*_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑃𝑎𝑔𝑒 𝑜𝑛𝑒_ _Free page_ *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._ .........Humm wato Bilyn Abdull atawa fahimtar da abinda shekaran jiyata da jiyata har zuwa yau ɗina tazo min dashi zan iya cewa JARUMTA itace asalin RAYUWA. HAƘURI shike jagorantar numfashi da samun tsahon rai ga kowanne halitta a cikin salama. A duk sanda wasunmu suka tambayemu minene adonmu? Amsa ɗaya muke fara kallo a zukatanmu da furuci (TARBIYYA). Sai dai a gareni ni nace sam ba haka bane. Zan kuma iya faɗa a hankali ko da amsa kuwwa harma da shelantawa. Kada kai mamaki ko fahimtata a bisa tsatstsauran ra'ayina ko zama mai bahagon hasashe. Bance tarbiyya bazata amsa suna ADO ba, sai dai magana ta gaskiya ADDINI shine mafi girman zama ƙololuwar ADO a waje na. Sannan akai kanka da ku kanku duk shine. Ina tsaye bisa wannan ra'ayine saboda ina girmama ADDINI NA bisa koman dake amsa komai na a rayuwa. DUNIYA itace MAKARANTAR farko ga kowanne ma'abocin numfashi, domin a cikinta ake fafutuka da hanƙoron neman SAKAMAKON zuwa MATABBATA. Sobada a yanda ka tafi da ita a haka take baka daraja da kima a wajen komai da kowanka. Kowanne mai numfashi yana tsoron MUTUWA, amma hakan baya hanamu buƙatar RAYUWA da fatan shiga ALJANNA, saboda a canne ake iya samun komai da komai da zukata basa iya hasasowa koda da tsayin motocin hange. Haka zalika ƙarewar kwanakin numfashinmu a kowanne wayewar gari baya hanamu sake tanadin BURIKANMU koda kuwa yaƙininmu na nufin baza muga GOBENMU BA. Duk wani ɗan adam zakiga RAYUWA na taka masa iya rawar abinda littafin ƙaddararsa tazo da shi ne kawai, duk kuma iya hanƙoronka da faɗi tashi akan neman DUNIYA ko guje mata baka isa zartama wannan ƙaddarar taka ba. Kar na kaiku da nisa bara na baku komai a buɗe a yanda zaku fi fahimtar abinda nake son faɗa ga Bilyn Abdull da ku baki ɗaya. Sunana shine *_SAMRAAH ABDUL-WAHAB GWARZO_*. A zahirin rayuwa ni ɗin ba kowa bace face ɗiyar Malam Abdul-wahab Gwarzo. Domin kuwa mahaifina bai kasance mutum mai mulki ba, haka ba attajiri bane, ba kuma babban malami ba. Shi ɗin driver ne dake aikin tuƙi a wani gidan attajirai. Sai dai ALLAH yay masa rasuwa sakamakon haɗarin mota tun inada shekara bakwai a duniya. Mu uku kacal ya haifa shi da mahaifiyarmu da itama dai ALLAH yay mata rasuwa bayan haihuwar ƙanina tun bamma cika shekara uku a duniya ba. Yaya Musaddiq shine babban yayanmu, sai ni Samraah da autanmu Hafizzullah. Tun bayan rasuwar mahaifiyarmu riƙona ni da Hafizzullah ya koma hannun ƙanen mahaifiyarmu Uncle Imam. Matarsa ita ta ƙarasa shayar da Hafizzullah tare da yaronsu data haifa itama kusan lokaci ɗaya da mamanmu, sai dai bamu da tabbacin ma kota shayar da shi ɗin ko batayi ba. Dan haka suka tashi tamkar tagwaye. Bayan rasuwar mahaifinmu riƙon Yaya Musaddiq ma ya dawo hannun Uncle Imam. Duk da mahaifinmu bamai arziki ko mai mulki bane ya tafi ya barmu da gonakin gado harma da gidan zama. Sai wasu ƴan kuɗaɗe a account. Itama mahaifiyarmu tabar mana gonaki data gada a wajen nata iyayen tare da Uncle Imam dan su biyu kacal iyayensu suka haifa suma. Kasancewar duka iyayenmu a cikin garin Gwarzo suke waɗan nan dukiya tamu duk tana acan ne. Sai gida da muka rayu kawai anan cikin birnin Kano. Karancin shekarunmu yasa duka abinda iyayenmu suka bar mana bayan an raba mana shi ba'a bamu ba, acewar Uncle Imam sai mun girma dan duk shi ya ɗauki komai ya ajiye, gonaki ya cigaba da nomasu, gida ya saka ƴan haya. Uncle Imam shine ya cigaba da ɗaukar nauyin karatunmu dama dukkan al'amura na rayuwarmu har sanda muka kawo girma. Duk da dai rayuwa a gidan Uncle Imam bata taɓa kasancewa mai sauƙi a garemu ba saboda mugun halin matarsa duk mun shanye wannan a ranmu. Amma tabbas mun ɗanɗana kuɗarmu a hannunta akan abubuwa daban-daban. Mun fuskanci ƙalubalen maraici kala daban-daban. Dan komai da zasuyi ma ƴaƴansu yanada bambanci da wanda mu za'a mana. Hatta da abinci takan fifita ƴaƴanta akan mu. Hakama a makaranta suna private school muna government school. Sutura akoda yaushe tasu nada banbanci da namu. Hatta da ɗakin kwana na yaransu nada banbanci da namu. Abin zai baka mamaki idan nace duk wannan wariyar launin fatar muna ganine har daga Uncle Imam bawai ita kawai ba. Kafin mu san kammu mukanyi kuka mu share hawayenmu, bayan mun mallaki hankalinmu musamman ma ni sai na fara maida murtani. Nakan shanye daga ƙyara da hantarar Mom da Abba. Amma bana iya kauda kai daga al'amuran ƴaƴansu. Dan hatta waɗanda suka girmeni idan suka nuna min yatsa saina karya shi nake samun nutsuwa koda za'a rama musu ne. Amma ga Yaya Musaddiq ba haka bane ba, dan shi mutum ne mai shiru-shiru, hakama Hafizzullah baida yawan hayaniya. To nima ɗin dai a zahirance bazakace ina magana ba, dan banda yawan surutu, sannan inada yanayin fuskar salihan mutane. Shiyyasa sometimes nakan aikata abu Mom ta faɗa ace ba'a yarda ba, ni ɗin nan dako yatsa aka saka min a baki bana ciza ba. Wannan halayya tawa na ƙona mata zuciya da ruhi, dan haka nafi sauran ƴan uwana cin wahala da azaba a hannunta harma da hannun Abba ɗin. A haka dai muka rayu cikin haƙuri da juriyar rayuwa har ALLAH yasa muka kammala secondary. Daga nan Abba yace baida kuɗin biya mana mu cigaba da karatun jami'a. Raina ya ɓaci matuƙa domin ganin yanata cuku-cukun biyama Abbas ɗansa dake sa'a da Yaya Musaddiq, da Baby mai sa'a dani. Dan haka na sameshi da batun tunda hakane ya biya mana da gadonmu. A saida gona guda a biya mana. Maruka nasha lafiyayyu masu gigitarwa a wajensa, daga ƙarshe ya koroni da zagi daga falonsa. Duk da ran Yaya Musaddiq ya ɓaci shima baice komai ba, saima faɗa daya shiga min akan abinda nayi. Acewarsa baikamata nayi magana ba, dan koba komai Abba ƙanin mahaifiyarmu ne, ya kumayi wahalar riƙemu kafin yau. Komai bance masa ba, face hawaye kawai da nake zirararwa. Shima bai sake cewa dani komai ba ya fice a gidan. Kwanaki biyu da faruwar hakan Yaya Musaddiq yazo min da labarin ya samu wajen aikin koyon kanikancin motoci. Duk da ni ba haka nake buƙata ba karatu nake son muyi sai na tayashi murna kawai da fatan alkairi. Daga lokacin Yaya Musaddiq ya fara zuwa gareji, dan koda ya faɗama Abba sai bai wani maida hankali ba face cemasa ALLAH ya bada sa'a a daƙile. Su Baby sun fara zuwa makaranta, yayinda ni kuma na koma mai aikin gidan. Dan dukkan wani aiki na cikin gidan a yanzu ya koma kaina ne gaba ɗaya har wanda banayi a da. Sai idan Hafizzullah ya dawo yake kama min da wasu ayyuka. Ina matuƙar jigatuwa, amma hakan bai hanani shiryawa na tafi islamiyya duk rintsi kuma koda za'a dakeni ne. Tun ma idan na sulale naje na dawo Mom kan dake ni har ta haƙura ta tattarani ta watsar, sai dai dolene bazan fita ba sai na kammala duka aikin data bani, samun wannan damar ya sakani jajircewa na gama komai akan lokaci dan na wuce. A wannan yanayin shekara ɗaya ta shuɗe da kammala sakandare ɗinmu, na samu nasarar yin saukar Alkur'ani, sai dai babu abinda akaimin na walima sai wanda Yaya ya ɗan mun, ban kuma damu ba. Yayinda su Baby keta zuwa makaranta, Yaya Musaddiq na jelen zuwa gareji. Dan in ya fita tun safe sai yamma yake dawowa. Da farko Abba bai damu da aikin Yaya Musaddiq ba balle abinda yake samu, sai daga baya da Mom ta zugashi wai yana samun kuɗi tunda yamun ɗinkin walima sai ya sharɗanta masa yo cefane kullum a gidan. Duk da hakan ya zafi Yaya Musaddiq saboda shi yanada burinsa akan shiga aikin bai nuna ba ko'a fuska, sai ya koma raba kuɗin da yake samu biyu yana ajiye rabi kamar yanda ya saba rabin yana cefanen. A wata ranar da tai dai-dai da cikar shekarar mu ɗaya da watanni biyar da gama sakandire sai ga wani malamin mu yazo neman Abba. Bayan sun ɗan gana na wasu mintuna akai kirana. Ranar da bazan taɓa mantawaba kenan a rayuwata, ranar data zama komai daga cikin TSIRON da yazama shine TUSHEN LABARINA. Ranar da ta zama MAFARIN da har yau ba'a kai ga zuwa ƘARSHE ba tunda numfashi bai rabu da gangar jiki ba.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐_ .......Mal Saminu yazo da daddaɗan labari garemu cewar na samu scholarship na cigaba da karatuna. Misalta muku yanda na shiga ɗunbin farin ciki a wannan ranar ni da ƴan uwana guda biyu ɓata lokaci ne. Yayinda Abba da Mom da su Baby suka nuna baƙin ciki da hassadarsu a fili akan hakan. Dan da farko ma Mom catai ƙarya ne babu inda zanje, Abba kuma ya goya mata baya, sai da Malam Saminu ya tabbatar musu da in har aka hanani akwai matsala. Dan kuwa gwamnati zata iya bibiyar al'amarin ta kuma hukunta duk wanda yay uwa yay maɗaukiya akan hakan. Jin wannan bayani ya sakasu barina dole nima a wannan shekarar aka shiga damawa dani a harkar karatu a B.U.K. inda Baby da yayanta Abbas suke nasu karatun suma. *_MATAKON FARKO_* Uhm dole a kira wannan ajin da matakin farko. Domin kuwa akansa ne komai ya fara, farawar da kamar itace farkon buɗe shafin rayuwata ta hankali, domin kuwa ko babu komai shekarata goma sha bakwai a yanzu. Zan iya cewa na shiga jami'a a sa'a. Domin kuwa course ɗin da nafi so da buri shina samu. A shekarar farko dana fara karatuna na fahimci halin da Baby ke ciki a school ɗin. Dan kuwa tuni ta ajiye karatu gefe sune shegun makaranta. Iyaka su shiga ofisoshin malamai su ɓata lokaci wani lokacin ma harda gidajensu ko a ɗaukesu a mota a fita da su, batun karatu kuwa sam babu shi tare da su, sunada group kuma. Amma abin mamaki sunansu na gaba-gaba a allon kafe jarabawa matsayin wanda suka cinye komai sai ɗan abinda ba'a rasa ba. Ga Yaya Abbas ɗin ma bata sauya zani ba. Dan shima ɗin dai yafi maida hankali ga siyasar makaranta da bin abokai masu motoci fiye da karatun. Bayan Yaya Musaddiq ban taɓa sanarma kowa a gidanmu ba, shima kuma tunda ya kwaɓeni akan hakan ban sake kawo masa zancen ba na maida hankali ga karatu na. Ina a wata na biyar da zuwa mukai karan batta da Mansoor. Mansoor Khalil Musa matashin yaro ɗan ƙwalisa. Ƙyaƙyƙyawan gaske mai tarin ilimi. Yana shekararsa ta uku a cikin b.u.k. A yanda Mansoor ke shigar suturu na alfarma da mota zai tabbatar maka da shi ɗin ɗan masu hannu da shuni ne. Sai kuma ƙwazonsa da ƙyawunsa ya sake jan hankalin ƴammata na cikin makarantar da yawa a kansa. Sai dai sam bai ɗaga ido ya kalli kowaccensu balle ya yarda magana ta haɗasu. Hakan yasa ake masa laƙabi da mutum mai girman kai. Domin kuwa bayan abokansa biyu babu wanda yake kallo da gashin arziƙi a ɗaliban dake ƙasa da shi harma wanda ke sama da shi. Amma sai me rana ɗaya ALLAH ya haɗamu a cafeteria. Muna tsaka da cin abinci ni da ƙawata ɗaya tilo Joy muna hirarmu cikin nishaɗi ya shigo tare da abokansa. Duk da yanda naji cafeteria ɗin ta ɗauki gunaguni a kansa banko kalla sashin da suke ba. Sai kawai jin abokinsa mukai kammu cikin gadara yace wai mu tashi zasu zauna. Cikin tsoro Joy tai niyyar miƙewa, amma sai na balla mata harara batare da nace komai ba. Zungurina tayi cikin roƙo da magana ƙasa-ƙasa ta ce, “Please Sam Gee mu tashi, ni sam bana son fitina. Kin san kuma halin guys ɗin nan ba mutunci ne da su ba”. Kai tsaye na buge hannunta a fusace da faɗin, “Idan kinga na tashi a wajen nan na gama abinda nake yi ne Joy”. Daga haka na cigaba da cin abinci na. Zaram Joy ta miƙe, amma a mamakinmu dama duk mutanen dake wajen sai muka tsinkayi Mansoor na faɗin ta zauna abinta, cikin rashin damuwa yaja kujerar kusa dani ya zauna shima. Hakan da yay ya bama kowa mamaki, duk da dama bawai an taɓa ganinsa yana faɗa da wani bane ba, kawai dai an sanshi shi mutum ne mai girman kai da rashin shiga shirgin kowa, abokansa ne masu zuba rashin mutuncin ga kowa. Dan ko magana ma sai yaso yayita da mutum. Suma abokan nasa zama sukayi bayan sun musu order ɗin abinda zasu ci, ko gezau banji ba, ban kuma kalli kowannensu ba harna kammala cin abincina na miƙe bayan na saki niƙab ɗin fuskata. Dan kullum nakan shigo makarantar ne cikin hijjabi har ƙasa da niƙab, ko kuma nurse mask da eyeglasses, dan haka ba kowa ne zai iya shaida maka fuskata ba hatta ƴan department ɗinmu ma. Hasalima sunan Hijjab girl na neman bina, dan kowa idan zai kwatance da sunana yakan kwatantani da hakan ne. Idan ka cire Joy da ke kirana da *_Sam Gee_*. Mun bar wajen yayinda mutane keta ɗan ƙusƙus ɗin magana, kun san dai ɗalibai da rashin raina abin kace nace, yayinda Mansoor ya bini da kallo tamkar ya samu television. Tun daga wannan ranar al'amarin kamar wasa, sai ya zam a duk sanda mukaje cafeteria cin abinci Mansoor da abokansa zasu zo. Kuma koda tare muke da wasu a tebiri sai sun tashesu sun zauna. Ban taɓa tanka musu ba balle nuna nasan sunayi har muka shafe kusan sati biyu a haka, kafin shi Mansoor ɗin da kansa ya fara biyan kuɗin abincin da duk muka amsa a kullum. Anyi na farko anyi na biyu a ran ta uku na taka masa birki dayin hakan cikin masifa da kowa bai san na iya ba, amma maimakon yaji haushi sai yay murmushi kawai ya tashi ma ya bar cafeteria ɗin abinsa. Naji haushi amma sai na dake, na kumayi alƙawarin saboda shi bazan fasa zuwa cafeteria ɗin cin abinci ba, yayinda shi kuma bai fasa biya mana ba, kuma koda mun biya ba'a amsar kuɗinmu sai ace ai anbiya mana. Abin na ƙona min rai, na kuma rasa yanda zanyi, ina kuma akan bakana na bazan daina zuwa cafeteria ba. Tun ina jin zan sharesa har na fara magana, nan ma a banza, sai kawai na daina dan na fahimci maganar tawa ke tunzurashi kamar. A haka muka cinye wata guda. Abu dai kamar wasa sai ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai shaƙuwa ta fara shiga tsakaninmu da Mansoor da abokansa. Takai idan ma basu zo cafeteria ɗin ba nakanji babu daɗi, kamar yanda shima yakanji idan bai ganni ba. Abinda zai baki mamaki kuma har lokacin ba wata doguwar magana ke shiga tsakaninmu ba, gaisuwa ce kawai sai zaman cin abinci.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ ......Tun dai muna shashshare juna har abinda ke cikin zuciya ya bayyana, domin kuwa Mansoor ya fito fili ya nuna min shifa sona yake. Tom kun san dai halin mutuniyar taku, ban gusa ba na balbalesa da masifar da zuwa yanzu wasu sun fara kallona da sumumu kasau macijin sari ka noƙe. Maimakon yaji haushi sai ya dinga sakar min murmushi, wannan shine karo na farko da nabar zuwa cafeteria da tunanin ai Mansoor zai ƙyaleni na huta, dan ni kam burina karatu ba soyayya ba. Sai dai kuma ba hakan bane ba, dan kuwa dai shima salo ya canja ta hanyar nuna ba soyayyar za'aiba yanzu karatu ne gaba, idan komai ya daidaita nan gaba sai soyayyar ta koma gaba. Tun ina shashsha masa ƙamshi harna miƙa wuya. Kafin wani dogon lokaci kowa yasan soyayyar mu da Mansoor kasancewar sa mutum popular a cikin makarantar, duk da dai kamar yanda ta faɗa karatune gaba ba soyayya muke ba, dan da wahala ma kaji ya saka min batun soyayya, sai yayta amfani da hakan shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tdakaninmu. Komai ya cigaba da tafiya yanda ya kamata, Mansoor na taimaka min matuƙa a ɓangaren karatu ni da ƙawata Joy. Hakan kuma ya sake fiddo ƙwazona. Sannan soyayyarsa na bani kariya sosai daga tsagerun ɗalibai harma da malamai ƴan bani gishiri na baka manda. Tun sauran ɗalibai na ɗaukar soyayyar yaudara ko wata manufa har suka yarda ɗari bisa ɗari da gaske muke, saboda komai muna gudanar da shi a tsaftace. Tafiya tai tafiya, shekaru sunja abubuwa sun canja. Su Mansoor sun kammala karatunsu, sai dai kuma muna nane da juna ta waya. Yana kuma zuwa gida duk da ban taɓa yarda kowa yasan da batunsa ba bayan Yaya Musaddiq. Koda yake su Baby sun sani, dan nasha jin ma wai ai Baby ta jima tana son shi, sai dai bansan minene ya faru koya katangeta da sanarwa a gida ina soyayya da wani ba, sannan ita bata taɓa tarata da batun Mansoor ba kai tsaye, sai dai tai habaici a wasu lokutan ko shaguɓe, ni kuma sai ban taɓa kulata ba ko nuna na fahimta. Ina zangon ƙarshe na kammala karatuna na fahimci ashe Yaya Musaddiq shike biyamin kuɗin makaranta babu wani scholarship dama. Ya haɗa baki da malamin namune kawai, dan a yanzu haka shima Hafizzullah yana a level 100 a jami'ar Umaru Musa ƴar-aduwa dake Katsina. Shima kuma dai da batun scholarship ɗin nan aka rufe bakunan su Uncle Imam duk da an kwashi tashin hankali sosai fiye da nawa lokacin kasancewar shi Nabil bai samu ya tafi ba har yanzu. Ranar da nasan wannan sirrin nasha kuka a gaban Yaya Musaddiq. Shiko ya dinga lallashina yana murmushi, a ranar ya sanar min da komai bai ɓoye min ba. Dan yace bazai taɓa iya zama bamuyi karatu ba, dan haka ya zaɓi bi ta wannan hanyar domin gina gobenmu. Shiko aikin kanikancinsa ya ishesa in sha ALLAHU. Na nuna masa ban yarda ba, shima dole ne musam yanda zamuyi ya koma karatu, dan kuwa zuwa yanzu yana samun kuɗi sosai, sai dai duk a hidimar gidanmu da karatunmu suke tafiya, dan har yanzu bai tsinanama kansa komai na rayuwa ba irin burin matasa na son gina gida da sauransu, hatta budurwa ma baida ita shi sam. Ya min alƙawarin idan lokacin komawar yayi zai koma in sha ALLAHU. Alhmdllh na kammala karatu cikin nasara, yayinda na riga Abbas da Baby da suka rigani farawa kammalawa saboda su sun saka wasa a karatun nasu. Bakuma su da niyyar gama school ɗin da alama, maybe sai an korosu su shiga hankalinsu oho, dan gasu nan koda yaushe cikin maimaita shekara suke. Bayan kammala karatuna da wasu watanni Mansoor yay uwa yay maɗaukiya ya sama min aiki a wani gidan tv da rediyo dake tashe a wannan lokacin. Hakan ya saka Yaya Musaddiq farin ciki, yayinda ran su Abba yay baƙi har suka kasa ɓoye hassadarsu a fili musamman ma Mom, dan da farko ma tuburewa tai akan tunda na gama karatu aure kawai ya kamata Abba yay min, wai akwai wani ɗan yayarta ya jima da cewa yana so na. Abba har ya ɗauki zancenta da muhimmanci niko na tibire nace wlhy idan aka aura min shi kashesa zanyi, dan ni ban shirya aure ba sai na fara aiki na. Ganin fa da gaske nake kuma sun san tsurin idona dan randa yaron yazo hira wajena zagin ƙare dangi na masa, hakan yasa Abba ya kashe maganar, sai dai ban san yaya sukai da matar tashi ba a ɓoye, a zahiri dai yace ya kashe wannan batu naje nai aiki na. Amma ya bani nan da ƙarshen shekarar nan na kawo miji. Oho ban wani damu dasu ba na fara aiki na, dan nasan dai inada Mansoor ɗina a hannu. Cikin nasara kafin kace mi na samu karɓuwa, albashina na farko dana biyu dana uku na haɗa da shi na sayama Yaya Musaddiq fili da taimakon Mansoor. Lokacin dana damƙa masa takardun sai kawai ya fashe da kuka. Nima kukan na fashe da shi tare riƙe hannunsa ina roƙonsa dan ALLAH ya daina, shifa uba ne a garemu yanzu, idan bamu masa hidima da abinda ALLAH ya azurtamu da shi ba wa zamuyimawa. Da ƙyar dai mukai shiru dan dama a wajen aikinsa na samesa, gudun kada na bashi a gida wani yaji a ƙwace. Tom Alhmdllh, yanzu dai a taƙaice watanni na shida kenan da fara aiki na, ina kuma matuƙar jin daɗin da nuna kwazo matuƙa. Dan bada ƙwaƙwalwa kawai nake aikin nan ba, harda zuciyata da ƙwanjina gaba ɗaya. Gashi ALLAH ya bani farin jinin mutane, dan tunda na fara gabatar da wani shiri akan matasa shikenan kamar nayi kiranyen masoya, dan da a iya rediyo ne kawai, amma wata guda kenan da fara gabatar da shi a television saboda yanda oganmu yaga shirin ya amsu yana sake jawo hankalin mutane ga channel ɗin tamu sai abin yay matuƙar birgesa. Dan haka aka sake ƙarfafa shirin ta hanyar fiddoshi a fanninmu na television ma, Alhmdllh kuma komai na tafiya fiye ma da yanda akai zato da tsammaninsa.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒐𝒖𝒓_ ______________ 💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫 *_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K'ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K'ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* .http://wa.me/+2347069711327 *_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Hadin amarya budurwa ko zawara* *Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)* *Maijego package (virgin gain)* 📦 *Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji* *Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci* *Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa* *Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji* *Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa* *Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,* *Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni'ima sha'awa da dandano* *Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki* *Kalolin Zuma masu saukar da ni'ima Nan take da gamsar da maigida* *Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni'ima da dandano irin wadda akeso* *Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano* *Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar danna wannan blue rubutun* 👉🏻 http://wa.me/+2347069711327 *Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni'ima da jimawa sosai ajikin mace* *Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha'awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha'awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* http://wa.me/+2347069711327 *Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto* _________________ ......A gurguje nake faman shiryawa saboda makarar da naso nayi. Ba kuma komai ya jawo min hakan ba sai sharaɗin girka breakfast ga masu gidan a kullum kafin na fita bisa umarnin Mom bayan gyara ko ina. Ban isa nace bazanyi ba, dan na fahimci hanyar da zata tuzguɗe ɗan aikin nawa take nema. Dan haka na tsarama kaina time table ta yanda bazan cutu ba. Kullum ƙarfe huɗu na asuba na tashi, zan shiga kitchen na ɗaura breakfast. Inayi ina ɗan wasu aikin gyara gidan har na kammala, dana gama na maida hankali ga sauran ayyukan, ALLAH na taimakona kafin ai kiran sallar farko zaka samu na kammala komai, da Yaya Musaddiq ya fahimta ma sai ya zam shima yana tasowa muyi tare dandanan saina kammala nai shiri. To yau an samu akasi ne da alama Yaya ya makara, dan har na kammala bai shigoba, gashi ma har na gama shirina. Nayi ƙyau sosai cikin baƙar abayar dana saka, nai rolling veil ɗin ta da ya sake fiddoni tsamm kamar wata ɗiyar larabawa. A ɓangaren ƙyawun fuska dana jiki babu abinda zance sai Alhmdllh, sai dai ban taɓa jin alfahari ko son yin ɗagawa da wannan baiwar da ALLAH yay min ba. Nakan gode masa ta hanyar suturta kaina da ƙyaƙyƙyawar shiga, dan kullum cikin dogon hijjabi nake da nose mask. Dan ƙaryane kace ka ganni babu nose mask a fuska. A lokacin dazan fara gabatar da shirin nan a sashen tv ansha gumurzu dani a ranar farko dan har hawaye saida nayi saboda ciresa, dole dai na haƙura daga ƙarshe ma toshe idona da eyeglasses sannan na iya gabatar da shirin, a hakanma ina jin kaina kamar ba daidai ba. Kamar kullum mask ɗina na saka, sai dai yau baƙi ne, yay min ƙyau sosai dan ƙyawawan fararen idanuna masu girma da cikar gashi kawai ake iya gani. Cikin takun nutsuwata na fito, ga wani ƙamshi mai sanyi yana tashi a jikina, sai dai bamai ƙarfi bane, dan sai ka kasance a kusa dani sosai zaka iya jinsa yanda ya kamata. Sauri nake, dan haka bana fatan haɗuwa da kowa na gidan. Sai da na leƙo na tabbatar babu kowa a falon sannan na ƙarasa fitowa. Nan ma da sanɗa na fita, inayi ina waigen bayana. Ban sami nutsuwa ba saida na ganni a waje, na sauke nannauyar ajiyar zuciya ina sakin murmushi, bag ɗita mai zubin school bag na rataya hannunta guda a bayana, ɗakin yaya na fara leƙawa, sai muka kusa cin karo dan shima yana niyyar fitowa ne. “Kandala ƴar jaridan Yayanta”. Ya faɗa cikin tsokana yana mun murmushi. Murmushin nima na mayar masa ina ɗan rufe fuskata da tafin hannuna. Sai kuma na janye ina ɗan ɓata fuska da faɗin, “Ai ni fushi ma nake da kai yaya. Na manta nai maka murmushi ma.” Cikin dariya ya ce, “Oh oh Tom ayi haƙuri Ƴar ficika, nasan laifin Yaya dai rashin shigowa taya aiki, wlhy jiya na matuƙar gajiya ne a gareji, shiyyasa tunda na samu na kwanta ko juyi banyi ba sai kawai naji ana sallame salla. Dan yau ma sai a ɗaki nayi tawa dan abin kunya”. Dariya na ƙyalƙyale da ita sosai saboda yanda yay da fuska kamar wani ɗan yaro. Sai kuma na kalla agogo da sake kallonsa. A zabure na ce, “Uhm Yaya zan makara. Ni dai taho muje ka saukeni, dan yau a mashin ɗinka zanje office, ina son na baka wani labari a hanya”. Babu musu yace min muje, saboda karna makara bai shiga gidan ya gaidasu kamar yanda ya saba ba. Ya kuma san sai yasha masifa akan haka ɗin, amma yafi buƙatar farin cikina. Cike da farin ciki muka bar ƙofar gidan tamkar bamu da wata damuwar rayuwa. Maganar da nace masa zamuyi na fara masa. Ba komai bane face batun fara gininsa, dan ina son a fara ya samu yay aure. Bai dai ce dani komai ba face murmushi kawai har muka isa, a ƙofar gate ya ajiyeni. Har lokacin fuskarsa da murmushi ya kalleni. Sai kuma ya ɗan ja fasali da harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallona. “Samraah!”. Ya kirayi sunana da tsantsar kulawa. Amsa masa nai nima da girmamawa. Numfashi ya sake furzarwa da ɗan duƙar da kansa ƙasa kamar mai nazari, sai kuma ya ɗago yana sake kallona. “Samraah inaga ba batun gini ya kamata muyi ba yanzu. Kamata yay ace mu tattali abinda muke samu domin kayan aurenki. Kin girma Samraah, kin kammala karatunki cikin aminci, ga aiki kin samu cikin sauƙi, kina da Mansoor a hannu, a ganina batun aure ya kamata ace kunyi da shi yanzu kafin ma lokacin da Abba ya baki ya cika. Kin san dai halin Mom basai na faɗa miki ba, wannan shirun da kikaga tayi wlhy bazai zama na alkairi ba. Gara mu fiskanci zahiri. Wannan ƙaramin jikin naki yabar kwasarki ba baya kike komawa ba shekaru ne ke ƙaruwa. mutanen wajene kawai suke miki kallon ƴar ƙarama ganinki ƴar ficit. Ni nawa batun mai sauƙi ne, namiji ne ni, konan da shakara goma bazan tsufa da aure ba ai. Ga Hafizzullah yanzu ya fara karatunsa, kamata yay har sai shima ya kammala koda zan yi batun wani aure, sai nake ganin kamar hakan zai fi, ni dama ba wata budurwa ba a ƙasa”. Ya ƙare maganar da zolaya. Baki na kumbura cikin ƴar shagwaɓa nace, “Yaya ni duk ban amshi wannan ƙorafin naka ba sam. Kadai bari mu samu lokaci mu zauna mu tattauna. Amma batun bazakai aure ba sai nayi ko Hafiz ya kammala makaranta duk baima taso ba. In dai Dan budurwar ce zan maka, amma bazan bari ka cigaba dama waɗan can mutanen bauta ba. Kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi. Wannan lokacin ya wuce muma yanzu munsan kammu”. Kansa kawai ya girgiza, nasan kuma ba komai ya sakashi yin hakan ba sai ganin yanda na ƙarasa maganar a hasale. A bayyane fushina da zafin mariƙanmu ya gama bayyana. Maimakon yace wani wani sai kawai yaymin nuni da gate alamar naje ciki. Banyi musu ba nai masa sallama na nufi shiga ciki ina kumbura baki da fiki-fiki da idanu najin haushi........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒊𝒗𝒆_ ______________ 💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫 *_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K'ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K'ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* .http://wa.me/+2347069711327 *_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Hadin amarya budurwa ko zawara* *Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)* *Maijego package (virgin gain)* 📦 *Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji* *Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci* *Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa* *Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji* *Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa* *Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,* *Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni'ima sha'awa da dandano* *Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki* *Kalolin Zuma masu saukar da ni'ima Nan take da gamsar da maigida* *Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni'ima da dandano irin wadda akeso* *Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano* *Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar danna wannan blue rubutun* 👉🏻 http://wa.me/+2347069711327 *Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni'ima da jimawa sosai ajikin mace* *Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha'awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha'awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* http://wa.me/+2347069711327 *Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto* ______________ ........Ina zama office ɗinmu daya kasance mu biyar ne a ciki Asiya data kasance duk tare muke anan ta shigo da sallama. Ganin takardu a hannunta ya tabbatar min da ba yanzu ne ta shigo ba. Gaisawa mukai farko, kafin ta ɗora da faɗin, “Samraah MD na kiranki kuwa. Ya ce ki maza kuma dan zaiyi baƙi”. Kaina na jinjina mata batare da nayi magana ba na miƙe ina sake gyara zaman facemask ɗina daya ɗan zamo ta saman hanci. A cikin takuna na nutsuwa da yanga da mutane da yawa ke fassarawa na fito. Duk wanda na gamu da shi nakan ɗaga masa hannu da cewa good morning, wasu sukan ɗan tsokaneni. Sai dai iyakata murmushi kawai dan nifa idan ba kayi dogon zama dani ba bazaka taɓa tunanin inada surutu ba sam. Ban cika yawan magana a ko ina ba sai in nice naga damar hakan. Shiyyasa da yawan mutane ke ɗaukata mai shiru-shiru. Har wasu kan dangantani da hakan da iya yardarsu. Basu sani ba idan aka taɓoni banda ragi banda ragowa sam. Na isa office ɗin MD, bayan nayi knocking sai da nai tsaiwar kusan minti ɗaya kafin ya bani izinin shiga ciki. Kallo ɗaya na masa na ɗauke kaina, dan mutum ne shi mai shegen son kallon mutane kamar zai cinyesu. Cikin son kawar da idanunsa dake yawo a kaina ya ce, “Zauna”. Zaman nayi a ɗarare nace da shi, “Good morning sir”. A taƙaice ya amsani da, “How are you?”. Batare da ya jira amsawata ba ya cigaba da maganarsa yana turomin wata ƙyaƙyƙyawar mujalla da wani envelope mai kama da invetion card. Bana ganin fuskar mutumin daya mamaye bangon farko na mujallar gaba ɗaya. Sai jikinsa dake sanye cikin wasu shegun suit sky blue zuwa ƙafarsa dake cikin cover shoes dake wani shining duk da kuwa a hoto ne. Zaune yake a kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya, hakan ya bani ɗan damar ganin hannunsa mai ɗauke da dogayen fararen farata dake riƙe da glass cup da guntun drink ke ciki. Sai zobe guda ɗaya mai ƙyau sosai a yatsarsa... Duk da baifi a sakanni goma na ƙarema hoton irin wannan kallon ba a ɗan kamar fusace naji gyaran muryar MD a kaina. Saurin gyara yanayina nayi na maida hankalina gareshi, fuskarsa a ɗan ɗaure yana famar yamutsa fuska ya ce, “Ɗauka ki duba”. Ɗaukar nayi, sai dai ban kallaba yanzu na maida hankali garesa da nuna alamar shi nake saurare. Shima sai naga ya ɗan sassauta yanayinsa. Ya nuna ni da faɗin, “Samraah na zaɓoki ne saboda nasan zaki iya. Wannan mujalla ce ta TAURARINMU A YAU data fita jiya. A gaba ɗaya abinda ke cikinta ya ta'allaka ne akan matashin ɗan kasuwar nan da sunansa ke amsa kuwa a ƙasashenmu na Africa dama duniya a ɗan tsakanin nan. Wato *_AWWAB EL-MU'AZZ._* sai dai kowa yafi saninsa da *_MAASH_* ne. Maash ɗan arewa ne haifaffen garin Kano sai dai mazaunin jihar Lagos. Yana da tarin cibiyoyin kasuwanci a kudancin ƙasar nan dama wasu ƙasashen Africa. Hakama a ƙasashen turawan da larabawa yana da rassan kasuwanci. Amma abin mamaki bai taɓa kafa wani abunsa a arewacin nan namu ba. Hakan yasa mutanenmu sukai masa ca, suke kuma sukarsa akan hakan, har takai suna ƙalubalantar dukiyar tasa musamman idan akai dubi da ƙarancin shekarunsa. Duk da kuwa an san mahaifinsa nada kuɗi, hakama Kakansa sanannen mutum ne, sai dai ko kwatar abinda shi MAASH ɗin ke da a yanzu mahaifinsa bai mallaka ba. Kace nace ya sake yawaita a kansa ne a watanni uku da suka gabata, dalilin bayyanar Companyn sa na jirage dake jigilar mutane daga Nigeria zuwa ƙasashen ƙetare. Domin a farko jirage goma ne ciff suka fara aiki. Sosai manyan gidajen jaridu sun so tattaunawa da shi amma Maash yaƙi bada kowacce irin dama. A duk lokacin da hakan ta taso sai dai a tattauna da P.A ɗinsa. To nadai taƙaice miki zance a yanzu haka bayan ka-ce-na-ce da aka sha yimasa akan gudun arewa da ƙaruwa Mujallar nan ta fitar da bayanan buɗe ɓoyayyen katafaren company da kusan wata uku kenan ana aikinsa batare da mutane sun san na wanene ba a cikin Kanon nan. Company ne na ƙera motoci da babura da abubuwa masu yawa da suka shafi ababen hawa. Irinsa shine na farko a Africa, a duniya kuma na uku. Kuma Maash da kansa zai zo Kano bikin buɗesa. Hakan yasa tunda naga mujallar nan na shiga na fita sai da na samo mana invetion card ɗin shiga wajen, dan hatta ƴan jaridar da zasu halarci wajen a ƙa'ide suke. Dan haka na kwana nazari a daren jiya, na kuma hanga na hango a kaf gidan nan kece nake ganin zaki iya mana wannan aikin, fatanmu kiyi duk yanda zakiyi kisa Maash ya magantu a gaban ƴan jarida karo na farko dan ALLAH. Hakan zai zama ba ƙaramar nasara ba a garemu da ma wannan gidan namu baki ɗaya. Sannan ke a karan kamki ma wata sabuwar ɗaukakace da nike da tabbacin zata zamewa rayuwarki alkairi in ALLAH ya yarda.” Wani irin nauyi naji kaina yamun, dan haka da ƙyar na iya fisgo kalma ɗaya akan harshena na furta. “Amma Sir kaifa kace bai taɓa yarda yayi hira da ƴan jarida ba. Taya kake tunanin ni zan iya samo wannan nasarar? Yaushe ma na fara aiki, wane matsayi na taka a cikinsa? Ni wacece da zanyi abinda manyan ƴan jarida gogaggu suka gagara yi cikin sauƙi haka?”. “Ba cikin sauƙi bane Samraah. Sannan al'amarin ba iyawa bace ko kaiwa wani matsayi. Sa'a ce kawai kuma kowa da irin tasa a rayuwa. Nima ba ina ji bane wai lallai sai hakan ta kasance ba. Fata dai nake yi da jin yaƙinin zaki iya in sha ALLAHU”. Shiru kamar bazance komai ba, kafin kuma na sauke nannauyar ajiyar zuciya. Na ce, “Shike nan Sir zan gwada na gani, ai da gwaji jirgin sama ya tashi sama daga bisa ƙasa. Amma dai bani kaɗai ce zanje wajen ba?”. Ƴar dariya yayi a karo na farko, cikin tsokana ya ce, “Kada kice min ke ɗin matsoraciya ce mana. Bayan kuma kallon jaruma nake miki. Kallabi a tsakanin rawuna”. “Humm Sir bazaka gane ba. Irin waɗan nan mutanen da suke jin tamkar ma duniyar su suke mata alfarma ba itace ke musu na basu fili a cikinta ba suna kallon mutane ne tamkar wasu dodannin tsaffi a rayuwa. Dan a kullu yaumin zaka gansu ne zagaye da masu tsaro a kowacce kusurwa ta rayuwarsu. Ni gaskiya bana son ƙasƙanci koda a wajen wanda ya fini ne”. “Wannan itace ɗabi'a ta cikakken mutum ai Samraah. Duk wanda yasan darajar kansa haka ake so kuma ya kasance. Kada ki damu bake kaɗai zaki je ba. Hasalima ke aikin ki shine gabatar da shirin kawai. Akwai Davido da Mansoor da Khulsoom a tare dake. Yanzu sai kije ki tsara tambayoyin da zaki masa ki kawo min, ki nutsu sosai wajen tsarasun daga nan har zuwa Monday, kinga kinada kwanaki kusan huɗu kenan tunda yau muna alhamis. Kije da wannan mujallar domin duba abinda suka rubuta a kansa. Za kuma ki iya wani binciken a kansa ɗin dai koda ta hanyar yanar gizo ne ko wasu mutane. Hakan da zakiyi ne zai baki damar tsara abinda ya dace a kansa ɗin, dan ina fatan mu zama mune taurarin mako mai zuwa”. Ya ƙare maganar yana murmushi. Nima dai murmushin nayi, dan ya ba ni dariya. “In sha ALLAHU zanje nayi nazarin Sir. Maybe ma kafin Monday ɗin kaga na tura maka duk abinda na tsara ɗin koda ta WhatsApp ne”. “Masha ALLAH, ALLAH ya bada ikon hakan. Amma dai baki da matsala kibi komai a sannu tunda nunada kusan kwana goma kafin ranar”. “To nagode Sir”. Na faɗa ina miƙewa hannuna ɗauke da Mujallar. Harna fice a office ɗin ina jin idanunsa a kaina. A raina nace (Maye kawai sai dai kaci kanka kasha baƙin ruwa).......✍️ _Tofa masu karatu yaya kuke tunani akan wannan aiki da MD ya damƙama Samraah. Shin zata samu damar haɗuwa da wannan matashi mai wahalar sha'ani mai suna *Maash* ko kuwa?_. _Idan ma ta haɗu da shi ɗin taya zata iya abinda wanda suka fita faɗa aji da gogewa akan irin aikinta suka kasa?_. _Shin wai wanene ma *Maash* ɗin nan ne? Minene dalilinsa na gudun yarda ya bayyana asalinsa ga ƴan jarida. Miyyasa yake ɓoye kansa? Minene baya son a sani game da shi ɗin?_ _Duka wannan amsoshin suna a kundin littafin TSUTSAR NAMA... masu iya magana sunce wai ITAMA ƊIN NAMA ce. Kuzo ku mallaki naku domin jin abinda littafin zai zo muku da shi, domin kuwa ƙumshe yake da abubuwa masu ban mamaki, al'ajabi, makirci, soyayya, cakwakiya, zamba cikin aminci, tare da ɗan karan munafunci daga ɓangarori daban-daban._ *_In sha ALLAHU sayen nagari maida kuɗi gida😊😉😉😘😘🫡🫡._* ______________ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙_ .......Zaune na kai jagwaf a kujerar zamana ina dangwarar da mujallar da MD ya bani a desk ɗinmu. Mujallar Ruƙayya ta ɗauka tana faɗin, “Woow kaga wani handsome guy anan. Sam G daga ina haka? Waye shi?”. Baki na ɗan taɓe kaɗan batare dana amsa mata ba na shiga ƙoƙarin kunna computer ɗin gabana. Itama batabi takan jiran amsar tawa ba ta shiga karanta abinda ke jiki. Wata ƴar zaburowa tai da zazzaro idanunta waje tana faɗin, “Kutt Sam-G wannan ai Maash ne.” Duk ɗagowa sauran abokan aikinmu sukai suma suna kallonta. Sai kuma suka maido kallonsu gareni kamar yanda take kallona. Ganin na ɗauke kai tamkar bamma san mi sukeyi ba yasa suka sake maidawa kanta tare da miƙewa suka nufeta. Rufuwa sukai akan mujallar suna karantawa su duka huɗun, jin yanda duk suka nutsu yasa na ɗago na kallesu, batare da nace dasu komai ba na warce mujallar a hannun Ruƙayya. Ƴar harara na sakar musu ganin duk yanda suka ɗago suna kallona. “Malamai kowa ya koma kan aikinsa. Kun wani zauna karanta abinda bazai amfaneku ba.” Ƴar dariya Usman da Asiya da Khalid sukai, yayinda Ruƙayya ta balla min harara. Magiya Usman ya shiga min yana faɗin, “Sam-G Please ki bamu mu ƙarasa karantawa, anya kinsan kuwa wanene wannan na jikin hoton?”. “ALLAH bazan baku ba kuje kuyi aikinku, mi sanin nasa kuma zai amfaneni da shi da zan damu da so.” Magiya suka shiga mun nace bafa zan basu ba, dole suka haƙura suka barni badan sun so ba. Sai dan ayyukan dake gabansu. Nima nawa aikin na cigaba dayi batare dana sake bi takan mujallar ba. Haka muka cigaba da aikin gabanmu har lokacin tashi yayi. Tarkacena na shiga haɗawa domin wucewa gida aɗan gaggauce, dan nasan Mansoor na jirana. A karo na farko idanuna suka sauka akan fuskar mutumin dake jikin mujallar lokacin da nake ɗakkota zan saka a jakka. Duk yanda naso kauda idanuna hakan ya gagara, dole nai tsai ina kallon ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. Sam a zahirance baya kamanni da ƴan Nigeria ma bare Kano, duk da kuwa muma munada ƙyawawan fiye ma da kamarsa, sai dai kuma yanda hasken fatarsa yake tsaka tsaki dan bai wani yi haske dau ba zaka iya kiransa ko haif caste. Abu mafi ɗaukar hankali a fuskar tashi siririn baƙin gashin daya zagaye kumatunsa har zuwa haɓarsa ya kuma zagayo ta bakinsa ɗan ƙarami kamar ba namiji ba. Sam babu fara'a akan fuskar, sai hasken idanunsa dake a wani irin salo kamar na mai jin bacci. Abin mamaki tsakkiyar ƙwayarsu blue-blue zaiba-zaiba bansan yazan kirashi ba, ataƙaice kamar dai na mage ko masu jajayen kunne oho duk yanda kuka fassara. Sai cikakkiyar girarsa mai faɗi. Sosai na sake waro idanu lokacin da nakai dubana ga sumar kansa. Kitso ne guda huɗu akan nasa a kusan tsakkiyar kan dan ta gefe-gefe an aske sai saisayayyen sabon gashin daya kwanta luf-luf baƙi siɗik. Daga ta bayan kunnensa kam a dai-dai dokin wuyarsa zanen tattoo ne anyi fuskar zaki. Kunensa ɗaya manne da ɗan kunnen stone daketa wani irin sheƙi da ɗaukar ido kalar sky blue mai garai-garai kamar diamond. Wani wawan tsaki da ban san dalilin yinsa ba naja ina mai tura mujallar a bag ɗin. Dan sam nikam abin bai mun ba. Ɗan musulmi haihuwar arewacin Najeriya cikin Kano ne haka tamkar wani jinin yahudawa. Toni wannan tunda ma ba wani kama yake damu ɗin ba sosai ai gara ma a dinga jinginashi da ƙasashen ƙetaran mu bar musu kawai yafi, dan gaskiya aka bincika kam a cikin iyayensa akwai wanda ba bahaushe ba ko nace ma ɗan Nigeria gaba ɗaya. Da wannan mitar na fita a office ɗin, dan kusan ma nice ƙarshe su Khalid duk sun fice. Horn da Mansoor yayi min ne ya ankarar dani in da yake, da alama dama ni yake jira, dan ina shiga yayma motar key muka fice. Har muka fita a layin da station ɗinmu yake muka hau titi sosai babu wanda yay magana a cikinmu. Sai zuwa can Mansoor ya katse shirun namu da faɗin, “Madam duk gajiyar ce haka?”. Cikin ɗan yatsine fuska na ce, “Kawai dai”. Maimakon yaji haushi sai yay murmushi kawai, dan ya fahimci yau ɗin ƴan shiru-shirun ne a kaina. Dan ko ɗazu da muka haɗu dama bawani hira nayi sosai ba. Baiyi fushi ba ya cigaba da jana da hira, tun dai ina amsawa a sama-sama harna ware, dan akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanina da Mansoor. Muna a gab da isa anguwarmu na takalo masa maganar da Uncle yay min akan aure kamar yanda Yaya Musaddiq ya bani shawarar nayi. Kamar wanda ya ɗan razana ya kallan, sai kuma ya maida hankalinsa ga titi da sauri ganin nima shi nake kallo.. “Lafiya kuwa? Naga kamar ka razana?”. Murmushi ya saki tare da ɗan dubana, sai kuma ya gangara gefen titi ganin yanda duk na wani tsaresa da kallo. Sai da ya kashe motar da ƙyau ya juyo yana fuskantata. Ɗauke nawa idanun nayi daga kansa. Murmushi naji ya saki mai ɗan sauti, sai kuma ya fara magana a hankali. “Dole ne na razana ai Baby, dan farin ciki ne da yazo min a matuƙar bazata. Kema kin san tsahon lokacin dana ɓata ina fatan jin wannan furucin daga bakin ki. Taya yau na jisa ba zanji kaɗuwar farin ciki ba. Ki godema ALLAH ma da ban saki kan motar mun daki fitila ba. ALLAH na gode maka da ganin wannan rana a gareni, ni Mansoor zan mallaki TAURARUWAR MATAN DUNIYA”. (🤥Ni dai banda ni eh🥱). Murmushi ne ya suɓuce min, na kauda kaina gefe inayi duk da kuwa akwai facemask a fuskata, harma da eyeglasses dakan ƙara fiddo tsarin ƙyawuna a duk sanda na saka shi. Ganin murnar tashi bazata ƙare ba ga shi lokaci na tafiya murya can ƙasa-ƙasa na ce, “Please ka tada motar nan magrib fa zai yi”. “A'a Madam, barni na gama murnata dan ALLAH. Mansoor ne fa zai mallaki Samraah Gwarzo. Wani shagalin ma ai sai naje gida hajjaju”. “To nidai kaini gidan, idan kaje sai ka cigaba dayi”. Da ƙyar na samu ya tada motar muka tafi, bakinsa baiyi shiru ba har muka ƙarasa. Nidai na sungumi bag ɗina na fice ina cemasa sai da safe. A falo na iske duk mutanen gidan. Amma babu Hafizzullah da Abbas, da Nabel, hakama Abba da alama bai dawo ba shi da Yaya Musaddiq. Koda yake shi dama Yaya Musaddiq sai kai ma wata baka gansa zaune a falon nan ba. Iyaka ya shigo ya gaida Abba da dare, daga haka ya koma ɗakinsa, abincin gidan ma yakan daɗe yanzu bai cisa ba duk da nauyin kawowa ta dawo kansa badan kuma Abban ya rasa ba sai dan haka Mum ta tsara ayi. Mum ta watso min wata muguwar harara da ta sakani tura baki ta cikin mask ɗina. Batare dana sake kallonta ba nace “Mum good evening”. “Ko kuma good uwarki ba”. Ta amsa a fusace. Dariya sosai Baby da Bibaa suka kwashe da shi. Sai autansu dake ta aikin homework ɗinsa kamar ma bai san abinda ake a falon ba. Tsawa ta daka min kan nazo. A hankali na nufi gabanta na durƙusa, bamma gama kaiwa ƙasa ba naji saukar lafiyayyen mari daya nema gigitani, dan har eyeglasses ɗina sai da ya faɗi. Idanun kawai na rumtse da ƙarfi, sai dai naƙi yarda hawayen da suka ciko min ido su zubo. A fusace ta ce, “K dan uban uwarki har ni zan sakaki aiki ki tafi sabgar gabanki ki bar min?”. Karo na farko na ɗan kalleta. Cikin danne kukan dake neman kufce min na ce, “Mum wlhy duk abinda kikace nayi ban tafi ba sai da nayi sa”. “Oh ƙarya nake miki ke nan ko? Miyar da kika bari akan wuta uwarki ce tai fatalwa ta ƙarasa min?”. Wani irin rumtse ido na sake yi ina cije lips. Babu abinda kemin ciwo a duniya sama da zagin iyayenmu da Mum kanyi. Kuma in har tayi hakan bana iya daurewa sai na mayar mata da murtani. Yanzun ma hakance ta kasance. Dan cikin kaushin murya da tsiwa na ce, “Mum ai kunsha tubarraki kenan, dan nasan duk abinda zai fito daga Ummie na mai albarka ne, to balle kuma ace fatalwarta, ai nasan albarkar sai ta ninka ma. Bara naje nai salla na sake mata addu'a dan gobe idan zatazo a fatalwar ta dafa mana har abincin ba ƙarasa miya kawai ba”. Ba Mum ɗin ba hatta su Baby sagade sukai suna kallona. Nikam ko'a kwalar rigata na miƙe tsam. Batare dana yarda na kalla kowa a cikinsu ba na nufi hanyar ɗakinmu ni da su Bibaa, dan Baby tun muna yara tace bazata zauna dani a ɗaki ɗaya ba. Hakan yasa aka haɗani da Bibaa da auta. Nasha wahalar yaran sosai, dan dukkan nauyinsu kaina ya koma, ga fitsarin kwance. Dole nabar musu katifar na dawo kwana ƙasa saman tabarma. Bayan na fara zama budurwa nazata za'ace nabar cikin yaran na koma ɗakin Baby, amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Sai ma wani sabon salon iskanci da ita Bibaa kan min yanzu, wai ita tana takura gaskiya a ɗakin dan munyi yawa. Ban taɓa cemata komai a kan hakan ba dai, dan fatana ma a yanzu Mansoor ya fito kawai ayi auren mu a wuce wajen. Shima Yaya Musaddiq yay nasa Hafizzullah ya koma gidansa ba shike nan ba mun bar musu gidansu........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒆𝒗𝒆𝒏_ .......Ina shiga ɗaki kukan da banyi ba a gabansu ya kufce min. Ban yarda nai zaman yinsa ba, na zame kayan jikina kawai na nufi bathroom. Tsayawa kawai nai ina kallon bayin raina a matuƙar ɓace. An masa kaca-kaca tamkar banyi wahalar gyaransa ba kafin na wuce. Nasan Bibaa ce tai masa haka. Dan tsabar iskanci har pad data cire guda biyu ta yasar a bayin da pants ɗinta. Inada ƙyanƙyami sosai a rayuwata, dan abu kaɗan ke ɗagamin hankali, shiyyasa ma nake bugar jikina na tsaftace gidan yanda ta kamata batare da jin ƙyashi ba. Hawaye tab da idona na shiga gyaran bayin, sai da na maidashi ƙal na tattara trash ɗin data tarama mutane na fitar. Har lokacin suna a falon zaune suna kallo har Mum ɗin, kai kace basu ji sallar magrib da akeyi ba. Na jima da fahimtar Mum saita gadama take salla, shiyyasa ƴaƴan nata ma dai gasu nan sai a hankali babu wanda ya damu da ibadar. A da Hafizzullah har ya fara ɗaukar ɗabi'ar, sai da na miƙe kansa ni da Yaya Musaddiq tamkar bama ƙaunarsa sannan. Sake zuwa nai na wucesu na koma ciki. Sai da nayi wanka na saka doguwar riga mara nauyi nai salla. Bayan na idar zaman yin karatun Alkur'ani nayi, ban ɗaga a wajen ba sai da akai isha'i, har lokacin kuma ina jiyo hayaniyarsu a falon, sallar dai bazasu tashi suyi ba. Falon na fito na wuce dan ɗaukar abinci na, amma sai na samu wayam. Banyi ƙasa a gwiwa ba na dawo ina tambayar Bibaa. Wani kallon banza yarinyar ta watsa min duk da kuwa na bata kusan shekara bakwai zuwa takwas, dan kwata-kwata yanzu take a shekara ta goma sha uku, a gadarance ta ce, “Kin bani ajiya ne. Ka jimin rainin wayo dan ALLAH mtsowww!!” ta maida kanta ta cigaba da abinda take yi. Bance komai ba na juya na koma ɗaki, dan hakan da tai na nufin yau banda abinci a gidan tunda na tafi aiki ban kammala miya ba, bayan kuma nayi komai har abinda ba'a sakani ba, miyar ma na barta ne kawai ta gama fidda mai dan karna makara tunda ta soyu. Wajen kwanciyata nakai zaune ina hawaye, dan haka kawai yau naji zafin abinda akai min ɗin duk da bawai yau ɗinne farko ba, amma kasancewar na dawo da yunwa sai abin ya zafeni. Tun muna yara idan Mum ta bushi iska takan hanamu abinci, haka Hafizzullah zaita kukan yunwa dan ni da Yaya Musaddiq mukan daure, ko zaiyi kukan mutuwa kuma bazata bashi ba sai dai Yaya Musaddiq ya fita ya samo masa a waje koda da bara ne, yanzu kam da muka girma idan aka hanamu zai sayo ya jamu ɗakinsa muci mu ƙoshi muna hirarmu. Sai kuma hakan ke ba Mum haushi take kai ƙararmu ga Abba wai muna haɗe kai muyita zaginta a ɗakin Yaya Musaddiq. Wani lokacin Abban kan mana faɗa, wataran kuma ya mata shiru, sai dai ta ƙaraci masifarta ita kaɗai. Ganin zaman bazai amfaneni da komai ba na miƙe ina share hawayena. Ƙaramin hijjab ɗina na zaman gida na ɗauka na saka, na ɗauki jakata dana fita aiki da ita na fito. Suna a falon har yanzu suna kallo, banko kalla kowa ba a cikinsu na fita zuwa ɗakin Yaya Musaddiq. Sai da na ƙwanƙwasa tare da yin sallama ya bani izinin shiga sannan na shiga. Tashi yay daga kwancen da yake a tabarmar barcinsa, dan koya sayi katifa amshewa Mum take ta bama su Bibaa su kasheta da fitsari ko a bama su Abbas. Kusan sau uku tana yin hakan shiyyasa ma ya bar saya shima. Murmushi yay min yana mai bina da kallo, na ɗan tura baki gaba ina zama a gefensa da ajiye jakar kamar a yanayin gajiye. Yaya Musaddiq mutum ne mai sauƙin kai sosai, da wahala ka iya ganin fushinsa a zahiri. Cike da kulawa ya ce, “Kandala miya faru kuma ake kumbura wannan cat face ɗin?”. Sake tura bakin nayi da faɗin, “Ni ba komai, yunwa nake ji”. Ɗan jimm yay yana kallona, sai kuma ya ɗauke kansa da sauke ajiyar zuciya ya miƙe. Rigarsa ya ɗauka ya saka a saman singlate ɗin jikinsa. “Ki jirani ina zuwa”. Kaina na jinjina masa ina kaiwa kwance a tabarmar tasa. Yana fita na ɗan lumshe idona. Kusan minti huɗu ina a haka sai kuma na miƙe zaune. Jakar tawa na jawo gabana, tare da zuge zip na ciro mujallar nan da MD ya bani ɗazun. Yanzu kam kai tsaye na zubama mujallar ido, sosai nama mutumin kallon ƙurilla a karo na biyu, badan baiyi haske dau irin na larabawa da indiyawa ba da tabbas zan iya cewa daga cikinsu ya fito. Dan daga suffar jiki har zuwa ta halitta fuska bai yi kama da ƴan Nigeria ba. Sai dai kuma abin mamaki fatarsa zamu iya cewa irin tamu ce. Duk da kuwa ba baƙi bane wulik, idan ma za'a kira farare za'a iya nunashi mu anan Africa, sai dai kuma farin nashi yasha banban, koda yake maybe camara ce ta maida shi hakan. Sake maida idanuna akan kitson kansa dake ɗaure a tsakkiyar kai kamar wani mace, sai kawai naja sirrin tsaki, banda ƙarshen duniya dai ace namiji da kitso da ɗan kunne. Kai ALLAH ya ƙyauta, inaga dai ɗan daudu ne gaskiya. Dangwarar da mujallar nayi gefe na sake komawa nai kwanciyata. A dai-dai nan Yaya Musaddiq ya shigo ɗakin da sallama. Amsa masa nai ina tashi zaune. Ya ajiye min ledar hannunsa yana faɗin, “Oya tashi kici”. Babu musu na tashi zaune, ina ƙoƙarin buɗe ledar shima yana kaiwa zaune ya ɗauki mujallar. “Tofa! Ke kuma ina kika samo _Maash_ haka kandala?”. Baki na taɓe da fara kai lokar indomie ɗina. Kafin na ce, “MD ɗinmu ne ya bani yau wai zanyi aiki a kansa”. “Aiki kuma?”. “Eh Yaya, so suke wai nayi hira da shi a ranar bikin buɗe Companyn sa”. “Kai lallai sun haɗaki da aiki. Amma ALLAH ya bada nasara”. “Amin” na amsa masa ina sake jin karaya. Sai kuma na kallesa, batare da nasan ya akai bakina ya suɓuce ba na ce, “Yaya amma dai shi ba musulmi bane ba ko? Sannan ba ɗan Nigeria bane?”. Sosai ya waro idanu waje da faɗin, “Kai! K waye ya gaya miki ba musulmi bane?”. “To Yaya wane musulmi ne zai zauna ai masa kitso a saman kai ya ɗaure haka kamar wani mace. Ga ɗan kunne kuma a kunne ga tattoo a wuyansa. Sannan kalli idonsa kamar na mage fa. Ni wlhy banji ya birgeni ba abu kamar ɗan daudu”. Dariya Yaya Musaddiq ya saki yana girgiza kansa. Ya ce, “Banda abinki Samraah dan mutum yayi duk wannan sai a fiddashi a musulunci ko a kirashi ɗan daudu. Wannan abun da kika gani yanzu shine samari suka ɗauka matsayin gayu da wayewa wai, baki ganin kuma shi ɗin mai lokaci ne da duniya ke ji da gani. Idan kuɗi na ɗibar mutum ai komai ma sai ya yi ba komai bane. Sannan shi ɗin kamar ance ruwa biyu ne. Tsakanin kakansa da kakarsa akwai wadda ba ɗan Nigeria ba, anan ma ya kwaso waɗan nan kamannin da kowa ke ganin ba ɗan 9ja ɗin bane ba. Amma asalin mahaifinsa ɗan kwanar Mashi ne ma, Kinga kuwa shi cikakken bakano ne, anan ma aka haifesa shi”. Baki na taɓe akan maganar yaya ta kusan ƙarshe, sai kuma na ce, “Humm, to ALLAH ya rabamu da irin wannan kuɗin masu mantar da bawa shi waye kuwa. Ni yanzu Yaya yaya zanyi to. Wlhy duk kaina ya gama kullewa fa?”. “Karki damu in sha ALLAHU zamu samo mafita. Ke dai kawai ki saka a zuciyarki zaki iya. In dai shi ba aljani bane nasan duk taurin kan Maash bazai gagari Kandalata ba ai. Dan itama tauriƙiƙin kantace ga naci akan abinda tasa gaba”. Dariya na ƙyalƙyale da shi da faɗin “Kai yaya?” Ya ce, “ALLAH ai nasanki ne fiye da yunwar cikina kandala”. Nanma dariyar nayi shima yana tayani, tuni Yaya ya mantar dani baƙin halin mutanen gidanmu. Ya kuma bani ƙwarin gwiwa sosai data bani karsashi akan tunkarar wannan aiki da MD ya bani, ban baro ɗakin ba sai da na fara hammar barci.... Washe gari ban ɗaga ko tsinke ba a gidan, dan banma tashi a barci ba sai ƙarfe bakwai. Salla nayi nai wanka nai shirin office nai tafiyata, dan har lokacin babu wanda ya tashi suna can suna barci ana jiran jaka ta gama girkawa a fito a ci. To ai na fisu iya tsiya, dan kamar yanda na saba in har aka gunziga min baƙin ciki a gidan sai na maida murtani. Yaya Musaddiq bai san tsiyar dana shuka ba ya ɗaukeni muka wuce a mashin ɗinsa. A hanya nake roƙonsa wannan weekend ɗin muje muga Hafizzullah a Katsina dan ALLAH idan baida aiki da yawa. Bai musa ba yace min in sha ALLAHU zamuje ranar asabar sai mu dawo lahadi. Sosai naji farin ciki, harma na manta da damuwata balle na sanar masa banyi breakfast ba na gudo yau. Yana sauke ni ya miƙamin 1500. Amsa nayi ina masa godiya da yima iyayenmu addu'ar samun rahama. Daga haka na shige shi kuma ya wuce. Kasancewar yau inada gabatar da program banfi zaman mintina talatin ba na tashi na fita tare Khalid. Kusan cin karo mukai da Mansoor dake ƙoƙarin fitowa. Baya naja da sauri, sai hakan ya sakani tuzguɗewa na tafi zan faɗi. Kusan tare suka kawo hannu shi da Khalid domin taimaka min, niko nai saurin sake maida jikina baya ta yanda kowannensu bai samu damar taɓanin ba, dan na gwammaci na faɗin kawai. Aiko faɗuwar nayi, na kuma ji zafi sosai, duk da kuwa na fuske Mansoor sai da ya fahimci hakan. Cike da damuwa yakai duƙe gabana tare da sake kai hannu zai riƙo nawa na ɗan hararesa. Murmushi kawai yay ya janye hannunsa yana kaisa saman kansa ya shafa cike da basarwa. Sai kuma ya sake maida idonsa gareni, a hankali ya ce, “Yanzu har kina da damar yin masifa babie. Naga dai hannun ai nawa ne”. Sake hararsa nayi tare da ɗauke kai ina ɗan murguɗa baki, na ce, “Sai ka bari sai ka biya ai”. Ina kai ƙarshen maganar na miƙe abina. Dariya ya saki mai sauti da faɗin, “Rigimammiya kawai ai saura ƙiris dai, mi kike ci na baka na zuba. Wata uku bazaki ƙaraba sai da igiya uku na ciff a kanki”. Murmushi kawai nayi ina ɗan murguɗa bakina dake cikin face mask ɗina na wuce na barsu a wajen Khalid na tayasa dariya. Sai da na gaishe da kowa kafin na wuce na ɗan ƙara gyara fuskata gaban mirror, suma su Mansoor sun shigo, dama mu zaije kira ashe. Hakama baƙonmu na yau ya iso tuni, dan haka babu ɓata lokaci aka fara gabatar da program ɗin........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒊𝒈𝒉𝒕_ __________________ Kuzo na kawo muku cookbook me recipe sama da 60 a farashi mai rahusa, kunsan azumi ya gabato ya kamata adinga canzawa Habibi abinci. Kar a dinga bawa maigida kullum doya da kwai, ko chips, nace ko kin san zaki iya sarrafa dankali ya baki sama da abinci kalla 5, kin iya? Ko de kullum chips kike bawa habibi? To ga cookbook na kawo ki zo ki saya ki saye zuciyar maigida ga kuma drinks and smoothie's shima kalla kalla, kai har da bonus din yadda zaki iya homemade yogurt and mayonnaise. Wannan cookbook din zaku same shi a farashin 2k amma first 10 people zasu bada 1k each. https://wa.me/message/MLUBB6FMKURYH1 __________________ .......Yau ma kamar kullum Mansoor ne ya ɗaukeni zuwa gida bayan an tashi. Mun ɗan fara tafiya nake sanar masa aikin da MD ya saka ni. Da mamaki ya juyo yana kallona da faɗin, “What! Dama ke ya bama aikin nan? Taya zai haɗaki da wannan aikin mai wuya bayan yasan wanene wannan mutumin. A tarihinsa fa bai taɓa yarda yayi hira da ɗan jarida ba har yanzu. Kuma karki ɗauka wai ƴan jaridar nan gida Nigeria kawai. A'a har manya-manyan ma irinsu BBC, VOA, Aljazeera da ire-iren su. A duk sanda aka buƙaci hira da shi sai ya haɗa mutane da P.A ɗinsa...” “Hu'umm, to amma shi miyyasa yake yin haka? Kamar ba wayayye ba? Ko kuma bashi da gaskiya ne shiyyasa yake gudun hakan?”. “To ALLAH kaɗai masanin gaibu, sai kuma shi da ya barma kansa sanin dalilin. Amma dai wasu na ganin girman kai ne kawai da giyar kuɗi dake ɗibarsa. Dan a yanzu fa shine matashi ɗan kasuwa na biyu a duniya dake juya manyan kuɗaɗe, anama hasashen nanda shekara mai zuwa zai iya zama na farko. Wasu kuma na ganin akwai dai wani babban dalili nashi, dan in har da girman kai ne ai zaiso ƙara bayyanama duniya shi ɗin wanene ta hanyar ƴan media ɗin. Wasu ko na ganin ko dodon tsafinsa ne yace kar yay hakan, kin san dai mafi yawan ƴan kwasuwar nan dake shahara a ƙanƙanin lokaci sai a hankali, shiyyasa ake yawan ɗora musu zargi, ALLAH dai masanin gaibu. Amma gaskiya al'marin dai nasa akwai ɗaure kai”. “Ƙila to aljanu ne da shi da basa son hira da ƴan jaridar. Ko kuma dai da gasken dodon tsafinne da shi. Dan ni naga yanda kowa ke misalta dukiyar tasa akwai ban tsoro kam”. Na faɗa cikin halin ko in kula. Dariya sosai Mansoor ya sanya, tare da faɗin, “Kai Babie baƙya rabo da wauta ALLAH. Aljanu kuma? Namiji da aljanu? Adai tsaya a dodon tsafin”. “To inba aljanu ba shi kam ai abin nasa yayi yawa, dodon tsafin ma kuma ai aljanu ne. Yanda yake nuna kansa a matsayin wayayye irin haka ai ya kamata ace an wuce wannan ajin. Amma ni kam in sha ALLAHU sai na sakashi ya magantu, ni halin nasa ma sai ya ƙara min ƙwarin gwiwar tunkararsa.” Sosai Mansoor ya juyo ya kalleni cikin nuna mamakinsa a fili. Sai kuma ya maida kansa ga titi yana faɗin, “Anya yarinyar nan kin san wanene *_MASH!?_* kuwa? Babu sauƙi fa a ɗaukar wannan alwashin naki. Ni dai ina gargaɗarki da kar kiyi wani abu mara ƙyau dan ALLAH. Idan kin samu dama kamar yanda kowa ke fata fine, idan baki samu ba ba faɗuwa bace. Dan haka be careful sweetie. Kar ki biye ta MD kujerarsa kawai yake yunƙurin saitawa”. “Karka damu, ni ba wani abu mara ƙyau zanyiba ALLAH. Kuma duk ma tambayar da zan masa ai sai na kaima MD ɗin ya duba. Kaima kuma zan baka ka gani kafin ma na turama MD ɗin har ma Yaya Musaddiq. Kawai dai ina fatan karya masa wannan alfaharin nasa ne”. Kansa ya jin jina min, ya ce, “To ALLAH ya bamu sa'a, dan zanfi kowa kasancewa a farin ciki ace kece kika karya ɗin kam. Dan har ƙyauta sai na miki na musamman”. “Tami?”. “A'a ai ba sai na faɗa ba. Yanzu dai ajiye ma wannan batun. Su Alhajina fa zasu zo wannan weekend ɗin. Dan haka yau ina buƙatar ganawa da Abba yaya za'ayi kenan”. Da sauri na juyo na kallesa, ya jinjina min kai alamar tabbatarwa. Kaina na ɗauke cikin jin kunya, sai dai wani irin farin ciki ne ke ratsa ƙashina da ɓargo har ina jin yanda jikin nawa ke rawa. Amma dai nayi juriyar dakewa. Sai dai ban sake cemasa komai ba har muka iso. Tunda ya tsayar da motar na kasa wani motsi, mun kai minti biyu a haka shi kuma yana kallona kamar ya samu tv kafin ya saki ɗan murmushi mai sauti. “Wai kunyar ce dai Babie?”. Sake kauda kaina nayi gefe batare dana bashi amsa ba. Ya saki ƴar siririyar dariya yana ɗan dukar sitiyari, sai kuma ya juyo gareni yana faɗin, “ALLAH ya kaini randa zan cire wannan kunya dai kowa ya huta, dan bazanyi sakaci ba a daren farko zata kama gabanta. Anya baki haɗa jini da fulani ba Samraah”. Hannu na kai ga handle ɗin ƙofar zan buɗe na gudu sai na jita gam alamar ya saka lock. Kasa sake wani yunƙuri nayi, na kuma kasa juyowa dan har lokacin ina jin kallon ƙurullar da yake min. “Kayi haƙuri ka buɗemin, zancen ganin Abba kuma ya kamata ka fara ganin Yaya Musaddiq dai first nake ga”. Sosai ya sauke numfashi mai nauyi, sai kuma ya amsa da, “Okay hakan ma yayi, zan bari to sai gobe in sha ALLAHU na samu Yaya a gareji”. Daga haka ya buɗe min. Wuff na fice abina kuwa. Batare da ko sallama nayi masa yau ba na shige gida, har lokacin kuma ina jin idanunsa a kaina. Ina rufe ƙofar gate ɗin na jingina a jiki ina sauke numfashi, sai kuma na kai hannuna saman ƙirjina da ke bugawa da sauri-sauri. Murmushi na saki kafin na buɗe idanuna a hankali na ɗan leƙa gate ɗin naga ko ya wuce. Sai lokacin naga yana ƙoƙarin yin reverse. Bazan ɓoye miki ba ina matuƙar ƙaunar Mansoor wlhy Bilyn Abdull, soyayya nake masa mai ƙarfin gaske da bama zan iya misaltata ba, dan Mansoor ya mun abubuwa na halacci da dama akan soyayya da bazasu iya ƙirgiguwa ba, na tabbata da aure kawai zan iya masa godiya a kansu amma bada fatar baki ko soyayyar saman titi ba. Cikin gidan na shiga kamar yanda na saba, sai dai acan ƙasan raina ina ɗan jin tsoro-tsoro. Sosai na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ganin ban samu kowa a falo ba yau. Zuruf na shige ɗakinmu, in da na tarar da Bibaa kawai tana kallo a wayarta. Yanda bata amsa ko sallamata ba nima ban sake bi takanta ba. Wanka na farayi duk da kuwa cikin ƙyanƙyamin bayin nai haka, dan yanda ban wanke ba haka Bibaa itama bata wanke ba, sai ma datti da suka ƙara masa. Gudun kar lokacin sallah ya wuce min yasa ni saka doguwar riga kawai na saka hijjab na tada sallar. Na kai raka'a ta biyu ina sujidar ƙarshe kawai naji saukar duka kaina. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un wata irin azabace ta ratsa ni, amma na daure sosai na cigaba da sallata. Abinda kuma zai baki mamaki ba'a daina dukan nawa ba har na idar. Karo na farko kenan dana ɗaga hannu sama ina kuka da neman sakayya wajen UBANGIJI na, ina ƙoƙarin shafa addu'ar dai dai nan Abba ya shigo kamar wanda aka jeho. “Haba Jalilah minene haka? Baki da hankali ne tana salla kina dukanta”. Ya faɗa a matuƙar hasale yana riƙe bulalar. Basu ba hatta ni sai da na shiga shock, dan nidai nasan ba yau ne karan farko da Mum take dukana ba a gidan nan. Hasalima ta dakeni a gabansa a lokuta barkatai amma bai taɓa cewa komai ba. Bama ni ba, hatta da Yaya Musaddiq yasha shan duka a wajen Mum, yanzu ne dai ta daina sai zaginsa da baƙar magana. Hakama Hafizzullah, sai dai duk ni na fisu shan wahala kasancewar akoda yaushe ni ina cikin gida a tare da su.... Mum ce ta katse min tunani na, dan cikin hargagi ta hayayyaƙo ma Abba a gabanmu. Idan ni bazata ji nauyina ba ai ya kamata taji nauyin su Babie kasancewar sa na mahaifinsu. Amma ko'a kwalar kwagirinta. Dan sai da takai ya koma bata haƙuri da lallashinta. Ni al'amarin nasu ma sai ya nema fasan kaina dan al'ajabi. Haka dai ya jata da ƙyar suka fice a ɗakin. Harara Baby ta watsa min da faɗin, “Shegiya mayya. To kurwar iyayenmu kur wlhy. Kuma indai Mum ce kaɗan ma ta miki wlhy, bari dai Abban ya fita duk da ma ko yana nan zata iya cigaba da cin ubanki, yanzu ɗin ma ta ƙyaleki ne kawai kiji da wannan tsamin jikin mtsowww makwaɗaitan banza da wofi anzo an cika mana gida an hanamu rawar gaban hantsi”. Daga haka ta fice kamar iska zata ɗibeta. Dan sam Baby bata da wani jikin kirki, ta girman amma na fita cikar halittar jiki sosai, wanda ma bai sani ba sai ya ɗauka nice babbarta. Sai da suka gama zageni tsaf ita da Bibaa suka fita sannan na fashe da kuka, dan illahirin jikina raɗaɗi yake min sosai. Da ƙyar na iya tashi na zare hijjab ɗina, abinka da farar fata wasu wajen ma har sun fashe. Cikin ƙanƙanin lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufeni, haka na kwana ina makyarkyata ga ciwon jiki. Duk kiran da Yaya kemin a waya ban ɗaga ba, har ya gaji ya daina kiran, nasan dai ya zata ko barci nayi ne... Humm wato Bily inada taurin kai fiye da yanda kike tunani. Zaki sha mamaki idan nace miki washe gari ma duk da dukan da naci haka na sake tsallakewa nai tafiyata wajen aiki batare dana ɗaga ko tsinke a gidan ba. Nasan dai nabar ƙura sosai, amma ko'a jikina nai gaba batare da na jira ko Yaya Musaddiq ba yau. Sai wajen 12 sai gashi yazo lokacin ina kwance zazzaɓi ya addabamin. Ruƙayya ce data lura da haka ta matsa min nasha paracetamol da ƙyar. Da Yaya Musaddiq ma yazo itace tazo ta kirani dan ta ɗan fita taci karo da shi shine tazo ta kamani muka fita. Kallo ɗaya na masa na duƙar da kaina. Dan sosai naga ɓacin rai tattare da shi. Sai dai shima yanayin da ya ganni naga ya ɗan raunana fushin nasa, dan muna isowa inda yake sosai naji ya sauke ajiyar zuciya yana mai furzar da huci mai zafi.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑵𝒊𝒏𝒆_ ........Sai da Yaya yayma Ruƙayya dake shirin barin wajen godiya sannan ya juyo gareni. Kallo ya ƙare min daga sama har ƙasa sannan cikin yanayin fusata ya ce, “Miyasa kike da taurin kai ne wai Samraah?. Yanzu ga abinda kikayi jiyan wace riba kikaci tunda kinfi kowa sanin halin matar nan?. Amma ke da yake ba'a taɓa faɗa miki kiji shine yau ma kika kuma. To ai gashi nan ta sake ƙulla miki sharri kala-kala ita da yaranta. Tun ɗazu ina gidan basu barni na fito ba sunata min masifa akan wai ni nake sakaki. Har Abban na saka sharaɗin ko dai ki ajiye aiki ki dawo ki cigaba da aikin gidan ko kuma ya aurar da ke ga wa wanda ita Mum ɗin ta kawo. Idan yaga shi zai barki yin aiki ki cigaba, amma albashinki dolene kema ki dinga rabawa biyu daga yanzu kina basu rabi ana haɗawa ayi cefane. Nama kawo masa batun Mansoor yaƙi ya saurareni sam. Wai shi bai san da wani Mansoor ba kuma bazai aura masa ke ba, wanda Mum ta kawo kawai ya sani kuma shi zai bawa dan yaron nada tarbiyya sosai, kuma shi ya gamsu da hakayensa....” Kuka na sakar masa mai taɓa zuciya. Hakan ya sakashi yin shiru ya gagara cigaba da magana ya zubamin ido kawai. Kusan mintuna uku ina kukan sosai kafin ya kai zaune kusa dani. A jikinsa ta gefe ya sakani kawai shima hawayen na cika masa ido. “Amma kin san bana son kuka ko Samraah”. Ya faɗa muryarsa na rawa. Ɗagowa nai a karo na farko ina kallonsa. Sai kuma na sake fashewa da wani sabon kukan ganin yanda idanunsa suka kaɗa sukai jazur gasu cike da hawaye. “Yaya ya kake so nayi, shike nan haka zamu lalace a yima waɗanda basu taɓa jin tausayinmu ba biyayya. Kullum burin matar nan wulaƙanta mu, Yaya tun fa ban isa iya aiki ba nake bautar gidan nan, amma ko sau ɗaya ba'a taɓa min adalci ba idan nai kuskure a yafe min. Kullum kuma a banayi nake. Su Baby na kwance. Yaya na gaji wlhy, ji nake kamar na gudu na bar gidan nan kawai....” “Shiii!!! Karna sake jin irin wannan maganar a bakin ki. Samraah ai wuya bata kisa. Da ace tana yi wlhy da bamu kai haka a rayuwa ba. Duk can baya baki ƙosa ba sai yanzu da aski yazo gaban goshi. Kwana nawa ma ya rage miki a gidan. Bama ke ba da kike mace zaki tafi gidan aure hatta ni da Hafizzullah in sha ALLAHU mun kusa bar musu gidansu. Gara kawai na tada gini na kamar yanda kike bada shawara mu koma can kawai. Amma dan ALLAH ina roƙonki kada ki sake maimaita abinda kika faɗa yanzu. idan kin gudu ina zaki? Ki daure ki cigaba da musu abinda suke so. Watarana sai labari ai. Maganarki kuma da Mansoor na yanke shawarar zuwa wajen dangin mahaifinmu, duk da sun watsar damu basu taɓa waiwayen mu ba tunda ɗan uwansu yabar duniya zanje na roƙesu su shiga wannan maganar a baki wanda kike so tunda dama sune ai da wannan alhakin ba Abba ɗin ba. Ki tashi kuma muje asibiti dan jikinki akwai zazzaɓi sosai.” Ɗagowa nai zanyi magana ya girgiza min kai alamar kar nace komai. Dole na haɗiye kuwa. Ruƙayya ya kira da wayata, yace ta tattare masa kayana dan ALLAH. Cikin mintuna kaɗan ko sai gata. Da taimakonta muka fita inda mashin ɗinsa yake. Ta taimaka min na hau muka wuce dan Mansoor yau baizo office ba sunje wani aiki Jigawa. Sai da muka fara tsayawa a camix aka dubani kafin mu ƙarasa gida dan nata roƙonsa kan bazanje asibiti ba, sanin da yay min na ƙin jinin asibitin shima yasa ya barnin mukaje camix ɗin kawai aka bani magani. Kamar yanda Mum ta shirya cin ubana shima Abba ya shirya hakan yau, sai dai a yanayin da Yaya ya shiga dani gidan ya saka jikinsa yin sanyi shi. Dan Mum ta fara min tujara da ƙoƙarin kai mari ya dakatar da ita. “Uhm Jalilah inaga ya kamata ayi hakuri ai, baki kula da halin da take a ciki bane? Kiyi haƙuri harta warke ni da kaina zan sauke mata taurin kan nan nata nayi miki alƙawari”. Wani shegen kallo ta watsa masa a fusace. Kamar zatayi magana sai kuma mita tuna oho tai shiru. Fuuu ta wuce bedroom ɗinta ta barmu tana faman huci. Wannan zazzaɓi dai shine ya ceceni a wannan rana. Washe gari kuwa duk da weekend ne asubar fari Mum tazo ta tadani. Bata damu da yanayina na har lokacin ban gama dawowa dai-dai ba. Nima sai bance mata komai ba na tashi na hau aikin da take buƙata, dan kwana biyun nan fa da banyi komai ba haka gidan yake zaune kaca-kaca. Kafin takwas na safe har brackfast na kammala haɗawa, na ɗauki na Yaya Musaddiq na kai masa. Na samu ya kammala shirin wucewa Gwarzo kamar yanda ya faɗa zaije. Ba haka naso ba, dan naso ace munje munga Hafizzullah kamar yanda muka tsara. Zama nai muka karya tare yana ƙara lallashina da mun nasiha, jinsa kawai nakeyi, dan gaskiya bazan iya haƙurin wani abun ba in har nayi wani. Amma dai zan rage taurin kan kodan shi. Ban bar ɗakin ba sai da ya ƙarasa shiryawa muka fito tare, yau zai dawo, amma ya musu tsaraba. Ciki na koma na samu mutanen gidan gaba ɗaya a falo zagaye da Abba. Sai dining dake kaca-kaca sun gama karyawa amma babu wanda ya iya kawar da ko cokali. Abban na gaisar, ya amsa min babu yabo babu fallasa, itako Mum bama ta amsani ba. Ban damu ba dan ba yau na fara ganin hakan ba ai daga garesu, na nufi ɗaki da nufin yin shirin islamiyya da nake zuwa duk weekend Mum ta dakamin tsawa. “K dan ubanki waye zai kwashe miki waɗan can kayan”. Ɗan jimm nayi a tsaye zuciyar na yunƙurowa, sai dai nasihar Yaya Musaddiq dana tuna ta sakani komawa cool. Batare da nace mata komai ba na nufi dining ɗin na shiga tattare kayan. Sauri-sauri na wankesu na fito, har yanzu suna a falon, ɗaki nai wucewata na shirya, na sake fitowa dai na samesu. Da harar Mum na fara cin karo, ɗauke kaina nayi kamar ban ganta ba, a ladabce naje gaban Abba na duƙa. “Abba zanje islamiyya saina dawo”. Kansa kawai ya jin jina min ya cigaba da kallonsa. Nima sai na miƙe. Mum dake watsamin hararace tai saurin faɗin, “Ya kake bata damar tafiya Abban Abbas, idan ta tafi ubanwa zai mana girkin rana? Islamiyya take zuwa ne ba yawon iskancinta ba”. Ƙoƙarin ficewa nake da sauri dan nasan zai iya dakatar dani. Amma a mamakina sai naji yana faɗin, “Baga su Baby nan a gidan ba suyi girkin su mana tunda sun ɓarar da tasu islamiyyar su....” daga haka ban ƙarasa jin abinda yake faɗaba nai wucewata ina murmushi. Wani lokacin idan Abban yay abu sai kaga kamar mai mutunci. Koda yake dama ba laifinsa bane ba, zama kawai ake ana shirya mana sharri a wajensa maybe ma harda asiri. Dan nikan ban taɓa ganin mijin dake tsoron ɓacin ran matarsa irin Abba ba. Oho koma dai minene su suka sani ina ruwana.. Tunda na isa islamiyya na samu ƙawayena biyu na manta da wata hidimar gidanmu. Sai ƙarfe huɗu muka tashi, anan nai sallar la'asar sannan na dawo gida. Abin dariya abin takaici, a galabaice na samesu wai babu wanda ya tashi yay girkin ana jirana, Abba dai ya fice sai su kawai. Sai Abbas dana samu a gidan shima ya shigo. Ko kallon inda yake banyi ba dan ni da shi bama magana. Haka na tuɓe uniform ɗina na shiga kitchen ɗaura musu girkin da suke jira ɗin. Abu mai sauƙi na musu nayi komawata ɗaki.. Yaya Musaddiq bai dawo a ranar ba kamar yanda yace. Koda na kirashi a waya sai yace nai haƙuri bai samu kawu Musa bane a gida, su kawu Sa'adu kuma sunce dole ya jirashi. Mun ɗan yi hira mukai sallama saboda kiran da Mansoor keta faman yimin. Hira sosai mukasha da Mansoor, dan sai kusan ɗaya mukai sallama. A hakan ma ba kwanciyar nayi ba. Tambayoyin da zanma wancan mutumin nai zaman tsarawa, har biyu sannan na miƙe na gyarama su Bibaa rufa na ɗauro alwala. Nice ban kwanta ba dai sai kusan biyu da rabi, amma hakan bai hanani tashi da asuba ba yin ayyukana. Washe gari da yamma Yaya Musaddiq ya dawo gidan. Na dawo daga aikan da Mum tamun rijiyar lemo wajen ƙawarta na samu ya dawo. Naji daɗi sosai, dan bamma shiga gidan kai aikar ba na zauna muka hau hira. Duk yanda sukai da su Kawu Musa ya sanar min. Sunyi faɗa sosai, da farko ma ca sukai su babu ruwansu. Shi Abban daya nuna musu shine dolenmu yaje ya aurar damu. Amma Yayan ya dinga basu haƙuru, da ƙyar dai suka haƙura, sun kuma tsaida shi kawu Sa'adu zai zo ya sami Abban. Hakan kuwa akai, dan washe gari Litinin sai ga kawu Sa'adu. Lokacin mu duk mun fice wajen sabgoginmu. Shima Abban a office kawun ya samesa suka tattauna. Duk da dai a farko taso tayi tsami a tsakaninsu. Kasancewar kowanne yana son nuna ƙarfin ikonsa a kammu da kuskuren da ɗan uwansa yay masa. Bayan dai sunyi sama sun faɗo suka dai-daita kansu. In da da ƙyar Abba ya amince da batun Mansoor........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* Up*_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒆𝒏_ .......Oho mu bama musan sunayi ba, dan lokacin da suke nasu bidiri ni inama can office ɗin MD na kai masa aikin daya saka ni. Kamar kullum yau ma a kwai mask a fuskata, sannan dogon hijjabi ne har yana jan ƙasa na saka. Dama dai shigar tawa kenan. Idan har ka ganni babu hijjab to abaya ce na saka kuwa. Amma gyale dai a jikina zan iya rantsuwar tunda ma mallaki hankalina na san kaina ban taɓa sakawa ba. To bamma da shi sam, sai ƴan madaidaita da nakanyi rolling idan zan saka abaya. Duk da yanda na suturta jikina bai hana MD zuramin idanu ba, dan shi indai kallone ya iya shi na masifa ma da UBANGIJI ya hanemu yi. Ni dai miƙa masa takardar nayi na maida hankalina akan wayata. “Wow! Kai Samraah sannu da ƙoƙari. Shiyyasa duk girman gidan nan ke na fara hangowa dan nasan bazanyi zaɓen tumin dare ba, saboda nai matuƙar yarda da basirar ki, kina da saurin ɗaukar abu wlhy. Sosai komai yayi, sai fatan ALLAH ya kaimu ranar kuma. Yanzu zuwa anjima sai kizo ki amsa kiyi printing nashi ko. Ki kuma je ki zama cikin shiri na musamman, dan wannan ranar muna fata ta zama ta musamman a garemu. Dan ALLAH kada ki saka dogon hijjabin nan tamkar matar limamin anguwa. Ki yi shiga ta ƴammatan zamani dan kin san irin manyan mutanen nan sunfi son komai na wayewa su balle shi matashi dake a ganiyar samartaka. Inda son samu ne ma ki saka sabbin kaya, ki samu makeup artist ta tsantsara miki irin kwalliyar nan taku ta zamani Please”. Yanda kuka san television haka nai galala ina kallonsa. To amma kun san tsiyar mutuniyar taku. Sai ban musa masa ba nayi murmushi kawai da faɗin, “In sha ALLAHU Sir”. Yako ji daɗi, dan tuni ya washe baki da jera min godiya. Niko sai nayi dariya kawai a raina. Kuga ɗan banza yana son iskantani kawai. Yo in ba son iskantawa ba taya zai ce nai irin wannan shiri dan kawai burge wani sakarai can da ban san ma a wace alƙibla yake ba, ta musulinci ko ta masu kaɗa ganguna. Humyim bai san halin ƴar Abdul-wahab ba ne ba, amma zan sanar da shi sannu a hankali. Office na koma na cigaba da harkokina. Bayan azhar kuma muka haɗu da Mansoor. Dan nifa da kuke gani na duk rintsi bazaka ganni office ɗinsa ba in ba a dalilin aiki ba. Dan tun farko daya fara nuna buƙatar hakan ta hanyar kirana wai nazo na samesa office na dakatar da hakan. Nama nuna masa anan fa aiki mukazo, ya kamata mu ajiye batun alaƙa gefe muyi abinda ke a gabanmu kamar yanda muka rayu a makaranta. Idan mun fita anan sai mu dawo da batun alaƙar. Mansoor mutum ne mai sauƙin kai da fahimtar abubuwa, sai in kana kallonsa daga nesa ne zaka fassarashi da girman kai. Ya fahimceni harma ya nuna jin daɗinsa da hakan. Bawai dan ina zarginsa da wani mugun haline nayi hakan ba. A'a nayine domin kare mutuncina da martabata ta ɗiya mace. Sannan kuma hakan da nayi zai ƙara bani kariya daga hare-haren irinsu MD da basu iya ɓoye maitarsu a fili ga ƴaƴan mitane. “Amarsu ta ango”. Daya faɗa ya sani ɗauke kai gefe ina murmushi. Shima ƙaramar dariya yayi yana dawowa ta inda na maida kan nawa. Ƙaramar harara na sakar masa ina sake ɗauke kaina. Ya ce, “Tab irin wannan harara haka amarya ai sai kisa na zube ƙasa wlhy. Kinga adana min ita sai nan da ƴan watanni kawai, kinga inma suma nayi dai ƙya farfaɗo dani da kanki babu wanda yaji ko ya gani ko?”. Dariya ya bani, amma kasancewar ba'a ganin bakin nawa sai nayi murmushi kawai na sake ɗauke kaina. ★ Alƙawarin ALLAH ya cika. Iyayen Mansoor dai sun kawo kuɗi gidanmu a ranar juma'a. Ranar ni naga baƙin halin Mum muraran. Dan zage-zage ta dinga yi da yima Abba masifa wai an munafunceta. Ashe bai gaya mata ba sai ganin su kawu Musa yasa ta fara tambayarsa abinda ya kawosu. Shine ya sanar mata iyayen wanda yake nemana ne sukace zasu zo yau. Takaici ya sakata zuba masa ido kawai, amma ta kasa cewa komai. Dai-dai isowar baƙi kuma sai ga abinci Yaya Musaddiq na shigo da shi da ruwa da lemo batare da tasan daga ina aka dafo shi ba. Shiko Yaya Musaddiq sanin halinta da yay ne ya sashi saka matar ogansa ta dafa abincin. To ranar dai munga tujara. Dan nima da ban san mike faruwa ba ina a wajen aiki ina dawowa na samu rabona. Baby kuwa banda kuka babu abinda take yi. Ni dai ko uffan bance musu ba, a wajen Yaya Musaddiq kuma naji komai yanda ya kasance. Iyayen Mansoor sun kawo 300k, amma su Kawu Musa sun barma Abba 200k su sun ɗauki 100k na ɓangaren uba. Hakan da sukai baimun ba. Dan kamata yay su su ɗauki 50k Abba 50k aba Yaya Musaddiq 200k dan nasan dai shine mai mun wahalar ba kowa ba. Ban dai ce masa komai ba muka ci gaba da hira. Dan banama sha'awar shiga gidan. Ko hijjabi na ma da zan saka a gobe idan ALLAH ya kaimu domin zuwa taron can anan ɗakin Yaya na gogesa. Sai kusan sha ɗaya na shiga. Baby kawai na samu a falon zaune. Bance da ita komai ba na kama hanyar shigewa ɗakinmu. Ji nai kawai an sakar min duka ta baya tare da damƙo hijjab ɗina. Da ƙyar naja numfashi saboda an shaƙe min wuya. Nai saurin riƙe hijjab ɗin ta gaba na yaga shi sannan na juyo ina sauke numfashi da ƙyar. Baby ce tsaye tana faman huci kamar mai shirin dambe. Na mata kallon sama da ƙasa kafin cikin mamaki na ce, “Lafiya kuwa baiwar ALLAH zaki shaƙeni kamar wadda ta ci miki bashi? Are you okay?”. “A haukace nake dan uwarki. Kuma kaɗan ma na miki, wataran idan na shaƙeki har sai kin daina numfashi zan ƙyaleki. Dan haka ina mai gargaɗinki in har kina son ranki ki fita a sabgar Mansoor wlhy. Ki kuma bar ganin ya kawo kuɗi da sunan na aurenki, wlhy sai dai in bana raye hakan zata kasance. Dan yanda ban samesa ba kema baki isa samunsa ba jaka kawai ƴan karoro a gidan mutane mai ƙwacewa yaran gida samari su mayya”. Murmushi kawai na saki mai faɗi dan wlhy ni dariya ma ta bani da tausayi. Bance mata komai ba nai shigewata ɗaki na barta tana ɗuran zagi kamar ba dare ba. Zuwa can kuma naji kamar maganar Abba sama-sama ita kuma tana kuka. Baki kawai na taɓe na gyara kwanciya dan so nake nai barci sosai kodan abinda zan tunkara a gobe in ALLAH ya kai mu. Sai dai duk da haka kamar kullum sai da na tashi nai ƙiyamullaili dan ya riga ya zame min jiki tashin a kullum, sai dai idan banda lafiya, amma ko prioud nake saina farka.... *_DAMA ACE....._* (Dama ace) kalmace mai harshen damo. Zaɓa mata gurbi a nawa labarin shine cigaba da nutsuwar saurarensa. Kamar kullum yau ma sai da nai duk ayyukan gidan kasancewar nasan yau ɗin Mum a cike take da haushina. Hatta shi Abban ban san a wane matsayi ya ɗauki auren nawa ba. Dan daya dawo da ga sallar asuba na gaishesa sama-sama ya amsa min ya shige ɗaki abinsa. Ga Baby a gefe da marasa kunyar ƙannenta su Bibaa da Nabil. Shiri na nayi kamar yanda na saba, dan baƙin dogon hijjabin jikina har jan ƙasa ma yake. Ban biye ta maganar MD ba, na kawo kuma face mask na saka kamar yanda na saba shima baƙi, na ɗaura sirrin farin eyeglasses ɗina da har ana iya ganin ƙwayar idona fes. Sai ƙamshi dake fita a jikina mai daɗin tsiya na humra da turare. Yaya shike sayamin turare da duk wani nau'in kayan kwalliya na mata. Hatta kayan ciki da suturu shine ke saya min. Hakan yasa banjin ƙyashin duk sanda salary na ya shigo account na tura masa su gaba ɗaya a account ɗinsa batare dana cire ko sisi ba a ciki. To idan na ajiye mizanyi da shi. Duk wani abinda nake buƙata baya gazawa wajen saya min. Idan abin yayi ya shigo zaka sameni a layin farko cikin masu sakashi. Da harda Baby yake saya, amma ta ce masa yama bar wahala bata so. Koda ta faɗa ɗin bai daina saya ba. Sai da yaga bata sakawa sannan ya daina. Hakan kuma baya hanashi bata kuɗi akan ta saya abinda take so. Wannan kam sukan amshe ita da uwarta kuma baza'a sayi abin kirki ba kuɗin zai gantale. Hatta da data sakara Yaya sakamin yake da credit, sai daga baya ne ma Mansoor ya amshesa wannan. Dan haka Yayanmu kallon uba nake masa ba yayaba wlhy, dan ya share mana kukan maraici tuni sai dai na kewar iyaye da bazai taɓa gushewa ba ga ƴaƴansu. Amma ta ɓangaren rayuwa komai Alhamdullah. Kamar yanda Yaya Musaddiq yay alƙawari shine ya ɗaukan a mashin ɗinsa da yasha wanki sai ɗaukar ido yake. Office ya kaini inda su Mansoor ke jirana dan da motar office zamu fita. Ba sauran abokan aikina ba hatta da Mansoor ƙuri yay kawai yana kallona cikin nuna mamakin ganin hijjab dana zuba har yana sharar ƙasa. Amma sai yay murmushi tare da kashe min ido ɗaya alamar yaji daɗin hakan da nayi. Nima murmushin nayi kawai na ɗauke kaina ina mai gaishesu. Duk suka amsa min da kulawa. Sai Davido ne ke magana akan shigar tawa. Ban tanka masa ba na shige mota abina na zauna batare da na yarda na kalla inda MD yake ba ko sau ɗaya, dan gaisuwa ma kaina a gefe nai masa. Naci sa'a dama sun gama loda komai dama ni suke jira. Kulsoom ma na ciki ita. Kusa da ita na zauna muka gaisa, sai gasu suma sun shigo. Da farko Mansoor na kula kusa dani yaso zama. Amma ganin yanda na koma jikin window muka saka bags ɗinmu a tsakkiya yasa shi haƙura ya zauna kujerar gabanmu, sai lokacin na ɗan saci kallon MD, yay kicin-kicin da fuska sai mazurai yake. Ƙasa nai da kai ina kwasar dariya, ɗan son banza an shirya ganin banza. To bata samu ba ai, sai a tafi wata tashar.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_ ........Tun kafin mu fice duk sun cika motar da hira, ni dai ban saka musu baki ba face ma bitar questions ɗin dake rubuce dan karna kwafsa. Dan a nawa shirin ina son masa tambayoyin ne batare da takarda ba. Duk da ma dai har cikin waya na kwashesu gudun samun matsala. Lokaci ɗaya naji motar ta ɗauki shiru, kamar zan basar sai kuma na gagara hakan, dole na ɗago domin ganin abinda ya sakasu nutsuwa haka. To nidai banga komai ba face uban cinkoso na ababen hawa da titin ya samu tamkar ba safiya ba kuma weekend. Da ƙyar drivern mu ya kutsa ya samu wajen parking ma. Haka muka firfito kowannemu na bin katafaran ginin da kallo. Dan sai yanzu na fahimci abinda ya saka su yin shiru ɗazun. Gini ne da akayisa da wani kalar zallar gilashi mai garai-garai ta gabansa. Ga wasu manya-manyan symbols da hoton motoci masu shegen ƙyau da mashina irin na masu kuɗin nan. Da manyan haruffan baƙi an rubuta *_MAASH_*. Tako ina jami'an tsaro ne, hakan yasa komai ke tafiya a nutse duk da alamu ma sun nuna duk wanda ka gani a inda motarmu ta samu damar shigowa to ba ƙaramin mutum bane, ko kuma dai yana da izinin zuwa wajen. Dan zuƙa-zuƙan motocine na nunama tsara. Yaku bayi kuwa na daga can tunkushe a titi an hanasu shigowa (🤥😞😏). Dan ƙa'idar sai ka nuna invition ɗin nan zasu bar motar ka ta wuce. A ƙafa muka cigaba da takawa saman lafiyayyen titin da aka ɗauka tun daga babban titi har zuwa cikin companyn. A dai-dai katafaren gate ɗin ma dai sai da muka nuna invition ɗin. Sannan akai searching namu aka tabbatar da bama tare da komai sannan muka shige bisa rakkiyar wani jam'i. Da alama wajen zaman ma a tsare yake kenan. Bazaka tabbatar da Companyn mugun ƙato na gaske bane sai ka shigo ciki. Ashe ta gaban duk wasan yara ne da ado kawai. Duk girman harabar an gyarata da uban decorations mai matuƙar ƙyau da ɗaukar hankali. Hakama an tsara kujerun zama cike da birgewa. Da ga can gefe abincine aka jera irin dai na taron ƴan gayun nan, dan ga masu zungura-zunguran hulinan nan irin nasu o,e a kitchen sun jeru kamar ƴan cocin yarabawa (😂lol). Mune ƴan jarida na farko da suka fara isowa, hakan ya mun daɗi, dan koba komai mun samu sits ɗin gaba a inda aka tsara domin ƴan jarida. Tuni su devido sun dasa camaras namu kuwa a inda komai bazai wucemu ba. Zuwan namu kamar ya buɗe ƙofa ne, dan sai ga mutane da ƴan uwanmu ƴan media nata shigowa a nutse babu wata hayaniya ko kace nace. Tun shigowarmu kuma tuni mun fara nuna komai live kamar yanda contract ɗin yake. Dan haka kusan komai daya fara da tushe kai tsaye ana fara ganinsa ne daga gidan tvn mu. Ni dai har lokacin ina a zaune dan ba'azo kan aikina ba. Kafin cikar awa guda waje ya gama cika taf da manyan mutane. Muryar mc kawai ake ji yana sanar da isowar manyan baƙi, sai mu kuma ƴan jarida dake namu bayanin domin gidajen tvn mu kai tsaye. Goma dai-dai dake tabbatar da duk wanda ake buƙata a wajen ya iso hatta da gwamna da sarki ma aka sanar da isowar mai gayya mai aiki. Wato *_Awwab El-Mu'azz Maashi_*. Tsitt wajen ya sake ɗaukar shiru kasancewar dai-dai nan zuƙeƙiyar baƙar mota da irinsu shugaban ƙasa kawai nake gani a ciki ta shigo. Ta gefe da gefenta da gabanta da bayanta kuwa wasu irin murɗa-murɗan basumadayen garada ne da gani kasan ba bugun Kano bane sai dai Lagos ɗin dan bamu da masu irin wannan suffar gaskiya😞. Su duka riƙe suke da bindigu kai kace zasu iya hana mutuwa ɗaukar wanda ke'a cikin motar ne😏. Har tsakkiyar filin motar ta shigo, inda mutanen dake a cikin motar bayansu suka fito a lokaci guda su huɗu. Mace ɗaya maza biyu. Wanda ke mazaunin driver ne ya buɗe booth da hanzarinsa ya ɗakko carpet maroon mai shegen ƙyau an rubuta *_Maash_* a jikinsa da golden mai ɗaukar ido. Yayinda macen baturiyar ta iso da sauri sauran mazan biyu a gefe da gefenta. Daka ganta kaga cikakkiyar baturiya. Duk tsaye sukai a ƙofar motar kowa cikin nutsuwarsa da kamewar girmamawa abin zam mamaki. (Humm jama'a MANDA fa duniya ce😜). Kusan minti ɗaya cif muna zuba idon ganin abinda ke faruwa kafin wanda ke gefen damar matar nan ya kai hannu jikin handle ɗin ƙofar ya buɗe tamkar mai gudun tashin yaro a barci. Wasu sakanni goma aka sake kwashewa kafin wani almurin baƙin takalmin haIf cover shoe mai adon golden ya sauka saman maroon carpet ɗin a hankali. Sai da aka sake jan wasu sakannin kamar uku sannan ɗayar ƙafar ma ta sauka baƙin wandon suit ya bayyana. Sannu a hankali sauran gangar jikin ma ta fito. Kaf wajen har masu ji da mulkin da kuɗin babu wanda bai bi wanna halitta da kallo da ga ƙasa zuwa saman ƙyaƙyƙyawar fuskar mamallakin jikin ba. Tsaye yake gam akan tsahonsa na tsayayyen namiji da babu ko ranƙwafawa. Suit ɗin jikinsa da basai an zauna ɓata lokacin lissafin kuɗin da suka lashe ba sun masifar zauna masa da tabbatar da shi a matsayin jaruminsa mai gara kan naira ta yanda duk yaso bisa damar da ALLAH ya bashi. Komai na jikin nasa baƙine, sai ɗan adon takalminsa da ta kasance golden da neck tie.. ɗinsa shima golden mai azabar ƙyau. Kamilalliyar fuskasa ma'abociyar kamewa da tsare gida ko nace baƙin hali a tsuke, sai kwantaccen gashin kumatunsa siriri daya zagaye bakinsa zuwa haɓarsa tamkar an zana ba biro. Yau ɗin ma dai akwai ɗan kunne ɗaya manne a kunensa, hakama zanen tattoo ɗinsa mai fuskar lion na nan zaune daram. Saɓanin hoto yau gashinsa ne a ɗaure kamar yanda mata ke parking sai dai shi nashi acan ta ƙasa ya ɗauresa har yana ɗan sauka jikin rigarsa dan babu kitso yau. Wanda bai sani ba tuni yake sakashi a jerin larabawa. Babu mai ganin idanunsa kasancewar sakaye suke a cikin eyeglasses mai masifar ƙyau daya ƙara fidda taswurar halittar ƙyawun hancinsa daya zauna ɗaram kan fuskarsa. Kafin kace mi tuni ƙamshinsa ya baje wajen kai kace mu namu turaren baida tasiri ne ko Companyn da suka wallafo namu basu iya zaɓar ƙamshi ba. Kai jama'a akwaifa ƙyawawa a duniya. Idan kaga wani sai kaga kamar ka yanka kanka ka ɓoye wuƙar ƙawai. Bily karfa ki zata wannan bayanin da nake zayyano miki a kansa ya wani birgeni ne. Mtsowww ko kaɗan.. Gaba ɗaya yaran nasa sake kame kansu sukai cikin nuna tsantsar girmamawa a garesa. Karan farko na ɗan taɓe baki takaici kamar zai halakani. Shike nan a wannan rayuwar in har kana da dukiya ka zama saraki ko mai mulki?. Kai wani abun ma da ake maka ko kai mulkin ba lallai ya samu ba. Dibi dai wannan mutumin yanda yake wani busar isaka da shan ƙamshi fuska tamm kamar wanda aka aikama saƙon mutuwar tsoffinsa. Cikin isa da bajinta, a slowly tamkar wanda ake ɗauka a faifan video yay wani kalar haɗe hannayensa duk biyu a waje guda ya ɗagasu sama alamar gaisuwa wa duk jama'ar wajen. Kusan kowa dake wajen sai da sukai yanda yay ɗin idan ka cire gwamna da sarki. Sai ko ni ƴar balaja'un ku da saida Khulsoom ta zunguran amma na fuske naƙiyi, sai ma laɓe mata baki da nai na sake maida idanuna dake cikin glasses kansa ƙurr kai kace nice camara ɗin ma. Har inda aka tanada domin zamansa a tsakkiyar sarki da gwamna yaran nasa sukai masa rakkiya. Sai da ya zauna sannan suka koma ta bayansa suma duk suka zauna. Isowar tasa ta saka taron fara motsawa yanda ya kamata. An fara da gabatar da addu'oi kafin gwamna yay bayani mai birgewa a matsayin uban taro, dan ya nuna jin daɗinsa da farin cikinsa matuƙa game da wannan cigaba da aka kawo jiharsa, yana kuma fata da kira ga wannan shugaban kamfani akan idan har yaranmu sun cancanta yana roƙon ace sun zama mafi rinjaye da zasu samu aikinyi a ciki, yana kuma fatan ALLAH yasa kamfanin ya zamewa Kano dama arewacin ƙasar alkairi baki ɗaya. Kowa yaji daɗin bayanin gwamna. Dan zaka tabbatar da hakanne a fuskokin jama'ar dake a wajen ma. Sai sarki shima dai a matsayin uban taron. Sosai jawabansu suka ƙayatar suka kuma birge shima ɗin dai. Dan yayi kiranye sosai ga masu arziƙinmu da su shigo su kafa cibiyoyin kasuwancin a arewa domin matasanmu su samu aikinyi, hakan da zasu dingayi zai rage mana raɗaɗin rayuwa da ake ciki a wannan ƙarni. Zai kuma ƙarama matasan himma da nisantasu da ga shaye-shaye ko ɗaukar makamin da bai dace dasu ba a matsayin neman abincinsu ko zaman banza a bakin tituna mara amfani. Idan kuma har masu arziƙi suka cigaba da janye jikinsu da dukiyoyinsu da ga arewa to lallai watarana sai an wayi gari kowa ya zama abinda ba'a so. Idan kuma hakan da ba'a fata ta kasance ba arewan kaɗai ba, hatta su ma kudancin da wasu maƙwaftan ƙasashe zata shafesu, suma kuma ta nakasasu kamar yanda muma muke a nakashe yanzu. Bayan waɗan nan bayanan wasu masu muhimmanci ma sun sake biyo bayansu kafin shi ma ya miƙe........✍️ _(🤭Ni dai nace faɗi gaskiya dai Samraah bama son kwana-kwana😜 idan Yaya Maash ya miki ne sai ai miki hanya🥱, dan kunsan bana ni gaskiya ƴar team Yaya Maash ce. Mu dama muna gidan kuɗi babu kwana-kwana🤣👌. Saura naji wani yace kwaɗayi🙄dan ɗan uwanmu ne Ya Maash ɗin na jini🤯, ai gwajin jini kuma a gani🤥😌)._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆_ .......(Kutumelacy). Na faɗa a zuciya lokacin da yay sallama da wata jarumar muryarsa cikin yanayin mazantaka da nuna kamewa tamkar wanda akama dole, dan hatta lips ɗin ma da ƙyar yake motsasu. Bayan an amsa ya cigaba da miƙa saƙon gaisuwa da sannu da zuwa nan ɗin ma dai a fiffisge alamar maganar ta zame masa dolene ko kuma gayune ko kuwa girman kai irin na masu hannu da maiƙon kaza oho masa. Ga wata hausarsa da ta gama gurɓacewa da harshen ƴan kudanci ko nace harsuna da yawa dan tamkar ba cikakken bahaushen da akace an haifa a gari irin Kano ba. A wata gaɓar ma hausar ƙwace masa take sai dai ya kwakuso turanci ko faransanci ya maka a wajen ya kuma fuske ya cigaba da jawabinsa. Kuga wani ɗigimi, da dai a turancin ya tsaya da yafi, to waye ya wani iya faransanci anan?. Koda yake ban sani ba tunda naga taron duk nasu ne na masu jiki duk chocolates. Haka dai ya haɗa jawabin mintuna uku da ƙyar yana faman mana haɗin gambizar yaruka uku a lokaci guda da kai hannu saman kai ya murza tabbacin dai maganar ta dole ce a garesa. Hummm duniya makaranta, yo ALLAH na tuba su mu kuma indai zance ne ai ko akkun farkon ƙarni ta sama mana lafiya, duk da dai nima sai naso nake nawa surutun. Amma dai na ƙara ilimi, tunda naga yayin ƴar jan ajin nan ake da fidda zance ɗaɗɗaya billa sake kame kaina zan dingayi tunda ban sani ba ko nan gaba nima na kuɗance. Yo Bily abin ai na ALLAH ne, bafa zaune nake kurum ba daga aikin jarida sai na gida. Ina ƴar sana'ar sai da hijjabai da takalma duk da jarin bai wuci na dubu ashirin ba. To nadai fi su o'e ai masu cika gida da munsharin barci ko. Duk da fa jawabansa sun ƙayatar sun kuma tsaru tamkar daga takarda yake karantowa ni ƴar iyar taku sai da na taɓe baki. Yayinda wajen ya ɗauki tafi gaba ɗaya, a cikin ƴan jaridar mu harda masu yin fito. Hakama wasu gungun samari ƙyawawan da kallo ɗaya zaka musu kasan akwai ƴan canji dan kamar sun zaɓo kansu ne dan ƙyau da gayu, bana kuma raba ɗaya biyu abokansa ne sai salute nashi suke suma dai cike da isa da ƙasaitar. A haka taro ya cigaba da tafiya cikin nutsuwa, mudai ƴan jarida munata ɗaukar rahotanni babu mai damar cewa komai a yanzu sai nan gaba. Dan ya bada damar a masa tambayoyi a karo na biyu da zai fito, amma akan abinda ya shafi Companyn kawai. Nikam na taɓe baki, dan na shiryo nawa questions ɗinne akan komai kuma in sha ALLAHU sai na masa su duka, dan zan fara da manya-manyan cikine da dole sai ya magantu koda baya son hakan. Ana tsaka da sauraren jawaban sauran manyan mutanen wajen fitsari yay mugun matsata. Sosai hankalina ya tashi, na shiga dana sanin shan shayin da nayi kafin na fito. Tun ina daurewa har dai na shiga mutsu-mutsun da Khulsoom ta lura dani. “Samraah lafiya kuwa?”. Ta faɗa tana tsareni da idanu. Fuskata dake cikin facemask a marairaice na ce, “Ina fa lafiya Khulsoom. Wlhy wani mugun fitsarine ya matseni kamar zai zubo. Dan ALLAH ki tashi ki rakani kada ayi abin kunya a bainar nasi. Maimakon mai buɗe Company ya zama topic of the day ni na zama.” dariya ta nema saki, amma ganin yanda na ɗaure fuska ya sata daurewa ta ƙunshe abarta. Cikin raɗa ta ce, “Kima Mansoor magana ya raka ki, dan wlhy tsoron waɗan nan jami'an tsaron da aka baza nake yi”. Wata hararar na sake watsa mata a karo na biyu, batare dana tanka mata ba na miƙe dan gab fitsarin yake da zubowa. Kasancewar wajen tsitt yake babu wani hayaniya kuma kowa a zaune yake a nutsensa sai tashina ya jawo hankalin mutane da yawa gareni. ALLAH ya soni komai nawa a rufe yake, idan ka cire tafukan hannuna da yatsunsu suka ƙawatu da jan lallale, na tabbata yau da ace ba hijjab na saka ba wannan idanun na jama'a sai ya sakani sakin fitsarin a wajen. Gudun karna taka doka ko yin abinda zai jawo min kunyata kai tsaye na nufi security dake kusa damu sosai. Gaishesa nayi cikin girmamawa bayan na sauke mask ɗina dan karma ya fassarani da abinda bashi nake nufi ba sannan nai masa bayani. Hakan da nai kuwa ya sakashi jin daɗi, dan har I'd card ɗina saida na nuna masa tunma kan ya buƙata. Wata mace a cikin jami'ansu ya yafito da hannu, ta iso wajen tana mai ƙamewa da salute nashi. Nuna mata ni yay yace ta rakani restroom. Da girmamawa ta amsa masa nan ma. Sannan muka wuce ta can bayan Companyn. Na zata anan bayin yake, amma sai naga ta shiga dani ta wata ƙofa alamar cikin dai Companyn zamu shiga amma ta baya. Dan ta gaba an gama zagayesa da zaren nan mai ribbon kuma ba'a kai ga yankawa ba. Lallai dukiya tayi aiki a wannan waje, duk da fa inda muka shiga bawani ciki-ciki bane ba. Amma tsayawa kwatanta miki Bily walla ɓata lokaci zamuyi. Har ciki muka shiga tare da ita, ta nunamin bayin farko, godiya nai mata munama juna murmushi. Ina shiga wayarta ta fara ƙara alamar shigowar kira, dole ta fita a wajen domin amsawa. Har kuma na gama abinda nake na fito babu ita. Mamaki ya kamani na shiga waige-waige. Ganin dai da gaske bata a wajen na nufi neman hanyar da muka shigo. Sai dai kuma na rikice dan hanyoyin da yawa ne ashe duk iri ɗaya. Canki in canka na shigayi a tsakani, ganin dai ba ganewar zanyi ba na shiga binsu ɗai-ɗai ina taɓawa. Sai dai me kowacce na taɓa sai na jita gam a kulle. Tun ina ɗaukar al'amarin wasa har hankalina ya fara tashi amma dai na dake ina ƙarama kaina ƙwarin gwiwa. Hope ɗina na gab da barina gaba ɗaya wata a cikin ƙofifin ta buɗe. Ji nai kamar na saki ihu dan daɗi, sai dai banyi hakan ba na saki ajiyar zuciya ina mai rumtse idanuna da buɗewa, cike da zumuɗi na sake kama handle ɗin ƙofar na murɗa, ina ƙoƙarin danna kai ciki naja wani wawan birki sakamakon abinda naci karo da shi mai ɗimauta zuciya da tunani. Sosai jikina ke rawa idanuna a matuƙar ware kansu. Ganin hankalinsu bai kawo kaina ba na sake jawo ƙofar sosai ta yanda bazasu iya ganina ba. Video recording na latso a wayata na fara ɗaukarsu. A dai-dai lokacin ya zare wuƙar da ga jikin mutumin, wani irin gurnanin ƙarasa fitar rai yayi ya ida zamewa da ga jikin bangon da yake yay ƙasa. Mutumin daya buɗe masa mota ɗazun ne a gefensa, gaban mutumin da suka kashe ɗin ya kai duƙe yana mai saka yatsunsa biyu a saitin hancinsa, a wani irin yanayi ya furta, “Ya mutu Sir”. Kansa ya ɗauke tamkar baiji miya faɗa ba. Hakan yasa wancan ɗin miƙewa batare daya sake cewa komai ba shima ya buɗe wani farin ƙyalle. Wuƙar ya saka masa a ciki tare da handkerchief ɗin daya riƙeta, sannan ya bar wajen cike da takun isa, bathroom dake cikin ɗakin ya nufa. Kusan minti ɗaya da wasu sakanni sai gashi ya fito yana goge hannu da ƙaramin farin towel alamun wankewa yayi. Sai da ya gama goge hannun yana ƙoƙarin ajiye towel ɗin yake faɗin, “Lukman ya shigo da kayan can, ya fita da gawan zuwa can anguwan”. Kai yaron nasa ya jinjina masa cike da girmamawa. Ƙofa ya nufo, dan haka nai saurin tsayar da video ɗin na koma wani ɗan lungu na lafe. Wajen sauri face mask ɗina dake a hannuna ya faɗi ƙasa. Cikin takunsa da baya fidda sauti ya fito, cak ya tsaya tamkar wanda ake controlling da remote yana kallo mask ɗina dake yashe a ƙasa. Sosai na waro idanuna waje ƙirjina na wani irin mahaukacin bugawa da sauri-sauri. Lokacin da yake ranƙwafawa yana ƙoƙarin kai pen ɗinsa mai masifar ƙyau ya ɗauka facee mask ɗin dashi jinai kamar numfashina zai rabu da gangar jikina. Sake lafewa nai sosai tamkar ina shirin keta bangon na shige ciki. Yayi kusan sakan ashirin yana kallon mask ɗin, sai kuma ya zaro wani ƙyaƙyƙyawan handkerchief a aljihunsa ya warwaresa ciki ya saka. Da baya-baya ya koma yana ɗan waige-waige, ƙofar ɗakin daya fito ya ɗan buɗe kaɗan, sai kuma ya maida ya rufe ya sake juyowa. Kusan taku goma ya sake tsayawa cak. Da sauri na kai hannuna kan bakina na rufe kamar zan saki kuka dan tashin hankali. A hankali ya juyo da alama dai yana ji a jikinsa akwai mutum a wajen. Bakina na sake dumtsewa tare da hanci ina mai runtse idanuna da ƙarfin masifa. Nafi mintuna biyu a haka kafin na buɗe a hankali, wayam na gani alamar ya fice. Cikin sauri na zame nai ƙasa ina mai janye hannuna da sakin numfashi mai ƙarfin gaske. Inaga tunda nasan kaina nai hankali ban taɓa cin karo da matsanancin tashin hankali irin na yau ba. Kisan kai fa, na mutum ba wani ƙwaro ko dabba ba. Lallai mutum abin tsoro ne, taya zakai tunanin wannan mutumin zai iya aikata wannan ta'asar, jibesa kamar wani mutumin kirki. Koda yake wanda ke iya zana tattoo a jikinsa ga ɗan kunne ya kuma ɗaure gashi a kai kamar wani mace ko yay kitso komai ma ai zai iya aikatawa. Aiko bazan taɓa yin shiru ba, dolene nai gaggawar nunama duniya wanene shi, yanzu kuma ya kamata a cikin taron nan ba sai anjima ba. Zaram na miƙe kuwa ina tattaro wayata dake yashe a ƙasa da sauri........✍️ _“🤯🤯Na rasa abin faɗa Samraah. Yaya kin tona asirin nasa kenan?”._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_ ......Humm Bily nayi yunƙurin hakan kamar yadda na faɗa miki. Sai dai ina miƙewa aka buɗe wata ƙofa da sai yanzu hankalina ya kai na fahimci a itane muka shigo tare da jami'ar nan ɗazun. Wani ne ya shigo da kaya a hannu, da alama Lukman ɗin daya faɗa ne. Jikin bangon na koma na sake lafewa, har sai da ya shige. Maimakon na sake yunƙurin fita sai zuciyata ke bani shawarar tsayawa naga yanda zasu fita da gawar. Ga kiran Mansoor sai shigomin ya ke da alama jirana suke. Sauƙina ma wayar a silent take. A plane mood na sakata, na sake shiga video recording. Ko sakan goma ba'ai ba sai gasu sun fito da gawar kuwa, duk da an naɗeta cikin wani abu jini duk ya ɓata mayafin. Da ƙyar na iya tsaida karkarwar da jikina ke min. Suna ficewa nai saurin fitowa da hanzari nabi bayansu nima. Inayi ina waige-waige. Maƙalewa nai ta jikin ƙofa ina cigaba da ɗauka har suka sakata a cikin motar. Ina ganin sun kammala Lukman ɗin ya shiga motar ɗayan na shirin juyowa ciki na sake komawa wani lungun da gudu. Dan kar yaji sautin hakkina hijjab ɗina na kama na cusa a bakina har sai da ya koma ɗakin, babu jimawa sai gashi ya fito da mopper yana goge duk inda jinin ya ɓata. Ganin ya sake komawa ɗakin na fito da sanɗa, ta hanyar da muka shigo nabi na fita. Inda wani zai ƙuramin ido tuni zai gane a gigice nake, gashi babu mask ɗin a fuskata yanzun. Dawowata wajen taron dai-dai ana mimmiƙewa zuwa inda ribbon ɗin nan yake. Hakan ta bani damar isa inda su Khulsoom suke. Bag ɗina kawai na amsa a hannunta na jefa wayata na ciro wani face mask ɗin na shiga sawa. Ganin yanda suka tsareni da ido ya sakani ɗaga musu hannu cikin dakewa na ce, “Kuyi haƙuri ina a inda bai kamata na ɗaga waya bane ba. Badai har yay jawabi na biyun ba ne ko?”. Khulsoom ce ta amsa min da “A'a bai yiba sai an gama yanka abin can.” kai na jinjina mata alamar fahimta. Yayinda nake ɗan satar kallon Mansoor ta gefen ido, dan shi baice dani komai ba face zubamin idanu da yay kawai. Da alama bai gamsu da amsar dana bada ba. Dama nasan in kowa bai fahimci halin da nake a ciki ba shi sai ya fahimta. Dan akwai shaƙuwa ta musamman tsakanina da shi ta yanda ko motsi ɗaya daga cikinmu yayi sai ɗan uwansa ya fahimci mi yake nufi. Ban sake yarda na kalla inda yake ba muka nufi inda za'a yanka ribbon ɗin. Duk yanda naso kame kaina daga kallon mutumin nan na gagara haka. Mamaki abinda ya faru a cikin ƴan mintunan da basu wuce talatin ba kawai nake. Ban fahimci na tafi tunani mai zurfin da har bana fahimtar mi ake a gurin ba sai da Khulsoom ta zungureni. Numfashi mai nauyi na kawo tare da yin firgigit na ce mata, “Na'am mi kike ce?”. Da mamaki ta ce, “mike damunki ne wai haka Samraah. Duk kinyi wani iri kamar wadda ke a rikice. Kalla yanda kike zufa ga hankalinki sam baya kan abinda ma akeyi”. Cikin son basar da ita na ce, “Cikina ne ke ɗan juyamin. Inaga awaran da naci ne da kabeji ɗazun da safe.” “Ayya sannu, amma tunda kin san yana baki matsala haka ai da baki ci ba, ke da zaki shigo cikin taro babu daɗi kaita zaryar toilet ai”. “Haka ne, nima na shafa'a ne kawai. Amma in sha ALLAHU ina fatan ma bazan sake zuwa toilet ɗin ba. Akwai maganin da nake sha a bag ɗina bari na sha shi”. Kanta ta jinjina min tana sake min sannu. Inda muke zaune na koma na zauna dan hakan sai yafi min sauƙi. A dai-dai nan aka saki tafi alamar har an yanka. Na sake tafiya a tunani naji saukar muryar Mansoor a kaina. Firgigit na dawo hayyacina ina kallonsa. Sai kuma nai saurin ɗauke idanun a kansa ina ƙoƙarin dai-daita nutsuwata. “Samraah mike damunki?”. In har kaji sunana kai tsaye a bakin Mansoor babu wasa sam a ciki. Saurin girgiza masa kai nayi da faɗin, “Babu komai fa. Na dawo nan nasha magani ne kawai”. “Ƙarya kike”. Ya faɗa kansa tsaye kawai. Nasan za'ayi hakan. Dan Mansoor ya gama sanina matuƙa kasancewarsa mutum mafi shaƙuwa a rayuwata bayan ƴan gidanmu. Shekara biyar ai ba wasa ba. Ƙasa nai da kaina kawai ina wasa da yatsun hannuna. Sai kuma na ɗauki wayata nai rubutu na tura masa. Ganin yanda ya cigaba da tsaiwa yana kallona ya sani ɗagowa ina masa nuni daya duba wayarsa. Baiyi musu ba ya zarota ya duba. Da sauri ya ɗago yana kallona. Sai kuma babu shiri shima ya kai zaune a kujerar kusa da ni. Sai da ya wawwaiga gefe da gefenmu sannan ƙasa-ƙasa ya ce, “Da gaske Baby”. Kaina na jinjina masa kawai ina ƙoƙarin riƙe hawayen da suka ciko min ido. Sai kuma na kallesa na ce, “Ina son nabar wajen nan yanzu. Dan na yarda face mask ɗina a ciki ya ɗauka. Na tabbatar zuciyarsu dole tana musu wasi-wasi akan dole wani ya shiga wajen. Dan na fahimci hankalin yaron nasa kamar tun ɗazun ma ya rabu biyu akan mutane.” “Ba tafiya bace mafita Samraah. Ki ƙara daurewa a kammala komai kawai. Sannan ki dawo da hankalinki jikinki, dan fitarki yanzu a wajen nan bazata zama mai sauƙi ba, sannan zasu ma iya ganewa ta hakan tunda baki da wani dalilin fita na zahiri. Kinga ma tashi mu shiga ciki kinga mutane sun kusa gama shiga za'a zagaya cikin companyn ne”. Badan naso ba dole na miƙe. A zuciyata kam sai addu'oi nakeyi. Kar kiga fa kamar na cika tsoro. Wlhy babu abinda ke tada min hankali sai ganin gawar mutum cikin jini. Dan abune da bai taɓa faruwa da ni ba. Kinga ko sanda Babanmu ya rasu banda wani cikakken hankalin daya kamata irin hakan yaban tsoro. Tunda shima har aka binne gawarsa yana a yanayin zubar jini saboda accident. Mamanmu kuma bamma san rasuwarta ba sam, tunda ban wuci 3years ba kwata-kwata. Haka dai da ƙyar na cigaba da riƙe kaina mukabi ayarin ƴan ganin cikin companyn. Ya haɗu matuƙa gaya. Ga wasu manyan machines a wani ƙaton hall da baida iyaka. Da alama daga nan za'a dinga ƙera motocin ko haɗa su ne ma oho musu. Bayan nan akwai wajaje daban-daban masu ɗauke da abubuwa kala-kala da bamusan na miye ba, duk da wani bature a cikin abokan nasa sunata ƙoƙarin yin bayani, ni dai ba wani fahimtarsu nake ba sam. Dan duk yanda wajen ya kai ga haɗuwa a yanzu ni sam baya birgeni. Sai ma ganinsa nake baƙiƙƙirin da duhu. An ɗauki kusan mintuna talatin a ciki kafin a fito. Ɗayan sashen da ya kasance shine ake fara gani daga titi, wanda an yisane da zallar gilashi aka sake nufa. Anan ne offices ɗin ma'aikatan yake ashe. Tun daga hawan farko har zuwa na biyar sai da muka shishshiga da taimakon lift... Duka offices ɗin sun haɗu, hatta na ƙananun ma'aikata dake a hawan farko ma duk da na haɗaka ne komai tsaf. Amma nasa na matsayin oga kwata-kwata yafi kowanne tsaruwa, dan tamkar ba'a Nigeria kake ba. Daga office ɗin kuma akan iya ganin cikin ƙwaryar Kano da ƙyau ta kowanne ɓangare. Sosai abin akwai ƙayatarwa. Sai dai ni bai ƙayatar dani ba. Dan yanzu baƙiƙƙirin ma nake kallon mai Companyn kamar baƙin maciji. Nan ma an kwashi wasu mintuna kafin a fito. ALLAH ALLAH nake kawai yayi jawabin ƙarshen nan na masa tambayar da zan masa na bar wajen. Amma sai akace abinci za'aci a yanzun, sannan aje salla a dawo a ƙarasa. Kamar zan fasa ihu haka naji, sai dai yaya zanyi. Dole yanda suka tsara haka kowa zai bi. An fara gabatar da abincin a nutse, za kuma azo har inda kake a baka zaɓin abinda kake son ci sannan aje a kawo maka. Koda aka yambayen nikam nace a'a. Dan na ɗau alwashin bazanci kuɗin jinin mutane ba. Wama ya sani ko tsafi yake yi ne. Ai dama al'amarin dukiyar tasa da mamaki, shiyyasama mutane suketa wasi-wasi a kansa. Haba mutumin nan ai yayi ƙarami da tara irin wannan dukiyar haka. Kwata-kwata fa bazai wuce talatin ba. Inma zai haura hakan kaɗanne kuwa. Yo ko iya wannan companyn akace ya mallaka a shekarun nan nasa ai abin ayi wasi-wasi ne balle kuma ace yana da ninkin baninkin hakan har dasu jirage. Jirgi ake magana fa dake tashi sama da ɗaruruwan mutane bawai kwale-kwale na katako da ake tsallaka ruwan ɓagwai ba. Sannan bama ɗaya ba, ba biyu ba fa.... “Baby!!”. Mansoor ya sake katse min tunani, dan yanzu a gefena yake. Firgigit na dawo hankalina. “please be smart mana. Ko so kike abokan tafiyarmu su fahimci wani abu ne?.” Kaina na girgiza masa. Cikin dauriya na kalla abincin da ya saka a kawo min. Maimakon naji sha'awar cinsa kodan ƙyawun da yay a cikin ido ga kaza har rabi a ciki sai naji sam baya wani birgeni. A hankali na sauke a jiyar zuciya da ce masa, “Na ƙoshi da abincin nan wlhy. Kayi haƙuri dan ALLAH.” Kallona kawai ya tsaya yi, ni kuma na ɗauke idanuna daga sashensa gaba ɗaya. Da ga ƙarshe ma na ɗauka wayata na shiga buga game wai duk dan dai na dawo da hankalina jikina. Sai dai tuni na kasa cigaba da buga game ɗin, na koma kallon mutane a ƙasan ido musamman ma yaronsa da duk wani motsin sa......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒐𝒖𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_ ........Kusan kowa da ke a wajen abincin yake ci. Amma banda sarki banda gwamna. A kansa idanuna suka sauka shima. Zaune yake ƙafa ɗaya kan ɗaya da takardu a saman cinyarsa yana dubawa. Gefensa baturiyar matar nan ce ke masa magana da nuna masa abinda ke a takardun. Babu komai a gabansa sai bottle ɗin ruwa alamar ba abincin zai ci ba shima. (Jibesa kamar na ƙwarai). Na ayyana a zuciyata cike da taicinsa, ji nake kamar naje na shaƙe mar wuya na kwarara ihu tare shelantama mutane wanene shi. Amma dai na dake. Mansoor ne ya farga da mugun kallon da nake masa, sunana ya kira a hankali. Hakan ya sakani dawowa hayyacina. Ina ɗauke idona daga inda yake kuwa yana ɗagowa shima. Da alama yaji a jikinsa ana kallonsa ne. Harararsa na ɗan yi ta gefen ido na ɗauke kaina gaba ɗaya da ga sashinsa. Bayan duk an kammala cin abincin aka fara shirin shiga salla. Akwai ƙaton massalaci a cikin companyn. Ƙasa na maza, upstairs na mata. Sarki ne da kansa yaja sallar. Bayan an idar aka fito domin cigaba da abinda ya tara mutane dan lokacin tashi ya kusa. Zaune nai a massalacin na kasa fita. Sai da Khulsoom tai kirana a waya. Mansoor na samu a ƙofar massalacin tsaye yay shiru alamar yayi zurfi a tunani. Tsayawa nai kawai ina kallonsa, kafin na ƙarasa gabansa naɗan jujjuya hannuna a saitin fuskarsa sannan ya kawo numfashi. Alamar (lafiya?) Na masa da kaina. Ya sake sauke numfashi da sakin murmushi. “Lafiya Lau Babie. Damuwarki ce ta daman. Gaba ɗaya bana jin daɗin yanayin nan da nake ganinki a ciki. Dan ALLAH ki saki jikinki har mubar wajen nan zamu san mafita, kinga lokacin da zakiyi aikin ki ya kusa cika”. Kaina na jinjina masa da faɗin, “In sha ALLAH zanyi ƙoƙarin hakan.” Cikin gamsuwa ya nunamin hanya alamar muje. Babu musu muka jera har wajen zaman mu. “Cikin ne har yanzu dai?”. Khulsoom ta faɗa dai-dai ina kaiwa zaune. Guntun murmushi na mata ina girgiza kaina. “A'a na tsaya ƙarasa addu'a ne kawai. Ga zaman nan na waje ɗaya baka ɗan motsawa kuma akwai gundira”. “Sosai ma kuwa. Bakiji yanda ƙafafuna sukai dayi ba. Amma ai an kusa tashi in sha ALLAH tunda naga ga shi ma yana shirin miƙewa yay jawabin ƙarshe. Sai ki shirya lokacin aikinki yayi”. Jinai ƙirjina yay wani kalar harbawa. Har sai da na ambaci hazbinallahu wa-ni'imar wakil sannan na ɗan ji sassauci. Cigaba da ambaton hazbinallah... ɗin nayi, yayinda shi kuma ya fara jawabinsa. Kamar dai ɗazun haka yake faman gwamutsa mana gurɓatacciyar hausarsa da turanci da faransanci. Dan in yay hausar yaji ya kakare sai kawai ya kwakuso turanci ya maka abinsa.. Gaba ɗayanmu ƴan Jaridar da aka bari muka shigo wajen munzo da ga gidaje bai fi takwas ba ne. Dan haka tambayoyin da zamu masan ma daga inda muke zaune ne zamuyi su. Kuma za'ayi ɗaya bayan ɗaya ne. Bayan ya kammala jawabansa ya kawo dubansa garemu. Da yanayin gajiyawa dan hatta muryarsa ta nuna hakan ya furta, “Bismillah zaku iya yin tambayoyinku. Sai dai Please akan abinda ya shafi companyn nan kawai. Bana son wasu silly questions da basu shafi abinda ya taramu anan ɗin ba”. Cikin gamsuwa duk suka jinjina masa kai, dan ni dai bakina na taɓe ina mai jan tsuki ciki-ciki da ni kaɗai naji kayana, wannan ma ai rainin hankali ne, yanama mutane magana a gadarance. Wani dattijo ne ya fara miƙewa rigarsa da tambarinsu ya fara tambaya. Idanu ya zuba masa tamkar bazaice komai ba, harma kowa yay tunanin ko bazai amsa bane sai akaga ya ɗan murmusa kaɗan iya lips ɗinsa dake ƴan ficit. Gasu pink sosai dan sun ciza. Sai kuma ya nuna PA ɗinsa dake bayansa alamar shine zai amsa wannan tambayar. Hakan kuwa akai PA ɗin nasa ne ya bada amsar, hakama tambaya ta biyu da ga wasu. Duk yanda naso na motsa nayi tamu tambayar na kasa hakan. Gashi mune kuma ya kamata ace mun ma zama na farko. Ganinfa bani da niyyar tashi kamar ma hankalina baya tare da su dan har ya rage saura ƴam gida ɗaya Khulsoom ta zungureni. Firgigit na dawo hayyacina. Sai dai kafin na tashi ma waɗan can sun tashi. Dole na haƙura har sai da ya amsa tasu sannan na ɗaga hannu da taimakon Khulsoom. Dama ya bani kamar yanda yake bama kowa. A hankali na miƙe kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Yanda ya zuba min ido da ma kusan duk jama'ar dake wajen ya sani taune lips ɗina dake cikin face mask da ƙarfin tsiya ina mai karanto hazbinallah wa-ni'imar wakil a zuciyata. Da ƙyar na iya dai-daita numfashina ina mai janye idanuna da suma ke a cikin eyeglasses tare da sauke mask ɗin ƙasan haɓata sannan na furta. “Sir a matsayinka na matashi da za'a iya shiga mamakin ganin yanda ka gina katafaren kamfani irin wannan da ya zama na farko a Africa, a duniya na uku kuma bama shi kawai ka mallaka ba, akwai wasu manyan cibiyoyi daka kafa a ciki da wajen Africa ma ba Nigeria kawai ba, ko nace duniya, shin ko zaka iya jan hankali matasa irinka dake tasowa dangane da neman na kai da asalin tarihinka dan su san kaima ba daga kwance ka kai wannan matsayin ba, sai da kai aiki tuƙuru, tare da tsallake ƙalubale masu yawan gaske kuma duk kai haƙuri ka jure har gashi a yanzu ka zama wani babban ginshiƙi tauraron duniya dake haska yankinsa da ƙasarsa, yarensa harma da addininsa?”. Bashi da naima tambayar ba, hatta sauran ƴan jarida ƴan uwana dama duk jama'ar dake wajen sai da suka zuba min ido, harma da masu hangame bakuna sama. Bama sai sun faɗi abinda ya basu mamaki ba, ni na sani. Yace kar a masa tambaya sai akan abinda ya shafi company, sannan tambaya ɗaya kacal zakayi. Amma ni dana tashi na haɗa kusan tambaya goma ne a cikin ɗaya, na kuma yi tambaya akan kamfani kawai da ya buƙata amma na saka abinda yake gudun a tambayesa ta yanda dolene sai ya amsa min ɗin. Yaja kusan mintuna biyu cif yana kallona kawai cikin wani irin yanayi, sai yatsun hannunsa daya dafe dogon tables ɗin da aka cika da mic.. yake ta motsawa, musamman biyun tsakkiya. PA ɗinsa ne ya ɗan yunƙuro amma sai ya ɗaga masa hannu alamar ya dakata. Tsayawar yayi, sai dai shima wani mugun kallo yake jefamin fiyema dana uban gidan nasa. Oho ko'a jikina, ni dai tunda nayi tambaya ta ai shikenan, amsa kawai nake buƙata. Motsawarsa da sakin wani shegen makirin murmushinsa ya saka kowa sake maida hankali kansa. Murmushin ya sake saki yana ɗan cizar lip ɗinsa na ƙasa. Yay wani ɗan diri-diri kamar wanda ya rasa abin faɗa sai kuma ya nuna ni yana sake sakin wani lalataccen murmushin. A hankali ya furta, “Hmmm you are very smart girl. A karo na farko na yarda zan bada wannan amsar, amma ba yau ba, ba kuma anan ba saboda munada ƙarancin lokacin hakan.” Wani ƙwarin gwiwa ne naji ya sake zomin. Kai na tsaye na ce, “Thanks you sir. Amma taya zan sake samun wannan damar kamar haka ku da ganinku ba wasan yara bane. Gashi kuma ina matuƙar son gamsar da ƴan uwana matasa da sake farkar da waɗanda suka shagala. Zan so ace na samu date da time tun anan tare da location kodan ni da ƴan uwana matasa mu kasance a cikin shirin ji da ga bakin gwarzon mutum irinka”. Ai da ƙarfi yanzu kam ya cije lips ɗinsa, yana wani kalar tsatstsareni da kaifafan idanunsa, dan duk da a cikin eyeglasses suke dolene ka fahimci hakan musamman yanda kai tsaye direction ɗinsa yake gareni. PA ɗinsa ne ya ɗan matso ya masa maganar da shi kaɗai ya ji abinsa. Yana gama faɗa masa ya ɗan ja baya kaɗan shi kuma ya juyo gareni. A bazata ga kowa ya furta, “Na baki dama, kisa date, kisa time ki faɗi location koda a office ɗin ku ne”. Kutumelacy, ai jina ƙafafuna na neman gagara ɗaukata. Yayinda gaba ɗaya wajen yay wani irin ɗaukar shiru duk aka zuba masa idanun mamaki. Dan abune da bai taɓa faruwa ba. Maash a gidan tv ko jarida ko rediyo ko mujalla ana masa tambaya akan tarihinsa ba harkar business ba yana bada amsa. Abin mamaki. In taƙaice muku har taron nan ya tashi ban dawo dai-dai ba. Dan duk da hakan shine burina a kwanakin nan, sai nake jin kamar bazai yiwu ba. Koda yake hatta a ƙiyamullaili ɗina na satin nan sai da naita saka addu'ar fatan ALLAH ya ɗorani a kansa banyi zaton zan samu damar ba sam, kuma a cikin sauƙi ma haka. Hummm al'amarin da ban mamaki kam.... Kasancewar duk abinda ake a office ɗin mu suna kallo ne live dama mutane wata kalar gagarumar tarba muka samu. Musamman ma ni. Dan mata-matan staffs ɗin nan namu rungumeni suka dinga yi da kwarzanta ƙoƙarina. MD kam bakinsa tamkar zai yage ne. Wannan abin alfaharine a garesa ace mutum kamar Maash ya amsa gayyata da ga gidan tvn sa a gaɓar da kowa ke matuƙar buƙatar hakan. Oho su suke shirmensu ni nawa hankalin ma ba'a kansu yake ba. Maganar kisan can ne yay matuƙar tsaya mun a rai da zuciya. A dalilin sallar la'asar na samu damar zame musu. Dan bamu tsaya munyi acan ba kasancewar an tashi gab da za'a fara kiran salla. Ana idar da salla na MD yace muje gida mu huta. Haka dama nake buƙata. Dan burina kawai na keɓe da Mansoor na ji yaya za'ayi da batun video dake a cikin wayata. Muna barin office ɗin kam zancen dana fara masa kenan. Shima da alama abinda ke cimasa rai kenan. Dan haka muka shiga tattaunawa. Koda ya isa dani ƙofar gida ma ban fita a motar ba. Zancen muka cigaba da yi. Ni dai ina a matsayar mu kaima hukuma video ɗin. Tunda dai duk hanyar da zasu bibiyi batun gawar zai zama mai sauƙi kasancewar ya faɗi inda za'a kaita. Amma sai Mansoor ya ce nadai bashi dama yayi nazari tukunna. Na kuma tura masa video ɗin. Babu musu na tura masa, nima na adana wanda ke wayar tawa da ƙyau duk da babu wanda ke taɓamin waya ma. Daga haka mukai sallama ya wuce ni kuma na shiga gida. Dan Yaya Musaddiq na wajen aiki........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏_ ........Daga ajiye Samraah gida ya wuce shima. Sama-sama ya amsa gaisuwar maigadin su ya shige ciki. Shi da ɗan uwansa a duk sanda suka dawo gida idan sun fita sukan fara shiga sashen iyayensu ne, musamman ma shi da akance yanada ƙulafucin uwa. Amma yau sai hakan ya gagara garesa. Dan ko motar tasa yau a gab da sashensu ya ajiyeta. A falo ya samu yayansa kwance cikin kujera yana kallo, hannu kawai ya ɗaga masa nan ma yay shigewarsa ɗakin barcinsa. Da kallon mamaki Attahir ya bisa. Dan abune da bai saba gani ba. Amma sai ya ɗan girgiza kai da sake maida kansa ga tvn da yake kallo, zuciyarsa na ayyana masa maybe ya gaji ne. Ya cigaba da kallonsa da tunanin idan yay wanka ai zai fito ya nema abinci, amma shiru kake ji har magrib na neman yi. Tsam ya miƙe ya nufin ɗakin nasa, ya ɗanyi knocking, kafin ma a amsa masa ya tura ya shiga. A tsaye ya samu Mansoor na faman kai kawo. Yay masa kallon tsaf sannan ya ce, “Kai wai lafiyarka ka kuwa? Ka dawo ma mutane kana ɗacin rai ka kuma shigo ka rufe kanka a ɗaki. Ko har ka fara tunanin auren ne? To bakai kace kana so ba, kama jirani kayi tsalle ka dire kai ba haka ba.....” Ganin Mansoor bai maida masa murtanin tsokanar ba yasa Attahir yin shiru, gabansa ya ƙarasa tare da dafa kafaɗarsa. Cike da kulawa ya ce, “Baka da lafiya ne Kiddo?”. Kai Mansoor ya girgiza masa. “To mike damunka?”. “Yaya babu komai fa. Kawai bana jin daɗine”. Jimm Attahir ɗin yay yana kallonsa. Sai kuma ya jinjina kansa da faɗin, “Okay shike nan. Shiga bayi kai alwala mu wuce massalaci. Dan kar Dad yay zaman jiranmu”. Kai kawai Mansoor ɗin ya jinjina masa yana nufar bayi. Attahir ya bisa da kallo har sai da ya shige. Shima kaɗa kansa yay ya fita yana ji a ransa ƙarya Mansoor ɗin ke masa. Duk da shi mutumin ne mara son hayaniya. Amma idan suna tare baka banbance wannan halin nasa na rashin yawan magana. Dan suna rayuwa ne tamkar abokai ba wa da ƙani ba. Sun tashi ne kamar ƴan biyu, komai nasu a tare yake. A halayyane kawai zaka iya banbance su. Dan tabbas sun banbanta tanan ɗin. Koda suka fito domin tafiya massalacin sun gamu da Dad ɗin su. Shima dai da mamaki yake kallon Mansoor ɗin. Harma ya gagara haƙuri ya ce, “Kai dama ka dawo gidan kabar Mamanku natama mutane shelarka?”. Kan Mansoor a rissine ya ce, “Dad amin afuwa na dawo ne kaina namun ciwo”. “Dole kai ciwon kai ai wannan hidima da kuka sha. Ku muje massalaci za'a tada salla”. Binsa sukai gwanin sha'awa suka fita har maigadi. Koda aka idar da sallar ma basu fito a massalacin ba har akai isha'i. A tare yanzu ma suka dawo gidan, kai tsaye ainahin sashen gidan suka nufa su duka. Sashene babba kuma mai ƙyau, dan komai yaji na ababen more rayuwa. Lallai gidan su Mansoor suna da kuɗi suma ba laifi. Dan idan wani ne ma zai iya cewa yafi ƙarfin aikin da yake yanzu, duk da kuwa yana a babbar kujera ne. Amma kuma aikin jarida hubby ɗinsa ne tun yana yaronsa. Sannan mahaifinsa nada babbar alaƙa ma da wajen aikin nasu, dan yanada hannun jari mai ƙarfi a cikin companyn. Shigowarsu dai-dai da fitowar ƴammata biyu masu kama da su Mansoor ɗin sosai daga wani ɗaki. Cike da murnarsu suka nufo Mansoor ɗin suna masa sannu, sai jera masa tambaya suke akan Maash. Amma a mamakin kowa ko a yaƙi ya furta, sai ma zagayesu yay ya wuce saman kujera ya zauna yana faɗin, “Malami kun isheni da surutu”. Babbar ce ta ɓata fuska tana kallon Dad ɗin su. Ya ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa alamar sunfi kusa. Sake ɓata fuska tai sosai. Ta ce, “Dad kallafa yanda yake basar da mu. Shi dama Yaya Man idan baiso abu ba ya iyama mutane wulakanci”. “To yayi fitinanniya.” Wata mata dattijuwa ta faɗa tana fitowa a hanyar dake tabbatar da kitchen ne, itama dai kama take sosai da su Mansoor ɗin. Hararar yarinyar tai da nuna musu hanyar data fito. “Ku wuce kuzo ku fiddo abinci. An gaya muku kowama irinku ne da shegen surutu. Yaro yaje aiki ya gaji kun wani sashi gaba dolene sai ya baku labarin abinda ya farun? Idan son gani kuke miya hanaku zuwa”. “To an taɓa ɗan lelen Mamy”. Cewar Attahir na ƴar dariya. Murmushi Dad shima yayi, yayinda Mansoor ya miƙe ya nufeta yana harar Yayan nasa. Yana zuwa gab da ita ya bata side hug, tare da kamo hannunta ya sumbata. A marairaice ya ce, “Mamy barsu kada ma kanki yay ciwo”. Kansa ta shafa fuskarta da murmushi. Kafin cikin kulawa ta ce, “Yaushe ka dawo?”. “Tun ɗazun ya dawo yau baya yayinki ne kawai Mamy”. Attahir ne ya faɗa yana kaiwa zaune a kujerar dining dan su Islam sun kammala jera abincin. Hararsa Mansoor yayi, tare da faɗin, “Mamy ƙyalesa so yake kawai ya haɗamu. Kaina fa ke ciwo amma nasha magani”. Yay saurin faɗar haka ne dan yasan yanzu zata iya ruɗewa. A hakanma tuni fuskarta ta nuna damuwa. Dan sai tattaɓa kan nasa take, daga ƙarshe dai ta ja hannunsa suka koma saman dining ɗin tana jera masa sannu, abincin ma a baki ta bashi dan kowa yasan ɗan gatan ta ne a gidan. Daurewa yay kawai ya ɗan ci abincin dan karta damu, amma gaba ɗaya hankalinsa na'a kan Samraah, babu abinda zuciyarsa ke hango masa sai yanda take a firgice har sanda ya ajiyeta a gida..... Bayan sun kammala cin abinci duk yanda Mamy taso suyi hira Mansoor bai cewa komai, zata nuna damuwa Dad ya dakatar da ita akan ta barsa yaje ya huta dole akwai gajiya. Mansoor yaji daɗin samun wannan damar, dan haka ya miƙe ya wuce sashensu. Yana shiga bedroom ɗinsa wayar Samraah yay ƙoƙarin kira. Cikin sa'a kuwa bugu uku ta ɗaga. Sai dai a yanda yaji muryarta na fita a shaƙe ya tabbatar har yanzu tana a cikin damuwa. Daɗaɗan kalamai ya shiga jera mata da lallashi akan ta kwantar da hankalinta. Ba shi yace mata zasuyi wani abu ba. Bafa itace ta aikata laifin nan ba da har zata takurama ranta haka suma dake tare da ita ta sakasu a damuwa. Sosai lallashin nasa yay mata tasiri, dan haka ya yanke kiran yana cewa bari yay shirin barci zai kirata video call. Yana yanke wayar Attahir na shigowa ɗakin, yanda ya kafesa da ido ya sashi duƙar da kansa, fatansa dai ALLAH yasa baiji wayar da sukai da Samraah ɗin ba. “Mike damunka Mansoor?”. “Yaya nace maka babu komai”. “Ƙarya kake yi. Idan kuma zakama kowa wannan ƙaryar ni kasan bazaka mun ba. Dan nasanka fiye da yunwar cikina. Koka sanar min, ko yanzun nan naje na kira maka Mamy da Dad maybe su ka sanar musu”. Ya ƙare maganar da juyawa kamar zai fita. Da sauri Mansoor ya riƙosa yana girgiza kansa. “Please basai ka kirasu ba. Ba wata damuwa bace mai yawa fa”. “Kasan dai bama ɓoyema juna damuwarmu. Karka fara daga yau to”. Numfashi mai nauyi Mansoor ya sauke tare da ajiyar zuciya. A ransa kuwa yana harhaɗo ƙaryar dazai sanar masa dan bazai taɓa faɗa masa gaskiyar zancen ba tunda yayima Samraah alƙawarin haka..... ★💫★💫★💫★💫 “Sir dan ALLAH kada ka saka kanka a damuwa. In dai batun yarinyar nan ne dai-dai yake da kaɗawar iska mai wucewa. Ita ta isa ta saka abinda bakayi niyya ba. Waye ubanta a ƙasar nan? Har micece ita a aikin jaridar ma. Yarinya ce fa ƙarama fitik”. Idanunsa dake lumshe ya buɗe a hankali. PA ɗin nasa dake magana ya zubama su kusan sakan arba'in. Sai kuma ya sake maidasu ya lumshe a kasalance. Dai-dai nan drivern sa yay sallama a ƙofar katafaren falon. PA ɗinsa ne ya amsa. Sai kuma ya bashi umarnin ya shigo dan yasan kayan boss ɗin nasu ne dake a mota ya kawo. Cike da tsantsar girmamawa yaje Centre table ɗin gabansa kuwa ya ajiye. Sai kuma yay ɗan jimm a duƙe kafin ya ɗago yana nuna wata jaka. “Sir wannan wani mutum ne yanzu nan ya kawo wai a baka. Naso ƙin yin hakan amma kausasan kalamansa suka daƙileni. Dan ya tabbatar min ƙin baka ɗin zai zama kuskuren da bazan yafema kaina ba kaima kuma bazaka yafe min ba. Dan saƙon nada amfanin da idan na wofamtar da shi dai-dai yake da gina harsashin tarwatsaka. Amin afuwa shine ya faɗi hakan”. A zabire PA ɗinsa ya furta, “What! Wane ɗan iska ne haka. Su securitys ɗin gate kuma suna aikin mi ya shigo cikin gidan nan, kai kuma ka zauna sauraren wawancinsa, are you mad?”. Shiko gogan ko motsi baiyi ba. Sai idanunsa da ya ɗan buɗe kaɗan a ƙasa-ƙasa yake kallon drivern nashi da su. PA zai sake magana ya masa alamar ya barsa. Hakan yasa driver tashi da sauri ya fita ya bar saƙon da aka nannaɗe a cikin leda mai ƙyalli. Sake maida idanunsa yay ya lumshe kawai. PA da hankalinsa gaba ɗaya ke'a kan saƙon sam ya kasa nutsuwa, ganin ogan nasa baida alamar bashi umarnin ya buɗe suka miye a ciki ya furta, “Sir ya kamata musan minene a ciki. Dan bamu san mi mai saƙon ya taka ba har yake irin waɗan nan kalaman.” shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya kaɗa masa kai alamar ya buɗe ɗin. Jikin PA har rawa yake wajen ɗaukar saƙon. Kamar ƙyaftawar ido ya gama buɗesa ledar da aka nannaɗe sa. Sai dai kafin ya ciro abinda ke'a cikin kwalin da aka naɗe ɗin text message ya shigo wayarsa. Kasancewar wayar mai muhimmanci ce dan ta business ce ya ɗauka dan ya duba saboda akwai saƙon da dama suke tsammani. Rubutu ne da bai wuce words ɗari ba. Dan haka ya fara karantowa. Sosai jikin Hayatu PA ke rawa yana mai ambaton “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Sir tabbas hasashenka ya zama gaskiya. A kwai wanda ya gammu, kuma tabbas shine mai face mask ɗin nan. Dan gashi anan ya turo saƙo?”. Idanunsa ya ɗan buɗe batare daya tanka ba yay masa alamar miya faru?. Cikin rawar jiki Hayatu ya fara karanto saƙon a fili kamar haka.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_ ........*_Barkan ka madubin wannan ƙarni. Ba sai na cikaka da gaisuwa ba, bari na tafi kai tsaye kawai. Ina buƙatar naira miliyan ɗari biyar daga gareka. Kuma cikin gaggawa. Idan ba hakaba, a daren yau zan rusa duk wani tanadinka da tunƙahonka da videon dake hannuna ta hanyar yaɗashi a social media. Kasan dai kisan kai ba abune mai sauƙi ba. Musamman ga mutum irinka sananne mai tarin magauta da masoya tako ina. Na baka awa arba'in da takwas. Idan kunne ya ji jiki ya tsira._* Ya jima bai motsa da ga zaman da yay a lallausar kujerar ba ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yayinda bayansa ke kwance jikin kujerar kansa a sama kaɗan. Yanda yay biris ɗin sai ka ɗauka baima ji ko fahimtar abinda PA ɗin nasa ya karanto masa bane ba sam. Yaja kusan minti uku PA nata kai kawo kafin yaja wani irin huci ya furzar yana mai buɗe idanunsa da suka sake wani irin garai-garai ai nahin suffarsu ta idanun mage na sake bayyana a fili. Zaune ya tashi da ƙyau, sai dai a nutsensa yake abin mamaki. Goran ruwa dake a Centre table ɗin ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa. Sai da ya shanyesa tas sannan ya jefar da bottle ɗin. Sake furzar da huci mai zafi yayi a karo na biyu yana sake nutsar da kansa, sai kuma kamar wanda ya tuna ya dubi PA ɗinsa. “Ina buƙatar duka cctv footage na company a daren nan?”. Cak Hayatu ya tsaya da ga kai-kawon da yake, sai kuma jiki a sanyaye ya ce, “Sir ka manta mun duba sanda muka shiga kafin faruwar abun amma basayi duk an kashesu”. “Hakane, amma kamar na kunna ukun farkon nan.” “Yes yes tabbas kuma hakane fa Sir. Wlhy sai yanzu na tuna. Aiko ko wanene wannan zaici ubansa.” baima jira umarnin ogan nasa ba ya fice da sassarfa tamkar zai kifa ƙasa duk kuwa da dare ne a lokacin. Dan kusan sha ɗaya ma ake nema, saboda bayan an tashi a taron company sun bu sarkine kamar yanda ya buƙa. Bayan sallar magrib suka bar gidan sarki, maimakon gida suka wuce wajen wani abokin harƙallarsa dan haɗuwar ta sirrice, sai goma saura suka nufo gida. Gashi yanzu ana harar sha ɗaya da wasu mintuna. Shima da ƙyar ya iya miƙewa da ga falon ya nufi bedroom ɗinsa. Tamkar mai hasashen ganin wani abu sai da ya gama kalle kowacce kusurwa da lungu da saƙon na ɗakin sannan ya kai zaune a bakin katafaren lafiyayyen gadon. Sabon gida ne fil dan yau ne ya fara shigarsa. Anyi aikin gininsa tare da Companyn nasa ne. Bai cika son zaman hotels ba a rayuwarsa sai in har ya zama tilas a garesa. Ta wani ɓangaren kuma gorin mutane akan kullum yana cika bakin shi ɗan Kano ne amma ko gida baida a arewa ma gaba ɗaya ya sashi ginin wannan gidan da ko makaho ya laluba yasan an kashe kuɗi. Dan yanda companyn ya haɗu shima gidan haka ya haɗu matuƙa. Yanda ya zauna shiru ya dafe kansa zaka ɗauka ciwo yake masa ne. Amma sam ba haka bane. Abubuwane kawai suke masa kai-kawo a rai da suka faru a wannan yinin. Kallon komai yake tamkar wani film ba zahiri ba. Ba yau ne ya fara cin karo da matsaloli da ƙalubalen rayuwa ba. Amma na yau ɗin na musamman ne. Dan duk sunzo masa a bazata. Hakan na nufin ya sakankance da yawa kenan. Sannan dole ne ya sake shiri in har yana buƙatar abubuwa su tafi masa a yanda yake buƙata anan batare da tangarɗa ba?. Amma dai bari ya jira P.A ɗinsa da sakamakon da yake buƙatar gani kafin ya tsara komai akan mizaninsa. Da ga haka ya miƙe yana mai fara zame kayan jikinsa domin shiga wanka... Yaja tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe ash color sabuwa dal. Dan yanda take wani maski-maski zai tabbatar da hakan. Ƙaramin towel da a hannunsa ya kai kan jiƙaƙƙiyar sumar kansa mai tsaho data kwanto masa a fuska sosai, hakama ta bayansa kai kace bai haɗa jini da babaƙen fata ba balle ma har a kirashi da suna bahaushe. Tamkar ba shi kaɗaine a ɗakin ba. Fuskar nan a tsuke babu alamun rahama a cikinta. Duk da tun fitowarsa wayarsa ke tsuwwa alamar kira na shigowa, yay biris da ita tamkar bai ji ba. Sai ma ƙoƙarin nufar ƙaton mirrorn dake a ɗakin yayi abinsa. Tuni Hayatu ya shirya masa kayan shafe-shafensa a mirrorn, dan zaiyi kamar 1week ne a cikin Kanon kamar yanda yake fata. Hand dryer da aka ajiye a saman mirror ɗin sabuwa fil ya ɗauka ya jona a socket, sumar tasa ya fara busarwa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya kammala gyarata alamar ya riga ya saba da hakan. Kafin ya ɗan shafa mansa sama-sama tare da sprays masu shegen ƙamshi kala har biyu sannan ya nufi doguwar wadrobe data cinye bango guda. Ta farko kawai ya buɗe, anan ko yaga kaya kusan kala goma duk ƙananu, sai ƴar akwatin da yazo da ita da suit kala uku a ciki. Yasan kayan dake a shiryen duk aikin Hayatu ne. Batare da yace komai ba ya ciri farin pyjamas mai shegen ƙyau da laushi, sai boxer shima dai sabo. Tsaf yay shirinsa tare da sake komawa gaban mirrorn yay sabon wankan tsadaddun turarurrukansa na barci da ƙamshinsu ba'a magana kamar ba dare ba. Tsaki yaja a hankali yana hararar wayarsa da ke cigaba da tsuwwa babu ko ƙaƙƙautawa. Ya san mai kiran nasa, dan ita kaɗaice take karya dokarsa akan hakan. Duk wanda ya sanshi yasan yanada doka a akan kira, dokar kuwa itace in har kamasa kira 1 bai ɗaga ba ka bada mintuna kamar biyar sannan ka sake. Idan nan ma aka samu akasi bai ɗaga ɗin ba to ka haƙura kawai, idan shi ya samu lokaci zai iya ya kiraka, idan bai biyo ba kuma ka ɗauka kiran naka baida muhimmanci ne. Wayoyinsa duk a hannun Hayatu suke. Wannan ce kawai yake riƙewa saboda Ummien sa. Gaban gadon ya ƙarasa in da ya yasar da wayar, cikin ƙara ɗaure fuska ya ɗauka dan yana son ta barsa. A daƙile ya kai wayar kunensa sai dai yaƙi cewa komai. Sai da yaja kusan sakan hamsin ya ce, “Thanks”. Kawai yaja bakinsa yay shiru. Kasancewar bai sauke wayar ba zai tabbatar ma da har yanzu magana ake daga can, dan sai wani yamutsa fuska yake da sake tsuketa kamar mai jin warin mai maganar. Kusan minti biyu ya sake furta, “Zanyi barci”. Daga haka ya yanke kiran gaba ɗaya. Wayar ya wurga a saman gadon tare da jan tsaki mai ƙarfi ya haye gadon yay kwanciyarsa. Kai kace ma baida wata damuwa a rayuwa. Sai da yay addu'oi barci sannan ya lumshe idanunsa. Kafin wani dogon lokaci ya fara sauke numfashi a hankali alamar yayi barcin..... ●´⌓`●●´⌓`●●´⌓`● Duk yanda nagaji na kasa barci. Sai faman juye-juye nake abubuwa na dawo min tamkar yanzu suke faruwa, dan ma ƴar wayar da mukai da Mansoor ta ɗan sani ƴar nutsuwa. Ganin ƙwaƙwalwata na neman tarwatsewa na tashi na ɗaura alwala. Salla na farayi, sai da na kwashe kusan awa ɗaya da rabi sannan na zauna ina istigifari. Kamar a mafarki naji wayata na verbration. A gogo na kalla, ƙarfe biyu da kwata. Mamaki ya kamani, dan ko Mansoor baya kirana a wannan irin lokacin, kuma ma ai munyi waya duk da dai yace zai sake kira video call amma bai kira ba, ganin lokaci haja yasa ban damu ba. Dan duk tsawon wayarmu baya wuce daga tara zuwa goma. Jin an sake kira bayan ta katse na yunƙura na ɗauka. Abin mamaki Mansoor ne. Ɗagawa nai hankali a tashe, a tunanina ko wani abu ya samesa. Amma sai naji yaymin sallama cikin taushin murya. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, sannan na amsa masa. “Dama naji a jikina zaki iya kasa barci, kiyi haƙuri Yaya ne ya ɗauke hankalina shiyyasa ban sake kiran ba. Haba Babie dan ALLAH ki cirema kanki damuwar nan. Ai ko ke kika aikata laifin nan sai haka”. Numfashi na sauke a hankali. Cikin sanyin murya na ce, “Ni ban kasa barci ba fa, na farka ne kawai”. “Uhhm yau kuma halin daba naki ba kika aro, to ai bai miki ƙyau ba dan baki iya ƙaryarba tunda ga harshenki yana rawa”. Ɗan murmushin ƙarfin hali nayi, sai kuma nakai kwance ina faɗin, “To amin afuwa gashi na kwanta. Amma kaima miya hanaka barci?”. “Saboda mahaɗin zuciyata batayi ba”. “Humm”. Na faɗa kawai ina murmushi. Shima ina jiyo sautin nasa murmushin. Mun ɗan yi shiru na wasu sakannin kowannemu na sauraren saukar numfashin ɗan uwansa. Kafin ya katse shirun da cewa, “Kin sanarma Yaya Musaddiq abinda ya faru ko?”. “A'a”. “Miyasa?”. “Kawai dai”. “Aiko Babie ya kamata ya sani. Dan ko zamu iya ɓoyema kowa shi banda shi. Maybe ma ya ƙaremu da shawara ai. Dan wlhy har yanzu ni kaina duk a kulle yake”. “Hakane zan sanar masa gobe in sha ALLAHU. Amma ni dai dan kaƙi ta nawane. Hukuma kawai ya kamata mu miƙawa ai”. “Baƙi naiba Samraah. Ina son ki fahimci wani abu. Mutumin nan fa ya wuce duk inda kike tunani a ƙasar nan. Yanzu koda mun miƙa video ɗin nan ga hukuma kina ganin zasu hukuntashi ne. Ko kin manta yanzu a ƙasar nan tamu KUƊI ne ke magana ba GASKIYA ba. Shi kuma ALLAH ya bashi su, Samraah Maash fa zai iya juya Africa a tafin hannunsa ta yanda yaso bama Nigeria ba. Ke hatta da ƙasashen masu jajayen kunnuwan yanada ƙarfin faɗa aji sosai fiye da yanda kike tunani ta wasu fannoni. Sai dai su banbancinsu damu zasu iya hukunta duk wani mai laifi koda shi wanene? Amma a ƙasarmu ba haka bane. Ko wanda bai kama ƙafar Maash ba zai iya shallakewa in har da kuɗi. Kiyi haƙuri dai mu nema mafita mai ɓullewa. Mu kuma samu jajirtaccen ɗan sandan da zai iya yin duk abinda ya dace batare da kuɗi sun iya tankwarashi ba saboda gaskiyarsa. In dai Maash ne bazamu ƙyalesa ba sai an ƙwatoma mutumin nan hakkinsa”. “ALLAH ya tabbatar to. Na kuma gamsu da bayaninka.” “Masha ALLAH dear, yanzu dai zan shigo gobe in ALLAH ya kaimu ki biyo Yaya Musaddiq gareji mu haɗu acan dan ina so mu tattauna da gaggawa mu nemo mafita kafin Maash ya farga. Saboda babu yanda za'ai ace babu camaras a wajen nan duk da Companyn bai fara aiki ba sai Monday”. Sosai zancensa ta ratsani dan har sai da na tashi zaune dingangan. Amma na gagara cemasa komai saboda yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri........✍️ _Tofa masu karatu yanzunne fa ainahin wasan zai fara. Dan da alama mun gama sharar fage zamu tafi mataki na biyu a labarin. Wa kuke tunanin ya rubuta saƙon nan? Sannan karku manta a cctv footage fa Samraah za'a gani. Shin ko itace dai ta rubuta saƙon? Ko kuma wani yaji sanda take faɗama Mansoor yay amfani da damar? Ko kuwa ba ita kaɗaice ta gani ba? Shin minene dalilin Maash nayin kisan nan ma wai? Wanene aka kashe?..... Kai kai kai cakwakiya ce fa iya cakwakiya a labarin nan. Amma dai ina son jin amsoshinku a comment section. Yau har masu laɓe su fito inba haka ba gobe babu posting sai bayan salla🚴🚴🚴._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_ .......*_WASHE GARI_* kamar yanda na saba na tashi nai ayyukana da sauri-sauri. Ana idar da sallar asuba nai wanka. Breakfast ɗin Yaya Musaddiq na ɗauka na nufi kai masa kusan bakwai da rabi. Nako samu har ya kammala shiryawa. Tunda na shigo yake bina da kallo, basai nace komai ba nasan ya gama fahimtar yanayina ne. Amma sai na dake. Sai dai ina gaishesa maimakon amsa min tambaya ya jeho min. Baki na buɗe zance babu komai yay saurin ɗaga min hannu da faɗin, “Karma kimun ƙarya. Faɗamin mike damunki?”. A hankali hawayen da nake riƙewa suka silalo. Nima babu shiri na silale ƙasa ina mai fashewa da kuka. Duk abinda ke a raina tun jiya ne ya samu damar fitowa. Kafin ma ya sake cewa da ni komai na shiga faɗin, “Yaya kisan kai yayi. Da idona na gansa yana zare wuƙa a jikin mutumin ga jini face-face. A kunnena naji yana faɗin akai gawar wani anguwa a ajiyeta.....” A cikin matuƙar tashin hankali ya katseni jikinsa na rawa. “Waye wai? Ki min magana a buɗe Samraah Please wa aka kashe waye kuma yay kisan?”. Maimakon bashi amsa sai na miƙa masa wayata kawai. Amsa yay da rawar jiki. Yana ko dannawa da video ɗin ya fara cin karo dan ni bana sakama waya password sam. A matuƙar birkice ya ɗago yana kallona tun a fara kallon video ɗin. Idanunsa a warwaje na shiga razana ya furta, “Samraah Maash fa?”. Kaina na jinjina masa da sauri ina faɗin, “Shi yaya! shi! Mutumin nan azzalumi ne bana kirki bane kamar yanda duniya ke kallonsa. Zata iya yiwuwa ma kuɗin nasa bana ALLAH bane na jinin mutane ne”. Tuni zufa ta wanke Yaya Musaddiq. Cikin tashin hankali ya ce, “Bayan ni wa kika faɗamawa?”. “Mansoor ne kawai Yaya. Tun jiya nace mu kai ma hukuma video ɗin amma ya hana. Shine ma yace na baka ka gani dan mu haɗu da shi a gareji mu tattauna”. “Gara daya hanaki Samraah. Dan dole wannan al'amarin na buƙatar nazari. Maash ba anyhow mutum bane da dokar hukuma zatayi tasiri akansa cikin sauri. Inaga yanzu ba zama zamuyi ba tashi mu wuce. Bara na kira Mansoor ɗin ya fito shima gara muyi abinda ya dace da wuri tun kafin ya bar garin nan. Dan bai zama lallai a sake samun irin wannan damar ba duk da naji ya amsa miki wai kiyi hira da shi. Ga gari nan duk ya ɗauki zance harda masu faɗin ba haka kawai kikaje masa ba akwai asiri saboda yanda ya amsa ɗin babu musu a gaban duniya. Amma ni zuwa yanzu na fara zargin akwai wata a ƙasa kam, bana raba ɗayan biyu ya ganki sanda kike ɗaukar video ɗin nan, ko kuma ta cctv, dan Company kamar nasa dole asamu camaras tako ina”. Idanu na waro sosai na matuƙar mamaki, Yaya Musaddiq ya jinjina min kai alamar tabbatarwa. “Samraah duk mai hankali dolene ya gane akwai dalilin Maash na amsa miki gayyatar da kikai masa cikin sauƙi. Dan bazai taɓa zama ya amsa miki bane kawai saboda kin jera masa tambayoyi. Kai ina dolene ma ya ganki fa, ya barki ne kawai bisa dalilinsa, sannan yazo a bainar jama'a ya amsa zaiyi hira dake, hakan na nufin akwai wani abu da yake ƙullawa”. Sosai na zubama Yaya Musaddiq ido, dan tabbas zancensa yasa na fara dawowa cikin hankalina yanda ya kamata. (Humm you are vary smart girl) kalmar daya fara ambata a kaina kenan. Tabbas wannan mutumin terror ne na gasken-gaske. Shin mi yake ƙullawa? Dan dolen dole akwai abinda ke ransa kamar yanda Yaya Musaddiq ya faɗa. Kai ina buƙatar ganin ma program ɗin jiya gaskiya..... “Kinga tashi muje, ba lokacin tunani bane yanzun”. Yaya Musaddiq ya faɗa cikin katse mun tunani. Miƙewa nai babu musu, dan basai na koma cikin gida ba dama.... 🤙❤️🤙❤️🤙❤️ A ɓangaren Maash asubar fari ya farka, da ƙyar ya iya tashi saboda gaɓɓansa duk ciwo suke masa. Ruwa ya fara watsawa ya fito a gurguje ya kimtsa cikin wando da rigar polo. Koda ya fito su Hayatu suma har sun fito zasu wuce massalacin. A tare suka fita, bayan an idar da salla bai koma cikin gidan ba yace ma Tijjani ya fito da mota zasu je wani waje. Da sauri Tijjani ya shiga ciki, babu jimawa ya fito da mota, suma guards ɗinsa suka fito. Komai baice ba Hayatu ya buɗe masa baya ga shiga, shi kuma ya shiga gaba kusa da Tijjani. Jihar Jigawa suka nufa, a wani ƙauye dan akwai business ɗin da zai yi a wajen. Duk da dai da farko bai wani ɗauki abin da muhimmanci ba, sai da zasu je massalacin nan ne Hayatu ke sanar masa mutumin da zasuyi kasuwancin ya kira, kuma yana son suje da wuri ne. Yinin ranar guda a Jigawa suka cinyesa. Ko abinci bai sakama cikinsa ba garama su su Hayatun. Sai Black tea kawai yake faman sha kasancewar duk inda yake yana tare da flaks ɗin ruwan zafinsa a mota, sai kuma chocolate dan mayenta ne da haɗaɗɗun biscuits. Sai bayan la'asar suka dawo cikin Kano a matuƙar gajiye. Musamman ma shi duk da dai yaci chocolate sosai amma yana buƙatar dafaffen abinci, dan rabonsa da dafaffen abinci sosai tun shekaran jiya a Lagos. Ko zama a falon baiyi ba ya wuce bedroom, suma dai su Hayatun duk a gajiye suke, dan haka kowa ya nufi sashensa danya watsa ruwa. Bathtub ya cika ra ruwan ɗumi sosai sannan ya shiga ciki, sai da yaji ko inansa ya miƙe sannan ya ɗauraye jikinsa ya fita. Duk yau sau ɗaya kawai yay waya da Ummien sa. Ji yake duk kewarta ta damesa. Sai dai yanzu yasan koya kira bazai samu ba dan ba lokacin kira bane dan sallar magrib aketa kira. Shiri yay tsaf cikin kaya marasa nauyi. Ya baɗe jikinsa da turare sannan ya saka slippers da ke ajiye yay ficewarsa. Tun kafin ya ƙarasa fitowa cikin falon Hayatu dake zaune yana jiran fitowarsa ya miƙe da sauri. Dan tun ɗazun ya dawo daga wanka da yaje yayo shima a sashensa. Ya dawo ne da wuri akan batun cctv footage na jiya, dan yana ganin ya kamata su duba issue ɗin kar a samu matsala. Kallo ɗaya ya masa ya ɗauke kansa, sai kuma ya nufi ƙofa a taƙaice ya ce, “Kayi alwala”. Cikin girmamawa Hayatu ya amsa da “Okay Sir”. Sai kuma ya saki murmushi yana mai binsa da kallo. A duniya boss ɗinsa da banne. Mutum ne mai abubuwan ban mamaki daban-daban. Ba kuma zaka tabbatar da hakan ba sai ka kasance a makusancinsa. ALLAH ya azurtashi da ni'imomi da yawa a rayuwa. Gadai ƙyawu kamar shine ya zana kansa. Ga dukiya, ga ilimin addini dana zamani. Yanada ƙyauta ga duk wanda ke tare da shi. Sai dai kuma hatsabibin kansa ne baifa mutunci a wasu fannin. Dan wani irin mutum ne a hagungunce da zaka iya ɗaukar lokaci baka fahimci alƙiblarsa ba. Ga taurin kam masifa da baƙar zuciya. Baya ragi ko ragowa ga duk ubanda yace masa kule. Yakan karya yatsar duk wanda ya nunashi dan baya ƙaunar raini. Shifa ko'akan business ana lallaɓa abokan harƙalla dan su dawo shi a garesa bai san wannan ba. Kana kawo masa hauka zai cireka a sabgarsa kawai. Sai dai baka isa tabbatar da waɗan nan halayyar tasa ba kai tsaye sai ka shigo gonarsa. Dan sumumu kasaune shi _*MACIJIN SARI KA NOƘE_*. A zahirinsa zaka ɗauka mutum ne mai sanyi da nuna halin ko'in kula, sai dai a kowanne motsi na cikin rayuwarsa a ankare yake. Domin indai brain ce ALLAH ya bashi. Irinsu ne ke juya akalar abubuwa a ƙanƙanin lokaci da kwanyarsu..... Firgigit ya dawo hayyacinsa jin kiran sallah. Da sauri ya shiga toilet ɗin falon ya ɗauro alwala ya wuce masallacin shima... Bayan idar da sallar isha'i suka shigo gidan. Sai dai Hayatu da Tijjani drivern sa sun rigashi shigowa. Dan su duka suna a gidan har baturiyar nan. Sai dai kowannensu yana a mabanbancin masauki da sai in shine ya buƙaci ganinsu zasu ganshin. Kusan mintuna goma suna a ƙaton compound ɗin gidan da ga jikin motoci suna hira sai gashi ya shigo shima. Ya ɗan dakata yay magana da masu gadi da suka kasance ƴan sanda har su uku sannan ya ƙaraso inda suke. Duk nutsuwa sukai kawunansu a ƙasa, baice da su komai ba ya wuce inda lafiyayyar ƙofar shiga sashensa take. Dan ta gilashi ce mai tsananin ƙyau da ɗaukar idon mai kallo. Gata golden daga waje sai walwali take kamar wani zinaren gaskiya. Da sauri Hayatu dake biye da shi ya buɗe masa ƙofar. Harararsa ya ɗan yi, Hayatu ɗin ya duƙar da kai ƙasa yana murmushi dan yasan laifinsa akan buɗe ƙofar ne tunda yana hanasu. Har ya shiga ya ɗan waiwayo. Driver dake ƙoƙarin komawa da baya ya dakatar ta hanyar faɗin, “Tijjani!”. Da sauri Tijjani ya amsa masa da “Na'am ranka ya daɗe”. Komai bai sake cewa ba ya cigaba da tafiyarsa ciki. Dan haka duk suka bisa. Duk da garin ba zafi ake ba, ba kuma sanyi ne mai tsanani ba dan ya fara bankwana falon a ƙanƙare yake da sanyin raɓar ac. Ga wani ƙamshi na musamman daya gaurayu da turarensa tamkar ba a jiya ne ya fara rayuwar cikin gidan ba. Zaune ya kai saman 3sitter. Kamar yanda ya saba zaman ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yanzun ma hakan yayi. Shiru kamar mai nazarin wani abu sai kuma ya ɗago yana ma Hayatu nuni da remote dake a Centre table. Remote ɗin Hayatu ya ɗauka da sauri, dan ko ogansa bai magana ba yana saurin gane karatun shirunsa saboda da hakan ya horesu tun farko. Dan shi bamai yawan magana bane sai idan shine yaso hakan da kansa. Sai kuma idan yana a gaban mahaifiyarsa ko mahaifinsa, shima a wasu lokutan ne yake hakan, sai ko Ammie. Volume ɗin tvn ya sassauta tare da canja tasha zuwa inda yasan yafi yawan kallo a irin wannan lokacin. Tasha ce ta addini, sai dai suna gabatar da duka programs ɗin su ne da turanci, hatta da wa'azi kuwa........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_ _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏_ .......Gyaran murya ya ɗan yi idonsa akan Tijjani. Cikin sauri Tijjani da idonsa ke akan tv ya maido hankalinsa garesa. Kafin ma yace wani abu cikin muryar nan tashi kamar ta rowa ya taresa da faɗin, “Ina za'a samu abinci mai tsafta?”. Cikin girmamawa Tijjani ya ce, “Ranka ya daɗe akwai gidajen abinci masu inganci dake tsaftace abincinsu sosai a garin Kano. Harma da masuyi a cikin gidaje sai dai kawai ai order suna da masu delivery da zasu iya kawo maka har inda kake, ko aje a amso”. “Good. Sai ka samo duka gidan. Ka tambayi kowa abinda yake buƙata” “In sha ALLAHU yanzu kuwa ranka ya daɗe”. Bai sake cewa komai ba ya maida idonsa a television dan an fara gabatar da program ɗin da yay zaman kalla. Hayatu ne ya miƙawa TJ kuɗi masu yawa. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Nidai jallop rice da ƙirjin kaza nake so.” Dariya TJ yayi ƙasa-ƙasa yana ƙumshe baki dan karta fito. Sai kuma yayma Hayatu nuni da ogan nasu da ido. Kai Hayatu ya jinjina masa yana sake gyara nutsuwarsa da maida hankalisa garesa ya ce, “Sir za'a karɓo maka kaima ko?”. Shiru kamar bazai tanka ba, dan yamayi biris tamkar baiji ba. Sai kuma batare da ya kallesu ba ya ɗan kalla agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa mai shegen ƙyau. Ya ɗan yamutsa fuska da jan siririn tsaki. “In dai bazai jima ba a samo min tuwon semo.. miyan kuka”. A tare suka amsa da girmamawa. TJ ya fita da hanzarinsa dan sun san baya cin abincin dare late, wani lokacin ma bai fiya ci ba. Yau ma suna ƙyautata zaton dan baici komai bane tun black tea ɗin safe. Haka yake abinci bai damesa ba, shiyyasa ga shi nan ko kaɗan baida wani tunbi, jikin ma badan yana haye-hayen waɗan nan tarkacen machines ɗin na motsa jikin zamani ba da zai kasance ne falen-felan. TJ na ficewa Hayatu ya katse tunaninsa tare da matsowa inda yake. Da ga tsayen da yake kamar soja ya ɗan rissina yana fito da flash da ga aljihunsa da faɗin, “Sir ga cctv footage ɗin an samo”. Juyowa yay ya ɗan kalli Hayatu ɗin a yanayin jin daɗin hakan. Sai dai kuma ko kaɗan fuskarsa bata nuna komai ba tana nan a ɗaurenta tamau. Kujera ya nunama Hayatu. Zama yay yana ɗaukar laptop dake a Centre table ajiye ya saka flash ɗin jiki. Kafin ya miƙe yaje har gabansa batare da yayi playing video ɗin ba. Ajiye masa yay a stool ɗin daya jawo a hankali gabansa sosai. Sannan ya zauna a saman carpet kusa da ƙafafunsa yana shiga inda folders ɗin videon suke. Duk zubama screen ɗin laptop ɗin ido sukai. Cikin ƙwarewar aiki Hayatu ya zaluƙo video ɗin sashen da abin ya faru, tare da dai-daita lokacin da komai ya faru sai dai baiyi playing ba ya ɗan ɗago ya kallesa. A hankali ya furta, “Kunna”. Kunnawar yayi. Ko'ina ya fara nuna shiru babu kowa babu motsin komai. Kusan minti ɗaya da wasu sakanni sai ga Samraah na bubbuɗe ƙofifi bayan ta fito da ga wani lungu da suka san restrooms na ma'aikatane a wajen. Yanda take taɓa ƙofofin tana ɓata fuska kamar zatai kuka zai baka tabbacin ta ɓata ne. Can cikin takaici ta fincike face mask ɗin fuskarta. Ƙyaƙyƙyawar fuskarta da babu zanen komai na kwalliya ta bayyana. Hayatu dai ya gagara haƙuri sai da ya furta “Masha ALLAH” a hankali. Dan ko makaho ya laluba fuskar Samraah yasan yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce, duk dama eyeglasses ɗinta har lokacin yana a idanunta shi bata cire ba. Isowarta ƙofar da suke ciki ya sanya Hayatu waro idanu sosai, sai dai bai iya cewa komai ba. Ta buɗe ta ɗan leƙa. Sai kuma tai baya a rikice alamar akwai abinda ta gani. Wayarta data zaro tai danne-danne ta kanga tabbacin video take musu yasa Hayatu kasa haƙuri ya furta, “What! Sir itace kenan?”. Bai samu amsa ba, dan ogan nasa ko motsi baiyi ba har sai da ya kai ƙarshe. Fitowarsa, tsintar nurse mask. Har cigaba da video da Samraah tayi sanda suke fita da gawar mutumin. Cikin ƙanƙanin lokaci Hayatu ya gama haɗa uban gumi kamar wanda ke a filin kokawa. Shi kam duk da a birkice take video ɗin yaga matuƙar ƙarfin halin yarinyar nan. Motsin da ogansa yayi yasa hankalinsa dawowa jikinsa. Ya ɗan ɗago ya kallesa. Sai da gabansa ya faɗi ganin yanda cat eyes ɗinsa suka canja launi. Dan gaba ɗaya gwaiduwar tsakkiya ta ɓace ta zama ƴar siririya exactly yanda na mage suke komawa idan suna a cikin haske. Batare da ko kallon Umar ɗin ya sake yi ba ya miƙe ya fara tafiya. Sai da yaje gab da ƙofar bedroom ɗinsa sannan cikin dakiyar muryar dake tabbatar da ransa a ɓace yake ya furta, “A nemota duk inda take. A cigaba da bin duk wani motsinta daga nan zuwa sati biyu”. “An gama Sir. Amma in baka manta ba ka bata damar yin hira da kai ma”. Hayatu ya faɗa cikin tsumar jiki. Cak ya tsaya daga ƙoƙarin shigewa da yake yi kamar mai nazari, sai kuma batare da ya juyo ba ya furta “Zanyi tunani akan hakan”. Buɗe baki Hayatu yay zai sake magana cikin nuna gamsuwa, sai dai harma ya riga yay shigewarsa shi. Hayatu ya rabga tagumi tare da faɗin, “Tab ƙyaƙyƙyawa kin shiga uku wlhy, bama ke ba duk zuri'arki kin sakasu a masifa. Ke miya kaiki shiga gonar da bataki ba. Aikata wannan aikin da ba'a sakaki ba, karanbaninki ya ɗebeki shiga fadar sarkin aljanu. Dan oga ALJANI ne irin ifiritan nan.” yana cikin wannan sambatun nasa TJ ya shigo da ledoji masu ƙyau an musu tambarin gidan abinci. Firgigit Hayatu ya dawo hayyacinsa tare da gyara yanayinsa. TJ da ma bai wani lura da halin da yake a ciki ba ya ajiye masa tasa ledar sannan ya ajiye wata a Centre table yana faɗin, “Wannan tuwon oga ne. Shi na tsaya ma sai da akayisa yanzu-yanzu gashi nan da zafinsa yanda zai masa daɗin ci.” “Ai wannan tuwon mawuyacine ya samu shiga kuma yanzu”. Idanu TJ ya waro a rikice ya furta, “Na shigangaɗi Hayatu badai na makara ba? Wlhy babu tuwonne amma matar tace zatayi da sauri tana da miya. Ni kuma naga tunda yace yana buƙatarsa yana so ne shiyyasa nace tayi da sauri...” “Kai ka kwantar da hankalinka badan ka daɗe bane ba kawai dai wani abunne daban ya ɓata masa rai. Amma bari na gwada faɗa masa ka dawo mugani”. Ajiyar zuciya TJ ya saki, duk da kuwa yanayinsa bai warware ba. Dan in har ogan nasu na cikin ɓacin rai ko damuwa suma sukan shiga matuka saboda yanda suka ɗauki al'amarinsa da matuƙar muhimmanci a rayuwarsu. Tashi Hayatu yay ya nufi hanyar bedroom ɗin nasa, sai da yay jimm a tsaye bakin ƙofar kafin yay knocking a ɗarare. Ko motsi ba'aiba, bai gajiyaba ya sake yi tare da sallama. Nan ma anja kusan minti ɗaya kafin ya amsa masa a daƙile. Sake nutsuwa Hayatu yay kafin cikin dauriya ya ce, “Kayi haƙuri Sir, dama TJ ne ya dawo, a kawo maka abincin nan ne”. “No! I'm okay”. Shiru Hayatu yay cikin nuna damuwa ƙarara a fuskarsa. Sai kuma ya sake raunana murya ya ce, “Please Sir, duk yau fa bakaci komai ba. Ko nace ma rabonka da abinci tun shekaran jiya a Lagos. Abu mafi saka Ummie damuwa a rayuwa shine ka kwana da yunwa. Dan ALLAH ko kaɗanne ka daure kaci, saboda nasan duk da bata tare damu zata ji a jikinta kamar yanda ta saba”. Wani irin cizar lips yay da ga zaunen da yake a bakin gadon hannunsa dafe da kansa. Hayatu ya matuƙar sanin lagonsa a rayuwa. Dan shine kaɗai yake iya bi da shi fiye da kowa bayan mahaifiyarsa. Hakan kuma nada alaƙa da sanin da yay masa tun ƙuruciya. Duk da dai shi ya girmi Hayatun da kusan shekara biyar ma, amma kasancewar sun tashi ne shi da iyayensa a cikin gidan kakansa da ya haifi Ummien sa yasa yay masa farin sani na gaske. Ya jima a gurin kamar bazai motsa ba sai kuma a daƙile ya furta, “Kawo nan”. Cikin sauri Hayatu yabar jikin ƙofar cike da farin ciki bawan ALLAHn kamar cikinsa zai kai. Babu jimawa kuwa sai gashi da tuwon. A can ya shirya masa shi saman table ɗin gaban sofa dake bedroom ɗin, har lokacin kuma yana a zaune bakin gadonsa hannunsa dafe da kansa. Yanayi ne dake nuna yana cikin zafin rai, dan Hayatu ya sanshi a rayuwa fiye da tunanin mai tunani. Ganin Hayatu ɗin baida niyyar fita yaja siririn tsaki yana ɗagowa, harararsa yayi da faɗin, “Ka tsaya gadi na ne sai naci ka gani?”. Ƙasa Umar yayi da kai yana ɗan murmushi. Sai kuma ya rissina tare da faɗin, “Ayi haƙuri Sir”. Daga haka ya fice a ɗakin. Wani tsakin ya sake ja sannan ya miƙe zuwa gaban sofa ɗin ya zauna. Hatta ruwan wanke hannu Hayatu ya tanadar masa. A nutsensa cikin yanayinsa na rashin gaggawa akan komai ya fara cin tuwon dan yana son tuwo sosai saboda fevorite food ɗin Ummien sa ne, ada sanda yana yaro idan tayi tace sai yaci yakan zauna yayta kuka shi bazaici miyan daddawa mai wari ba. Amma bayan wani lokaci da rayuwa ta canja kanta zuwa abinda bai taɓa mafarkin riska ba a cikinta sai ya maida tuwon fovorite nashi shima. Yaci kusan rabin malmala ɗaya ya ajiye duk da kuwa tuwon ya masa matuƙar daɗi, sai dai bai cika son cin abinci late haka ba. Shiru ya ɗan yi zaune a wajen kafin ya tashi zuwa toilet. Brush yayi da sake gyara jikinsa ya fito. Ya samu Hayatu har ya shigo ya tattare komai harda sakama ɗakin freshener ya ƙara dai-daita masa ac. Komai baice ba ya rage kayansa zuwa na barci, sai dai maimakon kwanciyar zama ya sake yi a sofar yana ƙoƙarin kunna laptop ɗinsa, dan yana son ƙarasa harƙallar wani business ɗinsa kafin ya kwanta. Dai dai kuma mi hakan kamar neman gagararsa yake. Dan tunda ya kunna ya gagara danna ko keyboard ɗaya tunaninsa ma neman tafiya yake wani sashe daban. Da ga ƙarshe dai ya ture laptop ɗin gefe ya ɗauki wayarsa. Wata number da aka saka Dude ya nemo tare da danna kira.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce) _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑵𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏_ ......Kusan lokaci ɗaya muka iso garejin da Mansoor. Dan haka babu ɓata lokaci muka nufi cikin motarsa, dan nan ɗin zaifi mana zama sirri fiye da ko'ina saboda abinda zamu tattauna ɗin. Gaba Yaya Musaddiq ya shiga ni kuma baya. Sun gaisa da Mansoor cikin mutunta juna kamar yanda suka saba nima na gaishesa. Amsawa yay idanunsa a kaina ta cikin mirror. “Ya kamata ki huta da kukan nan Samraah. Sai kace kece kika aikata laifin nan. Kinga kuwa yanda idanunki suka koɗe”. Mansoor ne yay maganar cikin nuna damuwa matuƙa. Yaya Musaddiq dake saurarensa ya ce, “Ai ita haka take bata bin al'amarin rayuwa a hankali ka ganta nan. So take sai ta jama kanta wani ciwon muma ta sake sakamu a wata damuwar sannan”. Idanuna na cikowa da hawaye na ce, “Kuyi haƙuri Yaya ba haka bane. Wlhy na kasa mantawane da ganin gawar kawai. Amma in sha ALLAHU bazan ƙara ba”. “ALLAH yasa hakan” Yaya Musaddiq ya faɗa. Yayinda Mansoor yaja numfashi ya fesar tare da amsawa da Amin. Idanuna na share tare da ƙoƙarin yin magana wayar Mansoor ta shiga ruri. Tamkar an saita sai tawama ta fara. Kusan a lokaci ɗaya duk muka kai hannu domin ɗauka. Sai kuma muka kalli juna tare da sake ɗagowa duk muka kalli Yaya dake tambayar mu “Lafiya kuwa?”. “Daga office ne”. Mansoor ya bashi amsa yana ƙoƙarin kai wayar kunnesa. Nima dai tuni nakai tawa tare da yin sallama. MD ne ya amsa daga can, batare daya bi takan gaisuwata ba ya ce, “I'am Sorry Samraah muna son ganinki a office yanzu Please”. “Yallaɓai lafiya kuwa?”. Na faɗa da sauri hankali a ɗan tashe. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, “Kinga kwantar da hankalinki ba wata damuwa bace. Mun samu baƙuncin babban baƙone mai matuƙar muhimmanci da muka daɗe muna fata. Ya kuma ce da ke kaɗai yake son ayi hira da shi”. “Ni kuma oga? Duk mutanen dake a gidan sai yace sai ni. Wanene haka da ƙarfin halin nan? Sai kace wani abin cin rabo. Ya kamata Ku faɗa masa ba sashin da nake aiki ba kenan”. “Humm Samraah Please mana. Dan ALLAH ki shirya kawai ga driver na nan ma na aiko gidanku ya ɗaukeki a motata”. Sake tashi hankalina yayi, sai dai kafin nayi magana oga ya yanke kiran. Sagale nai kawai ina kallon wayar kamar wata gunki. Wane irin baƙone da zai tada hankalin oga har haka. Sannan kuma ma yace ni yake so nai hira da shi. “Kodai mutumin nan ne?”. Na faɗa a zahiri batare da nasan maganar ta suɓuce min ba. Atare Yaya Musaddiq da Mansoor da shima yay zororo alamar kiran da akai masa nada nasaba da nawan suka juyo suna kallona. Yaya Musaddiq ne yay ƙarfin halin cewa “Wane mutumi?”. Firgigit na dawo hayyacina. Dan na fahimci zancen zucini ne ya fito fili. Idanuna ne suka cicciko da ƙwalla. Cikin rawar murya na zayyane musu komai da MD yace min. Mansoor ne yay saurin faɗin “Tabbas akwai alamar tambaya. Dan nima akan abinda suka kirani kenan. Amma ina ganin ki kwantar da hankalinki bari muƙarasa office ɗin domin ganin wanene ɗin ko kuwa Yaya Musaddiq?”. “Tabbas shawararka yayi Mansoor. Tunda akan aikine bai kamata ayi sakaciba kam. Kuje idan kun dawo ma ƙarasa maganar in sha ALLAH. Nima zuwa lokacin na ɗan ƙara yin nazari.” Mansoor ne kawai ya iya amsa masa. Nikam sai binsu da kallo kawai nakeyi. Yaya Musaddiq ya fita yana buɗe baya yace na fito na dawo gaban. Ganin banda niyyar hakan ya buɗe ya kamo hannuna ya fiddoni ya maida gaban. Key kawai Mansoor yayma motar ya haura kan titi. Babu wanda ya iya sake yin magana a cikinmu. Kafin mu isa office ɗin kuma sai danno mana kira MD yake yana kuma sakawa amana. Da wasu kalar shegun zuƙa-zuƙan motoci na alfarma muka fara cin karo a harabar gidan. Sai mutane cikin baƙaƙen kaya tsatstsaye ƙiƙam kamar masu tsaron ƴan fashi. Mudai wucesu mukai muka shiga abinmu. Duk da lahadine mun samu ma'aikatanmu dake duty a wannan ranar dukansu. Harma da wadanda aka kira irinmu da ranar suna hutu suma kamar mu ɗin dai. Office ɗin MD muka wuce kamar yanda aka sanar damu yace muyi. Anan ɗin ma mun tadda mutane biyu irin waɗanda ke a haraba su biyu a jikin ƙofar. Matsa mana sukai muka shiga bayan Mansoor yayi knocking an bamu izinin shiga. Mun fara cin karo da ƙamshin turare mai armashi sosai. Sai sanyin ac a office ɗin kamar ba safiya ba. Wannan kuma ba halin MD bane zama cikin ac da ƙarfi haka. Akan MD idanunmu suka fara sauka. Kafin dattijon dake zaune a kujerar kusa da shi cikin shigar ɗanyar shadda mai tsananin ƙyau da ɗaukar hankali sai maiƙo take da walwali. Ƙyaƙyƙyawane sosai baƙi ga dogon hanci da shiryayyen farin gashinsa daya ƙawata taswurar fuskar tasa. Gaishesa muka farayi kawunanmu a ƙasa. Dan tun shigowarmu ya zuba mana idanunsa manya farare yana murmushin bajinta. Yanzun ma da fara'ar ya amsa mana. Sai kuma ya kalla MD ɗin yana faɗin, “Inaga idan kun shirya mu fara abinda ya kawomu kawai. Dan na faɗa maka zanbi jirgin ƙarfe biyu ne domin komawa Lagos, ina kuma da wasu uzirin bayan wannan. Gashi yanzu 10:30.” “Hakane ranka ya daɗe” MD ya faɗa cike da tsantsar girmamawa ga dattijon. A karo na farko muka kalla juna ni da Mansoor. Sai kuma muka maida kan MD da yay kiran sunanmu a tare. Idonsa akan Mansoor ya ce, “Mansoor ka duba tare da tabbatar komai yayi dai-dai a can ɗin. Muma gamu nan fitowa.” Amsa masa Mansoor yay cikin nuna ƙaulani, sai dai baice komai ba ya juya ya fita. MD ya maido da idanunsa kaina yana miƙamin takardun hannunsa. “Ke kuma Samraah ga wannan. Sune tambayoyin da zakiyi, ki ɗan dubasu ko. Sai kuma ya kamata kije ki gyara makeup naki kema gamu nan fitowa.” Ɗan jimm nayi kamar bazan amshi takardar ba, MD ya wani marairaice fuska tamkar zai fasa ihu cikin nuna alamar roƙona da idanu. Jinai kamar na balla masa harara. Amma dai na daure na amsa takardun kawai ina faɗin, “Okay Sir” a hankali. Ina daga tsayen na dudduba komai, batare da nace komai ba na ajiye masa a saman tebir ɗin. Sannan na juya na fita. Da ga shi har baƙon nasa ina jin idanunsu a kaina. Da ƙyar na iya ficewa zuciyata na ƙara nauyi ga mamaki da cushewar kai na rashin iya gane komai a wannan al'amari. Dan magana ta gaskiya duka tambayoyin da MD yace sune zan masam sun matuƙar bani mamaki. Na kuma sake tabbatar da lallai akwai wata a ƙasa. Watan da shi kansa MD idan yay wasa sai ya zurma ciki ƙwarai da gaske.... “Tofa, mi kuke tunani masu karatu🤥? Nima fa kamar na shiga ƙaulanin ne🤔”. ✨・o・✨・o・✨・o・✨ Sosai yasha barci mai lafiya a safiyar ta yau kasancewar a daren jiya ya jima bai kwanta ba. Dan tunda ya dawo massalaci sallar asuba da Ummiensa kawai yayi waya ya sake komawa ya kwanta. Bai tashi ba sai yanzu babu jimawa. Wanka kawai yayi tare da gyara jikinsa cikin wando 3quater mai laushi kalar baƙi da rigarsa fara da adon baƙi kaɗan itama mai laushi. Dogon hannune da ita tare da hula. Sai dai ya saki hular a bayansa, sannan bai saka zip ɗin rigar ba. Hakan ya bama farar singlate ɗinsa damar fitowa sosai tare da ɗamammen cikinsa da har kana iya ganin kwanciyar gurayen kansa dake nuna shi matsayin mutum mai tsananin motsa jiki. Yau dai bai ɗaure gashin ba, sai dai yasha gyara sosai dan daga shi har siririn kwantaccen sagensa sai uban ƙyalli da ƙamshi sukeyi. Ga gashin ya ɗan sakko masa har kafaɗa kaɗan. Magana ta gaskiya babu wanda zai kalla bawan ALLAHn nan ya yarda wai ya haɗa jini da baƙaƙen fata. Dan sam baya kammani da su sai dai fatarsa da tai ɗan diff ba kamar na fararen dake kasancewa jazur ko fari fat ba. Amma shi yanayin da fatar tasa take ma sai ya ƙara masa wani ƙyawu na musamman. Kai tsaye ga coffee machine ɗin sa da ke a falon ya nufa. Cikin mintina kaɗan ya haɗa coffee. Ƙyaƙyƙyawan mug ɗinsa na zallar farin glass ya ɗauka ya tsiyaya fin rabi a ciki. Sannan ya tako a hankali yana kaiwa bakinsa zuwa cikin falon sosai. Furucin daya fito daga cikin television dake aiki a falon ya sashi karkata hankalinsa ga tvn. Dai-dai nan Hayatu ya shigo kamar wanda aka koro. Kaɗan ya juyo ya kallesa cikin yanayin nan nasa na rashin sakewa, sai kuma ya sake maida kansa ga tvn yana sake kai mug ɗin kan ɗan ƙaramin bakinsa ya zuƙi coffee ɗin duk da zafin da yake da shi. Hayatu da gaba ɗaya hankalinsa ke a tashe ya ce, “Sir kaga abinda ke faruwa kuw......” sauran maganar ta maƙale sakamakon saukar idonsa akan tvn shima. Da sauri ya ɗan yi baya kamar wanda ke shirin faɗuwa. Ya dai samu nasarar dafe hannun kujerar dake kusa da shi yana bin ogan nasa da ya ƙarasa ya zauna cikin kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya da kallo. Yasan halinsa sarai akan dakiyar masifa dayin biris da abu kamar bai damar ba. Amma magana ta gaskiya wannan bai kamata ai biris ba. Zama yay ya samarwa kansa nutsuwa. Kafin ya furta, “Amma Sir mizai sa Baba prof.. zuwa Kano a yau har yayi hira da yarinyar nan ne? Kodai ya amince da batun buɗe companyn yanzu? Wlhy ni du kaina ya kulle ma”.........✍️ _Ni ma dai mai ɗaukar rahoton neman ruɗar fani ɗin kuke Hayatu PA.🤥🤔_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚_ .......Kamar yanda Hayatu yasan bazaice komai ba baice ɗin ba kuwa. Sai ma aikin shan coffee ɗinsa da yake hankali kwance idanun nasa dai a tvn dan har an fara program ɗin. Gaba ɗaya hirar anyita ne akan abinda ya shafi harkar ilimi a Nigeria. Da rawar da su malamai ɗin suke takawa domin ganin matarbar ilimin ta dawo hayyacinta da ga mutuwar tsayen da tayi musamman daya kasance tun daga tushene. Dan yanzu secondary schools tafi kowace gaɓa lalacewa a harkar karatu, in ba makarantar kuɗi zaka kai yaranka ba sai a hankali. Gashi kuma Sakandire ɗin nan ne ake ganin tamkar mahaɗar dake riƙe da kowanne reshen ilimin dan anan ne ake karatu tuƙuru cikin halin ƙuruciya da babu wasu damuwoyin fara fuskantar ƙalubalen rayuwa irin na girma. Wannan hira ta matuƙar ɗaukar hankalin mutane, inda ta haifar da cecekuce sosai tare da yaba ma prof... ɗin. Dan tun kafin a kammalata saƙwanni sun cika kowane dandalin sada zumunta na wannan gidan tv da rediyo. Yayinda wasu ke tattaunawa a dandilansu na sada zumunta. A cikin awa ɗaya da akai da Prof.. K/Mashi an amsa harda wayoyin mutane, ya kuma bada cikakkun amsoshi masu jan hankali da suka sake birge mutane da ganin kimarsa da girmansa. Duk da a baya ana zaginsa akan yanda yake aiki tuƙuru ma kudancin Najeriya ɗin kasancewarsa mazaunin can shi da gaba ɗaya zuri'arsa. Dan wasu na ganin a komai nasa bama ya alaƙanta kansa da arewa sam, tamkar ma baida wani alaƙar dasu, musamman idan yana sukar ƴan siyasar arewan da ƙalubalantar shuwagabannin yankin. Koda aka kammala ma babu alamar Maash zaice wani abu. Zuwa yanzu dai kansa na jingine da kujerar idanunsa a lumshe. Ta ƙasan ido Hayatu ke kallonsa da nazartarsa. Sai kuma a hankali ya furta, “Sir miza'a kawo maka breakfast?”. Shiru babu alamar zaima motsa balle ya tanka masa. Sai kuma dai cikin motsa lips da ƙyar ya furta, “Waka ɗora akan aikin bincike akan yarinyar nan?”. Ƙasa Hayatu yay da kansa, cikin girmamawa sosai ya amsa da, “Da kaina nayi Sir. Dama abinda nazo kawo maka kenan. Sai kuma wanda zai ringa bibiyar tata ne kuma ina kan nazari. In sha ALLAHU daga nan zuwa yamma zan kawoshi shima.” Yana daga kwancen ya ɗan buɗe idanunsa yana kallonsa. Hayatu ya ƙara rissinar da kansa yana ɗan murmushi, dan yasan abinda yay ɗin ya faranta ran ogan nasa koda bai fito ta faɗa ba. Ci gaba yay da faɗin, “Sunanta Samraah Abdul-wahab Gwarzo. Wasu kan kirata Sam-G. Tana da yaya Musaddiq da ƙani Hafizzullah. Musaddiq ɗin makanike ne, shike riƙe da rayuwarsu, ƙanin nata kuma na jami'ar Umaru Musa Yar'adua dake Katsina yana karatu. Iyayensu sun jima da rasuwa, a hannun Uncle ɗinsu suke tun suna ƙanana. Akwai wani yaro Mansoor da ko yaushe suna tare shine zata aura dan har maganar iyaye ta shiga. A zahiri Samraah bata da hayaniya ba kuma sabgar kowa take shigaba sai in itace taso hakan. Sai dai kuma tana da tsiwa a wasu lokutan musamman ga wanda ya shigar mata hanci. A shekarun baya kaɗan ta fara rubuce-rubuce kan abubuwa masu muhimmanci musamman da suka shafi ƙananun yara mata dake tallace-tallace a tituna. Sai dai tunda ta fara wannan aikin ta ɗan rage hakan. Bincikena kuma ya tabbatar min tanada fans sosai, dan a duka shafukanta akwai fallowers dake fallowing ɗinta sosai. Na tabbatar da yanda suke jin daɗin karatun rubuce-rubucen nata ne ta hanyar comments da suke mata. A office kuwa tana fannin ƙananun ma'aikata ne. A ɓangaren rediyo ta fara aiki kuma. Sai dai ƙwazonta da yanda program ɗin data bada shawarar samarwa akan matasa ya amsu, ya saka suka maidata itace mai gabatar da program ɗin. Da kuma a iya rediyo kawai akeyinsa, amma yanayin karɓuwarsa yasa suka koma gabatar da shi har da television, sannan shi MD ɗin su ne ya bata power sosai a al'amarin. Shiyyasa ma ake zargin yana sonta ne duk da yasan akwai alaƙa mai ƙarfi tsakaninta da shi wancan yaron Mansoor, amma har yanzu bai san iyayensa sunje gidansu ba ma har anyi maganar aure.” ɗan matsawa yay gabansa yana yunƙurin ajiye tab.. ɗin dake a hannunsa yana cigaba da faɗin, “Nayi fallowing duka shafukanta, gashi ko zaka duba”. Hayatun ya ɗan kalla sai kuma ya ɗauke idanun nasa. A daƙile ya ce, “Ba buƙata. Ka kammala komai dan zuwa jibi maybe zamu wuce. Ka tura ma MD nasu takardar amsa gayyatar da tai min, sai dai kar ya wuce gobe” daga haka ya miƙe. Har ya shige bedroom ɗin sa Hayatu da kansa ke ƙasa na binsa da kallo. Sai kuma yaja numfashi tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yana kaiwa zaune cikin lallausar kujerar dake a falon. Tagumi ya zuba da hannaye biyu, gefe ɗaya mamakin komai yake yi, wani gefe kuma na ayyana masa akwai abinda ogan nasa ke shiryawa. Kuma tabbas da wahala ace zai kasance mai daɗi, yana tausayin yarinyar nan, dan ta taroma kanta match. Bashi da zaɓin daya wuce cika umarni, dan haka ya ɗauka tab.. ɗinsa. A take yay kiran wani tare da buƙatar number ɗin MD na gidan tvn na AlHERI. Ko mintuna biyar ba'a cikaba kuwa sai ga saƙon Number ɗin ya shigo masa. A take ta shirya text message ya tura musu kamar yanda Maash ya umarcesan..... Yayanmu nima fa ka fara ban olo gaskiya😌🥺🥺. 🌟(☉。☉)!(☉。☉)!(☉。☉)🌟 Sam nutsuwa bata ɗan dawo jikina ba sai da aka kammala duka program ɗin. Bayan an ɗauke camara daga kanmu na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ina mai lumshe ido. Ɗan kallona prof.. yay a kaikaice sai kuma yay ɗan murmushin manya yana miƙewa. Yana fita a ɗakin shi da MD sauran ƴan uwana ma'aikata sukayo kaina. Ruwa aka fara bani nasha, na sake samun nutsuwa sannan nima na miƙe. Muna daga harabar gidan ni da Mansoor dake lallaɓani muje muci abinci aka aiko kiranmu. Dole cikin muka koma. Inda muka samu dukkan ma'aikatan da suka bada gudunmawa a program ɗin har ƴan bayan fage a office ɗin MD. Zama mukayi kamar kowa muma. Daga haka Prof.. ya fara mana bayanin godiya, tare da sanar mana dalilinsa na gabatar da wannan program ɗin cikin gaggawa haka. Sosai muka nuna gamsuwarmu. Musamman ma ni da kaina duk ke a ɗaure da farko. Ƙyauta dukanmu ya danƙa ma kowa a envelope ɗinsa. Daga haka yay mana godiya muma muna masa. Sai dai me ni sam hankalina ya gagara tsayawa waje guda akan hakan. Kallo na fara bin sauran ƴan uwana da shi, kafin na miƙe zaram kamar wadda akaima allura nabi bayansa da sauri. Mansoor na ƙoƙarin tsaidani da son jin ina zanje bamma sauraresa ba na fice da sassarfa. Isowata yayi dai-dai da buɗema prof.. mota zai shiga. Ga mutanensa zagaye da shi kamar zasu iya hana mutuwa ɗaukarsa. Amma ko'a jikina nai sallama kaina tsaye. Su duka juyowa sukai suna kallonna musamman MD da yay rakkiya tare da Prof.... Fuska ɗauke da murmushi Prof.. ya ce, “A'a ɗiyata ko kinyi mantuwa ne?”. Ƙasa nai da kaina ina ɗan murmushin ƙarfin hali. Kafin cikin ladabi da dakiyata na ce, “A'a ranka ya daɗe. Dama uhm....” sai kuma nai shiru na kasa cigaba da faɗa ganin yanda suka tsatstsareni da idanu su duka. Murmushi mai sauti Prof... yayi yana sakin murfin motar ya juyi gareni da ƙyau. “Daughter yi maganarki ƙofa a buɗe take ai. Ko mu koma gefe ne?”. Da sauri na ce, “A'a Sir ba sai munje ko'ina ba. Mun gode sosai da karamcinka garemu, amma dan ALLAH kayi haƙuri zan dawo da wannan dan ana biyana albashi akan aikina, kuma yana wadatar dani”. Bashi ba hatta MD ina ganin yanda yay wani irin sororo yana kallona. Ni dai na ɗauke kaina ina miƙama yaronsa daya raba mana envelope ɗin. Ganin ya tsaya yana kallona bashi da niyyar amsa na ɗaura masa kan kayan hannunsa na juya a nutse na bar wajen. Ina jin yanda idanunsu sukai min riiiii aka. Amma ban waiwayo ba. Cin karo muka kusan yi da Mansoor da alamu suka nuna biyoni yayi. Na ɗan ja da baya ina faɗin, “Ya salam I'm sorry ban san ka taho bane”. “Babu damuwa” ya faɗa yana kallon hannuna. Fahimtar hakan yasa kai tsaye nace masa “Na mayar musu ne?”. “Mi ɗin?”. Ya faɗa cikin waro idanunsa sosai waje. Bakina da ke cikin face mask na tura gaba da faɗin, “Yo abinda suka bamu. Ni gaskiya bana ra'ayi dan zuciyata sam bata ma kwanta waje ɗaya ba. Ta yaya mutum zai taso rana tsaka ya ce muyi hira da shi babu wani goron gayyata babu notes sannan ya kuma kawo wani abu ya bamu wai matsayin ƙyauta. Dan ALLAH kai baka ji abin banbarakwai ba? Shine fa wanda kwanaki akaita kace-nace ɗin nan akansa game da abinda ya faɗa akan shugabannin arewa. Gashi kuma da bakinsa ya faɗa shi haifaffen jihar Kano ne. Amma bai ragi balle ragowa wajen sukar mana mutane kamar wani maƙiyinmu”. Idanu kawai Mansoor ya zuba min kamar mai nazari. Ya buɗe baki zaiyi magana sai ga MD ya iso kamar a fusace. Dan cikin yanayi kamar faɗa-faɗa ya ce, “Samraah sameni a office”. Sai da na taɓe bakina dake a cikin face mask sannan na amsa masa da to ciki-ciki. Yana juya baya kuma na bisa da harara. Ƙin tafiya nai har sai da Mansoor ya mun magana. Batare da shima na tanka masa ba na wuce fuu nabi bayansa........✍️ *_“Amma Samraah miyyasa kika ƙi amsa bayan kuma kema kin gamsu da bayanin da yay muku na dalilin hirar? Sannan kin siffantashi da mutane kirki a halittar jiki da yanayinsa, kuma bayanansa sunja hankalin mutane da yawa a yau ɗin har hakan ya sake ɗaga darajar gidan tvn ku?”._* _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝑶𝒏𝒆_ .......Humm Bily a zahirance banda wani dalilin yin hakan kamar yanda kowa zai iya gani ko fahimta. Sai dai ni a ƙasan zuciyata ina jin dole-dolene bai kamata na amsa koma miye ɗin ba. Dan babu dalilin hakan bisa hujjoji da dama. Amma ban sani ba ko kema zaki iya fahimtar hujjar tawa a yanzu. Ko kuma sai anan gaba cikin abinda zai zo a labarin nan nawa. Dan a yanzu kam tabbas babu wani dalilin da nima zan tilasta miki gamsuwa dani. Amma dai muje zuwa ofishin MD dake kirana. (Babu musu na jinjina mata kai, amma magana ta gaskiya al'amarin wannan Sam-G ɗin taku yana ɗan rikitani. A ido zaka iya mata kallon like innocent people. Sai dai a ɗan zaman da nai da ita na fahimci taƙadarar kanta ce. Sannan akwai taurin kai yana jinjirin jaki. Kar dai na cikaku da zance ku muje zuwa dan jin yaya ta kaya a offishin MD) Tsaye na samesa yana faman kai kawo a tsakkiyar office ɗin nashi. Sai faman furzar da huci yake kamar wani bajimin rago. Ko ɗar banji ba a raina na rafka sallamata. Juyowa yay yana kallona da idanunsa da suka kaɗa sosai. Kamar wanda ke shirin dukana ya wani zaburo kaina har sai da na ɗan ja da baya ina waro manyan idanuna waje. “Samraah kin san mi kikayi kuwa? Kin san wanene wannan mutumin kuwa? Kin san ƙyautar mi ya baki kuwa? Amma kika watsa masa ƙasa a ido ta hanyar maida masa bayan ya fifitaki sama da kowa. Kuɗi duk ya bama sauran 50-50k, amma ke makullin mota ya baki batare da ko dubawa kinyi ba kika ɗauka kika maida masa...” “Mata fa dai?”. Na tambaya da iya gaskiya ta. Shima cike da ƙwarin gwiwa ya amsa min da “Yes Mota Samraah. Shiyyasa a kullum nake faɗa miki ke ɗin mai sa'a ce dear”. Kaina na ɗan girgiza da murmushin basarwa, na ce, “Humm to amma Sir mi zanyi da shi idan na riƙe? Sannan wace amsa zan bama iyayena idan sun tambayen a ina na samu mota? A shi karan kansa mi ma zaisa ya mana irin wannan ƙyautar haka dan kawai munyi hira da shi?”. “Tab ɗin, wlhy yarinyar nan baki da hankali...” ya faɗa cikin ƙunar rai, a take na sake tamke fuskata dan kalmar tasa ta mun matuƙar zafi a zuciya. Duk yanda naso na shanye na gagara hakan, kai tsaye nace masa, “Sir minene abin rashin hankali anan? Bayan kuma na faɗa maka hujjata. Wannan fa rayuwata ce” Wani irin tsayawa yay duka hannayensa riƙe da ƙugunsa kawai yana kallona tamkar ya samu television. Ni kam na sake fuskewa kamar ban san yanayi ba. Na fahimci takaicina ne ya maƙureshi ya hana shi cigaba da magana. Dan a fusace ya sa ƙafa ya tunkuɓar da flower base ɗin da akai ado da ita a office ɗin, sannan ya ce, “Samraah out. Get out of my office now..” Ko kallonsa banyi ba na juya nai ficewata. In ma ca yay na bar Company ɗin gaba ɗaya daga yau banda matsala da hakan. Ko takan Mansoor banbi ba nai ficewata gaba ɗaya daga gidan. Napep na tare zuwa garejin su Yaya Musaddiq. Na samu suna shirin shiga sallar azhar, sai dai shi Yaya bai kai ga tafiya ba yana ƙoƙarin ɗaura alwala ne. Tun kafin na ƙarasa inda yake na fahimci ya zuba min ido. “Lafiya kike?”. Ya faɗa dai-dai ina isowa gabansa shi kuma yana wanke ƙafarsa. Mai makon amsa sai na tura masa baki. Kansa ya girgiza kawai yana sake faɗin, “Je can ki zauna muyi salla to, idan na dawo sai kiyi taɓarar”. Daga haka ya wuce ya barni a wajen dan ya kammala alwalar... 💫´⊙ω⊙💫⊙ω⊙💫⊙ω⊙`💫 Zaune yake a falo tare da Hayatu da Juliet, tab.. ce a hannunsa, ƙafafunsa miƙe saman Centre table da aka turo gabansa sosai. Hankalinsa gaba ɗaya nakan screen ɗin tab ɗin, hannunsa ɗaya rike da haɗaɗɗiyar chocolate yana ci a hankali tamkar baya so. Yayinda Juliet ke bayani akan abinda ya zaunar da su ɗin, dan itama dai laptop ce a hannunta, sai Hayatu dake riƙe da takardu ta gefenta. Abinda juliet ɗin ta faɗa na ƙarshe ne ya sakashi ɗagowa cikin rashin sakewar nan tasa ya zuba mata ido. Da sauri ta risinar da nata dan Maash nada wani kwarjini dakan hana mai kallonsa iya masa kallon ido cikin ido na tsawon lokaci, koda kayi jarumtar yin hakan da zaran shi ya zuba nasa cikin naka zaka ji ka takura. A ɗan daƙile ya ce, “Ina son magana da Mustapha. Sannan ai cancel ɗin Thailand a cikin schedule namu a maida Finland”. Atare su duka biyun suka amsa masa dan zancensa ya shafi kowannensu. Babu ɓata lokaci kowanne ya shiga yin abinda aka saka shi. Juliet ce ta fara ɗagowa cikin harshen turanci tana tambayarsa, “Sir komai zai zama ne de same date?”. Kamar baima jita ba aikinsa yake, sai da ya mula dan kansa sannan ya bata amsa da “Uhm”. Cikin girmamawa ta jinjina kanta da amsa masa ta cigaba da aikinta. Dai-dai nan shima Hayatu ya taso daga inda yake da waya a hannunsa. Ta gefensa ya ɗan tsaya cikin risinawa ya miƙa masa. Batare daya ɗago ba a hankali ya furta, “Sa a hans free”. Da sauri Hayatu ya maidata hans free, sai ga muryar wancan da ya kira da Mustapha rangaɗam. Duk da a cikin waya yake cikin girmamawa ya gaishesa, zaka tabbatar da hakanne ta yanda yake magana cikin ƙanƙan da kai. Shikam kamar yanda ya saba ya amsa a taƙaice. Sannan suka tsunduma maganarsu, duk dai akan harkar business ne, mafi yawan maganar kuma Mustaphan keyinta.. ba wata doguwar magana sukai ba ya barsa suka cigaba da magana da Hayatu. Dai-dai Hayatun na ajiye wayar shima alamar sunyi sallama ɗaya daga cikin securitys ɗin gate yay sallama tare da yin knocking. Hayatu ne yaje garesa yana amsa masa sallamar. Jin abinda security ɗin yace ya sashi ɗan wara ido waje. Sai kuma ya juya cikin falon da sauri. Cikin ɗan yanayin rawar harshen wanda ya shiga ruɗani ya ce, “Sir Baba prof.. ne a gate”. Cak Maash ya dakata da abinda yake, sai kuma ya lumshe idanunsa tare da buɗesu luuu gaba ɗaya akan Hayatun. Bashi da alamar cewa wani abu, Hayatu kam duk ya ƙagu yace ɗin. Idanun nasa ya maida ga tab ɗin abinsa batare da yace komai ba. Sake birkicewa Hayatu yayi, sai dai baida tacewa. “A buɗe masa”. Zabura Hayatu yay yana sauke nannauyar ajiyar zuciyar da sai da ta saka Juliet danne dariya. Dan haka ya harareta ya nufi hanyar fita da sauri. Shiko Maash aikin gabansa ya cigaba dayi hankali kwance. Mintina huɗu ba'a cikaba sai gasu kuwa. Baba prof.. ne a gaba. Tun a taku biyu ya tsaya yana bin falon da kallo, kafin ya sauke ƙyawawan idanunsa na tsufa akan santalelen jikan nashi mai ji da lokacisa. Murmushi ya saki a hankali, sai kuma ya cigaba da shigowa cikin falon guards ɗinsa guda biyu biye da shi. Sai Hayatu a gefe. Juliet ma tuni ta miƙe tsaye. Cikin girmamawa ta shiga gaishesa, ya amsa mata da kulawa, har lokacin kuma Maash bai motsa ba balle ya kalla kakan nasa. Hayatu ne yayma guards ɗin Baba prof... da Juliet magana dan haka suka fice suka barsu su biyu. A karo na babu adadi Baba prof.. ya sake sakin murmushi. Idanunsa akan Maash ya ce, “Fushinne har yanzu? Common sweetheart ya kamata ka huce mana. Kaifa yanzu babban mutum ne ba little Awwab ɗin nan ba mai hawa saman wuyan grandpa ɗinsa yay doki saboda fitinarsa. Be a man mana my baby boy”. Fuska Maash ya sake tsukewa. Batare da yayi magana ba ya dangwarar da tab.. ɗin hannunsa yana miƙewa kamar a fusace zai wuce. Caraf Baba prof.. ya damƙo hannunsa, jawosa yay kawai ya faɗa jikinsa ya rungumesa tsam-tsam yana dariya. Sun jima a haka Maash nata faman sauke ajiyar zuciya, yayinda Baba prof.. keta murmushinsa shi dai. Sai da ya tabbatar ya gama haɗiyar zuciyar kafin ya ɗagosa. Hannu yasa saman kansa ya birkita gyararriyar sumarsa da yau bai ɗaure ba. Babu shiri Maash ya saki murmushi daya sake ƙawata ƙyawunsa. Baba prof.. kuma ya ƙyalƙyale da dariya tare da jamasa dogon hancinsa sannan ya sake maida hannunsa kan sumar tasa ya shiga kwantar da ita yanda take. “Dibeka so cute idan kana murmushi. Amma ka dinga ɗaurema mutane fuska har ni ɗin ma Kakanka ban tsira ba. Kai nidai naga takaina da kai balaraben Nigeria”. Murmushin Maash ya sake yi, batare da yace komai ba ya girgiza kansa kawai yana nufar kujera ya zauna kamar yanda Baba prof.. yayi. Cikin girmamawa ya gaida kakan nasa, shiko ya amsa masa cike da kulawa, sai kuma yabi falon da kallo yana cigaba da faɗin, “Mutumina alƙawarin ALLAH dai ya cika ka dawo mafari. Hakan nada ƙyau kuma naji daɗi kwarai da gaske. Ina fata kuma za'amin afuwa da rashin cika alkawarin dawowa da nai jiya. Gangar jikin nawane kawai acan, amma zuciyar na nan. Shiyyasa ma ina sauka a Lagos ko gida banje ba na sake biyo jirgi zuwa nan ɗin.” “Ba komai ya wuce ai, ina fatan ka dawo cikin ƙoshin lafiya”. Maash ya faɗa cikin tausasa harshe duk da dai maganar da ƙyar take fita. Baba prof.. bai damu ba, dan yafi kowa sanin wanene jikan nasa. Wannan yanayin nashi kuwa halittarsa ce, tun yana ƙaraminsa baida sakewa da mutane. Sannan haka yake dai babu yawan magana. Wasu abubuwa da suka faffaru kuma suka sake maidashi dunɗun dukum ya zama miskilin gasken gaske. Gashi nan dai babu yabo babu fallasa a ɓangaren kirki. Dan babu wanda ke ɗaga masa yatsa bai karya ba. Ya iya rikici da rigima ƴar gaske. Dan tabbas Maash akwai rikici, tsagerane na bugawa a jarida, sai dai yanayinsa na shiru-shiru yasa sai ya zuba maka tsiya yay kamar bashine yayi ba, in kuma za'a tambayi mutum dubu su shedesa suma akan bashi ɗin ne yay ba. Sai dai su da sukai masa sanin ciki da bai na rayuwa, musamman ma shi kakansa da mahaifinsa da mahaifiyarsa sun san shine ya yin......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 - 𝒕𝒘𝒐_ .......“Da kika gudo kika barni yanzu ban kawo kaina ba?”. Mansoor ya faɗa dai-dai suna ƙarasowa inda nake shi da Yaya Musaddiq. Baki na ɗan murguɗa ta cikin mask ɗina, a zahiri kam nai ƙasa da kaina sai dai bance komai ba. Sai Yaya Musaddiq ne ke dariya. Ni dai bance komai ba, sai da Mansoor ya sake faɗin, “Bazaki ban haƙuri ba?”. Bakin na sake turawa. Sannan na ce, “To kayi haƙuri”. Murmushi Mansoor yay yana kaiwa zaune. “Ai dole ma na haƙura dan bana iya dogon fushi da ke. Ga yaya Musaddiq nan ma shaida ne”. Murmushi Yaya Musaddiq ya sake saki, ni kuma na ɗan harari Mansoor ɗin. Shima murmushin yay a lokacin, tare da ɗan taɓe bakinsa ya ɗauke kansa gefe. Sai kuma ya sake juyowa gareni. “Mi MD yace dake?”. Mask ɗin na cire ina kumbura fuska kamar MD ɗinne har yanzu a gabana. Labarin komai na basu, shi kuma ya faɗama Yaya Musaddiq komai tun daga farko. Sosai naga farin cikin abinda nai ɗin a fuskar Yaya Musaddiq, har takai ya kasa haƙuri ya dafa kaina da faɗin, “ALLAH yay miki albarka Kandalata. Abinda kikayi shine dai-dai, dan nima anan banga wani dalilin da za'a baki ƙyauta harta mota ba ki amsa. Ki cigaba da haka, dan gaskiya itace RUHIN dukan MUSULMI na ƙwarai. Sannan ita mace tana bine ta kowacce hanya domin kare mutuncinta da kimarta a al'adance da kuma addinance.” “Nagode Yaya”. Na faɗa cikin zumuɗi da jin daɗi. Dan kalamansa sun ƙaramin ƙwarin gwiwa ƙwarai da gaske. Ganin Mansoor bai tanka ba na ɗan juyo na kallesa. Murmushi ya sakar min, nima sai na mayar masa da murtani. Kaina tsaye na ce, “Amma kaima zaka maida musu?”. “In sha ALLAHU”. Ya bani amsa cikin tabbatarwa. Nan ma nayi farin ciki, daga haka na mance da dukkan damuwata muka koma hira mai daɗi. Harga ALLAH ina matuƙar son waɗan nan mazajen biyu, dan sunada matuƙar muhimmanci a rayuwata. Sun kuma taka rawa mai ƙarfin gaske da in har zan nuna kaina sai na haɗa da koda inuwarsu ce. Ko kaɗan bamuyi maganar videon nan a wajen ba saboda tsaro, sai da muka koma motar Mansoor sannan muka ƙarasa. Yaya ya bada shawarar mu binciki ɗan sanda mai gaskiya da zamu iya damƙama video ɗin kawai batare da sunanmu ba, kokuma mu haƙura a gogeshi mubar zancen, ko bajima ko ba daɗe idan har halin mutumin nan ne hakkin rai bazai barsa ba. Amma maganar yin fito-na-fito da shi bama ta taso ba a garemu. Harga ALLAH maganar Yaya Musaddiq bata mun daɗi ba, taya kawai dan mutum nada kuɗi a dinga nuna tsoronsa haka bayan akwai hujja mai ƙarfi a tare da mu. Amma sai na danne yanayina nace mu sakesa a media kawai, dan a wannan zamanin banga wani ɗan sandan da suke hasashen samu ba. Su duka basu goya da bayana ba. Shima Mansoor yana bayan shawarar Yaya Musaddiq ɗin ne. Dole nima nabi ra'ayinsu, duk da tun farko dama ni na fara kawo shawarar kaiwa ƴan sandan, banbancin shawarar tasu da tawa ƙalilance. Bayan mun kammala tattaunawar munbar Yaya anan ni kuma Mansoor ya wuce kaini gida. Muna tafiya muna hirarmu mai daɗi, duk da yaso mu tsaya muci abinci naƙi yarda da hakan. Koda mukaje gidan ma sai da muka ɗan ƙara taɓa hira, duk da dai hirar tamu ma dai akan bikinmu ne, dan iyayensa zasu sake zuwa a satin sama domin saka rana. Ya kuma tabbatar min da bawani lokaci mai tsayi za'a saka ba. Dan shi ya gama kammala komai amarya kawai yake jira. Naji kunyar furucin nashi sosai, dan haka na ɓalle murfin motar na fita abina. Ina jiyo sautin dariyarsa ban kulashi ba, sai da zan shige gida gaba ɗaya ne na juyo. Ido ɗaya ya kashe min, aiko nai wuff na afka ciki.. A falo na samu duka mutanen gidan tsaye carko-carko har Abbas yau yana gida. Ga kayana a barbaje an musu filla-filla. “Yauwa ga ɓarau-ɓarau ɗin nan ta dawo”. Furucin Bibaa ya dawo da hankalina kansu. Kafin nai wata magana kawai naji saukar mari. Duk da azabarsa ta matuƙar ratsani banyi ko gezau ba. Sai wanda ya marenin na zubama ido kawai, ba kuma kowa bane face Abbas. Nunani yay da ɗan yatsa tamkar zai tsokale min ido ya ce, “K dan uwarki kawo sarƙar Mom da kika sata, shegiya ɓarauniya mai kama da aljanun daren salla”. Cikin dakiya irin tawa na ce, “Karka sake zagar min uwa. Sata kuma kanku ya kamata ku bincika, tunda kune ke shiga ɗakin Mom ɗin ai. Ni ba ɓarauniya bace, kuma in sha ALLAHU babu wani tsananin rayuwa da zaisa na aikata ta”. Daga haka na duƙa domin tattare kayana. Amma sai ji nai an shaƙoni ta baya. Har hijjab ɗina na matsemin maƙoshi. Da sauri nasa hannu naja hijjab ɗin sama. Sannan na miƙe. Baby ce mai riƙon nawa yanzu, itama hannu ta ɗaga zata maran, sai dai kafin ta sauke min ni na sauke mata nawa yatsun biyar akan farar fuskarta. Saurin janye nata hannun tai tare da sakina ta haɗa duka hannuwanta biyu ta riƙe kuncinta. “Karki soma fara wannan wasar dani a gidan nan, shima daya maran ɗin ba ƙyalesa nai ba balle ke shashasha”. “Toni bari na marekin sai ki haɗa ki rama” Mom ta faɗa tana wani zaburowa kaina. Banyi ko motsi ba harta ƙaraso ta maran ɗin a haggu da dama. Sannan ta shaƙoni. Kakari na fara, amma ko gezau bata da alamar sakina. Sai ma faɗi take, “Dan ubanki ina sarƙata? Ina kikaje kika saida ta? Dan nasan fitar da kukai ke da annamimin mai saki yin komai a gidan nan abinda kuka je saidawa kenan. Kuma wlhy bazan yarda ba, sarƙata ko kuɗinta”. Zuwa yanzu kwata-kwata bana iya numfashi da ƙyau, hakan yasa Abba da tun ɗazun baice komai ba ya ƙaraso da sassarfa yana ƙoƙarin cire hannun Mom ɗin daga wuyana. “Kinga Jalilah saketa Please. Sakarta ta faɗa inda take kada ki kasheta mana”. Sam bata da alamar sakin nawa kuwa. Dan haka ya tureta da ƙarfinsa har sai da tai taga-taga zata faɗi, ni ma dai zubewa nai a wajen ina sauke wahalallen numfashi a gwagwgwame. Ga tari dake neman sarƙeni. Da sauri auta yazo gabana ya duƙa yana miƙamin ruwa. Banyi musu ba na amsa, dan ina buƙatarsa. Sauri-sauri na fara sha, sai ji nai an kaɓe ruwan ya zube jikina gaba ɗaya. Yayinda Auta ya fasa wani kukan azaba. Da sauri na tashi zaune, dan bata ruwan da aka zubarmin nake ba ta shi nake. Yaron na sona sosai a gidan, kawai dai dan baida yawan magana ne sai idan shi yaso, dan miskili ne na bugawa a jarida. Ba komai akai masa ba, Baby ce data figesa daga kusa dani kawai yake ma ihun kuka, Bibaa kuma na huci alamar itace ta kaɓar da ruwan da ya bani...... ✨(☯෴☯)(☯☯)(☯෴☯)✨ Badan Maash yaso ba dole ya shirya suka fita da Baba prof.. zuwa Company, daga can suka tsaya sukaci abinci a wani haɗaɗɗen restaurant. Daga haka suka wuce airport domin masa rakkiya, dan ya rasa jirgin sha biyu sai ya sake bucking na yamma. A hanyarsu ta zuwa airport ɗin ne Baba prof.. ke tsegunta masa yama yarinyar da tai hira da shi ɗazun ƙyauta amma ta dawo masa da shi. Dan haka mamakin yarinyar ya kasa barinsa har yanzun. Shiru Maash dake saurarensa yay tamkar bai ji ba. Sai dai a ransa faɗin yake (Ai bazata amsa ba. Ita dake harin miliyan ɗari biyar). “Wai baka jini bane?” Baba prof.. ya katse masa tunani. Cikin basarwar tasa da magana ciki-ciki ya ce, “Ban san mi zance bane Grandpa”. “A komai ai dama kai baka da abin cewa. Ko akan hirar ya kamata ma ka tambayi dalilina nayin hakan, amma ka share abinka. Awwab wai yaushe ne zaka canja? Anya matar da zaka aura zata iya ɗaukar wannan baƙin halin naka kuwa?”. “Ni nace zanyi aure ne?”. Ya faɗa a wani yanayi mai kama da jin zafi. Murmushi kawai Baba prof.. yay yana girgiza kansa. Sai kuma ya ce, “Oh haka zakaita zama kenan?”. Bai tanka masa ba sai ma ɗauke kansa da yay. Shima Baba prof.. ɗin sai bai sake magana ba har suka iso. Sama-sama sukai sallama, batare da yaga tafiyarsu ba ma yace Tijjani ya juya da shi gida. Abinka da lafiyayyar mota, cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan. Security ya buɗe musu gate cike da girmamawa. Tun kafin motar ta tsaya idanunsa suka sauka akan matashin saurayi da ke zaune a ɗan tudun da akai wajen flowers, Hayatu na daga gefensa zaune a kujerar roba dan bada shi suka fita ba. Sai dai tunda motar ta shigo ya miƙe tsaye. Suna gama dai-daita parking kuma ya iso da sauri kafin ma Guards dake tare da su ko Tijjanin ya fito ya buɗe masa shi ya buɗe masa. “Sannunku da dawowa Sir”. Hayatu ya faɗa yana rissinar da kai. Shima kan kawai ya jinjina masa yana kamo gefe da gefen jacket ɗinsa ya saka maɓallinta guda ɗaya jal dake a tsakkiya. Batare da ya sake kallon inda saurayin nan da yay galala yana kallonsa ba ya wuce hanyar falonsa cikin takun dake tabbatar da shi a sadaukinsa, kai daka gansa kaga tsayayyen namiji da iskar lokaci ke kaɗa masa. Wayoyinsa biyu da ya fita da su Hayatu ya kwaso a motar, sai wata ƴar ƙaramar bag mai ƙyau da Baba prof.. ya bashi, ba komai bane a ciki kuma sai turare mai azabar tsadar tsiya da ƙamshi. Saurayin nan ya kalla ya ce, “Ka jirani anan Sani ina zuwa”. Cikin girmamawa saurayin ya amsa masa da “To Yaya a fito lafiya”. Zaune ya samesa bayansa jingine da kujera ya lumshe idanu alamar gajiya. A hankali ya ajiye masa wayoyin gefensa, bag ɗin kuma a saman Centre table. Sai kuma ya nufi freight ya ɗakko ruwa da glass cup. A gabansa ya zo ya ajiye, tare da tsiyayawa ya miƙa masa cike da girmamawa. “Sir ga ruwa”. Shiru kamar bazai motsa ba, sai kuma ya miƙa hannu ya amsa batare da ya ɗago ko ya buɗe idanu ba. Ɗan jimm Hayatu yayi, sai kuma ya sake daurewa ya ce, “Sir dama yaron da zai yi aikin nan ne yazo gashi can a compound, a shigo da shi ne ka gansa?”. Nan ma yaja wasu sakanni kafin yace, “Shigo da shi”. Da ga haka ya ɗan ɗago ya kurɓi ruwan, sai kuma ya sake maida hannunsa a goshinsa yana ɗan murzawa........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ ......A tare Hayatu da saurayin sukai sallama. A saman lips ya amsa musu. Suna ƙarasowa saurayin ya zube a ƙasan lallausan carpet ɗin tsakkiyar kujerun, sai faman kalle-kalle yake kamar wanda ya buɗe ido da ga makanta. Sai da Hayatu ya ɗan zunguresa da ƙafa sannan ya dawo hayyacinsa ya ɗan nutsu. Ganin idon Maash a kansa ya sake nutsuwa tare da faɗin, “Ranka ya daɗe ina wuni”. A hankali Maash ya ce, “Lafiya, miye sunan ka?”. “Sani”. Ya bada amsa da sauri. “Kayi karatu?”. “Eh ranka ya daɗe, har matakin N.C.E na kai. Sannan na sauke Alkur'ani tare da littatafan addini masu yawa”. Kai kawai Maash ya jinjina masa, dan shi hausan ma ba wai duka yake ganewa ba. Sai dai yaji dukkan bayanin saurayin. Hayatu ya kalla, dan haka yay saurin gyara tsaiwarsa da ɗan matsowa kusa da shi. Dan shi koda ido Maash ya kallesa yasan mi hakan ke nufi. Kai tsaye ya ce, “Na sanshi sosai Sir farin sani, dan ɗan uwana ne, da mahaifiyarsa da mahaifina uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Sai dai su anan Kano suke. Yasan ciki dabai na garin Kano, sannan ita kanta yarinyar ma ya santa a dalilin shirin da take gabatarwa na matasa, har hira ta taɓa yi dasu wata biyu da suka shige lokacin bai kammala makarantarsa ba”. Nanma shirun yay ƙafarsa ɗaya akan ɗaya yana kallon saurayin kawai, sai da ya mula dan kansa sannan ya furta, “Ka tabbatar zai iya?”. “In sha ALLAHU zai iya Sir. Kuma zai riƙe sirrin dan in ma ya tona kamar kansa ya tonama asiri ne. Mu bamu sanshi ba bamu da alaƙa da shi idan aka samu kuskure”. “Fine.” Ya faɗa a taƙaice yana miƙewa abinsa. Ƙofar bedroom ɗinsa ya nufa, sai da yana gab da shiga corridor ɗin ya ce, “Ka bashi key ɗin mota da 500k na mai. Sallamarsa sai ya gama aiki”. Daga haka yay shigewarsa. Waro idanu sosai Sani yayi, jikinsa na rawa ya ce, “Yaya dubu ɗari biyar fa. For mai ɗin mota kawai? Na shiga uku ni Sani ɗan inna”. Dariya abin ya bama Hayatu, sai dai baiyi ba yay murmushi kawai da faɗin, “Kaga tashi muje waje sai kai murnar. Ka jirani bara na kai masa wannan”. Ai kafin ma Hayatu ya rufe baki Sani ya kai ƙofa da sassarfa... _😂Sani a taimakan dana data mana🤣😝._ 💢💦💢💦💢💦💢 A rikice Yaya Musaddiq ya iso gida sakamakon kiran da nai masa ina kuka. Sai dai kafin ma nakai ƙarshen abinda zan gaya masa Baby ta kaɗar da wayar tawa gefe ta daki tayis. A take tai ƙarar fashewa. Koda na ɗagota screen ɗin yay rugu-rugu ta koma fari gaba ɗaya alamar ta samu matsala. To anan ne fa na kasa haƙuri, bamma san sanda nai kukan kura a kanta ba sai ganina sukai na haye ruwan cikinta ina jibga tamkar ALLAH ya aiko ni. Aiko Bibaa da Abbas suka shigar mata suma suka hau dukana. Auta kuwa ya hau ihu da kururuwar kuka. Abba zai rabamu Mom ta riƙesa da makircinta. Sarkin yawa yafi sarƙin ƙarfi, duk da nima na more akan Baby suma sun dakeni sosai harda jimin ciwo. Wannan faɗa bai rabu ba sai da Yaya Musaddiq ya shigo. A haukace ya faɗo falon batare da neman izini ba ya hankaɗe Abbas gefe tare da Bibaa. Sannan nima ya ɗagani akan Baby. Sake yo kaina Abbas yay Yaya ya shiga tsakkiyar mu yana daka masa tsawa. “Abbas!! Kai miyasa baka da wayo ne? Maimakon ka rabasu matsayinka na babba amma rashin hankali da kai ma akeyi?”. Maimakon Abbas ya bada amsa sai Mom ce ta taso a fusace taba Yaya Musaddiq ɗin amsar. Daga ni har shi take haɗawa tana zagewa da kirani ɓarauniya, kai har iyayenmu ma haɗowa take. Yayinda ƴaƴanta ke faman huci kamar zasu daki Yayan shima. Duk da abinda ake Abba na falon ya gagara sake cewa komai. Karon farko dana ga ɓacin ran Yaya a fili game da abinda ake mana a gidan. Dan muryarsa har zuga take wajen faɗin, “Mom ki daina danganta Samraah da sata dan bata taɓa yima wani aka gani ba. Fitarta ta yau kuwa kowa yasan inda taje tunda abune a bayyane. Ya kamata dai ki binciki sarƙarki a tsakanin ku da kuke gidan zaune.” daga haka yaja hannuna dan mu fice. Amma sai Mom ɗin da Abbas suka sha gabanmu. Abbas ne ke faɗin, “Kai har ka isa ka fiddata anan bata ajiye sarƙa ko kuɗin sarƙa ba. An kuma kirata ɓarauniyar ko akwai abinda zakayi ne?”. Wani daƙilallen murmushi yaya Musaddiq ɗin ya saki a karo na farko. Sai dai baice komai ba ya sake jan hannuna zamu raɓasu mu wuce. “Mussadiq!”. Abba ya ambata a karo na farko. Cak ya dakata, sai dai bai juyoba bai kuma yi magana ba har sai da Abban ya sake magana. Still dai hannun nawa na riƙe a nashi muka dawo gaban Abban. Da hannu yay masa nuni daya zauna. Nan ɗin ma kamar bazai zaunaba ɗin sai kuma dai ya zauna. Hakan yasa nima na zauna a kusa da shi. Mom ya kalla ita da su Abbas suma yace suzo su zauna... Kusan mintina uku falon yay tsit sai ƙwafa da Mom keyi a jajjere tana harararmu ni da Yaya Musaddiq. Sai da Abba ya tabbatar kowa zuciyarsa ta nutsu kafin ya fara magana. “Bana jin daɗin wannan rayuwar da akeyi a gidan nan sam. Mu ace kullum sai maƙwafta sun jiyomu muna ihu da hayaniya kamar wasu marasa abinyi ko wanda basu je ajin makaranta ba. Bakwa ganin hakan zubarma da kammu mutunci ne?....” “Abban Abbas kaje ga maganarka kai tsaye nifa bana son wani kwana-kwana. Batun sarƙata ake anan ba wani mutunci ko yanda maƙwafta ke kallonmu ba. Su ya dama, sun kuma ga zasu iya ne. Dan haka ka musu magana su futomin da sarƙata in har ana son zaman lafiya a gidan nan. Inba haka ba wlhy police station zan kai su. Ai acan dole su fito da ita ya arziƙi ko tsiya.” Daga haka ta miƙe fuuu tabar falon. Shima Abbas miƙewarsa yay ya fice. Baby ta taɓe baki itama ta miƙe ta fita. Bibaa dai bata tashi ba, amma itama sai harare-harare take. Gaba ɗaya yanayin Abba ya sake sauyawa, sai dai mun san babu abinda zai iya. Ilai kuwa hankalinsa ya maido kammu. Babu kunya babu tsoron ALLAH ya shiga faɗin, “Ke Samraah ki fito musu da sarƙarsu ko ki faɗi ina kika saida aje a amso kinji, wlhy wannan fitinar ta isheni. Ku barni da abinda ya daman mana”. Kai Yaya Musaddiq ya girgiza kawai, yayinda ni kuma nakema Abban wani kallon takaici da baƙin ciki. Zanyi magana Yaya Musaddiq ya dakatar dani da faɗin, “Amma Abba bai kamata dan an nema wani abu an rasa ace Samraah ce ta ɗauka ba tunda ba ita kaɗai bace a gidan. Sannan ba kuma taɓa kamata akai da halin ba balle a kafa hujja da ita ɗin ce ba. Idan Samraah ta ɗauka sarƙa mizatai da shi. Karfa a manta tana aikinta, sannan ma kowa shaidane Mom bata taɓa barin tsakanin ni ko Samraah da Hafizzullah mu shigar mata ɗaki tun muna ƙanana. Amma tunda har kaima ka yarda da ita ɗince ta ɗauka ita Mom ɗin ta faɗin kuɗin sarƙar tata in sha ALLAHU za'a biyata. Amma kuma da ga yau zamu cigaba da gayama ALLAH kuma zamusa a tayamu kafin wani a cikinmu yabar duniya ALLAH ya tona asirin wanda ya ɗauki sarƙar”. “Amin ya rabbi, ba addu'a a Nigeria ba ku tafi gaban ka'aba kuyi mara mutunci. Ai dama na daɗe da sanin kaima ƙwallen shege ne nata ne kawai ya fita ita fitsararriyar. Sarƙata kuma naira dubu ɗari huɗu na sayeta sai a biyan kuma bana son ya wuce yau ɗin nan. In ba hakaba wlhy kaiwa police station babu fashi”. Murmushi kawai Yaya yayi, batare da yace komai ba ya miƙe. Kallona yay ya ce, “Tashi ki tattara kayanki ki maida ɗaki zanje na dawo”. Daga haka ya fice ni kuma na miƙe na shiga tattara kayan. Baka jin komai a gidan sai banbami da masifar Mom da zagin da take loda mana. Amma Abba kamar an ajiye gunki domin ado ko uhum bai sake cewa ba. Ni dai na tattare komai na nufi ɗaki, dan tuni na daina hawaye sai zuciyata dake wani irin suya da ƙuna tare da sake jin tsanar gidan da kowama na cikinsa. Yanda zuciyata ke mun zafi da raɗaɗi ji nake kamar nai kiran Mansoor nace masa gobe iyayensa suzo a tsaida bikinmu sati ɗaya kawai. Ni ko babu wani biki a ɗaura auren kawai na tare. Amma dai na dake dan bazan iya hakan ba, hasalima ni ban taɓa nunama Mansoor munada wata matsala a gidanmu ba, saboda hakan sirrinane bakuma zan iya tona sirrin cikina ga saurayi ba watarana yay min gori da hakan ko ya dinga kallon ƴan uwana a wulaƙance koda munyi aure. Koma dai mi suke mana su ɗin jininmu ne dai bamu da wanda ya fisu. Shiko wataran zai iya canjawa koma ya ɓata ɓat a rayuwata duk da bana fatan hakan kodan tsananin ƙauna da soyayyarsa da nake ji a cikin zuciya da ruhi na.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_ ......Sallamar Yaya Musaddiq da naji a falo bayan sallar isha'i ta sani miƙewa daga kwancen da nake zazzaɓi ya rufe ni. Nasan kuma ba komai ya jamin hakan ba sai caskalen da mukayi dan da gaske naci duka a wajensu. Daga inda nake na zubama Yaya Musaddiq daya dire baƙar leda a gaban Abba idanu na dake cika da ƙwalla. Yayinda kunnena ke sauraren abinda yake faɗa. “Abba ga kuɗin sarƙar nan a bata. Naira dubu ɗari huɗu ne kamar yanda ta faɗa”. Daga haka ya miƙe ya nufi hanyar fita. Cikin sauri na take masa baya batare da nabi takan shewar da Mom keyi ba kuɗin daya ajiye ɗin a hannunta dan bata bar Abba ko taɓawa yayi ba. “Yaya!”. Na kirasa da sauri ganin bai san ina bin bayansa ba. Tsayawa yay tare da juyowa yana kallona. Ina isa garesa na kamo hannunsa na wani ƙankame ina mai fashewa da kuka mai ƙarfi. Shiru kawai yay yana kallona. Tsahon minti ɗaya batare daya ce komai ba ya kama hannuna kawai muka nufi ɗakinsa. A bakin tabarmarsa ya zaunar dani, sai kuma ya sake fita batare da yace dani komai ba nan ma. Tun ina kuka daga zaune har na zame na kwanta Yaya bai dawo ba. Sai da ya ci kusan mintuna goma sha biyar sai gashi da ledar magani da dafaffiyar indomie. Zuwa sannan nabar kukan sai jan ajiyar zuciya nake kawai. Abincin ya tasani gaba mukaci tare cikin lallashi, ya kuma bani magungunan nasha suma da ƙyar dan bana son magani, allura kam tsoron da nake mata ai ba'a magana. Ganin baida niyyar cemin komai har sannan akan kuɗin daya basun muryata na rawa nace, “Yaya ina ka samu kuɗi ka basu bayan kasan kuma ban aikata ba. sharrinsu ne kawai ya tashi ko kuma makircin Mom dan ta samu kuɗin dama”. Ɗan murmushi ya saki tare da ɗora hannunsa a kaina. “Ki kwantar da hankalinki kada kuma ki damu da abinda sukayin, tunda ALLAH yasan bake kika ɗaukar musu kaya ba ya rage nasu. Bana son naga kina wannan kukan sam. Kuɗi kuma wanda nake asusune dama akan hidimar aurenki tuni, ALLAH zai kawo mana mafita kafin lokacin dan shi mai rahama ne mai jin ƙai, dan ko a yanzu da suka amshi wannan nasan bazamu kunyata ba daga abinda ta rage mana. Kar kuma ki saka abinda sukayi ɗin a cikin ranki ko kice sai kin rama dan na sanki kuma bajin magana kike ba, ki bari UBANGIJI da kansa ne zai rama miki wannan faɗan, dan bazan gushe ba ina mai kai masa ƙarar su garesa, kasancewar sa Sarkin daya haramta zalunci a karan kansa balle ga bayinsa nasan bazai barsu ba Samraah. Ki cigaba da haƙuri kinji, watarana sai labari, komai zai shuɗe tamkar ba'a taɓayi ba. Kwana nawa ma ya rage miki a cikin gidan, ƙarƙari ki ƙara wata biyu fa, dan ko yau mun sake magana da Mansoor a weekend ɗin nan iyayensa zasu sake dawowa a tsaida rana, dan su sun ma so ayi komai a randa sukazo Abba ne bai basu haɗin kai ba. Ke dai kawai ki cigaba da haƙuri, dama in aski yazo gaban goshi yafi zafi”. Wasu hawayen ne masu zafi suka sake ɓalle min, Yaya Musaddiq yasa hannu yana sharemun da murmushinsa. Wanda ni nasan yana yinsa ne kawai amma shima ransa a ɓace yake matuƙa. Dan idanunsa jazur suke sosai..... 💦💦💦💦💦💦 Da ƙyar Sani ya iya nutsuwa Hayatu ya masa bayani dan shigar 500k ɗin nan a account ɗinsa ta rikitashi matuƙa, daɗin daɗawa kuma Hayatu ya ƙara masa da 100k ƙyauta injisa kash a hannu. Ga kuma key ɗin mota da zai yi aikin da ita. Sai kawai Sani ya fashe da kuka. Dan abunne yazo masa ɓakatatan babu zato. Harga ALLAH zai iya rantsuwa bai taɓa ganin dubu ɗari biyar a dunƙule ba. Dan su talakawane sosai, ko karatun nan yayisane da ƙyar cikin buga-buga saboda yana matuƙar son yin karatu a rayuwarsa. A hakanma da ƙyar aka kammala, dan dai ALLAH ya bashi ilimine ma dan yanada basira sosai.. Kasancewar Hayatu har gida yaje yayma babansa bayani akan ogansa ya ɗauki Sanin aikin tuƙi koda yaje gida da mota babu wanda ya tambayesa, sai ma murna da suka taya shi. Kuɗi kuwa ko na wajen hayatu ma bank ya wuce aka saka masa su. Da dubu ashirin kawai ya shiga gidansu kamar yanda Hayatu ya bashi shawara, gaba ɗaya a yinin wannan ranar bakinsa yaƙi rufuwa. Motar ya kai aka duba kamar yanda Hayatu ya umarcesa, bayan an tabbatar komai zam ya koma da ita gida... 🌟💞🌟💞 🌟💞 🌟 A ɓangaren su Hayatu da ogansu Maash kuwa babu wanda ya sake saka shi a ido sai da la'asar, dan shi baya sakaci da ibadarsa, duk wanda ya san Maash ya sanshi akan hakan. Mutum ne mai matuƙar riƙo da ibada, ko'a tsakkiyar taron turawa yake, komai muhimmancin kasuwancin da yake in har lokacin salla yayi sai yay excusing kansa ya fita yayita, koda kuwa zai iya rasa wannan kasuwancin ne hakan bai damesa ba. Koda ya dawo sallar ma ciki ya koma abinsa. Sai bayan sun dawo sallar isha'i ne Hayatu ke sanar masa saƙon da gidan tv'n ALHERI suka turo game da amsa gayyatarsu da yayi. Sun buƙaci ya bada lokacin da duk yake so daga takwas na safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu har zuwa tara na dare. Sai da yay ɗan jimma kamar bazai tanka ba kafin ya kalla agogonsa. Da wani salon lumshe idanu dai-dai yana ɗagowa ya furta, “Ƙarfe nawa Abubakar zai zo?”. “Eh Sir kamar yace zuwa four na pm ne. Dan zai baro Abuja kamar Three”. “Kafin lokacin akwai wani abu ne?”. “A'a gaskiya. Dama dai ganawa da Senetor Kibiya ne, kuma kace Juliet tai magana da shi.” “Okay ka sa musu ten to eleven kawai. Dan awa ɗaya zan iya basu”. “Ai hakama sun gode Sir”. Hayatu ya faɗa yana danne mamakinsa. Da ga haka Maash bai sake tankawa ba. Dan haka Hayatu ya fice ya barsa dan ya huta..... (◕‿◕)➜(。◕‿◕。)