AMANI 2 Littafin SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI) takorikabara@gmail.com THE AMINA-BRIDE A can cikin gida Amani ce sunkuye tana jan ruwa a rijiya domin tayi wanka, sai ta ji muryar Kawun ta Malam Idrisu daga zaure yana fadin a shigo da goron da alewa a kai dakin Talatu ta raba ta baiwa kowa. Sannan ya shiga kwalawa matar sa Baba Talatu kira yana cewa kina ina ne Talatu? An daura auren UWA da wannan yaron (Mukhtar) yanzun nan, turo min ita, ga nan sadakin ta in bata a hannun ta. Talatu ta fito daga dakin ta tana daura kallabi ta dubi inda Amani ke tsaye a gindin rijiya wadda a lokacin ta dakata da jan ruwan kadan, tana sauraron me Kawun ta Baba Idi ke cewa, Talatu ta ce ai gata nan a tsaye, tana jin ka. Kawu Idrisu yace au to! Banza kika yi da ni kenan Uwa? To bar jan ruwan ki same ni a daki in baki sadakin ki Amani ta cigaba da jan ruwan ta wani malolon bakin ciki ya zo ya tsaya a makogaron ta, ya ki wucewa ya tokare numfashin ta, ta ma kasa fahimtar me Kawun ta ke nufi data same shi a daki. Kawai sai gani suka yi ta saki gugan a cikin rijiyar ji kake cundum! Ta wuce dakin da aka sauke ta. Kayan ta ta hau tattarawa tana dannawa a jakar da tazo da ita. Baba Idi na can yana jiran zuwan ta ya bata sadakin ta, ta sulale ta fice daga gidan ba tare da kowa ya ankara da fitar ta ba. don Talatu ta koma daki tana shiri don fita ta gayawa yan uwa da abokan arzikin su daurin auren da aka yi yau dinnan da gayyatar su wunin biki a gobe. Daddy da Mukhtar suna dakin da aka sauki Daddy din, suna tattauanawa bayan daurin aure, kan Mukhtar a sunkuye yana jin yadda Hon. Usman ke masa magana cikin tsananin raunin murya, wadda babu komai a cikin ta sai kauna da tausayin diyar sa Amani, wadda a yau ya danka amanar ta a hannun mijin aure mafi soyuwa a zuciyar sa. A daidai lokacin Amani ta fice daga gidan ba tare da sun sani ba, dan acaba ta tare ta ce ya kai ta tasha. Tunda take a rayuwar ta bata taba hawa acaba ba sai yau. Da ya fizgi babur din saura kadan ta wuntsilo kasa, ta kama rigar dan acaban nan ta damke tana salati, nan tsamin hammatar dan Acaba ya kusa sumar da ita. A haka ya fizge ta zuwa tasha yana fadin Hajiya sakar ni don Allah kada kisa duk mu kifa, in baki iya hawa ba ki taka sayyadar ki mana? A can dakin Baba Idi, Hon. Usman ya cigaba da cewa Mukhtar wanda a yanzu ya tashi daga yaron sa ya koma surukin sa. Mukhtar bana neman komai daga gare ka sai tausayi da kyautatawa ga Amani, bata san kowacce irin wahalar rayuwa ba kada ka bar ta ta sha wahala, amma na yarda duk inda zaka shiga a duniya ka tafi tare da ita, ka tausaya mata, ka kasance mai hakuri da halayen ta, na san zaka iya shi yasa na baka, da na san bazaka iya da ita ba ko kusa ba zan fara tunnanin hada ku aure ba. Na lamunce maka kuyi amfani da duk abinda ta mallaka tare, ka taimaka mata ta cigaba da juya dukiyar ta ko bayan rai na. Sannan Baban ku Idi yayi magana a kan cewa yana son muje ga dangin ka mu kai musu matar ka idan iyayen ka basa raye. Yace hankalin sa ba zai taba kwanciya ba in ba ya ga asali da tushen ka ba, ka yi hakuri da abinda ya ce dinnan, ba rashin kauna bace gaskiyar aure kenan, ta fanni na bani da matsala da wannan, ka sani ko ba ka da kowa a duniya na riga na amince ka zama suruki a gare ni. To amma nima inada na gaba da ni wanda shine waliyi a gare ta, kamar yadda na zama waliyin ka, dole a yi masa uzurin da yake so na dangana ta da iyayen ka. Mukhtar ya yi shiru, kansa na kasa, sai kara dukar da kan nasa kasa yake yi yana jin faruwar komai kamar a mafarki. Wai Amani ta zama matar sa ta sunnah daga yau. Wannan alamari sounds unbelievable! Amma baa mamaki da ikon Allah. Zuwa yanzu ba zai ce ga gurbin da ya ajiye Amani a zuciyar sa ba, da wannan sabon matsayin nata na mata a gare shi. Illa iyaka ya san zuciyar sa bata kin auren. Amma kuma maganar da Alhaji ke yi yanzu a bar dubawa ce, Alhaji yayi kokari matuka da ya bashi auren yar sa ba tare da ya san kowa nasa ba, ba kuma tare da ya san wani abu akan sa ba (asali, tushe da nasaba). Sai ya shiga tambayar kan sa ko shi a karan kan sa ya shirya komawa gida din? Idan bai shirya ba sai yaushe? Mutuwa bata sallama, duk da cewa har yanzu zuciyar sa bata huce ba, bata shirya komawa ga iyayen sa ba, amma hakika yana son ganin Ummami. Ko da ba don mahaifin sa ba zai koma saboda ita, ta kasance mace mai rauni karkashin ikon mahaifin sa wasu abubuwan da yawa da yake zarginta da su ya kamata ya yi mata uzuri a kan su, cewa ba ta da karfi a kan rayuwar sa sai abinda mijin ta da kuma aladar su ta wanzar a kan ta, wato tana bin norms, culture and tradition ne na daular su. Me yasa tuntuni bai yi wa Ummami wannan uzurin ba? Da Daddy ya ga Mukhtar ya yi zurfi a tunani, sai yace Mukhy, in fa baka son komawa ni ba zan takura maka ba, amma ya kamata kayi tunanin cewa yanzu yaya zaka tara wadanda dole wataran zasu bukaci sani ko ganin dangin su, na fahimci akwai abunda kake boye mini, ko ince yake damun ka da baka so in sani, amma ina ganin mun wuce wannan stage din yanzu, mun zama daya fa Mukhy, feel free with me ka gaya min damuwar ka da abinda ya rabo ka da gida don Allah. Mukhtar ya muskuta sannan yayi ajiyar zuciya, a hankali ya soma baiwa Alhaji amsa duk da cewa bai shirya bashi amsar ba. Alhaji ka yi hakuri ka bar maganar zuwa Diffa zuwa nan gaba kadan, ka bani dama in fara cikawa Amani alkawarin dana daukar mata first, na kai ta ga mahaifiyar ta bisa amincewar ka. Nayi maka alkawarin bayan wannan in muka dawo zan dauke ku duka har Baba Idrisu da Baba Sahura mu tafi Diffa ku ga asali na mu kuma gabatar da Amani ga mahaifa na. Im very sorry Alhaji, da na boye maka cewa iyaye na suna nan a raye, koda yake da baki na ban taba furta maka cewa basa raye ba, kai ne kake tsammanin hakan. Hon. Usman ya shiga Hamdala yana fadin masha Allah, to shikenan Mukhtar, take your time. Na amince ka dauki Amani ku tafi Sierra Leone daga nan ku nemi mahaifiyar ta. Zan baka adireshin gidan iyayen mahaifiyar ta a rubuce. Sai kayi muku booking jirgi gobe in Allah ya kai mu sai ku wuce, na so in yi muku biki na alfarma kafin tarewa amma yanzu ina ganin ku fara isa ga mahaifiyar ta ko hankalin ta ya kwanta, in yaso ayi komai tare da dangin ta na Uwa dana uba zai fi sa ta farin ciki har ta karbi auren da sauki, ka san halin mutuniyar taka har yanzu ba wai ta amince bane, nayi gaban kai na ne na abinda addini ya ce in yi, wato a matsayin ta na budurwa in zaba mata miji nagari, ba tare da na bi raayin ta ba. To amma na amince sai in ba Da na Mukhtar bane mijin Amani, in shi ne kuwa bani da haufin nan bada jimawa ba zai sarrafa min Amani zuwa yadda nake burin ku zauna tare cikin kauna da soyayya mai yawa. Ina kara cewa ka yi hakuri da Amani, hakuri ba dan kadan ba, har ka aro wani ka kara a kan wanda kake da shi, mai hakuri shi ya kan dafa dutse har ya sha romon sa. Ina mata kwadayin samun tarbiyya wadda ta dace daga gareka. Daga nan Alhaji ya ce ya gyara masa shimfida yana so zai kwanta ya huta, ya jaddada masa cewa ya yi booking masu jirgin tafiya Saliyo tun a daren yau, ya kuma shiga cikin gidan ya gayawa Amani yanzu idan ya fita cewa ta shirya gobe zai cika mata burin ta. shi kuma Mukhy zai cika mata alkawarin ta. Bayan ya bar dakin da Alhajin yake dakin da aka sauke shi ya nufa wato dakin Kamilu, sai ya tsaya daga zaure ya kira Isyaka da ke wucewa ya ce in ka shiga ciki ka turo min Amani, kace sakon Alhaji zan bata. Kunya ta sa ya kasa shiga gidan kamar yadda Alhaji ya umarce shi. Yaro Isyaka ya je cikin gidan ya duba har dakin Laure ya duba da na Baba Talatu amma bai gan ta ba, ya tambayi Laure ko tana ina? Tace nima tun dazu ban ganta ba. naje makaranta yanzu na dawo. Ya koma ya gayawa Mukhtar bata nan. Mukhtar ya ce ya koma ya tambayo Baba Talatu, ko ta gaya mata zata wani wuri, Talatu ta ce rabo na da ita tun da na gan ta a gindin rijiya bayan daurin aure, kafin in fita zuwa makwabta, Kawun ta ya yi mata kiran duniyar nan ta karbi sadakin ta amma yarinyar nan tayi funfurus ta yi banza da shi bata je ba har ya gaji ya fita masallaci. Mukhtar bai san sanda ya baro zauren ya tako ya shigo gidan ba, har da shi aka caje gidan kaf babu Amani babu ko tsinken ta. Daga baya kwakwalwar sa ta gaya masa babu shakka Amani ta samu labarin daurin auren su ne daga bakin Baba Idi, ta kuma yanke hukuncin gudu. Da dai ta bi umarnin mahaifin ta a kan sa. Zuciyar sa tayi bakikkirin, ran sa yayi mummunan baci da Amani, yana mamakin kafiya da taurin kan ta, wai shi mace ke gudu! Macen ma wadda in ba don darajar mahaifin ta ba ko kallo bata ishe shi ba, bai ji ya damu da inda ta tafi ba don ya san dai ba zata yi nisa ba, tunda bata da adireshin Maman nata, yana ji a jikin sa Balogun Sunday yaudarar ta kawai yayi, yafi damuwa da halin da Alhaji zai shiga in aka gaya masa cewa ta gudu! Ya dade tsaye cikin kunan rai, ya tambayi kan sa ko meye aibun sa haka da Amani ke masa irin wannan kiyayyar, bayan na kasancewar sa yaron Baban ta kamar yadda take yawan ikirari??? **** **** **** “THE RUNAWAY BRIDE” A mani Faskari, jingine jikin tagar motar haya ta Sharon mai tafiya garin Bauchi, ta yi kuka tayi kuka a cikin mota har ta godewa Allah. Da wuya wani abu ya sanya Amani kuka, mace ce mai dakakkiyar zuciya kuma jajirtacciya mai jin cewa ko me namiji zai iya itama zata iya, amma yau da ta tabbatar da igiyar auren Mukhtar ta hau kan ta, daga bakin da ba zai mata karya ba, igiyar kuma ba ta kowa ba ta Mukhtar Diffa, babu shakka an shammace ta, domin bata taba kawowa haka da wurwuri Daddy zai yi wanan danyen hukuncin ba, ta dauka ko zai yin sai ya nemo dangin Mukhtar tukunna wanda kafin nan ita ta yi kokari ta gudu gun Innar ta. A wannan lokacin she cannot control her tears domin ji tayi tagama faduwa kasa warwas! Babu class dinnan, ta kare mata, kuma yanzu bata fi sauran mata ba tunda ta kare a yaron Baban ta. Kenan sunan TAFISU ya bar ta yanzu, bai dace da ita ba yanzu, duk sauran mata sun fi ta aji, ajin ta ya fadi! Tunda a karshe duk gatan nata da ego din ta da Daddy ke fadi ta kare a bada sadakar auren ta ga mijin da zata kira yaron gidan su, mara asali mara nasaba da ko tushen sa baa sani ba. Tana da tabbacin Daddy sadakar ta ya baiwa Mukhy, tana da tabbacin sadakin ta ma Daddy ne ya biya, don Mukhy ta tabbata ba zai taba cewa yana son ta ba ko da yana son ta din, balle zata iya rantsuwa ta ci laya kan cewa yadda bata kaunar sa haka shima baya kaunar ta, ko magana da yake mata a kan dole ne bisa tirsasawar Daddy da ko kallo bazata ishe shi ba a dai wannan girman kan nasa da rashin son raini, kamar yadda itama koda kuskure bata taba jin son sa a ranta ba sai jin zafin sa, na kwace mata soyayyar mahaifin ta da yayi, tana bakin cikin wannan abu, tana kishin Mukhy for that, tana jin haushin wannan matsayi da yake da shi a gun Alhaji mai girman da ya kamo nata ko tace ya zarta nata yanzu a wurin mahaifin ta Hon. Usman. Babban abunda ke sa ta kara tsanar Mukhy shi ne rashin walwalar sa, kamewar sa mai hanawa ka tunkare shi da maganar da ka yi niyya, ko ta shirya ci masa mutunci ko rama rashin mutuncin da yake mata kallo daya zai yi mata ta ji bazata iya ba, a takaice yanayin rayuwar sa mai matukar aji da yanayin halittar sa na rashin daukar wargi ko raini yana ci mata tuwo a kwarya, yana hanawa ta taka shi a duk sanda ta so. A wurin ta wadannan halaye ne da bata so a Da namiji, domin zasu hana ta jan zaren ta yadda take so a gun mijin auren ta. Allah da ya halicce ta yayi ta mutum ce mai tsananin izzah da fadin rai, wato mai tsananin son a bata girma, mai son mulkar mutane a karkashin ta, ta yadda in sun ganta har suyi ta bare-baren jiki don cika umarnin ta, a duniyar ta mutum ce ita mai son kowa ya zauna a kasan ta, tana juyawa tana mulki yadda take so, tana kuma taka duk wanda ya shiga hancinta. Tun tasowar ta a haka ta taso da wannan mummunar dabia, tunda a kan ta Daddyn ta ya raine ta, cewa ta fi kowa gata, ta fi kowa iko, wato ta riga ta taso a matsayin mutum mai juya mutane a karkashin ta da basu order su bi, sai ta ke fatan hakan ya dore har a gidan auren ta, har kuma karshen rayuwar ta wato shima mijin duk da ta aura ya ya zama tana juya shi kamar hakan. Amma auren Mukhtar ta tabbata babu shakka sai dai ita ta koma kasan sa, a irin halaye da dabiun sa da ta dade da sani, wanda wannan wani abu ne da bazata taba yarda da shi ba. Daddy ya gama kaskanta ta, don haka ta yanke shawarar barin su shi da Mukhtar din nasa, ta bar musu gidan ta bar musu garin, in ya so Daddy yayi zuciya ya haifawa Mukhtar din sa wata yar a gobe ya aura masa. Tunda ya asirce shi har yana fadin bai iya surukuntaka da kowa sai shi. Ita wallahi sau dubu gara mata Alhaji Sadi akan Mukhy, ko babu komai zata juya shi yadda take so, musamman data fahimci yadda ya gama macewa a son ta, zai yi wuya tasa kara ya tsallake duk yawan shekarun nan nasa. Sannan zai yi ta tarairayar ta ne irin na tsohon da ya dau yarinya, amma Mukhtar??? Wani kukan ya kara kwace ma Amani, ta kifa kai a kan tafukan ta tana ta yi ba kakkautawa. Wato duk wasu plans din ta na gidan aure Daddy ya rusa mata su, ta hanyar aura mata wanda ya fita izza. Mujin da yake da tabbacin bazata iya mulka ba. Iyaka tunanin ta bata ga ina ya dace ta je ba, in ta shiga duniya saboda bakin cikin Mukhtar ita tayi asara domin kuwa sunan ta ne zai koma karuwa hakan kuma ba zai hana Mukhy rayuwar sa cikin sukuni da sakewa tare da mahaifin ta ba, kamar yadda yake yi tana nan, watakila ma har Daddy ya nema masa wata yar mutuncin ya aura masa, ita su manta da ita da rayuwar ta gabadaya, su shafe babin ta, wannan itace babbar nasarar da Mukhtar zai yi a kan ta da zata dauwama tana haunting din ta, ta dauwama cikin cizon yatsa ba tare da ta iya ramawa ba. Don haka ta yanke shawarar tafiya Bauchi gun Hamidah. Kafin ta samu damar da zata wuce Sierra Leone daga Bauchin, ko a kafa ko a kan fiffiken ta, zata nemo Innar ta. Duk da ta san Hamida bazata taba bin bayan ta ba, cewa zata yi a nemi zabin Allah a yi wa iyaye biyayya. Ta tabbata wadannan sune kalaman Hamidah da basa taba canzawa daga haka. Tuni ta haddace su har bata son kari. Zata iya yi wa Daddy kowacce irin biyayya amma banda ta auren kaskanci irin wannan da ya yi mata, babu kaskacin daya wuce mata wannan a duniya, duk mazan duniya a ce ta rasa miji na kece raini kamar yadda take macen kece raini sai Mukhy, wato yaron sa da tafi tsana a duniya a bisa dalilai da hujjojin ta wadanda take ganin sun isa hana ta karbar wannan auren ko me Daddy zai yi mata a kan sa kuwa. Sai da tafiya ta mika sosai, suka yi wa shiyyar garin Katsina fintinkau sannan ta gaji da kukan, ta fiddo hankaci ta share fuskar ta, ta fyace hancin ta sannan ta dauko wayar ta data kashe ta kunna. Kamar jira wayar take a kunna ta, sai ga kiran Hamida Balewa ya shigo. Ta yi ajiyar zuciya, ta sani Hamidah is always there for her whenever she needs her, duk da basu da raayi guda a kan komai, amma a kalla tana sauraron ta attentively tana taya ta damuwa da damuwar ta, in abin kuka ya sameta suna kokawa tare, in na bakin ciki ne ma suna yi tare, kuma tana bata shelter a gidan su a duk sanda ta bukata, da shawarwari masu inganci duk da ba duka take dauka ba, kafin ta daga wayar muryar ta duk ta dusashe don kuka. Hamidah tace Sahibah kina ina? Gani a gidan ku, maigadin ku na fadin baku nan duka gidan kun yi tafiya, yanzu ina zan same ki? Da dusashshiyar muryar ta data ci kuka ta koshi ta ce, Hamdy, mun yi sabani toh, ina hanyar Bauchi yanzu haka nima, wajen ki na nufa, don bani da wajen zuwa. Ta fashe da kuka. Hamidah na jin haka ta fahimci komai, ko dai an daura, ko ana gab da daurawa shine ta gudo. Alright Sahibah, ki isa Bauchi lafiya, zan yi waya da Mama yanzu a gyara miki daki na don watakila ki rigani isa, zan sa direba ya juyo da ni Bauchi nima yanzu duk da na gaji, amma ba zan kwana a koina ba tunda ba kya nan gara in juyo, tafiyar dare ce dai na san ta same mu. Suka aje wayar a tare. Sannan Hamida ta kira Mahaifiyar ta Hajiya Muna ta gaya mata batun zuwan Amani, amma bata gaya mata ko a kan menene ba, mutum ce mai kiyaye sirrin wanda ya amince mata kwarai da gaske, ta roki Maman ta Haj. Muna kan ta lallashi Amani ta ci abinci tayi wanka ta kwanta ta huta kan ta iso. Ta kuma ce, don Allah Mama a nemi Panadol a bata ta sha kafin ta kwanta. Sai dare suka shiga Bauchi, suna ta waya da Hamida, ita tasa direban Baban ta ya zo tasha ya dauki Amani zuwa gidan su dake unguwar Fati Muazu. Har dakin Hamidah mai aiki ta shiga da kayan Amani bisa umarin Hajiyar Hamidah. Sannan aka kaita falon Haj. Muna. Hajiya Muna ba tun yau ta san Amani ba, da irin amintakar da ke tsakanin ta da Hamidah tun suna sakadire a Ulul Albaab Science Secondary School Katsina suke tare, ta dubi kyakkyawar fuskar Amani ta ga duk ta yi zuru-zuru idon ta ya kode don kuka tayi wujiga wujiga da wahalar zaman motar haya don bata saba ba, nan take ta gane ba zuwan arziki Amani ta yi ba wannan karon kamar yadda ta saba, don duk zuwan da take yi Bauchi a jirgi take zuwa har wani lokacin da rakiyar yar aikin ta Rakiya wadda ke daukar mata jaka. Yau kuma ta gan ta helter-skelter daga ita sai jakar kayan ta babu alamun tun wayewar garin yau ta yi wanka. Amma tunda basu gaya mata me ya faru da ita ba da yasa ta irin wannan balaguron wahalar sai itama bata tambaya ba, tace a ran ta in ta yi wari zata ji ne. Ta sa aka shiryo abinci mai rai da motsi ta saka ta a gaba da lallashi da ban baki irin na uwa har sai da ta yarda ta ci kadan, amma jin abincin nan Amani ke yi tamkar dussa sabida yadda zuciyar ta ke cunkushe da bacin ran Daddy da abinda yayi mata. Ba don mahaifi mahaifi bane kotu zata yi karar su su biyun alkali ya bi mata hakkin ta. Amma me? Ta sani duk tsiya tana jin Daddy a ran ta, tana son Baban ta wani irin so, ba zata so ya tsaya a mumbarin shariah da yar sa ta cikin sa ba ko da kuwa ace ta samu tabin hankali ne. Amma Mukhtar kam will pay for that, btunda ya amince aka yi mata auren dole da shi bazata taba yarda ta zama matar sa ba, bai isa ba bai kai wannan matsayin ba, bari Hamidah ta zo su nemi mafita, tana tunanin tafiya Saliyo a cikin satin nan kawai in ta je kuma ta tafi kenan, ko a gidan talbijin da radio ne zata nemo Maman ta mai suna Jalan, tunda Daddy ya ce suna kama sak, kuma sanda ta haife ta kamar girman ta take in ji Daddy. In ya so sai ta yi amfani da hoton kanta da kanta ta nemi Maman nata da shi (a wautar ta). Duk da dai ko hoton ta bai taba nuna mata ba. Amma dai zata je Saliyo kota halin kaka, ko da zata bi lungu-lungu layi-layi ne tana tambayar mai suna Jalan mai kama da ita. Abu daya kenan da zata iya fadi a kan Maman nata watau sunan ta. Haka tayi ta tunani irin na soki burutsu da rashin madafa. Ta yi wanka a dakin Hamida ta yi sallolin da ke kan ta. Tana cikin sallah tana kallon kiran Mukhtar na shigowa wayar ta da sunan da tayi saving lambar sa da shi. Ya kira sau biyu bata daga ba sai bai kara ba. Don shi mutum ne mara jure wulakanci. Can kuma sai ga na Daddy. A lokacin ta idar da sallah. Amma daga Mukhtar din har Daddy din sai ta rufe ido taki amsawa, babu wanda ta amsawa don a ganin ta basu da abinda zasu gaya mata ta yafe wannan laifin da Daddy yayi mata. Ta bar su suka yi ta kira har suka gaji suka saurara mata. Daddy ya mata dogon text wanda a ciki yayi ta lallashin ta abun tausayi, yana tambayar inda ta shiga? Yace tana so hawan jinin sa ya tashi ko? Tana so rabin jikin da yake motsawa shima ya karasa mutuwa saboda damuwar rashin ta ko? Amma ko karantawa Tafisu bata yi ba ta share shi (deleting) don ta san data karanta zata samu rauni a zuciyar ta ta fasa aiwatar da kudurin ta. Sai ta kira Hamidah ta gaya mata ta sauka lafiya da irin tarbar da Mama tayi mata, tace I really appreciate Mamas welcome, sai naji kamar Mama na ce, kin ji dadin ki Hamdy, mother is everything, yanzu wa ya isa ya yi miki auren dole Mama na raye? Auren ma da bawan gidan ku. sai kuka. Hamida ta yi maza ta ce akul Sahibah! Ki gyara kalaman ki, ta ina ya zama bawan gidan ku? Don kawai yana ma Daddy aiki yana biyan sa albashi? Kin san bauta kuwa? Kin san tun a wane karni aka daina bauta sai ta Ubangiji? Tukunnama ta ina neman halal da dogaro da kai ya zama bauta? Sahibah, Ubangiji da ya halicci dan adam ya girmama shi ya karrama shi a kan duka sauran halittu, ki daina kaskanta dan adam ko waye shi wai don yana ci a karkashin ki, musamman shi Mukhtar a yanzu, ki ringa sanin irin kalaman da zaki ke furtawa a kan sa yanzu, sabida mijin ki ne, da iyaye suka daura muku aure na musulunci ke da shi. Ba ruwan malaikun ki (Raqib da Atid) da cewa wai bakya son sa aka aura miki, dukkan furucin ki da ayyukan ki a kan sa zasu rubuta ne kawai ga lahirar ki. In haka ne ina amfanin kalaman batanci da kaskanci ga mijin auren ka ko yaya yake? Balle Mukhtar bai yi kama da yadda kike kaskanta shi ba, bai yi kama da wulakantaccen mutum ba. Wai me kika dauki kanki ne Amani? Inna akramakum indallahi atqaakum! Yanzu dai ki bar komai a hannu na sai na iso, sai mu shawarta abun yi, ki kwantar da hankalin ki kin ji Sahibah? Idan ina nan babu mai miki abinda ba kya so in zuba ido, wallahi sai inda karfi na ya kare wajen taya ki kwatar hakkin ki, amma banda akan mahaifin ki, ko yaushe ki dinga tuna matsayin Daddy a gare ki, da wahalar da yayi dake da rayuwar ki, da tsayin lokacin da ya dauka yana faranta miki, ko a cikin iyaye shi na daban ne, ya fi karfin yayi hukunci a kan rayuwar ki ki tsallake ki zauna lafiya da Ubangijin ki. Ko nasihar Hamida ta shige ta, to fa bata bar ta ta yi tasiri mai yawa a tare da ita ba, duk da ta san Hamida gaskiya ta fada. Sai ta hau lullube tasirin kalaman Hamidah da hujjoji na son zuciya, tare da cewa ko me Daddy yayi mata a rayuwa hakkin sa ne ya yi mata tunda