❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ' Wannan labarin kirkiro shi na yi , duk yadda ya yi kama da labarin wata ko wani babu hannu na a ciki , ban yarda ba wani ya sauya min ko da kalma daya ce da ga cikin aiki na , yadda mu ka fara shi cikin Amincin Allah ina fatan mu ida shi a haka ' ❤ Wannan page naku ne massoya na ❤ Allah ya bar mu tare forever and ever BOOK 1 ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ [29/06/2024] PAGE 1 ❤🔥 BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM NIGERIA ( KANO STATE ) Wata kyakyawar yarinya ce ta ke tafiya a hankali saman titi ta na tafe ta Na wassa , a shekaru ba za ta wuce 14 years ba Kyakyawar ce gaskia jinin haussa Fulani , skin din ta chocolate , ta na da shape kamar coca cola duk da karancin shekarun ta breast din ta a cike ya ke kuma a tsatsaye ga M Skuma hips , ta na dara daren idanu barare kal kamar madara , kwayar idanun ta black ce har wani kyali ta ke , ga dogon hanci mai kyau , ga dan karamin bakin ta , lips din ta pink colour yarinyar ta hadu kamar ita ta yi kan ta Sanye ta ke cikin wando dark brown da riga zuwa guyiwa egg white , ta daura dan karamin hijab zuwa kirji shi ma egg white, ta na rataye da Bag yar karama a baya , ga Dukan allamu da ga school ta ke Ta na tafe ta na wasu juye² ta na yar waka da ga gani kassan har yanzu ta na dawainiya da yarinta Sai da ta karasso bakin hanya za ta tsalaka titi ta tsaya ta na dube dube Cen ta hango wani makaho a daya gefen titin , ya na sanye da bakin glass ya na rike da sandar shi ya na tafiya cikin konciyar hankali Makahon kyakyawan gaske ne , fari kal da shi me zubin larabawa , ya na sanye da wandon jeans baki da riga fara , kafar shi na sanye cikin boot bakake su ma , ya hadu over , ya na da dogon hanci da dan karamin baki lips din red colour kamar jini na sama ya yi wani shape kamar heart , ga wani kontancen saje a gefe da gefen fuskar shi , gashin kan shi baki kirin da shi so smooth ya zubo mishi bayan keya sai wasu sirarren da su ka zubo mishi a gaban goshi , ya na da tsayi ga murdaden jiki kamar dan dambe , damtsen shi a murde su ke kamar za su fassa hannun rigar , ga wani kyakyawan gashi konce luff saman hannayan shi , idan ka kare face din shi kallo da kyau ya na da wani dan karamin zane baki geffen wuyan shi na dama amma gashin shi ya rufe shi ba a iya ganin shi da kyau , zannen ya fito kamar CROWN an dasa misi wata SWORD a tsakiya Tun da ta hango shi ta saki wani kyawatencen murmushi Da sauri ta kali damar ta , ta kali hagun ta , ta ga babu motoci sannan ta fara tafiya da dan sauri ta tsalaka titi Da gudu ta bi bayan shi Sai da ta zo dab da shi ta tsaya geffen shi ,cikin wata kyakyawar murya mai dadi ta ce " Yaya Zayd " Bai ce da ita komai ba su ka ci gaba da tafiya a jere Sai da su ka yi nisa cikin tafiyar su sannan ta kale shi ta ce " Yaya Zayd gida za ke je ko kuma wajen Abba za ka wuce " Jinjina mata kai ba tare da ya ce mata komai ba Haka su ka ci gaba da tafiya ta na zuba mishi surutu shi kuma ya na sauraron ta , sai in ta yi mishi tambaya sai ya girgiza mata kai ko ya jingina mata Sai da su ka iso bakin kofar wani gida , gida ne madaidaici an mishi shafen siminti da kofar gidan Light green, gida ne irin na ma su hali dan bai yi kama da gidan wadan da ci da sha ke yi musu wuya Su na isowa kofar gidan su ka tsaya a tare kamar ya san sun iso Juyo wa ta yi ta kaleshi ta ce " Yaya Zayd ni zan shiga ciki nagode da rakiya " ta kai karchen ta na murmushi Jinjina mata kai kawai ya yi , ya fara takawa ya yi gaba abun sa Ya na barin wajen ita ma ta juya ta shiga cikin gidan ta na sallama Wata mace ce ta zaune tsakiyar gidan saman tabarma , ta na tsintsar wake A hankali ta dago kan ta kali kofar shigowa ta na amsa sallamar , ta na ganin yarinyar ta saki dan karamin murmushi ta ce " Inaya har ki dawo , ina ki ka baro Nesrine " Takowa yarinyar ta yi ta zo geffen ta ta zauna ta cire jakar ta ta ajiye gefe sannan ta kama tray din hannun ta ta na fadin " mun riga su fitowa shi ya sa na tafowa ta " Murmushi matar ta yi kafin ta ce " shikenan tashi ki je ki cire kayan ki , ki watsa ruwa kin debo rana " Jinjina mata kai ta yi kafin ta ce " toh mama , amma bara na ida tsintse waken sai na tafi " Matse fuska mama ta yi ta kai hannu ta karbi tray din ta na fadin " Inaya tashi ki je na ce ko " Dan murmushi ta yi kafin ta kai dan lips din ta saitin kumatun ta, ta sumbata kafin ta mike ta dauki jakar ta ta wuce dakin da ke fuskantar su Ta na shiga dakin mama ta ji ana sallama Murmushi ta saki ta na amsa sallamar kafin ta ce " Nesrine ina ki ka tsaya haka " Wata kyakyawar budurwa ce ta shigo cikin gidan ta na sanye da uniform din school irin da Inaya, skin din ta chocolate ita ma kamanin ta sak irin na Inaya ba dan ta fi ta dan jiki ba da shekaru sai ayi musu daukar Twins , a killa a shekaru ta kai 17 zuwa 18 Geffen mama ta zo ta zauna ta kontar da kan ta saman kafadar ta sannan ta lumshe idanun ta ta ce " mama ni fa na gaji da zuwa makarantar nan, dubi duk jiki na ciwo " " karbi nan ja'ira kawai, in baki je makarantar ba ki yi mi ko aure ki ke so na yi miki, shikenan zan ce ma Zayd ya ka kudin sadakin ki tun da na lura ya na son ki " mama ta fada ta na ajiye tray din geffen ta , sannan ta yi kokarin tashi Da sauri Nesrine ta ce " a'a wlh mama, me zan yi da makaho kuma kurma, ai ba maza su ka kare duniya ba " Dariya maman ta yi ta na shirin magana su ka jiyo muryar Inaya ta na fadin " Ai ko cikin mazan yaya Zayd na daban ne , ba dan Nakassar da Allah ya jarabe shi da ita, da wlh ko yar aikin shi baki kai matsayin zama ba " ta kai karchen ta murguna mata baki Hararrar ta Nesrine ta yi kafin ta kali mama ta ce " mama kun gani ko, ita fa ta ke tsokana ta sai in na dake ta, ku ga laifi na " " Ni ai gaskia na fada, kin san dama an ce gaskia daci gare ta " ta fada ta kama hanyar toilet " mamaaaaa" Nesrine ta fada ta na jan sunnan Kallon ta mama ta yi kafin ta ce " kin ga ko kar ki kuskura ki daura hannu saman ta kin san halin baban na ku da Abdoul ba su son abun da ya taba autar su dan haka kyale ta , ai kuma laifin ki ne kin fi kowa sanin yadda ta ke ji da Zayd shi ne za ki wani bata mishi sunna " Kumbure fuska ta yi ta na fadin " amma mama haka zan zuba mata ido ta min magana yadda ta ga dama na fa girme ta sh........" Mama ta katse ta de cewa " to sai ki kama girman ki ko ki kyale ta " Ta na gama fadar haka ta juya ta shiga kitchen Tsaki Nesrine ta yi kafin ta mike ta dauki jakar ta, ta wuce dakin da Inaya ta fito Daki ne dan madaidaici sai yar katifar su da ke karchen dakin, da closet din kayan su ya na fuskantar katifar sai yar karamar dressing mirror Ta na shiga ta Fada saman gadon ta yi rub da ciki ko hijabin jikin ta ba ta cire ba A hankali ta fara sakin kuka kassa kassa ( ko kukan me ta ke oho 🤔🤷‍♀️) Ta na cikin kukan nata Inaya ta shigo dakin ta na sanye da hijab zuwa guyiwa Ta na jin shigowar ta ta yi saurin kauda kan ta gefe ta saka kanta tsakanin pillow ta na goge hawayen ta A hankali Inaya ta ke takowa cikin dakin ta na dan wake waken ta , ta wuce wajen closet din su ta bude ta dauki wata gown mara nauyi launin blue ta saka sannan ta dauki hijabin ta ta saka ta dauki daddumar ta, ta koma bakin gadon ta shinfida Kallon Nesrine ta yi kafin ta ce " Nesrine tashi ki je ki yi Alwalla lokacin sallat ya yi " Shiru Nesrine ba ta amsa mata ba, ko motsi ba ta yi ba Dan tsaki Inaya ta ja ta na kunbure fuska ta ce " kar ki tashi in kin ga dama " Ta na gama fadar haka ta fara gabatar da sallar ta Nesrine ta na jin ta fara sallat ta yi sauri ta mike ta koma gaban closet ta tsaya ta bawa Inaya baya Da sauri sauri ta cire hijabin jikin ta ta cire uniform din ta ta daura wata towel fara sannan ta saka hijabin ta , ta yi sauri ta fice dakin ta wuce toilet After some minutes ta shigo cikin dakin Lokacin har Inaya ta Kamala sallar ta , ta na zaune saman gadon su ta jingina a bayan gadon ta na rike da littafin ta ta na karantawa Da sallama ta shigo dakin ta na sunkuyar da kai Ba ta ce da Inaya komai ba ta wuce wajen closet din su , itama ta saka gown irin ta Inaya sai dai ta ta launin Red ce Bayan ta saka rigar ta dauki hijab ita ma ta saka ta dauki daddumar ta Inda Inaya ta shinfida ta ta , nan ta shinfida ita ma sannan ta gabatar da sallar ta Ta na tsaka da sallar ta mama ta shigo dakin ta na sallama Dago kan ta Inaya ta yi ta na amsa mata sallamar ta " Yawwa Inaya, dan Allah tasso ki je kiyo min cepane yaran nan sun koma sangayar su " ta na gama fadar haka ta sa kai ta juya Da sauri Inaya ta diro da ga saman gadon ta na murmushi dan dama na son fita amma ba hali A hanzarce ta saka hijabin ta, ta saka dan takalmin ta ta fito A harabar gidan ta isko mama cikin yar runfar da ke bakin kofar dakin ta , ta na zaune saman yar karamar kujera Gaban ta ta karaso ta tsuguna ta na fadin " gani mama " Dan murmushi mama ta yi kafin ta ce " to malama an ji za a fita shi ne ki ka tasso da sauri ko " Sunkuyar da kai ta yi ta na murmushi dan mama ta gano ta Dubu dayan da ke cikin hannun ta, ta mika mata ta ce " shikenan karbi ki sayo min albassa da timatir na dari biyar biyar ki yi sauri kin ga fa rana ta yi kar ki tsaya wannan shirmen na ki " Yar dariya ta yi kafin ta ce " mama ni fa ba na tsaya wa shirme kin ga kullum sai na riga Nesrine isowa gida " Ta na gama fadar haka ta tashi ta nufi hanyar fita gidan Da kallo mama ta bi ta har ta fita gidan sannan ta ce " kai ni wannan yarinyar Allah ka shirya min ita, a ce ki na girma ki na cin kassa " Inaya kuma ta na fita gidan ta fara wake waken da ta saba yi A hankali ta ke tafiyar har ta karaso wajen wata bishiya Cen ta hango wani datijo zaune kassan inuwar bishiyar ga wasu kananan yara zagaye da shi su na rike da allo su na karatu Tun da ta hango shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta fara takowa da sauri ta tinkaro bishiyar ta na sallama A hankali ya dago kai ya na amsa mata sallamar ta Wani dan murmushi ya saki kadan kafin ya ce " Auta me kuma ki ke yi nan " Riko hanayan ta baya ta yi ta na yar jujuyawa cikin shagwaba ta ce " mama ce ta aike ni cepane " " shikenan yi sauri ki je, kin ga rana ta yi " ya fada ya na kokarin mike wa tsaye Jinjina mishi kai kawai ta yi ta na murmushi ta wucewar ta Ta na barin wajen ya kali yaran ya ce da su " ku ci gaba da karatu ina zuwa " " Toh malam " su ka fada a tare A hankali ya ke tafiyar shi ya na sanye da manyan kaya , ka na ganin ka san wannan datijon ya na cike da haiba da mutunci Ya yi tafiya wajen minti biyar kafin ya iso gidan da Inaya ta fito Bakin shi da sallama ya shigo cikin gidan Mama ta na zaune inda Inaya ta baro ta ba ta motsa ba Ta na ganin shi ta saki murmushi ta ce " sannu da zuwa Abban Abdoul " Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce " Amina ba na ce miki ki bar barin yarin yar nan ta na fita ba " Sunkuyar da kai mama ta yi kafin ta ce " yi hakouri malam Nesrine ce ta na sallat shi ne na aike ta " " Amina da sai ki bari ta Kamala, kin fi kowa sanin hatsarin da ke bibiyar Inaya cikin rayuwar ta tun shigowar ta duniya me a ba mu fuskanta ba , a dalilin ta mu ka baro Kaduna saboda barazanar da a ke mana , yanzu in su ka samu labarin mu na nan kin san fa baza mu tsira ba , ni ko makarantar da su ke zuwa dan kin matsa ne na hakura na bar ta, ta na tafiya , ba dan Zayd ya na bibiyar ta ba ban san abun da zai faru da ita ba , dan Allah ki bar barin ta na fita wlh bazan iya jure rashin ta ba " ya fada cikin rauni zuciya ( GA DUKAN ALLAMU AKWAI WANI BOYAYEN AL'AMARI A TATARE DA AHALIN GA 🤔🤔 ) Wasu hawaye ne su ka zubo mata ta cikin zafin zuciya ta ce " yanzu dan Allah malam haka za mu ida rayuwar mu kullum mu na gudu , mi mu ka yi musu da za su ringa bibiyar mu haka , kawai dan ka hana ma d'an su auren Inaya shi ne su ke neman su kashe mana ita, meye laifin ta a cikin wannan abun yarinya karama su na neman su lalata mana rayuwar ta " ta kai karchen kuka na kubce mata Da sauri ta juya ta koma cikin dakin ta Ajiyar zuciya Abba ya sauke kafin ya bi bayan ta shi ma ya shiga dakin ya na sallama Bakin gadon ya isko ta zaune ta na kukan ta Geffen ta ya je ya zauna ya kai hannu shi bayan ta ya na dan bubugawa ya ce " kiyi hakuri Amina, in sha Allah ba abun da zai faru da ita dan na mallaka ta a hannun wanda zai kulla min da ita fiye da mu " Dago kai ta yi ta kale shi cikin kuka ta ce " ban gane ba malam, wa ka mallakawa ita kuma me ka ke nufi " Hannun shi ya kai ya goge hawayen ta sannan ya mike tsaye ya ce " in sha Allah in lokaci ya yi za ki san komai " Ya na gama fadar haka ya juya ya bar dakin Ya na fitowa harabar gidan Inaya ta shigo ta na sallama hannun ta rike da leda baka sai murmushi ta ke gwanin ban sha'awa Ya na ganin ta ya saki murmushi shi ya ce " Auta har kin dawo " Jinjina mishi kai kawai ta yi ta ci gaba da takawa ta shiga kitchen Ta na shiga shi ma ya fara takawa ya nufi hanyar fita gidan Ya na fitowa waje ya isko Zayd ya na tsaye bakin kofar gidan ya jingina da bangon gidan ya na rike da sandar shi ya dan daga kan shi ya na kallon gaban shi Abba na ganin shi ya saki murmushi ya ce " A Zayd ashe tare ku ke " Jinjina mishi kai Zayd ya yi sannan ya juya ya fara takawa Murmushi Abba ya yi ya girgiza kan shi ya bi bayan shi su ka ci gaba da tafiya a tare Sai da su ka karaso kofar wani gida dan nesa kadan da na Abba su ka tsaya a tare sannan Abba ya kale shi ya ce " Zayd za ka zo cin abincin da dadare dai ko na ga jiya ba ka zo ba " Girgiza mishi kai kawai ba ta tare da ya ce komai ba Dan murmushi Abba ya yi kafin ya ce " haba Zayd wai in ka na tare da ni din ma sai ka yi min kurmancin na ka " Dan karamin murmushi geffen fuska ya yi kafin ya yi magana cikin wata zazzakar murya cike da nitsuwa ya ce " uncle ba na jin dadin maganar ne , so ku bar matsa min ina magana please " ya fada cikin wata kwarbabiyar haoussa kamar wanda ke koyo ( WAIT ! WAIT ! WAIT ! BAN GANE BA KENAN DAMA BA KURMA BA NE KO YA NE WANNAN ZANCEN YAKE 😳😳😳😳😳 ) Jinjina kan shi Abba ya yi kafin ya ce " ba komai, amma fa mu na jiran ka yau kar ka zauna ba ka zo ba " ya na gama fadar haka ya yi gaba ya ci gaba da tafiyar shi Ya na fara tafiya shi ma Zayd ya juya ya nufi kofar gidan ya na sa hannu shi cikin aljihu Sai da ya karaso kofar gidan ya tsaya ya ciro wasu keys da ga cikin aljihun shi ya bude kofar sannan ya shiga ya na medo kofar Gida ne mai kyau dai'dai me hali amma fa ya fi na Abba Girma da kyau A hankali ya ke takowa ya nufi terrace din gaban shi ya Haye Nan ma ya sa key ya bude kofar shiga falon Masha Allah duk da falon karami ne amma ya hadu , an saka mike wasu sofas red colour , buyi two seaters, daya three seater sai guda one seater , a tsakiyar su kuma wata yar karamar table ce ta glass sai wasu remote da ke saman ta Da ka shigo bangaran dama ka na fuskantar wata yar karamar dining room mai dauke da dining table karama mai kujeru guda hudu Sai wata yar drawer da ke karshen dining room din ta na dauke da kayan breakfast kamar su madara sugar coffee da sauren su Bangaran hagu kuma wata door ce wadda za ta sada ka kitchen din Bayan sofa mai three seater wani corridor ne mai dauke da wasu door guda biyu wanda ina kwaytata zaton bedroom ne Bai tsaya bin ta falon ba ya wuce kai tsaye corridor din Door ta karshe ya nufa ya kama handle din kofar ya murda ya shiga ciki ya rufo kofar SAI MUN HADU GOBE 🤘 KAR KU MANTA KU NA TARE DA ALKALAMIN ANISH , WANNAN SO MA TABI NE ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 2 ❤🔥 After some minutes ya fito sanye da wandon three cuter black colour da t-shirt fara mara nauyi , babu takalmi a kafar shi , ya na sanye da bakaken glass kamar kullum Takowa ya ke cike da izza da kwarjini , hannun shi na rike da wata dankareriar waya kirar Iphone 13 pro max mai launin Gold sai shining ta ke kamar zinaryar gaske A hankali ya shigo falon ya nufi sofa three seaters ya Haye ya konta Bayan ya konta ya daura hannun shi daya saman forehead din shi, dayan kuma ya fara latsa wayar shi ( KENAN BA MAKAHO BA NE DUK BASAJA CE YA KE 🥺🥺 TOH ME YA SA SHI YIN HAKAN 🤔🤔 ) Bai fi ten minutes ba da konciyar shi wani kyakyawan matashi ya shigo falon ya na sallama hannun shi rike da ledodin restaurant Ko motsawa Zayd bai yi ba , ko sallamar shi cen kassan makoshi ya amsa mishi ita Dan karamin murmushi saurayin ya yi kafin ya tako ya zauna saman sofa two seaters da ke geffen wadda Zayd ke konce sannan ya ajiye ledodin hannun shi saman table " Al-Amir Nawfel ga abinci ka nan " ya fada ya na kallon shi ta wutsiyar ido A dubu dari Zayd ya mike zaune ya matse fuska ya nuna saurayin da dan yatsa cikin turanci ya ce " kar na sake jin ka kira ni da wannan sunnan Diya idan ba haka ba " Dariya sosai saurayin ya yi shi ma da turanci ya ce " In haka ne ni ma ka daina kira na da Diya , ni fa yanzu suna na Moussa " ya kai karshen ya na kashe mishi ido guda Dan tsaki Zayd ya ja kafin ya ajiye wayar shi gefe ya matso bakin sofar , ya kai hannu ya janyo table din gaban shi sannan ya bude ledodin da Diya wato Moussa ya kawo mishi Moussa kuma kallon shi ya ke ya na murmushi har sai da ya ga ya fara cin abincin sannan ya ce " Zayd wai ka na da labarin......... " Bai karasa maganar shi ba Zayd ya daga mishi hannu akan ya isa haka " Haba Amir yanzu haka za mu ci gaba da zama yanzu wajen shekara hudu kenan , ba ka kewar Al-Amira Tesnim da Malikat Al'Umu ka na tunanin halin da su ke ciki , ko kuma ka manta da Malik " Shiru Zayd ya yi bai ce komai , ya ci gaba da cin abincin shi Sai da ya ida sannan ya mike tsaye ya nufi dining room ya bude fridge ya dauki gorar ruwa guda ya dawo ya zauna inda ya tashi sannan ya bude ta ya fara sha Jinjina kan shi Moussa ya yi cikin ranshi ya ce " Gaskia kam jinin sarauta ba wassa ba ne , ko da ba cikin masarautar ya ke ba " " Amir wai yanzu haka za mu ci gaba da wannan zaman , mu fa jinin mayaka ne , zama ba na mu ba ne " Moussa ya fada cikin raunin murya Sai da Ya ida shan ruwan shi sannan ya mike ya nufi corridor ya na fadin " ai ka san hanyar komawa ni ban tare ka ba " Ya na gama fadar haka ya shige corridor ya shiga bedroom din da ya fito Jinjina kan shi kawai moussa ya yi ya na murmushi ya ce " ni anya ba diyar malan din nan ya fara so ba , ka san dama an ce soyayya ke meda sarki bawa " ya kai karshen ya na bushewa da dariya Sai da ya ida dariyar shi sannan ya mike ya dauki ledodin saman table ya kai kitchen sannan ya dawo ya nufi corridor ya shiga dayan bedroom da ke kussan wanda Zayd ya shiga Misalin karfe 8 na dare Gidan su Inaya Zaune su ke cikin harabar gidan saman tabbarma su na sanye da hijab dark blue har kassa , Malan na gaban su zaune ya na karatun kur'ani , su kuma sun sunkuyar da kai su na sauraron shi Mama kuma ta na zaune geffen shi ita ma ta na sanye da hijab amma fari Su na a haka wani dan matashin saurayi ya fito da ga cikin dakin da ke fuskantar na su Inaya Ya hadu ba laifi skin din shi chocolate kamar ta Inaya amma ta Inaya ta fi dan haske Ya na da dogon hanci da kontancen saje , ya na da dara daren idanu brown colour , ya na da dan tsayi da mudewar jiki amma ba sosai ba a shekaru ba zai wuce 26 ba amma ya tare kassunba ga kwarjini Sanye ya ke da wando three cuter Fari da shirt red kamar jini ya na rike da waya kirar Tecno pop 6 sai latsawa ya ke Bai bi ta kan mutanan gidan da le zaune kussan kofar dakin shi ba ya sa kai ya fice da ga gidan Malan na kallon shi ta kassan ido amma bai ce da shi komai ba , sai da ya ida karatun shi saman ya dago kai ya kali su Inaya ya ce " Auta, ina ga za mu tsaya a nan gobe sai mu ci gaba " Jinjina mishi kai su ka yi a tare ba su ce komai ba , su ka mike su ka shiga dakin su dan su ajiye littafan su Bayan mintina goma Inaya ta fara fitowa ta na sanye da doguwar riga irin ta barci da dan guntun kyale ta ya yafa a kan ta Ta na fitowa ta ji ana sallama Cak ta tsaya ta na kallon kofar gidan kafin ta amsa sallamar Wani dan karamin murmushi ta saki ganin waye ke tare da yayan na ta Da gudu ta je ta fada jikin yayan ta ta na fadin " yaya Abdoul kenan yaya Zayd ka je nemowa " ta fada ta na kallon Zayd ta geffen ido Raba jikin ta ta yi da na Abdoul sannan ta ce " sannu da zuwa yaya Zayd " Jinjina mata kai kawai ya yi bai ce komai ba Duk abun da su ke Malan ya na kallon su amma bai ce komai ba sai ma murmushi da ya ke " malan Zayd ku karaso mana " malam ya fada cikin zolaya Yar dariya Inaya ta yi ta riko hannun Abdoul, shi kuma ya riko hannun Zayd su ka fara takawa a jere Saman tabbarma sa malam ke zaune su ka karaso Saki hannun ta Abdoul ya yi sannan ya ce ma Zayd su zauna A tare suka zauna geffen Malam su ka sa Zayd a tsakiya Ta na ganin sun zauna ta juya ta fara takawa ta nufi hanyar kitchen dan ta taimaka wa mama Kamar an ce ya dago kai ya kali gaban shi Ya na dagowa idanun shi ba su sauka ko ina ba sai saman hips din ta , gashi rigar da ta ke sanye yar shara shara ce a na ganin shape din ta Sai da ya ji zuciyar shi ta buga a dubu dari ya sunkuyar da kan shi dan ya yi arba da abun da ya fi karfin shi Malam sa Abdoul sarai su ka lura da shi, dan Abdoul har kumshe dariya ya ke Dan murmushi Malam ya yi kafin ya matso cikin rada ya ce " Zayd in ka shirya ni ban da matsala ka zo ka dauki matar ka ta tare a dakin ka " Dago kai ya yi ya kali malam ya na zaro idanu duk da su na cikin bakin glass Yar dariya malam ya yi dan dama tsokanar shi ya ke son yi Shi ma Abdoul yar dariya ya yi kafin ya daura hannun shi saman kafadar Zayd ya ce " Bro ka yi sauri fa dan kar ayi maka wufff da ita " Dan tsaki Zayd ya ja ya na kauda kan shi gefe Dai'dai lokacin da Inaya je fitowa da ga kitchen ta na rike da tray Da sauri ya kauda kan shi dayan geffen cikin ranshi ya na fara danasanin abun da ya yi shekarun da su ka wuce Gaban su ta zo ta ajiye tray din sannan ta mike ta juya ta koma dakin su Ta na barin wajen Abdoul ya kai hannu ya janye tray din na sama , ya dauki spoon ya mika ma Zayd da malam sannan ya ce musu bismillah A tare su ka fara cin abincin , har su ka Kamala ba wanda ya ce ma dan uwan shi wani abu Sai da su ka ida mama ta zo ta gyara wajen ta kawo musu jug na ruwa da glass biyu , su ka sha sannan Zayd ya ce da Abdoul ya raka shi gida Sai da ya tsokane shi sannan su ka tashi su ka bar gidan a tare Ya na fita Inaya ta fito da ga dakin su Ta na ganin malam zaune shi kadai Da sauri ta karaso wajen shi ta ce " Abba yaya Zayd har ya tafi " ta kai karshen ta na kallon wajen kofar gidan Dan murmushi yayi kafin ya mata nuni da gefen shi Ba musu ta tako ta zauna geffen shi ta na sunkuyar da kai ta fara wassa da yatsun ta Hannu shi ya daura saman kan ta kafin ya ce " Auta , fada min gaskia , ki na son Zayd " A razane ta dago kai ta kaleshi ta na zaro idanu, ta ma rasa amsar da za ta bashi Daga mata gera yayi kafin ya ce " ba ki ba ni amsa ba " Da sauri ta ce " a'a Abba ba ni son shi " ta na gama fadar haka ta mike da sauri ta koma dakin su Ya na kallon ta har ta shiga dakin su , sannan ya saki murmushi ya na girgiza kan shi Bangaran Inaya kuma ta na shiga dakin su ta fada saman gadon su ta yi rub da ciki Bugun ta a baya Nesrine ta yi kafin ta ce " ke dan Allah malama yi a hankali kar ki kare mana gado " Dago kai Inaya ta yi ta zauna ta na kallon ta Dan turo baki tayi cikin shagwaba ta ce " kin ga ko ku daina bugu na ko in fada ma Abba " " ina ruwa na tashi muje na raka ki ma " ta fada ta na meda kallon ta saman book din hannun ta Marairaice fuska Inaya ta yi kafin ta ce " Nesrine, wai Abba tambaya ta ya yi in ina son yaya Zayd " ta kai karshen kamar ta yi kuka Dago kai Nesrine ta yi ta kale ta da kyau kafin ta bushe da dariya har da dafe ciki Marairaice fuska Inaya ta yi kamar ta yi kuka ta ce " haba Nesrine ya zan yi miki magana ki yi zaune ki na yi min dariya " Dan tsagaita dariyar ta Nesrine ta yi kafin ta ce " Yau ni tambayar Abba ce ta bani dariya , yo mi ne abun so cikin wannan abun , mutumin da ba ya magana , ba ya gani wa zai iya zama da shi ai ni ko sadaka a ke bani shi wlh ba ni so " ta kai karshen ta na sake bushewa da dariya Hararrar Inaya ta yi kafin ta ce " kin ga matsala ta da ke wlh ba a iya magana da ke " " yo ai wannan ba magana ba ce zancen gaskia wa zai iya son Zayd, ba dan kyawon shi ba ai ko kallo bai isa wani ba " " wai ke me ya sa ki ke yawwan cin zarafin mutane, me ya yi miki, kullum sai kin kaskantar da shi , ko dan kin ga ba ya da kowa ba ya da idon gani , ba ya da bakin magana ko dan bashi da kudi , kin je makaranta ki yi karatun kur'ani ki san Allah ba ya son mai kaskantar na kassa da shi , yanzu in kin wayi gari kin koma kurma ko makafniya ki na tunanin wani zai so ki ne , wlh Nesrine ki ji tsoron duniya wannan jiji da kai da ki ka dauko ba na familyn mu ba ne , ba mu gado wannan ba gwara tun wuri ki tambayi kan ki ina ki ka dauko su " " ke dan Allah malama ya isa dan kawai na tabo wani banza cen shi ne za ki yi zaune ki na min fada kamar wata uwa ta , ai ba karya na yi ba dan ko ke da kan ki da ki ke kare shi ba son shi ki ke ba dan haka ki bani lfy sakara kawai , kamata ya yi ki tafi massalaci ki dauki speaker ki ringa yi musu wa'azi ko ba komi kin samu lada no sens " ta kai karshen ta na saukowa da ga saman gadon ta fice da ga dakin Ta kallo Inaya ta rakata har sai da ta fita sannan ta ce a fili " wlh karya ki ke, duk abun da zai sa mace ta so namiji yaya Zayd ya malake shi , dan ya ma fi sauran mazan wlh ko cikin dubu za ki duba da wuya ki samu kamar yaya Zayd " ta kai karshen hawaye na zubo mata Da sauri ta koma ta yi rub da ciki ta fara kuka kassa kassa Zayd Tafiya su ke saman hanya shi da Abdoul, sai zuba ya ke mishi amma shi kuma ko kalma daya bai ce da shi ba " Zayd wai mi ne sunan ka na gaskiya " Abdoul ya tambaye shi Cak ya tsaya da tafya ya na kallon gaban shi kamar ya ga wani abu ya kassa gaba ya kassa baya A hankali ya medo da kallon shi kan Abdoul ya zuba mishi ido mai ce komai Ganin ya yi shiru kuma ya tsaya ya na kallon shi ya sa Abdoul cewa " ko sunnan na ka ma ka manta " Jinjina mishi kai Zayd kafin ya fara takawa ya yi gaba Dan murmushi Abdoul ya yi kafin ya ce " to tun da ka san hanya ni zan koma gida " ya fada ya na daga mishi murya Bai ce mishi komai ya ci gaba da tafiyar shi Ganin bai ce komai ba ya sa Abdoul juyawa ya koma gida Shi ma Zayd hanyar gidan shi ya kama Bai fi minti biyu ba ya iso gida Da sallama bakin shi ya shigo falon gidan nan ya isko Moussa ya na zaune saman sofa da ga shi sai short da singlet ya na latsa wayar shi Dago kai ya yi ya na amsa mishi sallamar shi kafin ya ce " Amir wai ina ka tsaya ne haka tun dazu ni ke jira ka " A hankali ya sa hannu ya zame glass din idanun shi Allahuma barik ashe ba banza ba ya ke saka glass ba Ya na da dara daran idanu Farare kal kamar madara Launin idanun shi Hazel mai bala'in kyau, sai wani shining ya ke abun har ya ba ka tsoro kamar idanun mage cikin dare haka su ke Karasowa ya yi cikin falon ya ajiye glass din saman table sannan ya jingina bayan shi a jikin sofar ya daga kan shi sama ya lumshe idanun shi Duk abun da ya ke Moussa ya na kallon shi amma bai ce da shi komai ba dan ya san abokin na shi ba karamin miskili ba ne ba bazan ba a ka kassa gano shi ba kurma ba ne Ajiye wayar shi Moussa ya yi saman table kafin ya matso bakin sofar ya kai hannu shi ya dafe cinyar Zayd Medo kan shi ya yi a hankali sannan ya bude idanun shi ya daga mishi gera allamar minene ? " Amir wai me ya ke damun ka ne , duk ka bi ka sauya kamar ba Al-Amir Nawfel ba magajin Malik , ko dai ka fada soyayya ne " ya kai karshen ya na kashe mishi ido guda Dan tsaki Zayd ya ja kafin ya kauda kan shi gefe kafin ya ce " Diya dan Allah ka bar kira na da wannan su nan, wannan sunnan ya goge da ga cikin rayuwa ta tun lokacin da mu ka shigo garin nan " " in haka ne ka daina kira na da Diya ni ma , yanzu Amir baza ka koma ka karbi mulkin ka ba " Da sauri ya katse shi da cewa " ai Malik bai mutu ba , har yanzu ya na kan mulki kuma ko ya mutu ba ni son mulkin, a kan shi a ka nemi halaka ni dan haka su je na bar musu kayan su , na ga ai kaima yarima mai jiran gado ne me ya sa baza ka koma masarautar ku ba ka karbi mulkin " Yar dariya Moussa ya yi ya na dauke hannun shi da ga saman cinyar Zayd sannan ya ce " haba kai ma Zayd ta ya zan karbi mulki bayan ni ne na uku babban yayan mu na raye zan ce na karbi mulki shi ya sa na baro musu kayan su , ni fa mulki sam ba ya cikin tsarin rayuwa ta ba yadda za ka yi an haifo ka cikin jinin sarauta dole ka hakura " Mikewa tsaye Zayd ya yi ya bar falon Har zai shiga corridor ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce " ka na da labarin Amira da Malikat Al'Umu ? " Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " kar ka damu su na cikin koshin lafya " Jinjina kan shi kawai ya yi sannan ya fara takawa ya shiga corridor din ya shiga bedroom din shi Ya na shiga shi ma Moussa ya mike ya koma bedroom dinshi shi ma Washe gari AMINU KANO COLLEGE OF EDUCATION Nesrine Zaune ta ke kassan wata bishiya cikin harabar college din ta na rike da wani book ta na karatu Kamar da ga sama ta ji an zabce mata book din ta A dubu dari ta dago kai , wata irin mumunar faduwa gaban ta ya yi lokacin da ta yi arba da wanda ya zabce mata book din ta Wasu samari ne guda biyu su na tsaye gaban ta Wanda ke rike da littafin ta ya fi dayan tsayi kadan ya kuma fi shi haske ya na da dogon hanci da kananan idanu ya dan tara gashin kai Ya na sanye da crazy jeans blue da t-shirt blue ita ma Daya kuma ya na da dan duhu kadan amma kamanin su daya sai dai wannan bai tara gashin kai ba, idanun shi brown colour ne , kuma ya na da saje lips din shi kuma sun dan yi pink kadan Shi kuma ya na sanye da jeans baki da t-shirt fara Wanda ke rike da book din ta ya fara magana ya ce " baby wai ba na ce da ke ba ki ringa samu na a wajen parking space lokacin break ba " Wasu yawu Nesrine ta hadiye murya na kerma ta ce " yi hakuri Hafiz bazan sake ba " Geffen ta ya zo ya zauna ya na mika mata book din ta ya ce " ba komai baby nan din ma ya na da dadin zama sai dai da mutane dayawa shi ya sa na ce ki ringa tarda ni parking space " Ta na shirin magana ta ji Muryar Inaya ta na yi musu sallama A tsorace ta dago kai ta kale ta Inaya kuma ta yi zaton classmate din nesrine ne sai ba ta ka komai a ran ta ba ta kali yar uwarta ta ce " Nesrine dan Allah in kin tashi tafya gida ki jira ni " Ta na gama fadar haka ta juya da gudu ta bar wajen kamar ta ga wani abun tsoro Tun da ta iso wajen saurayin da ke tsaye ya tsare ta da idanu sai kallon ta ya ke ya na hadiye yawu Sai da ta bar wajen ya na kallon ta har ta kure wa kallon shi sannan ya dawo da kallon shi kan hafiz ya ce " bro wacece wacen yarinyar ta hadu fa, she look so innocent " Dum Nesrine ta ji gaban ta ya fadi dan ta san in Moctar ya lakewa Inaya ta shi ga uku cikin college din nan dan sai ya azabtar da ita shi ma ba karamin mugu ba ne ga son mata Ta yi nisa cikin tunanin ta sai ji ta yi an daura hannu saman cinyar ta A razane ta dawo cikin hayacin ta, ta na kallon hannun hafiz da ke saman cinyar ta " lfy baby ina tambayar ki kin yi shiru " ya fada ya na leko face din ta " minene ? " ta fada cen kassan makoshi Dan murmushi yayi kafin ya ce " who is she , ko sister din ki ce " Da sauri ta ce " a'a kawai saman hanya na hadu da ita " " okay meye sunnan ta " ya tambayeta ya na tsare ta da ido Wasu yawu ta hadiye kafin ta ce " ban sani ba " Tass ta ji saukar mari a face din ta Da sauri ta kai hannu ta saman kumatun ta ta na dafe wajen wasu hawaye na zubo mata Mike wa tsaye ya yi cikin bacin rai ya daga mata murya ya ce " ni za ki raina wa hankali ke har kin isa ki min karya " Ya na gama fadar haka ya kai hannu ya shake ta ya hada kan ta da bishiyar cikin tsawa ya ce " meye sunnan ta na ce miki " Cikin kuka ta ce mishi " Maryam sunnan ta Maryam " da kyair kalmar ta karshe ta fito dan ba karamar shaga ya yi mata ba Ganin ya na neman ya kashe ta ya sa Moctar kai hannun shi ya dafa kafadar shi ya ce " bro sake ta kar ta mutu " Da sauri ya janye hannun shi da ga wuyan ta , ya ja baya kadan kafin ya ce " nan gaba ki san irin amsar da za ki ba ni in na tambaye ki " ya na gama fadar haka ya juya ya bar wajen Bin bayan shi Moctar ya yi su ka bar wajen Su na barin wajen ta fadi kassa ta konta ta na sauke kuka mai cin rai Sai da ta share wajen good 30 minutes ta na kukan sannan ta mike a hankali ta na jan kafa ta nufi toilet din mata ta wanke face din ta sannan ta dawo ta dauki school bag din ta ta tafi class ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 3 ❤🔥 After some hours Tafiya su ke saman titi a jere , Nesrine ta yi nisa cikin tunanin ta , ita kuma Inaya sai wassan nin ta ta ke kamar karamar yarinya Su na tsaka da tafiyar su wata mota fara kirar Mercedes ta tsaya a gaban su ta tare musu hanyar wuce Dum Nesrine ta ji gaban ta ya fadi dan ta san ko wanene Inaya kuma ta yi tsaye ta na kallon motar dan ita ba ta san ko su waye ba Su na tsaye a hakan su ka ga an bude kofofin gaban na motar Hafiz da Moctar su ka fito Gaban su ka zo su tsaye sannan Moctar ya ce " yan mata ku zo mu rage muku hanya mana " Dan murmushi Inaya ta yi sannan ta riko hannun Nesrine ta ce " mun gode amma mun iso gidan ai " ta kai karshen ta na rabawa ta geffen su za ta wuce Da sauri Moctar ya sha gaban su ya ce " haba yan mata taimako ne fa " " babu komai mun gode gidan mu fa cen karshen layin ne , ka ga kuma ba ni son Abban mu ya kan ki zai mana fada " Ba ta gama rufe bakin ta ba ta tsinci Muryar Hafiz ya na fadin " ke Nesi wuce cikin motar nan na kai ku gida " Wasu yawu Nesrine ta hadiye ta na tsoron ta shiga motar in malam ya gan ta zai yi mata fada, in kuma ta ki ta san halin Hafiz yanzu zai yi mata Dukan mutuwa kuma ba izinin ramawa, kawai sai ta tsaya ta na faman muzurai Ta yi nisa cikin tunanin ta sai tsintar Muryar Abdoul su ka yi ya na fadin " Nesrine me ku ke yi a nan ? " A razane ta juyo ta na kallon shi zuciya na duka uku uku Ya ko tsare da wadanan dara daren idanun shi " yaya Abdoul dama classmate din su Nesrine ne su ka ce wai su rage mana hanya shi ne na ce musu mun ma iso gida amma su ka ki yarda " Inaya ta fada babu ko tsoro " shikenan ba komai wuce ko tafi gida yanzu " Tun bai rufe bakin shi ba Nesrine ta kamo hannun Inaya ta raba ta geffen Moctar da sauri ta bar wajen Su na barin wajen Abdoul ya juyawar shi shi ma ya yi tafiyar shi su ka bar Hafiz da Moctar tsaye a wajen Bayan Abdoul ya bar wajen Moctar ya kali Hafiz da ke ta hura hanci ya ce " kai dan malam rage wannan fushin na ka, ga shi yanzu sun tafiyar su ba tare da mun ga gidan su ba " Dan tsaki Hafiz ya ja sannan ya juya ya fara takawa ya na fadin " ai mun hadu school " " kai malam kar ka manta ba college din ba mu ke , yawwan zuwan mu cen ya janyo mana matsala " Geffen driver Hafiz ya bude ya shiga Ya na ganin ya shiga motar shi ma ya bude geffen mai zaman banza ya shiga Bayan ya shiga Hafiz ya tada motar su ka bar wajen da mugun gudu Duk abun da ya faru a kan idon Zayd , dan ya na biye da su Inaya amma su ba su gan shi ba , ya na shirin ya je ya yi ma su Hafiz Dukan tsiya ya ga Abdoul ya shawo kwanar ya nufi su Inaya kawai sai ya yi tsayiwar shi sai da ya ga tafiyar su sannan ya juya ya kama hanyar komawa gidan shi Bangaran Inaya kuma , sai da su ka isa cikin gidan babu wanda ta ce da yar uwarta wani abu Sai da suka shiga cikin bedroom din su sannan Inaya ta kwace hannun ta da karfi ta dan ja baya ta na kallon Nesrine ta ce " wai me ya same ki Nesrine kin ga yadda saurayin cen ya yi miki tsawa kuma ki ka kassa ce mishi wani abu " Cire hijabin ta Nesrine ta yi ta ajiye saman sannan ta zauna geffen gadon ta dago kai ta kali Inaya ta ce " Inaya ke karama ce baza ki gane ba amma wlh ki raba hanya da samarin nan ko cikin school in ki ka gan su ki tsere ki buya dan wlh ba mutanan kirki ba ne " ta na gama fadar haka ta tashi ta fice da ga dakin Inaya dai ta na tsaye ta na kallon ta har ta ida maganar ta ta tashi ta bar dakin ba ta ce mata komai ba Nesrine kuma bayan ta fita kai tsaye toilet ta shiga Maimakon ta yi wanka sai ta jingina a jikin bangon toilet din ta aza kuka Cikin kukan nata ta ke fadin " ya Allah na roke ka raba ni da Hafiz , ya Allah ko ba ka raba ni da shi ba kar ka bari ya kusan ci yar uwata , ban San me na yi mishi a duniya ba ya ke neman ya cutar da ni , na shiga uku ni Nesrine , RAMATOU kin cuce ni kin hada ni da bala'i da na sani bazan taba yarda da abotar ki ba, Allah ya isa tsakani na da ke " Haka ta yi ta dimimuwan ta har ta gaji ta yi shiru sannan ta yi wanka ta fito ta koma bedroom din su Ta na shiga ta tarda Inaya har ta yi barci dan gajiya Misalin karfe 5 na yamma Inaya Zaune ta ke bakin kofar gidan su saman wasu duwatsu ta na faman wassa ita kadai kamar karamar yarinya Tun da ga nesa ya hango ta zaune ta cikin bakin glass din shi Ya na tare shi da Moussa, ya na sanye da wandon jeans baki da t-shirt dark blue , shi kuma Moussa jallabiya ce fara ya ke sanye da Lokacin da Moussa ya gan ta ya saki murmushi ya kali Zayd ya ce " Amir ga fa babyn ka cen ta na wassa " " ina ga yarinyar nan ta na da matsala a kwakwolwar ta " ya fada mishi cen kassa kassa ta yadda shi da Moussa kawai su ka ji abun da ya fada Jinjina mishi kai Moussa ya yi dan ya lura yanayin ta bai yi kama da masu cikakiyar lafya ba a shekarun ta Haka su ka ci gaba da tafiyar su har su ka karaso inda ta ke zaune su ka yi mata sallama A hankali ta dago kan ta, ta na amsa musu sallamar su kafin ta ce " ina wuni yaya Moussa " Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " lafya lau babyn malam , ko dai in ce babyn Zayd " Dan zaro idanu ta yi ta na kallon Moussa sannan ta kali Zayd da ya tsareta da ido Turo dan bakin nan nata ta yi gaba ta shagwabe fuska sannan ta ce " a'a ni babyn malam ce ni na ma tafiya ta wajen Abba " ta kai karshen ta na mikewa ta fara tafiya Da sauri Moussa ya ce " to tsaya mu raka ki mu ma cen za mu je " Da sauri Zayd ya kale shi dan ya lura Moussa na neman ya kwabo mishi ruwa Jinjina mishi kai kawai ta yi ta ci gaba da tafiyar ta Su kuma juya su ka bi bayan ta, ba yadda Zayd ya iya dole ya hakura ya bi bayan shi su ka tafi Tun da su ka kamo hanya ya ke kallon ta ta cikin glass Ita kuma sai wasu juye'juye ta ke ta na halba kafa ta na wassa yadda kassan me shekara biyar haka ta ke Shi kuma Zayd wannan abun da ta ke ya na yawwan tuno mishi da kanwar shi dan ita ma haka ta ke da rawan kai Kawai sai ya tsinci kan shi ya na jin wani bakon yanayi , cikin zuciyar shi ya ce " she is so cute and innocente why malam zai aura min ita da karancin shekarun ta haka , ya kamata na tambaye shi dalilin shi na yin hakan " Sai magana ya ke cikin zuciyar shi har su ka karaso sangayar Malam bai sani ba, sai da Moussa ya kai hannu ya taba shi ya na fadin " Amir ba ka ji ne malam na gaida ka ? " A dan razane ya juyo ya kali Moussa sannan ya meda kallon shi kan Malam da ke zaune saman tabbarma sanye da manyan kaya ga Inaya geffen shi ta rungume shi ta na murmushi Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " malam Zayd tunanin mi ka ke haka " Girgiza mishi kai kawai Zayd ya yi allamun ba komai sannan ya dawo da kallon shi kan Moussa ya mishi allamun su tafi Jinjina mishi kai ya yi sannan ya kali malam ya ce " malam za mu wuce sai mun dawo " Dan murmushi malam ya yi ya ce " shikenan Allah kiyaye hanya , Auta baza ki raka su ba " ya fada ya na medo da kallon shi kan Inaya da ke konce a jikin shi kamar baby Cikin shagwaba ta ce " Abba yanzu fa su ka rako ni , sannan kuma na sake rakiyar su , ni gaskia babu inda zan je " Malam na shirin magana ya ga Zayd ya kama hannun Moussa ya ja shi su ka bar wurin Ta na kallon su ta kassan ido har su ka bar wajen sannan ta mike da ga jikin malam ta ce " Abba , yaya Zayd sunnan shi ne hakan na gaskia ko " Jinjina mata kai malam ya yi ya na son ya ji abun da za ta cewa " to amma Abba me ya sa yaya Moussa ke