaisa ta durƙusa ta ce "Papa dan Allah ka tashi, ka sakani a duhu, ni ban gane me ka ke nufi ba, ka tashi dan Allah, a gaban mutane ne fa" Mahmud ne ya tashi ya kama Adam, ya miƙar da shi tsaye, ya ja hannunsa ya cewa rumaisa su tafi. Ƴan sanda suka tattara duk wasu bayanai da suka kamata, wanda rumaisa ta bayar, da zanen Abdallah da aikin da Yasir yayi, Bashir ya karɓe ya ce sai sun kammala na su binciken tukuna, zasu gani idan da yiwuwar ba wa ƴan sanda. Wambai kansa ya girgiza da jin lamarin, tausayin ɗan uwansa turaki ya kama shi. Sosai babar Jamil ke kuka, tana cewa turaki ya saka baki, ya ƙaryata abun da suka faɗa, ya sanya a saki Jamil. Wambai yayi mata tsawa, ya ce su tashi su tafi sai ya sake nemansu. Mummy godiya ta yi wa Allah, da ba a faɗi komai a kanta ba, Hajiya Lubabatu ta zube tana yi wa wambai magiya ita ma a kan a taimaka a sanya baki, a saki Jabir. Mummy ta ce "Wallahi ba ta isa ba, ba zai lalata mata ƴa ya ci bulus ba" jin abubuwa babu Allah a ciki, dagulewar lamuran yayi yawa, ya sanya wambai cewa su tafi su je su ƙarata a wurin ƴan sanda. Sai da ya rage daga shi sai turaki, sannan turaki ya samu zubar da hawaye, ya daɗe matar nan tana citar da shi da Aisha, amma ba ya iya ɗaukar mataki, dama tun a farko rumaisa ta gaya masa komai, sai dai bai tabattar ba sai a yanzu. Wambai ya dafa kafaɗarsa ya ce "Ina neman afuwarka ɗan uwana, na rashin tsayawa in fuskance ka a abubuwa da dama. Dama na san biyayya ce ta sanya ka auri Sa'adatu, sai dai wannan abu ba kai kaɗai ya shafa ba, zan yi iya ƙoƙarin ganin cewa maganar nan ba ta fita ba" "Kar ka yi haka, ko kayi hakan, ko ba kayi hakan ba, dole sai maganar ta fita, Allah ya jiƙan fulani da mahaifiyarta, rumaisa kuma Allah ya yi mata kyakykyawan tukuici da ita da iyayenta. Mahmud kai tsaye har gida ya kai Adam da rumaisa. Adam na kwance a jikin rumaisa kamar uwa da ɗa, sai aikin rarrashin sa take yi, tana bashi haƙuri. "Rumaisa, ni wakili yake gayawa sai in dai in yi haƙuri, ran matata ya salwanta a banza, saboda wautata da rashin hankali, kuma wai ba wani abu da zan iya yi a kai" "Ban gaya maka ba? Na ce zaka iya bincike ne kawai, amma in dai a ƙasar nan ne, kar ka yi tsammanin samun adalci, mu bar wa Allah papa, you try your best, Allah shaida ne" Mahmud ya ce "Takawa dan Allah ka daina kukan nan haka, kar ka tayar mata da hankali, ga ciki tana fama da shi". "Mahmud baka san me nake a zuciyata ba, ba zaka gane ba" "Na sani mana, saboda sauƙaƙa maka raɗaɗin da ni da rumaisa muka yi aiki tare dan sauƙaƙa maka aiki. Ina mai baku haƙurin rashin exposing Mummy, amma ita ma very soon in sha Allah, ka yi haƙuri dan Allah" Cikin kuka ya sake cewa "Jamil fa mahmud, a ɗakin Ammi muka yi wasa tare muka faɗi muka tashi, amma ni Jamil zai din ga yi wa wannan cin dunduniyar? Me nayi masa? An kashe mini mata kuma ya cigaba da bibiyata da ƙoƙarin ɗora mini sharri? Me nayi masa ne?" "Baka yi masa komai ba Papa, hassadar ka fi shi komai ne kawai da kwaɗayin abun duniya ya sanya shi haɗa kai da maƙiyanka, gashi wanda ka ke yi wa kallon maƙiyin, shi ne ya taimake ka, duk lalacewar ɗan uwa naka ne papa". "Na gode mimi na gode sosai" "Dan Allah ka daina yi mini wannan godiyar, ni ba abun da na yi " Mahmud ya miƙe ya ce "Daughter, ki kula mini da shi sosai dan Allah, zan je gida wurin ammi, na san tana cikin damuwa ita ma" Ruma ta ce "Wait, wai ba daga gadon asibiti ka taso ba?" "Rabu da ni na warware " "Amma ka yadda maman jabir tayi maka wani abu?" Ya ce "Na yarda, Kamar yadda muka saka Yasir bibiyar wayar Mummy, ya kunna mini wayar da Mummy tayi da Hajiya Lubabatu. Na karɓi duk wata shaida ta hannunsa, jibi in Allah ya kaimu zai tafi wurin Anty laila, kar ma a samu wata matsala saboda aikin da ya yi mana" Ruma ta ce "When are you exposing her?" "Soon in sha Allah" "Idan ba zaka yi ba, allow me to do it" "I will in sha Allah" ya juya ya fita. Haka ruma tayi ta aikin rarrashin Adam, dan abun ya dake shi sosai da sosai, duk iya tunaninsa bai ga ta ina zai iya jayayya da SMOKE ba. Kuma dolensa ya haƙura da cigaba da duk wani yinƙuri a kan garkuwa da aisha, saboda rayuwar rumaisa. *** Kwanaki uku kenan, gidajen sarautar suka shiga ɗimbin tashin hankali, komai ya damalmale, ba kama hannun yaro, aka gaza samo bakin zaren abubuwan da suka riga suka dagule, Kodayake ba komai ne zai gyaru ba, kasancewar wata ɓarakar ta samo asali ne tun shekarun da suka gabata, ba tare da an mayar da hankali an gyara su ba. Kodaye rumaisa ta kawo gagarumin cigaba da kuma gyara wasu abubuwan. Ba tare da wani cikakken shiri ba, Mahmud ya ce lallai sai Yasir ya tafi canada, Yasir ya so ayi bikin yaya Abubakar yana nan, amma ba dama, aikuwa sai da yayi kuka saboda rabuwa da mama da ƴan uwansa. Mahmud kuma ya ƙarfafa yin hakan ne, kar wani abu ya samu Yasir, saboda aikin da yayi musu, dan a wata fuskar laifi ne abun da ya aikata ɗin, kutse da satar bayanan mutane ba tare da izinin su ba. Haka ya tsallaka ya tafi ya bar Nigeria. Abdallah kuwa Bashir ya ce sai sun tafi da shi Abuja, mama ta tashi hankalinta ganin kamar ana yi wa yaranta ɗauki ɗaya-ɗaya, amma ya bata tabbacin babu wata damuwa, a kan Jamil ne ita ma rumaisa Adam ne zai wakilce ta, saboda tsohon cikinta. Ranar da zasu tafi Abuja, takawa yayi ta rarrashin ruma, tare da bata tabbacin, Abdallah zai dawo lafiya, tun da har da shi zasu tafi. Rumaisa suna ta shirin fara Waec, sai dai fa nauyin ciki ya hanata sukuni sosai, tun da ta dawo daga makaranta, mararta take yi mata ciwo da ƙafafuwanta, kuma takawa ya riga ya tafi, dama ya ce mata idan ba zata iya zaman gidan ba, ta tafi gida wurin mama ko ammi. Jin ciwo yaƙi ƙarewa, ta kira Usman a waya, ta ce ya zo zata mutu. Ya je ya tarar da ita duk a firgice, ta bashi mukullin ɗaya daga motocin takawa, ta ce ya kaita asibiti. Suna tafe a hanya ya ce "Ko dai haihuwa zaki yi?" "Edd ɗin bai cika ba fa" Ya ce "Ikon Allah, muna zaune yarinyar da muka goya, muka yi wa wanka za ta haihu, haryanzu muna gararamba, bakomai akwai lokaci" Bakin rumaisa bai mutu ba, sai da aka ce mata haihuwa ce a asibiti, ita dai ta san lokacin haihuwa da saura, aka ce usman ya je ya kwaso kayanta. Maimakon ya kira mama a waya, ko ammi, kawai sai ya kira Aliyu da Huzaifa, sannan ya ƙarasa gidanta, ya ɗaukko akwatin da ta kwatanta masa, dan tuni takawa ya gama sayen komai na jariri. Mamaki ya kama nurses ɗin, suka ce babu wata mace wadda za ta zauna da ita duk sai maza. Huzaifa ya ce "Hajiya gidanmu ita kaɗai ce mace, babarmu kuma tsohuwa ce ba ta da cikakkiyar lafiya, duk abun da mata zasu yi, mu ma zamu yi" Nurse ɗin ta ce "A dai duba dangi a samo wata" Usman ya ce "Hajjaju, wallahi zamu iya komai, ki ƙyalemu kawai". "To ina mijinta?" Aliyu ya ce "Tafiya ce ta kama shi ɗazu" Ta jinjina kai ta ce "Lallai ƘANWAR MAZA" Rumaisa ta sare da al'amarin, saboda tun da mama ta haifeta ba ta taɓa jin masifaffen ciwo kamar wannan ba. Mai sunan baba kuwa, ganin