shi ya haife ta ya kuma raba ta da uwar ta, amma bashi da ikon yi mata auren dole. Ta koma ta jingina bayan ta a gadon ta kwanta a gadon Hamidah ta rufe idon ta, ta ja duvet ta lullube har saman kan ta, tana jin duniya na kara kuntata a gare ta in ta tuna igiyoyin auren Mukhy har ukku sun hau kan ta. A haka Hamidah ta iso gidan ta tadda ita. Ta dauka barci ta ke yi, bata san ta dai rufe ido bane kawai tana dandanar azabar zuciya, sai ta aje jakar hannun ta da mayafin ta ta shiga toilet domin ta rage marar ta, kafin ta fito Mukhtar ya cigaba da kiran layin Amani. Wayar na gefen kan ta amma ta saka ta a silent don ma kada su cigaba da damun ta shi da Alhaji don haka bata san ma ana kiran nata ba. Mukhtar kuwa Alhaji ne ya saka shi a gaba da magiya kan yayi ta kiran layin nata ko Allah zai sa ta dauka, yayi mata albishir din ta dawo gida daga inda ta yi kaura a kaita Sierra Leone har dakin mahaifiyar ta in har an same ta a raye, in dai zata yi hakuri da mijin da ya zabar mata, ya ce, Mukhtar ya lallashe ta kawai ta dawo, in yaso ta fadi duk abinda take so ya yi mata, don cikin hukuncin da ya yi babu canji har abada ko bayan ran sa Mukhtar zai cigaba da rikon igiyar auren ta. Shi yadda Alhaji ke shagwaba Amani yana tattashin ta da gudun bacin ran ta abun yana matukar bashi mamaki da tuajjibi, wai dama akwai irin wadannan iyayen a wannan zamanin da muke ciki, ko a kasar shi ne kawai babu irin su? Ko a nashi lardin ne kadai babu su? Hamida taga wayar Amani na haske sai ta lallaba ta leka. Sunan da aka yi saving mai kiran da shi shi ya tabbatar mata Mukhtar ne da kiran nan ba wani ba. DIRTY HUMAN BEING!. Dariya ce mai karfi ta ji tana son kwace mata, ta toshe bakin ta. Ta lallaba ta dauke wayar ta fice da ita can harabar gidan su ta samu kujerar roba fara tas ta zauna a karkashin bukkar shan iska ta gidan su, sannan ta amsa wayar Mukhtar da sallama. Daga jin sallamar da amon muryar da nutsuwar da ke ciki muryar kai har ma da tarin respect ya san ba Amani bace. Ga dukkan mamakin sa, sai ya ji wani tsoro da fargabar abinda zaa ce masa ya samu mai wayar na shigar sa, a hankali ya amsa sallamar Hamidah, sannan duk suka yi shiru na yan dakikai irin na rashin sabo da juna, Hamidah ce ta karya shirun da cewa. Mr. Mukhtar ne ko? Ya amsa mata, rather subdued, cikin sautin sa da alamar mamakin inda ta san shi haka farat daya ta ambaci sunan shi, bai yi tunanin ma Amani ta yi ajiye numba din sa ba balle a ce tanazancen sa da wani nata a yadda ya san bata son sa dinnan bata kuma son zaman sa a gidan su, kuma bata so wata alaqa take hada su. A kasaice yace mata eh, nine. Excuse me pls, Ko zan iya sanin daga ina aka amsa wayar nan? Hamidah tace daga garin Bauchi ne. Bauchi?! Mukhtar ya tambaya cikin mamaki, a me ta je, kuma wa ya kai ta? Ya jerowa Hamidah tambayoyin a jere a sukwane, don kuwa bai ga alamun ta fidda ko sisi daga account din ta ba, balle ya yi tunanin ta hau jirgi. Hamidah ta gaya masa gaskiyar komai na yadda suka yi sabani ita da Amanin, ta tafi Katsina wajen ta ita kuma ta taho wajen ta a Bauchi. Mukhtar har da ajiyar zuciya da ya ji cewa a (Sharon) wato motar kasuwa ta je Bauchi ita kadai, ya tausaya mata a ran sa, don ya san wani abu ne da bata saba ba, duk a cikin kiyayyar sa ne ko meye ma ya san zata iya, yace, pls my sister do me a favour, kada ki gaya mata na kira kuma kin amsa, ki bani address din gidan naku zan zo in tafi da ita gobe, saboda a bisa umarnin mahaifinta Sierra Leone zamu wuce daga nan gidan ku kai tsaye in sha Allah, zan canza booking din da nayi mana ya zama daga Bauchi zamu wuce Lagos, inda zamu hau jirgin Freetown. Hamidah ji tayi farin ciki ya lullube ta kamar ita ce Amanin, burin kawar ta at last zai cika. Zata ga Innar ta! Ta san kowacce irin damuwa Amani ta saka kanta a ciki a kan auren ta da Mukhtar zata zo da sauki muddin zata ga mahaifiyar nan tata data kallafawa rai. In ta ga dama ma tace bazata dawo ba, hakan zai fiye mata kwanciyar hankali in har Amani tana tare da Maman ta, fiye da in ita Hamidan ta ki bata goyon bayan bijirewa Daddy ta bar gidan su ta nausa wani wajen da bazaa gan ta ba, don ta san halin aminiyar ta sarai ba tun yau ba, bata saba in tana son abu ko ta saka kanta abu a hana ta ta karfi ba, tunda ta taso ya riga ya saba da yi mata komai take so komai tsaurin sa, shi yasa yanzu Daddyn ke shan wahalar ta da ya zo yana son tankwara ta ta karfi, bayan tun tasowar ta ba haka ya sabar mata ba. Sun yi sallama da Mukhy a kan in ya sauka a Bauchi goben zai kira ta, ta bashi lambar wayar ta, har rokon sa ta yi da kada ya kama hotel in ya iso, tace akwai gidan saukar baki a nan cikin gidan su, tunda dole sai sun kara kwana a Bauchi kan su wuce Lagos din. Bayan sun gama wayada Hamidah ya gayawa Alhaji ashe wajen kawar ta ta tafi a Bauchi. Nan dai hankalin su ya kwanta suka soma shirin komawa Katsina washegari. Baba Idi ya ce wallahi idon sa idon Amani sai ya zane ta. Sai da suka tsaya a Funtuwa Sahura ta yi sallama da yayanta ta dauki kayan ta sannan suka wuce Katsina, har da Kamilu, wanda Mukhtar ya ce ya dinga kula da Alhaji har ya dawo tunda zai yi tafiya gobe. Duk irin kulawar da yake masa ya nunawa Kamilu, ta ci da sha da shan magani da tsaftace masa jikin sa, kuma Kamilu yayi alkawarin kwatantawa. Alhaji ya sa Rakiya ta kai Sahura dakin Haj. Rabi ya ce ta zauna a nan, Kamilu ma aka bashi daki a cikin gidan daura da na Alhaji. Mukhtar ya gaya masa sai ya dawo daga tafiyar da zaiyi zai kai su kamfani da Boutique din Amani, in yaso su zabi in da zasu yi aiki tsakanin shop da kamfani. Sauran kannen na kamilu da Alhaji ya baiwa aiki ba a gidan sa zasu zauna ba, duk ya basu gidan zama ne can kusa da kamfani. Kamilu ne kawai zai zauna da su saboda kula da Alhaji da tafiyar da Mukhy zai yi wadda shi kan sa bai san tsayin kwanaki nawa zata dauke su ba shi da Amani, idan har ta yarda sun tafi taren kenan. Sai ko Baba Sahura da dake dakin Haj. Rabi. Su kenan a gidan sai Rakiya mai girki. Da maigadi Malam Tajuddeen da sauran maaikatan waje Sai dai Mukhtar ya san mawuyaci ne duk bacin ran da Amani take ciki, da halin kuncin da ta saka kan ta a ciki na babu gaira babu dalili sai kiyayyar auren sa a ce mata ga ido tace doyi yake. Wato bazata iya tankwabe zuwa gun Innar ta ba, iyakaci in aka je din ta ce ba zata dawo ba, ya riga ya san hakan ce zata faru, kuma ya shiryawa hakan. Karfe sha biyu na ranar washegari Mukhtar Diffa ya sauka a filin jirgin saman Sir Abubakar Tafawa Balewa. Sanye yake da farar shadda kal Wagambari babbar, ya aza hula zanna bukar a kan sa mai ruwan kasa-kasa ta zauna daram a cikin tarin sumar kan sa, kamar yadda takalmin kafar sa na fata kirar Italy shima ruwan kasar ne, haka fatar agogon rolex da ke daure a damtsen hannun sa na hagu wanda bakin lallausar gashi ya kwanta a hannun itama brown ce. Yana takun sa cikin nutsuwa da haiba yadda ya saba yana tura matsakaiciyar jakar matafiya. Hamidah da kan ta ta tuko motar ta ta zo daukar sa, ta baro Amani ta shiga wanka bayan ta tashi barci ta more ta sau nutsuwa. Ba yadda Hamida bata yi da ita kan ta karya kumallo ba amma Amani ta ki, ta ce daga ranar yau ta daina cin komai, ta daina shan komai, ta fi son yunwa ta yi mata illar da har har sai ta mutu, in ya so Hamidah ta kai wa Mukhtar da Alhaji gawar ta, tunda Hamidan ta ce abinda suka yi mata din ba laifi bane, kauna ce. Hamida sai ta kada kai ta fita tana dan murmushi. Har falon Haj. Muna Hamida ta yi wa Mukhtar iso, ta gaya mata angon Amani kenan. Jiya aka daura auren, shine Amani ta taho basu sani ba. Yanzu Daddy ya ce Mukhtar ya zo ya tafi da ita zasu wuce wajen Maman ta a Freetown. Haj. Muna tace ikon Allah, masha Allah tabarakarrahman, dalilin tahowar ta a motar haya babu sanin ku ranar daurin auren ta nake son sani, ko bata son auren ne da wannan miji sardidi haka son kowa? Kunya ta kama Mukhtar ya kara dukar da kai kasa. Shi kansa yasan Allah ya kyautata halittar sa ko mutane basu fad aba, amma baya so ana fada sai yaji wani iri, Hajiya ta cigaba da fada tana cewa. Da sabon aure haka a kan ta tayi wannan kasassabar, tahowa har Bauchi babu iznin mijin ko na Baban ta? Maza kirawo min Amanin, in wanke ta tatas, haka ta zo tana langabe min jiya kamar mutuniyar kirkin da ke cikin matsala, ashe ashe gudun nata na aure ne. Hamida da Mukhtar babu wanda ya tanka, amma sun ji dadi da Hajiya zata wanke musu Amani wankin babban bargo, illa yayi kasa da kan sa da ke duke yana danna wayar hannun sa. Zaune yake bisa kilishi kafafun sa a tankwashe, yana fuskantar Haj. Muna, wadda ke kan kujera tana masa nasihar yayi hakuri da Amani irin hakurin da zai yi da kanwar sa, kasancewar bata tashi tare da mahaifiya ba wani abun sai ana mata uzurin sa. Don dabiun ta ba irin na wadanda suka tashi da uwa da dangi bane. Goyon namiji ce. Shi kam Mukhtar har ya gaji da cewa da ake yayi hakuri da Amani, wai wane irin hakuri? Ita tafi kowa shafuwa da mai ko yaya ne? A wurin sa ai saidai duk su yi hakuri da juna don shima ba kanwar lasa bane, in ta so a zauna lafiya a zauna, in ta zabi tsiya a tsiyace, shi duk wanda ta zaba daidai ne a gun sa. Babu diya macen da zata daga masa hankali, don in dubu yake so a rana zai samu, bai yi raayi bane. Koko ya ce lokaci bai zo ba. Amani yana jin ta da matsayi na dabam ne saboda karamcin mahaifin ta gareshi da irin kauna da yardar da ya yi masa, da tausayin halin da yake ciki na rashin lafiya, sannan kuma yana da son rama alkhairi da alkhairi. Ba don haka ba Amani ta yi kadan ta wahalar da shi irin haka, ko ta saka shi yawon da bai shirya ba irin haka, yana bin ta gari-gari kamar wani jelan ta. Yana cikin wannan mitar a ran sa ya ji kamshin turaren Amani a falon. Ko kusa bata kawo a ran ta wanda ke duke gaban Haj. Muna Mukhtar ne ba, ta ina ma zata yi tunanin ya san inda take? Ko ya sani tunanin ta bai taba bata zai iya ajiye girman kan sa ya biyo ta har nan ba, balle kuma tayi tunanin Balewa zata iya tona mata asiri ta fadawa Mukhy tana gidan su a Bauchi. Har ta zauna a kujerar da ke fuskantar Hajiya bata gane Mukhtar ba, sabida keyar sa ce kawai a duke, duk da hasken fatar sa daban ne dana mutane da ke saurin fallasa shi hankalin ta bai kai kan sa ba, watakila kuma don bata taba kawowa ran ta ganin nasa anan bane. Mukhtar ya dago fusatattun idanun sa ya dubi Amani da su a lokacin da take zama a kujerar kusa da shi, bayan ga Hajiyar ma na kan kujera, wato rashin tarbiyyar nata a koina ma yin sa take yi har a bakon wuri, tunda dai gashi tana ganin daga shi har Hamida sun zauna a kan carpet Haj. Ce kadai a kan kujera amma ta dare kan kujera tana fuskantar Haj. Muna. Haj. Gani, Balewa tace kina kira na. Haj. Muna ta jefa mata harara sannan ta dunkule hannu ta mika mata ta ce ungo naki (dakuwa) sannan ta nuna mata Mukhy da ke zaune yana hararar ta shima wata irin sassanyar harara. Ga mai kiran naki nan, ba ni bace, dauko mayafin ki kafin in kyafta ido na, sawun ki a likkafa ki bi shi duk inda ya sanya kafa bisa umarnin mahaifin ki, ina maki kallon mai wayo ashe Amani sakarai ce ke? Ki sa kafa ki taho ke kadai tun daga Faskari ba da iznin mijin ki da sanin mahaifin ki ba? Shin kina son albarka Amani ko kuwa kin fi mahaifin ki sanin abinda yake daidai a gare ki? Sai a lokacin Amani ta gane Mukhtar ne, da kuma ainahin fadan da Hajiya ke yi. A firgice ta juya ta kalle shi suka kuma hada ido, saura kadan fitsari ya kwace mata da irin zazzafan kallon da Mukhtar ke mata. Hankalin ta in ya yi dubu to ya tashi tsaye, nan take ta hau yi wa Haj. Kuka mara sauti tana fadin Hajiya ki yi hakuri ni ba zan koma Katsina ba, idan kin kore ni ma gaba zan nausa Hajiya tace ki wuce birnin Sin, amma tare da mijin ki ba da ni ba, maza Hamidah dauko mata kayan ta kisa a bude musu guest house yanzu, su kwana gobe sai su yi sammako tunda dare ya riga yayi yanzu. Amani ta wuce dakin Hamida tana kuka wiwi tana tattara kayan ta. Hamidah ta shigo dakin tana fadin da gaske Sahibah ba wanda ya isa ya gaya miki ki ji? Na dauka Hajiya ta matsayin uwa take a gare ki, ta dauka zata yi miki fada ki ji ko ba kya so, tunda tace ki bi shi sai ki bi shi, baki san alherin da ya zo miki da shi ba. Nan ta gaya mata cewa Mukhtar ya zo ne don ya kai ta Sierra Leone. Amani tayi tsit! Kamar ruwa ya cinye ta, jikin ta yayi dan sanyi, da gaske yake ko kuwa yaudara ce don ta yarda ta bi shin? Me ya hana tun lokacin da yayi mata alkawarin ya cika? Sai yanzu da ta zama matar sa da bata da iko da kan ta? Hamida ta shiga lallashin ta, tana cewa ki bashi dama Sahibah, hes a very serious person babu batun wasa a abinda ya gayawa Mama, da gaske Sierra Leone zai kai ki. Amani ta rage kukan ta ce Hamida, idan da amana bazaki gaya masa inda nake ba, daga yau na san ajin da zan ajiye ki, ya kamata tuntuni in fahimci kema kina yin mutumin nan, in ba ke ba babu wanda zai gaya masa inda nake. Hamida ta soma kokarin kare kan ta da cewa wallahi tausayi Daddyn ki ke bani Amani..bashi da lafiya kuma yana cikin damuwar inda kika shiga ni bana baki tausayi ko? Ni da a ka yi wa auren dole da wannan green snake din? Hamida ta ce wato sunayen nasa kala-kala ne har haka, shine Dirty Human Being yanzu kuma shi ne Green Snake, sannan Sumumu-kasau, duk shi kadai bawan Allah! Tsaki Amani tayi tace in dai Bauchi ce yau zan bar miki kayan ku, zan shiga duniya tunda hakan kike so, ba zaki bani refuge daga auren dole ba. Hamida ta yi murmushi tace don Allah Mama ta ce in kin tashi shiga duniyar ki wuce har bangon ta (birnin Sin). Suna wannan cece-kuce din Hajiya Muna ta shigo dakin, don ta ga Amani ta bi umarnin ta ko aah, mai aikin ta biye da ita dauke da fakadeden tray da ake jera abinci da abin sha a kai, ta ce, Amani ga nan abinci dauki ki kai masa da kan ki, Hamida ki raka ta masaukin bakin, na sa Ali ya raka shi tun dazu. Hamida ta ce da mai aikin ta wuce gaba ta kai masa abincin zasu zo yanzu. Ta dauka Amani zata bi umarnin Hajiyar ta, amma ga mamakin ta Hajiya na bada baya Amani ta yi rantsuwa ba inda zata je, in kuma Hamida ta takura mata sai ta fita to kuwa ta fita kenan har abada itada sake zuwa inda Hamida take. Hamida ta dauka wasa take yi, amma sai ta ga ta rantse ta kara rantsewa kan cewa bazata kwana inda Mukhtar yake ba, har ta ce saboda daurewa karya gindi sai ki sauke shi a gidan nan? Koda yake dama ai ke kika gayyato shi, don haka sai ki karasa ladan ki ki kai masa abinci. Ki kuma kwana kina taya shi hira. Hamida ta rasa yadda zata yi da Amani, ta tabbata wajen taurin kai da kafiya babu na biyun ta duk fadin garin su Faskari tabbas ta Faskari kowa, sannan a tarbiyyar da aka yi mata baa koya mata bin umarnin na gaba ba, sai dai ita tayi wa wani umarnin. Hamida zata soma yi mata waazi ta mike ta hau hada kayan ta ta soma kuka a haukace, fadi take in dai don na zabi yin mafaka a wajen ki ne kika tona min asiri haka bari in tafi gidan karuwai cikin daren nan, in kika takura sai na je inda yake. Hamida ta rike jakar kayan nata ta ce na kyale ki Amani, ba zan kara takura ki zuwa guest house ba, amma kin manta ya ce wajen Maman ki ya zo ya kai ki? Ta ce don wannan na yarda zan bi shi, ai zaman jirgi ne kuma babu transit, daga nan Bauchi kai tsaye a hau jirgin da zai je Freetown, inba haka ba na hakura, wallahi bana ko son ganinsa Hamida. Hamida ta hadiye dariya, ta soma mayar mata da kayan da take kwasowa cikin jakar ta, tace kada ki manta hausawa dai sun ce komai wayon amarya.?!. Hararar da Amani tayi mata kamar idanunta zasu fado kasa tasa ta ficewa daga dakin da sauri tana cigaba da tillika dariya. Masaukin Mukhtar din ta nufa, so take ta ji yaya tafiyar tasu zata kasance goben, tunda ta gane transit ne Amani bata so a yi a koina, bata kuma jin akwai jirgin Freetown daga Bauchi dole sai daga manyan birane wato Abuja ko Lagos. Hamidah tayi sallama a kofar guest room, daga ciki Mukhy ya amsa, bai kuma taso ya bude ba amma don ya ji muryar Hamida ne, a hankali ta ce Hamida ce, zan iya shigowa? Sannan ne ya taso ya bude, kallo daya Hamida tayi masa cikin kayan barci na DKNY ta ji zuciyar ta ta tsinke, sannnan ta doka da karfi, a zuciyar ta ta shiga neman tsari daga sharrin zuciya dana shaidan masu gaya mata tace da shi, ya kyale Amanin da ta tabbatar bata kaunar sa ita ya zo gare ta. Ta yi maza ta yi taawizi ta nemi tsarin Allah daga sharrin zuciya dana cin amana, ta bi bayan Mukhtar zuwa cikin falo, suka zauna a kujerun da ke fuskantar juna a falon, har ya yi wanka ya canza shaddar jikin sa zuwa shirt da wando marasa kauri blue samfurin DKNY. Yana shirin taje sumar nan tasa da ta jike jagab da ruwa ta mammanne a saman fatar wuyan sa, da alama bai kai ga taje ta ba, fitowar sa kenan daga wanka Hamida ta kwankwasa masa kofar. Kamshin kakkarfan turaren sa na Azzaro Visit da ya fesa yanzu-yanzu, ya mamaye dakin, ya cakude da sanyin air conditioner ya bada wani atmosphere mai dadi a falon da sanyaya zuciyar duk wanda ya shake shi. Hamida ta russuna ta gaida Mukhy with much respect, kwarjinin sa na kara rikita nutsuwar da ta shigo da ita. Shikuwa ya kara daure fuskar nan tamau kamar yadda take as usual. Duk sai ta kara firgicewa, ga kwarjinin sa ya mamaye dakin. Yarinyar bata yi kama da masu kawo shirme ba amma me zata gaya masa da zata biyo shi har inda suka sauke shi a irin wannan lokacin? Da karfin sunan Allah a bakin ta Hamida ta samu nutsuwa ta ture duk abubuwan da shaidan ke kissima mata, ta ce. By the way, ni ce Hamidah Balewa, ni kawar ta ce tun muna secondary school. Mukhtar yace I can relate, tunda har zata iya gudowa wajen ki har nan tun daga Faskari ba da izni na ko na Alhaji ba. Ya fada da dan fusata a muryar sa, na ganin ta ita kadai ba tare da Amani ba, wanda kai tsaye ba sai an gaya masa ba ya gane bazata zo su yi magana akan tafiyar su ta gobe ba. Hamidah ta karya murya tana fadin, ka yi hakuri Mr. Mukhtar, Amani sai a hankali, ina so in san tsarin tafiyar taku ne ta goben in mata bayani, don nayi kokari mu taho tare yanzu ta ki. Da fusata sosai ya ce then bani da say da ita, in har bazata zo da kan ta ba, in baza ta je bama ni zan koma Katsina gobe, amma ki tabbatar mata kafata kafar ta, bisa umarnnin Alhaji. Hamida ta ce in sha Allahu ma zata je, ai tafi kowa son ganin Maman nata. Mukhtar yace matsalar ku ce wannan, zuwan ko rashin sa, bani da asara a ciki, ki dai gaya mata in bazata je Sierra Leone din ba ta sanar da ni a daren yau ta waya, don in saki booking din, in kuma zata je shima ina son sani don in san ina muka nufa goben daga nan. Ta bani amsa ta waya ya wadatar. Zan jirata har karfe tara na safe, don booking din mu zuwa Lagos 12 na rana ne, daga can ne zamu hau jirgin Freetown, babu jirgi mai zuwa Sierra Leone anan Bauchi. Hamida ta ce a ranta transit dole Sahibah! Allah ya fishsheki daga fushin wannan Zakin. Ta dawo dakin su shi kuma ya rufe masaukin nasa ya kwanta. Ya dauki wayar sa ya kira Alhaji, Kamilu ne ya dauka suka gaisa ya tambaye shi ya hanya, ya gaya masa ya isa lafiya, sannan ya hada shi da Alhajin, ya gaya masa ya sauka a Bauchi lafiya, kawar tata Hamidah da iyayen ta mutanen kirki ne, don a gidan su ma suka bashi masauki, sun roke shi kada ya sauka a hotel. Alhaji ya ce ai tuntuni na san Hamida mutuniyar kirki ce ba irin Tafisu ba, shi yasa na ke son abotar tasu, da mutum yana shirya mutum da tuni Hamida ta gyara min halin Amani, to abotar tasu ba irin wadda ake kira ta abokin barawo- barawo bace. Sun dade suna tattaunawa, Mukhtar ya gayawa Alhaji dole sai sun kwana a Lagos kafin washegari da asubah su bi jirgin Freetown. Alhaji yace ta dai yarda zata je din ko? Mukhtar ya nisa, kafin a hankali ya ce Alhaji maganar yarda ta je ko rashin yardar ta duk basu taso ba, abu ne dana sani ba abinda take so kuma take buri a yanzu sama da ganin Innar tata, don haka zata bi ni ne ko bata so, donmai binciken nata dan damfara ne kawai, alkawari ne na yi mata kuma dole in cika shi, zan damkata gun mahaifiyar ta in yaso in ta ga dama don Allah kada ta biyo ni mu dawo. Ni ba a matse nake ba!. Kunya ta kama Alhaji, sai ya hau Mukhtar da fada, na tambaye ka wannan? Kullum ana gaya maka ka koyi lallashin mace kana kara fandarewa Mukhy, ina gaya maka wannan ne (based on experience), da a ce na lallashi Jalan, na bi ta a hankali, na yi hakuri da ita da shirmen ta na rashin so na, ban kuma yi zuciya ba na saketa a asibiti wai don tana ikirarin bata so na, da na jure da har yanzu muna tare bamu rabu ba. Da Allah kadai ya san yawan yayan mu tare. Yau ga shi na tsufa da soyayya a kasan rai na ina ta nadama, don duk matar dana aura na rantse maka a bayan Jalan take, kuma na kasa son ko dayan su irin son da nake ma Jalan. Matar fari ka tattalata Mukhy, domin bazaka samu kamar ta ba, daban Allah yake bamu su. Abinda ya dade bai yi ba shi ya yi yanzun wato murmushi, yace a ran sa wato Alhaji bai sha da dadi ba a hannun soyayya shi yasa yake ji masa tsoro. Shi kam ai mata a kasar su sai wadanda ya zaba in ya so, mata kamar hurul eeni ma, wadanda suka fi Amani komai. Ita Amani ta ladan noma ce, kyautar ubangidan sa da ba zai iya cewa baya so ba, ta ja zaren ta yadda take so in ta gama jan nata lokaci zai zo da shima zai ja nasa watarana. Haka ya kwana da sake-saken abin a ran sa. Na irin yadda zai aro kalmar hakurin nan da kowa yake jaddada masa ya rataya a wuyan sa a kan Amani. Tunda ta zama dolen da ba zai iya kaskantawa ba. Da asubah ya ga sakon ta a wayar sa, da sunan da yayi saving no. dinta da shi watau AUF (AMANI Usman Faskari) mai nuna ta amince zata bi shi Saliyo. A gajarce ga abinda Amani ta ce da mijin ta Mukhtar, ba tareda ta kara komai a kai ba. Yes, Im going!. Ya dan sakawa sakon nata ido yana nazarin sa, wato bazata ko ce masa yaya ya kwana ba, balle ya gajiyar hanya, wai miji a kewa magana haka gatsau cikin gadara, shi ina ya san mace