AMANI 3 Littafin SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI) takorikabara@gmail.com 07030137870 TAFIYA ZUWA DIFFA M asu iya magana suka ce tafiya mabudin ilmi, wasu kuma suka ce tafiya yankin azaba. To duka dai Alhaji da iyalin sa da yan uwan sa babu wanda basu fuskanta ba a hanyar su ta zuwa jihar Diffa ta kasar Nijar. Ga Karin ilmi suna ta samu a kan garuruwa da Baba Idi ke musu bayani kasancewar ya taba zuwa fatauci Nguigmi daga Maiduguri tun yana saurayi, ga kuma yanayi na wahalar zafin ranar sahara wadda tasa hatta A/c din motar daina bada sanyi ta ke yi lokaci-lokaci saboda zafin rana da zafin rairayi irin na sahara. A hakan ma don sun yi zagaye ne ta Maine-Soroa da Nguigmi basu bi ta cikin Bama din Maiduguri ba. Kasancewar sun fito tun asubah, tafiya non-stop, kuma mota lafiyayya, zuwa yamma sai gasu a cikin Maine-Soroa, makwabtan Diffa, anan ne suka tsaya suka yi sallah azahar da laasar da ta riske su a hanya, suka sayi gasashshen naman rakumi da madarar rakumi mai dumi sabuwar tatsa da sabon cukui a nan cikin garin Maine-Saroa suka ci, suka sha, Mukhy har Shayin su na Tubawa ya saya ya sha, dama kuma dai sun yo guzurin su yadda ya dace na abinci da abin sha, wanda tun dare Rakiya ta shirya musu suka taho da su, wadanda ba masu lalacewa ba, snacks ne da soyayyun kaji (pepper chicken), don haka basa tare da yunwa har suka shiga jihar Diffa. Shigar su garin ke da wuya komai ya soma kwancewa Mukhtar, (his in-born character) ya soma aiki a kan sa, ta yadda hatta gashin jikin sa dana kan sa sai da ya mimmike da duk wani gashi da ke jikin sa. Amani da ke gefen sa yana tuki, ta lura da yadda Mukhtar ke canzawa a yanayin sa da halittar sa, wata irin kamala da nutsuwa suka bayyana a tare da shi, suka lullube ainahin Mukhy saurayi nan dan gaye suka maida shi cikakken MOUKHTAR din sa, tsigar jikin sa har wani tashi take yi kamar mai jin sanyi. Jinin Issouffou Massaoudou ya soma circulating yana kurdawa a cikin jikin sa, yana sauya shi daga normal Mukhtar din sa da kowa ya sani zuwa Mainan Diffa na asali. Amani bata san me Mukhy yake kwancewa daga leda ba ta ga dai Mukhtar ya saka hannu ya janyo wani farin kyakkyawan tsohon amawali (rawani) daga cikin leda, ya kashe motar su a gefen titi. Rawanin nan ya hau nannadawa cikin iyawa da kwarewa, saida ya nade kyakkyawar fuskar sa tsaf, sai tsinin karan hancin sa da manyan idon sa ne kadai ya bayyana, kwatankwacin yadda taga nadi a fuskar mafi yawancin jamaar garin maza, wato nadin rawani irin na buzayen asali ko kuwa Tubawa, ko kuwa a kira su da yadda aka san su da shi wato Larabawan Diffa. Sai bata yi mamaki ba, don kuwa ta san cewa baa canzawa tuwo suna, Mukhtar duk dadewar sa tare dasu, idan aka taho gida, shi buzu ne na hakika. Ya ja motar suka cigaba da tafiya. Baba Idi na tsokanar sa wato kowa ya bar gida-gida ya bar shi, kyawun kowanne tsuntsu yayi kukan gidan su. Mukhtar yayi dan murmushin miskilanci ta cikin amawalin sa, bai ce komai ba. Amma ya yarda da maganar Baba Idrisu cewa kukan gidan su har da kururuwar gidan su yake yi yanzu. Zuwa lokacin sun shiga tsakiyar gari, Amani ta bude hanci da ido tana shan kallon alummar wannan jiha dake cikin janhuriyyar Nijar, ta fahimci cewa sittiru, kamanni na halitta da dukkan aladar su ta barranta da ta inda ta fito, suna ta gudanar da harkokin su na yau da kullum cikin sukuni da godiyar Ubangiji, domin kuwa alummar wannan yanki na Diffa mafi yawa talakawa ne likis, masu abin yi daga kiwon dabbobi (livestock production), kasuwancin waje (export trade), jimar fatar rakumi da sauran su. Sun kuma kasance maabota biyayya ga shuwagabannin su, wato sarakunan yankin Diffa. Shiga nan fita can Muktar bai manta hanya ba, bai manta koina ba, kamar wanda ake bankado komai daga cikin kwakwalwar sa ana nuna masa, kamar jiyan nan ya tafi daga Diffa. Haka yake ji yanzu da ya dawo cikin ta kamar ba shekara goma sha biyar ba, haka rayuwar sa ta baya ke rewinding kamar kaset din video a cikin kan sa, tana tuna masa duk abinda ya faru a baya. Sai suka hau wani mikakken titi dodar mai nisa, wanda daga shi Amani ta soma hango wani dogon kasaitaccen gini, wanda tsahon sa da fadin sa ya kai daidai da kilomeita (2,988), wani katafaren gini suke dosa wanda daga can sama aka rubuta da harshen larabci Al-iimaarat-al Diffa wato Diffa Emirate da harshen turanci. Suka cigaba da tafiya Amani na cewa a ran ta wato in ka zo garin, sai ka fara kaiwa sarki gaisuwa dole, kafin a bar ka ka tafi cikin gari inda ka zo. Can kuma ta ce Watakila kuma Baban sa bawan sarki ne, shi yasa ya tura shi birni neman kudi maimakon ya makale abin sa su yi bauta tare. Ai kuwa ta kasa shiru, ta kasa barin tunanin ta a ran ta, lokacin da ta ga sun hau titi fetal wanda ya mika har cikin fadar Diffa. Masu tsaron babbar kofar masarauta ta farko suka tare su a kofar shiga, amma da Mukhtar ya sauke tagar sa, suka ga wannan nadin dake kansa da wannan amawalin da kuma tambarin da ke jikin rawanin, sai kawai suka daga musu kofa suka wuce ciki. Gasunan gasu nan har gate na biyu, shima kamar na farko daga ya sauke glass sun ga irin nadin sa da amawalin sa sai suka daga masa kofar masarauta suka nausa ciki. Daga nan sai gate na karshe, wanda shine na uku kuma daga shi sai fada. Anan ne aka dan takura da binciken bayan motar su kafin Mukhtar ya sauke glass, Amani na cewa Daddy ashe dan naka bawan sarki ne? Ko ko dan bayi ne ka ga duk sun san shi. Mamma Jalan ta kusa zagin ta, don ita jikin ta ya fara bata abubuwa masu yawa, amma Amani tana haukan ta irin wanda bata san ranar shiryuwar ta ba. Baba Idi ne ya ce mata shi dan bayi ba mutum bane? Jaira marar mutunci. Sai tayi dif! Wani tsohon bafade tukuf, ya dogaro cikin kayan dogarai na jikin sarki sosai ya zo bakin tagar da Muktar yake, yace Samari, na gan ka da Amawalin gidan nan, Amawalin dana baiwa Mainan Diffa, amma ban shaida ka ba, ko zaka bude amawalin in gan ka sosai, kafin mu yi muku iznin yin parking a kofar fada? Sai kawai Mukhtar ya sa hannu yana warware rawanin kan sa, yanayi wa tsohon nan murmushi idanun sa fal hawaye. A hankali ya ce Baba na Katchalla! Tsoho Bafaden nan sai ya fadi kasa, yana fadin Allah ya taimaki Mainan Diffa, barka da dawowa hasken Diffa! Wannan batu da wannan tsohon bafade ke yi shi ya janyo hankalin sauran fadawa duk suka taho da gudun gaske, wajen hannu goma ne ya budewa Mukhtar kofa a gigice, suna faduwa suna tashi suna fadin Hasken Diffa ya dawo, barka da dawowa hasken Diffa, barka da dawowa tauraron Diffa, Maina ka sauka lafiya ka taka a hankali. Allah ya kare tauraron Diffa, haske maganin duhu, hadari malafar duniya. Daga nan aka bude musu kofa a ka bazawa Mukhtar babbar riga aka kareshi ya sauko daga motar. Tuni har wani ya sheka labari cikin gida wai ana tsammanin Mainan Diffa ya dawo, zancen nan nan da nan ya isa kunnen Sarki Issouffou Massaoudou, wanda ke kwance a turakar sa a lokacin bayan ya sha magani, ya soma shirin dan mikewa ya kwanta kafin lokacin da zai fita fada. Sai ga wayar sarkin fada wanda ya manta shekaru nawa rabon da ya kira shi a waya, don a kaida fadawa basa kiran sa a waya. Kamar bazai dauka ba amma sai yayi tunanin banza bata kai zomo kasuwa haka kawai Katchalla ba zai kira shi ba, sai ya daga. Yana dagawa kuwa sarkin fada ya fashe da kuka yana fadin nayi rantsuwa da Allah ga Maina ya dawo, ka san dai cikin kowanne hali bazan kasa gane shi ba ko da bai zo da rawanin sa ba. Sarki Issouffou Massaoudou a kwance yake, amma sai ganin sa yayi a bakin kofa ya manta cewa jar hula ce da ake kira Dara da rigar shan iska mara hannu kadai a jikin sa, ya kama hanyar kofar da zata sada shi da hanyar fada. Fadawan da ke tsaron kofa sun kidima da ganin fitowar Sarki a haka yana ta surfa uban sauri, aka kuma rasa wanda zai tare shi ya tuna masa babu amawali da alkyabbar sa a tare da shi. Farin dattijo amma ba tukuf ba, kyakkyawan Balaraben Diffa na gaske wanda yawan shekarun sa bai boye kyawun surar sa na lokacin kuruciya da tsananin kamannin sa da Mukhtar ba. A lokacin har an shigar dasu Mukhtar fada, baka jin komai sai tashin kirarin da fadawa ke zubewa a kasa suna yi masa. Hadari malafar duniya, hadari sa gaban ka inda kake so, gaba salamun, baya salamun, haske maganin duhu Zaki dan Zaki, Majina gishirin yaro, tsawa mai ratsa gidan arna. Kunun bagaruwa cika ciki har makogaro. Dan Sarki jikan Sarki kuma sarki mai jiran gado. (Wannan kirari ba da hausa suke yin sa ba, suna yin sa ne da vernacular language din su wato Chadian Arabic daya daga cikin yaren Diffa Arab). Wani babban bafaden kuma yace Zakin duniya makiyanka fadawan ka, ana kin ka ana rusuna maka, ba yin kan ka bane yardar Allah ne da adduar iyaye ya dawo mana da kai. Allah Ubangaji ga Mukhtar dan Issouffou Massaoudou ya dawo gida. Hasken Diffa ya dawo, duhu ya yaye!. Amani da iyayen ta da ke kallon abinda ke faruwa kamar a majigi, sun kasa ko motsin kirki. Amani ta lura hatta tafiyar Mukhtar ta canza kan ta da kan ta, ba irin wadda yake yi a baya bace. Me ke faruwa ne haka a gaban idon ta? Wanene wannan Mukhtar din? Wane alamari ne tattare da shi haka? Jalan, wadda ke tura Alhaji cikin wheelchair zamu iya cewa mamakin ta ragagge ne, ko dama a tunanin ta tun ganin ta da shi na farko, bai yi mata kama da komai ba sai dan sarauta maabocin kyakkyawar nasaba, duk wasu attributes na sarauta sun bayyana kan su a tare da shi da halayen sa. Baba Idi da Baba Sahura sai zare ido suke don kuwa Sahura har fitsari ta yi a wando data ga wani katon Zaki mai rai a zaune, amma bai ci kowa ba, sai daga baya ta gane zane ne da aka yi da ceramic (architect) amma kamar real image na zaki mai rai, tambarin Issouffou Massaoudou Kenan, wato Zaki dan Zaki, zakin Diffa. Alhaji Usman dai hawaye yake sharewa a fakaice, ba tare da ya bari an gane kuka yake ba, Mukhtar ya shammace shi yadda baya zato, ashe dan sarkin Diffa ne mai jiran gado yake masa bauta iya bauta shekaru kusan goma! Dadin abun ya kyautata masa ya kaunace shi, irin yadda ko yan wan sa na jini bai yiwa hakan ba. Allah ne ya hada shi da Mukhy amma bai taba kawowa ran sa wai dan sarki bane mai jiran gado. Yafi dangantawa ma da cewa bashi da kowa a duniya shiyasa baya ko so a yi masa zancen ya je ganin gida. Karyar ku makiya da mahassada, karyar ku ta kare mahainta, yau Allah ya maido Mainan Diffa gida (Maina na nufin Yarima mai jiran gado a Diffa, kamar yadda Biyamaradi yake a Maradi). Ire-iren kirarin da ake ta yi wa Mukhtar kenan har aka bashi kujera kusa data Sarkin Diffa, amma sai ya ki zama ya zube a kasa yana kukan farin ciki da godiya ga Allah. A haka Sarki ya fado fadar, sarkin fada ya biyo shi da Alkyabbar sa da amawalin sa suka rufe kofar fadar aka hana kowa shiga bayan shigewar Sarki. Yana zuwa da Mukhtar ya fara tozali, ya ce Mon pils (Da na) Mukhtar da gaske nake gani? Koko ire-iren mafarkai na ne? Sai yayi baya luuu! Zai fadi, kasancewar dama yana fama da hawan jini tun tafiyar Mukhtar wanda ake treating din sa tun lokacin, cikin zafin nama Mukhtar ya tare mahaifin sa ya rungumo shi a kirjin sa, (for the first time) a rayuwar sa da jikin sa ya shafi na mahaifin sa, suka zube a kasa tare. Nan fadawa suka kare scene din da hannayen manyan rigunan su aka umarci kowa ya fita sai manyan fada kadai. Mukhtar sai firfita yake ma sarki da rawanin sa yana fadin ka yafe ni Ya Abiy, na dawo kenan babu inda zan kara zuwa, koda zan cigaba da rayuwa yadda kake so. Da kyar aka samu Sarki Issoufou ya zauna a kujerar sa, sannan ya yi umarni da ayi wa wadanda suka kawo Mukhtar sauka ta alfarma a babban masaukin bakin sa. Ummami na can cikin gida amma tuni labari ya kai mata ta bakin Jakadiyar Sarki marikiya ga Mukhtar, wadda ta shiga turakar ta kai tsaye ba tareda ta jira an mata iso ba, ta same ta tana haki, tana cewa yanzu wani bafade ya gaya mata wai Maina yana cikin fada bata san ko da gaske bane don yace an kulle fada, an hana kowa shiga. Mowar Sarki, sai ta mike ba tareda rakiyar kowa ba aka ga ta kama hanyar fita, akwai wata boyayyar kofa ta cikin turakar Sarki wadda yakan shiga fada ta cikin ta wani lokacin, ta can Mowar Sarki ta bi ta isa fada, Mukhtar sai ganin Ummami yayi a gaban sa, ta dubi Mukhtar shima ya dube ta ta taba shi ta tabbatar dan ta ne kwalli daya a duniya Mukhtar dan Issouffou Massaoudou, wanda ya bar su yau shekaru goma sha biyar! Kafin Mukhtar ya ambaci sunanta wanda ya kakare a makogaron sa ya kasa fita, Ummami ta fado jikin sa luuu! A sume. Mukhtar yana fadin Ummami kada ki yi min haka.. kada ki mutu bamu gana ba, bamu fayyacewa juna zuciyar mu ba. Na yi nadamar tafiya ba tareda na fayyace muku abinda ke rai na ba, kuma kun bani uzurin ku! Yanzu da girma ya same ni na san kuna da uzuri fiye da nawa. Aka yayyafawa Ummami ruwa ta farfado sai ta rike Mukhtar ta fashe da kuka. A lokacin an fita dasu Amani da Mamma da Daddy da su Baba Idi zuwa masaukin da Sarki yayi umarnin a kai su. Wani hamshakin gini ne na sarauta da yaji kujeru royal chairs na alfarma, da dakunan barci da aka kawata da gadaje na kasaita, babu abinda babu a wannan guest house din ga dakunan barci rututu. Aka shiga sauke musu kabakin abinci har da naman Dawisu, aka ce su kintsa kafin washegari Sarki ya gama ganawa da Maina zai neme su. In ka ga fuskar Amani a cikin guest room dinnan ta koma kamar jikakken tsumma, sabida yadda tayi cooling, tana ambaton Ya Salaamu sallim, a cikin ran ta, harda su istighfari, tana neman wanda zasu hada ido ko karin bayani ne ta samu, amma ina! Mamma Jalan ko kallon ta taki yi, sai hidima take da mara lafiyan mijin ta. Wata irin nadama da dana sani suka zo suka lullube Amani, mutumin data raina ta ke wulakantawa, ta cewa shege, ta cewa bawan gidan su, kai babu irin sunan kaskancin da bata kira Mukhtar da shi ba shekara da shekaru ashe ya fi ta kyawun nasaba, dan Sarki ne jikan sarki mai jiran gado, wanda in nasaba zaa bi ba ikon Allah ba, da bata isa zama matar sa ba. Ta daga ido tana kallon wannan kasaitattar hamshakiyar masarauta wadda ko masarautar Katsina bakidaya data sani bata kama kafar ta a kasaita da shaharar mulki ba. Kada dai Allah ne yake yi mata talala da laifukan ta, kalaman ta marasa Tauhidi da girman kan ta? Yanzu wace izza zata kara yiwa Mukhtar da gorin nasaba? Dama Jalan ta ce mata ta guji ranar dana sani. Ya Ilahal alaameena na tuba! Na tuba Ya Ubangiji na tuba, daga yau baki na ya daina fadar abinda ba alkhairi bane a kan kowanne dan adam, na daina raina kowa, na daina tunain nafi kowa gata! Ita kadai take furta wadannan kalaman kamar zautatta sabon kamu, cikin kidima, Mamma da Daddy duk suna jin ta, Sahura na yagar cinyar Dawisu ta ce ah to ai duniya makaranta ce, ta ishi kowa riga da wando har da hula. Allah da kan sa yayi hani da girman kai, ya bada misali da Shaidan da Annabi Adamu Alaihissalamu, Ubangiji da ya halicci dan adam ya karrama shi akan dukkan halittun sa, kai dan adam waye da zaka kaskanta dan adam dan uwan ka, don kawai kana tunanin ka fi shi arziki? Ai ko hausawa sun ce rabon bawa da arziki mutuwa ce. Baba Idrisu ya ce kwarai da gaske, baka debewa bawa tsammani da arziki sai ya mutu! Uwa ki ji tsoron Allah ki gyara halayen ki na raina mutane, kiyi karatun ta nutsu, nan dai kin gani gidan sarauta ne babu ta yadda zaayi su dauki halayen ki na banza da wofi, idan ma bamu koma tare ba kenan, tunda ke din ba yar sarauta bace, na san kuma yayan sarakuna yayan sarakuna ya uwan su kawai suke aure. Mamma Jalan ta ce da ta fi gane shayi ruwa ne. Don in ba Mukhtar din ba sarkin hakuri da girmama iyayen ta wa zai iya kwasar ta? Ai Amani an rako mata! Yau dai gaki gidan sarautar Diffa, ko ki iya takun ki, ko ki ji ki a kofar masarauta, ko kuma ki kare karkashin azaba da mulkin kishiyoyi. Idanun Amani suka wani irin raina fata, zuciyar ta ta tsinke, wai bata san tana da kishi ba sai yau da Mamma ta yi mata fatan kishiya, to ta Allah ba tasu ba su duka, ta san Mukhtar yana son ta ko bai fada ba, ta ga hakan muraran ranar su ta karshe da shi a Saliyo gidan Mamma, ta san ko saboda Alhaji ba zai wulakantata ba balle yayi mata kishiya. Ta san ta yi kuskure ba kadan ba amma a bata dama zata gyara. Ba wai a bita da mugun fata ba. Sai ta saka kuka tana cewa. Mamma ke uwa ta ce, duk abinda kika fada zai iya kama ni, ki fadi alkhairi a kaina da Mukhy ko kiyi shuru. Ta yaya zaki yi min fatan kora ko kuma na kishiya? Baba Sahura ta fashe da dariya tana fadin yau kuma? Lallai Amale ya ga Zaki. Yarinya wa ya gaya miki Bornu gabas take, miji irin wannan ake cewa baa so banda wauta da hauka? Daddy ne kawai ya ji tausayin ta, yadda suka taru suka yi mata caaa! Ganin yadda duk ta bi ta muzanta. Yanzu kam ta gama saddaqarwa Mukhy ya fi karfin ta, idan bata yi saa bama tare da iyayenta zata koma Katsina a matsayin sakakkiyar bazawara. Sunan ta ya koma bazawara. Irin iskancin da ta tata masa da kaskanci da rainin hankali da kyar zai iya yafe mata tunda ya dawo cikin gatan sa. Na tuba Ya Ubangiji na tuba! Amani ta fada a fili tana hawaye. Alhaji daga zaune ya mika mata hannu ya ce zo nan Uwata, rabu da su kin ji! Bakin su ya sari danyen kashi. In dai Mukhtar dina ne dana sani wallahi zai yafe miki, kuma shi mutum ne kaifi daya bana jin rashin hankalin ki na damun sa, tunda yace ya amshe ki to da gaske ya amshe ki, bana jin dawowar sa gida zata sa ya canza magana. Ke dai ki yi kokari daga rana irin ta yau ki canza halayen ki, ta hanyar komawa AMINA ba AMANI ba. Aminatu Mamar Manzo maaobociyar ilmi da hankali da iya zama da mutane, kin ji? Ya shiga bubbuga bayan ta yana lallashin ta domin kukan nadama take yi tukuru. Tana mai adduar kada Allah ya kama ta da laifukan ta a kan mijin ta Mukhtar. Daddy kai kadai ne ka yi min fatan alkhairi, na gode Daddy har abada na san inada kai, na san ba zaka bari a wulakantani ba, wai don nayi laifi na kuma gane na yi laifi na tuba. Mamma don Allah ki hyi hakuri ki sa min