kiran shi da Amir , Amir ai ya nufin yarima " ta fada ta na kallon malam Shi kuma malam juya kan shi ya yi ya kali su Zayd da su ka yi nisa cikin tafiyar su Ba tare da ya juyo ba ya ce " ni ma ban sani ba, halan sunnan da ya ke kiran shi ne da shi lokacin su na kanana kin San ba dole sai dan sarki ba a ke kira da Amir " Cikin ranshi kuma ya na tambayar kanshi shin wanene assalin Zayd din da su ka sani ( TOOOO ! MU MA DAI MU NA SON MIJI WAYE AINAHIN ZAYD DIN NAN 🙄 ) Haka ta zauna wajen malam ta na ta zuba mishi shagwaba shi kuma ya na biye mata sai da su ka ga magriba ta gaba to sannan su ka tashi su ka koma gida a tare , ta na rike da hannun shi ta na wassa da shi ( Ita dai wannan yarinyar da wuya ta zauna ba ta motsi 😑😑 ) Bayan sun koma gida , da kanta ta debo ma malam ruwa cikin buta ya yi Alwalla sannan ya tafi mosque Bayan ya fita ita ma debo ruwa ta yi Alwalla ta koma bedroom din su dan ta yi sallat Ta na shiga dakin ta tarda Nesrine ta na zaune saman dadduma ta daga hannayan ta sama ta na adu'a Dauko daddumar ta Inaya ta yi ta zo ta shinfida geffen Nesrine sannan ta tada sallar ta Ba su tashi da ga kan daddumar sai da su ka hada da sallar isha su ka yi a tare Bayan sun ida Nesrine ta mike ta nade daddumar ta ta mayar da ita wajen ta sannan ta fito da ga dakin Ta na fitowa ta ji sallamar Abdoul Dum ta ji gaban ta ya buga dan ta san da wuya ya kyale ta bai mata fada ba Kamar ko ta sani da sauri ta juya za ta koma dakin su ya kira sunan ta Wasu yawu ta hadiye a hankali ta juyo ta ce " na'am " Takowa ya yi ya zo gaban ta ya tsaya sannan ya ce " su waye samarin nan da na gan ku a tare " Sunkuyar da kai ta yi , Cikin in'ina ta ce " ni ma ban san su ba kawai sun tseda mu ne saman hanya wai mu je su rage mana hanya " Jinjina kan shi ya yi sannan ya ce " shikenan nan gaba kar ku sake tsaya wa ko sun muku magana ku kyale su " " to yaya Abdoul " ta fada ba tare da ta dago kai ba dan tsoron ta ke ji ya wanke ta da mari Shi kuma tsaya wa ya yi ya kare mata kallo da kyau ya ga yadda ta ke ta rawar jiki kamar ya ce zai dake ta Sai da ya dan jima a haka sannan ya juya ba tare da ya ce komai ba ya shiga bedroom din shi Ita kuma ta na jin ya fara takawa ta dago kai ta ga ya nufi dakin shi ta sauke ajiyar zuciya har da dafe saitin zuciyar ta ta na jan nunfashi a hankali Sai da ta nitsu da kyau sannan ta kama hanyar kitchen ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 4 ❤🔥 Da sallama a bakin ta shigo kitchen din, nan ta isko mama gaban murhu, har ta gaba girki Dan juyo wa mama ta yi ta kali Nesrine sannan ta ce " lafya idanun duk sun kumbura haka ? " Ta na shirin magana ta tsinci muryar Inaya ta na fadin " kuka ta yi shi ya sa " A tare duk su ka jiyo su ka kale ta Ta na tsaye bakin kofar kitchen din ta na sanye da doguwar riga mara nauyi ta saka dan karamin hijab zuwa kirji Hararrar ta Nesrine ta yi kafin ta ce " tooo malama miye ruwan ki a ciki ? " Hannayan ta duka biyu Inaya ta sa ta rike kugun ta, ta ce " da ruwana , sai dai ki yi abun da za ki yi " ta kai karshen ta na murguna mata baki Da sauri Nesrine ta dauki wani plate ta juya za ta bugawa Inaya Da gudu Inaya ta juya ta bar kitchen din ta na kara Ita ma Nesrine bayan ta ta biyan ta ta na fadin " yau sai na yi maganin ki " Inaya kuma ido a rufe ta yi da gudu za ta bar gidan Har ta kai bakin kofa ba ta sani ba, kawai sai ji ta yi ta bugi wani abu da karfi ta yi baya za ta fadi ta na sakin kara mai karfi, wanda ya sanya shi toshe kunnuwan shi da duka hannayan shi biyu Cak Nesrine ta tsaya ta na kallon su ta na zaro idanu Malam ne da Zayd su ka shigo gidan sai da su ka yi sallama amma Inaya ba ta ji su ba , har sai da ta bugi kirjin Zayd da karfi Shi kuma ya kassa taro ta dan ya na tsoron ya taro ta wani ya lura da hakan ya yi mishi wata magana da za ta bata mishi rai shi ya sa ya kyale ta ta fadi Inaya kuma ta na faduwa kan ta ya bugu dum ga kassa har sai kassar ta dan girgiza Da gudu Nesrine ta saki plate din hannun ta ta nufo ta da gudu ta na fadin " Inaya, Inaya , Inaya " kamar ta yi kuka Shi ma malam da ke tsaye geffen Zayd da gudu ya yi kan ta ya talabo ta ya na kiran sunan ta Ina ita ko jin su ba ta yi sai kuka ta ke kamar karamar yarinya Ganin yadda su ka bi su ka rude ya sa shi kauda kan shi gefe ya saki dan siririn tsaki A hankali ya fara takowa inda ta ke konce ta na kuka Dukowa ya yi gaban ta, ya sanya hannayan shi duka biyu ya dauke ta cak kamar baby ya mike tsaye sannan ya nufi tabbarma da ya gani a shinfide kussan dakin Abdoul Da sauri malam ya bi bien shi , ita kuma Nesrine ta tsaya ta na kare mishi kallo cikin ran ta, ta na tunanin ya akayi ya san tabbarma ta na cen wajen Malam kuwa bai kawo komai a ran shi ba dan ya san akwaye makafi dayawa da su ke aiki kamar ma su idanu ba mamaki ya hadace inda su ke zama kullum shi ya sa ya nufi wajen kai tsaye ( HAKAN NA NUFIN MALAM YA SAN ZAYD BA KURMA BA NE AMMA BAI SAN SHI BA MAKAHO BA NE 🤔 ) Sai da ya karaso wajen tabbarma sannan ya kontar da ita a wajen ya koma gefe ya zauna , ita kuma har yanzu kuka ta ke kamar baby ba ta ma san an dauke ta ba Ya na kontar da ita malam ya karaso wajen ya zauna geffen ta ya talabo kan ta ya zaunar da ita ya rungume ta ya na fadin " ya isa haka auta daina na kukan nan haka kar ki janyo wa kan ki ciwo " A hankali ta fara rage sautin kukan ta ta na hadiyar zuciya Ta na a haka ta ji an tabo mata kafar ta Ta na konce a jikin malam din ta dago kan ta ta kale shi Ya na ganin ta dago kan ta ya kai hannayan shi biyu ya rike kunnuwan shi ya dan sunkuyar da kai allamun ya na bata hakuri Wata yar karamar dariya ta yi cikin kukan nata sai da dan dimple din ta na geffen dama ya banyana karan farko kenan da na gan shi kuma gashi ba karamin kyau ya na kara mata ba A hankali ya dago kan shi ya na kallon ta ta cikin glass din shi, abun har dariya ya so ya bashi yadda ta ke dariya ta na kuka lokaci guda " Shikenan auta ya wuce ko ? " malam ya fada ya na kai hannun shi ya goge mata hawayen ta Jinjina mishi kai ta kafin ta kai hannun ta bayan kanta ta ce " Abba wajen zafi ya ke min " ta kai karshen cikin shagwaba Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " babu komai auta na zai wuce tashi ki je daki, ki konta " Da to ta amsa mishi sannan ta fara kokarin mike wa da ga jikin shi Da sauri Nesrine da ke tsaye waje guda tun dazu ta na kallon su , ta karaso wajen ta kamosu hannun ta guda ta taimaka mata ta mike tsaye su ka nufi cikin daki Su na shiga cikin dakin Inaya ta Haye saman gadon ta yi rub da ciki ta na sauke nunfashi a hankali ta lumshe idanun ta Ita kuma Nesrine ta juya ta baro dakin ta tafi kitchen Ta na shiga malam ya kali Zayd ya ce " Zayd me ya sa ba ka taro ta ba, yanzu da ta ji ciwo fa, dama ta na da tabo a kan ta na dauke shi ne ya motsa yadda na ga ta na kukan nan " Kallon shi Zayd ya yi cikin sanyi murya ya ce " sorry uncle , amma wane tabo ne wannan ? " ya tambaya ya na son ya ji karin bayani Ya na shirin magana Abdoul ya fito da ga dakin shi ya na sanye da jallabiya brown mai dogayen hannu ya zo geffen su ya zauna ya na musu sallama A tare su ka amsa sallamar amma ta Abba kadai a ka ji , dan Zayd in ba kallon bakin shi ka yi ba baza ka gane ya amsa ba Sai da ya zauna sannan ya ce "malam, na ji wani ya yi kara, cikin gidan nan ne ? " Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " ba komai, auta ce ta dan fadi amma ba ta ji ciwo ba " Jinjina kan shi kawai Abdoul ya yi ba tare da ya ce komai Su na a haka Nesrine ta fito da ga kitchen ta na rike da plate ta shiga dakin su Ta na shiga mama ta fito da ga kitchen din ta na rike da tray madaidaici ta karaso wajen su malam ta yi musu sallama ta ajiye tray din gaban su , sannan ta koma kitchen ta dauko musu jug na ruwa da glass biyu ta ka ta ajiye musu sannan ta wuce dakin ta Ta na shiga dakin Abdoul ya bude musu tray din ya mika ma kowane spoon guda sannan ya ce musu bismillah Kamar yadda su ka saba haka wannan karan ma haka su ka ci Sai da su ka Kamala ba wanda ya ce ma wani ufan Ya na tsaka da shan ruwa Inaya ta fito da ga dakin su ta na dafe kai da hannu guda ta na dan lumshe idanu kamar mai jin barci A tare duka su ka dago kai su na kallon ta ba wanda ya ce da ita komai Ta na tsaka da tafiyar ta ta ji wani jiri ya debe ta yi fuuuuu baya ta tafi za ta fadi Da sauri Abdoul ya yi kokarin tashi dan ya taro ta amma sai dai mi ? Tun kafin ya mike ya ga Zayd ya mike a dubu dari ya nufe ta , taku biyu kawai ya yi ya riko hannun ta ya janyo ta, ta fado saman fafadar kirjin shi Baki sake Abdoul da malam ke kallon shi sannan su juyo su kali juna su na son su yi magana amma baki ya ki buduwa Basu Ankara ba sai kawai ganin su ka ya dauke ta cak ya komo inda ya tashi ya kontar da ita, sannan ya kai hannu ya dauki glass din ruwa ya zuba kadan ya yarfa mata a fuska A hankali ta ware idanun ta ta na karanto kalmar shahada Ajiyar zuciya malam ya sauke ya na lumshe idanun shi a hankali sannan ya bude ya kali Abdoul ya ce " Abdoul meda ta dakin su " Da to ya amsa mishi sannan ya mike tsaye ya kai hannu ya dauke ta cak kamar baby ya nufi bedroom din su da ita Ya na barin wajen malam ya kali Zayd ya ce " Zayd na san kai ba kurma ba ne amma yau abun da na gani makaho bazai iya yin haka " Shiru Zayd ya yi ya na sauraron shi amma ya kassa bude baki ya yi magana Dafa kafadar shi malam ya yi kafin ya ce " Zayd ni fa na yarda da kai, dalilin da ya sa na aura maka Inaya nassan ka na da kyakyawar zuciya amma ban San assalin ka ba kuma bazan ce ka fada min har sai randa ka yi ninya amma zan so in sani meyassa ka ke karyar wadanan nakassa al'halin ka na cikin koshin lafya ? " Malam na gama fadar haka Abdoul ya fito da ga cikin dakin su Inaya ya dawo inda ya tashi ya zauna Ya na zama Zayd ya ce " Ni ban taba ce muku ni kurma ne ko kuma makaho ku ne ku ka yi hassashen ku a haka " Dan zaro idanu malam ya yi dan fa maganar Zayd ba karya ba ce dan tun lokacin da su ka shigo garin kano su ka hadu da Zayd kullum shiru da shi ko an mishi magana sai dai ya girgiza kai ko ya jingina da haka har su ka yi tunanin ko shi kurma ne , gashi kullum ya na sanye da bakin glass wani lokaci ya na rike da sanda kamar makaho dalilin da ya sa su ke tunanin shi kurma ne kuma makaho Kallon shi da kyau Abdoul ya yi kafin ya ce " Zayd ka na nufin yanzu ka na iya gani na " Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " of cours ina iya ganin ka, ka na sanye da jallabiya brown mai dogayen hannu , ni fa ba ni son yawwan magana dan Allah ku daina saka ni dole sai na bude baki na yi magana zan iya fadar abun da zai bata muku baki daya " ya fada kai a sunkuye Jinjina kan shi Abdoul ya yi kafin ya ce " don Allah Zayd zan so na ga idanun ka ko da so guda ne ka ga yanzu four years kullum ina ganin ka da glass wannan karan na so na gan su " Dago kan shi ya yi a hankali ya na kallon Abdoul ta cikin glass din shi kafin ya sa hannu a hankali ya zame glass din shi A tare zuciyar malam da Abdoul su ka buga da su ka ci karo da wadanan hazel eyes na Zayd ga shi ko ya na fuskantar lamps din wajen sai idanun shi su ka yi reflecting hasken lamps din sai su ka yi wani kyali na musaman su ka zama kamar idanun mage Da sauri Abdoul ya ce " don Allah meda glass din ka wlh sai da na ji tsoro " A hankali ya sunkuyar da kai ya Meda glass din shi sannan ya dago kai ya kali Abdoul ya ce " yanzu dai baza ka ce ba ka taba ganin idanu na ba " " ni ko na gan so , ai wadanan ko a mafarki na gan su sai na gane su " ya kai karshen ya na yar karamar dariya Malam dai ya yi sumar zaune ya rasa wane irin mutun ne Zayd , sam bai yi kama da mutanan Nigeria ba karewar zancen bai ma yi kama da mutanan Africa ba ki daya Haka su ka ci gaba da hirar su wadda yawancin Abdoul da malam ke yin ta shi Zayd ya na zaune kamar gunki Sai wajen karfe 10 na dare sannan ya mike zai koma gida, Abdoul ya dan raka shi kadan kafin ya komawar shi gida Bayan ya koma gida bai tsaya bin ta kan Moussa ba kai tsaye ya wuce bedroom din shi ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 5 ❤🔥 Washe gari Yau ta kama week-end ce Inaya da Nesrine ba su tafi college ba, sai misalin karfe 9 na safe Nesrine ta farka da ga barci Inaya kuma sai wajen karfe 10 ta farka , ko da ta farka ta ji kan ta na yi mata dan ciwo amma sai ta jure Ta mike ta fito dakin ta shiga toilet ta yi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wando jeans baki da doguwar riga zuwa guyiwa pink colour ta saka dan karamin hijab zuwa kirji sai tashin kamshi ta ke Kai tsaye kitchen ta nufa dan ta taya mama girki tun da yau week-end A tare su ka yi dafuwar su cikin konciyar hankali har misalin karfe 12 na safe sannan su ka Kamala Bayan sun ida Inaya na shirin shiga dakin ta ta tsinci Muryar malam ya na fadin " Auta dan Allah dauki abincin Zayd ki kai mishi " ya fada ya na ida shigowa cikin gidan Dan murmushi ta yi sannan ta ce mishi to ta juya ta koma kitchen Dama mama ta fida mishi na shi cikin wani kwano ta ajiye gefe dama sun saba fida mishi abincin rana kullum wani yaro da ke sangayar malam ke zowa ya kai mishi wannan karan ne na farko da za ta kai mishi da kan ta Jim kadan ta fito rike da wani dan basket a hannun ta, ta fita gidan, a lokacin har malam ya shiga dakin shi A hankali ta ke tafiya saman hanya ta na kallon kassa kamar mai tunanin wani abu Sai da ta karaso kofar gidan sannan ta dago kai, ta kai hannu ta tura kofar ta shiga ta na sallama Wannan karan farko da ta shigo gidan shi , Ta sha ruwan mamaki ganin yanayin gidan, har da wata mota fara ta tambayi kanta ta ina motar ta shigo , in ta shigo ai fitar ba za ta yi wuya ba kuma ita kofa daya ta gani kuma karama ce A hankali ta ci gaba da takawa har ta isa terrace din gaban ta Ta kai hannu ta bubuga kofar, sau daya Shiru ba a bude ba sai ta sake bugawa karo na biyu Wannan karan bai fi one minute ba ta ga kofar ta bude Sai ga Moussa ya na tsaye rike da kofar ya na sanye da wando three cuter da t-shirt ya na shan iska Sallama ta yi mishi ta gaishe da shi cikin fara'a sannan ta mika mishi basket din hannun ta ta ce ga abincin su in ji malam Dan murmushi yayi kafin ya dan ja gefe kadan ya ce " bismillah shigo mana dama yunwa na ke ji idan mun ida sai ki koma da basket din ko " Jinjina mishi kai ta yi ta na murmushi kafin ta sa kafa ta shiga falon ta na sallama Ya na zaune saman sofa da ke fuskantar kofar shigowa, ya na sanye da jallabiya fara mai kananan hannu, ya na sanye da wadanan glass din na shi baki, ya jinjina a bayan sofar ya daga kai sama ya lumshe idanu duk da su na cikin glass Ya ji sallamar ta amma ko motsi bai yi bare ya amsa mata A hankali ta karaso cikin falon ta na bin shi da kallo gaskia ya yi mata kyau Ta na cikin dube duben ta ta tsinci Muryar moussa ya na fadin " ko kin dawo nan da zama " Girgiza mishi kai ta yi ta na murmushi sannan ta karasa ta ajiye basket din hannun ta saman table ta ce " ina wuni yaya Zayd " Shiru bai amsa mata ba ko motsi bai yi ba Da sauri Moussa ya ce " barci ya ke " dan ya kare dan uwan shi Murmushi ta yi sannan ta koma bakin sofar da ke wajen kofar shigowa ta zauna kassa saman carpet Karasowa Moussa ya yi ya zauna saman sofar da Zayd ke zaune, ya kai hannu ya janyo table din gaban shi ya kai hannu ya ciro kwanonin da ke ciki da plate guda ya fara serving din kan shi ya fara ci ya na yi mata hira ta na amsa mishi a kai a kai Duk abun da su ke Zayd na sauraron su dan ba barci ya ke ba kawai dai ya lumshe idanun shi Sai da ya Kamala cin abincin tass ya cinye komai sannan ya meda kayan cikin basket ya tashi ya je dining room ya bude fridge ya dauko gorar ruwa guda sannan ya dawo inda ya tashi ya zauna ya bude ya sha ruwan Sai da ya ida sannan ya koma ya jingina a bayan sofar ya lumshe idanun ya bude a hankali ya kali Inaya ya ce " Gaskia abincin nan ya yi dadi " Shiru ta yi ta kurewa waje guda ido babu ko kiftawa " Inaya tunanin mi ki ke " ya tambayeta ya na kallon ta Nan ma shiru ba ta motsa ba Tasowa ya yi da ga jikin sofar ya kai hannu ya dan bubuga cinyar Zayd A hankali ya ware idanun shi ya taso da jikin sofar shi ma ya kali Moussa " duba ka ga, ko tunani me ta ke ? " Moussa ya fada ya na nuna mishi Inaya A hankali ya juyo kan shi ya kale ta Ta yi zugum waje guda kamar wadda ta suma Mikewa tsaye ya yi ya koma saman sofar da ke bayan ta ya zauna ya kai hannun shi ya dafa kafadar ta A razane ta dawo cikin hayacin ta , ta na sakin kara ta kai hannayan ta ta toshe kunnuwan ta ta na fadin " Ku kyale ni , ku kyale , kar ku tabani , wayo Abba na, aaaaaaaaaaaa " A rude ya sauko kassa ya riko ta da hannayan shi biyu, shi ma Moussa da sauri ya tasso ya koma gaban ta ya tsuguna ya na fadin " Inaya lafya me ya faru " Ina sam ba ta jin shi ta toshe kunnuwan ta Da karfi Zayd ya sa hannayan shi duka biyu ya riko nata ya yanye su da karfi ya sauke su kassa ya kali Moussa Jinjina kan shi Moussa ya yi sannan ya karanto ayatul kursi'u dan a tunanin shi aljanu ne gare ta Kamar da gaske ya na fara karanta, ta fara nitsuwa ta na kallon shi ta na sauke ajiyar zuciya a hankali ta lumshe idanun ta ta fada jikin Zayd Sai da ya karanta ajatul kursi sau biyar sannan ya bari ya kali Zayd ya ce " Amir ba dai aljanu ne da ita ba ? " Girgiza mishi kai Zayd ya yi ba tare da ya ce komai ba ya na rungume da ita Ya na jin ta sauke ajiyar zuciya ta ke a jere idanu a lumshe Sai da ta ji ta nitsu sannan ta bude idanun ta, ta mike da ga jikin Zayd ta na kallon Moussa Dan murmushi ta saki kafin ta mike tsaye ta ce " yaya Moussa zan koma gida " " shikenan muje na raka ki " ya fada ya na mikewa tsaye ya dauki basket din saman table ya riko hannun ta ya ce mu tafi Ba musu ta bi bayan shi su ka bar falon Shi ma Zayd mike wa ya yi ya bi bayan su a hankali dan nesa kadan da su Sai da su ka iso bakin kofar gidan sannan ya saki hannun ta ya mika mata basket din ta ya ce ta shiga Karbar basket din ta yi sannan ta ce mishi sai an jima ta shige gidan su Har ya juya zai bar wajen Cak ya tsaya ya na kallon Zayd da ke tsaye bayan shi cike da mamaki " yaushe ya biyo mu kuma ? " ya tambayi kanshi Ya na shirin magana ya riga shi cewa " shiga ka yi min magana da uncle " Ba musu ya juya ya shiga gidan ya na sallama shi kuma ya tsaya nan ya na jiran su Jim kadan Moussa ya fito , malam na bayan shi Sallama malam ya yi mishi sannan ya bashi su ka yi musbaha Sai da su ka gaisa sannan Zayd ya ce " Uncle ina son muyi wata magana " " ina sauraron ka, mi ka ke son muyi magana a kai ? " Malam ya fada ya na tsare shi da ido Ajiyar zuciya Zayd ya yi kafin ya ce " uncle ina son in san dalilin da ka aura min yarinyar nan " Nan take yanayin face din malam ta sauya ya rasa amsar da zai ba shi Ga kuma Zayd ya tsare shi da ido Wasu yawu malam ya hadiye kafin ya ce " Zayd ba zan iya fada maka ba a yanzu ka gane lokacin in ya yi za ka gane komai " " shikenan next week zan zo na dauki matata zan gano abun da ake boye min da kai na " ya na gama fadar haka ya juya ya bar wajen ya na taku cike da izza (TO FA NA MULKIN SUN FARA TASHI 🤣🥀 ) Ba karamin kwarjini ya yi ma malam ba kawai ya tsaya ya na kallon shi ya rasa me zai ce Kallon shi Moussa ya yi sannan ya ce mishi " malam zan tafi " sannan ya juya ya fara takawa Jinjina kan shi malam ya yi sannan ya fara takawa dama ya fito zai je mosque ya ji sallamar Moussa Bayan sallar isha Inaya A hankali ta ke fitowa da ke fitowa da ga cikin dakin su Ta na sanye da gown pink colour mara nauyi da hijab pink shi ma zuwa guyiwa A hankali ta ke takowa cike da nitsuwa ta ke takowa ta nufi kitchen Har ta kai kofar kitchen ta jiyo mama na magana sama sama A hankali ta juyo ta nufi kofar dakin mama dan a tunanin ta ita ka dai ce ko da ita ta ke magana ba ta ji da kyau ba Har kai kofar dakin ta bude baki za ta yi sallama ta ji Muryar malam ya na fadin " abun da ki ka ji Amina, auta dai na aurar da ita tun shekara biyu da su ka wuce kuma yanzu mijin ta ya ce ya na son ta koma gidan shi " Dumm ta ji gaban ya buga da karfi nan take idanun ta su ka kawo ruwa da gudu ta juya ta bar wajen Maimakon ta koma bedroom din su , sai ta bar gidan baki daya Gudu ta ke da iya karfin ido a rufe Da karfi ta bangaje kofar gidan shi ta shiga ta nufi wajen motar da ke cikin gidan ta buya a baya ta Zube saman guyiwowin ta ta aza kuka da karfi Ba ta fi ten minutes da shigowar ta wajen Moussa da Zayd su ka fito da ga cikin falon Su na sanye da jeans baki da t-shirt amma ta Zayd fara ce ta Moussa kuma blue Su na tsaka da tafiyar su su ka jiyo kukan mutun Cak su ka tsaya a tare su na kallon juna su na zaro idanu A hankali su ka fara bin wajen da kallo ba su ga kowa ba Cen Moussa ya ce " ko dai aljanu ne ke wannan kukan ? " Girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya fara takawa a hankali ya nufi motar shi ( WATA SABUA MAKAHO DA TUKA MOTA 🤣✌) ya na kara nufo motar sautin kukan na karuwa A hankali ya fara zagayen motar har ya iso inda ta ke Ta na zaune ta cusa kan ta tsakanin cinyoyin ta sai kuka ta ke kamar ba gobe A hankali ya tako ya zo geffen ta ya zauna shi ma sannan ya kai hannu ya dafa kafadar ta , Moussa kuma ya na tsaye gaban su A hankali ta dago kan ta cikin kukan nata fuskar ta duk ta yi jaga'jaga da hawaye Ta na daura ido saman shi ta ji wani kukan ya zo mata Da hannu ya mata allamun " minene ki na kuka ? " TO A NAN ZAN DASSA AYA SAI MUN HADU GOBE✌✌✌✌ KAR KU MANTA KU NA TARE DA ALKALAMIN ANISH ❤ ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 6 ❤🔥 Da hannu ya mata allamun " minene ki na kuka haka ? " Cikin wata disashashiyar murya ta ce " yaya Zayd wai Abba ya yi min aure " Da sauri Moussa ya ce " to mine matsalar ba ki na son wadan a ka aura miki ba " Medo da kallon ta ta yi kan Moussa cikin kukan ta ce " yaya Moussa ni fa ina da wanda na ke so , kuma ni ban ma san wanda Abba ya aura min , ni ko ma wanene ba na son shi , dan Allah yaya Moussa ka je ka same shi ka ce ya raba auren nan wlh ba ni son shi " ta kai karshen ta na meda kan tsakanin cinyoyin ta Dan satar kallon Zayd ya yi kafin ya ce " shikenan babyn malam , yanzu fada min wa ne wannan wanda ki ke so " Da sauri ta dago kai ta ce " yaya z........." kut maganar ta yanke ta zaro idanu ta na kallon Moussa Shi dai Zayd ya na zaune ya zuba mata ido ya na jiran ya ji sauran maganar in da gaske akwai wanda su ke soyayya to ya dauki niyar zai sake ta ya aura mata wanda ta ke so Ganin ta yi shiru ta tsaya sai kallon Moussa ta ke sai ya kai dan yatsun shi saitin face din ta ya kyasta mata Sai da ta dan razane sannan ta medo da kallon ta kan shi Tambayar ta ya yi minene Girgiza mishi kawai sannan ta meda shi tsakanin cinyoyin ta amma ba kuka ta ke ba wannan karan Kallon Moussa ya yi sannan ya daga mishi gera guda Jinjina mishi kai Moussa ya yi sannan ya sunkuyo gaban ta ya ce " shikenan yanzu tashi mu koma gida ko " Ba tare da ta dago kai ba ta ce " ni wlh ba inda zan je " Ya na shirin magana Zayd ya daga mishi hannu ya na girgiza mishi kai Mikewa tsaye moussa ya yi ya dan ja baya kadan Shi ma Zayd mike wa tsaye ya yi sannan ya fara takawa ya bar gidan Ta na jin ya fara takawa ta dago kai a hankali ta na kallon shi ta wutsiyar ido Sai da ta ga ya fita gidan sannan ta sake sakin wani sabon kukan Juyawa Moussa ya yi zai bar wajen sai ya dawo ya ce mata " tashi ki shiga cikin gidan tun da baza ki koma gida ba " Ya na gama fadar haka ya sa kai ya fice shi ma Cen ya hango Zayd har ya yi nisa da tafiyar shi Da sauri ya fara takawa har ya kamo shi dai'dai ya karaso kofar gidan su Inaya Su na karasowa wajen Abdoul da malam su ka fito da sauri kamar sun ga wani abun gudu Da sauri Moussa ya ce " Abdoul ina za ku je haka da sauri wani abu ya faru " Abdoul na shirin magana malam ya riga shi cewa " Inaya ce ba ta cikin gidan nan ban San inda ta yi ba " Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " ku kontar da hankalin ku , yanzu nan mu ka baro ta gidan mu, kar ku damu ba abun da ya same ta " Ajiyar zuciya malam da Abdoul su ka sauke a tare " uncle kun san da yarinyar nan ta na da wanda ta ke so " su ka tsinci Muryar Zayd ya na fada Kallon juna Abdoul da malam su ka yi kafin su kali Zayd har su na hada baki wajen cewa " ita da kanta ta fada maka hakan ? " Jinjina musu kai ya yi bai ce komai ba Dan murmushi malam ya yi sannan ya ce " yo ai wannan ba matsala ba ce dan..... " Da sauri Zayd ya katse shi da cewa " no uncle tun da ta na da wanda ta ke ni zan nemo shi in aura mata shi da kai na , baza ta ji dadin zama da mutuman da ba ta so , a karancin shekarun nan na ta bai kama ta ta shiga cikin kunci ba , dama ni ta yi min karama sosai " bai jira amsar malam ba ya juya ya bar wajen Sai da ya bar wajen sannan malam ya kali Moussa ya ce " wai maganar me ya ke yi ne haka ? " Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " wai zai saki babyn malam tun da ta ce ta na da wanda ta ke so , ku kyale shi yayi ta neman kan shi , zan koma gida sai da safe " ya juya ya bar wajen Da sauri Abdoul ya yi shirin bin bayan shi, amma malam ya riko hannun shi ya ce " nassan auta ce za ka je daukowa kyale ta, sa safe sai mu je a tare " Jinjina mishi kai Abdoul ya yi sannan ya juya ya koma cikin gidan malam ya bi bayan shi Da sallama su ka shigo cikin gidan Da sauri Nesrine da ke konce ta tada kai da cinyar mama ta na kuka, ta tasso ta tarbo malam cikin kukan ta ke cewa " Abba ina Inaya ta yi ne " Dan murmushi yayi kafin ya ce " kontar da hankalin ki, ta na gidan mijin ta " Dan zaro idanu ta yi ta na maimaita kalmar miji cikin ranta Ta geffen ta malam ya raba ya wuce ya karaso inda mama ke zaune shi ma ya zauna Shi kuma Abdoul ya wuce bedroom din shi Ya na zama Nesrine ta juyo da sauri ta nufo malam ta zo gaban shi ta tsaya ta ce " Abba wane mijin kuma, Abba Inaya fa shekarun ta 15 ina ta kai aure ko period ba ta fara ba " duk cikin kukan ta ke mishi wannan maganar ta ma manta da mahaifin ta ta ke magana Malam na shirin magana mama ta riga shi cewa " yanzu dan Allah malam ina Inaya ta isa aure me ma ta sani a kai , ka hada ta da wanda ba mu san shi ba , wanda ba son shi ta ke ba yanzu in ya je ya cutar mana da ita da wane za muji malam bibiyar da ake mana ko wannan " ta kai karshen ta na sakin kuka Da sauri Nesrine ta karaso wajen ta ta Zube saman guyiwowin ta ta rungume mama ita ma ta na sakin kuka " yanzu Amina ya ki ke son na yi kin fi son na saka ido wancen yaron ya gano inda muke ya zo ya dauke mana ita, kuma na fada miki auren ya yi wajen shekara biyu yanzu , kuma ta na son mijin na ta dan ni da kai na na tambaye ta in ta na son shi , ku yanzu a tunanin ku in Sudais ya gano inda muke ba sai ta fi shiga cikin matsa la ba dan Allah ku kontar da hankalin ba abun da zai faru da ita " ya kai karshen ya na kai hannun shi saman kafadar mama A hankali mama ta dago da ga jikin Nesrine ta kali malam ta ce " shikenan na ji abun ka fada amma ba ka fada min wanene wanda ka aura mata " Jinjina kan shi ya yi kadan sannan ya ce " ba kowa ba ne face Zayd " A dubu dari Nesrine ta mike tsaye ta na fadin " Zayd ???? " da karfi ta na zaro idanu, yanzu mutumin da ko hanya ba ta fatan ta hada su wai shi ne mijin kanwar ta, mutumin da ko gani ba ya yi kamm akwai ta " e Zayd , wanda ke zowa gidan nan wanda ku ke ma kallon makaho da kurma shi din dai " malam ya fada ya na kallon ta Cikin bacin rai mama ta ce " haba malam, wannan makaho ta ya zai iya kare mana yarinyar mu , ko shi ta kan shi ya ke , ya zai kula da ita, inda ma abokin shi Moussa ne da sauki amma Zayd ? " Mikewa tsaye malam ya yi cikin bacin rai ya ce " bara ku ji aure dai an riga da an aura ku ba bazai sake ta ba in kun ga dama ku karbe shi in kun ki ku ta matsewa " Ya na gama fadar haka ya kama hanyar dakin shi ya shige ya bar su nan tsaye Juya wa ita ma Nesrine ta yi ta koma dakin ta da gudu ta na sakin sabon kuka Ita ma mama ta juya ta koma dakin ta zuciya ba dadi Duk abun da su ke Abdoul na jin su amma ya yi banza da su ya yi konciyar shi Zayd Bayan ya koma gida kai tsaye bedroom din shi ya wuce, ga Dukan allamu ya manta da Inaya da ke cikin gidan Shi ma Moussa ya na shigo wa ya wuce kai tsaye cikin falo A tunanin shi ta na nan amma da ya shigo ya ga ba kowa a cikin falon Da sauri ya juya ya fita falon ya koma wajen da su ka baro ta Ta na nan kamar yadda ya baro ta , amma ta daina kuka sai ajiyar zuciya ta ke saukewa a hankali allamun ta yi barci Dan murmushi yayi kafin ya juya ya koma cikin gidan Kai tsaye bedroom din Zayd ya wuce Sai da ya yi mishi knocking sannan ya shiga dakin ya na sallama Ya na zaune saman gadon shi ya jingina a bayan gadon ga computer a gaban shi , ya cire wadanan glass din na shi na gado Karasowa wajen shi Moussa ya yi ya tsaya gaban shi ya ce " Amir don Allah je ka dauko babyn malam ta yi barci a wajen motar " Ba tare da ya dago kai ba ya ce " kai me ya hana ka dauko ta ? " Hararrar shi Moussa ya yi kafin ya ce " Amir ban San rainin sens ka fi kowa sani ba muharama ta ba ce bazan iya dauko ta ba , dan haka malam tashi ka je ka dauko matar ka " Dago kai Zayd ya yi ya wurga ma Moussa wani mugun kallo Shi Moussa dariya ma abun ya bashi dama da gangan ya ki dauko ta , ya zo ya tada shi ya je ya dauko ta Wani file da ke geffen shi Zayd ya doko ya tila wa Moussa Da sauri Moussa ya kwace gefe ya na dariya ya ce " to malam da ga taimako na ga dai matar ka ce ba tawa ba in ka ga dama ka bar ta a cen mutu " Ya na gama fadar haka ya juya ya fice dakin ya shiga bedroom din shi Dan kauda kai gefe Zayd ya yi ya na jan tsaki a fili ya ce " wlh sai na yi maganin ka, jarabbabe kawai " Ya na gama fadar haka ya ajiye computer din geffen shi sannan ya sauko da ga saman gadon ya fito dakin Kai tsaye parking space ya nufa inda su ka baro ta Ya na zuwa bai tsaya wani dogon tunani ba ya sa hannayan shi biyu ya dauke ta cak kamar baby ya koma cikin gidan da ita Maimakon ya wuce bedroom din shi da ita sai ya kontar da ita saman doguwar sofa sannan ya juya ya koma bedroom din shi ya ci gaba da aikin shi Washe gari Inaya Washe gari ba ta farka da ga barcin wahalar ta ba sai wajen karfe 10 na safe, ko da ta farka ta ga ba motsin kowa a cikin gidan allamun sun fita Jin hakan ya sa ta mikewa ta fara takawa ta bar falon ta fito harabar gidan Abun mamaki babu motar nan a cikin gidan, to ta ina ta fita ? Ganin ba ta da me ba ta amsa kawai sai ta sa kai ta bar gidan baki daya ta koma gidan su A hankali ta ke tafiya kamar wadda a ka zarewa lakar jiki har ta karaso gidan su Bakin ta dauke da sallama ta shigo gidan A hankali mama ta dago kan ta, ta amsa mata sallamar ta Ganin ita ce ya sa mama sakin wani dan murmushi ta ce " Auta zo nan ina son magana da ke " Ba musu ta tako a hankali ta zo geffen mama ta zauna ta na sunkuyar da kai ta na gaishe ta Sai da mama ta amsa mata sallamar ta sannan ta ce " Auta a ina ki ka kwana ? " Ba tare da ta dago kai ba ta ce " gidan su yaya Moussa " ta fada a takaice Jinjina kan ta mama ta yi kafin ta ce " Auta fada min gaskia ki na son Zayd a yadda ya ke hakan ? " Sai da ta dan doki lokacin kafin ta dago kan ta slowly ta ce " shin mama ko ina son shi ai yanzu lokaci ya kure, Abba ya aura min wani cen daban wanda ban sani ba " ta kai karshen kuka na kubce mata Ta tashi da gudu ta shige dakin su Mama sai kiran ta take amma ina sam ba ta jin ta Dama tambayar da ta yi mata dan ta tabbatar da abun da malam ya ce na ta na son mijin ta, gashi ta tabbatar amma ta lura ita Inaya ba ta san waye mijin na ta ba , ta so ta fada mata ta ki tsaya wa Jinjina kanta kawai mama ta yi ta ci gaba da yanke kayan lambun sa ke gaban ta ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 7 ❤🔥 Bayan ta shiga bedroom din su , kai tsaye saman gadon ta Haye ta yi rub da ciki ta na sakin sabon kukan Ta na shiga bedroom din su Nesrine ta shigo gidan ta na sallama hannun ta rike wasu ledodi allamun mama ta aike ta cepane , amma duk yanayin face din ta babu alamun fara'a a cikin Inda mama ke zaune ta karaso ta zauna ta na ajiye ledodin gaban ta sannan ta ce " mamwawai har yanzu Inaya ba ta dawo ba ? " Murmushi mama ta yi kafin ta ce " hmmmm ta dawo ta na cikin dakin ku " Da sauri Nesrine ta mike ta nufi dakin su da gudu Kallon ta mama ta yi ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " ke ma Allah ya ka miki mijin auren in rabu da wannan shirman naki " Nesrine kuma ta shiga dakin su ba budurwa ko sallama ta hango Inaya konce saman gado ta yi rub da ciki sai kuka ta ke A hankali ta tako ta karaso bakin gadon ta zauna ta kai hannu ta, ta dan bubugi kafar Inaya Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya a hankali ta mike zaune ta kai hannu ta dauki pillow din ta , ta rungume shi a kirjin ta ta na kallon Nesrine Dan murmushi Nesrine ta yi kafin ta kai hannu kan face din ta , ta goge mata hawayen ta sannan ta ce " haba sister di na, na miye kuka kuma ? " Hadiyar zuciya Inaya ta yi kafin ta ce " Nesi wai fa ki na ji Abba aure ya yi min , ni fa wlh ina da wanda na ke so ba ni son wadan aka aura min " ta kai karshen ta na boye face din ta cikin pillow " sannu malama yanzu har kin San minene so ? " Nesrine ta fada cikin sigar zolaya Dago kan ta ta yi ta wurga mata hararra Yar dariya Nesrine ta yi kafin ta ce " shikenan yi hakuri ai ni dama sai da na fada miki , ba wadda za ta iya son wacen makaho ga shi kuma kurma am........." Ba ta ida maganar ta ba Inaya ta katse ta da cewa " wai dan Allah me ya yi miki a duniya da ki ka tsane shi haka, na ga bai taba shiga harkar ki ba , ko gaisuwa ba ta taba shiga tsakanin ku ba amma kin dauki tsanar duniyar nan kin daura mishi, in ke baki son shi toh wlh akwaye ma su son shi dayawa a duniya ciki har da ni " Ta na gama fadar haka ta tila pillow din hannun ta gefe sannan ta diro da ga saman gadon ta fice dakin Ta na fita Nesrine ta rike habar ta ta ce " yanzu fa ta ce ba ta son shi amma wai shi har da kare shi yanzu ko a tunanin ta ita kadai ke iya cewa ta na son shi ko ba ta son shi " Dan tsaki ta ja sannan ta mike ta fito dakin Ta dawo inda mama ke zaune ta zauna ta na tsuke fuska ta ce " wai wannan yarinyar minene matsalar ta , yanzu fa ta ce ba ta son yaya Zayd, yanzu kuma za ta sake cewa ta na son shi " Yar dariya mama ta yi kafin ta ce " kyale ta haba ina ga ba ta san da shi ne Abba ya aura mata " Kauda kai gefe Nesrine ta yi ta na tsaki ta ce " yanzu dan Allah mama haka za mu zuba ido mu na kallo Abba ya bawa wacen makahon auren Inaya, yanzu da wane ido zai kula da ita , da wane bakin zai yi mata magana ni fa gaskia ban yarda da hakan ba " " toh Nesrine ya za ki yi na ga ba ki da izinin raba auren nan , ko kin ki, ko kin so Inaya matar Zayd ce , ni gwara ZAYD din ma da wancen dan iskan Sudais , ko ba komi ya na da tarbiya da kyawawen halaye kuma nakassar shi bai sa ya zama rago ba, ki na gani tun safe ya ke fita ya tafi aiki duk da baya gani da kan shi ya ke neman abincin shi, to me ya fi wannan ka ci halal din ka , ko wa ya na maka shedar mutumin gwarai, bara ki ji , ni wlh ko da ya fi makaho da kurma, zan aura mishi Inaya dan na san zai kula da ita duk da ba mu San assalin shi ba shekara hudun nan da mu ka yi da shi ya isa ka gane shi wane irin mutun ne " " hmmmm yanzu kennan mama kin yarda da auren nan, autar ta mu guda za a dauka a bawa kurma, makaho wanda bai ma san da me ta ke kama ba " Yar dariya mama ta yi kafin ta ce " to ina ruwan Allah da wannan ai zuciyar mutun ya kamata ki duba , sai ki ga mutun kamar shi ya yi kan shi dan kyau amma zuciyar a bushe ta ke kamar kafiran farko, amma sai ki ga wanda bashi da kyau ya na da zuciya mai kyau tsarkakiya, ke yanzu a ganin ki Zayd bai fi Inaya kyau ba kuma a hakan ya yarda ya aure ta , duk da bai gan ta ba kin ga wannan auren na su ya ishe ki ishara Allah ba ya barci , kaddara ce kawai ta hada su , amma ba dan haka ba ni na san inda zayd na da cikakiyar lafya wlh ko inda ya taka ba ki kai ki taka ba " Nesrine na shirin magana Inaya ta fito da toilet, ta wuce bedroom din su ko kallon inda su mama su ke ba ta yi ba Dan zaro mama ta yi ta na girgiza kai sannan ta ce ma Nesrine " kin ga tashi ni ki yi min aiki na " Da to Nesrine ta amsa mata sannan ta tashi ta shiga kitchen A takaice ranar yau Inaya a cikin bedroom din su ta yi ta, ko harabar gidan ba ta leko ba, abinci ma sai Nesrine ta kai mata daki su ci , abu guda ke fido ta sallat , Zayd kuma yau tun safe da su ka bar gidan shi da Moussa har bayan sallar isha ba su dawo ba Washe gari Yau ta kama ranar monday, tun karfe 6 Nesrine da Inaya su ka tashi su ka yi duk wani aiki na gidan sannan su ka shirya sai karfe 7:30 su ka bar gidan su ka kama hanyar college Tun bisa hanya Nesrine ke yi ma Inaya magana amma ta kyale ta ko kallon ta ba ta yi ba Sai da abun ya bawa Nesrine haushi ta daina mata magana ma Har sai da su ka iso AMINU KANO COLLEGE OF EDUCATION sannan ko wace ta wuce class din ta 11pm Zaune ta ke cikin cafeteria din school din , ta na rike da book , ga bottle drinks nan a gaban ta saman table ta na karatun ta cikin konciyar hankali Ta na a haka wasu yan mata guda biyu su ka zo table din ta su na mata sallama Ko dago kai ba ta yi ba ta kale su amma ta amsa musu sallamar su cen kassan makoshi Dayar na mini skert da yar t-shirt colour din uniform din college din babu hijab a jikin ta sai wani dan karamin veil da ta nada a kan ta , ta yi simple make up Dayar kuma ta na sanye da uniform din ta kamar na Nesrine wato wando da riga zuwa guyiwa da hijab zuwa kirji , ta na rike da hand bag guda biyu Wadda ke sanye da mini skert din ta ja chair din da ke fuskantar ta Nesrine ta zauna sannan ta kai hannu ta karbe book din hannun ta ta na fadin " me ki ke karantawa ne haka ? " Hararrar ta Nesrine ta yi kafin ta mike tsaye ta tatare kayan ta sannan ta mika wa yarinyar hannu ta ce " ban Boko di na dan Allah zan koma class " Mikewa tsaye yarinyar ta yi ta ce " haba Nesi me ya yi zafi haka " " kin ga Ramatou ki ban book di na, sannan kuma sunana Nesrine ba Nesi ba " Dayar yarinyar da ke tsaye ta ce " tooo ! Me ya yi zafi haka ? " Cikin fushi Nesrine ta kale ta ta ce " kin ga Halima ban sanyo da ke ba " Dariya yarinyar da ta kira da RAMATOU ta yi kafin ta ce " yanzu wannan fushin Nesi duk dan Hafiz ya miki fada ne jiya ? " Dawo da kallon ta kan RAMATOU ta yi sannan ta ce " kin ga ko wlh tun wuri ki ce mishi ya fita da ga harka ta , ba ni son shi , in kuma ya matsa na sa yaya na ya yi mishi dan banzan duka " Dariya RAMATOU ta yi har da dafe ciki sannan ta ce " to sai mi in kin fada mishi me zai yi , wlh ko karar shi ya kai gaban yan sanda ba abun da za ayi mishi dan haka tun wuri gwara ki karbi soyayyar shi, ni ban ma ga abun so cikin dirty girl irin ki ba , ni ko abotar da mu ke kawai dan ki na temakamin ne ina samun good grades ba dan haka ba ko kallo ba ki ishe ni ba , ke ba ki san yan mata nawa ne ke biyar yaya na ba da sunnan soyayya amma ya ki dan ya ce ya na son ki shi ne za ki wani ja mishi aji, yar rainin sens kawai, sannan ki ji yaya Moctar ya ga kanwar ki kuma ya ce ya na son ta , na fada mishi gaskiyar sunnan ta da kuma karyar da kika yi mishi na cewa hanya ce kawai ta hada ku wlh idan ki ka matsawa Inaya ta ce ba ta son shi " ta kai karshen ta na kyasta mata dan yatsun ta saitin fuskar ta Cike da izza ta ce " to wlh ki kuka da kan ki " Ta na gama fadar haka ta tila mata book din ta a fuska sannan ta juya ta bar cafeteria din Halima na biye da bayan ta Su na barin wajen Nesrine ta koma ta zauna ta daura kan ta saman table din sannan ta saki kuka kassa kassa Sai da a ka koma cikin class sannan ta tashi ta fara shiga toilet ta wanke face din ta sannan ta wuce class Nassan kowa ya na son ya ji wanene Hafiz , to nima ina son ji 😂✌ Hafiz dai babban d'a ne ga governor din Kano, Moctar na bi mishi sannan Ramatou sai autar su Nabila , a shekaru zai kai 25 , Moctar kuma 21 , Ramatou 19 years sai Nabila da baza ta wuce 15 years ba Tun bayan mahaifin shi ya zama governor wata izza da jiji da kai su ka