na ma miji magana a haka? A inda ya taso sujjada ce kadai mace bata ma mijin ta saboda respect, soyayya, kulawa da kankan da kai. Mukhtar ya dan kyabe baki a fili yace. Kada ma Allah ya sa ki je!. Yayi alwallah ya fita zuwa masallacin gidan wanda Baban Hamida ya gina like da gidan sa. Hamida da Amani kwanan zaune suka yi Hamida na gaya mata sai ta yi a hankali da Mukhtar Diffa, domin maza irin sa wuyar shaani ne da su, in ba ta yi wasa ba ita zata dawo tana cin kwakwa a hannun sa, tace Mukhtar dinnan mutum ne har mutum, wanda ya gama sanin ciwon kan sa, ya san daraja da mutuncin kan sa bana jin zai dauki halayen ki Amani, babu alamun wasa a tare dashi ko sakin fuskar da mace zata raina masa hankali irin yadda kike yi. Imagine ko sannu da zuwa babu, ko gaisuwa balle ya hanya, abinci wannan kin ki dauka ki kai masa haba Amani! Miji duk lalacewar sa sunan sa miji balle irin naki Amani wanda kyautar Allah ne a gareki kuma zabin mahaifin ki. Me zai hana ki kwantar da hankalin ki ku yi zaman ku lafiya ki yi tunanin hanyoyin mallake abin ki? Amani ta girgiza kai cikin takaicin Hamidah, tace wai sau nawa zan gaya miki bazan taba son mutumin nan ba? Ko da shine Hurul eenin maza bakidaya? Ni na kirawo shi da zan masa ya gajiyar hanya? Ke da kika kirawo shi ba kin masa ba ina ce ya wadatar? Yaron Baban nawa zan je ina ma ya gajiyar hanya? Na ce miki na shirya zaman aure da shi ne da kike min wani fatan hanyoyin mallakar sa? Ta yaya mutum yana aiki a karkashin iko na kuma a aura min shi? Ba don komai Daddy ya yi haka ba sai don ya bashi lasisin cigaba da wulakanta ni, tunda tun kan in zama karkashin sa ma yana yi min duk wani launi na wulakanci da kaskaci ga fadin rai kamar firauna. Na fahimci ko me zan gaya miki hujjata ta rashin kaunar Smart Ass, Bad Egg din nan ba zaki bani goyon baya ba Habeebty, saboda kema ya asirce ki. Hamida abun na Amani ya daina bata haushi yanzu don ta koma bata tausayi, tana hango mata in ta bari tayi asarar Mukhtar bazata samu makwafinsa ba, wajen sanin darajar iyayen ta, ba wai bazata samu miji ba tunda itama banda halayen ta bata da makusa, ta yarda duk abinda take fada bilhakki take fadar sa daga kasan zuciyar ta da gaske bata son nasa, ta sha wahala wajen lallashin Amani kan ta yi masa text tace zata je Saliyo din. Don Amani cewa tayi ba zata masa wani text ba dan rainin wayo kawai. Sai da Hamida tace zata je a daren ta gayawa Hajiya Muna cewa ko abinci data ce ta kai masa bata kai ba. Ta ce kuma wallahi in Hajiya ta ji haka a daren nan zata tasa keyar ki dakin sa, in ya so ki je ki masa dibar albarkar a kunnen sa. Sannan ne fa ta typer masa Yes, Im going din. Don ta san Hamidah zata aikata. Ita kuma bata san meyasa ba duk tsiyar tata da tijarar tata tun da Kawu yace an daura auren su ta ji kalmar ta yi mata girma a rai, aure fa! Ba karamin alaqa ne aka kulla tsakanin su ta har abada ba, ji take bazata iya kara hada ido da shi ba balle kuma zuwa inda yake shi kadai ba tare da kowa a tare da su ba. Yadda Mukhtar ya kwana sake-sake a kan Amani da halayen ta, da yadda zai jure ma zama da ita matsayin matar sa uwar yayan sa haka itama Amani ta kwana nata sake-saken, sai dai nata sabanin nasa ne domin kuwa kwana ta yi tana saka hanyar da zata bi ta kubutar da kan ta daga auren sa. A haka garin Allah ya waye musu Tun asubah tayi wanka sakamakon wani irin doki da ke cin ran ta na son haduwa da mahaifiyar ta. Ta zuba doguwar riga mai fadi na wani tattausan cotton lace ruwan goro da aka yiwa dinki babban riga Senegalese, ta kawo wani dan mayafi cantitly kamar abin tatar koko ta yafa a kafadar ta exactly yadda ta ke shigar ta a can baya. Amma yau bata shafa lip stick ba ko powder bata shafa ba. Man shafawar ta kawai ta shafa wato Elizabeth Arden Lotion. Sai ta hau hada kayan ta a trolley dinta. Sai lokacin Hamidah ta farka ta gan ta ta saka jaka a gaba cikin tunani, ba komai take tunanin ba kuma sai yadda zata yi tafiya mai nisa irin haka tare da Mukhtar Diffa. Farin Baabzinen nan da ya zo rayuwar ta rana daya ya rikita duniyar ta. Ya canzata ya hautsina ta, ina ta taba kawowa kan ta aure nan kusa, ban da kutsowar Mukhtar Diffa cikin rayuwar su mai tsafta ita da mahaifin ta??? Amani ta ji hawaye sun kawo wa idon ta cafka, aure na nufin karewar kuruciyar ta kenan fa. Auren na nufin ita da Mukhy daga yanzu sun zama abu guda! Ya ilahy! Ina zata kai wannan kayan bakin cikin da Daddy ya kunsa mata? Ai abu daya zata yi kawai ta huce shine ta yi hakuri ta jure ta gan ta gaban Innar ta, daga nan kuwa saidai a yi wani labarin ba dai nata da Mukhtar ba. Abun nufi, yanzu kam ta ajiye duk wasu makaman yakin ta don ta samu ya dangana ta da Innar ta, daga nan kuwa ko sama da kasa zata taru a kan ta ba zata dawo ba, tunda Daddy ya daina son ta. Hamida ta tashi zaune ta gan ta ta hada kai da guiwa tana rafzar kuka har da sheshsheka, kewar Baban ta take tun kafin ta bar shi, amma ta zabi ta bar shin, tunda shima ya zabi Mukhtar tsintacce a kan ta. A ran Hamida cewa ta yi Sahibah! Dadi ne yayi mata yawa". A fili kuma sai ta tambayeta shin kin yi sallah ne da kika ci wanka da asubahin fari? Sai a lokacin ta tuna bata yi sallar ba. Ta mike ta shiga bayi don yin alwallah. Wajen karfe takwas nasafe Haj Muna tasa aka kaima Mukhtar karin kumallo, sannan ta shigo dakin nasu hannun ta rike da katuwar leda, ta gan su tsaf da su duk sun shirya don Hamidah tana so ta raka su har airport, Haj Muna ta zauna a bakin gadon Hamidah da suke zaune kowacce hankalin ta na kan wayar ta, don hira ta ki dadi tsakanin su, tun sanda Hamidah tace ta yi kwalliya ta gyara idon ta da ya kode Amani ta fusata kwarai. Ta ce kada ta saka mata ido, ita ina ruwan ta da wani Mukhtar da zata yi kwalliya domin sa? Sai Hamidah ma ran ta ya sosu, ta ce Sahibah! Kiyi duk abinda kike so in sha Allah ba zan kara yi miki nasiha ba. Shikenan duk suka zama kurame a dakin kowacce ta ki kara kula yar uwar ta har zuwa shigowar Haj. Muna. Ta zaune gefen Amani sannan ta shiga fiddo kayayyakin dake cikin ledar data shigo da ita, tana yi ma Amani bayanin yadda zata ke shan magungunan da ke ciki, Haj. Muna tace, ya ta Amani, sai an gwada akan san na kwarai, ni na gaya miki da kudin ki zaki zo neman kari, kin gan su tafiyayyu ne tun daga Nijar na yo odar su don amfanin kai na. Wannan Uwa ce kawai zata iya baki su, yanzu nake so ki sha kowanne a gaba na sannan ki daure sauran ki wuce da su. Amani tayi sakatoto! Tana kallon Hajiyar da kayan hannun ta, kafin ta ce innocently Hajiya maganin menene? Ni ai lafiya ta kalau, Sahibah ce take bata min rai, shine kika ganni kamar mara lafiya Hajiya ta ce na sani Amani lafiyar ki kalau, bahaushe kuma ya ce "in kana da kyau ka kara da wanka". Dalili na anan shine. Na hango miki wani irin miji mai babban alamari irin wadanda ke wahalar da matayen su a dalilin tarin baiwarwakin da Allah yayi musu. Mijin ki ga dukkan alamu babban mutum ne, mai tarin ilhama, ban ga ta inda zaki samu kan sa ba sai ta wannan hanyar kadai, don baki da wayo da kissa da su kisisina irin na yaya mata sai dolanci. To cigaba da dolancin ki, amma ki kama shi ta nan ta nuna can kasan Amani. Hamida bata san sanda dariya ta kubuce mata ba don ta lura Amani kallon Haj. Muna kawai take tana cewa toh! amma kwata-kwata bata san inda zantukan Hajiyar suka dosa ba, ta dai karba ta aje ta kuma yi godiya. Amma ta ce ba zata iya cin komai a ciki ba yanzu sabida tana jin yunwa. Hajiyata sa aka kawo musu abinci suka karya amma Hajiyar na fita ta tattara magungunan ta mayar a ledar su. Ta cewa Hamidah "in kin gama dariyar muguntar taki sai ki je ki gaya masa na shirya. Hamida ta ce ga yar aiken ki ko? To da mecece? Hamida sai ta dauki wayar Amani ta danna ma Mukhtar kira ta na cewa ki ji tsoron Allah Amani, mijin naki ne Dirty Human Being? Smart Ass, Bad Egg. Ai ko karen gidan ku bakya kira da wadannan sunan ba balle mutum dan adam. Ita dai bata ce komai ba amma ta sa a ranta zata canza sunan koda ba da wani sunan mai maana ba, amma dai zata canza wannan din, ganin yadda Hamidah ke Magana a kai kamar zata yi kuka. Hakan yasa ta tabbatar bata son sunan ga Mukhtar. Ko yaya ne tana ragawa Hamidah saboda duk tijararta ta san Hamida Balewa mai kaunar ta ce. Mukhtar na cikin sanya links din hannun rigar da ya sanya ta ash colour getzner ya ga AUF na kiran sa, dauke kai yayi kamar kada ya daga don ya san arziki ba zai sa Amani kiran sa ba. Abu daya yasa shi amsawa ganin lokacin tafiyar su filin jirgi yayi. Don haka ya amsa, amma ba tare da ya ce uffan ba. Sai ya ji Hamidah ce, ta ce sun gama shiryawa kuma direba yana bakin entrance na masaukin sa da mota bakar land cruiser zasu raka su har filin jirgi. Mukhtar sai ya samu kan sa da cewa Hamidah madallah da karamcin ki. Madallah da kawa irin ki. Allah ya baki miji na gari kema. Ki yi min godiya wajen Hajiya mun gode sosai, da zumunci, Alhaji ya ce a yi muku godiya". Zuciyar Hamidah ta cika da jin dadin wadannan kalamai na Mukhtar, sai ta ji wani karfin guiwa ya shige ta na son kara taimakawa aminiyar ta ta zauna da wannan mutum da babu wada ya taba shiga ran ta kamar sa. Hakika Mukhtar Diffa, yana da charisma ta farin jini a duk inda ya shiga, ba ga manya ba ba ga yara ba. Duk wanda wata kankanuwar muamala ta hada shi da shi sai ya so shi, ya kuma bar shi da begen son cigaba da alaqa da shi idan ya bar wajen. Har dakin Hajiya Muna Hamida ta raka Amani ta yi mata sallama daga nan suka wuce maadanar motocin gidan. Tana janye da jakar Amani. Tuni Mukhtar direban ya bude masa mota ya shiga gidan gaba ya zauna yana jiran fitowar su, yana yi yana duba agogon fatar dake daure damtsen hannun sa samfurin RADO. Da suka karaso ta cikin farin glasses din da ke idon sa wanda ya makala shi saman dogon karan hancin sa ya hango Amani tana tahowa, da gantalallen mayafin da ta yafa, tafiyar nan tata kamar ta macen Dawisu bai canza ba, duk da cewa zuciyar ta da kamannin ta sun canza zuwa na bacin rai zallah. A hakan kuma sai tayi wani irin kyau ba dan kadan ba. amma mayafin da ta yafa wanda saman kirjin ta kawai ya lullube ya bakanta masa rai. Haka ya shanye abin a ran sa albarkacin direba da Hamidah. Suka shiga baya su biyun ita da Hamidah direba ya saka jakar kayan ta a boot kusa da jakar Mukhtar, sannan ya shiga mazaunin sa ya ja motar suka fita daga gidan su Hamidah. Sai da suka hau kwalta sosai Hamidah ta gaida Mukhtar, kamar ba zai amsa ba sai kuma ya amsa din, har ya ce mata "yaya fama da bakuwa?" Sai ta yi murmushi ta ce ai na saba da wannan bakuwar tawa mai rigima, mai giggiwa. Ta mudubin motar Amani da Mukhtar suka hada ido unexpectedly ta sakar masa harara, bai yi kasa a guiwa ba wajen maida mata da wadda tafi tata zafi. Ya kuma maida kan sa bisa titi. Hamida tace don Allah Mr. Mukhtar da kun sauka ku kira ni in tabbbatar kun sauka lafiya. Ya ce "in sha Allah". Duk Amani na jin su, amma ko kallon su bata kara yi ba. Sai haushin Hamidah da ya kara cika ta. Sun tarar jirgin da zasu hau zuwa Lagos har ya kusa gama lodi, don haka a gurguje suka yi sallama da Hamidah ta bashi jakar Amani a hannun sa, ya hada da tashi yana turawa Amani na bin shi a baya, yana cewa a ran sa yau shi Mukhtar ne da dakon kaya, Alhaji ya ce yayi komai don ya lallaba ta, amma kuwa dakon kaya ai is frustrating, musamman ga namiji kamar sa, to amma ita yanzu din iyalin sa ce. Annabi SAW kuma yayi umarni da a tausayawa mata, dattijai da kananan yara, a agaza musu. But duk da haka yaji abin weird a gare shi. Seat din shi a cikin jirgin kusa da nata ne, tana daga jikin taga a takure yana gefen ta. Amani tana ji ana a daura belt jirgi zai tashi amma taki daurawa. Ba don tana da burin ganin Innar ta ba, kafin Allah ya dau ran ta da ta roki Allah jirgin ya fado duk su mace da dai ta zauna da shi har abada a matsayin mijin ta uban yayan ta. Jirgin Max Air ya daga da su, Mukhtar sai ya saka hannu a bayan kwibin ta yana fastening mata belt din, ko babu komai diyar Alhaji ce shi kuma servant din Alhaji ne, don haka ba faduwa bane don ya hidimta mata a dalilin Alhaji Usman Faskari ne, jirgin bai dire su a ko'ina ba cikin dan kankanin lokaci sa a birnin Ikko. Da suka sauka shi ya dauko kayan su again suka fito daga terminal, mai taxi ya zo gaban su yana tambayar ina zasu je? Mukhtar sai yace masa any nearest good hotel. Amani bata ji ba, don a lokacin tana waya ne da Hamidah tana gaya mata gasu a Ikko, amma bata ga an ce a tsaya a shiga jirgin Freetown ba, Hamida ta fashe da dariya ta ce to kika sani ko jirgin yamma ne ko na dare? Ta ce, bar zancen wasa Hamidah, kina gani fa ya tsayar da taxi, gidan wa zamu je?" Hamidah ta kasa tsayar da dariyar ta ta ce "ki fidda ni a lamarin ki, tunda babu arziki a ciki, naga alama baki san Annabi ya faku ba, ina laifinsa ya baro komai nasa da ayyukan sa da Alhajin sa, don ya dangana ki da Maman ki?" Amani ta ce "to ni na saka shi? Ban ce a bar ni a ga iyawa ta ba? ban ce a bar ni zan kai kaina ba? Kuma in jirgin yamma ne zamu shiga ba waiting lounge zamu je mu zauna ba? Hamidah ta ce. "Ki tambaye shi mana da kan ki ina zaku je din? Me yasa zaa yi transit? Ni Hamida ina nan Bauchi ina na san me kuke ciki ke da mijin ki a birnin Ikko? Dole ta kyale Hamidah don daga karshe ma ta kashe wayar ta daga gama fadin hakan hakan, bata so Mukhtar ya san da ita Amani take waya kada ya dauka ko da saka hannun ta a rashin mutuncin da Amani ke yi masa, fatan ta Allah yasa wannan tafiya ta zama silar shiryawar su da kuma sanadin alkhairori a cikin auren su. Already mai taxi ya saka kayan su a bayan motar, ya budewa Mukhtar gidan baya ya shiga. Hajiyar tsayawa tayi kikam tana jiran karin bayani na inda zaa je daga gare sa. Amma bata ga alamar Mukhy na da niyyar yi mata bayanin komai ba, sai ma wata muguwar harara da Mukhtar din ya sakar mata, wadda ita kan ta ma amsa ce na cewa ba bayanin da zata samu daga bakin sa. Zata yi magana ya ce a fusace, idan kika sake kika tambaye ni ina zamu je? Zan ce miki sayar da kan ki zan yi a Ikko malama. Don kan naki zai yi tsada, kamar yadda kike yarinya mai tsada, na tabbata zai isheni in ja jarin da zan yi kudi, in tashi daga matsayin yaron Baban ki, ko kya daina raina ni. Sakatoto ta yi da baki tana kallon sa. Kafin ta yi aune taji ya fizgi hannun ta ya saka ta a bayan motar ya rufe. Shi kuma direba bai bata lokaci ba ya ja motar. Hotel din dake manne da Lagos International Airport ya kaisu wa to Legend Hotel. Mukhtar ya sallame shi da kudin da suka zarta abinda ya bukata, Amani ta zauna na tsayin lokaci a cikin motar, ta kasa fitowa daga motar nan, kai ko kwakkwaran motsi ta kasa, ta rasa inda zata saka kan ta ta ji dadi a wannan lokacin. Sai wani irin kokawa take da numfashin ta saboda bakin ciki. Saboda (this will be the first day) da zata kebe da namiji, kuma mai amsa sunan mijin ta a muhalli guda, sannan wai a ce ba kowa bane mijin face MOUKHTAR DIFFA. Wani kwayan mutum guda daya da duk duniya babu wanda ta ke wa kallon bai isa ba, kallon abnormal human being, kuma matsala ga farin cikin ta irin sa. Ta tsani halayyar sa, girman kan sa da charismatic personality din sa, ta raina shi kamar yadda ta raina Karen kofar gidan su, tana ganin sa a ba komai ba, face yaron gidan su, mai hidimtawa Alhajin ta don samun na abinci, wanda karfi da yaji ya kwace mata mahaifi, ya shiga tsakanin soyayyar dake tsakanin ta da mahaifin ta, soyayya mai asali da tushe wadda Alhaji ke yi mata. Zuwan Mukhtar cikin rayuwar su ya canza wannan. Ya sauya rayuwar gidan su gabadaya, ya sauya mata mahaifi da dabiun sa. A dalilin shi mutum ne mai charismatic personality da duk inda yaje sai an so shi. Ta fahimci kamar ita kadai ke kin Mukhy a duniyar subhana, kuma kamar shi din ya zame mata dole a yanzu, aure ba wasa bane duk da bata da ilmin sa, abinda ta sani akan aure shine mijin da igiyoyin auren ta ke hannun sa, sai yadda ya ga damar yi da rayuwar ta da gangar jikin ta har wani lokacin, da zuciyar ta. Ya Rabbal Alamin. Wane irin balaI ne ya tunkaro ta haka? Saukar ta daga motar nan na nufin yau zata kwana daki daya da Mukhtar Diffa! Matsayin miji da mata na Sunnah. Wannan wace irin bakar rana ce da bata san kaddarar da ta yi mata sanadin ta ba? Ai ko Mukhtar bai sayar da kan nata ba kamar yadda ya ce cikin gatse, ta tabbata sai ta gwammace bata san wani mai suna Mukhtar ba, daga irin halayen sa da ta fuskanta na son girma da rashin daukar raini, muddin bazata sauke kai ta yi masa irin girmamawar da yake so, ya kuma taso ya ga ana yi masa ba, ya ga mace (wato mahaifiyar sa) na yi wa mijin ta (mahaifin sa) a gidan su ba, wani zubin tamkar ta yi masa sujjada, to kuwa zata sha wahalar sa. Ya riga ya san babu wannan tarbiyyar a tare da ita, to daga yau zata fara daukan ta bisa dole, in ba haka ba bai da wani courage na kai ta gaban iyayen sa a matsayin matar sa uwar da ya zabawa yayan sa. Tunanin ta ya gama bata cewa Mukhtar ya tsayar da su a Lagos ne don ya samu damar da ya dade yana neman samu a kan ta, wato damar da zai wulakantata son ran sa, a inda bata da mai ceton ta sai Allah, shine dalilin da yasa ya shirya musu kwana wuri guda da sunan transit, bata yi tunanin cewa Mukhtar mijin ta ne da shariah ta halarta zaman nasu waje guda ba a yanzu. Har Mukhy ya je ya kama masu daki ya dawo Amani na zaune cikin mota bata ko motsa ba tana ta tunanin da bai bata mafita ko guda daya ba. Ya dauki kayan su a booth ya kai ya dawo tana nan yadda ya bar ta; ihu ne kawai bata kurma ba. Damuwar duniya da bacin ran da take ciki ya gama bayyana kan sa a kan kyakkyawar fuskar ta, wadda yanzu ta hade tayi jazur idanun ma suka yi jazur abin ki da farar mace. Mai taxi ya kunna mota ya ce ta fita shi zai wuce, sai ta juya kai ta dubi inda Mukhtar ke tsaye, ya harde hannuwan sa a kirji yana kallon ta, yana jira ta gama sake-saken wadda zata fishsheta, kafin ya gaya mata cewa shima bai shirya kwana daki daya da mace ba, don bai taba ba, kuma bai shiryawa rayuwar sa hakan a nan kusa ba, don bai shirya sallama samartakar sa ga macen da bata san darajar shi ba. Da a ce zai iya, da ya gaya mata hakan ko don hankalin ta ya kwanta, cewa daki ciki da falo ya kama musu; shi ciki ita falon, don ma ta daina kissima abinda take kissimawa wanda shi bai taba kawowa ran sa ba. Mai taxi sai ya koma masifa yana fadin ta fitar masa a mota zai tafi, haka dole kanwar na ki, Amani ta ja dogayen kafafun ta ta fito masa daga mota, rataye da yar farar hand bag din ta mai matukar kyau samfurin LV (Louis Vuitton), da cokalelen takalmin ta kamar zai huda kasa, sai Mukhtar ya saki ajiyar zuciya ba tare da ya san ya yi ba. Ya juya, ita kuma ta bi shi a baya, a haka suka isa har cikin lifter, inda suka shiga ya tashi da su ya sauke su a kofar dakin da ya shigar da kayan su. Bata da zabi banda na bin sa ciki, tana tafiya tamkar ba ita ba, sabida yadda tayi cooling. Kan ta yayi down, bata ko iya dago kan ta. Duk da haka ba wai ta rasa komai bane daga izzar ta da takamar ta na halitta ba. Wadanda da su Allah Subhana ya halicce ta. Kuma dai an ce hali zanen dutse ne amma tabbas a wannan lokacin bakin ta kanwa yayi laasar. Sai dai da yake an ce aure yakin mata, ni TAKORI na yarda da wannan zaurancen, domin kuwa hakika yau naga tasirin sa a tare da jarumar mu mai kasaita da izza wato Amina (Amani) domin tasirin sa ya kurda cikin jikin ta yana yaqar ta ta koina ba tare da ta sani ba, dalilin da yasa tayi dan sanyi kenan, a lokacin da Mukhtar ya sanya mukulli ya bude kofar dakin nasu, ya bata hanya ta fara shiga, sannan ya wuce ciki ta bishi a baya, sai dai a wannan lokacin idan ka lura da kyau zaka fahimci gab take da fashewa da kuka wanda ta san idan ta yi shi babu mai taimakon ta!!! **** **** **** Suna shiga dakin Mukhy ya maida kofar ya rufe, sannan ya dau jakar kayan sa ya wuce ciki batare da ya kara bi ta kan Amani ba. Don yunwa yake ji sosai, in yana jin yunwa kuma (at times) zuciyar sa a kusa take. Da ta gaji da tsayuwa dole ta nemi kujerar falon ta zauna, tana maida numfashi, so ta ke ta yi wanka ko ta ji dadi a ran ta da jikin ta, sabida yadda jikin ta ke mata danko danko na gajiyar tafiya, amma ta daure don tana jin nauyin shiga toilet alhalin yana dakin. A ran ta tana jira ya zo ya ce ta shiga ciki ita ta hau gadon, kada ta yi ciwon baya in ta kwana akan kujera, in ya so shi ya kwana a falon, amma gogan nata sai ji ta yi yana kakkabe gadon, da alama kwanciyar sa zai yi. Ita kuwa ko oho. Amani ta dauki kayan wankan ta a jakar ta ta shiga toilet ta kulle da key ta ciki, sannan ta yi wankan ta a hanzarce kuma a darare, don ji take kamar zai bude ta a toilet din, ta samu ta ji dadin jikin ta, sai ta dauro alwallah ta zo ta bada faralin sallar azahar ta wuce su a hanya. Mukhtar tunda ya canza kayan jikin sa zuwa na barci yayi sallah sai ya kishingida yana hutawa a kan sofa-bed na dakin cike da gajiya, ko ci kan ki bai ce mata ba. Daga bisani yunwar cikin sa ta dame shi, sai ya janyo kan telfon din hotel din ya kira restaurant din su, ya bada odar abinda yake so ya ci wato pounded-yam and egusi soup, sai ya tuna Amani bai san favourite food din ta ba tun sanin sa da ita, do haka ya fito ya tadda ita, da kan telfon din a hannun sa ya fito falon da ya bar ta a zaune, ya samu ta yi wankan ta har ta shafa mai, tana sallah lokacin, daidai ta sallame sallar ta ta mike kenan tana nade mayafin ta, ya dube ta ya ce. Hajjaju may I know what you want to eat? Amani tayi banza da shi kamar ba ta ji shi ba, wai ita ce Hajjaju, irin ya maida ita tsohuwa din nan, ko me yake nufi da wannan sunan? Ko duk cikin ire-iren wulakancin sa ne zai dubi yarinya yar kwalisa kamar ta ya ce mata Hajjaju? Ganin ta yi kicin-kicin da fuska kuma bata amsa shi ba, yayi kasa da murya ya ce ba da matar dakin nan nake magana bane? Ko Hajjaju bata ji na? A fusace ta juyo, ta