hankalin Adam yayi wani wurin, mahmud kuma ya warware, ya sanya ya yi wa mahmud zancen, mahmud ya din ga murna, ya ce dole su je Lagos tare, dan tabattar da wannan lamari, dan haka ya ce zai yi musu booking Flight su je, su yi abun da za su yi, saboda su koma bakin aiki. Mai sunan baba ya kira Huzaifa a waya, yana masa faɗan duk suna ina, gida ba kowa sai mama itakaɗai a gidan. Mama ta ce "To yarinya ce ni, da lallai sai sun zauna a gida?". Huzaifa ya gaya masa in suka tafi, ba tare da ya gaya wa mama abun da ake ciki ba, ya tafi asibitin. Ƙarshe sai da suka cika asibitin, Abdallah da Yasir ne kawai babu. Gaba ɗaya suka zama abun kallo a asibitin, wai sun kawo ƙanwarsu haihuwa a asibiti. Ruma ba ta haihu ba sai bayan magariba, babyn pre term ne, watanni bakwai da sati biyu. Nurse ta fito ta ce "Kun ga ga mahaifa, ga kayan jini, dan girman Allah ku nemo mace" "Sai kuma ki yi, karɓar haihuwar ma da kin matsa sai mu karɓa, ko abun da ya fi kayan jini ne zamu gyara, babarmu tsohuwa ce, bamu da ƴar uwa mace, dangi ba kowa ke son ka katse masa hidimomin sa ba, dan haka ba jini ba, ko menene zamu iya" Mai sunan baba ya ce "Ina jaririn?". "Nursery zamu kai shi, sa an saka shi a kwalba" Sai da suka jira aka basu damar shiga su ga ruma, tana kwance kai da ganin idonta ka san an sha gwagwarmaya. Nurses suka ce a kawo mata abinci, sai a lokacin mai sunan baba ya tafi gida, ya gaya wa Iman, ruma ce ta haihu. Mamaki ne ya kamata, dan washegarin taron nan sun haɗu a gidan ammi, ta ce mata haihuwarta da saura. Nan da nan ta yi girki, jiki na rawa tare da mamakin haihuwar ruma, ta kira ammi ta sanar mata. Ammi ta ce "Ba dai rumaisa ba, takawa ya ce da saura ai" "Wallahi ammi da gaske nake, yanzu yaya umar ya shigo ya gaya mini". Nan da nan aka cika asibitin, ƴan barka, sai dai ba ganin jariri, rumaisa kuma ba baki, duk wanda yayi mata sannu, sai dai ta jinjina kai kawai, amma ta san halin tashin hankalin da ta shiga a haihuwar. Mama ta kalli rumaisa ta ce "In ce dai ta bakin ki ka haifo ɗan naki, yau mata sun ga ta in da ake haihuwa" ruma tayi murmushi kawai. Da ƙyar ta iya cin abincin ma, ta fara cewa ita a kawo mata ɗan ta fa, saboda lokacin da ta haife shi, tana gani ana ta fama, ya ƙi yin kuka yadda yakamata. Abdallah ya sha tambaya a babbar headquarter Dss ta Abuja, dan sai da aka karɓi zanen aka sa shi sake yin wani, suka yi iya binciken da zasu yi, babu ko shakka Jamil ne, Wanda dama already yana hannunsu, takawa yayi kamar ya gaya musu da sanya hannun wakili, amma tayaya meye hujjarsa? Rumaisa ce kawai ta ji sun ambaci wakili, idan da wanda zai faɗi da sanya hannun wakili, to Jamil ne yakamata ya faɗa. Duk wani report na bincike lokacin ɓatan aisha da suka yi, sai da suka gabatar da shi a wurin hukumar, laifin Jamil ya zama biyu, da na tuhumar fitar da sirrin hukumar, da kuma haɗa baki tare da yin garkuwa da ƙanwarsa, ga kuma ɓatawa Adam suna da yayi. Ko da ana nunawa Jamil zanen nan, da Abdallah yayi, sai da ya zabura, saboda tabbas ya san shi ne. Adam ya ce "Jamil ka tabattar wannan kai ne? Jamil me muka yi maka ni da Aisha? Idan ma wani abun na yi maka, meyasa zai shafi aisha? Ka haɗa kai da wakili ka cutar da ni?" "Adam jin dalilin hakan ba shi da wani amfani a gareka, tun an riga an kama ni, sai ka je ka cigaba da rayuwarka, ka ƙyaleni. A kan me mahaifinmu zai fifita aisha a kanmu? Kuma duk wani abu na cigaba, ko na masarauta sai dai ya sanya ka a ciki alhalin gani. Wallahi da na san yarinyar nan ta gane ni, da ban barta ta rayu ba" Adam yayi murmushi mai ciwo ya ce "Na gode sosai Jamil, sai dai ka sani, duk da ciwon hauka da nake fama, na tsaya ga Allah, shiyasa nake cigaba, kuma na barka da Allah Jamil, Jabir ma har shi da duk wanda ku ka cutar da ni, kamar yadda rumaisa ta faɗa, ta ce in bar ku da Allah, zan ga yadda zai yi da ku, na bar ku da Allah" Takawa suka koma masauki shi da Abdallah, tare da Bashir. Sosai suke bawa Adam baki, tare da bashi ƙwarin gwiwa. A lokacin yake sanar da su abubuwan da wakili ya kira shi ya sanar da shi. Sun girgiza sosai da sosai, Bashir ya ce "A gaskiya na girgiza, dama biri yayi kama da mutum, yadda aka kasa magance wannan Smoke ɗin. Amma ina ga kamar yadda madam ta faɗa, ka yi ƙoƙarin gano wanda suka yi maka maƙarƙashiya, amma hukunta su sai Allah". Ammi ce ta kira Adam a waya, ta sanar da shi rumaisa ta haihu, sai dai yaron an saka shi a kwalba. Adam kansa abun ya ɗaure masa kai, wace irin haihuwa ana zaune ƙalau, ba tare da cikakken lokaci yayi ba. Gashi bai bai gama da abuja ba, amma ya ce dole ya koma kano. Zai bar Abdallah da Bashir ko za a buƙaci wani abun, idan komai ya lafa sai su taho, shi kansa Abdallah abun ya bashi mamaki, a kan ya aka yi rumaisa ta haihu a wannan lokacin. Sai dai cikin ƙudura ta Ubangiji mai kyauta da ƙari, yaron da mimi ta haifa ya koma ga mahaliccinsa cikin dare, dama ana ta fama, yaƙi kuka amma d girmansa ba ka ce bai kai lokacin haihuwa ba. Aka yi shiru ba a gayawa mimin ba sai washegari da safe, aikuwa rumaisa ta dira rigima, ta din ga kuka, tun mama na rarrashinta, sai da ta ƙular da ita, ta fara zaginta. Mama ta ce "Ba zaki rufe mini baki ba?" "Mama baki san me nake ji ba ne" Mama ta ce "Dan ubanki ƴaƴa biyu na binne, da zaki ce ban san me ki ke ji ba". Ammi ta ce "Maman rumaisa ki yi haƙuri, yarinya ce kuma dole za ta ji babu daɗi" Aka naɗo jaririn, aka kawo wa rumaisa, kamarsa ɗaya sak da Adam. Sabir da yake zaune a kusa da rumaisa ya kalleta ya ce "Mimi, baby ya buɗe ido" yayi maganar cikin yarinta. "Boy babynmu ya mutu" Ammi ce ta karɓi jaririn, ana jiran shigowar adam, ayi masa sutura. Ƙarfe tara na dare Adam ya dira, ko gida bai je ba, kai tsaye asibiti ya taho, ammi tuni ta sanar masa da rasuwar yaran, dan haka hankali a tashe ya ƙarasa asibitin jikinsa duk a sanyaye. Ya tarar tuni Ammi na can ita da nusaiba, mama tana wurin rumaisa. Ya durƙusa suka gaisa, ammi ta tambaye shi ya ake ciki, ina Abdallah?. Ya ce mata yana lafiya, yana tare da Bashir, akwai abun da zasu ƙarasa. Ammi ta miƙa masa jaririn, ya karɓe shi ya buɗe zanin, kamar mai bacci, kamar sa ɗaya sak da shi duk da jikinsa yayi fari, amma da gani ka san yaron fari ne. Ya miƙawa ammi shi, ya ce "Allah ya sa mai ceto ne" suka amsa da amin. Mama tuni ta tashi ta bar ɗakin, ya ƙarasa gaban gadon mimi, ya zauna a kusa da ita ya riƙo hannunta. Kawai ta fashe da kuka ta ce "Papa babyna ya mutu, kuma ina son shi" Ya rungumota jikinsa ya ce "Am sorry mimi, ni kaina na ji ba daɗi, amma Allah ya fi mu sanin me ya dace da mu, kiyi haƙuri ki daina kuka" Yayi maganar yana shafa bayanta, shi kansa ya ji mutuwar yaron, sun sanya rai da yaron sosai da sosai. "Ko dai abubuwan da suka faru ne, ya sanya ki ka tashi hankalinki ki ka fara labor?