➜(◕‿◕) Washe gari Monday da ƙyar na iya danne zuciyata nai aikin gidan kafin nai shirin fita. Nayi aikinne kawai dan nasihar Yaya Musaddiq. Ina kammalawa kuma ko karyawa ban ba nai ficewata. Na samu shima Yaya Musaddiq ya shirya, dama yace min yanada uziri akwai aikin wani mutumi da zai ƙarasa saboda yau da safe zai zo ya amsa motarsa. Tunda muka fara tafiya babu wanda ya tankama ɗan uwansa tun bayan gaishesa da nayi, a haka har muka iso. Yana ajiyeni ya bani 1500. Godiya na masa na shige shi kuma ya wuce. Sani da tun fitowarsu gida yake biye da su daga can nesa da wajen ya samu waje yay parking. Kujerar motar ya kwantar abinsa yay kwanciyarsa ya buɗe data da sabuwar wayarsa daya siya jiya. Tunda yanzu babu aikin wahala ai kuma abinyi ya samu kenan. (🤣) Ina shiga office ɗinmu na samu kira office ɗin MD. Takaici kamar nace bazanje ba amma dai na miƙe dan nasan hakan bai dace ba. Kamar yanda na saba sai da nai sallama ya bani izinin shiga sannan na shiga. A ciki na samu wata ma'aikaciyarmu mai suna Bashira, tunda na fara aiki a gidan nan nake ji ana faɗin son MD take kamar ta mutu. Amma shi yaƙi bata haɗin kai. Ina shiga da harararta na fara cin karo, ni saima taban dariya, amma dai banyi ba na ɗauke kaina kawai dan ba itace a gabana ba. Batare dana sauke face mask ɗin fuskana ba na ce, “Good morning Sir?”. A sake ya amsa min da “How are you?”. Kamar bashi ne jiya ya gama tijareni harda korana a office ɗinsa ba. A taƙaice na ce, “Alhamdullah Sir ance kana kirana”. “Eh zauna”. Ban musaba na zauna saboda ganin cika da batsewar da Badhira keyi. Sai da na zauna a daƙile nace mata, “Morning”. Duk da tana sama dani. Aiko harzuƙa naga ta sake yi. Sai dai kafin tace wani abu MD ya tari numfashinta da faɗin, “Uhhm inaga na gama da ke ko Bashira, zaki iya tafiya zuwa anjima zan shigo department ɗin naku dan ina son ganin yanda zakuyi aikin”. Kamar bazata muƙe ba sai kuma dai ta tashi a fusace tana cewa, “Okay”. Fuuu ta fita a office ɗin harda bugo ƙofa ji kake jifff. Daga ni har shi ƙofar muka kalla, ya girgiza kansa ni kuma na taɓe baki. Sai kuma ya kallan yana yin ƙaramar ƙwafa. “Sam bata da wayo. Ban cika son mace shasha mara aji irin haka ba”. Ban tanka masa ba ni dai, dan babu abinda ya shallan sunfi kusa. Nima ban wuce ya zagan da abinda yafi haka ba tunda dai namiji yake. Ganin ban tanka ba shima sai ya saki batunta ya kama wani. Cikin lallashi ya ce, “Samraah sam banji daɗin abinda kikayi jiya ba ga babban mutum irin professor K/Mashi ba. Mutum ne mai mutunci da dattako. Yanda kike zatonsa sam ba haka yake ba. Kuma bada wata manufa ya mana wannan ƙyautar ba face dalilin abinda kikayi a wajen taron jikansa. Yaji daɗin yanda kika sakashi ya maganantu har ya amsa zaiyi hira da wannan gidan tvn namu. Maganar yin tasa hirar kuma bawai a jiya ne aka shiryata ba. Dama mun jima da tura masa goron gayyatarmu har a karo uku tun sanda akai wannan dogon yajin aikin na wata biyu daya shuɗe har yaya wata magana akan gwamnonin arewa datai matuƙar tada hazo amma yana bamu haƙuri saboda baya ƙasar, yana india ganin likita ne. Yanzu haka a jiyan kuma daga can nan ya sauka saboda taya jikansa murnar buɗe company da kuma amsa gayyatarmu. Kuskuren da aka samu dai shine da yace ba zaiyi hira da kowa ba sai ke saboda abinda kika yi a jiyan ya matuƙar ƙayatar da shi”.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_ .......A karon farko na sauke ajiyar zuciya. Sai kuma a hankali na ce, “Kayi haƙuri Sir an samu kuskuren fahimta ne kawai saboda ni bakamin bayanin komai ba. Kuma nima banƙi amsar ƙyautar tasa da wata manufa bane, kawai dai albashin da ake bani ya wadatar dani”. “Humm kuma gashi ya dawo min da abinda ya bakin akan lallai na maida miki. Na kuma baki haƙuri tare da roƙonki kan ki amsa dan ALLAH.” “Gaskiya bazan amsa ba Sir kuyi hakuri. Dan Yayana zai ɓata min rai matuƙa. Nima kuma a karan kaina ma nayima kaina alƙawari a gafarce ni”. Shiru kawai yay yana kallona. Nasan mamakin taurin kaina yake yi. Dan har fuskarsa ta fara nuna jin haushi. Sai dai bai sake cewa komai ba akan batun face, “Okay ba damuwa. Sai batun mutuminki, a jiya PA ɗinsa ya turo mana takardar amsar gayyatar da kikai masa. Tare da bamu zaɓin lokaci amma kada mu wuce yau. Adai taƙaice yanzu haka ya tabbatar mana zai shigo kafin 11am, amma awa ɗaya kacal zai yi da mu. Dan haka yanzu zaki je ki kasance cikin shiri, nama su Tsanyawa magana akan su shirya kayan aiki da zauren da zaman zai kasance. A yanzu haka kuma sun fara in sha ALLAH”. Har cikin raina sai da naji zantukansa na dukana. Amma sai na dake na amsa masa da to kawai. Shima bai sake cewa komai ba ya miƙamin takardar gabansa. “Ki nazarci wannan, idan kina da wata idea sai ki ƙara, nan da awa ɗaya ki kawo min na gani. Zaki iya tafiya”. Zaram na miƙe kuwa na fice abina ko waiwayensa banyi ba. Zuciyata kuwa sai wani irin kai-kawo take. Ina fita kuma na dallama office ɗin harara. Ɗagowar da zanyi muka haɗa ido da Bashira, ashe tana tsaye a wajen bata tafi ba. Ko takanta banbi ba dan ba'itace a gabana ba nai wucewata a raina ina faɗin (Ballagaza kazar sakarai). Koda na koma office duk yanda naso samun damar tunani hakan bai yiwu ba. Dan su Ruƙayya tuni sun baibayeni da surutu akan ɗan ta'addan mutumin can mai kisan kai dako sunansa ban riƙe ba. Bana kuma fata ko ra'ayin riƙewar ma. Dan haka nafi maida hankali akan aikin gabana fiye da hirar tasu dan dama ba tofawa nake ba. A haka har lokacin da MD ya ban ya cika. Miƙewa nai na fita maida masa file ɗin. Yanda naga yana faman washe baki na tabbatar da abinda nai ɗin ya masa. Dan a take ya ɗaga waya yay kiran sauran wanda zamuyi aikin tare. Bayani ya sake mana ta yanda zamuyi komai ya ƙayatar ya kuma sake ɗaga kimar gidan namu. Ni sai ma naji kamar na makesa. Dan na fara saka MD a cikin jerin sunayen mutane mayun kuɗi. Jiba yanda yake rawar ƙafa tamkar zai ci da ka. Yana sallamar mu muka fice zuwa inda aka gyara domin gabatar da shirin. Makeup ɗin da akace na ɗanyi ƙi nai, sai ma shashsha musu ƙamshi nake famar yi. Sai da MD ya dinga lallashina sannan na ɗan sake saka fauda da ɗan lips gloss, daga haka ban sake bi takan komai ba na nema waje na zauna. 10:42am dai-dai aka sanar da isowar sa. Gaba ɗaya wanda ke a ɗakin MD yace mu fita a tarosa. Ko motsi banyi ba. Bamma da alamar hakan. Ganin MD na ƙoƙarin maido hankalinsa kaina nai saurin miƙewa nace zanyi fitsari. Babu yanda suka iya dani dole suka barni na fita zuwa bayi, su kuma suka fita tarbosa. Sai da na kwashe mintuna biyar da nake jin tabbacin duk ƙasaitarsa ya riga ya shigo sannan na koma. Har yanzu face mask ɗina na a fuskata dan haka baka isa gane yanayina ba. Tun kafin na ƙaraso na fara cin karo da gardawansa. Kallo ɗaya na musu na ɗauke kaina, dan ganinsu ma takaici yake sani. Yo banda rashin tawakkali miye na ajiyesu shi ba jami'in tsaro ba, shiba jinin sarauta ba, kawai dai giyar kuɗi da iyayi. Koda yake maybe al'adarsu ce hakan, tunda naga shima kakansa da nashi shekaran jiya. Baki na laɓe dai na ƙarasa shiga cikin takuna na nutsuwa da kowa kema kallon na yanga. Kaina tsaye na koma ɗakin da za'a gabatar da shirin, iya ma'aikatan mu kawai na samu a ciki suna ƙara gyagygyarawa. Ciki-ciki na sauke ajiyar zuciya ina mai ƙarasawa ciki. Ban tambayi kowa ya iso ko bai iso ɗin ba. Sai Usman ne yay tsulum yana faɗin, “Sam-G ki kasance cikin shiri baƙonmu na office ɗin MD yanzu haka. Nan da ƴan mintuna zasu shigo nan”. Cikin taɓe baki na ce, “In dai ba mala'ikan mutuwa ne zai zo ba kuma dai Usman ai shirina yayi”. Dariya ya sanya ƙasa-ƙasa. Ni kuma na cigaba da duba takardar hannuna. Goma da mintuna hamsin da biyar dai-dai Tsanyawa ya shigo yana sanar mana gasu nan tafe shi da MD. Sake kimtsawa kowa ya shigayi, banda ni kam, dan ko motsi banba daga yanda nake zaune balle na cire idanuna daga takardar dake a hannuna. Duk da face mask dana saka bai hana turarensa dukan hancina ba. Wannan dai fitina da yawa take, nikam bana rabe muku ɗayan biyu shima turaren na jinin tsafi ne shiyyasa yake danne ƙarfin duk wani turare idan mai shi yana waje. To nidai gaskiya ba yafewa zan ba, dan nawa kamfanin turaren suna iya nasu ƙoƙari suma. Jin yanda ɗakin yay tsitt kamar babu mutane yasa takaici sake kume ni. Chewing gum PA ɗin nan nasa ne ya fara shigowa, dole ne a kirasa chewing gum saboda koda yaushe dai yana manne da shi. Kusan a tare suka shigo da MD, sai wani rawar jiki yake da ƙanƙan da kai abin takaici. Duk wanda ke a zaune miƙewa sukayi, banda ni da takaicin MD ya sani ɗauke idona da nake musu kallon ƙasa-ƙasa da ban san mike faruwa ba. Ashe su Usman da ke zaune a inda nake duk sun tashi wai domin girmamawa. “Samraah!”. MD ya kirani ƙasa-ƙasa, banji ba dan haka Usman dake tsaye ta gefena ya ɗan bubbuga kujerar. Da farko sharesa nayi, dan nazata surutunsa ne ya tashi, ganin ya cigaba na ɗago ina harararsa. Idanunsa ya ɗan rumtse cikin yanayin matse fuska tare da mun nuni da MD ƙasa-ƙasa. Sai lokacin na lura da kallon da MD ɗin ke mun. Kowa na ɗakin nabi da kallo, ganinsu duk a tsaye shi kaɗaine zaune a inda za'a gudanar da program ɗin PA ɗinsa tsaye a kusa da shi ya ɗan ranƙwafa yana nuna masa abinda ke cikin tab ɗin hannunsa ya sani miƙewa batare dana sake kallon MD ba na ce, “Sorry Sir”. Kansa kawai ya ɗan girgiza da mun nuni da can ɗin. Komai ban sake cewa ba na wuce inda zai kasance nawa mazaunin. Kujeru ne guda biyu kacal suna ɗan facing juna kaɗan, sai table a gabansu an ɗaura glass cup guda biyu masu ɗauke da ruwa, sai dai an rufe su da ɗan ƙananun fai-fai. Ta ƙasan ido na ɗan kallesu dan koda na zauna ban tanka musu ba ban kuma cire face mask ɗin fuska na ba. Yau ma dai suit ɗinne jikinsa milk colour, rigar ciki, belt da takalmansa ne kawai suka kasance coffee. Sai wani almurin agogo dake hannunsa da duk da ban san kuɗin agogo ba a kallo guda zaka san ba'a sayesa da kuɗi kaɗan ba. Dan coffee fatarsa ma kawai ka kalla kasan ba'a magana. Yau ma babu kitso bai kuma ɗaure gashin ba. Ya sakesa ne kawai baya ya sakko masa har akan kafaɗa kaɗan, akwai kuma coffee ɗan kunne ɗaya a kunnensa na dama yau ma ya manna. Sannan babu neck tie, maɓallan ma rigar cikin ta sama a buɗe suke.... Umarnin cire face mask ɗin fuskata da aka bani ya maidoni hayyacina. Cikin taɓe baki na janye idanuna dake cikin eyeglasses daga kansa ina yin abinda akace ɗin, dan lokacin fara gabatar da shirin yayi. Shima PA ɗin nasa wajen ya bari, yayinda ɗaya daga cikin abokan aikina ya ƙaraso gabansa, cike da ladabi ya maƙala masa abin magana a jikin jacket suit ɗinsa. Nima miƙomin yay na maƙala a jikin hijjab ɗina. Sai da aka tabbatar mun gama kimtsawa sannan aka ɗora camara a kanmu. MD ne cikin yanayin marairaicewa yay mun alamar na ɗan saki fusakata, jinai kamar na hararesa, amma na dake kawai cikin basarwa. Kamar bani ba, tuni yanayina ya koma zuwa sauƙaƙa fuska, sai da na kalla camara naima masu kallo sallama tare da gaisuwar barka da wannan lokaci da musu albishirin shiryawa tsaf domin ganin babban kamun da wannan shiri yayo musu yau a bazata sannan na juya garesa a yanayin jan class ɗina na ce, “Assalamu alaikum ranka ya daɗe”. A hankali ya motsa lips ɗinsa ya amsa min da “Wa'alaikissalam” cikin muryar nan tasa a daƙile. Bazaka taɓa fahimtar kallona yake ko ba hakaba, saboda akwai eyeglasses mai duhu a idonsa. Yinai kamar ban damu da abinda yay ɗin ba nima, na cigaba da faɗin, “Wannan shiri na maka barka da zuwa, tare da nuna farin ciki matuƙa na cika alkawarin amsa gayyata a cikinsa a lokacin da kowa baiyi zato ba. Na tabbata hatta masu kallo ma zasu kasance cikin farin ciki maybe ma harda mamaki. Amma dai barkan ka da zuwa”. Nan ma a takaice ya furta, “Barka. Tare da fatan alkairi ma kowa”. (Ɗan rainin hankali) na faɗa a zuciyata. A zahiri kam na ce, “Masha ALLAH. To masu kallo, zan iya cewa duk sai ku sake matsowa gaban akwatinan talabijin naku, masu rediyo su ƙara sauti domin ji daga bakin babban baƙon namu.” Sake juyowa nai garesa ina faɗin, “Ko zamu iya sanin cikakken sunanka ranka ya daɗe?”. Cike da wani salo da sake harɗe ƙafafunsa da yay crossing cikin motsa lips ɗinsa kaɗan ya ce, “Awwab El-Mu'azz K/Mashi. Sai dai Maash akafi sani”. “Aiko nasan masu kallo zasu so sanin minene ma'anar Maash ɗin nan ranka ya daɗe?”. Sai da ya bushi iska na wasu sakanni sannan yay wani ɗan murmushin gefen baki, a taƙaice ya ce, “Kwanar Mashi ne ainahin sunan tushena kenan, abokai suka maida shi Maash tun ina secondary school, daga nan kawai ya zama ana kirana da shi”. “Uhhm Masha ALLAH. To ko zamu iya sanin wanene Maash a takaice. Dan wannan amsa ce da mutane suka jima suna son ji daga bakin ka amma basu samu damar hakan ba?”........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_ .......Ɗan jimm yay kamar bazai amsa ba, sai kuma ya kai hannu ya shafa ƙasunbarsa. Duk da glasses dake idonsa sosai nake jin kaifin idanun nasa yanzu kam a kaina. Amma sai na basar. Cikin yanayin rashin mafita da gurɓataccen harshensa ya bani amsa yana gwamutsa hausa da turanci sai na gyara masa ma wani lokacin. “Awwab El-Mu'azz shine Maash. Asalin ɗan jihar Kano girman Lagos. Karatu zuwa matakin masters, wasu courses sun biyo baya duka dai a fanin kasuwanci. Ɓangaren karatun addini ma Alhamdullah. A yanzu haka business man”. “Masha ALLAH. A yanda dai kake bayanin zabbirgewa, da daɗin saurare, sai dai a zahirance kafin aga Maash a haka nasan ansha gwagwarmaya bata wasa ba. Tare da ƙalubale kala-kala. Shin yaya ma akai ka fara kasuwanci?”. “Business tamkar logo ne na family ɗin Ummie na. Kusan zan iya cewa na gada ne daga wajenta. Dan tun ina mitsitsi na nake ganin yanda take tsaye akan ƙafafunta ita da mahaifinta, grand father ɗin a kenan, sai hakan ya zaburar dani tashi akan wannan burin, kuma Alhamdullah yanzu an cimma buri. Batun ƙalubale kam ga duk wani rai mai numfashi koda bai tashi da nufin motsawa ba sai an fuskanta, amma Alhamdullah komai ya zama tarihi, dan ko yanzu haka an cimma burika da yawa harma da waɗanda ba'a tsara za'a cimmawa ba”. “Gaskiya ne to Alhamdullah. Kafin yanzu Maash na kiran kansa ne kawai da suna bakano ɗan arewacin Nijeriya, sai dai mutane na ƙorafe-ƙorafe game da ko gidan kiwon tsuntsaye bai taɓa samarwa a arewacin ba duk da yanda ALLAH ya baka damar baza harkokin kasuwanci a duniya. Sannan ko cikakken Hausa ma bai iya ba. Shin ko Maash nada wani dalilin hakan?”. “So babu wani dalili gaskiya. Kawai lokacin yin hakan ne baiyi ba, amma yanzu yayi ai gashi mun fara. Za kuma mu cigaba da yi in sha ALLAHU. Batun yare kuwa kowane ɗa kan fara tashi ne da yaran mahaifiya. Kasancewar mahaifiyata ba yarenta bane yasa na samu rauni a kansa, amma nasan ko yanzu zan iya fafatawa da kowa a kansa”. Dariya maganarsa ta ƙarshe taban. Amma sai na dake na ce, “Kai ashe kace mu sake shiri bayan Companyn ƙera motoci akwai wasu ire-iren sa tafe ma kenan?”. “Haka muke fata a cikin tsare-tsaren mu.” “ALLAH ya cika buri”. A saman lips ya amsa min da “Amin”. “Mi ya ja hankalin Maash buɗe katafaren Company irin haka a Kano da ba'a taɓa zato ba? Sannan ko Maash zai iya dawowa da rayuwarsa garin Kano gaba ɗaya?”.. “ALLAH ya rubuta anan ɗin ne za'a samar da shi. Idan ALLAH ya ƙaddara hakan kuma game da dawowa ɗin mizai hana”. “Ko Maash nada aure?”. “A kasuwa yake”. “A saka tallarsa kenan ko za'a samu wacce zata saya?”. Fuska ya ɗan tsuke. A ɗan daƙile ya furta, “Ba'a gaji dani a gidanmu ba ai”. (Wama zai so ka ɗan rainin wayo) na faɗa a zuciya. A fili kuwa sai na murmusa kawai na cigaba da faɗin, “Miyasa Maash baya son hira da ƴan jarida duk da suna ƙoƙarin ganin anyi hakan kodan tarin masoyansa da matasa irinsa da ake fatan su kallesa matsayin madubinsu?”. Shiru yay baice komai ba, kusan minti ɗaya sannan ya furta, “Nothing”. A daƙile. Nima a karan farko na ɗan kafesa da idanuna dake cikin glasses mai haske, dan sam ban gamsu ba. Amma sai MD dake bayan fage yay min nunin na barsa. Jinai kamar na dalla musu harara su duka. Amma na dake na cigaba da faɗin, “Wane kalar kaya Maash yafi so?”. “Kowanne”. “Abinci?”. “tuwo”. Wani kalar ɗan waro manyan idanuna nai waje a kansa. Shi kuma ya ɗan ɗauke kai cike da basarwa. Nima sai na ɗan basar ɗin kawai. Na cigaba da faɗin. “Wace shawara zaka bama matasa irinka dake tasowa?”. “Su zama masu jajircewa, juriya akan duk abinda suka sa gaba, dan kayi karatu ba dole sai kayi aiki ba. Dan ka fara business ba dole sai kayi kuɗi kamar ƙyaftawar ido ba. Ka kasance mai Gaskiya akan komanka, neman zaɓin ALLAH da haƙuri akan halak duk ƙanƙantarsa. Ka kuma zama mai tarin wadatar zuci, dan in babu wadatar zuci ko zaka cika duniya da dukiya zakaita jin baka gamsu ba ne. Shaye-shaye baida wani amfani face maida matashi bayan baya a cikin al'umma. Shi iskanci ba'a koyansa, kowa da kake gani zai iya yi, zama mutumin kirki shike da matuƙar wahala, sai mu faɗama kammu gaskiya kafin duniya ta faɗa mana”. “Masha ALLAH muna godiya da wannan shawara. Minene buri, ko nace shirin Maash na gaba?”. “Maash nada tarin burika da shirye-shirye masu yawa da shi kansa bai san adadi ba. Amma manya daga cikinsu a dai yanzu sune samar da companys da zasuna fitar da abinci kowane nau'i in sha ALLAH. Zamu fara tsara komai a yanzu haka, muna fatan kuma zuwa ƙarshen shekarar nan komai ya zama ready”. “Ko zamu iya sanin a ina wannan babban project ɗin zai kasance?”. “Duka anan arewa ne in sha ALLAHU. Amma sai lokacin yayi za'a sani”. “ALLAH ya cika buri”. “Amin” ya amsa a taƙaice. “Mi Maash yafi so a rayuwarsa?”. “My Parents”. “Miye baya so?”. “Cin amana”. “ALLAH ya hanemu zama masu fuska biyu” na faɗa a yanayin kalma mai harshen damo ina ɗauke kaina daga kansa. Juyawa nai ga camara, fuskata ɗauke da ɗan murmushi na ce, “To masu kallonmu, gadai hira ta kwararo cike da daɗi, sai dai lokaci ya mana tsiyar tasa. Amma zance ku zama a cikin masu fatan wataran Maash ya sake zama a wannan kujerar domin amsa muku tarin tambayoyin dake a ranku da bamu kawo a wannan dandali ba yanzu saboda ƙarancin lokaci. Amma dai, ko a hakan ma mun gode, dan ALHERI TV ta kafa babban tarihi”. Sake juyawa nai garesa, na ce, “Ranka ya daɗe mun gode sosai da cika alkawari. Muna fatan ALLAH ya maidaka gida lafiya. Zaka iya yin sallama da masu kallo suma”. Hannu kawai ya ɗaga yana mai sakin murmushi kaɗan ya ce, “Fatan alkairi”. Ana ɗauke camara daga kammu ya wani sauke numfashi mai ƙarfi yana furzar da shi tare da jan siririn tsaki. Yinai kamar ma ban san da shi a wajen ba. Dan kafin ya tashi tuni na miƙe ni ina ɗaukar ruwan da aka ajiye mana da babu wanda yasha nabar wajen. Ban tsaya a ɗakin ba na fice gaba ɗaya. Office ɗinmu na koma. Bayan kamar mintuna sha biyar sai ga su Asiya sun shigo. Baibayeni sukai su duka har Usman da Khalid. Kowa na jinjina ƙoƙarin da nayi. Tare da nuna zumuɗinsu na fatan zuwan randa za'a saka shirin wa kowa dan su sake kallonsa a tsanake. Murmushi kawai nai musu nidai bance komai ba. Aikinmu muka cigaba dayi, har lokacin sallar Azhar yay muka fito gaba ɗaya. Bayan idar da salla kamar yanda muka saba na haɗu da Mansoor. Fita mukai restaurant ɗin kusa da ma'aikatar tamu cin abinci kamar kullum. Kusan a tare muka shiga da wani saurayi shima fuskarsa da fase mask. Bai mana magana ba bamu masa ba, kowa ya nema wajen zama ya zauna. Munci abincinmu cike da nishaɗi muna ƴar hirarmu. Bayan mun kammala muka fita. Mun koma office kan ayyukanmu. Banfi zaman mintuna biyar ba sai ga MD har cikin office ɗinmu Harun biye da shi. Duk miƙewa mukai domin girmamawa a garesa. Fuskarsa ɗauke da murmushi yay mana alamar mu zauna. Shima ya zauna a kujerar dake facing ɗina. “Sannu da ƙoƙari jarumarmu”. Ya faɗa idonsa a kaina. Sosai na waro nawa idanun dan mamakinsa. Kasa haƙuri nayi sai da na furta, “Jaruma kuma Sir, sai kace wata ƴar Film?”. “Ba'a Film kawai ake jarumta ba Samraah. A yau kinyi namijin ƙoƙari ƙwarai da gaske. Na tabbatar duk randa aka saki wannan hirar taku wa masu kallo ba ƙaramin tada hazo zatayi ba. Domin Maash yayi abinda bai taɓa kwatanta yi ba. Da ace kuma zan iya babu shakka sai na tambayesa ko miyyasa ya amince mana?. To amma ina, yana da wata irin kima da girma ga kwarjini mai saka shakkar koda kallonsa ne. Kin cancanci a kiraki kallabi tsakanin rawuna. Kuma in sha ALLAHU a dalilin wannan hirar zakiga babbar karramawa wa wannan gida dama duk wanda suka taimaka a ɗaukar shirin”. Tafi su Khalid suka shiga yi cikin ihu. Yayinda MD ke faman washe baki shima cikin nuna a nishaɗi yake. Ni dai na tsaya kawai ina kallonsu ne galala. Su dai murnarsu kawai sukeyi basu bi takaina ba, Asiya ce ma dai na ɗan ga yanayinta ya canja, da alama abinda suke ɗin bai mata ba, ko kuma zantukan MD ne suka zafeta oho mata. Sallama MD yay mana ya fita. Ni dai na sauke ajiyar zuciya kawai. Yayinda Ruƙayya ta rungumoni. Duka na kai mata kaɗan, ta sakan tana dariya bayan ta ja min hanci. Babu shiri nayi murmushi nima. Ruƙayya nada kirki sosai. Sannan halayenta na matuƙar burgeni. Shiyyasa a wasu lokutan sai naji kamar nace ma Yaya ya nema auranta dan ALLAH su sasanta. Amma ina tsorom halin maza kada yace bata masa ba. Duk da dai nasan babu wani namiji da zai kalli Ruƙayya yace bata masan ba. Dan ƙyaƙyƙyawar yarinya ce sosai. Tana da haske gata ƴar duma-duma abinta. Itama ta taɓa gaya min mahaifiyarta ta rasu a wajen haihuwarta. Kuma ita kaɗai ta bari, hannun kishiyar uwa ta tashi. Duk da bata fito ta faɗa min duka matsalarta ba na fahimci bata jin daɗin zaman gidansu, sai dai haƙurinta yasa bazaka taɓa gane hakan ba kai tsaye sai in har itace ta faɗa maka.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ........Tunda suka fito Hayatu ya zuba masa ido ta cikin mirror ɗin gaban motar, dan shi yana zaune ne a kusa da Tijjani driver. A hankali kamar mai ɗan jin shakka ya ce, “Sir ko zamu koma gida ne ka huta?”. Shiru kamar bazai tanka ba. Sai da ya mula dan kansa batare da ya buɗe idanunsa dake a rufe ba, ko gyara zaman ƙasaitar da yay ya motsa lips ɗinsa kaɗan. “Ba buƙata”. Ya faɗa a taƙaice. Kai kawai Hayatu ya jinjina yana mai haɗiye yawu. Kai tsaye Company suka nufa. Dan akwai zaman meeting da zasuyi sakamakon fara ɗaukar ma'aikata da za'ayi a gobe in sha ALLAHU. Sun samu duk wanda ake buƙatar gani a zaman meeting ɗin yazo. Tunda aka buɗe masa mota kuma ya fita kowa keta ƙoƙarin gaida shi cikin girmamawa. Hannu kawai yake ɗaga musu da bin yanayin wajen da kallo ƙasa-ƙasa. Hatta da turawa da Chaines ɗin da zasu jagoranci aiki a companyn girmamashi sukeyi. Kai tsaye hall ɗin da meeting ɗin zai gunada suka nufa. Wajene da akai matuƙar tsarawa da ƙawatawa. Sai da ya zauna a babbar kujerar dake tsakiyar dogon tables ɗin sannan suma kowa ya zauna. Ya ƙare musu kallo ƙasa-ƙasa ta cikin gilashinsa ɗaya bayan ɗaya kafin suka fara gudanar da abinda ya tarasu.. ★ A matuƙar gajiye liƙis suka bar Company bayan sallar la'asar. Koda suka isa gida sun samu baƙonsa Abubakar yazo. Saboda yanda yake jinsa a takure bai iya ganawa da shi ba ma ya shige bedroom. Wanka ya farayi sannan ya ɗan kwanta. Tabbacin ya gaji sosai cikin ƙanƙanin lokaci barci mai nauyi yay awon gaba da shi kuwa. Bai fito ba sai lokacin sallar magrib, sai da kuma akai isha'i ya dawo gidan. A sannan ne yay ɗan zaman awa guda da Abubakar da Hayatu. Suna kammalawa ya bama Hayatu umarnin su shirya jirgin sha biyu na daren yau ɗin nan zasu bi zuwa Lagos. Hakan ba sabon abu bane a gare su. Dan shi duk sanda abu ya kaɗa masa yinsa kawai yake yi, ko dan jirgin nasa ne na kansa yake hakan oho masa . Tunda ma har aka tsaida time ɗin tafiyar yasan Juliet ita ta sani, amma duk da haka bayan ya sanar da guards da Tijjani su shirya sai ya nufi sashen da take. Hayatu na gab da shiga falon wayarsa tai tsuwwa alamar shigowar saƙo. Baibi takanta ba ya ƙarasa. A falo ya samu Juliet ɗin tana waya. Ganinsa yasa ta katse sukai maganar da zasuyi ya fito. Shima nasa masaukin ya nufa domin kimtsawa. Duk da dai akwai ɗan sauran lokaci ma. Daga aljihu ya cire wayarsa da nufin ajiyewa sai kuma ya fasa saboda tuna shigowar saƙon ɗazun. “What!” ya faɗa da ƙarfi, sai kuma ya miƙe da saurinsa cikin sassarfa ya fice. Kai tsaye sashen ogan nasu ya koma. Sallama ɗaya yay batare da jiran izini ba ya afka ciki. Dai-dai nan kuma Maash ke fitowa da ga bedroom ɗinsa kunnen sa manne da bluetooth alamar waya yake yi, yanda ya tsuke fuska matuƙa zai tabbatar maka koma da waye yake yinta bada daɗin rai bane. Kallo ɗaya yay ma Hayatu daya shigo kamar an korosa ya ɗauke idonsa. Cikin kujera ya kai yana wani kalar cije lips ɗinsa. Sai kuma kamar a fusace ya furta, “Nifa ba fushi nake ba Paa. Maganar yarinyar nan kuma nace a barta bana so. Ni ban taɓa cewa ai ina ra'ayin zama da ita ba, kuma ban taɓa cemata ina sonta ba”. Ɗan shiru yay alamar yana saurare, sai kuma ya sake ɓata fuska a yanayin shagwaɓa ya sake cewa, “Paa Please mana. Understand me.” Sai kuma ya sake yin shiru. Kusan minti ɗaya ya ce, “Okay naji, amma ni daga nan zan wuce Finland ne, bazan dawo ta Lagos ba. Kwana shida zanyi kawai in sha ALLAH”. Guntun murmushi ya saki kaɗan, sai kuma a hankali ya ce, “I love you too. Bye ka gaida Ummie da Mamma.” daga haka ya cire bluetooth ɗin yana maida hankalinsa kan Hayatu. Hayatu da dama kamar a ɗofane yake a saman wuta yay wata zabura zuwa gabansa. Cikin rawar hannu ya miƙa masa wayar yana faɗin, “Sir yarinyar nan ce fa ta sake turo saƙo ta number na. Ban san taya ta samu ba, ko yau da mukaje office ɗinsu ne?”. Komai baice ba ya amshi wayar. Kasancewar da turanci aka rubata text message ɗin yasa ya fahimci komai. Ya jima bai motsa ba ya ƙurama wayar kawai cat eyes ɗin shi, sai dai fuskarsa ta sake komawa wani bala'in kicin-kicin har blue ɗin cikin idanunsa na ƙoƙarin ɓacewa. Hayatu ne ya katse shirun da faɗin, “Wlhy Sir al'amarin yarinyar nan mamaki yake bani, na jima banga mace mai busashiyar zuciya irinta ba. Just small girl ɗin nan wai tasan yin irin wannan ta'addacin haka. Jiba yau yanda take wani basarwa da shan ƙamshi fa. Ni wlhy dan kawai kace a barta ne ai. Amma har ita wacece da bazamu sa a tattaro mana kaf zuri'ar gidansu ba taga ƙaryar tsagerancin nata. Haba ita wacece da zata zauna tana rainama mutane hankali. Kawai na kira Sani a daren nan ya kawo mana ita gidan nan a amshi wayar tata a gabanta mu goge video ɗin sannan mu danƙata hannun hukuma, muda muke da makami ma a kanta, dan biyowa ta bayan gida fa tai akan hira dakai har yanzu ba'a daina cecekuce a kansa ba a media, wani abun ma nasan sai randa aka saki hirar, tabbacin mutane da yawa na asiri tazo da shi wajen har ka yarda ka amsa matan zai sake gitowa”. Shi gaba ɗaya ma surutun Hayatun saka masa ciwon kai yake. Dan haka ya wurga masa wani kallon da ya sakashi nutsuwa, tare da jan bakinsa ya tsuke. Shiru falon ya sake ɗauka kowa na cuɗawa da kwancewa a cikinsu. Kafin shi ya miƙama Hayatu wayar yana faɗin, “Ba buƙatar mata komai a yanzu. Ina son ganin iya gudun ruwanta. Ka amsa mata da za'a bata 500m ɗin, amma a ina za'a haɗu da ita ta bada recording ɗin”. “Amma Sir.....” Hannu ya ɗaga masa, a daƙile ya ce, “Na gama magana”. Yawu mai ɗaci Hayatu ya haɗiye. Sai kuma ya jinjina kansa cikin girmamawa ya ce, “Okay Sir, in sha ALLAH za'ayi yanda kace. Na barka lafiya”. Daga haka ya juya ya fice. Ta gefen ido Marsh ya bisa da kallo. Sai kuma yay wani kalar furzar da iska yana maida kansa a kujera ya kwantare tare da lumshe idanunsa a hankali. Shi kaɗai yasan mi yake ji a ransa game da yarinyar nan. Ya fahimci lallai bata fahimci a ramin da take neman jefa ƙafarta ba. Amma zai bata lokaci ta gama nata kalar ƙaramin wasan kafin ya fara buga babban game da sai tayi dana sanin saninsa a rayuwarta a kanta. Idan ita ƙaramar ƴar iskar layi ce, zai tabbatar mata shi na duniya ne baki ɗaya, dan ba neman kuɗi kawai ya iya ba harda cin uban duk wanda ya shiga sabgarsa. Ko abubuwan data dinga yi yau duk a rubuce suke a brain ɗin, ya fahimci tanada taurin kai da tsageranci. Duk zai sauke mata su kuwa nan bada jimawa ba. Ya jima a wajen zaune har Hayatu ya dawo ɗauke da abincin da Sani yayo order. Amma sai yace bazai ci ba. Ya haɗa masa coffee kawai. Umarninsa Hayatu yabi. Ya kawo masa coffee amma ya haɗo da biscuits mai daɗi. Dan yasan waɗan nan sune kalar ciye-ciyen da ogan nasu yafi so a rayuwarsa. Shiyyasa a duk inda yake baka rabashi da kalolin biscuits da chocolates kala-kala masu shegen daɗi. Sabone tun na ƙuruciya ya riga ya kamashi. Sake fita Hayatun yay ya barsa, shi kuma ya maida hankalinsa ga tv yana kallon film ɗin da sukeyi yana shan coffee ɗinsa da biscuit ɗin kamar baya so. Koda ya kammala zamansa ya cigaba dayi har sai da film ɗin ya ƙare sannan ya shige ciki. Maimakon kwanciya bathroom ya faɗa, ya haɗa ruwa mai ɗumi cikin bathtub tare da haɗa kayan ƙamshi kala-kala a ruwan sannan ya shiga ciki. Sai da yay minti talatin cur ruwan na ratsashi da miƙar masa da kowace gaɓa sannan ya fito ya shiga wajen wanka ya ɗauraye jikinsa. Bayan ya fito salla ya fara gabatarwa tare da shafa'i da wutiri sannan ya shiga shiri. Yayi ƙyau sosai cikin shigar tasa tamkar ka sacesa ka gudu. Ga wani uban ƙamshi na tashi uwa kamfanin haɗa turare kamar ba dare ba. Sumar nan tasha gyara daka gansa kasan ya haɗa jini da masu jajayen kunne. Hakama kwantaccen gashin sajensa sai walƙiya yake gashi kwance luf-luf ya sake fidda taswurar doguwar fuskarsa. Sai da ya tabbatar komai ya masa yanda yake buƙata sannan ya fito cikin nutsuwarsa da takunsa na tsayayyen namiji. Baiyi mamakin ganin Hayatu a falon ba. Dan duk inda aka gansa dolene aga Hayatun. Duk da yana jin idonsa a kansa bai kallesa ba. Hakan yasa Hayatu ɗauke idonsa shima a ransa yana kirari wa UBANGIJI mahaliccin wannan ƙyaƙyƙyawar halitta, gaskiya dole ma aso mai ƙyau, dan ko shi dake a namiji, kuma ana yawan sanar masa shima ɗin ƙyaƙyƙyawane har ga ALLAH ogansa na birgesa. Dan mutum ne daya san hakkin tsara ado. Ya iya tsara saka sutura ta zauna ɗam ya haskata kuma tamkar dan shi kaɗai ake saƙa kaya irinsu. Ganin zai ɗago da sauri ya wuce sumu-sumu zuwa bedroom dan ya kashe komai ya gyara kuma abinda ya ɓata tunda basu san ranar dawowarsu Kano ɗin ba kuma. Suda suke kullum a tafiye-tafiye kamar ƴan sama jannati.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ .......Kamar ko yaushe yau ma Mansoor ne ya maida ni gida, koda na shiga na samu gidan tsitt. Banbi takan kowaba na shige ɗaki, auta na samu yana barci, ga books ɗinsa a gefensa barbaje alamar homework yake barcin ya kwashesa. Ɗagashi nai na maida kan katifa. Sannan na tattare books ɗin na ajiye masa gefe bayan na duba abinda yake. Yaron akwai brain, inba ni ba babu mai zama damuwar koya masa homework, sai idan Abba. Wani lokacin ma sai kika yayi da kansa kafin ma na dawo, sai dai na ɗan masa gyararraki kawai. Wanka nai ƙoƙarin shiga, sai dai bayin duk an ɓata shi, nasan Bibaa ce zatai wannan aikin ba wani ba. Na rasa mike damun kan yarinyar nan, amma zan koya mata hankali. Tanada ɗakinta ita kaɗai amma tsabar shaiɗanci tace tsoro take ji a can, shine Abba yace ta dawo nan mu zauna wai sai ta ƙara girma. Da farko na ɗauka haka ɗinne, sai daga baya na fahimci Mom ce ta sakata yin hakan dan ta dinga ɗaukar rahoton duk motsina tana kai musu. Tun wani lokaci da naji tana faɗama Mom wayar da mukai da Mansoor nagane hakan. Bayin na sake gyarawa sannan nai wankan. Harna fito na gyara jikina banji motsin kowa ba. Ba'a wani ɓata falonba yau sosai, dan haka na wuce kitchen. Shi kam yana nan jibge da kayan wanke-wanke tun daga kofunan kalacin safe har na rana da sukaci. Kaina na girgiza ina mai jin tausayin Bibaa da Baby a rayuwa. Dan ita Mom gani take gata take musu bata san kashe musu rayuwar take ba, haka kullum da rayuwar take a gidan, idan nai aikin safe na fita babu abinda suke kaudawa har sai na dawo na sake yi, badan nima na zama jan wuya ba abincin rana ma sai na musu na saka a kula. Sai da na nuna musu nima tsagerar kaina ce sannan, shiyyasa kullum basu da abincin rana a gidan sai taliya ko cus-cus ko macaroni, indomie. Sai idan akwai stew ne zakiga sun dafa farar shinkafa. Stew ɗin kuma zakiga dole nice zanyita, Mom taƙi yarda a ajiye mai aiki wai ita kishi, randa nayi aure to naga ubanda zai zo ya musu. Kwanikan na fara tattarewa na wanke, ƙafafuna duk sunyi tsami saboda tsaiwa. Haka dai na daure na kammala na maida komai muhalinsa sannan shima kitchen ɗin na shiga gyaransa. Ƙaramar indomie na dafa guda biyu, na raba biyu naci tawa anan na juyema auta tasa a plate. Har lokacin babu wanda ya dawo, mamaki ya sake kamani da tunanin ina sukaje haka ne?. Har akai sallar magrib sai mu kaɗai a gidan. Sai bayan an idar Abba ya shigo. Fita mukai ni da auta daya tashi muka gaishesa. Na wuce na kawo masa ruwa na koma ɗaki abina na barsu anan falo. Sun fita sallar isha'i nima zan kabbara tawa naji hayaniyar shigowar su Mom. Banbi takansu ba na tada sallata. Sai da nai har shafa'i da wutiri sannan na fito musu sannu da dawowa. Kaya na tarar barbaje a falon kashi-kashi. Na sakawa dana kwalliya harda na ciye-ciye alamar dai daga kasuwa suke. Ganin hankalinsu baya kaina dan ko gaisuwar ma da kai Mom ta amsa min na juya na koma abina ina mamaki, dan tabbas da kuɗin Yaya na jiya akai wannan sayayyar kenan. Jinai raina ya ɓaci matuƙa, dan haka na fito na wucesu. Yanzun ma hankalinsu babu alamar yana kaina. Ta ihun murnar kayansu suke kawai. Ɗakin Yaya Musaddiq na nufa, yana tsaye da alama yanzu ne yake dawowa massalaci. Ganina rai ɓace ya sashi faɗin, “Jikin ne?”. Kaina na girgiza masa ina kaiwa zaune. Cikin zafin rai na ce, “Wlhy Yaya zancen kuɗin sarƙar nan shirine kawai. Ko kasan matar can yau kasuwa suka shiga ita da ƴaƴan nata gasu can sun baje kaya a falo kamar za'a buɗe kanti. Kasan kuma babu yanda za'ai hakan ta faru Mom ta iya kashe kuɗin sarƙar nan a banza haka da gaskiya ne”. Murmushi mai sanyi Yaya Musaddiq yay hana kaiwa zaune kusa dani. Cikin sauƙaƙa murya tare da riƙo hannuna cikin nashi ya furta, “Cool down sweetheart. Sune a ƙasa ai. Bakiji shata na faɗin ku gargaɗi mai gina ramin mugunta ba. Ni nasan dama koda an ɗauki sarƙar ma bata kai ta kuɗin data faɗa ɗin ba. Amma ba komai ALLAH zai bamu wasu. Yanzu ma Abba ya bar ɗakin nan”. “Miya faru ya shigo?”. Na faɗa cikin mamaki tunda nasan dole akwai dalili. Hannuna ya saki yana miƙewa da ɗan taɓe bakinsa. Ya zare jallabiyarsa ya ajiye sannan ya koma ya zauna dan jikinsa akwai dogon wando da t-shirt fara. “Yazo ya sameni akan wai tunda yaga inada kuɗi ni ne ya kamata na miki komai na aure. Dan shi gaskiya yana a cikin damuwar rashin kuɗi. Saboda hakane ma yaƙi yarda su tsaida rana a randa iyayen Mansoor suka zo. Amma da yasan har inada wannan kuɗin haka aida an kammala komai. Dan haka zai kirasu suzo weekend ɗin nan a tsaida ɗin. Na kuma bashi aron 200k zuwa ɗan wani lokaci zai bani..” “Kuttt! Amma mutumin nan ko! Wai mike damun Abban nan ne?. Dama ko bai faɗaba waye ke jiran wani abu da ga garesa mtsowww aikin banza. Sannan kuma bashin ka amsa zaka bashi Yaya?”. Murmushi Yaya Musaddiq ya saki mai haɗe da dariya, sai kuma ya girgiza kansa. “Kai wannan yarinya masifaffiya ce ke wlhy, wanda basu sanki bane kawai suke miki kallon mai haƙuri. Ni ALLAH har ma na fara tausayin Mansoor bawan ALLAH shi gashi da sauƙin halin tsiya”. Baki na tura ina faɗin, “Kai Yaya nice masifaffiyar?”. “Ta bugawa ma kuwa a jarida kandala. Wani lokacin da idan kina abu sai naga kamar ma kece Yayar tawa. Shiyyasa Hafizzullah ke cewa da kece Mamanmu da mun shiga uku”. Dariya na ƙyalƙyale da shi. Na ce, “Masherancine yaron nan ai. Dan ALLAH Yaya weekend ɗin nan muje mu gansa tunda wancan ya shuɗe. ALLAH ina kewarsa”. “Karki damu zamuje in sha ALLAHU. Dan na kammala masa ma siyayyarsa.” Cike da farin ciki nace “Yauwa Yayanmu, kuma Babanmu. Yanzu dai yaya mi kacema Abban?”. Sai da yay murmushi ya ce, “Mizan ce masa kuwa Samraah. Na gaya masa kuɗin dana bama Mom ɗin jiya ne kaɗai dama a wajena, sai abinda ya rage baifi saura dubu arba'in ba nama cire wani abu a ciki na haɗama Hafizzullah provision. Dama na tara wancan kuɗinne dan na basa shi da Mom ɗin su rage hidimar biki. Ga kuma abinda ya faru yanzu. Ina gaya miki sai kawai ya hauni da faɗa. Wai to wlhy sai nasan inda zan nemo wasu kuwa. Dan shi dai baida wani kuɗin yin hidimar nan bai kuma da hanyar samunsu. Inba hakaba kuwa sai dai a kaiki gidan mijin a haka.. inada yake shiga dai bata nan yake fita ba.” Wata shegiyar dariya na bushe da ita harda kwanciya ina hawaye. Yaya Musaddiq kuwa yay sagale yana kallona. Sai da yaga dariyar tawa ta tasamma ta hauka sannan ya ce, “Samraah kin samu motsuwar kai ne?”. “Babu wani motsuwar kai wlhy Yaya. Show ɗin ne yay matuƙar burgeni. Su Abba an lallaɓo aci banza. Banza bata samu ba, shine ya ƙare da borin kunya. To waye ya faɗa masa na damu a kaini da kayan ɗaki? Ko cokali ma kada su saya waye zaiji kunya”. “Shirme maganinka ALLAH kenan”. Yaya Musaddiq ya faɗa yana girgiza kansa. Da sauri na ce, “Yaya gaskiya fa na faɗa. Ni wlhy ban damu ba amin kayan ɗaki ko a kar ayin. Badai muna son junanmu ni da Mansoor ɗina ba”. “Baki da kunya, a gabana kike cewa kuna son juna”. Hannu nasa na rufe fuskata ina dariya. Shima sai ya shiga tayani... Washe gari koda na kammala aikina na shirya na fito na samu Abba a falo na gaishesa bai amsa min ba. Ko'a kwalar rigata nai ficewata. Yaya ga ɗaukan muka wuce ina bashi labari ina dariya. Shi kam murmushi kawai yayi yace “ALLAH ya ƙyauta”. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya gidan Abba babu daɗi sai haƙurin UBANGIJI kawai. Yayinda a waje aiki ke caja kai kuma. Kamar yanda mukai shiri ranar asabar muka tafi Katsina ganin Hafizzullah. Ƙiri-ƙiri Mom ta nuna baƙin cikinta akan hakan. Ta shiga zuga Abba wai ya hanamu zuwa. Sai dai Yaya ya nuna musu babu abinda zai sakamu fasawar. Haka dai muka tafi Mom na banbaminta na rashin gaskiya. Hafizzullah yayi matuƙar farin ciki da ganinmu. Dan harda kukansa na murna. Ya rame saboda karatu, naita tsokanarsa nikuwa muna faɗanmu da muka saba. Tare da shi muka yini. Da zamu wuce masauki kuma ya bimu akan shi tare damu zai kwana. Nan ma raba dare mukai muna hira kafin su koma ɗakin Yaya Musaddiq su kwanta ni kuma nai kwanciyata ni kaɗai muka sha waya da Mansoor dake bani labarin an shirya komai tsaf gobe in sha ALLAHU za'a tsaida date. Jinai duk wani iri, amma a ƙasan raina ina farin ciki da hakan. Koba komai ai zan samu ƴancin kaina. Na kuma samawa ƴan uwana. Dan insha ALLAHU Hafizzullah gidana zai koma, Yaya kuwa zan cigaba da dagewa akan yay aure..........✍️ _Kandala ta malam Mansoor 😘_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_ ........Washe gari kamar yanda Mansoor ya faɗa muna a hanyar dawowa gida ya turamin saƙo na jerarrun kalaman godiya ga ALLAH. Tare da sanar min an tsaida wata ɗaya kacal, nanda kwana talatin in sha ALLAHU na zama mallakinsa. A gidansa zanyi azumin watan Ramadan. Duk da naji farin ciki ban maida masa reply ba, dan ina cikin mood mara daɗi na rabuwa da Hafizzullah. Shima mun barosa harda hawayensa. Munko samu gida cike da kayan sweet, biscuits da drinks a falo. Harda su goro sai akwatina guda biyu. Yanda babu wanda yay min magana akan kayan nima banma kowa ba. Sai auta ne ke faɗamin Uncle Mansoor ya gaya masa kayana ne. Sai kuma habaicin da Baby keta saki ranta a ɓace. A kallo ɗaya da nai mata kuma na fahimci tasha kuka. Ban kulata ba dan ba itace a gabana ba. Washe gari Monday na wuce aiki da wuri. Bayan mun dawo na tarar da Gwaggo Gudidi tazo daga Dawanau. Kakace a wajenmu, dan ƙanwar kakarmu ce, mahaifiyar su Abba da mamanmu kenan. Ba sosai take zuwa gidan ba saboda wulaƙancin da Mom ke musu. Mu kuma Abba baya barinmu zuwa wajenta, garama Yaya yanzu daya mallaki hankalin kansa yana zuwa abinsa. Yanzun ma shine ya kirata ya gaya mata komai ganin Abba baida niyyar saka danginsa ko ɗaya a batun auren nawa. Ƴan Gwarzo kuwa sun kwashi nasu kason kayan da za'a rabama mutane sun wuce dasu tun jiyan, dan bamu samesu ma a gidan ba. Nayi murna ƙwarai da ganin Gwaggo Gudidi. A take na shiga hidima da ita dan naga babu alamar ko abincin kirki ma an bata. Duk da hararar da Mom ke mun banbi takanta ba na shiga hidima da kakarmu. Bayan sallar isha'i kuma Yaya ya sayo mata kayan ƙwaɗayi yazo ga zauna muka sha hira. Dan dole Abba ma yazo ya zauna akayi da shi shima. Mom da ƴaƴanta kuwa kowa yay shigewarsa ɗaki sai Auta da uwar gulma Bibaa kawai a wajen. Bamu tashi a falon ba sai sha biyu. Abba ko tun sha ɗaya matarsa tazo ta tasashi suka shige ko kunyar Gwaggo Gudidi bata ji ba balle mu ƴaƴa. Shimfiɗata na barma Gwaggo, dan Yaya Musaddiq ya kawo mata babban bargonsa. Zan kwanta a ƙasa tace na hawo kan bargon. Badan naso hakan ba na hau dole. Sabuwar hira muka buɗe da ita har sai ɗaya sannan barci ya kwasheta. Niko alwala na tashi nayi nai nafilfilina kamar yanda na saba sannan na kwanta. Hakan kuma bai hanani tashi uku da rabi ba na shiga ayyukana. Kafin kace mi na kammala, dan har abinci naima Gwaggo na saka mata a kula nakai ɗaki dan nasan ba lallai da rana a bata na kirki ba. Gashi ban dawoba lokacin. Kalacin ma isashe na ɗiba mata. Itako tanata mitar yanda nake wannan uban aiki ga fitar safe kuma. Ni dai bance komai ba face murmushi kawai. Yau kam Yaya Musaddiq ya shigo gidan domin gaisheta. Ya ajiye mata kayan shayi da ƙaton bread ɗin ta harda soyayyan ƙwai. Albarka ta dinga saka mana sannan mukai mata sallama muka wuce dan kar mu makara. Gwaggo Gudidi itace ta raba komai na kayan sa ranar nan. Har maƙwafta sai da tasa Auta ya kai ma kowa gida-gida. Sannan dangin su ta ƙulla na kowa daki-daki. Wanda ke anan cikin Kano ta saka Yaya Musaddiq ya kaita ta kai ma kowa. Na Gwarzo ma tare sukaje takai duk na ɓangaren danginsu dai. Yaya Musaddiq ma da Hafizzullah ta ɗiba musu. Nima komai sai da ta ɗiba min. Hakama jama'ar gidan kowa da nashi. Kuma kowa zai iya rabama abokan arziƙinsa idan yaso. Amma sai Mom tai biris da nata anan falo har Gwaggo ta wuce bata ɗauke ba daga ita har ƴaƴanta. Abba dai ganin Gwaggon yasa shi zama ya ƙuƙƙula ya fita dasu wai zai rabama abokansa da ƴan wajen aikinsu. Ya raba ko bai raba ba oho masa. A ranar da nakai ma ƴan office ɗinmu kowa ya sake sanin alaƙata da Mansoor, dan wasu basu ɗauka gaske soyayya muke ba saboda yanda muke komai cikin taku. MD kuwa ai kamar zai mutu. Dan masifa yayta zubama kowa a wannan yinin babu gaira babu sabar. Har dai ƴan uwana ma'aikata suka fahimci kishi yake yi. Ni dariyama ya bani wlhy. Mansoor kam yaji daɗin abinda nayi, dan bai ɓoye ba sai da ya sanar min. Murmushi kawai na masa nidai. Bayan an tashi aiki ya buƙaci kaini naga aikin gida da ake ƙarasawa. Amma sai nace masa ba yau ba ya bari weekend zai fi. Shima ya yarda da shawarar tawa. Dan haka ya maidani gida. A ranar ne kuma na fahimci wata farar mota na binmu a baya. Duk da naji tsoro sai banyi magana ba, nace bari dai na tabbatar. Ganin munzo titin shiga layinmu motar ta wuce yasa na sauke ajiyar zuciya har Mansoor na kallona. “Lafiya irin wannan ajiyar zuciya haka kamar wadda nai shirin sacewa. Ko tsoro kike kada na wuce dake ne?”. “Ai kaima bazaka fara hakan ba sai an baka”. Na faɗa cikin kauda kai ina murmushi. Shima ƙaramar dariya yay da sake faɗin, “Hakane. Amma da zama a taimaka a banin yau zanfi kowa farin ciki. Maybe ma na ƙara samun ƙarfin aikin yanda ya kamata”. “Humm” kawai nace na buɗe motar na fice ina murmushi. Godiya na masa kamar kullum. Yanata son mu haɗa ido amma naƙi yarda da hakan. Sai ma na wuce da sauri na shige gida abina. Amma na maƙale jikin gate ina leƙansa. Yaja kusan minti ɗaya idonsa a gate ɗin fuskarsa da murmushi kafin ya tada motar ya wuce... ★★★ Abubuwa kullum ƙara tsamari suke a gidanmu. Dan kullum al'amarin Mom da yaranta gaba yake yi. Ina sake samun tsangwama da hantara fiye da baya a yanzu sakamakon wannan batun auren. Yayinda Baby ta fito da maitarta akan Mansoor yanzu. Shi kansa ya fara nuna min tana matsa masa. Ashe tun da can ma da bata fiddo abubuwanta fili game da shi akwai abinda take shakka daga garesa, na kuma fahimci wani babban sirrinta ne ya sani duk da yaƙi fitowa fili ya faɗa min. Sam ba'a wani shiri irin na aurar da ƴa a gidan, musamman ma mace da bikinta ke da yawan hidima. Ko kaɗan hakan baya damuna. Dan nasan Yaya Musaddiq tsaye yake akan al'amurina ta bayan fage. Dan yanzu kusan duk sati zakiga Gwaggo Gudidi tazo mana. Da alama akwai abinda sukeyi ita da Yayan. Duk da madai ashe shi Mansoor ya samu Yaya akan shi baya buƙatar komai na gida duk zai zuba. Ni shaidace akan abinda ya faɗa ɗin domin ya kaini naga gida. A randa mukaje ɗin kuma na sake kama motar nan na binmu. Hankalina ya tashi fiye da ranar, amma nai jarumtar dannewa saboda kada na tada hankalin kowa. Nayi kuma alƙawarin saka ido sosai dan na tabbatar shin da gasken binmu ake kokuwa zargina ne kawai. Tun daga wannan lokacin na saka ido fiye da koda yaushe. Babbar magana kenan wai ɗan sanda yaga gawar soja, nako tabbatar bibiyata akeyi ɗin. Dan harna haddace Number motar duk da dai mai ita kan canja ne kusan da kala uku, sannan ita kanta motar wani lokacin bada ita ake bina ba da napep ne. Al'amarin ƙuruciya irin nawa da wauta, maimakon na sanarma ko Yaya ne sai nai tunanin kada na tada masa da hankali, gara na fara sanin wanda ke bibiyar tawa dai. Wannan ɗammara dana ɗauka tasa na fara ƙin daina bin yaya na koma shiga napep. Hakama Mansoor wataran sai na ƙi biyosa, ina amfani da yanayin da yake ciki na busy yanzu akan shirin biki. A ranar farko dana fara yin ƙundun balar tarar motar nan sai aka gudu. Karo na biyu ma haka. Ganin haka na sake himma dan a ganina tsorona ake ji. A karo na uku na haɗa kai da ƴan ƙato da goran anguwarmu a ɓoye akan idan ma fita su bini a baya. Na basu numbers na motar da ake amfani da su har kala uku. Abin zai baku mamaki, dan kamar mai motar nan ya fahimci abinda nake ƙullawa ranar sai bai bini ba. Tsahon kwana uku haka na ƙara yarda yaji tsorone na sallami ƴan ƙato da goran. Sai me a randa na sallamesu a ranar na cigaba da ganin motar kuma. Raina yakai ƙololuwar ɓaci. Na fara zargin MD ne kemin hakan ko kuma Abba ko Mom ko Baby. Kai har Mansoor sai da na zarga, to sai dai kuma shi danmi zai sa a bibiyan bayan kullum muna tare. (Bincike) zuciyata ta ayyana min. Ban gamsuba, dan in bincikene ai iyayensa ne zasusa ai musu. Sannan bata wannan hanyar ba, anguwarmu zasu je. Amma duk da haka sai nace bari na gwada kowannensu. Da Baby da Mom na fara. Sai banga wata alamar hakan ba daga garesu. Shima Abba haka. Sai kawai na koma kan Mansoor. A randa na taresa da zancen ina magana cikin tsiwa kan basai fa yasa ana bibiyata ba zai san halina. Idan bincike yake son yi a kaina yazo ga ƴan anguwar dana tashi cikinsu tun ƙuruciya har girma mana. Amma sakawa ana bibiyata kamar son firgitar da ni ne. Tare da nuna rashin aminci a tsakanina da shi. Sagale yay yana kallona da mamaki, sai dai bai iya cewa komai ba harna fita a fusace. To ashe daga nan bai zame ko ina ba sai wajen Yaya Musaddiq suka tattauna akan hakan. Lokacin da Yaya Musaddiq ya dawo aiki yay kirana ɗakinsa.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_ _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚_ .......Da faɗa ya faramin tare da turkeni kan saina faɗa masa dalilina na jifan Mansoor ɗin da waɗan nan kalaman. Da farko naso dojewa. Amma ganin yanda ya birkicemin a yanayin da bai taɓa ba bamma san na saki layi ba na zayyane masa komai. Tashin hankali na gani sosai a tattare da shi. Ya sake balbaleni da faɗa cikin ruɗani. “Amma Samraah baki da hankali. Yanzu wannan abin na faruwa da ke tsahon sati biyu amma kika ja bakinki kikai shiru sai yanzune kike faɗa. Shima badan kunyi haka da Mansoor ɗin ba da bamu kamo bakin zaren ba. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un Samraah baki da wayo, wlhy sam baki da wayo. Dan tabbas bana raba ɗayan biyu mutumin nan ne yasa ake bibiyarki. Dolene ma ya gano kin ɗauki videon nan. Wannan abin shi nake gudu tun farko daman, shiyyasa kullum nake cikin tunanin mafita ashe nima nayi sakaci...” “Yaya ban gane ba. Wai kana nufin wancan mutumin mai ɗaure gashi Maashi yake komi ma oho masa”. “Idan bashi ba wanene Samraah. Tabbas dole shine zaisa a iya miki irin wannan bibiyar. Samraah kodai kinyi wani yunƙurine a kansa batare dana sani ba, dan na sanki da shegiyar wautar tsiya”. “Wlhy Yaya ni babu abinda nayi, kaima kasan kuma bazanyi komai ba sai da saninka. Ka tambayi Mansoor ALLAH ne shaidata shima shaidatane. Daga office bana zuwa ko'ina sai gidan nan. Weekend kuwa islamiyya ce kawai ko Malam Umaru zai tabbatar maka da hakan shima. Toni wanema yunƙuri zanyi tunda kunce nabar komai a hannunku. Wlhy ko video ɗin tunda na adanashi ban sake waiwayarsa ba balle ma na kalla har wani yaji ko ya gani. Hatta da Mansoor ranar yake cemin ALLAH ya kiyaye yana rage abubuwa ya goge video ɗin nan, da ace banda shi a wayata da an samu matsala. Amma dan ALLAH na sake adanashi kada nayi sakaci tunda na sanshi shi da goge-goge a waya na tsiya.” “Nasan baza'a samu matsala daga gareki ba Samraah. Amma dole mutumin nan yanada cctv camara ai, idan kuma mai yawan bibiyar abubuwane to tabbas anan ya gano shine yasa ake bibiyarki. Ko kuma wani ya ganki. Ina dai zuwa bari na kira Mansoor yazo ya same mu”. Ban iya cewa da shi komai ba. Sai faɗawa duniyar tunani kawai da nayi. Harya kammala wayar bamma sani ba. Cigaba yay da kai kawonsa alamar haɗa lissafin abubuwa. Cikin abinda baifi mintuna talatin ba sai ga Mansoor yazo. Kasancewar lokacin sallar isha'i yayi suka tafi massalaci. Sai da aka idar suka dawo ina ɗakin Yaya ɗin dai har sannan. Mansoor na gaida daga haka suka shiga tattaunawa danni gaba ɗaya zuciyata bata tare da gangar jikina. Sai da Mansoor yaymin tambayar ni da waye muka je restroom ɗin a ranar? Dan tambayace da ya kamata ma ace sun min tun a waccan ranar amma basu yi ba. Saida na sauke ajiyar zuciyar dawowa hayyaci sannan na sanar musu ɗaya daga cikin securitys ɗin da suka bada tsaro a ranar ce. Na sake maimaita musu yanda mukayi. Sun sake tambayata bayan ita ban haɗu da kowa ba? Sannan itama ɗin sanda ta tafi yin wayar bata dawo bane nemana?. “Eh gaskiya ni dai banga ta dawo ba, kasancewar ma hankalina ya tafi akan abinda ya faru ban sake bi takanta ba. Dan haka ban san miya hanata sake komawa ba. Kuma ni gaskiya bana jin nama sake ganinta har aka tashi”. Kallon juna Yaya da Mansoor sukai. Cikin ƙarfin hali da nuna tashin hankali Yaya Musaddiq ya ce, “Anya kuwa security ɗin nan bata koma ba a lokacin. Idan lissafina yayi dai-dai, ta koma domin su fito tare kamar yanda ta mata alƙawari, maybe bata sameta ba ta shiga nemanta, ko kuma ta sameta a lokacin da take bude-buɗen ƙofar ko ma ɗaukar video ɗin. Dan inba haka ba babu yanda za'ai tai ɓatan dabo gareta. Hasashe na biyu lokacin da take faɗa maka ko wani ya jiku. Cikin biyun nan dole ɗaya ya tabbata, kuma duk inda zancen ya fito to tabbas an samu Maash an fargar da shi komai shiyyasa yasa ake bibiyarta.” Cikin jinjina kai Mansoor ya ce, “Tabbas hasashen ka zai iya zama gaskiya Yaya. Amma ni a wannan gaɓar ma sai hankalina yaso rabuwa biyu akan wasu dalilai. Maash bawai ƙaramin mutum bane. Kana ganin ya aikata wannan kisan ya kuma san ya aikata har wata ace ta ɗaukesa a hoto mai motsi ya sani kuma ya zauna sakaci. Duk da yanda muke tunani abinda masu hannu da shuni ɗin nan suka tsana a rayuwarsu shine su binne wani laifinsu amma ya zama yana a hannun waninsu ko waninsu ya sani. Zakaga suna gaggawa wajen ganin sun daƙile komai. Idan lissafina yayi dai-dai wata fa kusan ɗaya kenan da faruwar komai. Kana ganin zai zaman ɓata lokacine akan wani bibiyar Samraah bayan yana da hanyoyi masu yawa dama zai karɓi video ɗin a hannunta batare da wata gargada ba. Karfa ka manta har hira yazo anyi da shi kuma itace tai da shi, randa aka saki hirar kuma ƙura ta tashi sosai da kace nace ɗin mutane harda masu cewa akwai alaƙa tsakaninta da shi, nasan dai kasan komai ba sai na sake maka bayani ba. Na kawo wannan hujjojin ne saboda bana son mu shagala da yawa a kan shine wanda kuma ke son ƙulla tsiyar na gefe. Kuyi haƙuri MD kansa na cikin zargina. Dan na jima da fahimtar yana son Samraah na hauka, randa kuma ta kai musu kayan saka bikin mu ya tabbatar ma da kowa hakan. Sai ƴar uwarku Baby. Tana sona matuƙa, wasu dalilai ne suke dakufeta, naji a majiya kai ƙarfi cewar tai alƙawarin sai tabi tako wace hanya domin ganin auren nan namu bai yiwu ba, dan tana da babban plan akan haka akwai kuma mai bata ƙwarin gwiwa ta bayan fage. Saboda yima kanta alwashin indai itama bazata sameni ba sai dai su rasa su duka. Da farko na ɗauki zancen shirme kawai irin nata na ƴan shaye-shaye, sai dai wannan abin na yanzu ya fara haskomin da gaske zata iya komai fa. Dan haka musa hankalinmu jikinmu domin tabbatar da ko wanene” “Shaye-shaye kuma? Wai babyn ce ke shaye-shaye ko wa?” na faɗa ina kafe Mansoor da idanu. Murmushi kawai ya mun da faɗin, “Hum Samraah kenan, ke dai ALLAH ya shirya mana zuri'a kawai”. Yaya na kalla a firgice, sai naga shi babu alamar mamakin zancen akan fuskarsa. Kasa haƙuri nayi sai da na ce, “Yaya kenan kaima kasan tana Shaye-shayen?”. Sai da ya sauke numfashi mai nauyi sannan ya furta, “Na sani Samraah. Na kumayi iya yina na ganin ta daina amma hakan ya gagara. Na lurar da Abba amma ya nuna sharri nake mata. Tun daga nan na tattarasu na watsar”. Zancen ya matuƙar girgizani gaskiya. Kamar yanda sosai maganar Mansoor tayi tasiri garemu ita game da MD da Baby da zasu iya sakawa a bibiyeni. Dan duk abinda ya faɗa gaskiya ne. Ni komai ma sai naji ya sake susuce min. Amma duk da haka Yaya yace bazamuyi sakaci da duka ɓangarorin uku ba. Zamu saka ido za kuma ku ɗauki matakin daya dace da kowanne. Dan haka zamu kai report wa yan sanda akan ana bibiyata, amma bazamuyi batun video ba fa, zamu bar ƴan sanda suyi aikinsu, idan ma Maash ɗinne da ga baya idan fito da videon ta kama sai muyi hakan. Nanma mun gamsu, kun kuma bashi goyen baya, duk da ni dai naso ace tun yanzu muka fidda video ma wa yan sanda. Amma ban san dalilinsu na son a ɓoye video ɗin nan kamar wani suna tsoronsa. Kwana biyu dayin haka aka kawo lefena da ga gidan su Mansoor. Akwatina har goma sha biyu shaƙe da kayan alfarma na gani na faɗa. Babu wanda zaice lefen nan bai birgesa ba. Sai dai anga tsagwaron hassada daga Mom dan ta kasa haɗiye komai. Harda zage-zagenta wai ai saurayin Baby ne na kwace da asiri. Kuma ba kowa ke kawo min asirin ba sai Gwaggo Gudidi. Abu kamar wasa dai sai da aka kwashi rigima. Dan ƴaƴan Gwaggo Gudidi duk sun zo suna gidan. Rikici akai sosai na gaske. Lokacin Yaya Musaddiq shi baya gida. Yana wajen aiki, kamar dai wancan karon ya damƙa komai hannun matar ogansa aima baƙi abincin tarba da kayan maƙulashe. A wajen aikin ma ba zama yay ba shi da Mansoor suka fita police station wajen batun ƴan sanda. Sun shigar da report tare da bada lambobin mota har uku dana basu.. Suna can har aka gama rikin nan kowa ya kama gabansa dan su Gwaggo ma sun ɗauke lefen nawa daga gidan sun wuce da shi can gidanta. Acewarsu barinsa gidan Abba bazai yiwu ba su Mom zasu iya salwantarwa saboda basu da isashen mutunci. Ashe ko hasashen su Gwaggo yay dai-dai. Dan su Mom sun shirya mummunan ƙudiri kuwa akan lefen nan aka ɓata musu shiri. Wannan yasa suka huce kaina sanda na dawo. Dan bana gidan ma ni ina gidan wata ƙawata ta islamiyya. Duk yanda naso daurewa na kasa. Ranar sai da nai kuka sosai da jin kewar iyayenmu. Daga ƙarshe nai alwala nayi nafilfilina tare da miƙama UBANGIJI kukana. Wannan ɓacin ran dana kwana da shi yasa banyi aikin komaiba a gidan. Sai ma shiri da nai tunda farar safiya domin wucewa gidan su Joy ko zan rage damuwa, amma zan ɗan fara zuwa office saboda saƙon da MD ya turamin jiya da dare kusan 12 kan dan ALLAH yana son ganina a office yau idan babu damuwa. Jin yace abu mai muhimmanci ne yasa na amince zanje ɗin, kuma bana ma son yinin gidanmu a yau ɗin sam. Na fito na leƙa ɗakin Yaya sai na samu ya fita. Nayi mamakin fitar tasa ta sassafe yau. Amma sai nai wucewata akan zan kirashi awaya. Zuwa da rana sai na samesa a garejin dan ina son mu ɗan tattauna wani abu. Napep na samu na shiga. Mun fara tafiya inata ƙoƙarin kiran numbern Yaya sai naji an kira sunana. Da mamaki na ɗago ina kallon wanda ke kusa da ni dana samu a napep ɗin, ganin babu wata alama data nuna shine yay kiran sunan nawa na kalla mai napep shima. Shima kuma babu alamar shi ɗin ne. Cikin takaici da jin haushi na sake ƙoƙarin maida kaina ina mamaki. Sai kuma aka sake faɗin, “Samraah!”. A fusace na ɗago yanzun kam. Kafin na samu damar cewa komai naji abu a fuskata. Yuuuu naji kaina ya fara mun. Cikin zabura nai yunƙurin dira daga napep ɗin sai dai na kasa hakan. Dan cikin ƙanƙanin lokaci jikina yay wani masifar nauyi na silale jikin kujera idanuna na lumshewa. Daga haka ban sake sanin mike faruwa ba kuma......✍️ _Duk da nasan Maash ya bada kwangilar bibiyar Samraah. Amma nima zancen Mansoor ya fara sakani a cikin ruɗani. Amma bana son ku ruɗe kumuje zuwa dai, dan har yanzu fa wasan ma bai fara ba. Yaya Maash ne da wannan aika-aikar ko kuwa MD? Zai iya zama Baby ma fa. Kai Mom ma ba barinta zamuyi ba. Shin waye yay kidnapping Sam-G🤥🤔?._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_ ......Tunda suka tashi Mom taga Samraah batai aikin komai a gidan ba ta ƙara harzuƙa. Lallai yau dolene taci uban yarinyar nan dai-dai gwargwado har sai taga ubanda ya tsaya mata a gidan nan. Fuuu ta nufi ɗakin barcinsu tunda tasan yau weekend bata fita aiki. Sai dai me wayam babu Samraah. Sai auta da Bibaa dake barci. Da farko tai tunanin tana wanka. Dan haka ta koma falo tai zaman bala'i tana jira. Bayan kamar mintuna goma sai ga Bibaa ta fito tana miƙa da alama tashinta kenan. “K koma ko kiramin yarinyar nan Samraah”. Da ɗan mamaki Bibaa ta ce, “Ai bata ɗaki Mom.” “K ban san iskanci ki duba toilet mana ina zata je”. “ALLAH Mom bata toilet yanzu fa na shiga bayin na fito. Kodai tana kitchen tana aiki?”. A ɗan ƙufule Mom ta ce, “Tunda ni makwauniya ce ko. Dalla fita nasan tana ɗakin shegen can shima munafukin na biyu. Jeki daga shi har ita ki kira min su”. Babu musu Bibaa ta amsa da to. Sai dai babu jimawa sai gata ta dawo wai ɗakin a kulle yake. Dai-dai nan Abba ke fitowa da ga ɗakinsa. Tambayar mike faruwa yayi dan tun ɗazun yake joyo hargagin Mom da ga cikin ɗaki. Aiko a cikin tsantsar masifa take sanar masa. Ɗan jimm yay kamar ba zai ce komai ba. Sai kuma ya zaro wayarsa a aljihu ya shiga neman Yaya Musaddiq. Bugu biyu kuwa ya ɗauka. Daga can ya gaida Abban cikin girmamawa. A daƙile ya amsa masa kamar yanda ya saba. Kafin ya ɗora da faɗin, “Kai kuna ina ne?”. Da mamaki Musaddiq ya ce, “Abba ina gareji. Akwai wanda zai zo ya ɗauka motarsa ne shiyyasa na fita da wuri”. “Uhhmyim ita Samraahn tana tare da kai kenan?”. “Samraah kuma Abba. Ni kam mi zaisa na taho da Samraah nan. Tana nan a gida ai na barta tunda yau bazata je aiki ba”. A harzuƙe Abba ya ce, “To bata nan”. Sosai zuciyar Musaddiq ta wani harba. Muryarsa na nuna alamar rawa ya ce, “Abba kamar ya bata nan. Ina Samraah zata je da sassafen nan bayan bata da office yau?”. “Sai ka tambayen tunda yawo nake da ita a bayana”. Daga haka Abba ya yanke wayarsa. Hankalin Musaddiq yay masifar tashi batare da yasan dalili ba, tunda ta saba duk inda zata ko baya gida sai ta kiransa ta sanar masa a waya. Dan haka babu arziƙi ya baro gareji da fatan ya zo ya samu Samraah ta dawo. Dan tunda Abba ya katse wayarsa ya maida akalar kiran kan Samraahn amma wayar na shiga anƙi a ɗauka. Daga baya ma aka kasheta duka baki ɗaya. Wannan kuma ba halin Kandalarsa bane ba, balle ma ace shine yay kiranta da kansa... Cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gidan, inda ya samu har lokacin Mum nata masifarta. Al'amarin kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai har sha biyun rana babu wani bayanin Samraah. Tun kowa na ɗaukar komai wasa har la'asar babu wani bayani. Zuwa lokacin anata buge-bugen waya wa ƴan uwa amma kowa sai yace bata je ba. Hakama ƙawayenta duk da Musaddiq yasan ita bamai yawan biye-biyen gidajen ƙawaye bace, ƴan uwan ma wace ala cika. Har gidan su Mansoor an sani zuwa sannan. Zuwa kusan biyar na yamma sai ga ɗayar wayarta an samu, wanda ya ɗaga ya tabbatar musu tsinta yayi. Harga ALLAH kuma ya yarda zai basu ne saboda yaga hoton Samraah ne a fuskar wayar. Hankali tashe Mansoor da Musaddiq sukaje inda ya kwantata yake, dan su ne dai keta faɗi tashin. Su Mom sunce basu yarda wani abune ya sameta ba sai dai idan yawon tazubar ɗin data saba tafiya ne ta tafi. Dan haka sukai burus da komai kamar basu san mima ake ba. Garama Abba yakan yi ɗan zugumm alamar tunani. Da Mom ta tsikaresa da hira kuma sai ya ware. Mansoor da Musaddiq sun amso waya tare da mask ɗin Samraah da eyeglasses ɗinta da aka tsinta. Ya kuma kaisu inda ya tsinta ɗin mutane kuma da yawa sun bada shedar tsintar yayi da gaske. Dan abun ya faru ne a idon mutane kusan uku dake sana'a a dai-dai wajen. Kasancewar suna fitowa da safe sosai suma. Sai dai sunce sunga wata napep da mota blue sun tsaya a wajen amma basu san mi sukayi ba, sai da suka wuce ne wanda ya tsinta wayar yake ganin abinda ya tsinta ɗin. Kuma yay magana da su bai ɓoye ba. Zuwa yanzu kam hankalinsu yakai ƙololiwar tashi, dan haka take suka kai report a station mafi kusa. Dalilin Mansoor nada ɗan halinsa tun a lokacin aka shiga traicing ɗayan layin Samraah. Dan kuwa wayoyinta biyu ne, kuma duk manya ne. Ɗaya tana amfani da ita saboda aiki, ɗaya kuma abinda ya shafi family ɗinta da ƴan abubuwanta ne a ciki. To ta aikin aka ajiye aka tafi da waccan. Har dare babu wani cikakken inpometion mai gamsarwa, zuwa sannan kuma dai tashin hankalin Abba ya fito fili. Dan Gwaggo Gudidi tazo tana faman kuka da faɗin lallai a binciki su Mom sun san inda suka ɓoye Samraah. Tunda kowa yaji dama abinda Mom ɗin ke faɗa a jiya gaban kowa. Mom zata hayayyaƙo maƙwafta da suka shishshigo suma suka nuna lallai akwai ƙamshin gaskiya a batun Gwaggo Gudidin. Kamar wasa kuwa sai ga rikici ya ɓarke. Dan zuwa gab da magrib su Musaddiq suka zo anguwar da ƴan sanda. Nanfa hankalin Mom yaso ya fara tashi, sai dai tana ta ƙoƙarin dannewa ita a dole kada aga gazawarta.. Tambayoyi ƴan sanda suka musu har Auta ba'a bari ba. Mum kamar a ruɗe take amsa komai, dan haka ɗan sandan da case ɗin ke hannunsa ya dasa mata ayar tambaya. Sai dai bai ce komai ba suka wuce akan zuwa safiya zasu iya dawowa kosu nemesu a can station ɗin su. 💫 (✧✧)✨(✧✧)✨(✧✧)💫 Sannu a hankali na motsa idanuna da sukai min matuƙar nauyi da ɗaurewa. Sai kuma na shiga buɗesu sannu-sannu, a wani ɗaki mai ƙarancin haske na tsinta kaina alamar yamma tayi. Dan kiraye-kirayen sallar magrib ma naketa jiyowa. Ƙirjina ne yay wata masifar bugawa. Nai saurin ambaton ALLAH ina sake lumshe idanuna da sake buɗewa. Tabbas ta tabbata anyi kidnapping ɗina. Da ƙyar na iya tashi kasancewar duk jikin nawa babu wani ƙarfi. Ga wani irin fitsari da nake ji. Jiri-jiri dake neman kwasata yasa da ƙyar na iya dafe bango na miƙe. Lalube na shigayi ko zan samu wani haske. Cikin ikon ALLAH na samu makunar fitila. Idanuna dake lumshewa da buɗewa na sake warewa da ƙyau. Ɗakine babba sosai. Sai katifa a ƙasa ƙarama irin ta ƴan makaranta, akwai bargo da filo an kuma shimfiɗa bedsheet a kanta. Gefe kuma handbag ɗina ce sai leda mai tambarin gidan abinci har guda biyu a kusa da ita. Tare da ledar ruwa guda. Da ƙyar na iya jan ƙafata zuwa ƙofa. Na shiga ƙoƙarin murɗawa amma sai na sameta rufe gam. Inda labule yake ma sake nufa da ƙyar dan nasan bazai wuce window ba, na turesu da ƙyar. Ita ɗince kuwa, sai dai a rufe, nai ƙoƙarin na buɗe da ƙyar. Amma ƙarfen da akai adonta da shi ƙanana ne sosai ta yanda ko hannu bazai fita ba ma. Sosai zuciyata ke rawa yanzun kam. Ban haƙuraba na sake nufar ɗayar, nan ɗin ma dai irinta ce. Inda ke da kamar ɗan corridor na nufa, amma sai na samu ƙofar bayi ce a wajen. Naga hakanne sakamakon buɗewa da nai. Bamma san sanda na silale a wajen ba na saki wani irin kuka mai tsuma rai da girgiza zuciya. Na jima zaune a wajen ina kuka kamar numfashina zai rabu da gangar jikina. Kafin na sake miƙewa da ƙyar na shiga toilet ɗin. Fes yake babu wani datti. An kuma ajiye wadataccen sabulun wanka, omo, toothpaste brush, sosan wanka. Kai harda kayan wanke bayi. Babu dai abinda zaka nema ka rasa daya shafi hakan. Alwala na ɗaura batare da nabi takansu ba, zuba ruwan alwalar a jikina ya ƙara taimakawa naji na ɗan warware. Anan ma sai da na duba window sai dai yayi sama sosai koma ƙarami ne. Haka na fito na dawo ɗakin. A saman tabarma dake gaban katifar malale nai sallar azhar da la'asar har magrib. Sake kife kaina nai a wajen na sake buɗe sabon shafin kuka. Nama rasa ina zan kai tunani na. Kamar wadda aka zaburar na zabura inda bag ɗina take. Da sauri na buɗeta na shiga laluben wayata jikina har wani mazari yake tsabar yanda nake a ruɗe. Ganin kamar laluben ma baya min kawai na zazzage komai na cikinta burina kawai wayata ya faɗo, amma babu ita babu alamarta, sai ƴan kayan shafana dana zuba lips gloss ne kuma da fauda sai ƙaramin oil misk da face mask guda biyu da bana rabo da ita a jaka akoda yaushe. Bamma san na sake sakin wani wahallen kuka ba a wajen tare da zubewa ƙasa daga ni har bag ɗin........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_ .......Kusan mintuna biyu ina zabga kuka, kafin na sake jawo jakar da tarkacen ciki dana juye ƙasa duka zuwa gabana. Sake zazzagawa na koma yi kamar wadda ta zautu. Ko abinda keda alaƙa da waya babu a cikin duka wayoyina biyu. Amma na kasa yarda, sai ƙara zazzagawa nake da ɗaɗɗaga kayan dana zazzage kamar wata mai neman barimar ɗan kunne. Sai da dai zuciyata ta tursasani akan babu ɗin da gaske sannan na sake fashewa da kuka tare da yin wurgi da jakar. Haka na kasance a wannan daren babu wata nutsuwa irin ta cikakken mai hankali a tare da ni. Sai dai koda wasa ban mance ambaton UBANGIJINA ba. Gab da asubahi wani wahalallen barci yay awon gaba dani, ban tashi farkawa ba sai kusan bakwai da kwata. A firgice na miƙe na nufi toilet na ɗauro alwala. Bayan nazo na gabatar da salla koda na idar a wajen na cigaba da zama na fara karatun Alkur'ani a hankali jikina duk babu ƙarfi, dan akwai yunwa ma tare dani, jiya gaba ɗaya banci ba ban sha ba. Nafi awa ɗaya da kusan rabi a wajen naji ana ƙoƙarin buɗe ƙofa. A zabure na ɗago daga cusa kaina da nai cikin ƙafafuna dan a haka nake karatun. Kallo ɗaya mai shigowar yamun ya ɗauke kansa, yana sanye da mask baƙi kamar yanda komai na jikinsa ke baƙi, dan hatta hannunsa akwai safar hannu baƙa. Ya kuma toshe idanunsa na baƙin eyeglasses da babu abinda zan iya ganewa ko gani nashi. Irin ledar dake ajiye a ɗakin ce a hannunsa. Batare da ya tankamin ba ya ajiye ya ɗauki ta jiya dako kallonta banyi ba ya nufi hanyar fita abinsa. Muryata na rawa nai saurin dakatar dashi ta hanyar faɗin, “Wanene kai? Miyasa kuka kawoni nan? Mi kike buƙata da ga gareni? Wani laifi na muku ko kuɗin fansa kuke nema?”. Duk da ya tsaya cak tun fara maganata bai juyo ba. Ina kammala faɗa kuma bai tanka ba ya buɗe ƙofar ya fice tare da sake kulleni ta baya. Ido kawai na zubama ƙofar wasu kalar hawaye na gangaro min da gudun tsiya. Lallai ina a tsaka mai wuya, gashi bamma san wanda zan iya zarga ba. Dan gaskiyar Mansoor ne. A wannan gaɓar hatta da Baby da MD kai har Mom da Abba kansa ni zasu iya shiga lissafina ma. To amma ni abinda ke damuna waɗan nan mutanen da duk na lissafo idan sunyi hakan gareni duk miye ribarsu? A yanzu ba kaina kawai nake tausayi ba ƴan uwana da halin da zasu shigane ke matuƙar tada min hankali fiye da komai. Ga Mansoor shima. “Ya rabbi ina roƙonka da sunayenka ƙyawawa masu tsarki ka kuɓutar dani da gaggawa. Kasa kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya a zukatan ƴan uwana da masoyana da ni kaina. Duk wanda bashi da laifi akan wannan al'amarin ya ALLAH ka hanashi shiga wahala. Mai hannu a ciki UBANGIJINA ka hanashi damar cutar dani koda yayi niyyar hakan a gareni”. Zamewa nai a hankali na sake kwanciya ina mai cigaba da karatun Alqur'ani na. A haka barci ɓarawo yay awan gaba dani tunda dama bai isheni ba. Ga kaina na wani kalar masifaffen ciwo. Barci nayi sosai, dan ban tashi farkawa ba sai da naji ƙarar an buɗe ƙofa. Firgigit na miƙe kuwa ina murza ido. Mutumin ɗazu ne dai kuma kamar ɗazun fuskar tasa a rufe. Wata ledar abincin ya sake ajiye min da wata babba fara ita kuma yanzu ma ya sake ficeewarsa batare da yamun magana ba ya sake kullenin. Kwata-kwata yanzu ma hawayen nawa sun kasa fitowa. Da alama zuciyar ta fara dakewa. Salloli da nake jiyowa anatayi a masallatai yasa na miƙe a hankali. Jikina sai ciwo yake tako ina. Na tabbatar harda rashin wanka dan ni mutum ce mai son yawan wanka a rayuwa. Kuma ko yaya idan banyi ba sai na dinga jin babu daɗi. Naso na daure kada nayi, kamar yanda nake ƙoƙarin hana kaina cin komai, dan ko ruwa sai a wajen alwala nake ɗan haɗiyarsa. Amma na kasa hakan dan wani ƙyanƙyamin kaina nama fara ji, harma zuciyata na wasi-wasi akan yin salla da su. Ledar kayan na janyo na shiga fiddosu. Dogayen riguna ne har biyar duk marasa nauyi da bazasu takurani ba. Sai hijjab biyu manya. Harda su b&p shidda-shidda. Sai kayan barci har uku da man shafawa da turare. (Ko wanene wannan anyi cikakken ɗan iska ma wlhy. Wato komai anyisa akan shirine, babu kuma alamar zan bar nan ɗin a kusa tunda harda tanadin kayan sakawa). Duk a zuciya nake wannan tunanin. Cikin jin ban aminta da ɗakin ba na ɗauka doguwar riga ɗaya da b&p na shiga toilet. Wanka nayi da ruwa masu ɗumi dan akwai hitter a toilet ɗin. Sai naji jikina ya rage nauyi, hakama zuciyata. Na ɗan ji ƙarfi da nutsuwa har ƙwaƙwalwa ta na iya sarrafa tunani yanda ya kamata. Brush shima nayi na ɗauro alwala na sake fitowa. Banbi takan mai da abinci ba na koma na kwanta a katifar na lumshe idanu kawai ina mai faɗawa duniyar tunani..... ✨💞✨💞✨💞✨ Zuwa safiya labari ya fara karaɗe gari da social media. Abinka da sananniya musamman ma a watanni biyun nan da sunanta yay amsa kuwwa a lungu da saƙo sakamakon abinda ya faru a wajen taron buɗe Companyn Maash da kuma hirar da tai da shi. Ta wani ɓangaren kuma wanda basa harkar yanar gizo sun santa ne a dalilin shirin da take gabatarwa ta hanyar rediyo. Duk wani wanda ke a office ɗinsu hankalinsa a tashe yake. Musamman ma MD da ƴan sanda suka gano shine mutum na ƙarshe daya tura mata text message akan yana son ganinta. Dan haka a ranar Monday ɗin ƴan sandan suka gayyacesa office ɗin su. Gefe kuma gasu Mom suma an tattare zuwa station saboda abinda sukaita faɗa a randa aka kawo lefen Samraah, ga kuma rikicin da suka sake yi a daren bayan mutane sun watse maƙwafta da suka ji komai sun faɗa da sake tabbatar da anyi hakan. ALLAH sarki Mansoor da Musaddiq sai su baka tausayi. Dan kwana ɗaya kacal duk sun fita hayyacinsu. Hafizzullah ma a ranar Monday ɗin ya tsallako karatunsa ya nufo Kano.. Shigar mahaifin Mansoor a zancen ya saka ƴan sanda sake ɗaukarsa da girma. Dan a yanzu D.c.o ɗin ne ma da kansa yake gudanar da binciken. A yau har Attahir ma Yayan Mansoor ba'a bari a baya ba, dan shima dai yana a station ɗin anata ɗan kai kawo dai akan batun... Al'amari kamar wasa akan ɓatan Samraah ƙaramar magana na neman zama babba. Dan ƴan sanda sun matuƙar takurama MD da Baby da Mansoor ya tabbatar da yana zargi. Sannan wani mai shago a anguwarsu ya tabbatar da yaga sanda Samraah ta tare napep ta shiga, dan har gaida shi ma tayi kamar yanda ta saba. Ya kuma tabbatar da zai iya gane napep ɗin dan har number ɗinta da tambarin dake jikinta ya riƙe saboda mai napep ɗin ya jima tsaye a ɗan nesa da shagonsa shi yama yi zaton ko wani yake jira a wajen. Sai can ya maida hankali ga sallamar mutane sai ga Samraah. Lokacin da take gaishesa tabbas ya ɗago ya kalleta yaga tana ƙoƙarin tsaida Napep. Sai dai bai ga mai shirin ɗaukar tata ba har sai da ta shiga ciki. Mai napep ɗin ma yaja sun fara tafiya, ya ɗan zabure da nufin tsaidasu dan hankalinsa yaji bai kwanta ba amma har sun wuce. Sai kawai ya bisu da addu'a tunda bawai yasan gaibu bane, kuma yaga bayan ita akwai wani kamar ma a ciki. Bayanin mai shagon nan yayi matuƙar yima ƴan sanda da duk wani masoyin Samraah daɗi. Dan koba komai an fara kama bakin zaren. Sakamakon kamar yanda mai shagon nan ya faɗi tambarin dake jikin napep ɗin nan haka mutanen da aka ajiye wayarta a inda suke suma suka maimaita dan tambari bai kamata a manta da shi ba. Wannan yasa duk wani masoyinta buɗe idonsa tarwai akan lura da shigi da ficin masu napep duk da kuwa kamar banza suke a Kano dan yawa. A ta gefen jami'an tsaro kuwa kai tsaye ofishin shugaban masu kula da ƴan napep suka je. Inda suka bada report akan napep ɗin da mai tuƙata. A take kuma babu ɓata lokaci aka shiga bincikenta. Abinka da komai a tsare a yinin ranar sai da aka gane wanda ke tuƙa napep ɗin. Tuni ƴan sanda suka saka aka cikuykuyosa shi da napep ɗin tasa. Inda wanda suka gani suka tabbatar da ita ɗin ce kuwa. Sai dai basu da tabbacin shine a ciki ko ba shine ba. Amma tabbas dai napep itace. Kasancewar dare yayi ba'a wani tuhumi mai napep ba a ranar sai washe gari da Samraah ke cika kwanaki uku kenan. Sai dai me, a yayin tuhumar mai napep yayi rantsuwa ya ƙara kan shi bai san komai ba. Hasalima a ranar napep ɗin ba'a wajensa ma ta kwana ba. Ya bama wani abokinsa da yamma akan zai yi aiki ya ɗan samu nashi har zuwa dare sai ya dawo masa da ita. To bai dawo masan da ita ba sai washe gari kusan takwas dan har sukai faɗa ma saboda ya karya masa alƙawari, ga shi shi kuma yana fita aikin wurine amma ranar yasa ya makara........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ ......D.c.o ya tura yaransa neman abokin mai napep, sai dai an samu wai baya nan yayi tafiya. Wannan dalilin yasa sukace zasu cigaba da riƙesa har sai an kamo abokin nasa. Hankalin ƴan uwansa ya tashi kamar yanda shima nashi ke a tashe. Amma dai d.c.o yaƙi saurarensu. Dan ya tabbatar musu da yana akan aikinsa ne. Babu yanda zasuyi dole suka haƙura suka tafi. A ɓangaren ƴan media suna nan suna cigaba da tattauna batun ɓatan Samraah. Yayinda hotunanta ke yawo lungu da saƙo kowa na faɗin abinda fahimtarsa ta bashi. Dan wasu har suna danganta komai da cewar ita ta jama kanta. Dama taya zata taɓa irinsu Maash tace zata zauna lafiya. Ai gashi nan ya mata lunbu-lunbu da ga ƙarshe ya ruftata dan mawuyacine ace bashine ya saka aka kwamusheta ba. Musamman in akai dubi da yanda ta samu damar tattaunawa da shi ta yanda manyan ƴan jarida suka daɗe suna fatan haka amma basu samu ba. Wasu ko na ganin wani ne ya saceta dan kawai a ƙullama Maash sharri. Wasu na ganin ko dai MD ɗin nasu ne musamman yanda zancen son da yake mata ya karaɗe ko'ina, ga shi kuma an saka mata ranar aure da ya rage saura sati uku kacal. Wasu dai kuma zarginsu na akan Maash ɗinne dai da tunanin son da yake mata ne ya sashi aikata hakan ganin an saka mata ranar aure da waninsa. Hakama wasu zarginsu bai bar kan Baby ba itama jin TAKUN SAƘAR dake tsakaninta da Samraah ɗin akan Mansoor ba, hakama mahaifiyarta da tun fil azal ba son su Samraah ɗin take ba. Ga kuma abinda tayi a randa aka kai lefe. Kai hatta da abokan huɗɗar Mansoor ɗin wasu a ciki sun shigo zargin jama'a. Tawani fannin kuma akance maƙiyane kawai ko kidnappers ne kawai saboda yanda sunan Samraah ɗin ya samu ɗaukaka cikin ƙanƙanin lokaci game da shirin da take akan matasa da yanda take nuna illar lalacewar matasa a cikin al'umma. Kaso marasa ƙarfi kuwa na ganin adai bunciki sauran samarin Samraah suma dan zasu iya aikata komai ganin Mansoor na shirin wuff da ita, ko kuma shi ƴammatan Mansoor ɗin. Kai zance ne dai gashi nan kala da iri harda wanda ma bashi da ma'ana. Kamar wasa a haka sati ɗaya ta shuɗe ana fakon abokin mai napep. Ba'a samu damar damƙosa ba kuwa sai a randa take cika kwanaki tara ciff. ★ “Kidnapping kuma? Ni wlhy yallaɓai bani bane. Mizai sa nai kidnapping mutum? Idan na ɗauketa ma ina zan kaita?”. Cikin tsawa yaron d.c.o dake tuhumar tasa ya ce, “Kai karka raina mana hankali. In ba kai bane ba to waye bayan abokinka ya tabbatar da kai ya bama key ɗin napep ɗin tasa? Kuma da ita aka ɗauketa daga nan ba'a sake jin labarinta ba har yanzu”. “Tabbas ni ya bamawa yallaɓai. Kuma ba ranar muka fara yin haka da shi ba. Saboda nima lokacin da nake da napep ɗin nakan bashi. Hasalima nine na koya masa tuƙinta, da taimakona kuma aka bashi napep ɗin ma a office ɗin mu. Amma wlhy ni banyi kidnapping kowa ba”. “Ƙarya kake yi kai ne. Tunda har ka iya barin gari sai yau kake dawowa a tunaninka komai ya lafa ko”. “Ranka ya daɗe ni ban bar gari dan komai ba wlhy. Ƙauyenmu naje da yake ina noma duk shekara. Shine na je nakai taki gonata. Can ɗin babu network shiyyasa wlhy bamma san mike faruwa ba. Sai yanzu da nake ji ma a bakinka. Amma na tuna wani abu, idan ban manta ba da safe abokinmu da shima mukanyi irin haka da shi yazo yace na ara masa key ɗin keken Salisu zai amso saƙo a tasha, tasa na gareji sai azhar zai amso.” Da sauri ɗan sandan ya ce, “Ka tabbata?”. “Tabbas anyi haka ranka ya daɗe. Dan ƙanina ma na ɗakin a gabansa akai komai. Yaje kusan awa biyu sai gashi ya dawo ya kawomin yay godiya. Har ma naji haushi saboda ya saɓa lokacin daya dace ace na maidawa Salisu kasancewar yana fitar sassafe shi”. “Yanzu ina zamu samesa?”. “Anguwarmu ɗaya da shi, sai dai ta bayan layinmu gidansu yake. Shima kuma yana harkar adaidaitan, nasan yanzu baza'a iya samunsa a gida ba sai irin takwas haka ko bayan magriba gaskiya”. “Karka damu zamu samoshi”. Ɗan sandan ya faɗa yana miƙewa. Kai tsaye office ɗin d.c.o ya nufa. Bayanin da yaron ya masa duk ya maimaita masa. Goyon baya d.c.o ya bashi akan su tabbatar sun samo wancan yaron kafin zuwa safiya. Ya tabbatar masa da in sha ALLAHU za'ai hakan kafin ya bashi damar fita. Cikin girmamawa yay salute ɗinsa sannan ya fice. Shiru kawai d.c.o yay yana mamakin wannan irin juya-juya. Dan case ɗin gaba ɗaya ya ɗauki zafi saboda yanda mutane keta ka-ce-na-ce akan batun yarinyar, shi kansa yanda yaga an ɗauki al'amarin nata da muhimmanci ya sashi bibiyar shirye-shiryenta na baya a daren jiya, tare da shafukanta na sada zumunta dake ɗauke da fallowers masu yawan gaske, sai yaji ta shiga ransa. Gata dai ƴar yarinya amma akwai kaifin basira da nuna kwazo akan aikinta. Ga mahaifin Mansoor da Mansoor ɗin sun addabama rayuwarsu. Kowane motsinsu yanzu yana a station ɗinsu ne. Azalzalar su kawai suke faman yi akan a gano musu inda Samraah ɗinsu take su dai. Hakama Yaya Musaddiq idan ka kallesa sai ya baka tausayi, rashin dauriya kawai Mansoor ya fisa. Shiko Hafizzullah sai dai kuka. Yayinda jikin Abba ya fara sanyi, sai dai yaƙi yarda ya nuna hakan ga mutane saboda shakkar Mom.. ⭐❤️⭐❤️⭐❤️⭐❤️⭐ Faɗa muku yanayin da nake ciki a kwanaki tara ɗin nan da suka gabata sam bazai yiwu ba. Dan koda da kwatance nace zanyi hakan bai zama lallai ku iya fahimtata yanda ya kamata ba. Abinda kawai nake so ku fahimta al'amarin sam bashi da sauƙi. Nayi kuka matuƙa Bily. Irin wanda ni kaina sai da na tabbatar da nayi sa. Sai dai ku sani badan kaina nake yinsa ba. Domin ƴan uwana biyu ne da nasan zasu fi kowa shiga tashin hankali ne. Sai kuma masoyina da ya rage saura kwanaki goma sha uku kacal ya amsa sunan mijina. Dai-dai da daƙiƙa ɗaya ban gaza wajen miƙama UBANGIJI kukana akan ya kuɓutar dani daga wannan ƙangi, ya sa ina da rabon komawa ga dangina. Bani da wani ƙarfin nuna yunƙurina saboda halin rashin lafiya da nake ciki. Ciwon kai da zazzaɓi sun kasa barina. Na kuma gagara faɗama wanda ke zaryar ajiyemin abincina da har yanzu bai taɓa min magana ba, ban kuma taɓa ganin fuskarsa ba. Sai a yau da safe kusan goma da rabi sai gashi ya shigo. Nayi mamakin shigowar tasa saboda ba lokacin kawo min abinci bane, kuma baya shigowa dama sai zai kawo abincin. Amma ganin waya a kunnesa yasa na zuba masa manyan idanuna. Har gabana ya ƙaraso, batare da yamun magana ba ya tsaya ƙiƙam a kaina kamar wani mai gadin gidan kallon kwallo. Wayar dake a kunnensa ya sauke. Batare da yamun magana ba ya ajiyeta a ƙasa gabana. Na ɗago da nufin kallonsa maganar da akai cikin wayar ta katseni. Da sauri na maida kallona akan wayar, wata dattijuwar murya ce da nake ji kamar na taɓa saninta, cikin nuna ƙarfin iko da tabbatar da rashin wasa aka furta. “Nasan zuwa yanzu kin fahimci inda kike ba wajen wasan yara bane ba. Ba kuma filin ɗaukar rahoto bane ko dandalin sada zumunta. Baƙya buƙatar wani bayani kam dogo yanzu ƴammata. Sanin wanene ni? Miye dalili? Mi kika aikata duk bana buƙatar ji. Video recording ɗin hannunki kawai nake buƙata, mi zanyi da shi, ko minene alaƙata da shi ba damuwarki bane. Na duba a duk wayoyinki babu kin ciresa a ciki, ya rage naki faɗar inda yake ko wajen wanda yake a bani ke kuma ki kama gabanki. Idan kuma kikace zaki zama mai taurin kai tabbas zaki dawwama a wannan ɗakin tamkar kabarinki, dan ko mutuwa kikai a ciki zamu gina miki kabari mu bizne ki batare da wani mahaluki ya taɓa sanin hakan ba har abada. Kuma zan mallaki video ɗin sannan na ɓatar da duk wani ahalinki daga doron ƙasa. Zaɓi ya rage naki lokaci na tafiya miki dan nasan kina shirin zama amarya”. Ni kaina ban san sanda murmushi ya suɓuce min ba. A karan farko na wani ja numfashi mai nauyi tare da sakin wata siririyar dariyar ƙarfin hali. Kaina tsaye na nima na furta,........✍️ _Shin wa kuke tunani ne? Gashi dai Sam-G tace muryar Dattijo, kai nafa ruɗe nima. Amma mu haɗu a comment section ko wani zai canko mana🤔😞_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_ ........“Oh oh wannan irin dogon zance haka Baba, bakinka ko gajiya bayayi. Kayi haƙuri ina jin girman tsufarka a cikin raina duk da ba ganinka nake ba. Sai dai ga saƙo zan baka. Ka faɗama shi wanda ta aikokan shin tsoron Samraah Abdul-wahab Gwarzo yake ne? Ko kuwa shi bai cika namiji bane daya laɓe a bayan tsufarka a yimin barazana? To idan yana kusa da kai ya buɗe kunnuwansa da ƙyau ya saurareni, idan kuma baya kusa ka masa recording. Ni Samraah Abdul-wahab Gwarzo ban yi video ɗin dan aimun barazana na bada ba. Idan buƙatarsa yake mu haɗu gaban hukuma. Idan kuma yana da ƙarfi yazo muyi gaba-da-gabq kwanta. Sai dai ya sani ko dungurin wani da ga cikin ahalina yayi bazai sauke hannunsa ba video ɗin zai baza duniya. Dan haka zaɓi ya rage nashi, ku farka daga wannan nannauyan barcin na barku lafiya”. Da ga haka na yanke wayar tun kafin shi ya yanke. A fusace wanda ya kawo min wayar yake hararata. Amma nai biris da shi na ɗauke kaina. Kiran wayar aka sake yi, da sauri ya ɗauka ya kai kunne. Ban san mi aka faɗa masa ba na ga dai ya sake hararata ya juya ya fita. Nima da harar na raka nasa bayan ina taɓe baki. Da ga haka na zame na kwanta zuciyata na wata irin tafasa. Sai dai a wani gefen ina jin daɗi dan koba komai na samu bakin zaren wanda yasa aka kawoni nan. Zargin mutane da yawa ya fitamun a dai zuwa yanzun, musamman ma jama'ar gidanmu. Barcina na sha yau da rana sosai, dan yanzu bani da wani aiki sai inci in kwanta ɗin, sai idan naji na gaji ne da zaman waje ɗayan sosai nakan ta zagaye ɗakin wani lokacin ma na ɗan motsa jikina dai, saboda na fahimci na fara ƴar ƙiba ba kamar sanda aka kawoni da bana cin abinci ba sai yawan kuka. Ganin zan halaka kaina a banza nama masoyana asara yasa na fara cin abincin tunda nasan ban isa canja abinda yazo a littafin ƘADDARA ba ai. A yanayin ɗan ƙarfin jiki dana tashi da shi ya sani jin zan iya tunkaresa koda zai ƙarar da numfashi na, sai dai zan fara da wannan mai kawo min abincin a yau ɗin nan. Amma sai zuciyata ke gargaɗina da hakan kai tsaye, dan haka na shiryama raina wata sabuwar dabara ina kuma addu'ar cin nasarar hakan amma sai na gwada plan ɗin farko baiyi ba tukunna dai. Kamar ko yaushe cikin ƙarfin hali na tashi nai wanka da ruwan ɗumi. Kaya na saka na sake dawowa na kwanta a katifar dan jiri nake ji na neman ɗibata. Ina nan kwance tamkar mai barci naji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Luff na sake kwantawa har aka shigo aka sake maida ƙofar aka kulle. Sai da ya shigo tsakkiyar ɗakin sannan ya tsaya cak. Idanu na ɗan ƙara buɗewa ta can ƙasa yanda zan gansa da ƙyau. Ƙofar bayi yake kallo, nasan kuma dalilin yin hakan, dan kan shower ɗin na ɓalle nabar ruwa nata zuba. Ka ɗan naga ya duƙa yana kai yatsansa biyu ƙasa ya dangwala, sai kuma naga yay saurin ajiye ledar abincin hannunsa ya nufi toilet ɗin da alama ruwan ne ya fara fitowa. “Lafiya miya faru?”. Na faɗa a hankali. Bai tanka min ba, bai kuma tsaya ba. Na saki murmushi ina tashi zaune. Bayansa na bi. Duƙe na samesa yana ƙoƙarin buɗe hanyar da ruwa ke fita gaba ɗaya da ɗayan hannunsa. Ɗayan kuma ya danne pipe ɗin shower ɗin ya cusa babban yatsarsa a ciki ya tsayar da ruwan. Sai dai duk da haka yana ɗan fita sii. Da wannan damar nai amfani nima na shigo ina faɗin, “Tun ɗazu nake kiranka dan ka duba amma baka amsamin ba.” Kaɗan ya juyo ya kalleni sai kuma ya sake maida kansa ga abinda yake yi. Ni ko na duƙa kamar zan janye masa boket dana jiƙa kaya ciki na samu nasarar zare wayarsa. Da sauri na tusata cikin rigata. Na janye bokatin na fita abina. Sake komawa nai cikin katifar nai kwanciyata. Sai dai zuciyata sai faman gudu take a ƙirjina. ALLAH ALLAH nake ya zo ya fita kafin ya farga babu wayar tasa. Amma bai fiton ba sai kusan bayan minti goma. Batare daya kallan ba ya nufi hanyar fita. Cikin rawar jiki ina jin ya kulleni ta baya alamar ya tafi kenan. Na ciro wayar. Naji daɗin ganin babu password jiki, cikin rawar jiki data hannau na saka number Yaya Musaddiq na danna masa kira. Harta katse bai ɗauka ba. Hankalina ya sake tashi jikina har kakkarwa yake. Sake ƙoƙarin kira nake ina kallon ƙofar. Nan ma ta shiga amma har tana neman yankewa babu alamar za'a ɗauka. Nama gama sadaƙarwa dan idanuna har sun cika da hawaye sai ya ɗaga. A yanda yay sallama cikin wani yanayi na mutum mai damuwa yasa idanuna sun ciko da ƙwalla. Cikin rawar muryar alamar son sakin kuka na ce, “Yaya Musaddiq nice. Nice kandalarka. Dan ALLAH kuzo ku fiddani anan karna mutu. Yaya banda lafiya ciwo zai kasheni. Sun kawoni nan sun ɓoye kullum sai dai suyita bani abinci kawa.....” Fittt naji an ƙwace wayar daga hannuna. Hannu ya ɗaga zai ɗauke fuskata da mari sai kuma miya tuna oho masa ya tsaya cak. Niko tsoron da naji na kar ya kai ƙaton hannunsa kaina ya sani dunƙilewa waje ɗaya na rumtse ido. Jin shiru banji saukar marin ba na buɗe idona. Dai-dai nan yake ƙoƙarin fita a ɗakin. Na taso kuwa da uban gudu na nufi ƙofar nima, ina gab da ƙarasawa ya datse da sauri. Zubewa nai a wajen na saki wani kalar kuka mai ban tausayi da cin zuciyar mai sauraro.. Ina a wajen ko cikakken minti biyu baiyi da fita ba sai gashi ya dawo cikin sassarfa. Jin saukar handkerchief kawai nai a saman face ɗina. Kamar waccan ranar nayi niyyar yunƙurin tashi amma abinda suka shaƙa min yaci ƙarfina. Kamar ƙyaftawar ido na sulale ƙasa, daga haka ban sake sanin abinda ke faruwa ba kuma.. ✨●●)(●●)(●●)(●●✨ Gaba ɗaya yanda Yaya Musaddiq da Mansoor suka rikice bama su fahimci wayar ya yanke ba. Dan suna tare ne a mota sanda Samraah ta kira wayar. Da farko hankalin Mansoor ba'a kan Musaddiq yake ba. Sai da yaga yayi wata shegiyar zabura yana ƙwala kiran sunan Samraah jikinsa har wani gab-gab yake na rawa sannan. Wayar shima ya fisga jikinsa na rawa yake faman kiran ta. Sake ƙarɓewa shima Yaya Musaddiq ɗin yayi. Duk sun rikice sun ruɗe, jin dai ɗif ɗin yayi yawa suka ɗan fara dawowa hankalinsu. Sai sannan suka fahimci wayarma ta yanke. Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga rige-rigen sakkoma Yaya Musaddiq. Dan harga ALLAH yana matuƙar ƙaunar ƙanwarsa. Mansoor ma dai idonsa cike yake da ƙwalla, cikin ƙarfin hali ya buɗe motar ya fita. A ɗan zabure Musaddiq ya figi wayarsa dai-dai sanda Mansoor ke fita a motar, dan tunawa da ya dace ma su kira d.c.o fa. Kiran nasa kuwa yayi, sai dai ba'a ɗagaba. Cikin tashi hankali ya cigaba da kira. Har 3 miscall, fita yay da sauri a mota. A jikin motar ya samu Mansoor jingine idonsa a lumshe. Cikin sauri-sauri yake faɗin, “Na kira d.c.o amma bai ɗagaba. Inaga ya kamata mu ƙarasa police station ɗin mu sanar masa”. Shima ɗan zaburar Mansoor yay, cikin alamar gamsuwa da zaburowa ya nufi motar yana faɗin, “Hakane yaya, wlhy ni kaina ma ya tushe na rasa mizan yi, amma bara na kira Yaya Attahir ya nemesa tunda abokinsa ne”. Musaddiq ya gamsu da hakan, cikin ƙanƙanin lokaci Mansoor ya sanarma yayansa halin da ake ciki, kafin suma su ɗauki hanyar zuwa police station ɗin. Sosai Mansoor ke gudu, hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci suka iso station ɗin. Sun samu d.c.o baya nan ya fita sai dai Yaya Attahir ya kira Mansoor ya sanar masa yay magana da d.c.o ɗin ta waya, gashi nan zuwa ma su jirashi. Dole sukai zaman jiran dawowarsa duk a ƙage. Sai bayan kusan mintina sha biyar kuwa sai gashi ya dawo. Ganin yanda suke hankali a tashe ya buƙaci fara ganinsu. Suna gaya masa kamar yanda Attahir ya sanar masa tun a waya, shiyyasa ma ya katse abinda yake acan ya taho, ya amshi wayar Musaddiq tare da kiran yaronsa yace ya kwashe number ɗin yanzun nan ai masa tracing. Amsa yaron nasa yay ya kwashe number ɗin ya fita da hanzarinsa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* _Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_ ......A matuƙar hanzarce cikin tashin hankali yake bin umarnin ogan nasa. Ita daya shaƙama abu ya fara kinkima ya kai mota. Ya sake dawowa ya tattara duk abinda ya shafeta ya fita da su suma. Hatta kayan data jiƙa domin wankewa bai bari ba. Bedsheet da komai ya tattare katifa kawai ya bari a ɗakin. Cikin abinda bai wuce minti goma ba ya bar gidan da ita da komai nata. Cikin uban gudu ya nufi hanyar inda ogan nasa ya sashi maidata. Yayi nisa a tafiyarsa saƙo ya shigo masa. Sanin wayar da mutum ɗaya take da alaƙa ya sashi taka birki da sauri ya ɗan gangara gefen hanya. Titine da bai cika yawan kai kawon motoci ba saboda sabuwar anguwace sosai kuma a gefen gari ne ma. Idanu ya waro matuƙa sakamakon ganin saƙon da ogan nasa ya turo masa, tare da sauri ɓalle murfin wayar kasancewar ƙarama ce dama ya cire batteryn shima ya zare layin. Karyashi yay huɗu yay cilli da shi yana mai kwanciya akan steering ɗin da sauke nannauyar ajiyar zuciya mai ƙarfi. Yayi kusa minti biyu a haka sannan ya ɗago. Samraah dake kwance a baya tamkar gunkiya ya kalla, cikin cije baki ya ɗauke kansa. Motar yay ƙoƙarin sake tadawa akai knocking glass. Da wani irin bala'in sauri ya kalla gefen nasa, dan motar tinted glass ne da ita shiyyasa. Yasan wanda yake ta wajen bai ganinsa, amma shi yana ganinsa. Ganin kamar babu wani alamun kasancewar sa jami'in tsaro ya sashi sauke gilashin a hankali. Matashin saurayi da bai wuce sa'ansa ba ya ɗan sake duƙowa da faɗin, “Barka oga. Badai wata matsala bace ba ko?”. Murmushi yay shima cikin sauri ya ce, “Barkanmu. A'a babu komai na ɗan tsaya amsa kiran waya ne kawai. Nama gama yanzu zan wuce”. “A to masha ALLAH, dama ina tunanin ko akwai matsala ne. ALLAH ya tsare hanya”. Godiya ya masa yana ƙoƙarin maida gilashin kawai yaga an buɗe murfin gefensa an shigo. Da sauri ya juyo nan ɗin. Mutum ne garjejen gaske gashi cikin baƙaƙen kaya kamar shi. Sai dai wannan yasan ko'a mafarki sukai wasan kokawa ɗagashi zai dingayi yana nanawa da ƙasa. Amma cikin dauriya ya ce, “Malam lafiya kuwa?”. “Itace ta kawo haka”. Mutumin ya faɗa a gadarance. Sai kuma ya sa hannu ya zare key ɗin motar yana faɗin, “Fita ka koma baya”. “Na koma baya kamar ya? Ni da motata ka shigo min babu wani neman excuse kace kuma na fita na koma baya. To kai a wa kuma?”. Uffan mutumin baice da shi ba. Sai ma ɗora masa bindigar daya zaro a jikinsa yay a saman cikinsa. Da sauri saurayin ya kalla bindigar, cikin son ɓoye tashin hankalinsa amma yana ta son bayyana kansa ya ce, “Malam miye kuma na bindiga anan?”. Shi dai bai tanka masa ba. Sai ma ƙoƙarin saƙala yatsarsa yake akan kunamar bindiga ɗin, shima sai kawai ya buɗe motar ya fita zuciyarsa na wata irin bugawa da sauri. Turus yayi jikinsa na tsuma ganin zuƙa-zuƙan motoci har biyu baƙaƙe wulik, ga Samraah ana ƙoƙarin sakawa a ɗaya. Sai garadan maza har uku irin wanda ya titsiyesa a mota tsaitsaye da bindigu suma. Yana ji yana gani haka ya shiga bayan motar dan dolensa, saboda babu makami ko ɗaya a tare da shi. Kodama akwai ai sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi. Sannan waɗan nan kam sunfi ƙarfinsa, dan yama riga ya sadaƙar kawai jami'an tsaro ne su ɗin. Shima abu suka shaƙa masa, a take ya sulale sai barci. Daga haka bai sake sanin a wace duniya yake ba sai farkawa yay ya gansa a inda bai taɓa sani ba. Dan ɗaki guda shima aka ajiyesa shi kaɗai. A yanzu kam hankalinsa ya fara tashi ƙololuwa. Dan ya fahimci ba ƴan sanda bane ba. To ko ogan nasa ne yasa akai masa haka? Amma mizaisa yay hakan kuma?. (Ka nema ɓata masa aiki mana) wani ɓangare na zuciyarsa ya ayyana masa. Kansa ya dafe da ƙyar, dan gaba ɗaya jikinsa yay masa nauyi. Jin kamar jiri na ɗibarsa ya ɗan zame ya sake kwanciya yana mai lumshe idanunsa... (✿(✿(✿)(✿)✿)✿) A ɓangaren su Yaya Musaddiq kam anyi traicing number da Samraah tai kiransa an kuma gano inda suke. A take babu ɓata lokaci d.c.o ya shirya mutanensa. Duk yanda yaso su Mansoor su zauna sun dage da roƙon son binsu, ya fahimci koda ya hanasu zasu iya binsu a baya, hakan kuma akwai haɗari dan haka ya haƙura aka fita har dasu. Sunyi tafiya baifi ta mintuna uku ba layin ya yanke. Da sauri yaron d.c.o ya sanar masa. “Oga akwai matsala fa. Da alama sun farga damu dan layin ya daina aiki. Hakan na nufin an ciresa a wayane, dan da yana kan wayar ko kasheta sukai zamu same su”. Shima hankalin d.c.o ya tashi, amma sai ya dake shi cikin bada umarni ya ce, “Ku ƙarasa har inda layin ya dakata da aiki”. “Okay sir”. Ya faɗa yana yanke wayar. Su Mansoor basu san halin da ake ciki ba. Dan suna a ɗayar motar ne. Gashi kuma an cigaba da tafiya kamar yanda aka faro. Cikin abinda bai gaza mintuna talatin da biyu ba suka iso dai-dai wajen, dan gefen gari ne sosai. Sun sami mota kaɗai, amma babu alamar mutum. A take duk suka fito, sauran da basu san mike faruwa ba duk sun zagaye mota da bindiga. Wanda dai yake kamar ogan tafiyar ne ya sake kiran d.c.o ya sanar masa cewar gafa mota sun samu, sai dai basu sani ba koda mutum a ciki ko babu. Nan ma umarnin bincikawa ya basu, dan haka suka fara aikinsu, sai dai an hana Mansoor da Musaddiq zuwa kusa da motar duk da yanda suke a zalame. Cikin kulawa da ƙwarewar aiki aka buɗe motar, sai dai me babu kowa a ciki sai kayan Samraah harda jiƙaƙƙun nan na botiki, sun cigaba da bincike motar tako ina, har suka samu nasarar ganin layin wayar a gefen titin an karyasa. Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga kwaranyoma Musaddiq, hakama Mansoor ya duƙar da kansa jikin motar ƴan sandan kawai da alama shima dai kukan yake yi. Dan ba sai an faɗa musu ba komai ya tabbatar musu da mutanen nan sun sake samun nasarar tserewa da Samraah kuma. Komai an tattara har motar aka wuce da su station. Wasu a cikin ƴan sandan kuma suka watsu a wajen ta cikin jejin har ma da cikin ƙauye dake ata wajen bisa umarnin d.c.o. Dan yana zargin wanda suka ɗauke tan ko dai sun shiga jejin, ko kuma sun shiga cikin ƙauyen domin tsira tunda har aka samu motarsu anan. Sauran ƴan sandan da suka wuce station nata ƙoƙarin kwantarma da su Musaddiq hankali. Dan a take sun nema bayanai daga companyn layin wayar da Samraah tai kiran Musaddiq. Za'a binciki dukan abinda akai da layin a kwanakin da suka gabata. Kai tunma daga randa aka sayesa. D.c.o ya tabbatar musu da in sha ALLAHU za'a dace tanan. Badan dai sun gamsu ba suka haƙura suka tafi, dan bayanan sai zuwa gobe za'a samesu... (✿(✿(✿)✿)✿) Tunda na farka daga nannauyan barcin dana kasa tuna lokacin farawarsa rufin ɗakin da nake kwance kawai nake iya kallo. Rufine dake tabbatar da ba'a ƙaramin gida nake ba. Dan yanayinsa da fentin bangon ɗakin kawai ya isa ya tabbatar da haka. Na jima a hakan kafin na motsa da ƙyar. Saman gado nake, tabbas hakan ne, na ayyana a raina cikin tabbatarwa da kaina. Komawa nai na sake kwantawa batare dana ƙarasa tashin ba. A take komai ya shiga dawo min dalla-dalla. Na zare wayar wanda ke gadina na kira Yaya Musaddiq, bayan ya ƙwace ya shaƙa min abu, daga haka ban sake sanin komai ba. Kenan dai ɗakkoni yay daga can gidan ya maidoni nan saboda gudun tonan asirinsa. Hakan na nufin babu rana balle watan komawa ga zuri'ata. A hankali wasu hawaye suka shiga silalo min masu zafi. Yau saura kwanaki takwas aurena, na tabbata duk hankalin wani masoyina ba'a kwance yake ba zuwa yanzu. Musamman Yaya Musaddiq, Mansoor, Hafizzullah... Wani murɗawa da marata tai ya katse min dukan tunani na. Faɗuwa gabana yay, Dan kuwa lallai lokacin prioud ɗina ne. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Aiko akwai matsala, idan na kasance a wannan halin anan waye zai kula dani? Dan ba ƙaramar wahala nake sha ba har sai an mun allura, wani lokacin ma ai allurar taƙi sauka. Shiyyasa har shan magani nake a ɓoye dan kar jinin yazo. Abinka daba uwa ba balle ta gani ta kwaɓa, sai babu wanda yasan ina hakan har yanzu, kuma na jima inayin hakan, dan ko yanzu kusan watana na biyar kenan banyi ba saboda bana wasa da maganin a duk sanda nasan kwanakin period ɗina sun gabato, yanzu ma da ace akwai shan kawai zanyi shike nan bazai zo ɗin ba. Jin yaɗan lafa min na sake buɗe idanuna tare da yunƙurawa da ƙyar na tashi zaune. Ɗakine babba, sai dai babu komai a cikinsa sai iya katifar da nake kai, ashe ba gado bane, irin ƙatuwar katifar nan ce irin wadda ba'a sakawa a gado. A hankali na miƙe da ƙyar, windows ɗin ɗakin nabi na lalleƙa, sai dai bana iya gane komai sai dai ina iya jiyo magana mutane ƙasa-ƙasa. Hakan yasa na nufi inda nake ƙyautata zaton ƙoface. Bugawa na shigayi babu ji babu gani ina kuka. Sosai nake ma ƙofar bugun hauka da nasan dolene ya damesu. Amma ƴan iskan nan kamar kurame, ga wani irin murɗi da marata kemun na azaba, tun ina ƙarfin hali har na sulale ƙasa jikin ƙofar na zube. Tuni nayi sharkaf da zufa na azaba, ga jikina dake rawa, sai kuma uban kuka da nake ina kiran sunan ALLAH da fatan Yaya Musaddiq ya zo ya ɗaukan.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_ .......Dukkanin bayanan da d.c.o ya buƙata an kawo daga companyn layin wayar mutumin. Dan haka yay zaman dubawa daki-daki. Sabon layi ne, an kuma buɗesa wata ɗaya daya gabata. Sai dai ba'a taɓa waya da kowa da shi ba sai number Yaya Musaddiq da Samraah ta kira. Sai kuma number ɗaya jal da sakwanni kawai aka dinga tura masa da ita. Dukannin sakwanin kuma a gajarce ne. Babu kuma wata ma'anar da za'a fahimcesu sai su da suka yi abinsu. A yanda kuma sakwannin suke kamar babu sanayya tsakanin wanda ke amfani da layin da mai tura saƙon da alamu suka tabbatar shine ya saka akai kidnapping Samraah ɗin. Abin ya tsayama d.c.o a zuciya. Amma dai ya sake bada number da ake tura saƙon itama a basu bayani a kanta. Nan ma sunce sai washe gari. Hakan yasa d.c.o sakawa ai masa traicing number ɗin kafin su kawo bayananta. Sai dai me sam layin babu shi akan network kwata-kwata ma. Hakan na nufin shima mai shi ya karya shi ɗin kenan ko ya yarda ko ya sauke. Wani irin dukan ɓacin rai d.c.o ya kaima desk ɗinsa. Dan ya fahimci wannan al'amari gaba ɗaya akwai rainin wayo a cikinsa. Duk kuma wanda ya shirya ɗauke yarinyar nan yana da basira ƙwarai da gaske. Dan bai ɗauketan ba sai da ya gama tsara dukkan hanyoyin ɓullewarsa daki-daki ta yanda gano wanene shi zai yi matuƙar wahala. Amma babu komai, ai dole ne ko yaya yayi kuskure. Da kuma wannan ɗan ƙaramin kuskuren kaɗai zasu iya kama shi in sha ALLAH.. Ranar da kansa ya zo gidan Abba ba yaransa ba. Lokacin kuma anyi sa'a duk suna gida. Hatta Nabil yazo weekend bai koma ba dan shi a hostel yake zama. Hafizzullah dai ya koma bisa tirsasawar Yaya Musaddiq. Da farko kicin-kicin Mum tai da fuska. Dan ita fa magana ta gaskiya zancen Samraah ɗin nan ya fara isarta. Zirga-zirgan da ƴan sanda ke musu kullum a gida yanzu ta fara cimata rai. D.c.o dake ta binta da kallo cikin dakewa ya ce, “Ina ganin muna gab da ganin Samraah in sha ALLAHU”. Mum data gama cika taf cikin ɓacin rai ta ce, “Yo dama kune ke wahalar da kanku, duk ma inda take ai itace takai kanta. Dan ni nasan abokan iskancinta tabi wani garin kawai suke zaman shashancinsu a wani wajen. Amma yallaɓai duk kunbi kun tadama kanku hankali muma kun gagara barinmu mu huta. Haba, Samraah dai Samraah dai kamar wata allura ko sarƙar gwal ko diamond”. “To amma Hajiya duk kin san da haka miyyasa baki sanar mana ba tun farko?”. “Ni! Rufamin asiri na mutu maza su kaini ba mata ba. Taya zan sanar muku kuwa yallaɓai. Ace kuma na laƙa mata sheri. Kadai san ɗan riƙo komi zaka masa ba tsira kake ba. Amma tun yaushe wannan yarinyar ke bin maza suna barin gari. Wane hotel ne bata san da zamansa a garin nan da wajen garin ba. Ai ni bana raba ɗayan biyu wannan yarinyar ta zubar da ciki sama da sau bakwai kuwa. Tunda nan zata dinga mana ihu da murƙususu wai mararta na ciwo, haka zakaga jini na binta, in ba zubda ciki ba kuwa mi tayi?”. Kai kawai d.c.o ke faman jinjina wa. Yayinda Abba keta hararar Mum da mata alamar tai shiru amma matar nan sai da takai aya ta haɗiyi yawu bakinta kamar an ɓarka zani. Kallon Abba d.c.o yayi bayan ya gama ɗan rubuce-rubucen sa. “Amma Alhaji matsayinka na uba duk kasan da hakan baka taɓa ɗaukar wani mataki ba?” Kafin Abba yay magana caraf Mum ta sake amshewa. “Matakin mi zai iya ɗauka a kanta yallaɓai. Bayan duk gidan nan babu wanda take shakka ko tsoro tafi ƙarfinmu. Sannan ɗan uwanta duk da saninsa take komai tunda shine kawalinta.....” “Amma Hajiya ina magana da mijinki ne. Shi kuma nake son ya amsa min wannan tambayar.” kai Mum ta ɗauke gefe tana laɓe baki. D.c.o ya sake maida hankalinsa ga Abba da yanayinsa ya nuna sam baya jin daɗin abinda Mum ɗin keyi, amma ya gagara tsawatar mata. “Kai nake saurare Alhaji”. “To yallaɓai ni mizance. Al'amarin ne gaba ɗaya akwai ruɗarwa. Amma ina yin iya bakin ƙoƙarina, sai dai kasan mu maza koda yaushe kana waje ba zaman gidan kake ba, shiyyasa ita ta fini sanin abubuwan”. Shiru kawai d.c.o yay tare da zubama Abba dake ta ƴan kame-kame ido. Yaya Musaddiq da idanunsa suka cika da ƙwalla cikin sarƙewar murya ya ce, “Ranka ya daɗe Samraah bata taɓa aikata fasiƙanci ba. Sannan inba akan aikin nan nata ba zan iya rantse maka bata taɓa shiga hotel ba. Sannan ciwo da takeyi tana yinsa ne duk wata sakamakon al'adarsu ta mata. Amma inaga abar maganar nan, duk kuma inda take in sha ALLAHU addu'armu na biye da ita. ALLAH ya bayyanata, ya kuma bata kariya daga sharrin duk wani mai sharri”. Maganganun Yaya Musaddiq sun sake saka Abba shiga wani yanayi, dan sai zufa yake kamar wanda ya haɗiyi kunama. Yayinda Mum keta ƙunƙuni ƙasa-ƙasa tana jin kamar ta rufe Musaddiq da duka. Sai dai babu damar hakan kodan d.c.o dake zaune. D.c.o ya gamsu da zancen Musaddiq, dan haka bai sake cewa komai ba ya miƙe. Miƙewar shima Musaddiq ɗin yayi batare da ya sake kallon inda su Abba suke ba ma, dan bai taɓa jin ɓacin rai mai tsanani akan abinda suke musu ba irin yau. Wani irin zafi yake ji a zuciyarsa game da su matuƙa.... ★💫★💫★💫★💫★💫 Ciwo ne sosai yaci ƙarfina. Harma nake ganin ya ninka wanda nakeyi a baya. Ko hakan nada nasaba da yanda nasha magani wata na biyar kenan ma banyi ba. Sama-sama nake jin ana buɗe ƙofar. Daga haka ma nai ɗiff alamar hankalina ya gushe daga gangar jikina. Da sauri wanda ya shigo ɗin ya koma baya ganin Samraah ta suma. Cikin tashin hakanli yake sanarma sauran ƴan uwansa, “Kai yarinyar nan fa kamar ta mutu”. “Mutuwa fa?”. Suka faɗa a tare suma cikin zaburowa. Komawa yay da gudu yana faɗin, “Kuzo to ku gani wlhy”. Duk binsa sukai cikin sassarfa suma. Wanda ke da ɗan yanayin hausawa a cikinsu ne ya ce, “Kamar suma tayi dai, Ayo ka kira oga Please, kasan dai irin gargaɗi da sharuɗɗan daya gindaya mana. Kar muce zamuyi shiru mu samu matsa”. “Exertly maganarka gaskiya ne.” ya faɗa yana ƙoƙarin danna waya. Duk cikin harshen nasara suke maganar. Baifi mintuna biyu ba sai gashi ya dawo. Ya sanar musu oga yace duk su fita a ɗakin za'azo da doctor yanzu. Hakan kuwa akai duk suka fita, Ayo ya kulle ɗakin kamar yanda aka umarcesa. Bako a cika minti talatin cif ba sai ga driver ya kawo doctor. Ita kaɗai ta shiga ɗakin bayan Ayo ya buɗe mata. Sai da ta ƙarema fuskar Samraah kallo kafin ta kira Ayo ya taimaka mata suka maidata saman katifar. Duk taimakon daya dace tai ƙoƙarin bata, cikin ko ƙanƙanin lokaci ta farfaɗo. Sai dai tana buɗe ido ta dafe mararta da hannu bibbiyu tana kuka da murƙususu sosai. Da ƙyar ma take iya amsa tambayoyin doctor ɗin. Kasancewar likitar ƙwararriya ba'a wani ja da nisa ba ta fahimci matsalar Samraah. A take tai kiran wanda ya sakata aikin. Ta sanar masa zata turo sunayen magungunan da alluran da take buƙata yanzun nan a sayo a kawo mata. Yace okay ba damuwa ta tura. Rubutawa tai ta tura, sannan ta cigaba da bama Samraah taimakon daya dace kafin a kawo. Ba'a ɗauki lokaci ba Ayo yay knocking, izinin shigowa ta bashi. Ya shigo ɗauke da leda yace an kawone a bata. Amsa tai da godiya, shi kuma ya juya ya fita. Duk zafin ciwo baya hanani shiga ruɗani a duk sanda za'amin allura. Yanzun ma hakane. Dan tunda na fahimci abinda take shirin mun na birkice mata. Duk yanda taso tankwarani kuwa ta kasa. Dan da gasken gaske na tsani allura harma da magani. Dole tai kiran wani wai yazo ya riƙeni. Nako tubure akan wlhy babu shegen gardin da zai taɓani. Ta ɗauka azabar ciwoce kawai ta sakani faɗin hakan. Sai da mutumin data kira ya shigo yana kawo hannu sukaga na rarumi handbag ɗinta zan kai masa duka sannan. Shiko yay baya da sauri yana yare da ɗaga hannaye sama. Ina kallonta tai murmushi da bashi umarnin fita. Ita kuma ta ɗauki waya, sai da ta daddana sannan takai kunne. Ina jinta sama-sama tana sanarma wanda ta kira cewar ina tsoron allura, na kuma ƙi yarda a riƙeni. Ban san mi aka gaya mata daga can ba na dai jita tana cewa okay. Daga haka ma ciwo yaci ƙarfina har tai allurar bamma sani ba saboda yanda marata kemin azaba har ina shiɗewa. Sai gani nai kawai ta haɗa kayan tafiya. Babu jimawa barci ya ɗaukeni, dama haka allurar kemin duk sanda akayita. In dai aka min irin allurar nan cikin amincin ALLAH da nayi barci na farka shike nan. Amma abin mamaki yau saɓanin haka. Dan cikin dare na farka amma da sabon ciwon mara da yafi na farko ma. Ciwo sosai harna suma sau kusan biyu. Bamma san yaya akai ba naga doctor ɗin ɗazun a kaina. Tare da wata fuska dana taɓa sani sai dai na mance a ina nasan fuskar dan ciwo ya sakani galabaita dishi-dishi nake ɗan ganinsu, amma tabbas nasan fuskar wannan mutumin, kuma ya kamata na tuna ina ne na sanshi.......✍️ _🥱Ya kamata ki tuno dai kam, koma fita a ruɗani muma Samraatu🚴._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ .......Yanzun ma dai barci ne mai nauyi sosai ya sake yin awon gaba dani batare dana gama tantance fuskar mutumin ba. Ban kuma farka ba sai washe gari da rana gatse-gatse. A yanzun ma dai ba farkawar daɗin rai bace ba. Dan still dai ciwon ne ya farkar dani ta yanda har sai da doctor ta sake dawowa. Yanzun kam naga alamun ruɗanin yanayin nawa a fuskarta itama. Dan bayan ta ɗan duddubani fita tayi tana danna waya, da alama magana take son yi da wani... Bata wani jima sosai ba ta sake dawowa. Allurar dai ta sake fakar idona tamun, sai dai da alama tamafi ta jiya ƙarfi. Dan ko minti biyu cikakku banyi ba na sake komawa barci, daga haka ban san wainar da ake toyawa ba kuma... A ɓangaren Doctor bayan tama Samraah allurar barci ya ɗauketa babu jimawa wanda tai kira a waya ya iso. Kamar yanda ta shawarcesa da kai Samraah asibiti ya amince. Sai dai da kansa ya nuna zai kaisu asibitin data tabbatar masa akwai dukkan tsaron da suke buƙata. Dan ya sanar mata alaƙarsu da yarinyar ta yanda hankalinta zai ɗauka bawai ainahin gaskiyar sato ta ko kwatota ne ma oho musu ba. Ita kuma jin wanda ya saka aikin yasa bata wani damu ko ɗarsa zargi a ranta ba take bata duk wannan kulawar. Dan tun jiya da tasan yana a garin Abujar nan take jin wani farin ciki, tasan kuma a dalilin aikin yarinyar nan zata iya haɗuwa da shi, duk da dai yanayin ciwon yarinyar yana buƙatar aje da ita asibitin da gasken.. Sun isa asibiti batare da wata matsala ba. An kuma yima Samraah dukkan binciken daya dace. Dan har dare suna a asibitin, sai kusan goma suka gano matsalarta. A take suka haɗo duk abinda zai taimaka mata a matakin farko kafin ai mata abinda ya dace. Gidan suka sake maidota aka saka mata drip kamar yanda ya buƙata, daga haka suka fice aka barta da masu tsaronta. Tunda suka shigo katafaren ginannen gidan take jin jina kai da sakin kurmushi. Duk da tasan wannan ba komai bane daga mamallakin gidan. Amma dai tayi mamakin yanda yaron nasa ya bata labarin an ginashi cikin ƙanƙanin lokaci tare da wani ma a Kano. Duk da kuwa tasan yana da gidaje sosai a Abujar nan da basu da adadi ma musamman ga ita da ba kowanne ta sani ba, amma tasan wannan ɗin na musamman ne gaskiya. Har kusan ƙofar falon ya kai kafin yay parking, cikin murmushi yay mata nuni da suje ciki. Babu musu ta ɓalle murfin motar ta fita, sai wani taku take cikin yauƙi da yanga. Tun a takun farko na shigowa falon wani sanyi da ƙamshi mai sauke gajiya suka ratsata. Ta wani shaƙi iska da dogon hancinta ta fesar a slowly. Ko makaho yasan falon ya haɗu tamkar mai shi. A hankali ta ɗan kai dubanta ta gefen damarta da take jin ƙamshinsa yafi yawaita a tanan. Shine kuwa zaune cikin kujera 1sitter da laptop a saman ƙafafunsa daya miƙe saman Centre table. Yanda keyboard ɗin laptop ɗin ke bada sautin ƙara zai tabbatar maka da typing abu yake. Da alama kuma mai matuƙar muhimmanci ne. Dan gaba ɗaya hankalinsa na kan screen ɗin, kuma yana dannawa ne da ɗan yanayin sauri na ƙwarewar sabo da hakan. Ƙananun kaya ne a jikinsa kamar ko yaushe. Dan sune suturar da yafi sakawa sai ko suit kamar dangin yahudu. Sai dai kasancewar wandon nasa kaɗan ya zarta gwiwa ya bama ƙafafunsa damar bayyana samɓal. Har suka kai zaune bai kallesu ba balle ya nuna yasan da shigowarsu. Sai da ya ɓata kusan mintuna shida curr sannan yay magana batare da ya kallesun ba yanzu ma. “Any problems?”. Ya faɗa a daƙile cikin silent voice ɗinsa. Hayatu ne ya jin jina kai yana mai sake sakama kansa nutsu da gyara tsaiwarsa cikin nuna girmamawa sosai. “Eh to Sir dama dai akan batun yarinyar can ne. Kasan tun jiya na sanar maka abinda ke faruwa na rashin lafiyar da take ciki, har kace Dr Rumaisa tazo ta dubata. To tun dai jiyan tayi duk abinda ya dace amma ba'a dace ba. Ɗazun dai dole tasa mukaje da ita asibiti domin a bincika matsalar ta shine dama muka zo sanar maka dan yan zun ne muke dawo wa...” Shiru kamar bazai tanka ba, sai da ya mula dan kasa ya furta, “Uhum ina sauraren ku”. Da sauri Doctor Rumaisa tai tsigil ta ce, “Ranka ya daɗe Good evening”. Bai amsa mata ba, illa ɗan jinjina kansa da yay kawai alamar amsawar kenan batare da ya kalleta ba kuma. Taji ba daɗi, dan ba haka taso ba. Amma sai ta daure ko za'a dace ta cigaba da faɗin, “Gaskiya yarinyar akwai babbar matsala a tare da ita. Da alama tun kafin yanzu tana fama da pain a duk sanda zatayi prioud, kuma yana mata tsanani. Maybe hakan ne ya jata ta dinga shan maganin hana zuwan prioud ɗin a duk sanda lokacinsa yayi, shine ya haifar da matsalar wannan karon ɗin. Dan sai wahala kawai take sha amma jinin yaƙi ya fita, yanzu dai in sha ALLAHU na mata dukkan abinda ya dace akoda yaushe zai iya fita ɗin, sai kuma ta kiyaye cigaba da shan wancan magungunan inba haka ba zatama kanta illa. Dan a yanzu hakan ma sai an ɗorata akan magunguna masu ƙarfi sosai da zai dai-daita mata komai, sai dai sunada wahalar samu maganin dan sunada tsada gaskiya, ba kowanne pharmacy zaka iya ganinsu anan ba ma”. A yanzu ɗin ma dai babu alamar zai amsa dan kamar ma bashi takema bayanin ba. Hakan yasa Hayatu bata amsar dan yasan Maash bazai sake magana ba kuma. “Sir zan ƙarasa komai in sha ALLAH. Dama dai na kawota ne kawai ta maka bayani yanda zakafi fahimta.” daga haka yayma Dr Rumaisa nunin ta miƙe shima yana tashi. Sam ba haka taso ba, dan fuskarta ma ta nuna. Ta kafe Maash da kallo tana mai fatan ya sake cewa wani abu koda bazai ɗago ɗin ya kalleta ba, dan dama ita ta matsama Hayatu akan ya kawota ta masa bayani da kanta. Amma sai bai ko kallonsu ba aikinsa ma ya cigaba dayi kamar yanda suka shigo suka samesa. Sai ka ɗauka ma ya manta da su a falon ne tsabar halin yarfin mutumin nan. Suna fita ta kalli Hayatu rai ɓace. “Amma ba haka mukai da kai ba Hayatu?”. “To yaya kike so nayi doctor. Kin san dai halin Boss ba sai na sake tisa miki ba. Ba yau ne kika fara masa aiki ba kuma. Shiyyasa naso ma ki bari muyi komai mu gama iya mu kaɗai tunda ba gagara zai yi ba. Tunda kuma shine yasa kizo zai buƙaci ku haɗu kafin mubar garin. Yanzu dai kiyi haƙuri a madadinsa. Kiyi kuma magana da pharmacy ɗin da kikace zasu turo maganungunan nata. Sannan ki bada account number da za'a saka kuɗin.” Gaba ɗaya fuskarta ta sauya da tsantsar damuwa da ɓacin rai. Duk da dai tasan zata shaƙi kuɗi a aikin nan, dan ko Hayatu hannunsa a buɗe yake tamkar boss ɗin nashi a wajen ƙyautatawa. Kamar zatayi magana sai kuma dai ta shanye da ƙyar, gaba tai idanunta na cika da hawaye ta buɗe motar da suka zo ta shiga. Murmushi Hayatu dake binta da kallo yayi, acan ƙasan ransa kuma yana jin tausayinta. Dan yasan tamkar ta ɗebo ruwan dafa kanta ne dakon soyayyar wanda soyayyar uwa kawai da familynsa ya sani sama data wata ɗiya mace a wannan rayuwar. Shi kansa har mamaki yake anya ogan nasa nada lafiya kuwa, dan shi dai zai iya rantsewa, bayan abokan huɗɗa dana aiki be taɓa ganin wata mace a gefen ogansa ba da sunan yana mata kallon mace mahaɗin rayuwa ko wani ɓangaren jin daɗin duniya. Shi dai kawai neman kuɗi, ina zaka business ina ka fito business. Abinda kawai ke birgesa da shi neman kuɗi bai taɓa shagaltar da shi bautan ALLAH ba. Ga shi dai nan da zubin tsagerun mutane, amma batun ibada babu wasa.. Motar ya shiga shima, yay mata key suka fice a gidan bayan securitys dake gate ɗin sun buɗe masa. Lallashi da daɗaɗan kalamai ya dinga gayama Doctor Rumaisa, acewarsa ta cigaba da addu'a, idan ALLAH ya ƙaddara Maash mijinta ne sai ya aureta. A hankali ta saki murmushi kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta, shi ko ya girgiza kansa dan shima ya san dai gangan yake faɗa, dan ga wata can ma a Lagos data fita wayewa da komai ana tirƙa-tirƙa bayan na bayan fage da iyayensu suke faman masa tallarsu wasu ko sune da kansu suke masa tallar kansun. Shifa yasha ganin ballagazayen wasu matan na kuka akan Maash ko kwanciya yay dasu idana bazai aurensu ba, amma ko kallonsu bayayi ma balle su samu karɓuwa. Gaskiya kuɗi a mafi yawan lokuta fitinarsu tafi alkairinsu yawa. Shi shaida ne. Dan shi kansa ma da bashi ke da dukiyar ba yana cin azaba balle shi Maash ɗin da kansa. Aure ma da ƙyar akai masa a shekarar data wuce, yanzu haka matar nada ciki, amma kullum cikin faɗa suke akan rashin lokacinsa. inaga kuma matar mai gayya mai aiki da ake fatan ta shigo, ai duk wadda zata zauna da shi a matsayin aure kam sai ta jajirce, ko dai ta dinga binsa duk inda zai je itama taji a jikinta dan yawon ma ba hutu bane, ko kuma ta cigaba da hakuri da abinda ta gani kawai.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ......Har gidansu dake anan Abujar Hayatu ya maida doctor. Koda ya dawo a inda suka barsa nan ya sake samunsa. Yanda yaga fuskarsa tai kicin-kicin sosai ya sashi sake nutsuwa, kamar yaron da yayma mamarsa laifi kafin ya tafi makaranta. Sun kai tsahon minti uku a hakan yana satar kallonsa, shiko yana aikinsa kamar bai san da shigowar tasa ba. Sai can a bazata cikin daƙilalliyar muryar nan tasa dake fita silent ya furta, “Bani black tea”. Da sauri Hayatu ya amsa da, “Okay Sir” yana nufar hanyar kitchen. Bai wani jima sosai ba sai gashi da abinda yace masan. Lokacin da yake amsa ya ɗan kallesa, hakan yasa Hayatu saurin rissinar da idanunsa, dan ko motsi ogan nasa yayi yasan abinda yake nufi. Shayinsa ya kai baki ya ɗan kurɓa sau biyu sannan ya sake kallon Hayatun. “Minace maka akan yarinyar nan?”. “Sir wlhy ba laifina bane. Kasan tanada shegen naci, nunawa tai ma idan ban kawota inda kake ba a jiya da ciwon yarinyar ya motsa bazata taɓata ba”. “Sai akace ita kaɗaice likita kuma?”. “Am sorry Sir. Anyi kuskure amma za'a kiyaye in sha ALLAHU”. Shiru kamar bazai sake tanka masa ba. Har sai da ya gama shan shayin ya ajiye kofin yana miƙewa sannan ya furta, “A dawo da yarinyar nan gidan”. Wani mugun waro idanu Hayatu yayi yana binsa da kallo. Sai dai shi bai ko waiwayo ba har ya gama haye stairs ɗin da zai kaika inda bedroom ɗin sa ya ke. Jagwab Hayatu ya zube a kujera tare da faɗin, “Boss rigimarka tafi ta sojojin yaƙin basasa wlhy. Kai komai idan zuciyarka ta raya maka sai kace ayi baka tuna abinda zai iya zuwa ya dawo. Yarinyar da ake nema ruwa a jallo kawota gidan nan ai haɗari ne, mun ɗakkota da ga Kano jiya ALLAH ya somu mun fito lafiya, yau kuma kace a kawota nan. Mu kuma da muka zo jiya zamu iya wucewa akoda yaushe ya za'ai da ita a gidan nan da ko ƴan aiki duk maza ne?” ya zabga tagumi bayan ya gama sambatunsa babu mai bashi amsa. Sai dai yasan ko giyar wake ya sha bai isa ƙin bin umarnin nan ba kuma. Dole ya miƙe ya tattare kayan daya baza falon ya koma tsaf. Shima ficewar yayi domin duba ɗakin daya dace a saka yarinyar idan sun ɗakkota..... 💞💥💞💥💞💥💞 A hankali nake buɗe idanuna da sukai min matuƙar nauyi. Hakama jikina jinsa nake tamkar ba nawa ba dan yayi min jingim. Ga laima ina jina kwance a ciki kamar wadda tai fitsarin kwance. Hannuna na ɗaga da ƙyar nakai inda nake jin laimar na taɓo, da ƙyar na ƙara ɗago hannun domin ganin minene. Duk da dama shi ɗin nai zaton gani sai da gabana ya faɗi, nai wani kalar rumtse ido da ƙarfin gaske ina cije lips ɗina shima da ƙarfi kamar zan huda su. A dai-dai nan naji ana taɓa ƙofar, sake faɗuwa gabana yay, nai ƙoƙarin yunƙurawa dan na tashi zaune amma har an riga an buɗe. Rashin ƙarfin jiki yasa na kasa jawo blanket ɗin dake a gefe, duk da ma wani sashe na zuciyata mamakin ganin kuma a inda nake ya kamani. Dan nan ɗakine mai ɗauke da kayan gado complete, sannan yafi wancan ƙyau fiye da zaton mai zato ma gashi ƙato sosai. Mutumin nan da sukai min allura tare da doctor a daren jiya ne ya fara shigowa. Sangamemen ƙato biye da shi da da ledoji a hannu. Muna haɗa ido da shi na kauda kaina. Shima nasa kan ya kauda, batare da ya sake kallona ba ya furta, “Waɗan nan naki ne zaki iya amfani da su. Bayan su duk ma abinda zaki iya buƙata akwaisa a ɗakin. Likitarki ta gama aikinta, har magungunanki gasu anan ta kawo”. Daga haka ya juya ya fita. Da kallo na bisa zuciyata na wani irin kai-kawo. Kenan dai da gaske mutanen nan ne sukai kidnapping ɗina. Sune kuma suka saka ake bibiyata? Hakan na nufin sun san na ɗauki wannan video recording ɗin dai kamar yanda nai tunani?. (Ya ALLAH ta yaya hakan ta kasance?) Na faɗa a zuciyata, a zahiri kam ina mai runtse idanuna dake cike da nauyi har yanzu. Na kai tsahon mintuna goma ina faman tunani kafin na yunƙura na tashi da ƙyar, dan dama yanayin da jikina ke ciki yasa bance da shi komai ba da ya shigo. Yanda na jiƙa wajen da jini ya bani tsoro sosai, kamar wadda tai ɓarin ciki jama'a, haka dai na daure na sakko, sai dai ganin an saka min abune a inda na kwanta ɗin ba ainahin gadon na ɓata ba na ɗan saki ajiyar zuciya. Abin mai kama da leda-leda katifa-katifa na tattare na ɗauke. Cikin ɗingisa ƙafata dake ciwo na nufi hanyar da nake ƙyautata zaton toilet ne. Shi ɗinne kuwa, sai dai ya tsaru matuƙa, dan da za'a bani zaɓin wajen kwanciya maybe na kawo katifata nan na shimfiɗa, bawai dan yafi ko ina ƙyau ba, kawai dai ya birgeni ne shima. Duk da rashin ƙarfin da nake ji haka nai ƙarfin halin gyara jikina yanda ya kamata, nai wanka da ruwa mai zafi sosai. Sai a lokacin kuma hankalina ke neman tashi tuna bani da pant balle azo ga batun bad, sai dai tuna abinda yace yasa na fito. Ledojin da suka ajiye na shiga buɗewa, ta farko abinci ne, ta biyu kuwa kayan ciye-ciye ne. Sai ta ƙarshe ce ke ɗauke da kayan sawa, a ciki na samu pants da bad ɗin. Duk da naji wani iri da ganin hakan banda damar ƙorafi, ɗauka nai kawai na koma ciki na kimtsa jikina na dawo ɗakin. Kayan na sake buɗewa na ɗauki doguwar riga na saka batare da na damu da sanin sauran abinda ke ciki ba. Bana jin yunwa, dan in har ina a wannan yanayin ban cika son cin abinci ba, sai masifaffen kwaɗayi kamar sabuwar mayya. Dan hankalina duk yana akan naman can dana gani, ko naso basarwa kuma bazan iya hakan ba, garama naci bai nak yanda zan samu ƙarfin sauke musu abinda ke kaina. Zama nai kuwa nacisa sosai har saida naji na ƙoshi, na fiddo magungunan dana gani na duba duk yanda aka tsara shansu suma nasha. A yanzu bana buƙatar zaman yin dogon tunani, tunda na fahimci a hannun waɗanda nake saɓanin kwanakin da suka gabata da nake canki canka da rashin tabbas. Yanzu babbar damuwata ahalina. Na tabbata duk inda Yaya Musaddiq da Mansoor suke hankalinsu a matuƙar tashe yake kodan kiran da nai a waya. Amma ina fatan askine yazo gaban goshi, dan nayi alwashin komi mutanen nan zasumin bazan taɓa basu video ɗin nan ba ko faɗa musu a inda zasu samesa, iyaka dai suce nima zasu halaka ni, ban damu ba, dan hakan da zasu yi shine mafi girman kuskure da zai tona asirinsu insha ALLAHU. Shan maganin ya ƙara saka min jin daɗin jikina. Sai dai damuwa data kasa ɓoyuwa a kan fuskata. Sai gajiyar zama waje ɗaya daban saba ba. Nida nake yini tsaye kan ƙafafuna ina faman bautar aiki, garama idan office naje akan ɗan samu sassauci tunda shi kusan daga zaune ne. Motsin sake buɗe ƙofa da naji ya sakani tashi daga kwancen da nake cikin kujerar ɗakin, ɗan kwalin abayar naja na rufe kaina zuwa ƙirjina da ƙyau. Dai-dai nan aka ƙarasa shigowa. Mutumin ɗazu ɗinne dai, daga bakin ƙofa ya tsaya yayinda ni kuma nake kallonsa a tsiwace. Dan sai yanzu ne komai ke dawo min game da sanin da nai masa. Tabbas shine yaron mutumin nan mai kama da ƴan daudu ko nace ɗan daba ma ko sara suka oho duk ya cancanta, shine kuma ya kira da PA ɗinsa a ranar wancan taron. Nai saurin kauda kaina ina ƙoƙarin dai-daita fuskata da jikina. Tsahon mintuna kusan biyu ɗakin shiru, kafin cikin son nuna jarumta na furta, “Dama kune kukai kidnapping ɗina?”. Maimakon bani amsar dana buƙata sai jinai cikin bada umarni ya ce, “Zaku iya shigowa”. Baima ko gama rufe baki ba kuwa garadan samari biyu suka shigo. Ko namiji yaga wannan samudawan dole ya ji tsoro balle ni, amma dai nayi ƙoƙarin dake zuciyata ban bari tsorona ya fito a saman fuska ba. Sai dai faman haɗiyar yawu nake da ƙyar zuciyata na faman kai da kawo a cikin ƙirjina. Umarnin tashi suka bani, bani da ikon yin musu ko dan bindugun dake a hannunsa, ɗaya daga cikinsu ne ya koma ta bayana ya ɗauro ƙyalle a saman idona, zanyi magana ya ce, “Shiii!! Young Lady, inba hakaba harsashi ya rufe miki baki”. Yawu na sake haɗiyewa mai kauri, daga haka ban sake magana ba har suka bani umarnin tafiya bayan sun saka min wani abu a hannu na riƙe. Tafiya kawai naji munayi batare dana san ina muke nufa ba, amma dai baka jin hayaniyar komai ko'ina tsitt sai kukan tsuntsaye daga ɗan nesa damu kaɗan. Da ace hannuna babu handcuffs wlhy sai na cire abinda aka rufen fuskar komai ma za'ayi ayi. A haka naji mun shigo wani waje mai shegen sanyi da ƙamshi na musamman. Nanma mun ɗan yi tafiya kafin naji mun tsaya cak a inda ƙafata ta taka wani lallausan abu.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_ ......Kamar yanda d.c.o ya nema washe gari an sake kawo masa bayani akan ɗayan daya buƙata. Sai dai abin baƙin ciki shima layin na taƙaitaccen lokaci ne kamar wancan, ba kuma a taɓa kiran wani da shi ba. Nasara ɗaya da suka samu itace na shi wanda yay register ɗin layukan duk mutum ɗaya ne. Kuma a lokaci ɗaya yayisa. Sun saka a nemo musu shi a duk inda yake. Hakama abokin masu napep an samu nasarar cafkosa a safiyar yau. Bayan kamar awa biyu da kawosa police station ɗin aka kaisa office ɗin d.c.o kamar yanda ya buƙata. Sai da ya gama masa kallon tsaf daga sama har ƙasa kafin ya tura masa hoton Samraah dake gabansa. “Kasan wannan?”. Ya faɗa kansa tsaye idanunsa ƙyam akan saurayin. Hoton saurayin ya ɗauka ya kalla na kusan sakan talatin, ɗagowa yay ya kalla d.c.o sai kuma ya rissinar da kansa yana ɗan jinjina kai. “Nasanta ranka ya daɗe. Sam-G ake kiranta, tana gabatar da shirin matasa kuma ina ɗaya daga cikin fans nata da shirin baya wuceni ta redio ko shafukanta na sada zumunta musamman YouTube da ake ɗora shirin, nakan je na kalla videos ɗinta”. Kai d.c.o ya jinjina masa da faɗin, “Masha ALLAH. Minene sana'ar ka?”. “Direban napep ne yallaɓai”. “Kozan iya sanin ranar goma ga watan nan kana ina? Da ga shida na safe har zuwa ƙarfe takwas?”. Jimm yay irin na mai son tunano abu. Har kusan minti ɗaya sai kuma ya ɗago yana girgiza kansa. “Na manta yallaɓai. Saboda kwanakin sun ja da yawa”. “Uhhm yayi ƙyau” d.c.o ya faɗa yana kallon yaronsa. “Azo da yaran nan su duka”. Kai yaron nasa ya jinjina cikin girmamawa. Fita yay babu jimawa sai gashi ya dawo tare da samarin farko da aka fara kamawa. Yanda suke kallon saurayin haka yake kallonsu. Duk da babu duka ko zagi da akai musu zaman waje ɗaya da ɗan karan Dauda yasa duk sunyi wujiga-wujiga dasu.... “Kasan waɗan nan?”. “Eh yallaɓai na sansu, su duka abokaina ne. Tare ma muke harkar napep ɗin ma.” “Kace ka manta mi kayi ranar goma ga watan nan da safe ko?”. “Eh yallaɓai a gafarceni”. D.c.o baice dashi komai ba. Sai abokinsa ya kalla ya ce, “Kai tuna masa”. Kai tsaye abokin nasa ya ce, “Kazo ɗakinmu ni da ƙanina bayan sallar asuba dan gari ma bai gama haske ba. Kace na baka makulin mashin ɗin Imran zakaje amso saƙo tasha kai taka tayar na gareji dan naka babur ɗin ya samu matsala tun jiya sai barinsa ma kayi ya kwana a gareji kan yau zaka kai musu tayoyi da zasu canja maka. A gaban ƙanina Isa akai komai kuma”. Da sauri ya dafe kansa ya ce, “Tabbas anyi haka Salisu. Tabbas abinda ya faɗa gaskiyane yallaɓai, amma a gafarceni inada yawan mantuwa ne wlhy. Na amshi mashin ɗin, abinda nace kuma zanyi naje nayi da shi”. “Masha ALLAH haka muke son ji ai dama. Ina ka kai yarinya to? Sannan waye ya sakaka kidnapping ɗinta? Ko raɗin kanka ne kawai?”. “Ya salam kidnapping kuma? Ni banyi kidnapping kowaba ranka ya daɗe. Duk wanda ke tare dani kuma yasan wannan ba aikina bane ba inada sana'a. Taya ma kuma na rasa wanda zan ɗauka sai Sam-G”. “Ƙarya kake yi, a waccan ranar ba gareji kaje da napep ɗin abokinka ba Yakasai kaje layin gidan su Samraah. Kai zaman jiranta na kusan mintuna talatin da huɗu. Zata iya yiwuwa kasan dama zata fito a lokacin ne. Dan haka tana fitowa da shirin tsaida abin hawa kazo ka ɗauketa. Ka tsaya a dai-dai fita anguwar ta titin bayansu gaba ɗaya. Ka cire wayarta da facemask da eyeglasses ɗinta ka ajiye saboda maybe kana tunanin za'a iya ganeka ko kuma wanda ya saka ka aikinne ya baka umarnin yin hakan. Ɗan saurayi ban kawoka nan dan ka raina min hankalina ba. Amma kana da zaɓi guda biyu. Fitomin da komai a yanda yake dan ka samu sassauci ko cigaba da raina min hankali na saka ka faɗa ta dole wanne ka zaɓa?”. Ɗan jimm yay na wasu sakanni, sai kuma ya sauke numfashi da faɗin, “Zan faɗa maka gaskiya yallaɓai....... 🌟(✧✧)🌟(✧✧)🌟(✧✧)🌟 Cikin fisgar zaren da suka ɗaure min ido naji sun warwaresa. Har sai da na ɗan ciza lips saboda yanda naji zafi, amma dai na dake ina mai buɗe idanun nawa a hankali, dan zan gama da ogansu ne sannan na dawo kansu shegu masu suffar bakaken aljanun kan kuka. Sosai gabana yay masifar faɗuwa dan kai tsaye idanuna akan mutumin dake zaune cikin kujera yay crossing ƙafafunsa idanunsa a tab.. dake a hannunsa suka sauka. Ga wani daddaɗan ƙamshinsa da ya cika min hanci da gauraye falon gaba ɗaya. Fuskarsa ciɗin-ciɗin kamar bai taɓa sanin abinda ake kira dariya ba ko saƙon wani bala'i ya riskesa a yanzu. yauma akwai kitso a kansa guda biyu rak da suka zanu tamkar an zana a takarda dan zaka rantse ba hannu ya kitsasu ba, sai farin sirrin gilashi da ya zauna masa ɗaram a fuska tamkar an haliccesa da shi ne. Yatsunsa biyu ya ɗan juya, da sauri sangama-sangaman samarin nan da suka rakoni da bindiga duk suka fice aka bar abokin cin mushen nasa kawai. Sai lokacin ya ɗago ya zuba min cat eyes ɗinsa. Kallon ido cikin ido mukaima juna. A take naji ciwon marata na neman dawowa sabo fil, ba shiri nai saurin duƙar da kaina ƙasa zuciyata na wani kalar masifaffen bugu kamar zata faso ƙirjina ta fita. Amma cikin ƙarfin hali na murguɗa masa baki bayan na saukar da idanun. Shima janye nasa yay cikin yanayin isa da ƙasaita. “Sit!” ya faɗa a daƙile yana maida kansa ga tab ɗin tasa. Duk da na gane dani yake banyi abinda yace ɗin ba har sai da yaronsa ya sake maimaita min a ɗan tsawace. Ta ƙasan ido na hararesu su duka, kafin na kai zaune saman lallausar kujerar falon, amma sai yaron nasa ya daka min tsawa da mun nuni da wai na zauna ƙasa. (Munafuki ɗan baƙin ciki) na faɗa a raina, a zahiri kam hararsa na sake yi sannan nayi yanda yace na zauna ƙasan carpet ɗin da ko makaho ya laluba yasan ya haɗu. Jikina na ɗan takure a waje ɗaya, na tallafo ƙafafuna duka da hannayena biyu idanuna na kallon carpet ɗin. Sai da kusan mintuna uku suka sake shuɗewa babu alamar zai sake magana, sai kuma a cikin daƙilalliyar muryar nan tasa ya ce, “Wa kike ma aiki a kaina?”. Sosai tambayar tai matuƙar bani mamaki, har takai na ɗago na ɗan kallesa. Amma a mamakina bama ni yake kalloba, wasu files ne a hannunsa yan rubutu a ciki ya ajiye tab ɗin yanzu. A hankali na maida kaina na duƙar, nima sai da na kwashe wasu sakanni kafin cikin siririyar muryata da yanayin gafara na bashi amsa, “Ni nafi ƙarfin yima kowa aiki ai, dan ni ma ɗin gayyace”. Shiru baice komai ba, dan haka na cigaba da ƙunƙuni ƙasa-ƙasa batare da tunanin zasu ji ni ba. (Ni ai nafi ƙarfin aiken wani, sai dai zuwan kai da kai. Dan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE ai. Idan kuma baka san haka ba kaje kayi bincike. Ashe ma matsoraci ne, tunda har baka iya fito na fito sai ta YAƘIN SUNƘURU...) Harara yaron nasa ya zuba min. Kafin cikin kakkausar murya ya furta, “Hattara dai ƴammata. Dan ba'a ado da furuci wani lokacin takobin yanka wuyan mai shi yake zama. Nan ba gidan jarida bane, fadar SARKI ce mai cikakken iko kike.” Murtanin harar nima na maida masa ƙasa-ƙasa. Sai dai na gagara iya cewa komai saboda yanda ogan nasa ya tsareni da shegun kaifafan idanunsa na maguna. Tsahon lokaci falon shiru, yayinda tuni ya janye idanun ya maida ga abinda yake yi. Sai zuwa can a wani irin daƙile ya furta, “A duk sanda wani ya nema shiga min hanci nakan ji farin ciki da mazantakar fyatosa. Shiyyasa abinda yafi birgeni a duniya sune mutane irinki masu taya business ɗin da bai shafesu ba. Well ba tabbatar miki da ni waye yasa nasa a kawoki nan ba, dan inada tarin ayyuka na kai da kai matuƙa. WAYE YA AIKO KI WAJENA?”. Takaicin maganganunsa yasa bamma san sanda na furta, “Umarnin kaina nake bi ni, na kuma faɗa ai”. A harzuƙe yaronsa ya katseni da faɗin, “Be careful ƴammata. Walƙiya ba tana nufin ado ne kawai ga sararin samaniya ba. Takan zama gargaɗi ga ma'abota shagala ne. Jirgin ƙasa duk ƙawatuwarsa a hanyarsa kawai yake iya tafiya, saɓanin hakan faɗuwar baƙar tasa zaiyi ta yanda ko kufansa bazai moru ba balle ma'abota shiga cikinsa. Ki dinga bambance tsakanin sama da ƙasa a duk lokacin da kikai tunanin hawa tsani da tunanin taɓa rana ko farin wata. Dan batun wanda zashi sama ya taka leda zance ne kawai irin na masu iya magana.” Baki na laɓe tare da watsa masa harara ta ƙasan ido. Cigaba yay da faɗin, “Kina da zaɓi biyu, bada abinda ke hannunki ki koma ki cigaba da rayuwarki cikin salama, ki kuma sakama ranki baki taɓa ganin komai ba a wacan ranar, ko nuna taurin kai ki dawwama anan har ƙarshen numfashinki, kin buƙaci 500m an baki rabinsu, amma ke kin kasa cika naki alƙawarin duk da an tabbatar miki idan kin bada za'a baki sauran 250m ɗin. Ke kin san kuwa dawa kike tare ana?”. Yanzu kam sosai na ɗago a razane matuƙa, tare da wurga masa hararesa dan naga yama fi ogan nasa zaƙewa. A kausashe nima na ce, “Lallai baka da hankali. Ni nace ku bani 500m?........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚_ _____________ _ADVERT👇👇_ MKBEES PERFUMERY _(GIDAN KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_ _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, _KAI DAKA FESA KAJI DADI NAKUSA DA KAIMA YAJI DADI.TOH KU MAR-MATSO KUSA_ _MUN KUMA ZUWA DA KAYAYYAKIN_KAMSHI MASU SANYA NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI _*KU GARZAYO MKBEES PERFUMERY _DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN CHADI DA SUDAN AKWAI OIL PERFUMES,AIR FRESHNER, CARPET SPRAY DA TURARUKAN MOPPING DANA WANKA DANA GADO,LABULE DA KUJERU , BANDAKI DA DRAWER . _AKWAI TURAREN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DAHANA TSAMIN GASHI DA KUMA LAUSHI. AKWAI HODAR HAMMATA ME TAIMAKAWA WAJEN HANA WARI DA TSAMI ACIKIN LOKACIN ZAFIN NAN,AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYEN DAYA DAYA. •_ _ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._ _INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN MKBEES PERFUMERY. KO BAKU SIYA KAYA BA KUYI SAVING NUMBER DINTA KUFADA MATA TAYI SAVING NAKU DOMIN KOYON DUBARUN KASUWANCI KYAUTA A STATUS DINTA. _NAMBAR WAYAR SU: 07011113951,07032456061. INSTAGRAM :Mkbees_perfumery. _YOUR NUMBER ONE PLUG FOR KOMAI KAMSHI A TRIAL WILL CONVINCE YOU. _______________ .......A kausashe nima na ce, “Lallai baka da hankali. Ni nace ku bani 500m?. Aikin naku ya wuce kisan kai da kidnapping harda sharri kuma. Lallai tatsuniyar gizo da ƙoƙi kenan young man, kasan kuwa gaibu ce dan hikimace kawai irin ta masu iya zance da rubuta hikayoyi. Idan har ka yarda ba'a mutuwa a dawo, to ka ɗauka abinda duk yake a hannun Samraah Gwarzo mallakinta ne ita kaɗai, ko a mafarki bazan taɓa cinikayyarsa da wani ba. An gaya maka nima faƙiriyace bana neman na kaina ne da zan zauna neman a bani fansar kuɗin jinin mutane akan video?. ALLAH ya sawwaƙe, Banyi lalacewar baƙar tasa ba ai, banga kuma wata dukiya da wani zai tara taja hankalina ba dan nima dai kasuwancin nan inayinsa. Ɗan jarin nan na dubu ashirin da ake rainawa na tara wataran sune zasu koma miliyan dubu ashirin ɗin. Dan haka kuma nema wanda ya amsa kuɗinku tun wuri amma ba ɗiyar Abdul-wahab ba. Idan kuma kaine ke yawo da hankalinsa ka faɗa masa gaskiya inma dan kaga baya jin Hausa ne, oho can dai muku matsalarku ce ma wannan dai. Dannni idan har Yaya Musaddiq da Mansoor na numfashi a duniya na maka alwashin nan da kwana takwas iyanzu ina can a tsakkiyar dangina suna shagalin taron bikin aurena tare da ni, yayinda ku kuma zaku kasance a police station kuna amsa tambayoyi”. “Yaro bai san wuta ba sai ga taka”. Yaron nasa ya faɗa “Babba bai san yaro ba sai ya latsa”. Na bashi amsa nima a kausashe ina sake balla masa harara kamar manyan idanuna da ke nuna yanayin bana jin daɗi zasu zubo ƙasa. Juyawa nai shima ogan nasa zan hararesa sai naga ya zuba min ido kamar wanda yay zurfi a tunani. Ban fasa hararar tasa ba, dan haka na maka masa kawai na ɗauke kai ina ƙunƙuni ƙasa-ƙasa (Garama ku sakan tunkan kuja a saka sunanku cikin jerin manyan ƴan ta'addan duniya dan wlhy tona muku asiri zanyi ni babu ruwana). Tsawa yaron nasa ya daka min alamar ya jini, duk da na tsorata amma mai kicin-kicin da fuska naƙi nunawa. Kuma bakina bai bar motsin ƙunƙuni ba. Wani shegen murmushi ogan nasa da tun maganar farko da yayi bai sake nuna yama san da zaman mu a falon ba ya saki. Tare da lumshe idanunsa cike da salo luuuu ya kuma buɗesu a slowly warrr. Batare da ya sake furta komai ba ya miƙe abinsa ya nufi wata hanyar gilashi data mamaye kusan bango guda na falon har kana iya hango ƙyawawan korayen ciyayin dake ta waje da ga nan, fita yay abinsa cikin wani irin takun mazantaka da nuna ƙarfin iko..... Wata ƴar siririyar dariyar da yaronsa ya saki ta sakani kallonsa. Ya rumtse hannunsa tare da nuna babban yatsar hannunsa kasa👎 yana wani ɗaure fuska ya furta, “Lallai na tayaki jaje ƴammata. Dan kin taro babban match da baki da defenders balle ƴan kallo. Tunda har kika bari boss ɗina ya taya wannan wasan sai kinyi dana sanin da sai tafi biliyan a cikin koguna biliyoyi. Dan shi giwa ne baya WAIWAYE. Sannan zaki ne ba'a gaba da gaba da shi. Ki jira TAKUN FARKO na wasan kawai, tun anan zaki raina kanki.” Baki na laɓe nima, tare da watsa masa harara. Cike da tsiwar ƙarfin hali na ce, “Shi kaɗai ka sani da dukkan salonsa. Abinda kuma ni zan iya sirrina ne, kaga kenan tsakanin ni da shi ba'asan maci tuwo ba sai miya ta ƙare a wasan. Dan haka ina baka shawara tunda kaine abokin sharrin nasa. Ka gaya masa da gaggawa ya maidani inda kuka saka aka ɗakkoni, idan ba haka ba, wlhy sai kunyi dana sanin shiga sabgata. Dan zan ajiye muku tarihin da bazaku sake gwada cutar da wani ba bayan ni. Koda kuwa kasheni kukayi fatalwata bazata barku ku zauna lafiya ba. Dan nasan abinda kuka iya kenan kashe mutane kuyi tsafi da jininsu ko”. Dariyar kularwa ya saki da faɗin, “Irinku dama boss yafi buƙata a wasa. Kema shaida ce tunda a gabanki ga faɗa da bakinsa. Tunda kin shirya game ɗin ga fili ga mai doki, ni dama nawa shawara ce. Kuzo ku maidata inda kuka ɗakkota”. Ya ƙare maganar ƙarshe cikin ɗaga murya. Baima gama rufe baki ba sai ga garadan ɗazun sun shigo kuwa.. (Tofa, Samraah miya faru kuma bayan hakan?). Humm Bily komai ma ya faru, dan zan iya ce miki a wannan gaɓar ma ne labarin ya ɗauki dai-dai saitin inda kowa ya kamata ya fahimci raunin daya taɓani da kuma nasarorin dana samu. Dan komai da kika ji a baya dai-dai yake da sharar fage. Konace shimfiɗar labarin. Amma kundinsa wannan gaɓar itace SHAFIN FARKO. An maidani ɗakin da aka fiddoni kamar yanda yaronsa ya bada umarni. Da ga haka ban sake ganin kowannensu ba. Sai dai ana kawo min abinci sau uku a kowanne rana. Kamar yanda na kasance a kulle a wancan gidan nan ɗin ma hakanne. Sai dai akwai masu tsarona anan, kuma na nan sun ma fi nacan firgitarwa. A ƙuntace nake matuƙar ƙunci, ga ciwon jiki dana zuciya. Ga kewar ahalina data masoyi. A kowane cikar minti ɗaya na agogo sai na lissafa sauran daƙiƙun da suka rage na cikar ranar aurena. Hakan yasa a duk sanda tunani ya nema fasan zuciya zaki sameni ina karatun Alkur'ani ne. Ina jin sauƙi sosai a raina, bayan na koma yin salla ma Alhamdullah na sake rungumar ibada ta. Dan akoda yaushe cikin kaima UBANGIJINA kukana nake. Ina kuma jin yaƙinin zai karɓa min.. Zakisha mamaki idan nace dake maganar da yaronsa yay na cewar na buƙaci su bani 500m kuma sun bada 250 a cewarsu ban wani sakata a raina ba. Danni a nawa wautar kawai sun faɗane bisa raɗin kansu da son min barazana ne dan na basu abinda suke son, dan haka na cigaba da harkar gabana kawai na manta da duk wani gargaɗinsu balle zuciyata ta fara min wani hasashe mai muhimmanci daya kamata ace nayi, ban san rashin yin shine zai zame min babban kuskure ba kuwa. Dan da'ace nayin maybe da abubuwa basu kasance a wani matsayi daban taɓa tsarama kaina ba bisa ƙaddarar rayuwa. Karna cikaki da zance muje zuwa dai..... 💞☞💞☞💞☞💞 “Ranka ya daɗe zan faɗi gaskiyar abinda ma sani. Sai dai yanda ka fahimci al'amarin sam ba haka yake ba. Wlhy wlhy duk abinda zan faɗa maka shine gaskiyar abinda ya faru. Tsoro ya hanani faɗar gaskiya tun ma a farkon fara case ɗin. Amma na gwada yin hakan tun sanda naji zancen ɓatar Sam-G da kuma kama Salis da akai. Ni bani na saceta ba, hasalima ban san ita za'a ɗauka ba. Wanda kuma ya ɗauketan wlhy ban san kidnapping ɗinta zaiyi ba. Kamar yanda na sanar ma abokina Isa da gaske na amashi mashin ɗin Salis ne a hannunsa domin zanje amsar sako tasha da aka turoma Mamana daga Maiduguri, da kuma tayoyi da za'a sakamin a nawa daya samu matsala. Na fito titin anguwarmu kaɗan wani bawan ALLAH ya tsaidani, banyi niyyar tsayawarba, saboda ina da uziri, ban fitoba kuma domin yin aiki ba. Gashi kuma safiya ce sosai dan ko haske gari bai gama yi ba. Sai dai ganin dattijo ne mutumin yasa naji tausayinsa. Dan harma na gotashi na dai dawo, tambayarsa nai inda zaije, dan naji ko yayi dai-dai da inda na nufa. Amma sai da ya shigo ya zauna yake gaya min. Ga abinda yace min da yasa na ɗaukesa tilas badan naso ba. (Yaro dan ALLAH ka taimaka min, Yakasai zanje, yarinyatace take da lalurar aljanu, jiya da dare muka nemeta muka rasa, sai ɗazun nan da asuba ƙanina yay kirana tana gidansa ta kwana acan Yakasai ɗin. To munsan zata iya barin nan ɗin akoda yaushe, kuma idan suka kaɗata bamu san ina zataje ba. Yanzu ma ko gidan bazamu ƙarasa ba zamu ɗan tsaya ne a kan layi data fito mu mata wayo, zan kira ɗan uwanta da zarar mun ɗauketa sai yazo ya ɗaukemu dan in kai tsaye ne bazata yarda ta shiga motarsa ba, amma idan na shaƙa mata maganinta zamu samu nasarar yin hakan). Yanda dattijon ke magana yasa na amince da shi, dan sam baiyi kama da wanda zai yi ƙarya ba, gashi kuma a cikin kamala. Lalura kawai daya kira yasa nai tunanin taimaka masa, dan nima ƙanwata nada irin makamancin lalurar, na kuma san irin tashin hankalin da muke shiga. Cikin nuna damuwa nai mata addu'ar samun lafiya, sannan na sanar masa gaskiyar ba aiki na fito ba, amma idan bazamu jimaba zan taimakesa, sai dai idan ta jima bata fito ba zan sakashi a wata napep ɗin ni na tafi uzirina dan abokina na jiran napep ɗin sa. Babu musu ya yarda da hakan har yana jeramin addu'oi ga hawaye yana faman yi. Ni dai na bashi haƙuri muka ɗauki hanya. Mun isa Yakasai, shine kuma ya nuna min inda zan tsaya, shi kuma ya fita ya maƙale a ɗan nesa dani. Nayi zaman kusan mintuna ashirin duk naji na ƙosa dan babu abinda nake sai faman tsaki, ina ma niyyar barin wajen ne sai gashi da saurinsa yake sanar min gatanan zuwa, dan ALLAH na taimaka kada na bari ta shiga ko wane mashin sai nawa. Yanda naga yana rawar jiki ga hawaye yana sharewa da gefen rigarsa yasa naji tausayinsa, duk kuma yanda ya tsara haka nayi. Mun fito a wajen mai saida lemo da aka tsinta wayarta daka faɗa yace na tsaya ga ƴaƴanta a mota.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_ .....Hakan kuwa akai na tsaya dai-dai motar dake a fake, wanda akace Yayanta ya fito cikin nuna alhini yana min godiya, su biyu suka kamata suka saka a motar, ni sai lokacin ma na lura sun shaƙa mata maganin da yace, amma sai ban kawo komai a raina ba tunda dai dama yace zai saka mata magani. Yayan nata ne ya bani kuɗi masu yawa, nace masa bazan amsa ba ni dan ALLAH nayi, kuma ma ai kuɗin daya bani sun wuce na hakkin aikina. Murmushi kawai yamun ya ajiye kuɗin ya faɗa mota. Daga haka suka wuce suka barni ina kallon kuɗin, wlhy ban san sun yadda wayarta da facemask harda eyeglasses ba. Kuma suma ina ƙyautata zaton basu san sun faɗi ba kuskure kawai aka samu maybe. Suna wucewa nima na wuce, ban kuma san mike faruwa ba sai da yamma nake jin labari, abinda ya tada min hankali shine yanda ake misalta al'amarin yayi dai-dai da abinda ya faru da safe ni da dattijo, washe gari kuma sai naji batun kama Salis dangane da napep ɗinsa. Wlhy iya abinda nasani kenan, amma banda alaƙa da ɗaukar tata nima sai da naji daga baya hankalina ya tashi wlhy. Dan da nasan abinda zasuyi kenan babu yanda zan taimakesu, idan ma naga sunfi ƙarfina zan kira ƴan sanda. Dan ka tambaya kaji munsha irin wannan taimakon, adalilin haka har karyani an taɓayi abokaina gasu nan shaida ne”. Shiru d.c.o yay na wasu mintuna kamar mai nazari, sai kuma ya sake kallonsa ya ce, “Zaka iya gane mutumin da saurayi yanzu idan ka gansu?”. “Tabbas zan iya ganesu musamman ma dattijon duk da ya saka hirami a kansa ranka ya daɗe”. Kai kawai d.c.o ya jinjina batare da ya sake cewa komai ba ya bama yaransa umarnin a maidasu cell. Hakan kayi, bayan an maidasu ya zauna da yaronsa dake kan case ɗin. “Ɗan Bakori mika fahimta a zancen yaron nan?”. “Ranka ya daɗe al'amarin ne akwai wuyar sha'ani, amma dai kamar akwai ƙamshin gaskiya a zancen nasa. Wani abu dana fahimta shine amfani kawai akai da shi, kuma tabbas in har da gaske bashi da hannu duk waɗanda sukai abun to sun sanshi dan dole sunada kusanci koda ta zaman anguwa ne. Shiyyasa sukai masa wayo da batun iska tunda sun san ƙanwarsa na fuskantar irin matsalar zai fi saurin afkawa. Zancen daya faɗa ya taɓa samun karaya akan taimakon wata yarinya kuwa gaskiya ne. Dan na samu wannan labarin a binciken da nayi tun a farko. Mutanen na shegune suna da wayo, kuma sun shirya komai yanda suke so kafin su tunkaresa. Abu na ƙarshe bana raba ɗayan biyu duk wanda yay aikin nan na jikinta ne, ta sanshi ya santa sosai, dan inba haka ba tayaya suka san zata fito a lokacin tunda ba ranar aiki bace ba?”. “Tabbas zancenka na akan hanya ɗan Bakori. A wannan gaɓar dole aikinmu ya ɗan sake komawa baya kaɗan. Wayarta da aka tsinta daga biyar na yammacin ana gobe abin zai faru har washe gari a duba dawa tai waya? Waye yay kiranta? Koya turama saƙo koya turo mata.” “Okay Sir, amma naji kamar Yayanta yace da waya biyu take amfani, kuma sun wuce da ɗayar”. “Wannan ba damuwa bane, duk da dai ta wani fanin kasancewar wayoyin duka biyu zai fi mana. Amma ɗayar ma zata taimaka mana. Dan kamar yanda yaron nan ta faɗa sam basu san sanda ita wannan wayar ta faɗi ba kuskure aka samu. Itama in sha ALLAHU zamu samu abinda zai taimaka mana ku bincika”. Cike da gamsuwa ɗan Bakori ya miƙe tare da yin salute ɗin sa sannan ya fita da sauri.... 💥💫💥💫💥💫💥 Ɗan taku yake cikin kai-kawo babu alamar rikicewa ko shiga wani yanayi a tare da fuskarsa a bayyane. Sai dai a can ƙasan zuciyarsa auna komai daya fita daga bakin Samraah yake kalma bayan kalma. Tare da ajiye kowanne word a mizanin hankali. A wannan yanayin Hayatu ya samesa. Ganin a yanayin da ogan nasa yake sai ransa ya ƙara ɓaci shima, dan haka a harzuƙe ya ce, “Sir yarinyar nan fa nada ɗan banzan wayo, ga bakinta kamar reza baya mutuwa. Ƙarya take tasan komai tana pretending ne kawai. Ba gashi yaron nan da aka amsheta a wajensa yace itace ta sakashi yay kidnapping ɗinta Dan ta bada ƙafa......” Wani irin murmushi Maash daya kafa masa ido ya saki a karo na farko, sai kuma ya girgiza kansa kawai tare da janye idanun ya maida kan ƙyawawan firannin fulawoyi da aka ƙawata wajen da su, baka jin komai sai daddaɗar iskar da suke badawa da ƙamshinsu a wajen. Shiru bashi da niyyar cema Hayatun komai har shi Hayatun ya ƙosa da shirun nasa duk da ba sabon abu bane a wajensa. Dan inma bai gadama ba zai iya sharesa yaƙi cewa komai kuma shikenan amsar tabi ruwa. Sun kai tsahon mintuna uku a haka kafin cikin silent voice ɗinsa a can ƙasan maƙoshi a daƙile ya furta, “Hayat be a man mana. Kullum ina sanar maka ka dinga lissafi akan abubuwa. Amma na fahimci brain naka harkar business kawai take iya ganewa. Mizai hana a duk sanda baka fahimci miya dace akan abu ba ka dinga bashi lokacinsa dan ka fahimta. Ina matuƙar tsoron kada maƙiyan dake bayana suyi amfani da wannan ruɗanin naka da rashin hange wataran su ci nasara akan ka. Yarinyar tanada tsiwa da raini. Sannan harshenta nada kaifi. Zan mata hukunci dai-dai da wautarta. Kuɗina kuma nasan inda suke, zakuma su dawo nan bada jimawa ba batare da rasa ko naira ba a cikinsu. Video kuma dake hannunta muna farautarsa ne mu da su a hannunta, sai dai basu san MAASH ba shashasha bane irinsu. Zan tabbatar musu kuma da hakan, dan a matakin wasan farko da su zan fara buga game ɗin kafin na dawo kanta. Ka siyama Sani ticket a yau ɗin nan ya biyo jirgi zuwa Abuja. Hakama Abubakar ina son ganinsa yau da dare”. Daga haka ya juya ciki batare da ko waiwayen Hayatu ba. Da kallo Hayatu ya bisa galala kamar idanunsa zasu zubo. A zuciyarsa ya shiga faɗin, (Idan nace mutumin nan Aljani ne ace ba haka ba. Yanzu dan ALLAH duk wannan zaƙewar da nake dama ni yakema kallon wawa? To wai tsaya ma. Shi abinda ban gane ba anan. Kuɗi dai ni aka saka na turasu a account no.. da mutumin ya turo. Kuma ni da shi mun tabbatar da sabon account ne aka buɗe muna saka kuɗin kuma aka ciresu tare da blocking account ɗin ma gaba ɗaya. To shi tayaya ya bibiya ya gano komai? Mutumin da kullum damuwarsa maida naira ta zama dala. Kai nikam fa na fara tsoron boss ɗina. Ko yanzu ma ji nake zazzaɓi na nemam rufeni, dole ne sai naje asibiti naga likita). Ya ƙare zancen zucin nasa da kai hannu ya taɓa goshinsa da wuyansa kamar wani ƙaramin yaro. (HAYATU na buƙatar ganin dacta. Likitocin gidan nan ku fito ku bashi agaji🤣😂🙏) 💞✨💞✨💞✨💞 A lokacin da ƴan sanda keta nasu ƙoƙarin, a ɓangaren Yaya Musaddiq shima yana can tare da su Kawu Musa da sukazo da ga Gwarzo. Ba wannan ne zuwansu na farko ba. Sun dai sake dawowa ne suji yaya ake ciki duk da suna waya da Musaddiq ɗin akai akai game da al'amarin. Da ƙyar Mum ta yarda ta basu abinci, dan saida ma Abba ya nuna mazantaka yau. Bayan sun gama cin abincinne suka zauna tattauna abinda ya kawosu. Kawu Lurwani ne ya fara magana alamar shi suka wakilta yayi. Sai da ya kalla Abba da Musaddiq sannan ya fara faɗin. “Wato Imamu magana ce mai muhimmanci ta kawomu nan tare da sake jajantama juna akan batun yarinyar nan. Al'amarin nata akwai mamaki da ban tsoro ƙwarai matuƙa. Dan zuwa yanzu dai duk mai hankali ya kamata ya fahimci ba waɗan nan mutanen bane masu cewa a basu kuɗi idan sun kama mutum. Dan da ace hakanne da tuni sunyi maganar kuɗin. Amma gashi yau har kwanaki goma sha uku da rasata babu wani bayani. Hakan na nufin aikin magautane tunda yarinya ce mai farin jinin mutane sakamakon aikinta. Yanzu mu kai tsaye bazamu ce ga wanda yay wannan aika-aikar gareta ba damu ma kammu da ke a cikin tashin hankali. Bamu ce kuma ƴan sanda sun gaza ba, dan suna iya ƙoƙarin su suma. Amma magana ta gaskiya bai kamata muma mu rungume hannu muna jiransu ba.....” “To Lurwanu yaya zamuyi idan ba hakan ba. Aikinsu ne ai, sune kawai suke da dabarun bincike, dan a yanzu haka since wanda ya ɗauke ta a napep yana hannunsu ma, sai dai yaƙi amsa laifinsa”. Abbane yay maganar cikin katse Kawu Lurwanu. Kai Kawu Lurwanu ya girgiza, “To ai ban kai ƙarshe ba nima ka katseni Imamu, abinda nake so nace bafa zama zamuyi mu rungume hannaye muna jiransu su kaɗai ba. Kamata yay muma mu saka roƙon ALLAH tako ina. Sai dai kasan mu ɗin ba masu ƙarfi bane, kuma al'amarin yana buƙatar sadaka. Dan haka muka yanke hukuncin dawo da waɗan nan kuɗi na aurenta da aka karɓa, dan dubu ashirin kawai mukaci a ciki aka ajiye tamanin akan idan lokaci yayi zamu ƙara da wasu a rage maka hidima. Kaga kaima saika kawo wani abu daga cikin wanda ke hannunka a haɗa a sai abinci da wasu abubuwa aita sadaka ana addu'a sai kaga anci nasara ALLAH ya bayyanata cikin sauƙi. Dan yarinyar nan kullum kwanakin bikinta sake matsowa sukeyi, dan ma yaron kirki ta samu, kuma danginsa basu da fitina, amma wlhy da wasu ne da yanzu sun fara zame-zame akan al'amarin nan. Amma kaga yaron nan da shi aketa faman faɗi tashi na son ganin an samota har ma da iyayen nasa. Amma yaya ka gani shawara ce?”. A ɗan fusace Abba ya ce, “Ni gaskiya babu kuɗin nan yanzu a hannuna. Sai dai idan shi Musaddiq nada su ya aramin idan na samu zan bashi”. Kaf falon babu wanda bai ƙwalalo idanu waje dan mamaki ba.......✍️ _Ai ni kaina idanun nawa a waje. Abba al'amarin ka ya fara ban tsoro da mamaki. Ya rabbi kasa mu rayu da ƴaƴanmu, maraici da banne wlhy a rayuwa😭_. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_ ........ Musaddiq ne kawai yay murmushi yana mai girgiza kansa. Ganin Kawu Musa na neman fusata dan dama shi akwai zuciyar tsiya yay saurin faɗin, “Uhm Kawu inaga babu damuwa ai. Kuma na wajenku ku barsu. In sha ALLAHU babu abinda zai gagara na sadakar. Ko daga gobe in ALLAH ya kaimu ake son fara duk abinda ya dace ni a shirye nake.” Sosai suke kallonsa zukatansu na ƙara rauni. Yaron jarumine na gaske da kowaɗanne irin iyaye zasu yi alfahari da shi. Gaba ɗaya halin Musaddiq irin na mahaifinsa ne. Ga sanyin hali ga haƙuri ga kirki da jarunta. Sun nuna masa zadai su bashi kuɗin amma ya dage kan bazai amsa ko sisi ba. Dole suka haƙura suka barsa. Ƙyawawan halayen yaron na sake saka musu jin kunyar wofamtar dasu da sukayi a lokacin da suke matuƙar buƙatar tallafinsu, amma kuma bakin alƙalami ya riga ya bushe yanzu kam sai dai haƙuri, dan ta wani ɓangaren suma ba laifinsu bane. Ƙanin mahaifiyarsu ne ya nuna musu shi ɗan boko ne kawai sjiyyasa sukai zuciya suka bar masa su. Kaf abinda ya faru a zaman sai da Mum ta tsare Abba ya sanar mata. Aiko ta sake zugesa akan babu wata addu'a sun zo ne kawai su yaudaresa su amshi kuɗin. In ba hakaba wace addu'a ce za'a wani ce sai da kuɗi. Daga ƙarshe ta sake ingizashi kan ya binciki Musaddiq duk yanda akai yaron kuɗine da shi, in ba hakaba taya komai ya taso sai yace zai yi. Daram kuwa ya hau ya zauna ko kunyar ALLAH babu washe gari yay kiran Musaddiq yay masa tujara. Ya kuma ce yana buƙatar 1mil a wajensa da za'aima Samraah kayan ɗaki, sannan ya bada kuɗin kayan kitchen suma Mum zatayi masa list ɗin komai. Sai da ya gama sauraren Abba kaf sannan yay murmushin sa mai sanyi. Cikin nuna rashin wata damuwa a fuska ya ce, “Ba damuwa Abba ka saurareni zan samo in sha ALLAHU”. Sallamarsa Abba yay yana ƙara jaddada masa. Yana fita Mum tai wuff ta fito alamar dama laɓe tai musu. Zama tai kusa da Abba tana faɗin, “Bana gaya maka ba Abban Abbas. Yanzu ka yarda ko? To ALLAH kaɗai yasan mi yaron nan ya tara yake raina mana wayo ya barmu da nauyin hidimar rawuwarsu. Ana gama hidimar bikin nan ya kamata ka sashi ya bama Abbas jari yabar wannan gantalin rashin aikin, sannan itama Baby ta fito da miji dan nagaji da yawon nan nata haka nan”. Babu wani dogon nazari ko tunani a wannan magana Abba ya amsa Mum tare da bata goyon baya ɗari bisa ɗari. Daga haka suka cigaba da hirarsu cike da soyayya. A ɓangaren Musaddiq kam shi al'amarin su Abba kam ya fara bashi tsoro. Dan ya wuce abin mamaki ko al'ajabi. Amma dai a wannan karon zai ari halin Samraah ko kaɗanne ya gani ko zasu fahimci shi ɗin bawai sakarai bane. Yana binsu ne kawai da halayensu saboda wasu dalilai. Yanzu banda rashin adalci bama damuwarsu ɓatar ƴar uwarsa ba kusan sati biyu kenan, shi dama gani yake Mum da Baby kamar farin ciki suke da rashin Samraah a gidan. Ko mi tai musu haka da zafi oho ya kasa fahimta. Yasan Samraah fitinanniya ce, to amma duk abinta saika shiga sabgarta ne, kuma mafi yawan lokaci sune ke fara takalarta ita kuma ta maida murtani. Washe gari kamar yanda suka tsara aka fara gudanar da addu'oi. A masallatai da islamiyoyi, aka kuma dafa abinci aka dinga rabawa mutane musamman ƙananun yara da almajirai. Dan har tsangayoyi aka kai abincin ma. Acan gwarzo ma su Kawu Musa abinda sukai ƙoƙarin yi kenan da kuɗin da Musaddiq ya basu. Dan Mansoor ya taimaka musu sosai da yaji shirin nasu. Dan ko abincin nan ma da aka dafa anan shine ya bada aka dafosa da taimakon Mamynsa. Kwana uku anata addu'oi da raba dafaffen abinci. Ga kwanakin biki nata sake matsowa daf. Gefe Musaddiq nata wasan ɓuya tsakaninsa da Abba da Mum. Yayinda su kuma suke zaman jiran a kawo musu kuɗi..... ✨★✨★✨★✨ Tabbas duk wanda ya miƙa al'amarinsa ga UBANGIJI babu shi babu taɓewa Bily, naga fa'idar hakan ƙwarai da gaske a wannan gaɓar. Domin kuwa duƙufar da nai wajen gayama UBANGIJI damuwata ya saka min ƙwarin zuciya da jin sabon ƙarfi na dawo Samraah ta tada. A daren da nake lissafin kwanakin aurena da Mansoor saura biyar kacal a bazata naji ana ƙoƙarin buɗe ɗakin da nake. Hakan ya bani matuƙar mamaki dan ba lokaci bane da ake kawo min abinci, kusan ƙarfe goma da wasu mintuna ake yanzu na dare. Hijjabina daya kasance ɗaya jal da nake salla da shi na ɗauka da sauri na saka. Bamma kai ga ƙarasa sakawarba har an riga an shigo. Baki na buɗe cikin ɓacin rai zanyi magana kawai ya jefamin wata muguwar harara. Ba kowa bane face yaronsa ɗin nan mai dogayen kunnuwa uwa na zomaye. Nima hararsa nai da mare baki, a fili na furta, “Daka daina burga dan baka da banbanci da damisar takarda. Kullum kana bayan wani kamar mai gadi”. A take fuskarsa ta rine zuwa ɓacin rai, ya ɗaga hannu kamar zai ƙwaɗan mari sai kuma miya tuna oho masa ya fasa. Ya dunƙule hannun yana ɗan kaima iska naushi a cikin takaici. Ni dariya ma ya bani, amma sai na dake banyi ba. A cikin zafin rai ya furta “Shigo ki mata”. Ban gama hahimtar mi yake nufi ba likitar ranar data dubani akan matsalar ciwon mara ta shigo. Matar ƴar gayuce sosai. Da gani kuma kasan itama ƴar masu kuɗice. Murmushi tai min cikin tsokana tace ashe dai patient ɗina ta miƙe?”. Watsar da ita nai kamar banji mita faɗa ba, dan haka kawai bata mun ba, nama ɗauke kaina gaba ɗaya. Magana tai yunƙurin sake yi mai kunnen zomaye ya dakatar da ita cikin magana zafi-zafi ya ce, “Doctor kimata kawai”. Itama amsa masa tai da to tana zaro syringe. Kambu idona idon allura na zabura zan miƙe, sai dai mi jinai kawai an damƙomin hannu an riƙe, kafin na farga ta saka min handcuffs. Ido rufe na buɗe baki zan balbaleta da masifa ta shamaceni kawai sai shigar allura naji a hannuna. Kafin wani dogon motsi ta zareta tana sauke ajiyar zuciya kamar daga jikinta take cirowar. Kaina ne ya fara juyawa na koma ganin ɗakin da su kansu bibbiyu, da ƙyar na iya ɗaga hannu ina nunasu amma na kasa magana. Dan idanuna lumshewa suke kaina na ƙara nauyi, a cikin abinda bai wuce minti ɗaya da wasu sakanni ba komai ya koma min ɗiff. Sai buɗe idanuna nai na ganni a inda banyi zato ko tsammani ba.... 💫💥💫💥💫💥💫 Duk da tasowar hadari mai ƙarfi na farkon damuna bai hana Musaddiq tashi ba jin an ƙwalla kiran sallar asubahi. Ya fara alwala aka fara yaf-yaf na yayyafi. A gagauce ya ƙarasa ya wuce massalaci. Kamar jira ruwan nan yake a idar da salla ya fara sauka da ƙarfinsa. Kusan duk wanda ke a massalacin da gudu-gudu ya fita domin shiga gida. Hakance ta kasance tsakanin Yaya Musaddiq da Abba. Kusan a tare suka ja wani bahagon birki a ƙofar gidan sakamakon cin karo da abinda basuyi tunani ba ko zaton gani haka. (Tabbas Samraah ce ba gizo bane, ba kuma mafarkin daya sabayi bane ba). Musaddiq ya ayyana a zuciyarsa dake faman gudu da uban sauri a cikin ƙirjinsa. Da sassarfa ya ƙarasa inda take. Dai-dai nan ta fara motsa jikinta sakamakon ruwan sama dake sauka da ƙarfi. Kuka Musaddiq ya saki tare da durƙushewa a gabanta. Gaba ɗayanta ya wawuso ya rungume a jikinsa. Hakkane ya saka Abba dawowa hayyacinsa shima ya nufesu. Cikin rawar murya data jiki ya furta, “Musaddiq da gaske Samraah ɗin ce?”. Bai jira amsarsa ba shima ya kai durƙushe gabansu. Duk wanda yazo gittawa ya gansu sai ya tsaya. Kafin kace mi maƙwaftansu sun ɗan taru a wajen. Duk mazane da aka dawo daga massalaci. Maƙwafcinsu da suke katanga ɗaya ne ya bada shawarar a shiga da ita cikin gida. Wannan shawara tasa ta saka Musaddiq miƙewa ɗauke da Samraah. Ta farfaɗo amma bata iya banbance komai kamar wadda ke a buge cikin maye. Wannan yanayi nata yasa da yawan wanda suka taru a wajen ransu ya ɗarsu da abinda bashine ba. Abba ne ya shiga kwala kiran sunan Mum. Sai gata a firgice. Da alama ma ita sai yanzu take tashi sallar. Su Baby ma ihun Abban ne ya tashesu a nasu barcin suma duk suka fito. Kowa yaci karo da Samraah sai yay wani irin ja da baya yana zaro idanu. Musaddiq ne kawai keta ƙoƙarin ganin ta buɗe idanunta da take lumshewa da buɗewa da ƙyar tamkar me maye. Kusan mintuna biyar kafin ta buɗe idanun da ƙyar sosai ta kallesa. Cikin siririyar muryarta data surka da mayen barci ta ce, “Yay..a Mu...sad...diq”. Jikinsa har rawa yake wajen amsa mata da, “Na'am Samraah! Kandalata nine. Buɗe idonki da ƙyau ki sake ganina. Alhamdullah ya rabbi Alhamdullah.” yanda yake sambatun yana hawaye ga dariya sai ka ɗauka ya zautu ne. Su dai su Mum na tsatstsaye ciko-ciko kawai suna kallonsu. Musaddiq da duk ya gama rikicewa ya zaro wayarsa da sauri. Mansoor ya fara kira, dan abokin kuka shi ake fara gayawa mutuwa, wani ihun farin ciki da Mansoor ɗin ya saki sai da ya janye wayar dan jin zai fasa masa dodon kunne. Daga nan yay kiran d.c.o shima dan ya sani. Shima yanda yake ta jera Alhmdllh zai tabbatar maka yaji farin cikin. Suma yan gwarzo yay kiransu ya sanar musu. Ai kafin kace mi anata shigowa gidan, dan Mansoor ma cikin ruwan nan ya taho duk da gari bai gama washewa ba, sai daga baya jama'ar gidansu suka biyosa. Sanda suka taho an wuce da Samraah asibiti domin duba lafiyarta kamar yanda d.c.o ya bada umarni. Dan sam Samraah bata cikin hayyacinta saboda allurar da sukai mata.......✍️ _Hummm dangin Samraah sai a barmu mu hyaƙata, ga ƴarku nan mun sakar muku. Su o'e duk an addabemu dama🚴🚴😞._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ .......Lokacin da goma tayi gidajen rediyo dana tv da yawa sun sanar da ganin Samraah. Gidan tvn su ne ya fara fitar da batun, dan danan sai ga ƴan jarida. Sai dai an hanasu kowace irin dama ta ganin Samraah, dan har lokacin barci ma takeyi ita. Ƴan gidansu ma da ƴan gidan su Mansoor duk suna daga waje ne. Sai wajen sha ɗaya ƴan Gwarzo suka iso suma. Nan fa asibitin ya ƙara cika. Dole doctor ya roƙa su ragu. Dan ana buƙatar sanda zata farko ta farka a cikin hayyacinta. Gamsuwa da hakan yasa aka ragu, Mansoor da Yaya Musaddiq da Abba sai Kawu Musa kawai aka bari, sauran duk suka wuce gida. Ƙarfe ɗaya da wasu mintuna Samraah ta farka. A lokacin babu kowa a ɗakin dan wanda aka bari asibitin duk sun wuce massalaci salla. Sai Nurse da aka bari ta kula da ita dan zata iya farkawa a koda yaushe. Hakance kuwa ta faru. Sai dai tana buɗe idanunta bakinta da addu'a Nurse ɗin nan ta miƙe. Sannu ta mata da farko, sai kuma ta ɗan fita kamar zatayi kiran Doctor ne. Babu jimawa sai gata ta dawo. A lokacin Samraah ta ɗan daddafa ta tashi dan wani irin fitsari take ji. Matsowa Nurse ɗin tayi gaban gadon tana mai cire wayar dake a kunnenta tai ɗan danne-danne da bai wuce sakan biyar ba ta nuna wayar akan fuskar Samraah dake kallonta. Dan ta rufe fuskarta ruff da face mask idanunta kawai ake iya gani. Baki Samraah ta buɗe zatayi magana da ƙyar dan ganin Nurse ɗin ta saka mata waya a gaban fuska. Amma saita mata nuni da wayar alamar nan zata kalla. Babu musu ta juya kanta a hankali tare da buɗe manyan idanunta da suka kumburo sosai sukayi ɗan ja a jikin fatar amma cikinsu tar-tar ta sauke su akan fuskar wayar. Numfashi ta nema janyo wa da sauri, amma hakan ya gagara sakamakon cin karo da fuskar wanda batai zato ko tsammanin gani ba shima ya zuba mata idanun nan nasa tamkar zai cinyeta ɗanya da su. Zaune yake ƙafa ɗaya kan ɗaya da salon zaman ƙasaitar nan tasa. A yanayin location ɗin da yake zai tabbatar maka da ba'a Nigeria yake ba ma. Duk da ta cikin wayane jinai kallonsa na neman yamutsa min kaina. Amma na dake a zahirance, sai ma wani irin mummunan kallo da nima nake jifansa da shi batare da nasan ina yi ba. Ƙara tsatstsareni yay da idanun cikin yanayin irin ke baki da kunya ko. Niko na yamutse fuska irin eh banda kunyar sai yaya. Hannunsa ya kai ya shafo gashin dake a haɓarsa, cikin salon ƙara tamke fuskarsa cike da gizago shi a dole bai san raini murya a kausashe ya fara magana da ƙyar dan yanda lips ɗin ma ke motsawa kaɗan-kaɗan sai ka ɗauka bazaka iya jin abinda yake faɗa ba. Amma kuma sai na dinga jin muryar tasa raɗam a kunnena kamar ba'a waya yake ba. “Ganinki cikin zur'arki bashi ke nufin wasan ya ƙare ba. Sai dai kina da zaɓi biyu. Bakin ki ya kasance shiru ki cigaba da rayuwa da waɗan nan mutane biyun”. Hoton Hafizzullah da Yaya Musaddiq ya bayyana. Bamma san sanda na waro idanuna waje sosai ba ina ɗan zabura. Shiko hankali kwance ya ciga da faɗin, “Ko ki buɗe sa da zance a kaina ni kuma na rufe miki shi ta yanda ko mai irin harafin farkon sunana kika ji sai kin firgita. Na barki lafiya”. Da sauri nima cikin jin wani ƙarfi na ce, “Yaƙin sunƙuru ai na mai tsoro ne. Idan ka cika namiji kabar laɓe-laɓe a bayan ƙarfin dukiya kazo muyi gaba da gaba sai a banbance waye jarumin tsakanin ni da kai. Ita Sam-G a ko ina Samraah ɗinta take, bana ado da wasu domin kare suna ko ƙarfin iko na. Sannan garkuwa da wasu domin cimma buri ai tsohon salo ne. Video ne dai bazan bayarba, kuma har abada bazaka taɓa sanin inda yake ba, kai ni kaina bazaka sake gani na ba”. Wani jahilin murmushi ya saki da sai da ƙirjina ya harba dan wani kalar mugun ƙyawunsa ne ya sake bayyana. Idanunsa ya ɗan lumshe da sake buɗewa a kaina cikin yanayin kallon ƙasa-ƙasa, bamma san na murguɗa masa baki da janye nawa ba. Ya ɗan taɓe baki cike da basarwa. Tare da motsa lips ɗinsa a daƙile ya ce, “Ina matuƙar son wasa da mutum irinki mai taurin kai da kaifin baki. Dan haka kar kiyi gaggawa, in dai yaƙin gaba da gaba ne yana tunkaro ki, dan haka jekiyi shiri na musamman, dan yaƙi da Awwab Maash dai-dai yake da tunkarar mayaƙan duniya. Bye sai mun haɗu a filin daga”. Ya ƙare magana da salon kashe ido ɗaya ya ɗaga min yatsu biyu. Ai bamma san na zabura baya ba ina waro idanuna gaba ɗaya waje dan al'ajabi, ka jimin kwarto zai iskantani, dan wannan abun da yay ai na ƴan iska ne. Baki na buɗe zanyi magana. Ɓat ya ɓace tamkar bai taɓa bayyana a fuskar wayar ba. A hargitse na kalla Nurse ɗin da ke ƙoƙarin amshe wayarta. Itama ni take kallo. Cikin tsumar jiki na ce, “Malama sake kiransa!”. Baki taɗan taɓe, a gadarance ta ce, “Ai shi Boss GIWA ne baya WAIWAYE.” Cikin ɓacin rai na ce, “Wacece ke?”. “Sanin wacece ni bazai amfaneki da komai ba. Kare rayuwar ƴan uwanki biyu shine mafi muhimmanci gareki da yin shirin yaƙin dake tunkaroki kamar yanda ya faɗa a yanzu, dan shi baya magana biyu, kada ki sakankance da yawa, in har yace zaiyi, to lallai ya gama shirya yin ne. Idan yace bazai yi ba, babu mai sakasa yin. Zan sake baki shawara akan abinda boss ya faɗa miki. Idan kin kiyaye tabbas kin tsira, domin shi tamkar ifiritin ALJANI yake. A duk inda kika saka ƙafarki yanzu ki ɗauka yana biye dake ne taku bayan taku. Rayuwar ƴan uwanki tana da matukar muhimmanci a gareki, kece kuma zaki tabbatar ma da duniya hakan ta hanyar sakawa a ranki kamar baki taɓa ji ko ganin komai ba akan Boss. Zaɓi ya rage naki, nima na barki lafiya”. Da sauri na yunƙura da nufin cafkota, sai dai wani irin jiri ya nema kwasata dole na koma saman gadon jagwaf ina mai dafe kaina dake juya mun. Dai-dai nan Doctor ya shigo tare da Nurse. A kaina suka rufu suna jera min sannu. Niko gaba ɗaya ma bawai ina jinsu bane ba da ƙyau. Dan hatta ɗakin jinake yana amsa amon muryarsa tamkar a yanzun ne yake jera min gargaɗin ko barazana zan jirashi ma ban sani ba. Sama-sama nake jiyo doctor na faɗin, “Barcin nan bai gama sakinta ba. Sister Fadila gyara mata kwanciya”. Daga haka ban sake jin su ba. ★★Sai yamma lis na sake farkawa. Yanzu kam Alhamdullah dan duk wanda ya kalleni yasan ina a hayyacina. Dukan ƴan uwana kuma an basu damar shigowa dubani. Ina zaune a gadon na jingina da filo Gwaggo Gudidi na bani shayi. Gaba ɗaya idona ya kasa barin kan Yaya Musaddiq, kaɗan-kaɗan kuma nakan ce masa ya kira Hafizzullah ya ji yana lafiya. Yanda nake ɗin sai kowa ke ganin kamar ban gama saki bane shiyyasa. Niko ni kaɗai nasan a halin da nake ciki. Wani furuci da Mum ta furta lokacin da ƴan gidan su Mansoor suka zo ya saka ɗakin yin tsit duk aka zuba min ido har ina jin jinina na yamutsawa. A gatsine bayan ta kallan da ga sama har ƙasa lokacin da Gwaggo ke lallaɓani na ƙarasa shan shayi ta furta, “Ai waɗan nan kidnappers ɗin ma dai masu mutunci ne da wayewar kai. Yanda duk wanda aka kama ke dawowa wujiga-wujiga amma ita Samraah gata nan fes da ita. Sai ma uban haske data sake ga fata sai ƙyallin jin daɗi take yi kamar mai yaron ciki. Koda yake ance idan sukaga masu ƙyau musamman ƴammata sukan maida su kamar matansu ne suyita musu gata kuma. Maza ne dai ke shan baƙar wahala da duka. Da alama kema dai sa'ar kika ciwo kansu ɗiyata, mudai in ma wani bai aureki a cikinsu ko ya lalata miki rayuwa ba ai Alhamdullah, duk da kema ɗin ba abin yabo bace tunda dama ko ina yawonki kike yi tumma kan faruwar hakan”. Gwaggo Gudidi ce ta katse shirun ɗakin idonta akan Yaya Musaddiq daya wani dunƙule hannu. Gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun gama fitowa alamar yau ɓacin ran maza ya fito fili. Ya ɗan motsa da alamar zai yunƙuro Gwaggo ta katse hakan ta hanyar duban Mum da ƙyau. Murmushi ta sakar mata itama, sannan ta furta,........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_ .......“To banda abinki Jalilah ai kidinafa ɗin dama kala-kala ne. Duk wanda ya fahimci wanda suka ɗauki Samraah kuma ai yasan ba masu neman kuɗi bane. Akwai wata manufa da ake son cimmawa. Ba kuma na raba ɗayan biyu akan rahamar da UBANGIJI yay mata ta samun miji kawai ake son aga an tarwatsa. Sai kuma ALLAH da yake shi maji roƙon bayinsa ne sai gashi ya rusa duk wani makircin masu makirci ƙarfin addu'a yayi tasiri dan gashi UBANGIJI ya dawo da ita gida a lokacin da magauta wannan aure basu so ba. Kuma in sha ALLAHU babu fashi ranar juma'a iyanzu tana nan da igiyoyi uku a kanta”. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Mansoor ya sauke yana mai lumshe idanunsa. Yayinda Mamyn sa tai ɗan murmushi kawai. Hakama Dad ɗinsa da su Kawu Lurwanu duk murmushin sukayi. Attahir kuwa mintsinin Mansoor yayi yana kashe masa ido ɗaya cike da tsokana. Hakama ƙannensa Islam da Sakeena dake zaune kusa da Samraah duk murmushin sukayi. Aiko Mum kamar zata haɗiyi zuciya, amma dai ta danne tana murmushin yaƙen itama kamar kowa. Abba ma baice komai ba, da ga ƙarshe ya wayance da an kirasa a waya ya fita yana amsawa. Yaya Musaddiq ma a hankali ya dinga sakin ajiyar zuciya jijiyoyin kan nasa na saki sannu-sannu, dan koba komai amsar da Gwaggo ta bama Mum ta fanshi duk wani ɗaci da fushin daya yunƙuro masa. Ni dai kaina a ƙasa ina satar kallon Yaya Musaddiq, zancen Gwaggo ya sakani jin kunyar kowa dake ɗakin musamman ma family ɗin Mansoor. Dan dama tunda suka shigo ban sake yarda na kalli kowa ba. Ko magana da ƙannensa ke mun ƙasa-ƙasa ɗan murmushi kawai nake musu. Lokacin sallar magrib kowa ya watse. Iyayen Mansoor da ƙannensa suka wuce. Hakama Mum da su Kawu Lurwanu Yaya Musaddiq ya tafi kaisu masauki. Shi dama Abba tun wayar nan daya fita bai sake dawowa ba. Su Baby kam har yanzu ban gansu a asibitin ba. Dan ko Abbas dake matsayin babbansu bana jin yama zo dubani, koma basu san na dawo bane oho, koda yake da wuya ace hakan ta kasance gaskiya. Daga ni sai Gwaggo Gudidi aka bari, sai bayan sallar isha'i ne Yaya Musaddiq da Mansoor suka dawo. Babu jimawa da shigowar tasu sai ga d.c.o da yaransa guda biyu. Sun nuna jin daɗinsu na ganina garau yanzun, dan doctor ma yace zai sallaman da safe tunda banda wata matsala a tare dani, sai rashin ƙarfin jiki na allurar da suka min, tun ma a daren yay niyyar sallamata Mansoor ya ce a barni sai washe gari dai na sake jin ƙarfi da kuzari. Mun gaisa da su suka jajanta min kan abinda ya faru. Kafin d.c.o ya tabbatar min dana kwantar da hankalina na kuma basu haɗin kai mutanen nan ko su waye su sai sun kamasu an hukuntasu. Amsa masa nai kawai da kaina dan nasan abinda yake faɗar bamai yiwuwa bane ba. Wani ma idan nace ga wanda yay kidnapping ɗina cazai ƙarya nake yi. Su kuwa koda ma sun san gaskiya babu abinda zasu iya yi ɗin kamar yanda yake faɗa. To shi hatsabibin aljanin ma zai basu wata ƙafane da zasu gane shine, dan magana ta ALLAH al'amarin mutumin nan ya fara sakani a firgici, dan bana jin na taɓa cin karo da makirin mutum, hatsabibin gaske da ko tsoro bazaka taɓa karanta a yanayinsa ba irin wannan mutumin. Ga shi yayta wani shan ƙamshi cikin gadara da karfin iko kai kace shike mulkar ƙasar. Ta wani ɓangaren kuma ina buƙatar rayuwar ƴan uwana. Dan wannan mutumin babu shakka zai iya aikata abinda ya faɗa koma fiye da shi tunda na gani da idona sanda yake zare wuƙa a jikin wani. Ga kuma abinda Nurse ɗin nan tace, a duk inda muke yana biye damu ƙafa da ƙafa. Zan kare rayuwar ƴan uwana kamar yanda yay min barazana, sai dai fa idan yasan wata baisan wata ba. Nayi alƙawarin saina ƙullama rayuwarsa tarkon da bazai taɓa iya kuɓutar da kansa ba. Dan saina tabbatar masa da *_TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE_* da ƴar Abdul-wahab Gwarzo yake magana. Nashi kuma wasa ne, bai san mi ake kira kaidin mata ba sai na tabbatar masa..... Taɓanin da Yaya Musaddiq yay ya sani dawowa hayyacina firgigit. Cike da kulawa ya furta, “Tunanin mi kike anata magana Samraah?”. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi, sai kuma cikin sanyin murya na ce, “Ba komai Yaya. Kuyi haƙuri”. Baki ya buɗe zai sake magana naga ɗan sandan ya masa alamar ya barni. Shirun kuwa yayi, suma sai sukai mana sallama akan zasu wuce. Amma an ajiye ƴan sanda biyu domin tsarona gudun abinda zaije ya dawo. Godiya Mansoor da Yaya Musaddiq da Gwaggo suketa jera musu, ni dai bance komai ba face zamewa na kwanta kawai. Dan a ganina bani ke buƙatar ƴan sanda ba Yaya Musaddiq da Hafizzullah ne. Tunda idan sake niyyar saceni yay nikam nasan abune mai sauƙi a garesa. Nama fara zargin bayan Nurse likitan ma nasa ne. Kai kowama dake asibitin kallon yana da alaƙa da shi nake yanzu. Sai dai ban san ta yanda zan fito na faɗi hakan ba kuma a fahimta a kuma gaskata ni..... 💢💢💢💢💢💢💢 Agogon dake bangon ɗakin ta sake kallo a karo na barkatai, sai kuma ta ja sirrin tsaki. Ɗagowa mijin nata yay ya kalleta. Ganin yanda ta ɗauke kai gefe ya sashi faɗin, “Lafiya kuwa kike Safina?”. Kanta ta ɗan girgiza, cikin nuna damuwa ta ce, “Ba komai. Yaron nan ne dai al'amarinsa ya fara bani tsoro. Kalla agogo maganar ɗaya ake na dare amma har yanzu bai shigo gidan nan ba. Hakan na nufin a asibitin zai kwana ko mi?”. Agogon ya kalla shima, sai kuma ya ɗauka wayarsa batare da yace mata komai ba. Kunnensa ya kai alamar kira yake bayan yay ƴan danne-danne. Ana ɗagawa kuwa bayan amsa sallama ya ce, “Ɗan uwanka bai dawo gidan nan bane har yanzu Attahiru?”. Ɗan jimm yay alamar saurare. Sai kuma ya janye wayar batare da ya sake cewa komai ba. Kallonsa Mamy tayi cikin ƙagara ta ce, “Bai dawo ba ko?”. Kansa ya jinjina mata alamar eh. Zai cigaba da aikinsa a computer ta dakatar da shi. “Ya kuma zaka cigaba da aiki ka dadynsu? Ka kirashi ɗan ALLAH mana muji yana ina”. Kafeta yay da ido na tsawon sakanni. Sai kuma ya girgiza kansa da faɗin, “Mansoor yaro ne ƙarami Safina. Karki manta shirin ɗaura masa aure fa ake nan da kwanaki huɗu. Kinga ko ai yasan abinda yake ko”. “Nifa gaskiya Daddynsu bana wani jin batun auren nan a raina yanzu. Kuma dama can kaima kasan dan ya nace ne akan yarinyar nan yasa ka zuba ido da kuma dagewa da nayi nima saboda yarinyar ta shiga raina da farko. Amma magana ta gaskiya maganar matar kawunta ta ɗazun ta shigeni matuƙa. Shiyyasa tunda na dawo gidan nan naketa auna abubuwa. Dan zancen abin a duba ne fa, musamman idan muka tsaida hankalinmu muka nazarci komai a yanda yake”. Idanu kawai ya zuba mata kamar zai cinyeta da su. Itako ta ɗauke kai tana wani kum-kum da fuska tabbacin zancen nata fa tun daga zuciya ne. “Safina kin san kuwa mi kike faɗa? Kin san fa yanda ɗanki ke matuƙar son yarinyar nan. Idan har a baya na kasa hanashi dake kanki a yanzu mi kike tunanin zan iya? Naga kece kika zaƙe da faɗar ƙyawawan halayyar yarinyar a baya duk da ni na nuna batai min ba. Ina baki shawarar kawai ki bisu da addu'a kamar yanda kika saba tun farko. Maganar matar kawunta kuma ai ba lallai ne ya zama gaskiya ba. Tunda ba'a san wani kalar kidnappers ne suka kamata ba.....” “Oh amma yallaɓai su Kidnappers ɗin har suna da wani banbanci da juna ne?. Ai duk wanda akace kidnapper to Kidnapper ɗinne kawai babu wani ba rabe a ciki. Na kula yanzu ba gane maganata kake ba, bayan kuma ada ba son yarinyar kake ba, ban san miya canjaka a yanzu ba kuma. Amma dai ka zauna kayi nazari kaima. Wlhy sam babu alamar wahala a tattare da yarinyar nan. Sai ma uban haske da ƙyau data ƙara duk da kuwa sau biyu na taɓa ganinta ido da ido. Amma ai biye nake da program ɗinta duk sati a gidan tvn su.” Shi kam dai Dad ɗin su Mansoor yama kasa magana. Dan mamaki ma da al'ajabi matar tasa ke bashi yau kam. Sai yake ganin kamar ma ba ita ba. Irin wannan kafiya haka har ina kuma. Anya kuwa ba wani ne ya zugata ba?. Bashi da mai bashi amsa. Dan haka ya girgiza kansa kawai yana ƙoƙarin manyan abubuwan dake ransa tare da haɗiyesu a zuciyarsa da ga shi sai UBANGIJINSA. Gudun damuwarta saboda tanada hawan jini ya sashi sassauta nasa yanayin, cike da kulawa ya ce, “Tom naji zanyi nazari kamar yanda kika ce in sha ALLAH. Kuma zan yi bincike. Shima ɗan naki bari na taɓasa a waya. Ki kwanta ki huta kema”. Kafin ma tace wani abu ya ɗauka wayarsa ya fara ƙoƙarin kiran Mansoor........✍️ _Tofa wata sabuwa masu karatu🥱_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_ ......Yana kai wayar kunnensa dai-dai nan ma yake jin horn ɗin motar Mansoor ɗin da ƙarar buɗe gate. Wayar ya sauke tare da ajiyar zuciya ya ce, “To Alhamdullah gashi can ma ya dawo ai. Sai ki kwantar da hankalinki Ajiyar zuciya Mamy ta sauke kuwa. Ta yunƙura zata miƙe Dad ɗin ya zuba mata ido. “Ina kuma zaki?”. “Zanje na duba shi ne mana. Kofa abincin dare baici ba. Kasanshi kuma da abinci, inba tsaresa akai ba ba wani son ci yake ba”. Kai Dad ɗin ya girgiza. Sai kuma ya ce, “Uhm kinga Safina zauna Please”. Babu musu ta koma ta zauna. Sake cemata yay “Kwanta sai da safe. Tunda dai Mansoor ba jariri bane balle kice baki gama rainonsa ba.” tasan halin mijin nata dan haka bata sake magana ba kuma. Sai dai zuciyarta gaba ɗaya tana akan son sanin a wane hali ɗan nata yake ciki. Amma tunda yace bazata je ba to bata isa fitarba kuwa. Shima dai hankalinsa ya sake maidawa ga aikinsa bai sake bi takanta ba kuma. Ga shi ya haɗe fuska dan bama ya son tace zata roƙesa ko ta takura masa da batun auren Mansoor ɗin kuma..... 💞🌟💞🌟💞🌟💞 Washe gari kamar yanda doctor ya faɗa aka sallameni. Gwaggo Gudidi taso wucewa da ni can Dawanau gidanta amma Yaya Musaddiq ya roƙeta kan ta barni na koma can gidan ɗin. Tunda har Mansoor yayi magana kan baya son a ɗaga bikin nan a yanda yake koda na kwana ɗaya ne kawai ayi a wuce wajen. Ya kamata kuma muje can gidan Abba a ƙarasa komai daya kamata kada halin Mum ya dameta. Badan Gwaggo taso hakan ba ta yarda. Tarba muka samu babu yabo babu fallasa da ga Mum. Hakama su Baby na zaune a falo amma babu wanda yay min sannu ko nuna farin cikin dawowata garesu. Sai auta ne ya tsillo da gudu ya ruƙunƙumeni. Duk da miskilancin yaron sai da ya furta, “Adda nayi kewarki. Adda Bibaa tace kin mutu bayan sake ganinki ba ashe ƙarya take min”. Murmushi kawai na masa tare da shafa fuskarsa. Yayinda Gwaggo ta riƙe haɓa da faɗin, “Ta mutu kuma? To in ALLAH ya yarda ba yanzu ba, mu bazamuga mutuwa ba sai alkairi nan da kwana huɗu. Ke kuma baƙin halin naki sak na uwarki dai ashe, da wani shegen goshinki kamar jirgin tsallake ruwan bagwai”. Ta ƙare maganar tana nuna Bibaa data tura baki gaba zomomo. Na zata Mum zatayi magana. Sai naji shiru ta dai sake tsuke fuska. Ni dai sai ma na yunƙura na nufi bedroom ɗinmu dan so nake na ɗan watsa ruwa ko zanji daɗin jikina. Yanda na tadda ɗakin kaca-kaca sai da ƙirjina ya buga. Abu sai kace turken dabbobi. Wai ni yaushe Bibaa zatayi hankali ni Samraah. Na jima tsaye zuciyata cike da takaici ga ƙyanƙyami dan bazan iya zama a ɗakin ba. Dole na juya na fita cikin ƙarfin hali da son ƙarfafa kaina. Har yanzu duk suna a falon, Gwaggo Gudidi tai saurin faɗin, “Ya kuma kika fito Samraatu lafiya dai ko?”. Kaina na jinjina mata a yanayin rashin ƙarfi jiki, cikin yamutse fuska na ce, “Gwaggo zan ɗakko kayan shara ne ɗakin yayi datti ina jin ƙyanƙyami”. Dukansu sai da suka ɗago suka kalleni. Yayinda Gwaggo ta riƙe haɓa da faɗin, “To kaji kuma wani sheɗancin kuma, yanzu duk waɗan nan zagada-zagadan ƴan matan uwa wa ƴan matan amarya a gida ashe hotiho suke. Yo ni dama tunda na shigo naga gidan yamun wani harmutsai a ido nasan ana ƙwaɓa hauka dan har bashi-bashi da tsami-tsamin dauɗa nake shaƙowa ma. Yanzu ke Julaila kike ko mima oho miki bayan koyama ƴaƴanki rashin kunya abinda zai taimaki rayuwar tasu ma kin tauyesu basu iya ba. Komai kun tattara akan marainiyar ALLAH. To wlhy ba mugunta kikai mata ba idan ma ke haka kike tunani, su waɗan nan da kike gani ƴan hutu a gabanki su kika kashewa rayuwa, dan su zasu gurji kan ubansu nan gaba kaɗan. Zaku ma ki tabbatar da hakan ke da su ranar da tusa ta ƙarewa bodari, ɗiya mace bata iya komai ba ai bata cika mace ba wlhy, babu kuma namijin da zai juri zama da ita, idan ma ya haƙura ya jure dan yanada kuɗin biyan wasu suyi to bazata taɓa daraja a idonsa ba dan wataran ko shine ƙaruna akan kuɗi zai so matarsa ta masa hidima. Kai ai wlhy baki birgeba kuwa. Ashe ma fuggukar taki da ɗaga hanci kamar ƙofar gora na wofine” ta ƙare faɗa a fusace. Bibaa ta nuna da Baby “Ku dan ubanku Imamu ku tashi ku ɗakko kayan shara, ke kuma zoki zauna anan wazai barki kiyi wani aiki kina fama da kanki. Zakiyya ma na hanya gyaran jiki zata fara miki yau ɗin nan dan duk da gaki nan fes da ke ga kuma ƙarancin lokaci bazai hana nasa a kwaskware min ke ba dan kowa ya sake tabbatar da amarya ƴar gata zan kai”. Sosai Bibaa da Baby ke kallonta ransu a ɓace, sai kuma su kalla Mum da taƙi cewa komai. Tsawa ta daka musu, babu shiri suka miƙe a zabure kuwa. Nayi mamakin shirun Mum dan nasan yanda suke ƴar tsama da Gwaggo Gudidi, rashin jituwar tasu ma ce tasa Gwaggon daina zuwa gidan gaba ɗaya. Amma dai dole a wannan shirun nata akwai ayar tambaya. Su Baby naji na gani Gwaggo ta turkesu sukai gyaran ɗakin, sau biyu tana maidasu su maimaita wai bai mata ba. Bayan sun kammala sunata zungure-zunguren baki tasa Bibaa ta tattara kayanta ta maida ɗakin Baby. Shima auta aka haɗa masa nasa aka sanda shi ɗakin Mum. Acewar Gwaggo nan sune zasu zauna har sai biki ya tashi. Ni dai dariya ma abin ke ban. Dan Gwaggo Gudidi fitinanniya ce sai dai idan bataso ba zaka ga ta watsar da kai kamar mai shiru-shiru. Halin namu dai na kamanceceniya sosai, ƙila dai ita na gado ma (🤣). Fuu Mum ta tashi batare da tace mana komai ba ta bar falon, mu duka da kallo muka bita, sai dai babu wanda yace komai. “Mum na shiga ɗaki waya ta ɗauka, sai faman huci take da jan numfashi, kai daka ganta kasan dama danne komai take da ƙyar kawai. Ko sallama balle gaisuwa batayi ga wanda ta kira ɗin ba ta fara magana a hasale. “Mama magana ta gaskiya bazan iya haƙurin da kikace da wannan tsohuwar ba. Kinga daga dawowarsu yanzu tabi ta addabar min yara. Nidai bazan iya ɗauka ba. Wannan plan ɗin naki na fara jin kamar bazan iya juresa ba. Ina dalili yara tun suna ƙanana sun tare min komai yanzu kuma an saka min ƴaƴa a gaba duk da kwacen saurayi da akaima Baby”. Siririyar dariya akayi mai sauti daga can. Sai kuma dattijuwar murya ta fara faɗin, “Jalila wani lokacin idan kina wani shashancin sai nake ganin kamar bani ce na haifeki ba. Ke matsalarki baki iya ɓoye abu aranki. Shiyyasa tun farko ko riƙon yaran nan nace ki yi na siyasa ta yanda koshi mijin naki bazai fahimci baki ƙaunarsu ko son zama daku ba. Amma ina kin kasa. Yanzu kina ganin matsala ta taso kaso biyu bisa uku na mutane har yanzu ke suke zargi da satar yarinyar nan har da ƴaƴanki. Ko ƴan sandan nan idonsu kema na'a kanki. Amma kin kasa fahimta. Ko shi mijin naki badan mun danne masa kai ba tuni kina ganin bake zai zarga ba ne? Shin wai rayuwa babu siyasa ta yiyu haka ne?”. “Wai Mama sai kice siyasa, siyasa. Dan kawai ina son na birge wani sai na dinga nunawa wanda bana so so. Nidai a bar wannan maganar, kawai ki faɗa min abinda zanyi na gaba dan na fara ƙosawa da halin tsohuwarnan, zan karta mata rashin mutunci wlhy bazata zo cikin gidana ta hanani rawar gaban hantsi ba”. “A'a ban aikeki ba nikam. Ki bari anjima kaɗan zan zo gidan. Dama ga ƴar uwarki nan tazo itama babu jimawa. Kuma ni abinda nasa a raina kofa auren nan akai sai munyi duk yanda zamuyi basu zauna lafiya ba. Dan yanda ta rabashi da takwarata itama bazata taɓa jin daɗin ba. Na fara ji kuma a raina wannan tsohuwar duk itace ke ƙulla komai, maybe ma itace ta amaso asirin da aka juya kan yaron nan. Shiyyasa sam ban sonta tun aurenki da Imam. Amma idan sun san wata su basu san wata ba ai. Daga su har ita zasu ci ubansu ne da ni suke zancen. Yanzu dai ki cigaba da kwantar da hankalinki bana son jin wata fitina. Bari na ƙarasa aiki mu fito”. “To Mama dan ALLAH kuyi sauri”. Suna ajiye wayar zama tai jagwab a bakin gado, ita kaɗai tasan irin ƙunar da take ji a ranta game da auren nan. Ji take kamar ta sakama yarinyar nan shinkafar ɓera a abinci ta mutu kowa ya huta, dan tafi sauran ƴan uwanta tsaya mata a rai, shegiya ga ƙyawu kamar wadda ta tashi a rayuwar hutu, duk baƙar izayar da take mata kullum zaka ganta fes-fes ga shegen Musaddiq ɗin can kullum cikin saya mata suturu yake. Tanada plans daban-daban da zata iya bi ta wargaza auren nan dama rayuwar yarinyar nan duka, amma Mamanta na hanata. Amma yau kam tana ji in har Mama bata iya tayi komai ba itafa zatabi ɗaya daga cikin plans ɗinta ne. Dan bazata taɓa yarda a ƙwacema ƴarta da tafi so abinda ke nata ba. Sai dai ko duk su rasa, ko kuma ƴarta ta samu ita.......✍️ _Humm Mom to bari muga yaya wasan zai kaya 🚴_. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_ ________ _Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me hamsin me dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata mai albarka..._ _idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo unguwar tarauni dake garin Kano sai akira number opay dincan dake sama_ _zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._ _kofa a bude take ga duk Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_ _____________ .......Bayan nayi wanka nayi sallar Azhar da tayi ina zaune ina ɗan tsakurar abinci zuciyata fal tunani. Zantukan mutumin nan kawai ke min kai-kawo a rai. Dan tun jiya nake son fassarasu amma na gagara hakan. Ina son na sanar ma Mansoor da Yaya Musaddiq gaskiya amma ina jin shakkun abinda zai je ya dawo. In har zai iya saceni harna tsahon kwanaki goma sha bakwai, kuma ya dawo dani gida batare da wani ya gani ko yaji ko gano shine ba har jami'an tsaro wane makami kuke tunanin zan iya ɗauka domin kare kaina?. Bily ina da taurin kai da kafiya. A wasu lokutan harda tsiwa ma. Amma fa babban weakness ɗina a rayuwa sune ƴan uwana guda biyu. Zan iya bada rayuwata a wajen karesu kamar yanda nasan suma zasu iya hakan. Dan su ɗin garkuwa ta ne. In dai hakane kenan ya kamata na kwantar da hankalina na nutsu waje guda har a gama bikin nan na koma ƙarƙashin ikon Mansoor. Na tabbata zai taimaka min da duk irin gudunmawar da nake buƙata game da bama ƴan uwana garkuwa batare da hatsabibin ya farga ba. Na kuma tona asirin sa ta hanyar da bai zato ba. Tunda yanada wayo shima ya kamata a tabbatar masa da TSUNTSU mai WAYO ta baki ake kamasa. Hakan kuma bazai yiwu ba har sai na nutsar da hankalina waje ɗaya na shirya nima tsaf ta yanda zan zame masa tamkar kifin tarwaɗa da baza'a taɓa iya kamashi da santsin kalkashi a hannu ba. Dan a yanzu ni kaɗai nasan inda video ɗin yake. Dan abinda Mansoor bai sani ba ni da kaina na goge na wayarsa, badan kuma ban yarda da shi nai hakan ba. A'a ina tsoron a masa barazana dani ne a amsa wataran. Shiko Yaya Musaddiq dama bai tura ba kwata-kwata. Dan haka na ciresa daga tawa wayar nima na maidashi a flash drive dana sayo na adanashi inda daga UBANGIJINA sai ni muka san inda yake..... “Oh Amarsu irin wannan zurfin tunani haka?”. Aunty Zakiyyar Gwaggo da bamma san lokacin data shigo ba ta faɗa cikin katseni ta hanyar taɓani na kawo nannauyan numfashi. “Har kin fara tunanin rabuwa da gidan ne raguwa? Sai bakin tsiya kuma”. Ta sake faɗa cike da tsokana. Murmushi na sakar mata ina duƙar da kaina. Na ce, “Kai aunty yaushe kika shigo bamma sani ba”. “A taya zaki sani kin lula duniyar tunani. Yaya jikin naki dai to?”. “Alhamdullah Aunty, dama babu inda ke min ciwo, allurar da suka min ce kawai ta sakani wannan dogon barcin”. “ALLAH sarki to Alhamdullah ai haka akeso. ALLAH kuma ya kiyaye gaba. Ya tona asirin duk wanda keda hannu a kan hakan. Damma dai Alhamdullah addu'a tayi tasiri ƙwarai da gaske. Kuma da alama duk ma wanda suka kamakin ba mugaye bane. Dan masu amsar kuɗin nan sunfi haɗari. Amma waɗan nan da alama suna da tasu manufar ne a kanki gaskiya. Na kuma fi ƙyautata zaton akan auren nan ne kamar yanda kowa ke zargi, musamman akan wannan maman taku da Baby. Kowa yafi dangantasu da al'amarin nan wlhy, dan zuciyarsu babu ƙyau komai zasu iya aikatawa tunda sun gagara ɓoye hassadarsu”. “In sha ALLAHU Aunty bazasu ci nasara ba kuma. Tunda gashi ma ALLAH ya kuɓutar dani cikin sauƙi, dan tabbas addu'ar ce tai tasiri a kansu suka sakeni batare da sun shirya ba, amma kuma ni bana danganta al'amarin da su Mum da dalalin auren nan kamar yanda kowa ke kallo, dan in dan auren ne ai kinga babu yanda za'ai su sakeni haka da sauƙi da sai lokacin bikin ya wuce ko”. “Tabbas hakanne kam Samraah kema kinzo da batun dubawa. Amma dai ai zaki iya ganesu? Dan naga angon nan naki da gaske ya shirya ɗaukar mataki, a yanzu haka suna ƙofar gida da ƴan sanda da Musaddiq da Yaya Imam.” Idanu na zuba mata kawai, sai kuma na nisa a hankali na ce, “Aunty bazan iya gane su ba. Saboda abinci kawai suke kawo min sau uku a rana. Kuma komai nasu a rufe hatta da hannayensu ma. Kuma basa mun magana sai dai su ajiye kawai su juya su fita. Ko'a ranar dana samu damar kiran Yaya Musaddiq ma kwato nayi, sai kuma suka kamani bayan sun amshe wayar suka shaƙamin abu suka ɗaukeni da ga gidan sai farkawa nai na ganni a wani sabon waje. Hakama yanzu sai da suka min allura sannan suka kawo ni ƙofar gidan nan.” Aunty Zakiyya na shirin yin magana dai-dai nan Yaya Musaddiq yay sallama. A tare muka amsa masa. Batare da ya shigo ba yace nazo. Miƙewa nai na ɗauki hujjab ɗina na saka sannan na fita. A falon baƙi na samesu shi da d.c.o da Mansoor sai Gwaggo Gudidi da Abba. Daga can gefe Baby ce ta masifar zubama Mansoor ido kamar zata cinyesa. Shiko sai wani cin magani yake tamkar an aiko masa saƙon mutuwa. Sai da muka haɗa ido ya ɗan sauke numfashi tare da sakar min murmushi. Murtani na mayar masa nima ina duƙar da kaina ƙasa. Gaisar da d.c.o nayi cikin girmamawa, shima ya amsa min da kulawa tare da tambayata ya jikina. Kaina a ƙasan na ce, “Alhamdullah bana jin ciwon komai Sir”. “Masha ALLAH, Alhamdullah haka muke son ji ai dama. Samraah wannan zuwan naki ne. Muna fatan zamu samu haɗin kai domin son sanin komai daya faru dake tun daga fitarki a gida a waccan ranar har zuwa yau da ALLAH ya maido mana ke bisa ƙarfin ikonsa”. Babu musu na jinjina masa kaina tare da faɗin, “In sha ALLAHU ranka ya daɗe zan faɗi abinda na sani”. Zamansa ya gayara sosai yana fuskantata. Kafin ya furta, “Yauwa Ina jinki”. Bayani na fara masa tiryan-tiryan tun daga shirin fitata. Kiran dana samu daga MD har zuwa fita cikin layi da tare napep. Jefamin handkerchief da wanda na samu a napep ɗin yayi bayan ya kira sunana tabbacin ya sanni ko yana son tabbatar da ni ɗin ce, har zuwa buɗe ido na ganni a wani waje daban. Yanda na rayu a gidan farko har zuwa kiran wayar Yaya Musaddiq da nayi da wayar ɗaya daga cikin mutanen da kuma canja min gida da sukayi. Sai dai na samu kaina da kasa faɗar wanda ya saka akai kidnapping ɗin nawa kamar yanda ya nuna min kansa da buƙatar na bashi abinda ke a hannuna da yayi, hakama dalilin ɗaukar tawa duk ban faɗa ba. Maidoni gida da sukayi da kuma kiran da yayma Nurse a asibiti ta bani. Kawai dai na sanar musu kamar yanda na sanarma Aunty Zakiyya ne. Sosai falon yay tsitt suna saurarena. Yayinda d.c.o ya kafeni da idanu ko ƙyaftawa bayayi. Jinai duk na tsargu, amma na dake abina kun dai san mutuniyar taku ai. Dan kansa ya gaji ya janye idanunsa a kaina. Cikin sauke numfashi ya furta, “Kin tabbata iya abinda ta faru kenan Samraah? Dan bana son ki ɓoye mana komai, kar kiji tsoron barazana ma idan sun miki babu abinda zai faru”. “Iyakarsa kenan yallaɓai. In har na ba mance wani abu to bashi da muhimmanci ne”. Kansa ya jinjina cikin nuna gamsuwa, kafin ya kalla yaronsa dake rubuta duk abinda nake faɗa, sai kuma ya maida idonsa kansu Yaya Musaddiq. “Inaga fa dole ne mu sake gayyatar MD ɗin nan nasu, dan komai idan aka tattara ya ta'allaka ne akansa. Amma bawai ina tabbatar da shi ɗin ne ba. Dan ita shiri'a saɓanin hankali. Kuma tunda har ta dawo gida cikin ƙoshin lafiya Alhmdllh, koma minene zai zo mana da sauƙi. Yanzu dai inaga sai a kiyaye gaskiya. Fita anyhow dole ta jingine ta. Mukuma duk inda ta saka ƙafa idan ma har ta fitan zata kasance a ƙarƙashin kulawarmu ne.” “In sha ALLAHU babu damuwa ranka ya daɗe. Dan ko batun zuwa aiki ma dama zata ɗan dakata, in ma zata cigaban ne sai bayan bikinta idan mijinta ya amince sai taje ɗin”. “Wannan ma dabara ce kam mai ƙyau sosai. Amma taron bikin nan fa dole ayisa da kulawa. Koda yake zamu haɗata da jami'ar mu mace domin ta kasance da ita ama duk inda take like handbag ɗinsu na mata. Hakan zai sauƙaƙa mana aikin mu insha ALLAHU.” Kowa a falon yaji daɗin zancen nasa kuwa. Dan har fuskokinsu sun gagara ɓoyewa. Ni dai kaina a ƙasa kawai abubuwa da yawa nata min kai kawo a zuciya. D.c.o ya ɗan ƙara tattaunawa da su Yaya Musaddiq kafin suyi mana sallama su wuce. Tare da jaddada min duk sanda suka buƙaci gani na zan iya ganinsu a gidan, ko kuma su aiko a ɗaukan zuwa office ɗinsu. Da to kawai na amsa musu ni dai. Gwaggo Gudidi sai jera musu godiya take. Mansoor da Yaya Musaddiq kuma suka tafi musu rakkiya waje. Muma miƙewa mukai muka koma cikin gidan. Dan Aunty Zakiyya ta tabbatar min da yau babu fashi zata fara min gyaran jiki. Ban musa ba, dan nima ina son zuwa fadar masoyina fes tamkar wata ɗan daren sha biyar.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ______________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/Cce1etNkvVKCBlgSqXa4Ek ___________ ........Tun daga shigowar ƴan sanda har fitarsu a gidan Mum ta sani, amma batako leƙo ba. Sun tafi ma babu jimawa sai ga Mamanta da ƙanwarta dake aure a Bauchi. Acewarta tazo ne bikin Samraah domin yima Mom Kara. Bata bari sun zauna a falo ba ta shige dasu bedroom ɗinta. Da kanta kuma ta fito ta haɗa musu abinci takai musu. Ko kunya babu yanda ƙanwarta ta cire mayafi ta fara lodar abinci haka itama Maman tayi. Kai bakace a gidan suruki take ba. Bayani ta sake ma ƙanwar tata akan duk yanda aka samo Samraah, dan ita Mamansu tasan komai. Ƴar uwar tata kai ta jinjina. Sai kuma tai ɗan jimm alamar tunani, kafin ta sake ɗagowa tana kallonsu bayan ta gama ƙulla abinda take ganin zai fanshi yarinyar nan tsakaninta da ALLAH. Dan magana ta gaskiya ita su Samraah sun jima suna bata tausayi, sai dai bazata iya fitowa ta faɗa ba dan tana shakkar Yayar tata da Mamansu saboda masifaffu ne na bugawa a jarida. Amma tana ji a ranta a wannan gaɓar bazata bari a cutama marainiyar ALLAH ba. Sai dai dole tai komai cikin siyasa. “Niko inada shawara”. Ta faɗa kanta tsaye.duk sake maida hankali sukai a kanta. Cike da zumuɗi Mum tace, “Miye shawarar Ikili, dan ALLAH faɗi muji”. Numfashi Ikilima ta sauke tare da ajiye cokalin hannunta ta sake fuskantarsu. “Ban sani ba shawarar ko zata gamsar daku, amma dai a yanayin da nake gani kamar guri ya ƙure mana a yanzu zata iya zama mafita. Mizai hana mubar yarinyar nan tai aurenta kawai. Bayan bikin mu duƙufa samowa Baby mijin aure na garari da yafi shi wannan yaron. Bayan itama ansha nata bikin mun nunama musu koda goma ta lalace tafi biyar albarka, sannan mu fara shiri akan komai ma da muke ganin ya dace akan auren nata. Dalilina na kawo wannan shawarar shine idan fa muka hana auren nan kamar mun gogama gidan nan wani baƙin fenti ne. Kun san dai halin mutane ai, hakan kuma na nufin kammu muka cutar tunda namu yaran ne dai basuyi aure ba a bayanta, dan ita wani zai iya jin tausayinta yazo ya aureta, sannan mu za'aita zagi da zargin mun hana ko muna mata baƙin ciki. Amma idan muka bari akayi hankali kwance babu mai aibanta mu balle idan mutanen kirki sun zo neman auren su Bibaa wani shege ya sokemu. Kunga mun samu nasara biyu kenan, mun kuɓutar da yaranmu, sannan mun sama musu abinda muke fata. Yo har miye wani Mansoor yake ma komi ALLAH na tuba. Shi da dukiyar ba tasa bace ta babansa ce. Mu ɗan gaske zamu samo mai dukiyar kansa da kansa. Dama ba akwai mutumin nan daya haukace akan baby na anguwarmu ba amma tanata masa wulaƙanci ita bazata zauna da kishiya ba. To wlhy yanzu yazo nan Kano yayi wani mahaukacin gida a hotoro g.r.a ina gaya muku kuma aure yake son yi ruwa a jallo ya saka matar anan, su kuma waɗan can zasu cigaba da zamansu can Bauchin saboda ya musu tayi sunce su bazasu iya barin mahaifarsu da ƴan uwansu ba. Amma yaya kuka gani?”. Cike da zumuɗi Maman ta ce, “Ni dai wannan shawara tamun wlhy Ikilima, amma ke Jalilah yaya kika gani?”. Shiru Mun tai kamar bazatace komai ba, sai kuma ta sauke numfashi mai nauyi da faɗin, “Nima shawarar ta ɗan mun, sai dai ina tsoron tsutsun Baby wlhy, Dan nasan yanda ta tsani kishiya...” “Yo biye mata zamuyi, tuni zamu shiga mu fita a dasa mata sonshi a zuciya sanda ma zata soshin fawa tai shawara. Mufa muka haifeta ba itace ta haifemu ba. Kishiyoyi kuwa ai dasu da babu duk ɗaya ne tunda ba'a waje guda zasu zauna ba”. “Yo Mama ko waje guna ne Baby bata da matsala. Dan matansa wlhy a hakan ma kowa rayuwarsa yake babu wadda ta damu da wata tunda kowa da gidanta kuma kowacce kuɗi take juyawa na hauka. Yi kishin ma fa dama matan malam shehune sukafi zaman yin na haukannan aita damben tsiya da hayaniya. Amma mata masu aji da kuɗin nan zakiga kishin ma na ƴan boko akeyi, itama kuma dai tanada iliminta babu abinda za'a nuna mata. Kuma tana shiga zai bata maƙudan kuɗi ta fara kasuwanci kamar sauran dan haka yake yi” “Hakane wlhy Ikilima. Ni kubar komai a hannuna kawai zanyi maganinta, yanzun kam hidimar biki duk mu ware aitayinta damu. Ai kwantan mage zamu musu a yayin kama ɓera, tuni sai suzo hannunmu batare da sun farga ba”.... (😂ALLAH ya rabamu da son zuciya to). 💦🌟💦🌟💦🌟💦 Zaune yake a office yana ƴan ayyukansa sakatariyarsa ta shigo ta sanar masa d.c.o yazo yana son ganinsa. Karo na farko da MD yaji ransa ya fara ɓaci da bibbinin da d.c.o ɗin ke masa. Idan yace da yana da dalili yanzu kam shi baiga dalilin ba. Samraah dai ce ta kuma dawo sai me kuma, shi ma yaje dubata tare da staffs nasu har asibiti. To minene kuma na zuwa masa office yau. Rashin amsa ya sashi jan sirrin tsaki, tare da bama sakatariya umarnin ta barsa ya shigo. Fitarta bai fi da mintuna uku ba ko sai ga d.c.o ɗin ya shigo, sun gaisa cike da girmama juna. Kafin MD ya ce, “Yallaɓai akwai wata matsala ne?”. “No babu matsalar komai MD. Waccan dai matsalar ce akan staff ɗinku Samraah Abdul-wahab Gwarzo. Dan kasan koda ta bayyana ya kamata mu cigaba da bibiyar case ɗin domin gano da kama wanda sukai kidnapping ɗinta kodan musan dalilinsu”. “Hakan nada ƙyau yallaɓai. Domin muma zamu so ace an kama sun. Sai dai muna ƙarama ALLAH godiya da kuɓutar tata cikin ƙoshin lafiya. Yanzu mike tafe da kai?”. “Uhm kamar dai yanda aka saba zamu sake gayyatarka office ɗin mu idan babu damuwa. Kana kuma da damar muje ka samemu a can, ko mu tafi tare”. Murmushi MD yayi mai ƙayatarwa. Sai kuma cikin rashin damuwa ya ce, “Babu matsala muje ɗin kawai, dan bawani aiki nake da shi ba sosai yanzun. Zuwa anjima kuma aikin zai iya shamin kai, kaga kuma bai ƙyautu ace ban amsa gayyatar ba” “To Masha ALLAH, hakane kam mun gode sosai”. Murmushi kawai MD ya sake masa yana miƙewa. A jere suka fice suna ƴar hirarsu tamkar wasu abokai. Dan haka sauran staffs basu fahimci komai ba face tunanin akan dai case ɗin Samraah ɗin ne. Kuma babu wani damuwa a cikin ganin MD da ƴan sandan dake bincike akan case ɗin tunda ba yau ne mafari ba. Suma kansu dai duk sai da suka sha tambayoyi a kwanakin baya.... 💢🌟💢🌟💢🌟💢 Kwanaki na biyu kenan da dawowa gida. Kwanaki biyu kuma kacal ya rage ɗaurin aurena. Dan zuwa yau har baƙin kusa sun fara isowa musamman dangi na jiki sosai. Ga Aunty Zakiyya ta duƙufa min gyaran jiki da ɗuramin abubuwa. Niko dana faki idonta sai na zubar dan bana sha sosai. Abinda zai baku mamaki duk da haramin biki da gida ya fara ɗauka ga masu gidan babu wani alamar motsi irin na biki a tattare da su. Dan hatta da abinci da aka girkama baƙin dake a gidan yau Yaya Musaddiq ne ya kawosa. Suko su Gwaggo suka girka batare da sun bi takan Mum daketa faman ɗacin rai ba. Shi dai Abba saboda su Gwaggo Gudidi yana ɗan nuna alamar damuwa da shirye-shirye. Sai dai fa bana aljihu ba na gayyatar mutanensa kawai, sai kuma takurama Yaya Musaddiq da yake ta bayan fage akan kuɗin kayan ɗakina da wanda za'ai hidimar abincin biki. Shiko Yaya Musaddiq nata masa zame-zame. Sai a yau ya fito fili ya shaida masa karya damu shi ya riga da ya kammala komai. Dan hatta da kayan kitchen ɗina ma a tanade suke tuni. Hakama kayan gado kafintan ya jima da kammalasu duk da Mansoor yace kar ayi shi baibi ta nasa ba. Wannan zance ya ƙona zuciyar Abba matuƙa. Amma ya gagara magana kodan mutane dake cike a gidan, yasan fitowar zancen babban abin kunya ne a garesa musamman a wajen danginsu dana ɓangaren mahaifinmu. Ban gayyaci wasu ƙawaye ba dan banda su, amma a ranar da yamma sai ga su Ruƙayya ƴan Office dinmu da gayyar ƴan ajinmu na islamiyya. Naji daɗin ganinsu sosai, dan ko kusa banyi zato ba. A bakinsu na fara jin ƙananun maganganu akan rashin kawo kayan da zanyi amfani dasu na biki da Mansoor ya ce sai daga baya dan ba'a saka ɗinkakken kaya ko ɗaya a lefen ba, kuma kowa na saka ran yau ne za'a kawo ɗin saboda kamu da ake shirin yi gashi babu kayan dazan saka. Amma har yamma shiru kake ji. Gashi yanzu banda waya a hannuna ko ɗaya. Rabona da Mansoor kuma tun jiya da dare. Koda yake nice nace yau kar yazo, kai daga jiya ma bazan sake yarda mu haɗu ba sai a gidansa. Shiko ya yarda da hakan acewarsa zai gwada yaga ko zai iya. Nayi tunanin kiranshi amma zuciyata ya ƙwaɓeni game da hakan, dan haka bance da su komai ba na haɗiye zancen a raina har sai bayan sallar isha'i da nasan Yaya Musaddiq ya dawo gida sannan na lallaɓa ɗakinsa na samesa, a wajen kamu kuwa Aunty Zakiyya ta samo kayan dana saka kawai........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ___________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/Cce1etNkvVKCBlgSqXa4Ek ___________ ........Kai tsaye ɗakin Yaya Musaddiq na nufa. Bayan na gaishesa ya ɗan tsokaneni nai masa zancen da naji ana tsogumi ɗazun a kai. Murmushi yay min da faɗin, “Kandala ƙyale batun mutane da halinsu. Dan su basu iya komai ba daman sai gulma kawai. Yanzun nan babu jimawa muka rabu da Mansoor ɗin ma, dan munje can gidan nasa ne da kafintan da yay kayanki saboda zasu kaisu da sassafe gobe in sha ALLAHU. Ya kuma min batun kayan sai gobe in sha ALLAHU zasu kawo wata ƙanwar Mamynsu ce da zatazo da ga Dubai a yau da dare ake jira dan akwai wasu kaya a hannunta, amma shima yana cikin damuwar rashin kawo su shiyyasa ma ya kasa neman ko Hafizzullah a waya ya haɗaku dan kunyarki yake ji”. Ajiyar zuciya na sauke a hankali. Dan nama san ƙanwar Mamyn tasu, yasha bani ita muyi waya. Murmushi yay min yana kai ma kaina rankwashi da faɗin, “Sam yanzu Kandala baki da kunya. Yanzu ni kike zuwa tambayar batun kayan aurenki ma”. Hannu na saka na rufe fuskata ina dariya. Shima dariyar yake yi. A dai-dai nan Hafizzullah ya shigo ɗakin da sallama. Dan tun washe garin da aka ganni yazo gida dama. Ledar hannunsa na warce ina faɗin, “Zaga gari mi kuma ka samo anan?”. Ƙoƙarin warce ledar shima yake a hannuna yana hararata. Ban yarda masa ba har sai da na buɗe. Ganin awara yasa na taɓe baki ina miƙa masa. “Oh oh kwantar da hankalinka ashema naman talaka ce”. “Oho dai, kema naga ci kike”. “Ai ni in naci ba komai bane. Amma kamarka dai saurayi mai hurama ƴammata hanci abin kunya ne. ALLAH yau da ina da waya saina ɗauki hotonka nasa a status ƴan matanka sun gani”. Dariya ya sanya da yimin gwalo, ya ce, “Ai sai ki samama kanki lafiya tunda baki da. Kuma sai na zuga Yaya Mansoor kar ya saya miki waya har sai kin shekara a gidansa”. “ALLAH sarki jiki duk baƙin ciki su Hafizu. Aiko zakasha mamaki, kafin rana ita yau kasa a ranka na mallaki waya”. Na ƙare maganar ina kai masa rsankwashi a kansa. 💥💫💥💫💥💫 Kamar yanda Mansoor ya faɗa hakance ta kasance. Dan washe gari misalin sha biyu na rana ƴan kawo kayan nan suka iso gidanmu su uku. Zuwa lokacin baƙi sun ƙaru. Dan wasu matan ma a cikin ƴan Gwarzo ma sun iso. Tuni Aunty Zakiyya ta shiga maƙwafta tai kiransu dan Mum taki aikawa a kira kowa aiki. Sai ma yi take kamar wadda ta ruɗe. Dan ma ƙanwarta na tare da ita tana saitota. Baby kam ban san ina ta tafi ba dan tun jiya da yamma ban sake ganinta a gidan ba kuma. Waɗan nan kaya sun matuƙar girgiza sukata. Dan da gasken gaske Mansoor da ahalinsa sun nuna bajinta. Duk da ba fariyya akayi ba komai na nan dai-dai misali amma kuma na bajinta da zai tabbatar maka an kashe kuɗaɗe sosai. Dan komai acan-acan ko maƙiyi yasan kaya sunyi ga kuma kayan lefe da dama sun riga sun kawo. Har aka gama karɓar kayan ni dai ban ko leƙo ba sam. Sai da dangin Mansoor suka wuce sannan aka maido kayan nan ɗakin da muke da su Gwaggo Gudidi sannan su Asiya suka tsareni sai na gani harda Aunty Zakiyya. Na ɗan kalla sama-sama na rufe akwatin ni dai. Har raina ina sake jin kima da girman Mansoor matuƙa dama ahalinsa gaba ɗaya.... 💦💦💦💦💦💦💦 “Aunty dan ALLAH ki kwantar da hankalinki ni banga aibun yarinyar nanba sam wlhy. Ga danginta mutanen kirki. Karfa kiga irin tarbar da akai mana ta girmamawa wlhy.” “Humm Anesa ni fa bance tanada aibu ba. Amma ya kamata ku fahimci abinda nake nuna muku. Yanzu dan ALLAH da kikaga yarinyar tayi kama da wadda akai kidnapping na tsawon sati biyu da wasu kwanaki? Nafa fiku son yarinyar nan, kuma har yanzu ina jin sonta a raina”. “Aunty wlhy ni ban ganta ba.” “Humm to ai naso ki ganta da kin tabbatar. Amma al'amarin da mamaki ace ai kidnapping yarinya budurwa ƙyaƙykyawa kamar wannan wai ta tsallake tarkon namiji. Sannan kuma basu nema kuɗin fansa ba saboda sun sami abinda yafi kuɗin kenan. Ya kamata kowa ya gane maganar matar kawunta da abar a duba ce fa. Dan dolene ɗayan biyu a samu ɗaya. Kodai da ƙafarta tabi wanda suka sacetan nan zuwa wani hotel ko guest house. Ko kuma wanda sukai kidnapping ɗin nata sun samu abinda yafi kuɗi a jikinta. Wai Kinga kuwa yanda ta ƙara wani fresh na haske da laushin fata tamkar wadda ke rayuwa a ac. Ai bana jin ko kafin a sacetan jikinta yay wannan luf-luf ɗin. Amma da yake yaron nan ya makance da shirme shi ko sau ɗaya bai zauna yayi tunanin komai ba. Na rasa mike damun kan Mansoor ne. Ga ubansa shima yama ƙi ya sauraran balle ya gane abinda nake nufi. Kema kuma gashi kina nuna bazaki fahimceni ɗin ba”. “A'a Aunty, ba fahimtarki ne bazanyiba nikam. Abinda kawai nake son ki duba bakin alƙalami fa ya riga ta bushe. Tunda gashi yau har sauran kayan lefe mun damƙa musu. Sannan Mansoor ya sanar min sun kai kayansu can gidansa wasuma a dangin nata na jerensu yanzu haka. Sannan Aunty gobe ne fa ɗaurin aure. Kuma kin ce Abban Attahir ma yaƙi fahimtarki balle ma shi Mansoor ɗin da kin gagara tunkararsa da batun, to tayaya kike tunanin zamu iya wani abu a ƙurarren lokacin nan?”