saukar mishi Duk abun da ya gani ya ce ya na so to sai ya same shi ko da ta karfi ce Ga shi ba ya da mutunci ko kadan mahaifin nashi ma in ya bata mishi rai sai ya bishi kaca'kaca dan ba raga mishi ya ke ba Tun haifuwar Nabila mahaifiyar su ta rasu , mahaifin na su ya sake aure har wajen sau uku Amma duk wadda ya auro ba ta one month ta ke barin gidan sakamakon Dukan tsiyar da Hafiz ke yi musu Mahaifin shi na sane amma ya ki yi mishi magana dan ya san ba karamin aikin Hafiz ne ba shi ma ya rufe shi da duka Shi ya sa ya ja bakin shi ya yi shirin ya zuba mishi ido dan ya fi karfin shi Duk wata badakala sa ya ke yi mahaifin shi na sane , sannu sannu har ya fara janyo Moctar cikin badakalar ta shi Kullum su ne tafiya nightclub, ga shan giya da kayan maye À takaice ba abun da ba su sha, sai dai ba su taba kusantar mace ba da sunnan Zina Karewar zancen Nesrine da Inaya su ne mata na farko da su ka gani su ka ji su na son ta Yadda a ka yi Hafiz ya hadu da Nesrine Wata rana ce driver din Ramatou bai zo daukar ta ba sai ta kira Moctar a kan ya zo ya dauke ta A lokacin su na tare da Hafiz Da su ka iso school din , su na tsaye bakin gate ita da Nesrine Tun da Hafiz ya daura ido saman ta ya ji ya na son ta Sai bayan sun koma gida ne ya ke tambayar RAMATOU wacece wanan yarinyar da su ke tare Nan ta fada mishi wacece Nesrine sai dai ba ta fada mishi ba ta na da kanwa Goben shi tun karfe 7 ya je bakin gate fin school din ya jiran ta Amma wani ikon Allah ranar nan Nesrine ba ta zo school ba Sai da ya gama tsayuwar shi ya gaji sannan ya koma gida , Goben shi ma haka ya dawo school din Wannan karan ta zo amma ta na baya dan Inaya ta riga ta fitowa shi ya sa a bai gane Inaya kanwar ta ba ce Babu ko sallama ya kira ta cike da girman kai Kallo guda ta yi mishi ta gane yayan Ramatou ne dalilin da ya sa ta fara sakin mishi fuska Sannu sannu ta fara ganin halayan shi na gaskiya Kullum sai ya zo college din su dan ya gan ta Wata rana har waya mai tsada ya kama ta amma ta ki karba Haka kuma ba karamin bata mishi rai ya yi ba har ya tsinka mata mari cikin fushi sannan ya bata wayar da karfi ya ce zai kire ta Inda ya ajiye wayar nan ta bar ta ta yi tafiyar ta ko wa ya dauke ta oho ! Washe gari bayan ta zo school ya isko ta ya ke tambayar ta ina wayar da ya bata Nan ta mishi karyar wai Mamar ta ta gan ta kuma ta amshe ta Bai yi mata magana ba kawai ya bar school din , sai da ya yi wajen sati bai zo ba Nan Ramatou ta zo ta hura mata kunne a kan Hafiz tsakani da Allah ya ke son ta ta daure ta ringa kula shi ko ya ji dadi Abotar da ke tsakanin su ya sa ta yarda da zancen ta, dan ko ba komi yayan ta ne bai kamata ta wulakan tashi haka ba Sannu sannu ta fara kula shi har ta fada soyayyar shi Amma shi kuma ya na nan kamar dai kullum, bai sauya ba sam dan wani lokaci in ta bata mishi har marin ta ya ke wai a haka wai ya na son ta ( ni dai na ce humm) Babu irin gift din da bai kama ta ba amma ko wane lokaci sai dai ta yarda shi tsakar hanya ko kuma ta bar shi nan inda ya bata shi Sannu har soyayyar da ke mishi har ta fita zuciyar ta dan a ganin ta, Hafiz ba al'heri ba ne a rayuwar ta shi ya sa yanzu ta daina kula shi, shi kuma hakan ba karamin zafi ya ke mishi ba TO KUN DAI JI WANENE HAFIZ DA KUMA ABUN DA KE TSAKANIN SHI DA NESRINE ✌ ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 8 ❤🔥 Zayd Zaune ya ke cikin motar su wajen mai zaman banza ya na rike da wayar shi ya na latsa wa ya na sanye da tracksuit sky blue colour ya na sanye da wadanan bakin glglass din nashi na gado Yayin sa Moussa shi kuma ke tukin, ya na sanye da Jeans baki da t-shirt Red colour Su na a haka Moussa ya katse shirun na su da cewa " wai Amir ka fada ma babyn ka za ka yi tafiya ne ? " ya kai karshen ya na dan satar kallon shi Shiru bai amsa mishi ba ko dago kai bai yi ba ya ci gaba da aikin shi Dan murmushi geffen fuska Moussa ya yi sannan ya ce " Amir wai me ya sa ba ka kula yarinyar nan " Ba tare da ya dago kai ba ya ce " meye ruwan ka a ciki ? " " babu kawai gani na yi bai dace abun da ka ke mata ba, ka ga fa kallon makaho da kurma ta ke maka ba ta san kai ainahin wanene ba, ba ta san kowa na ka ba, ko cikeken sunnan ka ba ta sani amma a haka ta ke son ka " A dubu dari Zayd ya dago kai ya kali Moussa ya ce " me ka ke son cewa ? " Yar karamar dariya Moussa ya yi kafin ya ce " lalle ma ka cika dan rainin sens, yanzu ka na son ka ce min duk soyayyar da ta ke maka ba ka ganin komai, lalle ma yau ka cika babban makaho " ya kai karshen ya na sake bushewa da dariya " wait ! Maganar me ka ke yi haka, wannan baby har ya san minene soyayya ? na ga ai gaban ka ta ce dakwai wanda ta ke so " ya kai karshen ya na medo da kallon shi kan wayar hannun shi ya ci gaba da aikin shi " humm wai kenan ba ka gane ba da sunnan ka ne ta so fada ba, dan ka na wajen ne ya sa ta yi shiru , kai a ganin ka duk abun nan da ta ke ma da sunnan makobtaka ne kawai, no Amir ! Wlh pure love ne ta ke yi maka, kallo guda za ka yi mata ka gane soyayyar ka a idanun ta, nassan wadanan bakin glass din ya hana ka gani, Amir kai ka ce min ka na son ka manta rayuwar ka ta baya , to wannan damar ka ce , ka karbi matar ka , and found your family " Shiru Zayd ya yi bai ce da shi komai ba amma cikin ranshi ya na tunanin kalmomin Zayd tabass wanda ke maka kallon makaho da kurma , kuma a hakan mutumin ya so ka ya tabbata soyayyar gaskia ya ke maka " no ! Gaskia she is to small for me , wannan ko dauko ta ba na tunanin za ta iya bare har a yi tunanin wata familyn, gaskia ban yarda da abun da Diya ke fada ba " ya fada cikin zuciyar shi Cen kuma wata zuciyar ta ce mishi " in ta tabbata yanzu kai ma ka na son ta ? " Da sauri ya girgiza kan shi ya ce " no ! Impossible i can't do that " Kallon shi Moussa ya yi kafin ya ce " what you can not do ? " Dago kai ya yi ya kali Moussa sannan ya ce " nothing ! " sannan ya meda bayan ya jingina a bayan kujerar shi ya lumshe idanun shi Daga kafadun shi Moussa ya yi irin ban damu ba cikin ranshi ya ce " in ta yi tsami ma ji " Haka su ka ci gaba da tafiyar su ba wanda ya ce ma wani ufan har su ka isa inda za su je Inaya Konce ta ke saman bed din su ta na kallon ceiling ta daura hannu daya saman ciki dayan kuma saman gashin ta, ko tunanin mi ta ke oho ! Ta na a haka malam ya shigo dakin ya na sallama Ba tare da ta motsa ba ta amsa mishi sallamar mishi Bakin ya karaso ya zauna sannan ya kai shi ya daura saman nata ke saman cikin ta ya ce " auta, wai me ya ke damun ki ne tun shekaran jiya na lura yanayin duk ya sauya ko waje na da ki ke zuwa kin daina ko laifi na yi miki ? " A hankali ta janye hannun ta , sannan ta juya ta bashi baya sai ta ce " Abba me ya za ku min aure ba tare da na sani ba, nassan ku na ikon yin hakan amma Abba ni ba ni son wanda a ka aura min , gaskia Abba a raba auren nan " " dalilin da ya sa wacen ranar na tambaye ki in kina son shi , amma ba ki ba ni amsa ba ki ka tashi ki ka tafiyar ki " " ni Abba ba ku tambaye ni in ina son shi ba , " " to shikenan yanzu bara na sake tambayar ki , ki na son Zayd ? " Da sauri ta ce " ina son shi , duk da ban san meye so ba amma har cikin raina na ke jin shi , amma gashi yanzu kun rabu har abada Abba ya zan yi na cire son shi a cikin raina " ta kai karshen kamar ta yi kuka Dan murmushi yayi kafin ya ce " to ai ba sai kin cire son shi ba a ran ki ba " " Abba ya zan je gidan wani ina son wani kuma, ni gaskia Abba ba ni son wanda a ka aura min , ko da ba za ku yarda na auri yaya Zayd dan Allah Abba kar ku aura min wanda ba ni so " " na ga yanzu ki ka ce ki na son ya kuma za ki juya zancen " Kuka ta saki ta fara harba kafafun ta kamar karamar yarinya ta ce " ni Abba ba shi ba na ce na ke so " Yar dariya ya yi dan da gangan ya ke jan mata rai Sai da ya ida dariyar shi sannan ya ce " to shikenan wanene ki ka ce ki na so ? " " yaya Zayd " ta fada cikin kukan nata Hannun shi ya kai saman kafadar ta sannan ya ce " yo ai ni ma shi ni ke cewa, shi ne wanda na aura miki , amma tunda ba ki so zan kira shi in ce ba ki son auren " ya kai karshen ya na janye hannun shi da ga saman kafadar ta ya mike ya zai bar dakin Har ya kai bakin kofar ya jiyo Muryar ta ta na fadin " sa gaske Abba yaya Zayd ku ka aura min ? " A hankali ya juyo ya na kallon ta Ta na zaune tsakiyar gadon ta na kallon shi idanun cike da hawaye Jinjina mata kai ya yi sannan ya sa kai ya fice dakin Wani irin sanyi ne ta ji cikin zuciyar ta lokaci guda ba ta san lokacin da wani kyakyawan murmushi ya kubce mata ba har da wata yar karamar dariya Ta dauko pillow ta boye fuskar ta, ta na dariya ta koma ta konta After one week Kwana biyar bayan Malam ya fada mata cewa Zayd ne mijin na ta, ya dawo da ga tafiyar da ya yi, a ranar nan kuma a ka kai Inaya dakin mijin ta , tun bayan ta koma gidan shi har yanzu ba ta daura ido saman shi ba, kullum a falo ta ke kwana saman sofa sai in ta na bukatar yin wanka ko alwalla sannan ta ke tashi ta shiga bedroom din shi ta wuce toilet ta yi Duk kayan ta su na cikin trolley din ta dama ba wasu kaya dayawa ba gare ta gashi ko lefe ba a yi mata ba Bangaran Nesrine kuma kullum in ta je school sai Hafiz da Moctar sun saka ta gaba a kan ina Inaya amma sai ta ce musu ta koma gidan mijin ta Nan Moctar ya tada tarzoma a kan karya ta ke ya bar college din cikin fushi shi da Hafiz Tun ranar ba su sake dawowa college din ba Abun da ba ta sani ba kullum sai sun zo , sun buya sai in an sauka su ke bibiyar ta amma kullum ita kadai ke tafiya gida har Hafiz ya fara gajiya ya kyale Moctar ya ci gaba da bibiyar ta shi kadai dan shi ya kwalafa rai sosai a kan Inaya Misalin karfe 5 na yamma Inaya Zaune ta cikin falon gidan ta buga uban tagumi kamar ta yi kuka ita kadai cikin gidan Ta na a haka ta ji a na sallama A hankali ta dago kan ta, ta amsa sallamar Zayd ne da Moussa su ka shigo gidan ko wane ya na rike da ledodi Ta na ganin su ta saki murmushi ta ce " sannu da dawowa " Moussa ne ya amsa mata ya na murmushi ya na takowa ya ajiye ledodin hannun shi saman sofa sannan ya zauna saman sofar da ke fuskantar ta ta Shi ma Zayd takowa ya yi ya ajiye ledodin hannun shi saman table sannan ya zauna geffen Moussa ya jingina a bayan sofar ya daga kai ya lumshe idanu shi ta cikin glass din shi Murmushi ta yi kafin ta mike ta nufi dining table ta bude fridge ta dauko jug na ruwa ta ajiye saman tray da glass biyu Sannan ta dauko tray ta komo falo , ta ajiye shi saman table ta zuba ruwan cikin glass ta mika wa Moussa Karba ya yi ya na murmushi ya yi mata godiya Har ta dauki guda glass za ta zubama Zayd Moussa ya yi saurin cewa " bari ba sai kin zuba mishi ba azumi ya ke " Dago kai ta yi ta kaleshi sannan ta saki dan karamin murmushi sannan ta mike ta koma saman sofar da ta tasso ta na sunkuyar da kai Ta na zama ko , Zayd ya mike tsaye ya nufi corridor ya shiga bedroom din shi Da kallo su ka raka shi ita da Moussa har sai da ya shiga bedroom din shi sannan ta kali Moussa ta ce " yaya Moussa ina ganin yaya Zayd ba ya so na " Dan murmushi yayi kafin ya ce " haba babyn malam ya isa ma ya ce ba ya son ki kawai aiki ne ya yi mana yawa kwanan nan shi ya sa ki ka ga ba ma yawwan zama gida " Jinjina mishi kai tayi sannan ta sunkuyar da kai ta fara wassa da dan yatsun ta Dan murmushi yayi kafin ya matso bakin sofar ya kai hannu ya dauki ledodin da su ka zo da su sannan ya mike ya tako gaban ta ya ajiye mata su sannan ya ce " Ga tsarabar ki nan, sannan ki shirya gobe za ki koma school " Da sauri ta dago kai ta kaleshi ta ce " yaya Moussa school fa ? Yaya Zayd ya yarda ? " Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce " yes ya yarda mana shi da kan shi ya je ya sayo miki sabon uniform , da sauran abubuwan da za ki bukata " Da sauri ta mike tsaye ta na tsale ta na dariya kamar karamar yarinya Shi dai Moussa ya tsaya ya na kallon ta ya na murmushi " she is si innocente " ya fada cikin ranshi dai'dai lokacin da ya ke juya wa zai shiga corridor Har ya yi nisa ya tsinci Muryar ta ta na fadin " nagode yaya Moussa " Ba tare da ya juyo ba ya ce " ba ni ya kamata ki yi ma godiya ba " Ya na gama fadar haka ya ci gaba da takawa ya nufi bedroom din Zayd Bai mishi knocking ba kawai ya wuce bedroom din kai tsaye ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 9 ❤🔥 Zayd Ya na zaune bakin gadon shi ya na rike da wayar shi amma ya cire bakin glass din shi Geffen shi Moussa ya tako ya zauna sannan ya ce " Amir ! " Ba tare da ya dago kan shi ba ya ce mishi " uhmm ? " " Amir na yi tunanin maganar da na yi maka za ka saurare ni , wai me ya sa duk abun da na fada maka in dai ba ka niya ba baza ka yi shi ba , yanzu sati guda da ka je gidan su yarinyar nan ka dauko ta amma ko kalma daya ba ka taba ce mata ba , ka ce min akwai binciken da ka ke son yi a kan ta, in ba ta zauna kusa da kai ba ta ya za ka yi binciken , Zayd wlh ba na jin dadin abun da ka ke mata , shin minene laifin ta a ciki, ka na ga karama ce sosai ko ba za ka iya soyayya da ita ba ka kula da ita a matsayin kanwar ka mana " Shi dai Zayd ko dago kai bai yi bare ya ce mishi wani abu Sai da ya gaji da zubar shi sannan ya ce " Amir ina son in san dalilin da ya sa aka aura maka ita " Wannan karan sai da ya dago kai slowly ya kale shi kafin ya ce " a kan hakan ni ke bincike " Dan zaro idanu Moussa ya yi kafin ya ce " ban gane ba kawai malam zowa ya yi ya ce ka aure ta kai kuma ka yarda ? In da ba ka son ta na minene za ka yarda " Ajiye wayar hannun shi ya yi saman bedside drawer sannan ya juyo da kyau ya kali Moussa sannan ya ce mishi " ba haka ba ne , shekara biyu baya , lokacin ka tafi Abuja dibo company , dai'dai na fito da ga cikin gida na hadu da malam ya na tafiya da sauri ko kallon gaban shi ba ya yi, a haka har ya kai min karo ya yi baya zai fadi , bayan na taro shi ya na yi min godiya kuka ya kubce mishi har da hawaye, na yi matukar mamaki ya babban mutun na kuka haka kamar karamin yaro , na so na ki dalilin kukan na shi , sai na ja hannun shi mu ka shigo gidan nan na zaunar da shi sannan da hannu na tambaye shi minene ya ke kuka nan ya ke ce min " Zayd kashe min auta ta za su yi yanzu shekara biyu ina boye ta amma ina ji a jiki na wannan karan sai sun gano mu ban San ya zan yi ba " ni sam ban gane abun da ya ke nufi, sai na tsaya ina kallon shi ina son in karanci abun da ya ke nufi, sai da ya ida kukan shi sannan ya riko hannu na ya ce min " don Allah Zayd ina son in roke ka wata Alfarma " jinjina mishi kai na yi , ina kallon shi ya mike tsaye ya dawo gaba na ya zube saman guyiwowin shi ya ce min " don Allah Zayd ina son ka auri Inaya " a rude na mike tsaye ina fadin " what aure ? " mikewa malam ya yi ya na zaro idanu ya na kallo na ya ce " Zayd, dama ka na magana ? " ban amsa mishi tambayar shi ba na ce " uncle yi hakuri gaskia babu aure a sha'anin rayuwa ta bare kuma wannan yarinya ta yi min kannan ta " komawa ya yi ya zube saman guyiwowin shi ya riko kafafuna ya roke ni da na yarda na aure in ba haka ba komai zai iya faruwa da ita kuma duk abun da ya faru da ita da hannu na a ciki tun da na samu damar ceton rayuwar ta amma na ki duk ya bi ya kashe min jiki ba yadda zan yi na yarda , a ranar a ka aure na da ita, limamin massalaci ya zama waliyi na, shi kuma malam na ta na biya sadaki a ka aura mana aure , duk lokacin da na tambayi malam dalilin da ya sa a ka aura min ita sai ya ce min in bari in lokacin ya yi zan sani , dalilin da ya sa na ce yanzu ta dawo gaba na na dinga ganin ta ko zan gano dalilin da ya sa malam ya aura min ita " ya kai karshen ya sauke ajiyar zuciya ya dan lumshe idanun shi dan ba karamar wuya ya sha ba wajen yin wannan maganar duka Jinjina kan shi Moussa ya yi kafin ya ce " yanzu me ka ke tunani a kai ? " " duk yadda a ka yi akwai wanda ke bibiyar rayuwar ta , ka manta ranar nan ta na zaune ta fara sakin kara kamar wadda a ka dauke da karfi , wai ba ka lura da wasu abubuwa da ta ke kamar mara hankali " Dariya Moussa ya yi kafin ya ce " O'O kenan ka na lure da duk wane abu da ta ke " " of course ba matata ba ce " ya fada a takaice ya na mike wa ya wuce toilet Da kallo Moussa ya raka shi har sai da shiga toilet sannan ya ce " matar ka ko , to za ka ga yadda zan yi wufff da ita dan rainin hankali " Sai da ya ida sambatun shi sannan ya mike ya fice ya koma bedroom din shi Bai jima da fita ba Zayd ya fito da ga cikin toilet ya yi Alwalla sannan ya fito dakin kai tsaye corridor ya baro ya shigo falo ta na nan zaune saman sofa ta na kallon Tv Har ya yi gaba zai wuce ya tsaya cak a hankali ya juyo ya zuba mata ido Ta na zaune waje guda kamar kungi ko kifta ido ba ta yi Slowly ya tako ya tsaya gaban ta ya dan sunkuyo ya na kallon face din ta Ko motsi ba ta yi kamar wanda ya suma Yatsun shi biyu ya kai saitin face din ta ya kyasta mata Da karfi zuciyar ta ta buga ta yi baya ta fadi konce saman sofar ta na nunfashi sama sama idanu a lumshe Shi duk ya bi ya rude ya rasa mai zaiyi ya tsaya kawai ya zuba mata idanu Sannu sannu nunfashin ta ya fara dawowa dai'dai A hankali ta bude idanun ta ta na kallon ceiling din falon A haka Moussa ya fito ya same su Ya na ganin su a haka ya saki murmushi cikin ranshi ya ce " me kuma ka yi ma y'ar mutane ? " Ya na gama fadar haka ya karaso geffen Zayd ya tsaya ya kale shi ya ce " Amir lafya wani abu ka yi mata ? " Girgiza mishi kai Zayd ya yi ba tare da ya ce komai Medo da kallon shi kan Inaya ya yi kafin ya kira sunan ta " Na'am " ta amsa mishi ta na kallon ceiling din " me ya faru ne ? " ya tambayeta ya na lekon face din ta A hankali ta fara kokarin dagowa ta gyara zaman ta sannan ta ce " yaya Moussa yi na yi kamar an danne min zuciya, duk ta yi min nauyi " Murmushi kadan Moussa ya yi kafin ya ce " shikenan ba komai har yanzu ki na jin hakan ? " Girgiza mishi kai ta yi kafin ta dago kai a hankali Idanun ta ba su sauka ko ina ba sai cikin nashi, shi ma ita ya ke kallon ta cikin bakin glass din shi Da sauri ta sunkuyar da kan ta ta takure waje guda Kai a sunkuye ta ga ya miko mata hannu Da sauri ta dago kai ta kaleshi ta na son ta yi magana amma ta ki fitowa A hankali ta medo da kallon ta kan hannun shi kafin ta dago nata slowly ta daura a saman na shi Dum zuciyoyin su su ka buga lokacin guda , dalilin mi ? Oho su kadai su ka sani Ta na daura hannun ta, ya janyo ta ta mike tsaye sannan ya juya su ka fara tafiya a hankali ya na rike da hannun ta Sai da su ka shiga bedroom din shi sannan ya saki hannun da hannu ya mata allamun " ki shiga ki yi Alwalla ki yi sallat sai ki konta " ( WAI DAMA ANA MAGANA DA HANNU 🤔🤔 ) Jinjina mishi kai tayi ba tare da ta ce komai ba Juya wa ya yi ya fara takawa har ya kai bakin kofar dakin ya tsinci Muryar ta, ta na fadin " a dawo lafya yaya Zayd ! " Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya juyo ba ya ci gaba da tafiyar shi Ya na fita ita ma ta juya ta shiga toilet din Shi kuma ya na fitowa ya tardo Moussa zaune saman sofa ya na latsa wayar shi Ya na ganin shi ya saki murmushi ya ce " na dauka , ka na cen ka cin angoncin ka ka kyale ni nan " Dan tsaki ya ja ya ci gaba da takawar shi zai bar falon Dariya Moussa ya yi kafin ya mike ya bi bayan shi da sauri Su na fitowa harabar gidan Moussa ya kaleshi ya ce " Amir ka gano abun da ke damun ta ne ? " Sai da su ka fita gidan sannan ya ce " na gano nan gaba " Jinjina mishi kai kawai Moussa ya yi su ka ci gaba da tafiyar su har su ka isa mosque Basu dawo gidan ba sai bayan sallar isha, nan su ka isko ta gyara gidan tsab sai kamshin turare ya ke , har da abinci ta girka musu ta jera komai saman dining table Kallon Zayd Moussa ya na murmushi ya ce " kai da ka cewa mu wuce restaurant mu sayo abinci, madam har ta shirya mana ashe " Kauda kan shi gefe Zayd ya yi sannan ya ci gaba da takawa ya shiga corridor ya wuce bedroom din shi Nan ma wajen a gyare ya ke sai tashin turare ya ke , ta share ko ina ta goge ta canja mishi bedsheet Sai da ta gyara komai sannan ta yi wanka ta sauya kaya ta Haye bed din ta konta Dan karamin murmushin geffen fuska ya yi sannan ya juya ya bar mata dakin dan ba ya son tada ta Falo ya fito nan ya ga Moussa saman dining table sai cin abincin ya ke Chair din da ke fuskantar tashi ya ja ya zauna sannan ya fara serving din kan shi dan shi ma fa yunwar ya ke ji , ya na iya jure komai a duniya amma banda yunwa shi ya sa duk irin fushin da zai yi bazai yi fushi da abinci ba Bayan ya yi serving din kan shi ya deba a spoon ya kai baki Sai da ya dan zaro idanu lokacin da ya ji taste din abincin, ba karamin dadi ya yi mishi ba Duk abun da ya ke Moussa na kallon shi ta kassan ido, cikin ranshi ya ce " tukunna ma sannu sannu sai ta mamaye wannan zuciyar ta ka ta dutse " Haka su ka ci gaba da cin abincin ba wanda ya ce ma wani kala har sai da su ka ida su ka sha ruwa su ka daura da juice sannan Moussa ya riga shi cewa " Amir gaskia da ga yau na daina cin abincin restaurant baby na zai dinga girka min " Kallon shi da kyau Zayd ya yi kafin ya ce " wane baby kuma ? " Dariya sosai ya yi sannan ya mike tsaye ya tatare dishes din ya gyara wajen ya meda su kitchen sannan ya dawo ya wuce falo Sai da ya zauna sannan shi ma Zayd ya taso ya shigo falon ya zauna ba wanda ya ce ma wani ufan har sai da Moussa ya koma bedroom din shi ya bar Zayd nan a falon Misalin karfe 12 na dare Ya na konce saman doguwar sofa ya daura hannun shi guda saman goshin dayan kuma saman ciki ya lumshe idanun shi Ya na a haka ya jiyo takun mutun, a hankali ya ware idanun shi dan dama ba barci ya ke ba kawai ya lumshe idanun shi ne A hankali ya dago kai ya kali saitin da ya ke jin takun mutun din Sai da ya dan zaro idanu ganin ta , ta na tafiya a hankali idanu a rufe Ya na kallon ta har ta shiga kitchen Da sauri ya mike ya bi bayan ta , ya na shiga kitchen din ya gan ta rike da wuka ta na shirin caka ma kan ta Dan zaro idanu yayi a dubu dari ya yi kan ta ya karbe wukar har sai da ta dan yanke shi , dan rumtse idanun kadan ya yi ya sake budewa a kan ta Ta na tsaye waje guda sai tangal tangal ta ke ido rufe " wai me ya ke damun yarinyar nan ' ya fada cikin zuciyar shi A hankali ya kai hannu ya dauke ta cak kamar baby ya juya ya baro kitchen din, kai tsaye bedroom din shi ya meda ta ya kontar da ita saman gadon sannan shi ma ya Haye ya konta ya na kallon ta , a haka har barci ya dauke shi Washe gari Misalin karfe 4 na safe ya farka da ga barcin shi Ya na bude idanu su ka sauka a kan ta , ta juyo su na fuskantar juna ta na sauke nunfashi a hankali Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya a hankali ya sauko kafafun shi kassa sannan ya mike tsaye ya nufi closet din kayan shi ya bude ya dauki kayan shi wandon jeans light blue da t-shirt fara sannan ya fice dakin Kai tsaye dakin Moussa ya wuce babu ko sallama ya shigo dakin kai tsaye ya wuce toilet Shi kuma Moussa sai kwana ya ke da ga shi sai short ko shigowar Zayd bai ji ba , sai da ya fara jin saukar ruwa sannan ya bude idanun a hankali ya na motsi Kallon kofar toilet din ya yi ya ga dakwai dan haske Murmushi kadan ya saki kafin ya fara karanto adu'ar tashi da ga barci ya mike zaune ............................. ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 10 ❤🔥 After some minutes ya fito sanye da kayan da ya dauko da ga bedroom din shi Kallon shi da kyau Moussa ya yi kafin ya ce " ango ! Me kuma ya kawo ka toilet di na " Ko kallon shi Zayd bai yi ba ya sa kai ya fice bedroom din Ya na fita Moussa ya mike ya na dariya ya shiga toilet shi ma Inaya Misalin karfe 6 ta farka da ga barcin ta Ta na bude ido ta fara bin dakin da kallo , Sai da ta dan dauki lokaci sannan ta mike zaune ta sauko kafafun ta kassa sannan ta mike tsaye ta fara takawa ta nufi toilet Bai fi five minutes ba da shigar ta toilet ya shigo dakin ya na sallama a tunanin shi ta farka Sai ya ga dakin ba kowa ga kuma karar ruwa Sai ya tako bakin gadon ya zauna ya kai saman drawer ya dauki bakin glass din shi ya sa , ya sunkuyar da kan shi kassa Bayan wasu mintina Ya na zaune a haka ta fito da ga cikin toilet din ta na daure da towel a kirjin ta Ta na ganin shi ta saki murmushi , a hankali ta tako wajen trolley din ta ta bude ta dauki uniform din ta Har ta juya za ta koma toilet wata zuciyar ta ta ce mata " ina kuma za ki koma mutumin da ba gani ba ya ke " Daga kafadun ta ta yi ta na turo baki nan na ta gaba ta koma ta ajiye kayan na ta saman trolley Sannan ta kai hannu zame towel din jikin ta, ta koma naked Hum kamar an ce mishi Zayd dago kai haka ya dago kai dai'dai lokacin da ta saki trolley din ya fadi kassa ta duka ta dauki pant din ta Da sauri ya rumtse idanun shi ya kauda kai gefe cikin ranshi ya ce " na shiga uku ni Nawfel ba ta ga da mutun ne cikin dakin ko ita ma ta koma makafniya " Tsab ta shirya war ta cikin uniform din ta, ita ta ma manta da mutun a cikin dakin Sai da ta gama shiryawa sannan ta dauki towel din da ta yadda kassa ta meda shi toilet sannan ta fice dakin Duk takun ta ya na jin ta amma ya ki bude idanu ya na tsoron ya sake bude su ya yi arba da ilahirin surrar jikin ta Sai da ya ji ta bude kofa ta fita sannan ya bude idanun shi slowly ya kali saitin kofar ya sauke ajiyar zuciya mai karfi Inaya kuma bayan ta fita kitchen ta wuce ta shirya musu breakfast Sai wajen karfe 7 cib sannan ta baro kitchen din ta shirya musu komai saman dining table sannan ta koma bedroom din ta Ya na nan zaune inda ta bar shi ko motsi bai yi ba Bakin ta dauke da sallama ta shigo dakin Cen cikin zuciyar shi ya amsa mata A hankali ta tako gaban shi ta tsaya sannan ta Zube saman guyiwowin ta ta ce " ina kwana yaya Zayd " Jinjina mata kai kawai ya yi bai ce mata komai ba Murmushi ta yi kafin ta mike ta nufi trolley din ta, ta dauki hijabin ta ta saka ta dauki school bag din ta sannan ta dawo gaban shi dan nesa kadan ta ce " yaya Zayd zan biya wajen Nesrine sai mu ta fi tare " Jinjina mata kai ya yi kafin ya sa sannu shi cikin aljihun wandon shi ya ciro gudi yan dubu dubu sun kai goma sannan ya mika mata Dan zaro idanu ta yi ta na kallon kudin ta na tunanin ina ya sami wadanan kudade duka Ganin har yanzu ba ta karba ba ya sa shi dago kai a hankali ya kale ta Da sauri ya rumtse idanun shi dan ya tino kallon da ya yi mata ta na naked Ita kuma ba ta lura ba da ya datse idanun shi ba dan ya na sanye da glass bakake Ajiyar zuciya ta sauke ta yi murmushi kafin ta ce " yaya Zayd ka barshi kawai " Girgiza mata kai ya yi ya mike tsaye ya tako a hankali gaban ta ya kara mika mata kudin Wannan karan ba yadda za ta yi sai da ta karba ta na yi mishi godiya sannan ta saka su cikin bag din ta Sai da ya ga ta sa kudin cikin jakar ta sannan ya juya ya fice Da sauri ta bi bayan shi ita ma ta fito dakin A nan falo su ka isko Moussa ya na zaune saman sofa ya na latsa wayar shi Ya na dago kai ya gan su ya saki dan murmushi ya ce " baby na har kin fito ? " Sunkuyar da kai kassa ta yi ta na fadin " ina kwana yaya Moussa " " lafya lau baby na , sa fatan wannan jarabbaben bai takura miki ba " ya kai karshen ya na medo da kallon shi kan Zayd da ya zauna saman sofa da ke fuskantar tashi Girgiza mishi kai tayi kafin ta ce " yaya Moussa na shirya muku breakfast din ku , ko ku na bukatar wani abu ne ? " Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " no baby hakan ma ya isa , sai kin dawo Allah kiyaye hanya " Da amine ta amsa mishi sannan ta fara takawa ta fita falon Ya na jin ta fita ya sa hannu ya janye glass din shi ya ajiye su geffen shi ya zubawa Moussa wadanan hazel eyes din shi Sarai Moussa ya lura da shi amma ya yi banza da shi ya tashi ya nufi dining room ya fara breakfast Inaya Bayan ta fita gidan ta fara tafiyar ta cikin minti biyar ta iso gidan su Da sallama ta shigo cikin gidan Mama na zaune bakin kofar dakin ta , dai'dai lokacin da Nesrine ke fitowa da ga dakin su ta na sanye da uniform ita ma Ta na ganin Inaya ta saki wani kyawatencen murmushi da gudu ta je ta rungume ta ta na fadin " na yi kewar ki sosai " Rungume ta ita ma Inaya ta yi ta na murmushi Cen su ka tsinci Muryar mama ta na fadin " toh malama kin sake ta, ta zo ta gaishe ni ko ? " A tare su ka yi dariya su na raba jikin su da na juna sannan Nesrine ta riko hannun ta su ka nufi mama Ta na isa mama ta bude mata hanayan ta akan ta zo Ba musu ta fada jikin ta ta na murmushi ta ce " ina kwana mama ? " " lafya lau autar mama ya ki ke komai dai'dai ko " ta fada ta raba jikin ta da na Inaya Kallon ta da kyau mama ta yi cike da mamaki ta ce " ban gane ba school za ki koma tun wuri haka " Murmushi Inaya ta yi kafin ta ce " eh mama yaya Zayd da kan shi ya sayo min uniform ki na gani ? " ta kai karshen ta na juyawa " shikenan sai kun dawo " mama ta fada ta na murmushi Hannu Nesrine ta kamo su ka juya ta ce " mu tafi " Jinjina mata kai Nesrine ta yi kafin ta juya su fara takawa su ka bar gidan A tare su ke tafiyar su cikin konciyar hankali su na tafe su na hira gwanin ban sha'awa Sai da su ka kawo bakin kofar college din , Inaya ta ga masu sayarda kayan marmari Da sauri ta saki hannun Nesrine ta nufi guda da ga cikin su Karasowa wajen Nesrine ta yi ta kai hannu ta daura a kafadar ta ta na fadin " to sarkin ciye² me kuma za ki saya " Kallon ta Inaya ta yi sannan ta ce " Apple mana , ina marmarin Apple sosai wlh " Ta kai karshen ta na meda kallon ta kan mai sayarwar ta ce da shi ya saka mata Apple shida ta na kai hannu cikin jakar ta, ta ciro kudin da Zayd ya bata Zaro idanu Nesrine ta yi ta na kallon kudin cike da mamaki ta ce " ke Inaya ina ki ka samu uban kudi haka ? " Ba tare da ta kaleta ba ta na kokarin ciro dubu biyu ta bawa mai sayarwa ta ce " yaya Zayd ne ya bani " ta kai karshen ta na karbar ledar Apple din ta juyo ta kali Nesrine ta ce " mu tafi ? " Ba musu su ka juya su ka shiga cikin college din su na tafe su na hira har sai da su ka kai bakin kofar class din su sannan su ka rabu After some hours Zaune su ke saman chair din cafeteria , Inaya sai faman cin Apple ta ke ,Nesrine kuma na kallon ta ta na murmushi Sai da ta kusa kamalawa ta dago kai ta kali Nesrine , murmushi kadan ta yi kafin ta mika mata Apple din hannun ta ta ce " za ki ci ne ? " Girgiza mata kai Nesrine ta yi ta na murmushi ta ce " a'a ci kayan ki babyn Zayd " Daga kafadun ta Inaya ta yi ta ci gaba da cin Apple din ta hankali konce Sai da Nesrine ta ga ta Kamala sannan ta ce " Inaya zan so na tambaye ki wani abu " Jinjina mata kai Inaya ta yi ta na fadin " wane abu kuma ? " Ajiyar zuciya Nesrine ta sauke sannan ta ce " da gaske ki na son yaya Zayd , a yadda ya ke hakan ba ya magana kuma ba ya gani ? " Murmushi kadan Inaya ta yi kafin ta jinjina mata kai allamun e " why Inaya ? Ki duba duk mazan da ke cikin duniya , ki rasa wanda za ki so sai kurma kuma makaho " " wai Nesrine wa ya fada miki yaya Zayd kurma ne , ko kuma shi ya fada miki shi makaho ne " Inaya ta fada cikin bacin rai ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 11 ❤🔥 Dan zaro idanu Nesrine ta yi ta na kallon ta cike da tantama ta ce " wai Inaya me ya ke damun ki ne , inda ya na magana duk shekaru hudun nan da mu ka yi tare da shi me ya sa ko kalma daya ban ji ta fito da ga bakin shi ba , kennan a haka ku ke rayuwa cikin gidan na shi , kennan rayuwa da kurma na yi miki dadi ? " Mikewa tsaye Inaya ta yi ta dauki jakar ta ta na fadin " kin ga Nesrine ban san me ya sa ba ki son yaya Zayd ba, ni fa ina son shi a haka kuma duk abun da za ki fada bazai sa na daina son shi ba , ku duka kallon kurma da makaho ku ke yi mishi amma ai ni ina gane abun da ya ke fada kuma da makaftar tashi ya ke aiki , kin ga ya fi karfin a ce mishi makaho kin ga idan ba za ki fadi abun al'heri a kan yaya Zayd ba ki daina yi min magana " Ta kai karshen ta na juyawa za ta bar wajen kawai sai ta ji ta bugi mutun Dan bayan kadan ta ja ta dago kai ta kaleshi ta ce " sorry " Murmushi kadan Moctar ya yi kafin ya ce " ba komai " Da sauri ta raba ta geffen shi za ta wuce Da sauri ya riko hannun ta ya ce " haba ina kuma za ki je , ni fa wajen ki na zo " Cikin bacin rai Inaya ta kwace hannun ta ta juya ta fara takawa za ta bar wajen Da sauri ya sha gaban ta ya ce " ba da ke na ke ba , za ki wuce ki kyale ni ? " Cikin bacin rai Inaya ta ce " ka ga malam ka ba ni hanya na wuce ni matar aure ce " Dariya ya yi har da dafe ciki Sai da ya tsagaita dariyar shi sannan ya ce " oh sannu madam to , shi ne za a yi biki ba'a gayace mu ba ? " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda Dan tsaki Inaya ta ja kafin ta raba ta geffen shi ta wucewar ta Da kallo ya bi har sai da ta kurewa ganin shi sannan ya juyo ya kali inda Nesrine ke zaune Sai dai kuma me ? Babu ita babu mai kama da ita, tun lokacin da ya bata baya ta tatare kayan ta a hankali ta tsere dan ta sani tabass Moctar ya na tare da Hafiz , idan kuma Hafiz ya zo wajen ta san tabass ba zai kyale ta ba shi ya sa ta tsere Abun da ba ta sani ba Moctar shi kadai ya ke tafe , Hafiz bai san da cewa college din zai zo kawai ya ce mishi zai fita ne Tsaki kadan ya ja kafin ya fara takawa ya fice cafeteria din Inaya Ta na barin wajen ta koma kai tsaye class din su ta koma dai'dai lokacin da prof din su zai shiga class din After some hours Bayan sun sauka da ga school ko wace ta wuce gida , Inaya kuma ta wuce gidan mijin ta kai tsaye ta wuce dan yau fa Nesrine da Moctar sun tado mata na bacin ran Zayd Su na zaune cikin falo shi da Moussa ko wane sai faman latsa wayar shi ya ke Su na zaune a haka Inaya ta shigo falon ta na sallama kassa kassa Dago kan shi Moussa ya yi ya na amsa mata sallamar ta da murmushi Ya na shirin yi mata magana ya ga ta wuce corridor kai tsaye ko gaida su ba ta yi ba Da kallo ya rakata har sai da ta shiga bedroom din Zayd sannan ya dawo da kallon shi kan Zayd ya ce " Amir ina ga yau wani ya tabo ran baby na " Slowly Zayd ya dago kan shi ya zubawa Moussa wadanan hazel eyes din shi ta cikin glass kafin ya ce " wai wanene babyn ka cikin gidan nan ? " Hararrar wassa Moussa ya yi mishi sannan ya ce " bayan wadda ka ke kira da matar ka wa ke cikin gidan nan, ita ce baby na mana, ka ga na ma tafi na rarrashi abu na " ya kai karshen ya na mikewa tsaye zai shiga corridor Da sauri Zayd ya riko hannun shi ya ce " kai Diya ban san rainin sens matar tawa ka ke kira da baby ? " Kwace hannun shi Moussa ya yi kafin ya ce " tun da kai ba ka so ni ina so wlh , ni wlh ka ci gaba da kyale ta ma , hakan ya yi min dadi , ko na samu son da ta ke yi maka ya dawo kai na , i really love her, i don't know how ko yaushe hakan ta faru i'm falling in love for her , ni da za ka min Alfarma ka sake ta na je na roki malam ya aura min ita tun da kai ba ka son ta " " Diya wai ka na jin abun da ka ke fada ne " " ka ga malam ni don Allah kyale ni , wai ba ka ga yadda baby na ta dawo ne gidan ko gaisuwar arziki ba ta yi min ba , ka ga ni na tafi rarrashin ta " ya kai karshen ya na juyawa ya shiga corridor ya nufi bedroom din Zayd Sumar zaune Zayd ya yi ya na jin abun da Moussa ya ke fada mishi nan take ya ji wani uban kishi ya taso mishi yanzu shi Moussa zai yanka a baya ya zagayo ya ce matar shi ya ke so kuma Da sauri ya girgiza kan shi ya ce " no ! No ! Impossible bazai yi yu ba " Ya na gama fadar haka ya mike tsaye da sauri ya shiga corridor kai tsaye ya wuce bedroom din shi cikin zafin nama ya bude kofar dakin ya shiga Cak ya tsaya bakin kofar ya na bin dakin da kallo , duk wajen a tirje ya ke , ga pillow duk an zubar da su kassa , an zare bedsheet an tila shi gefe guda Cen ya hango Inaya zaune a kassa ta saka kan ta tsakanin cinyoyin ta, ga jakar school din ta cen gefe ta tila ta Tsaya wa ya yi ya na bin dakin da kallo ya na son ya ga Moussa amma ita kadai ya gani Abun da bai sani ba shi dama Moussa wassa ne ya ke yi mishi dan ya san abokin shi da mugun kishi nan take zai fara bibiyar Inaya duk wane abu da za ta yi sai ya Ankara da shi , dalilin da ya sa ya ke yi mishi wannan abun amma shi gaskia ba son Inaya ya ke ba ko yanzu da ya shiga corridor din bedroom din shi ya shiga ba na Zayd ba A hankali ya fara takowa cikin dakin har ya karaso inda ta ke zaune shi ma ya zauna gaban ta ya yi irin zaman cin tuwo ya zuba mata idanu, da allamun ba kuka ta ke ba Sai da ya gaji da kallon ta sannan ya kai hannu shi ya kyasta mata dan yatsun shi biyu saitin kunnen ta Da sauri ta dago kan ta ta na kallon shi dan ita ba ta ji shigowar shi ba cikin dakin har lokacin da ya zauna gaban ta , duk ta yi nisa cikin tunanin ta Dan murmushi ta saki kafin ta gyara zaman ta, ta yi irin zaman da ya yi ta sunkuyar da kai ta riko tafin kafarta guda da hannayan ta duka biyu Ganin ba ta da niyar yi mishi magana ya sa ya kai hannu ya dago habar ta ya na kallon face din ta , sam babu digon hawaye a kai , to me ya faru kennan ? Ita kuma murmushi kadan ta saki kafin ta ce " yaya Zayd me ya faru ? " Janye hannun shi ya yi kafin ya girgiza mata kai sannan ya kai hannu ya nuna nata sannan ya mata allamu da hannu " me ya ke damun ki ? " Sunkuyar da kan ta yi kafin ta ce " yaya Zayd wlh Nesrine ta na yawwan takura min wai na auri kurma kuma makaho duk cikin mazan da ke cikin duniyar nan wai shi na zaba, ban San minene matsalar ta ba , ni na fada mata ina son ka a hakan amma ta ki jin magana har wasu classmate din ta ta fadawa yanzu duk sun bi sun takura min a school , ni wlh in ba ta bani lafya sai na fadawa Abba , shin minene matsalar in baka gani ko baka magana na ga kai ma mutun ne ka na da tsoron Allah , ka na sallat ka na azumi ka yarda da Allah da manzon sa , kuma ka na da zuciya mai kyau , amma ita duk ba ta ganin wannan , wlh ina jiye mata duniya ba ta san abun da zai faru da ita ba nan gaba , sam ba ta ganin darajar mutane , duk abin da na ke son na gwada mata ta ki gani amma a haka wai ta ke ce maka makaho al'halin ita a bata gani " Tun da ta fara magana ya tsare ta da idanu ya na kallon ta cikin ranshi kuma cewa ya ke " Moussa ya yi gaskia she is so innocente , her heart is so pure , duk zaman da na yi a Nigeria ke ce mace ta farko da ta ce min ta na so na a matsayin makaho kuma kurma al'halin ba haka ba ne , ina ga zan yarda da maganar Moussa na amshi soyayyar ta , muyi sabuwar rayuwa nassan bazan samu wadda za ta zauna da ni tsakanin ta da Allah kamar ke ba " Kawai sai ganin kan shi ya yi ya saki wani kyawatencen murmushi ya mike tsaye ya juya ya fara takawa ya fice dakin Ya na fitowa falon ya isko Moussa ya na konce saman sofa ya na latsa wayar shi Ya na ganin Zayd ya fito ya mike zaune ya na murmushi ya ce " har ka ida rarrashin baby na " Ko kallon shi Zayd bai yi ba ya sa kai ya fice falon, ya bar gidan baki daya Tafiya ya ke cikin konciyar hankali ya na taku cike da izza har ya karaso bakin kofar gidan su Inaya, ko me ya zo yi oho ! Ya na shirin shiga gidan Malam ya fito da cikin gidan ya yi shirin tafiya massalaci dan lokacin sallat ya yi Ya na ganin Zayd ya saki wani kyawatencen murmushi ya mika mishi hannu su ka yi musbaha sannan ya ce " a'a malam Zayd yau kai ne a gidan na mu haka , ina fatan ba dai laifi autar tawa ta yi maka ba " Girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya ce " no ba maganar ta ba ya kawo ni gidan nan uncle ! " " toh , lafya kuma ? Maganar mi ta kawo ka in haka ne ? " malam ya fada ya na tsare shi da ido Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " uncle ina so in san dalilin ka na aura min Yarinyar nan al'halin ba ka san ko ni wanene ba ka san kowa nawa ba za ka dauki d'iyar ka ka bani ita haka kawai " Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " Zayd na fada maka in lokacin ya yi za ka sani amma tun da ka matsa bara na fada maka wani dan karamin abu saman ta , Inaya da ka ke gani ba kamar kowane mutun ba ta ke , akwai wata baiwar da Allah ya yi mata wadda ko ita ba ta san da ita ba , a kan wannan baiwar a ke bibiyar rayuwar ta , abu guda ne zai iya sa ta iya gane ta na da wata baiwa har ta iya anfani da ita shi ne ta hanyar aure , kafin mu baro kaduna wasu azaluman mutane sun so su yi anfani da ita wajen mugayan manufar