watsa masa manyan idanun ta da ke cike da tsana, raini da fushi mai yawa, ta ce idan na ji, ka kuma ban ga damar amsawa bane sai me? Sai a ka ce dole sai na amsa? To bana cin komai, ko dole ne sai na kula ka? Ina ruwan ka da cin abinci na ko rashin sa? Hanya ce kawai ta hada mu, zuwa Saliyo, kuma da sannu zata raba mu, so ka tsaya iya matsayin ka na abokin kan hanyar Saliyo. Mukhtar ya ce ni kuma na yi rantsuwa sai kin bani amsar me zaki ci, kin yi kadan in yi miki magana ki mayar min da zancen banza, ni zaki gayawa hanya ce ta hada mu alhalin kina matsayin matar aure na dana biya sadaki dagumi na ba na wani ne ya biya min ba? Ya soma takowa zuwa gare ta kafin tayi aune ya saki kan telfon din hannun sa ya yi wuf! Ya kama tsinin karan hancin ta da bakin rashin kunyar ya murde su tare, sai da Amani ta saki kara don azaba, tana son kiran ka cece ni Daddy! Amma Mukhy ya murde bakin da hancin ya hana sauti fita sai da wasu hawayen azaba suka feso mata. Sannan ya sake ta yana fadin this is last warning! Kika kara yi min rashin kunya wanda ya fi shi zan miki. Kuma duk abinda nasa a ka kawo sai kin ci wallahi ba zan yi asara ba. Ya zauna a kujera ya kira kitchen, ya ce su kawo masa tuwon dawa miyar shuwaka. Shi kuma pounded-yam with egusi soup. Ba jimawa aka kawo, tana tsaye inda ya murde mata baki tana hawaye dafe da bakin nata wanda take ji kamar Mukhtar ya tsinke shi daga jikin ta, ya ce zauna mu cinye shi tas tace Allah ya sauwake in ci abinci da kai, abincin ma tuwon dawa, nayi maka kama da yar talaka ne? Ko aka ce maka kowa ma faqiri ne irin ka? Maganganun ta sun tsorata Mukhtar don rashin tarbiyyar magana da ke cikin su ya isa, ya ce sannu yar Qaruna, wato bakin naki har yanzu bai mutu ba ko? Yana bukatar sabon garambawul ya mike ya doshe ta tayi maza ta haura bayan kujera kamar wata yar wrestling. Mukhy ya ce mara kunyar karya, ki tsaya mana in ba tsoro ba? Ki gani in ban yi reshaping bakin ba ta hanyar kara miki girman sa? In the way and manner da gobe da kudi aka ce ki yi min rashin kunya da gorin arziki wallahi baza ki yi ba ta ce ba tsoron ka nake ba, bana son ganin ka kusa da ni ne, balle kodaddiyar fatar ka ta gogi tawa, don ban sani ba wannan farin naka ko ka hada dangi da zabiyu (albinos). Mukhtar ya hadiye zafin da maganar ta yi masa ya ce Allah ko? Su zabiyu ba mutane bane kenan? Zaki ga zabiyu ganin idon ki, ranar da kike shayar min da fararen yaya na masu kama da zabiyu, na lura fata ta ta tsole miki ido, don tafi taki haske, idan ke mayya ce ki ci kan ki, ni kurwa ta kur! Amani ta soma hawayen bakin cikin kalaman sa ta ce Kada Allah ya nuna min wannan ranar, ko makamanciyar ta ko a cikin mafarki! Wato ranar da zan haihu da kai. Aka kwankwasa kofa ya je ya karbo abincin ya dawo. Ya zauna ya fara cin abincin sa cikin nutsuwa da dadin rai ya manta da ita a tsaye, Amani na nan tsaye har zuwa lokacin kamar soja ta ki zama, don ta fara tsorata da irin kalaman sa kamar ba Mukhtar ba, ya ce ki zauna ki ci tuwon nan ki kuma cinye shi tas, ba zan yarda ki kwana da yunwa ba saboa hakkin ciyarwa, kin ji ko yar Qaruna? Idan kuma kika ki, wallahi mai raba ni da ke a dakin nan Allah ne kadai,. Amani bata san sanda ta zauna gaban tuwo tana kuka ba, bakin ta har yanzu bai daina radadin murdar da ya sha ba, bata so a kuma, ta ce fisabilillahi ka takura min, ka na son matsanta min, ni bana taammali da tuwon dawa, sai ka saiwa kan ka sakwara ni ka saya min bakin tuwo? Saboda Allah amanar da Daddy ya baka kenan? Mukhtar ya hadiye dariyar da ta bashi ya ce to naji mu yi musanye, na gan ki babu kumari ne, fingi fingi kamar kazar mayu, ina so kashin ki yayi kwari ne kafin ranar amarcin mu, wato ranar saka kwallo a raga, ranar da zan yaye duk wani hijabin raini dake tsakani na da ke, kafin zuwan ranar nake so ki yi kwari, ki yi kumari, yadda zan ji dadin hutawa sosai a kan kowacce gaba babu fargabar zan iya ballaki, ko kasusuwa su zo suna suka na, shi yasa nake son ki fara taammali da tuwon dawa tun yanzu, don ki samu sinadarin carbohydrate sosai a jikin ki. Ai jin abinda Mukhtar ke cewa sai bakin Amani ya mutu bakidaya daga nan, bata taba zaton yana magana haka ba, balle kuma a ce ita yake gayawa, ta san dai tsakanin su babu ragayya, amma bata san akwai sabo irin wannan ba ba da har zai iya furta mata wadannan maganganu masu nauyi haka, ko kuwa su maza daga ranar da aka daura musu aure shikenan kunyar su da bakunta ga diya mace ya tafi shikenan? Amani ta tambayi kan ta, amma bata iya ta baiwa kan ta amsa ba, sabida kallon da Mukhy ke mata A rude ta zauna ta hau jefa loma bayan loma bayan wata hararar bakin ciki da ta zabga masa, sai ta cigaba da jefa lomar tuwon dawa babu kakkautawa, bata ma bi ta kan sakwarar da ya ce ya yarda su yi musanye ba, ba don komai ba sai don yadda maganganun nasa suka kidima ta suka gigita ta, suka rikita ta duk a lokaci guda, don bata taba zaton su daga bakin mutum kamamme irin Mukhtar ba. Duk da a yawan shekarun ta ta san cewa shaani na aure ya fi gaban nan. Sannan babu babba babu yaro when it comes to marital affair. Amma bata taba zaton Mukhtar zai iya furta mata su ba, in aka yi laakari da irin personality din sa na kamewa, fadin rai, girman kai da rike girma, da yadda ta dauka cewa kwatakwata ya tsaneta ba ya son ta. Ba ta yi tunanin zai taba wannan hasashen na samuwar yaya a tsakanin su ba, wanda ke nufin yana hasaso physical relationship (bodily contact) watarana a tsakanin su. Gara ta cinye tuwon dawa komai yawan sa a kan dai Mukhy ya kara yi mata wannan sabon da kunnen ta ba zai iya jure ji ba, sabida nauyin da maganar ta yi mata a kwanya, don ji ta yi tamkar Mukhtar yayi babban sabo, yo sabo mana! Tana kara maimaitawa a zuciyar ta .... kada Allah ya nuna mata wannan ranar da yake hasashen zuwan ta! Sai da ya tabbatar ta cinye tuwon sannan ya kyale ta, kuma ya yi mamakin ganin yadda ta cinye shi kamar kiftawar ido, bai san tsabar rudewar da kalaman sa suka saka ta bane yasa ta cinyewa cikin rashin sani, ya mike ya wanko hannun sa sannan ya fita zuwa reception don ya yi waya da Alhaji, yayi wayar wajen tsayin awa guda kafin ya dawo dakin, nan ya ga Amani a kan doguwar kujera tayi wata irin takurarriyar kwanciya, ta kuma kankame jikin ta cikin rawar dari sabida sanyin air condition da rashin abun rufa. Da kyar in wuyan ta bai rike ba a irin wannan kwanciyar da tayi a kan kujera. Sai ya kasa wucewa toilet din da ya yi niyya domin ya yi wanka, ya koma uwar dakin ya dauko duvet din sa da filo guda daya, yana gayawa ran sa Amani amana ce ita a hannun sa, da mahaifin ta ya damka masa ba don ba ya so ba, ko don ya gaji da zama da ita ba, sai don aure shine cikar rayuwar diya mace, ya rabu da ita ya bashi ba don ya gaji da ita ba duk irin halin ta, ya bashi ne domin ya cikasa rayuwar ta ta diya mace. Duk abinda ya yi mata dazu yana sane, so yake ta rage masa kaifin baki amma ba shi da wata manufa a kan ta a daren yau, kai daga nan har zuwa wani lokaci mai tsahon da ba zai iya kintatawa ba bai da wata manufa ta dabam a kan ta. Ya zo ya rufa mata abin rufar, sannan ya soma kokarin saka mata filon a kasan wuyan ta da ta dora a kan masangalin kujera, kayan da ta zo da su ne a jikin ta har zuwa lokacin bata canza su ba, duk kuwa da cewa ta yi wanka, wai don kada Mukhy ya zaci tayi kwalliya saboda shi ya kara raina ta, duk da ta yi wanka amma sai ta mayar da kayan da ta tube. Gashin kan ta baki sidik mai laushi da tsayi ya watsu a kan hannun kujerar da ta tada kan ta. A hankali Mukhtar ya russuna yana kokarin saka mata filon da ya dauko a kasan wuyan ta, faffadan kirjin sa ya yi mata rumfa, sai ya ji ya kasa dagowa daga sunkuyon, sakamakon wani lallausar kamshi da ya shaka ta cikin gashin kanta, ya kara kusanta hancin sa zuwa daf da gashin kan ta, wanda ke fidda kamshin tsadadden turaren gashi na musamman, Mukhtar ya zama glued a hakan, yana ta shakar kamshin gashin Amani. Wanda hakan ya yi sanadin da wani bakon alamari ya bakunce shi, tun daga yatsar kafar sa ya tafi har zuwa cikin kwakwalwar sa..... Kamar cikin mafarki Amani ta ji ta shaki sansanyar kamshin turaren maza na Azzaro Visit, wani masculine perfume da kamshin sa ya ratsa ya tafi har cikin ruhin ta, ya kai ziyara hancin Amani da ke barci sadidan a cikin yan dakikai, sai ta muskuta ta gyara kwanciyar, yadda zata ji dadin cigaba da shakowa sosai, don ta dauka cikin mafarki ne. Hakan ya bashi access na ganin kyakkyawar fuskar ta sosai. Mukhtar ya tsura mata ido, yana kallon wannan kyakkyawar halitta ta Ubangiji, sai ya samu zuciyar sa da cewa inama yadda ta ke da kyan nan haka halin ta ma yake da kyau! Babu shakka shi kam da ya gama morewa. Yana dagowa don barin wurin dan yatsan sa ya sarko silin gahin kan ta, wanda hakan ya sa ta bude lumsassun idanun ta masu cike da barci da gajiya, da tabon busashshen hawayen da ya saka ta, suka sauka a hankali cikin nasa, sai Mukhy ya ji abinda bai taba ji a rayuwar sa ba. Ta mutstsike ido, ta kuma bude shi tangararau, nan ta tabbatar wa kanta da gaske Mukhtar ne sunkuye a saman kan ta tsayin lokacin da bata sani ba. She cant believe it, in aka ce kallon da ya dauki lokaci yana mata ba tareda ta sani ba na soyayya ne ko makamancin ta, to kallon me yake mata haka bayan ya gama ci mata mutunci? Shi kuma sai kawai ya wuce toilet cikin borin kunya ba tare da yace mata komai ba, don bai so ko kadan ta kama shi cikin wannan yanayin da ya same shi ba. Jin dumi data yi ne yasa ta duba jikin ta, sai ta ga ashe duvet din gadon ya dauko ya lulluba mata. Ta yi maza ta cire shi daga jikin ta ta ajiye a gefe, in ma wani abun ya saka mata a ciki don ya cutar da ita, to ta Allah ba tashi ba. Ya shiga toilet ne da niyyar ya dauro alwalla ya fito amma a yanayin da ya samu kan sa ya san wanka ya gama kama shi, kunyar kan sa da haushin kan sa suka taru suka lullube shi, yana wankan a shower yana cewa Amani masifa ce, ko kallon ta mutum ya cika yi wato sai janaba ta kama shi. Da ya fito sai ya kasa hada ido da ita, tana zaune tana tufke kanta da ya warware, anan falon ya shimfida darduma zai fara sallah, sai itama ta tuna bata yi sallar ba, ta mike ta nufi toilet ta dauro alwallah. Sai kawai ya fasa tada sallahr har sai da ta fito. Ba tare da ya dube ta ba ya ce mu yi jami, yin hakan sunnah ne, sannan ki bi ni muyi nafila za ta yi musu da harare-hararen ta data saba ya ce is an option, not compulsory. Sai kawai ya tada sallar sa ya rabu da ita. Mukhtar da ya idar da sallah, sai ya zauna a kan kafafun sa yana lazimi, Amani ta tada tata sallahr a gefen sa ita kadai don ta ki yarda ya limance ta, har cewa take a ran ta haka kawai bata san asalin mutum ba zata yarda ya ja ta sallah? Da mayafin ta mai kama da abin tatar koko ta rufa a ka ta tada sallah, ta ki yarda suyi jamin sam, tana sallahr yana observing sallar tata, abin mamaki so many kurakurai a cikin sallar ta, ko zaman tahiya ba daidai ta yi ba. Data idar sai ya kasa shiru, ya ce Amani haka kike sallah a gurguje? Da wannan mayafin mai kama da abin tatar ko....? Takaici ya hana shi karasawa yayi shiru. Yana so ya ce ta yi masa karatun da ta ke yi a cikin sallar ya ji, sai ya ga cewa ba wannan ne lokacin da ya dace da duk wannan ba. Lallai aiki ne jawur a gaban sa. Yana jiran ta gaida shi, irin gaisuwar kauna da girmamawa da ya san Ummami na yi wa mahaifin sa, a duk lokacin da suka idar da sallahr farillah ita da shi, amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa, sai ma komawa data yi ta kwanta a saman kujerar data tashi, ta dauki wayar ta ta soma shiga yanar gizo, ta ture duvet din da ya rufa mata gefe guda don dai ta nuna masa bata bukatar komai da kowanne taimako da ya fito daga hannun sa. Mukhtar bai damu ba, jikin ta ko nasa? Amma ya riga ya sanyawa ran sa kin hakuri da rashin gaisuwar nan tata, a zuciyar sa ya ji takaicin wannan rashin tarbiyya nata, ya kuma gane ba karamin aiki ne jawur a gaban sa ba, in ya bar ta a haka me zata koyawa yayan sa? Murya shake, ya ce ba ki iya gaisuwar bayan idar da sallah ba ko AMINA? Baki san gaida na gaba da ke ba? Baki san muhimmancin yin jami tsakanin mace da miji ba? Baki san yawan ladan da ke cikin hakan ba? Gaisuwa ga miji in an idar da sallah alada ce mai kyau ta iyayen mu da kannin mu. Amani ta murguda baki ta kauda kai, ta ce a ran ta in Ustazu ya koma sai ya nemo duro, zata bashi kyautar lasifika. Bata san cewa a fili maganar ta fito ba. Mukhtar ya fusata ya ce haka kika ce? Fine. Abinda ya fi ustazu ma ki kira ni, amma dole ki gyara dabiu da tarbiyyar ki muddin muna tare, ba zan dauki ko dayan su ba, don ba haka na taso na ga ana yi a gidan mu ba. Oya! Ki gaishe ni ko a zuciyar ki ne, in ba haka ba mu koma gida kawai a fasa zuwa Saliyon. Juya kai tayi tana kunkunin fadin in dai sai ta gaida shi ne, to kuwa saidai a koma gida din. Ya tabbatar ba zata gaishe shi din ba, takaicin ta kamar ya kashe shi, sai aka kira shi a waya shi yasa ya rabu da ita da zancen gaisuwa ya amsa wayar. Tana jin sa yana waya da wani mutum, wanda ta ji ya kira Abdussalam Faytoory, Alhaji ne ya hada su, cewa da sun sauka a Sierra Leone su kira shi, shi zai kai su har gidan su Jalan a Kenema. Shi Abdussalam din tsohon abokin harkar sa ne a Saliyo lokacin da yana harkar fitar da Iron ore, da Aluminium ore. Da turanci suke magana shi da Mukhtar, ya gaya masa suna Lagos, zasu tafi Airport da asubahin washegari daga nan su taso Sierra Leone. Ya dubi Amani bayan ya gama waya da Faytoory, ya na so ya ce ta tashi ta yi wankan kwanciya barci ta canza kayan jikin ta zuwa na barci su koma ciki, in ya so ya bar mata gadon, don ya ga zaman ta a kan kujerar ya takura ta, sai ya ga cewa wani daddadan barci irin na gajiya yayi awon gaba da ita. Ba da sanin Amani ba, Mukhtar ya ware ido tsab yana kallon ta, kallo sosai, irin wanda bai taba yi mata kwatankwacin sa ba. Kamar mai karewa halittar ta kallo, koda yake hakan ne, kallon kyautar da Alhaji yayi masa yake yi a nutse, a zaune, a tsanake, kallon da ya san a yanzu yana da hurumin yin sa ba tare da shamaki ba ko daukar zunibi ba. Ji yayi wani abu mai kama da shaawa na sake darsuwa a cikin ran sa, sauri ya yi mike ya bar wurin zuwa uwar dakin, ya haye gadon ya yi light off, ya kwanta, rokon Allah ya ke kada ya baiwa zuciyar sa ikon abinda take son darsa masa a daren yau, don bai shirya ba, itama kuma ya tabbata bazata taba yarda ba, bai san yana da lafiyar mazantaka ba sai yau da ya kebe da Amani, amma ya gwammace har abada ya dawwama cikin samartakar sa, da dai ace wani abu makamancin hakan ya hada shi da Amani. Wani irin wahalallen barci Mukhy ya yi, da bai taba yin irin sa a wahala da tsayi a rayuwar sa ba, shi kadai ya san yadda zai fassara shi, da izayar da ya sha a cikin sa a dalilin yana daki daya da Amani. Da irin tsayin da daren ya yi masa, kafin a kira assalatu. Da asubahi tunda assalatun fari ya tashi yayi wankan da ya tabbatar ya dada kama shi karo na biyu, ba tare da ya amfana da komai daga yar mutanen Faskari ba. He sighed! In the toilet, saying to himself this lady is dilemma to him. Ya fito ya tada sallah, bayan ya idar ya soma hada kayan sa da ya fidda daga jaka. Saida ya kammala tattare kayan sa da ya zo dasu ya fahimci Amani ta tashi ta shiga wanka itama, don yana jiyo karar saukar ruwa a shower, ya fito falon ya zauna a kujerar da ta tashi da jakar kayan sa a gaban sa yana hada mata nata shirgin kafin ta fito, yanzun an yi saa ta canza kayan jikin ta, ta sanya wasu wankakkun zani da riga na atampa super holland a jikin ta, wadanda da su ta shiga toilet din a hannun ta, fuskar nan tayi fresh da santsin sabulu mai kamshi sai daukar ido take. Mukhtar ya juyar da kan sa wani gefen daban, ji da yayi wani ignition irin wanda ya kwana cikin sa na tsunkulin sa, fatar bakin ta ta yi pink shar, tayi wani irin sumul kamar kasa hannu ka latsa don kaji irin sulbin ta, tasirin kebantuwar mace da miji a ranar farko ya cigaba da aiki a jikin sa yana waskewa da karfin hali irin nasa..., wadannan pinky lips din nata kawai ya ji ya ke son sumbata, musamman da ta sunkuya don daukar gyalen ta, ya hango abinda ya firgita shi ta cikin rigar ta, tsaye suke kyam cikin brazier, wadanda ake kira masu gindin tasa, da sauri ya kauda kan sa ya mike tsaye, saboda gabadaya ji yayi jikin sa na vibrating, yana amsar sakon da kwakwalwar sa ke darsawa, at the same time, ya shiga neman agajin Ubangiji a cikin ran sa, wani bakon alamari ne ya same shi again irin wanda ya kwana cikin sa jiya, shine ya sake ya dawo masa sabo, alamari ne mai wuyar fassaruwa a gare shi wanda bai taba kwana cikin irin sa ba sai jiyan, dukkan ilahirin jikin sa ke vibrating yana karbar sabon yanayin da ke sauka masa yana kashe kuzarin sa, ta hanyar sanya masa unbearable feelings na matukar son hada jiki da Amani. A rayuwar sa bai taba yi wa wata mace irin kallon da ya yi wa Amani jiya da yau ba, watakila hakan ne ya janyo masa fadawa wannan masifar. Bai taba saka idanun sa sosai a kan kowacce mace ba, don kiyaye dokar Ubangiji, sai yau a kan Amani Usman Faskari, da yake da tabbacin a yanzu ta zama matar sa, wato halalin sa. Mukhtar ya fahimci cigaba da zaman su wuri guda shi da Amani hatsari ne babba a gare shi, mai barazana ga mutuncin sa da kimar sa da girman sa a idanun ta, don Amani ba irin matan da lafiyayyen miji zai gani ya iya kauda kai bace. Sai kawai ya mike ido jajir ba tare da ya dube ta ba ya ce, Hajjaju, zamu wuce idan kin gama. Amani ta dauki dan yalolon mayafin ta na raka ni gantali (cantitly) ta yafa, sannan ta zuge jakar kayan ta, bata amsa masa ba don duk ta bi ta tsargu da kallon da yake yi mata tun jiya kamar sabon maye, tafiyar tasu daga dakin nan zai fi bata ventilation da sassanyar iska, domin dai tun jiya bata shakar numfashi daidai yadda ya kamata idan ta tuna akwai Mukhtar da mayatattun idanun nan nasa a cikin dakin, abu daya ya kwantar mata da hankali jiyan, tayi barcin ta har da munshari, da ta fahimci ya bar mata falon ita kadai, ya shige cikin daki har ya rufo kofa da key ta ciki, bai kuma kara fitowa ba sai dazun da ya fito don yayi sallah. Sai kawai ta yi gaba zuwa kofa, ya janyo jakar sa ya fito shima ya rufa mata baya. Ya bada mukullin a reception sannan mai taxi ya dauke su zuwa filin jirgin Murtala Mohammed. Zuwan su ba jimawa suka tarar jirgin da zasu hau ya sauka. Ethiopian Airlines ne ya daga da su birnin Freetown, wato babban birnin kasar ta Sierra Leone. **** **** **** FREETOWN S aukar su ke da wuya suka tarar da Abdussalam Faytoory wato abokin Alhaji ya zo daukar su daga nan filin jirgin saman Freetown, Lungi Airport. Abdussalam ya san lokacin da suka taso da kuma na saukar su. Don haka tun kafin su sauka yana arrival yana jiran saukar su. Abdussalam dan asalin kasar Saliyo ne kuma lardi (province) daya suka fito da iyayen Jalan. Ya karbi jakunkunan su yasa a bayan mota, gajiya ta gama bayyana a fuska da jikin Amani, amma bata so ta yada zango a koina yau sai dakin mahaifiyar ta. Son samu ta kwana a bayan ta, tana mai jin dumin ta itama. Amma Abdussalam kamar ya san damuwar ta, suna tafe a hanya yana tuki su kuma suna ta kallon gine-ginen birnin Freetown, wanda ya banbanta dana inda suka fito, sun shagaltu ga kallon mutane mabanbanta a halitta da suttura da wadanda suka saba gani a arewacin kasar Najeriya, duk da cewa suma Saliyo bakar fata ne amma yawancin su zaka samu dogaye ne masu kyawun sura mazan su da matan su, Faytoory ya ke gaya musu cewa yau a gidan sa zasu kwana, sai gobe in sun huta zasu wuce Eastern Province (Kenema) kenan, wato lardin da mahaifiyar ta take zaune, ya gaya musu shima dan can ne, kasuwancin fitar da iron ore ne ya ke kawo shi cikin Freetown. Kenema, shine jihar su Jalan wanda ke kan boarder din kasar Guinea da ta Liberia (Eastern Province), nanne mahadar mining din diamond industry na kasar Saliyo bakidaya. Ya kuma tabbatar musu Jalan tana raye ita da Yayar ta amma iyayen su sun jima da kwantawa dama, da yayan ta biyu mace da namiji tare da ita wadanda mijin ta Lukman ya mutu ya bar mata, amma Yayar tata bata Saliyo yanzu haka, itama aure take yi a wata kasar daban cikin kasashen Africa. Mukhtar kusan ya fi Amani nuna farin cikin jin cewa Mama Jalan na raye, tsabar yadda ta zaqu su raba hanya da Mukhtar yasa ta kasa nuna farin cikin ta da wannan labarin da aka basu, tunda Faytoory ya ce sai ta kara kwana a Freetown kafin su wuce Kenema wanda ke nufin sake kwana tare da Mukhtar duk walwalar ta ta kau, dan farin cikin data samu kan ta a ciki, na jin cewa Mamanta na raye, da kasancewar ta cikin kasar da aka haifi mahaifiyar ta ta da ya bakunceta duk sai ya bace daga kan fuskar ta, komai ya daina burge ta, ko dama can ita bata taba sakawa a ran ta cewa mahaifiyar ta bata raye ba, Alhaji ne kawai yake tantama, cewa da tana raye da zuwa lokacin ko sau daya ne ta nemeta, tunda ta san garin da ta baro ta, ya bi ya take laifin sa kullum na Jalan yake hangowa, bayan shine da laifin komai. A kullum cikin mafarkin ta ta kan gan su tare ita da Maman nata, suna zantawa cikin kauna da soyayya irin na zantawar nan ta Uwa da diyar ta. Kyakkyawan dakin baki mai hade da toilet Faytoory ya basu a cikin gidan sa daga harabar shigowa, shi kuma ya shige cikin gidan don iyalin sa na Kenema, ya shigar musu da kayan su ya ce su kwanta da wuri don su samu hutawa sosai don gobe in sha Allahu karfe shidda zasu dauki hanya don tafiya ce a gaban su bata wasa ba zuwa lardin Kenema. Ai Abdussalam na bada baya, kamar jira take, ta samu bakin kofa ta zauna ta hada kai cikin guiwa ta soma girzawa Mukhtar kuka irin mai sosa zuciyar mutum, ya hana shi sakat, yasa shi a damuwar da zai kasa sukuni. Kuma idan ya ce kukan da ta soma bai bashi tsoro ba, bai taba shi ba, bai hargitsa shi ba ya yi karya, don sam bai ga me aka yi mata na kuka ba. Ga dai