. “Zamu iya kuwa Aneesa. Dan anma zauna a filin ɗaurin aure ya watse ballema wannan da sai gobe. Mansoor da kike gani sam bashi da wani isashen wayo. Wlhy koda yasan yarinyar nan bata ƙwarai bace zai iya shanyewa saboda son da yake mata na masifa da ni sai a yanzu ma zuciyata kemin wasuwasin bana lafiya bane. Dan abun yayi yawa wlhy. Wace soyayyar haukace haka kamar wani labaran littafin hausa. Ku shaida ne nima naso yarinyar nan a baya, dan ina gaba-gaba wajen shawo kan Abban Attahir harya amince da auren nan duk da fama da aka sha sosai saboda dagewar da yay akan sai Attahir ya fara aure sannan Mansoor ɗin yayi. Amma magana ta gaskiya zancen matar kawunta na jiya ya dawo dani a hankalina. Sannan ganin yarinyar a cikin hayyacinta fes saima ƙyau data ƙara shima ya tsaya mun a rai. Dan haka shekaran jiya nace Mansoor ya kamata ya nema likita yasa a mata gwajin ciki amma yaron nan sai ya koma min wani kalar tausayi kamar zai yi kuka, yana faman roƙona nabar wannan maganar dan ALLAH kada wani yaji, shi yasan wacece Samraah. Da ace wata matsala ta faru da ita acan sai ta faɗa masa bazata munafuncesa ba. Kajimin yaro fa dan ALLAH”. “Humm Aunty kar kiga laifinsa. Dan dama abin da kamar wuya ace ya fahimta kai tsaye. Amma dai kam al'amarin akwai ɗaure kai”. “Bana wasa ba ma. Inda shi wani ne dan ALLAH basai ya haƙuraba, idan ma ya matsune yay auren dole a goben basai a ɗaura da Waleeda ba. Nasan dai Daddynta bazai ce komai ba wlhy”. Idanu sosai ƙanwar tata ta waro waje. Sai kuma ta ɗan murmusa da faɗin, “Kai Aunty wannan ai babbar magana ce. Ni dai abinda nake gani anan kawai addu'a ce tafi dacewa. Sannan kisa a ranki in sha ALLAHU abinda zuciyarki ke ayyana miki bazai zama hakan ba.” Baki kawai Mamy ta taɓe batare data sake cewa komai ba..... 💢💫💢💫💢💫💢💫💢 *_RANA BATA ƘARYA BILYN ABDULL. MASU IYA MAGANA SUN CE SAI DAI WAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA_*. Na yarda da batun masu hikimar zance. Domin kuwa nima da kaina na yarda wannan rana tawace kam. Sannan in har Mum na amsa sunan uwa a gareni to taji kunyar kuwa. Dan halayyar da take nunawa yasa dangin mahaifinmu suka gagara haƙuri sai da suka yayyaɓa mata magana. Dan har Kawu Lurwanu na iƙirarin mata dukan tsiya. Yaya Musaddiq ɗin da take gani aba komai ba a gareta ne yayta basu haƙuri da kareta har aka samu ƙurar ta lafa. Gida ya gama cika danƙam da mutane. Dangi na kusa dana nesa sun nuna halacci. Ga abinci kala-kala anyo daga Gwarzo batare da an zaman jiran sauraren na nan gidan Abba da kunya ta sakashi kawo buhun shinkafa a jiya da dare ba, sai wasu ƴan kayan miya cakwat da nama a baƙar leda abin zakkunya dai. Kafin goma na fito shar dani a amaryata. Ga ƙunshin da ƙanwar mijin Aunty Zakiyya ta rangaɗa min a daren jiya ja da baƙi yay masifar fitowa kamar kaci. Duk da gyaran ƴan kwanaki akai mun na fito fes dani kamar fure a tsakkiyar lu'u-lu'u. Wani cotton lass ne a jikina lemon green ɗaya daga cikin kayan da suka kawo jiya aunty Zakiyya ta ciro min. Dan duk kayan da zanyi hidimar biki dama sai da Mansoor ya ɗaukan mukaje tela ya gwadani tun kusan wata biyu da ya shige. Aiko ɗinkin yay masifar zaunamin a jiki. Sai wata stones sarƙa mai ƙyalƙyali da walwali tamkar diamond na gaskiya. Awarwaraye zobba da komai sunji a hannayena. Ta sama gashina da a daren jiya shima yasha wanki daga ƙanwar mijin Aunty Zakiyyar dai dan aikinta kenan shima sai ƙyalli da ɗaukar idanu yake. Bayan ta gama tsaramin kwalliyar da naita zame-zame a farko aka naɗa min ɗauri na azo a gani. Nan take hasken camara na waya ya shiga kai-kawo a kaina. Nanfa wasu sukace sai sun turama ango fa. Ciki harda Hafizzullah. Ban tanka musu ba face murmushi kawai da nake yi........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_ ____________ _Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me hamsin me dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata mai albarka..._ _idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo unguwar tarauni dake garin Kano sai akira number opay dincan dake sama_ _zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._ _kofa a bude take ga duk Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_ ______________ ......Daga can tsakar gida kam taro yay taro gida ya kacame da hayaniya irin ta biki, anan ɗakin ƙawayena na zagaye dani. Wasu na hotuna wasu na kwalliya, wasu na hirarsu akan batun dinner da za'ayi bayan an kai amarya. Dan can gidan su Mansoor ɗinne suka shirya. Kiran da Yaya Musaddiq yazo yamin ne ya sakani saka gyale na rufe har fuskata. Shine ya kama hannuna har falon baƙi. Tunda muka fito kuwa gidan ya sake ruɗewa da buɗe-buɗe. Ni dai kaina na ƙasa a cikin gyale dan haka kawai sai naji ina jin kunya kowa. Ban ida daburcewa ba sai da muka isa falon baƙi. Dan ganin kaf kawunaina na ɓangaren uwa da uba harda Abba. Sai gwagganni da innoni suma dai duk suna nan na kusa sosai. A tsakkiyarsu Yaya Musaddiq ya kaini ya zaunar ƙasan carpet. Shima sai ya nema waje ya zauna. Kawu Musa ne ya fara min da nasiha mai ratsa jiki. Kafin sauran ma su dinga karɓa ɗaya bayan ɗaya. Daga baya suka koma faɗa da gargaɗi, yayinda ni kuma nike sharɓan kuka ta cikin gyale. Dan babu abinda ya tadamin hankali sai jin muryar Yaya Musaddiq na rawa alamar karaya sanda yake min addu'ar zaman lafiya a gidan aurena. Abba ma dai yamun tasa a taƙaice, daga baya kiran wayarsa da akai ya nema excuse ya fita, da alama kuma kiran da akai masan nada matuƙar muhimmanci ne. Dan naga sai da ya fara magana da Kawu Musa suka miƙe tare suka fita. Fitar tasu bai hana iyayena cigaba da mun nasiha ba, sai da suka gamsu sun min yanda suke buƙata kafin suka sallaman Inna Hauwa ta kamani ta maidani ciki, dan mazan zasu wuce massalaci ne daga can kuma za'a ɗauro aure. Dole sai da aka sake min kwalliya bayan nayi sallar azhar saboda na ɓata fuskar dan kukan da nasha. Kaya na canja zuwa wata shadda da taci uban aiki da stones sai walwali take yi. Ga ƙamshi irin na amare ƴan ƙwalisa ina zubawa. Acan ƙasan zuciyata kuwa jina nake duk wata iri kamar yanda aka san duk amarya da shiga irin wannan yanayin a irin ranar nan. Lokacin da ƙarfe biyu ke cika maza suka fara dawowa alamar an ɗauro auren gabana sai ya shiga wani irin luguden daka da sauri-sauri. Wani irin tsoro da fargaba na ratsa min cikin ɓargo da jijiya har ina jin wani kalar sanyi-sanyi duk da kuwa uban zafi ake zugawa a gari kasancewar watan azumin Ramadan na kawo jiki. Ƙawayena sun shiga min shaƙiyanci da buɗa a saman kai, sai na samu kaina da sakin hawaye masu zafin gaske da ban san dalilin yinsu ba. Shin murna da farin cikin mallakar matashin saurayi ƙyaƙyƙyawa ɗan ƙwalisa mai cikar kamala da dattako irin Mansoor ne, ko kuwa fargabar rabuwa da ƴan uwana biyu ne da ke a cikin tarkon wancan terror ɗin. Bily a lokacin sam na kasa ganewa. Na gagara banbance komai a yanda ya dace na fahimcesa. Sai ma wani sabon bugun zuciyar da na sake ji sakamakon shigowar aunty Zakiyya kamar a firgice tana kiran Gwaggo Gudidi data shigo tana miƙamin fura a kofi da aka dama wai na sha. Koda Gwaggo ta tambayeta lafiya, sai tace mata su Kawune ke kiranta kuma sunce tai sauri dan kamar dai akwai wata matsala. Da saurin kuwa ta fita alamar itama tana a cikin ruɗanin ne.. Na cigaba da zama kamar butun butumi a tsakkiyar ƙawayena daketa hotuna abinsu batare da su sun fahimci kamar akwai abinda ke faruwa ba. Muna nan dai shiru hayaniyar gidan na sake ƙaruwa alamar mutane na sake cika gidan ƙananun magana suka ɗan fara fitowa. Sai dai anƙi a fito da komai a fili ana ta son basar da mutane dai. Abinda ya ɗan fara tsayamun a rai shine rashin zuwan Mansoor gidan. Dan a burikanmu akwai zuwa hotuna bayan ɗaura aure da yace zasuyi shi da abokansa da kuma ni da ƙawayena da ƴan uwana. Amma dai zuciyata nata tausata akan masa uziri, dan maybe mutane sun masan yawan da hakan bazai yiwu ba ya cika wannan alƙawarin. Wannan tunanin yasa na danne zuciyata na ajiye wannan batun a gefe. Isowar masu kiɗan ƙwarya bayan sallar la'asar yasa Inna Hussaina zuwa ta fita dani a ɗakin ni da ƙawayena. Sosai gidan ya cika da mutane har sai da naji ƙwalla ta cika min ido. Dan ban san munada taron dangi har kamar haka ba da zasu iya nuna wannan soyayyar garemu a irin wannan ranar. Ko a wajen kiɗan ƙwaryar ma duk da ba rawa nake ba tsaye kawai nake tsakiya ƙawaye na da ƴan uwana masu rawar zagaye da ni sai da dinga shigowa ana min liƙi, wasu kuma sukanyi hoto dani a waya harda masu video. Kusan ƙarfe biyar sai ga Gwaggo Magajiya riƙe da hannun Yaya Musaddiq da Hafizzullah wai sai sun min liƙi. Kallo ɗaya na musu su duka biyun na fahimci sunyi kuka. Dan idanun Yaya Musaddiq jajur suke. Na Hafizzullah kuwa har sun kumburo saboda shima fari ne kamar ni, dan mu biyun munfi Yaya Musaddiq haske. Hankalina ne ya tashi a take nima idanuna suka ciko da ƙwalla ina binsu da kallo. Amma sai suka ƙi yarda mu haɗa ido sai liƙi da sukemin kawai ana ihu kawunansu a ƙasa suna murmushin da ni kaɗai na fahimci na yaƙe ne. Duk yanda naso riƙe kukan nawa hakan ya gagara, bamma san sanda na riƙo hannayensu su duka ba cikin nawa. Dole suka kalleni a tare. Kukan na sakar musu kawai na faɗa jikin Yaya Musaddiq. Shima sai Hafizzullah ya ya rungumemu mu duka biyun ya saki nasa kukan. A take wajen yay tsitt, wasu na ganin mun birgesu da fassara abin namu da tsananin shaƙuwa ne da soyayyar juna. Wasu ko da suka san wani abu dake ɓoye sai suke jin tsananin tausayinmu da jin karaya suma. Nan take aka ringa tuno alkairan iyayenmu da musu addu'a. Dole dai Yaya Musaddiq ya jamu muka fita daga filin. Nan Gwaggo Gudidi ta jamu zuwa ɗakinsa ta dinga lallashinmu da mana nasiha. Haka kawai maganganun nata sai suke ta min kai da kawo dan na gagara fahimta da fassara wasu nikam. Kiran Yaya Musaddiq da akai a waya ne ya sashi miƙewa ya fita. Babu jimawa ya dawo yay kiran Hafizzullah. Anan ne Gwaggo ke tambayarsa lafiya? Sai yake sanar mata zasu maida kayan can gidan ne dan an gama kwashesu. Cikin nuna gamsuwa tace, “Oh to hakan yayi, bari na tattara su Zakiyya su sameku acan yanda aikin zaiyi sauri. In sha ALLAHU ai yanzu zakaga an kammala”. Da to ya amsa mata yana ficewa. Hafizzullah ya canja riga suka fice. Babu abinda na gane a zancen nasu, amma na gagara haƙuri sai da nace, “Gwaggo kodai akwai abinda ke faruwa ne? Naga sai magana kuketa yi kamar a ƙudundune?”. Kai tsaye tace min, “A'a babu komai ƴar nan. Kinga tashi mu koma ciki dan da anyi magriba zaki yi wanka a wanke wannan fentin da aka cika miki a fuska. Koda masu ɗaukar amarya dai sun zo ɗin sai dai mu yazam mune muka jirasu basu zasu jiramu ba”. Banda tacewa face bin umarninta. Tunda dama nasan dai ya kamata a kainin da wuri kodan dinner da su Mansoor suka shirya. Amma kwalliya kona wanketa dole a sake wata basai munje can gidan ba kuma aita dibi-dibi nasan Mansoor da ƙosawa akan abu, sam baya son jira. Acan ƙasan zuciyata kam ina jin babu daɗi saboda rashin ganin duk jama'ar gidan a cikin sha'anin bikin nawa. Dan yaran duka babu wanda na gani har Auta da su Yaya Abbas da Nabel da shi banama zaton yazo gidan yana makaranta. Gara ma ita Mum ɗin bayan ɗaura aure sanda Yaya Musaddiq yazo ya fita dani ɗin nan zuwa falon baƙi na ganta ita da wasu ƙawayenta a tsaye sunata faman dariya da alama akwai abinda suke tattaunawa a tsakaninsu. ★★Bayan nayi sallar magrib kamar yanda Gwaggo ta faɗa aka haɗamin ruwa mai zafi da kayan turaren ƙamshi a ciki nayi, koda na fito da taimakon Gwaggo na kimtsa jikina. Ta kuma tsareni sai da naci abinci da wani nama na musamman mai romo a cikin kula. Naman yayi daɗi dan haka na saki jiki naci sosai, koda tace sai na cinyesa ma ban musaba na dage na cinye nasha romon. Hakan yasa cin abincin bai armashi ba garan sosai. Tun ina kallon agogo harna daina. Sai dai a raina inata mamaki, dan tara dai-dai ya kamata ace muna a wajen dinner. Amma gashi anan har taran yama wuce ba'a kaini gidan su Mansoor ba balle ai batun zuwa dinner. Bily kar kiga kamar na cika zumuɗi ne fa. Kawai dai bana son naga an saɓama Mansoor alƙawari ne, to amma yaya zanyi, sai sanda aka kaini. Matsalata kawai da babu waya a hannuna. Muna nan zaune Gwaggo na ƙaramin nasiha kusan goma saura akace su Yaya Musaddiq sun dawo sai a fito da amarya ga motoci sun zo. Sai a lokacin kuma naji duk na rikice. Nanfa na saki musu kuka. Duk yanda akaso na miƙe naƙi nai hakan har sai da Kawu Musa da kansa ya shigo yana faɗa sannan. Kuka nake sosai har numfashina na shiɗewa. Amma babu wanda ya saurareni, sai ma gaban Mum da aka kaini na roƙi yafiyarta. Cikin taɓe baki tana wani fisge-fisge ta ce, “ALLAH ya yafe mana baki ɗaya sai aje aita haƙuri, dama ita rayuwa ai haka take babu tabbas...” ganin tana neman sakin layi Gwaggo ta kamani muka fito. Abba ma an sake kaini na masa sallama. Yaya Musaddiq kam ya rufe kansa a ɗaki yaƙi yarda. Nasan kuka yake, dan haka nima na ƙara ƙarfin nawa kukan ina tutturjewa, amma babu wanda ya saurareni sai dai wasu nata bani haƙuri wasu na tayani matsalar ƙwallar aka fita dani. A rikicen da nake yasa bamma san kala ko adadin motocin da suka zo ɗaukata ba. Ni dai kawai an sakani a motar da ƙamshin da take yaso sakamin razani a zuciya, sai dai kuma rashin ƙarfinsa sosai da ruɗanin da nake a ciki na rabuwa da ƴan uwana ya hanani bama abin muhimmanci. Gwaggo Gudidi da Inna Magajiya ne tare da ni, sai gaba Ruƙayya ce ta office ɗin mu data zame min kamar babbar ƙawa ita da ƙanwar mijin Aunty Zakiyya........✍️ _🤭Uhummm inji mai ciwon haƙori._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚_ _______________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 _______________ .......Har muka iso kuka nake sosai, haka dai aka fita dani kaina a lulluɓe. Ina jin mutane nata yaba gidan. Hakan baisa naji wani abu daban ba saboda nasan gidan Mansoor kam tabbas yayi ƙyau da tsari. Sannan babu laifi babbane. Da addu'a na shiga kamar yadda Gwaggo ta bani umarni. Dan motar da aka ɗakkoni ce kawai dama ta shigo har cikin gidan. Sauran duk a waje suka tsaya. A falo aka ajiyeni kamar yanda Inna Magajiya tace. Mutane suka ɗan shishshiga kitchen da inda ba'a rasa ba. Bedrooms dai a rufe suke duka biyu dake a gidan kamar yanda naji suna faɗa. A karan farko na ɗan ji mamaki, dan nasan bedrooms huɗu ne a gidan Mansoor. Amma dai banda tacewa, bayan mutane sun gama zazzagawa suka fita dan dare ya farayi za'a maidasu gida. Sai da kowa ya fita sannan Gwaggo ta kama hannuna ta kaini bedroom da naji tana faɗa bayan ta buɗe da makulli, anan ne na gane ashe keys ɗin na hannunta sune dai suka hana mutane shiga wai dan kar a ɓata tunda dare yayi babu damar zama a gyara min. A bakin gado ta zaunar dani, tana sake jaddada min kalmar haƙuri, haƙuri dai da duk abinda zan gani, dan shi aure ibada ne bawai wasan yara ko nanaye kamar yanda mu yaran yanzu muke tunani ba. Ni dai kuka kawai nake zabga mata. Tadai samu ta zame jikinta ta gudu ta barni. Kuka na sake fashewa da shi irin mai cin rai da zuciya ɗin nan, harna zame na kwanta a gadon batare dana sani ba na cigaba da kukana. Tun ina darzar kuka da tunanin Mansoor zai iya shigowa har al'amarin ya fara bani tsoro. Dan gari yay wani irin shiru sai kukan karnuna amma babu Mansoor babu labarinsa. Kai komai ya fara canja min daga yanda nake tunani da hasashensa. Dan daga jiya zuwa yau komai da nake gani ba irin tsare-tsaren Mansoor ɗina bane. Komai yana zuwa min a banbancin abinda muka tsara. Mi hakan ke nufi, Mansoor ne ya canja komai a yanda na sanshi ko yaya al'amarin yake ne?. Banda mai bani amsar ko ɗaya daga cikin tambayoyi na. Dan haka na cigaba da kwanciya a wajen ga ciwon kai mai tsanani na ratsani, kafin ma wani dogon lokaci na fara rawar sanyi. Ina jin yanda wata iskar hadari ke tasowa da ƙarfin tsiya amma na kasa ko motsi. Haka na cigaba da kasancewa a wajen na tsawon lokacin da ban san adadi ba har barci yay awon gaba dani batare dana farga ba.... Hasken rana irin mai kashe idon nan ne ya addabi fuskata. Dole na buɗe idanuna da sukai min wani masifar nauyi saboda kukan da nasha. Ganin a inda nake nada banbanci da inda na saba ya tuna min da mike faruwa. Zumbur na miƙe zaune ƙirjina na luguden daka. Ɗakin na shiga bi da kallo, madaidaici ne ba wani ƙato ba can. Sai dai kayan sun masa ƙyau cas. Abu na farko dana fara lura da shi sam ba irin fentin gidan Mansoor bane ba, kuma bedroom da Mansoor ya nunan a matsayin nawa randa mukazo ƙatone sosai. Ƙirjina yay wata irin girgiza. Sai dai tunawa da banyi sallar asuba ba yasa na tattare komai zuwa gefe na miƙe. Ƙofar da na gani da nakema zaton bayi ne na nufa. Nan ma dai ba irin toilet ɗin gidan Mansoor bane. Kai ƙwalwar kaina fa na neman juyewa. Amma dai na sake ƙoƙarin dakewa nayi alwala na fito. Akwatin dana gani saman bed side drawer na buɗe, na samu hijjab kamar yanda nai fata, dan haka na nutsu domin gabatar da salla.. Ina idar da sallar na miƙe kamar zararriya, dan kaina gaba ɗaya a juye yake da komai. Fitowa nai gaba ɗaya daga bedroom ɗin. Ganin wani dake a kusa da shi yasa na buɗe na shiga nan. Gabana ya faɗi. Dan babu komai a ciki sai ƙatuwar katifa irin wadda ba'a sanyawa a gadon nan. Sai wani ɗan ƙaramin akwati mai shegen ƙyau. sai takalma haif cover suma dai masu ƙyau sosai, a saman katifar da agogo da waya kusa da shi, sai can gefe kaya ne da aka cire shadda honey color data ciza sosai. Ga wani ƙamshi na musamman dake tashi har ina jin kamar nasan ƙamshin, amma dai na hana zuciyata hasasowa. Fitowa nai ƙwaƙwalwata na sake birkicewa. Falo ne dake tsaka tsaki, shima dai yayi ƙyau da kayan da aka jera masa, saukar idanuna akan wanda ke zaune daga can cikin ɗaya a kujerun dining ya saka zuciyata wata irin girgizar da ya rage kaɗan ta biyo ta bakina ta fito. Karkarwa jikina ya shiga yi, irin wadda bamma san na cigaba da tafiya ba cikin matuƙar sassarfa. Har na iso gaban dining ɗin bai ɗago ba. Yanata danne-dannesa a laptop hankali kwance. Ga mug dake ta turiri alamar shayi ko coffee a ciki. “Wanene kai? Miya kawoka nan? Ina ka kaimin mijina?”. Tambayoyi uku a jere suka fito a bakina dake rawa. Kamar baima jini ba, ko nace bai san da zuwana wajen ba. Dan ko motsi baiyi ba balle ya ɗago ya kallan, aikinsa kawai yake hankali kwance cike da ƙwarewa. A matuƙar harzuƙe hawaye masu zafi na rige-rigen sakko mini cikin daka tsawa na ce, “Da kai nake magana malam!!”. Cak ya tsaya daga danna keyboard ɗin laptop ɗin da yake yi. Nasan kuma yanda nai tsawar ne da matuƙar ƙarfi ga jikina na girgizar tashin hankali da ɓacin rai. Na sake zabura zan masa wata tsawar ganin nan ma bai amsa min ba yay wata irin juyowar da ta saka ni yin tsalle a lokaci guda da zuciyata saboda tsabar kiɗima. Sai gani rijif a ƙasa wanwar. “Ba'a min tsawa”. Ya faɗa a dakensa cikin silent voice ɗin nan nasa na gadara babu alamar damuwa da halin da yaga na shiga kuma. Sai ma ɗauke kansa da yay ya sake maidawa ga screen ɗin laptop ɗin. Yaraf kake jina na ƙarasa zubewa ƙasa gaba ɗaya. A hankali sai kaina ya fara juyawa, yayinda lips ɗina ke wata masifaffen rawa ina nunasa da yatsana da shima ke rawar. Tun ma ina banbance tsakanin haske da duhu har hakan ya fara neman gagarata. Tuni na tafi luuu ƙasa gaba ɗaya alamar ina neman suma. Daga haka ban sake sanin mike faruwa ba sai farkawa nai na sake gani na a inda na faɗin yashe. Da ƙyar na iya miƙewa hannuna dafe da kaina dake faman juya min. Kai tsaye inda nasan yana zaune na kai idona. Wayam babu kowa daga shi har laptop ɗin nasa. Sai mug ɗin nan na shayi kawai ajiye. Falon na juya ina sake ƙarema kallo. Yanzu kam ni kaɗaice a cikinsa da alama, sai zuciyata ke ayyana min kodai mafarki ma nake yi ne? A gaskiya sai dai mafarkin kuwa, dan wanda idona ya ganarmin a gidan nan nafi fatan ya kasance a mafarkin ne. Kasa daurewa nai, cikin layin juyewar kai tamkar wata ƴar maye na nufi ƙofar da nake ƙyautata zaton hanyar fita ce. Da ƙyar na iya lalubar handle ɗinta na buɗe, cikin yanayin dishi-dishi na dinga bin harabar gidan da kallo, ba wata babba bace dan bata wuce ɗaukar motoci uku ba suma a ɗan takure. Motar da nake ƙyautata zaton an ɗakkoni a ciki jiya kawai ce a ajiye. Saukar idanuna akan buzun dake zaune a gate yana fifita wuta alamar shayi yake dafawa yasa ni jin ƙarin gwiwar nufar can. Sai dai ina kai rabin harabar wani mahaukacin farin kare mai kama da tumakin turawa a gashi ko nace zaki a ƙarfi da girma ya wani irin zaburowa kaina daga inda yake kwance a saman motar yana haushi na hauka ga harshensa waje. Daburcewa nai na rikice dan na tsani kare. Balle irin wannan mara ƙyan gani da suffa, sauƙinsa ɗaya daya kasance fari. Ganin yana gab da iskoni na ƙwalla ƙara ina durƙushewa a wajen na ƙanƙame jikina dake rawar mazari. “Laalah!”. Aka faɗa a ɗan tsawace, sai dai hakan bai hana fitar muryar tasa acan ƙasan maƙoshi ba. Sannan karen ya tsaya cak bai ƙaraso inda nake ba. Sai kallonsa da yay yayi haushi sau biyu yana kallona kamar mai son masa ishara dani. Da alama ya fahimci mi karen ke nufi, dan a daƙile ya sake faɗi, “leave here”. Abin mamaki tinƙas-tinƙas karen nan yabar inda nake ya koma saman motar daya taso yay kwanciyarsa kamar bashi ba. Sai lokacin na samu damar sake fashewa da kuma. Ganin ya juya abinsa zai koma inda ya fito na miƙe a zabure nima. Kusan atare muka shigo falon. Batare dama nasan mi nakeyi ba a tsawace na furta, “Ina ka kaimin mijina? Mi kayima Mansoor ɗina? Miya kawoka gidan aurena? Yanzun ma kidnapping ɗina kayi?”. Bai ko kallan ba ya cigaba da tafiyarsa zuwa bedroom ɗin nan mai katifa. Ai bamma san lokacin dana daka wani uban tsalle ba nabi bayansa nima. Dan amsoshin tambayoyina kawai nake buƙata. Dole kuma ya bani, inba haka ba kuwa zaiga tsagwaron tashin hankali, kuma a wannan karon saina tabbatar masa da kaidin mace, dan ko dare bazan sake kaiwa a gidan nan ba. Ina isa ƙofar ɗakin yana rufota bamm, handle ɗin na kama da rawar jiki na fara murɗawa da jijjiga ƙofar amma ko motsi batai ba alamar ya kulle ta ciki. Wani irin kuka mai tsuma zuciya na sake fashewa da shi ina cigaba da jijjiga ƙofar da bugata a haukace amma mutumin nan ko tari baiyi ba. Galabaita ta sakani silalewa jikin ƙofar zuwa ƙasa wasu zafafan hawaye na rige-rigen sakkomin da masifar gudu. Cikin jin karaya da sarewa na shiga furta, “Awwab why? Why Maash? Why zakamun haka a ranar da tafi kowacce rana muhimmanci a garemu. Mike shirin faruwa? Ina mijina Mansoor?!! Miyyasa ka sake satoni zuwa nan a ranar auren...” kuka ya sarƙeni na kasa cigaba da maganar✍️ 🤔🤔🤔😞 Alhamdullah 🙏. Anan zamu dakata a book one na wannan littafi mai suna TSUTSAR NAMA. sai kuma ALLAH yasa muna da rabon kaiwa bayan salla. ★Tofa masu karatu yaya take ne?. ★Mike shirin faruwa?. ★Ina Mansoor ango?. ★Miya kawo Maash a madadinsa? ★Kidnapping Sam-G ya sake yi kamar yanda take tunani itama kokuwa yaya al'amarin yake? ★Waye yay kidnapping Sam-G a farko tunda Maash ya tabbatar mana bashi bane?. ★Waye Maash ya kashe ma wai? ★Wake amfani da sunan Samraah wajen amsar kuɗi maƙudai haka a wajen Maash? Tunda tace ba ita bace. ★Maash zai samu nasarar amsar videon a wajen Sam-G kuwa? ★Magana fa ake ta an kawo amarya gidan mijinta amma ango ya rikiɗa zuwa wani daban. ★Hhhhh masu karatu akwaifa gurmi. Gurmi gagarumi ma kuwa na musamman. Dan littafin nan ɗauke yake da nasa salon shima. Hargitsi da cakwakiyar dake cikinsa kuwa. Hhhhumm ba'a magana, dan bama mu fara komai ba sai a book 2 da zai zo bayan salla, kuma komai da kuke buƙata yana a cikinsa ne. ★Dan shi kansa Maash fa akwai wani ƙunsashen al'amari a tashi duniyar dako fara taɓota bamuyi ba. ★Kai kar dai na cikaku da surutu, ku shirya kawai tsaff zuwa bayan salla idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya domin samun duka wannan amsoshin a TSUTSAR NAMA BOOK 2 har ma da wanda baku sani ba. ★Ya rabbi ka karɓi ibadunmu, ka gafarta mana ka yafe mana kurakuran mu. Ƴar uwa! Ɗan uwa! Duk wanda naima ba dai-daiba ya gafarceni. Nima na yafema kowa. Kada ka bari ko ki bari ku zama cikin jerin mutanen da zan iya kaima UBANGIJINA kuka a kansu a acikin wannan watan mai tunkaromu. Wannan shawara ce. Dan nima bazanyi fatan nazama cikin wanda kuma zaku kai ƙarata wajen UBANGIJINA ba. Fatana kumin addu'ar fatan alkairi nima na muku tare da iyayenmu baki ɗaya. Taku har kullum👎 BILKISU IBRAHIM MUSA (Bilyn Abdull 💞) (C)2024. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒐𝒏𝒆_ _Assalamu alaikum masoya. Fatan alkairi a gareku tare da barka da salla. Ya rabbi ka amshi ibadunmu ka yafe mana kurakuran mu. Ka gafartama iyayenmu. Kafin komai dole na fara da tarin godiya a gareku musamman wanda suka sayi kayan salla a wajena. ALLAH yabar zuminci. Nagode sosai da yanda kuka nuna ƙarfafawa a gareni akan wannan kasuwanci. Ina sake albishir a gareku da in sha ALLAHU wasu kayanmu na gab da sauka musamman abayoyi da handbags na yara dana manya. Sai kowa ya ƙara zuba kuɗi a asusu 😂. Gamu mun dawo filin daga. ALLAH ya bamu ikon sauke nauyin juna mu daku, ALLAH ya haneku cin hakkinmu, muma ALLAH ya hanemu tauye hakkinku 🙏. Godiya ta musamman gareku baki ɗaya 😘😘😘🙏_. .......Kuka nayi sosai a wajen. Dan har sai da kaina ya dinga sara min tamkar zai rabe gida biyu sannan na miƙe. Cikin layi irin na rashin ƙarfin jiki na koma ɗakin dana kwana. Handbag ɗina na ɗauka tare da hijjabin danai sallar asuba. Gudun haɗuwa da shegen karensa ya sakani bi ta kitchen duk da ban san takan gidan ba. Ta bayan na bi, hakan yasa har na zagayo inda gate yake banga karen ba. Zaram maigadi dake zaune yana jin waƙa ya miƙe. Bakinsa har rawa yake wajen gaidani. Ban amsa masa ba. Face cemasa “Buɗe min!” cikin kakkausar murya da tsawa. Cikin daburcewa da wuru-wuru ya ce, “Amma Hajiya oga baice....” “Wlhy idan baka buɗe min ba zan haɗa kai da ogan na danna muku zagi.” nai maganar ina fisgo sandarsa dake ajiye saman bench. “Zaka buɗe min ko sai na ɗora maka ita a saman kanka”. “ALLAH ya huci zuciyarki Hajiya bara na buɗe”. Ya faɗa cikin rawar jiki yana nufar ƙaramar ƙofar. Key yasa ya buɗe, na watsa masa harara sannan na fice. Sai da na tabbatar na fita sannan na jefa masa sandarsa nai gaba. Dogon street ɗin nabi da kallo, mai ɗauke da lafiyayyen titi. Sam ban gane a wace anguwa bane ba. Dan haka hankalina ya tashi. Amma sam banji na sare ba na cigaba da tafiya sauri-sauri duk da rashin ƙarfin jiki da nake ji. Addu'a kawai nake ALLAH ya kawo mai napep. Kai koda mota ce zan nema taimako. Na ɗan yi nisa a tafiyar inayi ina waigen bayana dan ji nake kamar makirin zai iya biyoni. Jiri ne ke ɗibata sosai, dan kaina har yafara harmutsawa. Na ɗan tsaya ina mai dafe shi da ambaton sunan UBANGIJI. Dai-dai nan wata farar mota da har ta gittani ta dawo da baya. “Baiwar ALLAH lafiya kuwa?”. Muryar matashiyar mace ta daki kunnuwana. Hannuna na janye daga saman kaina. Cikin kallonta dishi-dishi a wahalce na furta, “Bakomai hajiya.” “A ya zakice ba komai. Gashi kinayi kamar ma zaki faɗi”. Tai maganar tana fitowa a motar. Riƙoni tai dan jirin ne ya ɗeban zai zubar. Muryarta da damuwa sosai ta ce, “Kinga bara na sakaki a mota. Sai ki faɗamin ina zaki na kaiki”. Ganin mace ce, kuma dama abinda nake buƙata kenan sai banyi musu ba. Da taimakonta na shiga motar. Ina zama na lumshe idanuna kaina na ƙara ƙarfin sarawa matuƙa. Koda ta shigo ta zauna tana tambayata ina zata kaini kasa bata amsa nayi, hakan yasa tai shiru ta bani ɗan lokaci da take tunanin na samu nutsuwa sannan ta sake tambayata. Da ƙyar na iya furta mata. “Yakasai”. “Okay ba damuwa. Amma ina ganin mu fara zuwa clinic sannan. Dan kina cikin halin buƙatar taimako. Ni likitace”. “Karki damu ki kaini gida kawai na gode”. Na faɗa a matuƙar wahale. “Bazai yiwu ba, kiyi haƙuri na taimakeki dan ALLAH”. (Dan ALLAH) data ambata yasa ban iya sake cemata komai ba. Daga haka ma na sulale ban sake fahimtar komai ba. ★ Hankali tashe maigadi ya nufi cikin gidan. A dai-dai ƙofar shiga falo ya samu Maash tsaye. Rikicewa yay, musamman da yay ma fuskarsa kallo ɗaya ya ganta a tsuke kamar hadarin gabas. Cike da tashin hankali ya zube ƙasa saman gwiyawunsa yana kwaso rantsuwa. “Wlhy tallahi ranka ya daɗe ba laifina bane ba. Tace idan ban buɗe mata ba zata fasamin kai ne.” Shiru baice masa komai ba. Maigadi ya sake rikicewa yana jera rantsuwa da magiya duk a gurbi ɗaya. Sai da ya mula dan kansa a hankali ya furta, “Jeka kan aikinka”. Duk da a sauƙaƙe yay furucin hankalin maigadi bai kwanta ba sam. Dan gani yake akwai abinda zai iya biyo baya. So yake ya cigaba da bada haƙuri har sai yasan ainahin gaskiyar abinda ke zuciyar mai-gidan nasa, sai dai kuma baiga muhallin yin hakan ba. Dan haka sum-sum ya juya bakin gate zuciyarsa na rawa matuƙa. Cikin taraddadi da ƙaulani ya koma, kusan mintuna goma da komawarsa yana zaune ya zabga tagumi akai horn. Firgigit ya tashi domin dubawa. Sai da ya buɗe ƙaramar ƙofa yaga mai horn ɗin sannan ya buɗe gate ɗin gaba ɗaya. Cikin girmamawa ya gaisar da Hayatu dake shigowa. Shi kuma ya ɗaga masa hannu yana ƙarasa shigewa cikin gidan. Yana fitowa a motar Laalah ya zaburo, inda yake yazo shi adole ya sanshi, hakan ya sakashi sakin murmushi da kai hannu ya shafa kansa yana faɗin, “Laalah how are you?”. Daga haka ya wuce zuwa cikin gidan. Koda yay sallama a ƙofar sai da aka kwashe kusan minti ɗaya kafin a amsa masa, tare da bashi izinin shiga. Sarakin na zaune tamkar babu abinda ke damunsa. Hasalima dukan hankalinsa naga wayar hannunsa ne. Koda Hayatun ya shigo ma bai ɗago ba. A haka ya amsa masa gaisuwar da yay masa. Sanin hali yasa Hayatu bai damu ba ya cigaba da maganarsa. “Sir Alhamdullah yanzu haka tana tare da ita. Sai dai tace akwai matsala. Dan tana shiga motar ta sume mata, a yanzu haka ma suna clinic, sun kuma tabbatar da jininta yayi matsanancin hawa da take buƙatar taimakon gaggawa saboda gudun samun matsala a zuciyarta. Amma nadai basu damar yimata dukan abinda ya dace”. Karan farko ya ɗan ɗago ya kalla Hayatun, sai kuma ya maida kansa ga wayar batare da yace komai ba. Tsahon mintuna biyu kamar yama manta da shi sai kuma ya ajiye wayar a gefensa. Hannunsa ya ɗan matsa tare da ɗagowa ya zubama Hayatun idanunsa. Dole Hayatu yay ƙasa da nasa kan dan baya iya jure irin kallon nan na ogansa mai kama da na abokin yaƙi a filin daga.. Cikin silent voice ɗin nan nasa da janye idanunsa daga kansa ya furta, “A sanarma Hameed ya shirya zuwa 9 zamu wuce Abuja. Sai kai magana da Faisal zamu iso masa da mara lafiya ya taremu a airport”. Sosai Hayatu ya zaro idanu waje. Duk yanda yaso haɗiye abinda ke masa kai kawo ya kasa hakan. Bai ma san sanda ya furta, “Amma Sir baka ganin tafiya da ita zai iya ɗarsama family ɗinta wani abu a rai kuwa? Jiya ne fa suka kawota nan a matsayin amarya. Kasan fa sunan arewa komai nasu na tafiya da addini da al'ada”. Ko motsi Maash daya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanu baiyi ba balle Hayatu yay tunanin samun amsa. Ya kuma san shirun nasa na nufin bazai tanka ɗin ba, ya kuma gama zartar da hukunci kenan. Jiki a sanyaye Hayatu ya juya zai fita. Yayinda yake ta sake-saƙen mai fishshesa a zuciya. Dan dolene fa suyi wani abu da zai gamsar da family ɗin ta. In ba hakaba akwai babbar damuwa fa, kwaɓarsu zata iya yin ruwa batare da sun farga ba, shi komai ma sake ruɗar da shi yake. Dan yarasa dalilin ogan nasa na ƙulla igiyar aure tsakaninsa da ƴar bala'in yarinyar nan. Tunda yasan idan amsar video ɗin nan yay niyya da tuni ya amsa tako wace hanya ai, duk da dai ya fahimci itama yarinyar akwai taurin kai, sannan tana da power a cikin al'umma game da aikinta, maybe shiyyasa ogan nasa yaƙi yin komai kai tsaye a kanta ya biyo ta wannan sigar. Gashi bai sanar masa komai akan shirin nasa ba. Hasalima sai a jiya shima ya san da batun auren bayan sun baro Lagos a jirgi yake sanar masa. Ya shiga shock matuƙa, sai dai bashi da hurumin iya cewa komai tunda ya riga ya zartar da hukunci, amma ya yini ya kwana al'amarin nan na juya masa a rai. Dan duk duniya shine kaɗai kuma yasan Maash ɗin yayi wannan auren, ko su dangin yarinyar basu san shine ba, saboda baije musu a Maash ɗin ba. To koma dai miye, shi kam zaiga yaya wasan zai kaya, dan shi ɗin shaida ne, ogansa mutum ne mai tsananin taurin kai da aljananci na gaske. Ga hatsabibancin masifa da dagiya akan abu, ya tabbatar ba son yarinyar nan yake ba, dan inda hakane kai tsaye zaije yace yana sontan saboda shi bai iya ɓoye-boye ba tamkar bature yake komai nasa kai tsaye yake yinsa. Ko minene a ransa kai tsaye yake fiddashi koda bazai ma kowa daɗi ba shi babu ruwansa idan yayi dai-dai da ra'ayinsa kansa kawai yake kallo.. Kai tsaye anguwar su Samraah ya nufa, dan dolene yaje ya tsara abinda ya dace gudun samun akasi.. ★★★ A gidan Abba kam sai a safiyar yau ƙananun magana suka fito sosai. Dan kuwa Mom ta titsiye Abba taji komai daya faru a wajen ɗaurin aure dama kafin ɗaurin auren. Dan haka ta shiga bazama na kusa da ita su kuma suka ɗauki zance ƙus-ƙus. Tun anayin abin a gwargwaɗe har dai komai ya fito cewar bada Mansoor aka ɗaurama Samraah aure ba da wani ne daban. Dan mahaifiyarsa ta shata layi akan auren nasu, duk da dai shi Mansoor ɗin yaso bijirewa amma su Kawu Musa suka ce bazasu bashi ba saboda abinda mahaifiyar tasa tazo tayi a jiyan har gida batare da matan cikin gida sun sani ba sai su Gwaggo Gudidi kawai. Tun dai zance na iya cikin gida har maƙwafta suka fara shigowa jin gulma da kawo wadda suka jiyo a waje. Yanda Mom ta nuna farin cikinta a fili akan abinda ya farun ya ƙona zukatan su Gwaggo Gudidi da ƴan Gwarzo. Sai ga faɗa ya kaure tsakaninta da Aunty Jimmai babbar ɗiyar Kawu Musa. Kafin kace mi gida hargitse. Suka haɗu sukama Mom tatas, dan babu abinda suka manta basu faɗa mata ba har sai da tai kuka. Kuma Gwaggo Gudidi ta tabbatar mata indai tana raye sai Abba ya ƙara aure. Da ƙyar da ƙyar dai Musaddiq ya kwantar da wannan tarzoma. A kusan kuma dai-dai lokacin Hayatu ya iso gidan. Inda ma ALLAH ya taimaka Musaddiq da Abba da su Kawu Musa na ƙofar gida a lokacin da ya iso ɗin, dan haka ya samu tarba ta mutunci. Cikin ɗar-ɗar da addu'a a ƙasan ransa bayan sun gaisa ya sanar da su abinda ke tafe da shi kamar yanda ya tsara domin bama ogansa kariya. Hankalinsu ya tashi da jin Samraah babu lafiya. A take babu ɓata lokaci suka muƙe domin binsa asibiti dubata. Bai hanasu ba, dan bashi da wani zaɓi, sannan hakanne ma zai taimaka masa tsarin nasa ya tafi dai-dai yanda yake buƙata batare da Maash ya rufta ba ko shi dake ɗan kore ba.........✍️ Hummmm🥱 _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐_ .......Hankalinsu ya tashi matuƙa da ganin yanayin Samraah a asibiti. Yayinda Dr Su'adah ta sake ruɗar da su da bayanin haɗarin da Samraah ke ciki. Tare da tabbatar musu idan ba'a sadata da ƙwararren likitansu dake birnin tarayya Abuja da zama ba za'a iya rasata, dan zuciyarta na gab da bugawa saboda yanda jininta yay tsananin hawa sama. Sam babu wanda yay musu akan yarda da hakan. Sai dai sun nema alfarmar Hayatu akan Musaddiq zai bisu zuwa Abuja ɗin. Rasa abincewa Hayatu yayi, dan ya tabbatar tafiya da Musaddiq bazai yiwu ba. Amma rashin mafita sai ya amsa musu da to su jira suji daga likitar yaya za'ai tafiyar. Sun gamsu da hakan, dan haka ya lallaɓa ya koma gefe ya sake samun Dr Su'adah akan ta taimakesa ya fita a tarkon mutanen nan, dan yana da dalilin da yasa baya so kowa ya bisu. Ita dai Dr Su'adah bata san ainahin mike faruwa ba, dan Hayatu ɗan uwanta ne na jini, abinda ya gaya mata kuma bashi ne ainahin alaƙar dake tsakanin Samraah da Maash ba. Dan haka babu musu ta taimaka masan. Ita ce ta tsara su Kawu Musa ta hanyar da dole suka gamsu akan za'a fara tafiya da Samraah ta jirgi ne, masu son bin bayanta sai suyi hakuri subi a baya ta mota nan da kwana biyu haka. Haka kawai sai hankalin Musaddiq ya kasa kwanciya, sai dai babu yanda zai yi tunda su Kawu Musa sun yarda. Haka dai yana ji yana gani aka shiga yima Samraah shirye-shirye dan wai za'a wuce da ita ne a jirgin ƙarfe takwas na dare... ★✓★✓★✓★✓ *_ABUJA AIRPORT_* Ƙarfe tara dai-dai jirgin daya taso daga Kano zuwa Abuja ya sauka a filin jirgin na birnin tarayya. Maash da tawagarsa na ɗaya daga cikin passinges ɗin wannan jirgi. Hakama Samraah da likitan da take tare da ita suna a jirgin. Sai dai a tsarin tafiyar sam babu abinda ya alaƙantasu da Maash. Hasalima shi yana a private section ne. Yayinda ita da likita suke a sashen kowa da kowa, koda yake ita bama ta a hayyacinta balle ta fahimta. Dan an shigo da ita ne a yanayin wadda take bisa umarnin likita da zataje gani a Anuja. Ko'a airport ɗin ma tuni Maash ya shige ɗaya daga cikin tawagar jerin motocin da suka zo ɗaukarsu. Yayinda ita kuma ambulance ta ɗauketa ta wani babban private asibiti da ake matuƙar ji da shi anan birnin Abuja ɗin.. *_KANO_* Anan Kano an wuce da Samraah an bar danginta da jimamami. Musamman ma Musaddiq da sam zuciyarsa ta kasa zama waje ɗaya. Kai shi tunma jiya hankalinsa a tashe yake da wannan aure. Sai dai babu yanda ya iya tunda su Kawu Musa sun bama mijin da suka aura matan yarda ɗari bisa ɗari. An ƙarasa dai wannan dare cike da jajantama juna bisa ga halin da Samraah ɗin ke a ciki. Daga ƙarshe dai a washe gari kowa ya shirya ya kama gabansa saboda wayar da akai da mijin na Samraah akan jikin da sauƙi suka ganta ta hanyar video call. Taro dai ya tashi an bar Mom da mijinta sai auta da Musaddiq da Hafizzullah kawai a gidan dan su Baby basa nan. Sai a washe gari suka dawo gidan. Hafizzullah ma dai shirin komawa makaranta yayi, duk da yaso zuwa wajen Samraah Musaddiq ya lallashesa akan yayi haƙuri tunda an kusa musu hutu, yanzu zuwa Abuja dubata ba nashi bane, shima ɗin da akace zai je su Kawu since ya dakata kada mijin yaga kamar ana nuna ya gaza ne. Badan yaso ba ya shirya ya wuce zuciyarsa duk babu daɗi. Dan duk wani masoyin Samraah ɗin zuciyarsa a ƙuntace take da abinda ya faru akan wannan aure da kuma halin ciwo da take a ciki yanzu. Dan idan ta shine ma baza'a ɗaura mata aure da wani da bata sani ba tun farko. Amma dai su Kawu Musa sun bada goyon baya babu abinda su zasu iya musamman ma shi dake amsa sunan ƙani a wajenta. Amma zai cigaba da binta da addu'a kamar yanda Yaya Musaddiq yace yayi. Musaddiq ɗin ne ya kaisa har Katsina da kansa. Ya sake masa nasiha sosai sannan ya juyo gida..... *_MANSOOR_* Kowa ka kalla a ahalin gidan hankalinsa a tashe yake. Dan kusan duk manyan suna a sashen su Mansoor da aketa ƙoƙarin gaggaɓe ƙofar ɗakinsa. Yau kwanaki uku kenan yana a kulle a ciki yaƙi ya fito. Lallashin duniya da roƙo yay biris da kowa. Tun ana ɗaukar abin nasa a fushi na ɗan lokaci har abin ya wuce makaɗi da rawa, dan zuwa yau ko motsinsa an bar ji a ɗakin, dole fa aka nemo mai gyara domin gaggaɓe ƙofar. Kuka sosai Mamynsu keyi tun jiya, dan ita kanta har sai da hawan jininta ya motsa. A yanzu haka a nane take da ƙofar ji take mai aikin ma kamar baya sauri ne. Ana ɓalle ƙofar mafi yawansu duk suka afka ciki, tsakanin Attahir da Mamy har turereniyar rige-rigen isa ake kan Mansoor dake kwance samɓal a ƙasa babu alamar rai a tare da shi. A tare suka ɗagosa, sai dai me yaraf ya koma alamar babu rai. Wani mahaukacin ƙara Mamy ta fasa mai firgitarwa, tamkar ƙiftawar ido sai gata ƙasa wanwar itama ta sume musu. Sake harmutsewa ɗakin yayi, dole aka kwashesu zuwa asibiti kamar yanda wasu suka bada shawara..... *_ABUJA_* Kaifin hasken rana da nake ji mai ƙarfi a saman fatar idanuna ya sani motsasu a hankali. Sosai sun min nauyi, dan illahirin jijiyoyinsu a takure suke waje guda. Hannuna da nake ji kamar an ɗaure nai ƙoƙarin motsawa domin kaiwa saman idanun, sai naji an sake damƙesa da ƙyau, tare da jin saukar wata murya cikin kunnena. “Bi a hankali akwai abu a hannunki. Sannu kin farka bari nai kiran likita”. Sosai naji gabana ta faɗi. A can ƙasan zuciyata na ayyana (likita) a fili kam babu abinda nake iya motsawa a jikina saboda illahirinsa yay min nauyi. Amma sai na shiga ƙoƙarin buɗe idanuna. Dishi-dishi nake gani, sai dai hakan bai hanasu sauka akan mutumin daya shigo bayansa da wasu mata guda biyu ba saboda yanda hayaniyar maganar da suke taja hankalina. Duk da ba ihu suke ba ko fidda sautin maganar tasu da ƙarfi. Ƙarasa buɗe idanun nayi da ƙyar sakamakon jin inuwar mutum a kaina. Wani irin faɗuwar gaba naji ta sake riskata, dan kuwa tabbas a asibiti nake, dan shigar wanda ke kaina tsaye kawai ta tabbatar min da shi ɗin likita ne. Sannu suka shiga jeramin, sai dai na gagara amsawa kowa a cikinsu, na dai zuba musu ido ne kawai ina binsu da kallon ƙurilla. Ko tambayoyin da likitan ke jeromin game da jikina na gagara amsa masa ko ɗaya. Fahimtar kamar a rikice nake da yanda nake bin ɗakin da kallo ya sakashi ƙyaleni shima. Sai cikin matan da ya shigo da su ne ke ƙoƙarin cire min allurar drip dake a hannuna. Kusan mintuna biyar muna a haka kafin ya sake juyowa ya fuskanceni. Cikin harshen turanci ya furta. “I understand that you are confused. This is a hospital, you are under the care of a doctor. Alhamdulillah, your body is very easy.” A hankali na kai hannuna saman kaina da har yanzu nake jinsa da nauyi, kafin na sake ɗagowa na dubesu murya a karye na ce, “Who brought me? Which hospital is this? Since when have I been?”. Da alama yanda na jera tambayoyin sun bashi mamaki, dan sai da ya ɗan waro idanunsa, sai kuma yay murmushi da faɗin, "Oh relax! You will all know. Now they will help you to fix your body, eat something and I will come back and answer your questions". Ya ƙare maganar yana nuna min Nurses ɗin. Fuska na ɗan ɓata, sai dai bance komai ba. Shi kuma ya juya ya fita da Nurse ɗaya ya barni da biyu. Da farko naso naƙi yarda, dan nafi son na fara sanin a ina nake. Sai dai yanda suka nuna damuwarsu da tabbatar min ƙin yardata zai iya taɓa aikinsu yasa na amince. Amma zuciyata taƙi gajiya da daina kai-kawon ganin ɗakin da naken matsayin wai asibiti. Saboda sam bai kama da asibiti ba fa, duk da gado da tarkacen ɗakin duk irin na asibitin ne, sai dai da gani na musamman ne su. Ga television ga freight, sannan toilet da suka kamani suka kaini a cikin ɗakin dai yake shima sam bai kama da asibi ba. Ciwon da jikina kemin ya sakani bin umarninsu nayi wanka da ruwan da suka tara min mai ɗumi. Nako ji daɗin wankan, na saka doguwar riga irin wadda na cire pitch color da alama ta asibitin ce. Bata sauka min har ƙasa can ba sosai, amma dai banyi tsirara ba. Gashi tana da faɗi babu wani takura. Alwala na ɗauro na daddafa bango na fito. Da sauri suka iso gareni suka taimaka min muka ƙarasa, a saman lallausar sofa ɗin ɗakin nace su zaunar dani, sannan na buƙaci hijjab na salla da sallaya. Sai dai da alama babu, sai ɗaya ce tace bari ta sanarma doctor a kawo min. Komai bance ba, na jingina kaina da kujerar na lumshe idanuna. Bata fi mintuna biyar ba sai gata ta dawo da sallaya da sabon hijjab a ledarsa. Ita ta ciromin shi, sannan ta shinfiɗa min sallayar. Har ƙasa hijjab ɗin ya sauka min sosai dan ko ƙafafuna ba'a gani, hakan yasa naji nutsuwa dan dama rigar bai gama sauka ba. Juyawa nai na tambayesa "What day is today?". A tare suka amsa min da, “Today is Monday”. (Litinin) na maimaita a zuciyata. A zahiri kam sai na sake tambayarsu alƙibla. Ɗayarce mai kama da musulma duk da shigarta zata iya saka kace ba musulmar bace amma akwai ƙaton tabon salla a goshinta ta nuna min tare da bayani, bance komai ba na kabbara sallata. Tun inayi a tsaye har hakan ya nema gagara. Dan dole na koma a zaune kasancewar duk sallolin da nasan suna kaina sai da na ramasu na kwanaki biyun nan da bana a hayyacina.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ .......Tun ina sallan shigowar doctor biyu. Sai dai ganin ban idar ba yana komawa. A na ƙarshe suka shigo su biyu dai-dai na idar ina zaune kawai nayi tagumi cikin dogon nazari da son sanin a ina nake wai. Jin muryar da banyi zato ba kasancewar nasan na kuɓuta daga garesu yasa na ɗago da sauri. Shi ɗinne kuwa. Wato yaron mugun nan Maash. Ganin yanda ina ɗagowa ya duƙar da nasa kan ƙasa kamar wani munafuki ya sani cigaba da kallon nasa kawai. Doctor ne ya katseni da tambayar yaya nake jin jikina yanzu. Cikin janye idanuna na amsa masa da Alhamdullah. Ya nuna jin daɗinsa kafin yay min nuna da mutumin nan. “Now you will get all the answers to your questions from him. I will send a nurse with your medicine. If you eat, she will give you.” daga haka ya juya ya fita. Shiru ɗakin ya ɗauka kusan na minti ɗaya, kafin a ƙufule cikin dasashjiyar muryata mai nuni da banda lafiya na furta, “Ya akayi na dawo gareku? Ina ne nan kuka kawoni?”. Sake duƙar da kai yayi kamar mai tsoron bani amsa, sai kuma a hankali ya furta, “Kiyi haƙuri nan asibiti ne. Yaya jiki?”. Wani irin takaici ne ya ƙuleni, dan haka cikin sake zafafa harshe na amsa shi da, “Ba ruwanka da jikina. Kaje ka sanar ma wanda ya aikoka yasa likitan nan ya sallaman. Sannan ku fita a sabgata. Idan ba haka ba zan sakaku nadama da dana sanin sani na. In ba hakaba zan tabbatar muku TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE”. Daga haka na yunƙura a hankali na miƙe, ko inda yake ban sake kallo ba na koma saman gadon. Dai-dai nan Nurse ɗin nan ta dawo... *_KANO_*. A matuƙar tashin hankali zuciyar Mamyn su Mansoor ta gama shiga. Dan suna isowa asibitin ta farfaɗo ita. Amma Mansoor kusan awani uku kenan likitoci na tare da shi ba kuma su musu bayanin komai ba. Sai dai faman kaiwa da komawa suke a tsakanin ɗakinsa zuwa ofisoshinsu. Tun tana hawaye har ma sun ƙafe ta koma na zuci. Nadama take ji na sake shigarta akan abinda ta aikata. Lallai tayi dana sanin biyema shawarar ƴar uwarta. Inama zata iya maida hannun agogo baya. Data goge komai da yake a yanzu da maida baya data shuɗe. Dan har ga ALLAH Mansoor shine ɗa mafi soyuwa a zuciyarta. Kodan tasha matuƙar wahala ne a yayin haihuwarsa, ko kuwa dan kamanin da yake da mahaifinsa. Sam bazata iya jure rasashi ba. Dan bazata taɓa yafema kanta ba. “Mamy dan ALLAH ki zauna ki huta, in sha ALLAHU ɗan uwana zai tashi. Kinga kema fa ba lafiyar ne da ke ba”. Attahir ne mai maganar cikin tsantsar damuwa ganin yanda Mamyn tasu ke faman kai kawo ga hannunta dafe da kanta. Yasan komai zai iya faruwa da ita, dan bata gama dawowa dai-dai ba ta fito a ɗakin da aka kwantar da ita. Anyi-anyi kuma taƙi ta koma dole aka haƙura aka barta. Dan Dad ɗin su ma haushin dagiyar tata ya sashi komawa can gefe ya zauna kawai bai sake kulata ba. “Attahiru bazaka gane ba. Nasan bazaka fahimta ba. Barni kawai kaji. Barni da abinda ya dameni. Ni da kaina na jefa rayuwar yarona a bala'i. Da nasan haka zata kasance da ban aikata ba. Da ban hanashi aurenta ba. Attahiru idan na rasa Mansoor nima zaku rasani ne wlhy”. “Dan ALLAH Mamy ki daina faɗa. In sha ALLAHU bazamu rasaki ba. Ki kuma daina zargin kanki kowa baya wuce kuskure ai. Mansoor zai samu sauƙi. Ki masa addu'a”. Kuka mai nauyi ta sakar masa tana ƙoƙarin dafe bango saboda jirin dake neman yaddata taji ya kwasheta. Da sauri yayi kanta ya riƙota. Da taimakonsa suka zauna yana jera mata sannu. Dai-dai nan shima Dad ɗin su ya taso, hakama ƙannensu da suka haɗe kai gefe suna kuka. A ruɗe duk suke tambayar miya faru, sai da ta ɗago ta ce musu ba komai sannan suka shiga sauke ajiyar zuciya. Hakan sai yay dai-dai da fitowar amintaccen likitansu Dr Gana. Kamar waɗanda aka zabura duk suka miƙe garesa har Mamy. Har rige-rigen tambayarsa yaya Mansoor suke yi. Shiko ya ɗan bisu da kallo cikin damuwa. Sai kuma a hankali ya furta, “Alhaji idan babu damuwa na ganka a office mana. Amma Hajiya tai zamanta Please”. Tsantsar tashin hankali ne ya bayyana a fuskokinsu. Yayinda Mamy ta fashe da kuka sauran ƙanensu na tayata. Shi kansa Dad ji yay ƙafafunsa sun masa matuƙar nauyi. Haka shima Attahir ya gagara tashi har sai da doctor ya sake musu magana sannan. Attahir ne ya fara jarumtar miƙewa, sannan shima Abban ya tashi suka nufi office ɗin su biyu kowanne na jin zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri tamkar zata faso ƙirazansu ta fito waje..... _Ni kaina Bilyn ku zuciyar tawa bugawa take. ALLAH yasa dai ba rasa Mansoor mukai ba😭😭🙆._ *_ABUJA_* ★Sosai na birkicema likitan nan akan nifa sai nasan a inda nake. Hankalinsa ya tashi, dan ya tabbatar min in har ban kwantar da nawa hankalin ba aikinsu zai iya komawa baya. Ganin fa ba saurarensa zanyi ba ya sanar min in a Abuja ne cikin MAASH HOSPITAL. “Abuja?!”. Kansa ya jinjina min da sauri. “Yes, yes. You were brought from our branch in Kano. Once you have finished receiving the medicine, you will return. Please calm down” Rasama mi zance masa nayi, sai kawai nayi shiru ina kallon PA da suka shigo kusan tare. Shi doctor ya zata na fahimcesa ne, dan haka ya sauke ajiyar zuciya da cigaba da kwantar min da hankali. Ko kulashi ban sake yi ba. Har ya gama ɓaɓatunsa ya fita. Ɗauke idanu nai da ga kan PA ina mai cije lips ɗina da ƙarfi. Na fahimci waɗan nan mutanen so suke sai mun kai matakin ƙarshe da su. So suke sai na bijire ma maganar Yaya Musaddiq da Mansoor. So suke sai na musu fallasar da zata ruguza dukkan tanadinsu. Kamar PA ya fahimci mi nake ayyanawa a raina. Takowa yay ya ƙaraso gaban gadon ya ajiye ledar hannunsa. Kafin ya ciro wayarsa a aljihu yay ƴan danne-danne batare da yace komai ba ya ajiye min saman table da akai crossing a tsakiyar gadon da magunguna a kai da dama sune Nurse zata bani na birkice musu. Harara na ɗago zan watsa masa sai idanuna suka sauka akan fuskar wayar. Tamkar waccan ranar yanzun ma tar-tar nake ganinsa. Yanda ya kafeni da shegun idanunsa kaifafa kalar na maguna ya sakani sake ɗaure fuska tare da ƙarasa antayawa PA ɗin nasa hararar da nayi niyya. Sai dai ashe shi harma ya fice ya barni da wayar. Wani irin takaici ne ya sake ruƙunƙumeni. Dan haka na rumtse idanuna da ƙarfi ina jin matuƙar zafi a raina. Kafin na buɗesu gaba ɗaya a fusace kan wayar. Shiko shiru yay kawai yana kallona da kaifafan idanunsa da nake jin tasiri su har a cikin jinina. Duk da yanda nake jin tasirinsu ban janye nawa dake masa kallon tsana da takaici ba. Cikin kaushin harshe da disashiyar muryata ta marasa lafiya na furta, “Kai ko akwai zuciya a ƙirjinka?”. Shiru babu alamar zai tanka min, sai ma janye idanunsa da yay a wani kalar slowly ya maida kan laptop dake gabansa. Dan alamu ya nuna kamar a study table yake zaune. Cikin sake jin wani sabon baƙin cikin na kai hannu saman kaina dake sara min. Fahimtar bazai amsa min ba ya sani cigaba da faɗin, “Anya kai Musulmi ne?”. Cak ya tsaya daga barin abinda yake yi, dan haka ya ɗago muna kallon juna cikin ido, idanunsa sun wani kaɗa blue ɗin gwaiduwar tsakkiya ta ɓace ta zama siririya like mage sak. Zamansa ya gyara na ƙasaita da isa da ke tabbatar da shi matsayin ingarman namiji, ga wani irin shegen kwarjini da nake ji ya mamaye ɗakin har kamar na matsu kai kace a gabana yake mayen. Ganin haka ya sakani cigaba da maganata batare da na damu da duk abubuwan dake tattare da shi ɗin ba. “Idan har kai musulmi ne bana jin kasan HARAMCI da HALLACIN dake cikin dokokin addinin musulunci. Idan kuma har da zuciya a ƙirjinka tabbas bata masu IMANI bace. Ina mai baka shawara kada kai wasa da wuta a tafin hannunka, dan wutar da UBANGIJI zai ladabtar da ma'abota bijirewa ta ninka wadda ake girka maka shinkafa a duniya kaci sau dubu bisa dubu. Idan baka sani bane zan faɗa maka a yanzu ni ɗin MATAR WANI CE. igiyoyin AURE ne a kaina ba igiyoyin ɗaure dabba a turken turka ba. Kaji tausayin kanka, da gujema saɓama UBANGIJI ka maidani inda ka ɗakkoni gidan aurena hannun MIJINA da IYAYENA.” “Idan nan ne GARIN AUREN ni ne MIJIN kuma fa?”. Ya faɗa cikin wata iriyar muryar dakiya da gizago mai tsarga zuciya. Dan yanda sautin amon muryar tasa da kaifinta ya tasirantar da furucin nasa a tsakkiyar kaina kaɗan ya rage zuciyata bata ɓullo ta bakina ta fito ba. Amma duk da hakan sai ga tari mai ƙarfi ya sarƙe min numfashi. Gaf-gaf jikina dake a cikin yanayin rashin ƙarfi ya fara rawa. Bamma san lokacin da bakina ba ya furta “MIJI?!”. Sai kuma kaina yay wani irin masifar sarawa da ban taɓa ji ko tsinkayen irinsa ba. Ga nauyi da idanuna sukamin har inajin jijiyarsu na ja kamar za'a fincike min su. In dai har wannan ake kira hawan jini to tabbas ya sameni kuwa a yanzun nan. Dan ƙirjina kansa yay wani irin nauyi. A karo na biyu hankalina ya sake neman barina. Nai yaƙin maidosa jikina tare da ɗagowa ina kallonsa domin son tabbatarwa. Amma a maimakon amsa ma da nake buƙata garesa hankalinsa kwance yake cigaba da aikin gabansa. Wani irin kallo nake masa mai kama da firgici, yayinda shima ya zuba min nasa cat eyes ɗin cikin yanayin i don't care tamkar zai cinyeni da su. Cike da salon izza da ƙasaita ya wani sake tsuke fuska da yamutseta sannan ya furta, “Har yanzu kina da sauran dama. Domin guri bai ƙure miki ba na komawa inda kika fito. Ki bama yarona video ko fadar inda yake a ɗakko gobe ki koma garinku. Saɓanin hakan cigaba da dawwama ƙarƙashin mulkin mallakar Maashhhh. Ke baki mori rayuwar taki ba. Ba kuma ki iya yin komai akan abinda kike tunanin iyawa ba”.........✍️ Yayanmu Barka da salla, ban sani ba ko a duniyarku kunyi azumin kuma🥱👩🏻‍🦯. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓_ .......Wani irin sake sarawa kaina yayi, dole na kai hannu na sake dafesa tare da saurin dafe ƙarfen gadon dan ji nake zan zube ƙasa, hasalima sam bana fahimtar maganganunsa a yanzu. Sai kalamansa ne na farko ke faman maimaita kansu a cikin kaina cikin matuƙar amsa kuwwar data zarce ƙarfin muryar daya sanar min su. (Idan nan ne GARIN AUREN ni ne MIJIN fa?) Kalamansa suka shiga min amsa kuwwa a cikin kunne tamkar wadda akema shelarsu. Gaba ɗaya ma brain ɗina ta toshe, sai nake jin kamar na kasa fahimta ko fassara su a bigiren daya dace. (Kai ina wannan gangan ne) wani gefe na zuciyata ya ambata. (Samraah dawo cikin hankalinki mana) sashen zuciyar tawa dai ya sake maimaitawa. Hannuna dake a saman kaina na sauke tare da kaisa saman kumatuna na ɗan bubbuga, dan nafi tunanin mafarkine kawai. (Kai amma wannn mummunan mafarki da muni yake) na sake faɗa ina bubbuga fuskar sosai da ƙarfin gaske kozan farka. Zafin daya ratsata ya sakani rumtse idanun da ƙarfi. A masifar jigace da ƙoƙarin haɗiye hawayena na ce, “Wai kai minene alaƙarka da ni ne? Mi kaje ka ƙulla? Miye matsalarka dani?”. Idanunsa ya ɗauke da ga kaina gaba ɗaya. Sai kuma ya ɗan taɓe baki alamar yanzun ma bazai tanka min ba. Rainin wayonsa ya gama zuwa min ko ina. Dan haka na fisgi ɗan ƙarfen dake cikin tasar asibiti a gefena na ɗago ina kaisa saman cikina cikin soyewar ido data zuciya. “Dana zauna da kai a matsayin miji gara na kashe kaina na san ban mori komai a rayuwata ba.” Idanunsa dake min wani kallon ƙasa-ƙasa ya sake ja luuu kamar zai rufesu gaba ɗaya. Sai kuma ya buɗesu warr cikin yanayin i don't care manners ya furta, “So! Ai ba hanaki zan ba. Abinda kawai nake buƙata kafin ki mutum ki bani video”. Wani irin sakartaccen kallon tsana da takaici nake masa. Na cije lips ɗina da masifar ƙarfi. “Har abada kuwa buƙatar taka bazata biya ba. Dan wannan videon bazai taɓa zuwa hannunka ba har gaban abada.” “Ashe kuwa ko kin mutu gawarki zata cigaba da zama a gareni. Ahalinki kuma zasu cigaba da amsar hukuncin laifinki”. “Idan kuma kai na kashe fa?”. Na faɗa ina jefar da ƙarfen cike da tsantsar fusata da tafi ta ɗazun. Idanunsa ya ɗan zuba min, sai kuma cikin nuna rashin damuwa ya janyesu yana wani shegen annamimin murmushi daya ƙona min rai. “Oh are you threatening me? Ai game dani ba wasan yara bane ba. Har yanzu bamu fara wasan ba, balle ki tunanin samun game over. Zan iya baki damar kwanaki domin shiryawa. Ba kince kinfi ƙarfin laɓewa bayan wani domin faɗan sunƙuru ba. To gana gaba-da-gaba nan kin samun bissmillah. Matsoraciya kawai. Kwana uku kacal har kin fara banbance tsakanin aya da tsakkuwa”. Bamma san lokacin da wani irin ƙarfin zuciya yazo min ba. Cikin tsantsagwaron ɗaukar alwashi da tsawa na ce, “Har abada nafi ƙarfin yin laushi a hannun matsoraci irin ka. Dan ni har yanzu banga MAZANTAKA ba anan tunda sai da ka laɓe a bayan aure yanzun ma. Kasaka a ranka daga yau ni Samraah bint Abdul-wahab Gwarzo, sai na sakaka lissafin lissafa kwanakin rugujewarka daga yau har zuwa ranar dana ɗeba maka da zan kuma koma ga masoyina. Ni nan sai na sakaka gudu, gudu irin wanda babu wajen zuwa a tsakkiyar sahara mai tsananin zafi rana da ƙarancin ruwa. Wlhy sai kasan ka ɗakko KARA DA KIYASHI. zakuma kasan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE”. Daga haka na ture wayar ƙasa batare da na jira jin abinda zaice ba. Sai ma wani irin izza da ƙarfin iko da naji yana ratsa gaɓɓaina, duk da sara min da kaina yake tamkar zai rabe biyu. Sai kuma hawaye sharr suka shiga kwaranyomin masu zafin gaske.... (🥱🥱tofa irin wannan alwashi haka Sam-G). 💦💞💦💞💦💞 “Magana ta gaskiya Alhaji yaronka Mansoor na cikin haɗari. Sai dai akwai mafitar da in na baku shawara kuka gamsu da ita ina fatan za'a dace......” Cikin tarar numfashi da taune harshe Dad ya furta, “Ka faɗi ko minene mu masu baka goyon bayane Doctor. Bama son rasa Mansoor dan ALLAH ka taimaka mana”. “Wannan duk na ALLAH ne Alhaji. Idan kuma muka cigaba da roƙonsa shi mai amsawa ne. Shawarar dama itace ai gaggawar barin ƙasar nan da shi zuwa India. Akwai ƙwararren likita dana sani game da ciwonsa. Kuma inada yaƙinin in sha ALLAHU zai basa dukan kulawar da muke buƙata koma fiye da ita. Sannan ku shirya yaƙi na gaskiya game da nisanta komansa da abinda ya sake jawo wannan matsalar tasa da mukai tunanin ta barsa tun a shekarun ƙuruciya. In ba hakaba akoda yaushe komai zai iya faruwa magana ta gaskiya”. Sosai zukatansu suka ƙara raunana da zancen Doctor. Dan duk dakiyar Attahir sai gashi yana share hawaye. Basu wani yi ja'inja ba dan basa fatan rasashi, tun ma yana yaro sanda matsalar ke da zafinta basu nutsu ba balle yanzu. A take aka fara shirye-shiryen fita da Mansoor zuwa India. Abinka da masu hannu da maiƙo, cikin kwana ɗaya da yini komai ya gama kammala. A cikar kwana na biyar da ɗaura auren Samraah da Maash aka wuce da Mansoor. Da ga shi sai doctor da Attahir ne suka wuce. Su Dad kuwa sai nan da kwanaki biyar saboda tsaiko da aka ɗan samu game da visa ɗin Amal. Duk wani masoyinsu ya bisu da fatan alkairi. Yayinda tausayin Mansoor ya sake cika zukatan wasu. Wasu ko nama iyayen nasa ALLAH ya ƙara kasancewar koma a wane hali yake sune suka jaza masa. Dolene kuma sakayyar Samraah ya bisa. Dan gashi itama ance babu lafiya har an wuce da ita asibiti. Dan tun a randa aka wuce da ita Abuja labari ya shiga kunnuwan mutane sakamakon shegen surutun Mom da ita take faɗa cike da nuna jin daɗi. Dan itafa jinta take fes uwa ya zuciyar sabon jariri haihuwar yanzu. Har faɗama mutane take ai mijin Samraah ɗin dama irin kwatakwalin yaren nan ne shiyyasa ma ya wuce da ita Abuja ɗin dan ya kaita ga danginsa a bata jiƙe-jiƙensu amma babu wani asibiti duk joni ne dan kar ai mata dariya. Wasu dai sun hau sun zauna, yayinda wasu ke fassara al'amarin nata da hassada kawai. Duk da dai mutane ba ganin mijin Samraah ɗin sukayi ba. Kowa dai batun an ɗaura aure da sunan wanda aka ɗaura ɗin mai suna Muhammad Mu'azz kawai sukaji. Sai kuma waliyayyansa da kowa ya gani ƙuru-ƙuru da ido dan wasu ma harda video sun ɗauka domin yaɗawa a media kasancewar Sam-G ɗin cele ce, yanda auren nata ya canja akala cikin ƙanƙanin lokaci sun san zai jawo magana. Ya kuwa jawo ɗin, dan har a yau da yake cika kwana biyar cif da ɗaurawa ba'a daina yawo da hotunanta da ƙananun magana ba harma dana Mansoor. Sai dai duk bin ƙwaƙwƙwafin mutane na son ganin sabon ango da iyayenta sukai mata auren huce haushi da shi har yanzu babu wanda ya gani. Duk da anata editing hotonta da maza daban-daban matsayin ita da angon nata. Masu ƙarancin hange sun yarda, masana da hangen nesa sun ƙaryata. Daga baya ma dai abokan aikinta da yawa sun fito sun ƙaryata ba ita bace editing ne.. ★★★★ Gwaggo dan ALLAH ki daina kukan nan hakanan. Ni wlhy ba wai ba zanji shawararki bane ko maganar ki. Ba kuma ina tsoron Jalilah bane da har zan gagara ƙara aure. Kawai dai ni ra'ayina kenan zama da mace ɗaya.” “Ra'ayinka ɗin banza da wofi Imamu. Har ni zaka gayama wani ra'ayinka can na yahudanci. Mika rasa ko wane sharaɗine baka cika ba na ajiye mace fiye da ɗaya? Kaje bazan sake magana ba. Amma ka sani wlhy in dai na haifu cikin Balkisu da Usama bazan sake shiga sabgar zuri'arka ba. Sannan ina so daga yau ka saɓe hannunka daga ƴaƴan ƴar uwarka. Dan ba sai gobe ba a yau ɗin nan Musaddiq zai dawo wajena da zama. Shima Hafizun yana gama makarantar nan zai dawo. Kaje ka cigaba da rayuwarka da naka ƴaƴan da matarka tunda dama haka take so kai ma kake so ku rayu daga ku sai ku batare da wani ya raɓeku ba saboda kada mu rage muku jin daɗin duniyarku..” “Amma Gwaggo dan ALLAH k.....” “Na gama magana ta Imamu, tashi kaban waje. Ka dai tabbatar min bani na haifeka ba kuma na amince da hakan. Sai dai Alhamdullah bakai kaɗai bane ɗa balle hakan ya dameni, gasu nan bila'adadin harda jikoki duk mun godema UBANGIJI”. Daga haka ta miƙe ta bar masa falon. Da kallo kawai Abba ya bita zuciyarsa na kai-kawo tamkar zata fito. Babu abinda ke dawo masa a rai sai furucin mahaifiyarsu a lokacin da take gargarar barin duniya dan jinya tayi mai tsanani, kuma Gwaggo Gudidi itace ta kula da ita har ta koma ga ALLAH. (Imamu kona bar duniya nayi imanin baku rasa uwa ba kai da ƴar uwarka. Dan haka in har kuka bijirema umarnin ƴar uwata ban yafe muku ba. Kuma in har ina da hakki a kanku a matsayina na mahaifiya nasan bazaku taɓa ganin dadai ba. Ku ƙyautata mata, ku bita tamkar yanda zaku bini in sha ALLAHU zaku ribantu da hakan ba kuma zakuyi kukan rashina ba). Sosai tsigar jikinsa yaji ta tashi da tuno wannan magana. Dan tamkar a yanzu ne mahaifiyarsu ke faɗa masa shi da ƴar uwarsa mahaifiyar su Musaddiq. Bayan rasuwar ta kuma Gwaggo Gudidi itace ta cigaba da riƙe su. Itace tai musu aure da ga shi har ƴar uwarsa. Bata taɓa kuma gazawa ba a ɗawainiyarsu data ƴaƴansu har zuwa yanzu da tsufa ya risketa. Anya kuwa idan ya butulcewa wannan baiwar zai ga dai-dai? Bakin mahaifiyarsu kuwa bazai kamashi ba? Dan yana ƙyautata zaton shine ma ya taɓashi a yanzu abubuwa ke masa gangal-tangal uwa ya motar tirela mai ɗauke da siminti akan gadar icce dake tsakkiyar teku, dan yasan wasu kaso na rashin mutuncin da Jalilah ta dinga ma Gwaggo nasa a baya. Sai dai baisan miyasa baya iya tsawatar mata ba duk da abin na masa matuƙar ciwo a zuciya. Sannan yana matuƙar ƙaunar Gwaggo Gudidi, yana kallon fuskar mahaifiyarsu ne akan tata fuskar saboda tsananin kamannin da sukeyi. ya rabba yana a cikin tsaka mai wuya, dan baya jin zai iya ma Jalilah kishiya, yana kuma tsananin tsoron bijirema Gwaggo Gudidi bakin mahaifiyarsu ya kamashi.........✍️ _🥱To Abba adai sake tunani._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒗𝒆_ ____________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 _____________ .......“Alhamdulillah, I am very happy today we will send you off. I am very happy with the way you calmed down and gave us your cooperation. May God give you good health and protect the future”. Murmushi na saki kaɗan ina jinjina kaina. Kafin a hankali na furta. “Thanks you doctor”. “Ni ya kamata nayi godiya”. Dariya yanda ya haɗa hausar da yanayin fitar kalaman ya bani, amma sai banyi ba nai murmushi kawai. A ƙasan raina ina jinjina karamcinsa gareni duk da kasancewarsa ba ƙabilata ba, sai dai ya nuna min kusancin musulunci dake tsakaninmu yafi na ƙabilancin. A kusan tare muka miƙe ni da shi, a dai-dai nan akai knocking ƙofar ɗakin jiyyar tawa. Kai tsaye ya bada izinin shigowa. Cikin gurɓatacciyar hausa hamshaƙiyar mace fara tas ƴar duma-duma tayi sallama ta shigo. Kallon cikin ido mukaima juna. Sai kuma matar ta janye nata tana maidawa kan doctor tare da rissinawa tana gaisheshi irin dai girmamawar ƙabilu. Ya amsa mata da kulawa. Sai kuma ya nuna mata ni. Hankalinta ta sake maidowa gareni tana murmushi. Sai kuma cike da kulawa ta gaidani da jiki. Amsa mata nayi a ɗarare, dan haka kawai naji matar batai min ba. Sai dai me bayani naji doctor na mata akan ya gama komai daya dace sai ta wuce dani. Kallonsa nayi a firgice zanyi magana sai kuma zuciyata ta ƙwaɓeni dan na tuna aljananci da hatsabibancin mai asibitin. A take na canja yanayi kawai na fara masa godiya. Nurse ɗin da suka kula da ni ne sukai min rakkiya har inda motar matar take. Babu abinda zuciyata take face luguden daka da saƙawa da kwancewa. Dole fa a wannan karon na kuɓutar da kaina dan wannan ce kawai dama ta ta ƙarshe ta ƙuɓuta a hannun mutumin nan. Saboda zuciyata ta gama tabbatar min shine ya turo matar nan, idan kuma bashi bane to tabbas zai iya min wani tarkon da ita kamar yanda akai min a Kano sanda na baro gidansa. “Ya rabba aiko nayi mantuwa”. Na faɗa dai-dai ina ƙoƙarin shiga motar da Semi ta buɗe min. Su duka kallona sukai, amma sai na sake zabura cikin hanasu damar min tambaya ina faɗin su jirani zan ɗakko na dawo yanzun nan. Yanda naga babu wacce tai yunƙurin bina nasan sun fahimceni, daga haka nai gaba cikin ɗan sauri-sauri da sassarfa irin ta mai gaggawa. Ina tabbatar da na ɓacema ganinsu na canja hanya. Duk da a rikice nake hakan bai hanani nemawa kaina dakiya ba na fara tafiyar nutsuwa. Da ƙyar nake iya gane inda nake jefa ƙafa har ALLAH ya fito da ni wajen wasu fanfuna da igiyoyin shanya. Akwai mutane tsiraru a wajen suna wanki, da alama wajen an tanadesa ne domin haka. Caraf idona akan hijjab dake shaye a igiya, tuni na tuɓe na jikina na ja wancan na saka, ɗan kwalin abayar jikina na naɗa a fuska tamkar niƙab. Daga haka na fito a wajen. Tambaya na dingayi har ALLAH yasa na fito a cikin asibitin gaba ɗaya dan babu laifi babbane sosai. Ajiyar zuciya mai haɗe da hawaye ne ya kufce min ganina akan titi, sai dai babban tashin hankalin banda ko sisi a jikina banda kuma abin siyarwa sisi. Ba kuma zan yarda kowa yaban lift ba dan an koyan hankali a baya. Haka na shari titi ina addu'a, ganin nayi nisa sosai da Asibitin zuciyata ta tabbatar min da zafa su iya biyo bayana su ganni duk da na canja hijjab. Ai tuni na kauce a titi na shiga wani street da naga an rubuta a ƙaramin symbol dake farkon shiga. Ganin an rubuta street nasan komai nisa zan fita, dan haka na zage damtse sosai naita tafiya duk da rashin ƙarfin jiki ga kuma rana mai zafi dake dukana ban damuba..... ★★★.... Tun su Semi na irga mintuna har suka kusan haɗa ashirin. Mamaki ne ya kamasu, dan haka ɗayar nurse ɗin tace Bara ta duba Samraah ko ta ɓata hanya ne. Mintuna uku da wasu sakanni ta dawo a hargitse tana sanar musu itafa bata ganta ba. Sannan mutanen dake ata wajen sun tabbatar da bata dawo ba. Su dukansu har matar da doctor da aka je aka sanar mawa rikicewa sukayi. A take kuma doctor yay kiran Hayatu a waya... Tako ina an bincike asibiti babu Samraah. Har cctv footage aka bincika, sai dai ta iya gaba kawai aka ga shigarta wajen inda ake wanki, kasancewar ta wajen babu camaras ɗin sai ba'a fahimci komai ba. Saboda ta canja hijjab sannan ta fita, ta inda ta fitan ma camara na wajen yana da matsala. Matuƙa Hayatu ya tada musu da hankali, gashi yayi kiran Maash ya sanar masa amma sai yaƙi ce masa komai. Ya kuma san minene ma'anar shirun ogan nasa, dan haka ya sake birkicewa ya birkita likita da Nurses har ma da matar nan da tazo ɗaukar Samraah ɗin. Kai dama kowa na asibitin dan har securitys basu tsira ba da sauran ma'aikatan... 💦💞💦💞💦 Ƙuuuuu!! Razanannen taka birkin ya karaɗe illahirin titin tare da sautin ihu mai firgitarwa. Ba hamshaƙiyar matar dake cikin danƙarereiyar motar kawai ba, hatta da mutane dake kai kawo a street ɗin tuni sunyo caa. Sosai Samraah da aka kusa kaɗewar ta matuƙar razana, dan durƙushe tai ta cusa kanta a cikin ƙafafunta nuna alamar sadaƙarwa kawai. Haushi da takaici ya saka mutane yimata caa da faɗa, dan duk wanda al'amarin ya faru akan idanunsu sun tabbatar da laifin ta ne ba mai motar ba. Ganin yanda wasu ke ƙoƙarin kai mata duka ma adalilin yanda har yanzu taƙi motsi daga durkuson razanar da tai yasa matar dakatar da su da sauri ta hanyar riƙota ta miƙar. Rawa jikin Samraah ya cigaba da yi har hakan na rinjayarta tamkar zata faɗi. Duk wanda ya kalleta yasan a gigice take har yanzu, dan haka matar ta shiga bama mutanen daketa faman hargowar zagin Samraahn haƙuri tare da jan hannunta ta buɗe motar a gefen mai zaman banza ta sakata. Sai da ta rufe sannan ta sake fuskantar mutanen da har yanzu sun kasa barin wajen.. “Kowa yayi haƙuri dan ALLAH kuma mu mata uziri. A yanayin halin rayuwar da ake ciki yanzu muma zamu iya tsintar kammu a fiye da yanda yarinyar nan take ciki yanzu. Tun dai ma komai bai sameta ba ai Alhamdullahi ko, sai muyi fatan ALLAH ya kiyaye gaba”. Da kalmar (Amin) suka shiga amsa mata cikin nuna gamsuwa da yabama ƙyaƙyƙyawar zuciyarta, dan ba kowa bane zai iya yin abinda tai ɗin. Daga haka kowa ya fara watsewa itama ta shiga motar dan ta tsarema mutane hanya har wajen ya fara tara mutane musamman masu gadi na cikin gidaje nata fitowa. Bayan rufe motar ta ɗan kalli Samraah ta sauke numfashi mai kauri, batare da tace komai ba taima motar key cike da ƙwarewa ta harbawa saman titi da ƙyau. Tafiyar da bata gaza mintuna uku ba ta samu waje ta gangare gefen titin, dan bata son tai nisa da anguwar ta zamto kuma anan yarinyar take duk da ta ganta da niƙaff a fuska. A yanzu ma dai yarinyar kanta ƙudundune yake a cikin ƙafafunta, yayinda sautin shashshekar kukanta ke fita kaɗan-kaɗan. “Ɗiyata a ganina godema ALLAH ya kamata muyi, dan da abinda yaso faruwa ya faru da ga ni har ke da ba wannan matsayin muke ba ai. Kiyi haƙuri ga ruwan nan kisha ki samu nutsuwa ko”. Shiru kamar bazata motsa ba, kusan cikar minti ɗaya kuma sai ta ɗago, Samraah ƙyaƙyƙyawace sosai ta yanda hawayen da suka ma fuskarta kaca-kaca bai hana bayyanar hakan ba. Idanu na tsira mata mai haɗe da sauke ajiyar zuciyar dawowa hayyaci, sai kuma na kauda kai na, a hankali na furta, “Ba kukan tsorata nake ba Hajiya, kukan baƙin cikin rashin tabbatuwar abinda nai fata ne ya sakani kukan nan. Inama ace kin kaɗeni na huta da wannan rayuwar da babu komai a cikinta face kayan ƙunci da baƙin ciki da ruɗani. Inama ace kin kaɗeni na mutu banko shuraba na tafi tafiya ta har abada da babu dawowa na iske su Abbana. Hajiya dan ALLAH ki fitar dani a motar nan na sake tarar gabanki ki bi takain.....” Cikin sauri ta katseni da faɗin, “Haba haba ɗiyata wace magana kenan! Miyay zafi haka da irin waɗannan furuci masu tsauri. Ai duk da mun san zamu mutu bama fatan mutuwar a kayinmu sai dai dan babu makawa sai ta zo ne. Amma muna addu'ar a koda yaushe ALLAH ya jinkirta mana kodan tara ayyukan alkairi da neman gafarar UBANGIJI da ga na sharri da muka aikata. Minene matsalarki? Miyasa kike ma kanki fatan mutuwa a wannan ƙarancin shekarun naki da zamu iya kallo a matsayin yanzu ma kika fara rayuwar, ko kika fara buƙatar ta? Idan ban shiga abinda ba hurumina ba ki daure ki sanar min ko zan iya fahimtarki da taimakonki da wani abu....” “Ba taimako nake buƙata ba Hajiya, sannan babu wani abin sha'awa ko birgewa da ƙawatarwa a labarina ko bayana. Ganni ki barni a yanda kika ganni yanzu kawai.” na ƙare maganar da yunƙurin ɓalle murfin motar zan fice. Da sauri Hajiyar ta riƙoni tana girgiza kai. “A'a ɗiyata yi haƙuri ki saurareni”. Juyowa nai na ɗan kalleta, sai dai bance komai ba........✍️ _Kuyi haƙuri da wannan Please. Zuwa anjima idan na samu damar yin wani zan ƙaro muku. Wlhy abubuwane suka min yawa amma ina fatan kammalawa na dawo muku da ƙarfina😘😘_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙_ ........A hankali ta ɗan sakar min murmushi da faɗin, “Ko zaki iya mun alfarma”. Cikin ƙosawa nace, “Tami?”. “Ta sanin inda zakije yanzu?”. “Ban san inda na nufa ba, sai dai ina fata da addu'ar koma ina ne ya kasance hanyar cimma ajalina”. Ɗan jimm Hajiyar tai kamar mai nazari, sai kuma ta saki murmushi mai ban mamaki tana wani juya idanu cike da salo, “Bazan hanaki tafiya ba, amma zan so ki bani dama ta ƙarshe muje gidana, maybe zan iya nuna miki hanyar cimma nasararki ta barin duniyar kamar yanda kike fata”. Idanu sosai na tsira mata tamkar mai son tankaɗe gaskiya da rairayeta akan fuskarta, kusan minti ɗaya na ɗan kauce zuciyata na ayyana min na bita na samu mafaka koda na wasu kwanaki ne, dan na tabbatar a yanzu na koma Kano makirin nan zai iya bina. Kuma Abba da su Kawu bashi ni zasuyi, amma yanzu idan na laɓe a bayanta zan iya kiran Yaya Musaddiq muyi shawara dan shiga Kano kai tsaye yanzu haɗari ne. Sai dai kuma ita kanta bawai ina jin na yarda da ita bane ba ma ai. Amma bari na gwada sa'ata mugani. fuskata na ɗago na ɗan kalleta da faɗin, “Kina so kiyi wasa da hankalina ne kawai Hajiya”. Da sauri ta dakatar da in da faɗin, “Ko ɗaya ba haka bane ba. Mizaisa nai wasa da hankalinki ni kuwa, dama kawai nake buƙata daga gareki zaki tabbatar da abinda na faɗa ɗin in sha ALLAHU”. Nan ma dai shiru nayi ina kallonta kawai, tai saurin faɗin, “Ki yarda dani koda na sati guda ne, idan kinga ba hakaba zaki iya ɗaukar mataki kowane iri”. Shiru na sake yi na wasu ƴan sakanni kamar mai nazari, sai kuma batare da nace komai ba na dawo da jikinna cikin motar sosai tare da jawo ƙofar na rufe kamar yanda take. Sosai Hajiya ta sauke ajiyar numfashi da har ya bani mamaki, sannan ta ɗan kalleni, sai dai batace komai ba. Nima ban sake cewa komai ba ina dai addu'a a zuciyata ALLAH ya hanata nasarar cutamin, ALLAH kuma yasa ba daga ƙarƙashin makircin makirin nan Maash tazo gareni ba. ★(✷✷✷‿✷✷✷)★ Tunda Hayatu yake bai taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba musanman a yanzu da yake waya da Maash yana mai sanar masa guduwar Samraah daga asibiti. Dan Maash ɗin yayi wata ƴar tafiya ne ta gaggawa, tunda ya fara harkar business duk inda zai je yana tare da Hayatu, amma a wannan gaɓar ya barsa saboda al'amarin Samraah da ya kasance da ga shi sai shi suka sani. Har tsawon mintuna biyu babu alamar Maash zai amsa. Kuma yana online. Hankalin Hayatu ne ya sake tashi, muryarsa har harɗewa takeyi wajen sake faɗin. “Wlhy nayi duk yanda kace Sir, zaman jiran isowarsu gidan kawai nake ma amma tai kirana wai basuganta ba. Ba laifina bane, ba daga ɓangarena bane aka samu kurkure ka yarda dani. Ka kuma bani izinin sanarma ƴan sanda na tabbatar tana cikin garin Abuja bata isa fita ba”. Shiru nan ma Maash yaƙi ya tanka. Wayar Hayatu ya cire daga kunnensa ya duba, har yanzu yana online ɗin dai tankawar ce bazai yi ba. Yafi kowa sanin halin Maash yanzu, dan ko iyayensa bazasu faɗa masa hakan ba. Ko motsi da idanu ogan nasa yayi yakan fahimci yaren balle. Ya tabbatar shirunsa a yanzu na ɓacin rai ne, kuma bazai tanka masa ɗin ba har sai idan shine yaso hakan. Hakan kuwa akayi, bai tanka masan ba shi kuma ya kasa yanke kiran saboda shakka, haka ya haƙura akaita ɗibar masa kuɗi har tsahon fin awa sai da shi uban gayyar ya gaji dan kansa ya yanke kiran sannan hayatu ya kai zaune cikin kujera jagwab dan tun ɗazun ko zaman ya kasa yi. Kansa kawai ya dafe yay shiru zuciyarsa na gudu. Dole ma duk yanda zai yi yayi dan gano yarinyar nan kafin cikar awanni ashirin da huɗu. Idan ba hakaba yasan akwai matsala..... 💞💞💞💞 Wata shegiyar dariya Alhaji Sadisu mai agogo babban aminin Abba ya saki harda ƙyaƙyƙyewa. Cikin ƙuluwa da nuna jin haushi kuwa Abban ya zuba masa idanu. Sai kuma ya yunƙura zai tashi amma Alhaji Sadisun ya riƙosa yana faɗin. “Afuwan afuwan Imamu. Wlhy abin naka ne zabban dariya. In kana abu sai naga kamar wani ɗan yaro bai mai garjejen saurayin ɗa kamar Abbas ba. Yo banda abinka Gwaggo ai gata tamaka wlhy. Ka buɗe bakin aljihu kawai malam musha biki ai ba wuce auren kai ba. Dama dai kaine kaso maida kanka pastor zama da mace ɗaya shekara fin ashirin bayan ALLAH ya baka dukan rufin asiri. Yo ALLAH na tuba da ana yin fin huɗu da ba tuni nayi ba”. “Amma dai ai na sanar maka matsalata ko Alhaji Sadisu. Kuma kaina shaida ne akan halin Jalilah tunda na gwada son ƙara auren a shekarun baya har sau biyu amma aka nema nakasa yaran mutane.” “Yo dan ta samu nasara a baya sai akace yanzu ma ka karaya zata samu. Alhaji Imam zama namiji kaji, tun farko kai ne kake ɓata shirin dama da kake sanar mata da wuri. Kayi shirunka yanzu har sai ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa sannan ka bada filin fara wasan jifa tunda tsoronta kake ji”. “Humm bazaka gane ba kawai, amma zan iya yarda da shawararka akan ɓoye matan. In kuma hakan zata faru fa sai dai na nema auren a wajen kano.” “Wannan duk mai sauƙine, kabar komai a hannuna kawai. Kai dai jeka ka fara shirin gyara inda amarya zata zauna nan da sati ɗaya zan maka jagora kai da kaina sai ka gode min saboda inda zan kaika wlhy”. Murmushi Abba yay a karo na farko, dan haka kawai yake jin kuma batun ƙara auren na sake masa tasiri a zuciya.... 🥱Hummm Abba cin amana ko. _________★ Gida ne mai ƙyawun gaske madaidaici muka isa a anguwar mai tama kamar yanda na gani a symbol, dan komai najin daɗin rayuwar gani da ido a kwaishi. Ƙamshi da tsarin gidan yafi komai ɗaukar hankalina, dan haka nake ta ɗan kalle-kalle a kaikaice. A karo na babu adadi Hajiya da tuni takai zaune cikin ɗaya daga kujerun falon ta dubeni ganin yanda nai tsaye a farkon shigowa. Cike da kulawa ta ce, “Ƙaraso ciki mana ɗiyata. Kar kiji wani shakku ko tsoro, wannan shine gidana anan Abuja, sai dai bana zaman daya wuce sati biyu a cikinsa a duk ƙarshen shekara. Sai kuwa idan wani uziri ne ya kawoni nakanzo nai kwana ɗaya biyu har ma zuwa uku wasu lokutan na koma. A yanzu haka ma kwana biyu ya rage na wuce”. A hankali na haɗiye yawu alamar son cewa wani abu, sai dai kafin nace ɗin Hajiya ta katseni ta hanyar ƙwala kiran sunan “Janny!”. “Yes Ma'am”. Wata murya ta amsa daga can gefen wata ƙofa da hanyarta aka shirya kujeru da tebiri. Kafin na gama nazarin tsarin da kujerun dining ɗin sukayi da zamansu a wajen wadda Hajiya ta kira da Janny ta fito. Budurwa ce itama sai dai zata girmeni sosai, da gani shigarta da uban gashin attachment dake saman kanta ya isa baka amsar ba musulma bace. Cike da girmamawa Janny ta sake gaida Hajiya tana ɗan satar kallonna. Nuna ni Hajiya tai da faɗin, “Kije da ita ciki, tai wanka a bata abinci”. Murmushi Janny tayi a karo na farko, cike da girmamawa ta amsawa Hajiya tana nufoni. “Sannunka”. Abinda Janny ta faɗa kenan tana mai riƙo hannuna. Ban amsa mata ba, sai ma ƙoƙarin turjewa da nayi alamar bazanje ba. Hajiya dake kallonmu ta sake sakin murmushi. “Kinga ɗiyata nasan mike a ranki, karki damu shi komai na rayuwa mataki-mataki ne tamkar ajin makaranta. Ki kwantar da hankalinki zamuje gaɓar da kike buƙata. Bani nai miki alƙawari ba”. “Amma Hajiya.....” “Shiiii!! Kar kice komai bita kawai”. Hajiya ta faɗa cikin katseni tana tsuke fuska a karo na farko. Canjawar fuskar Hajiyar ya ɗan firgitani, dan haka nabi Janny kamar yanda aka bata umarni tun farko.... Cikin dauriya da danne duk abinda ke mun kai-kawo a cikin rai nayi wanka na fito fes dani cikin doguwar riga mara nauyi ƴar kanti da Hajiya ta bani na saka. Ga wani ƙamshi mai daɗi na tashi a jikina. Hatta da dunƙulallen gashina da zaman asibiti yasa baya samun gyara sai da na wanke na busar da hair dryer dana gani a toilet ɗin. Yanda na fito da shi ne a buɗe yasa Janny sakin baki tana kallona. Fuska na ɗan tsuke amma sai hakan bai sata yin shiru ba sai da tayi magana. Da ga ƙarshe ta laƙemin wai zata tayani gyarawa. Mai sosai Janny ta saka min masu daɗin ƙamshi da ma wasu abubuwan da suka sake miƙar da tsahon gashin nawa daya fara dankwafewa tsaff, sannan ta fake min shi a ribbons. Ni a karan kaina sai da naji daɗin kan nawa dama a kwanakin nan ya isheni da ƙaiƙayi. Shiru nayi kawai zaune ina ƙarema kaina kallo, a take naji tausayin kaina ya kamani. Wasu hawaye masu zafi da ɗaci suka shiga sakko min. Hannu nakai na sharesu da sauri, saboda tuna nayi alƙawarin bazan sake kuka ba akan halin da nake ciki. Plate ɗin da aka kawo min na abinci na ɗan tsurama ido, sai kuma na tureshi gefe dan bana buƙatarsa a yanzu duk da uban ƙamshin dake tashi mai tabbatar da abincin zaiyi daɗi koda banga minene ba. Zamewa nai kwance a saman lallausan carpet ɗin da shima ke ta tashin wani irin ƙamshi mai daɗi, gashi tsaf babu datti. Gajiya da wahalar dana sha ya sa barci yin awon gaba da ni cikin ƙanƙanin lokaci..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ......“Madam bafa taci abincin nan ba, ko buɗe plate ɗin ma batai ba kuma tayi barci.” Janny ta faɗa cikin nuna damuwa. Ƙaramar dariya Hajiya ta sauke tana wani lumshe idanu, sai kuma ta buɗesu akan Janny cike da salon irin na wayayyun mata da suka gogu da sanin duniya. “Barta yunwar ai ba ƴar gidansu bace, dan kanta ma zata ɗauka taci”. Dariya tayi itama Jannyn da jinjina kanta. “Hakane Madam. Amma yarinyar yana da ƙyau fa sosai, ina ka samo shi haka? Ko dashi zamuje Lagos ne?”. “Tsintacciyar mage ce, dan haka ma na dawo da tafiyarmu gobe kafin ta canja shawara. Saboda na kula babbar kaddarace wannan, kwalliya da sutura kawai take buƙata”. Sosai Janny ta washe haƙwara, dan duk hausar da Hajiya tai tsaff ta gane kasancewar taji hausa sosai. Hajiya ma murmushin taketa faman yi, dan ita kanta tasan zata ƙaru da yarinyar sosai... ★Washe gari kamar yanda Hajiya ta faɗa suka tashi da shirin wucewa Lagos, harda Samraah nan dako sunanta basu sani ba har yanzu. Tunda suka tambayeta sau ɗaya tayi shiru basu sake tambayar ba. Tun jiyan kuma tana ɗaki kwance sai dai akai mata abinci a ɗakko kwano.. Janny ce mai ƙoƙarin kai-kawon, Hajiya dai nata bada umarni kawai, bakuma ta sake neman ganin Samraah ba tun shigowarsu gidan sai a yanzu da suka kwana suka yini dan tafiyar yamma zasuyi. Ita dai Samraah bata san ina zasu je ba. Koda ta tambayi Hajiya kuma sai cewa tai ta jira zata gani. Badai tace ita ƴar Kano bace, zata bata mamaki ne. Al'amarin kamar asiri Samraah ta gagara cewa da Hajiya komai. Hasalima jinta take jikinta duk ya gama mutuwa ga bakinta ya mata nauyi. Sannan bata jin zata iya tsallake umarnin Hajiya sam koda cewa tai ta shiga wuta ta ƙone ko ruwan teku. Tunda suka fito Janny taga Samraah na faman laɓe-laɓe a bayanta, Idanu Hajiya ta zuba musu kawai. Sosai ƙyawun yarinyar ya ɗauki hankalinta, sai taga tama ɗara yanda Jannyn keta kurantawa tun jiya. Baki ta buɗe zatai magana Samraah tai saurin faɗin, “Ina yini” cikin risinawa. Murmushi Hajiya ta ɗan yi tare da ɗauke kai, sai kuma ta sake maidawa ga Janny. “Wai nikam ashe amarya na kawo gidan nan ban sani ba. Irin wannan ɓoyo haka”. Dariya Janny takeyi sosai itama idonta akan Samraah dake ta faman sinne kanta, da alama dai itama taji kunya, tunda koba komai ya kamata ta fito ta gaida Hajiyar da safe amma taƙi yin hakan. Duk sun fahimci taji kunyar ne suma, dan haka Hajiya ta kamo hanunta tana murmushi. “Daughter ai ko gaisuwa a fito muyi tunda dai naga baki son musan sunanki. Da alama dai yana da tsadar gaske, ko sai mun saya ne?”. Karan farko na ɗago dara-daran idanuna masu shegen haske na sauke akan Hajiyar ina mai girgiza kaina da sauri, idanuna cike da ƙwalla alamar ina gab da shirin sakin kuka, dan haka kawai naji wani irin tsoro da shakkar matar ya shigeni mai tsananin gaske.. “A'a da alama dai ɗiyar tawa shagwaɓaɓɓiya ce, to mun haƙura tunda dai ba'a son mu sani. Mu sai mu saka miki namu sunan ai kawai kinga an huta canki canka ko”. Hajiya ta sake faɗa cike da salo tana murza hannuna a hankali. Janny dai dariya take, yayinda ni kuma na duƙar da kai kawai, sai dai abinda Hajiyar ke min a hannu sam bana so, amma tsoron janye hannuna nakeyi.. “Baby zata shiga gaba koni Hajiya?”. Janny ta faɗa dai-dai muna isowa gaban hamshaƙiyar motar Hajiya data sha wanki take ta ƙyalli. Kallon Janny Hajiya tayi, yayinda ni kuma na ɗan ɓata fuska, a raina ina ayyana (baby kamar wata ƴar tsanar wasan yara) a fili kam sai na girgiza kaina a hankali na ce, “Sunana *_Samraah_*”. A kusan tare Hajiya da Janny suka kalleni, Hajiya ta saki murmushi, Janny ta ce, “Woow nice name dear. Dole ki mana yanga irin wannan golden name haka”. Ta ƙare maganar tana ɗan rungumoni. Jikina na ɗan jaye daga nata batare dana sake cewa komai ba. Hakan yasa Hajiya ɗan harararta akaikaice alamar ta sakeni. Jayewa Janny tai tana faɗin, “I'm sorry maa”. Bata tanka mata ba ta kama hannuna muka shiga baya, dan tuni driver ya buɗe mana. Gaba Janny ta shiga, daga haka driver ya harba mota zuwa gate. Mun ɗan tsaya a bakin gate Hajiya tai magana da maigadinta, tare da bashi kuɗi masu yawa da suka bani mamaki. Shiko sai faman godiya yake bakinsa a washe har motar tai nisa da gate ɗin bai bar ɗaga mana hannu ba.... ★ A cikin tafiyar ƙanƙanin lokaci muka iso airport, hakan sai yay matuƙar bani mamaki. Dan na fahimci airport ne muka zo, sai dai na gagara iya cewa komai dan ji nake tamkar an ɗaureni ne da sarƙa, bakina kamar an saka masa padlock. Wani irin sarawa naji kaina namin da tunani barkatai akan inda zasu kaini, a wane rami kuma na sake jefa rayuwata ni Samraah, kamar fa batun Lagos naji mutanen nan nayi, sai kuma zancen Hajiya ya sake tabbatar min da hakan. Dan bayan fitarmu a motar take sanarma drivern ta yay ƙoƙarin wucewa Lagos da sassafe gobe, bata son ya kwana a hanya bai iso ba. Shiko yana tabbatar mata da in sha ALLAHU cikin girmamawa. Daga haka Janny ta gungura akwatinansu ita kuma Hajiya taja hannuna muka shige ciki. Mun ɗan yi zaman mintuna goma a wasu kujeru kafin mu miƙe lokacin da ake sanar da parssinges ɗin Lagos suyi himma. Cikin kasa haƙuri da suɓutar baki saboda sunayen ALLAH da naketa ambato a ƙasan zuciyata na ce, “Muma wai jirgin zamu hau Hajiya?”. Kusan lokaci guda Janny da Hajiya suka saki ƙaramar dariya, kafin Hajiya ta kamo hannuna cike da kulawa. “Eh Samraah muma jirgin zamu hau zuwa Lagos, dan yafi sauƙin tafiya sai kiga nanda wani ƙanƙanin lokaci mun isa. Idan kuma baƙya son zuwa ne bazamu takuraki ba, tunkan driver yay nisa sai na dakatar da shi ya koma da ke, amma fa ba can gidan zaki koma ba, dole garinku zaki faɗa ya maidaki gidanku”. A take batare da nasan dalili ba na ruɗe, na shiga girgiza kai idanuna na cika da ƙwalla. Cikin rawar murya na ce, “Hajiya kiyimun rai. Wlhy dana koma gida gara ma ki kasheni kawai. Sannan kuma shima ya tabbatar min zai iya salwantar da dangi.....” sai kuma nai shiru tamkar wadda aka tsawatarwa har ina kai hannu saman bakina na dafe. Ganin kallon tuhumar da Hajiya ke bina da shi da Janny ya sani sakin hawayen suka zubo. “Na yarda Hajiya ki kaini koma inane, amma banda maidani gida, zaki sameni a mai yi miki biyayya ɗari bisa ɗari...” “Miya samu dangin naki?”. Hajiya ta katseni tana mai tsatstsareni da idanu. Ruɗewa nayi jikina ya fara rawa da lips ɗina. Saina fara ƙoƙarin jan jikinna baya daga kusa da su. Dai-dai nan aka sake shelanta neman passinges na flight Lagos. Hajiya ta ɗan ja numfashi ta fesar, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da kamo hannuna. “Ok ok kiyi haƙuri ba sai naji ba. Muje kawai kar jirgin ya wuce ya barmu”. Ƙoƙarin tirjewa nayi Hajiya ta sake damƙoni da ƙyau tana min magana a hankali mai nuna alamar lallashi, sai dai nauyinta ya wuce duk yanda mai karatu ke hasashe.... Sosai jikina ke maƙyarƙyata a cikin jirgi saboda zantukan Hajiya. Sai faman maƙurewa nake a waje ɗaya alamar dai a firgice nake. Hajiya kam na riƙe da hannuna katamau tamkar zan tsere mata ne. Janny dake daga can ɗayan gefenmu kam kallonmu kawai take tana danne dariya. Dan duk wanda ya kalleni zai ɗauka ƙauyanci ne cike taf a kaina ba wai tsoro ba. A haka dai jirgi ya lula sama harda yunƙurin amai na amma na danne, bayan ya gama dai-daita dole sai da Hajiya ta rakani restroom nayi sa. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga zazzaɓi ya rufeni ruff abinka da wadda bata gama murmurewa ba dama. Koda muka sauka a Lagos kaina a juye yake ma gaba ɗaya. Dan bana iya gane komai yanda ya kamata har muka shiga mota zuwa anguwar da Hajiya take.... Babbar anguwace mara yawan cinkoson jama'a kamar ba'a cikin Lagos da nake jin ana faɗa ba. Duk da kuwa kafin mu iso cikinta mun shiga cinkoson matuƙa wani gurin ma da ƙyar muka fita, dan tafiyarmu daga filin jirgi zuwa gida yafi tafiyarmu daga Kano zuwa Katsina nisa, duk da dai shi wancan gari da gari ne, wannan kuma cikin gari dole akwai banbanci. Iya ƙagara na ƙagu a zo gida, dan a yanzu ma amai ne keta faman taso min tunda muka shiga motar. Da alama Hajiya ta fahimci halin da nake ciki ne ya sata siya min lemon zaƙi a hanya tace na dinga shanshana ɓawon, sai goro da shi kuma na dinga ɗan ci kaɗan-kaɗan. Wannan ne ya riƙeni zuwa gidan Hajiya. Anan ɗin ma dai maigadi ya buɗe mana gate, sai faman washe baki yake da jerama Hajiya sannu da zuwa. Da taimakonsa mai taxi ɗin daya ɗakkomu ya fidda mana akwatinansu biyu madaidaita. Janny ta tsaya biyan mai taxi ɗin, yayinda ita kuma Hajiya ta kama hannuna muka nufi wata ƙyaƙyƙywar ƙofa fara da adon golden. Wannan gidan yafi gidan Abuja girma, lokacin da muke shiga falon kuma ya sake tabbatar min da yafi wancan ɗin kayan alatun more rayuwa ma. Dan falon ƙato ne na gaske, ga wasu manya-manyan hotunan Hajiya da wani mutum a jiki tamkar zasuyi magana dan girma. Sai ƴammata biyu masu tsananin kama da juna sannan suna kama da mutumin. Fitowar wasu ƴammata biyu da dattijuwa ya katse min kalle-kallen hotunan da nakeyi. Nai tsai ina kallon dattijuwar da ƴammatan da suka zube gwiwa bibbiyu suna gaida Hajiya da jera mata sannu da zuwa. Itako amsawa take cike da nuna isa da gadara tamkar ba Hajiyar dana sani daga jiya zuwa yau ba. Dan bayan ta gama amsa su a taƙaice tai musu nuni da ni. “Kuje da ita sashenku kafin na nemeta, duk kuma wanda ya mata wata any magana sai na wulaƙantasa ta yanda sai yayi dana sanin sani na a gidan nan. Ina sauran suke?”. Da sauri dattijuwar ta amsa mata da “Madam Oyinka ta ɗauki Surayya da Umayyah, dan tare sukazo da wata baƙuwa tun jiya da yamma kamar yanda na sanar miki a waya”. Kaɗan Hajiya ta yamutse fuska tana kallon agogo, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, dai-dai nan Janny ta shigo maigadi biye da ita jaye da akwatuna. Hannu kawai Hajiya ta ɗagama Dattijuwar alamar suje. Miƙewa duk sukayi suna min nuni da ƙofa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ _______________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ____________ ......Wani irin yamutsawa kaina ya shiga yi, dan gaba ɗaya suffar ƴammatan nan da dattijuwar batai kama data mutanen kirki ba, sai irin gogaggun matan barikin nan da idanunsu ya gama gogewa. Juyowa nai a karan farko na dubi Hajiya, itako ta ɗauke kanta gefe fuskarta babu alamar wasa a yanzu. Kamar ba itace keta faman min murmushi ba a Abuja da lallaɓani. Kallona na maida ga Janny da itama take kallon Hajiyar, a karo na farko na ce, “Dan ALLAH Hajiya ku barni a wajenku”. Wata irin tsawar data gigitani Hajiya ta daka min. “Ka jimin shegiyar yarinya, su ɗin sama suka ce miki suna da gida bayan wannan da suke ciki?!! Zaki wuce ko sai na banbance miki tsakanin aya da tsakkuwa ku gammin yarinya da tsurku. Kin fini sanin abinda ya dace ne!”. Rawa jikina ya cigaba dayi har ina neman kifewa ƙasa. Bamma san sanda nabi wanda akace nabin ba. Da harara Hajiya ta raka bayansu, sai dai suna ficewa taja tsaki da fincike gyalen abayar data naɗe kanta da shi. Tuni gashin dokin kanta ya bayyana, ta jefar da ɗan vail ɗin tana magana cikin yare, sai kuma ta miƙe ta fincike abayar ma. Anan ɗin ma wani wandon bomshot ne na jeans ya bayyana a jikinta da riga best.... “Hajiya ya haka?”. Cewar Janny tana dariyar shaƙiyanci. Da sauri ta harari Jannyn da zagaya hannunta saman kai ta ce, “God for bed yoo, sunana Jannifer Can hajiyansu su ƙarata da shi bani ba Mtsowww!!. Yanzu ma zanyi shirin Church pastor yay min addu'a akan hakan. I beg, give me wine na ɗan sha ma ko zandawo hankalina da ƙyau”. Tai maganar tana komawa saman kujerar ta zube. Wucewa Janny tai hanyar kitchen, babu jimawa ta dawo da kwalban giya mai tsadar gaske da cups guda biyu. Ita ta ɓalle ta zuba musu tare da miƙamata itama ta ɗauki ɗaya, sai da suka ɗan haɗa kofunan alamar chess sannan kowa ya kai bakinsa yana murmushin samun nasara. Dan kuwa dai sun samo nasarar da suke buƙata a wannan tafiyar. (Tofa abin mamaki, idan na fahimta dai wannan Hajiya ta bogi ce, hasalima ba musulma bace, ba kuma bahaushiya ba. Ko kuma dai bahaushiyar ce musulma ada tayi ridda? Tirƙashi, muje zuwa wai maƙwafcin mai akuya ya sai kura).. _______★ “Duk yanda na lissafa miki kayan nan haka zatai amfani da su Jalilah. Sannan wannan da za'a dafa abincin da shi ki tashi da kanki kiyi girkin bawai kiba wannan shegiyar mai aikin da kika kwaso ba. Ni wlhy haka kawai yarinyar sai bata min ba, dan kawai kinƙi jin shawara ne”. “Wai Umma ya kike so nayi dan ALLAH. Mai aikin nan fa dolece. Sanin kanki ne da ga Baby har Bibaa babu abinda suka iya na aikin gida, ni kuma wlhy yanzu na riga na sangarce tunda shegiyar yarinyar can ke komai tun tana ƙanƙanuwarta. Da nasan haka abin zai ƙwaɓe min ALLAH da auren zan hanata gaba ɗaya a rayuwarta”. Dariya Umman tata tayi da faɗin, “Daga baya kenan. Ni dai muyi abinda ke gabanmu nata kuma ya zama labari ai tunda kin ɗebi rabonki. Yanzu babban burina Bibalo da takwarata su auri mazan kere sa'a. Dan haka bana son wasa. Awakina na sayar har Niger naje amso kayan nan kema kin sani, dan haka kiyi yanda nace ni zan wuce bana son mijinki yazo ya sameni anan. Magana ta gaba kiyi duk yanda zakiyi waɗan nan samarin biyu ƴan uwan yarinyar nan suma su bar miki gida dan nafi son na cigaba da ganin daga ke sai ƴan ƴaƴanki a cikinsa.” “Banƙi na naki ba Umma, sai dai fa yaron nan yanzu shine komai na gidan nan, ina mora a jikinsa wlhy bazan so yabar gidan ba. Shiko ƙaramin dama yana makaranta sai lokaci-lokaci yake zuwa. Mudai sake shawara yanzu ne lokacin cin amfaninsu su dama macen ce nauyi ai”. “Eh to da kuma wannan dan wannan. To wai tsaya ma, idan yaron nan kinga yana samun wasu manyan kuɗi ne mizai hana mu haɗa shi aure da Bibaa”. “Bibaa kuma Umma?”. “Ƙwarai da gaske. Ga gida bai ƙoshi ba sai a kaima dawa. Ke dai ki nutsu ki sake tabbatar da nauyin aljihunsa. Dan ni dama hidimar da yay a bikin ƙanwar nan tasa da wadda yake a baya tana firgitani”. “Amma Umma iyakar yaron nan fa Sakandire”. “Ina ruwanmu da wani Sankandire ɗinsa ko digiri. Shi namiji ai aljihunsa adonsa. Yo ko besan (A) ba indai akwai babbar (N) a aljihunsa miya damemu. Kidai yi nazari nima zan sake tunani”. Cikin jimamami Mom ta ce, “To shikenan Umma ALLAH yasa mu dace, sai na jiki ko kin jini.” “To mu huta gajiya. Amma ki tabbatar sunzo sun gaisheni fa ita da shi idan ya iso”. “Zasu zo Umma kar ki damu”. Tofa ban ganeba wai anyi gabas da kare🤔🥱 ★★★★ Gaba ɗaya a firgice nake da komai, dan wani irin juyewa ƙwaƙwalwar kaina ke neman yi. Musamman ma da naga inda ƴammatan nan suka nufa da ni. Tacan bayan gidanne alamar Bq. Sai dai an raba tsakaninsu da inda su Hajiyan suke da katanga harda ƙofa. Akwai ɗan filin tsakar gida, wanda ke da ƴan kayayyakin ajiya kamar su drum na ruwa guda uku, sai botikai da yan tarkace na aiki. Sai murhun gawayi guda biyu da wasu tukunya masu girma guda biyu. Duk da gidan a share yake tsaff ko kusa bai kama ƙafar ƙyawun inda muka baro ba. Lokacin da muke ƙoƙarin shiga ƙofar da nake ƙyautata zaton ɗaki ne na kusa cin tuntuɓe da tarin takalman dake a wajen, sai da ɗaya daga cikin ƴammatan ta taroni. Sannu tai min cike da nuna alamar tausayawa, na gyaɗa mata kai kawai ina mai haɗiye abinda ke min kaikawo a maƙoshi. Ƙaton falone sosai, sai dai babu komai a cikinsa sai carpet blue da aka malale ƙasa da shi. Sai ƙofofin ɗakuna a jajjere a kowanne bango akwai biyar. Shima falon dai babu datti, sai dai carpet ɗin yay masifar tsufa har a wasu wajajen ya yage wani gurin kuma ya gurje alamar yawan takawa, duk naga hakane saboda hasken wutar lantarki dake haske dako ina. A hankali nakai zaune kamar yanda suka umarceni, na takure jikina waje guda ina ɗan kalle-kalle. Kusan minti uku dattijuwar nan ta kawo min abinci a plate ɗin roba. Shinkafa ce da wake da mai da yaji. Sai ruwan ƙwara ɗaya. “Bissmillah kici abinci ƴar nan. Sai kije kiyi wanka kizo ki kwanta”. Kasa cema tsohuwar komai nai, sai binta da kallo kawai nake. Babu alamar ta damu da hakan itako tai gaba abinta ta sake fita. So nake na danne komai a raina karna sakama kaina wata damuwa ko tsoron inda na tsinta kaina. Dan haka na shiga turereniyar ture komai na fara cin abincin. Kaɗan naci abincin dan bakina sam babu daɗi har yanzu, hakama jikina babu ƙarfi sosai. Ruwanne na shanye gaba ɗaya, cikin sauke numfashi nai hamdala ga UBANGIJI. Ƙoƙarin miƙewa nake dattijuwar nan ta shigo, kallonna tai ni da plate ɗin abincin, da yanayin mamaki da gurɓatacciyar hausarta da zaman Lagos ya ɓata ta ce, “Ƴar nan badai har kin ƙoshi ba?”. A hankali na gyaɗa mata kai alamar hakane. Mama tai ɗan jimm kamar mai tunani, sai kuma ta amshi plate ɗin ta ajiye tana faɗin, “Shikenan muje kiyi wankan sai ki kwanta ko?”. Kai na girgiza mata, cikin yanayin dana tsinta kaina na sanyi da rashin ƙarfin zuciya kamar wadda aka jefa na ce, “Mama zan kwanta kawai basai nayi wankan ba, dan in har nayi zan iya samun matsala koda da ruwan zafi ne”. Jimm mama tayi kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Cikin sauke ajiyar zuciya tai min nuni da hanyar ɗaya daga cikin ƙofofin dana gani. “Ba damuwa muje ciki to”. Ɗaki ne ƙarami sosai. Amma duk da haka akwai katifu ƙanana irin na ƴan makaranta har guda biyar jere reras. Kowace katifa akwai filo da bargo. “Nan shine zai zama ɗakin ki. Ba kuma ke ɗaya bace za'a iya sake kawo wasu kuna kwana a tare. Sai dai a yanzu babu kowa sai ke kaɗai dan ankwashe wanda suke ɗakin gaba ɗaya”. “Mama saboda mi to?”. Na faɗa cikin suɓucewar baki da jin wani irin ƙarfin zuciya a lokaci ɗaya. Komai mama batace da ni ba. Sai ma juyawa da tai abinta ta fita kawai tana faɗin “Sai da safe”. Sosai mamaki ya saka ni ƙurama ƙofar ido na tsawon lokaci. Sai kuma zuwa can na taɓe baki da ɗage kafaɗa alamar oho muku nai kwanciyarta. Amma a can ƙasan raina aikin jaridancin ne ke faman yinƙuromin, dan haka kawai nake ji a raina a wannan gidan akwai abinda ake ƙullawa. Abin mamaki na farko canjawar Hajiyar nan da mai aikinta a lokaci ɗaya, ita da suketa tattalinna tun daga jiya kamar wata ƙwai amma muna shigowa gidannan kamar basu ba. Na biyu wannan ƴammatan dana gani anan da kuma shi kansa wannan part ɗin da alamu suka nuna mutanene da yawa ke mu'amala da shi. Na uku ganin kusan ƴammatan duk hausawa ne musulmai haihuwar arewa. Lallai ina buƙatar nasan wani abu kam. Sai dai ta yaya? A wajen wa?. Wannan shine babban tsallen baɗaken.... Washe gari kiran sallar farko Maman nan ta tadamu, salla muka farayi, muna idarwa ta tattaramu zuwa ainhin cikin gidan. Babu motsin kowa alamar mutanen gidan basu tashi a barci ba. Aiki Mama ta rarraba mana, ta kuma tsaya a kanmu sai da kowa ya kama nashi yanda ya kamata. Kafin kace mi cikin abinda baifi awa ɗaya da rabi ba mun kammala ko ina ƙal, sai ƙamshin fresheners ke tashi da girkin da Mama keyi a kitchen. Can sashen nasu muka koma, yayinda muka bar mama na ƙarasa girkin, a can ɗin ma ba zaman mukai ba, gyara ko'ina muka shigayi, wasu kuma na haɗa wutar gawayi domin ɗora abincin kari. Ni dai duk abinda akace nayi yinsa nake yi, yayinda nake faman bin kowa da komai da idanu cike da nazari. Babu wanda ya tambayi sunana nima kuma ban tambayi sunan kowa ba, sannan ko'a junansu bana jin suna hira balle ambatar sunayen juna, kowa aikin gabansa kawai yake baki ruff. Kafin goma na safe mun kammala komai, masu shiga wanka nata ƙoƙarin yi duk da banɗaki biyune kacal a sashen na toilet dana wanka, amma haka suke bin layi kamar wasu ƴan makaranta. Kasancewar basu da yawa sosai basuja wani dogon lokaci ba suka kammala wanka. Zuwa sannan mama ta dawo, ita ta rarraba mana abincin kowa yazo ya ɗauki nasa yaja gefe yana ci, sai a sannan wasu ke ƴar hira ƙasa-ƙasa. Ni dai nama gagara cin abincin sai kallonsa kawai nake har sai da Mama tai min magana akan na maida hankali naci dan Madam na buƙatar ganinmu.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆_ .......Wanke-wankenta take hankali kwance, yayinda bakinta ke faman raira waƙar Ado gwanja ta Chass. Sosai zazzaƙar muryarta siririya ke faman ratsa zuciyar Abba dake falo zaune yana waya. Shi kaɗai ne a gidan sai ita. Dan tun ɗazun Mom da Baby da Bibaa suka fita kasuwa wai yi cefane Baby zata yi baƙo. Sai Auta dake ɗaki yana barci saboda zazzaɓi da yake yi kwana biyu. Abbas kam ma yanzu sai ya gadama yake kwana a gidan. Shiko Nabeel yana hostel ne. Ya Musaddiq ma ganinsa yayi wuya a gidan yanzu. Halime kenan sabuwar mai aikin Mom da ta saka wata ƙawarta ta nemo mata tun bayan wucewar baƙi ƴan biki da kwana biyu. Dan kuwa daga ita har su Baby sun gagara gyaran gidan ga hargitsewar da yayi na hidimar biki. Da gaggawa ta buƙaci samun mai aikin dan haka ƙawar tata ta kawo mata Halime da itama ta samo wajen wata mata mai kawo ƴan aiki daga ƙauye. Da farko Mom taso ƙin amsar Halime, saboda ƙyaƙyƙyawar yarinya ce ga ƙirar jiki irin ta manyan mata ALLAH ya bata. Rashin gyara ne kawai da rashin suturar kirki ya ɓoye baiwar da ALLAH ya matan. Sai kuma ɗan shirme na rashin ilimi. Har tace ƙawar tata ta koma da ita a samo mata wata su Baby suka shiga roƙonta dan su kam aikin suke gudu, dole ta haƙura ta amshi Halime akan nan da wani lokaci za'a sake samo mata wata sai ta sallameta. Sai dai duk da haka ta kafama Halime dokoki sosai a gidan musamman akan Abba. Dan tunda tazo gidan ma kusan sati uku da wasu kwanaki kenan bai taɓa ganinta ba, itama bata taɓa ganinsa ba. Yau ma Abban har ya fita kasuwa mantuwa tasa ya dawo gidan, kiran wayarsa da akayi ya sakashi zama a falon yana amsawa. Gaba ɗaya wayar ta gundiri Abba, dan sosai muryar take sake tasiri a zuciyarsa. Sallama yay ya miƙe zuwa ɗakin barcinsa yana ƙwala ma Mom kira dan bai san basa gidan ba tunda ba gaya masa tayi zata fita ba. Cak Halime ta tsaya daga raira waƙar da take yi, tai ɗan jimmm alamar saurare. Jin da gaske dai muryar namiji take ji na kiran hajiyarta yasata ɗauraye hannunta a fanfo ta fito a kitchen ɗin. Dai-dai lokacin Abba na ƙoƙarin shigewa bedroom ɗin da cigaba da ƙwala kiran sunan Mom. Cike da rashin wayo da gaɓanci Halime ta ce, “Ikon ALLAH kai kuma waye haka kake kiran mafarauta sanƙamemen ƙato har ɗakin kwanan mutane?”. A bazata furucin nata ya shiga kunnen Abba, dan shaf yama manta da wata batun mai aiki da Mom tace masa zata kawo, tunda shi dai bai taɓa ganinta na tunda tazo gidan, dan haka ya juyo gaba ɗayansa. Idanu sosai ya tsira mata, ganin yanda ta riƙe ƙugu tana hura siririn dogon hancinta da tura madaidaicin bakinta ya bashi dariya. Amma sai baiyi ba cikin suɓutar baki ya furta, “Aljani ne”. “Na higa uku ni Halime aljani kuma? Ita dama Hajiya tasan da aljanu a gidanta ta kawoni nai mata aikatau”. Murmushi Abba ya saki a karo na farko, yayinda a kaikaice yake sake ƙarema yarinyar kallo. A fuska dai bazata wuce sha bakwai zuwa kaɗan ba. Amma a jiki akwai ƙira ta manyan mata, dan tako ina a cike take. Ganin tana neman zurawa da gudu yay gyaran murya. “Kinga kwantar da hankalinki ba aljani bane. Mai gidan ne. Ina hajiyar taki?”. Da mamaki Halime ta waro idanu waje sosai, sai kuma ta dafe baki tana juyawa ta kalla makeken hoton dake falon, wanda tunda tazo gidan Ita dai bata gajiya da kallonsa saboda ƙyawun da sukayi a jiki shi da Mom da su Baby. Su Samraah dai babu su daga ita har su Yaya Musaddiq. Tabbas mutumin dake zaune kusa da Hajiya ne. Amma duk da haka sai da ta sake juyowa ta kalla Abba. Kamar wadda aka tsikara ta zube ƙasa tana faɗin, “Na shiga uku wlhy kuwa kaine ɗin. Alhaji dan ALLAH ai min aikin gafara”. Murmushi Abba ya sake yi, sai kuma a hankali ya furta, “Ba damuwa tashi abinki. Ina hajiyar taki?”. Miƙewa Halime tayi, sai dai yanzu kanta a ƙasa alamar jin kunya. Cikin ƙanƙan da kai ta furta, “Sun fita da Aunty Baby da aunty Bibaa”. Ɗan jimm yay yana kallonta. Sai kuma bai ce komai ba ya kaɗa kansa zai shige bedroom ɗin. Sai da ya juyo zai rufe ƙofar suka sake haɗa ido da Halime dake kallonsa itama. Da sauri ta juya masa baya har jikinta na kaɗawa. Numfashi ya ɗan furzar da cewa, “Je ki cigaba da aikin ki”. Bai ma kai ƙarshe ba ta zura da gudu hanyar kitchen. Kansa kawai ya girgiza yana murmushi shima ya ƙarasa shigewa ciki.... 💦★💦★💦★💦 Washe garin da nake cika kwana biyu a gidan bayan kammala aikin dana fahimci wajibine a garemu a gidan muna dawowa wanka nayi na shige inda ke matsayin ɗakina batare dana shiga aikin namu sashen ba. Kwanciya nayi wasu hawaye masu zafi na sauka min batare dana sani ba. Gaba ɗaya na rasa mike damuna. Koda tunani nai ƙoƙarin yi akan kaina da zaman wannan gidan sai kaina ya fara ciwo. A yanzu haka har ya fara saramin. Dole na tattara komai na watsar na cigaba da kwanciya shiru a wajen har suka kammala aikinsu Mama tazo tai kirana dan a zatonta banda lafiya ne. Da ƙyar na iya faɗa mata na ƙoshi. Jimm tai tana kallona, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta juya ma ta fita. Kusan mintun talatin da fitar tata sai gata ta dawo. Wai na taso Hajiya na kiranmu. Babu musu na miƙe dan bama zan iya musun ba. Hasalima sai wani irin tsoron Hajiyar ne naji ya sake shigata har zuciyata na rawa. Haka dai muka fito duk a ɗarare. Mun kai tsahon mintuna goma a tsaye bayan shigar Mama cikin falon kafin a bamu izinin shiga ciki. Hamshaƙan mata muka samu har guda uku zaune cikin shiga ta alfarma. Basai an faɗa ba, a kallo ɗaya da zakai musu zai baka tabbacin daloli sun zauna musu bama naira kawai ba. Hajiya na zaune itama cikin tata shigar alfarmar tamkar mai shirin fita ma. Gefenta Janny ce ke tausa mata ƙafafu a hankali. Gaishesu mukai a tare, duk suka bimu da kallon ƙurulla batare da sun amsa ba. “K fita anan banda ke”. Furucin Hajiya ya samu ɗagowa gaba ɗaya dan bamu san dawa ake ba a cikinmu. Sai dai ganin kai tsaye ni ta nuna yasa sauran maida kawunansu ƙasa. Cikin dokawar ƙirji na yunƙura zan fita a cikinsu kamar yanda ta umarceni. Amma sai ɗaya a cikin matan ta katseni da faɗin, “Kamar ya banda ita? Ai ni gaba ɗaya ma hankalina a kanta yake Madam”. Kai Hajiya ta girgiza mata. “No Alajah ita wannan sabuwa ce. Babu abinda ma ta koya balle nai cinikinta. Sannan ba aikatau ne aikinta ba”. “Babu wani damuwa a hakan ni tamun. Dan dama irinsu nake so sunfi daɗin sha'ani ya zama komai kaine ka koya musu. Nima zayi gift da itane kar ki damu”. “Amma Alaja.....” “Basai kince komai ba zan ninka kuɗinta sau uku. Domin zanyi ƙyauyar girma ne”. “Uku?”. Madam ta faɗa cikin waro idanuwa da sakin murmushi. Amsa Alaja ta bata da, “Yes nan gaba ma idan aikinta yay ƙyau har ƙyauta ta musamman zaki iya samu. Dan gidan girma za'a kaita dake kanki sai kin san kin zama mai sa'a a wannan gaɓar”. A take kuwa Madam ta sallama. Babu ɓata lokaci matar tai kiran waya driver ɗinta ya shigo da jakkar da bamu san minene a cikinta ba. Daga ganin yanda yayma Hajiya gaisuwa kasan shima ɗan gida ne. Suma sauran duk sun zaɓi ƴammatan ɗaɗɗaya. Bayan suma an kawo tasu jakar da bata kai ta Alaja girma ba Mama ta umarcemu da mu fito. Ni gaba ɗaya ma sai naji kamar an ƙara ɗaureni da sarƙa. Sannan yanda nake jina ko wuta Hajiya tace na faɗa zan iya hakan. Sabbin kaya Mama ta bamu mu ukun nan wai mu saka. Bayan mun kammala tace muyi sallama da sauran ƴan uwanmu dan zata iya yiwuwa rabuwar kenan, idan iyayen gidanmu sunji daɗin zama damu ba lallai mu sake waiwayen nan ɗin ba. Mu dukanmu tamkar waɗanda ake sarrafawa da remote mukai sallama da su. Sai dai ƙasan zukatanmu mu kaɗai muka san halin da muke a ciki sai UBANGIJINMU. Haka muna ji muna gani aka fiddomu harabar gidan inda hamshaƙan motoci suke har guda uku. A ta farko da tafi kowacce ƙyau da tsaruwa akace na shiga gaba. Yayinda aka buɗema Alaja baya ita kuma ta shiga. Sauran ma duk shiga sukai motocin suka fice. Haka kawai wasu hawaye masu zafi suka shiga sakkomin. Duƙar da kaina kawai nayi na cigaba da kukana batare da na bar sautin ya fita ba. Haka kawai nake jin takaicin kaina da sauyawata. Jina nake tamkar bani Samraah Abdul-wahab Gwarzo ba. Gaba ɗaya tamkar an kashemin zuciya da kuzari. Abinda kawai nake ganewa shine bin umarni. Munyi tafiya mai nisa kafin na share hawayena na ɗago. Bansan lokacin dana furta (Masha ALLAH) ba a zuciyata ganin wata irin ginanniyar anguwa da muka shigo. Sam tsarin anguwar baiyi kama da a cikin ƙasata Nigeria ba. Victoria island na gani rubuce a babban symbol. Hakan na nufin sunan anguwar kenan. Tun a farkon shiga street da shima aka rubuta a symbol sai dai banga farkon sunan ba securitys suka tsaidamu. Sai dai ganin Alaja yasa suka bamu damar shigewa alamar dai sun riga sun santa.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒆𝒏_ _______________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ____________ .......Su Alaja na ficewa a gidan dasu Samraah Madam tai wani ƙasaitaccen murmushi da cije lips ɗinta. Wayarta ta shiga daddanawa tana tafiya har ta shige ciki. Dai-dai tana kai wayar kunnenta takai cikin kujera. Cikin wani salon gogaggun matan bariki ta shiga jera kirari ma wadda tai kira a maimakon gaisuwa. Bamu ji abinda aka faɗa mata daga can ba. Sai dai yanda ta saki siririyar dariya zai baka tabbacin mai daɗi ne. Sai da tayi mai isarta sannan ta ɗaura da faɗin, “Ina godiya da wannan ƙyauta hajjaju masu Lagos da wajenta. Kai Africa ɗin ma duka taku ce. Na kiraki ne domin wani babban albishir da nai imanin zai faranta miki ranki matuƙa”. Ta ɗan yi jimm alamar saurare. Wani murmushin mai faɗi ta sake saki da cigaba da faɗin, “Godiya nake hajjaju. Dama akwai babbar haja da a yanzu akai cinikinta zuwa gidanku. Na tabbatar irin kalarki ce shiyyasa ma na sayar babu ja'inja bayan na gane daga ina masu sayen suka fito. Na tabbata idan kikaga wannan hajar sai kin sake min sabon biya dan ni kaina buƙatar kuɗi kawai ta sakani sallanawa amma raina ya biya sosai.” Amsar da Hajiyar ta bata daga can ya sata sake sakin dariya. “Ayyah! Hajjaju Ayya. Ai ku manyanmu ne. Kodan girmamawa ma kauda kai ga abinda ya dace daku. Sai dai kinga kayan dan na tabbatar yanzu suna gab da zuwa gidan naku. Duk da dai tace zata bada as gift ne. Kuna wani shagali ne a gidan naku babu gayyata Hajjaju?”. Shiru alamar saurare, sai kuma ta tashi zaune da ƙyau tana furta, “Woow fantastic Hajjaju. Ai dolene muzo wannan birthday party kuwa kodan ke. Dan haka sai kin gammu”. Daga haka sukayi sallama ta yanke wayar tare da ajiyeta gefe tana wata kalar shaƙiyyar dariya. A ranta tana ayyana (lallai yarinyar nan tazo da arziƙi. Ai tun da na ganta nasan mabuɗin arziƙina ce ita, dan zoben da babalawo ya bani yay wani irin haske da bai taɓa yi akan sauran yaran da nasarata ke samowa ba. Sai dai fa nima yawuna ya biya, dan komai yaji a jikin yarinyar nan, ga wani shegen fata kamar na dorinar ruwa. Dan haka sai na ɗanɗana koba yanzu ba) ta saki wata dariya a zahiri. Hakan yay dai-dai da shigowar Janny. Ko kaɗan batai mamakin gani da jin dariyar da Madam ɗin tata keyi ba. Sai ma takowa da tai cike da yauƙi jiki na girgiza ta faɗa mata a jiki...... (Hummm🥱) 💥💥💥💥 *_MAASH MANSION_* Shine rubuce da manyan baƙi da akai da kalar ruwan gold a jikin babban makeken baƙin gate ɗin gidan da ya mamaye kaso mai yawa na street ɗin. Ƙirjina yay wata irin masifar harbawa, ba sai an min bayani ba, hakan na nufin wannan katafaren gini shine gidan su Maash ko gidan Maash. (Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un) to yaya hakan ta faru? Maash ɗin dana sani ne a Lagos ko kuwa wani ne mai irin sunansa?. Bani da mai bani amsa sai jikina dake rawa sosai amma babu wani yinƙuri da zan iya yi. Dan tuni wasu garɗa-garɗan securitys dake tsaren ƙofar sun miƙe, sai da suka gama kallemu ɗaya bayan ɗaya da gaida Alaja cikin girmamawa sannan ɗaya daga cikinsu ya danna remote da ke hannunsa, a hankali gate ɗin ya shiga zuge kansa. A jere motocin uku duk suka shiga makeken compaund ɗin da sam baida iyaka ga mai kallo, kowacce ta tsaya a muhalin da ake son ganinta. Dolene ka shigo wannan gida ka tsarkake sunan UBANGIJI mai rahama mai jinƙai, dan shike samarwa ga wanda ya so a lokacin da yaso. Gini ne daya ginu karkashin mahaukatan maƙudan kuɗaɗe da sam zaka iya rantsuwa da ALLAH ba'a Nigeria kake ba idan kana a cikinsa. Dan a iya compaund kawai da abinda ke zagaye da gidan, da kallon ginin a tsaye ya isa tabbatar maka da naira tayi kuka. Wani irin ɗunƙulallen gini ne mai matuƙar armashi da ƙayatarwa. Ga wasu irin korayen ciyayi da furanni masu azabar ƙamshi da sanyaya gida da ƙawatashi da sukaima ko'ina ado. Ga jibga-jibgan motoci jere a cikin rumfuna kusan biyar a tsare acan nesa sosai, wasu ma rufe suke da tempol. Sosai ma'aikata ne ke kai-kawo, dan dole irin wannan gidan yana da masu kulawa ta kowanne fanni. Driver ne ya fara fita a motar ya buɗema Alaja. Kafin ita kuma tai min nunin na fito. Jikina a matuƙar sanyaye na fito ina mai bin katafaren harabar gidan da kallo. Brain ɗina gaba ɗaya ta gama kwancewa, dan tunanina ya rabu biyu ne tsakanin haɗuwar gidan da sunan dana gani rubuce ɓaro-ɓaro matsayin mamallakin gidan. “Oya muje”. Furicin Alaja ya katse min tunani. Tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki na fara takawa a hankali ina bin bayansu. Drivern ta ne yay saurin buɗe dankareriyar ƙofar mai wani irin zubin ƙyau da ɗaukar hankali da duk mai kallo zai iya tabbatar da an sayeta da kuɗaɗe masu nauyi. Alaja ce ta fara shiga da sallama, yayinda ni kuma ke biye da ita kamar bindi. Sai sauran abokan tafiyarmu biye damu. Sai dai babu sauran yaran da aka ɗakkomu tare da alama an barsu a mota. A haɗaɗɗen falo dake matsayin main perlor muka fara ratsawa. Komai na cikinsa a tsaftace yake ga ƙamshi da sanyin ac kamar ka ɓingire barci. Sai dai babu kowa a cikinsa ko television ma a kashe yake. Bamu tsaya anan ba, mun shiga falo na biyu daya kasance katafaren gaske. Haɗuwar falon ba'a magana. Dan ya ƙawatu da ƙawatuwa ta musamman. Komai sai ƙyalli da ɗaukar ido yake tamkar ba'a talauci a duniya. Shima dai ƙamshin ke tashi mai nutsuwa, sai ƙafar bene da suka zama mahaɗar sassan gidan guda uku. Gashi ƙaton gaske bana wasa ba, dan duk da set na kujeru kusan biyar da ke cikinsa group-group zama a iya kawo wasu set goma sha biyar duk ya ɗauka batare da wasu sun matsi wasu ba. Anan kam akwai mutane. A hankali dattijuwar matar dake zaune cikin kujera 1sitter da laptop a gabanta tana sarrafawa a group na set ɗin kujerun dake farkon shigowa ta ɗago fuskarta ƙawace da murmushi, laptop ɗin da tun shigowarmu ta dakata da sarrafawa ta ture gefe, cikin ƙasaitacciyar muryarta ta furta, “Idanu na ne kemin gizo ko kuwa mafarki nakeyi? Da ganin Auta”. Dariya Alajah tayi tare da nufarta ta rungumeta. Dai-dai nan wasu ƙyawawan ƴammata uku dake can ɗayan rukunin kujerun suka taso suma a guje suna faɗin, “Oyoyo Aunty Mamah. Juyowa tai ta rungumesu suma cike da kulawa da farin ciki. Sai da suka gama murnarsu suka nutsu kafin su maida hankalinsu garemu. Ni suka fara zubama idanu, kafin su maida ga sauran hajiyoyin fuskokinsu a washe da murmushi suna musu barka da zuwa cikin nuna girmamawa. Ni dai ina daga tsaye gefe dan haka kawai naji shakkar ƙarasawa garesu har sai da Alajah tai kirana tare da nuna min na zauna. Inda ta nuna min ɗin nakai zaune ƙasan carpet. Kaina a ƙasa batare dana kallesu ba na shiga gaishesu. Hajiyarce kawai ta amsa, amma ƴammatan nan ko kallo ban ishesu ba. Musamman ma babbar ciki wani kallon tsana data wurgamin tun farko sai da najisa har a ƙasan raina. Dan haka nima sai banbi takansu ba... Munyi zama na kusan mintuna talatin a wajen kafin hajiyoyin nan biyu da muke tare da su su miƙe alamar zasu wuce. Hajiya da Alajah ne sukai musu rakkiya. Yayinda ni kuma aka barni nan maƙure waje guda ƴammatan nan na bina da kallon banza. Kusan mintuna biyar sai gasu sun dawo. Basu zauna anan ba, sai umarni da suka bama ƴammatan cewar ai kiran Mama Bilki shugabar masu aikin gidan taje dani sashensu zasu nemeta. Hakan kuwa akayi, dan atake babbar cikin ƴammatan ta ɗaga telephone tai kira, cikin gadara da izza ta isar da saƙon Alajah da tuni sun haye upstairs ta ɗaya daga cikin ƙafar bene ukun data ƙawata makeken falon na alfarma. Ba'a ɗauki wani lokaci mai tsaho ba sai ga wadda nake ƙyautata zaton Mama Bilki tazo. Babbar mace ce sai dai baza'a kirata tsohuwa ba. Abin mamaki kuma jikinta fes kamar bamai aiki ba, amma tabbas zata iya haihuwar kamata. Cikin fara'a da kulawa ta bani umarnin tasowa na bita. Nima sai na miƙe jiki a sanyaye nabi bayanta ina mai sakin ajiyar zuciya. Dan dama zama a tsakiyar shegun yammatan duk ya gundireni. Ina jin wata a cikinsu na sakin tsaki amma sai nan juyoba balle naga wacece. Tafiya mukai mai tsaho sosai data bani mamaki dan kamar bama a cikin gidan muke ba. Kasancewar bata hanyar da muka shigo dasu Alaja bane yasa ban iya na fahimci komai ba. Sai ma sake zama wata baƙauya nayi dan kalle-kalle nakeyi iya iyawata. Sosai nake sake girmama girma da ƙudira ta UBANGIJI. Dan wannan gida sai ka rantse ba hannu ne ya gina shi ba saboda ƙawatuwa da ɓannar dukiya da akai wajen saka masa kayan alatu. Ban sake tabbatar da gidan ƙaton gaske bane sai da muka ɓullo wata hanya data fiddomu wajen ginin tanan ma. Ashe ta gaban girmansa ba komai bane. Ta can baya da ginin apartment na masu aiki yake ɓangaren maza daban na mata daban shine ainahin ƙaton gaske. Dan shi ta can gefe akwai ƙaton garden da ko ba'a faɗa maka ba kasan shi ɗin ne. Sannan daga hannun dama akwai wani ƙaton wajen wasanni na yara da manya. Akwai wajen ƙwallo, wajen..... Kai dama wasu daban da ban gama tantancewa ba dan iya abinda idona ya hango kawai nake sanar miki Bily. Shi kansa sashen masu aikin da muka shiga sai da notikan kaina suka nema kwancewa. Dan tamkar ba na masu aiki ba. Komai fes akwai kuma kayan ƙawar suma duk da basu kai na sashen masu gidan ba ko kusa ko kaɗan. Amma dai duk mai hankali ya kalla yasan an girmamasu an mutuntasu. A tare ƴammata kusan takwas da muka samu a falon zaune suna kallo suka zuba min ido fuskokin wasunsu da fara'a, wasu ko kallo ɗaya sukai min suka ɗauke kawunansu. Sannu wanda suka nuna kulawar su suka shiga yi min, hakan yasa nima na amsa musu da kulawa tare da gaishesu duk da sukansu bazasu wuce sa'anni na ba har ma da waɗan da zan iya girma..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_ __________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ___________ ......Wajen zama Mama Bilki da naji sun ambata da Mama ta nuna min, babu musu na zauna. Ta nuna wata dake gab da inda nake tana faɗin, “Sayyada kawo ma baƙuwarmu ruwa da abinci ko”. Cike da fara'a wadda aka kira Sayyada ta amsa tana miƙewa. Wata ƙofa dake a falon can inda ƙaton dining table yake na katako ta nufa, mintina ƙalilan kuwa sai gata da tire madaidaici a hannunta. A gabana ta dire tana murmushi da faɗin, “Sister ga abinci ko.” “Nagode”. Na faɗa a hankali nima ina murmushin yaƙe. Wajen zamanta ta koma ta zauna. Yayinda ni kuma na zuba ma abincin ido nai shiru har sai da Mama Balki ta zungureni sannan na kawo numfashi. Abincin ta nuna min alamar naci, na ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai kuma cikin tausasa murya nace, “Mama dan ALLAH zan fara salla tukunna”. Cike da fara'a tace min, “Lah ai babu komai ɗiyata. Kinga A'i tashi ki rakata ɗakinku sai tayi a can kunga kun samu abokiya kuma kun zama ku uku kamar kowa. Ɗan tsuke fuska wadda aka kira da A'i tayi, sai dai kuma batace komai ba ta miƙe. Nima miƙewar nayi nabi bayanta ɗan lungun da naga ta nufa. Dogon corridor ne mai ɗauke da ƙofifin ɗakuna kusan goma. Hannun dama biyar haggu ma biyar. Babu yabo babu fallasa bayan mun shiga ɗaki na biyu a hannun dama ta nuna min ƙofar bayi. “Ki shiga nan”. Daga haka ta juya ta fita. Komai bance da ita ba nima, face cikowa da idona yayi da ƙwalla. Ji nake komai ya ƙwace min, gaba ɗaya nama gagara hasashe balle tunanin komai akan wannan rayuwa dana jefa kaina. Dan a yanzu kaina nake zargi ba kowa ba. Ina ma kaina kaico akan bin hajiyar nan da nayi, sai naji inama tashar na nufa koda roƙo na samu kuɗin motar zuwa Kano. To amma bakin alƙalami ya riga ya bushe. Ni bama wannan ne tashin hankalina ba. Son sanin wanene mai wannan gidan shine tashin hankalina. Karfa ya zamto ANYI GUDUN GARA ne AN FAƊA GIDAN ZAGO. Kai amma da nayima kaina kaico. In sha ALLAHU ma bazai kasance hakan ba. Bayan na idar da salla na jima zaune a wajen shiru, dan har sai da A'i ya biyo bayana sannan na miƙe na bita. Kamar yanda na barsu haka na samesu. Sai dai an sake samun ƙarin mutum uku suma duk manyan mata dan da kaɗan Mama Balki zata iya girmarsu. Gaishesu nayi a ladabce, duk suka amsa min babu yabo babu fallasa. Na ɗan ji jikina yay sanyi, sai dai ban bari al'amarin nasu yayi tasiri a raina ba na fara cin abincina. Ka ɗan na tsakura nace na ƙoshi, Mama Balki tai murmushi da faɗin, “Ƴar nan baƙunta zakiyi mana?”. Murmushi kawai nayi kaina a ƙasa batare da nace komai ba. Itama sai tayi ƴar dariya da cigaba da faɗin, “To ai shikenan. Bara nayi wani karanbani duk da Aunty Mama bata sanar min ke wacece ba ko matsayinki. Amma dai duk wanda aka kawo nan mun san namu ne ai. Minene sunanki?“. Shiru nayi jimmm kamar bazance komai ba. Sai kuma na sauke ajiyar zuciya a hankali na furta Kandala”. Su dukansu sai da naga alamar shock a fuskokinsu game da jin sunan nawa. Amma ganin yanda na fiske abuna ya sasu basarwa. Wasu a cikinsu suka furta Masha ALLAH. Yayinda wasu suke taɓe bakuna a yamutse. Mama Balki ce ta katse yanayin da nuna kanta. “Ni sunana Balkisu, amma suna kirana da Mama Balki kamar yanda kika ji. Ni ce shugabar duk wani ma'aikacin wannan gida musamman mata. Mijina kuma shugaban ma'aikata maza. Wannan kuma ta kusa dake Sayyada, sai Afrah, sai Sumayya, sai A'i, sai Asiya, sai Bintu, sai Mansura, sai Kairat, sai Bahijja, sai Sadiya suna kiranta Aunty Sadiy, itama tana da miji. Ta nuna ɗaya daga cikin manyan matan nan uku da suka shigo daga baya. Sai Aunty Kubrah itama tana da miji, sai aunty Falilah. Dukanmu muna aiki ne a wannan gida. Kowa kuma da fannin sa. Wasu gyara, wasu wanke-wanke. Kowa kuma da sashen da yakema aiki dan komai a ƙa'idarsa yake. Idan har kema tamuce zamuji fannin da aka kawoki ki kasance”. Sosai ƙirjina ke wani kalar luguden daka tunda ta fara. Sai dai inata dauriyar danne yanayin nawa. A rain kuwa komai ya dagule min, babu abinda nake ambato sai kalmar (Na shiga uku. Yanzu kuma boyi-boyi na koma kenan? Mike shirin faruwa dani ne haka?). Bani da mai bani amsa, dan haka na maida hankalina ga Mama Balki dake cigaba da min bayani. Sai dai sam bana fahimta har tayi ta gama. Mun cigaba da zama har akai kiran sallar la'asar. Sai a sannan dukanmu muka miƙe. Ɗakin dai ɗazun naje tare da wadda ta rakani A'i sai abokiyar kwananta Bahijja. Bahijjar akwai fara'a, dan sai jana take jikinta cike da kulawa. Muna idar da salla ta kwashe tarkacen kaya da suka jibge a ɗayan gadon ɗakin dan uku ne ta ce, “Nan shine gadonki Kandala”. Yanda tayi maganar da murmushi ya sani nima mayar mata da murtani ina jinjina kai, kafin na ɗora da mata godiya. A'i dai na jinmu amma tai kamar bata ɗakin. Bahijja dake ƙoƙarin saka uniform ta sake kallona da faɗin, “Kiyi kwanciyarki ki huta mu zamu je can sashen yin aikin yamma. Idan kuma zakiyi kallone to muje falo”. Da sauri na girgiza mata kaina. Sai kuma na murmusa da faɗin, “A'a bari na kwanta ɗin, ai bazaku jimaba ko?”. Tsaki akaja kafin ta bamu amsa, atare muka kalla A'i dake ƙoƙarin ficewa alamar itace tayi tsakin. Murmushi Bahijja tayi da maido idonta gareni. “Karki damu da ita haka take kamar mai aljanu. Nima farkon zuwana haka ta dinga min kamar mai jin haushin mutane. Amma bari kiga nan da kwana biyu zata fara kulaki. A'in ce kamar mai aljanu wlhy”. Murmushi nayi yayinda ita kuma ta ƙare maganar da sakin ƙaramar dariya. Daga haka ta cigaba da faɗin, “Ya danganta da yanayin aikin da zamu tarar. Musamman ma ni, dan iyayen gidan nawa mutuncinsu ragaggene bare ma idan akace miki Aunty Azizat. Tana abu kamar mai jin warin mutane. Bari naje dan in nayi latti zan sha maruka gashi ƙa'idarta ne iyanzu take wankan yamma”. Kasa cewa komai nayi, sai kaina dana ɗaga mata kawai sunan wadda ta kira na min kai-kawo a rai batare dana san dalili ba. Bayan ficewarta na saki nannauyar ajiyar zuciya. Sai kuma na miƙe cikin kasalar jiki zuwa gadon da tace nawa dake a farkon shigowa. Na can ƙarshen bango na A'i, na tsakkiya nata. Sai ni a bangon ƙarshe na farkon shigowa..... ❤️★★★❤️ Tsakanin Halime da Dady dai tun wannan ranar ba'a sake haɗawa ba. Dan washe gari uban aiki taci kamar kurar wasa. Dan kaf girke-girken da aka tanadama Alhaji Rufa'i itace tayi su. Tayi kuma gyaran gidan musamman falon tarar baƙi da Mom ta sakata ƙalƙalewa kamar za'a canja bangonsa. Ita dai bata san dalilin uban aikin da taci ba sai da yammaci take ji a bakin auta wai Baby ce tayi baƙo. An kuma ce ta saka hijjab da niƙab takai masa abinci falon baƙi. Bata da yanda zatai dole tabi umarnin Mom tayi shigar da akace taje takai komai. Da ɗunbin mamaki ta fito mara misali. Yayinda taketa jarumtar danne dariyar dake cinta har sai da ta shiga ɗakinta. Bata tsaya a tsakar ɗakin ba ta shiga toilet ta rufe kanta duk dan kar a jita sannan ta fara kwasar dariya harda hawaye. “Kambu taƙashin nan. Yanzu ni Halime ina Baby ta samo wannan tulun giyar, wlhy cikinsa kamar an kifa masakin Baba Lauren gidanmu na Daudawa. Gashi sanƙameme kamar samudawan da suka zo mana a labari. Tab ɗi jan, daga dai ganin wannan kasan sai dai a so shi dan kuɗi duk da dai ƙyaƙyƙyawa ne a fuska.” kiran da Mom ke ƙwala mata ya sata fita a guje dan tasan idan tai na uku sai ta sha maruka a wajenta. Gab da magrib taji ihun Bibaa da Abbas ya cika gidan. Ta kitchen ta kasa kunne sai ta jiyo ihun nasu wai duk murna ne akan Alhajin nan ya bama Baby makulin mota, tare da alƙawarin kujerar maka gareta da Mom da Dad da kuma Abbas, su kuma su Bibaa da Auta da Nabil yay musu ƙyautar wayoyi iphones. Hakan dai na nufin su duka banda Yaya Musaddiq bawan ALLAH kowa ya samu alkairi daga Alhaji Rufa'i. Baki ta yaɓe ta cigaba da aikinta. Daga haka bata sake bi takansu ba sai washe gari da kakarsu tazo take jin har ƙyautar kuɗi yay ma yaran gidanta itama wai naira miliyan ɗaya. Itama kuma kakar tasu harda ita a zuwa saudia, da yaje gidanta kuma ya bata waya mai ƙyau ƴar dubu ɗari biyu harma ta sayar da ita yau. Sosai Halime ta jinjina kwaɗayin wannan mutane da mamakin maganganun da taji suna tattaunawa. Dan sai da Mom ta farga da ita sannan tasha maruka aka korata waje, daga haka bata san mi suka ƙarasa tattaunawa ba. WASHE GARI kuwa bata ma san lokacin da Mom ta fita a gidan ba tare da Baby. Sai Bibaa da Auta da suka wuce makaranta. Shi dama Abbas ba'a sakashi a lissafin gidan. Yaya Musaddiq kuma ta lura jiya kamar bai kwana a gida ba. Tana a falo tana shara da raira waƙarta cikin zazzaƙar muryar nan tata taji kamar ana kallonta. Ɗan jim tayi cikin nuna tsarguwa. Sai kuma ta cigaba da shararta amma ta daina waƙar da take rerawar ta (kwanana ya kusa ƙarewa a gidanmu zan tafi ɗakina. A gidan mijina zan rayu zaman kaɗaici ya kusa yankewa). Cikin sauke ajiyar zuciya da rashin jin daɗin daina raira waƙar tata Abba ya ƙarasa fitowa daga jikin ƙofar ɗakin barcinsa da yake maƙale.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆_ __________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ____________ .......Ƙamshin turarensa mai armashi daya bigi hancin Halime ya sata ɗagowa a zabure. Hakan yay dai-dai da isowar Abba inda take. Aiko suka kusa cin karo. Tsalle tayi baya jikinta na rawa. Tako tafi zata zube ƙasa yay saurin riƙota. Rawar jikinta ce ta ƙaru sosai sai faman zazzare idanu take tamkar bazazzage a hannun kanawa (😂😜lol). “Please kinga calm down nutsu”. Abba ya faɗa da sauri ganin yanda duk ta gigice. Kasa nutsuwar tai, sai ma mutsu-mutsun son ƙwacewa da take kawai daga hannunsa. Sakinta yay, aiko ta kwashi tsintsiyarta ta zura da gudu hanyar kitchen dan nan ne kawai takema kallon wajen ɓuya. Murmushi Abba ya saki mai haɗe da ƙaramar dariya yana girgiza kansa da jinjina wawtarta. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya mai kauri zuciyarsa na sake tabbatar masa da yanayin dake son hawa kansa batare daya shirya ba. Dan duk yanda yake son ƙaryata zuciyar tasa hakan ya gagara. Dole ya haƙura a yau tare da tabbatar da da gaske fa son yarinyar nan da ko sunanta bai sani ba yake. Lallai yasan shima ya taro match babba, mai aikin gidansa fa. Randa Jalilah tasan wannan sirrin nasa sai abinda ALLAH yayi ai. Maybe yankan raguna zata musu shi da yarinyar nan.... 📯📯📯📯📯 Zancen Bahijja ya tabbata. Dan kuwa bata dawo ba sai bayan sallar magrib. Haka ta shigo idanunta balo-balo alamar taci kuka. A take zuciyata ta motsa. Sai dai bance da ita komai ba ganin itama ta dake tana min murmushi. Dan cike da kulawa ta shiga faɗin, “Lah baki je falo ba bayan gasu A'i can duk sun dawo su tun ɗazun. Su Mama Balki ne kawai su sai anjima saboda girkin masu gidan kowa da abinda yake so. Balle ma Uncle Boss yana gida aikin yafi tsamari kodan gayyar yaransa”. Dariya sunan data faɗa ya bani, wai Uncle Boss. Amma sai haka kawai naji gabana ya faɗi, cikin ƴar in ina nace, “Waye Uncle Boss kuma?”. Numfashi ta sauke mai nauyin gaske. Sai kuma tai murmushi da faɗin, “Uncle boss shine gidan dama ƙarfin ikon kidan baki ɗaya. Shine babban ɗa a gidan kuma. Bari dai kada na shagala da yawa banyi sallar magriba ba, har an kusa isha'i. Kuma Malam da anyi isha'i idan ka makara zuwa makarantar dare duka yake yi”. Da kallo kawai na bita dan babu abinda na fahimta a zancen nata. Sai kawai na cigaba da lazimina harta fito ta kabbara salla ban sake cewa komai ba. Tana idarwa ana kiran sallar isha'i. Dan haka muka tashi a tare muka kawota. Muna idarwa ta miƙe ɗauke da Alkur'ani tace na taso muje wajen karatu. Ban musa mata ba na tashi na bita kuwa. Mun samu duk kusan ƴammatan nan sa'anninta suma sun fito, a tare muka rankaya waje. Can muka nufa cikin wajen wasannin nan dake ƙwanyar da hasken lantarki tamkar rana. Hakama tsakar gidan yake tako ina. Ga hasken ya sake ƙawata gidan tamkar ba'a duniya ake ba. Mun samu malam har ya iso, dan haka babu wani ɓata lokaci muka zazzauna a ƙatuwar dardumar dake shimfiɗe a wajen. Yayinda shi kuma yake zaune a saman kujera abinsa. Kamilun mutum dattijo. Dan shekarunsa da gashin fuskarsa zuwa kansa dake fari fat ya isa tabbatar maka da shi ɗin ba yaro bane ba. Mun gaishesa a tare, ya amsa mana da kulawa kafin a fara karatu babu ɓata lokaci dan kowa ya riga yazo. Naji daɗin karatun, duk da kuwa nayi sauka tuni. Kusan awarmu ɗaya da rabi dan sai takwas da kusan arba'in muka tashi. Sai dai yanata kallona amma baiyi magana ba balle tambayar dalilin shigowar baƙuwar fuska ajin karatunsa. Can sashen muka koma, sai dai wasu basu zauna ba suka shiga canja uniform wai zasu koma can sashen su ƙarasa ayyukansu, ciki kuwa harda Bahijja da tafi kowa rawar jikin komawa. Sun bani matuƙar tausayi, amma dai bance komai ba dan bani da abin cewar. Shiru babu wanda ya dawo a cikinsu ni dai har na fara hamma saboda sabon barcin wuri da nayi tun fil azal. Mama Balki data rigasu dawowace tace naje na kwanta. Babu musu na miƙe na wuce ɗaki kuwa, dan ni kaina nasan ina buƙatar barcin, amma ba lallai tunanin dake danƙare a zuciyata ya barni yinsa ba. Koma dai yaya ne zanyi yaƙi da zuciyata wajen ganin na yisa kodan na samu nutsuwar fuskantar abinda ke gabana. Dan Alhmdllh, ɗan zuwa islamiyyar nan ta ɗazun da nayi sai nake jin kamar yanayin da nake jin kaina sanda nake a gidan Hajiya ya fara sakina... A hankali na buɗe idanuna da sukai min matuƙar nauyi irin na mai barci. Akan Bahijja na sauke su. Da mamaki nake kallonta. Ta sakar min murmushi da nuna min agogon ɗakin. Sosai na waro idanun waje mamaki fal raina na ganin asubahi. Kenan nayi barci sosai yau. Tab ɗi, abinda na daɗe banyi ba a rayuwata. Dan ko kwanciya asibitin da nayi ni shaida ce akan allurar da suke min ke bugar da ni bawai normal barcina ba. Bayan mun idar da sallar asuba muka gaisa da Bahijja. Itama A'i dake faman ɗauke min kai gaisheta nayi. A mamakina sai naga ta amsa da sauri har ma abin nata ya bani dariya. Amma sai na danne banyi ba sai dai guntun murmushi kawai. Alkur'ani na ɗauka na fara karatu, yayinda A'i ta shiga wanka, ita kuma Bahijja ta fara ƙoƙarin gyara mana gadajenmu. Ina nan zaune harta kammala tace na koma saman gado zatai shara. Hakan kuwa nayi, tana kammala shara A'i ta fito, a gurguje ta ƙarasa morping itama ta shiga wanka. Bata jima ba kamar A'i ta fito. Su dukansu shiri sukayi a cikin Uniform ɗinsu wankakku harda guga dan na fahimci suna dasu ne da yawa ba ɗaya bane. Suna kammalawa harda fesa turare, na fahimci hakan kamar yana cikin dokar aikinsu a gidan zama cikin tsaftar jiki. Fuskar Bahijja da murmushi ta kalleni. “Sis.. mu zamu wuce aiki. Ki kwanta ki hutama ranki kafin a kawo break fast. Tunda kinga har yanzu ba'a sanar da aikin da zakiyi ba, ALLAH dai yasa ba tafiya dake aunty Mama zatayi ba”. “Waye aunty Mama?”. Na tambayeta cikin sanyin murya. Kai tsaye ta bani amsa da, “Itace wadda kukazo tare. Ita ba'a Nigeria take zaune ba. Yanzu ma nasan bikin birthday ɗin Hajiya Babba ne ya kawota. Dan ana yinsa ne tamkar bikin aure duk shekara. Ana gamawa kuma zata koma ita da nan sai babbar salla”. Kai na jinjina mata cikin nuna gamsuwa. Sai kuma na sauke ajiyar zuciya ganin itama ta nufi hanyar fita dan tuni A'i ta fice dama... *_10:30am_* Ina kwance a ɗaki da littafi a hannuna ina dubawa na Hadith nasu Bahijja ɗaya daga cikin ƴammatan jiya da ban gama tantancewa ba duk da an faɗa min sunansu ta shigo tai kira na. Tare muka dawo falon. Na rissina cikin girmamawa na gaida Mama Balki da muka samu ita kaɗai zaune. Ta amsa min da kulawa tana murmushi. Sai kuma ta nuna min dining table tana faɗin, “Kije kiyi break fast gashi can kar ya huce. Dan Ban sani ba ko'a buƙaci ganinki yanzu da safe. Ina fatan dai kinyi wanka?”. Murmushi nayi mata, dan haka kawai naji ƙaunar matar na shigata. Kaina a ƙasa na amsa mata da, “Eh mama nayi wanka, kayane dai ban canja ba”. “Karki damu da wannan. Nasan Hajiya Mama na sane da ke zata kawo kayanki in sha ALLAHU. Yanzu dai ki karya sai ki dawo nan ki zauna kisha iska ni zan koma bakin aiki kada yaran suyi shirme”. “Na gode mama ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara girma”. “Amin ya rabbi ɗiyata ALLAH yayi miki albarka kinji”. Yanda ta faɗa ɗin ya bani tabbacin taji daɗin girmamawar da nake bata. Zama nayi naci abincina, duk da dai bawani na kirki bane naji yamun daɗi. Bayan na kammala falon na dawo kamar yanda Mama ta umarceni. Ina zama sai ga Mama ta dawo. Cike da kulawa ta ce, “Yauwa to taso ɗiyata, dama nace miki Aunty Mama zata iya buƙatar ganinki”. Da girmamawa na amsa mata da to ina miƙewa nabi bayanta. Sosai nake ƙara tsarkake sunan UBANGIJI daya bama waɗanda suka tsara ginin wannan gida fiƙrah da fasahar yinsa tamkar an ɗakko an dasa ne ba hannu yayisa ba. Ashe jiya kallon tsoro nayi masa. Lallai na yarda masu arziƙi na inda suke. Ashe su Mom iyayen alfahari da kuɗin Abba basu wuce ƴan aiki ba a wani wajen. Ashe duk kuɗin da take kallon iyayen Mansoor suna da shi ba komai bane ba. Zuciyata tai wata irin jijjiga dalilin tuna masoyina Mansoor. A take naji hawaye sun cika min ido. Amma ban bari sun zubo ba na haɗiyesu. Mayataccen ƙamshi da sanyin ac ke fara maka sallama tamkar ba safiya ba. Ga wani irin shiru da gidan ya bada tamkar babu wani rai mai motsi a cikinsa. Wata irin ajiyar zuciya ce ta kufce min batare da nasan dalilin hakan ba. A cikin takun nan nawa na nutsuwa da rashin hayaniya na cigaba da bin bayan Mama. (Ya Al-malik) na furta a zuciyata lokacin da muke gama haurowa upstairs ɗin tsakkiya. Ashe saman ma wasu shegun faluka ne da sukafi na ƙasan ƙawatuwa da barazana tamkar ba duniya za'a mutu a barsu ba. Rasama ina zan nutsu na kalla nayi nikam. Tako ina na gama diriricewa. Sai dai a zahiri baka isa tabbatar da yanayin nawa ba dan na shanye komai a raina ni da zuciyata mukeya bidirinmu kawai a baɗini.......✍️ _😂Ku cigaba da haƙuri dai, ni kaɗai nasan yanayin da nake ciki😞._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_ _____________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 _____________ ......Daga ni har Mama Balki ƙasa muka zube gaban Alaja dake zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya tana daƙilar tab. Gaisheta na shiga yi, batare data ɗago ba ta amsa min. Kusan mintuna biyu muna zaune kamar masu neman gafara sannan ta ɗago tana cire eyeglasses ɗin idonta da bana raba ɗayan biyu na ƙara gani ne. A kaina ta zube idanun nata, sai kuma ta ɗan saki murmushi. “Ƴammata sorry fa. Tunda mukazo ban sake waiwayarki ba ko? Nayi busy ne da yawa.” “Ba komai Mama”. Na faɗa kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hanuna ta cikin hijjab. “Ohkay, yanzun ma bani da isashen lokaci. Maman Nana kije da ita wajen Sunusy ya gwadata a ɗinka mata uniform itama. Sauran kayan da zata iya buƙata kuma sai ki shirya zuwa anjima kuje shopping. Zata cigaba da zama a hannunki kafin tasan aikin da zatayi”. “To Hajiya in sha ALLAHU yanda kikace haka za'ayi. ALLAH ya ƙara nisan kwana da rayuwa mai albarka”. A hankali ta amsa da amin. Jin godiyar da Mama tayi nima sai nayi godiyar. Duk da kuwa wani irin abune mai masifar nauyi ke neman riƙe min ƙirji. Ban san a wace kalar rayuwa kuma na jeho kaina ba. Lallai na tafka kuskure. Inama Kano na nufa abina. Kai anya kuwa kuskuren nawa ba daga baro asibiti bane da nayi. (Tun daga baro gidan mijinki dai a Kano) wani gefe na zuciyata ya ayyana min. Jinai tsigar jikina yay wani irin tashi sama. A saman lips na maimaita kalmar “Miji”. (Kai ina ai bazan taɓa zama matar kowa ba sai Mansoor in ALLAH ya yarda).. “K! waye wannan kika hayo mana har sama da shi?!”. Muryar dana tabbata naji irinta a jiya ta faɗa cikin daka mana tsawa dai-dai muna sauka steps na biyun ƙarshe. Ganin yanda Mama Balki ta dakata da sauri cikin nuna shakka ya sani mamaki. Cike da girmamawa da sauke kai ta furta “ALLAH ya huci zuciyarki Aunty Azizat. Dama mun cika umarnin Aunty Mama ne. Dan itace ta buƙaci ganinmu”. Fuska ta wani yamutse tana balla mana harara. Da alama dai bata da abincewa. “K kuma uwar miye kike wani kallona? Shegiya mai kama da mayu!!”. Ta sake faɗa a fusace tana wani ware idanu a kaina sosai cike da nuna tsagwaran tsanar da ban san laifin dana mata ba. Duk yanda naso jin na bata girma a matsayin wadda na shigo gidansu da kuma girmata da tayi a shekaru dan zata iya kaiwa sa'ar Yaya Musaddiq amma sai naji hakan ya gagareni. Sai ma tsareta nai da idanu ina ƙare mata kallo daga sama zuwa ƙasa.... Tauuuu!!! Naji saukar wani shegen azabebben mari asaman fuskata babu zato babu tsammani. A take ta rashin jin ya yunƙuro, bamma san lokacin dana ɗaga nawa hannun ba na sauke mata nawa yatsun biyar nima a saman fuskarta dake fara sosai a dama da haggu kuma. Daga gani kasan akwai ƙarin farin kanti dan har wani yellow-yellow takeyi. Tamkar mutuwa ta ratsa gidan haka yay wani irin tsittt na wuccin gadi. Kafin tai wani irin zuba min ido like wadda tai suman tsaye. Bama ita ba hatta da Mama Balki wani irin waro idanu tayi da ɗaura hannuwa duka a saman kai bakinta buɗe. Cike da dakiyar nan tawa da taurin kai na watsar da su tamkar banga komai ba na raɓa zan wuce. Dai-dai nan ta wani saki kururuwa da girgiza tamkar tsohuwar dodanniya ta damƙo min hijjab ta baya. Sai kawai ji nai an shaƙureni tare da jawoni baya. Tabbas da banyi azamar damƙe hijjab ɗin ta gaba ba da zamesa da sauri babu abinda zai hanata kaini ƙasa a wajen. Idan kuwa na faɗi zan iya buguwa, idan ma da tsautsayi zan iya rasa rayuwata. Gaba nayi gaba ɗaya, dan yanda ta fisga ni kuma na fisge sai yay kamar an hankaɗoni ne. Na gama sallamawa babu makawa a wannan gaɓar sai na kai ƙasan mayen marbles ɗin nan mai tsananin sheƙi da ɗaukar idanu tamkar zakaga fuskarka a cikinsa. Dan haka na runtse idanuna gaba ɗaya ina mai ambaton sunan ALLAH da sallamawa baki ɗayana...... ★★★★ Cikin mintuna ƙalilan Halime ta dawo ɗauke da tray. Haka kawai take ji bazata iya tsallake umarnin Abba ba. Duk da tana jin shakkar uwar ɗakinta tasan ta ƙetare umarninta. A hankali ta dire tray ɗin a gaban Abba dake zaune a dining. Tun fitowarta kuma yake famar binta da kallo ta gefen ido tamkar zai cinyeta. Ƙoƙari barin wajen take yi tamkar mai raɗa ya furta, “Baza'a zuba min ba?”. Duk shirmen Halime sai da taji zuciyarta ta tsarga. Hannunta na rawa ta shiga zubama Abba abincin. Ta kammala tana ƙoƙarin barin wajen ya katseta da faɗin, “Uhhm Kinga zo mana”. Nan ma ƙiri tai tana kallonsa, kafin cikin sanyin jiki tai ƙoƙarin durƙusawa a ƙasa. Amma sai yay saurin girgiza mata kansa da mata nuni da kujera. Gabantane ya sake faɗuwa. Tai masifar waro idanu waje tana jijjiga masa kanta alamar dai bazata iya ba. Ƙyaleta yay, cikin gyara yanayinsa ya ce, “Minene sunanki?”. Ganin yanda yaci serious ya sata nutsuwa itama. Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta amsa masa da, “Halime”. “Halimatussa'adiyya kenan?”. “Eh ta faɗa a hankali”. “Ina ne garinku?”. “Ƴan tumaki”. Ta bashi amsa kai tsaye. “Ƴan tumaki?”. Ya maimaita da ɗan waro idanu a kanta a tunaninsa shaƙiyanci ne. Amma sai a mamakinsa yaga ta jinjina masa kai na tabbatarwa. Kasa haƙuri yayi sai da ya furta “A wane state ne?”. Girgiza masa kai tayi da faɗin, “Katsina ne. Amma dai muna kusa da Musawa”. Jin sunan Musawa ya sashi fahimta Katsina state kenan ɗin dai da gaske. Humm mutanenmu da ganganci, ka turo yarinya mai cikar halitta jiki kamar wannan aikatau har wata jiha. Cigaba yay da faɗin, “Miyasa kike aikatau?”. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla. cikin rawar murya ta ce, “Inna ce tace Baba ya turani na samo kuɗin kayan ɗakin aurena”. “Ita Innar mamanki ce?”. “A'a gwaggona ta rasu tun ina ƙarama. Matar Babana ce, amma uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da Gwaggona. Bayan ta rasu aka aurama Babana ita dan ta riƙemu ni da ƙanina. Sai dai kuma ta tsanemu, kullum cikin mana mugunta take, gadonmu ma da Gwagginmu ta barin mana duk ta cinye. Gashi Baba baya iya cemata komai, shima tsoron masifarta yake ma”. Haka kawai yaji wani abu mai nauyi ya tsikarar masa zuciya. Tamkar walƙiya hoton Maman su Samraah yazo masa a cikin idanu. Da sauri ya ture zancen zucin gefe ya cigaba da faɗin, “ALLAH ya gafarta mata. Toke kina da saurayi ne da aka turoki samun kuɗin kayan ɗaki?”. Ƙasa ta ƙara yi da kanta sosai alamar jin kunya. Wasa ta farayi da yatsunta sannan cikin in ina ta ce, “Duk wanda yazo wajena Inna korarsa take yi. Tace saina haihu a gida ɗan shege ko zata bari nayi aure. A hakan ma sai su Lami sun gama yin nasu auren”. Sosai zuciyar Abba ta sake raunana da tsinkewa. Da ƙyar ya iya furta, ”Wacece ita Lami ɗin?”. “Ƙanwata ce ita ta haifeta da su Lailah”. Kasa sake magana Abba yayi tsahon lokaci. Sannan yace ta tashi taje ta cigaba da aikinta. Shima sai ya miƙe dan ya gagara cin abincin kuma ya koma ɗaki. Shirin fita yayi zuciyarsa na masa kaikawo. Bai wani jimaba ya kammala ya bar gidan batare da ya sake neman Halime ba.... Duk yanda Abba ke son yaƙar zuciyarsa game da abinda take ƙwaɗaita masa hakan ya gagara. Tun yana iya danne al'amarin har yana son fin ƙarfinsa. Yakan rasa sukuni a duk ranar da baiga Halime cikin idanunsa ba. Al'amarin tun yana bashi mamaki har ya koma bashi tsoro. Dan haka kawai yanzu rana tsaka zai baro kasuwa yayo gida dan kawai yaga Halime. Tun Mom na masa uziri idan yace mantuwa yayi harta fara tsarguwa da tunanin ya saka mata ido ne akan yawan yawon da take kwana biyun nan. Hakan ya sakata ɗan nutsuwa a waje guda. Yayinda shi kuma Abba zaman nata a gida ya zame masa takura. Dan idan tana nan ko giccin Halime baya gani saboda yanda take jin tsoron saɓa umarninta. A haka da ƙyar akai kwana huɗu. A daren cikar na biyar ya gagara haƙuri ya nufi gidan abokinsa Alhaji Sadisu mai-agogo. Tsaff ya kwashe komai ya sanarma Alhaji Sadisun. Shiko ya dinga dariya yana tsokanar Abba har sai da yaga ya ƙulu sannan ya bashi haƙuri tare da bashi shawarar yanda ya kamata suyi dan ganin komai ya tafi dai-dai. Sosai shawarar tayima Abba kuwa. Ya tafi gida cike da farin ciki.... ★★★ Wata irin ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi jin na faɗa kan abu mai taushi saɓanin inda na gama sadaƙarwa zan faɗi. Rawar tsorata dana riga nayi jikina keyi, dan haka na sake ƙanƙame abinda na faɗawar ina mai sake matse idanuna dake a kulle. Sai dai me, wani kalar wakitawa ƙitjina da zuciyata sukayi a lokaci guda, a take tsigar jikina ta fara mimmiƙewa. Gabana ya sake faɗuwa jin yanda wajen ya koma tsitt tamkar babu wani rai mai numfashi. Gaba ɗayan numfashina ne ya ɗauke daga illahirin gangar jikina nima, tare da wata irin girgizawar zuciya taban mamaki. Sake ƙanƙame abinda na faɗawar dai na sake yi. Wani irin jifff!! Ƙirjina ya sake bugawa a karo na biyu jin tabbacin mutum ne, mutum ɗin kuma daga ji ba jikin mace bane, sannan ƙamshin dana shaƙa na neman jirkice min tunani gaba ɗaya. Ga tsitt ɗin da wajen ya ɗauka lokaci ɗaya tamkar an tsaida numfashin kowa da komai na gidan. Sassauta riƙon da naima koma minene na fara yi, sai kuma na shiga ɗago kaina a hankali ina ƙoƙarin buɗe idanuna. Akan farin riga armless ta sport wear fara tas na fara saukewa. Sai ƙaton damtsen hannu dake a murɗe sosai fari mai ɗan duhu kaɗan dan fatar batai irin tas ɗin nan na mahaukacin fari ba. (Jikin namiji) zuciyata ta ayyana min, dai-dai da bugar hancina da ƙamshin turarensa ya sake yi. Cikin wani irin sauri da shiga tsananin tashin hankali na ɗago gaba ɗayana na sauke idanuna akan fuskarsa.........✍️ _🥺🥺Hukumar tawada da alƙalami tace a tafi yajin aiki.🥱_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_ .......Cak numfashina ya tsaya, illahirin jikina ya saki gaba ɗaya. Da ga ni har shi muka zubama juna ido. Yamutsawa kaina ya farayi saboda wani sinadari mai ƙarfi dake fitowa daga cikin cat ayes ɗinsa yana shiga cikin nawa. Wani irin kallo yake min mai kama da gargaɗi koma tsanace ban sani ba. Dan duk yanda naso dakewa hakan ya gagara. Tuni naji wani irin kwarjininsa ya gama mamayeni da cikani tamkar mu kaɗaine a wani matsatsen lungu. Hatta da iska ma ta fara min wuyar shaƙa neman komawa fisgar numfashi nake yi. Wani matsiyacin kallo daya dalla min tare da ƙoƙari janye jikinsa daga nawa ya sani tafiya gaba ɗayana baya zan faɗi. Bamma san na fasa ƙara ba da komawa gaba ɗaya jikin nashi na ƙanƙamesa tamkar zan huda shi na shige ciki... Kusan kowa dake a wajen sai da ya sake waro idanu. Yayinda tuƙuƙin baƙin ciki da kishi mai tsanani ya gama mamaye zuciya da ruhin Azizat. A yanda take jin bawan ALLAHn nan a ranta ko macen sauro ta tsani ta taɓa mata shi, ai tuni idanunta sun sake rufewa. Batama san lokacin data isa gabansu ba. “Wlhy sai na kasheki ƴar iska. Bayan maita ma harda bin mazan mutane”. ta faɗa cikin ihu mai ƙaraji tana damƙo hannun Samraah da ƙoƙarin janta baya daga jikin Maash. Wani mugun kallo ya watsa mata. Sai kawai ta fashe da kuka tare da sakar min hannun tana ƙoƙarin kaimin mari. Nima tamkar wadda aka farkar a barci dai-dai nan na dawowa a hayyacina, Cikin wani irin sauri da shiga tsananin tashin hankali na sakesa gaba ɗaya tare da turashi. Sai da me ko gezau, yana nan a tsayensa ƙyam saman ƙafafunsa tamkar dasashiyar bishiyar data kafu a muhallin daya dace da ita. Kallo ɗaya yay min da shegun idanun nan nasa kalar na maguna ya janye tamkar wanda ba'ai komai ba ma. Ga fuskar tsamm babu alamun rahama ko sassauci balle ma kai tunanin ya taɓa sanin mai kama dani a rayuwarsa. Duk yanda naso janye nawa idanun daga kansa na gagara hakan saboda tsabagen shiga ƙololuwar baƙin ciki, ruɗani da mamakin makirci da mugun halin mutumin nan, kenan da gaske shi MAASH ɗin ake nufi da sunan gidan nan?. Tayaya ma to hakan ta kasance?, farkon labarin a kano, cigabansa a Abuja, ƙarashensa a Lagos. Duka a ƙarƙashin ikonsa, kenan da gaske yayi winning kamar yanda yake iƙirari da cika bakin shi ba'a game da shi baiyi winning ba. Kai impossible... Mugun zagin da Azizat ta lailayo min da sake yo kaina ya maidoni a hayyacina, raina a dugunzume na janye idanuna a kansa na dawo da shi gareta, dan wlhy tana sake taɓani duk haushi da takaicin mugun nan saina juyesu a kanta yanzun nan. Tana gab da kai hannunta jikina aka kira sunanta da ɗan faɗa-faɗa. “Azizat minene haka wai?!”. Mu dukanmu kalon Aunty Mama da tayi maganar mukayi, yayinda itama ta dakata tana hararata da famar huci sai kace wata kububuwa. Cikin sake bada umarni daga inda take tsaye ta dubi Mama Balki. “Kuje inda na turaku”. “Godiya muke ranki ya daɗe, ALLAH ya ƙara girma”. Mama Balki ta faɗa tana risinawa tare da kama hannuna. Tamkar wadda aka zarema illahirin lakar jiki na shiga binta zuciyata na wata kalar suya da raɗaɗi mai zafi. Yayinda idanuna ya kasa daina kallonsa, nama rasa wana kalar tunani kuma ya dace nayi. Muna gab da fita muka haɗa ido, wani irin lumshe nasa yay da yamutse fuska ya motsa lips ɗinsa a hankali, (First Game) sai kuma ya cije gefen lips ɗin da wani salo ya ɗauke kansa gaba ɗaya daga garemu. Da ƙarfi na rumtse idanuna dake cikowa da ƙwalla. Cikin ɓacin rai na shiga ƙoƙarin son fisge hannuna daga na Mama Balki. Dan bazan iya haƙuri ba sai na maida masa murtani. Kai yau ma duk abinda za'ayi sai dai ayi wlhy. Sake damƙe min hannu Mama Balki tayi tare da jawoni gaba ɗaya daga cikin falon muka fito cikin main falo, sai da muka fito anan ma gaba ɗaya wajen compaund sannan. Cikin lallashi da ɗan faɗa ta furta, “Ya isa mana. Ki ƙyaleta. Banda abinki ina ke ina faɗa da ƴar masu gida. Kin san kuwa fitinar Azizat musamman akan bawan ALLAHn nan. Zuciya ba taki bace ba ɗiyata, anan a ƙarƙashinsu muke dole muyi haƙuri da koma mi zamu gani. Kima godema ALLAH Alhaji ƙarami yazo wajen da wlhy abinda zai faru ALLAH kaɗai ya sanshi. A hakan ma ALLAH ya taƙaita duk barci jama'ar gidan suke. Ita kuma Aunty Mama tana da sauƙi a cikinsu da ko gidan nan bazaki sake kwana ba. Kema dai na lura akwai ƙarfin hali, ki daure ki sauke wannan zuciyar taki kada ki sake kwatanta abinda kikayi yau”. Zantukan Mama Balki sake ƙona min rai suke. Dan haka na sakar mata kuka kawai tare da faɗawa a jikinta na ƙanƙameta. Itama sai ta riƙeni hannu bibbiyu tana lallashi na..... Su Samraah na gama ficewa a falon Azizat tayo kansa. “Yaya Please kace afitar mana da ita a gida. ALLAH yarinyar nan mayya ce. Tun jiya da aka shigo da ita gidan nan naji na tsaneta, jinake kamar ma na kashe banza. Dan bazan taɓa yafe mata rungumar da tayi maka b.....” Ko kallon inda take baiyi ba, sai ma motsa lips ɗinsa da yay a hankali cikin silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Good Morning Aunt” yay wucewarsa. Wani irin tsayawa tayi cak jikinta na tsuma. Duk da ba yau ne farau ɗin hakan ba a tsakaninsu sai take jin na yau ɗin ya mata zafi. Da kallo ta bisa idanunta nayin narai-narai alamar gab take da sakin kuka. Murmushi Aunty Mama tayi da ɗan girgiza kanta tana binsa da kallo. Har sai da ya ɓacema ganinsu ta janye idanun, ganin Azizat ta zabura zata bisa ta sakko ta kama hannunta batare da tace komai ba ta jata suka koma saman dan tasan bin nasa bazai haifar da ɗa mai ido ba. Dama ga wata wutar dake neman tasowa akan matsalarsun.... ★★★ Cike da nishaɗi Abba ya koma gida. Sai dai me, yana shiga ya samu Mom na jibgar Halime har Bibaa na tayata. Yayinda Baby ke kwance a kujera wanwar alamar tasha kayan nata. Tuni yay wata irin zabura batare daya sani ba ya hankaɗesu su duka. Sannan ya ɗauke fuskar Bibaa da mari. “Kinci gidanku Habiba. Dan uwarki wannan ɗin sa'arki ce?”. Kafin Habiba dake kuka ta bada amsa Mom data sake shiga cikin matsanancin ɓacin rai ta hayayyaƙo masa. “Mitai maka zaka daketa. Akan ƴar aiki wulaƙantacciya da iyayenta ma suka sallama ma duniya saboda baƙin talauci”. Wani irin ɓacin rai ne ya tasoma Abba. Cikin rufewar ido ya furta, “Jalilah! Halimatussa'adiyyar ce wulaƙantacciya?”. “Kuturun ubancan! Imamu harma sunanta ka sani? Harda ƙara masa wani ƙaimi. To ko dai kana zagayowa ne ban sani ba ta zama karuwarka. No wander yanzu kullum sai ka dawo gida da rana. Idan ka zauna kuma kata waige-waige kenan...” “You are vary stupid Jalilah! Ni kike dangantawa da fasiƙanci?”. “Yo in ba fasiƙin ba minene kai? Taya akai kasan wannan tsinanniyar yariyar anan gidan ma? Bayan na mata gargaɗi kaima kuma nayi maka. To wlhy kuwa zaku mutu yau ku duka...” ta ƙare maganar da rarumo flower base tai kan Halime dake maƙure gefe tana kuka. Damƙota Abba yayi da masifar ƙarfi, aiko ta juyo gaba ɗayanta ta buga masa abin a kai. Lokaci ɗaya Bibaa da Halime da Baby da hayaniyarsu ta sakata buɗe ido suka ƙwalla wata irin masifaffiyar ƙara da duk maƙwaftansu sai da suka jiyo. Yayinda fuskar Abba ta gama wankewa da jini. A take ya faɗi wanwar ƙasa. Ai sai su Bibaa suka sake ƙwala wata ƙarar da tafi ta farko. Itama Mom ta yadda guntun flawer base ɗin daya rage a hannunta tayi wani uban tsalle gefe tana ware idanu. Halime kuwa tuni ta gigice tazura waje a guje....... 💦❤️💦❤️ Komai na daina ganewa. Komai ya tsaya min cak. Ba brain kawai ba, hatta zuciyata da gangar jikina komai dake taimaka musu ya tsaya cak. har muka baro inda Alajah ta sakamu zuwa anan cikin gidan bana iya gane komai. Bin kowa kawai nake da kallo tankar wadda ke a duniyar mafarki. Koda muka koma can sashen Mama Balki bata shiga ba. Tace na shige ciki ita zata koma kan aikinta. Shiru sashen babu kowa, hatta tv a kashe take. Ban zauna a falon ba na shige ciki, saman gadon dana kwana na kai zaune, cikin gushewar tunani na dafe kaina tare da fasa wata irin ƙara illahirin jikina na rawa har ta kaini da faɗowa ƙasa.... Da gudu Bahijja data shigo sashen domin shiga toilet ta ƙaraso ɗakin, dan da farko ma ita tsorata tayi, sai da tajiyo ihun kamar daga ɗakinsu ne sannan cikin ɗari-ɗari ta nufi can. Sosai ta waro idanu, sai kuma ta zabura kan Samraah tana faɗin, “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!. Kandala! Kandala! Miya farune haka?...” Ƙanƙameta Samraah tayi sosai tana cigaba da kuka mai tsuma rai da zuciya. Sai kawai itama Bahijjar ta sanya kuka. Dan yanzu su Sumayya ke bata labarin abinda ya faru tsakanin Samraah ɗin da Azizat. Sun kai kusan mintuna biyu a haka kafin su sassauta kukan nasu. Cikin lallashi Bahijja dake rungume da ita ta fara faɗin, “Kiyi haƙuri Kandala kinji. Haka take sam bata da mutunci. Bata ɗauki ɗan adam komai ba sai abin wulaƙantawarta. Sai kace itama ba cin arziƙi tazo yi gidan ba. Tunda ba gidan ubanta bane ba. Ai wlhy naji daɗin abinda Uncle Boss yay mata, azzaluma. Nima kullum sai ta mareni ga bautar gyara mata ɗaki da nake kamar jaka, hatta da pants ɗinta nike wankewa. Amma sam bata gani, komai akai mata ba'a iya ba, bayan ita ɗin ma babu abinda ta iya sai barcin tsiya da gantali. In sha ALLAHU Uncle Boss bazai aureta ba zamu gani”. A hankali na ɗago ina kallon Bahijja, haka kawai kalamanta sukai wani irin tasiri a zuciyata. Har ban san sanda na furta kamar ya ba ƴar nan gidan bace Bahijja?”.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏_ 💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥 *_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K'ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K'ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* .http://wa.me/+2347069711327 *_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Hadin amarya budurwa ko zawara* *Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)* *Maijego package (virgin gain)* 📦 *Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji* *Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci* *Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa* *Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji* *Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa* *Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,* *Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni'ima sha'awa da dandano* *Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki* *Kalolin Zuma masu saukar da ni'ima Nan take da gamsar da maigida* *Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni'ima da dandano irin wadda akeso* *Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano* *Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar danna wannan blue rubutun* 👉🏻 http://wa.me/+2347069711327 *Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni'ima da jimawa sosai ajikin mace* *Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha'awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha'awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* http://wa.me/+2347069711327 *Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto* ============= .......Zama Bahijja ta gyara fuskarta cike da gulma. Sai kuma ta miƙe ta leƙa waje sannan ta dawo ta rufe ƙofar. Hannuna ta kama muka koma saman gadon A'i dake can ciki. Cikin sake sauke murya can ƙasa tace, “Eh mana ba ƴar gidan nan bace ba. Uncle Boss shi da ƙaninsa kawai aka haifa a gidan nan. Ita ɗin da ƙanwarta Hindu mahaifiyarsu yayar Baban su Uncle Boss ce. Ni na rasa gane musu, ko bata da mijine yanzu oho mata, dan nidai tunda nazo anan gidan nake ganinta zaune ita da ƴaƴan nata. Sai Ashna, ita kuma agola ce. Matar Baban Uncle Boss ta yanzu itace mahaifiyarta. Bata nan sunyi tafiya ne ita da Baban Uncle boss ɗin amma nasan yau zasu dawo. Itama wadda tazo dake Aunty Mama ƙanwar Baban Uncle Boss ce ba'a Nigeria take aure ba. Ƙanin baban dai da shima yake da nasa iyalan anan gidan basa nan sunje Niger biki suma yau zasu dawo yaransu uku. Suma duk basu da kirki musamman babbar su da suke takara da Azizat akan Uncle Boss dan itama sonshi take kamar zata mutu. Shiko ko kallo basu ishesa ba....” “A'a, to shi ina mahaifiyar Boss ɗin ko ta rasu ne?”. Na faɗa cikin tare numfashinta. A take naga jikinta gaba ɗaya yayi sanyi, sai kuma idanunta suka ciko da ƙwalla. Cikin raunin murya irin ta tausayi ta ce, “Tana nan raye bata rasu ba. Amma bata da lafiya....” Sagade nayi kawai ina kallonta. Sai kuma cikin ƙarfin hali na furta, “Tana asibiti kenan tana jiyya?”. Nan ma idanunta ne suka sake cika da kwalla. Sai kuma ta girgiza kanta. “Tana a cikin gidan nan kulle a sashenta. Babu mai shiga inda take sai masu kula da ita, suma basa haɗa wata a gidan nan suke guduwa duk da ɗunbin kuɗin da ake biyansu na albashi, mun rasa miyasa basa zaman. Idan kinga masu gidan sun shiga su kuma to sai dai an ɗaureta ne ko an mata allurar barci mai ƙarfi”. “Ɗaurewa kuma? Sai kace wata dabba?”. Shiru tayi dan hawaye ne sosai ke ɓulɓulowa daga idanunta. Har tana jan ajiyar zuciya kamar zata shiɗe. Sosai hankalina ya sake tashi, sai dai ban iya cemata komai ba na dai riƙe mata hannu alamar lallashi. Kusan mintuna biyu ta haɗiye kukan da ƙyar. Sannan ta cigaba da faɗin, “Humm bazaki ganeba Aunty Kandala. Amma ni dai zuciyata na ayyana min abubuwa da yawa a gidan nan wlhy, sai dai bamu da wani ƙarfin iko ne shiyyasa kawai na zama cikin masu kallo. Mahaifiyar Uncle Boss tana da ciwon hauka ne, shiyyasa suka killaceta ba'a bari kowa ya shiga inda take sai masu kula da ita. Sai kuma likiticin dake dubata duk bayan sati biyu. Duk randa kikaga masu gidan sun shiga inda take to an ɗauretane, dan sunce duka take yi.....” “Har su ƴaƴan nata?”. Yanda nai maganar a ɗan tsawace yasa ta zabura. “I'm sorrry”. Nace mata dan na fahimci na fara rasa nutsuwata. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi, alamar samun nutsuwa. “Ai Uncle Boss ne kawai. Shi ɗayan baya ƙasar, nima tunda nazo ban gansa ba sai a hoto kawai.....” “Shi ɗin baya shiga kenan?!”. “Yana shiga, sai dai ba koda yaushe ba. Saboda shigar tasa bata haifar da ɗa mai ido ne. Yau ma bakiga abu a gefen girarsa ba. Shekaran jiya ne daya shiga dubata bayan ya dawo ta jimasa wannan ciwon. Da ƙyar aka fiddosa a ɗakin ma”. Ta kare maganar tana hawaye. Cikin kukan ta cigaba da faɗin, “Wlhy yana bani tausayi aunty Kandala. Dan abubuwa da yawa idan yanayi zai tabbatar maka da yanda yake matuƙar son mahaifiyarsa. Itama kuma zakiji tana kuka duk dare tana kiran sunansa. Amma al'amarin nasu kamar wani abun sihiri basu isa haɗuwa a waje ɗaya ba kamar maƙiya. Wlhy da ace inada abinda zan taimaka masa koda da duk abinda na tara ne zanyi aunty Kandala. Ki duba fa kiga yanda ya inganta rayuwarmu a gidan nan tamkar ba ƴan aiki ba. Muhalli mai ƙyau, ilimin addini dana zamani kullum akwai malaman dake zuwa karantar damu. Ga albashi mai tsokar gaske. Rayuwarmu a killace ta yanda wani bazai taɓa ganinmu a ƙasƙance ya wulaƙantamu ba. Cimmu, shan mu, sutura, magani idan muna ciwo bai taɓa gazawa ba. Dan ALLAH dami zamu sakankama wannan bawan ALLAH?. Har sonake naga wace mai sa'a ce zata dace da samunsa matsayin mijin aure? ALLAH zan tayata murna harda azumin godiya ga UBANGIJI. Nasan bazaki gane duk abinda nake nufi ba. Amma nan da wata ɗaya kacal duk zaki maimaita abinda na faɗa, dan ma ba zama yake ba sosai saboda harkokin kasuwancinsa dana mahaifiyar tasa ance duk sun koma hannunsa, dan itace mai kuɗin fa. Ko wannan katafaren gidan ance ita ta fara gina shi sannan Uncle Boss ɗin yana ƙarami, sai da ya girma shi kuma ya ƙarasa saboda ita ciwo bai barta ba”. Tana kaiwa nan ta miƙe zaram idanunta akan agogon ɗakin. “Tabɗi na shiga tara, Aunty Kandala bari na koma wlhy minti biyar ta bani, nasan zansha mari”. Kafin nace wani abu ta fice a guje. Shiru kawai nayi ina kallon ƙofa tamkar zan zuƙota da idanu. Akaf labarin data bani wanda ya shafi mahaifiyarsa ne kawai ya tsaya min a rai. To dama tana a haukan ta haifesu? Kokuwa daga baya ne haukan ya sameta? Bani da mai bani amsa dan haka na zabga tagumi kawai. A karo na farko naji ina kwaɗayin jin labarinsa. Ko shiyyasa baya son a tambayesa tarihinsa? Randa nai hira da shi ya shiga dawo min a rai. Tabbas a ranar bai amsa koda kalma ɗaya data shafi privet life ɗinsa ba. Na sake tuna ranar taron buɗe kamfaninsa. gargaɗinsa akan ƴan jarida baya buƙatar kowace tambaya sai akan kasuwanci. Hakan na nufin akwai abinda yake ɓoyewa ko baya son a sani dangane da shi. Kai dolene nasan komai, to amma ta yaya? Wannan shine tsallen baɗaken a gareni. Gashi ba wani jituwa muke ba, to wannan ma jiji da kansa zai barsa huɗɗar arziƙi da mutane.... ★★★ Tunda Samraah tabar gidan ya sake zama sukuku. Wani lokacin ma ya gwammace ya kwana a gareji kawai. Yakan yi kwana biyu bai shiga cikin gidan ba. Duk da kuwa bai fasa musu dukkan abinda yake musu na hidimar yau da kullum ba mussaman cefane da ya dawo bisa kansa. Idan har bazai zo ba yakan bama wani almajiri dake a garejinsu ya kawo cefanen. Duk da asha ruwan tsuntsaye da yakema zuwa gidan Abba bai taɓa tambayarsa ko cigiyarsa ba. Sai hakan ya sake ƙona masa zuciya da jin komai yama fice a ransa. Yakan ɗan ji sanyi ne kawai idan ya kira Hafizzullah ko mijin Samraah yaji yaya jikinta. Yakan so a bata su gaisa, sai dai hakan baya faruwa kasancewar duk sanda zai kira tana barci. Amma dai mijin kan kirasa video call ya ganta a wasu lokutan. Harga ALLAH yana son zuwa ya ganta, sai dai ta bakin su Kawu Musa baya son mijin nata ya ga kamar an nuna ya gaza ne shiyyasa ya haƙura yake kawaici. A kwanakin nan kuma sai ya koma baya samunsa duk sai hankalinsa ya tashi, yana shirin zuwa Abujan sai ga shi ya kiransa yana mai bashi haƙuri akan jinsa shiru wai yayi wata ƴar tafiya ne, amma yana gab da komawa gida idan ya koma zai haɗashi da Samraah. To tun daga ranar kuma basu sake waya ba dai har yanzu... Yana cikin damuwar rashin ji daga mijin Samraah ɗin sai ga ogansa yazo masa da wani batu. Wai Companyn Maash na ƙera motoci da aka buɗe kwanaki sunzo garesa suna buƙatar matasan kanikawa masu kwalin secondary. Shi kuma ya bada sunansa dan yasan yana da su. A yanzu haka kuma sunce zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suna buƙatar ganinsa interview. Rasama abin faɗa yay, sai hawaye da suka cika masa ido yana kallon ogan nasa kawai. Bai san mizai sakankama bawan nan da shi ba a rayuwa saboda ɗunbin ƙaunar da yake nuna masa da alkairan da yay masa... “Wai namiji da kuka Musaddiq?”. Ogan nasa ya katse masa tunani cikin nuna damuwa. Hannu yasa ya share hawayen da shi kansa bai ma san sun zubo ba. Sai kuma yay murmushi tare da buɗe baki zaiyi magana. Da sauri ogan nasa ya dakatar da shi da faɗin, “Basai kace komai ba Musaddiq. Ka cancanci fiye da haka a wajen nan domin kai ɗin ɗan hakal ne wlhy. Da ace inada abinda yafi hakan zan maka a rayuwa. Fatana dai ALLAH yasa wannan canjin da zaka samu ya zama sanadin alkairin ka a rayuwa kai da zuri'ata. Kuma ina mai farin cikin sanar maka nima basu barni haka ba. Akwai aikin dazan dinga musu, dan haka zasuzo su gyara wannan wajen ya koma na zamani kamar yanda suka faɗa”. A take farin ciki ya sake mamaye Musaddiq. Sujidar shikur ya farayi kafin yaje ya rungume ogan nasa. Dariya ya shiga yimasa, dan har ga ALLAH yana matuƙar ƙaunar Musaddiq saboda gaskiyarsa da riƙon amana. Ga biyayya da kwazon aiki, da wahala kaga fushi a fuskarsa koda kuwa faɗa yay masa. Mutum ne mai juriya da shanye komai koda bai masa daɗi ba.... Rasa inda Musaddiq zai kai wannan farin ciki yayi, har ya danna Number Abba sai kuma ya fasa sakamakon tsoratar da shi da zuciyarsa tayi kodan halin Mom. Haƙura yayi, sai da yamma ana tashi daga aiki ya wuce Dawanau wajen Gwaggo Gudidi. Ita ya kaima wannan labarin farin cikin, ai ko baiwar ALLAH harda kukanta tana ƙara godema ALLAH. Daga ƙarshe ta gargaɗesa akan kada ya sanarma Abba yanzu kodan mugun halin matarsa zata iya shiga ta fita ta jefesa da wani sharrin. Yana dai ganin halin da aka shiga game da auren Samraah abu kamar a film ko a labaran hikayiyin marubuta. Ya yarda da shawarar Gwaggo ɗari bisa ɗari. Daga haka suka koma hirar Samraah. Itama Gwaggo ta shiga damuwa sosai hankalinta kuma ya fara tashi, anya kuwa basuyi gangancin aurama Samraah mutumin nan ba? Duk da dai a fuska yazo musu da suffar mutanen kirki. Amma dai zatai magana da Kawu Musa domin a tuntuɓi magabatansa da sukai masa waliccin auren.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ______________ ......Sosai hirarmu da Bahijja ya tsaya min ƙyam a rai da zuciya. Duk yanda nake yaƙin son turesa hakan ya gagara. Gashi tun ranar ban sake ganin makirin ba. Hakama cikin gidan ban sake shiga ba. Bahijja dai ta sanar min Babansa da matar babansa sun dawo daga tafiya, hakama ƙanin baban nasa da iyalinsa sun dawo suma dai. Sannan yau gaba ɗaya sunyi busy wai ana aiki ne acan sashin saboda bikin birthday da za'ayi wai na mahaifiyar tasa. Ni al'amarin ma sai na ɗaukesa hauka. Yo inba hauka ba, koma nace sunfi ita mai ciwon haukan zama mahaukata mara lafiya dake buƙatar addu'a ce wai za'ama wani shegen birthday party. Kai yawudanci ma baiyi ba. Ko kuwa dukiyar tasu ce ke neman zauta musu ƙwaƙwale ma oho musu. Sosai takaici ya kumeni, ji nake kamar na buɗe ido na gansa a gabana. Wlhy da ko zai tsireni sai na faɗa masa gaskiya sai dai ya mutu shiya sani. Ina nan kwance ina ƙullawa da kwancewa wajen ƙarfe biyu su Mama balki suka fara dawowa. Hayaniyarsu tasa na fito falo nima. Sannu na shiga musu, wasu su amsa wasu su shareni batare dana san mina musu ba. Mama Balki ce ta dubeni da murmushi, cikin kulawa ta ce, “Ai kema daga gobe za'a fara miki sannun. Dan Aunty Mama tace zaki fara aikinki. Kinga sai ki shirya idan mun gama zamu wuce dake tare wajenta kamar yanda ta bada umarni”. Sosai naji wani irin abu mai nauyi ya soki zuciyata. Na dai danne da ƙyar ina murmushin yaƙe. Da girmamawa na amsa mata da “To mama nagode”. Daga haka ban sake cewa komai ba saboda baƙin ciki. Ni kuma haka rayuwata zata ƙare. Wahalar gidan Abba. Rabani da masoyina, auramin azzalumin mutum irin wannan mutumin da bai san komai ba a rayuwa sai kansa. Daga ƙarshe ma maimakon na shigo gidansu matsayin matar aure a ƴar aiki nazo. Nasan shine ya tsara hakan, kuma zan tabbatar masa ya tsara ramin muguntar da shine zai afka ciki daga ƙarshe. Dani yake magana Samraah Abdul-wahab gwarzo..... _Hummm Sam-G tamu. Koda yake aunty kike tunda matar Yayanmu ta🥱🥱🚴_ ❤️ Kamar yanda Mama Balki ta umarceni wanka nayi nima. A'i da yanzu ta ɗan fara kulani itama ta kawo min doguwar riga ta farin Material da suma naga sun saka a jikinsu inji Mama Balki. Nayi mamakin kayan, dan sababbine ƙal kuma daga gani ba ƙanana bane ba. Haka dai na shirya ina zancen zuci. Ganin yanda Bahijja ta tsaya tana kallona ya sani mata alamar lafiya? Da idanu. Murmushi tayi da sauke ajiyar zuciya. “Wlhy Kandala baki ganki ba. Sam bakiyi kala da masu aiki ba. Kayan nan sun sake fiddo da ainahinki na ƙyaƙyƙyawar mace wayayya. Dan ALLAH idan bazaki damu ba ki sanar min labarinki. ALLAH sai nake ji a raina ko sunanki ba gaskiya kika sanar mana ba”. Idanu na ɗan waro mata kamar zanyi magana sai kuma na fasa nayi murmushi kawai. Dan babu abinda na ɗauki zancen nata sai shirme. A girme zan iya girmar Bahijja, amma yanayin inda take rayuwa da kuma halitta ta na mutum mai jiki yasa a ido zaka iya cewa sa'anni ne mu. Riƙoni tayi zata sake yin magana Afrah ta shigo. A wulaƙance tace, “Malamai ku Mama ke jira kuka wani zo nan kuka haɗe kawuna dan munafunc....” Ta gagara ƙarasawa saboda saukar idanunta a kaina. Ɗauke kaina nayi tamkar banga kallon da take min ba. naja ƙaramin mayafin Bahijja na yafa nai ficewata na barsu.. “Kan uba Bahijja kinga kuwa abinda na gani tattare da yarinyar nan?”. Afrah ta faɗa cikin jimami da shiga ruɗani. Ƴar dariyar shaƙiyanci Bahijja tayi. “Yo mi kika gani?”. “Bahijja anya ba ƴar leƙen asiri bace ba. Sam yarinyar nan batai kama da wadda ta fito a cikin wahala ba. Musamman kwana biyun nan da tayi a gidan nan jikinta ya sake murjewa sai ainahinta ya fito. Duk da muma yawancinmu badaga ƙauye aka kawomu ba rashin gata ne da neman rufin asiri amma yarinyar nan fa ta fita daban a cikinmu wlhy.” Cikin son basar da zancen Bahijja ta ce, “Babu wani leƙen asiri. Itama dai neman rufin asirin ne ya kawota. Acikin ƴaƴan talakawan ma ai akwai ƙyawawa da yawa irinta har ma da wanda suka fita. Kin san dama irinsu gatan ne kawai babu, amma da sun samu kulawa sai ki gansu tarr da su”. Badan Afrah ta gamsu da bayanin Bahijja ba tai shiru. Dan Bahijjar na gama bata amsa ta nufi hanyar fita itama. Kai kawai Afrah ke jinjinawa da sake tabbatar ma kanta dole ne ta sakama yarinyar nan ido a gidan nan, dan sai ta san ko ita wacece.... Koda na fito falon ma gaba ɗayansu suka zubomin ido. Hatta da Mama Balki naga alamar shock a tattare da ita. Tuni na ƙara gyara yanayina, dan na fahimci fa nima sai na yarda na ari wata rayuwa kafin na cimma burina akan mutumin nan dama zaman gidan nan. Sam bana fatan zama a cikinsa na dogon lokaci. Amma ina da burin son sanin sirrin cikinsa da mutumin nan keta faman ɓoyema duniya. Hakan kuma bazai taɓa ya kasance ba sai na zauna a matsayin da kowa ke kallona a yanzu na ƴar aiki. Ta wani gefen kuma begen ganin mahaifiyarsa da tausayinta na tsungulin min rai da zuciya. Sai dai ban san ta ina zan kama ba har yanzu. Gaishesu nayi kawai na koma gefe kaina a ƙasa... “Tab ɗi lallai akwai rigima a gidan nan. A banga laifin Hajiya Azizat ba. Anya kuwa babu alamar tambaya anan gurin?”. Aunty Falilah ce tai maganar cikin nuna baƙin cikinta muraran a kaina. Dama na fahimci ita da sauran ƙawayenta su Aunty Kubrah basa ƙaunata sam. Kafin wani ya sake magana Mama Balki tace muje. Dole kowa ya haɗiye abinda ke a ransa muka fice. Cikin raɗa Bahijja dake ta gefena ta ce, “Kiyi haƙuri karki damu da su. Su dama su Aunty ƴan neman fitina ne, sam basa riƙe girmansu a cikinmu saboda suna gadarar yaran Mammah ne a gidan. Itace mai juya akalar kowa a gidan kuma hatta da mai gidan kansa da matarsa”. Murmushi kawai nayi batare da nace komai ba. Dan ta gefena su Afrah ne idan har nayi magana zasu jini. Sosai an sake ƙawata gidan. Tako ina ka kalla kasan za'ayi shagali ne. A maimakon cikin gidan yau garden muka nufa. Bamma san sanda na furta “Masha ALLAH” ba a zahiri. Dan tsayawa muku misalin haɗuwa da tsaruwar da garden ɗin nan yayi ma ɓata lokaci ne. Sai dai abin mamaki bamu tsaya anan ba. Ta wata ƙofa da ganyen flower ya baibaye muka sake ratsawa sai gamu a wani killataccen waje da yafi wancan ƙatoton da muka ratso, wani irin shiryayyen adon furanni da koriyar ciyawa akai masa tako ina masu ƙamshi. Ga ƙaton swimming pool da ruwansa ke wani kalar ƙyalli da walwali tamkar ba normal ruwa ba. Ƙasa-ƙasa Bahijja dake kusa da ni ta furta, “Wannan sashen garden ɗin babu mai shigowa cikinsa sai a irin wannan ranar. Sau ɗaya a shekara kenan kawai”. Da mamaki nace mata, “Saboda mi?”. “Saboda bana kowa da kowa bane. Bakiga an zagayesa da waya ba. Uncle boss kaɗai ke shigowa cikinsa, dan tanan shine jikin part ɗinsa”. Ta ƙare maganar da ɗan nuna min wata hanya da aka ƙawata da koriyar ciyawa tamkar a irin lambun mafarkin gaibu ɗin nan. Na jima ina kallon ƙofar abubuwa masu yawa namin kai-kawo. Sai dai bance komai ba face ɗan kalle-kallen garden ɗin da nake yi. Komai a tsare a tsaftace. ga Docorretion ɗin da akai masa ya bala'in sake ƙawatashi. Hannuna da mama tazo ta kama ya sani kallonta firgigit, murmushi tamun da faɗin, “Zo muje ke anan zaki zauna har sai an buƙaci ganinki”. “Mama saboda mi?. “Saboda Aunty Mama bata bada umarni na shigo da ke har nan ba”. Komai ban sake iya cewa ba har taja hannuna muka fito a wajen. A ƙaton garden ɗin na farko muka dawo. Ta kaini can wani ɗan lungu ta ce, “Zauna anan. Kar kije ko ina dan ALLAH dan akoda yaushe zan iya zuwa kiranki”. Kaina kawai na jinjina mata. Dan koda bata roƙeni ba ma bazan tashin ba. Nakai zaman mintuna talatin a wajen dukan tunanina naga Yaya Musaddiq. Yau wani irin kwaɗayin son jin muryarsa nake shi da Hafizzullah. Tamkar wadda hankalinta ke dawowa jikinta a wajen nake jin ƙarfin zuciyata da komaina dake neman ƙwacemin a kwanakin nan na fara dawowa. Sai kawai naji harshena ya ɗauki ambaton sunayen ALLAH. A jere na ringa sauke ajiyar zuciya kai kace a barci na farka. Ratsa kunnenna da sautin muryar malam tayi yana karanto addu'a ya sani lumshe idanuna a hankali. Ji nake hatta da jinin jikina yamutsawa yake yi har a cikin farautana har malam ya kammala. Ajiyar zuciya na sake saukewa a karo na babu adadi, dai-dai nan sai ga Mama Balki ta dawo kirana. Nasha mamakin ganin wajen yanzu dan cike. Dan komai da alama an tsarashi ne hatta da mutanen dake a wajen. Ɗan bin kowa da kallo nake ƙasa-ƙasa nima har muka isa inda su Bahijja ke tsaye jere. Dai-dai nan mc ke shelanta fitowar mai gayya mai aiki tare da tabbatar da shi a madadin mai birthday ɗin. Tsitt wajen yayi kowa ya sake maida hankalinsa ga hanyar da Bahijja ta nunamin ta sashensa. Duk da yanda zuciyata ke tafasa na kasa ɗauke idanuna daga kallon wajen nima. Ƙanjamammiyar baturiyar nan mai shegen iyayi da yaje da ita wajen taron buɗe companynsa ce ta fara fitowa sanye cikin doguwar riga milk da wasu shegun dogayen takalmanta. Siririn tsaki na saki tare da ɗauke kaina a wajen gaba ɗaya. “Woow masha ALLAHU”. Da Bahijja dake a gefena ta faɗa ya sakani ɗagowa na kalleta. Ganin yanda ta saki baki da hanci da idanu tana kallo ya bani mamaki, kaina kawai na girgiza zan ɗauke caraf ta kamo hannuna. ”Dan ALLAH ki kalla ado ya namijin ɗawusu Aunty Kandala. Wlhy Uncle Boss na kasheni da salonsa, komai ya saka a jikinsa sai kiga kamar danshi dama akayi kayan, wani lokacin sai nakeji kamar na ciza uwawuna”. Takaicin shirmenta ya sakani dalla mata harara. Nai ƙoƙarin fisge hannuna amma ta sake damƙeshi. Haushi ya sakani kallonta, amma sai naga ma ita hankalinta sam baya a kaina. Takaici ya sani girgiza kai kawai nakai dubana ga abinda take zuzutawar batare da nasan dalili ba nima..........✍️ _Bayin ALLAH kuyi haƙuri dani Please. Wlhy biki gareni na ƙanwata asabar ɗin nan. Jiya kuma rasuwa akai mana data bugeni sosai. Amma in sha ALLAHU komai ya kusa dai-dai da amarya taje ɗakinta zaku cigaba da ganina yanda ya kamata. Kuyi hakuri da asha ruwan tsuntsayen nan nawa na yanzu🙏_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_ ......Akan takalman ƙafarsa na fara sauke idanuna, yanda suke sheƙi da ɗaukar idon mai kallo ya isa tabbatar maka almubazzaracin da akai da kuɗi wajen sayensu. Coffee brown suit ne a jikinsa, sai rigar ciki milk color. Kamar kullum botiran farko a buɗe har ana iya hango jikinsa kaɗan. Luf-luff gashin kumatunsa ke kwance a saman fuskarsa tamkar masu barci, sai wani irin sheƙi suke suma. Hannunsa ɗaya a cikin aljihun wandonsa ɗayan riƙe da wayar dake manne a kunnensa yana wani motsa ƙananun pinkish lips ɗinsa a hankali kamar wanda akaima tilas. Kamar kullum kunnensa ɗaya manne da ɗan kunne, daga tacan saman kansa zane da kitso ƙwara biyu zane ata gefe da gefe, tsakkiya wiving kusan biyar, cikkune dan haka ɗaure yake a tsakkiya ƙarshen kitson kuma gashin a warware ba'a kitseba dan haka ya sakesa kawai a baya yana lilo. Wani irin takaici da haushi ya sakani kallon fuskarsa duk da nasan tabbas yayi ƙyau. Karaf kuwa idanuna a cikin nasa. Bamma san lokacin dana balla masa harara da murguɗa nawa bakin ba. A mamakina sai kawai naga ya lumshe nasa idanun tare da buɗesu a lokaci guda yana cije gefen lips ɗinsa ya ɗauke kansa. nima ɗauke nawan nayi kamar zan fasa kuka, ji nake tamkar naje gareshi yanzu na zazzage masa abinda ke a raina. Amma dai na dake, sai harara dana sake jefama jelar PA ɗinsa dana fahimci tunda idonsa ya sauka a kaina yay suman tsaye. Niko na ɗauke kaina tamkar ban san da zamansa a wajen ba. Tunda nasan dai duk abinda mugun ogansa ya ƙulla tare da shine makirin shima. Addu'ar da aka fara gabatarwa ya saka kowa a wajen sake nutsuwa. Mu dai marasa gata duk muna a tsaye kan ƙafafunmu, yayinda suko ke zaune a kujerun da aka ƙawata wajen. Sosai yanda akai addu'ar wa kowa harda iyayenmu ya sake saka min nutsuwa har idanuna na tara ƙwalla. (ALLAH sarki rayuwa, da ace muma namu iyayen na raye babu yanda za'ai mu tsinta kammu a cikin wannan gararin rayuwar. Amma ko yanzu ma alhmdllh, koba komai mun rayu cikin aminci tunda gallazawar rayuwa batasa mun lalace ba). Kewar su Yaya Musaddiq ce ta sake taso min sabuwa har na zurfafa a tunani batare dana farga ba. Taɓanin da Bahijja tayi ne ya maidoni a hayyacina. A hankali na sauke ajiyar zuciya da nannauyan numfashi. Cikin raɗa-raɗa a saitin kunnena ta ce, “Aunty Kandala muje zamu fara bada drinks”. Kaina kawai na iya jinjina mata, dan gaba ɗaya babu wani ƙarfi a tattare da ni. Ta wajen babban table ɗin da aka shirya nau'ikan abinci dana lemuka da ruwa muka nufa. Bahijja ta zari handglob guda biyu ta miƙamin tare da mun nunin na saka. Itama ta zara ta saka a nata hannun sannan ta buɗe ƙatuwar kular da kayan ruwan ke ciki ta ɗiba lemunan da ruwa duk ta loda a babban tray data jawo guda biyu. Sai da ta gama zuba nata da nawa sannan ta ce, “Yauwa to muje. Kowa a gabansa zaki fara ajiye ruwa sannan ni kuma na ajiye lemon da suka buƙata”. “Kamar ya?”. Na tambaya cikin rashin fahimta. Ƴar dariya tayi. Kafin ta ce, “Na zuba miki ruwa ne dan kar su baki wahala. Shi ruwa zaka ajiye ne kawai. Amma lemo dole sai mutum ya zaɓa sannan”. Kaina na jinjina mata alamar gamsuwa, sannan na kama tray ɗin na ɗaga ina ɗan taɓe baki. Ai da sauri na maida na ajiye ina waro idanu. Ai wlhy bazan iya ɗauka ba yamun nauyi. Ragewa na fara yi, hakan ya sata zaro idanu waje alamar nuna mamaki. “Lafiya kike ragewa?”. “Yamun nauyi wlhy Bahijja bazan iya ɗauka ba”. Sake waro idanu tayi, niko ban sake kulata ba na rage fin rabi sannan na ɗauka. Kallo take mun na tama rasa abin faɗa. Ni ko na sake ɗauke kaina gefe kamar ban ganta ba. Dole itama ta barni muka bar wajen tana gaba ina biye da ita. Suma sauran kowa ya fara aikinsa dan komai a tsare yake. Mun fara da table ɗin farko. Mai ɗauke da mutane huɗu kamar ko ina. Maza biyu masu tsananin kammani, a fisge kuma suna kama da mutumin can Maash. Sai dai kawai su baƙaƙe ne. Tabbas nasan mai irin fuskar nan amma na manta a ina. Sai mata guda biyu ƙyawawa suma, ɗaya fara tas ɗaya black beauty. Su duka sunci ado sosai mai tsananin ƙawa. Ganin kallon da suke min na rashin sani yasa naji kamar duk na daburce. Amma sai na dake kaina a ƙasa na shiga haishesu ƙirjina na bugawa da sauri-sauri. Mazan ne kawai suka amsa min, yayinda baƙar matar ta dubi Bahijja a gadarance ta furta, “Wannan fa?”. Jikin Bahijja har ɓari yake. Cikin in-ina ta amsa da, “Au...aun..Aunty Mama ce tazo da ita randa ta iso”. Su dukansu ɗan kafeni sukai da kallo, sai kuma duk suka janye cike da basarwa. Jiki a sanyaye na bar wajen, batare da ina kallon gabana ba saboda zancen zuci na iso table na gaba. Ganin nayi tsaye kawai Bahijja ta ɗan zungureni, firgigit na kawo numfashi, ɗagowar da zanyi na sauke idanuna a kansa. Zaunensa yake a harɗe fuskar nan kicin-kicin tamkar ba wanda ya tara jama'a ba. Gaba ɗaya hankalinsa na akan tab dake a hannunsa ne. Yanda yay serious a kanta zai baka tabbacin abinda yake yi mai muhimmanci ne. Ga uban ƙamshin turarensa da ya mamaye wajen gaba ɗaya. Fuska na yamutse tare da ɗauke kaina. Harara na ballama ɗan koren PA ɗinsa dake table ɗin bayansu. Ƙasa naga yayi da kansa yana murmushi. Jinai zuciyata ta ƙulu da murmushin nasa, amma sai na danne tare da cije lips ɗina kawai.... “Woow! fine girl ko ana mana rowan ruwan ne?”. Ɗaya daga cikin waɗan da ke zaune a table ɗin tare da shi ya dawo dani a hayyacina. Ni sai ma yanzu na lura da sauran dake zaunen a tare da shi. Su duka su nasan fuskokinsu a wajen taron buɗe Companyn sa na Kano. Dan ALLAH ya bani baiwar da dawahala nai maka gani ko ɗaya ne na manta fuskarka koda ace ban riƙe suna ba ko a inda na sanka ba. A hankali na ɗan yamutse fuska ta. Batare da nace komai ba na fara ajiye musu ruwan. Uku na ajiye abina batare da nashi ba, dan kowa a gabansa na ajiye amma shi banda shi. Na ɗaga tray ɗin zan bar wajen wannan dai da yay maganar ya ɗan waro idanunsa yana nuna min shi. “Beauty baki ajiyema boss ba fa”. Yi nai tamkar ban jisa ba sai da Bahijja tasa hannu ta ɗauka ruwan ta ajiye masa jikinta har yana ɗan rawa. Harararta nayi batare dana san dalili ba. Itako ta waro idanunta na nuna mamakina. Tray ɗin na sake ɗagawa da nufin barin wajen ina dallamasa harara ta gefen ido dan tunda mukazo wajen ko sau ɗaya bai motsa ba balle kai tunanin yama san da zuwan namu, batare da nasan yanda akai ba, ta yaya kawai tray ɗin ya suɓuce min na tafi gaba ɗaya na. Idanu kawai na runtse tare da sallamawa, amma sai na jini zaune jikin mutum, yayinda shi kuma tray ɗin ya suɓuce a ƙasa sauran ruwan suka tarwatse. Wani irin zuƙa da nayima mayataccen ƙamshin turarensa ya saka gabana faɗuwa. Da sauri na buɗe idanuna dake a rufe. Sai kawai na waro su tare da yunƙurawa da sauri zan miƙe amma hakan ya gagara. Dan sake zamewa nayi na koma jikin nasa gaba ɗayana har ma fiye da farko. “Sai kice son hawa kike ba sai kinyi pretending ba”. Naji saukar muryarsa a cikin kunnena. A wani irin zafafe na sake yunƙurawa gaba ɗaya na na miƙe jikina har tsuma yake, sai da Bahijja data gama firgita ta riƙoni. Jinai bazan iya daurewa ba, idanuna na tara ƙwalla na watsa masa harara, sai dai ina motsa lips ɗin na nufin juye masa abinda ke raina naji na gagara hakan. Sakamakon wani shegen kallo daya tsatstsareni da shi tare motsa lips ɗinsa a hankali, “Kina cewa tak sai kowa yasan ke MATAR MAASH ce”. Da masifar ƙarfi na cije lips ɗina hawaye na sake ciko min idanu. Badan na samu horo akan aikina game da salon da yay maganar ba da bazan fahimta ba. Amma gamu ƴan jarida yaren magana da ido ma an karantar da mu balle na motsa lips. Da wani irin salon rainin hankali ya kai yatsarsa manunuya saman goshinsa tamkar zai gyara silin gashi yay salute tare da sakin wani matsiyacin murmushi gefen baki ya kanne ido ɗaya. “Sai na tarwatsa rayuwarka”. Na faɗa nima a saman lips ɗin ina haɗiye hawayen da suka ciko min idanu. Sanin zasu iya zubowa na kai durƙushe nima ina taya Bahijja tsinci ruwan daya tarwatse. Sai faman haɗiyar zuciya kawai nakeyi dan ni kaɗai nasan abinda nake ji a cikinta, nu mutumin nan zai cema ina son hawa masa jiki ne dama. Ƙasa-ƙasa Bahijja ta furta, “Aunty Kandala kice masa yayi haƙur....” ruff ta rufe bakinta tare da haɗiye sauran abinda ke bakin nata saboda hararar dana balla mata. A fusace na miƙe tare da sunkutar tray ɗin nabar wajen. Mama Balki ce tai min nuni da nazo inda take. Dole na nufi inda muka ɗebo ruwan. Amsar tray ɗin tayi tana faɗin, “Badai kiji ciwo ba ko ɗiyata? Alhamdullah ma Alhaji ƙarami na kusa ya taimaka miki da kinyi muguwar faɗuwa ai. Sai naci ƙaniyar Bahijja kuwa, tunda bance harda ke za'ayi aikin nan ba amma ta jaki”. Sosai naji raina ya ƙara zafafa. Wato su abinda suka fahimta kenan nazo zan faɗi ya taimakeni, alhalin ina zargin taɗeni akayi da ƙafa, tunda karo naci da abu a bazata, kuma babu wani dutsi ko ƙarfe balle ace shine. Ko rantsu nayi ba'a bina bashin kaffara mutumin nan shine silar faruwar komai, dan shine ya taɗeni da ƙafarsa........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏 _*_Assalamu alaikum. Gaisuwa a gareku da fatan alkairi bayin ALLAH. Dan ALLAH kuyi haƙuri! kuyi haƙuri! kuyi haƙuri!!. Ba haka naso al'amarin ya kasance ba. Sai dai kana naka ne ALLAH na nashi. Nashi kuma shine gaskiya. Saboda ku na tsara kwanaki biyar, amma suka koma kwana tara. Amma in sha ALLAHU gamu mun dawo filin daga. Zakumin haƙuri na dinga baku ko 2pages ne dan na samu na rage nawa aikin nima daga nan ko zuwa kwana uku ne. Ngd Ngd sosai da haƙurinku gareni da uzirin da kukayi min. Wanda suka kirani kuma, kuma nagode, wanda sukai ma amarya da mai rasuwa addu'a a group duk na gode ALLAH ya bada ladan zuminci😘😘🙏._ ........“Kinga maza jeki ki zauna dan baƙya cikin wannan aikin”. Mama Balki ta katse min tunani. Kaina kawoi na iya ɗaga mata da faɗin, “Nagode” a taƙaice na wuce ina haɗiyar zuciya. Inda muke tsaye da da Bahijja na koma na tsaya, sai dai duk bayan sakan sai na harari inda yake. Haka dai taron ya cigaba da gudana. An ƙara gabatar da addu'a musamman akan wadda aka tara taron da fatan ALLAH ya bata lafiya, na fahimci ba kowa yasan ainahin ciwon da take tare da shi ba, dan ina jin wasu mata biyu na gulma ƙasa-ƙasa game da hakan. Wai shekara da shekaru anata ciwo-ciwo amma anƙi sanarma duniya wane kalar ciwo ne. Sosai suka bani mamaki, a raina nace duniya kenan, mutum na jikinka amma baya maka so dan ALLAH. Natsuwar fara addu'ar na samu damar fara bin kowa dake a wajen da kallo daki-daki. A hankali Bahijja da duk hankalinta ke a kaina dan tuni sun kammala raba lemon da ruwa sun dawo inda muke ta furta, “Aunty Kandala kinga waɗanda ke a table ɗin kusa da nasu Uncle Boss ta hannun dama da muka fara bama ruwa da drinks mai milk shadda shine mahaifinsa. *_El-mu'azz Mashi_ kenan. Sosai na tsurama wanda ta faɗa ɗin ido ta gefe dan ɗazun ban iya musu wani kallon kirki ba. Eh tabbas da gani babu tambaya, dan ya ɗebo wasu a cikin kamanninsa. Kamar tsaho, dogon hanci da makamantansu. Sai dai shi baƙine sannan alamun girma ya bayyana kaɗan a tare da shi. Musamman akan gashinsa akwai furfuta tsilli-tsilli. Haka kawai nake sake jin tabbas nasan fuskar, sai dai a ina? Na manta sam dan na kasa tunawa. Cikin katse min tunani Bahijja ta cigaba da faɗin, “Sai matar dake kusa da shi. Hajiya ƙarama kenan. Itace matarsa ta biyu kuma amaryarsa. Itace mahaifiyar Arwa. Ance ta taɓa haihuwa da shi sau ɗaya tagwaye duk maza a shekarar farkon aurensu amma duk sun rasu, ba kuma ta sake ba. Arwa dai da ita tazo. Matar bata da damuwa sosai, sai dai akwai miskilanci da mulki tamkar itace ma uwar Maash ɗin. Sai dai abubuwa nata da yawa na matuƙar birgeni, duk da dai wasu na bani haushi musamman yanda Hajiya Mammah ke takata yanda take so amma bata iya cewa komai ko nuna ikon ta na matsayin matar gida, wani lokacin ma sai ka ɗauka itace matar gidan ba Hajiya ƙarama ɗin ba”. Sosai na tsurama matar idanu itama. Ƙyaƙyƙyawar mace kam ga suffar kamala black beauty da ita. Amma da gani kasan miskilar ce dan sam babu fara'a a fuskarta kamar dai ɗazun da tai tambayar ni wacece a daƙile. Bahijja ta cigaba da faɗin, “Na kusa da shi kuma Alhaji Abdullahi Mashi, ƙani wajen Alhaji El-Mu'azz kenan. Uwa ɗaya uba ɗaya. Ta kusa da shi Hajiya Mubeena matarsa uwar ƴaƴansa uku. Itama dai tana da ƙarancin damuwa, sai dai ta hannun damar Hajiya Mammah ce dan ƙiri-ƙiri take nuna banbanci tsakaninta da Ummi ɗin (Hajiya ƙarama) na taɓa jin su Aunty Falila suna gulma wai ai dama ƙawarta ce acan ƙasar Niger da tayi aure, kin san mahaifin su Azizat buzu ne, shiyyasa kike ganinsu da shegen gadarar nan da masifa duk da dai shima wannan family ɗin masifa kamar a jininsu take, fitinannun mutane ne na bugawa a jarida, Uncle Boss ne kawai nake gani ma shiru-shiru a cikinsa ko magana da wahala kaji yana yinta, in ma yayi ɗin ba lallai kaji sautin muryarsa ba, sai ko Aunty Mama itama tana da sauƙi sosai, idan kinga tana faɗa an ɓata bata rai ne matuƙa. Daga table ɗin gefensu akwai Azizat ita kam kin haddaceta” tai maganar da shaƙiyanci, sai kuma ta cigaba da faɗin, “Sai Mabrukah autar Hajiya Mubeena, sai....” Da sauri tayi shiru saboda yafito ta da Azizat ɗin tayi, jikinta har rawa yake ta nufeta. Wani takaici ne naji ya ƙwaƙume min zuciya. Bamma san na saki sirrin tsaki ba da taɓe bakina na ɗauke kaina daga sashensu ma gaba ɗaya. A bazata suka sauka akan Hajiya data ɗakkoni daga Abuja. A mamakina sai naga ta sakar min murmushi harda kashe ido ɗaya. Ɗan tsira mata idanu nayi cikin nazartar yanayin nata dan haka kawai komai daya faru a tsakaninmu tun daga Abuja ya shiga dawo min. Yanda take wani bina da kallon ƙurilla ya sani balla mata harara na bar wajen gaba ɗaya dan muna facing juna. Dai-dai nan mc yay kiran sunan uban taro cike da girmamawa. A tunani na Alhaji El-Mu'azz ɗin ne zai tashi, amma sai naga makirin nan ne ya miƙe cike da ƙasaita bayan ya gama shan ƙamshi da busar iska da fesarwa. Taku yake tamkar mai tafiya a kan gilashi, dan sai ka ɗauka ma bazai ƙarasa inda mc ɗin yake ba dan jiji da kai. Mic ɗin ya amsa, sai kuma yay ɗan shiru kamar wanda ya rasa abin faɗa. Baki na taɓe tare da watsa masa harara sai idona a cikin nashi. Da sauri na ɗauke ina mai murguɗa bakina kawai.... “Hummm!!” ya faɗa cikin mic ɗin ta yanda kowa dake a wajen sai da ya ji sa. Amma a mamakin kowa ya sake ɗinke fuska kamar bashi ne yace hummm ɗin ba. Sai ma cigaba da maganarsa da yay cikin harshen turanci mai haɗe da faransanci, yau dai ALLAH ya taimake mu ba'ai Hausa ba balle a ɓaga mana yare. Godiya ce kawai yayi a taƙaice tare da roƙon cigaba da tayashi addu'a ALLAH ya bama Ummiensa lafiya. Sai kuma yay shiru kansa a ƙasa fuskarsa na nuna tsantsar damuwa. Kusan minti ɗaya kafin ya ɗago yana mai kai handkerchief saman fuskar sa ya goge. Sai kuma ya saki wani lalataccen murmushi yana ɗan lumshe idanunsa da buɗewa a lokaci guda ya saukesu akan mahaifinsa. Murmushi ya sakar masa, sai kuma ya miƙe tare da nufosa shima. Yana isowa ya rungumesa yana ɗan bubbuga bayansa alamar lallashi. Daga haka ya amshi mic ɗin hannunsa shima ya fara magana. Kusan abinda dai ɗan nasa ya faɗa shima ya maimaita, sai abubuwa kaɗan daya ƙara a kai sannan suka yanka cake a tare. Baban ne ya fara ɗibowa ya kai bakinsa. Cikin wani yanayin narke fuska ya motsa ƙananun lips ɗinsa kaɗan, sai dai baban na zuwa gab da bakin nasa sai ya juya hannunsa zuwa nasa bakin ya cinye cake ɗin tare da lakata masa sauran na hannunsa a saman hanci. A take wajen ya ɗauki tafi da dariya. Shima murmushi yayi yana kauda kansa. Sai baban ya rungumosa yana dariya. Haka kawai na tsinta kaina da yin murmushi akan wasan nasu, sai kuma na haɗiye da sauri dan tuna akan wa akeyi. Bayan sun je sun zauna Hajiya Mammah, Aunty Mama, Hajiya ƙarama, Hajiya Mubeena, Alhaji Abdullahi duk sun fito sunyi bayani tare da addu'a ga Hajiya Ummu-Hidaya kamar yanda naji suna ambata dama rubutawa da akai jikin ƙaton cake da wani irin golden color mai sheƙi tamkar ba cake ba. Gaba ɗaya zaman wajen bai wuce na awa biyu da mintuna arba'in ba. Aka raba ƙyauta har da mu daga haka taro ya tashi. Bayan tsirarun baƙin da aka gayyato irin su Hajiya sun wuce Aunty Mama ta bama Mama Bilki umarnin zuwa dani garesu bayan sallar isha'i. Ta amsa mata da girmamawa yayinda ni kuma nai kamar ban jisu ba dan hankalina gaba ɗaya ya tafi wani waje daban..... 🌜🌟🌛 Matuƙar tashin hankali Musaddiq da Halime tai gudu ta kira ya shiga ganin Abba cikin jini. Rasama abinda zai yi yay har sai da maƙota suka shigo. Sune suka ambaci asibiti sannan hankalinsa ya dawo jikinsa. Ga Bibaa da Auta na famar darzar kuka. Baby kuwa sai surutai takeyi. Duk wanda ya shigo kuma sai ta nuna Mom data maƙure gefe jikinta na maƙyarƙyata. “Kun ganta nan itace ta kashe mana Abba. Kawai itama a kasheta dan nice alƙali na yanke hukunci”. Abinda Babyn ke faɗa kenan cikin Muryar ƴan maye da surkulle. Duk da kowa kanji shock da abinda ta faɗa ɗin da kuma yanayin da take ciki babu mai bi takanta. Burin kowa dai a kai Abba asibiti kada ya rasa ransa.... Koda suka isa asibitin da ƙyar aka amshi Abba, dan sai da Yaya Musaddiq yay ƙaryar faɗuwa yay a banɗaki sannan. Da gaggawa suka shiga bashi kulawa, yayinda aka bar su Musaddiq kai-kawo a waje kowa na addu'a a zuciyarsa. Sun kwashe tsahon lokaci kafin doctor ya fito. Bayanin da yay musu na cewa yaji ciwo sosai a kan nasa kuma bai farfaɗo ba har lokacin ya sake tada hankalin Musaddiq. Duk yanda yaso daurewa ya kasa. Dan harga ALLAH duk abinda Abban ke musu shi da ƴan uwansa bai taɓa jin ya tsani ƙanin mahaifiyar tasu ba. Saboda yana kallon fuskarta ne akan ta kawun nasu. Tun a daren yay kiran ƴan Gwarzo da Gwaggo Gudidi. Sai dai suma bai faɗa musu gaskiyar al'amarin ba dai. Hankalinsu ya tashi, washe gari kuwa tunda sassafe sai ga Gwaggo Gudidi. Wajen tara sai ga ƴan Gwarzo suma har da su Kawu Musa saboda kara. Dan su ta ɓangaren mahaifinsu suke bata ɓangaren Abban ba. Har Azhar Abba bai farfaɗo ba, asibiti ya ciga da dangi amma babu Mom. Sai su Bibaa da Baby. Abbas ma sai kusan azhar ya iso hankali tashe. Dan bai san mike faruwa ba sai da yaje gida yake ji a anguwa. Koda ya shiga cikin gidansu ya samu Mom nata darzar kuka gefenta mahaifiyarta Inna zaune jigum ta zuba tagumi da hannu biyu. Bai iya cewa da su komai ba dan yanayinsu da sambatun da Mom keyi ya tabbatar masa da abinda mutanen suka faɗa. Kiran Musaddiq yay a waya ya sanar masa asibitin da suke. Sai ko gashi ya iso. Hankalinsa ya sake tashi da jin Abba fa yaƙi farfaɗowa, harma likitocin na maganar ya tafi doguwar suma........✍️ _Wayyo Abbanmu kada ka tafi ka bar Halime😌😌_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏_ .........“Wlhy sai na kashe yarinyar nan da hannuna na jefar da gawarta inda ko angulu basa gittawa!!”. Yanda take maganar cikin fushi ga idanunta cike da hawaye jikinta na rawa ya tsorata Arwa. Riƙota tayi tana mai danne abinda ke cin tata zuciyar itama kamar yanda ta saba. A take zuciyarta ta hasko mata nasararta, dan tabbas wannan dama ce da zatai amfani da Azizat game da yarinyar nan taci nasarar samun cikar burinta itq. Cikin dakewa tamkar bata ga komai daya faru ba ta ce, “Aunty Azizat cool down mana. Wai mike faruwa? Mi akai miki? ki faɗa min ko ina da taimakon da zan miki. Shin waccan ƴar shishigin ce Malikah ko?”. Ɗari bisa ɗari Azizat ta yarda da Arwa. Dan ƴar team ɗinta ce, duk da iyayensu basa jituwa hakan bai hanasu aminci ba su. Ta kuma sha bata shawara akan Malikah taci nasara. Hawayen da suka gama wanke mata fuska ta share. A matuƙar zafafe ta furta, “Malikah ɗin banza. Ita har ta isa nai mata kuka Arwa, kada kema ki ɓata min dan ALLAH. Idan baki san abinda zaki faɗa ba fita ki bani waje...” “Kiyi hakuri to ba yanda kike nufi bane. Faɗa min mike faruwa?”. Shiru ta sake yi kamar ba zata ce komai ba har sai da Arwa ta sake zingurarta. “Arwa ki ƙyaleni dan ALLAH. Har zaki ce bakiga sanda waccan karuwar sabuwar mai aikin yarinyar da Aunty Mama ta kawo mana gida yau ma ta sake faɗawa a jikin Yaya Awwab ba?”. “What?!! Jikin Yaya Awwab fa? Bayan na waccan ranar da tayi kuma yau ma ta sake again? Eh lallai kam na yarda dake wlhy yarinyar nan karuwa ce Aunty Azizat. Kuma tabbas ba haka nan ta shigo gidan nan ba akwai asiri tare da ita, sannan akwai manufa, ni dama wlhy tun kallo ɗaya da nai mata nake ji a raina batai kama da masu aiki ba. Idan ba hakaba taya za'ace ranar tayi yau ma ta sake aikatawa kuma? Koda yake babu mamaki ai ba'ai mata gargaɗi ba ne a waccan ranar. Ke kuma da alama ta danne miki baki tunda na ga ko Mammah baki sanar mawa ba”. Sosai kalaman Arwa suke tasiri a zuciyar Azizat. Zuciyarta ta shiga tabbatar mata lallai akwai asiri a al'amarin kam. In ba hakaba yama za'ai hakan ta kasance. Kuma wai abin ƙarin mamakin ma yanda abin ya faru kowa ya nuna tamkar bai gani ba. Koda yake komai ya faru ne tamkar ƙiftawar idanu dan bai wuce cikin minti biyu ba, tun daga faɗawar tata har tashinta daga jikin nasa. Sannan a yanda shegiyar tayi sai ka ɗauka accident ne bada sani ta aikata ba... Ganin yanda ta sake tafiya duniyar tunani Arwa ta sake taɓota. Cigaba tayi da fanfata har sai da ta hau ta zauna. Sannan ta tsara mata abinda ya kamata suyi domin ɗaukar mataki. Sosai kuwa Azizat ta yarda, dan a take ta jawo kan wayar telephone tayi kiran sashen masu aiki. Ana ɗagawa ta miƙama Arwa kan wayar, itako dama ALLAH ya bata iya canja murya, a take ta koma muryar Aunty Mama. Tana gama faɗar abinda suka tsara ɗin ta yanke kiran, kallon juna sukai ita da Azizat ɗin suka saki murmushi. Sai kuma suka tafa alamar nasara ta samu.... ✨💞✨💞✨ Wajen la'asar ana ƙoƙarin maida Abba wani ɗakin sai ga Mom da Inna da ƙawarta wadda ta kawo mata Halime. Kallon inda take kowa baiyi ba, dan zuwa yanzu kowa a wajen yasan sanadin al'amarin sakamakon Baby data zazzage musu zance. Har an canjama Abba kaya za'a wuce da shi sai ga Nurse a guje yana ƙwala kiran doctor. Kusan dukansu suka afka ɗakin dan azatonsu Abba ya cika, koda Nurse ɗin da doctor suka shigo sun cika ɗakin tare da rufuwa a kansa. Da ƙyar doctor ya samu duk suka fice su kuma suka fara aikinsu. Kowa ka gani yana cikin farin ciki da farfaɗowar Abba. Sai kuma fatan ALLAH ya bashi lafiya. Bayan kamar mintuna Talatin kuwa Doctor ya sake musu albishir ɗin farfaɗowar Abban. Sai dai ba'a bar kowa ya shiga wajensa ba sai a washe gari. Alhamdullah jikin nasa da sauƙi sosai, sai dai kansa yasha bandage abin tausayi. Babu wanda yace ma Mom komai duk wani rawar kan dafo abinci da take tana kawowa safe da rana da dare. Shima Abban kuma baya ko kallon inda take duk maganar da zata masa bai amsawa. Dama jiyyarsa Kawu Isuhu ne keyi. Ƙani yake a gurinsa dan ɗan wan mahaifinsu ne. Kwanansa uku aka sallamesa. Ya samu rakkiyar dangi data abokai irin su Alhaji Sadisu. Tun isowarsu ya fahimci Halime bata gidan, bai dai ce komai ba har sai da yay wanka ya samu nutsuwa. Falo ya dawo ya kwanta saboda masu shigowa dubasa ƴan nan cikin anguwa. Su Gwaggo Gudidi na zagaye da shi anan ɗin ma. Basu sami lafawar mutane ba sai kusan goma na dare, alokacin ne fa Gwaggo Gudidi ta fara tsiya saboda tayin shiga ɗaki ya kwanta da Mom ta masa. Gwaggo tace babu inda zaije a ƙarasa hakalashi, Musaddiq ya kaisa ɗakinsa yaje can ya kwana. Sosai Mom ta shiga shock, dan batai zaton sun san ainahin abinda ya farun ba, amma sai ta dake ta shiga bama Gwaggo haƙuri da shi kansa Abban wai sharrin shaiɗan ne bazata sake ba. Harda ƴar ƙwallarta kamar yanda Ummanta tace tayi. Fata-fata Gwaggo ta mata a gaban su Musaddiq, sai da ƙyar aka samu tayi haƙuri. Ita dai Mom yau babu bakin magana kuma sai haɗiyar zuciya..... 💥❤️💥❤️💥 Bayan sallar isha'i dole na haƙura da batun bin su Bahijja Islamiyya domin amsa kiran Alajah. Muna gaba da shiga sashen Mama Balki ta dakatar dani, cikin nuna kulawa da kwantar da murya ta furta, “Ɗiyata dan ALLAH yau ki danne zuciyarki. Kar ki kula Azizat komi zata miki. Mutanen nan da kike gani sunada rigima sosai, idan aka zo fagen faɗa da bare kansu haɗe yake wajen ɗaukar mataki. Ki ringa haƙuri mu neman arziƙi ya kawo mu. Fatanmu mu samu abin rufama kammu asiri shike nan kawai. Kina ƴar ƙaramarki da ke kar ki biyema wanda suka fi ƙarfin ki kinji”. Duk da zantukanta sun tunzurani sai ban nuna ba a zahiri na haɗiye, sai ma jinjina mata kaina da nayi, a hankali na amsa da “In sha ALLAHU Mama komai ya wuce. Ranar ɗin ma akasi kawai aka samu”. Cikin nuna gamsuwa da sake lallashina ta sanya min albarka. Daga haka taja hannuna muka ƙarasa shiga ciki. Duk da nasan banjin shakka ko tsoron kowa a raina sai da nayi addu'a sannan na shiga. Da hayaniyar surutunsu yau muka fara cin karo. Kasancewar ta inda muka shigo duk suke a ƙatoton dining yasa sukai min wani farrr cikin ido. A hankali naja numfashi na fesar ina mai karanto (Hasbinallahu wa-ni'imal wakil) a cikin zuciyata. Da farko ba kowa ya maido hankalinsa kammu ba, dan koda mukai gaisuwa bai fi mutane uku suka amsa ba. Ciki harda Alajah data furta, “A'a Mama Balki ba nace sai mun kammala cin abinci ba?”. Cike da mamaki Mama Balki ta ce, “Eh da haka kikace Hajiya, amma kuma yanzu da kika kira sai kikace kada mu wuce mintuna talatin shiyyasa kuka taho”. Sosai mamaki ya bayyana a fuskar Aunty Mama. Harma ta gagara daurewa ta ce, “Ni ɗin?”. Da girmamawa Mama Balki ta amsa mata da, “Eh” tana murmushi. Kai Alajah ɗin ta jinjina, sai kuma ta furta, “Kuɗan jirani na kammala dinner to please, dan ina son mu ƙarƙare komai a yau tasan aikinta ni zuwa gobe zan koma”. Kallon juna Azizat da Arwa suka yi, sai kuma suka saki murmushi suna kashema juna ido ɗaya. “Aunty Mama! Wai waye ake nufin za'a ɗauka aiki anan gidan? Badai wannan mai suffar mamiyo na ruwan ba?”. Kafin ni ko Mama Balki wani yace wani abu Azizat ta faɗa a zafafe har tana wancakalar da spoon ɗin dake hannunta. Kusan atare duk wanda ke'a wajen ya ɗago, a dai-dai nan mayen sirrintaccen ƙamshin turaren Maash kuma ya mamaye wajen. Dan haka hankalinsu ya rabu biyu. Yaran suka shiga gaishesa. Ban ji ya amsa musu ba, dan ban ɗago ba kaina a ƙasa ina ƙoƙarin danne abinda ke taso min akan wannan shegiyar Azizat ɗin. Zungurin da Mama Balki tai min ya sakani kawo nunfashi, na ɗan kalleta. Nuni tai min na gaishesa. Ban musa mata ba a taƙaice na furta, “Barka da dare” a hankali. Kamar yanda bai amsawa ƙannen nasa ba nima bai amsa min ba. Dan haka na ɗago kaina cikin takaici, dai-dai yana kaiwa zaune a kujerar da ƙyaƙyƙyawar budurwar da zasu iya sa'anni da Azizat tai saurin gyara masa. Kasancewar kujerar itace ta kamar a ƙarshen table ɗin mu kuma muna daga farko tsaye yasa mukai facing juna. Wani kallon tsana naga Azizat na jefama budurwar, sai kuma ta cije lips ɗinta alamar dai akwai abin faɗa a bakinta amma babu dama. Sai daga baya na fahimci agolar gidan dake kusa da itace ta hanata magana ta hanyar riƙe mata hannu. Alajah ce ta katse yanayin da faɗin, “Azizat wai ina ruwanki da yarinyar nan ne? A kanki zata zauna idan ma anan ɗin zata zauna?”. Baki sosai ta tura gaba. Cikin nuna jin haushi sosai ta ce, “Ni dai bana sonta Aunty Mama. Ba kuma nason ganinta dan na tsaneta. Idan kuma har akace a gidan nan zata zauna wataran sai na kasheta. Ta kwana da sanin marin da taimin wlhy sai ta biya bashinsa da fansar ranta....” “K! K! Azizat ban gane ba. Mari? Wa ɗin aka mara? Waye kuma yay marin?”. Hajiyar nan da muka samu a falo randa muka zo wadda kuma Bahijja ta tabbatar min itace mahaifiyar Azizat ɗin kuma Yaya ga mahaifin Maash, sannan mai mulkin komai da kowa na gidan ta faɗa a wani irin fusace. Kallon Alajah Azizat ɗin tayi, sai kuma ta ɓata fuska tana fiki-fiki da idanu. Da alama dai Aunty Mama ce tai mata gargaɗi. Tsawa mahaifiyar tata ta daka mata. Ba ita ba hatta ni sai da naji hanjin cikina sun wakita. A take kuwa Azizat ta fara rattafo bayanin komai daya faru a ranar da safen dalla-dalla harma da ƙarin gishiri da magi..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚_ ........Wani irin huci Mahahaifiyar tata take tana kallon Alajah. Idanu Alajah ta rumtse tana ɗan dafe kanta. Sai kuma ta ɗago idanunta akanta. “Please Aunty Nafee relax. Bafa yanda kike tunanin al'amarin b....” “Kamar ya ba yanda nake tunani bane Mashi'a! Ƴar aiki ta mari mun yarinya a gabanki amma ki gagara ɗaukar mataki sai ma ki hanata sanar min. Wai ke bazaki taɓa canjawa bane ba. Shike nan nagode, ai kin tabbatar min bake kika haifi Azizat ba. Da Imran ko Sahla ta mara ai da kin ɗauki mataki ko. K!! Kuma zaki ci ubanki. Zan sauke miki rawar kan da kika shigo da shi. Ai dama tun randa tazo dake na fahimci idanunki a buɗe suke irin na marasa mutunci.” Idanu na na runtse sosai dan har cikin ƙwaƙwalwar kaina nake jin hargagin nata. Na tabbatar da ace ta kusa da inda take nake tsaye babu abinda zai hanata kai min duka. Abinda ya matuƙar sake bani mamaki shine babu wanda ya iya tanka mata a wajen hatta shi Alhaji El-Mu'azz ɗin. Balle kuma ƙanin nasa ma. Matansu kuwa kawunansu duk a ƙasa kai kace mala'ika ke kansu. Karo na farko na kai idamuna a kansa. Fruit salad ɗinsa yake sha hankali kwance. Sai ka rantse ma baya wajen dan ko sau ɗaya bai kalli kowa ba duk wannan hargagin da akeyi. Hasali ma a dai-dai sanda Hajiya Mammar ko nace Aunty Nafee kamar yanda Alajah ta ambaci sunanta ke faɗin, “Na soke maganar aikinta na farko. Daga gobe zata fara aiki a sashena. Ke kuma Azizat tashi ki rama marinki”. A kusan tare duk wanda ke a wajen ya ɗago yana kallon ta. Yayinda Azizat ta miƙe zaram cike da farin ciki ta nufo inda nake alamar dai zata zo rama marin kenan. Idanu duk suka zuba min musamman Aalaja da ranta yake a ɓace. Amma shi sai ya ma miƙe abinsa tamkar baiji mima ake faɗar ba. Cike da takun nan nasa mai cike da ƙasaita ya ratsa ta bayansu yazo ta gabana ya gitta kamar ɗazun zai wuce. Wani kalar kallo dana kasa fassarawa ya jefa min.... “Muhammad!”. Alhaji El-Mu'azz ya faɗa dai-dai zai raɓani ya wuce gaba ɗaya.. Amamakina sai naga ya tsaya cak. Tamkar bazai juyo ba sai kuma ya koma da baya tamkar wanda akama dole a hankali ya amsa da, “Yess Paah”. Idanu mahaifin nasa ya ɗan tsira masa. Sai kuma yay ɗan murmushi cike da kulawa ya ce, “Ba zaka ci abincin ba kuma? Naga fruit salad ɗin ma kaɗan kasha fa”. A daƙile, sai dai cikin sanyin Muryar nan tasa ya ce, “I'm okay Paah. Kaina namun ciwo ina son na ɗan kwanta”. Sosai fuskarsa ta nuna damuwa. Hakama sauran duk sai kowa ya maida hankalinsa a kansa musamman Azizat da budurwar nan data gyara masa wajen zama sanda yazo. Dan har wata ƴar zabura sukayi a kusan tare. Cikin jimantawa da kulawa sosai suka shiga masa addu'a. Kansa kawai ya jinjina musu yay wucewarsa ya fice. Sosai zuciyata ke ƙara jinjina rashin mutuncin mutumin nan. Ashe bamu ƴan waje kawai ba hatta family ɗinsa basu tsira da wannan baƙin halin nashi ba. Lallai sai a jinjina masa. Ganin yanda duk suka maida hankalinsu a kansa nasa ƙafa na taɗe Azizat dake ta leƙensa kamar mai son binsa. Razananniyar ƙarar data fasa ya saka kowa zabura sukayo kanta. Da wannan damar Mama Balki taja hannuna da sauri hankalinta tashe muka sulale muka fice. Ashe ita taga abinda nayi, suko sai suke tambayar miya faru? Yaya akai ta faɗi. Oho mudai tuni mun ware bamu san yanda suka ƙare ba kuma.... 