su , dalilin da ya sa na aura maka ita kenan, dan kar su samu damar cin ma manufar su , ni nassan har yanzu su na bibiyar rayuwar mu su na neman inda mu ke amma ka ga cikin wani ikon Allah har yanzu ba su gano inda mu ke ba , kai baza ka dalilin hakan amma ni na sani abu guda zan roke ka , ka kula min da yarinya ta dan rayuwar ta na da matukar mahimanci musaman a cikin rayuwar ka " Jinjina kan shi kawai Zayd ya yi ya na son ya ji wace irin baiwa ce haka wadda za ta sa ka a dinga bibiyar rayuwar mutun haka , to su da su ke bibiyar ta me su ke so da ita ? Ko kuma wannan baiwar da malam ke fada ita ce dalilin da ya sa ta ke wasu abubuwa kamar karamar yarinya ? Ya kamata ya ji micece wannan baiwar " uncle zan so na ji wace irin baiwa ce wannan wadda zai sa a dinga bibiyar ku haka ? " Zayd ya tambayi malam Murmushi malam ya yi kafin ya ce " Zayd bazan iya fada maka ba , amma zan so ka sani , Inaya ba ta tune da rayuwar mu ta baya , ko za ka bude baki ka tambaye a ina mu ka yi rayuwa kafin mu dawo kano baza ta iya fada maka ba , amma idan ka tambaye ta wani abu saman ka, ko da abun ya yi shekara 20 sa wucewa za ta fada maka shi har ma wanda ba ka sani ba , amma hakan bazai yiyu ba har sai kun zama abu guda " Daga gera guda Zayd ya yi cikin zuciyar shi ya ce " kennan madubiya ce ko kuwa ? " A fili kuma ya ce ma malam " amma uncle ya za ayi ta manta rayuwar ta, amma ta san rayuwar wasu ko kuma amnesia ce ? " Dariya malam ya yi kafin ya ce " yo malam Zayd kai ka san minene hakan dan ni ban yi boko ba, yanzu dai mu tafi lokacin sallat ya yi kar mu rasa jam'i " Malam na shirin tafiya Zayd ya yi saurin cewa " uncle ina son nayi magana da Nesrine kafin mu tafi " Juyowa malam ya yi ya na kallon cike da tambaya, ko dalilin mi ya ke son magana da Nesrine ? Ya tambayi kan shi Shi kuma Zayd ya tsaya ya zuba mishi idanu ta cikin glass din shi ya kassa yi mishi magana ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 12 ❤🔥 Murmushi kadan malam ya yi kafin ya juyo ya nufi cikin gidan ya na fadin " mu je to bara na kira maka ita " Ba musu ya bi bayan shi su ka shiga cikin gidan malam na sallama , dai'dai lokacin da Abdoul ya fito da ga cikin dakin shi sanye da jallabiya fara allamun shi ma massalacin za shi Ya na ganin Zayd ya saki murmushi ya ce " a'a yau ango ne a cikin gidan na mu " ya fada cikin zolaya " kai dan Allah ya isa haka je ka kirawo min Nesrine ya na son magana da ita " malam ya fada mishi Ba musu ya taka ya shiga bedroom din Nesrine ya na sallama Ya na shiga mama ta fito da ga cikin toilet ta na rike da buta Ta na ganin Zayd a tsaye geffen malam ya rike hannayan shi a baya ya na kallon gaban shi Ta saki murmushi ta karaso wajen ta na fadin " malam Zayd sai yau a ka yi niyar dawowa gidan na mu ? " Ko kallon inda ta ke bai yi ba ya ci gaba da tsayuwar shi Ta na gama rufe bakin ta Abdoul ya fito da ga cikin bedroom din Nesrine ya karaso geffen mama ya tsaya ya na fadin " ga ta nan " ya kai karshen ya na nuna kofar dakin Ya na rufe baki Nesrine ta fito da ga cikin dakin ta na sanye da hijab blue har zuwa kassa ta karaso ta tsaya gaban shi dan nesa kadan ta na fadin " gani Abba lafya ya ke nema ta ? " Daga kafadun shi malam ya yi kafin ya ce " ni ma ban sa ni ba , Zayd ga ta an kira maka ita " ya kai karshen ya na dawo da kallon shi kan Zayd da ya zubawa Nesrine ido Shi kuma Zayd sai da ya dauki lokaci kafin ya tako a hankali cike da izza ya tsaya gaban Nesrine ya zuba mata ido ta cikin glass din shi Sai da ya dauki wajen good two minutes kafin ya kai hannu slowly ya zame bakaken glass din shi Dum Nesrine ta ji gaban ta ya fadi dan ba karamar razana ta yi ba da ganin wadanan hazel eyes din na shi ga shi sai wani kyali su ke saboda hasken rana Ta na a haka ta jiyo wannan zazzakar Muryar ta shi ya na fadin " ban san abun da na yi miki ba da ki ka tsane ni haka , a sani na tun lokacin da ku ka shigo gidan nan ko kalma daya ba ta taba shiga tsakani na da ke amma yau sai da ki ka sa na yi miki magana ba da so na ba , kamar yadda ki ke ji ni ba kurma ba ne ina magana kamar yadda ki ke magana sannan kuma ina ganin ki kamar yadda ki ke gani na a tsaye gaban ki , ban zo gidan nan dan na fada muku ko ni wanene ba , na zo ne dan na fada muku dalilin da ya sa ku ke min kallon makaho da kuma kurma , shekara biyar kenan da na zo Nigeria kuma a nan kano na sauka , Lokacin da na shigo Garin nan ba na jin haoussa da ga turanci sai larabci kuma ba kowa ba ke jin su dalilin da ya sa na dinga yin shiru dama cen ni ba ma'abocin magana ba ne shi ya sa duk wata magana da zan yi sai dai na yi ta da hannu in kuma tambaya ce na girgiza kai a haka har mutane su ke min daukar kurma kuma kuka zo ku ka same ni a hakan, sannan kallon makahon da ku ke min na san ya samo nasaba ne da bakaken glass di na da na ke sanye da kullum, ina saka su ne saboda nassan a nan Africa ba kowa ba ke da colour din idanu na hakan na tsoratar da mutane su na yi min wani kallo cen daban dalilin da ya sa na ke saka su , sandar da ki ka ga ina yawwan rikewa kuma " Ya kai karshen ya na sa hannu shi cikin aljihun shi ya fido wani dan abu kamar remote Ya na danna shi nan take abun ya yi wata kara ya kara tsayo ya koma kamar sanda Sannan ya sake danna button din sandar ta koma kamar da farko " ba sanda ba ce kamar yadda ki ke tunani , duk wani mumunar zato da ki ke yi a kai na yau na tabbatar miki da ba gaskia ba ne , zan so nan gaba ki fara sannin wanene mutun kafin ki kaskantar da shi , da zan fada miki ainahin wanene ni to za kiyi mamaki ki tambayi kan ki abun da ya kawo ni nan amma bazan fada miki ba nassan wannan karamar kwakwolwar ta ki baza ta dauka ba amma ki sani ba sunana Zayd ba duk ranar da ki ka samo sunana na gaskiya ki zo ki fada min zan baki kwatar dukiyar da ko jikokin jikokin ki sai sun ci albarkacin ta " ya na gama fadar haka ya meda bakin glass din shi ya juya ba tare da ya ce komai ba ya bar gidan Nan ya bar Nesrine baki sake tun lokacin da ya fara magana ta na zaro idanu Sai da ya fita sannan ta kali mama ta kali malam Ta na shirin magana Abdoul ya riga ta cewa " Nesrine me ki ka ma Zayd kuma " Cike da mamaki ta ce " yaya Abdoul ba ka mamakin yadda yaya Zayd ke magana ko dai kunnuwa na ne " Malam ne ya bata amsa da cewa " ba kunne ki ba ne Zayd ya na gani kuma ya na magana , a sani na bai taba bude baki ya ce miki shi kurma ne ko makaho ni ban san me ki ka mishi ba amma zan tambaye shi , kai Abdoul wuce mu tafi massalaci " ya kai karshen ya na juyawa ya fita gidan Shi ma Abdoul takawa ya yi ya bi bayan shi su ka bar gidan su ka bar mama da Nesrine nan tsaye sai faman muzurai su ke Sai yanzu Nesrine ta tuno da kalamun Inaya da ta ke ce mata " wai Nesrine wa ya fada miki yaya Zayd kurma ne , ko kuma shi ya fada miki shi makaho ne " kennan Inaya ta san cewa ba makaho ba ne shi ya sa ta ke son shi ? Ko kuma ya zancen ya ke ? Nesrine na shirin magana mama ta riga ta cewa " kar ki tambaye ni abun da ki ka ji shi na ji " ta na gama fadar haka ta wuce ta shiga dakin ta Ita ma Nesrine ta juya ta koma dakin ta zuciyar ta na duka uku uku kamar ta ga abun tsoro Inaya Ta na jin ya fara takawa ya bar dakin ta dago kai ta bi bayan shi da kallo har sai da ya fita dakin sannan ta mike tsaye ta gyara komai na cikin dakin sannan ta shiga ta yi wanka ta shirya cikin wandon palazzo pink colour da riga zuwa guyiwa white colour ta saka dan karamin hijab zuwa kirji Falon gidan ta fito nan ta ga babu kowa duk sun fice , sai ta wuce kai tsaye kitchen dan ta shirya musu abinci Misalin karfe 5 na yamma ta Kamala girkin ta shirya komai saman dining table sannan ta gyara gidan tsab har da bedroom din Moussa ta wanke toilet din dakin , har da harabar gidan sai da ta fito ta share sannan ta koma ta feshe gidan da turare Wajen kiyaye²n sallar magriba ta koma dakin ta ta yi wanka ta dauro Alwalla sannan ta sauya kayan jikin ta ta saka gown mara nauyi purple sannan ta saka hijab har kassa shi ma purple sannan ta gabatar da sallar ta , bayan ta gama ta zauna yin karatun kur'ani , ba ta Kamala ba sai da a ka yi kiran sallar isha ta tashi ta gabatar da sallar Misalin karfe 8 na dare Ta na zaune cikin falon gidan ta cire hijabin jikin ta , ta ajiye shi gefe ta saki wani dark hair din ta har cikin baya , kun san fulani su ma ba baya ba wajen gashi bare uwa bafulatana uba bafulatani kun ga ba mamaki ta yi gashi Ta na zaune ta na kallon tashar Arewa 24 a Tv duk hankalin ta ya na wajen Tv din a na shirin mata a yau Ta na a haka ta jiyo sallamar Moussa Dan murmushi ta yi kafin ta amsa sallamar shi ta na yi mishi sannu da zuwa Murmushi ya yi kafin ya tako a hankali ya zauna saman sofar da ke fuskantar ta ta Ya na zama Zayd ya shigo falon ya na sallama cen kassa kassa yadda shi kadai ya san ya yi abu ne Abun mamaki kuma sai da Moussa ya amsa sallamar dan ya san abokin shi da wuya ya shigo wuri bai yi sallama ba, ko da kuwa ba wanda ya ji ta A hankali ya karaso cikin falon ya zauna geffen Moussa Sannu da zuwa Inaya ta yi mishi ta na murmushi , jinjina mata kai kawai ya yi ya na kallon ta ta cikin bakin glass din shi , kamar bai taba ganin ta ba Ya na a haka ya tsinci Muryar Moussa ya na fadin " baby me kuma a girka mana ni fa yunwa na ke ji " Da sauri Zayd ya juyo ya kaleshi ya juya ya kali Inaya sai ganin ya yi ta saki murmushi ta mike tsaye ta dauki hijabin ta ta saka ta ce mishi " yaya Moussa ni fa tun dazu na gama ina jiran ku " ta na gama fadar haka ta shiga dining room Mikewa Moussa ya yi ya bi bayan ta ya shiga dining room ya ja kujera guda ya zauna sai bin ta ya ke idanu Shi kuma Zayd sai kallon su ya ke wata zuciyar na ce mishi ya tashi ya shake Moussa ko ya rage zafin kishin da ya ke ji Ya na kallon su har Inaya ta yi serving din shi ta mika mishi plate din ta na murmushi sannan ta janyo kujerar da ke fuskantar tashi ta zauna ta yi serving din kan ta , sannan ta fara ci Da allamun ta manta da mijin na ta baki daya sai abincin ta ta ke ci su na hira ita da Moussa har da dariya Zayd kuma ganin abun na su na neman ya yi mishi katutu ya sa ya mike a hankali ya nufi corridor ya shiga bedroom din shi kai tsaye ya Haye saman bed din shi ya yi rub da ciki Moussa da Inaya kuma sun ma manta da shi sai hirar su su ke , sai da su ka Kamala cin abincin su sannan su ka tatare dishes su ka kai kitchen su ka wanke a tare sannan su ka dawo falo su ka zauna, Moussa ya saka musu wani horror film su ka fara kallo Su na a haka Zayd ya fito da ga cikin corridor sanye da wando three cuter baki da t-shirt purple yanzu ma ya na sanye da bakin glass din shi ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 13 ❤🔥 A hankali ya takowa cikin falon cike da izza kai a sunkuye Har sai da ya karaso sofar da Moussa ke zaune ya zauna shi ma ya na kallon Tv din Jim kadan da zaman shi Moussa ya mike ya ce ma Inaya sai da safe shi zai shiga barci da to ta amsa mishi sannan ya juya ya shiga corridor ya wuce bedroom din shi ya bar ta nan ita Zayd A haka su ka ci gaba da kallon film din a tare har sai da a ka zo wajen wata scene mai ban tsoro Da karfi Inaya ta saki kara ta tashi da gudu ta fada jikin Zayd ta kankame shi ta na sakin kara , ( KO NI SAI DA NA NEMI NA FADA MISHI A JIKI WANNAN SCENE DIN BA KARAMIN TSORO YA BA NI BA , SHI MA MOUSSA DA GANGAN YA KE YA ZAI SAKA MA YARINYA KARAMA IRIN WANNAN FILM 😠😠😠 ) Da gudu Moussa ya fito da ga cikin bedroom din shi ya na sanye da jallabiya fara ya karaso wajen ya na tambayar lafya Cak ya tsaya ya zuba musu idanu ya na sakin wani kyawatencen murmushi, da gudu ya koma bedroom din shi ya dauko wayar shi ya dawo ya dauke su hoto sannan ya komawar shi daki Inaya kuma ita ko fitowar Moussa ba ta ji ba ta na zaune saman cinyar Zayd ta boye fuskar ta a kirjin shi ta datse idanun ta da karfi ta kankame shi da kyau kamar na ce zan kwace mata shi Shi kuma bawan Allah Zayd duk ya bi ya yi sumar zaune dan babu wata macen da ta taba zama saman cinyoyin shi har ta rungume shi haka kawai sai jin shi ya yi cikin wani bakon yanayi ya tsaya ya zuba mata ido ta cikin glass din shi Dan lumshe idanun shi ya yi ya daga kan shi saman ya sauke nanauyar ajiyar zuciya har sai da Inaya ta bude idanun ta jin ya sauke ajiyar zuciya Ba shiri ta ji ya mike tsaye da ita a jikin shi ya sa hannayan shi ya dauke ta kamar baby ya juya ya fara takawa ya nufi corridor ya wuce kai tsaye bedroom din shi ta ita Bai dire ta ko ina ba sai saman bed din shi ya kontar da ita sannan ya mike ya juya zai bar dakin Taku daya ya yi ya ji ta riko hannun shi ta saki kuka ta ce " don Allah yaya Zayd kar ka tafi wlh tsoro na ke ji bazan iya kwana ni ka dai ba " ta fada cikin kukan nata Dan lumshe idanun shi ya yi cikin zuciyar shi ya ce " kai Diya , ina hankalin ka da za ka saka mata horror film yanzu ga shi kan janyo min " ya kai karshen ya na dan karamin tsaki ya bude idanun shi Ba dan ya so ba ya koma ya zauna saman gadon ya jingina bayan shi a bayan gadon ya lumshe idanun shi Inaya kuma ta na ganin ya dawo ya zauna ta saki murmushi ta konta ta zuba mishi ido sai kallon shi ta ke Sannu sannu har ya dauke ta ta na kallon shi Ya na jin ta fara sauke nunfashi a hankali a hankali ya sa ya juyo ya na kallon ta " wannan yar karamun abun wai ita ce matata ? Ni ban ma san dalilin da ya sa na yarda da auren nan gashi yanzu a neman a janyo min matsala , kai da sake wlh " ya fada a cikin zuciyar shi ya na sakin dan karamin tsaki ya kauda kai gefe Ya dan jima a haka kafin ya sauko fararen kafafuwan shi kassa sannan ya mike tsaye ya fara takawa ya fice dakin Dakin Moussa ya shiga, nan ya tardo shi ya na konce ya yi rub da ciki saman gadon shi da ga shi sai short da singlet Takowa ya ci gaba da yi ya karaso bakin gadon ya zauna, ya cire bakin glass din shi ya ajiye saman bedside drawer sannan ya karasa Hayewa gadon ya konta Ya na kontawa Moussa ya farka a tsorace ya na fadin " waye ne ? " Ya na gama fadar haka idanun shi su ka sauka a kan Zayd da ke konce geffen shi ya daura hannu daya saman forehead din shi dayan kuma saman cikin shi ya lumshe idanu Tsaki Moussa ya ja kafin ya mike zaune ya na hararrar Zayd ya ce " kai malama me kuma ka ke min a cikin daki ka ga don Allah tashi fitar min da ga daki " ya fada ya na nuna mishi kofar dakin Ko bude ido Zayd bai yi ba bare ya amsa mishi Ganin ya na shirin ya bata mishi rai ya sa Moussa juyawa ya sauke kafafun shi kassa ya ce " shikenan konta a nan, ni zan je na kwana tare da baby na , sai da safe " ya kai karshen ya na mikewa tsaye ya nufi hanyar fita dakin Har ya kai bakin kofar dakin ya ji an shako shi ta baya da karfi a ka tila shi gefe ya fadi kassa A dubu dari ya dago kai ya na kallon Zayd da ke tsaye gaban shi Ya na shirin magana ya ga ya juya ya koma wajen bed ya Haye ya konta kamar da farko ya bar Moussa nan Zube a kassa Tabe baki Moussa ya yi ya na kokarin mike wa tsaye ya na fadin " amma Allah Amir ka cika dan rainin hankali, yanzu dan na ce zan je na kwana da baby na shi ne za ka min haka, ina ruwan ka to ? " ya kai karshen ya na karasowa bakin gadon ya zauna ya bawa Zayd baya , ya daura hannun shi daya saman bayan wuyan shi ya na shafawa a hankali dan ba karya Zayd ya damko shi da karfi Ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " Diya wai me ya sa ka ke yawwan takura min ne haka ? " Ba tare da ya juyo ba ya ce " ni ban takura maka ba kai ne ka takura min ina cikin barci na mai dadi ina mafarkin malam ya ba ni auren baby na shi ne za ka zo ta tashe ni , na ga kai ma ka na da dakin na ka me ya sa ba ka je ka kwana a cen ba , shikenan tun da baza ka iya kwana a cen ba ni zan koma cen dan ni bazan kwana da kato ba " Bude idanun shi Zayd ya yi ya kali Moussa kafin ya ce " amma fa ka san a kan matata ka ke wannan maganar ? " Juyowa Moussa ya yi ya kale shi cikin ido ya ce " eh na sani a kan matar da ba ka so na ke magana, kuma gobe sai na je na fadawa malam ba son ta ka ke ba ya matsa maka ka sake ta na aure ta " Ya na gama fadar haka ya ida Hayewa gadon ya konta ya juyawa Zayd baya Zayd kuma ya na kallon shi har sai da ya konta sannan ya ce " Diya in har ka na son ta me ya sa tun farko ba ka nemi auren ta ba sai da ka bari lokaci ya kure " Juyowa Moussa ya yi su na fuskantar juna ya ce " ai yanzu ma lokacin bai kure ba na ga ai matar ka matata ce ka ga ai lokaci bai kure ba " " ka yi fa karatun kur'ani " Zayd ya fada ya na kallon shi " na ga kai ma ka yi karatun kur'ani, kassan sarai mi a ke nufi da aure, ka kuma san hankin da yarinyar nan ta ke da a kan ka , ba na ciyar da ita da tufatar da ita kadai ba , ta na bukatar ka a kusa da ita , you know she is too young, duk a shekaru baza ta wuce 15 years ba a ka aura maka ita, har yanzu fa da kuruciya a tatare da ita amma ba ka gani , Zayd yanzu wajen two weeks da ta dawo gidan nan da zama amma ko so daya ba ka bude baki ka yi mata kalma daya da za ta sa ta ji dadi cikin gidan nan , shin ka san wani abu dazu da na tambaye ta dalilin mi ta ke son ka haka har ta yarda da auren ka da karancin shekarun ta baza ta tsaya ta more rayuwar ta ba , ce min ta yi ta fi son ta more rayuwar ta cikin gidan mijin ta , ko da ba ka iya ganin ta, ko da in ta yi maka magana baza ka amsa mata ba , ta na jin dadin zama da kai a hakan , ta ce min tun kafin ta san minene assalin so ta ke fama da soyayyar ka a cikin zuciyar ta , ta tambayi kan ta so adadi dalilin mi ta ke son ka amma ko wane lokaci zuciyar ta amsa guda ta ke bata shin kassan micece wannan amsar ? " ya kai karshen ya na daga mishi gera guda Girgiza mishi kai Zayd ya yi allamun a'a Murmushi kadan Moussa ya yi kafin ya ce " Kaddara , kaddarar ta ce kamuwa da soyayyar wanda ko ganin ta bazai iya yi bare har ya kamu da son ta saboda kyawonta , a haka kuma ta amshi kaddarar ta hannu bibiyu , na tambaye ka lokacin da ka ke Amir Nawfel , mata nawa ne a basu tunkare ka ba da kalmar so , da d'iyan sarakuna har na cikin gari, mace nawa a bata kawo maka kanta ba da sunnan ka yi konciya da ita ma kawai, saboda dukiya da tarin mulkin da Allah ya yi maka , amma yanzu duba ka gani inda rayuwa ta kawo ka tun shigowar mu Nigeria ban ga macen da ta zo ta bude baki ta ce ta na son ka , sai wannan yarinyar da ko wuta ka ce mata ta fada sai ta fada saboda irin son da ta ke maka , duk da ba ta san ko kai waye ba ba ta san assalin ka ba, karewar zancen kallon kurma da makaho ta ke yi maka amma a hakan ta ke son ka , ba ka tunanin kai ma ta ka kaddarar ce ta hada ka da ita, ba ka tunanin kashe ka da a ka yi kokarin yi cikin masarauta har ka tsero nan Nigeria ba dan ku hadu ba ne kai da ita , wlh Amir na yi rantsuwa babu ko kaffara duk ranar da yarinyar nan za ta daina son ka wlh wlh baza ka taba samun Macen da za ta so ka tsakanin ta Allah da zuciya daya kamar wannan " Ya na gama fadar wannan ya juya ya bawa Zayd baya ya lumshe idanun shi Zayd kuma da ya zuba mishi ido tun da ya fara magana ya na kallon shi har sai da ya ida ya juya ya bashi baya Duk jikin shi ya bi ya mutu jin abin da Moussa ya fada mishi sai juya kalaman shi ya ke cikin kai Sannu sannu har barci ya dauke shi ya na wannan tunanin Washe gari Inaya Misalin karfe 6 na safe ta farka da ga barcin ta , ta yi duk wasu ayikan gidan ta shirya musu breakfast ta ci , sannan ta koma bedroom din Zayd ta yi wanka ta shirya cikin uniform din ta, misalin karfe 7 ta bar gidan ba tare da ta nemi kowa ba bare ta gaishe da su Bayan ta baro gidan kai tsaye college ta wuce ko gidan su ba ta biya ba wajen Nesrine dan har yanzu ta na fushi da ita A haka ta isa school ita kadai ta wuce class din su , ko lokacin break ba ta fito ba ta na cikin class har sai da su ka Kamala lokacin saukar su ya yi sannan ta fito nan ma ba ta nemi Nesrine ba ta kama hanyar gida A hankali ta ke tafiyar ta saman titi ita kadai, ta sunkuyar da kai Ta na a haka ta jiyo Muryar Nesrine ta na kiran sunan ta , sarai ta ji ta amma ta ki tsayawa ta ci gaba da tafiyar ta ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 14 ❤🔥 Da gudu Nesrine ta tunkaro ta ta na kwalla mata kira amma Inaya ta ki tsayawa Har sai da ta karaso wajen ta ta na fadin " ke Inaya ki na ji na za ki kyale ni " A hankali Inaya ta dago kan ta, ta kali Nesrine da ke ta faman haki saboda gudun da ta yi ta ce " lafya ki ke nema na haka ko yanzu ma kin zo ki ci zarafin yaya Zayd ne ? " Hararrar Nesrine ta yi kafin ta ce " Inaya wlh ba ki da kirki yanzu kennan duk son da ki ke ma yaya Zayd dan kin san gaskiyar shi ba makaho ba ne , ba kuma kurma ne ba amma ki ka shanye ki ka ki fada min " Tsaki Inaya ta ja kafin ta juya ta fara takawa ta na fadin " ni ban san maganar me ki ke ba kin fi kowa sanin yaya Zayd kurma shi ne za ki zo min da wata magana cen daban kin ga ni don Allah kyale ni sauri na ke na koma gida " Da sauri Nesrine ta bi bayan ta , ta dafa kafadar ta Cak Inaya ta tsaya ta juyo ta na kallon ta " Inaya ki na son ki ce min ba........." kut maganar ta yanke sakamakon wata mota da ta tunkaro su da gudu Sarai Nesrine ta gane waye ke cikin motar , har sai da gaban ta ya fadi ta na zaro idanu Kallon ta Inaya ta yi sannan ta juya ta kali motar da ta nufo su da mugun gudu Dan rumtse idanun ta tayi sannan ta bude a kan motar dai'dai lokacin da ta ke jan wani wawan burki har sai da kura ta tashi Motar na tsayawa Hafiz da Moctar su ka fito da ga cikin motar Inaya na ganin Moctar ta saki tsaki ta kauda kai gefe , ta juya za ta bar wajen Da sauri ya sha gaban ta ya na fadin " ina kuma za ki je ki gaisawa ba mu yi ba" Hararrar shi ta yi da ga sama har kassa ta ce " ka ga malam ka bani lafya na fada maka ni matar aure ce " Dariya ya yi kafin ya ce " yo ai ni ma mijin aure ne " Tsaki ta ja ta raba ta geffen shi za ta wuce Da sauri ya riko hannun ta ya na fadin " ki tsaya ki ji mana ! " Cikin zafin nama Inaya ta juyo ta wanka mishi wani gigitacen mari ji ka ke tassss Sai da Nesrine da Hafiz su ka zaro idanu su na kallon Moctar kuma a dubu dari ya dago kai ya na kallon ta , idanun shi duk sun sauya sun koma ja sai rawar jiki ya ke murya na kerma ya ce " ni ki ka mara ? " Cikin ko in kula ta hararre shi ta ce " eh na mare ka me kuma za ka yi sakare kawai " Ta na gama rufe bakin ta, ta ga ya daga hannu shi saman zai mare ta Da sauri ta rumtse idanun ta ta sa hannayan ta biyu ta toshe bakin ta na jiran saukar marin Amma dai ba ta ji saukar marin ba , a hankali ta janye hannayan ta , ta bude idanun ta slowly sannan ta dago kai Dum ta ji gaban ta ya fadi ganin Zayd tsaye ya na rike da hannun Moctar sai kallon juna su ke cikin ido Murya na kerma ta bude baki ta ce " yaya Zayd " Ba tare da ya juyo ya kaleta ba ya ce " wuce ku tafi gida " Da sauri ta juya har ta yi taku daya ta tsaya cak ta na zaro idanu ta bude baki ta na tantamar abun da ta ji yanzu Shi kuma Zayd ya na fada mata hakan ya saki hannun Moctar ya ce mishi " kar na sake ganin ka kusa da ita if not " Kallon shi sama da kassa Moctar ya yi kafin ya juya ya ce ma Hafiz su ta fi cikin zuciyar shi kuma ya dauki alwashin sai ya rama abun da Inaya ta yi mishi ba za ta mare shi ta ci bilis ba Da wannan tunanin su ka shiga cikin motar su su ka bar wajen Su na barin wajen Zayd ya fara takawa ya yi gaba ya kali Nesrine ya ce me ku ke jira wuce ku tafi Jinjina mishi kai tayi kafin ta karaso wajen da Inaya ke tsaye ta riko hannun ta ta ce su tafi Ta na rufe bakin ta ta na ga Inaya ta sulale ta Zube a kassa Da karfi ta saki kara ta na kiran sunan ta Da sauri Zayd ya juyo ya kale ta, ta na konce a kassa sumamiya Da sauri ya dawo inda ta ke ya tsuguna sannan ya sa hannayan shi duka biyu ya dauke ta cak kamar baby sannan ya tashi ya juya ya fara takawa Nesrine na biye da bayan shi su ka bar wajen A haka su ka ci gaba da tafiya har su ka karaso bakin kofar gidan su Inaya sannan ya ce ma Nesrine " wu ce ki shiga gida sannan kar ki fadawa kowa abun da ya faru , idan yamma ta yi za ki iya zuwa ki gan ta " Ya na gama fadar haka ko amsar ta bai jira ba ya wucewar shi Ita kuma ta shige gidan ta na sallama Yayi tafiya kadan sannan ya iso gidan shi Da sallama bakin shi ya shigo cikin falon gidan A hankali Moussa ya dago kai ya na amsa mishi sallamar Da sauri ya mike tsaye ya nufe shi ya na fadin " Amir me kuma ya same ta " Bai amsa mishi ba ya wuce ya kontar da ita saman doguwar sofa sannan ya ajiye bag din ta saman table Ya kali Moussa ya ce " ba komai ina ga yar firgita ne ta yi " ya kai karshen ya na zama saman sofa Komawa Moussa ya yi ya zauna geffen shi ya na fadin " firgita kuma garin yaya " Kallon shi Zayd ya yi kafin ya ce " na ga kai kace min na yi mata magana to shi ne nayi " Bushewa da dariya Moussa ya yi kafin ya kai hannu ya bugi damtsen Zayd ya na fadin " kai amma Allah Amir ka cika dan duniya , dan na ce ka yi mata magana ai da sai ka bari ta dawo gida mana " Hararrar shi Zayd ya yi ya na shirin magana ya ga Inaya ta fara murkuso ta na neman tashi Kallon Moussa ya yi kafin ya ce " toh ai gashi nan ka tayar da ita " ya kai karshen ya na dan siririn tsaki ya tashi ya nufi corridor ya koma bedroom din shi Ya na barin wajen Inaya ta bude idanun ta a hankali ta na karanto kalmar shahada Sai da Moussa ya ji ta ida karanto kalmar shahada sannan ya ce " babyn Zayd , ya har kin tashi na dauka doguwar suma ki ka yi " ya kai karshen ya na yar karamar dariya A dubu dari ta mike zaune ta na zaro idanu ta kaleshi ta ce " yaya Moussa , amma abun da na ji ba gaskia ne ba ko ? " Daga mata gera ya yi kafin ya ce " wane abu kuma baby ? " Cike da tantama ta ce " yaya Zayd na ji wai ya yi min magana " Dan karamin murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " to minene a ciki dan ya yi miki magana ko ba ki son ya na yi miki magana ne ? " " yaya Moussa ce maka fa na yi yaya Zayd ya yi min magana " " eh na ji abun da ki ka fada " " kuma shi ne ba za ka damu a kai ba yaya Zayd fa kurma ne ba ya magana ace lokaci guda ya yi magana babu shiri " Yar dariya Moussa ya yi kafin ya mike tsaye ya kale ta ya ce " shi ya kamata ki yi ma wannan maganar ba ni ba " Ya na gama fadar haka ya fara takawa ya nufi corridor ya shiga bedroom din shi Nan ya bar Inaya sai faman muzurai da ido Ta na zaune a haka Zayd ya fito da ga cikin corridor din ya na sanye da jallabiya dark blue mai dogayen hannu ya na sanye da bakin glass din shi Tun da ya fito corridor din ta zuba mishi ido har sai da ya kai bakin kofar fita falon sannan ta ce " yaya Zayd " Cak ya tsaya shi bai juyo ba shi bai yi tafiyar shi ba Shiru ta yi ta zuba mishi ido ta na son mishi magana amma harshen ta ya yi mata nauyi ta kassa Shi kuma jin yadda ta yi shiru ta tsaida shi ba tare da ya juyo ba ya ce " zan je massalaci idan na dawo ma yi magana " ya kai karshen ya na ficewar shi dan ya san maganar da ta ke son yi mishi kennan Ta na kallon shi baki sake har ya fita sannan ta koma ta zauna saman sofar ta na zaro idanu ta rassa me za ta yi dan ta na neman ta zauce A haka Moussa ya fito ya same ta shi ma sanye de jallabiya fara , bai bi ta kanta ba ya wucewar shi ya bar gidan Da kallo ta raka shi har ya fita sannan ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta shiga corridor ta nufi bedroom din Zayd Kai tsaye toilet ta nufa ta yi wanka ta daura Alwalla sannan ta fito ta shirya cikin doguwar riga mara nauyi sannan ta gabatar da sallar ta Bayan ta Kamala ta shiga gyaren gidan har da bedroom din Moussa ta gyara sannan ta nufi kitchen ta shirya musu abinci Misalin karfe 5 na yamma Ta na zaune cikin falon gidan ta kurawa Tv ido amma a zahirin gaskia hankalin ta ba a kan Tv ba ya ke ta fada duniyar tunanin ta Ta na a haka Zayd da Moussa su ka shigo falon su na sallama amma ta Zayd cen kassan makoshi ya ke yin ta, ta Moussa kadai ta fito fili A tare su ka karaso cikin falon su ka zauna saman sofar da ta ke fuskantar ta ta Kare mata kallo Zayd ya yi ya na son ya karanci wani abu saman face din ta Duk sun yi nisa cikin tunanin su , su ka tsinci Muryar Moussa ya na fadin " baby me kuma ki ke kallo haka ko sallama ba ki amsa mana ba ? " Ko motsi ba ta yi ba, ta kura wa Tv ido A hankali Zayd ya mike tsaye ya karaso sofar da ta ke zaune , ya zauna geffen ta ya kai hannu a hankali ya kyasta mata yatsun shi biyu saitin face din ta A razane ta dawo cikin hayacin ta , ta na sauke ajiyar da karfi Slowly ta dawo da kallon ta gare shi Daga mata gera guda ya yi allamun minene ? Wasu yawu ta hadiye cike da tsoro ta ce " yaya Zayd ka na iya gani na ? " Jinjina mata kai ya yi ba tare da ya ce komai ba " kuma ka na iya magana ? " ta sake tambayar shi Jinjina mata kai yanzu ma ya yi ya na tsare ta da idanu shi Lumshe idanun ta tayi a hankali ta sake bude su a kan shi cikin zuciyar ta ta na fadin " kenan yaya Zayd mayaudari ne , duk abun da muka sani kan shi ba gaskia ba ne ? " TIR KASHI AIKI SABO, YANZU YA INAYA ZA TA YI JIN ZAYD BA MAKAHO BA NE BA KUMA KURMA BA NE ZA TA CI GABA DA SON SHI ? HMM SAI DAI GOBE IN MUN HADE ZA KU JI AMSAR ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 15 ❤🔥 Ta yi nisa cikin tunanin ta ta tsinci wannan zazzakar Muryar ta shi ya na fadin " ni ba mayaudari ba ne kamar yadda ki ke tunani " Da sauri ta kaleshi kennan ya san abun da ta ke tunani ? Ta tambayi kanta Ta na tsaka da wannan tunanin ta ga ya sa hannu a hankali ya zare bakin glass din shi ya zuba mata wadanan Hazel eyes din shi Da sauri ta dafe saitin zuciyar ta , ta datse idanun ta da karfi dan ba karamar tsorata ta yi ba A hankali ya juyo ya kali Moussa da ya zuba musu ido tun dazu ya na murmushi Ya na ganin kallon Zayd ke yi mishi ya sa ya mike tsaye ya koma bedroom din shi ya basu wuri dan ya san haka kallon Zayd ke nufi Ya na barin wajen ya dawo da kallon shi kan Inaya , slowly ya ce da ita " kin tsora ta ne ? " Jinjina mishi kai ta yi ba tare da ta bude idanu ba Jinkirtawa ya yi kafin ya ce " open your eyes ba abun da zai faru " Girgiza mishi kai tayi cikin murya kamar za ta yi kuka ta ce " yaya Zayd bazan iya ba " " bude idanun ki ina son muyi wata magana " ya fada mata cikin sanyi murya Yanayin da ya yi mata maganar ya sanya ta sauke ajiyar zuciya , a hankali ta fara kokarin bude idanun ta Karafff ko sai cikin nashi dan shi ma ita ya ke kallo Sai gani ta yi ba karamin kyau ya kara yi mata ba , wadanan eyebrow sun fito ainahin su a cike sun konta luff kamar shi ya zana su , da wasu zarazaren eyelashes din shi sun kara kayata fuskar ta shi , da ya cire glass din shi sai ta face din kamar ba tashi ba Duk sai ta ji ta tsargu sa kallon shi ta kassa janye idanun ta da ga cikin nashi Su na a haka ta jiyo wannan zazzakar Muryar ta shi cikin nitsuwa ya ce mata " nassan za ki tambayi kan ki dalilin mi na meda kai na makaho da kurma , nassan cikin zuciyar ki ki na min kallon mayaudari , amma zan so ki san ba haka ba ne " Dan lumshe idanu ta yi kafin ta bude su a hankali ta sunkuyar da kai ta riko hannun ta kafin ta ce " ban san dalilin ka na yi haka ba yaya Zayd , a ce duk wannan shekarun da muka dauka tare ko kalma daya ba ka taba fada ba a gaba na , ni ba ma wannan ba yaya Zayd ina son in san wanene kai " , Sunkuyar da kai kassa shi ma ya yi ya riko hannayan shi biyu kafin ya fara magana kamar haka " ba zan iya fada miki ko ni wanene a yanzu ba , kawai ki yi min kallon Zayd dan haka na ke , babu abun da zai sauya ko na fada miki , ni a sani na tun lokacin da na shigo garin nan ban taba ce ma wani ni kurma ne ko makaho akasi ma ni haka na ke magana nauyi ta ke yi min ko yanzu ji na ke kamar harshe na zai fado kassa , lokacin da mu ka zo garin nan ba na jin haoussa duk yadda zan yi magana mutane ba su ganewa haka ya sa na dinga yin shiru kawai , a dalilin mourir da shi ma da kyair ya koyi haoussar ya koya min , ni fa har yanzu ba wata cikakiyar haoussa na iya fa " Bai karasa maganar shi ba sakamakon yar dariyar da Inaya ta yi ta na fadin " yadda ka ke wannan maganar kuma ka ce ba ka iya haoussa , wanda bai sanka va zai ce a bakin ka a ka yi haoussar " Wani dan karamin murmushi geffen fuska ya yi ba tare da ya dago kai ba ya ce " nassan abu mai wuya ne ki yarda da hakan amma bazan ga laifin ki ba , har yanzu ke yarinya ce , ko na fada miki wasu abubuwa baza ki fahimta ba , amma zan so ki sani , ni ba mayaudari ba ne banzo nan da niyar cutar wa ba , ban aure ki ba da niyar cuta , akasi ma ba a son raina ba a ka yi wannan auren kuma ban san manufar wannan auren ba , bazan iya sakinki ba , kuma bazan iya daukar ki a matsayin matata ba , kin yi min kannanta gaskia , amma zan rike ki a matsayin sister di ta , kema zan so ki dauke ni a matsayin brother din ki , duk wani abu da za ki bukata ki fada min , kar ki ji kunyar yi min wata magana , idan har kuma Allah ya saka miki soyayyar wani a cikin zuciyar ki zan so ki fada min da kai na zan aura miki shi a matsayi na na brother din ki " Ya kai karshen ya na dago kai ya kale ta Ita ma dago kai ta yi ta na murmushi ta kaleshi ta ce " shikenan yaya Zayd ni ma zan dauke ka a matsayin brother di na duk da dama a hakan na dauke ka " Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce " shikenan sister yanzu kin ga lokacin sallat ya yi sai ki tashi ki tafi ko , nan da next week ina son mu sauya gida dan ina ga fa wannan ya fara yi mana kananta " Yar karamar dariya ta yi har sai da fararen hakoran ta su ka bayana sannan ta ce " shikenan yaya Zayd , kai ma ka tashi ku tafi massalaci idan kun dawo mu ci abinci a tare yau " " okay ba matsala " ya fada mata a takaice Murmushi ta yi kafin ta mike ta nufi corridor ta shiga bedroom din shi Ta na shiga Moussa ya fito ya ce ma Zayd su tafi Ba musu ya tashi ya bi bayan shi su ka tafi mosque After one week A takaice haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a cikin wannan gidan , Tsakanin Inaya da Zayd shakuwa ta shiga tsakanin su sosai , idan ya na gida kullum su na a tare su na hira duk da yawwan ci ita ke yin ta , wani lokaci shi da kan shi ya ke rakata school , sannan in lokacin tashin su ya yi , kuma ya koma su dawo a tare , ya na kula da ita kamar kanwar shi ta gaskia , shi duk wannan abun da ya ga ta na yi mishi a zaton shi ta daina son shi , shi kuma bai san tarko su ka shirya mishi ita da Moussa ko wane tarko ne wannan oho ? A cikin yan kwana kin Nesrine ta je ta bawa Zayd hakuri da mumunar kallon da ta ke yi mishi , ya nuna mata babu komai , da ga haka Inaya ta roke ta ta dinga zuwa ta na taya ta hira idan ba ta da aikin yi amma ta nuna baza ta iya ba dan ta na tsoron yin karo da idanun Zayd A takaice dai su na rayuwar su cikin konciyar hankali duk sun manta da wata damuwar su Inaya Zaune ta ke cikin falon gidan ta na kallon shirin Akushi da Rufi na tashar Arewa 24 , Ta na zaune a haka Zayd da Moussa su ka shigo su na sallama kamar dai kullum ta Moussa a ka ji Da murmushi a face din ta ta amsa musu sannan ta yi musu sannu da zuwa Moussa ne ya amsa mata sannan ya wuce corridor ya shiga bedroom din shi Shi kuma Zayd ya karaso ya zauna saman sofa da ya ke fuskantar ta ta Ta na ganin ya zauna ta juya kai ta ci gaba da kallon Tv din ta , shi kuma ya kura mata ido a cikin bakin glass din shi Sai da ya dauki lokaci ya na kallon ta kafin ya ce " Za muyi tafiya ni da Moussa , baza mu wuce one week ba , idan kin ga baza ki iya zama nan ke kadai ba za ki iya komawa wajen uncle duk lokacin da ki ka so , sannan ki kiyaye wajen zuwa college babu fashi , akwai kudi cikin bedside drawer ko da kin bukaci wani abu duk lokacin da ki ka yi niyar zuwa wajen uncle za ki iya tafiya " Jinjina mishi kai ta yi ba tare da ta juyo ta kaleshi ba ta ce " yaushe za ku tafi yaya Zayd ? " " yanzu " ya fada a takaice Da sauri ta juyo ta kaleshi lokaci guda idanun ta su ka kawo ruwa Ta na shirin magana ya riga ta cewa " no please kar ki yi kuka , just one week za mu yi , sannan akwai waya a cikin bedside drawer zan ringa kiran ki kullum dan na ji ko lafya , ki kontar da hankalin ki , baza mu dade ba " Ya na gama fadar haka ya mike tsaye dai'dai lokacin da Moussa ya fito da ga cikin corridor janye da trolley din su Hawayen da su ka tsaya mata a ido ne su ka fara zubowa a hankali ta na kallon Zayd da ke kallon ta shi ma Dan lumshe idanun shi ya yi kafin ya bude su a hankali cikin zuciyar shi ya na jin ba dadi zai rabu da ita ba karya yan kwana kin nan da su ka yi ya saba sosai da ita dan ta na rage mishi kewar kanwar shi A hankali ya bude hannayan shi ya yi mata allamun ta zo Da gudu ta taso ta fada saman fafadar kirjin shi ta na sakin kuka Shi kuma ya rufe hannayan shi ya rungume ta tsam kamar na ce zan kwace mishi ita Tabe baki Moussa ya yi ya na kallon su cikin ranshi ya na kara godewa Allah da ya nuna mishi wannan ranar Da sauri ya ciro wayar shi da ga cikin aljihun shi ya dauke su hoto har wajen biyar Bayan ya meda wayar shi cikin aljihu ya yi musu gyara murya ya na fadin " Romeo saki Juliette don Allah mu tafi kar mu makara " ya kai karshen ya na gumshe dariya sannan ya fara takawa ya fice falon A hankali Zayd ya zame hannayan shi da ga bayan ta ya raba jikin su sannan ya kai hannayan shi saman face din ta ya goge mata hawayen ta sannan ya ce " ki kula da kan ki zan kira ki idan mun isa " Jinjina mishi kai kawai ta yi ta na sunkuyar da kai dan kar wasu hawayen su zubo mata idan ta kaleshi Ya na fadar haka ya juya ya fara takawa zai bar falon Har ya kai bakin kofar ya tsaya , sai da ya dauki wajen good one minute kafin ya juyo a hankali ya tako ya tsaya gaban ta Babu shirin ta ji saukar wadanan lalawsan lips din shi saman forehead din ta Dan zaro idanu ta yi kafin ta lumshe su à hankali ta na sauke a zuciya Kafin ta bude idanun ta tuni ya fice falon Kallon kofar ta yi kafin ta saki wani dan murmushi ta ce " Allah ya kiyaye hanya yaya Zayd, Allah ya medo ku lafya " Ta na gama fadar haka ta koma zaune saman sofa ta buga uban tagumi ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 16 ❤🔥 Washe gari Washe gari kamar dai kullum yau ma karfe 6 na safe ta farka da ga barcin ta , ta yi duk wasu ayika na cikin gidan sannan ta shirya breakfast din ta ta ci sannan ta shiga wanka Misalin karfe 7 ta baro gidan ta na shirye cikin uniform din ta, ta na rike da school bag din ta, ta na tafiya cikin konciyar hankali Dai'dai ta karaso kofar gidan su Nesrine ta fito tare da malam Ta na ganin malam ta fada jikin shi da gudu ta na murmushi ta ce " ina kwana Abba " Murmushi shi ma ya yi ya na kai hannu saman kanta ya shafa ya na fadin " lafya lau Auta , ya ki ke ? Ina mai gidan na ki ? " Raba jikin ta da nashi ta yi kafin ta ce " sun yi tafiya shi da yaya Moussa " " shikenan Allah ya medo su lafya, wuce ku tafi car ku yi late " Da to su ka amsa mishi ita da Nesrine kafin su riko hannun junna su yi tafiyar su Sai da malam ya jima ya na kallon yada su ke tafiya su na wassa sannan ya juya ya koma cikin gida Su Inaya kuma sai da su kussa isowa college din su sannan Nesrine ta ce mata " yaya Zayd bai fada miki lokacin da zai dawo gida ba ? " Ba tare da ta kaleta ba ta ce " one week ya ce min za su yi " Jinjina kanta Nesrine ta yi su ka ci gaba da tafiyar ba wanda ya ce ma wani uppan har su ka karaso college din su, a nan ne kowace ta nufi class din ta After some days Yanzu kwana shida kenan da tafiyar su Zayd , Inaya kuma ta koma gidan malam dan ya ce ya na tsoron wani abu ya same ta a cikin gidan , akasin sa a ka samu lokacin da ta dawo gidan malam ta manta ba ta dauko wayar da Zayd ya ce mata ta dauka cikin bedside drawer , ranar da ta koma gidan malam a ranar ya yi mata kira na farko ba ta daga ba tun da ga lokacin kullum sai ya kira ta amma ba ta dagawa, sannu sannu har ya fara damuwa a kan ta , Inaya kuma sam ba ta san abun da ke faruwa ba dan ta na cen gidan su ta na sha'anin ta da Nesrine da ga school sai gida , sai kuma islamyar da malam ke yi musu a cikin gidan kuma , kwana biyu duk ta bi ta wanke dan wannan karan mama ta ce ba za ta bar ta ta koma gidan mijin ta a haka ba , kun dai san Haoussa fulani da iya gyaren jiki to haka Inaya ta sha gyara har wani