ta a Saliyo, gab da haduwa da Innar ta, to kukan na magani da menene? Kafin wani haushi ya zo ya tsaya masa a makoshi, ganin kukan nata har da shure-shure, na tabara da sakarci, tana yi tana fadin ita a daren nan zai dangana ta da mahaifiyar ta, ba zata kwana a dan tsukukun dakin nan tare da shi ba, ga babu wadatar iska da A/C, abincin da Abdussalam ya shigo musu da shi tasa kafa ta shure ya kife, tace munafurci ne suka shirya shi da Faytoory tun a waya, cewa su kwana a gidan sa kada su wuce a yau, don kawai ta kwana yana kare mata kallo ta wutsiyar ido, irin kallon da ya kwana yana mata a Lagos. Ai ta lura in tana barci sa ta yake a gaba yana kare mata kallo, har da taba mata gashi, ina ruwan sa da ita? Ko ta gaya masa ta karbi sadakin sa da hannun ta ne ba wajen Baba Idirisun ta baro mishi abin shi ba? Mukhtar yayi sukuti! Yana kallon ikon Allah, domin kuka take yi sosai mai hawaye da majina da sheshsheka. Tana fadin ko ya kai ta wurin Maman ta a daren nan, ko ta saka kururuwar da duk makota sai an ji su, in aka zo tace sato ta yayi. Mukhtar bai san lokacin da ya isa gaban Amani ba ya damki kullin gashin kanta dake cikin ribbon ya mikar da ita tsaye cikin zafin nama, yace, idan baki yi kururuwar kin gaya musu cewa na sato ki bane baki cika butulu ba, daga abun kirki zaki yi min tukuicin tsiya? In baro komai nawa don in cika alkawarin dana dauka don kyautata rayuwar ki, ki saka min da wannan ihun da kika san bana so? Kin san yadda kukan mace ke kassara ni ya ji min ciwo a zuciya? Kin san ba abinda na tsana irin kuka a kunnuwa na? Kukan ma na mace, macen kuma matar aure na? Budar bakin Amani sai cewa ta yi ta ina nazama matar taka? Na dauka sai na karbi sadakin ka da hannu na da amincewa ta ne na zama matar taka? Koma ka tambayi Malamai, sadakin ka yana gun Baba Idi sai dai in shi ka aura. Idan mafarki kake to ka farka, ni Amani na fi karfin auren yaron gidan mu, matsiyaci irin ka kuma faqiri, sai zuciyar firauna, me zai kai ni auren mutum mara asali da nasaba irin ka. Tunda ka zo gidan mu mun taba ganin wani naka? Ko beran masallaci bai taba zuwa wajen ka ya ce mana shi jinin ka bane ba, a hakan kake mafarkin ka aure ni? Ni da ke da gata na da arziki na da komai? Allah ya tsare ni. In mafarki kake Mr. Mukhtar ya kamata ka farka. Wa ya sani ko a bola a ka tsintoka? Dama an ce shegun yaya shegen kyau ne da su....... Sai ya sakar mata gashin kan ta jikin sa yayi laasar bakidaya. Yau idan da ace ya taba furta cewa yana son Amani, da ya nemo kalaman sa duk inda suka shiga a kunne da kwakwalwar ta ya mayar da abin sa cikin cikin sa. Madallah da bai taba furtawa ba, sai ya yiwa kan sa murna da fatan alkhairi. Shin Alhaji ya san irin kalar gallafirar matar da ya aura masa mara ko kankanin tunani, ko sanin ya kamata? Wadda bata san darajar dan adam ba? Wadda babu humanity a zuciyar ta? Alhaji da kansa ya taba gaya masa Amani bata tauna magana in zata fade ta musamman in ran ta ya baci, kuma ba ruwan ta da lahanin da kalaman ta zasu yi wa mutum, amma duk da ya kwana da sanin hakan bai taba zaton zata iya budar baki ta ce masa shege ba. Ya koma gefen gado ya zauna dafe da kan sa yana maimaita inna lillahi wainna ilaihi rajioun. Ita da kan ta data fadi kalaman sai ta ji tana son mayar da su, ganin yadda suka taba shi sosai. To amma aka ce magana zarar bunu.... ta riga ta fita. Haka kawai ta dade tana kissimawa a ran ta Mukhy shege ne, shi yassa kyan sa yayi yawa, bata san kaikayin bakin da ya kai ta furtawa yau a gaban sa ba. Tafi alaqanta qaiqayin bakin nata da huce kan damin haushin kwana daki daya da Abdussalam ya sake hada su. Mukhtar ya dago idanun sa jazur, fuskar sa ma ta yi jazir abinki da farin mutum a cikin bacin rai, ya dubi Amani dake tsaye duk guilty ya lullube ta, zuwa yanzu ta daina kukan tabarar data ke yi masa. Ta kama bakin ta. Shi kam da son samu ne ya furta mata saki uku shine kawai zai huce. Amma sai ya tuno fuskar Alhaji Usman wadda rabin ta baya aiki, da jikin sa cikin wheelchair, da rokon da ya rika yi masa a kan yayi hakuri da Amani, abu ne da zai karasa shi lahira nan take idan ya ce masa ya saki Amani, saki har uku!. Ya shiga tuno tarin alkhairori Alhaji gare shi sai ya zama cikin dilemma na tunanin ya saki Amani ko aah? A lokacin ita kuma sai ta ji tana so ta bashi hakuri, if possible, ta ce na maida kalamai na, ganin irin lahanin da suka yi masa, amma izzar ta da ego din ta suka hana ta. Sai ma tsaki data yi ta haye gadon ta bar shi nan zaune a gefen gadon, idanuwa sun kada, har tiriri suke, ta ja bargo abin ta har kan ta ta dukunkune jikin ta a ciki. A irin sake-saken da yake yi a yanzu sai ya ga ba abinda zai daidaita fushin da ke hankoro a kirjin sa, banda kwatar hakkin sa ta karfin tsiya a jikin Amani, ta hakan ne kadai zai huce abinda ta yi masa yanzun nan. Ya kuma goge rainin nan da take yi masa daga zuciya da kwakwalwar ta. Sai dai kuma, sai fuskar mahaifin sa ta gilma masa, wata kamilalliyar dattijiyar fuska mai cike da farin gemu da kamala, nannade cikin nadin larabawan Diffa, wanda ya rufe har rabin dogon karan hancin sa, ya tabbata mahaifin sa bai taba sakawa mace karfi a shimfida da sunan aure ba, wai don ya huce fushin sa daga tarin akuyanci da rikicin da suke masa a gida, (shi da ya tara su da yawa kenan ma), har ba adadi. Idan ya kasa hakuri da guda daya amanar ubangidan sa mai dimbin karamci a gare shi, wadda dama ubanta ma ya san halin ta, ya dauka ya bashi a haka, with good hope na zai iya taimaka masa su gyara halaye da dabiun ta, ashe kuwa ba zai iya kara guda ukun dake jiran sa a nan gaba ba, da kwarkwarori ma in ta kama, ya yi hakuri da su da halayen su kamar yadda mahaifin sa Issouffou Massaoudou ke yi da iyayen su mata ba. Yau shi Mukhtar tilon dan Issouffou Massaoudou mace mace ke ce ma shege sabida ta gan shi yana neman abinci a karkashin mahaifin ta!!! Life is not fair for him at all!!! Ko yace iyayen na sa su suka jawo masa!!! Zubewa ya yi a gefen Amani cikin kasala da mutuwar jiki, wadda zuwa lokacin ita har ta fara sakin minshari, sabida dadin barcin da ta samu nan take. Ko babu komai ta fadawa Mukhy abinda zai hanashi nashi baccin yau, itama huce bakin cikin kwana da shi daki guda again da suka hada baki shi da abokin Alhaji suka yi mata sanadin sa. Ga dakin wani dan akurki, gadon (6 by 4) wanda mutum biyu ba zasu iya kwanciya a kai ba tare da sun mannu da juna ba. Ga rashin naurar sanyaya daki sai fanka ta tsaye a daidai kan su. Mukhtar ya gayawa kan sa idan Amani ta kira shi shege shi ya jawo, sai bango ya tsage kadangare ke samun mashiga, abinda ta gani ne ko take tunani ne ta fada, Baban ta kuma bai mata adalci ba da ya bata wanda bata san asalin sa ba. Babu wani nasa da ya zo ya karba masa auren ta dole tayi masa gori har da mafi muni wato na shegantawa. Karo na farko da tunanin komawa gida ya zo wa Mukhy, ya ji ba abinda ya ke so irin ya bude ido ya gan shi a gaban iyayen sa da yan uwan sa. Ko da basu canza daga yadda ya san su ba. A kalla a yanzu ya san ciwon kan sa zai iya yi musu uzurin da a baya baya iya yi musu idan ya ji uzurin su daga bakin su. Wani irin gumi ya shiga yanko masa tun daga tsakar kan sa har zuwa yatsar kafar sa..... sai ka dauka ruwa aka kwara masa kwanon sha guda. Jikin sa ya hau rawa. Dai dai lokacin da maharbin ya harbi kurciyar dake kan bishiyar tsamiya, wadda ke rataye da kankanuwar jar laya a wuyan ta. **** ***** **** Z azzabi da masassara mai zafi ne ya taru ya rufe Mukhtar daga wannan lokacin, lokacin da ya mirgine ya kwanta a gadon cikin barin jiki da karkarwar sa bai sani ba. Sanyi ke kada shi ko ta ina, yana neman abun rufa, ga Amani ta janye bargon ita kadai ta cukuikuiye a cikin sa. Dan karfin da ya saura masa ba zai ishe shi kwatar bargon nan daga jikin Amani ba. Sai kawai ya kwanta ya kama ta ya kankame jikin sa yana bari da karkarwa, hakoran sa na haduwa da junan su, ji ka ke kaf-kaf-kaf. Zafin zazzbin jikin sa sai da ya huda har cikin bargon nan, ya tadda fatar Amani, bayan kamar rabin awa da kwanciyar Mukhy a jikin ta, ba tun yau ba ita mutum ce mai nauyin barci sosai, hakan ne yasa har Mukhtar ya dade yana samun dumin jikin ta bata sani ba, ga hucin zazzabi dake fita daga hancin sa zuwa fuskar ta da bata rufe da bargon ba. Duk nauyin barcin da ke kan ta haka ta soma kokarin bude ido don ji take kamar an danne ta. Kamar numfashi na mata wuyar shaqa. Ilai kuwa da idon ta ya bude sosai, Mukhtar ne ta gani kankame da jikin ta cikin wani hali na numfarfashi tamkar ran sa na son fita. Idan ta ce bata tsorata ba, kuma bata wartsake nan take ba, ta san ta yi karya. Kokarin raba shi da jikin ta ta soma nan ta ji irin zafin da jikin nasa ya dauka. Kidimewa ta hanata daukar matakin da ya dace wato ta dauki wayar sa ta kira Faytoory, sai ta kama rawar jiki da kaduwa itama tana tunanin maganganun ta ne suka jefa shi a wannan halin. Tace na shiga uku ni Amina, shegen baki na zai kashe mutum! Sai ta fara hawaye tana fadin na mayar da kalamai na, can cikin ciki na Mukhtar, wallahi I dont really mean it. Ina! Mukhy, bai san tana yi ba don zuwa lokacin ya gama zama unconscious, wato ya suma gabadaya. Fitsari ya kwacewa Amani daga tsaye ta sake shi piiiiiii, ta nufi kofa da gudu ta zare sakata tayi waje, sai ta rasa inda zata nufa. Kofa ta gani a rufe wadda tayi cikin gidan ta hau bugawa da karfi. An yi saa Abdussalam idon sa biyu sallah ma yake yi da yake Malamin addini ne sosai. Amani saboda rudewa ce masa ta yi ka zo don Allah ba ya motsi, wallahi ba da niyya na fada ba, ba ni na kashe shi ba, ko da bana masa so na soyayya, ba zan kashe shi ba, ban ma san yadda ake kashe mutum ba. Kafin ta rufe bakin ta Abdussalam ya kai kofar dakin. Ya ciccibo Mukhtar daga gadon ya kwantar a tsakar dakin, sannan ya rike tsintsiyar hannun sa ya tabbatar jijiyar tana motsawa. Kallo daya ya yi masa ya gane halin da yake ciki wato; sihiri mai karfi ke fita daga jikin sa. Ya ce da Amani ta shiga dakin da ta ga ya fito ta duba bayan kofar dakin zata ga kwarya ta dauko masa, zata ganta da ruwan ganyen magarya a ciki, da gudu ta je ta kawo, ya karanta wasu kebantattun surori da taawizai na karya sihiri ya tofa a ciki, sannan ya ce ta taimaka masa ya cirewa Mukhtar riga. In ka ga bare-bare a gurin Amani wanda hannnun ta ke yi yayin cirewa Mukhy riga kamar tsohuwa yar shekara casain, tana kici-kicin cirewa Mukhy riga, tana kauda kai cikin jin kunya da faduwar gaba, kamar ta ce kasar ta tsage ta shige, kafin ta kalli kirjin sa mai cike da lallausar gargasa, baka wuluk, irin ta gashin kan sa, haka ta cire rigar ta jefar, ta koma can gefen su ta rufe ido tana ta tuba, na tuba ya Ubangiji na tuba! Astagfirullah kuwa a jejjere haka ta hau jero ta ta kai sau hamsin, don ita gabadaya ta baiwa kan ta laifin ta ne, muggan maganganun ta ne suka jefa Mukhtar a wannan halin na mutu kwakwai, rai kwakwai. Abdussalam ya shafe duka jikin sa da ruwan maganin nan, har fuskar sa da gashin kan sa, ya bar shi daga shi sai short nicker da ke jikin sa, sannan ya maida shi gadon ya ja bargon ya rufe shi da shi, yana kallon yadda Mukhtar ya bude ido a hankali ya kuma mayar ya rufe, alamar barci mai nauyi yayi gaba da shi. Fatar bakin sa dake motsawa da ace zaka fahimta, ka kuma san abida ke zuciyar sa, zaka gane sunan garin su yake ambata watau. DIFFA......DIFFA.......DIFFA!, (With extreme nostalgia). Daga baya bakin ma ya daina motsin kiran Diffan, ya yi shiru, ya mike sosai a cikin bargon don barcin sa yayi nisa. Faytoory ya maida duban sa ga takurarriya mai barin jiki, Amani, yace kada ki tashe shi sai ya tashi don kan sa, hakika akwai sammu a jikin sa wanda nake da tabbacin yanzu, ya fita. Amani ta dago a zabure, tana tambayar Faytoory menene sammu? Ya ce sihiri iyakar tsorata Amani ta tsorata, don ta san ba ka da mai yi maka wannan sai makiyi, to shi kuwa Mukhtar da ko aboki bai da shi a Katsina bayan Alhaji, wa zai yi masa sihirin? Ta damu kwarai da jin wannan zance, don tana ganin rashin farfadowar sa da safe a kan lokaci zai janyo mata tsaiko ko wani jinkirin na isa ga Kenema. Ba lafiyar sa ce ta dameta ba. Allah cikin ikon sa ma da Asubah da kan sa ya tashi ya shiga toilet ya yi alwallah, sai da ya fito ya lura da ita a dai dai kafar gadon tana gyangyadi, da alama a haka ta kwana a zaune. Ya shiga mamaki yana son tuno abubuwan da suka faru daren jiya ganin barci take amma tana hawaye, amma kadan yake iya tunawa. Yasa kafa ya shure ta ya ce dallah malama ki tashi ki sallah. Amani ta bude ido a firgice, ta dube shi tana kulubi, tana kunkunin cewa in gama jinyar ka, in kwana a zaune saboda kai, amma ka ce min Dalla Malama, wannan rashin godiya har ina! Amma kadan da aikin dan adam, ka yi masa rana ya yi maka dare. Ka yi da yar halak, cikin Usmanu da Jalan!. Dan murmushi Mukhtar ya yi, ya daga hannu zai tada sallah sai ya fasa ya ce in jira ki ki yi alwalar muyi jami tare? Ko har yanzu kina kan bakan ki na bazaki bi limancin shege ba? Idon ta ya firfito waje, ta dauka ya manta sakamakon jiya ya fita daga hayyacin sa, ta dauka zancen ya wuce, ashe babu abinda ya goge daga cikin kan sa, ko da ya kwana ba cikin hayyacin nasa ba. Wannan karon ba musu ta dauro awallar ta fito ta bi shi jamin, don ta tsorata da furucin sa, wanda yanzu cikin kwanciyar hankali yayi shi babu bacin rai ko kankani a tare da shi, sai da ya fara da rakaatainil fajr, sannan suka bada faralin asubahi tare, ya nuna mata yadda ake zaman tahiya na sosai ba irin yadda take yi ba shakwar-kwar a kan kafar ta ba, ya kuma ce ta yi masa tahiyar ta a fili ya ji. Nan ne Amani ta zumbura baki ta ce ai ban ga shaidar zaman ka Alaramma ba tukunna, na dai ga shaidar karatun ka a kan kasuwanci, wadda kuma a kan sa na san ka. Ka bar ni da sallah ta in bar ka da halin ka kai ma tunda dai ba kabarin mu daya ba. Mukhtar ya kasa cewa komai, don Amani ta zarce da tunanin sa a rashin hankali. Gashi kan sa yana dan sara masa kadan-kadan, ba ya son yawan magana, sai ya jingina da bango yana jan carbin sa, yana cewa. Ya Allah ka taya ni, da abinda ka san bazan iya ba a kan yarinyar nan, Allah ka shirya ta, idan mai shiryuwa ce, idan ba mai shiryuwa ba ce Allah ka yi min musanye da mace tagari mafi alkhairi a kan ta. Ka shaida ya Ubangiji ban kasance butulu ba, mai manta alkhairi, shi yasa na ke hakuri da halayen ta. Ka horemin duk wani naui na hakuri da fin karfin zuciya, daga cikin wanda ka baiwa Annabawan Ka tsarkaka. Wai sai taji adduar tasa bata yi mata dadi ba, (idan ba mai shiryuwa ba ce Allah ya musanya masa da mafi alkhairin ta). Me Mukhtar yake nufi da wannn muguwar adduar a gare ta? Yana nufin Allah ya bashi wata macen data fi ki alkhairi, wadda bazata dinga cutar da shi daga kalaman bakin ta marassa dadi ba. Zuciyar ta tayi gaggawar bata amsa. To ta Allah ba taka ba, in ma mutuwa kake roka min don ka auri wata, saboda kana jin nauyin Alhaji in ina raye!. Zai shige toilet domin yin wanka ya dan dakata jin abinda take fada, ashe kin san da auren? Ai na dauka ko sadakina baki karba ba Baba Idi kika barwa, Baba Idi na aura? Ta fuske kamar ba da ita yake ba, ya gyada ya shiga wankan sa. Kafin karfe shiddan da Abdussalam ya deba musu sun kintsa suna jiran sa, ji take kamar tayi tsuntsuwa ta bar su, don ta ga kamar su duka yanga suke mata. Ko da Faytoori ya zo ma sai da ya bashi magani cike da kokon duma ya sha sosai, ya bashi kullin wasu a leda ya ce ya jika kullum ya sha ya kuma yi wanka. Da Mukhtar ya nemi baasi sai kawai ya ce masa na fahimci baka da lafiya ne, wannan kuma ba komai bane tsari ne da dafai irin nawa na baka. A motar Abdussalam suka wuce zuwa filin jirgin kasa, a nan ya bar motar tasa suka hau jirgin kasa mai shiga har cikin Kenema Province. Zuciyar Amani sai tsalle take a cikin kirjin ta tana kissima ko wacce irin tarba Mamanta Jalan zata yi mata? Ko zata yarda cewa itama yar ta ce da ta haifa tunda an ce ta samu wasu yayan bayan ita??? **** **** **** KENEMA PROVINCE, SIERRA LEONE G idan da suka nufa matsakaicin gida ne da bai cika girma ba, akwai karamin gate wanda mota zata iya shiga har cikin sa. Taxi din data dauko su daga fili jirgin kasa zuwa gidan ta ajiye su a kofar karamin gate din. Suka karasa, Faytoory ya danna kararrawa yana gaya musu nan ne gidan da Jalan ke rayuwa, tun bayan rasuwar mijin ta uban yaranta, ta ci gadon wannan kyakkyawan karamin gidan ita da yayan ta. Fajur, baki ji ana danna kararrawa bane? In ji Yayan ta Safwan wanda kan sa ke kan allon kwamfutar bisa cinya (laptop). Rubutu nake yi, bana son tashi. Ta bashi amsa cikin hausar su da ba sosai take fita ba, amma a junan su suna yawan yin ta, saboda yaren su na Krio da ya mamayi harshen su wanda shine Lingua Franca na kasar, musamman a lardin su na Kenema. Hajiya Jalan data fito daga kitchen sai kawai ta karasa ta bude kofar da kan ta. Don ta san halin Fajur da kiwa. Tunda tace hakan bazata tashi a kan lokaci ba. Don ta san kiwa irin ta Fajur, zata bar baki ne su yi ta tsayuwa sai ta mula don kan ta zata tashi ta bude. Fara, doguwa kuma siririyar yarinyar da ke tsaye a wurin ta bi da kallo, doguwa sambaleliya mai kira da tsayin matan Saliyo, (a perfect replica of herself) idan ba idon ta ne ke mata gizo irin wanda ya saba yi mata ba, exactly kamar yadda take a tsaye dirarriya shekaru ashirin da daya a baya. Tana son tuno inda ta san ta amma ta kasa. Sai dai feeling of familiarity da wani maternal sensation dake kara mamayar ta. Kamar ta san ta a wani wajen! Kamar ta dade da sani da sabawa da yarinyar da ke tsayen haka ta ji a ran ta. Amma iyaka tunanin ta bata iya ta tuno a ina ta san ta din ba. Amani ta jingina da kofa tana kallon Maman ta da bata bukatar a yi mata karin bayani, Jalan ce, Jalan din Daddy Usman, wadda ta hana shi iya rayuwa da kowacce mace sabida wannan kyawu nata da haiba da ba duk mata Allah ya yi wa ba, gata nan da kuruciyar ta har yau (at the age of fourty), wasu hawayen farin ciki suka soma tsera a kan fararen kundukukin ta. A hankali bakin ta dake rawa ya motsa cikin furta haruffan. Ma.....Ma... Mama na!. Jalan, wadda ta zama kamar an soma rewinding casette a cikin kan ta, ta soma zaro idanun ta sosai, kafin ta mika mata hannu ita kuma ta tafi da gudu ta shige. Suka rungume juna kamar bazasu saki ba suka saki kuka a tare mai sauti. Mukhtar da Faytoory sai suka koma daga gefe cikin tausayawa, Mukhtar ya ji hawaye na son tsatstsafo masa domin sai ya ji wannan rungumar inama shi Ummami ta yi wa, ya tuno tasa Ummamin, yau shekaru kusan goma sha biyar kenan rabon sa da ita. Yana ji Faytoory na cewa Amani ta cika ta haka a yayin da shikuma yake tsane hawayen sa da bayan hannun sa. Mama Jalan cikin jin kunya ta janye jikin ta daga na Amani, tace musu barka da zuwa ku shigo daga ciki. Safwan da Fajur, suka mike suna kallon su da bakunta a idanun su, har falon ta ta yi ma Mukhtar da Faytoory iznin shiga, jikin ta har bari yake, sam ta manta babu mayafi a jikin ta domin jini ya gama bayyana kan sa, ya gaya mata yar ta ce ta Alhaji Usman Faskari ta biyo ta. Dama ta riga ta sani ko ba dade ko bajima zata zo gare ta, in har tana raye. Shi yasa bata taba damun kanta a kan ta ba, tunda dama babu shakuwa ta shayarwa a tsakanin su. Amma lokaci lokaci ta kan tuna cute fuskar jaririyar mai tsananin kama da ita, wadda bata dauko munin mahaifin ta ba ko a farce, ta kuma tambayi kan ta sau tari ko ta rayu? Zafafan hawaye ne suka zubo mata tana kallon Amani, wadda har zuwa lokacin kukan farin ciki take yi ta hada kai da bango. Mukhtar ya dubi Jalan sosai da tsoro da mamaki domin yatsan ta na karshe mai cindo da ya dauki hankalin sa a duka hannyen ta, da wasu attributes na ta da yawa, musamman data juya baya tana tafiya takun ta a kan duga dugai irin na Ummami, duk da kai tsaye bazaa ce tana kama da Ummami a fuska ba, amma a wulge suna kama din, musamman idanun ta da dirin jikinta mai kauri ba irin na Amani dan shalaf ba, ga kuma cindon nan guda biyu dake hannun Ummami a nata hannuwan duka biyu hagu da dama itama. He was shocked! Truely shocked! Amma wace hujja gare shi na cewa Jalan jinin Ummami ce? Shi kan sa bai san komai akan Ummami ba, ko kasar data fito bai sani ba, babu wannan shakuwar a tsakanin su tun yana yaro, da zata yi hira da shi balle ta gaya masa wani abu makamancin wannan. Ya dai san Ummami ba yar Nijar bace, ba kuma haihuwar Diffa ba, wato bakuwar haure ce da aka auro tun ana cinikin auro matan Saliyo ga masu mulkin kasar Nijar, amma bata taba yi masa matashiya a kan kasar data fito ba ko zancen wani nata, yo ina ma ya gan ta ya zauna da ita? Sabida har ya bar gida ba shi da wannan alfarmar irin ta shakuwar Da da mahaifi da ita. Nan da nan wannan boyayyar suffar tasa ta bacin rai da rashin walwala mai bayyana lokaci lokaci a tare da shi ta zo ta lullube yanayin sa na annuri da yake ciki a yanzu, wato fuskar nan tasa ta bacin rai da hadewar fuska wadda da ita ya fi kamantuwa a koda yaushe. Faytoory kan sa sai da yayi noticing canzawar fuskar Mukhtar, a lokaci guda yayi jazur ya hade kamar hadari, duk wata walwala da ke kan fuskar sa a baya ta bace. A ran sa cewa ya ke Dubi dai yadda uwa ta rungume yar ta a bainar jamaa tana kuma zaune da yayan ta biyu a falo guda, daya tana homework daya na aiki a computer, ita kuma tana dafa musu abinci amma shi? Umh! Ummami bai taba samun zama irin wannan da ita ba tunda ta haife shi, sai ka ce ba haihuwar sa ta yi ba, ko kuma tana dana sanin haifar tasa. Kada ki so ki ga yadda fuska da idanun sa suka koma a wannan lokacin. Kafin ka ce meye wannan Jalan ta cika gaban su da kayan abinci da abin sha na alfarma, fadi ta ke ku ci ku sha, na tabbata kun sha tafiya, na tabbata daga Nigeria kuke. Ko daga Freetown zuwa Kenema sai mutum ya jigata a jirgin kasa. Tana zama a kujera domin su gaisa Amani ta kara komawa jikin ta sai