albarka. Mamma ta kora ruwan tataccen inibi a tambulan na tangaran mai garai garai ta dube ta yanzu da rahma a idanun ta, ta ce idan da gaske kike kin tuba, Shi Ubangiji mai afuwa ne kuma yana son masu yawan tuba daga laifin da suka san sun aikata. Ni kuma zan taya ki da adddua a kan Allah ya huwwace miki zuciyar sa, ya baki dukkan soyayyar da ke zuciyar sa, ya kade fitina a zaman ku, ya baku zuria mai albarka. Amani ta ruga da gudu ta rungume Maman ta tana na gode Mamma, na gode sosai. Sun kwana suna tattauna alamarin nan cikin tuajjibi da mamaki iri-iri, Mukhtar dan baiwa ne hakika, wanda bai taba alaqanta kan sa da wata daukaka irin haka ba a inda ya tabbatar baa san ko shi waye ba, amma hakika wasu attributes nasa da yawancin personality din sa masu tsinkaye a cikin su irin Mamma, sun ce sun sha alaqanta shi da babbar sarauta ko babbar nasaba. Suka kwana hira da tsarkake tsarkin mulkin Ubangiji. **** **** ***** Haka suma Uba da dan da mahaifiyar sa, sun kwana tare a turakar Sarkin Diffa, kamar su maida dan nasu Mukhtar cikin su. Wani abu ne da Mukhtar bai taba samu tare da su ba tun haihuwar sa, wato closeness sai yau. Don haka (he cant control his tears). Maina ina ka je? Maina ina ka shiga? Maina ka bar mu, shekara goma sha biyar ba kwana goma ba Maina in ji Ummami, tana share hawaye da gefen laffayar ta. Ummami I thought kun fi son hakan, kun fi son in yi nisa da ku din, ba kwa so in rabe ku, kamar ba ku kuka haife ni ba. Na yi kokari na jure hakan tun haihuwa ta amma dana fara girma sai abun yake neman zame min ciwo a zuciya ta, dole na zabi in tafi in yi rayuwa a inda bazaku ko samu labari na ba, tunda zamana tare da ku bai da wani amfani a gare ku. Daga baya kuma kullum na yi kokarin juyowa gida bana iyawa sakamakon dabaibayin dake zuciya ta. Rana daya Allah ya yaye min wannan dabaibayi, naji hankali na ya yo gida, Im so sorry Ummami, har aure na yi babu jimawa bada sani da yardar ku ba, but I have no choice, saboda mahaifin ta has been my savior, my shelter for a very long time. Nan ya gaya musu cewa bayan ya karbi kwalin kammala karatun sakandire tare da yayan bayin gidan a makarantar gwamnatin Diffa da yayi ya kasa cigaba da zaman kasar Nijar, ya yanke shawarar shiga duniya ya nemi ilmin da zai taimaka masa ya dogara da kan sa. Tunda sun nuna basa bukatar shi a rayuwar su sun bar shi a bangaren bayi yana rayuwa tare da yayan bayi, karkashin kulawar Jakadiya da mijin ta Sarkin fada, wato Bafade Katchalla wanda shi ya fara gane shi yanzu ma da ya dawo. Ya ce tunda na taso na ganni a hannun jakadiyar Ummami, ita ta raine ni, saidai lokaci lokaci ta kaini gun Ummami ta kuma dawo dani bangaren da take wato bangaren bayi. Dana fara girma, ma sai ta rage kai ni gun Ummami, itama ba koyaushe take wuni da ni ba tafi wuni a cikin gida, sai dai in yi ta wasa da yaranta maza guda biyu saanni na, sai na dauka ma su suka haife ni wato ni dan jakadiya da Baba Katchalla ne, musamman da suka saka ni a makaranta tare da Shettima da Ari, wato yayan su, muke zuwa tare kullum muna dawowa. A hakan sai na fara mantawa da Ummami, wadda nake gani lokaci lokaci, kai kuwa Maimartaba dama ba a zancen ka, don tsakani na da kai sai dai in hango ka a turakar ka ko a fada, ko a kan Rakumi idan ana wani festivities din kamar misali bikin sallah ko na aure ko na nadin sarauta. A baya Baba Katchalla na zuwa da ni fada mu zauna a gefe nida shi, bazan manta ranar da kayi masa tsawa ba, ka ce kada ya kara kawo ni fada, mai bakin baya ne ni, tunda ga kai na ko batan wata baa kara yi a gidan ka ba. A ranar ne ma wasu a fada suka san ni dan Sarki ne. Nan ne aka yi ta kuskus a gari wai ashe Sarki yana da Da namiji amma baya son yaron. Ya barwa bayi shi. Wannan zance har a makaranta an yi min gorin sa, lokacin ina karatun sakandire. A wani dare na tsuye jakadiya ina tambayar ta da gaske ni dan sarki ne? Kuma Mowar Sarki wato Ummami da muke zuwa wajen ta lokaci lokaci har wani lokaci ta bani apple ita ce mahaifiya ta? Jakadiya ta tabbatar min haka ne, amma bata san dalilin ku na ajiye ni tare da su ba, kodayake tace Sarki da Mowar gida basu da trusted servants a cikin bayin su kamar ita da Katchalla. Tace Sarkin Diffa ba mai yawan haihuwa bane, shiyasa yake ta aure daga kasa-kasa don ya samu haihuwa, a irin haka ne ya auro mahaifiya ta daga wata kasa cikin kasashen Afrika, yayan sa biyu kacal kuma duk mata ne tare da matar sa ta lalle wato uwargidan sa da mai bi mata wato mata ta biyu. Daga kan su bai kara samun haihuwa ba sai da ya auri Ummami, kuma tun haihuwa ta suka bata ni, shayarwa ma a boye Ummami ta shayar da ni don sai ta bita cikin sirri ta roke ta. Bayan ta yaye ni ma kuwa bata bukatar a kai mata ni inda take. Ni ne dai dana yi hankali na ji ba wanda nake so a duniya irin ki Ummami, sai nake satar jiki ina zuwa inda kuke, wani lokacin inna leka inda kuke zama da laasar zan same ku kuna sallah tare ke da Sarki, ko kina zuba masa abinci ko kina masa yankar farce, har rannan wani bafade ya kama ni ina leken ku ya taska min mari, shine fa ban kara leken ku ba daga ranar. Watarana Baba Katchalla yace muje ana bikin Yaya ta a cikin gida, nan na bishi muka je har fada naga irin auren gata da aka yi wa yar uwata, akan taguwa aka kai ta Tahoa inda ta auri dan sarkin Tahoa, ni kuwa inna shiga cikin gidan na hau rabe-rabe kenan kamar mara gaskiya, hatta sittiru na tare ake din ka mana da Ari da Shettima, babu wani banbanci tsakanina da su. A makaranta ma ajin mu daya da su. Dana fara hankali sai nake tambayar kaina to meye dalilin hakan da sarki da Ummami suka zabarwa rayuwa ta? Na sa a raina bakin bayan da ya taba ambata min ne dalili, wato daga kaina ko batan wata wata matar sa bata kara yi ba har ita Ummamin. Amma ai wannan bai isa dalilin da zasu sarayar da rayuwa ta a hannun bayin su ba, sai ma dai yayi dalilin da zasu daukaka daraja ta fiye data kowa a masarautar. Bani da wata shakuwa ko kusanci da ku da zai sa na iya yi muku wannan tambayar. Ban ma isa in je inda kuke kai tsaye ba. Na yarda iyaye na kun haife ni ne da gaske, amma kuma baku kauna ta! In na tuna hakan sai wani irin bakin ciki ya murde ni, har ya zame min habit, daga baya bayan na kammala sakandire na ji bazan iya cigaba da zama a Diffa ba, gara in tafi inda bazaku kara jin labari na ba, tunda kun haife ni bisa kuskure amma bakwa kaunata ko miskala zarratin. Wannan abu ya cigaba da bakanta min dare da rana, har na koma tamkar depressed, na daina walwala, na daina shiga cikin saanni na, na yarda bakin baya na zai iya shafar kowanne yaro iyayen sa su tsane shi. Duk da babu abinda Baba Katchalla da Jakadiya suka raga min, suna ma kula da ni ne har fiye da yadda suke kula da yayan su Ari da Shettima. Rana daya na yanke shawarar barin Diffa, to amma ina zani bani da ko sisi? A hakan ne aka ce sakamakon mu na sakandire ya fito, kuma na ci jarrabawa ta da sakamako mai kyau wanda yafi na kowa, don haka gwannatin kasar Nijar ta dauki nauyin karatun mu ni da wasu dalibai zakakurai iri na zuwa kasar goyon mu wato Faransa. Aka damka min admission dina da tikitin jirgi, na so in gayawa Baba Katchalla amma zuciya ta ta kwabe ni, kan cewa zai iya hana ni tafiya, ku kuwa dama na san ba damuwar ku bace rayuwa ta ce, baku da matsala da wannan, hasalima na yi amanna farin ciki zaku yi in yau aka ce na bar Diffa. Hatta malaman makarantar mu basu san cewa ni Maina ne ba, sun dauka ni dan bawa Katchalla ne wanda kusan kullum shi yake kawo mu makaranta ya kuma zo ya dauke mu. Don haka da aka fara jigilar daliban da suka samu scholarship na sulale na tafi Agadez tare da sauran dalibai yan uwa na, inda daga can jirgin mu ya daga zuwa France. Acan ne aka rarraba mu zuwa jamioI daban daban a cikin Faransa, ni aka bar ni a Jamiar Paris Saclay University. ***** **** **** RAYUWA TA A FARANSA R ayuwa ta a matsayin dalibi a birnin Paris, rayuwa ce irin ta kowanne dalibi mara gata sai na gwamnati, mai fafutuka da neman ilmi da gumin sa, gwamnatin kasar mu na bamu alawus wanda da shi muke rike kan mu. Na yi wani dogon rashin lafiya bayan tahowa ta kamar bazan rayu ba, don sai da na kwashe watanni biyu a asibiti bansan inda kaina yake ba, bayan na farfado da kyar, na ji a cikin kaina bani da buri irin na kara nesanta kaina da gida, kuma har Paris din ji nake ta min kusa da Nijar amma hakika ina son samun kwalin degree dinnan, shiyasa na tsaya. Da kyar na samu na hada karatun domin banida cikakkiyar lafiya kuma likitocin kasar duk kwarewar su sun kasa gano takamaimai me ke damu na. Akwai wani abokin karatuna Musulmi, Faiq, da ya zo daga kasar Masar, shi ya bani laqanin kullum in karanta ayatul kursiiyu kafa bakwai in tofa a ruwa da safe in sha kafin in ci komai. Da wannan lakanin na fara samun lafiya har na kammala karatu na da kyakkyawan sakamako. Daga wannan lokacin ne tallafin da kasar mu ke bamu ya yanke mana, wato dama scholarship din mu iya degree ne, sai na shiga tunanin hanyar da zan bi in yi sponsoring karatu na na gaba wato masters, duk dai don in samu damar cigaba da zama a Paris kada in koma gida. Ayyuka na neman rufin asirin dalibi iri-iri babu wadanda ban yi ba, tun daga wanke-wanke da share-share a hotel, direban bus, jiran shago, zaman library da kuma receptionist, da haka na kukkulla na kukkula na dinga biyan kudin karatun masters dina in instalments (a rarrabe) har Allah ya taimake ni na samu shaidar kammala degree na biyu, daga nan na dukufa neman aiki kwakkwara amma ban samu ba, ko in ce ban dace ba, ina tunanin fallewa zuwa Hong-Kong again, don neman aikin yi, Allah ya hada ni da Ubangida na na yanzu, wato Alhaji Usman Faskari. Nan ya labarta musu komai na irin haduwar da suka yi da Alhaji, ya biyo shi Najeriya ya bashi gida da aiki ya kuma ja shi jikin sa da amana irin yadda ko yan uwan sa bai yi wa ba, duk tarin alkhairin Alhaji gare shi sai da ya fada musu har zuwa lalurar data same shi wadda tayi sanadin bashi auren AMANI da Alhaji Usman yayi. Yadda a rana daya yaji duk wani dabaibayi da ke zuciyar sa a kan Diffa ya yaye, da kuma karfin zuciyar da ya samu na dawowa gida karkashin umarnin Alhaji duk ya fada musu. Tun kafin Mukhtar yayi nisa da labarin nan daga Maimartaba Sultan Issoffou Massaoudou har maidakin sa Ummami kuka suke yi sosai. Sarki Issoufoou ya janyo Mukhtar jikin sa ya rungume shi yana kuka sosai da hawayen sa, yana rokon sa ya yafe masa, ya ce da Mukhy (cikin vernacular language din su). Moukhtar, duk abinda muka yi dinnnan muna sane, we did it to protect you from envy, hatred, evil eyes, bad luck, and to save you, as the only male child that I have, to make sure you get the throne of Diffa Emirate at an appropriate time. Ni da kaina na hana mahaifiyar ka jan ka a jikin ta, nida kaina na ce ta fidda kai daga ran ta, Allah zai raya mana kai. Ba zaka taba zama sarki ba idan ka samu gatan da yayan sarakuna ke samu, kasancewar kai din daban ne, zagaye nake da makiya haka mahaifiyar ka zagayeta ke da kaidin mata yan uwan ta iri iri musamman da ta haife ka, kasancewar ni mutum ne mai yawan aure-aure, amma tunda muka watsar da kai sai duk hankalin su ya bar kan ka, ya koma kan yadda zasu yi su samu nasu yayan suma, don na nuna bana kaunar ka ban damu da rayuwar ka ba. Mukhar dauriya iya dauriya irin wadda ba duka iyaye zasu iya ba a kan dan da suka haifa kwalli daya muka yi a kan ka, domin mu tseratar da rayuwar ka, amma duk halin da kake ciki a gidan Katchalla wallahi mun sani. Kuma muna kulawa da komai naka. Hatta tafiyar ka Farisa mun san da ita, nine kuma na sa aka baka scholarship daga ofishin Baare Mainasara (shugaban kasar Nijar na wancan karnin). Haka daga sanda ka bar Farisa ne muka daina samun labarin ka sannan bamu san ina ka koma ba. Malamai na daban-daban na cikin gida kullum gayamin suke in kwantar da hankali na domin kana raye, kuma a kyakkyawan hannu mai tsafta, amma na kasa kwantar da hankalin nawa. Kullum (blaming) kaina nake yi kan ko dai hukuncin dana yi wa rayuwar ka ba dabara bace karbabbiya? Ko dai kuskure na yi maimakon (saving life) din ka? Wannan tunanin da wannan nadamar su suka taru suka kwantar da ni na lokaci mai tsaho. Musamman da aka tabbatar min ka bar Farisa baa san inda ka shiga ba kuma. Har gobe a kan treatment nake, mahaifiyar ka kuwa ka gan ta yanzu bata gani sai da Gilashi, sabida yawan kukan tafiyar ka Maina. In mun yi kuskure cikin abinda muka aikata muna rokon Allah ya yafe mana, kai ma ka yafe mana. Sannan madallah da jin cewa kayi aure, lokaci ya yi da zan bayyana ka ga duniya. Zan maka bikin aure irin wanda baa taba yin irin sa a masarautar Diffa ba, zan gayyato duk sarakunan jamhuriyyyar Nijar, in gabatar da kai gare su, sannan zan baka sarautar Diffa tun ina raye. Kafin nan zan maka nadin sarautar Mainan Diffa ka fara zama a fada tare da ni don ka koyi shaanin mulki na lokaci mai tsaho. Duk wadannan abubuwa da ke faruwa yau, Mukhtar couldnt believe them, don ya dauka mafarki yake yi, ire-iren mafarkan da dan adam in yana yin ba ya so ya farka, yana rokon Allah da dai ya farka daga wannan mafarkin, gara ya zarce a cikin niimar sa, wato ya karasa mutuwa a cikin dadin sa.. ***** ***** ***** WASHEGARIN RANAR Da wayewar gari, Sarki Issouffou Massaoudou ya aiko a tafi da su Alhaji cikin masarauta, yasa aka kai su dakin da yake ganawa da manyan bakin sa, sannan aka shirya musu karin kumallo tare da Sarki da Ummami. Wanda ya kai su shigifar ya ce su jira kadan, Mai Diffa na zuwa tare da Mowa. A lokacin Mukhtar na can yana ramuwar barcin gajiya bai ko tashi ba, don kwanan zaune suka yi da iyayen sa, tun bayan da suka dawo masallaci sallar asubahi aka bude masa wata shigifa da ke kusa da na mahaifin sa, yake barci har zuwa lokacin, barci na kwanciyar hankali irin wanda bai taba samu ba. Su Jalan sun nutsu suna kallon sarautar Allah, domin ko a cikin masarautun Nijar Diffa na sahun farko, komai na masarautar mai ban shaawa ne da ban mamaki kuma irin ancient dinnan amma aka zamanantar da shi, suna kalle kalle suna jiran isowar Mai Diffa da Maidakin sa, wadda suka ji an kira Ummami (Mowa). Can suka jiyo takun sa ya durkako inda suke. Cikin taku na haiba da kamala. Yana shigowa duk suka mike domin girmamawa. Haske da kwarjinin addinin Musulunci ya bayyana sosai a tare da farin balaraben dattijon. A nitse ya zauna a kujerar da ita kadai ce kujerar mulki a dakin, wanda yafi dacewa a kira shi palace, ba jimawa da zaman sa sai wata kofar ta kara budewa. Doguwar matar cikin kyakkyawar laffaya da farin gilashi a idanun ta, ta shigo, ita kadai ba tare da kowa ya rako ta ba. Ta nemi guri gefen maigidan ta ta zauna kasan kafafun sa, fuskar su fal annuri da maraba dasu. Kafin kowannen su ya ce komai aka ji Mamma Jalan ta tsinke da salati ta ce Yaya AISATA! A firgice Ummami ta juyo, jin muryar kanwar ta, Jalan. Da gudu Jalan ta sheka ta isa gareta ta rungume ta. Sai kuma ta saka kukan farin ciki. Da kyar Aisata ta banbarota daga jikin ta. Ta ce Jalan, ke ce koko ido na ne? Aah ke zan tambaya da gaske ke ce? Kuma Mukhtar dan ki ne kenan? Aisata (burst into tears) tace ban taba gaya miki cewa na haihu ba, sabida bamu kara haduwa ba tun rabuwar mu sai aike ne a tsakanin mu, sabida a kaida matan gidannan basa fita, ko asibiti bama zuwa saidai likita mace ta zo har daki ta duba mu, sannan da matsalolin da suka biyo bayan haihuwar tasa, da muka fara waya dake bayan kin yi aure na biyu kenan, ni ban san meyasa na kasa gaya miki ina da Da ba, kodayake bana maganar sa sam, balle irin wannan a muhimmiyar magana ta hada mu da wani nawa ta waya, daga baya kuma bama tare dashi ma, daidai lokacin rasuwar Abbu sanda na aiko dan aike na wajen ku, aike na na farko gida Kenema, lokacin Maina ya riga ya gudu. Me ya kai ki Najeriya yanzu? Na dauka kun rabu da mijin ki na can tun su Abbu na raye, har kin yi wani auren da Lukman kin samu yara? Daga baya kika gaya min a waya ya rasu, ta ina kika hadu da yan Najeriya bayan na san kina Kenema? Suka rungume juna ana ta mamakin wannan ikon Allah, Jalan ta gaya mata Alh. Usman shine mijin ta na fari wanda aka aura mata a kasar Katsina, suka rabu bayan ta haihu, itama rabon ta da yar tun lokacin, sai yanzu da kaddara ta sake hada su. Ta nuna mata Amani dake ta sakin fitsari a kai-a kai daga zaune ta cikin wandon ta a lokacin, sabida yadda ta kara firgicewa da alamarin Ubangiji, wato Mukhy Yayan ta ne na jini kuma?! Bayan nadamar data sha jiya bata ko gama fita daga cikin ta ba, yau ga gagarumar nadamar data fi ta jiya ta kara samun ta. Jalan ta nunowa Aisata ita da hannun ta manuni. Kin gan ta itace yar da na haifa na baro a Najeriya sunan ta Amina, sai da girman ta na gan ta, kuma ita ce matar Mukhtar a halin yanzu, domin a hannun mahaifin ta ya zauna a gidan su duk tsayin wannan lokacin. Ummami sai ta mikawa Amani dukkan hannuwan ta tana hawaye tana fadin Ya ki nan diya ta, ta kaina! Amma Amani ta kasa tashi sabida yadda ta jika jikin ta da fitsari a zaune, sai da Sahura ta ciccibata, ta isa ga Aysata, ita kuma ta saka dukkan hannuwa ta rungume ta a ciki, tana fadin dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, mai rahma mai jin kai, mai yawan hikima ga rayuwar bayin sa. Sai lokacin Sarki yayi gyaran murya ya ce hakika Ubangiji mai hikima ne, madallah da ku, madallah da kariman mutane irin ku, masu mayar da dan kowa nasu. Ya dubi Daddyn Amani yana murmushi ya ce yadda ka rike min Mukhtar da amana ba tareda ka san komai a kan sa ba, haka nake fatan in rike Amina daga nan har karshen rayuwar mu, ko da bata kasance yar uwar sa ba. Allah ya saka maka da alkhairi ya kuma baka lafiya. Sai ga Mukhtar ya shigo dakin daga shi sai farar jallabiyya kal da bakar hular larabawa a kan sa, kallo ya koma gare shi suna mamakin yadda cikin kwana daya tal ya canza ya koma tamkar ba shi ba, yayi kyau, yayi wani irin fresh tamkar balaraben Madina. Kamar da ka latsa shi jini zai yi tsartuwa. Nan