haske ta kara skin din ta ta kara fitowa chocolate gwanin burgewa kamar ka sace ta ka gudu Shin cikin ku ba wanda zai tambaye ni da Moctar kuma ? Hum tun ranar da Inaya ta mare shi ya saka mata ido , har tafiyar da Zayd ya yi ya na sane da ita , har komawar ta gidan su duk ya na sane , lokaci kawai ya ke jira dan ya aiwatar da abun da ya shirya mata TOHHHH KO WA NE ABU NE WANNAN , DA GA JI DAI NA SAN BA AL'HERI BA NE 😓 Washe gari ( week-end ) Abuja Zayd Wani katafaren office na glass , da ga ciki ka na iya hangen abun da ke waje amma na waje ba ya iya ganin na ciki , komai na cikin office din fari ne kal , har tiles din wajen farare ne kal sun sha mopping sai kyali su ke kamar yanzu a ka saka su , a geffen dama wasu lalawsan sofas ne farare guda uku , guda three seater da biyu two seaters su na fuskantar juna , sai wata yar karamar table a tsakiya , bayan doguwar sofar wani madaidaicin fridge ne , a geffen hagu kuma wani closet ne dauke da wasu files colour daban daban , sai wani desk da ke fuskantar kofar shigowa office din da wani computer a sama, sai dan takardu da files a gefe daya, a daya geffen kuma wani kwalin tissue ne , bayan desk din wata lalawsar chair ce fara kal cikin ledar ta da allamun sabuwa ce , office din sai tashin wani dadaden kamshi ya ke A hankali ya turo kofar office din ya shigo kai a sunkuye ya na kallon wayar shi , ya na sanye da wando jeans baki da t-shirt purple , gashin kan shi ya dan taru dan yanzu ya kai mishi har bayan wuya ya zubo saman shoulder din shi , sai baza kamshi yake duk irin kamshin da office din ya ke sai da kamshin turaren shi ya kashe shi Slowly ya ke takowa, Moussa na bayan shi ya na rike da wani file ya na dubawa sai magana ya ke mishi amma sam ba ya jin shi ya yi nisa cikin duniyar tunanin shi Sai da ya karaso wajen sofas ya zauna saman three seaters ya na latsa wayar shi, Moussa na biye da shi ya na mishi magana Sai da su ka dauki lokaci kafin Moussa ya dago kai ya kaleshi ya ce " me ka ke tunani a kan wannan file din " Dago kan shi ya yi slowly ya kali Moussa ya ce " wane file " Zaro idanu Moussa ya yi kafin ya ce " ka na nufin duk abun da na yi ta fada maka sam ba ka ji ni ba " " dama magana ka ke yi ne " ya kai karshen ya na meda kallon shi kan wayar hannun shi Hararrar shi Moussa ya yi ya ce " amma wlh Amir ka ci uwar raina min hankali, yanzu duk zubar da na yi zaune ina yi ba ka ji ni ba , tsaya ma tukunna me ka ke kallo cikin wayar nan " Shiru za ya yi bai tanka mishi ba, sai da ya dauki lokaci kafin ya mike tsaye ya fara takawa zai bar office din ya na fadin " ka shirya mu koma kano yanzun nan " Da sauri Moussa ya ce " Amir mu koma fa , ko aikin da ya kawo mu ba mu gama ba ka ce mu koma " Ba tare da ya tsaya da ga tafiyar shi ya ce " za ka iya zama ni ka ga tafiya ta " ya fada dai'dai lokacin da ya isa bakin kofar ya ficewar shi Da kallo Moussa ya raka shi har sai da ya fita sannan ya ce " hmmm ni na san ba a banza ka ce mu koma kano , kawai ka kewar babyn ka amma ba ka iya fitowa ka fadi ba komai hakan ma wata nassara ce " ya kai karshen ya na mikewa ya bar office din shi ma Kano ( Gidan malam ) Misalin karfe 10 na safe Zaune su ke cikin yar runfar kofar dakin mama saman wata tabbarma Nesrine na tsintar shinkafa , Inaya kuma na yankar kayan lambu , mama kuma ta na kallon su gwanin ban sha'awa Su na a haka Inaya ta kali mama ta ce " mama ina son in koma cen gida in gyara shi , gobe yaya Zayd zai dawo dan gobe ya ke cika one week da tafiya kuma ya ce min one week za su yi " Murmushi mama ta yi dan har cikin ran ta ta ji dadin maganar Inaya " babu komai bari in malam ya dawo zan fada mishi , in yamma ta yi sai ku tafi ke da Nesrine ta kama miki " Da to ta amsa mata kafin ta ci gaba da aikin ta Misalin karfe 4 na yamma bayan sun ida girki sun yi duk wasu ayika na cikin gidan sannan su ka tafi gidan Zayd , nan ma su ka gyara gidan tsab su ka share ko ina har da bedroom , su ka yi mopping , sannan su ka kunna ma gidan turaren wuta da mama ta basu su biyo da shi Sai wajen kirayen sallar magriba sannan su ka Kamala , Nesrine ta so su koma gida ita da Inaya amma ta ce nan za ta kwana a haka ta hakura ta koma gida ita kadai Inaya kuma bayan ta gabatar da sallar magriba ta fara daura girkin abun da za ta ci , sai bayan sallar isha sannan ta Kamala A nan falo ta zauna ta ci abincin ta ta na kallon Tv hankali konce ba ta ma tsoron wani abu ya same ta cikin gidan Bayan ta Kamala cin abincin ta , ta gyara wurin ta kai dishes din kitchen ta wanke sannan ta dawo ta ci gaba da kallon Tv din ta Sai wajen karfe 11 na dare ta tashi ta shiga bedroom din Zayd ta konta ba jimawa barci ya yi gaba da ita Misalin karfe 1 na dare A hankali ya ke takowa cikin corridor din gidan hannun shi rike da torch ya na haska inda ya ke takawa Sai da ya kai bakin kofar dakin farko ya kai hannu ya murda handle din a hankali kamar barawo ya tura kofar ya shiga Sai da ya haske ko ina na cikin dakin da torch din hannun shi ya ga babu kowa sannan ya juya a hankali ya bar dakin Ya ci gaba da tafiyar shi har ya karaso kofar dakin da Inaya ke ciki A nan ma a hankali ya kama handle din kofar ya shiga a hankali Ya na shiga dakin ya fara haske wajen da torch din shi Cen Moctar ya hango Inaya konce ta gadon ta na sanye da kayan barcin ta wando da riga rigar ta nade mata har a na iya ganin cibiyar ta , wannan dark hair din ta ya baje saman pillow ta na barcin ta cikin konciyar hankali Ya na ganin ta ya saki wani makirin murmushi ya nufi dressing mirror ya ajiye torch din hannun shi a hankali sannan ya fara takowa a hankali ya nufi gadon Sai da ya tsaya ya kare mata kallo da kyau cikin zuciyar shi ya ce " yau dai zancen ya kare ba ni ki ka mara zan miki abun da zai kin mutu ba ki manta ba " Ya na gama fadar haka ya kai hannu ya cire rigar jikin shi ya tila ta saman gadon sannan ya zame belt din wandon shi ( WAYOOO , ALLAH KA KAWO MA BABYN ZAYD DAUKI KAR YA CUTAR DA ITA 😭😭 ) Tila belt din ya yi saman rigar shi ya kai hannu zai zame wandon shi , sai ya ji an damko hannun shi ta baya Dum zuciyar shi ta buga dan bai yi tunanin dakwai mutane cikin gidan Ya na shirin juyowa ya ga ko wa ya riko shi ya ji an toshe mishi baki, aka murde daya hannun da a le rike da da karfi har da ya yi wata kara Nan take idanun Moctar su ka kawo ruwa ya na son ya yi kara dan zafi amma ba hali Ya na a haka ya ji an juyo da shi a ka fara tura shi su ka bar dakin ba tare da an janye hannun da ya toshe mishi baki Su na fitowa falon gidan, Moussa ya shigo ya na janye da trolley Zaro idanu Moussa ya yi ya na kallon su cike da mamaki ya ce " Amir wanene wannan kuma " Bai bashi amsar tambayar shi ya wuce zai bar falon Da sauri Moussa ya kauce ya bashi hanya ya na sakin trolley din hannun shi ya bi bayan su da sauri Shi kuma Zayd ya na fitowa ya nufi parking space , Wani corridor ya bi ya koma bayan gidan wajen wata katuwar kofa ta mota , Sai da ya ka bakin kofar sannan ya janye hannun shi da ke saman bakin Moctar ya juyo da shi su na fuskantar juna Ido cikin ido ya kaleshi kafin ya ce " ka yi sa'a ba ka taba ta ba , zan kyale ka a haka amma duk ranar da na sake kanin ka ko da cikin inuwar ta ne sai na kashe ka " Ya na gama fadar haka ya kai hannun shi ya bude kofar ya tila shi waje , ya fadi kassa kan shi ya bugu da wani dutse nan wajen ya fashe Zayd kuma ya na tila shi ya rufe kofar ya juya zai bar wajen nan ya ga Moussa ya na tsaye ya zuba mishi ido " wai Amir wanene wannan, mi ya ke a cikin gidan nan " Moussa ya tambaye shi Takawa ya fara yi zai bar wajen , sa sauri Moussa ya bi bayan shi su ka bar wajen a tare Sai da su ka shiga cikin falon gidan sannan ya zauna saman sofa ya jingina a bayan sofar ya daga kai ya lumshe idanun shi ya na sauke ajiyar zuciya Geffen shi Moussa ya zo ya zauna ya na son ya ji abun da ke faruwa dan shi an bar shi cikin dufu ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 17 ❤🔥 Sai da su ka dauki lokaci a haka ba wanda ya ce ma wani ko uppan sannan Zayd ya sauko da kanshi ya bude idanun shi Kallon Moussa ya yi kafin ya ce " ban san ko wanene yaron nan ba , amma ya kai sau uku ina ganin shi ya tare wannan yarinyar , a na karshen ta mare shi dan ya ruko hannun ta , zai ramawa na iso wajen na yi mishi kashedin kar na sake ganin shi kusa da ita, nassan ya ji haushi maganar dalilin da ya sa ya fara bibiyar ta ya ga a ina ta ke in kuma ita kadai ce , tun ranar da muka tafi ta koma gidan uncle sai yau ta dawo gidan nan , dan ya san ita kadai ce a nan shi ya sa ya yi anfani da hakan ya zo ya yi raping din ta " Da sauri Moussa ya katse shi da cewa " what ? Rape fa ? " Jinjina mishi kai Zayd ya yi kafin ya ce " tun safiya na ke jin gaba na na faduwa na rasa dalili , sai da na ce maka mu tafi tun lokacin da na yi maka magana amma ka shiga ce min sai ka Kamala aikin da ya kawo mu , in ba dan Allah ya sa mun iso da sauri kai ka san irin abun da zai mata " Ya na gama fadar haka ya mike ya nufi corridor Jim kadan ya fito rike da torch din Moctar da rigar shi da belt , ya ajiye su saman table sannan ya ce wa Moussa in ya tashi ya jefar da kayan da ga haka ya koma bedroom din shi ya bar Moussa nan zaune a falon Ya na shiga bedroom din shi ya koma bakin gado geffen ta ya konta , ya daura hannun shi daya saman goshi dayan kuma saman cikin shi , ya lumshe idanun shi ya na tunanin da yanzu bai zo da wuri ba a wane irin hali zai tardo ta , sa yanzu Moctar ya cutar da ita da wane ido zai kali malam Da irin wannan tunanin barci ya yi gaba da shi Washe gari Misalin karfe 6 na safe ta ware idanun ta a hankali ta na karanto adu'ar tashi da ga barci Juyo kan da za ta yi ta gan shi konce a geffen ta sai da gaban ta ya fadi , cike da mamaki ta bude baki a hankali ta ce " yaya Zayd " Ya na jin ta kiri sunnan shi ya bude idanun shi slowly ya na kallon ceiling kafin ya dawo da kallon shi kan ta Dan murmushi tayi kafin ta ce " yaya Zayd ba sai gobe za ku dawo ba , shi ne za ka yi min irin wannan bazatar, ni na dauka aljani ne ma " Kallon ta ya ke cikin ido babu ko kiftawa ya ki ba ta amsa Ganin kallon nashi ya fara takura mata ya sa ta yi sauri ta yi kokarin mikewa za ta bar wajen Da sauri ya riko hannun ta ya janyo ta da karfi ta koma ta konta ya na fadin " ina za ki je ne yau fa week-end , konta ki huta " Kallon shi ta yi ta na murmushi kafin ta ce " amma yaya Zayd zan je ne f......" Da sauri ya dora yatsar shi saman lips din ta ya katse ta da cewa " shiiiiiiiiii ki konta na ce , ko kema yanzu Nesrine ta koya miki kin jin magana ? " Da sauri ta girgiza mishi kai ta na son ta ce mishi sallat ta ke son ta je ta yi dan yau ba ta samu ta tashi da asuba ba amma ya hana ta magana Daga mata gera guda ya yi ganin yadda ta kura mishi ido ya ce " why ki na kallo na haka , ko za ki dake ni " Da sauri ta girgiza mishi kai ta na murmushi Slowly ya janye yatsar shi da ga saman lips din ta Kamar jira ta ke dama, ya na janye yatsar shi ta bude baki za ta yi magana Da sauri ya meda yatsar shi ya na fadin " no shiru za ki yi yau baza ki cika ni da surutu ba , bakin dan guntu amma sai bala'i surutu kamar parrot " Matse girar ta ta yi ta turo dan bakin nan nata ta fara gunguni kassa kassa wai ita ta ji haushin ya ce ta na da surutu " oh babyn malam duka na za ki yi , shikenan zan janye yatsa ta amma kar ki yi magana kin ji ko ? " Da sauri ta girgiza mishi kai allamun to A hankali ya janye yatsar shi ya zuba mata idanu Sai da ta dauki lokaci dan ta shan'mace shi sannan ta ce " ni ba di surutu kamar parrot " ta kai karshen ta na murguna mishi baki Dan zaro idanu yayi ya na kallon kafin ya ce " ke wa ki ke ma wannan abun " Hararrar shi ta yi kafin ta ce " kai na ke ma , ni yaya Zayd ka kyale ni mun ma bata " " da wani shiri mu ke bare ki ce mun bata , amma shikenan tun da haka ne bara na tashi na koma inda na fito " ya kai karshen ya na kokarin mike wa zaune Ya na shirin sauko da kafafun shi kassa ya ji an buga mishi pillow a baya Da sauri ya juya ya na kallon ta Ta na zaune saman guyiwowin ta na rike da pillow sai hura kumatu da iska ta ke Ta na ganin ya juyo ta kara kai mishi wani bugun da pillow a fuska ta ce " wlh yaya Zayd ba bu inda za ka koma , sai dai mu tafi tare " Ta na rufe baki ya ce " ke lafiyar ki za ki buge ni ? " Bai gama rufe baki ba ta kai mishi wani bugun a fuska ta ce " e na buga , kuma na kara " ta kai karshen ta na kara kai mishi wani bugun Ta na shirin yi mishi na biyar ya damko pillow ya ce " kin yi na ki saura nawa " Dan zaro idanu ta yi ta na jan pillow din da karfi amma ina da hannu daya ya damko shi amma ta kassa kwace shi " yaya Zayd ka sake min pillow na " ta fada kamar za ta yi kuka Da karfi ya janyo pillow tare da ita ta fado saman fafadar kirjin shi , ya na kallon ta cikin ido ya ce " sai bala'in jan fada amma ba karfi " Kallon shi ta ke ita ma cikin ido sai ta ji ba za ta iya janye idanun ta daga cikin nashi ba Sun dauki lokaci su na kallon juna cikin ido ba wanda ya iya cewa wani abu Cen kuma Inaya ta ce dashi " yaya Zayd , ka taba kamuwa da soyayyar wata a cikin zuciyar ka " Ya na kallon ta cikin ido sai da ya dauki lokaci kafin ya koma slowly ya konta da ita a saman kirjin shi , a hankali ya kai hannu ya janye jelar gashin da ta zuba mata a geffen fuska ya ci gaba da kallon ta cikin ido Sai ya da ya jima a haka kafin ya ce " never ! Ko so guda ban taba jin ina son wata mace a cikin zuciya ta bayan Ammie na da kuma sister di ta sai kaka ta, su kade matan da na ji ina son su har cikin zuciya ta , bayan haka ban taba jin ina son wata mace ba , assali ma ni ko kallon mace ba na yi , ko magana idan mace ta yi min kyale ta na ke , idan har ba da maganar aiki ta zo min ba ko kuma an aiko ta ta kamin sako " Cikin zuciyar shi kuma ya ce " amma ban dalilin da ya sa ko wane lokaci na ke da bukatar ganin ki ba , ban san dalilin da ya sa kullum ni ke son na yi miki magana , ban san dalilin da ya sa ko wane lokaci na ke jin zuciya ta na bukatar ki kusa da ita " NI KUMA NA CE HUMMM TUKUNNA MA BA KA GA KOMAI BA 😝😂😂 Ya yi nisa cikin tunanin shi ya tsinci Muryar ta ta na fadin " yanzu yaya Zayd ka na da sister amma ba ta taba zuwa nan ba, ko dai kai ka ke tafiya ka gan ta " Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " no ba ta zuwa ni ma ba na zuwa assali ma a tunanin su na mutu , shi ya sa na kyale su amma kullum su na cikin raina duk lokacin da na yi sallat sai na saka su a cikin adu'a , ko ina son in je wajen su bazan iya ba , ba dan rashin kudi ba, sai dan abun da zan je na tayar , ba na bukatar shi a rayuwa ta amma ya zaman min dole, shi ya sa na ci gaba da zama na a nan gashi kuma Allah ya bani wata familyn daban " " yaya Zayd minene wannan abun da ba ka son ka tayar da shi da zai sa ka rabu da duk familyn ka , har su ringa tunanin ka mutu , kennan guduwa ka yi ? " ta kai karshen ta na zaro idanu Dan karamin murmushi geffen fuska ya yi kafin ya kai hannu shi saman face din ta ya ce " e guduwa na yi dan an nemi a kashe ni , amma ba su yi nassara ba , na san duk lokacin da na koma sai sun ida cika aikin su , shi ya sa na bar musu kayan su har lokacin da kaddara za ta meda ni amma ba ni fatan komawa na fi jin dadin zama a nan " A hankali ta kontar da kan saman kirjin shi kamar ta yi kuka ta ce " ban san abun da ya sa dan Adam ke yawwan son abun duniya , har ya kai ga kashe yan uwan shi saboda wani abun da a nan duniya zai bar shi , abun ba zai anfane shi da komai ba a ranar gobe kiyama sai ma ya jefa shi a halaka , ban san dalilin abun da ya sa su ke neman kashe ka ba yaya Zayd amma na san ko sun mallaki wannan abu ba za su rike shi tsakani da Allah , in har za su iya kashe mutun saboda shi " Hannun shi ya kai a saman bayan ta ya na shafawa a hankali sannan ya ce " ikon Allah ne kawai ya cece ni a ranar nan , kuma na gode mishi da ya kawo ni a cikin wannan garin , ko so guda ban taba yin nadamar guduwar da na yi , amma har ga Allah ina kewar family na amma ba zan iya komawa ba " Dago kan ta tayi ta na kallon face din shi ta ce " yaya Zayd don Allah ina son in san wanene kai , da ga ina ka ke , minene wannan abun da ya sa a le neman kashe ka har ka gudu ka bar familyn ka, don Allah yaya Zayd fada min " Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " ba zan iya ba gaskia , labari na me tsawo ne , ban shirya ba ki shi yanzu ba amma wata rana zan fada miki , wata rana za ki san wanene ainahin ....." kut maganar ta yanke sakamakon wani abu da ya tuno Kallon ta ya yi cikin ido kafin ya ce " kafin ku dawo kano da zama za ki iya tuna wane gari ku ka baro ? " Daga kan ta sama ta yi kamar mai tunanin wani abu kafin ta medo shi ta na kallon shi ta girgiza mishi kai tace " gaskia bazan iya tunawa ba , ni dai a sani na a nan kano na tasso " " ni fa za ki iya sannin da ga ina na gudo na zo Nigeria ? " ya tambayeta zuciyar cike da tsoro kar abun da ya ke tunani ya zama gaskia Dariya ta yi kafin ta ce " yaya Zayd ta ya zan iya sani bayan ka ki fada min " Hannu ya kai ya ja kumatun ta ya ce " na ji yanzu tashi ki je ki yi wanka ki shirya , sau je mu yi breakfast " Da to ta amsa mishi kafin ta yi kokarin tashi da ga jikin shi , ta sauko da ga saman gadon da gudu ta shiga toilet Ya na kallon ta har sai da ya ga ta shiga toilet ta rufo kofar , sannan ya mike ya nufi closet ya dauki kayan shi , wandon jeans brown da t-shirt fara , sannan ya fice dakin ya nufi bedroom din Moussa ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 18 ❤🔥 Tsaye gaban dressing mirror ya isko Moussa ya na fessa turare Bai tsaya bin ta kan shi ba ya wuce toilet kai tsaye Jim kadan ya fito sanye da kayan shi , ya karaso bakin gadon Moussa ya zauna a lokacin shi ma Moussa ya na zaune bakin gadon Kare mishi kallon da kyau Moussa ya yi kafin ya ce " me ya ke damun ka , na ga ka sauya lokaci guda " Shiru ya yi bai amsa mishi ba ko kallon shi ba baya yi ya fada duniyar tunanin shi Hannun shi Moussa ya kai ya dafa kafadar Zayd kafin ya ce " Amir me ya ke faruwa ne ? " Ajiyar zuciya ya sauke ba tare da ya dago kai ba ya ce " Diya wlh har yanzu zuciya ta zafi ta ke yi min , har yanzu ina jin zafin yadda ya so ya bata mata rayuwa , dama kashe shi na yi na huta da wannan zafin da na ke ji " Wani iska mai zafi Moussa ya furza da ga bakin shi kafin ya ce " ni kai na ina jin zafin abun nan , dama da ita muka tafi ko ba komi ta debe mana kewa , yanzu da wani abu ya same ta wlh ba zan iya kallon malam ba cikin ido , amanar ta ya ba mu ka ga dole mu kula da ita , ba kowa ne cikin duniyar nan zai dauki d'iyar shi guda ya bawa mutuman da bai san assalin shi ba , ko ainahin sunan shi bai sani ba, amma a haka ya yarda da kai ya baka ita ya kamata mu kula da ita tamkar rayuwar mu " Dan karamin hijab geffen fuska Zayd ya yi sannan ya ce " ta na yawwan tino min Amira Tesnim , wani bangaran cikin zuciya ta, ta na debe min kewar ta " Murmushi Moussa ya yi shi ma kafin ya ce " Amir yaushe za mu koma ne wai , ina kewar ahalin mu gaskia " " very soon in sha Allah , amma kafin nan , na yanke wata shawara " " wece shawara kuma ? " Jinkirtawa ya yi kafin ya ce " za mu koma gidan mu na Abuja da zama , da ga yau ta daina zuwa college , zan fara nema mata admition a wani private college daban a cen Abuja , zaman ta a nan ya na da hatsari zai iya dawowa yace ya rama abun da mu ka yi mishi a kan ta , ni kuma ba zan so hakan ba " Mikewa tsaye Moussa ya yi , ya yi takura guda gaba sannan ya ce " hakan ma shawara ce mai kyau amma ka na gani malam zai yarda ? " Mikewa tsaye shi ma Zayd ya yi , ya tako ya tsaya geffen Moussa ya ce " zai yarda , ba ni shakkun hakan " Ya na gama fadar haka ya taka ya bar dakin Ya na fitowa ya koma bedroom din shi kai tsaye , amma abun mamaki ba ta ciki A tunanin shi har yanzu ta na cikin toilet sai ya koma bakin gado ya zauna ya ciro wayar shi da ga cikin aljihun shi ya fara latsawa , Sannu sannu har ya share wajen good 30 minutes babu ita babu mai kama da ita A hankali ya mike tsaye ya meda wayar shi cikin aljihu sannan ya nufi toilet Bakin kofar ya tsaya ya kai hannu ya bubuga ya na fadin " wai har yanzu ba ki gama wankan ba ne " Shiru ba a amsa mishi ba , ko karar ruwa ba ya ji Hakan ya sa ya kai hannu ya tura kofar a hankali amma sai ya ga toilet din babu kowa a ciki Da sauri ya juya ya fice dakin ya nufi dakin Moussa dai'dai lokacin da shi ma ya ke shirin fitowa har su ka bidi yin karo Da sauri Moussa ya ce mishi " lafya ka ke irin wannan sauri haka ? " " ba ka ga inda yarinyar nan ta shiga ba , na diba bedroom di na ba ta nan " " kontar da hankalin ka ta na cikin gidan nan mana ya wuce ta na kitchen " Tun kafin ya gama rufe bakin shi Zayd ya juya da sauri ya bar wajen Kai tsaye kitchen ya nufa Tun kafin ya shiga kitchen din ya gan ta ta fito rike da tray , ta na sanye da wando palazzo sky blue da t-shirt fara ta saka hijab zuwa kirji shi ma sky blue Ya na ganin ta ya sauke ajiyar zuciya ya lumshe idanun shi Ita kuma ta na ganin shi ta saki murmushi ta ce " yanzu da na ke shirin na je na yi muku magana da yaya Moussa ku zo muyi breakfast " Ta kai karshen ta na shiga dining room ta ajiye tray din hannun ta saman dining table ta janyo chair ta zauna Ya na kallon ta har ta zauna sannan ya tako cikin dining room din ya janyo kujerar da ke fuskantar ta ta ya zauna dai'dai lokacin da Moussa ya fito corridor Ya na ganin su hakan ba karamin burge shi ba ya yi , sai da ya ciro wayar shi da ga cikin aljihu ya yi musu hoto a haka sannan ya karaso cikin dining room din ya na sallama A tare su ka amsa mishi amma ta Inaya a ka ji Zayd cen kassan makoshi ya amsa mishi Chair din geffen Zayd ya janyo ya zauna Serving din su ta fara yi sannan ta gyara musu coffee su ka fara yin breakfast Ko wane ya dukar da kai sai cin abincin shi ya ke cikin konciyar hankali Cen su ka tsinci Muryar Inaya ta na fadin " yaya Zayd ka san ina ne Daular Saudiya ? " Dum ya ji gaban shi ya fadi , a dubu dari su ka dago kai shi da Moussa su na kallon ta Kan ta na sunkuye sai cin abincin ta ta ke kamar ba ita ta yi magana ba Zayd na shirin magana Moussa ya riga shi cewa " ina ki ka jiyo wannan sunnan " Daga kafadun ta ta yi allamun ban sani ba kafin ta ce " kawai ya shigo min a kai ne " Kallon Zayd Moussa ya yi, shi ma Zayd Moussan ya ke kallo ya na son ya yi magana amma ya kassa kawai sun kurawa juna ido babu mai bakin magana Sai da su ka Kamala breakfast din su , ta tatare dishes din ta kai kitchen Ta na barin wajen Moussa ya ce ma Zayd " ya a ka yi ta san Daular Saudiya ko dai kai ka fada mata ? " Girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya ce " no ban fada mata ba " " to ya akayi ta san hakan dan ni ma fa ban taba fada mata ba " Shiru Zayd ya yi ya na tunanin wani abu , sai da ya jima bai ce komai ba sannan ya mike ya nufi falo ya zauna saman doguwar sofa Ya na zama Moussa shi ma ya tasso ya zauna geffen shi ya na kallon shi Su na a haka Inaya ta fito da ga kitchen ta karaso cikin falon ta zauna saman sofa two seaters ta fara kallon Tv Da ga haka ba wanda ya sake cewa wani abu kowa ne ya fada duniyar tunanin shi Ba su tashi da ga wajen nan ba sai da su ka ga lokacin sallat ya yi , sannan Zayd da Moussa su ka tashi a tare su ka tafi bedroom din su dan su yi Alwalla Jim kadan su ka fito Moussa ya na sanye da jallabiya fara amma shi kuma Zayd ya saka trouser black da shirt red Nan su ka ce da ita sun tafi mosque , da to ta amsa musu kafin ta tashi ta shiga bedroom din Zayd dan ita ma ta yi sallat Misalin karfe 7 na dare ( bayan sallar isha ) Inaya Zaune su ke cikin falon gidan su na kallon film a Tv , Moussa da Inaya su na hirar su Zayd kuma ya na zaune kamar gunki ya zubawa Tv ido Su na a haka su ka jiyo a na sallama Kallon Moussa Zayd ya shi ma kallon shi ya yi irin kallon nan ka na jiran wani Su na a haka su ka ga Inaya na shirin tashi ta je ta dubo ko waye Da sauri Zayd ya mike ya ce " zaune zan je na duba " ya na fadar haka ya nufi door ya fice Ya sha ruwan mamaki ganin malam cikin gidan shi cikin wannan gidan ga kuma duk yanayin shi a birkice da allamun wani abu ya faru Da sauri Zayd ya yi kan shi ya na fadin " uncle ya na gan ou cikin wannan halin, lafya dai ko ? " sai jero mishi tambayoyi Zayd ya ke ya ki tsaya ya ji abun da ke faruwa Wasu yawu malam ya hadiye kafin ya ce " Zayd ina cikin tashin hankali " ya fada kamar zai yi kuka Dafa kafadar shi Zayd ya yi ya ce mishi " mu shiga da ga ciki uncle sai ka fada min " ya kai karshen ya na yi mishi bismillah da hannu Da sauri malam ya girgiza mishi kai kafin ya ce " Zayd ba zan iya shiga ciki ba , Idan auta ta ji abun da ke faruwa matsalar za ta zame min biyu dalilin da ya sa na kassa shiga ciki dan kar ta gan ni " Katse shi Zayd ya yi da cewa " uncle kontar da hankalin ka , ka yi min bayani yadda zan gane wane ya faru ne ? " Ajiyar zuciya malam ya sauke kafin ya ce " Zayd , Nesrine ce tun safe da a ka aike ta cepane har yanzu ba ta dawo ba , yanzu haka da ga police station mu ke ni da Abdoul na kassa hakura ya sa na zo na fada maka ka taimaka mu tafi neman ta " ya kai karshen kamar zai yi kuka TIR KASHI , YANZU KUMA INA NESRINE TA SHIGA HMMMM NI DAI NA DASSA AYA A NAN SAI MUN HADE GOBE 🤘 ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 19 ❤🔥 Dan lumshe idanun shi Zayd ya yi ya kara bude su a hankali kafin ya ce " uncle calm down , yanzu ka fadawa mamar ta abun da a ke ciki ? " " to ya zan yi Zayd dole ta san abun da a ke ciki, yanzu haka da na baro ta ta na kuka sai da Abdoul ya samu ya rarrashe ta " Jinjina kan shi Zayd ya yi kafin ya ce " okay ! Yanzu uncle ka koma gida ku kontar da hankalin ku, duk inda ta shiga zan nemo ta amma ku bari har da safe " Da sauri malam ya katse shi da cewa " Zayd har da safe fa ka ce , gaskia bazan iya ba mu tafi yanzu don Allah kar aje wani abu ya same ta " Girgiza mishi kai Zayd ya yi ya na fadin " no uncle ba abun da zai same ta, yanzu ko mun fita ina za mu je neman ta , mu jira mu gani ko da ma su garguwa da mutane ne za su kira mu , idan ba haka ba gobe sai mu je police station, amma cikin wannan daren ba abun da za mu iya yi " Haka dai ya yi ta lalaba shi har ya hakura ya koma gida nan ma sai Zayd ya raka shi har gida su na tafe ya na kara kontar mishi da hankali Bayan ya raka malam gida ya dawo gidan shi Yadda ya bar Moussa da Inaya haka ya dawo ya same su su na hirar su Inda ya tashi nan ya koma ya zauna Ya na zama Moussa ya kaleshi ya ce " mi ya tseda ka haka ? " Cikin harshen larabci ya ce mishi " gobe za mu je police station " Cikin harshen larabci shi ma Moussa ya amsa mishi da cewa " me kuma za mu je yi police station , wanene ma ya zo ? Na ji kamar murya malam " " e shi ne , yayar wannan yarinyar ce ta bata har yanzu ba ta dawo gida ba tun safe " " whatt ? Ina kuma ta shiga ? " " i don't know ! Kawai kai dai ka shirya tun safe mu tafi police station , sannan ka ce da yarinyar nan kar ta fita gobe ko da school ne " Duk maganar nan da su ke cikin harshen larabci ne su ke yin ta dan kar Inaya ta ji abun da su ke fada Sai da su ka Kamala maganar su sannan mourir ya kali Inaya ya ce " babyn Zayd ina ga gobe ba sai kin je school ba " Da sauri ta kaleshi ta marairaice fuska ta ce " why yaya Moussa gobe fa monday " Moussa na shirin magana Zayd ya riga shi cewa " na san gobe monday , ina neman muku admition cikin sabuwar makaranta ke da yayar ki , so ba sai kin je ba " Jinjina mishi kai tayi ba dan ta so ba ta ce " shikenan yaya Zayd " Ta na fadar haka ta tashi ta nufi corridor ta shiga bedroom din Zayd Ta na barin wajen Moussa ya kali Zayd ya ce " ka tashi ka je ka rarrashi babyn ka , ba ka ga ran ta ya baci " Ko kallon shi Zayd bai yi ba ya ci gaba da kallon Tv Girgiza kan shi Moussa ya yi cikin ranshi ya ce " duk ranar da soyayyar ta ta kama ka wlh ba za ka yi da sauki ba , ba kai ba izza da miskilanci za ka gane kuran ka " Da ga haka ba wanda ya sake cewa wani abu har wajen karfe 11 na dare su ka tashi daya bayan daya kowane ya koma bedroom din shi Zayd Bayan ya shiga bedroom din shi ya isko ta na konce saman bed din shi ta yi rub da ciki ta na sanye da kayan barci fara har ta yi barcin ta Kai tsaye toilet ya wuce ya yi wanka Jim kadan ya fito sanye da bathrobe, kai tsaye closet din kayan shi ya nufa ya dauki kayan barcin shi , shi ma farare ya koma toilet Bayan minti biyar ya fito sanye da kayan barcin shi ya nufi bed din shi Geffen ta dan nesa kadan ya konta ya na kallon ceiling ya daura hannun shi daya saman goshin shi daya dayan kuma saman cikin shi , ya lumshe idanun shi kamar mai barci Ya dan jima a haka kafin ya bude idanun shi a hankali ya juyo da kan shi ya na kallon ta Ya na tsaka da kallon ta ta juyo suna fuskantar juna , duk gashin kan ta ya zubo ya rufe mata fuska ta zama kamar wata aljana Sai da ya dauki lokaci ya na kallon ta a haka kafin ya kai hannun shi slowly ya janye mata jelar gashin ta Kamar jira ta ke ya na janye mata ta bude idanu ai ko sai cikin nashi sai da ta ji tsoro lokacin da ta ci karo da Hazel eyes din na shi Da sauri ta yi baya za ta tashi da ga saman gadon Hannun ta ya riko ya lumshe idanun shi dan ya san su ne su na bata tsoro cikin wata cool voice ya ce " dawo ina za ki je " Cak ta tsaya ta lumshe idanun ta ta koma ta konta ta na sauke ajiyar zuciya A hankali ta juyo da kan ta ta na kallon shi , ganin ya lumshe idanun shi ya sa ta cewa " yaya Zayd lafya ka rufe idanun ka " Ba tare da ya bude su ba ya ce " no kar ki damu konta ki yi barchi ki " " to Amma yaya Zayd ka bude su mana in gani " " ba za ki ji tsoro ba , la ga kin tsorata da farko shi ya sa na rufe su " Dan matsowa ta yi kusa da shi kadan , ta rage sautin Muryar ta ta ce " ka bude ba zan ji tsoro ba yaya Zayd " Jinjina mata kai ya yi kafin ya fara bude idanun shi slowly , sai cikin nata dan ita ma shi ta ke kallo Haka su ka tsaya su ka kurawa juna ido babu ko kiftawa duk sun kassa janye idanun su " wai me ya ke shirin faruwa da ni ne haka, duk lokacin da na kalli yarinyar nan sai na ji zuciya ta ta yi min wani sanyi, why ? Na ke jin haka , na san a shekaru na ninka nata amma me ya sa ko wane lokaci na ke ganin kamar ta na dai'dai da ni ? " ya fada cikin ranshi ya na tsare ta da wadanan hazel eyes din na shi Ita cikin ranta cewa ta ke " ban san dalilin da ya sa ni ke maka irin wannan son haka , why kai ma baza ka so ni ba ? " ta na fadar haka ta saki wani cool murmushi ta lumshe idanun ta slowly A hankali shi ma ya lumshe idanun shi , ba jimawa barci ya yi gaba da su Washe gari Misalin karfe 8 na safe , Zayd da Moussa su ka bar gidan , su ka bar Inaya ita kadai ta na ta barci dan yau ba school ba za ta je Gidan malam su ka nufa , dai'dai sun isa bakin kofar gidan , malam da Abdoul su ka fito da ga cikin gidan su na ta sauri har su ka wuce Zayd da Moussa ba su sani ba Da sauri Moussa ya taro su ya na fadin " uncle ina zuwa haka " Juyowa malam ya yi ya kaleshi ya ce " zan je police station na gaji da zaman jiran nan " Jinjina kan shi Zayd ya yi kafin ya fara takawa ya na rike da hannayan shi a baya ya yi gaba ba tare da ya ce musu komai ba Da sauri malam da Abdoul su ka bi bayan shi tare da Moussa A haka su ka jera su ka nufi police station Sun dauki wajen good 10 minutes su na tafiya kafin su iso police station Zayd ne ya yi magana officer din bayan ya gaishe da shi ya ce mishi ya na son ganin DPO Nan officer din ya ce mishi " sai dai ka yi hakuri in kara ce ku ka kawo ni za ku fada ma ba DPO ba " Cikin sanyi Zayd ya ce mishi " ka yi hakuri ka sada mu da shi maganar ta na da mahimanci sosai " Fir officer din ya ki ya ce " na fada muku duk karar da za ku shigar ni za ku fada ma DPO ba shi da lokacin kananan case " Cikin bacin rai Zayd ya ce " an fada maka karamin case ne ya kawo mu , kanwa ta fa ta bata, ina son magana da DPO now ! " ya kai karshen ya na buga desk din da karfi Da sauri sauran officer din su ka karaso wajen su na fadin " kai malam nan fa ba gidan ku ba ne , ka yi a hankali ko kuma na sa ka cell " Tsaki Zayd ya ja ya kauda kan shi gefe kafin ya juya a hankali ya fice da ga cikin police station din Ya na barin wajen malam ya matso ya ce da officer din " yi hakuri yaro zuciya ce ta debe shi , mun zo shigar da kara a kan batar yarinya ta, tun jiya da safe a ka aike ta har yanzu ba ta dawo ba " Cikin ko in kula ya ce " ya wuce ta bi saurayin ta sun tafi yawon cin duniyar su ku na nan kun damu a kan ta , ta na cen ta cin dadin ta " ya kai karshen ya na dariya Su ma sauran officer din su ka bushe da dariya KAI JAMA'A YANZU KO GIRMAN MALAM BAI GANI BA DA YA FADI HAKAN 😔😔 ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 20 ❤🔥 Maganar ba karamin bata musu rai ta yi ba , da Zayd na wuri ya yi maganar da tuni zuciya ta debe shi ya musu dukan mutuwa , shi fa Zayd irin mutanan nan ne da ba su son raini duk girma kan idan ka ce za ka raina shi to wlh sai dai a dauki gawar ka , dalilin da ya sa ba ya sakewa Inaya fuska dan kar ta ga ranar shi raini ya shiga tsakanin su Su na tsaka da dariyar su DPO ya fito da ga cikin office din shi ya na sanye da kakin su na soja , ba laifi ya dan lattijantaka , ya na da kyasumba amma ba sosai ba ya na sanye da hular su irin ta sojawa ba a iya ganin gashin kan shi , fuskar shi babu yabo babu falassa Su na ganin shi kowa ya shiga tai'tayin shi , duk su ka sara mishi su na fadin " sir! " Bai bi ta kan gaisuwar su ba ya ce " dariyar me ku ke yi haka ? " Da sauri daya da ga cikin su ya ce " ba komai sir " ya fada cikin girmamawa Jinjina kan shi ya yi kafin ya kali daya da ga cikin officer din da ke tsaye bakin kofar office din shi ya ce " PDG din Shell Petrolium ya na waje , je ka mishi iso zuwa office di na " Ya na gama fadar haka ya juya zai koma office din shi , officer din kuma ya mike zai fita Har ya yi nisa ya jiyo DPO ya na fadin " ya na sanye da jeans black da t-shirt white " sa ga haka ya shige office din shi officer din ya fice Ya na fita Moussa ya dafe forehead din shi ya ce " Amirrrr ! Ba dai kiran DPO kai tsaye ka yi ba ? " Da sauri malam ya kaleshi ya ce " me ka ke nufi Moussa " Cike da rudu Moussa ya kali malam ya na zaro idanu shi ya ma manta da su na tare da malam Officer din kuma bayan ya fito harabar police station Ya duba dama ya duba hagu bai ga kowa ba Har ya juya zai koma ya hango wani mutun cen nesa tsaye ya bashi baya ya na sanye da jeans baki da t-shirt fara kamar yadda DPO ya fada mishi ya sunkuyar da kai ya na latsa wayar shi A hankali officer din ya tako gare shi ta bayan shi ya tsaya ya sara mishi ya ce " Good morning sir " Ko juyowa Zayd bai yi ba bare ya amsa mishi ya ci gaba da latsa wayar shi Ganin bai amsa mishi ba ya sa officer din cewa " sir DPO n........" kut maganar ta yanke sakamakon juyowa da Zayd ya yi ya fara takawa ya bar wajen Officer din sumar tsaye ya yi kennan shi ne PDG din Shell petrolium, tun dazu ya ce ya na son magana da DPO amma su ka raina mishi hankali , yanzu zai iya kai kararshi gaban DPO ma kuma ta zauna shikenan an koreshi ? Da sauri ya juya ya bi bayan Zayd da har ya kusa shiga police station din Kafin ya shiga ya tarbo shi ya mara mishi baya Babu ko sallama Zayd ya shigo police station din kai tsaye ya na sanye da bakin glass din shi , ya rike hannayan shi a baya , ya nufi office din DPO Officer din nan na farko na ganin shi ya matse fuska ya ce " kai gidan ku ne nan da za ka shigo babu ko sallama " Da sauri officer din da ke bayan Zayd ya girgiza mishi allamun ya yi shiru Malam da Abdoul na ganin irin shigowar da ya yi duk su ka bi su ka rude sun ka ce anya wannan Zayd ne , dan fa nan kwarjinin shi ya karu fiye da farko taku ya ke cike da izza da isa kamar shi ne president din Nigeria baki daya Su na isa bakin kofar office din , DPO ya fito ya na murmushi ya mikawa Zayd hannu ya ce " welcome sir ! " Kallon hannun DPO ya yi kafin ya dago kai ya kali Moussa , ya juya ya shiga office din DPO ya bar shi nan tsaye Da sauri Moussa ya karaso wajen ya riko hannun DPO su ka yi musbaha ya na murmushi ya ce " Sorry DPO bai cika gaisawa da mutane ba ne " Murmushi DPO ya yi kafin ya " ai ba komai na san labarin sir Latif , mutumin da ba kowa ya taba ganin shi ba ai ban yi mamakin haka ba , bismillah mu shiga da ga ciki " Murmushi Moussa ya yi kafin ya jinjina kan shi ya shiga office din , DPO ya bi bayan shi Su na shiga Abdoul ya kali malam baki sake ya ce " Abba wai wanene wannan ba dai Zayd din da muka sani wajen shekara biyar , shi ne mamalakin babbar company ta sayar da bakin oil a Nigeria baki daya ba " Malam na shirin magana daya da ga cikin officer ya riga shi cewa " yanzu ku na nufin ba ku san shi ne PDG din Shell petrolium " Officer din da ya tarbe su da farko ne ya amsa mishi da cewa " kai dan Allah matsa , kai yanzu duk Nigeria ka taba jin wanda ya fito ya ce maka ya taba ganin shi , ko kuma DG din shi , duk wani taro da za ayi ba su zuwa duk wata magana da za su yi da yan jarida ta voice call su ke yin ta , ko kwangila ka kai musu iya kar ka da ga manager din su , shi zai kai musu file din kwangilar ka in sun yarda manager din nan sai zai fada maka , mutane nawa su ka yi aiki da shi amma ba wanda zai fito ya ce maka ga kamanun shi , kai karewar zancen ko his excellency da ya nemi zama da shi manager din shi ya je a madadin shi , wannan mutumin ya tara uban kudade dole ganin shi ya zama kamar kallon rana " HMMM A HAKAN MA BA KU SAN AINAHIN ASSALIN SHI BA AMMA MU JE ZUWA 😌😌 Kallon malam Abdoul ya yi baki sake ya na shirin magana su ka ga Zayd ya fito da ga cikin office din DPO Su na ganin shi duk officer din wajen su ka mike su na sara mishi Ko kallon su bai yi ba ya ficewar shi Da kallo malam da Abdoul su ka raka shi har ya fita sannan su ka kali junan su Ya na fita Moussa ya fito shi ma DPO na biye da bayan shi Sai da su ka ida maganar su sannan Moussa ya karaso wajen su malam ya ce " uncle mu tafi " ya na fadar haka ya yi gaba Da sauri malam da Abdoul su ka bi bayan shi su ka bar police station din baki daya Su na barin wajen DPO ya kali officer din wajen ya ce da su " zan turo ma kowanan ku hoton wata yarinya, nan da two hours ina son in gan ta cikin office di na, ku nemo ta duk inda ta ke " Sara mishi su ka yi baki daya su na fadin " okay sir ! " Bai tsaya basu amsa ba ya juya ya koma office din shi Tafiya su ke saman hanya su na a jere malam, Moussa da Abdoul , Zayd kuma ya na cen gaban su ya na rike da hannayan shi a baya ya na taku cike da nitsuwa Sai da su ka yi tafiya mai dan nisa kafin malam ya kali Moussa ya ce " Moussa , in shi ne assalin sunan ka , wanene Zayd ko in ce Latif dan yanzu na fara tantama a kan ku " Murmushi Moussa ya yi kafin ya daga kai ya kali Zayd su na ci gaba da tafiyar su ya ce " gaskia ne uncle Moussa ba shi ne cikaken suna na ba , sai dai ku yi hakuri bazan iya fada muku komai ba a kan mu , amma zan fada maka , Zayd da Latif duk ba su ba ne cikaken sunan shi ba , ya yi anfani da sunnan latif lokacin da muka bude company din mu , Zayd kuma dan in ya ce sunan shi latif mutane za su dinga dangan tashi da PDG din Shell petrolium shi ya sa ya ke sauya sunaye a waje daban daban , kuma personallity din shi ke sauyawa tare da sunnan , amma da za ku san wanene ainahin Zayd ko daga kai baza ku yi ku kaleshi ba , duk cikin kassashen duniya babu wadda ta fi karfin Zayd ya je cen ya yi rayuwar shi yadda ya ga dama amma kaddarar shi ta kawo shi Nigeria , kaddarar shi ta haduwa da yarinyar ku , har aure ya shiga tsakanin su , ku godewa Allah da ya hada Zayd da yarinyar ku uncle dan ba kowace mace a duniya za ta samu irin wannan damar ba " Ya na gama fadar haka ya yi sauri ya yi gaba dan ya kamo Zayd Kallon Abdoul malam ya yi kafin ya ce " Abdoul ni fa yanzu na fara tambayar kai na a kan assalin Zayd " " Abba ba ku kadai ba, ni ma ina tambayar kai na , amma babu mai ba mu amsa " ya kai karshen ya na dawo da kallon shi kan Zayd Dai'dai lokacin da Moussa ya kamo shi Ya na isowa geffen Zayd , Moussa ya kaleshi