da ta san yadda tayi ta kwanta a jikin ta, kunya ta kama Jalan, ita kuwa Fajur ta kasa hakuri, ta matso tana tambayar Maman nasu Mamma wacece wannan mai kama da ke haka? Ke! Daga mun Mamma na Safwan yace Yayar mu ce ta Nigeria ko? Sai kuka ya kwacewa Jalan. Amani ta mika musu hannu ta jawo Fajur da Safwan jikin ta. Jalan ta hada su su duka ta rungume a jikin ta tana cewa alhamdulillah! Jiki na ya dade yana bani kina raye dama, ko ba dade ko baji ma kuma na san zaki zo gare mu muddin da gaske na haife ki a duniya. Mukhtar ya zamo kasa ya na bata hakuri cewa ta daina kuka, ga yar ta nan Alhaji ya ce a kawo mata. Yana rokon gafarar ta, kuma yana so in babu damuwa zai kira Alhaji a vedio call su yi magana da ita. Ta ce babu komai amma ba yanzu ba sai ta gama ganawa da diyar ta. Faytoory ya yi musu sallama cewa zai wuce gidan sa, ya ce ko Mukhtar ya bi shi gidan sa ko hotel mafi kusa zai kai shi? Sai Mamma Jalan ta ce shi din Mukhtar waye a wurin Alhaji Usman Faskari? Mukhtar ya sunkuyar da kai kasa sosai ya kasa amsawa, sai Abdussalam ne ya gaya mata cewa mijin Amani ne. Angon ta. Alhaji ya gaya masa ya daura musu aure ko tarewa basu kai ga yi ba, tasa fitina sai an kawo ta, shine Mukhtar din ya ce sai an fara dangana ta da mahaifiyar ta kafin tarewar ta. Wata irin soyayya da kaunar Mukhtar ta zo ta lullube Jalan, sai ta tsura masa ido tana murmushi tana jin wani irin son sa a ran ta, kwatankwacin yadda ta ji Amani yanzu a ran ta, tace da Faytoory, tunda haka ne ai ita ce da masaukin su su duka, akwai bangaren maigidan zata bashi ya sauka, in ya so in zasu koma Katsina sai Malam Abdussalam ya zo ya tafi da su filin jirgi. Ai Amani da jin Jalan tace haka ta zaburo ta kuma zumburo baki tace wallahi na zo kenan. Ni da Nigeria har abada! Daddy ya daina so na, me zan koma in yi? Shi dai ya koma, shine dan sa yanzu ba ni ba. Ai tun baa je koina ba Jalan ta kai wa bakin Amani mahangurba da hannun daman ta, ta kuwa same shi a daidai, tana fadin ke kuma ashe baki da kunya? Mijin naki kike wa magana haka babu ladabi babu ganin girma? Hausar Jalan bata da karfi sosai amma sun gane abinda take fadi din, duk da cikin yaren Krio ta karasa fadin bazamu shirya ba ni da ke idan ba ladabi ga babba!. Mukhtar sai ya dago da kyar don kunya ya ce mata ai shi a gobe zai koma Katsina, sabida ya baro ayyukan kamfani da yawa ga Alhaji ba lafiya, don ma dai yanzu ya samu dan sa Kamilu na kula da shi. Amma Mukhtar ya zabi komawa immediately ne don har zuwa lokacin a cike yake da Amani. Ya san Alhaji bai da matsala yanzu tunda yana tare da dangin sa, ga kuma kanwar sa a gidan wato Sahura. Ayyukan kamfani kuwa duk yana tafiyar da su ne ta yanar gizo da kwamfuta, sannan yana da mataimaka na kwarai. Amma so yake yayi nisa da Amani. Bayan sun ci abinci Faytoory yayi musu sallama ya tafi. Mama Jalan tace bata yarda ba sai ya yi kwana uku sun gana sosai. Tasa Safwan ya kai masa kayan sa dakin marigayi dake harabar shigowa gidan bayan fajur taje ta share ta kunna turaren wuta. Fajur da Safwan suna zaune manne da Amani, sun kasa matsawa ko nan da can kada ta tafi ta bar su. Safwan zai yi shekaru sha biyar Fajur kuma goma. Ta umarci Safwan ya raka Mukhtar ya huta, sai suka shiga daki ita da Amani da Fajur. Ta hada mata ruwan zafi mai kamshi tayi wanka sannan suka zauna suna kara gaisawa. Sallah ce kawai ta tayar dasu a wannan ranar don kwana suka yi a zaune, Amani na baiwa Maman ta labarin rayuwar ta da mahaifin ta gabadaya tun daga sanda ta fara wayo har zuwa yanzu, da yawan matan da ya dinga aura yana saki sabida ita, da artabun su da matar shi ta karshe Haj. Rabi, da halin da yake ciki a yanzu na shanyewar barin jiki, ta bata labarin haduwar shi da Mukhy a Paris, da kawo shi gidan su da yayi, ya bashi gida daura da nasu, ya kuma sakar masa ragamar kamfanonin ta da shagunan ta, yadda ya dinga fifita alamarin sa, da irin yardar da ke tsakanin su wadda take ganin ta rage mata daraja a gun mahaifin ta, har zuwa aura mata Mukhtar da yayi ba tareda yardar ta ba wanda shine abinda ya kara sawa ta tsani Mukhtar ta kuma amince Daddy yafi son sa yanzu a kan ta. tace Mamma wallahi bana son sa, ko kadan, ko ganin sa bana son yi, kyawun sa ko ilmi sa ko yanayin kasaitar sa dake burge Balewa bai taba ruda ta sun saka ya birge ni ba, ban taba son sa ba, kuma har gobe bazan so shi ba, sabida yaron Daddy ne a kasa na yake, kuma mara kirki mara dadin muamala ba ya girmama ni. Mara asali mara nasaba gashi nan dai shi ba tsintacce ba shi ba Da ba. Cikin halayen sa bakidaya babu guda daya da zan iya ce miki mai kyau ne. Ga girman kai ga fadin rai, baa saka shi baa hana shi, a haka Daddy yake tunanin zan iya zaman aure da shi? A rayuwata in ba mijin da zan juya kamar waina a tanda ba, bazan taba yarda in aura ba. Duk mazan duniya Daddy ya rasa wanda zai aura min sai wanda baida asali kuma a karkashi na yake? Ai karshen kaskantawa Daddy ya gama yi min ita, shi yasa na ce ba zan koma Katsina ba har duniya ta nade. Ta fashe da kuka tana cewa ko sadakin su ban karba ba, don haka babu wani auren sa a kai na ni. Baba Idin ma ya san ban karba ba shi na barwa abin sa, sai dai in Baba Idin ya aura. Jalan tayi taawizi. Tun baa je koina ba Mama Jalan ta gama karantar wacece Amani, halayen ta da dabiun ta marassa kyau na girman kai, alfahari da dukiyar uban ta, fariya da izzah na rashin sanin darajar da Allah yayi wa dan adam. Yawan alfahari da rashin kunya na rashin mafadi ko tarbiyya mai inganci. Tausayi mai tsanani ya kamata sai ta kasa ce mata komai. Sabida ita ta koina Mukhtar yayi mata, har tsoron kwarjinin sa da ilhamar sa ta ji, don kwarjinin sa da kasaitar sa cika mata ido da falo suka yi, ta yi duba don gano makusa a tare da shi da ta sa Amani fadin abubuwan da take fada a kan sa ta rasa. Sai kawai ta gane cewa Amani wawuya ce, doluwa, gaula kuma goyon namiji. Mai halin yan fari, kuma wadda gata da kudi ya jika har ya yiwa yawa har ya taba hankali da nutsuwar ta. Bata samu tarbiyyar uwa da wadatar ilmin addini ba sai na zamani. Sanan bata samu religious background na musulunci sosai ba. A yanayin da take magana ma ga kowa, gatsau ba respect ba taunawa tana gatsine baki na raini ga Mukhy ya tsorata Jalan. Kamar Mukhtar itama nan take ta gayawa ranta cewa jan aiki ne a gaban ta jawur, don haka zata roki Mukhy ya bar mata Amani zuwa nan da watanni biyu haka. In hakan ba zai cutar da shi ba. Yo Allah ta tuba ina wani kwanciyar hankali da miji zai samu a tare da Amani mai abubuwa irin na zararru? Ai gara ma ya bar ta aga abinda zaa iya a kan ta ko kadan ne, tunda baa bari a kwashe daidai, kuma icce tun yana danye a ke tankwara shi. A halin yanzu tana so ta karance ta ciki da bai, don ta san ta inda zata bullo mata, da yadda zata gyara gurbatattun dabiun ta da halayen ta ko da ba duka ba, kafin ta shiga dakin miji ya zama ko manner of speaking ta gyara mata. Tunda an riga an baro kari tun ran tubani. Duk da haka zata yi iya yin ta cikin yan watannin da zasu yi tare, sauran sai ta barwa Allah mai kowa mai komaia, ta kuma hada da addua da rokon Allah ya baiwa Mukhtar zuciyar dauka da soyayyar da zata rufe masa ido daga ganin aibun munanan halaye da dabiun yar ta. Sai bata ce mata komai a kan Mukhtar ba a wannan daren, ta barwa ran ta, don so take ta gano root causes na matsalolin sangartar Amani da rashin good upbringing din data samu, sannan ta yi tunanin hanyoyin magance su a ilmance. Duk da ita ma din ba wai ta samu zurfin ilmin zamani bane amma tayi sakandire kuma tana da ilmin addini sosai, sannan ga shekaru ga kyakkyawan hankali. Amani ta nemi ta bata nata labarin. Bayan rabuwar ta da mahaifin ta. Nan ta gyara zama ta soma bata labari ta gaya mata cewa bayan Daddy ya sake ta a gadon asibiti basu taho ba sai da ta warke tas, suka dawo Saliyo tare da iyayen ta. Maman ta tayi mata jego, har ta warke. Mahaifin ta yayi fushi da ita fushi mai tsanani a kan rashin biyayyar data yi masa na kin zama da Alhaji. Ta hana shi samun makudan kudaden da yake samu a hannun Alhaji Usman. Yace yanzu gashi ta janyo ya raba ta da diyar data haifa kuma babu tabbacin yarinyar zata rayu ko aah, ko zasu sake haduwa, tunda babu wanda zai shayar da ita. Ni kuma kullum na yi sallah sai na roki Allah ya raya abinda na haifa koda bamu sake ganawa ba, yasa rayayye ne kuma ya amfani musulunci da alumma. Daga baya bayan wasu watanni, Luqman tsohon saurayi na dana ke so ya dawo neman aure na. Da kyar na samu mahaifi na ya yafe mini, yace Yaya ta Aisata tayi mishi biyayyar da ni ban yi mishi ba, don ita kam sayar da ita ma yayi a Nijar ga wanda bai ko sani ba, don haka kada in taba tsammanin zai barni in zauna a gidan sa, in kawo miji kawai talakan dana ke so yayi min aure ya huta. To dama ni da Luqman mun dade tare kuma a kan sa ne naki zama da Alhaji Usman, da kuma nasa halayen wadanda na san ba sai na fada miki ba, tunda baban ki ne ya kamata ace kema kin san su. Muka yi auren kauna da soyayya ni da Luqman, wanda shine mahaifin su Fajur, maaikacin kamfanin Tama da karafa ne (Steel Rolling Company), wannan gidan, shine gidan da muka rayu a cikin sa tsayin shekaru goma sha tara ni da Luqman, cikin rayuwar aure ta soyayya da fahimtar juna wadda mahaifin ki bai iya ko daya ba, shi dai ya yarda kudin sa ne zai samo masa duk irin matar da yake so a duniya. Shekara na zagayowa na haifi Safwan, sai bayan shekaru biyar da haihuwar sa har mun fidda rai sannan daga baya na haifi Fajur, a shekaru ukun baya ne Allah yayi masa rasuwa bayan gajeruwar rashin lafiya. Iyayen mu kuwa sun jima basa raye, Aisata ya sayar da ita a kasar Nijar ko zuwa Saliyo bata kara yi ba tun karbar ta da aka yi aka tafi da ita aka bashi Rakuma masu yawa, wato shi mahaifin namu a matsayin sadakin ta, lokacin rasuwar mahaifin namu ne ban san ya akayi ta samu labari ba ta aiko min wasika ta taaziyya ta gaya min watarana zata aiko a kaini inda take aure a Nijar, kuma tun daga wannan lokacin ne ta soma yi min aiken kudi lokaci-lokaci duk da bana cikin bukatar komai, ina tare da miji na cikin kwanciyar hankali da rufin asiri lokacin, bayan rasuwar Baban su Fajur na aika mata ta hanyar dan aiken da ke kawo wasika a tsakanin mu wanda dan kasar nan ne mai kasuwancin Rakuma a Nijar, shine fa ta bude min asusu, wanda kai tsaye duk wata take turomin kudade na Saifa masu kauri, wadanda da su ne na cigaba da daukar nauyin karatun yaran nan, muke kuma cin abinci, na kuma soma sanaar kiwo, ga abinda mahaifin su ya mutu ya bar mana muna juyawa a gona, muna samun amfani daga noma da kiwon kaji da kiwon shanu. A takaice kin ji wannan itace rayuwar da muke yi a halin yanzu. Safwan yana rubuta jarrabawar kammala sakandire yanzu a nan makwabtan mu wato Gambia, ya zo hutu ne, Fajur tana karatu anan wata karamar sakandire ta kudi a bayan gidan nan, kullum da kanta take zuwa ta dawo ta huta ta wuce Islamiyya. **** **** **** MOTHERHOOD Z uwa washegarin ranar, hatta makwabtan Jalan bakidaya sun san da zuwan yar ta dake Najeriya aka shigo ana yi mata barka, wasu na aiko abinciccikan kwadayi wa Amani, kasancewar Jalan ta mutane ce mai yawan kyauta da kyautatawa ga makwabtan ta, anata mamakin kamannin su ita da Amani in ka dauke cewa Jalan mai jiki ce Amani siririya. Duk abokan arzikin iyayen su dake raye sai da ta kai Amani a washegari suka gan ta. Basu dawo gidan ba sai da yamma lis. Shima Mukhatr baya gidan tun safe Faytoory ya zo ya dauke shi, sun shiga gari yana nuna masa wurare masu tsohon tarihi na Kenema, da inda ake Mining din Diamond. Daga can suka wuce gidan Faytoory suka ci abinci da iyalin sa sai lokacin suka dawo gidan su Amani. Faytoory ya ajiye Mukhtar kenan suna sallama da cewa gobe in sha Allah da wuri zai zo ya tafi dashi Freetown, inda daga can zai hau jirgin Lagos. Mama Jalan ta aiko Safwan ya kira shi su ci abincin dare yadda suke yi kullum, a lokacin yana hada kayan sa a jaka yana tunanin tunda su ka zo rabon sa da kebewa da Amani ko da da sunan su gaisa, wato ya gama mata amfanin da zai mata, tunda ta dafe uwar ta a gefen ta shikenan. Sai ya shiga tambayar kan sa na me zai yi wannan tunanin ma? Amani ce fa! Wadda ya sani ba tun yanzu ba. Ai ya dade da sanin Amani ba yar goyo bace shakiyya ce ya sani dama, kuma ta fada ta kara haduwar su ta kan hanya ce da zarar ta ga uwar ta babu ita babu shi. Ya tuna cin mutuncin data yi masa sa Freetown da zagin fitar hankali na sheganta shi, sai ya ji zuciyar sa na kara tafarfasa, Amani na kara fita a ran sa. Amma mutuncin iyayen ta a zuciyar sa na kara ninkuwa. A ladabce Safwan ya shigo ya gaida shi, sannan ya gaya masa sakon Mamma na ya fito su ci dinner tare. Ba tare da ya dago ya dubi yaron ba don baya so ya ga idanun sa, a dai yanayin da suke ciki yanzu na tsananin bacin ran Amani. Ya ce ya je ya gayawa Mamma cewa a koshe yake, ya ci abinci a gidan Faytoory kuma yana so zai shigo yayi mata sallama don gobe in sha Allah zai koma Katsina. Safwan ya je ya dawo ya ce Mamma ta ce ya shigo, a gaskiya a lokacin baya son shiga cikin gidan a yanayin da fuskar sa ta koma yanzu, wato boyayyen yanayin nan nasa da ba kowa ya san yana da shi ba ya bayyana, domin baya so Hajiya Jalan ta ga hidden side din sa na rashin walwalar nan. Gashi idan ya zo baya iya controlling din sa har sai ya bace don kan sa. Sannan haka kawai yake jin muryar Mamma Jalan da accent din ta kamar yadda yake jin tashin muryar Ummami, wanda hakan ke kara tono bacin ran dake kasan zuciyar sa na kewar Ummami da jin zafin ta (as well), yana kara bayyana a kan fuskar sa. Ba yadda ya iya dole bayan yayi wanka ya canza kayan jikin sa zuwa farar jallabiyya kal kirar Dammam, ya yi sallah a masallacin kofar gidan sannan ya shiga cikin gidan da karamar tazbaha mai kyau a hannun sa. Nan ya gan su complete family a kan teburin cin abinci abin gwanin ban shaawa. Amani ta sha ado da laffaya koriya sharr da irin matsatsiyar rigar nan ta roba mai dogon hannu daga cikin laffayar light green itama. An yi mata wai irin setting din gashi wanda ya zubo a saman goshin ta ya zarce har bayan kunnen ta. Bakin nan sai shining yake da Elizabeth Arden Lip gloss kamar ka sace ta ka gudu (looking takeaway), idon nan nata mai kama da kwan zabo ya sha mascara gashin idon ya fito gazar-gazar. Rabon ta da yin ado irin wannnan bazata iya tunawa ba. Sai ko yanzu da take jin kanta a daidai wato bata da damuwar komai, tunda rayuwa ta koma mata daidai, ga ta ga uwar ta a duniya, ga kanne, sosai take cikin nishadi, barin ma data ji Safwan ya zo ya fadi sakon Mukhy na cewa gobe zai koma Katsina. Ai kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, yi ta yi kamar ta tashi ta ka rawa, murnar tata har kasa boyuwa ta yi sai da Mamma ta gane bakin ta ya ki rufuwa don Mukhy ya ce gobe zai koma ya bar ta a nan. A cikin zuciyar ta Jalan tana mamaki, ko meye aibun Mukhtar haka da matar sa ta kasa son sa? Mutum son kowa da shi a halitta da dabia, abun alfaharin kowacce mace wajen kamun kai da kamewa da girmama iyayen ta, amma Amani na neman maraba da shi irin haka bata ko jin zata yi kewar sa don ko a waya bata ga sun gaisa ba balle text din soyayya. Kwata-kwata ta gama lura Mukhy baya ran ta, kamar kishin sa take akan Baban ta kamar kuma zuciyar ta bata taba kimsa mata soyayya a kan sa ba. Ta riga ta dauke shi rival a zuciyar ta, ko kuwa wani wanda ya tare mata gaba ya hanata rawar gaban hantsi. Sai Jalan ta shiga tambayar kan ta ko yar tata bata da lafiya ne irin ta yaya mata ko kuma tana da shafar jinnu. Ta lura bayan dolonci, rashin kunya, rashin ilmin addini, rashin cikakkiyar tarbiyya har da rashin sanin muhimmancin da Allah ya baiwa miji a kan ta, da rashin sanin hakkin aure. Kada dai tarihi ne yake maimaita kan sa, tunda itama abunda ta yiwa Uban ta Alh. Usman kenan, kusan tsayin shekaru biyu tana wahalar da shi a dalilin bata son sa. Tunda ya aure ta sau daya ya taba samun saar ta, shima ta karfi, wanda daga baya ta gane rabon Amani ne ya rantse. Tana kuma lura da cewa tunda suka zo Amani bata je inda yake ba, bata kara bi ta kan sa ba, bata kara yin zancen sa ko kula da alamarin sa ba a matsayin su na sabon aure, balle ta damu da sanin halin da yake ciki a masaukin nasa, ko ta tambaya an kai masa abinci ko aah? Don in an kira shi ya ci ma baya zuwa. Sai ta ji tausayin Mukhy mai tsanani da kaunar sa kamar dan cikin ta ya kamata, bata san dalili ba amma jin sa tayi ya kwanta a ranta kamar dan ta Safwan, ba banbanci, don in ba kuskure idanun ta suka yi mata ba ita ta hango kwantacciyar soyayyar Amani maras misaltuwa a can kasan kasaitattun idanun sa masu sheki da sparkling a duk sanda ya juya su a kan Amani. Ita a wurin ta Alhaji Usman ya kware shi, da ya hada shi da auren Amani, hakika ya so kan sa, domin Mukhy data ke faman kira yaron Baban ta ita sai taga ajin sa da kasaitar sa sun dame na Amani. Gashi ya san irin tarbiyyar da yayi mata amma ya hada dan mutane nagartacce, kamamme mai alkunya da wahala, don ya gan shi mai hakuri da biyayya. Ga wata irin nutsuwa da kamala a tare da shi irin wanda tsayar da addini da kula da sallah ke haifarwa namiji, wanda bata taba gani a matasa kamar sa ba. Ta shiga hangowa kan ta irin asarar surukin kwarai da zata yi, idan shashashar diyar nan tata tayi masa rikon sakainar kashin da zai gaji ya yakice ta. Sai ta yi maza ta mike tana tunanin abun yi na gaggawa, don kankarowa Amani mutunci ka idon Mukhtar kafin ya karasa zirarewa. Mukhtar yayi sallama duk suka amsa banda Amani, wadda a lokacin ta kai fork da ta cokalo dankalin turawa a jikin sa bakin ta, tana wata tauna a yangace kamar bata so. Jalan ta nuna masa kujerar da zai zauna mai fuskantar ta Amani ya tsugunna har kasa ya gaishe ta, yana ta kokarin kin dagowa ta ga fuskar sa, amma a kulawa irin ta Jalan, sai da ta hango yanayin da yake boye mata din, kuma a matsayin ta na babba ai ta san dalilin sa. Amma sai tace lafiya Mukhtar na gan ka haka babu walwala? Mukhtar ya ki zama a kujerar don ba zai iya tana kujera shima yana kan kujera ba, sai ya ce mata Mamma zan koma Freetown gobe da sassafe, daga can zan tashi Nigeria in sha Allah. Ta kusa ce masa Amani fa? Don sai ta ji kamar bata kyauta ba in ta rike masa mata har tsayin watanni biyu nan gaba, bayan bashi da wata matar a can gida Katsinan. Kamar Mukhy ya san me Jalan take tunani sai yace, ita Amina Alhaji ya ce ta zauna da ke na dan wani lokaci, ta saba da nan din Jalan ta soma lalubo idon sa da yake boyewa da nata wayayyun idon na iyaye, ta ce. Are sure you are okay with her stay here? Cewa nake daurin aure kawai aka yi muku baku tare ba ko sau daya? In don ta ni ce ba abunda zata yi min alhalin tana da miji a gefe, gara ta wuce ku koma tare, zai fi min kwanciyar hankali da kai kan ka. Ai jin haka Amani ta soma buga kafa irin wanda takewa Alhaji, tana fadin ita ta zo kenan, ba inda zata sake zuwa. Alhaji ne yasa take zaune a Katsina kuma ita kam yanzu ta barwa Mukhy shi halak malak. Sai ji kike gwajab! Mamma Jalan ta gwabje bakin da ya sha lip gloss, tace, Amina! Ashe baki da daa baki da ta ido? A gaban kannen ki kikewa mijin ki wannan diban rashin albarka? Tashi ku je ki bashi hakuri, na ce ki bashi hakuri har sai ya huce, ku yi sallama cikakkiya, kada in ganki a cikin gidannan sai da safe!. Tuni Mukhtar ya kai bakin kofa don in ya cigaba da zama a wajen nan Amani ta kara magana ta rashin amincewa da umarnin ta, ko ta kara furta wani abu akan hakan ya san Mamma Jalan zata kara kai duka, da alama mai saurin hannu ce. Sosai dukan Jalan ya samu bakin Amani, tuni leben sama ya kumburo. Zata yi magana ta ji bakin ta ya mata nauyi, sai ta fara hawayen da baya yi mata wuya, a ranta ta ce shikenan itama uwa ta yayi sumumu-kasau dinsa na munafurci ya raba mu, Mamma kuma ta yi rantsuwa ta kara ta tashi ta tafi wajen mijin ta ko ta sassaba mata kamanni yanzun nan. Ko me ta tuna? Ta ja hannun Amani zuwa dakin ta da zafin nama saboda idanun su Fajur da suka bubbude suna kallon su, suna shiga ta rufo kofar da mukulli, ta dube ta da tausayi, don ta ga tsanar Mukhtar tsantsa a cikin idon ta. Ita victim ce ta kiyayyar auren dole ta san me Amani ke ji. Ta ce. Amina, bana so ki zamo daya daga cikin matan da aure da hakkin sa ke kai su wuta. Ba sai ya ce bai yafe miki ba Allah zai dubi hakkin sa a kan ki ya fidda masa, na san a shekarun ki kin san aure, kin san maanar sa, amma a dolancin ki kina sa kafa kina takewa. Shin ya ta ko kin san irin kyautar darajar da Allah yayi miki kuwa da wannan salihin mijin da ya baki? Ina jiye miki ranar dana sani.... wadda aka ce ..... keya ce, tun da sauran mutuncin ki ki kankaro shi a idon Mukhtar, kafin ranar da zaki yi nadama mu kuma bama tare da ku. Jalan ta cigaba da yi mata nasiha iri-iri mai kashe jiki amma banda jiki mai kunnen kashi irin na Amani. Don nasihar da waazin wani na shiga ne wani na fita ta daya kunnen. Ta kawo wasu kwayoyin magani ta bata ta ce ta hadiya yanzu tana gani kuma a gaban ta. Sai Amani ta tuno Haj. Muna, itama hakika ta bata irin wadannan kwayoyin kuma bata yarda ta sha ba, yanzun ma da Mamma Jalan ta dage sai ta sha a gaban ta, can kasan harshen ta ta kai su ta danne su da harshen ta ta kora ruwa. Mamma Jalan ta hada garwashin lantarki (burner) nan da nan ta zuba wani turare irin nasu na musamman tace ta tube ta turara jikin ta. Wanna ba musu ta yi, tunda turare ne kawai, sannan Jalan ta raka ta har kofar entrance na masaukin Mukhtar, tace ta wuce ciki tana kallon ta. Haka ta tsaya daga nesa sai da ta tabbatar Amani ta buga kofar, ta ga sanda Mukhy ya zo ya bude, da farko kamar ba zai bata hanya ta shiga ciki ba, don ta ga kamar jayayya suke, bata dai jin me suke fadi sosai kasancewar (by nature) din sa, Mukhy bai da daga murya wannan sai Amani idan ta so yin rashin kunya. Mukhtar yana bude kofar ya ga Amani ce, sai ya ki bata