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "To shikenan, Allah ya bamu mai amfani, ya sanya wannan mai ceto ne, na sanya masa sunan mahaifina Muhammad, Allah ya bamu wani" rarrashinta ya din ga yi tana jinjina masa kai. Iman ta shigo ita da Usman, Usman sai da ya sunkuyar da kai, kunya ce ta kama shi, ganin yadda takawa ke zaune ya rungume mimi yana rarrashinta, ga ammi a zaune. Abun da bai sani ba shi ne, har abun da ya fi haka yi suke, ita ba abun da ya dameta bane ba, domin ita kanta bata manta lokacin da aka yi mata aure, ba shirmen da ba sa yi ita da marigayi galadima, dan haka duk taɓrar da ruma take ba ta damunta. Usman suka gaisa da Ammi, ammi ta ce wa Iman "Ina mai sunan baban?" "Ƙarfe takwas suka tafi Lagos shi da yaya mahmud, wai wani abu za su je su yi" Ammi ta ce "To, ni yanzu Mahmud tsoro nake ji, kar ya sake ɓallo mana ruwa, ba a gama da wannan tarzomar ba, kodayake tare suke da mai sunan baba, ba zai bari yayi wani rashin jin ba. Aka sallami ruma daga asibiti, tare da jaddada mata yadda za ta kula da kanta, saboda ɗinkin da aka yi mata. Mutane suka din ga zuwa barka, Adam yayi mursisi ya ce ruma ba zata tafi gida ba, gidanta za ta koma, a ɗaukko mai kula da ita. Ya kafa hujja da mama ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba. Gashi ya samu labarin su Huzaifa ne suka kawota asibiti. Mai sunan baba kuwa lokacin da suka isa lagos, suka je gidan Alhaji Aminu, suka tarar yayi tafiya, Ade kuma ta koma Gombe!. Ayshercool. 08081012143. *WANDA KU KA KARANTA MINI LITTAFI BA TARE DA KUN BIYA NI HAKKINA BA, BA KUMA DAN BAKU DA SHI BA, IDAN KUN SHIRYA BIYANA HAKKINA GA ACCOUNT NUMBER NA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK* Mahmud ya ce wa mai sunan baba, bai kamata su yi sanya ba, idan da dama kamata yayi kawai su tafi Gomben su bita can. Mai sunan baba ya ce "Tayaya ni ban san a ina take a gomben ba" "Tambayar mutanen gidan zamu yi, ba zamu yi sanya ba" Ba tare da wani ɓata lokaci ba, mutanen gidan suka basu kwatancen in da Ade take, kasancewar sun san mai sunan baba. *** Rumaisa kuwa gwaggo ce ta je zauna mata, saboda biƙi, mutane suna ta zuwa duba ruma tare da jajanta mata abun da ya faru. Tana zaune a ɗakinta, suna video call da laila, sai kuka take yi mata, wai babyn ta ya mutu. Laila sai rarrashin ta take yi, tana kwantar mata da hankali, tare da jaddada mata, idan komai ya dai-daita, lallai ta nemi maman Khadija, da maman ilham ta gyara, duk da yaron ya rasu, akwai buƙatar ta gyara jikinta sosai. Rumaisa ta ce "To anty laila, in sha Allah ai ina da numbern su, ina Yasir". Laila ta ce "Yaya bacci yake yi bai tashi ba" Ruma ta ce "Inyee su yaya manya, ina fatan dai ba ya miki rashin ji?" "Ba wani rashin ji, rashin ji ai sai ke, wallahi na ji daɗin zuwan Yasir gidan nan rumaisa, very kind and brilliant guy, darling ya yi masa registration ma, very soon zasu fara lectures, baki ga daɗin da babansu ya ji ba zuwansa, su anam ma suna ta murna" Ruma ta ce "Sai wani yabon sa ki ke yi" "Dole in yabe shi mana, dole a sarawa mama, yaranta gaba ɗaya masu tarbiyya ne da nutsuwa, ke ce kawai mara ji" Ruma ta ce "To nima papa yana yabona, yana sona a haka" "Ai shi dama ba zai ga rashin jin da ki ke ba. Yauwwa mimi ya hatsaniyar gidan kuwa ta lafa?" "Ina fa lafawa, suna can suna cigaba da tashin hankalin su, ni ina nan ina fama da kaina, da mutuwar ɗa na, mummy sun watse da Hajiya Lubabatu, ashe Jabir lalata suke shi da ruƙayya, abun duk babu daɗi mahmud dai ya rufe shi" Laila ta ce "Lamarin gidan nan sai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa mu dace kawai mimi, bari na bari ki huta" "To anty laila na gode sosai" Tana gama wayar, Gwaggo ta shigo da kunun kanwa, ta ce ruma ta sha. Ruma ta ce ita wallahi ta gaji da wannan kunun kanwar, gudawa yake sakata. "To idan baki sha ba nonon ya zube ki huta ai, gyara ki nake son yi, na bayar da dawa ma a niƙota in sheƙa miki tuwo, ga yajin daddawar ki nan" "Gaskiya gwaggo ba zan ci tuwon dawa ba, in haihu ki bani wani tuwon dawa taɓ. Kunu kuma ina da sauran sabayata, yaushe zan ta shan kunun kanwa cikina yana ciwo". "Kya ji da shi dai, ana yi miki abun arziki kina na tsiya" Haka rumaisa suke faɗa da gwaggo, komai sai ruma tayi raki. Yanzu ma Adam ne ya je ya tarar da ita gwaggo na ta masifa, kamar ta ari baki, a kan rumaisa ta tashi ta je ayi mata wanka, tun yamma ake dafa ruwan, amma Rumaisa taƙi yadda ayi,  ta maƙale tana kuka, wai wallahi fatarta duk ta dahu saboda ruwan zafi. Takawa ya shiga ɗakin suka gaisa da gwaggo, ya dubi ruma ya ce 'Mimi meyasa ki ke da gardama ne?" "Saboda ba ka ga uban tururin da ruwan zafin yake ba, da wanne zan ji, zafin haihuwa ko mutuwar ɗa na, ko na ruwan zafi?" "Ai ni kin san bana jin zafin ruwa, zo mu je" yayi maganar yana miƙa mata hannu, ba kunya ta zagaye gwaggo ta bi takawa. Gwaggo ta saki baki tana kallon ikon Allah, daga rumaisa har mijinta ba su da kunya ko kaɗan. A banɗakinsa ya haɗa ruwa zafin dai-dai jikinta, ya taimaka mata, ta gyara jikinta ta yi wanka, sai dai rumaisa akwai langwai. Suka fito ya bata abinci ta ci, sannan ya ɗauki magungunan ta ya bata ta sha. Ya kalleshi ta ce "Na gode sosai papa, ya ku ke ciki a abujan ne, yaushe Abdallah zai dawo?" Takawa ya kwashe komai da ya faru ya gaya mata. Tayi ta rarrashin sa, tare da bashi tabbacin, Allah baya barin zalunci, amma kar ya ce zai cigaba da dagewa sai ya ga bayan wakili, saboda yana da goyon bayan manyan ƙasar. Ya ce "Haka ne, in sha Allah na bar wa Allah" Cikin dare rumaisa nono ya cika, ya takura mata da ciwo, saboda ba ta shayarwa, dan haka kwana tayi kuka, har da zazzaɓi. Gaba ɗay tausayinta ya cika takawa, su mata komai na su abun tausayi ne, ta haihu ta rasa ɗan, amma akwai wani pain ɗin na daban. Anty laila ya kira directly ya sanar mata, ta ce su yi haƙuri, da safe su kira maman ilham a waya, su sai maganin ta na gyaran nono, mace ko yaye tayi yana hana mata jin zafi, kuma baya bari nono ya lalace. (0813 561 3021zaku iya neman maman ilham kai tsaye ta lambar wayarta. Haka zalika kar ku manta da haɗin maman Khadija na sabaya 0703 777 7442) Da safe har wurin ƙarfe goma, sanna suka tashi ita da takawa, Gwaggo har ta gaji da jiran fitowar ruma ayi wanka, sai ganin ta tayi tsaf, ta sha wankanta sun fito ita da takawa. A kunyace gwaggo ta gaisa da takawa yayi musu sallama ya fita. Yana tafiya Gwaggo ta din ga yi mata faɗa "Saboda rashin gado, kina jego ki ka bi miji ku ka kwana tare ko? Ki cigaba da biye masa wani cikin zai yi miki ya bar ki wahala, tun jikinki bai gama ƙwari ba, dama gashi kin ƙi bari ayi miki jegon kirki, ki je ki ƙarata". "Ni fa gwaggo ke ba kya lallaɓa ni kamar yadda yake yi mini, jiya har ranƙwashi na ki ka yi" "An ƙi a lallaɓa ki, ku ƙara ina yin sati biyu zan gudu, ba zan iya baɗala ba" haka gwaggo ta cigaba da mita, ruma kuwa ko a jikinta. Turaki tun da aka watse daga taron nan kuwa, kwanansa biyu ya rufe kansa a turakarsa, yana jinyar zuciyarsa daga raɗaɗi da ɗacin abun da iyalinsa suka aikata. Wanda ya ɗora alhakin hakan a kansa, da kuma rashin jajirtacciyar uwa ga yaransa, kodayake auren biyayya