aka gaya masa ko me ke akwai, wato Jalan kanwar Ummami ne ta jini, uwa daya uba daya. Mukhtar sai kamar bai yi wani mamaki ba, cewa yayi ai ni naso in gane hakan tuntuni, kawai ban san komai akan Ummami bane ko dangin ta, wanda zai karfafa zargin nawa, amma tabbas na ga alamu, tun sanda na ga cindo Ummami a hannun ta da wasu attributes da dama, sannan jiki na ya bani, son da na samu kaina ina ma Mamma, kamar na Ummami ne, musamman da ita ta sake da ni sosai ba kamar Ummami ba cikin yan kwanakin da nayi tare da ita. Nan aka shiga mayar da zance, aka dauko tarihi tun daga farkon sa, tarihin masarautar Diffa da yadda kakan sa Sultan Oumarou ya bada sarautar ga dan sa Sultan Massaoudou tun yana raye, bayan rasuwar sa Sarki Issouffou ya gaji sarautar daga hannun mahahifin sa Sarki Massaoudou. Ya ce sun kasance su masu karancin haihuwa ne a jinin su, shiyasa suke aure-aure daga kasashen Africa daban daban daga kyawawan matan Africa, wadanda suke saye suna sa-daka dasu (concubines) basu cika maida su matan aure ba. Ya ce amma ita tunda aka kawo ta gaban mahaifiya ta ta ganta da tabon sujjadah a goshin ta, sannan aka gaya mata daga Saliyo take sai tace aure zaa daura mana bata yarda in yi sa-daka da ita ba. Marigayiya mahaifiya ta tace matan Saliyo mata ne na musamman, daban suke a halitta da sauran matan Africa, Allah yayi musu baiwa ta auren manyan mutane, tace sanda zata kwace Mowar Diffa daga hannun Ummu Aymana, bazan sani ba. Sarki yayi murmushi yace and thats exactly what happened today, Aisata Mowar Diffa! Kafin ita ina da matan aure guda biyu, uwargida Ummu Aymana yar sarkin Zinder tana da ya daya; Sayluba. Sai Tarha diyar sarkin Agadaz wadda itama na samu haihuwar diya mace da ita. Sai aka daura mana aure na Sunnah da Aisata, na bata dakin mace ta uku a gidan sarautar Diffa. Kasancewar duk matan da ake kawomin matsayin sa-daka nake basu, wannan ya tada hankalin mata na; Ummu Aymana da Tarha. Musamman da ya kasance har zuwa lokacin babu wadda ta samu haihuwar Maina cikin su. Suka daga hankalin su a kan Ummami nima suka daga min, sanda ta samu cikin Mukhtar kuwa ina wuta su saka ta, aka hanamu aure ta hanyar saka min tsanar ta a shimfida, aka saka mata warin gaba, aka saka mata kurarraji kai matsaloli marassa dadin ji iri-iri a dalilin wannan ciki kamar ba zai kai labari ba. Don daga baya ko dokin haihuwar tata na daina. Na koma ganin abinda zata haifa min din a matsayin matsala. Sai malaman fada ne suka saka ta gaba da addua don kowa yana so Diffa ta samu Maina, basa so sarautar ta bar gida na, don ina da yan uwa a raye, amma ni ko a jiki na. Uwargida na da bakin ta ta gayamin cewa muddin Aisata ta haifi Da namiji sai ta salwantar da rayuwar sa, na kuma san zata iya, a yadda ta cika zuciyar ta da burin ita zata haifa mun Maina. Sai bayan an haife shi an kawo min shi hannu na zuciyata ta cika da kaunar sa, gashi cikin yan uwa na ma da suke da yara maza basu so na samu Maina ba, sun so ya kasance na mutu babu magaji don sarautar Diffa ta koma hannun yayan su. Don haka na san ta koina Mukhtar yana cikin hadarin makiya musamman da ya kasance kamar an tsaga kara ni da shi a kamanni. Sai na shiga tunanin ta hanyar da zan bi in kare rayuwar sa. Nan na zaunar da Aysata, na ce wannan yaro kin haife shi dai ko? To ki godewa Allah komin runtsi sunan sa dan ki, amma ki nema masa kariya ta hanyar rashin nuna kauna da kulawa a gare shi. Ta yi min kallon rashin fahimta nan na wayar mata da kai, na ce mata na barshi karkashin kulawar bayin mahaifi na na tun tali-tali, wadanda nima gadar su nayi a gun mahaifa na saboda amanar su, wato Katchalla sarkin fada da Jakadiyar dana bata. Na ce ta runtse idon ta daga kan yaron nan, ta bar shi ya rayu a hannnun su. Zasu kula da shi kamar yadda zasu kula da yayan su amma rayuwa irin ta yayan su. Da yake Aysata mai fahimta ce, mai kuma bani hadin kai akan duk abinda na zo mata da shi sai ta yarda. Amma ta roke ni in bar ta ta shayar da shi ko a boye ne, ko na tsayin shekara daya ne, na amince mata. Don na san muhimmancin nonon uwa, kuma inaso ya tsotso irin kwakwalwarta da kyawawan dabiun ta. A takaice wannan ne dalilin da yasa muka yi wa Mukhtar rainon da muka yi masa, yau gashi Allah ya raya shi yadda nake fata, duk wani da ya nufe shi da sharri na tabbata ya ga abun sa a kwaryar shan sa, domin koda aka gaya min kurciya aka yi masa daga baya ni ban damu ba, na bar shi ya je ya koyi rayuwa har zuwa lokacin da ni da kai na nasa malaman fada suka karya sihirin, tun a daren ne kuma aka gaya min Ummu Aymana ta fita daga gidan nan, ta tafi har Zinder a kafa, ita ba mahaukaciya ba, ita ba mai hankali ba, ta dai koma kamar tababbiya, kuma kalamanta kullum. Mainan Diffa dana yi wa kurciya zai dawo yanzu ya karbi Diffa. A halin yanzu tana can hannun iyayen ta ana mata magani amma tace bazata dawo gida na ba in dai Mukhtar na cikin sa. Don haka a jiya na datse igiyar aure na da ita na aikawa mahaifin ta sarkin Zinder. Diyar da muka haifa nida ita (Sayluba) na dade da aurar da ita a Tahoa, tana da yaya basu fi uku ba itama ta gado rashin yawan haihuwa ta, sai kanwar ta yar wajen Tarha (Saadiyya) itama tana aure a kasar Guinea kusa da Liberia ga Amabasadan Nijar a Guinea. Bayan Aisata ta haifi Mukhtar shiru shiru babu karin haihuwa a gida na, sai na kara aure da Balqissa, wadda aka kawo min ita daga kasar Abidjan. Har yau itama bata haihu ba, Mukhtar mai bakin baya ka hana ni samun ko yaya matan ne sabida alhakin ka Ubangiji ya hana ni.. Ya karasa fadi cikin zolayar Mukhtar. Sai da kowa a wajen yayi dariya Ummami ta ce kada ka damu MAI DIFFA! Ba da jimawa ba in sha Allah diyata Aminatu zata cika maka gida da yaya. Jalan ta ce ni nafi so a kara mishi da sadakoki yadda yaran zasu fi saurin taruwa dariya kowa yayi, amma banda Amani da Mukhtar, wadanda duk suka bi suka daddaure fuska, kuma kowanne yaki yarda ya kalli inda dan uwan sa yake. A zuciyar ta cewa take ta Allah ba taki ba Mamma. Ga dukkan jin dadin ta sai Ummami tace in har ba ya zama (Mai) din Diffa ba (Sarkin Diffa) babu mai bashi sa-daka a halin yanzu. Yanzun Maina ne kawai, ku bar su su mori kurucciyar su don Allah. Sai Amani ta hau addua a cikin ran ta; Ya Allah kasa kada a taba baiwa Mukhtar sarautar gidan su, Allah ka kara nisan kwanan mahaifin sa, yayi ta zama a muhallin sa na Mainan Diffa. (Ta manta Sarki ya ce tun da ran sa zai baiwa Mukhtar kujerar sa). Sarki yayi umarni da su Jalan su koma bangaren Ummami da zama har Amani. Gobe-goben nan zaa saka tubulin ginin bangaren matar Maina. Ya kuma ce a yau dinnan zai soma aika takardar gayyata zuwa ga sarakunan jamhuriyyar Nijar, wato gayyatar bikin auren Maina da nadin sarautar sa ta (MAINAN DIFFA). **** ****** ****** MOUKHTAR ISSOUFFOU MASSAOUDOU (MAINAN DIFFA) B aka jin komai sai tashin bushe-bushen algaita da kade kaden ganguna irin na masautar Diffa, a yau Asabar, wadda ta kasance ranar bikin auren Maina da nadin sarautar sa. Cikin wadanda suka halarci wannan kasaitaccen biki har da Yayar shi gimbiya Sayluba daga Tahoa, mai bi mata da yake tana Guinea, bata samu zuwa ba don tayi nisa sosai, mahaifin ta ya aika mata kan ta zo ga dan uwan ta Maina ya dawo gida, ta ce sai ta haihu zata zo daga baya, tana cikin watan aifuwa. Tunda aka soma shagulgulan bikin nan wanda zaa kwashe kwana bakwai ana yi Amani bata saka Mukhy a idon ta ba ko daga nesa, rabon ta da shi tun washegarin zuwan su Diffa, wato ranar da suka gana da iyayen sa, yana can cikin sarakuna abokan Baban sa da yayayen su saannin sa, wadanda iyayen ke kokarin kulla abota da zumunci mai karfi tsakanin yayan nasu, kamar yadda nasu iyayen suka yi masu. Ba iya masarautun Nijar kadai Sarki ya gayyato ba har daga bangarorin masarautun Songhai, Mali, Gao, da Kanem-Bornu. Haka ya gayyato aminin sa Sarkin Burkina-Faso, wuri yayi wuri, taro yayi taro sai Rakuma ake kayarwa ana gashewa ana kyafewa. Abinci kuwa duk iya diban ka haka zaka gaji da diba ka bari. Umami tasa an yi wa Amani kwalliya irin tasu, da kaya na shudin karen miski da sarkokin zinare har a hancin ta, an dorata akan kujerar Mowar Diffa, wato kujerar da Ummami take zama a kai koyaushe, abin gwanin ban shaawa, shagalin sai wanda ya gani. Kwana bakwai aka kwashe ana wadannan shagulgulan na ban mamakia Al-Imaraat Al-Diffa, an nadawa Mukhtar rawanin sarautar jiran gadon mahaifin sa Mainan Diffa, wato dan sarki mai jiran gado. **** **** **** MATAR MAINA “ Kuma shikenan don ya zama Maina ganin sa ma ya zama jan aiki? Amani ta tambayi Baba Sahura babu ko kunya, koda yake dama kunyar ta mata karanci ai, ranar da suka cika sati biyu a Diffa bata sanya Mukhtar a idanun ta ba. Kai ko daga nesa bata hango shi ba. Don ko yana son magana da Ummami baya shigowa sassan ta, don ma kada ya hadu da Amani, can a turakar Mai Diffa suke haduwa da mahaifiyar tasa su yi duk maganar da zasu yi. Baba Sahura ta bantari farin goro sal, sannan ta fashe da wata shashashar dariya, ta dubi Amani tana mamakin rashin kunyar ta, wai yau ta murje ido tana cigiyar Mukhy a gicciye da idanu, ta ce, ki na so ki gan shi fa kika ce? To kewar sa kike ko yaya abin yake? A dan yimin bayani? Baba Sahura bana son irin wannan rainin hankalin naki, daga magana sai kimin wata fassara daban, na ga dai mutumin nan tare muka zo, kuma don shi muka zo, ai ya kamata ya dinga zuwa ganin lafiyar mu, in bai zo don ni da ya raina ba ya zo saboda ku da yake ganin girman ku ni kike cewa na raina miki hankali? Wato har yanzu bazaki gyara halshen ki ga na gaba ba ko? To lafiyar ku ke da wa? Aa Uwa, ki cire mu cikin lissafin ki da rashin kunyar ki, mu kam ai muna gaisawa da shi a waya, bai banzatar da mu a kasar sa ba, ko dazun nan ya kira Jalan, yace ko tana son wani abu, ta ce cukui take so sabon yi, a kawo mata, kuma yasa an kawo shi faranti guda mai laushi. Haushi ya kara turnike Amani, ita din dai ita kadai Mukhtar ya raina, kuma baya son ganin ta ko jin yadda take rayuwa a garin su mai shegen zafi, ta tashi ta bar mata wajen cikin kunan rai. Baba Sahura na kara kyakyatawa kyal-kyal-kyal don ta gano damuwa sosai a tare da ita. Tun daga ranar kuwa duk sanda Baba Sahura ta ga Amani ta yi tagumi sai ta fashe da muguwar dariya. Ummami kuwa, yanzu ta mayar da hankalin ta ne kacokam! Ga shirin tariyar diyar ta Amani, shiri na musamman take yi wa Amani, shiri irin wanda ake yi wa yayan sarakai in zasu dakin miji, masu yi mata gyaran jiki daga Maine-Saroa har su biyu ta kirawo ta ce daga yau har sati daya su gyara amaryar Maina, gyara na musamman fiye da wanda suke yi matai ta Ummamin, Sarki kuma ya saka ana ginin bangaren su a gefen nasa, wani irin kasaitaccen gini shiyasa har zuwa lokacin basu tare ba. Amani a daya daga dakunan sassan Ummami take zaune, an bata bayi mata masu kula da komai nata har su biyar, amma in suka nemi yi mata wata hidima ma korar su take yi saboda haushi, haushin kowa take ji, saboda Mukhy bai neme ta ba ko sau daya, mai hali dai da baya fasa halin sa. Sahura da Mamma ma dakin su guda, Sarki ya hana su komawa Katsina yace sai sun raka Amani ta tare a dakin ta tukunna. Ginin Maina zai dauki sati biyu ana yi don gini ake ba na wasa ba wanda duk masarautar Diffa babu ginin da ya zanu, ya kuma zamanantu kamar sa. Duk da rashin ta idon Amani sosai ta samu kan ta da jin kunyar Ummami, bata sani ba ko sabida yadda take jan ta a jiki ne, ta ce kuma ita ya take da ita ba suruka ba, don haka ba karamin tanadi take yi wa tariyar ta ba. Da nata, ya tata, komai tuwon ta man ta, farin cikin hakan har ya so yayi mata yawa. Shi yasa take yin komai da karsashi. To amma yadda Mukhtar ya share Amani tun zuwan su, ko zancen ta bai kara yi ba ya damu Mamma Jalan a kasan ran ta, bata dai nuna ba, don ta san yayi hakuri iya hakuri da Amani, yanzun lokacin sa ne, amma bata fatan ya ce zai rama wulakancin Amani gare shi, don ko babu komi yar uwar sa ce, ta san idan ma Amani ta ce tana son sa yanzu, ai wata fassara zai yi mata daban, don hankali ba zai kama ba. Don haka ta shiga rokon Allah a boye a kan ya daidaita tsakanin su ba tare da sauran mutuncin Amani ya zube daga idanun Mukhtar ba. Ita kuwa Ummami yawan sabgogin dake kan ta na mijin ta da bayi da tariyar Amani yasa bata fahimci cewa Maina ko gaisawa baya yi da Amani ba. ba kuma ya zuwa inda ya san a can take. Allah kadai ya san me ke zuciyar Mukhy a kan Amani, don har zuciyar sa baya mararin sake ganin ta, duk da cewa hes absolutey busy kuma busy din da yake ciki da jamaa da iyaye da yan uwan sa ne ya hana shi zuwa inda suke, amma yana kiran Mamma Jalan a waya akai akai, har Baba Sahura ma, kuma dai duk da hakan Amani tana nan a like a ran sa, yana tuna ta a yawancin lokuta in ya kadaice domin kwanciya barci, amma bai damu ya gan ta ko ya neme ta don ya gan ta ba, duk a kan kalaman ta na Saliyo, da har zuwa lokacin ya kasa manta su, ya kasa yafe su, ya kasa share effect din su daga ran sa, kuma in ya tuna suna masa maqaqi a rai, amma ba don wai ya dawo cikin gatan sa da take masa gori bane ko don halayen ta da ya riga ya sani bane ya sa bai neme ta ba. Aka fara yima amarya Hamam Hallawa daga shi aka yi mata Dilka Gomage irin na matan Diffa, washegari aka yi mata wankan madara da wankan lalle. Sai kunshi, wanda ya zama shine na karshe a gyaran amarci da aka yi wa Amani a Diffa. Yau da yamma da aka gama kunshin, aka cire ya kama radau, kamar ka sace kafar da hannun ka gudu, mai gyaran jiki ta ce ta je ta yi wanka da ruwan turaren data sirka mata a toilet din Ummami, sun gama gyaran yau kenan sai kuma na gobe in Allah ya kai mu. Mukhtar yana son ganin Ummami ya duba inda suka saba haduwa bai gan ta ba, dole ya shig sassanta har addua yake Allah yasa kada ya hadu da Hajjajun nasa. Mukhy ya shigo dakin Ummami ne don ya gaya mata zasu tafi Burkina Faso yau, domin kai Daddy wajen wani mai maganin shanyewar barin jiki na gargajiya da Sarki ya ce a kai shi. Bisa umarnin abokin sa sarkin Burkina Faso da ya tambaay ko akwai masu irin wannan maganin na wannan lalurar ta shanyewar barin jiki a kasar shi bayan na asibiti? Shi kuma yace tabbas akwai, kuma shi zai dauki nauyin maganin, da duk masu raka Alhaji har sai ya samu lafiya. Don haka suka gama shirya tafiyar Alhaji Usman da yan rakiyar sa karkashin jagorancin dan sa kuma surukin sa Maina Mukhtar. Da sallama ya shiga har kuryar dakin Ummami don bai gan ta a falon data fi zama ba, sai hadimanta suna ta ayyuka a falon wajen tsaftace shi da turare shi, bayan an gama kunshin amarya, ya duba duk inda zai gan ta har turakar Mai bata can, kuma dole yana so yayi mata sallama saboda zasu kai sati biyu a Burkina Faso in sun tafi gobe ana yi wa Daddy gashin kashi na gargajiya, don har Mamma Jalan zasu tafi, kuma ya gay mata ta waya cewa ta shirya, don ta dinga kula da Alhajin sosai da daddare. Bai ga Ummami a dakin ba, sai wani fitinannen kamshi da ya baibaye dakin ta koina, can kuma sai ya jiyo karar ruwa a shaya, daga toilet din Ummamin, nan ya gayawa kan sa Ummami tana wanka ne, don haka ya samu kujerar sofa kwalli daya dake dakin barcin Ummami ya zauna yana jiran fitowar ta, hankalin sa bakidaya a kan wayar sa da wannan kamshi da yake ji yana fitowa ta toilet ne ko ta falo ne dun sun bi sun rikita gidan, da wani turare mai tada hankalin yan maza. Zuwa can Mukhy yaji an bude kofar toilet din, sannan a hankali ta fito daure da faffadan tawul, gashin ganta ya sha wanki don kitso zaa yarfa mata gobe, dagowar nan da zai yi sai ga Hajiyar tasa ce tana fitowa daga wankan turare data shiga, ta zama tamkar hurul-eenin larabawan Diffa. Mukhtar ya samu kan sa da fara tazbihi a cikin ran sa da sauri da sauri. Gabadaya iskar dakin ta debi kamshin sihirtaccen turaren da Ummami ta sa aka hada musamman saboda Amani, yau kwana bakwai da shi take wanka, wanda Ummami tun daga TChad ta aika aka kawo mata shi, daga ita sai dan faffadan towel wanda ko guiwar ta bai kai ba, tayi wani irin sumul ta yi jazur kai har wata yar kyakkyawar kiba ya ga ta yi kamar ba Amanin da ya sani kamar a bushe ta ta fadi ba don rashin kauri. Yo kam ta ci Dawisun Diffa ta koshi. Da farko ita bata gan shi a dakin ba sam, har rausaya take tana rera wani baiti cikin wakar mutuniyar ta wato Nancy Agram, da harshen larabci, a haka ta isa ga mudubi domin ta sharce jikakakken gashin kan ta data wanke, nan ta hango Alhajin nata zaune yana kare mata kallo, ta cikin mudubin ta hangoshi, sosai ta tsorata duk ta firgice, don bata san da shi a dakin ba. Mukhy ya dan rikice da kama shi da tayi yana mata kallon kurillah, duk ya zama wani upset don bai taba ganin real Amani irin yadda ya gan ta yau ba, ita ma ta diririce don bata san tana da kunya ba sai yau, tana kokarin komawa bandakin don suturta jikin ta ya daure fuska sosai ya ce ke da Allah malaam! Tsaya, tambayar ki zan yi, ina Ummami? Ba wajen ki na zo ba balle ki yi min yanga idon Mukhy na walainiyar da basu san suna yi ba a kan kirjin ta wanda ya dago sosai kamar an an kara hura mata shi ya zama kamar balloon, sai zagin idanun sa suke ta cikin kakkauran towel, da zara-zaran hannayen ta da suka sha jan lalle da hallam hallawa, suka zamar da fatar ta tamkar na jaririya don taushi, wadannan abubuwan guda biyu, gabadaya sun gama tada nutsuwar Mainan Diffa, ya kasa dauke ido a kan ta tsayin lokaci, Amani ta juya don komawa toilet ba tare da ta amsa masa ba. Mukhtar bai san lokacin da ya mike ya soma taku zuwa gaban Amani ba, ya sha gaban ta yana cewa ba tambayar ki nake ba? Nan da nan ta fara rawar jiki don dadin ganin sa da ta ji, ga kuma kunyar yadda ya gan ta, sannan a gaban ta ya tsaya yana fadin, shin sai yaushe zaki yi hankali ne ke? Ko gaisuwa ga miji har yau baki iya ba, gaida miji ma sai an ce ki yi? Ni kam anya Alhaji ya san irin shashashar matar da ya bani? Mukhy yana maganar nan cikin takaici mai yawa, muryar sa na canzawa cikin yar inina, ta dalilin tasowar wani kwantaccen feelings daga