ya ce " Amir me ya sa za ka kira DPO kai tsaye , yanzu uncle sai da ya tambaye ni a kan ka " A hankali Zayd ya juya kai ba tare da ya tsaya da ga tafiyar shi ba ya kali malam kafin ya juyo ya kali gaban shi ya ce " zan fada mishi amma ba yanzu ba , ka kira manager ka ce ya tura a gyara gidan mu na Abuja cen za mu koma da zama har da su malam " Cak Moussa ya tsaya da tafiya ya na kallon Zayd ya na maimaita abun da ya fada cikin kwakwolwar shi Sai da ya dan jima kafin ya ci gaba da tafiyar shi a haka har su ka karaso gidan malam Nan Moussa ya tsaya ya juya ya ce da malam duk abun da DPO ya sanar da su za su kira shi su fada mishi Da to malam ya amsa mishi kafin ya shiga cikin gidan, su ka yi sallama shi da Abdoul Sannan ya juya ya kama hanyar gidan su , cen ya hango Zayd har ya isa bakin kofar gidan ya tura kofa ya shiga Gyada kan shi Moussa ya yi kafin ya ci gaba da takawa ya iso gidan shi ma shiga Bakin shi dauke da sallama ya shigo falon gidan Cen kassan makoshi Zayd ya amsa mishi sallamar shi ya na zaune saman sofa ya zubawa Inaya idanu ta cikin glass Geffen shi Moussa ya karaso ya zauna ya kaleshi sannan ya kali Inaya ya ce " lafya ka kura mata ido haka " Ba tare da ya juyo ya kaleshi ba ya ce " nothing " ya fada a takaice Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " wai har yanzu ba ka shirya daukar ta a matsayin matar ka ba ? " " never, bari ma wannan zancen , yarinyar nan fa ko period ba ta fara ba " Salati Moussa ya yi ya na kama habar shi ya ce " Amir yanzu yarinyar nan ido ka saka mata har ka san ba ta fara period ba " " ni ban saka mata ido ba , kawai abun da na gani ne na fada maka " " okay kennan in ta fara period za ka dauke ta a matsayin matar ka " Sai da ya dan dauki lokaci kafin ya ce " i don't know " Hararrar Moussa ya yi kafin ya ce " you'll know very soon , Idan mun koma masarauta a ka matsa maka sai ka auri diyar sarkin Rouma za ka gane kuran ka " ya kai karshen ya na dariya Juyo da kan shi ya yi ya kali Moussa ya ce " wai wa ya fada maka zan koma " ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 21 ❤🔥 Da sauri Moussa ya tsagaita dariyar shi ya ce " ban gane , Amir wai ka na nufin baza ka koma gida ba, me ya sa abun da ya faru ya riga da ya wuce " Katse shi Zayd ya yi da cewa " Diya na sani , kuma har ga Allah ina kewar Ammie da mamie da kuma Tesnim amma zuciya ta bata yarda na koma ba , ina ji idan na koma wani mugun abu zai faru wanda ya fi na farko , ina jin tsoron komawa ta ga ahali na ya janyo musu assarar sa bazan maye gurbin ta ba , Diya ka fi kowa sanin Mai martaba a ka so a kashe ba ni ba , akasi ne kawai aka samu ranar ni na kwana a part din shi , da yanzu na san shi zai mutu a madadi na , dalilin da ya sa su ka kyale shi yanzu dan sun san ba shi da wanda zai gaje shi , ko ba su kashe shi ba in lokacin shi ya yi dole zai tafi su zauna saman karagar mulkin " Dafa kafadar shi Moussa ya yi kafin ya ce " na sani Amir , amma dole ka koma ka karbi kujerar ka , yanzu ka na ji ka na gani wani zai zauna saman gadon ka , Amir kai kade ne fa magajin Daular saudiya tsawan shekaru sama da dari biyu duk sarkin da ya hau karagar muliki ba zai taba haifuwar da namiji ba , cikin wani ikon uban giji mai martaba ya same ka , ba ka ji sunan ka ba Nawfel , kyauta mai daraja , ba a banza a ka saka maka wannan sunnan ba " Jingina bayan shi Zayd ya yi a jikin sofar ya lumshe idanun shi ya ce " Diya na san wannan duka, amma ba yadda zan yi kassan ba zan iya tafiya na bar yarinyar nan ba ko " Ya kai karshen ya na bude idanun shi ya kali Inaya da ta sharar barcin ta kamar babu ita a wajen " shikenan yanzu ina son ka fada min za ka koma masarauta ko kuma ba za ka koma ba " Moussa ya tambaye shi Dawo da kallon shi ya yi kan Moussa kafin ya ce " za mu koma Diya, za mu koma amma ba za mu zauna ba , tafiyar tsaye za mu yi " Ya na gama fadar haka Inaya ta fara motsi ta na son tashi A tare shi da Moussa su ka dawo da kallon su saman ta A hankali ta ware idanun ta , ta fara karanto adu'ar tashi da ga barci , ta fara bin wajen da kallo Idanun ta na sauka kan Zayd ta saki wani dan murmushi ta mike zaune ta kai hannun ta guda ta na murza idon ta cikin shagwaba ta ce " yaya Zayd tun da safe na ke ta jiran ku ku dawo mu yi breakfast har kwana ya dauke ni " Murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " sorry baby na , wlh wani aiki ne ya tseda mu " Murmushi ta yi ta na bude idanun ta ta kai kallon ta kan Zayd da ya tsare ta da wadanan hazel eyes din na shi ta cikin glass Ta na shirin magana wayar Moussa ta fara ringing Da sauri ya sa hannu cikin aljihu ya fido ta ya na kallon screen , dago kai ya yi ya kali Zayd da ya kurewa Inaya kallo Daukar kiran ya yi ya kai ga kunne ya na sallama A daya bangaran kuma amsa mishi sallamar shi DPO ya yi kafin ya ce " sir an gano inda yarinyar nan ta ke " Da sauri Moussa ya mike tsaye ya ma manta da ya na gaban Inaya ya ce " da gaske ta ina to " " sir muna jiran ka babban likitan gari " ya na gama fadar haka ya katse kiran Kallon screen din wayar ya yi ya ce " babbar likatan gari kuma , me ya kai su cen " Ya na gama fadar haka ya dafa kafadar Zayd ya ce " Amir an gano inda ta ke amma ya ce min su na likita " Lumshe idanun shi ya yi a hankali kafin ya sake bude su ya mike tsaye ya kali Moussa ya ce " shikenan mu tafi za musu san abun da ya faru " Ya kai karshen ya na medo da kallon shi kan Inaya ya ce " yo hakuri za mu je mu dawo ba za mu jima ba " " shikenan yaya Zayd a dawo lafya , amma in za ka dawo ka biyo min da sweet " ta fada cikin shagwaba Da to ya amsa mata kafin ya juya ya fara takawa ya fice falon Moussa na biye da bayan shi Su na fita ta tashi ta shiga kitchen dan ta shirya musu abun da za su ci Zayd kuma bayan sun fita kai tsaye babban Hospital su ka nufa Ba yin da Moussa bai yi ba a kan su tafi da motar su amma ya ki ya ce da kafa za su tafi Sun dauki wajen good 30 minutes kafin su iso Hospital din da DPO ya fada musu Su na isa Hospital din su ka tardo DPO a reception ya na jiran su Ya na ganin su ya mike ya ce da Zayd " sir mu karasa dakin ta , anyi mata duk wani abu da za ta bukata , amma ta shiga doguwar suma " Da sauri Zayd ya kaleshi ya ce " what doguwar suma ? Me ya faru da ita ne " " zai fi idan ka gan ta za ka gane abun da ya faru da ita " Ya na kai karshen maganar shi DPO ya yi gaba Da sauri Zayd da Moussa su ka bi bayan shi duk da bai cika tafiya da sauri ba yau sai da ya yi ta Da sallama bakin su , su ka shigo dakin da DPO ya kawo su Cen su ka hango Nesrine konce saman gado ta na sanye da wata riga blue zuwa guyiwa, hannun ta sanye da catheter a na mata karin jini , fuskar ta duk ta kumbura kamar wadda ta kwana ta na kuka , ga wasu allamun yaga a hannayan ta kamar wadda ta yi fada da mage Cike da rudu Moussa ya kali DPO ya ce " me ya same ta haka ? " Cikin girmamawa ya ce " sorry sir ta rasa jini dayawa dalilin da ya sa ta shiga doguwar suma " Cikin tsawa Moussa ya katse shi da cewa " How ? ta ya ta rasa jini haka , ba dai kokarin kashe kan ta ta yi ba ? " Dan jinkirtawa DPO ya yi kafin ya ce " sorry sir , raping din ta a ka yi , allamu sun nuna ba sau daya ba a........" Bai karasa maganar shi ba sakamakon katse shi da Zayd ya yi da cewa " me ku ke jira har yanzu ba ku kamo wanda ya yi hakan ba ? " ya fada cike da nitsuwa Sunkuyar da kai DPO ya yi dan bai da amsar da zai ba shi ( TOOOO , KO WA YA YI WA NESRINE WANNAN AIKI HAKA ? 😭😭😭 ) ONE DAY BEFORE NESRINE Misalin karfe 8 na safe Nesrine ta farka da ga barci da ya ke yau week-end ne , Bayan ta share gidan ta yi duk wani aiki na gidan da ya kamata , wajen karfe 9 ta shiga wanka sannan ta fito ta shirya cikin riga da skert ta zauna cikin dakin ta ta na karatu Ta na tsaka da karatun ta mama ta shigo dakin ta na sallama Amsa mata sallamar mata Nesrine ta yi ta na dago kai Murmushi mama ta yi kafin ta ce " abokiyar fadan ta tafi ko ? " Murmushi ita ma Nesrine ta yi kafin ta ce " mu daman ba fada ne mu ke yi ba mama , ita ce dai ta cika tsokana ta " " ke kuma ba ki da hakuri gashin ai yanzu ba ta nan " " ina kewar ta sosai mama har mafarkin ta na yi jiya wai ta na da ciki " ta kai karshen ta na bushewa da dariya " yanzu ke Nesrine takurar da ki ke ma auta har ya kai ki yi mafarkin ta da ciki , to minene matsalar a ciki ai ni abun da na ke son gani ma kenan " " laaaaa mama abun da ki ke son gani fa ? Tabbb ai in wacen tsohon makahon ya taba min kanwa sai na kai karar shi , da wasu idanun shi kamar na mujiya " Dariya mama ta yi kafin ta ce " ai gwara ita ta na da makahon mai idanun mujiya ke fa har yanzu gaban iyayen ki ki ke, ga kanwar ki cen gidan mijin ta " Turo dan bakin ta ta yi cikin shagwaba ta ce " yo ai mama komai lokaci ne , ni ma lokacin nawa na zuwa " Murmushi mama ta yi sannan ta ce " shikenan Allah ya kawo shi wannan lokacin , yanzu dai tashi ki je ki yo min cepane tun rana ba ta fito ba " Ta na gama fadar haka ta juya ta bar dakin Ta na fita Nesrine ta sauko da ga saman gadon ta ta nufi closet ta dauki hijabin ta ta saka sannan ta fito Cen bakin dakin ta ta hango mama ta na zaune ta na jiran ta Gaban mama ta karaso ta tsuguna ta na jiran mama ta bata kudin cepane Nan ta mama ta ba ta dubi biyar ta fada mata duk wani abu da za ta bukata sannan ta mata gargadi a kan banda tsayawa ragaita Dariya Nesrine ta yi ta na kokarin mikewa ta ce " ni fa mama ba Inaya ce ba , ita ce in ka aike ta sai ka manta da ita " Ta na gama fadar hakan ta juya ta fice gidan Da kallo mama ta rakata har sai da ta fita sannan ta mike ta shiga dakin ta Nesrine kuma bayan ta fito gidan, ba ta tsaya wani bata lokaci ba kai tsaye ta nufi shagon da su ke yin cepane kullum Bayan ta Kamala ta juyo ta kama hanyar gida , ta na tsaka da tafiyar ta kwatsam wata mota ta buge ta Da sauri mutane su ke yi kan ta su na tambayar ta lafya Da sauri shi ma matukin motar ya fito , ya na sanye da jeans baki da t-shirt blue, ya na sanye da face mask baki shi ma da wata cap baki ita ma , sam ba ka iya ganin face din shi da kyau ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 22 ❤🔥 Da sauri shi ma matukin motar ya yi kan ta ya na tambaya ba ta ji tsiwo ba Girgiza mishi kai ta yi murya na kerma dan tsoron da ta ji ta ke fadin " ba ba komai ba...n ji tsiwo ba " Da sauri matukin motar ya ce " yi hakuri yar uwa ban gan ki ba ne amma don Allah tashi mu tafi Hospital a duba ki kar a je kin ji rauni " Da sauri ta yi kokarin tashi ta na dafa gaban motar shi ta ce " a'a na gode a na jira na a gida " Cikin dabara ya sa kafar shi ya bike kafar ta har sai da ta saki kara ta fadi ta konta Da sauri mai shagon da ta yi cepane ya ce " Nesrine yi hakuri ku tafi likita, kar a je kin samu rauni, kar ki damu zan fadawa malam abun da ya faru sai ya tarda ki cen likitar " Jinjina mishi kai ta yi dan ta san mai shagon ya san gidan su kuma ya san malam sosai A haka ta yarda ta tashi da taimakon matukin motar ya shigar da ita gidan gaba wajen mai zaman bazan Sannan ya gewayo ya nufi mazaunin driver ya na yi ma mai shagon godiya Ba komai me shagon ya ce mishi sannan ya juya shi clients din shi da su ka fito su ka koma cikin shagon dan ya sallame su Nesrine kuma ta na shiga motar ta jingina a jikin kujerar motar ta lumshe idanun ta har driver din ya shigo ya tada motar su ka fara tafiya Sannu sannu har sun dauki wajen good one hour su na tafiya Nesrine ba ta sani ba idanun ta na a lumshe Sai da ta ji motar ta tsaya sannan ta tasso ta bude idanun ta slowly ta fara bin wajen da kallo Sam bai yi kama da Hospital ba , wajen duk ciyayi ne babu alamun mutun ko da guda kamar irin gidan gona Ta na tsaka da kallon wajen ta ga an bude kofar geffen ta a ka ce " madam fito ko ! " Cike da rudu ta daga kafa ta fito da ga cikin motar ta na kara bin wajen da kallo Ta na tsaka da kale kalen ta , ta tsinci Muryar shi ya na fadin " madam mu je daga ciki " Da sauri ta girgiza mishi kai ta na neman ta yi kuka ta ce " don Allah malam ka maida ni gidan mu " Ba ta gama rufe baki ba ya daura da cewa " kar ki damu ni ma sauri na ke wani sako ne zan daukowa sai mu tafi " Duk yadda ta so ya ta ki shiga gidan gonar nan sai da ya yi mata wayo ya sa ta shiga ba dan ta so ba Su na shiga parlour din gidan ya juya ya rufe kofar da kai Da sauri Nesrine ta ce " don Allah mu tafi ka meda ni gida " ta kai karshen kamar za ta yi kuka Juyowa ya yi ya saki wani makirin murmushi ta cikin face mask din shi ya fara nufar ta a hankali Duk taku daya inya yi , ita ma sai ta yi taku daya bayan ta na girgiza mishi kai idanun ta su ka kawo ruwa Ba tare da ya tsaya ba ya sa hannu ya zare cap din kan shi ya tila gefe sannan ya zame face mask din shi slowly ita ma ya tila gefe Dumm Nesrine ta ji gaban ta ya fadi lokacin da ta yi arba da fuskar Moctar Murya na kerma ta ce " Moctar me ya sa ka kawo ni nan , ka ga ka kyale ni na tafi " Wata shegiyar dariya ya yi ya na kallon ta ya ce " wane gida kuma bayan wannan , ai tun da ban samu abun da na ke so ba tare da wacen kanwar ta ki , za ki biya a madadin ta " ya kai karshen ya na kai hannun shi zai taba ta Da sauri ta buge hannun shi ta na fadin " kar ka taba ni , ka kyale ni na tafi don Allah " Murmushi yayi kafin ya ce " ga hanya nan ban hana ki tafiya ba, ni dama wassa na ke miki " ya kai karshen ya na nuna mata kofar futa Da gudu ta nufi kofar da su ka shigo , sai dai kuma ta na isa ta ji kofar a like ta ke , ta yi ta kokarin ta bude ta amma ko motsi ba ta yi ba har ya kai ta saki kuka Ta na tsaka da kukan nata ta jiyo sautin dariyar shi Cak ta tsaya da abun da ta ke ta sunkuyar da kai ta na ci gaba da kukan Ba ta Ankara ba kawai sai ji ta yi , ya damko breast din ta ta baya ya murza da karfi har sai da ta saki kara Da sauri ta fara kokarin kwace kan ta amma ina ya mata rikon sa baza ta iya kubce wa ba Su na a haka ya sa hannu shi guda ya raba ta da hijabin jikin ta , Da duk karfin ta ta sa hannu ta ture shi ya yi baya Ido a rufe ta yi geffen shi da gudu za ta bar wajen , sai dai ki taku biyu na kirki ba ta yi ba ya damko kugun ta ya juyo da ita ya sabba ta a kafada Sai kara ta ke saki ta na bugun shi a baya amma kamar ba ya ji Sai da isa wajen doguwar sofa ya kontar da ita Tassss ta ji saukar mari saman kuncin ta har sai da ta dauke lokaci guda Shi kuma ya na marin ta ya nuna ta da dan yatsar shi ya ce " ki yi min shiru ko kuma na kashe ki a wajen nan " Ya na gama fadar haka ya mike ya cire duk kayan jikin shi ya bar short kadai Sannan ya Haye saman sofar ya zauna a tsakiyar sawunta ya kai hannu ya yage hannayan rigar ta da karfi har sai da ya yage mata hannaye Duk sai ya bi ya raba ta da kayan jikin ta, ya meda ta naked ba ta sani ba dan tun marin da ya yi mata ta fita cikin hayacin ta ta kurewa ceiling ido babu ko kiftawa Bai tsaya yin wani wassa ba , kai tsaye ya afka mata , ya keta mata hadi babu ko tausayi a idanun shi Wata irin razananiyar kara ce ta saki ta na dawowa cikin hayacin ta lokacin da ya yi dis virgin din ta ta damko damtsen shi da karfi ta matse Cikin mugun ta ya yi raping din ta har sai da ya ji ya gaji sannan ya fada saman jikin ta ya konta ya na nishi Nesrine kuma baiwar Allah tun karar nan da ta yi ta dauke lokaci guda kamar an dauke wutar nepa duk abin da ya yi mata sam ba ta cikin hayacin ta Sannu sannu har barci ya dauke shi ya na saman jikin ta Bai farka ba sai wajen karfe 6 na yamma ya fara jiyo sautin kukan ta a hankali ta na bugun shi a baya A hankali ya ware idanun shi ya zubawa face din ta da ta yi jaga jaga da hawaye , shi sai yanzu ya ji wani mugun son ta ya shige mishi zuciya Dan murmushi kadan yayi kafin ya bude baki ya ce " haba baby na , kukan na minene kuma ? " Cikin fitar hayaci ta ke kai mishi bugu a baya ta na fadin " mugu , azzalumi , mara imani , Allah ya isa tsakani na da kai ba zan taba yafe maka ba , mugu kawai " ta kai karshen ta na sakin sabon kuka Shi duk abun nan da ta ke kara tunzura shi ya ke Ta na tsaka da kukan nata kawai sai ji tayi ya hade bakin su waje guda ya na kissing din ta Zaro idanu ta yi ta na kallon shi , ya rufe idanun shi Da karfi ta din ga kai mishi bugu a baya ta na harba kafafun ta , Dama kamar jira ya ke , da sauri ya kai hannayan shi ya riko kafafuta ya ware su ya sake afka mata , Yanzu ma sai da ta saki kara dan ba karamin ciwo ya ja mata ba , Haka ya ci gaba da sharholiyar shi saman ta , har sai da ta sake sume mishi bai sani ba Sai da ya gaji iyakar gajiya sannan ya sauka da ga saman ta ya dauki short din shi ya sa ka bai tsaya bin ta kan ta ba kawai ya nufi stair ya Haye After some minutes ya sauko sanye da wando three cuter brown da t-shirt fara ya na rike da wayar shi ya na latsawa Ya na isa bakin sofar da ta ke konce ya ajiye wayar shi saman table ya zauna bakin sofar ya na murmushi ya kai hannu ya dan bubugi kumatun ta Shiru ko motsawa ba ta yi ba , sake bubuga ta ya yi nan ma shiru ba ta motsa ba Da sauri ya kai hannun shi wajen hudar hancin ta , nan ya ji ko nunfashi ba ta yi A razane ya mike tsaye ya na kallon ta ya na zaro idanu ya na fadin " no no no ba dai mutuwa ta yi ba " Bai kai ga rufe bakin shi ba ya ji kara a na kokarin bude kofar falon za a shigo Da sauri ya juyo ya na kallon kofar zuciyar shi na duka uku uku , dai'dai lokacin da Hafiz ya shigo gidan kai a sunkuye ya na sallama Dum Moctar ya ji gaban shi ya fadi ya kassa ko wani motsin kirki Hafiz kuma ya na dago kai idanun shi su ka sauka kan Nesrine da ke konce naked saman sofa cikin jini Slowly ya dago kai ya kali Moctar da ya yi sumar tsaye ya na kallon Moctar A hankali Hafiz ya fara takowa ya nufi Moctar ya na kallon shi cikin ido Wasu yawu Moctar ya hadiye kafin ya bude baki murya na kerma ya ce " bro me ka k......" Bai kai ga karasa maganar shi ba Hafiz ya kai mishi wani wawan bugu a ciki har sai da ya zube saman guyiwowin shi ya na daura hannayan shi saman ciki Cikin bacin rai Hafiz ya kai hannu ya damko kwalar rigar Moctar ya mikar da shi tsaye ya daka mishi tsawa ya na fadin " why za ka min haka Moctar , why ? ka fi kowa sanin irin son da na ke yi ma Nesi , kafi kowa sanin auren ta na ke son yi har Daddy ya san da maganar, shi ne za ka yi mata haka , me ta yi maka , me ya sa za ka karbi abun da ya ke nawa " Ya kai karshen ya na sakin shi ya sake zubewa saman guyiwowin ta , shi kuma Hafiz ya nufi Nesrine , ya zauna bakin sofar ya kai hannu ya dan bubuga ta ya na fadin " baby please tashi , i'm sorry kin ji zan yi maganin shi , tashi don Allah " Shiru ko motsi ba ta yi ba , sa sauri ya kontar da kan shi saman kirjin ta ya na son ya ji bugun zuciyar ta , sai dai kuma shiru zuciyar ta ba ta bugawa Da sauri ya mike tsaye ya na girgiza kan shi ya dunkule hannu ya bugi table din tsakiyar falon har sai da ta watse glass din ya fassa mishi hannu ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 22 ❤🔥 Da sauri ya mike tsaye ya na girgiza kan shi , ya dunkule hannun shi ya bugi table din tsakiyar falon har sai da ta watse glass din ya fassa mishi hannu , sai zubar da jini ya ke , duk ya bi ya birkice idanun shi sun yi jazir don bacin rai Cikin fitar hayaci da kai ma Moctar bugu a fuska har sai da bakin shi ya fashe , ya na fadin " na tsane ka Moctar , ka na matsayin kane na amma za ka ci zarafin matar da zan aura , duk irin iskancin da mu ke yi ka fi kowa sanin ko so guda ban taba kallon mace da sunnan so sai a kan ta , shi ne za ka kashe min ita , me ta yi maka Moctar , me na yi maka ? " ya kai karshen kamar zai yi kuka Cikin kuka Moctar ya dago kai ya kale shi ya ce " i'm sorry bro , wlh ban si yin hakan ba zuciya ya ce kawai ta debe n......." Bai karasa maganar shi ba Hafiz ya sa hannayan shi duka biyu ya tura shi ya fadi kassa ya ce mishi " ka je cen kaida zuciyar ka , ka kashe ta , ka huta ko ?" Ya na gama fadar haka ya juya cikin bacin rai ya Haye stair ya bar Moctar nan konce Jim kadan ya sauko rike da jallabiya dark blue , bai tsaya bin ta kan Moctar da ke konce kassa ba , ya nufi Nesrine ya saka mata jallabiyar sannan ya dauke ta cak kamar baby ya fice da ita , ya nufi motar shi ya kontar da ita gidan baya Sannan ya juya ya koma cikin gidan inda ya bar Moctar nan ya tardo shi , ya na zaune saman guyiwowin shi ya sunkuyar da kai A hankali ya tako ya tsaya gaban shi ya ce " duk abun da ka yi bazan iya cire ka ba a matsayin dan uwa na ba , amma wannan abun da ka yi bazan iya yafe maka shi ba , Moctar ni ka yi wa ba ita ba , ka sani wannan abun da kayi bazan kyale ka ba a haka , ka jira kiran yan sanda " ya na gama fadar haka ya juya ya bar wajen Kai tsaye motar shi ya nufa ya shiga ya bar wajen da uban gudu Dai'dai lokacin da Moctar ya fito da ga falon ya na kiran sunan Hafiz amma ina ya tafi Da sauri ya koma cikin falon ya dauki wayar shi da ta fadi kassa ya shiga kiran layin babban shi Cikin fitar hayaci ya kira Abban shi kira na farko ya daga kiran , babu ko sallama ya ce " Daddy please help me , big bro kara ta zai kai police station " Da sauri ya katse shi da cewa " calm down my son , kontar da hankalin ka ka fada min abun da ke faruwa " Wasu yawu ya hadiye kafin ya fara ba shi labarin duk abun da ya faru tun haduwar su da Inaya har zuwa yanzu maganar da Hafiz ya yi mishi Cikin ko in kula ya ce " kontar da hankalin ba abun da zai faru da kai , yanzu ka yi zaman ka a nan gidan gonar zan ji da Hafiz " Da to ya amsa mishi kafin ya sauko da wayar ya kashe kiran ya koma bakin sofa ya zauna ya rike kan shi da hannayan shi duka biyu NESRINE da mugun gudu ya bar gidan gonar cikin abun da bai kai one hour ba ya isa cikin gari Kai tsaye police station ya wuce da ita ya shiga da wani matsanincin gudu , dai'dai lokacin da su Zayd su ka bar police station din su ka koma gida Ya na shiga ya yi parking , maimakon ya fito sai ya tsaya ya kontar da kan shi saman steering din motar Sai da ya dauki lokaci a hakan kafin ya dago kan shi slowly ya bude kofar motar ya fito , sannan ya bude kofar bayan ya dauko Nesrine da ke konce kamar gawa Ya shiga police station din, dai'dai lokacin da DPO ya bada umarnin a tafi neman Nesrine Ya na sallama ya shigo police station din , duk officer din da ke wajen sai da su ka sara mishi dan sun san wanene Hafiz Jinjina musu kai ya yi kafin ya nufi wani banci sa ya hango cen gefe ya kontar da Nesrine , Sannan ya dago kai ya kali dayan officer cikin sanyin murya ya ce " ina son ganin DPO " Da sauri dayan officer ya juya ya nufi office din D.P.O Ko minti daya bai yi ba su ka fito shi da D.P.O Ya na sauke idanun kan Nesrine ya nufe ta da sauri ya na kare mata kallo , cike da rudu ya dago kai ya kali Hafiz ya ce " Hafiz ina ka samo yarinyar nan ? Yanzun nan mu ke shirin fita neman ta " da ya ke ya san Hafiz ya na yawwan zuwa gidan su amma shi sam bai san halin Hafiz ba Cikin wata sanyayar murya ya ce " uncle ku yi hakuri bazan iya fada muku inda na dauko ta ba, amma please ku taimaka ku fara kai ta Hospital da sauri kafin ku kira ahalin ta bazan so su gan ta cikin wannan halin ba " Ya kai karshen ya na sa hannun shi cikin aljihu ya ciro bandir fin kudi dan dari biyar biyar ya mikawa D.P.O ya ce " ga wannan ku kai ta asibiti amma don Allah duk abin da likitan zai fada muku ya tsaya a iya tsakanin ka da shi please " ya kai karshen ya na marairaice fuska sannan ya juya ya fice police station din Ya na barin wajen wayar D.P.O da ke cikin aljihun shi ta fara ringing Da sauri ya sa hannu cikin aljihu ya ciro wayar ya na tunanin ko Zayd ne ya sake kiran shi Amma sai ya ga governor ne da kan shi ya ke kira, sa sauri ya daga kiran ya kai kunne ya na sallama Bai tsaya bin ta kan sallamar shi ba ya ce " D.P.O ina son case din yarinyar da Hafiz ya kawo ya mutu ba na son maganar nan ta fita waje " Da sauri D.P.O ya katse shi da cewa " bai fadi komai a kan ta ba cewa kawai ya yi a kai ta Hospital da ga haka ba wani abu da ya fada , amma familyn ta sun zo sun yi report a kan batar ta " " that's good , ba ni son a bude wani file a kan ta kawai ka kaita Hospital ba na son kowa ya san abun da ya faru da ita maganar da tsaya da ga ni sai kai , ba shawara na ke baka ba , umarni ne da ga na sama da kai " ya na gama fadar haka bai jira amsar D.P.O ba ya katse kiran Kallon wayar D.P.O ya yi cikin ranshi ya na tunanin wai me ya samu yarinyar nan ne da governor da kan shi zai ce a kashe case din ta Ya dan jima a haka kafin ya kali dayan officer ya ce ya tada mishi mota zai kai ta asibiti shi kadai Bai kai ga rufe bakin shi ba officer din ya fita da gudu , shi kuma D.P.O ya duka ya dauki Nesrine ya fice da ita ya nufi motar da officer ya kawo mishi bakin kofar Da sauri ya bude kofar baya ya kontar da Nesrine sannan ya shiga mazaunin driver ya tada motar ya fice Cikin abin da bai fi 20 minutes ba ya isa babban Hospital na garin kano Kai tsaye parking space ya nufa ya yi parking sannan ya fito ya bude kofar baya ya dauko Nesrine ya shiga likitar da ita Ya na shiga ko nurse ta tafo ta na ture da gadon jinya ta ce ya kontar da Nesrine sannan ya tafi reception ya cika duk wasu files da kuma kudin duba ta Ba musu ya kontar da ita sannan ya juya ya tafi reception , kudin da Hafiz ya ba shi ya ciro ya biya , sannan ya koma saman chair din reception ya zauna ya na jiran doctor ya fito After one hour Bayan awa daya doctor ya fito da ga A&E room ya nufi D.P.O Tun da D.P.O ya gan shi ya mike ya tunkare shi ya na tambayar shi me ya same ta " mu je office di na mu yi magana " doctor ya fada ya na juyawa ya nufi office din shi Da sauri D.P.O ya bi bayan shi su ka isa office din shi ya ce mishi ya zauna Ba musu D.P.O ya zauna ya na fuskantar doctor ya ce " please doctor me ya same ta ? " " calm down D.P.O , zan fada maka komai amma zan so in san minene alakar ka da ita ? " doctor ya fada ya na tsare shi da ido " ban san ta ba, kawai an kawo karar cigiyar ta ne , saurayin sa ya kawo ta ne ya ce na fara kai ta likita kafin na kira familyn ta " Jinjina kan shi doctor ya yi kafin ya ce " ya yi tunani mai kyau dan na san idan su ka gan ta cikin wannan halin ba za su yi dadi ba " Da sauri D.P.O ya katse shi da cewa " don Allah doctor fada min me ya ke damun ta ne " Cikin sanyi doctor ya ce " calm down , zan fada maka , gaskia sai dai ku yi hakuri raping din ta a ka yi , ga Dukan allamu kuma ba sau daya ba har dinki sai da mu ka yi mata , sannan ta zubar da jini dayawa hakan ya jefar da ita cikin doguwar suma , ta yiyu ta tashi ko kuma akasin haka , i'm sorry " " Ina'lillahi wa'ina illaihi raji'un " shi ne kadai abun da ya ke fitowa da ga bakin D.P.O Cikin ranshi ya na fadin " kenan shi ya sa governor ya kira ya ce a kashe case din dan ya san dan shi ne ya yi aikin " Shi a tunanin shi Hafiz ne ya yi hakan saboda shi ne ya kawota sam bai kawo Moctar a rai ba Ya na a haka ya tsinci Muryar doctor ya na fadin " ya kama ta ku kira familyn ta ku fada musu mun riga da mun yi na mu aikin , yanzu haka ku na iya zuwa ki gan ta an sauya mata daki " Godiya D.P.O ya yi wa doctor kafin ya mike ya fice office din ya tafi dakin da a ka kontar da Nesrine Bai fi ten minutes ba ya fito ya kira Moussa ya sanar da shi inda su ke ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 22 ❤🔥 STORY 🔥 A hankali Zayd ya juyo ya na kallon D.P.O ya na shirin magana Moussa ya rika shi cewa " D.P.O ka ba ni amsa mana , kun kamo wanda ya yi mata hakan " " ku yi hakuri bazan iya kama shi ba , umarni a ka ba ni daga sama a kan na rufe case din nan , ko da na san wanda ya yi hakan bazan iya kama shi ba , kuyi hakuri " D.P.O ya fada cikin rarrashi Da karfi Moussa ya ce " what ? Kun san wanda ya yi mata hakan, ina ruwa na da umarni da ga sama ya yi laifi dole a kama shi ....." Da sauri Zayd ya dafa kafadar shi ya katse shi da cewa " Diya yi hakuri , abun da ya faru ya riga da ya faru , ko da an kama shi bazai goge abun da ya yi mata ba " ya fada cikin nitsuwa Katse shi Moussa ya yi da cewa " Amir me ka ke fada haka kennan yanzu ya yi mata hakan ya ci bilis kennan ba za mu dauki wani mataki a kai ba " Girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya ce " a'a bai ci bilis ba , ya je shi da Allah , nasan dole ka ji zafin abun da ya faru saboda son da ka ke mata , amma ka san ba laifin ta ba ne abun da ya faru , nasan da wuya yanzu a ce ka ci gaba da son ta bayan abun da ya faru , ina mai baka hakuri a madadin ta " Ya na kai karshen ya juya ya fara takawa zai bar dakin Har ya riko handle din kofar ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce " zan yi magana da doctor , za mu tafi da ita Abuja yanzun nan , za a ci gaba da kula da ita a cen , idan har yanzu ka na da sha'awar auren ta ka min magana zan nema maka auren ta wajen uncle " Ya na gama fadar haka ya yi ficewar shi ya bar D.P.O da Moussa nan tsaye Sai da ya tafi sannan D.P.O ya ce da Moussa " ni zan tafi , don Allah ina mai kara ba ku hakuri akan abun da ya faru " sannan shi ma ya ficewar shi D.P.O na fita Moussa ya zauna saman chair din bakin gadon ya zubawa Nesrine ido Bangaran Zayd kuma ya na fita ya nufi office din doctor ya sanar dasshi zai kai yar uwar shi Abuja za a ci gaba da kula da ita a cen Ba musu doctor ya yarda ya sa a ka shirya musu ambulance din da za ta dauke ta Da ga haka kuma ya baro likitar baki daya ya yi tafiyar shi After some minutes ya iso gidan malam Kai tsaye gidan ya shiga ya na sallama , ban ya isko duk mutanan gidan su na zaune harabar gidan sun yi zugum kamar an turo musu mutuwa A tare su ka dago kai su na amsa sallamar shi Malam na ganin Zayd ya mike da sauri ya nufe shi ya na fadin " Zayd an gan ta ne ? " Riko hannun shi Zayd ya yi ya dawo da shi inda ya tashi ya ce " uncle zauna zan yi wata magana " Ba musu malam ya koma ya zauna dan shi fa yanzu ba ya cikin halin yin jayyaya da shi a kan wani abu Tsaya wa Zayd ya yi ya na rike da hannayan shi a baya ya zuba musu idanu ta cikin glass din shi Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " ku kontar da hankalin ku uncle an gan ta , amma sai dai ku yi hakuri ta samu hatsari dalilin da ya sa ma ta kassa dawowa gida , yanzu haka na sa an wuce da ita Abuja za a ci gaba da kula da ita a cen , ina son ku shirya kayan ku nan da two hours zan sa a zo a dauke ku tare za mu koma Abuja da zama " Da sauri malam ya mike shi da Abdoul ya na fadin " Zayd mu fa ba mu da gida a Abuja idan mun je ina za mu zauna , karatu na da aiki na duk na yi yaya da su ? " " duk ba damuwa ba ne , ka fadi duk makarantar da ka ke so a Abuja ka fada min zan nema maka admission, batun gida kuma a gida na za ku zauna , ku shirya nan da two hours za a zo daukar ku " ya na gama fadar haka ya juya ya na taku cike da nitsuwa ya bar gidan Ya na fita Abdoul ya kali malam ya ce " Abba ya za muyi ne , haka za mu bar gidan nan lokaci guda ? " Malam na shirin magana mama ta mike da sauri ta ce " e tafiya za muyi , wlh duk inda yarinya ta , ta tafi sai na tafi bazan kyale ta wani abu ya sake faruwa da ita " ta kai karshen kuka na kubce mata ta juya da sauri ta shige dakin ta Ta na barin wajen malam ya kali Abdoul ya ce " to ba yadda za muyi , la shiga kawai ka shirya kayan ka sai mu tafi " Da to Abdoul ya amsa mishi sannan kowa ne ya kama hanyar dakin shi dan su shirya kayan su Zayd Bayan ya baro gidan malam kai tsaye gidan shi ya nufa Bakin shi dauke da sallama ya shigo falon gidan , kai tsaye ya nufi doguwar sofa ya zauna ya jingina a bayan sofar ya daga kan shi sama sannan ya sa hannu ya cire glass din shi ya ajiye gefe shi ya lumshe idanun shi Ya na zama Inaya ta fito da ga kitchen ta na rike da tray dauke da kwanonin abinci ta nufi dining room ta ajiye Ta na juyowa ta ga Zayd a zaune har sai da ta ji tsoro dan ita sam ba ta san lokacin da ya shigo gidan ba A hankali ta fara takowa ta karaso inda ya ke , ta zauna geffen shi ta na kare mishi kallon cikin ran ta , ta na fadin lalle akwai abun da ya ke damun shi dan yanayin shi ba haka ya ke kullum ba A hankali ta gyara zaman ta ta konta ta tada kai da cinyar shi , A razane ya sauko da kan shi ya bude idanun shi ya na kallon ta , shi sam bai san lokacin da ta iso wajen Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mayar da kan shi ya sake lumshe idanun shi , ta kai hannu saman kan ta slowly ya fara shafawa Ta na jin saukar hannun shi saman kanta ta saki dan karamin murmushi ta ce " yaya Zayd me ya ke damun ka ne ? " Ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " me ki ka gani ne ? " " yadda ka fita ba haka ka dawo ba , duk yanayin ka ya sauya , me ya ke damun ka ne " Gaskia maganar ta ba karamin dadi ta yi mishi cikin zuciyar shi , kennan har ta iya gane yanayin da ya ke ciki lokaci guda haka " ba komai , ba abun da ya ke damu na kar ki damu " Da sauri ta katse shi da cewa " a'a yaya Zayd ni na san akwai wani abu da ya ke damun ka amma ba ka son ka fada min " A hankali ya bude idanun shi ya sauko da kan shi ya na kallon face din ta ya ce " shikenan fada min ta ya ki ka san akwai wani abu da ke damu na ? " Gyara konciyar ta tayi ta juyo da kan ta yadda su na iya fuskantar juna Dan murmushi ta saki kafin ta ce " yanayin face din ka ya sauya, ba kamar yadda ka fita ba , yanzu kuma duk ka yi sanyi kamar ba kai ba " Hannun shi ya kai saman face din ta ya shafa a hankali kafin ya janye ya daura shi saman cikin ta ya koma ya daga kan shi ya lumshe idanun shi ya ce " don't worry ba abun da ke damu na , kawai dai na gaji ne , tashi ki je lokacin sallat ya yi , Idan kin Kamala ki shirya kayan ki za mu koma Abuja da zama har da su uncle " Da sauri ta dago kan ta ta na sakin wani kyawatencen murmushi ta ce " da gaske yaya Zayd za mu koma Abuja da zama " Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya bude idanun shi ba Da sauri ta tashi da ga jikin shi ta nufi corridor ta shiga bedroom din shi Ta na shiga wayar shi ta fara ringing Ko bai duba ba ya san wanene ke kiran shi Hannu ya kai ya ciro wayar da ga cikin aljihun shi ya daga kiran sannan ya kai kunne ya yi shiru bai ce komai ba A daya bangaran kuma, Moussa ya na jin ya daga kiran ya ce " please ka shirya min kaya na zan bi ambulance din mu tafi Abuja tare da ita " " okay " Zayd ya bashi amsa a takaice , sannan ya sauko da wayar ya kashe kiran Sannan ya tashi ya shiga bedroom din Moussa ya wuce toilet ya yi wanka ya dauro da Alwalla sannan ya fito ya shirya cikin kayan Moussa , wandon jeans brown da t-shirt fara yi gabatar da sallar shi nan cikin dakin Bayan ya gama sallar shi ya shiga shirya kayan Moussa cikin trolley biyu sannan ya fito da su falo ya koma ya shiga bedroom din shi Nan ya tardo Inaya ta shirya musu kayan su da na shi da natan duka cikin trolley guda hudu dama nata yawancin cikin trolley su ke so aïkido bai yi mata yawa ba Ya na shiga dakin bai bi ta kan ta ba ya janyo trolley din ya fitar da su falo sannan ya dauki trolley din daya bayan daya ya saka su cikin motar shi sannan ya gewaya ya bude babbar gate din gidan da kan shi Sannan ya dawo cikin gidan inda ya tardo ta , zaune cikin falo saman sofa " tashi ki jire ni bakin gate ina zuwa " ya fada ya na wucewa corridor ya shiga bedroom din shi Ya na shiga ta tashi ta fito waje ta fita gidan ta tsaya baki kofar kamar yadda ya ce Ta na fita ya fito shi ma ya na rataye sa wata purse ya fito gidan ya shiga motar shi ya tada ya fice Ya na fitar da motar ya tsaya ya like gidan Ya na shirin shiga cikin motar shi wani dattijo ya iso wajen shi ya na mishi sallama Cen kassan makoshi ya amsa sallamar shi sannan ya mika mishi keys din gidan ba tare da ya ce komai ba ya shiga motar shi ya bar wajen da gudu ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 23 ❤🔥 Inaya Bayan ta fito gidan ta tsaya ta na jiran shi , ta dauki wajen five minutes ta na tsaye a wajen sannan ta hango shi cikin mota ya tunkaro ta Gaban ta ya tsayar da motar ba tare da ya ce mata komai ba , bai kuma fito da ga cikin motar ba Ganin hakan ya sa ta tako a hankali ta zagayo geffen mai zaman bazan ta bude kofa ta shiga ta zauna Ta na shiga ya ja motar su ka yi gaba Sai da su ka yi tafiya mai dan nisa kafin ta kaleshi ta ce " yaya Zayd ba tare da yaya Moussa za mu tafi ba " Sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " ya riga mu tafiya ma " Gyada kan ta kawai ta yi ta medo da kallon ta kan hanyar su Tun ta na ganin gidaje har ya kai ta daina ganin komai bayan itace Sannu sannu har barci ya dauke ta ba ta shirya ba After one hours A hankali ta fara motsi ta na son tashi da ga barcin ta Slowly ta faro karanto adu'ar tashi da ga barci ta na ware idanun ta Ta sha ruwan mamaki jin ta konce saman gado al'halin ita a sanin ta cikin mota ta ke A hankali ta fara bin dakin da kallo Dakin babba ne gaskia komai na cikin dakin white colour ne , har closet da ke fuskantar dressing mirror duk white ne Gaban gadon dakwai wani carpet sky blue me ratsin white gwanin burgewa , gadon ya na fuskantar wasu sofas guda uku suma white , biyu one seater su na fuskantar juna sai three seater a tsakiyar su , da ga tsakiya kuma akwai wata table ta glace mai kyau Geffen gadon na hagu dan nesa kadan dakwai wata door wadda ina kyautata zaton toilet ce Sai da ta karewa dakin kallo da kyau kafin ta mike zaune ta sauko kafafun ta kassa , ta mike tsaye ta fara takawa a hankali ta nufi wata kofa da ta gani bude a geffen dama na bed din Nan ta fito parlour na sama mai bala'in kyau ya sha fournitures da ga gani kassan tsadadu ne , sai kofofi biyar na bedroom , amma ta karshen ta yi nessa da sauran Ba ta tsaya bin ta kan falon ba ta nufi daya da ga cikin stair din da ta gani ta sauko kassa Ni fa gaskia ban iya description ba dan haka kowa ya yi tunanin yadda falon na kassa zai kassance yawwa 😌😌 Ta na saukowa ta hango shi cen zaune saman sofa three seater ya daga kai sama ya lumshe idanun shi A hankali ta karaso inda ya ke ta tsaya gaban shi ta ce " yaya Zayd ? " Slowly ya medo da kan shi ya bude idanun shi ya na kallon ta Sai da ya dauki lokaci ya na kallon ta kafin ya mika matta hannu a kan ta zo Ba musu ta daura hannun ta saman na shi ta fara takowa gare shi Zaunar da ita ya yi saman cinyar shi , sannan ya daga mata gera guda allamun minene " yaya Zayd wannan gidan wanene ? " ta tambayeshi ta na karewa wajen kallo Cen bayan sofar da su ke zaune ta hango dining room dauke da dining table zagaye da chair goma sha biyu , sai wata kofa ta kitchen amma ta glass ce Ta yi nisa cikin duniyar ta, ta tsinci Muryar shi ya na fadin " ya dai ? Bai miki ba ne ? " Girgiza mishi kai ta yi kafin ta ce " ya na da kyau sosai yaya Zayd " " shikenan tashi ki je ki yi wanka , ki yi sallat , sai ki sauko ki ci wani abu na san ki na jin yunwa na sa a shirya miki lunch " " to amma yaya Zayd ina ne bedroom din nawa " ta fada cikin shagwaba " duk wanda ki ke so , amma bedroom din da ki ka fito cen na saka kayan ki , in bai miki ba zan sa a sauya miki " Da sauri ta ce " a'a yaya Zayd wannan ma ya na da kyau " ta kai karshen ta na kai mishi kiss saman kumatu sannan ta tashi da sauri ta Haye stair ta koma bedroom din da ta fito Da kallo ya rakata har sai da ya ga ta shiga bedroom din sannan ya koma jikin sofar ya daga kan shi saman ya lumshe idanun shi After two days Bayan malam da ahalin shi sun dawo gidan Zayd da zama duk sai da su ka sha ruwan mamaki ganin gidan Zayd musaman mama sam ba ta yi tunanin haka gidan ya ke ba Bangaran Nesrine har yanzu dai shiru ko yatsa ba ta daga ba , amma an maido ta word room na gidan, nan Zayd ya dauko doctor musaman wanda zai kula da ita amma har yanzu malam da mama da Abdoul ba su san abun da ya same ta ba su dai a tunanin su accident ne ta yi dan haka Zayd ya fada musu In muka leko Inaya kuma bayan barci da kallon cartoon ba abun da ta ke , ko girki akwai yan aikin da su ke kula da komai na gidan da ga mopping har girki akwai ma su yi Kwana biyu bayan zuwan su gidan , Zayd ya nemawa Moussa auren Nesrine Malam ya yi farin ciki sosai shi da mama , a ranar a ka daura auren duk da Nesrine ba ta cikin hayacin ta In mu ka leko Zayd kuma bawan Allah kullum cikin