🤣🤣ALLAH ya shiryeki Sam-G. ❤️★❤️★❤️ “Gwaggo maganar auren nan dama nake son mu tattauna kafin ki wuce. Dan ina son ayi komai a gaggauce cikin watan nan”. Cike da ɗunbin farin ciki Gwaggo Gudidi ke kallon Abba dake maganar, ta saki dariya tare da yin guɗa. “Kai kai da ace na iya ghuɗa babu abinda zai hanani tsallarata sama har sai duk ƴan anguwa sunji Imamu. Ka daɗe baka sakani a farin ciki irin yau ba. ALLAH yay maka albarka. Amma ince dai ƴar mutunci ka sama mana ba irin wannan matar taka ba dan bana son a sake yin jifar gaffiyar ɓaidu”. Kai Abba ya girgiza yana ɗan murmushi, “A'a Gwaggo in sha ALLAHU sam ba halinsu ɗaya ba. Yarinyar da suka doka ɗin ce dama.” “Kai kai to Masha ALLAH. Aiko kayi ƙyan kai, dan hakan da zakayi shine babban murtani da zaka maidawa matarka tasan ka haifu cikin uwa da uba. Amma kuma ai naji yaran na faɗin ta gudu tun a ranar da abin ya faru? Ko kasan inda take ne?”. “A'a Gwaggo ban sani ba. Amma dai ta sanar min da garinsu. Nasan kuma insha ALLAHU can ɗin zata nufa tunda Alhaji Sadisu ya bincika daga inda Jalilahn ta ɗakkota ance bata koma can ba. Dan haka nake son muyi azamar bin bayanta tun kafin abin yayi nisa”. “Eh to hakan ma dabara ce ai. ALLAH ya bada sa'a da nasara. Yaushe zaku je ɗin?”. “Da dai gobe idan ALLAH ya kaimu ne. Sai shi Musaddiq ya jamu dan ni bazan iya tuƙi ba. Alhaji Sadisu ko baida jimirin yin tuƙi a doguwar tafiya sam”. Ɗan jimm Gwaggo tayi alamar tunani, dan in bata manta ba Musaddiq ya sanar mata gobe ne zai je gwaji da akace za'a musu a inda aka ɗaukesa aiki. Da ɗan sauri ta girgiza kanta. “A'a inaga shi Jafaru sai ya jaku kawai dan yasan ƴan tumaki sosai tunda shima matarsa ƴar wajen garin ce. Kaga ko ai faɗuwa tazo dai-dai da zama ba sai anta faɗi tashin tambaya ba”. Cikin nuna farin ciki da gamsuwa Abba ya shiga tabbatar mata da hakan yayi, ya ɗora da godiya. A take kuma babu ɓata lokaci yay kiran Jafaru ɗin. (Jafaru shine ɗa na biyu a wajen Gwaggo Gudidi. Kusan sa'anni suke ma da Abba dan komai na rayuwarsu tare sukayi. A dalilin Mom tarayyar tasu ta samu rauni. Dan yanda take nuna bata ƙaunar ƴan uwansa su raɓesa duk wanda yazo sai ya tafi da tabon rashin mutuncinta yasa Jafaru janyewa daga jikin Abba. Saboda akwai wani zuwa da yayi Mom ta cimasa mutunci harda ƙwallarsa. Daga lokacin ya tattara Abba ya ajiye gefe sai dai su gaisa sama-sama ta waya ko idan wata sabgar ta haɗasu ta dangi ko in sun haɗu a gidan Gwaggon. Abin na damun Gwaggo amma ta gagara sasantasu, sau yanzu ga dama ta samu kuma).... ✨💫✨💫✨💫 Ko kaɗan Mama Balki batai min faɗa game da abinda naima Azizat ba. Sai ma Sosai yanda ta nuna tashin hankalinta ita da su Bahijja game da batun komawata aiki sashen Hajiya Mammah ya bani mamaki. Dan na sake fahimtar al'amarin babba ne. Duk da kuwa Bahijja ta ɗan bani labarinta a ƙaice ni banga wani abun tsoro tattare da ita ba, idan masifa ce na saba data Mom da ƴaƴanta ai. Sambatu suke sosai da nuna jimantawa har Mama Balki na faɗin na gudu kawai tun ma kafin komai ya faru. Zata saka mijinta ya taimaka min na fita a daren yau. Murmushi na saki a hankali duk da kuwa nima ina jin shakkun al'amarin a zuciyata. Sai dai wani sashe na ƙarfafani dan koba komai zan samo labarai. Haka kawai kuma ina son sanin gaskiyar labarin tushen komai. Atake naga fuskokin masu dariya da nuna farin ciki a kaikaice a cikinsu na sauyawa a dalilin murmushin nawa. Nima sai kawai na basar da canja yanayina. Ƙwallar ƙarya nayi ƙoƙarin tarama idanuna. Tare da nuna tashin hankali ina mai roƙon Mama Balki data taimaka min na gudu ɗin... A bazata mukaji an saki tsaƙi, kusan mu dukanmu muka kalli mai tsakin. Ba kowa bace face aunty Kubra. Yanayin shock na gani a fuskar Mama Balki, da alama dai ta fahimci tayi ɓaranɓaramar sakin zancen gaban kowa. Sai dai bata iya cewa komai ba Cike da taɓe baki Aunty Kubra ta cigaba da faɗin, “Mama ina baki shawarar ki rufama kanki asiri. Ke dai kinfi kowa sanin halin Hajiya Mammah a gidan nan. Sannan ita ɗin ba ita ta jama kanta ba. Banda kauɗi da rawar kai uwarwa ya kaita marin ƴar masu gida. Jarumta tafi wani a cikinmu da muke haƙurin shekara da shekaru da su ko mi? Kinga yanzu ai ya rage nata ta ajiye kauɗinta da iyayi gefe ta nemawa tsoffinta kuɗin cin tuwo cikin sallama. Idan ba hakaba wataran ba sashen Hajiya Mammah ba Sashen Hajiya Babba zasu kaifafa ko kuma da karnukan gidan nan wlhy zasu haɗata”. Daga haka ta miƙe tai ficewarta tana wani rausaya da girgiza jiki. Shiru kowa ya gagara cewa komai, sai shashshekar kukana kawai kake ji. Kusan mintuna biyar Mama Balki tayi ƙarfin halin bama Bahijja umarnin tafiya dani ɗaki na kwanta. Babu musu Bahijja ta miƙe ta kama hannuna. Sai naga itama A'i ta miƙe fuskarta cike da tsantsar damuwa itama ya kama ɗayan hannuna.... Duk yanda naso rintsawa barci a wannan daren kasawa nayi. Dan komai ya tsaya min arai ne. Duk yanda nake jin rashin damuwa game da yin aiki a sashen Hajiya Mammah ɗin wani sashi na zuciyata na tsoratar dani da nuna min illar hakan, dan na fahimci matar bata da mutunci sosai. Dan duk mai hankali ya auna yanda kowa ke nuna damuwarsa akan batun zai sake tabbatar da bada wasan yara bane al'amarin. Ganin yanda zancen yaƙi barin raina sai kawai na tashi na ɗauro alwala na fara nafilfili. Har asuba ban runtsa ba sai da nayi salla..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_ .......Ina idarwa na ɓingire a wajen sai barci. Ban tashi farkawa ba sai da A'i ta tasheni wai Hajiya Mammah na kira na. Yanda take maganar cikin nuna tsoro da damuwa ya sakani tsira mata ido. Sai dai bata bani damar mata tambaya ba ta juya sukuku ta fice tana faɗin, “Kiyi sauri ki shirya muje kar mu sake wani laifin kuma. Dan ga Mama Balki can tasha maruka akan guduwar da kukayi jiya da dare duk da ƙaryar kareki da tayi kan baki da lafiya ne shiyyasa”. Sosai naji wani irin masifaffen ɓacin rai. A take ta bududdugin ta motsa (zuciya) na shiga taunar lips da ƙarfi-ƙarfi tamkar zan hudashi. Gaba ɗaya wata irin tsanar matar mai tsananin gaske ta shiga zuciyata. Yanzu dan ALLAH babbar mace kamar Mama Balki ce za'a mara wai. Kai wannan wane irin gidane haka na marasa tarbiyya da girmama mutane. Dan kawai mutum nada dukiya sai akace zai iya taka kowa a yanda yake. Kaicon wannan rayuwa mara fasali da rashin sanin daraja da kimar ɗan Adam. A gurguje nayi wanka na shirya cikin Uniform ɗin da A'i ta ajiye min. Koda na fito a falo na sameta tsaye tana jirana. Kallon juna mukayi. Ta ɗan kafeni da kallo sai dai batace komai ba tayi gaba na bita a baya... 💞👉💞👉💞 “Alhamdullah su Abba sun isa ƴan tumaki lafiya. Tafiyar da Mom bata da masaniya a kanta, dan har yanzu Abba baya shiga harkarta. Ita kuma ta tada hankalinta sunata bibiyar teachers domin sabunta ayyuka akan Abban dan ta lura komai fa na neman canjawa. Kullum cikin ƙaryar fita take duk da kuwa yana gida yana jinya. Bai taɓa hanata ba, kamar yanda Gwaggo Gudidi bata taɓa tanka musu ba. Da tambaya da kwatance suka gano gidan su Halime da ƙyar kasancewar sun sami cikakken address wajen mai kawosu aikatau daga ƙauyen. Wadda da ƙyar suka samu ƙawar Mom ta sanar musu bayan sun danƙa mata kuɗaɗe. Tako kai su amma ta roƙi Abban da kar ya sanarma Mom ita ta faɗa, duk da kuwa ita bata san manufar Abban ba. Ya sanar mata ne kawai zasu bincika idan Halime taje gida kar a samu kuskure tayi wani wajen daban. Ta gamsu ɗari bisa ɗari dan tanama Abban kallon girmamawa duk da tasan aminiyarta ta daɗe da gamawa da shi. Koda yake itama ɗin ta gama da nata mijin ai duk da basu taɓa tarayya da Mom wajen zuwa gidan teachers ba. Kowa nayin al'amarinsa ne a bayan fage.. Sun ɗauki kusan mintuna talatin a gidan mai anguwa da sukai dabarar fara zuwa kafin Baba da aka aika kira ya ƙaraso. Tun shigowarsa Abba keta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, dan ko makaho ya laluba yasan shine mahaifin Halime saboda kama da sukeyi matuƙa tamkar yayi kaki ya ajiyeta. Sake gyara nutsuwa Abba yayi, hakan har ya saka Alhaji Sadisu sakin murmushi. Bayan Baba ya gaisa da mai anguwa ya juyi gasu ba. Kafin ma ya gaishesu su sun shiga gaida shi. Dan ko babu batun abinda ya kawosu zai girmesu gaskiya. Bayan an kammala gaggaisawar mai anguwa ya nunama baba su Abba. “Malam Yusufa baƙine dama suke neman gidanka. Naso saka yaro ya rakasu sai suka buƙaci haɗuwa da kai anan shiyyasa na aika akayi kiranka”. Da ɗan nuna alamun mamaki Baba ke kallon su Abba. Ganin yanda Abba ya duƙar da kansa Alhaji Jafaru ya fara magana a nutsensa. “Ni sunana Jafaru, wannan sai ƴan uwana Alhaji Sadisu da Alhaji Imam. Baba baka Sammu ba gaskiya. Wannan ɗan uwan nawa Alhaji Imam shine mai gidan da ƴarka Halimatu take zaune acan birni.....” Sosai Baba ya waro idanu, tare da sakin salati ya ce, “Kai kai Masha ALLAH. Bawan ALLAH ashe baka rasuba Sa'adiyya duk ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tunda ta iso garin nan kwana biyar kenan kullum bata da aikin daya wuce kuka. ALLAH mun gode maka”. Murmushi Abba yayi cike da jin sanyi a ransa Halimensa ta damu da shi. Murya a sanyaye ya ce, “ALLAH kam shine abin godiya Baba. Nima kuma ina ƙara gode masa da ya zamto gida tayo ba wani wajen ba. Dan muna can hankalinmu duk a tashe da ƙyar aka samo wadda ta ɗauketa daga nan ta bamu address.” Sosai Baba ya nuna jin daɗinsa da wannan kulawa. Fuskarsa washe da murmushi shima ya ce, “Ai dama duk tsanani Sa'adiyya bazata nufi ko ina ba sai gida. Nima Nagode sosai da wannan kulawa taku, lallai na yarda da gaske yarinyata tana a hannun mutanen kirki. ALLAH ya kiyaye gaba ya ƙara lafiya”. A tare duk suka amsa da Amin. Kafin Alhaji Sadisu ya ɗora da bayani bayan sun ɗan yi jimm na wani lokaci. “Baba dan ALLAH idan bazaka damu ba muna neman wata alfarma ne”. “Ku faɗi komi kuke buƙata a gareni kai tsaye in dai baifi ƙarfina ba zan muku shi in sha ALLAHU”. Cike da jin daɗin furucin nasa Alhaji Sadisu ya cigaba da faɗin, “Muna neman alfarmar ka bamu auren Halimatu”. Ba baba kawai ba hatta da mai anguwa sai da ya waro idanu sosai cikin nuna ƴar tsorata...... 🌛🌟🌜 Kallo ɗaya nayima Mama Balki dake gurfane gaban Hajiya na ɗauke idanuna zuciyata na suya. Da ƙyar na iya control ɗin kaina nima na kai durƙushe. Latse-latsenta take a laptop tamkar batama san da zuwan namu ba. Gefenta Azizat ce kwance itama tana latsa wayar fuskarta mamaye da fara'a. Sai da ta mula dan kanta sannan ta ɗago bayan ta rufe laptop ɗin. Fuska a yatsine kamar taga kashi ta daka min tsawa. Dakewa nayi batare da nuna razana ba. Sai cemata da nayi “Ina kwana”. “Daban kwana ba ƙya ganni firiritacciya. Ke mai ido a tsakar kai kinzo cin arziƙi gidan mutane har da marin ƴar masu gida ko?”. “Ko kuma ƴar cin arziƙin itama ba”. Na faɗa ƙasa-ƙasa. “What! Mi kikace?”. Ta faɗa a matuƙar tsawace. Idanuna na ɗago na kalleta fuska a shagwaɓe. “Nifa bance komai ba Mamma. Please ki daina faɗan firgitani kike sake yi”. Ba ita ba hatta Azizat ɗin Tata sai da ta juyo tana kallona da mamaki ƙarara a fuskarta. Balle su Bahijja da suka waro idanu da wangale bakuna. Niko yi nai tamkar ban gansu ba na sake shagwaɓe fuskata da taɓeta. Sai kuma na ɗauka ruwan dake a cikin kofi a gabanta na miƙa mata. “Kisha ruwan sanyi Mamma zuciyarki zatayi sanyi. Ba'a son masu shekaru irin naku da yawan faɗa za'a iya samun matsalar hawan jini daga nan ta zama ta zuniya”. Galala ta sake yi tana kallona. Niko na tsatstsareta da idanu ina sake tura baki da marairaice face. Da wani irin masifar ƙarfi ta cije lips ɗinta tamkar zata hudasu. Sai kuma tasa hannu ta kaɓar da kofin hannun nawa. A take ruwan ya tarwatse mana a jiki har ita. Cikin masifar ƙaraji da wutar bala'i ta ce, “Balki!!!”. A razane Mama Balki ta amsa tana miƙewa daga durƙuson da tayi zaram. “Na.. na... Na'am Hajiya”. “Ɗauki yarinyar nan ku ɓace min anan kafin na haukata jikunan ku da duka ku duka. Na kuma fasa aikin nata a sashena ki kaita sashen Hajiya Babba ta gyaro shi kafin nan kafin azhar”. Wani irin waro idanu na masifa Mama Balki tayi, cike da tashin hankali da suɓutar baki ta furta, “Sashen Hajiya Babba kuma Hajiya?”. “Ko bazaki kaitan ba ne?!!”. Cikin rawar jiki mama Balki ta shiga girgiza kanta da faɗin, “To to to Hajiya ALLAH ya huci zuciyarki, za..zan kaita mana.” mama Balki ta faɗa tana kama hannuna jikinta na rawa sosai. Da ƙyar na iya danne dariyar dake cina har muka baro wajen, dan tana ambaton Hajiya babban naji tamkar na dirga tsalle dan daɗi. Muna kammala hawa upstairs ɗin a stairs ɗin ƙarshe na ɗan kallo ƙasan, sai da na haɗiye dariyar dake cina sannan na kwaɓe fuska kamar zan fasa kuka. “Mammah dan ALLAH ni dai ina neman alfarma. In dai akwai matsala da zarar kunji na banka ihu a kawo min ɗauki koda sassaƙa-sassaƙan garadan nan na bakin ƙofar gida ne a turamin idan ma ku bazaku iya ba”. A matuƙar fusace ta watso min muguwar harara da gwala-gwalan idanunta “Sai dai a turo miki Ubanki. Ƴar iskar yarinya sheɗaniya. Da alama kema dai mahaukaciyar ce get out of my side kafin na canja miki kamanni”. Baki na tura mata cikin sake narke fuska da yamutseta na ce, “Ai dai ubana yana aljanna in sha ALLAHU badai shi b....” Kafin ma na kai ƙarshe Mama Balki ta fisga hannuna jikinta na rawa. Duk yanda naso ta sakan taƙi yin hakan har sai da muka ɓacema ganinsu. Kamar zata saki kuka ta ce, “Kandala baki da hankali ko? Yanzu wannan hukuncin da suka zartar a kanki bai isheki ishara ba ki koya kimtsa bakinki? Dan ALLAH ƴar nan kada ki sakamu a masifa mutanen gidan nan sun wuce fiye da yanda kike tsammani a fitina wlhy. Kiyi fatan Alhaji ƙarami bai bar gidan nan ba yazo ya fiddaki a wajen nan da wuri, zanje na samesa yanzun nan”. Da sauri na ce, “A'a mama dan ALLAH kada ki kirashi. Miye dan tace nazo nayi aikin anan?”. “Yarinyar nan baki da hankali, wautarki tayi yawa wlhy. Kandala wannan sashen da kike gani baida maraba da rami mai kwazazzabo da in ka faɗa a cikinsa sai abinda ALLAH yayi. Gara kiyi aiki a sashen Hajiya Mammah ɗin dan ita masifa ce kawai da takura, amma nan ranki ma zaki iya rasawa. Ni dai ki jirani anan zan je na duba Alhaji ƙaramin ALLAH yasa bai fita ba”. Ƙasa kawai nayi da kaina batare da nace mata komai ba.. Ita ma sai bata sake magana ba tai gaba.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_ ___________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ____________ ......Riƙota nayi ina girgiza kaina. Ta tsaya tana kallona. Idanuna cike da ƙwalla na ce, “Kiyi haƙuri Mama ki buɗe min zan gwada na gani. Koba komai itama mutum ce kamar mu. Muma kuma bamu san ya rayuwa zatai damu ba anan gaba. Dan ALLAH ki buɗe min kawai ALLAH yana tare da ni”. Sosai alamar sanyayar jiki ya bayyana a gareta na jin kalamai na. Dan haka ta nufi ƙofar dake a falon batare da ta sake cemin komai ba. Bayanta nabi ina mai jin tausayinta. Babbar mace kamila yanayin rayuwa yasa tana gurfana a gaban wadda bata wuce sa'arta ba. Lips ɗina na ciza. Kafin na furzar da iska nabi bayanta nima. Sosai tsaruwar falon farko na sashen yay matuƙar ɗaukar hankalina. Fes yake yana ɗaukar ido saboda kayan alatun da yasha. Da alama ana gyarashi kullum. Kamar zanyi magana sai kuma nayi shiru dan ganin yanda Mama Balki ke ɗari-ɗarin buɗe ƙofa ta biyu. Sai da ta runtse ido da karanto addu'a sannan ta murɗa handle ɗin. Da sauri tayo baya tamkar mai shirin zurawa a guje. Kallonta na tsaya yi kawai cike da nazari, sai kuma na sauke numfashi. “Uhhh mama, inaga kije kawai daga nan babu damuwa zan ƙarasa ni kaɗai.” Waro idanu Mama tayi, sai kuma ta marairaice fuska idanunta na cika da ƙwalla. Ƴar nan dan ALLAH kiyi addu'a kinji, ko ki zauna a wannan falon sai zuwa anjima ta tashi ki gudo, Kinga shike nan an rabu lafiya”. Murmushi mai kama da yaƙe kawai na mata ina jinjina kaina alamar to zanyi. Numfashi ta sauke mai nauyi, sai kuma ta haɗiyi yawu jiki a sanyaye ta juya ta fita tana waigena. Ni dai kallonta kawai nake har sai da ta maida ƙofar falon ta rufe a hankali. Sai kuma ta sake buɗewa. “Karki sake ko kulle kowacce ƙofa dan ALLAH Kandala. Ki barsu a buɗe yanda zaki samu damar gudowa koda an sami akasi”. Kaina na jinjina mata nan ma ina murmushi. Ta sake ɗan jan ƙofar batare data rufe duka ba ta barta. Shiru nayi kawai a wajen tsaye har zuwa wani lokaci. Ni kaina a tsoracen nake. Amma inata ƙoƙarin dakewa kun dai san ɗan jarida da jarumtar wahala. Shiru sashen yake babu alamar motsin mai rai, sai ɗan yanayin kamar bashi-bashi dake bugowa daga ƙofar da Mama ta buɗe. Ƙofar na tsurama idanu na wani lokaci, kafin nayi ƙundun balar nufarta cikin sanɗa da ambaton sunan UBANGIJI...... 📯📯📯📯 Farin cikin da Musaddiq yake a wannan rana bazai taɓa musaltuwa ba a zahiri. Sai dai ya barma UBANGIJI komai. Tsaff ya fito cikin shirinsa na shadda ruwan ƙasa mai haske harda hula. Sai ƙamshin turarensa yake mai sanyin daɗi. Hannunsa riƙe da takardunsa yake ƙoƙarin kulle ƙofar. Juyowa yay da sauri jin kamar mutum ata bayansa yana kallonsa. Ilai kuwa ido huɗu sukai da Umma mahaifiyar Mom da alama isowarta gidan kenan. Kauda tsarguwar kallon ƙurillar da take binsa da shi yayi, tare da sakin nutsatstsen murmushinsa ya ƙaraso inda take. Cike da girmamawa ya ce, “Sannu da zuwa Umma. Ina kwana? Anzo lafiya?”. Cikin ɗan daburcewa da dawowa a hayyaci ta shiga amsawa bakinta a washe. Dan harga ALLAH yaron ya gama firgita mata zuciya da guntun lissafin ta. Wani kalar mahaukacin sirrintaccen ƙyawu fa taga yayi mata da ƙiba harda haske. Ga arziƙi muraran ya nuna a jikinsa kai kace ma shine ɗan masu gidan ba ɗan riƙo ba. Dan ko mahaukaci ya kallesa ya kalla Abbas yasan akwai banbanci da tazara mai yawa ta cigaban rayuwa.... “Ki shiga Umma ai su Mom ɗin suna nan ciki”. Ya faɗa cikin katse mata tunanin data lula. Firgigit kuwa ta dawo a hayyacinta. Sai kuma ta washe baki cikin in ina ta ce, “T... t.. to ɗan nan nagode kaji, ALLAH ya muku albarka ya ƙara arziƙi. Bari na shiga ɗin dai to”. Ta ƙare maganar tana tafiya da waiwayensa a lokaci guda har taci tuntuɓe tana neman faɗuwa. Ta dai samu ta dafe gini idonta a kansa har lokacin ga baki a washe kamar sakara. Shi dai Musaddiq cike da al'ajabinta yay ficewarsa. Kaɗan-kaɗan sai ya kalla kansa ko zaiga abinda takema kallon ƙurulla a jikin nashi. Amma sai baiga komai ba. Haka dai ya tare napep ya shiga komai na masa kai-kawo a rai da zuciya. Koda ya iso gate ɗin companyn sai da ya nuna ɗan katin da ogansa ya bashi sannan aka barshi ya shiga. Sosai yake jinjina ƙudira da rahama ta UBANGIJI. Dan gaskiya wannan Company ya matuƙar tafiya da imaninsa. Gini ne iya gini da baka iya ƙuresa da idanu. Ga ma'aikata nata faman kai-kawo da securitys. Ga kayan aikin tako ina da zai tabbatar maka da komai fa da gaske ake babu wasa. Da taimakon wani security akai masa rakiya office ɗin Manager..... 💦✨💦✨💦 Ji Abba yay tamkar ya tashi ya buga ihu da tsalle dan farin cikin hukuncin Baba. Domin ya tabbatar musu in dai Halime na son Abban zai bashi ita. Hakan yasa aka aika aka kira Halime. Koda tazo taci karo da su Abba sai da ta nuna ƙololuwar mamakinta har ta gagara yin magana sai da Babanta yay mata magana ma ta iya gaishesu muryarta na rawa. Zata ɗora da zance Abba daya san mi zata iya faɗa yay saurin katseta. Dan baya fatan ta tona asirin komai musamman akan abinda ya faru a randa ta gudo ɗin, saboda ya fahimci bata sanarma su Baban komai ba. Shirun kuwa tayi kamar ta fahimci abinda yake buƙata, daga haka mai anguwa ya sanar mata abinda ya kawo su Abba. Sake diriricewa kuwa tayi tana faman zare idanu. Da ƙyar Abba ya iya danne dariyarsa. Alhaji Jafaru da Alhaji Sadisu kuwa sai da suka dara kaɗan. Mai anguwa ma dai yayi kaɗan kafin ya ɗora da tambayarta ko tana son Abba ɗin.... Ai baima rufe baki ba suka tsinceta can ta zura a guje cikin gidan mai anguwar. Basu Abba ba hatta da Babanta yanzu kam sai da ya dara. Fuskarsa da sauran dariyar ya dubi Abba. “Imamu kaga fa shirmen mutuniyar taka. Anya zaka iya da ita? Dan Sa'adiyya akwai wauta a tattare da ita ta ƴaƴan fari. Ni kaina wani abun idan tayi a wasu lokutan ƙuleni sukeyi. Sai dai kuma akwai himma ga biyayya. Duk abinda kaso daga Sa'adiyya zaka samesa. Gwargwado na bata ilimin addini, na zamanin ma ta fara wasu dalilai yasa dole aka yankesa....” Fuskar Abba da murmushi kansa a ƙasa ya ce, “Karka damu Baba, ni ɗin ita nake so ba shirmen ba. Sannan nagartattun halayen nata da tarbiyyar ta suka jani gareta. Dan wauta wataran zata daina in sha ALLAHU yanzu ma akwai ƙuruciya ne”. “To Alhamdullah Imamu, naji daɗin jin wannan batu daga gareka. Dan haka ina sake maka albishir da baka auren Sa'adiyya. Kuma bana son kubar garin nan sai an ɗaura, in har da sadaki a tare da kai da anyi sallar zuhur yanzu kawai sai ayi”. Wannan furuci shi ya sake rikita Abba. Dan baba bai kammala rufe baki ba ko ya zaro kuɗi masu yawa a aljihunsa ya dire gaban Baban. Dariya su Alhaji Sadisu suka sanya masa. Cike da tsokana Jafaru ya ce, “Ai ka bari dai ni na biya maka Alhaji zumuɗinka”. Dariya su mai anguwa suka saka da Baba. Yayinda kunya ta kama Abba ya kaima Alhaji Jafaru harara yana ɗauke kansa gefe. Da ga haka suka miƙe domin haramar masallaci.... Al'amarin tamkar almara bayan idar da sallar azhar aka dakatar da mutane. Mata dake cikin gida sai shelanta ɗaura auran Halimatussa'asuyya Yousufa da angonta Imam Gwarzo suka jiyo. Bakin Abba kamar zai taɓa kunne. Sai faman gaisawa yake da mutane cike da farin ciki. Kafin kace minene har labari ya fara yawo a gari. Gidan mai anguwa aka koma da su Abba. Sai da sukaci abinci sukai nak sannan Baba yay musu jagora zuwa gidansa kamar yanda ƙannensa biyu da akai komai da su suka bada shawara.... 💢💦💢💦💢 A hankali na tura ƙofar idanuna a rufe na shiga cikin sanɗa. Yayinda zuciyata ke wani irin harmutsawa saboda ƙarni da tsamin dake tashi sosai a falon. Abin mamaki da al'ajabi shima ƙaton falone da aka zubama komai na more rayuwa da ƙawa. Sai dai mafi yawan abinda ke a cikin nasa an gama faffasashi. Dan hatta da television dake a jikin bango an mata rugu-rugu. Ta saman farin Mable's ɗin kuwa mai tsananin sheƙi tako ina fitsari ne har da su katsi, abinci ruwa da wasu nau'in kayan ciye-ciye kamar su fruit duk sun ruɓe. Hatta a saman carpet ɗin ma da ya gama fita a hayyacinsa al'amarin ba'a magana. Kai labuloli kansu wasu an fincikosu wasu kuma an goge datti da su. Sai ɗigo-ɗigon jini a wajaje daban-daban shima har a jikin bango. Bamma san sanda zuciyata ta karye ba sai ɗumin saukar hawaye da naji a saman kumatu na. Sosai nayi kuka a wajen kafin na cigaba da ƙarema falon kallon. Akwai dining table ta can gefe da aka ƙawata a cikin glass da ya raba tsakaninsa da falon. Sai dai shima an gama hargitsashi wasu kujerun ma a karye suke. Table ɗin ma kansa tuni an maida sama a ƙasa. Ta ɓangaren damata akwai ƙofofi guda huɗu, sai tsakkiyarsu ƙafar bene da akai ma wani kalar style mai ɗaukar hankali da birgewa. Numfashi na sauke a hankali nan ma tare da yunƙurawa na nufi ƙofifin, har na kusa sai kuma na tsaya cak saboda shawarar da zuciyata ta bani akan fara gyara wannan falon koda ma zan shiga cikin tunda ban san mizan tarar ba ko tarbar da zan samu daga mai sashen......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ___________ .......Komawa nayi baya ta hanayar dining ɗin nan ina mai addu'ar samun kayan shara. Ƙofar kitchen ɗin akwai key a jiki, dan haka na murɗa a hankali, sai da na leƙa cikinsa sannan na shiga gaba ɗayana ina sauke numfashi. Babu komai a cikinsa shima. Sai dai shi ɗin fes yake babu wani datti sai ƙura ta rashin gyarawa. Sosai kitchen cabinet ɗin da aka ƙawatashi da shi yay matuƙar ƙyau kamar ka zauna kayita kallo. Ganin ina neman shagala a kallon cabinet na zabura neman kayan shara. Cikin Sa'a kuwa sai gasu na samo a store dake cikin kitchen ɗin duk masu aiki da wuta. Cike da ɗoki da zumuɗi na kwaso duk abinda zan buƙata. Tun daga store ɗin da shima babu tarkace sosai na fara gyarawa har zuwa kitchen, sannan na fito dining ɗin. A nan kam na jigatu kafin na dawo falon mai gayya da aiki. Tun ina yin aikin da marmari har na fara jigata. Amma haka na dinga dauriya. Sau biyu ina jima hannuna ciwo. Na maida abinda zai iya maiduwa. Wanda suka tashi a aiki na tattarasu na fitar can barandar da aka ƙawata ta waje bayan na zuge labule na ganta. Ashe wajen glass ne amma an rufesa da wani irin abu mai taushi nasan duk dan kar taji ciwo ne. Kaf labulolin data jeho na tattaresu dan duk abincine da fitsari a jikinsu. Hakama carpet ɗin na cireshi shima. Hatta wanda sukai min nauyi da yawa haka na dinga turasu, sai santsin Mable's ɗin ya dinga taimaka min har na kaisu balcony ɗin duka. Ni kaina yanda falon ya dawo a hayyacinsa sai da nayi murmushi. Na baɗe ko ina da freshiners masu ƙamshin daɗi dana gani a wata drawer. Ac na kunna kaɗan dan falon ya sake samun nutsuwa. Ganin lokacin salla na neman ƙuremin na dawo falon farko nayi salla ganin akwai toilet a cikinsa shima. Duk da matuƙar gajiyar da nayi da buƙatar hutu da nake da shi haka na sake miƙewa na koma. Yanzu kam ina ƙara ƙarfin addu'a a bakina na tunkari ƙofofin ɗakunan nan biyu. Ta farko na murɗa amma sai na jita a kulle. Na koma kan ta biyu sai naji ta buɗe ita. Da sauri nayi baya saboda wani irin wari dake fitowa a cikinsa mai ban tashin hankali. Take zuciyata da cikina suka shiga yamutsawa, dole na fito a guje zuwa bayin dake a falon farko. Amai sosai na shiga yi kamar zan amayar da kayan cikina. Tun ina amaryar da ruwa dana sha kawai har na koma yunƙuri kawai babu komai, da ƙyar na samu nutsuwa na wanke bakina na fito ina hakki. Har na yanke shawarar fita na haƙura zuciyata ta zabureni akan muhimmancin aikin lada. Hawaye naji sun cika min ido dan zuciyata na ayyana min idan Umminmu ce a wannan halin kenan zanji ƙyanƙyamin kasa tsaftace mata wajen kwananta? Da sauri na shiga girgiza kaina tamkar mai magana da mutum. Bamma san lokacin dana zabura na koma ba. Sai dai ina zuwa ƙofar na zame vail ɗin kaina na nannaɗe fuskata gaba ɗaya har zuwa hancina sosai. Amma duk da haka ina ɗan jin warin kaɗan-kaɗan. Haka dai na dake ina karanto addu'a a bakina ga hawaye na ɓulɓulo min cikin idanu saboda tausayi da tashin hankali. Yanzu nan ɗan adam mai rai, mai gata ne a irin wannan ɗakin? Bily ban san yaya zan musalta miki ba. Amma duk yanda kike hasashe abin ya wuce nan, ƙazantace sosai a ɗakin mara daɗin misali. Amma haka na duƙa na fara tattarewa ina kuka. Dole naje na kwaso labulolin dana cire a falo da burin wankesu na dinga naɗe ƙazantar a ciki. Sai da na tattare komai tare da fito da katifar ɗakin da ƙyar dan itace kawai anan sai labuloli da wadrobe ta jikin bango. Ina jin mutanen gidan sun fara hayaniyar wari-wari, dan da gayya na kaita falon can na farko da zaka iya hanga ta dawn stairs. Juyawa nayi na koma ciki ina ayyana kowa yau dan ubansa sai ya shaƙa shima. Shine punishment ɗin ku. Sam ban kawo cewa tana a cikin ɗakin ba, dan ganin ban ganta ba a farko kuma har nayi kusan kashi ɗaya bisa ukun gyarashi yasa nai zaton tana ɗayan ɗakin ne ko can sama hawan ƙarshe. Toilet na nufa, cike da tsantseni na buɗesa. Bamma san na daka uban tsalle ba nayo baya cikin matuƙar razani jikina na karkarwa. Gurnani da nishin dake fitowa a toilet ɗin yasa hankalina ya sake tashi, a take hoton abinda na gani ya shiga dawo min da kansa. Mutum zaune sarƙa a ƙafa da hannayenta an saƙalo jikin fanfo. Gaba ɗaya hannunta da ƙafafun sunyi jina-jina alamar son ƙwace kanta ya kaita ga jin ciwon. Kanta a duƙe yake shiyyasa banga fuskarta ba, sai gashinta dake a wani irin cirkuɗe danƙare a kanta mahaukaciya dai cikakkiya. Tausayi da tashin hankali ya sakani durƙushewa a wajen ina kuka. Nafi minti uku sannan na miƙe na sake komawa toilet ɗin. Sosai idanuna sun gama rufewa, nama bar tunanin zata iya cutar dani kamar yanda Bahijja ta faɗa tana duka. A gabanta na zube zuciyata a dake na shiga kwance sarƙar ƙafafunta da suka kumbura suntum sukayi jina-jina. Har na kammala kwancewa bata ɗago ba, sai nishin nan dai mai ban tausayi da tashin hankali kamar wadda numfashi ke shirin barin gangar jikinta. Da ƙyar na iya kammala kwance sarƙar ƙafafun, na shiga shafa ƙafar hawaye na cigaba da zararo min. Wata irin ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske ta sauke. Sai kuma ta ɗago a hankali. Wani irin bugawa da sauri-sauri zuciyata ta shiga yi saboda ganin yanda fuskarta tayi kaca-kaca da tabbunan raunuka, sai sabbin da har sun fara bushewa suma kusan uku. Gaba ɗaya baka iya shaida kamaninta saboda dauɗa data gama mamayeta. Dan kayan jikinta ma duk a yayyage suke fata-fata. Rawa jikina ya cigaba dayi, hawaye masu zafi na sake gudu a cikin idanuna. Bamma san lokacin da na kai hannuna saman fuskar tata ba ina shafawa. “Kiyi haƙuri Ummi, dan ALLAH kiyi haƙuri, ALLAH ya gaggauta saka miki, ALLAH ya baki lafiy.....” kuka ya sarƙeni na gagara ƙarasawa. Ƙara ta saki a hankali sai kuma ta shiga fisgar hannunta a galabaice. Zaram na miƙe cikin karkarwar jiki. “I'm sorry Ummu, I'm so sorry bari na cire miki. In sha ALLAHU koda fansar raina ne zan bada wajen taimakonki. Sai na ƙwato miki hakkinki, sai na san gaskiyar mafarin lalurarki. In har da saka hannun wani sai na tarwatsa masa tanadi”. Sambatu nake da kuka ina kwance mata hannayen suma. Suma dai sun kumbura sosai duk taji ciwo. Ga tabbuna nan da sayin sarƙar alamar ba yau ne aka fara ɗaureta hakan ba. Ina gama kwancewa ta saki ƙara mai ban tausayi da alama hannun ya mata nauyi, durƙushewa nayi a gabanta nai ƙoƙarin kamo hannuwan nata ra riƙe. Sosai kuka mai ƙarfi ya sake kuɓuce min harda shashsheka. Ɗago idanuna nayi ina kallonta, sai naga itama ni ta tsurama ido tana kallo kamar mai lafiya. Murmushi na saki mai haɗe da kuka. Sai kuma na buɗe baki da nufin bata haƙuri a bazata naji an damƙi wuyana. Sosai na waro ido waje dan azaba. Sai kuma na saki wahalalliyar ƙara jikina na rawa dan shaƙa ce bata wasa ba. Tamkar wulgawar walƙiya aka jehoni cikin ɗakin. Razanannen ihu na ƙwala na azabar buguwa da kaina yayi da bayana. Kafin na yunƙura na tashi domin ceton kaina har ta iso gareni, sake kai hannu tayi a wuyana ta shaƙoni...... 💦💫💦💫💦 Sosai Musaddiq ke a cikin farin cikin da baki bazai iya musaltashi ba duk da bai samu tabbacin samuwar aikin ba. Sai dai yanda interview ta kasance ya matuƙar bashi ƙwarin gwiwa. Ga karramashi da akayi sosai a wajen har abin yaso bashi mamaki. Sai dai ganin harda wani da ya samu da nasa takardun shima ya cirema kansa shakku. An sallamesu akan kowa zaiga massage daga nan zuwa safiya. Cike da ɗoki kuwa ya dawo gida, ga wani irin farin ciki daya gama mamaye masa rai, sai dai wani fanni na zuciyarsa na matuƙar jin kewar Kandalarsa, da yanzu ita zai fara sanarma albishir ɗin komai da bata labari. Amma ba komai ko yanzu ma bata ɓaci ba. Waya ya jawo ya shiga laluben layin mijin nata. Sai dai har ta tsinke ba'a ɗaga ba. Sake kira yay har sau uku nan ma shiru. Hankalinsa ya nema fara tashi sai ga shi an kirasa back da number ɗin. Cike da zumuɗi ya ɗaga. Suka gaida da mutunta juna. Mijin ya ɗora da bashi haƙuri akan ba'a kusa yake ba sanda yay kiran. Cikin mutuntawa Musaddiq yace babu komai. Sun ɗan yi shiru kowa da tunanin da yake yi, sai kuma suka yunƙuro kusan atare zasuyi magana. Dariya abin ya basu, dan haka Musaddiq ya dara, da ga can kuma mijin na Samraah ya murmusa har Musaddiq ɗin najin sautin murmushin nasa. “Afuwan ina jinka”. Da sauri Musaddiq ya ce, “Ni zan nema afuwa ai ina jinka”. “Okay, dama zance ma bana gida ne, amma in sha ALLAHU dana koma zan haɗa ku. Sannan in babu damuwa tsoffin numbers nata ka ɗan turamin dan a mata welcome back ɗin su”. Cikin jin daɗi Musaddiq yay masa godiya. Daga haka sukayi sallama. Dole ya haƙura yay kiran Hafizzullah dake makaranta yay masa albishir ɗin shi, murna suka dingayi, daga ƙarshe suka koma hirar Samraah ɗin dan da gaske kowa a cikinsu yayi kewarta sosai........✍️ _Humm, ni dai inada tambaya anan😂. Yayanmu Maash ne ko kuwa🥱🥱Bara dai bayi hiru to._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_ .......Zuwa yanzu labari ya gama shiga kunnen mutane da dama game da wannan aure na baƙo daga Kano da Halime. Ciki kuwa harda innarta da sauran matan gidansu kasancewar family house ne part-part. Dan har ƙannen mahaifinta da matansu duk a gidan suke suma. Koda su Abba suke isowa sun samu gida a matuƙar hargitse innarta nata tsiya da bori ana rirriƙeta. Abin nata zabban takaici. Dan suna shigowa ta dire tsalle ta shaƙe wuyan rigar Baba tana surutai da girgiza, ga zagi manya-manya. Da ƙyar ƙannensa da matansu suka ɓanbareta. ALLAH sarki Baba duk sai ya daburce. Fahimtar yanayin nasa yasa su Abba dakewa su. Tare da nuna masa cewar hakan ba komai bane daga halin banza irin na wasu mata kamar su Inna. Abba kuma ya sake ƙarfafawa Baba gwiwa akan in sha ALLAHU zai riƙe Halime da daraja ta yanda sai Inna ta yi kuka da idanunta. Baba yaji sanyi a ransa, hakan yasa yayma Abba alƙawarin nan da sati guda Halime zata tare kawai. Yanzu ɗin ma dan yana son sanarma dangin su Innar (dangin mahaifiyarta kenan) shiyyasa bazai basu ita ba. Sun gamsu da hakan, saboda suma suna buƙatar komawa su ɗan kimtsa. Gidan mai-anguwa suka koma aka kira musu Halime. Sai dai da ƙyar ta fito fiskarta a ƙunshe cikin Hijjab. Duk yanda Abba yaso ya ganta taƙi yarda ta buɗe fuskar. Aiko Alhaji Jafaru da Alhaji Sadisu nata ƙumshe dariya. Abba ko nata balla musu harara. Da ga ƙarshe ya korasu waje. Suna fita yay kan Halime yana lallashi, kamar almara yana kai hannu kan hijjab ɗin nata da nufin ɗagewa ta zungura da gudu cikin gida ta barsa da hannu a sage. Duk da yanda yaso dannewa ya gagara, tuni ya shiga ƙyalƙyala dariya yana mai jinjina wautar ta. Lallai akwai aiki gabansa tuƙuru kenan.... ★•★•★•★ Duk yanda mama Balki taso samun nutsuwa ta gagara hakan. Sai faman kaiwa da komawa take yi hankalinta gaba ɗaya na akan Samraah. Tun tana irga sakanni har ta koma mintuna, amamakinta sai ga awa ta shuɗe. Awa ɗaya, biyu, uku itama ta shuɗe. Tsaye take akan kula da girkin rana dasu Kubrah keyi amma kaɗan-kaɗan sai ta fito daga kitchen ɗin, tun ma basu fahimtaba suma har suka fara tsarguwa. Cikin gulma suka dinga nunama junansu ita da ido da baki. Sam Mama Balki bata san ma sunayi ba, saboda hankalinta a rabe yake. Ƴar hayaniyar su Arwa dake falo da zagin da taji sunayi ya sata fitowa zumut daga kitchen ɗin. Hannu taga duk sun saka suna famar toshe hancina. Yayinda tuni Muhsin ya fara kakarin amai. Dai-dai nan itama mahaukacin warin ya daki hancinta, da sauri takai hannu ta toshe hanci, sai kuma ga jama'ar gidan suma sun fara fitowa daga sassansu kowa na tambayar warin minene haka?. Rasa mai bama wani amsa akai sai nuni da sama saitin sashen Hajiya Babba kawai akeyi. A dai-dai nan katifar da Samraah ta jingina jikin ƙarfen da aka ƙawata adon wajen da shi da bata zauna dai-dai ba ta sulmiyo downstairs ɗin gaba ɗaya. Ihu yaran suka buga a tare suna tarwatsewa. Sai kuma yunƙurin amai dan gaba ɗaya falon ya ƙarasa gumamewa. Cike da fusata Hajiya Mammah ta koma upstairs ɗin tana ƙwala kiran Samraah da “K!! K!! K!!” dan ko sunanta bata sani na. Ihun nata yaja hankalin sauran iyayen dama su Azizat ɗin suma suka bita. Hakama su Falilah ba'a barsu a baya ba. Mama Balki ce ƙarshen bin bayansu. Isowarsu ƙofar dai-dai da ƙwalla ƙarar azaba da Samraah tayi, a take kowa ya tsaya cak. Ƙarar da Samraah ta sake fasawa kuma duk sai suka ja da baya. Dan basa buƙatar ƙarin bayani ta ƙwaɓe ne tsakaninta da mai sashen. A matuƙar tashin hankali Mama Balki ta juya da gudu ta sauka downstairs ɗin jikinta na ɓari. Bama tasan sanda takai kanta sashen Maash ba. Kawai tsintar kanta tayi a gabansa durƙushe cikin kuka da roƙo ta kama ƙafafunsa.... “Alhaji ƙarami dan ALLAH ka taimake mu. Kandala. Kandala ce gata can a sashen Hajiya Babba...” numfashinta ya nema ɗaukewa gaba ɗaya saboda yanda take a kiɗime. Shiko Maash da tun shigowar tata a guje da tsawar da Hayatu yay mata na son ta dakata ya tsaya cak daga duba abinda Hayatun ke nuna masa a tab sai dai bai ɗago ba sai da ta ambaci Hajiya Babba dan shi bai ma san waye wani Kandala ba. Idan ka cire ita a gidan da mijinta sai wasu tsiraru a masu aikin da suka daɗe a tare da su kawai zai iya cewa ya sani har ma ya shaidasu koda a wajen gidan ya gansu. Amma daga basu ɗin ba babu wanda zai iya shaidawa a cikinsu. Cak Hayatu shima ya dakata da ga yunƙurin maganar da yake, dan sai a lokacin yama fahimci wacece ɗin. Shine yay ƙarfin halin faɗin, “Mama waye Kandala? Mi kuma ya faru da Hajiya Babba?”. So take tai magana amma ta kasa, sai nuna ƙofa kawai take ga hawaye na kwaranya mata. Ƙarasowa Hayatun yay da sauri inda take. Ya kama hannunta ya miƙar daga gaban Maash da take durƙushe. “Kinga relax. Calm down kiyi magana yanda za'a fahimta. Rufe idonki ki shaƙi iska ki fesar Mama”. Kai mama Balki ta shiga jinjinawa tana haɗiyar kukan da sauri-sauri. Yanda duk Hayatun yace tayi tayi, ya miƙa mata ruwan gabansa ta sha maƙwarwa biyu sannan ta sauke nannauyan numfashi. Shi dai Maash kallonsu kawai yake amma ya gagara cewa komai. Cikin ƴar nutsuwar data samu ta sake faɗin, “Kan...kandala ce sabuwar mai aikin da Aunty Mama ta kawo. Ta..ta tafi sashen Hajiya Babba gata can tana ihu da alama....” sai kuma ta kasa ƙarasawa. Sosai Hayatu ya waro idanu a firgice. Yayinda Maash yayi wani masifar runtse nashi da ƙarfi, sai kuma ya ajiye tab ɗin hannun nasa ya miƙe. Baima tsaya ƙarasa jin zancen ba ya nufi ƙofar da kan sadashi da sashen mahaifiyar tasa kai tsaye daga sashensa. Sai dai kuma a kulle take. Jikinsa ya shiga shafawa neman key, amma da alama baya tare da shi, har ya kalla Hayatu zai yi magana sai kuma ya fasa. Komawa yay da baya ya fito, da sauri Hayatu da Mama Balki suka take masa baya. Ta babban falon gidan da ya gama gumamewa da warin katifar nan ya ratsa, da bibbiyu ya dinga haɗa stairs ɗin tsabar tashin hankalin da yake a ciki. Dan duk duniya bai haɗa al'amarin mahaifiyar tasa da komai ba. Cikin rufewar ido da ɗimuwa yake sa hannu ya ture duk wanda ya tare masa gaba. A haka har ya shige ciki gaba ɗaya dan su mutanen gidan suna a falon farko ne cirko-cirko sun gagara shiga ciki dan tsoro. Sai hayaniya da suka cika wajen da shi. Yana shiga securitys ɗin da sukai kira na cikin gidan na isowa. Suma takema Maash ɗin da Hayatu baya sukayi... Sosai nake kakarin mutuwa. Idanuna kam sun gama firfitowa. A wannan gaɓar na sallama da rayuwa. Ta ALLAH kawai nake jira ta kasance. Wata irin bugawa da tama kaina a bango ya sani fasa wahalalliyar ƙara da ko sautin kirki babu yanzu saboda galabaita dana gama yi. Daga haka ban sake sanin mi kuma duniya ke'a ciki ba... Shigowar Maash dai-dai da wancakalo Samraah da Hajiya Babba tayi kai kace irin an yadda magen nan. Baya yay taga-taga zai faɗi, sai da Hayatu ya riƙesa. Da sauri ya kai dubansa kan abinda ta wurgo ɗin, a kuma dai-dai nan itama ta sake wawuro abin morpping irin na wutar nan da Samraah ta ajiye tare da sauran kayan shara. Ji kake bummm!! Akan goshinsa. Kamar ƙyaftawar ido ta sake rarumo wani abun, jifan kan mai uwa da wabi ta shiga musu kamar yanda take yi a duk sanda take a irin wannan yanayin. Dole su Hayatu suka shiga fita a guje. Yayinda Maash ya kasa yin hakan shi. Dan shi damuwarsa ba ciwon data jimasan bane. Kar ita ta jima kanta ciwon. Ƙoƙarin nufarta yayi da son kwashe sauran kayan sharan. Amma ina jifa kawai take kai masa dasu tako ina... Cikin wani irin karyewar murya ya shiga ƙoƙarin kai hannu gareta yana faɗin, “Please Ummie na kar kiji ciwo, dan ALLAH ki ajiye zai ji miki ciwo. Hannunki Ummie hannunki.” Ina ita bama tasan yanayi ba. Jifan kawai take kai masa har sai da taga kayan sun ƙare, sai kuma ta koma kai masa duka da hannu. Cikin sa'a shima ta shaƙuro wuyarsa. Dai-dai nan masu kula da lafiyarta da akai kira a waya suka iso. Da ƙyar aka ɓanɓare Maash a hannunta bayan sun mata allura mai ƙarfin gaske. Zama yay ƙasa batare da jin ƙyanƙyamin komai ba ya riƙeta a jikinsa ya zubama fiskarta idanunsa da suka rikiɗe gaba ɗaya. Yanda Adams apple ɗin sa ke kai da kawo zai tabbatar maka da kukan zuci yake yi. Yafi mintuna goma zaune a haka shiru, duk maganar da su Hajiya Mammah suke masa bai ko motsa ba. Sai da Paah ya shigo ya kai duƙe kusa da shi, hannu ya fara kaiwa ya riƙo na Ummie dake kwance ka shirɓan allamar barcin nata yay nisa matuƙa, idanu ya zubama hannun cike da tausayawa shima nasa na cika da hawaye, dan har yanzu har gobe yana matuƙar ƙaunar matar tasa rufin asirinsa kuma. Hawayensa ya share kafin ya sauke ajiyar zuciya tare da kiran sunan Maash da bai ko motsa ba. “Muhammad”. A hankali ya ɗago idanunsa ya zubama Paah ɗin nasa batare da ya iya cewa komai ba, sai kuma ya ɗauke ya maida kan (Ummi) Hajiya ƙarama da ke tare da sauran masu kula da lafiyarta dan itama likita ce. Sake ɗaukewa yay ya maida kan Samraah dake kwance gefe a sume babu wanda yabi takanta. Yanda ya tsurama wajen ido na tsahon mintina kusan biyu ya saka kowa maida kanhalinsa ga kallon abinda yake kallon. Shima kansa Paah sai a lokacin ya lura da Samraah ɗin.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_ .......Cikin tashin hankali ya miƙe yana ambaton, “Subahanallahi. Ita kuma wannan mike faruwa haka?”. Idanun Muneef cike da hawaye ya ce, “Paah ai itace ta fara shigowa yima Hajiya Babba shara shine sai....” ya gagara ƙarasawa saboda hararar da Hajiya Mammah ta wurga masa. Duk da kowa ya fahimci Hajiya Mammah ɗin ce ta kwaɓi yaron babu wanda ya iya tankawa. Shi dama Maash kansa a duƙe yake kawai yana duban mahaifiyarsa kamar bai san mi sukeyi ba. Yanda bai kallesu ba bai tanka musu ba ya miƙe ɗauke da Ummiensa. Fita yay daga ɗakin gaba ɗaya da ita. Dole suka shiga darewa suna bashi hanya. Can falon da Samraah ta gyara yaje ya kwantar da ita. Anan ɗin ma sai dai ya tsira mata ido na kusan minti ɗaya kafin ya juya ya koma ɗakin. Yanzu kam ya samu Azizat na ƙoƙarin sheƙa ma Samraah ruwa a jiki cike da mugunta da wulaƙanci, wani irin kallo daya wurga mata ya sakata daburcewa taja da baya tana faman sinne kai. Yanzun ma baice da kowa komai ba ya ƙara da inda Samraah ɗin ke kwance. Sunkuyawa yay gaba ɗayanta ya ɗauka. Dukansu sai da kowa ta waro idanu waje musamman Malika da Azizat da Arwa, yayinda ran Hajiya Mammah ya gama ɓaci amma bata ce komai ba. Kamar ɗazun darewa sukai suka bashi hanya, cike da takun nan nasa na bajinta da ƙarfin jini ya fice ɗauke da Sam-G dake a sume batama san inda kanta yake ba. Kallon kallo aka fara yi, kafin Paah da shi dama komai bai canja ba daga garesa ba sai ma daɗin kulawar da Maash ɗin ya bada akan yarinyar yaji ya bi bayansa. Dan shi dai abinda kawai ya sama ransa dole Maash ya taimaka ma yarinyar, amma yana mamakin ma yaya akai tazo har nan ɗin tunda yasan babu mai shiga sashen Hajiya Mammah ɗin kai tsaye haka sai masu kulawa da ita, tunda kuma waccan ta gudu kusan wata guda kenan ba'a sake kawo wata ba. Ganin Paah ya fita duk suka zabura suma suka bi bayansa. A falon ƙasa suka samu Maash na ƙoƙarin sauke Samraah saman kujerar falon tare da kaiwa zaune shima ya kwantar da kanta a jikinsa. Dai-dai nan Hayatu ya iso gabansa da first eld box. A gabansa ya dire, jikinsa har rawa yake wajen fara fiddo abinda za'a fara buƙata. Maash ɗin ya miƙawa auduga, da farko zubama audigar idanu kawai yayi kamar bazai amsa ba. Sai kuma miya gani oho masa ya kai hannu ya amsa. Jinin goshinta da har lokacin ke fita ya fara ƙoƙarin gogewa, ganin kamar kaɗar bata masa yanda yake so sai kawai ya jawo handkerchief dake jikinsa fari tass ya shiga kwashe jinin da duk ya gama ɓata mata fuska. Sai da ya goge shi tass sannan ya saka ƙaramin bandage dan ciwon ba wani ƙato bane can sosai amma ba laifi da ɗan girmansa. Ganin ya kammala komai Hayatu ya miƙo masa goran ruwa. Karɓa yay ya zuba kaɗan a cikin hannunsa ya shafa mata a fuskar zuwa wuyanta. Numfashi mai nauyi sosai ta kawo, sai kuma ta zabura cikin yanayin firgita ta ƙanƙamesa jikinta na rawa. A hankali ya lumshe idanunsa batare daya ko motsa daga yanda yake ba.. kusan mintuna biyu suna a haka kowa ya zuba musu ido kowai, yayinda zukatan wasu suka gama hasala, wasu ko na tausaya mata... Shigar ƙamshin turarensa a cikin hancina ya sakani tsayawa cak, wani irin bugawa ƙirjina yayi, ga zuciyata na tafiya da sauri-sauri a cikin ƙirjina, komai daya faru ya shiga dawo min daki-daki. Fara sassauta riƙon da naima koma wanene nayi, sai kuma na sakesa gaba ɗaya na yunƙura zan tashi, sarawar da kaina yayi ya sani kai hannu na dafesa tare da faɗin, “Wash ALLAH na” na koma na kwanta a inda naken. A bazata naji saukar tattausan hannu mai zafi sosai a saman nawa hannun, janye nawan akayi a hankali, hakan ya sani sake buɗe nauyayyun idanuna. Harga ALLAH sai da zuciyata ta harba da ƙarfi Bily saboda saukarsu a cikin na wanda banyi zaton gani ba. Duk kuma yanda naso janyewa hakan ya gagara, kallonsa nake a tsakkiyar ido kamar yanda nima yake kallona. Ga hannunsa riƙe da nawa shi bai sakar min ba, bai kuma ajiye ba.... “Are you okay?!”. Ya faɗa cikin yanayin motsa lips batare da fitar sautin murya ba, gaba ɗaya naji wata irin kasala ta saukar min, sanyi ya shiga ratsani a cikin ƙashi da ɓargon jikina. A maimakon bashi amsa sai kawai na lumshe nawa idanun a hankali nima, wasu hawaye ne da suka jima maƙale a cikin idanun nawa suka sami damar silalowa batare da nasan dalilin hakan ba... “Hayat muje hospital”. Furicin sa cikin sauƙaƙa harshe ya sani buɗesu da sauri. Kaina na girgiza masa da sauri ina ɓata fuska da tura baki, sai kuma na yunƙura zan tashi a jikin nasa ina faɗin, “Ni dai bance ina son zuwa asibiti ba ai”. Bai tanka min ba, sai maidani da yay a yanda nake ya sake kwantarwa a jikin nasa. Jinai kamar na fasa kuka, amma dole na haƙura dan nasan koma sake yunƙurin tashi bazan iya ba. Saboda wani irin sarawa kaina keyi da juya min. Azizat ce ta fara jan sirrin tsaki ranta a ɓace tabar wajen duk da bajin abinda suke faɗa sukai ba, sai Maleeka da hawaye suka gama wankema fuska dan tsabar takaici. Dan lokaci ɗaya taji tsanar yarinyar ta gama baibaye rayuwarta. Wata mace kwance a jikin Awwab ɗinta ba ita ba... Dawowar Hayatu ya katsema kowa zancen zucinsa. Cike da girmamawa ya sanar masa ga Doctor nan a hanyar zuwa. Kamar ko yaushe bai amsa ba. Sai Hajiya Mammah ce cikin ɗan faɗa-faɗa ta furta, “Yanzu ga Hajiya ƙarama a gida matsayin doctor sai an kira wani likita dubata kuma dan ɗigimi?”. Hayatu rasa abinda zaice mata yay, sai kallon ogan nasa da ya ɗan yi. Da gaske bashi da alamar bama Hajiya Mammah ɗin amsa, dan kansa ma na a ƙasa ne yana faman latsa waya. Sai da Hajiya Ƙarama ta furta, “Ciwon nata ma kamar bamai tsanani bane, magani kawai zata sha in sha ALLAH jikin zai mata sauƙi.” ta ƙare maganar da ƙarasowa ta duba magungunan first eld box dake gefensa. Duk maganin daya kamata nasha ta ware, sannan ta nunama Mama Balki duk yanda zan sha su. Tana kammalawa Hajiya Mammah tace su kamani su tafi dani can sashen masu aiki. Batama rufe baki ba na yunƙura na tashi daga jikinsa hannuna dafe da kaina. Mama Balki da A'i ne suka kamani. Muna ƙoƙarin barin wajen na ɗan ɗago na kallesa, idanu muka haɗa, sai kawai na tura masa baki. Dan luuu yay da idanunsa kamar zai lumshe sai kuma ya ɗauke kansa gaba ɗaya... ❤️★❤️★❤️ Kwanaki huɗu kenan da ɗaura auren Abba da Halime. Har zuwa yanzu kuma bai sanarma Mom ba. Dan bama shiga sabgarta yake ba har yanzu. Itace dai take son su shirya saboda ko abincin gidan baya ci. Ga abubuwa teacher ya bata amma ta rasa yanda zatai da su. Yau ne ma da saurayin Baby ya sake zuwa Abban ya ɗan sake a gidan har suka ga haƙoransa a waje. Kai tsaye kuma batare da kwana-kwana ba ya bashi damar turo magabatansa har hakan yaso bama Mom ɗin mamaki. Amma dai batace komai ba sai da ta kira Ummanta take sanar mata sai tace mata aikin malamin ne ya fara cinsa. Tunda dama yace zai musu wani a bayan fage bayan na abincin da aka basu a saka masa. Wannan ne ya sanyaya zuciyar Mom ta samu nutsuwar cigaba da warisarta akan kuɗin da saurayin Baby ɗin ya danƙara musu yau ma. Kwana ɗaya da zuwan saurayin Baby kwana biyar da ɗaura auren Abba ya fara gyaran gidansa. A haukar Mom dama kowa dake gidan shine Abba ya ƙirƙiri gyaran ne domin auren Baby ɗin. Shiko baicewa kowa komai ba. Garama kwana biyu da fara aikin ya zauna da Musaddiq ya buƙaci ya bashi aron kuɗi. Babu musu kuwa Musaddiq ɗin ya bashi kuɗin, jin daɗin hakan ne ya saka Abba kwancemasa abinda ke faruwa game da auren nasa. Duk da zuciyar Musaddiq ta girgiza sai da ya saki murmushin da har ya so bama Abba mamaki. “ALLAH ya sanya alkairi Abba. Amma baka ganin akwai damuwa a haɗa Mom da Auntyn a gida ɗaya kuwa?”. Murmushi shima Abba yayi a karo na farko, sai kuma ya dafa kafaɗar Musaddiq ɗin. “Gaskiya ka faɗa Musaddiq, sai dai hakan da zanyi zai fi bani kwanciyar hankali ni kuma. Dan Maman nan taku zata iya aikata komai saboda bata ƙaunar kishiya. Amma kaga idan suna a tare waje guda koyaya zamu dinga sani wani motsinta ai ko”. “Hakane kuma Abba. ALLAH ya sanya alkairi to. Ya kuma kauda fitina”. “Amin ya rabbi Musaddiq. ALLAH yay maka albarka. Ku ƙara haƙuri dani kunji”. Murmushi Musaddiq yay kawai amma baice komai ba. An kammala gyaran gida tsaff a cikin kwanaki uku, duk wanda ya kalla fa sai ya yaba. Yayinda kan Mom ya sake girma ta fara hurama ƴan anguwa kai. Daɗin wannan gyara ya sata sake sauke kai ƙasa ta sake bama Abba haƙuri. Shi kuma bai ja ba yace mata komai ya wuce. Cikin farin ciki ta rungumesa ana sakar masa kisses. Shi dai komai baice mata ba, sai ma zame jikinsa yay cikin dabara. Bata damu ba ta gyara zama tana tsara masa yanda zasu gyara gidan. Dan ita a haukarta sashen da Abba ya gyara ɗin nasu Bibaa ne zasu koma. Saboda ta daɗe dama tana masa nacin ayi hakan ba'ayi ɗin ba, yanzu kuma a tunaninta yayi gyaran ne dan su shirya.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_ .......Wani ɗan iskan Murmushi Abban ya sake mata da cewa to kawai. Hakan ya sakata sake shiga cikin farin ciki da tabbatar da lallai aikinsu ya ci Abban. Washe gari kuwa sai ga kaya ana kawowa danƙara-danƙara. Sosai farin cikin Mom ya kasa ɓoyuwa a wannan yini, dan har sai da ta kira Ummanta ta sanar mata. Da yamma kuwa masu aikin na gab da kammalawa sai gata ta isa gidan. Har sashen suka shiga ita da Mom ɗin, sunata faman santin kayan da yaba aikin malamin. Tun a ranar Mom ta fara haɗa ƴan kayanta, dan a bata haukar itace zata koma can abarwa yaran inda take. Da Abba ya dawo gida da yamma ya sami tarba ta mutunci daga Mom ɗin, hatta da abincinsa ranar da kanta ma tayisa bata saka sabuwar mai aikin ta ba. Shi dai komai baice mata ba, duk abinda tace shi yake yi, a can ƙasan ransa kuwa dariya take bashi... ★★★.... Bayan wucewar su Samraah ya jima zaune a wajen batare daya tankama duk surutun su Hajiya Mammah dake a falon ba. Sai da Paah ya kira sunansa sannan ya ɗago ya ɗan kallesa sai kuma ya sake maida kan nasa ya duƙar ba tare data amsa masa ba shima. Shiru falon yayi dan kowa zuwa yanzu ya fahimci ransa a ɓace yake har shi Paah ɗin. Ilai kuwa basu gama zancen zucin nasu ba ya sake ɗagowa yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya tamkar mai lissafa yawansu. Da sauri yaran suka shiga rige-rigen barin wajen, hakama Hayatu saurin fita yayi hankalinsa a tashe, dan dama duk a ɗari-ɗari yake da yanayin ogan nasa. Suna gama fita Maash daya tsare iyayen nasa da kallo cikin daƙilallen yanayin nan nasa dake sake fiddo tsantsar ɓacin ransa ya furta, “Paah sayin mi na gani a hannu da ƙafar Ummie? Ina masu kula da ita da har yarinyar nan ta shiga inda take?”. Kai Paah ya shiga girgizawa, kafin cikin nuna damuwa shima ya furta, “Muhammad tare da kai muka bar gidan nan a shekaran jiya. Na dawo jiya da dare ka dawo yau da safe. Ban san komai ba kamar yanda kaima baka sani ba”. “Har yanzu baka shiga duba Ummie kenan?”. Ya faɗa a zafafe. Dabircewa Paah ɗin yayi, zai fara kare kansa Maash ya katsesa ta hanyar maida kallonsa ga Hajiya Mammah. Sosai ta fara mazurai. Sai dai shi ko'a kwalar rigarsa dan itama tasan baya tsoron duk wani hargaginta. Kame-kame ta fara tunma kafin yace da ita komai. “Ko yau da safen nan na shiga duba ta ni dai, kuma banga wani ciwo a jikinta ba Awwab. Sai dai idan munafukar yarinyar nan ce ta aikata mata wani abun. Shiyyasa sam yarinyar bata min ba tun randa Mashi'a ta kawota. Ni inama zargin wani ne ya aikota dan ta cutar damu, yarinyar fa sam bata shakkar gasawa mutane magana, kai ma shaida ne ai tunda a gabanka ance ta mari Azizat....” Idanunsa ya runtse da ƙarfi yana mai masifar cije lips ɗinsa. A take jijiyoyin kansa duk suka firfito ruɗu-ruɗu. Idanunsa suka kaɗa gwaiduwar tsakkiya ta koma siririya. A matuƙar zafafe da akan daɗe ba'a gansa a yanayin ba ya miƙe. Gashin jikinsa har mimmiƙewa suke saboda masifar dake cin zuciyar ƴan maza. Cikin daka tsawa ya ce, “Mammah!! Idan itace ta jimata ciwo shi kuma dattin dake a sashen itace ta zuba shi kenan?! Dama wannan dalilin ne yasa a duk lokacin da nake gari ake maido Ummie falon sashenta na farko!!!”. “Muhammad!!”. Paah ya kira sunansa a tsawace shima. “Kana cikin hankalinka kuwa? Addata kake ma tsawa haka kamar kana magana da wata sa'arka?!!”. “Ni kuma ina magana ne akan mahaifiyata idan ita ɗin Addarka ce Paah! Idan kuma kana son tuna min kana nan baka canja ba to nima fa akan Ummie ban canja ba. Ba kuma zan taɓa canjawar ba. Kaf ɗinsu har kai ɗin ban ma kowa tilas a zaman gidan nan ba, tunda dama ban gayyaci kowa yazo ya zauna da mu ba a cikinku kune kuka kawo kanku. Ku gaya min na taɓa tsallake dai-dai da rana guda wajen biyan masu kula da Ummie ne? Ko na taɓa tauye wani likita a cikin masu duba lafiyarta. Kai da Baba kuka tirsasani wannan kai da kawon kasuwancin badan ina so ba. Kuka kuma min alƙawarin kulawa da mahaifiyata bakin rai bakin fama har takai da an tattaro wannan gayyar an zube a gidan nan. Idan kun manta bari na tuna muku wannan gidan mallakin wadda kuke wulaƙantawar ne. Amma ku kuna zaune cikin salama da tsafta ita tana cikin ƙazanta. Saboda son zuciya kuma kuna lulluɓe duk wata hanya dazan fahimci haka. Shin dama kun tirsasani barin kulawa da itane dan ku tozarta min it...” ya kasa ƙarasawa saboda hawayen dake neman kufce masa. Ga wani irin masifar sarawa da kansa yayi cikin ƙanƙanin lokaci falon ya shiga juya masa. Hannu ya kai da ƙyar yana ƙoƙarin dafe kan amma hakan ya gagara, sai ma layi daya fara. Gaba ɗayansu sukai kansa hankali a tashe. Dai-dai ƙarasowar Paah inda yake ya tafi gaba ɗayansa zai zube ƙasa babu alamar numfashi tattare da shi. Da ƙyar Paah da Hajiya Mammah da Mummy suka iya tallabesa. Dan Maash tsayayyen mutum ne ƙaƙƙarfa a tsayensa. Ihun Azizat dake laɓe daga upstairs tana sauraren komai ya jawo hankalin su Hayatu dake main perlor. Da gudu ya shigo hankalinsa a tashe. Dama abinda yake gudu kenan tun farko. Tunda ya fahimci ran ogansa a ɓace yake yasan akwai matsala. Ba shi ba ko shi kansa ransa ya ɓaci da ganin yanda sashen Ummie ɗin yake. Yana ji a ransa kuma an jima ana wannan ha'incin sai yau ne ALLAH yayi asiri zai tonu. Dan a watan nan zai iya cewa ko sau ɗaya basu shiga ainahin sashen Ummie ba. A falon farko suke isketa a duk sanda suka dawo suka shiga dubata, kuma Hajiya Mammah ce kan tsatstsare ta babbake komai ta hanasu shiga can cikin. Ashe akwai abinda ake ɓoyewa. ★★★★... Da taimakon Mama Balki na gasa jikina da ruwa mai zafi, dan duka dai kowa yasan na sha shi. Ina fitowa daga bayin zazzaɓi mai zafi ya rufeni, sai rawar sanyi. Al'amarin kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan ciwo sosai har washe gari ina kwance, ban san abinda ke faruwa ba a gidan sai da safe bayan su Bahijja sunje sunyi aikinsu sun dawo kowa ya dawo sai naga ya dawo jiki a sanyaye. Hankali tashe na shiga tambayar Bahijja mike faruwa? Kuka ta fashe min da shi, kafin ta sanar min ai gidan ne babu lafiya ciwon Uncle Boss ya tashi. Da mamaki nake kallonta, kafin na ce, “Ciwonsa? Dama yana da wani ciwo ne?”. Kai ta shiga jinjina min tare da sake fashewa da kuka. Cikin sarƙewar harshe da jan ajiyar zuciya irin ta mai kuka ta ce, “Eh, sai dai nima tunda nazo gidan nan sau ɗaya ya taɓa tashi masa. Amma yau naga hankalin kowa a tashe yake sosai alamar abin babbane. Dan naga har Baba prof ma yazo shi da akan daɗe ba'a gansa a gidan nan ba sai idan yazo duba Hajiya Babba ne ko wani babban dalili.” Idanu kawai na zuba mata cike da nazari, kafin na ce, “Wane irin ciwo ne ke damunsa?”. “Nima ban sani ba aunty Kandala. Yakan dai yanke jiki ya faɗi ne, daga nan yakanta ciwon kai mai tsanani har sai wani bawan ALLAH babban masani yazo ya bashi magani daga ƙasar Togo. Dan ance ya taɓa bama Hajiya Babba ma magani harta samu sauƙi sai kuma abin ya sake dawowa sab......” ta kasa ƙarasawa sakamakon shigowar Mama Balki. Sai ma miƙewa da tai cikin wayancewa ta fice wai tana zuwa. Da kallo kawai na bita kamar yanda itama Mama Balkin ta bita da kallo. Sai da ta fice na sauke ajiyar zuciya mai nauyi ina maida kallona ga Mama. Itama ni take kallo yanzu. Sannu tai min da tambayata yaya jikina. A hankali na amsa mata, sai kuma na tashi zaune sosai dai-dai itama tana ƙarasowa inda nake ta ajiye kwanon hannunta. Hannun nata na kamo dan haka ta juyo tana kallona. Hawayen da nake ta riƙewa ne suka ziraro min. “Ya salam Kandala miya faru kuma? Jikin ne?” Kaina na shiga girgiza mata ina ƙoƙarin share hawayena. Itama sai kawai ta riƙoni jikinta tana lallashi. Tsawon lokaci muna a haka har sai da na daina kukan sannan ta ɗagoni, cike da kulawa ta ajiye abinci a gabana. Kaina na girgiza mata. Cikin damuwa na ce, “Mama na ƙoshi, sai dai ina son kimin wata alfarma”. “Alfatma kuma Kandala? Ta mi?”. “Ta bani tarihin wannan gida. Dan ALLAH mama ina son sani. Idan har kema kin sani badan ni ba dan rahamar da UBANGIJI yay mana.” Jimmm tai alamar tunani, kusan mintuna biyu sannan ta nisa a hankali. “Kanda kin roƙeni tare da haɗani da wanda bazan iya bijirewa ba. Sai dai abinda kike buƙatar sani jinsa a bakina zai iya zama haɗari idan har wani ya jimu. Amma ina mai baki haƙuri da in sha ALLAHU watarana zan gaya miki duk abinda na sani. Dan ina aiki a ƙarƙashin wannan ahali tun ina da ƙarancin shekaru koma nace miki iyayena ma sun hidimta musu suma. Wannan baiwar ALLAHr da kika gani a halin jarabawar rayuwa yau itace ta suturtani da ilimin addini dana zamani dan kusan tare muka tashi da ita amma ta girme min. Ta kuma yimini aure da mutumin kirkin da ƙaddara ta rabamu badan mun shirya ba. Bayan rasuwarsa ne na sake auren Malam Umaru dake koyar daku karatun addini a yanzu. Abinda kawai nake so dake ki kula, gidan nan ya wuce duk yanda kike zatonsa. Ki bi komai a hankali kinji. Muma badan bazamu iya bane muka zuba ido sai dan anfi ƙarfinmu ne kawai.” Ajiyar zuciya na sauke ina jinjina mata kaina. “Shike nan na gode Mama. Amma dan ALLAH ki amsa min tambaya ɗaya”. “Ina jinki”. “Dama haka ake ɗaureta?”. Sai da ta ɗan waiga ta kalla ƙofa kafin ta juyi tana ƙara sauke murya ƙasa cikin raɗa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ .......“Sai idan Alhaji Ƙarami baya nan suke mata hakan. Da sunga zai dawo suke kwanceta su dawo da ita falon nan na farko shiyyasa bai sani ba. Yau ɗin ma ALLAH ne yayi da rabon zai gani kuma akai sa'a sarƙar taci mata jiki dan kwana biyu kenan da ɗauretan randa yay tafiya. Da alama kuma basu san yau zai dawo gidan ba ne shammatarsu yayi. Ban kuma san yaya akai yaransu basu sanar musu da shigowarsa ba dan mafi yawan masu aikin gidan nan su sukema aiki”. Kasa daurewa nayi a zafafe na ce, “Mama dan ALLAH su waye wai?, Nasan dai harda Hajiya Mammah ɗin nan ko?”. Kai ta girgiza min tana miƙewa. “Duk yanda kike tunanin al'amarin ya wuce haka kandala. Ke dai kawai kar ki saka kanki a masifa”. Daga haka ta nufi hanyar fita abinta. Badan naso ba na yarda na haƙura. Sai dai maganganunta sun sake ruɗar dani matuƙa. Har takai damuwar dana sakama raina ta sake assasa zazzaɓina. Dan yinin ranar gaba ɗaya a kwance na yisa rijif cikin ciwo har washe gari ma. Sai a cikar kwanaki uku da faruwar al'amarin zuwa yamma ya ɗan sakeni naji dama-dama. Amma a haka Hajiya Mammah ta aiko a kirani a wannan ranar. Cikin dauriya da ƙarfin hali na isa sashen nasu. A falon ƙasa na samu su Azizat zaune kowa na harkar gabansa. Ko kallon inda suke banyi ba nai nufin wucewata. Amma sai kawai gani nayi ansha gabana. Ban yi niyar ko kallon ma wanene ba, na raɓa zan wuce aka sake shan gabana. A hakan ma ɗauke kaina nayi na koma damana nan ma aka sha gabana. Runtse idanuna nayi da ƙarfi tare da cije lips ɗina ina ƙoƙarin controlling kaina. Kafin na ɗago gaba ɗayana babu alamar wasa a tattare dani. “Oh da kika ɗago a fusace kamar wata zakanya zaki dakeni ne?”. Maleeka ta faɗa a wulaƙance cikin huci. Maimakon amsa murmushi na sakar mata mai sanyi. Sai kuma na lumshe idanun na buɗe cikin yanayin isa da ƙasaita. A hankali na motsa lips ɗina na furta, “Karki fara abinda bazaki iya ba. Dan wannan kogin ko manyan jirage da takatsantsan suke gittashi balle ke da baki wuce matsayin jirgi mai saukar angulu ba”. Daga haka na raɓata na wuce abina. Da alama hausar tawa take ƙullawa da kwancewar fassarawa. A falon sama na sami Hajiya Mammah ɗin da Alaja. Cikin girmamawa na gaishesu, Hajiya ƙarama ta tambayi yaya jikina. Na amsa mata cikin nuna jin daɗi da kulawarta. Baki Hajiya Mammah ta taɓe, kafin ta kalleni a wulaƙance ta jefo min tambaya. “K kin iya girki?”. Ɗan jimm nayi kamar mai tunani, sannan na amsa mata da, “Eh na iya Mammah.” Sai da ta ɗan ƙara taɓe bakin ta cigaba da faɗin, “Kije ki mun abu mara nauyi yanzun nan. Ba kuma nason ɓata lokaci”. Kaina na jinjina mata ina miƙewa. Dai-dai zan bar wajen muka haɗa ido. Sosai zuciyata ta harba da ganin wani irin shegen kallo da take bina da shi na ƙwaf-ƙwaf. Sai dai ban kawo komai ba nai tafiyata ina mai karanto addu'ar neman tsarin ALLAH daga sharrinta gareni. Inda nabar ƴammatan gidan anan na sake samunsu. Sai dai a yanzu hankalinsu baya kaina, amma da alama cecekuce da zagin da suke duk a kaina ne, dan haka har na wuce basu sani ba. Karo na farko na fara shiga kitchen ɗin gidan. Da mamaki su Aunty Kubrah duk suka watso min idanu, cikin dakiya na gaishesu tare da sanar musu abinda ya kawoni kitchen ɗin. Sai gani nai Aunty Falilah da Aunty Kubrah ɗin sun kalla juna suna yamutse fuska. Kafin Falilah taja tsaki ta cigaba da aikinta. Hakan da sukai min yay min ciwo, dan haka nima na watsar da su na ƙarasa shiga kitchen ɗin ina kallon tsarinsa da haɗuwarsa tamkar ba'a Nigeria ba. Dai-dai nan sai ga Mama Balki tamkar an jehota... “Kandala miya kawoki nan keda baki da lafiya?”. A shagwaɓe nace mata “Mama an sani aiki ne?”. Cikin nuna mamaki tace, “Aiki kuma? Waye ya sakaki ke da baki da isashen lafiya? Kuma banan bane sashen aikin ki”. “Nice ko ban isa ba?”. Aka amsa mata daga bayanmu. A tare duk muka juya, jikin Mama Balki na rawa ta ce, “A'a Hajiya ALLAH ya huci zuciyarki ai ban san kece ba.” Tsaki taja tana ɗauke kanta ta dawo da shi gareni. Cikin isa da bada umarni ta lissafo min duk abinda take buƙata. Kafin ta kalla Aunty Kubrah tace ta sameta da black tea bedroom ɗinta tai ficewarta. Ina kallon Aunty Kubrahn ta bita da uwar harara, ni dai sai na fara ƙoƙarin neman tukunya hannuna dafe da kaina dan bana jin daɗin jikina da har yanzu. ALLAH sarki da taimakon Mama Balki nayi girkin, yanda take ta nuna damuwarta akan sakani aikin da Hajiya Mammah ɗin tayi sai ya dinga bani mamaki. Amma sai ban ce da ita komai ba ni dai dan bama fahimtar inda ta dosa ɗin nayi ba, na dai dinga ƙarfafa kaina dan na rage mata damuwa. Mun kammala da ƙyar ina faman dafe kai sai ga Hajiya Mammah ɗin ta dawo. Tsaf take cikin sabuwar kwalliya da alama wanka ta sake. Abubuwan dana zuba abincin ta shiga buɗewa a yamutse. Sai da ta gama tsaff sannan ta kalleni. “Kije kiyi wanka ki sameni da kayan abincin bedroom ɗina”. Karan farko na ɗan kalleta. Kamar zanyi magana sai kuma na fasa ganin harta juya abinta ta fice. Side ɗin da Mama Balki take na duba. Ganin yanda fuskarta duk ta nuna damuwa ya sani sakar mata murmushin ƙarfin hali. Itama murmushin ta ɗan sakar min. Fuska na ɗan ɓata cikin marairaicewa na ce, “Amma Mama matar nan ta cika mulkin mallaka da iyayin tsiya. Yanzu kai abincin ne sai nayi wanka? ALLAH kaina ke ciwo ina son naje na kwanta”. Cikin yanayin damuwa ta amsa min da, “To yaya zamuyi Kandala. A ƙarƙashinsu muke ai. Sannu kinji ALLAH ya sawwaƙe. Kije kiyi wankan sai ki sameni na tayaki ɗauka kinji. Ni dai bana fatan a dinga yawan kuka da ke a gidan nan balle har a fara kaima Alhaji ƙarami ƙararki.” Zuwa yanzu na fahimci wa take cema Alhaji ƙarami a gidan, dan haka bance komai ba na fita hannuna dafe da kaina. Kai tsaye sashenmu na wuce, na samesu duk sun koma dan yanzun lokacin hutunsu ne. Bedroom na wuce na shiga wanka. Bayan na fito na gyara jikina da ƙyau kamar yanda na saba sannan na fito. A'i ce ke tambayata ina zanje. Kai tsaye na bata amsa aikin da zanyi na dawo. Babu wanda yace komai face a dawo lafiya da Bahijja tai min. Nayi mamakin samun Hajiya Mammah a kitchen ɗin yanzu ma, sai dai ban nuna ba face gaisheta da nayi na fara ƙoƙarin haɗa kayan abincin. Ita kaɗaice a ciki babu Mama Balki. Ina gab da kammalawa akai kiran wayarta, sam ban maida hankali a kanta ba balle nasan da wanda take wayar, sai da ta ajiye kan wayar ta kirani da “K!” sannan na juyo. Cikin yanayin kafeni da idanu tamkar zata cinyeni da su ta ce, “Ki haɗa abincin nan a wani tray ki kaima Awwab sashensa ki dawo yanzu ina jiranki.” ɗan jimm nayi kamar mai tunani, sai da ta daka min tsawa sannan na amsa mata da to. Yanda ta bada umarni haka nayi, na haɗa komai a wani tray ɗin daban sannan nace mata, “Mammah ban san sashensa ba ai”. Shiru babu amsa, na ɗago na kalleta sai naga ta zuba min idanu ne kawai kamar ɗazun. Jinai raina ya fara ɓaci da kallon ƙurillar nan nata. Amma sai na dake na sake maimaita mata tambayar tawa. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tana mai ɗauke kanta daga gareni, sai kuma ta fice tana faɗin na biyo ta.... 💢🌟💢🌟💢 💢✨💢✨💢 Cike da kulawa da tattali bayan Abba ya kammala cin abinci Mom ta kwanto jikinsa. Sai da ta saka hannunta cikin nasa murya a narke ta fara magana da kissa. “Nagode sosai Abban Abbas. Dan ALLAH ina sake roƙonka ka yafemin kuskuren da nayi, wlhy sharrin shaiɗanne amma bazan sake ba. Ni nasan kai mutumin kirki ne, dan gashi ka tabbatar min da hakan ta hanyar gyaran gidan nan da kayi. Kaga zamuyi bikin nan cikin mutunci batare da muma anga raggarmu an rainamu ba”. Shiru Abba baice mata komai ba. Sai wani murmushin da ya saki mai faɗi da akwanakin nan baya barin fuskarsa. Ganin haka itama sai ta sake lafe masa a jiki da kai hannunta saman fuskarsa tana shafawa. Komai baice mata ba, bai kuma hanata ba dan shima yana buƙatar hakan duk da gobe in sha ALLAHU amaryarsa zata iso gidansa. Amma yasan cakwakiyar da gobe zatazo da shi ba lallai ne ya kai ga hutawar ba. Dan haka ya biyema Mom ɗin. Sosai kuwa ya sami nutsuwa dan an bi da shi ta hanyoyin da shi a karan kansa sai da ya manta kan nasa.........✍️ _Hummmmm Abba adai bi a sannu ehe🥱_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ......Washe gari Mom ta tashi da shirin komawa sashen da akaima gyara. Sai dai tsabar wuce wuri batayi hakan kai tsaye ba ta shiga gayyato ƙawayenta da maƙwafta ta waya wai zata shirya walimar komawar tare da bikin baikon Baby. Aiko zuwa sha biyu sai ga gida cike da ƙawayenta da maƙwafta da take ɗan gaisawa da su. Gida fa yaci decorretion harda su dj. Ana gab da fara shagali Gwaggo Gudidi da yaranta da wasu a dangi suka fara isowa da kulolin abinci. Duk da al'amarin ya bama Mom matuƙar mamaki sai tayi ƙoƙarin ajiye komai gefe tai tunanin ko Abba ne ya sasu suzo dan su tayata murnar baikon Baby ɗin. A take kuwa ta hau musu gwalangwaso har da habaici ƙawayenta ke jefa musu. Isowar su Gwaggo Gudidi baifi da mintuna talatin ba sai ga mata har mota guda daga Gwarzo. Sai ga Musaddiq da ruwa da drinks masu yawa. Anan ne fa al'amarin ya fara girmar kan Mom, ta tare Musaddiq da tambaya. Rasa amsar da zai bata ya sashi faɗin, “Mom kuyi magana da Gwaggo kamar zaifi”. Daga haka ya juya yay ficewarsa ya barta da kallon kallo tsakaninta da ƙawayenta. Zabura tayi hankalinta a tashe zata fice a ɗakin dan dama kwalliya ake mata ƙawayen nata suka dakatar da ita. Sune suka tausheta kan ta dakata dai Abban ya shigo taji mike faruwa a bakinsa kamar zaifi. Badan taso hakan ba ta dakata sai dai ta shiga dokama Abba kira ta waya dan rabonsa da gidan tun da safe. Shiru bai ɗauka ba har kusan kira biyar, sai da wata ƙawar tata dai ta fargar da ita lokacin salla ne maybe yana massalaci sannan ta dakata. Bayan kamar mintuna biyar dan ita ko sallar ma bata nema yi ba, dama can ba damunta tai ɗin ba balle yanzu da aka zuba kwalliya. Bugu ɗaya kuwa Abba ya ɗauka, sai dai tana fara magana ya dakatar da ita da cewar gashi nan tafe gidan. Wayar ta cillar tana kaiwa zaune wutar bala'i na cin zuciyarta. Ko mintina ashirin kuwa ba'a cika ba su Abba suka iso. Tsaiwar motoci da jin buɗe-buɗe ya saka zuciyar Mom harbawa da masifar ƙarfi. Hakama ƙawayenta gaba ɗaya sukai tsitt da surutun da sukeyi dan tabbatar da inda ghuɗa ke fitowa.... 💞✨💞✨💞 Muna fitowa mukaci karo da mama Balki. Ita ta bama umarnin rakani sashen ita kuma tayi gaba. Gani nayi Mama Balki ta sauke ajiyar zuciya. Kamar ba itace duk na ga cikin damuwa ba yanzu. Har ƙofar da zata sadani da sashen nasa dake ta cikin main perlor ta nuna min. Nai mata godiya na shige kaina tsaye dan naji farin cikin sakani wannan aiki da akayi. Hanyace mai ɗan tsayi daga main perlor ɗin kafin akai ainahin sashensa. Tun daga cikin dogon corridor ɗin zaka iya shaida mayataccen ƙamshin turarensa da baya ɓoyuwa a duk inda yake. Baki na taɓe tare da yamutse fuskar takaici. Dan ni kaɗai nasan kalar rashin mutuncin da yau zan zazzage masa tunda na samu damar ganinsa matsoraci kawai, ba ruwana da rashin lafiyarsa ba raga masa zan ba. A rufe ƙofar da zata sadaka da sashen nasa take. Dan haka na danna bell da ɗan ƙarfi ina hararar ƙofar. Shiru babu alamar za'a buɗe min har cikar minti ɗaya. Sake dannawa nayi nan ma shiru, na bada wasu sakanni babu dai alamar za'a buɗe ɗin. Cikin fusata na danna bell ɗin da ƙarfin tsiya batare da na ɗaga yatsana a kai ba harda su cije baki. Sai gashi kuwa an buɗe ƙofar kamar a fusace. Baki na taɓe da ɗaga ido dan ganin wanene ya buɗe ɗin, sai a cikin mayun cat eyes ɗinsa kuwa. Yanda yay wani masifar yin kicin-kicin da fuska gashi ya tsatstsareni da idanu ya sani sake tamke tawa nima ina laɓe baki. Ɗauke nasa yayi tare da juyawa ya bar wajen. Da kallo kawai na bisa cikin yanayin harara. Sosai ya zube a tsaye cikin ƙanƙanin lokaci, sai dai a zahirance bazaka taɓa ma yarda baida lafiya ba dan yana nan a dakensa. Kamar bazanbi bayansa ba sai kuma dai nabi shawarar da zuciyata ta bani, dan haka na sunkuya na ɗauki basket ɗin nabi bayan nasa ina kwaikwayon yanda yake tafiya. Ina saka ƙafata a katafaren falon da ya haɗu ya gama haɗuwa shegen karen nan nasa dana taɓa gani a Kano ya taso a zabure. Ai bamma san na fasa ƙara da ƙoƙarin sakin tray ɗin ba. Sai dai jin ban faɗi ba ni da tray ɗin ya sani buɗe idanun nawa a hankali ina mai sauke ajiyar zuciya. Kallon cikin ido mukaima juna. Ban san lokacin da numfashina ya fisga ba alamar neman barin ƙirjina da gangar jikina, da ƙyar na fisgoshi na maidoshi cikin ƙirjina ina sake waro idanun nawa waje gaba ɗaya. Shima sake tsatstsareni yay da nasa tamkar zai cinyeni da su duk yanda naso haɗiye razanata ta ganin karen nasa tsaye a kusa damu na kasa hakan. Illahirin jikina da duk wata gaɓa da jini ke gudana ta cikinta sun bar aiki. “K! Baki gajiya da pretending ɗin faɗuwa dan a tare ki”. Ya faɗa a daƙile cike da rainin wayo. Har cikin tsakkiyar kaina naji haushin furucin nasa. Da sauri na sakesa gaba ɗaya tare da ƙoƙarin turashi nima nai baya. Sai da me ko gezau, yana nan a tsayensa ƙyam saman ƙafafunsa tamkar dasashiyar bishiyar data kafu a muhallin daya dace da ita. Kallo ɗaya yay min da shegun idanun nan nasa kalar na maguna ya janye tamkar bai fahimci abinda na jima haushin ba. Ga fuskar tsamm babu alamun rahama ko sassauci balle ma kai tunanin yayi maganar ne dan raha. Duk yanda naso janye nawa idanun daga kansa na gagara hakan saboda tsabagen shiga mamakin mutumin nan da rashin mutuncinsa ga shegen sonma mutane sheri. Kamar ko yasan mi nake tunani akan nasa ya raɓani ya wuce yana mai kiran sunan shegen karen nasa acan ƙasan maƙoshi. Da gudu kuwa ya bisa yana wani kaɗa bindi. Da harara ba rakasu su duka tare da ajiye basket ɗin hannun nawa ina bin falon da kallo. Dan babu ƙarya ya haɗu iya haɗuwa. Karaf kuwa sai idanuna suka sauka akan wayoyinsa dake a saman Centre table ɗin har uku, sai laptop a gefensu. A take wani tunani yazo min. Cike da rawar jiki da zumuɗi na ɗauka ina addu'ar ALLAH yasa babu password. Sosai na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, tare da shiga loda number ɗin Mansoor. Cikin sa'a kuwa ta shiga. Sai dai harta yanke ba'a ɗaga ba. Kamar zan sake kira sai kuma na fasa na saka ta Yaya Musaddiq. “Mr M” ya fito ɓaro-ɓaro. Da mamaki nake kallon sunan da sake duba numbers ɗin. Number ɗin Yaya Musaddiq ɗin ce dai. To miya kawota cikin wayar wannan mutumin? Bani da mai bani amsa, dan haka nai dialing kawai dan tabbatar wa. Bugu biyu kuwa aka ɗaga, na ɗan yi shiru. Sai ko ga muryar Yaya Musaddiq tar-tar yana sallama. Sai dai muryar tasa a ɗashe alamar barci ya tashi ko yake son yi. Maimakon amsa sai hawaye suka cika min ido. Muryata na rawa na furta, “Yaya!”. Ina jin alamar yanda ya zabura. Sai kuma cikin rawar harshe ya furta, “Samraah ke ce?”. Kuka na sakar masa kawai maimakon amsawa. Sai naji duk ya sake rikicewa. Kukan na sake fashe masa da shi da faɗin, “Yaya anya kana sona har yanzu kuwa?. Tsahon wata guda mutumin nan ya sace ni ya sace min Mansoor ɗina amma babu ku babu labarin ku. Yaya ina Mansoor ɗina kada ya halakar min da shi.....” Cikin wata irin sautin sauke ajiyar zuciya Yaya Musaddiq ya tari numfashina. “Samraah relax. Ki kwantar da hankalinki, babu wanda ya ɗauki Mansoor yana gidansu. Shi kuma wannan ɗin shine mijinki yanzu ba Mansoor ba. Yayanki kuma na sonki har gobe da jibi da gatan gata ma”. “Yaya!!!”. Na faɗa a matuƙar razane jikina na rawa, dan duk da shi ɗin ya sanar min shi mijina ne jin tabbaci a bakin Yaya Musaddiq ɗin sai ya sake sakani a matsanancin ruɗani. Sake tareni yay da faɗin, “Nace ki kwantar da hankalinki dan ALLAH Samraah. Yanzu yaya jikin naki kuma?”. “Yaya taya kake son na kwantar da hankalina? Ta yaya kake son kaji naji sauƙi? Bayan an ɗaura min aure da Mansoor na ganni kuma tare da wani ace na kwantar da hankakina”. “Samraah dama ba'a ɗaura miki aure da Mansoor ba. Da shi ɗin dai wannan mai suna Muhammad aka ɗaura miki aure. A yanzu kuma shine mijinki. Ki manta da Mansoor da duk abinda ya shafesa dan ALLAH ki fuskanci sabuwar rayuwarki da in sha ALLAHU muna fatan bazamuyi nadamar kaiki cikinta ba. Haba Samraah kefa mai ilimice. Har kin manta da wannan rayuwar izayar ta gidan Abba da kika sha ne?”. Baki na buɗe zanyi magana hawaye na rige-rigen sakko min kawai naji an zare wayar. Gaba ɗayana na juyo, dai-dai yana yanke kiran da jefa wayar cikin aljihun wandonsa. Afusace nake kallonsa, shima ɗin kallona yake tsakiyar ido. Tsahon minti ɗaya muna a haka batare da ɗayanmu yayi yunƙurin janye nasa ba wayar daya ƙwace a hannun nawa kira ya shigo cikinta. Nasa idanun ya janye tare da zaro wayar daga aljihun daya sakata, ya ɗan tsira mata idanu na sakani kafin naga ya kaita kunnensa tare da barin wajen ya nema kujera ya zauna. Da farko ban fahimci dawa yake wayar ba, sai da ya ɗago ya kalleni cikin yanayin ɗage gira da amsar da naji ya bada sannan. Da sauri na nufesa, babu zato yaji na zare wayar nima kamar yanda yay min. Kafin yay wani yunƙuri na nufi ƙofar dana shigo da gudu. Sai da naje jikinta sannan na juyo na masa gwalo nai ficewata.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_ ______________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ___________ .......Ba Mom kawai ba hatta ƙawayen nata sumar tsaye duk sukayi. Sai da suka sake jinfa tabbas a cikin gidanne sannan suka fara rige-rigen fitowa. Tamkar Mom zata tashi sama tai dirar mikiya a gaban wanda ke riƙe da amarya Halime. Cikin huci da fara birkicewa ta furta, “Kai lafiya? Daga ina haka? Su wanene ku?”. Murmushi Hajiya Asabe uwargidan mai anguwa ta saki. Cikin dattako da cikar kamala ta bata amsa da, “Baƙi ne na alkairi da ga jihar Katsinan dikko ɗakin kara, kunya garemu tsoro babu”. Duk da har cikin rai Mom taji shakkar matar, dan duk da mazauniyar ƙauye ce irin matan nan ne da aji a cikin jikinsu yake. Duk da dama can ita ba haihuwa da girman ƴan tumakin bace aurene ya kaita ƴar asalin cikin birnin Katsina ce. “Ke matsayinku ya dama, ni ba wannan ne matsalata ba. Wannan abar da aka lulluɓo nake son sanin matsayinta da dalilin shigowarku gidana”. Tai maganar tana nuna Halime da ke lulluɓe lafe a jikin Innarta Suwaiba. Duk abinda Mom ɗin keyi kuma tana jinta. Dan murmushi ma take yi ta cikin gyalen. Kai tsaye Hajiya Asabe ta sake bama Mom ɗin amsa da, “Wannan ba huruminmu bane ba, inaga mijinki ne ya cancanci baki amsar kamar”. Daga haka ta sake jan hannun Halime zasu wuce. Idon Mom ya fara rufewa kuwa. Tana shirin sake magana Gwaggo Gudidi ta iso wajen, dama tana sallane shiyyasa bata fito a ƴan tarbar amaryar ba. Ko kallon inda Mom take batai ba ta shiga yima baƙi lalale marhaban, tare da isa inda Halime take ta kama hannunta tana faɗin, “Sannu da zuwa ɗiyata sannu kinji ƴar albarka”. Yunƙurawa Mom ta sake yi a fusace zatayi magana wata maƙociyarta ta riƙeta. Cikin raɗa-raɗa ta ce, “Maman Baby kwantar da hankalinki, inagafa mutanen nan so suke kawai suyi yawo da hankalinki. Anya ba matar ɗanku bace Musaddiq”. Da dauri Mom ta dubeta da idanunta da sukai jazur, cikin ɓacin rai da tashin hankalin daya gagara ɓoyuwa gareta ta ce, “Maman Nana Musaddiq kuma? Shine dan Musaddiq zaiyi aure sai a munafunceni? Sannan tayaya ma shi Imam zaiyi gangancin kawo min matar Musaddiq mu rayu a gida ɗaya. Kenan ma su ƴaƴana sun rako na wasu ne duniya”. Ɗan jimm Maman Nana tayi, sai kuma ta jinjina kanta cike da gamsuwa. “To amma Maman Baby idan fa har ba hakan bane to tabbas Abban Abbas ne yayo aure batare da kin sani b....” Wata muguwar ashariya Mom ta lailayima Maman Nana tare da wanke fuskarta da mari. Tuni hankalin kowa ya fara dawowa kansu. Dan kafin Mom ta sauke hannunta itama Maman Nana ta sauke mata marin. Su kam dangin amarya tuni sun gama shigewa cikin ɗaki da amaryarsu batare da sunbi takan hayaniyar data kaure tsakanin Mom ɗin da Maman Nana ba. Zaburar Mom da nufar sashen amaryar ya saka Gwaggo Gudidi cimmata ta tare ƙofar. Ƙoƙarin tureta Mom keyi cike da raini Aunty Na'ima ta janyeta rai ɓace. “Wai ke Jalilah miyasa baki da isashiyar tarbiyya ne? Ke yanzu sai ki ture Gwaggon kike nufi?”. “Yo mizai hana nayi hakan, ai ni idan tsoho baiji kunyar hawa jaki ba, nima bazan ji kunyar kado shi ƙasa ba kuwa wlhy.” “K Jalilah ki shiga hankalinki wlhy dan yanzu ba da bace. Kin kuma san ko ada ɗin ma ana ƙyaleki ne darajar wanda ya kwasoki cikinmu amma badan ana jin tsoronki ba. Hauka kuma dama kin saita kanki kafin ɗan sauran mutuncinki daya rage ya ƙarasa zubewa. Dan amarya dai ce Yaya Imam yayi babu yanda kika iya da ita zama daram anan gidan da izinin UBANGIJI. Sai dai ke ki fita ki barta kuwa dan nan da wata tara ma in sha ALLAH muna nan muna bikin sunan babys”. Cak numfashin Mom ya tsaya tare da harbawar zuciyarta. (Dan amarya dai ce Yaya Imam yayi babu yanda kika iya da ita zama daram anan gidan da izinin UBANGIJI. Sai dai ke ki fita ki barta kuwa dan nan da wata tara ma in sha ALLAH muna nan muna bikin sunan babys) kalaman suka shiga maimaita kansu a cikin ƙwaƙwalwarta cikin amsa kuwwa. A hankali ta ɗago tana kallon Aunty Ni'ima, sai kawai idanunta suka sauka akan Abba daya shigo. Rawa jikinta ya farayi, cikin ɗimuwa da sassarfa ta nufesa. Cak ya tsaya yana kallonta harta ƙaraso inda yaken. Yanda ta cakumo hannunsa zai tabbatar maka da bata a cikin hayyacinta, dan harshenta har sarƙewa yake wajen faɗin, “Abban Abbas wacece wannan aka kawo min gida? Matar wacece? Dan ALLAH kace min Abbas kaima aure”. A hankali ya girgiza mata kansa tare da riƙo hannunta. “Jalilah Please relax mana..” “Naƙi nayi relax ɗin Imamu ka faɗa min wacece ita?”. “Zan faɗa miki amma ki muje daga ciki”. “Wlhy babu inda zanje sai ka faɗa min anan. Kuma kaima ɗin baka isa kabar wajen nan ba....” Gwaggo Gudidi ce ta ƙaraso wajen. Idonta akan Abba ta ce, “Miye kake wani zazzame mata Imamu, ka fito fili ka faɗa matan tunda ita ta nema da kanta. Ai shiyyasa ake son mace ta zama matar ƙwarai kodan irin wannan ranar. Idan ka zama ɗan arziƙi mai tarbiyya taya har miji zai ɗakko maka abokiyar zama batare da saninka ba. Ai dama halinka sabulun wankanka. Mata dai taka ce muma duk mun shaida. Hargowarta ko shirmenta bai isa sakawa a goge hakan ba. Dan in har kai gigin sakin wannan baiwar ALLAHr daka auro koda bayan raina ne wlhy kaf mu ahalinka bazamu yafe maka ba. Ballema nasan bazaka fara kwatanta hakan ba dan kaima kana ƙaunar matarka. Dan haka ka fito ka sanar mata aure ka ƙara dan bazaka cigaba da zama daga kai sai ita a cikin gida ba ta kasheka watarana kamar yanda ta rabaka da duk danginka damu iyayenk.....” Babu wanda ya san ta yanda akai kawai hannun Mom aka gani a wuyan Abba ta cakumosa. So take tayi magana amma hakan ya gagara saboda numfashinta ma fisga yake. A mamakin kowa sai gani sukai tayi baya gaba ɗayanta alamar suma. Ƙasa take neman zubewa sai da Abban ya riƙota..... 🌜🥱🌛 Tunda tabar falon bai iya ya motsa daga inda yake zaune ba. Sai ma tsurama ƙofar da tabi idanunsa yay tamkar tana a wajen har yanzu. Yana nan zaune kusan mintuna goma shigowar Hayatu ta katse tunanin nasa. Koda Hayatun ya gaisheshi ma hannu kawai ya ɗaga masa. Shi dai Hayatu ya riga ya saba shiyyasa bai damu ba. Sai ma kaiwa da yay zaune bayan yaje gabansa ya ajiye takardun dake a hannunsa dan yau shi bai fita office ba sakamakon yini da sukai akan Hajiya Babba da likitocinta, tare da tsaftar sashenta aka fidda duk kayan da Samraah ta tattara dama sauran duk na sashen aka canja mata katifa kafin a kawo wasu. Shiyyasa Hayatun ya kawo masa duk wani document mai muhimmanci da zai duba ya saka hannu... Ina fita na saki murmushin farin ciki. Yau dai na samu wayar yin magana da ƴan uwana. Duk da ko a da da nayi niyya zanyi hakan dan su Bahijja duk akwai waya a hannunsu. Abinda yasa ban taɓa ara ba saboda bana buƙatar kowa yasan sirrina. Farin cikin waya ya mantar dani wani batun aikin Hajiya Mammah. Dan amaimakon kitchen daya kamata na koma ficewata nayi daga sashen baki ɗaya ko su Azizat dake zaune acan rukunin ƙarshe na kujeru bana tunanin sun ma ganni. Ban nufi sashen mu ba na wuce garden ɗin gidan. Tsabar wuce wuri kuma maimakon babban garden sai na shige ƙaramin da akace nasa dan na samesa a buɗe da'alama aikin gyarashi akayi saboda kayan aiki dana gani an tule. Can na shige kusan ƙarshe duk dan dai na samu wajen ɓuya nai wayar a tsanake. Kaina tsaye na sake danna kiran layin Yaya Musaddiq. Sai dai harta katse bai ɗaga ba sai da na sake kira na biyu. Hayaniyar da naji ya sani faɗin, “Yaya ya nake jin hayaniya ko kana kasuwa ne?”. Maimakon amsa ƴar dariya yayi da cewa, “Har kin gama darun?”. “Kai Yaya ni har wani daru ne da ni?”. “Sosai kuwa Kandalata. Ai ke naki ma na musamman ne.” Karon farko na saki dariya, sai kuma na shiga gaishesa da girmamawa. Ya amsa min da kulawa tare da tambayar lafiyata da kuma jiyyar da nayi. Na amsa masa da Alhamdullah, tare da tambayarsa mi ake a gidan naji hayaniya. Kansa tsaye ya ce, “Mamarki akema kishiya”. Da mamaki nace, “Mamata kuma Yaya? Wa kenan?”. “Mom mana. Abba ne ya ƙara aure”. Tuni na miƙe daga zaunen da nake dan mamaki, sai kuma na shiga ƙyalƙyala dariya. “Wai dan ALLAH yaya da gaske kake ko wasa? Mom fa akaima kishiya? Ta yaya Abba ya samu wannan ƙwarin gwiwar haka? A ina kuma ya samo matar?”. Tsaf Yaya Musaddiq ya kwashe labari ya bani, tun daga zuwan Halime gidan har kawo yau da suke jiran isowar amarya batare da Mom ta sani ba. Tsabar farin ciki bamma san lokacin dana rangaɗa ghuɗa ba. Sai da Yaya yace min, “Ƙaniyarki kandala” sannan na bari ina dariya. Haka kawai nake jin raina fes da wannan al'amari. Dai-dai nan sautin muryar aunty Zakiyya data rangaɗa sallama ya ratsa kunnuwana. Bayan sun gama magana da Yaya Musaddiq yake cemata gani a waya. Amsa tayi cike da zumuɗi muka gaisa, kafin cikin raunin murya da lallashi ta ce, “Samraah shike nan kuma babu kira duk kinsa hankalinmu ya kasa kwanciya?”. Murmushi nayi hawaye na cika min ido. Muryata na rawa na ce, “Aunty bani da waya ne. Kuma kuma kun sallamani ga wanda ban ko sani ba kamar bani da kowa a duniya”. “Haba Samraah, shin bazamu iya haƙuri da karɓar ƙaddara ba a duk lokacin da tazo mana? A maimakon tada hankali a ganina godiya ya kamata muyima UBANGIJI dan a maimakon tozarcin da akaso ganinmu a ciki alkairi ne ke lulluɓe da mutuncin mu. Samraah kiyi haƙuri dan ALLAH, ki karɓa da hannu biyu sai ALLAH ya sauƙaƙa komai a yanda ba kowa yay zato ba. A kowace daƙiƙa ta rayuwa kuma kina ranmu. Kawai dan bamu san ta yanda zamu sameki bane ba”. Babu daɗi kalamanta suke sake saka ni. Dan haka na sake raunana murya, “Aunty kina nufin maganar da wannan mutumin ya faɗa da Yaya gaskiya ce? Da shi aka ɗaura min aure, kuma aka kawo ni garesa? Shike nan kuma kun barmasa ni?”. Ƴar dariya tayi, cikin wasa ta ce,.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚_ _________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 _____________ ........“Ya zamu bar masa ke. Sai dai ya ɗauki rabi ya bar mana rabi. Ke dai ki kwantar da hankalinki kinji. In sha ALLAHU ni da Musaddiq muna nan tafe har inda kike. Dama a tunaninmu idan kinji sauƙi zai dawo mana dake gida ne shiyyasa. To amma uzirin daya kawo akan zaman naku anan yanzu dole a haƙura har sanda ya kawoki da kansa ɗin. Ni dai kawai roƙona ki kwantar mana da hankalinki, ki mance da Mansoor kamar yanda mahaifiyarsa ta buƙata, ALLAH shine shaidar mu ba laifinmu bane sune sukaƙimu. Dan a ranar ɗaurin aurenku mahaifiyarsa da kanta tazo tace sun fasa ɗanta bazai aureki ba saboda ba'a san mi aka aikata miki ba da akai kidnapping ɗinki. Babu yanda su Kawu Musa basu lallasheta ba har gwaji sukace aje ai miki amma fir matar nan taƙi sai ma cin mutunci da gori data shiga musu. Suko sun san mutuncin kansu ai, dan haka suka janye suka bama wannan bawan ALLAHn ke dan su mutuntaki da mu kammu. Dan inba hakaba wannan mugun baƙin fentin da sukai miki zaita bibiyar rayuwarki ne harma mijin ya gagara gareki a gaba”. Sosai maganganun aunty Zakiyya suka ratsa min jiki. Mamaki da al'ajabin mahaifiyar Mansoor ya tsaya min a zuciyata. Harna kasa daurewa na ce, “Amma Aunty shi yaya akai yasanni yazo neman aurena? Ko su kawun sun sanshi ne su?”. “To ni dai bazance ba gaskiya. Amma dai kamar naji ance shine yazo yace yana son aurenkin da kansa. Ki dai tambayi Gwaggo tasan komai kuma nasan zata sanar miki. Ko kuma shi mijin naki ki tambayesa ai bazai ƙi sanar miki ba”. Shiru nai tsahon lokaci na kasa cewa komai. Sai kuma can na ce, “Okay Aunty in sha ALLAHU zan tambayesa”. Nasiha suma suka min cikin lallashi ita da Yaya Musaddiq. Bayan munyi sallama na jima zaune a garden ɗin ina tunani kafin na miƙe na koma sashenmu bayan na kashe wayar na sakata a jikina. Ina shiga Aunty Sadiy ta shigo wai naje Hajiya Mammah na kirana. Idanu na ɗan waro dan harga ALLAH nama manta da batunta... A ɗarare na tafi amsa kiran nata, sai dai cikin sa'a ina zuwa na samu wai tana da baƙuwa sun ma fita yanzun nan. Ajiyar zuciya na sauke na juya na koma ina godema ALLAH. Dan dana sameta ban san mi zance ba wajen kare kaina. ✨★✨★✨ Da ƙyar aka samu Mom ta farfaɗo. Tana kuwa farfaɗowar wasan ya koma sabo. Dan tuni Ummanta da su Baby da basa gidan sun dawo harma da wasu ƴan uwanta. Faɗa ne mai ƙarfin gaske ya ɓarke tsakanin dangin Mom da ita kanta da dangin Abba. Dan dangin amarya su dai ƴan kallo suka zama. Sai dai kuma ransu ko ɗar balle gezau akan ƴarsu bazata iya zama ba. Sai ma murna suke da rahamar da UBANGIJI yay mata na samun wannan danƙareren gida a matsayin gidan aurenta. Itama ɗin dai Halimen ko'a kwalar rigarta. Yo ita wane kalar masifa da bala'i ne bata gani a wajen Innarta ba. Sannan faɗan kishi babu irin wanda ba'ayi a gidansu. Dan kaf matan kawunanta ba su ɗaɗɗaya bane Innace ma kawai ita kaɗai a wajen Baba. Amma sauran daga mai mata uku sai mai biyu harma da mai huɗu. Kuma haka ake shan cakwakiya a gidansu gashi gidan yawa. Ita dariya ma abinda ke faruwa ke bata. Sai da Hajiya Asabe ta ƙwaɓeta daga yanda take kwasar dariya tana leƙe ta window sannan ta nutsu. Shi dai Abba ma tuni ya fita ya bar musu gidan bisa umarnin Gwaggo Gudidi. Haka aka ci uwar sabada mata anguwa nata shigowa. Masu yima Mom dariya da ALLAH ya ƙara sunfi yawa. Dan har a cikin ƙawayen nata wasu abin ya musu daɗi. Ummanta ce data fahimci al'amarin fa shiryayye ne dan dangin Abba sun kafa sun tsare yasa ta janye Mom ɗin suka shige ɗaki. Ba'a sake ganinta ba har kusan goma na dare sai ga likita wai yazo zai dubata hawan jininta ya tashi. Babu wanda yabi takan batun kowa ya cigaba da sabgarsa. Sai ita da ƴaƴanta da Ummanta ke ƙulle-ƙullensu can a sashenta su kaɗai. Har washe gari daga ɓangaren Mom dai babu daɗi, gashi Abba yaƙi shiga inda take tun dubatan da yaje yay na farko bai sake zuwa ba, dan yana shiga ta sake birkicewa harda shaƙeshi tana kuka da faɗin sai ta kasheshi sai dai duk su rasa. Har ita zai tozarta yama kishiya, to wlhy ya sani ya ɗakko bala'i da masifar da bazata taɓa ƙarewa ba har sai cikin abu uku ɗaya ya faru. Kodai ta kashesa, ko kuma ya saki yarinyar a yau danginta su koma inda suka fito da ita, ko kuma idan ita ta mutu. Kuma koda ta mutu yace zai sake aure sai ta dinga masa fatalwa. Abin nata kamar wasa ya nema zama babba, dan da ƙyar aka fiddo Abba a ɗakin tana neman murɗe masa jikinsa ALLAH dai ya taƙaita masa wahala akwai babbar riga tare da shi. Su dai ƴan uwansa da dangin amarya sabgar gabansu suke hankali kwance dan basu san mike faruwa a cikin ba sai da su Gwaggo Gudidi suka fito da Abba ne suke jin komai. Aiko fa kowa ya shiga ALLAH wadarai da wannan baƙin hali na Mom, daga nan kowa ya sake ɗaura ɗammara a kanta. Dan a ranar dangin amarya sukai walima tare da rabon kayan gararsu cikin bajinta da aka san katsinawa da ita a wajen rabo. Al'amarin ya ƙayatar da kowa a dangin Abban, sun kuma yaba da ƙoƙarin mutanen. Ana yin sallar azhar motocin da zasu maidasu gida suka kwashesu aka bar amarya Halime na kwasar kuka. Sai da su Aunty Zakiyya suka jata ɗaki suna lallashi. Daga ƙarshe ma dai su suka cigaba da zama da ita suna ɗebe mata kewa har washe gari da suma kowa yay haramar kama gabansa bayan sun kimtsa gidan. Har kuma sannan babu wanda yaga idon Mom. Sai dai duk sun fahimci akwai abinda suke ƙullawa ita da uwarta dan sai shigi da fici Ummar tata keyi a kwana biyun nan, saboda rashin sanin ciwon kai a gidan take kwana itama har a yau da bikin ya tashi. Ƴan Gwarzo ma sun rigata wucewa. Ganin bata ma da niyyar tafiya ne yasa Gwaggo Gudidi itama ta fasa tafiya a yau duk da dai dama wasu a dangin sun kawo shawarar Gwaggon ta ɗan zauna har gidan ya dai-daita gudun kar'a cutar da yarinyar mutane. Kowa kuma ya gamsu da shawarar dan haka Gwaggon tai zamanta. Sai hakan kuma yayima Abban daɗi shima. Dan dama yana tunanin ta yanda zai fita yabar Halime daga ita sai Mom ɗin a gidan har sai ya gama saita gidan... 💦💥💦💥💦 Kwanaki biyar kenan da faruwar dukan da naci a sashen Hajiya Babba. Alhamdullah jikina yayi sauki, dan hatta ciwon da taji min ma ya warke sarai sai tabo. Tun wannan ranar ban sake gigin komawa ba duk da hankalina na'a kanta. Haka shima uban gayyar ban sake ganinsa a gidan ba. Sai ma a bakin Mama Balki nake jin wai yayi tafiya ai tun a washe garin faruwar al'amarin da dare. Ranar da Hajiya Mammah ta aikani sashensa kai masa coffee kenan harna taho masa da waya. Bakina kawai na taɓe na cigaba da harkar gabana, dan damuwar data daman daban, duk da kuwa tana da alaƙa da shi. Sosai ina buƙatar zama dashi a wannan gaɓar, dan ina son jin yanda akai har ya je gidanmu ya nema aurena. Ai abin da mamaki, dan Mansoor mahaifiyarsa ta hanashi aurena shi kuma ace yaje ya auran bayan babu wata alaƙa data alaƙanta tsakanina da shi bayan ta kidnapping ɗina da yayi da hira da nai da shi a station ɗinmu... Zuwa yanzu aikina ya koma sashen Hajiya Mammah, nice kullum mai mata gyaran sashenta safe da yamma. Da farko dai abinda na fara fahimta ga halayyar matar shine nuna isa da mulki. Na biyu shegen kallon raini na ƙurillar tsiya kamar zata cinyeka da idanu. Sai masifa komai kayi sai ta maka jaraba kamar itace ta halicceka. Shiyyasa idan na tashi kafin ma ta tashi a barci na gama gyara ko'ina nabar sashen, sai kamar 11 sai na koma na gyara mata bedroom lokacin ta fito. Yau ma kamar kullum da wuri na kammala aikin nawa, sai dai ina ƙoƙarin sauka dawn stairs na jiyo kamar sautin kuka na fitowa ta sashen Hajiya Babba. Tsamm nayi da raina kusan mintuna uku, jin dai da gaske tanan ɗin ne bamma san lokacin dana juya cikin sauri da sassarfa ba. Idanuna a rufe na faɗa sashen batare dana tuna da wahalar dana sha a hannunta kwana biyar da suka wuce ba. Ganin key a ƙofar ya sani murɗawa na afka ido rufe, jikina har rawa yake jin sautin kukanta da yanda take ambaton kiran sunan “Muhammad” dan zuwa yanzu na fahimci Maash kadai suke kira Muhammad a gidan ita da Paah. Zubewa nai a inda take zaune can karƙashin ƙafar bene ta cure jikinta waje guda fuskarta cikin ƙafafunta. “Ummi miya sameki? Baki da lafiya?”. Na faɗa cikin rawar murya ina kamo hannayenta dake ɗauke da sayin ɗauri har yanzu amma duk ciwukan sun warke. A mamakina sai naga ta ɗago a hankali. Yanda idanunta suka kumbura sukai jaa sosai ya sake tayar min da hankali. Ga hawaye face-face da fuskar tata. Sai kawai nima na fashe da kuka tare da faɗawa a jikinta. Tsamm ta rungumeni itama tana ƙara fashewa da kukan da cigaba da magana cikin sambatu. “Muhammad ciwo, kaina ciwo zai fashe Muhammad. Ga jikina ƙaiƙayi yake min. Muhammad ina jin yunwa”. Kuka na sake fashewa da shi ina mai ɗagowa a jikin nata. Amma sai ta hanani tashi ta sake matseni sosai. Duk da zafin da nake ji ban sake yinƙurin tashin ba. Tsahon mintuna biyar muna a haka har na fara numfashi da ƙyar. Sai kuma ta sakeni ta dafe kanta da riƙe cikinta. Zumbur na miƙe jikina na rawa, ga hawaye sun kasa tsaya min, “Kiyi haƙuri Ummie ki daina kuka dan ALLAH, yunwa kike ji ko?, Zakici abinci na kawo miki?”. A mamakina kai ta ɗaga min tare da kamo hannuna ta ɗaura a saman cikinta hawaye na sharara ta shiga jujjuya min kanta. Ta ce, “Yunwa Muhammad yunwa”.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_ .......Da sauri na jinjina mata kai ina ƙoƙarin miƙewa. “To Ummie in sha ALLAHU yanzu zan kawo miki abinci bani ɗan lokaci ƙalilan.” ban jira amsawarta ba na tashi na fita a guje dan nasan bama amsawar zatai ba. A falonta na farko naci karo da wasu mata guda uku sabbin fuska daban sani ba a gidan. Nayi mamaki dan ɗazun ban gansu ba, ko kuma ban lura dasu bane oho. Takan kowa banbi ba a cikinsu nafice zuwa downstairs na afka kitchen, ganin an gama komai har an gyara kitchen ɗin ma fito dining, komai an shirya na breakfast, sai dai babu kowa a kai dan sai sun gama barcin safensu suke fitowa karyawar. Hajiya Ƙarama ce kawai bata a gidan ta wuce wajen aiki. Komai sai da na ɗiba tare da haɗa shayi mai ƙauri na ɗauka ruwa. Da gudu na koma saman, inda na barta nan na sameta, sai dai yanzu tana kwance ta naɗe a waje guda sai nishi take alamar yunwar tacita ta cinye matan nan na tsaitsaye a kanta kamar a tsorace. Ina shigowa duk suka zabura kanta. Tsawa na daka musu tare da nuna musu ƙofa alamar su fita. Har rige-rigen fitar kuwa sukeyi. Basket ɗin hannuna na ajiye, sannan na durƙusa gabanta na ɗagota. A jikina na sanyata ina kuka da bata haƙuri, shayin dana haɗa dai-dai zafi na ɗauka na kai bakinta, jikinta har rawa yake wajen damƙe kofin, tsam ta dafesa tare da hannayena kamar mai lafiya, kwal-kwal ta shiga kwankwaɗar shayin tamkar ta samu ruwa. Kafin wani dogon lokaci ta shanyesa gaba ɗaya, sai ga zufa na karyo mata tako ina ta fara sauke ajiyar zuciya jikinta na saki. Jinai hawaye sun ƙara ziraro min, na kwantar da kanta sosai a saman cinyata ina shafa cuɗaɗɗen gashinta daya danƙare saboda datti. Tabbas ɗiya mace daban ce, da ace baiwar ALLAHr nan nada ƴa mace a cikin ƴaƴanta duk tsanani bazata dinga barinta a cikin wannan dattin ba. Amma kalla yanda aka saketa kamar mara gata. Dukiyar tatace, gidan ma nata ne, ɗan da suke taƙamar da shi a yanzu haka nata ne. Amma ita bata san daɗin ko ɗaya a ciki ba, sai wasu banzaye da sukazo suka cika gidan badan su amfana mata da komai ba. In sha ALLAHU na ɗauki alƙawarin daga yau koda baiwar ALLAHr nan zata halakani sai na ƙwato mata ƴancin rayuwarta a gidan nan, tun daga kula da ita har zuwa sanin tushen wannan ciwo nata da nake ji a raina ba banza ba. Kai harma ɗan nata da alama ba haka suka barsa ba shima. Sai da na tabbatar shayin da tasha ya faɗa mata sosai sannan na jawo abinci, ban tasheta a jikin nawa ba, a haka na dinga bata da kaina kuma tana amsa. Sai kallona take dan har ta kauda kanta alamar ta ƙoshi idonta a kaina ƙyam. Lemo na ɗakko zan bata ta kauda kai, sai na ajiye na ɗauki ruwa. Ina saka mata a baki kuwa ta hau sha. Sosai tasha tana sauke numfashi, sai kuma ta gyara kwanciya a jikina, mintuna bai fi biyu ba barci mai nauyi ya dauketa. Ganin barcin nata yay nisa na fara kwance mata kitson kanta da yay bala'in danƙarewa, da naga ta motsa sai na ɗan dakata, sai ta koma barcin sai na cigaba. A haka na kwance gashin tana barci a jikina. Sosai take da gashi, da alama shima a wajenta ya gaji wannan gashin nashin da yakema mutane iyayi da shi. Ganin barcin nata yayi nisa na lallaɓa na kwantar da ita, gyaran sashen na fara, harda wancan ɗakin da naci duka a ciki wancan karon. Da yake na saka aikin a raina kuma an rage dattin da yay wancan karon sosai koma nace an gyara komai ƙal sai dai ban san wanda ya gyara ba kafin wani dogon lokaci na kammala tsaff, amma ina zargin matan nan dana gani sabbin ma'aikata ne aka kawo mata, maybe kuma sune sukai aikin. Ko'ina sai ƙamshi yake kamar ba shi ba, ruwa na haɗa inata tunanin ta yanda zatai wanka, dan harga ALLAH jikinta na buƙatar wanka, saboda alamu sun nuna an ɗan rage dattin jikinta ba kamar a ranar farko dana sameta na, harma kayan bana waccan ranar bane ba, sai dai kamar kuma ba'a sake mata ba tun waccan ranar ɗin. Ni kuma bamma san ta yanda zan iya cewa zan mata ba dan ina jin kunya. Dabara ce ta faɗo min, na fita zuwa kitchen dan nasan yanzu sun dawo aikin rana. Babu kowa a falon kuwa, cikin sa'a kuma na samu Mama Balki a dining tsaye tana waya. Tana ganina ta yanke kiran. Sai da ta wawwaiga ta tabbatar babu kowa a wajen sannan ta kama hannuna. Can ƙarƙashin stairs muka je, fuskarta cike da damuwa ta ce, “Ina kika shiga Kandala? Tun ɗazun ake nemanki a gidan nan amma babu ke”. Kaina tsaye nace mata, “Mama ina sashen Hajiya Babba fa. Yanzu ma kiranki nazo yi ki taimakeni”. Sosai fuskarta ta nuna mamaki, ta ce, “Sashen Hajiya Babba fa?”. “Eh wlhy Mama. Dan ALLAH kizo ma muje kiga taimakon da zaki min kafin wani ya gammu anan a hanamu. Bata musa ba muka hau upstairs. Ni kaina tsaye nake tafiya, yayinda ita kuma take ta faman waige-waige da gani duk a tsarge take. Ita kanta sai da tayi mamakin yanda na ƙara gyara sashen, Hajiya Babba dake kwance na nuna mata. “Mama ki taimakeni jikinta na buƙatar wanka ne. Idan akai mata zataji sanyi. Ga kanta na buƙatar wanki ma, sannan matan can dake zaune a falon farko wai su wanene?”. Ɗan jimm tai alamar tunani, sai kuma ta amsa min da, “To yanzu yaya za'ayi kenan? Kin san fa dole aka saka mata ruwa a jiki dole ta farka. Kuma hakan akwai matsala shiyyasa ma Alhaji ƙarami ya hana a jika mata kai ranar. Waɗan can matan kuma sune sabbin masu aiki da Baba ya kawo tun ranar da abin can ya faru tsakaninku”. “Mama in sha ALLAHU baza'a samu matsala ba. Dan yanzu da kanta taci abinci. Kota farka kuma da izinin UBANGIJI babu abinda zai faru mama. Su kuma ki gargaɗesu dan ALLAH ko kuma suje waje idan anjima sa dawo”. Badan ta gamsu ba ta yarda da magana ta, da taimakona muka kamata zuwa bathroom. Sannan ta fita ban san yaya tayi da matan ba ta dawo. Sake ɗaukar ta mukayi zuwa toilet. Ganin ta buɗe idanunta alamar ta farka cikin ruwan dana haɗa a bathtub muka sakata. Da farko taso zabura, sai da na dafe mata hannu da sauri cikin lallashi da roƙo ga hawaye a fuskata ina tofa mata addu'a sannan ta haƙura ta koma ta zauna. Kanta muka fara ƙoƙarin wankewa, sai faman sauke ajiyar zuciya take a jajjere. Yanda wata muguwar dauɗa ke fita ban san lokacin dana ƙara ƙarfin kukana ba dan tausayi. Kai da kaga wannan baiwa kasan kafin lalurar na anyi manyan hamshaƙan mata. Amma jiba yanda ƙaddara ta maidata, ɗan adam kenan ba'a bakin komai yake ba. Bamu bar kan ba sai da ya koma fidda farar kumfa sol da ruwa mai ƙyau, baiwar ALLAH sai sauke ajiyar zuciya take, barci ma ɗibarta yake. Fitowa nayi nabar Mama Balki tai mata wanka, duk da na fahimci ita tana komai a tsorace ne. Sai dai Alhamdullah ta daure ta mata wanka na gaske duk da ni na fito duba kaya kozan samu. Anan dai ɗakin da muke babu, sai da na duba ɗayan kusa da ita dake a kulle sai nayi sa'an samu, ashe ɗakin duk kayan sawarta ne da duk wani abun buƙata na gyaran jiki. Da alama tana ɓatawa ne shiyyasa ake rufesa abar key ɗin a jiki, sai dai kuma babu tabbacin ana mata amfani da su, dan da jikinta baiyi wannan masifar dattin ba ai. Komai da za'a iya buƙata na ɗauka harda towel sannan na koma inda suke. Har lokacin basu fito ba, dan haka na miƙama Mama Balki towel guda biyu, na ajiye duk abinda zasu buƙata na fita dan ta samu damar shiryata. Ina daga falo zaune kusan mintinan talatin sai ga Mama Balki ta fito tana sharar hawaye ga murmushi akan fuskarta. Zumbur na miƙe ina tambayarta ko lafiya. Maimakon amsa saita jawoni jikinta ta rungume tana mai fashewa da kuka mai ƙarfi da sanya min albarka. Ban iya kwace jikina ba har sai da tayi mai isarta ta ɗagoni dan kanta. Hawayen nima na share kafin na sake tambayarta abinda ke faruwa. “Babu abinda ya faru Kandala. Ke dai ALLAH yay miki albarka. Kin kwatanta abinda wani bai taɓaba a gidan nan. Ashe baiwar ALLAHr nan ba kowane lokaci bane take a yanayin da ake gudunta. Dama ƙyaƙyƙyawar mace ce mai ƙyawun siffa da cikar haiba amma ƙaddara ta maidata haka. Zo ki ganta Kandala zo kiga cikar zati da asalin kwarjinin manyan mata dan ALLAH”. Jiki na rawa nabi Mama Balki. Muna shiga ciki sai da na kusa faɗuwa dan mamakin abinda naci karo da shi. Lallai anan Awwab ya gado cikakken ƙyawu da asalin kwarjini. Hatta da idanun magen nan nasa irin nata ne. Bamma san lokacin dana ƙarasa gareta cikin sassarfa ba na durƙushe, hannayenta duka na kamo a cikin nawa na runtse, tamkar wadda ke cikin hankalinta sai ta sakar min wani guntun murmushi tare da lumshe idanunta a lokaci guda ta buɗe sai kuma ta sake maidasu ta lumshe. Bamma san lokacin da ƙaunar matar ya ƙara mamaye jini da ɓargona ba. Nai zaman dirshan a gabanta na cigaba da kallonta tamkar na samu television. Tsahon lokaci ina a haka har sai da mama Balki ta fargar dani muyi mu fita kafin mutanen gidan su farga da zamanmu a ashen. Gashi su kansu wadancan matan bamu san a ƙarƙashin ikon wa suke ba. Kaina tsaye nace “To mama minene dan sun san muna anan? Dama ba so suke su sami mai kulawa da ita ba? Nifa waɗan nan matan bazasu cigaba da zama da ita ba sai dai su koma inda suka fito”. “Hummm” kawai Mama Balki tace dani batare da fashin baƙi ba. Daga haka ta fita tana mai tabbatar min nayi sauri na kammala tunda tayi barci na fito ita zata koma akan bakin aikinta. Da to kawai na amsa mata badan zanyi yanda tace ɗin ba, dan tana fitar ma kayan gyaran gashi na jawo tare da gyara zama na hau gyara gashin Ummie. Gashine mai uban yawa ga tsayi shiyyasa nasha wahala sosai. Ban bar mata shi a haka ba nai zaman kitsa mata shi. Nan ɗin ma dai ansha cakwakiya kafin a kammala, dan takan farka ta dafe hannuna tana yamutsa fuska. Har sai na tsaya ta huta ina tofa mata addu'a sannan nake cigaba. Sanda muka gama barcinta yayi nisa sosai, dan haka na miƙe na tattare kayan dana kawo mata abinci ɗazun da wanda nai gyaran gashinta na maida inda suke na fita da sauran samo mata wani abincin. Kusan cin karo mukai da yarinyar da Bahijja tace min agola ce a gidan, tana ƙoƙarin hawowa upstairs ina ƙoƙarin sauka ni kuma. A ɗan yamutse da kallon raini tace min nazo ana nemana........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_ .......Uffan bance da ita ba na cigaba da sauka ƙasan. Tunkan na ƙarasa nake jiyo hargowa da ihun Hajiya Mammah. Nadai dake na cigaba da sauka ina kallon Mama Balki dake durƙushe gabanta kamar ma kuka take yi, sai matan nan guda uku suma durƙushe a gefenta, ai kafin ma na ƙarasa gabanta nima naji saukar mari. A take azaba ta sakani watsar da kayan hannuna suka tarwatse a wajen. Ban gama dawowa a hayyacina ba ta shaƙure min wuya da faɗin, “K wai wacece? Ƴar uban wacece a ƙasar nan dazan ce ga abinda zakiyi ki canja da naki tsarin?”. Sam bana ma fahimtar mi take faɗa, sai kakari neman fitar rai kawai nake ga idanuna sun gama firfitowa waje. Wani marin ta sake yarfa min sannan ta hankaɗani baya. Buguwa nayi da kujera da Azizat dake ta wajen, sai itama kawai ta sake hankaɗoni na dawo. Na gama sallamawa sai na kai ƙasa, amma a mamakina sai na jini a jikin mutum babu zato... Tun faɗowarta jikinsa a bazata ya tsaya cak tamkar bishiyar kuka. Bai kalleta ba, bai kuma motsa ba, bai kuma janyeta a jikinsa ba. Sai dai fuskar ta sake wani irin tsukewa mai tsanani dake sake fidda ɓacin ransa muraran ga duk wanda zai iya kallonsa. Duk da shi dama ba abin wasan kowa bane a gidan yanayin fuskar yasa ta sake saka kowa firgita. Hakan yasa numfashinsu ɗaukewa gaba ɗayansu a lokaci guda. Daga masu ɗora hannaye duka a saman kai, sai masu wage baki, sai masu waro idanu waje. Hatta da ita kanta Hajiya Mammah ɗin ta shiga shock da ganinsa dan babu wanda zaice ga sanda ya shigo falon. Amma da yake macece data goge a iya barikanci sai ta zaburo inda suke tana cigaba da masifa. Har isowarta inda muke na gagara tashi a jikinsa. Saima ƙanƙamesa dana sake yi ganin takai hannu zata finciko ni. Jin bata fincikonin ba na buɗe idanuna dana rumtse. Sosai na warosu waje dan mamakin ganin shine ashe ya tare hannun nata da nasa. Ai zumbur na miƙe kan ƙafafuna na. Cikin ƙara zaburowa ta ce, “Barni Awwab naci uban yarinyar nan da bata da kunya da mutunci. Ni ban san a ina Auta ta kwaso mana ita ba. Baka san abinda tai ba da baka tare ni ba. Abinci na bada a kai sashen Hajiya Babba da magungunanta kafin naje na bata shine na tadda shegiyar yarinyar nan ta amsa a hannu masu kuka da ita tana floshing ɗin tables ɗin a cikin toilet saboda ita cikakkiyar ƴar iska ce. Kai dole ne ma musan miya kawota gidan nan yau”. Ta ƙara kai min duka. Kasa motsawa nayi a yanzu. Dan sumar tsaye nayi a wajen da jin kalaman makirci da sharrin da take min. A take idanuna suka ciko da hawaye. Na cije lips ɗina sannan na kallesa. Kansa a ƙasa yake bashi da alamar cewa komai. Sai da na share hawayen da suka ziraro min sannan na ce, “Wlhy ba haka ban...” Bamm ta buge min baki da ƙarfi har sai da ya fashe. “Dan ubanki kina nufin ƙarya na miki ke nan. Lallai yau kam zanci ubanki a gidan nan. Anya kuwa yarinyar nan keba ƴar leƙen asirinmu bace ba ma? Ba wani ya turoki ba dan ki cutar da mu. Dan Ni ba'a taɓa fitsararriyar ƴar aiki tsagera mara kunya irinki ba anan gidan.” Cikin tura baki gaba na ce, “To ni dai Mammah ai bamma kowa rashin kunya ba sai wanda ya shiga harkarta. Ni kuma bana son ana min sharri akan abinda banyi ba. Kuma manya idan suna ƙarya mutuncinsu zubewa yake yi”. Ɗauu naji saukar wani marin mai azabar zafi da yafi na ɗazun a saman fuskata. Tsabar yanda ya shigeni har sai da jina ya ɗauke na wucin gadi. Ina ɗagowa ta sake ɗaga hannu zata ƙara min ya shiga tsakkiyar mu. Cikin silent voice ɗin nan tasa mai cike da ƙasaita ya furta, “Mammah it's enough.” Babu wanda mamakin jin abinda ya fito a bakinsa bai bayyana a fuskarsa ba. Duk da mafi yawansu sun san ba sabon abun bane gatsa magana kai tsaye daga garesa musamman idan yana a ɓacin rai, sai dai dalilin yin ta yau ɗin ce ta Bama kowa mamaki. Irin wannan tsawa haka. Cike da azabar masifa itama Hajiya Mammah ta daka masa tsawa. “Awwab!! Kana fa jin abinda shegiyar yarinyar nan ke faɗa har kake iya cemin ya isa. Ka barni na dawo da ita a hankalinta idan bata san matsayina a gidan nan ba ta sani da ga yau!”. Maimakon bata amsa ko barinta dani ɗin sai jinai kawai ya kama hannuna ya fara tafiya. Bani da zaɓin daya wuce bin bayansa. Tsitt falon babu wanda ya sake yin koda tari har muka shige ta hanyar nan data nuna min ranar na kai masa shayi.... ⭐💞⭐💞⭐ Rashin wucewar Gwaggo ya ɓata shirinsu Mom. Duk da dai ita dama Ummanta ce ke tausarta. Saboda tafi ganewa ta fito ayima duk wacce za'ayi amma Umman tace a'a subi komai a sannu suma fara sanin wacece yarinyar tukunna. Gefe kuma rashin jin daɗin jikinta ya hanata iya komai. Dan da gaske jinin nata ya hau ga ciwon kai da ƙirji mai tsanani dake damunta... A ɓangaren Halime amarya sai da aunty Zakiyya ta sakata gyara jikinta tsaff ta kuma ƙara tsaftace mata sashenta sannan ta wuce. Dan haka daga ita har sashen nata banda bulbula ƙamshi babu abinda sukeyi. Tayi fes da ita ƙyawunta da rashin kula ya ɓoye ya sake fitowa sosai. Duk wanda ya kalleta yasan tana cikin farin ciki da walwalar sabuwar rayuwar data tsinta kanta a ciki. Sai dai ta wani sashen zuciyarta rashin ganin Abba tunda aka kawota gidan na ɗan sosa ranta. Dan tun jiyan da suka iso bata sake ganinsa ba. Sai da safen nan da taji muryarsa yana gaida iyayenta dake falo. Tayi zaton zai nemeta amma sai taji shiru. Lokacin da ƴan uwan nata ma zasu wuce taji muryarsa a tsakar gida, sai dai kukan da take yasa batai yunƙurin kallon sashen da yake ba. Tunda kuma suka wuce bata sake jin motsinsa a cikin gidan ba. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke a hankali, sai kuma ta taɓe bakinta dan tasan zama ta iya ganin fiye da hakan kodan matar nan tasa a zababbiya. Jifa yanda aketa cin uwar sabada a gidan tun isowarsu jiya, a hakan ma tasan dan bata san itace matar da aka auro ɗin ba ma... Yanda take ta faman yamutse fuska da taɓe baki ya saka Abba dake tsaye a kanta tun ɗazun kasa daurewa ya saki murmushi. Sai kuma a hankali ya kai zaune kusa da ita yana mai kai hannu ya shafi fiskarta. Tsorata tayi, dan harga ALLAH bataji koda ƙamshin turarensa ba balle motsinsa. Dan haka ta miƙe a firgice zata ƙwala ihu. Da sauri shima ya riƙota yana mai ɗora hannunsa saman bakin nata tare da jawota gaba ɗayanta cikin jikinsa yana faɗin, “Calm dawn Halimatussa'adiyya please calm down ni ne”. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da numfashi a jajjere. Sai kuma taji duk kunya ta baibayeta. Ƙoƙarin zamewa tayi daga jikin nasa ya hana hakan ta hanyar sake matseta da ƙyau a cikin jikin nasa. A cikin kunnenta ya shiga raɗa mata, “Amin afuwa na tsorata amarya ko.” Halime babu bakin magana dan gaba ɗaya a kunyace take. Sai ma mutsu-mutsu da takeyi na son tashi shiko yaƙi barinta. Dole ta haƙura ta nutsu ganin bafa barin nata zaiyi ɗin ba dai. Sun kai tsahon mintuna goma a haka sannan Abban ya sassauta mata yana sauke tagwayen ajiyar zuciya tare da mannama goshinta da kan hancinta kisses. Ina ma ƙasa ta tsage Halime ta shige ciki dan kunya. Sai dai babu damar hakan dole ta haƙura tana faman cikuykuye kanta a jikinsa. Yanda take yi ɗin yay matuƙar saka Abba dariya. Dan haka ya shiga tsokanarta da raɗa mata wasu kalamai a cikin kunne da suka sake birkita mata lissafi... 💦★💦★💦 Muna shiga ya sakar min hannu. Ganin yana neman raɓani ya wuce nasha gabansa wani irin kuka mai ƙarfi na suɓuce min. Ƙin kallona yayi, ya sake raɓawa zai wuce ta side ɗin dama ta. Nan ma taresa nayi hannayena duka riƙe da ƙuguna. Tuni na cire duk wani tsoronsa da shakkarsa cike da tsiwa na ce, “Malam wai mi kake nufi da ni ne? Ka maidani gaban iyayena daka ɗakkoni bazan iya rayuwa a wannan gidan da ba'a san darajar ɗan adam ba”. Tamkar bazai kallan ba sai kuma ya yamutse fuska tare da sake tsuketa. Cikin gadara ya furta, “Ki gayama wanda ya kawoki. Sannan bana son rashin kunya”. Daga haka yay wucewarsa. Wani irin takaici da bakin ciki ne suka sake turniƙe ni. Tuni na shiga kokawar maida hawayen dake neman zubomin. Dole ne fa ayita yau ta ƙare dan bazan iya wannan zaman ƙasƙancin ba saboda ni ba jaka bace ba. Bazan taɓa zama a maidani yanda aka maida mahaifiyarsa ba. Kaina tsaye na nufi hanyar da yabi dan idanuna sun gama rufewa da masifa. Babu ko gezau a tare dani na bankaɗa ƙofar farko dana gani a wajen. Sai da zuciyata ta jijjiga saboda karo da abinda banyi zato ba. Da sauri na juya masa baya ina mai rumtsewa da ƙarfi, jikina har rawa yake dan tunda nasan kaina ban taɓa ganin namiji babba a yanda yake yanzu ba. Su Yaya Musaddiq ko da boxer da singlet basa zama a gida. Balle kuma ace daga su sai pant kamar yanda yake. Gashi a tsaye ƙyam da suffar ƙarfi dogo masha ALLAH. Bazan iya kallon wannan abin kunya ba, dan haka na fara laluben hanyar komawa inda na fito cikin sassarfa, amma sai hakan ya gagara. Maimakon kama handle ɗin ƙofa da nake lalube sai na damƙi lallausar fata mai santsin tsiya. Da sauri na cire hannun nawa tare da daka tsalle baya ina buɗe rumtsatstsun idanun nawa. Idanu huɗu mukai da shi, tsabar rashin kunya kuma yana a yanda na gansan. Sake juya baya nayi da sauri jikina na rawa. (Wannan wane irin fitsararren mutum ne haka wai) na faɗa a zuciyata ina ƙoƙarin riƙe numfashina da tsumar da jikina keyi........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ .......A bazata naji saukar muryarsa cikin kunnena. “Ba abinda kika zo gani ba kenan?”. Ya faɗa a hankali cikin daƙilalliyar muryar nan tasa. Bamma san lokacin dana juyo a fusace na ce, “ALLAH ya kiyaye sai kace wata ƴar iska. Kuma ni ka bani hanya na wuce”. Maimakon bani hanyar ko tanka min sai ya shiga matso ni. Baya na farayi hankalina a tashe, idanuna na fitowa gaba ɗaya waje. Shi kuma bai fasa biyonin ba har sai da muka dangane da ƙaton gadonsa dake a dunƙule tamkar zero. Ganin baida alamar dakatawa na faɗa saman gadon idanuna cike da ƙwalla. Gaba ɗayansa ya ranƙwafo kaina yay min runfa hannayensa duka biyu dafe da gadon ta gefe da gefe na. Kaina na shiga girgiza masa idanuna cike da hawaye. Kafin na buɗe baki da ƙyar cikin ƙarfin hali na ce, “ALLAH zan maka ihun da kowa na gidan nan sai yazo sashen nan”. Wani lalataccen murmushi ya saki da ɗage gira ɗaya sama. A hankali ya sake matso da furkarsa gab da tawa. Ai babu shiri na ƙanƙame jikina tare da rumtse idanuna na kauda fuskata gefe. Amma duk da haka ina jin saukar dumin numfashinsa akan fuskar tawa. Kafin cikin maganar raɗa a cikin kunnena ya furta, “Da kuwa kowa a yau yasan ke ɗin *_MATAR AWWAB EL-MU'AZZ MAASH_* ce. Idan kuma kin cika matsiwaciya dan ALLAH ki gwada ki mana”. Hannu nasa na ture fuskarsa batare dana buɗe idanun ba, sai kuma na yunƙura zan tashi dan ji nake tamkar an sakani a kuttun man shanu tsabar yanda kusancinmu ya dabaibaye ni. Da sauri na koma ina mai dafe kaina daya bugu da nasa. Tare da buɗe idanuna ina ɓata fuska tamkar zanyi kuka. Shima tashi fuskar a yamutse take hannunsa dafe da goshinsa alamar yaji zafi, ban san sanda na bushe da dariya ba tsabar jin daɗi. Ganin yanda ya zuba min idanu ya sani haɗiye dariyar na ɓata fuska da harararsa na ɗauke kaina gefe. “Baki da kunya ko?”. Ya faɗa cikin wani yanayi dana kasa fassarawa. Baki na sake murguɗawa fuskata a gefe a tunanina bai gani ba. Sai jinai ya furta, “Humm harara a duhu ai na mai tsoro ne. Idan kin isa kiyi ido cikin ido ni kuma zan banbance miki tsakanin aya da tsakkuwa. Bani phone ɗina”. Da sauri na juyo na kallesa danni nama manta da wani batun wayarsa a hannuna. Sai kuma na maida kaina gefe nace, “Ta ƙarfi ce. Kuma ni ka tashi min a kai, wannan ai rashin kun.....” na kasa ƙarasawa. Bai tashin ba bai kuma tanka min ba. Kusan tsahon mintuna biyu sai da ya mula dan kansa sannan ya miƙe kamar wanda akai ma ishara da hakan, dan da ƴar sassarfa ya bar wajen haƙoransa cije da lips ɗinsa. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, har ina kai hannuna na fara ma kaina fifita da shi dan sam ko sanyin acn dake ɗakin baya wani ratsani. Jin rufe ƙofa ya sani zabura, sai naga bathroom ya shiga. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sosai tare da miƙewa. Dan gwara nabar masa ɗakin kafin ya fito min a tsirara kuma tunda naga idanunsa ba kunyace a cikinsu ba. Turus na tsaya tamkar zan fasa ihu jin ƙofar a garƙame, a take naji sabon tashin hankali da hajijiya na neman kwasata, dan na fahimci ƙofar ya rufe kenan.... ⭐💞⭐💞⭐ Yanda take safa da marwa cikin ɗimuwa a ɗakin zai tabbatar maka da ranta a ɓace yake. Tabbas kuwa ran nata a ɓacen yake. Dan tunda take ba'a taɓa raina mata hankali irin na kwanakin nan ba. Musamman ma yau. Ranar Awwab ya gasa musu magana harda gorin gidan uwarsa ta tursasa kanta shanyewa batace komai ba saboda wani dalili. Yau kuma yarinya ƙarama tai mata rashin kunya da tsallake dokarta shi kuma ya mata tsawa ya kuma hana ta hukuntata. Kowa fa a gidan nan tsoronta yake ji, amma har yau a samu yarinyar da zata ƙaryatata a gaban ƴan aiki da ƴaƴanta. Lallai sai ta ajiye lesson mai ƙarfin gaske akan yarinyar nan. Kai hatta da Awwab bazata ƙyale ba saboda goyan bayan yarinyar ta fahimci yake yi. Ai ba yau ta fara cin uban ƴan aiki a gidan ba. Kuma ko yana zaune a wajen take yi ɗin ko ɗaga kai ya kalla baya yi ma. Amma ta kula akan yarinyar nan yana neman kawo musu wani sabon salo. Jiba randa Hajiya Babba ta daketa, ɗaukartafa ya dinga yi harda ɗorata a jikinsa yay treating nata da kansa. Kai ita fa gaba ɗaya ma kanta ya kulle. Waya ta jawo tai kira. Ana ɗagawa ko sallama bata tsaya yi ba ta fara magana cikin damuwar dake tabbatar da ɓacin ranta. Abinda ya faru tun daga randa aka kawo Samraah gidan take sanarma wadda ta kira har zuwa yau ɗin nan. Sai kuma tai ɗan jimm alamar sauraren abinda na can ɓangaren ke cewa. Tsawon kusan mintuna uku kafin ta saki murmushi mai ƙayatarwa, tare da furta, “Kai amma na gode Hajiya Rubayya, Please kiyi maza ki shigo ina saurarenki. Dan wannan shawarar taki na fara jinta a jikina ƙwarai da gaske.” ajiye wayar tai tana sakin dariyar nasara. Sai kuma ta miƙe tamkar ba itaba ta fara zame kayan jikinta cike da nishaɗi. Tana kammalawa tiɓi-tiɓi ko kunyar kanta bata ji ba ta nufi bathroom ɗinta a haka da alama wanka zatayi..... 💞💞💞💞 *_INDIA_* Kuka take sosai da ƙoƙarin riƙe hannunsa daga haɗa kayan da yake tayi. Sai dai ko kallon inda take baiyi ba balle ya dakata da abinda yake ɗin. Cikin matsanancin takaici da fusata Attahir da ya gama harzuƙa da abinda ke faruwa ya fisge jakar yana mai dakama ƙanin nasa tsawa. “Mansoor are you mad ne wai?”. “Yes! I'm. Na ce I'm!. Ba haka kuke son ku ganni ba. Ko ba haka kukafi buƙatar ganina ba?. Nace muku ga wadda nake so, kun rabani da ita batare data ma wani cikinku laifin komai ba. Duk da abin yana min ciwo har yau har gobe ban taɓa ce muku komai ba. Amma hakan bai muku ba kuma sai ace min wai ga mata an ɗaura min aure da ita. Tunda nake da ku na taɓa ce muku ina son wannan yarinyar ne? Wlhy da nayi rayuwar aure da wannan yarinyar gara na shiga duniya. Na gaji da wannan rayuwar haka nan haba. Sai kace ba jininku bane ni, yaya kuke so na cigaba da rayuwa cikin salama ns wa....” kuka ya sarƙesa ya kasa cigaba da magana. Sai ma zubewa da yay a saman gadon yana mai dafe kansa dake sara masa da duka hannayensa biyu, tare da cusa hannunsa cikin sumarsa ya yamutsata. Sosai jikinsu ya sake yin sanyi. Musamman Mamy da tafi kowa kasancewa a cikin ɗimuwa. Itama zubewa tayi a gaban Mansoor ɗin tare da kamo hannayensa cikin nata tana sake fashewa da kuka. Dad ne da tun ɗazun baice komai ba ya furzar da iska mai kauri daga bakinsa, tare da kai hannu saman kansa ya shafo. Sosai kukan Mamy da Mansoor ke cizon zuciyarsa. Sai dai shi baima san ta inda zai fara ba game da wannan hargitsi daya rasa tushensa balle iyaka..... Kakarin da Mansoor ya fara ne ya maidosa a hayyacinsa. Kusan a tare shi da Attahir suka zabura kansa. Yayinda Mamy ta sake ɗimaucewa. Yunƙurin amai ya fara sai ga jini bula. Ihu Mamy ta fasa, yayinda Attahir ya fita a guje yana faɗin bari yay kiran asibiti... Kafin cikar mintuna goma ambulance ta iso. Lokacin da aka fito da Mansoor daga ɗakin hotel ɗin da suke ya gama fita a hayyacinsa. Dama yau kwana uku kenan da sallamosa baya kwanakin kusan wata guda daya kwashe yana jiyya. Samun lafiyar tasa ya saka walwala da farin cikin kowa dawowa a cikin ahalin nasa. Dan nan da kwanaki biyu ma suke shirin komawa gida Nigeria. Sai kuma aka samu akasi Husnah yarinyar Auntynsa da aka ɗaura masa aure da ita a randa aka fasa da Samraah dake Dubai ta ɓaro musu aiki tai kiransa a waya. Kalaman da tayi amfani da su a wajen gaisawar tasu ya sakashi neman fashin baƙi a wajen yayansa Attahir. Shi kuma batare da tunanin komai ba ya buɗe masa zancen cewar ai da gaske Husnah ɗin take an ɗaura mata aure da shi a randa aka fasa da Samraah. Wannan shine dalilin rikicin na yanzu, ga shi kuma da alama aiki ya koma baya..... 🌜🌟🌛 Ina nan tsaye abin duniya duk ya isheni ya buɗe ƙofar bathroom ɗin alamar zai fito. Koda gigi ban yarda na kalla wajen ba balle ma na saka kaina a uku. Har tsawon mintuna uku ina ɗan jin motsinsa cikin yanayin rashin hayaniya. Cikin ƙarfin hali da dakiyar zuciya na ce, “Ni ka buɗe min ƙofa na fita bana son taɓara”. Shiru babu alamar zai amsa min, daurewa nai na sake maimaitawa cike da tsiwa. Nan ma banji alamar zai kulani ɗin ba. Sai kawai na taune lips ɗina ina jin kamar naje na rufesa da duka. Tsahon mintuna goma ina dai wajen a tsaye ban juya ba ban kuma gusa ba. A bazata naji sautin muryarsa a bayana. “Bani phone ɗina”. Da sauri na juyo har ina buge hannu da ƙofa. A tsayen kuwa yake ƙyam a bayan nawa shantali guda dashi, dan duk nawa tsawon sai na ganni ɗis a gabansa. Ga fuskarsa a tsuke babu alamar wasa tattare da shi. Duk da yanda naji zuciyata ta motsa na tsorata sai na dake nima ina mai tsuke tawa fuskar tamau harda su hura hanci.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_ ......Matsawa nayi baya ina kumbura fuska. “To ka buɗe min mana ba tana sashen Ummie ba. Oh Hajiya Babba”. Nai saurin gyarawa saboda kallon da naga ya wani kafeni da shi. Kamar bazai tanka min ba sai kuma a daƙile kamar an masa tilas ya ce, “Miya kaita can?”. “To ina ruwanka, kai dai ka matsa naje na ɗakko maka”. Shiru bai matsa ba ya dai zuba min ido kawai. Sai da ya mula dan kansa sannan ya sake furta, “Da gaske abinda Mammah ɗin ta faɗa kenan?”. Karon farko na ɗago na kallesa. Dan yanda yay maganar a dakensa ba ƙaramin tsargani yay ba. Idanuna cike da ƙwalla har muryata na rawa ma na ce, “Miye ribata idan na aikata zalunci akan baiwar ALLAHr da bataji ba bata gani ba. Idan har zan iya cutama Ummie nima zan cutar da tawa mahaifiyar kenan idan tana raye. Ko an faɗa maka kowa ma irinka ne da kansa kawai ya sani sai kuma neman dukiya baya taɓa waiwaye da tuna bayansa. Ka saki hakƙokin wadda inda kaine a kwatankwacin halin da take ciki ko barcin mintuna bazata taɓa bari ya ɗauketa cikin daɗin rai ba saboda damuwa. Dan zata iya sallama komai da komanta dan ganin ka samu ingantacciyar rayuwa da kulawa da lafiya. Na tabbatar wlhy bazata taɓa barinka cikin yunwa ko datti ba. Bazata taɓa miƙa ragamar kulawa da kowane motsinka a hannun masu aiki ba. Koda zataje inda kake ka raunatata koma ka sumar da ita gobe bazai sakata fasa sake zuwa inda kake ba dan ta dubaka. Ina mai baka shawara a wannan gaɓar da kada kayi sakaci da damar da UBANGIJI ya baka ta neman aljannarka a ƙarƙashin kulawa da mahaifiyarka. Ku tausayama baiwar ALLAHr nan dan ALLAH ku nutsu ku fuskanci halin da take a ciki. Idan ba hakaba watarana kaine zakai kuka da dana sani mara adadi dan su waɗan nan da sukazo suka cika gida suna ci daga arziƙin da UBANGIJI ya bata suna fankama da hura hanci ko a kwalar rigarsu maybe ma basu ƙi ta kwanta ta mutu ba ko ta dawwama a haka cikin halin lalura dan komai ya zama nasu.....” “Your are vary stupid!!”. Ya faɗa cikin katseni da daka tsawa. A take kuma idanunsa suka jirkice ƙwayar tsakkiya ta koma siririya, zaibar ta sake duhu exactly na maguna dai musamman idan suna a cikin hasken rana. Har cikin raina naji tsawar tashi ta ratsa ni, a take kwarjininsa da shakkarsa suka sake dabaibaye ni har na gagara sake magana. Sai da ya buɗe ƙofar a fusace ya fice sannan na sauke nannauyar ajiyar zuciya ina mai rumtse idanuna. Lallai wannan mutumin yayi nisan da bai jin kira. Sannan akwai abinda ya kamata na sani dan na fahimci sam baya son abinda zai taɓa ahalinsa kenan. To lallai babbar magana. Dan ni inaji a jikina lallai akwai ɓoyayyen al'amari mai cike da darasi a ƙarƙashin ciwon mahaifiyar nan tasa. Amma in sha ALLAHU koma minene ni *_SAMRAAH ABDULL-WAHAB GWARZO_* nayi alƙawarin sai na bankaɗosa. Uban kowa sai ya kwashi kashinsa a tafin hannunasa cikin MAASH MANSION.. (Tofa babbar magana. ALLAH ya bada nasara Kandala🥱). Cikin cije baki da tabbatar da alwashina na nufi ƙofar nima. Dan nayi alƙawarin bazan sake bari mutumin nan yaga gazawata ba duk da ina jin shakkar tasa. Abincin rana dana tuna shine dalilin fitowata na ɗibama Ummie yasa hankalina tashi. Harna nufi hanyar barin sashen na fasa, dan sama-sama na ke jiyo magana ata falo. Falon na nufa, acan ɗin kuwa na samesa tare da ɗan kaɗafin PA ɗinsa. Yana zaune hannayensa duka dafe da kansa alamar akwai abinda ke damunsa ko kuma kan nasa na masa ciwo ne oho masa, PA ɗinsa tsaye ata gefensa cikin tsaiwar nuna girmamawa da alama magana yake masa. Ina fitowa yay shiru. Harara na watsa masa dai-dai muna haɗa ido. “Barka da rana ranki ya daɗe”. Ya faɗa dai-dai ina isowa inda suken. Wani ƙululun takaici ne naji ya shaƙuremin maƙoshi. Sai dai na danne na watsar da banza tamkar ma banjisa ba. Ledojin dana gani a gaban ogan nasa da bana raba ɗayan biyu abincine na ɗauka. Harna ɗauka ɗaya na sake tattaro sauran biyun ma na kwashe. Dai-dai na ɗago zan bar wajen PA ɗin nasa ya ce, “Ranki ya daɗe ɗaya ne extra, sauran na Boss ne”. “Ko zaka ƙwatar masa?”. Na faɗa a kausashe ina watsa masa wani shegen kallo. Da sauri ya girgiza kansa da faɗin, “A'a ayi haƙuri”. Tsaki naja mai ƙarfi, ina sake balla musu harara su duka biyun. Sai dai har yanzu kan ogan nasa na ƙasa bai ɗago ba, tamkar ma bai san mike faruwa a falon ba. Nima ba shine a gabana ba, dan haka nai gaba abina ina jan tsaki mai ƙarfi.. ★Tana shigewa Hayatu dake kallon ogan nasa da tunanin zaice wani abu amma babu alamar hakan ya sauke ajiyar zuciya. Cike da kulawa da girmamawa ya ce, “Sir bari to na samo maka wani abincin tunda ta ɗauke wannan ɗin duka ko?”. Shiru kamar Maash ɗin bazai tanka ba. Dan har Hayatu ya fidda rai da samun amsa sai kuma ya ga ya ɗago ya kalla hanayar da tabi, ɗauke idanunsa yay ya maida ga Hayatun. Cikin yanayin nan nasa a daƙile ya furta. “Barshi kawai. Kaje ku ƙarasa abinda zakuyi. Ina sake gargaɗin ko su Juliet kar su san ina ƙasar nan yau.” “In sha ALLAHU zan kiyaye Sir. Amma idan mun tafi yau wazai dinga samo maka abinci? Ko dai nayi magana da gidan abincin kullum su dinga kawo order sau uku har cikar sati ɗayan”. Shiru kamar bazai ce komai ba. Sai kuma miya tuna oho. A hankali ya furta, “Kayi hakan”. Cikin jin daɗi Hayatu ya ce, “A huta kafiya”. Duk da yana mamakin ogan nasa akan daina cin abincin gidan a ɗan tsakanin nan bazai iya tambayar dalili ba. Dan tun washe garin birthday party ɗin Ummie ya sallami kukunsa dake masa girgiki, duk da ma dai ba ko yaushe bane yake cin abincin nasa yana cin na can cikin gidan a wasu lokutan musamman idan Aunty Mama na gari... 💞⭐💞⭐💞 Tunda suka idar da sallar kanta ke a ƙasa ta gagara ɗagowa ta kallesa. Yayinda shi kuma ya kafeta da idanunsa cike da nazari. Ganin yanda ta takure kanta waje ɗaya ya sashi ɗan sauke ajiyar zuciya. Kafin a hankali yay kiran sunanta.. “Halimatussa'adiyya”. Da ƙyar ta iya ɗagowa tana amsa masa da, “Na'am”. Dai-dai suna haɗa ido. Saurin maida kanta tai ta sunkuyar. Murmushi ya saki da sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya gyara yanayinsa cikin kame kai ya ce, “Wanene ni a wajenki?!”. Kasa cewa komai tayi, sai da ya sake maimaitawa. Muryarta na rawa tana sake sunkuyar da kai a hankali ta ce, “Baba!”. Murmushi yay mai faɗi tare da girgiza kansa. “Halimatussa'adiyya ni ba babanki bane. Mijinki ne ni, nasan kuma kin sani.” Kanta ta sake sunkuyarwa alamar dai ta san haka ɗin ne. Shima sai ya cigaba da faɗin, “Halimatu nasan ke mai tarbiyya ce da ilimin addini gwargwado. Dan naje har tushenki naga gidan da kika fito. Kema a karan kanki a ɗan zamanki cikinmu gidan nan na tabbatar da hakan. Fatana dai ALLAH yasa abinda na gani yasa ya ɗore har abada. Zuwa yanzu kema nasan kin san gidan da kika shigo. Kin kuma san wanda kika aura. Ni ba yaro bane ba, inada ƴaƴa biyu maza Musaddiq da Abbas da suka girme miki, inada ƴaƴa biyu mata Samraah da Sakina (Baby) da zaku iya sa'anni, inada waɗanda zaki iya girma Hafiz, Nabil, Habiba auta Jamal. Ina roƙonki dan ALLAH ki zauna lafiya da su, ki jasu jikinki matsayin uwa. Kada kiyi dubi da matsayin wadda suka girma ko kuke sa'anni. Mahaifiyarsu karki damu da abinda ke tsakanina da ita. Ki zauna da ita lafiya ki bata girmanta. Dan ALLAH duk wata hanya da zata zama ta raini a tsakaninku kada ki buɗeta. Ni kuma na miki alƙawarin in sha ALLAHU zan ƙare miki mutuncinki tako wane ɓangare. Nima na baki amanar kaina. Ki riƙeni da hannu biyu Please Halimatussa'adiyya. Dan ni da ke duk marayune”. Cike da mamakin jin kalmar Maraya daya kira kansa yadata ɗagowa ta kallesa. Cikin lumshe ido ya jinjina mata kansa. “Hakane Halimatu, nima maraya ne da babu uwa babu uba sai Gwaggo na kawai da ku da ALLAH ya bani matsayin iyali, sai ahalina na Gwarzo da sai a hankali zaki san kowa da kowa”. Kanta ta jinjina masa, sai kuma takai hannu ta share hawayen da suka zubo mata. Murmushi ya saki tare da mika mata hannunsa na dama yana faɗin, “Zo nan”. Da ƙyar ta iya motsawa zuwa gabansa, sai dai tabar ƴar tazara a tsakaninsu. Dan haka ya kamo hannayenta ya jawota sosai ya manna da jikinsa. Zata noƙe ya sake mannata da jikin nasa tare da zame hijjab ɗinta ya ajiye gefe. Ledar takeaway daya shigo da ita ya jawo gabansu. Ta gefen ido Halime take satar kallon dankareriyar kazar da ƙamshinta ya gama cika ɗakin. Yawu ta haɗiya zuciyarta na zallo, sai dai kunya ta hanata yin ƙwaƙwƙwaran motsi. Cike da kulawa Abba ya ɗiba naman ya kai bakinta. Babu musu ko kwana-kwana ta amsa sai dai idanunta a rufe dan kunya. Shi dai Abba dariyama ta bashi, amma ya danne abarsa. Sai da Halime tai nak da naman kaji da yogurt sannan ta kauda kanta.......✍️ 🥱Gara da kikaci abinki Aunty Halime😂😜. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_ .......Rashin kowa a falon ya bani damar haurawa saman hankalina a kwance. Sai da na sauke ajiyar zuciyar jin daɗi saboda samun Ummie a yanda na barta tana barci. Ledojin abincin na ajiye gefe, na nufi bathroom nayo alwala. Sai da na gabatar da sallar la'asar sannan nai zaman yin karatun Alqur'ani da ka dan babu Alkur'anin a sashen. Tun ina karatun naji shigowar saƙo a wayarsa dake a hannuna. Ban maida hankali ba har sai da na kammala surar da nakeyi ta Baƙara. Kammalawa ta dai-dai da farkawar Ummie, dan haka na nufeta da sauri ganin tana fisge-fisge tamkar wadda ta farka a firgice. Riƙota nayi a jikina ina karanta mata addu'oi, a hankali-ahankali sai ta fara lafawa. Shiru kusan mintuna biyar kuma ta buɗe idanunta tana kallona. Murmushi na sakar mata, kafin a hankali na ce, “Ummie zaki ci abinci?”. Sai da tai ɗan jimm kamar bazata amsa min ba, sai kuma a hankali ta motsa lips ɗin ta ta ce, “Muhammad yunwa”. Murmushi na ƙara mata idanuna cike da ƙwallar tausayinta. Da taimakona ta ɗan tashi zaune, kamar ɗazun na jinginata a jikina da kaina na dinga bata abincin. Abin tausayi yanzun ma sai taci sosai, hakan ya sakani jin farin ciki, na bata ruwa ta sha, batare da tace min komai ba ta koma ta kwanta kanta a saman cinyata, cikin lokaci ƙanƙani barci ya sake kwasheta. Murmushi na saki ina mai rungumo kan nata a jikina, tsawon lokaci ina hawaye kafin na barta saboda sake shigowar saƙo a wayarsa dake hannuna. Wayar na ɗauka, fuskata a taɓe na buɗe saƙon. _(Ko zan ƙare rayuwata a bibiyar taka rayuwar bazan taɓa gazawa ba ko ƙosawa da hakan tauraron duniya. Zan kuma cigaba da roƙonka ka taimaki rayuwata ka aureni koda na wata ɗaya ne. Wlhy na maka alƙawarin maka hidima tamkar baiwa da uwargijiyarta. Kuma koda kullum kake dukana da zagina bazan taɓa daina sonka da maka biyayya ba Gwarzona.)_ wannan shine saƙon farko da aka turo tun ɗazun. Baki na taɓe tare da jan tsaki sannan na buɗe na biyu. _(Ka taimaki rayuwata Tauraron duniya. In ma bazaka aureni ba ko kwanciya kayi dani koda sau ɗaya dan ALLAH kozan rage ƙishirwarka)_ “Kitttumelecy kice ɗan iska ne ashe shima, shiyyasa yayta wani fiki-fiki da idanu uwa na kifi tarwaɗa, kamar wani ustazun ƙwarai hummm” na faɗa a fili bayan na ƙare karanta saƙo na biyu. Ai tini na shiga komawa sama ina karanto na tun daga farko, kaɗanne da alama ana gogewa, ko sau ɗaya kuma bai taɓa bada amsa ba. Koda yake munafukin maybe gogewa yake. Fitowa nayi na shiga masa bincike a messages ɗin nasa, sai gashi na ci karo da wanda sukafi nama farkon ƙazanta daga ƴammata da ban da ban. Ina cikin karanta wani daya firgitani matuƙa dan har na gagara daurewa ina surutai fittt naji an fige wayar. Da sauri na juyo nima a firgice. Sai kawai na gansa tsaye a kaina ƙiƙam yana faman mazurai, fuskar nan tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa. Sai da ya kalla wayar sannan ya sake ɗagowa yana watsa min wani kallon dana kasa bama fassara. Baki na murguɗa masa tare da gallara masa harara nima na ɗauke kaina na maida kan Ummie dake kwance kanta a saman cinyata. Ya daɗe tsaye a kammu batare dana san mi yake yi ba dan ban sake ɗagowa na kallesan ba nima. Kafin ya kai durƙushe gaban mahaifiyarsa ya ɗan ranƙwafo kanta yana mai kai ƙyaƙyƙyawan hannunsa mai ɗauke da dogayen fararen akaifa saman fuskarta ya shafa. Ɗan ɗagowa nayi na kallesa, a mamakina sai naga kamar ƙwalla a cikin idanunsa. Jinai tsigar jikina ta tashi, da sauri nai azamar ɗauke kaina ina sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Saukar hannunsa akan nawa dake a saman kanta ya sani juyowa na sake kallonsa, dai-dai nan ya ture min hannu ya maye nasa a gurbin nawan yana shafa kitson da nayi mata. Baki na tura nima na ture nasa hannun ina harararsa. Ɗagowa yay ya kalleni cikin yanayin kamar harara shima. Sai kuma ya sake ture nawan, ban bar masa ba na sake ture nasan nima ina hararar tashi. “K baki da kunya ko!”. Ya faɗa a dakensa a daƙile kuma. Sai da na taɓe baki sannan na ce, “Yo ni rashin kunyar mina maka. Bana rigaka ba kazo kana nemana da faɗa alhalin ban kulaka ba. Kaje kaji da ƴan iskan ƴanmatanka kwartaye ma ya isheka tunda ba'a gayyaceka ba anan ɗin” Wani irin kallo yake min da ya saka tsigar jikina tashi gaba ɗaya. Bamma san sanda na murguɗa masa baki da gatsinawa ba na janye nawa idanun da ƙyar. “I will teach you to be smart”. Ya faɗa a lalace yana ɗauke kansa. “Ka fara koyama kanka da ƴan iskan ƴammatanka”. Na bashi amsa nima ina ɗauke nawa kan gefe. Daga haka shima ya miƙe tsaye batare daya sake kulani ba. Nima sai ban sake kulashin ba har ya gama dube-dubensa a ɗakin ya fita... 💫💫💫💫💫 Baƙuwar Hajiya Mammah ta iso. Kasancewar kowa yasan ita dama baƙinta ba'a saukarsu a falon ƙasa yasa Mama Balki mata rakkiya har can sama na part ɗin Hajiya Mammah ɗin. Sannan ta koma ta kawo kayan motsa baki. Ta ajiye tana ƙoƙarin fita cike da isa Hajiya Mammah ɗin tace ta turo mata yarinyar nan. Ɗan jimm Mama Balki tayi na shakku, sai kuma dai a ɗarare ta ce, “Tana a sashen Hajiya Babba Alhaji ƙarami ya sakata aiki”. Dan gara ta faɗi haka ɗin kafin wani yazo mata da gulmar sake ganin Samraah a sama abin ya zama babbar matsala. Shiru Hajiya Mammah bata amsa ba. Sai dai fiskarta ta nuna tsantsar ɓacin ranta. Fahimtar hakan yasa baƙuwarta sallamar Mama Balkin. Tana fita ta kamo hannun Hajiya Mammah ɗin cikin nata. “Relax mana Hajiya Nafee. Ina gaya miki a koda yaushe ki ɗan dinga controlling fishinki akan al'amarin gidan nan. Ki daina barin ana gane miki haka da wuri musamman ma masu aikin nan naku munafukai. Yanzu dai ina son kimin bayanin mike faruwa?”. Shiru kamar Hajiya Mammah bazatayi magana ba. Sai kuma cikin ƙunar rai ta shiga ma aminiyar tata bayani tun daga farkon zuwan Samraah gidan har kawo yau ɗin nan kamar yanda dai ta sanar mata ta waya. Ƙawar tata ta jima batace komai ba alamar nazari, kafin ta saki murmushi da kallon Hajiya Mammah. “Ni ina ganin mafitace tazo mana ai akan yarinyar nan. Za muyi amfani da ita dan ta zame mana zaren ƙulla auren Awwab da Azizat. Kinga cikin sauƙi kema zaki samu cikar burinki”. “Ban fahimceki ba Rubayya. Ita wannan abar har wacece ita da zata zama zaren cimma burukana? Sai dai burin kore ƙishi”. “Yamzu kuwa zaki ji. Badai kince yarinyar na shishshige masa ba? Sannan tana shigema uwarsa duk da wahalar da taci a hannunta?”. “Hakane”. “Wannan salon nata shine ai makamin namu. Dan dashi zamuyi amfani da ita mu sarƙo wuyan shegen yaron nan mai taurin kai da rashin mutunci. Yanda yake nuna shi mata basa gabansa da ita zamu tabbatar ma duniya munafunci ne.” “Kinfa san bana son kwana-kwana a zance Rubayya. Fito fili ki faɗa min inda kika nufa dan ni ban fahimci komai ba”. Dariya sosai Hajiya Rubayya ta saki harda ƙyaƙyƙyewa. Kafin ta ce, “Daɗina dake rashin haƙuri Aminiya. Bari to na kaiki. Fyaɗe zamu saka ya mata na rashin imani. Mu kuma mu dinga masa barazanar yaɗa zancen ta yanda sai ya tsani kansa. A cikin tsakiyar rikicin muyi duk yanda zamuyi ya auri Azizat. Inada tabbacin bazai mana jayayya ba a lokacin dan bashi da wata mafita neman ma wajen tsira yake yi..” “Humm to idan kuma yarinyar ta samu ciki fa? Ko kuma shi ya ce zai aureta saboda faruwar al'amarin?”. “Mu dama ai cikin muke buƙatar ma ace ya matan. Dan aikinmu zai fi tafiya dai-dai. Idan kuma yace ma zai auretan mu dai-dai ne. Hakan kuma zai sake ƙarfafa aikinmu.” “Ta yaya?”. “Idan yace zai aureta kuma ga ciki ai dole dai zai bari ta haihu. Ku kuma ai ba yarda zakuyi ba matsayin iyaye musamman ma ke. Mu kuma zamuyi amfani da hakan mu zubar da cikin, a wajen zubar da shi zata bar duniyar. Sabon zance zai tashi akan shine ya kasheta, dama zuwa lokacin Azizat na tare da shi. Sai muyi amfani da wannan rikicin da yanayin da zai shiga shi da sauran mutanen gidan naku kema ki samu cikar burinki, fatanmu dai ace lokacin Azizat nada ciki ko ƙarami ne. Amma kidai zauna kiyi tunani. Sai dai fa dole ki rage wasu abubuwan ki sake jawosa jikinki fiye da kowa a gidan nan. Ta yanda idan komai ya ƙwaɓe ke kaɗai zai dinga tunkara ko tattauna damuwarsa. Itama yarinyar haka. Amma ɗan ALLAH ki shanye maitarki a kanta nasanki da ƙananun yara baki da haƙuri”. Sosai Hajiya Mammah ta sauke ajiyar zuciya. Sai kuma tayi ɗan murmushi da faɗin, “Tabbas shawarar nan taki tayi Rubayya. Sai dai kuma kin san dai akwai matsala. Dan halin Awwab ba ɓoyayye bane akan duk wanda ke mu'amala da gidan nan. Tayaya muke tunanin zai yima yarinyar nan fyaɗe cikin sauƙi yana a hankalinsa. Kai ƙo wata ƙwaya muka bashi bazai yiba kema kin sani tunda mun taɓa gwada hakan. Ni wlhy zuwa yanzu ma gani nake kamar yaron baida isashen lafiyar mazantaka”. Dariya sosai Hajiya Rubayya ta sheƙe da shi harda ƙyaƙyƙyewa. “Kina bani dariya Aminiyata. To wlhy bari kiji lafiya garas yake. Matsiyacin taurin zuciyane kawai ke ɗawainiya da shi. Kin san fa yaron namiji ne ɗan gaske. Akwai aji da girman kai ga miskilancin jaraba. Ai irinsu koda sha'awar mace zai kashesu wlhy ko'a fuskarsu bazaki taɓa ganewa ba sai idan sune suka so. Tabbas desire tablets bazasu biya mana bukata ba. Wajen mutumina kawai zamuje ya banko masa yasin da manya-manyan aljanuns.....” “Nifa kin san bana son wannan sabgar Rubayya ko”. Hajiya Mammah ta faɗa cikin katseta da sauri. Baki Hajiya Rubayya ta taɓe da faɗin, “Okay to nikam na barki lafiya. Sai ki nema wata hanyar dan kin san dai wanene wannan yaron. Kuma badan munje inda kike gudunmawa ɗin ba ai da baki samu biyan buƙatar farko akansa ba da waccan shegiyar matar yayan naki”. Riƙota Hajiya Mammah tai tana bata haƙuri, da ƙyar ta haƙura ta dawo suka cigaba da tattaunawa. Daga ƙarshe suka ɗauki hanyar data zama sanadin alaƙantasu har suka zama aminan juna.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_ .......Bayan fitowarsa ya jima tsaye a ƙofar ɗakin yana kallonta batare da ta sani ba, kamar ɗazun ma sai da ya jima tsaye tun tana bama Ummie abinci batare data sani ba sannan ya shigo. Dan yana fita ta cigaba da karatun Alqur'ani tana tofama Ummie. Wata irin bahaguwar ajiyar zuciya ya sauke tare da kai yatsarsa babba ta wutsiyar idonsa alamar ɗauke hawaye. Sai kuma ya cije lips ɗinsa da sakin wani mitsitsin murmushi da ba lallai ka fahimci yayi ɗin ba sai in ka kasance mai lura. Juyawa yay a hankali cikin yanayin mutuwar jiki yabi ta hanyar daya shigo. Koda ya shiga sashen nasa kai tsaye bedroom ɗinsa ya wuce. Yay tsaye gaban dressing mirror ɗinsa yana ƙarema kansa kallo kawai. Tamkar abin almara ya dinga ganinta tana masa gizo ta cikin mirror ɗin. Kasa motsawa yayi, sai ma sautin muryarta da amsa kuwwar kalamanta ke maimaita kansu cikin kunnensa tamkar yanzu take zano masa su da mitsitsin bakinta na rashin kunya. _(“Miye ribata idan na aikata zalunci akan baiwar ALLAHr da bataji ba bata gani ba. Idan har zan iya cutama Ummie nima zan cutar da tawa mahaifiyar kenan idan tana raye. Ko an faɗa maka kowa ma irinka ne da kansa kawai ya sani sai kuma neman dukiya baya taɓa waiwaye da tuna bayansa. Ka saki hakƙokin wadda inda kaine a kwatankwacin halin da take ciki ko barcin mintuna bazata taɓa bari ya ɗauketa cikin daɗin rai ba saboda damuwa. Dan zata iya sallama komai da komanta dan ganin ka samu ingantacciyar rayuwa da kulawa da lafiya. Na tabbatar wlhy bazata taɓa barinka cikin yunwa ko datti ba. Bazata taɓa miƙa ragamar kulawa da kowane motsinka a hannun masu aiki ba. Koda zataje inda kake ka raunatata koma ka sumar da ita gobe bazai sakata fasa sake zuwa inda kake ba dan ta dubaka. Ina mai baka shawara a wannan gaɓar da kada kayi sakaci da damar da UBANGIJI ya baka ta neman aljannarka a ƙarƙashin kulawa da mahaifiyarka. Ku tausayama baiwar ALLAHr nan dan ALLAH ku nutsu ku fuskanci halin da take a ciki. Idan ba hakaba watarana kaine zakai kuka da dana sani mara adadi dan su waɗan nan da sukazo suka cika gida suna ci daga arziƙin da UBANGIJI ya bata suna fankama da hura hanci ko a kwalar rigarsu maybe ma basu ƙi ta kwanta ta mutu ba ko ta dawwama a haka cikin halin lalura dan komai ya zama nasu.....”)_ Da ƙarfi ya rumtse idanunsa cikin wani irin yanayi. Sai kuma ya kai hannunsa saman kwantaccen gashin fuskarsa ya shafa, hoton Ummiensa a yau cikin tsafta da cikar kamala na dawo masa. Wata sassanyar ajiyar zuciya ta kufce masa, sake tuno lokacin da take bama Ummie abinci yayi. Sosai tsigar jikinsa ta shiga mimmiƙewa tuna yanda Ummien ke amsa a yanayin buƙata. Kalamanta ne suka shiga sake dawo masa. Da ƙarfi ya kai hannunsa ya harbar da kayan saman mirrorn tare da faɗin, “I hate myself Ummie! I hate myself!!”. Yanda yay maganar cikin ƙaraji jikinsa har rawa yake yi. Tunda yake ba'a taɓa faɗa masa kalaman da suka tada masa hankali irin na yau ba. Cikin ƙanƙanin lokaci jijiyoyin kansa da gashin jikinsa duk suka miƙe. Tuni idanunsa sun jirkice sun koma golden maimakon blue. Sake dunƙule hannunsa yay ya kaima mirror ɗin naushi. A take ya shiga tsagewa. Sake kai masa naushin yayi. Sai ga jini ta gaba ɗaya bayan yatsun alamar yaji ciwo. Bai damu ba, sai ma hannuwan da ya kai gaba ɗaya saman kansa dake wani kalar mahaukacin sara masa ya dafesa gaba ɗaya, jiyay gaba ɗaya ɗakin na juya masa. (Wannan ba sabon abu bane a garesa. Aduk sanda zai zurfafa tunani ko damuwa da al'amarin mahaifiyarsa ko san ɗaukar mataki akan wani abu da bai masa ba game da ita tofa sai ciwon kai. Sai kuma hankalinsa ya gushe gaba ɗaya. Idan kuma ya farko shike nan ya manta komai bazai sake tunawa ba ko magana ko maida hankali akan wani abinda ya shafeta). Yanzun ma dai zubewa yay a kan gadon, tare da cure jikinsa waje guda wani kalar masifaffen sanyi na ratsa illahirin ƙasusuwansa, sai zazzaɓi mai masifar zafi da nuƙurƙusar ɓargon jiki.... 💥💥💥💥💥 Nutsuwar data samu game da shawarar Hajiya Rubayya ya sata ajiye batun hukunta Samraah. Sai ma zuciyarta data gama tsara mata fara shirinta a yanzu. Zuciyarta fes ta fito falon. Arwa da Muhsin kawai ta samu a falon suna kallo. Sai masu aiki dake ɗan kai kawo na tsaftace sa duk da babu wani datti. Komawa tayi da baya zuwa ɗakin Azizat. Kwance ta sameta da waya a hannu tana charting, sai Bahijja dake cikin closet ɗinta tana maida kayan data watso ƙasa. Batare data kalla uwar tata ba ta ce, “Mammah any problems?”. Maimakon taji haushin yanda Azizat ɗin tai magana a tsaitsaye sai ma tai murmushi. Cike da kulawa takai zaune a kusa da ita tana shafa kanta. “Babu komai Baby na. Aikenki dai zanyi sashen Yayanku”. Da sauri Azizat ta ɗago fuskarta da murmushi. Sai kuma ta tura baki tana mai haɗiyewa. “Mammah bayan Yayan ya sake fita shi da tawagarsa. Ina kuma ƙyautata zaton wata tafiyar ma ya sake yi”. Da mamaki Hajiya Mammah ke kallonta ta ce, “Tafiya kuma? Bayan yau ya dawo?”. Sai kuma ta dauki wayarta ta shiga daddanawa batare data jira amsa ba. Kunnenta ta kai. Batare da yin ko sallama ba ta ce, “Kuna ina?”. Cikin girmamawa da ga can aka bata amsa da, “Gamu a airport zamu wuce Chaina”. “What! Shine ba labari?”. “I'am sorry Maa. Da alama tafiyar gaggawace ta tasoma Boss ne.” Ƙwafa tayi, tare da yanke kiran. Batare da tace komai ba kuma ta miƙe tai ficewarta. Da kallo Azizat ta bita sai kuma ta taɓe baki itama ta cigaba da charting ɗin ta..... ✨✨✨✨ A ɓangaren Paah shima hankalinsa ba'a kwance yake ba. Dan tun randa abin nan ya faru bai sake saka samun ko kallon arziƙi daga ɗan nasa ba. Ko jiyyar kwanaki uku da yay a gidan idan ya shiga dubasa sai ya ƙirƙiri barcin ƙarya. Yana samun sauƙi kuma ya tattara ya bar musu gidan. Sai yau ne matarsa ke sanar masa Awwab ɗin ya dawo gida. Shine dalilin barowarsa inda yake a gaggauce yazo gidan. Kai tsaye sashen Awwab ɗin ya nufa, amma tun kafin ma ya shiga Hayatu daya samu a compaund ke sanar masa Awwab ɗin na sashen Hajiya Babba. Sashen Hajiya Babban yaso nufa shima. Sai dai hakan ya gagara saboda shakkar haɗuwar tasu. Dan yasan a rayuwa Awwab bai haɗa al'amarinsa dana mahaifiyarsa da komai ba. Taɓashin da Hajiya ƙarama tayi ne ya sashi dawowa a hayyacinsa firgigit. Cike da mamaki ta ce, “Lafiya kuwa Abban Awwab?”. Numfashi ya sauke mai ƙarfi, sai kuma cikin damuwa ya amsa mata da, “Ba komai” yana miƙewa. Da sauri ta riƙo hannunsa. “Ya zakace babu komai bayan ga damuwa ƙarara a fuskarka? Nasan dai bazai wuce akan fushin da Awwab yake ba. Ni a ganina mizai hana kaje ka samesa. Sai ka lallashesa dan yaron nan ya fimu gaskiya, shiyyasa kullum nake nusar da kai illar biyema Addah a gidan nan. Dan koba komai Hajiya Babba uwar ƴaƴanka ce”. Wani mugun kallo ya watsa mata. Sai kuma ya fisge hannunsa batare da ya tanka mata ba yaja tsaki. Fuuu ya fice abinsa batare da ko waiwayenta ba. Da kallo kawai ta bisa itama. Sai kuma ta girgiza kanta ranta duk a dagule.... 💕💕💕💕 *_INDIA_* Kai kawo take kawai tana kuka ita kaɗai a ɗakin, a kallo ɗaya zaka fahimci tana a cikin matsanancin tashin hankali da bai da misali. Kanta ta shiga girgizawa cike da sakin zantukan da suka zame mata sirrinta cikin sambatu. “Kai ina bazai yiwu ba. Bazan halaka yarona da hannuna ba wlhy. Saimah bazai yiwu ba. Na tafka kuskuren farko bazan bari na sake aikata na biyu ba”. Ta ƙare maganar tana rarumar wayarta. Number ƙanwarta Saimah dake Dubai ta shiga lalubowa. Cikin sa'a kuwa ta sameta a sama-sama dan ko a jiya sunyi waya. Kira ta danna mata, sai dai harta fidda rai da za'a ɗauka tana gab da tsinkewa aka ɗaga. Mamy da zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri tamkar zata fito ko sallama bata tsaya yi ba ta ambaci sunan yar uwar tata kai tsaye. “Saimah!”. Cike da mamaki da shiga tashin hankali ta amsa mata daga can. Sai kuma ta ɗora da faɗin, “Lafiya kuwa Aunty najiki cikin tashin hankali? Kar dai kice min mun rasa Mansoor ne?”. Wani irin suka ƙarshen zancen Saimah yayiwa Mamy a zuciya. Dan haka a fusace ta bata amsa da, “Oh haka kuke zaman jiran ji kenan shiyyasa kika saka ƴarki ta kirasa a waya ta tada masa da hankali da yake bata da isashiyar tarbiyya. To bai mutu ba, ba kuma zai mutu a sanadin auren shashashar ɗiyarki ba in sha ALLAHU....” A fusace Saimah ta ce, “Wace irin magana ce wannan kuma daga tambaya Sadiyya?”. “Kin fini sani Saimah. Nace kin fini sani. Duk wata masifa kece ummul ana isin sakamu cikinta. Kai haba nagaji bazan iya jurewaba gaskiya. Maganar auren Mansoor da Husnah babu shi tunda baya so”. Wata shegiyar dariya Saimah ta sanya daga can. Sai da tayi mai isarta sannan ta ɗora da faɗin, “Wannan shine kuskure mafi muni da zakiyi a rayuwarki kuwa Sadiya. Dan in har Mansoor zai ce bazai zauna da Husnah ba to kemafa ki shirya tsaff dan auren shekara talatin da takwas zai guntule shima. Zan sanarma mijinki da ɗanki abinda kika aikata game da auren Mansoor na farko. Na kuma sanarma duniya komai. Ya rage naki yanke hukunci. Kin san kuma shima Maash ɗin ba kanwar lasa bane dan ya tabbatar miki da hakan”. Ɗit-ɗit ta yanke wayarta. A matuƙar fusace Mamy tai wani irin masifar yin cilli da wayarta. Sai kuma ta zube a saman gadon ɗakin hotel ɗin tana fashewa da kuka mai masifar ƙarfi... “Mi kike ɓoyewa Halimatu?”. Firgigit ta juyo tana kallonsa. Sai kuma ta mike zumbur tana goge hawayenta jikinta na karkarwa. Cikin rawar murya da kaƙaro murmushi take girgiza masa kanta. “Abban Attahir yaushe ka shigo? Dama kana ɗakin nan? Ai ban san kana nan ba wlhy....” Hannu ya ɗaga mata. Dole tai shiru. Cikin ɓacin rai ya sake maimaita mata tambayar farko. Sake daburcewa tayi. Harshenta na sarƙewa ta ce, “Ba komai. ALLAH ba komai. Ko kaji wani abu ne?”. Maimakon amsa mata idanunsa kawai ya dasa mata. Sai kuma ya jinjina kansa batare daya sake tanka mata ba ya juya ya fice abinsa. Gaba ɗaya ji Mamy tai ɗakin na juya mata tsabar tashin hankali. Birkicewa ta sake yi tamkar sabon kamun hauka. Itako idan har Abban Attahiru yaji wayar nan tata ta shiga uku. Wannan wace kalar rayuwa ce ta jefa kanta da ɗanta a ciki saboda kwaɗayin abin duniya. Wane irin son zuciya ne? Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un... Da ƙyar likitoci suka iya controlling sabon yanayin da Mansoor ya shiga. Dan a baya baya aman jini sam. Gashi yanzu iyayensa sun sake jangwaɓo abinda yafi na farko. Bayan dawowa a hayyacinsa hana kowa akai shiga ganinsa har na tsawon kwanaki uku. Sai da suka tabbatar komai ya dawo normal sannan suka barsu ganinsa bayan anja musu dogon gargaɗi. Sunji farin cikin samun lafiyar tasa. Sai dai bai kula kowa a cikinsu ba har suka gaji da zama suka fito saboda adadin lokacin da aka basu ya cika. Suna fitowa Dad yay wucewarsa, dan har yanzu babu jituwa tsakaninsa da Mamy. Ya tattarata ya watsar da al'amarin ta. Bai kuma sake mata magana akan komai ba. Itako duk wanda ya kalleta yasan bata a cikin hayyacinta a kwanakin nan. Dan komai ya gama ƙwace mata. Ta rasa ina zata kama danta mafi soyuwa a ranta da mijinta na neman kuɓuce mata a dalilin son zuciyarta........✍️ _Humm Mamy wai mi kika aikata ne haka? Miya kuma alakantaki da Maash??🤔_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ......A kunyace ta fito daga banɗakin bayan kammala canja kayan da Abba ya bata na barci. Tana fitowa suka haɗa ido da Abba dake zaune a bakin gado saitin ƙofar toilet ɗin. Ƙara cikuykuye Hijjab ɗin nata tayi da saurin duƙar da kanta ta koma jikin bango ta lafe. Murmushi ya saki tare da miƙa mata hannu alamar tazo. Sai dai ta gagara yin hakan sai ma idanunta ne da sukai ƙwalƙwal kamar zata fasa kuka. Murmushi Abban ya sake yi da sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya miƙe ya nufeta. Hannunta ya kamo ya jawota jikinsa ya rungume. Kafin a hankali cikin dabara ya zane Hijjab ɗin nata ya cilla saman kujera ƙwara ɗaya dake ɗakin. Ƙoƙarin raba jikinsa da nata yayi amma taƙi yarda da hakan. Sai ma sake ƙanƙamesa da tai tana jujjuya kan nata alamar dai bata son ya ganta a kayan barcin. A hankali ya ranƙwafa saitin kunnenta ya raɗa mata, “Mu kwana a haka kenan bazaki gaji ba?”. Kafaɗa ta noƙe masa alamar a'a. Sai kuma cikin rawar murya ta ce, “Dan ALLAH zan saka hijjab ɗin dai”. “Kin taɓa ganin amarya da hijjabi a gaban angonta?”. Ya sake raɗa mata cikin kasala. Kasa iya cemasa komai tayi, sai ma cusa kanta da ta sake yi cikin jikinsa. Shima sai bai sake magana ba ya ɗagata cak sai tsintar kanta tayi a gado. Yanda tai wani mugun duƙunƙunewa waje guda kamar ƴar mage ya bashi dariya. Gadon ya hau shima tare da rage wutar ɗakin ya sake jawota jikinsa ya rungume.... ★“Umma ki buɗe min, na rantse da ALLAH Imamu bai isa ya kwana ɗakin tsinanniyar yarinyar can ba.” “Jalilah bazan buɗe ba. Wai miyasa ke baƙya jin nasiha ne a rayuwarki. Wannan shirmen naki wai kina tunanin zai haifar mana da ɗa mai ido ne? A gabana a gaban ƴaƴanki fa ya rantse ya maya akan in har kika cigaba da ɗaga masa hankali sai ya sake ki babu ko shakka balle kunyata. Amma har kike kasa maida hankalinki jikinki ki nutsu mubi hanyar mai ɓullewa. Imamun yanzu fa ba irin na da bane ba. Ko so kike ya sake kin ki tafi ki bar mata gidan ne shike nan taci nasara a kanki?”. Kuka mai ƙarfi Mom ta saki. Batare data amsawa Umman tata ba ta zube a wajen tana kara ƙarfin kukanta har numfashinta na seizing tamkar zai rabu da gangar jikinta. Duƙawa Umma dake cikin matsanancin damuwa tayi itama tana cigaba da lallashinta... ★Zumbur Halime ta miƙe tana zare idanu jin hannun Abba akan jikinta. Shima Abba sai ya miƙe cikin mamakinta ya kunna fitilar ɗakin. “Lafiya kuwa Halimatu?”. Kai ta girgiza masa tan ƙoƙarin sauka a gadon, riƙota ya sake yi, sai kawai ta fisge hannun ta sauka gaba ɗaya har tana haɗawa da kamar gudu. Zuba mata ido kawai Abba yay mamaki na neman kasheshi. Itako tana lafe jikin bango sai zare idanu takeyi. Murmushi Abba yayi da girgiza kansa. Sai kuma cikin ɗan rage murya ya furta, “Kina son wani abu ne?”. Kanta ta girgiza masa. Shima sai ya sake jinjina kan. “Okay miya faru to?”. “Zan je falo na kwanta?”. “Saboda me?”. “Naga zaka kwana anan ne”. “Ai nan ne ya dace dana kwanta Halimatussa'adiyya”. Da sauri ta ce, “Hu'imm tabb”. (Badaƙala) Abba ya faɗa a zuciyarsa yana cizon lips ɗinsa. Sai kuma yay ƙoƙarin sakkowa a gadon. Tana ganin zai nufota ta kwasa a guje zatai falo. Ai baima san lokacin daya buga tsalle ya cafkota ba. Kuka ta fashe masa da shi. “Dan ALLAH kayi haƙuri Alhaji. Ni wlhy babu ruwana bana so. Kai fa babba ne”. Hankalin Abba tashi ya nema yi, a zuciyarsa ya ayyana (Haba Halimatu taya zan iya haƙuri da wannan baiwar taki) a fili kuwa sai ya jawota ya matse a jikinsa. Duk yanda take mutsu-mutsu yaƙi ya saketa. Dan ya tabbatar tana samun sa'a wlhy sai dai yaji a salansa. Shiko yanda ya samu ya killafa Mom ai gara dai ya angwance dan ganin Halime matsayin amarya zuwa gobe sabon show ne yasan zai tashi. Gara ya mora yasan ya mora duk ma wadda za'ayi sai ayi kawai ko. Cak ya ɗaga Halime zuwa saman gadon. Aiko ta ƙwalla ƙara tana ƙoƙarin turesa. Duk da su Abba an girma ai ƙarfin ba ɗaya ba. Ganin ma tana neman tona mas asiri gida cike da ƴaƴa ga suruka ga Gwaggo sai kawai yay maganin bakin ta hanyar rufesa da nashi. Daga haka ya shiga tabbatar ma Halime shima ɗin da duk da shekaru sun ja da sauransa.... Wani masifaffen ihu da Halime ta fasa tuni ya gama karaɗe gidan. Sai ko a kunnen kowa musamman Mom data gagara rintsawa ita da Ummanta. Dan Gwaggo Gudidi tuni tayi barcinta hankali kwance. Wani irin masifar yankawa zuciyar Mom tayi. Sai ko gata ta ɓaro daga saman gado jikinta na masifar rawa da karkarwa. Ƙofa ta nufa cikin rufewar ido tana dannama Abba zagi da tsinuwa. Tana buɗe ƙofar tayo baya da sauri tare da saka duka hannayenta biyu ta toshe kunnuwanta tana mai fashewa da kuka.. Cikin sauri Ummanta ta miƙe. Kanta tayo da sassarfa. Sai dai me, itama tana zuwa jikin ƙofar ta jiyo kukan Halime da roƙon da takema Abba. Tare da surutan Abba cikin sakin layi... “A'uzubillahi minnashshaiɗanirrajim. La'ilaha illalahu Muhammadurrasulillahi Sallallahu alaihi Wasallam. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un Imamu ka gama tambaɗewa. Imamu kayi asara kayi girman kwabo. Wlhy ka gama watsewa Imamu gagararre mara mutunci” ta danna ƙofar da ƙarfi cikin sambatu da ruɗewa. Tuni tsohuwa ta rikice taji abinda yafi ƙarfin rashin kunyarta🥱. Yayinda Mom ta sake gigicewa dalilin salatin Ummanta. Sai kawai ta dinga numfashi da ƙyar kamar zata shiɗe..... 😒Mom ƙyale Abba kinji, ai zai dawo ne zaici mutanen garinsu gwarzo 🥱🤥. 💢💢💢💢 *_INDIA_* A India kam sama da ƙasa an nema Mansoor an rasa. Dan a daren jiya ya gudu daga asibiti. Matuƙar ƙololuwar tashin hankali iyayensa da ƴan uwansa sun gama shiga. A take suka shiga bincike. Sai gashi an gano cewar yabi jirgin zuwa Abu-dabi a daren jiya. A yanzu hakama awanni biyu kenan da saukar jirgin. Hankalin Mamy ne yafi na kowa tashi a wannan karon. Dan haka ta azalzalesu akan su bishi. Da farko Dad yaƙi bata goyon baya, sai da Attahir yayta roƙonsa dan shi baisan mike faruwa ba sannan ya amince bisa shawarar da tashi zuciyar ta bashi shima na bari suje ɗin yaga ƙarshen abinda Mamyn ke shiryawa. A ranar basu sami jirgin wucewa Dubai ɗin ba. Sai kuma hakan ma ya zame musu alkairi dan Mamy a daren ta samu labarin zuwan ƙanwar tata Nigeria, dan haka ta sauya akalar tafiyar tasu suma zuwa Nigeria. Dan ta tabbatar in har Mansoor yaje Dubai bai samu Sakinar ba shima Nigeria ɗin zai nufa. Hakan kuwa ce ta faru, sai dai a washe garin ma basu sami jirgin Nigeria kai tsaye ba sai na Dubai ɗin. Hukuncin UBANGIJI a Dubai ɗin kuma sai jirgi ya haɗasu da Mansoor da shima zai wuce Nigeria ɗin. Nunawa yay ma kamar bai gansu ba, sai da Attahir yaje har inda yake ya masa magana cikin tsokana da lallashi sannan ya kulashi. Suma su Dad ya gaidasu a ciccinkushe. Shi dai Dad ɗin bai kulashi ba. Sai Mamy ce keta nan nan da shi. Koda suka iso Nigeria tun a airport suka sake nema Mansoor suka rasa. Tashi hankalin Mamy ya sake yi, bata ko saurari Dad ba ta shiga taxi tace ya kaita anguwar su Sakina. Dan suna da gida anan Kano da in sunzo suke sauka. Attahir ne cikin damuwa yay ƙoƙarin tsaidata, amma sai bata ko sauraresa ba dan haka yay zuguy yana kallon motar. Sai kuma ya juyo yana kallon Dad da shima yake tsaye cikin matsanancin ɓacin rai bai ce komai ba. Rasa abin cewa Attahir ɗin yayi, sai kawai ya duƙar da kansa yay shiru zuciyarsa duk a dagule dan shi kam ya rasa mike faruwa haka kuma a tsakanin iyayen nasu cikin kwanakin nan..... 💞⭐💞⭐💞 MAASH Har dare bai san inda hankalinsa yake ba. Sai gabannin asubahi zazzaɓin ya sakesa. Ajiyar zuciya ya ringa saukewa a jajjere. Kafin ya miƙe zaune cikin dauriya saboda kiraye-kirayen sallar asubahi da ake tayi tako ina. Cikin nauyin jiki da rashin ƙwari ya nufi bathroom yana haɗa hanya. Ruwa mai zafi ya samu ya shiga. Sai da ya tabbatar ya ratsashi tare da watsakke masa jiki sannan yay wankan da alwala ya fito. Dukkanin sallolin daya rasa jiya saboda yanayin da yake ya fara ramawa. Bayan ya idar da sallar asubahi har zai kwanta sai kuma zuciyarsa ta gargaɗesa akan hakan. Alkur'ani ya ɗauka ya fara karatu, tun yanayi da ƙyar har jikinsa ya fara sakewa nutsuwa ta fara riskarsa. A jajjere ya dinga sauke ajiyar zuciya nan ma. Sai da ya kai har inda yake buƙata kafin ya miƙe ya hau gadon ya kwanta. Shi ba ma'abocin yawan kwanciya barci bane musamman ma na safe saboda yawan uziri. Amma rashin samun na dare yana kwanciya barci mai nauyin gaske yay awon gaba da shi... A lokacin da Maash ke a sashensa yana fama da ciwo a ɓangaren Samraah tsaye take ƙyam akan ƙafafunta tana miƙama UBANGIJI kukanta. Kaso biyu bisa ukun daren ta rayashine da ƙiyamullail. Kafin ta ɗora da karatun Alqur'ani har asubahi. Tana idarwa duk da barcin dake a cikin idanunta haka ta ɗora shi ta cigaba dayi. Tanayi tana tofama a ruwan data ajiye botiki guda. Da yake tasa himma kafin goma tayi taci kusan izifi ashirin da wani abu. Motse-motsen da Ummie keyi ya fargar da ita, (yunwa) ta ayyana a ranta tana ƙoƙarin miƙewa. Ilai kuwa sai gashi tana farkawa da kiran sunan “Muhammad yunwa. Yunwa Muhammad” ta fara cin karo. Zumut ta miƙa ta nufeta har tana tuntuɓe da katifa............✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ........Sosai mamaki ya kama Paah jin wai Maash ya sake barin gidan. A take ya ɗaga waya yay kiran Hayatu dan yasan ko kiran Maash ɗin yay a yanzu ba lallai ya ɗaga ba. Dan a ganinsa har yanzu fushi yake akan abinda ya faru. Amsar da Hayatun ya bashi na tabbacin sun wuce ya sake tsaya masa a rai. Sai kawai yaji duk yana ƙara zargin kansa da kansa. Da sauri ya miƙe ya nufi sashen Hajiya Babba. Sai dai me ya samu sashen a kulle. Kai tsaye zargin Maash ne ya kulle yazo masa. Jiki a sanyaye ya sakko yana jin lallai dole shima ya nufi Chaina a yau ko gobe su haɗu da Maash ɗin. 🌟🌟🌟 Cikin barci ya farka da matsanancin ciwon kai. Duk da yanda yaso samun nutsuwa hakan ya gagara. Har magani yasha duk da tsanar da yay masa amma ina. Ya jima yana tsintar kansa a irin wannan halin a mabanbanta lokuta. Sai dai na yau ya tsananta sosai. Dan duk yanda yaso sake komawa ya duba Ummie ya gagara hakan. Har dare yana cikin mawuyacin hali. Salla kawai ke tada shi. Ai kusan ƙarfe ɗaya babu shiri dole yabar gidan. Dan ji ya dinga yi tamkar ana masa yayyafi da garwashin wuta. Ya tsani gidan da komai na cikinsa matuƙa. Kasancewar cikin dare sosai ya fita a gidan babu wanda ya sani da ga ALLAH sai shi sai mijin Mama Balki da ya kira ta waya. Hatta da securitys ɗin gate sanin matsayin Malam Baba agidan yasa koda zai fita da baƙo babu wanda ya iya cewa komai. Azatonsu ma ko mai magani ne tunda yau ciwon Hajiya Babba ya tashi sosai tun safe aketa fama.. Can wani gidansa ƙarami dake a wata anguwa daban dole Malam Baba ya kaisa, anan yay jiyyar kwanaki uku ya dawo ragal, sai sannan yake ji a bakin Malam Baba ai jikin Ummie ya motsa sosai amma itama dai da sauƙi. Dan baƙuwar yarinyar nan na tsaye akan al'amarin dan ma taji mata ciwo. Kasa cewa komai Maash ɗin yayi, sai guri ɗaya daya zubama idanu kawai a yanayin da baka isa tantancewa a kansa ba.... ★★★★ Sam gidan babu kwanciyar hankali. Dan tun washe garin da naima Ummie kitso jikinta ya birkice. Sai ma abin ya nema fin na baya. Dan a ranar naci ɗan karan dukan da kowa sai da ya tausaya min. Dan har asibiti sai da aka kaini. Duk da azabar wahalar da naci a hannunta hankalina nakanta. Sam na kasa samun nutsuwa. Akoda yaushe cikin nazari da aune-aunen abubuwa nake. Dan motsawar ciwon nata ya tsaya min a rai. Ga duk wannan abun da akeyi banga ko giccin ɗanta ba a gida. Alamu kuma sun tabbatar da baya nan kenan. Sosai naji takaicinsa ya mamayeni. Har inaji a raina anya mutumin nan da curin hankali a brain ɗinsa kuwa. Rashin man kan yayi yawa matuƙa. Mahaifiya ai tafi gaban wasa. Amma shi duk motsinsa dai a neman kuɗi yake kawai baya tuna gabansa da bayansa. Kai dolene na saita masa layi ko zai tsireni, tunda na fahimci maganata ta ranar bata dawo dashi a hayyacinsa ba. Bayan kwanaki uku jikinta yayi sauƙi Alhamdullah. Haka na sake komawa gareta. Ranar kuka nayi sosai ganin sun ɗaureta. Haka na kwanceta ina zubda hawaye. Na rungumeta a jikina duk da nasan komai zai iya faruwa. Sai dai alhmdllh babu abinda tai min face kukan yunwa-yunwa. Yau ma kamar ranar haka na fita na nemo mata abinci, ina bata ta ɓingire barci. Gyaran sashen na shiga yi bayan nayi kiran Mama Bilki ita kuma ta taimaka ta mata wanka. Dan sabbin masu aikin nan da aka kawo fa sun gudu tun daren da abin ya faru ta fashema ɗaya kai. Bayan Mama Balki ta mata wanka da taimakonta na ƙarasa gyaran sashen. Sai ko gashi ita da shi duk sun dawo a hayyacinsu. Duk wanda ya shigo ma sai yayi sha'awa. Nata yima Mama Balki tambayoyi akan wannan al'amari sai dai bata ce da ni komai ba. Dan haka nima na haƙura na duƙufa kula da al'amarin Ummie ɗin tare da ƙara ƙaimi. Dan yanzu ruwa na samu na ajiye na gorori a cikin kowane kwana biyu saina sauke Alkur'ani a ɗakin da tofawa cikin ruwan. Sam na hana kaina isashen barci. Nama daina fita a sashen gaba ɗaya sai neman abinci. Da farko Hajiya ƙarama taso taka min birki akan abinda nake yi ɗin, sai Hajiya Mammah tace ta barni. Duk da abin ya bani mamaki dan ita ma nai zaton zata hanani sai bance dai komai ba. Sai daga baya nakema Mama Balki zancen, shine tace ai Paah ne yace a barni na cigaba da kula da Ummie ɗin, sai dai bata san dalilin Hajiya ƙarama na son hanani ba. Kodan ita likitace tana ganin kamar Ummie zata iya cutar dani ne oho. Na gamsu da hakan, dan haka na cigaba da sabgata. Sai dai na sakama kowa na gidan ido dan ina son sanin wanda ke ɗaure Ummie ɗin a duk lokacin da ciwonta ya motsa.... ✨✨✨💫 Tun asubar fari Mom ke bugama su Abba ƙofa. Amma babu alamar ma ya jita balle amaryar tashi. Sai dai abinda bata sani ba duk zagi da bugun da take musu yana jinta. Bashi da lokacinta ne kawai dan hankalinsa nakan Hamile dake faman masa kuka har yanzu. Babu irin taimakon da bai bata ba harda su magani amma yarinyar nan ta tasashi da kukan iya shege da duk ya hargitsashi. ALLAH ya soshi ma har kayan shayi ya shigo mata da su, akwai kuma kettle a ɗakin nata kasancewar ba'a haɗa mata hitter ɗinta ba na toilet yasa yayi dabarar ajiye mata kettle ɗin. Tsabar iya shege irin na Halime Mom na buga ƙofar ɗakin tana zaginsu sai ta sake sakama Abba sabon kuka. A rikice ya riƙota jikinsa yana tambayarta mi take so. Baki ta laɓe tana sake saka kukan da turza ƙafafunta. “Ai dai Abba kai kace na girmamata. Amma gashi can tana zagar Innata da Babana bayan kuma Innata ta rasu. Ni wlhy bazan yarda ba.” Cike da lallashi Abba ya sake sakata a jikinsa yana faɗin, “Kinga yi haƙuri barta, haba Halimatussa'adiyya na. Keda kike tare da mijinki ina ruwanki da duk abinda take. Ko kina so nima nayi miki kukan ne. Jibafa jikinki zazzaɓi ne ki kwanta ki huta ko na sake sakaki a ruwan ɗumin”. “Uhm uhm” ta faɗa tana maƙe kafada da tura masa baki. Murmushi yayi da sake sakata sosai jikin nasa. Komai yarinyar tayi sake shiga masa rai take. Ga alkairin data kawo masa har gadon barcinsa na ƙara sakashi jin ƙaunarta mai tsanani da kimarta harma da mutuncin iyayenta. Shagala a lallashin Halime yasa bai san lokacin da Mom ta bar buga ƙofar ba ma. Yana samu tayi barci ya tashi yayi shirin massalaci ya fita sallar asuba. Da yakan bari gari yay haske sannan ya dawo gida. Amma yau ana idarwa ya dawo gidan. Wajen Halime ya koma sai da ya tadata tayi salla ya bata shayi tasha da magani tana masa taɓara yana lallashi, bayan ta koma barci sannan ya sauke ajiyar zuciya ya fito. Ɗakin ya rufe mata ya nufi ɗakin da Gwaggo Gudidi ta kwana suka gaisa. Acan ya samu Musaddiq wajen Gwaggo suna hirarsu hankali kwance. Dan haka ya zauna ana hirar da shi. Anan ne yake jin wai Musaddiq ɗin ya samu aiki a companyn Maash na ƙera motoci. Kusan satinsa uku kenan ma yana zuwa. A yanzu haka ma company ya masa alƙawarin turashi ƙarin karatu ƙasar Chaina. Gaba ɗaya sai yaji kunya ta rufesa. Yay ƙasa da kansa kawai yanata jinjinawa. Daga Musaddiq har Gwaggo Gudidi sun fahimci kunya ta rufe Abba, dan haka Musaddiq ya saki zancen ya kama wani. Itama sai Gwaggon ta koma masa nasiha akan kada ya biyema Mom duk haukan da take a gidan kodan darajarsa matsayin namiji uba da kuma yaƴansu. Ya mata alƙawarin in sha ALLAHU bazai biye mata ba. Daga nan suka ɗan ƙara taɓa hira ya tashi ya fita zuwa ɗakin Mom ɗin. A falo ya sami Auta da Bibaa. Auta yazo garesa da gudu yana murnar ganinsa. Bibaa kuwa sai ta ɗauke kanta kamar bata ganshi ba sai da shi da kansa ya kira sunanta sannan ta gaishesa tana faman fushi. Murmushi kawai yayi ya wuce dan ya fahimci kishi take taya uwarta. Hannunsa riƙe dana Auta ya shiga bedroom ɗin Mom. Dai-dai lokacin take fitowa daga wankan da Umma ta sakata yi dole. Sosai ya ƙura mata udanu yana kallon yanda idonta suka kumbura sunyi jazur je dama fuskarta. Itama wani mugun kallo take watsa masa mai cike da tsana da takaicinsa. Dan wani irin ƙyau da kwarjini taga ya ƙara mata. Daka gansa kaga sabon ango shar daya sha sharafinsa. A take abinda ya ringa musu a gida jiya ya shiga dawo mata. Fashewa da kuka tayi tana rarumar kwalbar turare ta jefesa. Da sauri ya kauce yana tura Auta bayansa. Cigaba da rarumo duk abinda ya tare mata gaba tayi tana jeho masa. Tun yana kaucewa har dai ta samesa. Dole ya fito yana dariyar data sake kular da ita. Dan harga ALLAH shifa dariya borin nata ke bashi yanzu. Da Ummanta yaci karo tana ƙoƙarin shigowa da shayi a hannunta. Haɗiye dariyar yayi ya rissina yana gaisheta. Da ƙyar ta iya amsa masa tana wucewa ko kallonsa batai ba dan itama dai al'amarin nasa na jiya ne ya shiga dawo mata a rai tamkar yanzu komai ke faruwa.......✍️ _🤣Maganin mai zama gidan suruki kenan ai Umma._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_ .......Alhamdullah sati biyu kenan da fara maida akalar al'amurana sashen Hajiya Babba. Tun ina ɗari-ɗari har na fara sakin jikina. Nayi tunanin Hajiya Mammah ko sauran matan gidan wani zai hana amma sai naji shiru. Sai ma jana da Hajiya Mammah ɗin ta farayi jikinta yanzu. Dan ta daina min faɗa sosai. Aikin sashenta ma idan naje yi iya bedroom take cewa na gyara kawai. Tun al'amarin nata naɗan bani mamaki har dai na tattara na watsar da tunanin ALLAH ne ya amsa addu'ata na fara samun sauƙi daga kowa. Abinda na fara fahimta ga lalurar Ummie shine tana ƙarfafa ne a duk sanda Awwab ya shigo inda take ko kuma yama zo gidan zance. Dan a kwanki ukun nan da yake a gidan gaba ɗaya mun kasa gane kanta. Yau da safe har ciwo ta jimin da ƙyar aka fito dani a wajenta. Dalilin hakanne ma na yini a sashenmu da zazzaɓi shine nake kwance har yanzu. Ban samu ɗagawar jikin ba sai dare. Kwanciyar ce ta isheni na tashi na fito. Shiru sashen dan kowa har ya kwanta. Harna zauna a falo sai kuma na tashi na fita gaba ɗaya. Ko'ina akwai haske a gidan kai kace rana ce, sai dai babu hayaniya mai ƙarfi dan wanda ma basuyi barci ba duk sun nutsu a ɗakunansu. Tsamin da jikina yay ya sani ɗan fara tattakawa ko zai sake min, duk da ina kwaɗayin zuwa na duba Ummie sai dai babu yanda zanyi dan yau ɗin kam zuwa kusa da ita haɗari ne babba. Cinkushewar zuciya da son mantar da kaina damuwata ya sani nufar garden ɗin gidan. Shi kam akwai ƙarancin haske a cikinsa, amma ko ɗar banji tsiro ba na samu kujera na zauna ina mai ƙurama korayen gayyakin cikinsa da ƙarancin haske ya sakasu yin duhu ido. Kamar da ga sama naji ana wata ƙara mara daɗin ji, gabana ne ya faɗi. Sai kuma na fara jin sambatu dake fita da wasu irin kalamai marasa daɗin saurare. Neman rikicewa nayi, da sauri na kai hannu na toshe kunnuwana. Ban san adadin mintinan dana ɗauka ba a haka kafin na buɗe kunnen. Yanzu kam shiru babu ihun, sai magana ƙasa-ƙasa da akeyi cikin raɗa. Miƙewa nayi cikin sanɗa na nufi inda nake jin maganar. Hango mutane tsaye mace da namiji, namijin na ƙoƙarin sakama macen kaya a jikinta ya sani lafewa jikin fulawoyi. Cikin shagwaɓa macen ke faɗin, “Wlhy ni na faɗama ban gaji ba. Miyasa yau duk baka son kasancewa da ni ne? Ko dai ka samu wata ne a cikin sabbin masu aikin nan?”. Da ɗan kaushin murya namijin ya bata amsa da, “Miyasa kike da zargi ne wai? Kin san fa minene matsalar. Muhammad na gidan nan ke miyasa baƙya lissafi ne! Kije sai da safe bana son damuwa”. Magana ta yunƙura zata sake masa ya ɗaga mata hannu. Sai naga ta faɗa jikinsa ta rungumesa. Niko tunda ya ambaci Muhammad zuciyata ke wani irin rawa. Dan kuwa a bakin mutum ɗaya ne nake jin sunan nan. Kuma ɗansa kawai yake kira da shi wato Awwab. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un” na faɗa cikin rawar baki sakamakon ganin wanda zuciyar tawa ke ayyana min. Paah tare da Siyama a garden suna aikata z... kasa ƙarasawa nayi, sai ma wani irin kuka daya kufce min. Dole nakai hannuna na toshe bakina har sai da suka fice sannan na durƙushe a wajen nayisa. Wannan wane irin zubar da mutunci ne. Mutum mai daraja da kima kamar Paah ace yana bin masu aiki. Kai ya Arrahaman. Gaskiya ya kamata nasan tarihin wannan gida, ko hakan zai taimakeni wajen fara rarrabe ƙarya da gaskiya. Tare da kallon kowa na gidan nan da siffarsa. Bayan kamar tazarar mintuna ashirin da fitarsu sannan na fita. Sashenmu nayi nufin komawa, amma sai naci karo da Mama balki da alama daga sashen namu ta fito. Idanu ta waro sosai a kaina. Sai kuma ta kama hannuna cikin sauke ajiyar zuciya tana tambayata “Daga ina haka? Yaya jikin naki? Badai sashen Hajiya Babba kika koma ba?”. Kaina na shiga girgiza mata. Hawayen da nake makalewa na kufcemin. Sake tashin hankalin ta yayi. Babu shiri taja hannuna. Siririyar hanyar sashensu da mijinta tabi dani. Sai gamu a madaidaicin falonsu da yau ne shigowata cikinsa na farko. A saman kujera ta zaunar dani itama ta zauna. Sai da ta bani ruwa nasha sannan ta fara jeramin sabuwar tambaya. Kaina na girgiza mata kawai. Tare da faɗin, “Mama babu komai. Amma dan ALLAH idan bazaki damu ba ki bani tarihin wannan gida a yau”. Ɗan jimm tayi kamar mai nazari. Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Wani abune ya sake faruwa kuma?”. Kamar zan faɗa mata sai kuma na fasa saboda kwaɓar da zuciyata tayi min. “Babu komai Mama. Kawai dai ina son jine saboda nasan ta hanyar dazan ɓullo wajen taimakon Ummie game da wannan ciwon nata.” Nan ma shiru tayi kamar bazata tanka min ba. Kafin ta nisa tana mai jinjina kanta. “Zan sanar miki duk abinda na sani Kandala. Saboda harga ALLAH tun randa na fara ganinki a gidan nan zuciyata ta sami nutsuwa dake. A kuma kwanakin nan da kikayi na gwadaki ta hanyoyi da dama banga wata alamar cin amana ko kasancewarki ba mutuniyar kirki ba. Amma duk da haka ina roƙonki ki riƙe min dukkan abinda zan faɗa miki amana dan ALLAH. Sannan zan taimakeki da abinda zan iya domin ganin munyi wani yunƙuri akan Hajiya Babba ko ALLAH zaisa mu dace.” “Nagode Mama.” *_Alonso_* aƙon haure daga ƙasar Spain zuwa Nigeria. Kwara-kwara, bature-batture, balarabe-balarabe gashi nan dai bamu san takamaimai ɗan wane ƙabila bane ko yare, kawai dai daga ƙasar Spain yazo. Abinda kawai kowa yake kallo a tattare da shi shine bashi da alaƙa da Africa sam. Alonso ba musulmi bane ba, baya kuma jin hausa ko zo na kasheka, daga turanci sai yaren Spanish. Da farko harkar kasuwanci ce ta shigo da shi ƙasar Nigeria. Dan yana kawo irin dish ɗin nan na kwanika kala-kala da mutanen da ke jere da su. Kafin a hankali ya samar da wajen yinsu anan cikin garin Lagos ya ɗauki yaranmu aiki yana kuma koyar dasu. Sannu a hankali kamfani ya fara bunƙasa kafin cikar shekara biyu duk yaran daya hora sun gama ƙwarewa har suma suna koyar da wasu. Adams shine kusan babban yaron Alonso saboda ƙwazonsa, ga biyayya da ya kema uban gidan nasa tamkar yaya da ƙane duk da kuwa Adams nada mata acan ƙauyensu dake Kano mai suna kwanar-mashi harda ƴaƴa biyu. Dan neman kuɗi ne ya kaisa garin na Lagos. Ƙyaƙyƙyawan halin Adams yasa Alonso yanke hukuncin kaisa ya ƙaro ilimi acan ƙasarsu ta Spain tunda ya faɗa masa yayi sakandire, sai dai bai kammala duka ba saboda matsala ta rashin kuɗi ga nauyin iyayensa da matarsa da duk ke a kansa. Alonso shine ya saka Adams dawowa da iyalinsa da mahaifiyarsa nan Lagos da zama. Tare da saka yaransa biyu mace da namiji a makaranta. Nafisa da Mu'azz, sai ciki da matar tasa ke da shi tsoho. Ganin a yanayin da take Alonso ya bama Adams shawarar tafiya da ita amma sai mahaifiyarsa ta hana. Ganin haka yasa Alonso neman wadda zata kula da ita matsayin mai aiki saboda mahaifiyar Adams bata da wani ƙarfin yin hakan saboda tsufa. Sai dai duk wadda aka kawo sai a samu matsala saboda masifar matar Adams. Dan mace ce azababbiya matuƙa... Rabi'atu yarinya ce budurwa da bazata wuce shekaru goma sha shida ba. Ɗiyace wajen mai abinci dake gab da kamfanin Alonso Kuma duk a wajensu suke cin abinci. Tayi matuƙar sabo da Adams harma wasu na ganin ko son juna suke. Sai dai sam ba haka bane ba. ALLAH dai ya haɗa jininsu ne kawai kasancewarta yarinya nutsatstsiya mai hankali ga ilimin addini da girmama na gaba da ita. Ba Adams kawai ba kowa a gurin Rabi'ah nada ƙyaƙyƙyawar alaƙa da shi har shi kansa oga kwata-kwatan wato Alonso. Ganin tafiyar Adams na matsowa ga matarsa taƙi kwantar da hankalinta ta zauna lafiya da masu aikin da ake ɗauka mata sai Adams ya roƙa Rabi'ah akan ta dinga zuwa tana ɗan mata gyare-gyaren kafin a samu wata. Babu musu Rabi'ah ta amince, dan akwai ƴar ƙyaƙyƙyawar alaƙa tsakaninta da matar Adams ɗin a dalilin kai musu abinci da take kullum gida saboda basu fara girki ba. Fara aikin Rabi'ah baifi da sati guda ba Adams ya wuce ƙasar Spain bisa ƙoƙarin uban gidansa Alonso. Bayan wucewar Adams Rabi'ah ta cigaba da ɗawainiya da matarsa Uwani har ALLAH ya sauketa lafiya. Bawai bata mata masifar bane ita, kawai dai tanada haƙuri ne sosai shiyyasa kowa ke ganin babu matsala. Bayan haihuwar matar Adams da wata biyu wani rikici ya taso, dan zuwa yanzu kanta ya ƙara wayewa tayi sabbin ƙawaye. Duk wahalar da Rabi'ah kemata da jaririnta da sauran yaranta biyu ta rufe idanunta ta mata rashin mutunci wai tana soyayya da mijintane. Rantsuwa sosai Rabi'ah ta shiga mata tana kuka akan ita bata da wata alaƙa da Adams face ta mutunci kamar kowa. Amma sam sai taƙi saurarenta har ta kaita da fusata ta watsa mata ruwan zafi dake akan risho da Rabi'ah ɗin ta ɗora zata mata girki. Hankali tashe aka kwashi Rabi'ah zuwa asibiti. Alhamdullah anyi sa'a ƙunar batai nisa ba. Dan ta iya hannunta zuwa gefen ciki ce kawai ta tashi. Ta fuska ALLAH ya taƙaita mata wahala. Hankalin Alonso ya tashi, dan haka ya shirya matar Adams da yaransa biyu suma ya turasu ƙasar Spain inda mijinta ke karatu. Shi kuma ya maido tsohuwa mahaifiyar Adams ɗin gidansa dan yayi alƙawarin kula da ita har su Adams su dawo. Ƴar shaƙuwar da Rabi'ah tayi da tsohuwa yasa bayan warkewarta ta cigaba da zuwa gidan Alonso tana mata hidima duk da kuwa an ɗauka mata masu aiki. Rayuwar yarinyar da ƙyawawan ɗabi'unta ya fara jan hankalin Alonso kanta. A hankali sai ya fara sanyama duk motsinta ido idan tazo gidan. Tun tsohuwa bata lura ba harta fuskanta. Tausayi ya bata sosai, dan tasan da kamar wuya a bashi auren Rabi'ah tunda shi ba musulmi bane. Amma dai tana kan masa addu'a itama na ALLAH ya shiryesa kodan kyawawan ɗabi'un da ALLAH ya zurtashi da su. Zamu iya cewa ALLAH ya amshi addu'ar tsohuwa akan gaɓa. Dan kuwa randa Alonso ya gagara daurewa ya amayarma Rabi'ah sirrin dake a ransa ta tabbatar masa bazai yiwuba saboda addini ya bambantasu a ranar ya musulunta. Wannan al'amari yay matuƙar yima tsohuwa daɗi, dan haka ta sanar da Adams ta hanyar telephone da ake amfani da ita a lokacin kuma sai a gidan ma wane da wane. Shima sosai ya tsinta kansa a farin ciki mara musaltuwa dan dama burinsa kenan.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚_ What you need to start making $500 from PromptEarn Dollar Affiliate 👇. 📍A smartphone 📱. 📍 Internet Connection. 📍Access to your AIM Course. 📍 Atleast 2 hrs of your daily time. If you still don’t know what this is, click the link below to know how you can start 👉https://wa.link/6f3908 ________ .....Musuluntar Alonso daya koma Ibrahim Khalil bai sa Rabi'ah ta amince da shi ba har sai da ta tabbatar yayi tubane domin ALLAH badan soyayyarta ba. Biki akayi na bajinta duk da kuwa kowa bai san iyayen Alonso (Ibrahim Khalil) ba. Sai Adams dake acan yana karatu. Shedar daya bada akan asalin Alonso (Ibrahim) yasa ba'a zurfafa bincike ba aka bashi kodan musulunci daya amsa ai ya zama ɗan uwa. Rayuwar Rabi'ah da Ibrahim rayuwace mai sauƙi da ƙayatarwa. Ga tsohuwa a gefe na ƙara ɗorasu kan ƙyaƙyƙyawar tirba. Shekararsu ɗaya da aure ya ɗuketa sukaje ƙasarsa. Acan suka iske Adams da iyalansa. Sosai Adams ya nuna farin cikinsa, sai dai ga matarsa sam ba haka bane ba. Banda harara da kallon banza babu abinda take bin Rabi'ah da shi har sai da Rabi'ahr ta tattarata ta watsar itama sannan tasha jinin jikinta. Satinsu biyu suka dawo Nigeria dan Ibrahim ya riga ya saba da rayuwar sabuwar ƙasarsa. Dawowarsu da watanni biyu iyayensa suka samu iftila'in gobara suka ƙone ƙurmus. Dole ya sake tattara Rabi'ah suka koma cikin tashin hankali. Sai dai zuwan nasu bai canja komai ba dan anyita ta ƙare Ibrahim ya rasa ahalinsa. Wannan shine dalilin dawowarsa Nigeria gaba ɗaya. Adams ma ya dawo shi da iyalansa. Har lokacin kuma Rabi'ah bata taɓa ko ɓatan wata ba. Hakama matar Adams bata sake haihuwa ba tun Abdullahi. Dawowar Adams yasa Ibrahim sake sakar masa ragamar kamfani sosai. Aiko cikin amincin ALLAH sai sake bunƙasa yake har sun fara buɗe wasu reshikan a jahohi. Kwatsam sai ga Rabi'ah da ciki. Musalta farin cikin Ibrahim da su Adams da suka zama ahalinsa a yanzu ma ɓata lokaci ne. Haka aka shiga jelar tattalin cikin nan har ALLAH ya sauketa lafiya aka haifo ɗiya mace ƙyaƙyƙyawa mai tsananin kamanni da mahaifinta. Yarinya taci suna Ummu-Hidaya kamar yanda Rabi'ah ta buƙaci a sanya mata. Duk wani gata Ummu-Hidaya na samunsa ga kowa. Sai dai hakan bai hana Rabi'ah tsayawa akan tarbiyyarta ba. Dan haka ta tashi yarinya mara kwaramniya ga kuma gatan iyaye da na yayu su Mu'azz da a yanzu su take kallo matsayin zuri'ar iyayenta. Tana da shekara huɗu Rabi'ah ta sake samun ciki. Nan ma anyi farin ciki matuƙa. Cikin nada watanni biyar tsohuwa mahaifiyar Adams ta rasu. Ibrahim yaci kuka dan sai ma ka ɗauka itace ta haifesa shima. Hakama Rabi'ah ta shiga ɗimuwa. Ba'a gama kukan mutuwar tsohuwa ba mahaifiyar Rabi'ah itama tai accident ta rasu. Ai sai Rabi'ah ta ƙarasa birkicewa. Dan bata san kowa ba a danginta a duniya sai mahaifiyarta. Tun bata da wayo take mata nacin sanin ina babanta da ƴan uwansu dan daga ita sai ita ta buɗe ido ta sani a Lagos sai masu tayasu aikin abinci amma bata sanar mata ba gashi har rayuwa ta ƙare. Sam lafiya taƙi samuwa ga Rabi'ah. Ga cikin na matuƙar bata wahala ƙwarai da gaske. A haka dai aka kai watan haihuwa da ƙyar. Sai dai kuma ranar haihuwa anta shan fama haihuwar tazo da gardama. Ganin za'a iya rasata ita da abinda ke cikinta aka yanke shawarar yimata cs. ALLAH sarki rayuwa, kana naka ne ALLAH na nashi, dan kuwa ana fiddo ɗan Rabi'ah daga ciki tace ga garinku nan itama. Ɗimaucewa Ibrahim yayi gaba ɗaya, dan takai sai da aka kwantar da shi asibiti shima. Kwanan jinjiri biyar a duniya shima ALLAH ya amsa abinsa... Shike nan komai ya ƙare komai kuma ya tsaya ga Ibrahim. Dai-dai da harkar Companyn ma ya tattara ya watsar sai Adams ne ke kula da komai. Gaba ɗaya rayuwarsa ya tattara akan Ummu-Hidaya ne. Shike mata komai, sai mahaifiyata da aka ɗakko aiki domin kulawa da ita a lokacin, amma hatta barci a tare sukeyi har sai da takai shekaru goma sannan ya raba musu wajen kwanciya. Zuwa yanzu ya ɗan fara haƙura, sai dai babu abinda ke saka rayuwarsa a farin ciki sai Ummu-Hidaya, musamman idan ya ganta a farin cikin itama, itako indai tana cikinmu yaran masu aiki tana wasa zaka sameta cikin walwala da yawan fara'a. Gata yake mata da cikakkiyar tarbiyya mai ƙayatarwa. Tare da fara koya mata harkokin kasuwanci daban-daban. Tun ma bata fahimtar komai a kasuwancin harta fara ganewa. Tana da shekara goma sha bakwai a duniya ta kammala secondary. Zuwa yanzu ta zama budurwa. Sai dai yanayinta da suffarta da bai kama da na baƙar fata ba yasa sam bata da wani jikin girma. Sai dai akwai ilimi ga tarbiyya da nutsuwa. Bata da yawan magana sam. Idan kaganta tana surutu sai da Babanta ko Mu'azz ɗan Adams na biyu ko Drivern Ibrahim Abdul-wahab da muke kira Jirgin mota a gidan. Amma Mu'azz shine abokinta a gidan sosai, sai kuma autar Adams ɗin da matarsa ta sake haifa masa bayan rasuwar Rabi'a mai suna Mashi'a, Nafisa yayarsu gaba ɗaya kuwa masifarta tasa ko harkarta Ummu-Hidaya bata shiga, sai dai tana girmamata. Tun ana kallon rayuwar Ummu-Hidaya da Mu'azz a matsayin shaƙuwa har kowa ya fahimci akwai soyayya mai ƙarfi a tsakaninsu. Sosai Adams da Ibrahim sukayi farin ciki da hakan. Dan koba komai zasu hada alaƙar jini a tsakaninsu bayan ta zuminci da ALLAH ya riga ya haɗa musu. Dan zuwa yanzu idan baka sani ba sai ka ɗauka Ibrahim da Adams yan uwane uwa ɗaya uba ɗaya. Sai dai kawai siffar jiki data banbantasu. Shi Ibrahim daka gansa zaka san dan ƙetare ne. Shiko Adams baƙine kuma ƙyaƙyƙyawa. Gogewa da ilimi da ya sake yi ga dukiya ta zauna gwargwado yasa idan ka gansa bazaka taɓa tunanin shi ɗin nan ne ba na ƙauyen k/Mashi da yazo leburanci garin Lagos. Saboda tuni Ibrahim ya bashi wani abu mai kauri a dukiyarsa shima ya kafa kansa. Shi kuma ya maida komai nasa daya mallaka matsayin na Ummu-Hidaya tare da tsayawa akanta ta koya harkar kasuwanci tun tana ƙaramarta. ALLAH kuma ya sanya albarka a tare da ita dan komai sai sake bunƙasa yake tamkar ba yarinya ƙarama ba. Bayan ta kammala secondary Ibrahim da Adams suka yanke shawarar aurama Mu'azz ita. Haka kuwa akayi aka musu auren gata. Bayan auren babu jimawa Ibrahim ya nema musu makaranta su duka. Dan shima Mu'azz ɗin zai sake ƙaro karatu duk da ya kammala degree dinsa na farko tun kusan shekara biyu kenan shima yana aiki a companyn Ibrahim..... Next please 🚦🚴 💕💕💕💕 Mahaukacin bugun da akema gate ɗin gidan ya saka maigadi tahowa da sauri ya buɗe. Zai yi magana Mansoor yasa hannu ya ingijesa ya danna kai ciki. A ƙofar falo suka kusan cin karo da Hajiya Sakina da bugun itama ya fiddota. Kallon kallo suka tsaya yima juna. Kasancewarta gogagguyar mace da idanunta suka gama buɗewa sai ta saki murmushi. “A'a masha ALLAH Son kai ne a gidan namu? Alhamdullah jiki yayi sauƙi kai barka-barka ALLAH mun gode maka”. Abinda ya tokare maƙoshinsa da ƙyar ya haɗiye, kafin ya kalleta a ɗage ya ce, “Ina ƴarki?”. Murmushi ta sake yi da faɗin, “Son ƴata ko matarka dai? Ina fatan dai ba zuwa kai kace a yau zata tare ba?”. Tsaki yaja mai ƙarfi da watsa mata kallon raini. “Ai bana tunanin ta cika macen da har zata tare a gidana. Ballema ni Bamma san da aurenta ba”. Cikin sosuwar zuciya Hajiya Sakeena ta ce, “Idan kai baka sani ba ai uwarka da ubanka sun sani Mansoor. Kai karfa kaga ina lallaɓaka ka nema gayamin magana. Ƙanwar uwarka ce ni idan ka manta na tuna maka”. “Na gode da kika fahimci sunanki ƙanwarta ba ita ɗin ba. A tunaninki munafuncin da kika ƙulla aka rabani da wadda nake so zai sa na auri ƴar iskar ƴarki sauran mazan Dubai ne. To kinyi kuskure, dan ko mata sun ƙare ballagazar ƴarki bata cikin matan da zan kalla matsayin mace dan bata da suffar matan. Dan haka na saketa saki ɗaya biyu uku”. Ya ƙare maganar da jefa mata takarda akan fuska ya juya abinsa. Mutuwar tsaye Hajiya Sakeena tayi a wajen, yayinda Husnah ta ƙwalla ƙara ta zube a wajen gaba ɗayanta. Sai a lokacin uwar ta dawo hankalinta. Itama ƙwala ƙarar kiran sunanta tayi da zabura kanta....... 💢✨💢✨💢 💢🌟💢🌟💢 A shekarar farkon aurensu ALLAH ya azurtasu da samun ƙaruwar ciki. Tunda labarin ciki ya iso kowa ke farin ciki, musamman Ibrahim (Abbie) daya kasa zaune ya kasa tsaye. Ƙarshe ma sai ya shirya shi da Adams (Baba prof... sukaje duba Ummu-Hidaya ɗin. Satinsu biyu sai gasu sun dawo, sai dai yanayinsu na komawa sanyi-sanyi duk ya bama kowa mamaki, sai daga ƙarshe muke jin labarin ai cikin ne ya zube ashe. Daga lokacin Ummu-Hidaya bata sake samun ciki ba. Ba kuma su dawo Nigeria ba sai da ta kammala karatun ta. Irin farin cikin da kowa ya tsinta kansa na dawowar tata bashi da misali. Daga ita har mijinta sun ƙara wani irin ƙyau da cikar haiba. Kai da ka gansu kasan hutu ya zauna a jikinsu. Musamman ita dake mace. Tunda suka dawo ta fara jana a jikinta, yayinda kuma taita faɗan miyasa ban cigaba da karatu ba. Mamana ce ta sanar mata ai Babana ya hana, yace boko kafurci ne. Murmushi kawai tayi bata sake cewa komai akan karatun nawa ba, sai ma maida akalarta da tayi akan batun ya kamata nayi aure. Ganin ta damu nan ma Mamana ta sanar mata ai babu tsayayye. Dariya mukaga tayi, tare da juyawa ta fuskanci mahaifinta dake zaune a gefe yana duba wasu takardu. Cikin nutsuwarta ta ce, “Abbie niko mizai hana ka bama Yaya Abdull auren Bilkisu ne?”. Mu duka sai da muka kalleta da mamaki, dan kowa yasan wa take cema Yaya Abdull a gidan. Wato dai drivern Mahaifin nata da muke kira jirgin mota. Girmama sunan duk ma'aikatan gidan tarbiyyar Ummu-Hidaya ce haka. Dan kowa bata faɗar sunansa kai tsaye sai ta haɗa da Yaya ko Baba ko Mama ko Aunty. Yanda take daraja mu masu aiki yasa kowa yake ƙaunarta sosai, babu mai son ganin ɓacin ranta sam hatta mu ƙanana.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_ .......A mamakinmu sai mukaga Abbien nata yayi murmushi mai ƙayatarwa da birgewa. Cike da kulawa ya ce, “To Ummuna kin tambayesu suna son juna? Ko kina ganin ya dace ai musu auren dole?”. “Lah a'a Abbie ba haka nake nufi ba. Nifa na jima da sanin suna son juna. Kawai dai sunƙi bayyanawa ne kasan duk matsorata aka tara daga Yaya Abdull ɗin har Balkisun”. Dariya kowa ya sanya, yayinda na miƙe da gudu nabar falon. Daga haka ban san yaya aka ƙare ba sai jin ana shirye-shiryen bikinmu kawai. Abdul-wahab mutum ne mai kunya dan haka shima ya gagara mun magana. Duk sanda ma muka haɗu sai dai yayi murmushi kawai ya sunkuyar da kansa. Nima hakan take a gareni. Cikin kwanaki kaɗan aka dasa hidimar biki, zakisha mamakin yanda akai bikin aurena tamkar yarinyar gida ba ƴar masu aiki da drivern gida ba. Bayan kammala bikin anan dai cikin gidan muka cigaba da zama. Sai dai mahaifiyata Ummu-Hidaya ta buƙaci tayi ritaya ta huta hakanan. Hakan kuwa akayi, ta ajiye aikinta suka bata ƙyautar ƙaramin gida ta koma can. Sun buƙaci shima Abdul-wahab ya ajiye aikinsa amma yaƙi, acewarsa bazai taɓa iya rabuwa da mutumin kirki irin Abbie ba. Haka dole suka barsa badan sun so ba. Da a ganinsu shima yanzu ya kamata a martabashi kafin matarsa ta fara haihuwa.. Watan aurenmu biyar da Abdul-wahab sai ga ciki ya bayyana a jikin Ummu-Hidaya. Kowa yasha mamaki dan ciki har kusan wata biyar amma babu wanda ya san da shi. Sai daga baya na fahimci ita fa tasan da abinta tana ɓoyewa ne kawai. Na shiga mamaki ƙwarai da gaske akan ɓoyewar tata. Dan nasan yanda kowa ke fata da zumuɗin samun cikin amma har ta iya ɓoyesa na tsawon lokaci haka. Rashin mai bani amsa yasa na tattara komai na watsar. Kulawar Ummu-Hidaya gaba ɗaya ta dawo kaina. Dan ta tabbatar min na sanya mata ido akan komai da zataci a gidan. Hatta da abinci idan tana so sai tace mu shiga kitchen ɗin tare, tana zaune zan dafa na bata taci abinta anan sannan mu fito. Hatta da ruwan shanta Abdul-wahab kawai ta aminta ya kawo mata daga Company. Ko wani abu take son ci shi kaɗai take aika ya saya mata. In ba shi ba ko an kawo bata ci. Abubuwan suna bani mamaki da ɗaure kaina sosai. Gashi ta gargaɗeni akan kada kowa yasan wannan tsarin nata hatta da mahaifinta. Dole kuwa na haɗiye duk wani abinda ke'a raina da damuwata, na dai cigaba da bada ƙaimi wajen kulawa da ita. Sauƙin ma cikin nata bamai laulayi bane sosai. Dan hatta company bai hanata zuwa ba. Tana gab da haihuwa suka sake buɗe katafaren companyn yin kayan gine-gine da kwalliyar gida. Ummu-Hidaya kuma ce ta samar dashi bisa fiƙirar da UBANGIJI yay mata. A randa akai shagali buɗe Company a ranar naƙudar ta tashi mata. Batare da kowa ya sani ba tasa na kira mata Mamana, ni da ita muka karɓi Haihuwar a gida batare da kowa ya sani ba. Sai wata Nurse ƙawarta da sukai secondary tare mai suna Lawisa (Hajiya ƙarama ina fatan kin gane). Alhamdullah ta sauka lafiya, yaronta santalele namiji mai tsananin kamanni da ita. Dan tsayin mahaifinsa kawai ya ɗakko amma kamanni tako ina na Ummu-Hidaya ne. Hatta da idanunta irin na maguna da gashin kai mai yalwa bai bar komai ba. Sai da ta haihu da kusan awa uku zuwa huɗu sannan tace mu sanar da mutanen gida, dan Abbie baya nan yayi tafiya. Da alama kuma ta sanar da shi, dan zuwa dare sai gashi ya dawo gida. Hakama Mu'azz baya nan a lokacin, shima washe gari ya dawo. Faɗa miki yanda ahalin biyu dama duk mai alaƙa dasu ke farin ciki ba'a magana. Dan hatta fitinanniyar surukarta a wannan rana cikin farin ciki da walwala take. Kafin wani dogon lokaci labarin wannan haihuwa ya zagaye jama'arsu na nesa dana kusa. Dan danan fa shagali ya tashi, abinka da akwai kuɗi, tako ina facaka ake da su tamkar ba'a san ciwonsu ba. Ranar suna yaro yaci suna *_Muhammad Awwab”_*. Yanda akai wasa da kuɗi a wannan shagalin suna al'amarin har ba'a magana. Sai dai abinda zai baki mamaki duk wani motsi Ummu-Hidaya na kaffa-kaffa da ɗanta ne. Daga ni sai Mamana ta yarda mu ɗauke sa. Sai ko Abbienta da Mu'azz. Sai surukanta Adams da mahaifiyar Mu'azz. Bayan bikin suna ya tashi kulawa da Awwab ya dawo kaina. Sai kuma ita Ummu-Hidaya ɗin idan tana gida. Dan tana gyagijewa ta koma harkar kasuwancinta. Kafin Awwab ya cika shekara biyu sun sake buɗe sabon kamfani na yin lass da atamfa da yadika. Sun kuma saka resunansu a jihohi ukku na kudancin ƙasar bayan Lagos. Muhammad Awwab yaro mai masifar wayon tsiya. Ga ƙyau da shiga ran mutane Masha ALLAH. Sai dai miskilancin tsiya. Baya yarda da kowa sai ni sai Ummien sa sai ko kakansa Abbie da Abdul-wahab. Hatta da mahaifinsa ƙiwa yake masa. Yaro ne mai zafin naman tsiya, dan haka ɓarna sam bata masa wahala. Yayi kuma ya cisgune fuska tamkar bai aikata ba. Yana da shekara huɗu aka sakashi a makaranta, a lokacin ne kuma aka sake kawo mana wata mai aikin, dan acewarta ni ba mai aiki bace ƙanwarta ce. Har kuka nayi kuwa da jin wannan furuci nata, dan haka na ƙara ƙaimi wajen kula da Awwab fiye da komai a gidan. Shekarar sabuwar mai aikin nan ɗaya a gidan itama ta aurar da ita ga drivernta. Shima mutumin kirki ne dan baida hayaniya, ƙani ne ga kai bayin bulawoyi a gidan shima. Shekararsu guda suma ALLAH ya azurtasu da samun haihuwa yaro. Lokacin Awwab nada shekara biyar cur a duniya. Yaronsu yaci suna Hayatu. Tunda aka haifi Hayatu Awwab ya ɗauki son duniya ya ɗora masa. Koda yaushe yana nanne da jinjirin nan. Makaranta ma da ƙyar ake samu ya tafi, yata fitina kenan sai da Hayatu. Tun abin na bamu mamaki har ya koma bamu dariya da birgemu. Shaƙuwar Awwab da Hayatu yasa shima rainonsa ya dawo hannuna dan har lokacin ni ko ɓatan wata ban taɓa yi ba. Hakama Ummu-Hidaya bata sake samun ciki ba. Tama maida hankalinta akan kasuwancinta sai mijinta da shima dai harkokin kasuwancin da suke yi taren yasa ba wani zama yake ba sosai. Dan haka har lokacin Ummu-Hidaya dai na a gidansu ne tare da mahaifinta da bai taɓa ko kwatanta sake yin aure ba. Zuwa yanzu ma shi ya ajiye komai na harkoki ya damƙa a hannun ɗiyar tasa. Yini yake damu a gida da Awwab da Hayatu. Sai idan Adams da ayanzu ake kira Baba prof.. a gidan yazo sunsha hirarsu ko sun fita wata sabgar. Awwab nada shekara bakwai cikin ta takwas Ummu-Hidaya ta sake samun ciki, abin mamaki nima sai ga ciki a jikina. Musalta miki irin farin cikin da muka tsinta kammu a ciki ma ɓata lokaci ne. Mun cigaba da rainon ciki a tare har zuwa watan haihuwa. Itace ta fara haifo ɗanta namiji mai kama da Mu'azz da a yanzu Awwab ke kira Paah matuƙa. Dan tamkar yayi kaki ya ajiye shi kuma. Idanun Ummu-Hidaya kawai jaririn nan ya ɗakko shi kuma. Ranar suna anyi shagali sosai, yaro yaci suna Fahad. Washe garin sunan Fahad nima na haihu mace. Sosai Ummu-Hidaya ta nuna farin cikinta dana duk wanda yake gidan. Ranar suna yarinya taci Ummu-Hidaya. Wannan abu yama Ummu-Hidaya daɗi, dan haka ta ɗauki son duniya ta ɗorama yarinya. Saboda sunata aka sakaya ake kiranta da Falak. Bayan sunan Falak suka tilasta Abdul-wahab ajiye aikinsa. Acewarsu shi yanzu uba ne. Alkairi suka masa mai yawan gaske da zai iya kafa kasuwanci mai ƙarfi, amma duk da haka ya roƙa Abbie akan shi dai zai cigaba da tuƙashi koda zai koma wani kasuwancin ne. Hakan kuwa akayi, duk da ma yanzu shi Abbie ba wani fita yake ba sai idan ta kama dole. Kusan rainon Falak da Fahad ya tashi ne a hannun Ummie da su Awwab, sai da ya shiga primary 5 sannan ya sakarma su Hayatu. A shekarar da Awwab ya shiga jss 2 a secondary ranar wata alhamis Abbie da Abdul-wahab sukai accident a hanyarsu ta zuwa Katsina daga Kaduna duba sabon companyn da Abbie ɗin ke ginawa na sarrafa karfe. Jirgi zasu bi sai aka tashi da hazo, dan daga nan Lagos ta jirgi suka je Kadunar. Mun shiga matsanancin tashin hankali a wannan rana da bazai taɓa musaltuwa ba. A daren ranar ALLAH ya amshi rayuwar Abdul-wahab yayinda Abbie ke cikin mawuyacin hali. Anso yima Abdul-wahab sutura anan Lagos sai dai bai yiwuba, dan yan uwansa tun daga kano sukaje can Kadunar suka ɗaukesa, shi kuma Abbie aka wuto da shi nan Lagos. Ina son tafiya Kano hakan ya gagara, dan ban san irin tarbar da ƴan uwansa zasu min ba saboda basa son auren tun fil azal. Shiyyasama bai taɓa kaini garinsu ba. Ina dai jin sunan a bakinsa. Sai matarsa da mukan ma juna aike idan zai je ko zai dawo. Sai bayan sati ɗaya da rasuwar bisa tirsasawar mahaifiyata muka shirya muka je. Da ƙyar muka iya gano garin Gwarzo. Hakan yasa muka isa a wahalce. Sai dai me duk da azabar tafiya da mukaci bamu sami tarba daga ahalin Abdul-wahab ba. Sai ma kaca-kaca da sukai mana, tare da tabbatar min su basu san Abdul-wahab nada wata mata ba bayan matarsa da suke tare anan gida da ƴaƴansa uku. Dan haka naje can na nemawa ɗiyata ubanta su bazasu karɓa ba tunda tun farko sun tabbatar min basa buƙatata a cikinsu amma na nace sai da na auri musu yaronsu.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_ ........Raina yayi matuƙar ɓaci, hakama na mahaifiyata. Dan haka a daren muka baro gwarzon rai ɓace, har ƙaddara ta samu mahaifiyata aka faɗi da ita a mashin. Ciwon da taji ne ya zama sanadin ajalinta. Dan mun dawo Lagos da kusan kwana tara ALLAH yay mata rasuwa ashe ciwo ya shigeta ba'a sani ba. Wannan al'amari ya sani yin alƙawarin tattara dangin Abdul-wahab na watsar, na cigaba da takaba ta. Ga tashin hankalin Ummie akan ciwon Abbie. Duk da nawa tashin hankalin nima sai na danne na shiga bata kulawa da shawarwari. Watan Abbie kusan uku a asibiti yana jiyya jikinsa yaƙi daɗi, a wani daren lahadi yay ganawar sirri da ƴarsa ɗaya tilo da lauyiyinsa da Baba prof.. sai Awwab dake da shekaru goma sha uku a duniya. Wannan zama da su kaɗai suka san mi suka tattauna sai ALLAH kuma shine zama na ƙarshe. A washe gari Abbie shima yace ga garinku nan. Tashin hankali da ba'a saka masa rana kenan. Dan baki labarin yanda Ummu-Hidaya da Baba prof... Suka kasance a wannan rana ba'a magana. Awwab kam kulle kansa yay a ɗaki tsahon kwana uku. Duk da yarone ƙarami dan shekaru sha uku fa amma a kallo ɗaya zaka san mutuwar nan ta bugesa. Saboda akwai shaƙuwar mai ƙarfi tsakaninsa da Kakan nasa, sannan yarone da ALLAH ya bama wayo sosai da nutsuwa.. Rasuwar Abbie ya fara canja al'amurra Ummie. Office ma ta daina fita kusan wata guda. Sai dai tayi zaune shiru tana kallon yaranta kawai Awwab da Fahad. Sam idanunta basa ƙafewa da zubar hawaye. Cikin ƙanƙanin lokaci ta rame sosai tai duhu. Tun kowa na ɗaukar al'amarinta a matsayin damuwar rashin mahaifi saboda shaƙuwarsu har muka fara fahimtar akwai matsala. Ƙawarta data zama likita a yanzu Hajiya Lawusa (Hajiya ƙarama) naje na sanar mawa. Dan bazan iya tunkarar Abban su Awwab ba ko Baba prof.. itace ta fara tabbatar mana da Ummie na cikin halin depression ne. Kowa ya tausaya mata matuƙa, yayinda Baba prof.. da Mijinta (Paah) suka maido hankalinsu kan bata kulawa sosai. Muma ba'a barmu a baya ba, kowa tattalinta da tattalin lafiyarta yake. Sai dai me al'amarin kamar wasa ƙaramar magana ta koma babba. Dan daga depression sai muka tsinci baiwar ALLAH a halin hauka tuburan. Gaba ɗaya komai ya ƙwace mata. Tun ana ɓoyema yaranta musamman Awwab har ya fahimci halin da take a ciki. Tuni ya tattara karatunsa ya ajiye, ya maida hankalinsa gaba ɗaya gareta duk da ƙarancin shekarunsa shike mata komai hatta da bata abinci da tsaftar muhalinta. Sai ya zama bata aminta da kowa ma sai shi kawai. Babu kalar likitocin da basu ganta ba amma da an fara ɗorata akan magani sauƙi ya fara samuwa sai kuma abu ya rikice. Sunsha bin yawon ƙasashe daban-daban akan matsalarta. Amma kamar dai baya. Da lafiya ta samu sai kuma jiki ya sake rikicewa. Wani bawan ALLAH ne ya bada shawarar gwada mata maganin Islamic da namu na gargajiya, dan acewarsa babu wani ciwon damuwa manyan aljanu ne ke damunta, basuyi jayayya ba kuwa suka sa aka fara kawo musu masana akan hakan. Kamar dai yanda kika sani, magani dace ne, kowa nata gwada tashi sa'ar, sai dai tsahon lokaci ba'a dace ba. Amma dai ana ganin ɗan sauƙi a wasu lokutan. Gaba ɗaya ragamar kula da Ummie a hannun Awwab take, dan tun bai iya wasu abubuwan ba har ya iya. Hatta da kitso zama yake yay mata kiga tamkar mace tayi mata shi. Sai dai me yana da shekara goma sha bakwai komai ya fara sassautawa. A hankali ya fara ja baya da al'amuran mahaifiyar tasa. Takai ma idan yaje gareta sai ta hausa da duka da jifa har saita jimasa ciwo. Idan ya matsama kansa da damuwa sai shi kuma ya hau ciwon kai koya yanke jiki ya faɗi babu rai. Tun kowa na ɗaukar abin wasa dai har ta tabbatar zamansu waje ɗaya bazai yuwuba. Sosai hankalinmu ya tashi da wannan al'amari nasu, musamman ma ni da sukafi shaƙuwa da ni. Canjawar al'amuran ya saka mijina na yanzu bama Awwab shawarar komawa makaranta ya cigaba da karatunsa. Amma sai ya nuna mana shi babu inda zaije. Ya haƙura da komai na rayuwa zai cigaba da kula da Ummiensa. Munta lallashinsa harda Yayar Mahaifinsa Hajiya Nafisa. (Hajiya Mammah). Kunyarmu da yake ji da addu'ar da muka duƙufa a kansa ta sanya ya amince zai koma. Dan haka da kansa ma yayma Baba prof.. da mahaifinsa maganar komawa makarantar. Sun nuna farin cikinsu suma, a take kuma suka shiga suka fita ya zana ssce ɗinsa. Cikin amincin UBANGIJI aka dace ya samu result mai ƙyau. Awwab ya shiga jami'a, kuma har lokacin yana nacin taimakon mahaifiyarsa amma dai babu daɗi dan wahala kawai yake sha. Yayinda Fahad ƙaninsa da shima a lokacin ya ke gab da kammala secondary. Hakama Hayatu suke ƙarƙashin kulawarsa. A farkon fara karatun Awwab ya ɗan fara kula da Companys ɗin mahaifiyarsa da ke neman durƙushewa duk da mahaifinsa tsaye yake akan komai, sai dai aikin ya masa yawa matuƙa dole sai da Awwab ɗin ya fara taimaka masa abubuwan suka fara dai-daita da dawowa fiye ma da yanda ya kamata. Dan shima UBANGIJI ya saka nasibi a hannunsa komai ya taɓa sai ya zama kuɗi. Yanda al'amuran nasa ke haɓaka sai ma ya fara danne na mahaifiyarsa. A haka ya kammala jami'a, yayinda ƙaninsa da Hayatu suke can ƙasar turai suna nasu karatun. Anan ɓangaren kuma Falak na nata a gida Nigeria, dan yanda Paah ya tsaya akan karatunsu itama bai banbanta da ita ba. A hankali ragamar kasuwancin ya koma hannun Awwab, yayinda yake kuma cigaba da karatunsa. Cikin amincin UBANGIJI a wannan lokaci kuma sai aka dace ta hanyar wani bawan ALLAH daga ƙasar Togo Ummie ta fara samun lafiya. Hakama al'amarin Awwab ya fara dai'daita.. Alhamdullah komai ya dawo dai-dai, farin cikinmu da duk zuri'ar Baba prof.. ma haka. Dan samun lafiyar Ummie ba ƙaramin kwanciyar hankali ya kawoma kowa ba. A lokacinne Hayatu ya kammala karatunsa ya dawo gida Nigeria. Saura Fahad da zai ƙara shekara ɗaya. Sai dai yana zuwa hutu musamman ma yanzu da Ummie ta samu sauƙi. Wannan gidan da kike gani itace da kanta ta fara ginashi a lokacin data samu lafiya. Acewarta tana fatan haɗa kan iyalinta waje guda idan su Awwab sunyi aure duk nan zasu zauna da matansu. Muma ta ware mana sashenmu tana mai tabbatar mana mune zuri'arta na ɓangaren mahaifa. Jin daɗin samun lafiyarta yasa Awwab sake maida hankakinsa akan harkar kasuwancin sosai. Yayinda itama take ƙara masa ƙarfin gwiwa. Sai dai me, ana murna ɓarawo ya tafi ashe yana laɓe a bakin ƙofa. Dan kuwa a wani dare labari ya koma baya. Jikin Ummie ya sake hargitsewar da yafi na baya muni da tashin hankali. A wannan lokacin ma dai Awwab sake tattara komai da komai yayi ya dawo da gaba ɗaya hankalinsa da ƙarfinsa akan mahaifiyarsa. Anyi-anyi ya koma kan harkokinsa yayi biris da kowa da komai. Bashi da aiki sai addu'oi da karatun Alqur'ani ga mahaifiyarsa. Da farko lafiya lau yake mata komai, sai dai zuwa wani lokaci matsalar baya ta sake dawowa ta rashin jituwa a tsakaninsu. Ya matuƙar tada hankalinsa akan hakan amma an rasa mafita. Manyan likitocin babu irin waɗanda ba'a gani, hakama masu maganin gargajiya dana Islamic duk inda aka jisu sai an kawasu. Shima na ƙasar Togon anje nemansa aka samu babu shi, wai dama zuwaune a wajen ba'a san takamaimai ɗan wane yanki bane ba. Shekara guda ana cikin wannan zaune tsaye aka bama Paah shawarar yin aure. Amma yaƙi firr sai da aka tsaya a kansa sannan da ƙyar ya amince. Sai dai kuma babu wacce zai aura kamar yanda ya faɗa. Yawan kulawa da Hajiya Lawusa (Hajiya Ƙarama) ke bama Ummie yasa Baba prof.. bada shawarar aurenta. Dan itama a lokacin mijinta ya rasu tanada ƴa ƙarama wadda ita kaɗai ta haifa. Sosai akasha fama kafin Hajiya ƙarama ta amince. Sai dai duk abinda ake Awwab bai sani ba sai daga baya. Sosai ya nuna ɓacin ransa da kishin mahaifiyarsa. Hakanne dalilin tada wannan ginin gidan ya cigaba da yinsa. Abinka da maganar kuɗi, cikin abinda baifi watanni uku ba komai an kammala. Shine ya dawo da mahaifiyarsa nan acewarsa ya bama Paah spiece da matar tasa su ƙarata, duk kuwa da can ɗin ma gidan mallakin Ummie ne. Dan gidan da mahaifinta ya gina da guminsa ya kuma rayu a cikinsa. Hakan yayima Paah zafi, dan Awwab ya tattara kowansu ya watsar, baya shiga sabgar Hajiya ƙarama duk da kuwa a baya kowa yasan aminiyar mahaifiyarsa ce, harma da mahaifin nasa ya tattarashi ya ajiyesa gefe. A ƙalla mun kusa shekara guda a gidan nan da dawowa muketa ɗawainiya da Ummie, dan Awwab dai ya ajiye zancen kasuwanci gaba ɗaya sai kula da mahaifiyarsa. Kullum cikin jimasa ciwo take amma hakan baya hanashi zuwa gareta. Baba prof.. ne akoda yaushe baya gajiya da kawo masu magani, zuwan wani da ga Niger ya bada shawarar Awwab ya rage zaman gidan, dan in har suna a muhalli guda da mahaifiyarsa to lallai lafiyarta zatayi wahalar samuwa. Dan an riga an saka rashin jituwa a tsakaninsu. A samar da masu kula da ita har ALLAH ya bata lafiya. Sam Awwab yaƙi aminta da wannan shawara. Kowa ya buga sai yace babu inda zaije. Hatta da mahaifinsa da basa jituwa a yanzu sai da yazo yana bashi haƙuri da lallashinsa amma ina firr yaƙi amincewa. Mu kammu duk yanda yake girmamamu da jin kunyarmu yaƙi sauraren mu. Hakama Baba prof da kakarsa ta wajen uba matar Baba prof... Ɗin. Ana cikin haka ɗan uwansa Fahad ya dawo ya kammala karatun, ana murnar dawowarsa sai kuma murna ta koma ciki. Dan kuwa sam babu jituwa tsakaninsa da Awwab. Sosai suke nunama juna tsana. Zama inuwa ɗaya ya gagaresu. Akwai randa babu wanda yasan abinda ya haɗosu kawai Awwab ya kama zanesa. Da ƙyar aka amshi yaron a hannunsa sai da ya kwanta asibiti kuwa saboda jigata. Yana samun sauƙi ko hanyar gidan nan bai dawo ba ya tattara inasa inasa ya koma inda ya fito. Daga ranar bai sake leƙo ƙasar nan ba har yanzu. Shima kuma Awwab ɗin bana jin ya sake waiwayar inda yake. Sai su Baba prof.. da Paah.