kasan ran sa, duk kuwa da cewa gashi korafi yake akan halin ta, ya yarda yana son Amani har gobe, duk da pretending din nasa, amma baya son halayen ta ko kadan, don haka yanzu ma kokawa yake da kan sa na kada ya sake kai hannun sa gare ta, komai zai faru da shi gara ya faru amma ba zai kara sake mata ba. Mukhtar ya kara taku ya tsaya a gaban Amani hannayen sa biyu cikin aljihun Caftan din jikin sa, ya ce Hajjaju ina fatan zafin kasar mu ta talakawa bai saka ki ciwo ba? Na san yayan Qaruna basa son zafi da rana da sauro. A yanzun yana maganar ne fuskar shi dab, da nata, a fakaice yana sunsunar wannan sihirtaccen kamshin ne dake neman bugar da shit un dazu, wanda yanzu ya gane daga jikin ta ya samo asali, mai neman bugar da numfashin sa, ya rasa inda suka same shi. In bai manta ba irin sa ne tayi amfani da shi a Saliyo ya kusa mutuwa a kan ta ba don kwanan sa yana gaba ba. Ta rasa me zata ce da shi, don kamar bakar magana ce ya gaya mata, shi kuwa tsakanin sa da Allah ya san garin akwai zafi, akwai Sauron ma at times, tana rokon Allah a ran ta yasa kada yau ma Mukhy ya tada zancen Shege! Har yayi abinda zai yi bar dakin nan. Zuwa wannan lokacin Mukhy ya kusan hade dan space din da ya saura tsakanin su, ban da makyarkyata ba abunda Amani take yi daga tsaye. Yace cikin tsananin takaici wai ashe ke kanwa ta ce duk wanan lokacin ban sani ba, na tsaya kika yi ta yi min rashin kunya a banza a wofi, kina kunsa min bakin ciki kina cin bulus, kina tada kai da bulus, to daga yanzu kika kara yi min rashin kunya ko hararar nan taki ta raini, na rantse da mai samada mai kasa gwabje bakin ki zan yi sai jini ya fito ta yi wani sunkuye da kai, sannan ta yi kasa da idanun ta bata ce komai ba, jikin takanwa y agama yin laasar. Mukhtar ya kara matsowa jikin ta don kamar wani magnet ya ji yana jan sa zuwa gare ta, abinda bai tsara bane yake neman zuwa da kankanuwar murya ya ce ba zaki koyi gaisuwa ba? Ya kara nacin fade, wannan karon cikin shakakkiyar murya, Amani sai ta soma kokarin gocewa kusancin su, ta yi gaba zuwa wardrobe don ta saka kaya a jikin ta, tana cewa cikin ran ta, Allah yasa kai ne Sarkin kasar Nijar bakidaya, ba mai jiran gado ba, ba zan gaishekan ba, tunda ta karfi ake saka gaisuwar, ayi mutum ba maganar arziki tsakanin sa da wadda yake kira matar sa amma babu lallashi a bakin sa kullum. An yi sati biyu ma baa hadu ba, yau an hadu tana mararin ganin sa amma ba maganar arziki, ai kuwa bata isa ga wardrove din ba ta ji Mukhtar ya riko gefen tawul din, sai ganin tawul din ta tayi a hannun sa ya rataya a wuyan sa, ta bude baki domin yin ihu, yayi maza ya toshe bakin da hannun sa yana zaro manyan idon sa, ya ce, baki da hankali zaki yi min ihu ki tara min mutane? Meye haka sai kace yanka ki nayi? Zaki jawo a zaci wani abun nake miki? Daga kawai na zare tawul? Amani ta rufe dukkan idanunta kamkam, cikin matsananciyar kunya da gigita, tana ambaton Allah a ran ta, domin Mukhtar ya damke bakin da kyau da hannun daman sa yadda bazata iya ihun da ta yi niyyar yi ba don Ummami ta kawo mata agaji. Shi kuma rufe idon da ta yi sai ya bashi damar karewa kyakkyawar halittar matar ta shi kallo, yana tazbihi a ran sa har ya fito fili. Amani bata san yaya aka yi ba daga nan, don idanun ta suna rufe, gara mata rufe idon da ta hada ido da shi cikin wannan situation din, ta san dai Mukhy ya tallafe bayan ta ya hanata kai wa kasa daga nauyin jikin ta da da kafafun ta suka gaza dauka, daga nan kuma sai saukar bakin shi ta ji a kasan dogon wuyan ta yana sunsunar ta, kafin ya saki wani wahalallen kiss, a asan wuyan nata ba tare da shi kan sa ya shirya ba, ya gangaro a hankali ya saka fuskar shi saman kirjin ta, bai san lokacin da yayi hakan ba domin tun dazu yake kokawa da kan sa a kan yin hakan, amma zuwa yanzu duk wata dauriya da duk wani azanci da ya san ya mallaka ya kwace masa, jaruntaka da ego da pride din sun subuce masa, wannan yasa ya yarda hakan wani miracle ne da Amani ke da shi a kan sa. Wato duk irin fushin da yake da ita baya jin zai kasa kusanta kan shi da ita, in har sun kebe. Mukhy ya tafi da yawa, Hajiyar kuwa da ke guilty na damun ta yanzu bata yi wani hobbasa na hanawa ba, ya manta cewa a dakin Ummami suke sai faman wannan smooth lallausar fatar da taji wankan madara dana lalle yake yi, yana hadawa da sunsunar ta kamar ba zai daina ba, sai dai kamar wancan karon, yanzun ma sai da kwakwalwar sa ta tuna masa AMANI FASKARI ce fa! Sarkin rashin mutuncin duk duniya, har yanzu bata yi hankalin da zai sake mata ba irin haka, balle yanzu da take matsayin kanwa a gare, shi tana bukatar ya bar ta ta kara hankali har zuwa lokacin da zata kara sanin ciwon kan ta afin ya soma irin wannan rayuwar da ita. Mukhtar ya saki Amani ta hanyar komawa bisa sofa din da ya tashi, ya kama kan sa da dukkan hannayen sa yana jin haushin kan sa, ya nutsa yatsun sa cikin tarin sumar kan sa ya runtse idon sa, ya tuna abinda ta gaya masa ana I gobe zasu taho nan, cewa tana regretting abunda ya shiga tsakanin su a Saliyo, me yasa yake bari ajin sa ke barewa muddin ya kebanta da Amani? Me yasa yake kasa controlling emotions din sa a kan ta, a irin wadannan lokutan??? Amsar da baya son samu daga kasan zuciyar sa dole ita ta soma pumping a cikin kan sa, wato duk da halaye da dabiun Amani Usman Faskari marassa kyau da baya so, wadanda a yawancin lokuta suke saka masa tsanar ta, ya fahimci duk da hakan still yana matukar son ta da kaunar ta. So kuma kwakkwara guda daya, mara algus, wanda ya san daga Allah ne ba don Alhaji ba. Shi kawai tun sanin sa da ita a gidan su yake da wani extra feeling a kan ta, ko ganin ta yayi daga nesa sai gaban sa ya fadi duk da kasancewar ta maras tarbiyya maras mutunta mutane. Idan kuwa ta matso kusa da shi, to kuwa sai ya ji hakan a dukkan jikin sa. Kunya ta sa Amani sanya doguwar rigar Ummami a baibai, wadda ta yayibo daga wardrove din ta, tana jin wata irin kunyar Mukhy, wadda a baya bata da ita a kan sa, tana zuwa tana baibaye ta. Da kyar Mukhtar ya samu ya koma daidai, ya mike yana faman daure fuska kamar yadda ya saba, ya ce, na tambaye ki kin min banza, nace wai ina Ummami na ta shiga ne? A kokarin ta na son adopting kyawawan dabiu daga yanzu, wadanda ta fahimci gaisuwa ga miji na cikin su a gidan sarautar Diffa, kamar yadda suka dauke ta a matsayin kyakkyawar alada, sai ta yi kasa da murya duk da har zuwa lokacin jikin ta bari yake yi, ta ce. Yaya Mukhy ina wuni? Bai amsa ba, don ko kyau ladabin bai mata ba, da yake bata saba ba, sai ma cewa da yayi a dan tsawace. Nace ina Ummami? Amma a kasan ran sa yana mamakin gaisuwar data yi masan, wadda ya ji ta kamar daga sama, ko kuwa kamar wadda aka tursasa sai tayi, ta yi gaisuwar ne ta hanyar kokarin danne girman kan ta, wanda har zuwa lokacin akwai burbushin sa tare da ita, bai bar ta gabadaya ba, duk da ta yi wa kan ta alkawarin dainawa, Ummami ta tai gun Mai ta bashi amsa murya na rawa da irin hausar gidan, bata gun Mai shima ya bata amsa, to ina jin tana dakin Mammah. Karo na farko a rayuwar su, da Amani ta yi masa Magana cikin kwanciyar jankali. Hakan yasa ya taso ya kara matsowa inda ta ke cikin son tabbatar da canjin da aka samu a tare da ita, na gaske ne ko gizo idon sa ke mata? Ya ce na zo in gay mata ne zamu yi tafiya Burkina-Faso, zamu kai Alhaji wajen mai magani, ko zamu jima, ban sani ba. Ga dukkan mamakin Mukhtar tashin hankali da tsantsar damuwa ne suka bayyana a fuskar ta, ta ce har wata kasa? Amma ai Daddy is doing well a hakan da yake, not like before, tunda yana motsa komai nasa tafiya ce kawai baya iyawa. Mukhy, ya kara matsowa jikin Amani yana jin dan sanyi a ransa na canjawar ta, ya ce, Wa ya gaya miki tafiya ce kawai baya iyawa? Ai Mamma Jalan bata yi tsufan da zata yi zaman zuba ruwa a buta da da daga ruwan wanka da kika zabar mata ba, kin gane? Kunya mai tsanani ta kama Amani ta harari Mukhy ba tare da ta sani ba, hararar da ta kara kunna shi dama ba wai ya zama satisfied bane yana so ko yaya ya sumbaci bakin nan nata na tsiwa kafin ya bar dakin, zuciya da ego da pride din sa na hana shi, tasa kai zata wuce shi don bata son cigaba da tsayuwa tare da Mukhy, kafafun ta rawa suke yi sakamakon kallon kurillar da yake bin ta da shi, sai Mukhtar ya riko hannun ta tana kokarin wucewa ta gaban sa. Na gaya miki zan yi tafiya, amma ba wani fatan alkhairi ba komai, me ya kamata kice min ko ki bani? Allah ya kiyaye hanya kawai zan ce. Ni me nake da shi da zan baka Yaya Mukhy? Ya ce abunda zai mantar da ni kalolin rashin kunyar ki, da kamanni na da shegu. Ai Amani kamar jira take sai ta saka kuka tana cewa. Allah ya gani ban san yaushe zaka bar maganar nan tabi ruwa ba Yaya Mukhtar, wai shi dan adam ba zai taba yin subutar baki ya hadiye ya ce ya mayar da su inda suka fito, a karbi tuban sa ba? Yace in dai ke ce baki san tuba ba, tubanki shi ake kira tuban muzuru, baya taba cika sharuddan tuba na addini, don ko bayan wannan din da kika fada a Freetown, bayan mun dawo Katsina me kika ce min a dakin ki??? Wane cin mutuncin ne baki yi min ba ana I gobe zamu taho nan? Ta gane ya koma neman rikici kuma, ya saki layin soyayyar da ke rinjayar sa da farko, tana kokarin cewa ta tuba tabi alah ta bi shi ego din ta na rinjayar ta, yana gaya mata kada Mukhtar ya ce don ta gan shi da matsayin sa na yanzu ne ta bashi hakuri. Don haka ta hadiye bada hakurin data so yi a cikin zuciyar ta. Amma hakika Amani tayi nadama mai yawa, just bata san hanyoyin da zata bi ta yi expressing hakan wa mijin ya gamsu ba, da kuma yadda zata yi repenting kura-kuran ta, amma ai darasin rayuwa da karatun ta nutsu da duniya ta gama daukar sa ita kam! Da a ce tana da wayewa a shaanin aure, da tuni ta saukewa Mukhy hadda, musamman da ya kasance mai rauni wajen yawan son (body contact) da ita. To bata da wannan exposure din sai na iya rashin kunya. Cikin rikici irin nasa kuma ya sake riko ta, wannan karon bakin sa ya hade da nata yana kissing, da wani irin zafin rai, kamar ta hakan ne zafin sheganta shi din data yi zai fita daga zuciyar sa, shi kadai ya san irin pleasure din yake samu daga irin wannan kiss din da yake yi wa bakin ta a karo na biyu kenan bayan wanda ya faru a Saliyo, wanda yake jin zakin sa ya fi na zuma, gardin sa ya fi na madara. Watakila kuma hakan ne kadai zai sa ya samu rangwame a zuciyar sa da gangar jikin sa na tasirin soyayyar ta mai zafi da ke damun sa, da kuma jin zafin maganar ta ta baya ta da yake yi akan maganar shege, yawan sumbatar ta na sakawa ya manta duk wannan, wani sako na zuciyar sa ya yarda cewa Amani masifa ce a gare shi. Eh masifa fa, tunda maganganun ta na Saliyo kadai sun isa su sa ya tsane ta, ya shata babban layi a tsakanin su amma ina! Kullum sai in bai gan ta ba, yana iya jurewa rashin ganin ta na wani lokaci amma da zarar ya ganta din shikkenan ya rasa duk wani control na kan sa. Ya cigaba da sakin zazzafan kiss din sa idanun sa a rufe, a kasan ran sa yana rokon Allah ya canza masa Amani, (from evil to good, and from devilish to saint), cikin wannna halin suka jiyo takun Ummami tana kokarin shigowa don suna jiyo kirarin da bayin ta ke mata daga waje. Da sauri Amani ta hankade Mukhy, ya ce ta baya ta rago bayan duk kin gama tsotse mata Dan ta, na kan manta ke kanwata ce nake wannan aikin zubar da girman da ke, in sha Allah ta yi kai, daga yau ba zan kara ba. Ya dauki wayar sa a kan sofa ya nufi kofar fita, ya bar Amani da budadden bakin mamakin sa. Mutum kamar mai iskokai, ya gama yamutsata yadda yake so har dakin uwar ta, kuma ya bita da wannan maganar, wai itace ta tsotse shi, ta yi dan murmushi tana cewa a ran ta Mukhy-Mukhy case ne shi wallahi, ko yaya ne dai, ni di kujera ce, dole a zo inda nake a zauna a kai na, duk da gorin hali da ake yi min din!. Yana saka kai zai fita daga dakin Ummami na shigowa, sun kusa karo, ya yi maza ya ja baya ya bata hanya, ta ce to kai kana nan ashe, ana can ana ta neman ka, duk sun fito kai suke jira zaku tafi airport Ummami ke na zo nema ni, bamu yi sallama ba aah ka dai zo yin sallama da matar ka, to gani me zaka bani? Mukhy sai ya riko hannun Ummami, ya sumbaci saman hannun nata ya ce wannan sallamar zamu yi. Kunya irin na rashin sabo ya kama Ummami, amma ta yarda Mukhtar yayi rashin wannan soyayyar tata, bata nadama, amma tana tausayawa faruwar hakan a tare da shi, yau gashi ai Allah ya raya musu shi, ya zama magidanci cikin koshin lafiya. Tabbas ka ki naka ne duniya ta so shi, amma mutanen duniyar ma ba kowadanne ne irin Alhaji Usman Faskari ba. masu maida dan kowa nasu, kodayake shima din saar sa aka ci don a baya halin mutanen duniya gare shi. Da wannan tunanin take so itama ta kwatanta, wajen rike masa tilon yar sa da amana duk da cewa itama yar ta ce. To Amani zata ci tudun alfarma har biyu kenan a wurin su. Ta dubi Amani dake ta sunkuye-sunkuyen kai, rashin gaskiya duk ya bayyana a tare da ita, da kyar in Ummami bata ga abin da ta gani ba, ta ce, ina fatan kun yi sallama, zasu wuce Burkina-Faso ne. Yace Ummami wace irin sallama ce tsakanina da ita? Baki san Amani bata so na bane? A firgice Amani ta dago ta kalle shi a tsorace, ya kuwa tsare ta da kyawawan idanun sa ya ce ko zaki ce karya nayi miki? Ba auren dole Alhaji yayi miki ba? Ko in gaya mata me kika ce da ni a Freetown gidan Faytoory?. Idanun sa suka kada, suka kuma tsaya a kan ta, kamar yanzu ta fadi maganar, ita dai ta shiga uku ta lalace da Mukhy a kan wannan maganar, mana daya ya ki yafe ta. Amani ta hadiyi miyau da kyar, ta girgiza kai, idanun ta fal hawaye, ga mamakin ta tafiyar da zai yi Burkina-Faso har tsayin sati biyu shi ya fi damun ta da daga mata hankali a yanzu, ba wannan tone-tonen nasa da neman rigimar tasa ba. Ummami duk da maganar ta buge ta kuma bata yi mata dadi ba amma ta waske, ta ce ta yaya zaayi hakan? Dole kanwa ta so Yayan ta yace banda wannan Ummami, ita bata son kowa daga kan ta sai kan ta da Amani ta ga zai tona mata asiri a gun Ummamin dake ganin mutuncin ta, sai ta saki kukan da dole zai dakatar da shi, kuka shiga yi riii-riii sosai, nan kuwa ba na komai bane na damuwar tafiyar sa ne. Ko har yaushe Mukhy ya soma samun matsuguni irin wannan a ran ta, da har take jin damuwar tafiyar sa matuka gaya haka a kasan ran ta? ita kan ta bata sani ba! Ummami ta hau shi da fadan girma, inda take cewa cikin fada-fada kada ya kara gaya mata wani abu da ya shafe su, tunda ita bai shafe ta ba. Sannan ta hau lallashin Amani, tace rabu da shi diya ta kin ji, gidan zai bari ki samu ki huta sosai Amani kamar ta cewa Ummami ita so take ma ta bi shi, babu wani hutu a nesantar ta shi sai karin damuwa da hakan zai zame mata, hakika yau ta samu kan ta a sabon yanayi, wato ta samu kan ta da enjoying dan short kiss din da yayi mata fiercely (a zafafe) fiye da wanda ya faru a gidan Mamma a Kenema, ita bata san ana soyayya cikin zafin rai ba sai yau. Memories din hakan, dana sumbatar da ya yiwa kirjin ta, ya like a kasan ran ta, kamar har zuwa lokacin Mukhy sumbatar nata yake ke cigaba da yi, don har zuwa lokacin tsigar jikin ta da Mukhtar yayi sanadin tashin ta bai koma normal ba. Ya saci kallon ta, kamar ya karanci situation din da ya bar ta a ciki, shima hakan take, ji yayi kamar ya ce da Mamma a tafi da ita su dan zauna tare, amma sai kawai ya share, yayi wa Ummami sallama sannan ya bar dakin ba tare da ya sake bi ta kan ta ba, yana so ya koma Mukhtar din sa na baya, mai daurarriyar fuska, rashin walwala, da cin magani, amma ina! Idan yana gaban Ummami yanzu, sai ya ji kan shi kamar yaron goye, farin ciki ya cika zuciyar sa, rayuwar sa ta haskaka ta zama cikakkiya, soyayyar da bai samu a kuruciyar sa ba ita yake samu yanzu wadda take yawan saka shi a nishadin da yake sawa ya manta previous situation din nasa. Wannan yanayin nasa na rashin walwala da bacin rai a yanzu ya zama tarihi a tare da shi. Ya gane hakan ne da ya ga har ya ga Amani duk da fushi da yake da ita amma kuma ya kasa ignoring din ta, karshe sai gashi ya bige da sumbatar ta, wanda ya jima da hana kan sa sake bari wani abu makamancin wannan ya shiga tsakanin su, sabida abubuwan data faffada masa ana I gobe zasu taho Diffa a dakin ta na gidan su sun kara kwaba waccan maganar ta farko. Duk da cewa ya rama da mai zafi har fiye da nata tun a lokacin, daidai da yadda yake so ya rama din, amma tsatsar maganganun har yanzu bata bar ran sa ba. Mukhtar, Alhaji, Mamma, Baba Idi da wadanda sarki ya wakilta su raka su har mutum biyar, sun tashi a jirgin sama zuwa makwabtan su wato Burkina Faso, ya zama sai ita da Ummami da Sahura da tarin bayi mata da ke shige da fice suna ayyukan su a bangaren Ummami. Tunda Mukhy ya kira Ummami yace sun sauka lafiya bai kira Amani ba, hakan yana cikin sababbin techniques da ya dauka don yana so ya koyawa kan sa tolerance a kanta, ita kuma ya koya mata sanin darajar sa, har zuwa lokacin da zata koyi son shi don radin kan ta, irin son da ya samu kan sa yana yi mata, ba wai so na tursasawa ba ko na cin alfarma, ko don idanun iyayen sa da take tunanin bashi da su a baya, ko na dangantakar jini da ke tsakanin su. Ummami tasa aka shirya musu zuwa wajen kishiyar ta wato Hajja Tarha domin Amani ta gaishe ta, an musu karba ta musamman a sassan Tarha ta kuma kira yar ta Saadiyya dake Guinea a waya ta hada su suka gaisa da Amani. Ummami ta yi haka ne don samar da sanayya tsakanin Amani da yayan Sarki guda biyu mata, wato Sayluba da kanwar ta Saadiya kasancewar su yan uwa biyu kacal da Maina ya mallaka a duniya. Kuma dai dama tsakanin ta da Tarha babu muguwar gaba ta azo a gani sai kishi, wanda baa iya kaucemawa, wannan sai Ummu Aymana, wadda Allah ya raba su a yanzu. Sayluba kuwa sun hadu tun a wajen bikin auren su data zo, har ta koma Tahoa tun kafin a kammala bikin, halayen yayan Sarki Issouffou mata kwata-kwata bai yi kama dana iyayen su mata ba. Suna da saukin kai sosai da son mahaifin su, don bai raga musu komai na