damuwa ya ke har ya yi wata yar rama , tambayar duniyar nan Moussa da Inaya su ke yi mishi amma ko wane lokaci sai ya ce ba komai , kullum ya na zaune cikin bedroom din shi ya lumshe idanun shi amma ba barcin ya ke ba , a takaice ko dare in ya yi da wuya barci ya ke dauke shi wani lokaci har sai an yi kiran sallar asuba ya na farke , Ko me ke damun shi ? Misalin karfe 12 na dare Zayd Konce ya ke saman daguwar sofa a falon kassa, ya daura hannun shi daya saman ciki, dayan kuma saman forehead din shi Ya na konce a hakan ya ji a na takowa stair a hankali Slowly ya ware idanun shi ya na kallon ceiling amma bai motsa ba Ko bai duba ba ya San ko wanene , dan ya san bayan ita ba wanda ke saukowa a irin wannan lokacin A hankali ya sauko da kafafun shi ya mike tsaye , sannan ya nufi hanyar dining table ya na taku a hankali cikin ranshi ya na fadin yau sai ya ga wainar da ta ke toyawa cikin daren nan Cen kassan makoshi ya yi sallamar shi , sannan ya tsaya bakin kofar kitchen ya zuba mata idanu , ya nade hanayan shi a kirji Sanye ta ke cikin kayan barci kanana pink colour , ta na tsaye gaban counter ta na yankar fruits Slowly ya fara takowa inda ta ke ya na yi mata gyaren murya Da sauri ta juyo ta ga ko wanene dan ita ba ta ji shigowar mutun cikin kitchen din ba Ta na ganin shi ta saki murmushi ta ce " yaya Zayd har ka bani tsoro " ta kai karshen ta na juyawa ta ci gaba da yankar fruits din ta Takowa ya ci gaba da yi har ya karaso geffen ta ya tsaya ya na kallon kananan hanayan ta , ta na yankar fruits cikin konciyar hankali A hankali ya kai hannun shi ya riko nata da sauri ta dago kai ta kali face din shi , yayin da shi kuma hannayan ta ya ke kallo Cikin sanyi murya ta ce " yaya Zayd me ya faru ? " Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " ba ki jin tsoron ki ji tsiwo da wadanan kananan hannayan na ki ? " Dan murmushi mai sauti ta yi kafin ta janye hannayan ta da ga cikin nashi slowly ta ci gaba da yankar fruits din ta Sai da ta Kamala sannan ta dauki tray din ta juya ta bar kitchen din ta bar shi nan tsaye Sai da ta fita sannan shi ma ya fara takawa ya fice falon Nan ya hango ta zaune saman sofa ga table gaban ta , ta daura tray din fruits a sama sai ci ta ke a hankali Geffen ta ya karaso ya zauna , a hankali ya kai hannu saman tray din ya dauki barin Apple guda ya kai baki Ba tare da ta kaleshi ba ta ce " yaya Zayd , don Allah ka fada min abun da ke damun ka " Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai ma konta wa da ya yi a jikin sofar ya daga kai sama ya lumshe idanun shi Dago kai ta yi ta kaleshi, duk sai ta ji zuciyar ta ba dadi Nan take idanun ta su ka kawo ruwa , ba ta san lokacin da kuka ya kubce mata ba Da sauri ya bude idanun shi ya dago ya na kallon ta Cike da rudu ya ce " me ya faru ki ke kuka ? " Ko kallon shi ba ta yi ba ta ci gaba da kukan ta , hawaye wasu na bin wani Duk ya bi ya rude sai tambayar ta ya ke me ya faru amma ina ko kallon shi ba ta yi Da ya ga abun na ta ba mai karewa ba ne sai ya kai hannu ya rungumo ta a jikin shi ya na dan bubuga bayan ta ya ce " stop crying please , me ya faru ki ke wannan kuka haka ? " Cikin disashashiyar murya ta ce " ba kai ne ba yaya Zayd , kullum sai na tambaye ka abun da ke damun ka amma kullum sai ka ce ba komai " Da sauri ya katse ta da cewa " i'm sorry, yi hakuri ki daina kukan nan wlh ba na so " Dagowa ta yi daga jikin shi ta na goge hawayen ta, ta ce " shikenan yaya Zayd na bar kukan amma don Allah ka fada min abun da ke damun ka ! " Mikewa tsaye ya yi sannan ya mika mata hannu a kan ta tasso Ba musu ta daura hannun ta saman nashi sannan ta mike tsaye ta na kallon shi cikin ido Ta na mikewa tsaye ya fara takawa ya yi gaba ita kuma ta bi bayan shi A haka su ka Haye stair a tare ya na rike da hannun ta A tunanin ta bedroom din da ta ke barci nan za su koma sai ta ga ya wuce ta A haka har su ka wuce duk bedroom din da ke sama , su ka nufi bedroom na karshe Tun da ta shigo gidan ba ta taba shigo shi , kuma ba ta taba ganin wani ya bude shi ba ya shiga A hankali ya kai hannu ya murda handle din kofar ya tura ta ya shiga Nan ta ga wani falon daban , dauke da wasu sofas biyu white colour guda three seaters dayar one seater sai wasu biyu two seaters sky blue , da ga tsakiyar su kuma wata table ce ta glass saman wani carpet fari mai ratsin blue , geffen doguwar sofa akwai wasu kananan tables na glass , sannan ta na fuskantar wata makekiyar Tv plasma makale a bango Ba ta ida shan mamaki ba, sai da su ka shiga bedroom din Kyawon bedroom din wannan book din ya yi kadan ya fade shi , girman shi ya fi falon part din , komai na cikin dakin white colour ne , Da ga shigo dakin sai saman wani makeken royal bed fari kal shinfida da bedsheet fara , ya na fuskantar wata makekiyar Tv plasma girman ta daya da ta falon da su ka baro A geffen gadon kuma na hagu wani dressing mirror ne dauke da perfume da lotion kala kala Dressing mirror din na tsakiyar wasu door , guda toilet guda dressing room ( a nawa tunanin 🤷‍♀️ ) A geffen dama na Tv din wata door ce ta glass wadda za ta sada ka da balcony din dakin ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 23 ❤🔥 Da kallo ta ke bin shi cikin zuciyar ta ta na tambayar kan ta wanene Zayd Ta yi nisa cikin tunanin ta ta cintsi murya shi ya na fadin " konta ki yi barci ina zuwa " Da to ta amsa mishi sannan ta saki hannun shi ta zauna bakin gadon Shi kuma ya ci gaba da takawa ya nufi daya daga cikin kofofin geffen dressing mirror Ya na shiga ta ida Hayewa gadon ta konta Bayan wasu mintina ya fito daga toilet sanye da bathrobe , bai tsaya shafa lotion ba ya wuce dayan door ya shiga dressing room Jim kadan ya fito sanye da kayan barcin shi ash colour ma su kyau Gadon ya nufa ya Haye geffen guda ya konta ya na fuskantar ceiling Cen ya juyo da kan shi ya na kallon ta , ta juya mishi baya har ta yi barci Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lumshe idanun shi ya sake bude su slowly a kan ta Cikin sanyin murya ya ce " ko na fada miki ba za ki gane ba , akasi ma ni da kai na ban san abun da ke damu na ba , amma na san duk lokacin da na ke tare da ke ina jin sauki a cikin zuciya ta , ina ji a jiki wani mumunar abu na shirin faruwa da ni kamar zan rasa wani abu mai mahimanci a rayuwa ta , duk da san ba tabas abun da na ke ji ya faru ba , amma ba ni fatan na rasa ki cikin rayuwa ta , dan a yanzu ke kadai ce family na , na so na yi miki irin son da ki ke yi min amma zuciya ta ta kassa ban san dalili ba " Ya kai karshen ya na juyo da kan shi ya fuskanci ceiling ya lumshe idanun shi Kamar da ga sama ya tsinci wannan zazzakar Muryar ta ta, ta na fadin " na sani yaya Zayd ba laifin ka ba ne dan ba ka so na , laifi na ne da na fada soyayyar ka da karancin shekaru na , na yi maka alkawari zan yi kokarin na cire shi da ga cikin zuciya ta " Cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " ni ban ce ki cire shi da ga cikin zuciyar ki ba " Slowly ta juyo ta kaleshi, sannan ta ce " me ya sa to baza ka iya so na ba , ba ni da kyau ne ? " " pleaseeee ni ba wannan ba , kin fi kowa sanin ki na da kyau Masha Allah " " to minene matsalar yaya Zayd ? " ta fada kamar za ta yi kuka Juyo da kan shi ya yi ya kale ta cikin idanun ta da su ka kawo ruwa ya ce " i have never been in love , na hadu da mata dayawa a duniya , masu kyau , masu dukiya da mulki amma ko kallon kirki ban taba yi musu ba , ni a tsarin rayuwa ta ban shirya zama da mace ba , amma ke kin shigo lokaci guda kuma har ga Allah ba ni fatan ni fita da ga cikin rayuwa ta " Ya kai karshen ya na mika matta hannu a kan ta zo Ba musu ta karaso ta fada jikin ta boye fuskar ta a kirjin shi Rungume ta ya yi a jikin shi , ya lumshe idanun shi a haka har barcin da ya jima bai yi ba ya dauke shi Washe gari Misalin karfe 10 na safe Duk mutanan gidan su na a zaune a falo na kassa Banda Nesrine da ke cen konce a word room Sai hirar su su ke cikin konciyar hankali banda Zayd da ya kurawa Inaya ido cikin bakin glass din shi , ita kuma ta kurawa TV ido kamar ita ta ke kallo Su na tsaka da hirar su su ka ga an turo kofar shigowa falon A tare kowa ya kai duban shi kan kofar Banda Inaya da Zayd Kowa ya zubawa kofar ido ya na jiran ya ga wanda zai shigo Nan su ka ga nurse din da Zayd ya dauko ta kula da Nesrine ta shigo falon ta na sallama ta na rike da Nesrine sanye da wata riga blue ta na jan kafa A dubu dari mutanan falon su ka mike su ka yi kan ta Mama har da sakin kuka ta rungume ta , ta na fadin " Nesrine di ta ke ce , Allah na gode maka, sannu kin ji " Ita ma rungume mama ta yi da kyau ta na sakin kuka mai cin rai Duk abun da ke faruwa Zayd ko janye idanun shi bai yi ba da ga saman Inaya Ita ma ta kurawa Tv ido babu ko kiftawa Ya na tsaka da kallon ta ya ga ta ja wani dogon nunfashi ta saki wata razananiyar kara da karfi ta ce " kar ku zo ku kyale ni , ku kyale ni ahhhhhhhhhhh " ta kai karshen ta na sake sakin kara Dan lumshe idanun shi Zayd ya yi dan dama abun da ya ke tunani kenan dan ya na tune ta taba yin hakan Da sauri mutanan gidan su ka jiyo su ka kale ta , ta sa hannayan ta duka biyu ta toshe kunnuwan ta sai kara ta ke Da gudu malam ya juyo ya yi kan ta ya na fadin " auta lafya ? Me ya faru ?" Cikin fitar hayaci ta ce " Abba sun san muna nan , sun sani , sun sani " ta kai karshen ta na sakin kuka Da sauri Zayd ya mike ya yi kan ta , sai dai kafin ya iso ta dauke lokaci guda ta sume a wajen Ya na isa bai tsaya yi wa malam magana ba kawai ya dauke ta da hannayan shi biyu kamar baby ya nufi stair da ita Malam na nan zaune ko wani kwakwaran motsi bai yi ba Sakin Nesrine mama ta yi ta tako wajen malam ta dafa kafadar shi ta ce " Abban Abdoul me ya same ta kuma " Ta na taba shi ya dawo cikin hayacin shi , da sauri ya mike tsaye ya nufi stair da gudu Ya na barin wajen Moussa ya kali Nesrine ya ce " sister ya jikin na ki ? " Dan karamin murmushi ta yi kafin ta bude baki ta ce " da sauki " sai dai lips din ta ne kawai su ka motsa sautin bai fito ba Murmushi shi ma ya yi mata ya jinjina mata kai sannan ya juya shi ma ya nufi stair ya Haye Dakin Inaya malam ya tafi sai dai ya na shiga ya ga bedroom din ba kowa a ciki Da sauri ya juyo ya fito dakin dai'dai lokacin da Moussa ya hayo wajen " Moussa ina kuma Zayd ya kai ta ? " malam ya tambaye shi Kallon kofar dakin Zayd ya yi, ya ga ta na bude kadan kafin ya juyo ya kali malam ya ce " uncle , ina ga bedroom din shi ya wuce da ita ! " " bedroom din shi kuma ? " malam ya tambaya cike da rudu dan a iya sannin shi kullum a falo ya ke ganin Zayd na barci Jinjina mishi kai Moussa ya yi sannan ya ce su tafi ya yi gaba Ba musu malam ya bi bayan shi su ka nufi part din Zayd Sallama Moussa ya yi sannan ya shigo falon part din , malam na biye da shi a baya Zayd kuma , ya na zaune saman sofa ya na latsa wayar shi , cen kassan makoshi ya amsa musu sallamar su Da sauri malam ya nufo shi ya na fadin " Zayd ina auta , ba abun da ya same ta dai ko " Ba tare da ya dago kan shi ba ya ce " zauna uncle , ina ga yanzu lokaci ya yi da za ka fadamin gaskiyar abun da ke damun ta " Wasu yawu malam ya hadiye kafin ya zauna geffen shi ya sunkuyar da kai Sai da ya dauki lokaci kafin ya fara magana kamar haka " ni dai suna na Ibrahim , cikaken bafulatani da ga gari yola , a cen a ka haife ni , a cen na taso , bayan na cika shekara 23 na baro Garin neman aiki na taho jahar kaduna inda mahaifiyar mu ke da wasu yan uwa na sauka a gidan su , sannu sannu na fara fitowa neman aiki har Allah ya hada ni da wasu abokanai na , Issa da Youssef , a tare mu ka tafi neman aikin har Allah ya sa wani mai kanti ya dauke mu a tare , to dai haka mu ka ci gaba da aikin mu tsawan watanni , bayan wani lokaci a ka kawowa Aunty ta wa wata yarinya da ga ilori za ta zauna a wajen ta ta dinga yi mata aiki , kawai sai na ji na kamu da son yarinyar nan , duk yadda zan yi ta kula ni sai da na yi , a haka har mu ka fara soyayya da ita , har mutanan gidan su ka sani , gudun kar shaitan ya shiga tsakanin mu ba su bata lokaci ba a ka daura auren mu , na kama mana gida mu ka koma cen da zama , bayan shekara guda haka Allah ya ba mu yaro wanda ya ci sunnan Abdoul , abun kamar da wassa sati biyu bayan zuwan shi duniya , uban gida na ya ba ni amanar shagon shi saboda wata tafiya da ta tasso mishi , cikin wani ikon Allah da ma na fara kula da shagon, kasuwanci ya habaka , kullum sai mun ninka ribar jiya , abun ba karamin dadi ya yi wa mai shagon ba , hakan ya sa ya buda min wani shagon daban na dinga kula da shi , abun da ban sani ba Youssef ya na bala'in kishi na, musaman da ya ga uban gidan mu ya ba ni shago na dinga kula da shi ....... " Katse shi Zayd ya yi da cewa " wait uncle ni fa ban gane inda ka dosa ba abun da na tambaye ka daban , why za ku ba ni wannan labarin ? " Malam na shirin magana Moussa ya riga shi cewa " kai fa Amir matsalata da kai gajen hakuri , ka tsaya ka saurari abun da zai fada ko " Jinjina mishi kai ya yi kafin ya kali malam ya ce " uncle ci gaba " Murmushi malam ya yi kafin ya ci gaba da cewa " a haka mu ka ci gaba da rayuwa , ina kula da shagon nan har bayan wasu shekaru Allah ya ba mu kyakyawar yarinya wadda na sakawa sunnan Nesrine , bangaran Youssef kuma kishin nan nashi ya na nan har ya kai wani lokaci ya daina zuwa zaman da mu ke yi bayan sallar isha a cen gida na , hakan bai dame ni ba dan a tunani na aiki ne ya yi mishi yawwa saboda shi ma ya na da nassa ahalin kuma ga shi ya shiga harkar siyassa , bayan shekara uku , Allah ya sake ba mu haifuwar kyakyawar baby kamanin ta sak da na Nesrine , na saka mata sunnan mahaifiya ta wato Inaya , ranar da a ka yi zanan sunan ta , mu na zaune bakin kofar gida ni da Issa da Youssef mu na hira , mu na a haka ingozomar da ta karbi haihuwar matata tun ta Abdoul ta fito za ta tafi , cikin murna na tare ta ina yi mata godiya har na bata dubu biyar na hanya , har ta tafi na dawo , ina zauna tare da su issa kawai sai ganin ta na yi ta dawo , na tambaye ta ko ta yi mantuwa ne na shiga na dauko mata sai ta ce min " a'a ban yi mantuwa ba , ya kamata na sanar da kai , wannan yarinyar da Allah ya baka, ba kamar kowace yarinya ta ke ba , na ji a jiki na ta na da kashin arziki kamar mahaifiyar ta , musaman ga mijin da za ta aura , sannan akwai wani boyayen al'amari a tatare da ita , na ji a jiki na ta na da wata baiwar da Allah ya yi mata dan ganin karshe wani zalinci , ka kula da ita kar ka bari ta fada hannun mara gaskia mai niyar cutar wa , kaddarar ta na gaba , na ga wani batacen bakko mai cike da ayar tambaya , tabas kaddara za ta hadasu , haduwa ta har abada " ta na gama fadar hakan ta juya ta yi tafiyar ta , ni duk cikin abun da ta fada kashin arziki kawai na rike , har da ma Youssef , ashe cikin zuciyar shi dakwai abun da ya shirya , sannu sannu lokaci na tafiya har ya kai Inaya ta kai shekara 7 , kassuwanci na sai habaka ya ke yi , yayin da Youssef ya shiga harkar siyassa ta mugayan mutane masu anfani da tsafi wajen ganin sun yi nassara , har ya kai matsayin minister cikin gida , bayan Inaya ta ci ka shekara 8 wani mumunan abu ya faru da ni , shago na ya kone kurumus babu abun da ya yi saura , wasu sun ce barayi ne , wasu kuma su ce ba mu kashe injin shagon ba , mun tabka babbar assara ni da uban gida na , da ya ke mutumin ya na da kirki sai ya ce Allah ne ya rubuta hakan ya hakura ba komai , ganin bazan iya ci gaba da kula da shagon ba sai na ce mishi ya dauki Abdoul ya dinga taimaka mishi , a lokacin ya na shekara 18 ba musu ya yarda, duk lokacin da Abdoul ya sauko da ga school sai ya tafi shagon wajen aiki , ni kuma na bude wata karamar makarantar islamya inda na ke koyar sa yaran unguwa da kuma nawa yaran , bayan Inaya ta cika shekara 10 Youssef ya tado zancen ya na son ya nemawa yaron shi auren ta a lokacin ta na karama sosai a waje na sai na ki yarda hakan ko ba karamin bata mishi rai ya yi ba , har ya dauki gaba ya bani , wata daya bayan faruwar hakan na je na bashi hakuri dan Allah ya sani da zuciya daya na ke tare da shi tun farko , ba musu ya yarda shi ma ya bani hakuri da cewar shi ne mai laifi ba ni ba , mu na zaune a wajen Inaya ta tardo mu da gudu su na wassa ita da Nesrine , ta na ganin Youssef nunfashin ta ya dauke lokaci guda , ta shiga yin kara kamar dai yanzun nan ta na fadin " Abba shi ne , shi ne ya kone maka shagon ka " cike da rudu na shiga rarrashin ta dan ni ban san abun da ta ke fada ba , ashe dalilin da ya sa Youssef ke son ya aurawa yaron shi Inaya , sun je wajen bokan su ne sai ya ke fada mishi abun da ingozomar nan ta taba fada mana , nan bokan ya ke ce mishi wai matata ita ce silar arziki na tsawan shekaru , kuma duk wanda ya auri Inaya duk kofofin arziki za su bude mishi, sannan ya gani cewa ta na da wasu aljanu na gado da ga wajen mahaifin mamar ta , wadanan aljanu ko shi bai san irin su , dole sai ya kawo mishi Inaya in har ya na son ya tantance wane irin aljinu ne gare ta , duk yadda Youssef zai yi don ya ga ya kai Inaya wajen bokan sai da ya yi amma da Inaya ta sauke idanu saman shi ta ke tserewa ta buya , har ya kai abun ya fara bawa Youssef haushi , ya fara yi mana barazana a kan dole sai na aurawa yaron shi Inaya in ba haka ba ya kashe mu ba ki daya , a lokacin na yi matukar girgiza don na san halin shi ba karamin mugu ba ne in har ya yi niya , cike da tsoro na tatara iyali na cikin tsohon dare mu ka bar gidan , mu ka bar kaduna baki daya mu ka taho kano inda ba mu san kowa ba , a ranar da na roke ka, ka auri Inaya , ranar ina zaune na ga issa ya wuce , cike da mamaki na tsayar da shi na ke tambayar shi ya mutanan gida me ya kawo shi kano kuma , nan take kuka ya kubce mishi lokacin da ya ke sanar da ni cewa bayan tafiyar mu Youssef ya tarda shi ya yi mishi barazana a kan ya fada mishi inda muke sai dai shi kuma bai sani ba , har ya sace mishi yarinyar shi babba ya bawa bokan su ita , dalilin haka ya tsere shi ma ya tafi kwayan su , ya ce min a yanzu haka Youssef ya zama vice-president na Nigeria kuma har yanzu ya na neman mu , jin hakan ba karamar girgiza na yi ba har na baro issa nan tsaye na tafi gida dan na ce musu su shirya yanzu ma mu bar Garin , kawai sai na gan ka , lokaci guda wani tunani ya fado min , idan na aura maka Inaya , ba sai na bar garin ba tun da yanzu aure tsakanin ta da yaron Youssef ba zai yi yu ba , ni a lokacin ban duba nakassar ka ba kamai ina neman ceton ran yarinya ta ne " Shiru Zayd ya yi kamar mai tunanin wani abu Yayin da Moussa ya zuba mishi ido ya na kallon shi , ya na son ya karanta yanayin sa Cen kuma sai ya dago kai ya kali malam ya ce " uncle zan iya sannin sunnan yaron da ku ke magana a kan shi " " e sunan shi Sudais " malam ya fada ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 24 ❤🔥 Mikewa tsaye Zayd ya yi ya shiga cikin bedroom din shi ya rufe kofar Ya na shiga Moussa ya mike tsaye shi ma ya ce wa malam " uncle ni zan tafi " Shi ma malam mikewa ya yi ya na fadin " mu je to , ni ma wajen Nesrine din na ke son zuwa " Dan murmushi Moussa ya yi ya na sunkuyar da kai dan malam ya gano shi A tare su ka jera su ka fito part din sannan su ka sauko falon kassa Zayd Tsaye ya ke bakin gadon shi ya zubawa Inaya da ke konce saman bed din shi ido , kamar mai barci Dogon nunfashi ya ja kafin ya karaso bakin gadon ya zauna ya na ci gaba da kallon ta ya rasa dalilin shi na yin haka Ya dauki wajen good 30 minutes a haka kafin ya ga ta fara motsi ta na son tashi Bai motsa ba ya ci gaba da kallon ta , har ta bude idanun ta , ta na kallon ceiling ta kassa motsi A hankali ya matso kussa da ita ya kai hannu saman kumatun ta ya ce " are you okay ? " Kallon shi ta yi cikin ido ta ce " yaya Zayd me ya faru ne ? " " nothing Mimi , ya jikin na ki ? " ya fada ya na taimaka mata ta zauna ta jingina a bayan gadon Dan murmushi tayi kafin ta ce " yaya Zayd ni fa lafya lau na ke " " kin tabbata ? " ya fada ya na daga mata gera guda Murmushi mai dan sauti ta yi har sai da dimple din ta ya lotsa , sannan ta jinjina mishi kai allamun e Geffen ta ya dawo shi ma ya zauna ya jingina a bayan gadon sannan ya kai hannu ya dauki remote ya kunna Tv din gaban su Sannan ya kale ta ya ce " za ki kali cartoon ? " Girgiza mishi kai ta yi kafin ta ce " yaya Zayd ni film na ke son kallo " ta fada cikin shagwaba Jinjina mata kai ya yi , ya kali Tv din ya na neman chanel din da su ka saka film a yanzu Cikin sa'a ko first chanel da ya saka , su na haska wani film na Avengers mai dadi A tare su ka kali film din har sai da ya kamala dai'dai an fara kiran sallat Ta na jin kiran sallat ta diro da ga saman gadon ta na shirin fita dakin Da sauri ya riko hannun ta ya na fadin " where are you going ? " Juyo wa ta yi ta kaleshi cikin shagwaba ta ce " yaya Zayd ba ka jin kiran sallat ne, zan je bedroom di na na yi sallat " Ba tare da ya saki hannun ta ba ya ce " ba za ki yi ta ba a nan " Noke mishi kafada ta yi ta na shagwabe fuska ta ce " yaya Zayd ai nan dakin ka ne " Da sauri ya katse ta da cewa " bedroom din mu ne , ni da ke , in bai miki ba na sauya ? " " to yaya Zayd dakin da na ke ciki kuma fa ? " " zan sa a medo kayan ki nan , in kuma wannan part bai miki ba sai a sauya shi " " yaya Zayd na ga duka dakunan gidan akwai mutane a ciki " Mikewa tsaye ya yi ya tsaya gaban ba tare da ya saki hannun ta ba ya ce " akwai wasu part bayan wadanan , amma na sirri ne , yanzu shiga toilet ki yi Alwalla ki yi sallat ina zuwa " ya kai karshen ya na sakin hannun ta Da to ta amsa mishi kafin ta fara takawa a hankali ta shiga toilet Da kallo ya rakata har sai da ta shiga sannan ya juya ya ficewar shi After some minutes ta fito da ga cikin toilet din Abun mamaki ta na fitowa ta ga duk trolley din ta jere bakin gadon Murmushi ta saki kafin ta tako ta karaso gaban trolley din ta bude guda , ta cire karamin hijabin ta ta saka a cikin ta dauki wani dogo har kassa ta saka , sannan ta nufi dan carpet din gaban gadon ta gabatar da sallar ta dan ba ta ga dadduma ba Ta na tsaka da sallar ta ya shigo dakin ya na sallama kassa kassa kamar ba ya son bude baki Ya na shigowa idanun shi su ka sauka saman trolley din ta Bai tsaya bata lokaci ba ya dauke su ya shiga dressing room ya shiga gyara mata kayan ta cikin closet Sai da ya Kamala sannan ya fito dressing room din , har yanzu ta na nan zaune ta daga hannayan ta sama ta na karanto aduo'i Bakin gadon ya zauna ya zuba mata idanu ya na kallon , gwanin burgewa ( na so Moussa na wajen ya yi musu pic ko da biyu ne 😭😭😭 ) Sai da su ka dauki wajen good ten minutes a haka kafin ta shafa adu'ar ta , sannan ta tasso ta tsaya gaban shi , ta shiga karanto mishi aduo'i cikin ranta sannan ta tofa mishi Dan lumshe idanun shi kadan ya yi , abun da ta yi ba karamin dadi ya yi mishi ba , har cikin zuciyar shi ya ji dadin adu'ar ta duk da bai san adu'ar micece ta karanto mishi ba , amma ya na da tambacin al'heri ne Ya na a haka ya tsinci wannan zazzakar Muryar ta, ta na fadin " yaya Zayd yunwa na ke ji " Slowly ya bude idanun shi ya na kallon ta , ta na tsaye gaban shi ta shagwabe fuska , ta rike hannayan ta a baya , sai hura kumatu ta ke Mikewa tsaye ya yi ya mika mata hannu , dan murmushi mai sauti ta yi kafin ta daura hannun ta saman nashi Ta na daurawa ya fara takawa ta yi gaba ya na rike da hannun ta , su ka bar part din baki daya Bari dai mu dan leko Nesrine nassan kafin nan sun Kamala cin abincin su Nesrine Zaune ta ke tsakiyar gado na cikin bedroom din Inaya ta ke da farko Ta daga kai sama , ta lumshe idanu sai ruwan hawaye ta ke yi , amma kukan ya ki fitowa Ta na zaune a haka ta jiyo a na sallama , sa sauri ta dube idanun ta , ta saka hannayan ta biyu ta na goge hawayen ta Ta shiga amsa sallamar ba tare da ta kali kofar ba A hankali ya tako ya iso cikin dakin ya na kallon face din ta Sai da ya kawo bakin gadon sannan ya tsaya ya ce " Nesi lafya ki ke kuka haka ? " Da sauri ta juyo da kan ta , ta na kallon shi jin ya kira ta da Nesi , Dan karamin murmushi ya yi mata ya na daga mata gera guda allamun lafya Da sauri ta kauda kai gefe ta rumtse idanun ta , nan take wasu hawayen su ka sake zubo mata Da sauri ya ce " don Allah ki yi hakuri ki daina kukan nan Nesi " Ba tare da ta bude idanun ta ba ta ce " don Allah yaya Moussa ka daina kira na da wannan sunnan " ta fada da dan karfi dan wannan sunnan da shi ne Hafiz ke kiran ta Bakin gadon ya hau ya na fadin " please sister ki daina kukan nan to , wlh ba na jin dadin ganin ki haka " Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan ta bude idanun ta sai cikin nashi su ka yi ido hudu Da sauri ta sunkuyar da kai ta ce " ina wuni yaya Moussa " Murmushi yayi kafin ya ce " da ga baya kenan , yanzu dai fada min ya jikin ki , ki na da bukatar wani abu ? " Dan murmushi kafin hali ta yi ta na girgiza mishi kai allamun ba komai Gyara zaman shi ya yi saman gadon sannan ya ce " shikenan to , tun da ba ki bukatar wani abu na zo muyi hira " Yanzu ma murmushi ta yi dan har ga Allah ta ji dadin hakan dama ta fara gajiya da zama ita kadai " hira kuma yaya Moussa ? " ta fada kassa kassa Gyada mata kai ya yi allamun e Dan karamin murmushi ta yi , ta lumshe idanun ta wasu hawaye su ka sake zubo mata Da sauri Moussa ya kai hannun shi zai goge mata hawayen , sai dai bai kai ga taba ta ba ya janye hannun shi da sauri dan ya San idan ya taba ta yanzu za ta iya birkice mishi Cikin sanyi murya ya ce " to shikenan in ba ki so sai in tafiya ta " Slowly ta bude idanun ta , ta na kallon shi ta ce " why lokaci guda ka sauya bayan lokacin da mu ke gida ko magana ba ta shiga tsakanin mu , akasi ma ko ka yi min magana sai dai na yi maka kallon wulakanci " ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 25 ❤🔥 Dan karamin murmushi ya yi kafin ya gyara zaman shi ya koma geffen ta , ya jingina a bayan gadon shi ma Sannan ya ce " kin ga ko ni fa ba mutun ne ba mai rike abu a zuciya , kin san fa ni tsiwar ta ki burge ni ta ke , shi ya sa na zo nan dan ki yi min dan tsiwar nan ta ki , kwana biyu na yi kewar ta " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda Dan murmushi mai sauti ta yi kafin ta ce " i'm sorry , duk wani abu da na yi maka ka yi hakuri ka yahe min " Da sauri ya katse ta da cewa " kin ga sister, ki daina ba ni hakuri ni fa ba ki yi min komai ba , don Allah ki bar tuno min baya , ni fa hira na zo muyi " Sunkuyar da kai ta yi ta na fadin " hirar mi kuma za ka yi ni , da dai ka tafi ka kira budurwar ka , ku yi hirar ku ba de da ni ba " " why ? Ko hira da ni ne ba ki so.? " Dago kai ta yi ta kaleshi ta na girgiza kai kafin ta ce " ba haka ba ne yaya Moussa k....." Da sauri ya katse ta da cewa " to minene ? " Sunkuyar da kai ta yi kassa kassa ta ce " ga ni kawai na yi ban dace da hakan ba " Dan matsowa ya yi kusa da ita , ya kali gaban shi ya ce " ni a waje na kin ma wuce hakan , na san saboda abun wacen saurayin ne ya yi miki ki ke fadin hakan , amma ina so ki san ba laifin ki ba ne , please kar ki rike wannan abun a ranki everything will be okay in sha Allah " Ya na gama fadar hakan ya ji kuka ya kubce mata , cikin kukan ta ce " a'a yaya Moussa , yanzu ya ka ke so na yi , yanzu wane namiji ne zai yarda ya aure ni bayan na rasa abun da ya fi komai daraja a rayuwa ta " Kallon ta ya ke yi babu ko kiftawa , sai kuka ta ke yi har da hadiyar zuciya Da sauri ya rungume ta ya na dan bubuga bayan ta ya ce " ya isa haka don Allah ki daina kukan nan , na fada miki ki daina ganin laifin ki , na yi miki alkawari wanda zai aure ki , tsakanin shi da Allah zai aure ki babu ruwan shi da abun da ya faru da ke , ki yarda da ni tsakanin shi da Allah zai so ki " Ajiyar zuciya ta sauke ta na rage sautin kukan ta Ba tare da ta dago kai ba ta ce " babu shi yaya Moussa , na san ka na fada min haka ne kawai dan na yi shiru , amma ni na san ba zan taba samun wanda zai so ni tsakanin shi da Allah ba " Hannayan shi ya kai saman kafadun ta , ya dago ta ya na kallon face din ta ya ce " ki daina cewa haka mana , ba ga ni ba " Tsit ta tsaya da kukan nata ta dago kai ta na kallon shi cikin ido , duk sai ta nemi kukan ta ta rasa kawai sai kallon shi ta ke yi cikin ido Ganin ta yi shiru ya sa shi sakin dan karamin murmushi ya na daga mata gera guda ya ce " to na mine ki na yi min irin wannan kallo kuma , ko na fadi ba dai'dai ba ? " Girgiza mishi kai kawai ta yi ba tare da ta janye idanun ta da ga cikin nashi ba " okay , yanzu tashi ki je lokacin sallat ya yi " ya kai karshen ya na janye hannayan shi da ga saman kafadun ta Sannan ya juya ya na kokarin sauka da ga saman gadon Ya koma bakin gadon ya yi tsaye ya na kallon ta fuska dauke da murmushi Ita dai ta tsaya ta na kallon shi ta rasa dalili Daga mata gera guda ya yi ya na fadin " ko sai na taimaka miki ? " Da sauri ta girgiza mishi kai ta sauko da ga saman gadon , a hankali ta fara takawa ta na jan kafa ta na rumtse idanun ta dan fa har yanzu zafi wajen ke yi mata Da kallo ya rakata har sai da ta shiga toilet sannan ya saki wani cool murmushi ya sa kafa shi ma ya bar dakin Bayan sallar isha Zayd Zaune ya ke cikin harabar gidan saman wasu chair irin na shan iska , ya daga kan shi sama ya na kallon stars Ya na zaune a hakan Moussa ya karaso wajen ya na yi mishi sannan sannan ya zauna saman daya chair din da ke fuskantar ta Zayd Cen kassan makoshi Zayd ya amsa mishi sallamar shi ba tare da ya sauko da kai ba Hannu Moussa ya kai ya bugi cinyar Zayd ya na fadin " kai dan Allah malam sauko da kan ka , kar ya yi maka ciwo " Ko sauraron shi ma Zayd ba ya yi ga Dukan allamu ya yi nisa cikin tunanin shi Murmushi Moussa ya yi ya na fadin " tunanin mi ka ke yi haka ne Amir ? " Sai da ya dauki dan lokaci kafin ya ce " Diya , ina ji a jiki na wani mumunan abu na shirin faruwa da ni " Da sauri Moussa ya katse shi da cewa " kontar da hankalin ka ba abun da zai faru da kai da yardar Allah " Lumshe idanun shi Zayd ya yi kafin ya ce " zan iya yi maka wata magana , please be serious " Gyara zaman shi Moussa ya yi kafin ya ce " ina jin ka mai martaba " ya fada dan yau ya ga allamun na mulkin ke sama Jinkirtawa Zayd ya yi kafin ya ce " ka na ganin zan iya komawa gida da wannan yarinyar " " me zai hana ran ka ya dade , na ga ai matar ka ce ta sunna dole ne ka tafi da ita , ta ga ahalin ka , su ma su ga sirikar su " " but ba na tunanin uncle zai yarda , it's not sure idan na je za su yarda su karbe ta a matsayin gimbiya , she is so small " " ran ka shi dade idan har kai ka karbe ta a matsayin matar ka , dole za su karbe ta " Dan tsaki Zayd ya yi ya na bude idanun shi ya sauko da kan shi ya na kallon Moussa ya ce " please Diya , ni fa yanzu friend di na , na ke bukata , kai daina cewa ranka shi dade , i don't like that " Murmushi Moussa ya yi ya na kallon abokin nashi ya ce " Amir na san ba wannan maganar ka ke son yi min ba , ka fi kowa sani , idan har ka koma Daular saudiya da ita ka ce matar ka ce , babu wanda ya isa ya ce a'a har shi Malik , kamar yadda ka ce friend's din ka ka ke bukata , zan yi maka magana a hakan , Nawfel , fada min gaskia ka na son yarinyar nan ko ba ka son ta " Ajiyar zuciya Zayd ya sauke kafin ya sake daga kan shi ya na kallon sama ya ce " i don't know " " you lie , ka sani sarai kawai dai har yanzu zuciyar ka ta ki yarda da hakan ne dan har yanzu kallon yarinya ka ke yi mata " Sauko da kan shi Zayd ya yi ya matse fuska ya ce " Diya ni ka ke cewa karya na ke ? " Da sauri Moussa ya mike tsaye ya nufi hanyar shiga falon gidan ya na fadin " e na fada karya ka ke " Da gudu Zayd ya mike ya bi bayan shi da gudu su ka shiga cikin falon gidan A cikin falon kuma Malam, mama da Abdoul su na zaune su na hira su ka ga Moussa ya shigo da gudu kamar an koro shi Da sauri malam ya ce " Moussa lafya ka ke wannan gudun " Bai kai ga rufe bakin shi ba ya ga Zayd shi ma ya shigo da gudu ya bi bayan Moussa su ka Haye stair Da kallo malam ya bi su ya na sakin dan karamin murmushi ya ce " Allah dai ya shirya tun da haka ne " Bangaran Zayd kuma , Moussa na Hayewa stair ya nufi part din Zayd Har ya kai bakin kofar ya tsaya ya juyo , ya na kallon Zayd da ya tunkaro shi da gudu Zayd na karasowa wajen ya kai hannu zai damko shi Da sauri Moussa ya gauce gefe , sai ga Inaya tsaye a bayan shi ta sunkuyar da kai ta na gyara hijabin jikin ta Zaro idanu Zayd ya yi ya na kallon ta , ya na kokarin ya dakatar da kan shi amma ina sai da ya fada mata , su ka yi fuuu baya su ka fadi Yar siririyar kara ta saki ta na datse idanun ta da karfi Gumshe dariya Moussa ya yi ya na sa kafa ya bar wajen , dama ya na shirin shiga dakin ya ga Inaya ta fito da ga cikin bedroom kai a sunkuye , kawai sai ya tsaya har ta karaso dan ya yi ma Zayd tarko , kuma ya fada Ya na barin wajen Zayd ya sa hannayan shi biyu ya mike ya mata runfa da kirjin shi ya na kallon face din ta , har yanzu ta na lumshe idanun ta Slowly ya bude baki ya ce " Mimi ba ki ji ciwo ba ? " A hankali ta fara ware idanun ta , sai cikin nashi Shiru ta yi ta na kallon shi cikin ido babu ko kiftawa ta kassa cewa komai Daga mata gera guda ya yi ya na fadin " me ki ke kallo ? " Da sauri ta dawo cikin hayacin ta , ta kauda kai gefe ta ce " ba komai yaya Zayd " " shikenan to , ai yanzu sai ki tashi ko " ya fada da allamun ya manta shi ne ya hana ta tashi A hankali ta juyo da kan ta, ta na kallon shi , kassa kassa ta ce " yaya Zayd tashi to " Daga mata gera guda ya yi ya na fadin " in tafi ina ? " Dan murmushi ta yi mai sauti kafin ta ce " yaya Zayd ka tashi da ga sama na na fara gajiya da koncin nan " A hankali ya dan lumshe idanun shi , sannan ya koma geffen ta ya zauna Ya na sauka da ga saman ta , ta tashi ta mike tsaye ta juya ta koma cikin part din Da kallo ya rakata har sai da ya ga ta zauna saman sofa sannan ya tashi , ya na taku a hankali ya shiga falon ya na sallama kassa kassa Kamar ta san ya yi sallamar a fili ta amsa mishi ta na kallon Tv Geffen ta ya karaso ya zauna ya na kallon Tv din shi ma A hankali ta juyo ta kaleshi cikin sanyi murya ta ce " yaya Zayd , yaushe zan koma school , na gaji da zama a gida " Ba tare da ya kale ta ba ya ce " okay gobe ki shirya , sai mu je ki ga college din da na zaba miki " Cike da murna ta washe baki ta na murmushi ta ce " da gaske gaske yaya Zayd ? " Jinjina mata kai kawai ya yi , bai kai ga bude bakin shi ba ya ji ta fado mishi a jiki ta rungume shi ta na fadin " nagode yaya Zayd " Tsit ya dauke na wucen gadi , dan bai shirya wa hakan ba da ga gare ta Ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe idanun shi slowly ya bude , ya kai hannu shi saman bayan a hankali ya dan bubuga cen kassan makoshi kamar mai rada ya ce " okay Ya isa haka " ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 26 ❤🔥 A hankali ta dago da ga jikin shi ta na kallon face din shi , Da sauri ya kauda kai gefe dan ba ya son ya kali face din ta Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta mike da ga jikin shi ta koma gefe ta zauna ta na kallon Tv Washe gari Misalin karfe 8 na safe Tsaye Inaya ta ke cikin falo, ta na sanye cikin wata gown mai bala'in kyau navy blue da na da wani madauri a tsakiya Ta saka wani dan karamin hijab zuwa kirji sky blue ta yi kyau over Sai kai kawo ta ke yi kamar mai jiran wani abu Ta na tsaye a haka , zayd ya fara saukowa da ga stair Ya na sanye da jeans Baki da t-shirt navy blue shi ma Ta na ganin shi ta tsuke fuska , tun bai karaso wajen ba ta ce " yaya Zayd tun dazu fa na ke jiran ka " ta kai karshen cikin shagwaba Dai'dai ta da ya karaso gaban ta ya tsaya ya na kare mata kallo da ga sama har kassa cikin zuciyar shi ya na kara yaba kyaun da ta yi cikin wannan rigar ( WAI NI KADAI CE NA LURA DA TSADADUN KAYAN DA INAYA KE SAKAWA TUN SU NA KANO , GA SHI BA TA TABA FITA TA SAYO KAYAN BA KO DAI ALJANAI KE KAWO MATA SU 🤔🤔🤔 ) Gaba ya yi ya na fadin " waya ta na manta , mu tafi yanzu " Murmushi ta yi ta na bin bayan shi su ka fice falon Su na barin wajen Nesrine ta fara tako stair a hankali za ta saukowa Har ta kai tsakiyar stair ta tsaya ta na meda nunfashi dan har yanzu ciwo ta ke ji in ta taka Ta na tsaye a haka Moussa da Abdoul su ka fito da ga cikin bedroom din Moussa dan shi ma Abdoul yau Zayd ya bawa Moussa kudi a kan su je su ga university da ya yi wa Abdoul a biya mishi ya ci gaba da karatun shi " Nesrine me ki ke yi a nan kuma ? " ta jiyo Muryar Abdoul ya na fada A hankali ta juyo ta na kallon shi ta saki dan karamin mais ta ce " Ina kwana " A tare shi da Moussa su ka amsa mata da lafya kafin Abdoul ya sake maimaita tambayar da ya yi mata Dan murmushi tayi kafin ta ce " yaya Abdoul dama zan je falo ne na gaji da zama ni kadai cikin daki " Abdoul na shirin magana Moussa ya riga shi cewa " da sai ki kira ni na zo na taya ki hira ko , tsaya ma , me ya tseda ki saman stair " Dan sunkuyar da kai ta yi ba tare da ta ce komai ba Da ya ke Abdoul bai San abun da ke damun Nesrine ba sai ya yi gaba ya na fadin " shikenan sauko yanzu ko " Wasu yawu ta hadiye kafin ta juya ta daga kafa a hankali ta tako stair din ta na rumtse idanun ta da karfi Ba shiri ta ji an dauke ta cak kamar baby har sai da ta dan razana Shi kuma ya na daukar ta ya sauko stair din da ita , sai kallon shi ta ke yi , shi kuma ya na kallon gaban shi Sai da ya nufi doguwar sofa ya zaunar da ita sama sannan ya kali face din ta ya saki dan karamin murmushi ya ce " ki daina wahalar da kan ki in ki na bukatar wani abu ki kira ni kawai " Ya na gama fadar haka ya mike ya yi gaba ya fice falon Duk abin da ya yi a kan idon Abdoul , dan dama bai fita ba , ya shiga dining room ne ya sha ruwa , ya na fitowa ya ga Moussa dauke da Nesrine ya ajiye ta saman sofa Da sauri Abdoul ya bi bayan Moussa shi ma ya fice su ka bar Nesrine nan zaune ita kadai Abdoul kuma ya na fitowa ya ga Moussa cikin mota bakin kofar shigowa falon , ya na jiran shi Geffen mai zaman banza ya nufa , ya bude kofar ya shiga, sannan Moussa ya tada motar su ka bar gidan cikin konciyar hankali Su na fita gidan Abdoul ya kali Moussa ya ce " na lura kwana biyun nan ka na yawwan zama tare da Nesrine , ko kai ma ka fada in sa malam ya baka ita " ya fada cikin zolaya Dan karamin murmushi Moussa ya yi ba tare da ya kale shi ba ya ce " kar ka bawa kan ka aiki , already dama ta wa ce " " ni fa da gaske na ke yi maka " Kallon shi Moussa ya yi kafin ya ce " ni ma da gaske na ke maka ai , ko malam bai fada maka ba ya aura min ita ? " Dan zaro idanu Abdoul ya yi ya na kallon Moussa ya ce " wait ! Are you serious ? Abba ya aura maka ita ba tare da sanin mu ba , ita ta sani ma ? " " ba ta sani ba , ban shirya fada mata ba yanzu gaskia , na fi son har ta manta abun da ya faru, duk da na san zai dauki lokaci " Cike da shakku Abdoul ya ce " ban gane ba , wane abu kuma ka ke magana a kai ? " Kallon shi Moussa ya yi kafin ya juya ya ci gaba da kallon titi ya ce " ban gane ba Amir bai fada muku Raping din ta a ka yi ba ? " Dum Abdoul ya ji zuciyar shi ta buga , har sai da ya fara ganin wani dishi dishi Ya na dafe saitin zuciyar shi , ji ya ke kamar an aiko mishi sakon mutuwa Dafa kafadar shi Moussa ya yi ya na fadin " Abdoul lafyar ka kuwa " Shiru Abdoul ya yi ya kassa cewa wani abu sai zaro idanu ya ke ya na kallon gaban shi Daga kafadun shi Moussa ya yi kafin ya janye hannun shi ya meda saman steering ya ci gaba da tukin shi Inaya Tafiya su ke cikin motar su, babu mai ce ma dan uwan shi uppan , har sai da su ka karaso wani babban private college Ya na shigowa ya nufi parking space ya yi parking din motar , sannan ya kashe ta ya kali Inaya ya ce " mimi , ki jira ni a nan ba zan dauki lokaci ba " Da to amsa mishi ta na murmushi , shi kuma ya bude kofar ya fice ya nufi hall din school din Da kallo ta raka shi har sai da ya kure wa ganin ta sannan ta juyo ta fara bin wajen da kallo Sai ganin yan mata da samari ta ke su na wucewa su Matan su na sanye da skert pink colour ya wuce guyiwa da kadan , da Shirt fara mai dogayen hannu , sai da karamin hijab zuwa kirji shi ma white colour Mazan kuma , wando