hanya, cewa yayi lafiya? Me kika zo yi wajen dan shege? Idanun ta suka yi rau-rau, a rayuwar ta bata taba yin maganar katobara ta yi nadama irin wannan maganar ba. Da ana amai a lashe da tuni ta lashe ta, ta maida ita cikin ta. Banda Mamma ta sako ta gaba me zai kawo ta dakin sa da daren Allahn nan har ya gaya mata bakar magana? Sunkuyar da kai tayi tana hura hanci da wasa da yatsun ta, sannan ta juya ta tofar da kwayoyin maganin da ke bakin ta, Mukhtar ya bi abinda ta tofar da kallo amma bai san mene ba, ta ce ai da gani na ka san nima takura ni a ka yi na zo, ka san da bazan zo ba, don bani da bukatar komai a wurin ka ya ce sai ki juya ji koma, shege baya bukatar komai a wurin ki shima. Ta daga idanun ta cike da hawaye ta ce a rayuwa ta ban taba bada hakuri ga kowa ba, ban taba yin magana nayi nadamar ta ba, amma wannan na yi, na maida wannan kalamin ciki na, na kora su da ruwa nayi flushing din su tun daren dana furta su. Ina baka hakuri a kan su, don nima na san basu dace ba, sharrin zuciya ne da fushi, amma idan ka cigaba da maimaita min su da rike ni da su a ran ka, hakika ka cutar da ni Mukhtar!. Mukhtar sai ya juya ya shige ciki ba tare da ya iya ce mata komai ba, don (hes cool and shocked) da sunan sa data ambata yau, ya kuma san da gaske take bata taba baiwa kowa hakuri ba sai yau. Tabbas UWA daban ce, kuma uwa ta yi a rayuwar diya mace. Wadda ta rasa UWA ayi mata jajen rashin da bazata mayar ba, har abada!!! (Allah ka yi wa iyayen mu gafara ba don sun mutu ba, wadanda suka rasa nasu Allah ka kai rahma da haske da kamshi kabarin su- Takori). Ba don Mammah ta yi rantsuwa sai ta kwana a dakin ba, da daga nan zata juya ta koma, ai dai ta yi masa sallamar data dace, kuma da ya bata hanya bai ce ta shigo ba, itada kan ta data gaji da tsayuwa ta shiga dakin a fusace, amma bata rufe kofar ba ta bar ta a bude fayau. Sai shi ne da ya ga sauro zai cika dakin, ya mike ya rufe ya wuce ya koma ya cigaba da abinda ta tarar yake yi kafin ta shigo wato booking din jirgin Lagos online, ta cikin system din sa. Da shigowar ta dakin atmosphere din dakin gabadaya ya canza da wani irin sihirtacccen kamshi irin na turaren da ake yiwa amaren kasar Saliyo, wanda a makwabtan su wato kasar Gambia kawai ake samun shi. Yana tambayar kan sa wane irin fitinannen turare ne haka Amani ta fesa, mai barazanar daga masa hankali? Ga gashin nan ya sha wani irin setting an kanannnade shi ya zubo a gaban goshin ta ya zagaya ta bayan kunnen ta, ya kwanta akan wuyan ta, kasancewar laffaya ce a jikin ta sosai gashin ya fito ya kwanta a kan dogon wuyan ta. Yana aikin amma hankalin sa ya rabu biyu, neman shidewa yake yi. Allah kadai ya san wane irin turare Jalan ta turarawa yar ta. Domin dai a karshe Mukhtar sai kashe kwamfutar sa yayi ba tare da ya san takamaimai ya gama booking din ko bai gama ba?. Sai ga vedio call din Alhaji ya shigo masa ta whtsp dinsa, alamar yana son magana da shi. Kasa daga wayar yayi ya dai zuba ma kiran ido, sakamakon yadda kasala mai yawa ta rufe shi kuma baya cikin irin mood din da zai iya magana da Alhaji. Tana kallon sa ya mika hannu ya kashe wayar bakidaya, ta tsaya taki motsawa daga inda take tsaye, ta harde dogayen kafafun ta ta kuma nade hannun ta a kirjin ta tana harare-harare, ita bata zauna ba ita bata rage laffayar jikinta ta kwanta ba. Mukhtar da kyar ya iya mikewa ya rage fitilar dakin mai haske ya bar shudiya mai rangwamen haske, wadda a turance ake kira dim light daga nan ya lallaba ya haye gadon sa ya ja bargo har kan sa ya kudundune, ya bar ta a nan tsaye don ya fahimci neman rigima take yi da shi. Amani ta yi kwafa, miskilancin sa ya kara fusata ta, sai ta karasa gadon ta dauki filo daya ta jefa a kasa, ta warware laffayar ta ninka ta biyu sannan ta rufu da ita, ta kwanta akan kafet mai laushi tana cewa a ranta me zai kaita hawa gadon nan ko da ya kula ta? Balle yayi wannan shakulatin bangaron da ita? Ai ko gadon zinare ne ta bar masa. To amma ta kasa barci bayan ta kwanta din, jin numfashin Mukhtar ya sauya kasancewar dakin yayi tsit, babu komai sai bugun numfashin su da sururun iya kwandishan, yadda numfashin sa ke sauka da sauri da sauri a kunnen ta, tamkar zazzabi da masassara irin wanda ya same shi a Freetown ya ci karfin sa. Tana jin sanda ya dauko filon sa ya dawo kasa shima, zazzabi sosai da sanyi yake ji, dumin jikin mace kawai yake bukata a wannan lokacin, ya fahimci cigaba da kwanciyar sa shi kadai a gadon daidai yake da ya haka rami ya kashe kan sa... akan matar da addini ya riga ya bashi damar komai yake so a kan ta. Akan me zai yi ta cutar da kan sa har haka? Shi ya san matsayin sa na namiji kuma matashi mai jini a jika, sannan jinin Issouffou Masaoudou, yayi matukar hakurin da ba kowanne namiji kamar sa ne zai iya ba a kan mace. Ya san yana da hanyar da zai samu kan Amani ko da bada yardar ta ba, amma kasaitar sa bazata bari ba, yana ji a ran sa yafi karfin ya yi forcing mace ta kwanta da shi (by force). A yanzun da tura ta kai bango, kuma Jalan ta warware ego din sa, ta hanyar wannan kamshi na jikin Amani da su kadai matan Saliyo suka san sirrin da ke cikin sa, a yanayin da yake ciki yanzu, sai ya manta ko waye shi, da wannan pride din nasa, sabida ba shi ke sarrafa jikin sa a yanzu ba. Hakanan ya tabbata suka kwana a haka Allah ma sai ya tambaye shi dalilin cutar da gangar jikin sa, alhalin jikin sa ma da kowacce gaba ta jikin sa na da hakki mai girma a kan sa, bai kamata yayi ta biyewa Amani yana cutar kan sa ba, yarinyar da kullum sai ta saka shi a tashin hankali da wankan janabar babu gaira babu dalili. Yaya akayi yaya akayi Amani bata sani ba don ta soma samun barci, sai kawai taji Mukhtar ya bi ya kwanta a gadon bayan ta, yana sakin ajiyar zuciya. Domin a yau dauriya da jarumtakar sa sun idasa karewa. Koko in ce, Mama Jalan ta karar da su da sirrin ta. Hannayen sa ya saka ya riko hannun Amani dasu, cikin siga ta nuna bukatuwar miji zuwa ga matar sa, matar ma wadda yake tsananin so, ya ratsa yatsun sa sosai cikin nata, sannan ya damke su da karfi, kwanciyar sa a gadon bayan ta da yanayin rikon da yayi wa hannun ta a bazata, ya tsorata ta, domin bata zata ba ko da wasa, a tunanin ta Mukhtar ba zai taba iya hada jiki da ita ba, don yadda bata son sa ta tabbata haka shima baya son ta, kuma wannan alamari ta san cewa baya faruwa sai da soyayyah, daga haka ta ji Mukhtar ya janye laffayar jikin ta data rufu da ita, da zafin nama ya janye laffayar, ya saura Amani da tiny rigar robar jikin ta, Mukhtar ya ga body structure din Amani ta cikin hasken dim light wanda hakika Allah ya yi wa Amani halitta wadda ta kasance daya cikin dubu, a cikin na mata dubu kafin a samu irin na matan Saliyo sai an tona, bai taba zaton haka Allah ya kera Amani ba, wanda hakan ya karasa susuta komai nasa, ya birkita dan mutanen Diffa. Kafin ayi haka Amani ta ji Mukhy ya rungumeta ta baya sosai, da wata irin tight hug (runguma tsatstsaura), ya manne ta a jikin sa yana sauke numfashi mai matukar wahalar fita daga huhun sa. Tana iya jin yadda jikin sa ke shaking, jijiyoyin jikin sa ke vibrating, yana kara shigewa sosai cikin jikin ta da kadan kadan har ya shige jikin ta bakidaya, wanda hakan ya gama tsorata ta, ta soma mutsu-mutsu na nuna rashin yarda da son ta kwaci kan ta, amma karfin ba daya ba, nan ta fahimci mai raba ta da Mukhtar yau sai Allah da ya halatta masa ita. Sai kawai ta soma hawaye masu zafi na tausayin kai, tana hango ego din ta yau ya tsiyaye a kasa..., tana hango budurcin ta zai kare yau a arha, ga wanda bai isa ba, mijin da aka baiwa sadakar ta ba don ya isa ba, bai kuma dauke ta da daraja ba duk da haka, kuma baya son ta kamar yadda bata son shi itama. Ba kowa ya janyo mata ba sai Maman ta Jalan, cikin kuka-kuka ta ce Mukhtar, are you trying to rape me? Kamar a mafarki Mukhy ya ji Amani ta fada cikin muryar kuka don ta rasa karfin da zata yi kokawa da shi, kamar itama sakon Mamma na aiki a jikin ta, don a lokacin ya gama sabule rigar robar jikin nata bakidaya ba tare da ta ankara ba, sabon zautuwa ya same shi. Sai yaji gaban sa ya fadi da wannan furucin nata, kuzarin jikin sa ya ragu, he hate the word RAPE don haka ya rage gaggawar sa, kamar a mafarki sai taji muryar Mukhtar yana kiran sunan ta yau cikin wani yanayi da yafi kama da lallashi na matsananciyar soyayya, ya kankame ta iya kankamewa affectionately, yana shafa bakin gashin kan ta cikin lallashi da neman hadin kan ta, kafin ya sanya bakin sa kasan wuyan ta ya saki mata wani sassanyar kiss, wanda ya kusan sumar da Amani daga kwancen da take. Ai daga wannan lokacin komai ya sauya, domin bata kara sanin meke faruwa da ita ba, kawai ta sakar wa Mukhy jiki ta daina kokawar kwace kan nata. Domin abunda ta ji a tare da ita da ya yi mata wannan kiss din, ya wuce misali. Mukhtar daya ji ya samu access tuni ya idasa sakin sauran kisses din sa a guraben da take jiran saukar su. A hankali ya ke moving upward da tattausan lips din sa yana sumbatar dogon wuyan nata wuri-wuri har ya isa ga bakin ta.... Amani couldnt explain whats happening from then, lokacin da Mukhy ya manne bakin su wuri guda, ya soma ma Amani wani irin zazzafan hot kiss, a lips din ta, kafin ya samu damar shigar da bakin sa cikin nata sosai, ta kuwa bude bakin tana jiran isowar sa, sai da Amani ta saki numfashi mai karfi (moaning), mai nuna deep and extreme pleasure din da Mukhtar ya sakar mata ba tare da ta sani ba. Ta hakan ne Mukhtar ya samu access din da bai zata ba, domin Amani ta gama sallama masa kan ta, nan ya sarke halshen su wuri guda yana sumbatar halshen nata hungrily kamar yaron da ya samu sweet a cikin bakin sa. Mukhtar ya gama kashe Amani a wannan lokacin ya kuma gigita kan sa ya koma kamar ya samu hauka, a irin yadda yake sumbatar Amani da yanayin da yake ciki ya tabbatar wa kan sa ba karamin kokari yayi ba wajen rike kan sa har zuwa wannan lokacin da ya cika shekaru talatin da biyar, bai taba zina ba, yana adduar har ya mutu kada ya yi, ya mayar da Amani ko dan yatsan ta bata iya motsawa domin ta hana shi abunda yake kokarin yi din, don nemawa kan sa da ita kan ta nutsuwa, maimakon hakan, sai ma samun kan ta da tayi tana enjoying sumbar da Mukhtar ke mata kusufa-kusufa yadda harshen ta ko biro bazai iya bayyanawa ba, amma ilahirin jikin ta ya karbi sakon Mukhy ta koina. Mukhtar sai jin yatsun Amani yayi sun ratsa cikin lallausar sumar kan sa da take cunkus, ta tura duka yatsunta cikin gashin sa tana kiran sunan sa da muryar da bata yi kama da tata ba, wanda hakan ya kara triggering stuation din nasu beyond expression. A wannan lokacin daga Mukhtar har Amani sun manta a duniyar da suke, ko wata rashin jituwa ko kiyayya mai dogon zango dake tsakanin su, burin Amani shine a kai ga babban alamarin ta gama shirya yin sallama da kuruciyar ta.... Amma sai wani tunani ya darsu a ran Mukhy, na cewa; shin ya shirya fansar da samartakar sa ne ga Amanin da bata san darajar sa ba sam? Bata dauke shi mutum ba, bata dauke shi komai ba banda daukar sa da take yaron gidan su? Amani har yanzu bata son sa..... kuma ta fada har abada bazata so shi ba. Wannan access din data sakar masa ya samu ba don SO bane, na shaawa ne da ya taimaka wajen kimsa mata ita, ta hanyar seducing dinta da kiss, kada ya yarda... kada ya sake, kada ya kuskura yayi saken da zai zama injin biyan bukatar gangar jikin Amani, alhalin ba shi da gurbin so da kauna na gaskiya a zuciyar ta. Matsayin sa da darajar da Allah yayi masa ya wuce haka! Wannan ne ya dakatar da Mukhtar daga kokarin sa na cika sunnar aure, da farantawa kan sa, har ma da Amanin da jira kawai take Mukhtar ya maida ita cikakkiyar matar sa. Ta gama sallamawa cewa a lokacin komai zai faru a shirye take, domin she cannot resist him a yau. Amani sai ji tayi tamkar an yi ruwa an dauke Mukhtar ya mike daga jikin ta ya koma gadon yana ta murkususun sa shi kadai. Sai a lokacin ta dawo hayyacin ta. Kunya da haushin kanta suka zo suka lullube ta, ta hau tambayar kanta me ya faru haka? Me ke faruwa yau kamar almara? Ina ego din ta? Ina pride, ina class din ta, ina kuma gatan ta da dukiyar ta data warawa Mukhtar kafa haka yau, tana jiran sa da abinda bata taba kawowa ran ta amincewa da shi ba, gashi ya mata dandani haukaci, ya tashi ya bar ta da kunya da takaicin kan ta. A haka suka kwana tana kuka, kukan ta baya ta rago in ji hausawa, kukan bakin ciki da haushi kan ta. Mukhtar kuwa falo ya koma bayan wani lokaci. A kan doguwar kujera ya kwana cikin wani hali na kaka ni kayi. Amma kafin asubah ya samu barci mai dadi, ko babu komai ya samu wani irin relief da bai taba samu ba. Da assalatun fari kiran sallah ya tashe shi, yayi maza ya shiga yayi wanka da alwallah, ya zo ya kunna fitilar dakin sai ya sameta ta hada kai da guiwa har lokacin tana kuka kamar ta kashe kanta. Jakar kayan sa ya bude, yau a gaban ta ya hau canza kaya. Yo kunyar ta yaushe kuma ya ga komai itama ta ga komai, sai ita ne ta dukar da kan ta kasa don kunya. Ya kammala shiryawa ya dube ta kan ta a kasa, tana ta hawaye, yace, to Madam, da alkhairi, Shege yayi harama zai koma Najeriya, ya bar ki a Saliyo ki yi yadda kike so da auren sa, a yi hutu lafiya, ko kina da sako gun Alhaji? Amani ta mike ba tare data tanka masa ba tayi toilet. Kafin ta fito ya kammala hada komai nasa ya na jiran fitowar ta domin Faytoory har ya iso, ya kuma kira shi a waya ya gaya masa ya iso yana mota yana jiran sa. Bata ce masa komai ba ta soma mayar da laffayar ta jikin ta. Mukhtar ji yayi kamar ya kara rungume ta, ganin har lokacin kuka take yi sosai kamar ta hadiyi zuciya, har da sheshsheka, amma ya hani kan sa da yin hakan. Ya yarda dai ta yi nadamar maganar nan da gaske, ta kiran sa mai kama da shegu, amma shi kuma ya rike ta bada wasa ba, har sai ta yi repenting iya repenting, yadda ya kamata, sannan zai daina tada wannan zancen. Ya isa inda take hannayen sa biyu zube cikin aljihun wandon Jeans baki da ke jikin sa, kokari ya ke su hada ido amma ta ki, don yau bata da bakin rashi kunya tunda ta gama zub da ajin ta. Mukhtar ya ce na ce baki da sako gun Alhaji? Hawaye fal idanun ta tace inada shi. Ka ce masa ina so ya mayar da auren sa da Mahaifiya ta, zan taya shi lallashin ta. Mukhtar yayi dif! Meyasa shi bai yi wannan tunanin ba tuntuni? Amma Alhaji.... ba shi da lafiya yanzu, anya Jalan din zata yarda? Sai ya ce in har zaki lallashe ta ta yarda Alhaji ba zai ki ba, sai dai ki tuna bashi da lafiya yanzu, bayan ta karfin jiki har da ta rashin iya aure. Amani tayi maza ta dago tana masa kallon neman karin bayani ta hanyar zazzafar harara, abu kazan uban sa take so ta zaga ko ta huce, wato rashin mutuncin sa bai bar kowa ba, har Alhajin ma! Sai ya gyada kai yace eh, Im not joking, sugar ya ci karfin sa, ba ya iya auratayya yanzu sam. Amani ta daburce, ga kunya ga tausayin Daddy, sai ta hau masifa, ta ce kuma aka ce kowa ne irin ka? Kowa ne yake aure don ya taba mace? Ko kuwa an ce maka kowa ne yake aure saboda wannan rashin kunyar? Baka san ana aure don mace ta dinga zuba ruwa a Buta tana kaiwa tsohon mijin ta bandaki ko dafa masa ruwan wanka ba? Dariya ce mai tsanani ta kama Mukhtar amma ya gintse, sabida ta hau kan tsini sosai, yace, irin naki auren ko? Ta sa kai zata wuce ya riko gefen laffayar ta, yace Shege zai koma, sai watarana! Idanun ta rau-rau, ta ce Allah yayi mana hisabi ni da kai, sabida yadda kake cutar da ni da kuskure na. Inda Allah ya cece ta daga Mukhtar shine kofa da ake bubbugawa, dole ya sakar mata laffayan, idanun sa kamar su hadiye ta, ya karasa ya budewa Fajur data kawo masa karin kumallo haka da wurwuri. brother sabahul khair, an tashi lafiya? Ga nan breakfast inji Mammah. Ya dubeta cike da kauna ya ce nagode Fajur, amma ki koma da shi ciki don na makara, kuma ban iya karyawa da wuri ba, tuni Faytoory ya zo dauka na. Brother zan bi ka in ji Fajur. Tana marairaicewa duk sai sai kamannnin ta da Amani suka bayyana. Ya ce kada ki damu matas, zaku taho tare da Yayar ki in ta gama hutun ta. Da wannan duk suka rankaya suka fito Fajur na cewa ya cika alkawari fa, ya dawo ya tafi dasu Najeriya tana son zuwa kasar Najeriya, kullum Mamma na basu labarin Najeriya mai GREEN WHITE GREEN flag. A harabar gidan suka samu Mamma tayi lullubi ta fito domin su kara sallama da Mukhtar, har kasa ya tsugunna ya gaisheta sannan ya shiga motar Faytoory. Amani ta wuce cikin gida ba tare da ta tsaya sun kara hada ido ba, balle ta kalli shigar sa mota, ko tace Allah ya kiyaye. Kuma a rashin tarbiyyah irin nata bata gaida abokin Baban ta ba wato Malam Abdussalam. Faytoory ya ja motar Mukhtar na gefen sa suka fita daga gidan, Fajur da Safwan na masa adduar sauka lafiya. Mamma na daga masa hannu idon ta cike da kewa da kunar sa. Tunda ta shigo gida take kuka, koma me ya same ta yau ta tabbata Mama Jalan ta jawo mata, don watakila magungunan data bata duk da ta zubar amma ai wasu sun narke mata a baki, da turarukan data yi mata ne suka sa Mukhy ya samu damar da ya samu yau a kan ta. Yanzu ya tafi ya bar ta da cizon yatsa. A haka Mamma ta zo ta sameta ta soma yi mata fada, a kan rashin gayar da Faytoory da rashin iya tattalin miji da kula da yi masa addua. Ta ce ban taba ganin sokuwa irin ki ba Amina, rashin tashi da Uwa hauka ne? Ai wani abun kana tsintar sa a social environment din da kake ciki da kuma aladu masu kyau na alummar da ka taso a cikin su. Ke kam kin rako mata duniya!!! Ta sake rushewa da kuka, tana son fadin Mamma taba ni yayi ta yi fa duk ya hargitsa ni amma ga mamakin ta wannan maganar ta yi mata nauyi a baki, a ce ta gayawa Maman ta ita. Gaar ta bar bakin cikin ya kashe ta. Sai ta yi shiru, tana jin ciwon kalaman uwar. Da tace ta rako mata duniya wajen rashin iya tattalin miji! Da ballagazanci!! Ta ce har da dolanci !!! ***** ***** ***** T un daga wannan ranar Mamma Jalan ta maida hankalin ta da lokacin ta kacokam! A kan gyaran tarbiyya da dabiu da addinin yar ta Amani. Gashi yau har Mukhtar yayi sati biyu da komawa Katsina, Jalan har girki tare suke yi da Amani don ta lura bata iya komai da ya shafi rayuwar mace a gidan aure ba. Kada girki ya ji labari. Hatta sallahr ta ta tsaya tana dubawa da gyarawa da saka Safwan ya dinga koya mata karatun Alqur ani kullum. Ba don bata san ranar komawar ta Katsina ba da a islamiyya zata saka ta. A hakan ma babu laifi don tana da kwakwalwa, tana daukar kananan surorin da Safwan ke kara mata kullum. Shakuwa mai tasanani ta shiga tsakanin Amani da kannen ta biyu wato Fajur da Safwan da mahaifiyar su da ke kokarin samar da kauna da shakuwa da hadin kai a tsakanin su. **** ***** **** KATSINA T unda ya tafi bai kira Amani ba, ko sau daya, kai ko da kuskure, domin ya tarar da very tight schedules a kamfani da shagon ta, amma tabbas ya san yana kewar ta da rashin kunyar ta, kai har ma da fitsarar ta. Ya kan tun ranar su ta karshe with so much adoration. Allah yayi mana hisabi ni da kai, sabida yadda kake cutar da ni da kuskure na! Sune kalaman ta da kullum yake yawan tunawa yayi murmushi. Masu tabbatar masa da cewa (for the first) tima tayi maganar da ta zo ta yi nadamar ta a rayuwa. Amma daga komawar sa Baba Idi har ma da Alhaji suka bude masa wuta kan sai sun dangana da iyayen sa ko danginsa don shima Baba Idi ya dage a kan hakan. Mukhtar kuma yafi son ya fara sulhunta Jalan da Alhaji tukunna kafin ya yarda su tafi Diffa, gabadaya har Mamma Jalan don dai ya kore curiousity din sa a kan cindon ta da na Ummami. Don haka ya gayawa Alhaji sakon Amani, na tana rokon su maida auren su shi da Maman ta. Alhaji Usman sai yayi dariya, yace a da can ma dana ke da cikakkiyar lafiya Jalan bata yarda ta zauna da ni ba sai a yanzu da nake da rabin jiki shanyayye, kuma ba zan iya sa ta haifar wasu yayan ba? Dube ni a cikin wheelchair. Mukhtar ya ji wani iri ya ce cikin tausayawa, ai Amani ta ce auren zuba ruwa a buta a kai bandaki da zuba ruwan wanka zaku yi. Ba sai don wannan kawai ake aure ba Alhaji, in ji ta. Alhaji bai san sanda ya bushe da dariya ba, ya ce ai ka sani Mukhtar ni bani da say, in dai a kan Jalan ne. Na bar komai a hannun ku kai da Amanin, idan har ta amince a hakan da nake ni ai zan fi kowa farin ciki. A daren Mukhy ya yiwa Amani gajeren text messege, yana so ko yaya ya tsokane ta, inda yace. Shege ya zo gida lafiya, duk da baki nemi jin hakan ba. Alhaji ya amince da bukatar ki na maida auren sa da Mamma, idan har zaki yi masa yakin neman amincewar ta. Su Baba Idi zasu taho a maida auren. A kasan sakon sa ya rubuta; _Mai kama da shegu. Sanda sakon ya shigo wayar ta girki suke yi itada Fajur, don haka bata duba ba duk da ta ji alamar shigowar sa sai da suka kammala. Ta runtse idon ta kadan, a kan wannan kalma da ya kara ambata mata, ta yarda Mukhy, mutum ne mai tsananin riko, irin wadanda da wuya a cuce su su yafe, ba tare da sun rama fiye da abun da aka yi musu ba ko mafiyin sa, ko da zasu huce din ma kenan. A ranar ta nemi jin ta bakin Maman ta kan komawa mahaifin ta, ta ce for my sake Mammah! Ta hada hannayen su wuri guda tana rokon ta. Har da hawayen ta. A karshe Jalan ta amince zata komawa Baban Amani, albarkacin Amani da Mukhtar don su yi zaman aure na jinyar Alhaji, koko zaman auren zuba ruwa a buta da kai ruwan wanka kamar yadda Amani ta kira auren. Wata biyu bayan nan Mukhtar ya yiwa Baba Idirisu da su Kamilu da Baba Sahura shirin tahowa Kenema, shi kadai ya tsaya tare da Alhaji da kamfani, cikin kwana uku da zuwan su aka maida auren Ahaji da Jalan, farin cikin da Amani ke ciki ne yasa ita da kanta ta hada musu kayan su don su taho Katsina tare da su Baba Idi, wai biki zata yi wa Daddy da Mammah, biki na kece raini, hararar ta Jalan ta yi ta ce, ki fara shirin naki bikin dai, ni ba saar wasan ki bace. Baba Idi dake wurin yace ai in suka isa Katsina ba zama zasu yi ba, mika ta wajen mijin ta