soyayyar Uba ba. Sannan tasa aka kai Amani gun amaryar Sarki ta yanzu wadda ita daga Somaliya ya auro ta. A daren Mukhy ya kira Mai Diffa, ya gaya masa in sha Allahu akwai alamun nasara a maganin da akewa Alhaji, don haka Sarki ya gayawa Ummami, inda ya ce ta gayawa Amani ta cigaba da yi wa mahaifin ta adduar neman lafiya mai dorewa. **** **** **** MALAMA BA SURUKA BA! W annan tafiyar da su Alhaji suka yi suka bar Amani tare da Ummami, shi ya haifar da wata kyakkyawar shakuwa a tsakanin su, kuma Ummami ma kamar kowa ta soma noticing rashin wadatar ilmin addini da rashin ingancin dabiun Amani, sakalcin ta, doloncin ta da sauran su. Amma ita ba kamar Jalan ba, bata duka bata hantara, sai tayi amfani da tafiyar su Mukhy Burkina Faso ta ja Amani a jikin ta, babu tsawa, babu duka ta soma koyar da ita muhimman abubuwa da ya kamata matar aure ta sani na addini, Ummami tun daga alwalah, sunnoni da farillan sallah dana alwallah da wankan janaba ta soma koya mata, domin ta sha mamaki da ta ce ta yi mata bayanin yadda ake yi ta ga ta hau kame kame, ko kuma kai tsaye ta ce bata sani ba, ko ta ce ta manta. Sannnan hatta yadda akewa sarakuna magana cikin ladabi da kwantar da murya sai da Ummami ta soma aikin koya mata, da yadda ake rayuwar aure da masu mulki, wani abun Amani ta ji kunya, wani abun ta gode har cikin ran ta. Ummami dai ta zamewa Amani malama ba suruka ba, shakuwar su ta kai ga cewa Ummami ta fahimci akwai rashin jituwa da rashin kakkarfar soyayya tsakanin Amani da Mukhtar, kuma auren hadin Alhaji ne ba wai su suka hada kan su ba, amma ta fannin dan ta Mukhtar dai ta san ko makaho ya shafa zai gane yana matukar son Amani a cikin idanun sa ma kadai, amma abinda ya fada ranar da zai tafi, ya dan tsaya mata a rai, da ya ce Amani bata son sa, auren dole Alhaji ya yi mata da shi, ta sunsuni akwai babbar matsala a kan hakan a tsakanin su. Ummami bata san cewa daga tafiyar Mukhtar zuwa yanzu an samu positive improvement wato canji mai yawa ba, a tare da Amina-Amani. Ta kasance cikin kewar Mukhtar, yadda bata zato, ba tare da ita kan ta ta san cewa tana kewar tasa ke damun ta ba, gabadaya tayi sanyi, duk ta zama wata irin shiru-shiru ba tsiwa, ba gayu ba cokala daurin kallabi. Mukhtar ya bar ta da kewar sa mai yawa a ranar da zai tafi, in ta tuna memories na abinda ya faru ranar da zai tafi kai mahaifin ta gidan magani, wato (sweet sensation) na lokacin ya ki barin ran ta, taji tana so ma ya dawo, ko ganin sa ne ta yi daga nesa, koda yake yace ba zai kara kiss ba, umh. Amma ita yanzu ne ma ta fara so da shaawar kiss din nan nasa, ta samu kan ta da son yayi maza ya dawo a maimaita sumbar, ko da cikin cokali ne wato wadda bata kai ta tsayin mintinan na ranar tafiyar sa ba. A wannan lokacin da wannan tunanin ya zo mata, Amani sai da ta tura kan ta cikin filo tana jin kunyar kan ta da kan ta, zuciya mai abun mamaki, zuciya tsokar naman kirjin dan adam mai yawan dawurwura (rashin tsugunawa a wuri guda), wai yau kuma Mukhtar take kewa, da bege haka, kai har ma da mararin gani, dan adam kenan mai saurin manta baya. Gaskiya ne da aka ce (no condition is permanent). Gaskiyar Balewa da ta taba cewa ta taka a sannu akan wannan bawan Allah bata san inda rana zata fadi ba. A wannan lokacin Hamida ta fado mata a rai, hakika bata kyauta ba, tun zuwan ta bata kira Hamida ba, akawari bai ce haka ba, gashi zata so ta bata labarin abubuwa da yawa da suka faru da ita dinnan a bayan rabuwar su din nan, masu dadi da marassa dadin, koda yake masu dadin kamar haduwar ta da Maman ta da dawowar Mukhy cikin nasa iyayen su suka fi yawa cikin labarin da zata baiwa Balewa, to amma wace irin fassara Balewa kan ta zata yi mata in ta ce mata yau gata dumu-dumu cikin kewar Dirty Human Being? Cikin mararin ganin Smart Ass da begen sumumu-kasau? In reality, Hamidah ta fi kowa gaya mata ta taka a hankali a kan Mukhy, ta ji tsoron kaddara, ta rage kiyayyar ta ga Mukhy, har ce mata ta taba yi bata san inda rana zata fadi ba, yau ga rana ta fadi da ita a gabas! Inda wanda ya san kin da ta yi wa Mukhtar da tijarar data zuba masa don wai yana matsayin yaron baban ta babu kamar Hamidah Balewa, ina ma dai da a ce Hamida zata zo har Diffa, ta ga yadda rayuwa ta yi kuli-kulin kubra da ita, iyakaci dai tayi mata dariya da shegantakar da bata san karshen su ba. Anyway, ya kamata ta kira Balewa, ta labarta mata duk abubuwan da suka faru a bayan ta, don abokin kuka baa boye masa mutuwa, shakiyanci ne dai ta san zata yi mata har sai ta gaji ta bari don kan ta. Amani ta kira wayar Hamida, cikin saa ba jimawa layin ya shiga, duk da ba koyaushe suke amun network mai kyau na yin kira Nigeria ba, saboda rashin kyawun network na yankin su. Hamida ta daga da hamzari, tana fadin. Sahibah, ke ce kuwa a kan layin? In da alkawari ruwa baya dafa kifi ba, kin makale a Saliyo, kin manta da ni Bestien ki? Anya alkawari ya ce haka? Amani tayi ajiyar zuciya ta ce da farko dai zan fara da baki hakuri Bestie, ki yi hakuri Hamdy, na shiga harkalla mai yawan gaske data sa ban samu damar kiran ki ba, sai yanzu da na samu nutsuwa. Kawata I have a lot to gist you with, muhimmi a ciki, ina mai farin cikin shaida miki cewa na hadu da Mama na Haj. Jalan a Saliyo, har an mayar da auren ta da Mahaifi na mun taho tare da ita, ki taya ni hango irin farin cikin dana ke ciki a sanadin hakan, amma a halin yanzu bama Katsina muna can yankin Diffa. Da tsananin mamaki Hamida ta ce Sahibah Diffa kuma? Wajen wa? Inane haka? Amani ta nisa tana fadin Bestie, wato labarin nan mai yawa ne, mai matukar ban alajabi, har ma da ban tsoro a cikin sa, na so a ce ga ni ga ki ne, in kwantar da kai a kafadun ki in yi kukan nadama, in kuma yi dariyar farin ciki as well, amma dai in takaice miki, na kwashi kashi na a hannun nadama, na kuma nade tabarmar kunya ta na yi gammo da ita a kai na. Abinda kika dade kina tunasar dani cewa in taka a sannu, kada watarana in zo ina nadama ya tabbata. Ashe Mukhtar da nake rainawa dan sarkin Diffa ne, mai jiran gadon sarautar gidan su, da daya kwal da Sarki Issouffou ya mallaka, wanda inda an bi ta nasabar da nake masa gori ne, ba zai aure ni ba. Diffa na daya daga cikin manyan biranen kasar Nijar, sannan kuma ashe dan uwana ne na jini, dan Yayar mahaifiya ta ne Haj. Aisata, wadda ke aure a can tun da jimawa. Hamida ta yi kabbara, ta sake yi, ji ta yi kamar ta shigo cikin wayar ta tadda Amani sabida zaquwa ga abinda take ji, ta ce ki bari Sahibah, bana so, bana son irin wannan zolayar kamar ta hikaya Amani ta yi rantsuwa tace babu zancen wasa a cikin magana ta. Ashe duk jini na na yiwa wannan tijarar, yau gani dumu-dumu cikin kogin nadama da wani sabon yanayi Sahibah, wanda nake so ki fidda ni a duhun sa. Ta dan yi shiru, domin ita kan tabtana jin kunyar abinda zata fada, kewar Mukhtar nake Hamdy, son ganin sa nake, matukar son ya sake kusanta ta na ke, sabida baya gari yanzu haka, ya kai Alhaji Burkina Faso tun satin da ya wuce ta tusa kanta cikin filo rike da wayar tana cewa na shiga uku Balewa, don ji nake abinda nake fada kamar sabo nake, amma gaskiyar abinda ke zuciya ta kenan, mararin ganin sa da dawowar sa daga Burkina Faso nake yi kamar in yi tsuntsuwa in cimmasa. Me yasa a da bana jin hakan ban da kiyayyar sa? Hamida bana so ya kasance sai da ya taka wani matsayi ne hakan ta faru da ni, don ban san fassarar da shi kan sa da alummar da ke zagaye da mu zasu yi min ba! Hamida ta yi kabbara ta sake yi, sannan ta fadi ta yi wa Allah sujjadah a dakin ta, ko babu komai ya karbi adduar da ta dade tana yiwa aminiyar ta, yau matsalolin ta sun warware ta kowanne bangare, jin abubuwan da take fada mata take kamar almara ko tatsuniya, tace Amani (sunan da ba kasafai take kiran ta da shi ba), are you sure duk wadannan abubuwan da kike gayamin daga bakin ki suke fitowa? Amani sai ta soma share hawaye cikin karaya da tsoron kada ya zamanto Balewa ce farkon wadda zata karyata ta, ta ce what are friends for? Shi yasa na gaya miki. Shi ya ce tuba na na karya ne, kada kema ki ce haka don Allah, in na boye miki ai bazan boyewa Allah ba cewa na yi nadama, Allah ya ga zuciya ta tayi wani irin damuwa da shi yanzu, ta share hawayen ta sannan ta ce, amma wa zan gayawa ya yarda da ni in ba ke ba? Ko cigiyar sa nayi cikin kuskure Baba Sahura mahaukaciya take maida ni, shin dan adam baya taba iya gyara kuskuren sa ne a karbi tuban sa? Don na tabbata in kowa zai yarda dani banda shi Mukhtar din, sabida wata bakar magana dana gaya masa cikin kuskure da ya kasa mantawa, da sauri Hamida ta ce kada ki gaya min, na san zaki aikata, ni na yarda da ke in kowa bazai yarda da ke cewa kina son Mukhtar ba Sahibah, ni na yarda kina son sa ba tun yau ba, wauta ce ta hanaki ganewa tun can kin damu da Mukhy, kin damu da duk wani takun sa a rayuwa ta hanyar yawan yin maganar sa with utmost hatred, and too much hatred so ne yake kawo shi. Haka yawan yin zancen mutum. Don haka yar uwa bamu makara ba zamu samo kan Yaya Mukhy din mu, ke dai ki tabbatar kin canza din da gaske kuma da zuciya daya, ki kuma tabbatar masa da canjin naki ta hanyar nagartattun halaye sababbi da zaki yafa yanzo, ki koyi bayyana soyayyar dake zuciyar ki a gaban sa da ladabi da biyayya, Sahibah ki nuna kulawa koda zai miki wata fassarar, to na dan lokaci ne, don na tabbata Mukhtar na son ki. Da sauri Amani ta damke wayar ta sosai a kunnen ta, hawayen farin cikin kalaman Balewa ya tsirgo mata ta ce da gaske kike Hamida Mukhtar yana so na? Kuma zai cigaba da son nawa bayan duk abubuwan batanci da tozarci da na yi masa? Zai cigaba da son nawa bayan ya dawo cikin gatan sa, ba zai fassara ni da wata fassarar ta daban ba? Hamida har ce masa na yi yana kama da.. Astagfirullah bana so in maimaita don na koyi sakawa harshe na linzami. Maganar ta yi wa Hamida gingiringin, amma ta san Amani neman wanda zai kwantar mata da hankali ta a ke yanzu, shi yasa har ta neme ta, tana neman mai bata support da assurance na cewa in ta gyara kurakuran ta zaa yafe mata, tunda ta ce ta koyi sarrafa harshen ta ta hanyar yin furuci mai kyau ga kowa, ance matar na tuba bata rasa miji. Hamida tayi ajiyar zuciya. Sun tattauna extensively kuma heart to heart yadda ya kamata aminai na kwarai su magantu, a kan wata masala data sha kan dayan su. Hamida ta gaya mata cewa har abada Mukhtar ba zai guje ta ba, ta gaya mata dalilan ta; inda tace bayan soyayya ta jini akwai soyayya gangariya a zuciyar sa a kan ta. Sannan ta gaya mata wasu maganganu na sirri na yadda zata nunawa Mukhtar cewa da gaske ta canza da zarar sun tare a gidan su. Amani da Hamida yau sun raba dare suna tattaunawa kuma Hamida ta taya ta murnar duk abubuwan da suka faru din. Kuma ta ce zata zo har dakin ta a Diffa watarana idan Allah ya nufa. Tun daga ranar dokin ta ga son dawowar Mukhy ya karu, har practicing/rehersing yadda zata yi masa sannu da dawowa take yi, da irin kallon da zata ke masa mai nuna kunya da ladabi ba irin na baya ba da take ware idanuwa ta zuba masa harara, yadda dai Hamida ta gaya mata, ya zama duk dare da tunanin Mukhtar ta ke iya barci, ta kuma gan shi cikin mafarkin ta, a yanayin da take kwadayin ganin nasu. Ummami bata san hakan ba ita, domin ta koma fara yi wa dan ta yakin neman soyayya, a fakaice (kamfen). Daga ranar data fara koyar da Amani karatu, in suka yi karatun addini suka gaji don ko wajen Mai bata zuwa sosai yanzu kullum tana like da Amani, don ta fahimci itama irin Mukhy ce ba soyayyar uwa ta tashi, gara ita ta samu ta uban shi kuwa fa? A kokarin ta na son kara cusa soyayyar tilon dan ta a zuciyar yar uwar sa kuma matar sa, tunda ta ji yaa ce bata son sa duk da ta musanta hakan, sai ta ga bari tayi amfani da damar wajen fayyacewa Aman tarihin Mukhy wataila hakan yasa ta tausaya masa a matsayin ta na yar uwar sa, tausayi da fahimta ta sani suna tasiri sosai wajen kimsa SO. Don haka rannan bayan sun gama karatu na addini da Karin Alqurani da take mata kullum sai Ummami ta sako zancen Mukhtar. Tace Aminatu kin san labarin mijin ki Maina? Cikin jin yar kunyar gaske da ta fara samun muhalli a tare da Amani yanzu, ko da yake in bata kunyar kowa tana kunyar Ummami, ta sunkuyar da kai, a lokacin tana taje ma Ummami dogon gashin kan ta da furfura ta soma samun muhalli, Ummami ta ce ta raba shi gida biyu ta yi mata tufka biyu ta gaji da shi a tsefe, mai kitson ta ta yi tafiya. Amani ta ce. Aah Ummami, ni dai kawai na tashi na gan shi karkashin kulawar Alhaji na, ban san inda ya samo shi ba kuma ban taba tambayar Daddy ba don bama jituwa ni da Yaya Mukhy ko kankani, shi baya son hali na nima bana son nasa, shi yasa kika ji yana cewa wai bana son sa!. Ta karasa fadi cikin karamar murya mai nuna kunyar idon uwa, amma gara ta gaya mata gaskiya a kan ta ci gaba da rikon ta a ran ta a kan bata son Mukhy, ba uwar da zata so a ce dan ta na auren macen da bata son sa sai dai ta yi kawaici, idan mai kawaicin ce irin Ummami kenan. Ummami ta gyada kai ta ce wato Amani, a duniyar Subhana ina tsananin tausayin Mukhtar Amani, shi yasa nake so kema ki tausaya masa, ki bashi soyayya wadda ban bashi ba, ki jiyar da shi dadin da mata hudu zasu jiyar da shi a lokaci daya, ki kuma kula da shi da rayuwar sa yadda nake kokari akan mahaifin sa ba don bai da wasu matan ba. Ummami ta nisa, sannan ta cigaba da cewa kin ga yadda ya bar gida duk gatan shi a shekarun balaga, a shekarun da ya dace a ce yana kusa da mahaifin sa a fadar sa yana koyar da shi shaanin mulki, amma ya zabi ya tafi uwa duniya sabida rashin samun kulawar iyaye. A hakan ma don baki san irin rayuwar da yayi tare da yayan bayi, a kuma sassan bayi ba. Idanun ta ya ciko da hawaye ta ce shi da ni sai dai leke daga nesa, ban taba goya shi a baya na ba, duk hakan bai isa ba aka zo aka bi shi da mugun asiri wai kurciya ya kara yin nesa da gida, kuma Baban sa bai damu ba ya cigaba da gudanar da harkokin mulkin sa rai kwance hankali kwance. A kan idanuna babu irin gatan da bai yi wa yan uwan sa mata Sayluba da Saadiyya ba. Tun ba lokacin auren su ba. ya zaba musu mazaje na fita tsara ya kuma yi musu auren gata. Kema kin san kafin uwa ta jure wannan kin san akwai wuya, meye laifin Maina don kawai ya zo a namiji? Amma haka na jure don farantawa miji na bisa raayin sa, ban taba kalubalantar sa ba tunda aka ce abinda babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba. Kullum jakadiya ta kawo min shi don in shayar da shi, nuna mata nake bana so, in ta isheni da roko sai in karbe shi, amma kuryar daki nake tafiya da shi ina shayar da shi ina kallon shi ina kuka. Ya kan kura min ido kamar yana tambaya ta dalilin mu na yi masa haka.??? Ummami ta share hawayen da suka kawo a idon ta, itama Amani zuwa lokacin nata idon ya ciko da kwallah, ta cigaba da cewa na san yana leken mu a shigifar sarki ko wajen hutawar sa da yamma a yawancin lokuta, wanda ba komai ke kawo shi ba sai bond din nan na soyayyar iyaye, wannan yasa na ke yawan zuwa wajen da Mai yake hutawar yammaci, dan mu yi sallar laasar tare, in mun idar in yanke masa akaifa ko in taya shi hira yana daga zaune bida karagar sa ina daga kasan kafafun sa cikin ladabi mai yawa, ba don komai ba sai don in ya zo leken namu nima ina samun damar ganin sa a sace. Ranar da aka ce min ya gudu ni na san dalilin sa, na kuma yarda da hujjar sa, tunda bamu taba zama da shi mun masa bayani, wanda zai gamsu da hujjar mu ba, don haka duk abinda zuciyar sa ta gaya masa ko ta fassara masa a kan mu a wancan lokacin a wurin sa shine dai dai. Suma na dinga yi ba tare da kowa ya san dalili ba, ana zuba min ruwa ina farfadowa. Daga ranar kuma ban kara sallah na tashi ban yi masa doguwar addua ba, kan cewa duk inda ya shiga Allah ya zama gatan sa, ya kare mun shi da karewar sa da kiyayewar sa, ya kuma kula da shi. Domin na yarda kulawar Ubangiji tafi tamu ta iyaye, kuma itace ta kawo Mukhtar yau inda yake. Ya yi rashin duk wata soyayya ta iyaye a kuruciyar sa, ina jin damuwa idan na tuna hakan. Da wannan nake rokon ki, a kan ki dubi girman Allah ki kula min da Mukhtar kin ji AMINA! Ko da a kasan ran ki babu soyayyar. Amani sai ta saka kukan data ke rikewa tun dazu a bakin ta, kuka mai sauti sosai, ta rasa abinda zata ce da Ummami wanda zai sa ta gamsu ba ta kin Mukhy yanzu, its true Mukhy had a traumatic childhood, and he deserve happiness a yanzu. Matsalar ta da shi riko. Ya ki sakin ran sa da ita su mori auren da kuruciyar su sai tsananin rikon ta da laifukan na baya da ya bari suka yiwa ran sa kaka-gida. Ko yayi kokarin sakin ran sa da jikin sa da ita wani time din, rikon dake zuciyar sa sai ya hana shi. Bayan rayuwar bakidayan ta sai ana ma juna afuwa, saboda rashin tsayin ta da rashin tabbas din ta. Life is very short and transient. Amma ai Allah ya san ta yi nadama, wadda ba lallai wanda ya santa a baya ya karba ba, zaa ce ne don ta gan shi da gata ne a yanzu. Don haka ta hadiye duk wani tunani a ran ta, nadamar ta da damuwar ta a kan Mukhy bata iya ta cewa Ummami komai ba, sai sheshshekar kuka take tana hadawa da ajiyar zuciya. Ummami ta ce to yanzu meye abin kuka daga magana? Ni labara kawai na baki don ki tausaya masa. Ba don in saka ki kuka ba. Koda yake Jalan ma haka take da saurin kuka, da abinda ya isa a yiwa kuka da wanda bai isa ba duk abin kuka ne a wurin ta tana karama, kin yi gado. Ni dai na baki amanar Mukhtar don dai gashi ya dawo gare mu ne, amma rayuwar sa zata fi yawa tare da ke, ke ce silar duk wani farin ciki da zai iya samu ko akasin sa, domin sai kin faranta masa daga gida ne zai fito cikin jamaar sa cikin annashuwa, ya ji dadin tafiyar da alummar sa da mulkin gidan su da tarin responsibilities din talakawa da ke kan sa, tun da dai kin ga shi Maina ne wato (Mai jiran gado). Da zata iya da ta gayawa Ummami cewa ta daina bata amanar MUKHY don Allah, don ita Uwar sa ce kuma bata san halin sa ba, amma shi ma ai takadarin kan sa ne na gani kashe ni, wanda baya bari