navy blue da Shirt white , su na sanye da tie navy blue ita ma Tsarin school din ya yi matukar burge ta , kawai sai ta ci gaba da kallon su , car Zayd ya dawo ya shigo motar ba ta sani ba Kawai sai ji ta yi ya tada motar A razane ta kai duban ta gare shi ta na fadin " yaya Zayd wlh ka bani tsoro " A hankali ya juya motar su ka bar parking space din , su ka kama hanyar fita school din sannan ya ce " tunanin mi ki ke yi da har ba ki ji shigowa ta ba ? " Dan karamin murmushi ta yi cikin shagwaba ta ce " yaya Zayd, wlh school din nan ya na da kyau sosai " Da sauri ya katse ta da cewa " ya yi miki kenan " Gyada mishi kai kawai ta yi, ta na cije lips din ta na kassa Ba tare da ya kale ta ba ya ce " shikenan , next week za ki fara zuwa kema " Washe baki ta yi, ta na murmushi , ta ma rasa abun da za ta ce mishi, kawai sai ta yi shiru ta , ta medo da kallon ta saman hanya Sun dauki wajen good ten minutes su na tafiya kafin su karaso unguwar su , Su na yin kwanar da za ta kai su gidan su , wata dankareriar mota baka kirin ta sha musu gaba har sai da Zayd da Inaya su ka buge kawunan su a jikin motar Da sauri Zayd ya dago ya daura hannun shi saman shoulder din ta ya na fadin " ba ki ji ciwo ba " Girgiza kai ta yi, ta na kai hannu ta dafe wajen da ta bugu Su na a haka wani katon basamude baki kirin ya fito da ga cikin motar, fuskar shi a daure tamau kamar kashi Duk da Zayd na da murdadan jiki wannan ya ce mishi ba ka san komai ba , kallon shi kadai ya isa hantar ragon namiji ta kada Takowa ya ke cike da kwarjini ya karaso geffen Inaya ya ja murfin kofar da karfi har sai da ta bale Hannu ya kai ya damko hannun Inaya , kafin ta yi wani yunkuri ya duka ya saba ta a kafada ya juya ya nufi motar shi Sai kara Inaya ta ke ta na kai mishi bugu a baya ta na ka sauke ni ka sauke ni , amma ina ko jin ta ba ya yi Da sauri Zayd ya fito da ga cikin motar ya nufi wannan katon ya na fadin " ina za ka je da ita maza sauke ta " Ko kallon shi katon nan bai yi ba ya ci gaba da takawar shi Da sauri Zayd ya sha gaban shi ya matse fuska , ya sa hannu ya cire bakaken glass din shi ya ce " sauke ta na ce " Hannu katon nan ya daga zai kai mishi bugu Cak Zayd ya riko hannun na shi ya na kallon shi cikin ido babu ko kiftawa ya daka mishi tsawa ya na fadin " ka sauke ta na ce " Bai kai ga rufe bakin shi ba ya ji saukar wani mugun bugu a bayan keyar shi , ban take wajen ya fashe ya fara kawo jini Baiwar Allah Inaya ba ta ma san abun da a le ba dan tun ta gaba karar ta da ta yi ta sume a kafadar wannan katon Slowly Zayd ya fara sakin hannun katon nan ya zube saman guyiwowin shi , Sai ga wani katon shi ma tsaye a bayan shi ya na rike da wata bat irin ta baseball Ya na ganin Zayd ya zube saman guyiwowin shi, ya kara kai mishi wani bugun a kai , har sai da ya furzo da jini ya fadi kassa a wajen kamar gawa Ya na ganin ya fadi ya kali katon da ke dauke da Inaya , cikin wata irin murya mara dadin ji ya ce " mu tafi " Ba musu ya daga kafa ya tsalake Zayd ya bude gidan baya ya kontar Inaya sannan ya zagayo ya shiga geffen driver ya tada motar su ka bar wajen da mugun gudu , kun san dama irin unguwan nin nan na ma su kudi , ba bu kowa a saman hanyar sai Zayd da ke konce a kassa ya na zubar da jini kamar gawa ( TO JAMA'A SU WA NE SU KA DAUKE INAYA ? KAR A JE ZAYD MUTUWA YA YI 😭😭😭😭 ) ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 27 ❤🔥 Ya kai wajen good ten minutes a wajen ba ya ko motsi , ya na a haka motar Moussa ta shayo kwana Wani irin wawan burki ne Mahaman Moussa ya yi , lokacin da idanun shi su ke me arba da Zayd konce, har sai da Abdoul ya kale shi ya na tambayar shi lafya ya danna birki haka Bai tsaya amsa mishi tambayar shi ba ya bude kofa ya sauka da wani irin gudu ya nufi ya na kwalla mishi kira Da sauri Abdoul ya bude kofar shi ya sauko shi ma ya nufi Zayd da gudu Ya na karasowa wajen Moussa ya zube saman guyiwowin shi ya talabo fuskar Zayd ya na fadin " Amir ! Ka bude idon ka Amir ! " Sai jijiga shi ya ke amma ina ko motsi Zayd ba ya yi , karewar zancen zuciyar shi ba ki daya ta daina bugawa amma Moussa bai lura da hakan ba duk ya bi ya rude Dafa kafadar shi Abdoul ya yi ya na fadin " mu kai shi asibiti da sauri tun......." Bai karasa maganar shi ba ya ga Moussa ya mike ya dauki Zayd ya saba a kafada ya koma wajen motar shi da gudu , ya bude gidan baya ya kontar da Zayd sannan ya shiga mazaunin driver ya tada motar ya bar wajen da gudu ko jiran Abdoul bai yi ba Shi kuma Abdoul bai kawo komai a ran shi ba sai ma motar Zayd da ya shiga , ya tada ya bi bayan Moussa da gudu shi ma Cikin kankanen lokaci su ka iso wani tanpasheshen private Hospital Da gudu Moussa ya nufi parking space ya yi parking Da ya ke yanayin Hospital din na kwararu ne , su na ganin gudun da ya shigo cikin Hospital din da shi wasu nurse su ka fito da gadon da a ke kontar da majinya ta su ka nufi motar Moussa Su na isowa ko ya sauko da ga gidan driver ya bude baya ya sauko da Zayd ya kontar da shi saman gadon sannan su ka tura su ka yi cikin Hospital din tare da nurse ko kofofin motar shi bai like ba Su na barin parking space Abdoul ya shigo da gudu da motar Zayd ya yi parking shi ma ya fito da gudu ya shiga Hospital din Ya na shiga ya ga Moussa tsaye bakin A&E Room ya na kai kawo Da sauri Abdoul ya karaso wajen ya na fadin " Moussa ya ? Ina Zayd ya ke " Wani dogon nunfashi Moussa ya ja kafin ya nufi chair din bakin kofar dakin ya zauna ya dafe kan shi da hanayan shi biyu ya ce " Abdoul , wlh in wani abu ya samu Amir Malik ba zai kyale ni ba , na shiga uku ni Diya " Chair din geffen shi Abdoul ya zauna ya kai hannu ya dafa kafadar shi , ya na fadin " calm down, ba abun da zai same shi in sha Allah ka kontar da hankalin " Ya na gama fadar haka wayar shi ta fara ringing Janye hannun shi ya yi da ga saman kafadar Moussa kafin ya kai hannun shi cikin Aljihu ya ciro wayar ya na kallon screen din * my mama * shi ne abun da ya bayana Mikewa tsaye ya yi ya juya wa Moussa baya kafin ya dauki kiran ya kai waya a kunne ya na sallama A daya bangaran kuma , Nesrine ce rike da wayar cikin kuka ta ce " yaya Abdoul wasu mutane sun zo sun dauke Abba har su ka jiwa mama rauni yanzu haka ga ta nan konce ta suma " ta kai karshen ta na sakin kuka Abun da ba ta sani ba tun lokacin da ta ce an dauke Abba ya saki wayar ta fadi kassa ya fice Hospital din da gudu Moussa ya na kallon shi amma bai tsaya tambayar shi lafya, shi da kan shi cikin mugun hali ya ke a yanzu Bangaran Abdoul kuma ya na fitowa ya nufi parking space da gudu ya shiga motar Zayd dama key din na hannun shi , ya tada motar ya fice Hospital din a 360 kamar zai tashi sama Cikin abun da bai fi five ba ya iso gidan , tun kafin ya iso bakin kofar ya ke danna uban horn Da gudu gateman ya taso ya bude mishi kofar gidan Da gudu ya danna hancin motar cikin gidan , ko parking space bai nufa ba, ya tseda motar ya sauko ko kashe ta bai yi ba ya nufi falon da gudu Babu ko sallama ya fado cikin falon Sai da zuciyar shi ta buga Falon duk a birkice ya ke kamar an yi dambe a cikin , ga mama nan konce tsakiyar falon , Nesrine na zaune geffen ta sai kuka ta ke Da gudu ya nufi Nesrine ya Zube saman guyiwowin shi geffen mama ya na fadin " Nesrine wai me ya faru ne haka " Cikin kukan ta ce " yaya Abdoul wasu mutane ne su ka zo su tafi da Abba , da ya kiya shi ne su ka dake shi su ka tafi da shi da karfi , mama ta yi kokarin tseda su , guda cikin su ya tura ta , ta bugu da bango da ga nan ta fadi ta suma " " kin gane ko su wanene " ya tambayeta cikin rudu " yaya Abdoul, wlh ban san su ba , kuma duka sun rufe fuskokin su " " shikenan kukan ya isa haka dauko min gorar ruwa guda " Bai kai ga rufe bakin shi ba ta tashi da gudu ta nufi dining room , ta shiga kitchen Jim kadan ta fito rike da gorar ruwa mai sanyi Da sauri ya karba ya bude ya zubo kadan a hannun shi ya shafawa mama a fuska Dogon nunfashi ta ja ta na sauke ajiyar zuciya kafin ta bude idanun ta a hankali ta na kallon ceiling Ajiyar zuciya Abdoul ya sauke, Nesrine kuma ta fada mata a jiki ta rungume ta " Nesrine ina Abban ku " mama ta jefo mata tambaya Mikewa da ga jikin ta Nesrine ta yi sannan ta taimaka ma ta , ta mike zaune " mama kontar da hankalin ki duk ina Abba ya ke zan kawo miki shi " Abdoul ya ba ta amsa Ajiyar zuciya ta sauke ta shiga karanto aduo'in tsari cikin zuciyar ta , dan mama irin matanan nan ne ma su ta'amali da Allah, ta san ko kukan ta tsaya yi ba abun da zai anfana gwara ta dinga yi mishi adu'a Ta na a haka ta ga Abdoul ya mike ya na shirin barin wajen Da sauri ta tseda shi da cewa " Abdoul ina kuma za ka je " " mama wlh Zayd ne ya yi accident , yanzu haka ya na cen Hospital " Kalmar shahada mama da Nesrine su ka yi a tare su na mikewa tsaye Cikin murya kamar ta mai kuka mama ta ce " ya Allah me ya ke shirin faruwa da mu ne haka " Da sauri Abdoul ya katse ta da cewa " in sha Allah mama ba abun da zai faru ki kontar da hankalin, bari na koma likita ni " " a'a tare za mu tafi " mama ta fada ta na yin gaba Da sauri Nesrine ita ma ta bi bayan ta su ka fice falon Girgiza kan shi kawai Abdoul ya yi kafin ya bi bayan su , Motar Zayd su ka shiga su ka bar gidan a tare Wannan karan bai yi gudu ba sosai dan ya san mama ba ta son gudu a mota Sun kai wajen good 10 minutes kafin su iso Hospital din, Abdoul ya yi parking su ka fito su ka shigo cikin Tun da su ka shigo su ka hango Moussa ya na nan zaune ya dafe kai da hannayan shi biyu Ya na jin sallamar Abdoul ya dago kai a hankali ya kale shi Bai amsa mishi sallamar shi ba ya ce " Abdoul lafya na ga ka tafi da gudu " " wasu mutane ne su ka je gida su ka dauke Abba , yanzu haka Police station zan je na kai kara, su ma dan kar wani abu ya same su ne na taho da su nan " Abdoul ya fada mishi Ya na shirin magana ya jiyo Muryar Nesrine ta na fadin " yaya Moussa ina Inaya " Dum ya ji zuciyar shi ta buga a dubu dari ya mike tsaye ya na zaro idanu shi da Abdoul, su sai yanzu su ka lura babu Inaya a wajen da su ka dauko Zayd Ganin ya yi shiru sai muzurai ya ke da idanu ya sa mama cewa " Moussa ina Inaya ta ke ne , ko ita ma ta ji ciwo ? " Cike da rudu Moussa ke kallon Abdoul ya ce " Abdoul ni fa ban ga Inaya a wajen da mu ka dauko Zayd, ko dai ta na cikin motar shi " Girgiza mishi kai Abdoul ya yi kafin ya ce " ni da kai na Zayd ne kawai na gani a wajen , sam tunani na bai kawo Inaya ba ta wajen " " kai dan Allah ku min bayani yanda zan gane, ina Inaya ta ke " mama ta fada ta na daga murya kadan A tare Moussa da Abdoul su ka kale ta su ka ce " mama, an sace Inaya " Sannan Moussa ya daura da cewa " tabass sace ta a ka yi , nassan wajen ceton ta ne Zayd ya ji ciwo " Bai gama rufe bakin shi ba, Nesrine ta saki wata irin razananiyar kara ta na kiran sunan Inaya , mama kuma sumar tsaye ta yi dama abun da malam ke gudu kenan yau ya tabata Da sauri Moussa ya nufi Nesrine ya rungume ta dan ya lura ta na neman ta fita cikin hayacin ta , haka ya shiga rarrashin ta har sai da doctor ya fito Da sauri Abdoul ya nufe shi ya na tambayar shi ya jikin Zayd " adu'ar ku ya fi bukata a yanzu , mu mun yi na mu aikin " ya na gama fadar haka ya yi gaba zai bar wajen Sakin Nesrine Moussa ya yi ya taro doctor ya ce " doctor ban gane abun da ka ke fada ba " " sorry , ya shiga doguwar suma saboda jinin da ya zubar , ga shi ya samu mumunan bugu a kai , mun yi mishi karin jini da duk wani abu da zai bukata amma ba na tunanin zai iya tashi , da wuya ya wuce yau ko gobe , adu'a kawai za ku yi mishi " ya na kai karshen ya bar wajen Sumar tsaye Moussa ya yi ya shiga girgiza kan shi ya fara juyawa waje guda kamar zarare ya na fadin " na shiga uku , wlh Malik kashe ni zai yi , yanzu shikenan Amir mutuwa zai yi , Kaiii, don Allah in mafarki na ke ku tashe ni " ya kai karshen kamar zai yi kuka Dafa kafadar shi Abdoul ya yi ya na fadin " ka kontar da hankalin Moussa da izinin Allah zai tashi adu'a kawai za mu yi mishi " " kai Abdoul akwai matsala in Amir bai tashi ba , wlh akwai matsala , cire min kai kawai Malik zai sa a yi " Shi dai Abdoul sam bai gane sambatun Moussa ba sai rarrashin shi ya ke , ya na kontar mishi da hankali Mama da Nesrine kuma ba su da bakin magana dan su ma cikin irin halin Moussa su ke , ba malam ba Inaya to su na ina ? Tashin hankali ba a sa maka date Ga Zayd konce tsakanin rai da mutuwa , an sace malam da Inaya a rana guda duka wane tashin hankali da me ya yi kama ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 28 ❤🔥 After some hours Inaya Konce ta ke cikin wani daki baki kirin babu haske ko kadan ciki ko Windows babu A hankali ta fara motsi ta na karanto kalmar shahada , sannan ta ware idanun ta slowly amma ba ta ganin komai Mikewa zaune ta yi ta dan jujuyawa ta na fadin " yaya Zayd ka na ina " Kamar da ga sama ta jiyo Muryar malam ya na fadin " Auta ke ce " Dum ta ji gaban ta ya fadi nan take kuka ya kubce mata ta na fadin " Abba , Abba , ina ka ke Abba " " kontar da hankalin ki Auta , kar ki motsa " ya fada mata ya na tashi ya fara laluban ta cikin wannan uban duhu Cikin sa'a ko ya gano ta da sauri ya Zube saman guyiwowin shi ya na fadin " auta, me ya kawo ki nan " Ta na jin ya tabo ta ta fada jikin shi ta na kara sautin kukan ta ta ce " Abba , ni ma ban sani ba, mu na tafe ne ni da yaya Zayd, wata mota ta tsaya a gaban mu wani katon mutun ya fito ya dauke ni , sai yanzu da na bude ido " Rungume ta tsam malam ya yi ya na fadin " ki kontar da hankalin ki , va abun da zai faru kin ji ko " Kassa amsa mishi ta yi saboda kukan da ta ke , haka ya shiga rarrashin ta har ya samu ta yi shiru su ka yi zugum waje guda kowa da irin abun da ya ke sakawa a cikin zuciyar shi After two days Kwana uku yanzu kennan da kontawar Zayd doguwar suma , a kullum bugun zuciyar shi kara rayuwa ya ke tun likoci na san ran zai tashi har ya kai sun daina , Moussa kuma kamar ya yi hauka don ya san idan Zayd bai tashi ba tabass shi ma sai ya bi shi Adu'a babu dare babu rana ya ke samu da ga wajen mama dan ba abun da ke tada ta da ga saman sallayar ta , kullum ta na cikin yi wa ahalin na ta adu'a Ga shi kuma har yanzu malam da Inaya shiru , sun je police station din amma abun mamaki sai dai a ce musu su je gobe su dawo , sau uku Abdoul ya na zuwa police station kai kara amma kullum su ce mishi ya dawo gobe har ya gaji ya bar zuwa ya mika al'amarin wajen ubangiji , ko da ma su satar mutane ne za su kira su Nesrine ma ba a bar ta a baya ba wajen yi ma yan uwan ta adu'a , dan yanzu ta samu dauki amma ba sosai ba , a yanzu kuma ita ke debe ma Moussa kewa ta na taya shi hira duk lokacin da su ka je kai mishi abinci likita dan har yanzu su na cen shi da Zayd In mu ka leko malam da Inaya kuma , tun ranar a ka sa su cikin wannan dakin , ba a sake waiwayar su ba , abinci ma sau biyu a rana a ke basu, shi ma bai fi ka yi spoon biyu ko uku ba Amma a haka har su na samun damar su mika kukan su ga ubangiji, kullum cikin adu'a su ke ita da malam babu fashi Misalin karfe 10 na safe Yau dai kwana hudu da faruwar wannan abun Inaya Konce ta ke ta tada kai da cinyar malam, ya sa hannu ya na shafa mata kai ya na karatun kur'ani Su na a haka su ka ga an bude kofar dakin Da sauri malam da Inaya su ka datse idanun su dan sun saba da duhun dakin Ba su kai ga bude idanun su ba su ka ji an dauke su an mikar da su tsaye a na fadin " mazza ku fita " Riko hannun Inaya malam ya yi su ka fito wannan dakin A hankali su ka fara ware idanun su , su na bin wajen da kallo Wani katon falo ne , dauke da duk wasu kayan more rayuwa , da ga sofa har zuwa su Tv , amma komai black colour ne dakin duk zagaye ya ke da irin wadanan gardin da ya dauke Inaya sun kai su goma , kowa sanye da bakaken kaya fuskar a daure tamau kamar hadari , sai shan tsami suke Cen su ka hango wani bokan zaune tsakiyar falon ga wata kwariya cike da wasu ruwa jajaye a gaban shi, sai wani karatu ya ke mara dadin ji Su na tsaye su na kallon shi wani ya turo malam ya yi gaba zai fadi Da sauri Inaya ta taro shi ta na fadin Abba Riko hannun ta ya yi ya na fadin ba komai , sannan ya mike su ka karaso cikin falon Cak malam ya tsaya ya na zaro idanu , zuciyar shi na duka uku uku Ba komai ba ne ya gani face Youssef , ya yi wani zaman kasaita saman sofa geffen bokan ya na kallon malam ya na sakin wani makirin murmushi Ya na ganin malam ya tsaya ya bushe da wata shegiyar dariya kafin ya mike tsaye ya karaso gaban malam ya tsaya ya na fadin " ohhhh Ibrahim , yaushe rabo " ya kai karshen ya na rungume malam Shi dai malam ya kassa motsi sai kallon waje guda ya ke ya na faman muzurai da ido Ganin bai motsa ba ya sa Youssef sakin shi ya yi baya kadan ya kali Inaya, Wani cool murmushi ya saki kafin ya ce " my daughter gaskia kin girma ba ki dai manta da uncle din ki ba " ya kai karshen ya na kai hannu zai taba fuskar ta Cak ya ji malam ya damko hannun shi Da sauri ya dago kai ya na kallon malam Cikin dakiya malam ya ce " kar ka kuskura ka taba min yarinya ta " Murmushi Youssef ya yi kafin ya kauce hannun shi ya juya ya koma sofar da ya taso ya zauna ya kali bokan ya ce " Barbushi ga yarinyar da na ke baka labarin ta " Dago kai barbushi ya yi kafin ya ce " tabass ita ce , dan ina jiyo kamshin arzikin ta , amma auren ka da ita ba zai yi yu ba " Mikewa tsaye Youssef ya yi ya na fadin " what kamar ya bazan iya auren ta ba " Barbushi na shirin magana malam ya riga shi cewa " Youssef kenan dama ba Sudais ka yi niyar aura ma ita ba , kai ne za ka auri yarinyar da ka yi jika da ita, saboda me Youssef , kawai saboda abun duniya , wlh ka ji tsoron Allah " Cikin tsawa Youssef ya katse shi da cewa " kai don Allah ya isa haka , lokacin da ka ke ci moriyar kudin ka , ka ji tsoron Allah ne , a tare mu ka fito neman aiki amma duk ka fi mu kama kudi duk da waje guda mu ke aiki , don Allah ya ba ka shi ne za ka yi wa wasu bakin ciki, wlh wlh duk yadda za ayi ko da in kashe ka ne sai na auri Inaya , wannan arzikin da ka ke ci ni ma sai na ci shi " Wasu hawaye ne ma su zafi su ka zubo ma malam ya na fadin " haba Youssef wane arziki kuma , dubi inda Allah ya kai ka duk da ba ta hanyar halal ba , amma wane arziki za ka nema bayan wannan da har za ka cutar da rayuwar yarinya ta , na roke ka ka kyale mu mu tafi " " Ibrahim bazan kyale ku ba , a yau din nan a wajen nan sai na auri Inaya , ai na ga ba kudi ne ba kadai arzikin ta ba ko ? " ya kai karshen ya na sakin wani makirin murmushi " ina lillahi wa'ina illaihi raji'un , haba Youssef da girman ka , yanzu ko kunyar fada min wannan maganar ba ka ji ba , kai con ka wlh , ka yi girman banza , Allah waddaran hali irin na ka Youssef na yi nadamar abotar mu , ta Allah ba ta ka ba wlh ba ka isa ka taba mamana ba , aure kuma ya haram ta tsakanin ku " ya kai karshen cikin kunar rai Duk abun da su ke fada Inaya na geffen malam rike da hannun shi sai in wannan ya yi magana ta kale shi , in wannan ya yi ta dawo da kallon ta gare shi Youssef na shirin magana barbushi ya riga shi cewa " gaskia ya fada ba za ka iya auren ta ba , saboda mijin ta na a raye har yanzu bai mutu ba " Kallon barbushi Youssef ya yi cike da rudu ya ce " kai barbushi ya isa haka, kar ka manta ko ni wanene , a yau din nan sai na aure ta " Dariya malam ya yi ya na fadin " ai auren ku ba zai yi yu ba , domin Inaya dai da ke gani matar wani ce , shekara biyu yanzu da na mata aure " ya kai karshen ya na sake bushewa da dariya Wannan maganar ba karamin konawa Youssef rai ta yi musaman dariyar da ya ga malam na yi abun ya kona mishi rai Cikin fushi ya kai hannu bayan shi ya fido gun ya harbe malam a zuciya Kara Inaya ta saki ta na toshe kunnuwan ta ta rumtse idanun ta da karfi , zuciyar ta na bugu da karfi A hankali ta bude idanun ta ta na kallon kassa , sai ganin malam ta yi konce a kassa ya dafe saitin zuciyar shi , babu rai a jikin shi Wata irin razananiyar kara ta saki ta na zubewa saman guyiwowin ta ta talabo kan malam ta na fadin " Abba , Abba ka tashi don Allah kar ka tafi ka barni na roke ka , wayoooo ni Allah na Abba " ta kai karshen ta na sakin sabuwar kara da ga nan ta sunkuyar da kan ta , ta gama goshin ta da na malam ta na kuka kassa kassa Ta na a haka ta ji Youssef ya riko hannun ta ya na fadin " ke tashi mu tafi " Shiru Inaya ta yi , ta lumshe idanun ta ko motsi ba ta yi Daka mata tsawa Youssef ya yi ya na fadin " ba za ki tashi ba ko dai ke ma na kashe ki " A dubu dari Inaya ta dago kai A razane Youssef ya saki hannun ta ya ja da baya ya na zaro idanu Ba karamar razana ya yi ba ganin yadda idanun Inaya su ka koma bakake kirin ko digon fari babu Bai ida shan mamaki ba sai da ya ga ta mike tsaye, cikin wata irin murya mai sauti ta ce " kai ne ka kashe min Abba na " ta kai karshen ta na takowa gaban shi Da sauri Youssef ya yi baya ya na fadin " barbushi me ya samu idanun ta haka " Mikewa tsaye barbushi ya yi ya na kallon Inaya ya ce " ba ita ba ce , aljanun ta , su ne s....." Bai kai karshen maganar shi sakamakon juyowar sa Inaya ta yi ta wurga mishi wani mugun kallo sai da ya sha jinin jikin shi Nuna shi ta yi da dan yatsar ta , a hankali ta fara yin sama da yatsar Nan take shi ma barbushi ya fara yin sama cikin iska ya na rike da wuyan shi da hanayan shi biyu , ya na reto da kafafun shi kamar wanda a ka shake Sai da ya daina motsi ya koma ga m'halluciné shi , sannan Inaya ta sauko da yatsar ta kassa , barbushi ya Zube a wajen Barbushi na faduwa a wajen waddaran katin gardin da ke zagaye da dakin su ka fara bacewa bat bat daya bayan daya Kenan dama ba mutane ba ne Youssef na ganin abun da ke faruwa ya saki wata irin kara kamar mace ya juya da gudu zai bar wajen Amma ina ya na juyawa ya ga Inaya tsaye a gaban shi , duk ta sauya kamar ba ita ba Zubawa ya yi saman guyiwowin shi ya rike hannayan shi ya na fadin " don Allah ku bar ni na tafi , ina da iyali , don Allah ku kyale ni " Shiru Inaya ta yi ta na kallon shi Sai da ta dan jima kafin ta dago da yatsar ta slowly ta nuna shi , ta fara yin sama da yatsar Kamar yadda ta yi da barbushi, haka shi ma Youssef ya yi tsaye cikin iska ya na reto , hannayan shi duka biyu a wuya an shakke qui Sai da ya bar motsi sam , sannan ta tila shi gefe da karfi ya bugi bango Bayan ta tila shi ta dawo da kallon ta kan malam Nuna shi , shi ma da dan yatsa ta yi , nan take ya fara reto cikin iska a konce Kamar ta san hanyar fita ta juya ta nufe ta, ta na taku kamar namiji , gawar malam na biye da bayan ta cikin iska ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 29 ❤🔥 Fitowa tayi ta ga harabar gidan cike da sojoji , da motoci wajen goma Sojoji na ganin ta su ka shiga tayi tayin su musaman da su ka ga idanun ta baki kirin Da sauri su ka saita ta da gun sa fadin ta tsaya nan Amma ina sai ci gaba da takowa ta ke ta na shirin barin wajen Har za ta bar gidan gonar ta tsaya ta juyo ta nufi wata motar ta bude gidan baya gawar malam ta shiga ciki Ita kuma ta juyo ta kali sojojin da su ka saita ta da gun , hanayan su sai kerma su ke dan tsoro , sun ma rasa ya za su yi da ita , idan su ka ce su harbe ta , in ba ta mutu ba to tabas su za su mutu Nuna guda cikin su ta yi kafin ta ce " zo ka meda ni gida " Da sauri ya saki gun din hannun shi ya nufi motar da gudu ya shiga gidan driver, Inaya kuma ta shiga wajen mai zaman banza Ta na shiga ya tada motar ya bar wajen da gudu Ita kuma ta jingina a bayan kujerar ta lumshe idanun ta ba ta sake cewa wani abu ba Sai da su ka yi tafiyar wajen good one hour kafin su iso cikin gari , nan ta ke ce mishi ya kai ta babban private Hospital Ba musu ya kama hanyar babbar private Hospital , inda a ka kontar da Zayd Cikin abun da bai fi 15 minutes ba su ka iso Hospital din Ta na jin motar ta tsaya, ta bude idanun ta slowly Wannan karan dai idanun ta sun dawo dai'dai A hankali ta bude kofar ta , ta sauko da ga cikin motar ta na ce ma sojan nan ya sauko da gawar mahaifin ta Ita kuma ta nufi hall din Hospital din ta shiga Ta na shiga ta ci karo da Abdoul , ya na sauri zai je gida ya dauko su mama Ya na ganin ta sai da zuciyar shi ta buga , ya na zaro idanu ya ke kallon ta ya ce " Inaya , ke ce ? " ya fada cikin rudu Ita kuma ko tsaya wa sauraron shi ba ta yi ba ta yi gaba abun ta Ya na shirin bin bayan ta ya ga sojan nan dauke da malam a saman kafada Da sauri Abdoul ya nufe shi ya na tambayar lafia , ya na gama fadar haka ya dinga kwala wa nurse kira Da sauri su ka nufo shi ture da gadon jinya Su na isowa sojan nan ya kontar da shi sama sannan ya juya da gudu ya bar wajen dama a kage ya ke ya tsere Ya na kontar da malam , Abdoul ya ga uban jinin da ke zuba da ga kirjin shi , dan zaro idanu ya yi ya na fadin " Abba ! Abba " Bai gama rufe bakin shi ba nurse din nan su ka tura gadon su ka shiga A&E room doctor na biye da bayan su Su na shiga room din Abdoul ya juya da gudu ya bi bayan Inaya da ta nufi dakin da a ka kontar da Zayd , kamar ta san inda ya ke A hankali ta tura kofar ta shigo ta sallama Moussa da ke zaune saman wata sofa cikin dakin , ya dago kai ya na amsa sallamar Ya na ganin ta ya mike tsaye cike da rudu ya ke fadin " sister , ina kuma ki ka shiga " Ita ko kallon shi ba ta yi , idanun ta na kan Zayd da ke konce saman gado , hannun shi sanye da catheter a na yi mishi Karin ruwa , jikin shi sanye da wasu kaya blue irin na ma su jinya Nan take idanun ta su ka kawo ruwa , da gudu ta nufe shi ta fada saman kirjin shi ta na sakin kuka ta na fadin " yaya Zayd don Allah ka tashi kar ka bar ni kai ma , na rasa Abba na a yau , bazan so na rasa ka ba a rana guda, don Allah ka tashi " ta kai karshen ta na kai mishi bugu a kirji Shi dai Moussa, da Abdoul sun tsaya su na kallon ta an rasa mai cewa wani abu Su na a haka su ka ji Zayd ya ja wani dogon nunfashi har sai da kirjin shi ya yi sama sannan ya koma Da sauri Moussa da Abdoul su ka yi kan shi su na ambatar sunan shi , Inaya na konce saman kirjin shi sai kuka ta ke Da gudu Moussa ya fita da ga dakin , jim kadan ya dawo tare da doctor ya nuna mishi Zayd ya na fadin " don Allah doctor ka duba shi , wlh duk a tsorace na ke kar a je mutuwa ya yi " Jinjina mishi kai doctor ya yi kafin ya nufi Zayd , Ya na isa ya ce da Inaya " madam tashi na duba shi " Girgiza mishi kai tayi cikin fitar hayaci ta ke fadin " ni ba zan sake shi ba , babu inda zan je " Da sauri Abdoul ya dafa kafadun ta ya na fadin " auta ki yi hakuri ki bari a duba shi " ya fada cikin rarrashi Ba dan ta so ba ta tashi da ga jikin shi ta fada jikin shi Abdoul ta rungume shi sai kuka ta ke Shi kuma doctor ya shiga duba Zayd Sai da ya dauki wajen two minutes ya na yi mishi wasu gwaje gwaje kafin ya juya ya kali Moussa ya na murmushi ya ce " Gaskia abu ya yi kyau, ban san yadda a ka yi ba , wajen kwana hudu mu na neman mu saita bugun zuciyar shi , amma ga shi lokaci guda bugun zuciyar shi ya dawo dai'dai , ku ci gaba da yi mishi adu'a , in sha Allah zai tashi " ya na gama fadar haka ya juya ya fice dakin Murmushi Moussa ya yi ya shiga jerowa Allah godiya da ya sa Zayd bai mutu ba Inaya kuma ta na ganin doctor ya fita ta saki Abdoul ta koma jikin Zayd ta konta ta na sauke ajiyar zuciya ta lumshe idanun ta Shi kuma Abdoul ya juya ya ficewar shi ya koma wajen Malam Ya na isa bakin A&E room din doctor ya fito Da gudu Abdoul ya nufe shi ya na fadin " Doctor ya jikin na shi " Dafa kafadar shi doctor ya yi kafin ya ce " i'm sorry ya riga mu gidan gaskia " Ya kai karshen ya na janye hannun shi ya yi gaba Sumar tsaye Abdoul ya yi ya kassa wani kwakwaran motsi har a ka fito da gawar malam a ka tafi da ita morgue ya na nan tsaye ya kura wa waje guda ido Ya dauki wajen good ten minutes a haka ko kifta idanu ba ya yi Kamar da ga sama ya jiyo Muryar mama ta na fadin " Abdoul lafya ka tsaya a nan , mun ga tun dazu ba ka zo ba , shi ne Nesrine ta ce mu shigo Taxi " Ba ta kai karshen maganar ta ba Abdoul ya fada mata a jiki ya rungume ta ya na sakin kuka kamar karamin yaro A rude mama ta dago shi ta na fadin "Abdoul lafya ka na kuka kamar yaro haka da girman ka , me ya yi zafi haka " Cikin kukan ya ce " mama komai ma ya yi zafi , sun kashe Abba , sun kashe shi" Dum mama ta ji zuciyar ta ta buga , nan take jiri ya debe ta ta sume a wajen Da sauri ya Zube saman guyiwowin ta talabo kan mama ya na kiran nurse Da gudu wasu nurse guda biyu su ka yo kan shi , har gudar ta juya za ta je ta dauko gadon jinya , gudar ta tare ta ta ce mata ta debo ruwa kawai jiri ne ya debe ta Da sauri nurse ta bar wajen, jim kadan ta dawo rike da glass dauke da ruwan sanyi Karbar glass din nurse ta yi , ta zuba kadan a hannun ta, ta shafawa mama a fuska Ta na yin hakan mama ta sauke ajiyar zuciya , ta na karanto kalmar shahada Dan lumshe idanun shi Abdoul ya yi ya na sauke ajiyar zuciya kafin ya kali nurses din ya yi musu godiya Jinjina mishi kai kawai su ka yi kafin su mike su ka yi tafiyar su Su na barin wajen mama ta mike zaune ta na kallon Abdoul ta ce " Abdoul , ina malam ya ke , don Allah ka bar min irin wannan wassan " ta kai karshen hawaye na zubo mata Shi ma wasu hawayen ne su ka zubo mishi ya na sunkuyar da kai ya ce " mama ta ya zan yi miki irin wannan wassan , ina shirin tafiya dauko ku , Inaya ta shigo likitar wani soja na biye da bayan ta , ya na dauke da Abba a kafada , bayan doctor ya duba shi ne ya ke ce min wai ya rasu , mama ko ni ban san abun da ke faruwa ba " Lumshe idanun ta mama ta yi kafin ta mike tsaye ta na kallon Abdoul ta ce " mu je na gan shi don Allah " ta kai karshen kuka a kubce mata Da sauri Abdoul ya mike ya riko ta , su ka nufi morgue dan su ga gawar malam A takaice dai ranar wannan ahalin sun ga ta kan su , sai da su ka ji duniyar su ba ki daya ta ruguje dan malam shi ne duniyar su Nesrine da mama sun sha kuka kamar za su mutu , har shi Abdoul da ya ke namiji sai da ya yi kuka Bangaran Inaya kuma ko digon hawaye ba ta yi ba , ba yin da mama ba ta yi ba a kan ta yi kuka ko da sau daya ne amma ina ta ki , sai dai ta yi zaune ta zuba wa waje guda idanu babu ko kiftawa In muka leko Zayd kuma jiki alhamdoulilah ya samu sauki sosai, sai dai har yanzu bai dawo cikin hayacin shi ba After some days Sati biyu yanzu kennan da rasuwar malam , har an yi jana'izar shi , an kai shi gidan shi na gaskiya , Mama kuma ta shiga takaba Tambayar duniyar nan Abdoul ke yi ma Inaya a kan ta fada mishi wanda ya kashe malam amma ko bude baki ba ta yi Tun ranar da ta dawo ta yi wa Zayd magana , tun da ga ranar ba ta sake bude baki ta yi magana Ko tambayar ta ka yi sai dai ta bi ka da ido amma ba ta cewa komai Tun abun na damun mutanan gidan , har sun daina damuwa su ka mika komai a hannun Allah Ita kuma Inaya, duk abun da su ke kar ta ke kallon su amma ta share , dan duk hankalin ta na wajen Zayd Kullum sai ta likita ta yi one to two hours tare da shi kafin ta koma gida , haka gobe ma za ta dawo Moussa dai kallon ta kawai ya ke , cikin ranshi ya na kara yabawa soyayyar da ta ke yi wa Zayd , dama a ce Nesrine za ta so shi a hakan Zayd kuma jiki sai kara sauki ya ke dan har an cire mishi dress din da a ka yi mishi a kai , A cikin sati biyun nan Moussa ya kira ahalin Zayd ya fada musu halin da a ke ciki ya kuma sun ce su na nan zuwa Misalin karfe 10 na safe Konce Inaya ta ke saman jikin Zayd sai faman surutai ta ke zuba mishi kamar ba ita ba ce in ka yi mata magana sai dai ta bi ka da ido Ta na a haka har barci mai dadi ya de ta a jikin shi Moussa dai tun safe ya bar likitar kuma bai sanar da kowa inda zai je ba ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 30 ❤🔥 Misalin karfe 12 na safe Zayd A hankali yar yatsar shi ta fara motsi , ta na yin sama A hankali ya dinga sauke ajiyar zuciya ya na girgiza kan shi Idanun a lumshe ya bude bakin shi a hankali ya ke furta sunan " mimi " ya kai sau biyar A dubu dari ya bude idanun shi ya na kallon ceiling sai juya su ya ke yi , ya na bin wajen da kallo Ya na kokarin tashi ya jiyo yauni a saman shi A hankali ya lumshe idanun shi , ya sake bude su a hankali kafin ya sauko da kan shi ya kali jikin shi Idanun shi ba su sauka ko ina ba sai saman ta , ta na konce a jikin shi face din ta dauke da wani dan karamin murmushi da allamun barcin ya yi mata dadi Dan zaro idanu shi ya yi ya na kallon ta , ya ma rasa bakin magana , ya na dawowa cikin hayacin shi ita ce mutun ta farko da ta fado mishi a rai , ga shi kuma ta na konce a jikin shi abun sai da ya bashi tsoro A hankali ya fara dago da hannu shi me sanye da catheter ya daura a saman bayan ta Ya dago gudan hannun ya daura saman kumatun ya na kallon din ta Kassa kassa ya ce " mimi " A hankali ta fara bude idanun ta cikin magagin barci ta ce " na'am " Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya meda kan shi ya lumshe idanun shi Wani irin dadi ne ya ji cikin zuciyar shi lokaci guda , bai San lokacin da ya rungume ta tsam a jikin shi ya na sumbatar forehead din ta Yar karamar dariya ta yi kafin ta ware idanun ta da kyau ta dago kai ta na kallon face din shi Zaro idanu ta yi ta na kallon cikin na shi ta , ta saki wani kyawatencen murmushi ta ce " yaya Zayd da gaske kai ne " Jinjina mata kai ya yi kafin ya daura hannun shi saman kumatun ta ya ce " mafarki ne na yi kennan " Nan take yanayin face din ta ya sauya ta koma ta konta a kirjin shi Da sauri ya ce " mimi why did you cry , ba abun da ya same ki dai ko ? " Kuka ne ya kubce mata ta na fadin " ba abun da ya same ni yaya Zayd, amma Abba , Abba ya tafi ya bar ni " ta kai karshen ta na kara sautin kukan ta Dum ya ji zuciyar ta buga , har sai da ya lumshe idanun shi da karfi dan su na shirin kawo ruwa , duk da ba shi da wata alaka da malam da farko , amma yanzu shi ma ya zama familyn shi , ya san duk duniya ba wanda zai yi mishi abun da malam ya yi mishi A hankali ya ware idanun shi ya na kallon ta ya ce " please stop crying , i'm here with you forever , don Allah ki daina kukan nan so ki ke ciwo na zama biyu " A hankali ta fara rage sautin kukan ta ta na fadin " shikenan yaya Zayd ka yi hakuri " Dago kai ya yi ya sumbaci forehead din ta ya ce " yi hakuri kin ji , Allah ya jikan shi , ya sa ya huta " Da amine ta amsa mishi kafin ta lumshe idanun ta , ta na sauke ajiyar zuciya A hankali shi ma ya lumshe idanun shi ya fara shafa bayan ta a hankali a haka har barci ya yi gaba da su a tare Misalin karfe 2 na yamma A hankali Moussa ya turo kofar dakin kai a sunkuye ya na sallama kafin ya koma geffe ya tsaya ya na fadin " Bismillah " Ya na gama fadar haka a ka bude kofar , wani dattijon ya shigo dakin ya na sanye da manyan kaya masu bala'in kyau farare kal Kamanin shi sak da na Zayd ba dan gemun shi ba da kuma shi ya na da dara daran idanun amma har colour din su hazel irin na Zayd ne a kila a shekaru zai kai 55 haka Bayan shi kuma wasu matane biyu , su na sanye da gown ma su bala'in kyau sun daura wata Alkyaba da ga sama , sun saka hular ta Gudar ta dan lattijantaka dan a kila ta kai 48 to 50 years haka amma kyakyawar gaske ce da ga ganin fatar jikin ta kassan ta na samun hutu Dayar kuma yar budurwa ce a shekaru za ta kai 23 years ta so ta yi kama da Zayd , amma ita idanun ta bakake ne ta yi simple make up , ta saki wani lalawsan curly hair din ta ya zubo mata ta cikin alkyabar ta A hankali Moussa ya dago kai ya kali saitin Zayd Dum ya ji gaban shi ya fadi , sam bai san da cewa Inaya ta na cikin dakin ga shi kuma ta na konce a jikin Zayd , kuma ya na rungume da ita Su ma mutanan da ke tare da shi sai da su ka sha mamaki Macen sai da ta kali Moussa ta ce " Diya wacece wanan a jikin Amir kuma ? " ta fada cikin harshen larabci Sunkuyar da kai Moussa ya yi kafin ya ce " Ran ki shi dade , ina ga Amir ya kamata ya baki wannan amsar " shi ma ya fada da larabci Medo da kallon ta matar ta yi kan Zayd kafin su ida shigowa cikin dakin Dattijon da ke tare da su ne ya karaso bakin gadon ya na kallon face din Zayd da larabci shi ma ya ce " Amir , tashi mu koma gida don Allah " ya kai karshen kamar zai yi kuka Kamar da ga sama su ka jiyo Muryar shi da larabci ya na fadin " ni babu inda zan je " Duka sai da zuciyoyin su su ka buga , a iya sannin su Zayd ya yi doguwar suma ya a ka yi ya amsa musu Tun lokacin da Moussa ya yi sallama ya farka da ga barcin shi , amma bai motsa ba , sai da ya jiyo Muryar matar nan ta na tambayar Moussa wacece a jikin shi Duk duniya ba zai iya manta wannan Muryar ba, amma ya shanye bai motsa ba Su na a haka yar budurwar da ke tsaye ta karaso wajen ta na fadin " Akhie ! " kamar za ta yi kuka Slowly ya bude wadanan hazel eyes din na shi ya na kallon mutanan da ke cikin dakin Bai ce da su kami ba ya kali Moussa ya matse fuska ya ce " why za ka fada musu da sai ka bari har in tashi sai mu tarda su a cen " Murmushi Moussa ya yi ya na sunkuyar da kai dan a halin yanzu ba ya da bakin magana Zayd na ganin haka ya ja dan tsaki ya kauda kan shi gefe Dattijon da ke tsaye bakin gadon ya ce " Amir kenan da ba mu so ba ba za ka je ba , Amir tsawon Shekara shida ka na raye amma ko so guda ba ka yi tunanin ka koma gida ba , ba dan Diya na kiran mu na gaya mana halin da ka ke ciki , da ba mu san cikin halin da za mu kasance ba " A dubu dari Zayd ya juya ya na kallon Moussa da ya sunkuyar da kai, ya ma rasa bakin magana Kawai sai ya ja tsaki kafin ya ce " please ya isa haka Abbi , ni ban ce ba zan koma ba , amma ai yanzu ku na ganin halin da na ke ciki kun iya bari na one minutes please " ya kai karshen ya na juyawa da Inaya a jikin shi ya ba su baya Yar budurwa nan ta fashe da kuka ta je ta fada saman bayan shi ta na fadin " Akhie don Allah ka tashi mu koma gida wlh na ki kewar ka sosai " " Amira , kontar da hankalin tare za mu koma kin ji ko " ya fada ba tare da ya juyo ba A hankali ta sake shi ta na murmushi ta koma gefe ta tsaya Dai'dai lokacin da Inaya ta bude idanun ta , ta tashi da ga barcin ta Ita ba ta lura da mutanan da ke cikin dakin ba, kawai sai ta mike zaune ta sauko da ga saman gadon Ba ta yi taku daya ba, jiri ya debe ta ta yi baya za fadi Da sauri Zayd ya mike ya taro ta , ta fado jikin shi , ya na kallon face din ta ya ce " are you okay ? " Jinjina mishi kai tayi ta na dan karamin murmushi ta ce " yaya Zayd , ina lokacin sallat ya yi zan je na yi " Ta na gama rufe bakin ta Abdoul ya shigo dakin ya na sallama Nesrine na bayan shi ta na rike da wani basket A hankali Inaya ta juyo ta kali saitin kofar , sai yanzu ta lura da mutanan da ke cikin dakin Ba ta san lokacin da zuciyar ta ta buga ta juya da sauri ta rungume Zayd ta boye fuskar ta a kirjin shi Gaishe su Abdoul da Nesrine su ka yi duk da ba su san ko su wanene ba sannan Abdoul ya yi sauri ya je ya rungume Zayd ya na fadin " Bro , sannu ya jikin na ka " Dan bubuga bayan shi Zayd ya yi kafin ya ce da sauki sannan ya kali Inaya ya ce " To madam sa ke ni ko , They are my family , our family " Da sauri Abdoul ya sake shi ya juyo ya na kallon mutanan da ke tsaye cikin dakin , ba karya kallo daya za ka yi musu ka san abun da ya fada gaskia ne Yarinyar da ya kira da Amira ta ce cikin harshen larabci " Akhie su waye wadanan ? " " Akhie ? " Abdoul ya maimaita kalmar da ya ke shi ya na jin larabci " Abbi , Ammie , Amira , wadanan nan ma family di na ne so ku kontar da hankalin ku " ya fada da larabci shi ma Kallon shi Abdoul ya yi baki sake kafin ya ce " Zayd , wadanan Familyn ka ne " ya fada da larabci Zayd na shirin magana Moussa ya riga shi cewa " Amir ina ga yanzu lokaci ya yi da za ka fadawa kowa gaskiya a kan ka " Hararrar shi Zayd ya yi kafin ya sa hannu ya raba jikin shi da na Inaya ya zaunar da ita bakin gadon sannan ya kali sauran mutanan dakin ya ce " ku samu waje ku zauna , kun yi tsatsaye sama na " ya kai karshen ya na zama geffen Inaya da duk ta bi ta rikice Ba musu duka sauran mutanan su ka nufi sofas din dakin su ka zazauna Amira kuma ta zauna daya geffen Zayd TO YA KAMATA MU LEKO TARIHIN RAYUWAR ZAYD YANZU ALHAMDOULILAH ALHAMDOULILAH ! YAU DAI NA KAMALA BOOK 1 DI NA , NA EXILED PRINCE SAI MUN HADU DA KU A CIKIN BOOK 2 DAN JIN WANENE AINAHIN ZAYD THANKS A LOT ❤❤