ne na haɗi, duk cikinsu sharif ne kawai yayi tutsu, ya ce shi sai wadda yake so. A kwana na uku, aka sanar da jikin galadima ya tsananta, dan haka ya shirya ya tafi jamus. Mahaifiyar su Jamil kuwa ta sha kuka, duk wanda ta san zata kira, ta roƙi a saka baki a bayar da belin jamil, kowa yaƙi. Samha ba ta taɓa zaton Jamil ne mutumin da wakili ya samu yake taimaka masa ba. Ko da ta kira shi a waya, ya ci mata mutunci ya ce kar ta sake kiransa, shi yanzu ya samu biyan buƙatar sa ya san koba koma, yanzu Adam ya san su ba sa'anin yin ba ne ba!. *** Su mahmud kuwa, basu wahala ba wurin kwatancen da aka basu, nan da nan suka isa gari da Ade take, kuma gidan ƙanin nata sam bashi da ɓaci. Ras ta gane mai sunan baba, ta din ga murna da zuwansa, sai dai ta din ga kallon mahmud, kamar ta san shi a wani wurin. Babu ɓata lokaci mai sunan baba ya wassafa mata abun da yake tafe da su, da kuma dalilin da ya sanya yake ta bibiyarsu tun a lagos, har biyo ta nan. Ba tare da ya gaya mata waye mahmud ba, jiki a sanyaye ta ce "Adamu ne?" Umar ya ce "Kin gane shi? Kin san Ammi?" Tayi murmushi mai ciwo ta ce "Na san Bintu, bintu ƴar ɗakina ce sosai da sosai, lokacin da tayi aure tana goyon yaronta na biyu, muka bar garin, nayi kewarta sosai da sosai, sai dai wasu dalilai ya sanya ko da muka bar garin ko sunan garin bana ƙaunar ji" Mahmud ya ce "Kin tuna jikar ki mairamu?" Ade ta fashe da kuka, ta ce "Yarinyar da aka bar amanarta a wurin jauro, da dabbobin mu, muka yi gaba, ya iskemu ya ce: wai ƴan fashi ne suka kai musu farmaki, an kasheta ita da mijinta, dabbobinmu ma duk an tafi da su, kamar wanda ya rufe mana baki, babu wanda ya ƙaryata shi haka muka sha kuka. Bayan wasu shekaru yara suka fara fita neman ilimi, wasu suka zauna a riga, muna katsina a ka kai mana farmaki shekara uku baya, aka sake kashe mana ƴan uwa, muka sake yin hijira, shi kuma jauro ya ce a can zai cigaba da zama, sai daga baya labari ya iskemu, ashe jauro ɗan fashin daji ya zama, kuma shi ya kashe mijin mairamu ya gudo shi da matarsa, yayi asiri ya rufe mana baki. Wai sojoji sun kashe shi kwanan nan". Mahmud ya ce "Kar ki ce mini mutumin da rumaisa ta zana ta ce yana kama da Iman kawunta ne? Shi ne ya kashe mahaifin ta?" Ade ta ce "Waye kuma ima?" Sai a lokacin suka warware mata abubuwan da suka faru bayan barin su garin. Jiki na rawa ta ce "Kuna nufin Bintu tana raye? Ita ta riƙe ƴar mairamu?" Mahmud ya ce "Ƙwarai kuwa wannan mijinta ne ma?" Ade ta rikice da kuka, tare da yi wa Allah godiya, da kuma sanya wa Ammi albarka. Ta ce "Wallahi yaro Bintu tana zuciyata, ka ga dai gani a cikin garin gombe, amma har yau ko tuna rigar da muka zauna bana yi, ko in hanyar garin take bana son ji, gaba ɗaya tsoron mutane nake ji, Jauro bai yi mini adalci ba, dan Allah ku tashi ku kaini na ga Bintu, naga abun da mairamu ta bari" nan ta din ga basu labarin kyawawan halaye irin na mairamu, na rashin magana da haƙuri, yadda ta rayu a gidan jauro, ana azabtar da ita, tun tana yarinya saboda kawaici suka baro ta, suka sauya riga, an yi mata aure sun taso tare suka ya da zango, ta haihu tukuna, amma jauro ya cuce su. Ade ta din ga murna tana cewa amma ta ji daɗi da malam umar ya zamana mijin jikarta. Nan da nan ta saka a kira Alhaji Aminu, tare da ce masa duk in da yake ya dawo, ko kuma yazo ya tarar ta tafi kano, an ga jikirta a birnin kano, tun da ba a kaita kano dan Allah ba, yanzu dalili ya samu dan haka babu mai hanata tafiya. Nan da nan riga ta ɗauka, an samu ƴar mairamu a raye, ashe kan ta mutu ta haihu, aka din ga zuwa ganin mai sunan baba da mahmud. Sun sha karramawa kala-kala. Washegari da wuri Alhaji Aminu ya sauka a garin, tare da jin batun tamkar almara, abun da ya faru shekaru kusan goma sha tara baya, yaya za ayi ace, wai an ga ƴar mairamu. Sai dai ya tsinke da lamarin, bayan saukarsa mai sunan baba ya nuna masa hoton iman. Alhaji Aminu ya ce "Malam Umaru, amma ka kasa gaya mini wannan abu, duk da ban wani san mairamu ba, amma wannan kamarta ɗaya da ade, kuma ba shakka jininmu ce, yanzu meye abun yi?" Mai sunan baba ya ce "Idan ba damuwa, sai mu taho da iman ɗin da amm... Ade ta ce "Wane mutum, da ƙafar nan tawa ko a ƙafa zan taka na je kano, na ga Bintu" Alhaji Aminu ya ce "Da wace ƙafar? Ƙafa duk sai saura? Ki zauna a shirya tafiya, sai a tafi gaba ɗaya " Nan ya sake warware musu irin zaluncin da jauro yayi musu, ya din ga haɗa kai da ƴan bindiga ana cutar da su, wanda hakan ya sanya da yawansu suka tarwatse, da farko basu gano shi ba, sai daga baya amma an ce sojoji sun kashe shi. Da daddare takawa ya ceea rumaisa, ta zo su tafi su kwanta, ta ce "Ba zani ba gwaggo ta ce idan na biye maka wani cikin zan samu, kuma wallahi haihuwa da wahala" Dariya yayi ya ce "Ai shikenan" Gwaggo ta kawo wa ruma abincin dare, ta ce "Yau ba zaki bishi ba?" "Ai na gaya masa kin ce bamu da kunya, kuma idan na cigaba da biye masa wank cikin zan samu da suri" Gwaggo ta ɗora hannu a ka ta ce "Rumaisa ba ki da hankali? Ki ka ce ni na faɗa, ashe halinki na wauta na nan, da wani idon zan kalle shi? Wallahi dole in tattara kayana in bar gidan nan" Ruma ta ce "Ashe kuwa zaki maimaita masa abun da ki ka faɗa mini, dan sai ya bi ba'asi" Ta samu ɗan kwali ta kwaɗawa ruma a baya ta ce "Shashasha uwar wauta, shikenan zai daina ganin mutuncina". ** Mahmud ya kira Ammi a waya, ya ce "Su shirya, su haɗu a wuri guda, suna tafe da manyan baƙi zuwa kano shi da mai sunan baba. Ba yadda ammi ba ta yi ba, amma yaƙi gaya mata ko suwaye, ya ce amma muhimmancinsu ya kai ace har mai girma wambai ko turaki yana wajen. Ammi ta ce "Turaki baya nan, ya je Germany wurin galadima, jikinsa ya tsananta, sai dai wambai" Mahmud ya ce "Baƙi ne masu muhimmanci, har mimi muna buƙatar ta a wurin" Ammi ta din ga mamakin wane irin baƙi ne kuwa haka?". Da ta sanar da wambai kuwa, ya ce babu laifi, a jira ƙarasowar ta su, aji wani irin baƙi ne, ya ce idan sun iso a kira shi. Ammi ta sanya aka yi ta ɗorawa da saukewa, duk da bata san wane irin baƙi ba ne, amma akwai buƙatar ayi girki. Duk nacin ruma da iman, a kan son sanin suwaye baƙin, ammi ta ce musu ita fa ba ta sani ba. Duk suna falon mai sunan baba ya yi sallama, iman ta tashi da sauri ta ce "Hero suwaye baƙin?" Ruma ta gwale baki ta ce "Su hero manya" Takawa ya ce "Umar kun bar mu a duhu kai da ƙaninka, ku muke ta jira" Yayi murmushi ya ce "Yanzu za su shigo" ya kalli iman ya ce "My yellow, yakamata ki bani tukuici kan ki ga baƙin nan fa" yayi maganar yana jan karan hancinta, a gabansu. Kunya ce ta kamata ta ce "To me zan baka?" "Saniya zaki sai mini" gaba ɗaya suka hau dariya, Ammi ta fito ta ce "Mai sunan baba kun sauka? Ina baƙin?" Mahmud ne yayi sallama, sai Alhaji Aminu a bayansa ya riƙo ade, sai ƙannenta guda biyu. Sakin carbin hannunta ade tayi, ta ce "Ade" da ƙarfi. Jiki na rawa saboda tsufa Ade ta ɗago ta kalli Ammi ta ce "Bintuna" Da sauri Ammi ta ƙarasa ta riƙo hannun Ade, hawaye ya wanke