zasu yi, zasu dunguma ne su wuce wajen iyayen sa a Diffa region, ta kasar Nijar. Kuma Mukhtar yace in sun tafi bazata dawo ba, sai ko da ganin gida. Maganar sai ta tunowa Jalan da Yayar ta Aisata dake Nijar. To ai kamar a Diffa din ne ma dan aiken dake tsakanin su yace take aure. Tsakanin ta da Aisata sai aike, don bata taba fita daga gidan mijin ta ba tun ranar data shige shi. Ta sa a ranta zata nemi jin hakikanin inda take a Nijar din in sun je, bata dai tabbatar da inda take a can din ba don taba zuwa ta yi ba, zata nemo mutumin ya bata adireshin Aisata ko don ta yi wa Amani Uwa a can da jinin ta kuma uwar ta. **** **** **** B a karamin shiri Mukhtar ke yi na isowar Maman su Jalan ba. Ya sa an fente gidan gabadaya da sabon farin fenti mai feshi, an shirya mata dakuna na alfarma da furnitures yan uban su. Sannan ya sa an shirya dakin Fajur kusa dana Amani, Safwan ma yasa na fidda masa daki daga waje kusa da na Kamilu. So gida ya zama full house, family house don hatta Baba Idrisu sun bashi dakin sauka a gidan duk lokacin da ya zo. Gidan Hon. Usman babban gida ne da ya lamushe dukiya mai yawa wajen ginawa a matsayin sa na Architectural Engineer, har gobe kuma kullum kara kyawun gidan ake da gyara shi yadda zai tafi daidai da zamani da duk wani sabon abun kawata da ya shigo da shi daga waje. Rakiya na ta hidimar dawowar uwar dakin ta, bata sama bata kasa don tabbatar da ta ajiye ma Amani komai na bukata, yadda suka saba. Ta ji labarin auren Amani da Mukhy a bakin Malam Tajudden tun kafin su dawo, tayi mamakin ta ita kadai ta bari. Yanzu kuwa Kamilu ya gaya mata har Babar Amani mahaifiya zaa dawo don haka girke-girke na musamman ta yi musu, zuwa yamma kuwa sai taji dirin motocin da suka je debo su sun shigo, wato dai sun iso gidan lafiya. Gidan ya kaure da hayaniyar farin ciki, Mukhtar yana gidan sa yana barci bai san sun iso ba, don jiya kwana yayi da maaikatan Alhaji ana meeting na amana, kan wanda zai jagoranci kamfanin Alhaji da gaskiya a cikin su tsofaffin maaikatan Alhaji, sabida shi zai koma gida, bada jimawa ba. Bai kuma da niyyar dawowa. Boutique din Amani ya koma karkashin kulawar Kamilu kasancewar shima kasuwanci ya karanta. A karshe Mukhtar ya zabi Alhaji Badaru Matawalle wani tsohon maaikacin kamfanin da sun fi shekara Talatin suna aiki tare da Alhaji, a shirya a bata, still dai an jure zaman tare na lokaci mai tsayi, an kuma san halin juna, Alh. Matawalle dan asalin Bindawa ne, shi Mukhtar ya baiwa kujerar sa karkashin saka hannun mutumin da Lauyoyin Alhaji, suka yi resolution kan zaa cigaba da gudanar da ayyukan kamfani yadda aka saba bisa amana da gaskiya, Mukhtar ya ce ko yaya suka fahimci wani abu ya biyo baya na rashin gaskiya a kamfani, to kuwa zasu rufe kamfanin ne kawai. Aka yi komai a shariance, sannan ya ce gobe zai ma Matawalle handing over na ofishin sa. Ba shi ya tashi daga barcin gajiyar da yake yi ba sai ana gab da kiran sallar maghriba. Don haka a gurguje ya shiga wanka yayi alwallah ya fito yana shiryawa a gaggauce, ya san yanzu su Amani sun dade da sauka. Ya rasa dalilin dokin da ke cin ran sa sai kace shi aka kawowa amarya ba Alhaji ba. Murmushi ya yiwa kan sa, wani abu da ba kasafai yake faruwa da shi ba, wato bai da yawan murmushi, kuma in yayin, shi kan sa ya san ba karamin kyau yake kara masa ba. Ya ce ma kan sa in haka ne ai shima yana da amaryar, sai dai tasa fitsararriya ce hamshakiyar shuuma mara kunya, ba irin ta Alhaji mai kirki da sanin ya kamata ba. Sanda yake fesa turaren sa watau Azzaro Visit bayan ya fito daga wanka, sai da wani farin cikin son ganin Amani ya darsu a ran sa. Yana duba wayar sa ya ga missed call din Alhaji dana Kamilu rututu, da sauri ya saka takalmi a kafar sa ya fita, bayan ya rufo kofar dakin da mukulli ya hau motar sa Bugatti wadda Alhaji neya bar masa ita zuwa gidan Alhajin, duk da ba nisa da nasa gidan tafiyar kafa ce kawai, ya kuma fi zuwa a kafan a yawancin lokuta, amma yau da yake cikin saurin isa gidan yake sai kawai ya hau motar. Yana parking yana fitowa da Safwan ya fara tozali, yaron ya zo da gudu ya rungume shi, bakin Mukhtar yau a bude, fararen hakoran sa a warwaje, kai ka ce shi ya mallaki kamfanin COLGATE, abinda ya baiwa su Malam Tajudden matukar mamaki, sai fara yake yana rike da hannun Safwan suka shiga gidan, yana ta bashi labarin zuwan su da abubuwan da suka gani na mamaki a hanya. Kai tsaye falon Alhaji ya nufa inda ya tadda su su duka a can, har Mamma Jalan, sun hada kai ana cin abinci tana zubawa Alhaji ruwa a tambulan, wannan abu yayi matukar faranta ran Mukhtar. Yau rayuwar Ubangidan sa ta koma irin wadda ya dade yana masa fata, rayuwa mai kyau da maana wadda addinin musulunci yayi koyi da ita, ba irin kazantacciyar rayuwar sa ta baya ba ta babu wani jinin sa da zai rabi niimar arzikin da Allah ya yi masa. Wadda watakila ita ta jawo masa yake ta shan wahala a rayuwar sa. Ya duba ya hanga a cikin su bai ga yar mulkin ba. Wadda tun zuwan su gidan da aka kauraye da hayaniya ta samu migraine wato ciwon kan barin kai guda wanda gajiya ta haifar mata, sai ta zame jikin ta ta haye sama dakin ta, ta shige ta kulle kan ta. Har da lika takardar data ke likawa Rakiya a jikin kofa an rubuta DO NOT DISTURB wato kada wanda ya zo ya dame ta. A duk sanda Rakiya taga ta lika mata wannan a jikin kofa bata kara zuwa kofar dakin sai ta neme ta don kan ta. To yau ma hakan, Rakiya ta zo don ta kawo mata nata abincin, don ta san bata cin abinci da mutane, nan ta ga abinda aka lika mata tuni ta yi ta kanta. Baba Sahura ta tambaye ta ina Uwa, ta san in ta ce UWA Amani take nufi, ta ce tana barcin gajiya ta lika kada a dame ta. Sahura ta ce Inye! Mulki sai mai shi. Wannan da basarake ta aura bansan ind zata kai mulki da iyawa ba. Shigowar Mukhtar falon aka kauraye da yi masa barka da zuwa daga bakin kannen sa Fajur, Kamilu da sauran yayan Baba Idi dana Sahura da suka zo daga Faskari yau. Baba Sahura na fadin ango ka sha kamshi, na Uwa farin mutum mai farar aniya alherin Allah ya kaiwa iyayen da suka haife ka. Sahura ta fadi hakan ne don ta san duk wannan kokarin na gyara rayuwar su data dan uwan su, kokarin sa ne bana wani ba. Shima yau ya kasa yin rowar murmushi, sai sakin sa yake gwanin shaawa. Ya zauna daf da Alhaji yana gaida Mammah, tace Mukhtar ya naga idanun ka sun tasa? Ina fatan lafiya dai? barci nayi mai yawa Mamma, da yake jiya mun kusan kwana muna meeting ta ce to madallah, ga abinci ta soma serving din sa burabuskon shinkafa da miyar ganye da naman tolo-tolo, ya ce Ai Mamma ban iya cin burabusko, shake ni yake yi ta mayar ta zuba masa fried sphaghetti da romon kaza sannan ya karba ya soma ci ana ta hirar Saliyo. Alhaji ganin kowa ya manta da Amani shi bai manta da ita ba, yar lelen sa tana like a ran sa. Yace Mukhy, ka gama cin abincin? Ya ce eh Alhaji. Alhaji yace yawwa, to maza tashi ka je ka zo min da TAFISU yau labarin rayuwar ka zaka bamu dukkan mu. Da abinda ya rabo ka da iyayen ka tun da ka ce min suna raye, da dalilin da yasa baka ko so a yi maka zancen gida ko na kasar ku. Amma ina so ya zama an yi komai a gaban Uwa ta (Tafisu). Don haka je ka zo min da ita. Kunya ta kama Mukhy, musamman da Jalan ta zuba masa ido, ta rasa mai yasa take jin sa kamar dan cikin ta, ta yaya zai iya tsallake Uwa da uban Amani ya je inda take a cikin gidan su? Sai da Alhaji ya sake maimaita umarnin sa, shi ba abun yace a aika Fajur ko Safwan ba, tunda Alhaji ne da kansa yayi magana. Da kyar ya iya mikewa ya bi matattakala da sassarfa zuwa sama, wato bangaren Amani. Yana zuwa kofar dakin ya ci karo da sakon ta na Do Not Disturb. A jikin marikin kofa. Dariya ce ta kama shi, sai kace a Hotel! Ai kuwa zata ga disturbance yanzun nan. Kofar ya hau kwankwasawa da karfin sa kuwa. Amani na tsakiyar barcin wahala barcin da migraine ya sabbaba mata, ta ji ana mata wannan bugun na rashin tsanaki. Ta mike cikin rangaji da sarawar kai ko kayan jikin ta da suka zo dasu a jikin ta bata cire ba balle dogon hill shoe dake kafar ta, haka ta afka gadon duka, tana tafe zuwa kofar a fusace, tana fadin mai raba ta da Rakiya yau sai Allah.....sai tayi kasa-kasa da ita, sai ta ci abu kaza-kazan ta. Tana budewa dogon baabzinen yana sako kai cikin dakin har yana kusan ture ta, saura kadan ta fadi don dama jikin ta ba kwari. Ta yi maza ta rike marikin kofar. Farin gilashin dake idon sa ya zare, yadda zai ji dadin kallon matar tasa rigimammiya Amani Faskari, ta yi yar kiba kib-kib ta yi jawur ta murje abinta. Mai nuna ta samu kwanciyar hankalin da bata taba samu ba a zaman ta a Saliyo. Ga wani uban su kunshi mai ja da baki da Mamma tasa aka yi mata a sawayen ta da zara-zaran tafukan hannayen ta. Ta fito a amaryar ta sosai sai rashin mutunci fal a idanun ta. Tace a fusace. Shin baka ga an saka do not disturb bane? Da zaka zo ka tada ni daga barci bayan bani da lafiya? Mukhtar ya ce do not disturb, a dakin hotel kike? Ko wata tsiya kike kullawa a dakin banda barcin asara? Kuma na dauka a gidan mutane kike ba a gidan ki ba, da zaki kwanta kina zuba iko? Kallon mamaki Amani tayi masa, ta ce gidan namu ne gidan mutane? Ni da gidan uba na? Ya ce aikin kenan! Alfahari da Uba, ko anan aka binne cibiyar ki baki da ikon cewa kada a dame ki a gidan nan, tunda ba gidan mijin ki bane gidan Mama Jalan ne yanzu. Amani tayi kwafa, ta koma gefen gado ta zauna tana fadin har akwai wani gida da ya fiyewa mace gidan uban ta? Mukhy ya ce sosai ma kuwa, gidan uban nata na wucin gadi ne, gidan da zata je ta haifi yaya shine comfort zone din ta, shine inda duk mulkin data zuba babu mai kalubalantar ta. Amani ta zo iya wuya, idan nace maka ni kuma babu wani comfort zone da ya fiye min gidan uba na muhimmanci zaka yarda? Idan nace maka baka da gidan da ya isa ka ajiye babbar yarinya iri na zaka yarda? Idan nace maka Alhaji ya cuce ni iya cuta da ya bada aure na gare ka kaskantaccen bawan sa zaka yarda? Idan nace maka kyan ka da ake fadi bai taba bugar da ni ya sa na ji ka da wani matsayi a rai na ba saboda baka kai matsayin da zan aure ka ba zaka yarda? Ina bakin cikin abinda ya shiga tsakanin mu ranar nan a Saliyo, saboda kai ba aji na bane, ka yarda? Mukhy ya juyar da idanun sa da suka canza launi, yana kokarin hadiye bacin ran da ya taso masa, ya ce me kuwa zai hana ni yarda tunda na kwana da sanin yar Qaruna ce, Tafisu wadda tafi sauran mata, kuma a hakan aka bani sadaqar ta, ana roko na Allah Annabi in karba da hakuri, saboda Alhaji kan sa ya san ba yar kwarai ya haifa ba; ballagaza ce, banza ce, mahaukaciya ce kuma jahila, wadda ta rako mata duniya!. Amani sai ta fashe da kukan da baya mata wuya na shagwaba da sakalci, amma na yau iya gaskiyar ta take yin sa bilhaqqi, domin Mukhy yayi mata cin mutunci da wani dan adam bai taba yi mata ba, tun baa je koina ba, ai ga irin ta nan, Daddy ya sayo mata gori da rashin daraja a wajen wanda bai isa komai ba, sai ta kara tsinkewa da kuka. Mukhy yayi kwafa, yace yarinyar nan ina tausaya miki domin baki san rayuwa ba ko kadan, baki san Annabi ya faku ba, baki san dukkan mu darajar sa muke ci ba, duk wani rawanin tsiya ya kare a kan ki, Ubangiji ya laanci shaidan ya kuma fitar da shi daga Aljannah ne sabida girman kan sa da jin cewa yafi kowa. Baki san Allah ya ce Inna akramakum indallahi Atqakum. Ubangiji yayi alkawarin dankafar da maabota girman kai dagawa da alfahari, masu girman kai iyalen shaidan ne, ni ina tausaya miki, ina kuma tausayawa kaina, sannan ina tausayawa yaya na idan kika haife su baki yi hankali ba. Ke kam ai dadi ne ya yi miki yawa, shi yasa kika kasance mara godiyar Ubangiji; Uwa da Uban ki na son ki, suna tarairayar ki da ririta ki da son ganin kin zama matar aure ta kwarai, wani kama na iri na bai samu wannan gatan da kika samu ba. Don haka in kin gama ki zo suna kiran ki a kasa. Daga haka ya juya ya fice ya koma wajen su Alhaji. Yana kokarin maida walwalar sa ta dazu, amma hakan ya faskara, domin kullum Amani ta ci mutuncin sa fita take kara yi a ran sa, baa jimawa kuma in ya huce zata dawo ta yi masa kaka-gida a rai, ya manta duk wani aibun ta. Ba jimawa sai gata ta sauko cikin shiga ta kasaita, ta ci hill shoe din ta kamar mai shirin tafiya dinar babbar aminiya, ta kafe dauri a gaban goshi tana tana taunar cingam rakakas-rakakas. Ita a lallai ga wadda tafi sauran mata. Da dane, da tuni Alhaji ya fara yi mata kirarin TAFISU! Amma yanzu da yake yayi hankali sai cewa ya yi Uwa yaya kika sakko babu mayafi? Maza koma ki yi lullubi ta zumburo baki sannan ta koma, Jalan tayi fatan a kusa da ita take ta kaiwa bakin da ya sha purple din jambakin Elizabeth Arden lipstick kalar material lace din dake jikin ta kyakkyawar mahangurba. Sai Allah ya ceci Amani daga can nesa da ita kafar bene ta tsaya. Ta dauko mayafin wanda dashi da babu duk daya dai ta dawo. Baba Idrisu yayi sallama ya dawo dakin don ya dan zaga toilet ne. Alhaji ya nuna mata gefen Mukhy ya ce nan ne wajen zaman ta family meeting zasu yi. Kallon da Mamma Jalan ke mata ne yasa ta yarda ta zauna a gefen Mukhy din, ba tareda ta yi musu ba. Jalan ji tayi kamar ta fashe da kuka a kan irin taunar cingam din da take yi a gaban kowa. Ta na Allah-Allah a tashi meeting din ta ci uban ta. A Saliyo ta dan samu saiti, wato yanzu an dawo gaban Alhaji da ke daure mata gindi shine zata koma halin ta? Ita kuwa Amani tana sane duk abinda take yi don ta kular da Mukhy ne, wato ta rama cin mutuncin da yayi mata, ta san baya son ta da cin uwar kwalliya irin haka. Balle daurin gaban goshi. Har taunar cingam din ma baya so ya taba ce mata ba tarbiyya bane. Alhaji bai san tana yi ba. Haka Mukhy bai bata hankalin sa ba balle ta kular da shi din data ke so, ya ce Mukhtar yau ina son in san tarihin ka, abinda ya fiddo ka daga gida, da kuma abinda yasa baka so ka koma kusan shekaru tara kenan. Lokaci yayi da zaka je gida tunda ka fara aje iyali. Ba fata ake ba, amma akwai mutuwa akwai kuma ciwo. Ba damuwa muka yi mu san cewa kana da asali ko baka da shi ba, amma lallai zamu kai Amani ga iyaye da yan uwan ka don su san da zaman ta, tunda auren sunna ne muka kulla, wanda muke fatan a samu zurria a mai albarka a cikin sa. Mukhtar ya nutsu sosai yana sauraron ubangidan sa kuma surukin sa a halin yanzu, ya san gaskiya ya fada, amma sabanin lokutan baya da in yayi masa maganar gida ransa ke baci yau shi da kansa cikin nostalgia (begen gida) yake domin ya fara gajiya da gorin Amani. Kuma ya saka a rana sa cikin satin nan in Allah ya yarda zai koma gida ko da Amani bazata yarda ta bi shi kasar su ba. Mukhtar ya ce. Labari na mai tsaho ne Alhaji, and very complicated, tragic story. Wanda nafi so in yi revealing din shi tare da ku da iyaye na a zaune gabadaya. Abinda zan iya cewa a yanzu shine iyaye na suna raye (as far as I know), ina kuma da labarin duk halin da suke ciki ta hanyar wani abokina na kuruciya mai suna Ari. Na fito daga yankin Diffa. Diffa din wani babban birni ne da ke kudu maso gabashin jamhuriyyar Nijar. Garin na da iyaka da tarayyar Najeriya daga kudu maso gabashin kasar. Birnin Diffa ya samu asali tun a lokacin daular Borno (Kanem-Bornu Empire). Wato tun lokacin 1900. Asalin mutanen da suka yi rayuwa a cikin ta a lokacin Kanurai ne (ko kuma Barebari). Amma yanzu Diffa ta hada kabilu guda uku; Larabawan Diffa wadanda ake kira (Diffa Arabs), Buzaye da kuma Tubawa, duka suna cakuduwa suna rayuwa a cikin ta. Diffa tana nesa da kimanin kilomita 1360 daga babban birni Niamey. Iyayen mahaifi na sune asalin kabilar Diffa Arabs, watau Tubawa ne, yaya ga Sultan Oumarou Mai Diffa, wadanda tarihi ya nuna kakannin su, su suka kafa daular Diffa Arab. Mohammed Bazoum kan sa, wato shugaban kasar mu na yanzu dan asalin Diffa ne daga kabilar mu ta Diffa Arabs. Sai Mukhtar yayi murmushi ya dubi Daddy, Alhaji iya labarin da zan iya baku kenan a kan inda na fito, maganar iyaye na ko abinda ya fiddo ni daga gida sai mun je gaban Ummami da mahaifi na Sultan Issoufou Massaoudou, a yanzu dana yi hankali na ga ya dace nayi exposing ciwon zuciya ta gare su, su san halin dana rayu ciki a kan su, maimakon in yi ta rike shi a kasan rai na ina fama da shi tun daga kuruciya ta har girma na. Alhalin su basu san ina da shi a kasan rai na ba. Ko sun sani, ban taba tattauna shi da su ba. Na dade ina fama da wani dabaibayi mai fizgata ga nesanta da gida, kullum dabaibayin nan cewa yake dani in kara nesanta kai na da Diffa, ta hakan ne kawai zan samu nutsuwa da kwanciyar hakali, idan ba haka bazan taba zama cikin nutsuwa ba. Rana daya tun zuwan mu Saliyo na tashi na nemi wannan dabaibayin a tare da ni na rasa, na nemi fargabar da ke mamayata idan na tuna Diffa na rasa, na ji komai ya yaye daga cikin kaina duhun da ke zuciya ta ya koma haske. Wannan alamari ya faru da ni a wannan tafiyar da muka yi zuwa Saliyo, tun daga lokacin hankali na ya koma gida da son ganin iyaye na, kuma jin zafin su da ke raina na samu yana decreasing gradually (raguwa a hankali), a halin yanzu ina iya yi musu uzurin da a baya bana iya yi musu, ina shaukin ganin su, sannan a shirye nake ga fuskantar abinda a baya nake tsoron fuskanta a gida, komai tsaurin sa. Na shirya komawa gida a halin yanzu. Hakika Alhaji yanzu na shirya ko ba don Amani ba zan koma gida. Lokacin tafiya ta gun Ummami yayi. Ina jin kaina a zan iya fuskantar kowanne irin kalubale da zai iya tunkaro ni with a very big and brave heart, wadda a baya ban mallaka ba, na rasa farin ciki tun ina yaro, na kasance cikin kadaicin rayuwa wato solitude mai sakawa dan adam inferiority complex, a dalilin iyaye na basu yi min abinda nake so ba. Alhaji na karbi auren da ka bani da hannu bibbiyu, banida bakin da zan godewa kyautatawar ka gare ni, da rikon da kayi min, na karbi Amani zan tafi da ita cikin ahali na duk da ikirarin ta na rashin son auren mu, ni na karba na kuma gode. Na kuma yi alkawarin rike ta da amana har karshen numfashi na. Alhaji sai ya saki hamdalah yana fadin, na gode Mukhtar na gode Allah ya yi maka albarka, Im the one to thank you for changing my life positively, tunda ka zo gare ni rayuwa ta ta canza, albarka ta lullube rayuwa ta, dukiya ta ta rubanya ta yi albarka yadda ban taba zato ba, don haka nine da godiya na kuma yarda duk lalacewar da duniya tayi, har yanzu akwai masu mutane masu amana akwai kuma mutanen kirki, kai dai kayi wa dan kowa alkhairi ba sai naka kadai ba. Baka san wanne zaka ci amfanin sa ba. Kuma baka san wanne ne zai ji kan ka ba. Sai ka shirya mana motocin da ya dace muyi tafiyar a ciki, wadanda basa makalewa a cikin sahara. Ya ce ai Alhaji a Land-Cruiser din ka kawai zamu tafi, tana da tsaho da fadi, a kalla zata dauke mu nida kai, Mamma da Baba Idi da Baba Sahura, da ita wannan. Ya nuna Amani da baki. Amani ta galla masa harara ta murguda baki cikin takaici, wai ita yake cewa ita wannan, alhalin ya lissafa sunan kowa, wato ita bata kai matsayin da zai fadi sunan ta ba, irin wannan rashin darajawar da yake mata shi yake sawa take kara tsanar sa, tunda gashi ya kara fadi a gaban iyayen ta da ita kanta cewa ya gode da sadakar ta da Alhaji ya bashi. Hawaye ya surnano daga idon Amani Faskari, yau ita ce zata koma rayuwa a kauyen Nijar! Wata alkarya da ko sunan ta bata taba ji ba, wai Diffa. Da sunan aure a inda bata da kowa. Mafarkin ta na tafiya yin masters a jamiar QUEEN MARY UNIVERSITY OF LONDON ya zama tarihi! Ya bi ruwa! Ta zama cikin Diffa Arabs, makiyayan daji da bata san ko yaya aladu da dabiun su yake ba. Sai gani aka yi Amani tana rafzar kuka, ita ba abun tace bazata ba, ta san ba mai bin bayan ta, Mukhtar bayan saye Ubanta da mugun sumumu-kasau din sa, Uwar ta ma ya saye yanzu, sai abinda ya ce. Shi kadai ne mutum a idanun su. Ta yi magana yanzu Mamma ta kumbura mata baki, tunda kuma a kusa da ita take zaune. Mukhtar ya fita yasa Tajuddeen ya fido Land Cruiser din Alhaji ya ce a kai ta service a kuma yi mata full tank, gobe asubanci zasu yi zuwa kasar sa. Kuma shi da kan sa zai tuka motar. Tajudden tun a lokacin ya soma kewar Mukhy, wani kwayan mutum guda daya wanda ya zame masa tamkar dan uwa a gidan Alh. Usman Faskari, ba irin alkhairin da baya yi masa. Ya yi wa Mukhtar fatan alkhairi, yana hawaye, tare da rokon sa ya dinga zuwa suna ganin sa lokaci-lokaci. Ko albarkacin Amani da zai dinga kawowa ganin gida. Haka yai ta sallama da duk maaikatan gidan. A daren kowa ya hada kayan da zai tafi da su banda Amani, sai Mamma ce ta zo ta hada mata da kan ta. Kwana ta yi akan kujera tana kuka, kafin asubah bayan ta ya rike, wuyanta ya kage, kuma a haka suka ce bazasu jira ta ta yi wanka ba ta yi sallah kawai su kama hanya, don already Mukhy (wanda yau wata irin shiga yayi, ta asalin ainahin larabawan Diffa), in ba har ka yi masa farin sani ba bazaka gane shi ba, ya shirya tsaf cikin kayan kasar shi a jikin shi wato traditional attire na Diffa Arabs ya fito a ainahin kamannin sa na Tubawa ko kuwa larabawan Diffa). Kasancewar duku-duku ne cikin su babu wanda ya ga irin shigar da Mukhy yayi, musamman da yana cikin mota ne a zaune, ya tada mota ya bata wuta a waje, su kawai yake jira su fito. Mamma duk zafin ta sai da tausayin Amani ya kamata ta hada da lallashi, ta kuma yi mata alkawarin zata kawo mata Fajur daga baya in ta gama makaranta, kuma zata bar Baba Sahura ta zauna da ita har sai ta saba da mutanen data tarar, kuma zata nemi Yayar ta dake Nijar ta hada su. Wannan ne ya dan sanyayawa Amani, amma in ta tuna ta bar comfort zone din ta kenan zuwa wani kololuwar kauyen Nijar bata sanin sanda take sake rushewa da kuka, tana laantar Mukhtar da kaddarar data yi sanadin zuwan sa gidan su. **** **** **** MU BIYO JARUMAR TAMU AMINA-AMANI, UWAR BABA IDI, SANNAN TAFISU YAR GIDAN BABAN TA… ZUWA YANKIN DIFFA A LITTAFI NA UKU DON GANIN YADDA ZATA KAYA TSAKANIN TA DA MIJIN TA MUKHY’ DAN KABILAR LARABAWAN DIFFA.