ko da wasa a taka shi, ko a danne hakkin sa da ya rataya a wuyan mutane. Sai ya kwaci abinsa ko ta karfi ne. Kamar misali in tayi masa kwauron gaisuwa kasancewar shi mutum ne mai so a bashi girman da ya cancanta, da son kowacce mace ta kasance da halaye da dabiu na kwarai na girmama miji kwatankwacin irin na Ummamin sa, to fa ba zai hakura ba sai ya nemi gaisuwar nan ko ta karfin tsiya ne da bakin sa, haka in tayi masa rashin kunyar nata mai lasisi, Mukhy ramawa yake yi babu jinkiri babu bata lokaci, wani lokacin da mai zafin da yafi nata zafi, wanda sai ta kwana tana hadidiye bakar maganar sa. Amma tayi relating da labarin da Ummami ta bata na kuruciyar Mukhy, sai ta ga cewa ita kam, duk da babu Jalan, kuruciya ta gata da yanci kuma mai dadi ta yi, har ma da jin dadin tafi kowa gatan uba, he really deserves happiness ko yaya ne a rayuwar girman sa ta yanzu, kamar yadda mahaifiyar sa ta ce. Kuma ba daga kowa wannan farin cikin zai fara samuwa gare shi ba sai daga cikin gidan sa, wato daga hannun ita matar sa. Can cikin kanta ta jiyo sassanyar muryar Ummami, kasancewar ta yi nisa a tunani. Kin min alkawarin kula da Mukhtar da bashi soyayya da farin ciki a rayuwar girman sa AMINA? Ni kuma in kika yi min hakan, na yi miki alkawarin ba dai kiyi kuka akan Da namiji ba, zan tabbatar na zame miki garkuwa a wurin sa, daga duk mai son shiga gaban ki. Fata na kawai shine Mukhtar ya samu kwanciyar hankali a rayuwar girman sa, wadda bai samu ko kadan a kuruciyar sa ba. Ni da ke, babu hijabin surukuta ko yaya a tsakanin mu, sakamakon cewa ke din ya ta ce ta halali, wadda ko babu Mukhy a tsakanin mu zamu kashe mu rufe tare, ba tare da ko Jalan data yi nakudar ki ta ji ba. Hakika Allah Subhana na so na da kwanciyar hankali a tsufa na, wanda ban samu a kuruciya ta ba cikin gidannan, shiyassa ya bani ke wato ya sallado min ke a matsayin suruka ba tare da dabara ta ba, ke da kika kasance ya ta halali a gare ni, bai yi min suruka da wata daga waje ba, wadda zata sa Mukhtar ya sha wuya a hannun ta, don kawai yana son ta, shi yassa na bude miki ciki na yau mu fahimci juna mu tallafawa juna ta hanyar bashi kulawa a farin ciki ni da ke, ki sa a ran ki ni na haife ki ba Jalan ba. Amani ta share yan kananan hawayen da suke ta tsatstsafo mata a kowanne furuci na Ummami, wadanda ta san ba na komai bane na tausayin Mukhy da Mahaifiyar sa ne, duk Ummami ta gama kasha mata jiki da kuzari. A hankali ta gyadawa Ummami kai, wato ta yi wannan alkawarin, na kula da Mukhtar, da sanya shi farin ciki da bashi soyayya. Kuma har cikin ranta ta yi din, domin jikin ta yayi wani irin sanyi, ta yi lakwas kamar jikaakken tsumma, jijiyoyin rashin kunya, na girman kai, na alfahari dana dolonci suka shiga tssitstsinkewa suna farkewa da kan su, hankali da nutsuwa har ma da tsoron Allah ya soma ratsa Amani a kusufa-kusufa daban-daban na kwakwalwar ta. Ta gamawa Ummami kitson cikin matsanancin mutuwar jiki, kuma dare ya yi, don haka ta ce mata zata je ta kwanta, kan ta na sarawa sabida kukan data yi mai tsanani. Kuyangin ta da aka bata su suka raka ta har dakin barcin ta, don har zuwa lokacin suna can suna jiran ta a inda suka saba zama su jira ta in ta zo gun Ummami, da suka dawo bangaren ta daya daga cikinsu ta hada mata tea mai kamshin nanaa bisa umarnin ta, ta sha a gefen gadon ta, sannan ta kawo mata Panadol ta hadiya, suka yi mata duk abubuwan da suke yi mata kafin ta kwanta kamar kashe kayan wuta, kunna A/C da kunna mata karatun Alqurani a radion bakin gadon ta cikin kiraar Mahmoud Khalil bisa umarnin Ummami, na kullum su kunna mata in zata kwanta daga kanan surori don ta kara iyawa da gyara karatun sallahr ta. Tahira da Sugra kenan, wadanda su tafi sanyawa aiki da ja a jikin ta cikin hadiman nata guda biyar da Sarki yasa aka bata tun zuwan ta, sauran biyun suna kula da girki da kitchen din ta ne, daya kuma sharar bangaren ta da goge-goge da wankin toilets, ta zabi Sugra daTahira su dinga zama a jikin ta ne don su ba yara bane kamar sauran ukun, suna da hankali da nutsuwa, kuma suna da aure har da yara. Koina zata shiga cikin gidan suna tare da ita. Tahira da Sugra suna bada baya, bayan sun mata light off da sai da safe, sun bar mata dim light shudiya, kukan ta cigaba da yi, mara sauti, da alama dai Amani Faskari, most at times, finds pleasure and comfort in crying, tana yi tana yin wannan kukan ne don tausayin Mukhy tana comparing rayuwar sa da nata. Sai ta ga cewa, ratar gatan da ta samu da wanda ya samu mai tsananin girma da fadi ne. bama zaa kwatanta ba. Da gaske kamar yadda Ummami tace ne Mukhtar yana bukatar kulawar su su duka yanzu, amma ta yaya? Ta ina zata fara tata kulawar? Ko ta yi kokarin hakan ba zai bata dama ba, saboda ya rike ta da yawa a ran sa. Wata zuciyar ta ce da Amani Ai kema Amani mace ce, ko da ake cewa kin rako mata! Ki yi tunanin hanyoyin dadadawa mutum, musamman mijin auren ka, ta yadda zai ji dadi, ya manta da laifukan ka komai girman su, ya sakar maka fuska da zuciyar sa gabadaya koda baya so, albarkacin kulawar ka gare shi. Tunda an ce zuciya na son mai kyautata mata. Sai ki hada da abubuwan da Balewa ta koyar da ke na kissa mai kyau ta waya, da kuma naki yan dabarun da bazaki rasa ba, da wadanda Ummami ma ta koyar da ke na tafiyar da Saraki. Daddyn ta ya fado mata a rai shima zai iya taimakawa wajen sayo mata yardarm Mukhy a yanzu, ta tuna tun tafiyar Daddy basu yi way aba sai ta dauko wayar ta, ta kuwa same shi online a kan whtsp. Sai ta yi masa kira ta cikin whtsp call. Yana dagawa ya ce Tafisu! Me kike yi har yanzu baki yi barci ba? Amani ta yi ajiyar zuciya mai nauyi, ta ce yanzu nake shiri ai Daddy, so nake in tambaye ka yaya jikin ka? Kuma Yaya Mukhy yana lafiya? Dadi mai yawa ya kama Alhaji, y ace na samu lafiya sosai Uwata, kuma ina iya mikewa ma yanzu, Mukhtar sai dai in ce Allah ya saka shi a aljannah y araba shi da iyayen shi lafiya, ko ke da na Haifa iyakar abinda zaki yi min kenan a rayuwa. Uwa in har baki bi Mukhtar sau da kafa ba wallahi sai Allah yayi mana hisabi ni da ke, na hore ki da ki bi shi ki nemi aljannar ki babu ruwa na dake duk ranar da Mukhtar ya kawo min karar ki. Amani ta saki kukan da ke cin ran ta, ta ce Daddy! Kuna ta dora min abinda yafi karfi na, bayan ba daga gareni bane matsalar yanzu, na riga na gane kuskure na, shine dai ya ki ya yarda da ni ya kuma saki zuciyar sa da ni. Hakika na yi kuskure, ina so na gyara in zai bani dama, ka roke shi ya karbi tuba na ya kuma bani damar gyarawa. Na yi alkawarin canzawa daga yadda kowa ya sanni dinnan, amma hakan ba zai yiwu ba sai ya yarda da ni. Yardar miji kuma yardar Allah ba! In sha Allahu Mukhtar zai karbi tuban ki musamman in kin ajiye girman kai. Nima kuma zan taimaka wajen ganar da shi halayen ki ba laifin ki bane, nawa ne. Musamman a yanzu da muke da lokaci ni da shi kullum muna tare barci kadai ke raba mu. Ina rokon Allah yayi wa rayuwar ku albarka bakidayan ku, ya kuma albarkaci auren ku da zuriar da zamu yi alfahari da ita mai yawa mai albarka. Ta tambayi Maman ta yace ta yi barci tun dazu. Sun dade suna hira irin tasu ta Tafisu da Daddyn ta. Washegarin ranar, a darussan su na yau, ita da Ummami, har yadda uwargida ke zama a gaban Sarki sai da Ummami ta koyawa Amani, da yanayin yin magana da Sarakuna cikin kankan da harshe da tausasa furuci, da hadawa da kirari na kambamawa da nuna soyayya. Wani abun har sai Amani ta rufe ido don kunya. Da gaske Ummami ta janye hijabin surukuta bakidayan sa. Tasaka na malunta. ***** ***** ***** BAKIN BURKINA FASO R anar da su Mukhy suka dawo Diffa daga Burkina Faso ana zabga wani irin ruwan sama kamar da bakin kwarya har da kankara. Labari ya isko su cewa Maina ya dawo lafiya tare da jamaar sa, suna fada wajen Mai Diffa. Tsakanin Mukhtar da Alhaji bata san wa tafi dokin gani ba, don an ce da su Alhaji na tafiya yanzu a kan kafafun sa. Wannan ya kusa saka ta shekawa da gudu don ta cimma Daddy har fadar sarki. Don haka ta roki Ummami Allah Annabi tana son zuwa masaukin su Alhaji. Ummami tasa kuyangin ta wato Sugra da Tahira suka raka ta har inda aka sauki su Alhajin, da gudu ta karasa shiga dakin tana kwarara kiran sunan Alhaji Daddy, Daddy na! Alhajin kuwa ta fara yin tozali da shi yana tsaye a kan kafafun sa yana waya da Matawalle da ke Katsina, da gudu Amani ta karasa ta rungume shi, tana kukan farin ciki, da godiyar Allah. Mamma ce ta hau ta da fada tana cewa ta yi masa a hankali, bashi da kwari, jiya ba yau bace, kuma da da yanzu ba daya bane a gareta ita kan ta, ta daina wannan haukan da take yi a jikin Alhaji. Ita matar gida ce yanzu Ta dube su duk sun murje sun yi gwanin kyau, tsufa duk ya bace, Alhaji yayi kiba yayi haske, ta hau dariya ta ce ai kawai Mamma ki ce honeymoon kika tafi kai Alhaji Burkina Faso ba jinya ba, wannan irin murjewa haka? Jalan uwar saurin hannu nan da nan ta kai mata duka. Amani ta goce tana tana ta dariya, Jalan na fadin na ga alama kin maida ni saar wasan ki, ni kike cewa na je honeymoon? Alhaji ya kammala wayar da yake yi ya rufe yasa a aljihu, yace Ya ki nan Uwa ta, kyale ta, sannan ya hau Jalan da fada, ni tunda nake ban taba ganin Uwa mai saurin dukan Da irin ki ba, to in bata yi wasa da ke ba da wa zata yi? Yar guda daya ita kenan Allah ya bani bazaki taya ni tattalin ta ba don ke kina da wasu ko? Amani tayi dariya ta ce aah Daddy, daina mata fada haka, kada ta yi zuciya taki yi min wasu kannen, biyu sun min kadan. Duk suka fashe da dariya har Mamman. Alhaji ya ce ta tashi ta koma cikin gida haka, don mai Martaba ya ce masa an gama ginin su, an saka komai, yau zaa kai ta bangaren ta kafin wucewar su gida Katsina. Su kuma in sha Allahu gobe zasu wuce Nigeria. Tuni jikin Amani ya mutu, yar farar data shigo da ita ta koma ciki, aure da rabuwa da iyaye ba wasa bane ba kuma sauki gare shi ba, damuwa da kewa suka bayyana a fuskar ta tun ma yanzu kenan, ta soma tunanin irin kewar su da zata yi tun basu tafin ba, musammamn Alhaji. Zata soma kukan tun kafin gobe ta yi, Ummami ta aiko jakadiya tayi kiran ta, don haka ta rike hannun Daddy tana hawaye ta rufa tafukan sa a kan fuskar ta, ta ce to yanzu Daddy ni da ku sai yaushe? Kai tsaye Alh. Usman yace sai kin haihu zamu zo, in kin min aboki ko sabuwar amarya, ki sa himma shekara mai zuwa sai ki gan mu gabadaya mun dawo radin suna, har Balewa zamu dauko miki da su Laure, da Kamilu. Kunyar da bai san Amanin shi da ita ba ya gani ta zo ta lullube ta, harda kare fuska da hannayen ta cikin jin kunyar Daddy yau. Jakadiya da kuyangin ta suka maida Amani wajen Ummami, aka soma shirya ta don wucewa nata bangaren, wanda ke can gefen dama na masarautar Diffa. Da ka wuce sassan Sultan Issouffou Massaoudou. An kawata ginin a zamanance, hakanan ya tafi da zubin sarautar Al Imaraat Al-Diffa duk da haka. Daga ciki ne aka zuba abubuwa na zamani. Bangaren Maina Mukhtar Bn Issouffou Massaoudou dake ciki Al Imaraat Al Diffa wato masarautar Diffa, zan iya kwatanta shi da Palace din da babu kamar shi a duk cikin fadin masarautar, in ka cire sassan Sarkin Diffa. An shirya musu dakunan barci har shidda, da shigifu (faluka) na alfarma wadanda aka yi wa design da furnitures kala daban-daban, wasu an yi musu zubin royal parlors, wasu kuwa English parlors ne, da kuma Francaise. Jalan na cikin hada kayan ta don gobe da asubah zasu kama hanya, Mai ya basu driver wanda zai kai su har Katsina sannnan ya dawo, Jalan ta ki yarda su yi sallama da Amani ta ce da Ummami a wuce da ita gidan ta kawai, ita bata son koke-koken banza na Amani, sannan duk wani abunda uwa zata fada mata ta san Ummami ta gama gaya mata, don haka Ummami tayi abunda baa taba yi ba a masarautar Diffa, inda tace da kan ta zata kai Amani har dakin ta. A daren Mukhtar yana tare da Mai, suna cin abinci a kwano guda, yana masa hirar abubuwan da suka faru dasu a Burkina Faso da yadda aka magance lalurar Alhaji Usman ta suga da shanyewar jiki ta hanyar maganin gargajiya ziryan. Mai cikin gamsuwa da taimakon da aminin sa sarkin Burkina Faso yayi masa ya ce da Mukhy, ya saka an warewa Alhaji Usman Rakuma hamsin, a fara yi masa kiwon su anan cikin bargar Rakuman sa, in kuma yana so a kai masa su Nijeriya ne duk zai iya sawa akai masa har can, sannan ya bashi sittiru irin nashi na alfarma da rawanin sarautar Diffa akwati guda, har da zoben azurfa mai matukar daraja. Mukhy ya taya Alhaji godiya sai ya ce Uwa ta fa? Me aka tanadar mata? I mean ita me zaa bata? (yana nufin Mamma Jalan). Mai ya ce ya bada bracelet na zinare a bata, har Baba Idi ma ya samu kyautar Rakuma goma daga Mai Diffa, Baba Sahura kuma Sarki yace Ummami ta ce a nan shiyyar Amani zata zauna tare da ita har sai ta saba da gidan da mutanen cikin sa koda zata koma Katsina. Duk da dai an bata wadatattun kuyangi da masu hidimar ta. amma zaman Sahura zai mata amfani. Mukhtar yana can suna wannan tattaunawar da mahaifin sa, ba tare da ya sani ba Ummami da Baba Sahura suka kai masa Amani dakin ta, bai san hakan ba don tun dawowar su bai nemi ganin Amani ba, kuma ko a hanya basu hadu ba, tunda yayi alkawarin daina kebewa da ita sai ta yi hankali ta kuma koyi son shi don radin kan ta, ya fahimci sai sun kebe ne take warware masa lissafi, da haka yake so ya koyawa kan sa hakuri daga shiga lamarin ta yanzu, ya fuskanci muhimman alamuran da ke gaban shi na taimakawa mahaifin sa kan shaanin mulkin sadon sauke nauyin alummah dake kan su. Don haka yayi gefe da Amani daga ran sa (for the mean time) na yana so ta koyi son shi domin Allah ba don wasu material attachements, ko nasabar da take goranta masa ba. Daga wajen Mai, sai ya wuce suka yi sallama da su Daddy, yana jin wata irin kewar Alhajin nasa, Mukhy har da hawaye ya yi, ya fiddo wayar shi ya yi ma Alhaji hoto, yace Alhaji duk tsayin lokacin nan wai ace bani da hoton ka a waya ta. Dariya Hon. Ya yi ya ce to gashinan ka samu, sai ka ajiye in ka tuno ni ka dauko ka duba. Tunda ni da Uwa bama kama balle take tuna maka ni, Jalan da yake ta fini karfin jini ta kwace wannan. Da kyar suka iya rabuwa don dare ya fara yi, daga wajen su sai ya wuce sassan Ummami. Ya same ta tana shirin kwanciya, sai ta ce Maina tun dazu nake jiran shigowar ka in kwanta don na gaji da yawa, hidima kan hidima yau na sha ta har na gode Allah. Alhamdulillah tunda komai ya nabbaa yanzu yadda na tsara Mukhtar ya samu kujerar sofa din ta ya zauna, ya ce ai ga ni yanzu, Sweet Mum, me zaki bani Ummami na? Budar bakin Ummami sai cewa tayi. Amanar diya ta Amina mana!. Maina ka sani daga yau zaka soma rayuwar manyantaka, ka kasance mai hakuri da yi wa matar ka adalci da rangwame a kan duk wani ajizancin ta, kai ne babba sama da ita, don haka babba juji, bayan kasancewar ta matar ka yar uwar ka ce, jinin ka ce, da ta fi karfin kowanne uzuri a wurin ka. Haka Ummami ta zaunar da Mukhy wajen awa guda tana masa wata irin nasiha mai ratsa zuciya, ta gaya masa ta kai masa Amani gidan sa yanzu haka. Ya dan yi shiru na yan sakanni, ya rasa a yanayin da yake ciki, finally, shi da Amani yanzu! A gida daya, daki daya, kuma gado daya. Tsakanin farin ciki ko akasin sa, bai san wane ne yake nukurkusar sa a kasan ran sa ba, a can wani sako na zuciyar sa yayi kewar ta, a wadannan sati biyun da bai sanya ta a ido ba kuma bai ji muryar ta ba, duk da yake busy da kula da Alhaji, amma kullum sai Alhaji ya masa zancen ta, mai nuna yay aye mat aba don halin ta ba, mai nuna tsanannin kaunar da shimahaifin nata yake yi mata, wanda ke sawa ya kara mannata a zuciyar sa shima ko ya ki Allah balle yana son ta, albarkar Alhaji sai son yake ninkuwa kullum. Amma ba don ita ba, ba kuma don halin ta ba, sai don an jarrabce shi da son ta da kaunar ta tun kafin haka, (no matter how worse her behaviours are). A haka suka yi sallama shi da Ummami, yana jin kan sa kamar wani sabon mutum yau da ya mallaki matar aure a cikin gidan sa, kuma yar Alhajin sa, Amani Tafisu da zuciyar sa ke matukar so fisabilillah, ya shiga ratsa falillukan Ummami ya wuce zuwa sassan nasu, dogarai na faduwa suna gaida shi a duk kofar da ya wuce. Tunda Ummami ta ajiye ta a bakin gado bata sauya wajen zama ba, dan irin kukan nan na amare babu shi a idon Amani Faskari, idanun kemadagas, kamar soyayyar gyada marau-marau, amma damuwa da taraddadin haduwa da Mukhy yau, ta mayar dasu yan kanana, data gaji da lullubin ta sauke shi saman kafadun ta, ta daga kai tana kallon irin wannan dukiya da aka zuba musu a wannan daki don su biyu rak, ta dade a zaune tana godiya wa sarki Allah akan komai ma, musamman a kan iyayen ta da suka koma auren su, sai kuma ta tuna bata yi sallahr isha ba, don haka ta tashi da sauri ta shiga inda take tunanin toilet ne, don yanzu bata wasa da lokacin sallah ko kadan sabida nasihun Ummami. Ta idar da sallahr tana addua ta ji motsin shigar sa dakin da ke kallon nata. Kamar ta je, kamar kada ta je, ta tunawa kan ta cewa ita fa amarya ce no matter how, Mukhtar shi ya kamata ya zo inda take duk mulkin sa. Don haka ta daure ta cigaba da zama akan dardumar da tayi sallah, daga baya tun tana addua a kan Allah ya gyara mata halayen ta da kowa ke kuka da su, har barci ya dauke ta a kan sallayar. Mukhtar na nasa dakin har washegari yana barcin gajiya, haka kawai zuciyar sa bata amince ya je ga Amani ba, ko ya so hakan zuciyar ta ki amincewa, haka kawai ya koyi juriya daga shiga alamarin ta. Basu suka hadu cikin gida ba sai da safe a falon sa na farko, ta fito cikin sassaukar shiga ta atamfa Holland, ta yi daurin kai dai-dai misali ba irin daurin ta na baya da ta saba yi ba wato Ture ka ga Tsiya yau daurin Amani kan sa ya russuna, kamar yadda zuciyar ta ta russuna, musamman da ta ga sun kwana gida daya da Mukhy amma ko da wasa bai neme ta ba. Jikin ta duk ya yi laasar ya jikakken tsumma. Mukhtar na kwance cikin kujerar zaman mutum daya a falon nasa ta shigo ba tare da ta san yana ciki ba, don ta duba abinda suka shirya musu na Karin