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ ....Abinda ya fara dai-daita tsakanin Awwab da Hajiya ƙarama kulawar da take bama Ummie. Wanda dama tun kan ta auri Paah tanayin hakan, shima kuma Awwab ɗin ya sani, shi dai auren ne yake ganin kamar akwai cin amanar mahaifiyarsa sai kuma kishi da yake tayata. Amma daga baya daya fahimci Hajiya ƙaramar bata canja daga duk abinda takema ummien ba sai ya sakko. Wannan dalili na shiryawarsu ya saka Hajiya Ƙarama da Paah dawowa gidan nan. Basufi watanni uku ba Hajiya Nafisa da suke kira (Hajiya Mammah) a yanzu yayar Paah da akai aurenta bayan haihuwar Awwab dan ta jima batai aure ba mijinta suka samu saɓani. A Niger take auren, koda tazo sai Ba prof.. yace bazata zauna masa gida ba, dan a yanda muke jin labari fitinarta ta hanata zama lafiya da mutane kamar yanda ta hanata aure da farko, ba kuma a wannan karon bane ta fara tahowa gida yaji, sai dai na wannan karon yayi tsamari sosai dan harda dukanta mijin yayi. Koda Baba prof.. ya bibiyi al'amarin sai ya gano itace bata da gaskiya, shine ya hanata zaman gidansa. Kakarsu Awwab ɗin ce tace ta dawo nan gidan ta zauna. Itama da farko Awwab yaso borema zamanta, sai dai bamusan yaya akayi ba kuma daga baya yayi shiru. Dawowarta gidan nan komai ya fara canjawa. Ta maidani sashen masu aiki ni da iyayen Hayatu wai matsayin data sammu da shi kenan. Bayan hakan bata sammu a cikin danginsu kona Ummie ba. Ba muji komai ba muka koma. Sai dai muna ji muna gani kulawa da Ummie ya fara gagararmu, an kawo sabbin masu aiki, tare da saka Awwab komawa kan kasuwancinsa. Yaranta biyu ƴammata sun baro Niger sun dawo nan suma. Gasu basu da tarbiyya sam, basa shakkar taka kowa da wulaƙanta kowa. Gasu malalata basu iya komai ba. Dan dalilin zaman nasu yasa Awwab saka a samo masu aiki ganin suna neman ƙazanta gidan. Hajiya Mammah bata wuce wata biyar a gidan ba ALLAH yay ma mahaifiyar Hayatu rasuwa, sosai na shiga kiɗimuwa hakama mahaifinsa da shi kansa Hayatun. Shima Awwab rasuwar ta girgizashi sosai. A dalilin wannan zaman gaisuwa Alhaji Abdullahi ƙanin Paah ya dawo gidan nan da zama shi da iyalinsa, matarsa ɗaya da yara biyu Malika da Muhsin. Dan koda aka gama komai sai suka ƙi komawa nasu gidan suma. Abin nan ya bani mamaki ya kuma ɗauremin kai, sai dai banda tacewa. Ashe basu kaɗai bane, sai ga mahaifiyarsu itama (Kakar su Awwab ɗin matar Baba prof..) wai itama ta dawo nan saboda sun samu saɓani da Baba prof ɗin akan ƙin komawar Hajiya Mammah gidan mijinta. Shikenan duk sun dawo, Baba prof.. da autarta Mashi'a ne kawai babu, dan ita ba'a Nigeria take aure ba. Sai dai duk ƙarshen shekara tana zuwa bikin ƙara shekara na Ummie da Paah ke shiryawa. Da farko su dukansu kulawa suke bama Ummie. Dan ko sashenta kaje sai ka san ita ɗin ƴar gatan dangi ce. Komai tsaff kamar ba wadda ke'a halin ciwo ba. Idan ba abin ne ya motsa ba ma bazaka taɓa cewa ga lalurar dake damun nata ba. Sosai Awwab ya samu nutsuwa a ɗan tsakanin. Hankalinsa ya kwanta har wata ƙiba yayi ya ƙara haske. Mu kammamu mun samu nutsuwa. Dan a lokacinne akai auren Hayatu da Falak ɗina. Bayan bikin shima Awwab ya bamu shawarar yin aure ni da mahaifin Hayatun. Da farko munso turjewa, amma suka dage shi da Hayatu dole muka amince. Watanni biyu zuwa uku tsakani kakarsu Awwab ta kwanta jiyya. Bata wani jima ba ALLAH yay mata rasuwa a ƙasar Egypt Cairo. Rasuwar ta girgiza kowa na family ɗin, musamman ma Baba prof.. da sai ya baka tausayi. Bayan gama jimami komai ya koma normal. ALLAH ya cigaba da riƙo da hannayen Awwab komai ya taɓa na kasuwanci sai yayi albarka. A cikin abinda bai wuce shekara ɗaya ba ya sake zama wani mahaukacin mai arziƙi da sunansa ke yawo tako ina ama duniya ba ƙasarsa kawai ba. Ba komai ya jawo hakan ba kuma sai ƙarancin shekarunsa da mutane ke gani amma ya tara irin wannan dukiya. Sannan mahaifinsa ba wani shahararren mai arziki bane balle ace ya gada ne. Sanda kakansa da mahaifiyarsa sukai nasu tashen basu ko kama ƙafar nashi arziƙin ba, ansan sunansu ne a iya wani yanki na garin Lagos, shiko duniya ce ke kallonsa a yanzu. Tun Awwab na ƙarami dama ba mutum bane mai yawan magana sai idan shi yaso. Sai dai akwai tausayi da girmama duk wanda ya girme masa. Bai san wulaƙanta mutane ba koda kuwa ƴan aikine wannan tarbiyyar mahaifiyarsa ce da kakansa Abbie. Babu abinda ya damesa da sabgar kowa tashi kawai yake yi. Tun bayan rasuwar Abbie Baba prof.. ne kawai amininsa. Dan da shi kawai zakaga yana dogon hira. Sai ko mu idan yaso wani lokacin zakiga yazo har nan sashen ya zauna koda ba zaiyi magana ba. Dan alokacin da mahaifiyata ta tarasu zaki ɗauka yanada alaƙar zuminci mai ƙarfine da ita. Sosai ya nuna damuwarsa. Tunda ayyuka da harkokinsa suka sha masa kai sai abubuwan gidan suka fara canjawa. Kulawar da ake bama Ummie ta fara ja baya. Ciwonta ya sake tsananta. Idan kinga ana kula da al'amarinta ya shigo gari ne, kuma a lokacin zakiga ciwonta ya tsananta. Duk yanda muka so mu kula da ita mu an hanamu, sashenta ma an mana iyaka da shi, duk randa kuma na shiga koda a sace ne al'amarin baya daɗi tsakanina da Hajiya Mammah. Hajiya ƙarama ce kawai ke nata ƙoƙarin bata taɓa fasawa ba dan hargagin Hajiya Mammah baya damunta. Sau biyu ana korarmu ni da Abban Hayatu saboda nacewa akan kulawa da Ummie, Awwab ne ke dawo damu. Dole muka tsaya matsayinmu na masu aiki dan mu zauna lafiya. Amma neman hanyar kuɓutar da Ummie da son gano bakin zaren kullum cikin yi muke. Masu aiki kullum cikin kawowa ake domin kulawa da Ummie, sai dai basa zarta wata ɗaya suke guduwa. Kowa ɗauka yake saboda ciwon Ummien suke guduwa. Ni kuma a raina inajin ba hakan bane ba akwai abinda ke korarsu. “Wannan shine tarihin wannan gida a taƙaice Kandala. Dan na yanke miki abubuwa da yawa ne a cikinsa saboda wasu dalilai. Sannan ina fata ki fahimci wasu da kanki kuma”. Hawayen da suka kasa tsaya min tun ɗazun na ƙara sharcewa. Cikin rawar murya data gama dasashewa na ce, “Amma mama miyyasa duk kika faɗa min wannan? Bayan baki sanni ba? Baki san koni muguwa bace, ko nama shigo gidan ne dan wata manufa”. Ɗan murmushi tayi itama tana share hawayenta. Kafin ta kamo hannuna cikin nata. “Nasan ke ba muguwa bace Kandala. Duk da dai da farko haka kawai naji ƙaunarki a cikin zuciyata. Sai kuma wata fuska da nake gani akan fuskarki da bansan dalilin hakan ba. Da ga baya Hayatu ya sanar mana alaƙar dake tsakaninki da Awwab....” Wani mugun zaro idanu nayi ina zabura gefe da fincike hannayena dake a cikin nata. Magana nake son yi amma na kasa. Sai lips ɗina dake rawa kawai. Murmushi ta saki tare da sake kamo hannun nawa ta ce, “Kwantar fa hankalinki Samraah. Kar kuma ki fasa aikin ladar da kika fara. Daga Ummie har Awwab da ɗan uwansa abin tausayi ne, suna buƙatar mai tallafama rayuwarsu. Mu kuma da muke da damar yin hakan bamu da wani ƙarfin iko. Dama fatan da muke masa yay aure ya samu mace ta gari da zata juya mulki da tsarin wannan gida ta inda kowa baiyi zato ba. Alhamdullah kuma muna fatan an samu, dan ko yanzu Awwab yaso nunama duniya matsayinki a gurinsa dole kowa ya girgiza, duk da ina tsoron kar su cutar dake dan mutanen nan hatsabiban kansu ne suma, dan ma taurin kan Awwab na rage musu tasiri a wasu lokuta. Sai dai duk abinka baka isa gane wanene na kirkin ba idan kika cire Baba prof.. Dan kowa da tasa illar da manufa da kike gani. Amma ke yarinya ce mai wayo da ilimin addini, dan har na zamani na fahimci kina da shi, ɓoyewa kawai kike kamar yadda kika ɓoye mana ainahin kanki da sunanki. Dan ALLAH ki daure ki taimaki waɗan nan bayin ALLAHn. Awwab mutumin kirki ne, yana iya ƙoƙarin sa wajen tsare mutuncin kansa ta hanyoyi da dama da samarin zamanin nan sukan kasa musamman idan kudaɗe na yawo a hannayensu. Kisa a ranki aikin lada kike yi sakamakon ki naga UBANGIJI. Kisa a ranki ceto zakiyi na Uwa da yaƴanta a cikin gobarar da bata da iyaka. Nasan bake zaki bama Ummie lafiya ba, amma zaki zama wani tsanin taimakawa mukai ga samuwar lafiyar tata. Dan in har kina a tare da ita duk maganin da mu kuma zamu nemo mun san zaki bata. Za ki kuma dinga mata addu'a har shi Awwab ɗin dan bana raba ɗayan biyu akwai sihiri mai ƙarfi shima a jikinsa. Fatanmu shima Fahad ya dawo gida su dai-daita da ɗan uwansa. Sannan waɗan nan mutanen da suka cika gidan nan kowa ya koma inda ya fito..” Karo na farko na saki murmushi mai ciwo. Sai kuma na girgiza kaina. “Mama zan iya tsayawa dai akan samun lafiyar Ummie in sha ALLAHU da kuma batun dawowar ɗan uwansa gida. Amma shi babu abinda ya shafeni da shi ko halin da yake a ciki. Yaje can ya nemo mai taimakonsa. Ai shi ba yaro bane kuma yana cikin hankalinsa. Miyasa bazai dinga ma kansa addu'a ba. Ko sai neman dukiya kawai ya iya. Su kuma dake zaune Mama ai banga amfanin subar gidan ba yanzu, gara suna a cikinsa ta samu lafiya suma su koma kwasar kashinsu a cikin hannayensu. Ai ni baki sani ba. Aduk lokacin da maƙiyi ke tare dani bana son yay nesa da ni, na fison ya cigaba da rayuwa a jikina dan ya cigaba da kallon cigabana da nasarorina zuciyarsa na zafi. Koba komai shi zai ƙare rayuwarsa da lokacinsa ne wajen ganin ya cimmani. A bayyane shike da asara. Bai ƙaru da komai a duniya ba, ya je lahira ya tadda bai ajiye komai a taskarsa ba. Mi yafi wannan daɗi dan ALLAH”. Murmushi Mama Balki tayi tana mai kai hannu ta shafa fuskata. Sai kuma tace, “ALLAH yayi miki albarka Samraah. Hakan ma Nagode. Amma dan ALLAH ayi haƙuri dai a haɗa da Alhaji Ƙarami. Yaron na cikin jarabawa mai ban tausayi. Karki damu da murɗaɗɗun halayensa abubuwane sukai masa yawa a cikin kai. Sannan da kike ganinsa nan mutum ne mai ibada da tarin ilimin addini. Kawai dai ana gusar masa da kulawa ne saboda kada yay ma kansa addu'ar. Amma a hakan ma azumin Litinin da Alhamis baya taɓa wucesa. Salla a cikin jam'i komi yake. Hayatu ya rantse min ya maya komai girman kasuwanci da abinda zai samu a cikinsa ko muhimmancinsa idan lokacin salla yayi sai ya barsa. Komai girman mai mulki ko wani muƙami ko dukiya dan Awwab na zaman meeting dasu baya hana da an kira salla ya miƙe ya barsu yaje yayi sallarsa. Sam bai haɗa bautama UBANGIJINSA da komai ba. Sadaka da taimakon marasa ƙarfi bazasu musaltu ba. Yasha yin ƙyautar gidajen zama da motoci batare da ya ko damu ba. Ɗaukar nauyin karatun yara da gyara makarantun addini da masallatai da asibitici ba'a magana. Idan zan ta lissafo miki alkairan Awwab zamu kwana nan, hatta samar da ruwa ga masu ƙarancinsa bai gaza ba, sai dai hakan bazai hana kuma ace yana da wasu halaye marasa ƙyau ba. Dan ɗan adam tara yake a komai na rayuwa bai cika goma ba. Ladanki naga UBANGIJIN talikai idan kinyi hakan”. Ban iya cemata komai ba face duƙar da kaina kawai ina wasa da yatsun hannuna. Sai kuma a hankali na furta, “Mama kinada hoton mijinki da ya rasu?”.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_ ......Ɗan jimm Mama Balki tayi alamar tunani, kafin ta jinjina kanta. “Za'a samu hotonsa, amma sai dai a wajen Alhaji ƙarami. Dan lokacin da muka dawo rai a ɓace daga garinsu abinda danginsa sukai mana ya sakani a damuwa sosai harna kwanta ciwo. Bani da aiki sai kallon hotonsa ina kuka. Ga kuma halin da Ummie take ciki itama duk na haɗu na ƙara hargitsewa. Shine Ummie ta saka Alhaji Ƙarami ya tattare hotunan duka daga wajena, ni kuma ban sake amsa ba bayan komai ya lafa na samu nutsuwa. Amma ina ganin zan tambayesa yanzu, ko kuma na saka Hayatu ya amso”. Kai na jinjina mata cikin gamsuwa. ✨❤️✨ Yau kwanaki biyu kenan Mom bata saka Abba a idanunta ba. Dan tun jifar da tai masa a washe garin angwancinsa bai sake shiga inda take ba. Hakama amaryar tasa taƙi fitowa. A tunaninta dana yaƴanta harma da Ummanta ai tsoro ya hana amarya fitowa. Dan haka suka fara jin alfahari a ransu musamman ma Mom. Haka zata fito tsakar gida tana habaici da yada magana. Daga Gwaggo Gudidi har Halime da Gwaggon ce ta kwaɓeta babu mai kulata. Hakama Abba yayi watsin ruwan tsarki da ita shan shagalinsa kawai yake da amaryarsa. Gaba ɗaya ya ajiye shekarun girmansa gefe yana koyama Halime salo-salo da tabbatar mata ita ɗin ma fa mace ce. Itako banda raki da taɓara babu abinda take ɓarar masa. Gaba ɗaya ta susuce bawan ALLAH baya ganin komai da tuna kowa a gabansa sai ita. Hatta kasuwa a kwani biyun nan babu inda yake zuwa a gidan yake yini salla kawai ke fidda shi. Dole kuma akayi abinci Gwaggo Gudidi taje ta ɗiba musu tasa Bibaa na kumbure-kumbure takai musu har falo. Yau dai zaman ɗaki ya ishi Halime. Tana ganin Abba ya fita sallar la'asar ta fito. Tsaff take cikin kwalliya, duk kwalliyar ba'a yi ta yanda ya kamata ba kaya data saka sun fiddo jikinta tsaff da yi mata ƙyau. Ga uban turare ta bulbula. Tun a gaban mirror ake gwada tafiyar da za'ayi, dan haka koda aka fito taku ake ɗaɗɗaya ana juya jiki su adole amare. Nan ko a cikin ɗaki raki takema Abba😂. Gwaggo Gudidi tai shirin fara gaidawa. Dan haka kai tsaye ɗakin da take ta shiga. Ta samu Gwaggon na haɗa kayan tafiya, dan magana ta gaskiya taɓarar da Abba ke zuba musu a gidan na kasa kimtsa bakinsa ya fara isarta itama. Bata ji na daren farko ba amma jiya da rana da yau gabannin asuba fes a kunnenta. Wannan taɓara da rashin sanin ciwon kai har ina. Gara dai ta gusa taɗan basu waje ai ita uwa ce. Maybe ma idan ta wuce ɗin waccan mahaukaciyar surukar tashi itama tayima kanta faɗa ta shirya ta tafi, dan har yanzu Umma na gidan ta fake da jiyyar Mom duk da itama fa abinda Abban keyi na damunta. Cike da farin cikin ganin Halime Gwaggo ke faɗin, “Oyoyo oyoyo ɗiyata amarya”. Kunya ce sosai ta kama Halime. Tai ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta. A ran Gwaggo tace (ashe ke da sauranki Imamu bai ida kakkaɓe sauran taki kunyar ba). A fili kam sai ta riƙo hannun Halime cikin nata. Durƙusawa Halimen tayi ƙasa cike da girmamawa da kunya tana gaida Gwaggo. Sai Gwaggo taji hawaye sun ciko mata. Dan abune da bata taɓa gani ga Mom ba. Ko sanda tana amarya fingai-fingai tazo musu babu alamar kunya tattare da ita. Amma ita wannan jiba dai yarinya ƙarama amma Alhamdullah. Bayan sun gaisa Gwaggo taita jan Halime da ƴar hira. Wani ta amsa wani tayi murmushi kawai cikin kunya. Sunfi mintuna ashirin a haka suka fara jin hayaniya na tashi. A tare suka fita, dan muryar Umman Mom suke jiyowa. Cak bakin Mom dake ƙoƙarin yin magana ya maƙale, tun daga bakinta da hanci da idanu duk akan Halime. Kasa haƙuri tayi ta nufo inda suke da sauri. Gaban Halime ta tsaya sai kuma ta nunata da yatsa lips ɗinta na rawa. Amma mi a mamakin kowa sai gani sukai Halimen ta saki murmushi tare da rissinawa a girmame ta ce, “Yaya ina yini? Fatan duk kuna lahiya ke da yara? Ya gajiyar bik.....” “Wacece ke? Miya dawo dake gidana dan ubanki?”. Mom ta katse Halime jikinta har ɓari yake. Murmushi Halime ta sake saki da ɗan bin Mom da kallo daga sama zuwa ƙasa. Sai kuma ta sake murmusawa da yin fari da ido tana wani watsa hannuwa gaba da baya cikin iyayi ta ce, “Halime mana nasan kin gane ai. Na dawo matsayin da kema kike a gidan, wato MATAR ABBA IMAM”. Wani shegen tsalle Mom tayi gefe tamkar wadda taci karo da baƙin maciji. Yayinda Gwaggo Gudidi da abin ya bama dariya ta saki murmushi da gyara tsaiwar ta. Wani irin zaburowa Mom tayi kan Halime tana faɗin, “Shegiya munafuka algunguma ƙarya kike wlhy, mi mijina zaiyi da kucaka ƴar aiki irin ki. Dan ubanki faɗa min miya kawo ki?”. Murmushi Halime ta saki, tare da ja baya kaɗan ta kaucewa cakumar da Mom ke ƙoƙarin kawo mata. Cike da fari da sake yarfar da hannu. Sai kuma ta ɗan duƙo cikin raɗa-raɗa ta furta, “Abinda mijin naki yake yi dake nima shi yake yi dani a cikin ɗaki” ta ƙare maganar da kashe mata ido ɗaya cike da son sake bata haushi ta gittata ta wuce cikin takun da aka gama kowa a gaban mirror. Gaba ɗaya Mom tai baya zata zube bakinta a hangane sai da Ummanta da itama tayi sumar tsaye ta tarota.... ❤️❤️❤️❤️❤️ Sosai abubuwan da naji a bakin Mama Balki suka sakani a cikin damuwa da ɗimuwa musamman akan mijinta daya rasu, dan gaba ɗaya suffofin data ambacesa dasu kama suke dana Babbanmu. Idan kuma ban manta ba Mom ta taɓa min gugar zana da cewar ai ubanmu har karuwa garesa a Lagos. Lallai tabbas ina buƙatar ganin hoton nan nashi. Damuwa tamun yawa sai dai ina matuƙar daurewa dan kada kowa ya gane min. Musamman Bahijja sarkin tambaya. Data ganni shiru tata nacin son jin mike damuna. Har cikin rai nima ina ƙaunar yarinyar, sai yanayinta ke ɗauke min kewar Auta. Kwanki biyun nan jikin Ummie da sauƙi sosai, dan na duƙufa addu'a. Yanzu hatta a ruwan wankanta da Mama Balki ke shiga a ɓoye tai mata safe da yamma sai nayi addu'a. Abincin ta da ruwan shanta duka. Dan na daina bata abinci gidan sai wanda nasan ni na girka ko Mama Balki. Damuwa da yawan tunani ya sani ɗan fitowa yau ina zagaya gidan ko zan rage nauyin zuciya da kewar ahalina, dan ina son kiran Yaya Musaddiq akan abinda naji amma na kwaɓi kaina har sai na tabbatar sannan. Wayar Bahijja ce a hannuna na gama magana da Yaya Musaddiq dake sanar min a wajen aikinsu sunce zasu turashi ƙasar waje ya ƙaro karatu. Farin cikin wannan magana ta sani cigaba da tsaiwa a wajen ina kallon kai kawon masu aiki maza dake sabgoginsu a garabar gidan. A dai-dai nan naga ana ƙoƙarin buɗe ƙaton gate ɗin gidan. Ban kawo komai a raina ba na ɗauke kaina ina cigaba da game a wayar. Har motocin suka gama shigowa ban ɗago ba, dan na ɗauka normal baƙine tunda gidan baya rabo da shiga da fitar motoci. Sai da naji tsaiwar mota a inda nake sannan na ɗago, dan dama a jikin wata motar nake a rumfar ajiyesu. Haka kawai sai da naji ƙirjina ya motsa da ganin wanda banyi tsammani ba. Dan rabonsa da gidan kusan sati ɗaya kenan dama wasu kwanaki. A hankali ya ziro ƙafafunsa dake cikin takalma boot brown masu laushi da ɗaukar idanu tamkar wani miski, gasu da ɗan tsaho ta sama dan har akan wandonsa sosai suka hau. Ko maƙiyi ya kallesa daga sama har ƙasa yasan yayi ƙyau matuƙa cikin shigar tasa. Ga mayen ƙamshin turarensa da tuni ya mamaye wajen kamar anyi ɓarinsa. Cike da matuƙar girmamawa duk masu aikin suka zube suna gaishesa, cikin lumshe idanu da sake dai-daita nutsuwarsa ya ɗaga musu hannayensa alamar amsawa. Kafin ya motsa lips ɗinsa kaɗan cikin silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Kuna lafiya?”. Cike da jin daɗi da girmamawa duk suka amsa masa. Shima sai bai sake cewa komai ba ya juyo gareni. Kallon cikin ido mukaima juna, na kauda nawa da sauri ina ɗan tura baki. Ganin yanda duk yaransa suka samun ido musamman Hayatu ciki-ciki na ce “Ina yini”. Bai amsa min ba, bai kuma daina kallona ba. Sai da ya mula dan kansa ya ɗaga ƙafafunsa zai bar wajen. A bazata naji shigar furucinsa cikin kunnena. “Karna sake ganinki a anan wajen”. Da sauri na ɗago, sai dai kafin na iya cewa wani abu yabar wajen yaran nasa na take masa baya. Sai Hayatu ne a hankali ya ce, “Good afternoon maa”. Harara na ɗago na watsa masa. Ya wuce yana murmushi. Masu aiki dake durƙushe har yanzu kansu a ƙasa duk miƙewa sukayi tare da darewa suka bashi hanya. Shiko ya ratsasu cike da takun nan nasa na mazantaka da tsantsar kamala da nutsuwa. Hayatu da wanda ban san sunansa ba da ƙyamusashiyar baturiyar nan Juliet suka take masa baya. Baki na taɓe tare da raka bayansu da harara. Sai kuma naji duk tsaiwar ta gundireni. Haka na koma ciki ina ƙunƙuni. Ban sake jin labarinsa ba dan ina sashenmu ina wanke kayan Ummie har yamma. Na kwaso kayan zanje na kai ciki aunty Zakiyya ta kirani a wayar Bahijja. Shine na ajiye na fito domin amsa wayar dan bana son su fahimci komai. Ina fara wayar ƙamshin turarensa ya mamaye wajen. Ɗagowa nai da sauri, sai na hangesa ɗan nesa da ni kaɗan ya nufi gate ɗayan mutumin nan daban san sunansa ba (TJ) biye da shi. Da alama masallaci zasu je dan sanye yake cikin blue jallabiya data fiddo da shi tamkar wani balaraben yankin sudani. Ɗauke idanuna nayi da sauri saboda hararar daya watsomin da ban san ta miye ba. Wayata na cigaba dayi da aunty Zakiyya ina dariya har sai da na kammala sannan na koma na ɗauki kayan Ummie na shiga ciki. Labarin data bani na ɗirkama Halime kayan mata dan ta rikita Abba yasa na kasa daina murmushi. Na samu ummie tana barci, dan yanzu abinda tafi yi kenan. Sai uban ƙamshin turarensa daya tabbatar min daya shigo sashen. Baki na taɓe na ajiye kayan na fita........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_ .......Wajen ƙarfe tara na fito nemawa Ummie abinci, dan nasan tana farkawa shi take fara nema. Ina shiga Hajiya Mammah dake kitchen ɗin ban san mi take yi ba ta aikeni sashensa. Cike da jin haushi na shigo ɗauke da abincin da Hajiya Mammah ɗin ta sani kawo masa. Ko sallamar ma ciki-ciki nayita. Tsaff katafaren falon nasa yake kamar ko yaushe, ga ƙamshin nan dana rasa daga ina yake samunsa dan ya bambanta da duk wani ƙamshi dana taɓa sani ko shaƙa a wajen mutane. Komai nasa dabbane dana saura. Sallama na sake yi a ƙuntace dai-dai isowata tsakkiyar falon sosai. Dan naga alamar basu ji ta farkon ba, inda dan shi kadai ne bazan damu ba. Dan koda yaji zai iya shareni wannan ƙaramin aikinsa ne, amma Hayatu bazaiyi hakan ba duk da takaicinsa da nake, shima kuma ƙwallon kansa ne. Yanzun ma dai Hayatun ne ya ɗago da sauri alamar dai basu san da shigowar tawa ba da gaske. Cike da kulawa ya amsa min yana wani ɗan rissinar da kansa. Harararsa nayi kawai na ɗauke kai, dan wannan girmamawar da yake min na baƙanta min zuciya. Shiko gogan baima nuna alamar yasan da shigowar tawa ba. Gaba ɗaya idanunsa da ƙyaƙyƙyawar fuskarsa na kan screen ɗin laptop ɗin cinyarsa da takardun hannunsa. Fuskar nan ciɗin-ciɗin babu alamar sassauci kamar wanda ma ke cikin ɓacin rai. Cikin i don't care na laɓe bakinna da dangwarar da tray ɗin saman Centre table ɗin daya ajiye ƙafafunsa masu tsananin tsafta da haske. Gashi cas babu wani girma sosai irin na maza. Dan wata macen ma sai ta fishi girman ƙafa. Da alama dungurarsa da tray ɗin ya ɗanyi ya saka shi ɗan ɗagowa a karo na farko ya ɗan kalleni. Sai kuma ya ɗauke idanun yuuu ya maida ga laptop ɗin. Nima nawa na ɗauke ina sake tsuke tawa fuskar na juya abina da nufin komawa inda na fito. “Bani ruwa marasa sanyi”. Ya faɗa a dake babu alamar wasa a cikin silent voice ɗinsa. To amma tunda ba suna ya ambata ba bai shafen ba tunda bani kaɗai bace a falon ai. Cigaba da tafiyata nayi dai-dai da yunƙurawar Hayatu alamar zai bashi ruwan. “Da ita nake”. Ya katse hanzarin Hayatun cikin gizagonsa. Duk da naji abinda yace ɗin ban kula ba. Ganin na cigaba da tafiyata cike da girmamawa Hayatu ya ce, “Aunt yace da ke yake fa”. Wani irin ɓacin rai ne naji ya ziyarcen. Dan haka na juyo a fusace ina watsama Hayatun mummunan kallo. “Wai malam banace maka ka daina kirana da wannan sunan ba. In ce dai kasan sunana Samraah ai”. Murmushi kawai Hayatun yayi yana mai rissinar da kansa ƙasa. Sai kuma yace, “Kiyi haƙuri bazan iya faɗa bane. Dan kina da kima da matsayin fiye ma da hakan a wajena”. Cikin gatse na ce, “Saboda a gida ɗaya aka haifemu?”. “A'a saboda kina tare da auren boss”. Duk da furucin nasa yay masaifar tsargani sai na dake. Cike da masifa na ce, “Kaima kasan wani auren boss ai, kar kuma ka sake jinginani da abinda ku ya shafa bani ba”. Baki ya sake buɗewa zai yi magana, sai dai hakan bai yiwu ba, dan kamar a ɗan fusace silent voice ɗin boss ɗin nashi ta daki kumnuwanmu. “Hayat! Kaje zan nemeka”. Abinda yay niyar faɗar ya haɗiye. Batare da wata jayayya ba ya miƙe zumbur. Takardun jikinsa ya tattara ya kai gabansa. Hakan yasa na watsa musu harara su duka na cigaba da tafiyata. Sai dai kafin nakai ƙofar har Hayatu yazo ya wuceni, yana fita ya wani rufo ƙofar. Ban damu ba na kama handle ɗin nima zan buɗe na jita gam. Wani irin takaici ne ya ratsa zuciyata. Dan na fahimci mutanen nan neman maida min rayuwa suke wata sha katafi. Shiru nayi tsaye a wajen har kusan minti ɗaya. Sanin banda wata mafita saita wajensa ɗin ya sani nufar dining room ɗin sa. A cikin haɗaɗɗen freight ɗin dake a wajen na buɗe na ɗakko goran ruwa masu sanyi sosai saɓanin wanda yace marasa sanyi. Batare dana ɗora a saman tray ba ko ɗaukar kofi na fito. Har yanzu yana a yanda yake hankalinsa a laptop ɗin. Ruwan na dangwarar masa kawai ina tura baki. Ganin yaƙi nuna yasan dani ma a wajen ya sani faɗin, “Ga ruwan nan zan tafi”. Shiru bai kulani ba. Baima ko motsa ba. Takaici ya sake riƙemin maƙoshi, sai dai nasan fushi na bazai haifar min da komai ba sai ma sake tunzurashi. Sassauta muryata nayi a hankali na ce, “Please ka bani key na fita”. Nan ma shiru bai da niyyar kulani, tuni idanuna sun fara cika da ƙwalla. Kusan minti ɗaya sannan ya magantu ciki-ciki. “Ban hanaki shiga cikinsu ba?”. Da farko ban fahimci abinda ya faɗa ɗin ba. Sai daga baya na fahimci akan ma'aikatan gidan nan ne maza da ɗazun a compaund. Dan haka cikin son manna masa rainin wayo na ɗan duƙo kansa kaɗan duk da yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri cikin dakewa na furta, “A matsayinka na wa?”. Wani irin lumshe idanunsa dake yawo a fuskata yayi, yayinda ni kuma na yunƙura da nufin barin wajen kawai naji an bugi ƙafafuna. Gaba ɗayana na tafi, duk yanda nai ƙoƙarin son riƙe wani abu hakan bai yiwu ba sai da na faɗa kansa na zauna daram a cinyar tasa. Yanda na faɗo ɗin fuskokinmu suka kasance gab-gab da juna. Wani irin kallo yake min cikin tsakkiyar ido daya hanani iya koda motsi, kafin a hankali ya sake matso fuskar tasa gab da tawa. A take gaba ɗaya tsigar jikina ta mimmiƙe. Sai kawai na lumshe idanuna a hankali dan nagama sadaƙarwa akan nawa lips ɗin zai sauke nashin. Amma a maimakon hakan sai jin saukar yatsarsa nayi a saman lips ɗina ya shiga zagayawa a hankali, tare da sassanyar muryarsa cikin kunnena ya furta, “I'm not interested”. Da sauri na buɗe idanun tare buge hannunsa dan har yanzu yana zagaya yatsarsa akan lips ɗin nawa. Bamma san sanda na watsa masa harara ba da ɗora hannayena akan ƙirjinsa na turashi baya. Ni kuma nai yunkurin tashi zumut. Amma tsabar mungunta sai ya sake taɗeni da ƙafar na sake komawa kan jikin nasa. Hannun na sake kaiwa jikin nasa zan turashi naji saukar nasa a bayana. Matsoni yay gaba ɗaya sai gani kwance a ƙirjinsa. A fusace na buɗe baki zanyi magana ya rufesa rufff da mitsitsin nashi. Waro idanun nawa waje nayi gaba ɗaya cikin tashin hankali da rikicewa, shima ya ɗan waro nasa kaɗan sai kuma ya kashe min ido ɗaya cike da salon iskanci. Ai ruff na sake rufe nawa idanun jikina na rawa. Duk yanda naso ƙwace jikina hakan ya gagara, dan yayi masifar min irin riƙon da ban isa ƙwatar kan nawa ba. Da wani irin kalar salo yake sarrafa halshena cikin bakinsa. Duk mintsinin da nake masa babu alamar yana jina ma. Sai da yay mai isarsa dan ko kiran wayarsa da ake faman yi bai kula ba, gaba ɗaya jikina ya gama saki. Koda ya sakan sai kawai na duƙunƙune a jikin nasa ina sauke numfashi a gwagwgwame jikina sai rawa yake. Shima cikin furzar da nasa numfashi da shaƙaƙƙiyar murya har tana siezing a hankali ya furta, “Na miki abinda kike buƙatar ai. Sai yaushe za'a ɗaga ni”. Bai ma gama rufe baki ba na miƙe zumbur. Batare dana kallesa ba na fisgi ɗan kwalina dake a jikinsa. Cikin haɗa hanya na nufi barin wajen, dan duk masifar da nake ji zan masa akan abinda ya faɗa min ɗin yanzu bazan iya furtawa ba. “Ribbon”. Ya faɗa ƙasa-ƙasa muryar tasa a shaƙe har yanzun. Kamar zan sharesa sai kuma dai na Juyo dan bana buƙatar barin komai nawa a sashen, ribbon ɗin nawa na hanga akan jikinsa. Sai da na runtse ido sannan na nufesa, hannu na kai zan ɗauka amma sai ya gyara zama ta yanda ribbon ɗin ta koma tsakkiyar ƙafafunsa. Kauda kaina nayi da sauri, tare da juyawa cikin sassarfa nabar wajen dan ni kaɗai nasan abinda idanuna suka gane min. A mamakina ina kaiwa ƙofa na murɗa handle ɗin sai gashi ta buɗe. Ƙoƙarin juyowa nayi na kallesa sai naga yana ajiye remote alamar shine ya buɗe ɗin kenan. Harara na watsa masa dayin ƙwafa cike da tsiwa na ce, “Kuma ALLAH ya isa na, sai na gayama Ummie”. Na ƙarasa fita da sauri har ina bugewa da ƙaton flowers base dake gefen ƙofar anyi decorretion da su.......✍️ _🤣Koba ALLAH ya isa ba. Muma to ALLAH ya isanmu jikinmu da aka hau🥱😜. Bara na ware kafin danginta su caskala ni🚴🚴🚴._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_ .....Tana fita ya runtse idanunsa da karfi, sai kuma ya fisgi gorar ruwan data ajiye masa ya ɓalle murfin tare da kafa bakinsa ya hau kwankwaɗa. Tass ya shanye ruwan yay jifa da robar tamkar itace tai masa abinda ya harmutsasan, sai kuma ya miƙe da hanzarinsa ya nufi side ɗin da bedroom ɗinsa yake yana famar haɗa hanya da furzar da huci a jajjere da taunar lips kamar zai huda su da haƙori. ★Kai tsaye nima side ɗinmu na nufa maimakon komawa ƙarasa abincin Ummie. Ko kallon waɗanda ke a falo banyi ba na afka bedroom. Karo mukaci da Bahijja, dan haka ta riƙeni gam cikin kiɗima da ganin yanayina ta ke furta, “Aunty Kandala lafiya kuwa? Mike faruwa dake na gankai haka a birkice? Ko hajiya babba ce?.” Hannunta na ture daga jikina batare dana iya magana ba. Cikin sassarfa na nufi bathroom ɗinmu dan bana fatan taji ƙamshin turarensa daba ɓoyayye ba a gidan a jikina. Ina shiga kai tsaye ƙarƙashin shower na shige na sakarma kaina ruwa kawai. Dan bani da wani zaɓin daya wuce hakan. A jajjere na dinga sauke ajiyar numfashi sai ga hawaye sharrr-sharrr kamar an buɗe fanfo.... 💦💦💦💦 Tun fitowar Samraah da ga sashen Maash Hajiya Mammah dake laɓe ta bita da kallo. Duk da ƙamshin turarensa da yanda Samraahn ta fito ya sata farin ciki dan ta tabbatar akwai abinda ya faru koda ba wanda sukayi fata bane. Amma dai ba haka taso ba. Taso a yau komai da suka shirya ya faru kawai dan itafa tafi son idan ta saka abu a gaba kawai tayisa a wuce wajen. Har ta nufi barin wajen sai kuma ta fasa. Part ɗin Maash ɗin ta nufa, kanta tsaye ta buɗe ƙofar ta shiga da sallama. Babu kowa a falon sai uban ƙamshinsa da sanyin ac. Sai television dake aiki sai dai babu ƙara sosai. Idanunta ne suka sauka akan tray ɗin abincinta. Trayn ta zubama ido na tsawon sakanni, sai kuma ta nufi inda yake. Tana gab da kaiwa ta tsaya cak, tabbacin jin motsi ya sata komawa da baya da sauri ta fita a sashen gaba ɗaya. Sai kuma abinda tayi ɗin ya sakata dariya. Kaɗan ta dara tana nufar nata part ɗin. Da kallo Hajiya ƙarama da komai ya faru akan idonta ta bita. Lips ɗinta ta cije da ƙarfi sai kuma ta saki ƙwafa. A zuciyarta tana ayyana lokaci fa yayi da zata amshi kayanta kafin wannan matar ta mata shigar sauri. Amma dolene ta bincika mi take ƙullawa akan Maash ɗin haka ne. Gaba tayi da yanzu bata da wannan lokacin asibiti ta nufa. Tanada aikin da zatayi na kuɗaɗe masu nauyin gaske. Dan haka tai ficewarta cike da takun kasaita irin na manyan mata gogaggun kuma ƴan boko... Hajiya ƙarama ke kuma....🤔 (To Bara dai nayi hiru.🥱 ✨💫✨💫 A ƙofar gate Mansoor yaci karo da Mamy. Ɗauke kansa yay tamkar bai ganta ba zai wuce. Amma sai ta riƙo masa hannu cikin tashin hankali. “Mansoor mika aikata?”. Kansa tsaye ya bata amsa da, “Sakinta nayi. Dan bazan iya koda zaman minti ɗaya da ita ba Mamy”. “Baka da hankali Mansoor. Kasan muhimmancin auren nan a garemu baki ɗaya?”. “Bana son na sani Mamy kiyi haƙuri”. Daga haka ya zare hannunsa yay gaba abinsa yana ƙoƙarin shiga taxi ɗin da yazo. Dan dama bai sallamesa ba. Binsa kawai Mamy keyi da kallo komai ya ƙwace mata. Har motar tabar wajen bata iya taɓuka komai ba. Sai da motar su Hajiya Sakeena da zasu wuce asibiti ta fito sannan ta dawo firgigit. Ƙoƙarin isa ga motar tai tana tambayar mike faruwa. Dan taga Hajiya Sakeenar na kuka. Cikin masifa da hayayyaƙowa tamkar ba yayarta ba ta ce, “Koma miya faru ba huruminki bane ba. Kije ki zauna gida ki jirani. Dan wlhy in har yarinyata ta mutu kota nakasa sai ke da ɗanki kunyi dana sani” daga haka ta dakama driver tsawa akan su je. Nan ɗin ma sake sumar wucin gadi Mamy tayi, ba kuma ta dawo a hayyacinta ba har sai da sukai nisa. Mansoor kam kai tsaye anguwar su Samraah ya nufa. Ya ɗan jima tsaye a ƙofar gidan sai ga wata mata ta fito tana ƴar dariya. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Jikin gate ɗin ya matsa zaiyi knocking sai ya jiyo kamar hayaniya. Fasawa yay yayi ɗan jimm alamar saurare. Masifa wata mata keyi harda zagi, sai kuma wata siririyar murya na dariya cikin shaƙiyanci. Mamaki hakan ya basa, sai dai yaji nutsuwa a cikin muryoyin babu na Samraah. Amma kuma bai taɓa zuwa gidan nan yaji haka ba. Yana tsaye a wajen sai ga matar ɗazun ta dawo. Daurewa yay ya gaisheta ta amsa masa da ɗan kallon mamaki. Dan kuwa dai ta ganeshi sosai. Ai Mansoor ɗin Samraah ba ɓoyayye bane a layin nasu kodan aikin gidan tv da sukeyi tare. “Ihmm niko kamar Mansoor?”. Cikin jin daɗin ta ganesa ya amsa mata da cewar shine. Tare da roƙonta ta turo masa Samraah dan ALLAH”. Murmushi tayi tana ɗan girgiza kai. Sai kuma ta amsa masa da, “Ayya Mansoor ai Samraah bata nan tana Lagos ne ko Abuja naji ance. Amma dai kamar Lagos ɗin”. Da mamaki yace, “Lagos? To yin me?”. Ɗan jimm tayi alamar tunani. Sai kuma ta kaɗa kanta da faɗin, “Tare da mijinta mana. Amma dai ka nema Abban nasu ko ƴaƴanta Musaddiq mana”. Daga haka tayi shigewarta tabar Mansoor da sakakken baki.... ❤️💦❤️💦❤️ A ciki kam Mom ce ke fitina akan Halime bata isa yin girki a gidan ba yau. Dan tun randa ta tabbatar itace sukai uwar fitina da Abba har takai ya shashsheka mata maruka tare da gargaɗi mai ƙarfi akan iskancin kai hannu jikinsa da take sonyi a kwanakin nan, zata shaƙe masa kwala, ko zata cutar da shi. Acewarta gara ta murɗe kowa ya huta. Wannan mari ya girgiza Mom har ma da Ummanta. Yayinda Halime take ɗaki tana kwasar dariya. Bawai marin bane ya bata dariya itafa. Firgicewar Mom da ganinta matsayin matar mijinta ne kawai ke bata nishaɗi. Dan a take abubuwa data ɗan sani a gidan na ƙarfin Mom ya shiga dawo mata. Tana ji Abba zai shigo ta haɗiye dariyar ta. Umma itace ta killafa Mom ta ƙarfi, ta kuma tabbatar mata idan fa bata kwantar da hankalinta ba har aurenta ya mutu to gaskiya kada tazo mata gida. Wannan hauka har ina aita tarota tana ƙwacewa kamar wata ƙaramar yarinya. Su nutsu su fuskanci abinda ya dace suyi amma ta zauna yin hauka akan wanda shi sam hankalinsa ma baya a kanta yanzu. Wannan faɗa ya sakata nutsuwa. Har Abba ya gama kwanakin angwanci a ɗakin Halime bata sake kula kowa ba. Da ya dawo ɗakinta kuma yaso nuna ɗaukar fishi da ita. Sai dai roƙon da Musaddiq yay masa ya sassauta abun. Dan haka ya haɗasu su duka gidan har Nabil dake makaranta yay musu nasiha tare da tabbatar musu da Halime itama yanzu ɗaya daga cikin family ɗinsu ce, sannan baya buƙatar damuwa daga kowa. Abbas da Musaddiq da Nabil ne kawai sukai magana da amsar Halime. Amma Baby da Bibaa ko kallon uban ma basuyi ba. Watsar dasu Abba yayi, sai ma maganar bikin Baby daya tabbatar musu ya gama tsayar wa nan da wata biyu, tare da sanar musu alkairin daya samu Musaddiq dan nan da sati biyu shi kuma zai wuce ƙasar Chaina. Yaso ayi bikin Baby da Musaddiq ɗin, sai dai hakan bazai yiwu ba saboda komai na tafiyarsa ya gama kammala. Wannan magana itace ta hargitsa Mom matuƙa har ta danne mata al'amarin Halime a kwanaki biyun nan. Ummanta ce ta bazama wajen teachers ɗin su. Shine jiya da dare aka kawo abinda zatai amfani da shi akan Musaddiq dan daƙile wannan batun tafiya. Yau kuma ake son yaci a cikin abinci. Da rana baya gida, dan haka ta gama shiryama girkin dare gashi ba itace da girkin ba. Sai kuma ga Halime ta shiga domin ɗorawa saboda kowa yasan ita ya kamata tayi girkin daren. Ga kuma Abba yay kiranta da sake tabbatar mata dan har ma ya aiko yaro da cefane. Shine Mom tace bata isa ba itace zatai girkin. A lokacin makwafciyarsu da sukai magana da Mansoor na gidan. Shine ta raba gardamar ta sake tabbatarma Mom cewar Halime dai ya kamata tayi girkin daren. Kawai sai Mom ta fara tura mata ashariya. Shine ta fito tana Murmushi yayinda Halime ke dariya. Dan ita al'amarin Mom ɗin yanzu dariya ma ya koma bata. Mace kamar mai mutsukku a cikin kai. Murhun gawayi makwafciyar tasu ta kawo ma Halime tunda dama abin girkin kawai take buƙata komai na ma'aikaci itama tana da shi. Harda ƙullin gawayi biyu... 💕🌟💕 Bluetooth ɗin dake cikin kunnensa ya zare yana mai sakin wani kalar lalataccen murmushi. Sai kuma ya sake maida fuskarsa ya tsuke tamkar bashi ba. Tamkar ba wanda ake jira ba ya shiga zare kayan jikinsa a nutse dan babu alamar wani gaggawa a tare da shi. Dogon wandon jikinsa kawai ya bari batare da ya cire ba ya nufi closet ɗinsa. Daga can kusurwar bango Ya danna wani maɓalli, a take adon wutsiyar wadrobe ɗin dake ta dai-dai kona ɗin ya shiga naɗe kansa. Zallar gilashi garai-garai da haskensa kesa a iya ganin komai dake a cikin wajen ya bayyana. Nan ɗin ma dai wani abu ya danna, a take gilashin yaja kansa ya shige cikin wadrobe ɗin. Zallar adon golden ya bayyana da bindigu har guda uku da aka manna a bangon wajen tamkar an zana sune. Hannunsa duk biyu ya tura a cikin aljihun wandon, tare da gyara tsaiwarsa ya zubama bindugun ido. Biyu ƙananu ne, ɗaya ƴar babba hakannan daka ganta kasan zatai haɗari da tsada. Cike da wani salon taƙadaranci ya cije lips ɗinsa tare da zare hannunsa ɗaya ya maida gashinsa daya sakko masa a fuska kaɗan saboda salon gyaran dayay masa ɗazun da yamma. Sauke hannun yay a hankali ya kai yatsarsa ɗaya saman bindigar farko, tamkar mai zana abu sannu-sannu ya dinga sakkoshi ƙasa har ya dire akan ta tsakkiya, nanma bai tsaya ba yay ƙasa har sai da yaje ta ƙarshe. Zagaya kan bindigar ya cigaba dayi da yatsar tasa kusan sakan biyu sai kuma ya sake maidashi sama ya ɗora akan ta tsakkiyar. Nan ma yaja kusan sakanni biyar ma tamkar mai nazari sai kuma ya laɓe baki cike da salon ɗage kafaɗu ya ciro bindigar alamar zuciyarsa tafi aminta da ɗaukar tata. Sauran mahaɗanta dake gefenta suma kowanne a mahallinsa ya cicciro harda bullet kusan biyar sannan ya maida komai a yanda yake ya fito. Cikin bedroom ɗin nasa ya dawo, ya zauna a katafaren bakin gadonsa ya haɗa bindigar tsaff cike da ƙwarewa ya ajiye, sai dai bai saka bullets ɗin ba ya jawo side drawer ɗinsa ta gado ya zuba su ciki. Bathroom ɗin ya nufa abinsa cike da takunsa na mazantaka da nutsuwa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ......Ina kitchen ina ƙoƙarin haɗama Ummie madara kamar yanda na saba a kowanne dare yanzu saboda naga tana sonta sosai Hajiya Mammah ta shigo. Kamar ko yaushe tsaff take cikin kwalliya mai ɗaukar ido da ke nuna ita ɗin wacece. Sosai take matuƙar bani mamaki matar nan. Itafa dare baya hanata kwalliya kamar jikanyar ifiritai, musamman idan akace tana da baƙuwa da zata kwana a gidan. Gaisheta nai a ɗarare da ƙoƙarin kauda kai daga kallon ƙurillar da take bina da shi daga sama har ƙasa. Kadaran kadahan ta amsa min sai dai fuskarta a sake. Juice ta ɗauka ta ɗaura a samar tray tare da glass cup, sai ƙaramin bowl da aka yanka fruit yay ƙyau sosai musamman yanda kalolinsu suka fito a farin glass bowl ɗin kamar an zana, sai kuma wani haɗaɗɗen kula shima mai ƙyau duk ta ɗora, har zata ɗauka sai kuma ta dakata. Kallona tai tare da tukunyar da nake dafa madarar. “Kandala mi kike dafawa anan?”. Fuskata a ɗan cinkushe, na ce, “Hajiya madarar Ummie ce”. Kanta ta jinjina tare da faɗin, “Okay Masha ALLAH. Ta kusa kammaluwa ne?”. “A'a yanzu na ɗora ai babu jimawa”. “Okay! To kinga zonan kimin wani aiki sai na jire miki. Awwab zaki miƙama wannan part ɗinsa. Azizat ya saka Paah ɗinsu kuma ya sakata aiki, Awwab kuma baya son jira zai iya fasa sha kuma nasan ba wani abu yaci ba”. Ji nai kamar na fasa ihu, sai dai nasan ban isa cewa bazanyi ba. Amma a cikin raina na ɗan yi mamaki, to amma ina ruwana ba yayar babansa bace. Cikin haɗiye yawu da ƙyar na amsa tray ɗin, ɗauke juice ɗin tayi da glass cup ɗin tana faɗin, “Banda wannan nawane. Kiyi maza zan koma sama ne”. “Okay maa”. Na amsa mata cike da jin haushi. Acan ƙasan raina kuwa jinake kamar na haɗiyi zuciyata na huta. Amma dai ba komai, dan nima kai fruit salad ɗin zai min amfani, dan dama ina son ganinsa. Dan akwai bashina a kansa, bazan taɓa barin maganar daya gasamin ɗazun da safe ba sai na maida murtani, idan ba hakaba zan iya kasa barci ma wlhy. Kamar koyaushe a nutsena nake tafiyata. Jikina da hijjab iya gwiwa mai hannu kamar kullum. Duk fa amatsayin ƴar aiki nake gidan kamar yanda shaiɗanin ya ƙalabamin akoda yaushe zaka sameni cikin tsaftata, dan inada ƙyanƙyami, ga son wanka kamar ƴar agwagwa. Komai a gidan free ne har gamu masu aiki, banbancin kawai komai zakayi kai da kanka ne masu gidan kuwa mune ke musu. A hankalin ƙamshin turaren da Ummie ta fesamin ɗazun har a cikin gashina ke tashi, sosai turaren ya kwanta min a zuciya. dan yana fidda wani sihirtaccen ƙamshi mai ratsa zuciyar mai shaƙa harma da kai daka saka. Na ɗakko ne zan saka mata ta fisge ta hau min feshi da shi a jikina tana dariya, bata kuwa barsa ba sai da nayi dabarar amshewa. Koba'a faɗa ba nasan an sayesa ne da kuɗaɗe masu nauyi. Murmushi na saki mai sanyi, dan yanda yake bama Ummien kulawa a gidan da kowanne nau'in abubuwan more rayuwa duk da lalurar dake tare da ita na ƙayatar dani. Sau kusan uku ina knocking amma babu alamar za'a buɗe min. “Ɗan wulaƙanci fitinanne mai girman kai”. Na faɗa a hankali ina murguɗa baki da hararar ƙofar. Cikin jin zafi na murɗa handle ɗin ƙofar na shiga falon. Kamar kullum babu yawaitar haske. Sai uban sanyin ac da mayataccen ƙamshinsa daya gama mamaye komai. Hatta kusa da mutum idan ya tsaya ko wani dalili yasa ya taɓaka koya zauna guri ya tashi ka zauna sai ka ɗeba mayen ƙamshin nan nashi. Narasa da wane shegen turare yake amfani haka. Koda yake ya wuce na tsafi. Na bama kaina amsa ina murguɗa baki. Ƙoƙarin ajiyewa nake a Centre table ɗin falon aka shigo da sallama bayan anyi knocking. Bakowa bane face Hayatu, dan haka na amsa sallamar tasa a zuciyata kawai batare dana kallesa ba na ƙarasa ajiye tray ɗin. “Barka da dare Maa”. Ya faɗa cikin girmamawa kamar yanda yake min yanzu musamman idan babu kowa a waje. Harara na ɗago na balla masa ina mai jan sirrin tsaki. Shiko yay ƙasa da kansa. Ƙafa na ɗaga zan bar wajen da sauri ya ce, “Dan ALLAH kiyi haƙuri. Ki kai masa bedroom inba hakaba bazai shasa anan ba. Dan muna uzirin fitane, Ummie kuma bata ƙaunar zamansa da yunwa duk yau babu abinda yaci kuma sai chocolate.” Wata hararar na sake balla masa. Shiko ya sake marairaicewa da faɗin, “Dan ALLAH dan ƙaunar da kike ma Ummie”. Idanuna na rumtse da ƙarfi. Kamar kar nayin sai kuma dai na ɗauka dan ni shaidace, duk randa Ummie ta cika fitina a gidan to dan gudan jinin nata ne. Sai dai kuma daya raɓeta babu sauran zaman lafiya musamman ace ya shiga ɗakin da take ko yazo kusa da ita sosai. Sai dai ya kasance a nesa da itane yanzu zata fa zuba masa ido kamar mai son tuna wani abu a kansa kosan sanin wanene shi har hotonsa haka take masa. Cikin ƴar fusatar da Hayatun ya sake saka min nai knocking ƙofar bedroom ɗin nasa da ƙaddara tasa zan masa shiga ta biyu. Nasan latsin rainin wayonsa. Zai ma iya kasancewa yana jina yay shiru, niko ina son komawa na kaima Ummie madararta tasha magani. Agadarance na murɗa ƙofar na shiga ina mai sake tsuke fuskasta da haɗa baƙar maganar dazan gasa masa da nake fatan ta hanashi barci. Wayam babu kowa a ɗakin, sai dai anan ɗin ma hasken akwai ƙaranci, sai dai yafi na falon dan anan ana iya ganin komai. Kayansa daya watsar a kan lallausan milk carpet ɗin dake a gaban gadon na ballama harara da taɓe baki. A bayyane na furta, “Ƙazami kawai sai iyayi da feleƙe, amma ba'a iya yima kai komai.” a saman bed side drawer na nufi ajiye tray ɗin, sai idona ya sauka akan bindiga. Sosai na waro idanu, jikina har tsuma yake wajen ajiye tray ɗin hannuna kaɗan ya rage ban zubar da shi ba na dai gyara masa zama ina ɗaukar bindigar. (Ta tabbata dai guy ɗin nan ɗan ta'addane. Yo anya ma ba ɗan fashi da makami bane? Kambu aiko yau zan tona asiri, zai ko tabbatar ya kawo ƴar jarida gidan nan) na ƙare zancen a zuciyata ina sakin ƙwafa a fili. Ƙofa na zabura zan nufa ina ƙoƙarin soke bindigar a cikin jikina. Dai-dai nan aka buɗe ƙofar bathroom. Naji firgici, dan yanayina ma ya nuna hakan sakamakon a yanda na jiyo na kalla wajen. Ganin shine ɗaure da towel iya ƙugu zuwa gwiwa yana riƙe da ƙarami a hannunsa zai kai shi fuskarsa amma ya tsaya yana kallona nai saurin ɗauke idanun nawa tare da zaburar son nabar ɗakin kafin ya farga da abinda na ɗauka. Sai dai me ina isa jikin ƙofar naji ta bada ƙitt alamar rufewa, duk da kuwa a rufen take dama. Ban fasa kai hannuna jikin handle ɗin ba, na murɗa na murɗa amma ko gezau tabbacin dai an kulle. (To ta yaya?) Zuciyata ta tambaya, rashin amsa da makama ya sani juyowa, sai ko idanunsu suka sauka akan ƙaramin black & golden remote dake hannunsa alamar da shi ya kulle ƙofar. Dan yanda ya ɗauke kansa tamkar baiyi komai ba ya sake tabbatar min da hakan. A ɗan zamana gidan na fara haddace mugayen halayensa a cikin kaina. Dan babu ubanda yake ragamawa da wannan murɗaɗɗen halin nasa na rashin mutunci. Ko kallona bai sake yi ba ya nufi gaban mirror ɗinsa hankali kwance. Saurin kauda idona nayi daga kansa dan dama dai a gaba ɗaya cikin sakanni da baifi goma bane komai ya faru, ban kuma iya masa ko kallon sakan ɗaya cikakke ba saboda yanayin da yake ciki, dan ma babu yawaitar haske a ɗakin ne shiyyasa. A bazata cikin dakewarsa da daƙilallen yanayi irin na mugayen muskilan mutane a silent voice ɗin nan nashi ya furta, “K idonki bazai daina gane-gane ba ko?”. Sam da farko bammayi zaton shine yay maganar ba. Sai da nai ɗan jimmm sannan na fahimta. Baki na murguɗa batare dana kallesa ba cike da tsiwa nima na furta, “In dai masu mugun halin ta'addanci na a inda nake gane-gane ma yanzu ya fara ai. Kuma in kere na yawo zabo na yawo wataran za'a gamu. Adai juri zuwa rafi. Saboda wataran tulu zai fashe a tsakkiyar kasuwa. Dan in ma an binne wani abun wani bazai binnu ba. Musamman ma Samraah Abdul-wahab Gwarzo”. Shiru bai tanka min ba. Ni kuma na kasa iya ɗaga ido na kallesa saboda a yanda yake samandagari guda babu riga ƙaton kawai. A bazata matuƙar bazata naji tsaiwar mutum a kaina daf, ai bamma san sanda na ɗago ba a harmutse. Ƙamshin turarensa ne yay mugun rige-rigen shiga min hanci saboda iskar razana dana shaƙa da ƙarfi. Kusancin namu yayi yawa dan haka nai matuƙar zabura baya ina ƙyaƙyƙyafta idanu uwa ya na namijin biranya. Hannu ya miƙomin alamar na bashi. Nasan bindigarsa yake nufi, amma sai na balla masa harara na ɗauke kaina. Dan ya kafeni da muggan idanunsan nan na maguna. Sai dai yanda nake a tsorace yasa a ankare nake karya shammaceni. Ina kuwa ganin ya motsa na sake zabura baya. Ganin kaina yayo na ɗage zan falla da gudu koda cikin bathroom ɗinsa ne tunda ya kulle nan mugun yasa ƙafa ya taɗoni, sai gani zube a saman gadonsa.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ......Da wani kalar sauri da rawar jiki na motsa zan tashi, zuciyata na wani kalar masifaffen gudu a cikin ƙirjina tamkar zata fito ta baki ya hana hakan ta hanyar ɗora ƙafarsa ɗaya a saman gadon ɗaya a ƙasa ya ranƙwafo yay mun rumfa. Hakan ya saka kammu gwaruwa waje ɗaya saboda na riga na ɗago. Wani azabane ya ratsa min goshina, da sauri na koma tare da dafewa da hannayena duka biyun ina faɗin “Wayyo ALLAH mai kan rodi ya fasan kai na”. Nayi kusan minti ɗaya a haka raɗaɗi na ratsani dan da gaske naji zafi kafin na janye hannun ina ƙoƙarin hana hawayen da suka cika min ido zubowa, bindigar na ciro daga hijjab ɗin na nunasa da ita, cike da masifa na buɗe baki zanyi magana amma a mamakina sai naji bakin ya gagara motsawa, sai rawa lips ɗina kemun kar-kar da motsi a hankali. Dan wani irin masifar jinai ya cika min ko'ina. Hatta ɗakin jina nake a matse matuƙa a cikinsa. Idanuna na rumtse da ƙarfi ina sake wayancewa na maida hannuna saman goshin na dafe, ɗayan kuma dai na nunasa da bindigar. A cikin zuciyata nake jera masa ALLAH ya isa. Jin kamar ana ƙoƙarin saka min abu a jikin tsintsiyar hannuna ya sani saurin ƙoƙarin janye hannun. Bamma san sanda na sake zaburowar ba ganin ya saka min handcuffs. Hannun nai ƙoƙarin fisga shi kuma ya cire key ɗin daya kulle handcuffs ɗin dai-dai nan. Bindigar hannuna ce ta faɗi. “Malam minene haka kayi?”. Na faɗa cikin gigita da ruɗewa. Bai tanka min ba, sai ma ƙoƙarin sauke ƙafarsa yake yi, cikin ƙunar rai da rufewar ido na sake buɗe baki zan yi magana tare da kai ɗayan hannuna zan damƙoshi batare dana san mi nake shirin yi ba ya wani kalar juyowa. Farin yatsarsa mai ɗauke da dogon farin farce ƙal-ƙal masu sheƙi ya ɗaura saman pink ɗan ƙaramin lips ɗinsa. “Shiii!!!” ya faɗa yana wani waro min cat eyes ɗinsa masu girma da cikar gashi. A take tsigar jikina tai bala'in tashi. Bamma san sanda nai saurin kauda kaina ba bakin nawa na rufewa bamm batare dana iya furta ko a ba. Ga hannuna da nakai zan riƙosa na tsaye ƙyam, ban sauke ba ban kuma ƙarasa kaisa jikinsa ba, dan sai yanzu nama fahimci taɓargazar da naso yi... Maash dake bin fuskarta da wani ɗan iskan kallo zuciyarsa na wani masifar hanƙoron mamakinta a cikin ƙirjinsa ya janye idanun ya saukesu akan hannunta. Sake tsuke fuskar yayi, a kausashe ya furta, “Idan wannan small hand ɗin ya sauka jikina You will regret it har wayewar garin yau”. Ya ƙare maganar yana kaɓar da hannun tare da ƙoƙarin ɗaukar bindigar nai saurin ɗaukewa kafin ya kai nasa hannun na tura cikin skirt ɗina. “Humm” ya faɗa yana wani shanye girman idanunsa da jan sirrin tsaki da yay matukar zafata. Sake rumtse idanuna nayi ina mai sake tsuke fuskata nima, cikin nuna alamar ɓacin rai, batare dana buɗe idanuna ba cike da tsiwa na furta, “ALLAH ma ya tsari ɗiyar Abdul-wahab da taɓa trash body irin naka, jiki duk ta'addanci da jinin mutane ma. Sannan ma ni ba ƴar iska bace dazan taɓa jikin maza. Kuma wlhy ka tashi min a kai tun kafin kai na saka kai regretting ɗin yanzun nan terror kawai an saba bin na hotels”. Ban gama rufe baki ba naji saukar yatsunsa a saman lips ɗina. Wata irin masifar azaba ce ta ratsani saboda yanda ya haɗesu ya matse a waje guda, tsabar iya mugunta da baƙin hali ya dinga murzawa. Kusan sakan talatin sannan ya daina murzawar tuni idanuna sun cika da ƙwalla. Yayinda ɗayan hannuna ya shiga kai masa duka akan ƙatoton damtsen hannunsa amma mugun ko gezau. A wata sabuwar bazatar da ruɗani da tashin hankali na sake jin saukar hannunsa a saman cikina. Ihu nake son ƙwalawa amma babu dama ya riƙe bakin. Da bala'i-bala'in ƙarfi na gimtse idanuna da ƙanƙame jikina saboda yanda ya damƙi bindigarsa dana tura a wajen tare da fatar shafaffen cikina. Ai da azabar ƙarfi na dunƙule hannuna na buga masa a damtsensa ina fisge kaina amma yaƙi sakin lips ɗin nawa saima sake matsesu yake. Ɗayan hannuna kuma dana dakesa da shi ya sake zuramin wata handcuffs ɗin itama ya ratayo jikin ƙarfen net ɗin da akai kwalliyar gadon da shi, dan ƙarfene a wajen. Fisge-fisge na farayi, amma ko'a jikinsa saima ya ɗakko salataf ya nane min bakin da shi bam. Tashi yay tsaye sosai akan ƙafafunsa, na fahimci hakan ne a dalilin jin iskar ac na ratsani dan rankwafowar da yay ɗazun a kaina koma jinta banayi sam. Idanuna a rumtse suke dan bazan iya kallonsa ba. Fisge-fisgen na cigaba da yi ina uhum-uhum! Na ƙoƙarin yin magana amma ko uhum banji yayi ba. Hakan ya sakani buɗe idanuna kadan, sai na hangosa can ya nufi ƙofar da nake ƙyautata zaton closet ɗinsa ne saboda labulen da aka saka a wajen fari ne shara-shara kuma ƙofar wajen an yita da girma sosai. Hawaye naji suna ƙoƙarin sakko min, amma nayi ƙoƙarin hana hakan dan bazan taɓa yarda yaga gazawata ba. Kusan mintuna goma sai gashi ya fito. Cikin ƙananun kaya baƙaƙe yana ƙoƙarin ɗora baƙar jacket milk mai ƙyalli a samansu. Ko kallon inda nake baiyi ba, ya ƙarasa gaban mirror ya fesa turare da ƙara kwantar da kwantaccen gashin fuskarsa dama nakan nasa da ya ɗaure waje guda. Boot takalman daya fiddo baƙaƙe masu ƙyau daga sama ya zauna bakin gadon ta kusa dani ya saka. Matsar da jikina nayi baya ina ƙunƙunin da ba'a ji tunda bakin a rufe yake. Sai da ya gama saka takalminsa batare da ya kallan ba ya miƙa hannu ya ɗauka tray ɗin dana shigo da shi, ƙaramin stool yaja gabansa ya ɗora, hankalinsa kwance ya fara kai fruit ɗin bakinsa a nutse tamkar baya so. Ɗauke idanuna nai daga kansa ina ƙwafar da ba'a ji sosai, amma nasan zai iya yajin shi. Sai dai mugun ko a jikinsa yama ƙi nuna yasan dani. Baifi cokali biyar yayi ba ya ture gefe, tissue ya ɗiba ya goge bakinsa yana miƙewa. Yanzun ma ko kallona baiyi ba ya nufi ƙofar fita ya buɗe ya fita duk da buge-bugen da nake uhhhum-uhhhum ɗin dai bai kulanin ba. Fitarsa da minti baifi biyu ba har na fara hawaye sai gashi an sake buɗe ƙofar. Shegen karen nan nasa ne ya shigo. Shi kuma biye da shi, ya tsaya daga bakin ƙofa idonsa akan karen cikin bada umari yay masa nuni da ni yana faɗin, “Ko yinƙurin cire abinda ke bakinta tayi Laalah ka gutsire lips ɗin na bar maka su ƙyauta”. Shegen karen kuwa kamar wani mutum ya wani kaɗa bindi yana nufo ta gefen gadon ta inda zai iya ganina ya kwanta ya zubamin ido. Yanzun kama rawa jikina ke min, dan wlhy tsoron makirin karen nan nake ji over. Ya riga ya masa wani azzalumin training da in akace maka yay wani abun saika ɗauka ma ƙarya ne. Wlhy da ace bakina a buɗe yake haƙuri zan bashi, amma ina zalumin ya rufeshi. A hankali ya tako cike da ƙasaita inda nake, ya ɗan hawo gadon tare da kwanciya yana facing ɗina. Fuskata na kauda. Amma sai ya saka hannunsa ya maidota ta inda yake. Gira ɗaya ya ɗage cikin ƙanƙance idanun da ƙara maida muryarsa low ya furta, “Kwantar da hankalinki kema yau zaki samu abinda nake bama na hotels ɗin, Ba sai kin nuna jealous ba, ke dai kawai jirani na dawo”. Baki na cije da matuƙar ƙarfi ina jin kamar na shaƙosa amma babu dama. Haka ina ji ina gani ya tashi bayan ya sumbaci gefen fuskata cike da shaƙiyanci ya rufe ƙofar ya fice abinsa. Sai kawai na sake fashewa da kuka dan bani da zaɓin daya wuce hakan. Hayatu da ƙin fitowar Samraah ta sakashi yawaita kallon ƙofar jin motsi ya sashi ɗagowa. Akan ogan nasa da sam bama shi yake kalloba shi ya zuba su. Sai dai kwarjininsa da cikar haiba ta cika masa idanun, janyewa yay tare da miƙewa cikin nuna girmamawa ya furta, “Barka da fitowa Yaya”. Kai kawai Maash ɗin ya jinjina masa yana mai cigaba da kalle-kallensa, can kuwa idanun nasa suka sauka akan abinda yake nema wato Laalah. A can ƙasan maƙoshi da silent voice ɗin nan nasa mai fita a daƙile lips ɗin na motsawa da ƙyar ya furta, “Laalah!”. Azabure karen ya miƙe da ga inda yake ya nufosa da gudu-gudu. Bai masa magana ba yay gaba shiko ya bisa. Da kallo Hayatu ya bisu da ga shi har karen ta ƙasan ido. Yana nan tsaye cikin mamaki sai gashi ya sake fitowa dan bai wuce mintuna biyu da wasu sakanni ba. Yanzun ma bai kallesa ba face nufar ƙofa da yay yana faɗin, “Let's go”. Da sauri Hayatu ya kwashi kayan daya zube a Centre table wanda duk takardu ne yabi bayansa. A maimakon ƙofar baya da sukafi bi yau ta babban falo suka bi. Duk da abin ya ɗan bama Hayatu mamaki sai baice komai ba, dan yasan ogan nasa yakan iya haɗa shekara ma baibi ta babban falon ba da sunan fita a gidan. Sai dai in zaije duba Ummie, ita ɗin ma sashenta na a jikin nashi ne shiyyasa akwai ƙofar da yake bi basai ya fito tanan ɗin ba, dan wannan kullum ne safe da yamma, idan ma ya yini a gidan zai iya zuwa biyar bai gaji ba.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_ .......Babu kowa a falon sai television dake aiki kasancewar dare ya fara duk al'ummar gidan sun shige ciki, hatta uwar dabar gidan Hajiya Mammah da alama yau bata kusa. Dan dama dai itace zaka zo ka iske a falon koda yaushe saboda sa idon masifa da son nuna ita a dole boss ce. Tuni guards ɗinsa da TJ sun gama shirya motocin fita. Fitowar tasa ta sakasu duk miƙewa da barin abinda suke yi. Gaishesa suka shiga yi da girmamawa. Hannu kawai yake ɗaga musu dan yau sosai ƴan miskilancin ne a kusa, ga abinda ya faru tsakaninsa da Samraah yanzu. Da sauri Hayatu ya buɗe masa bayan farar zananniyar motar da TJ ya fiddo, wadda ko makaho ya shafa yasan eh lallai kuɗi yay aiki wajen sayen ta. Dan sai wani irin sheƙi take da ƙyalli mai ɗaukar ido. Gata nan wata ƴar ƙumbula bata cika hayaniya ba, ba kuma ta cika mamaye waje ba. Tsaf take kala da yanayin matasan zamani irinsa da ke gara kan kuɗi ta yanda suke so saboda amincewar UBANGIJI garesu. Sai da ya zauna Hayatu ya maida ƙofar ya rufe sannan kowa ya zabura ya shiga mazauninsa. Hayatu da TJ na gaba kamar koyaushe. Securitys ɗin sa na'a wata motar kamar ko yaushe suma. Da dasu uku ma kawai zaiyi fitar. TJ na ƙoƙarin tada mota ta fito da ɗan saurinta. Kamar kullum tana a cikin kwalliya dake ƙara fidda mata ƙyawunta da bayyana wayewarta. Hayatu ne yay ma TJ nuni daya dakata, dan haka ya tsaya ɗin harta ƙaraso, kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta, dan direct bayan ta nufa saitin inda Maash da bai san ma da fitowar tata ba yake. Dan hankalinsa nakan takardun daya ɗauka a gefensa da Hayatu ne ya ajiye masa su dan ya duba. Cikin shagwaɓaɓɓiyar muryata data haɗe da gayu ta furta, “My bro.. please zan bika, nasan dai club zaka je”. Idan kujerar motar nan ta motsa shima ya motsa duk da kuwa muryar tata tazo masa a bazata tunda shi bai san da fitowar tasu ba. Ƙara narke murya tayi cikin nuna damuwa da shirun nasa ta sake cewa, “Please mana Yaya Awwab na shigo?”. “Kai kana jiran miye?!”. Ya faɗa cikin yanayin fusata batare daya ɗago ba. Ai jikin Tj har rawa yake wajen murzama motar key dan ko kallonsu ogansu yayi sun san mi yake nufi balle magana da baki. Da wani kalar mayen kallo Azizat tabi motar, ga wani irin sanyi ƙalau da jikinta ke komawa kamar an zubama bread ruwa. Dai-dai motocin na isa katafaren golden an black gate ɗin gidan da aka wangale musu wasu hawaye masu zafi suka shiga rige-rigen sakkowa saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Bata motsasu ba, bata kuma yi yinƙurin barin wajen ba. Ashe turaren da Mammah ta bata duk na ƙarya ne tunda gashi tazo gabansa amma bai kulatan ba. Arwa dake ta bayansu ce laɓe ta tako zuwa inda take bayan ta gama cin dariya, dan tun fitowar Azizat daga ɗaki tabiyo bayanta, dama kuma itace ta ɗauke turaren da Mammah ɗin bama Azizat ɗin dan a kunnenta komai ya faru sanda take bata batare da su sun sani ba. Hannunta ta kama kawai tare da janyota ta faɗa jikinta. Rungumeta tayi cikin sigar nuna lallashi batare da tace mata komai ba, sai dai shafa bayanta kawai da takeyi dan babu wani abu da zata faɗa mata kuma wanda ita bata sanshi ba. Sai dai kawai taƙi yarda ne kamar yanda kowa ya sani. Dan tunda yayansu yaface bayayi tofa babu ubanda ya isa cewa yayin sai Umminesa, itako batama da cikakkiyar lafiyar hankalin fahimtar abinda ake a gidan, a shi kansa ma bata masa kallo irin na mutum face ojujun dake sake hargitse lissafin brain ɗinta. Bata ganin laifin Azizat wani lokacin, dan wlhy ko ita da suke kamar uba ɗaya da Yaa Awwab ɗin a lokuta da dama takan ji inama-inama. Amma yanda tasan yana mata kallon ƙawa uba ɗaya yasa take dannewa kawai. Sun ɗan jima a wajen kafin ta kama hannunta su koma ciki... 🌜❤️🌛 A yanayin da ya shigo duk yanda Dad ke ɗauke kansa akan al'amarin nan sai da ya zuba masa ido cikin tashin hankali. Hakama Attahir da ke zaune jigum zaram ya miƙe akan Mansoor. Sai dai yana kamo hannunsa da ya dafe kansa da shi Mansoor ɗin ya kaɓe. Sai kuma ya zube cikin kujera. Amamkinsu ji kawai sukai ya fashe musu da kuka. Dole Dad ya miƙe shima. Su duka biyun sukai kansa da tambaya. Bai iya ya amsa musu ba, face kukan da yake yi da sambatun faɗin, “Shike nan na rasata. Ta auri wani bani ba. Kun cutar dani. Da kunsan irin son da nake mata da baku aitaka abinda kuka aikata ba”. Hannu Dad ya sanya a bakinsa ya rufe, kafin cikin kulawa da tausayawa da lallashi ya shafa kansa. “Please Mansoor cool down. Nasan an maka badaidai ba. Nima kuma ina ji a raina mun cuta maka. Amma yanzu in sha ALLAHU a shirye nake na gyara kuskurenmu”. “Taya zaku iya gyarashi Dad? Ta yaya? Bayan wadda kuka rabani da ita ta min nisa?. Iyayenta sun mata aure Dad, Samraah tayi aure, ta auri wani bani ba. Wlhy Dad ina sonta so na gaskiya da ban taɓa kwatanta yima wata ɗiya mace irinsa ba”. Gaba ɗaya jikin Dad sanyi ya ƙara yi, sai ma ya rasa abinda zai sake faɗa. Kusan mintuna biyu kowa yay shiru a falon sai kai-kawon zuciyoyi kawai sukaji an faɗo musu babu ko sallama balle excuses. Hajiya Sakeena ce ke faman huci da cika da batsewa. Ta watsa musu wani mummunan kallo su duka sannan ta dire idanun nata akan Mansoor. “To mara mutunci haƙarka bata cimma ruwa ba. ALLAH bai karɓi rayuwar Husnah ba kamar yanda kaso kayi fata. Kaje ka gaggaya min magana son ranka har gidan mijin aurena. To yanzu ko zakaji amsa...” Kamar an jeho Mamy itama sai gata. Kai tsaye kan Hajiya Sakina tayi. Cikin tashin hankali da mamaki ta zube a gabanta tana kuka da roƙonta ta rufa mata asiri. In sha ALLAHU indai batun auren Husnah ne zata saka Attahir ya aureta. Wata shegiyar dariyar rainin hankali Hajiya Sakina ta sanya. Kafin ta tafa hannaye da faɗin, “Iye nanaye caras-cass. Ai daga baya kenan, kema kin sanni bana manta bashin gaba ai Aunty. Ɗanki yaci zarafina ga ɗiyata ɗaya can tilo kwance a asibiti rai a hannun ALLAH. Dama na faɗa miki, in har Mansoor ya saki Husnah wlhy kema sai kin rasa naki igiyar auren dan sai na fallasa abinda kike binnewa”. “K!! Sakeena!!”. Attahiru daya gama kaiwa maƙoshi da abinda ke faruwa ya dakama Hajiya Sakina tsawa tare da yunƙurowa kamar zai mareta. Cike da rainin wayo tai wani irin ja baya tana ɗaga duka hannayenta sama alamar surrender. Sai kuma ta kwashe da dariya tana tafasu. Tsitt falon yayi kowa na kallonta har Mamy. Sai da tai Mai isarta kafin ta nuna Attahir ɗin tana haɗe fuska. “Oh lallai ashe kaima ka girma Attahiru? Ai ban sani. Sai ka saurara bada kai nake yi ba yanzu da tsoffinku nake”. Ta wani ɗauke kanta ta maida kan Dad da ya zuba mata ido kawai. Sai kuma takai zaune zama irin na ƙasaita da ƙularwa. “Kayi haƙuri Yaya idan kaga an ɗaure alƙali a kotu tofa ɗaurowa tayi. Nasan zaka so sanin yanda akayi matarka ta dage dan hana yiwuwar aure tsakanin ɗan ka da budurwarsa. Da kuma ƙullawa tsakanin Husnah da ɗanka.” Cikin ɓacin rai Dad ya tareta da faɗin, “Sakeena ki tafi maganarki kai tsaye kin san bana son shashanci”. “Uhhm hakane Yaya kayi hakuri”. Ta faɗa tana maida kanta kan Mansoor da Attahir da suka gama cika da batsewa. Kamar bataga a yanayin da suke ba ta fara bayaninta. “Idan Mansoor da Attahir basu manta ba a ranar da matashin ɗan kasuwar nan da sunansa ya shahara a ƙasar nan dama duniya yay bikin buɗe Companynsa a garin kano wato *_Awwab El-Mu'azz Adams_* da akafi sani da *_MAASH_* kun tattauna wani batu akansa da daddare daya shafi video recording da budurwar Mansoor tai masa”. Da wani irin sauri Mansoor ya ɗago yana kallon Attahir. Saurin girgiza kai shima Attahir ɗin yayi zai fara rantsuwa Hajiya Sakina ta dakatar da shi. “Kwantar da hankalinka Mansoor ba Attahir bane ba. A sanda kuke tattauna batun wannan video Aunty ta shigo sashen naku saboda damuwar rashin cin abincin kirki da Mansoor yayi. Ta kawo masa kunun tsamiya data dama masa akan ko zai sha tunda tasan yana sonshi sosai. Sai dai tana ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar ta tsinkayi Mansoor yana sanar ma Attahiru batun video tare da nuna masa shi, ya kuma roƙesa akan dan ALLAH ya rufe wannan sirrin har sai sun gano gaskiya. Ya kuma taimaka musu akan tabbatar da gaskiyar saboda shi yana da abokai ƴaƴan manyan ƙasar nan da sukayi karatu tare a us masu alaƙa da Maash. Cikin jimami Attahir yay masa alƙawarin bincikawa. Sai dai ya tabbatar masa da sam baya jin Maash zai aikata wannan al'amari da gangan in ma harfa ya aikata ɗin. Dan ya ɗan san Maash ɗin shima sama-sama duk da ba wata mu'amala mai ƙarfi bace ta haɗasu face zaman makaranta ɗaya a us. Ya kuma gargaɗi Mansoor ɗin akan ya gargaɗi budurwarsa ta adana video ɗin da ƙyau gudun kada wani ya gansa har yayi tunanin yin wani abu na cutarwa ga Maash. Dan yanzu mutane sun lalace. Ganin Maash mutum mai tarin dukiya za'a iya amfani da video dan yimishi barazana. Ɗari bisa ɗari Mansoor yaji wannan shawara ta ɗan uwansa, ya kuma tabbatar masa da zai nema itama Samraah ya gargaɗeta a daren nan ma basai gari ya waye ba. Da baya da baya Aunty ta bari sashen, ta samu kai kanta falon, ta samu ka shige sai su Amal kawai na kallo, dan haka ta samu damar shigewa ɗakinta da sauri itama. Kai kawo ta shiga yi zuciyarta na ayyana mata abubuwa da yawa akan abinda ta jiyo. Kaima dai Yaya kasan aunty akan batun kuɗi. Mace ce mai son ace ita itace. Shiyyasa ko'a sutura bata saka ƙarama. Koda bazaka saya mata ba tasan buga-bugar da zatayi ta samarwa kanta. Hakan yasa ma kuke yawan samun matsala da ita. Dan idan ban manta ba har ƙararta kasha kaiwa gida akan wannan halin nata na idan taga abu a wajen wane sai da tayisa itama hankalinta ke kwanciya tun ma baka da komai. To awannan gaɓar ma bikin Mansoor take hari. Ta riga ta gayyato ƙawayenta ƴan ƙarya irinta da matan oganninka na wajen aiki, gashi kai kuma ka kwafsa mata kaƙi yarda da duk tsare-tsaren sharholiyar da muka tsara, ka kuma ce bazaka bata ko sisi ba. Haka shima Mansoor yaƙi. Attahir ne ma ya ɗan biye mata ya bata 1mil yace ta ƙara dana wajenta tayi haƙuri. Dan haka jin wannan batun video da maganar Attahir ta kawo mata wuta a cikin kai.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚_ .......A ranar daƙyar ta iya barci kamar yanda ta faɗa min, washe gari tunda farar safiya tai kirana. Da farko kwana-kwana nima ta dinga min, sai da na nuna mata ta fito kawai a mutum muyi magana tasan dai ni mai rufa mata asiri ce sannan ta buɗe min komai. Koni zancen nata ya girgizani gaskiya. Bakomai yasa hakan ba sai jin batun Maash. Dan ni nasan wani abu kaɗan daga Maash ɗin sakamakon mijina yaronsa ne. Saboda a Companynin sa na Abayoyi dake anan Dubai yake aiki. Na buƙaci nima ta ɗan bani lokaci nayi tunani, ta roƙeni karna wuce yinin yau to. Banko wuce yinin ba, dan ta hanyar mijina na ɗan ƙara bincika halin Maash da ƙarfin ikonsa. Amsar daya bani akan cewa Maash mutum ne murɗaɗɗe, sannan yana da zafi sosai. Amma da wahala ka masa abu a farko ya maida hankali a kanka. Sai idan ka cigaba da aikatawar ne, idan har fa ya maka gargaɗi na farko baya sake na biyu sai hukunci. Wannan amsa tashi ta bani ƙwarin gwiwa, dan koba komai dai mu ai bama fata bayan na farko mu sake, yo inama zamu sake ganinsa. Wannan ɗin ma rabonmu ne ALLAH ya kawo mana har gida. Husnah ta jima tana son Mansoor amma yaƙi saurarenta, aunty kuma taƙi ƙarfafa al'amarin duk da ta sani, dan haka kawai naga ai wannan wata hanya ce ta samun cikar burina, sannan nima dai dani za'a ci kuɗin. Kai tsaye nai kiran aunty muka tattauna da tsara yanda komai ya kamata ya tafi, tare da bada sharaɗin in fa har akaci nasara a 500mil inada kaso biyu. Ma'ana inada 200mil kenan. Aunty ta nuna min bazai yiwu ba, sai dai na amshi 100mil nayi haƙuri, tunda nasan abinda ke gabanta ai. Kai tsaye na fito mata a mutum. (Aunty ke tayaya kike tunanin auren Mansoor da yarinyar nan zai kuma kasance? Mufa zamu amshi kuɗin nan ne a hannun Maash da sunanta, idan ma har ya bibiya ita zai saka a kama. Sai dai auren Mansoor ya koma kan Husnah tunda dama ba'ayi invetion ba wai ko baki gane ba). Da sauri ta amsa min da hakane fa Sakeena. Wlhy kaina duk ya cure. Yanzu dai a daren nan zan samo video daga wayar Mansoor. Ke kuma sai ki samo mana Number Maash a wayarki. Na amsa mata da karta damu, kafin ma na samar da Number zan saka a fara aika masa saƙon barazana gidansa dan akwai wani yaron mijina dake tare da Maash ɗin kuma ya san sabon gidan nasa... 🌛❤️🌜 Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso guesthouse ɗinsa. Gidane daya amsa suna gida sai dai bashi da girma sosai. Amma a ƙyau da tsaruwa ba'a magana. Dan yanda akai kusan rabin gidan da gilashi dolene ya ɗauki hankalin mai kallo. Ga wata green ciyawa da aka malala a harabar gidan aka ratsa lafiyayyen baƙin kwalta da mota zata iya bi kawai kota tsaya. Sai furanni da ƙamshinsu ya cika gidan da kukan tsuntsaye. Babu wani hayaniya, dan anguwar ma shiru ce sai uban karunuka ata waje duk da kuwa akwai securitys da baka isa ka shigoba sai da izininsu. Cikin girmamawa security ɗin daya wangale musu gate da remote ke ɗaga musu hannu, koda ya maida ya rufe motocin ya biyo. Dai-dai Hayatu na buɗema Maash mota ya iso wajen. Sannu da zuwa da gaisuwar girmamawa yake jerama ubangidan nasa. Maash dake ƙoƙarin fitowa hannu kawai ya ɗaga masa. Kafin bayan ya gama fitowa a motar a taƙaice ya furta, “How are you Semuel?”. “I am fine Sir”. Samuel ya faɗa cike da zumuɗi. Ga bakinsa washe kamar gonar auduga. Dan ya jima baiga boss ɗin ba kasancewar kwana biyu bai shigo nan ɗin ba. Tamkar wani mai mulki haka yake tafe cikin takun mazantaka da rashin hayaniya guards ɗin nasa da su Hayatu harma da TJ da Samuel biye da shi. Hayatu ne ta ɗan gefensa amma ya zartashi a taku ke masa magana ƙasa-ƙasa. Shiko yana tafiya tamkar bada shi ɗin yake ba. Dan inda yake ajiye ƙafa kawai yake kallo. Da sauri wanda ke tsaye a bakin ƙofar shiga wajen ya wangale musu ƙofar shima tare da risinawa kwasar gaisuwa wajen boss. Hannu shima kawai ya ɗaga masa. Babu alamar damuwa a tare da shi alamar dai duk wanda ke tare da shi yasan ɗabi'unsa, da girmamawa ya cigaba da faɗin, “Sir ya iso tun kusan awa ɗaya. Kamar yanda ka bada umarni securitys basu barshi ya shigo da mota ba. Kuma da yaronsa biyu aka barshi ya shigo kawai.” “Good job” ya faɗa a taƙaice yana tura kai ciki. Dan shima tun shigowarsu anguwar yaga motocin Minister ɗin tare da yaransa da aka dinkare a waje. Da ga shi sai Hayatu da TJ sai amintaccen guard ɗinsa Shu'aibu suka shiga. Kallo ɗaya yayima Minister da ya gama cika da takaici ya ɗauke kansa. Babu wani alamun damuwa ko nadamar shanyasa da yayi ya ƙarasa kujera ɗaya tal data banbanta da duk kujerun dake a haɗaɗɗen falon ya zauna. Wani shegen zaman ƙasaita da gadara yayi, yayinda Shu'aibu ya koma bayansa ya tsaya kamar saƙago. TJ ya ajiye kayan dake hannunsa a stool ɗin gefen kujerar na sashen damarsa. Hayatu kuma yakai zaune a ɗaya daga kujerun falon ta gefen kusa da shi. Bakin Minister daya miƙe domin girmamawa a washe kamar bashine ke faman tsinema Maash ɗin ba a zuciya. Amma kuma dama birgar ta bayan idoce kawai. A kallon ido cikin ido ko ganawar fuska da fuska Maash tamkar lu'u-lu'un narkakken ɗanyen zinare yake a cikin idanunsu. Duk da ƙarancin shekarun nan nasa shi fa takalmin ƙarfe ne baya takuwa a yanda kaso. To kaɗan daga aikinsa yace bazaiyi business ɗin da kai ba. Kuma babu ubanda ya isa yace komai, idan kuma kace zaka kona wajen wani saboda ka saɓa da Maash, to ka tabbata kuwa babu mai saurarenka kuma koda a ƙetaren ƙasar ne. Sai da ya tabbatar Maash ɗin ya gama zama sannan ya miƙa masa hannu cikin murmushi. Amma mi, sai Maash ɗin yaƙi bashi nasa, a maimakon hakan ma sai ya haɗe hannayensa biyu a daƙile alamar ya amsa masa. Shiko minister sai faman murmushin yaƙe yake dan abinda Maash ɗin yayi ya baƙanta masa zuciya, dan gaisuwar ma shine yayi Maash ya amsa a taƙaice. Bai nuna ya damu ba, dan lallaɓawa yake kasancewar ya jima yana neman alfarmar wannan zaman amma abin ya gagara, dan kusan wata biyu kenan. Yanzun ma da ƙyar sai da ya biyo ta wasu hanyoyin yaran Maash ɗin sannan ya dace. “Ranka ya daɗe ai kusan 1hour kenan da isowarmu”. Ya faɗa cikin son nuna an shanyasu a wayance. Kamar Maash ɗin bazai tanka ba dan hankalinsa nakan wayar hannunsa da yake daƙila, kusan minti ɗaya har ma Minister ya fidda rai da samun amsa sai tsine mar yake a zuciya a daƙilen nan ya furta, “10:30 ne ƙa'idar zuwana nan dama”. Yawu mai nauyi Minister ya haɗiye yana jinjina kai da washe baki, “Hakane kuma gaskiya. Hakan ma na gode.” Maash ɗin baice komai ba, sai ajiye wayar yay gefensa ya ɗan ɗago ya zubama Minister cat eyes ɗinsa masu kaifi da ƙarfin gani. “Zamu iya fara abinda ya zaunar damu dan banda lokaci”. Ya furta ƙasa-ƙasa batare daya janye idanun ba kuma. Ji Minister yay duk kamar ya daburce. Cikin sarƙewar harshe da in inar da bai san daga ina tazo masa ba ya fara magana yana kaɗa kai kamar tsohon jandala gwaja na ƙadangare. “Yes! Yes mizai hana. Bussines ne dama nake son mu ƙulla ranka ya daɗe, na turoma PA ɗinka kuma dukkan bayanai na. Motoci nake son a shigo min dasu kamar guda dubu biyu, idan babu damuwa bana son su wuce wata biyar. Dan nayima yarona alƙawari bana son na saɓa. Sai dai za'amin alfarmar biyan kaso ɗaya bisa biyun kuɗin daga nan zuwa ƙarshen shekara zan sake bada kaso ɗaya kasan al'amarin namu harkar gwamnati tasa fidda kuɗi kai tsaye zai iya jawo mana matsala, next shekara a wata biyar ɗin farko sai na ƙarasa biya harma da ƙarin wasu kuɗaɗe a sama. Amin alfarmar nan dan ALLAH badan ni ba badan na isa ba. Idan kuma kana buƙatar kaya sai muyi gishiri na baka manda a shirye nake” Shiru babu alamar Maash zai amsa saima cigaba da kallonsa yake wani ƙasa-ƙasa batare da yasan kallon na hargitsa jinin minister ɗin bane. Hayatu daya fahimci Maash bazaice komai bane ya fuskanci ministar a karo na farko. Kansa tsaye ya furta, “Sir amma na gaya maka akwai ƙa'idoji sosai, sannan mu bama bada bashi kai tsaye sai kabi dukan ƙa'ijin mu. Bazai kuma yiwu ka bamu kuɗi ɗaya bisa biyu ba mu kawo maka kaya. Ƙa'idarmu zaka bada biyu bisa uku ne, tare da takardun kadarorinka na adadin sauran kuɗinmu dake kanka, lauyanka da namu su saka hannu muma mu saka. Mune kuma zamu baka lokacin biya, sannan bama buƙatar kuɗin ruwanka, zamu sakama kayanmu iya ribar da muke buƙata ta cinikayya kawai wannan kuma sirrinmu ne. A sunayen motocin daka bada kuma akwai waɗanda dokar ƙasa ta hana shigo da su kwata-kwata. Mu kuma bama ƙimma doka biyayya saboda duk wanda zai mu'amalance mu dolene muma yabi tamu dokar, idan ya kauce kuma ya rage nasa. Da farko dai fara karanta wannan sune dokokinmu da sharɗin ƙulla kasuwanci damu first. Ƙa'idarmu kuma gani ɗaya ake mana, dan daga wannan zaman boss bazai sake zama da kai ba face to face. Idan ka shirya daga nan har zuwa 3 lokcinka ne”. Tuni fuskar ministar na ƙoƙarin canja yanayi, amma dai yana ƙoƙarin hana bayyanar hakan. Takardar da Hayatun ya taso ya ajiye masa a saman table ɗin gabansa ya ɗauka. Da sauri ya ɗago ya kalla Maash ɗin da yay biris da su, dan idanunsa ma a lumshe suke kamar namai barci. Sai dai makirin tsaff yake kallon Minister da su har yanzu. “Amma ranka ya daɗe yaya haka? Sannan nace inada kaya a hannu ko yanzu zan iya baku su muyi ciniki nima”. “Tsarin kenan?”. Ya faɗa a yanda yake alamar kunnesa dai na'a kansu.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_ .....Baki Minister ya buɗe zai sake magana Hayatu ya taresa da faɗin, “Ranka ya daɗe bama canjawa a yanda muke. Zaɓi biyune kawai yarda matsayin amincewa, ko haƙura ka nema wasu kuyi business ɗin kawai mu bamu da damuwa, sannan bama buƙatar wasu kayanka mu nan dan duk abinda muke nema mun san inda muke samunsa”. Wani mugun yawu minister ya sake haɗiyewa. Ji yake kamar ya zaro bindigar jikinsa ya fasa kan Maash ɗin da shegen PA ɗin nasa ma kowa ya huta. Sai dai hakan bashi yiwuwa, dan Maash na zama ya zaro tasa bindigar ya ajiye ta yanda kowa yake ganinta ƙuru-ƙuru, idan girma ne da cika aiki kuma tafi tashi a komai. Ashe girman kai da wulaƙancin yaron nan da ake faɗa masa ma ya wuce duk hakan. Yaro ƙarami da bai wuce sa'an ƴaƴan cikinsu ba sai gara rayukansu yake akan tituna saboda ya tara dukiyar da ba'asan tayaya tai tashin hauhawar gwauron zabi cikin ƙanƙanin lokaci haka ba. Gashi ya mamaye komai sai da shi a manyan Business ɗin ƙasar da ada sune masu juyasu a yanda suka so. Dolene ma suyi maganin terror ɗin yaron nan da sam babu tsoro ko shakkar kowa a cikin idanunsa shege mai ido a tsakar kai. Wata fitinar zasu ƙullo masa ta yanda ko allura bai isa sake sarrafawa ya siyar a ƙasar ba cikin daɗin rai. Dan tsalle target ɗin su na farko akan ƙin ko ganin Bussines ɗin daya zo masa da shi bashi ke nuna zasu barsa bane, akwai plan A har zuwa Z da suka tsara a kansa.... Kallon agogo da Maash yayi ya saka Hayatu daya san abinda yake nufi faɗin, “Sir kowane irin lokaci boss zai iya barin wajen nan mi ka yanke?”. Firgigit Minister ya dawo hayyacinsa. Murmushi danne ɓacin rai ya saki da faɗin, “Shike nan na amince ɗin”. “Okay zamu iya fara ciniki, lawyer ɗin mu na hanyar zuwa nan ɗin. Muna fatan tare kake da naka kai ma?”. “Eh muna tare, yana can waje inda securitys suka ce su tsaya.” Kai hayatu ya jinjina kawai yana rubuce-rubuce a file ɗin hannunsa. Kafin ya ɗauki ɗaya daga cikin wayoyi huɗu daya zube a gefensa, danne-danne yayi tare da miƙewa cikin girmamawa zuwa gaban Maash. Amsa Maash ɗin yayi batare da yace komai ba. Sai da ya kai wayar kunnensa cikin bada umarni ya furta “Lawyer ɗinsa ya ƙaraso”. Daga haka ya miƙama Hayatu wayar. Amsa Hayatu yayi shi kuma ya ajiye masa file ɗin hannunsa a stool ɗin gefensa.... Ƙarfe kusan uku suka dawo gidan, a matuƙar gajiye ya shigo, ga kansa na masa ciwo sosai na hargagin da surutun da Minister ya sashi yi. Dama sun sauke Hayatu gida, shi da TJ ne kawai da guards ɗinsa suka ƙaraso nan. Kai tsaye ya wuce bedroom, ya bar Tj na ƙoƙarin kashe sauran abubuwan dake kunne a falon. Kamar yanda ya saba kansa tsaye ya buɗe ƙofar ɗakin nasa ya shiga da sallama ciki-ciki yana ƙoƙarin zame jacket ɗinsa. A kan Laalah idonsa ya fara sauka. Har zai fara fusata tunda ba barinsa yake ya shigo masa nan ya kwanta ba sai kuma idonsa ya sauka a kanta. (Ya ALLAH) ya faɗa acan ƙasan ransa. Dan wlhy shaf yama manta ya barta anan ɗin. Sosai ta wani lafe can jikin fuskar gadon alamar a tsorace tai barcin saboda Laalah. Saletaf da handcuffs daya saka mata kuma na nan duka. Wani irin murza goshin yayi. Sai kuma yaja sirrin tsaki a ɗan kausashe da nuna harzuƙa ya furta, “Laalah get up!”. Zumbur kuwa karen ya miƙe shege da kunnen maciji dan barci yake fa. Amma tun motsa ƙofar ya wani tada kunnuwa sama alamar saurare, da alama kuma tunda bai miƙe ba tun farko ya gane ubangidan nasa ne ya dawo. Ƙofar ya buɗe masa kawai ya ce, “Go and sleep, goodnight thanks”. Bindi karen ya kaɗa masa ya fita abinsa shi kuma ya maida ƙofar ya rufe tare da ƙarasa cillar da jacket ɗin daya cire ɗin saman sofa. Gaban gadon ya ƙarasa tare da lalubar aljihunsa ya ciro keys ɗin Handcuffs ɗin ya cire mata daga hannayenta, dama bai wani matse ba, sai dai hannunta bazai iya fita ba. Kamar wadda ke a ido biyu kuwa ta wani sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi sosai da ya saka shi ɗan kallonta. Idanun ya zuba mata kusan sakan goma kafin ya kai hannun a hankali ya shiga ɗaye saletaf ɗin a hankali, da yaga zata motsa sai ya dakata. Sai ta sauke ajiyar zuciya ta koma sai ya cigaba. A haka ya gama cirewa duka. Aiko ta wani turo lips dinta gaba da suka sake zama jazur suka tsuke sosai kamar an gyara mata su ne da gayya. Sai lokacin yaga sawun hawaye da suka bushe alamar an dai ci kuka. (Trouble Maker ). Ya faɗa a ransa yana kauda kansa da barin wajen. Ta riga ta juya kwanciyar tata zuwa jikin fuskar gado, dole ya koma ta can side ɗin hannunsa ɗauke da blanket ɗin dake a gadon ya lulluɓa mata dan yanda ta takure waje ɗaya yasan sanyin acn nan ne ya takurata. Shi kuma harga ALLAH bama zai iya zubar da kansa ya tashe ta ta koma side ɗinsu ba. Tunda zuwa yanzu ya gane a side ɗin Ummien sa take kwana. Dan baya ma jin ta cika sati a biyu tabar kwana a side ɗin masu aiki...... 💞✨💞 Duk yanda Mom taso amfani da maganin nan hakan ya gagara, dan Halime ta kafa ta tsare kamar ta fahimci mi take shiryawa. Gashi koda ta kira Abba akan itafa sai dai a raba abinci Halime tayi nata ita tayi nasu ita da yara kai tsaye yace bai amince ba. Daga ƙarshe ma sai gashi ya dawo gidan. A gabansa Halime ta gama girki ta ɗibar musu ita da shi ta samo kula mai ƙyau kuma a kayanta ta zuba wani. Koda Abba ya tambayeta na waye, kai tsaye ta sanar masa na “Yaya Musaddiq ne. Yana babba a gida amma aita bashi abinci a wulaƙantaccen kwano bayan shike cefanen. Ni ba haka naga su Gwaggo nama su Yaya Buhari ba a gidanmu”. Shiru Abba yay yana kallonta dan ya gagara yin magana. Sai ma wani nauyi ne yaji kansa ya masa tamkar Musaddiq ɗin na gabansa. Wannan abu ya ƙonama Mom zuciya. Tako shiga surfama Halime zagi, amma ko tari ƙinyi tai, sai da taga zagin na neman zama na fitar hankali ta fashe da kuka. Hankali tashe Abba yay kanta yana tambayar ta lafiya. Kukan ta sake fashewa da shi sosai. “Innata na tuna, tana cikin kabari amma ana zaginta. Kaicon wannan rayuwa, ban ja mata addu'a ba sai zagi, gaskiya bazan iya zaman gidan nan ana zagarmin mahaifiya ba”. Rikicewa Abba ya sake yi, tuni ya manta da wata Mom a wajen ya kama Halime ya rungume. “Haba Halimatussa'adiyya na, ke da barin gidan nan ai sai dai in mutuwa. Kiyi haƙuri ai duk wanda ya zagi wani iyayensa ya zaga. Karki sake faɗar haka kinji, ALLAH yay miki albarka”. “Amin nagode _my Rabon alkairi_. Na kuma yarda da kai bazan sake damuwa ba. Ai lobiyu irin kamar kainuwar tafkin bayan gidanmu ɗin nan”. Ta ƙare maganar da fakar idon Abba tai ma Mom da tai mutuwar tsaye sagale tana kallonsu. Sai kuma ta wani sake narkewa jikin Abban tana shashashar kukan ƙarya. Ai tuni Abba ya sake rikicewa, hannunta ya kama tare da ɗaukar kular abincin Musaddiq data zuba ɗin suka shige ɗaki yana sanarma Mom ga nasu nan a tukunya ta ɗauke su sun shige. Rasa ma abinyi Mom tayi, sai kawai taji hawaye na rige-rigen sakko mata. Shiru tai tsaye a wajen hawayen na tarara, tana ɗagowa suka haɗa ido da Halime na leƙenta ta window tana dariya. Gwalo tai mata dayin fari da ido ta saki labulen. Yuuu Mom taji jiri na neman ɗibarta, har sai da ta kaita da dafe bango zuciyarta na mata zafi kamar zata buga. Wai ita Jalilah dake juya gidanta yanda take so, idan ta bama Imam umarni har rawa jikinsa yake don ganin ya cika mata akan lokaci. Amma yau a gabanta yake rawar jiki akan yarinya ƙarama sa'ar ƴarta har yana faɗa mata magana a kaikaice wai wanda yay zagi iyayensa ya zaga. Kai wane irin juya baya duniya ke son yimata ita kuwa a rayuwar nan.... To bari na tayaki tambaya momcy🤣🥱 💞⭐💞⭐💞 A ranar ni na samar da Number, na kuma tura saƙo ga Maash ta hanyar yaron mijina, amma ita har tsawon sati tana fakon wayar Mansoor, randa ta samu kuma tace bataga video awayar Mansoor ɗin ba iya bincikenta. Hankalinta duk ya tashi, amma sai na kwantar mata da shi ta hanyar tunatar da ita ai in shi babu a wayar tasa ya goge ko ya kwashe yarinyar nada shi. Bai kuma zama lallai ace an rasashi ta wajenta ba. Ta gamsu da zancena, dan haka tace nabar komai a hannunta zata samo video ɗin. Amma ya kamata a fara turama Maash saƙo fa kafin samuwar video dan guri nata ƙurewa kada wani ya rigamu. Ta bani dariya sosai, dan son kuɗin Aunty mai lasisi ne. Na yarda da shawarartata duk da ban gaya mata na fara turawa ba, dan haka a ranar muka fara turama PA ɗin Maash saƙo. Munyi hakane saboda saƙon zaifi isa garesa fiye da mu tura a wayarsa. Koda muka tura dai shiru babu wani reply har tsawon kwanaki, dan haka muka sake turawa. Anan ma babu amsa ga video ya gagara samuwa a hannun budurwar Mansoor. Sai kawai wani tunani yazo min. Munfa riga mun danganta video da ita yarinyar, Maash kuma ba sakarai bane zai iya bibiyarta. Gashi mu kuma babu video ma a hannunmu. Sai kawai muka yanke shawarar kidnapping ɗinta. Komai kuwa yazo mana cikin sauƙi da taimakon maigadi na dana bama dubu ɗari. Sai dai abin takaici babu video a wayar Samraah. Munyi-munyi kuma ta bada shi amma taurin kan yarinyar taƙi badawa........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_ ......Muna akan haka sai kawai ga reply PA ɗin Maash a randa muka aika saƙo na uku. Akan an amince za'a bamu 500m, amma da sharaɗin sai mun bada footage ɗin nan sannan a cika mana. Munta nazari akan hakan da tunanin akwai talala a batun, daga baya aunty tace babu abinda zai faru in sha ALLAH. Wannan ƙwarin gwiwa ya sakamu zuwa muka buɗe sabon account da sunan mai gadina, kai komai ma da nashi akai amfani har account ya samu muka turama Maash. Kuɗi kuwa a ranar suka shigo. Munta murna da ganin madarar kuɗin nan ziryan, sai hakan ya ƙara mana ƙaimi sosai. Cikin abinda bai fi mintuna talatin ba muka cire kudin zuwa account ɗin aunty, shi kuma wancan muka rufesa gaba ɗayansa. Ga kuɗi sun samu amma video ya gagara samuwa a garemu. Sai ma wani tsautsayi daya so giftawa. Yarinyar ta samu nasarar cirar waya a jikin mai tsaronta tai kiran da aiki ya kusa buɗe mana. ALLAH ya taimakemu dai-dai sanda Mansoor ke kiran Attahiru akan ya kira dcp ya sanar masa Aunty na tare da shi. Shine tai kiran yaron namu akan yayi maza yabar gidan da yarinyar kada kuma ya kuskura yabar wani abu a gidan. Hakan kuwa akayi, sai dai labarin ya canja kansa a dalilin satar data saci sata. Dan kuwa dai an tare yaronmu an ƙwace Samraah, shima kuma anyi ram da shi. Mun shiga tashin hankali da baida misali, musamman ma Aunty, dan kuka ta dinga min a waya kan na rufa mata asiri dan ALLAH kada wanda yaji wannan magana. Niko na tabbatar mata zanyi hakan amma da sharaɗin bayan auren Mansoor da Samraah da sati ɗaya zamu saka ya saketa ya auri Husnah. Tace ta yaya?. Na amsa mata da zamu bar Mansoor ya auri Samraah ne dama dan mu amshi video ɗin hannunta. Da zarar mun amsa zamu ƙulla mata sharrin da bama shi kaɗai ba kowa sai yaji ya tsaneta. Ta jinjina al'amarin tare da sanar min ita ba itace abin ji ba Yaya ne da Mansoor. Niko nace mata karta damu komai zamu yisa a tsare ne, yanzu dai mu jira Samraah ta fito dan a lokacin bamu san Maash bane ya amsheta mun zata ƴan sanda ne. Sai daga baya muke jin ba ƴan sandan bane sai kuma hankalinmu ya sake tashi. Muna cikin yanayin ƙullawa da kwancewa sai ga Samraah ta fito. Farin ciki babu irin wanda bamu yi ba, dan mun san plans ɗinmu zasu cigaba da tafiya kenan. Mun cigaba da tsarinmu yanda ya kamata ana gobe ɗaurin aure kuma sai komai ya canja daga yanda yake. Dan mun tafi amsar kayanmu wajen tela da wanda amarya zata saka da ba'a kai ba akai ram da mu.... 💞✨💞✨💞 Shirin kwanciya yayi, lokaci-lokaci yana ɗan jan ƙaramin tsaki dan yunwa yake ji. Da farko chocolates ɗin nashi na fama ya ɗebo, sai kuma ya maidasu yana jan gajeren tsaki. Harga ALLAH abinci kuma yafi buƙata dan rabonsa da cin wani abu matsayin normal abinci 2days kenan. Daga kayan fulawa sai fruits da chocolate yake zubama cikinsa. Saukar idanunsa akan tray ɗin data shigo da shi ɗazun ya sashi nufar wajen. Kwanikan ya buɗe tamkar wanda akaima dole. Dan sai faman yamutse fuska yake da ɓata rai. Fruit salad ɗin daya ɗan sha ɗazun ya zuba ma ido da gasashen naman kaza daketa ƙamshi alamar zai yi daɗi. Harya maida ya rufe kamar bazai ci ba sai kuma dai ya sake buɗewa dan gwara yaci koda kaɗan ne so yake yay barci kada yunwar ta takurasa. Saboda in har yaji damuwa da yunwa tofa da gaske yunwar yake ji. Duk yanda kuma yaso riƙe kansa bashi yiwuwa. Ya tsakuri kazar zai kai baki akai kiran wayarsa. Yaso sharewa sai dai ganin Abubakar ne babban yaronsa ne shima dake riƙe da harkokinsa a ƙetare ya sashi saka ta hannunsa daya ɗiba a bakin nasa yana ɗaukar wayar. Yaci kusan lauma biyar yana wayar, sai da ya kammala magana da Hayatun ya fahimci ko bissmillah baiyi ba. Kansa ya dafe yana yamutse fuska. Sai kuma yayi bissmillar sannan ya cigaba da ci. Da yake yunwar yake ji sosai yaci ya kuma sha fruit salad ɗin shima sannan ya koma bathroom yay brush ya fito. Kansa tsaye ya nufi gadon zai kwanta sai kuma ya tsaya cak yana kallonta. Gefen lips ɗinsa ya ɗan ciza sai kuma ya ƙarasa ya ɗauki pillow biyu ya koma saman sofa ya kwanta. Bawani yaji daɗin kwanciyar bane ba kasancewar bai saba kwanciyar a hakan ba. Iska ya furzar kaɗan tare da lumshe idanunsa kawai. Barcin ya ɗan jashi da nisa kaɗan saboda gajiyar da yayi aka fara masa mintsine-mintsine a jiki. Idanunsa ya buɗe kawai batare daya motsa daga kwancen da yake ba. Tun yana ɗaukar al'amarin wasa har dai yaji yau fa dabance, a farko ya ɗauka normal ne kamar kullum, dan ya jima yana fuskantar irin wannan yanayi amma jarumtarsa na tattare komai ta bizne saboda ya riga ya sakama ransa in har ba Ummie ta samu lafiya ya ganta a farin ciki ba baya jin yana da wani spiece a rayuwarsa na kallon wata mace da wannan siffar. To tayaya ma zai yarda hakan ta kasance. Ace mahaifiyarsa na kwance cikin lalura mai ban tashin hankali shi kuma hankalinsa nakan samawa gangar jikinsa abinda take buƙata. Kai impossible. Cikin cizar lips ya sake lumshe idanunsa a yanayin tilastama kansa kamar yanda ya saba. Dan shi bai taɓa shan wani magani domin hana faruwar haka ko samun sassauci ba. Ya dai riƙe azumi tare da takure kansa matuƙa saboda jarumta. Sai idan al'amarin yayi tsamarine yake amfani da lemon tsami bisa shawarar abokinsa Taj.. daga ba hakanba baya shan komai. Cikin ƙanƙanin lokaci wata irin zufa ta gama jiƙe masa jiki, amma bawon ALLAH ko motsawa baiyi ba yana daga kwancen yana sauraren hukuncin UBANGIJI. Tsanantar al'amarin ya sashi yunƙurawa a karo na farko ya tashi zaune haƙoransa ya datse da lips ɗinsa kamar zai huda shi. Zaman ma gagararsa ya nema farayi, ya miƙe tsaye zuciyarsa na tsananin bugawa. Taku ɗaya biyu ya tsaya cak, saboda ƙullewa da cikin yay sosai ƙafafun ma kansu riƙewa suke. Ga idonsa ya sauka akan wadda ke kwance a saman gadonsa tana barcinta hankali kwance. Duk da ba ganin fiskarta yake da ƙyau ba saboda ƙarancin haske yanda tai luff cikin lallausan blanket ɗinsa ya tabbatar masa da hakan. Kansa ya kauda, sai kuma ya nufi Bathroom da ɗan yanayin sassarfa na tilastama kai jarumta. Babbar shower ɗin mai ƙarfi ya sakarma kansa. A cikin ƙanƙanin lokaci jikinsa ya gama jiƙewa sharkaf, sai dai ta saman kansa yayi amfani da shower cap gudun kada ruwa ya taɓashi yay mura. Dan shi bashi da wahalar yin mura. Sosai ruwan ya dakesa amma baiji komai ya canja ba. Sai ma sake ruruwa da yake jikinsa na sake tabbatar ma da yau ɗin fa yau ce. Cire kayansa yayi ya fito bayan ya ɗaura alwala. Sai dai raka'a biyun farko ma da ƙyar ya iya kaisu saboda yanda al'amarin ke sake ta'azzara. Shiru ya cigaba da zama a saman sallayar, kafin kuma dai ya miƙe da ƙyar. Saman gado ya tafi da nufin hawa sai kuma ya tsaya cak, karan farko ya zubama fuskar Samraah dake shaƙar barcinta a nutse idanunsa da suka juye gaba ɗaya. Ba wani tar-tar yake iya ganinta ba, sai dai yanayin ƙarancin hasken sai ya ƙara ƙawata masa ƙyawunta abinka da wanda ke cikin yanayi. A hankali ya fara takawa tamkar hawainiya mai tsohon ciki. Ya kai hannunsa duka biyu yaja igiyoyi biyu dake ɗaure da net ɗin da aka zagaye gadon tamkar rumfa. Cizar lips ɗinsa ya sakeyi yana mai duƙar da kansa tamkar wanda ke jin abinda zai aikata ba dai-dai bane. Har ya motsa jikinsa da nufin komawa sai kuma ya sake tsayawa cak sakamakon nauyin da ƙafarsa tai masa. Ga zuciyarsa na ƙara tabbatar masa da (Awwab matarka ce fa, ALLAH ya halatta maka miyyasa zaka cutar da kanka kaƙi karɓar ni'imar da yay maka. Kaje tareta, kaje) Da wani irin tashin hankali ya tura yatsunsa cikin sumar kansa ya harmutsata ya furta, “Ya rabbah Ummie! Ummie! Na, ban mata adalci ba. My ALLAH help me! I beg you”. A dai-dai nan Samraah tayi juyi, bargon daya rufa mata har wuya ta janye ƙasa alamar ya isheta. Tamkar wadda ake juyawa da remote ta juyo sosai ta inda yake tana facing ɗinsa. Saukar idanunsa a saman ƙirjinta ya sashi runtse idanunsa da ƙarfi tare da cije lips ɗinsa har sai da ya fasashi da haƙori. Sai kawai ya zube a saman gadon hannayensa duk biyu dafe da kansa. Tsawon mintina ya ɗauka a hakan kafin zuciyarsa ta gama yanke masa shawarar mafita. Fitilar dake cikin gadon ya kunna tare da haurawa gaba ɗayansa. Cikin barci na dinga jin saukar numfashi mai ɗumi a saman fuskata. Sosai zuciyata ta yanka na buɗe idanuna. Tar-tar na saukesu akan fuskarsa data gama canjawa zuwa yanayin da ban taɓa ganinsa ba. Sake faɗuwa gabana yayi na waro idanun gaba ɗaya a kan fuskarsa. Idanunsa dake a kaina fes ya lumshe a bala'in slowly sai kuma ya sake buɗesu cikin tsakkiyar nawa. Yanzun kam kasa jurewa nayi, cikin rawar murya data lips na furta, “Na shiga uku Awwab minene haka kake y.....” “Shiiii!!!!” ya faɗa yana sake matso da fuskarsa daf-daf da tawa tare da ɗaura yatsarsa saman lips ɗina dake rawar tsorata. Cikin wata irin murya mai tsananin sanyi da zama low can ƙasan maƙoshinsa, ta kuma shaƙe ya furta, “Bana son surutu”........✍️ ________________ *Aleenah’s Refreshing Scent* Ta kawo muku ingatattun turaruka na ruwa (perfumes), oil, Humra, Turaren wuta and more. Kunsan kamshi dai rahama ne, ingantaccen kamshi me rike jiki da Kaya me sa nutsuwa da shiga taro cikin kasaita. Ina hajiyoyi, uwargida, Amare da kuma masu niyyar shiga daga ciki? don’t afford to miss this golden opportunity. Aleenah’s refreshing scent ta kawo muku kayan kamshi masu kyau, inganci da kuma sauki……. Akwai Kaya Kala kala na nau’in turaruka Akan farashi me rahusa. Muna Nationwide delivery 🚚 09034259662 08081693351 Koda kuɗinka sai da rabonka. Ai ƙamshi duniya ne 😘😌😌 __________ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ ......Hajiya Mammah na ganin Samraah ta wuce da aikar da tai mata ta wani saki ƙayataccen murmushi. Sai kuma tabar kitchen ɗin da sauri. Fita tayi daga sashen baki ɗaya zuwa na Maash. Cikin sanɗa ta leƙa ta window ɗin falon. Kusan abinda ya faru na farko a idonta ya faru. Sai dai ganin Maash zai fita yasa hankalinta tashi. Da sauri tabar wajen, ɗakinta ta koma, ranta a dagule ta rarumi waya tai kiran Rubayya. Bugu biyu kuwa ta ɗaga... “Gaskiya na gaji Rubayya. Ni fa shiyyasa kikaga sam babu ruwana da wani tsigunne-tsugunnen malaman nan. Gara na tashi da kaina nayi aiki nasan ni nayi sa”. “Haba hajjajuna relax mana. Mike faruwa irin wannan ɓaɓatu haka ko shaƙar numfashi bakiyi?”. “Ba dole nayi ɓaɓatu ba. Yaron nan fa yau ma gashi can ya tsallake abincin can bai ciba. Sai ma shirin barin gidan yake”. “Ita yarinyar tana ina?” “Mtsoww, oho ma shegiya, ban dai ga ta fito ba daga bedroom ɗin nasa”. “Fantastic! Ai muna da sauran hope kenan”. “Ta yaya muke da wani sauran Hope bayan na faɗa miki yama fita a gidan, shegen kamar wani ɗan fashi yayi shigar baƙaƙen kaya yan koransa biye da shi. Wlhy sai nayi maganin shima wancan shegen ɗan masu aikatau ɗin Hayatu yake koma wa oho mas”. Dariya Rubayya tayi da ga can, tare da faɗin, “Ai abin naki da yawa Hajiyata. Yanzu dai kwantar min da hankalinki. Zuwa zakiyi ki kafa ki tsare ta ko wane hali kada yarinyar tabar sashen nan. Ina kuma turaren daya baki”. “Mtsoww ke ni ajiye wani batun turare har yanzu banyi ba. Banda rainin wayo taya za'ace saka turare a wuta zai sa wanda ke nesa da gida dawowa koda ba'a Nigeria yake ba”. “Humm. Aike kinji matsalata da ke gardama. Ke dai ki gwada mana kiga idan bai yi miki abinda yace ɗin ba sai ki faɗi koma minene yazo ranki. Amma dan ALLAH ki kwantar da hankalinki kiyi komai yanda ya kamata daga nan har zuwa safiya idan komai bai farun ba sai musan matakin ɗauka.” Badan zancen ya shigi Hajiya Mammah ba tayi duk abinda Rubayyan ta faɗa. Dan sashen Maash taje ta kunna turaren wuta. Yana fara hayaƙi tai kiran sunansa, “Awwab duk rintsi ka kwana a gida yau. Kayima yarinyar nan fyaɗe. Ka mata kaca-kaca, fata-fata, yaga-yaga. Kona minti ɗaya kada kaji tausayinta Awwab, karka raga mata”. Ta ƙare maganar tana kokkora hayaƙin da hannu tako wace kusurwa. Sai da ta tabbatar tayi duk yanda malamin yace sannan tayi murmushi da fatan dacewa ta fice. Koda ta koma sashen nata ba kwanciyar tayi ba. Dakon zaman jiran dawowar Maash tayi tacan balcony ɗin sashenta na upstairs. Duk yanda take jin barci har gyangyaɗi na ɗibarta bata tashi ba a wajen har sai da su Maash suka dawo wajen 1-30. Jitai kamar ta daka tsalle taita ihu dan daɗi. Tana ganin ya shige ciki shi jaɗai ta ƙara sauke ajiyar zuciya. Da alama ɗan koran nashi y sauka a gida kenan. Cikin sauri ta sauka downstairs. Kai tsaye ta can baya ta zagaya cikin garden. Dan windows ɗin Maash na bedroom duk tacan baya suke. Tako ci Sa'a bai rufe ba. Sai dai gaba ɗaya labulolin a sake suke. Cikin dabara ta ɗan janye tana leƙen bedroom ɗin. Maash ta hango yana lulluɓa ma mace blanket, sai da tayi tsamm da ranta ta tabbatar da Samraah ɗince. Jitai kamar ta kurma ihu dan daɗi, amma sai ta kanne, tadai gyara tsaiwa domin ganin yaya wasan zai kaya.. Komai daya faru tun daga ciwon Maash har zuwa hawansa saman gadon akan idanunta ne. Maash na gab da cimma burinsa taji abu yabi takan ƙafarta, firgitar da tayi da jin kamar motse-motsen mutane da gittawarsu ya sata barin wajen cikin rawar jiki. Wannan shine ya hanata ganin ƙarshen faruwar komai. Amma da tabbas taso komai-da-komai sai ta ɗauka a wayarta dan tana son tayi komai da shaida. Amma ko'a yanzu ɗin ma wanda ta ɗauka ya wadatar da ita... Hummmm 😒 ❤️💕❤️ Hannunsa dake saman lips ɗina na ture, tare da yunƙurawa zan tashi ina faɗin, “To ka tashi min a jiki mana” A yanayin ƙara shaƙewar muryar tasa dake seizing ya ɗan sake ƙanƙance min idanunsa cikin tsakkiyar nawa, sai kuma ya shiga hura min iskar bakinsa a hankali, babu shiri na lumshe nawa idanun ina haɗiyar numfashi. Cigaba yay da hura min iskar ta saman wuyana har a cikin kunne na, gaba ɗaya naji kamar numfashina zai ɗauke. Bam ma san na sake ƙanƙamesa ba. Sautin fitar murmushinsa naji, tare da fara min magana cikin raɗa a kunnen nawa. “Ba abinda nake ma ƴan hotels ɗin kike buƙata ba kema?”. Sosai na waro idanuna da suka gama cika taf da hawaye ina ƙoƙarin ture kansa. Amma ko gezau, cike da shagwaɓar da ban san tazo min ba na ce, “Ni yaushe nace, kada kamun sharri. Dan ALLAH ka matsa Ummie nake dafa ma abu a kitchen fa”. “Kin san da Ummien ai kika kawo kanki nan”. “Na kawo kaina fa? Wlhy Hajiya Mammah ce ta aiko ni kai kuma dan mungunta ka ɗaureni, ƙilama cocaine ka shaƙa min dan nayi barci.” Bai amsa min ba, sai wani lumshe idanunsa da yay yana matse fuska alamar da abinda ke damunsa. Gabana ne ya faɗi, saboda tunawa da zancen Mama Balki akan yanayin ciwon da yake shiga akan Ummie, sai nai tunanin ko dan na ambaci sunanta ne. Cikin suɓutar baki na ce, “Baka da lafiya ne?”. Na faɗa cikin rawar murya hawaye na rige-rigen sakko min a guje. Maimakon amsa min sai ya wani lumshe idanunsa da matso da fuskarsa kan tawa sosai. Idanuna na runtse da sauri ina ƙanƙame jikina tare da kauda fuskar tawa gefe. Sai kawai naji saukar numfashinsa akan wuyana zuwa ƙasan wuyan nawa da cikin kunnen yana shinshinata ta. “Na shiga uku, dan ALLAH Awwab ka rufa min asiri, wai minene haka kake yi kamar wani mage”. Na faɗa cikin zaburowa a ɗan sauran ƙarfin daya rage min. Gocewa yay daga rankwafowar da yay ya koma gefena. Da alama tanƙwaɓar hannunsa da nayi ne. A zatona na kuɓuta, sai kawai jinai ya yaye bargon gaba ɗaya ya rungumeni tsam a cikin jikinsa har ina numfashi da ƙyar. Cikin kunne ya raɗa min, “Idan na rufa miki asiri ni wazai rufe nawa Samr!”. Yanda ya ambaci sunan nawa da wani irin salon cire wasalin kowacce harafi yasa jinina yamutsawa gaba ɗaya. Kuka na sake fashe masa da shi. Ina mai jujjuya kaina dake kwance a ƙirjinsa. “Dan ALLAH Awwab ka bari zan cutu”. “Zan fiki cutuwa idan nayi hakan”. “Wai dan ALLAH kai baka da tausayi ne? Baka da.....” “Nace bana son surutu”. Ya faɗa cikin muryar data sake firgita ni, yana sake ƙanƙameni. Ɗif naga hasken cikin gadon ya koma duhu. Mutsu-mutsu na farayi na son ƙwatar kai amma yamin riƙon da ban isa aikata hakan ba. Sai kawai na buɗe baki na fasa masa ƙara. “Gayyato wani nan bazai hana ni karɓar HALAL ɗina ba, dan ina da taurin kai, idan har nace ZANYI, to sai NAYI Samrh” ya ƙare maganar da rufe min baki da nasa. Daga haka bai sake bani wata dama ba koda ta shaƙar numfashi ne cikin sauƙi. Gaba ɗaya ya canja daga wancan Maash ɗin zuwa wanda ban taɓa gani ba. Tunda nake a rayuwata ban taɓa tunanin akwai makamancin irin wannan tashin hankalin na kana ji kana gani ba sai yau. Sam baya jin roƙo, baya jin magiya. Saima sake tabbatar min da shi ɗin mayuncin zaki ne da in ya ɓalle abinda ya fito nema kawai yake farauta. Tun ina iya banbancewa har komai ya ƙwace min daga gangar jiki zuwa fitar numfashi.... 🌿🌿🌿🌿🌿 Matsanancin firgicin da muka shiga na ganin wanda yasa aka satomu bazai musaltu ba. Dan kuwa ba kowa bane face Maash. Duk da sau ɗaya na taɓa ganinsa a rayuwata hakan bai hanani gane sa ba. Roƙonsa muka dinga yi da magiya amma ko sau ɗaya bai ɗaga kai ya kallemu ba. Sai da ya mula dan kansa kusan mintuna ashirin sannan ya furta, “Su wanene ku?”. Kasa fahimtar tambayar tasa mukayi, sai da yaronsa ya daka mana tsawa sannan na bada amsa ina nuna Aunty. Nace wannan Yayata ce ni kuma ƙanwatarta ce”. Shiru bai sake tanka mana ba. Sai yaronsa ne ya tura mana tab da hoto a jiki, cikin tsawa ya ce, “Miye haɗinku da wannan yarinyar?”. Hoton muka kalla, ba kowa bace face budurwar Mansoor. Kasa bashi amsa mukayi, sai da Maash ɗin da bai sake tankawa ba ya jawo bindiga ya nuna mu batare da yayi magana ba shima. Atake jikinmu ya fara ɓari, kallan kallo muka fara, kafin tuni bakin Aunty ya buɗe ta shiga zayyano bayani akan alaƙarmu da Samraah. Har takai aya babu wanda ya tanka a cikinsu har tsawon wasu mintuna. Miƙewa Maash dako kallonmu bai sake yi ba yayi, sai da yaje tsakkiyar falon batare da ya juyo ba ya furta, “Ka basu Account details su saka min kuɗina. Ka kuma faɗa musu tun kafin na sakasu nadama su janye abinda suke shirin ƙullawa. Ciki harda auren yarinyar wa ɗansu, idan kuma sukayi taurin kai, su kuka da kansu. Dan sai na sakasu dana sani”. Da ga haka yay ficewarsa batare daya sake ko waiwayo mu ba. Muna ji muna gani muna hawaye yay kiran waya aka kwashe kuɗaɗensu dake account ɗin aunty da wanda ke hannuna. Sannan ya sake tabbatar mana da musan mi mukeyi kafin lokaci ya ƙure mana. Dan Maash baya magana biyu. Akoda yaushe zamu iya ganin jami'an tsaro da ƴan jarida har gidajenmu... Bayan an dawo damu a inda aka ɗauke mu bamu nema shagon tela ba muka dawo gida a hargitse. Shawara muka shiga ƙullawa, dan ko kaɗan bamuga imani a cikin idanun Maash ɗin nan ba. Dan haka muka shawarar tsaida batun auren Mansoor da Samraah, ta hanyar zuwa gidansu muka sami iyayenta maza mukayi rashin mutunci. Aunty harda marin wan mahaifin yarinyar. Wannan shine ya fusata su sukai alƙawari har abada bazasu haɗa zuri'a damu ba. Mu kuma sauraresu a yau sai sun ɗaurama ƴarsu aure da miji gangariya..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_ .......Iyakar galabaita Samraah ta kai ƙololuwa a hannun Maash ta yanda a shi karan kansa bai san aika-aikar daya aikata ba sakamakon abinda ke aiki a jikinsa. Duk da yaso binta a nutse a farko, sai dai tsafi gaskiyar mai shi, sannan ƙaddara ta rigayi fata. Tuni komai ya ƙwace masa. Tun yana iya jiyo kuka da magiya da roƙon da Samraah ke masa har ya daina ji da gane komai sai abinda ya saka gaba. Burinsa kawai ya cimma manufarsa ko zai samu sassauci da rangwamen wutar masifar dake ruruwa a jikinsa. Koda ya cimma inda yake fatan kaiwar sai komai ya sake ƙwace masa. Wani irin fitinannen ciwon kai mai azaba yay masa dirar mikiya. Bai sake gane ainahin halin da yake cikiba, da kuma jefa yarinyar mutane da tuni numfashinta ya rabu da gangar jikinta sai da gari ya waye gangaran. Zafin rana da haskenta suka dallare masa idanu. Da ƙyar ya iya buɗesu kuwa. Ganin hasken ranar ne muraran ya saka zuciyarsa motsawa da ƙarfi, saurin kallon ƙaramin agogon dake a bed side drawer ɗinsa yayi. 7:2am. “Ya subahanallah”. Ya faɗa yana yunƙurawa gaba ɗayansa zaune. Tashin hankalin tuna baiyi fa ko sallar asuba ba ya sashi zabura ya sauka a gadon batare da hankalinsa ya kai kan Samraah da har yanzu ke a sume ba. Cak ya tsaya yana kallon jikinsa, sai kuma ya kalla gadon da sauri zuciyarsa na tsitstsinkewa. Ji yay gaba ɗaya ƙafafunsa na neman kasa ɗaukarsa, dan take komai daya faru a daren na jiya ya shiga dawo masa dalla-dalla. Wani irin tashi tsigar jikinsa ta farayi, cikin rawar hannu ya kai hannun nasa saman blanket ɗin kusan rabin jikinta ke a cikinsa. Janyewa yay a hankali zuciyarsa na cigaba da bugawa tamkar zata fito ta bakinsa. Da wani irin sauri ya saki blanket ɗin yay baya yana waro gaba ɗaya manyan idanunsa kalar na maguna waje. Blue ɗin tsakkiyarsu ya sake fitowa raɗam. “Innalillahi wa'inna-ilaihi raji'un” ya shiga ambata. Sai kuma ya tura hannunsa cikin sumar kansa ya hargitseta tare da maidata gaba yay kuma baya da ita yana furzar da wani irin zazzafar huci. Rasa ma abinda ya dace yayi yay, sai da zuciyarsa ta sake ayyana masa (sallah) sannan ya zabura bathroom bayan ya sake jan blanket ɗin ya rufamata. Wanka yake amma maƙoshinsa sai kai-kawo yake. Ji yake tamkar ƙirjinsa zai fashe. Gaba ɗaya hannayensa ya tura cikin gashin kansa da ruwa ke jiƙawa. Da ƙarfi ya ƙwala kiran sunansa jikinsa na wata irin karkarwa. “Awwabbbbbb!! Are you mad?!”. Da gaske zuciyar ƴan maza ta motsa, dan a take idanunsa gaba ɗaya suka gama juyewa. Wani irin jiri ya fara yawo kansa. Tako ina jijiyoyin jikinsa sun bayyana kansu fiye da yanda gashin jikinsa ke a mimmiƙe. Ji yake kamar yayta dukan kasan ko zai samu sassaucin abinda yake ji. Sai dai babu dama. Dole ya gaggauta yin wanka ya fito. Sallar da zuciyarsa keta sake jaddada masa ya fara gabatarwa. Gara yayi ko zai dawo a hayyacinsa ya fuskanci mike damunsa. Koda ya idar sai ya kasa motsi. Yana zaune kawai a saman sallayar ya zubama guri ɗaya idanu, sai Adams apple ɗinsa ne ke wani irin kai-kawo da sauri-sauri. Ga idanunsa gaba ɗaya sun gama juyewa. Yafi mintuna goma a wajen kafin yay jarumtar miƙewa. Kai tsaye gadon ya nufa, ya kai zaune ta gefen kanta da ɗaukar goran ruwa dake a bed side drawer ya zuba a hannunsa kaɗan sannan ya shafa mata a fuska. Shiru bata motsa ba, dole ya sake yin haka, sai da yay sau uku kafin ta zabura. Sai kuma ta ƙwalla ƙara gaba ɗayanta ta faɗa jikinsa ta ƙanƙamesa. Sai rawa jikin nata yake kaf-kaf-kaf abin tausayi. Da farko kasa ko motsi yayi, sai kuma a hankali ya kai duka hannayensa biyu a saman bayanta ya manneta a jikin nashi da ƙyau, tare da lumshe idanunsa sambatunta mai cike da roƙo da magiya da neman agaji na ratsa masa cikin kunne. Sunfi mintuna biyar a hakan kafin ya buɗe idanunsa a hankali. Da ƙyar ya iya buɗe lips ɗinsa cikin wata iriyar muryar da baka isa fassara yanayin da yake a ciki ba ya furta, “Stop crying”. Zabura Samraah tayi, sai kuma ta fincike jikinta gaba ɗaya dake karkarwa. Da alama jin muryar tasa ne ya firgitata. Wani irin fisga numfashinta ya shigayi, ta dinga jan jikinta dake rawa baya daga nasa da ƙyar tana jujjuya kai. Hawaye kam ai gaba ɗaya sun gama wanke fiskarta har zuwa saman wuyanta. Sai kawai ta tafi zata zube gaba ɗayanta alamar numfashin nata ya jaa. Da sauri ya riƙota ta faɗo jikinsa. Tare da yin cak ya zubama fiskarta data gama dagulewa firgitattun idanunsa kawai. Tsahon mintuna biyu ya jasu yuuuu kamar zai lunshe sai kuma ya buɗe. Kwantar da ita yay a hankali, tare da jan blanket ɗin ya sake rufa mata a jiki. Bathroom ya nufa bisa umarnin shawarar da zuciyarsa ke bashi. Sai dai me, yana tsaka da haɗa ruwan ɗumi ya ji hayaniya. Tsai yay da ransa alamar saurare, ji yay hayaniyar na sake matsoshi, jin tabbas a sashensa ne fa ya sashi miƙewa tsaye sosai. Sai dai kafin yayi wani yunƙuri yaji saukar muryar Hajiya Mammah a tsakkiyar kunensa tabbacin ta shigo ne har cikin bedroom ɗin nasa. Yanda take ƙwala kiran sunansa a haukace ne ya sashi buɗe ƙofar ya fito a nutsensa. Fitowar tasa dai-dai da buga wani uban tsalle da tayi tana zabga salati. Sai kuma ta shiga nuna Samraah dake a saman gado. “Na shiga uku ni Nafi, Awwab mi zan gani haka? Wacece wannan a gadonka? Miya kawo mace ɗakinka a irin wannan lokacin kai da ba aure ba!! Mu'azz! Mu'azz!!”. Ta shiga ƙwala kiran sunan Paah. Sai lokacin ne Maash yay wani irin datse haƙoran ɓacin rai yana watsa mata wani irin shegen kallon takaici, a zafafe ya nufi ƙofar da ake ƙoƙarin buɗewa ya dinkare. Itama a kausashe cike da gizago yay mata nuni da ƙofar yana faɗin, “Ki fita anan”. “Anƙi a fitan dan ubanka, yanzu Awwab kamana adalci kenan. Yarinyar mutane kai ma fyaɗe!! Shiyyasa tun dare muke nemanta amma ko sama ko ƙasa a gidan nan. Kashemu kake son kayi? Can ga rundunar ƴan sanda nan da farar safiya sunzo kamaka, ashe kana anan kana aika-aika kuma”. Zaka rantse bai jima mitake faɗa ba, dan ƙoƙarin sakama ƙofar key kawai yake yi, ga shi tacan baya kuma Paah nata bugawa da kiran sunansa. Zuwa yay zai wuceta yaji Paah ya fashe da kuka yana sake buga ƙofar. Cak ya tsaya daga yunƙurin isa gadon da yake yi. Ya ɗauki kusan minti ɗaya a hakan kafin ya motsa jikinsa a hankali ya koma baya, ƙofar ya buɗe, sai dai baice komai ba ya sai kallon Paah. Kafin ma yay magana Paah ɗin shi ya kamo hannunsa yana faɗin, “Muhammad akwai damuwa fa, gidan nan zagaye yake da jami'an tsaro wai zasu kamaka. Muhammad mike faruwa ne? Mi kayi musu?”. Idanu kawai ya zubama Paah ɗin tamkar wani gunki, dai-dai nan Hayatu ya shigo shima a hargitse. Daga shi sai jallabiya alamar fitar bata shiri bace ba. Ko iya gaida Maash ɗin baiyi ba ya fara magana cikin tashin hankali. “Sir akwai shiri a wannan al'amarin babba. Dan ALLAH karka fito komi zasuyi. Ni zan bisu muje, ba sunce dai tambayoyi bane zan amsa musu duk irin wadda suke buƙata”. Shiru Maash ɗin nan ma bai tanka ba. Sai juyawa yay ya watsama Hajiya Mammah wani irin kallo. Cikin silent voice ɗin nan tashi a daƙile ya furta, “Out!”. “Out? Awwab ni kake cema out!”. Cike da fusata ya sake furta, “I say Out”. Ya ƙare maganar yana matsa mata a hanya alamar dai ta fitan kawai. Gaba ɗaya jikin Mammah ya gama sanyaya. Mamakin Maash ya gama kasheta da rashin mutuncinsa. Wata wutar bala'i data hango cikin idanunsa ya sakata fitar, cikin ɓacin rai ta ce, “Mara mutunci fitsararre gani na fitan, ita kuma yarinyar daka gama wulaƙantama rayuwa a ciki fa ko sai ta mutu zaka fiddo ta?.” Cikin mamakin furucin Hajiya Mammah ɗin duk aka zuba mata ido. Ganin ta samu nasarar samun attention ɗin kowa a wajen ta fara matse ƙwallar munafunci. “Yarinyar da ake nema tun daren jiya ce a ɗakinsa kamar matacciya. Na tambayesa miya faru yaƙi amsa min, shike nan Awwab bazai barmu muji da tashin hankali ɗaya ba fisabilillahi. Idan ba zubar da mutunci ba miya kawota cikin ɗakinsa?”. Kallonsa Paah yayi, cikin ɗan zafi-zafi ya ce, “Muhammad mike faruwa? Wace yarinya ce a ɗakin ka? Mi take yi kuma?”. Shiru tamkar bazai tanka ba. Sai kuma a hankali batare daya kalli Paah ɗin ba ya furta, “Kayi haƙuri abinda ya shafeni ne Paah”. “Abinda ya shafe ka?”. Paah ɗin ya maimaita da mamaki. Sai kuma ya cigaba da faɗin, “Muhammad wai miyyasa kai bazaka canja bane? Yanzu wanne kake son mu ɗauka a cikin waɗan nan tashin hankalin? Jiran da jami'an tsaro ke maka a waje runduna guda tamkar wani shugaban kidnappers kona yan fashi? Ko kuwa abinda Adda ta faɗa ka aikata anan?”. Idan dutse ya motsa to Maash ya tankama Paah ɗin. Sai ma dai-dai nan TJ ya shigo a haukace yana kuka. Ƙasa ya durƙushe cikin matsanancin tashin hankali yake sanar musu gafa Hayatu can zai miƙa kansa ga DSS ɗin can. Sannan su kuma sun tattare ma'aikatan gidan har da su Mama Balki wai zasu wuce da su. Idan sunyi hakan Boss dole ka miƙa kanka wai”. Idan ma yace baya a cikin tashin hankali yayi ƙarya, sai dai jarumtarsa ta shanye komai baka isa karantar abinda ke akan fuskarsa ba bayan canjawar launin idanunsa. Shi ba damuwarsa masu jiran nashi a waje ba. Yarinyar nan dake buƙatar taimakonsa itace tashin hankalin sa. A fili kam komai baice ba face raɓa Paah da Hajiya Mammah da Hajiya ƙarama, sai kawunsa Abdullahi da matarsa ya fice abinsa. Cikin sauri Paah da Tj da Uncle ɗin suka take masa baya. Ganin haka itama matar Uncle ɗin ta bisu, aka bar Hajiya Mammah da Hajiya ƙarama na kallan kallo. Sai kuma suka zabura suma suka bisu saboda kururuwar ihun da sukaji da basu san kona wanene ba ga ƙarar harbin bindiga......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_ ......Fitowarsa cikin takun nan nasa na isa da izza tamkar babu wani abinda ke damunsa ya saka su Azizat nutsuwa. Dan dama sune ke ihun saboda harbin da jami'in yayi sama. Duk da kasancewarsu jami'an tsaro kwarjininsa da gizago sai da ya tsarga musu zukata. Wani irin tsaiwar ƙasaita da zuba ma jami'in daya ɗaura bindiga a saman kan Hayatu yayi har kusan minti ɗaya, sai kuma ya miƙama TJ dake ta bayansa yana rawar jiki hannu, a hankali ya furta “Phone”. Da sauri TJ ya zaro wayarsa ya miƙa masa cike da girmamawa. Batare da Maash yace komai ba, a kuma tunanin kowa wani zai kira, amma sai kawai sukaga ya shiga ɗaukar hoto. Sai da yay a ƙalla kala huɗu kafin ya tura wayar aljihu ya sake gyara tsaiwarsa. Cikin daƙilalliyar muryar da sauke idanunsa akan ogansu ya furta, “Wace doka ce ta baku damar shigowa cikin gidana kuyi harbi batare da kun samu wani dalilin yin hakan ba? Wace doka ce ta baku damar shigowa har cikin gidana kuci zarafin ahalina? Bayan ba'a turoku domin su ba an turoku ne gareni ni ɗaya”. Rasa wace amsa ya kamata su bashi sukayi, sai ƴar kallan kallo suke. Sai da ogan nasu yaga zasu muzanta cikin aro jarumtar dole ya matso inda Maash ɗin ya ke ya miƙa masa takardar hannunsa. “Munada cikakken lasisin shigowa gidanka Mr Awwab El-Mu'azz Adams”. Da ga shi har takardar Maash yabi da kallon wulaƙanci batare da ya amsa ba. “Baka amsa min tambaya ta ba ai”. Ya faɗa a daƙile. Kame-kame jami'in ya fara cikin son aro jarumtar dole. Sai kawai Maash ya zare takardar daga hannunsa yana faɗin, “Okay bama sai ka amsa ba anan. Next time kawai”. Ya ƙare maganar cike da rainin wayo yana kallon takardar. Yana gama karantawa ya saki wani shegen murmushi, a saman lips ɗinsa ya furta “Mr Paul” dan ya fahimci kai tsaye daga inda saƙon yake. Nuni yay ma Hayatu da ya tashi. Babu musu kuwa ya miƙe ya nufosa. Hannu yasa a aljihu ya ciro wayar TJ daya amsa da key ɗin bedroom ɗinsa ya miƙa masa. “Ka bama Mama ta dubata. Idan akwai matsala kuje da ita asibiti zan sameku acan. Juliet taje ta ƙarasa meeting ɗin jiya”. “Amma sir...” Ɗauke kansa yay alamar baya buƙatar jin komai da ga Hayatun. Tj ya kalla tare da faɗin, “Bani key ɗin mota”. Cikin sauri TJ ya zaro ya miƙa masa. Batare da ya kalla ko inda su Hajiya Mammah suke ba ya matsa ga jami'an tsaron. Wani ne ya yunƙuro da Handcuffs a hannunsa da sauri. Wani banzan kallo da Maash ɗin ya masa bai ma san ya taka burki ba harda cin tuntuɓe. Wucewarsa yay ga motarsa ya buɗe ya shiga mazaunin driver. Sai da yazo saitin ogan nasu ya tsaya, batare da ya kallesa ba ya furta, “Zan iya wucewa ni kaɗai?”. Kallonsa kawai shugaban jami'an yake. Dan shi kam yanzu yake sake tabbatar da rashin mutuncin Maash ɗin da ake faɗa ya zarta duk yanda aka gaya masa ashe. Ga yaron da shegen kwarjini. Duk da kasancewarsa jami'in tsaro, a shekaru kuma zai iya haifar Maash ɗin, wata irin shakkarsa yake ji har ƙarƙashin zuciyarsa. Har takai ya fara jin nadamar amsar wannan aikin da yay. Yaransa biyu ya bama umarnin shiga bayan motar, shi kuma ya shiga gaba kusa da Maash ɗin. Sauran kuma suka fita da sauri wajen gate inda motocinsu da sauran ƴan uwansu suke. Shi Maash ma sai abin yaso bashi dariya ganin yanda aka cika kusan rabin street ɗin da jami'an tsaron kai kace sunzo kamo wani ƙasurgumin ɗan ta'adda ne daya addabi duniya. Lalataccen Murmushi ne ya suɓuce masa kaɗan. Dan in ba kallonsa kake ba bama zaka taɓa fahimtar yayisa ba. A nutsensa yake jan motar tamkar wanda baya so, har suka iso babban headquters ɗin DSS ɗin dake a garin na Lagos babu wanda yay ko tari a motar..... ★★★ Motocin na gama fita a harabar gidan Hayatu yay wani irin sauke numfashin damuwa. Sai kuma ya maida kallonsa gasu Paah dake ƙoƙarin nufar motoci alamar zasubi bayansu. Nufarsu shima yayi, cikin girmamawa ya dakatar da su. Bayani yay musu akan suyi haƙuri kar suyi gaggawar binsu har sai ya sanar da lawyers ɗinsu yanzu. Duk sun nuna gamsuwarsu akan hakan, shima sai yay ƙoƙarin ciro wayarsa a aljihu ya shiga kiran lawyers ɗin nasu har su uku. Yayinda shi kuma Paah ke ƙoƙarin neman Baba prof.. da baya ma ƙasar kusan sati uku kenan. Hayatu na gama kiran lawyers ɗinsu ya isa ga Mama Balki dake ta faman share hawaye ita da su Bahijja. Key ɗin da Maash ɗin ya bashi ya bata, tare da mata bayani. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke a karo na farko, dan dama hankalinsu a matuƙar tashe yake tun sabe na rashin ganin Samraah ɗin, ita a zatonta ma ko guduwa tayi. Dan ko'ina na gidan babu inda ba'a duba ba har sashen Hajiya Babba daya zama na farko amma babu ita. Batare da kowa ya farga ba Mama Balki ta zare jikinta sashen Maash. Dan su Hajiya Mammah sunata bige-bigen waya ne... Matuƙar tausayin Samraah ne ya cika Mama Balki har sai da tayi hawaye. Bata kawo a ranta wani dalili ne ya saka Maash yin wannan ɗanyen aikin ba, sai ƙila gardama Samraah ɗin ta masa. Amma yanda tasan Maash da tausayi da ƙoƙarin tsare hakkin kowa a rayuwa da mamaki wannan al'amari. Dan gaba ɗaya al'amarin babu tausayi a ciki. (Koda yake ƙila shima ya kasa riƙe kansa ne) zuciyarta ta ayyana mata tana mai ƙoƙarin ganin bataji zafin Maash ɗin ba a ranta. Ruwa ta shafa ma Samraah ta kawo numfashi, kukan data fashe da shi cikin zabura ya saka Mama Balki riƙota jikinta ta rungume. Sai kawai itama ta fara hawayen tana lallashinta. Jin muryar Mama Balki yanzu ba shi ba ya sakani jin nutsuwa. Sake ƙankameta nai cikin kuka ina mata magiyar dan ALLAH ta fita dani a ɗakin, idan ta barni kasheni zaiyi bashi da imani. Lallashina ta shiga yi da kalamai masu sanyi, sai da taga na sake nitsuwa sannan ta kwantar dani tana faɗin na jirata. Hawayena na cigaba dayi harta dawo bayan wasu mintina. Babu abinda ke mun kai kawo sai abinda ya farun. Sam hawaye sun gagara ƙafe min, koda Mama Balki ta kamani domin tashi sam na kasa. Sai ma kukan fitar hankali dana sakar mata dan wata irin azaba ce ta ratsani tun daga yatsun ƙafata har tsakkiyar ƙwalwata. Itama ganin bafa zan iya tashin ba ya sakata sake jin matsanancin tausayina. Rigar wankansa data ɗakko daga bathroom ɗinsa ta saka min ta sake gyarawa, sai kuma ta kamani cike da jarumta ta ɗaga gaba ɗaya na. Haka tana nishi baiwar ALLAH ta kaini har Bathroom ɗin. Sai da tamun gajeriyar nasiha da lallashi sannan ta taimaka min na shiga ruwan data haɗa. Bakina na dumtse ina mai fashewa da kuka jikina na rawa. Haka ta rirriƙeni tana cigaba da mun nasihar duk zaburar da nake bata yarda nabar cikin ruwan ba sai da ya huce. Wani ta sake haɗawa, sai da tamun haka sai uku abinka da dattiwar data san takan duniya sannan ta baroni nayi wanka. Kuka naci sosai har sai da tamun knocking ƙofar sannan nayi wankan. Cikin jarumta da son daurewa na ɗauka wata rigar wankan na saka dan wancan ta jiƙe saboda bata cireta a jikina ba ta sakani a ruwan da ita. Duk yanda naso taka ƙafafuna na fita da kaina hakan ya gagara. Kuka na sake sanyawa mai sautin da har sai da Mama Balki taji ta shigo. Kallona ta tsaya yi, kafin cike da tausayi ta furta, “Samraah bazaki iya tafiya ba yanzu ma?”. Kaina na jinjina mata ina sharce hawaye. A sanyaye tace, “Kiyi haƙuri kinji, in sha ALLAHU zaki ci riba a rayuwarki tunda bata hanyar banza kika tsinta kanki a wannan halin ba. Amma lallai dole zamuje asibiti kenan”. Kuka na sake fashe mata da shi batare dana iya cewa komai ba. Yanzun ma itace ta fiddoni. A saman kujera ta ajiye ni. Ta gyara ɗakin fes kamar bashi ba. Dan hatta da bedsheet ɗin ma ta canja wani. Kayana da ban san waya kawo mata ba ta bani tace na saka. Ita kuma ta koma bathroom ɗin bayan ta shinfiɗa min abin salla. Kayan na saka ina hawaye na sakko domin yin sallar, da ƙyar na iya yinta a tsaye, inayi ina kuka. Ina idarwar na zame a wajen na kwanta, kafin mama Balki ta fito zazzaɓi mai azabar zafi ya rufeni. Barci ya ɗan fara figata mama Balki ta tasheni nasha tea, kasa sha nayi, sai kuka nake mata kawai. Baiwar ALLAH duk ta shiga damuwa sai lallashina take yi. Wani barcin ne ya sake figata, gigitaccen bugun ƙofar da ake ya farkar dani. Buɗe ƙofar Mama Balki taje tayi, ɗauuuu kake jin saukar mari a fuskarta. Kafin Hajiya Mammah ta hankaɗota ciki. Taga-taga tayi zata faɗi ALLAH ya taimaketa ta rike ƙarfe net ɗin gado. Har cikin rai naji zafin marin nan da taima Mama Balki yau. Cikin matuƙar masifa ta shiga surfama Mama Balki zagi wai itace kawaliyarsa dake kawo masa yara ashe yana musu fyaɗe, to yau kam sai sunci ubanta a gidan nan. Duk yanda take son musu bayani kowa yaƙi yarda da ita, sai tambayoyi suke jefe mata kuma sunƙi bari ta basu amsa. Shiɗewa numfashina ya farayi saboda yanda hayaniyar Hajiya Mammah ke shiga har cikin tsakkiyar kaina dake ciwo. Sama-sama nake jiyo muryar Hajiya ƙarama na bada shawarar kaini asibiti. Daga haka ban sake gane komai ba........✍️ _Huuuum tofa masu karatu ƙaƙa raƙa ƙaƙa.._ *_Yaya zata kaya kenan? Maash zai sanarma ahalinsa wacece Samraah a yanzu ko zai cigaba da ɓoyewa?._* *_Shin waye Mr Paul daya saka a aka kama Maash? Mi kuma kuke tunanin zai faru?_* _Samraah!! Samraah!! Wane hukunci kuke tunanin zata iya ɗauka akan Maash kan abinda ya faru, da labarin da taji na al'ummar wannan gida?._ *Hajiya Mammah?* *Hajiya ƙarama?* *Paah?* *Uncle Abdullahi da matarsa?* _Shi kansa Maash bakwa tunanin akwai abinda yeke binnewa kuwa?._ _Gidan Abba, gidan su Mansoor, nan ma fa duk akwai sabuwar cakwakiya._ *_Hummm kar dai na cikaku da surutu, mu tara ranar Monday in sha ALLAHU. Banda pages dole zanyi hutun weekend ɗin nan insha ALLAHU. Dan munzo gaɓar da komai yake buƙatar fita da fitarsa. Ku muje zuwa TSUTSAR NAMA BOOK 3 Guys._* _Bana son naga numbers ɗin na tsaho ganda rubutun nake ji wlhy, dan haka zamu tafi part 3 yanda zamuyi maza kafin salla mu kammala in sha ALLAH 😘😘😘_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒐𝒏𝒆_ _______ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 __________ .......Suna shiga cikin headquter ɗin Lawyers nashi na isowa shima. Sai dai kafin su ƙarasa gareshi an shige dashi wani ɗakin bincike. Table ne kawai da kujeru biyu masu facing juna. Sai da ya gama ƙarema ɗakin kallo fuskarsa a yamutse kafin yaja kujerar ya zauna. Yana zama cikin jami'an wani shigo, da girmamawa yake tambayarsa ko yana buƙatar wani abu kamar su tea haka. Ɗan jimm yay yana kallon ma'aikacin, sai kuma ya murmusa kaɗan alamar a'a. Fita Jam'i yayi, shi kuma ya jingina bayansa da kujerar sosai ya lumshe idanunsa kawai. Kusan mintuna fin ashirin sannan aka sake buɗe ƙofar. Bai motsa ba bai kuma buɗe idanunsa ba har jami'in ya kai zaune. Kaɗan ya ɗan buga table ɗin, sai dai a hakan ma Maash ɗin ƙin motsawa yayi. Sai da ya mula dan kansa sannan ya buɗe idanunsa ya zubama jami'in batare daya tashi ba. Ji Jami'in yay bazai iya jure kallon ba, sai ya kauda idanunsa cike da basarwa yana furta, “Sir bamu da isashen lokaci. Idan ba damuwa ka amsa mana wasu ƴan tambayoyi mana”. “Jeka maganarka kai tsaye” Maash ya faɗa a daƙile. Ran jami'in ne ya sosu, sai dai baice komai ba ya cigaba da faɗin, “Akwai containers ɗinka da suka tashi daga Lagos a shekaran jiya da dare zuwa ƙasar Ghana. An samu yara ƴammata a cikin ɗaya da muke da tabbacin safararsu aka shirya yi. Still dai a cikin container ɗin anyima yaran makwanci, a ƙasan shi mun samu kayan laifi”. “Kamar......?” Maash ya faɗa cike da rainin hankali. Yanzu kam a fusace jami'in ya kallesa. Sai dai kuma bai iya cewa komai ba ya cigaba da faɗin, “Drivers ɗin sun tabbatar mana da cewar sun fito daga companyn ka ne”. Ya ƙare maganar da tura masa hotuna gabansa. Batare da Maash ya ɗauki hotunan ba ya zuba musu ido kawai. Kansa ya ɗan girgiza cike da rashin damuwa ya furta, “A staff ɗina bana tunanin nasan waɗan nan fuskokin”. “Ba zamu tabbatar da hakan ba, dan zaka iya hiding nasu. Sai dai kuma su containers ɗin ai bazai yiwu kace ba naka bane ba”. Shiru babu alamar Maash ɗin zai tanka, sai da ya mula dan kansa sannan ya saki ɗan gajeren murmushi da kai hannu ya shafi kwantaccen gashin fuskarsa. Zamansa ya gyara da ƙyau gaba ɗaya hannayensa akan table ɗin ya zubama jami'in ido. “Mr Man kamar ya dace ka tuna kai jam'i ne ba alƙali ba. Damar samuwar amsar tambayoyinka kuwa zaka same su ne kaɗai a bakin lawyers ɗina”. Daga haka ya gyara zamansa ya sake lumshe idanunsa duka hannuwansa harɗe a ƙirjinsa. Iya ɓacin rai Jam'in nan ya shiga. Dan haka ya miƙe a fusace ya fice abinsa. Murmushi Maash ya saki mai ɗan sauti batare da ya buɗe idanunsa ba. Har yamma Lawyers na Maash na fafatawa a station ɗin, shi dai yana a inda aka kaisa har yanzu. Sai da lokacin Sallah yayi ya buƙaci yin alwala. Basu da damar hanashi. Abincin da Hayatu ya kawo masa kuwa ko kallonsa baiyi ba. Dan shi fa sam bawai cakwakiyar station ɗin ma bace damuwarsa. Hankalinsa ma gaba ɗaya baya a wajen. Gab da magrib Baba prof... Ya iso, da ga airport kai tsaye shima station ɗin yayo, anan ya samu kusan duk ahalin gidan. Paah, Uncle Abdullahi, Hajiya Mammah, Maman Maleeka (Matar Uncle Abdullahi) sai Hayatu dake kai kawo tsakanin asibiti da aka kwantar da Samraah zuwa nan. Ko bayan isowar Baba prof.. ɗin shima ya kai awanni uku a station ɗin kafin su samu bell ɗin Maash ɗin bisa wasu sharuɗɗa masu tsauri. Ƙarfe tara da wasu mintuna aka fiddo Maash da ga ɗakin nan. Kallo ɗaya yay ma ahalin nasa ya ɗan kauda idanunsa. Sai kuma ya cigaba da takowa a nutsensa har inda suke. Baba prof.. ne ya riƙosa ya rungume yana faman ambaton Alhamdullah. Shi dai Maash baice komai ba. Bayan ya sakesa kuma ya koma tattaɓashi da jera masa tambayoyi. “Kana jin yunwa? Akwai inda ke maka ciwo? Sun maka wani abu ne?.....” “Grandpa! I'm not small boy now”. Ya katse Baba prof.. ɗin cikin wata irin murya mai cike da rashin damuwa. Murmushi Baba prof.. yayi da kai hannu ya yamutsa masa sumar kansa kamar yanda yake masa a duk sanda suka haɗu. “Oh na manta Muhammad Awwab ɗina dutse na rimi ne baka fargaba sai ta ruwa.” Dariya su Paah suka ɗan yi, kafin shima ya matso ya rungume Maash ɗin, hakama Uncle Abdullahi. Maman Malika ma tai masa barka. Ganin haka itama Hajiya Mammah ta bashi side hug. Shi dai komai bai cema kowa ba. Sai hankalinsa da ya ɗan maida ga lawyers ɗinsa da Hayatu dake fitowa. Cike da girmamawa suka shiga gaisheshi. Tare da jajanta abinda ya faru suma. Idanunsa ya lumshe kaɗan da sake buɗewa, suma ɗin dai batare da yace ma kowa komai ba ya motsa a hankali ya fara tafiya. Suma duk ƙoƙarin ficewar sukayi, kowa da abinda ke a zuciyarsa. A motar da yazo da ita da safe ya shiga. Sai dai yanzu Hayatu ne a mazaunin driver. Har sun ɗauki hanyar gida a kasalance Maash da idanunsa ke rufe har a lokacin a hankali ya furta, “Hospital”. Cikin girmamawa Hayatu ya amsa masa, tare da fita a cikin sauran motocin ya ɗauki hanyar asibiti. Sauran abokan tafiyar basu farga ba sai da akaje sauke Baba prof a gidansa. Da farko sun ɗauka ko gida su suka wuce saboda Maash ɗin ya huta, sai da drivern Baba prof ɗin ya sanar da inda yaga sunyi sannan ne a fusace Hajiya Mammah ta ce, “Eh lallai, al'amarin Awwab kullum sake gawurta yake wlhy. To amma kuma anya ba wani abun yaje aikatama yarinyar nan ko hana likitocin faɗa ba saboda ya rufe sirrinsa.” Har cikin rai zancenta ya soki zuciyar Paah, sai dai baice komai ba. Baba Prof ne ya tambayi abinda ke faruwa? Har zagwaɗi Hajiya Mammah keyi wajen zayyane komai daya faru da safe har neman yarinyar da suka dinga yi da daddare. Wani yawu mai kauri Baba prof ya haɗiya idanunsa akan Paah da Uncle Abdullahi. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Wayarsa ya amsa a hannun drivern sa daya kwaso kaya zai kai ciki, dan duk abinda Hajiya Mammah ta faɗa ya laɓe yana jinta. Kai tsaye Baba prof ɗin wayar Hayatu yay kira, bugu ɗaya kuwa ya ɗaga. “Kuna ina?”. Da ƴar in ina Hayatu ya ɗan kalla Maash dake ƙoƙarin fita a mota daya buɗe masa dan isowarsu ke nan. “Bab ba baba muna CLINIC”. “Clinic! Yin me?”. “Zamu duba mara lafiya ne”. Ƙittt Baba prof ya yanke kiran batare daya sake cewa komai ba. Cikin damuwa Hayatu ya dubi Maash ɗinya ce, “Baba Prof”. Komai baice masa ba, sai ma ƙoƙarin raɓasa da yake yi zai wuce abinsa. Dole shima ya haɗiye abinda ke bakin nasa ya bisa. ★★ Mama Balki na zaune a saman abin salla idar da shafa'i da wutirinta kenan akai knocking ɗin ƙofar. Miƙewa tai tana kallon agogo, azatonta ma Nurse ɗin data sakama Samraah ruwa ce ta dawo. Ruwan ta kalla taga ko rabi bai kai ba ma, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ƙofar ta nufa, sai dai kafin ta buɗe sai da ta tambaya waye?. Hayatu ne ya amsa mata da cewa, “Mama mune”. Da sauri ta buɗe tana murmushi, tana ƙoƙarin bashi hanya ya shigo idonta ya sauka akan Maash. Wani irin washe baki tayi tana ambaton Alhamdullah. Da jerama UBANGIJI kirari. Ɗan lumshe idanunsa yayi tare da sakin gajeren murmushi ya shiga gaidata. Amsa masa tai tana ƙara godema ALLAH daya sa komai ya zama mai sauƙi. Nan ma murmushin kawai ya saki baice komai ba, sai Hayatu ne ke tayata murnarta. Ƙarasa takawa yay a hankali zuwa gaban gadon idanunsa a kanta. Tana kwance samɓal idanunta a rufe alamar barci take. Fuskarta ta wani irin yin fayau da ita, sannan har yanzu idanunta a kumbure suke alamar taci kuka mai yawa. Lips ɗinta sun bushe tare da tsukewa waje guda sun ƙara pink sosai. Take wasu abubuwa suka shiga dawo masa game da ita. Cikin sauri ya kauda su tare da janye idanun nasa daga lips dinta, akan hannunta da aka saka ruwa ya sauke. Madaidaitan farcinanta dake da ɗan sauran jan lalle na biki kaɗan da bai gama fitaba yaja kusan mintuna biyu yana kallo, kafin ya maida ga ruwan da ake ƙara matan. Sai kuma ya janye gaba ɗaya ya matsa gaban side drawer dake a gefen gadon ya ɗauki file ɗin da aka ajiye ya fara dubawa. Juyowa yay da nufin yin magana sai ya ga ɗakin wayam, ashe Mama Balki da Hayatu sun fice. Kansa kawai ya girgiza yana ajiye file ɗin, sannan ya zagaya ta ɗayan side ɗin gadon inda hannunta ke free ya zauna kusa da ita jikinsa na gogar nata. Hannun nata ya kamo cikin nasa, ya zubama dan sauran lallen dake jikin faratan nata ido, abubuwa da yawa zuciyarsa ke tunano masa da suka shafi Ummie, mace ce mai tsananin son jan lalle, tunda ya santa kafin lalurarta lalle baya gama fita a hannunta take yin wani. Hakan ya sashi tashi da son lalle shima, lokacin yana ƙarami yakan saka mata rigima shima sai an masa. Takan ce masa maza basa lalli, amma ya tubure ya dinga bori ko yaje ya tsare Mama Balki ko mahaifiyar Hayatu akan dole su sai sun masan, dan a farkon ciwonta kafin komai ya damule har da kansa yake mata lallin a yatsun hannu saboda yasan tana so. Murmushi ne ya suɓuce masa da shi a karan kansa ya mance tsahon shekarun daya ɗauka baiyi irinsa ba. Sai kuma ya kai babban yatsarsa ya ɗauke guntun ƙwallar da suka taru masa a gefen ido kaɗan........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 _______ .......Ɗan motsi Samraah tayi fuskarta a yamutse baki a taɓe kamar mai shirin sakin kuka. Idanu kawai ya zuba mata yana kallon yanda take laɓe bakin, ƙoƙarin motsa hannunta da tai ya sashi sakin wanda ya riƙe ya riƙe mata wancan gudun karta goce ruwan, sake yamutse fuskar tayi da ƙara tura baki. “Cry. Cry”. Ya faɗa a hankali saman lips ɗinsa yana kai ɗayan hannunsa a karo na farko kan fuskarta ya ɗan shafa gefen kumatun kaɗan. Idanunta ta shiga motsawa a hankali, sai kuma ta buɗesu gaba ɗaya. Cikin yanayin wadda barci bai saka ba ta ɗan zuba masa su, shima kallon nata yake... Tar tar fuskarsa ta fara bayyana cikin idanun nawa sosai. Wani irin harbawa zuciyata tayi babu shiri na zabura. Sai dai jin an riƙeni yasa na kallesa a marairaice, batare dana san hawaye sun ɓalle min ba na fara roƙonsa cikin magiya. “Na roƙeka dan ALLAH kayi haƙuri ya Awwab, wlhy zan iya mutuwa bazan iya ba”. Ganin bashi da niyyar tanka min sai rikitattun idanunsa daya zuba min yasa na sake fashe masa kuka mai ɗan sauti. Kansa ya ɗan girgiza tare da sakin hannun nawa ya kuma janye wanda ke a fuskata sannan ya miƙe, kaɗan ya ranƙwafo ya kama bargon. Sake marairaice masa fuska nayi ganin yanda ya duƙo kaina sai yanayin ya sake min kama da na wancan lokacin, idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe cikin soft voice ya furata, “I will go now. calm your mind”. Ya ƙarasa lulluɓa min bargon har saman ƙirjina. Idanuna na lumshe sauran hawayen dake cikinsu na ƙarasa gangarowa. A bazata naji saukar lips ɗinsa saman goshina. Kafin na buɗe idanuna a firgice harya juya yabar wajen. Ƙofar daya maida ya rufe na zubama idanu, a hankali bugun zuciyata na sauka. Shigowar Mama Balki ɗakin ya sani kauda kaina daga kallon ƙofar. Kaina tayo kanta tsaye tana faɗin, “Kin tashi Samraah?”. Kaina na jinjina mata da ƙoƙarin kai hannu na share hawayena, zama tayi a gefena tana mai kamo hannuna cikin nata. Cike da lallashi da kulawa ta ce, “Kukan nan ya isa mana haka Samraah. Abinda ya faru dai ya riga ya faru ai. Sai fatan ALLAH ya baki lafiya. Ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, bana son ko a fuska ki nunama Alhaji ƙarami wani abu. Koba komai shi ɗin mijinki ne, kowace mace kuma da haka ta girma. Komai zai wuce kamar bai faruba. Naga ya fita kamar cikin damuwa, gaki ke kuma kina kuka. Dan ALLAH ki daure ya samu sassauci ko'a wajenki ne. Kinga yanzu daga police station ya fito tun safe amma ko gida baije ba sai da yazo nan domin dubaki. Alhaji ƙarami abin tausayine wlhy”. Idanuna na buɗe a hankali ina kallonta, sai kuma na kai hannuna na sake share hawayen da suka gagara tsaya min. Cikin dasashjiyar muryata na ce, “Mama ni babu abinda nai masa fa. Kawai dai shi yasan mike damunsa. Mi yaje yi police station kuma?”. “Nasan babu abinda kikayi masa Samraah. Amma nasan kukan nan da yaga kinayi ma ya isa ya sake ɗaga masa hankali. Ki daure ki daina kinji. Idan shima yaga kin kwantar da hankalinki zai fi samun nutsuwa wajen baki kulawar da duk kike buƙata. Sannan ya fuskanci abubuwan dake gabansa. Dan nasan akan batun nan naku wata sabuwar cakwakiyace kuma. Su suna kallo al'amarin da wata suffa daban, idan kuma baya gadama ba duk abinda zasu yi bazai sanar musu alaƙarku ba dan da kike ganinsa nan akwai taurin kai da kafiya. Bamu san abinda ya faru ba da safe folisawa suka cika mana gida wai sunzo kamashi” daga haka ta cigaba da lallashina har na sake komawa barci raina fal mamakin zancen kamashi da tace anyi, a yanda yake da kuɗi da power ɗin nan har jami'an tsaro zasu iya kamashi ashe?... 💦💢💦💢💦 “Ni nai sa'a da masoyi mai fara'a, shi ya fara sa shadda duk garinmu an shaida bai ɗaya. Ni na shirya, zana baka soyayya, koda ƴan baƙin ciki zasu haɗiyi zuciya. Ni na dace, na faɗa ko na dace, da sahibi imamullah mijin ƙwarai”. Halime kenan, ke raira waƙarta cike da nishaɗi tana wanke-wanke a babban kitchen dake mallakin kowa da kowa. Wanke-wanke take na kwanikan da akaci abincin rana da tayi, yau kuma ne zata fita a aiki Mom ta amsa. Da farko aikinta take hankalin kwance sai dai shigowar Mom kitchen ɗin da abinda tai mata ya ƙona mata rai. Maimakon ta biyema Mom ɗin sai kawai ta shiga raira waƙa. Idan tayi wannan sai ta saki ta kama waccan harta kammala wanke-wanken. Kasa haƙuri Mom dake tare da mai-aikinta tana bata umarnin abincin dare da zata ɗora musu tayi. Cikin fusata ta shaƙo wuyan rigar Halime ta baya ta fusgota. “K ƙaramar ƴar iska waƙe-waƙe ai bazai kai miki ba. Rama abinda nai miki ya kamata kiyi sai na san kin cika matsiyaciya”. Idanu kawai Halime ta zuba mata, sai kuma tayi murmushi da kai hannu ta janye hannun Mom ɗin a jikinta. Ƙoƙarin juyawa take ta ƙarasa aikinta Mom ta sake ƙoƙarin damƙota cikin masifa da haushin shirun da tai matan, dan so take ta tanka mata akwai abinda zata saka mata a gashi. Wani shegen tsalle Halimen tayi gefe kai kace tayi gamo da wani bala'i ne. Hakan yasa mai aikin Mom da ita kanta Mom ɗin sai da suka zabura. Sai kawai tsabar wulaƙanci Halime ta fashe da dariya. Galala Mom da mai aikinta sukai suna mata kallon mamaki. Itako sai ta kallesu sai ta fashe da dariya, da tayi kamar zata tsagaita sai ta kallesu ta sake fashewa da dariyar. Wani irin tuƙuƙi zuciyar Mom ta shiga yi, tana yunƙurowa a fusace zata sake shaƙo Halimen sai kawai ta kauce mata tare da ɗaukar kayanta data tara a kwandon kife kaya tai ficewarta. Sai dai taje bakin ƙofa sannan ta ɗan dakata. Juyowa tai ta kalla Mom har lokacin fuskarta da sauran dariyar ta ce, “Ƴar baƙin ciki, so kike na biye miki muyi dambe dalin Imamu ya talauce saboda ke kin gama shan daɗin romin zabbi. To wallahi bashi yiwuwa nima sai na dandali arziƙin nan. Ɗan romon kifin nan dana kaji da ban samu naci a gidanmu ba sai na sha farina ya sake fitowa nayi ɓul yanda zanje ƴan tumaki ana ku matsa ga matar Alhaji Imamu nan ta iso haaaah”. Ta ƙare maganar da gatsine mata baki tana yin gaba abinta. Kasa ko motsi Mom tayi, sai zuciyarta dake wani bala'in yunƙurowa. Wai itako yaya zatayi da mahaukaciyar yarinyar nan a gidan nan. Tayi bala'in, tayi fitinar, tayi boren, tana kan asirin amma duk a banza. Babu irin maganin da batai amfani da shi ba a kofar shiga ɗakinta da cikin abincin da Abba da Halime zasu ci amma ko gezau. Jiya har layun da teacher ya bata ta shiga har ɗakinta ta sanya a ƙarƙashin gado amma ko gezau, bayan kuma Umma ta tabbatar mata idan har ta saka layun yarinyar nan ta kwanta a gadon bazata kwana a gidan ba sai dai gidan Ubanta. Kuma komai dare sai ta koma garinsu a ƙafa. Haka ta kwana zaman saurare amma har gari ya waye babu ko dogon motsi daya faru a gidan. Sai ma da farar safiya Halimen ta tashi ta damesu da aiki da waƙe-waƙenta na iskanci kai kace ita ɗin jikar barmani choge ce ko shata. A fusace itama ta bar kitchen ɗin tana dakama mai aikinta tsawa.... 💢🌟💢🌟💢 Suna akan hanya nufar gida Hayatu ke bashi labarin rikicin da Ummie tayi yau a gida na neman Samraah. Har falon ƙasa ta sakko yau tana riƙe duk wanda ta gani ta bisa da kallo, sai kuma ta girgiza kai ta saki wanda ta kama ɗin ta tafi na gaba. Bayan ta gama bin kowa bata ga wadda take neman ba sai kuma ta zauna ta sanya kuka. Abin yayi matuƙar bama kowa mamaki. Nima na koma amso kayan da zasuyi amfani da shi ne na tadda wannan drama. Da ƙyar na lallaɓata bayan na ambata mata sunan Aunt sai ta shiga gyaɗa kanta alamar dai tabbacin ita ɗin take nema. Lallashinta nayi tare da tabbatar mata zanje na kirawo mata ita sannan ta yarda ta koma saman. Shine dana kai musu kayan na samu abinci na kai mata taci na bata magungunanta. Tana kammala ci sai barci. Koda na koma bayan magrib ɗin nan na samu har lokacin tana barcin. Yaya abin nan yamun daɗi, da'alama Ummie ta fara samun lafiya, tunda har take iya banbance mai ƙyautata mata. Lallai Aunty Samraah alkairi ce a rayuwarmu. Lallai akwai hikima a cikin sanadin shigowarta rayuwarmu”. Kamar yanda Hayatu yayi tsammani baice komai ba. Sai dai a bazata badan kar ace yayi ƙarya ba sai yaga kamar yayi murmushi. Amma dai baya ce ba, tunda ba gani yay ƙuru-ƙuru ba kasancewar fuskarsa na gefe. Shiru ya samu gidan da alama kowa ya kwanta, maimakon wucewa nasa sashen duk da yunwa da gajiyar dake addabarsa sai ya nufi sashen Ummie. Daki-daki yake bin ko'ina da kallon tsaff, gaba ɗaya sashen ya canja yanzu akoda yaushe cikin ƙamshi da tsafta yake. Duk da a yanzu falon farko ne kawai mai kujeru, amma sauran duk an kwashe komai tunda Samraah tayi magana. Duk da a ɗari-ɗari yake bai dakata ba sai da ya dangane da bedroom ɗin da a yanzu yafi samunta. Sassanyar ajiyar zuciya ga sauke yana mai jingina da bango da lunshe idanunsa sannan ya buɗe a kanta. Barci take har yanzu, sai kuloli masu ƙyau ata gefenta alamar abincine a ciki, yasan wanda Hayatun ne ya kawo, dan haka ya ƙarasa a hankali cikin takun sanyin jiki ya bubbuɗe kulolin. Lafiyayyen abincine da ko ba'a faɗa ba yasan Falak ce ta yisa duk da tana fama da kanta itama. Ajiyar zuciya ya sauke tare da furzar da iska mai nauyi daga bakinsa. Sai kuma ya maida komai ya rufe ya koma bakin katifar ya zauna. Blanket ɗin data ɗan zazzame ya gyara mata, a hankali ya kai hannu ya gyara mata hularta da ita ta zame. Sosai ya zuba mata idanunsa da suka kaɗa sosai. Daka gani kasan kukan zuci yake yi. Ya jima zaune a ɗakin duk da uban barcin da yake ji har kusan gabannin asuba ciwon kai ya takura masa sosai sannan ya miƙe........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _______ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 _______ .......Tsaff sashen nasa yake an gyara komai tamkar koman bai faru ba. Yasan aikin Mama Balki ne wannan. Dan hatta bedsheet ɗin saman gadonsa da blanket an canja su da wani fari tass mai ƙyau da masifar laushi. Bathroom ya shiga, can ma ɗin dai an tsaftacesa. Sai kawai yayi wanka tare da ɗauro alwala ya fito. Sai da ya fara gabatar da shafa'i da wutri sannan ya kwanta dan barci sosai ke cin idanunsa ga ciwon kai da baya raba ɗayan biyu a dalilin zaman sashen Ummie da yayi ne. Dan lafiya lau suka shigo gidan sai gajiya dake damunsa. Yana kwanciya kuwa barci mai nauyi yayi awon gaba da shi... Da asuba makarar da yayi ce ya sashi yin salla a ɗakinsa ya sake kwanciya. Barci ne mai nauyi ya ɗaukesa har ya manta ma safiya ce ba dare ba. Duk da kuwa shi da wahala kaga yana barcin safe ko rana. To inama yaga wannan lokacin kullum abubuwa sun ma kansa yawa. Idan har kagansa yini guda a gida yana hutawa lallai ba lafiya ba. Ko kuma akwai wani ƙwaƙwƙwaran dalili. Dan ko nan ta samu ya gudo dan ya huta baka rabashi da laptop ko tab a hannu yana harkokinsa. Cikin barci sautin knocking ɗin ƙofa ya addabesa. Dole ya buɗe idanunsa yana mai karanto addu'a. Sai da yaja kusan mintuna uku kafin ya miƙe zaune cike da takaicin wanda ke damun nasa. Agogo ya kalla goma da wasu mintuna na safe. Yaɗan furzar da iska kaɗan tare da zuro clean ƙafafunsa ƙasa. Nan ɗin ma sai da yaja wasu sakanni sannan ya ɗauki remote ya danna ƙofar ta buɗe kanta. Paah ne ya shigo, dan haka ya zuba masa ido kawai yana kallonsa. Sai kuma ya motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Good morning”. Amsa masa Paah ɗin yay da, “Morning dear, ka tashi lafiya?”. “Alhamdullah”. “To masha ALLAH. Dama Baba ne yazo tun ɗazun, da yace kar a tashe ka harka tashi da kanka, sai kuma ga baƙi munyi da ga human right, wai sunzo ne akan case ɗin yarinyar nan. Bamu san wanene yaje ya sanar musu ba a gidan nan. Muhammad wai miya kaika aikata al'amarin nan? Bayan nasan wannan ba halinka bane ba. Baka aikata a waje ba sai a cikin gida, haba Muhammad da mahaifiyarka na cikin lafiyarta mi kake zato”. Komai Maash bai ce ba har Paah ya gama maganarsa. Cikin ɓacin rai ya juya ya fita yana mai bashi umarnin fitowa yanzun nan ana jiransa kada ya ɓata musu lokaci. Da kallo kawai ya bishi na tsawon mintuna har biyu, kafin ya furzar da nannauyar iska ya miƙe. Bathroom ya nufa, bai wuce mintuna biyar ba ya fito. Ba tare daya canja pyjamas ɗin jikinsa ba ya zura bedroom slippers ɗinsa masu taushi farare tas kamar pyjamas ɗin nasa ya fito. Baiyi zaton a falonsa suke ba. Dan haka yay ɗan turus yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Gaba ɗaya manyan gidan ne sai baƙi fuska mata biyu da maza biyu. Ɗauke idanunsa yay cike da basarwa, a dakile ya furta, “Good morning”. Yana kaiwa cikin kujera da ke gefen Baba prof alamar shi aka barma wajen zaman dama. Duk da dai kowa ya samu nasa gurin kasancewar falon bawai kujeru bakwai bane ba kawai. Yanda ya tsuke bakinsa da ga gaisuwar farko kowa ya fahimci jam'i yayi. Kuma bazai sake wata ba. Harara Hajiya Mammah ta watsa masa. Hakama Hajiya ƙarama sai da ta ɗan cija lips. Maman Malika ce kawai tayi ɗan murmushi da faɗin, “Awwab babu dai wata matsala ko?”. Kansa ya jinjina mata. Sai kuma a hankali ya ɗan motsa lips ɗinsa ya ce, “Alhamdullah Mamy”. Da fara'a itama ta ce, “Alhamdullahi mun gode ALLAH. ALLAH kuma ya kiyaye gaba”. Baba prof, Paah, Uncle Abdullahi suka amsa da amin. Duk da dai fuskokinsu babu walwala suma. Kallonsa Baba prof yayi kamar mai nazari, kafin ya masa nuni da baƙin fuskar yana faɗin, “Baƙine daga human right. Wai sun zo ne akan case ɗin yarinya da akai raping anan gidan. Sunyi-sunyi da ita tun jiya wai ta faɗa musu amma taƙi. Shiyyasa suka zo domin ganawa da kai, suna son a basu izinin yin bincike akan case ɗin”. Shiru babu alamar Maash zai amsa kamar ba da shi Baba prof ɗin ke magana. Dan tun kallo ɗaya da yayma mutanen bai sake ba. A yanzu ɗin ma da yaji bayanin komai daga baba prof ɗin bai kallesun ba bai kuma tanka ba sai da ya mula dan kansa. Zamansa ya gyara cike da ƙasaita a wulaƙance ya kallesu a karo na biyu. Cike da gizagonsa ya furta, “Ko zan iya sanin mai kai report ɗin?”. Kallon juna sukayi, sai kuma cikin ƙarfin hali namijin dake facing Maash ɗin ya furta, “Ranka ya daɗe wannan ai sirri ne bama buɗesa. Duk wanda ya kawo mana report akan wani case yana da cikakkiyar kariya a garemu tako wace fuska. Amma idan munyi kuskuren shigowa bada izini ba ayi mana afuwa. Muna akan aikinmu ne”. Kamar bazai tanka ba dan har sai da kowa ya zuba masa ido a falon, sai kuma ya yunƙura ya miƙe yana faɗin, “Okay tunda har kuka fahimci hakan da kanku ina fatan zaku gane hanyar da kuka shigo. Dan bana buƙatar fitowa na sameku koda a gate ɗin gidan nan ne”. Daga haka yay wucewarsa cike da takunsa na izza. Duk binsa sukai da kallo, sai da Baba prof ya katse yanayin cikin wayancewa ya saki murmushi da faɗin, “Kufa yi haƙuri, shima tun jiya ransa a ɓace yake da faruwar al'amarin. Wani dalili ne ma daya ɗan gitta yasa bai ɗauki mataki ba. Amma na tabbatar tunda har kuka zo nan da kansa zai nemeku idan ya huce. Maybe shigowar karan tsaye da kukayi mana ne ya tunzurashi. Amma in har komai ya dai-daita ni da kaina zan nemo ku in sha ALLAH”. Badan sun gamsu da bayanin Baba prof ɗin ba suka miƙe. Sai dai sun tabbatar da yanda suka karanci tsagwaron rashin mutunci a fuskar Maash ɗin to lallai idan har ya dawo ya same sun komai zai iya faruwa. Har gate Baba prof yay musu rakkiya yana ƙara basu haƙuri. Sai da ya ga fitar motarsu sannan ya dawo. Zama suka sake yi jugum-jugum amma babu alamar Maash zai sake fitowa. Hajiya Mammah ce ta katse zaman shirun nasu da faɗin bara ta sake kiran Maash ɗin. Amma sai Baba prof ya dakatar fa ita akan ta barsa yana son yanzu shi yaje asibiti yaga yarinyar kafin su san ta hanyar da zasu ɓullo ma al'amarin. Sam bata so haka ba, sai dai ganin sauran duk sun bada goyon baya yasa ta yin shiru.... Maash kam daga falon hanyar da zata sadashi da sashen Ummie ya nufa. Ya samu sashen na sabon ƙamshi alamar an masa gyara. Sosai yayi mamakin waye kuma? Tunda yasan ita tana asibiti. Yana shiga yaci karo da mama Balki na shirin fitowa. Cikin kasa ɓoye mamakinsa ya ce, “Mama kece?”. Murmushi tayi cike da kulawa ta ce, “Eh Alhaji ƙarami. Ai mutuniyar taka ce tun asuba data farka take ta roƙona nazo na duba mata Ummie, tasan maybe bata ci abinci ba. Harda kukanta. Dan haka ina yin sallar asuba gari yay haske nai shirin tahowa sai kuma ga Hayatu ma yaje kai abinci shine na biyosa ya kawoni. Gata nan har ma taci abinci tasha magani barci ya ɗauke ta. Sauri nake kuma na koma can asibitin yanzu dan zata iya ƙin shiga ruwan zafin dana bar mata itama”. Idanunsa ya ɗan lumshe tare da buɗewa a lokaci ɗaya. Sai kuma a hankali da silent voice ɗin nan nasa ya furta, “ALLAH ya saka da alkairi Mama”. “Amin Alhaji ƙarami ai yiwa kaine. Bismillah ka shiga, Bara naje Hayatu na jirana zai maida ni”. Shiga yay ita kuma ta fice. Ya jima a ɗakin yana kallon Ummie har sai da kansa ya fara juya masa sannan ya fito. Da gaske sauƙi ya fara samuwa. Dan inda dane a yanda ya shigo ɗin nan komai barcin da take yi saita tashi kansa. Amma kalla jiya yafi zaman awa biyu amma harya fita bata ko motsa ba sai shine da ciwon kai ya addaba. Sashensa ya koma batare daya bi takan su Paah dake a falo ba. Yay wankansa ya shirya tsaff da shi. Bayan ya gama fesa turarurtukansa masu ƙamshi da tsada kala kusan biyar, shiyyasa ba'a gane ainahin turaren da yake amfani da shi yay zaman saka takalmi. Wayarsa da akai kira ɗazun bai ɗauka ba ya duba. MD ɗin companyn sa ne na Kano. Kiransa yay back, dan yasan akan maganar Musaddiq ne. Cike da girmamawa baturen mutumin ya gaishesa da ga can. Kafin ya ɗora masa bayani akan komai na Musaddiq ɗin ya kammala. Zuwa next week zai biyo jirgi zuwa nan Lagos daga nan sai ya wuce. Kamar yanda ya saba amsa wayarsa bata wuce ɗaya biyu koda zakuyi maganar awa ne ya amsa masa da “Okay” kawai ya yanke wayar. Daga haka ya ƙarasa shirinsa ya fito. Hayatu da Tj kawai ya samu a falon suna jiransa. Bai zauna ba da ga tsayen ya amsa gaisuwarsu yana mai ɗan kallon agogon hannunsa mai shegen tsada da ƙyau. Sai kuma a hankali ya furta, “Let's go”. Duk miƙewa sukayi, yana gaba suna binsa a baya, sai ma Hayatu ne dake ɗan masa bayani daya shafesu dan akan kasuwanci ne har suka iso gaban motocin da aka gama shiryawa domin fitar tasa. A tare guards ɗinsa da sauran ma'aikatan gidan suka dinga kawo gaisuwa da jajanta abinda ya faru, tare da masa addu'ar kariya daga sharrin duk wani abun sharri. A karo na farko ya ɗan saki gajeren murmushi tare da haɗe hannuwansa a waje guda alamar ya gode. Kamar ko yaushe yana baya TJ na mazaunin driver Hayatu a gefensa. Sai motar guards ɗinsa guda biyu ata gaba da baya su suna tsakkiya. Sam yawo da guards ɗin nan ba sonshi yake ba. Sai dai baida wani zaɓin daya wuce hakan saboda yanayin ƙasar tamu balle shi mai yawan maƙiya da masoya. Yasha tsallake tarko da aka shirya halaka rayuwarsa. Ana kusan ƙarshe ne da har ya samu harbi gab da shirin buɗe Companynsa na kano har aka harbesa, ALLAH dai ya taƙaita wahala harbin ya samesa a gefen kafaɗarsa ta hagu, daga nan ne Hayatu ya dage akan fitarsu da Guards ɗin. Tsaiwar motocin ya sashi kauda tunanin ya ɗago, ganin asibiti ya sashi ɗan kallon Hayatu daya buɗe masa ƙofa. Murmushi Hayatun yayi yana duƙar da kai da sosa ƙeya. Komai baice masa ba face ɗan girgiza kansa kawai ya zuro ƙafafunsa ya fito. Ciki suka nufa batare da ya lura da motocin su Paah ba, amma shi Hayatu sarai ya gansu dan tsakanin isowar tasu da tasu ma ƴan mintuna ne.........✍️ To Masha ALLAH. Barkan mu da dawowa, ku tayani addu'ar dagewa na gama book ɗin nan kafin salla😀🥰 _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓_ _______ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ____________ ......A ɓangaren su Paah kuwa isowarsu kenan asibitin suma. Ba kuma su san da su Maash a bayansu ba. Kai tsaye suka nufi cikin ɗakin bisa rakkiyar Mama Balki da sukai kira a waya. A tsorace cikin damuwa ta musu jagora dan bata san dami suka zo ba. Sai dai babu yanda zatayi dole tabi umarninsu. Sauƙin ma taga akwai Baba prof a tare da su. Sun shigo Samraah na zaune a kan gadon jingine da filo tana shan tea ɗin da Mama Balki ta haɗa mata a hankali. Fes take dan har tayi wanka saboda gashin ruwan zafi da Mama Balki tai mata bisa umarnin likitan. A hankali ta ɗago ta kallesu. Sai da zucuyata ta motsa da ganin waɗanda banyi zato ba. Idanuna na maida na rissinar ina ƙoƙarin haɗiye mamakina da ƴar tsorata. Sai da suka gama zama a inda Mama Balki ta nuna musu sannan na gaishesu cikin muryata da sam bata fita saboda kukan da naci na kwana da yinin jiya. Wasu sun amsa wasu basu amsa ba. Ni kuma sai banji damuwar komai ba tunda nasan dama ba lallai duk su amsa ɗin ba. Kasa cigaba da shan tea ɗin nayi ban kuma ɗago na kalla kowa ba a cikinsu, suma kuma babu wanda ya sake yin magana. Dai-dai nan aka ɗan sake knocking ƙofar. Mama Balki ta zabura domin buɗewa. Jin yanda take jaddada kalmar sannunku da zuwa cikin jin daɗi ya sani ɗan ɗago idanuna na kalla ƙofar. Tamkar abin shiri sai karaf suka faɗa a cikin nasa. Wani irin ɗan jan nasan yayi yuuuu zai lumshe nai saurin fara ɗauke nawa da maida kaina na duƙar. Sai kuma naji duk zaman yama gundireni, ga wani bugawa da zuciyata keyi dan harga ALLAH ko ganinsa tsoronsa yake ƙara min, ni kaɗai nasan kalar masifar dana gani a daren shekaran jiya hannun mutumin nan, dan haka ko matsoraciya kika kirani a wannan gaɓar Bily ni bazan damu ba. Kofin tea ɗin na ajiye a side drawer ɗin gadon na zame a hankali na kwanta tare da lumshe idanuna. Ƙasa-ƙasa na tsinkayi wata muryar dattijo da kamar na taɓa jinta na masa magana. Banji amsar daya bashi ba kasancewar shi dama idan zai yi magana sai in yaso kowa ya jisa ne. Ya ringa yinta acan ƙasan maƙoshi kamar mai jin haushin mutane. Kaɗan nai ƙoƙarin buɗe idanuna dan ina son ganin mai muryar nan sai naga ya nufo inda nake gadan-gadan. Sai da zuciyata ta sake harbawa. Babu shiri na maida idanun nawa na lumshe. A bazata, matuƙar bazata naji alamun rankwafowar mutum da mayataccen ƙamshin turarensa da saukar numfashinsa akan fuskata. Ai babu shiri na ware idanuna. Shi ɗin ne kuwa, gaba ɗayansa yamun rumfa hannayensa duka biyu ajiye a saman gadon ta gefe da gefena. (Kambu! Anya mutumin nan nada kunya?) Na faɗa a zuciyata ina waro gaba ɗaya idanuna waje. Amma shi sai ya wani kaɗa min cat ɗin nasa da ɗage gira hankali kwance. Tuni ƙwalla sun cika min ido, cikin marairaicewa na shiga motsa lips ɗina zanyi magana. Sai kawai naji saukar yatsarsa a saman bakin nawa, idanunsa cikin nawa, cikin salon lumshe idanu da maida muryarsa low sosai ya ce, “Shiii!! Bana son surutu”. Kunya takaici suka lulluɓeni a lokaci ɗaya. Gefe na kauda kaina tare da ture yatsansa daga saman lips ɗina, dan kalmar baya son surutun faifan taswirar daren shekaran jiya ta dawo min da shi fes. Hannun ya saka ya taro fuskar tawa ya maidota inda take. Baki na tura masa, ina son na hararesa amma shakkarsa da kwarjininsa sunyi masifar min ɗaurin goro, ga mayataccen ƙamshinsa dake tsarga min zuciya. “Bakin nan yana buƙatar wani abu ne halan?” ya faɗa cikin soft voice yana ƙoƙarin maida yatsarsa a saman lips ɗin nawa. Hannu na na kai da sauri na rufe bakin ina zaro idanu, amma shi ko gezau zama ka iya rantsewa ba shine ke maganar ba. Hankalina sake tashi yayi na saci kallon inda ƴan gidansu suke. Duk suna nan a ɗakin har Mama Balki ma. Tamkar zan fasa ihu idanuna cike da ƙwalla na ce, “Duk suna kallonmu fa”. Ƙoƙarin juyawa yay zai kallesu, ai bamma san na kai hannuna ba da sauri kan fuskar tasa na dawo da shi. “What? kuma. Bakin ce na faɗa musu ne su fita kina son mijinki ya ɗanyi kissing ɗinki ba”. Ya faɗa cikin salon kashe ido da ɗan ɗage gira sama murya can ƙasa kamar mai raɗa yana ɗora hannunsa kan nawa da nake ƙoƙarin janyewa daga fuskar sa. Harararsa na ɗan yi hawaye na cika min ido na ce, “ALLAH ya kiyaye ni yaushe na ce hakan? Kuma ni ba ƴar iska bace”. “Oh really”. Ya faɗa cikin ɗage gira sama yana ɗan taɓe baki kaɗan da sake matso da fuskarsa daf da tawan. Wani irin bugawa zuciyata ta shiga yi da sauri-sauri tamkar zata faso ƙirjina ta fito. A hankali na fara jin saukar iska da ƙamshin mouth freshener mai ƙamshin strawbarry. Luff nayi zuciyata na sauka a hankali daga bugawar da take da motse-motse a cikin ƙirjina, harda tura baki batare dana sani ba. Ɗal ya ɗalle lips ɗin da yatsunsa murya can ƙasa ya furta “I'm not interested maida bakin”. Cikin sauri na buɗe idanuna wani irin tuƙuƙi na turnuƙe min zuciya da takaicinsa. Dai-dai nan yake ɗagawa da ga duƙowan yana wani yin fuuuu da idanun nasa. Jinai kawai hawayen da nake riƙewa sun wani irin silalowa a hankali... Maash kam da ya ɗago kallo ɗaya yayma kowa na ɗakin ya ɗauke kansa tamkar baiga irin kallon da duk suke masa ba na tsantsar mamaki da tu'ajjibi. A zafafe Hajiya Mammah ta yunƙura zatayi magana Baba prof ya girgiza mata kai alamar kar tace komai ba. Badan taso ba tai shiru, sai dai kallo ɗaya zaka mata ka fahimci yanda ta gama cika tai famm. Duk abinda ke faruwa hankalinsa na kansu ta wutsiyar ido, amma yay tamkar hankalin nasa akan file ɗinta daya ɗauka yake dubawa. Dai-dai nan likitar da ke dubata ta shigo ɗakin Nurse biye da ita. Ita ta fara gaishesu, dan duk inda akaga Family ɗinsu ana gurmamasu saboda Maash ɗin. Sai da suka gama gaisawar sannan shi da bai ko kalleta ba ya ɗago shanyayun cat idanunsa ya ɗan kalleta, sai kuma ya kauda kansa cikin dakewar nan tasa ya mika mata takardar daya zare jiya a cikin file ɗin ya miƙa mata. Amsa tayi cikin mamaki, sai kuma ta kalla takardar. Ɗagowa tai cikin rashin damuwa, sai ma gani da take ai tayi abin arziƙi dan haka baki a washe ta ce, “Sir komai da ya kamata mun rubuta kamar yanda binciken mu ya bamu akan fyaɗen, dan a yanzu haka ma muna muku albishir ɗin samar da ƙwararriyar lawyer da zata tsaya mata akan case ɗin. Yau kuma zan kai report ɗin ma police dama izininku kawai nake jira kasancewar ita Hajiya tace ba huruminta bane sai kai yayanta kazo. Amma gaskiya sir ina ƙara bada shawaran kowa ya aikata irin wannan zalincin ga baiwar ALLAHr nan shima ya ɗanɗana kuɗarsa. Dan ALLAH ne kawai ya taƙaita al'amarin da zata ma iya kamuwa da matsalar yoyon fitsari. A yanzu haka ma dole tana buƙatar kulawa sosai saboda ɗinkin dake jikinta abin sam babu daɗi, dan ban taɓa ganin case ɗin fyaɗe na tsagwaron zalunci irin wannan ba. Banama jin mutum ɗaya ne ya aikata abi.....” “Ina buƙatar sallama by now”. Ya faɗa cikin katseta da yanayin da kowa ya kasa fassarawa daga garesa. Sororo likitar tayi tana kallonsa. Sai kuma ta ɗan marairaice fuska cikin nuna damuwa ta ce, “Sir ko akwai wani kuskure da mukayi ne anan ɗin? Wlhy duk kulawar da kake buƙata muna kan bata ita yanda ta kamata. Yanzu fa nake maka bayanin har lawyer ƙwararriya mun samar akan case ɗin”. Komai baice ba, sai ma ɗauke kansa da yay cikin nuna ƙosawa da maganar tata. Da yaga bata da alamar fahimtar shirun yake buƙata sai kawai ya nufi gadon da Samraah take cikin takun ƙasaita da bajinta hannayensa duka zube a aljihu. Duk abinda ke faruwa ina jinsu, dan haka zuciyata ke wani irin gudu raina fal mamakinsa. Guy ɗin nan he is stubborn mutum wlhy. Rayuwarsa har mamaki take matuƙar bani, mutum kamar wani dutsi baka taɓa iya gane gabansa da bayansa. Cak ɗin da aka ɗagani ya dawo dani hayyacina, sosai na zazzaro idanuna waje cikin matuƙar mamaki da ruɗani, rawa lips ɗina suka kamayi. Da ƙyar na iya haɗa kalmar, “Mi...miye haka kake yi?”. Ko kallona bai yi ba, sai ma takawa daya fara a hankali babu wani alamar jin shi yayi ba dai-dai ba ya bi ta tsakkiyarsu ya fice. Nikam ai sai naji bazan iya jurewa ba kawai na cusa kaina cikin ƙirjinsa tare da saƙalo duka hannayena ta wuyansa na saki kukan da ban san dalilin yinsa ba........✍️ _Ehem ehem Yayanmu ikon ALLAH, na Samraah bada kanka a sare kace ma su baba prof ya faɗi🤣🤣🤣_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒗𝒆_ .......Da sauri Hayatu dake tsaye daga bakin ƙofa yaja da baya kansa a ƙasa yana ƙoƙarin ƙumshe dariyar dake neman kufce masa. Isowarsa dai-dai saitinsa ya sashi haɗiye dariyar da ƙyar ya buɗe masa ƙofar da sauri yana ƙoƙarin matsawa. “Kuzo da kayan”. Ya faɗa a hankali dai-dai yana ficewa gaba ɗaya daga ɗakin. “A lallai Mu'azz ka haifoma kanka jaraba wlhy.” Hajiya Mammah ta faɗa cikin tafa hannaye da riƙe haɓa. Babu wanda ya iya cewa da ita komai dan duk abin faɗar ya gudu musu a bakuna. Sai ma Baba prof ne daya motsa a hankali kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki yabi bayansa. Dole duk suma sauran duk suka motsa suka take masa baya. Sai da suka gama fita Hayatu ya ƙarasa gaban doctor ɗin. Kallon Mama Balki yay yayi murmushi. Itama sai ta murmusa tare da nufar kayayyakin su kawai ta shiga haɗawa. Doctor data gama shiga cikin ɓacin rai kallon Hayatu tayi zatai magana. Da sauri ya katseta da faɗin, “Doctor kiyi haƙuri kawai ki bada takardar sallamar nan. Dan wlhy boss da kike gani baya magana biyu. Tunda ya yanke hukunci ya yanku, ya kuma fiki sanin muhimmancin wannan patient ɗin taki”. Cikin ɗan ɓacin rai ta ce, “Wane muhimmancin ta ya sani anan?. Ana gaya masa haɗarin da yarinya ke a ciki saboda zaluncin da akai mata yana nuna kamar ma baya fahimta. Ni ban taɓa sanin guy ɗin nan stubborn bane sai yau. Idan ma ɗakin ne bai masa ba way not yay magana sai a canja mata da wani”. Murmushi kawai Hayatu yayi dan ya fahimci bafa zata fahimta ba. Itama sai ta fita rai a ɓace tana mita dan gani gake shima Hayatun neman raina mata hankali yake yi. Binta kuwa yayi bayan ya amshi kayan da Mama Balki ta haɗa suka fito tare. Yana zuwa office ɗin doctor ta miƙo masa takardar sallamar a harzuƙe. Komai baice mata ba ya ɗauka ya juya abinsa ya fito. Samunsu yay suna shiga mota, dan shi gogan nasa ma har ya shige abinsa. Gaba ya buɗe ma mama Balki ta gefen sa ta zauna, shima yana ƙoƙarin shiga Baba prof ya ƙaraso wajen, umarni ya bama Mama Bilki kan ta fito ta koma motarsa, shi kuma ya shiga gaban ya zauna yana bama Hayatu umarnin suje *_KARAMCI HOSPITAL_* asibitin Hajiya ƙarama kenan. Amsawa Hayatu yay yana satar kallon Maash dake a baya tare da Samraah ta cikin mirror. Jingine kansa yake da kujera idanunsa a lumshe tamkar bai san mike faruwa ba. Shi kuma ya tabbatar duk yana jinsu. Kallo ɗaya yay ma Samraah dake kwance kanta a saman cinyar Maash ɗin itama idanunta a rufe ya ɗauke kansa yana ɗan sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya...... 🌿❤️‍🔥🌿❤️‍🔥🌿 Hajiya Sakeena na kai ƙarshen bayaninta Mansoor ya fasa wata gigitacciyar ƙara da ɗaga Centre table ɗin gabansu ya wancakalar. Babu wanda bai firgita ba. Ƙafa yasa ya bugi table ɗin da masifar ƙarfi, badan takalmin dake a ƙafarsa ba babu abinda zai hanashi jin ciwo. Da sauri Attahir ya miƙe yana ƙoƙarin riƙo hannunsa da kiran sunansa. Amma sai shima yay wani irin wancakalar da shi gefe har sai da Attahir ɗin ya zube a kujera. Cikin zafin zuciya da basu taɓa sanin yana da ita ba ya nuna Hajiya Sakeena da Mamynsa da take wani irin kuka tamkar ranta zai fita. Cikin kaushin murya da rufewar idon da fushi ya haifar masa ya ce, “Na tsane ku. Ku biyun nan ba bana son sake ganinku a rayuwata har abada. Kuma yanda kuka zama sanadin rabani da ita kuma na barku har abada!!!!!!”. Daga haka ya figi bag ɗinsa fuuuu zai fice. Ƙoƙarin miƙewa Attahir yay cikin ƙarfin hali yana kiran sunansa. Yayinda Mamy tai wani irin fashewa da kuka ta bisa da gudu ta riƙo rigarsa. Ko juyowa ma baiyi ba yasa hannu ya kaɓe natan tare da hankiɗata yay ficewarsa. Kafin ta miƙe tabi bayansa tuni yama fice a gidan ko mai kama da shi babu a compaund. Nan ɗin ma fita Attahir yay a guje, sai dai yana fitowa napep ɗin data ɗauki Mansoor na barin ƙofar gidan. Komawa yay cikin gida da gudu bawan ALLAH duk ya ruɗe. Dan key ɗin mota yake lalube amma ya gagara ganin ko guda ɗaya. Haka ya sake fitowa da gudu ya fita shima ya tare napep ya shiga suka bi bayan Mansoor. Amma ko mai kama da shi basu gani ba. Har airport yasa suka bishi a tunaninsa can zaiyi. Sai dai nan ɗin ma babu alamar Mansoor ɗin. Abinda bai sani ba kuma Mansoor bai je airport ba, dan ya fahimci abu na farko da zasu farayi kenan dan haka yaje ya kama hotel anan anguwarsu da yasan bazasu taɓa tunanin zai tsaya anan ba. Na kwana ɗaya ya kama, dan daga yau zuwa gobe yake son sake barin ƙasar nan. Sam bazai iya zama ba. Gara yayi nesa nesa can inda bazai sake ganin kowa ba a cikinsu har ƙarshen rayuwarsa... Duk wannan budiri da ake Dad bai ko motsa ba. Yana zaune ne kawai kamar saƙago a falon. Ba haka Hajiya Sakeena taso ba. Taso ace tana gama bada labarin nan yanda Mansoor ya fusata shima Dad ya fusata ya dinga ɗirkar Mamy da jera mata kalmomin saki uku sannan yace ta bar masa gida. Amma ba komai, ko yanzu ma ai tasan ƙurar bawai ta ƙare bane ba. Dan ita shaidace akan zuciyar Dad tamkar akku kuturu yake. Kusan zuciyar tasa ce ma yau Mansoor ya kwatanta. Shi kansa shirun da yayi ta tabbatar zuciyar ce ta kume ƴan maza wayaga kutu-ban-ban. Haka ta fito babu tausayi babu imani ta tsallake Mom da nunfashi ke neman ƙwacewa tai ficewarta. Acewarta ai itama haka Mansoor ya tsallake tata ɗiyar ɗaya kwallin kwal a duniya ya tafi babu tausayi balle imani bayan ya gama zana mata kalaman saki uku da gasa mata magana iya son ransa... Duk neman daya dace Attahir yayi ma Mansoor amma bai gansa ba. Dole ya haƙura cikin maɗaukakin tashin hankali ya koma gida ransa duk a dagule. Yana zuwa kuma ya iske Mamy a sume a farkon shiga falo. Tashi hankalinsa ya sake yi, dan ga Dad zaune tamkar saƙagon gunki zuciya ya kumesa tamkar shima ɗin ya suma. Baima san ya sunkuci Mamy yay waje ba cikin tashin hankali yana kwala kiran sunan drivernsu..... 🪴🪴🪴🪴🪴 *_KARAMCI HOSPITAL_* asibiti ne da zamu iya kiransa tsaka tsaki a girma. Dan bai kasance ƙaton gaske ba, bai kuma kasance ƙarami ba. A ɓangaren kayan aiki komai an wadatashi da shi. Duk da sunansa asibitin kuɗi ana aiki a cikinsa tamkar ƙyauta ne saboda sauƙi da sauƙaƙama al'umma. Hakan yasa mafi yawan talakawa suke saurin garzayowa jiyya da karɓar magani a cikinsa. Sai dai da yake komai nasu a tsare yake bazaka taɓa samunsa barkatai ba komansu a tsare yake. Kamar dai yanzu daya kasance rana ta fara ɗagawa, tako ina tsaftace yake sai ma'aikata dake ɗan kai kawo. Sannan shiru yake babu wata hayaniya ko yawan kai-kawon mutane bayan ma'aikatan saboda dokarsu ce irin yanzu ba'a zuwa duba mara lafiya sai yamma daga huɗu zuwa shida. Koda motocin su Maash suka iso ma da farko securitys ɗin ƙin tashi sukayi su buɗe saboda dokarsu ce ba'a ganin mara lafiya da dare ko safiya zuwa kafin cikar huɗu ko kai wanene, sai da Hayatu yay kiran number Hajiya ƙarama sannan securitys ɗin suka tashi cikin rawar jiki suka wangale gate ɗin. Suna gama parking Tsaki Hajiya Mammah tayi tana mita harda zagin Hajiya Ƙarama lokacin da take fitowa. Babu dai wanda yace da ita komai. Hajiya ƙarama da kanta ta fito tana musu barka da zuwa dan ita tunda safe tana anan asibiti batama san sunje duba Samraah ɗin ba, ana gama case ɗin human right ta baro gidan. Cikin girmamawa ta gaida Baba prof.. ya amsa mata tare da mata bayanin maido Samraah da sukai nan dan a cigaba da kulawa da ita duk da dai shi ba sunanta ya ambata ba ya dai ce yarinyar dake jiyya. Amma kuma yanata tunanin a ina yasan fuskar yarinyar ne tun ɗazun. Cike da girmamawa Hajiya ƙarama ta amsa musu. Tare da musu jagora har cikin manyan ɗakunan jiyyarsu na vip na ƙarshe a daraja. Kowa baiyi mamakin rashin biyosu da Maash yayi ba, dan sai da Baba prof ya koma da kansa ya masa umarnin bari a shiga da ita kasancewar tare ya tafi da nurses dake ɗauke da gadon ɗaukar mara lafiya. Amma mi, ammakinsu ma ko kallon inda Nurses ɗin suke baiyi ba yanzun ma ya sake ɗaukarta camak yay cikin asibitin. Da kallo kawai Baba prof ya bisa abubuwa da yawan gaske na masa kai-kawo. Dan a wannan gaɓar ya gama sarewa da al'amarin jikan nasa. Sai ma yake wasiwasi anya kuwa shine ya aikata fyaɗen nan kamar yanda Nafisa ta faɗa. Dan al'amarin akwai matuƙar ban al'ajabi a cikinsa da ma ban tsoro. Acan daga ciki suma kansu kallonsa kawai suke kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa musamman ma Hajiya ƙarama da bata ga abubuwan daya faru a farko ba sai wannan ɗin. Dan baki ta hangame har sai da taji iska na kai mata har maƙoshi sannan ta iya haɗiyewa da ƙyar.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙_ ......Baba prof da bai koma ciki ba Nurse ɗin nan ya aika yace a sanarma su Paah su fito yana jiransu. Babu jimawa kuwa sai gasu ɗaya bayan ɗaya. Hajiya Mammah da Mama Balki da Hayatu sai shi uban gayyar kawai aka bari. Dan haka Baba prof ya sake aika Uncle Abdullahi yace yay kiran Hajiya Mammah saboda sanin halinta shi kuma baya buƙatar jan wannan maganar a waje shiyyasa ma da Maash ɗin yace a bama yarinyar sallama bai tanka ba. Ya kumace a kawota nan ɗin ne tai jiyya dan yasan asirinsu zai kasance a rufe tunda dai Hajiya Ƙarama ta gida ce. Rai a ɓace Hajiya Mammah ta fito. Dan itafa gaba ɗaya an ɓata mata shirinta. Dan har magana ta gama da waccan likitar akan ta riƙe Samraah har sai nan da wasu ƴan kwanaki da za'a iya fahimtar da ciki ko babu. Idan akwai ta fallasa a gaban kowa, idan kuma babu zata biya ko nawa ne aima Samraah dashensa sai kowa ya gama sani sannan ta tafi plan na gaba da za'a zubar da cikin wajen zubarwar a kashe Samraah. Sai kuma gashi cikin abinda bai wuce awa guda ba shegen yaron nan daya zame mata masifa da bala'i ya hanama rayuwarta rawar gaban hantsi tun yana mitsitsinsa ya rushe komai. Suma waɗan nan ƴan human right ɗin sai taci abu takazansu dan sun mata aiki ba'a yanda tace musu ba. Idan kuma basuyi himmar ƙarasawa ba ALLAH sai sun biyata maƙudan kuɗinta... A ɓangaren Maash kuwa bai bar asibitin ba sai da aka gama yima Samraah dukan abinda ya dace. Duba magungunanta da sake bincikata in and out. Sai dai kuma anan ɗin ma dai doctor ɗin data duba Samraah ɗin dan ba Hajiya ƙarama bace saboda ba faninta bane. Abinda ta fara bincike da tambaya shine reping ɗinta akayi ne?. Shiru Maash bai tanka ba, bai kuma da alamar tankawar. Dan haka Mama Balki ta girgiza mata kai alamar a'a. Rasa abin cewa tayi, dan dukkan alamu na jikin Samraah ya tabbatar da anje mata babu tausayi. Amma tunda ita Mama Balki tace ba haka bane sai ta tambayi mijinta, acewarta tana son ganinsa taji dalilinsa na nuna irin wannan rashin tausayi akan yarinya ƙarama. Kasa sake cewa komai Mama Balki tayi, sai ɗan satar kallon Maash ɗin da take ta gefen ido. Shi kuma yay masifar haɗe girar sama data ƙasa dan haka doctor ta haɗiye maganganunta a cikin rai dole. Ruwa tasa aka sakama Samraah dan tana buƙatarsa. Kasancewar akwai cannula ɗin wancan asibitin da ba'a cire ba sai hakan ya sauƙaƙa musu. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa barcin ya fara ɗaukarta dan shi dama suke buƙata tayin. Kiran wayar da Paah ya addabesa da shi ya sashi miƙewa cikin ɗan ɓacin rai sai dai bai ce komai ba bai kuma ɗaga wayar ba. Ƙofa ya nufa abinsa batare da yayima ko Mama Balki sallama ba. Dishi-dishi nake ɗan hangosa, cikin mayen barcin dake ɗaukata a hankali batare da tunanin zai ma jini ba na furta, “Dan ALLAH ka dinga duba min Ummie akai-akai da bata abinci da maganinta. Kace kuma ina gaishet....” Cak ya tsaya daga yunƙurin fitar da yake yi, hannayensa duka a cikin aljihun wandon suit ɗin nasa. Tamkar mai ciwon wuya ya juyo da kansa a hankali ya zuba su a kanta. Idanunta masu cikar gashi dake a ɗan kumbure har yanzu a lumshe suke. Kallon kusan minti ɗaya yay mata ciff kafin ya motsa a hankali cikin tafiyar nan tasa tamkar baya so ya fice. Da kallo Mama Balki ta bisa, sai kuma ta saki murmushin da har haƙoranta suka bayyana. A hankali ta furta, “Humm Alhaji Ƙarami”. Sai kuma ta juya ta zubama Samraah da har ta fara sauke munshari idanun nata. Shigowar Hayatu ne ya katseta. Sallama yay mata dan yasan ba lallai yau ya samu damar sake shigowa asibitin ba tunda suna tare da boss. Gashi ma acan office jiransu ake sakamakon meeting da yasa Juliet ta tara na gaba ɗaya exco ɗin companynsa na cikin Lagos dama wajen Lagos masu alaƙa da abinda ya faru. Ya kuma tabbatar dole meeting ɗin zai jasu lokaci mai tsayi.... 🌺🌺🌺🌺🌺 “Magana ta gaskiya sai kun kula Attahir. Kun fa san Hajiya nada hawan jini. Yanzu badan ALLAH ya taƙaita ba a wannan faɗuwar da tayi fa komai zai iya faruwa. Dan ɗayan biyu ne. Paralysis ko heart attack. Saboda a kwanakin nan bincikenmu ya nuna zuciyarta na samun matsi sosai da yawan damuwa. Dan haka dan ALLAH ku kula. Zamu riƙeta anan zuwa 2days, ga wannan sai kaje konan pharmacy na asibiti ka samo dan data farka za'a buƙacesu”. Numfashi mai nauyi Attahir ya sauke tare da jinjina kansa. Kafin a hankali ya ɗaura da yima doctor ɗin godiya sannan ya miƙe. Tafiya kawai yake amma shi baima san a inda yake jefa ƙafa ba. Dan shi a karan kansa yana buƙatar gadon ne a wannan gaɓar. Da ƙyar ya iya kai kansa pharmacy ɗin cikin asibitin ya miƙa musu takardar da doctor ɗin ya bashi kawai. Koda pharmacist ɗin ya duba ya sanar masa kuɗin baima bi takansa ba ya zaro ATM ɗin sa a wallet kawai ya miƙa masa. Hakama da aka saka adadin kuɗin bai wani dubaba ya amsa ya saka pin ɗinsa. Ledar ya amsa ya koma ɗakin da aka kwantar da Mamy. Har dare yay nisa babu Dad babu Mansoor. Babu kuma wanda ya kirashi koda sau ɗaya yaji yaya Mamyn take. Haka ya kwana cikin asibitin shi kaɗai, sai a washe gari bayan sallar asuba yana fitowa a massalaci fita yay a asibitin dan likita ya tabbatar masa Mamy zata iya kai sha ɗaya ma bata farka ba. Kai tsaye gidan ƙaninsa na ɓangaren Ummie ya nufa. Kakarsu mace ta rasu, sai tsoho mai ran ƙarfe da ya ragema Ummie kawai. Bai tsaya kwana-kwana ba ya zayyane masa komai dake faruwa. Sosai hankalin kakan nasa ya tashi, Attahiru na gabansa ya shiga bugama sauran ƴaƴansa waya duk yace suzo yana buƙatar ganinsu. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa duk sai gasu, ALLAH ya taimaka ma abin ya haɗa da weekend. Sake saka Attahir yay ya maimaita duk abinda ya faɗa masa. Suma ransu yay matuƙar ɓaci da wannan hali na ƴar uwarsu. Tun tana budurwa sunyi matuƙar yaƙi na ganin ta ajiye waɗan nan banzan halayen amma a banza. Kullum shari'arta da miji bata wuce akan wannan halin na son kuɗi da ƙarya. Gashi nan dai sai da takai ta watsa farin cikin gidanta da kai wa matsayar da suka dinga guje mata sannan hankalinta ya kwanta. Itama autar tasu Sakeena zama da gurɓataccen miji ashe ya canja musu ita ta koma irinta. Ɗunguma sukai su duka harda tsoho zuwa asibiti suka dubata. Sunko samu ta farka, haka duk suka jajanta mata sama-sama. Gaba ɗaya kunya ta hanata iya kallon kowa a cikinsu musamman ma Attahiru. Nauyin yaron take ji, dan yanada matuƙar haƙuri da kawaici. Duk irin banbancin da take nunawa tsakaninsa da ɗan uwansa bai taɓa ɗauka ya sakama ransa balle har taga ɓacin ran hakan akan koda fuskarsa ce. Yau ga wanda take matuƙar nunama soyayyar ya tsallaketa ya wuce akan mace. Duk da dai tasan ita duk ta jawo komai, sosai take jin dana sani da nadamar ƙwaɗayayyar rayuwarta a yau. Kwananta biyu a asibiti babu ko ƙyallin Dad. Tana son ta tambayi Attahir tana jin tsoron jin abinda bashi zuciyarta take son ji ɗin ba. Dan tana matuƙar so da ƙaunar mijinta. Hasalima kamanninsa da Mansoor ya ɗebo yasa take fifita soyayyarsa akan sauran yaranta. A ranar aka basu sallama. Tun da suka baro asibiti taga an ɗauki hanyar gidan babanta gabanta ke faman faɗuwa. Sai dai tsoro ya hanata tambaya har suka iso. Isowarsu babu jimawa suma su Amal suka iso. Dama suna Abuja gidan kawunsu ne. Sanda zasu wuce India su aka turasu can sai yau suke dawowa. Anan ɗin ma babu wanda yace mata komai har tsawon kwan biyu, abu ya dameta amma itama tsoron jin abinda bashi take son ji ba ya hanata iya tambaya. Zuwan Sakina biyu gidan babu mai tankama wani ita da ita. Su duka sun ɗauki zafi da juna tamkar ba ƴan uwa ba jini ɗaya. Hasalima a baya sun fi shiri da juna matuƙa, dan rayuwar ƴammatanci gaba ɗaya Sakeenar a gidanta tayita ma.. Attahir dai yakan zo da safe kullum kafin ya wuce aiki ya gaisheta. Hakama idan ya tashi sai yazo nan ya gaisheta sannan yake wuce gida. Kamar wasa a haka kwanaki suka dinga tafiya tana a gidansu. Ga baba ma sama-sama yake amsa mata gaisuwa. Baya shiga sabgarta baya kuma bata damar shiga tashi har gata da watanni biyu cif a gida. Su Amal ma tuni suka tattara kayansu suka gudu gida. Dan sunce bazasu iya zama gidan Baba ba saboda gidansu komai najin daɗin rayuwa suna da shi. Nan ko duk da ƴaƴan baban maza sun tsaya akan al'amuransa shima kasancewar matarsa ba itace kakarsu ba abubuwa da yawa sai a hankali kawai. Ta kankane komai daga ita sai nata jikokin Mamy ma sai tayi da gaske wataran take samun abinci a gidan. Dan ma Attahir baya gajiya da kawo mata kayan shayi da ƴan kayan maƙulashe. Amma itama da tuni yunwa ta kai rayuwarta ƙasa kam.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ........Tun fitarsu a ɗakin jiyyar yarinyar har barinsu asibitin akan idanunta ne. Numfashi ta sauke mai nauyi tare da ture ɗan kwalin kanta baya. Dauriya kawai take da danne abinda ke matuƙar cimata zuciya. Wayarta ta ɗauka a ɗan zafafe, tai ƴan danne-danne tare da kaiwa kunnenta. Ana ɗagawa daga can ta ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai kuma cikin ɗan farin ciki mai gauraye da sauran damuwa ta furta, “Sabon labari”. Cike da zumuɗi daga can akace mata “Name fa Hajjaju masu Lagos da kayan cikinta.” “Hummm Jannifer bar batun wasa Please. Yarinyar nan ce fa suka maido asibitin nan yanzu”. “What! Kina nufin Samraah?”. “Yess. Yanzu haka tana nan tare damu. Ban san miya faru ba suka maidota nan ɗin. Naga dai mutuniyarki a zafafe cikin matuƙar damuwa kuma. Yanzu kam na fara zargin akwai abinda take ƙullawa. Na kuma yi alkawarin sai na bincikosa a koma ina taje ta bizne shi”. “Karki wani damu Hajjaju wannan duk mai sauƙi ne. Ko ni nan na isheta. Har mi akai akayi Alaja Nafee kuma. Matar da bata iya komai ba sai da shawaran banzan Madan Rubayya ɗin nan. Ni dai kawai yanzu shawaran da zan baki kawai kiyi ƙoƙarin ki kula da yarinyar nan da ƙyau, tunda dama tun farko kayanki ce. Kin zauna sakaci ne Alaja Nafee ta nema ƙwacewa. Banzama irinta da ta ƙare a ƙarƙashin guzumomi irin su Rubayya. Dan bana raba ɗayan biyu shakkar Rubayya ɗinne ya hanata taya yarinyar kafin ke, tunda itama ai mayyar ce. Saboda haka kiyi amfani da wannan damar akan ita yarinyar kiyita banka mata maganin da zai fidda mata sha'awar namiji gaba ɗaya a ranta, ina tabbatar miki da kanta zata kawo miki kanta tana kukan ki mora albarkacin jikinta. Haba Alaja Lawusa kamar baku bane Lagos ɗin. Ni fatana ma idan zakije honeymoon da ita aje dani koda a ƴar riƙon handbag ce”. Dariya mai ƙayatarwa Hajiya ƙarama ta saki, tare da sake lume kanta a cikin kujera idanunta a lumshe tana siffanta cikakkiyar surar Samraah data jima tana birkita mata lissafinta. Dan tun randa Jannifer tayi kiranta ta sanar mata da zuwan yarinyar gidan matsayin gift da Mashi'a tai shirin kawoma Hajiya Babba dan ta kula da ita ta gama jin ƙaguwa da son ganin yarinyar. Saboda haka ta azalzali Paah suka dawo Nigeria washe gari badan ma sun kammala abinda ya kaisu ba. Koda suka iso tai ido biyu da Samraah sai da numfashina ya nema shiɗewa. Dan yarinyar irinsu ne ake kira da full option. Komai yaji yanda ya kamata. Sai dai kash abubuwa da dama sukai mata katanga da hakan, tayi ƙoƙarin riƙe kanta har zuwa sanda ta gama shiryawa sai kuma ga wannan abin ya faru da yay matuƙar ƙona mata rai, dan a yanzu haka ita kaɗai tasan irin kalar zafin yaron nan Awwab da take ji a rayuwarta. Wani irin kishi take ji tamkar ta kashe banza a wuce wajen dan son Samraah take na gaske. Har ma ta gama yankema kanta shawarar auran yarinyar zatayi ta ɗauketa daga Nigeria zuwa duk ƙasar da take so sai ta dinga kai mata ziyara.... “Alaja!”. Jannifer ta katse mata tunani. Firgigit ta dawo hayyacinta tana mai sauke nannauyan numfashi. Cike da basarwa taja ɗan sirrin tsaki da faɗin, “Sorry Jannifer na tafi wata sabgar ne kuma.” Dariya Jannifer ta ƙyalƙyale da shi daga can, cike da shaƙiyanci ta ce ko dai kin tafi tunanin kayan alatu ba”. Murmushi Hajiya Ƙarama tayi tana mai cije lips ɗinta. Kafin a hankali ta ce, “Ke dai Jannifer sheɗaniya ce wlhy. Lallai da ace bakiyi ridda daga musulimci zuwa kiristanci ba da ba ƙaramar sheɗaniyar matar hausawa musulma akayi ba. Amma yanzu mun bar musu, dan inba ma wanda ya sani ba taya zai taɓa yarda kin haɗa iri da fulani. Humm ALLAH dai ya jiƙan General. Ya tafi yabar baya da ƙura. Maybe da za'a shawarcesa a dawo da shi duniya yaga Munirra ɗinsa yanda ta koma kamar bata taɓa haɗa jini da yan arewa da musulunci ba da dakansa zai kashe kansa ma wlhy”. “Hummm Hajjaju kenan masu Lagos da jama'ar cikinsa. Ai duk nawa wasan yara ne. Idan kuna guri mu kuma wake ta tamu ƙananun ƙwari. Mufa a riddar kawai muka tsaya sai ɗan cinikin goron nan da muke kafawa a faifai da ɗan hutawar nan muna more ƙuruciya. Ku kuwa fa, idan akace ai tone-tone ai kema musulman sai sun gwammace riddar kikayi wlhy”. “Uhhm to ya isa. Dan ke baki gajiya da zakuɗe-zakuɗe. Yanzu dai sai anjima idan na tashi zan zo gida na sameki mu ƙarasa. Dan zan ɗan shiga theater”. “Hummm” kawai Jannifer tace daga can tare da yanke wayar tana dariya. Itama sai Hajiya ƙaramar tai dariyar kawai tana ƙoƙarin ajiye wayar, a dai-dai nan wani kiran ya sake shigo mata. Ido ta zubama number na tsawon lokaci, YALLAƁAI ɓaro-ɓaro ya fito. Mamaki ya sake kamata dan rabon da mai number yay kiranta ta jima sosai, dukan tara-tara ƙirjinta ya shiga hi har sai da wayar ta kusa yankewa ta dawo a hayyacinta. Da sauri ta ɗauka tana miƙewa ta nufi ƙofar office ɗin ta murza key cike da rashin gaskiya.... _🤔Hummm wai ina matan nan suka dosa ne? Sannan waye yay kiran Hajiya Ƙarama kuma? Idan na fahimta dai Hajiya Ƙarama na waya da Madam ne a farko, matar data ɗakko Samraah daga Abuja zuwa Lagos. Tab ɗin babbar magana. Ashe ita ɗin musulma ce shine tai ridda. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Anya wannan duniya kuwa. ALLAH mun tuba badan halinmu ba😭🙏._ __________________ *_THREE DAYS LATER_* Kwanaki uku kenan da faruwar komai. Sam Maash yaƙi yarda ya zauna da family ɗin nasa akan batun Samraah. Dan haka ran kowa a matuƙar ɓace yake. Amma shi ko'a jikinsa sai manna musu hauka kawai yake. Dan gaba ɗaya ma ya maida hankalinsa ne akan binciken yanda akai containers ɗin companyn sa suka ɗiba yara da wiwi saɓanin lodin kayan abinci. Dan suna shirin tunkarar Mr Paul ne da ƙarfinsu a court saboda sun shigar da ƙara ne kafin shi bisa shawarar lawyers ɗinsu. Ta gefe kuma ga jikin Ummie da ya rikice. Ga kuma Samraah dake asibiti har yanzu ba'a sallamota ba itama, sai dai wata irin kulawa take samu ta musamman da tattali a wajen Hajiya ƙarama har Mama Balki ta fara shan jinin jikinta. Sai dai abinda Mama Balki bata sani ba ita kanta Samraah nazartar Hajiya ƙarama take sannu a hankali. Gefe kuma tana kaima ALLAH kukanta. Koda labari Mama Balki bata sanar mata da ciwon Ummie ba sai yau da Falak tai kiran wayar Mama Balkin, a lokacin ita kuma ta ɗan fita dan haka Samraah ta ɗaga. Har yanzu basu taɓa haɗuwa da Falak ba sai dai tana cin abincin gidanta kullum. Bata da lafiya ne tana fama da tsohon ciki shiyyasa bata zo tama dubata ba, sai dai sun gaisa ta waya har kusan sau uku. Yanzun ma sun gaisa cike da kulawa ma juna tamkar dama can sun san junan nasu, kafin Samraah ta sanar mata Mama ta ɗan fita ne, amma idan ta dawo zata faɗa mata sai ta ƙara kira. Daga can Falak tai murmushi da faɗin, “Okay ba damuwa ALLAH ya ƙara lafiya, dama zanji ko yaya jikin Ummie ne dan na kira Yaya Hayat ashe garin sauri yama bar phone ɗin a gida, gashi yanda ya fita a hargitse duk na kasa nutsuwa”. Ɗan jimmm nayi zuciyata na bugawa da sauri-sauri jin ta ambaci Ummie, da ƙyar na iya tambayarta “Ummien Maash Mansion? Wani abu ne ya sameta?”. Batare data fahimci kan tambayar ba cikin damuwa muryarta na rawa ta ce, “Eh ita, kin san kwana biyun nan jikin nata duk babu daɗi, to yau dai da alama ya tsananta ne dan shima Yaya Hayat a rikice ya fita TJ ya kirashi. Wlhy ina tausayawa Ummie, da ace inada wata babbar dama akan baiwar ALLAHr nan abinda zan farayi shine tsayawa akan samun lafiyarta, amma muna gani an hanamu taimakonta. Wanda keda ƙarfin yin hakan kuma an kulle masa tunani gaba ɗaya, dan wlhy da ace Yaya Awwab basu shiga tsakaninsa da lafiyar baiwar ALLAHr nan ba da kowama yaci ubansa, ai sun san shi ɗin ba kanwar lasa bane har Baba prof ɗin da Paah ba iya tankwarashi suke ba. Amma ba komai ALLAH yana nan, watarana sai labari”. Tuni ma ni ba fahimtar zantukanta nake da ƙyau ba, rawa sosai jikina ke mun, ga hawaye suna bala'in gudu a saman fuskata. Ashe shiyyasa duk jiya bai zo asibitin ba, yau ma haka. Ko Hayatu mai ƙoƙarin zuwa sama da sau uku yana kawo musu abubuwa jiya sai dare ya shigo ya duba ta. Abinci ma TJ ne ke kawowa. Amma Maash tun daren shekaran jiya da zai tafi take cemasa ya dinga duba mata Ummie da bata abinci bai sake zuwa ba, harta ƙullacesa ma ita da, da tunanin ya gama cin moriyat ganga zai yada kwautrnta, ashe abinda ke faruwa kenan... “Ya subahanallah Samraah! Wani abu ke miki ciwo ne? Ko tashi kikayi da ƙarfi kika fama ciwon?”. Mama Balki ce mai maganar nan a rikice. Ɗagowa nayi ina kuka mai tsanani dan shashshekar da nake tasa har fisga numfashina keyi. Lallashina Mama Balki ta shiga yi tare da bani ruwa tace nasha. Da ƙyar na amsa nai maƙwarwa uku, jikinta ta jawoni ta rungume, hakan sai ya taimaka min wajen samun nutsuwa na fara sassauta kukan. Kaina na a saman cinyarta tana shafa gashina ta ce, “Samraah”. Cikin dasashjiyar muryata na amsa mata da, “Na'am Mama”. “Mike faruwa?”. Da ƙyar na iya danne kukan dake taho min na ce, “Mama Ummie. Ashe bata da lafiya amma shine babu wanda ya sanar min”. Iska ta ɗan furzar cikin damuwa. Kafin ta ce, “Waye ta faɗa miki?”. “Falak”. Na bata amsa ina sharce hawaye.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ___________ ......Kanta ta girgiza da faɗin, “Ni ban san sai yaushe bakin Falak zai iya dinga koyon shiru ba. Kiyi haƙuri an ɓoye miki ne saboda kema ga yanayin da kike ciki. Shekaran jiya ne Alhaji ƙarami ya shiga yana ƙoƙarin bata abinci shine fa kawai jikin ya rikice. Ta jimasa ciwo sosai a hannu da ƙyar aka iya fiddoshi a ɗakin, daga nan duk wanda ya shiga da duka take korosa, to yau kuma sai ta yanke jiki ta faɗi saboda kwana biyun nan bata ci bata sha rashin abinci jikinta yayi week. Amma ki kwantar da hankalinki zuwa yanzu sun ce Alhamdullah komai ya dai-daita. Dan Hayatu ma ya tabbatar min tana barci saboda drip ɗin da aketa ƙara mata.” Duk da na ɗan ji nutsuwa sai da na sake sharce hawaye, ɗan shiru mukayi kafin a hankali nace, “Mama”. Da kulawa ta amsa min da, “Na'am Samraah”. “Mama a yanzu sai nake ganin kamar shi yafi dacewa ma abinda ke tare da shi ya rabu da shi kafin a samu nutsuwar yima Ummie magani. Duk da dai wani abu ya jima yana damuna. Yanzu duk kuɗinsa ace gidan nan babu cctv camaras tako ina?”. “Tabbas gaskiya kika faɗa Samraah. Sai dai mun kwatanta hakan muma bai yiwu ba, a dalilin tsanar magani da Alhaji ƙarami yayi tun yana ƙaraminsa. Ko yaya ruwa ya surka wlhy bazai sha miki shi ba koda da kala ne. Shiyyasa yin maganinsa keda matuƙar wahala. Gashi kuma shi ba'a zaune yake ba waje ɗaya, duk yanda muka so fara bashi koda ruwan addu'a ne sai kiga abin ya zama shiririta. Ina da tabbacin kuma wanda ke wannan aikin kullum cikin sabuntashi suke bawai sun koma sun kwanta bane suma. Maganar camara kuwa ai Alhaji ƙarami yasha sakawa amma sai a wayi gari duk an ciresu. Har ɓoyayyar camara an saka a gidan nan amma kamar abin maita wlhy sai da aka cireta. Hakan na nufin koma su waye a biye suke, shiyyasa ma kikaga ina sake jin tsoron al'amarin gidan nan da mutanensa. Dan idan bana jikinka ba banga wanda zai dinga maka wannan bita da ƙullin ba a nesa da kai”. Baki na buɗe zanyi magana sai naji kamar amalar motsin tsayawar mutum a ƙofa. Shiru nayi bance komai ba, sai kuma kamar ance na ɗaga ido na hango inuwa ta jikin window. Magana Mama zatayi na wayance ina mai zame kaina da ga cinyarta na ce, “Mama barci nake ji. Dan ALLAH idan Nurse ɗin nan tazo kice bana son allurar nan ni nama warke karki bari tamun”. Kallon mamaki da naga Mama namun yasa nai mata nuni da window da ido. Tuni ta ɗauki haske kasancewar dama a ankare take. Itama sai ta wayance ta shiga ƴar dariya da faɗin, “Ja'ira ai allurar nan sai an kaita har ƙarshe, bari ma Hajiya tazo zance ta sake ƙara miki kwana biyu kiyi digir dake yanda zamu koma gida da ƙarfinki”. Shagwaɓa na shiga mata da faɗin ni bana so. Itako tana dariya. Daga haka mukayi shiru. Kwanciya nayi zuciyata na faman kai-kawo. Tabbas lokaci yayi fa dazan dawo hankalina. Dan na fahimci in har shi bai fita a halin da suke sanyashi ba baiwar ALLAHr nan bazata taɓa samun ingantaccen lafiya ba. Domin sauƙi yana samuwa a gareta, sai dai yanayin kwan-gaba kwan-baya da ake fuskanta yasa al'amarin ke taɓarɓarewa. Idan kuwa har za'a iya hana cctv camaras zama lafiya to lallai waɗan nan mutanen ba ƙaramin shiri sukai ba. Suma kuma suna buƙatar a shirya musu yanda ya kamata. Dan dole wayo al'amarin yake buƙata da hikima kamar yanda suma suke komai ta cikin basira”. Wannan tunane-tunanen da hawayen da suka kasa barin idanuna ne suka haifar min da zazzaɓi mai zafi, gashi naƙi gayama Mama har bayan sallar isha'i. Dan da ƙyar ma nayi alwala saboda sanyin da nake ji. Ina idarwa na haye gado na kwanta tare da duƙunƙunewa cikin bargo. Sosai na gaji da zaman asibitin nan, fatana kawai ALLAH yasa yazo dan shine kawai zaisa a sallameni. Yan gidansu dai dama babu wanda ya sake zuwa sai Hajiya ƙarama da nake gani, ita kam kullum ne sai ma tazo sama da sau uku, sai daga baya na fahimci ai dan asibitinta ne shiyyasa itama muke yawan ganintan..... 🩸🌟🩸 Sosai damuwar halin da Ummie ke ciki a kwana biyun nan yasa bai sake waiwayen asibitin ba. Duk da kuwa wani sashe na hankalinsa na'a can ɗin. Sai dai rashin isashen lafiya shima dana lokaci ta sashi baiyi wani yinƙuri ba. Yau kuma zafi da ƙuncin da gidan ya masa matuƙa ya sashi ɗan kimtsawa bayan ya dawo sallar isha'i. Tun la'asar ya kora Hayatu gida dan haka shi kaɗaine a sashen sai Laalah da TJ dake leƙowa akai-akai duba shi shi da Shu'aibu amintaccen guard ɗinsa. Tsaff ya fito yana zuba mayataccen ƙamshin nan nasa tamkar ba dare ba. Tj da Shu'aibu na ganinsa suka miƙe da sauri, hakama sauran ma'aikatan gidan sai gaisuwa suke miƙawa. Hannu kawai yake ɗaga musu dan kwana biyun nan miskilawan ne a kusa. Da ga shi sai TJ da Shu'aibu sukai fitar dan hana sauran guards ɗin binsu yayi. Tj ke driving Shu'aibu a gefensa. Shi kuma yana baya zaune idanunsa akan wayarsa yana daƙila. Kicin-kicin fuskar nan take babu alamar ya taɓa sanin minene ma dariya. Cike da girmamawa TJ ya ce, “Boss ina muka nufa?”. Shiru bashi da niyyar amsawa. Sai da ya mula dan kansa ya furta, “Hospital”. Cike da girmamawa TJ ɗin ya amsa masa tare da ɗaukar hanya. Har sun gota wani bakery yace TJ ɗin ya dakata. Tuna duk lokacin da zasu je asibitin tare da Hayatu sai ya sa an tsaya ya sayi wasu abubuwan ya sashi cewa a dakatan. Shima TJ ɗin tun bai furta ba ya fahimci abinda yake nufi tunda dai koda yaushe da shi ake zuwa asibitin shima. Fita yayi zuwa cikin bakery ɗin batare daya amshi wani kuɗi ba, dan boss ya wuce fiye da haka a wajensu ai. Bai wani jima ba ya fito ɗauke da ledoji masu ƙyau har guda uku. Booth ya buɗe ya sakasu sannan ya dawo cikin motar. Zuwa yanzu ba wayar yake daƙila ba kansa ya kwantar a jikin kujerar ya lumshe idanunsa. Koda suka iso ma sai da ya ja kusan mintuna biyu tamkar mai nazarin ta yanda zai shiga cikin asibitin sannan ya fito. Yana gaba cikin takun nan nashi na ƙasaita da isa su TJ na biye da shi. Babu yawaitar mutane har ma ma'aikatan jefi-jefi ne. Ko kallon wanda suke a reseption ɗin kuwa baiyi ba yayi wucewarsa. Sai su TJ ne suka gaishesu. Suko suka bishi da kallo tamkar wasu tsoffin mayu. Sai faman washe bakuna suke yau gasu ga Maash, mutumin da yafi kuɗi wahalar gani a Nigeria. Dama wasu a abokan aikinsu sun sanar musu da zuwansa a kwana biyun nan, sai dai su basu taɓa cin karo da shi ba sai yau ɗin... Har yanzu duƙunƙune nake a cikin bargo ina rawar sanyi dan zazzaɓi nake ji sosai. Ga hawayen damuwa da halin da Ummie ke ciki sun kasa tsayawa a idanuna. Ita mama Balki ta ɗauka nayi barci ne, dan haka ta maida hankalinta a kallon tv tana sauraren wa'azin malam Ali isa fantami da aka saka a African tv3. Knocking ƙofa da akayi a hankali kamar abin dole ya sata rage ƙarar tvn, shiru kamar baza'a sake ba sai kuma aka ƙara. Miƙewa tayi zuwa jikin ƙofar tana tambayar waye? Jin ba'a amsa ba ta buɗe. Ni dai duk ina jinsu amma da yake har kaina na'a cikin bargo ba ganin komai nake ba. Murnar da naji tana yi da ambaton sunan Alhaji Ƙarami ya sanya gabana faɗuwa. Sai ko ga mayataccen ƙamshinsa ya gama isowa har cikin hancina. Wasu muryoyi biyu naji suna gaisheta da tambayarta mai jiki. Na gane muryar driver ɗinsa. Ɗayan ne dai ban gane waye ba amma nasan ba hayatu bane ba. Sai da naji alamun fitarsu da rufe ƙofa sannan shima naji muryarsa a daƙilen nan can ƙasa-ƙasa kamar abin dole yana gaida Mama. Ita ko da kulawa take amsa masa da tambayarsa jikinsa da kuma na Ummie. Nan ɗin ma da ƙyar ya amsa itama yana tambayarta ya mai jiki. Itako da fara'a ta ce masa, “A jiki da sauƙi sosai. Yau ne ma ta so birkicewa saboda samun labarin jikin Ummie daya motsa da tayi. Dan har bayan sallar magriba ɗin nan tana shartar hawaye sai da na ɗan mata nasiha sannan tai shiru, inaga shine ma dalilin kwanciyar da wuri sai kuma barci ya ɗauke ta. Banji yace komai ba, sai dai haka kawai na dinga jin kaifin idanunsa a jikina. Shiru ɗakin na kusan minti ɗaya sai kuma naji ƙarar buɗe ƙofa da rufewa. A zatonta shine ya fita, dan haka cike da shagwaɓa na janye bargon daga saman fuskata zanyi magana da Mama. Zuuuu naji jinina na falfala uban gudu ta cikin jijiyoyina tsabar shock ɗin cin karo da abinda nai zaton shi ya fita. Da sauri na kauda kaina na sake maida fuskata cikin bargon. A bazata naji alamar an zauna a kusa da ni, Ji nai na sake daburcewa kamar zan fasa ihu, amma sai na dake tare da yin luff a cikin bargon ina addu'ar ALLAH yasa kada yace sai na buɗe kaina........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆_ ......Shiru ɗakin har na fara murna. Kusan mintuna uku muna a haka babu motsin komai sai naji yayi ɗan gyaran murya. Idanuna na sake rumtsewa da ƙarfi batare da na yarda na motsa ɗin ba dai. Sake yi yayi, nan ma naƙi na motsa, sai da yay ta uku sai kuma a hankali ya ɗaura da faɗin, “Dama Ummie c....” A zabure na yaye bargon gaba ɗayansa. Na ware dukan girman idanuna a kansa. Lips ɗina na rawa a marairaice na ce, “Ummie mi?”. Maimakon amsa min sai kafe cikin idanuna yayi da nasa cat eyes ɗin masu matuƙar girma da yalwar gashi. Wani irin tashi tsigar jikina tayi, sai kif-kif kawai nake faman yi da idanu. Sai faman kokawa nake da numfashina dake seizing. “Stubborn girl”. Nakasashiyar muryarsa ta daki cikin kunnena duk da kuwa cikin low voice yayi ta, badan ma idanuna na akansa ba babu yanda za'ai na jisa dan pinkish lips ɗinsa ne kawai suka motsa a hankali. Kamar wata sakarai na jujjuya masa kaina a hankali. Motsa lips ɗina dake ƴar rawa na shiga yi, da ƙyar na iya haɗa kalmar, “Mi ya sa mu Um mie?” a rarrabe ina rissinar da idanuna da suka ciko da hawaye. Dan duk yanda na ƙudirci masa tsiwa ko kallon cikin idanunsa nayi magana sai naji sam na gagara yin hakan. Mutum ne mai masifar kwar jini da cika wuri. ALLAH ya azurtashi da wani irin girma a gaban duk wanda ya tsaya koda ace ya fisa a shekaru da matsayi. Saukar tattausan tafin hannunasa saman fusakata ya sani sake ɗago idanu da sauri na kallesa. A cikin nashi cat idanun suka sake faɗawa. Kallon juna muke a wani irin yanayi har na tsawon shuɗewar wasu sakanni. Kafin a kasalance na motsa nawa dake tara ƙwallan da ban san na minene ba. Shi ko har a lokacin kallon nawa yake yi batare da ya ƙyafta ba, sai ma cikin wani irin soft voice and silent and slowly ya furta, “She is missing you, and she need you”. “I miss her too”. Na faɗa nima a hankalin ƙwallar data cika min idanu na gangarowa. Idanunsa ya sake ɗan lumshewa tare da buɗewa a lokaci guda ya cigaba da kallona ina kuka sosai harda shashsheka. Shi bai lallasheni ba, bai kuma janye hannunsa dake a kan fuskata ba har yanzu. Tsawon mintuna biyu ina kukana, dan shirunsa sake tunzurani yake. A bazata matuƙar bazata cikin low voice ɗin sa ya furta, “Samrh”. Cak na tsaya da kukan da nake, tare da ɗago jiƙaƙƙun idanuna na kallesa. Kallon nawa shima yake da shanyayun nashi da suka canja launi zuwa golden an blue. “Why are you crying?”. Ya sake faɗa muryarsa na sake komawa can ƙasan maƙoshi. Samun kaina nayi da sake sakar masa sabon kukan. Tare da riƙo hannunsa dake akan fuskata na ƙan ƙame. Idanunsa da suka gama canja launi kawai ya zuba mata. Sai Adams apple ɗinsa ne ke faman kaiwa da komawa a cikin maƙoshinsa. A hankali ya kai ɗayan hannunsa saman kafaɗarta, riƙota yayi tare da ɗagota gaba ɗayanta batare da ya janye hannun nasa data ƙanƙame ba sai da ya kaita gab da jikinsa sannan ya janye ya turata cikin jikin nashi gaba ɗayanta. Tsam ya rungumeta yana mai lumshe idanun nasa ƙam-ƙam shima saboda zafin da jikinta ya ɗauka duk da da akwai kaya a jikinsu su duka sai da ya bala'in ratsashi. Ni kam jina a jikin nasa ya sakani sake fashewa da kuka. A hankali na fara ɗan dukan bayansa ina faɗin, “Why! Why? Why? Suke wahalar da rayuwarta? Mita musu da zafi haka? Da ga ganinta She is an innocent and strong woman. Basu barta haka ba, sun rabata da ku jininta da zata ji sanyi a wajen ku. Natsane su, wlhy na tsanesu. I promise my self sai na ɗaukar mata fansa koda zasu maidani fiye da yanda suka mata. Sai na sakasu gudun ceton rai da babu mafaka Ya Awwab. I promise....” Kuka ya sake sarƙeta. Sai wani irin jan nunfashi take a sarƙe kamar mai ciwon asthma. Da sauri ya rabata da jikinsa, tare da kwantar da ita a kan cinyarsa. Sosai numfashin nata ke fisga, hannayensa ya saka duka biyu a kumatunta ya shiga ɗan bubbugawa da kiran sunanta. “Samrh! Samrh! Please keep calm. I know you can, please calm down. Hundred percent I am with you.” Ina da gaske ƙoƙarin ƙwacewa numfashin nata yake. Ai baima san ya figi bottle na ruwa dake a side drawer ba ya zuba a hannu ya shafa mata duk da kuwa tana numfashi, sai kuma yay saurin kai mata ruwa a baki amma bakin ya gama datsewa ruwan yaƙi shiga. Da sauri ya kai kan nasa bakin ya zuƙa, batare da wani tunani ba ya ranƙwafo kanta ya ɗaura lips ɗinsa a saman nata ya shiga juye mata ruwan tare da riƙe hancinta. Wani masifar jan nunfashi tayi ta baki sai gashi ta zuƙe ruwan gaba ɗaya. Hancin nata ya saki tare da janye bakinsa. Ita kuma ta fara tari sosai. Sake ɗagota yayi a hankali ya maidata jikinsa ya rungume suna sauke ajiyar zuciya a tare. Sunfi mintuna uku a haka sai da ya tabbatar zuciyarta ya gama sauka sannan ya raba jikinsu ya kwantar da ita a gadon a hankali... Kasa buɗe idanuna nayi, sai ajiyar zuciya kawai nake saukewa a jajjere. Jin saukar abu mai taushi da ƙamshi a saman fuskarta ya sani buɗe idanuna a hankali. Shine ke goge min hawaye da farin handkerchief ɗinsa tass. Idanunsa ya saka cikin nawa har ya gama. Batare da ya janye handkerchief ɗin ba da ɗan yanayin lumshe idanu da buɗewa ya furta, “Miyasa fitina baya miki wuya? Samrh! Ba'a gaggawa a al'amarin maƙiyi, idan ba haka ba zai fika gudu ne wajen cimma manufa. Lokacin da zaka isa sai ka samu shi har ya gama ya juyo. Be a gentle okay”. Sosai zantukan nasa suka shigeni tare da canja min wasu tunanina da yawa a kansa. Cikin suɓutar baki muryata a dusashe na furta, “Kana nufin kaima duk abinda ke faruwa kana sane?”. A bazata naga ya wani ɗan taɓe gefen small pinkish lips ɗinsa da lumshe idanunsa sannan ya saki murmushi. Bily idan nace miki kaɗan ya rage zuciyata ta ɓaro akan murmushin nan nasa da salon da yayisa ki yarda da ni kawai. Badan yafi kowa iyawa bane, sai dan murmushi ya kasance ba ɗabi'arsa bace. Amma tabbas magana ta gaskiya murmushin ya ɗebeni iya ɗiba. Dan kaɗan ya rage na fallasa ɓoyayyen al'amarin da na jima ina binnewa a kansa. (Kin sani a duhu mutuniyar, kodai kin jima kina son Maash ne?). “Hummm Bily kenan abar dai zancen sai lokacin yinsa yayi”. Na faɗa cikin ƴar dariya. (Lallai kam, to shike nan na bari muje zuwa labari). Yanda yay murmushin har ban san na kafesa da mayataccen kallo ba. Idanunsa ya ɗan waro min waje da ɗagesu alamar kallon fa?. Cikin sauri na kauda fuskata gaba ɗaya ina tura baki da faɗin, “Miye abin kallon ma anan”. Bai tanka min ba, sai ma ɗan kauda kansa da yay gefe. Banyi zaton jin shirunsa a wannan gaɓar ba. Amma nima dai sai na basar kawai tare da ture hannunsa na janye sauran jikina dake a nasa tare da jan bargo na juya masa baya. Dan in banyi hakan ba akwai babbar matsala, dan komai zai iya fitowa saboda yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri abinda ke can ƙasanta a ɓoye na azalzalota. Shiru ban sake jin motsinsa ba. Ban kuma yarda na kallesa ba har fin mintuna biyar. Sai a lokacin naji motsin buɗe ƙofa, ɗan juyawa nai kaɗan. Sauka idanuna sukayi akan bayansa dai-dai yana ƙarasa ficewa da jan ƙofar ya rufe a hankali. Nima lumshe idanuna nayi ina sauke ajiyar zuciya. Sai kuma na sake dunƙule jikina a cikin bargon dan ji nake kamar zazzaɓin na ƙaruwar min ma. Mintuna bai fi huɗu da wasu sakanni ba aka sake buɗe ƙofar, idanun na sake buɗewa a hankali. Yanzun kam Mama Balki ne da Doctor sai shi a ƙarshen shigowa. Hannayensa duka biyu a cikin aljihun baƙin wandonsa. Idanun na maida kawai na rufe, dan nasan bai wuce akan zazzaɓin jikina yaje yayo min wannan gayyar ba. 🩸🌟🌟🌟🩸 A hankali take faman kaiwa da komawa a cikin ɗakin nata kai kace safa da marwa take ko motsa jiki. Sai dai sam ba haka bane. Abubuwane masu yawa ke matuƙar damunta da cizar mata zuciya. Dan tun zaman da sukai da Yallaɓai ɗazun da magrib ta gagara samun sukuni. Gaba ɗaya taji ta kasa komawa asibitin da taci burin komawa dan akwai wani baƙo da zatai mai muhimmanci. Maganganunta da Yallaɓai ne suka shiga dawo mata dalla-dalla tamkar a yanzu suke tattauna su.... “Yaushe yarinyar nan tazo aiki gidanku? Waye kuma ya kawota?”. “Lokacin muna Dubai muma zuwa kawai mukai muka sameta anan. Amma ance Mashi'a ce ta kawota”. “Mashi'a?!”. “Yes ita fa. A cewarta kuma ta kawota ne as a birthday gift wa mahaukaciyar matar can. Tunda masu aikinta sun sake guduwa a lokacin babu mai kula da ita”. “A ina ta ɗakkota?”. Ɗan jimm tayi, sai kuma ta ce, “Gaskiya wannan ne ban sani ba”. Kasa sake cewa komai yayi, sai ma kai-kawo daya shiga yi hannayensa goye a bayansa..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒆𝒏_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ___________ .......Yayi kusan sau fin huɗu sannan ya dawo ya zauna. Cikin kaushin murya da dakewa ya furta, “Dole ne yarinyar nan ta mutu a asibitinki. Kuma a yau zuwa gobe nake buƙatar sanin daga inda ta fito? Miye dalilin Mashi'a na kawota?. Zaki cigaba da riƙeta har zuwa kwanaki uku da za'a gama min bincike na”. Idanu Hajiya Ƙarama ta zubama mutumin zuciyarta na gudu da sauri-sauri a ƙirjinta. Cikin ɗan rawar lips muryarta na seizing ta ce, “Amma yallaɓai hakan fa zai iya zama kuskure. Dan yarinyar nan gaba ɗaya komanta ya gama dai-daita raunin daya jimata ne kawai ya rage ya ƙarasa warkewa mu sallameta zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ko jibi. Sannan case ɗinta bama fa a hannuna yake ba doctor Larai ce ke kula da ita. Daɗin daɗawa Awwab. Yaron nan fa ya wuce duk inda kake zato da tsammanin sa kaima ka sani. Ni wlhy zuciyata ma ta fara bani kamar a ankare yake da abubuwa da yawa. Gashi sam baya jin tsoro ko shakkar kowa. Yanzu ka dubafa yarinyar mutane yama fyaɗe a cikin gidansu amma komansa bai canja ba face ma wani irin kulawa da yake bata ga girman kai sabo da yake ji da sam na gagara fassara al'amarin nasu”. “Mtsooww Lawusa, ke kin san dai idan na faɗi magana ko zartar da hukunci bana canjawa ko? Dukan waɗan nan hujjojin naki basa gabana. Gawar yarinyar nan kawai nake buƙatar gani fine and done”. Ya ƙare maganar a wani irin hankali yana zazzaro mata idanunsa da sukai mugun kaɗawa saboda giyar da yake ta faman lodama cikinsa tun kan tazo. Yawu masu kauri ta haɗiye. Sai kuma ta shiga jinjina kanta. “Okay shike nan naji zan kashe yarinya bayan ansan wacece. Sai dai fa kaima ya kamata ka tuna lokaci yayi da zaka yi komai a wuce wajen. Nifa ina buƙatar shares ɗina, dan lokaci yayi da zan mora wahalata ta shekaru gaskiya. Tunda ba ƙuruciya nake ƙarawa ba. Yaron can Fahad banga amfanin saba ai, shima ya cancanci mutuwa. Sannan magana ta gaskiya mahaukaciyar matar nan na gaji da shiga da fita ina shan warin sashen ta itama. Ya kamata kayi wani abu, dan nasan dai zuwa yanzu kaima ka fanshe dukan alƙawarinka da alwashinka a kanta. Kaga sai muje next target wato Awwab. Dan Doctor Ram ya tabbatar min ko a yau muke son poison ɗin nan a shirye yake da aiko mana shi Nigeria.” Iska mutumin da tunda ta fara maganar ke kallonta yake ta faman furzarwa. Sai da ta kai har ƙarshe kafin ya ɗauka kofin giyarsa ya kai baki, ƙarasa shanye wanda ya rage a ciki yayi ya dire glass cup ɗin a saman Centre table ɗin gabansa yana wani girgiza kansa. Sai kuma ya maido jajayen idanunsa ya zuba mata. “Dont warry Lawusa. Komai da kika sani a tsare yana nan bai canja ba. Sai ma ƙarin shares da kowannen mu ya samu sakamakon sake hauhawar dukiyar nan. Dan yaron nan ba ƙaramin mahaukacin arziƙi ya tara mana ba. Shiyyasa nake son ki fahimceni akan kashe yarinyar nan. Dan sam na kasa jin nutsuwa akan barinta raye tun kan nasan wacece ita. Kije ki ƙarasa aikin ki a next zama zaki ji mina tsara game da Fahad ɗin shima”. “Shike nan yallaɓai ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana. Na barka lafiya a huta gajiya”. Hannu kawai ya ɗaga mata da maida idanunsa luuu ya rufe cikin mayen barcin buguwar da yayi...... Iska ta furzar mai zafin gaske. Tare da tura hannunta cikin hular kanta. A take hular ta zame ta faɗi, gashinta mai ƙarancin tsayi da cika ya bayyana. Bata damu ba, dan abinda ya dame ta shi ya dameta. Tunda ta haɗu da Yallaɓai bai taɓa saka mata doka ko sanyata aiki ta gagara yinsa ba, saboda ra'ayinsu bai taɓa banbanta ba. Sai dai a wannan gaɓar an samu akasi. Dan yallaɓai ya sakata yin aikin da ita kanta tasan idan tayisa sai ta cutu. Matuƙar cutuwa. Domin kuwa ita kaɗai tasan irin son da takema yarinyar nan with all her heart. Duk da tana jin zafin abinda shegen yaron nan mai kama da ɗanyen attaruhu yay mata ɗigon sonta bai ragu a zuciyarta ba. Jinta take a yanda ta jure kwanakin baya akanta yanzu bazata iya ba. Dan wani irin mayataccen buƙatar son kasancewa da ita takeyi. A jiya kaɗan ya rage tabi dare a asibitin ta lalubeta. Sai dai ba haka take so ba. Tafi son su mori juna yanda ya kamata. Dan tana jinta a ranta banban da sauran waɗanda ta mu'amalata daga fara wannan harkar zuwa yanzun. Yarinyar akwai kayan marmari fresh a jikinta matuƙa da har wani sashe na zuciyarta na ƙin ganin bebekin Awwab akan abinda yay mata. Yo ita mace ma ta kasa nutsuwa balle shi namiji mai ji da shekarun ƙuruciya da hutu. Sosai tana jinta a tsaka me wuya... “Yau ma wani ɗinne ya mutu da kika kasa nutsuwa?”