mata fuska ta ce "Dan Allah gaske ne ba mafarki nake ba, Ade ke ce a gabana? Ade ba irin neman da ban yi miki ba" Suka rungume juna ita da ita. Alhaji Aminu ya ƙurawa iman ido, ya ce "wannan ce ƴar ta mu?" Kamar sokuwa haka iman ke bin su da kallo. Mahmud ya ce "Hajjaju ga ƴan uwanki, mijinki ya nemo" Jiri ne ya fara ɗibar iman, saboda ba ta san mafarkin nan ya cigaja da yaudararta. Umar ya riƙe ta ya ce "Iman, calm down mana menene" "Dan Allah ka tashe ni daga baccin, kamar ba zai faru a gaske ba fa?" "Ba mafarki bane ba fa" yayi maganar yana zama tare da ita, saboda har numfashinta ya fara sama. Alhaji Aminu ya ƙaraso gaban iman, ya riƙe hannunta, ya ce "ƴa ta ba mafarki bane ba, mu ne ahalinki" bayan gama kukan ammi ta ce Aminu haka ka girma sosai? Iman ga Ade da nake baki labari, wannan su ne ahalin mairamu" An sha koke-koke, Ɗan aike ammi ta tasa, aka kira wambai, sai dai yaji kunya da nauyin abubuwan da suka din ga yi wa Ammi da iman, a kan rashin sanin wacece, wanda hakan yana da alaƙa da zigar Mummy. Nan Alhaji Aminu ya gaya musu cin amanar da jauro yayi musu, da ƙiyayyar garin da ya sanya musu, suka kasa komawa, balle su binciki abun da ya faru gaske ne ko ƙarya. Takawa ya ce "Tabbas wannan mutumin shi ne rumaisa ta zana mini, ta ce da wa yake kama? Na ce mata iman, ta ce a yanayin da ta ganshi ne ya sanya ba zata taɓa cewa ta ga wani mai kama da iman ba, kasancewar sa mutumin banza, dan har tattaunawa da shi ta yi" Iman ta rasa mai zata cewa mai sunan baba saboda murna, sai kuka take yi. Bayan an nutsa, ammi ta saka aka kawo abinci, takawa ya ce "Shi da matarsa zai ci abinci, mai sunan baba ya ce shi ma haka. Mahmud ya ce "Ni za a yi wa gori? Sai in ci da ammina" Haka suka wuni cikin raha da dariya, iman ta rasa in da zata tsoma dan farinciki. Labari ya bazu, Mijin iman da Mahmud sun gano iyayen Iman. Hankalin Mummy ya ƙi kwanciya, sai da ta zo ta ganewa idonta, Ade ga jikarta, amma ta yi ram da rumaisa, saboda yadda yarinyar ta yi mata. Da yamma ammi ta ce ruma ta tafi gida, tun da jego take yi, takawa ya ce ta ƙyaleta, duk tare za su zauna, su taya iman murna. Mai sunan baba ma barin iman yayi a gidan, ya tafi gida dan ya huta. Iman da rumaisa gami da nusaiba, sun kewaye Ade, sai dariya take basu, suna yi mata tambayoyi, har bacci ya kwashe su. Takawa dama yana ɗakinsa na sashin Ammi, fitowa yayi, kusan sha ɗayan dare yana nunawa ammi wayarsa, ya ce "Ammi ina mimi, a taso mini ita" A daren aka wallafa labarin kama Khalifa wakili a Mexico da cocaine. Ammi ta ce "Bacci take yanzu, ka bari da safe" Ya ce "Ammi ba zan iya jira ba, a taso mini ita dan Allah" Haka Ammi ta je ta taso masa ruma, ya ja ta ɗakinsa ya nuna mata. "Ban gaya maka ba papa, duk wani azzalumi da ya fi ƙarfinka, bai fi ƙarfin Allah ba, ka zuba ido zaka ga yadda Allah zai ɗaiɗaita azzalumai, yanzu ma ga ta in da ɗan nasa zai yi takara, kuma wannan abun da aka kama ɗan sa da shi, ya isa ya saka baban nasa ma su faɗi zaɓe". Alwala takawa yayi, ya din ga salla yana godewa Allah, ko wannan tashin hankali ya isa hana wakili sukuni, ɗan sa yayi laifi da ƙasar da bashi da halin yin cuwa-cuwa. Ruma kasancewar jiya ba ta yi bacci da wuri ba, ya sanya take ta bacci da safe. Ammi ta saka aka ɗorawa ruma ruwan zafi. Ade ta ce lallai a kai su su gaida iyayen mai sunan baba ma, Ade ta yi wa Ammi addu'a da iyalan ta da fatan alkhairi, bisa jajircewa kan riƙe amana. Takawa ne ya je yana tashin ruma, ta buɗe ido ta tashi zaune, ya ce "Ammi ta ce ki tashi haka, ki yi wanka sabuwar kakar ki ma tana nemanki". Wani irin zilllo ruma ta yi tana haki, ta yakushi takawa a wuya ta fita da gudu daga ɗakin, bayan ta ya bi yana kiran sunanta, ta baya ta ɓulla in da ake girki idan da baƙi a gidan, ta kefa wani abu a cikin murhu. Kan ya ƙarasa wurin kuma ta faɗi, cikin tashin hankali ya ɗauke ta, ya kaita ɗaki, sai dai a sume take. Ammi ya je ya gayawa abun da yake faruwa, hankali tashe suka nufi ɗakin da take. Kasancewar iman nursing take yi, ta dudduba ruma, amma babu wani abu da yake nuna akwai matsala a vitals ɗin ta. A hankali ta yi juyi, ta ta da kai da hannunta kamar mai bacci, Ammi ta ce "Alhamdilillah, iman ku ɗaukko mp a kunna karatun Alkur'ani, ko wani abun ne ya sameta" iman ta jinjina kai ta aiwatar da abun da Ammi ta ce. Mutane na ta zuwa ganin dangin iman, su Ade sai godiya suke yi musu na riƙe musu ƴa. Ade ta dame su da tambayar ina rumaisa, iman dai ta fito ta gaya mata halin da ake ciki. Har kan rumaisa Ade ta je, ta dafa kan rumaisa ta ce "Wannan ai kamar shaiɗanu ko sihiri" Tun sanin da Ammi ta yi wa Ade, mace ce mai ibada da yawan addu'a, duk da kasancewar ta ba wata mai ilimi mai zurfi ba. Ta dafa kan rumaisa tana ta yi mata addu'a, a hankali ruma ta ce "papa" "Na'am mimi" "Wata mage ce za ta sha maka jini a wuyanka, ta kasa" "Babu wata magge fa, tsorata ki ka yi, bacci ki ke yi" "A'a ta yakushe ni a hannuna, idonta hayaƙi ma yake yi" ta nuna musu hannunta, in da aka karta mata farata. Ade ta ce "yarinya na jego kun barta tana yawo ko ina, gashi ba ta son ɗan kwali, idonta ne ya buɗe take gane-gane ai". Aka samu dai ruma ta farfaɗo, sai dai ba ta magana sosai. A yammacin ranar su Ade har gida suka je, suka gaida mama, dan a washegari suke son komawa. Mai sunan baba ya tabattar musu da yardar Allah, zai kawo musu iman, ta ga dangin ta. Har gida suka sake bin mai girma wambai, suka sake yi masa godiya, turaki kuma a lokacin yana Germany. Hajiya Lubabatu wani irin ciwon kai ta din ga fama da shi, mai tsananin gaske, da har ta kai ba ta gane mutane sosai, kuma ba ta son haske sai duhu, tayi ta surutai na fita hayyaci, haka aka kaita asibiti aka ajiye. Ranar da su Ade suka koma, ranar mai sunan baba ya koma lagos shi ma, sai dai mahmud ya rasa sukuni, amma bai gayawa kowa abun da yake damunsa ba, iman ta yi wa mahmud godiya, daga shi har mijinta, bisa ga namijin ƙoƙarin da suka yi mata Still a yammacin ranar, wani tashin hankalin ya sake afkuwa, Allah ya yi wa galadima rasuwa, wato mahaifin jabir, Senator wakili kuma ya hau jirgi domin zuwa Mexico, sun samu plane crash, da shi da wasu manya-manyan ƙusoshi a Nijeriya, wanda galibin su tare suke harƙallar smoke duk suka mutu. Duk mutuwa mutuwa ce, takawa yana jimamin rashin ɗan uwan mahaifinsa, gefe guda kuma yana farincikin hukuncin lokaci ɗaya, da Ubangiji Allah ya haɗa azzalumai yayi musu. Ahalin masarautar kuwa suka shiga taradaddi da damuwar gagarumin rashin da aka yi, turaki ne ya yi clearing komai, ya taho da gawar Kano. Ga matarsa na can kwance a asibiti, ɗan sa kuma aka kawo shi cikin sarƙa, sai a lokacin mutane hankalin su ya koma kan cewa matar galadima ba su suka yi jinyarsa ba, baro shi suka yi a can, aka din ga Allah wadai da ita. Kwanaki uku da rasuwar galadima, ba a ga Mummy ba, mutane suna ta tambayar Ammi, wai ba su ga Mummy ba. Kwana na huɗu mahmud ya je ya samu ammi, ya roƙeta dan Allah ta kira takawa da rumaisa da iman, su haɗu a sashin Mummy. Ammi ta ce masa ba damuwa, dan kuwa yanzu ba ta ƙaunar duk wani abu da zai sanya mahmud ɗin damuwa. Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, da suka ga Mummy, gaba ɗaya jikinta a ƙone, sai ihu take tana kiran sunan rumaisa, ruma kawai ta fashe da kuka ta rirriƙe takawa saboda tsoron da Mummy ta bata. Wambai ya kalli Mummy ya ce "Jamila, ya aka yi ki ka ƙone haka?". Cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ta din ga faɗar miyagun abubuwan da ta aikata ita da Hajiya Lubabatu, babu wanda yafi ɗaga musu hankali, irin yadda ta kai Adam wurin boka a ka zuƙi jininsa, kuma duk shekara irin bala'in da yake shiga saboda asirin da tayi masa. Kasancewar sa da runaisa ne, ya sauƙaƙa masa wasu abubuwan, kuma a wannan karon ma, aljanar ce ta zo shan jini da take duk shekara, ta kasa ta sanya ruma naƙudar dole ta kashe ɗan, still ta cigaba da bin adam ta sha jinin da ta saba, saboda ba zata iya cigaba da aikin da aka bata ba, sai da jininsa, shi ne take ta dambe da rumaisa, ta fito a suffar mage, rumaisa ta jefata a murhu. Shi ne ta shiga jikin Mummy, ta ce sai dai tayi jinyar a jikinta, idan mutuwa ce su mutu tare tun da tsayin shekaru ita take yi wa aiki. Wannan matar da rumaisa take gani, da hayaƙin da idonsa ke yi, aljanar take gani. LA ILA HA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINA ZALIMIN, da rumaisa ta riƙa, tun da lokacin da ta san falalarta, take ganin fa'idarta a rayuwar ta. Wambai ya ce "Anya ba surutan ciwo ne ya sanya take maganganun nan ba". Mahmud ya girgiza kai ya ce "Ba zafin ciwo bane, muna bibiyar duk wayar da Mummy take yi, kuma tun asali na san wasu abubuwan, ba abun da zan iya yi a kai ne" Kuka ammi take kamar ta fita a hayyacinta ta ce "Jamila me nayi miki haka a rayuwa ne? Haba Jamila shikenan bawa ba zai ɗau ƙaddara ba, duk saboda marigayi ya fara aure na?" Mahmud ya zube a gaban Ammi ya ce "Ammi, dan girman Allah ki yafewa Mummy, na sam ta cutar da mu, amma ta riƙe ni kamar ita ta haifeni, dan Allah ki yafe mata" Ruma ta ce "Wallahi ba zata yafe ba, nima ban yafe ba, dukkanin mu bamu yafe mata ba, dare na din ga bi, ina kai ƙarar ku wurin Allah, sunayenku na din ga gaya wa Allah, kuma yayi mana maganinku, yau na cika alƙawarin da na ɗauka". Su Fauziyya sai kuka suke yi, wambai ya ce "Jamila baku yi wa kanku adalci ba, ki ka saka na din ga ganin baiken Binta, ina goyon bayanki, kanki ki ka yi wa. Binta ki ɗauki yaranki ki tafi da su, Allah ya haɗa miki kansu, mun yi magana da mai martaba da ƴan majalisar sarki ma, Adam ne zai gaji kujerar galadima. Binta ki yafe mini abubuwan da suka din ga faruwa, ke kuma wannan yarinya rumaisa Allah ya ƙara haskaka rayuwarki, kin kawo sauye-sauye da tarin alkhairi a wannan gida". Ammi ta rungume Mahmud tana rarrashinsa, sosai yake kuka yana Ammi ta yafe musu baki ɗaya. Su Fauziyya sai kuka suke yi, ruƙayya na gefe ba ta iya magana, dan tun da Mummy ta fara rashin lafiya abun ya shafeta, take abu kamar taɓaɓɓiya. Kwanaki uku aka yi bikin naɗin sarautar takawa zuwa galadima, shi kuma ya yi wa rumaisa sarautar garkuwar galadiman kano. Kwananta arba'in da haihuwa, ya biya musu umara, shi da ita da ammi da mama, suka tafi domin nuna Godiyar su ga Allah. Kamar yadda mai sunan baba yayi alƙawari, Iman ta je ta ga danginta, mutane masu karamci da tarin dukiya. Kamar yadda ammi ta yi alƙawari, sabir na isa shiga makaranta, ta basu ɗan su, lokacin ruma ta kammala secondary school, sai dai da laulayin wani cikin ta shiga makaranta, take karantar criminology. Kamar yadda suka yanke shawarar hakan ita da takawa. Cike da tausayawa mai sunan baba yake kallon iman, ta shirya ranar graduation ɗin su, cikin ta kamar yayi magana saboda girma, scaninc ya nuna tagwaye ne a cikinta. Mai sunan baba in dai yazo baya bari ta yi aikin komai, manyan mutane sun halarci bikin kammala karatun su iman. Hajiya Lubabatu brain cancer ta samu, kanta ya din ga ɗurar ruwa, aka fita da ita ƙasashen ƙetare, sai dai duk da an saki Jabir, bai iya zuwa yayi jinyarta ba, sai ƴan uwanta. Mahmud ya koma aiki, idan ya zo kuwa, kullum sai ya je duba Mummy, sai dai abun nata babu cigaba, kullum ciwo ƙara jagwalewa yake yi, an kai ta asibiti dressing ake yi, amma ƙuna sake jagwalgwalewa take yi, tana wani irin wari. Turaki ya tattara iyalin sa yayi watsi da su, duk wani abu na kyautatawa tsakanin su, ya daina yi musu, Jamil aka din ga iƙrarin ya mutu a hannun DSS saboda babu wanda ya san a in da yake. Mai sunan baba kan Iman ta haihu, ya canza musu gida, gida mai kyau sosai da sosai, daga Lagos yake sayo kaya yana aiko wa da Usman da Aliyu kayan takalma, computer da yadiddika da lesuna da ga Aba yana aiko musu da shi, iman da ruma da nusaiba suka haɗa kuɗi, suke tura masa suma suna karɓar takalma da laces. Yaya Abubakar da yayi aure, jigawa ya koma, saboda a can yayi karatu ya saba da mutane, kuma cikin ikon Allah ya samu aiki a can. Alhaji Aminu ya din ga jan mai sunan baba a jiki, yana koya masa yadda ake importing kaya daga ƙasashen ƙetare, mai sunan baba ya ce a koyawa su Aliyu, sune suka fi ga harkar kasuwanci, kar son rai ya shiga lamarin tun da yana aiki da hukumar hana fasa ƙwauri. Tagwayen mata aka yi wa Iman aka ciro mata, masha Allah kyawawa tamka su suka yi kansu, lokacin mimi ma ta yi nauyi sosai, aka sha shagalin suna, an yi wadaƙa da shanu da nono a haihuwar nan, mai sunan baba ya sanya sunan Ammi da mama. Abdallah ma a DSS ya samu aiki, yana abuja tare da Bashir, cikin ikon Allah babu wanda Allah bai ɗaukaka a ƴaƴan mama ba, kuma galibi duk a sanadin rumaisa ne. Kasuwanci ya buɗewa su Yaya Aliyu, suka tattaga aure, mama ta ce duk su yi Allah ya taimaka. Mahmud ma yayi aure, Yasir kuwa sai ƙarshen shekara yake samu yazo ya koma, zaman canada ya yi masa daɗi yana ta karatunsa, ga wata irin shaƙuwa tsakaninsa da ƴar anty laila. Mijin anty laila yana ta jaddada mata, shifa idan Yasir ya kammala karatun sa, a nan zai samu aiki su cigaba da zamansu, sannan kuma da ya kammala karatun ya bashi anam. Ƴan mazan mama, gidaje uku suka saya, a jikin nasu, suka faɗaɗawa mama shi, dan cewa tayi dan Allah yayi musu arziki ba zata bar unguwar nan ba, tana fatan suma su ci albarkacin ruma da ƴan uwanta. Hakan ya sa suka gyara layin, aka yi masa kwalta da kwalbati, aka sassaka sola, wannan ya shiga da abun alkhairinsa wannan ya fita. Mummy ta koma tamkar mushe da rai, saboda wari, kuma tana ji tana gani, gida ya koma hannun ammi, ta malleke komai da take ta ƙoƙarin hana faruwar hakan. Ba tare da ƙyashi ba, ammi ta din ga nemawa ruƙayya magani, ta ce in dai tana raye ba zata bari ɗan marigayi galadima ya wulakanta ba. Adam ya sauyawa ruma gida, manyan motocin take ja, da ƙananun shekarunta sai ta birgeka, saboda har a lokacin ba ta haɗa shekara ashirin ba, ta saka ya ɗaukko mata ɗan mai unguwa mai hanata shiga lambu sata, yake kai Sabir makaranta ana biyansa