kumallo, ya yi wata irin kwanciya kamar mai barci amma a zahiri ba barcin yake ba, yana tuna maganar da suka yi da Mai ne, na cewa Mai Diffa yana so ya karbi sarautar Diffa tun yanzu, sabida shi tsufa ya cimmasa abubuwa da yawa baya iyawa yanzu, sabida rashin karfin jiki. Ya tuna amsar da ya baiwa Mai a lokacin. Allah ya taimaki Mai Diffa, ina rokon a bari zuwa gaba kadan, tunda Allah ya hore maka lafiya da koshin lafiya da abinda lafiya zata amfana, ina so in kara samun nutsuwar da zan kara fuskantar yadda shaanin mulkin yake daga gare ka. Takun sawun Tafisu da kamshin turaren ta ne ya ankarar da shi isowar ta, a daidai kafafun Mukhy Amani ta zauna, har yanzu gajiyar tafiya bata sake shi ba, shiyasa yake ta kwanciya tun jiya ya kasa fita yau, ya bita da kallo tana zama a daidai kafafun nasa, har ta zauna fuskar ta ba yabo ba fallasa sai damuwa da kulawa, ga dukkan mamakin Mukhtar sai cewa ta yi. An dawo lafiya Ya Mukhy? Sai kuma ta tuna zaman da Ummami ta ce irin shi zata dinga yi in tana gaban Maina, ai kuwa ta gyara zaman nata da irin zaman Ummami din, kamar zata shige cikin jikin sa russunawa da kulawa kamar baiwa a gaban Sarki, shi dai Mukhy kallon ta yake daga kwance yana cewa cikin ran sa wannan canjin nata ba na kalau bane, don ganin abun yake banbarakwai, wai namiji da suna Hajara. Haka nan dai ya daure ya amsa mata (with straight face), sai kuma ta ce masa ka ci abinci? I mean breakfast? Ya dan kalle ta da wutsiyar ido yana mamaki, sai ya biye mata da yadda ta zo, ya ce aah ban ci ba tukunna, wani abu ne ya faru? Tashi na kenan daga barcin da na koma bayan sallahr asubahi, shine na zo nan nake hutawa, kafin lokacin fita ta ya yi. Mukhtar yayi bayani, don ya kasa gane inda ta dosa da sabon canjin, yafi sawa a ran sa wani abun take so shiyasa, don bai saba da concern din da yake gani yau daga gareta ba. Amani ta karya kai, Allah ya taimaki Maina to ai ga abincin can sun shirya shi tun dazu a kan dining-table, Maina ko zaka taso mu je mu karya tare? Mukhtar ya kasa hadiye mamakin sa har ma da dariyar sa, ya ce Amani ce kuwa? Don hatta lafuzzan ta da wani irin taushi da rangwada suke fito masa. Tayi murmushin jan hankalin miji, sannan ta ce ko a kawo maka abincin nan ne Ya Mukhy? Idan ba ka son tashi daga nan din?. Sai ya ce umh kawai, ya koma yadda ta zo ta same shi a kwance, ya sake maida hankalin sa kan wayar sa, don ya kasa gasgata abunda yake gani daga gare ta dinnan. Maiyuwuwa gizo idaun sa ke masa. Amani sai ta tashi ta tafi ta kawo abincin daya bayan daya, ta shimfida ledar cin abinci a gaban sa, ta hau hadawa Mukhy black tea mai kamshin kanimfari da citta, don Ummami ta ce mata lallai su duka su dinga yawan shan kaninfari, tana cewa ni bana shan tea da madara fa, ban sani ba ko kai ma haka? Mukhy ya tashi zaune sosai, sannan ya harde hannuwa a kirji, ya kuma harde kafafun sa, ya zuba mata kyawawan idanun sa, ya sake cewa umh, kawai, yana ta mamaki dai, don still ya kasa yarda ita ce, sai ta mika masa kofin shayin da ta kammala juyawa da Zuma maimakon sugar, ta bashi cikin girmamawa. Mukhtar sai ya karba, ba tare da ya ce komai ba, ya kuma kai bakin sa ya kurba, kamshin kanimfarin ya masa dadi a makoshi, bai ce aah ba, amma bai yi wata kwakkwarar magana ba har yanzu. Amani ta cigaba da zama a yanda take, abin ki da rashin sabo da kyakkyawar muamalar data ke son assasawa, duk ta kasa sakewa da zaman da tayi din, shi kuma ya cigaba da sipping shayin sa ko a jikin sa. Ganin ya karba ba tare da ya gwale ta ba har yana sha, sai ta samu karfin guiwar zuba masa farfesun naman kaza, ta sa spoon a ciki ta mika masa. Ya karba again, ya soma shan romon da cokali, yana yi yana daga ido yana kallon ta, ta kara da zuba masa chips and fried egg wanda ya ji albasa da koren tattasai, ta sake mika masa, ya karba babu musu, don yana jin yunwar sosai, rabon shi da abinci tun jiya, amma kuma babu magana a tsakanin su sannan babu nagode. Ta zauna ta cigaba da latsa wayar hannun ta wanda chatting ne suke yi da Balewa, ta ce Bestie, Im done with step one, but he seemed careless da kokari na. Balewa ta turo mata Emoji na jinjina da kwanji, ta ce, dont worry, keep up the good work, saura kwashe kwanukan da ya gama cin abinci, ki tabbatar rigar ta zazzago gaba kuma a saitin idanun sa kin masa flashing. Dariya ce ta kama Amani ta yi yar sheshshekar dariya ba shiri, ta ce Balewa ba dama! Sai da Mukhtar ya dago daga cin abincin sa ya dube ta, ke da wa Hajjaju? Ya tambaya cike da tsegumi, don kuwa Amani ba mutum ce mai yawan fara ba balle a je ga dariya a iya sanin da ya yi mata. Yau kuwa sai fara take kamar gonar auduga. Yanzu kuma har da kyakyatawa. Ya Mukhy ni da Balewa ne. Oh I see! Ki ce Your role model!. Ta yi murmushi, domin bata yarda da abinda yace din ba, hakika da aboki yana maida abokin sa role model din sa, da tuni Balewa ta dade da zame mata role model tuntuni ba sai yanzu ba da duniya da kan ta ke koya mata hankali. Domin iyakar hankali da sanin ya kamata, mutunci da sanin ciwon kai da rikon addini suna tattare da HAMIDAH HASHIM BALEWA, ita din ce a baya bata yarda ta yi copying halaye da dabiun Hamida Balewa ba, don a nata tunanin, a sanda take kan ganiyar ta it ace wayayya Balewa bata waye ba, shi yasa take yin simple life duk da kasancewar ta yar gata, kuma a nata ganin simplicity din Hamida yayi yawa, zai sa kowa ya raina ta. Sai yanzu ne ta san Balewa ce wayayya ba ita ba. Ita shirme da kidifiri da girman kan banza kawai ta sani, ta kuma kware a kai. Mukhy ya ci ya koshi, ta tashi don ta kwashe plates da bowl din farfesun, ta yi yadda Balewa ta ce ta yi, kuma cikin saa Mukhtar dagowar sa kenan idon sa ya fada kai, ba zato ta ji ya mike shima, zata tafi da kwanukan sai ya dan rungumo ta ta baya, ya ce. Na gode da kulawar nan, nagode da dan canjin nan dana gani, honestly I cant resist it!. Sannan ya dora karan hancin sa saman gashin kan ta yana rike da ita daga bayan ta, ya mannota sosai zuwa jikin sa, yana sunsuna gashin ta yana cusa dogon karan hancin sa a ciki, wanda hakan ya sa dankwalin Amani ya sabule ya fadi kasa ta baya. Gabadaya gashin da ya shag yara ya zubo bisa kafadun ta. Ya Ilahee! in ji Mukhy. Yadda Mukhtar ya shiga goga tsinin karan hancin sa cikin gashin kan ta ya haifar mata da yar rudewa, daburcewa da bakuwar kasala, duk ta san cewa ita ta tsokano shi, hakan yasa kwanukan dake rike a hannun ta subucewa suka zube a kasa, da na tangaran ne ba abinda zai hana su fashewa su yanke su sabida yadda suka subuce daga rikon ta ba zaton ta, amma hakan bai sa Mukhy fasa abinda yake yi ba, ta fahimci bat un yau ba, babu kamshin da Mukhy yake matukar so a jikin ta irin kamshin tsakiyar gashin kan ta, wanda ya fahimci turaren gashi na musamman ne take amfani da shi a cikin gashin ta, wanda iyayen ta Jalan da Aisata dake bata shi kadai suka san sirrin da ke cikin sa. Kamshin gashin nan ya tsokano abubuwa da yawa da yake ta kokarin dannewa tun dazu, kuma dai dama ko ta ina aka je aka dawo Mukhtar ya san yayi kewar Tafisu, ba ita kadai ba har tsiwar tata, kidifiri da rashin kunyar duk ya yi kewa yadda ba ya zato, a kwanaki goma sha hudun da ya yi a Burkina Faso. Sai kawai ya jirkito Amani bakidaya ta fado masa ya soma kissing din ta gently, wani abu data tabbatar ya matukar kwarewa a kai fiye da komai watau gentle kiss, duk ta kara daburcewa kafin kisses din Mukkhy ya soma shigar ta yadda ya kamata. Gangar jikin ta kuma ta soma responding. Tafiya ta soma yin tafiya, Mukhtar na kara birkita Amani da duk wani nauI na romancing na miji ga matar da yake matukar so, yana kara sanya mata son amsa kiran sa ta koina da sumbar nan tasa mai shiga rai, a kowacce gaba mai bukatar hakan a jikin ta, wannan karon ma kamar wadancan karon, Amani ta gama sakarwa Mukhy komai, da dukkan zuciyar ta da sahalewar ruhin ta, gabban jikin ta sun gama nuna amincewar ta, ta shirya welcoming din sa (as a husband), har addua take a ran ta koma meye zai faru ya faru a yau, kuma a yanzu. Zata jure, in dai hakan zai faranta ran Mukhy ya daina rikon ta a ran sa ya bari su zauna lafiya. Lokaci daya Mukhtar ya tuna Amani fa ba wai son shi take yi ba har yanzu, kada yar canzawar nan da ta yi ya rudar da shi ga sanin ainahin wacece Amanin sa, Tafisu wadda tafi sauran mata tinkaho, yanzu haka tana da dalilin ta na wannan dan canjin da ya gani a tare da ita. Maiyuwuwa wani abun take so yayi mata, amma a sanin da yayi mata, Amani bata da kirki, kuma bata kirki domin Allah. Sai tana neman wata alfarma a gare ka. And he will not be selfish anan, duk inda ya kai da son ta, da son kasancewa tare da ita don bayyana wannan son da tabbatar da shi, yafi karfin yayi auratayya da macen da baya ran ta kwata-kwata, bata kuma yi masa irin son da yake yi mata, sai dai ta amince da shi bisa dole don ba yadda zata yi da auren sa, tunda iyaye suka hada shi bisa karfin ikon su a kanta kuma sun fi karfin ta. A yanzu kam baya jin akwai abunda ba zai iya hakura da shi ya zauna lafiya ba a rayuwar sa, ya hakura da iyayen sa ma shekaru sha biyar, kuma ya rayu da numfashin sa balle soyayyar mace, alhalin yana karkashin gatan sa? Amani sai gani tayi Mukhtar ya sake ta ya ja da baya cikin mutuwar jiki, yatsun sa ya saka cikin tarin sumar kan sa, ya ce Im so sorry for that, I know you dont love me Amani, and I will not force you to love me or to sleep with me, because I will not be selfish! In na yi hakan na so kai na. Ya dauki dankwalin ta da ya sabule ya dora mata saman kujera, yana fadin Sorry for making you to regret this again, I just couldnt resist your changes for today, I like this new you. Ina ma wannan sabuwar Amani tawa ta dore! Ya sumbaci goshin ta ya ce by Allah! You will be the death of me Amani, je ki kada ki sa in kasa controlling kai na kuma, in yi abinda zai zo ya dame ni, kema ya dame ki, tunda har gobe na kwana da sanin ba kya so na. Dole aka yi miki a kai na. Na rasa me yasa? Komai na kudurta a raina don tsira da mutunci na daga fitinar ki, in kika zo gaba na sai kin san yadda kika yi kika rusa min shi. Amani, why? Why are you playing with my heart? Me yasa bazaki bar ni in zauna lafiya ba? Ko don kin ga bani da juriya a wannan bangaren Im very fragile? Kullum sai kin san yadda kika yi kika tsokano ni wato ko? Do you know how Im suffering after touching you? Na rasa ko ke wace irin mai halin hawainiya ce, yau ki zama fari gobe baki. Kasancewar kin san ni mutum ne mai son a kyautata min, a kuma yi min ladabi shiyasa kika bullo min ta nan ba don kina so na ba? Na bi ladabin ki da gudu na tattake ba takalmi a kafa ta in dai da shi zaki yaudare ni yau Amani! Ya sake ta ya kama hanyar ficewa daga falon, ta karfin hali da bin karfin zuciya da kuma bravity na son kiyaye pride irin nasa domin hakika yanayin da fuskar ta ya koma yayi tsananin bashi tausayi, ya bar Amani a wani yanayi na rashin jin dadi da takurar zuciya wanda har a fuskar ta ya nuna nadama, ta cigaba da tsayuwa a wurin kamar an kafe ta. Kafin kuka mai tsananin karfi na nadama da dana sani ya kwace mata. Ta riga ta san it will not be easy for him and for her, ya yarda da ita, ya amince da tuban ta farat daya, amma bata zaci har haka ya rike abun a ran sa ba. Duk kuwa da cewa ta san yana da riko. Haka ta wuni sukuku a cikin gidan ta, cikin rashin jin dadin abinda ya faru tsakanin su ranar, it made her whole day black! At the same time, ta wuni tana takaicin dandani haukacin nan da Mukhtar ke yawan yi mata. Sai ta sakankance yau zata zama matar sa sai kawai ya fasa, yana nufin, this is his punishment a gare ta ko me? Ko ya fahimci tana son sa ne yanzu, tun kafin ta bayyana hakan da bakin ta gare shi, shi yasa yake faman yi mata dandani haukaci wanda yafi ramuwar gayya ci mata rai? Bayan wannan dan romance din na Mukhy da ya hana Amani barci daren yau bakidaya, tunda ya fita lokacin bata kara ganin sa ba sai washegari da safe a sassan Ummami. Don sanda ya dawo gidan ta riga ta yi barci, kuma bai yarda ya kwana a dakin ta ba. ya dai leko ya gan ganta tana barci ya wuce dakin sa. Ta shiga kenan domin ta gaishe da Ummami, sai ta samu Uwar da Dan suna magana, wato suna magana shi da Ummami amma maganar da ta dan ja hankalin ta, don ji tayi Ummami na gaya masa Sarki ya karba masa kyautar sadakoki wato kwarkwara guda biyu na yammata daga Sultanate of Damagaram. Amani ta yi sallama a shigifar Mowar Sarki, saidai kuma cikin rashin saa ta riga ta ji magana ta karshe da Ummamin ta gama fadi wa Maina yanzun, sai ta samu wuri gefen kafar Ummami ta zauna, kamar ta ji Ummami tana fadin Sarki ya ce an baiwa Maina kyautar Sadaka, Ummami din tana tambayar sa ko yana da bukatar amsar su? Yara ne masu matsakaitan shekaru yanmata, lafiyayyu. Ummami ta kara bayani. Kamar da gayya don Amani ta ji. Amani wadda ta ji zancen alhalin tana shigowa, amma bata gane sosai ba, don haka sai ta tambayi Ummami cikin rashin fahimta bayan ta samu wuri ta zauna a gefen ta. Ummami meye kuma Sa-daka? Ta tambaya ne ganin kamar Mukhy bai so ta ji abinda suke tattaunawa ba, ya zama kamar mara gaskiya daga shigowar ta, kuma fuskar sa ta ki karantuwa duk ya bi ya daure fuska. Sannan bai ce komai a kan kyautar da Ummamin ta ce an yi masa ba, sai faman hade giran sama dana kasa yake yi yana Harare-harare. Ummami ta ce cikin kwantar da murya. Sadaka yana nufin kwarkwara (concubines). A dan rikice Amani ta ce kwarkwara kuma Ummami? Me yasa aka bashi? Kwarkwara a wannan zamanin? Shi din ne ya ce a bashi ko shi ya ce yana son su? Amani ta jero tambayoyin cikin rudewa, rikicewa da da karkarwar murya, ba tare da ta san lokacin da ta jero su din ba, tsakanin Mukhy da Ummami, sai ka rasa wa ta jefawa tambayoyin, sai zare ido take a tsakanin su su biyun, tana jiran dayan su ya bata amsa. Amma duk suka yi mata shiru. Tsabar rudewa ta ma manta da wacece Ummami a gare ta. Haka ta kafawa Mukhtar ido cikin tuhuma da tashin hankali. Mukhtar sai ya tashi zai fice daga dakin, yana mamakin dalilin gigicewar ta da rikicewar ta haka don kawai an ce an bashi kwarkwara, ba dai zai ce Amani kishi take ba, saboda ya sha jin ana cewa sai da SO mata ke kishin mazajen su. Shi kuwa ai baida wannan gatan da wannan alfarmar a wajen Amina-Amani. Ta soma harzuka, tana kokarin komawa Amani Faskarin ta da kowa ya sani wadda bata barin ko ta kwana, ganin ta rasa mai bata amsa a cikin su. Gashi yana kokarin ficewa daga dakin ba tare da ya bata amsa ba. Ya Mukhy! Magana nake yi. Yaya zaka fita baka bani amsa ba? Kai kace a baka sadakan, me na yi maka? Am I not enough? Mukhy har ya kai bakin kofa zai fita, sai ya juyo ya dube ta da warning look a idanun sa, wato ta san a gaban wa take, da irin maganar da zata furta, da alama ta manta Ummami na wajen, ya ce cikin fushi. Are questioning or accusing me? Na yi kama da saan wasan ki da zaki jefa min query? To ban sani ba din, sai kin matse baki na zaki ji amsar tambayar taki. Yayi tsaki ya fice ya bar musu dakin. Rudewar da take ciki ya sa ta mancewa ko wacece Ummami gare ta, ta ce don Allah Ummami shi ya roka? Ko shi ya ce muku yana son sadaka? Ummami sai ta fito mata a mutum sak! Itama, ta dube ta ido cikin ido ta ce, Amani! Kin ga na lura tun zuwan ku kallon juna kuke kamar ba aure ne a tsakanin ku ba, alamu kuma sun nuna min tun a Nigeria ma haka kuke zaune, Mukhtar in ya je fada Baban sa ya lura baya iya komai sai damuwa, in an yi Magana sai yace naam wato sai an maimaita, shi kuma Mukhtar da kike gani, Yarima ne maana (Maina ne) Sarki mai jiran gado, shine wanda ake fatan ya gaji mahaifin sa a komai, bazai yiwu a kyale shi haka babu kulawar mata ba, ko da sadakan ne don samun nutsuwar sa. Shi yasa muka ga gara a bashi sadakan ko ba yawa kafin ku daidaita kan ku, da sabanin da ke tsakanin ku, ki sani Mukhtar Sarki ne, halittar su daban da ta sauran maza da kika sani a kan mata, kusan in ce miki, duk yawancin sarakuna. A shekarun Mukhtar yayi hakurin da ya zarce kima babu mace, gara kada a kure hakurin a bashi karin wasu matan na hutawa, su kuma yi muku hidima ke da shi har zuwa ku daidaita. Ko ita dakikiya ce zuwa yanzu ta fahimci me Ummami ke nufi yanzu, tunda dai ta shiga aji, ba wai bata taba shiga aji ba. Gata suke nufin zasu yi wa dan su, don sun gane bata bashi kulawar data dace mace ta baiwa mijin ta na auratayya. Kasa magana tayi, tayi kokarin rike hawayen ta bata bari sun zubo a gaban Ummami ba, don kada a ga rashin juriyar ta da raunin ta, sannan ta mike ta koma sassan su cikin sanyin jiki, sai Kuyangar ta mai kula da kitchen wato Ramu ce ta biyo ta da wayar ta, don a can dakin Ummami ta manto ta tsabar ta shiga rudu mai yawa, kuma Ummami bata sake bi ta kan ta ba, bayan bayanin da ta yi mata. Ta san ta ahada mata bom yadda take so ya tashi. Duk da sanyin AC mai karfi da ke aiki a falon ta. Amma Amani zufa take yi in ta tuno zancen nan. Idanun ta ba abunda suke hararo mata sai kyawawan yammata abzinawan usli tare da Mukhtar, cikin irin yanayin su da suka kasance jiya shi da ita, wannan alamari ba karamin daga hankalin Tafisu ya yi ba. Fisabilillah me yasa baa yi ma Mukhtar aure tun sanda ta tsane shi ba sai yanzu da ta soma saka shi a ran ta, ta soma tsara musu rayuwa ta soyayya mai tsafta a cikin zuciyar ta, kiris ya rage mata ta samu dama ta bayyana masa son da take masa? Mafarkin ta na haifa ma Ummami da Mai Diffa jikoki daga Mukhy ita kadai ran ta, ya tashi a banza Kenan muddin aka bashi wasu matan suka riga ta shiga jikin sa? A hankali ta soma sheshekar kuka, bata san cewa Mukhy yana cikin dakin da ta jingina da kofar sa ba. Sautin kukan ta ya dame shi, yana ci masa rai, don bilhaqqi take yin sa, hakan ya fiddo Mukhy daga dakin barcin nasa, ya bude kofar saura kadan ta fadi, don a jikin kofar ta jigina duka jikin ta, tunda ya baro su ita da Ummami gidan sa ya dawo, ya kwanta a daki ya rufe kan sa yana tunanin karbar tayin mahaifin sa ne ko aah? Ita bata ma san yana ciki