. Firgigit ta dawo hankalinta tare da juyawa tana kallonsa. Shima kallonta yake fuska babu yabo babu fallasa. Paah ya sake watsa mata kallo murya a kausashe ya furta, “Dan iskanci kinzo nan kin shanyani bayan ina can ina jiran ki kawo min coffee”. Ajiyar zuciya Hajiya ƙarama ta sauke da ƙoƙarin controlling kanta. A hankali ta saki murmushi tare da canja yanayinta like she is innocent woman, cikin kwantar da murya ta ce, “Kayi haƙuri Abban Awwab. Ƙafata ce fa ta riƙe daga fitowa a bayi shine nake ɗan mammotsata. Amma wlhy kana raina tunda naga lokacin shan coffee ɗinka yayi. Amma ganin baka kirani ba yasa nai tunanin ko baku dawo daga masallaci bane”. “Tunda nine limamin masallacin ba”. Ya faɗa a gatsine cike da sake tunzura. Sake kwantar da murya tayi da shiga bashi haƙuri. Uffan bai sake cemata ba ya fita fuuuu yana harare-harare dan dama borin kunya ne kawai ya naɗe da hauka. Tun ɗazun yana a garden ɗin Maash tare da Siyama suna holewarsu. Dan tunda ya fahimci Maash baya gidan ya tura mata saƙo a waya kan ta samesa a garden ɗin Kasancewar yasan anan ɗine zasu iya zama safe fiye da ko'ina a gidan irin wannan lokacin. Sai yanzu ne yake fitowa dan yasan duk inda Awwab yake yana gab da dawowa gidan.... Itama da kallon harara ta bisa. Kafin taja tsaki da faɗin, “Nadai kusan yarda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda stupid man. Dan ɗauke beauty yarinyar nan zanyi mubar ƙasar zuwa can muyi aurenmu mu more rayuwar mu. (Umarnin yallaɓai fa?) Zuciyarta ta ayyana mata. Kanta dake wani irin sara mata ta dafe kawai zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Lallai dole ne tasan mafita a daren yau basai gobe ba. Dan tafi kowa sanin wanene yallaɓai akan duk abinda ya sa gaba. Amma bari taje ta bama wannan sakaran coffee dai ta dawo..... (Tofa 🤔 kaji kuma wani lissafin 🥱🤫) 💢🪴💢🪴💢 A gidan Abba Imamu rayuwa ta matuƙar juyama Mom baya. Dan sam ta kasa gane komai akan al'amarin Halime. Yarinya ce shu'uma matuƙa. Ga kalolin baƙin ciki da take tura mata iri daban-daban. Yanzu har takai Abba ya sallami mai aiki yace kowa tai aikinta ranar girkinta. Mom son jiki, Bibaa da Baby basu iya komai ba. Sai yazam a gidan duk ranar aikin Mom yini ake da yunwa, dan ko anyi abincin da wahala ya ciyu. Daga ƙarshe su ƙare da rigima ita da Abba. Dan ya tabbatar mata shi kam bazai ɗauki wannan banzan halin ba da almabazarancin abinci. Ashe da can duk wahalar gyaran gidan da abinci dama Samraah ce keyi ita kaɗai nata ƴaƴan na kwance. To ta sani bata cutar masa ɗiyar ƴar uwa ba kanta ta cuta. Dan ba baki ya mata ba ƴaƴanta in har a haka zata kaisu gidan miji to ta shirya kuwa za'a dinga koro mata su. Wannan magana tasa ta ƙona mata rai a ranar sai da suka tafka rigima sosai data kaisa da bata wan shika. Aiko dai tace babu inda zata. Kota kanta baibi ba yay ficewarsa. Sam Halime bama tasan abinda ke faruwa ba ita. Dan kwanakin nan gaba ɗaya bata ganema kanta. Kullum bata da aiki sai barci, itama dai aikin gidan a ranar girkin nata ƙarfin hali kawai take yi wajen yinsa. Sai yamma taji zazzaɓi yace salamu alaikum. Bazata taɓa samun nutsuwa ba sai irin sha ɗayan nan na dare. A yau ɗin ma da aka tafka rigimar har ya bama Mom sakin tana barci bata san bikin da akeyi ba. Amma mi, Bibaa da Baby na ganin Abban ya fita suka afka ɗakin Halimen wai zasu daketa. Sun san itace ke ƙullama Mom ɗinsu munafunci. Miye-miye dai magana tsaff a bakunansu. Cikin barci kawai Halime taji an sauke mata uban dundu. A firgice ta farka tare da sakin ihu. Sai kuma ta tsaya cak ganin Bibaa da Baby tsaye kanta suna huci. Kallon mamaki ta bisu da shi, sai kuma ta tashi da ƙyau cikin dakewa ta tambayesu ko lafiya?. “Uwarki zamu ci, shegiya annoba. Wlhy yau sai mun miki jina-jina a gidan nan dan ubanki”. “Tofa babbar magana, wai kishiya taga abin cikin zanen kishiyarta”. Halime ta faɗa tana yayimar ɗan kwalinta ta aza bisa kai tare da sakkowa a gado. Waya ta ɗauka tana cigaba da faɗin, “Ai ku jira bani kaɗai ya kamata ku cima uwar ba, dole na kira Imamu kamar abin zaifi armashi. Kunga sai ku tuɓe ƙaton banza ku haɗamu ku lakaɗa mana dukan tsiya tunda shine ya kawoni gidan”. Sororo Baby da Bibaa sukai suna kallonta. Kafin cikin ƙarfi hali da tsiwa Bibaa ta ce, “Badan Abbanmu ne ƙaton banza ba dan ubanki. Sai dai idan kece ƙatuwar banza. Kuma wlhy yau sai kin ban mana gidanmu”. Dariya sosai Halime ta sheƙe da shi, kafin ta riƙe haɓa da faɗin, “Oh ni Halimatu. Gidanku dai gidanku dai. To ke banda abinki Habi wace sakarar mace ke alfahari da gidan tsohonta? Ai macen data kai mace gidan mijinta take ma fata da alfahari, dan acan ne idan ta tadda komai rigijif-jif-jif sai kiga ta gyara gidansu albarkar iyaye ta bata tsaro tako ina. Dan haka riƙe cika bakin nan naki wannan gidan Halime ne da Jalilah, Habi dai har yanzu bata da gida sai na raɓe-raɓe. Garama ita wannan galwalin ta kusa shiga daga ciki”. Tai maganar tana nuna Baby.. Cikin fusata Baby tace, “Waye Galwali? Aiko yau sai na tabbatar miki na fiki hauka da tashanci”. Fuuu tayo kan Halime.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_ ......Kafinma ta kai hannu kanta ita ta ɗauke fuskar Baby da maruka. Ta shaƙo wuyan Bibaa dake bayanta itama ta bata nata. Basu gama dawowa a hayyacinsu ba ta shiga musu dukan kan mai uwa da wabi. Yo har a gayawa Halime iya danbe. Ita da ake kira giwar dambe a wajen ɗibar ruwa a garinsu. Kai hatta a islamiyya duk wanda ya sake ta haɗosu da Halime aka haɗu a lungun kaci uwaka bayan an tashi to ranar kuwa sai yaci uwar tasa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta musu lis da duka. Sai gasu a ƙasa suna faman ribzar kuka. Itako ta ɗauki sabuwar wayarta da Abba ya siya mata kwanan nan tayi kiransa tana kuka wai yazo gasu Baby da taɓare zasu bigeta. Bawan ALLAH sai gashi a haukace harda Alhaji Sadisu. Suka ko sameta kwance tana ɗan nishi ita adole ga wadda taci duka. Gashi ta kawo jan baki ta ɗan sassaka a wasu wurare na fuskarta da hannu wai duk sayin duka ne. Abinka da fara saika ɗauka haka ɗinne. Ido rufe Abba ya dinga sauke musu maruka abinda bai taɓa koda kwatanta yi ba. Sai dai ma idan Mom ta zugashi akan Samraah yana mata faɗa ita yana marinta suna dariya. Haukace masa Mom tayi da kuka da ihu, amma ada idan ta zuga aka mari Samraah daɗi take ji, ya kuma tabbatar mata idan har ta matso shi sai ya ƙara tsinke igiyar aurensu data rage. Dole taja birki tana kuka sai Alhaji Sadisu ne ya amshesu da ƙyar. Amma sai da yay musu lilis da duka ga wanda Halime tayi musu. Ya kuma tabbatar da ya matso da auren Baby nanda ranar juma'a ko daga shi sai mutanen anguwa ne za'a ɗaura ta tafi haka dan ta ishesa. Itama kuma Bibaan idan bata kama kanta ba zai aurar da ita ga duk wanda ya masa babu abinda ya shallesa da wani karatunta. Haka suka dinga kuka. Shiko ya kama Halimensa sukai ɗaki yana lallashi. Sai dai ita kuma duk jikinta yayi sanyi, dan harga ALLAH batayi zaton zai dakesu haka ba. Ita kawai tayi ne a tunaninta faɗa kawai zai musu a wuce wajen. Koda suka shiga ɗaki sai ta kasa haƙuri ta fito ta sanar masa gaskiyar abinda ya faru harda dukan datai musu. Tama nuna masa video data ɗauka dan sanda tace zata kirashi da farko bashi ɗin ta kiraba ashe video tajeyi. Wannan halin nata shine abu na farko da yake sakashi jin ƙaunarta fiye da koda yaushe. Dan a ɗan zamansu sam ya fahimci Halime bata iya ƙarya ba. Sannan bata taɓa kawo masa ƙarar Mom ta mata wani abu a gidan ba idan baya nan kosu yaran sun mata. Sai dai ita Mom ɗin ta tonama kanta da kanta asiri ta hanyar gaya masa. Shiyyasa yau data kirashi ya taho a rikice. Amma Mom wani lokacin ma tun suna rigimar take kiransa ta sanar masa ƙarya da gaskiya cikin kunfar baki. Idan ya dawo gida yana jiran yaji Halime tace wani abu sai yaji shiru, ko yama samu tana firinfijimarta a gidan hankali kwance tamkar komai bai faru ba. Dan ita in har akwai wuta tv na kunne shikenan tace bata da sauran takaici a duniya. Balle ta haɗa uban shayinta cikin ƙaton kofi da burodi ta soya ƙwai ta zauna tana sha tana kallo ai ji take duniya babu ya ita. Har da rana da yamma shan shayi take saboda masifar ƙaunarsa da takeyi tun tana ƙaramarta. Abinci ma bai cika damunta ba in dai akwai shayi da burodi balle ga madara a ciki yaji da sauran kayan shayi ace kuma akwai soyayyen ƙwai wayyo jinta take kamar a aljanna. Yasha gwadata akan magana da Mom take sanar masa game da ita. Amma mutuniyar sai ta basar tama nuna ita yaushe akayi hakan, idan ma anyi to ta manta. Koda yake harga ALLAH bawai tanayi don makirci bane ko wani abu. Kawai ita har cikin ranta da halayenta da anyi abu ya wuce shikenan kawai sai wani ya taso kuma. Wannan dai ta gama da babinsa. Idan ko har kakaga Halime ta riƙe abu a rai ya dameta to lallai al'amarin babbane matuƙa. Dan wahalar data sha a hannun innarta da ace tana riƙewa a rai da tuni hawan jini da ciwon zuciya sun kai rayuwar yarinyar ƙasa.... ❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥 Ƙarfe sha ɗaya da wasu mintuna suke shigowa gidan. Har gaban dashensa TJ ya faka motar, da sauri Shu'aibu ya fito ya buɗe masa. Koda ya fita maimakon shiga sashen nasa sai ya koma ainahin ƙofar shiga babban sashen gidan. Babu kowa a falon sai Azizat dake dakon jiran dawowarsa. Yana shigowa kuwa ta miƙe zambar. Fuskarta ɗauke da murmushi ta nufosa tana masa sannu da zuwa cike da shagwaɓa. Sai da tazo gab da shi ya wani watsa mata mummunan kallo yayi wucewarsa upstairs. Kai tsaye sashen Ummie ya nufa ya barta nan tsaye baki sake tana binsa da kallo ga hawaye na gudu a fuskarta. Sai kuma ta kwasa da gudu tai sashen Hajiya Mammah itama. Sai dai tana murɗa ƙofar bedroom ɗin ta tajita a rufe gamm. Jingina tayi jikin ƙofar tana sake fashewa da kuka. Sai kuma wani ɗan nishi-nishi da take juyowa kamar daga cikin bedroom ɗin ya sata fara sassauta kukan nata tai tsai alamar saurare. Tabbas daga ɗakin mahaifiyar tata ne. Knocking ƙofar ta farayi da kiran sunan ta amma babu alamar za'a buɗe, sai dai kamar anyi shiru an daina nishin. Sake fashewa tayi da kuka tare da barin jikin ƙofar da gudu tai ɗakinta. Wata shegiyar dariya Arwa dake laɓe tun ɗazun tana kallonta dan komai akan idonta ya faru ta saki, sai kuma cike da farin ciki ta furta, “Iska na wahalar da mai kayan kara” ta juya cike da takun girgiza jiki ta koma nata ɗakin dake a sashen uwarta Hajiya ƙarama. Dan su dukansu kowanne a sashen mahaifiyarsa yake har suma su Malika.... ★ A ɓangaren Maash kuwa bai wani jima ba a sashen Ummie ya fito, dan ya samu tana barci ne alamar sauki na samuwa. Baya buƙatar wata matsalar ta sake samuwa a dalilin shigowar tasa dan haka ya juya ya fita a kan lokaci. Har zai wuce sai kuma yay tunanin shiga sashen Paah dan akwai maganar da yake sun suyi. Gobe in ALLAH ya kaimu kuma ya sanar masa da baƙi da zaiyi da wuri zai fita a gidan ba lallai su haɗu ba. Sashen Paah ɗin ya nufa da tunanin shi kaɗaine dan yasan da wahala Hajiya ƙarama idan tana a gidan kasancewar ya ganta a asibiti ɗazun. Knocking yay har sau biyu amma baiji motsin komai ba. Yasan Paah da kallon labarai yanzu haka hankalinsa nacan baima jisa ba. Dan barci dai yanada tabbacin baiyisa ba zuwa yanzun kam. Kansa tsaye ya tura ƙofar ya shiga kawai, sai dai kuma da saurin tsiya ya tsaya cak dai-dai yana ɗaga kafarsa zaiyi taku kusan na biyar a cikin falon sakamakon furucin da Paah ɗin yayi waya a kunnensa. Da ƙarfi yaja numfashinsa da ke neman fisgewa daga cikin ƙirjinsa. A wani irin harzuƙe da kaushin harshe ya furta, “Paah!!”. A bala'in rikice Paah ya juyo tare da sakin wayar ƙasa yan zazzaro idanunsa. Fuuuu Maash ya juya ya fice a falon tare da bugo masa ƙofar da masifar ƙarfi har sai da ya zabura. “ Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un”. Ya shiga maimaitawa cikin tashin hankali. Shi ya haifi Awwab, amma wlhy zai iya rantsuwa da baya jin tsoron wani sama da yanda yake shakkar yaron nan. Kai hatta Baba prof daya haifesa baya jin yana shakkarsa kamar Muhammad. Koda wasa baya son Muhammad ya kamasa da wani laifi musamman akan abinda za'ace ya shafi mahaifiyarsa koda kuwa ɗan kaɗan ne... Sashen Maash ɗin Paah ya nufa a ɗarare cikin kuma tashin hankali, dan Gara yaje suyita kawai baya son ya ɗauki fushin nan da shi. Kasancewar ta ainahin ƙofar shiga sashen ya fita yabi kansa tsaye ya shiga. Shu'aibu ya samu a falo da TJ. Cikin girmamawa suka shiga gaidashi. Da ƙyar ya iya danne yanayinsa ya amsa musu. Kafin ya ɗora da tambayar ogan nasu. Kai tsaye TJ ya amsa masa da, “Alhaji yana ciki”. “Okay to bari na gansa ko?”. Da girmamawa suka amsa masa da to. Shi kuma yay gaba kai tsaye sashen bedrooms ɗin Maash, suma sai suka fice dama abubuwan da suka dawo da shi a mota suka shigo da su ciki. A bedroom ɗin da yafi ƙyautata zaton samunsa yay knocking. Kusan mintuna biyu aka buɗe ƙofar. Ɗan zuba masa idanu Maash dake ɗaure da towel jikinsa na raɓar ruwa alamar daga wanka ya fito yayi. Sai kuma ya ɗauke kansa fuskarsa na sake zama kicin-kicin. Batare da ya ce komai ba ya saki ƙofar ya juya ciki. Bin bayansa Paah ɗin yay shima, a bakin katafaren gadonsa ya zauna, yayinda shi kuma yake daga ɗan lungun closet ɗin sa yana ƙoƙarin zira jallaniya fara tass mai gajeren hannu. Fuskarsa a tsananin ɗaure ya sake fitowa. Batare daya kalli Paah ɗin ba ya jingina da mirror daga tsaye yana kallon wani gefen. Kaɗan ya motsa lips ɗinsa wajen faɗin, “Good Evening”. Karan farko Paah ya saki murmushin ƙarfin hali, sai kuma ya amsa da, “Evening dear, how are you?”. Shiru Maash bai amsa masa ba. Sai ma ƙara ɗauke kansa da yay gefe. Shiru ɗakin shima Paah bai sake magana ba yana ƙulla ta inda zai fara. Kafin ya nisa a hankali ya sake furta. “Muhammad magana nazo muyi”. “Ina jinka”. Ya amsa masa a daƙile. Kai kawai Paah ya girgiza. Sai kuma ya cigaba da faɗin, “Kana fushi da ni ko? Akan abinda kaji ina faɗa. Haba Muhammad, kafa san yanda nake ƙaunar Ummu-Hidaya. Taya zan iya wofantar da ita saboda ta samu lalura”. “Paah ka faɗi abinda ya kawoka kai tsaye Please”. Maash ya katsesa cikin zafin rai.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆_ ......Zuru Paah yay masa yana kallo, sai kuma ya haɗiye yawu masu kauri yana jinjina kansa. “Muhammad wai sai yaushe zaka yarda dani akan mahaifiyarka ne? Ƙarshen maganata da kawai kaji baka san akan mi nakeyi ba, ba kuma kasan dawa nake yi ba”. Fuska sosai Maash ya yamutse ransa na ƙara masa suya akan halin mahaifin nasa. Duk yanda yaso danne kar ya biye masa bazai iya ba, a fusace ya bashi amsa da, “Sai randa ka canja Paah. Sai randa ka ajiye son zuciya ka tuna da halacci. Bazan hanaka yin dukkan abinda kai niyya ba. Sai dai wlhy ina gab da ɗaukar mummunan mataki. Sannan yaronka na bashi nan da kwana uku ya sallami waɗan nan ƴan iskan yaran daya tara min a company, idan ba hakaba duk wani mai alaƙa dasu ya kuka da kansa. Kuma shima ya ajiye aiki da hannunsa kar ya bari na ziyarci Company yana ciki” Cikin ɓacin rai da tsarguwa Paah ya ce, “Muhammad kana zargina ne?”. Shiru yay yaƙi tankawa. Sai da Paah ya miƙe zuwa gabansa. Cikin sauke murya ya sake furta, “Muhammad miyyasa kai baka yafiya ne? Miyyasa kake da riƙo? Sai yaushe zaka yarda dani? Dan kawai kaji ina waya sai ka fasaarata da wata siga daban har kana tunanin sallamar waɗanda basu ji ba basu gani ba daga aiki”. “Sai randa ka daina saka wannan ɗan iskan yaron na maka kawalcin yara ana kawosu da sunan wai ma'aikata. Paah na sanka fiye da yanda nasan kaina. Dama na jima ina zargin waɗan nan yaran zaman iskanci suke min a company. To wlhy na basu daga daren yau zuwa gobe su koma inda suka fito, in ma gidan karuwai zaka buɗe musu bai shafeni ba rayuwarka ce”. Rumtse idanu Paah yayi da ƙarfi. Sosai kalaman ɗan nasa ke masa amsa kuwwa a cikin kunne. Yasan wanene Awwab idan yay fushi. Sam baya tauna magana yayin faɗarta balle shakka. Jin alamar zai bar wajen ya sashi buɗe idanunsa. Cikin ɓacin rai ya dakatar da shi da faɗin, “Miyasa baka tauna magana yayin furtata? Ina matsayin mahaifinka amma baka shakkar tauna magana yayin furta min ita. Komai ya zo maka a rai saika yaɓosa waje” A daƙile da yanayin zafin rai shima Maash ya furta, “Ni ɗankane bani da hurimin hanaka duk abinda ka tsarama rayuwarka kam. Amma ka sani bazan iya cigaba da jurar ganin kana kana takamin mahaifiya a ƙarƙashin takalman ƙafarka ba Paah. Abinda na ɗauka kafin yanzu bazan iya ɗaukarsaba a yanzu. Idan da kace rashin mace ke saka aikata abinda kake aikatawa yanzu minene hujjarka kuma tunda kana da wata matar? Kai da kanka kamin alƙawarin dainawa, ashe baka fasa ɗin ba. Idan mace ɗaya ta maka kaɗan ka ƙara auren mana. Ka ƙaro uku su zama huɗu yafi min wannan mummunar ɗabi'ar taka mai zubar da mutunci ga zunubi wajen UBANGIJI.....” ya ƙare maganar cikin ƙaraji dasa hannu ya watso kayan saman mirror ɗinsa gaba ɗaya. Sai kuma ya kaima mirror ɗin naushi, a take kuwa ya shiga tsatstsagewa. Sake kai masa wani naushin yayi, ya kuma tsagewa tare da jimasa ciwo. Sai ga saman yatsunsa duk jini ya ɓata. Da sauri Paah ya kamo hannun nasa jikinsa har rawa yake. Amma Maash ɗin sai ƙoƙarin ƙwacewa yake yi. Dan so yake kawai ya ƙara kaima mirror ɗin duka ko zai samu sauƙin zugin da zuciyarsa ke masa... “Please sweetheart relax. Dan ALLAH try to calm down. Jifa yanda kake jima kanka ciwo Muhammad”. “Is not your business Paah. I beg you leave me alone”. “Naƙi ɗin, nace maƙi na barkan! Miyasa kake da zuciya ne Muhammad. Fushinka yayi yawa. Taya zan Barka ka cigaba da jima kanka ciwo. Nace kayi haƙuri! Haba Muhammad”. Ya ƙare maganar cikin sanyin murya tare da jawoshi jikinsa ya rungume. Abinka da su duka dogaye, sai gasu kai ɗaya. Ƙarfi da cikar zati kawai Maash zai nuna masa saboda shi yana akan ƙuruciyarsa, shiko koba komai girma ya kamashi. Luff Maash yayi a jikin mahaifin nasa, sai faman sauke zafafan ajiyar zuciya yake a jajjere. Yayinda Paah ke jin yanda zuciyar tasa ke gudu da ƙarfi. Sunfi mintuna uku a haka sannan ya ɗagosa. Kama hannun nasa yay suka nufi wajen gadon, zaunar dashi yay sannan yaje ya ɗakko first aid box ya dawo kusa da shi ya zauna. Hannun nasa dake ta tsatstsafo da jini ya kamo, cike da kulawa ya fara masa treating. Ko sau ɗaya Maash bai motsa ba, bai kuma kalla mahaifin nashi ba har ya kammala ya naɗe masa da bandage. Zama yay zai fara magana Maash ɗin kawai ya miƙe, da sauri Paah ya riƙosa ya maida shi ya zaunar. Bai musa ba ya zauna, sai dai yaƙi kallonsa yanzu ma. Shiru Paah yay yana kallonsa, sai kuma ya sauke numfashi a hankali yana sake tattaro abinda yake son faɗar. “Muhammad kayi haƙuri, tabbas nasan bana ƙyauta muku, sannan ban yima kaina adalci ba. Bazan kira abinda nake aikatawa da ƙaddara kawai ba, harda sa kai. Shiyyasa tabbas a rayuwa ka guji aikata mummunan aiki a ƙuruciya, idan kuma ya zama jarabawarka ce ka fara kayi gaggawar tuba. Idan ba haka ba wannan abin zai ta bibiyarka ne a lokacin girma, a lokacin da kuma kake son ka daina ɗin amma abin yabi jininka. Wannan maganar mahaifiyarka tasha faɗa min ita da maimaita min a duk sanda ta sameni a halin rashin gaskiya. Amma mi a lokacin bana gane karatunta, gani nake ai duk sanda na shirya zan iya dainawa”. Yay murmushin takaici, mai nuna ainahin ciwon da yake ji a zuciyar yasa. Cikin ɗan yarfar da hannu ya cigaba da faɗin, “Abubuwa da yawa sun faru, wasu ma suna kan faruwa da ni kaina ban san adadi ba. Ni ne ya kamata ace na tsaya muku, amma sam ban taɓa yunƙurin hakan ba koda sau ɗaya. Hatta da rashin Fahad a kusa da mu yana damuna. Sai dai ban san taya zance komai ba. Muhammad! Banso ace halin da nake ciki yayi nason da zai shafeku ba kamar yanda mahaifiyarku tasha yin fata. Sai dai a wannan gaɓar na fahimci zancen nan na masu iya magana da kance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. Wlhy bazan ɓoye maka ba, case ɗinka akan yarinyar nan ya tsaya min ta yanda na kasa haɗiyeshi, sannan yanda kake bama yarinyar kulawa tamkar ba abinda ake gudu bane ya shiga tsakaninku na sake ɗaga min hankali. Bana son ace sunanka ya ɓaci a duniya Muhammad, wlhy bana son abinda wani zai aibantaka da shi, koda bazan ce komai ba ina jin zafi, matuƙar zafi a cikin zuciyata. Dan ALLAH ina roƙonka idan an sallami yarinyar nan daga asibiti gobe idan ALLAH ya kaimu zan haɗa mata sha-tara ta arziƙi tare da siya mata ticket ɗin jirgi idan ba ƴar cikin garin nan bace ta koma garinsu. Idan kuma a cikin garin nan take da iyayenta nasan zata iya yiwuwa a gidan haya suke ko wani muhalli ƙaskantacce. Zan saya musu gida a ɗaya daga cikin jihohin arewa su koma can, kar su sake waiwayar Lagos har abad....” Karan farko Maash ya zuba masa idanun kawai yana masa wani irin kallo mai wahalar fassara. Kallon ne ya dinga ratsa Paah sai ya gagara ƙarasa abinda ya faro ya ja bakinsa kawai yayi shiru. Wani irin murmushin ƙasaita da ɓacin rai Maash yayi, sai kuma ya ce, “Ya kayi shiru kuma, ina jinka Paah.” “Saurarena kawai kake amma ba jina ba Muhammad abar maganar kawai”. Ya faɗa cikin ɗan borin kunya da kame-kame. “Ka kwanta ka huta dare yayi, zuwa safiya sai mu ƙarasa, amma ka daina kira min ƙara aure har ma na mata uku, kai ka sakar min Ummu-Hidaya ɗin ne da kake cireta a matsayin matata”. Ya sake faɗa yana nufar ƙofa cikin ƴar sassarfa ya fice. Tsahon lokaci Maash ya ɗauka yana kallon ƙofar kawai. Sai kuma ya cije lips ɗinsa da masifar ƙarfi zuciyarsa na masa wani irin suya. Yasan mahaifinsa fiye da sanin da kowa ya masa a rayuwa. Amma bazai ce komai ba ALLAH mai ji ne mai gani. Yana kuma roƙonsa ya shiryeshi... 🤥Humm, kai dai Paah ALLAH ya shiryeka dai to gaskiya😏. Yayanmu kayi haƙuri mahaifi mahaifine koda na banza ne😭. 💦✨💦✨💦 Tun wucewarsa daga asibitin abubuwa suka sake cinkushe min kai. Kalamansa sai faman maimaita kansu suke a cikin kaina. Duk da nasha magani zafin zazzaɓin nan yaƙi bari na. Zaune na tashi ina kallon Mama Balki da barci ya ɗan fara figa. Sai kuma na miƙe cikin sanɗa na nufi ƙofar fita. “Samraah ina zaki je?”. Muryar Mama Balki a bazata ta daki cikin kunnena. Cak na tsaya tare da runtse idanuna. Sai kuma na juyo a hankali cikin son wayancewa zanyi magana ta dakatar da ni. “Baki iya ƙarya ba Samraah, kada ki farata yanzu”. Sosai furucin nata ya dakeni, dan haka na sauke ajiyar zuciya tare da dawowa a hankali na koma saman gadon na zauna. Kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hanuna nace, “Kiyi haƙuri Mama. Ba wani abu zanyi ba. Reception zanje na samo pen da takarda zanyi amfani da su”. “Amma a daren nan Samraah. Na kula tunda Alhaji ƙarami ya tafi baki da nutsuwa. Bana fatan ace kina son samo takarda da biron ne dan kiyi rubutun da zaki bar masa ki gudu”. A karo na farko nayi murmushi tare da girgiza mata kaina. “Haba Mama, ai a yanzu wlhy koda shine da kansa yace na tafi gidanmu bazan je ba. Dan insha ALLAHU sai na sauke alkawarin dana ɗauka akan Ummie. Kawai zanyi amfani da sune dan ina son yin lissafi dalla-dalla. Ba kuma zai yiwu a cikin ƙwaƙwalwa ba dole sai da taswira a rubuce”. Ajiyar zuciya Mama ta sauke. Batare da tambayata abinda zanyin ba ta miƙe. “Shike nan ki zauna ni bari na fita na samo miki. Kin san dai ba'a son ki yawaita motse-motse mai ƙarfi saboda ɗinkin jikinki”. Bance mata komai ba sai duƙar da kaina dana sake yi. Itama sai ta fice abinta bayan ta zumbula Hijjab ɗin ta..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_ ......Mintuna basu fi biyar ba kuwa sai gata ta dawo. Cike da farin ciki ta miƙa min takarda da biron tana faɗin “Kinga Alhamdullah na samu ƴar arziƙi a reception ɗin ma. Ina tambaya babu musu ta ciro ta bani har shida, gasu kuma manya nasan dai zasu isheki ai ko?”. Nima fuskata a washe da murmushi na amsa ina faɗin, “Yauma Mama Nagode sosai. In sha ALLAHU zasuyi harma ƙila suyi yawa.” File ɗina na ɗauka na ɗaura a samansu tare da gyara pen ɗin. Gaba ɗaya ahalin Maash Mansion na shiga lissafowa a jere. Wanda na manta ina tambayarta. Hatta da adadin masu aiki maza da mata da aikin kowa sai da na rubuta su. Kafin nabi duk manyan gidan na zana halin kowa dana fahimta agaban sunansa. Hatta shi kansa Maash ɗin harda shi. Daga haka nai shiru ina nazari tsahon lokaci, kafin na ɗaga katifar na saka takardar. Toilet na nufa na ɗauro alwala. Duk da yanda nake jin jikina haka na nutsu na kabbara salla domin miƙama UBANGIJINA kukana tare da kai ƙarar wasu mutane garesa dan ya shigemin gaba wajen gano ainahinsu kozan san inda zan kama a wannan tafiyar dana shirya yi.... 🌿💞🌿💞🌿 Sosai biki ya kankama a gidan Abba Imamu. Sai dai gaba ɗaya bai zoma Mom a yanda ta shirya shi ba. Dan har yanzu Abba yaƙi maidata ɗakinta. Babu irin haƙurin da bata bashi ba, hakama Ummanta tazo ta saka wanda yake jin kunya amma yaƙi sauraren kowa. Kasancewar tana a cikin gidan har yanzu yasa mutane da yawa basu san abinda ke faruwa ba. Abun zai baku mamaki idan nace muku tunda Halime ta fuskanci abinda ya faru tsakanin Mom da Abban itama ya kasa gane kanta. Kuka ta dinga masa da magiya da roƙon ya maida matarsa, idan ba hakaba itama gaskiya sai dai ya saketa. Ita haka kawai yaja mutane su tsaneta a dinga cewa dan ya aurota ne ya saki uwar ƴaƴansa. Duk yanda ya nuna mata babu ruwanta a ciki taƙi haƙura ta barsa. Kullum cikin masa nagiya take da kuka gashi bata da lafiya sosai. Dan ta kai ma a yau sai da suka je asibiti saboda yanda take amai gaba ɗaya ta galabaita. An tabbatar musu tana da shigar ciki. Zo kuga murna wajen Abba. Yayinda Halime ido yay gwalo-gwalo. Tabbas tana son yara sosai, kodan yanayin rayuwar data gashi ta tsangwama da rashin sakewa. Bata da wani wanda zatace yau ya zame mata amini tunda ƙaninta ya rasu. Ba kunya Abba na dawowa gida ya barbaɗama Auta. Murna da tsalle Auta ya dinga yi da ga ƙarshe ya kwasa da gudu yaje ya barbaɗama Mom dake tare da ƙanwarta da Ummanta da suketa tsare-tsaren biki da za'a fara nan da kwanaki biyu. Neman ɗaukewa numfashin Mom ya yi, har sai da takai hannu ta dafe goshinta dan wani irin sara mata kanta yayi na masifa. Ganin tana neman ɗagama kanta hankali Ummanta da ƙanwarta suka shiga lallashinta da mata nasiha akan tafa kwantar da hankalinta. Wata fitina ko nuna wani abu a yanzu ba nata bane. Ita da ake lallaɓawa ya maidata ɗakinta ya kamata ace ta nutsu, kai kodan bikin nan da za'a tara mutane ta rufama kanta asiri karta bari ƴan uwansa su samu lagonta. Dan yanda bata riƙesu hannu biyu ba sumafa a yanzu dole su ringa nuna mata cewar amarya ta fita a wajensu. Sannan duk hanyar da zasu ƙuntata mata a shirye suke da nemota komai ƙanƙantarta. Shi kansa Abban yanda yake jin kansa on top akan yarinyar nan yanzu idan fa ta cigaba da matsawa sauran igiya biyun ya tsinketa ba abinda zai damesa bane. Wannan nasiha da ƙanwarta ta mata ne ya sakata kama kanta badan taso ba. A haka aka shiga shagalin bikin Baby. Danginta da ƴan gwarzo sun cika gida tako ina. Tun ranar alhamis aka fara event, dan wasu irin mahaukatan kuɗaɗe mijin Babyn ke kashewa tamkar baisan ciwonsu ba. Duk da kuwa bikin Abba ya dawo dashi baya ne akan yanda aka sanyashi an zaftare har sati biyu a ciki. Ranar juma'a aka kawo lefe na nunama tsara harda key ɗin motar da aka zubo kayan. Wannan bajinta ta ragema Mom raɗaɗin dake damunta a cikin zuciya game da cikin Halime. Ta dinga yanka ƙananun habaici da ɗagawa ma mutanen Gwarzo. Faɗa take yanzu ne akai biki na ƴar gata ba irin na Samraah da har yanzu basu san ina ya dosa ba. Maybe ma Abba da Musaddiq sun saidata ne ko turata karuwanci. Yo inba haka ba wane irin aurene wata kusan takwas basu taɓa sanin miji ba itama bata taɓa zuwa gida ba. Ai dole ne akwai abin ashshar da ake ɓoye wa. Duk da kalamanta sun tada hankulan su Gwaggo Gudidi duk da zuwa yanzu suna waya da Samraah dan hatta su Kawu Musa tana ɗan kira sai suma suka ji kamar basu ƙyautama Samraah ɗin ba. Amma dai sun shanye a fuskokinsu babu wanda ya tanka Mom da haukarta. Washe gari asabar aka ɗaura aure. Abu na farko daya fara bama mutane mamaki shine ango daga shi sai abokansa guda uku yazo wajen ɗaurin auren. Sune suka amsa masa auren a matsayin waliyyay. Kowa yayi zato da tsammanin yanda yake faman ɓarin kuɗi kamar babu gobe sai ƙofar gidan Abba an rasa wajen faka motocin gayyarsa data ango. Amma sai gasu su huɗu a mota ɗaya rak kamar dangin mayu. Jikin Abba shi kansa ya fara sanyi, sai dai bai iya yace komai ba har aka kammala. Zuwa dare maimakon an shirya amarya a miƙata ɗakinta sai akacema Abba wai ai wajen dinner za'aje sai zuwa gobe ango zai ɗauki amaryarsa daga gidansu sai airport zasuje honeymoon ne. Sai bayan sun dawo zai wuce da ita gidanta. Tofa anan ne fa ƙananun magana suka ɗan fara tashi, haka aka shirya tafiya dinner kowa bakinsa da abin faɗa. A wajen dinner an ɗan ga wasu mata a matsayin danginsa. Sai abokansa da suka ɗan zazzo da matansu. Dan ko wajen bada tarihinsa ƙanwarsa ce ta bada. Dinner kam tayi dinner, dan anci kaji ansha lemon roba gwargwadon iko. Ga bag da aka raba cike da kayan rabo a ciki. Amarya baby da ƙawayenta sai feleƙe ake abin nema ya samu. Haka Mom dan tare da ita akaje dinner sai nuna isa ake. Hatta da Umma sai da taje abinta ko kunya. Ƙarfe ɗaya da wani abu na dare aka tashi, su dai ƴan Gwarzo ma tun kusan goma da wani abu suka saka Musaddiq ya dinga fito da su yana sakawa a napep ana maidosu gida dan sun gaji. Lokacin da su Mom suka dawo su tuni sunyi nisa a barci. Ita kam Halime dama bata da wani sakewa a bikin saboda laulayinta mai addaba ne. Koda yaushe tana ɗaki kwance. Da ƙyar take ɗan yin dauriyar fitowa ta gaida ƴan gwarzo. Dan hakama dinner ɗin bataje ba sukai zamansu ita da Abba a gida yana tattalin kayarsa da lallashi itako tana zuba masa taɓara.. Washe gari lahadi da aka tashi da shirin wucewar baby da mijinta shi kuma Musaddiq ya shirya wutowa Lagos. Sunyi waya da mijin Samraah zai je wajenta ya kwana washe gari litinin zai haɗu da wanda zai masa jagorar wucewa ƙasar Chaina kamar yanda MD ɗin sa ya bashi a rubuce. Dan haka ya shiga sallama da ƴan uwa anata koke-koke. Abinka da tsoffi gani suke tafiya Chaina ɗin nan kamar tafiya lahira ne. Dan wasu ma da farko da ca sukai basu yarda Musaddiq ɗin yaje ba. Sai da Abba ya dinga basu haƙuri da nuna musu muhimmanci da cigaban da Musaddiq ɗin ya samu har suna wataran zai shafesu sannan suka haƙura badan sun so ba. Sai dai sunyi farin ciki da jin shi da Hafizzullah zasu je wajen Samraah ne a yau kafin shi ya wuce gobe. Dan rigima da Hafizzullah ya saka masa akan son zuwa shima yaga Samraah ɗin ne yasa shi fidda yan kudaɗensa ya saya masa ticket ɗin jirgi saboda shi ta sama zaibi zuwa Lagos ɗin sai ya saima Hafizzullah ɗin shima zasu wuce tare. Kafin ma mijin Baby ya iso su sun fito, dan motar company ce zata kai Musaddiq ɗin airport. Haka suka wuce ƴan uwa da abokan arziƙi na musu fatan alheri. Tare da saƙon gaisuwa ga Samraah buhu-buhu aunty Zakiyya harda saƙo a cikin kwali datai nannaɗe da su Musaddiq basu sani ba. Hakama Gwaggo Gudidi ta haɗa kayan maƙulashe irinsu tuwon madara, carbin malam, gullisuwa, aya, gyaɗa, riɗi, cike da leda viva tace a kaima ɗiyarta. Wai maybe tanada ciki kunya ta hanata faɗa, ba kuma a raba masu ciki da son kaya kwaɗayi irin waɗan nan. ALLAH sarki Halime itama sai da ta bada zuma mai yawa a gora da uban aya da take saidawa a kaima Samraahn duk da a hoto kawai ta santa. Ta kuma saka Abba dole ya bada naira dubu hamsin a kaima Samraah ɗin. Sosai Musaddiq yayi mamaki bada waɗan nan kuɗi, amma haka kawai sai yaji a ransa aikin aunty amarya ne. Sosai yaji kima da darajar yarinyar na ƙaruwar masa a rai, har sai da ya share ƙwalla. Dan tunda tazo gidan nan abubuwa da yawa suka sauya. Abincinsa, tsaftar ɗakinsa bata ƙyashin shiga ta gyara, komai kuma tana yimasa a mutunce da girmamawa. Yana kiranta aunty tana kiransa Yaya. Da yay magana sai tace ai ita ɗan uwa take kallonsa kuma babban yaya bawai ɗan mijinta ba. A bata da lafiyar nan duk rintsi bata bari ya fita da safe bai karya ba koda ba ranar girkinta bane. Haka tunda Hafizzullah yazo take hidima da shi da jansa a jiki shima kai kace ƙaninta ne uwa ɗaya uba ɗaya. Duk yanda Hafizzullah keda ƙin sakin jiki da mutane sai gashi dandanan ya saki jiki da ita. Hatta da jakar kayansa yanzu haka a ɗakinta ya bari dan ɗakin Musaddiq ɗin akwai baƙi maza yan gwarzo da basu kai ga wucewa ba.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ____________ ......Lokacin da suka iso airport ɗin su duka sai da ƙwalla ya cika musu idanu. Dan abune da basu taɓa zato ko tsammani ba a rayuwarsu. Sune yau da hawa jirgi daga Kano zuwa Lagos. UBANGIJI al-musawirru mai sassauya al'amura a sanda yaso ga kuma wanda yaso. Da suka shiga jirgin sai Hafizzullah ya rungume yayan nasa yana hawaye. Dole shi ya haɗiye nasa ya dinga lallashinsa. Bayan yayi shiru kuma ya dinga musu video wai dolene ya nunama Aunty Samraah yau sun hau jirgi. Dariya Musaddiq ya dinga masa har ALLAH ya saukesu lafiya garin Lagos. Sunyi mamakin ganin zuƙeƙiyar motar da tazo ɗaukarsu. Amma sai Musaddiq bai kawo komai a ransa ba tuna cewa dafa companyn Maash yake aiki, mai lamba ta ɗaya a Africa, na uku a duniya a matasa. Ai hakan ba komai bane ba. Sunyi da MD dama motar company zata daukesu daga airport ta kaisu duk inda zai je, sannan idan ya kammala gobe idan ALLAH ya kaimu zai kira aje can gidan ƴar uwar tasa a ɗaukesa zuwa wajen GM, daga nan zai wuce kuma.... 🩸🩸🩸🩸🩸 Kamar kullum alarm ɗinsa ne ya tashesa. Hannu ya kai idanunsa a rufe ya lalubosa a saman side drawer ya danne wajen kashewar dan shifa ko yaya ƙara take damun rayuwarsa take. Shiyyasa bazaka taɓa ganin wayarsa da ringing ton ba. Kullum cikin vibration phones ɗinsa suke. Hakama television da wahala kiji ya buɗeta caaa tana surutu. Cikin mayen barcin da bai gama isarsa ba ya nufi toilet. Sai da yay wanka kamar yanda abun ke neman zame masa sabo saboda mafarki duk da ba kullum yake tashi a irin yanayin ba sannan ya ɗauro alwala ya fito. A ɗan gurguje ya busar da kansa ya shimfida sallaya yay raka'atainul fijir sannan ya fice masallaci. Ana idar da salla bai yarda sun haɗu da Paah ko Uncle Abdullahi ba ya dawo gidan. Jallabiyarsa ya zare ya ɗauka sports wear ya saka masu kalar blue da rashin white. Sosai kayan sukai masa ƙyau duk da baya sakasu ne domin kwalliya ba. Ya kama gashinsa ya haɗe a tsakkiya tare da ɗauresa da siririn baƙin band. Duk da gudu zai fita sai da ya sakama jikinsa turare ya maƙala bluetooth a kunensa sannan yay zaman saka takalma spots na companyn nike. Yana fitowa falo Laalah dake kwance ya miƙe ya nufosa. Kansa ya shafa cikin lumshe idanu da silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Let's go my friend”. Cikin kaɗa bindi kuwa ya bisa abin cike da mamaki. Daka gansu kasan karen ya gama samun training na musamman a hannun uban gidan nashi. Gashi fari tass babu alamar wani dattin ƙazanta a tare da shi. Wanda ma bai sani ba sai ya ɗauka ba kare bane saboda yanda jikinsa ke duguzum da gashi. Yana nufar gate da ɗan gudu Laalah biye da shi ƙafa da ƙafa dan a jere suke tafiya su Sha'aibu dake zaman jiran fitowarsa na take musu baya suka fice yana ɗagama ma'aikatan daketa faman gaishesa hannu. Gudun ya fara tun daga wajen gate ɗin a hankali Laalah a gefensa guards ɗinsa biye da su. Haka suka miƙe street ɗin nan. Sosai sukayi nisa bana wasa ba. Jefi-jefi suna gamuwa da mutane da suma suka fito jogging ɗin. Hannu kawai suke ɗagama juna kowa ya wuce. Sai wasu ƴammata ne da suka dai-daita gudun kusan da shi dan suna a ɗan gabansa kaɗan amma ko kallo basu ishesa ba. Sunyi nisa sosai ya jiƙe sharkaf da zufa har yana ɗiga sannan suka sake juyowa bayan ya kalla agogon dake a tsintsiyar hannunsa. Suna isowa kwanar da zata sadasu da gida ya tsaya cak. Nuni yayima Shu'aibu daya bashi ruwa cikin sauke numfashi da sauri-sauri. Da sauri ya nufesa tare da ajiye ƴar jakar da abubuwan da zai buƙata ke'a ciki. Kamar su bottle water, towel da abinda ba'a rasa ba. Ruwan ya amsa ya buɗe murfin haɗaɗɗiyar bottle water ɗin ya kai bakinsa. Kansa ya ɗaga sama ya shiga kwararawa. Wani irin kaiwa da komawa maƙoshinsa ya shiga yi, illahirin ƙofifin gashin jikinsa na buɗewa zufa na fitowa da gudu. Sai da ya sha fin rabi sannan ya sauke gorar yana sauke numfarfashi. Laalah ya zubama kaɗan a jiki, shiko yay wani irin matsawa yana girgiza jiki. Yanda yay ɗin ne ya saka Maash ɗin sakin wani ɗan guntun murmushi yana sake kai goran bakinsa ya ɗan kurɓa sannan ya rufe ta ya miƙama Shu'aibu da suma duk suke shan nasu ruwan tare da masa alamar ya bashi towel. Da sauri ya miƙa masa fari tass ɗin towel ɗin hannunsa dake a linke. Sai da ya fara gogo wuyarsa zuwa gashi dake kwance a kumatunsa sannan yay magana batare da ya kalli su Shu'aibu ba. “Kira Tijjani ya samemu anan da mota”. Duk da a hankali yay maganar sarai Shu'aibu ya jisan. Sai dai yayi mamakin jin abinda yace ɗin. Amma bashi da hurumin musawa. Sai ma waya daya zaro yay kiran TJ ɗin. Cikin ƙanƙanin lokaci motocin biyu suka iso. Ta farkon aka buɗe masa ya shiga shi da Laalah. Ta bayan guards ɗinsa ne. Sai TJ da Shu'aibu a gaba tunda ba Hayatu. A ɗan ɗarare TJ ya ce, “Sir ina zamu je?”. Shiru kamar bazai ce komai ba. Sai kuma can a ƙasan maƙoshi ya furta, “Hospital”. Da girmamawa TJ ya amsa da, “An gama ranka ya daɗe” yana tada motar. Kansa kawai ya kwantar jikin kujera ya kumshe ido. Har lokacin zufa na faman tsatstsafo masa. Bai ɗago ba har sai da suka isa asibitin. Shu'aibu ya buɗe masa da sauri ya fito. Sai dai banda Laalah shi an barsa a motar. Cikin takun nan nasa ya nufi cikin asibitin Shu'aibu da TJ biye da shi. Tako ina tsirarun ma'aikatan cleaners da ma Nurses da sauransu sai kalonsu suke. Koda suka shiga reception tuni yammatan dake a kan katan sun miƙe bakunansu a washe suna masu Barka da zuwa idanunsu a kansu kamar tsoffin mayu. Ko kallo basu ishesa ba sai su TJ suka amsa musu... Kuka na gama zabgama mama Balki akan nifa yau ko su sallamen daga asibitin nan kona gudu gida. Dan bazan sake kwana banje naga halin da Ummie ke a ciki ba. Lallashina taitayi akan nayi haƙuri jikina ya ƙara ƙyau tunda doctor tace sai nan da kwana biyu, jikin Ummie kuma da sauƙi sosai. Tirjewa nayi akan nifa sai na tafi. Ganin yanda nake zabga uban kuka yasa Maman cewa shike nan naje nayi wanka idan Alhaji Ƙarami yazo anjima itama zata sake masa magana da kanta. Badan naso ba nabi umarninta. Kamar kullum sai da ta fara taimaka min na shiga ruwan zafi na mintuna goma sha biyar zuwa ashirin da nake yi sau uku a rana. Sannan ta fito akan nayi wankan bara taje ta dawo. Wankan na ƙarasa batare da tunanin kowa zai iya shigowa ba na fito ɗaure da towel kawai. Dan masu shara tun sanda zan shiga cikin ruwa Mama Balki ke cemin sun shigo aikinsu. Haka dama sukeyi, kullum tunda sassafe zaki gansu, wani lokacin ma ana idar da sallar asuba. Daga nan kuma sai da rana, sai kuma yamma. Fes kuwa na samu ɗakin harda turaren wuta sun kunna. Jikina na goge da ɗan hanzari. Bana son Mama Balki ta shigo ban saka kaya ba duk da nasan ko tazo ɗin tsayawa take bakin ƙofa sai ta tambayi na shirya sannan ta shigo, dan kunyarta nake ji matuƙa. Ƴar jakar kayanmu na buɗe na ciro b&p da zan saka dan ni ina amfani da kayan asibitin ne. Bra ɗin na fara ƙoƙarin sakawa da sauri-sauri, na saka hannu ɗaya ina ƙoƙarin saka ɗayan kawai ya zaro ta baya. Fuska na ɓata kamar zan fasa kuka, abinda dai nake gudun sai ya faru, tunda dole na jira Mama Balki tazo ta maƙala min ko kuma na cire na sake sakawa tazo ta sameni, amma bari muga na gwada dai kozan iya nawa ƙoƙarin. Kicin-kicin maidawa na fara ina famar cizar lips, sai kawai naji saukar lallausan hannu mai bala'in sanyi akan nawa dake riƙe da hannun bra ɗin. Tabbas wannan ba mama Balki bace, dan wani irin mayataccen ƙamshi ne ya shiga ratsa ƙofofin hancina. A birkice na juyo gaba ɗaya na nama manta da wani batun saurin da nakeyi. Saukar idanuna cikin lulu cat ɗin nashi ya sani ja baya jikina har tsuma yake. Shiko ko gezau, sai ma wani irin kallon ƙurilla yake bina da shi idanunsa a shanye. Inda naga ya kafama idanun nima na kalla da sauri, ai da sauri na naɗe hannayena a wajen ina tura baki kamar zan fasa kuka. Kafaɗa ya ɗan ɗage tare da taɓe baki irin shi baiga abin kallo ba, ina ƙoƙarin sake juya masa baya sai kawai ya shiga takowa a hankali. Baya na sake jan jikina yana cigaba da biyoni duk na ruɗe. Jin na dangane da abu yasa na juya da sauri na kalla, sai naga bangone, tashin hankali anzo the end kenan inji bature. Banda zaɓin daya wuce kawai na juya masa baya na kalla bangon. Idanuna a runtse murya na rawa na ce, “Wai da ALLAH minene haka kake yi? Ni dai ka fita kayafa zan saka, sai Mama ta shigo ta ganka”. Maimakon amsa min ko ya fitan sai kawai naji ya saukar hannunsa akan kafaɗata, da ƙarfi na sake matse idanun nawa jin yanda yake wani irin tafiya da yatsun kamar mai yi da gayya........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏_ .......Hannun bra ɗin ya maƙala min a inda ya zare, a tunanina zai matsa ne sai naji saɓanin hakan. Matsoni ya sake yi ta yanda har nake jin saukar numfashinsa a saman wuyana, sai kuma ya saƙalo hannun nasa ɗaya ta saman cikina. Yanda na sake matsewa a bangon bai hanashi jawoni baya ba a hankali, kansa ya ɗoro a saman kafaɗata tattausan gashin kumatunsa dake da laimar da nake ƙyautata zaton zufa ce tunda sports wear ne a jikinsa na gugar gefen fuskata. Ɗayan hannun ya ɗaura a saman nawa dake rufe da ƙirjina har yanzu zai zame, aiko naƙi yarda na sake ƙanƙamewa. “Na cire towel ɗin kenan?”. Soft voice ɗin sa dake fita low sosai cikin maƙoshi ta ratsa kunnuwana. Kaina na girgiza masa alamar a'a idanuna na cika da ƙwala. “Oya remove your hand kona ciresa tas”. Nasan zai iya, dan kaɗan daga ƙaramin aikinsa ne. Dan haka na shiga zamesu a hankali hawayen da nake maƙalewa na sake taruwa cikin idanun. Sake matsesu nayi jin yanda yake jan towel ɗin a hankali, har ya gama sauke b ɗin kan jikina babu kunya babu tsoron ALLAH ya gyarata ta zauna da ƙyau sannan ya maida min towel ɗin a sama. “I love white musamman yanda wannan ta miki ƙyau”. Ya faɗa cikin kunnena cikin raɗa. Da sauri na toshe kunnena tare da ture masa kai dan bana ma son ji. Maimakon ya barni kamar yanda naso sai ma ya sake nanne ni da jikinsa tare da sumbatar wuyana da hannun dana toshe kunnen. Ni kaɗai nasan kalar masifaffiyar kunyar da nake a ciki da mamakin tasa rashin kunyar dan shi komai yana yinsa ne kansa tsaye. Mun kai tsahon mintuna biyu a haka sannan ya janye jikinsa a nawa tare da kama hannuna. Ban buɗe idanuna ba, sai alamar zaunar dani da naji yayi a bakin gado. Jin kamar ya jawo kujera ya zauna gab dani dan har ƙafafunmu na a cikin na juna ne ya sani buɗe idanuna dake mar-mar. Kamar yanda nayi hasashen hakanne kuwa. Ya jawo kujera gab da ni ya zauna hannunsa ɗauke da rigar asibitin da aka ajiye min a saman gadon. Idanunsa kan p ɗin dana ajiye. A zabure na kai hannu na ɗauke ina ɓata fuska kamar zan yi kuka na cikukuyesa a hannuna na tura ƙarƙashin cinyata. Mayatattun idanunsa ya zuba min tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Hand”. Bani da zaɓin daya wuce miƙa masan kawai, dan nasan ko cewa nayi bana so bazai barni ba. Inaji ina gani ya saka min rigar sannan ya miƙar dani a gabansa kamar wata ƴar yarinya ya zare towel ɗin ya ajiye gefe. Hannu ya miƙa min wai na bashi p ɗin dana sake saurin ɗaukewa. Kafaɗa na maƙe masa ina juyar da kaina gefe. shima sai ya taɓe nasa bakin kawai. Turaren dana ajiye gefe ya ɗauka ya ɗan duba jikinsa, sai kuma ya ɗan sake taɓe baki kaɗan, batare da yace komai ba ya ɗan fesa min ya maida ya ajiye. Ni dai uffan bance masa ba, kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hannuna. So nake na tambayesa yaya Ummie amma duk ya dabaibaye ni da salon da ban taɓa zaton gani daga garesa ba. Gashi duk abin nan da yake fuskar nan na'a tsukenta kamar bashi keyi ba. Da ƙyar na iya dauriyar faɗin, “Ina kwana? Yaya jikin Ummie?”. Jin shiru bai amsa ba ya sa na ɗago idanu na a hankali kamar wata matsoraciya. Kamar yanda nayi zato shima nasan a kaina suke, dan haka da gudu nai yunƙurin kauda nawa amma sai ya riƙo haɓata da yatsunsa biyu. “Ina miki aiki bazama kince kin gode ba”. Baki na tura masa. Cike da ƴar jarumtar dana tattaro a tsiwace nace, “To ni dai ai bance ina so ba”. Maimakon ya bani amsa sai naga ya saki wani shegen murmushi. Cike da suɓutar baki da mamaki na ce, “Lah yau ma kayi murmushi”. Janye hannunsa yayi, tare da tsuke fuskar. Ni sai ma abin ya bani dariya. Sai kace wani ɗan yaro. Dariya nayi ina ƙoƙarin kare bakina na ce, “Ikon ALLAH, to kai baka so ace kayi murmushin ne? Sai kace wani abun mugun abu. ALLAH idan ma kayi murmushin kafi ƙyau. Amma kullum fuska a ɗaure kamar wani ma'aikin mutuwa.” na ƙare maganar ina haurawa saman gadon gaba ɗaya tamkar banga irin kallon da yake faman bina da shi ba. Sai da naja bargon na rufe ƙafafuna sannan na kuma marairaice fuska. A hankali na ce, “Yaya Awwab!”. Shiru yaƙi amsa min, sake maimaita kiran sunan nashi nayi a shagwaɓe. “Yaya Please answer me”. Nan ɗin ma kamar bazai amsa ba. Na sake ƙoƙarin yin maganar cikin harara ya katseni da faɗin, “Ba kunni ke ji ba ne”. Baki na tura sosai. Na ce, “To ai dai ba daɗi mutum yayi magana aƙi amsa masa.” Banza yay min bai tanka ba. Nima sai na cigaba da faɗin, “Dan ALLAH ka taimaka a sallaman yau a asibitin nan. Idan ba hakaba ALLAH zan gudo gida. Ina missing ɗin Ummie sosai. Ni wlhy na warke fa”. “Na gani”. Ya faɗa kamar bashi ba yana ƙoƙarin yaye bargon dana rufama ƙafafun nawa. Da sauri na waro idanuna ina riƙe hannunsa. Kaji mun mutum to mizai gani?. Shanyayun idanunsa ya ɗago ya zuba min, ni kuma na marairaice fuska har idanuna na tara ƙwalla. Hannun ya janye kawai batare da yace min komai ba. Nima sai na sauke ajiyar zuciya dan al'amarin wannan mutumin yasha kan nawa ƙaramin tunanin gaskiya. Sake matsar da kujerar da yake zaune yayi gaban side drawer. Batare da yace komai ba ya shiga ƙoƙarin haɗa tea dan akwai babban basket mai murfi dake cike da kayan shayi kala-kala da su chocolate da kullum Hayatu baya gajiya da sayowa. Yo ni Hayatu ai zance tunda dai shine ke zuwa da su. Banda jiya da bai zo ba ɗayan yaron nan nasa da har yanzu ban san sunansa ba ya kawo snacks. Tea ɗin ya haɗa a zatona shine zai sha, har na fara gulmarsa a zuciyata sai naga ya miƙa min mug ɗin. Tsayawa nayi kawai ina binsa da kallon mamaki, dan haka muka ƙurama juna ido. Kusan minti ɗaya muna a haka kafin ya janye nasa da suke juyewa golden ƙwayar tsakkiya na zama siririya a wani irin salon yuuu ya ɗan lunshe su. Nima nawan na ɗauke da sauri ina haɗiyar wani yawu mai kauri dan gaba ɗaya jinai maƙogwarona ma ya bushe. Kofin ya ƙara miƙamin kansa a gefe, sai kuma ya miƙe. Haka kawai kallon nima yay matuƙar min tasiri a cikin jiki da ma jinina, dan haka na gagara sake kallon inda yake har ya buɗe ƙofar ya fita. Ajiyar zuciya mai nauyi na sauke tare da rumtse idanuna na cije lips da ƙarfi. Tea ɗin na cigaba da sha da ɗan zafi-zafi batare dana san abinda nake ba. A haka aka sake buɗe ƙofar, a zatona shine dan haka na gagara ɗaga ido na kalli wajen. Sai da mama Balki ta rangaɗa sallama sannan na ɗago da sauri fahimtar itace. Inda nake ta ƙaraso cike da tsokana take faɗin, “A lallai ɗiyata ta fara samuwa. Yau kece da haɗa shayi da kanki batare dana sha fama ba kina bata fuska da korafin bakinki ba bu ɗanɗano. To UBANGIJI ya ƙara sauƙi.” A hankali nace Amin, dan a zatona bata haɗu da wannan pepper ɗin mutumin ba, sai naji hakan yamun daɗi. Sai dai me, bayan kamar mintuna biyar da zaman Mama Balki sai gashi ya sake dawowa tare da doctor. Miƙewa Mama Balki tayi fuskarta ɗauke da murmushi tana faɗin, “Har an kammala Alhaji ƙarami?”. Cikin girmamawa, muryansa can ƙasa ya ce, “Eh mama sai ku shirya”. Jin abinda ya faɗa ɗin ya sani ɗagowa da sauri na kallesa. Sai muka haɗa ido. Da gudu na janye nawa na maida kan doctor dake min magana ɗan ji nake kamar ma kowa zai gane abinda ya faru tsakaninmu yanzu. Tambayoyi tamun tare da bani shawarwarin yanda zan kula da jikina yanda ya kamata har komai ya ƙarasa dai-daita. Duk bayan kwanaki biyu kuma zata zo har gida koni nazo asibitin za'a dinga sake dubani. Dan ba yau suka so sallamata ba. Sake ɗagowa nayi da mamaki sashen da yake. Yana tsayen dai har yanzu sai Mama Balki ce ke fita da kayayyakin mu tana dawowa alamar a iya ƙofa ake amsarsu. Yanda ya maida hankalinsa akan wayar hannunsa sai naji nutsuwa da alama baya jin duk abinda doctor ɗin ke faɗa. Taimaka min doctor tayi na sakko a saman gadon, hannunta riƙe da nawa ta ce, “Muje ki ɗan tattaka ƙyaji daɗin ƙafafunki tunda kwana da kwanaki kina zaune waje ɗaya babu ko babban motsi. Kaina kawai na jinjina mata, ta ɗauki hijjab da Mama Balki ta ajiye sabo ta saka min da kanta. Har ƙasa hijjab ɗin ya kaimin kamar wanda nake amfani da su a gida. Sai naji daɗi sosai dan yaushe rabo. Ta gabansa mukazo muka gitta bai kallemu ba bai kuma motsa ba har sai da muka fice gaba sannan. Kusan ƴammatan Nurses ɗin nan da suka dinga kulawa dani dasu aka ɗunguma min rakkiya har gaban mota. Sosai motar tai min ƙyau, banyi tunanin yana bayanmu ba, sai da muka iso ina sallama da Nurses ɗin da doctor naga an buɗe masa ya shiga, ba'a rufe ƙofar ba alamar ni ake jira. Ji nai kamar na fasa kuka, dan hakan na nufin a kusa da shi zan zauna kenan. Babu yanda zanyi, dan doctor da kanta ta taimaka min na shiga. Sai da aka maida ƙofar aka rufe har Mama Balki itama ta shiga gaba an ma tada motar muna shirin barin asibitin sannan na lura da shegen karen nan nasa dake tacan jikin waccan ƙofar. Wani irin fasa ƙara nayi tare da daka tsalle na faɗa jikinsa a matuƙar firgice, bazaki gane yanda nake masifar tsoron kare ba wlhy Bily.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏 *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_ ......Da uban sauri TJ ya taka birki dan shima firgita yayi, hakama Mama Balki, ya juyo zaiyi magana da sauri ya kauda kansa dan gaba ɗaya Samraah ta koma saman jikin ogan nasa ne. Mama Balki ma kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kanta tana Murmushi. Shiko gogan tun faɗa masa jiki da tayi idanunsa kawai ya lumshe saboda ƙarar da tai har cikin tsakkiyar brain ɗinsa ya jita. Shi mutum ne da sam baya son hayaniya. Taɓasan da Laalah ya ɗan yi yana gurnani ya sa ya fahimci abinda take ma tsoro. Lumsassun idanunsa ya buɗe, ya ɗan kalli Laalah ɗin sai kuma ya kalleta. Tayi masifar cikuykuye sa daga ita har ƙatoton hujjab ɗinta. Shi sai abinma ya so bashi dariya. Amma sai ya danne baiyi ba. Cikin silent voice ɗin nan tasa yay kiran sunan TJ. Amsa masa yay da girmamawa, sai kuma ya buɗe motar ya fita. Kasancewar glass ɗin ta inda Laalah yake an saukesa ya sa ya ɗan duƙo ta wajen sai dai kansa a ƙasa ba kallonsu yake ba. Maimakon amsa masa sai ya ɗan shafa kan Laalah ɗin tare da furta, “Maidashi wajen su Shu'aibu”. Kaɗa bindi Laalah yay alamar dai yaji ubangidan nasa. Tj na buɗewa ya dira da kansa. Duk abinda suke ina jinsu. Ina jin ya fita na sauke ajiyar zuciya mai nauyi tare da zame jikina daga kan nasa. Ban yarda na kallesa ba na koma can jikin ƙofa na lafe. Ban kuma sake yarda na ɗago ba har muka iso gida. Sosai naji wani irin farin ciki da zaƙuwar ganin naje ga Ummie, dan bazan ɓoye miki ba har cikin tsakkiyar rai nake jin ƙaunar baiwar ALLAHr nan wlhy bily. Ƙagara nayi motar ta tsaya, amma sai bata tsayan ba sai da akaje har ƙofar sashensa. Muna fitowa ina zumuɗin tafiya na koma waccan ƙofar Mama Balki ta dakatar da ni, magana na ɗago zanyi ta dakatar dani, tare da jan hannuna muka shige sashen nasa dan shi tuni yama shige abinsa. Mamaki ne ya kamani, yanzu kam kasa haƙuri nayi sai da nai magana kamar zanyi kuka. “Mama mi kuma zamuyi anan? Dan ALLAH mu tafi sashenmu ko wajen Ummie”. Kanta tsaye ta ce, “Banda ikon yanke wannan hukuncin Samraah. Sai dai mu jira daga bakin Alhaji ƙarami”. Sosai mamaki ya ƙara kamani, zan sake magana ta kama hannuna tai ciki dani. Zaune muka samesa a falo TJ na ajiye masa kofin coffee daketa tururi alamar yanzu nan ya haɗo masa shi. Tj ne ya amsa sallamar tamu, amma shi ko kallon ta inda muke ma baiyi ba. Wajen zama Mama Bilki ta nuna min, ban musa mata ba na zauna fuskata a kumbure. Kobi takaina batayi ba ta juya ta fita. A zatona wani abu zata ɗakko ta dawo, sai naji shiru har tsawon wasu mintuna. Ga TJ shima ya fice da ga ni sai shi. Karo na farko cike da ƙosawa na ɗaga kai na kallesa. Coffee ɗin sa yake sha hankali kwance tamkar ma bai san da zamana a wajen ba. Jinai raina ya sake ɓaci, amma sai na danne murya a sanyaye na ce, “Dan ALLAH zanje wajen Ummie na ganta”. Kamar bai jini ba, sai da ya mula dan kansa sannan ya ɗan ɗago idanunsa ya kalla ta inda nake. Dai-dai na ɗan hararesa ni kuma batare da tunanin zai ɗago ɗin ba. “Oh hararata ma kike?”. Ya faɗa fuska a dake. Da sauri na marairaice fuskata kamar bani ba, cikin kalar tausayi na ce, “No ALLAH ba haka bane. Kawai an samu kuskure ne ni yazan harareka”. Na ƙare maganar a matuƙar karyar da kai. Ɗauke idanun nasa yay cike da basarwa ya cigaba da shan coffee ɗinsa. Naji tamkar na fasa ihu kona kamashi da duka. Amma duk babu dama. Sai kawai na dake tunda na fahimci ƴan wulaƙancin ne a kansa.... 🌜💮🌛 Kamar kullum tsaff ta fito cikin gayunta. Arwa ce riƙe da handbag ɗinta tana mata shagwaɓar ta bata kuɗi. Itako sai faman latsa waya take tana tafiya kamar ma bata jin ɗiyar tata. Sai da suka gama sakkowa da ga upstairs ɗin sannan ta miƙa mata hannu alamar ta bata handbag ɗin. Sake marairaicewa Arwa tayi da maida hannunta baya ta ɓoye jakar. “ALLAH Ummy ni bazan baki ba, just 200k fa nake so bawani kuɗi masu yawa ba. Gift da zan sayama Lubnah yau birthday ɗinta. Kuma motana fa nace miki duk friend ɗina sun sanni da shi, dan ALLAH ki bani baƙin naki, ALLAH bazanyi tuƙin banza ba i promise ”. “Riƙe promise ɗinki. Dan bazan baki motana ba. Ga dai 100k nan na saka miki je kiyi manage da shi banda kuɗi yau. Give me my bag jare. Kuma ki tabbatar kin dawo gidan nan kafin ten na dare. Dan karna shigo ban sameki ba. Zan ɓata miki rai”. Baki cike da iska Arwa ta miƙa mata handbag ɗin, babu ko godiya ta juya fuuuu ta koma sama. Kai kawai Hajiya ƙarama ta girgiza ta juya tai tafiyarta. Babu kowa a falon sai su A'i dake gyarawa. Gaisheta sukeyi cike da girmamawa. Itako tana amsa musu a nutsen nan nata babu alamar hayaniya a tattare da ita. Daka ganta kaga mace mai haƙuri da iya zama da mutane. Compaund ta fita, kai tsaye tai wajen motarta dan ita sam bata da driver. Bata yarda da kowa ba ita ke tuƙa kanta, tana ƙoƙarin ajiye handbag ɗinta a side ɗin mai zaman banza dai-dai nan Hajiya Mammah ke fitowa itama cikin wani shegen shiga na manyan mata dake ji da kansu. Kallon juna sukai, amma sai Hajiya Mammah ta watsar da Hajiya ƙaramar tamkar bata ganta ba ma. Lips Hajiya ƙarama ta cije tare da faɗin, (zanyi maganinki ne) a zuciyarta. A zahiri kam sai ta saki murmushi tare da nufar Hajiya Mammah ɗin cikin girmamawa ta gaisheta. A ɗage Hajiya Mammah ta amsa tana ƙoƙarin shigewa motar da drivern ta ya buɗe mata. Itama sai Hajiya ƙaramar tai murmushi ta juya ga tata motar ta shiga. Kusan a tare suka fice a gidan. Sai dai suna fitowa babban titi kowa yay hanyarsa. Ita Hajiya Mammah gidan Baba prof ta nufa, itako Hajiya ƙarama asibiti ta nufa... ⭐⭐⭐ Gidane babba mai ƙyau kuma sosai. Ga masu aiki tako ina nakai kawo maza kai kace akwai wasu mutane da yawa a ciki. Guri drivern Hajiya Mammah ya samu yayi parking, sannan ya fito cikin rawar jiki ya buɗe mata, sai faman cika take da batsewa wa ma'aikatan dake ta faman gaisheta da girmamawa. Ko sau ɗaya bata amsa musu ba, sai ma tana fitowar tuni wani yazo ya amshi handbag ɗin hannunta dan sun san halinta sarai. A yatsine take bin jibga-jibgan motoci ukun dake fake a compaund ɗin wanda bata san da su ba a gidan da kallo. Cike da isa ta dubi wanda ya amsa mata bag ɗin ta ce, “Waɗan nan motocin fa?”. Muryarsa har rawa take wajen bata amsa da, “Na baƙine da Alhaji yayi ranki ya daɗe”. “Baƙi?”. Ta maimaita da sigar tambaya, sai dai kuma kafin ya bata amsa tayi gaba bakinta a taɓe. Bayanta yabi da sauri. Kanta tsaye ta shiga ta main perlor ɗin gidan ta shiga ainahin falonsu. Babu kowa a ciki, sai ƙamshin air fresheners dake tashi da kuma ɗan sanyin ac kamar ba safiya ba. Baba kam akwai son tsafta. Duk da rayuwarsa yake shi kaɗai a gidan babu mace zaka samu komai tsaf-tsaf. Dan tunda mahaifiyarsu ta rasu bai sake aure ba. Suma kuma ko yace zai yi ɗin bazasu bariba wlhy. Dan yanda ba'ama uwarsu kishiya tana raye ba bayan ta mutu ma baza'ai mata ba. Zaune takai saman luntsuma-luntsuman kujerun falon. Tuni ta wani lume a ciki dan sunada bala'in taushi. Baban nasu ɗan gata ne, dan duk shekara sai Awwab ya canja komai na gidan an sake masa sabon fenti. Kukun gidan daya fito ne yana gaidata ya katse mata tunani, a ɗage shima ta amsa masa fuska a yamutse. Har zai juya ta dakatar da shi, umarnin haɗa mata breakfast ta bayar. Cike da girmamawa ya amsa mata yana komawa ciki. Babu jimawa kuwa ya kammala komai ya kawo ya ajiye gabanta. Zama ta gyara da ƙyau ta fara kwasar girki tana chart da Rubayya dake ƙara tsara mata yanda zata tunkari Baban. A haka Baba prof ya shigo falon ya sameta. Kanta dake duƙe ta ɗago ta kallesa, yana sanye cikin farar jallabiya tas data ƙara fiddo tsufarsa. Dan bashi da wani jikin kirki, gashi dogo masha ALLAH kamar dai su Paah dan duk shi suka biyo har su Maash duk tsahonsa ne. Kanta ta ɗan rissinar tare da faɗin, “Barka da fitowa Baba”. “Yauwa Nafisatu kece a gidan?”. Ya faɗa yana kaiwa zaune. Murmushi tayi, tare da sake rissinawa ta shiga gaishesa. Da kulawa ya amsa mata yana tambayarta mutanen gidan da jikin Ummie. Cikin ɗan ɗage kafaɗa ta ce, “Da sauƙi to Baba. But ba shiga nake ba dan tun dai randa ta faɗin nan gaskiya”. Fuskarsa a ɗan ɗaure yace, “Ban gane ba?”. Fahimtar katoɓarar da tayi yasa ta ɗan ƙaryar da kai gefe. “Baba ba wani abu nake nufi ba fa. Wlhy ina jin tsoro ne shiyyasa. Kasan idan Ummu-Hidaya na'a wannan yanayin akwai haɗari shiga inda takene. Amma nasan da sauƙi gaskiya, tunda kaga ba'ai kiranka ba”. Kansa ya jinjina cikin nuna gamsuwa. Ita kuma ta sauke numfashi. Sai kuma tayi murmushi da sake ɗan dubansa. “Baba wai motocin suwaye na gani haka a gidan nan?”. Hannunsa ya ɗan yarfar da taɓe baki, sai kuma ya ɗauka black tea ɗin da kuku ya kawo masa ya fara kurɓa, sai da yay kusan sau uku kafin ya kalleta. “Shugaban jam'iyyar ACC ne na ƙasa da wasu ministoci guda biyu. Suna damuna a kwanakin nan akan son na shiga siyasa. Ni kuma abinda bai taɓa birgeniba kenan Nafisatu. Yanzu ma shugaban ƙasa ne da kansa ya turosu. Ni dai na faɗa musu gaskiya ina akan bakana. Amma sun dage matuƙa. Shine nace suje zanyi shawara”. Cike da zumuɗi da zamala Hajiya Mammah ta gyara zamanta. Gaba ɗaya 32teeth ɗinta washe suke. “Amma Baba mizai hana ka amshi tayinsu. Ni banga wani aibu ba a siyasa ai. Sannan kowane irin sharuɗɗa ka cikasu da ko ɗar bazakaji na shiga ba. Tayinfa kujera suke maka mai matsayin farko a jihar nan. Zamu kasance cikin matuƙar farin ciki a kiramu first family na wannan state mai girma irin Lagos. Baba dan ALLAH ka amsa”. Ta ƙare faɗa cikin shagwaɓa. Ajiyar numfashi ya sauke tare da gyara zamansa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ____________ .......Tsahon lokaci muna zaune shiru batare da ya sake magana ba. Coffee ɗinsa kawai yake sha a hankali yana kuma daƙilar tab da ke a saman ƙafarsa da yay crossing. “Wane hukunci kika yanke?”. Tambayarsa ta iso cikin kunnena a bazata. Ɗan ɗagowa nayi na kalla inda yake, dan da farko ma banyi zaton shine yay maganar ba. Yanzu ɗin ma daƙilar tab ɗin kawai yake, dan haka na ce, “Wai kaine kayi tambaya?”. Ɗago manyan idanunsa yayi a hankali ya kalleni. Sai kuma ya sake maidasu kan abinda yake yi. A taƙaice ya ce, “Uhmm”. Ajiyar zuciya na sauke da faɗin, “Okay. Amma ban gane tambayar ba. Akan mi kake nufi?”. “Komai!”. Ya faɗa can ƙashan maƙoshi. Jimmm kawai nayi ina tunani bayan na sake maimaita komai ɗin a zuciyata. Kai gaskiya ban gane ba, dan duk da ina zargin ahalinsa ai nake ga bai dace na fito fili na nuna ba, tunda ba sanin nasan tarihin gidansu yay ba. Gara idan shine ya sanar min wani abu ai. Fuska na marairaice a sanyaye na ce, “ALLAH kuwa Ya Awwab ban gane ba”. Komai baice min ba. Yanzu ma ko ɗagowa ya kalleni ɗin baiyi ba. Kusan mintuna biyu ya ajiye kofin coffee ɗin da yake sha sai kuma ya gyara zamansa. Da hannu yay min alamar nazo. Idanu na waro masa alamar mamaki, amma sai ya ɗauke kansa cike da basarwa yana sake tsuke fuska. Banda zaɓin daya wuce bin umarninsa. Dan sam bazan iya musa masa ba. Ina jinsa da wani irin girma da kima fiye da ko yaushe a yanzu. Sannan wani irin shakkarsa nake ji, kwarjinin sa gaba ɗaya ya cika falon har ina jin yama mana kaɗan. A hankali na miƙe kamar wadda tai laifi take tsoron duka. Dan da sanɗa na isa gabansa. Ƙoƙarin kaiwa ƙasan carpet nake ya min nuni da saman cinyarsa. Kaina na maƙe masa alamar a'a, sai ya ɗan taɓe baki ya nuna gefensa batare da yayi magana ba. Dole na canja na koma kan kujerar gefensa dai na zauna. Sai kuma na ɗan saci kallonsa ta gefen ido. Da sauri na maida kaina ƙasa dan dai-dai shima yana ɗagowa ne. Wani irin ratsawa muryarsa ta sake min har cikin kaina, duk da kuwa yayi maganar ne ba cikin tsawa ko hayaniya ba, dan ko a falon kake ba lallai ka jisa ba dan nima na kasance gab da shine. Amma ban sani ba, kodan sai da ya kamo yatsun hannuna cikin nashi tattausan hannun ne sannan yay magana oho. Sake matsa yatsun nawa yay a hankali ina kuma jin kaifin idanunsa har cikin jijiyoyin da jinina ke yawo. “Idan nace komai ina nufin ina nufin komai da komai. Nasan zuwa yanzu kin san wanene Awwab a zahirance da baɗinance. Dan kinji komai a wajen Mama, kin kuma san komai a makwancinsa”. Da sauri na ɗago ina ware idanuna duk da zancensa na ƙarshe ya bani kunya. Cikin ɗan rawar lips da nuna mamaki na ƙarara akan fuska na ce, “Ya akai ka sani mama ta faɗa min?”. Wani ɗan makirin murmushi ya sakar min da lumshe idanunsa sai kuma ya buɗesu luuuu ya zuba su a cikin nawa. Ƙyaƙyƙyafta idanu na fara da ƙoƙarin janye yatsuna dake a cikin nasa har yanzu. Amma sai ya hana hakan ta hanyar sake riƙesu da ƙyau yana girgiza min kansa. Sai kuma ya janye idanun kamar a kasalance ya ɗaura yatsarsa manuniya mai ɗauke da dogon farce fari tass har wani ƙyalli yake tsabar yanda yake fes, akan zobena ya saka yatsan yana wani zagayawa. Zoben na kalla da sauri nima dan sam ban gane inda ya dosa ba. Sai da ya gama zagayesa sannan ya zaresa a hankali daga cikin yatsata. Ɗan jujjuya min shi yay akan fuska, sai kuma ya runtsesa a cikin hannunsa yana kallona gira ɗaya a ɗage. “Ke yarinya ne Samrh, tsiwanne kawai yayi miki yawa da shegen kauɗi. Shin bakiyi tunanin taya akai kika zo gidan nan ba haka kai tsaye bayan kin gudu min? Nasan hakan zai iya faruwa, amma dai abune da zai zama mai wahalar gaske musamman idan mukai duba da hannun da kika faɗa....” Kasa haƙuri nayi, cikin tare numfashinsa na furta, “Dama da saninka nazo nan gidan ke nan?”. Idanu ya ɗan lumshe ya sake buɗewa a kaina. A bazata naji saukar hannunsa kan hancina. Ya ɗan jashi kaɗan da faɗin, “Yanda kike stubborn ɗin nan ai sai da kula. In ba hakaba zaki ɓaro min aiki ne ƴar jarida”. Duk da naji kunya sai da na ɗan tura masa baki. A shagwaɓe na ce, “Ai ALLAH kaine stubborn a gidan nan. Ni dama nata wasi-wasi, duk da nasan kaɗan daga ikon UBANGIJI hakan ta kasance. Amma dan ALLAH Ya Awwab ya akayi nazo?”. Shiru yayi kamar bazai tanka min ba. Sai da na marairaice masa kamar zanyi kuka sannan. Yana a kwancensa jikin kujera idanunsa a lumshe yanzu. Hakan ya bani damar zuba masa idanuna ina kallon yanda yake motsa lips kamar abin dole. “Tun a guduwan farko nasan zaki iya maimaitawa. Shiyyasa na samar da zoben nan exactly irin naki ta yanda zan san duk wani motsinki. Kina asibiti a Abuja na sa miki, bayan dinga nuna kin inda kike har magana idan akayi ko kikayi zan iya jinki”. Ya ƙare maganar yana nuna min abinda ke a kunnensa kamar bluetooth sai dai shi ƙarami ne bai kai bluetooth girma ba Cikin ɗan yarfar da hannu da mamaki na ce, “Bala'i, dama kaje asibiti ka duba ni ne? Wlhy naci kai. Taya ban taɓa ma lura da zoben nan ba nawa bane?”. Idanu ya ɗan buɗe yana kallona. Kamar bazai ce dani komai ba sai kuma ya motsa small pinkish lips ɗinsa a hankali. “Saboda ke yarinya ce”. Jinai kamar na harararesa amma bazan iya ba. Sai wani cemin yarinya yake. Amma duk da haka sai da na ɓata fuska. Hannu na miƙa masa na ce, “Bani zoben na gani dan ALLAH”. Idanunsa ya maida ya lumshe. A taƙaice ya furta, “Ya gama aikinsa. Ina jinki mi kika yanke dan bani da lokaci zanyi baƙi”. “Ni ban yanke komai ba, akan samun lafiyar Ummie kawai nake da plans”. Idanu ya buɗe sosai yana kallona. Sai na ɗauke nawa daga kallonsa dan bazan iya jurewa ba. A hankali kamar mai jin tsoro na furta, “Ya kamata Fahad ya dawo gida kamar yanda kowa yake gida”. “Nooo!!”. Ya faɗa a tsawace yana ƙoƙarin miƙewa. Duk da yanda ƙirjina ya buga da rawar da jikina yake yi sai da nai saurin kamo hannunsa. Muryata a karye kamar zanyi kuka na ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri ka zauna. Bafa kaji ƙarshen maganata ba Please”. Ƙin zaman yay har tsawon lokaci. Sai faman huci ma yake yi abin mamaki da tsoro. Hatta da gashin jikinsa duk sun mimmiƙe. Muryata na rawa cike da magiya na sake faɗin, “Dan ALLAH dan ALLAH. Burinka fa shine samun lafiyar Ummie, kuma wannan hanyar da zan faɗa maka in sha ALLAHU ina fatan zata taimaka mana. Kayi haƙuri ka danne duk abinda kake ji game da ɗan uwanka. Dan wlhy komai bazai yiyu ba sai mun haɗa ƙarfi da ƙarfe. Ni, kai, shi, Hayatu, Mama, Baba, da duk wanda ka aminta da shi a cikin yaranka. Idan har wanda baka haɗa komai da su a duniya ba zasu ci arziƙinka yanda suke so har su bama ƴan uwansu kai mi kake jira akan naka gudan jinin ɗaya tilo. Kana ganin idan lafiyar Ummie ƙalau zata barku a cikin wannan halin? Ko a yanzu da take a cikin halin jarabawa wlhy maybe tana jin zafi da kewar rashin ganin ɗan uwanka dan bata san taya zata furta bane kawai. Karfa ka manta shima nan gidansu ne Ya Awwab. Yanda kake da iko da komai na cikinsa shima haka yake da iko da shi dan ko'a addinance matsayin magada masu kaso kai ɗaya kuke amsawa. Duk duniya fa baka da kamarsa, kamar yanda shima baida kamar ka. Duk mu ɗin nan da muke zagaye da kai son zuciya ko wani dalili zai iya sakawa mu gujeka, amma shi komi ka zama bazai daina jin ƙaunarka a zuciyarsa kamar yanda kaima nasan kana ƙaunarsa. Wannan ƙiyayyar dake tsakaninku ƙirƙirarriyar ƙiyayya ce, kune kuma ya kamata kuyi yaƙi da zukatanku wajen ganin kun canjama abokan gaba nasararsu. Kaifa ka tunatar dani ba'aima maƙiyi gaggawa, idan ba haka ba zai rigaka kai inda kake hari harma ya juyo kai baka kai ba. To kenan in har zaka tafin sai ka kasance mai kula gudun kar ya saka maka tarkon da zai riƙeka ya hanaka isar kafin shi ɗin ya iskoka kuma. Dawowar Fahad gidan nan shine first target ɗin mu akan kowa da komai wlhy. Amma na baka dama kaje kayi tunani ka gani, sannan ka nema zaɓin ALLAH. Ni kuma na maka alƙawarin duk abinda ka yanke zanyi biyayya a kansa sai muje plan na gaba, ni dai fatana kawai Ummie ta samu lafiya ne”. Daga haka na saki masa hannu a hankali. Kaina na duƙar na saki kuka. Dan harga ALLAH yanzu wani masifar tausayi yake bani. Bawan ALLAHn nan yana cikin wani irin bahagon ƙulli ne mai tsaurin gaske. Shiyyasa aketa amfani da shi ana azabtar da mahaifiyarsa da ɗan uwansa. Nayi zaton tafiyar tasa zaiyi, sai naga a hankali ya koma ya zauna cikin kujerar tare da dafe kansa da duka hannayensa yay masifar cije ɗan ƙaramin lips ɗinsa kamar zai hudashi da haƙori. Ha jima a haka kafin ya ringa sauke wasu irin zafafan huci da naji ƙarin tsoronsa a raina. Dan tuni na maƙure a cikin kujera kamar mage taga ƙare a lungun mai hanya ɗaya tal.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏_ .......Mun jima zaune a hakan kafin ya mike a fusace. Taku ɗaya biyu ya tsaya cak, batare da ya juyoba cikin kaushin murya ya furta, “Daga yau zaki cigaba da zama anan”. Wani irin zabura nayi yan hanjin cikina na wantsalawa tare da bugun zuciyata. Bamma san sanda na furta, “Anan kuma?”. Ko kallon inda nake baiyi ba yayi wucewarsa hanyar bedroom ɗinsa. Wani irin bugawa zuciyata keyi diff-difff!! Dan har ga ALLAH maganar tashi tayi masifar ratsa min ƙashi da bargo. Wane irin neman bala'ine haka dan ALLAH. Taya zan cigaba da zama a side ɗinsa bayan Mama Balki ta sanar min babu wanda yasan akwai aure tsakanina da shi. Sannan yan uwansa ma abinda ya faru kallonsa suke ama tsayin fyaɗe. “Na shiga uku ni Samraah mutumin nan zai kasheni. Ni wlhy koma ba duk wancan ba bazan iya zaman anan da shi mu biyu kacal ba. Mutumin daya nema kusan kasheni ina gaskiya bashi yiwuwa. Gara ma tun kan wankin hula ya kaini dare na kama gabana. Inama laifin yace na koma sashen Ummie dan ALLAH. Zaram na miƙe, har haɗawa nake da sassarfa na nufi ƙofar fita. Sai dai kuma gam take alamar an kulle. Idanuna ne suka cika da ƙwalla. Ji nake kamar na saki ihu. Na jima a wajen kafin na yanke shawarar zuwa na bashi haƙuri tare da fahimtar da shi illar wannan hukuncin nasa dan bazai haifar mana da ɗa mai ido ba daga ni har shi ɗin.... 🌜🌜💮🌛🌛 “Nafisatu ai ba amsar bane matsalar. Maganar kuma zamowarmu kuma family na farko a jihar nan a tunanina tuni muna ɗaya daga cikin masu wannan matsayin ama Nigeria ba jihar Lagos ba. Ɗanki ya jima da samo mana wannan sunan ama duniya ba'a ƙasar haihuwarmu kawai ba. Siyasa ta wuce duk yanda kike tunani, cike take da rikice-rikice da matsaloli iri-iri. Bazaki gane hakan ba sai mun farata. Amma dai ki bari zan tattauna da Awwab. Kin sanshi yanada experience akan irin waɗan nan abubuwan”. “Baba yanzu nan duk mu yawan yaranka har mu huɗu cif babu wanda zaka iya shawara da shi a shekarunmu sai jika. Awwab har wani hankaline da shi wanda ko aure baiyi ba.” “Humm Nafisatu, aure ai lokacine da shi ko?”. “Baba yana da lokaci, amma kuma kaima ya kamata ka motsashi, yanzu irin wannan abun daya faru idan da maganar nan ta fita mi muke tunani? Ni yanzu ma tsorona ALLAH tsorona yaji daɗi ya cigaba da aikatawa tunda ba kunya garesa ba. Ballema yaga ba'a ɗauki wani mataki ba akai ai kaga abun bamusan kuma ina zai tsaya ba. Tun fa yana taɓa ƴan aiki wlhy wataran kan ƙannensa zai dawo. Dan Awwab yariga yayi gaurin da macen kawai yake buƙata fa. Ya kamata a duba wannan zancen Baba. Idan yana akan bakansa shi baiga wadda yake so ba ai ga ƴar uwarsa nan Azizat. A haɗasu mana kawai tunda Ita dai bazataƙi bin umarninmu ba. Shima kuma idan yaga kowa yaƙi saurarensa ai dole ya amince a wannan karon tunda koba komai yana son asirinsa ya rufu kar duniya ta sani”. Jinjina kai kawai Baba yake. Sai da takai har ƙarshe sannan ya nisa. “Shawararki abar dubawace Nafisatu, kuma zan duba. Awwab ɗinne sai a hankali, yaro ne mai shegen taurin kan tsiya. Yanzu fa ki duba ki gani saboda yasan abinda yay ba dai-dai bane sam yaƙi zuwa gidan nan. Idan naje can duk yanda zai zame ya gudumin ya sani. Amma barshi nasan mi zanyi. Zanzo yau da dare na ritsashi in sha ALLAHU. Da zarar ya shigo gida ki kirani kawai”. Cike da farin ciki Hajiya Mammah ta amsa da, “To in sha ALLAHU kuwa Baba. Amma maganar siyasar nan itama dai dan ALLAH a duba mana. Yaya kaga Nafisatu Adams K/Mashi ɗiyar gwamnan jihar Lagos”. Yanda tai maganar tasa baba ƙyalƙyalewa da dariya. Itama dariyar takeyi.... ❤️❤️❤️❤️ Kamar mai tsoron a jita a hankali nai knocking ƙofar, shiru babu motsin komai. Sake yi nayi har fin sau uku. Ganin dai bazai kulani ba na yanke shawarar buɗewa kawai ma shiga. A hankali na murɗa handle ɗin kuwa. Sai ko gashi ya buɗe. Sai da na sauke ajiyar zuciya tare da tsayawa na daidaita kaina sosai sannan na tura na shiga da sallama. Turus na tsaya ina kallonsa dan zaune yake akan sofa daga shi sai towel da waya a hannunsa yana magana cikin yanayin nan nasa a daƙile kamar wanda akama dole. A hankali na maida ƙofar na rufe ina mai duƙar da kaina dan bazan iya jurar kallonsa a yanda yake ba. Nafi minti biyu a wajen ina sauraren wayar tasa dana fahimci da Hayatu yake yinta. Sai dai abinda ya ɗan ja hankalina jin yana faɗin idan sun huta Hayatun ya kawosu nan gida. To ko su waye keda irin wannan matsayin haka. Dan na fahimci tunda nazo gidan nan ban taɓa ganin wani baƙo daya shafesa ba yazo. In banda ranar birthday ɗin nan da Bahijja tace min wanda suke zaune a waje ɗaya abokansa ne, kuma duk ba'a ƙasar suke ba idan ka cire ɗan sarkin Lagos ɗin. Ganin har ya kammala ya miƙe yana ƙoƙarin nufar mirror ya sani gyara tsaiwata. Dan ya wani basar tamkar baima ganni ba. Kuma na san yasan na shigo ɗin rainin hankalinsa ne kawai. Kaina a ƙasa daga ƙofar ɗakin na furta, “Dan ALLAH ina son muyi magana”. Bai tanka min ba, bai kuma fasa abinda yake ba. Sai da ya mula dan kansa kusan minti biyu sannan ya magantu. Cikin silent voice ɗin nan tasa a daƙile ya furta, “Ki wuce wanka baƙi zasu shigo”. Ji rainin hankali, ina masa wata maganar yana min wata. To ina ruwana da wasu baƙinsa. A zahiri kam sai na ƙara sauke murya har lokacin kan nawa a ƙasa. “Dan ALLAH kayi haƙuri ka barni naje can inda na saba. Ko kuma na koma sashen Ummie tunda dama a yanzu kusan acan ɗin nake. Ya Awwab taya zan dawo nan bayan kasan akwai matsala. Babu fa wanda yasan akwai wani maganar aure a tsakaninmu a gidan nan. Mi kake tunani zasu fassara zaman nawa?”. “Su fassara duk yanda yay musu! Idan kuma kina buƙatar su sanin ne, yanzun nan sai na tarosu su sani”. Da sauri na ɗago ina kallonsa. Yanda yay maganar kansa tsaye babu wani alamun ya ɗauki zancena da muhimmanci. Kai wlhy stubborn mutumin nan ya fara isata. Da ƙyar na iya dannewa muryata na ɗan rawa na ce, “Idan kai zaka iya fuskantar su ka kuma ɗauka komai wlhy ni bazan iya ba. Sannan ba wannan rigimar nake so ba yanzu lafiyar Ummie ce damuwata. Dan ALLAH ka duba zance na yana da muhimmanci...” “Kin dameni Madam wuce wanka kafin nazo kanki”. Ya faɗa da ɗan kaushin harshe yana ajiye cumb ɗin hannunsa yana barin wajen. Karan farko naji hawaye sun gangaro min. “Karna fito na sameki a wajen”. Ya sake faɗa dai-dai yana shigewa cikin cikin closet ɗinsa. Hannuna na dunƙule kamar zan kaima bango naushi sai kuma na tausayama kaina dai. Dan nasan nice zan sha wahalar a ƙarshe hannunna ya rugurguje a banza. Hararar inda ya shige ɗin nayi ina cizar lips ɗina da ƙarfi, ga hawaye share-share a fuskata. Jin motsin kamar zai fito ya sani zabura na nufi bathroom ɗin. Dole ina ji ina gani na haɗa ruwan wankan nai ƙoƙarin fara yi. Wankan nake ina hawaye da hango irin bala'in da zai iya biyo baya. Dan wlhy abin bazai zama mai sauƙin ba a gareni. Gara sashen Ummie da nake zama shi wannan suna ganin ai kamar ina cutuwane shiyyasa aka ɗagamin ƙafa. Amma nan fa? Ni kaina idan an titsiyeni ban san mizan ce ba. Dan nayi alƙawarin in har bada kansa ya fito ya bayyana musu wacece ni ba wlhy ko za'a kasheni bazan faɗa ba. Sai da na kammala wankan sannan hankalina ya tashi, dan ban san yaya zanyi da kayan sakawa ba kuma. Bathrobe ɗin sa na ɗauka na saka. Sallar walha da nake son zuwa nayi dan lokacinta yayi ya sani haƙura na fito, amma sai da na leƙa cikin ɗakin sannan. Shiru babu motsin komai, sannan a iya hangena ban hango alamar akwai mutun ba. Ɗan ajiyar zuciya na sauke na fito a ɗan ɗarare. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ganin tabbacin baya ɗakin, tunanin sauri na shafa mai yazo min, dan haka na nufi gaban mirror ɗin nashi. Zama nayi tare da bin kayan dake akai da kallo, cikin ɗan taɓe baki na furta, “Sai kace mace”. Da ƙyar na iya gane man shafawa, ina son na fara dubashi ina tsoron yin jinkirin da har zai dawo ya saman a wajen. Da sauri-sauri na shafa man da duk abinda zan iya amfani da shi a wajen. Na miƙe raina fal tashin hankalin kayan daya kamata ace na saka ya shigo. Daburcewa nayi dan abin yazo min a bazata. Rasa makamar riƙewa ta sani komawa kan stool ɗin kujerar na zauna tare da duƙar da kaina. Baiyi magana ba, sai madaidaicin akwati da yazo ya ajiye gab dani. Juyawa yay yayi ficewarsa yana faɗin, “Zanje wajensu, da munyi salla zasu shigo. Zaki iya zuwa duba Ummien kafin”. Daga haka yay ficewarsa. Da kallo na bisa duk kaina duk a ɗaure. Sai dai furta zan iya zuwa duba Ummie ne yay matuƙar wanke min zuciya. Mikewa nai cike da zumuɗi harda daka tsalle dan farin ciki, tuni na nema damuwata da tunanin wasu baƙi da ya ishi mutane da zancensu na ɗauki akwatin daya ajiye ɗin. Saman gado na kaisa na buɗe.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏_ .......Kayane ɗinkakku har kala biyar, sai kayan ciki b&p 12-12. Sosai naji kunya ta kamani. Wani gefe na zuciyata kuma na mamakin inda yasan seize ɗina. Hatta da ɗinkunan dai-dai jikina cif. Zumuɗin tafiya wajen Ummie ya sani ajiye komai gefe na shirya cikin doguwar rigar lass pink mai ƙyau mara nauyi kuma. Komawa nayi gaban mirror ɗin ina kallon kaina fuskata cike da murmushi. Na dawo Samraah ta ƴar jarida ƴar gayu. A take yaya Musaddiq yazo min a rai. Hawaye naji sun cika min ido na kewarsu. Tunda abin nan ya faru bamuyi waya ba. Dolene idan na dawo wajen Ummie na roƙesa aron waya nayi kiransu har su aunty Zakiyya ma. Da wannan tunanin na ɗauki turarensa na fesa tare da ɗaukar ɗankwalin nai simple ɗauri. Mayafin cikin akwatin guda uku na ɗauka ɗaya nayi salla dan babu hujjab. Ina idarwa na miƙe cike da zumuɗi na tattare duk kayayyakin dana baza na maida bathrobe ɗin danai amfani da ita da towels ɗin daya cire na maida bayin. Sake ɗan gyara fuskata nayi da faran fauda ɗin dana gani sannan na fice. Nayi mamakin ganin falon ƙal yanzu yana zuba ƙamshi ga sanyin ac duk da dai ɗazun ma ba wani datti bane. Amma daga gani yanzu kasan an sake gyarashi. Kaina tsaye na fito batare da jin damuwar idan na haɗu da wani yaya zanyi ba. Koda na shiga sai da na sauke ajiyar zuciyar jin daɗin ganin babu kowa a falon. Dama ba lallai na samu masu aiki ba, dan yanzu lokacin hutu ne an gama na safe sai kuma azhar tayi. Kaina tsaye na haye sama harda ɗan guduna. Naji matuƙar farin cikin samun sashen Ummie fes da shi, ga ƙamshi na tashi tako ina. Da alama aikin Mama Balki ne kuwa. Ilai kuwa a ciki na sameta tana bama Ummie abinci. Da gudu na naje na faɗa jikin Ummie ina mai sakin kuka. Dariya Mama Balki ta sanya min, niko ko'a jikina murnar ganin Ummie kawai nakeyi. Sai da na gama murnata na ɗago ina kallonta. Itama kallona kawai takeyi kamar ta samu television. Murmushi na sakar mata idanuna cike da ƙwalla na ce, “Ummie na i miss you”. A bazatar da ta bamu matuƙar mamaki mukaga ta saki murmushi tare da kai hannu ta shafa kaina. Sai kuma ta saki kuka. Ruɗewa mukai mu duka. Ƙoƙarin miƙewa nake a jikinta amma sai ta riƙeni da ƙyau, sai kawai na sake rungumeta nima ina kukan. Mun jima a haka kafin na ɗago jin kamar jikinta ya saki. Mama na kalla, ta sakar min murmushi itama tana share ƙwallar idonta. A raunane ta ce, “Tayi barci. Dan tasha maganinta bayan na gama bata abinci. Gani nayi ga sake jawo kwanon sai nayi zaton bata ƙoshi ba shine na sake zaman bata kika shigo.” Nawa hawayen nima na share. Sai kuma na tashi a jikinta muka taimaka mata ta kwanta. Zama nayi a kusa da ita hannunta cikin nawa ina jin matuƙar farin ciki da ganinta. Sai matuƙar tausayinta dake cimun rai da zuciya dan duk ta rame min a ido alamar ciwon ya bugeta sosai wannan karon... 🩸🩸🩸🩸 “Kamar ya an sallamesu? Waye ya sallame sun?”. Ta faɗa cikin daka tsawa. Ƙanƙame jiki nurse ɗin tayi jikinta na rawa. Cike da tsorata da birkicewar Hajiya ƙaramar ta ce, “Am sorry Maa. Wlhy ni ban san wanda ya sallamesu ba, naga kawai sun fito ne amma Dr Larai ce ta musu rakiya har mota. Muma ganin haka yasa muka rakasu”. Wani irin tashi sama jijiyoyin Hajiya ƙarama sukayi, a fusace ta sake dakama Nurse ɗin tsawa. “Get out of my side!!”. Ai da gudu Nurse ɗin ta fice kuwa. Har neman faɗuwa take, ALLAH dai ya taimaketa ta dafe bango. Tana fita itama Hajiya Ƙarama ta fice a fusace. Sai da taje ƙofar office ɗin Dr Larai sai kuma ta gyara yanayinta cikin jan numfashi da saukewa. Knocking ƙofar tayi, aka bata iznin shiga. Dr Larai na zaune da waya a hannunta da alama akwai abinda take yi. Shigowar Hajiya ƙaramar ya sata ajiye wayar tana murmushi. Da girmamawa matsayin Hajiya ƙarama na shugaba a asibitin ta ce, “Welcome Doctor ashe kin shigo? Yanzu nake tunanin zuwa na duba kafin na wuce gida ai dama”. Murmushin yaƙe Hajiya ƙarama tayi, tare da jan kujera ta zauna. Hakan yasa itama Dr Larai komawa ta zauna. Gaisuwa sukai a mutunce. Kafin Hajiya ƙarama ta tambayi bataga petient ɗinta ba. Kota canja musu ɗaki ne?. Da ɗan mamaki Dr Larai ta ce, “Kunyi saɓani kenan? Dan sun wuce gida. Yaron nan naku rigimamme ne na bugawa a jarida. Dan har office ɗin nan yazo ta tirkeni sai na bama yarinyar nan sallama. Babu irin son fahimtar da shi ɗin da banyi ba dan ya barta ta ƙara samun sauƙi sosai amma fir yaƙi. Wai a dinga zuwa gida ana dubata. Ko kuma ya kawota asibitin kullum. Rikitaccen mutum ne na lura mai ra'ayin riƙau gaskiya.” Da ƙyar Hajiya ƙarama ta ƙaƙaro murmushi. Sai kuma ta miƙe tana faɗin, “Ai in dai Awwab ne ƙyaga da yawa wlhy. Shike nan bari zanje gidan mu haɗu ai.” Murmushi itama Dr Larai tayi da faɗin, “To shike nan hakan ma yayi, amma ina tausayama matarsa dan zata sha fama. Stubborn namiji irin wannan idan baka karancesa ba wahalar zamane da su. Dan su abinda suke so kawai za'ayi tilas.” Murmushi kawai Hajiya ƙarama tayi dan ita abinda ya dameta shi ya dameta. Cikin wayancewa dai tace bara taje taga petient sun taru. Miƙewa itama Dr Larai tayi tana tattara kayanta. “Okay nima ai wucewa zanyi. Nasan Alhaji bazai wuce ba sai na koma.” 💦🩸💦🩸💦 Tuni ganin Ummie yasa na manta da dokarsa ta kar na daɗe. Na shagala sosai da kwance mata gashinta bayan nayi sallar azhar, kanta na a saman cinyata ƙamshin turarensa ya cika ɗakin. Da farko ban maida hankali ba saboda nasan na saka wani a jikina. Sai da naji alamun mutum na nufoni sannan na farga. Shi ɗinne dai sanye cikin brown wando da ash ɗin riga mai gajeren hannu. Gashin nan a ɗaure ta can ƙasa sosai dan har yana taɓa bayansa. Saukar iska a cikin idanuna ya sani jan numfashi da ƙarfi na lumshe idanun, sai kuma duk kunya ta kamani irin wannan abin kunya haka na kure bawan ALLAH da ido. A zatona zaiyi maganar kallon sai naji baice komai ba. Sai ma hannunsa da ya ɗaura saman nawa dake tsefe kan Ummie. A hankali na ɗan ɗago na kallesa. Shima ni ɗin yake kallo. Ƙure juna mukai da ido ga hannayenmu akan Ummie. “Kinga mamanki kin manta da umarni na ko?”. Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa. Fuska na ɗan marairaice masa da karyar da kaina gefe a shagwaɓe na ce, “Kanta ne fa ya tsufa”. Idanunsa ya ɗan ja luuu kamar zai lumshe sai kuma ya buɗesu tar akan nawa. Bazan iya jurar salon kallon nasa ba a yanzu dan haka na janye nawa a hankali na duƙar da kan. Shima sai bai sake cewa komai ba ya ɗan janye hannun nawa ya ƙarasa tsefema Ummien. Dama ɗayan da nake yinne ya rage. Dan bana mata kitson da yawa. Koda ya kammala cumb dake saman cinyata ya ɗauka ya taje mata kamar yanda naima sauran. Sannan ya tattare gashin cikin hannunsa. Kallona yay a hankali ya furta, “Cire band ɗin kaina, idan kin dawo kwayi kitson”. Kai kawai na jinjina masa. Kafin a kunyace na kai hannuna saman gashinsa dake kwance luff yana ƙyalli kona wata macen albarka na zame sililin baƙin band ɗin daya haɗe da gashin sai ma ka ƙura ido kake ganewa. Koda yaushe kuma zakaga da irinsa yake ɗaure gashinsa. Ina gama zarewa gashin nasa ya tarwatse a baya. Sai kawai na shagala da kallonsa har sai da naji saukar hannunsa cikin nawa zai zare band ɗin sannan na dawo hankalina. Duƙar da kaina nayi kunya duk ta isan. Yau dai na kula kamar ina sakin layi da yawa. Sai dai yanda ya basar yasa na ɗan ji nutsuwa. Yana gama ɗaure mata ya gyara mata kwanciya shima ya miƙe yana faɗin, “Lets go”. Dole na mike a hankali ina gyara mayafin jikina. Wani kallo ya dinga bina da shi daga sama zuwa ƙasa. Sai kawai nai gaba da sauri. A falo muka samu mama Balki ashe bata fita ba. Tana ganinmu ta saki murmushi da faɗin, “Har kun fito.” a kunyace na jinjina mata kaina. Shi kuma ya sanar mata akwai baƙi a gidan zuwa anjima zai kira wayarta tazo su gaisa. Ya kuma roƙeta ta rufe ƙofar falon ko Paah ne yazo karta barsa ya shigo. Maganar tasa ta ɗan ban mamaki, har na kasa haƙuri sai da na kallesa. Amma sai ya ɗauke kansa kamar ma bashi ne yay maganar ba... A falon ƙasa muka ci karo da su Azizat. Tunda muka fara sakkowa duk suka miƙe tsaye tamkar waɗan da ke cikin shock. Dan su duka bakunansu a buɗe suke kallonmu idan ka cire wata farar budurwa da ban sani ba a gidan dake zaune ita bata tashi ba. Sai dai itama ta zuba masa ido kamar zata cinyesa. Kallo ɗaya na musu na ɗauke kaina. Kamar yanda shima naga baima nuna yasan da zamansu ba ya wucewarsa. Ina jiyo Malika na yin ashar a hankali. Ban san miya basu mamakin ba. Ganina a gidan? Ko kuwa ganina tare da shi?. Oho dai can ta matse musu. Dan ni su duka ukun a yanzu na shirya duk wadda tace zata shigo sabgata wlhy sai na mata zanen yarabawa a fuska. Koda muka iso ƙofar shiga sashen nasa sai da na tsaya na ɗan gyara mayafina sannan na bisa dan shi har ya riga ya shiga. Da Hayatu na fara cin karo tsaye a ƙofa yana waya, muna haɗa ido ya wani rissinar da kai. Harara na balla masa na wuce ciki abuna. Bana ganin fuskar waɗanda ke a zaune, sai dai haka kawai zuciyata ke wani irin sanyi da jikina. Gani nike kuma kamar na sansu. Tamkar wadda ƙwai ya fashema a ciki na ƙarasa sosai cikin tsakkiyar kujerun ina sake yin sallama ƙasa-ƙasa batare dana kallesu ba. Turus na tsaya zuciyata na bugawa da ƙarfi sakamakon jin muryoyin da ko'a cikin barci bazasu taɓa iya su ɓace min ba. Jikina har rawa yake na ɗago dan tabbatarwa. Sai kawai naci karo da fuskar Yaya Musaddiq da ke faman min murmushi da ta Hafizzullah. Yanzu kam sosai rawar jikina sake bayyana tayi, ga lips ɗina na rawa kamar yanda hannuna ke rawa ina son nunasu amma na kasa........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* _Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ........ ......Cikin rawar jiki na nufesu da wata irin sassarfa na faɗa jikin Yaya Musaddiq na saki wani irin kuka da ni kaina bamma san na minene ba, sai kuma na jawo hannun Hafizzullah shima na haɗasu na rungume. “Oh oh Kandala na ashe bata canja hali ba har yanzu jama'ar ALLAH”. Yaya Musaddiq ya faɗa cike da tsokana yana ɗagoni a jikinsu. Cikin dariya da sharar hawaye Hafizzullah ya ce, “ALLAH Yaya bata canja ba sai ma abinda ya ƙaru.” hannu nasa a kansa na dungure nima ina sharar hawayen na ce, “Magulmaci kana nan da hali”. Dariya muka sanya mu duka ukun. Kafin na sake kamo hannayensu cikin nawa su dukan. Cikin shagwaɓa na sake fashe musu da kuka ina faɗin, “Ya akai kuka zo nan? Waye ya kawoku? Yaya wlhy nayi kewarku, kullum da dare sai nayi kukan rashinku. Yaya dan ALLAH kuce kun dawo nan zaku zauna tare dani?”. Murmushi kawai yaya Musaddiq keyi, sai Hafizzullah ne cikin dariya ƙasa-ƙasa ya ce, “Sai dai idan zaki bimu mu koma Kano. Dan ni ban wani yarda kinyi kewarmu ba Addah. Jibeki kinyi wata fresh kamar ɗanyan nama sabon yanka. Ga ƙiba kin haɗa kamar ke kaɗai ake ma tirka a gidan. Kai gaskiya ba wani kewarmu ke dai gidan miji daɗi kinma manta da mu”. “Yaya ka ganshi yana tsokalana ko?”. Na faɗa a shagwaɓe batare dama nasan mi nake ba. Dan wlhy duk jina nake a ruɗe kamar a cikin mafarkin dana saba. Dana farka zan nemesu na rasa ne. A hankali Yaya Musaddiq dake murmushi har yanzu yana kallona kawai ya kai hannu ya share min hawayen yana faɗin, “Manta da shi, har kin manta da halin auta ne ma. Bayan da yaji zanzo badashi ba ya zauna ya dinga rusa kuka harda birgima a tsakar gida wai shi idan baizo yaga Addarsa ba zai faɗa rijiyan gidan su Mama Sadiq maƙotanmu”. Dariya na ƙyalƙyale da shi, tare da kai hannu kan fuskar Hafizzullah daya kwaɓe ta cike da shagwaɓa naja kumatun, sai kuma na dunguresa da faɗin, “Ashe dai yaron nan na sona har yanzu”... Duk abin nan dake faruwa yana zaune a falon. Binsu kawai yake da kallon ƙasan ido wani abu na masa motsi a zuciya. Daka gansu kaga waɗanda sukai matuƙar shaƙuwa da juna, suke kuma tsananin so da ƙaunar juna. Wani irin lumshe idanunsa yay murmushi na suɓuce masa a bazata. Hoton Fahad ne ya fara masa gizo a cikin idanunsa dake rufe, da sauri ya buɗesu yana cizar lips. Dan wani irin zafi zuciyarsa ta fara masa. Ƙoƙarin ture tunanin dake neman kutso masa a zuciya yayi ya sake maida dubansa kansu. Hakan sai yay dai-dai da Samraah ta juyo suka haɗa ido kuwa. A mamakinsa sai ta sakar masa murmushin da har ya bayyana haƙwaranta. Sai ya samu kansa da lumshe idanun da buɗewa. A hankali ya furta, “Dama haka ake tarban baƙi da surutu?”. Murmushin ta sake sakar masa tana miƙewa daga durƙuson da tayi a gabansu. Muryarta kanta na nuna alamun farin ciki ta ce, “Ya Awwab ALLAH daɗine naji kamar ya kasheni. Ashe dama kasan yan gidanmu amma baka tafa faɗa min ba? Nagode, Nagode kaima ALLAH ya faranta maka fiye da yanda ka faranta min”. Kansa ya ɗan girgiza yana sakin murmushin daya kasa riƙewa. Sai kuma ya maida kallonsa ga su Yaya Musaddiq da suma ke murmushin, muryarsa da alamun tausasawa ya furta, “Bara na ɗan je bazan jimaba zamu dawo. Please ku ƙara cin abinci sosai nan ɗin gidanku ne.” Faɗaɗa murmushin yaya Musaddiq yayi, cike da girmamawa ya ce, “Mun gode sosai ranka ya daɗe. ALLAH ya saka da alkairi”. “Don't say me thanks you or ranka ya daɗe ɗin nan. You are my brothers. By now we are family ne okay. Nine zan kiraka Yaya, sai kuma small kiddo Hafiz a gefe”. “Yes babban Yaya”. Cewar Hafizzullah cike da farin ciki. Yayinda Yaya Musaddiq keta murmushi dan shi sake ganin al'amarin yake kamar a mafarkinsa. Duk da bayanin da Hayatu yay masa tare da Maash ɗin kafin shigowar Samraah zuciyarsa ta kasa daina mamakin komai. Cikin jinjina kai ya furta, “Ni ne ya kamata na kiraka Yaya, kaga dama ni kaɗaine banda Yaya. Yanzu kuma na samu. I am so happy inada wanda idan nayi ba daidai ba zai tsawatar min, inada wanda nima zan yima kuka a jiki. Ka mana komai na rayuwa. Daba dan kai ba da yanzu ban san a wane hali muke ba, dan in har wani abu zai taɓa rayuwan Samraah mu dukanmu tamu rayuwar zata girgiza ne. Saboda mu duka biyun itace rauninmu. ALLAH ya faranta maka fiye da yanda kai mana”. Hayatu da Maash ɗin suka amsa da Amin. Dan gaba ɗaya ma Maash ɗin ya rasa abin faɗa. Idanu suka haɗa da Samraah dake kallonsa tana murmushi. Cikin ɗan ƙanƙance cat eyes ɗin nashi ya ɗage gira sama da ɗan ɗage kai alamar kallon fa. Samun kaina nayi da jin kunya, dan haka na duƙar da kan nawa kawai ina murmushi. Dan har ƙasan raina ban taɓa jin ya sakani a farin ciki irin na yau ba. Ji nake kamar naje na rungumesa. Amma ina jin kunya. Ɗagowa nayi na ɗan kalli Hayatu, shima a karo na farko na ce masa, “Thanks You”. Murmushi shima ya sakar min yana yin ƙasa da kansa. Sai kuma ya jinjina kansa da faɗin, “Nine zan gode ai Aunty na”. Yanzu kam Harara na balla masa ina ɗauke kaina da murguɗa baki. Sai ko muka sake haɗa ido da ogan nasa. Ɗauke fuskata nayi gaba ɗaya daga sashensu. Sai da naji Hayatu nama su Yaya Musaddiq sallama akan sai sun dawo sannan... 🌿🌿🌿🌿 A hargitse Hajiya ƙarama ta koma office ɗinta. Kofar ta kulle dan bata buƙatar ganin kowa. Kai-kawo ta shiga yi cikin Safa da marwa. Kafin ta jawo waya ta shige cikin toilet. Sau uku tana kira amma ba'a ɗaga ba. Kanta ta dafe cike da takaici. Yanzu haka yana can yasha giyar tashi yana shaɓar barci. “Motsoww” taja tsaki tare da fitowa. Wayar ta wurga saman desk ɗinta, itama ta zube a kujera tana mai dafe kai. Ji take yana wani irin sara mata. So take tai magana da wani ko zataji daɗi. Amma dawa ɗin zata yi. Da sauri ta sake rarumo wayar ta danna ma Jannifer kira. Bugu ɗaya kuwa ta ɗauka. Jin muryarta wani iri ta sata jan tsaki. “Malama dalla koma dawa koke tare ta tashi taba mutane waje magana zamuyi.” “Bara dai ni in tashi”. Jannifer ta faɗa tana ƴar shaƙiyar dariya. Tsaki kawai Hajiya ƙarama tayi batace komai ba. Sai da Jannifer ta sanar mata ta fito tana jinta sannan ta sake jan tsaki da fara magana. “Jannifer wai ina kika samo yarinyar nan ne? Wlhy tunanina gaba ɗaya nan birkicewa yake a wannan gaɓar?”. Da mamaki Jannifer ta ce, “Kamar ya? Wani abu ne ya sake faruwa?”. “Miye ma bai faruba. Yanzu nan nazo asibiti na samu wai banzan yaron nan Awwab yazo ya ɗauke yarinyar nan sun wuce gida?”. “Tofa babbar magana. Wai Maash kike nufi?”. “To in ba shiba waye zaima mutane wannan gadaran”. Dariya ce ta kufcema Jannifer, sai da tayi mai isarta kafin da ƙyar cikin dariyar ta ce, “Kai amma yaron nan ƙwallon shege ne wlhy. I like him style wlhy. Komansa yake baya tsoron uban kowa. Ya taka na waje kuma na gidan bai barku ba ciwon kan da gwale-gwale yake baku. To wai kodai son yarinyar nan yake ne? Abinfa da mamaki wlhy, dan ni bammaga wani damuwa a tattare da shi akan abinda ya aikata ɗin ba. Ka ɗirkama yarinya fyaɗe amma ka dinga abu It's like you don't care, I really like this boy's style.” “Mtsowww!! Jannifer ban son shirme. Ina miki maganar serious kina mun wani soki burutsu.” “Ehm sorry Maa. ALLAH abunne ya ban dariya ya kuma burgeni. Samun irin stubborn mazan nan ba ko inaba. A Abuja nasan yarinyar ni gaskiya......” ta kwashe komai data sani akan Samraah ɗin tun daga haɗuwarsu da abinda ya faru kuma duk ta gaya mata”. Cikin damuwa Hajiya ƙarama ta ce, “Amma kema kinyi ganganci da baki san labarin nata ba”. “To banda abinki Hajjaju mizai sa na damu da labarinta. Ni fa dama irinta na fita nema. Sai kuma na samu miya rage min. Kaiwa na ɗako nazo na samu kuɗaɗena ai.” “Mtsoww!! Aikin kenan. To ita kuma Mashi'a ya akai ta zaɓi yarinyar? Bayan nasan idan kin kawo yara sai sunyi fin wata biyu ma kafin ki saida su. Musamman irinta ma ai baki badata a masu aiki?”. “Hummm ki bari kawai, wlhy kuɗaɗe kawai na gani. Dan an samu kuskure ne dana aika a kira min su ta biyosu. Nace ta koma Alaja Mashi'a ta ganta ta nace ita take so harda ninka min kuɗi. Ni kuma kawai naga bazan iya ba na sallama. Dan nasan ko ƙasar waje na kaita ba lallai na samu abinda na samun ba a wajenta. Kuma ina ma jin nauyin Alaja Mashi'a wlhy. Kin san dai ba wannan karon ne na farko dana fara samo mata masu aiki ba. Tunda kusan yaran gidankun nan duk a wajena aka amshesu mafi yawanci kuma itace ke zuwa da ɗauka musamman ma masu kula da Hajiya Babba.” Numfashi Hajiya ƙarama ta furzar, dan tasan gaskiyar zance Jannifer ke faɗa mata. Mashi'a tana kallon Jannifer ne kawai a mai kawo ƴan aiki. Kuma zama ta iya cewa itace ta nuna mata gidanta a lokacin da take neman masu aiki da zata wuce da su can Germany, shine take faɗa mata gidan Jannifer ɗin. Tunda ta ɗauka wancan yaran biyu ta wuce da su taji daɗin zama da yaran sai yazam duk sanda ta shigo Nigeria takan ɗaukama Hajiya Babba masu kula da ita. Ko idan taji wasu nason masu aiki takan musu hanya. Da yake itama halin Maash ne da ita yanzu haka yaran data ɗauka su biyu duk sunyi karatu a can. Ɗaya a cikinsu ma ta kusa aure da ƙanin mijin ita Mashi'a ɗin. Ƙaramin tsaki taja da ture batun Mashi'a ta koma wanda zai amfaneta. Amma ba komai, ita Awwab ɗin ma ya saukaƙa mata aiki, a gidan ma wasan zaifi armashi tunda yarinyar a sashen masu aiki take. Zata dakata ta dawo sashenta da kwana, ta nuna saboda abinda ya faru ta ƴanta yarinyar. Zata nema mata makaranta kawai a wata ƙasar daga haka shikenan ta gama samun cikar burina..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_ .....Suna gama ficewa cike da zumuɗi na maido hankalina kansu Yaya Musaddiq. Ƙoƙarin zama nake Hafizzullah ya ce, “Wlhy ji nake kamar a mafarki. Wai aunty Samraah kece matar mutum kamar Maash. Ya ALLAH Maash fa. Wai dan ALLAH Adda yaya akai haka ta kasance? Kodai dama ke kin san wa kika aura? Dan wlhy duk da sun sanar mana komai yanzu kuma a gabana komai ta faru lokacin auren sai nake ganin kamar dama dai kuna son junan ku ne ke da shi.” Harararsa na ɗan yi, sai kuma na koma kusa da Yaya Musaddiq na zauna ina sauke ajiyar zuciya. “Yaya dan ALLAH mi sukace muku? Sannan dama kaima baka san shi bane?”. Murmushi sosai Yaya Musaddiq yayi yana kallona. Sai kuma ya jinjina kansa. “Samraah wlhy har yanzu ni kaina ina a cikin yanayin da Hafizzullah ɗin yake ciki ne. Dan harga ALLAH ban taɓa sanin Maash ne mijinki ba, taya ma zan kawo hakan a raina to. Bama ni kaɗai ba, hatta su Abba babu wanda yasan wa kika aura. Koda aka ɗaukeni aiki a companynsa na amsa ne saboda dalilai uku. Na farko dai bazan iya bijirema umarnin ogana ba. Saboda yana treating ɗina like uba. Ko Abba dake ƙanin mahaifiyata muke a hannunsa tun bamu san kammu ba bana jin ya damu da tarbiyyata kamar yanda ogana ya tsaya a kaina. Hakan yasa babu abinda zai ce nayi a rayuwar nan naƙi yinsa sai dai ina na saɓama ALLAH ne ko cutar da wani. Wannan kam bazan masa biyayya ba. Na biyu maganar video ɗin nan. Na yarda zanyi aiki a companyn da tunanin ko zan fahimci wani abu dan na sanki da naci akan abu, komai tsahon lokaci da za'a ɗauka bazaki taɓa barin maganar video ɗin nan ba. Na uku amsar aikin kamar samun wata hanyar cigaban rayuwa ne yazo mana mu duka. Dan bamu da kowa sai junanmu. Dolene nayi aiki tuƙuru in har bana saɓama ALLAH bane domin cigaba da gina rayuwarmu. A lokacin da aka samu matsala game da aurenki, mahaifiyar Mansoor tazo har gida taci mutuncin su Abba akan ɗanta bazai taɓa ya aureki ba, su bazasu haɗa zuri'a da ke ba, idan kuma muka matsa zata iya ɗaukar kowane irin mataki dan ganin ta rabaki da ɗanta. Kin san Kawu Musa da zuciya, dan haka shima ya balbaleta, sai kawai ta ɗaga hannu ta maresa. Kafin ta sauke hannunta mukaji itama an sauke nata marin. Ta gigita sosai, haka muma da mamaki muke kallon bawan ALLAHn daya maretan. Mutum ne cikin shigar kamala harda gemunsa, maganganun daya gayama mahaifiyar Mansoor a lokacin sun matuƙar birgemu. Sai muka ji sauƙin yanda kalamanta suka ƙona mana rai dama kowa na wajen a take muma mukace ko Mansoor ne autan maza kin barsa har abada. An gama duk wannan rikici Maman Mansoor ta wuce bawan ALLAHn nan shima zai wuce Kawu Musa ya dakatar da shi. Godiya ya masa muma haka. A mamakin mu sai kawai muka ji ya fara jera masa tambaya. (Yaro munene sunanka?) Yace masa Muhammad. Anan kake? Yace masa eh to yana aiki anan amma asalinsa ba mazaunin nan ɗin bane. Kana da aure? Sai da yay jim kamar mai tunani kafin yace masa a'a. Kana shirin yi ne? Nan ma ya amsa masa da a'a. Iyayenka fa? Yace suna nan a raye. Sai mukaga kawai Kawu Musa yayi murmushi. Batare da wani tunani ba kawai ya ce (kowa ya shaida. Ni Musa a matsayin yayan Abdul-wahab na bama wannan bawan ALLAHn Muhammad auren ɗiyata Samraah. Ina fatan bazaka taɓa watsa min ƙasa a ido ba. Ina fatan zaka tabbatar min da ƙyautata maka zato da nake yi. Ina fatan zaka riƙeta amana bazaka taɓa cin amanata ba. Idan kuma har akwai matsala ka fito ka sanar min wlhy zan fahimceka. Nima kuma badan bana son Samraah na baka ita ba. Ba kuma dan na zubar mata da darajanta nayi hakan ba. Yarinyata mai ilimin addini ce dana zamani. Sannan ƙyaƙyƙyawace mai tarbiyya. Kaga dai ban sanka ba, ban san daga inda ka fito ba. Komai daya faru daga UBANGIJI ne ba daga mu ba. Dan abinda kayi yanzu yasa nake ji a raina ko daga ina ka fito kai ɗin mutumin kirki ne, dan ɗan halak shike kare martabar tsoho a duk inda yaga za'a yaga masa rigar mutunci.” “Wlhy Kandala ya matuƙar jimawa tsaye bai motsa ba a wajen. Har sai da Kawu Musa ya dafa shi da faɗin. Idan fa har kaga akwai matsala kada ka saka kanka a cikin damuwa. Mu duka dake nan babu wanda zai zargeka da rashin ƙyautawa har abada. Kuma mun ƙulla zumunci da kai kenan har abada. Murmushi yayi, sai kuma ya ɗan jinjina kai da roƙon a bashi wasu mintuna zaiyi waya. Kai tsaye Kawu Musa ya bashi dama. Tafiyarsa waya muka samu damar tattaunawa muma, Kawu Musa ya fahimtar damu dalilinsa na yanke hukuncin nan. Ni dai dan banda yanda zanyi ne bazan iya jayayya da su ba na amince. Hakama Hafizzullah atake yace shi dai dan ALLAH a barki. Amma sai Kawu Musa ya mana nasiha da nuna mana illar barinki ba'a ɗaura auren a ranar ba. Ya kuma ce mu cigaba da miki addu'a in sha ALLAHU sai kinci ribar wannan auren. Dawowarsa ta katse zancen mu. Ya tabbatar ma su Kawu ya amshi aure, sannan waliyyinsa na tafe in sha ALLAHU kafin lokaci yayi. Shima kuma zai je ya dawo. Badan muna da hope ɗin dawowar tasa ba muka barshi, amma abin mamaki na takaice miki sai gashi muna ƙoƙarin wucewa masallaci. Sunzo tare da babban malamin nan Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain a matsayin waliyyinsa. Sai wannan Hayatu da suke tare yace ƙaninsa ne. Sheikh Muhammad dai ba ɓoyayyen mutum bane a garin Kano dama Nigeria baki ɗaya, dan haka duka damuwarmu da wani wasiwasi ya kau. Sheikh Muhammad ya tabbatar mana Muhammad tamkar ɗa yake a wajensa, kuma in sha ALLAHU bazamuyi kukan haɗa jini da shi ba. Idan ma muna tunanin wani abu mu cire, dan wata hikima ce ta UBANGIJI shigowarsa rayuwarmu. Bai kuma ɓoye masa komai game da abinda ya farun ba. Kawu Musa yafi kowa shiga a farin ciki. Dan haka a take aka ɗaura aurenku bayan idar da sallar juma'a, aka kuma kwaso kayanki da aka kai gidan Mansoor aka maida gidan daya bada matsayin nasa. Bayan an kaiki kuma sai aka samu akasin ciwo da kika shiga har ya taho dake Abuja, daga baya ya sanar mana kuna Lagos wajen iyayensa. Koda yaushe muna waya da shi, amma bai taɓa gaya min komai da ya shafeshi ba. Sai a yau da muka iso an kaimu masauki kawai naci karo da fuskarsa matsayin mijinki. Bayan kuma ni sai a gobe zan gansa matsayin ogana bayan munzo wajenki. Kin san kuwa ruɗanin dana shiga Samraah. Har kusan faduwa nayi sai da Hayatu ya rikeni. Bayan sun bani ruwa nasha mun zauna a ɗarare Hayatu ya min bayani komai tun daga batun ɗaukar video har zuwa kidnapping ɗinki da mahaifiyar Mansoor tasa akayi, da karɓarki da yayi a hannunta sanadin bincike da yayi saboda kuɗi da aka nema a hannunsa da sunanki har 500m. Bayan ya gano bake bace amfani kawai ake son yi da sunanki ya kuma gano anyi kidnapping ɗinki shine ya kubutar dake. Yaso amsar video ɗin a hannunki lokacin kodan gudun kada ki sake shiga wata matsalar sai kikaƙi bashi. Sai kawai ya haƙura ya sake ki akan zai cigaba da bibiyarki har sai ya amsa dan in ba haka ba yasan wataran wani zai iya sake yunkurin cutar dake a kansa in har akasan da shi. Ya tabbatar mana shi ya kubutar dake daga auren Mansoor ne saboda kawai yasan bazaki taɓa samun farin ciki ba dan mahaifiyarsa da ƙanwarta ya tabbatar da zasu iya aikata komai akanki, yanda kuma basu samu kudin nan ba kema bazaki samu yanda kike so ba. Ko ran daurin auren da yazo ya biyo mahaifiyar Mansoor ne cikin ɓadda kama dan ya tabbatar tayi abinda auren zai fasu amma sai kawai tai abinda ya sashi tilas bayyana kansa garemu alhalin shi beyi niyyar hakan ba. Sai kuma kawai Kawu Musa ya masa ƙyautarki. Yace bazai iya watsama tsohon kasa a ido ba saboda sun bashi tausayi, koba komai shine ya saka auren rugujewa, idan bai amsa ba ai ya sake raunanasu kema kuma an cutar dake shiyyasa kawai ya amince. Sai kuma gashi auren shima ya zame masa alkairi, dan ya ce mana yanzu kin tallafi rayuwar mahaifiyarsa dake fama da jiyya shekara da shekaru. Nagode Samraah, Nagode matuƙa da kikayi haƙuri kika amshi ƙaddararki da hannu biyu, Nagode da kika kasance ɗiya ta ƙwarai, Nagode da kika cigaba da riƙe tarbiyyar ki. Dan tabbas naga tsagwaron jin daɗi a fuskar Maash game da ƙyautatama Mahaifiyarsa. Na tabbatar da koda a baya ba soyayya ce ta haɗaku ba yanzu kam yana sonki. Yana ƙaunarki, dan wannan alkairin naki ne muma ya jawo mana alkairin. Yanzu na fahimci dama Maash yaje garejinmu kai tsaye ne domin kawai ya ɗaukeni aiki, dan sai yanzu nake sake tariyo yanda aka ɗaukeni aikin cikin sauƙi ake kuma mutuntani da girmamani sama da ma'aikata da yawa. Gashi har an turani karatu wata ƙasa. Samraah tabbas ke ɗin alkairi ce. Gaba ɗaya halayen iyayenmu kin kwashesu. Dama ance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. tabbas na yarda da wannan batu na malam bahaushe”. Ya ƙare maganar yana share hawaye. Da gani har Hafiz muma kukan muke. Dan labarin ya matuƙar girgizani. Ashe haka abubuwa suka faru ni ban sani ba. Ashe mahaifiyar Mansoor ce tasa akai kidnapping ɗin a da farko. To amma tayaya akai hakan? Da sanin Mansoor ɗin kokuma? Idan bada saninsa ba taya akai tasan da videon nan? Shiyyasa ba'a son zargi, na daɗe ina zargin Maash akan ɓata min aure dan shi ya aureni ya cutar dani ya amshi video ashe abin duk ba haka bane ba. Kai jama'a, lallai masu iya magana sunyi gaskiya da sukace zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya. Nagodema ALLAH da ban taɓa masa tambaya akan auren ba duk da nasha son yin hakan kwarjininsa da shakka na hanani. Sosai nake jin kimarsa na sake ƙaruwa a cikin zuciyata. Ashe shine ma ya kubutar da ni daga hannun mahaifiyar Mansoor. Kai ban taɓa zaton matar nan zata iya aikata irin wannan al'amarin ba. Wato mutum kai dai kawai gansa ka barsa yanda ALLAH yayisa, akan kuɗi baka iya banbance mutumin banza dana ƙwarai da wuri, dan sanin zuciya sai UBANGIJIN kawai........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_ ......Sai ƙarfe kusan uku mijin Baby ya iso gidan cikin ƙatuwar motar da ta sake haukace imanin su Mom. Sam ita bama damuwarta rabuwa da ɗiyar ba. Sai santin motar suke da sake kambama irin dukiyar mijin Babyn. Faɗa ma ta yarda akai baby iyayenta na Gwarzo su mata batayi ba. Sai sake shiryata da akai ciki wata alƙyabba mai ɗan karan ƙyau. Itako ido ƙemaƙayau ba ko ɗigon hawaye. Hasalima inda kwalliyarta batayi ba gyara abinta take ko tace a sake mata kaza bata son kaza. Su dai su Gwaggo Gudidi sunyi sororo suna kallon ikon ALLAH. Abba baya nan ya fita, dan baiyi zaton mijin Babyn zai iso a lokacin ba kasancewar yasha jira kafin azhar amma shiru. Sai Alhaji Jafaru babban ɗan Gwaggo Gudidi ya jashi suka tafi wata gaisuwa a gyaɗi-gyaɗi. Su Gwaggo Gudidi suna tunanin ai za'a jira Abban su dawo. Amma mi sai gani sukai an fito da amarya baby tana taku ɗai-ɗai ko irin rufe fuskar nan ta amare batai ba. Sai ma hirarsu suke da kakarta Umma suna dariya. Babu wanda aka kalla a cikinsu aka wuce da Baby ƙofar gida aka sakata a narƙeƙiyar motar da angon nata yazo a ciki. Abu mafi ban mamaki mijin ko kallonsu baiyi ba. Sai Mom ɗin da Umma ne suka gaisheshi yana amsawa cike da shan ƙamshi. Baki a washe Umma tace, “ALLAH ya tsare to Alhaji. ALLAH kuma yasa ku dawo lafiya da babbar tsaraba ta tattaɓa kunnena. Alhaji mu ya maganar tafiyarmu saudia ne?”. Duk maganar da Umma take harararta Baby keyi, miye na wani tabbayar zuwa makka dan zubar da mutunci. Badai shine da kansa yace ya biya musu ba ai sai tayi hakuri taga lokacin yayi baice suje ba ko. Shikam ma ɗan mannin rainin wayon hannu kawai ya ɗaga musu a taƙaice ya ce, “A jira lokaci”. Daga haka ya ɗauke kansa tare da bama drivern sa umarni ko kallon amaryar tasa baiyi ba. Driver kam umarnin ogansa ya cika. Ya tada mota abinsa yay reverse har yana neman taka su Mom dake tsaitsaye. Ai tuni mutane suka shiga faman jinjina kawunan mamaki. Ƴan anguwa suka guntsa kowa da abinda ya fassara al'amarin. Dan kuwa dai sunga sabon salon ɗaukar amarya ganin idonsu. Duk abinda ake Halime batama sani ba. Tana can tunda ta idar da sallar azhar ta kira Abba tace ya saya mata rake da gyaɗa tai kwanciyarta. Har aka tafi da Babyn kuma bata sani ba. Sai da hayaniya ta fara tashi ta ƴan gwarzo sannan ta farka... 💦🌟💦🌟💦 Duk yanda Hayatu ke ƙoƙarin danne abinda ke cimasa zuciya ya kasa. Sai satar kallonsa yake ta cikin mirror har suka iso babban companyn da Ummie ta fara ginawa da hannunta tun mahaifinta na da rai wanda Paah ne ke riƙe da ragamar komai na companyn. Ƙatone bana wasa ba, sannan akwai ma'aikata jingim a cikinsa. A farkon ginashi ana sarrafa kayan suturu ne, bayan abubuwa sun kwaɓe akan ciwon Ummie companyn ya durƙushe harma ya daina aiki na tsawon shekaru. Sai daga baya Maash ɗin ya farfaɗo da shi tare da sake faɗaɗashi aka maida shi wajen sarrafa kayan abinci. Kusan kowane nau'i na kayan abinci har su mai magi duk companyn na fitarwa. Suga, gishiri, harsu omo da sabulai sannan kayan abinci tun daga kan shinkafa, taliya, fulawa, garin alkama, da ire-irensu, da dangoginsu. A yanzu dai a Africa babu companyn dake fidda kayan masarufi irinsa gaskiya. Dan tako ina suna kai abinci kuma sunada wasu reshika a wasu kasashen da dama. Duk ta inda suka gitta gaisuwar girmamawa ake bama Maash. Shi ko yana mai amsa musu a daƙilen nan nasa dan motsin lips ɗinsa kawai suke gani sai kuma hannu da yake ɗaga musu. Duk wanda yayma Maash farin sani a rayuwa yasan wannan halin nasa ba wulaƙanci bane yanayinsa ne kawai a haka. Dan magana inba ta zamar masa dole ba, da wahala kaga yana yinta. Idan ma yayin bazaka taɓa jin sautin muryarsa sama ba. Sai fa idan an ɓata masa rai yayi matuƙar iya hargagin da ke gigita mutum. Kai tsaye office ɗinsa ya nufa Hayatu biye da shi dan shima yana da office a companyn. Har yanzu suna kan bincike game da case ɗin nan na samun yara a containers ɗin sa na kaya da suka tura Ghana. Monday ɗin nan zasu shiga court yau kuma zai sake zaman meeting da lawyers ɗin su da Paah, duk da dai kwata-kwata an nuna case ɗin bai shafesa ba duk da kasancewarsa shugaban companyn shiyyasa ma yake tsula tsiyarsa da matan da ake ɗauka aiki a ciki har Maash ɗin ya gano sa ranar yake tujara. Sun samu Paah ɗin baya nan, lawyers ɗin kuma basu kai ga ƙarasowa ba. Sai hakan ya bama Hayatu damar fidda abinda ke ransa. Kallon Maash dake zaune cikin kujerarsa ta office ɗin yana daƙilar keyboard ɗin computer ɗin saman desk ɗinsa yayi. Sai kuma yayi ƙasa da kansa cikin girmamawa yace, “Yaya kamin afuwa, zan sake maimaita maganar nan dai ta kwanaki dana taɓa maka kaƙi cewa komai”. Shiru kamar maash ɗin bazai amsa ba. Sai kuma can yace, “Uhumm ina jinka”. Kai hayatu ya ɗan sosa yana sake ƙasa da kansa ya ce, “Nifa ALLAH yaya yau saina sake ganin kamanin Yayan Aunty sosai da Baba Abdull sun sake fitowa. Shi kuma ƙanin nan nasu Hafizzullah banbancinsa da Falaq kawai ita mace shi namiji. ALLAH tun ɗazu a ruɗe nake dauriya kawai nake yi. Ita kanta Auntyn yau sai naga suna fisgar kama da Falaq ɗin, kawai dan ita farace ita kuma aunty bata kaita has......” Ruff bakin Hayatu ya rufe batare daya ƙarasa faɗa ba saboda kallon da Maash ɗin yay masa. Sai ya wayance da faɗin, “Yaya ALLAH ka duba lamarin nan iya gaskiyata nake faɗa”. Ya ƙare maganar cikin shagwaɓa kamar ba Hayatu PA ba. (Wato na lura akwai lokacin da Maash matsayin oga yake a wajensa. Akwai kuma lokacin da yaya yake😀). Hararsa kawai Maash ɗin yayi ya ɗauke kansa ya maida ga aikinsa.... 🩸🩸🩸🩸 “Ban gane mi kike son faɗa ba? Kin san dai bana son rainin wayo ko”. “Wlhy yallaɓai babu rainin wayo a maganata. Kai ma kasan bazan yi hakan a gareka ba. Naje na samu nima ta sallameta. Kuma shi Awwab ɗin ne yaje ya sakata yin hakan”. Wata shegen ashariya Yallaɓai ya kutuntuma. Sai kuma ya miƙe zaram yana kaima Centre table duka har sai da Hajiya ƙarama ta zabura tana ƙanƙame jikinta. Sai kuma ya juyi a fusace yana nunata da yatsa. “Idan har na samu matsala a aikina saboda ke na rantse da ALLAH sai na koya miki hankali”. Sosai hankalinta ya tashi, dan tasan mugun nan komai zai iya aikatawa akan buƙatarsa. Amma ba komai lokacinsa ne. Zata bisa yanda yake so gaba kaɗan zatayi maganinsa ai itama. Dan ta gama shirinta a kansa tun shekarun baya. Murya ta sauke cikin nuna tsorata ta furta, “Kayi haƙuri nayi kuskure, amma na samo hanyar gyara kuskuren nawa. Na tabbatar bazai kaita ko'ina ba sai gida. Koda yake nama bincika an tabbatar min suna gidan. A wannan karon zan nuna abinda ya faru ina jin tausayinta na dawo da ita sashena. Kokuma na nuna zan share mata kukanta akan abinda ya faru ta hanyar nema mata makaranta ta cigaba. Da ganan sai musan abinda ya dace, kaga munma samu sauƙi”. Shiru ya ɗan yi alamar nazarin maganarta. Sai kuma ya kai zaune yana mai jinjina kai. “Hakan ma yayi, sai dai ina mai gargaɗarki ki kiyaye. Dan bana buƙatar wata matsala kuma.” “In sha ALLAHU babu abinda zai faru, shi mai bincike a kantan ya dawo ne?”. “Zuwa jibi ne ƙarshen kwanakin daya ɗiba min. Dan ko jiya munyi waya da shi ya kuma tabbatar min da aikin na tafiya yanda zanyi farin ciki”. Itama murmushin ta saki duk da ba haka taso ba. Dan a nata ɓangaren tasa itama a bincika mata wacece Samraah ɗin?. ✨✨✨✨ Gaba ɗaya ganin ƴan uwana ya wanke min duk wata damuwata. Hirarmu muke cike da farin ciki suna bani labarin cakwakiyar gidan Abba ta yanzu da amaryarsa, tare da yanda auren Baby ya kasance, sun dai baro ana jiran miji yazo ya ɗauke ta. Matsama Yaya Musaddiq nai ya kiramun aunty Zakiyya. Daga nan fa mukaita gaisawa da mutane harda amaryar Abba da kawai naji matuƙar ƙaunarta. Daga ƙarshe jikina yayi sanyi jin batun zuwan mijin Baby yanzu babu jimawa da yanda tafiyar ta kasance. Mun cigaba da jimanta abun bayan katse wayar. A haka lokacin sallar la'asar ya riskemu. Ina tunanin yanda zasu fita salla sai ga guard ɗinsa yazo yace suzo boss yace ya kaisu suyi salla. Kafin su dawo nima nayi tawa, na sake gyara sashen naje kuma na gano Ummie. Alokacin nake cema Mama Balki tazo su gaisa da bakin da yace. Ta ce tana zuwa idan ta kammala abinda take yi. Harta bani abinci na kai musu. Duk da sunci sun ƙoshi dan acan inda aka fara saukesu sunce sunci abinci, nan ma kuma da Hayatu ya rakosu da kayayyakin ciye-ciye suma mukaita ci muna hira sai da na ɗauka musu abincin. Sake zaman hirar mukayi, dan ji nake kamar mu dawwama a haka. Koda suɓutar baki ban sanar musu komai daya shafi gidan nan ba. Hirar abinda ya shafemu kawai mukeyi hankalinmu kwance. Hatta zancen alaƙar Mama Balki da nake zargi da baba ban gaya musu ba, shiyyasa ma na matsu tazo su gaisa. Dan duk wanda yasan mahaifinmu ya kallai Yaya Musaddiq yasan suna matuƙar kama, musamman yanzu da yake sake girma kamanin na sake fitowa sosai. Wajen ƙarfe biyar ina shirin zuwa na sake ganin Ummie da ga nan nayi kiran Mama sai gashi ya dawo. Sannu da zuwa su Yaya suka shiga yimasa da gaidashi. Ganin haka yasa nima na gaisheshi batare dana yarda na kallesa ba. Sai dai shi ina jin idanunsa na yawo a jikina, dan haka ma naƙi kallon nasa. Ciki ya shige yana faɗa musu bari ya ɗan watsa ruwa. Sukai masa fatan fitowa lafiya. Na gyara zama zan cigaba da hirata Yaya Musaddiq ya hararen, tare da mun nuni da ƙofar da ya bi. Baki na tura cikin shagwaɓa nace, “Kai yaya mi kuma zanyi”. Sosai yake kallona fuska a tsuke, “Oh kice karatun Mom kema kin ɗauka kenan?”. Da sauri na shiga girgiza masa kaina. “Wlhy Yaya a'a”. “Inafa a'a tunda gashi na gani da idona. Abba yakan dawo gida bai ishi Mom kallo ba. Kema ga mijinki ya dawo ko kallon inda yake bakiyi ba. Abba yakan dawo gida Mom bata bashi ruwa ba, ya shige yay hidimarsa. Kema kuma gashi mijinki ya dawo babu ruwa babu abinci, maimakon ki bishi kiji yaya ya dawo, miye matsalarsa kin gyara zama ke ga mai ƴan uwa sunzo ko. Haka kike so muma idan munyi aure matanmu suna mana?”. Da sauri na sake girgiza masa kai idanuna na cika da ƙwalla. Ya ce, “Okay to aya maza tashi, haba Kandalata ina islamiyyan ya tafi? Mu kin bamu munci mun ƙoshi yan uwanki shi dake wahalar nema ko oho. Ko kina so Hafiz ya rainaki”. Da sauri na sake girgiza kaina ina Hararan Hafiz ɗin dake kumshe dariya. Tashi nayi na nufi ƙaton freight ɗin dining room. Ruwa na ɗauka da lemo na sa a tray dana ɗakko a kitchen sai glass cup mai ƙyau. Ni sai ma naji abun banbara ƙwai wai namiji da suna Hajara. Haka dai na daure dan bazan taɓa iya bijirema Yaya Musaddiq ba.......✍️ 🥱A fito lahiya matar yayanmu _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ ------------- *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ========= .......A hankali nake tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashema a ciki, koda na isa ƙofar bedroom ɗin na yi kusan minti ɗaya kafin nayi knocking a hankali. Banji motsin komai ba balle na saka ran za'a buɗe min. Hannu na kai zan sake knocking ɗin aka buɗe ƙofar. Da sauri na janye hannun nawa na riƙe tray ɗin da ƙyau kaina a ƙasa. Jin shiru ya sani ɗagowa a tunanina juyawa yay ya koma. Amma sai na gansa tsaye kawai ya zuba min cat eyes ɗin nan nasa. Sosai tsigar jikina ta tashi, dan wani irin kallo yake min mai wahalar fassara gashi da ga shi sai guntun towel iya gwiwa. Kaina nai ƙoƙarin sake saukewa cikin ɗan rawar harshe na furta, “D... dama ruwa ne...” Bai bari na ƙarasa ba ya matsa min hanya alamar na shiga. Raɓawa nayi na wuce, kai tsaye na ajiye tray ɗin saman Centre table na buɗe ruwan na tsiyaya a cup tare da ƙoƙarin ɗagowa. Ido muka haɗa da shi, yana tsaye jikin mirror ƙafafunsa a harɗe yay folding hannayensa a ƙirji ya zuba min ido kawai. Ƙasa nayi da nawa, tare da takawa a hankali inda yake, batare dana kallesa ba na miƙa masa kofin ruwan. Shiru babu alamar zai amsa, dan haka na ɗago cikin yanayin kamar mai shakku na kallesa, har lokacin idanunsa a kaina suke, samun kaina nayi da marairaice face ɗina kamar zanyi kuka na ce, “Pleaseeee!”. Ɗan luuuu yayi da idanunsa kamar zai lumshe sai kuma ya buɗe a kaina har sai da naji tsigar jikina ta tashi, hannuna dake riƙe da kofin ya ɗan fara rawa-rawa kamar zan saki kofin. Hannayensa dake harɗe a ƙirjinsa ya warware a kasalance, dan haka na ƙara ƙasa da kaina dan bazan iya kallonsa a yanda yaken ba. Jin saukar hannunsa a saman nawa mai riƙe da kofin ruwan ya sani lumshe nawa idon batare dana ɗago na kallesan ba. Ina ƙoƙarin sakar masa amma ya hana hakan, sai ma saukar ɗayan hannun nasa naji akan gefen cikina, a hankali ya fara tafiya da shi har zuwa bayana, kafin ya matsoni ya manne da jikinsa. Sannan ya kai ruwan da ke a cikin hannayenmu saman lips ɗinsa. Yasha kusan rabi ya zare kofin ya ajiye. Ni dai har lokacin ban sake yarda na kallesa ba. Sai dai na furta, “Nagode sosai Ya Awwab. ALLAH ya saka da alkairi, ya bama Ummie lafiya da tsohon rai mai albarka. ALLAH ya kareka da sharrin masu sharri. ALLAH ya yarda dakai”. Jinai kawai ya ɗora ɗayan hannun nasa ta saman bayana shima ya mannoni da jikinsa gaba ɗaya ya kwantar da kaina a saman faffaɗan ƙirjinsa. Luff nayi ina mai shaƙar narkakken ƙamshinsa mai matukar tasiri da saka nutsuwa a zuciyar mai shaƙa. Munfi mintina biyar a hakan har wani bacci-bacci nake ji yana neman ɗaukata. Sai naji ya ɗagoni a slowly tare da juyamu na koma jikin mirror ɗin shi kuma ya koma inda nake da. Dagowa nai da nufin yin magana ya ranƙwafo ni gaba ɗayansa, daɓas na koma saman mirror ɗin na zauna, shi kuma yamun rumfa hannunsa ɗaya dafe da mirror ɗin, ɗayan kuma ya saukesa akan haɓata ya ɗago fuskata. Cikin matuƙar low voice ya furta, “Open your eyes”. Jinai Sam bazan iya masa gardama ba, dan haka na shiga yin far-far da idanun kafin na buɗesu da ƙyar na saukesu akan ƙyaƙyƙyawar doguwar fuskarsa dake ƙawace da kwantaccen gashi baƙi siɗik. Kallon juna muke cikin ido da mu kammu bazamu iya fassara yanayin da muke a ciki ba. Sai wani irin tashi tsigar jikina keyi, a hankali a hankali idanuna suka fara tara ƙwalla. Kasa jurewa nayi na lumshesu slowly ina sauke tagwayen ajiyar zuciya. Dan mutumin nan zai kasheni da salonsa. A bazata matuƙar bazata naji saukar abu mai sanyi da taushi saman lips ɗina. Da sauri na buɗe idanuna. Ai babu shiri na maida su da gudu na kulle zuciyata na tsargawa. A salon da yake kissing ɗin nawa yasa gaba ɗaya jikina ya saki har ban san na kai hannuna saman kansa ba nariƙosa. Har ga ALLAH hakan da nayi kawai nayi ne amma bada wata manufa bane, tsabar na rasa ina zan dafa na samu sassaucin ruɗanin dana shiga ne yasa hannuna sauka a saman kan nashi batare dana shiryama hakan ba. Ashe shi hakan armashi ya ƙara masa, dan wajen kicin-kicin ganin na janyesa harda zame band ɗin dake ɗaure da gashinsa na tura yatsuna duk biyar cikin gashin ina yamutsawa. Munfi mintuna uku a haka, kafin ya janye lips ɗin nasa tare da ɗaura goshinsa saman nawa, hancinanmu na gogar juna, kowannenmu na sauke numfashi. Wajen minti ɗaya sannan ya ɗago kansa, kasa kallonsa nayi, sai ma hawayen da suka cika min idone suka ɗan silalo badan ni kaina nasan dalilina nayin su ba, gaba ɗayana ya jawo ya rungume tsam-tsam a jikinsa. Nima samun kaina nayi da ƙanƙamesan dan jikina rawa yake yi.. nan ma mun kwashe wasu mintuna biyun a haka kafin ya kai bakinsa saitin kunnena cikin raɗa ya furta, “Kema baƙi ƙoshi ba ko? A ƙara”. Ji nai kamar na tsaga jikinsa na shige dan kunya, sai kawai na sake ƙanƙamesa. Wani irin ratsa kunnena sassanyan sautin murmushinsa yayi a bazata. Sai kuma ya ɗagoni yana ƙoƙarin kallon fuskata amma naƙi yarda yay hakan.... A dai-dai lokacin da acan Maash da Sam-G ke a wata duniya anan falo Mama Balki ce ta iso domin gaishe da baƙi. Cikin fara'arta da kazar-kazar ta shigo bakinta ɗauke da sallama. Amsawa su Musaddiq sukayi dama ransu fal tunanin ganin wannan uba-uban ƙaton gida amma basuga giccin kowa ba sai masu aiki maza. Ɗagowa sukayi su duka a tare da nufin gaisheta, kawai saita ja birki da uban sauri har tana buge ƙafa da kujera. Kallon Musaddiq take kamar zata cinyesa da idanunta, jikinta sai rawa yake yi. Sai kuma ta sake maida kallonta ga Hafizzullah shima. Sai kawai gani sukai ta fashe da wani irin kuka tana faman jan jikinta baya. A ruɗe duk suka miƙe suna tambayarta lafiya? Mike faruwa?. Sam ta gagara basu amsa, sai sake cin tuntuɓe da tayi da carpet hakan yasata tafiya gaba ɗayanta zata faɗi ta baya suka hau salati da nufarta su duka biyun suka tare a tare.... Cak Maash ya dakata daga yunƙurin sake maida lips ɗinsa da yake saman na Samraah. Itama sai ta buɗe nata idanun da sauri duk suka kalla ƙofar. Dan su dukansu sunji salatin su Hafizzullah ɗin Kasancewar da ƙarfi sukayi. Kallonta yay, itama ta kallesa, sai kuma a hankali ya zame hannayensa da ga jikinta ya ɗaga gaba ɗayanta ya sauke daga saman mirror ɗin daya ɗaurata. Zan nufi ƙofa da sauri ya riƙoni, fuska na marairaice masa kamar zanyi kuka. Sai yay min nuni da gyalena da ɗan kwali dake yashe a ƙasa. Gyalen kawai na ɗauka dan hankalina ya tashi, kada wani ya cutar min ƴan uwafa a gidan nan? Da wlhy sunga ainahin baƙin halina dan saina gallabi kowa da kowa har uban gayyar tasu bazan bari ba. Dai-dai ina isowa falon suke ƙoƙarin zaunar da Mama Balki a kujera, sai nai turus ina kallonsu. Ruwa Yaya Musaddiq ya bata, yayinda Hafizzullah daya juyo ya ganni yake sanar min abinda ya faru. Da sauri na nufi Mama Balki. Zama nayi a kusa da ita cikin damuwa ina tambayarta mike faruwa?. Dai-dai nan ya fito shima sanye cikin baƙar jallabiya da tai masa wani masifar ƙyau. Muna haɗa ido na kauda nawa da sauri. Mama dake kallonsa itama fuskarta share-share da hawaye ta nuna masa Yaya Musaddiq. “Alhaji ƙarami dan ALLAH kalla bawan ALLAHn nan. Kalla yanda yake tsananin kama da Babanku. Inda ace mutum na mutuwa ya dawo da ƙuruciyarsa babu abinda zai sa bazan dage Abdul-wahab bane ya dawo Alhaji Ƙarami”. Shiru kamar bazaice mata komai ba, sai kuma ya ɗan nisa a hankali tare da kaiwa zaune cikin kujerar dake facing ɗinta. Zaman ƙafa ɗaya kan ɗaya yay yana mai kwantar da kansa a jikin kujera tare da lumshe idanunsa. A haka ya furta, “Please Mama relax. Wannan ba Baba bane, dan Baba ya tafi ya barmu tafiya ta har abada.” ɗagowa yay da kansa ya ɗan zuba mana idanu mu duka sai kuma ya sake furzar da iska kaɗan yana ɗan mana nuni da Mama Balki. “Wannan matsayin uwa take garemu mu duka. Ban sani ba ko kun san Baba yana da mata a zamansa na Lagos harda yarinya ɗaya. Itace wannan”. Da sauri Yaya Musaddiq ya kalla Mama, sai kuma ya juya ya kalla Maash ɗin. Sake gyaɗa masa kai yay cikin lumshe idanunsa tabbacin haka ɗin ne. Ni ko da Hafizzullah a ruɗani muke kallonsu. Gwarama ni dama na jima da wannan al'amarin a zuciya. Sai kawai mukaga Yaya Musaddiq ya duƙar da kansa yana hawaye. Kafin ya miƙe a hankali yaje gaban mama Balki ya tsugunna. Hannunta ya kamo cikin nasa hawaye na cigaba da masa gudu a fuska ya furta, “ALLAH na gode maka daka saka inada rabon ganin wannan rana kafin nabar duniya. Mama dan ALLAH kiyi haƙuri, kiyi haƙuri kiyi haƙuri. Tun daga randa nasan kaina, tare da labarinki a wajen Gwaggo Gudidi ban taɓa fashin addu'ar ALLAH yasa kafin nabar duniya na haɗu da ke da ƴar uwarmu da akace tana tare dake ba. A dalilinki sau biyu ina zuwa Lagos bayan na tuhumi iyayena akan kuskuren da sukayi suka nuna min nadamarsu suma, sai dai dan basu san ina zasu ganoki ba suma shiyyasa suka cigaba da zama da damuwar a rayukansu. Tabbas mama an cutar dake. Muma kuma an cutar damu, tunda da mun sanki na tabbatar bazamuyi kukan rashin iyaye a duniya ba. Dan ALLAH mama kiyi haƙuri ki yafema ahalinmu kada hakkinki ya cigaba da hanasu kwanciyar hankali a rayuwarsu. Kuskure ne sukayi a wata gaɓar da mu kammu bamu tsira ba. Dan mu ɗin ma komai sai da ya ƙwaɓe tsawon shekaru tsakaninmu dasu babu wani jituwa sakamakon amsata da ƙanin mahaifiyar mu yayi ya riƙe bai bar musu ba, duk da dama tun raduwar mahaifiyarmu ita Samraah da Hafizzullah suna a hannunsa ne. To nima sai yace zan koma hannunsa, amma suka nuna basu amince ba suma su Samraah sai a dawo musu da su. Kowa ya fahimci gadon da aka barmana sukemawa shiyyasa dangin mahaifiyarmu suka dage shine akai rabuwar tashin hankali suka manta damu sai da ga baya naita bibiyarsu har komai ya dai-daita. Zamma iya cemiki dawowarsu garemu sosai-sosai lokacin amsar kuɗin auren Samraah ne”. Kuka yaci ƙarfinsa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_ ......Muma kukan muke ni da Hafiz sosai. Hakama Mama kuka take har tana siƙewa. Sai da ya mana magana cikin gyaran murya sannan kowa ya ɗan tsagaita. Cikin yanayinsan nan na rashin son hayaniya ya furta, “Kuka ba shine alama ta godiyar ALLAH ba. Abinda ya faru ya riga ya faru, ku fuskanci wanda yake a yanzu itace rayuwa. Ya kamata bayan magrib itama Falaq kuje can dan ta ganku tunda tana fama da kanta bazata iya tazo nan ba. Gashi babu wani lokaci shi Musaddiq zai wuce gobe in sha ALLAHU”. Duk mun gamsu da zancensa, yayinda Mama ke jinjina kai ta ce, “Alhaji Ƙarami dama kasan inda suke kenan? Shiyyasa ka auro Samraah?”. Ɗan luuu yay da idanunsa kamar abin dole ya saki murmushi. Babu wanda ma yay zaton zai amsa a cikinmu saboda yanda ya jima baice komai ba. Sai kuma ya ɗan furzar da iska cikin sauke numfashi. Kansa ya girgiza a daƙile ya furta, “A farkon ganina da ita ban san ita wacece ba. Ban kuma taɓa kawo wani abu game da ita ba. Sai dai sunanta ya ɗan so ya ja hankalina har ya tunamin da Baba a ranar. Abubuwa ne da yawa suka faru da suka alaƙanta wannan auren Mama, dan har ga ALLAH ni banje da nufin ɓata mata aure ni na aureta ba. Kawai na hana wancan ne dan na kuɓutar da ita daga halin banza na mahaifiyarsa. Sai kuma Uncle nata yace ya bani, naso kawo musu wani dalili sai kawai naci karo da fuskar Musaddiq nima a lokacin, shine kawai nace na amsa. Bayan barina wajen kafin a ɗaura auren na saka akamin bincike shine na gano su ɗin yaran Baba ne”. Sosai kowannenmu ke jinjina iko da hikima ta UBANGIJI. Hafizzullah da bai fahimci komai ba a zancen yay tambaya. Nice na masa bayani. Sai kawai ya hau murna wai muma ashe munada Mama. Abinda yay ɗin ne ya sakamu darawa mu duka. Hatta shi uban gayyar ina kallon sanda yay ɗan munafukin murmushin nan nasa dai-dai yana miƙewa. Ciki ya koma ya barmu anan da Mama. Aiko sai labari ya ɓalle a tsakaninmu, dan Mama wayayyar mace ce mai kuma tsananin kirki da dattako. Fita tayi sai gata tazo da Malam Baba. Mahaifin Hayatu kenan, mijinta kuma a yanzu, aminin mahaifinmu. Shi kansa ya shiga mamaki matuƙa, ya kuma yi farin ciki da ganin ƴaƴan amininsa. Duk da ya jima zuciyarsa na masa wasi-wasi a kaina ashe. Shiyyasa tun ranar farko daya ganni agidan yake kallona. Dan duk da bana kama da Babanmu, gaba ɗaya komaina na mahaifiyarmu ne idan ka cire ɗan duhun da nake da shi dan mahaifiyarmu farace tass, su su yaya Musaddiq duk sun ɗakko farinta amma kamanin Baba. Maganar aure kuma dake a tsakanina da Maash ya sani Hayatu ya faɗa masu dama. 🌺🌺🌺🌺 Ganin har gab da magriba bai sake fitowa ba munata hirarmu da Mama a falo Yaya Musaddiq yay min nuni da hanyar bedroom ɗinsa cikin hikima. Jinai duk kunya ta gama kamani, sai dai bazan iya musa masa ba. Dan haka na tashi sum-sum na wuce. Yanzun kam ban tsaya knocking ba na murɗa handle ɗin ƙofar a hankali na shiga kaina a ƙasa. Dan har yanzu ina jin nauyi da kunyar abinda ya faru a tsakaninmu ɗazun. Jin ɗakin shiru kamar babu motsi ya sani ɗan ɗagowa ina kallon ko ina. Sauka idanuna sukai a kansa. Yana zaune a cikin sofa sanye da bathrobe alamar bai cire ba tunda ya fito wankan, bowl ne na glass a saman cinyarsa da uban chocolates a ciki. Da mamaki nake kallon chocolates ɗin kafin na ɗan ɗaga idanuna akan fuskarsa. Da farko na zata ma barci yake a hakan, sai da naga gashin idonsa dogaye sosai sun ɗan motsa alamar kallona yake ƙasa-ƙasa. Kauda nawa idanun nayi kamar zan juya naji ya furta, “Zo nan”. Idanuna na ɗan rumtse, dan duk sanda saukar muryarsa zai shiga cikin kunnuwana sai na jisu har tsakkiyar brain ɗina. Sai da na ciza lips da sauke numfashi sannan na juya kaina a ƙasa na nufesa. Ban zauna a kujerar da yake ba doguwa sai na zauna akan ɗayar dake gefensa dan guda uku ne dama. Doguwa ɗaya sai biyu masu zaman ɗai ɗai a gefe da gefen ta. “Mi kike buƙata?”. Ya faɗa a daƙile yana kai sauran chocolate ɗin hannunsa ƙaramin bakinsa. Satar kallonsa nayi ina mamaki a raina, namiji da cin chocolate, ai kayan yara ne da mata, duk yau banga ni dai ya ci abinci ba, sai dai ko da suka fita yaci. Ganin ya zuba min ido na ɗan girgiza masa kaina da faɗin, “Ba komai, kawai na jika shiru ne baka fito ba. Ga kuma abinci duk yau naga baka ci ba”. Shiru bai tanka min ba tsahon kusan mintuna biyu, kafin ya ɗago a nutsensa zaune sosai tare da ajiye bowl ɗin chocolates ɗin nashi a Centre table. Murya can ƙasa ya ce, “Gashi ina ci”. Yay maganar yana nuna bowl ɗin chocolates ɗin. Da mamaki na ɗago idanuna sosai na warosu a kansa. Tare da furta, “Chocolate ne abinci? Abin kwaɗayin yara ne fa. Kai kuma ƙatoto da kai ka zauna kana ci, kuma amma ce fa maza basa cin zaƙi hak.....” Ganin yanda yake kallona da mayatattun idanunsa na kasa ƙarasawa, sai ma na miƙe cikin wayancewa na ce, “An kira magrib bari na shirya kar su zo suna jirana”. Na wuce bayi da sauri. Da kallo ya bita harta shige, sai kuma ya girgiza kansa shima yana miƙewa zuwa closet ɗinsa yin shirin massalaci. 💕💕💕 Bayan sallar magrib Hayatu da kansa yazo ɗaukarmu. Ogan nasa bai dawo ba. Amma tunda shi yace zamuje dama sai ban damu ba na shirya tsaff cikin atamfa riga da skirt a kayan daya kawo min. Ni da Hafizzullah da Mama a baya, Yaya Musaddiq da Hayatu a gaba. Yanda naga bakinsa yaƙi rufuwa saboda farin ciki nasan Mama ta gaya masa komai ko mahaifinsa. Nayi matuƙar mamakin ganin ƙayataccen gidan da shima yake a ciki. Sai na sake yarda da batun Mama Balki da tace su suna zaune a Maash Mansion ne kawai saboda Ummie. Shine gaba muna biye da shi, sosai ta ciki ma gidan yay ƙyau da tsaruwa. Sai da muka zauna ya kwala kiran mai aikinsu wata ƴar budurwar yarinya ta fito. Gaishemu tayi sannan ya bata umarnin kawo ruwa da abinci shi kuma yay sama. Babu jimawa sai gashi ya fito riƙe da ƙyaƙyƙyawar matashiya, gaskiya zata iya girmata koda shekara uku ne, da ƙyar take tafiya saboda cikin jikinta da yay girma sosai. Duk da fuskarta ta ɗan yi fushi irin na masu ciki hakan bai ɓoye kammaninta da Hafizzullah ba. Yanda muka zuba mata ido haka itama ta zuba mana nata. Lokacin da suke isowa gab da mu jikinta har rawa yake yi. Haka ta dinga bimmu ɗaya bayan ɗaya da kallo, kafin ta maida kan Mama da ke kallonta itama fuskarta ɗauke da murmushi. Cikin langaɓar da kai ta ce, “Mama ina ji a jikina su ɗin jinina ne. Dan ALLAH Mama kada kuce dani ba haka bane ba. Yaya Hayat yace bazai faɗa ba sai dai na gani da ido na”. Murmushi mukayi mu dukanmu, kafin Mama ta gyaɗa mata kai. “Tabbas su ɗin jininki ne Falaq. Ga babban yaya Musaddiq, sai Samraah ban ƙanwa, sai auta Hafizzullah”. Kuka ta saki a hankali idonta akanmu muduka ta ce, “Wlhy yaya kamar Baba, suna kama sosai”. Ta faɗa tana sake fashewa da kuka mai ban tausayi. Gaba ɗaya muka miƙe muka rufu kanta. Yaya Musaddiq akwai son ƴan uwansa, tuni ya janye ta daga jikin Hayatu ya kamata ya zaunar a kujera, gabanta ya durƙusa cikin lallashi yake mata daɗaɗan kalamai. Sai ta fara dariya ga hawaye. Ganin haka nima na zauna a kusa da ita na shiga share mata hawayen nata. Sai ta haɗamu ta rungume, tare da miƙawa Hafizzullah hannu alamar shima yazo. Ta ɗayan gefenta ya zauna shima muka haɗe kai waje guda muka bar Mama da Hayatu ƴan kallo. Mun jima a haka kafin Mama su dinga lallashinmu. Sallar isha'i data gitta ya samu miƙewa, mazan suka fita mu kuma mukayi anan gida. Koda suka dawo sabon babin hira muka buɗe, Yaya Musaddiq da Mama nata bamu labarin Baba. Dan Hayatu fita yayi wai Maash ya kirashi akwai inda zasu je. Banyi mamaki ba, dan sukam ko aljanu haka suka gansu suka barsu saboda shegen yawonsu. Sai naji tausayin Falaq ya kamani, haka take haƙuri (kema haka zakiyi haƙurin) zuciyata ta ayyana min. Da mama ke sanarma Falaq ɗin ni matar Maash ce a yanzu wani irin ihun farin ciki ta saki tana rungumeni, koba komai ƴar uwarta ta dawo kusa da ita. Tsaff suka bata labarin yanda komai ya faru, ta dinga farin ciki da ƙorafin Hayatu ita bai sanar mata ba. Kamar wasa sai ga lokaci yaja. Dan sai da sha biyu tayi sannan Hayatu ya dawo, shine yake cewa ga Maash a waje yana jiranmu. Kuka Falaq ta sanya wai anan zamu kwana, ita bata gaji da ganinmu ba. Cikin dariya Hayatu yace, “Nikam babu ruwana Hubby, keda yayanki jeki gashi can”. Aiko miƙewa tai tana ɗaukar mayafina, itako Mama Balki ta miƙe tana faɗin, “A'a nidai kam nayi nan”. Dariya muka sanya mata, dan muma ba son tafiyar muke ba, saboda hirar bata ishemu ba. Sai addu'a nake a zuciyata ALLAH yasa ya yarda. Kusan mintuna biyar sai gata ta dawo tana tuttura baki. Mayafina ta cire ta miƙamin tana faɗin, “Ya yarda da ƙyar su Yaya su kwana anan ɗin, amma wai ke kije lil sis...”. Ɓata fuska nayi nima kamar zanyi kuka. Nace, “Amma baki roƙesa ba ko Aunty?”. “ALLAH har kuka na masa. Kin san taurin kan Yayana kuwa. Idan yace a babu mai canja masa zuwa b. Cayay da ma wai idan na haihu zaki zo. Bama gobefa kenan”. Dariya Hafizzullah ya fashe da ita, harara na balla masa da ɗaukar mayafina fuuu na nufi hanyar fita... Shima dai Yaya Musaddiq da ke riƙe dariyarsa da Hayatu sai da suka dara, kafin su miƙe subi bayanta. Sanda suka iso ina tsaye jikin motar ta saitin inda yake ina masa magiya amma ɗan mannin bai ko buɗe idonsa dake lumshe ba ya kallan bare ya tanka. Haushi da takaici ya sani balla masa harara na koma ta ɗayan side ɗin dan Mama ce a gaba kusa da TJ, da sauri TJ ɗin dake a waje ya buɗen ƙofar yana wani risinawa. Ko kallonsa banyi ba na shiga na zauna na juya ƙeyata. Koda su Yaya Musaddiq suka iso wajen inaji yana magana da su wai ƙanwarsa ta masa fin ƙarfi shi da baƙi ita da ƙwacesu su kwana. Ina jin yanda suke ƴar dariya da bashi haƙuri. Basu wani jimaba yace ma TJ muje Mama ta gaji. Suna min sallama ƙin kallonsu nayi, ina jiyo dariyarsu su duka ukun sai naji idanuna sun cika da ƙwalla........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ 𝑷𝒂𝒈𝒆 twenty five ........Koda muka iso gidan na gama shiryama raina abinda zanyi. Dan haka ina fitowa na zabura zanyi sashen masu aiki caraf aka riƙeni. A fusace na juyo, sai dai kafin ma na samu damar cewa wani abu camak ya ɗagani a cikin hannunsa ko kunyar su Mama Balki da TJ da sauran ma'aikatan dake a harabar gidan da basu yi barci ba baiji ba. Salati na ɗauka ina wawwaro idanu na da suka cika da ƙwalla waje. Amma sai yay biris dani kamar ma baiji ba, takunsa ma yake ɗai-ɗai like bai ɗauki komai ba. Tafi mukaji da salati, da sauri na ɗaga ido na kalla saman ginin dan tanan ne ake yi. Sai ko idanun nawa suka sauka akan Hajiya Mammah dake tacan sama a balcony na upstairs. Mutsu-mutsun son sauka na farayi, amma ko alamar zai taimaka ya saukenin baiyi ba. Bai kuma nuna shi yama jita ba balle ya kalla inda take. Bai kuma direni ba sai a gaban ƙofar sashensa. Yana riƙe da hannuna ya buɗe muka shiga. Muna shiga falon na sakar masa kukan shagwaɓa ina faɗin, “Ni ka sakan min hannu wajen Ummie zani, kuma ka daina bani kunya gaban mutane”. Hanya ya nuna min alamar naje. Yanzu kam kasa haƙuri nayi sai da na kallesa. Sai kuma na shiga ƙyaƙyƙyafta idanu. Muryata na ɗan rawa na sake ɗagowa zanyi magana yay mun alamar zipping akan bakinsa tare da sake nuna min hanya. Kamar zan fasa kuka na shiga tafiya a hankali yana biye da ni har cikin bedroom. Koda muka shigan ma sake nuni yay min ba bathroom. Nan ma sum-sum na wuce dan babu alamar wasa a tattare da shi. Gaba ɗaya a tsorace nake, idan yace abinda ya aikata zai maimaita nama san mutuwa zanyi kawai.. Wankan nayi tare da ɗauro alwala amma sai na kasa fitowa duk da bathrobe na saka. Ina tsayen ina faman ƙullawa da kwancewa kawai ya shigo shikin bayin, idanu na waro sosai na mamaki, sai ya wani lumshe min idanunsa yana nufoni, da sauri naja da baya na manne da bango, na gama sadaƙarwa kaina zai zo sai kawai ya wuce ni. Ajiyar zuciya na sauke mai nauyi tare da fita a hanzarce cike da sassarfa. Na ji daɗin ganin kayan barci daya ajiye min wando da riga masu kauri, ɗauka nayi na saka a gurguje, tare da ɗaukar mayafina na yafa. Har na kammala abinda zanyi dan ya ɗan jima a cikin bayin sai kuma gashi ya fito sanye da bathrobe fara tas shima. Idanu muka haɗa, nai saurin ɗauke kaina ina sake ɓata fuska. Shima sai yay wucewarsa kamar bai ganni ba. Ya jima a cikin closet kafin ya fito nan ma, ina kwance kan sofa ina game da wayarsa daya ajiye a Centre table sai gashi ya fito shima cikin kayan barci sky blue da suka masa ƙyau sosai. Batare da ya kallan ba yace, “Muje”. Wani ɗan karan daɗi ne ya kamani, cike da zumuɗi na bisa dan a zatona ya barni naje can ɗin na kwana. Bare ma dana ganni a sashen Ummie ta hanyar da ban taɓa sanin yana da ita ba. Mun sami Ummie har tayi barci. Zama yay yana mata addu'a, ganin haka nima sai na zauna ina mata addu'ar. Tsahon mintuna goma sha muna a ɗakin ya fara riƙe kansa. Muƙewa yay a hankali tare da riƙo hannuna ya ce, “Lets go”. Tsoro naji yanda naga ya riƙe kan, dan haka banyi musu ba na bisa. Sai da naga zamu koma sashensa nai ƙoƙarin yin magana amma ya hanani hakan. Muna shigowa a bakin gado ya kai zaune, yana sake dafe kan nasa da hannu bibbiyu. Tsoro ne ya kamani da tausayinsa, har bamma san naje gabansa na durƙusa ba ta tsakanin ƙafafunsa na dafa gwiwarsa ɗaya, ɗayan hannun kuma na kaisa saman nasa hannun daya dafe kai. A hankali na janye nasan muryata a raunane na ce, “Ya Awwab miya faru? Baka da lafiya ne?”. Shiru kamar bazai kulani ba, sai kuma ya ɗago shanyayun idanunsa da launinsu ya sauya zuwa golden yana kallona. Cikin motsa lips ɗinsa kamar baya so ya furta, “My head”. “Ciwo yake?”. Idanunsa ya lunshe min alamar eh. Cikin damuwa nace, “Na maka kamu?”. Nan ma kan kawai ya jinjina min yana maida idanunsa ya rufe. Miƙewa nayi sosai dan na fara gajiya da durƙuson, hannunsa na janye, na ɗaura nawa a wajen na fara masa addu'a. Inayi ina kamun da tofa masa addu'ar. Har na kammala ina faɗin, “ALLAH ya ƙara lafiya”. Ya amsa min da amin akan lips ɗinsa, ƙoƙarin barin gaban nasa nake naji saukar hannunsa a saman ƙuguna. Da sauri na kallesa tsigar jikina na tashi. “Ina zaki?”. A raunane na ce, “Saman sofa”. “Gadon fa?”. “Amma....”. “Shiiiiii!!!”. Ya katseni tun kafin na ƙarasa faɗa. Tare da nuna min saman gadon babu wasa sam akan fuskarsa. Duk da shi dai ba banbance farin cikinsa ko damuwarsa kake dama a saman fuskar ba. Tunda akoda yaushe babu alamar fara'a a tare da shi. Sai idan shine ya so ya saki wannan munafukin murmushin nasa iya lips. Jikina har rawa yake wajen hawa gado. Idanuna kam tuni sun tara ƙwalla. Haka na kwanta ƙarshe gadon na wani naɗe jikina tamkar ƴar mage. Shiru banji ya hawo ba bai kuma tashi ba. Kaɗan na ɗan buɗe ido na kallesa. Yana zaunen har yanzu dafe da kan nasa alamar bai gama sauka ba. Jinai tausayinsa ya ƙara kamani, bamma san cikin raunin murya na furta, “Ko dai yunwa ce? Nifa duk yau banga kaci abinci ba”. Shiru baida alamar amsa min. Baima motsa a yanda yake ba har na gaji na maida idanuna na rufe. Mintuna baifi biyu ba ya hauro saman gadon, tuni zuciyata ya fara mutsu-mutsu, barema da ya kashe wutar ɗakin ya bar lamp ɗin side ɗinsa kawai itama ya maidata can ƙasa ba wani hasken kirki kasancewar muna a cikin net ne da yayma gadon rumfa gaba ɗaya. Jira kawai nake naji yamin irin na waccan ranar amma sai naji shiru baima ko matso inda nake ba. A hankali a hankali na fara samun nutsuwa har barci ya ɗan fara figata. Sai can na saki jikina sosai sannan na jisa a bayana. A ɗan firgice na farka, sai da ya riga har ya birkitoni na koma jikinsa gaba ɗayana ya rungumeni. Kasa daurewa nayi, sai da nayi magana cikin rawar murya irin ta wanda ke cikin tsoro. “Yaya wlhy akwai ciwo”. “Nace zanyi wani abu ne”. Ya faɗa cikin kunnena da wata irin muryar da sai da tsigar jikina ta tashi. Ƙam na runtse idanuna ban sake cewa komai ba. Shiru har kusan mintuna biyu muna a haka kafin a hankali ya dai-daita fuskata da tashi, goshinsa a saman nawa hakama hancinsa sai lips ɗinmu sai dai su ba'a haɗe ba. Duk da a cikin duhu-duhu muke yanda idanuna ke a rufe shima nasa a rufen suke. Cikin wani irin soft and low voice ya furta, “Yanzu dai so kike ayi wani abu ko?”. Da sauri na shiga girgiza masa kaina hawayen da nake riƙewa na zubowa da gudu. “To mi kike so?”. “Barci”. Na bashi amsa har ina taune lips ɗina jikina na tsuma. “Ni kuma bana jin barci ya za'ayi?”. A marairaice na ce, “Ka tashi kayi salla to ko karatun Alkur'ani”. “Uhum-uhum. Ni matata nake buƙata”. Har cikin tsakkiyar brain sai da naji saukar furucin. Muryata na matuƙar rawa na ce, “Ya Awwab wlhy akwai ciwo. Kuma doctor tace ba...bai...war...ke...b.....” Nama kasa ƙarasawa. “Yanzu mi kike so ayi to?”. Da sauri na sake maimaita, “Barci”. “Kin tabbatar?”. Kaina na shiga jinjina masa. Da sauri-sauri. “Tom bari na saki barcin”. Ya faɗa acan ƙasan maƙoshi. Kafinma nace wani abu naji saukar small lips ɗinsa kan nawa. Tun ina mutsu-mutsun ruɗewa da firgici har na nutsu luff, dan wani irin salo yake min mai shagaltar da gangar jiki, cikin ƙanƙanin lokaci na gama sallamawa gaba ɗaya na batare da ni kaina nama san minake ba. Ban tashi fahimtar kuskure na ba sai da aka ɗauki wani layi daban. Duk da a yanda yau yake bina a mugun nutse, cike da tattali da kulawa bamma san sanda na sakar masa kukan azaba ba jikina na matuƙar rawa..... ❤️★❤️★❤️ Tun a balcony ɗin take faman jera manya-manyan ashariya wa Maash. Koda ta afka bedroom ɗinta gaba ɗaya ta kasa haƙuri saboda yanda zuciyarta ke mata hanƙoro. Wai mi yaron nan ke shirin maidasu? Ƴan iska ko mi? Yanzu har Ummu-Hidaya ta haifi abinda zaifi ƙarfinsu kenan. Yarinyar da aka haifa a gabansu, balle shi karan kaɗa miya. Kai wlhy bazai yiwu ba. Dole ne ta ɓaro aikin da dolema ayita ta ƙare a gobe. Ina dalili Rubayya ta sakata aikata abinda ke neman juyewa da ita. Banda yaron nan ƙwallon ɗan iska ne ka haikema yarinya amma ka koma kana wani abubuwa irin ga matarka ɗin nan kayi first night ko. To wlhy daga daren yau zuwa gobe sai ta tada hankalin kowa na gidan nan sai dai anyita ta ƙare. Munafukai kowa yayi shiru da bakinsa irin komai ma bai faru ɗin nan ba. Waya ta jawo, ta shiga daddanawa. Number baba prof ta kira. Sai da ta kusa tsinkewa ya ɗauka cikin alamun wanda ya fara barci. Kuka ta fashe masa da shi a maimakon sallama. Cikin tashin hankali ya shiga tambayarta abinda ke faruwa?. Amma taƙi magana sai kuka. Sai da ya mata tsawa cikin tashin hankali kafin ta fara magana tana jan sheshsheka. “Baba wace irin ƙazamar rayuwa kuma ke neman zuwa mana gidan nan. Mun shiga uku Awwab ya ɓalle. Baba kaga kuwa abinda na gani yanzun nan. Ya gama lalata wata gata can kwance a asibiti gashi can kuma yaja wata sashensa zai ƙara. Kuka yarinyar take tana roƙonsa amma bai barta ba. Har magana nayi masa amma ya hauni da zagi, wai bamun damesa yay aure ba, to haka zaita haye ƴaƴan mutane har ƴaƴanmu ma su jira zuwansa. Mu kammu idan bamu kama kammu a gidan nan ba sai layi ya biyo ta kanmu. Baba wlhy Awwab ya gama iskancewa, yaro ya tambaɗe ya lalace, kai ko jinin turawa na yawo a jikinsa. In baiyi bama ai bai cika jikan sifanawa ba (Spain 😂). Wayyo Baba mun shiga ashirin watan zubewar mutuncinmu yazo a duniya. Ƙilama a wannan karon har bbc saita bugamu...” A rikice Baba yay mata tsawa, dan gaba ɗaya ta gama ruɗar da shi yama kasa yin tunanin daya dace. Ƙitt ta yanke kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya. Dariya ta sanya cikin yanayin basanci ta ce, “A'a badai nice ba. Ai sai kaci baban uwarka Alonso Awwab. Gobe-gobe sai ka zama mijin Azizat ɗina. Kwantar da hankalinki ƴar albarka kukanki na kusa sharesa, nima kuma burina ya kusa cika.” ta sake ƙyalƙyalewa da dariya.......✍️ Hummm munsha yajin aikin dole ko🥱😂 *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 twenty six .......Fita tayi a sashenta, kanta tsaye tai sashen Paah shima. Wani irin mahaukacin bugu ta dingama ƙofar tana kuka da ihun da sai da kusan kowa ya tashi. A masifar firgice Paah da Hajiya ƙarama suka fito. Ko bari su tambayi ma abinda ke faruwa batai ba ta hau rusar kuka da sanar musu kamar yanda ta sanar da Baba prof ta waya. Hankalin Paah da Hajiya ƙarama duk tashi yayi. Suka shiga salati da sallalami. Dai-dai nan sai ga kiran Baba prof ta wayar Uncle Abdullahi da suma bugun Hajiya Mammah ɗinne ya tashesu. Kururuwar da Hajiya Mammah keyi har yanzu ya sashi tsawatar musu kasancewar a hansfree Uncle Abdullahi ya saka wayar. “Miyasa bazaku nutsu ba ne wai. Baku da hankali ne sai kowa ya fahimci abinda ke faruwa. Darene fa? Gida cike da ma'aikata. Idan abinda ke faruwa bai zama tonon sililin ba wannan shirmen naku da tatarako ai zai zama. Kowa ya wuce ya kwanta. In sha ALLAHU da safe zan shigo gidan zai ci ubansa ne ai”. Kowa ya gamsu da bayaninsa, yayinda Hajiya Mammah ke kwasar dariya a zuciya. Paah kuwa jiri ma yake jin yana neman ɗibarsa. Sai da ya dafe bango dan tashin hankali. Ita kanta Hajiya Ƙarama zuciyarta sai mutsu-mutsu take a ƙirji. Ji take kamar tayi tsuntsuwa a sashen masu aiki dan ta tabbatar ita dai ba Samraah ɗinta yaron nan ya sake haikemawa ba. Sai dai babu damar yin hakan. Dole ma sai itace ta kama Paah suka koma ciki. Uncle Abdullahi da matarsa ma suka koma nasu sashe. Itama Hajiya Mammah ta juya tana dariyar ƙeta. Ranta fes wlhy dan gwara ayita ta ƙare..... 😂😂Hegiya Hajiya Mammah kin iya haɗa guri ko, to bari muga yaya wasan zai kaya🚴. 🌿❤️🌿❤️🌿 Ni a karan kaina ban san iya adadin kukan da naci ba. Dan gwara waccan ranar daga ƙarshe suma nayi, yau kuwa har ma fata nake ko zan suman na samu sassauci amma sumar taƙi zuwa. Azaba iya azaba da kwantata badai baki ba. Ban sani ba, ko hakan ya faru ne dalilin ina cikin tsoro da kuma ban gama farfaɗowa a waccan baƙar wahalarba oho. Duk da a yau komai yana yinsa gently ne ni banga wannan gentle ɗin ba sam. Kuka na gidan duniya na shashi har ina jin idanuna kansu sun min wani uban nauyi. Roƙo magiya harda cizonsa nayi amma bawan ALLAHn nan sai da ya kai inda yake buƙata. A Bathroom ma wani sabon kukan na sha, amma sam baiji tausayina ba sai da ya tabbatar ruwan zafin ya ratsani sosai yanda ya kamata sannan ya taimaka min na tsaftace jikina. Yanda ya ɗaukeni da kansa ya kai haka ya sake ɗakkoni ya maido saman gadon. Da ƙyar na amshi magani daya bani, ina gama sha ya kwantar dani, bamma san barcin wahala yay awan gaba dani ba. Dan tun ina jinsa sama-sama yana salla har nayi barcin ban san ya dawo saman gadon ya kwanta ba sai asuba.... ★★ Yanda Maash bai bari sunyi wani barcin kirki ba a wannan daren haka mafi yawan iyayensa basu runtsa ba. Hajiya Mammah dai na sake ƙulla abinda zata zo da shi gobe idan ALLAH ya kaimu. Paah na cikin tashin hankali da damuwa tare da nadamar abinda yake aikatawa. Dan shi kawai zuciyarsa na bashi TSUTSAR NAMA CE TA ZAMA NAMA. Ɓarnar da yake aikatawa ce tai naso wa gudan jininsa. Shiyyasa masu iya magana ke cewa ƊAN GADO HAR YA ZARTA. A wannan gaɓar kam ya yarda. Dama ance zina na bibiyar jini, idan kayi da ƴar wani sai anyi da taka. To shi bashi da ɗiya mace, shine ALLAH ya jarabci ɗansa babba da wannan ta'asar da ƙila zata zama sanadin tashi fallasar shima. Harga ALLAH bai taɓa fyaɗe ma kowa ba, amma fa tun yana secondary school ya fara neman mata. Saboda irin rayuwar da suka tashi, rayuwar turai. Uwa babu kwaɓa uba ba tsanani. Dan Ummansu nada faɗa, amma gasu ƴaƴanta soyayyace ziryan take musu. Garama mahaifinsu, yakan ɗan yi faɗan idan yaga abubuwan sunyi yawa. Shi kansa bai san adadin matan dayay mu'amala da su ba a rayuwarsa. Tun ma yanayin mai aji har gashi ya koma mu'amala da mai aiki. Dan da Siyama kawai yake mu'amala a gidan, hasalima ya santa ne tun kan ta fara aikin, koma yace saboda shi ta dawo aiki gidan, dan tace suyi aure yace a'a, shine ta zagaya ta samu aiki a gidan sai kawai ganinta yayi. Ya shiga matuƙar shock a lokacin, amma da yake ƴar duniya ce sai da ta maida shi ruwa a kanta duk da kuwa shi in har ya mu'amulanci mace ya rabu da ita da wahala ya koma. Amma akan Siyama sai tarihin ya canja, dan ta rantse masa in har yay sanadin data bar gidan sai ta tona masa asiri, shiyyasa ma ya barta saboda ya fahimci yarinyar hatsabibiya ce kwarai da gaske. Amma yau sai gashi ɗansa nayin yanda yaso a cikin gida batare da kunya ko shakkar wani ba. Ita ko Hajiya ƙarama tashin hankalinta kada ace Maash ya sake haikema ƴar gaban goshinta Samraah ne. Har bayi ta shiga ta gwada kiran Mama Balki sai kuma ta fasa, saboda tunawa da Mama Balki nada miji fa. Ita dai damuwarta kawai kada Maash ya sake taɓa mata yarinya. Acan Uncle Abdullahi da matarsa sun shiga wasi-wasi. Dan su zukatansu sun fara nusar da su anya kuwa ba magauta bane suka asirce Maash ɗin ke wannan irin ta'asar babu kunya babu tsoron ALLAH a cikin gida kamar wata rayuwar kafurci. Kai da sakal fa. Yaron nan na buƙatar manyan malaman ruƙuya a kansa. Ita dai Maman Malika ma harta fara batun maida Malika Niger sai abubuwa sun dai-daita. Idan har abinda Hajiya Mammah ta faɗa Awwab ɗin ya faɗa to lallai basuga ta zama ba kuwa. Dole abar gidan da ƴammatan yaran nan guda huɗu zankaɗa-zankaɗa. (😂Yayanmu kaga idi. Kowa zai fara killace ɗansa saboda kai🌚, wannan aiki yayi tsamari🤣). A ɓangaren Baba prof shima ba barcin daɗin ran yayi ba. Dan ya jima ma bai runtsa ba bayan ajiye wayar da yayi. Har gwada kiran wayar Maash yay amma ba'a ɗauka ba (😂ina zai ɗauka kuwa kandala ta kanainayesa, danginta na murna an kwace mana Yayanmu🥶). Haka ya dinga kai-kawo kamar mai Safa da marwa, sai da yaji ƙafafunsa na neman sagewa ya haƙura ya kwanta. Aiko asubar fari ya miƙe dan ko'a barcin nasa mafarkin Maash ɗin kawai yake yi ya haikema yarinyar mutane (kuji masifa🥱. Yo banda sa kai a uku kai tsoho ina ruwanka😝). 🩸🌟🩸🌟🩸 Saukar iska mai sanyi akan idanuna ya sani buɗesu a hankali dan sun min nauyi jingim saboda kukan dana sha. Ga barci da nake ji matuƙa dan sam ɗan wanda nayi bai wadaceni ba. Dishi-dishi nake ganin abinda ke gab da ni, cigaba da huramin iskar ya sani ƙarasa buɗe idanun sosai. Fes suka shige cikin nasa da sukai wani irin fitowa blue sosai, hakama golden ɗin daya ratsasu ya sake yin garai-garai tamkar zinare na ƙyalli a cikin glass. A hankali na ƙoƙarin sake maida nawa zan kulle saboda wani irin kunya ne ya baibayeni. Cike da karsashi ya ɗaura soft hannunsa saman fuskata yana sake matso da tasa fuskar gab da tawa, har hancinmu na gogar juna. Da silent muryar nan tashi mai fita acan ƙasan maƙoshi kamar abin dole ya furta, “No! Baby. Open your eyes”. Baki na taɓe kamar zanyi kuka. Cikin shagwaɓa da ban san ni kaina nayi ba na ce, “I'm not baby”. Sake manne fuskarsa da tawa yayi, tare da sake maida muryarsa can ƙasa ya ce, “Yes you are not ni shaida ne”. Yanda yay maganar yana kai hannunsa saman jikina da sauri na saka nawa na ɗan buge nasan ina sake ɓata fuska zan saki kukan. Na kuma janye fuskata da ga jikin tasa na juya baya. Zafin da naji ya sani sakin ƴar ƙaramar ƙara. A hankali ya kwanto ta bayana duk da ma ya rufeni gaba ɗaya ƴar tsitt dani a jikin nasa. A cikin kunnena ya furta, “Still Pain?”. Maimakon amsa kuka na sakar masa. Sautin murmushinsa naji a cikin kunnena, sai kuma ya saka hannunsa a saman fuskar tawa ya shafo hawayen. Hannuna nasa na ture nashin in ƙara ƙarfin kukan. Baice komai ba ya miƙe, har nayi tunanin ya barni ne sai naga ya zagayo ta gabana. Duvet ɗin da nake ciki ya yaye, tare da duƙowa ya ɗagani gaba ɗaya. Luff na kwanta a jikinsa tare da lumshe idanuna. Sai da muka shiga bayin na buɗe ganin yana ƙoƙarin cewa zai min wankan ma. Da sauri cikin shagwaɓa na ce, “Ni ka fita zan iya”. “Kin tabbatar?”. Ya faɗa cikin tsatstsareni da idanu. Kaina kawai na jinjina masa. Shima sai baice komai ba ya juya ya fita, yana gab da ƙarasa ficewar ya ce, “Ki tabbatar kin shiga ruwan nan”. Daga haka ya ficewarsa. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi, ni ba haushinsa nake ji ba. Tausayin kaina kawai nake ji, in dai haka zata cigaba da faruwa wlhy na kaɗe har ganye na. Dan al'amarin sam bashi da sauƙi. Ban cuci kaina ba na nutsu na gyara jikina yanda ya kamata, kamar kuma yanda Mama Balki ta koya min hakama Doctor. Sai kuma naji na ƙara jin nutsuwa. Wanka nayi na ɗauro alwala. Cikin sanɗa da jan ƙafa na fito. Naji daɗin ganin babu kowa a ɗakin, sai doguwar riga mara nauyi da hijjab dana samu a saman sofa. Ɗauka nayi cikin sauke ajiyar zuciya na saka dan har shida da wasu mintuna. Sallar asuba nayi, koda na idar duk yanda naso yin karatun Alqur'ani kasawa nai, anan inda nai sallar na ɓingire barci. Bamma san ya shigo ya ɗagani ya maida a saman gadon ba..........✍️ *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ 𝑷𝒂𝒈𝒆twenty- seven .......Kamar yanda Baba prof yay alƙawari ƙarfe shida da kusan rabi a Maash Mansion ta masa. Sosai ma'aikatan gidan sukayi mamakin ganinsa da wannan uban safiya. A ƙasan rai kuma kowa na tunanin ko jikin Hajiya Babba ne ya sake motsawa. Dan in har ba ciwon Hajiya Babba ba baka ganin Baba prof ɗin a gidan sai dai wani babban dalili. Fitowarsa a mota dai-dai da fitowar Maash daga sashensa sanye cikin farare ɗin tas sports wear. Gefensa Laalah ne sai baƙin bluetooth daya manna a kunnesa ƙafarsa da sport shoes na kamfanin adidas. Kallon kallo aka tsaya tsakanin shi da Baba. Kafin shi Maash ɗin ya fara rissinar da nasa idon a yanayin nan nasa mai ban haushi. Inda Baban yake ya ƙarasa, ƙasa-ƙasa ya ce, “Good morning grandpa”. Danne komai Baba prof yayi, cike da kulawa ya amsa masa da, “Morning dear, how was your night?”. A takaice ya ce masa, “So good”. “Hummm Masha ALLAH haka ake so ai. Amma inaga zaka bar fita Jogging ɗin nan kamar?”. Cikin wani irin tsare kakan nasa da ido ya furta, “But why?”. Haɗe fuska Baba prof yay dan karma ya masa gardama. Kai tsaye ya amsa masa da, “Nazo ne muyi magana mai muhimmanci”. Shima fuska Maash ɗin ya ƙara tsukewa, tare da kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa baƙi mai ƙyau. Kansa ya ɗan girgiza fuskar na sake komawa tamau. “No grandpa am sorry. Ka shiga ciki, jus 30minutes am come back”. Baima jira mi Baba prof ɗin zai ce ba ya raɓashi ya wuce. Matuƙar sosuwa ran Baba prof yayi, dan ko iya cewa komai baiyi ba ya bisa da kallo kawai shi da karen nasa. Sai guards ɗinsa da suka take masa baya. Gefen lips ɗinsa ya ɗan cija kawai yana nufar hanyar babban sashen. Duk ta inda ya gitta masu aiki zubewa suke suna gaishesa. Ɗaya bayan ɗaya masu gidan suka fara fitowa suna gaishesa suma tunda duk sun san da zuwansa. Su dai yaran basu san mike faruwa ba dan ko barci ba tashi sukai ba balle ai batun yin sallar asuba. Hajiya Mammah tayi zaram zata wuce kiran Maash Baba ya dakatar da ita. Sanar musu Maash ɗin ya fita yayi, amma yanzu zai dawo. Sai a lokacin Paah ya ɗan sauke ajiyar zuciya. Tashi yay ya haura sama ya duba Ummie. Barcinta ma take hankali kwance. Sai mama Balki dake ɗan siɗaɗowa da tayi sallar asuba ta gyara sashen ta mata wanka ta bata abinci. Cikin girmamawa ta gaida Baban. Shiko yanata faman saka mata albarka da wannan ƙoƙarin nata. Murmushi dai ta dinga yi ita dai kawai. Bayan ya dawo ƙasan suka ɗan fara tattaunawa akan al'amarin Maash ɗin. Hajiya Mammah nata sakko batun Azizat, acewarta hakan shine kawai maganin wannan matsala data kunno musu kai. Uncle Abdullahi ya bata goyon baya, shi dai Paah da farko shiru yayi, sai da Hajiya Mammah ta balbalesa da masifa ne ya ce shifa bawai baya so bane. Kawai yana tunanin ta yanda za'a sake tadawa Awwab ɗin maganar ne baya kuma anyita a watannin baya sai dai rai ya ɓaci kawai a banza. Kowa ya fahimci uzirin Paah ɗin, dan taurin kan Maash a bayyane yake ga kowa na gidan. Dan in fa har bashi yace zai yi abuba babu ubanda ya isa ya sanya shi ya yisa. Hajiya Mammah dai ta nuna musu wannan karon za'a masa zagir-zagir ne, dolene su nuna masa su suka haifesa ba shine ya haifesu ba. Domin kafa hujja aka aika Maman Malika wai taje sashen Maash ɗin ta duba wace yarinya ce ya kai. Taso noƙewa, amma girman suruki ya hanata dole ta miƙe ta tafi, babu jimawa ta dawo ta sanar musu yafa kulle ƙafarsa. “Tunda yasan miya ajiye ba dole ya kulle ƙofa ba. Ai mudai Ummu-Hidaya ta haifa mana bala'i cikin zuri'a”. Duk da furucin Hajiya Mammah ɗin baima kowa daɗi a wajen ba babu wanda ya tanka mata. Kusan a dai-dai lokacin ne kuma Maash ɗin yake dawowa gidan. Yayi zufa sosai sai furzar da huci yake. Dan yayi amfani da ƙarancin lokacin ne yay gudu sosai. Kai tsaye ƙofar babban sashen ya nufa, bayan ya amshi bottle water ɗin sa da towel a hannun Shu'aibu, Laalah biye da shi ya shiga da sallama ciki-ciki. Tuni su Afrah dake gyaran sashen sun fara zubewa suna gaishesa da girmamawa. Sau ɗaya ya amsa musu kawai yana ƙarasawa ƙaramin falon da iyayen nasa suke, wanda in ba irin meeting ɗin nan ba da wahala ma kaga wani a cikinsa. Kasancewar an rabashi da glass ne da babban yasa ko damuwa da kai-kawon masu aikin basu yi ba. Dan ba'a jiyo magana, na waje kuma baya ganin na ciki, na ciki ne ke hango ma waje. Kowa bai kalla a cikinsu ba ya kai zaune a kujerar farkon shiga falon da babu kowa a kai. Ruwansa ya ɗaga sama yana tsiyayawa a baki kamar daya shigo bai ga kowa ba. Sai da ya sha sosai ya ajiye a gabansa, karensa nata gefen ƙafafunsa ya kwanta shima yana huttan gudun da suka sha yau ɗin. Sai lokacin ya ɗan kalla iyayen nasa da duk suka zuba masa ido. A taƙaice ya janye yana cigaba da goge wuyansa zuwa ƙeyarsa ya furta, “Good Morning” Paah ɗin ne kawai ya iya ƙarfin halin amsa masa da Uncle Abdullahi da Maman Malika. Amma Hajiya ƙarama da Hajiya Mammah wani shegen kallo suke binsa da shi. Na Hajiya ƙarama ba'a bayyane ba, amma ita Hajiya Mammah kamar idanunta zasu faɗo kansa. A masife ta ce, “Eh ai ba sai ka nuna mana kai tarbiyanka bai cikaba Awwab. Mune kakema gaisuwa like wasu sa'anninka ko. Kaje ai duniya ce zaka gani, wanda baima zo ba jiransa take”. Ko kallon inda take baiyi ba ma. Sai zamansa ya gyara cike da ƙasaita yay crossing ƙafafunsa ya jingina kansa da kujera ya wani lumshe idanu. Takaici, baƙin ciki, haushi. Babu wanda bai kumesu ba. Sai dai babu wanda ya tanka sai Baba prof ne ya ce, “Awwab!”. Batare da ya ɗago ba ko gyara zamansa ya ce, “Na'am”. Sake danne zuciya Baba prof yayi ya cigaba da faɗin, magana ce mai muhimmanci ta taramu anan, kuma amsa muke buƙata daga bakinka, ba wannan shirun naka ba. Wancan karon kata mana zame-zame, na barka ne kawai dan na tabbatar da abinda akace kayin, ashe kuwa bazaka fasa ba tunda gashi ka maimaita. Kana ganin wannan rayuwar ta dace da kai kuwa Awwab, kaifa muka dinga fama da kai yin aure watannin baya amma ka nuna baka buƙata, why kuma yanzu ka zaɓi wannan rayuwar? Bayan tako ina ALLAH bai tauyeka ga yin auren ba? Na farko ya faru, anyi na biyu, to baza'a sake na uku ba, dan haka mun yanke shawarar daga nan zuwa next month za'a ɗaura maka aure da ƴar uwarka tunda a wata kusan tara ka kasa samo matar sai ka fara shiri”. Wani shegen murmushi Maash ya saki a bazata. Dukansu sai da murmushin ya basu mamaki, hakan yasa duk suka zuba masa ido cikin ɓacin rai. Kasa haƙuri baba prof yayi yanzu kam cikin ɓacin rai ya furta, “Oh dariya ma na baka ko?”. Murmushin ya sake saki yana mai buɗe manyan idanunsa a kansu. Yanda sukai wani tar-tar blue ɗin ya fito sosai zai tabbatar maka da baya tare da kowace irin damuwa. Cikin halin ko'in kula ya ɗan lumshe idanun ya buɗe, tare da motsa lips ɗinsa a nutsensa ya furta, “Shike nan zan iya tafiya?”. Yanzun kam hatta Paah sai da ya zuba masa ido. Yayinda cikin masifa Hajiya Mammah ta shiga tafa hannaye da jera salati. Ta ce, “Ni Nafisa ALLAH kana gani, Awwab wai anya kuwa kai kam ba shaiɗani bane? Gaba ɗaya neman maida mu watsatstsu kakeyi ma dai na kula. Yanzu nan a duk zantukan nan da baba yay maka saboda sheɗanci da raini baka da abin cewa. Magana ta ALLAH Mu'azz ka haifa mana jaraba a family”. Ko motsi baiyi ba balle yama nuna yasan mi take cewa, sai da yaja fin mintuna biyu sannan ya wani irin buɗe idanunsa, kai tsaye a kanta ya sauke su, cikin wani irin salon kallon raini, gaba ɗaya sai ta daburce ta fara kame-kame da zaginsa. Ɗauke kansa yay daga gareta ya maida kan Baba prof, cikin motsa lips a daƙile ya furta, “Daga farkon fara wasan har zuwa yau ai duk itace Director, ni ina amsa sunan actor ne kawai. Dukan amsoshin da kuke son ji a gareni ita ke da su.” Wani irin kuka Hajiya Mammah ta fashe da shi tana zagin Maash da yaɓo maganar da duk tazo bakinta. Ko kallo bata sake isarshi ba ya miƙe abinsa yana mai ɗaukar bottle water ɗin sa. Da sauri Laalah ya miƙe shima. Cike da takun nan nasa na ƙasaita ya nufi ƙofa sai da ya kama ƙofa zai buɗe sai kuma ya ɗan dakata, kamar wanda yay mantuwa ya juyo, “Oh nace ba. Zan baki first and last warning. Idan kikace zaki cigaba da bin sawuna, wlhy wataran sai taɓo mai danƙo ya riƙe miki ƙafa ta yanda har sai naje na dawo daga inda zanje na sake dilmiyaki a ciki, kona datse ƙafafun kowa ya huta.” ya kare maganar cikin karkaɗa yatsarsa, daga haka yay ficewarsa kamar baiga kallon da suke binsa da shi ba.........✍️ *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 twenty-eight .......Tsuru-tsuru kawai sukayi suna bin ƙofar da kallo, sai Hajiya Mammah ce ke zazzaga masifa cikin borin kunya. Dan sosai maganarsa ta ƙarshe ta wani irin shigarta. Ganin kallon da Baba prof ke mata yasa ta miƙe. Murya a ɗan zafafe ya ce, “Koma ki zauna Nafisa”. “Amma Baba kana fa jin abinda ya faɗa min, wlhy sai naci uwar yaron nan a gidan nan. Yanzu har lalacewar wannan gidan takai kamar Awwab ya gaya min baƙaƙen magana a gaban Mu'azz amma yay kamar baima ji ba. Ba shi ba hatta uwarsa a gabana aka haifeta.” Cikin damuwa da ɗan ɓacin rai Paah ya ce, “Amma Adda mi kike so nace muku?. Duk dai mai hankali yaji wannan furucin na Muhammad zai fahimci akwai wani abu a tsakaninku ke da shi. Tabbas Muhammad bashi da ragowa, kuma in ransa ya ɓaci komai yazo bakinsa faɗa yake, amma tunda muke da shi bai taɓa maidama wani murtani ba a cikinmu sai yau. Duk kuwa abinda kiga Muhammad ya magantu a kansa to lallai wannan abun ya kai karen kure. Kuma ni kam gaskiya zuwa yanzu zuciyata ta fara bani akwai abinda yaron nan ke ɓoye mana, inda ace abinda ya faru a farko ne kawai zan iya yarda ƙaddara ta kaisa ga aikatawa. Amma muyi tunani, Muhammad fa duk da tsagerancinsa bazai zauna yana lalata yara ba irin haka a cikin gidan nan, dan duk da mahaifiyarsa na'a halin rashin lafiya bai haɗa mutuntakarta da komai ba. Mudai ƙara bincike gaskiya. Domin mu dukanmu mun san waye Muhammad”. Da ga haka ya miƙe abinsa ya fice shima. Shiru falon yay babu wanda ya iya motsawa. Sai Hajiya Mammah dake wani irin cika da batsewa da famar jinjina kai. Ta bakin baba prof kowa ke son ji amma babu alamar zai ce wani abu. Sai ma miƙewa da yay shima ya fice a binsa. Ganin haka shima Uncle Abdullahi da Matarsa suka miƙe. Wani irin shegen murmushi Hajiya Ƙarama da ke kallon Hajiya Mammah ta ƙasan ido ta saki, sai kuma ta mike itama batare da tace komai ba ta fita. Dan ta ciki na ciki ne kawai..... 🪴🪴🪴🪴 Watanni huɗu kenan Mamy na gida, babu labarin Mansoor tako ina. Gashi Dad baizo gida ba kuma kowa bai sanar mata ya saketa ba ko bai saketa ba. Gaba ɗaya ta fige ta rame saboda damuwa. Dan har ga ALLAH tana matuƙar so da ƙaunar mijinta. Ta tura masa text message yafi sau dubu. Ta kirashi yafi sau dubu goma. Amma babu amsa babu reply na masseges ɗinta. Ga ciwo ya addabeta a tsaitsaye har dai sai da ta kaita da kwana asibiti ranar. ALLAH sarki Attahiru shine tsaye akan komai. Ganin fa yanda jikin Mamy yay tsamari a wannan karon yaje ga Dad ɗin su ya dinga kuka yana roƙonsa ya yafe mata, sannan ko sau ɗaya yazo ya ganta. Dan sam Mamy bata a cikin hayyacinta. Babu abinda take faɗi sai neman gafarar Dad ɗin. Da farko Dad koran Attahiru yayi, sai da yaga yanda ya riƙe ƙafafun nasa yana rabzar kukan abin tausayi sannan. Dan har ga ALLAH a yanzu tausayin babban ɗan nashi yake yi. Attahir akwai haƙuri, gashi da son ƴan uwansa. Ga biyayya a gare su. Yanzu tunda aka fara abin nan yazo neman ma Mamy afuwa ya masa gargaɗin kada ya sake masa maganar ta bai sake koda kwatantawa ba duk da abin na damunsa. Amma kullum dare yana lura da shi sai yaci kuka. Haka kuma zaita salla yana neman ɗaukin UBANGIJI da yima Mansoor addu'ar ALLAH ya karesa a duk inda yake. Shima sai hakan yaja hankalinsa yake tashi yin ibadar daren. Yanzu da yake roƙonsa duk sai jikinsa yay sanyi, kamashi yay ya rungume. Sun jima a haka kafin ta ɗagosa yana lallashi. Ya kuma tasashi gaba suka je asibiti suka duba Mamy. Abinda Dad ɗin yayi ya faranta ran kowa. Dan duk wanda yasan Mamy yasan ta horu da horonsa matuƙa. Wannan zuwa na Dad shi ya kawo masalaha ga ciwon Mamy, ta dinga jin sauƙi har al'amura suka fara daidaita. Koda aka sallameta sai suka koma gida. Nan ma ta cigaba da roƙon Dad ɗin gafara yaran suka tayata har sai da yace mata ya yafe mata. Ya kuma kafa mata sharuɗa da dokoki. Ko guda ɗaya kuwa bata musa ba a ciki. Doka ta farko data fara bi shine shiryawa sukaje har gidan Abba suka bashi haƙuri tare da neman gafarar Abban da sauran mutanen Gwarzo da basu wuce ba da su Gwaggo Gudidi. Sun so ganin Yaya Musaddiq aka sanar musu ai ya wuce Chaina yau ne ma ranar tafiyar tasa zai bi ta Lagos. Abin ya basu mamaki. Sun kuma tayashi murna. Sun kuma yi alkawarin zuwa weekend zasu je har gwarzo domin bama su Kawu Musa haƙuri, dan su tunda suka zo aka ɗaura aure da su suka kama gabansu tunda bikin bana ɓangaren su bane ba. Wannan ban haƙuri da su Mamy suka zo sukayi har gida ga ƙonama Mom rai, dama ga baƙin cikin tafiyar Yaya Musaddiq na cimata zuciya. Har ta kasa haɗiyewa sai da tai ta zabga habaici. Da yake dama Abba a ƙufule yake da ita akan tafiyar Baby basu bari ta masa sallama tama danginsa ba ya ce idan har Mom ta sake cewa ko uff a bakin aurenta. Dan ya tsinke sauran igiyoyin biyu da suka rage. Wannan magana ta matuƙar girgiza Mom da duk danginta. Nan fa suka shiga tausarta da nuna mata kuskurenta. Daga nan akayi zaman sasanci aka sakata bama Abban haƙuri da su Gwaggo Gudidi.... 🌜🌜❤️🌛🌛 Tunda ya shigo ɗakin yay tsaye kawai yana kallonta nannaɗe a ƙasa kamar ƴar mage. Barcinta take hankali kwance. Kaɗan ya ɗan jaa idanunsa kamar zai lumshe sai kuma ya buɗe. Durƙusowa yay ya ɗauketa gaba ɗayanta ya maida a saman gado, kafin ya shiga ƙoƙarin zame mata hijjab ɗin. Firgigit ta buɗe idanunta dake jajur duk sun ɗan kumburo alamar anci kuka an gode ALLAH. Sosai ƙirjina ya shiga bugawa da sauri-sauri ganin yanda ya ranƙwafo kaina, zaram nayi ƙoƙarin tashi jikina na rawa, sai dai zafin daya ratsani ya sani komawa da sauri na kwanta hawaye na ziraro min. Cikin ɗan jujjuya masa kai, lips ɗina da suka sha wahala a wajensa na rawa muryata a ɗashe na ce, “Please Ya Awwab don't do wahala for me again. Wlhy zan iya mutuwa. I'm just 23years only zakai child abuse fa”. Shiru bashi da alamar cewa uffan, sai idanunsa masu tsananin kaifi da ya zuba min kawai kamar zai cinyeni da su. Cikin kuka sosai na sake buɗe baki zanyi magana ya ɗaura yatsarsa manuniya akan lips ɗin nawa yana mai sake matso da fuskarsa gab da tawa ya ce, “Shiii! Oya sleep”. Ya ƙare maganar can cikin maƙoshi da ɗaura hannunsa ya rufe idanuna. Babu musu na rufe ɗin duk da a cikin tsoro nake. Tun ina ɗari-ɗari har wani barci mai daɗin tsiya yay awan gaba da ni saboda yanda yake shafa kaina a hankali. Ganin yanda ta fara sauke numfashi a hankali alamar tayi barci ya sashi yin ɗan guntun murmushi. A hankali ya furta, “You are a tiger, Samrh”. Sai kuma ya sake sakin murmushin gefen baki saboda tuno kalmar child abuse data faɗa. Sam yarinyar nan bata jin magana. Ga baki kaman parrot. Vibration ɗin da wayarsa keyi alamar shigowar kira ya katsesa da ga kallon da yake mata. Dan kallon wayar yay dake a kan side drawer. Sai da ta kusan tsinkewa kamar abin dole kafin ya kai hannu ya ɗauka. Ɗagawa yay ya kai kunnensa yana ƙoƙarin barin wajen. Koda Juliet da tai kiran ta gaishesa a taƙaice ya amsa mata. Bata damu ba ta fara masa bayani kan aikin da ya sakata. Ta tabbatar masa ta kammala komai yanzu haka jirgin da zai taho da shi ya ɗakko hanyar Nigeria. Cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara ya lumshe idanunsa dake canja launi. Shi kaɗai ya san mi yake ji a zuciyarsa, amma zai jure in sha ALLAHU. Sunayin sallama kiran Hayatu na shigowa. Gaisawa sukai shima sannan ya bama su Yaya Musaddiq suka gaisa. Kasancewar tafiyar ta Musaddiq sai dare ma ya bama Hayatun umarnin zagayawa da su suga gari zuwa anjima sai ya kawosu nan. Dan yau shi bazai fita ko ina ba zai yini a gida. Murmushi Hayatu yayi da ga can, amma duk da haka sai da ya tambayesa ko baida lafiya. Dan yasan abinda zai iya hana ogansa kuma yayansa fita ba ƙarami bane. A taƙaice yace masa no kawai ya yanke wayar, Hayatu ya jima shiru yana nazari sai kuma yay ƴar dariya. Anya kuwa! Anya ogan nasa bai faɗa lobayyar pepper ƙanwar tasu ɗin nan ba. Rashin mai bashi amsa ya sashi haɗiye komai ya cigaba da sabgarsa. Shi kam koda ya kammala wayar shiru yay a cikin kujerar lafe na kusan mintuna ashirin, kafin ya miƙe a hankali ya bi ƙofar dake sadashi da Ummie, ko'ina fes sai ƙamshi yake, ganin kwanikan abinci ya sashi tabbatar da har ta karya. Kusa da ita ya ɗan zauna ya shafa kanta dan barcinta take hankali kwance. Ga wani irin annuri da fuskanta keyi ƙyawunta da dauɗa ya dusashe na sake fitowa. Hawaye ne ya cika masa idanu, amma sai ya haɗiye su dan ƴan mazan maza ne akoda yaushe. Ya ɗan jima a ɗakin har Mama Balki tazo ta samesa duk da yanda kansa ke juya masa da ciwo. Bayan sun gaisa yana ƙoƙarin danne damuwarsa da ciwon da kansa ke masa yay mata bayanin a saka cikin yaran can wasu su gyara sashen Fahad. Yana gama faɗa ya miƙe da sauri ya fice a ɗakin kamar wanda ake tunzurawa. Da kallo Mama da har tsigar jikinta ke tashi da jin wannan batu ta bisa. Sai hawaye sharrr suka shiga ɓulɓulo mata, ga murmushin farin ciki. Wani irin ƙaunar Samraah na ratsa mata zuciya. Yarinyar nan ta cika alƙawarinta kenan. Dan dama ta mata alƙawarin sai ta masa maganar dawowar Fahad ɗin gida. Kasa haƙuri tayi sai da ta koma ta sanarma mijinta. Shima farin cikin ne ya dabaibayesa har murmushi ya gagara barin fuskarsa. Ranar da wannan farin cikin suka yini, tuni kuma an saka masu aiki gyaran sashen Fahad dake manne dana Maash ɗin batare da kowa ya sani a gidan ba. Dan su suna can ma ran kowa ɓace da abinda Maash ɗin ya musu yau........✍️ *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 twenty-nine .......A hankali Maman Malika da tun da suka dawo sashensu ta ɗago ta kalla mijinta. Shima dai zaune yake shiru da alama akwai abinda yake tunani. Agogo ta kalla sannan ta sake kallonsa. Murya a sanyaye ta ce, “Abban Muhseen yau bazaka fita aiki bane wai? Time fa yaja sosai”. Numfashi ya sauke a hankali, kafin ya kalleta fuskarsa na nuna damuwa sosai. “Zanje Mubeena. Al'amarin gidan nan ne ya fara damuna wlhy. Daga wannan sai wannan. Ga yaron nan sam baya ganin girmanmu. Shi kuma Yaya baya ƙaunar laifinsa sai ma kiga kamar yana tsoron sa.” “Humm Abban Muhseen ba tsoro bane ba. Sannan wlhy Awwab bawai baida mutunci bane ko kunya. Yaron yana cikin damuwa matuƙa. Ku kuma kun kasa fahimtar hakan. Kowannenku abinda ke gabansa kawai yake yi. Yanzu ko maganar nan daya gayama Adda fa abin a dubace. Dan babu rami miya kawo rami? Tabbas akwai abinda Addar ta sani game da abinda ke faruwa. Idan fa baka manta ba ko waccan ranar ita ta fara fasa zancen yama yarinya fyaɗe, duk da ana cikin tashin hankalin zuwa kamashi ita ba wannan bane damuwarta. Yau kuma itace fa ta tashemu a barci jiya. Ƙarfe sha biyu da wani abu bata kwanta ba mi take yi? A barshi ma batai barcin ba, miya kaita sashen Awwab har tasan yana aikata wani abu? Mufa buɗe zukatanmu mu kalla gaskiya a matsayin gaskiya in ba hakaba ALLAH zamu yi dana sani. Kadai san halin Adda ai da fitinarta, musamman daya kasance burinta a gidan nan Awwab ya auri Azizat. Baka tunanin zata iya shirya komai dan hakan ta kasance tunda an bisa ta lalama, an bisa ta tsiya duk yaƙi. Sannan na fara ji a jikina akwai abinda Awwab ke ɓoyewa a gidan nan. Babu yanda za'ai duk rashin kunyarsa ya dinga lalata yara a cikin gida mudai nemo gaskiya.” Sosai maganganunta suka shigi Uncle Abdullahi. Yay shiru yana nazarin kowane harafi dalla-dalla da yi masa fashin baƙi.... 🪴🌼🪴🌼🪴 Tunda ta iso asibitin ta gagara taɓuka komai. Sosai abinda ya faru a gidan keta mata faman kai kawo a zuciya. Kalaman Awwab sun farkar da ita wasu abubuwa. Tabbas sau biyu tana kama Hajiya Mammah ta fito a sashen Awwab, na farko ranar da ta aiki Yarinyar nan da abinci, na biyu daren ranar da abin ya faru kusan misalin ƙarfe ɗaya ta fito daga ta backyard kamar wacce ke a firgice. Abinda yasa a lokacin bata maida hankalinta a kanta ba itama daga wani waje ta dawo. Abu na uku Hajiya Mammah ta damu akan zancen fyaɗen nan a safiyar ranar, sannan jiya ma itace tazo musu da zancen ga Awwab da wata. Da farko bata damu ba, sai yau da safe data bincika yarinyar nan a sashen masu aiki akace mata bata dawo ba ai. Bata samu damar ƙarasa binciken ba Baba prof ya iso gidan.. Mikewa tai tana mai girgiza kanta, dolene taje ta ƙarasa binciken data fara kafin wankin hula ya kaita dare. Daga nan tana buƙatar yin magana da Yallaɓai a wannan gaɓar. Handbag ɗinta ta ɗauka ta fice a office ɗin. Ko kallon tulin patients ɗin dake zaman jiranta batai ba dan hankalinta ma baya a kansu gaba ɗaya..... ✨💞✨💞✨ Barci sosai nasha. Dan ban tashi farkawa ba sai wajen sha biyu. A hankali na buɗe idanuna bakina na ambaton sunan ALLAH da karanto addu'ar tashi a barci kafin na yunƙura da ƙyar na tashi zaune saboda ciwon da illahirin jikina ke mun. Sam banyi tunanin yana a ɗakin ba, dan haka na miƙe cikin ƙarfin hali saboda wani irin fitsari nake ji sosai. Wani irin motsawa zuciyata tayi sakamakon saukar idanuna a kansa. Zaune yake cikin sofa kamar wani saraki. Laptop ɗin jarabar a saman ƙafarsa sai dai ya saka throw pillow sannan ya ɗaurata. Ta gefensa a saman side table ɗin kujerar bowl ne da chocolate a ciki sai mug alamar ansha coffee ko tea. Ledojin chocolate ɗin da yaci ya zubar a ƙasan na bi da kallo, haka kawai sai naji tausayinsa ya kamani. Dan abinda na fara fahimta da shi kamar bai damu da cin abinci ba sai waɗan nan tarkacen kayan chocolate ɗin. Tabbas koda ace bai son cin abincin akwai ƙarancin gatan mai tsayawa ya bashi ya ɗin.. ganin ya ɗan dakata da danna keyboard ɗin computer ɗin alamar yaji a jikinsa ana kallonsa ya sani saurin kauda idanuna da ƙoƙarin son barin wajen, a ko dai-dai nan ya ɗago manyan idanunsa ya sauke a kaina. Basarwa nayi kamar ban gansa ba na wuce bathroom ɗin. Ina shiga na jingina da ƙofa ina mai sauke ajiyar zuciya mai nauyi da godema ALLAH da ya taimaken bai kamani ina kallonsa ba. Wanka nayi da ruwa mai ɗumi sosai na sake gyara jikina yanda ya kamata, dan har ruwan zafin na shiga. Yau banyin walha ba ina barci, alwala nayi dan naga har sha biyu da kusan rabi yanzu. Hankalina duk yana akan su Yaya Musaddiq shiyyasa ban zauna wani noƙe-noƙe ba na fito sanye cikin bathrobe ɗin sa sky blue. Inda na barsa anan na samesa. Sai da na zo gab da shi ya ɗago kai ya kallan. Murya a sanyaye alamar nasha kuka batare dana kallesa ba na ce, “Ina yini”. Bai amsa min ba, sai idanunsa masu azabar kaifi daya zuba min. Ji nai duk ina neman daburcewa, dan haka nai ƙoƙarin barin wajen amma sai ya miƙa min hannu alamar nazo. Jinai kawai bazan iya musa masa ba, a hankali na fara takawa zuwa garesa, ɗan nesa kadan da shi na tsaya kaina a ƙasa. Soft hannunsa ya ɗaura akan nawa da nake wasa da su ya matsoni gabansa sosai, a bazata na jini zaune a saman cinyarsa alamar ya ajiye laptop ɗin da pillow ɗin. Sake matsoni yay cikin jikin nasa ya rungume tsam har ina iya jin bugun zuciyarsa kaɗan-kaɗan. Luff nayi wata nutsuwa na ratsani. “Yaya jikin ya daina zafi?”. Ya faɗa cikin silent muryansa a cikin kunnena. Sosai kunya ya sake ƙamani, maimakon amsa masa sai na sake ƙanƙamesa ina ɓoye fuskana a jikin nasa. Kaɗan naji yunƙurin murmushin sa cikin ƙirjinsa. Shiru kusan mintuna biyu ya sake furta, “Kona duba ne?”. Kafaɗa na maƙe masa da faɗin, “Uhm-uhm” cikin shagwaɓa ina ƙoƙarin tashi. Amma sai ya hanani yin hakan, hannayena ya kama cikin nashi ya zubama fuskata ido sosai yana kallo. Kasa kallonsa nayi ni dan bazan iya jurewa ba sam. A hakan ma ji nake kamar na gudu. Sake maida muryarsa ƙasan maƙoshi yay da kai hannu a haɓata ya ɗago fuskata da ƙyau ya ce, “Look at me”. Da ƙyar na iya ɗago idanun na kallesan. Cikin ɗan ɗage gira ya ce, “Shin bakin ƴar mutan Gwarzo ya mutu ne kwana biyu?”. Bakin na ɗan tura masa kaɗan. Girarsa ya ɗan ƙara ɗagewa da jinjina kai ya ce, “I see, bai mutu ba ashe. Yanzu idan su Ya Musaddiq suka zo mi zaki ce da su ya samu wannan idanun da ya kumbura?”. Karan farko na ɗago na kallesa. Idanun nawa ya sarƙe cikin nashi, kallon juna muke cikin wani yanayi mai wahalar fassara. Jin yanda tsigar jikina ke tashi jinina na yamutsawa ya sani lumshe nawa a hankali. Murya ƙasa-ƙasa kamar mai koyan magana na ce, “Zan ce kai ne”. Na ƙare maganar in ɗan buɗe idanuna kaɗan. “What a surprise, ni ne fa? To nayi me?”. Ai babu shiri na buɗe idanun gaba ɗaya ina harararsa da tura baki. Sai kuma na yunƙura zan tashi ina ƙunƙuni. Sake maidani yay ya zaunar ya ce. “Answer me”. Shagwaɓe fuska nayi ina kaucema kallonsa na ce, “Ni dai ba ruwana. Ka sakan na saka kaya na je na ga Ummie na”. Ɗan lumshe idanunsa yay ya sake buɗewa, sai kuma ya ɗan sauke numfashi, kamar wanda ke shirin sakin murmushi ya ɗan taɓe baki. Yatsun hamnuna dake cikin nasa ya ɗan matsa da murza farcen. “Shi wannan hannun yaushe za'a masa lalle?”. Hannun na kalla nima, sai kuma a hankali nace, “Ai babu lalli ne. Da dai nasan su Yaya zasu zo da sunzo min da shi. Kuma ma ina son wanke kaina ya fara cushewa.” Kansa ya jinjina min alamar amsawar kenan. Nima sai nai ƙoƙarin miƙewa. Taimaka min yay na tashi, ina shirin barin wajen shi kuma zai maida laptop ɗin sa a ƙafa ya ce, “Mi zaki ci?”. Kallonsa na ɗan juyo nayi muka haɗa ido, sai kuma na kalla ledodin chocolates ɗin da yasha batare da nayi magana ba na nuna su. Idanunsa ya ɗan ƙanƙance a kaina. Sai kuma ya girgiza min kai a daƙilen nan nasa. “Kince ba abinci bane ai”. “To kaima ai shi kake ci”. “Humm”. Kawai yace ya maida kansa ga wayarsa daya ɗauka. Ganin ya kai kunne alamar wani ya kira ya sa na wuce abina dan na shirya. Ban wani jima ba na fito cikin skirt da riga na atamfa. Sosai kayan sun min ƙyau tare da fiddo ainahin surar jikina. Ni kaina sai da na sakarma kaina murmushi ta cikin mirror. Dauri nayi mai sauƙi bayan na shafa turarensa da mansa. Koda na juyo sai na samu ni yake kallo shima. Da sauri na ɗauke kaina kunya na kamani. A ɗan daburce nace, “Zanje can sashen na ɗakko kayan kwalliyana Please Ya Awwab.” Sai da ya maida kansa ga aikinsa kamar bazai kulani ba kafin a hankali ya ce, “No”. Baki na ɗan tura batare dana sake cewa komai ba na nufi gadon. Tsaff na gyarashi, na tattare net ɗin. Dai-dai nan shima ya miƙe ya shiga bathroom. Babu jimawa ya fito alamar yin alwala.........✍️ *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆- thirty ......Ina a inda ya tashi ina gyara wajen da tattare ledodin chocolates ɗin da ya zubar naji tsaiwarsa gefena. Juyowa nayi na kallesa, ya ɗan ɗage min gira alamar kallon fa, ƙoƙarin kauda kaina nayi ya kamoni, a bazata naji saukar sumbata a goshina. Idanuna na lumshe a hankali. Shi kuma ya kai lips ɗinsa kan kunnena a matuƙar low voice ya furta, “You are beautiful tiger girl”. Da sauri na buɗe idanun a kansa. Kamar zan yi kuka na ce, “Tiger fa?”. Ido ɗaya ya kashe min kawai yay gaba batare da ya amsa min ba. Yana buɗe ƙofar nima cikin shagwaɓa na ce, “Kaima Lion”. Wani shegen murmushi kawai ya sakar min batare da yace komai ba ya buɗe ƙofar ya fita abinsa. Nima sai na samu kaina da sakin murmushin har haƙorana na bayyana. Sosai murmushinsa ke sakani farin ciki da nishaɗi. Dan yana bala'in ƙara ƙyau a duk lokacin da yayi sa. A gurguje na ƙarasa gyara ɗakin, nasa turare na fito falo bayan nayi salla. Fes na samu ko'ina anan alamar yasha gyara. Sashen Ummie na nufa ta hanyar da yabi da ni daren jiya. Na jima a can dan yau ma har sai da Mama Balki tace naje gasu Yaya Musaddiq nan zuwa harda Falaq. Cike da farin ciki da zumuɗi na tafin kuwa. Tuni na manta da halin da nake ciki saboda farin cikin ganin ƴan uwana duk uku. Nan fa na zauna muka buɗe sabuwar hira, har sai da Aunty Falaq ta tsareni naci abinci wai inji Yaya Awwab. Ni saima abin ya ban mamaki. Sai dai ban ja zancen ba na basar dan tunda na shigo na fahimci baya nan. Bayan sun tafi sallar la'asar nace mu shiga muma muyi a bedroom Aunty Falaq taƙi, nayi-nayi da ita tace ALLAH bazata taɓa iya shiga bedroom ɗin Yaya Awwab ba. Zata je sashen su Mama tayo. Sosai nake mamakin yanda suke mugun girmamasa, sai kuma hakan ya birgeni. Tare muka nufi sashen su Maman da ita. Bayan nama guard ɗinsa magana sun kulle sashen. A hanya muka gamu da Hajiya ƙarama ta dawo maybe daga asibiti ne oho mata. Sai dai muna gaisheta sai ga hajiyar nan data ɗakkoni da ga Abuja ta fito a mota itama. Sosai na zuba mata ido, dan tun ranar birthday ɗin nan ban sake ganinta a gidan ba. Itama kallona take kamar wata tsohuwar mayya. Dan haka na tsuke fuska ataƙaice na gaisheta naja hannun Falaq muka wuce. Har muka shige sashen Mama ina jin idanunsu a kammu su duka biyun.. Koda mukai sallar a sashen Mama Balki muka cigaba da zama. Suma su Yaya Musaddiq nan suka samemu. Sabuwar hira muka sake zamanyi yanzu kam harda Mama Balki da mijinta. Sunata bamu labarin Baba muna jin daɗi, sai gab da magriba Hayatu ya shigo yake cewa sun dawo. Yaya Musaddiq yazo suje ya ƙarasa kimtsawa jirginsa na nine ne. Gaba ɗaya kuma duk sai jikinmu yay sanyi, amma babu yanda muka iya tunda cigaba ne yazo mana. Sai kuma munyi haƙuri zamuci ribarsa. Anan mukai sallar magrib ɗin, sannan muka ɗan sake gyara jikinmu dan muma muna son masa rakkiya airport ɗin. Ana kuwa idar da sallar isha'i sai gasu sun dawo. Nasiha sosai Mama Balki da Baba suka sake ma Yaya Musaddiq, sannan muka haɗu mukai masa addu'a. Ya sake kiran su Abba yay musu sallama har nima muka gaisa. Mun fito muka samu har mitsocin da zamu tafi da su airport ɗin an shirya. Da farko nayi mamaki, sai da naga boss ɗin ya fito alamar da shi za'ai rakkiyar sannan na fahimci dalilin shirya motocin da yawa haka. Dan kusan mota biyar. Biyu ta guards ɗin sa. Sai Mama da Baba da Yaya Musaddiq suka shiga ɗaya. Hayatu, Falaq, Hafizzullah suma suka shiga ɗaya. Sai ni da shi a ta tsakkiya duk da ba haka naso ba. Amma Falaq ta turani a motar da tsiya-tsiya tana dariya. Waya yake sanda na shiga, dan haka muna haɗa ido nayi saurin kauda kaina. Sai da mukai nisa da gidan sosai sannan ya kammala wayar, batare dana kallesa ba nace, “Ina yini”. Bai amsa min ba, sai kaifin idanunsa da nake ji a kaina. Kasa jurewa nayi a hankali na ɗago na ɗan kallesa. Caraf kuwa ya cafke idanun nawa a cikin nasa kamar dama mai jiran hakan. Wani irin kallo yake mun mai tada tsigar jiki da saka jini tsinkewa. Bamma san sanda cikin rawar murya da shagwaɓa na ce masa, “Ni ka bar kallona”. A hankali ya lumshe idanun ya sake buɗewa, sai kuma ya riƙo hannuna batare da yayi magana ba yanzu ma ya jawoni jikinsa kawai ya rungume. Luff nayi dan nima da alama abinda gangar jikin nawa ke buƙata kenan. Tuna bafa mu kaɗai bane akwai driver ya sani saurin yunƙurin tashi, amma sai ya maidani ya sake matsewa. A marairaice na buɗe baki zanyi magana ya dakatar dani. “Bana son surutu”. A hankali na sauke ajiyar zuciya tare da haɗiye abinda nake son faɗar kuwa. Dan ji nai bazan iya masa musu ba sam. A hakan muka isa airport ina a jikinsa. Munfi tsahon mintuna biyar bayan isowar tamu kuma kafin ya bari muka fita. Jinai gaba ɗaya kunya ta kamani ganin kowa ya fito ashe sai mune kaɗai a mota. Yaya Musaddiq yaja gefe sukai magana. Ban san mi suka tattauna ba dai naga Yayan nata murmushi da kallonmu. Sai kuma ya ɗan sosa kansa kamar wanda yaji kunya. Daga haka kuma naga shima Yaya Musaddiq ɗin yazo yaja Baba da Mama suka koma can. Anan ɗin ma sun ɗan jima, kowa fuskarsa ɗauke da murmushi idan ka cire uban gayyar da shi daman sai yaso yake murmushin. Shiyyasa da wahala ka gane farin cikinsa da akasinsa sai ka masa farin sani na haƙiƙa. Bayan sun gama zantukansu muma munata hirarmu suka dawo inda muke. Baifi mintuna biyar ba aka buƙaci ganin su Yaya a ciki. Tofa ai tuni kuma kuka ya tashi ni da Hafizzullah. Ganin haka itama Aunty Falaq ta fara. Mama Balki da Hayatu na ta mana dariya. Baba ko sai lallashinmu yake, shiko ai kamar ma bai san munayi ba. Haka dai muna ji muna gani Yaya Musaddiq ya wuce ya barmu da kewa. Hafizzullah da Hayatu da Falaq can gida suka wuce. Mu kuma muka nufi gida muma inata mita dan nazata yau a wajenmu muma Hafizzullah ɗin zai kwana. Bai dai tanka min ba har muka isa gida. Hakan ya ƙara tunzurani. Dan haka nama rigashi fita a motar. Badan su Mama Balki dake wajen ba ma da bazanje sashensa ba. Nafi mintina goma da shiga sannan ya shigo. Lokacin har na shiga wanka. Na fito na sameshi zaune a bakin gado yana waya. Wucewa nai cikin closet ɗinsa na shirya. Ina fitowa yana shiga bayin shima. Sai na saka sallaya nayi shafa'i da wutri. Na idar na tashi na fita. A karo na biyu na shiga kitchen ɗin sashensa. Kai tsaye store na shiga na ɗakko catton biyu na bottle water na fito. Bedroom ɗin ba dawo dasu. Har lokacin kuma bai fito ba. Gaba ɗaya na fito da ruwan tare da buɗe musu murfi sai dai ban cire su a jiki ba sannan na ɗauka Alkur'ani na fara karatu. Surorin da duk akace suna karya sihiri nake karantowa ina tofawa a cikin ruwan bayan na ɗaɗɗaga murafan. Nayi nisa sosai a karatun sannan ya fito. Duk da nayi mamakin daɗewar tasa a ciki ban kula ba na cigaba da karatuna a nutse... Sosai karatun nata ke ratsa masa zuciya. Ga yanda zazzaƙar muryarta ke fita cikin nutsuwa da bama komai hakkinsa na wani irin shiga masa har cikin jinin jikinsa. Cikin jin wata irin kasalar dake saukar masa ya ƙarasa closet ɗin sa. Shirin barci yayi shima, ya fito gaban mirror ya saka turare sannan ya ƙarasa saman sofa ya zauna yana satar kallonta ta gefen ido.... Barci nake ji amma tsoron abinda zai iya biyo baya ya hanani tashi naje na kwanta. Koda na kammala addu'oin ma sai na miƙe na kabbara salla. A mamakina sai naga shima ya miƙe ya saka sallaya ya kabbara salar. Mun jima muna miƙama UBANGIJI kukanmu dai sai wajen uku ya katseni cikin bada umarni yace naje na kwanta. Bazan iya masa musu ba. Dan sam banga hayar yin hakan ba a garesa, ga zazzaɓi ya rufeni haka dai na daure naje na kwanta. Duk yanda naso nayi barcin na kasa, sai dai nayi luff a kwancen har ya kammala tashi sabgar yazo ya kwanta. Lokacin da ya sakani a jikinsa wani irin dukan ɗari-ɗari zuciyata ta dinga min, na gama sadaƙarwa yau ma zansha wata azabar sai naji saɓanin haka. Sai ma tadani da yay ya bani maganin zazzaɓi ya sake maidani jikinsa muka kwanta. Babu jimawa kuwa mu duka barci yay awan gaba damu. Koda muka tashi a washe gari babu zazzaɓin, sai dai yanda nake tafiya da ɗan ɗingishi ya sashi min tambaya. Kasa bashi amsa nayi sai idanuna da suka cika da ƙwalla. Shima sai baicedani komai ba ya ƙyaleni kawai yama fita. Kusan ƙarfe goma na idar da sallar walha bayan naje naga Ummie sai gashi ya shigo, kaina a ƙasa na gaidashi, dan rabona da shi tun fita motsa jiki. Kai tsaye yace min ga Doctor tazo dubani. Sosai mamaki ya sani kallonsa, sai dai shi tuni ya ɗauke kansa ma. Ficewa yay abinsa kamar baiga kallon da nake masa ba. A dai-dai nan akai knocking ƙofar, tashi nayi na buɗe, sai ko ga Doctor naci karo da ita. Haka kawai nake jin nauyin matar, dan a haife ta haifi waɗanda ma suka fini, kaina a ƙasa na gaisheta. Yayinda ta amsa min tana kama hannuna muka dawo cikin ɗakin.........✍️ *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 thirty-one ......Ina ji ina gani dole na bar doctor ta dubani, kanta kawai naga tana girgizawa cikin damuwa. Sai dai bata iya cewa komai ba tamun allura da buƙatar ganin Mama Balki. Kaina a ƙasa na bata amsar cewar ba'a nan side take ba. Amma za'a iya kiranta a waya ta bari ya shigo. Babu jimawa kuwa sai gashi ya shigo kamar dama kunnensa a kammu yake. Kallo ɗaya na masa na ɗauke idanuna, sai ma kawai na zame na kwanta abina na juya musu baya. Ina jin lokacin da Doctor ke sanar masa tana buƙatar ganin Mama Balki yace ta sanar masa koma minene ke faruwa karta damu. Ta ɗan jima shiru jimm kafin ta fara masa bayanin daya gama sakani a kunya. Dan bayani ta masa akan lallai ina buƙatar hutu da kulawa. Saboda ciwukan farko basu gama warkewa yanda ya kamata ba. Ga shi kuma an famasu shiyyasa ma nake jin zazzaɓi nake kuma ɗingishi. Badan ma jikina nada ƙyau ba ciwo na saurin warkewa da za'a iya samun matsala. Ta sake tabbatar masa da ina da dauriya, dan ba kowacce mace ke iya ɗaukar irin yanayin ba haka gab-da-gab gaskiya. Ko fargaba da tsotata ya ishi mutum ai. Ta dai jima suna magana da bashi dabarun daya kamata a kula dani domin samun dai-daiton komai yanda ya kamata kuma cikin ƙanƙanin lokaci. Daga haka ta sake bani wasu magungunan ta wuce bayan ta tabbatar masa zata dinga zuwa kullum dubani har na tsawon sati, kuma dan ALLAH na ɗan sami hutu kona satin ne. Koda ta wuce ban iya motsawa ba. Sai dai ina jin kaifin idanunsa a kaina tsahon lokaci kafin ya shige bathroom. Kafin ya fito barci ya kwasheni. Ban tashi farkawa ba sai gab da azhar. Babu kowa a ɗakin sai ɗan short note da naci karo da shi ya ajiye min a gefen fillon da nake kwance. Na jima ina kallon rubutun mai ƙyau kamar ba hannu yayisa ba kafin na saki murmushin daban shirya ba. Na ɗan ji daɗin jikina fiye da yinin jiya dana wuni a ƙuntace, kasancewar su Yaya Musaddiq kawai yasa na dinga dauriya. Wanka na ƙarayi na gyara ɗakin sannan nai zaman cin abincin da yace ɗin, kai tsaye na fahimci Mama Balki ce ta kawosa. Sosai naci na sha magani, sai da nayi salla sannan na tattara kayan abincin na fita zuwa sashen Ummie.... 🪴🪴🪴🪴 Su amarya Baby an isa ƙasar California lafiya. Sai faman iyayi take da wani yauƙi ita a dole ga amarya. Ƙalubale na farko data fara fuskanta a wajen angon nata shine tun a airport ya sakata a taxi wai taje zai ƙaraso. Ya bama mai taxi address ɗin hotel ɗin daya riga yay booking musu tun kafin su iso. Hankalin Baby ya ɗan tashi, amma dai tai ƙoƙarin dannewa tunda yace mata uzirine daya shafesu. Batasha wahala ba kasancewar ta samu mai jiran isowarta cikin ma'aikatan hotel ɗin. Da alama dai mijin nata sananne ne a wajen. Sai ta sake jin kanta ya fasu sama sosai. Wani irin santi da sambatu ta dingayi ganin irin katafaren ɗakin da aka kawota, gashi ya jiƙu da kayan alatu. Dama tun a wajen hotel ɗin take faman sambatu a zuciyarta. Sai da ta gama taɓe-taɓenta da kalle-kalle da santi sannan ta kwanta barcin gajiya, babu batun salla ko duba lokaci, dan a cikin jirgi ko tuna tashi tai salla batayi ba. Yanzu kuma sun sauka maimakon tayi ƙoƙarin ramawa ko'a jikinta. Wankan ma tunda ta shiga tai fitsari taga ta kasa amfani da kayan bathroom ɗin shiyyasa ta haƙura. Tayi nisa a barci sosai aka tasheta. A firgice ya buɗe ido babu addu'a babu komai ta mike zambar tana ƙoƙarin ɓarka ihu. Tsawa ya mata da zabga mata harara da manyan idanunsa. Sosai tsoro ya kamata da ganin yanda duk kamaninsa suka canja. Idanunsa sunyi wani irin jazur kamar ba mijin nata ba. Har ga ALLAH ba wani sonshi take ji ba, kawai kuɗinsa da zigar su Mom yasa ta amince da aurensa. Ta kuma gama shiryama ranta da shawarar ƙawayenta zaman shekara biyu zatayi da shi ta tara abinda ta tara tasa ya saketa ta samu dai-dai da ita yaro mijin wuce sa'a ta aura. Da ƙyar ta danne wata irin tsanarsa da ta sake ji na tsarga mata. Dan komawar idanunsa jajayen nan sai ya sake fito da tsufarsa. Duk da kuwa a fuska ƙyaƙyƙyawane, sai dai ƙaton cikin nan ya masa cikas da tsufa daya fara taso masa. Ɗan murmushi tayi cike da wayancewa da danne abinda ke ranta ta faɗa jikinsa ta rungumesa tana zabga masa kalamai wai tayi missing ɗin sa. Shiru bai rungumeta ba, bai kuma tureta ba, har sai da ta gaji dan kanta ta ɗago. Matsawa yay daga gaban gadon yana ƙoƙarin cire kaya. Da sauri ta kauda fuskarta, dan tulelen cikinsa kamar na mace mai cikin ƴan uku dake gab da haihuwa. Tas ya gama sannan ya nufi hanyar bayi daga shi sai boxer. Yana gama shigewa ta sauke ajiyar zuciya. Itako taga takanta, wai tayaya zata iya dauriyar bin shawarar ƙawayenta? Tuna burikanta ya sata sauke numfashi. Tana nan zaune abin duniya ya isheta sai gashi ya fito. Yanzu dai towel ne a jikinsa. Zaram ta miƙe tana faɗin, “Bara nima nayi wankan to, dama gajiya tasa banyi ba na kwanta kawai ga yunwa kuma ina ji”. “Okay”. Kawai yace mata ya cigaba da harkar gabansa. Da ƙyar ta iya samu ta kunna shower tai wankan, cikin son ta birgesa ta fito da ɗan guntun towel. Tako birgesan, dan duk inda tayi biye yake da ita da kallo kamar tsohon maye musamman bayanta. Bayan ta gama shiryawa cikin ƙananun kaya kamar yanda shima ya zuba ƴar shara da wando ta dawo kusa da shi ta zauna. Kamar abin arziƙi suka ci abinci tare tana faman masa shagwaɓa ita a dole ga amarya. Sai da yaci yay nak abinsa yay miƙar ƙoshi sannan ya miƙe a wajen. Barci ya ɗan fara figarsa a kujerar tana jikinsa akai kiran wayarsa. Janyeta yay ya tashi ya fita, kusan mintuna goma sai gashi ya dawo.. Da kallo ta dinga binsa, dan abinda aka ɗirka mata sai tsikarinta sukeyi. So take ko ɗan taɓata yayi, amma mutumin nan bashi da wannan niyyar. Ganin fa wankin hula zai kaita dare ga shi tun a yau take son fara tatsar kuɗaɗe dan Mom taci bashi sosai a bikin nan wajen shirya mata ɗaki tana son ta tura a biya kada asirinsu ya tonu. Tashi tai tsam ta nufi gadon da taga yaje ya kwanta. Cike da shagwaɓa ta faɗa masa a jiki. Shiru yay yana kallonta, itako babu kunya babu kawaici ta fara masa abubuwa. Barinta yay tai kiɗanta tai rawarta, kafin shi kuma ya fara maida mata murtani. Abinka da wadda tasha kayan iri-iri harda wanda bai kamata abama amarya irinta farin shiga ba. Gaba ɗaya ta gama sallama masa har bata ma san mi take ba. Hankalinta ya matuƙar gushewa taji kawai yana ɗaɗɗaureta. Da mamaki take kallonsa. Sai ya sakar mata makirin murmushi. Bata iya ta maida masa ba, dan a yanda ya kifata rufda ciki ya ɗaure ɗin ya sokar mata zuciya. Kafin ta samu damar neman ba'asi ya bita ya taushe. Duk da bata wani nutsu tayi islamiyya ba sosai hanyar da mijin nata ke neman bi a jikinta ya matuƙar firgitata. Cikin tashin hankali ta shiga tambayarsa mi yake sonyi haka? Abinda yake son aikatawa fa haramunne, taya zai yi ƙoƙarin mu'amalatar ta ta baya kamar wasu aladu. Ko kallo bata isheshi ba, tana ji tana gani ya aikata saɓon ALLAH da ita, maimakon bin hanyar da ALLAH ya halatta masa yabi wadda ya harta masa. Babu kuma tausayi babu imani sai da yay mata fata-fata. Tun tana kuka da roƙonsa da magiya harta ma suma dan azaba. Gashi ya ɗaureta duka hannayenta da ƙafafu babu damar koda kare kanta ne..... ❤️‍🔥✨❤️‍🔥✨❤️‍🔥 A ɓangaren Baba prof koda ya koma gida a jiya yaso bama al'amarin lokaci dan yay nazari, sai dai hakan na neman gagararsa. Washe gari duk da uziririn dake gabansa bai iya fita a gidan ba har kusan sha biyu na rana, dan ya kwana da tunane-tunane ne ya tashi dasu. Wayarsa ya ɗauka har ya danna kiran number Maash sai kuma ya yanke yana mai girgiza kansa. Akalar kiran ya maida kan Hajiya Mammah. Harta tsinke ba'a ɗaga ba wai tana waya. Sake kiran yay dan bazai iya jira harta gama ta kirashi ba. Yanzun ma tana wayar, sai dai kuma tana gab da katsewa aka ɗaga. Cikin bada umarni ya ce, “Nafisa ki sameni a gida yanzun nan”. Daga haka ya katse kiran. Shiru kawai Hajiya Mammah da tun jiya abin duniya ya isa tayi tana bin wayar da kallo. Ita bata motsaba ita bata ajiye ba. A haka kiran Hajiya Rubayya ya shigo mata. Da ƙyar ta iya ɗagawa takai kunnenta. Daga can cikin zumuɗi Hajiya Rubayya ta ce, “Miya faru? Ya kukayi da Baban?”. “Ca yay na samesa a gida. Ni kuma bana jin zanyi hakan Rubayya. Dan ban san mizan ce da shi ba, kin dai san halin Baba akan ɗan iskan yaron nan”. “Uhm uhm kar kice haka kije. Ai idan kikaƙi zuwa zai ma yarda da abinda ya faɗa kenan. Wannan fa wata gaɓace da zamu kama mu riƙe. Dan ita kawai ta rage mana yanzu. Dan haka tashi kije. Ki kirani ina jin abinda Baba ke faɗa zan dinga faɗa miki amsar da zaki bashi”. Matuƙar yarda Hajiya Mammah tama Hajiya Rubayya. Dan haka bata kusa ba ta miƙa ta hau shirin tafiya. Ta fito cikin takun nan nata na isa da taƙama sai dai daka ganta kasan ranta a ɓace yake. Gaisheta ma'aikatan gidan keta faman yi cike da girmamawa. Sai dai gaba ɗaya hankalinta ba'a garesu yake ba. Dan dai-dai nan ɗaya daga cikin ƙosassun motocin Maash da ba kasafai yake fita da su ba sai abu mai muhimmanci ta shigo, sai motar guards ɗinsa ɗaya biye da ita. Da farko ta ɗauka Maash ɗinne ya fita yake dawowa, sai da aka buɗe motar taga wanda ya fito a ciki tai tsaiwar sojan badakkare kamar wadda ta suma a tsaye... A hankali black beauty matashin saurayin dogo mai tsananin kammani da su Paah sai dai idanunsa sak irin na Maash ya wani yamutse fuska da bin gidan da kallo. Sam gidan baya wani birgesa a zahirance. Amma acan ƙasan ransa yana jin kewar Ummien sa da son kasancewa da ita. Matsala ɗaya ke masa katanga da yunƙurin zuwa gareta, ɗan uwansa. In har Yayansa na waje komai buƙatar da yake ma wajen shi bazai taɓa iya kasancewa ba. Dan yana jin kamar ya soka masa wuƙa ko ɗaukar bindiga ya harbe masa kai kawai. Sai da ya gama ƙarema gidan kallo batare da hankalinsa ya kai kan Hajiya Mammah ba ya ɗauka side bag ɗinsa irin ta maza matasa masu ji da gayu ya saka. Kansa tsaye babban ƙofar sashen ya nufa, dan sai ya fara zuwa yaga Ummiensa kafin ya ƙarasa sashensa. Yasan dai yanzu su Paah duk basa gida suna office........✍️ *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 thirty-two .......Zaune nake cikin dauriya kan Ummie a saman cinyata ina mata kitso tare da raira karatun Alkur'ani a hankali. Duk da dai Alhamdullah yau ina jin jikina da sauƙi ba kamar jiya ba. Tunda na shigo Mama Balki ta sanar min ai Hafizzullah yazo da safe tare da Hayatu amma sun fita har da Maash sai kawai nace bara nai zaman yima Ummie kitsonta da tun jiya naso yi ALLAH bai ƙaddara ba. Muna fara kitson Mama tace bara taje ta duba su Aunty Falila a kitchen dake girkin rana. Da to na amsa mata na cigaba da kitson ina karatun. Fitar tata baifi da mintuna biyar ba aka buɗe ƙofar ɗakin, sai ban damu ba na cigaba da kitsona ina karatuna da tunanin ko itace ta dawo ɗaukar wani abu. Jin shiru bata ƙaraso ba bata kuma yi magana ba ga wani baƙon ƙamshin turare da ban santa da shi ba yasa na ɗago idanuna na kalla ƙofar. Cak na tsaya da kitson ina bin black beauty matashin saurayin da kallon mamaki kamar yanda shima ya zubamun idanunsa sak irin na Yaya Awwab. Ganin kallon nasa na neman wuce gona da iri fuska a yamutse na ce, “Malam lafiya? Wanene kai? Miya kawoka nan?”. Gira ya ɗan ɗage cike da salon iya shege sai kuma ya saki wani faffaɗan murmushi. Hannu ya kai ya ɗan shafi dan tsigigin gemunsa na ɗaukar magana ya wani karkace kai gefe tare da furta, “FAHAD EL-MU'AZZ ADAMS. Kefa ƙyaƙyƙyawa?”. Maganarsa ta ƙarshe ta sani ƙin cemasa komai duk da naji wani daɗin jin sunan daya ambata ɗin . Sai ma ɗauke idanun nawa da nai na maida kan Ummie. Takowa yay shima a hankali zuwa inda muke. Zama yay kusa da Ummie ta ɗayan side ɗin, kamar wani ƙaramin yaro ya kwanto jikinta yana mai rungumeta. Cikin rawar marya ya ce, “I miss you mom. I love you with all my heart. You are my world and everything.” sai ga hawaye sharr, sake ƙanƙameta yay sosai a jikinsa. Sosai wani irin tausayinsa ya shiga ratsa min zuciya. Kaina na kauda daga kallonsu nima hawayen na zubo min. Da sauri na share su tare da ƙoƙarin cire kanta a jikina ya ɗago. Da sauri ya ce, “Oh oh beauty sai ki tafi kuma? Ki bari na gama da Ummie na zan dawo kanki”. Harara na zuba masa. Kafin na girgiza kaina da faɗin, “Ka kama kanka fa.” Da sauri yako damƙe kan nasa. Sai kuma ya saki murmushi cikin komawa serious saboda hararar dana zabga masa. Hannayensa ya haɗe waje guda. Ya ce, “Am sorry. Barka da rana. Sunana Fahad El-Mu'azz Adams. Autan Ummiensa da Paah”. Na kula akwaisa da shaƙiyanci, dan haka nayi murmushi da ɗan girgiza kaina. Cikin komawa serious nima nace masa sannu da zuwa. Sai dai yanzu ba kaine autan Ummie ba nice.” Cikin marairaice fuska ya ce, “A'a dan ALLAH kada kimun haka. Na yarda ki zama aunty na kawai. Daga yanzu ma zan na ce dake aunty beauty”. “Dama Auntyn taka ce ai”. Muka tsinkayi muryar Mama a bayanmu. Da sauri ya juya, sai kuma ya miƙe cike da farin ciki ya nufeta. Babu kunya ya rungumeta. Dariya Mama ta shiga yi da ɗan bubbuga bayansa tana faɗin, “Oh ni maigado sai yaushe ne Fahad ɗina zai girma. Haba autan Ummie kafa isa aure”. “Ina ban isa ba Mama. I miss you wlhy”. “Muma munyi kewarka sosai Fahad. ALLAH yay maka albarka kaji.” ta faɗa tana ɗagosa. Daka gansu kaga waɗanda ke a cikin farin ciki sosai. Cike da girmamawa ya gaisheta, tare da tambayarta jikin Ummie yana mai bin sashen da kallo. Ta amsa masa da kulawa. Kafin ya tambayeta wai wacece ni dan ya matsu ya sani. Ƙaramar dariya Mama tayi, tare da faɗin, “A'a bakaji a bakina ba. Ka bari zaka sani”. Cikin yanayinsa na mutum mai sauƙin kai a yanda na fahimta ni dai ya ce, “Okay Mama ba damuwa. Bari naje nayi wanka sai na dawo ALLAH yasa Ummie ta tashi ta ganni na ganta da ƙyau. Ina fatan kin min farvorite food ɗina dai?”. “Sasai ma kuwa autan Ummie. Dan har sai kaci ka ture.” Sosai farin cikin sa ya sake bayyana. Ya ɗaga min hannu yana maida bag ɗinsa da faɗin, “Bye Aunty beauty ki jirani nazo muyi hira. Dan sai kin faɗa min wacece ke zan barki.” Sosai ya bani dariya. Hakama Mama Balki dariya take yi. Yana gama ficewa na dubi Mama fuskata da sauran dariyar na ce, “Mama wannan ɗan naki akwai dai rashin ji a jikinsa”. Dariya ta sake yi sosai tana kaiwa zaune. Ta ce, “Humm bar Fahad inda kika gansa ya dai so yin barkwancin ne. Amma shima da kike ganinsa wani lokacin akwai miskilancin. Sai dai bai kai Alhaji Ƙarami bane kawai. Halinsu ma sam ba iri ɗaya bane ba. Dan shi Fahad na surutu sosai, shiko Alhaji ƙarami maganar ma aiki ce. Nan fa ta shiga bani labarin Fahad da halayensa. Wani nayi mamaki wani nayi dariya wani al'ajabi. Surutunmu ya tada Ummie ma. Tana farkawa ta fara kiran “Yunwa Muhammad! Yunwa”. Aikin kenan yanzu, daga taci abinci sai barci. Idan kaga ta farka yunwar ce ta sake tashinta. Shiyyasa jikinta yake wani irin murjewa tana ƙiba kwarjininta na sake fitowa. Kwana biyu dai Alhmdllh bata wannan bige-bigen. Bamu sani ba ko hakan nada nasaba da canja mata magunguna da akayi ne. Dan a ranar da jikinta ya motsa sosai ina asibiti a yanda Mama ke bani labari anzo da wani baƙon likita tun daga ƙasar RUMAN (Dole mu tuna Shahan-shan namu na Iffan😘😀). shine ya dubata tare da canja mata allurai da magunguna. Acewarsa a gwada waɗan nan sabin samfir ne da a shekarar nan aka samar dasu akan masu matsalar ƙwaƙwalwa. Ya bada wata ɗaya zai sake dawowa yaga idan an dace. Amma duk da haka a kullum sai doctors daya bari zasu ke kula da ita zasu dinga aika masa da cigaban da ake samu. Sannan ya dakatar da su Hajiya ƙarama da sauran doctors ɗinta a komai acewarsa shi baya haɗa aiki da waɗanda ba wanda yake tare ba. Sosai naso ace sanda abin ya faru ina wajen. Dan ina buƙatar fahimtar yanayin kowa a cikin doctors ɗin nata na baya. Dan nasan ko suna da gaskiya hakan bazai musu daɗi ba. Amma ko yanzu na ɗauki ɗamarar yin hakan..... 🌛🌜❣️🌛🌜 Ya ALLAH🙏 Wanda ke da rabon shiriya a masu ɗakkowa, da masu yaɗawa, da masu jiran a ɗakko su karanta a matsayin bati, ya UBANGIJIN al'ashi. Ya mai RAHAMA da jinƙai. Ya mai fidda rayayye a cikin matacce, ya fidda matacce a cikin rayayye. Nayi tawasalli da sunayenka masu tsarki, waɗanda ka kirayi kanka da su ka kuma sanar damu, da wanda ka barwa kanka saninsu ka keɓancesu gareka. Nayi tawasalli da ɗan gatan nan naka, wanda kace idan muka so shi, mukabi abinda yazo mana da shi na shiriya ka gafarta mana. Ina roƙonka ka shiryar dani da su. Ya rabbi kafisu sanin wahalar da nake sha a yayin rubutun nan. Nakan hana kaina barci domin sauke hakkin masu saya a lokacin da su suke barcin, nakan yini da ciwon kai, ina fama da ciwon idanu, ina fama da ciwon yatsu. Ina fama da ciwon baya. Wataran nakan wayi gari banama jin farin ciki ko sha'awar rubutun, wataran na tashi da uzirin baƙi ko fita. Amma duk nakan kuntata kaina domin naga nayi. Idan har ban kasance na cutar dasu da komai ba a rayuwarsu, ya rabbi! ya rabbi! ya rabbi!! ka shiryar dasu su guji taɓa hakkin daba nasu ba. Ka shiryar dasu su guji ɗaukarma kansu nauyin da zasuyi dana sani a ranar da ake fansa da lada da zunubi. Ya rabbi ka gafarta mana kurakuranmu. Ka shiryar damu, ka nisanta mu ƙuntata zuciyar kowa koda kuwa dabbace. ALLAH kasa mu samu sauƙaƙƙen hisabi batare da an jinkirta mana ba saboda hakkin wasunmu da mukaci a duniya. Dan ALLAH, dan ALLAH. Dan girman ALLAH mu saukaƙama kammu kunji bayin ALLAH. Ni kaɗai nasan a yanayin da nake wannan rubutun musamman a ɗan tsakanin nan, kada ki bari UBANGIJI ya kamaki da laifin hakkina nima bazan so haka ba. Dan bana son akai gaɓar da zan iya tashi tsakkiyar dare domin miƙama UBANGIJINA ƙararki ko ƙararka. Dan ALLAH, dan ALLAH, dan ALLAH. In har da gaske ke masoyiyar MANZON ALLAH ce kina fatan tashi a tawagarsa ranar da kowa ke fatan hakan, idan har da gaske kin yarda da mutuwa da ranar hisabi, idan har kin yadda wannan rubutun hakkina ne ALLAH zai iya cirar min hakkina a jikinki, idan har kin yarda ban taɓa cutar dake da komai ba, idan har kina fatan kema ALLAH ya kiyaye hakkinki ko hakkinka, ku daina ɗakkowa a inda na killacesa, ki daina yaɗawa, kema ki daina karantawa. Wannan itace maganata ta farko kuma ta ƙarshe in sha ALLAHU, ALLAH ya yafe mana kurakuran mu baki ɗaya.