kuɗi mai yawa. Adam ya ɗauke mata komai, dan haka kuɗin kasuwancin ta a sama suke, sai dai tayi ta kyauta kasancewar ta mai kyauta ce. Ba ƙaramin girmama rumaisa suke yi ba, saboda rawar ganin da taka a rayuwar Adam, dan shi kansa duk wani abu da zai taɓa mutuncinta, ko tayar mata da hankali fito na fito yake da shi. Ƴan unguwarsu ruma har murna suke su ga danƙareriyar mota a ƙofar gida, sun san akwai kaɓakin alkhairi ranar. Hajiya Lubabatu ce ta fara mutuwa, ba tayi arba'in ma Mummy ta bita, ammi ta ji mutuwar nan ba kaɗan ba, hakan ya sa ta ce duk ta yafe musu, kuma ta rungumi Fauziyya da ruƙayya ta cigaba da riƙo, baba uwani a can garin su mahaifinta aka ganota, Cancer ya kama mata ƙafafuwa ita ma, babu kuɗin da za ayi mata aiki, ammi ba ta yi shawara da wani ba ma, ta tura sidi aka biya kuɗi, aka cire mata ƙafafuwan ta saya mata keken guragu tare da bata jarin sana'a. Rumaisa kafin ta gama makaranta sai da ta haifi ƴan maza biyu, ta din ga Addu'a "Allah kar ka sa na yi irin ta mama na haifi ƙanwar maza, ba zan iya ba" takawa ya din ga yi mata dariya ya ce ashe kina sane ki ke tsiyata ku. Idan ta tuna wasu rashin hankalin da tayi a baya, ta ji kamar ta yi wa kanta duka, babban abun da ya bata mamaki, bai wuce duk shekarun nan takawa yana ajiye da wasiƙar da ta rubuta masa, na cewar ya taɓa mata nono, yayi ta tsokanarta yana dariya. Samha kuwa rayuwa ta juya mata baya, dan abun da Jamil ya aikata, da wanda tayi ita ma, ya zame mata baƙin fenti, aka rasa mai aurenta, duk gayu da ƙwalisar samarin duk suka watse. Runaisa ba ta bar harkarta ta zane-zane ba, dan har rubuce-rubuce take yi, kamar wasa ta zama popular manyan mutane suke sayen zane-zanenta. Cikin ikon Allah rumaisa ta zama criminal lawyer, sunanta ya shahara sosai, ga ta lawyer, ƙwararriya wurin zane-zane da rubuce-rubuce, kuma ƴar kasuwa. A duk lokacin da aka yi hira da ita, ta kan ja hankalin mutane a kan cewa a duk lokacin da aka samu ɗa mara ji kamarta a cikin al'umma, kar a tsangwame shi, a ja shi a jiki a duba wace irin baiwa Allah ya yi masa a dafa masa a kanta, saboda Allah baya halittar abun da ba shi da amfani. Kamar dai ita da tun a tasowarta ko makaranta ba ta so saboda rashin jin ta, amma cikin ikon Allah a yanzu, ilimi na addini da na zamani sai dai ta koyar da wani bisa jagoranci da jajircewar mahaifiyarta yayyenta da kuma mijinta ta zama abun da ta zama a yanzu. TAMMAT BI HAMDILLAH!!! GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN TAIKAI MAI KOWA MAI KOMAI, DA YA BANI IKON FARA RUBUTUN NAN YA BANI ARON RAI DA LAFIYA NA KAMMALA SHI. ALLAH YA SANYA A AMFANA DA DARUSSAN DA KE CIKI, AKASIN HAKA KUMA ALLAH YA YAFE MANA. SAƘON GAISUWA TA MUSSAMAN, UWAR KIRKI UWAR ALJANNA UWA TA TA KAINA, MALAMA NAFISU ADAMU, DA MUKA FARA TARE HAR NA KALLAMA ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MIKI HAR GADON BACCINKI. GODIYA TA MUSAMMAN GA ƳAN UWANA. ZEE KUMURYA NIMCY LUV, TARE DA SAURAN MARUBUTA MAIMOON, MARYAM MAI ƘOSAI ANTY ZEETY, KUNA DA YAWA GASKIYA DUK INA JI DA KU DAI. BAN MANTA DA KU BA, MUTANEN DA SUKA BANI TALLACE TALLACENKU MAMAN MEENAT COLLECTION MAMAN KHADIJAH MAI SABAYAR ƳAN GAYU TARE DA MAMAN ILHAM KUN GA DAI YADDA SUKA KANKARO RUMA A GIDAN AURENTA, KAR A GAJI DA CIGABA DA PATRONIZING KAYANSU, TESTED AND TRUSTED RUMA TA YI AMFANI DA SU KUN GANI. WAƊANDA SUKA YI SUPPORTING ƊINA, WURIN SAYEN LITTAFINA, ƳAN NORMAL GROUP, SPECIAL DA AKE TURAWA TA PC, ƳAN AREWABOOKS DUK INA GODIYA, DA SUPPORTING ƊINA ALLAH YA ƘARO MUKU ARZIKI DA BUƊI MARA YANKEWA. WAƊANDA SUKA DIN GA FITAR MINI TARE DA KARANTAWA, BA TARE DA KUN SAYA BA, DA WANDA SUKA YI MINI AMFANI DA SHI WATA SIGAR BA TARE DA IZININA BA, INA YI MUKU TUNI DA ALLAH BAYA YAFE HAKKIN WANI A KAN WANI, IDAN KUN SHIRYA BIYANA HAKKINA. 0009450228 AISHA ADAM JAIZ BANK. DOMIN GYARA SHARHI, KO SHAWARA ƘOFATA A BUƊE TAKE. SAI MUN SA 08081012143 Rumaisa ta ja numfashi, sannan ta fito da wata waya, duk ta sha jiki, screen ɗin ma duk ya tsage, ta ce "Wannan wayar, ita ta fara haɗani da takawa, kafin ƙaddara ta sake haɗa mu a karo na biyu. Silar haɗuwarmu na farko wannan abu ne da ya shafi rayuwarmu ni da shi, bai shafi abubuwan da suke faruwa a yanzu ba" Ta ɗan yi shiru sannan ta cigaba da cewa, "Kamar yadda wasu suka sani, yayyena maza ne, nice ƙarama da duk wanda ya sanni, aka yi mini shaidar rashin ji. Wannan wayar na ɗauke da wasu abubuwa da ka iya taimakawa jami'an tsaro, saboda a rashin ji na, bani da tsoro, kuma cikin ikon Allah ranar da mu ka tafi kai ziyara dangin mahaifina, muka haɗa mota da ƴan bindiga. A cikin wayar akwai hotunan wurare da abubuwa da na yi ta ɗauka, ciki har da jakar bullet mai ɗauke da wasu lambobi, da sunan SMOKE. A rashin ji na, na tattauna da ƴan bindigar, har shugaban su yake ce mini, ƙasa ta san da zaman su, dan kuwa akwai kason su, a kasafin kuɗi da ake duk shekara. Kasancewar a lokacin bakomai nake ganewa ba, amma na fuskanci wasu abubuwan. Zuwana garin su babana, wanda ƴan bindiga kusan suke mulkar garin, nan ma nayi wata tattaunawar da wani dattijo da aka ƙona rigar su, sai shi kaɗai, wanda shima yana da alaƙa da ƴan ta'adda. Daga nan har zuwa lokacin da aka yi garkuwa da ni, abubuwan dai tamkar a mafarki, duk yadda za a bawa mutum labarin yadda abun yake, sai ya je ya gani. Na sha baƙar wahala saboda ina da taurin kai da rashin jin magana, na daku kamar ba mutum ba, saboda ban daina rashin kunya ba. Kwatsam! Aka kawo matar da silarta abubuwa da dama suka faru, mace da tsohon ciki, ta din ga magiyar a bari ta tafi, ko dan cikin jikinta, aka ce a kula wannan ajiyar wakili ce". Ɗiff ɗakin yayi, Wambai ya ce "waye wakili, wane waikilin tukuna". Turaki ya ce "A daina katse ta, mu bari ta kammala tukuna". Rumaisa ta ɗora da cewa "Lokacin da ta zo ina tsaka da rashin lafiya, halin da take ciki bai dameta ba kamar ni, ta kula da ni sosai da sosai, sai dai wasu lokutan sai tayi ta kuka, idan na bata haƙuri sai ta ce; ba sace ta da aka yi ne dameta ba, mijinta, ba yadda bai yi da ita ta fasa tafiya ba amma taƙi, sai kuma sanya hannun ɗan uwanta a wurin saceta. Ta bani labarin mijinta, iyayensa, yadda suke rayuwarsu, da kuma irin rayuwar da tayi a nasu gidan. Ta gaya mini mahaifinta ya saka sunanta a kadararsa, kuma wasu kuɗinsa na shiga account ɗin ta, saboda ita bai taɓa mallaka mata wata kadara ba, saɓanin ƴan uwanta, da kowa yana da wani muhimmin abu da ya bashi. Ta gaya mini matar mahaifin ta da yayyenta, sun uzzura mata sosai a kan hakan, kuma babu wanda ya san da zuwanta Nigeria, sai yayanta da ta gayawa, ta sanar masa ga ranar da zata je dubiya.... "Ƙarya ne, me ki ke nufi, Jamil ne ya sanya aka yi garkuwa da aisha, wallahi ƙarya ki ke yi, ni za a yi wa sharri, a cuci ɗa na a ɓata mana suna" Wambai ya ɗagawa babar su Jamil hannu, ya dubi ruma ya ce "Wani tabbaci zaki bamu a kan haka, ta yaya zamu yarda da ke?". "Na yi wa anty aisha alƙwarurruka, bayan ta ce mini ta bani amanar