ba, ya zo kan ta cikin fushi dama kuma ran sa a bace yake da abinda ta yi masa gaban Ummami mai kama da raini, cikin tsawa ya ce ke lafiya zaki zo ki daga min hankali da kuka haka ina kokarin samun barci? Me aka yi miki? Wani aka ce ya mutu? Koko rashin hankalin ki da kika saba? Amani ta daga jikakkun idanun ta ta galla masa hararar nan tata da ta dade bata yi masa irin ta ba. Sai yau da ji take gabadaya ta tsane shi bata ko son ganin shi a idon ta. Sannan ta juya tana share hawayen ta don bata so ya kama ta tana kukan nan ba, ko don tsira da sauran ajin ta, ta yi masa banza ta cigaba da share hawayen ta da habar laffayar ta. Ba gara mutuwa ba ta san kowanne mai rai mamaci ne. Wannan kuwa tashin hankali ne na har abada ya same ta, in har ta bari ya faru, kishiya daga zuwan ta gidan miji! Mijin ma Mukhy dan uwan ta da ta soma kallafawa a ran ta bada jimawa ba, wanda bata kwatantashi da komai a yanzu, son sa take bilhaqqi. Mukhtar ya sassauta murya ganin cewa fada da daure fuska bazasuyi tasiri a gare ta ba, har ya samu ta gaya masa kukan me take yi, ya ce pls Amani! Na hadaki da Allah ki yi shiru, ki gaya min abinda ya yi sanadin wannan kukan babu gaira babu dalili. Don sosai ta firgita shi, don kukan nata ba na wasa bane yau, ko na sakarci irin wanda ta saba a yawancin lokuta, aah wannan kuka ne mai fita daga kasan zuciyar matar da ke tsananin son mijin ta, kuma dare daya ya zo ba zato ya ce zai mata kishiyoyi, kuka ne take yi bilhaqqi, baka da zuci, mai nuna tsananin kishin ta akan abinda take so da zuciya daya. A matukar fusace Amani ta dago, idanun ta sun yi jawur, hawaye ya hade da majina ta ce ina rokon ka Allah Annabi ka bace min da gani Ya Mukhy, sabida bana son ganin fuskar ka, ka tafi gun sadakan da ka je ka roka a baka sabida na gaza, ka tambaye su kukan me nake yi, tunda kai baka da hakuri, baka da bin komai a sannu. Son da na samu kaina da fara yi maka, ina rokon Allah ya sa ya koma inda ya fito, kada Allah ya bar ni da koshin wahala. Mukhtar ya hadiye mamakin sa da dariyar data zo masa nan take, sai yanzu ya gane musabbabin kukan, wanda bai taba ganin Amani na yin mai zafi da cin ran sa ba, ya ce. Tafisu yau ni kike kira mara hakuri? Shin a duniya akwai miji mai hakuri ma iri na? Ni da aka kira bawan Alhaji, mara galihu, mara nasaba kai har mai kama da shegu an ce min kuma na yi hakuri na Manzon Allah, ban taba kallon ki da kalaman bakin ki ba, sai matsayin diyar ubangida na mai daraja a idanu na. Ni tsintacce a bola, ke komai ma na batanci da rashin galihu ni ne. To ki gayamin ya kike so in yi idan ban karbi wadanda zasu so ni a yadda nake ba? Ke da yake yar Qaruna ce kin ki yarda mu daidaita kan mu har yanzu, sabida baki son yaron Alhaji, ni kuma iyaye na na na son ganin yaya na da wuri, Maimartaba kuma na son gani na cikin nutsuwar data dace da kowanne dan gata. Kullum in naje fada bani da nutsuwa in na ga babu yayan Mai ko daya bayan ni, ina son samun yara wa iyaye na yara masu yawa, tun da su Allah bai basu yaya masu yawa ba. Ki fada min yanzu da lafiya ta da komai, an yi mana aure ya kusa rufa watanni nawa amma har yanzu ban san irin nawa ba, Tafisu zina kike so in je in yi in ban karbi kyautar sadakoki ba? Ko kuma durkusa miki zan yi in roki alfaramr ki so ni, ki kuma bani hakki na? Ai gara sa-dakan, ko ba su nake wa Son da nake yi miki ba, a kalla zan dinga rage zafin da kike kunsa min dasu. Amani ta zuba masa jikakkun idanun ta da ke zuba cikin tashin hankali, bata ko kyaftawa, bata taba zaton Mukhtar zai iya wadannan maganganun ba, Mukhy mai kawaici da kamewa. Mukhy ya kalle ta yana murmushin tura haushi, ya kara guma mata da cewa. Kuma banda abun ki, banda shirme irin naki Sadaka ai ba matan aure bane na hakika a wurin sarakuna, da zaki yi kishi da su, kada ki damu ababen hutawa ne ga sarakuna kadai. Amani na neman zaucewa yanzu ta ce au, bama daya bane har nawa ne ka roko? Yace na roka ko aka bani kyauta? Su biyu ne kawai aka kawomin daga Sultanate of Damagaram. A wannan gabar Amani ta kusa dawowa tsohuwar Amanin ta yanzu, domin jijiyoyin rashin kunya sun mimmike, tsigar jikin ta har tashi take, manyan idanun ta suka firfito waje, ta ce. Mukhtar! To kai din wane irin jarababbe ne da zaa kawo maka mata biyu a lokaci daya? Plus me, three? Kwatakwata shekarun ka nawa?. Mukhtar ya buda hannuwa irin na (ba matsalar ki bace) ya ce har goma in ina so zan hada a lokaci guda, in kika bani dama ko yanzu sai ki ga irin jarabar tawa. Ya soma tunkaro ta, idanuwan sa na nuna yau ba mai raba shi da Amani sai Allah yana balle botirin wuya da links din hannun farar shaddar jikin shi, ta ce. Allah ya suwake in hada miji da wasu, wallahi sai ka maida ni gidan Uba na, kafin ka karbo su, ai ba kai kadai ne dan gata ba, nima nan da kake gani na TAFISU ce har yanzu har gobe, bar ganin na yi sanyi, ina nan a Tafisu na da ka sani in aka tabo ni. In banda mugunta na taba cewa kada ka kusance ni? Ko kuwa ba kai kake dakatawa don radin kan ka ba da son saka ni a damuwa Ya Mukhy? Za dai ka karba ne don ka sanya ni a bacin rai, don ka ga na fara son ka Mukhtar ba don komai ba! To idan so cuta ne to hakuri magani ne! na barwa sadakoki kai, ka maida ni inda ka dauko ni gobe goben nan. Ta rushe da kuka, ta ce wallahi Katsina zan koma wajen iyaye na, sai dai ka zaba ko ni ko sadakoki, ai da aka bar ni a nan ba wai an ce gata na ya kare bane. Mukhy, yau ji yayi kamar yayi juyi a gaban ta don dadi, murmushin da ke kan fuskar sa sai karuwa yake, for the first time ya fahimci Amani ta fara son sa don radin kan ta, ba abinda yafi dadi ga da namiji irin ya fahimci matar sa na tsananin kishin sa irin haka, yau ga Tafisu na kukan kishi a kan sa kamar ta shide. Niyyar sa da farko shine ya rungume ta, ya lallashe ta ya sumbace ta son ran sa daga nan koma me zai faru ya faru yau, in yaso gobe yace a bar sadakokin baya so, ya yi amfani da wannan damar ya gaya mata cewa son da yake mata mai yawa ne da ya isa cike gurbin mata hudu! Ba wata mace da zai iya yi wa irin son da yake mata. Amma ko me Mukhtar ya tuna? Sai ya fasa rungumeta din da yayi niyya ko ya lallashe ta, ya sa kai zai wuce ta gaban ta ba tare da ya tsinka mata ba, amma a ran sa yana mamaki yana karawa, wato duk shakiyanci ne abun nata, Amani ta san SO. Yau wace irin ranar saa ce a gare shi? Amani ganin zai tafi ya bar ta a wurin, wato bashi da lokacin sauraron ta, don bai dauke ta mai cikakken hankali ba, bata san sanda ta sha gaban sa ba. Ba inda zaka je Mukhy, na rantse sai ka zaba ko ni ko sa-dakoki. Kai tsaye Mukhtar ya wani irin dago, ya zuba mata fusatattun idanun nan nasa masu kama da an diga musu zaiba, ya ce bani hanya in wuce kafin in yi huce kan dami a kan ki, me zaki iya idan na ce na zabi sadakokin, tunda zasu bani abinda Amani-Tafisu bata bani, zasu so ni su kaunace ni, son da Amani-Tafisu bata yi min, zasu so ni duk rashin asali na da rashin kowa nawa. Amma Amani fa? Wadda kyawun Mukhy da ake fadi bai taba bugar da ita ta So shi ba, saboda Mukhtar bai isa komai ba a idanun ta tunda ni hadimin gidan su ne! Amani wadda da ta aure ni, ni da bani da asali, kuma ba dan kowa bane gara ta auri tsohon mai kudi saan Baban ta Alhaji Sadisu Talle? Ni kuwa me zai hana ni karbar sadaka, idan har ba maza na rako duniya ba kamar yadda Tafisu ta rako mata? Kamar wani wani wanda bai san gatan iyaye ba irin wanda Amani ke tutiya da shi a koda yaushe? Kullum ki saka a ran ki a wurin Alhaji ne kadai kike amsa sunan TAFISU, amma baa wurin Mukhtar da sauran mutane ba, tun da ni ban yarda Amani ta fi sauran mata komai ba sai iya sai rashin kunya da rashin daa, duk halin banza shi ta fi su iyawa!. Maganganun sa sun ratsa ta, domin ta fahimci ya fidda tsatsar duka maganganun ta ne dake kwance a ran sa, duk tsayin lokacin data yi masa su, tana fatan tunda ya furta su yanzu, bayan ta jima da gasa masa su, daga yau ya samu sanyin su daga ran sa, ko ta samu su bar zuciyar sa gabadaya. Ta sunkuyar da kai. Guilty conscience na aikin sa ta koina yana nunawa a fuskar ta. Jikin ta duk yayi dan sanyi musamman da ta ji a jikin ta Mukhy ya kafe ta da kyawawan idanun sa, yana karantar reactions din nata, amma Amani-Amani ce har gobe, sai in baka tabo ta ba, masu iya Magana suka ce. A bar hali a ci me? to hakan yake ga Amani yau ma. Domin kuwa share tasirin maganganun sa ta yi gefe ko ince ta hadiye tasirin da suka yi mata ta ce. Tunda ban fi su ba, shine na hakura na bar musu Mukhtar din, tunda a duniyar ka mutum ba ya taba yin kuskure ya dawo ya tuba. Ko mai yasa? Ita kan ta Amani bata sani ba. Amma ta san bata taba jin faduwa da karaya sun same ta ba irin yau, duk da dai Mukhy yau cikin subutar baki yayi gangancin gaya mata YANA SON TA, son da baya iya kwatanta shi dana kowacce mace. Sai hawaye ya kara tsinkewa Amani, ji take gabadaya yau tata ta kare. Ta samu kanta kawai da kifa kai a kirjin Mukhtar ta shiga sakin kuka wiwi, tana rera shi cikin zaki muryar ta kamar sarewa. Ba kasafai kukan Amani ke bashi tausayi ba, saboda ya riga ya san ita zuma ce sai da wuta, ta hakan ne kawai zai iya rama kadan daga abinda ta dade tana yi masa, hakika Amani ta dade tana cutar da shi da kalaman fatar bakin ta, yana shanyewa yana hadiyewa albarkar mahaifin ta. Amma ganin irin karayar data same ta yau, ga ta kuma kwance akan kirjin sa sai ya ji shima rauni ya shige shi, ya kuma san lallai dagaske Amani ta canza, ko a ce ta fara canzawa, domin a irin zafin kan ta, babu karaya ko kadan a tare da ita cikin tsarin ta. A ajandar halayen ta duka babu given up, ba zai ce saboda sa-daka bane ta fara canzawa, ya dade yana karantar ta, ya san tun kafin maganar sadaka ta samu canji a kan sa a zuciyar ta, haka ya san baka taba kishin mijin da baka so har haka. Zame ta yayi daga jikin sa cikin karfin hali, domin ta saka masa kasala ba yar kadan ba, ya juya zai fita, cikin mutuwar jiki, ba tare da ya kara cewa komai ba. Amani ta sake ruko shi da karfi, murya na karkarwa ta ce, Mukhy! Will you believe me, if I said I LOVE YOU? Sai ya juyo da dukkan idanun sa yana mata wani kallo, kamar na warning din ta daina rike shi, amma kuma ya firgita da jin kalaman, domin sun zo masa a bazata, a cikin idanun sa soyayya da kaunar ta ne tsantsa, haka nata jikakkun idanun abinda ke kwance cikin su kenan, kallon da sukema juna ya shiga tado wata irin shaawar juna ta shiga tarnaki a zukatan su, ta shiga ruruwa tun daga kwakwalen su har yatsar kafafun su, in bai yi kuskure ba kamar yau ya taba jin sunan sa a bakin ta. A yanayin da fuskar ta ta koma yanzu, kamar ta rasa duk wani gatan ta sai shi kadai, a irin kallon data ke masa yanzu, kamar shi kadai ya rage mata a fadin duniya, hawaye na zubar mata wasu na korar wasu ta zame daga jikin sa ta durkusa masa, ta rike kafafun shi tanaci gaba da kukan sosai, tana rokon sa da murya mai ban tausayi ya yi hakuri da duka halayen ta, daga yau ta yi alkawari ta daina! Ya Mukhy, na yarda ka yi min komai don ka huce hali na na banza, na yarda hali na da yawa mara kyau ne, na yarda zan canza daga Amanin da baka so, zuwa Aminar da kake so, na yarda zan zama matar Maina Mukhtar daga daren yau, abokiyar rayuwar sa ta har abada kuma abar hutawar sa karkashin inuwar aure. Amma ka yi min rai! Banda kishiya ko sadaka, saboda bana son su, zuciyata baza ta iya dauka ba Ya Mukhy. Saboda bazan iya sharing Mukhy dina da wasu matan ba. Hakan zai iya manna min ciwon hauka da ciwon damuwa. Ya Mukhy don Allah ka yi hakuri, ka yi min rai, kada ka karba! Kaga ni tun fil azal ba Maina na aura ba Mukhtar na aura, ban san da wadannan traditions din naku ba, na roke ka kada ka bari kokarin tabbatar da culture and tradition na gidan ku da basu zama dole ba a addidni su rusa kyakkyawar dangantakar mu, da rayuwar dana yi mana tanadi daga yau. Amani ta russuna ta sumbaci babban yatsan kafar sa cikin roko, duk hawayen idon ta ya koma diga akan kafar sa. Zuwa yanzun kam hes touched, extremely touched! Kuma ya yarda abinda take fada daga zuciyar ta yake fitowa, ba daga fatar bakin ta ba, mamakin hakan da birbishin tausayin da so ke kimsa masa, suka taru suka soma rinjayar dakiyar sa da pretending din sa, suka hana shi magana suka hana shi motsin kirki, ita kuma ta kai sumba yatsan kafafun shi, Mukhtar yayi mutuwar tsaye, amma dai yana gargadin kan sa a kan yayi taka-tsa-tsan da nadamar Amani don akwai gaggawa a cikin ta, kuma sadaka da bata so ne sila, yaushe har Amani ta fara son sa irin haka, da har ta shirya rayuwa da shi haka? Komai aka ce masa mace zata iya, in dai a kan kada a yi mata kishiya ne yau kam zai iya yarda. Mukhtar ya san tsakanin sa da Ubangiji yana matukar son Amani, halayen ta da dabiun ta ne dama baya so. Ganin ta tana neman shidewa a gaban sa yau a kan kishin kada wasu matan su rabe shi ya yi matukar tasiri a tare da shi ba kadan ba, ya kara masa son ta da jin tausayin ta, ya rage masa kuzarin muzanta mata. Duk da haka wani devilish bangare na zuciyar sa bai yarda da ingancin nadamar tata da soyayyar tata ba, ya fi dangana yanayin ta na yau da KISHI. Amma a irin kukan da take yi rike da kafafun sa harda sumbata, sai ta soma saka masa rauni, wato ta soma samun weakness din sa, sabida baya son ganin kukan mace balle matar sa AMANI-AMANAR ALHAJI. Domin ji yake sumbar da take ma yatsun sa na neman sumar da shi daga tsaye, duk wasu tsofaffin feelings din sa a kan Amani na sake dawowa sabbi kar, suna sake sakin sabuwar yabanya ta korran ganyayyaki a fadin zuciyar sa. Yau Ga TAFISU a kwance a kan kafar sa, tana neman gafara da jin kan sa, daga soyayyar sa da kin kishiya, a irin yanayin da yau ko me ya nema zai samu har mafiyin sa, ba tare da ya yi hurting feeling din ta ba. Amma duk da haka taurine rai irin nasa ya ki bari ya dago ta, yana gayawa kan sa kada ya yarda ya bada kai yanzu, sai ya tabbatar da ingancin wannan nadamar tata da canzawar tata, aka ce kowa ya tuba don wuya ba lada, duk da cewa a cikin idanun ta ya ga nadama da soyayya tsantsa, sai dai ya san wasu mata ko basa son miji suna kishin sa, tunda aure ne a tsakanin su. Sai kawai ya janye kafafun sa daga rikon ta a hankali, cikin karfin hali ya taka ya fice ya bar ta a falon, zuciyar sa kamar ta fashe da son Tafisu, da ke kara tumbatsa a kowanne sako na cikin ta. Yana gayawa kan sa Amani Zuma ce sai da wuta, gara ya kara rike shaawar sa a kan ta komai karfin ta, zuwa lokacin da ya dace da ya amshi nadamar tata, amma ba yanzu da tsoron sadaka ne yafi rinjaye a ran ta ba, ba soyayyar sa ba (a ganin sa). **** **** **** AMANI A wajen da Mukhy ya bar ta ta ci kukan ta ta koshi, tana gayawa kan ta Mukhtar baya ta tata yanzu tunda ya zo cikin gatan sa, ko dama can yaya lafiyar Kura? Dubi dai irin lallashi da roko da bada kan ta data yi amma yayi funfurus! Itama kawai gara ta koyawa zuciyar ta hakuri da shi ta yi zaman Ummami cikin gidan nan, tunda uwar ta ce ko ba Mukhtar a tsakani, tunda in tace ta barwa sadakoki Mukhtar din, ita a maida ta Katsina ba sauraron ta zaayi ba, ba kuma maida ta zaa yin ba, ta san ta shigo gidannan kenan har abada ba saki ba yaji, sunan auren nan mutuka raba in ji Ummami, zata koyawa kan ta juriya ta rabu da shi ya auro ko goma ne ta koma gefe ta yi kallon su. Tunda shi baya amsar tuban dan adam, baa kuskure a nemi gyarawa ya yarda ya bada second chance, Allah da kan sa mai afuwa ne, kuma yana son bayin sa masu afuwa, yana amsar tuban bayin sa idan sun yi repenting, sun tsarkake zukatan su daga sake aikata wannan kuskure, then why not him? Wanda shima ba sama yake da aikata kuskure ba, tunda ba maasumi bane ba kuma Annabi b. Ai bari kawai ta nuna masa har gobe tana nan a Tafisun ta, ajin ta bai tsinke ba, halin ta na banza na girman kai da raina mutane da wulakanta su kawai ta bari. Tana wannan sake-saken tana hadiyar zuciya sabida kukan data ci, daga bisani ta wuce uwar dakin ta ta kwanta bisa gado, da tunanin Mukhy barcin wahala ya sure ta a wajen. Cikin barcin ta, tsabar yadda ta saka Mukhy a ran ta, da son ya lallashe ta koda da kalaman fatar baki ne, amma ya saka kafa ya fice ya yi banza da kukan ta, ba tare da ya ce ya fasa amsar sadakokin da aka yi masa tayi ba wadanda tunanin su kadai neman haukatata yake. Ta tsinci kan ta a duniyar mafarkin ta tare da MOUKHTAR ISSOUFFOU MASSAOUDOU cikin wani nauI na soyayyar auratayya mai shiga jiki da zuciya, tare da dan Issouffou jikan Massaoudou Balaraben Diffa mai abun mamaki, ta gan su cikin mafarkin Mukhtar yana sumbatar ta iya sumbata, yana juya ta duk ta yadda yake so, daga hakan sai kawai ta ji ya dauke ta suna tafiya zuwa turakar sa, yana rada mata cikin kunnuwan ta cewa. Tafisu kin fi sauran mata a zuciya ta!. Irin mafarkin da in dan adam yana yi baya so ko sauro ya cije shi ya farka. Sai kawai Amani taji muryar Baba Sahura a cikin kwanyar ta. Uwa Uwa, Uwa, ke wai lafiya kike barci haka a kasa, ko fadowa kika yi daga gadon, da baki na faman motsi kamar kina cin tsutsa, ga hawaye kina faman yi, kuma a bakin kofar daki kamar wata wadda uwa ta yi wa baki? Sai lokacin ta ankara wai ashe duk wannan a mafarki ne, kenan ita tata soyayyar bata zo da wasa ba, Mukhtar har a cikin mafarki neman zautata yake don ya ga ta gama mika wuya ga soyayyar sa. Ta mike zaune, bata san yaushe ta fado daga gadon har ta mirgina kofar daki ba, ita dai ta gan su suna mirginawa a cikin korran ciyayi ita da Mukkhy, sannan ta dubi Baba Sahura, ta tabbatar mafarki take hakan bai faru ba, Mukhtar tunda yasa kafa ya fice bai dawo gidan bama, ta kama Babar ta Sahura ta rungume jikin ta na kyarma, sai ta fashe da kuka, ta ce Baba Sahura wai kin ji sadaka zaa bashi? Sahura ta ce, Au! Shine kike neman haukata kan ki Uwa? Yo in dai a kan zancen sadaka ne Uban ki ma ya auri mata yana saki sun fi goma, shi a kan me zaki hana shi cika alada? Gaki ke ban ga alamar kina masa wani amfani ba sai shegen kaudi da rashin kunya da kika fi kowacce mace iyawa. **** **** ****