🙏 🪴🪴⭐🪴🪴 Ran Baba prof a ɓace yake kallon Hajiya Mammah dake gaishesa. Bai amsa ba, sai nuna mata agogon dake falon nasa mai shegen ƙyau da ɗaukar hankali yayi. “Kalla time, sai yanzu ne kike zuwa bayan tun 12 da wasu mintuna nai kiranki Nafisa?”. “Kayi haƙuri Baba. Wlhy na fito zan taho sai ga Fahad. Bamma ko tsaya ya ganni ba na taho dan kar kaita jirana. Wlhy duk a tsorace nake, kada su sake ƙoƙarin ƙona mu a cikin gida kamar wancan karon. Ban san wace jaraba ce ta dawo da yaron nan ba ana zaune lafiya.” Ɗan jimmm na wucin gadi ne ya riski Baba prof.. kafin tamkar mai koyon magana ya ce, “Wai wane Fahad ɗin?”. Cikin rashin damuwa Hajiya Mammah ta ce, “Fahad namu mana Baba. Wlhy gashi can ya dawo abinsa. Abinda ma dai ya ɗan bani mamaki shine ganin a motar fitinannen ɗan uwan nasa aka ɗakkosa. Ko sun shirya ne bamu sani ba. Idan ma hakanne ta kasance ai mu abin farin ciki ne a garemu, dan wlhy tsoron tashin hankalin nan nasu nake suzo wataran su ƙonemu ƙurmus mu da gidan kana dai ganin wancan karon da ƙyar muka sha suka so sakamu a tara. Kai ai nikam wannan jini na Ummu-Hidaya ai ba'a cewa komai. Bala'i kala-kala daga wannan sai wancan”. Yanda Baba prof yay shiru da alama ba fahimtar zantukan Hajiya Mammah yake ba ma shi. Dan sai da ta ɗan kai hannu ta taɓashi sannan ya dawo firgigit. Murmushi yayi zai yi magana dai-dai nan akai knocking ƙofa. Tsaki Hajiya Mammah tayi tana hararar ƙofar dan tasan bai wuce ma'aikatan gidan ba. Cike da wulaƙanci ta bada izinin a shigo. Ilai kuwa cikin ma'aikatan ne. Kansa a ƙasa da girmamawa ya kai durƙushe yana sanarma Baba prof yana da baƙo. Agogo Baba prof ya kalla, cikin ɗan ɓacin rai yace, “Bani da apartment da kowa yau, koma su waye a sanar musu suje sa dawo next time”. Kai hadimin ya jinjina. Har zai miƙe sai kuma ya koma ya durƙusa. Kansa a ƙasa cikin ɗari-ɗari ya furta, “Ranka ya daɗe Commando ne fa, kuma kaine kace ko baka gidan nan yazo nemanka a sanar da kai”. Cikin masifa Hajiya Mammah ta juya zata fara danna masa zagi Baba prof ya dakatar da ita. “Uhmm Nafisa kinga barshi umarni na ne. Kinga jeki gida kawai idan na gama da shi zan zo na sameki. Komi ke faruwa ki dinga sanar dani ta waya. Sannan kiyi ƙoƙarin Mu'azz da Abdullahi su dawo gida gudun tashin hankali, idan kuma Awwab baya a gidan ki sanarma Mu'azz ya hanashi komawa gani nan zuwa yanzu nima”. Maganar yake yana tafiya, dan haka kafin ma ta bashi amsa har ya shige hanyar da zata sadashi da falon baƙi. Galala tai kawai tana kallonsa, can ƙasan ranta mamakin miya rikitashi haka take yi. Tare da mamakin girman wannan baƙo a wajensa. Amma dai koba komai ita hakan yayi mata. Dan ta kuɓuta daga abinda take gudu dai ke nan. Cikin taɓe baki ta miƙe, tare da saɓar handbag ɗinta ta fice hankalinta kwance. Ai garama taje taga show ɗin can gidan, dan babu wasu su Paah da zata kira sai abubuwa sun kankama..........✍️ *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 thirty-three .....Abincin na fara bama Ummie bayan na wanke mata baki da taimakon Mama Balki. Ci kuwa take sosai kamar ko yaushe a kwanakin nan. Lauma biyu uku sai na bata ruwan addu'a ta sha. Ba ruwan addu'ar da nake mata bane kawai, Baba ma na mata, haka akwai wani da Hayatu ya kawo yace daga Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain yake amsowa, tuni kuma ana kawowa masu kula da ita wai ke bata. Dan haka dana tashi sai nake haɗesu waje guda ina bata, kullum kuma Mama Balki kan shafa mata sau uku a jiki, safe, rana da dare idan zata kwanta. Shi kansa Yaya Awwab daga jiya zuwa yau sune ruwan shansa batare daya sani ba. Dan kaf ruwan dake a cikin freight na kwashe na sanya masa na addu'oin a ciki, duk da ina ɗar-ɗar ɗin karya gane wajen buɗe murfin, dan haka nake ta kaf-kaf ɗin bashi ruwa yanzu da kaina. Dawowar Fahad ɗakin ya katse mana shirun da mukayi. Dan yana yin sallama yay tozali da Ummie dake zaune ina bama abinci ya ƙaraso cikin sassarfa ya wani rungumeta har sai da ta saki ƙaramar ƙara tana turesa. Ɗagowa yay cikin tsananin damuwa idanunsa share-share da hawaye yana kallonta. Itama kallon nashi take yi, sai kuma ta kauda kanta tare da zamewa ta kwanta ta juya mana baya. Ƙoƙarin komawa side ɗin data juya yayi, amma sai Mama Balki ta dakatar da shi ta hanyar riƙesa. Yayinda ni kuma ƙwallar tausayin ɗa da mahaifiyar suka cika min idanu. Dai-dai nan aka turo ƙofar aka shigo. Tuni ƙamshin turarensa ya wani irin mamaye hancinanmu. Hakan ya samu ɗaga kai mu duka muka kallesa. Shima tsaye yay cak kamar wanda akama umarnin tsayawar. Yayinda Fahad yay wani kalar ɗauke kansa. Mama Balki ce tai ƙarfin halin masa sannu da zuwa. Da ƙyar ya amsa mata yanayinsa na ƙara komawa na ainahin stubborn ɗinsa. A cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara batare da ya karaso ba ya juya ya fita abinsa yana jan sirrin tsaki dake bayyana fushinsa. Harara Fahad ya raka bayansa da shi shima yana jan tsakin mai kauri. Sai kuma a hankali ya furta, “Mugu kawai azzalumi”. Har cikin tsakkiyar kaina naji shigar zagin nan. Na ɗan kalla Fahad ɗin naga yanda yake wani cika yana batsewa. Maimakon naji haushinsa sai ya bani tausayi, dan hatta da jijiyoyin kansa duk sun fito raɗa-raɗa haka ma idanunsa sun wani bala'in kaɗawa jazur a ƙanƙanin lokacin nan. Kamar wanda aka tsikara shima ya miƙe zaram. Dai-dai nan Hayatu ya shigo ɗakin da sallama. Cak Fahad ɗin ya tsaya daga yunƙurin fitar da yake yi. Sai kuma murmushi ya ɗan kufce masa, da sauri ya nufi Hayatun yana faɗin, “Oyoyo sweet Yayana”. Tuni shima Hayatu ya ajiye kayan hannunsa ya buɗe masa hannayensa suka rungume juna. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, sai kuma na miƙe batare da nacema kowa komai ba na fita.... 🩸🩸🩸🩸 Cikin yanayin gajiya ta shigo gidan. Ga damuwar dake a ƙarƙashin zuciyarta a kwanaki biyun nan game da rashin ganin Samraah. Tun a jiya bincikenta ya tabbatar mata da Samraah ce a sashen Awwab dai Hajiya Mammah da bata san an sallamota ba ta gani ba wata ba. Taso sanar ma Yallaɓai amma ta kasa hakan dan tana son ta fara sanin mi bincikensa ya samo masa akan yarinyar. In har wanda zata iya canja ra'ayinsa ne daga kasheta daya ambata sai ta fara shirinta. Idan kuma na wanda bazai iya canja ra'ayin nasa bane nan ma sai ta ɗauki mataki. Dan a wannan gaɓar bazata taɓa bashi goyon baya ba. Tanama Samraah wani irin mahaikacin so mai taɓa zuciya. Ita kaɗai tasan a halin matsanancin kishin da take ciki na Awwab a ƴan kwanakin nan musamman daga jiya zuwa yau. Babu kowa a falon sai ƙamshi da sanyin ac. Tasan su Arwa sun fita yawonsu, dan Muhseen ne kawai ke zuwa makaranta yanzu a gidan sai Aneesa autar Hajiya Mammah ƙanwar Azizat kenan. Cikin rashin kuzari ta kama ƙarfen upstairs zata fara haura steps ɗin ta tsaya cak. Rawa jikinta ya nema fara yi sakamakon abinda idanunta ke kallo. Cikin wani irin bugawar zuciya da rawar baki ta furta, “Fahad!”. “Yes Ummy. Surprise”. Ya faɗa cikin fara'a yana ƙarasowa gareta. Cikin rashin kula da yanayinta ya bata side hug abinsa. Da ƙyar Hajiya ƙarama ta iya jan numfashi da kokarin controlling kanta. Amma ina jikinta karkarwa yake. Dan koda Fahad ya ɗago yana gaisheta sam bama fahimtarsa take ba. Sai da ya ɗan tanƙwaɓeta da zai gittata yana dariya sannan taji abinda yake faɗi na ƙarshe. “Oh Ummy mamakin ganina da alama ya sumar dake. Bari naje dai yanzu zan dawo karki faɗama su Azizat na dawo”. Daga haka yay wucewarsa ya barta a yanayin ƙaulani. Sosai taji fitsarin dake a mararta na ƙoƙarin zubowa. Tuni ta saki handbag ɗinta a wajen ta juya ta fice a falon ƙafafunta na matuƙar rawa. Tana shiga motarta motar Hajiya Mammah na shigowa gidan. Ko bi takanta batayi ba ta wani irin yin reverse da mahaikacin gudu kamar ba'a cikin gida take ba ta fice har tana kusan takama ɗaya a cikin securitys ɗin ƙofar ƙafa ALLAH dai ya taƙaita yaja baya da sauri. Babu wanda ya kawo komai a ransa sai tunanin kiran gaggawa maybe ta samu daga asibiti. Dan sometimes takan yi irin wannan fitar idan hakan ta faru. Sai in ta dawo ta basu haƙuri da sanar musu abinda ya rikita tan. Shiyyasa kowa a gidan ke mata uziri da mata kallon innocent woman dako hannu ka saka mata a baki bazata ciza ba. Wani irin mahaikacin gudu tayi ko'a titin. ALLAH dai ya taƙaita titin anguwa ne. Gashi kuma anguwan masu kuɗi ba wani yawan kai-kawon mutane ake samu ba, motocin ma sai jefi-jefi. Yanzu kam dama rana da wahala ka gani kasancewar duk ana wajen aiki. A cikin ƙanƙanin lokaci ta iso gate ɗin gidan yallaɓai. Horn ta dinga dannawa daya rikita maigadi, jikinsa har rawa yake wajen buɗewa. Ruɗanin da take ciki ya sata mantawa gaba ɗaya yau bata saka niƙaff ba. Sannan kuma da motarta ta amfanin ko yaushe ta shigo gidan bata ɓadda kama ba kamar yanda ta saba. Kasancewar a duka kamanni biyun na baɗini dana zahiri tana da power ɗin shigowa gidan yasa babu wanda yay mamakin ganinta sai dai mamakin yanda ta shigo. To amma idan suka auna da kafin zuwanta wadda tazo zasu iya kallon abin a wani abu daban kuma. A dai-dai ƙofar falon gidan tai parking, ko rufe motarta batayi ba ta afka ciki. Babu kowa a falon, sai tv dake magana ƙasa-ƙasa. Hannunta ta kalla da nufin neman waya, wayam babu handbag. Tunanin ta barta a mota ya sata jan tsaki. Juyawa tai da nufin ɗakko wayar dai-dai nan wanda zata fita ɗakowar dominsa ya fito. Baiyi mamakin ganinta ba, dan yasan zata iya zuwa ɗin dama.. Zaune ta kai dan wata irin hajijiya take ji na neman ɗibarta. Da ƙyar ta iya haɗa kalmar, “Fahad ya dawo, yanzu haka yana gida”. Zaune ya kai shima a hankali batare daya ce mata komai ba. Sai ma file ɗin hannunsa daya ajiye yana mai dafe kansa da duka hannayensa biyu. Jin shiru baice komai ba ta ɗago ta kallesa. Muryarta har rawa take wajen sake faɗin, “Yallaɓai baka ji abinda na faɗa bane?”. Wani irin murmushi ya saki, mai bayyanar da tsantsar ɓacin rai da tsufarsa. Ya ce, “Na jiki sarai, shima wanda ke bincike akan yarinyar nan ya kawo sakamakon yanzu”. Bai gama rufe baki ba ta ɗauki file ɗin ta fara dubawa cikin rawar jiki. Abubuwa masu muhimmanci kawai take dubawa. Abu na farko daya fara jan hankalinta shine cikakken sunan yarinyar. Samraah Abdul-wahab Gwarzo. Na biyu aikin mahaifinta da sanadin rasuwarsa har ma da inda ya rasu. Na ƙarshe MATAR AURE. Rawa bakinta ya fara da ƙyar ta iya haɗa kalmar, “Ba...ban fahimci komai ba yallaɓai”. Murmushi ya sake saki, sai kuma ya kalleta da idanunsa dake jazur kamar tsohon maciji. Musamman yanda tsufarsa ta sake fitowa fili sai taga har baƙinsa ma ya sake bayyana fiye dana baya mai tsananin shining ɗin hutu. Shima ɗin kallonta yake cikin ido, batare daya janye ba ya furta, “Ita ɗin ɗiya ce ga Abdul-wahab Gwarzo (jirgin mota)”. Kaɗan ya rage zuciyar Hajiya ƙarama ta ɓaro. Ta wani irin miƙe zambar jikinta na karkarwa tace, “What! Jirgin mota? Drivern mahaifin Ummu-Hidaya da kenan?”. Kansa kawai ya ɗauke daga kallonta alamar tabbatarwa. Cikin kaushin murya ya cigaba da faɗin, “Tabbas nayi kuskuren ƙin bibiyar bayan Abdul-wahab kamar yanda nake biye dana Ibrahim Alonso. Idan baki manta ba nayi hira da yarinya shekara ɗaya data gabata a Kano sakamakon turamin program ɗin bikin buɗe Company da Awwab yayi. Zargin akwai dalilin da yasa ya amsa mata zaiyi hira da ita alhalin bai taɓa yi da ko manyan channels ba yasa na baro India nazo danna tabbatar da ko akwai alaƙa a tsakaninsu. Tako ina bincikena babu ta inda wata alaƙa ta alaƙanta su, dan haka ban maida hankalina ga cikakken sunan yarinyar ba....” “Wai kana nufin itace yallaɓai?”. Hajiya ƙarama da gaba ɗaya take a gigice ta jeho masa tambaya cikin katsesa. Iska ya furzar mai kauri tare da miƙewa tsaye. Taku ya fara hannayensa duka biyu a goye ya ce, “Of course itace yarinyar”. “Tashin hankali. To amma tayaya tazo Lagos bayan ma'aikaciya ce? Ta yaya kuma Lagos ɗin ma take zaune a Maash Mansion? A ƙarshen zance shine tayi aure bayan fasa aurenta da saurayinta da suka jima a tare. Abin tambayar anan waye ya auretan? Waye kuma yay kidnapping ɗinta kafin auren har sau biyu? Tabbas akwai abinda ya kawota Maash Mansion, minene shi?. Yallaɓai wlhy zan haukace, wane irin ruɗani da tashin hankali ne haka yazo mana a rana ɗaya? Gashi mun gagara magance batun likitocin nan abu sai ƙara nisa yake, duk da dai ba wannan bane kaɗai hope ɗinmu wancan ma zasu iya mana illa tunda ko ganinta bamayi a yanzu balle sanin halin da take ciki”. Amaimakon amsa mata dukkan tambayoyinta da maganganunta a mugun fusace yay wurgi da ɗan abin deco.. ɗin dake a saman Centre table ɗin gabansu........✍️ *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 thirty-four ......Mugun tsorata Hajiya ƙarama tayi har sai da ta rumtse idanunta da toshe kunnenta jikinta na rawa. Shima nashi jikin rawar yake yi na tsantsar ɓacin rai. Kafin ya shiga maimaita kalmar, “Dole akwai abinda Awwab ya sani, dole shine ya shirya komai. Ta ya yarinyar dake a Kano zata dawo Lagos? Ta ya ɗiyar Abdul-wahab zata shigo Maash Mansion matsayin ƴar aiki? Ta ya?!!! Ta ya?!! Ta yaya?!!!!”. Ya faɗa cikin wani irin ƙaraji da ya sake firgita Hajiya ƙarama. Dan bata taɓa ganinsa a irin wannan fushin ba duk da kuwa ita shaidace akan hatsabibancin sa tun ba yanzu ba. Da wani irin fushi ya danna gefen kujerarsa, zuuuu sai ga gurin ya buɗe. Wata ƴar loka ce ta bayyana, kwalaben manyan haɗaɗɗun giya masu tsadar gaske suka bayyana. Ɗaya a ciki ya ɗauka, batare da tuna akwai mai amsa suna surukarsa ba a wajen ya ɓalle murfin ya dasa a bakinsa ya shiga kwankwaɗar kayansa. Shike sha, amma Hajiya Ƙarama ita ke binsa da kallo kamar tsohuwar mayya. A yanda take jinta yau ɗin nan kamar fa ta amsa itama ta kora. Sai dai kuma tasan hakan zai iya ɓallo mata aiki ne a wajen Paah. Tas ya shanye abinda ke ciki, tare da yin wurgi da kwalbar sannan ya koma cikin kujera yay wata irin lafewa yana sauke numfashi da ƙarfafan ajiyar zuciya tamkar wanda yay wani uban gudu a sahara. Sun kwashi mintuna biyar a haka shiru, kafin ya miƙe batare da ya kalleta ba ya ce, “Kije gida zan nemeki.” Baki ta buɗe zatai magana ya ɗaga mata hannu alamar baya son jin komai. Kanta kawai ta jinjina tare da miƙewar ta fice. Da harara ya raka bayanta, yana jin a ransa amfaninta ya kusa ƙarewa a garesa. Juyayyun idanunsa ya maida kan ƙaton hotonsa dake a falon shi da mahaifin Ummie wato Ibrahim. Hoton yay matuƙar ƙyau musamman da suka kasance cikin manyan kaya, su sukansu kuma bakunansu ɗauke da murmushi. Hannayensu riƙe da jariri dake a cikin showal mai tsananin ƙyau da ɗaukar ido. An yi hoton ne a ranar sunan Muhammad Awwab. Shine kuma jinjirin dake a hannun nasu suna kallonsa fuskokinsu ɗauke da murmushi. A fusace ya rarumi ɗayan deco ɗin saman table ɗin ya wulwula sai ko akan hoton. A take gilashin jikinsa ya tsatstsage. Yatsansa ya karkaɗa alamar gargaɗi ma hoton sannan ya wuce fuuuu zuwa bedroom ɗinsa.... A hankali Kukunsa dake laɓe yana kallon komai ya shiga jinjina kansa. Da baya-baya ya koma ya shiga ta cikin store. Stick ya ɗauka cikin dabara ya janye abinda ya kare cctv camaras ɗin dake a kitchen ɗin ta koma yanda take kamar komai bai faru ba. Dan duk leƙen da yay da naɗar abinda ke faruwa a rubuce camara ɗin bata ɗauka ba. Ba yau ya fara hakan ba, domin a ankare yake, ko it kanta camara ɗin babu wanda yasan ya fahimci akwai ta a kitchen ɗin fama cikin gidan baki ɗaya, sai dai bai taɓa cin karo da samun abinda yasan ogansa zaiyi farin ciki ba irin yau, dan koshi kansa a yau ɗin nan ya matuƙar girgiza da shiga mamakin ganin fuskar Hajiya ƙarama a matsayin wadda ta jima tsahon shekaru tana kawoma Baba prof ɗin ziyara amma bai taɓa ganewa ba saboda shigar ɓadda kama da take yi idan zatazo. Ba kuma su taɓa zama a wannan falon sunyi magana ba sai yau ɗin. Aikinsa ya cigaba dayi kamar yanda ya saba.... 💓★💓★💓 A hankali na murɗa handle ɗin ƙofar na tura kamar mai jin tsoron gamo da wani abun firgici. An rage hasken ɗakin ya koma dif sosai. Sai sanyin ac da ƙamshin fresheners dana saka kafin na fita. Ɗan dube-dube na fara kafin idanuna su sauka akansa. Yana can tsaye daga jikin window duka hannayensa goye a bayansa ya ƙurama waje kallo. Cikin sanɗa na ƙarasa shiga ɗakin. Tray ɗin dake hannuna na ɗaura saman Centre table dake a tsakiyar sofas. Kafin na ƙarasa takawa har inda yake cikin sanɗa. Cikin rufe ido da killace duk wata kunya dake cike da zuciyata na ƙarasa ta bayansa a hankali na warware hannayensa dake goye a bayansa na rungumesa ta baya, hannayena zagaye da shafaffen cikinsa. Dan abinka da dogo bawani na iya kai koda kafaɗarsa bane. Data samansa ne ma hannayena bazasu iya kullesa ba saboda yanda ƙirjinsa ke a buɗe alamar motsa jiki. Jikinsa akwai zafi sosai alamar zazzaɓi ko kuma duk ɓacin ran ne oho. Duk da dabaibayin dana masa sam bai motsa ba, na ɗan ciza lips ɗina ina mamakin taurin zuciyarsa. A zahiri kam muryata na maida can ƙasa da ƴar shagwaɓa na ce, “My Lion!”. Shiru bai amsa ba. Na ɗan yi jimm kafin na motsa hamnuna na mintsinesa a saman cikinsa kaɗan na sake faɗin, “My hot! Please answer me ko naita maka kuka”. Nan ɗin ma kamar bazaice komai ba. Dan kusan fin minti ɗaya kafin naji saukar hannunsa saman nawa. Sosai shima ɗumin hannun nasa ya ratsa min nawa har sai da na ciza lips ɗina kaɗan. A hankali ya jawoni daga bayansa ya maidoni ta gabansa ya tsayar da ni. Har cikin jini da ɓargo na nake jin kaifin idanunsa na ratsani. Dan haka koda kwatance ban iya gwada ɗagowa na kallesa ba. Saukar hannunsa mai ɗumi naji akan haɓata, ya ɗago fuskata sama ta yanda zamu iya ganin juna. Amma sai na lumshe nawa idanun dan bazan iya kallonsa ba. Yafi minti ɗaya yana ƙarema fuskar tawa kallo, ina jin hakanne ta hanyar kaifi da tasirin ƙarfin idanunsa a kaina. Da wani irin ƙyar, tamkar wanda akama dole cikin maƙoshi ya furta, “Mi kike buƙata?”. Sai da na ƙara runtse idanuna da ƙyau kafin na ɗaga hannuna na ɗaura yatsana manuniya akan jikinsa alamar shi. Ina ji ya ɗan furzar da numfashi mai ɗan sauti kafin ya furta, “Open your eyes”. Kafaɗa na maƙe masa da faɗin, “Uhm-uhmmm!”. Cikin shagwaɓa. “Why?”. “Ina jin kunyan ka”. “What is kunya?”. Bamma san sanda na ware duk girman idanuna ba a kansa. Cikin suɓutar baki na ce, “Bama ka sanshi ba?”. Kansa ya jinjina min kawai idanunsa da gaba ɗaya suka canja launi a cikin nawa, ya wani ƙankancesu da shanyesu sun koma wasu luu-luu da su tamkar mai son yin barci. Kasa jurewa nayi, na rissinar da nawa idanun a hankali ina maida fuskata ƙasa. Sai kuma na ɗaura bayan hannuna akan hannunsa da har yanzu ke akan haɓata. “Yaya jikinka fa zafi, baka da lafiya ne?”. Shiru kamar bazai amsa ni ba, sai kuma ya jawoni jikinsa a hankali ya rungume. Da ƙarfi na sauke ajiyar zuciya, dan wani ratsani zafin jikin nasa yayi har cikin ƙashi. Cikin kasa daurewa na sake faɗin, “ALLAH baka da lafiya. Please muje kasha magani”. “Nooh!”. Ya faɗa da ɗan kaushin murya yana sake ƙanƙameni. Tuno maganar Mama nayi da tace baya ƙaunar magani. Sai naji abin ya bani dariya ma. Namiji da shi babba amma yake tsoron magani. Mun jima tsaye a haka kafin na ɗago dan ƙafafuna sun fara gajiya. Cikin raunin murya kamar zanyi kuka nace, “ALLAH yaya ƙafafuna sun gaji ni dai”. Baice komai ba, baima da alamar motsawa. Sai da ya mula dan kansa kafin ya ɗagoni. Ajiyar zuciya na sauke. A saman sofa ya kawoni ya zaunar, shi kuma ya wuce closet. Da kallo kawai na bisa ina mai sauke ajiyar zuciya. Sosai tausayinsu ya kamani shi da ɗan uwan nasa. Dan a kallo ɗaya zaka iya fahimtar tsantsar ƙiyayyar da sukema juna a bayyane take. Nayi nisa sosai a tunani har ya dawo ban sani ba. Sai da ya kama min hannu na dawo firgigit tare da ɗagowa na kallesa. Da sauri na kauda kaina, dan bathrobe ce a jikinsa blue black bai ko ɗaure igiyoyin ba, hakkan ya bama boxer ɗinsa damar bayyana da murɗaɗɗen jikinsa. Magana na buɗe baki zanyi yay min alamar zipping akan lips. Dole na haɗiye sai dai zuciyata sai faman dukan uku-uku take. Tsorona kar yace wanka zan masa. Wani wawan ajiyar zuciya na sauke ganin saɓanin hakan. Dan ƙofa ya buɗe muka fito, sai kuma na shiga wasi-wasin ina zamuje haka. Bamu fita ba a ta wajen bedroom ɗin nasa ya buɗe ƙofar da na daɗe ina tunanin ta bedroom ce itama, ashe ba haka bane. Dan gani nai kawai mun fito ta wani ƙyaƙyƙyawan waje da ƙaton swimming pool ne kawai a cikinsa. A yanayin kamar a ɗaki, sai dai ta saman ginin kana iya hango sararin samaniya, hakama ta jikin bango zallar gilashi ne da kake iya hango cikin garden ɗin nan. Ata ƙasa an matuƙar ƙawatashi da green carpet tamkar koriyar ciyawa farkon toho. Sai hakan ya bada wani irin ƙawa musamman da yanayin ruwan shi kuma ya kasance blue yana wani walƙiya da ƙyalli kamar kaci da haƙori. Sosai dogayen fararen kujerun da kallo ɗaya zakama tausasan katifun samansu kasan zasuyi laushi suka sake ɗaukar hankalina. Na shagala matuƙa da kallon wajen har ban san ma ya zame bathrobe ɗin jikin nasa ba. Sai da ya rungumeni ta baya sannan na ja ajiyar zuciya. Yanda yake mun numfashi ata bayan kunne yay matuƙar saka tsigar jikina ta shi. Bamma san na ƙanƙame hannunsa dake saman cikina ba ina ƙara manne bayana da jikinsa idanuna a rufe. Cikin soft and silent voice ɗin shin nan yana wani irin mun salo a cikin kunne ya furta, “Za kiyi wanka a ciki?”. Sosai na ƙara ƙanƙame jikina ina jujjuya masa kaina dake a saman ƙirjinsa. “Why?”. Ya faɗa yanayi kamar zai ciza kunnena. Jinai jikina yana neman fara rawa. Lips ɗina na rawa na ce, “Yaya wlhy tsoro nake ji. Ban taɓa shiga ruwa ba irin haka”. Komai baice min ba, sai ɗan kwalina daya zame yana ƙoƙarin cusa hannunsa cikin gashin. Tanan kuma ɗayan hannunsa na yawo a jikina. Cikin ɗan ƙarfin da ya rage mun da sauri na janye jikin nawa dake ƙoƙarin fara rawa ina sauke numfashi da sauri-sauri. Komai baice da ni ba, bai kuma kallan ba, sai ƙarasa sakimmin hannun da yay a hankali. Idanuna na runtse, kusan minti ɗaya na buɗe su da sauri saboda jin ƙarar faɗawarsa cikin ruwan. Waro idanuwan nayi sosai ganin yanda ya wani nutse can ƙasa gaba ɗayansa sai motsin ruwan kawai kake gani ta sama.......✍️ *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_ ......Gaba ɗaya na shagala nayi da kallon yanda yake action a cikin ruwan da style kala-kala tamkar wani kifi. Yafi minti biyar kafin ya miƙe tsaye ta jikin bango ya wani furzar da ruwan dake bin fuskarsa da gaba ɗaya kwantaccen gashin dake kumatunsa da na saman kansa suka kwanta luff kamar ka zauna kaita kallonsu. Idanunsa kam sun ɗan kaɗa tare da kanƙancewa. Da hannu yay min nuni wai na zauna a ta bakin ruwan. Kafaɗa na maƙe masa. Sai ya ɗan tsuke fuska. Hannu na kai na ɗan shafa gefen wuyana, sai kuma na shiga takawa a hankali har zuwa inda ya nuna ɗin na zauna. Nuni yay min da ƙasan rigata. Nan ma sai da na marairaice fuska amma yay kamar bai gani ba. Dole na nannaɗe rigar idanuna a lumshe na saka ƙafafuna a cikin ruwan. A tunanina zan jisa da sanyi sosai sai naji ɗumi. Bamma san na saki ajiyar zuciya mai ƙarfi ba da sakin ƙafafun gaba ɗaya a ciki har iya kusan gwiwata ruwan ya kawo. Daga sama kuma ina zaune ne na naɗe rigata da ƙyau. Murmushi na saki tare da ɗan kallonsa na ce, “Ashe ruwan akwai ɗumi Yaya”. Fuska ya ɗan yamutse kawai batare da yace min komai ba ya ɗauke kansa. Nima sai na murguɗa baki dan yanda yay ɗin ya bani haushi. Cikin ruwan ya koma ya nutse, ban farga ba kawai na gansa ya fito ta gabana har sai da na tsorata ina neman cire ƙafafuna zanja baya ya riƙeni. Kallonsa nai ina ɓata fuska kamar zan yi kuka. Fuska ya ɗan ɓata shima, ƙananun pinkish lips ɗinsa ya ɗan taɓe da yarfa min ruwan hannunsa a kan fuska. Baki na tura ina kai hannu na ɗiba ruwan nima da faɗin, “Ni sai na rama”. Karon farko ya saki wani makirin murmushi tare da riƙe hannun nawa ya jawoni gaba ɗayana cikin ruwan. Tsabar tsorata bamma san na fasa ƙara ba. Ruff kuwa ya rufe min baki da nasa. Sosai na ƙanƙamesa dan illahirin jikin nawa na cikin ruwan har kusan saman kafaɗa ta. Badan yama riƙeni ba duka zan nutse a ciki. Ya jima yana yanda yaso da ni kafin ya ɗago ya zubama fuskata ido. Koda wasa ban yarda na buɗe idona ba, dan wata irin matsananciyar kunyarsa nake ji matuƙa. Jin hannunsa a bayana yana sauke zip ɗin rigata da sake nutsani a cikin ruwan ya sani buɗe idanuna da sauri. A cikin nasa da sukai wani irin mugun canja launi zuwa na gawurtaccen zaki ya sani jin firgici na shiga jujjuya masa kaina. Da idanunsa yay mun nunin na rufe nawa idanun, da gudu kuwa nabi umarninsa ina sake shigewa jikinsa. Tsaff ya zame rigar gaba ɗaya, tare janye ɗan kwalina shima tsefaffen gashina ya bayyana. Ribbon ɗin dana kamashi da shi ya zare gaba ɗaya. Kunya tsoro gaba ɗaya sun sakani manne masa, wace irin rayuwace wannan da ranar ALLAH a maka tsirara a bainar nasi. Yo tsirara mana tunda da ga ni sai b&p kawai. Inaji ina gani ya shige dani cikin ruwan bayan ya maƙalamin gilashin shiga ruwa. Da ƙyar nake iya riƙe numfashina, sai nayi kamar sakan biyar sai ƴa ɗagoni sama. A gigice nake furzar da ruwa ina girgiza kaina, ina gama dai-daita zai sake maidani. Haka ya dinga yawo dani a cikin ruwan ina a jikinsa da salo kala-kala. Har sai da yaga ina neman jigata sannan ya ɗagani cak ya ɗaura saman dakalin wajen, ya yinda shi kuma ke jingine a jikina daga tsaye a cikin ruwan. Kunya ta isheni ga wahalar ruwa, na rasa yanda zanyi dole na haƙura na zauna a haka yana ƙare min kallon nan nasa na ƙasan ido.... ✨✨✨✨ Tun shashsharewar ƴan biki Halime ta sake jangwaɓema Abba. Dan da gaske cikin na wahalar da ita. Da ga ƙarshe dai dole Gwaggo Gudidi tazo ta ɗauketa ta maida gidanta. Dan yarinyar na bata tausayi matuƙa. Komawar Halime gidan Gwaggo Gudidi tai matuƙar janye hankalin Abba zuwa can. Dan barci kawai ke kawoshi gidan nasa saboda har yanzu basu shirya da Mom ba. Sai dai ya maida aurensu batare daya sanar mata ba. Gwaggo Gudidi da Alhaji Sadisu da Alhaji Jafaru ne kawai suka sam hakan. Gwaggon taso ya faɗa mata, amma yace tayi haƙuri ba yanzu ba sai Jalilian ta sake ladabtuwa. Dan ya fahimci auren nan na Baby ma kamar sake tunzurata yake tana ɗaukar kanta wata tsiya. To a ɓangaren Mom ɗin ma dai ta tattara Abban ta watsar. Dan gaba ɗaya hankalinta yanzu nakan ta yanda zata biya basikan mutane da taci a bikin nan. Sai kuma fatan itama Bibaa ALLAH ya kawo mata irin mijin ƴar uwarta. A gefe kuma sunata shirin tafiya saudia da jiran mijin Baby. Itama dai Babyn jiran nata suke dan gaba ɗaya maganar biyan bashin nan ta ta'allaka ne da ita. Amma sai sukaji shiru har kusan sati kenan babu wayarta babu saƙo. Ko message ɗin sun sauka lafiya bata tura musu ba. Sam basu kawo komai a ransu ba. Sai tunanin ai amarcine ya riƙe ta, dan sun san magungunan da suka ɗika mata bazasu taɓa tafiya a banza ba ai. Wannan hope ɗin ya sasu tattara batun Baby gefe ɗan sauran kuɗin hannunsu suka shiga karkaɗar da su a neman hanyar da cikin jikin Halime zai salwanta da kuma yanda batun tafiyar Musaddiq China zai canja daga ƙaro karatu zuwa wani bala'i daban. Kai hatta ita kanta Samraah a wannan gaɓar bata tsira ba. Dan sunanta ya sake komawa wajen teachers akan sunaso a ƙuntata rayuwarta a gidan aurenta ta yanda bazata taɓa ta samu wani jin daɗi ba sam. Ta rasa ina zata dafa taji daɗi. Dan suna son duk randa Samraah zatazo gida tazo wujiga-wujiga da ita kamar korarrar ƙauyen cikin sahara a wulaƙance kuma dan su sami abin yin dariya da maidama dangin Abba murtani.... 💞💞💞💞 Duk yanda yake ƙoƙarin hiding abubuwa game da ahalinsa al'amarin ya kasa yiyuwa. Dan tun barinsa gida bai yada zango ko ina ba sai ƙasar Niger. Kusan watansa ɗaya ya shirya ya sake wucewa Dubai wajen wani abokinsa. Damuwar da yake a ciki da halin fushi ya bama abokin nasa damar fara masa huɗubar shaiɗan da sake bin hanyoyin busar masa da zuciya. Jan ra'ayin Mansoor ɗin yake sosai akan fara safarar cocaine da miyagun ƙwayoyi har ma da wiwi. Tun Mansoor na dojewa har dai zuciya ta fara ingiza shi akan yayi abinsa. Miya rage masa a wannan duniyar banda ta neman arziƙi kawai tunda ya rasa masoyiyarsa ahalinsa basa ƙaunarsa. A ranar farko daya amsa zaiyi ya kasa barcin dare sam. Sai zuciyace ke faman masa kai kawo. Tunani da rashin barcin suka haddasa masa tashi da matsanancin ciwon kai. Tun yana ƙoƙarin dannewa har al'amarin ya fito fili ranar dai abokin nasa bai samu damar kaisa wajen ogansa da yay alƙawari ba. Kwana biyu yana kwance kafin ya warke. Ya sake yunƙurin shiryawa abokin nasa ya kaisa wajen boss abokin nasa ya faɗi a bayi yaji ciwo. Nan ma aka shafe wasu kwanaki yana jiyya kafin ya samu sauƙi. Kuɗin hannun Mansoor sun fara janyewa, kasancewar kashewa kawai ake ba wasu ke shigowa ba. A karo na uku da za'a sake kaisa. Sukai accident ALLAH dai ya taƙaita basu ji ciwo sosai ba. Sai ma shine ya ɗan ƙuje a gefen fuska. Nan ma bai yiwu sunje ba. Daga nan fa Mansoor ya fara shan jinin jikinsa. Zuciyarsa ta fara buɗewa ya fara fahimtar al'amarin nan fa ba alkairin bane garesa shiyyasa aketa fuskantar ƙalubale. A karo na huɗu da abokin nasa yace suje sai ya doje. Nan fa ya shiga masa naci, sai kawai ya fito masa a mutum yace ya fasa. Ran abokin nasa ya ɓaci, dan babu ɓoye-boye ya tabbatar masa da bazai yiwu yasan sirrinsu ba ya kuma kware musu baya. Dole ne cikin biyu ɗaya ta faru, kodai ya shigan kamar yanda sukai magana tun farko, ko kuma ya shirya amsar hukunci. Mansoor akwai zuciya, aiko take ya yayyaɓama abokin nasa baƙaƙen magana suka rabu walle-walle ya canja wajen zama. Shiru kamar abokin nan ya barsa, dan har ya samu aiki a wani companyn saida kayan yara yana ɗan samun kudaɗensa na shiga dan har ma ya manta abinda ya faru da abokin nasa sai kwatsam rana tsaka police suka zo kamashi har cikin companyn da yake aiki. Da farko dai ogan companyn da yake aikin yaso tsayawa a fito da shi, sai da yaji abinda ake tuhumar Mansoor ɗin da shi wai safarar cocaine, a yanzu haka ma an kama wata yarinya ne da ita cikin kaya tace shine oganta, shine dalilin da yasa aka kamashin ma. Da farko Mansoor ya ɗauka zai iya kare kansa saboda yana da hujjoji da kuma ƙwarin gwiwar abokinsa ne ya masa sharri. Sai daga baya ya fuskanci al'amarin fa ba wasan yara bane ba. Dan ƙulline shiryayye mai kuma zaman kansa. A hakan ma yayi ƙoƙarin ganin bai tada hankalinsa ba, sai dai kuma ina da alama awannan gaɓar ƙarfin zuciya ko jarumta bata da wani tasiri. Dan ba jami'an Nigeria bane ba ƙasar sa ta gado da wasunsu kan juya baƙi ya koma fari in har aljihunka da nauyinsa taf.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ......Tunda muka dawo ɗaki na fahimci yanata faman dafe kansa. Ga jikinsa akwai matuƙar zafi har yanzu dan ya matsa sai da na shafa masa mai. Black tea ya buƙaci na bashi. Hakan ya sani fita zuwa kitchen ɗinsa a karo na farko na dafa abinda ya umarceni, sai kuma na haɗa da ɗan spaghetti ko zai ci dan inaga kamar harda yunwa a al'amarinsa. Koda na dawo kwance na samesa yama ja bargo jikinsa. Har cikin rai sai da naji gabana ya faɗi. Tray ɗin na ajiye a side drawer na hau saman gadon. A hankali na ɗaga bargon ta saitin kansa. Hannnuna na ɗaura a saman goshinsa. Zafi sosai da har sai da tsigar jikina ta tashi. Jinai gaba ɗaya na daburce. Cikin damuwa na shiga faɗin, “Yaya Awwab baka da lafiya sosai. Dan ALLAH ka tashi muje asibiti. Ko kuma na kira maka Yaya Hayatu yazo kuje”. Na ƙare maganar ina ƙoƙarin sauka a gadon. Cak na dakata jin an riƙo hannuna. Juyowa nayi na kallesa zafin hannun nasa ma na ratsa jikina. Idanuna na tara ƙwalla na ce, “Please Yaya ka barni naje na kira su. Wlhy bazan iya ganin ka a halin ciwo haka ba na barka.” “Samrh”. Ya kirayi sunana a wani irin can ƙasan maƙoshi. Muryata na rawa na amsa. Bai sake magana ba sai jawoni da yay a hankali na faɗo jikinsa. Duk da akan bargon dake lulluɓe jikinsa nake ina jin zafin zazzaɓin duk da kaurin duvet ɗin. Fuskata ya shafa a hankali yana wani lumshe idanunsa da gaba ɗaya launinsu ya gama canjawa. “Bana son kowa ya sani bani black tea ɗin na sha”. “Amma Yaya.....” “Shiii!!!”. Ya faɗa yana mai lumshe idanun nasa da sake riƙoni jikin nasa da ƙyau. Bani da zaɓin daya wuce bin umarninsa. Dan haka na miƙe jiki a sanyaye na zuba masa black tea ɗin a kofi. Hannu ya miƙo min alamar na kamashi ya tashi. Badan zan iya ba na miƙa masa nawa. Sai dai koda na kama shin sai ya zam nice ma na faɗa jikinsa alamar ya rinjayeni. “My Tiger ashe babu ƙarfi”. Ya faɗa cikin kunnena kamar mai raɗa. Tashi da tsigar jikina tayi ya sani mikewa zumbur ina tura baki. Shima sai bai sake magana ba ya tashi zaunen. Nuni yay min da filo, dan haka na ɗauka na sanya masa a baya jikin fuskar gadon ya zauna tare da jingina ƙafafunsa na a cikin duvet ɗin. Zama nai daga bakin gadon a kusa da shi ina facing ɗinsa. Na ɗauka mug ɗin na miƙa masa. Cat eyes ɗin sa masu tsananin tasiri a gareni na kaina ya amsa. Koda ya fara sha ɗin ma bai janye ba sai nice na duƙar da kai kawai ina tunane-tunane. Tas ya shanye dan irin mitsitsin kofin nan ne na rowa. Cewar da yay a ƙara ya sani ɗagowa na kallesa. Amma sai na janye ina amsar kofin da girgiza masa kaina na ce, “A'a ka barsa haka ka ɗan ci abincin ko kaɗanne. ALLAH ko zama da yunwa ya saka ciwo. Baice komai ba har na ɗakko tray ɗin na aza saman cinyata na buɗe plate ɗin. A take Ƙamshin taliyar ya gama cika wajen. Ba wani dahuwar ƙaƙale na mata ba. Dan attaruhu ne kaɗan sai vegetables da kifin gwangwani dana saka a ciki. Kodan ƴar kaɗan ce dama na dafa sai ya bani wani kalar ƙyau a idon mai kallo. ALLAH dai yasa tayi dadi ma a baki. Tray ɗin na ɗaga zan maida jikinsa ya dakatar da ni. Da mamaki na kallesa, shima kallona yake yi. Cikin wani irin luuu da idanun kamar zai lunshe hannayensa harɗe a ƙirjinsa ya min nunin na ajiye a saman jikin nawa. Nan ma kasa Musa masa nayi, sake min nuni yay da spoon ɗin shima. Nan ma na ɗauka babu musu. Ya nuna min abincin tare da buɗe mitsitsin bakinsa alamar na bashi. Sosai na ɗan waro idanuna waje, sai ya ɗan ɓata fuska da ƙoƙarin zamewa zai koma ya kwanta. Riƙosa nayi da sauri cikin marairaicewa na ce, “Yi hakuri to zan baka”. Ƙaramar harara ya ɗan mun sannan ya koma ya zauna. Niko sai mita nake a zuciyata. Mutum kamar kurma sai iya shege fal cikinsa. A zahiri kam abincin na fara bashi a nutse. Shiko ya zuba min idanunsa kawai yana wani taunawa tamkar baya so. Sai da yay kusan lauma uku sannan ya wani lumshe min idanunsa cike da salo tare da haɗe babban yatsarsa da manuniya 👌alamar yayi. Bamma san na sakar masa murmushi ba nima. A mamakina shima sai ya murmusa kaɗan. Zuba masa ido kawai nai ina kallonsa, dan tabbas murmushi yanama bawan ALLAHn nan ƙyau, sai kuma a kaf rayuwarsa, inaga abinda yafi masa wahala kenan sai magana. “Samrh”. Ya kirani a hankali. Firgigit na dawo hayyacina. Sai kuma na ɗan ɓata fuska dan na fahimci na saki layi da yawa. Ƙoƙarin dojewa nake dan a tunanina zai min magana ne akan kallon nasa. Sai naji saɓanin hakan. Sake kiran sunan nawa da yay can ƙasan maƙoshi da silent muryar sa ɗin nan yana sake narkar da cat eyes ɗinsa kaina ya sa na amsa nima idanuna a ƙasa. “Minene burinki a duniyar nan?”. Ƙaramin murmushi nayi, tare da ɗebo abincin nakai bakinsa. Buɗewa yay ya amsa, na ɗan janye hannuna batare dana kallesan ba dai na ce, “Yaya Awwab! Ina da burika da yawa. Sai dai dukansu sun ta'allaƙa ne a ƙarƙashin dai-daiton rayuwa da samuwar dunƙulalliyar tafiya a yanzu. Dan na jima da shafe babin burikan da wauta da ƙuruciya ta ƙirƙira a baya saboda wasu dalilai.” abincin na ƙara ɗiba zan bashi ya girgiza min kai alamar ya ƙoshi, fuska na marairaice ina kallon abincin, sannan na sake kallonsa na ce, “Please kaɗan fa kaci. Ka daure ka ɗan ƙara sai kasha magan...” Ai tun kafin ma na ƙarasa kalmar maganin ya wani yamutse fuska da ɓata rai. Dariya naji ya bani, wai namiji babba kamarsa da tsoron magani. Bance da shi komai ba face maida abincin na rufe na ajiye. Maganin dana riga na ɓalla nasa a ƙaramin plate na rufosa na buɗe na ɗiba. Ina juyowa yaga abinda nayi kawai yay saurin jan bargon zai kwanta na ɗane gadon ina dariya. A saman cinyarsa na zauna na hanashi kwanciyar tare da riƙo fuskarsa. Kansa ya shiga jujjuya min kamar zaiyi kuka. “Please my tiger wlhy bana so. I hate medicine! leave me alone I beg”. Hancinsa na ɗan ja da faɗin, “Noo sai fa My Lion ya sha maganin nan zan barsa. Ni ina son naga ka samu sauƙi, jikinka ƙara zafi ma yake”. “Pleaseeee”. Ya sake faɗa fuskarsa a yamutse kamar zai fasa ihu. “Nima Pleaseeee manya fa basa tsoron magani. Haba ɗan Ummiensa. Bafa wani wahala da yanzu ma kasha. Zakafi samun sauƙi da wuri”. “No kawai ki rungumeni zan daina ji”. “A'a, sai kasha sannan zan rungumekan. Rufe idonka ka gani ka buɗe bakin haba mana, be a good boy my Lion. Hhaaah”. Kafaɗa ya maƙe mun duk ya marairaice abin dariya. Kamar ba stubborn Maash ɗin nan ba mai yin komai cike da rashin mutunci ba. Cikin ƙoƙarin sake dabara na ce, “To yanzu yaya kake son ayi?”. Bakin ya buɗe zaiyi magana kawai na shammacesa na cusa maganin. Na saka tafin hannuna na danne bakin. Duk ƙoƙarin turewa da yake yana yunƙurin amai ban barsa ba saida na ɗauka ruwa, ina janyewa zai ɓaro maganin na danna masa kofin kan baki tare da riƙe masa hacci da yatsuna dole ya zuƙi ruwan. Sai da na tabbatar ya shanye ruwan maganin kuma ya wuce gaba ɗaya sannan na saki masa hanci ina dariya. Ganin yanda yake riƙe wuya yana yunƙurin amai yasa na daina dariyar dan na fahimci abin nasa fa na gaske ne. A hankali na riƙe fuskarsa da tafukan hannuna duk biyu tare da kai lips ɗina saman small nashi duk da yanda zuciyata ke dukan tamanin-tamanin ga kunya amma na daure. Cak kuwa ya tsaya da kakarin ya shiga sauke numfashi. Kusan minti ɗaya na tabbatar nutsuwarsa ta dawo jikinsa na janye bakina ina mai tusa kaina cikin ƙirjinsa dan harga ALLAH kunya naji sosai. Abu goma da ashirin gani a saman cinyarsa kuma zaune ɗane-ɗane kai ni Kandala ansha abin kunya. Saukar hannayensa akan bayana da yanda ya wani irin rungumeni tsamm ya sani lumshe idanuna dake rufe tare da jan numfashi a hankali. Mun kusa mintuna uku a haka kowa na sauraren bugun zuciyar ɗan uwansa kafin ya kwantar dani a hankali shima ya kwanta yana jan duvet ya lulluɓemu. Sosai yanzu kam gabana ya faɗi. Dan raba jikina nai ƙoƙarin yi da nashi ya girgiza min kansa, cikin mugun low voice a kunnena ya furta, “Please! stay, I need hakan babu abinda zanyi”. Ajiyar zuciya na ɗan sauke mukai shiru. Har ma na ɗauka barci ya kwashesa a bazata na sake jin muryarsa a cikin kunne na. “Tell me mine burinki?”. Sai da nayi ɗan murmushi kafin na sake shigewa jikinsa, dan yanzu kam zafin jiki nasa daɗi yake min kasancewar nima kamar na fara jin sanyin abinka da wadda bata saba shiga ruwa ba. A hankali nima nace, “Yaya Awwab”. “No faɗin yaya Awwab again. Sabon sunana nake so”. Da mamaki nace, “Wane sabon suna? Yaushe ka samoshi”. “Yanzu da za'a mun muguntan bani magani mana. In ba hakaba ni gaskiya zanbi takan dokan likitar nan”. Ai harda ƴar zabura nayi, amma sai ya maidani ya sake matsewa da faɗin, “Toki faɗa”. A shagwaɓe na ce, “Nifa nama manta”. Sai da ya ɗan mintsineni sannan ya ce, “Mai zafinki”. Jinai gaba ɗaya kunya ta gama kamani ma. Ko yaushe nayi wannan irin ɓaranɓarama haka. Irin wannan bama auntys ɗina na DANDALIN TSUTSAR NAMA kunya (🤣😂😜).......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ......Firgigit na dawo hankalina jin hannunsa a cikin jikina. Hannun na riƙe tare da marairaicewa na ce, “Please Yay... Uhmm uhmm M..y Ho..t” na faɗa kamar mai koyan magana ina ƙara cusa kaina cikin ƙirjinsa. Ina jin motsawar ƙirjinsa alamar yin murmushi. A zuciyata nace mugu ɗan masa. “You are my Hot too Aljannar duniyata. Faɗa min minene burin naki?”. Gaba ɗaya jinai tsigar jikina na tashi saboda yanda yake min magana a cikin kunne a wani kalar hankali. Ajiyar zuciya naja cikin dauriya da nuna juriya a hankali nima na ce, “Babban burina yanzu a duniya shine Ummie ta samu lafiya. Na biyu Yaya Musaddiq yay aure. Na uku ku daidaita kaida Yaya Fahad Please Yaya Awwab. Nasan ba son ranku bane. Amma kaine baba, kana amsa tamkar sunan uba ne a garemu baki ɗaya. Komi kake ji a ranka ka dinga daurewa dan ALLAH. Sannan ka yawaita ambaton sunan ALLAH da istigfari, salatin ANNABI da ambaton Hasbinallahu wa-ni'imal wakil akoda yaushe. In sha ALLAHU zamuyi nasara. Dan haɗuwar kanku shine tsanin samuwar lafiyar Ummie, idan ba hakaba zamu cigaba da zama a ƙarƙashin igiyar tufƙa da warwara ne. A yanzu haka mataki na farko da nake so ka fara ɗauka bayan canja mata doctors ɗin nan da kayi shine maidota nan sashen. Tunda samanka babu kowa a maidata can, ko kuma kai ka koma can ita ta zauna nan ƙasa idan zaifi mata sauƙi. Hakan zai bamu damar kulle kowacce irin ƙofar nasarar cimma buri daga duk mai mummunar manufa. Bani da wani buri a yanzu daya wuce tabbatuwar waɗan nan abubuwan guda uku wlhy”. Wani irin matseni yay a jikinsa har sai da na saki ƙaramar ƙara ya sassauta min. Yanda naji jikinsa na rawa yasa gabana faɗuwa. Da sauri na ɗago tare da yaye duvet ɗin. Hannunsa yake ƙoƙarin kaiwa saman kansa ga wani irin juyewa da idanunsa ke neman yi. Da masifar sauri na tashi zaune jikina na rawa. Gaba ɗaya bargon na yaye, na wani irin ɗaga kansa na maida saman jikina tare da fisgar gorar ruwa na ɓalle murfin. Ɗiba nayi cikin hannuna na shafa masa a fuska, sannan na saka masa kan baki hawaye na rige-rigen sakko min. Da ƙyar na samu ya sha kaɗan, banyi magana ba na fara karanto addu'oi ina tofa masa. Tamkar wani mai aljanu sai ya fara lafawa a hankali a hankali har barci ya ɗaukesa. Tagumi kawai nayi na zuba masa ido, nama rasa wane kalar tunani zanyi. Ina nan zaune shiru na fara jiyo kamar hayaniya da dukan ƙofa. Jinai gabana ya faɗi, a hankali na zame kansa a saman jikina na maida saman fillo tare da gyara masa bargon na sauka. Har nakai ƙofa na dawo, dan bathrobe ce a jikinmu daga ni har shi kasancewar daga swimming pool muke, sai ƙaramin towel da kaina ke naɗe a ciki. Sauri-sauri na canja zuwa doguwar riga na saka hijjab kawai na fito. Babu kowa a falon, daga waje ne ake hayaniyar. Buɗe ƙofar nayi na fita gaba ɗaya. Turus na tsaya jikina na rawa ina kallonsu. Fahad ne riƙe da wani shegen kaifaffen wuƙa irin na chinis ɗin nan da zakaga suna faɗa da shi a films, sai faman riƙesa ake yana rantsuwa sai ya kashe ɗan uwansa da hannunsa. Shi ya tsanesa, baya sonshi baya son ganinsa sai ya kashesa. Abinda yay matuƙar bani mamaki kaf ahalin gidan idan ka cire Paah da Uncle ɗin nan nasu kowa yana nan. Amma duk sunyi tsaitsaye Baba ne kawai mijin Mama Balki ke ƙoƙarin ma Fahad magana, sai Mama dake roƙonsa itama tana kuka. Sai kuma Hayatu da guards ɗin Maash dake rirriƙe da Fahad ɗin. Sai Hafizzullah da ban san ma yana gidan ba na ƙoƙarin amsar wuƙar a hannun Fahad ɗin cikin lallashi da dabaru. Ido muka haɗa da Hajiya ƙarama dake faman taɓe baki, da sauri ta wayance ta gyara fuskar tata takai hannu tana sharar hawaye ita a dole kukama take yi. Kaina na girgiza na maida kan Hajiya Mammah. Waya ce a hannunta yanayinta da alamar damuwa da gani akwai wanda take son kira ko kuma tanata kiran ba'a ɗaga ba. Na maida kan Maman Malika. Kanta a ƙasa tana hawaye. Sai su Azizat da Arwa da yanayinsu ya nuna yanzu ma suke shigowa gidan suma sunyi tsuru-tsuru a cikin yanayi mai wahalar fassara. Sai masu aiki da fuskokinsu ke nuna yanayi mabanbanta. Bahijja dake kuka sosai kamar zata shiɗe na zubama ido fiye da kowa, A'i na riƙe da ita itama tana sharɓan hawayen. Idanu na ɗan lumshe na buɗe ina mai sauke ajiyar zuciya.. Nayi alƙawarin bakina bazai taɓa furta ni matar Maash bace, sai dai in har shine da kansa ya sanar musu. Amma lokaci yayi da zan fara buga nawa acting ɗin nima a cikin wasan nan. Sai da na karanto addu'a tare da dawowa ainahin Sam-G ɗita da kowa ya sani. Cikin dakiya fuska a ɗaure da ɗan ɗaga murya kaɗan na ce, “Ku sake shi!”. A tare gaba ɗaya, da wanda suka ganni tun ɗazu, da wanda basu san da fitowata ba duk suka ɗago suna kallona da matuƙar nuna mamaki a fuskokinsu. Ganin basu da niyyar sakin nasa a kausashe na sake faɗin, “Ku sakesa nace ko”. Hayatu ne ya fara sakinsa a hankali, sai Hafizzullah dake min wani irin kallo idanunsa duka a waje. Bamma nuna na gansa ba ni sam, ganin Hayatu ya saki Fahad ɗin suma guards ɗin Maash duka sakesa, sai dai daka gansu kasan a tsorace suke. Hannayena na warware daga ƙirjina, kafin na shiga takawa a hankali na sakko a ɗan steps ɗin dake gaban ƙofar sashen nasa. Dai-dai nan Hajiya Mammah ta wani irin zaburo a masife da nunani da yatsa ta ce, “Kai! To ke kuma fa a waya kike wannan maganar a gadarance haka?”. Ko kallon inda take bayi ba, na cigaba da takawa har gaban Fahad dake wani irin huci da ƙarasa zaro wuƙar dake cikin kufenta dan dama bai gama cireta duka ba kasancewar Hafiz ya riƙe masa hannu. Saurin riƙeni Hajiya ƙarama tayi batare dana san sanda tama zo inda naken ba. Cikin girgiza kai ta furta, “No Please ƴammata. Zai iya jimiki ciwo baki ganin bashi da hankali”. Kaina na ɗan karkata na kalleta da ga sama har ƙasa cikin ɗage gira, sai kuma na ɗan girgiza kan nawa da gyara tsaiwata na ce, “Ayya ashe mahaukacine shima”. Daga haka na ɗauke kaina na maida ga Fahad dake ƙoƙarin gittamu. Babu alamar wasa a tattare da ni na ce, “Yaya Fahad!”. Cak ya tsaya kamar wanda ake sarrafawa da remote. Sam banyi zaton zai tsaya ɗin ba, kawai na gwada sa'ata ne ƙasan raina ina roƙon UBANGIJI akan ya hanani jin kunya. Dan haka tsayawar tasa ta sakani wani irin jin sanyi a raina, ban damu da kallon da Hajiya Mammah da Hajiya ƙarama kemun ba, kai dama kowa na wajen. Da baya na ɗan ja na koma gabansa. Ganin yanda yake hucin da cika da batsewa jikinsa na rawa ya sakani sakin murmushi. Batare da nayi magana ba na miƙa masa goran ruwan hannuna. Ƙin karɓa yayi, dan haka na sake sakin murmushin da raunana murya nace, “Haba dai Autan Ummie, ko sokake na saka rigima ban yarda na bar maka autancin ba. Dan dama fa haƙuri nayi kawai amma ina son autancina. Kasha kaji, muje mu duba Ummie na tabbatar tana matuƙar buƙatarmu a kusa da ita. Shiko Yaya Awwab da kaina zan maka maganinsa. Yau sai ya bar mana gidan nan dan bazamu zauna da shi yana sakaka fushi ba. Ina dalili ina ɗan mafari Yayana yafi gaban raini ai, ungo kasha kaji”. Na ƙare maganar ina ƙara miƙa masa ruwan da miƙa ɗayan hannuna kuma alamar ya bani wuƙar. Kamar mai shakkun yin hakan ya amshi ruwan ya bani wuƙar. Bamma san wani wawan ajiyar zuciya ya kufce min ba. Da ƙyar na danne hawayen da suka cika min ido ina satar kallonsa. Tuni ya ɓalle murfin goran ya kai bakinsa yana sha da irin salon da ɗan uwansa yake shan ruwa a wasu lokutan. Sai da ya shanye tas ya miƙomin roban. Amsa nayi ina murmushi da faɗin, yauwa yayana you are the best Yaya in my life. Oya let's go wajen Ummien mu kafin ƙuda ya rigamu”. A hankali ya saki murmushi. Muryarsa a ɗashe ya ce, “Kema you are the best ƙanwa in my life”. Ya ƙare maganar yana miƙa min hannunsa wai na kama. Kafaɗa na maƙe masa tare da girgiza kai. A hankali na furta, “Wanan hannun na sarki ne”. Alamu yay min na bai ji minace ba wai. Sai kawai na sakar masa murmushi da nuna masa hanya. Kafaɗa ya ɗan ɗage sama da taɓe baki... “Na shiga uku ni Nafisa. Wai mi nake shirin gani haka ne nikam? Ke kuma naki salon kenan kibi wa kibi ƙani. Jama'a karuwanci a cikin gida”. Kallonta na ɗan yi na kashe mata ido ɗaya. “Iyeeeh!! Dan ubanki ni kike ma wannan abun? Kin san ko matsayina a wannan gidan?”. “Ƴar cin arziƙi mana”. Na faɗa a hankali dai-dai zamu gittata. Wani bala'in zaburowa tai kaina tare da kai hannu zata fincikoni. Kamar walƙiya Fahad ya sha gabanta. Cikin nuna tsantsar fusata ya ce, “Mi zakiyi? Dukanta wai? Aiko da sai na datse wannan hannun naki ta yanda bazaki sake morarsa ba har abada Mammah”. Wani irin tsuruu Hajiya Mammah tayi tana kallonsa. Dan gaba ɗaya fuskar yayansa take gani akan tashi fuskar. Mamaki take wai yaushe ma yaron nan ya zama ƙwallon ɗan iska haka shima. Ko duk karuwancin yarinyar nan ne dai halan?........✍️ _Gaskiya dangin Sam-G kuna mata nasiha, rashin ji bashi da ƙyau Hajiya Mammah da Hajiya ƙarama sukanta ne fa🥱😝😂._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ......Ba Hajiya Mammah kawai ba, kowa dake wajen sai da mamaki ya nema kasheshi. Dan babu wanda bai saki baki ba. Sai ma Hayatu ne da abin ya bashi dariya. A zuciyarsa ya ce (pepper ƙanwar mu is back). A zahiri kam yana a layin ƴan kallo ne shima. Hafizzullah ma dai dariya yake ƙoƙarin dannewa, shima a ransa ya ke gulamar (Humm Adda ƙarfin halinki dabanne a rayuwa). Mama Balki ma dai mamaki take, a ƙasan ranta kuwa jin wani alfahari take yi, lallai yanzu ne in sha ALLAHU aikin su zai tafi dai-dai. Baba kansa murmushi yake a zuciyarsa, lallai ya sake tabbatar da yarinyar nan jinin Abdul-wahab ce, dan sam Abdul-wahab bai san wani abu tsoro ba a rayuwarsa. Shiyyasa ya ƙare rayuwarsa a bama ubangidansu da bazasu taɓa mantawa ba har abada garkuwa... A ɓangaren Hajiya ƙarama baki ta saki kawai, ga ƙafafunta na wani irin rawa. Mamakin yarinyar da tu'ajjibinta na neman halakata. Gaba ɗaya hoton mahaifinta ke dawo mata da abubuwan da suka dinga faruwa a tsakaninsu. Ta ɗayan gefen kuma shi kansa Fahad yau ya goge mata hadda tas. Dan gaba ɗaya ya juye Maash sak. (Yallaɓai muna cikin tashin hankali) ta faɗa a zuciyarta wata irin zufa na ketoma illahirin jikinta. A ɓangaren ma'aikatan gidan musamman su Bahijja kusan suma a sumen suke da mamakin Kandalar, duk da dama a cikin shock ɗin ganinta ma suke a gidan kasancewar sunji ƙus-ƙus ɗin da akeyi a gidan na wai Boss ɗin su ya mata fyaɗe. Duk da mafi yawansu basu yarda ba sudai, dan wani irin kima da mutuncin Maash suke gani a rayuwarsu saboda ya musu abubuwa da yawan gaske da suka rasa a gidajen iyayensu... 🩸🩸🩸🩸 Koda ya shiga ɗakin kai-kawo ya dinga yi tamkar mai safa da marwa kafin ya ɗauki waya ya danna kira. Kasancewar ba number Nigeria bace ya jima kafin ya samesa. Dan har ma ya fara tunanin komawa ta WhatsApp suyi video call, sai kuma akai sa'a ta shiga. Bugu biyu aka ɗaga, bai tsaya ko sauraren gaisuwar da yaron nasa ke masa da ga can ba ya wani daka masa tsawa. “Na baka awa ashirin da huɗu na ganka a gabana. Idan ba haka ba, wlhy! wlhy! Sai na saka an yo maka ɗaukar amarya da ga UK zuwa Nigeria. Wawa kawai, har ni zaka yaudara, ina baka ci da sha da ɗaukar buƙatunka ashe sakarai ka maidani wanda baima san abinda yake ba...” “Yallaɓai wlhy! Wlhy ba yanda kake zato bane. Ni kaina ina a cikin tashin hankali. Tun ɗazun na rasa ta yanda zan kiraka na sanar maka yaron nan ya gudu. Wlhy sai da aka tsara komai dan a yanzu haka akan yazo Dubai hutawa ne shida abokansa, kuma na sanar maka a ranar. Nima na sayi ticket ɗin tafiya Dubai ɗin kamar yanda kace ama jirgi ɗaya zamu wuce aka samu matsala a airport ɗin, na cigaba da ƙoƙarin ganin na samu next flight sai kawai na tsinta zancen wai Nigeria ya wuce da ga bakin abokin nasa. Nayi yunƙurin biyosan tun a jiya jami'an tsaro suka kamani ko awa ɗaya banyi da fitowa ba. Yanzu haka cikin ƙoƙarin ganin jirgin da zai tashi nan da awa ɗaya dani ne dan na fahimci komai an tsara shi ne har kamani da akayi set-up ne kawai. Amma dan ALLAH yallaɓai ka gafarceni. Ina nan tafe”. Kasa iya cewa da shi komai Baba prof yayi, sai ma wurga wayar da yay saman gado yay wani irin kaiwa zaune hannayensa duk biyu dafe da kansa dake wani kalar jujjuya masa kamar brain ɗinsa zata wulƙice. Ya jima a haka, sai da yaji bugun zuciyarsa na neman canjawa sannan ya kai kwance. Barci ya sha sosai, sai dai kafinma yayisa ya jima yana sambatun ambaton sunan Ibrahim Alonso da zuri'arsa. Sai da ƙyar barcin yay awan gaba da shi. Bai tashi farkawa ba sai yanzu kusan goma sha biyu na dare. Ya jima idanunsa akan agogon ɗakin nasa tamkar mai lissafa adadin daƙiƙun da suka rage a rayuwarsa, kafin ta miƙa zuwa bayi. A cikin ma ya kwashe lokaci kafin ya fito ya rama salloli sannan ya zura jallabiya ya fito falo. Tamkar fitowar tasa kuku ke jira, dan tuni ya fito ya jere masa kayan abinci a gabansa kasancewar yasan da dare baya hawa dining cin abinci. Duk yanda yake jin matsananciyar yunwa bai iya cin abincin ba ma, sai black tea ɗin nashi na fama ya buƙaci a kawo masa. Shine ya ɗan samu ya sha. Fitilar falon ya rage batare da kunna tv ba ya zauna shiru yana nazartar abubuwa yanda ya kamata. Dan ɗazun gaba ɗaya a birkice yake, shiyyasa hatta bayanin Commando bakwai komai ya gane ba. Dawowar nan ta Fahad ta matuƙar dagula lissafinsa. Sai batun yarinyar da bai taɓa sake maida hankali kanta a lissafinsa ba tun randa ta gitta tamkar walƙiya a tsakkiyar hadarin daya kankama zai zubda ruwa. File ɗin da commondo ya kawo masa ya sake ɗauka, ya shiga binsa daki-daki dan ɗazun kamar sama-sama ya duba shi. Sai da ya duba tsaff sannan ya fara lissafi. Tayi aure, an kaita gidan miji, har gidan da aka kaita commando yaje amma babu kowa sai maigadi. Ya binciki maigadi, amma bai samo komai ba, dan babu abinda ya sani face ogansa da yake kira da oga. Abinda ya kawo masa ruɗani a wannan gaɓar shine kwanan amaryar ogansa ɗaya a gidan ta gudu da safe, har tai yunƙurin fasa kansa idan bai buɗe mata ƙofa ba. A binciken Commando bata koma gidansu ba, amma tayi jiyya a wani pravet hospital. Ya bibiyi asibitin amma bai samu komai ba sai sunan likitar data kula da yarinyar tama kawota asibitin, a yanzu kuma bata asibitin wai, bincike iya bincike na commando kuma bai ganota ba ko inda take har yanzu balle ita yarinyar sai iya kawai an mata transfer zuwa Abuja. Abuja wane asibiti? Basu gano ba shima.. Kansa yay wani irin dafewa yana mai furzar da huci. Sai kuma ya jawo waya yay kiran Commondo. Bai tsaya amsa ko gaisuwarsa ba yace ya samesa gida. Kawai ya yanke kiran. Bako a cika mintuna talatin ciff ba sai ga amintaccensa yazo ya sanar masa Commando yazo yana falon baƙi. Hannu kawai ya ɗaga masa alamar yaje. Bayan ya wuce shima ya miƙe yabi hanyar da zata sadashi da falon baƙin tanan cikin falonsa. Da sauri commando dake zaune a kujera ya miƙe tsaye kansa a ƙasa domin girmamawa. Ba zamu kirashi yaro ba gaskiya. Dan shekaru kam zasu iya tasamma hamsin da wani abu. Sai dai yanayinsa ya nuna lallai a lokacin ƙuruciya anyi rashin ji sosai, a yanzun ma bai zama lallai an bari ba. Nuni Baba prof ya masa kan ya zauna. Babu musu ya kai zaune sannan ya sake gaidashi. Nan ma kansa kawai ya ɗaga masa sai kuma sukai shiru. Kusan minti ɗaya kafin baba prof ɗin ya ɗago yana sauke ajiyar numfashi. “Commando aikinka yayi ƙyau sosai, bance komai bane saboda rana a ɓace yake a ɗazun”. “Na sani boss, babu wani damuwa kayi komai ba komai girmanka ne”. Murmushi Baba prof yayi da gyara zamansa. Sai kuma ya ɗan furzar da numfashi. “Ya akai bincike bai ƙarasa inda nafi buƙata ba. Dan ina son sanin wanene mijin nata fiye da komai”. “Na sani boss, nima naso nakai har can ɗin amma komai ya datse kansa. Sai dai duk da haka bawai na dakata bane. Na kawo maka wannan ɗin ne saboda naga ka matsu. Amma akwai ƴan uwanta Maza guda biyu zan maida akalar aikina kansu, ai dole dai su san wanene ta aura? Sai shi wanda ya riƙeta shima yana cikin tsarina. Kar har walliyin auren da wahala ya tsira”. Murmushi mai faɗi Baba prof yayi, dan yanda yaron nasa ke wani magana a ciccije yana birgesa. Kansa ya jinjina da gyara zamansa. “Shiyyasa kake birgeni sosai, dan nasan in har zan damƙa aikina a hannunka banda wata matsala a kai. Yanzu ma inada wani aiki a ƙasa, yana da alaƙa kuma da wannan ɗin da kake yi”. “A to oga lafiya lau ne. Watso umarninka kawai a shirye nake na cafesa da hannu biyu”. “Ina godiya. Zan ɗan baka aikin kaɗan a buɗe yanda zakafi fahimtarsa. Ita yarinyar da kake wannan binciken a kanta yanzu haka tana a Maash Mansion ne”. Wani irin dalalo ido Commando yayi waje. Tare da dafe bakinsa ya ce, “Kan ubancan kai. Amma ta barni naketa walankeɗuwa kamar wani shaho. A to lallai tana buƙatar ɓalli-ɓalli a kan fuskarta kenan”. Murmushi Baba prof yayi kawai, tare da cigaba da faɗin, “Ai bamu zo nan ba Commando. Abinda nake son kamun a kanta biyu ne zuwa uku. Na farko ina son sanin mi tazo yi Maash Mansion. Na biyu ka tabbatar min da tanada alaƙa da Awwab ne tako wane irin fanni ko bata da? Na uku a cikin gidan tanada alaƙa da wani ne? Misalai, masu aiki, ko cikin masu gidan, ko masu huɗɗa da gidan ta waje. Na ƙarshe wanene ya shigo da ita Lagos dan a matsayin mai aiki take a Maash Mansion” “Oga duka aikinka masu sauƙine a garan kaima ka sani, sai dai magana ta ALLAH tsaurin a waje guda yake. Nifa kasan in dai sabga da Zakin gidan nan naka a ciki tsoronta nake gaskiyar magana. Ka sani na sani aljani ma nan ya ga Maash ya barsa. Dan duk iskancina na tsawon shekaru yaron nan yakan goge min hadda tsaff. Kaga dai Jaga, duk yanda na gatanta yaron nan daga turashi aiki jikinsa sai da yaron nan ya saɓemin ya koma bayansa. Badan munyi wuff mun ƙaddamar mas ba da yanzu ya buɗe mana aiki fa. Boss kasan da haka ta faru fa babu tantama China Maash zai kaimu a markaɗe namominmu da ranmu a ɗurisa a gwangwanaye a dawo dashi Nigeria a dinga sayarwa matsayin naman tsakkiyar shawarma. Kai kanka yanda nake ganin idanunsa zai iya sawa a masa bandarka...” “Commando!!”. Baba prof ya faɗa a fusace cikin daka masa matsanancinyar tsawa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ......“Kaiyya oga sa'a dai sa'a dai. Kafa san ni a ɓangaren gaskiya ba ruwana feɗewa nake filla-filla. Amma dai tunda baka son ji bari nayi kurumm. Zanje na fara aiki amma dai ka ƙara tunani akan Maash, Nima zanyi tunani muga. Matsalar shi ba mata yake bi ba, baya hawa network kuma, amma da komai yazo da sauƙi ai”. Gaba ɗaya Baba prof ya gamsu da bayanin Commando. Shi kansa shiyyasa yake a cikin ruɗani akan batun yarinyar nan da kuma abinda ya faru tsakanin Awwab ɗin da ita. Maash baya neman mata, shi shaida ne akan hakan. Sannan akwai wani dalilin da yasa baima kawo cewar shine ya aureta a ransa ba, dan yayi imani da shirinsa a kansa matuƙa. Shiyyasa ko fyaɗen nan har yanzu zuciyarsa bata gama yarda shine ya aikata ba. To amma abinda ya faru a asibiti fa? A gabansu fa yaron nan yay kissing yarinyar (Randa Maash ya samesu a asibiti, su a tunaninsu ma lokacin kissing ɗinta yayi🤣). Dan ɗauka bai wani ɗauketa da muhimmanci ba, hakama kulawa a asibitin, komai zai iya yi dan yana da tausayi. Kai gaba ɗaya shi yama rasa ina zai kama gaskiya.. Waya ya ɗauka har zai dannama Hajiya ƙarama kira sai kuma ya fasa. Saƙo ya tura mata ya kashe wayar tare da miƙewa ya fita. Amintaccensa ya kira suka fita a gidan duk da kuwa dare ne dan har ƙarfe ɗaya ma ta gota.... 🤍🌿🤍🌿🤍 Tunda na janyo ra'ayin Fahad muka nufi sashen Ummie ban sake bi takan ahalin gidan ba. Dan ko Hayatu da Hafiz anan suka samemu. Da yake muna a falon farko ne na shiga sashen sai muka baje munata hira abinmu harda Mama Balki. Kamar wasa abota ta ƙullu tsakanin Hafiz da Fahad duk da kuwa Fahad ya girmi Hafiz sosai. Dan koni ma ya girma balle shi. Da alama hakan ya faranta ran Hayatu, dan daga ƙarshe cayay su tashi suje yawo tunda yau boss na hutu. Har zasu fice na ma Hayatu magana. Duk da dai yanzu kunyar abinda na dinga masa nake ji, amma dai na daure na ce, “Yaya Hayat dan ALLAH idan babu damuwa kuma oganka bazaiyi faɗa ba mizai hana a sayo kayan amfani na kitchen ɗin sashensa naga wanda suke ciki basu da wani yawa. Tare da kayan abinci sai na dinga mana girki acan. Naga sam bai damu da abinci ba sai kayan chocolate. Sannan ita kanta Ummie ya kamata ace nike mata abinci hidimar nama Mama Balki yawa. Ga kuma Fahad ma ya ƙaru”. Sosai fuskarsa ta ƙawatu da murmushi. Ya ce, “Wannan shawara ce mai ƙyai Auntynmu. Kuma naji daɗi kamar yanda nasan Boss zaiji daɗi fiye ma da yanda naji ɗin. In sha ALLAHU ki bamu nan zuwa anjima duk abinda kike buƙata za'a kawoshi. Yanzu hakama zanyi waya da companyn da zasu zo su gyara kitchen ɗin su saka komai daya dace, kafin su gama mu kuma mun haɗo cefanen”. “Nagode sosai Yaya Hayat”. “Muke da godiya Auntynmu. Koba komai kwanan nan Yayanmu zaiyi kaurin wuya da tunbi”. Dariya sosai zancensa ya bani, amma sai na murmusa kawai. Shima fita yay yana murmushin dan su Fahad tuni sun fice abinsu... Kamar ko yanda ya faɗa ɗin haka ce ta faru. Dan na fita zuwa yin sallar la'asar daga nan na dubasu na samu drivern sa (TJ) da Guard ɗinsa da nake yawan ganinsu tare shima (Shu'aibu) tare da baƙi. Gaisheni sukai TJ ɗin ya bani waya. Jin Muryar Hayatu ya sani sauke ajiyar zuciya, shine yamun bayanin na basu damar shiga tare da masu company da zasuyi aiki. Duk da nayi mamaki ganin yammafa tayi yaushe har za'a kammala? Sai ban musa ba na basu dama ni kuma na shige ciki domin duba shi. Da sallama na shiga ɗakin kamar mai jin tsoro, ganinsa tsaye gaban mirror yana fesa turare ya sani jin farin ciki. Ɗan kallonsa nayi na ɗauke kaina. Dan fesa turarensa yake kamar ma bai san da shigowata ba. Wannan halin nasa na shariya da ɗaukar kai na ban mamaki. Jinai kamar na watsar da shi nima na wuce abina. Amma sai na daure tunda koba komai na barsa babu lafiya. Muryata can ƙasa batare dana sake kallonsa ba na ce, “Ashe ka tashi, yaya jikin?”. Nai ƙoƙarin wucewa abina. Har na gittashi naji ba'a amsa min ba, sai na tsaya cak, dan magana ta ALLAH ban san wulaƙanci sam. Cikin ɗan yanayin jin haushi na ɗago manyan idanuna na kallesa. A mamakina sai na samu shima ni ya zubama ido. Dan ya daina fesa turaren ma ya jingina da mirror kawai yana kallona. Baki na tura masa tare da juyawa zan cigaba da tafiyata caraf aka cafke hannuna. Ƙin juyawa nai na kallesa. Sai dai ban ƙwace hannuna ba daga riƙon da yay min. Munfi sakan goma a haka shi bai sakeni ba shi baice komai ba. Jinai wani takaici ya sake kume mun zuciya, sai nai ƙoƙarin jan hannun nawa. Sake riƙeni yay da ƙyau, tare da matsoni jikinsa ya juyoni gaba ɗaya na muna fuskantar juna. Ban yarda na kallesa ba, ban kuma ce da shi komai ba. Sai kawai ya ƙarasa jawoni jikin nasa ya rungume. A kusan tare ni da shi muka saki ajiyar zukata, kafin ya dagoni fuskata a cikin tafukan hannunsa duka biyu. “Yau ba magana ne?”. Ya faɗa da soft murya kuma can ƙasa da ni kaina dan yana a kusa dani ne na jisa. Ban kallensan ba, ban kuma ce komai ba sai kafaɗa dana maƙe masa. “Oh! Why?”. Sai da na ɗan murguɗa baki sannan nace, “Ai kaima baka yi ba”. “Uhhmyim. Dan banyi ba sai kema ba zakiyi ba?”. Kaina na jinjina masa alamar eh. “Humm Aku na ta zama kurma kenan yau?”. “Ni dai ba Aku bane”. “To miye? Banan kike cika mana kunni da surutu ba ke a dole ƴar jarida”. Farr nai da idanuna, tare da ɗan jujjuyasu, sannan na ɗan murguɗa baki na ce, “Kaima ai shaida ne tunda na karya maka record. Ko nayi ƙarya”. Na ƙare maganar ina waro masa idanuna sosai. Maimakon ya tanka sai kawai ya saki murmushi, tare da kissing idanun nawa. Kunya ce ta kamani kuma. Dan haka nayi yunƙurin kwace fuskata amma yaƙi barina. Dole na haƙura amma na rufe idanuna naƙi yarda na sake kallonsa. Sai dai kuma shi ina cigaba da jin tasirin idanunsa a kaina sosai. Ganin bashi da niyyar barina a shagwaɓe na ce, “Gashi can za'a shiga salla fa”. Tamkar wanda na dawo a hayyacinsa ya furzar da wani irin nannauyan numfashi. Sai kuma ya saki mun fuska a hankali. Jin kamar ba hanyar fita yayi ba na buɗe idanuna. Sai na hangosa zai shige bathroom. Mamaki hakan ya bani, sai dai bance komai ba na tsaya a wajen, babu jimawa kuwa sai gashi ya fito da alama alwala ya ɗauro. Har ya gittani zai wuce sai kuma ya ɗan dawo baya. Dawowar tasa ya sani ɗagowa na kallesa. Dai-dai da ya kawo fuskarsa gab da tawa, dan haka a bazata naji saukar sumba a saman goshina. Kafin ma nayi wani yunƙuri ya fice a binsa. Bamma san sanda na saki murmushi ba da kai hannu na shafi lips ɗina da goshina a hankali. Kasan raina kuma ina dariyar al'awar da ya sake, wato mutumin nan ja... Humm bari dai nayi shiru kada danginsa su min ca.. (Kin taimaki kanki kuwa, dan ba barinki zamuyi ba😎😌.) Fitowarsa ya saka su TJ masu jagorantar companyn nan dake shigo da kwalayen kayan aikinsu rissinawa suna gaishesa. Kallonsu kawai yake batare daya amsa musu ba. Dan haka Shu'aibu ya fara masa bayanin cewa Hayatu ne ya turo companyn ya kuma kira su akan su sami Aunty ta basu izinin shiga da kayan. Shine yanzu da zata shiga suka sanar mata ta basu izini.. maimakon ya amsa musu bayanin da sukai masan sai ya ɗauke kai tamkar ma bai ji bayanin ba. Takunsa ya cigaba dayi cike da bajinta da mazantaka. Sai da yaje gaf da fita a daƙilen nan nasa ya furta, “Ina fatan dai kunyi salla? Su kuma aikinsu ya koma ta back door”. Daga haka ya ficewarsa. Sanin basuyin ba ya sasu ajiye aiki suka bar wanda ba musulmai ba. Amma kamar yanda yay umarnin komawarsu ta back door sai suka kulle ƙofar tanan nan falo suka koma ta can ƙofar baya ta kitchen ɗin..... ❤️‍🔥❤️‍🔥💦❤️‍🔥❤️‍🔥 Jigatuwa iya jigatuwa Baby tayi, dan bata tashi farkawa ba sai a hannu Doctors. Su kansu likitocin ma firgitata sukayi. Dan daga ganinsu kaga irin manyan gawurtattun ƴan iskan turawan nan da akafi gani a cikin films matsayin criminals. Illahirin jikinsu ne tattoo baƙi da jaa. Ga wasu irin yan iskan abubuwa kamar stones sun manna a fuska harda haƙora babu ƙyan gani. Sun kuma irin zama ɓarka-ɓarka ɗin nan saboda workout. Idanunsu kam harda kwalli ga ƴan kunne. Kai tako ina dai basu da ƙyan gani. Tana ji tana gani sukai treatment ɗinta. Ba wannan ya tada mata hankali kawai ba. Sai da nishi ya isheta ta waiga ta gefenta kasancewar ko iya zama batayi sai kwance rigingine sai kawai tayi tozali da mijin nata na aikata irin abinda ya aikata da ita da ɗaya daga cikin yan iskan dake a kanta matsayin likitoci. Wani irin uhun tashin hankali ta saki. Sai dai a mamakinta ko'a jikinsu kamarma basu jita ba harkokin gabansu suke, sai wasunsu ne ma da suka kwashe da dariya. Haka ta dinga musu ihun kuka tana zaginsu da Hausa da turanci, tare da tsine musu ta uwa ta uba tana kiransu ƴan wuta. Oho ita tama san mi take faɗa, dan hatta turancin nata babu alamar suna ganewa. (A Nigeria kuma sune wayayyu ma'iya turanci😝🤣). Haka sukai kunnen uwar shegu da ita har suka gama hidimarsu sannan suka fice suka barta a ɗakin ita kaɗai sai mijin nata daya shiga wanka shi da ƙaton da suka gama aikata alfasha. Tana nan tana cigaba da cin kukanta suka fito riƙe da juna kamar wasu mata da miji. Sai kawai taji numfashinta ma na neman ɗaukewa. Dan duk iskancinta da ƙarancin rashin ilimi tasan wannan aiki ya ƙazanta........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚_ .......Wato jama'a kuɗi! Kuɗi! Kuɗi!! Humm dole ma musha wahala akan kuɗi wlhy. Yo duk in kana son abu a rayuwarnan a yi maka shi tamkar ƙyaftawar idanu tofa lallai sai da kuɗi. Shiyyasa gasu nan sun zame mana masifar rayuwa. Talaka da baida su yafi kowa shan wahalar rayuwar. Karna dai cikaku da surutu. Ba komai ya sani muku sambatun nan ba sai da na fito ganin kitchen ɗin da aka shirya cikin abinda bai gaza awa uku ba. Tsaff an gama shirya duk wani abinda za'a buƙata a cikinsa kalar kitchen cabinet ɗin. Tuni ya canja kamar bashi ba a ɗazun tsurarsa sai cabinet. Ban sake tsinkewa ba sai da na shiga cikin store naga yanda aka ajiye wasu extra kayan aikin iri daban-daban. “Tab ɗin, ALLAH dai ya gafarta mana to. Ya bama kowa halalinsa ya kuma bamu tsahon ran mora da neman lahirarmu a cikin duniyarmu”. Na fito inata ƙara jinjina al'amarin na sameshi a falon da alama shigowarsa kenan. Dan tun fita massalaci sallar la'asar bai dawo ba sai yanzu da ake shirin gab da magriba. Cike da ɗauki na ƙarasa inda yake na zauna ta kujerar gefen. Duk da kunyar yanda ya wani zuba min idanunsa nake yi haka na fuske abina. “Hummm Yaa Awwab kaga kuwa yanda suka maida kitchen ɗin nan? Tab ɗin jan aljannar duniya. ALLAH yanda kasan mutum ya koma can ya saka gado kawai ace canne ɗakinsa. Gaskiya mutanen nan sun iya aiki tabb”. “Shi kuma wannan bakin ya iya surutu”. Ya faɗa yana wani lumshe idanu da buɗewa tamkar wanda ya sha yay marisa. Ɓata fuska nayi tare da tunzura bakin na ce, “Namayi fushi, dama ka samu nake baka labari ko”. Na tashi fuuu zan gudu. Ji nai kawai an fisgoni, sai gani daɓar a saman cinyarsa. Ƙoƙarin ƙwace kaina na shiga yi ina kukan taɓara da faɗin, “Ni ka barni babu ruwana da kai. Kowa yay sabgarsa, ni wajen Ummiena ma zan koma”. Tsam ya matseni a jikinsa yana mai cusa fuskarsa a gefen wuyana. Yayinda numfashinsa ke shiga cikin kunnena da sautin dan murmushinsa. Ban fasa yunƙurin sauka a jikin nasa ba har sai da ya ɗan cizar min kunne, gaba ɗayana na naɗe masa jiki tare da sakin ƴar ƙara, a shagwaɓe na ce, “Wayyo Ummie King zai cire min kunni. ALLAH ni bazan yarda ba sai na rama cizona”. Na faɗa ina mai hayewa jikin nasa gaba ɗaya nima na shiga kokawar laluben kunnensa ni a dole saina ciza.. “Oh my god, yarinyar nan baki son zaman lafiya sam”. Ya faɗa kamar zai saki kuka yana kare kunnensa duka biyu da hannayensa. Oho bamma nuna na jisa ba, na shiga cigaba da ƙoƙarin zame hannunsa da hannu ɗaya, ɗayan na kaisa gefen cikinsa ina mintsina. Hannunsa ɗaya dake a saman kunnen ya cire yana ƙoƙarin buge nawa dake mintsininsa. Ai ko sai na samu caraf na cafke kunnen. Kaɗan na ciza amma mutumin nan ya wani saki ƴar ƙara da faɗin, “Ouchhh! Ummie kunnina, tiger ta ciresa”. Sosai na ƙyalkyale da dariya. Na yunƙura zan gudu ina faɗin, “Sai tsoro ga jan faɗa”. Caraf ya riƙoni yana ɓata fuska. Marairaice tawa fuskar nayi kamar zanyi kuka na ce, “Ayya Yaa Awwab ayya!. Nifa ƴar ƙararrama ce kar kace zaka rama”. Harara ya zuba min yana sake ɓata fuska da murza kunnensa da hannu alamar har yanzu yana masa zafi ko kuma shagwaɓa ce ta motsa abinka da Ajebota. Ganin yanda ya zuba min idanunsan nan na maguna kamar zai cinyeni da su, ga fuskarsa babu alamar fara'a ya sani sake narairaicewa. “Na tub...” “Shii!!!” ya katseni yana sake ƙanƙance idanun da shanyesu kamar mai jin barci. Sai kuma ya ɗan yamutse fuskar da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Sai fa na rama”. “Mi ɗin?”. Na faɗa cikin waro idanuna. Hararata ya ɗan yi, da sake matso da fuskata gab da tashi, sosai na sake waro idanun da marairaice fuska zanyi magana a hankali ya wani irin sauke small pinkish lips ɗinsa a kan nawa. A salon daya cafka lips ɗin nawa yasa bamma san na ƙanƙamesa ba..... “Yau na shiga uku! Mizan gani haka ni Nafisatu Adams”. A bazata muka ji saukar muryar Hajiya Mammah a saman kammu. Kici-kicin ƙwace kaina na shiga yi duk da shi bashi da niyyar yin hakan kuma sarai yaji abinda naji. Amma bawan ALLAHn nan sai ya wani sake matseni da komawa wani irin salo na taƙadarin namiji da sam babu ɓarɓashin kunya tattare da idanunsa. Ina jin ta sake saka salati har muryarta na rawa... Ba muryar Hajiya Mammah ba hatta jikinta rawa yake yi. Ba komai ya firgitata ba sai ganin ko kallo bata ishi Maash ɗin ba ma. Sai ma wani sabon salan iskanci da yake yi a jikin Samraah ɗin. Duk da iskancin ɗan iska akwai a inda idan akai wani iskancin shi da kansa kunyar kansa da kansa yake. Dan haka Hajiya Mammah taga abinda zai tsiyayar mata da idanun ganinta batama san lokacin da tai wufff ta fice waje ba jikinta na ɓari, mamaki ma take wai yaushe Maash ɗin yay irin wannan fitsarewar ne? Dama yaron nan bayan iya wulaƙanci da raini ma mutane tantirin ɗan hau ne?. Ai ko baiji kumyar kansa ba ya tuna ita ɗin yayar ubansa take fa... Fuuu-fuuuu take wucewa kamar wadda ake controlling da remote. Ko kallon masu gaisheta batayi ta afka ɗakinta ta kulle kanta. Jingina tayi da murfin ƙofar tana sauke numfashi a gwagwgwame. Ita wannan yaron zaima tantiranci haka? Daga ta nuna masa hanya shike nan abu na neman zama bala'i. Tayi barazana wa hukuma amma ko'a jikinsa ma. Hasalima sai ya bita yana gasa mata magana. (Yi baga yarinyar ba ma ɗazun ta gasa miki) wani sashi na zuciyarta ya ayyana mata. Tab ɗin jan, babbar magana ɗan sanda yaga gawar soja. Shin ko dai bayan abin farko ya faru yaron nan zuwa yay ya zagaye aka ɗaura masa aure da yarinyar nan? Yo inba auren ba taya za'ai ma wai a dinga wannan kwamacalar ne haka. Ko ƴar iskar yarinyar nan dai dama ta saba da harkar nan ita ke ƙara kanainayesa. Ko kuma ta masa barazana idan bai cigaba da mata ba zata tona shi. Kai yafa kamata su dawo cikin hankalinsu... Laluben waya ta shiga yi, cikin Sa'a kuwa ta samota a aljihun doguwar rigarta. Har rawa jikinta yake wajen son kiran Baba prof. Sai dai har ta yanke ba'a ɗaga ba. Kiran ta sake yi nan ma shiru. Sai kawai ta tura masa saƙo tasan dai idan ya gani zai kirata. Daga haka taja ƙafafunta da ƙyar zuwa kan sofa ta zauna ta zabga tagumi. Iskancin Maash na mata kai-kawo a cikin idanu da ba shegiyar yarinyar nan mai kama da afiruwa..... 🌿✨🌿✨🌿 Ram jami'an tsaron Dubai sukayi da Mansoor batare da bashi damar yin wata magana ba wai sai a office. Duk yanda yake son kare kansa da tabbatar musu gaskiyar al'amari sunƙi saurarensa. Sai ma tabbatar masa da sukai duk da abinda ya faɗa shine zai zama hujja garesa a wajen alƙali a court. Yana ji yana gani kuwa suka sakayashi a cikin cell cikin manyan criminals.. Abin kamar wani wasa sai gashi kusan sati uku shi ba'a kaisa court ɗin ba, ba kuma a yarda an samar masa da lawyer ba. Sun kuma hanashi neman kowa a waya dan dama sun amshe tasa a hannunsu. Sannan ko buga wayar cikin station da suke da ita sun hanashi wannan damar. Ganin tun komai zai iya zama labari amma ya gagara zaman ya fara tada ma Mansoor hankalinsa. Ance duk wanda yabar gida gida zai barsa, to lallai hakance ta fara faruwa da al'amarin sa. Dan kuwa gadai shi cikin masifar rayuwa da yake kallonta ba komai ba a farko amma rashin wani nashi da zai san halin da yake ciki na neman dulmiya rayuwarsa a masifar da babu wanda yasan iya ina zata tsaya kuma. Iyaye ba wasa ba, ko da ɗan iska zaka zama idan da albarkar iyaye wlhy kafin cin ribar iskancin (🤷idan har masuyi na ganin akwai ribar a ciki fa kenan. Dan kar ace Bilyn Abdull tace iskancin akwai riba da albarkar iyaye bance ba😂😵). A ranar cikarsa wata guda suka fara kaisa kotu, musawar da yay a zama na farko da dagewa akan shi bai aikata abinda ake tuhumarsa da shi ba yasa aka ɗage Shari'a aka miƙashi ajiya prison. Cikin amincin UBANGIJI a wannan zama wata baiwar ALLAH ƴar Nigeria taci karo da shiri'ar. Haka kawai tun a ganin Mansoor ɗin ta fahimci lallai akwai lauje cikin naɗi, sannan kishin juna na baƙin fatar da kasancewarsa ɗan ƙasarta ya sata shiga da fita har sai da ta samu damar ganinsa a prison ɗin bayan kwana biyar. Da yake akwai ilimi sai da ta samu nasarar yin hakan..... 💞⭐💞⭐💞 Duk yanda naso kuɓuta daga hannunsa a wannan gaɓar bai bani wannan damar ba sam. Sosai hankalina ya tashi da tsoron kar wani ya sake shigowa ya samemu a wannan halin kamar yanda Hajiya Mammah ɗin tayi. Amma bawan ALLAHn nan ko'a kwalar rigarsa bidirinsa yake yi. Sai da yayi yanda yake so sanan ya barni tare da rungumeni tsam-tsam a jikinsa. Duk da nima riƙen nake da shi fatana ya sakeni na sauka a jikin nasa. Amma bashi da niyyar hakan. Da ƙyar nayi ƙarfin halin fisgo furucin dake bakina na furta, “Yaya Hajiya Mammah fa”. Ya jima shiru babu alamar yama ji mina faɗa, dan har na fidda rai da samun amsa ko samun damar barina sai naji a hankali ya fara sassauta min riƙon. Sai da na fara murnar zan samu dama na tashi sai naji muryarsa da tai matuƙar shaƙewa can ƙasan maƙoshi a cikin kunnena. “Waye ita?”. Tsabar mamakin mutumin nan bamma san na manta da wata aba kunya ba na ɗago manyan idanuna da suka gama shigewa ciki suka canja launi na zuba masa. Cikin suɓutar baki na ce, “Hajiya Mammah ɗin?”. Fuskarsa a yamutse ya ɗaga min kai alamar eh. (Mutumin nan zai kasheni da halinsa) na faɗa a zuciyata ina mai ƙura masa ido. A zahiri kam sai na yunƙura kawai zan sauka daga jikinsa. Amma sai ya hana hakan, sai ma a ɗan kausashe da daƙilalliyar muryar nan tasa da ke fita so silent ya furta, “Idan kika tashi ALLAH sai na ɗauke ki naje da ke har cikin ɗakin barcinta na miki abinda yafi wanda ta gani ɗin. Idan kuma baki yarda ba bissmillah”. Sosai na saki baki da hanci da idanu dama gangar jiki duka ina kallonsa uwa wata saƙago. Yako wani kashe min ido ɗaya da shegen salonsa na manyan shegun yara da suka gogu da sanin duniya. Ni sai ma abin ya bani kunya. Tuni na rissinar da kaina a cikin ƙirjinsa kawai dan banda abin cewa kuma. Shima kawai sai ya sake rungumeni tsaff. Tare da furta, “Shiyyasa nace miki you are tiger”. “Ni ba damisa bace, kai ne dai Zaki da baya banbance na gida dana waje”. Na faɗa cikin ƙunƙuni ina sake cusa kaina jikinsa hannayena duka biyu zagaye da shi. Ina jin alamun murmushinsa, nima sai na ɗan murmusa kaɗan. Dan a duk sanda yay murmushi wani irin nishaɗi nake ji a raina nima........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 .......Kamar ko yanda Hayatu yay alƙawari bayan sallar isha'i sai gasu niƙi-niƙi da kaya shi da Fahad da Hafizzullah. Lokacin shi ogan baima dawo massalaci ba. Da yake ina falo a lokacin sakamakon jini dana gani, dama dai ina ɗan jin alamunsa hakan tun safe. Alhamdullah tun maganin da yasa aka bani lokacin da yay kidnapping ɗin nan nawa bana azababben ciwon marar nan, sai kuma a wannan karon nafi samun sauƙi fiye da ko yaushe. Dan duk da na rage yin mai zafi idan lokaci yayi musamman randa zai zo nakanji ciwon. Amma yau alamarsa kawai naji sai ɗan karen ƙwaɗayi dake damuna, ashe zancen Ruƙayya gaskiyane data taɓa faɗa min idan kayi aure kakan daina duka. Kasancewar ta ƙofar baya ma'aikatan gidan ke shiga da kayayyakin yasa ban tashi a falon ba. Nayi mamakin yanda Fahad ya sake daya shigo. Dan zama sukai rashe-rashe suna bani labarin wuyar da suka ciwo. Niko ina musu sannu da kumshe dariya. A ɗan abinda na fahimta game da matsalar sa da ɗan uwansa a yanzun nan shine waje ɗaya ne kawai basa iya zama. Idan kuma har ɗaya na waje koda basa ganin juna suna jin zafin kansu. Amma idan babu ɗaya normal ne. Dan gashi dai Fahad kamar bashi ba anan duk da kuwa yasan a sashen wa yake. Munfi awa guda da shigowarsu dan har inata mamakin a ina ya tsaya shi tunda anyi salla dai tuni sai gashi ya shigo Hayatu biye da shi. Kamar amma Fahad allura zaram ya tashi tsaye. Tuni kuma murmushin dake fuskarsa ya ɓace ɓat. Hannun Hafizzullah ya kama da faɗin, “Dude lat's go”. Kallonsa Hafizzullah yay zaiyi magana na girgiza masa kai. Sai kawai ya miƙe ɗin. Amma sai da ya gaida Maash da shima yay wani irin masifar kicin-kicin da fuska cikin girmamawa. Kai kawai ya ɗaga masa alamar amsawa, kafin ma ya fahimci a yanda ya amsa masan har Fahad ɗin ya ja hannun nasa sun fice. A hankali na sauke ajiyar zuciya, sai nima na miƙe jiki a sanyaye ina masa sannu da zuwa. Nima ɗin kai kawai ya jinjina min yana kaiwa cikin kujera. Ban damu ba na sake ma Hayatu sannu tare da godiya sannan na wuce ɗaki. Banfi mintuna goma da shigar ba ina ƙoƙarin canja channel a tv sai gashi ya shigo. Kallo ɗaya na masa na ɗauke kaina. Shiko ma bana zaton ya kallan ɗin. Sai da ya gittani na ɗan bisa da kallon ƙasan ido. Mutum dai gashi nan sundum-sundum😎 kamar wani kurma. Kai ina zan iya ƙuntata kaina haka. Duk da nima sai naso dai nake magana amma nashi yayi yawa wlhy. Shifa a rana zaka ma iya lissafa furucin bakinsa tsaff..... “Oya zo nan”. Silent muryansa ya katse min tunani. Ɗagowa nai na kallesa. Ganinsa tsaye tacan bakin closet ya canja kaya yasa na miƙe ina ajiye remote ɗin hannuna. Koda na karasa garesan bai yi magana ba ya dai kama hannuna muka shige ciki. Babu wani bayani ya hau zame min kayan jikina. Koda na kallesa zanyi magana sai ya girgiza min kansa yana wani lumshe ido. A zuciyata na fassara abin nasa da (bansan surutu. Koba haka ɗan uwan naku ke faɗa ba Bliy😎?). Oho shi dai bai fasa abinda yake ba. Ga kunya kamar na nutse. A bazata matuƙar bazata naji kawai a cikin kunnena ya furta, “Time for Menstrual pain ba”. Da sauri na ɗago cikin waro idanun waje sai ya wani ɗage min gira. Cike da salon iya shege ya furta, “Duk zufan nan da nasha ashe ban farauto baby ba. Ba komai thanks you my ALLAH. Ina addu'a da roƙon samun little Ummu-Hidaya a next”. Gaba ɗaya jina nai a rikice. Dan haka nai ƙoƙarin janye jikina a nasa, amma sai naci karo da kunyar da tafi ta farko dan babu kaya a jikina. Sai kawai na sake komawa na ƙanƙamesa. Yunƙurin murmushinsa kawai naji a ƙirji, amma ina da tabbacin a zahiri babu alamarsa a kan fuskarsa. Bai sake cewa komai ba shima sai ƙoƙarin saka min wasu kayan da ban san daga ina ya samosu ba. Wani shegen ƙyaƙyƙyawan abaya ne mai azabar ƙyau milk da kwalliyan golden a jikinsa. Ƙamshin ma da take kawai abin ɗaukar hankali ne. Kasa haƙuri nayi sai da na kallesa fuskata da murmushi na ce, “Woow Yaya ina ka samo a bayar nan ta haɗu wlhy”. Banyi tunanin zai amsa min ma, amma sai kawai ya ɗan ranƙwafo ya lakace min hanci kaɗan, cikin raɗa-raɗa ya ce, “Ƙanwata BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING mana. Indai kina son Abayoyi ƴan yayi da fidda kwalliyar kece raini jeki can kawai My Tiger, har masu sari suna kawoma kaya tun daga ƙasar Egypt akan farashi mai sauƙi da kai ma zaka sayar ka samu taka riban 09032345899”. “Woow, gaskiya madalla da Bilyn Abdull online shopping da ya sauƙaƙa mana wahal halun neman abayoyi muna a gidajenmu kwance. Jiba dai yanda rigar nan ke wani wal-wal na fito kamar jinin sarauniya Aminar zazzau.” A hankali ya saki murmushi da kanne ido ɗaya ya ce, “Bilyn Abdull online shopping ai duniya ne”. Jikinsa na faɗa na rungumesa. Na ce, “Tabbas na shaida hakan”..... Koda muka kammala shiryawa tsaff hannunsa riƙe da nawa muka fito. Babu abinda kake ji sai mayataccen ƙamshin turarensa. Dan ni kam sam ba'a jin nawa. Da kansa ya kulle ƙofar ya saka mata security. Ko'ina na gidan akwai haske sai kace a turai. Kasancewar ba dare ne yay ba tako ina ma'aikatan da basa barcin wuri nata kai kawo. Sosai nake jin kunyar yanda ya riƙe hannuna ram kamar zan gudu masa. Suko duk wanda ya mana kallo ɗaya baya sakewa sai yay ƙasa da kansa yana gaishe mu kawai. Muna gab da isa parking space mukaci karo da Hajiya ƙarama dake fitowa a mota. Da alama shigowarta gidan kenan dai itama. Yanda ta ke kallonmu kamar wata gunki ya sani ɗan risinawa na gaisheta. Lips ɗinta na rawa ta amsa min. Shiko gogan ko kallon inda take banga yayi ba muka gittata muka wuce. A gaban wata motar dake rufe da tempol muka isa. Sai ga TJ kuwa da ɗan gudinsa ya iso. Yaye tempol ɗin yay. Wata arniyar farar dunƙulalliyar mota da ban san yaya zan siffanta muku ƙyawunta ku gane ba. Gashi naci kai ban san sunayen motoci ba. (Su o'e ƴar uwarku bata san mota ba fa😝) ta bayyana. Kasa daurewa nayi sai da nace, “Woow” a hankali ina sake damƙe hannunsa dake riƙe da nawa. TJ na gama yaye tempol ɗin yabar wajen, ɗan kallonsa nayi, dai-dai da ya ciro key ɗin motar ya ɗan ɗaga min shi sai tin fuskata. Murmushi na sakar masa har haƙwarana na bayyana. Dan na fahimci dai da kansa zai yi driving ɗin kenan abinda ban taɓa gani ba. Hannuna kuwa ya ja har gaban motar yana mai danna key ɗin tai ƴar ƙara. Sai ko ga murafanta sun wani shiga ɗagewa sama kamar fukafukai. Tofa yau naga jalalar rayuwa. Mota dai dana sani buɗe mata murfi ake kamar ƙofar ɗaki. Amma wannan al'amari haka tab ɗin. Ina kallon yana murmushi, nasan kuma bai wuce yanda yaga na saki baki ba ina zuba ƙauyanci. Da kansa ya sakani a motar, sannan ya zagaya ɗaya side ɗin ya zauna. Wani abu ya danna a hankali murafan suka shiga komawa yanda suke. Wani irin ƙamshin motar da sanyin ac daya kunna suka fara ratsani. Juyowa yay ya kallan cikin wani irin shanye cat eyes ɗinsa. “Are you like it?”. Yanda yay maganar cikin motsa lips ɗinsa a wani kalar hankali yasa tsigar jikina tashi, nima a hankali idanun nawa a cikin nasa na furta, “Fiye ma da yanda kake tunani Yaya”. “I'm not your Yaya, change this name for me. I no like it”. Fuska na ɗan shagwaɓe kamar zan yi kuka nace, “Yaya Musaddiq ƙaninka, Aunty Falaq ƙanwarka. Hafizzullah ƙanwar ka. Hayatu ƙaninka, Fahad ƙaninaka, sai ni ce kaɗai za'a ware a dangi. To ALLAH ma nayi yaji da ga yau zan koma wajen Ummiena”. Na ɗauke kaina. “Ai nasan bama zaki iya ba, yin nesa da ɗan santalelen mijin nan naki tab. Asibiti mafa matsawa kikai a sallameki dan ki dawo kusa da ni”. Da wani masifar sauri na juyi na kallesa. Ya wani tsatstsareni da idanu hannayensa harɗe a ƙirjinsa, sai wani ƙara shanye idanun yake ƙasa-ƙasa. Kafin ma nace wani abu, a saman lips ya furta, “Ki rantse ba haka bane Kandala”. “Ni ALLAH bance ba. Kuma ni ba Kandala ba, in ba haka ba ALLAH kaima Yaya to”. Karan farko naga yayi murmushi mai wahalar gani akan fuskarsa. Dan haƙoransa har sai da suka bayyana. Ya dunguremin kai da faɗin, “Kema Yaya to”. Dariya na ƙyalƙyale da ita. Shima sai ya wani shafa kansa yana mai ma motar key. Sosai mamaki ya kamani ganin har lokacin Hajiya ƙarama na tsaye a inda muka barta ɗazun idonta a kammu. Kaina na ɗauke abina kawai har lokacin fuskata da murmushi. Yanda yake juya steering cike da gwaninta ya sani kasa haƙuri sai da na furta, “Dama ka iya mota amma kullum ake tuƙaka”. Baice komai ba sai ɗan murmushi kawai ya cigaba da tuƙinsa. Nima sai nayi shiru kawai na sake maida hankalina a kallon gari. Dan yau itace rana ta farko da nake ganin birnin Lagos da ƙyau duk da ma dare ne. Tabbas Lagos ta cancanci zama cikin citys na duniya. Dan adai ta inda muke zaka ɗauka ma a turai kake ba Nigeria ɗinmu ba. Jinai na sake so da ƙaunar ƙasata sosai. Isowarmu bakin katafaren ruwan nan na Lagos da muke ta jin labari ya sa kaina sake susucewa. Duk da darene akwai mutane sosai anata harkokin arziƙi. Kai da ka gani kasan duk wanda ke'a wajen yaci ya tada kai. Yo wannan irin holewa haka ina talaka yaga lokacin yinta. Sosai mamaki ya kamani ganin mu anzo an taremu cikin tsaro da matuƙar girmamawa. Sannan maimakon wajen taron mutanen nan mu can ta gefe aka mana rakkiya mu kaɗai a wajen ƙwallin ƙwal. Sai dai akwai haske sosai da zaka iya ma yarda allurarka a cikin yashin nan ka ɗauki abinka. Sai ƙarar ruwa dake wani irin ambulowa na hanƙoro a gaɓa, sai kuma ya janye ya koma. Na zata nan kawai zamu tsaya mu kalla ruwan mu koma, sai kawai ga wani ɗan madaidaicin jirgi fari tass mai masifar ƙyau ko'a kallonsa ya iso gaɓar ruwan. A hankali ya juyo ya kallan ta re da motsa lips ɗinsa kaɗan ya ce, “Les't go”. Idanu na ɗan waro waje da faɗin, “Cikin jirgin?”. “Yerhhh”. Ya bani amsa a taƙaice yana jan hannuna.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_ .......Tamkar wata shasha haka na koma wajen kallo har muka shige ciki. Jinai har numfashina na sama da ƙasa saboda haɗuwar cikin jirgin da kayan alatun da aka shirya masa. Zaune ya kai cikin lallausan wajen da aka shirya tamkar falo, tare da kamo hannuna a hankali ya jawoni saman cinyarsa ya zaunar. Ajiyar zuciya na sauke nima a hankali, tare da juyawa na kallesa. Sai kawai ya saka soft hannunsa cikin nawa ya ajiye min key ɗin motar nan. Hannun nawa na kalla na ɗago shima na kallesa. Ya wani irin kashe min ido ɗaya da ɗage gira sama. Tashi tsigar jikina tayi, dan haka nai ƙasa da kaina ina jujjuya key ɗin, muryata na ɗan rawa na ce, “Key! Karfa na yarda”. Sake rungumoni yayi jikinsa tare da ɗaura kansa a kan wuyana yana wani shinshinawa sannu-sannu har ya kai saman kunnena. A hankali ya kama kunnen da haƙori ya ɗan ciza. Jikina na ƙanƙame lips ɗina na rawa alamar son yin magana amma na kasa. Sai ƙoƙarin ɗaura hannuna da nai akan nashi da yake yawo a saman cikina. Raɗar da yake min akan kunnen ta sani ƙanƙame hannun nasa da masifar ƙarfin da ban san daga ina yazo ba. “It's yours”. Kasa magana nayi tsabar yanda yake neman haukata min jiki da salon sa. Sai kawai na saki hawayen da suka cika idona na, lips ɗina na rawa na ce, “Mota fa?”. “Uhhmm!”. Ya faɗa yana ƙara cusa hancinsa cikin wuyana. Kasa jurewa nayi, dan jikina ya fara rawa. Sai kawai na birkito na faɗa jikinsa na ƙanƙamesa kawai tsam-tsam ina sauke numfashi a gwame... Wani irin shegen murmushin mugunta Maash ya sake yana sake turata a cikin jikinsa da ƙyau. Shi kaɗai yasan mi yake ji akan wannan ƴar ficilar yarinyar mai wayon tsiya.... 😎Humm su Yayanmu fa to🥱Bara dai nayi ciluuu. 💦💦💦💦💦 Sosai jikinta yay sauƙi a ɗan tsakanin nan, sai ma wata irin murjewa da ƙyawu da cikin ya ƙara mata. Ga haskenta ya sake fitowa bazaka taɓa cewa Halimen ƴan tumaki bace ba. Yawan kwaɗaita mata karatu da Aunty Zakiyya keyi ya fara jan hankalinta. Aiko Abba na zuwa yau da dare ta ce masa tana son komawa makaranta. Kallonta yake da mamaki, itako ta shagwaɓe masa fuska kamar zatai kuka. Dole ya saki murmushi da faɗin, “Haba Halimatussa'adiyya, karatu kuma? Keda ke fama da jikinki wane karatu”. “Ni dai naji sauƙi, ina son komawa na samu ƙarin ilimin addini dana zamani kodan nasan ta yanda zan cigaba da bautama UBANGIJINA na kuma shiga duk inda nake so a duniya. Yanzu dan ALLAH ina daɗi kamarka ace matarka bata iya ko karanta sunanta ba balle ta rubuta. Dan ALLAH ka duba dai Dalin”. Murmushin ya sake saki yana ƙumshe dariya, dan yasan idan yayita a waje to za'a samu matsala shi da ita. Saboda cikin nan fushi yake sakata sosai ga masifar tsiya. Gwaggo Gudidi dake saurarensu daga waje ce ta shigo, zama tayi itama ta saka baki akan maganar komawar Halimen makaranta. Dan in ta koma ɗin ko abinda zata zauna da Mom ta samu ai anci riba. Saboda ita kanta ta fahimci Halimen na buƙatar ilimin zamani sosai kodan zama da irin su Mom. Shiyyasa ma da Zakiyya na zugata bata ce musu komai ba. Cikin hikima duk tama Abba bayani sai ya fahimta... Yin maganar nan da kwana baifi uku ba kuwa sai ga Abba da form ɗin wata makaranta. Suna boko da safe islamiyya da yamma. Sosai Halime ta shiga murna. Hakama Gwaggo Gudidi. Nan dai Abba ya cike mata Form ɗin ya maida, tare da ɗan yin duk abinda ya dace. Randa suka bukaci a kaita su mata interview ya zo ya ɗauketa ya kaita. Tsabar yanda ya matsu da son kasancewa da ita sai ya wuce da ita gida. To ita kanta dai tana buƙatar, dan haka ko musa masa batai ba. Sun samu Mom bata gidan, sai Aunta kawai da sabuwar mai aikin da Mom ta kawo. Haka Abba ya saka mai aikin ta gyara ma Halimen sashenta tsaff. Koda Gwaggo ta kirashi akan ta jisu shiru sai yace mata ai suna gida Halimen zata ɗan ɗakko wasu kaya ne. Har Gwaggo ta yarda, sai kuma zuwa can ta sake kira bayan tayi wani tunani tace Halimen tai zamanta kawai tunda ma ta samu sauƙi. Ba ƙaramin daɗi hakan yayima Abba ba kuwa. Aiko ba kunya ya ɗaga halime sama yana juyi da ita... Mom bata san wainar da ake toyawa ba, suna can yawan leƙe-leƙensu da Ummanta. Sai dawowa tayi da yamma sosai ta samu part ɗin Halime da hasken fitila. Hankalinta ne yay masifar tashi, dan ta gama zagaye gari da labarin ai Abba ya saki Halime ya korata garinsu. Miye-miye zantuka gasu nan dai barkatai tako ina. Sai kuma ga Halimen ta dawo kamar an jehota daga sama. Shin yaya akai ne haka ta faru, ba malamin nan ya tabbar musu da anyi an gama ba. Haka dai taita ƙullawa da kwancewa ita kaɗai, gashi dare yayi balle ta fita. Ta kira wayar Ummanta bai shiga ba sai daga baya ta tuna bata da caji.... 🌜★🌛🌟🌜★🌛 Cikin ƙosawa da zaman shirun da suke tun ɗazun Hajiya ƙarama ta sake kallon Yallaɓai ta gefen ido. Har yanzu dai yana a yanda yake zaune. Sosai takaici ya fara kamata. Ta rasa mi yake tunani haka. Shin maganganun data gaya masa akan abinda ya faru yau a gidan ne komi? Ko kuwa fitar su Awwab data gani yanzu da itama yasa ta kasa zaune ta kasa tsaye sai da ta fito a daren nan. Numfashi da ya furzar tare da ajiyar zuciya yasa ta kallesa da sauri. Sai taga shima ita yake kallo. Murmushin ya sakar mata dake bayyana ainahin wanene shi, dan duk wanda yaga murmushin yasan na baƙin mungunta ne. Dan haka cike da zumuɗi itama ta ce, “Yallaɓai ka samo mana wani abu ne?”. Kai ya jinjina mata yana ƙara sakin murmushi. Sai kuma ya gyara zamansa da ɗaukar waya yay kira, shiru yay yana sauraren bayanin da akai masa da ga can. Sai da aka gama sannan yay ƴar gyaran murya cikin bada umarni ya furta, “Ina son video ɗinsu da hotuna daga yanzu har sanda zasu baro bakin ruwan.” “An gama ranka ya daɗe”. Katse wayar Baba prof yayi, tare da juyawa ya kalla Hajiya ƙarama data tsaresa da idanu. Kafin ma yay magana ta taresa da faɗin, “Amma yallaɓai mi kuma zamuyi da hotonsu ko video? In dama a club ne ko wani wajen daban sai muce munada alamar tambaya a kansu. Amma yanzu minene wani bakin ruwa”. Ƙaramar dariya ya saki da faɗin, “Ai ke wani lokacin idan kina abu kamar mara wayo. Bari na baki a buɗe. Har yanzu bamu da matsayar sanin alaƙar Awwab da wannan yarinyar. Duk da dai a duk mai hankali zai iya bama alaƙar suna da abinda muketa ƙoƙarin ƙin yarda ko ɗauka saboda wasu dalilinmu. Idan na ɗauki kalmar yarinyar tayi aure, na haɗa da Awwab ya mata fyaɗe amma ko damuwar hakan babu a tare da shi duk da kasancewarsa mutum mai kiyayewa, a mahanga ta hankali mi zai iya baki?”. Ɗan jimmm Hajiya ƙarama tayi na tunani, sai kuma kamar wadda aka tsikara ta zaburo tana mai waro idanunta gaba ɗaya waje ta ce, “Mun shiga uku ni Lawusa. Yallaɓai kodai yaron nan yaje ya binciko yarinyar ne dan ya aureta. Anya ba shine ke aurenta ba kuwa? Sai dai ta yaya zai yi aure bada saninku ba sai kace mahaukaci. Yo wama zai masa walicci? Sannan shi ba ɓoyayyen mutum bane, babu yanda za'ai yaje neman aure ba'a gane shi ɗin wanene ba? Kai bama wannan ba, Awwab bazai taɓa yin aure bada sanin ku ba tunda bawai wani abu kuka taɓa masa da zai ji a ransa zai yi hakan ba. Ko Jaga da yaso ɓata mana shirin an kawar da shi”. “Humm Lawisa Kenan. Nima daga daren shekaran jiya zuwa yinin jiya da daren jiyan zuwa yau, duk nayi irin wannan lissafin naki. Har ina tilasta kaina ƙin gaskatawa dan bana jin akwai wata hujja da Awwab zai iya yin hakan. To amma dai yanzu ina da plan, shiyyasa ma nasa commondo ya samo min hotunan da video ɗin”. Da mamaki ta ce, “Wane irin plan?”. Wani makirin murmushi Baba prof ya saki da maida kansa ya jingina da kujeran. Kansa tsaye ya ce, “Ki jira zaki gani ai”. “Amma nake ga kamar ya kamata ace na sani”. “Zaki sani, amma ba yanzu ba. Give me just one day”. “Okay ba laifi, ni bara na tashi na wuce. Kasan gidan namu yanzu baya rabo da labarai. Komi kenan zuwa safiya dai ina saurarenka. Dan dole na taƙaita zuwa gidan ka saboda kar a fara mun wata fassara kuma daban gaskiya. Daga suriki...” “Hakan nada ƙyau. Idan ma ina son ganinki zaki dinga ganin address ɗin wajen haɗuwa”. “Okay ba damuwa, na barka lafiya”. Ta faɗa cikin girmamawa har da ɗan rankwafawa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 .......Sosai nake kallonsa ina ƙara jujjya key ɗin motar, shi ko yana zaune zama irin na ƙasaita ya wani yi crossing ƙafafunsa, tare da folding hannayensa a ƙirji ya zuba min ido kawai shima. Idanun nawa na ɗan rissinar, tare da sake kallon key ɗin sannan cikin ƙarfin hali na ce, “Amma Yaya Awwab motar nan ta mun girma, duk da ban san mota ba, kuma zan iya maka rantsuwar yau na fara ganin irin wannan ɗin ma. Mizai hana ma dai ace ƴar ƙarama haka dai-dai ni”. Shiru baida alamar cewa komai. Sai ma jingina kansa da yay da jikin kujerar ya wani lumshe idanu. Jinai gaba ɗaya na ƙagara yace wani abu, amma bawan ALLAHn nan baida alamar cewar har kusan mintuna goma. Sai da ya mula dan kansa yana a yanda yake zaune batare daya tashi ba ko buɗe idonsa ya ce, “Samrh”. Ya kirayi sunan nawa so soft. Nima sai na samu kaina da amsa masan a can ƙasan maƙoshi ina ɗan sauke ajiyar zuciya. “Kin san wa kika aure kuwa?”. Kaina na ɗan ɗago na kallesa. Kansa ya jinjina min a hankali tare da cigaba da faɗin, “Idan irin wannan motar kike so guda goma za'a kawo miki. Idan wadda ta fita kike buƙata ko kwana biyu bazasu wuce ba batare da an kawo miki ita ba. Ke ko zana hoton mota kikayi da hannunki, kika ce so kike a miki irinta da sunan ki ki zama ta farko kuma ta ƙarshe mai irinta kisa a ranki an gama kawai.” Sosai na sauke ajiyar zuciya ina mai lumshe idanuna, da gudu hawayen da suka cika shi suka shiga rige-rigen sakkowa. Sake damƙe key ɗin nayi a cikin hannuna, kafin na miƙe a hankali har zuwa gabansa na durƙusa. Muryata na rawa na ce, “Yaya ban san taya zan fara maka godiya ba, bamma san taya zan musalta maka abinda nake ji a raina ba.......” Ɗagowa yay a hankali tare da mun alamar zipping akan bakinsa. Gashi ya wani kalar zuba idanunsa a cikin nawa. Tashi tsigar jikina take yi saboda mayataccen kallon da yake min a cikin tsakkiyar idanun sosai nake jin tasirin su. ALLAH ya saka baiwa da tsantsar kwarjini a cikin idanun bawan ALLAHn nan. Kuma kamar yasan da wannan baiwar shiyyasa yake yanda yaso da idanun akan mutane. A hankali ya fara motsa lips ɗinsa ta yanda badan kallonsa nake ba, babu yanda za'ai na fahimci mima yake faɗa, dan sam babu sautin murya sai motsin lips ɗin kawai.. “A farin ciki kawai nake buƙatar ki kasance”. Ya ƙare maganar da salon kashe min ido ɗaya tare da wani kalar jan su shuuuu kamar zai lumshe, sai kuma ya miƙe abinsa. Cikin takun nan nasa dake tabbatar da shi a ingarma kuma jarumin namiji ya ƙarasa can ƙarshen jirgin ta inda zai iya kallon ruwa hannunsa riƙe da glass cup dake ɗauke da non alcoholic wine. Hannunsa ɗaya ya dafe ƙarfen jirgin da shi, ɗayan na riƙe da kofin yana kallon uba-uban ruwan da ya isa ka sake yarda cewar ALLAHn fa ALLAH ne, dan duk da dare ne yanda ruwan ke ƙara da ɗan walƙiya ta gefe gefen da fitilar jirgin ta haska shi ya isa ka ƙara godema UBANGIJI. Sai wani irin kaɗa gashinsa iskar keyi tana maidosa baya. A hankali na sauke ajiyar zuciya da ɗan kauda kaina a kallon nasa. Sai kuma na miƙe nima na nufesa. Duk da ina tsoron kallon ruwan haka kawai zuciyata ke ingizani kan na matsa kusa da shi. Duk da ina da tabbacin yaji motsin isowata wajen bai ko kallan ba. Nima sai ban damu ba, dan zuwa yanzu na fara fahimta da haddace halin kayana. Jikin ƙarfen na jingina. Sai dai na juyama ruwan baya ina facing cikin jirgin ne. Batare dana kallesa ba nima hannayena a ƙirji nayi shiru kawai ina kallon cikin jirgin daki-daki. Nafi minti biyu a wajen kafin ya ɗan juyo kaɗan ya kallan. Duk da naji kaifin idanunsa a kaina ban kallesan ba ni. “Hummm!” ya faɗa yana mai ɗauke kansa tare da kai kofin lemon nan daya kasa shanyuwa bakinsa. Kaɗan ya sha ya sake janyewa. Duk ta gefen ido nake kallonsa ina mamakin baƙin halinsa. Kasa daurewa nayi, dan sai nake ji a raina kamar haushi yaji, dan haka cikin dakiya da marairaita na ce, “Yaya fushi kayi?”. Nan ɗin ma kamar bazai tanka ba. Sai da ya mula dan kansa kafin a daƙilen nan nasa kamar wanda ya gaji da magana ya ce, “for what?”. “Saboda nace mota tamun girma.” Tsaye ya tashi sosai, sai kuma ya kamo hannuna ya maidoni gabansa sosai. Kallona yake sosai ta yanda har nake jin ni banzan iya kallonsa ba. Dan haka na kasa ɗagowa ina dai tsayen a gabansa kaina a ƙasa. Saukar hannunsa saman haɓata ya sani ɗan ɗagowa, muna haɗa idon na maida nawa na rissinar. Sake ɗago kan nawa yayi da kawo fuskarsa gab da tawan ya haɗe goshinmu waje ɗaya, kaɗan na so buɗe idanun nawa, sai dai da gudu na maida su na rufe saboda jin saukar mincili lips ɗinsa akan nawa. Sam ban san akwai abu a bakinsa ba, sai da naji ya fara juyemun lemon cikin bakina a hankali da wani shegen salo mai tada kan mutum. Ya Arrahaman, guy ɗin nan bala'i ne. Ni dai kodan irin wannan rayuwar baƙuwace yanzu gareni shiyyasa nake jin duk wannan oho. Abinda kawai na fahimta nima banda juriya, ja'irar kaina ce, in har yay knocking sai na buɗe masa ƙofar batare dama nasan mi nake ba. Maybe wasu su kalla hakan gazawa, sai dai ni a karan kaina nasan ba hakan bane. Ɓoyayyen sirrin dake a raina ne ke kasa cigaba da bizne kansa. Maash ya cancanci a soshi, sai dai kawai ka basar saboda tunanin bazaka samu ba. Ga marasa iya juriyar riƙewar ne ke kai masa tallar kansu. Tun ban maida hankali akan abinda yake yi ɗin ba har na fara maida masa murtani. Tsabar taɓara da tasirin da hakan ya masa sai kawai naji muku mutumin nan ya saki kofin hannunsa tsulum cikin ruwan. Ya wani ɗaukan camak. ALLAH ya rainani, yanda akoda yaushe yake mun ɗaukar amaryar nan. In sha ALLAHU sai na dage na ƙara ƙiba ko zanyi maganinsa (Sam-G fa na magana. Ashe dai ƙibar nan abin so ne. Mune fa ake yayi yanzu😜😂). Cusa kaina nayi kawai a jikinsa. Dan wata kalar matsananciyar kunyarsa nake ji har tsakiyar brain. Ashe wannan wasa ne farin girki. Dan daga wannan ɗaukar kawai jina nayi a tsakiyar wani shegen lallausan abu, dole na ɗan buɗe idona sai naga ashe gadone a kuma cikin jirgin ne a wani ɗan ɗaki da akai matuƙar ƙawatawa da wasu irin fitilu da furanni masu azabar ƙamshi. Kai kai duk yanda zan musalta muku ba lallai ku gane ba. Kawai dai anyi babu ku kudai. Kusa rigima kawai kuma mazanku su kaiku wajen nan ku kashe kwarkwatar ido😜. (Kuji min mata da iyayi, anata Masara da hinkafa wake ta wani holewa a jirgi😏, bammu tabarma ma a tsakar gida aka kunna hitilar kwai ya ihemu cin soyayya😒. Yo ALLAH na tuba mu harma... Bara dai nayi hiru amma abar ziga mu ehe😠🌚). Da farko hankalina ya tashi musamman dana tuna karo biyu wahalar dana sha. Amma dana tuna halin da nake a ciki sai naji nutsuwa. A hakan ma dai ban tsallake ba, dan na cuɗu matuƙa har sai da ya samu yanda yake so ko nace muka.... (😎 Zancen ya tsaya iya nan to😌). Na jima ban yarda na ɗago koda wasa na kalla sashen da yake ba. Dan wata irin matsananciyar kunyarsa nake ji fiye da yanda kuke zato. Hummm kar kuga laifina, Ni kaɗai nasan karatun da aka ɗaura min a cikin wajen nan. Koda aka kawo abinci ma ya ce na tashi naje nayi wanka na ci, ƙi nayi, dan shi ya riga yayi wankansa. Sai ma sake shigewa cikin lallausan farin duvet ɗin nayi na nutse a katifar da ƙyau. Sai da yace idan na bari ya hauro sai na yabama aya zaƙinta sannan na tashi ina tuttura baki. Cikin shagwaɓa batare dana kallesa ba nace ya ban kayana to. Sai ya miƙamin wata shegiyar rigar baci fara, wadda da iya da babu duk ɗaya. Duk da kuwa a tsaho nasan zata iya kai fin har gwiwa. Kawai yanda take shara-shara ne abin zakkunya. Sauka nai jikina gaba ɗaya nannaɗe a duvet ɗin, ganin zan tafi a haka a daƙilen nan nasa na magana kamar dole ya ce, “Kima dawo ki ajiye musu duvet, in ba haka ba ke da su ne ni zan wuce ne na barki a wajensu”. Ƙafa na fara bubbugawa a ƙasa ina kukan taɓara. Sai ya ɗauke kansa tamkar bai san inayi ba ya fara kai coffee ɗin da ya sa aka kawo masa baki. Nikam dai na gama shiga ɗari tara da cassa'in da tara, ni kam ina mutumin nan ke son kaini ne?. Ganin bashi da niyyar cewa komai dole na ajiye musu duvet ɗin na kwashi rigarsa da idona ya kai kai na saka sannan na wuce bayin ina murguɗa baki da jajjan rigar ƙasa dan rabin cinyoyina duk a waje. Haka kawai naji a raina yayi murmushi, aiko ina shigewa nace “Fitinanne kawai, shiyyasa ƴammata suka dameka”. (😎Kishi phone store)......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_ ......Koda na shiga bayin naji wani irin daɗin ganin p&pad a ciki. Duk da nayi mamakin hakan sai kawai nai tunanin ko suna ajiyewa ne dama in case. (Ko kuma shine yasa aka ajiye miki ba) wani sashe na zuciyata ya ayyana min. Sai abin ya sake bani kunya. Mutumin nan ɗan duniya ne sai dai kawai a barsa. Nima bathrobe ɗin na saka na fito fara tas kamar tashi, ko da wasa ban yarda na kallesa ba, duk da shi bana raba ɗayan biyu kallon nawa yake dan kujerar dana zauna tana facing ɗinsa ne. Su kaɗaine kuma a wajen sai wannan gado. Mugun ƙwaɗayin da nake ji ya sani cin gasashen kifin da aka wani ma gashi na musamman sosai. Sai naji na samu nutsuwa. Duk wata samuwar kwaɗayina ta tafi. A karan farko na ɗan ɗago na kallesa. Ganin yanda hasken screen ɗin laptop ɗin da yake dubawa ya haske masa fuska ya sani shagala kallonsa. Tun inayi a sace har na tafi direct abuna na shagala sosai. Ko kaɗan banyi tunanin hankalinsa na'a wajena ba, dan yanda yay serious a daƙilar computer ɗin ko kaine zaka ɗauka baya tare da duniyar mutane, sai kawai a bazata naji cikin silent voice ɗin sa ya furta, “Kina buƙatar wani abu ne?”. Kaina na kauda, kamar bazance da shi komai ba dan naji kunya. Sai kuma na fuske nima ƙasa-ƙasa na furta, “Ba zamuje gida ba?”. Cak ya tsaya da abinda yake yi, sai kuma ya ɗan ɗago ya kallan. Rissinar da nawa idanun nayi ina wasa da yatsun hannuna. Shima sai ya ɗauke kansa ya cigaba da abinda yake yi. Sai da ya mula dan kansa a taƙaice ya furta, “Next tomorrow”. Da sauri na ɗago tare da gwalalo idanu waje. Na ce, “Zamu tafi? Ummie fa?”. Ɗan dakatawa ya sake yi, sai kuma ya cigaba da aikinsa batare daya tanka min ba. (Tab ɗin, aiko bazan iya zama anan har jibi banga Ummie ba. Sai dai kai ka zauna) na ayyana a zuciyata ina miƙewa. Bayin na koma na saka rigar barcin nan daya bani sai na lulluɓo gyalena dana shiga da shi. Fitowa nai na haye gadon abina tare da jan bargo na shige ciki. Addu'ar barci nayi dan shi nake ji sosai, duk da wani gefe na zuciyata duk gana akan can gidan saboda Ummie, sai dai idan na tuna Mama nan ga Fahad sai naji sanyi a raina. A haka barci mai nauyi ya kwasheni ban san sanda ya baro latse-latsen nashi ba yazo ya kwanta.... 🌿🌿🌿🌿 Idan ma tace abin duniya bai isheta ba a ɗan tsakanin nan wlhy tayi ƙarya. Tama rasa ina zata kama. Gaba ɗaya haushin Rubayya take ji, shiyaysa ma ta daina amsa mata waya a kwana biyun nan. Tunda ita ta bata shawarar da gashi nan ta rubza a ciki. Anya kuwa bazata tafi plan bi b ba. Shegen yaro sai jarabebben taurin kai. Ga wannan ƴar iskar yarinya sheɗaniya sun nuna mata hanya itama tana neman zame musu ƙalliƙalallah. Dolene ma ta ɗauki mataki akan yarinyar nan itama. Amma sai plan ɗin ta ya gama kankama. Shima Fahad tunda ya fara koyon tsagerancin ɗan uwan nasa zata gyara masa zama. Dole ne fa itace kaɗai zatai mulkin Maash Mansion. Kuma dole Awwab ya auri Azizat ta hakane kawai zata cigaba da mallakar kowa na gidan. Koda wataran ALLAH ya bama Ummu-Hidaya lafiya bata isa jaa da ita ba tunda dai a yanzu Maash shine mai dukiyar. Murmushi ta saki har haƙoranta na bayyana. Cike da izza ta furta, “Baba tunda ku bazaku iya komai ba kuna tsironsa, ni Nafisatu bint Adams zan ƙwatama kaina abinda ku kanku anan gaba sai naso ku samu. Dan ɗaya bayan ɗayanku sai na maida muku murtani wlhy. Musamman ma Mu'azz. Sai na tabbatar masa da ni suka haifama Awwab shi da Ummu-Hidaya. Badai ni ya ɗagama murya ba, hahahahaha sai ka koma ƙasan ƙafafuna kuwa muje zuwa”. Ta wani miƙe tana juyi kamar ƙaramar yarinya.. Ni sai ma abin ya bani dariya😂😜. 💓🪴💓🪴💓 Washe gari kamar yanda Maash ya bama Hayatu umarni akan gyaran sashensa bisa shawarar Samraah sai ko gashi da companyn da zai yi aikin. Bayan sun shiga sun dudduba ko ina da gwadawa aka shiga fitar da komai da ba'a buƙata. Bedroom ɗin Maash ɗin ne kawai ba'a taɓa ba sai kitchen da akama gyara jiya. Aikin bai tsaya anan ba harda sashen Fahad shima. Sai da suka kammala kwashe komai aka fitar tsakar gida sannan suka fara aikin fenti da canja wasu abubuwan duk da kuwa babu abinda gidan yayi, amma abinka da masu kuɗi, a duk sanda za'ai sabon gyara ana ƙoƙarin ya tafi da irin wannan zamanin ne ko tsarin kayan da za'a canja ɗin. Mutanen gida basu san mike faruwa ba sai gani sukai kawai anan aiki. Yayinda ake maida kayan sashen Maash ɗin sashen su Mama Balki dan kayan sabbine ko shekara basuyi ba. Kawai dai anso ciresun ne saboda ba'a matsalar kuɗin canjawar. Wannan abu ya sake harzuƙa zuciyar Hajiya Mammah, harta gagara haƙuri sai da ta tsare Hayatu da masifa dan duk shekara biyu ko ɗaya da rabi ita ake bama kwangilar canja kayan gidan, duk da dai ta karɓi hakan ne da ƙarfin tsiya dan da Hayatun ne. Sai kuma abinda taso za'a sakama kowa iyakaci ta tambayi kalar da kake son kawai. Sai gashi wannan karon taga ana aikin kuma ko shekara batai da canja kayan ba. Abin ma takaicin banda nasu sashen. Komai Hayatu baice da ita ba, sai da yaga azabar tayi yawa ya sanar mata umarnin boss ne. Shi nashi kawai tsayawa kan masu aikin. Sake tunzurata zancen yayi, take ta hau neman layina Maash. Sai dai switch off. Wani irin tuƙuƙi taji yana sake turnuƙeta. Ita a ganinta taya za'a hau canja kaya yanzu bayan ga biki na tahowa, dan tana nan akan bakanta yanda Baba yace nan da wata ɗaya za'ai bikin Maash da Azizat babu fashi sai hakan ta tabbata. Shiyyasa ma zata ƙulla plan b domin masa ɗaurin goro shi da kowa na gidan. Fuuuu ta nufi sashen su Paah. Yana zaune dan yana kallon wani program da alama yau bazai fita office ba ta shigo. Kallonta kawai ya tsaya yi har sai da ta iso gabansa sannan ya ɗauke kansa tare da gaisheta a fisge. Dan wannan ɗabi'ar Tata ta shigama mutane ba sallama na ƙona masa zuciya. Ya tabbatar idan bata fasa ba wataran sai taga abinda zai dameta wlhy. Yanda yay mata ɗin yasa ranta sake ɓaci, a take ta balbalesa da masifa akan laifin Maash kamar wani ɗanta ba ƙani ba. Ƙanin ma fa sako bawai na can-can nesa ba. Banda ma ta raina masa wayo a yanzu duk wanda ya kalleta ta kallesa baza'a taɓa cewa ta girmesan ba saboda shi namiji ne. Amma bai sani ba ko wannan linda-lindar jikin nata ne ke kwasarta tana ganinta shirum kamar matar sarkin yarabawa. Karan farko da ya fara manna mata hauka har taci jarabarta ta tsire bai tanka mata ba. Sai Hajiya ƙarama ce data fito da shirin fita asibiti ta ke bata baki. Bata kulata ba, hakan kuma ba sabon abu bane ba. Dan tun tana ma amarya basa shiri, duk da kuwa da farko farkon auren babu wata matsala saboda Hajiya Mammah na murna amma Ummie kishiya, kasancewar a lokacin akoda yaushe cikin saka ran zata warke suke. Sai dai a dalilin wani abu da su suka san tsakaninsu ya saka su ƴar walle-walle. Duk da kuwa ita Hajiya ƙarama taƙi nuna akwai matsala kowa laifin Hajiya Mammah kawai take gani da tunanin itace tama Hajiya Ƙaramar koma minene. Rai ɓace Paah ya tashi ya bar mata falon. Ai ko sai ta hayayyaƙo masa harda shan gabansa tana daka masa tsawa. Ai ko shima ya daka matan cikin matuƙar fusata da hargagin da bai taɓa koda kwatanta mata ba ya nunata da yatsa tare da faɗin, “Addah! Leave me alone!. Get out of my side kafin na nuna miki ainahin true color ɗina wlhy. Kin isheni! Kin isheni!!. Haba wai ƴaƴana sune kaɗai ƴaƴa a family ɗin nan da kullum dai sai ance sunyi-sunyi. Musamman Muhammad bashi da wani filin shaƙar iska mai daɗi a gidan nan. Kullum cikin wahalar nema da kai kawo yake na ganin ya ƙyautata rayuwarmu da ingantata amma bazamu masa addu'a ba mu gode masa sai zaman lissafa kurakuransa. Kuskuren ma daba kuskure ba dai Muhammad. Yanzu ki duba Fahad tunda ya iso gidan nan wlhy ko kallo ban ishesa ba. Yama nuna gaba ɗaya bai san dani a cikin gidan nan ba. Shekara nawa ban gansa ba, ko naje ƙasar da yake guduwa yake baya barin ma mu haɗu sam. Shi kansa Muhammad idan bai so ba sai ya shafe wata biyu ban gansa ba kuma yana cikin ƙasar koma cikin gidan. Miyyasa wai bazaku tausaya min bane ku barni da damuwata. Shin da halin da uwar ƴaƴana data zama sanadin rufin asirina da ku zan ji ko da fitinarki Addah?!!. Ke wane kalar iskanci ne yaranki basayi kin ma taɓa nuna kin san suna yi ɗin. Please! Mind your business and leave me alone!!!!”. Ya wuce abinsa fuuu cikin bedroom. Ba Hajiya Mammah da Paah yayima ihun ba. Hatta da Hajiya ƙarama sumar tsaye tayi. Dan abune da bai taɓa kwatanta faruwa ba a gidan koda a mafarki. Mu'azz na ɗaga murya ma wani. Kai kai koda ƴan aiki bata taɓa ji ba. Shi mutum ne mai shiru-shiru, dan zata iya cewa ma rashin magana kamar a wajensa Awwab ya gado shi. Sannan shima wani lokacin akwai miskilanci, dan in bai gadama ba sukan iya gaɓar sati biyar ita da shi wlhy bata ishesa koda kwallo ba. Sai dai ita ta gaji ta sauka. Amma jiba yau ya koma kamar wani mafaraucin zaki.. Ido suka haɗa da Hajiya Mammah data suma a tsayen itama. Sai kawai ta wani balla mata uwar harara tai gaba abinta.. sai kawai murmushi ya suɓucema Hajiya ƙaramar batare data shirya ba. Wayar dake hannunta ta kalla, sai kuma ta kwashe da dariya, tare da shiga WhatsApp ta turama Baba prof recoding ɗin da tayi na duk abinda ya faru. Tana turawa ta kashe wayar gaba ɗaya ta koma cikin ɗaki dan ga fasa fita aiki kuma. Sai taga ƙarshen wasan........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_ .......Koda kiran salla ya farkar da mu da asuba nayi mamaki. Sai daga baya na fahimci daga wayarsa ne ya saita hakan. Tashi yay ya shiga bayi. Bayan ya fito ya kabbara salla nima sai na shiga domin gyara jikina na kuma yo wanka. Sai dai ƙasan raina ina cikin damuwar kayan sakawa. Koda na fito sai da na gyara gadon sannan na zauna. Wayarsa na ɗauka na duba naga ko akwai app na Alkur'ani. Nayi sa'ar samu kuwa, dan haka nayi zaman yin karatu, shi kuma da alama azkar yake yi dan yana dai zaune a inda yay sallar idanunsa a lumshe ya jingina bayansa da kujerar wajen. Mun jima a hakan har sai da gari yay haske sosai ya miƙe, nima sai na ajiye wayar batare dana kallesa ba kaina a ƙasa na gaishesa. “Kin tashi lafiya?”. Ya amsa min a taƙaice. Numfashi na ɗan sauke a hankali ni ma nace masa, “Alhamdullah”. Fita yay, ni kuma na ɗan sauke ajiyar zuciya. Ina a wajen zaune babu jimawa sai gashi ya dawo riƙe da wata ƴar ƙaramar bag mai shegen ƙyau. Kusa da ni ya ajiye batare da yayi magana ba ya wuce bathroom. Da kallo kawai na bisa har sai da ya shiga na ɗauka jakar na buɗe. Abinda ko nayi tunanin ganin ne wato kaya. Har cikin raina naji sanyi, dan haka na miƙe a gurguje na shirya cikin doguwar rigan mai ƙyau sosai. Yana fitowa ɗaure da towel kallo ɗaya na masa na ɗauke kaina, har ya kammala shiryawa ban sake maimaitawa ba. Sai da yazo har inda nake ya kama hannuna sannan na ɗago na kallesa. Da ido yay min nunin na tashi, ban musa ba na miƙe, sai dai a raina ina mamakinsa. Gurin jiya muka fito, ganin da nai masa na yau sai naji ya sake ƙayatar da ni. Gamu a gaɓar ruwa yanzu kam al'amarin zabbirgewa da ƙayatarwa, sai dai bata inda muka baro bane nan ɗin ma babu kowa shiru sai kukan tsuntsaye. Bamma san na saki murmushi ba. Ganin yana kallona nayi ƙoƙarin ɗauke kaina ina gimtse abina. Nima gwara ai na koya irin halin nashi Aita zaman kuramen kawai. Ƙayataccen breakfast ɗin da aka shirya mana mukai zaman ci. Koma nace naci, dan shikam ma tsakurar komai yake kamar abin dole. Na fahimci sam baya son abinci, ya dai fi ganewa kayan ƙwalam ɗin nan da maƙulashe... Ana kiran wayarsa ya tashi a wajen, can ya koma ya tsaya. Ban tsaya jiransa ba na ƙarasa cin abincin na tashi. Ciki na koma ban jima ba na dawo. Na samu ya gama wayar, ma'aikatan jirgin ma na tattare kwanikan da mukaci abincin. Kallona naga yayi kamar mai nazari, sai kuma ya ɗauke kansa da maidawa kan wayarsa dage vibration dan shi sam baka jin ƙara a duk wayoyinsa. “A ƙaraso da su”. Kawai yace yana mai yanke wayar. Mamaki ne ya kamani, na kalla gabas da yamma kudu da arewa naga dai a tsakiyar jajeji muke sai ruwa. To ta'ina ma wani zai samu damar zuwa nan ya same mu. Bari dai naga ikon ALLAH. Aiko na gani, dan ba'a cika minti biyu ba sai ga ma'aikacin jirgin ya shigo bayansa da mutane guda uku. Ɗaya babban mutum ne mai cikar kamala da mutumtaka. Ni sai ma naga kamar nasan fuskar. Sai matashin saurayi da bazai wuce sa'an Hayat ba, shi kansa saurayin kamanninsa da Bahijja sosai ya mugun jan hankakina. Sai dai na cije kawai na kame kaina, sai Hayatu dake biye da su. Araina nace (bindin Maash kenan). Ganin Maash ɗin ya miƙe cike da girmamawa yana ma dattijon barka da zuwa da kiransa da Abbah yasa nima suna zama na gaishesa cikin girmamawa kaina a ƙasa. Sosai yake murmushi, kafin cikin jinjina kai ya ce, “Masha ALLAH, abu yayi ƙyau Muhammad Awwab. ALLAH kaine abin godiya, ALLAH ya ƙarama wannan aure albarka”. A mamakina murmushi naga yayi yana ɗan rissinar da kai alamar jin nauyi, nace (tofa, dama akwai wanda Maash kejin kunya a duniya ashe). Gaisuwar da saurayin nan ya mun cike da girmamawa ta katse min tunani na. Na amsa masa shima ina ɗan murmushi. Muka kuma gaisa da Hayatu na tambayesa aunty Falaq yace tana lafiya. “Samrh!”. “Na'am”. Na ɗago ina amsawa da ɗan kallonsa. Inda dattijon nan yake ya ɗan kalla, tare da sake maido idanunsa a kaina ya ce, “Wannan shine Malamina kuma kamar Abbana. Shiyya fara koyar da ni ilimin addini kamar yanda ya koyar da kakana mahaifin Ummie kenan da ALLAH yayma rasuwa tare da Baba. Shine kuma ya amsar min walliccin aurenki. Nasan dan da wahala ace baki san wannan fuskar ba. Dan Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain ba Nigeria ba a Africa ma sananne ne”. (Haba no wander nifa nace nasan fuskar nan) a zahiri kuma sai na jin jina kaina da sake rissinawa na ce, “Sannu da zuwa Abba. ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana masu albarka”. “Amin ya rabbi ɗiyata. ALLAH yay miki albarka. ALLAH kuma ya jiƙan mahaifinki Abdul-wahab da rahama. Mutumin kirki mai gaskiya da riƙon amana. Mai sadaukarwa. Ina fata da addu'ar ALLAH ya gadar da ƙyawawan halayensa ga ku zuri'arsa. Dan masu iya magana kance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. Nayima mahaifinki ƙyaƙyƙyawan sani gaskiya. Har takai ina jin kunyarku matsayin zuri'ar daya tafi ya bari da ya kasance bamu taɓa bibiya ba har sai a gaɓar da UBANGIJI ya zartar da ikonsa. Amma tabbas nasha yin hasashe a kanki a duk lokacin dana ganki a tv. Saboda iyalan gidana na bin program ɗin da kike gabatarwa. Tun ina faɗa da yawan kallon tashar har dai na nutsu nima naga abinda suke kallon a wata rana. Amfanin shirin da hikimar iya zance da ALLAH ya baki yaja hankalina matuƙa. Sai kuma a raina nake jin kamar na taɓa saninki amma a ina shine na manta. Har dai randa Muhammad ya kirani da bayani akan rikicin aurenki da hukuncin kawunki. Kasancewar yana faɗin min wadda yay hira da ita a Alheri tv yasa na gano kece. Abinda yay matuƙar sake ɗaukar hankalina kuma hoton da ya tura min na ɗan uwanki dake tsananin kama da mahaifinku, kema ashe jininsa nake gani a jikinki shiyyasa nake ganin kamar na sanki. Dan haka na buƙaci yazo ya sameni. Mun tattauna sosai akan abinda bamu tabbatar ba, a take nan ya saka aka masa bincike aka kuma tabbatar mana ke ɗin jinin Abdul-wahab ce. Madalla da ƙyaƙyƙyawan tsiron alkairi. ALLAH ya gafartama Abdul-wahab Gwarzo”. Sosai nake kuka. Yayinda Malam ya cigaba da zabgama Baba addu'a har ma da kakan Maash ɗin. Maash na amsawa da Amin, dan Hayatu da saurayin nan suna can gefe sun bamu wuri. Nima dai ina amsawar sai dai kuka yaci ƙarfina. A hankali naji saukar hannunsa saman nawa kasancewar muna zaune ne a kusa da juna. Na kuma ɗan dafe kujera da hannun, ina sharar hawaye da ɗayan. Sosai ya runtse hannun cikin nashi tare da ɗan murzawa alamar lallashi. Sai kuma ya zato tissue a cikin kwalinsa dake saman Centre table ɗin kujerun wajen ya miƙa min. Ban musa masa ba na amsa. Hawayen na share, sai kuma ya miƙa min ruwa. Nan ɗin ma amsa nayi na sha kaɗan na ajiye. Sai da na ɗan samu nutsuwa kafin Malam ya cigaba da faɗin, “Samraah kinyi ƙoƙarin, ALLAH ya saka miki da alkairinsa. Mijinki yana min duk bayani akan kula da mahaifiyarsa. Tare da cigaban da ake samu yanzu sosai. Waɗan nan halayyar sune halayen mace ta gari. Sune irin halayen da kowane namiji zai so samu ga matarsa koda kuwa akwai wani special abu da yafi so ga mace. Ki cigaba da yanda kika fara kar ki canja kinji. Kema in sha ALLAHU ALLAH zai kula dake. Ba kuma zai taɓa taɓar dake a ƙarƙashin ƙafafuwan ƙasƙantattu ba masu bijirema gaskiya”. “In sha ALLAHU Abba Nagode sosai. ALLAH ya ƙara rahama da jin ƙai a gareka.”. “Amin ya rabbi ɗiyata, tare dake da zuri'armu baki ɗaya. Akwai magunguna da nazo da shi da ruwan addu'a duk suna a motarku. Idan kun koma gida sai a cigaba da yimata amfani da su. Hatta kuma zaku iya sha da amfani da su ɗin ba komai bane, har a girki kina saka muku musamman ruwan addu'ar zaki iya abinci da shi. Sai kuma a ƙara dagewa da addu'a da sadaƙa. Kiyaye dokin ALLAH, kiyaye hakkokin mutane. Azkar, karatun Alkur'ani. In sha ALLAHU muna fatan nasara a wannan gaɓar. Sannan Bahijja ta sanar min dukkan abinda ya faru a ɗazun akan Fahad, shima kar ai wasa dan abinda ke jikinsa a yanzu yafi na ɗan uwansa ƙarfi sosai gaskiya, dolene zai fishi zafi da son ayima duk wacce za'ai. Jarabawa ce ALLAH ya bamu ikon cinye wa baki ɗaya”. Sosai nayi mamakin jin sunan Bahijja a bakinsa. Amma dai na daure na amsa da “Amin ya rabbi. ALLAH ya tabbatar Abba. In sha ALLAHU shima komai zai tafi dai-dai”. Na faɗa fuskata cike da murmushi. Shima murmushin ya min tare da faɗin, “Kina mamakin nace Bahijja ko?”. Kaina dake a ƙasa na jinjina ina murmushi. Shima sai ya sake murmusawa. Tare da nuna saurayin da suke tare da Hayatu. “Wancan yarona ne shima. Sunansa Hameed. Yayane ga Bahijja mamansu ɗaya. Mijinki shine ya kawo Bahijja gidan nan domin yimana wani aiki, kuma Alhamdullah ana cin nasara. Sai dai itama ban sanar mata ke ɗin matar Yayan nasu bace ba.” Kasa daurewa nayi sai da na ɗago na kalla Maash da hankalinsa gaba ɗaya ke a kan wayarsa yana daƙila. Mamakin duniya ya kasheni, amma sai bance komai ba na sake maida hankalina kan malam da fuskarsa ke a ƙawance da Murmushi. Ya ce, “Karki damu, a hankali zaki fahimci komai. Dan gidan nan naku sai mijin naki ne ya iya musu ai. ALLAH dai ya shiryar camu”. “Amin” na amsa masa a hankali, ina sake mamakin mutumin nan. Tabbas na yarda shi ɗin yafi Aljani taƙadaranci kamar yanda Hayatu ya taɓa faɗa min... Daga haka suka cigaba da tattaunawa da Maash, a tattaunawar tasu ne na fahimci shima Hameed ɗin an kawosa ne yin wani aiki a asibitin da Hajiya ƙarama ke aiki. Abin ya bani mamaki, sai dai ban iya saka musu baki ba tunda zancensu ne. Amma wai abu dana taɓa ji a asibitin nan sanda nake jiyya sai Sosai wannan zama ya jamu lokaci mai tsayi, dan sallar Azhar ce ta tashemu........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ......Malam shine ya ja musu sallar azhar a cikin jirgin. Maash da malam ɗin sun sake sabon zama da ga shi sai malam ɗin daya jasu har zuwa la'asar, kai da kaga zaman zaka san abu mai muhimmanci suke tattaunawa, nan ma ya jagorancesu sallar la'asar sannan suka tafi. Ni lokacin ma ina ɗaki kwance ya kirani mukai sallama. Bayan tafiyarsu na zata muma zamu wuce sai naga wasa farin girki. Dan kuwa zama daram mai naƙuda ta samu katifa. Haka ina ji ina gani muka sake kwana a cikin jirgin nan dake ta faman shawagi kawai a cikin ruwa. Daren ranar ɗin ma dai bai ƙyaleni ba nasha jagwalgwala har sai da nayi laushi a hannunsa. Kai jama'a mutum ina ma prioud ɗin ban tsira ba. Kamar yanda ya faɗa kuwa washe garin cikarmu kwana biyun gabanin magrib muka bar cikin jirgin. Sai kuma naji du kamar kar mu wuce. Dan rayuwa a cikin jirgin nan rayuwace mai tsayawa a zuciya da bazamu taɓa mantawa da ita ba da ga ni har shi. Ga wata shaƙuwa ta musamman data shiga tsakanina da shi. Duk da kuwa yana nan da halinsa da kuka sani na rashin son magana babu abinda ya canja. Wani lokacin ma idan na gaji da shirun nasa sai na ɗauka wayarsa naita game abina. Dan zuwa nai na dinga ɗakkosu a play store iri-iri. Wani lokacin ma ina a jikinsa zanta abina yana kallona. Kokuma yana aikinsa a computer ni kuma ina game ɗina ko kallon films tunda ga datan banza. Yo ta banza mana tunda shi koyaushe data ɗinsa a buɗe yake. A motar da mukazo dai muka koma. Sai dai maimakon gida ma wani wajen yay dani. Ganin ƙaton companyn da muka zo ya sani tambayarsa ina ne nan. Bai bani amsa ba sai da ya gama shan ƙamshinsa ya ce, “Na Ummie ne. Shine ta fara ginawa”. “Woow Masha ALLAH”. Na faɗa tare da cigaba da yaba haɗuwar companyn da girmansa. Har ciki muka shiga a office ɗin dana fahimci nashi ne. Dan babu kowa sai masu gadi a ciki da waje. Kujera ya nuna min shi kuma ya shiga bayi, koda ya fito ficewa yay da alama zaije massalaci. Ina jin ya kulleni ta baya. Ban damu ba na miƙe ina bin hotunan saman desk ɗinsa da kallo. Kusan biyar duk shi da Ummie ne da Paah da wani da aka rufema fuska da wani emoji kwalliya. Mamaki ya kamani na ɗan kware ɗaya sai naga fuskar Fahad. Murmushi kawai nayi tare da jin tausayinsu. Dan masifa ma ace a hoto ma basa son ganin juna. Duk inda fuskar Fahad take ya rufeta. Da ga shi sai Paah da Ummie sai wani ƙyaƙyƙyawan baturen dattijo dake tsananin kammani da Ummie da shi kansa Maash ɗin daya ɗan ɗebe wasu abubuwan da ƙyaƙyƙyawar mace baka. Tabbas wannan shine Ibrahim (Alonso) kenan, ita kuma macen Rabi'ah. A take naji ƙaunar dattijon ya shiga raina yayinda na shagala a kallon Rabi'ah, wlhy ji nake kamar na san fuskar nan. Addu'ar samun rahama na musu tare da mahaifina sannan na maida hotunan a yanda suke na koma na zauna inata son tuno a inda na san fuskar Mama Rabi'ah. Zamana baifi minti biyu ba ya dawo. Zama yay tare da ɗaukar wayarsa dake vibration tun ɗazun ya kai kunne. “Office”. Kawai ya faɗa yana mai yanke wayar. Ɗan juyowa yay ya kallan, sai kuma ya ɗauke kansa tare da nuna min wani ƙofa ya ce, “Jeki ciki”. Kamar zanyi magana sai kuma na fasa. Mikewa nai na nufi inda ya nuna ɗin, a cikin raina ina mitar ALLAH ko'a jikin ƙofa ne sai na maƙe naga wanda zai shigo. Ai ko hakan nayi, ina maƙe a jikin ƙofar ina kallo da ido ɗaya ta ɗan wajen nan mai kamar camara. Saurayine matashi ya shigo, sai dai fuskarsa kusan a rufe take da hirami, sai gilashi daya rufe idanunsa tas ba'a iya ganin komai. Idan ka gansa saika ɗauka baida gaskiya. Cike da girmamawa ya rissina ya gaishesa. Ina kallo ya amsa masa da alamun jinjina kai. Sai kuma ya nuna masa kujera. Zama yayi, tare da yaye hiramin ya cire gilashin. Ban sanshi ba, bamma taɓa ganinsa ba. Oho su suka sani wannan kuma. Ganin bazan iya jin abinda zasu faɗa ba na ɗan buɗe ƙofar kaɗan. Dai-dai nan ko saurayin ya miƙa masa wani abu kamar yana faɗin, “Alhamdullahi Sir, naci nasarar ganin fuskar ɗaya daga cikin masu zuwa gidan da ɓoyayyar fuska. Sai kuma ita Hajiya Nafisa kwana biyun nan tana yawan zuwa gidan gaskiya. Guy ɗin nan mai suna Commondo da muka bibiya kwanaki shima kwana biyu nan yana zuwa akai-akai gidan. Sauran baƙin kuma da suka ɗan zazzo duk akwai sunayensu da fuskokinsu anan zaka gani. A jiya tattaunawasu da commondo ya bada damar a bibiyar masa brothers ɗin wata yarinya da suke zargin tana anan cikin Mansion ɗinka kamar mai something suna Samraah. Wadda naji Hajiya Nafisa ma tazo da batunta. Sai ita mai ɓoyayyar fuska data bayyana itama tazo da batunta. Kamar dai itace ya bada umarnin a kashe a asibiti ranar.” Shiru Maash ɗin bai ce komai ba. Har kusan mintuna biyar kafin ya buɗe baki da ƙyar ya furta, “Ya akai ka fito kai yanzu?”. “Baya gida tun around 11am ya fita. Amma dai akwai abinda yake ƙullawa gaskiya, sai dai bai faɗi komai ba akan shirin dan an sanar masa kun fita a gida tun shekaran jiya, lokacin suna tare da ita matar nan yace zai yi wani abu amma itama yaƙi sanar mata, amma a randa kuka fitan aka sanar masa. Jiya ma bai yini a gidan ba, yau ma gashi kusan hakan”. “Kai mi kake tunanin yana shiryawa?”. Ya faɗa a daƙile. “Eh gaskiya bazan ce ba kai tsaye. Amma dai ina hasashen koma minene tabbas zai iya shafarka. Dan haka ma na saka abu a jikin driver ɗinsa. Idan har an dace bai farga ba ya cire to zamu iya ganin wani abu koda ba duka ba ta nan. Sai dai gaskiya Sir ya kamata ka ƙara ninka tsaro a mansion. Dan shirin nan na musamman ne kuma daɗaɗɗen shiri kamar yanda Jaga ya faɗa. Sannan har yanzu kowa ba abin yarda bane a gidan nan. Ita kanta yarinyar da suke magana na fahimci a al'amarin nata akwai lauje cikin naɗi, musamman yanda naga al'amarinta na ɗaga musu hankali matuƙa, dan a nasu bincike sun gane tana da aure, amma sun gagara binciko ainahin mijin nata. Shiyyasa nake ga muma kamar ya kamata mu binciko ita ɗin wacece kafin su su binciko”. “No wannan ba aikinka bane. Yanzu abinda nake so da kai shine. Ka tabbatar Hameed ya samu karɓuwa a wajensa hundred percent ta yanda samun aiki a asibitin bazai masa wahala ba. Akwai yarinya mai suna...” ya ɗan yi shiru alamar tunani. “Oh na manta. Ka kira Bahijja zata faɗa maka. Ina son kama oganka bayani ya kamata daga nan zuwa sati biyu. Kaima bazan sake ganinka ba sai nan da four to five weeks haka. Dan zan yi tafiya gobe in sha ALLAH”. “Ba komai Sir, ALLAH ya kaimu. In sha ALLAHU kuma komai zai cigaba da tafiya fiye da yanda muke fata. Zan kuma sanarma oga saƙonka in sha ALLAHU. Komai da kake buƙata zaka gansa a flash ɗin nan ga kuma bayanai a file ɗin shima oga na bashi copy ɗin komai”. Hannu naga ya bashi, sukai musabaha wancan ɗin ya fice. Kasa motsawa nayi a wajen. Dan tunda suka fara magana komai ke mun kai-kawo a zuciya.. “Idan kin gama laɓen ki fito”. A bazata matuƙar bazata na ji saukar furucinsa tsakiyar kaina. Sosai na waro idanu waje. Tare da dafe ƙirji na kallesa. Yana zaune a yanda yake. (Kambu, yaya akai ya san ina laɓen? Ka jimun aljani) na ayyana a zuciyata. A zahiri kam sai na tunzura baki ina danne kunyar da naji na fito. Hankalinsa na akan file ɗin da aka kawo masa, dan haka na ɗan hararesa da murguɗa baki kaɗan. Har zan zauna gefe sai wata zuciyar ta ƙwaɓeni zama kusa da shi kodan naga mike a file ɗin. Sai dai me, ina zaman naci karo da hoton Hajiya ƙarama da shima ya ƙurama ido... “What!?”. Na faɗa cikin tsananin mamaki ina mai kai hannu na amshi hoton. Bai motsa ba, bai kuma ce dani komai ba. Sai da na ƙarema hoton kallo ciki da bayansa na sake tabbatar dai da ita ɗin ake maganar sannan na kallesa. Sosai naga jijiyoyin kansa sun wani irin tashi, yanayinda gaba ɗaya ya sauya. File ɗin na zame gaba ɗaya daga jikinsa nima nawa jikin na rawa na shiga dubawa daki-daki. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un”. Na faɗa wani irin abu mai nauyi namun kai-kawo. “Tabbas biri yayi kama da mutum. Dama matar nan tana a cikin suspect ɗina a gidan, ashe kuwa. Amma Yaya abinda ban gane ba wane Baba prof ake magana? Wlhy kaina ya kulle gaba ɗaya, zuciyata bugawa take da ƙarfi”. Shiru bashi da niyyar motsawa tsahon lokaci. Sai kuma ya ɗago a hankali ya kalleni. Sake firgita nayi zuciyar tawa na ƙara ƙarfin gudu da ganin idanunsa da sukai wani kalar masifar juyewa. Gaba ɗaya sun koma golden kai kace irin gawurtattun zakunan nan ne da suka addabi jeji tako wacce kusurwa. Ga wani irin tsananin fusata dake nuna ainahin stubborn Maash ɗin nan da bai san komai bace rashin mutunci. Rawar jikina ƙaruwa tayi, na shiga girgiza masa kaina hawaye na cika min ido. “Please Yaya ka daina kallona idanunka tsoro nake ji”. Shaaa hawayen da nake maƙalewar suka zubo. A hankali yay wani luuu da idanun, sai kuma ya miƙe murya a matuƙar shaƙe ya ce, “Les't go”. Kasa tashin nayi dan har sai da yaje ƙofa kafin na miƙe jikina na rawa ina sharar hawaye. Har muka isa motar ma kukan nake, gaba ɗaya komai ya ƙwace mun. Sam bana son yarda Baba prof ɗin su ake nufi ya ce a kasheni. Idan fa har shine shima akwai lauje cikin naɗi a tattare da al'amarinsa kenan. Kai mun shiga uku wannan duniya to waya kamata mu YARDA da shi?. Waye zamu YARDA MASOYINMU ne na gaskiya? Wai kenan da gaske anzo zamanin da zakama mutun ALKAIRI ya maida maka da SHARRI ke nan? Da gaske ne maganar malamin nan da yace wannan al'ummar na wannan gaɓar tamu sune MAFI SHARRIN AL'UMMA?. Mu zauna mu auna mana. Wlhy da wahala, matuƙar wahala a yanzu ka ƙyautatama mutum biyar ka samu ɗaya ƙwaƙwƙwara za dai maido maka da ALKAIRI. Mai ɗan sauƙi a ciki ne sanda ka masa zai nuna jin daɗin yimasan da kayi zuwa anjima ya manta. Wani ma kana bashi, bakinsa a washe a gabanka yana matsawa ya zageka da nuna ai dole ma kayi masan. Haba mutane why! Why! Why! Mukafi buƙatar yima WUTA tanadin kammu tun a duniya saɓanin ALJANNA. Why muka fi yarda da rayuwa da ruɓaɓɓiyar ZUCIYA saɓanin tsarkakakkiya?. Ni gaba ɗaya ma zuciyata ta cure waje ɗaya........✍️ _To adai ji tsoron ALLAH kar a samu naman salla a manta dani🥱_. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ *_Masha ALLAH, Barkanmu da salla. ALLAH ya maimaita mana da rai da lafiya. Mahajjata ALLAH ya karɓi abadu da mu da mukai tamu anan 😀. ALLAH yasa muma baɗi iyanzu muna can. Har yanzu dai banga naman salla ya fara sauka ba. A dingayi ana rage rowa fa🌚🌚._* .......Ganin uban gudun da yake damu da magribar ALLAH ya sani sassauta kukana na share hawayena. Matsowa nayi a hankali ta jikinsa na dafa hannunsa dake a saman steering. Cikin shaƙewar muryar da nake ƙoƙarin controlling na ce, “Please yaya kayi haƙuri. Ban san ainahin mi kake bincike ba, amma ina ji a raina yana da alaƙa da Ummie tunda naga maganar Fahad ya shigo ciki. Dan ALLAH kayi haƙuri zuciyarka ta sauka karka shiga gida da wannan fuskar, yaƙin sunƙuru ai suƙunrun ake masa. Sannan kaike na koya min dabarun zama da maƙiyi” Na ƙare maganar da kwantowa jikinsa na lumshe ido. A hankali ya fara sassauta gudun kuwa, jin mun tsaya yasa na buɗe idanuna. A hankali na ɗago na kallesa sai kuma na kalla inda muke. Gefen titi ne kawai, nima sai na sauke ajiyar zuciyar. Goran ruwan dake saman cinyata wadda ɗaya daga cikin ruwan addu'ain da Malam ya kawo ce kuma ruwan zam-zam ne a ciki na miƙa masa bayan na cire murfin. Babu musu ya amsa yasha sosai. Sai ya jingina da kujerar ya lunshe idanunsa a hankali yana wani irin sauke nannauyan numfashi. Har cikin raina naji daɗin saukar tasa, sai kawai na sake kwantowa akan hannun nasa nima na lushe idanun ina sauke nawa numfashin. Mun jima a wajen har na fara tunanin barci yake kafin ya tada motar, sai da muka fara tafiya na fahimci mugun zagaye yayo damu ashe, nafayi mamakin ganin ranar bamu daɗe ba mukaje bakin ruwan, amma yau mun gagara kaiwa gida da wuri..... ❤️🪴❤️🪴❤️ Alhamdullah Halime karatu dai ya kankama, dan kuwa dai ta fara zuwa makaranta. Kasancewar kanta fresh yake kuma akwai karatun addini sosai a tattare da ita sai na bokon yake shiga cikin sauƙi. Gashi ta saka kanta ga kuma zugar aunty Zakiyya a gefe na tasiri. Shi kansa Abba har mamakin brain ɗin Halimen yake. Dan in ya dawo gida tata damunsa da tambaya akan kaza da kaza. Kai har Auta da gantalin uwarsa ya fara jawo hankalin sa ga Halimen dake bashi abinci ita babu ruwanta zama take ya koya mata abu. Ba a karatun kawai ba, rainon cikinta ma na tafiya yanda ya kamata. Dan yanzu kam laulayi ya ragu sosai. Sai cika da kara ƙyawun dake firgita Mom kawai take zubawa. A hankali iya shegenta ya fara dawowa sabo fil a gidan yanzu tun randa ta kama Mom na zuba magani a abincin Abba. Aiko ta fara raira waƙar, (Ashe makashinka yana nan tare dakai duk inda kake ya bika ga kaina ka riƙe min alƙawari karka sake Imamu na) tun Mom na shareta har dai ta tsargi kanta ta tanka mata. Tana shirin shaƙota ta daka uban tsalle gefe da zazzaro ido waje. “Ni Halime, Yaya rufamin asiri ina ni ina dambe da ɗan masu gida kwance a mahaifa. Irin wannan jan salalan tsiya ke mai biyar rigis kamar kin saro a kurmi ni ɗan ɗayan ma dako iskar duniya bata sha ba ko ya sha na biye miki ya watse. A'a rabani watsiya Yaya Jalilah”. Ta mata kallon banza ta shige ɗaki. Ji Mom tayi kamar ta shaƙo wuyan Halime har cikin ɗakin, wannan yarinya ita dai ta zama mata jaraba da bala'i. Ji take kamar ta wanke banza da tafasasshen mangyaɗa ko ruwan zafi kowa ya huta. Ga damuwar rashin jin Baby ta fara taɓata. Ga batun Musaddiq yi take amma har yanzu babu wani motsi. Hakama Samraah yanzu kusan kullum sai taji suna waya da Abba ko Halimen. Nasara ɗaya taci shine maida aurenta da Abba yayi. (A haukarta aikintane yaci Abba ya maidata🥱). ✨✨✨✨✨ Isowarmu gida da abinda na tarar ya goge min dukkan abinda muka shigo da shi na damuwa. Sosai nayi matuƙar mamaki da ganin irin gyaran da akama sashen namu. Daɗin daɗawa yabi shawarata ya dawo da Ummie sashensa. An gyara mata nan ƙasa shi kuma nasa ɗakin har ma da nawa a yanzu suna sama. A saman ma katafaren falo ne ashe bana wasa ba. Sai bedrooms guda uku. Yanda aka tsara shi da kayan more rayuwa ya matuƙar saka zuciyata yin rauni har sai da ƙwalla suka cika min idanu. Rasa ma abinda zance masa nayi, sai kawai naita kallonsa. Gira ya ɗan ɗage mun alamar kallon fa?. Kasa jurewa nayi naje na faɗa jikinsa kawai na saki kuka. Ban taɓa sanin zanga irin wannan ranar ba. Ban taɓa sanin zan iya bama mutum kamar Maash shawara ya amsheta ba. Sosai ya rungumeni shima batare da yace komai ba. Mun jima a hakan kafin ya ɗagoni, a cana ƙasan maƙoshi ya ce, “Kukan bai isa ba?”. Maimakon amsa masa sai na sake sakin kukan. Hancina ya ja kaɗan da sake faɗin, “Nifa ba'a min kuka”. “Toni ba kai nake wa ba ai”. Na faɗa ina tura baki. “Humm” kawai yace.. Da dare ina ɗakin Ummie na nan sashen nasa a yanzu, ko nace ɗakinsa na da dan daga su biyu ne kaɗai bedrooms anan ƙasa dama muna ɗan hira da Mama balki dake ƙarasa saka kayan Ummien a closet nake tambayarta asibitin Hajiya ƙarama na waye?. Kallona tayi da mamaki, sai kuma tai ƴar dariya. “Miyasa kika tambaya?”. “Haka nan Mama. Kawai ina son sani ne. Dan naga asibitin na kuɗi ne kuma kamar itace ke controlling ɗinsa.” Ajiyar zuciya Mama ta ɗan sauke. Kafin ta cigaba da faɗin, “Asibitin Ummie ne. Dan itace ta gina mata shi da kanta. Da farko ƙaramine, daga baya Abbie ya gyarashi da sake faɗaɗa shi. Shima kuma Alhaji ƙarami ya sake ƙawata shi a shekarun baya. Irin kulawa da shaƙuwar dake a tsakanin Ummie da Hajiya ƙarama bayan haihuwar Alhaji ƙarami ta damƙashi a hannun Hajiya ƙarama ɗin. Sai yazam itace mai kula da komai kuma har yanzu ba'a taɓa canjawa ba. Dan a dalilin asibitin ne ma ita Ummien ta sake tura Hajiya ƙarama ta ƙaro karatu har ƙasar India, daga Nurse ta koma cikakkiyar likita”. “Kenan yanzu kuɗin shiga da fitar asibitin a ƙarƙashin ikon Yaya Awwab suke?”. “Eh to, haka ba haka ba gaskiya. Dan duk da asibitin na kuɗine kusan komai ana yinsa ne kamar ƙyauta. Sai dai a dalilin kayan aiki da suke da shi yasa aka ware vip saboda masu hannu da shuni. Sai ya zama kuɗin ana amfani da su ne kuma ta hanyar taimakawa marasa lafiya musamman waɗanda tai tsamari sai an fita da su ƙasashen waje. Sai kuma biyan ma'aikata albashi da ɗan abinda asibiti ke buƙata na gyara, amma bana jin gaskiya Alhaji ƙarami na amfani da komai na asibitin ne. Nasan duk wannan nan ne a dalilin mahaifinku tun asibitin bai kai haka ba. To daga baya dai bayan rasuwar su shi da Abie da kuma faruwar ciwon Ummie ban san mike faruwa ba gaskiya, har ya faɗaɗawa zuwa yanzu ban sani ba ko suna akan wannan tsarin. Sai dai ko zaki tuntuɓi Alhaji ƙarami”. Kaina na jinjina mata cike da gamsuwa. Nasan kowa zai yi mamakin wannan tambayar da nayima Mama, to akwai dalili, abinda ya faru yau ya dawo min da wani abu da na ɗan taɓa ji sanda ina asibitin. Ana gobe za'a sallameni kusan ɗaya na dare fitsari ya farkar da ni. Bayan naje nayo sai nake jin duk kwanciyar ta isheni. Na buɗe ƙofa na fita dan na ɗan tattaka ko anan inda ɗakunmu suke ne. Ɗan tattakawar yasa naji daɗi sosai har ta kaini da ɗan fita. Shiga nake ko ina batare da nasan ta inda nake ba, har na gota wani ƙofa na dawo saboda jin ƙusƙus ɗin da ake yi a ciki kamar kuma ana faɗa wani kuma na kuka. Ta jikin windown na je naɗan maƙale. Sai naji muryar mace ce ke faɗan mai kukan ma mace ce. Mai kukan ke rantsuwa da ALLAH ita wlhy bata san yanda akai ba, kuma ita ba'a bata wani kuɗi ba akan hakan. Matar ta sameta ne kawai ta tambayeta aikin mi akama wadda suka fiddo shine ta sanar mata an cire mata appendix ne. Iya kuma abinda tace da ita kenan matar ta juya ta tafi.. wani irin mari aka sauke ma mai kukan da ni kaina saida na zabura, dan har tsakiyar kaina na jisa kamar ni aka mara. Cikin masifa wadda tayi marin da zagi ta ce, “To ubanki yace ki gaya mata koma mi aka cire ɗin. Nawa ake biyanku albashi a asibitin nan, a matsayinku na waɗanda na aminta da su muna aiki tare nawa nake baku a duk ƙarshen wata? Ya ninka abinda asibiti ke baku. Amma har kina da bakin faɗin abinda ba'a tambayeki ba. Kinga kenan zaki faɗi abinda ma yafi haka nan gaba ko?”. “Wlhy a'a maa. Dan ALLAH ki gafarceni wannan ma kuskure ne. Na kuma miki alƙawarin bazan sake ba. Kuma....” Tafiya da naji kamar a bayana yasa na zabura na bar wajen. Zuciyata tata min kai-kawo da son jin ƙarshen zancen nan amma dole na haƙura na koma wani waje na maƙale, can sai ga yarinyar ta fito tana sharar hawaye, naji daɗin ganin fuskarta, amma ban mata magana ba na bar abin akan saina warke. Nata jujjuya batun da cuɗawa da kwancewa amma ban iya na haɗa komai ba. Sai kawai na binne maganar a raina na cigaba da harkoki na, koda muka dawo gidan abubuwa kuma sukai yawa sai na manta. Sai yau ne da naji yana batun tura wani yin aiki asibitin matsayin bincike abin ya dawo min a rai. Lallai akwai abinda ke faruwa a asibitin nan, amma yanzu in sha ALLAHU da yayi tafiyar nan nima zanyi nawa hoɓɓasa.q.... Maganar Mama ta katse min tunani. Firgigit na kawo numfashi tare da sauke ajiyar zuciya. Koda na ɗago sai naci karo da shi tsaye ya zuba min ido kawai. Numfashi na ƙara saukewa tare da masa sannu. Dan tun bayan dawowar mu baifi da ƴan mintuna ba ya fice sai yanzu yake dawowa kusan sha biyum dare. Bai ce dani komai ba, sai hankalinsa da ya maida kan Ummie dake barci........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 .......Shigowarsa gidan kenan yaci karo da commondo na jiransa. Duk da a gajiye yake tiɓis ga dare yayi hakan bai hanashi zaman saurarensa ba. Kamar ko yaushe cikin girmamawa commondo ya gaida shi. Tare da ɗorawa da bayaninsa. “Boss bayani ne nazo da shi dan na kasa haƙurin haɗiyewa har na kammala binciken nan.” Cikin ƙara nutsuwa Baba prof ya ce, “Tofa ina saurarenka miya faru?”. “Akan ahalin yarinyar nan ne, brothers ɗinta biyu da nake faɗa maka bincike ya tabbatar da suna anan Lagos. Ɗaya makanike ne. Watanni bakwai da suka wuce sabon companyn Maash dake Kano sun ɗauke sa aiki........” “Whatttt!!! Maash Company?” “Humm boss ai ban kai the end ba. A yanzu haka zancen da nake maka ma sun turashi karatu ƙasar ƙetare, ban dai gano ƙasar ba. Kuma jirginsa ta nan Lagos ya tashi ma. Abinda kawai bamu tabbatar ba shin da sanin Maash ɗin ne ko kuwa companyn ne tunda sun ɗauki yara kanikawa aiki da yawa bashi kaɗai ba. Shi kuma ɗayan yana cikin Lagos ɗin nan har yanzu, a ina yake shine ban sani ba. Amma dai inaga ka bincika a cikin Maash Mansion tunda har yarinyar na gidan to tabbas shima dole za'a sameshi a ciki” Rasa ma abin cewa Baba prof yayi tsabar shock ɗin da yake a ciki. Da ƙyar ya iya motsa hannunsa ya ɗauki wayarsa domin tabbatarwa. Layin Hajiya Mammah ya kira. Bugu biyu kuwa ta ɗaga. Ko takan gaisuwar da take masa bai bi ba. Kai tsaye ya ce, “Nafisa! Kuna da baƙi a gidan nan ne daga sati ɗaya zuwa yau?”. Ɗan jimm tayi alamar tunani, sai kuma ta ce, “Eh tabbas kamar haka kam Baba. Naso ganin baƙon saurayin yaro a rikicin faɗan shekaran jiya na Fahad. Inata so nai magana sai abubuwa suka ɗauke hankalina. Yaron ma kamar yana kama da yarinyar nan matar Hayatu. Dan ni da farko ma wlhy na zata itace sai da na sake kallonsa naga namiji ne shi. Ban kuma sake ganinsa ba tun ranar sai yau ɗin nan. Nama kira ka ɗazun na faɗa maka iskancin da yaron nan ya ƙirƙira. Ashe gyaran da yake yi uwarsa zai maida sashen nasa. Ɗazun nan na dawo su Azizat ke sanar min ai an maida Hajiya Babba sashen Yayansu. An kuma kwashe kayan sashenta duka da alama aiki za'ayi”. Ita ke bayanin amma zuciyar Baba prof ke bugawa da sauri-sauri. Babu shiri ya yanke kiran tare da dafe kansa dake wani kalar masifar juya masa. Cikin mamaki Commando ke tambayarsa ko lafiya? Bai amsa masa ba har tsawon lokaci. Kafin ya miƙe yana faɗin, “Kaje zan neme ka. Ance min akwai yaro a gidan zanje na bincika da kaina”. Miƙewa kawai Commando yayi, dan yasan idan ran ogan nashi ya ɓaci baya son ko magana. Amma idan ya huce da kansa ma zai iya kiransa a waya koda a daren yau ne... Da ƙyar Baba prof ya iya kai kansa ɗakin barcinsa. Yana isa ya wani zube a gado hannunsa dafe da ƙirjinsa. Wani irin zafi mai tururi yake jin yana masa sosai. Dan ko iya haka bincike ya tsaya ta tabbata Awwab shine ya auri yarinyar nan?. Amma ta yaya hakan ta faru? Yaya akayi? Yasan wacece yarinyar ko kuwa shawarar daya bashi ce yasa shi komawa ya auretan? To amma idan har hakanne miyyasa zai koma ya aureta bada saninsu ba? Sannan mizai sa ya ɓoye yayin auren nata a matsayinsu na iyayensa? A barsa ma ya ɓoye ya aureta, minene na shigo da ita gidan matsayin mai aiki har ya ɓoye musu wacece ita? Dolene yana buƙatar bincikar Mu'azz kenan a wannan gaɓar, dan yasan ko zai mutu Awwab sai ya gadama sai masa bayani. Karfa yaron nan ya zame masa ya kashe maciji bai sare kansa ba. Dan abubuwa sun fara canja kansu a tsakanin shi da shi tun akan zancen buɗe Companyn nan na Kano. Idan har baiyi ƙarya ba rabon da Awwab ya ɗaga waya ya kira shi har ya manta. Sannan yanzu sam baya sanin al'amurrasa kamar da da kowanne motsinsa sai ya sanar masa ko neman shawararsa. Mi hakan ke nufi kenan? Lallai yana buƙatar ajiye kwalaben giya ya dawo a hankalinsa. Dan ada farko tunaninsa na nuna masa kawai dai Awwab ɗin yayi busy ne a tsakanin nan, to ashe ba haka bane. Eh dole a yanzu yace ba haka bane. Dan idan ya haɗa 1+1 fa zai iya samo amsar tambayarsa. Anya kuwa yaron nan Jaga bai jiƙa musu aiki ba kafin mutuwarsa. Dole ne akwai abinda Commondo bai sani ba, dan a dalilin Jaga ɗin kawai suka samu ɓaraka..... Akasin lissafi baba prof 🥱😎. 🪴🪴🪴🪴 Washe gari da kaina na haɗa mana break fast. Na gyara sashen da taimakon Mama duk da inata hanata amma taƙi. Har nayi wanka na gyara jikina bai dawo gidan ba tun fita motsa jiki da yay bayan dawowarsa massalaci. Ummie naje na bama abinci da sabbin magungunan wajen Malam. Ina a haka sai ga Fahad da Hafizzullah. Sanye suke da sports wears suma. Hakan yasa na gane suma fita sukai motsa jikin kenan. Bayan mun gaisa nake tambayar Hafiz batun komawa school. Ya ce min yayima Yaya Hayat magana amma yace ya dakata zai koma a acikin satin nan in ji Yaya Awwab. Ban sake cewa komai ba suka fita da shirin zuwa suyi wanka su dawo suyi break fast. Bayan fitarsu shima na fita duba shi. Sai na samu ya dawo har ma ya shiga wanka. Kofar bayin na harara, tare da fitowa a ɗakin baki ɗaya, yanzu daban zo ba bazan san ma ya dawo ba kenan. Ɗakina na koma na ɗan ƙara gyara inda zan gyara a kwalliyata sannan na sake fitowa. Ina ƙoƙarin sauka ƙasa sai gashi ya fito. Tare muka sauka ƙasan, direct kan dining dana shirya abinci ni na wuce, shi kuma ya leƙa Ummie. Bai jimaba ya fito. Da kaina naja masa kujera ya zauna sannan na fara buɗe masa abinda na shirya. Kallona kawai yake yi baice komai ba. Baki na ɗan tunzura, sai ya ɗauke kansa kawai ya nuna min doya. Ban damu ba, dan na fahimci yau yan miskilancin ne a kusa. Koda yake tun ma juya dai ransa a ɓace yake. Dan kusan raba dare yay yana aiki, na farka kusan 3 na gansa kuma yanata salla. Ina gama saka masa nima na saka. Dai-dai nan su Fahad suka shigo. Ƙoƙarin ajiye spoon yake nai saurin dafe hannunsa. Murya a raunane na ce, “Dan ALLAH kada ka tashi, ka daure kaifa uba ne. Sai kana ƙoƙarin tausar zuciyarka kaita karanta Hasbinallahu wa-ni'imal wakil da izinin UBANGIJI babu abinda zai faru.” Baice min komai ba, amma bai tashi ba. Har cikin raina naji daɗin hakan. Dan haka na maida hankali kan Fahad da shima suke gab da zuwa ya juya zai koma da alama sai yanzu ya lura da shi. “Yaya Fahad!”. Na kirashi kamar zanyi kuka. Tsayawa yayi, sai dai bai juyo ba. Cigaba nayi da faɗin, “Zo ka zauna dan ALLAH. Yau fa favorite ɗinka nayi a gidan nan. Haba autan Ummie ƙanin Yaya Hayat ɗan Mama da Paah. Sannan Yayana ni kaɗai” Sai da yaja mintuna kafin ya juyo yana kallona kamar zai yi kuka. Nima sai na marairaice masa fuska kamar zanyi kukan na ce, “Dan ALLAH ”. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi, tare da tahowa yaja kujera shima ya zauna kusa da Hafiz yana jan sirrin tsaki. Ɗagowa Maash ɗin yayi idanunsa har sun sauya kamanni. Da sauri na dafe masa hannu ina girgiza masa kai, ƙasa-ƙasa na ce, “Please”. Cin abincin ya cigaba da yi bai sake magana ba. Dan haka dining ɗin yay shiru sai motsin cokula dana filet. Munyi nisa da cin abincin kawai mukaji ana knocking. Hafiz ne ya miƙe ya nufi ƙofar ya buɗe. Da ga inda muke muna jin yanda ya gaishe da mai knocking ɗin amma babu alamar an amsa masa. Kamar ma babu motsi. Juyowa Hafiz ɗin yay yana kallonmu. Kansa tsaye ya ce, “Yaya Baba ne”. Ɗan jimmm yay kamar mai tunanin wane Baba, sai kuma ya ɗan kallan, ganin ya sake ɗauke kansa na fahimci so yake yaga koda mayafi jikina. ALLAH ya soni akwai. Cema Hafiz ɗin yay ya shigo, ya sake maida kansa ga abincin. Hafiz dai ya isar da saƙo, amma har ya dawo ya zauna ba'a shigo ba sai da Fahad ya miƙe yaje. “Oh ALLAH Grandpa wai kaine da ma?.” yay maganar da kamo hannunsa suka shigo. Kallo ɗaya naima tsohon na fahimci a cikin shock yake. Sai kawai abin ma yaso bani dariya. A take kaina ya kawo wuta. Kaina tsaye nace ma Fahad, “Fahad kuzo nan Baba yaci abinci”. Murmushi ɗauke a fuskar Fahad kuwa yazo da shi har dining. Gogan kam tunda ya maida kansa ya duƙan bai sake kallon kowa ba abincinsa yake ci kamar baya so. Gaishe da Baban nayi ina ƙoƙarin zuba abinci a plate. Yanda ya amsa min kamar wanda ke'a cikin shakku har yanzu ya sani sakin murmushi da faɗin, “Baba ga abinci a saka mana albarka”. Murmushin yaƙe yayi, tare da jinjina kansa alamar to, daga haka kowa ya cigaba da cin abincinsa. Sai zuwa can a bazata mukaji ya ce, “Good morning ”. Mu dukanmu sai da muka kallesa, musamman ma Baba prof ɗin. Murmushi ya saki mai nuna tsantsar taɓuwar zuciyarsa. Kafin ya ce, “Ai na zata baka ganni bane.” A mamakin mu sai Maash ɗin ya saki wani makirin murmushi. Kamar bazai ce komai ba sai kuma a hankali ya furta, “Wani abu ya faru a gidan ne na ganka da sassafe?”. Ba baba prof da yay ma tambayar ba hatta ni dake saurarensu sai da na shiga shock. Dan bai zama lallai Hafiz da Fahad su jisu ba sun ɗan yi nesa da mu, sannan hankalinsu nakan waya ne alamar akwai abinda suke kallo........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_ .......A mamakina murmushin Baba prof ɗin ya ƙara saki, sai kuma ya kai hannu saman kan Maash ɗin ya wani ɗan birkita sumar da yau bai ɗaure ba. Cike da son danne komai da fuskarsa ke son bayyanawa ya ce, “Ja'iri, dama sai wani abu ya faru nake zuwa da sassafe?. Kwana biyu ban zo naga daughter ɗina bace. Nayi busy da yawa shiyyasa yau dana samu chance nace bari na shigo”. “Hummm”. Kawai Maash ɗin yace. Bakin Baba prof ɗin ne ya motsa kamar zai yi magana sai kuma yay shiru sakamakon shigowar Hajiya Mammah. Mu duka kallonta mukai banda gogan. Harara ta zuba mana ta ɗauke kanta. Niko sai na fuske nace mata “Mammah ina kwana”. “Daban kwana ba zaki ganni ƴar tsirku. K! K! Ki kiyayeni ki fita idona. Wlhy idan kika bari na waiwayo kanki tofa kin shiga dubu bama uku ba. Idan su waɗan nan sihirinki ya cisu to ni bai cina. Dan nafi ƙarfin iyawarki nima shegiyar kaina ce nan da kike gani. Haba wace irin masiface wannan yarinya kin zame mana ƙadagangaren bakin tulu. Ƙiri-ƙiri kin mallake uwa da ƴaƴanta ke ga ƙwalluwar tantiriya. To wlhy yau sai kin bar gidan nan da ƙafafunki”. “Ko kuma ke ki bar mata ba. Wai ke Mammah minene matsalarki? Masifa dai masifa dai kamar grandma. Ita mun samu ta mutu mun huta da nata jaraban ashe ta bar mana gadon ki. Can kin ishi mijinki ya koroki kin zo nan kin dame mu. Ina ruwanki, ba mallakewa ba tama haɗa wuta tayi farfesunmu ta cinye a cikinta ai dai ƴar uwarmu ce. To bari na baki labari wannan tana da matsayi mai girma a wajen mu. Dan har abada bazamu taɓa wulaƙanta zuri'ar Uncle Abdul-wahab ba. Ke kwanan nan ma zaku ganta matsayin matar aure a gidan nan kin ishe mu”. Ya wani ture plate ɗinsa ya bar wajen yana jan hannun Hafiz. Mu dukanmu da kallo muka bisa, a raina tausayinsa na kamani, dan na fahimci shi Fahad sona yake. A mamakina sai naga gogan da tun da aka fara ihun yake ma latsa waya ya wani saki murmushi. Yayinda Hajiya Mammah ta kira sunan Fahad da ihu sosai. Amma tsabar wulaƙanci sai da yaje ƙofa ya juyo ya harareta da faɗin, “Kin je kin kira Grandpa to shima sai dai ya sake share musu waje dan yasan muhimmanci Uncle Abdul-wahab idan ke baki sani ba. Amebo woman a canja hali.” ya mata gwalo ya fice. Haukacewa ne kawai Hajiya Mammah batai ba saboda azabar masifa. Dan har sai da takai Paah da Uncle Abdullahi sun zo sashen, can sai ga Maman Malika da Hajiya ƙarama. Kuka sosai Hajiya Mammah keyi wai Fahad ya zageta ta uwa ta uba kuma nice na sakashi. Sannan Awwab na zaune baice masa komai ba. Ita wlhy yau bazata yarda ba sai ta bar gidan nan. Har kamar ita Fahad zai wulaƙanta saboda tana zaune a gidan uwarsa. Ta ma fahimci Paah ne ke sakasu musu rashin mutunci. Rai a ɓace Paah ya ɗaga mata hannu da faɗin, “Point of correction Addah, nifa ki daina sakani a sabgarki da yaran nan yanzu. Dan kin fimu sanin mike tsakaninku. Bafa rami babu abinda zai kawo rami. Dan haka a can da kuka ƙulla ku warware kanku.” “Ni kake gayama haka Mu'azz? Ni kake gayawa magana akan ƴaƴanka?”. “An gaya miki Adda, wai yaya kike son nayi ne nikam. Dan ALLAH ku barni da abinda ya dameni. Nifa gaskiya nama fara gajiya da zaman kowa a gidan nan. Idan akwai matsala ne kowa ya koma inda ya fito mana. Ai nan ɗin su gidan mahaifiyarsu ne. Bamu da wani dalilin kuma zuwa mu tare a cikinsa. Koni da nake auren Ummu-Hidaya idan bata yarda na zauna mata gida ba bani da wani ƙarfin ikon yin hakan. Idan ance Awwab nada taurin kai kowa yasan Fahad a gidan nan na kowa ne. Amma gashi nan shima kuna neman kangarar min da shi bai shakkar kowa bai kunyar kowa a yanzu. Baba ya kamata kayi wani abu a wannan karon, idan ba hakaba magana ta ALLAH ka cigaba da shiru ana cigaba da aibanta min yara tofa ni da kaina zan ɗau mataki wlhy, dan ina sonsu fiye da komai, zan kuma tsaya na kare musu mutuncinsu kamar yanda kowa ke kare mutuncin nasa ɗansa. Da ɗin ma ina muku kawaici ne kawai amma na fahimci Adda bata san kawaici ba. Kai kuma a matsayinka na babba baka taɓa ganin laifinta balle ka tsawatar mata. Sai kace wai a barta da halinta ta gado Mama ne. Mama ai uwace a garemu zamu iya haƙuri da ita amma ita ɗin fa. To na gaji kowa ya koma inda ya fito kawai a barsu a gidan mahaifiyarsu su huta suma”. Yana gama faɗa ya fice fuuuu harda bugo ƙofa da masifar ƙarfi. Yanda falon yay tsitt zai baka tabbacin kowa yayi sumar wucin gadi ne. Idan ka cire mai gayya da aiki da har yanzu yake faman latse-latsensa a waya daɗa duniya baya a wajen ne. Fuskokin kowa na fara bi da kallo. A mamakina Uncle Abdullahi murmushi yake yi. Hakama matarsa. Amma Hajiya Mammah, Hajiya ƙarama, baba prof ba'a magana. Hajiya Mammah dai hawaye take sharewa (gaskiya sai anyi shari'a, taya za'a saka gimbiya mandiya Hajiya Nafisatu bint Adams kuka😂😝). Hajiya ƙarama kam kamar jikinta rawa yake, ga wata irin zufa ta jiƙeta kamar ba ac a falon. Haka ma Baba prof zufa kawai yake har jikin hularsa ta nuna shatin laima, kansa dai a ƙasa baka ganin idanunsa da fuskarsa da ƙyau. A hankali na zare jikina daga wajen na shige ɗakin Ummie, a laɓe na samu Mama da alama itama show ɗin take kallo. Murmushi ta sakar min dan haka nima na maida mata murtani. Sai tamun jinjina. Dariya abin ya bani na ce, “Kai Mama. Ai ɗanki ne abin jinjina. Jibafa yanda yake zaune kamar baima san ana komai ba ya bama banza ajiyar kowa. Ga kuma Auta ya tunzura ya gudu. Ashe shima haka yake?”. Ƙaramar dariya tayi da faɗin, “Ai hakan shine dai-dai. Dama shi Alhaji Ƙarami haka yake musu ya manna musu hauka ya watsar da su musamman a tsakanin nan na rasa miyasa. Fahad kuwa ai da zafinsa ya dawo da alama addu'armu na karɓuwa. Alhaji Mu'azz bai taɓa birgeni a rayuwa irin yau ba. Bawan ALLAH ashe shima yana ƙaunar ƴaƴansa. Ni kam zargina ya fara barin kansa. Amma bakiga murmushin da Alhaji Abdullahi da Maman Malika suke ba”. “Na gani sarai, amma abinda zai baki mamaki su kamar babu wata damuwar komai tare da su sai ma daɗi da suke ji”. “Tabbas naga hakan. Amma mutum ne baka yarda da shi sai yazo ya maka kwaf ɗaya. Shi kansa Paah ɗin sai fa naga ƙuru-ƙuru baida laifi zan yarda”. “Haka ne kuma gaskiya Mama, ALLAH dai ya daidaita Yaya da Fahad a fara aikin Maja”. “Amin ya rabbi ƴar albarka. Ai kece ginshiƙin komai” Hannu nasa na rufe fuskata ina murmushi. Jin shiru alamar sun bar falon yasa na fita. Har yanzu gogan na wajen zaune. Tattare kayan na shigayi. Batare dana ce masa komai ba nima. Ina kitchen ina wanke kwanikan da muka ɓata ɗin sai gashi ya shigo. Ni tsoro ma naji da farko. Dan yazo gab dani ne ya tsaya. Koda na juyo har karo muka ci. Da ga ni har shi sai da kowa ya dafe inda ya bugu. A ɗan shagwaɓe na ce, “Yaya ALLAH ka bani tsoro. Mi kake so?”. Cikin tsareni da idanun nan nasa ya nuna min lips ɗina. Sosai na waro nawa idanun, sai ya ɗaga min gira. Kunya ce ya kamani. Nai ƙoƙarin juyawa amma ya hana hakan. Mun ja kusan minti uku a wajen dan sai da yay yanda yaso sannan ya janye lips ɗin nasa daga nawa. Hakan ya sani faɗawa jikinsa na rungumesa dan ƙafafuna ma ji nake sun gagara ɗaukata. Nan ma munja kusan minti biyu kafin na ɗago a hankali. Ina ƙoƙarin juyawa ya dakatar dani. Muryarsa a shaƙe ya ce, “Inaga zamu wuce yanzu”. Da mamaki na kallesa na ce, “Ina?”. “Nema mana”. Sosai naji gabana ya faɗi, ni har ina murna ya ɗan rage tafiye-tafiyen tsiyar tashi ashe ba haka bane ba. Kuma tsabar manni irin na mutumin nan ace zakai tafiya amma sai yanzu kake sanarma matarka. Jinai raina ya sosu. Amma sai na daure na danne na masa murmushi. Dan na fahimci nice zan canjasa, amma yanzu ban isa cewa ga yanda nake so ba tunda a haka ya tashi komai sai a hankali. Addu'a na shiga masa da fatan nasara. Yanda yake lumshe idanunsa nasan addu'ar ta masa daɗi. Sake rungumeni yay kusan na mintuna biyu kafin ya kamo hannuna muka fito. A falo muka samu Hayatu da Mama na magana. Dan haka nai ƙoƙarin zame hannuna a cikin nasan amma ya hana hakan. Gaba ɗaya naji kamar na nutse, da ƙyar na iya gaida Hayatu da tun kallo ɗaya da yay mana ya ɗauke kansa. Mama ko bama ta nuna taga mi muke ciki ba, sai addu'a take kwarara masa. A hankali ya amsa mata da amin tare da godiya. Sannan ya ɗora da faɗin, “Mama Falaq zata dawo gida ta haihu. Inaga sai a saka a gyara mata bedroom ɗin nan na kusa da Ummie. Sannan za'a kawo sabbin masu aiki nan sashen.” Murmushi Mama tayi da satar kallon Hayatu da ya ɓata fuska yana kallon Maash ɗin. Kamar zai fasa ihu ya ce, “Yaya nace maka a camma fa babu wata matsala”. Hararsa yayi da faɗin, “Na gama magana. Idan ta haihu ka ɗauketa kuma tafi bangon duniya, yanzu dai zata dawo gida ta haihu”. Dariya abin nasu ya bani, nai ƙasa da kaina ina murmushi. Mama ma ina ganin tana murmushin, yayinda Hayatu ya cika yay fam.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚_ .......Hannuna yaja muka shiga wajen Ummie, tana zaune shiru abinta ta zubama television da ake karatun Alkur'ani ido dan yanzu haka muke yini da kwana da karatu. Har gabanta mukaje muka durƙusa, ya kamo hannunta ya riƙe cikin nashi. Juyowa tayi ta kallemu, sai kuma ta kalla hannunsu ta kuma maida ta kalla nawa da nashi dake a haɗe. Ta jima tana kallon hannayen namu kafin ta ɗauke kanta. Yanda yake mata magana da roƙon ta masa addu'a sai da naji hawaye sun cika min ido. Haka dai muka fito batare da tace masan komai ba. Sai dai har cikin raina naji daɗi da banji yayi complain kansa na ciwo ba yau. Alhamdullahi hakan na nuna ALLAH na amsar addu'armu... Har waje haka ya fita hannuna a cikin nashi. An gama shirya motoci harda ƙyamishashshiyar baturiyar nan. Ashe har lokacin Baba prof na gidan. Dan muna fitowa shima yana fitowa tare da Uncle Abdullahi da Hajiya Mammah. Ko kallon inda suke baiyi ba, sai ma jinginani da yay jikin motar ba kunya ya sunkuya ya sumbaci goshina da lips ɗina. Inaga tunda nake a rayuwata ban taɓa shiga cikin kunya irin yau ba. Tabbas na yarda mutumin nan bai san kunya ba. Compound ɗin da mutanene sosai. Masu aiki, su baba prof, su Hayatu kai jama'a ina cikin jalala ni dai. “Hafiz zai biyomu zuwa jibi in sha ALLAHU. Dan na canja masa school. Barinsa a Nigeria yanzu akwai haɗari saboda za'a iya amfani da shi domin cin dundumiyar mu. Ta ko ina bana san ya cutu akan laifin da ba nasa ba. UBANGIJI ne bangona. Ke kuma kece Hope ɗina Samrh. Dan zan barki ne matsayin tarko. Ga Ummie nan, ga Fa.. ha ..d nan”. Ya fadi sunan a rarrabe da ƙyar. “Dan ALLAH motsin kowannensu na dinga sani, suma tarko ne. Duk abinda kike buƙata ga TJ nan ga Shu'aibu. Ki faɗama Fahad zai samesu. A yanzu tako ina a sashen nan akwai camara da securitys, da ɗin ma dan bana zama ne babu kowa shiyyasa. Yanzu ko nasan ina da Tiger a gida na ko?”. Yanda ya ƙare maganar ne ya sa nayi dariya. Shima sai ya murmusa. Ba ƙaramin shock na gani a fuskokin wasu da murmushin nasa ba. Koda ya shiga mota da aka buɗe mosa sai naji kuma duk babu daɗi, kaina a ƙasa na sake jera masa addu'a. Lips ɗinsa ne kawai ke motsawa alamar Amin. Kafin a hankali yace, “Wuce kije ciki”. Banyi masa musu ba na juya na tafi, sai da naje zan shiga na juyo, a kan iska na rubuta masa (I miss you) na shige abina ina murmushi idanuna cike da ƙwalla. Tabbas na yarda sabo ake ma kuka ba mutuwa ba. Cak na tsaya ina kallon Ummie dake jikin window ɗin falon tana leƙen komai. Harga ALLAH sai da naji shock. Amma sai na dake na nufeta ina share hawayen nawa. A mamakina ina zuwa gab da ita ta buɗe min hannayenta alamar nazo gareta. Ai da gudu na ƙarasa na shige jikin nata ta rungumeni tsam. Tana jin motsin tahowar mutane ta sakan da sauri ta nufi ɗaki. Sagade nayi a wajen uwa wadda ta suma. Har sai da Mama Balki ta taɓani sannan na dawo hayyacina. Murmushi tamun da faɗin, “Ko dai nace ya dawo ɗiyata zata bisa”. Kaina na duƙar ina murmushi yaƙe, sai kuma na nufi ɗakin Ummie da ɗan gudu. Tabbas naji kunyar maganarta, amma ba shine maƙasudin gudun nawa ba. So nake naje na sake tabbatar da abin al'ajabin dana gani. Shin Ummie ɗin ce ko kuma gizo tamun yanzun nan. Kwance na sameta tamkar mai barci, sai gaba ɗaya na sake jin kaina na neman juyewa. Koda mama Balki ta shigo ta tambayan barci take. Kaina kawai na iya ɗaga mata dan ban san abinda zance ɗin ba nikam. Da ga ƙarshe ma sai na fito a ɗakin na haura sama...... 💢✨💢✨💢 Maimakon gida guesthouse ɗinsa ya wuce. Inda yakan daɗe baije ba saboda wasu dalilai. Gaba ɗaya ko gani bayayi da ƙyau. Yana shiga ciki Hajiya ƙarama ma na isowa. Dan biye take da shi a baya batare da ya sani ba. Koda ta shigo falon da farko shiru yay baima nuna yasan da zuwan nata ba, sai da taga shirun yayi yawa ta fara magana cikin muryarta dake nuna tsantsar tashin hankalinta. “Tabbas yallaɓai muna a cikin tashin hankali. Gaba ɗaya a kwanakin nan abubuwa taɓarɓarewa suke neman fara yi. Irin wannan na guda shiyyasa tun samun lafiyar Ummu-Hidaya na farko nace maka muyi abinda ya dace, amma kaƙi fahimtata. Wlhy idan bamuyi wani yunƙuri ba a wannan gaɓar da wuri to fa lallai wankin hula na gab da kaimu dare. Dan zuciyata ta fara kaini ga zargin anya kuwa yaron nan Awwab baya biye da mu? Dan take takensa a wannan gaɓar sun fara bani tsoro. Sannan kaga wannan ifiritiwar yarinyar daya kawo ya ajiye wlhy shaiɗaniya ce. Kuma tabbas aurenta yayi, idan har abinda ya faru a farko ya zama kuskure to bayan faruwar hakan ya aureta dan ya binne abinda ya faru. Idan kuma zamuyi tunani na hankali ance tana da aure, dan ya mata fyaɗe a kuskure kuma zai aureta ne da aurenta? Duk yanda muke son sakama ranmu ba haka ba to tabbas fa tun farko Awwab shine mijin yarinyar nan. Shi kansa Mu'azz abunuwansa na kwanakin nan sun fara bikita min lissafi da har nake ganin dole akwai abinda ya sani, sai dai ban sani ba ko ya shafemu ko ba haka ba. Ka duba yanda yaron nan shima Fahad ya dawo a fetsare kai kai lallai muna buƙatar dawowa cikin hankalinmu, dan wlhy ɗayan biyu ne. Kodai aikin dake jikin kowa ya fara barinsa, ko kuma sun san abinda ke faruwa....” Wani irin watsi da kayan saman Centre table ɗin Baba prof yayi, kafin cikin matsanancin tsawa ya ce, “Lawusa!! Get out of my house now!!”. “Yallaɓ....” “I say get out!!!!”. Jitai gaba ɗaya illahirin jikinta na rawa. Dan idanun baba prof ɗin sun gama jirkicewa sun juye gaba ɗaya. Fuskarsa ta wani irin canja gaba ɗaya tsufansa ya bayyana kansa. Tunda take da shi bata taɓa ganin matsanancin fushisa irin na yau ba. Tafiya take a gwagwgwame tana waigensa. Tana zuwa compound ta afka motarta ta tada. Ai a guje tabar gidan batare da ita kanta tasan mima take yi ba. Sai da tayi nesa da gidan ta samu waje tai parking. Ruwa ta fisga ta hau kwankwaɗa, sai da ta sha fin rabi kafin ta kifa kanta jikin steering tana sauke numfashi a harɗe. Mike damun tsohon nan ne? Shi indai yana a cikin fushi gaba ɗaya sai kiga ya juye mahaukaci. Tun fa da sauran ƙuruciyarsa haka yake da wannan halin mahaukatan. Ya kamata ace ya nutsu mu tattauna musan mafita amma haukar tashi na neman motsawa. Magana ta gaskiya idan naga zata ƙure bafa zan zauna ta kife da ni ba. Amma shike nan duk wahalar da nayi ta tsahon shekaru ta tafi a banza kenan. Kai impossible. A zuciyarta take ta faman ƙullawa da kwancewar nan ita kaɗai. Tafi awa guda a haka kafin ta tada motar ta cigaba da tafiya. Ba gida ta nufa ba, kai tsaye cikin Agege ta nufa. Ta ɗan yi zurfi a anguwa sosai kafin ta samu waje tai parking. Wayarta ta ɗauka tayi kiran layin Commondo. Kamar bazai ɗauka ba sai tana gab da tsinkewa gashi ya ɗaga. “Ina anguwarku, ta wajen wani shagon saloon ka sameni Please idan babu damuwa. Gashi zan ɗauka hoton wajen na tura maka ta WhatsApp”. Banji mi akace da ita tacan ba. Ta dai yanke kiran bayan ta amsa da okay gashi zan tura. Mintuna kaɗan kuwa wani mai sanye da p-cap daya rufe fuskarsa sosai ya buɗe motar ya shigo. Ajiyar zuciya Hajiya ƙarama ta sauke, tare da kallonsa dai-dai yana cire p-cap ɗin. Shima kallonta yayi tare da kashe mata ido ɗaya cike da salon taƙadaranci ya ce, “Yau tsohuwar love ce ta tashi halan Lawy Baby”. Harararsa ta ɗan yi ta ɗauke kai. Ya wani kwashe da dariyar mungunta tare da kaima kafaɗarta duka ya ce, “Ki gama zagaye-zayenki kema kin san bazaki taɓa ƙara samun jarumi kamar ni ba Lawusa. Dan tunda kike tare da ni kin taɓa kallon wata mace da suffar da kike kallonta yanzu. Jarumi kennan ba irin wannan lusarin mijin naki ba da ko ciki ya kasa baki kusan 18years. Kima shirya aikin nan na zama done no more mata a cikin rayuwar mu”. “Kai dai ka sani”. Ta faɗa cikin taɓe baki. “Kema zaki sani ai. Ina my sweet daughter? Ina fata baki takura min yarinya ko? Dan duk duniya a yanzu banda kowa sai Arwa. Itace farin cikina itace nishaɗi na a itace mafarkina. Dan a yanzu duk wahalar da nake wajen ganin na tara dan ita ne. Ina son duk randa zata kalleni a matsayin mahaifi tasan cewa eh na cancanta.....” “Hummm kaga ba wannan ya kawoni ba. Akwai matsala fa. Wawan tsohon nan nason raina mana hankali. Tana neman ƙwaɓewa amma ya zauna fushin banza da wofi a maimakon mafitar da zata ɓulle”. Yanzu kam serious commando ya koma.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒗𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_ .........A cije ya ce, “Miya faru kuma?”. “Humm! Miye ma bai faru ba”. Tsaff Hajiya ƙarama ta kwashe labarin komai ta bashi. Har korar da Baba prof ya mata yanzun nan. Ta ɗora da faɗin, “Nifa na fara tunanin tafiya plan b. Kawai mu kauda tsohon nan dan na gaji da harkar nan wlhy. Ina buƙatar zuwa na huta. Tuni da mun gama aikinmu amma tsohon nan sai raina mana hankali yake yana jammu a ƙasa, shi banda ma kansa a toshe yake a shekarun nan nasa an gama barbaɗa masa gishirin mutuwa uwar mi zaiyi da kuɗin nan? Amma yabi duk ya maidamu yaransa, garama kai dama yaronsa ne, amma Ni dan uwar ubansa ba aiki mukeyi kai da kai ba, nafa fara gajiya da raina min hankalin da yake dan yana ganina mace, wlhy na fisa bushewar zuciya”. “Bake kaɗai bace kika gaji da aiki da wannan mutumin, ni kaina na fara gajiya. Dan na fahimci kansa kawai ya sani. Sannan kuma tunaninsa sam baya tafiya yanda ya kamata. Yanzu ko akan zancen yarinyar nan da ake tayi da kuma Maash na bashi ƙafa ne naga ko zaiyi tunani irin na masu hankali. Sai dai da alama giya ta cinye brain ɗinsa. Sam baya tunani irin na masu hankali. Maash fa ba shashasha bane ba, dan shi yana aiki ne da ƙwaƙwalwa da zuciya a lokaci ɗaya. Idan da bai san wanene shi ba tabbas da alama yanzu ya fara farga, dan idan har zamuyi lissafi irin na masu hankali a bayanin da kikamin yanzu akwai lauje cikin naɗi. In babu rami to miya kawo rami. Ya ɗauke mahaifiyarsa ya maida sashensa duk da azababben asirin da oga ya musu. Ƙaninsa ya dawo, a gaba ɗaya yanda yaron ya dawo kuma an tsarata ne. Mi hakan ke nufi”. “Abinda naso ya fahimta kenan ai amma shi jaki ya wani kironi. Nifa yanzu wannan duk matsalarsa ne. Kawai mu tafi plan b. Dan bazamu cigaba da zama yana juyamu ba. Idan bai sani ba shine a tafin hannunmu ba mune a tafin hannunsa ba. Sannan muke juyashi, ba shike juya mu ba. Duk randa kuma yasan su waye mu wlhy sai zuciyarsa ta buga”. Dariya sosai Commondo ya kece da ita, sai da yayi mai isarsa kafin ya kalleta yana wani rausayar da kai irin na manyan ƙwari. “Barsa wasa yake da wuta, amma bai san itace zata ƙona shi ba. Na yarda dake kaiwa mu tafi plan b”. Idanu ta kashe masa tare da bashi hannu suka tafa. Sai kuma ta ce, “Kai tsaya! tsaya! Kayi maganar akwai alaƙa tsakanin yarinyar nan da Awwab. Kana nufin akwai abinda kake ɓoyema yallaɓai akan binciken daya sakaka akan ta ne? Danni fa na gama yarda da gasken gaske yarinyar nan Awwab ya aureta”. Wani shegen murmushi Commando ya saki, a zuciyarsa yace (Shegiya tsuntsuwar kanari mai wayo. Ai kema bazaki sani ba dan da wannan makamin zan yaƙeki. Yanda zamu haɗu mu kauda yallaɓai haka nima zan kaudaki, kudai gama yimin wahalar, ɗiyata kuwa sai ta dawo hannuna) a fili kuwa sake faɗaɗa murmushin yayi har haƙoransa na bayyana ya ce, “Karki damu zaki sani idan ma akwai in babu sai nan gaba. Yanzu dai ina da uziri. Amma mu haɗu zuwa gobe kamar zai fi.” (Matsiyaci tabbas akwai abinda kake ɓoyewa. Amma zanyi maganinka. Mudai gama da Yallaɓan kaine next. Dan ku dukanku sai na goge muku hadda. Badai Arwa ce mai gadonka ba, ka gama amsar kason ka kaima na kaudaka dan har abada ƴata bazata san kaine mahaifinta ba. Kamar yanda na sanarma iyayena ka jima da mutuwa da itama kanta har abada a haka zamu cigaba da tafiya) Hajiya ƙarama ce ke wannan zantuka a zuciyarsa. A zahiri kuwa sai ta saki murmushi da faɗin, “Yanda kace ai haka za'ayi Abban Arwa. Kadai tabbatar ka kirani da wuri dan muyi mu gama kasanshi baya tsayawa waje ɗaya. Dan yana ganin yanzu tana neman ƙwaɓewa wata hanyar zai nemo balle ga Awwab ɗin yayi tafiya”. “Baki da matsala kema kin sanni ai. Na barki lafiya”. Ya ƙare maganar yana buɗe ƙofar ya fice abinsa. Yana gama fita ta dallama bayansa harara tare da taɓe baki. Mamaki ma take yanda akai ta auri guy ɗin nan. Babu yanda Ummu-Hidaya bata bata shawara ba amma a lokacin ta dage akan itafa taga miji. Haka tayi zaman shekaru kusan biyu da shi suka haifi Arwa. Arwa nada shekara ɗaya aka kamashi akan laifin kisan kai. Prison aka kaisa ɗaurin rai da rai. Hakan yasa kawai ta yanke hukunci da tsarama iyayenta da duk danginta cewar yayi haɗarin mota ya mutu dan ba'anan Lagos aka kama shi ba a arewa ne. Kowa ya yarda da ita dan yanda ta tsara komai dole ne ma a yardan, balle ita ba cikakkiyar bahausa bace tana da yare. Anyi zaman makoki da komai da akema mamaci tayi basajar yin takaba. Bayan nan da shekara ɗaya da wasu wattani sannan Arwa nada kusan shekara uku ta auri Alhaji El-Mu'azz, kusan shekara huɗu da aurensu kwatsam sai ga Commondo ya dawo, ba kuma kowane ya fiddosa ba sai Baba prof.. fitowar commondo taso zame mata matsala, dan ya ta mata barazana akan indai bata bar Paah ba sai ya tona mata asiri ya kuma halaka ta. Barazanar nan yasa ya dinga cin kuɗi a hannunta na hauka, har sai da taga abin ya tasarma gurguntata sannan ta zauna ta sanar masa planning ɗinta na auren El-Mu'azz. Tun daga lokacin suka shirya sabon plan akan yallaɓai kasancewar shi commondo yaron yallaɓai ne na ammana kusan ma yana ɗaya a cikin waɗanda suka ƙara kangarar da shi a sanda ya fara rashin ji. Dan haka ɗan amana ne na Baba prof matuƙa shiyyasa suke ganin zasu kadashi cikin sauƙi. A mafi yawan lokuta idan ya ƙulla sukan warware masa batare daya sani ba. Hakama Hajiya ƙarama idan ta ƙulla commondo na warware mata batare data sani ba. Shima kuma commondo ɗin Hajiya ƙaramar kan warware masa. Haka dai suke wannan rayuwa tacin amanar juna amma a zahiri su amintattun juna ne.... 🌿🌿🌿🌿🌿 Ranta a ɓace yake har ƙololuwar zuciya. Ta kuma gama yankema kanta koyama Fahad da yarinyar nan dama Awwab ɗin hankali. Hatta da ɗan uwanta bazata ƙyale ba. Waya ta ɗauka tai kiran Auta. Kamar itace ta mata laifin cikin masifa ta zayyane mata komai. Mashi'a sam bata da son fitina. Sai kawai ta shiga bata haƙuri da tabbatar mata cewar tana nan tafe in sha ALLAHU. A satin nan zata shigo Nigeria dan sutukarta ma babu lafiya. Jin hakan ya ɗan sakama Hajiya Mammah nutsuwa. Amma duk da hakan sai da tai kiran Rubayya da rabon da suyi waya harta manta. Da farko Rubayya masifa ta balbaleta da shi. Sai da itama Hajiya Mammah ɗin ta hayayyaƙo mata sannan suka koma dai-dai. Amma duk da hakan ita Rubayya tace bazata zo Maash Mansion ba sai dai ita taje gida ta sameta. Da yake itace ke so kuma a ƙage take ko gardama batai mata ba tace tana jirata gata nan zuwa. Hakan kuwa akai, ta tashi tai shiri cikin shiga ta alfarma da fariyya data saba ta fita drivern ta ya jata suka wuce gidan aminiyar tata.... To ALLAH yasa a ƙulla alkairi ƙawar o'e🥱😵. 🩸💦🩸💦🩸 Na jima a kwance ina ƙullawa da kwancewa akan rayuwa da kwamacalar gidan nan, tare da abinda na gani game da Ummie. Sai kewar mijina data addaban, dan kona faɗa kona ɓoye haka dai al'amarin yake ina jin kewarsa matuƙa. Hirarsa ta jiya da mutumin nan a office ce ta sake dawo min. Tuna abinda ya bashi flash da file yasa na miƙe na fito. Ɗakinsa na shiga, komai tsaff kamar yanda na gyarashi a ɗazun. Bincike na fara a closet ɗinsa dan tabbas ina son sanin mike a cikin flash ɗin nan. Duk inda nai hasashen zai iya ɓoyesa ban ganshi ba, sai a ƙarshe a banza na samosa ata inda ma mutum bazai taɓa tunanin an ajiye ba. Ganin harda file ɗin yasa na yarda shine. Iya flash ɗin kawai na ɗauka, dan nafi damuwa da son ganin abinda ke'a cikinsa. Sai dai yanzu damuwar a ina zan samu waya ko laptop na kallonsa? Badan babu wayoyi a gidan ba, sai don komai na son sirri ai a rayuwa. Musamman ma wannan shima bazai so ace na saka a wayar wani na kalla ɗin ba. Ban samu makamar kamawa ba. Dan haka na maidashi na ajiye a wajen na fito akan sai na samu mafita. Ƙasa na sauka domin nema mana abincin lunch, amma sai da na leƙa Ummie. Na samu Mama na kwance mata kai sai kawai na fito nima na shiga kitchen ɗin. Ban jima da farawa ba sai ga Fahad da Hafiz. Nan fa sukai zaman tayani munayi muna hira. Ni harma mamakin shaƙuwar Hafiz ɗin da Fahad nakeyi. Sai ka rantse sun san juna tuntuni. Muna kammala abincin salla muka nema, daga nan kowa yayo wanka muka fito.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_ ......Bayan mun kammala lunch su Fahad suka tafi ɗakko Aunty Falaq. Basu wani jimaba kuwa sai gasu. Matuƙar farin ciki duk muka tsinta kammu. Yanda naga Falaq ta rungume Ummie tana kuka da yanda Ummien keta faman shafa kanta da cikinta yasa na sake shiga ƙaulani. Tabbas akwai shaƙuwa a tsakaninsu daka gani, amma duk mai hankali zai iya sakama yanayin Ummien alamar tambaya. Daga baya kuma da taga kamar zamu farga sai ta canja yanayi tama kwanta. Dole muka dawo falo aka buɗe babin sabon hira, salla kawai ke tada mu. Kamar wasa da dare sai ga TJ da saƙo wai inji boss. Ina buɗewa sai ga waya, harda sim card a ciki da cajinta da komai. Nayi farin ciki sosai kowa kuma ya tayani har Mama. Samun wayar nan ya matuƙar sakani a farin ciki. Dan ji nai kamar na taka rawa. A falon na barsu nacema aunty Falaq zanje nayo shirin barci nazo a ɗakinta zan kwana. Kai tsaye ɗakinsa na wuce na ɗakko flash ɗin nan. Ɗakina na koma jikina har rawa yake. Kamar mai tsoron a kamata sai da na kulle har windows bayan ƙofa sannan na haye gado na saka flash ɗin jikin wayar..... 🌟🌟🌟🌟 Karan farko a rayuwarsa da tun cuɗewar abubuwa ya zauna yin nazari. Sosai abubuwan dake faruwa a gidan ke dawo masa dalla-dalla. Tabbas lokaci yayi da zai gyara mu'amalarsa da ƴaƴansa. Ya kuma tsaya tsayin daka wajen ganin lafiyar matarsa rufin asirinsa. Baya ganin laifin Awwab da Fahad, dan suna da hujjojin da zasu juya masa baya a rayuwa. Suna son mahaifiyarsu, babu kuma wani ɗa na kwarai da za'a wofantarwa da mahaifiya ya iya kawaici koda kuwa mahaifinsa ne. Tun suna masa alkunya da tunatar da shi muhimmanci mahaifiyarsu a garesa har sun daina sun wofantar da shi kawai. Dan gara-gara ma Muhammad na ɗan rangwanta masa sai idan ta ƙurane yake magana. Amma Fahad ko kallo bai siheshi ba. Yanzu haka tunda ya dawo ko hangosa yay sai ya canja hanya. Jiya ne ma data ƙure suka haɗu babu yanda zai yi ya ce masa ina yini. Bai ko jira ya amsa ba yayi wucewarsa... Shigowar kira ya katse masa tunaninsa. Kamar zai share sai kuma dai ya kalla wayar. Ganin Baba ya sashi sauke ajiyar zuciya. Ɗagawa yay cike da girmamawa ya gaishesa duk da kuwa bai jima da barin gidan ba. Baba prof kam dako amsawa baiyi ba kai tsaye yace yazo ya samesa a gida yanzu nan. Ya amsa masa nan ma da girmamawa. Bai kuma ɓata lokaci ba ya shirya ya fita amsa kiran mahaifin nashi... Kusan a tare suka shigo gidan, har shi Paah ɗin ma yayi mamaki dan da'alama tunda Baban yabar Maash Mansion sai yanzu ne yake dawowa gidan. Sai da ya dakata Baban ya fara shiga ciki sannan shi yabi bayansa. A falo ya samesa, duk da basu jima da rabuwa ba ya sake gaishesa yana mamakin ganin yanda duk fuskar mahaifin nasu ta birkice. Daga ƙarshe ma kasa haƙurin yayi sai da ya tambaya. “Baba kana lafiya kuwa?”. Murmushin yaƙe Baba prof ya ɗan yi, sai kuma ya jinjina ma Paah ɗin kai cikin furzar da numfashi ya ce, “Idan nace da kai babu komai Mu'azz na maka ƙarya.” Cikin tashin hankali paah ya ce, “To baba miya faru?”. “Ba daga ni bane Mu'azz daga kune. Al'amarinku ya fara tayar min da hankali musamman kai da ƴar uwarka. Sai kuma Awwab. Yanzu kuna ganin a matsayina na mahaifin ku da mahaifiyarku ta tafi ta barni da ku kun min adalci kenan ku dinga cima kan ku mutunci?. Yanzu har kun kai girman da zaku dinga gorantama kanku akan ƴaƴanku. In ce kamata yay ni da ku mu nutsu mu fuskanci abinda Awwab ke ɓoye mana dangane da yarinyar nan. Ko kuna ganin zancen fyaɗen nan ba komai bane....” “Baba kayi haƙuri bana katseka bane. Amma bana tunanin Muhammad zai aikata wannan mummunan aikin da gangan. Mu zauna mu auna maganganun Addah da abinda ya faɗa mata ranar. Dole akwai abinda ya kamata musani.” “Humm banƙi ta taka ba, amma dai ni da kai duk munsan wacece Nafisa ko. Tunda mun san ita fitina bata mata wahala mizai hana mu mata uziri. Ƙaramin abu kaɗan daga aikinta ta maida shi babba.” “To amma Baba su kuma sai a dinga musu adalci ai. Bai kamata ace muna ƙara musu zafi ba a rayuwarsu. Sun rasa mahaifiyarsu tun suna ƙanana. Duk da bawai ta bar duniya bane amma banbancin kaɗan ne. Ni kuma a matsayina na mahaifi son zuciya ya hanani fuskantar su, na kasa rungumarsu na zame musu madadin uwa na kuma amsa sunan uba. Birinƙyaɗuwata kawai nake yi kuma a matsayinku na iyayena da ita dake matsayin yaya a gareni kun kasa nuna min kuskurena. Badan ALLAH ya kiyaye yaran nan ba wlhy tuni sun iya faɗawa criminals rayuwa. Dan kaine ma mai ɗan jan Muhammad a jiki da, sannan ya samu tattalin Abie kafin yabar duniya. Amma Fahad sam bai samu gatan nan ba. Baba mufa duba al'amarin nan da mahangar adalci.” Kai kawai Baba prof ke jinjinawa kamar tsohon ƙadangare. Sai da Paah yay shiru kafin yaja gwauron numfashi da faɗin, “Shike nan na yarda duk munyi wannan kuskuren. Sai muyi fatan haɗuwa mu gyara mu duka a yanzu. Amma ita wannan yarinyar da Fahad yace ɗiyar Sarkin mota ce ita da ɗan uwanta kai dama kasan da hakan?”. “Wlhy sam ban sani ba sai yanzu nima daya faɗa ɗin na sani. Amma nakega ai hakan ba komai bane ba. Dan Abdul-wahab ya cancanci kowane irin ƙyautatawar mu. Ka kuma san shaƙuwar dake tsakanin Abdul-wahab da Muhammad zai iya yin komai domin ganin ya binciko sauran zuri'arsa. Tunda mu bamuyi hakan ba. Da kuma Ummu-Hidaya na lafiya na tabbatar da tuni tayi hakan. Shiyyasa ni sam ban wani yi mamakin hakan ba sai ma daɗi da naji dan sun tabbatar da su ƴaƴan halak ne da basa manta alkairi”. “Hakane”. Baba Prof ya faɗa cikin ɗacin rai. Kafin ya nisa da cigaba da faɗin, “Hakan da Awwab yayi na jawo yaran jiki abin a jinina masa ne kam. To amma batun maganar fyaɗen da ake zargin ya mata kuma fa?”. “Wannan batun Baba yana buƙatar bincike. Kuma shine maƙasudin zargina akan akwai abinda ita Adda ta sani akan al'amarin. Ya kamata kuma ka binciketa, tanan ne kawai zamu iya kamo bakin zaren.” Nanma kai Baba prof ɗin ya jinjina. Yana dai ta danne zuciyarsa. Sai can yace, “Amma baka tunanin aurenta Awwab yayi?”. “Aure fa Baba? Yayi aure shi Muhammad ɗin batare da mun sani ba? To waye zai masa walicci? Minene kuma dalilin da zai sa ya aikata hakan? Tunda yasan mu dukanmmu burinmu shine yayi auren?”. “Nima irin waɗan nan tambayoyin naka sune a raina Mu'azz. Amma tabbas mu zauna muyi tunani irin na masu hankali. Idan har mun tabbatar Awwab zai iya nemo zuri'ar Sarkin mota dan ƙyautatawa taya zai haikema yarinya batare da dalili ba. Gashi nan yin hakan ya zame masa matsala, ya kuma zame mana muma ahalinsa. Duba nan ka gani, na tabbatar zuwa gobe wannan labarin shine zai zama latest”. Jikin paah har rawa yake wajen amsar magazine ɗin da Baba prof ɗin ke bashi. A shafin farko yaci karo da abinda ya nema rikito masa zuciya waje. A take rawar jikinsa ta ƙara ƙarfi. Idanunsa suka kaɗa jazur. Muryarsa na rawa da yatsarsa dake nuna abinda Mujallar ta rubuta da kuma hoton Maash da yarinyar (Samraah) ya ce, “Bab....ba ya akai wannan maganar ta fita?”. “Taya zan sani Mu'azz, ni kaina wannan tashin hankalin yasa ka ganni haka. Ina fitowa da Mansion na samu kira. Wani ma'aikacin Mujallar ne ya min gulmar tare da turo min ita. Ya kuma tabbatar min nayi gaggawa kafin su saketa yau ɗin nan. Sai dai ashe na makaro, dan ya turo saƙon ne tin daren jiya ban lura ba sai a yau. Koda na isa gidan Magazine ɗin aikin gama har ya gama.” “Aiko wlhy Baba sun takalo rigimar da bazasu iya maganinta ba. Dan yau ɗin nan ba gobe ba sai na saka an kama duk wani shege dake aiki a gidan wannan mujallar” ya miƙe a matuƙar fusace ya fice batare da ko sallama ya sake ma Baba prof ɗin ba. Wani shegen murmushi baba prof ɗin ya saki har haƙoransa na bayyana. Sai kuma ya jawo waya ya hau danne-danne tare da kaiwa kunnensa. Ana ɗagawa cike da bada umarni ya furta, “Duk su saki labarin. Ina son daga yanzu zuwa safiya kaf Nigeria dama duniya su san da wannan labarin”. Ƙitt ya yanke kiran, tare da kwashewa da dariya tamkar ba baba prof ɗin nan ba da tsufa ya gama cinyema rayuwa gaba ɗaya sai abinda ya sara kuma. Kai duniya ɗan adam abin tsoro. Idan har jininmu basu tsira daga zaluncinmu ba, to waye kuma zai tsira daga garemu. ALLAH ka gafarta mana kurarenmu, ka hanemu son zuciya da zalunci ga waninmu koda dabba ce😭🙏......✍️ _Masha ALLAH kowa na buƙatar samun lokacin kwalliya a gobe idan ALLAH ya kaimu, jibi kuma suyar mama😋, (to kar dai a manta da ni gaskiya ɗan hanji-hanjin nan na gobe ina jira). ALLAH ka karɓi ibadunmu da wanda sukaje hajji, ALLAH ya dawo mana da su gida lafiya. ALLAH kuma ya maimaita mana da rai da lafiya. ALLAH ya rufama kowa asiri ya hana kowa cin bashi. Mata ƴan uwana dan ALLAH kada a takurama maza yin abinda basu da shi. Duk abinda suka kawo mu amsa kuyi haƙuri mu sanya albarka, ALLAH sai ya bamu ladan haƙuri._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ ........Wani irin suya ta bala'i zuciyar Paah keyi. Kai tsaye ya bama driver ɗinsa umarnin wucewa da shi DSS office. Sai dai me suna ɗaukar hanyar a tafiyar da bata fi ta mintuna biyar ba kawai wata mota tasha gabansu, ga titin baida yawan mutane haka sosai sai jefi-jefi. Rai ɓace Paah ya fito ganin drivern sa na ma mai motar magana amma bashi ma da niyyar gyara musu balle fitowa ya basu haƙurin ɓarnar da yay musu dan ya gogi musu mota sosai. Saitin drivern yaje yay knocking glass ɗin wajen. Ana buɗewa kawai aka huro masa abu a fuska. Babu shiri ya haɗiye abinda yake son faɗa ɗin yay baya yana kai hannu a fuskarsa ya share abinda aka huro masan, yana ɗagowa kawai luuuu ya tafi zai faɗi. Ihu drivern sa ya ƙwala yana yo kansa da kiran, “Alhaji! Alhaji!!” kawai suka harbesa har sau biyu. Kafin wani lokaci mai tsayi sun saka Paah a mota sun bar layin driver kwance cikin jini yana magowar mutuwa dan sun samesa ne a ƙirji da cikinsa...... 🤔Waye da wannan aiki kuma??. ❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥 Gaba ɗaya ji nake tsigar jikina na tashi sosai. Dan har ga ALLAH zuciyata ta ƙara girgiza da ganin Baba prof ɗin da Hajiya ƙarama. Duk da ba komai na fahimta ba game da zantukansu. Amma kenan hirar da yaje nayi da ni a wancan lokacin tana da manufa kenan. No wander naji duk zuciyata bata aminta da shi ba. Shine harda zuwa ya dinga ɓarin kuɗi harda kuma bani mota. Bama wannan ba, a cikin zantukansu shi da Hajiya ƙarama akwai wajajen da nake buƙatar yima nazari. Kamar... _(Tabbas nayi kuskuren ƙin bibiyar bayan Abdul-wahab kamar yanda nake biye dana Ibrahim Alonso...)_ “Abdul-wahab dai Baba fa kenan. Alonso Abie ɗin Ummu. To miye ribarsa idan ya bibiyi bayanmu?. Sannan su kansu bayan Abie dai na nufin Ummie, Maash, Fahad ko. Ikon ALLAH to mi hakan ke nufi kuma? Tunda dai Fahad da Awwab ai jikokinsa ne da ɗansa na cikinsa ya haifa”. _(Yallaɓai wlhy zan haukace wane irin ruɗani da tashin hankali ne haka yazo mana a rana ɗaya?. Gashi mun gagara magance batun likitocin nan abu sai ƙara nisa yake, duk da dai ba wannan bane kaɗai hope ɗinmu wancan ma zasu iya mana illa tunda ko ganinta bamayi a yanzu balle sanin halin da take ciki)._ Furucin Hajiya Ƙarama ya sake min amsa kuwwa a zuciya. “Sun gagara magance batun likitoci, sannan basa ganinta, Ummie kenan ko wa? Anya kuwa mutanen ba sune keda hannu akan al'amurin Ummie ba?”. _(Dole akwai abinda Awwab ya sani. Dole shine ya shirya komai. Ta ya yarinyar dake a Kano zata dawo Lagos? Ta ya ɗiyar Abdul-wahab zata shigo Maash Mansion matsayin ƴar aiki? Ta ya! Ta ya! Ta yaya?!)_ “Wannan magana ma alamar tambaya gareta, Maash nada dalilin ɓoyeni matsayin matarsa kenan?. Ya ALLAH wai wannan wane irin ruɗaɗɗen gidane haka? Na gagara fahimtar komai, gaskiyar Mama da tace kowa ma abin zargi ne, gida kamar jinin sarauta, koda yake miye banbancin gidan masu dukiya da sarautar. Su waɗan can mulki da dukiya suke ma farauta da yaƙi. Su kuma waɗan nan dukiya da ƙarfin iko suke ma farauta. Idan za'a auna ai ɗan juma ne da ɗan jummai. Gane mai gaskiya kuwa ta hanyar bincike ne kawai dan nasan Maash bazai faɗa min ba. Dole ne zuwa gobe na ziyarci asibitin can, amma bari na fara magana da aunty Falaq.... Da wannan tunanin nai shirin barci. Wayata kawai na ɗauka sai hijjabin salla na wuce. Na samu kuwa Mama har sun kwanta. Aunty Falaq ce kawai ke zaman jirana. Muma sai muka kashe komai muka wuce ɗakin da akai mata masauki. Ɗaki ne babba da komai na buƙata a cikinsa. Zama nayi saman gado ita kuma ta wuce bayi. Kamar jira ina zama kira na shigowa wayar hannuna. Shiru nayi ina kallon no ɗin dan bata Nigeria bace, sai da tana gab da tsinkewa na ɗaga dan zuciyata ta gama bani Maash ne. Koda na kai kunne shiru babu magana, nima sai kawai nayi shirun. Munfi minti ɗaya a haka ganin baida niyyar magana na ce, “Assalamu alaikum wanene Please? Dan kana kiran matar aure ne”. Nan ma shiru kamar bazai tanka ba, sai can ya ɗan motsa a ƙasan maƙoshi sosai dan da ƙyar nake iya jinsa ma ya ce, “Nima mijin aure ne”. Murmushi nayi a karo na farko, a fili kam na bashi amsa da, “Uhhyim to wa kake nema?”. “Mrs Maashhhh”. Ya wani jaa h ɗin ƙarshe har sai da naji tsigar jikina ta tashi. Da ƙyar na iya saita kaina na ce, “kayi ɓatan kan number wannan Mrs Muhammad Awwab ce”. Ina jiyo sautin murmushinsa sai dai baice komai ba. Dan haka nima na murmusa ina kaiwa kwance. Yaja wasu sakanni kafin ya amsa ni da, “Miya hana ki barci har zuwa wannan lokacin?”. A hankali na ce, “Ba komai”. “Kin tabbatar?”. “Uhmm! Kai miya hana to?”. Ɗan shiru yayi sannan ya ce, “Kewarki”. yanda ya faɗa ɗin ya sakani ɗan lumshe idanu, gudun karya fara ɓaromin manya-manyan magana ya sani cewa, “Naga waya nagode sosai ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara buɗi mai albarka. Ya yaye maka dukkan damuwarka. Ya maida maƙiyanka ƙasan takalman ƙafafunka. Ya ɗaukaka darajarka a duniya da lahira”. Maimakon amsa ƙitt naji ya yanke kiran. Mamaki ya kamani nai zuru ina kallonta kawai. (To addu'ar ce baya so ko mi) kafin na samo amsata sai ga video call ya shigo. Ajiyar zuciya na sauke kafin na tashi zaune na jingina da gadon sannan na ɗaga. Ƙaramar ajiyar zuciya na sauke da ɗan binsa da kallo. Kafin na ɗan rissinar da idanuna ƙasa dan babu riga jikinsa sai raɓar ruwa da yake alamar wanka ya fito. A hankali ya furta, “Cire wannan hijjab ɗin”. Idanuna na ɗago cikin ɗan warosu waje na ce, “Saboda mi?”. “Haka nake so”. Ji nai kamar na kwafɗesa, amma yaya na iya dole na cire ɗin bayan na kalla ƙofar bayi kada aunty Falaq ta fito. Da ga baya ma sai na miƙe na fita gaba ɗaya na koma falon sama. Sai da na zauna sannan na kallesa na ce, “Sorry”. Komai baice min ba sai wani shegen kallo da yake bina da shi har ina jin kunyar kaina da kaina duk da rigan ba wani ya nuna min jiki bane, wando ne da riga amma ta ciki best ce sai yar jacket ɗin samanta da take har gwiwa. Ta cikin ta kama min jiki sosai saboda ta wajen a buɗe take. Baki na ɗan tura na ce, “Wai mi kake kallo?”. Maimakon bani amsa sai ya ɗan sakin murmushi da faɗin, “Ina jinki maimaita”. “Mi kuma?”. “Du'a”. Sai naji kunya ma duk ta kamani. Amma sai na daure na maimaita masa kamar yanda na faɗa a farko. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke mai nauyi lips ɗinsa na motsawa. Dai-dai nan na fara jiyo hayaniya na tashi sosai a gidan, hanyar down stairs na kalla da sauri, kafin na miƙe da sauri ina faɗin, “Ya Awwab gidan nan fa kamar babu lafiya”. Banma jira amsawarsa ba na katse kiran na sauka da sassarfa. Na samu har Mama da Aunty Falaq ma sun fito, har buge juna muke wajen ƙoƙarin fita. Sosai hankalinmu ya tashi lokacin da muke ƙarasa fitowa ganin police ne sai ma'aikatan gidan zagaye da wani abu, mace ce ke kukan da alama itace aka zagaye. Kusan a tare muka iso da Hajiya Mammah. Sai yazam tsawar da tayi ma'aikatan sun buɗe hanya. Hakan ya bamu damar ganin abinda ke faruwa. Falilah ce rungume da mijinta tana kuka kamar ranta zai fita. Jikinsa duk jini har mayafin da aka rufa masa data yaye. Sosai gabana yay mummunar faɗuwa. Ita kanta Hajiya Mammah idanu ta waro sosai da maida kallonta ga police ɗin, sai dai ta kasa cewa komai sai Baba ne yay ƙarfin halin tambayar lafiya.. Kai tsaye ɗan sandan ya bashi amsa da sun tsincesa ne a bakin hanya yashe a ƙasa babu jimawa. A dalilin number motar suka gane daga gidan nan yake. Dan da zasu wuce da gawar ta shi asibiti suga dai ya dace su fara zuwa da shi nan ɗin su tabbatar. Muryar Baba na rawa ya ce, “Tabbas na nan ne. Drivern Alhaji ne, kuma tare suka fita ɗazun ai. Ina shi Alhajin?”. “Gaskiya shi kaɗai muka samu, kuma harbinsa akayi”. Sosai hankalin kowa ya tashi, Hajiya ƙarama ta fashe da kuka tana kiran ta shiga uku. Driver tare yake da Paah. A take aka fara neman layin Paah amma yaƙi shiga. Yan sanda da sukaga abin na gaske ne fa suka ce to zasu je office ai tracking layin Paah ɗin, gawar kuma za'a aikata asibiti domin ayi bincike, zuwa da safe sai a samesu a can office. Idan kuma Paah ya shigo kafin safiya a kira su su sani.... ALLAH sarki da ƙyar aka iya ɓanɓare Falilah a jikin gawar. Haka suka wuce aka barmu jugum-jugum. Nayi ƙoƙarin kiran layin Maash back amma yaƙi shiga. Dole na haƙura. A wannan dare duk wanda yace yayi wani barci to lallai yayi ƙarya. Sai dai in ɓarawo dan babu Paah babu labarinsa. Hatta Baba prof ya zo gidan tun a daren shima hankalinsa a tashe........✍️ Wai ni mima zance anan ne🤔?? Mu tattauna a comment kawai😩😩 _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_ .....Zan iya cewa rashin barci da kwanan tashin hankali ya haifar min da zazzaɓi mai zafi. Haka na lallaɓa nayi wanka da asuba ganin baƙona ya wuce. Na ɗan yi mamakin hakan amma sai banbi ta kansa ba nayi salla. So nake na kwanta amma bazan iya hakan ba. Koba komai ina buƙatar son samun Maash a waya duk da nasan manyan gidan bazasu ƙi kira su sanar masa ba. Miƙewa nayi kawai jiri ya wani kwasheni, babu shiri na faɗa saman gado na kwanta. Sai kawai naji hawaye na zubo min. Sannu a hankali barci ya dinga rinjayar idanuna har mai nauyi yay awan gaba dani batare da na shiryama hakan ba. Nayi nisa sosai a barcin wani irin mahaukacin bugun ƙofa ya farkar da ni. A firgice na tashi har ina ɗimaucewa na rasa hanyar ƙofa sai da lalube na samota. Ina buɗewa kawai aka ɗauke min fuska da mari, ban gama dawowa a hayyacina ba aka sake ɗauke ni da wani marin, tare da fisgar hannuna ƙeyyy akai waje dani har falo. Sai a lokacin ne na fahimci Hajiya Mammah ce. Dan wani irin ihu tamun a saman kai da ya neman toshe min jina gaba ɗaya tana mai min nuni da television. Juyayyun idanuna na kai ga tvn, dai-dai ana nuno hotona dana Maash a cikin jirgin nan. Ba hoton bane ya bani mamaki, ganina riƙe da bindiga, na nuna Maash ɗin da ita daka ganni kaga ƴar daba. Dan wando ne ma da riga a jikina na rashin tarbiyya. Bayana wasu mugayen zaratan maza ne abin tsoro suma sun nuna Maash ɗin da bindugun hannunsu. Sai kuma na gaba guntun video ne na harba masa wani ɗan abu kamar kibiya da ɗayan hannuna dake a ɓoye sai kawai a kan maƙoshinsa, kafin ya yunƙura cikin ƙattan nan dake bayana ɗaya a bayansa ya kai masa yanka da wuƙa a saman hannun da yake ƙoƙarin kaima maƙoshinsa zai cire kibiyar. Kaina na shiga girgizawa da wani irin sauri jikina na rawa. “Wlhy wannan duk ƙarya ne ba gaskiya bane ba. Ba abinda ya faru kenan a cikin jirgin nan ba. Wlhy bani bace, waɗan nan mazan ma ban sansu ba, ba kuma suje inda muke ba ni da Yaya Awwab. Taya zan cutar da Mijina da hannuna to”. “MIJIIII?!!! A gidan uban naki ya zama mijinki munafukar yarinya. Yallaɓai oya ku kamata idan taje can tayi bayani. Munafuka ce dama tunda tazo gidan nan muke zargin akwai abinda ya kawota, dole ma itace tai kidnapping Mu'azz. Dan tun bayan da Awwab yay hira da ita shike nan ta saɗaɗo ta biyosa”. Hajiya Mammah ce mai maganar a zafafe. Kuka na sake fashewa da shi dan gaba ɗaya na ruɗe. Gashi bani da wani ƙarfi jiri nake ji sosai fiye da ɗazun. Sai waige nake ko zanga Fahad da Hafizzullah amma babu su a wajen. Sai Mama da ke kuka tana son yin magana amma sun hanata. Ga aunty Falaq a gefe ta zube tana murƙususu da alama naƙuda ce. Banma san sanda nace “Mama aunty Falaq! Aunty Falaq!!”. A gigice Mama ta juya ga aunty Falaq, dai-dai nan matan ƴan sandan suka kamani suka fice da ni a falon. A tsakar gida na samu an tattare ƴan aikin duka waje guda har su Shu'aibu duk an saka a mota da su TJ, su Bahijja har Falilah dake fama da raɗaɗin mutuwar mijinta ba'a bari ba. Haka nima aka tausani dan inda suke wajen ya mana kaɗan. Gashi an gwamutsa mazan da matan duka. Halin da nake a ciki yasa numfashina ya fara fisga, tun ina ƙoƙarin janyo shi har hakan ya gagara. Ban tashi tsintar kaina a ko'ina ba sai a cikin cell yashe a ƙasa an saka min drip.... 💥💥💥💥 Ganin Mansoor na mintuna goma da Salimah ta samu tayi shine ya taimaketa dawowa Nigeria neman iyayensa. Dan bata tambayesa komai ba sai inda ya fito da address ɗin gidansu. Duk da dai da ƙyar ta samu ya faɗa mata dan shi yace yama fi son dawwama a can. Sai da ta takurashi har lokacin da aka bata na neman ƙarewa sannan ya sanar mata shi ɗan Nigeria ce a Kano state. Bako tayi ƙasa a gwiwa ba ta garzayo. Sai dai kafin ta taho ɗin ta nema taimako wajen shahararren matashin ɗan kasuwar nan da yay matuƙar ƙarfi a Dubai ɗin wato Maash. Duk da dai bata samu ganinsa ba ta gana da makusancinsa. Shine ya taimaketa ya haɗasu a waya sukai magana ta minti biyar ko kuma tace ta masa bayani, dan akaf mintuna biyar ɗin nan bataji yace da ita ko ci kanki ba. Ko gaisuwa da tai masa kawai yace Uhmm ne. Bayan ta gama faɗar ne wanda ya haɗasun ya amshi wayar yace ta jirashi. Kusan awa ɗaya ya kirata back. Ya sanar mata Maash yace taje ta nemo iyayen shi guy ɗin, idamasu hali ne suzo Dubai tare, idan marasa ƙarfi ne ta kira ta sanar za'a tura mata kuɗin jirginsu da duk wani shigi da ficin shigowa wata ƙasa. Sosai taji daɗi tanata ma Maash addu'a da shi daya taimaketa. Yace mata babu damuwa ta dai yi ƙoƙari dan Maash zai shigo Dubai a nan da kwanaki uku, kuma kwana biyu zaiyi kacal, ba lallai kuma ta sake samun damar ganinsa ba. Ita asalinta ƴar medugiri ce. Harkar kasuwanci ta kai Babanta can Dubai shine ya maida su can. Dan mahaifiyarsu ta jima da rasuwa daga ita sai ƙanwarta yanzu sai Babansu da shima girma ya fara kamawa. Tayi karatu mai zurfi a fannin Shari'a, tana kuma harkar kasuwancinta daga Dubai zuwa ƙasashenmu na nan masu makwaftaka da Nigeria. A randa Salima ta iso aranar batai ƙasa a gwiwa ba sai da ta samu gidan su Mansoor. Inda ta fara cin karo da Attahir zai kai Mamy asibiti ganin doctor. Da farko bai saurareta ba sanin halin matan zamanin nan (🤔Su wai mazan nan sun ɗauka kowace mace ma irin su Azizat ne😏). Sai da ta ambaci sunan Mansoor sannan ya saurareta bayan ya jawota daga cikin asibitin suka yo waje da Mamy na ganawa da doctor kasancewar har asibiti Salima ta bisu. Bata wani ja masa aji ba ta warware masa komai dake faruwa da ɗan uwansa. Hankalinsa yayi mummunan tashi, babu shiri yay kiran Dad ya masa bayani. Dan baya son Mamy ta san komai kodan yanayin jikinta a yanzu. Shima hankalin Dad ya tashi sosai. Dan haka yace a kawo Salima office ɗinsa shi kuma Attahiru yaje ya maida Mamy gida ya samesu a office ɗin. Hakan kuwa akayi, sai dai anan asibitin Attahir yace Salima ta jirashi ya je ya kai Mamy gida ya dawo sannan ya ɗauketa. Suna tafiya yana ƙara mata tambayoyi har suka iso office ɗin Dad ɗin. Tsaff ta kwashe duk yanda ta sanar ma Attahir shima Dad ɗin ta sanar masa. Har neman taimakon da tayi wajen Maash dan ta tabbarar in har ya saka baki a maganar Mansoor zai iya kubta. Musamman da ya kasance ba gaskiya bane set up ne. Daga Attahir har Dad sun girgiza da jin sunan Maash. Amma yaya zasuyi tunda ta riga ta kai zancen can, sun kuma san taimakon nasa ne kawai zai fidda Mansoor da gaggawa. Cikin gaggawa suka fara shirin wucewa Dubai batare da Mamy ta sani ba. Dan basu sanar mata komai ba sai shi Dad ɗin ne yace mata zai je Dubai wani Bussines zai kuma je da Attahir. Bata kawo komai a ranta ba dan yanzu daga ita har Dad ɗin jan Attahir ɗin sukeyi jikinsu sosai. Hatta aurensa da ke gabatowa shiri suke masa na musamman. A shekaran jiya suka isa Dubai. Basu kuma samu ganin Maash ba sai a daren jiya ɗin nan. Sam shi bai wani gane Attahir da Dad ba. Saboda ba dasu yay waccan harƙallar ba Mamy ce. Saima ɗaukar hankalinsa da kammanin Dad ɗin sukai ya zuba masa ido ƙasa-ƙasa, sai da Attahir ya katsesa da bayanin fitowa filo ya gaya masa gaskiyar zance gudun kada sai ya je fiddo Mansoor ko ganinsa yaga shine yace bazaiyi ba. Amma a mamakinsu sai sukaga ko shock ma fuskarsa bata nuna ba. Face bada umarnin kira masa lawyers ɗin sa da yayi. A take kuma PA ɗin nasa ya aikata yanda ya buƙata. Ya gana Da lawyers ɗin nashi da Attahir da Dad sai shi Hayatu na mintuna ashirin, kafin su ɗunguma zaman court ɗin da za'ayi na biyu akan case ɗin Mansoor ɗin. Sai dai shi banda shi. Suna wucewar ne ma ya shiga yay wanka, ya fito ya nema no ɗin Samraah. Bayan kuma ta yanke bata sake samunsa ba shi kuma duk da yaji mita faɗa bai nemota ba har yanzu. (🤔Anya kuna ganin lafiya kuwa? Kumu dai je zuwa muji ina Maash ya shige ne haka to? Duk da yaji batun Samraah na cewar gida babu lafiya🤷). 🪴🪴🪴🪴 Tun bayan wucewar motocin police da duk ma'aikatan gidan harda Baba mijin Mama Balki baban kuma Hayatu gidan yay tsitt, sai magowar Falaq mai naƙuda. Da farko duk fita sukayi batare da kowa yazo takanta ba har Baba prof. Sai kuma ga Hajiya ƙarama ta dawo wai Mama Balki ta tashi ta shirya falaq ɗin a wuce da ita hospital. ALLAH sarki Mama Balki a ruɗe take, dan haka ta amsa mata da to. Jiki na rawa ta tashi ta nufi ɗakin da akama falaq ɗin masauki. Ita kuma Hajiya ƙarama ta juya ta fita akan suyi sauri tana jiransu. Tana fita tai kiciɓus da Baba prof shima yay sau da baya. Kallon kallo suka tsaya yima juna tamkar wasu zakaru ko ragunan da suka gama tara ƙahunna da basu da aikin yi sai son yin dabbe. Kallonsa take kamar yanda yake kallonta. Kafin shi ya basar cike da ɓoye abinda ke barazanar bayyana akan fuskarsa. Ciki ya shigo, itama sai ta biyoshi. Mama Balki na'a kan Falaq dan harta wuce ɗaki da dawo da baya, ganin irin kallon da suke mata su biyun batare da sunyi magana ba ya masifar tayar mata da hankali, kafin Baba prof ɗin ya furta, “Su waɗan nan mi sukeyi a gidan nan da ba'a wuce da su ba?”. Cikin marairaice fuska kamar ta ALLAH Hajiya ƙarama ta ce, “Baba yarinyarta naƙuda take yi, asibiti zamu wuce yanzu da ita kayi haƙuri dan ALLAH”. A mamakin Mama Balki baiyi magana ba, sai wani irin kallo da Baba prof ɗin yama Hajiya ƙaramar ya ɗauke kansa, sai kuma ya juya ya fita yana mata wani irin inkiya da hannu. Bin bayansa tai da sauri itama tana sake tabbatar ma da Mama Balki ta tashi ta shirya falaq ɗin su wuce asibiti........✍️ (🤔Ya kamata nayi tambaya anan ma ko na wuce???) _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_ ......Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya zagaye ƙasa. Dan ta ko ina ƴan media yaɗashi suke abinka da babban mutum. Gashi daɗin daɗawa an tabbatar da zuwa yanzu Maash na gadon asibiti ne ma a wajen ƙasar. Ga batun mahaifinsa da ba'a gani ba. Ma'aikatan jirgin da aka nuna wancan guntun video sun fito sun tabbatar ma duniya duk abinda aka gani ya faru, dan a yanzu haka suma suna a asibiti ne saboda raunikan da aka ji musu, biyu da ga cikinsu ma sun rasu. Mugun kiɗimewa Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain yayi da gani wannan labari. Dan shi bai san mike faruwa ba yau ya tashi baya jin daɗi ko television bai buɗeba balle redio, hakama waya. Sai da Hameed ya kira shi yana sanar masa sannan ya buɗe tvn yaga wannan ƙulli. Dan daga gani kasan an shirya komai ne ma'aikatan jirgin nan kuma su ci kuɗi. Number ɗin Maash ya fara nema sai dai kuma bata shiga. Hayatu, nan ma bata shiga. Haka ya dinga bin duk wani yaron Maash makusanci dake a ƙasar da wajen ƙasar dan so yake yaji ina Maash ɗin yake wannan al'amari ke faruwa haka? Ko da gaske yana a gadon asibitin ne?. Amma amsa ɗaya yake samu suma basu san inda Maash yake ba. Hayatu ma an nemesa an rasa tun barowarsa prison da suka sami damar fitar da Mansoor bayan an tashi a shari'ar da lawyers ɗin Maash ɗin suka kawo ƙarafafan hujjoji da ya tabbatar da komai shiryashi akai akan Mansoor. Abinka da komai akan tsari a ranar suka saki Mansoor ɗin aka cafke abokin nasa... Su kansu su Attahir ɗin a kiɗime suke da jin abinda ke faruwa. A take Attahir ya fito yay magana a media. Bayan ya kira wani abokinsa ma'aikacin BBC. Zancen Attahir ya fara saka mutane a ruɗani, ba'a gama hakan ba sai ga Sheikh Muhammad shima ya fito ya ƙaryata batun abinda ya faru a jirgi. Ya kuma tabbatar da Samraah matar Maash ce shi da kansa ya amshi walliccin aurensa, ya kuma bada hotuna da bidiyo da akayi a wajen ɗaurin auren dama saboda gudun abinda zai iya zuwa ya dawo kasancewar aure ne na babban mutum da akai kamar a sirrance tunda babu wanda ya sani har family ɗinsa. Tofa, zantuka sun fara canja salo, dan an rasa ina za'a ɗauka a yarda. Batun farko na Maash na asibiti bayan Samraah da yaranta sun nema halakashi? Ko kuwa batun Attahir da mahaifinsa da suka tabbatar da a yau ɗin nan sun gana da Maash a Dubai kuma lafiyarsa ƙalau. Harma da taimakon da yay musu basu ɓoye ba. Hakama Salima da lawyers nashi, sun kuma tabbatar da shima Hayatu ko awanni biyar ba'ai da ɗaukesa ba. Dan lafiya Lau suka fito a prison da shi suka shiga mota ya shiga sun iso gidan Maash ɗin sukaga babu motar da yake ciki a tare da su. Nan kuma gidan Maash an zagayesa da securitys. Basu sani ba Maash na cikin gidan har yanzu, ko kuwa? Amma dai sun tabbatar lafiyarsa ƙalau su dai akwai dai abinda ya faru? Ko batun babban malami da kowa ke mutuntawa da gani girma daya tabbatar da shi da kansa ya amsawa Maash auren Samraah harma ga shaidu?. Kasancewar Samraah sananniya ce a baya, da irin yanda zancen kidnapping ɗinta da batun fasa aurenta da aurenta na biyu ya zagaya media sai aka dinga dawo da labarin yanzu. Sai dai abinda ya so raba kawunan mutane ko'a baya ba'a san takamaiman mijin Samraah ba. Wanda akaita haɗata da su editing hotunan akayi. Amma sanin waye malam yasa da yawa aka amince da wannan zance..... 