mijinta da ɗan ta, duk da ƙarancin shekaruna, na fahimci abubuwa da dama a labarin da ta gaya mini" rumaisa ta basu labarin komai, har kan mutuwar aisha. Ta kalli Abdallah ta ce "Bismillah" Abdallah ya dawo tsakiya, ya zauna da kayan zanensa. Ruma ta ce "Wannan yayana ne, kuma ƙwararre ne wurin iya zana abubuwa, da shi nake koyi, ya sanya nima na iya zane-zane, amma kasancewata ƴar koyo, zan ba shi damar ya zana wani abu, kar ace na yi son zuciya ko sharri nake son yi wa wani, yana daga in da yake zaune, zan siffanta masa abun da zai zana ɗin, Abdallah ba ya nan aka sace ni, nikaɗai aka sace, dan haka you should be good in judgment" Kowa yayi shiru ya zuba musu ido, sannu a hankali take siffanta masa abubuwa yana zanawa, bai ja lokaci ba ya kammala zanen ya miƙa musu takardar da yayi zanen a kan ta. Ta siffanta masa Mutanen da suka je suka ɗauki gawar aisha ne, da motarsu, da yanayin da suka ɗauki gawar. A yadda rumaisa ta suffanta masa ya zana, Jamil ne a gaba cikin kayan ppe, amma yanayin tsayuwar da sashin da aka iya gani na fuskar sa, zai tabbatar maka da shi ne, idan har ka san shi. A lokacin takawa ya tuna a tsukin lokacin yayi ta fama da faɗuwar gaba, da fita hayyaci, kuma Jamil yayi balagro a lokacin. Mahaifiyarsa ta cigaba da bala'i, da iƙirarin wannan shegantakar banza ce ba Jamil ba ne ba. Mahmud ya ce "Allah ya baku yawan rai, muna da shaida ta gaba, ban sani ba kafin ni, ko ta gaya wa wani, amma ta same ni da maganar, kuma da ni da wasu daga cikin ƴan uwanta maza muka yi aikin nan. Akwai lambar waya da ta bani, lokacin tana magiyar a kai aisha asibiti kan ta rasu, ita ce lambar da aka kira, na bayar an yi tracking ɗin ta, haka zalika ɗan uwanta Yasir yayi tracking ɗin ta, an daina amfani da layin, amma Jamil ne yayi register da layin, Yasir na da tracking result ɗin sa, ni ma ina da nawa da police suka yi" Wani daga cikin ƴan sandan ya ce "Amma wannan ai aikin police ne, mu yakamata ace mun yi shi, ko shi Adam tun da jami'in tsaro ne". "Ban ji na yarda da kowa ba da zan iya ɗaukar shaidu, masu muhimmanci na bawa ƴan sanda ba, dan a lokacin na ji takaicin ace ƙasata da jami'an tsaro amma aka kasa kuɓutar da ni, daga hannun ƴan bindiga, kuma ƴan bindiga da kansu, suka tabbatar mana da kun san da kune ku ke sauƙaƙa musu aiki, ku jami'an tsaro. Takawa kuma ban gaya masa komai ba, saboda a wancan lokacin yana cikin damuwa da tashin hankali ne, da kuma fuskantar matsin lamba daga mutane, a yadda yake a zuciye zai iya ɓata komai a wannan lokacin. Maganar ina ƙoƙarin ɓata zumunci ta hanyar haɗa husuma kuma, ina da shaida babu wanda na yi wa sharri, ranka ya daɗe wannan ledar ta gabana, cike take da kayan tsubbu da na sanya baba uwani tsohuwar hadimar ammi tonewa, kuma nayi amfani da wayar ɗaya daga cikin ma'aikatana, na naɗi duk abubuwan da aka saka ta yi mini, suma suna cikin wannan wayar na tura a ciki". Adam ya tashi jiki a matuƙar sanyaye, ya ɗauki excuse ya fita amsa waya. Tun da suka shiga ake kiran wayar, sai dai da ya duba ya ga private number na. A yadda ruma suka tsara da Mahmud, shi ne zai faɗi abubuwan da suka shafi ɓangaren Mummy, kutungwilar da take shiryawa amma ya kasa. Turaki ya sunkuyar da kai zuciyarsa na yi masa raɗaɗi, saboda abun duniya yana ciki ɗaya da aisha, ubansu ɗaya, ya sanya aka saceta, kuma yake ta ƙoƙarin sanyawa a ɗora zargi a kan Adam, Adam ɗin da ya kasance abokinsa ɗan uwansa da suka tashi tare. Kuka matar turaki take yi, ta ce "Ita haryanzu ba ta yadda da cewa Jamil zai iya aikata mummunan abu irin haka ba sharri ake yi masa". Bashir ya ce "Hajiya sai dai ki yi haƙuri, domin kuwa jami'anmu sun riga sun kama shi ma" Mahmud kuwa ya dubi Jabir, sannan ya mayar da idonsa kan Hajiya Lubabatu ya ce "In faɗi me Jabir yayi, ko kuma in bari ku faɗa da kanku?" Suka yi tsit babu wanda yayi magana, Mahmud ya ce "Dole ka cigaba da zama a hannun 'yan sanda su kammala bincike" Wambai ya ce lallai a nemo masa baba uwani duk in da take, gaba ɗaya falon ya hargitse da hayaniya. Rumaisa ta ce "Babban roƙon da zan yi muku shi ne, kar wanda yayi ƙoƙarin yin wani abu a kan wakili, saboda nikaɗai ce shaida a kansa, sai dai in Jamil ne ya yi magana a kan sa, idan ba haka ba". Bashir ya ce "Haka ne, amma ban taɓa tsammanin wakili zai kai haka ba, saboda tsamar da ke tsakanin sa da Adam ba" Adam ya ɗaga wayar tare da yin sallama "Na san ko ban yi magana ba, ka san da wanda ka ke magana, Senator mai wakili ne. Ina tayaka da ƴan team ɗin ka murnar gano suwaye SMOKE. Sai dai nikaɗai ka sani a SMOKE, amma ka sani gano smoke ba shi da wani amfani, saboda su kansu wanda ka ke tunanin zasu ɗaukar maka matakin suna cikin SMOKE. ministan man fetur ke da shiyyar satar mai, Ɓangaren tsaro suna da kamasho a kasafin da ake yi, da wasu manyan mutane a ƙasar nan. Talakawan da ka ke yi domin su, basu isa su yi maka komai ba, duk wata shaida da kake tunanin kana da ita a kanmu, akwai gaɓar da idan aka kai, kai ne zaka kwana a ciki, dan na san baka isa ka yi jayayya da shugabannin rundunar tsaro ba, ba ka da wata shaida a kan sa. Dan haka kai zaka kwana a ciki, duk yaranmu da ku ka samu ku ka kama, babu wanda ya san suwaye SMOKE, kai kaɗai ka yi nasarar gano suwaye, ɗan uwanka Jamil yaron Khalifa ne, tare da shi suka yi aiki, sai dai shima bai san mune SMOKE ba, mun yi amfani da sace matarka, wurin ɗauke hankalin ka daga kanmu, kuma cikin ikon Allah ta haihu ta rasa ranta. Abu ɗaya zuwa biyu nake son gaya maka. Ka bar al'amarin nan a iya haka, idan ba haka ba zaka yi ta ranka, ko kuma ran matarka da ɗanka, dan kuwa  ita ce duk sanadin komai, dan kuwa duk motsin ku, da duk abun da take yi, muna samun labari ta ɓangaren Jamil. Dan haka sai ka zaɓi ɗaya, fito na fito da masu ƙasa, ko kuma ka rasa rayuwarka da na matarka, dan ka san ba abu ne mai wahala ba. Sai dai fa ka yi haƙuri, domin kuwa rayuwar matarka ta salwanta kamar ko wani karabutin ɗan ƙasa, duk da kasancewar ka mai kaki, kuma jinin babbar masarauta, ire-iren yaranmu ne kisan su baya tafiya a banza. Kuma duk wani abu da zai faru Jamil ba zai taɓa furta sunana ko na ɗa na ba. Dan haka gara ka watsar da duk wani yinƙurinka, ka tattala abun da yayi saura a rayuwarka, kan mu gama ɗiaɗaita ku" ya katse wayar. Duk da hatsaniyar da ta kaure a falon, yanayin da takawa ya shigo, ya sanya kowa yin shiru, wani irin gumi yake yi, jikinsa yana tsuma, kuma aka rasa mai tambayarsa meyafaru, kowa ya zuba masa ido. Ruma ce ta miƙe tsaye, ta ce "Papa lafiya kuwa?" Gabanta ya ƙarasa, jiki a matuƙar sanyaye ya zube a kan gwiwoyinsa ya furta "Na gaza, dama kin gaya mini, na gaza rumaisa ba laifina bane, na yi iya yina, abun ya fi ƙarfin yadda nake tunani, na barwa Allah, tun da a cikin gidanmu ma aka kware mini baya, ba ni da saurin ƙwarin gwiwa. Da izzar da tawa da sarautar tawa da komai na zube su a kan gwiwoyina, na gode rumaisa, na gode. Ke alkhairi ce ga rayuwata da ahalina, wataƙila ba dan ke ba,