💞💫💞💫💞 Gaba ɗaya Mama Balki ta rikice. Ta rasa miya kamata tayima Falaq, ga shi bata son tafiya asibiti da ita tabar Ummie ita kaɗai a gidan nan akwai haɗari. Dan tabbas komai zai iya faruwa. Hawayenta ta ƙara sharewa, tare da bubbuga fuskar Falaq da ke neman shiɗewa. A dai-dai nan aka fara taɓa ƙofa alamar za'a shigo. Hankalinta ne ya sake tashi, dan tayi alwashin data bar Ummie gara ta haƙura ta rasa Falaq ɗin. Ta gama sallamawa a bazata taji ana kulle ƙofar, da wani irin sauri ta ɗago dan tasan dai da ga ita dai Falaq sai Ummie da tun ɗazun ma take barci bayan likitocin ta sun zo sun dubata sun mata allura. Sai dai a mamakinta sai taga Ummie ce ke rufe ƙofar, bata gama dawowa a sumar wucin gadin da tayi ba Ummien ta baro ƙofar ta iso garesu. “Bilkisu Kamata” ta ce kawai tana ƙoƙarin kama Falaq. Duk da maganar bata fita sosai harshen ma a karye yake kamar mai koyon magana Mama Balki taji abinda ta faɗa. Tuni wani ƙarfi yazo mata ga hawaye na kwarara tana kuma kallon Ummie ɗin suka ɗaga Falaq. Jin yanda ake buga ƙofar da wani masifar ƙarfi ana ƙwala kiran sunan Mama Balki yasa Ummie sake faɗin, “Mubar gidan nan Bilkisu”. Ta wajen swimming pool ɗin nan suka fita, ita dai Mama Balki sai kallon Ummie take hawaye sun gagara tsaya mata. Da wani irin ɓacin rai Hajiya ƙarama ta koma, Baba prof na tsaye a babban falon sashensu yana kai-kawo su Azizat cirko-cirko Hajiya Mammah na zaune na sharar hawaye, hakama Maman Malika kuka take. Uncle Abdullahi dai ya fita tun ɗazun a gidan akan batun Paah. Iya su kaɗai ne a gidan sai police a ƙofar gate biyu da aka bari, amma da securitys ɗin ƙofar, da na gidan, da duk wasu ma'aikata maza da mata an tattaresu zuwa police station. Babu ma wanda yabi takan batun Fahad da Hafizzullah da basa gidan duk wannan dambarwar da ake yi. A yanda Hajiya ƙarama ta faɗo falon ne yasa duk suka ɗaga kai suka kalleta. Cikin shashsheka da sauke numfarfashin gudun da ta ɗan yi ta ce, “Ta kulle ƙofa fa matar can. Ina tsoron ba wani abu take shiryawa akan Hajiya Babba ba”. Su dukansu babu wanda bai zabura ba. Cikin matuƙar ihu Baba prof ya ce, “Ubanwa yace ita su barta ita da ƴar tata. Idan wani abu ya samar min Ummu-Hidaya sai na kashe matar nan. Ni dama sam ban yarda da ita ba itama...” Babu wanda ya iya cewa komai akan maganar tasa. Sai rige-rigen ficewa da sukai a sashen zuwa sashen Maash ɗin. Wani irin mahaukacin jijjiga ƙofar suka dinga yi su duka suna zagin Mama Balki. Ruɗewa Mama Balki da duk suke iya jiyosu kasancewar sun zagayo ta can baya ta sake yi. Ga Falaq ta sume musu ta ƙara nauyi. Jikin Ummie ba wani ƙarfi yake da shi ba. Amma ta daure matuƙa duk da itama jikin nata rawa yake yi. Jin motsin ana nufo inda suke dan su Baba prof na ƙoƙarin zagayowa ne su biyo ta baya tunda duk sun san da ƙofar cikin garden har biyu yasa cikin kuka Mama Balki da jikinta ke ƙara ƙarfin rawa ta ce, “Ummie ki gudu ke kawai, bari na kira Isma'il amintaccen Alhaji ƙarami ne in sha ALLAHU zai taimakemu ya kaiki wajen da wani bazai taɓa sani ba har Alhaji ƙarami ya dawo. Amma zamanki anan akwai haɗari”. Kai ta girgiza mata, tare da mata nunin su ɗauki falaq ɗin. Babu yanda Mama Balkin ta iya haka suka sake ɗaukar Falaq, cikin flowers suka shige hannayensu dafe da bakunansu. Daga ta inda suke suna iya hango Baba prof da Hajiya Mammah dake ƙoƙarin shiga ta ƙofar swimming pool da suka bari a buɗe. Dai-dai nan Falaq ta kawo wani irin bahagon mummunan numfashi da ya saka Baba prof dake ƙoƙarin shigewa tsayawa cak. Jikin Mama Balki na wani masifar ɓari ta cire ɗan kwalin kanta ta toshe bakin Falaq dake zabura. Garrr wata ƙatuwar baƙar kunama ƙirin ta fito daga ƙarƙashin Falaq ɗin ta shige tsakanin Mama Balki da Ummie. Hakan na nufin kunamar ce ta sari Falak. Su duka kasa motsi sukayi, musamman Ummie da dama tun can fil azal tana masifar tsoron kunama a rayuwarta da maciji da ƙadangare. Kuma Mama Balki ta san da hakan. Ga shi in har suka sake wani motsi Baba prof da har yanzu ke'a tsaye sai ya gane. Haka suka zauna zukatansu na bugawa ga wata irin zufar tashin hankali data gama jiƙe Falaq babu tantama haihuwa ce ga azabar kunama...... ✨✨✨✨ A can Kano kuwa ɓangaren Abbah kam neman yanke jiki yayi zai faɗi a lokacin da yaci karo da tashin hankalin da ke faruwa. Dan illahirin jikinsa karkarwa ya shiga yi. Baima san sanda ya fara ƙwala kiran Mom da duk abinda ake tana a kusa da shi tana gani ba daɗi kamar zai kasheta. Ƙin amsawa Abba kiran da yake matan tayi sai ma murmushi da ta saki duk da wani ɓangare na zuciyarta na mata raɗaɗin jin Maash wai Samraah ta aura. Amma babu komai tunda ga a yanda aka ƙare hakan ma nasara ce. Halime da sam ita bama tasan wainar da ake toyawa ba jiyo muryar Abba dake kamar rawa ya sata tashi a ɗan firgice daga kwanciyar da tayi a kujera. Dan yau bazata fita makaranta ba bata jin daɗin jikinta. Da ƙyar ta iya lalubar ɗan kwali ta ɗaura, a karo na farko da tun zuwanta gidan matsayin matar Abba ta shiga sashen Mom. Dai-dai nan Abba yayo baya zai faɗi da sauri ta saka hannayenta biyu ta tarosa ya faɗa a ciki. Duk da nauyin da yay mata, ga ƙaton cikinta daya ƙara fitowa haka ta daure jikinta na rawa ta kai durƙushe da shi. Kuka take tamkar ranta zai fita, UBANGIJI gafurin rahimun sai ga Alhaji Jafaru da Gwaggo Gudidi tamkar an jehosu gidan. Kukan Halime da neman temako da take yaja hankalinsu sashen Mom ɗin suma suka nufi can da sassarfa. Mom ɗin najin motsi itama ta fara kuka tana kaiwa durƙushe gaban Abba ta kamoshi daga jikin Halime ta maida nata jikin. Salati Gwaggo Gudidi da Alhaji Jafaru suka shiga yi suma suna nufar kan Abban da gaba ɗaya numfashinsa ya gama ɗaukewa.....✍️ 🤦🤦🤦🤦🤦 _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_ .......Baba Prof ya ɗan jima yana waige-waige kafin ya ƙarasa shigewa ganin baiga komai ba. Yana shigewa Ummie ta miƙe jikinta na rawa saboda azababben harbin kunamar daya ratsata har tsakkiyar kanta itama. Cikin ƙanƙanin lokaci zufa ta gama wanke mata jiki. Ƙoƙarin nufota Mama Balki tayi, amma sai ta mata nuni da su kama falaq kawai, hawaye ne suka ciwo idanun Mama, dan ta tabbatar cizon kunamar nan ya shigi Ummien amma ta nuna dauriya. Haka suka kamata da ƙyar sai nishi take saboda babu damar yin kuka kasancewar ɗan kwali da Mama Balki ta saka mata a baki, yayinda ita kuma Ummie keta faman taunar lips ɗinta. Ta cikin garden ɗin Maash daga can ƙarshe da filawoyi suka lulluɓe bangon gaba ɗaya Ummie tayi da su. Mamaki ya kama Mama Balki lokacin da Ummie ta saka hannu ta shiga yaye filawar wajen duk da ƙayoyin dake famar fasa mata hannu, ƙofa ce ta bayyana da bazaka iya taɓa yarda akwaita a wajen ba saboda ta mugun sajewa da katanga matuƙa. Da ga gani kai kasan an tsara wajen ne sosai. Dan ƙafa, ce ta gasken gaske. Wani abu daga can ƙasa Ummie ta danna sai ga ƙofar na buɗewa da ƙyar, dan wani irin mugun ƙarfi ne da ita gata ta zallar ƙarfe. Dai-dai suna gama fita suka jiyo Arwa na ƙwala kiran su Baba prof. Suna ɗaga kai suka hangota ata can saman Maash ta balcony. Tabbas ta gansu, kamar yanda suka ganta. Dan haka Ummie taja ƙofar da masifar sauri ta datse. Kuka Mama Balki ta sanya tana neman number ɗin Isma'il. Amintaccen Maash da ke matsayin Kuku a gidan Baba prof, duk da dai itama Mama Balkin bata san da hakan ba, bama yasan cewar Isma'il ɗan sanda bane kawai dai yakan zo amsar bayanai a hannunsu na wani abu idan ya faru gidan lokaci-lokaci. Harta tsinke bai ɗaga ba. Hankalinta ya sake tashi, dan ta tabbatar suka zo ga ƙofar nan bata buɗe ba zasuyi yinƙurin zagayawa ne, ga Ummie dake shan azabar kunama, ga Falaq data haɗa biyu naƙuda da kunama utama. Kiran ta sake yi, sai data masa uku sannan ya ɗaga, batama zauna saurarensa ba ta shiga masa bayani. Shima can hankalinsa ne ya sake tashi, dan dama a tashin hankalin rasa inda Maash yake suke shi da duk ɓoyayyayun da ba kowa ya sani ba. Ya tabbatar musu su ɗan bar wajen kaɗan gashi nan zuwa, dan dama yana kusa da gidan yaje kasuwa ne. Ko tahowa su Baba prof sukai daga cikin gidan kafin su su zagayo shi ya iso. Hakan kuwa akayi, dan cikin ƙanƙanin lokaci ya iso kasancewar su su Baba prof na can suna kokarin neman ƙofa da Arwa ta tabbar musu ta gani da idonta an buɗe su Mama Balki sun fita harda Ummie da suka duba basu gani ba a kaf sashen. Ganin fa babu ko alamar kufan ƙofa a wajen wasu suka fara ƙin yarda da Arwa ɗin. Yayinda Baba prof yace bazasu tabbar da hakan ba sai sun zagaya ta baya dan ga sayin ƙafafun su Mama Balki nan ɓaro-ɓaro a garden ɗin. Dan haka aka bar su Hajiya Mammah da yaran, shi kuma shi da Hajiya ƙarama suka zagaya. Isowarsu dai-dai da tashin motar Isma'il daya kwashi su Ummie sai number ɗin motar da ƙurarta suka gani. Wani irin mahaukacin reverse Hajiya ƙarama tayi tare da ƙarama motar wuta suka bi bayansu. Gaba ɗaya hankalin su duk ya tashi, da ita Ummie ma duƙar da kanta kawai tayi dan juya mata yake yi sosai. Isma'il na ganin zasu ƙure musu ya wani irin yin reverse shima ya dawo baya, kasancewar ita kuma ta riga ta kwashi motar da yawa domin ƙoƙarin cimmusu sai ta kasa tsayawa. Da wannan damar ya samu shigewa wani layi da bashi da tabbacin yana ɓillewa ko a'a... Wani kalar taka birki da dukan steering Hajiya ƙarama tayi. Shima Baba prof ya kaima glass ɗin window ɗin gefensa naushi. Gaba ɗaya idanunsa sun gama kaɗewa jajur, wayarsa ya fisga a take ya shiga kiran number DCO ɗin da case ɗin Paah ke hannunsa. Yana ɗagawa ya masa bayani akan kidnapping Ummie da aka sake yi tare da bashi number ɗin motar. Yana ajiye wayar Hajiya ƙarama dake masa kallon tashin hankali ta ce, “Yallaɓai amma fa wannan ganganci ne. Tunda kaima kasan ba kidnapping ɗin nata akai ba. Nifa na kasa ganema gaba ɗaya wannan shirin naka dake neman harmutse komai.” Ko kallon inda take baiyi ba bare ya amsa mata ya buɗe motar yay ficewarsa. Jitai kamar ta shaƙo shege ta farka mar wuƙa kowa ma ya huta. Motarta itama ta fisga a fusace ta bar wajen batare data sake kallonsa tsaye a gefen titi yana waya ba. Tasan Commando yake kira, ita ma kuma tana buƙatar ganin commondo ɗin yanzun nan. Dan su ya kamata su ɗauki Ummie kafin shi..... ❤️‍🔥💫❤️‍🔥❤️‍🔥💫❤️‍🔥 An miƙa Abba asibiti da gaggawa. Halime sai kuka take yi Gwaggo Gudidi na lallashinta. Har yamma basu ji wani ƙwaƙwƙwaran bayani akan al'amarin nasa ba. Sai kusan bayan isha'i doctor ya ɗan kwantar musu da hankali tare da son ganin Alhaji Jafaru. Dagewa Halime tayi akan saita bisa, da ƙyar Gwaggo ta dinga lallashinta Alhaji Jafaru ya fita ya tafi shi kaɗai. Babu jimawa sosai sai gashi da takardar magunguna. Wayarsa daya bari ya ɗauka ya fita. Gwaggo na tambayarsa yaya ake ciki yace mata kawai da sauƙi ayi masa addu'a. Gaba ɗaya jikin Gwaggo ya ƙara yin sanyi, yayinda Halime ke kwasar kuka. Ita kanta Mom duk tayi wani sukuku dan zuwa yanzu ta fara jin hankalinta na tashi. Gashi su Gwaggo duk sun ƙi kulata sam.... ❤️🌟❤️🌟❤️ Tun a mota faya ta fashema Falaq, da ƙyar ALLAH yasa suka isa gidan da Isma'il yake rayuwa kafin fara aikinsa a gidan Baba prof.. dole shi da Mama Balki suka kamata zuwa ciki, dan Ummie kam bazata iya ba zuwa yanzu ƙarfin ta ya gama ƙarewa. Ita kanta sai da suka komo suka kamata suka fita da ita a motar zuwa ciki. Suna shigowa kukan jariri na jaraɗe gidan. Da sauri Mama ta nufi ɗakin, har ta shiga sai kuma ta dawo jikinta na rawa ta buƙaci sabuwar reza da ko towel ne. Zuwa Isma'il yay ya ɗako, yana kawo mata ta koma ciki. A mamakinsa sai ya ga Ummie ma ta miƙe. Ƙoƙarin dakatar da ita yayi amma sai ta masa murmushi kawai cikin ƙarfin hali ta shiga ɗakin itama. Mama Balki na hanata amma a hakan cikin yanayin da take sai da ta taimaka mata suka amshi haihuwar Falaq ɗin. Dan ma Alhamdullah komai yazo da sauƙi. Dan suna gama yanke cibi sai ga uwa itama ta biyo. Mama ce ta cigaba da gyara Falaq, yayinda Ummie ke rungume da jinjiri a jikinta hawaye na sauka mata da alama akwai abinda ta tuna ko yake dawo mata da irin wannan yanayin. Haka dai Mama ta gama tsaftace komai ta gyara jariri da uwarsa ta kuma taimakawa itama Ummie ta gyara jikinta daya ɓaci. Bawan ALLAH Isma'il sai gashi da kayan da duk zasu iya buƙata na sakawa harda na jinjiri sai likitan Ummie. Yana ajiye musu tare da abinci ya nunama Mama Balki komai yay, likita ya duba Falaq duk da yace ba aikinsa bane aka kuma duba Ummie su duka akai musu allaurar dafin harbin kunama sannan suka musu sallama akan zai koma kan aiki kar a nemesa. Addu'a Mama balki ta masa Ummie dai na kwance rungume da jariri kamar mai barci.... 🌿✨🌿✨🌿 Dole Isma'il yay hanzarin shiga kasuwa yay cefane sannan ya kama hanyar komawa gidan Baba prof. Yana zuwa kuwa motar data ɗakko baba prof na isowa. Gaishe shi yayi kamar yanda kowa ke gaishe shi a ransa yana mamakin ganin yanda duk Baba prof ɗin ke'a hargitse. Haka dai ya lallaɓa ya shige kitchen ganin Commondo ya iso shima. Yana shiga kitchen ɗin ya ɗauka ruwa da lemo ya kai falo, in da ya samu har commondo ya shigo. Yana ajiyewa ya juya ya koma kitchen ɗin. Inda ya saba laɓewar ya laɓe yau ma. Aiko sai ga muryar Baba prof ɗin cikin tashin hankali... “Daga nan zuwa dare ina buƙatar ganin gawar Lawisa a Maash Mansion ”. A wani kalar firgice Commondo ya juya ya kallesa. Batare da yasan ma mi yake ba ya ce, “Yallaɓai saboda me?”. “Saboda daman hakan shine plan ɗina, sai dai ba a yanzu naso yin hakan ba. Amma naga tana neman shiga min hanci dolene kuma na fyatota.” “Eh bazan ƙi baka goyon baya ba ranka ya daɗe. Sai dai inaga ya kamata mu dai sake nazari. Lawisa nada sirrikan ka a hannunta da yawa. Sannan ko babu komai kana buƙatarta a yanzu.” “Duk wani sirri dake a hannunta bashi da wani amfanin da zai min. Kawai a kaudat......” “Niko keda sirrin da zai maka amfani Adams”. A bazata sukaji muryar Hajiya ƙarama a kansu. A tare duk suka kalleta, a yau babu kunya babu tsoro ta nuna Baba prof da yay galala yana kallonta. Dan sam baiji ko alamar shigowarta falon ba ma kodan a gigice yake........✍️ 🥱Tofa. Manyan shegu yaya dai?. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ .....“Lallai kai ka tabbata ɗan kunama Adams, har ni kake bada kwangilar a kashe yau? To lallai kayi babban kuskure, dan Lawisa da kake gani ƙadangaruwar bakin tuluce. A barni na ɓata ruwa, a karni kuma a kar tulu. Kuma wlhy kayi kuskuren barin abinda ke ranka ya fito fili har na jisa. Wato dama planning ɗinka kenan kasheni. Kai wannan tsohon ban taɓa ganin asararre irinka ba tsohon najadu da zai ƙare rayuwarsa a rumfar asara. Koda yake bazanyi mamaki ba, tunda har hassada ta kaika ga cin amanar wanda ya ɗaukeka daga rana ya kaika inuwa dama nima nasan za'azo wannan gaɓar, sai dai kuma ita wannan Lawusar ba Alonso bace. Ba kuma Ummu-Hidaya bace da ka raina. Wlhy sai naga bayanka. Baƙin azzalumi, dama wannan ruɓaɓɓen plan ɗin ka shirya shiyyasa kaketa wani ɓoyema mutane ko, to kaje ka samu likitoci su maka wankin brain, dan naga alamar taka dattin giya ya cikashi. Na kuma maka alƙawarin ni Lawisa sai na fara ganin bayanka. Kai kuma ɗan koranka an saka ka kasheni ko, idan zaka gwada bissmillah”.. ta ƙare maganar da karkaɗa yatsunta a gaban fuskar Commondo ta juya fuuuu ta fita a falon. Babu wanda ya iya motsawa a cikinsu. Dan kowa da abinda yake tunani. Sai zuwa can Commondo ɗin ya ja numfashi ya fesar. Cikin yanayin nan nasa na ciccijewa ya fara magana. “Oga kafayi kuskuren saka mace a wannan sabgar taka. Musamman ma wannan mai buɗaɗɗen idon, dan wannan daga ganinta kaga hatsabibiyar da zata iya aikata komai dan cikar burinta. Tabbas da ace ina nan ka shirya ƙulla alaka da ita da bazan bari ba. Amma karka damu, ko yanzun saina nuna mata babba babbane. Badai duk abinda take taƙamar da shi a ƙarƙashin ikonka yake ba. Sai na koya mata darasi kafin na kaudata. Amma saka batunta a gefe, ina son wannan abun dake neman ƙwaɓewa mu gyarashi da shiri na musamman dan na fara zargin itace ma ta kuɓutar da matar nan a gidan”. Karo na farko da tun bayan fitar Hajiya ƙarama Baba prof ya ɗago ya kalla Commondo. Kai ya jinjina masa alamar tabbatarwa. Tare da faɗin, “Yes oga ka auna mana. Idan babu rami miya kawo rami?”. Sosai Baba prof ya gamsu a wannan gaɓar, domin kuwa ya ɗan buɗe mata wani abu a lokacin da sukai kiciɓus a ƙofar sashen Awwab ɗin kallon data masa ya kamata ya saka masa alamar tambaya, amma duk da haka ya mata nuni da ta kauda matar da ƴarta, shine tai amfani da Ummu-Hidaya ta fitar kenan a gidan?. To anya kuwa ba itace ma tai kidnapping masa Mu'azz ba?”. Kallon Commondo yayi cikin jinjina kai ya ce, “Zan iya yarda da zancenka dan ƴarta ce ta ankarar damu sanda suke guduwa. Sannan itace taja motar sanda muke binsu. Ta kuma kasa cimmusu har suka gudu. Sannan na fara zargin Mu'azz na hannunta. Dan idan ka haɗa 1+1 amsa guda zai baka. Dama tana da shirin cin amanata kenan?”. “Bazamu tabbatar da haka ba sai mun bita a sannu. Idan ta tabbata cin amanar taka take shirin yi kuma. Aiko sai tayi nadama Boss. Ka bani nan da zuwa dare zanyi tunani. Amma kaima kayi wani abu guda. Yana da ƙyau na dinga sanin mi ka shirya saboda gudun samun matsala. Dan tun farko da nasan abinda ka shirya kenan baza'a saki wannan maganar data karaɗe lungu da saƙo ba har sai mun fara yin abu biyu. Sannan zamu rushe uku a ciki”. Kai Baba prof ɗin ya kaɗa masa. “Dama banyi aikin don yin wani abu ba. Nayi ne kawai dan ɗauke hankalin mutane. Dan nasan zancen zai ɗauki lokaci ana tattaunashi”. “Hakane kuma oga. Amma abinda ya fi tsaya min a rai shine batun Maash na asibiti. Taya hakan zata kasance bayan lafiyarsa ƙalau?. Sannan Maash FURAR DANƘO ne akan shekara ana damunsa bashi farau-farau.” “Lafiya Lau yake. Yana Dubai a cikin gidansa. Na saka an katse network ɗin gidanne kawai da wuta da ruwa, an kuma zagaye da securitys yanzu haka shi baima san mike faruwa ba sam. Yaronsa kuma na hannunmu.” Kasa magana ma Commondo yayi, dan yasan wanan ramin sam bai ginu ba. Gaskiyar Lawisa wannan tsohon dattin giya ya gama cinye masa ƙwaƙwalwa wlhy. Jiba wani wawan shiri dan ALLAH. Amma ba damuwa, shi bari yayi wasa akan nashi wasan dana Lawisa. Tunda yanzu ya fahimci tun a duniya ake fara nafsi-nafsi. “Oga ka bani nan zuwa dare zanyi tunanin mafita. Kaima ya kamata kayi wani tunanin mu haɗa plans kamar biyu mu gani. Yanzu mu dukanmu muna buƙatar hutu”. Sosai Baba prof ya gamsu da hakan. Dan tabbas kansa ma shi gaba ɗaya a juye yake. Sannan ya yarda da Commondo fiye da ɗari bisa ɗari a rayuwarsa. Baya taɓa kawoma ransa zai iya cin amanarsa. Kallan Commondo ɗin yayi, cike da yarda ya ce, “Suma ahalin yarinyar nan ya kamata muyi tunani a kansu. Dan nayi tuya na manta da albasa kasancewar ban san makirin can ne ya karɓi waliccin auren ba. Bana son maganar nan ta lafa da ga nan har zuwa randa zan saka a buɗe Awwab. Dan ina son lokacin da zai fito kansa yay matuƙar ɗaukar zafi ya rasa ina zai fara kamawa, ta hakanne kawai zan iya cimma burina a kansa. Sai maganar Ummu-Hidaya, bana son akai safiya bamu san inda suke ba. Hakama Mu'azz”. “Ka ɗauka wannan matsalar na maganceta ma. Dana fita daga nan zan fara samar da masu binciken ne ta ɓangarori biyun”. Kai kawai Baba prof ya jinjina masa. Sallama commondo ya masa, shi kuma ya samu giyarsa ya kwankwaɗa sannan ya tashi ya shige ciki.... Commondo na barin gidan Baba prof gidansa ya wuce. Bai yi mamakin samun Hajiya ƙarama ba, gaba ɗaya ta hargitse masa falo da hayaƙin shisha. Ƴar dariya yayi tare da kaiwa zaune. Dan yasan dai bata shan komai yau kuma gata da shisha. Lallai ran manyan mata ya ɓaci kenan. Yanda take bulbula hayaƙin sai kawai yaji yana buƙatar kasancewa da ita. Miƙewa yay ya shige ɗakinsa. Babu jimawa ya fito da allura. A kusa da ita ya zauna tare da kama hannunta kawai ya fara mata. Kan shisha ɗin ta wurgar tare da juyowa a fusace. “Oh har ya baka allurar guban da zaka mun ɗin na mutu ne?”. Murmushi yayi tare da rungumota jikinsa yana magana ƙasa-ƙasa kamar ba commondo ba. “Haba kema kin san bashi da wannan matsayin, ya sani na kashe uwar ƴata da hannuna. Never for ever sai dai shi ya wuce. Cool down na miki allurar nan ne dan ki samu nutsuwa musan miya kamata muyi. Dan na jiyo mana komai akan plan ɗin nasa”. Jikinta ta janye tana mai sauke ajiyar zuciya. Daga haka barci ya fara rinjayar idonta. Wata shegiyar dariya yayi da ɗaukarta gaba ɗayanta duk da tana da jiki badai can sosai ba yay cikin ɗakinsa da ita. Duk tana jinsa, sai dai bata da ƙarfin hanashi. Daga ƙarshe ma allurar na fara mata aiki a jiki da kanta ta fara kai masa kanta. Haka ya shiga yin yadda yaso da ita. Ya kuma tabbatar daga nan har zuwa gobe allurar zata iya kaiwa jikinta, dan haka daren yau na party ne gaba ɗayansa kawai... 💢🌿💢🌿💢 Matsanancin ciwon cikin dana farka da shi ya sakani fara fisge-fisge. Tuni na fincike ruwan da aka saka min. A dai-dai nan naji wata muryar da nake da tabbacin nasan mai ita tana ma ƴan sandan dake bakin cell ɗin da aka sakanin tsawa. Har rige-rigen buɗe ƙofa suke su shigo. Ciwo yaci ƙarfina bamma tantance maza bane ko mata suka ɗaukan, sai da aka shiga da ni mota na iya kallon mutum ɗaya a cikinsu wadda mace ce. Da ga haka na maida idanuna na lumshe gaba ɗaya. Sama-sama nake jin kai-kawon komai har isarmu asibiti da taimakon da likitoci suka shiga bani. A ɗan maganarsu nake jin wai ina zubar da jini. Daga haka ban sake fahimtar komai ba sai farkawa nayi na ganni kwance a gadon asibiti police mace a gefen gadon da nake zaune. Sannu tayi min, tare da kiran likita. Ya ɗan dudduba ni ya tabbatar ma da ƴar sandar yana buƙatar ganin mijina ko wani a cikin ahalina. Kai tsaye ta bashi amsa da ina a ƙarƙashin kulawar su ne. Za'a iya sanar musu minene matsalata. Ɗan jimm likitar tayi kamar mai tunani sai kuma ta ce, “Mijin nawa dai tafi buƙatar gani. In har za'a iya yi mata wannan alfarmar zata so hakan”. Cikin rashin damuwa jami'ar tace zata duba. Daga haka likitar ta sake fita ni kuma barci ya sake rinjayata. Ban sake farkawa ba sai cikin dare sosai. Na tashi da wata masifaffiyar yunwa. Tun ina juye-juye har na fara kuka da roƙon a bani abinci. Tsaki ƴar sandar tayi cikin masifa take faɗin itafa na takura mata na hanata barci, a ina zata samo min abinci yanzu cikin daren nan. Ban iya amsata ba na cigaba da murƙususu na kawai. Sai kawai ta tashi ta fita rai ɓace. Tun ina saka ran zata dawo harna fidda rai, ga cikina yay wata irin masifar ƙullewar yunwa na cure waje guda ina hawaye. A hankali wani irin daddaɗan ƙamshi ya dinga ratsa min cikin hanci, tun yana a nesa da inda nake har na fara jinsa a gab-gab da ni. Ƙoƙarin buɗe idanuna dake alumshe nayi jin saukar hannun mutum akan jikina. Bana iya ganin ko waye da ƙyau, sai dai a tsaye yana da tsayi, akwai kuma facemask a fuskarsa, gashi ya ɗaura hular rigar jikin nasa a saman kai ta yanda har ba'a iya gane ainahinsa, dan hatta idanunsa akwai glass........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ........Kamani yay gaba ɗaya ya tada zaune, shima ya kai zaunen tare da sakani a jikin nasa ya rungume. Wani kalar nutsuwa ce ta fara ratsani, irin wadda nake ji a tare da mutum ɗaya kacal a duk sanda ya rungume ni irin hakan. (Tabbas bana tantama wannan Maash ne, Awwab ɗina ne). Na faɗa a zuciyata hawaye masu zafin gaske na gangaro min suka sauka a kan ƙirjinsa, sake ƙanƙameni yayi sosai. Munfi mintuna biyu a haka kafin ya ɗagoni ya gyara min zama da ƙyau, wani ɗan mitsitsin flaks ya ciro a jikinsa mai ƙyau sosai ya buɗe. Sai da ya ɗan kalla abinda ke ciki kafin ya kawosa saman lips ɗina, ganin na tsaya kallonsa ya jinjina min kai alamar na sha.. kamar wadda ake bama umarni a hankali na ɗaura nawa hannun akan nashi dake da handglove na gyara zaman flaks ɗin a bakina da ƙyau, ai ko tunda na kafa kai ban janye bakina ba sai da na shanye shayin dake a ciki mai matuƙar daɗi da kauri duka. A take wata irin zufa ta shiga karyo min tako ina a jikina. Sake kwantar da kaina nai a jikin nasa ina sauke numfashi, na jima a hakan kafin na ɗan ɗago ina kallonsa. Hannu na kai a hankali saman fuskarsa zan cire facemask ɗin fuskar tasa ya hana hakan ta hanyar riƙe min hannun yana ɗan jujjuya kansa gefe. Cikin dasashjiyar muryata na ce, “Why?”. Maimakon bani amsa kafaɗuna ya kama da hannu biyu ya kwantar dani a gadon tare da jamin bargo ya rufa min. Sai kuma ya min nuni dana rufe ido batare da yayi magana ba har yanzu. Babu musu nayi hakan, kamar abin tsafi sai wani irin barci ya sake yin awon gaba da ni da alama dama yunwar ce ta tada ni.... *_WASHE GARI_* Yana tsaka da aiki a kitchen kusan shidda na safe kira ya shigo wayarsa. Ringing ɗin da yaji wayar nayi ya nema birkita masa lissafi. Dan ya tabbar ringing ne daya saka shi domin mutum ɗaya. Sai ogansa ma nasa daban. Sai dai kuma mai wannan kiran a daren jiya ya gama jin cewar baya ma ƙasar, shima kuma ya shaida hakan. Da ƙyar ya iya ƙundunbalar ɗaukar wayar ya duba. Tabbas shine kuma da no ɗin Nigeria. To mi hakan ke nufi kuma? Rashin samun amsa ya sashi ɗagawa kafin ta tsinke. Yana kaiwa kunne tare da yin sallama aka katsesa da faɗin, “GGC GARDEN yanzu” daga haka aka yanke wayar ƙittt. Shiru yayi yana mai nazari tare da mamaki. Shi jami'in tsaro ne mai matuƙar fiƙra na sirri. Yasan kaɗan da ga aikin mutanen banza tsara komai. To amma kuma tabbas wannan muryar mai number ɗin ce. Kenan mi hakan ke nufi? Wani ne ya kwaikwayi muryar? Bayan ya samu nasarar samun wayar. Ko kuwa dai su Baba prof sunyi BONONO ne rufe ɗaki da ɓarawo kamar yanda yay zato. Sun shuka ne an tone. Kai shi kam dama dai yayi mamaki ace Maash aka rutsa a Dubai. Duk da hakan zata iya faruwa kasancewar shiri ne babba amma kuma idan za'a haɗa 1+1 ai amsa ɗaya zata bada. Dan shima Maash ɗin shegen kansa ne akwai hatsabibanci... Wayar ya sake ɗagowa ya ƙura ma number ɗin ido, da ga ƙarshe dai ya yanke shawarar fara neman ogan nasa ya sanar masa. Yana ko ɗagawa ya zayyane masa komai. Shi kansa ogan nasa yayi mamaki ƙwarai da gaske da jin wai Maash a Nigeria. Amma sai yace ya dakata bari suyi bincike. Yana nan zaune cikin shirin kira da tafiya ba'a cika mintuna biyu ba kuwa ciff ogan nasa yay kiransa yace yaje Maash ɗin ne dai. Rasama abin faɗa Isma'il Kuku yayi. A ransa kam faɗi yace, (anya Maash ɗin nan kuwa ba aljani bane, anya)..... (😂Nima dai Isma'il na fara tsoron Yayan nan namu gaskiya😝😝). Koda ya isa GGC GARDEN ƙoƙarin sake kiran Maash ɗin yayi, sai dai harta tsinke ba'a ɗaga ba. Sai ma knocking window ɗin side ɗin da yake akai masa. Sauke gilashin yayi, batare da wanda yay knocking glass ɗin yayi magana ba yay masa nunin ya sakko. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Fitowa yay ya kulle motar yabi bayansa. Duk da akwai ƴar tazara a tsakaninsu bazaka taɓa ma tunanin tare suke tafiya ba. Sai dai a ransa yana mamakin a maimakon su bada umarni matsayinsu na jami'ai sune ake bamawa, lallai ƙarfin dukiya na nuna iko a wannan tafiyar. Can cikin vip na garden ɗin ya kaisa, bai kumayi magana ba anan ma ya juya ya fita. Wajen yayi ƙyau sosai, ga haske tako ina kamar rana. Idanu ya ɗan zubama bayan wanda ke tsaye ya juya ma ƙofar shigowar baya. Baƙaƙen kaya ne a jikinsa hatta da hannunsa dake zube a cikin aljihun wando da alamun handglove a tare da su. Hakama kansa yaja hular rigar. Sallama ya sake yi a karo na biyu, zuciyarsa na masa ɗari-ɗarin Maash ɗin ne ko kuwa ba shi ɗin bane. Shiru har fin minti ɗaya kafin ya juyo. A hakan ma fuskar a rufe take da facemask ga gilashi ga hular ta taimaka wajen hana ganin fuskarsa da ƙyau, batare da yayi magana ba ya nuna masa wajen zama shima yana kaiwa zaune. Hannayensa ya harɗe a ƙirji ya zubama Isma'il ɗin ido na tsawon sakanni. Kafin a hankali cikin silent voice ɗin san nan ya furta, “Gaba ɗaya wasan ya canja a gaɓar da banyi zaton fara yaƙin ƙarshen ba.” A karo na farko Isma'il ya saki murmushi, dan tabbas yanzu ya sake yarda da Maash yake magana. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, tare da faɗin, “Ranka ya daɗe wlhy gaba ɗaya zuciyata a ɗari-ɗari take, na kasa gaskata kai ɗin ne ko waninka.” Hannayensa ya warware da ga ƙirjinsa, tare da kai yatsu biyu saman fuskarsa ya zame mask ɗin zuwa ƙasan haɓarsa. A daƙilallen yanayi ya furta, “Ina Ummie na da Mama da ƙanwata?”. Mamaki ne ya ɗan kama Isma'il amma sai yay niyyar latsashi. Cikin ɗan nuna firgita ya ce, “Ranka ya daɗe ban gane ba?”. Shiru yay kamar bazaice komai ba kansa a duƙe, kusan mintuna biyu sannan ya ɗago yana kallonsa. Duk da idanun sakaye suke a cikin gilashi sai da Isma'il ɗin ya dinga jin kaifinsu, dan haka shi ya ɗan rissinar da nashi. Da wani irin taurin zuciya ya furta, “Isma'il ni ba jami'in tsaro bane. Amma brain ɗina da zuciyata na aiki fiye da ta wasu jami'an tsaron dake a cikinku. Ba kuma dan na kasance na daban ba. Sai dai na rayu ne a matsayar ƙin yarda da kowa hatta kaina.” Kai Isma'il ya jinjina yana mai sake rissinar da kansa. Cike da girmamawa ya ce, “Suna gidana. Ƙanwarka kuma ta haihu namiji. Ina mai farin cikin kasancewa wanda zai fara maka albishir guda biyu. Na haihuwa dana alamomin samuwar lafiyar Ummie. Dan da taimakonta suka fito a gidan kamar yanda Mama ta sanar min.” Wani shegen murmushi daya saka Isma'il tsayawa kallonsa ya saki, batare da yace komai ba. Sai da ya ɗan bubbuga table ɗin gabansu da yatsa sannan Isma'il ɗin ya kawo numfashi, sai kuma yaji kunya. Ɗauke kai Maash ɗin yayi da faɗin, “Bayan nan fa?”. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi. “Abunuwa da yawa sun faru a cikin gidan, nasan kuma ƙarin bayani kawai kake son ji, dan in har baka sani ba a yanzu kana da hanyar saninsu ko anan gaba. Sun ɗauke Alhaji, amma abinda na fahimta ba Prof.. bane ba.....” “Nasan inda yake”. Ya faɗa a daƙile. Sai Isma'il kawai ya saki baki yana kallonsa. Sannan cikin in ina ya ƙarasa faɗin, “Anyi uwar watsi tsakanin Hajiya Lawisa da Prof...” Sake sakin murmushi Maash ɗin yayi a karo na biyu, kafin a wani kalar soft voice ya ce, “Miya haɗasu?”. Tsaff Isma'il ya kwashe komai ya sanar masa. Kafin ya ɗora da faɗin, “Amma ranka ya daɗe naji yana sanarma yaronsa Commondo cewar kana Dubai ya maka tarko, yasa an yanke wutar gidan da kake ciki, da network, da ruwa. Sai kuma gaka a Nigeria. Wlhy ni gaba ɗaya ma sai na raina kaina. Anya yallaɓai baka cancanci zama jami'in sirri ba”. Maimakon ya amsa masa sai ya miƙe yana mai maida mask ɗinsa. “Zaka iya tafiya, da ga yanzu zuwa asuba zan tura a ɗauka su Ummie”... Da kallo kawai Isma'il ya bisa, sai da ya ga ya ɓacema ganinsa ya sauke wani nannauyan numfashi yana miƙewa. Kamar ɗazun yanzu ma rakashi akai har mota, yana barin wajen office ya wuce. Dan bazai iya haɗiyewa ba sai ya gana da ogansa.... A ɓangaren Maash ma Isma'il yana gama ficewa ya ɗaga waya yay kira. Cikin bada umarnin ya furta, “Ina son scorpions dake rayuwa a cikin yashi mai zafi kamar guda ashirin nau'i daban-daban daga nan zuwa gobe in ALLAH ya kaimu”. Da ga haka ya maida wayar cikin aljihu batare da ya kashe ba ya shige ƴar bukkar dake a wajen da aka yi ta domin hutawa kawai. Abu ya ɗakko ya fito suka bar Garden ɗin........✍️ Munga idi. Yayanmu kunamai kuma😳? Mi zakayi da shi🤦? To gaskiya kowa yay ta kansa ni dai ba ruwa na🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_ ......Duk wanda yace yayi barci mai daɗi a daren jiya tako wane ɓangare yayi ƙarya. Dan kowa da abinda ya damesa. Daga masu shiryawar har waɗan da aka shirya mawa ɗin. A Maash Mansion dai an samu cigaban isowar Aunty Mama (Aunta Mashi'a) da duk labari ya sameta ta kuma ga komai. Abinda ya tada mata hankali shine rashin sanin inda Ummie take da Paah. Sannan ance Hajiya ƙarama da Baba prof sun bi bayansu suma har yanzu basu dawo ba. Da yake hankalin su Hajiya Mammah ɗin a tashe yake ita da Maman Malika basuyi tunanin bincika gidan Baba prof ɗin ba sai Aunty Mama ɗin ce tai tunanin hakan. Sun ji daɗin jin ya koma gida, itama Hajiya Ƙaramar sai sukai tunanin ko tana asibiti damuwa ta hanata dawowa gidan. Abu na biyu da aunty Mama ɗin tayi shine haɗuwa ita da Uncle Abdullahi da abin duniya yama yawa dan shima dai sai dare ya shigo gidan yanayinsa yasa Maman Malika bashi maganin barci aka samu ya runtsa. Police station sukaje suka fito da duk ma'aikatan gidan da aka rufe. Anan ne suke jin Samraah babu lafiya tana ma asibiti ita. Kasa magana ma Aunty Mama tayi dan ɓacin rai, sai Uncle Abdullahi ne ya balbalesu da masifa. Itama dai sunje asibitin sun ganta. A lokacin tana barci suka gana da likitar dake kula da ita. Bata basu a ɓoye ba ta sanar musu Samraah nada ƙaramin ciki ne, sai dai akwai ɗan matsala dan yaso fita sai dai ALLAH ya taimaka tana fara bleading ɗin aka kawota asibitin. Sunyi nasarar tsaida shi amma tana buƙatar bed rest gaskiya. Sannan duk wani abu da zai tayar mata da hankali ba'a sonshi. Akwai Ummie da take yawan kira ya kamata tazo asibitin ko hakan zai bata nutsuwa. Sai mijinta shima da suke buƙatar gani. Sosai Aunty Mama ta nuna farin cikinta da har ya bama Uncle Abdullahi mamaki. Dan shi dai yasan cakwakiyar da akeyi akan batun yarinyar nan a gidan. Amma yaga autar tasu ita ko'a jikinta ma. Bai daiyi magana ba sai da suka fito daga asibitin. Gefen titi ya samu ya faka motar yana kallonta. “Auta wai halan baki san mike faruwa bane? Duk fa wannan tashin hankalin akan batun yarinyar nan ne”. Murmushin itama tayi tana mai fuskantarsa. Ta ce, “Yaya nasan komai. Sai dai hakan bazai hanani murnar samun ƙaruwar da mukayi ba. Dan koba komai cikin dake jikin yarinyar nan jininmu ne.” “Amma bata hanya mai ƙyau aka samar da shi ba ai kin sani”. “Kamar ya?”. “Fyaɗe fa Awwab ya mata”. Karo na farko dariya ta suɓucema Hajiya Mama. Ta ce, “Humm yaya kenan, wai ku har yanzu kuna akan keken ɓeran da Awwab ya sakaku kenan? Zuwa yanzu ya kamata ace kun gama haddace halayyarsa sai dai ku bama na waje labari kuma. To wannan yarinyar matarsa ce da gaske. Duk abinda kaji Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain ya faɗa shine gaskiyar magana. Abinda keta kai-kawo kuwa shirine kawai na magauta bana raba ɗayan biyu kuma abokan kaduwancisa ne”. “To ke ya akai kika sani?”. “Yaya labari ne mai tsaho, amma bari na gajarce maka shi. Tiryan-tiryan ta bashi labarin komai tun bayan ɗaura aure, ciwon Samraah da kawota asibiti Abuja har zuwa guduwar da tayi ta faɗa hannun Madam Jannifer da sakata amsota da Maash yayi, da kawota gidan matsayin ƴar aiki kamar yanda ya buƙata. Rasama abin cewa Uncle Abdullahi yayi, dan harga ALLAH zancen ya girgizashi. Sai tausayin yaron ya sake kamashi. Tabbas matarsa ta faɗi gaskiya da tace basu damuwa da damuwarsa sai ayyukansu kawai. Haka ya tada motar jiki a sanyaye suka koma gida. Sun samu Hajiya Mammah nata masifa akan dawo da masu aiki da akayi, sai da Hajiya Mama ɗin ta mata bayanin sune suka je suka saka aka sakosu. Cikin masifa Hajiya Mammah ta ce, “Amma banda waccen shegiyar yarinyar ko?” “Saboda mi Adda?”. “Saboda bata da gaskiya, ita dake matsayin ƴar jarida a Kano ubanmi ya kawota nan? Dan ko kunsa an fiddota wlhy sai na maidata. Sai ta faɗi inda Mu'azz yake”. “Addah kina kwantar da hankalinki idan abu ya faru dan ALLAH. Samraah bata da hannu akan kidnapping Yaya sam saboda ita ɗin matar Awwab ce da gaske, kuma shine yasa na kawota nan gidan a wancan lokacin” tsaff ta kwashe labarin komai ta basu kamar yanda ta bama Uncle Abdullahi. Gaba ɗaya falon yay wani irin tsitt tamkar ruwa ya cinye kowa. Hatta da Baba prof dake ƙoƙarin shigowa ƙamewa yay a ƙofar duk da ya jima da yarda da hakan, ya kuma ji bayanin Sheikh Muhammad ɗin, amma jin komai a bakin autar tasa da yanda Maash ya shigo da yarinyar gidan sai yafi jin labarin kamar shine ainahin na gaskiya. Daɓar Hajiya Mammah ta kai a kujera, yayinda Malika da Azizat suka fasa ihu a tare. Da ga ƙarshe ma Azizat zubewa tai a wajen wai ta suma..... 💥💥💥💥 Wani irin kallo take ma jikinta da Commondo dake a gefenta kwance. Bama tasan lokacin data fasa ihun masifa ba a kanshi. Firgigit ya tashi fuska a yatsine. Kafin cikin jin haushi ya ce, “Haba Lawy baby, miyyasa kike abu kamar wata ƙaramar yarinya. Ina barci na mai daɗi da nishaɗi kin wani tadani”. “Nayi ɗin, amma baka da hankali ko? Mika mun?”. Dariya ya kwashe da ita harda ƙyaƙyƙyewa. “Ka jimun ƴar iska. Mi kika kawo kanki na miki dai. Naga keda kanki kika dinga jawoni kina roƙon nayi. Shegiya kinji mazan ƙwarai ko. To miye ma in nayin, naga dai har yanzu matata kike. Kona sake ki ne? Karki manta da aurena kika je kikai aure. Dan haka inada hakki a kanki. Yanzu ba gashi kin tashi fresh ba, basar kawai hajjaju kije kiyi wanka muzo mu tattauna abinda ya dace kafin shegen tsohon nan yasan ina mahaukaciyar matar can take. Dan mune yafi cancanta mu samota mu haɗa da Mu'azz dan uban Maash tsoffinsa duka na hannunmu ai dole ya bamu abinda muke so.” Takaicinsa ne ya hanata yin magana. Batare data tanka masa ba ta miƙe ƙawai ta hau saka kaya. Shiko dariya kawai yake kwasa ta wulaƙanci. Fuuu ta fito a ɗakin sai jin tashin motarta yaji. Baki ya taɓe dan ko'a jikinsa, shi dai ya samu abinda ya ke so. Kuma ya jisa fiye da yanda yay fata. Ya kuma san da kanta zata dawo dan yanzu a tafin hannunsa take neman mafita kawai ce hanyar binta.... ✨✨✨✨ “Isma'il lafiya na ganka haka kamar wanda aka koro?”. “Humm oga am sorry, ai badan ma na riƙe kaina ba zaka iya ganina a fiye da hakan. Tabbas Maash yana gari, dan daga wajensa nake yanzu. Anya mutumin nan bashi da aljanu? Shifa aka nuna bashi da lafiya a asibiti sannan da kunne na naji prof.. na zancen yasa a yanke wutar gidan da yake da network da ruwa, aka kuma zagaye gidansa da jami'ai. Kuma yana da tabbacin yana a cikin gidan fa. Kuma mu kammu mun tabbatar ya shiga Dubai a shekaran jiya. Amma gashi yau alamu sun nuna a Nigeria ya kwana. Wlhy ni a karan kaina da nake amsa sunan jami'in tsaron sirri al'amarin sa ya fara bani tsoro. Irin waɗan nan ne idan suka zama cikin jami'an tsaro suke aiki mai ban mamaki, idan kuma suka kasance criminals suke mummunar ɓarna dan suna da matuƙar wayo da fiƙra. A yanzu haka bana raba ɗayan biyu dama yasan da shirin duk za'a masa haka a Dubai ɗin shine ya basu ƙafa, dan ya tabbatar min yasan inda mahaifinsa yake ma”. “What?!”. “Wlhy oga haka yace ya sani, kaga tabbacin duk motsinsu kenan yana sane. Sai dai abinda ya ɗan ruɗar da ni anan prof ba shine yay kidnapping Alhaji Mu'azz ba, kuma bana jin Maash ɗin zai yi hakan saboda kisan da akama drivern. Anya kuwa matar nan ko Commondo ɗin nan basa cin dundumiyar prof ta ƙarƙashin ƙasa?, dan bana raba ɗayan biyu Alhaji Mu'azz na hannunsu”. Nannauyan numfashi ogan nasa ya sauke dan tabbas maganar yaron nasa abar a duba ce. Idan kuwa haka ne lallai wannan wani point ne da zaisa su sami Commondo ko Hajiya Lawisa a hannu. Dan dolene su kama ɗaya a cikinsu. Lokacin da zai fara motsi shima yayi a garesa. Maganar ɓoye kai da ainahin matsayi ta ƙare. Sun cigaba da tattaunawa musamman akan takun da Maash ɗin yazo da shi. Shi kansa ogan nasa kai kawai yake jinjinawa da hatsabibancin yaron. Dan tunda suka fara aiki akan wannan case ɗin matsayin jami'an sirri da yawan bayanai shine ke basu kafin su su binciko. Dan ba ƙaramar gudunmawa yake basu ba akan aikin nan, hatta baza mutane cikin family ɗin shine ya bada shawarar da ƙirƙirarta. Kuma har yanzu bai san ainahin shine ogan ba saboda wani dalilinsa da ya barma kansa sani. Shi kansa Isma'il ɗin sai kwanan nan ya sanshi, kuma shima bai san ainahinsa ba balle alaƙar data alaƙantashi da Maash ta zahiri.......✍️ 🤔To oga kai waye? Muma ya kamata mu sani ai koya kuka ce🤷?. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚_ ......Ba ƙaramin shock ta shiga ba lokacin da take shigowa gidan taci karo da duk ma'aikatan sun dawo gida. Ga batun auren Maash da Samraah zance dai ya fito. Ko kallon inda Baba prof yake batayi ba. Ita ta duba Azizat tai mata allura aka maidata ɗakinta. Tana ƙoƙarin tashi ta shige ƴan sandan dake bincike akan ɓatan Paah suka zo gidan kusan tare da Uncle Abdullahi da ya fita. An samu wayar Paah da sukai tracking, sun sameta a gaba kaɗan da inda aka sami gawar drivern sa, da alama an yardata ne daga baya. Dan a yanzu haka suna kan yin wani bincike na duk inda aka shiga da wayar a jiya kafin a yardar da ita suna fatan samun nasara. Sannan an samu sayin yatsun hannu har na mutum uku a jiki shima suna kan bincike, shiyyasa zasu bibiyi duk inda yaje ɗin...” Tamkar jira Baba prof keyi cikin nuna jin daɗi ya ce, “Idan ko hakanne officer ya kamata a fara da duka sayin yatsun hannayenmu mu da muke gidan nan, tunda daga nan ya fita zuwa gidana. Can ma kuje ayi komai yanda ya dace kafin shegun su farga su ɓadda sawu” ya ƙare maganar yana wani sakin murmushin mungunta da kallon sashen da Hajiya ƙarama ta ke. Da sauri ta gyara yanayinta tana mai watsa masa wani mugun kallo ta ɗauke kanta. Sai ya sake sakin wani murmushin da cije lips ɗinsa. A ransa yace (ƙaramar shegiya zanyi maganinki. Sai na dafaki a tsaye ai. Zaki tabbatar da ni Uban ubanki ne a iya hatsabibanci). Ɗari bisa ɗari ɗan sandan ya yarda da batun Baba prof ɗin, sai dai yace zasu je su dawo dan babu kayan aiki a tare da su yanzu. Duk kuma wanda ya fita daga gidan zuwa kafin su dawo yana cikin suspect nasu. Daga haka suka fice.. Fitar tasu bai fi da mintuna ba wayar Hajiya Mama ta fara tsuwwa. Ganin mijinta yasata ɗagawa cike da zumuɗi. Duk idanu suka zuba mata. Wani irin miƙewa tayi cike da tsantsar farin ciki ta furta, “Alhamdullahi ALLAH mun gode maka. Yanzu haka kuna a cikin gidan nashi kenan?”. “To Masha ALLAH muna zaman jiran ji daga gare ku, dan fatanmu kawai asan ina Awwab yake yanzun”. Ɗan jim tai alamar saurare kafin ta yanke kiran ta dubi duk wanda ke a falon da wani irin zaƙuwa ta ce, “Ana fatan samun Awwab a cikin gidan nan. Ashe an katse masa duk network da wutar gidan ne da ruwa. A yanzu haka Daddyn Irfan ya tabbatar min sunata shiga da fitar ganin an ɓalle ƙofofin gidan, idan har yana a ciki zuwa dare zasu taho Nigeria da shi”. Wani irin makirin murmushi Hajiya Ƙarama ta saki tana kallon Baba prof da zufa ta gama jiƙema gaban goshi. Da yatsa ta masa alamar 1-1 tana kashe ido ɗaya. Sai kuma ta miƙe zumut tana faɗin, “Alhamdullahi, mun godema ALLAH”. Yanda tayi ɗin ya saka kowa maimaita kalmar Alhmdllh ɗin Maman Malika da Hajiya Mama harda rungume juna. Ita kanta Hajiya Mammah ta nuna farin cikinta duk da har yanzu batun auren nan na Maash ya kasa haɗiyuwa a wuyanta. Zancen Baba prof ne ya katse musu murnar tasu. “Anya kuna ganin ya kamata Awwab ya dawo ƙasar nan babu iyayensa a gidan nan, babu matarsa, babu Fahad?”. Gaba ɗaya murnar tasu ta koma ciki, dan gaskiya Baba prof ɗin ya faɗa. Wayarsa ya ɗauka yana miƙewa da faɗin, “Abdullahi bamuga ta zama ba muje ko”. Miƙewa Uncle Abdullahi yayi yana faɗin, “Baba bara na ɗan canja kaya” ya nufi hanyar sashensu, yayinda Hajiya ƙarama ta saki murmushi dan ta gane wayo ne kawai ya sashi barin gidan. Duk da kuwa wanda aka lissafa ɗin duk bai san inda suke ba. Amma jin za'a buɗe Maash yake son zuwa ya nemo mafita.... Uncle Abdullahi na shiga bedroom ɗinsa ya ɗakko wata ƴar ƙaramar waya. Kunnawa yayi sannan yay kira. Ana ɗagawa. Daga can cikin bada umarni ya ce, “Ku saki yaran nan daga nan zuwa awa ɗaya da kwata. Sai dai ku tabbatar basa a hayyacinsu”. Daga haka ya yanke wayar yana wani makirin murmushi. Kasheta yay gaba ɗaya ya maida inda ya ɗakkota sannan ya canja kayan ya fita kamar bashi ba... Bashi kaɗai ba, a ɓangaren Hajiya ƙarama ma a hargitse ta wuce ɗakinta. Kira ta dannama Commando. Yana ɗagawa zai fara mata surutun banza a tsawace ta ce, “Akwai matsala fa. Mun manta wayar nan duk mun taɓata da hannayenmu kafin a jefar da ita, sannan bamu kasheta ba. Yanzu ƴan sanda sun samo wayar kuma shirinsu shine bibiyar sayin yatsun mutane uku da suka gani a jiki. Kaga kuwa akwai nashi, nawa, naka. Ga shi wannan tsinannen tsohon yace a fara da nan gidan kuma nasan danni yayi haka. Sai dai da yake bani da hakkin matsiyaci yanzu ake sanar ma Mashi'a ana ƙoƙarin buɗe gidan Awwab ashe sakawa yay aka yanke masa wutar gida da network da duk wani abinda zai iya tabbatar da yana a gidan sannan yasa jami'an tsaro suka zagaye gidan kamar dai yanda ya taɓa sawa akama Shamsu. Shine ya wayance da wai bai kamata Awwab ya dawo babu iyayensa babu Fahad ba. Kaji makiri fa, nasan neman mafita ya tafi dan in har aka samu Maash a gidan nan ya kuma fito a yau kashinsa ya gama bushewa”. Ƴar dariya commondo ya saki daga can da faɗin, “Cakwakiya kenan. Yanzu yaya za'ayi to?”. “Ya kamata dai musan mafita kam. Dan in ba hakaba tofa wasan zai canja salo in har Awwab ya fito. Kai dai kasan halin mutumin nan kansa kawai ya sani. Duk kuma yanda zai yi yaga ya fidda kansa a wannan gaɓar zai yi ɗin tunda babu wata alama data tabbatar da shine ya ƙulla duk wannan harmutsin jiya zuwa yau ɗin. Shi kuma Awwab ba kanwar lasa bane ba” “Ya kamata kizo ki sameni. Dan bamuga ta zama ba.” Daga haka ya yanke kiran..... 💢⭐💢⭐💢 Alhamdullah jikin Abba yayi sauƙi, ƴan Gwarzo da labarin komai ya sama suma ta ɓangaren su Gwaggo Gudidi da ɓangaren mahaifin su Samraah ɗin su kawu Musa kenan duk sun shigo ganinsa. Basuyi ƙasa a gwiwa ba kuma suka haɗa community zuwa gidan Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain. Sai dai basu sami ganinsa ba ance ya wuce Lagos. Haka dole suka haƙura suka koma gidan Abba da shima aka sallama. Sun sake zaman meeting kan zuwa can Lagos ɗin. Dan har yanzu basu san halin da Samraah take ciki ba su. Sun kira no bata shiga, an kira ta Hafizzullah duk ba'a samu. Ga Musaddiq da yaga komai a Media yanata faman kiransu cikin tashin hankali. Dan har yana tabbatar musu da shifa zai dawo gida. Sai da sukaita tausarsa dai.... A yayin da su suke cikin wannan damuwa da tashin hankali ita Mom ranta fari ƙal. Sai ma siɗaɗewa tai tabar gidan zuwa gidan Ummanta. Cike da nishaɗi sukaita tattauna batun. Duk da zaka iya fahimtar tsantsar hassadar su a cikin zancen game da jin wai Samraah Maash ta aura. Sai da suka gama ƙulle-ƙullen sharrinsu sannan suka koma kan tattauna batun Baby dake matuƙar ɗaga musu hankali. Abu kamar wasa kwanaki nata sake tafiya. Bata ba mijin nata babu batun zuwa makarsu bayan sun gama baje gari da zance. Dan su har yanzu hankalinsu bai fara basu akwai babbar matsala ba, balle su fara ƙoƙarin neman ahalin mijin baby ɗin. Bata jima ba ta koma gida tunda ta baro shi cike da mutane. Sai Halime baiwar ALLAH dake ta fama da kanta keta hidima da su ga hidimar Abba shima. Dan ma su Aunty Zakiyya na tayata..... 💓💓💓💓 A guje ɗaya daga cikin securitys ɗin ƙofa yazo yana sanar ma su Hajiya Mama dake cikin gida duk da ita tana ma ƙoƙarin wucewa duba jikin Samraah ne ita da yaranta. Haka itama Hajiya ƙarama ta fito ne zata wuce wajen commondo amma da shirin asibiti kamar can ɗin ta nufa. Yanda jikinsa ke rawa ya gagara iya cewa komai ya saka Hajiya Mammah daka masa tsawa. Da ƙyar ya iya nutsuwar shaƙar numfashi da fesarwa sannan ya sanar musu ga wata mota ta ajiye su Fahad a ƙofar layin nan. Yanzu nan securitys ɗin farkon layi suka kawosu wasu kuma sunbi mai motar. Kafin ya gama rufe baki ma'aikatan gidan suka shigo ɗauke da su Fahad da ke cikin yanayin barci. A saman kujeru aka shinfiɗar da su, hakan yasa kowa yin cirko-cirko kawai ana kallonsu. Musamman ma Hafizzullah da Hajiya Mama ta zubama ido. Sai zuwa can tai ƙarfin halin tambayar shi wanene?. Maman Malika ce ta bata amsa da bayani gamsashe. Murmushi ta saki tana mai jinjina kanta.. Sai kuma ta juya ta zaro waya tai kiran Baba prof. Kamar wanda ya daburce ya shiga amsa mata harshe a cuɗe, ita harma yanda ya ruɗe ɗin yaso bata mamaki. Amma dai batace komai ba. Babu jimawa kuwa sai gashi ya iso. Dai-dai nan suma ƴan sandan nan suka dawo. Su kansu sunyi mamakin dawo da su Fahad ɗin, duk da dai su dama ba'a ma san ainahin abinda ya faru da su ba. Tunda aka fara dambarwar nan babu su a gidan. Hajiya ƙarama ce ta dubasu domin tabbatar da lafiyarsu. Yanda ta ɗago tana wani jijjiga kai ya sakasu zuba mata ido. Cikin nuna damuwa ta ce, “Babu abinda ya samesu da alama ma shaye-shaye sukayo.” “Shaye-shaye?!!”. Kusan atare kowa na falon ya faɗa. Sai da taji zuciyarta tayi wani irin tsargawa amma ta dake tace eh. Masifa Hajiya Mammah ta fara akan Hafizzullah ne ya koya ma Fahad to, dan Fahad dai baya shaye-shaye duk sun san da wannan. Babu wanda ya iya cewa komai a falon. Sai Baba prof dake a cikin ruɗani. Sai kuma Uncle Abdullahi daya kafe Hajiya ƙarama da kallon mamaki. Dan a wannan gaɓar dai shi shaidane tayi ƙarya.. Ma'aikatan gidan aka kira suka ɗaukesu suka maida sashen Fahad ɗin, daga haka kowa ya kama gabansa tunda su ana ganin babu wata matsala a tattare da su sunje sun shawo kayan maye ne........✍️ Uhhmmm Uncle Abdullahi??? To bance dai komai ba🤔🏃 _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_ ........A hankali na dinga buɗe idanuna da sukai min matuƙar nauyi, ɗakin na fara bi da kallo. Take komai ya shiga dawo min dalla-dalla. Ciki harda abinda ya faru a daren jiya. Waige-waige na fara yi, sai dai babu ko alamar wanda nake son ganin, sai ƴar sandar nan kaɗai zaune a kujerar gaban gadon da nake tanata zabga game a waya. Wani irin rauni naji zuciyata tayi, dan na fahimci tabbas nayi mafarki ne a daren jiya kenan. A cikin mafarki Maash ya kawo min ziyara harda shayar dani shayi mai daɗi. Hakan na nufin koda bama tare zukatanmu na tare. Idanun kawai na maida na kulle, sai da na ɗan sake jimawa a hakan kafin na yunƙura na tashi zaune. Dai-dai nan Nurse ta shigo. Da sauri tayo kaina batare data damu da ƴar sandar nan ba. Zanyi salla nace mata. Babu ko musu ta kamani zuwa bayi. Ita ta taimaka min nayi al'awar ta sake fito da ni. Ganin bazan iya tasowa ba ina ganin jiri tace nayi sallar a zaune. A zaunen kuwa nayi ta, ina idarwa na zame a wajen na kwanta dan babu abinda kuma nake buƙata yau sama da waje mai sanyin. Dai-dai nan Alaja ɗin nan data ɗakkoni daga hannun Madam Jannifer wadda Mama ta sanar min autar su Paah ce ta shigo da sallama. Likita biye da ita sai wasu yara masu ƙyau sosai daka gansu kaga ƴan hutu. Wani kalar faɗuwa gabana yayi, babu shiri na zabura na tashi tsaye. Da sauri doctor ɗin ta kamani ta zaunar a bakin gadon tana faɗin, “Please calm down kada ki ruɗar da kanki. Dan yanzu yin wani babban yunƙuri a gareki haɗari ne.. Murmushi itama Alaja ɗin tai mun, tare da zama a kusa da ni ta rungumoni jikinta. “Cool dawn my Daughter cool down.” Sai a lokacin na sauke ajiyar zuciya. Zancen Yaya Awwab na wancan ranar na dawo min akan batun shine ya sakata ta ɗakkoni ai da ga gidan Madam Jannifer. Gaisheta nayi, ta amsa min da kulawa, tare da tambayata jikina. Na tabbatar mata da Alhamdullah. Suma yaran suka gaisheni. Amsa musu nayi, tare da miƙa musu hannu cikin ƙarfin hali ina murmushi. Babu musu kuwa duk suka zo gareni.. sai da taga suna neman haye min jiki ta dakatar da su. Baki suka dinga turawa cikin shagwaɓa. Ni sai ma suka bani dariya dan su duka sun kai kusan 12years da 10years. Amma Abinka da rainon madara. Hajiya Mama da kanta ta bani abinci naci, doctor ta shigo ta dubani ta bar Nurse ta bani magunguna sannan suka fita. Duk yanda naso daurewa na kasa. Sai da na tambayeta Ummie na lafiya, sannan anga Paah. Aunty Falaq kuma ta haihu?. Sai da tayi ɗan jim kafin ta saki murmushi da faɗin, “Everyting Alhamdullah daughter. Yanzu ki kwanta ki huta, idan kika samu lafiya duk zaki ji komai, za kuma ki gansu.” Kaina na ɗan jinjina mata kawai. Ina son tambayar ta Maash ko ya kira waya amma ina jin kunya. Dan ban san yanda zata fassara al'amarin ba tunda koba komai matsayin suruka take a wajena. Haka na haƙura na kwanta ina mai lumshe idanuna.... 💢⭐💢⭐💢 Gaba ɗaya komai ya ida daburcewa Baba prof.. suna isa gida yace driver ɗinsa ya biyosa dan tun a can Maash Mansion suka rabu da Uncle Abdullahi. Ya turashi wani waje akan shima zai je wani waje. Cikin rawar jiki kuwa ya bisa har falo. Wasu azababbun maruka har huɗu ya dinga sakar masa. Kafin ya shaƙe mas wuya ya buga kansa da bango. Wahalalliyar ƙara ya saki jikinsa na rawa. Sai da prof yaga numfashinsa na barazanar barin jikinsa sannan ya wancakalar da shi gefe aiko ya faɗa akan hannunsa ji kake ɓasss alamar karaya. Wata ƙarar ya sake saki da ko fita batayi, sai ga zufa na wanke masa jiki. Babu ko tausayi a idanun Baba prof ɗin ya take hannun daya karye ɗin tare da duƙowa kansa ya sake shaƙar wuyarsa ya ce, “Ya akai waɗan can yaran suka fito??”. “Wlhy! Wlhy ban sani ba yallaɓai. Na rantse da ALLAH inda kace na kaisu can na kaisu. Kuma ko daren jiya na kai musu abinci. Yau ne kawai ina shirin fita da safen nan zuwa wajensu kace min zamu fita shine na bari akan sai in mun dawo naje ɗin. Amma wlhy ban san tayaya akai hakan ba. Ban san wanene ya fito da su ba, babu kuma wanda na saka ya tayani aikin balle nace wani yaci amanata”. Sake falleshi da mari yayi. Ya mutsika hannun da ƙafa har sai da ya saki fitsari. Cikin azababbiyar murya ya ce, “Idan baka faɗa da arziƙi ba zaka faɗa ta tsiya ai dan ubanka. Sai kayi dana sanin sani na”. Ya ƙare maganar yana kai waya kunnesa. “Commondo ka sameni yanzun nan a gida”..... Kallon Hajiya ƙarama da ke tsaye Commondo yayi, cikin taɓe baki kasancewar taji komai ta ce, “Wannan wawan fa ya fara haukacewa wlhy. Jeka dai ka jiyo mana mike faruwa zan jiraka. Dan nina a haukacen nake. Dolene fa yau muyi wani motsi”. Kamar Commondo zaiyi magana sai kuma ya fasa. Miƙewa yay yana murmushi, sai kuma ya kai mata runguma ta kauce tana harararsa. Dariya ya kwashe da ita yana ajiye karan sigarin hannunsa a ɗan bowl ɗin daya tarasu da yawa ya fice. Raka bayansa tayi da harara itama tana kaiwa zaune. Wayarta dake ringing ta ciro a jaka tana kaiwa kunnenta. Bayan sun gaisa ta ce, “Jannifer ki kasance cikin shiri fa, da zarar na tura miki text ko na kiraki ku shiga gidan. Dan ina gama jin cikin wawan nan shima yanzu aikinmu zai fara”. “Baki da matsala hajjaju na. A yanzu haka na shirya tsaff ni da yarana”. Jannifer ta faɗa daga can cike da nishaɗi. Wayar Hajiya ƙarama ta yanke itama tana murmushi. Dan ita kaɗai tasan nata plans ɗin, daga Commondo har Prof a tafin hannunta suke..... A ɓangaren Commondo yana isa ya samu Baba prof cikin bikitaccen yanayi, ga driver ɗinsa kwance a tsakkiyar falon hannu ya kumbura sosai, bawan ALLAH har yayi sumar wahala. Kallo ɗaya commondo yay masa ya ɗauke kansa. Kan Baba prof ya maida yana mai faɗin, “Ranka ya daɗe gani”. Wata irin iska mai masifar nauyi baba prof ya furzar. Kafin cikin shaƙaƙƙiyar murya ya ce, “Commondo akwai matsala. Wannan wawan ya jiƙa mana aiki ɗaya”. “Aiki? Wanne kenan a ciki ranka ya dade?”. Kallon Commondo ɗin yay da juyayyun idanunsa ya furta, “Yaran nan sun kuɓuta. Fahad da ƙanin yarinyar nan”. “What?!!”. Commondo ya faɗa yana wani miƙewa. Dan shi kansa yanada babban target akan Fahad a daren yau. Dan tunda Prof ɗin ya sanar masa suna a hannunsa sune farkon plan nashi. Hannu baba prof ɗin ya yarfar shima cikin zafin rai ya ce, “Wai mike shirin faruwa ne? Tabbas ana bibiyar bayanmu”. “Yallaɓai waye zai bibiyi bayanmu amma? Kafa ce Maash yana ƙarƙashin ikonka shi da jarababben PA ɗin nan nashi. Yarinyar nan tana asibiti a ƙarƙashin kulawar likita da jami'an tsaro. To kodai Mahaifiyar Maash ɗin ce? Dan tabbas ina ji a jikina matar nan ta samu lafiya......” “Nooooooooo!!!! Bazai yiwu ba Commondo bazai yiwu Ummu-Hidaya ta taɓa samun lafiya ba har sai idan nine naso hakan. Kuma zanyi hakanne a gaɓar dana shimfiɗe gawawwakin yaranta biyu a gabanta na durƙusar da ita bisa gwiyawunta ta damƙa min dukiyar da tai min gadara a kanta sannan, dan banaso Ummu-Hidaya ta mutu yanzu. Sai ta wulaƙanta, ta rasa inuwaf raɓawa taji sanyi. Idan har kuma wani ya bata wannan inuwar wlhy sai ta gwamci GARA RANA DA ITA...” Kai kawai Commondo ya jinjina masa, sai kuma cikin sauke numfashi ya ce, “Banƙi ta takaba oga. Amma yakamata fa zuwa yanzu mufara tunani irin na mutane guda biyu. Idan ba haka ba taya akai ta gane hanyar da zasu gudu a ranar? Sannan da suka gudun shi wanda ya taimakesu wanene shi?. Oga akwaifa tufƙa da warwara a al'amarin nan na wannan karon. Anya kuwa? Anya Maash bai baka ƙafa ba? Ka kuwa tabbatar guy ɗin nan zai yarda ya faɗi ƙasa irin haka da sauri. Maash ba ba wawa bane kansa na aiki fiye da gudun sakannin agogo. Ina baka shawarar kayi bincike shin da gaske ne har yanzu Maash na'a gidan can? Hakama PA ɗinsa. Idan har mun samu wannan tabbacin to dolene a cikin yaranka bayan Maash akwai wanda yasan wani abu kuwa. Ko kuma dole mu yarda Ummu-Hidaya ta samu lafiya. Dan kowowar su Fahad gida kam akwai ayar tambaya akai....” Kasa magana Baba prof yay, sai idanu da ya tsurama Commondo tamkar mai nazarin zantukansa. Jirin dake neman yadda shi ƙasa ya sashi kaiwa zaune. Hannunsa har rawa yake wajen ƙoƙarin ɗaukar wayarsa. Danne-danne ya shiga yi tare da kai wayar kan kunensa. Sai dai layin ɗaya kira yaƙi shiga. Sake gwadawa yay har sau fiye da goma amma bata tafiya. Kallon Commondo ɗin yayi cikin ɗan rikicewa. Kafin ma yay magana Commondo ya ce, “Miya faru? Waka kira?”. “Zain bin Abideen. Kuma layinsa yaƙi shiga. Dole ne nai shirin tafiya Dubai daren yau da sunan duba jikin Awwab”. “Shawara mai ƙyau sir”. Commondo ya faɗa cike da bashi ƙwarin gwiwa. Daga haka suka cigaba da tattaunawa. Bayan sun kammala Commondo ya ɗauki drivern na baba prof ya fita da shi zuwa mota. Shi kuma sai ya miƙe yana mai cigaba da neman number Zain bin Abideen. Ganin bazai samu ba yay kiran airport cewar yana buƙatar ticket ɗin Dubai. Sun tabbatar masa yau jirgi bazai tashi ba sai gobe dan sunada matsalar hazo. Bai damu ba dan a haukarsa yana da isashen time ɗin kaiwa goben zai dai cigaba da neman Zain.... 🌟🌟🌟🌟🌟 A ɓangaren Maash kamar yanda ta faɗa bayan sallar la'asar shi da Hayatu da isowarsa ƙasar kenan suka ɗunguma zuwa gidan Isma'il Kuku. Lokaci Ummie na zaune bayanta goye da jinjirin Falaq da Mama taima wanka. Yayinda Falaq ke kwance kanta a cinyar Ummien tanata mata surutu akan Awwab da Fahad Ummie na murmushi kawai dan bata iya doguwar magana. Da ga Maash har Hayatu sumar tsaye sukai. Dan harga ALLAH shifa Maash ba yarda yay da maganar Isma'il ba ɗazun. Duk da yasan kaɗanne daga hukunci UBANGIJI ace Ummien ta samu lafiyar. Duk da dai tun kwanaki ya ɗan so gano wani abu game da ita amma taƙi bashi kowace irin ƙofa. Wani kalar tsuma jikinsa ya farayi jijiyoyin kansa na miƙewa lokacin da take kai hannu saman kan falaq ɗin ta shafa tana Murmushi. Cikin karyayyen harshenta ta ce, “Muhammad ɗina bai canja ba dai”. Ƴar dariya Falaq ɗin tayi da faɗin, “Tabb Ummie ai Yayana bazai taɓa ya canja ba ALLAH. Kinga yanzu ƴan gidan nan duk tsoronsa suke fa. Shi dai kinga sai ya gadama in kayi magana goma ya amsa maka ɗaya. Baka isa gane ainahinsa b....” Ta kasa ƙara sawa sakamakon kaiwa ƙasa da Maash yay rijiff........✍️ Zazzaɓi🥶🥶🥶🥶🥶. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_ ......A firgice duk suka juya suka kallesa. Da ga Ummie har Falaq sai da suka ji shock, bare ma Mama Balki dake kitchen tana haɗa musu abinci dan babu wanda yaji motsin shigiwarsu. Jikin Ummie rawa ya fara yi, duk ta daburce, ƙoƙarin kwance Babyn bayanta take da alama so take ta koma yanayinta na da amma Mama Balki ta riƙe hannunta. Kuka ta fashe da shi tana mai girgiza mata kai. Ta ce, “Dan ALLAH Aunty karkiyi haka. Kada kice zaki cigaba da ɓoyema Alhaji ƙarami wannan ni'imar. Ɗan ZAKI ya riga ya girma aunty. Wannan ba Muhammad Awwab ɗin da kika sani bane da zaki iya zama da yanayin wahala domin bashi kariya. Wannan na yanzu ke zai bama kariya da ƙarfin ikon ALLAH”. Wani irin kuka Ummie ta fashe dai-dai Maash na kai goshinsa ƙasa yay sujidar shukur. Ya jima dirƙushe a hakan shi da Hayatu da tuni ya bisa shima yayi. Yana ɗagowa Hayatu ya faɗa jikinsa ya wani kalar rungumesa yana sakin kuka tamkar ba Hayatu ba. Ca yake “Yayanmu Ummie ta dawo garemu. Ummie ta dawo? Ummie ta dawo Yayanmu. Dan ALLAH kar kuce mafarkin dana saba yi ne”. Sai kuma ya sake ƙanƙamesa kamar yanda shima Maash ɗin ya wani matsesa a jikinsa dan gaba ɗaya ma shi baya a hayyacinsa. Karan farko Ummie ta share hawayenta tare da sakin Murmushi tana mai miƙewa. Goyon Babyn ta gyara sannan ta nufesu. A hankali ta kamo kan Maash ta rungume, tare da riƙo hannun Hayatu ta sumbata. Sai kawai ta sake fashewa da kuka. Da gudu itama Falaq ta taso ta rungume Ummie. Miya rage, itama kawai sai Mama Balki ta nufosu. Sun jima a haka suna kuka su dukansu. Yayinda idanun Maash suke a rufe har yanzu dan shi babu ɗigon hawaye a cikinsu. Sai dai jijiyoyin kansa sunyi wani kalar masifar tashi dama na illahirin jikinsa kasancewar rigar jikinsa mai ƙaramin hannu ce. Hatta gashinsa duk sun mimmiƙe. Wani irin sakin Hayatu yayi ya damƙe Ummie ya rungume tare da sakin kuka mai ƙarfin gaske. Abinda Hayatu da Fakaq basu taɓa gani ba kenan tunda suke a rayuwarsu. Gara Mama Balki ita tasan ƙuriciyarsa. Duk da Maash tun yana yaronsa duk abinda kaga yama kuka lallai wannan abu ya kai intaha kuwa. Fashewa suma sukai da kukan Hayatu na kama hannun Falaq suka shige bedroom suka rufo. Itama Mama Balki dake kuka kamar ranta zai fita sai kawai ta wuce kitchen da sassarfa... Kuka sosai Ummie keyi da Murmushi a lokaci ɗaya tana mai shafa kan Maash dake kwance a kan ƙirjinta. Sai kuma a hankali ta fara raira masa waƙar da take masa lokacin yana ƙarami. Tare da ɗago kansa tana kama kumatunsa duka biyu ta ja. Dariya kuwa ya saki irin wadda da yawan mutanen da suka sanshi zasu iya rantsuwar basu taɓa ganin yayi ba. Itama Ummien dariya ta fara tana dungure masa kai da jan hancinsa sannan ta fara goge masa hawayen da manyan yatsun hannunta biyu. Sai da ta gama taass sannan ta jingina goshinta akan nasa tana murmushi. “U...m...m...ie”. Ya kira sunanta a wani irin rarrabe. Da harɗaɗɗiyar muryarta ta ce, “Na'am Muhammad Awwab ibn Ummu-Hidaya Ibrahim”. Dariya ya sake yi da rungumeta da ƙyau. Dan sunane da yake kiran kansa da shi yana yaro a duk sanda ya fahimci Paah ya ɓata mata rai. Duk da tana ƙoƙarin ganin basu fahimta ba amma ƙulafucin Awwab sai ya gano. Dan ko yaya ya ga fuskarta ta canja yata bin ƙwaƙwƙwafinta kenan har sai yasan waye ya ɓata mata ran. Idan Paah ne bazai sake masa magana ba. Zai kuma ce sunansa ya koma Muhammad Awwab ibn Ummu-Hidaya Ibrahim... Sake ƙanƙameta yay da faɗin, “Da gaske ba mafarki nake ba kamar yanda na saba Ummie na?”. “Ba mafarki kake ba my heartbeat. Ummien ka ce. Itace a gabanka. Kayi haƙuri Muhammad, kayi haƙuri. Nayi komai ne dan ku. Na karɓi komai ne dan ku. Nayi haƙuri da komai dan ku. Duk da bani da tabbacin zaku rayu ko ni na rayu har zuwa wannan lokaci. Amma ina fatan hakan a raina a duk lokacin da hankalina ya dawo jikina kafin magauta su farga su maida ni ruwa. Nayi haƙuri da rasa Abie a dalilin rashin fahimtar gadar zare, amma bazan iya haƙuri da sadaukar da ku ba a lokacin dana banbance baƙi da fari. Muhammad ina Fahad, ina Autana yake. Ina yarinyata take. Dan ALLAH ka kaini naga Fahad da Samraah yanzun nan”. Da sauri ya ɗago yana kallonta. Sai kuma ya motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Samrh!”. “Yes dear. Ina son naganta?”. Kafe Ummie yay zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri. So yake yay magana amma ya kasa. Fahimtar hakan ya sata sakin murmushi. Ta ɗan girgiza masa kanta tana mai kaiwa zaune dan ta gaji da durƙuso akan gwiyawun nata. Da sauri ya kamata ya zaunar da ƙyau, murmushi ta sake sakar masa da kama fuskarsa ta sumbataci goshinsa. Sai kuma ta lakace masa hanci da faɗin, “Kallon fa. Kana mamaki ne?”. Kasa cemata komai yay sai idanu daya kafeta da shi. Murmushi ta sake yi da faɗin, “Nifa bana son miskilanci”. Murmushi ya sake mata a hankali yana kai rissinar da idanunsa. Itama sai ta saki murmushin tana mai sauke numfashi. “Ummie tun yaushe kika warke?”. “Muhammad kowane labari nada nashi tushe. Kamar yanda gini ke farawa da tushiya, tsirrai ke farawa da mafari. Ɗa a cikin uwa ke farawa da gudan jini. Samraah na cikin mutanen da suka shigo rayuwata a ƙarshen labarina. Amma tana cikin mutane masu muhimmancin da kwatantashi bazai yiwu da baki ba. Ka bar batun su Bilkisu, waɗan nan sunansu JINI NA, kamar yanda kai da Fahad kuke JINI NA. Amma tabbas warkewa ta ta fara ne daga lokacin da Samraah ta shigo rayuwata bisa hukunci da amincin UBANGIJI. Muhammad ka tashi, maza tashi ka kaini ga Mahaifinku da Samraah da Fahad. Ko kaje ka kawo min su na gansu, ina son mu bar ƙasar nan mu duka a yau kafin maƙiya su farga da mu na roƙe ka”.... “Kinfi ƙarfin barin ƙasar nan saboda WAWAYE Ummie. Sai dai su su GUDU su barta, dan a yau zaki kwana a cikin MAASH MANSION ne ma”. Ya faɗa da wani irin salo mai nuna gwarzantaka da tsantsar bajinta da babu ɗigon tsoro a cikinta. Kai Ummie ta girgiza masa cikin rauni. “No Muhammad. No. Bazan sake komawa gidan can ba, kasan kuwa su wanene ke cikin gidan nan? Kasan kuwa ƙarfin bushewar zukatansu? Kasan kuwa ƙarfin rashin imaninsu da abinda zasu iya?.” “Ummie!!! Please. Kar kice na BARI. Dan kansu kawai suka sani, kisa a ranki kawai yanzu ne WASAN ZAI FARAAAAAAAAA!!!!”. Yanda yay maganar yana bubbuga yatsarsa a ƙasa jijiyoyin jikinsa na wani irin masifar tashi ruɗu-ruɗu abinka da mai buɗaɗɗen jiki, ga idanun gaba ɗaya sun gama birkicewa. Sai da Ummie ta firgita. Wata irin amsa kuwwa Muryar mahaifinta ta shiga mata a cikin kunne. A lokacin da suka je Spain harda Abie kawai sun fita yawo shi da Abie ɗin sai gasu sun dawo wuyan Awwab zane da tattoo ɗin fuskar zaki a gefen wuyarsa da har yanzu shine dai. Da mamaki ta kamashi tana dubawa. Hankalinta ya tashi ta fara masa faɗan waye ya masa Tattoo? Abie yana ina aka masa. Babu shakka ko tsoro ya ce, “Ni naje aka mun Abie ya biya saboda ni ZAKI NE”. Haushi ya saka Ummie mangaresa. Sannan rai ɓace ta tafi wajan Abie ta kai ƙara duk da yace mata Abie ɗin ne ma ya biya kuɗin Tattoo ɗin. Sai kawai Abie ɗin ya ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “An masa ne saboda yana so. Dan JIKANA ZAKI NE!!!”. Sai kawai tama rasa abin faɗa a lokacin, dan yanda Abbie ɗin yay magana babu alamar damuwa tattare da shi sai ma ƙarfi da karsashi... Kuka ta fashe da shi tana mai ƙanƙame Maash ɗin a jikinta ta ce, “Yeess Abie JIKANKA ZAKI NE”..... 😂YAYANMU ZAKI NE muma mun yarda Abbie😌, dangin Kandala ma sun shaida😝😂. 💓✨💓✨💓 10:12pm na dare da abubuwa da yawa ke kan faruwa wanda ya damalmale na kowa ya faru. A ɓangaren su Fahad da Hafizzullah sun farfaɗo tun bayan Magribar da tai dai-dai da isowar Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain Maash Mansion bisa jagorancin Baban Hayatu da kaɗai yasan da zuwansa. Dan haka suka kasance a ƙarƙashin kulawarsa dan kai tsaye sashen Fahad ɗin Baba ya kai Sheikh Muhammad ɗin batare da kowa na gidan ya sani ba sai Shu'aibu da TJ. Hakan ta farune kasancewar ma'aikatan gidan yau jikinsu duk a sanyaye yake. Hajiya ƙarama bata gidan. Hajiya Mama na asibiti wajen Samraah. Hajiya Mammah tana sama tare da aminiyarta Rubayya data kawo mata ziyara suna tattauna cakwakiyar gidan. Wanka Baba ya sakasu sukayi aka basu abinci sukaci Sheikh ya basu ruwan addu'a sannan yay musu tambayoyi akan ina suka je. Amsa ɗaya suka bashi shine su dai sun kwanta barci daga haka suka farka suka gansu a wani waje daban an ɗauresu. Sai wani dake kawo musu abinci sau biyu a rana. A kuma daren shekaran jiya aka zo aka canja musu wajen zama. Sosai baba da Sheikh suka jinjina zancen, dan haka suka buɗe musu komai dake faruwa harda videos ɗin da aka saki akan Maash da Samraah, dana Maash a asibiti. Wani irin rawa jikin Fahad ya fara, kafin cikin kuka ya fara roƙon su kaisa Dubai ya ga Yayansa. Yanda yake ambaton yayan nasa duk a rikice yasa suka fahimci al'amari fa da alama ya dai-daita. Kallon juna Baba da Sheikh sukayi, kafin su zaunar da Fahad suka lallasheshi shi da Hafizzullah dake kuka sannan a nutse suka warware musu ainahin gaskiyar abin duk shiri ne. Sai dai ba'asan inda Maash yake ba yanzu taka maimai. Suka kuma warwarema Fahad alaƙar Maash da Samraah, yayinda Hafizzullah ya ƙara masa bayani dalla-dalla. Ai kawai gani suka Fahad ya miƙe a fusace, suna kiransa ko saurarensu baiyi ba ya nufi ainahin baban sashen. Sai kawai ihunsa da hargaginsa suke jiyowa yana ƙwala kiran sunan jama'ar gidan ɗaya bayan ɗaya. Ƙoƙarin miƙewa Baba yayi Sheikh ya hanashi yana mai girgiza masa kansa yana murmushi. A dai-dai lokacin Hajiya ƙarama da yau ma Commondo yayma fata-fata ta shigo ranta a ɓace. Cak ta tsaya kamar wadda aka dokama guduma a kai. Hakama Hajiya Mammah ta fito daga ita sai ɗaurin ƙirji Hajiya Rubayya biye da ita ta cikuykuye jiki da zanin gado. Dan irin mafaraucin kiran da Fahad kema kowa na gidan ko a bayi kake zaka iya fitowa a guje tsirara batare daka fargaba musamman idan kanada wani tabon laifi tattare da kai. Hatta su Azizat sun fito. Maman Malika ce kawai ta fito a nutsenta tana ƙoƙarin kiran mijinta da Hajiya Mama akan suzo gida fa ga abinda ke faruwa. Hakama Hajiya Mammah jiki na rawa ta koma ɗakinta ta ɗauki waya tai kiran Baba prof.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ .....A dai-dai lokacin Baba prof ke waya da Teacher ɗinsa dake ƙasar Togo sai ga kiran Hajiya Mammah ya shigo a ɗayar wayarsa. Yanzu baya wasa da kiran kowa, dan haka bama ta gama ringing biyu ba ya ɗaga yana kaiwa kunne da ajiye kiran teacher ɗin nasa. Cike da tashi. Hankali Hajiya Mammah tace, “Baba dan ALLAH kazo gida yanzu babu lafiya. Shima Fahad ya ɓalle gashi nan da zandareren takobin nan nashi ya ce wlhy idan bamu fito masa da Awwab ba da Mahaifiyarsu sai ya ma kowa yankan rago yau a gidan nan”. Bata ta jira cewarsa ba ta yanke kiran ƙittt. Kasare yay yana kallon wayar. Dan yama rasa yanda zai fassara zancen nata ko hasaso wani abu sai jikinsa ne ke rawa. Sai kuma ya tura wayar a aljihu da sassarfa ya fito yana haɗa hanya da ƙwalama driver ɗinsa kira yama manta ya kaishi fagen rabin mutuwa ɗazun. Sai da ɗaya a cikin ma'aikatan gidan ya iso ya sanar masa ai driver tunda suka shiga ciki tare bai fito ba. Kansa ya dafe tare da masa nuni da mota ya ce, “Kaini Maash Mansion”.... Cikin in ina ya ce, “O...ga ai ban iya mo..ta ba”. Wani firgitaccen tsawa Baba prof ɗin ya masa cikin ƙara ji yace, “Nace ka kainiiiiii!!!”. Rawa sosai jikin dattijon ya fara dan tsawar ta ratsashi. Dai-dai nan ɗaya daga cikin guards ɗin sa ya iso ya amshi key ɗin motar..... Suna fita a gidan Isma'il ya saki murmushi, tare da ciro wayarsa ya ɗanna ma Maash kira. Ya ce, “Ranka ya daɗe saƙo ya samesa. Yanzu haka ɗaya daga cikin guards ɗinsa ya tafi kaisa Maash Mansion kuma zaku iya tafi”. Sai da yay ɗan jimmm alamar saurare sannan ya saki murmushi da faɗin, “Thanks you Sir ina kan aikina ne”. Daga haka ya yanke kiran...... 🌿🤍🌿🤍🌿 A hankali Maash dake rungume da Babyn Falaq ya sauke wayar tare da sake rungume jinjirin yana mai kaima goshinsa sumbata. Sai kuma ya juya ya kalla Ummie da tai sabon shirin cikin wani ubansu lass da aka kawo mata mai shegen tsada da ƙyau. Ga gwala-gwalai Falaq ta mata ɗan simple kwalliya da ya sake bayyana ainahinta na UMMU-HIDAYA IBRAHIM ɗin ta. Sai wani uban ƙamshi da take bulbulawa. Gaba ɗaya wannan shirin an ƙirƙiresa ne daga ɗazun bayan sun gama kukan samun lafiyar Ummie sun koma murnar samun sabon Baby da atake Hayatu yace yaba Ummie wuƙa da namar zaɓa masa suna Maash kuma ya masa huɗuba. Babu ko wani kwana-kwana tace MUHAMMAD AWWAB. hakan kuwa akai masa huɗuba da shi kuma Maash ɗin ne yayi duk da baya jin daɗin jikinsa amma ya kasa gaya musu. Bayan ya kammala yace su tashi su wuce Hayatu ya ce, “No Yaya ba'a haka ba. Sai Ummie ta kimtsa ku bani awa uku kawai.” baima saurari amsar Maash ɗin ba ya fice. Kamar ko yanda ya buƙata awanni ukun ma basu gama cika ba sai gashi da duk kayayyakin da Ummie ɗin ta saka. Kawo kayan ya saka Maash haɗa sabon plan shima. Dan haka yay kiran Sheikh da ya sauka Lagos babu jimawa yay masa bayinin akan Fahad. Dan yana fatan yanda yake jin sakawai game da ɗan uwan nasa a yanzu babu wannan ƙiyayyar shima ta kasance hakan. Kuma ko shi abin bai sakesa ba ya san ko akan Ummie da Samraah zai iya yin duk abinda suke so. Sai gashi kuwa komai ya tafi musu dai-dai a ƙanƙanin lokaci Fahad ya haye dokin da suka azashi.... Ummie taso ganin Samraah kafin shigarsu Maash Mansion amma Maash ɗin ya lallaɓata akan tayi haƙuri, akwai dalilin da yasa baya son su haɗu a yanzu dan zata iya shiga shock ɗin da matsala zata iya afkuwa. Dole ita tana buƙatar a bita mataki-mataki yanda komai zai zo mata da sauƙi. Amma ya mata alƙawarin yanda zata kwana a maash Mansion itama Samraah a ciki zata kwana in sha ALLAHU yau.. wannan ne ya bata ƙarfin gwiwar haƙuri suka tafi... Rikicin daya ɓarke acan babban falon gidan da kowa yay cirko-cirko yana kallon Fahad dake garzaza tsiya da rantsuwar idan har basu fiddo masa Yayansa da Ummiensa da Paah da Samraah da Hayatu da su Mama Balki da Falaq kamar yanda suka fiddosu shi da Hafizzullah ba. Ya rantse da ALLAH yau sai kowa ya kwana da zanen yarbawa a fuskarsa kafin da safe yasa a kwashesu zuwa police station gaba ɗayansu yasa basu ko ji motsin shigowar motar su Maash ɗin gidan ba. Tun a main perlor suke jiyo hargagin Fahad. Wani irin makirin murmushi Maash ya saki yana mai lumshe idonsa baby har yanzu na'a hannunsa ya kwantar da shi a kafaɗarsa ya riƙe Ummie da hannunsa na dama. Mama Balki ce ta fara shiga da sallama mai ɗan ƙarfi. Hakan yayi dai-dai da juyowar Fahad yana nuna Baba prof dake tsaye kawai zufa ta gama jiƙesa dan kalaman Fahad wani masifar ratsashi suke, ballema yanzu da yake nunasa da takobin yana faɗin, “Wlhy da kai zan fara Baba. Dan ma su san da gaske nake yi babu ruwana da kai ka haifi Paah zaneka zanyi da takobin nan tsaf da zanen yarbaw.....” yay ɗiff ya gagara ƙarasawa yana kallon Mama Balkin kamar yanda take kallonsa tana murmushi. Baki ya motsa zaiyi magana sai kuma ga Hayatu, kafin yace tak Falak ta shigo da sallama itama. Ya yunƙura zai nufesu kamar yanda Hajiya Mama da Maman Malika suka yunƙura suma sai ga mai gayya da aiki Muhammad Awwab El-Mu'azz Adams riƙe da hannun Ummie ga abu dake a kafaɗarsa dake tabbatar da Baby kuma. Yanda kuka san an saka remote an tsaida Film ɗin dake tsaka da aiki haka kowa ya tsaya cak a yanda yake. Musamman Hajiya ƙarama da Baba prof. Yayinda karyayyen harshen nan na UMMIE daya rangaɗa sallama ya ratsa kunnen kowa tamkar yanda sautin kiran salla kan ratsa kunnen mai barci a bazata. Karo na farko Baba prof ya wani zabura ya manne da bango. Hajiya ƙarama ma tai baya tana mai sakin handbag ɗin hannunta zuciyarta na wani girgiza a cikin ƙirjinta. Hajiya Mammah dai baki ta saki da waro idanu waje gaba ɗaya. Haka Maman Malika sai da ta ɗan ja baya.. Fahad kuwa wani kalar suɓucewa takobin hannunsa tayi tare da ƙafafunsa ya tafi ƙasa ragwafff ya dire gwiyawunsa a ƙasa tamkar irin tsohon raƙumin nan daya galabaita a tsakkiyar sahara... Yaran kam da su ganin Hajiya Babba cikin ado kuma tana sallama ne ya hargitsasu duk sai suka cure waje guda suka ƙanƙame juna. Dan tuni an gama cusa musu zancen Hajiya Babba mahaigakciya ce tuburan da zata iya kisa ba kuma lallai ta warke ba... Da wani kalar sassarfa Ummie ta ƙarasa ga Fahad, tarosa tayi gaba ɗayansa dan neman rasa numfashi yake tsabar firgita. Wani irin ƙanƙamesa tayi a jikinta cikin matuƙar dakiya ta furta, “Oh my sweet Auta don't fall down” dan tayi alkawarin bazata sake barin maƙiya suka gazawarta ba. Ina Fahad fa ya shiɗe farin ciki ko firgici sun sakashi suma. Hayatu ne yay saurin ɗakko ruwa ya kawo. Ɗago Fahad ɗin yayi daga jikin Ummie da nauyinsa ya sata zama dole ya shafa masa ruwan. Nannauyan numfashi ya kawo mai azabar ƙarfi. Sai kuma ya kalla Hayatun da Maash dake tsaye a kansa. Muryarsa na rawa hawaye na kwarara ya ce, “Yaya mafarki nayi Ummie ta warke harta shigo ta ganni na ganta fa. Dan ALLAH miyyasa kuka tadani ku barni na koma ko magana muyi da ita”. Ya faɗa yana sake rumtse ido. “Ba mafarki bane kiddo. Da gaske ne buɗe idonka”. Tamkar matsoraci jikin Fahad ya fara rawa, hatta idanunsa mar-mar sukeyi yana buɗesu a hankali har ya buɗe gaba ɗaya kan ƙyaƙyƙyawar fuskar UMMIE da ke kallonsa tana hawaye itama. Hannunsa dake rawa ya shiga ɗagawa a hankali a hankali har ya isa saman fuskarsa ya ɗora. Da sauri ya janye tamkar wanda ya dafa wuta. Sai kuma ya miƙe zaune daram ta sake kai hannun yana kallonta yana hawaye. Caraf ta riƙe hannun tare da ɗorawa saman fuskar tata ta ƙanƙame. Sai ga hawayen da taketa riƙewa sun zubo sharrrr. Wani irin firgitattacen ihun da faɗin “Ohhhh Myyyyy Goooood!!!” Fahad ya fasa yana rungumeta gaba ɗayanta sai kuma ya fashe da kuka. A hankali Maash ya kauda kansa gafe na tsawon minti ɗaya kafin ya maidosa kansu. Hayatu ya miƙama Babyn sannan ya kai duƙe a slowly tamkar wanda baya so ya ɗago Fahad daga jikin Ummie. Miƙar da su yay tsaye su duka ya kama fuskar Fahad da hannu biyu ya fara share masa hawayen da yatsunsa manya yana wani ɗan jujjuya masa kansa”. Jikinsa kawai Fahad ya faɗa suka wani ƙanƙame juna da iyakar ƙarfin ƙwanji. Cikin kuka Fahad ya ce, “Yaya dan ALLAH da gaske UMMIE ta samu lafiya? Da gaske ba mafarki nake ba kamar yanda na saba?”. Ɗagoshi Maash ɗin yayi ya tsurama fuskarsa ido. Sai kuma ya sakar masa wani shegen murmushi daya kusan ɓaro zukatan wasu tare da motsa lips ɗinsa kaɗan, cikin silent voice ɗin nan tashi ya furta, “Ba barci kake ba Kiddo. Ummien ce a gabanka da lafiyarta. Dan haka ga saƙo ka faɗama MAƘIYA GASKIYA!!!” ya ɗan ɗaga sautinsa anan ta yanda kowa sai da ya jisa. “Su fara gudu, gudu na ceton rayukansu. Gudu na cigaba da bizne abinda suka shuka. Idan ba haka ba. Bayan ka musu zanen Yarabawa. Ni Muhammad Awwab El-Mu'azz nayi musu alƙawarin sai nayi gunduwa-gunduwa da kowanne gaɓa ta jikinsu ta yanda ba za'a iya iya banbance kowanne ɓangare na halittar su ba!!!”. Tamkar wani abun shirin Film kawai Fahad ya bushe da wani ɗan iskan dariya. Sai da yay mai isarsa kafin ya kalla yayan nasa. Cike da jin sabuwar izza ya ce, “My sweetheart yayana. Idan ka fatattaka namansu. Na maka alƙawarin siyo ƙatuwar tukunya da ƙatin iccen nan na dahuwan naman raƙumi, na bama Aunty Samraah ta mana DABGENSU mu baje a ƙaton tray UMMIE da MAMA su dinga bamu a baki muna taunawa da korawa da ruwan kamfanin MAASHHHHHHH”. Dariya abin ya bama Falaq. Tako kasa haɗiyewa ta fara ƙyalkyatawa. Sai kawai Hajiya Mama da itama abin ya birgeta ta shiga yin dariyar. Ai kawai sai su Mama da Hayatu da Maman Malika suka hau tayasu. Gogan kan sai ya wani lumshe idanu kawai yana mai tura hannayensa duk biyu a cikin aljihu. Da wannan damar Hajiya Mama da Maman Malika suka sami damar tahowa rungume Ummie. Tsabar makirci sai itama Hajiya ƙarama ta taho da gudu tana kuka zata rungume Ummien wai. Ajiyar zuciya Hajiya Mammah ma ta saki tana sakkowa. Ganin hakan yasa su Azizat fara sakkowa daga upstairs da suka maƙale a guje suma duk da bawani saninsu Ummie ɗin tayi ba duk suna ƙananu sosai, sai ɗan sanda ta samu lafiyar nan lokacin kuma ba'a tare suke ba. Suma duk nufar rungumetan sukayi. Amma mi duk kafin su isa gareta sai kawai Fahad yasha gaban kowa ya tare ta. Cak duk suka tsaya suna kallonsa kamar yanda shima yake kallonsu cikin wani irin ɗage kan rainin waye da girgiza hannu ya ce, “Inaa ai babu mai taɓa Ummie a gidan har sai anyi searching”. Yana gama faɗa yaja hannun Ummie yay hanyar sashen Maash da ita dake ta cikin falo yana wani kalar takun buɗewa daka gani kaga tsageran matashin zamani mai shirin a mutu ko ai rai🤣😂. Shi kansa Maash a wannan gaɓar sai da yay gajeren murmushin da kowa zai iya gani a kan fuskarsa yana mai ɗan girgiza kan kaɗan. Batare da yace ma kowa komai ba yay ma Falaq nuni da hanya ita da mama Balki. Gaba kuwa sukayi ya bisu a baya bayan ya juya ya kalla Baba prof cikin ido ya sakar masa murmushi, ya sake juyawa ga Hajiya ƙarama ita kuma ya mata wani shegen kallon da su duka sai da suka nema zubewa ƙasa. Cikin nashi takun bajintar shima yay gaba. Yayinda falo yake tsitt har yanzu tamkar an jera gunkunaye. Kowa da abinda yake rayama zuciyarsa. Rawar da ƙafafun Baba prof keyi yana shirin zubewa a ƙasa ya maidosa hayyacinsa daga sumar tsaye da yayi sakamakon kallo da murmushin da Maash ya masa. Yay taga-taga zai faɗi sai da Hayatu ya taroshi yana faɗin faɗin, “Subahanallahi Baba”. Cikin wani irin jan numfashi dake shirin ƙwace masa a hankali ya ce, “Kaini na zauna Hayatu zaunar da ni.” Babu musu Hayatu ya kamashi har kan kujerar dake kallon ta Hajiya ƙarama da itama ta kai zaune sakamakon jirin dake neman yarda ita ya zaunar. Sai kawai ya ƙara yin shakaff a kujerar dan kaɗan ya rage zawayin dake ƙoƙarin ɓarke mas ya samu ƙofar fara tsirarowa.........✍️ (😂😂😂😂Baba prof sannu kaji, abin tausayi wlhy🥱🥱🥱). _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_ .......Shigowar Uncle Abdullahi gidan da labari ya kaimawane ta dawo da kowa a hayyacinsa. Sai tarin da ya sarƙe Baba prof. Su duka su kansa sukayi, banda Hajiya ƙarama data samu hanyar hayewa sama. Kallon kallo sukaima juna ita da Hajiya Rubayya da har yanzu ke tsaye tana kallon komai. Sai kawai suka sakima juna murmushi. Cikin rawar murya Hajiya ƙarama dan ita kaɗai tasan halin da take ciki itama ta ce, “Ki tattara su Falilah subar gidan nan zuwa gobe bayan kowa yasan wacece Nafisa”. “An gama ranki ya daɗe”. Hajiya Rubayya ta faɗa cikin kashe ido tana sakin wani makirin murmushi. Gaba Hajiya ƙarama tayi zuwa sashensu. Sai da ta tabbatar ta dannama ƙofar key kafin ta wurgar da bag ɗinta bayan ta ciro wayarta. Kira ta dannama Commando, yana ɗagawa bata jira cewarsa ba cikin bushewar zuciya ta furta, “Wasa ya canja gaba ɗaya. Dole ne a mutu har liman. Uwar tafiya ta dawo hayyacinta, yanzu kam kan mai uwa da wabi kawai. Ka canjama Mu'azz wajen zama a daren nan. Shi kaɗai ne makamin mu a yanzu”. Tana gama faɗa ta yanke wayar. Jannifer ta kira, itama tana ɗagawa tace, “Bana son kuskure. Idan har naga kiranki ya zama Mu'azz da Commondo na a hannunki ne”. Wayar ta wani irin jefa saman gado. Sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya ta kuma fashe da kuka duk a lokaci ɗaya, tamkar itama dai kan nata ya fara taɓuwa. Hajiya Lawisa sorry woohoo😂😂🤣🥱. ✨✨✨✨ Commondo ya jima zaune da waya a hannu shi bai ajiye ba shi bai motsa ba. Dan shi kansa ba ƙaramin dukan zuciyarsa zancen Hajiya Ƙarama ɗin yay ba. Yanzun nan fa yake ganin text message ɗin wani yaronsa da tun ɗazun ya turo masa kasancewarsa da Hajiya ƙarama yasa bai lura ba. A saƙon yana sanar masa cewar ya gano inda Mahaifiyar Maash take. Har ya tura masa address yanzu haka shirin da yake kenan na zuwa su ƙwamusota ransa fari ƙal zai fara aiwatar da nasa plans shima. Kansa ya girgiza, dan haka kawai yaji kamar bai yarda da batun Hajiya ƙarama ɗin ba. Wayar ya fara daddanawa, yana zuwa kan sunan da yake nema ya danna mata kira. Siyama da tun ɗazun take a bayan window laɓe ita da wasu ma'aikatan gidan mabanbanta suna kallon komai dake faruwa dan tun isowar su Maash duk wanda idonsa ya gansu bai zauna ba ya biyo saboda son tabbatar da Hajiya Babba ɗin ce ko watace ke musu gizo wayarta ta hau tsuwwa. Da sauri tabar wajen ganin Commondo ne. Sai da ta shige cikin garden sosai sannan ta ɗaga tana mai maida muryarta can ƙasa ta ce “Boss”. “Siyama mike faruwa a gidan nan?”. “Hummm! Boss ai komai ma ya faru ko nace yana kan faruwa. Jira nake kawai akai ƙarshen Film ɗin na kiraka na baka bayani.....” tsaf ta zayyane masa komai fiye da yanda Hajiya Ƙarama ta sanar masa. Sannan ta ɗora da faɗin, “Mutuniyarka ta haye sama kamar zata zube. Dan numfashinta ma kamar siezing yake. Kakansu ɗin nan da yau na ɗaura alamar tambaya a kansa gashi nan za'a wuce da shi gida naji suna kiran likitansa”. Murmushi Commondo yayi, dan yasan Siyama bata san komai akan Baba prof ba. Ya turata jikin Paah ne domin ɗaukar fansa da sanya masa ido akan duk wani motsin Hajiya ƙarama. Tunaninsa ya katse tare da yin gyaran murya. Sannan ya ce, “Zamanki ya kusa ƙarewa a gidan nan. Sai dai ki saka min ido akan Lawisa sosai-sosai a tsakanin nan. Koda tari tayi na sani”. “An gama Boss”. Ta faɗa cike da girmamawa. Dan commondo ya cancanci fiye da komai a wajenta. Ya taimaketa a lokacin da kowa ya ƙyamacesu akaƙi taimakonsu ita da mahaifiyarta. Ita kaɗai ta tashi gaban uwarta batare da sanin kowa a danginta ba da mahaifinta. Tunda tai girma tayi wayo takan tambayi mamanta ina babanta saboda ganin sauran yaran da iyayensu ke haya a gidan da suke duk suna da Baba. Maman tata bata bata amsa. Sannu-sannu idan faɗa ya haɗata da yara sai a dinga zaginta da kiran mamarta karuwa ita kuma ƴar shege. Tun abin baya mata zafi harya fara. Ta dinga tsare mamarta tana kuka amma bata cewa da ita uffan. Daga ƙarshe ma suka bar gidan. A anguwar da suka koma ɗin ma komai bai canja ba, dan nan ɗin ma dai Hausawa ne. Tasha kama mata a lokuta da dama na gulmar mamanta akan ita munafukar karuwa ce. Kullum tana nuna ita ta ALLAH ce sai dare yayi ta fita aikata aikin ta. Tun abin baya mata tasiri har itama ta fara tsarguwa da fara sakama Maman nata ido. Sai dai hakan ya gagara dan barci na hanata rawar gaban hantsi. Tunda tai wayo bata iya wuce takwas na dare batai barci ba, takan kuma rasa dalilin hakan. Sai daga bayan nan data duƙufa bincike ta gano Maman nata ce ke bata abinda ke sakata barci ashe a cikin wata FURAR ƙaddara data sabar mata sha tun tana yarinya. Dan haka tafa canja taku itama. Furar ta fara sayowa tana ɓoyewa a duk sanda Mamanta ta bata wadda keda maganin sai ta ƙi sha ta canja da wadda ta sayo ta ɓoye waccan. Haka zatai likimo har Maman tata ta gama shirinta cikin ƙazamar shiga irin ta karuwan dare ta zabga hijjab har ƙasa sannan ta fita. Randa ta fara gani tayi kuka sosai, daga baya ma sai ta sha furar nan barci dole ya ɗauketa. Sai da sukai haka da mamanta fin sati sannan a cikon kwana na takwas tabi bayanta. Hankalinta yay mummunan tashi da abinda ta gani, dan tabbas Mamanta Karuwa ce. Karuwarma ƙazamar karuwa da ake nema ta gaba da baya. Kaɗan ya rage a ranar Siyama bata bar duniya ba. Dan har jiyya ta kwanta na wasu kwanaki. Bata da aiki sai kuka. Ko kallon Mamanta bata ƙaunar yi. Kwatsam a washe garin da aka sallameta asibiti sai ga Mamanta an kawo jage-jage da jini wai wata ta soketa da kwalba a club. Duk yanda taso barinta zuciyarta bata yarje mata hakan ba. Haka ta rungumeta tana kuka da roƙon a taimaka mata. Amma mi kaf anguwar babu wanda ya taimaketan sai Commondo. Shi ya saka yaransa suka ɗauki Mamanta aka kai asibiti, ya biya kuɗin komai harna gado. Tsahon sati uku da tai a asibitin nan har nauyin abincinsu shiya ɗauka. Sai dai me tunda suka dawo gida sai sabon ciwo ya tashi ma Maman tata. Bata ɗauki hakan komai ba sai tunanin wajen yankan ne bai gama warkewa ba. Sannu-sannu suna zuwa asibiti ganin likita kwatsam randa jiki ya rikice sai aka tabbatar mata Mamanta fa nada ƙanjamau. Ga tsutsa na fita mata ta baya Sakamakon abin da take aikatawa dan bata amfani da maganin da masu wannan ɓarna ke sha. Hankalinta ya tashi, taje domin sanarma Commondo ya sake taimaka musu ta samu baya nan yayi tafiya wai. Hankalinta ya tashi, dan asibitin basu riƙesu ba dole suka dawo gida. Wata sabuwar ƙyama da tsangwamace aka fara musu, bataga laifin mutane ba dan ko ita dauriya take saboda warin da mahaifiyarta ke fitarwa ta bayanta daya zazzago. Takai ko zama bata iyayi ma sannan toilet baya iya riƙuwa gareta. Babu kalar kukan da batai ba da magiya amma ina abinci da zasu ci ma ya gagaresu balle omon da zata tsaftacema Mamanta jiki. A haka suka kwashi watanni uku. Kwatsam wata rana zuciyarta ta ayyana mata zuwa wani company neman taimako anan bayansu. Dan haka ta shirya taje. Securitys basu barta ta shiga ba duk da magiya da kukan data dinga musu. Dole ta tsugunna a bakin gate ɗin ta cigaba da kukanta. Tafi minti talatin a haka sai ga wata dalleliyar mota mai azabar ƙyau. Harta gotata aka dawo baya. Magana driven ya mata, hakan yasata miƙewa zaram jikinta na rawa ta nufoshi. Cikin tsawa-tsawa ya tambayeta mi take yi a wajen?. Jikinta har rawa yake dan tsoro ta sanar masa taimako take nema. Sai da ya gama saurarenta yay mata tsawa tabar wajen. Har ta juya zata tafi tana kuka sai kuma ya dakatar da ita. Hotonta ya ɗauka yay danne-danne a waya. Babu jimawa taga ya ɗago ya kalleta da murmushi. “Yarinya kakarki ta yanke saƙa shiga mota oga yace zai taimakeki a kaiki”. Cike da farin ciki ta shiga motar, shi kuma yay reverse ya koma batare da ya shiga companyn ba. Wannan shine mafarin haɗuwarta da Paah. Dan an kaita garesa wani gida, Maimakon ya taimaka mata bayan ta gama zayyane masa damuwarta kamar yanda ya buƙata sai ya nuna mata sai idan ta biya masa buƙatarsa. Da farko taƙi har tai fushi ta tashi zata fita. Sai dai tuna halin da mahaifiyarta ke'a ciki ya sakata komawa garesa. Babu ko tausayi kuwa ya keta mata haddi, a kuma ranar ta fara sanin namiji. Bayan ya gama abinda yaso ya bata kuɗi har naira dubu ɗari biyu. Haka ta tafi tana kukan baƙin ciki da na farin cikin samun kuɗin da zata kai mahaifiyarta asibiti. Sai dai me tana zuwa ta samu mahaifiyarta ta mutu an jehota ma bakin bola mutane yayyaɓe da ita suna kallo da zagin gawarta. Wannan al'amari ya ɗimautata. Ɗimautawar data yanke jiki ta faɗi bata tashi farkawa ba sai a gadon asibiti. Bayan ta farfaɗo ta fahimci commondo ne ya kawota asibitin... Wannan shine sanadin komawarta hannunsa. Ta bashi labarin komai daya faru, ya nuna ɓacin ransa tare da tabbatar mata ita da kanta sai ta ɗauki fansa dan yasan wanda yay mata wannan aikin saboda sunan companyn data faɗa. Commondo ne ya kawota Maash Mansion a sanadin Jannifer da ya jima da sani ta sanadin Hajiya ƙarama. Da farko Paah ta firgita da ganinta, dan ta tabbatar masa saita tona masa asiri a wajen ɗansa da abinda yay mata. Aiko fa ya rikice yace ta faɗi duk abinda take so. Sai da ta gama ja masa rai sannan tace zata cigaba da zama a gidan, duk wata kuma zai yanka mata albashin naira miliyan ɗaya. Hankalinsa ya tashi ya nema ta sassauta masa dan miliyan ɗaya duk wata tayi yawa ai. Badan baida kuɗin bane ko hanyar samunsu. Sai dai gudun kar Awwab ya gano shi ne. Dan dole de kuɗin zai dinga fiddasu ne daga asusun company. Da ƙyar ta yarda da 200k duk wata. Dole kuma hakan yake biyanta. A hankali kuma ya fara jan ra'ayinta suka cigaba da mu'amala. Koda ta sanarma Commondo sai yace ta cigaba da biye masa ta hakane ai zata cimma burinta itama.. ta cigaba da biye masa, tare da cigaba da ɗibama Commondo bayanan duk da yake so a gidan musamman akan Hajiya Ƙarama da zuwa yanzu ita kanta ta gama gane alaƙarsu, ta kuma san Arwa ƴarsa ce. Sai dai bata taɓa tunanin bama wani bayanan nan ba dan da iya gaskiyar zuciyarta take ƙaunar Commondo matsayin Yaya daya taimaketa a lokacin da kowa ya gujeta.........✍️ _(Hummm ALLAH ya rabamu da mummunar ƙaddara. Da yawan yaranmu idan mummunar ƙaddara ta gitta ma rayuwarsu nakasassun zukatanmu suka gagara taimakonsu a matsayinmu na al'ummarsu, sheɗancin mutane irin su Paah yay tasiri a kansu ko muka dinga musu hisabi da laifin iyayensu ko wasu ahalinsu sai irin su Commondo da akema kallon gurɓatattu su rungumesu, su tallafesu, komi tsarkin zukatansu sai su koma irinsu suma. Kamar dai Siyama. A yanzu zuciyarta ta gama bushewa. Ko kisa Commondo yace tayi wlhy zata aikata saboda shi kaɗai takema kallon girmamawa. Dan ALLAH mutane mu gyara, mu kiyayi hukunta wasu da laifin wasunsu. Hakan na maidamu bayane da sake raunana al'ummar mu da fiddo gazawarmu a fili. ALLAH ka yafe mana kurakuranmu baki ɗaya. Ka shiryemu ka shirya mana zuri'a. ALLAH ka rabamu da mummunar ƙaddara. Ka kiyaye mana mutuncin mazajenmu karsu jawo ma ƴaƴanmu da mu abin kunya ta hanyar aikata mummunan aiki😭🙏. Yanzu idan Awwab yasan gaskiyar irin waɗan nan abubuwan da Paah ya aikata dan akwai ire-iren hakan da yawa da wace kalma zai iya kare kansa. Ummie Ummie Hummm ya rabba🙏😭)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_ ......Kuka sosai Fahad yaci a jikin Ummie itama tana taya shi da sake jin tausayinsa, dan kiyayewar UBANGIJI ce kawai tasa yaronta bai lalace ba. Sai Mama ke lallashinsu. Dan Maash ya fita zuwa asibiti ɗakko Samraah kamar yanda yay ma Ummie alƙawari. Ina zaune a saman abin salla dana idar da shafa'i da wutri hannayena biyu tallafe da fuskata na afka duniyar tunani. (Ko ina Yaya Awwab ya shiga ne? Ina Fahad da Hafizzullah? Da har yanzu ko mai kama da su ban gani a asibitin ba. Shin Ummie fa? Aunty Falaq kota haihu?) Waɗan nan tambayoyin sune fal zuciyata. Sai kuma zancen ɓatan Paah ɗin nan yana cimun rai da saka tunanina rarrabuwa akan Matarsa da Kakansu. Saukar soft hand mai sanyi akan nawa ya sani ɗago idanuna. Sosai naji shock ɗin ganin wanda banyi zato ba. Dan sam ba ƙamshinsa bane dana sani kamar dai ranar nan. Sai kawai raina ya bani yau ma na sake yin mafarkinsa kenan. Numfashi na ɗan sauke da cigaba da kallonsa dan na gama yarda mafarkin nakeyi ɗin. Cike da wani irin salo ya ɗan ɗage girarsa duka biyu da mun alamar kallon fa?. Samun kaina nayi kawai da ɗan ɓata fuska. Cikin ɗan ƙunƙunin da nai zaton duk a mafarkine kawai na ce, “Ni ka bar min gizo”. Idanu ya ɗan lumshe a hankali. Tare da rungumeni a jikinsa. Gaba ɗaya naji jikina ya wani mutu. Musamman da ya ɗaura mitsitsin bakinsa akan kunnina can ƙasan maƙoshi ya furta, “Kona mutu sai na dinga zuwa miki a fatalwa ma”. Da sauri nayi ƙoƙarin janye jikina zuciyata na harbawa da sauri-sauri. Amma sai ya hana hakan yama sake ƙanƙameni da ƙyau yana sakar min numfashin sa a cikin kunne. Dole na sake ƙanƙamesa muryata na rawa na ce, “Please Ya Awwab mafarki nake ko gaske kai ne?”. Baiyi magana ba, sai mintsinin da ya sakar min a gefen cinyata babu shiri na ɗan gantsare tare da faɗin, “Ouch!!”. Ina ɗan kai masa duka a bayansa. Ɗagoni yay yana kallona cikin ido, kafin ya motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Kin yarda ido biyu ne?”. Murmushi na sakar masa nima tare da faɗawa jikinsa na ƙanƙamesa. Cikin rikicewa nake jera masa tambayoyi. “Yaushe ka dawo? Ina ka shige ne? Ina Ummie na? Aunty Falaq ta haihu ne? Anga Paah? Ina Fahad da Hafizzullah ban gansu ba.......” “Shiiii!!!. Wanne zan amsa a'a ciki to? Ammien unborn”. Ya faɗa cikin kunnena da raɗa. Ajiyar zuciya na sauke tare da ɗagowa ina kallonsa. Idanuna cike da ƙwalla na ce, “Please My Lion duka ka amsa min, waye kuma Ammien Unborn ɗin?”. Nunani yay da yatsa. Sai naji gabana ya ɗan faɗi, muryata har rawa take na ce, “Ban gane ba ALLAH Yaya”. Ido sosai ya zuba min kawai yana kallona. A hankali na fara ganin ƙyalli a cikin idanunsa alamar hawaye na taruwa. Sai kuma ya ɗan duƙo ya sumbaci idanuna dake kallonsa da hancina da baki na. Kafin ya riko hannuna shima ya sumbata. Murya can ƙasan maƙoshi lips ɗinsa na motsawa a hankali ya furta, “Samrh! ALLAH ya mana ƙyauta da abinda kuɗi ko ƙarfin mulki basa badawa. Naso yin kuskuren wasa da rayuwar ƙyautar da UBANGIJI yay mana. Am sorr...” Da sauri na kai hannu na rufe masa bakin ina girgiza masa kai. Hawaye na silalo min na ce, “Baka min laifin komai ba Yaya. Dan ALLAH karka bani wani haƙuri. Komai daka gani a rayuwar bawa ƙaddararsa ce tazo da hakan. Ina tayaka murnar samun ƙaruwa”. Na ƙare maganar da shigewa jikinsa sosai na ɓoye fuskata dan kunyarsa naji tana sake shigata mai tsananin. Ga wani irin farin ciki na matuƙar ratsani wai ni Samraah ke ɗauke da ciki irin na haihuwa. Nima zan zama Mama”. Sake ƙanƙameni yay sosai a jikinsa shima kamar zai maidamu abu ɗaya cikin kunnena ya furta, “Nima ina tayaki murnar samun ƙaruwa Aljannata”. Dariyar na sake ƙyaƙylƙyalewa da shi ina sake ɓoye kaina a cikin jikinsa. Sosai naji motsin fitar sautin nashi murmushin shima a cikin ƙirjinsa. Mun jima a haka kafin ya ɗagoni ya sumbaci lips ɗina. Tare da nuna min nashi alamar nima nayi masa. Kafaɗa na maƙe masa alamar naƙi ɗin. Fuska ya ɗan yamutse yana wani ɓata ta. Hakan ya sani kai yatsana manunuya na ɗalli small pinkish lips ɗinsa ina murguɗa baki da faɗin, “Ɗan kurma kawai”. Ƙaramin murmushi ya ɗan saki da alamunsa kawai na gani ya ɗauke kansa. Batare da yayi maganar ba dai ya miƙe dani a haka ya nufi ƙofar fita. Mamakine ya kamani, da sauri na ce, “Yaya bafa a sallaman ba. Ina zaka je da ni”. “Saidawa”. Ya faɗa a taƙaice yana ficewar dani. Dole sai nice na lumshe idanuna tare da ɓoye fuska a ƙirjinsa saboda kunyar mutane. Dan muna fitowa a ƙofar ɗakin mukaci karo da ƴar sandar nan. Mugun sandamewa tai tana kallonmu, sai da muna gab da gitttata ta ɗan dawo hayyacinta tana gaishesa. Amma bai ko kalleta ba balle naji ya amsa yay gaba. Sai jina nai ya saka a mota shima ya shiga. Kwantar dani yay kaina a saman cinyarsa. Bamma san wanda ke janmu a motar ba sai da Hayatu ya ce, “Auntyn mu yaya jikin?”. Da sauri na buɗe ido muryata har rawa take na ce, “Yaya Hayat da ma harda kai?”. Ƙaramar dariya yayi da faɗin, “Eh mana”. Ajiyar zuciya na sauke mai ɗan nauyi. Ban sake magana ba sai yunƙurin tashi zaune. Sai dai gogan ya maidani ya kwantar yana tsuke fuska. Dole na haƙura na koma na kwanta. Daga ƙarshe ma na lumshe idanuna tare da juyar da fuskata ina facing cikinsa. Daga haka nayi luff sai sauraren wayar da aka kirashi yake amsawa nakeyi. Sai dai furucinsa yay matuƙar ɗaukar hankalina. Dan cikin kaushin harshe yake faɗin, “Ko waye ya taɓa koda bangon gidan ne a cikinsu ku kamashi yallaɓai”. Ban san mi'akace masa daga can ba. Na dai ji ya yanke wayar kamar a ɗan fusace ya wurgata sit ɗin gaba na gefen Hayatu dake driving. Daga haka ya kwantar da kansa shima jikin kujerar ya lumshe idanu. Babu wanda ya sake magana har sai da naji alamar gida muka dawo. Bamma san na ware idanu ina kallon ikon ALLAH ba. Har ƙofar sashensa Hayatu ya faka motar. Duk yanda nake masa kallon mamaki shi yaƙi yarda mu haɗa ido, sai ma taimaka min da yay na fita a motar, kafin nai wani yunƙuri ya ɗaukeni cak babu ko kunyar Hayatu dake a wajen ya nufi sashensa da ni. Ni dai na riga na faɗa a hannun ƴan sari sai a hankali. Dan kunya dai kam wala a idanun Maash. Banyi zaton akwai kowa a sashen ba sai da muka shigo falon, jin ya tsaya cak yaƙi saukeni yaƙi magana kuma yasa na buɗe idanun nawa. Haɗa ido mukayi, dan haka na ɗan ɗaga gira da kaɗa idanun nawa alamar yaya dai. Nasa kan shima ya jinjina da cat eyes ɗinsa ya mun nuni da cikin falon. Ai babu shiri na kalla falon da sauri wlhy duk zatona wani abu yake nuna min. Amma mi sai caraf idanuna akan Fahad, Hafizzullah, Aunty Falaq. Ummie, Mama Balki. A wani irin ruɗewa na dirgo jikin nasa. Na koma bayansa da sauri na ɓuya ina jin tamkar ƙasa ta tsage na shige ciki. Dariya Falaq da Hafizzullah da Fahad suka kwashe da shi. Hakan ta sani sake maƙalewa a bayansa ina jin kamar na saki ihu. “Haba ƴar Ummie yaya da ɓuya kuma?”. Wani karyayyen harshe mai nuna rauni da sanyi ya ratsa cikin kunnena. Fuskar Ummie da tai min kamar gizo a kallon dana musu ɗazun ce ta shiga dawo min. Da sauri na ɗan leƙo kaina daga ta bayan nasa zuciyata na harbawa. Sai kawai Maash ya damƙoni ya kawo gabansa. Rawa jikina ya fara ganin tabbas fuskar Ummie ce zaune Hafizzullah da Fahad sun sakata tsakkiya ga baby a cinyarta. Da ƙyar na haɗiye busashen yawu na na furta, “Ummie!”. “Yes dear”. Ta faɗa fuskarta na sake ƙawatuwa da fara'a. Sake daburcewa nayi, na juya na kalla Maash dake bayana a tsaye har yanzu. Sosai idanuna suka firfito. Sai dai na gagara magana. Hannuna ya kama tare da fara tafiya da ni a hankali har gabanta. Bamma san na ƙwace hannun ba na zube a gaban nata gwiyawu biyu a ƙasa jikina na rawa. Hannunta ta miƙomin, ai da sauri na ɗaura nawa akai ina ƙarasawa jikinta da jan gwiwa. Sai kawai na samu kaina da fashewa da kuka na faɗa jikinta na rungume ita da jinjirin saman cinyarta. Itama ƙanƙamenin tayi da ƙyau a tare muka saki kuka. Munfi mintuna biyu a haka har sai da yay ƴar gyaran murya Mama Balki tazo ta ɗagomu Hafiz ya zare jinjiri da muka matse sannan muka tsagaita. Fuskata Ummie ta riƙe a cikin tafukan hannayenta cike da nuna ƙauna ta ce, “Yaya jikin naki?”. Kuka na sake fashe mata da shi da rungumeta sosai na ce, “Ummie na warke. Ummie dama kin gama ibadar ALLAH shine babu wanda ya sanar min. ALLAH kaine gagara misali. Ikonka da hukuncinka zartaccene akan komai. Ya rabbi muna godiya da dukkan ni'imokinka garemu. Ya ALLAH ka hanamu saɓa maka akan son zuciya”. Sai kuma na zame a hankali nayi sujidar shukur. Naja tsahon mintuna kafin na ɗago ina mai jera godiya ga UBANGIJI. Kafin na sake ɗagowa na rungumeta.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_ .......Zuwan likitan Ummie ya taƙaita zaman namu. Duk da dai an ɗan taba hira da zaka iya rantsuwa da ALLAH mun jima da sanin juna musamman ma Ummie da ke jan kowa jikinta. Barcin da allurar ke saka Ummie yasa dole taje ta kwanta. Mu kuma muka dasa sabuwar hira duk da dai akan abinda ya faru ne ga kowannenmu a kwanakin nan uku. Mama Balki ce da taga dare na ƙara zurfi dan Maash tunda ya raka Ummie ɗaki ya haye sama abinsa bai sakko ba tace nima na tashi na wuce tunda ba lafiya gareni ba. Badan naso ba dole nabi umarninta dan dama ƙarfin haline kawai sam bana jin daɗi. Shima kuma Ya Aawab koba komai nayi kewarsa. Sai da na leƙa na duba Ummie dake barcinta hankali kwance sannan na haura saman. Banyi mamakin ganin ko'ina babu datti ba. Har na nufi ɗakina sai kuma na fasa na maida akalata ga nashi ɗakin. Nayi mamakin samunsa tsaye a bakin window tsaye yana kallon waje. Ko kayan jikinsa bai cire ba. Sai da na masa kallon tsaff na gane waya yake yi dan akwai bluetooth a kunnensa. Kamar zanyi magana sai na fasa. Jikina a sanyaye dan wani masifar son kwanciya nake a waje mai sanyi na kai zaune kan carpet. Cikin dabara na kwanta tare da jan jikina na koma saman tiles na kwanta. Aiko sai na shiga sauke ajiyar zuciya a jajjare dan jin daɗin samun abinda nake so. Na lumshe ido kenan naji kawai an ɗagani a wajen. Buɗe idanun na nayi da sauri ina ɓata fuska sai ya harareni. Baice dani komai ba ya wuce dani bathroom. A bazata kawai na jini a cikin ruwan ɗumi. Kafin nai wani yunƙuri shima ya shigo cikin bathtub ɗin. Jikinsa kawai na shige na rungumeshi. Shima hannu biyu ya amshe ni sai kuma ya fara laluben lips ɗina ya haɗe da nashi. Tuni ya shagaltar da ni har ya cire kayan jikina ma ban farga ba. Sai da ya sakar min lips ɗin kuma naji kunya. Shiko ko'a jikinsa sai ma wanka da ya shiga mun..... Da zamu fito kam ban yarda ya ɗakkoni ba. Dan nama rigashi fitowa shi ya tsaya alwala. Gaba ɗaya na fice a ɗakin zuwa nawa. Dan nasan babu wanda zan samu a saman namu. Tsaf nai shirin barci na ina mai tsayawa kallon kaina a mirror. Gani nai kamar na canja ma ni a kwanki ukun nan kar kuce na cika ƙarya. Maimakon ni da nasha jiyya a asibiti aga na fige na fita a hayyacina sai na ganni ma na murje fata ta ta wani yi kalar ɗan golden brown kaɗan mai haske bamai duhu ba. Haka dai na shirya na haye gadon na kwanta dan bana jin zan sake komawa ɗakinsa. Sai dai a mamakina ina kwanciya yana shigowa. Daga saman gadon na ɗago ina kallonsa har ya ƙaraso inda nake. Laptop bag ɗinsa ya ajiye tare da wani ɗan bowl mai ƙyau idanunsa shima a kaina. A kusa da ni ya zauna tare da kamo hannuna cikin nashi cikin low murya ya furta, “Baƙya jin yunwa kika zo nan kika kwanta?”. Kaina na jinjina masa. Sai kuma na yamutse fuska tare da faɗin, “Tea kawai zan sha sai anjima kuma.” “Why?”. “Yanzu bana jin yunwa barci ma nake ji.” Kansa ya jinjina min tare da ɗan shafar kumatuna ya sakko da hannunsa saman cikina nan ma ya shafa. Sai kuma ya yunƙura zai tashi. Hannun nasa na riƙe, hakan ya sashi komawa ya zauna yana kallona. Duk da tsigar jikina ta tashi dan bana jure kallonsa cikin ido haka na daure. Cike da ƙarfin hali naja kumatunsa. “Please My Lion Smalling kodan murnar samun lafiyar Ummie. Ya kamata a yau fuskar nan ya zama tamkar buɗaɗɗen sabon fire mai ƙamshi”. Idanunsa ya ɗan lumshe sai kuma a bazata ya ɗan saki murmushin. Cike da farin ciki na rungumeshi ina faɗin, “Thanks you my Handsome.” yanda nayi maganar ina hura masa iska a kunne sai kawai naji ya birkitoni. Banyi zaton halin da ake ciki zaisa ya nuna wata buƙata ba. Amma mi sai labarin ya canja salo. Duk yanda naso zame kaina bai fa barni ba sai da abinda nake gudun ya kasance. Sai dai fa misalta muku yanda yau ɗin ta kasance hummmm abine da bazai yiwu ba. Dan wannan sirrina ne, amma dai ta shiga cikin jerin wasu kwanaki masu matuƙar muhimmanci da bazan taɓa mantawa ba a rayuwa ta. A shi kansa nasan hakanne, sai dai ba lallai ka gane ba kasancewar halittar sa ce kamar hakan yakan iya shanye komai a zuciyarsa shi kaɗai. Da yawan miskilai akance idan abin farin ciki ya samesu kakan iya gani koda a fuskarsu ce shi dai bawan ALLAHn nan sam ba haka bane, zai iya haɗiye miki farin ciki da damuwa ka kasa gane masa. Duk da dai kam na jigata sosai, dan da ƙyar na iya yarda ya taimaka min muka gyara jikinmu saboda barcin da ya gama cinye idanuna ga zazzaɓi. Bamma san yaya akai ya sakan wani kayan barcin ba sai can fitsari ya tadani na gansa ya baje takardu a saman carpet shima yana daga kwance ruf da ciki yana faman daƙilar laptop, gefensa akwai sallaya da Alkur'ani alamar salla ya idar ya kuma dawo wannan aikin. Nayi mamaki, dan banyi zaton zai iya sake wani abu ba musamman a yanda komai ya kasance. Shine ya taimaka min nayi fitsarin dan jiri nake gani, ya sake maidoni ya kwantar. Gabannin asubahi na farka da ciwon ciki. Kafin kiran salla sai amai nake yi ga zazzaɓi sosai a jikina. Hankalinsa yay matuƙar tashi. Babu shiri ya nemo doctor Larai ta asibitin su Hajiya Ƙarama bayan an idar da sallar asuba. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gata. Sama-sama nake jiyo muryar Ummie da Mama Balki da doctor Larai ɗin a kaina... Sai da Ummie ta riƙoni jikinta ta rungume sannan na ɗan buɗe idona, da ƙyar na iya furta “Ummie ruwa zan sha”. Fuskarta cike da damuwa ta ce, “Ruwa kike so?”. Kaina na ɗaga mata hawaye na zubo min. Dan sam bana jin daɗin jikina. Har Mama Balki ta ɗakko ruwan Dr Larai ta hana su bani, ta tabbatar musu amai zanyi idan nasha. A ɗan samu na ɗumi dai a bani kafin ta gama haɗa ruwan da zata saka min. Haka dole akayi, sai dai ni ruwa mai sanyi nake so. Dan haka na sanya musu kuka. Dai-dai nan Maash ya shigo da abu a hannu. Tunda yay sallama idonsa a kaina ƙyam, kai tsaye in da naken ya ƙaraso, Ummie nata ƙoƙarin lallashina nasha ruwan ɗumin. Da ƙyar dai na yarda nasha maƙwarwa biyu kawai. A hakan ma sai da nai yunƙurin aman ALLAH dai yasa banyi ba. Bayan doctor ta gama haɗa ruwan ta buƙaci a gyara min kwanciya. Nayi zaton zai bar Ummie da Mama Balki sumin amma babu kunya ya kamani da kansa daga jikin Ummie ya kwantar da ni saman dagon duk yanda doctor ɗin ta buƙata. Yana zaune a gefena shi da Ummie sun sakani tsakkiya hannunsa riƙe da nawa aka ɗaura min ruwan. Da farko yamutse-yamutsen fuska na dingayi da ruwan ya fara shigata, sai da ya fara gauraye jikin nawa sannan na fara sauke ajiyar zuciya. Ummie ce cikin sauke numfashi ta dubi Dr Larai, da karyayyen harshen nan nata ta ce, “Doctor kodai asibiti zamu koma ne. Yarinyata na buƙatar text gaskiya musam dalilin ciwon cikin nan da take ta complain.” Murmushi Doctor Larai tayi, cike da girmamawa ta ce, “Ranki ya daɗe in sha ALLAHU nai miki alƙawarin samar da duk wata kulawa gareta anan gida. Text kuma ina ganin basai mun sake mata ba. Dan result ɗin da wancan asibitin suka bada game da ciwon nata babu wani kuskure. Sai dai kamar yanda suka faɗa tana buƙatar bed rest sosai gaskiya. Dan cikin nan har yanzu bai zauna da ƙyau ba.” Idanu sosai Ummie ta waro da ga ita har Mama Balki. Duk da ita Mama Balki taso zargin hakan. Itama Ummien taso zargin hakan amma dai tafi son ji a bakin likitar dai. Murmushi Dr Larai tayi da faɗin, “Oh baku sani ba ashe. Da alama Alhaji ya shirya muku bazata ne dai kenan”. Ta ƙare maganar tana ɗan kallon sashen da Maash yake kamar yanda Ummie ma ke kallonsa. A mamakinsu sai suka ga ya ɗan kauda kai yana murmushi. Kasa haƙuri Mama Balki tayi sai da ta sanya dariya. Sannan ta ce, “Kai Masha ALLAH. Alhaji ƙarami kuma sai a ɓoye mana mijin? Ko dai kishiya ce shiyyasa ba'a son mu sani?”. Ɗagowa yay ya kalla Ummie, sai kuma ya maida idonsa akan Mama har lokacin da guntun murmushin a fuskarsa. A nutsen nan nasa ya ce, “Ni Mama ba ruwana. Ita ce tace nayi shiru da bakina tana jin kunyarku, tana son kuma mu rama yanda Ummie ta ɓoye mana samun lafiyarta muma”. Bamma san na buɗe idanuna da sauri ba duk da nauyin da suka min. Fuskata a marairaice kamar zanyi kuka. Da wani shegen salonsa ya kashe min ido ɗaya tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Koba haka kika ce ba?”. Tsabar kunyar da naji bamma san na saki kuka shagwaɓa da faɗin, “Ummie kin gansa ko. ALLAH ni sharri yake mun”. Ranƙwashi Ummie ta kai masa bisa kai, kafin hamnun nata ya sauka a kan nasa ya miƙe yana murmushi yay hanyar ƙofa. Dariya Dr Larai da Mama Balki suka sanya. Itama Ummien sai ta girgiza kai tana murmushi da kamo hannuna cikin nata ta ce, “Ƙyalesa kinji. Nasan shine bake ba. ALLAH ya baki lafiya, ya saukeki cikin aminci kinji”. Kasa amsawa nayi da Amin, dan sai naji gaba ɗaya kunya ta lulluɓeni fiye da farko. Wlhy Maash na neman sakani taɓarewa. Ban sake yarda na buɗe idanun nawa ba, ina dai saurarensu sunata cigaba da murnarsu Ummie harda sujidar shukur tayi, lallashin da Mama Balki naji tana mata yasa na fahimci hawaye take yi. Ban san yaya suka ƙare ba dan barci ya fara cin ƙarfi na. Ko shigowar Fahad da Hafizzullah sama-sama na jiyo barci yay gaba da ni........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ .......A ɓangaren Baba prof sai da likitansa yaje gida ya dubashi. Dan Uncle Abdullahi na tare da shi. Doctor ya tabbatar masa da jininsa ya hau sosai. Ya kamata kuma ya kwantar da hankalinsa koma mike faruwa dan bugun zuciyarsa har ya canja. Nan dai ya bashi shawarwari tare da masa allurar barci dan ya ce yana buƙatar hutu na awa kamar goma. Baba prof ɗin bai musa ba. Dan shima a karan kansa yana buƙatar hakan kam gaskiya... Uncle Abdullahi bai baro gidan ba sai da yay barci ko nace aka kira wayarsa. Yanda ya baro gidan a gaggauce yana bama ɗaya daga cikin ma'aikatan umarnin kwanciya a falo dan ya dinga ankare motsin Baba prof ɗin zaka tabbatar da kiran da akai masa mai muhimmanci ne. Wanda aka saka kwanciya a falon yana ganin Uncle Abdullahi ya fita ya wani faɗa saman kujera ya kwanta, koba komai banza ta faɗi yau. Dan har wani barbaje ƙafafu yake ransa fes. Bai wani bi takan Baba prof ya hau barcinsa harda minshari. Da wannan damar baƙon da basu san da shi ba a gidan tun ɗazun ya sami damar shigowa ya wuce har bedroom ɗin Baba prof ɗin. Tsaye yay a kansa yana kallonsa, sai kuma yay dariya da faɗin, “Mugu kenan uban mugaye”. Ƙaramin kwandon kaba dake a hannunsa ya buɗe yana kallon kunamin ciki manya-manya har guda uku. Baƙa, sai fara tass tamkar mara jini. Ga kuma mai kamar gold. Yanda suke ta faman ɗaga bindina sama zai baka tabbacin dama kawai suke jira. Murmushin mungunta kawai ya saki tare da ɗaukar su ɗaya bayan ɗaya da hannunsa dan shi yasha maganinsu babu abinda suke masa, Safar ƙafar prof ya buɗe ya saka ɗaya. Ya buɗe wandonsa😳 ya saka ɗaya. Sannan ya ɗakko hula a gefensa tsabar iya mungunta ya saka ɗaya a ciki ya kifama Baba prof hular a ka. Hancin sa ya kama ya ɗan ja cike da shaƙiyanci ya ce, “Barci lafiya tsoho, ni JAGA ina gaisuwa”. Ya juya yay ficewarsa yana dariya.... Jaga🤔😳??????. 💦💦💦💦💦 Kai kawo kawai take tana faman lissafa mintuna. Kaɗan-kaɗan kuma ta kalla wayarta dan babu abinda take fatan gani a yanzu sai kiran Jannifer. Rawar da ƙafafunta keyi da jin zuciyarta kamar zata wantsalo saboda ƙaguwa ya sata faɗawa saman gadonta. Ƙirjinta ta dafe tare da shaƙar numfashi ta fesar. Ita likita ce ta san irin wannan saka abu a rai yayta azalzalarka zai iya kawo heart attack ma. Dan bugun zuciyarta yay masifar ƙara ƙarfi. Kamar da wasa taji abu ya soketa. Jimm ta ɗan yi sai kuma ta share. Ƙara sukar ta akayi a wani wajen da ban. Azabar data ratsata ta waje biyu a lokaci guda yanzu kam ya tilastata tashi zaune tana kai hannu wajen da ɗan wawwaigawa amma babu komai a inda taken. Tashi tai ta fara ɗage-ɗagen filos da duvet, ɗayan hannun kuma tana taɓa inda zugin ke ƙaruwa mata har waje biyu. Kamar wasa sai da azaba ta sata sake kaiwa kwance, nan ma aka sake ɗalla mata. Ina bazata iya jurewa ba, da sauri ta mirgina ɗayan gefen tana sakin ihu. Aka ƙara bata wani harbin. Kafin dai ta fasa ihun da aka kawo mata ɗauki an mata ɗalli yafi bakwai. Zufa kuwa ta gama jiƙeta ta sharkaff harda sakin fitsari. Da sauri Bahijja dake laɓe ta fice tana dariya. Kusan cin karo sukai da Rubayya dake ƙoƙarin zuwa ta sanar mata plan ɗin su fa na neman rugujewa dan Hajiya Mammah na tare da ƴar uwarta Mashi'a a ɗakin Mashi'ar bata san mu suke tattaunawa ba, ko kallonta Bahijja batai ba tai wucewarta. Da kallo ta bita ita kuma zuciyarta na ayyana mata itama nemanta Hajiya ƙarama keyi, shiga tai ranta a ɓace, sai ta sameta cikin wannan hali. Kamata tai ta riƙe dan yanda jikin Hajiya ƙarama ke rawa ga zufa ta mata sharaf ya isa baka amsar babu lafiya. Neman shiɗe mata take, dan haka ta rungumota jikinta sai ko ta samu nata rabo itama aka bata har harbi biyu. Tuni ta saki Hajiya ƙarama a ƙasa ta ƙwalla ƙarar data jawo hankalin mutanen gidan. Har rige-rigen shigowa Hajiya Mammah da su Arwa akeyi. Mamaki ya kama kowa yanda Hajiya Rubayya ke birgima a ƙasa tana ihu da rike inda aka harbeta. Ga kuma Hajiya ƙarama kwance a ƙasa tai sharkaf da zufa tama kasa kukan ita dan abinda ke harbin nata fa na jikinta kuma basu daina ba. Arwa ce ta fara nufarta, hannu tasa ta kamo mahaifiyar tata zuwa jikinta, kafinma ta gama mannata an bata rabonta. Ƙara ta ƙwalla da sakinta timm a ƙasa tai baya tana ɓalla ihu da riƙe hannunta. Da sauri Hajiya Mama ta ce, “Ya Salam mike faruwa ne haka? Ke Arwa lafiya?”. Tai maganar tana kaiwa zata taɓa Hajiya ƙarama Hajiya Mammah ta riƙeta da jawota baya. “Auta! Baki da hankali ne. Kina ganin daga taɓa da ƴarta tayi itama tana ihu ga Rubayya kwance ke sai ki kai kanki?”. “Amma Adda ya kamata musan mike faruwa ai”. Hajiya Mama ta faɗa cike da damuwa. Masifa Hajiya Mammah ta fara mata dan ita wani irin kishi ne ya taso mata. Ganin Rubayya a ɗakin Hajiya ƙarama sai zuciyarta ta ayyana mata amanarta suke ci ALLAH ya saka mata. Duk yanda Hajiya Mama taso taimaka musu Hajiya Mammah ta hana. Ashe shi tsautsayi baya wuce ranar sa. Dan Azizat na maƙale a baya sai ji sukai ta ƙwalla ƙara. Juyowar nan da zasuyi kanta sakamakon tsallen data buga gefe kawai Hajiya Mammah ta maye gurbin ƙafarta akan baƙar narƙeƙiyar kunamar data ɗalli Azizat ɗin a ƙara. Itama ƙarar ta fasa tana mai yin tsalle gefe dan har cikin tsakkiyar kai taji harbin nan. Ai ko kaɗan ya rage Hajiya Mama data firgita itama ta taka ALLAH dai ya kiyaye Ilham ta riƙeta da sauri tana faɗin “Mama Scorpion”. Garrrr kunamar dake neman ceton ranta itama ta shige ƙasan gado Hajiya Mama na kallonta da Ilham. Sai yanzu suka fahimci abinda ke faruwar... Dole fa aka kira ma'aikatan gidan. Anci sa'ar akwai wanda suka sha maganinta. Dole sune sukai kama-kamar ɗaga su Hajiya ƙarama zuwa mota. Anan ne wasu kunamun har biyu suka faɗo ashe a jikin Hajiya ƙaramar suke. Asibiti aka wuce da su su duka biyar din. Su sunata ihu Hajiya ƙarama kuwa tuni ta suma ma ita dan azaba. Wannan al'amari ya matuƙar bama kowa mamaki. Duk da ana shan kashe kunamu a gidan harma macizai a wasu lokutan saboda garden amma ba'a cikin gida ko ɗaki irin haka ba. Abinma tambayar miya kawo kunama har cikin jiki haka? Ba kuma ɗaya ba har uku, Babu mai basu amsar tambayar nan dan basu sani ba. Duk wannan bidirin da akeyi fa babu wanda ya sani a ɓangaren su Maash. Sai Hafizzullah ne dake salla ya ɗan fito. Ana wucewa da su asibiti kuma ya koma ciki shima abin na bashi mamaki. Shine ya samu Fahad ya tashi. Tambayarsa yayi ina yaje? Ya bashi amsa da “Gidan ne fa babu lafiya. Kunama ta harbi har mutum biyar gasu can an wuce asibiti da su.” “Ikon ALLAH kunama kuma a gidan nan? Dawa-dawa?”. “Wlhy nima abin yaban mamaki. Hajiya Mammah da wata mata baƙuwa sai budurwar nan mai iyayin tsiya mai kama da sadakar yalla da kuma wadda ka saka ranar ta kawo mana abinci baƙar nan da Mamanta ita tama suma”. Dukansu ya gane su, idan ka cire baƙuwar da bai san wacece ba. Haka kawai sai baiji komai a ransa ba ya ce, “ALLAH ya ƙyauta” kawai ya tashi ya shige toilet. Alwala yayo shima dan yanzu ya dage ta tashi sallar dare saboda Hafizzullah da ya ga yanayi. Dan Hafiz akwai ibada gaskiya. Training ne kuma daya samu daga Yaya Musaddiq tun yana ƙaraminsa. Dan tun sanda ya fara wasa da salla ganin Mom nayi da yaranta Musaddiq ya dage a kansa har sai da yaga ya dawo hankalinsa. Daga nan kuma abin ya shigesa sosai bai sake sakaci ba sai ma Alhmdllh.... 💢✨💢✨💢 Masu iya magana kance rana dubu ta ɓarawo ɗaya rak take zama ta mai kaya. Tabbas hakanne ta faru a daren yau da mutane guda biyu da yaransu. Dan jami'an tsaro sun samu nasarar cafke Commondo da yaransa biyu. Sai Madam Jannifer da yaranta huɗu harda dattijuwar tsohuwar nan ta gidanta Mama. Su dukansu kuma an cafkesu ne a lokacin da suke shiga gidan da suka ɓoye Paah batare da shi Commondo ya san da zuwan su Jannifer ba. Amma su su Jannifer sun san da zuwansa dan sun mayi shirin ƙwamushesa ne shima bisa umarnin Hajiya ƙarama. Sai dai basu san an saka tarko a gidan ba tun yammaci sakamakon bayanin da Maash ya bama su Isma'il akan inda su Commondo ɗin suka kai Paah. Gaba ɗayansu hankalinsu ya matuƙar tashi. Duk da dai shi Commondo yana ganin kamar duk iya ma miza'ayi zuwa safiya sai Baba prof ya fitar da shi. Itama dai Jannifer ɗin tana da ɗan nata hope ɗin na ganin manyan ƙwarin da take huɗɗa da su zasu fitar da ita zuwa gobe. Yaransu ne dai hankalinsu ke matuƙar tashe musamman yaran Jannifer da irin haka bai taɓa faruwa da su ba. Wasu ma a cikinsu kuka sukeyi. Abinda kuma ya sake ɗaga musu hankali da akaje station ɗin da su gaba ɗayansu rarrabasu akayi babu wanda aka haɗa da ɗan uwansa... Kai tsaye asibiti aka wuce da Paah duk da babu wani rauni a jikinsa. Sai dai yunwa ta galabaitashi dan ko sun bashi abinci baya wani ci sosai sakamakon azababben yajin da suke cika masa. Gashi yana da urlser. Taimakon gaggawa aka shiga bashi, sai dai ba'a sanar da kowa a gidansu ba kasancewar dare ya riga yayi. Garama Isma'il ya turama Maash text message sai dai shi kuma hankalinsa bai kai ba dan lokacin kam yana wani tsagin daban kuma. Da safe suka tashi da tashin hankalin yanayin Samraah. Sai da doctor ta dawo duba jikin Samraah da azhar suke jin ai su Hajiya Mammah na asibitinsu an kaisu jiya da dare kunama ta harbesu. Musamman ma Hajiya ƙarama har yanzu tana cikin azaba. Tana tsaka da musu wannan bayani aka kirata wai tazo asibiti akwai matsala ga Baba prof an kai shima kunamu sun masa kaca-kaca da harbi har a saman kansa. Yanzu ma'aikatan gidansa suke kawosa... A firgice tama su Ummie bayani ta fice akan tana zuwa. Abin mamaki Maash ko tari baiyi ba sai ma hayewarsa yay sama kamar ma bai ji mi aka faɗa ba........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ .......Da kallo kawai su Ummie suka bisa har ya ɓacewa ganinsu. Uwa uwa ce koda kuwa sakarai ce. Dan a take kan Ummie ya kawo mata haske. A zuciyarta ta raya (Anya ba Muhammad bane?) Sarai tafa sanshi idan aka masa sai ya rama. Wannan halin nasa tun yana mitsitsinsa yana matuƙar damunta. Tasha masa addu'ar ALLAH ya yaye masa shi. Ganin ya lafa daga baya sai tayi tunani ai ya barsa gaba ɗaya. Ashe-ashe. Falaq ce ta fara ƙyaƙykyalewa da dariya da faɗin, “ALLAH yaja kwana Yayana”. Kallonta duk sukayi, ta ɗauke kanta kamar ba ita tai maganar ba. A take itama Mama kanta ya kawo haske. Lallai kam zata iya yiwuwa Awwab ɗin ne. Wato ya rama musu abinda ya faru da su. Kai jama'a wannan hatsabibin yaro sai a barshi. Itama dai sai da ta murmusa. Hafiz da Fahad basu fahimci komai ba. Dan haka sukabi Falaq suna mata nacin tambaya. Cikin raɗa ta faɗa musu komai da abinda ta fahimta. Idanu Hafiz ya waro, yana haɗa 1+1 a ransa. Eh lallai biri yayi kama da mutum. Idan ba haka ba tayaya kunamar sai selecting mutanen data harba harda ma wanda bai kwana a gidan ba. Wato Maash abin tsoro ne. Dariyar Fahad ta maido Hafizzullah hayyacinsa. Sai kawai shima ya fara dariyar suka tafa.. ita Falaq ma sai ta koma ƴar kallo, dan ta kula sun fita iya shege... Sai da sukai mai isarsa Hafizzullah ke faɗin, “Ya Fahad anya kuwa ba yarinyar nan bace tai aikin nan? Dan lokacin da ake fita da su gidan nan na ganta tana dariya acan baya laɓe”. Cikin zaro idanu waje Fahad ya ce, “Kuttt wace yarinya?”. “Kamar Bahijja naji suna kiranta cikin masu aikin nan”. Salati Fahad yasa kafin yaja hannun Hafizzullah suka fita. Kai tsaye sashen masu aiki suka nufa. Karo na farko kenan tun zuwan Hafizzullah ya shigo nan ɗin, iyakarsu sashen su Mama Balki. Shi kansa Fahad ɗin zai iya rantsuwar bai fi sau biyu ya taɓa shiga ba. Cikin sa'a ma suna buɗe ƙaramin gate ɗin sashen suka hangota tana shanya kaya da alama wanki tayi sai raira ƴan wakoƙinta take. Kiran da Fahad ɗin ya mata yasa ta ɗan juyo a firgice, sai kuma duk ta daburce dan ya tsuke fuska hakama Hafizzullah. “Biyomu”. Ya faɗa murya a dake yaja hannun Hafiz suka juya. Gaba ɗaya sai ta ƙara rikicewa. Haka tabi bayansu hawaye na taruwa mata a ido. Itafa tana shakkar Ya Awwab sosai saboda baya wasa da yara. Amma wannan Ya Fahad ɗin tafi tsoronsa barema yanda yake cewa zai ma mutane yankan rago. Ganin sun nufi sashen Fahad ɗin ta sake ruɗewa. Dogarewa tai ƙoƙarin yi a bakin ƙofa Fahad ya daka mata tsawa. Ai babu shiri ta shigo tana hawayen da take dannewa. Ƙasa ta durƙushe daga ɗan bakin ƙofa. Yanda duk take a ruɗe dariya ke bala'in cinsu. Amma duk suka danne Fahad ya ɗakko takobinsa ya ajiye. Murya a dake ya ce, “Kece kika sakama ƴan gidan nan kunamu jiya ko?”. A wani mugun firgice ta ɗago tana zabga salati kamar tsohuwa. Zata fara rantse-rantse ya zaro takobin a cikin kufanta. Hafiz ya kalla ya ce, “Broth rufe min ƙofar falon nan ka riƙe min ita idan bata faɗa ba saina cire mata harshe.” “Lahhhh ina ha illahu.... Ni Bahijja na shiga uku. Dan ALLAH Uncle Fahad kar muyi haka da kai.” “Idan baki son muyi hakan faɗa min yanda akai kunama taje jikinsu?”. Kuka Bahijja take sosai dan ta shiga tsaka mai wuya. Tunda take abubuwanta a gidan nan wani bai taɓa kamata ba sai yau. Bata son faɗa amma tana tsoron Fahad ɗin nan. Ganin dai Hafiz ya rufe ƙofar falo ta ƙara sakin kuka da faɗin, “Wlhy ni ce. Na sakama Hajiya ƙarama a kayan barcinta data ajiye saman gado ne tana wanka. Na saka biyu a aljihun wando biyu a aljuhunan rigar. Shine shine na laɓe, to bata fara cizonta ba sai bayan kusan mintuna goma, su kuma sauran taimakonta suka zo yi suka sami rabonsu....” Kafinma ta kai ƙarshe Fahad ya bushe da dariya. Ganin haka itama sai kawai ta fara dariyar saboda tuno yanda Hajiya ƙarama ta dinga yin ƙaramin disko. Cikin dariya Fahad ya nuna Bahijja yana faɗin, “Yarinyar nan ALLAH ke muguwa ce. Ina kika samo kunama da bata cijeki ba?”. Sai da ta ɗan sosa kanta sannan tace, “Ai nasha magani. Na kuma ramawa su Uumie ne ranar da suka sa ta cijesu”. “Oh woow! Aiko nima dole a bani maganin nan kodan irin wannan ranar. Fantastic”. Haka dai sukaita nishaɗin su ita dai Bahijja ma sai ta zama ƴar kallo.... ★★★ Zuwan likitan Ummie yasa bata nema Maash dan taji gaskiyar magana ba. Ga zancen cikin nan na Samraah ya ɗaukaka farin cikinta yau matuƙa. Kasancewar suna mata allura tasha magungunanta sai barci yau ma hakanne. Doctor kuma ya sake tayata murna da in sha ALLAHU bai wuce ya ƙara shan magunguna na watanni uku zuwa huɗu ba abubuwanta su dai-daita. Abinda yasa ma zai kai haka saboda an jima ana mata allurorin da suka so jawo mata babbar matsala. Sai dai Alhamdullah komai zai zama labari. Shima bazai basu bayanai bane saboda akwai abinda yake shiri kan likitocin da suka kula da ita ɗin ta bayan fage. Sai ya kammala bincikensa sannan zai mata cikakken bayani. Ummie ta gamsu, ba kuma ta matsa da sai taji ɗin ba. Barci ne ma ya rinjayeta har doctor ɗin suka ƙarasa abinda suke suka fice bata sani ba kuma.... ❤️🤍❤️🤍❤️ Ban tashi farkawa ba sai gabannin azhar. Yana kwance a kusa da ni da alama shima barcin ne ya kwashesa. Nauyayyun idanuna kawai na zuba masa tsahon lokaci, kafin na sauke ajiyar zuciya da kai ɗayan hannuna saman tattausan gashin kumatunsa na shafo. Janyewa nayi ƙoƙarin yi ya riƙe hannun tare da buɗe idanunsa a hankali ya saukesu kaina. Idanu muka zubama juna cikin wani bahagon yanayi kafin ya lumshe nasa tare da matso da fuskarsa daf dani har hancinanmu na gogar juna. “Kin ta shi?”. Ya faɗa yana ɗaura hannunsa akan wuyana. Idanuna na ɗan lumshe masa na buɗe alamar eh. “Mike ciwo yanzu?”. Kaina na ɗan girgiza masa alamar babu. Numfashi ya ɗan sauke da sumbatar lips ɗina kaɗan, sai kuma ya janye hannunsa dake saman wuyana ya maida saman cikina. Yanzun ma da raɗa ya ce, “My Baby fa?”. Hannunsa na ɗan mintsina cikin tura baki na ce, “Ni ban santa ba”. “Jealous ba?”. Yay maganar da ɗan goga hancinsa kan nawa. “Ba wani jealous nima ai Ummie na na sona. Ga kuma Mama”. “Kidai tsaya a Ummien taki banda ƙwacen Mamana. Dan kin san ita ɗin tawace ni kaɗai. Falaq ma sammata nake”. Murmushi nayi a karo na farko. Na ce, “Yaya!”. “Uhhmyim My Tiger”. “Har yanzu ba'a san inda Paah yake ba? Ina ka shige duk wannan dambarwar baka zo ba sai daga baya?”. Shiru ya ɗan yi kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya buɗe idanunsa yana kallona. Yayinda hannunsa ke saman fuskata yana shafa gashin girata da yatsarsa babba. Muryarsa can ƙasan maƙoshi ya furta, “Paah dama nasan a inda yake, na barsu ne kawai naga iya gudun ruwansu Samrh”. Idanu sosai na waro da faɗin, “Yaya da gaske?”. Kansa kawai ya jinjina min. Murmushi nayi tare da sumbatar mitsitsin bakinsa kaɗan, ina ƙoƙarin janyewa ya riƙe lips ɗin nawa da nashi. Sai da ya tabbatar ya samu yanda yake so sannan ya barni. Muryarsa a shaƙe cikin kunnena ya furta, “Kema kina buƙatar mijinki ba?”. Maimakon na bashi amsa sai kawai na shige jikinsa na rungumeshi dan kunya maganar tashi ta bani, shi ba ruwansa kai tsayensa yake magana ba kwana-kwana. Sosai ya riƙeni shima batare da ya sake cewa komai ba. Daga haka ɗakin yay shiru tsawon lokaci tamkar barcin muka koma amma duk idonmu biyu. Kiran salla ya sakashi sauke ajiyar zuciya, tare da ɗagani a hankali zai gyara min kwanciya na yunƙura nima. Sai kawai ya zaunar dani na jingina jikinsa. Yanda ya tsareni da kallo yasa na kasa kallonsa ni. Sai naji ya ɗan furzar da numfashi. Sauka yay tare da ɗagani cak a gadon. Fuskata a marairaice na ce, “Nifa ina iyawa”. Komai baice dani ba har sai da muka shiga ciki bayin ya direni a bathtub sannan ya kamo jaw ɗina. Ɗago idanuna nai nima ina kallonsa. Yanda yake wani bina da narkakken kallo yasa tsigar jikina tashi, har sai da na sauke ajiyar zuciya a hankali. Shima iska ya ɗan furzar kaɗan, tare da furta, “In dai ina cikin gidan nan kin daina komai sai kula da ni shima a be.....” da sauri na kai hannuna saman bakinsa na rufe. Janyewa yay yana murmushi. “Kin san mizan faɗa ne kika wani rufen baki”. Bakina na ɗan tura nima da faɗin, “Nidai ba ruwana. Ga abinda nake son ka faɗa min ka tafi wanda ba'a sakaka ba”. “ALLAH yarinyar nan kin lalace. Toni mi nace zan faɗa kike neman fassara min zance?”. Kaina na juyar ina murguɗa baki na ce, “Ni dai ba ruwana”. Murmushi ya sake saki mai ƙayatarwa da kai hannunsa saman cikina ya shafa. A mamakina sai jinai ya ce, “My blood kada kiyi rashin jin Ammien ki kinji”. Harararsa nayi nima na ɗora hannuna saman cikin na ce, “My blood kada kayi miskilancin Dadaan ka kaji”. Dariya muka saki a tare, ya dunguremin kai. Nima hancinsa naja da alama mun manta a bayi muke........✍️ (Nima dai na fara tunanin kun manta a bayin kuke🏃🏃🏃🤣). _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_ .......“Wai kai lado yau mike damunka ne? Motsi kaɗan sai ka wani kwashe da dariya. Kai ko damunka abinda ya faru da oga kamar baiyi ba ma. Alhalin idan binciken inda aka samo kunamu aka zo yi wlhy kai zasu kama tunda kaine ka kwana da shi”. Dariya wanda aka kira lado ya sake kecewa da ita, sai da yay mai isarsa sannan ya ce, “Bazaka gane ba Hamisu. Wlhy ko kaine zakai dariyar da tafi tawa ma. Ka koga wani gigitaccen ihu da Yallaɓai yayi, ai ni nasha kallo. Da gudu fa ya fito falo ya kwaɓe wandon sai ɗan panti. Hannunsa kan jikinsa ya damƙe yana rabga ihu. Badan Kuka ya taimaka ya rufe ƙofaba da har tsakar gidan nan zai fito a haka hhhhhh!!!!” ya ƙara kwashewa da dariya. Da ƙyar ya cigaba da faɗin, “Kama-kama mukayi da Kuku wajen kamashi amma ina sai rawar disko dansa yake. Ashe bawan ALLAH abune goma da ashirin ya ishe shi. Kunama a wando, kunama a cikin hula ga wata a ƙafa tana bashi wuta. Haka dai muka dannesa muka cire panti da ƙyar shegiyar ta manne kuwa tanata aikin da aka sakata. Shiyyasa jikinsa fa ya kumbura tunkan a bar gidan nan sai bargo aka lulluɓa masa. Bakaga har mukaje asibiti dubasa da alama babu wandon ba hhhhhh!!! ALLAH alhakinmu ne anƙi bamu albashinmu, ALLAH yay ma wanda yasa kunamar nan albarka hhhhhhhh!!!!”. Duk yanda Hamisu yaso ƙin biyewa lado hakan ya gagara. Shima sai da ya shiga kwasar dariyar..... Baba prof ashe haka abubuwa Suka kasance harda rawar disko dansa😝😝, Sai munzo dubiya dai to, ALLAH yasa sannan ka fara saka wando😂🏃🏃🏃. ⭐✨⭐✨⭐ Kusan lokaci ɗaya Ummie da Samraah zamuce sun farka. Wanka ta farayi dan in dai tai barcin nan sai ta jita Alhamdullah jikin kuma yay mata sakayau. Kasancewar Mama Balki na yawan shigowa dubata sai ta kawo mata abinci ganin ta tashi. Bata wani zauna ba dan tana acan sashensu ne tana shiryama Baba abincin da zai kaiwa Malam can masaukinsa. Koda Ummie ta fito salla ta farayi, ta yi karatun Alqur'ani sannan ta zauna cin abincin dan yanzu kam tana cin abinci saboda magungunan na sakata jin yunwa. Tana farawa Fahad da Hafizzullah suka shigo. Cike da farin ciki take kallonsu. Dan har cikin ranta take jin son Hafizzullah. Duk da har yanzu babu wanda ya faɗa mata wanene shi sai take zargin Mama Balki ce ta haifesa saboda tsantsar kamarsa da Falaq. Zama sukai suka sakata tsakkiya. Fahad ya amshi spoon ɗin hannunta ya cigaba da bata abincin, itama saita dinga basu a baki Fahad nata tsiyaya mata surutu akan halin da su Baba prof ke ciki na harbin kunama dan su da sai da sukaje asibiti dubiya ko nace sa ido, shi dai Hafizzullah nashi dariya ne. Sai in anzo gaɓar daya sakosa ko yace koba haka ba? Dan tabbatarma Ummie sannan Hafizzullah ɗin ya bada amsa. A haka Maash ya shigo ta samesu. Sanye yake cikin baƙar jallabiya mai gajeren hannu data masa ƙyau sosai. Idanu duk suka ɗago suna kallonsa, kafin Hafiz ta fara gaishesa. Shima Fahad sai ya gashesa tare da faɗin, “Yaya irin wannan ƙyau haka, kamar kaine ma ke rainon Babyn wlhy”. Idanu Hafizzullah ya waro sosai akan Fahad, dai-dai Maash na ɗaukar gwangwanin turare akan mirror ya wulwulo masa. Da gudu Fahad ɗin ya miƙe ya fice. Hakan yasa Hafizzullah dake ƙunshe tashi dariya shima miƙewa ya fita da gudu. Ummie ma dariya take yi, cikin dariyar ta ce, “ALLAH ya shiryeka Fahad”. Fuska Maash ya narke a marairaice ya ce, “ALLAH ya rainani Ummie. Ranar fa ina jinsu wai zaimun yankan rago”. Dariya Ummie ta sake kwashewa da shi. Dan itama a ranar komai a kan idonta akayi tana leƙensu ta balcony ɗin sashenta batare da su sun lura da ita ba. Sai dai a tunaninta ma shi baya gidan a lokacin tunda bataga ya fito ba sai Samraah. Sosai dariyar Ummien ke sakashi farin ciki. Dan Doctor ya tabbatar masa duk cikin nasarorin samun lafiya ne. Yanda ya zuba mata idanunsa da ɗan ruwan hawaye ta cika yasata miƙewa ta buɗe masa hannayenta alamar yazo gareta. Babu musu kuwa ya iso. Shigewa yay ta rungumesa. Sai kawai ta sakar masa kuka. Daburcewa yay ya ɗago da sauri jikinsa har tsuma yake. Fuskarta cikin tafukan hannunsa muryarsa na ɗan rawa ya ce, “Ummie miya faru kuma?. Kar kuyi kuka dan ALLAH”. Murmushi ta saki tana mai kai nata hannun itama ta shafa fuskarsa. “Muhammad ina kukan farin ciki ne barni nayi. ALLAH ya muku albarka kaji. Gaba ɗaya zancen cikin nan na matarka ya wanke dukkan dattin zuciyata. Na godema UBANGIJI da ya bani rahamar samun waraka tare da ƙyautar zuri'a daga tsatsonka. Ka saka a ranka wannan itace ƙyauta mafi girma da kuka fara bani bayan samun warakata.” Rungumeta ya sake yi shima cike da farin ciki yana mai ƙoƙarin haɗiye hawayen da suka cika masa ido. A hankali ya furta, “In sha ALLAHU Ummie zamu cigaba da baki irin wannan ƙyautar har sai kince sun isheki da amincewar UBANGIJIN rahama mai badawa a sanda ya so ga kuma wanda yaso.” “ALLAH ya tabbatar Muhammad ɗina.” Daga haka suka zauna. Sai kallonta yake yi yanaji kamar ya haɗiyeta dan tsananin ƙaunar da yake mata a rayuwarsa. Kamar yanda itama take jin matsanancin ƙaunar gudan jinin nata. Muryarta a sanyaye ta ce, “Ya kamata muje muga su Baba asibiti. Amma harbin nan na kunamu ya bani mamaki kamar an tsara musu hakan”. Kauda kai Maash yayi kamar baiji ba. Sai da ta ce, “Nasan ka jini ai. Na kuma tabbatar a yanzu cewar kai ne”. “Ummieeee!”. Ya faɗa fuska a narke. “Ba wani Ummie anan. Miyyasa kayi haka?”. Murmushi ya ɗan yi da faɗin, “Kai Ummie sa ido ne fa wannan”. “Nayi saka idon ja'iri”. Ƙaramin murmushi yayi kawai, sai zuwa can ya ce, “Yanzu ma aka fara, har sauron da suka saka ya cijeki sai na rama miki”. Salati Ummie ta sanya tana tafa hannaye. “Oni Ummu-Hidaya kai ɗin ne dai kenan Muhammad. Ya ALLAH ka shirya min wannan yaron da ya girma bai san ya girma ba. To ai basu suka saka kunama ta harbemu ba ALLAH dai ya ƙaddara”. Ƙin cewa komai yayi sai fuskarsa daya tsuke kamar bashi ba. Juyawa yay ya fuskanci Ummien da ƙyau. Cikin dakewar nan ta shi ya ce, “Ummie ina son na san gaskiyar komai a yau?”. Murmushi tayi mai ƙyatarwa. Tare da kamo hannunsa ta sumbata. “Karka damu My dear zaka sani amma ba yau ba. Kai nake son ka sanar min abinda duk ya faru da ga lokacin dana sake komawa halin haukar nan har zuwa yau? Amma kafin hakan ina son nasan Companyn dana ce ka buɗe a Kano ya fara aiki?”. Kansa ya jinjina mata.. A hankali ta saki murmushi mai ƙayatarwa tare da lumshe idanunta ta furta, “Alhamdullahi ya Rabba. Muhammad ALLAH yay maka albarka. Hakan na tabbatar min zuwa yanzu kasan ainahin fuskar kowa a wannan family naku”. “Tabbas Ummie. Dan komai ya fara buɗewa ne daga ranar bikin buɗe Company. Sai dai komawarki a halin ciwo a lokacin ya sake tayar min da hankali. Sai dai koba komai na fara fahimtar daga ina ainahin komai yake, duk da anyi yunƙurin daƙileni da sihiri fiye dana farkon daya raba tsakanina da ke. Aka kuma sake ta'azzara ƙiyayyata da Fahad. Sai kuma ALLAH ya shigo da Samrh rayuwata a lokacin...” tiryan-tiryan ya kwashe komai ya bata labari hatta aurensa da Samraah. Har zuwa wannan rikicin da ya faru na kwana biyun nan. Kuka sosai takeyi kamar yanda Fahad dake laɓe yana saurarensu yake yi shima. Hakama Samraah da ko Fahad bai gani ba kuka take yi. Dama tazo gaida Ummie ne, saɗaf-saɗaf ta koma da baya tunda ALLAH yasa kowa bai ganta ba. Daga ƙarshe dai shima Fahad ya faɗa ɗakin. Rungume Maash yayi da Ummie yana mai basu haƙuri. Murmushi Maash da gaba ɗaya yanayinsa ya canja yayi yana mai shafa kansa. “Kai zan bama haƙuri Fahad, dan na maka abubuwa da yawa marasa daɗi, na kasa riƙe amanar Ummie. Na kasa kula da tarbiyyarka. Ban san cinka ba bansan shanka ba balle muhallin da kake rayuwa. Duk da ina son yin hakan a ƙasan raina amma bazan iya ba. Akwai lokacin danai yunƙurin neman inda kake amma hakan ya gagara, sai da nayi jiyyar sati biyu. A randa nai maka mugun dukan daka bar gidan nan sai da nayi kuka naji sanyi a raina. Ka yafe min kaji Kiddo, dan wlhy ni kaina ban san duk taya nayi waɗan nan abubuwan ba sai da Abbah ya fargar da ni shi da Baba (Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain da Baban Hayatu). Amma duk da haka na gagara basu haɗin kan shan maganin da suka tabbatar min in sha ALLAHU suna fatan ya zama waraka a garemu”. Kuka sosai Fahad ya sake fashewa da shi shi da Ummie. Sosai ya rungume Maash fiye da farko. “Ni Yaya bakamin komai ba. In ma kamin na yafe maka. Dan koda baka yimun da hannunka ba Yaya Hayat na mun komai. Kuma koda zanji haushi yana sanar min da kuɗinka yamun. Wlhy bazan taɓa yafema mutanen nan ba. Kuma ni dan ALLAH ku gaya min waye-da-waye ALLAH sai na musu yankan kifi”. Dariya Ummie ta sanya, yayinda Maash yay murmushi da dungure masa kai. “Kai bakinka baya gajiya da ambaton yanka mutane?”. Cike da shagwaɓa Fahad ya ce, “To yaya ai kaima dai jiya kace zaka yanka min”. Yanzu kam dole sai da Maash ya ɗan dara da faɗin, “ALLAH ya shirya min kai. Ni tadani naje na duba Matata kaji”. Cike da shaƙiyanci Fahad ya ce, “Uhhm su Yaya fa an zurma da yawa. Ummie ki ƙara godema Aunty Samraah ita babbar ƴar su ce tunda ta kamo babban kifin nan naki a kogi cikin ƙanƙanin lokaci”. Mi Ummie zatai banda dariya. Maash ya kama kunnen Fahad ya murɗa har sai da yay ƙara sannan ya sakar masa ya fice yana murmushi kawai... Rungume Ummie Fahad yayi cike da farin ciki ya ce, “Wlhy Ummie da gaske yana bala'in sonta. Kigafa yanzu murmushi baya masa wahala.” “Kaima saika dage ka samo min wadda zata maka irin wannan kamun kaji Autana”. “Kwantar da hankalinki ke dai Ummie ai ni biyu ma zanyi rana ɗaya”. “Biyu fa Auta?”. “Yes Ummie na, ba gara na more da ƙyau ba”. “ALLAH ya shiryeka”. Ta faɗa tana dungure masa kai. Dariya yayi, sai kuma ya marairaice mata wai ta bashi labarin abinda ya faru a bayan dan shi bai taɓa tunanin ciwonta nada alaƙa da wani abu ba. Saboda babu wanda ya taɓa zama ya nuna masa.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚_ ......Ƙarfe biyu da rabi na rana bayan jami'an tsaro sun gama bincike-bincikensu suka saki labarin kama Commondo da Madam Jannifer. Tare da samo Paah da aka tabbatar da Commondo ɗin ne yay kidnapping ɗinsa ya kuma kashe drivern sa. Ita kuma Jannifer suna kan bincike domin sanin dalilinta na yunƙurin sake zuwa domin ɗaukar Paah ɗin a daren jiya. Sakin wannan labari dai-dai da isowar tawagar motocin Maash har bakwai asibitin. Dan gaba ɗayansu suka taho hatta da Falaq mai jego ba'a bari ba. Samraah ma ce yaso hana ta biyosu. Aiko ta saka masu kukan taɓara. Sam baya son ganin damuwa a tattare da ita, dole ya barta ta biyosun amma ya saka TJ yin tuƙi a hankali. A waje wajen motocin suka bar wasu guards ɗin nasa. Wasu kuma suka take masu baya har ciki. Ummie da Mama Balki ne a gaba su Sha'aibu na jagorantarsu. Sai Falaq da Samraah biye da su, Samraah na ɗauke da Baby Awwab. Maash da Hayatu sai Fahad da Hafizzullah na take musu baya. A ƙarshe sauran guards ɗin. Tako ina suka ratsa daga ƴan dubiya har ma'aikata da patients kallonsu sukeyi. Ɗakin da aka kwantar da Baba prof suka shiga. Yana kwance sharkaf, a kallo ɗaya zaka fahimci ya jigata da cizon kunamar nan. Ga wani uban ƙullutu a goshi da alamu suka nuna ya buga kanne a bango maybe waje neman ceton kai. Ƙafafunsa a wawware suke an yafa masa duvet kamar dai babu wando ne ta maganar Lado(🥱🤭😝). Ummie ce ta fara gaisheshi da masa yaya jiki. Idanu kawai ya zuba mata batare daya iya amsawa ba. Ba kuma dan baya magana ba sai dan bakin nasa ya gaza koda motsi ne, sai kallon tsana da gargaɗi yake mata kamar zai cinyeta da idanun. Murmushi ta sakar masa tamkar bata fahimcesa ba ta ce, “ALLAH ya kiyaye na gaba”. Sai su Mama da su Samraah suka gaidashi a jimlace. Fahad kam ko kallon inda yake baiyi ba. Maash ma dai da farko bai tanka ba, sai da ya mula dan kansa ya wani taka cike da ƙasaita da izza hannayensa duka a aljihu ya matsa gaban gadon. Zama yay a kujerar gabansa yay crossing ƙafafunsa tare da folding hannayensa a ƙirji ya wani zuba masa cat eyes ɗin nan nashi masu kaifi da kwar jini. Ji kawai baba prof yay wani abu na tsarga masa. Dan gaba ɗaya kamanin Awwab ɗin rikiɗa masa sukai tamkar Ibrahim Alonso. A daƙilen nan nashi cike da manners ya furta, “Ya kake?”. (Ya kake?) Baba prof ya maimaita a zuciyarsa, zuciyarsa tasa na masa zogi. Da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya bashi amsa da, “Awwab kasan a gaban wa kake kuwa?”. Murmushi rainin wayo Maash ɗin ya wani saki. Sai kuma ya kalla haɗaɗɗen agogon hannunsa mai shegen tsada yana ɗan wani laɓe small pinkish lips ɗinsa. Hannun ya sauke yana ɗan juya idanunsa ya maidasu ga Baba prof ɗin. Kansa tsaye ya furta, “Mahaifin Paah ɗina”. “Mahaifin Paah ɗin ka?”. Baba prof ɗin ya sake maimaitawa a fili yana wani tsare Maash ɗin da idanunsa. Ta cikin wando kuwa saboda harbi da wajen ya sha baya iya riƙe fitsari sosai yanzu ma sai da ya tsillo. Dan wani banzan kallo Maash ya sake masa yana faɗin, “Bayan hakan ko akwai wata alaƙar? Oh sorry ashe yaron Grandpa ɗina ne kuma, sorry Mr Adams K/Mashi”. Tsuuuu!! Fitsari ya ɗan sake kufcewa Baba prof again. Jikinsa ko har ɗan rawa yake duvet ɗin da aka lulluɓa masa ne kawai ya rufa asiri. Ashe tsugunne bata ƙare ba. Dan Maash na rufe baki Fahad da idanunsa ke kan television ɗin ɗakin ya ce, “What!! Uncle Abdullahi!!”. Yanda ya ambaci sunan da ɗan zabura yasa hankalin kowa komawa can banda Maash da bai ko motsa ba. Uncle Abdullahi ɗinne kuwa ke bayani matsayin babban ɗan sandan sirri da yaransa suka samu nasarar cafke Commondo da Madam Jannifer a daren jiya. Ta re da tabbatar da sun amso Alhaji El-Mu'azz k/mashi. Babu wanda baiyi mutuwar tsaye ba a ɗakin, wasu ma har murza idanu suke domin son ƙara tabbatarwa. Kasa haƙuri Fahad yay jikinsa na tsuma ya tako gaban Maash da ke zaune baida alamar nuna yasan mike faruwa. Amma kuma kunnesa na jin dukkan bayanin Uncle Abdullahi ɗin. Riƙo hannunsa Fahad yayi murya na karkarwa ya ce, “Kaga fa Uncle Abdullahi wai ɗan sandan sirri. Imagine”. Karo na farko Maash ɗin ya ɗago. Idanu ya zubama Fahad ɗin, sai kuma ya janye a hankali ya maida ga television ɗin. Fuskar Uncle Abdullahin kawai ya zubama idanu, sai kuma ya saki murmushi tare da lumshe idanunsa ya sake buɗewa akan Fahad. A taƙaice ya furta, “Na gani”. Ba Fahad ba hatta Ummie sai da ta waro idanunta waje. Mama Balki kam ai baya tai ɗan mamaki sai da Hafizzullah ya ɗan riƙota. Babu zato suka ji an faɗo ƙasa timm. A tare duk suka juya, mi zasu gani Baba prof ya sulmiyo ƙasa dan kiɗima. ALLAH ma ya taimaka jikinsa cikuykuye yake da duvet da anyi abin kunya. Rawa jikinsa yake sosai yana nuna television da yatsansa. Magana yake son furtawa amma ko harafi guda ya gagara fita a bakin nasa. Sai kawai ya zube gaba ɗaya raƙwam alamar suma. Hayatu ne yay ƙarfin halin kiran doctor, akai kama-kama aka maida Baba prof saman gado. Dole kowa ya fito aka barsa da doctor. Daga nan suka shiga inda aka haɗa su Hajiya Mammah su duka. Sukam da sauƙi dan tunda akai musu alluran kashe dafi ta sauka. Barcin da aka sakasu yine ya jasu har zuwa yanzu. Sai Hajiya ƙarama ce dai ansha wahala. Sun samu suma duk sun ɗimauce da labaran da ake nunawa a television. Ba labaran ne yaja hankalinsu ba ganin Uncle Abdullahi a matsayin ɗan sanda. Sun samu itama dai Hajiya Ƙarama na mazarin jiki. Dan abu biyu ne ya ɗimautata zuwa uku. Ganin an kama Commondo da Madam Jannifer, sai Uncle Abdullahi matsayin ɗan sanda babba kuma na sirri. Ƙarin tashin hankalin ma wai shine ya kama su commondo. Itama dai sai da aka nemo likita kanta. Daga nan ɗakin da aka kwantar da Paah muka fara shiga. Ɗakine na musamman dake zagaye da tsaro na musamman. Barci yake shi kam hankalinsa kwance. Duk da ya rame alamar yasha wahala. Rawa jikin Ummie ya fara. Ta ƙarasa gaban gadon da sassarfa. Tuni ta manta da wanda ke tare da ita batama san ta kai dirƙushe ƙasa ta kamo hannun Paah ɗin ba hawaye masu zafi na rige-rigen sauka mata a kumatu. Karyayyar muryarta na rawa ta furta, “Azz! kaine haka? Ya Arrahaman”. Sai kawai ta saki kuka tana mai rungumesa. Da baya-baya na koma na fice a ɗakin, dan haka kawai naji tausayin Ummie ya masifar shigata. Karo naci da mutum, dan haka na ɗaga kai da sauri na kalleta ina mai ambaton ban haƙuri gareta. Itama dai-dai ta ɗago zata bani haƙurin. Ban iya na ƙarasa ba ni, sai idanu dana zuba mata zuciyata na wani irin sauka a hankali. Raɓani tai zata wuce na damƙo hannunta, sai ta juyo a girgice zatai magana nai azamar girgiza mata kaina da zipping ɗin bakina alamar tai shiru. Cikin rawar jiki ta haɗiye maganar da take son yi kuwa. Ni kuma naja hannunta muka bar ta wajen duka. Sai da muka bar ƙofar ɗakin na tabbatar ba idon kowa ata inda muke sannan na ce, “Miye sunanki?”. Sosai fuskarta ya nuna alamar mamakin tambayar da nai mata. Amma ganin na haɗe fuska babu alamar wasa a tattare da ni, ga shi na tabbatar tasan wacece ni dan yanda muka shigo suna kallonmu ko ita bata gammu ba nasan za'a bata labari, ga kuma tranding da hotunana dana Maash sukai a kwanakin nan koma nace suke kanyi. Amma duk da haka sai da na ƙara mata da faɗin, “Sunana Samraah Abdul-wahab Gwarzo, Mrs Awwab El-Mu'azz Maash. Nasan kin sani. Minene sunanki?”. Kanta ta shiga jinjina min tana ƴan waige-waige, mutyarta na karkarwa ta ce, “Murjanatu Usman”. “Masha ALLAH Murjanatu kwantar da hankalinki ba wani abu bane ba, magana nake son nayi da ke amma bazai yiwu anan ba. Ko zaki iya bani number naki?”. Yawu masu kauri ta haɗiye da ƙyar. Cikin ƙara daburcewa ta ce, “Dan ALLAH Maa kiyi haƙuri idan akan turekin nan da nayi ne. Wlhy ban san kin tahoba sam shiyyasa”. Murmushi na mata dan naga ta firgice. Cikin son dai-daita yanayi na na ce, “No kwantar da hankalinki ba wannan bane ba. Tambaya zan miki akan wani abu daya shafi mace mai ciki, amma bana son yi anan shiyyasa”. Da masifar ƙarfi ta sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta sake sauke numfashi da faɗin, “Wlhy ranki ya daɗe harna tsorata. Kin san abunne akwai tsoro balle ku manyan nan. Na zata ko na miki wani laifine. Ba damuwa ko gida kike son nazo zanzo na same ki ai. Sai dai matsalar baza'a barni na shiga ba”. “No karki damu zansa azo har nan ɗin a ɗaukeki. Ko zaki iya bani number ɗinki?”. Cike da zumuɗi ta amsa min tana amsar wayar hannuna. Ni saima taso bani dariya. Dan hannunta har rawa yake wajen loda number ɗin. Amsa nayi nai saving. Da murmushi na ce mata, “Zaki iya ji kirana akoda yaushe in sha ALLAHU. Amma fa maganar nan ta tsaya iya ni da ke kawai. Dan na fahimci kina da hankali da nutsuwa tun wancan kwanciya asibitin da nayi shiyyasa”. Sosai ta sake washe baki cike da farin ciki tana Murmushi. Da ga haka muka baro wajen. Sai da naji shock da hango Maash tsaye da alama ta inda zan fito yake son gani. Amma sai na dake abina a nutsena na ƙarasa inda yake. Batare da nayi magana ba na zare wayar da yake dannawa daga cikin hannunsa. Sai da yana wani sakanni kafin ya ɗan ɗago cat eyes ɗinsa ya kallan. Ido ɗaya na kashe masa cike da salon basar da shi na ce, “Tsaiwa anan kamar wani dogari”. Maimakon tanka min sai ya wani cigaba da kallona, kusan minti ɗaya sannan ya motsa lips a hankali ya furta, “Let's go”. Yana kama hannuna. Banda zaɓin daya wuce bin nasa. A haka muka dinga keta mutane ana kallonmu. A karan farko naji banji kunyar hakan ba. Sai dai a raina ina jin wasu fa zasu iya ɗaukar hotonmu musamman a wannan gaɓar da dama ake neman labari a kammu. Kamar ko ina gani har hanji, dan bamu ƙarasa gida ba sai ga hotunanmu sun fara yawo a media. Sosai na tsarkake sunan UBANGIJI da jinjina halin gulamar mutane da ƙaikayin hannayensu nason yaɗa abinda sam bai shafesu ba. Dan su birge ne ko dan ace a bakinsu aka fara ji oho musu........✍️ Zazzabi ya tasani gaba posting yanzu sai a slow. Ayi hakuri dai in sha ALLAHU muna gab da tsargewa kowa ya huta🥲. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_ .......Washe gari tunda Baba prof da Hajiya ƙarama suka dawo hayyacinsu duk sai suka matsa a sallamesu a safiyar. Iya ƙoƙari doctors ɗin sunyi dan ganin sun fahimcesu musamman ma Baba prof da tai masa illa a inda ya kamata ya samu kulawa amma sam hakan yaƙi yiwuwa. Dole suka haƙura suka sallamesun. Dama shi Paah tun a daren Maash yasa aka sallamesa saboda Ummie ta tada hankalinta akan zataje asibitin zaman jiyyarsa. Shiko bai amince da hakan ba. Shiyyasa ya yarda da a dawo da Paah ɗin gida likitan ya cigaba da zuwa dubashi anan. Kai tsaye sashen Maash ɗin aka kaisa ɗakin da Ummie take. Sai ganinsu kawai tayi. Sosai ta nuna farin cikinta taita sanya musu albarka. Su dai basu ce komai ba musamman ma Maash da ke matuƙar jin zafin Paah har yanzun. Isma'il ne yay kiran Maash ya sanar masa ai an sallamo Baba prof gashi a gida. Baiyi mamakin hakan ba, dan haka baice komai ba sai murmushi. Lokacin da kuma yake fitowa ya shiga ya duba Paah ya fito zasuyi break fast su Fahad ke sanar da itama Hajiya ƙarama ta dawo gida yanzun nan. Dama su su Hajiya Mammah tun jiya aka sallamosu. Uffan shi dai Maash baice ba, sun kuma san bazai ce ɗin ba daman.... ✨✨✨✨ Iya faɗin yanayin da Baba prof ke ciki kawai sai dai kintace, dan a matuƙar harmutse yake. Duk da yanda yake jin rashin ƙarfi a jikinsa suna isowa gida wanka yay tare da yin shiri cikin manyan kaya. Sai da ya fito sannan ya tuna babu drivernsa fa a gidan yanzu. Gashi bai san ina Commondo ya kaisa ba. Zaune ya kai cikin kujerar falon kawai yay shiru. Sai da yaja tsahon lokaci a haka kafin ya ɗauka waya yay kira. Ana ɗagawa da ga can batare da ko sallamar da akai masa ya amsa ba cikin bada umarni ya furta, “Ka sameni a gida yanzun nan”. Ƙitt ya yanke kiran. Sake zabga tagumi yayi na wani lokaci, sai kuma ya miƙe ya fara safa da marwa a falon cikin rashin ƙarfin jiki. Tsahon awa ɗaya ciff sannan Uncle Abdullahi ya iso gidan. Ya nuna mamakin ganin mahaifin nasa a gida, kasancewar duk sun san bai isa a sallamesa ba haka da wuri dan jikin nasa da saura. Ga Doctors ɗin ma sun tabbatar da yana buƙatar hutu.. “Baba ina kwana? Yaya ƙarfin jikin?”. Ya faɗa cikin ƙoƙarin danne komai dake a ransa. Shiru Baba prof bai amsa ba, sai da yaja lokaci mai tsaho sannan ya juyo a wani irin yanayin mai wahalar fassara yake kallon sa. Kasa jurewa Uncle Abdullahi yay ya duƙar da kansa ƙasa, ya san minene laifinsa, ya kuma shirya amsa komai da za'a tuhumesa da shi. Kamar ko yanda yay zato a zafafe Baba prof ya furta, “Abdullahi!! Wanene ni a wajenka?”. Sosai tambayar ta bama Uncle Abdullahi mamaki, amma ya daure kansa a ƙasa ya amsa da, “Baba mahaifina ne kai, wanda yay sanadin kawoni duniya, ya tarbiyyace ni ya tufatar da ni da ciyar dani a lokacin ƙuruciya da kula da ilimina duk bisa amincewar UBANGIJI”. “Ban yarda da hakan ba Abdullahi. Ƙarya kake yi!. Da ace ni ɗin mahaifinka ne da baka zaɓi wata rayuwa bayan idanuna ba. Da ace ka yarda ni Adamu ni na ciyar da kai, na tufatar da kai, na biya maka kuɗin makarantar da har kayi kaurin wuyan aikata abinda ka aikata to lallai fa da baka kasance wani abu a bayan ganina ba. Abdullahi idan ban manta ba ni da kaina na hana ɗan uwanka aikin interpol a sanda ya ƙwallafa ransa. Amma shine kai ka zagaye ka zama jami'in sirri bada sani na ba. Hakan na nufin akwai wani abu a ranka ke nan ko kake shiryawa”. Hankali tashe Uncle Abdullahi ya ke girgiza ma Baba kai. “Wlhy Baba sam ba abinda kake zargi bane ba. Kuma a lokacin daka hana Yaya Mu'azz zama jami'in interpol na ɗauka wannan aikinne kawai baka ra'ayin muyi. Zama wannan jami'in kuwa wasu dalilai ne suka kaini ga zama hakan. Ban kuma ɓoye ba domin wata manufa tawa sai dan yanayin aikina kenan. A jiyan ma dole ce ta tilasta ni fitowa har duniya ta sanni da wannan matsayin. Amma idan har na ɓata maka rai ka gafarceni dan ALLAH”. Shiru Baba prof kamar bazai tanka masa ba. Sai da ya mula dan kansa kafin cikin bada umarni ya furta, “Bazan taɓa aminta da kai ba Abdullahi a yanzu sai na tabbatar. Sai dai a matsayina na mahaifi ina baka umarnin ka saki wannan yaron Commondo....” A bala'in firgice Uncle Abdullahi ya ɗago yana kallonsa. Har bai san sanda ya furta, “Baba saboda mi? Akan mi kuma zanyi hakan bayan shi ɗin mai laifi ne. Dukkan bincikenmu ya tabbatar mana da cewar da hannunsa a yin kidnapping ɗin Yaya Mu'azz. To wai kai minene ma haɗinka da shi da har kake so a sakesa Baba?”. “Babu ruwanka da alaƙar dake tsakanina da shi. Kidnapping Mu'azz kuwa ni da kaina zan hukunta shi na kuma ji ba'asinsa nayin hakan”. Wani murmushin ɓacin Rai Uncle Abdullahi yay da faɗin, “Baba to ai kai ba jami'in tsaro bane. Dan mi zan barka kayi hakan? Sannan babu ta inda dokar ƙasata ko aikina suka bani damar sakin Commondo a halin yanzu. Saboda yanzu haka ana kan binciken mugayen ayyukansa ne ma. Shawarar dazan baka ma shine Baba kai gaggawar barranta kanka da shi idan ma wata alaƙa ta taɓa alaƙantaku. Dan wannan mutumin mugayen ayyukansa zasu iya kaisa ƙasa dama duk wanda yake tare da shi. Ka gafarceni Baba na barka lafiya”. Ya ƙare maganar yana miƙewa ya fice. Dan gaba ɗaya kansa juya masa yake. Idan bai bar gaban Mahaifin nasa ba zai iya rasa control ɗinsa ne gaba ɗaya... Ko sau ɗaya Baba prof ya kasa motsi. Sai kalaman Uncle Abdullahi ne ke masa wani irin amsa kuwwa acikin kunne har bai ma san ya fita a falon ba. Cigaba da jin sautin muryar Uncle Abdullahi na masa ihu cikin kunne ya sakashi fassa wani ihu shima yana wancakalar da Centre table ɗin gabansa. A guje wasu a cikin ma'aikatan gidan suka fara rige-rigen shigowa ciki harda Kuku da ke lafe yana jin komai. Sai dai shi kansa a yau ba ƙaramin girgiza zuciyarsa tayi ba da ganin abinda bai taɓa zato ba. Yanzu nan duk irin aibanta Baba prof da tsiyatakunsa da ya dinga yi a wajen ogan nashi ashe mahaifinsa ne. Kan bala'i jan. Wannan wace kalar cakwakiya ce haka. Sai yanzu ya fassara sunan Uncle Abdullahi da ƙyau. *_Abdullahi A.KM_* wato (Abdullahi Adams K/Mashi) kenan dai. Jiyyar gaba ɗaya haddarsa ta gama gogewa. Jiyay kawai buƙatar ganin Maash yake, shin shima yasan ogansa kawunsa ne ko kuwa sai a jiya da yay bayani?. Da ƙyar suka samu Baba prof ya zauna. Haka suka shiga kimtsa falon shi kuma ya shige bedroom. Giyarsa ta samu ya kwankwaɗa ya zube ƙasa sai barci. Dan inba hakan yayi zuciyarsa zata iya bugawa a yanzun nan..... 🌿🩸🌿🩸🌿 Da mamaki Uncle Abdullahi ke kallon Maash da ke shigowa office ɗin nashi. Sam baiyi zaton shi bane ba. Dan shigowarsa station ɗin kenan rai a ɓace daga gidan Baba prof. Baifi zaman mintuna biyar ba akace yayi baƙo. Da farko yace baya buƙatar ganin kowa. Sai kuma yanda yaga yaron nasa ya yi shiru kamar mai son cewa wani abu yace yaje ya shigo dako waye. Amma mintuna goma kawai zai iya bashi. Shine fa kawai sai ya ga Maash ya shigo alamar shine dai baƙon da aka nemawa iso kenan. Da ƙyar ya iya ɗaga hannu yay masa nuni da wajen zama. Shima sai Maash ɗin ya kai zaune batare da yace komai ba. Sai da yaron Uncle Abdullahi ya fita a office ɗin sannan a hankali Maash ya furta, “Good morning Uncle”. Murmushi Uncle Abdullahi yayi da faɗin, “Morning Awwab. Daga ina haka?”. Ƙaramin murmushi shima Maash ɗin ya saki a karo na farko. Sai kuma ya ɗan kalla Uncle Abdullahi ya ɗauke idanunsa a daken nan nashi ya ce, “Daga gida, kuma wajenka nazo”. “Dama nasan zan ganka, amma banyi zaton da wuri haka ba. Kar dai na jaka da nisa mike tafe da kai?”. Numfashi mai nauyi ya sauke da gyara zamansa da ƙyau babu alamar wasa tattare da shi. “Uncle basai munja komai da nisa ba tsakanin ni da kai kamar yanda ka faɗa. Nasan kasan abubuwa da yawa da suka shafeni wanda ba kowa ya sani ba a gidan nan. Wasu ma da kaina na buɗa maka saninsu saboda na jima da sanin kai ne ogan Isma'il da Shu'aibu. Nasan hakanne tun lokacin da ka bada su Shu'aibu matsayin guards ɗina....” “What a surprise!.” Uncle Abdullahi ya faɗa cikin nuna matuƙar mamaki da al'ajab har yana miƙewa. Ƙasa kawai Maash yay da kansa yana furzar da isa. Ɗan bugar desk Uncle Abdullahi ya ƙara yi yana sake jinjina al'amarin sosai. Kallonsa Maash kawai yay ya sake ɗauke kansa kamar mai ɗan jin nauyin Uncle ɗin nasa. Zama Uncle Abdullahi yayi zuciyarsa na sake mamakin hatsabibancin yaron nan. Amma sai ya dake........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_ .......Cikin girgiza kai ya ce, “Nama rasa mizan ce Awwab. Kenan da ban fito a wannan gaɓar na bayyana kaina ba haka zamuyita tafiya ina maka kallon biri kana min na ayaba?.” Murmushi Maash yay da faɗin, “No Uncle! No! Just forget. Hakan ya kasance ne saboda wasu dalilai. Kamar yanda yanzu ma dalilan ne suka kawoni nan. Isma'il ya sanar min duk yanda kukayi da Baba. Duk da bai kamata ace ya sanar min ɗin ba. Sai dai ruɗanin da ya shiga shima na gane cewa munada alaƙa har haka mai ƙarfi ya kaisa ga hakan. Uncle Please ina riƙonka ka bama wani case ɗin nan. Saboda....” “Saboda ban cancanta ba? Ko saboda Baba ya kasance mahaifina kai kuma ɗan ɗan uwana?”. “No Uncle Understand me. Abin zai zamar min wani iri nima. Shiyyasa ba kowane imformetion zakaga nake baku ba, wasu lokutan nake yin wasu abubuwan da kaina ta bayan fage. Magana ta gaskiya case ne da bazan iya bari ba, ba kuma zan so sarƙaƙiyarsa ta shafi har waɗanda bai kamata ta shafa ba irinka.” Sosai Uncle Abdullahi ke jinjina kai idanunsa da suka canja launi akan Maash. Murya a shaƙe ya ce, “Muhammad Awwab!”. “Yes Uncle”. “Kasan mi nake so da kai?”. Kai kawai Maash ya girgiza masa. “Kasa a ranka sunana Abdullahi A.km. da yay rantsuwa wa UBANGIJI zaiyi aiki tuƙuru domin kare ƙasarsa dayin adalci wa mutanen cikinta walau talaka ko mai arziƙi, ko mai mulki. A tsarin aikinmu babu zancen family. Babu zancen kasuwanci, babu zancen abota ko makwaftaka. Tabbas a lokacin dana amshi wannan case ɗin ban san nasu wanene ba. Sai da aka hari rayuwarka ta farko sannan har na yanke komawa cikin Maash Mansion. Bayan nan ne na zauna nayi bincike mai zurfi tare da saka mutane da yawa a cikin ku. Abinda yasa na ɓoye kaina gareka dan ka samu damar sanar min komai batare da kaji wani ɗar ba. Ashe ma nayi shuka a idon maƙwarwa ɗan nawa ƙwaron kansa ne”. Murmushi nan ɗin ma Maash ya ɗan yi kaɗan batare da ya yace komai ba. Uncle Abdullahi bai damu ba ya cigaba da yin maganarsa. “Ina son kamar yanda kayi kawaici ƙin nuna kasan nine a da yanzu ma ka cigaba da tafiya a hakan kawai na baka san ni ɗin waye ba. Dan tunda na fara aikin nan sai fa na kaisa in sha ALLAHU”. “Uncle Amma....” “Chapter is closed Awwab”. Uncle Abdullahi ya faɗa cikin katseshi. Numfashi Maash ya furzar da faɗin, “Shi ke nan. Yanzu wane taimako kake buƙata. Dan duk yanda kake tunanin abun ya wuce hakan”. “Nasani Awwab. Dan laifukan da masu laifukan sun kasance rassa daban-daban. In dai akwai wasu imformetion a wajenka ka bani su kawai zakaga yanda aikin zai cigaba da tafiya. Na kuma maka alƙawarin komai gareka zai zama a buɗe. Hatta da shawara zamu iya nema ta wajenka dan na fahimci kai bana wasa bane”. Girgiza kai Maash yayi kawai batare da yace komai ba. Sai daya ja kusan minti ɗaya kafin ya ɗago. “Baka da matsala ina sha ALLAHU. Sai dai ina son ka bama Baba damar ganin Commondo dan hakan nada matuƙar amfani. Musamman ga ita matar nan dan akwai abinda take ƙoƙarin shiryawa kenan da ya kamata muyi saurin ganota”. “Okay na fahimceka. Wato shiyyasa taje ta shirya ma Baba wancan ƙazon kuregen kenan na cewar Commondo ne yay kidnapping Yaya? Duk da ni inama zargin kamar tasan komai”. Ɗan wani luuu da idanu Maash yayi sai kuma ya buɗe akan Uncle Abdullahi. “Tare da ita sukai komai”. “What! Kana nufin harda ita akai kidnapping Yayan? Kenan itama tana da alaƙa da Commondo ɗin?”. Ƙaramar dariya data bama Uncle Abdullahi mamaki Maash ya saki. Sai kuma ya ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa. Kansa tsaye ya ce, “Uncle wannan zaren tsayinsa yafi na igiyar wutar lantarki. Idan nace zan maka bayani yanzu akan komai, bama zaka iya fahimta ba. Amma ka bani lokaci”. Ya ƙare maganar yana miƙewa. Cikin girmamawa yay masa sallama ya fice abinsa yana wani makirin murmushi. Dan kuwa shi kaɗai yasan mi yake shiryama ransa. Zuwansa nan kuwa nada dalili da nasaba da son sanin ainahin abinda ke a ran Uncle ɗin nasa da kuma son tantance a wane matsaya yake yanzu... Da sauri Jaga da Hayatu dake zaman jiransa duk suka miƙe. Gaba yay suka take masa baya. A waje ma su Shu'aibu na jiransa. Nan ma TJ ne ya buɗe masa mota. Jaga da anan suka haɗu da shi dama Maash ya ce ya shiga gaba. Shi kuma Hayatu ya dawo kusa da shi.. guards ɗin kuma duk suka shiga motocin su suma.... 💢🌟💢🌟💢 Kamar yanda Baba prof ke a hargitse haka Hajiya ƙarama ke a harmutse. Dan ita koma wankan bata nema yi ba tana isowa gidan ta shige ɗaki ta kulle kanta. Bige-bigen wata ta fara. Ana ɗagawa ta ce, “Please ina son mu haɗu”. Ban san amsar da aka bata daga can ba ta dai jinjina kan ta yanke kiran. A gurguje ta canja kaya dan yanda take jinta bata jin zata iya wani zaman yin wanka. Cike da fatan ALLAH yasa kada ta samu kowa a falon ƙasa kamar yanda ta shigo bataga kowa ba tayi. An koyi Sa'a babu kowan, dan akwai sauran safiya duk basu tashi barci ba masu gidan. Mota ta shiga ta fita a gidan duk da yanda take jin jikinta babu daɗi. Yanda take ɗibar motar yasa ta isa inda take harin zuwan da wuri. Can gefen gari ne wani ɗan ƙauye ko kuma ma mu kirashi club kawai dan mahaɗace ta gawurtattun ƴan iskan criminals ɗin Lagos ɓoyayyu da wasu manya suka ɗaurema ƙugu. Mata ne da maza a wajen ana ashararanci. Sai cinikayyar mugayen abubuwa na maye dana ta'addacin da ake gudanarwa. Mafi yawan waɗanda suka san wannan waje ƴan ɓadda sawune. Kasancewar safiya ce tsirarun mutane ta samu dan ansha shagalin dare duk sun zube barci wasu kuma sun kama gabansu. Sai masu kula da wajen ne keta aikin tsaftacesa sai kuma irin ogan da sunci dubu sai ceto kansu na iya ɗaukar kowane kalar kayan maye yanzu batare da sun jigata ba. Kamar yanda ƙa'idar take sai da aka binciketa tsaf sanan aka nema mata iso wajen boss ɗin. Mintina kusan ashirin aka shiga da ita ciki. Ƙaton falone da yaji kayan more rayuwa dan an shirya liyafar duniya a cikinsa. Gini ne to iya gini aka zuba a cikin jejin nan. Sai kuma aka bisa da iccen bamboo aka rufe ta yanda zaka ɗauka da shi aka yi san. Tana nan zaune kusan mintuna biyar ma sannan ya fito. Fari ne tass ƙarfaffan gaske jiki duk ya buɗe ya kuma sha zanen tattoo. Rantalelen kansa sai ƙyalli yake saboda yanda aka ƙwalƙwale gashin tsaf. Sam fuskarsa babu walwala amma yana ganin Hajiya ƙarama ya ɗan saki murmushi yana kaiwa zaune da faɗin, “Manyan ƙasa yau dai aƙalla an tuna da ni kenan?”. Cikin harshen turanci Murmushin yaƙe ta saki da faɗin, “Hummm Marcel dama ban manta da kai ba. Kawai dai abubuwa ne suka min yawa. Ya naka?”. “Komai normal muna nan muna zubawa? Da alama ta ƙwaɓe dan naga an kama mutuminki. Sai dai abinda ya ɗauran kai kamar wanda kike zaune a wajensa yanzu naga ance yayi kidnapping ko har yanzu dai yana sonki?”. “Hakane Marcel. Sai dai duk abinda ya faru tare mukayisa. Abinda yasa na nemoka saboda Jannifer itama dai yarinyarka ce. Nasan kuna harkar bussines sosai batun yanzu ba. Na kuma san a tsarinka duk wanda ke tare da kai in har ya faɗa hannun jami'an tsaro kasheshi kake sawa ayi. Shiyyasa nazo neman alfarmar shima Commondo a kawar da shi kawai a lokacin kawai da Jannifer”. Wata shaƙiyyyar dariya Marcel ɗin ya saki, sai da yay mai isarsa sannan ya tsagaita da faɗin, “Ada Jannifer ke yarinyata. Amma tuni na saidata ga Bancy. Shiyyasa bani da wata alaƙa da abinda ya sameta yanzu”. Da mamaki Hajiya ƙarama ta ce, “Amma bata taɓa faɗa min ba”. “To wannan tsakaninku ne kuma. Yanzu dai idan kina son aiki akan Commondo sai muyi ciniki kenan. Sannan batun Jannifer ki samu Bancy ɗin dan tabbas bazai barta a hannun jami'an tsaro ba. Daga nan kuma zuwa dare zai iya sakawa a saketa dan shi kinsan ba irin tsarinmu yake ba.....” Sosai hankalin Hajiya ƙarama ya tashi, dan tsakaninta da Bancy fa sam babu jituwa. Idan kuma har yasan akan yimata aiki Jannifer ta shiga hannun kwalawa tabbas ya samu makamin yaƙarta kenan. Ina bazata faɗi ƙasa haka wanwar a tsakkiyar ƴan iska ba. Dan haka kai tsaye ta fito fili ta ce, “Akwai matsala kenan Marcel. Dan kasan bama shan inuwa ɗaya da Bancy yanzu. Idan har ban kawar da Jannifer ba zai yi amfani da wannan damar domin fallasa ni.” “Eh kema kince wani abu. Sai dai gaskiya zan gaya miki dan kin san ni bana ɓoye-ɓoye a aiki. Ni da Bancy akwai yarjejeniyar da ta hana mana yin aiki a tsakanin mutanenmu. Dan haka banda lasisin kashe miki Jannifer sai dai Commondo kawai. Dan haka kije ki sake sabon tunani akan Jannifer saboda kin santa bakinta reza ne.” Sosai hankalin Hajiya ƙarama ke'a tashe. Amma sai ta danne ta amsa masa da “Babu damuwa. Ka faɗi ko nawa kake buƙata akan Commondo, sannan yaya maganar poison ɗin nan na wajen doctor Khunal?”. “Ki nemesa kuyi magana. Tunda kema kin san laifinki ne. Tun 3 to 4years ya haɗa abunnan amma kina jan jiki. Ki dai yi fatan bai saidama wani ba kawai. Dan kin sanshi dai akan kuɗi baya wasa mugun ba indiyen mam”. “Ba damuwa zan nemesa. Lokacin amfani da abunne bai taso ba sai yanzu. Miye kuɗin aiki na? Dan bayan an gama da shi akwai wasu har huɗu. Idan kuma su haɗuwarsu zai zama wahala ko a rarrabe a ƙaddamar dan bana son a wuce kwanaki uku nan to a sakama gidan duka wuta. Sai dai kafin hakan ina buƙatar Maash, Mu'azz & Ummu-Hidaya a raye”. Dariya sosai Marcel yayi da faɗin, “Fantastic. Wai har yanzu kina wahala akan wannan project ɗin? Koda yake bakiyi jiran banza ba, tunda ta ƙara mai kam. A bazan ji tausayinki ba kawai naji babban alert. Ta shi kije kawai daren yau labarin mutuwar Commondo zata zo gareki. Sauran aikin kuma ma ƙarasa zancensa a waya”. Murmushi kawai Hajiya ƙarama tayi tana miƙewa. Sai kuma ta miƙa masa hannu sukai musabaha sannan ta fice..........✍️ 🤔Matar nan ko?.. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ .......Kasancewar yau ma sharkaf na tashi har sai zuwa ƙarfe ɗaya saura na samu zazzaɓin jikina ya sauka yasa ni bansan wainar da ake toyawa ba a gidan. Cikin ƙarfin hali na taƙarƙara nayi wanka nayo alwala. Koda na idar da sallar ban wani damu kaina ba na saka doguwar riga mara nauyi na ɗan saka turare. Ina ƙoƙarin fitowa wayata ta hau tsuwwa. Ɗauka nayi na duba sai naga shine. Zaune nakai kafin na ɗaga. Saukar sassanyar muryarsa cikin kunnena ya sani sauke ajiyar zuciya. Sallamar tashi na amsa masa tare da gaisheshi. Shima cike da kulawa ya tambayan yaya jikin?. “Alhamdullahi, Yaya shine ka fita ban sani ba”. A hankali Maash ya lumshe idanunsa dan shagwaɓar tata ya jita har tsakar kansa. Cikin sake sauke murya shima ya ce, “Am sorry. Uzirin fitar ne ya taso min dole My Tiger. Ina fatan dai yanzu babu zazzaɓin?”. “Ya sauka, har nayi wanka zanje wajen su Ummie yanzu ma”. “Masha ALLAH, ki daure kici abinci to, nima anjima kaɗan zan dawo.” Cikin sake narke murya da shagwaɓeta na ce, “Karfa ka daɗe”. Ina jin saukar sautin murmushinsa cikin kunnena, sai kuma ya ce, “Okay bye” ya yanke kiran. Ajiyar zuciya na sauke tare da kafe wayar da kallo, sai kuma na ɗan sumbaceta. Duddubawa nai naga miss call nashi ritutu, sai na Gwaggo Gudidi da Abba. Ya Musaddiq ma yamun ɗaya. Sai Fahad da Hafizzullah da Aunty Falaq. Ajiyar zuciya na sauke nayi kiran Abba muka gaisa harda amaryarsa. Ya sake tabbatar min da yana nan tafe in sha ALLAHU shi da Kawu Musa. Nayi murna sosai ya bama Auta shima muka gaisa yau baije school ba wai babu lafiya. Gwaggo na kira itama muka gaisa, mun ta hira da ita har na sauka ƙasa. Acan mukai sallama. Babu kowa a falon dan haka na shiga ɗakin aunty Falaq mai jegon ƴan gayu. Yo jegon ƴan gayu mana tunda sabgoginta taketa zubawa ba kamar yanda naga masu jego na nutsuwa waje ɗaya ba ko ɗan suna ayi sannan. Amma ita yau kwana shida ko ina ƙafarta zuwa take a gidan nan. Na samu tana barci. Dan haka banyi magana ba na fito. Ina son shiga na gaida Ummie amma na kasa saboda yanzu ba ita kaɗai bace a ɗakin. Har na nufi kitchen dai na daure na koma ƙofar ɗakin. Knocking nayi kamar mai jin tsoro sannan nayi sallama. Bammayi zaton za'a jini ba sai naji an buɗe ƙofar. Hajiya Mama ce, tana ganina ta saki murmushi da faɗin, “A'a Masha ALLAH daughter ce? Jiki yayi sauƙi kenan”. Murmushin nima na sakar mata kaina a ƙasa na rissina na gaisheta. Ta amsa min da kulawa tana jan hannuna ciki. Paah na zaune ya jingina da fuskar gadon Ummie a kusa da shi tana bashi magani a baki. Jinai nutsuwa ta ƙara ratsani ganin Ummie jiki dai nata ƙara sauƙi, gashi itama har tana jiyyar wani. Har ƙasa na durƙusa na gaishe da Paah ɗin tare da tambayarsa jikinsa. Ya amsa min a hankali dan muryar tasa bata fita sosai. A mamakina nima sai ya tambayen yaya nawa jikin? Sake ƙasa nayi da kaina kawai ban iya na amsa ba. Dan haka kawai naji kunyar amsawar. Ƙaramar dariya Ummie da Hajiya Mama sukayi. Sai kuma Ummie ta ce, “Zo nan Babyna”. Babu musu na tashi zuwa gareta, zan durƙusa ƙasa ta kamoni ta zaunar kusa da ita. Duk sai naji na daburce. Amma ta hanani saukar da nake son yi. A haka na gaisheta da tambayarta jikinta dana Paah. Ta ce duk Alhamdullah yaya nawa nima. Itama kasa amsa mata nayi sai tai murmushi kawai. Cikin basar da zancen tace, “Ai munje dubaki ni da Mashi'a amma kinata barci. Kaina a ƙasa na ce, “ALLAH Ummie bamma san kunje ba”. Cikin murmushi ta amsa ni da faɗin, “Shiyyasa dama bamu tadaki ba. ALLAH dai ya ƙara afuwa. Mi kike son ci yanzu?”. “Ummie bana jin yunwa”. “No bazai yiwu ba. Rabonki da abinci tun daren jiya. Faɗa min mikike son ci?”. Kafin na bada amsa akai knocking ɗin ƙofar, ba kuma a jira anyi magana ba ko anyi sallama kawai aka shigo. Hajiya Mammah ce. Sai da ta gama kallemu sannan cikin harzuƙa ta ce, “Eh lallai. Mu an hanamu zuwa amma Mashi'a na nan. Wai ko dai zancen Fahad ɗin gaskiya ne mune ake zargin mun haukata kin Ummu-Hidaya?”. Murmushi kawai Ummie tayi batare da tace mata komai ba. Sai Hajiya Mama ce ta ce, “Kai Adda wane zancene haka kuma?”. “K! saurara min da'alla auta. Wai shin gaskiya a buɗe sai muƙi faɗa saboda muna tsoron wa? Yo inba da gaske mune dai ake ganin mun haukatatan kamar yanda ɗan ta ya faɗa ba wane take-take ne wannan? To idan ance ke kada mu dubaki ai ya kamata ma musan shi ɗan uwanmu yana gidan muzo mu gansa muji daɗi ko. Ni narasa wannan al'amari haka komai a munafunce. Yaranki sun rainamu a gida, kowanne sai ya gasa mana magana. Ƙarshen raini ma da nuna mu ba'a bakin komai muke ba aure Awwab yaje yayi a ɓoye saboda gamu mayu kada mu sani mu cinye matar ko? Ko miye abin ɓoyewa ga ƴar drivern gida? To fa gaskiya ni ina son gidan nan ayi zama, dan bazan bar waɗan nan abubuwan da suka faffaru su wuce a banza ba nan gaba a sake samun hanyar wulaƙantamu ehe. Dan haka ALLAH ya baka lafiya Mu'azz sai anyi zama wlhy. Shima Abdullahi naga ashe ya fara zama almunafunfun, yo inba munafunci ba dan ya zama ɗan sanda sai ya wani ɓoye fisabilillahi. Gida dai gaba ɗaya babu saiti kamar an koro mu da ga dawa kowa ruɓaɓɓe”. Babu wanda yace da ita komai. Ita Ummie ma ta maida hankalinta kaina ne kamar bata san tanai ba. Sai na fahimci itama fa tana da irin shariyar Yaya Awwab. Sai Paah ne ya kalleta cikin mamaki ya ce, “Abdullahi kuma Addah?”. “Ƙwarai kuwa Mu'azz Abdullahi dai daka sani. Ni ba zamansa ɗan sandan bane ya ɓatan rai ba, yanda ya ɓoye mana sai kace abun wani mugun abu. Ko miye a cikin ɗan sanda kuma mtsoww!!”. A mamakin kowa sai Paah ya saki murmushi. Bai kuma sake cewa komai ba ya zame ya kwanta abinsa. Nima kama hannuna Ummie tayi muka fita a ɗakin muka barsu....... 💦💦💦💦💦 Kai tsaye gidan Baba prof ta wuce. Dan ta gama tsara dole ta sake neman kusanci da shi in har tana son aikinta ya tafi yanda ta tsara shi. Tako yi sa'adar samun farkawarsa a barcin da giya ta sakashi kenan. Zuwanta yasa aka isar masa da saƙo. Ya jima baice komai ba dan mamaki, sai da ga baya kawai ya jinjina kansa da yin alamar ta shigo. Tunda ta shigo cikin takun ƙasaita da izza yake kallonta kamar yanda itama shi take kallo. Sai da ta kai zaune ta saki wani murmushi da faɗin, “Barka da rana”. Maimakon amsa mata gaisuwar sai ya ce, “Miya kawoki nan?”. Murmushi ta sake saki tana langaɓar da kai gefe sai kuma ta daidaitashi. “Da gani har kai ka sani na sani muna buƙatar juna a wannan gaɓar”. “Haka tunaninki ya baki”. “Kaima haka naka tunanin yake yallaɓai. Kada kai wasa da wannan damar. Daga ni har kai muna yaƙi akan abu guda ne, sannan maƙiyanmu guda ne. Idan munce yaƙin ne bazamu iya tare ba lallai munyi kuskure. Kafin kuma cimma burinmu da kai maƙiyanmu ƙasa to sune zasu fara kaimu domin sun ɗakko hanya. Commondo da ga ni har kai ya shirya cin amanarmu ne. Dan yayi kidnapping Mu'azz batare da mun sani ba, bai kuma sanar mana ba saboda yana da wata manufa a zuciyarsa game damu. A binciken dana gudanar yanzun na tabbatar da shine ya gayyaci Jannifer domin su canja ma Mu'azz wajen zama shine aka kama su”. “Lawisa! Kinsan ko mi kike faɗa?”. “Niko na sani Yallaɓai, idan baka yarda ba kalla wannan video ɗin”. Tai maganar tana miƙa masa wayarta. Amsar wayar yay, yayi playing video ɗin data latso masa. Rai-rai kuwa abinda ta faɗa ne a video ɗin. Dan ga Commondo zaune tare da Jannifer suna tsara komai. Dunƙule wayar Baba prof yay a cikin hannunsa zai yi jifa da ita Hajiya ƙarama tai saurin tashi ta riƙe kayarta. “Please! calm down, yanzu fa ba lokacin fushi bane ba. Lokacin yin faɗan ƙarshe ne kawai. Idan ba hakaba wahalarmu ta shekara da shekaru kuwa zata tafi a banza. Muna da ƙalubale daban-daban dake zagaye damu. Na farko dai Ummu-Hidaya ta warke, na biyu ƴaƴanta Awwab da Fahad dan shima yaron tsagera ne abinda kai musu ya warware. Ga Abdullahi matsayin jami'in tsaro kuma shinema case ɗin su Commondo ke a hannunsa. Ga Commondo ya juya mana baya. Sai dai ban sani ba ko kasan dama shi ɗin Abdullahi ɗan sanda ne?”. “Ya kamata nasan tun yaushe Commondo ke cin dunduniyata”. Baba prof ya faɗa a kausashe maimakon amsa zantukan data lissafo masa. Tasan wannan mutumin ya gama zarewa, amma bazatayi sake ba dan mugune, dan haka kawai ta saki murmushi. Cikin ɗan laɓe baki ta ce, “Wannan duk mai sauƙine zamu iya bincike. Amma dolene muyi duk yanda zamuyi mu gansa a yau kafin gobe, in ba hakaba yayi magana mun kaɗe”. Kai kawai ya jinjina mata tare da tabbatar mata karta damu zuwa anjima zataga kiransa akan hakan. Amma ta kasance cikin shiri.. cikin gamsuwa tai masa sallama ta wuce tana wani makirin murmushin nasara. Tana fita daga nan gida ta wuce ranta fes. Dan kaso arba'in cikin ɗari na damuwarta ya kwaranye. Koda ta iso gidan wanka ta farayi, dan zuwa yanzu ta samu ƙwarin gwiwar yin hakan. A'i ta saka ta kawo mata abinci, ta ɗan ci tasha magungunanta sannan ta nemo Rubayya a waya. Ta sake tabbatar mata kada ta bari aikinta ya wuce gobe. Dan haka tayi ƙoƙarin zuwa ta kwana a gidan yau. Bata jira cewarta ba ta yanke kiran. Tana gama wayar ɗakin Arwa ta shiga domin dubata. A bakinta take jin ai an sallamo Paah a asibiti tun jiya da dare ma kafin su amma yana sashen Awwab suma duk an hanasu ganin sa. Kasa cewa komai Hajiya ƙarama tayi sai idanu data zubama ƴar Tata na tsawon lokaci. Kafin taja numfashi ta fesar tare da miƙewa kawai ta fita........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏 *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_ .......Daga station Maash guesthouse ɗinsa suka wuce. Da ga shi sai Hayatu da Jaga suka shiga ciki. Sun fi zaman mintuna talatin Maash ɗin baice komai ba yana dai zaune ƙafafunsa a harɗe ya jingina kansa da kujera idanunsa a lumshe da alama ya tafi dogon nazari ne. Jaga zaiyi magana dan ya matsu Maash ɗin yace wani abu Hayatu yay masa nunin yay shiru cikin alamar yin zipping lips nashi. Ajiyar zuciya Jaga ya saki da rufe bakin nasa ruff ya koma ya zauna yanda yake. Maash ya jima a haka har akai kiran sallar azhar sannan ya buɗe idanunsa. Miƙewa yay ya nufi bedroom yana ce musu suma suje suyi alwala. Hakan kuwa sukayi, bayan sunyo duk suka wuce massalaci. Koda suka dawo daga massalacin ma sai da yay waya da matarsa babu ko kunya a gabansu kuma. Shi dai Hayatu murmushi kawai yake. Yayinda Jaga keta wani sinne kai shi ga ɗan duniya (😂😝). Wayar Maash ya ajiye fuskarsa da alamun murmushi, yana kallonsu yaga yanayinsu sai ya gimtse cike da basarwa ya gyara zama da faɗin, “Muktar!”. Ɗan sosa kai Jaga yayi dan in ba Maash ɗin dake kiran ainahin sunansa yanzu ba mantawa ma yake da sunan sa wani Muktar can. Cike da girmamawa ya ce, “Na'am babban yaya”. “Ina ganin lokacin da zaka fara naka aikin yayi”. Wani irin miƙewa Jaga yay ya taka rawa sai kuma ya ware baki zaiyi ihu. Da sauri Hayatu yay gyaran murya. Baki jagan ya dafe da hannu biyu shima da sauri yana waro idanunsa waje. Sai kuma ya koma ya zauna kansa a ƙasa ya ce, “Afuwan babban yaya. Kasan hankalin bai gama zama ba sai kun haɗa da addu'a”. Komai Maash baice masa ba sai ma maida hankalinsa da yay akan tab dake hannunsa. Sai Hayatu ne ya ƙumshe baki yana ƴar dariya ciki-ciki. Shima ɗagowar Maash ya sashi saurin haɗiyewa ya daidaita yanayinsa. “Wa zaka fara kaima ziyara?”. Cike da zumuɗi Jaga ya ce, “Commondo”. Murmushi ya nema suɓuce ma Maash amma sai ya gimtse yana mai ɗan taɓe baki cike da basarwa ya ce, “Okay good and fine. Kanada damar yin hakan a yau. Dan Iyayen gidan nasa na shirin ganawa da shi a daren yau suma. Kana da damar basu assignment lokaci ɗaya.” Wani irin daɗi ne ya ratsa zuciyar Jaga. Nan take ya shiga sambatun godiya kamar wanda aka yima wata ƙyauta. Ga shi dai a zahiri da shiga kamar ba shi ba ya shiryu. Dan bayan an gama jiyyarsa daga suƙar wuƙa Maash da kansa ya kaisa Rihab akan matsalar shaye-shayensa. Ya zauna tsahon watanni har ALLAH yasa aka dace batun shaye-shaye ya zama tarihi. Shine ya sake ɗaukarsa zuwa ƙasar Canada aka sakashi wata makaranta domin fara sanin minene ma amfanin rayuwa. Yayi wata biyu acan aka sake maidashi ƙasar Saudiyya a yanzu haka yana ɗaukar karatun addini dana zamani. Wannan zuwan nashi Nigeria ma anyi amfani da hutun makaranta da suka samune. Yanzu kam a rayuwarsa ji yake babu ya Maash. Shine uwa shine uba. Komai ya sakashi zai iyayi barema akan waɗan nan mutanen da shi kansa burinsa ɗaukar fansa a kansu musamman ma Commondo da ya zama sanadin ta'azzarar lalacewar rayuwarsa. Sannan ya shirya kashesa a gaɓar da yake ganin zai kuɓuce masa duk da wahalhalun bashi kariya daya kasance yana yi a tsahon shekaru. A duk ta yanda zai ziyarci cell da taimakon Isma'il Maash ya tsara masa. Da ga haka suka ɗan ƙara tattaunawa sannan suka fito. Wani wajen suka sake zuwa shi da Hayatun, shi kuma Jaga ya tafi masaukinsa. Daga nan gida suka wuce, inda suka tarar su Fahad baje a falo anata tsara yanda shagalin bikin sunan gobe in sha ALLAHU zai kasance. Dan zasuyi walima kawai anan cikin Mansion ɗin. Duk sannu da zuwa sukai musu. Hayatu ne kawai mai amsawa. Mai gayya da aiki kam hannu ya ɗaga musu kawai idonsa akan Samraah dake goye da baby a baya tana cin abu a bowl da bai san ko minene ba. Itama dai ɗan kallonsa tayi, sai kuma a hankali ta sauke idanunta muryarta can ƙasa ta ce, “Sannu da zuwa”. Kai kawai ya jinjina mata tare da janye idanunsa a kanta a wani kalar slowly. Sai kuma ya nufi ɗakin Ummie cikin takun nan nasa..... 🌿✨🌿✨🌿 Tun Commondo da Jannifer na saka ran zuwan iyayen gidansu har al'amarin ya fara basu mamaki. Musamman ma Commondo. Dan yayi tsammanin in har ya kwana Baba prof bazai barsa ya yini ba. Amma sai gashi har ana shirin fuskantar wani daren babu Baba prof babu Lawisa. Koda yake yasan ita bazata zo ba. Saboda gaba ɗaya ya haɗa lissafinsa akan shirinta na turo masa Jannifer. Tun kuma daren jiya ya gama kitsama kansa yanda zai wargazata. Har shine zata shirya ma tarko. Ashe shirin nata ba'a kan yallaɓai kawai yake ba har da shi. Lallai zata san ta taɓo gidan rina wlhy. Dan ko bai fita a wajen nan ba akan lokaci yayi alƙawarin sai ya tarwatsa rayuwar Lawisa tazo ta samesa anan kusa... A ɓangaren Jannifer ma dai hakanne. Dan zuciyarta ta fara bata Hajiya ƙarama na shirya wani abu ne tayi amfani da ita. Idan kuma ba haka ba tsautsayine ya faɗa mata. Amma ya kamata ace Hajiya ƙaramar tazo dan fitar da ita. Sai kuma gashi shiru wai malam yaci shirwa gashi oganta bai san tama amshi wannan aikin ba. To wlhy ta ɗauki alƙawarin in har Hajiya ƙarama batayi wani abu daga nan zuwa gobe ba har wani daga cikin sirrinta ya fito lallai itama sai ta kaita ƙasa dan sai dai suyi mutuwar kasko wlhy..... 💥💥💥💥 Muna zaune a inda ya barmu sai gashi ya fito. Narasa miyyasa yanzu idan ya shiga ɗakin Ummien bai wani jimawa. Kuma haka zai fito fuska ciɗin-ciɗin. Ina ji a raina kamar hakan nada nasaba da Paah dake a ɗakin yanzu. Ko saboda mi babu jituwa tsakaninsu da mahaifin nasu oho? Dan in batun sihiri ne zuwa yanzu ai Alhamdullah. Amma in sha ALLAHU shima Paah ɗin zanyi ƙoƙarin fara shayar da shi ruwan addu'ar da muke sha tunda ALLAH ya dawo da zamansa nan ɗin. Ganin bai kalla kowa a cikinmu ba ya haye sama nima sai na miƙe riƙe da bowl ɗin madara da sugern dana haɗa waje ɗaya nake sha. Dama Ya Hayat ya amshi Baby. Ruwa na ɗauka nasa a tray sannan na nufi ɗakin nasa. Tsaye ba samesa da ga shi sai dogon wandon jeans ɗin jikinsa ya cire rigar har singlet ɗin ciki. Wandon ma ya kwance belt ɗin amma bai zaresa ba. Wayata ce a hannunsa yana dannawa, da mamaki na ɗan kallesa na ɗauke kaina. Dan wannan jikin nasa a bubbuɗe sam bana son ganinsa sai inji duk ina ƙara tsorata da shi. A hankali na ajiye tray ɗin ruwan ina faɗin, “Sannu da dawowa.” Wayar ya ajiye tare da ɗan kallona ni da tray ɗin. Ban damu da kallon da yake min ɗin ba na kai zaune ina ɗaukar bowl ɗin madarana da shuga na cigaba da sha. Shima zaman yayi yana mai ɗaukar goran ruwa dana ajiye na addu'oi ya ɓalle murfin ya kai bakinsa. Sai da ya shanye tass ya ajiye goran sannan na kauda kaina a kansa. Yunƙurin miƙewa nake na wuce bathroom haɗa masa ruwan wanka a bazata matuƙar bazata naji saukar muryarsa yana furta, “Wacece ita?”. Sosai naji ƙirjina ya motsa. Amma Abinka da ƴar jarida sai na dake na kallesa cikin nuna mamaki da rashin fahimta na furta, “Wake nan?”. Shiru bai da alamar sake tanka min, sai kuma ya ɗago ya zuba min idanun nan nasa masu firgitarwa. Babu wasa a tattare da shi ya ce, “Samrh! Who is she?”. Baki na murguɗa kaɗan, sai kuma na marairaice fuska da faɗin, “My hot ban ga gane wa kake magana ba Please. Naga dai tunda ka shigo iya mu kaɗai ne ka samu zaune”. “Hummm!”. Yace kawai yana miƙewa. Murmushi na saki a karo na farko, sai kuma na matso inda yake nasha gabansa ganin niyyar barin wajen yake. Kallona ya tsaya yi kamar yanda nake kallonsa nima cike da shauƙi. Sai kuma na matsa a hankali na shige jikinsa na rungumesa. Ajiyar zuciya muka sauke a tare, na sake ƙanƙamesa da faɗin, “Yarinyar jiya kake magana?”. “Uhmm!”. Ya faɗa acan ƙasan maƙoshi. “Labarin mai tsada ne. Sai idan nima zaka gaya min wanda nake son ji na maka alƙawarin faɗa maka. Dan tabbas abinda ya shafi yarinyar a garemu mai muhimmanci ne”. Shiru kamar bazai ce komai ba. Har ma na fidda ran ji sai naji saukar hannayensa saman bayana ya sake rungumoni da ƙyau. A cikin wani kalar salon rikita ni ya fara shinshinar wuyana. Ji nai ina daburcewa dan haka na mintsinesa ta re da ƙoƙarin janye jikina na ce, “Wayyo ni My Lion please”. “Anƙi please ɗin faɗa min”. “Anƙi wayon nima sai ka fara faɗa min”. Numfashi ya ɗan furzar tare da ɗagowa ya sake rungume ni. “Naji”. Ya faɗa a takaice kamar abin dole. Duk da naji haushi sai na daure. Musamman ma ganin la'asar ta gabato. Kamar yasan mike a raina shima sai ya kalla agogon. Kallona yay idanunsa a ƙanƙance. Cikin motsa lips ɗinsa ya ce, “Salla first”.. Nima sai na ce “Wanka fa?”. “Na gaji ki mun”. Kafaɗa na maƙe masa alamar a'a. Kansa ya nuna alamar wai shi ɗin? Na ɗaga masa gira ina murmushi. Hannu ya kai zai damƙoni na goce da sauri ina dariya. Sai ya ɗan ciza lips irin zaki gane idan na kamakin nan ya wuce bathroom ɗin.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_ ......Bayan idar da sallar la'asar ɗin ya jima bai shigo ba. Harma nai zaton ya gudu ne sai gashi ina falon saman zaune ina waya da Gwaggo Gudidi da miss call ɗinta dana sake gani ya sakani kiranta naji ko wani abu ne ya faru. Bedroom ɗinsa ya wuce babu jimawa sai gashi ya fito. Zama yay a kusa da ni tare da zame jikinsa ya kwanta kansa a saman cinyata. Ɗayan hannuna ya kama ya riƙe kan nasa ya ɗaura a saman shafaffen cikinsa ya harɗesa cikin nashi da yay folding a ƙirji. Jinai gaba ɗaya wayar ma na kasa cewa komai. Amma dai na dake har muka kammala. Sallama nake ƙoƙarin mata ya buɗe idanunsa da mun nunin na bashi wayar. Sai da na waro ido sosai amma sai bai sauraran ba ya kai wayar kan kunnensa. A mamaki na sallama yay cike da girmamawa da gurɓatacciyar hausarsa da sai anyi da gaske ake gane wasu kalmomin. Shiyaysa ma ni nafi ganewa muyi magana da turanci a koda yaushe. Shima yama fi yin hakan. Amma a raina na ɗauri ɗammarar koya masa Hausa in sha ALLAHU. Nasan ba gane maganarsa Gwaggo keyi ba dan haka hirar bai tsaho ba ya bani wayar. Sallama nai mata batare dana saurari tsogumin da take akan rashin gane abinda yake fada ba na yanke kiran. Wayar na ajiye da kai hannun nawa cikin sumarsa daya warware na fara tausa masa kan nasa da yin wasa da gashin. Idanunsa ya lumshe da ƙanƙame hannuna dake a cikin nasa har yanzu. Cike da sanyi na ce, “My Hot!”. A can ƙasan maƙoshi ya ce, “Umyim”. Ban damuba na ce, “Abinci fa?”. Kansa ya girgiza min alamar bazai ci ba. Cike da damuwa na ce, “Miyyasa?”. Idanunsa ya buɗe ya kafeni da su. Sai kuma ya lumshe da sake buɗewa cikin motsa lips ɗin sa ya furta, “later”. Kaina kawai na jinjina masa da gyara zamana. Dan nasan tunda yace bazaicin ba ba cin zaiyi ba fa ko miza'ayi. Sakin batun abinci nayi na kama mai muhimmanci. A ɗarare na ce, “Na maka laifi fa. Amma dan ALLAH kayi haƙuri ka yafe min tun kan na faɗa”. Shiru kamar bazai ce komai ba sai zuwa can ya ɗan buɗe idanunsa da suka sirka yanayi, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya da miƙa hannu ya ɗauka laptop ɗin sa daya ajiye saman Centre table. Filo ya ɗauka ya ɗaurata a saman cikinsa duk yana daga kwancen, sai da ya fara ƙoƙarin kunnata ya ce, “Ai nasa zaki ɗauka ki sake dubawa shiyyasa na ajiye miki inda zaki gani”. Da mamaki na ce, “Kasan akan mi kuwa nake magana? Flash ɗin ranar fa?”. Murmushi kawai ya saki da ɗan jinjina min kansa batare da yace komai ba. Gaba ɗaya sai ma na gagara cewa komai dan mamakinsa. Harga ALLAH mutumin nan ya fara bani tsoro, sai kuma can da nai tunanin camara ya saka a ɗakin nashi yasa na ɗan ji nutsuwa. Abinda ya kunna a laptop ɗin ne ya ɗauka hankalina. Sai na nutsu ina kallo. Gaba ɗaya abinda ya faru jiya ne lokacin da suke shigowa gidan da Ummie. Kasa daurewa nayi sai da nayi dariya, tare da jan hancinsa ina faɗin, “Oh My Lion ashe kaima bakinka ya iya magana haka. ALLAH ya shirya Yaya Fahad wlhy, harda wani faɗin a dafasu a tukunya a baku kunci kuna kora ruwan companyn Maashh.” Murmushi kawai yayi baice komai ba. Nima sai na cigaba da faɗin, “Amma Ya Awwab ka kalla yanayin Baba kuwa? Da Hajiya ƙarama? Sannan video ɗin waccan ranar ka kallesa?”. Kansa ya jinjina min. Sai kuma a hankali ya furta, “Mi kika fahimta ke?”. Ɗan jimmm nayi alamar tunani, dan bazan iya katoɓarar fitowa fili na sanar masa ainahin abinda ke'a raina ba gaskiya. Kakansa ne fa, tab ɗin ba ruwana. “talk”. Ya faɗa yana matsa hannuna. Murmushi na ɗan masa da faɗin, “Uhmm inaga mubi a hankali kawai watarana zaka fahimta. Dan zata iya yiwuwa abinda ni nake tunani daban wanda yake gaskiya daban. Amma dan ALLAH ka amsa min abin nan ɗaya kuma yana cimun zuciya. Shin mutumin nan da naga ka zare wuƙa a jikinsa lokacin bikin buɗe Companyn ka kai ne ka kashe shi? Ko miya faru?”. Ɗan murmushi ya saki a karo na farko, tare da kai hannuna dake cikin nasa kan mitsitsin bakinsa ya sumbata. “Yau kuma aikin jaridar ne ya tashi?”. Cike da shagwaɓa na ce, “Oh ALLAH daga tambaya”. “Nima ai bance bazan amsa ba”. Ya faɗa yana ɗago ido ya kallan. Sai kuma ya gyara kwanciya da maida su ya lumshe. Numfashi ya ɗan furzar da fara magana a hankali. “Mama ta baki tarihin gidan nan dan haka zan faɗa miki daga dalilin buɗe Company.” Kaina na jinjina masa cike da zumuɗi. Cigaba yay da faɗin, “A tsakanin da Ummie ta samu lafiya aka ƙirƙiri samar da companyn Kano. Kusan ma itace ta zo da shawarar hakan dan mace ce mai matuƙar experience akan Bussines. Sai dai koda najema Baba da batun sam bai bada goyon baya ba shi. Sai ma illolin yin hakan daya nuna min game da ƴan arewa. Abin ya tsayan a rai na sake samun Ummie da batun amma sai ta balbaleni da faɗa tare da cewar umarni ai ita ta bani ba shawara ba. Dan haka nabi Umarnin aka fara samar da Company. Ban sani ba ko hakan ne ya ɓatawa baba rai sai ya fita daga batun gaba ɗaya. Ana gab da gamawa jikin Ummie ya ɗan fara motsawa. Hankalinmu ya tashi matuƙa muka shiga neman mai maganin nan na Togo amma babu shi babu alamarsa. Tun muna ɗaukar komai zai dai-daita har abu ta ɓaci sosai, abubuwa suka ƙara rikicewa. Haka dai cikin dauriya na ƙarasa gina wannan gidan na muka tare. Sannan na shirya batun buɗe Companyn Kano. Tun bayan sakowa da ga batun auren Paah da Hajiya ƙarama yanda take nuna damuwarta akan Ummie da ni yasa nake ɗan sakewa da ita. Har itama na koma kiranta da Ummy, ko bana gida takan kirani ko na kirata a raina ina jin bayan Mama kamar itama uwa ce. Dan hatta cin abinci takan nuna damuwarta da naci ko ban ci ba a duk sanda ta kirani. Hakama idan ina gida ko asibiti ta dawo a gajiye takan tsaya ta samar min abinda zanci hakan yasa na ƙara bata muhimmanci fiye ma da Paah da nake matuƙar jin zafi. Sai dai me a gaɓar bikin buɗe Company duk sai suka ƙi shirin halarta har Baba dan barin ma ƙasar yay shi. Raina ya sosu nai fushi na fita batunsu da ga ni sai su Hayatu da yarana muka tafi. Kwatsam an fara gudanar da taro lokacin da kike barin wajen akai kiran hayatu a waya. Ta gefen ido nake kallon yanda yake amsa wayar yan zufa, kafin ya sauke a daburce ya matso inda nake. Sai dai yana ta ƙoƙarin ganin ya saita kansa dan kar a fahimta. A kunne ya gwargwaɗa min kiran da Jaga yay masa da abinda ya faɗa masa, dan haka nai excusing kaina na shiga ciki Hayat ya biyo ni. Da taimakon wayar hayatu muka gano ɗakin da Jaga yake. Da farko na ɗauka set up ne akayi, sai da Jaga ya shiga sanar mana wanda ya sokesa da aikin da ya kawosa jikina da abinda aka aikosa yi a yau amma ya canja shawara shine aka kawosa nan ɗakin dan a kasheshi a kuma maida abun kaina. Dan haka cigaba da rayuwarsa nada muhimmanci garemu dan yana da muhimman abubuwa da zai faɗa mana da zasu amfane mu. Wannan daliline yasa nai ƙoƙarin cetonsa duk da Hayatu na nuna min na barsa ƙarya yake yi. Amma ban saurarensa ba. Ina ƙoƙarin zare wuƙar da aka saka masa ke kuma kika iso batare da mun sani ba. Ashe har muka fita da shi kina biye damu. Duk da dai a lokacin da nake fitowa a ɗakin ƙamshin turarenki yasa naso na farga da ke, amma hankalina ba'a wajen yake ba dan haka na fice kawai. Ansha matuƙar wahala kafin samun rayuwar yaron, sai dai da yake ALLAH ya ƙaddara akwai sauran kwananasa gaba yasa ya warke kamar komai bai faru ba.. Ambatar sunan Grandpa ɗina a wannan ranar da shi Muktar Jaga yayi da ita Lawisa yasa na tabbatar da gaskiyarsa dalilin zuwan sa Kano a bazata har hirar da yay da ke. Tun daga lokacin nai doubling question mark ɗin dana sakama kowa a kansu. Nasa ya zama biyu. Na kuma janyema Lawisa sosai . Wannan video kuma ya tabbatar min da inahin fuskar ita Lawusar dai ce ba wata ba..” A hankali hawayen da naketa riƙewa suka silalo min. Muryata na rawa na ce, “Hajiya ƙarama?”. Kansa ya jinjina min alamar eh kawai. Wasu hawayen ne suka sake ɓulɓulo min. Cikin sake ƙanƙamesa na ce, “Yaya Awwab kayi haƙuri, amma wlhy zuciyata na bani sune suka kashe Abie da Babana......” Da wani irin mugun sauri ya ɗago idanunsa da launinsu ya canja gaba ɗaya ya kalleni. Kaina na jinjina masa nima cikin tabbatarwa na ce, “Tabbas Yaya akwai ƙamshin gaskiya a magana ta. Dan na bibiyi videon ɗin nan da ƙyar tare da tankaɗesa da rairaiye sa. Kuma alamu sun nuna Ummie tasan wani abu shiyyasa ya durƙusar da rayuwarta zuwa wannan yanayin”. Ai sosai ya tashi zaune gashin jikinsa na wani mimmiƙewa. Muryarsa har rawa take wajen faɗin, “Samrh miyyasa kikayi wannan tunanin?”. “Yaya hujjoji da yawa. Dan kasan jami'in tsaro, da lauyoyi, da likitoci, da ƴan jarida al'amarinsu na kamanceceniya da juna. Saboda komai nasu yana tafiya ne a bigiren bincike. Shiyyasa zakaga a mafi yawan lokuta indai masu wannan ayyukan sun san abinda suke basu da wahalar fuskantar case irin wannan da saurin kama bakin zaren sa.” Hannu ya kai saman yay wani kalar shafosa tamkar mai sharce ruwa ya yarfar. Bawai yau ya fara irin wannan tunanin ba shima. Sai dai a kaf bincikensa bai taɓa samun wanda ya ƙarfafa wannan hasashen nashi kamar ita ba a yau. Dan yanda ta fassara abin da confidence abin a duba ne.. Yunƙurawa yay zai tashi na riƙosa da sauri. “Yaya ina zaka je?”......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_ .......“Ina son naga Ummie”. Ya faɗa da alamar ran ƴan maza ya ɓaci. Kaina na girgiza masa da sake damƙe hannun nasa na ce, “No Ya Awwab ba yanzu ba. Ummie da bata bukatar kowane irin matsi daga garemu akan son sanin gaskiyar al'amarin kamar yanda doctor ya faɗa al'amarin ta daki-daki yake buƙata. Dole mu cigaba da haƙurin binta mataki-mataki dan akwai abinda itama take shiryawa, kar kuma ka manta ya sanar mana ba komai ya dawo kanta yanda ya kamata ba a yanzu. Sannan tanama naka takun tankaɗa da rairaya ne shiyyasa taƙi fitowa fili ta gaya maka koda abinda ya rage a zuciyarta ne. Dan haka mizai hana muyi wani abu domin gabato da komai a gaggauce”. Idanu kawai ya zuba min batare daya amsa ba. Ban damu ba na cigaba da faɗin, “Ban san tsare-tsaren ka ba. Amma a nawa tunanin ya kamata kayi wani abu saboda dalilai biyu. Na farko matsayin Baba prof mahaifin Paah. Bafa abune ƙarami ba fiddo da ainahinsa ta ɓangarenka kai tsaye ko ɓangaren Ummie. Hakan zai kawo rabuwar kan family ɗin nan, dan koba komai sunan mahaifi yake amsawa a garesu. A kai kanka ma bar ganin ba komai bane wlhy sai ka jigata matuƙar jigata dan jini ya wuce wasa. Sannan babu alfanu duniya ta raja'a akan rikicinka da Family ɗinka. Hanya zaka bama abokan gaba na bayan fage suci tuwo a kanka tako wane fanni. Kasan dai masu iya magana sunce, DAUƊAR GORA CIKI KA SHATA. Dan haka kamar yanda ka fara yaƙin ta hanyar sunƙuru, tofa mafitar ɗayace a ƙarasashi ta hanyar TURNUƘU FAƊAN IBILISAI. yaro bai gani ba balle ya raba. Ma'ana mu zuba kamar yanda suka ɗauki shekaru suma suna zubawa. A maimakon baƙin fenti ya shafe ka, ruwan sama ne zai wankeka tatas ya kuma wanke Ummie su da bakinsu su faɗi ainahin abinda suka shuka, idan ma tonama kan nasu asiri sukai wa duniya sune suka zaɓi hakan. Ya kaga wasan zai kasance”. Na ƙare maganar da kashe masa ido ɗaya. A mamakina sai naga kawai ya saki murmushi da cije lips ɗinsa. Hannunsa ya dunƙule tare da miƙo min🤜🤛 Nima kawai sai nayi yanda yay ɗin muka buga. Da sauri na janye nawa ina yarfarwa da faɗin, “Shiiii azaba wanan hannu kamar rodi”. Ƙaramin murmushi yayi da ɗan ɗallamin lips kaɗan da yatsarsa. Sai kuma kawai ya jawoni jikinsa ya rungume tsammm. Ajiyar zuciya muka dinga saukewa a tare. Na ɗan motsa zanyi magana a hankali ya ce, “Shiiii bana son surutu”. Sai kuma ya ɗaukeni cak yay bedroom da ni. (Ba sai kunji miya faru ba kuma ehe😉 dan naga fans ɗin bily kun cika sa ido😌🥱😝🏃) Lallai yau Samraah taci tuwo a kammu bari mu ware🏃🏃🏃🏃, danginta kuma har daku shinnnnnn😂😝?. 💢🌿💢🌿💢 Ƙarfe goma na dare Baba prof da Hajiya ƙarama suka kama hanyar station. Dan dama tana asibiti tun bayan sallar magrib. Ta can ma Baba prof ɗin ya ɗauketa kasancewar da kansa yay driving abinda ya jima baiyi ba. Amsar tuƙin hajiya ƙarama tayi. Kasancewar al'amarin hanya ce daga babban jami'in da yafi Uncle Abdullahi faɗa aji yasa tun a gate aka tarbe su. Baba prof ya yankema zuciyarsa sai ya fara jin tabakin commondo da tabbatar da gaskiyar Hajiya ƙarama sannan ya fitar da shi, dan ba fitar da shi ɗin ne mai wahala ba, amma maganganun Hajiya ƙarama suka canja wancan tunanin nasa. Yana son tabbatarwa, idan gaskiya ta faɗa shi da kansa zai saka a ɓatar da Commondo tun a daren yau. Idan kuma ƙarya take zai saka a fiddashi batare da saninta ba. Daga ƙarshe hukuncin da yay niyyar ma Commondo zai sa Commondo ɗin ya maidashi a kanta. Kamar yanda yake nasa tsarin a zuciya itama yana yin nata ne. Dan tayi waya da Dr Khunal yanzu haka zuwa gobe abinta data biya maƙudan kuɗi ita da Baba prof ɗin domin Maash zai iso a daren yau. Za kuma tayi aiki da shi akan Maash kamar yanda suka tsara tun farko, da shi Baba prof ɗin da Mu'azz. Ummie kuwa nata tanadin na musamman ne. Shiko Commondo ta riga ta gama bada kwangilarsa. Jannifer ma Baba prof zai ƙarasa mata ita shiyyasa ta azashi a keken ɓera. Tunaninta ya katse lokacin da aka shigo da Commondo da Jannifer hannayensu duk da Handcuffs. Ga raunuka a jikinsu dake tabbatar da Dukansu akai babu jinawar nan. Dan bayan la'asar Uncle Abdullahi ya bada umarnin fara tuhumarsu amma su duka sunƙi cewa komai saboda damar da duk suka ƙudiri aniyar bama iyayen gidan nasu na yau kawai. Idan basu zo ba zuwa gobe zasu fara buɗe aiki. Shiyyasa suka jure da dukan bawai dan basa jin zafi bane ba ko ciwo... Cikin tsawa jami'in daya kawosu ya nuna musu ƙasa matsayin wajen zama. Sannan ya koma daga ƙofar ɗaki ya tsaya dan yasan basu da wata hanyar guduwa tako ina office ɗin zagaye yake da jami'an tsaro irinsa. Daga Hajiya ƙarama har baba prof kallon Commondo da Madam Jannifer sukeyi kamar yanda suma suke kallonsu kallo irin na ƙurilla... Kusan mintuna biyu kafin Baba prof ya janye nasa idon cikin gyara zama da kafe Commondo da ido ya ce, “Commondo ya akai aka faɗi a ragaya?”. Murmushi Commondo yay da jinjina kansa. Sai da ya kalla gefen Hajiya ƙarama ya furta, “A ɓaɗinance talalace! A zahirance kuma ɗaurin goro ne!”. “Akasin lissafi kenan fa”. Baba prof ya faɗa cike da waro idanu. “Na dukkan lissafi ne ma aka samu a wannan gaɓar oga. Dan shi macijin cikin ciyawa idan har yay kala da ciyawar sai yayi illa batare da ma'abocin taka ƙafa ya farga ba. Rafi da kogi zasu iya haɗa tafiyar wucewar ruwan cikinsu a hanya ɗaya. Amma shi kududdufi da gulbi koda suna maƙwaftaka akai rami a tsakaninsu ba lallai ruwan ɗaya ya ɓulla a cikin ɗaya ba. Dan ramin su baya kogo kamar na rijiya”. Cikin ɓacin rai Hajiya ƙarama ta tare numfashin Baba prof dake ƙoƙarin yin magana. “Amma kun san magana cikin duhu haramunne a wannan tafiyar tamu. Anan duk ɗaya muke. Dan itama Jannifer abokiyar cin mushe ce. Banga dalilin ɗaure zance ba bayan muna neman hanyar gudu tare mu tsira tare ne a wannan gaɓar. Idan kuma har kukace wasan na nuna zalama ne, to karfa ku manta ku duk biyun nan linzamin dokin Lawisa ne. Musamman ma kai ɗin nan”. Ta ƙare maganar da nuna Commondo. Wani shegen murmushi Commondo ɗin ya saki. Cikin ɗage gira ya furta, “Lawisa! Ke ƙaramar giwace, ragon layya kawai yay dogon miƙi zai iya yaddaki a dokar jeji. Ashe baki shirya wasan ba da ƙyau amma kikayi tunanin tararsa. Shi zuciyarki bata baki tabbacin ko Giwa ta faɗi tafi ƙarfin wawason ƴaƴan damisa ba. Shike nan, tunda kince muje a buɗe, muje ɗin, kin san dai ni bishiyar dabino ne wlhy bani ƴaƴan banza. Dan ko a ɗanyena nake rububin cina akeyi”. “Kamar yanda kasan nafi ƙarfin damisar takarda. Sannan ni uwar bakirikice ba yarinya ba. Duk wanda ya sanni a cikinta ya ganni ba raino na akai ba. Miyyasa ka shirya cin amanata?”. “Saboda kema naki shirin kenan?”. “Amma kasan komi nayi akwai dalilinsa?”. “Kamar yanda kika san nima bana komai sai da dalili. Miyyasa na ɗaukeki Hadari zaki maidani hazo?”. “Ohooooooh!! da ƙyau!”. Baba prof ya faɗa yana wani kwashewa da dariya da tafa hannaye. Gaba ɗayansu juyawa sukai suka kallesa. Duk kuma sai suka sha jinin jikinsu. Cikin daina tafin da musu nuni da hannu ya ce, “Ku cigaba mana, miyyasa zaku bari kuma?”. “No oga relax. Kada ka ruɗar da kanka kadai san makircin wannan wawuyar”. Cewar Commondo da sauri. Da saurin itama Hajiya ƙarama ta cafe da faɗin, “Sai dai wawaye. Kai ni fa a wannan gaɓar banƙi a mutu ba har liman wlhy. Dan na gaji da tafiya da maciya amana waɗanda kansu kawai suka sani. Na kuma gaji da barin jakai ina dukan tanki.” “Oh really?! To ai Lawisa ke ce babbar mai cin amana a cikinmu. Dan kece kika nunama kowa tashi ta fisheshi. Oga shine ya jawoki a wannan tafiyar ya kuma maidaki abinda kike a yau amma har kike tunanin watsar da shi...” “Hahahaha!!! Commondo! Commondo!! Commondo!!. Lallai kai jaki ne na yarda. Wai shin kana yin duk wannan ne saboda tunanin wannan abun zai iya fiddaka a wannan wajen? To lallai kayi kuskure dan anzo gaɓar jifar gaffiyar ɓaidu. Dan anzo gaɓar da shi ɗin ma takansa yake bazai iya maka komai ba. Idan ma lissafin barin nan ɗin kake to ka bari, dan zama daram mai naƙuda ta samu katifa hahahaha!!!”. Wani irin kallo Commondo yake ma Baba prof. Cikin zafin rai ya ce, “Oga!!”. “Don't call me Oga again!!”. Baba prof ya faɗa a matuƙar zafafe. Wani shegen murmushi Commondo ɗin ya saki da jinjina kansa. Tabbas badan handcuffs ɗin hannunsa ba babu abinda zai hanashi raunata mutanen nan guda biyu, har shi zasu haɗema kai. Amma babu komai zai musu abinda sai sun gwammace inama raunin yaji musu. Cikin tsantsan tsana ya kallesu ɗaya bayan ɗaya, “Lallai ku sani ku dukanku zaku tafka babban kuskuren da sai kun dawwama kuna nadamarsa a rayuwarku. Dan ni Commondo tauraro ne mai wutsiya. Sannan cinnaka nake ban san na gida ba. A tafiyata kuwa bana GUDU DA WAIWAYE. Idan har kaga nayi, abu mai matuƙar muhimmanci na dawo ɗauka. Kada ku taɓa tunanin ƙarfin iko ko faɗa ajin da kuke taƙama da shi zai tserar da ku daga tarkon Commondo. Dan *_TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE_*. Kusa a ranku yanzu ne wasan zai faraaaaaa!!!!”. Daga Hajiya ƙarama har Baba prof sai da suka ja baya saboda yanda Commondo ya ƙarasa magana ta ƙarshe a kausashe kuma da tsawa. Yayinda Jannifer ta kece da dariya. Sai da tayi mai isarta duk suna kallonta sannan ta dubi Hajiya ƙaramar.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ......“Hajjaju wannan duk damuwarku ce dan ku kuka san kanku. Ni a wane matsaya nake? Dan bana buƙatar sake kwana a wannan wajen da ga ni har yara na. Kin san fa ni ba irin Commondo bace, da an cigaba da takura min bakina buɗewa yake caaaaaa!!!!! Da magana”. Fushin Commondo yasa Hajiya ƙarama watsama Jannifer harara. A harzuƙe ta furta, “In bakin naki bai buɗeba baki cika ƴar halak ba Jannifer. Shashasha kawai ana batun masu hankali kina sako ruɓaɓɓen bakinki. K! har kina da bakin ma jefama mutane maganar banza batare da an sakoki ciki ba”. “Oh yeer! Hajiya Lawisa amma dai kin san ni tururuwace bana jidon banza ko?”. “Duk jidon naki kiyi dan iyakarki tsintar gero da dawa amma ƙashi ko nama ƙaryarki”. “Haka kika ce?”. “Nama ce fiye da haka. Dan ku dukanku anan zan iya da ku”. “Ai ba abin mamaki bane dan MAGE taci amanar KARE!!”. Wata murya a bazata ta daki dodon kunnensu. Gaba ɗayansu suka juya ga ƙofa da basu san yaushe aka buɗeta ba har mai maganar ya shigo musu babu notis. Kusan a tare Hajiya ƙarama da Baba prof sukai baya. Yayinda Commondo yay wata irin zabura da ga zaune yana ƙwalalo idanu waje. Jannifer da bata san ko waye ba kuwa ta ce, “Wannan gaskiya ne ɗan uwa”. Murmushi Jaga ya sakar mata tare da kashe ido ɗaya yay mata alamar jinjina. Sai kuma ya wani ɗan jujjuya kai yana mai gyara tsaiwa cike da gadara ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Kafin ya tsaida idanun kan Commondo. Rawa jikin Commondo ya farayi sosai. Da ƙyar ya iya furta kalmar, “Jaga! Fatalwa?”. “Yes I'm. Amma ni ba fatalwa bane JAGA!!!! ne”. Ya ƙare maganar da wani irin kashe ido ɗaya cike da salon iskanci. Lokaci ɗaya Hajiya ƙarama da Commondo suka saki ihu. Yayinda zuciyar Baba prof kawai ta tsarga lokaci ɗaya cikinsa yay wani irin kalar bada sauti sai gudawa tsuuuuuu!!! Daga tsaye. Dariya Jaga ya kwashe da ita. Sai kuma ya nuna Baba prof da yatsa, ya nuna Commondo, ya nuna Hajiya ƙarama sannan ya kai hannunsa kan wuyansa yay alamar yankawa. Tuni itama Hajiya ƙarama fitsari ya ɓalle mata ƙafafunta suka fara rawa. Cike da mamakin abinda ke faruwa da yanda zakunan dake hanƙoro kusan na mintuna talatin babu mai jin wani duk suka gigice Jannifer ta kalla Jaga cike da rashin damuwa ta ce, “Ɗan uwa halan kai ɗin waye dan ALLAH?!”. “JaGa!!!! Gawa ta ƙi rami kenan. Sun gina naƙi shiga, ɗan Badamasi ke nan ajiyar ALLAH, mutuwarka sai cikar kwanakinka. Namiji ƙi gudu sa maza gudu. Ki basu shawara, yanzu ba lokacin gardama bane ba lokacin GUDUN CETON RAI NE. Domin gab ZAKI na gaskiya yake da fitowa shawagi. Dan haka mun shiga ƙarnin MAI RABON GANIN BAƊI YA GANI. Maƙiyanka fadawanka. A kafta Yaya Maaaaashhhhhhh!!!”. Ya faɗa yana tafa hannunsa sai ko ɗiffff wuta ta ɗauke duhu ya bayyana. Wani irin masifaffen ihu Hajiya ƙarama ta fasa dan a zatonta fa Maash ɗinne ya shigo, itama sai gudawa zuuuu. Yayinda Baba prof ya yanke jiki ya faɗi kawai. Commondo kansa a gigice yake dan shi fa kamar su duk sun ɗauka fatalwa jaga yay musu, sannan ganin Maash anan ɗin tamkar ƙarshen numfashinsu ne. Ita kanta Jannifer da bata fahimci tushen zancen ba jin sunan Maash ya saka ƙirjinta fara karkarwa ta kawai fashe da kuka. Ga duhu office ɗin...... 😂Wai miyyasa mutanen ke tsoron Yayanmu haka🤣. Koda yake shifa mara gaskiya ko a ruwa jiɓi yake🥱 🩸✨🩸✨🩸 Gaba ɗaya ya hanani sake sauka ƙasa. Sai shine yaje massalaci. Bai dawo ba sai da akai isha'i. Da wannan damar nai amfani na sauka na haɗo masa abinci. Ummie na ciki saboda Paah, su Hafizzullah ma da alama suna masallaci tare da shi. Aunty Falaq ma na ɗaki dan haka harna gama abinda zanyi babu kowa a farlon. Ina idar da sallar isha'in na kwanta a wajen dan ɗan sanyi-sanyi nake so. Daga azhar har zuwa gabannin asubahi zaka sameni lafiya Lau kamar banda wata damuwa. Ana ce miki asuba tayi da ƙyar nake yin salla sai zazzaɓi da amaye-amaye har sai rana ta ɗaga kuma. Jin an ɗagani na buɗe idanuna, dan nasan mai mun hakan sai dai shi. Kallonsa nayi tare da ɗan tura baki gaba. Cike da shagwaɓa na ce, “Please My Hot ALLAH can yafi daɗi”. Bai tanka min ba sai da ya sauke ni saman gadon. Yana ranƙwafe a kaina idanunsa cikin nawa yana bina da wani kasalallen kallo da zuwa yanzu na fara fahimtar fassarar halin da yake ciki a duk sanda yake mun shi. Cikin motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta, “Kina son ki haifar min yara da sanyi?”. Kai na girgiza masa a marairaice kamar zanyi kuka na ce, “ALLAH yafi min daɗi ne fa”. Bai ce komai ba ya kwanta ta gefena yana mai rungumeni a jikinsa. A tare muka sauke ajiyar zuciya. Nima sai na sake shige masa da sake ƙanƙame shi. Mun jima a haka kafin ya fara canja salon kwanciyar tamu zuwa wani abu daban. Mamaki ya sani ɗagowa na kallesa. Ɗazun nan fa barowarmu falo ya.... Tunanina ya katse jin saukar mitsitsin lips ɗinsa kan nawa. Yanda ya iya bin hanyoyin mantar da mutum kansa yasa tuni ma na saki ragamar duk da nasan wahala ce dai bazan fasa shanta ba. Dan shi ɗin bana wasan yara bane. Marmarine da ga nesa.... Nako ji a jikina, haka na lafke masa wanka ma sai da taimakonsa. Dan ma yunwar da nake ji ta sa na kasa kwanciya na ce masa abinci zanci. Da kansa ya zubo abincin yazo ya zauna ya dinga bani. Nima sai na amsa ina bashi. Hakan ya ɗan taimaka min na ɗan ci shima yaci. Ina cewa na ƙoshi shima kuwa yace ya ƙoshi. Mamaki yake bani dan ban taɓa gamo da wanda bai damu da zaman cin abinci ba irinsa. Kwance zan kai ya kamani ya zaunar yana girgiza min kai alamar karna kwanta. Cikin shagwaɓa na ɗan tura baki dan kwanciyar nake so. Bai kulani ba sai jinginani da yay da jikinsa kawai ta ɗauki wayarsa yana latsawa. Ajiyar zuciya na sauke kaɗan, idona akan wayar nima nace, “Ya Awwab”. “Uhhyimm”. “Yarinyar nan ya kake ganin zamuyi da ita?”. Shiru kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya ajiye wayar yana furzar da numfashi. “Ki bar komai a hannuna dan zuwa yanzu haka ma tana hannu”. “What! Ya akai hakan?”. Na faɗa ina tashi zaune da ƙyau. Kallona yay shima sai kuma ya ɗan lumshe ido ya sake buɗewa akaina. Akan lips ya furta, “Bana wasa da DAMA”. “Ni shaida ce”. Na faɗa cikin kashe masa ido ɗaya da kai baki a hankali na sumbaci kumatunsa. Murmushi ya saki mai ƙayatarwa ya jawoni jikinsa ya rungume. Kiran wayarsa ne ya katse mu. Ɗauka yay, kasancewar muna a kusa da juna yasa naji duk abinda Hayatun ke faɗa. Yana ajiye wayar ya miƙe nima na miƙe. Kallona yay na ɗaga masa gira da faɗin, “Lokacin da zan taimaki mijina da tawa basirar yayi. Let's go”. “My baby”. Ya faɗa da soft murya yana kallon cikina. Nima ƙasan nayi da muryata ina mai ɗora hannuna saman cikina na furta, “Yana tare da kariyar UBANGIJI”. Baice komai ba yay gaba. Nima sai na juya na fita zuwa nawa ɗakin. Babu jimawa na fito, sai naci karo da shi a ƙofa yana niyyar shigowa. Batare da yace komai ba ya kama hannuna kawai..... 💥💥💥 Sai da taimakon Isma'il Baba prof ya koma gida. Tsabar ɗimuwar da yake ciki yasa baima fahimci wanda ya maida shin ba. Hakama Hajiya ƙarama ita kanta bata san a yanda ta dawo gidan ba. Kawai dai ta tsinta kanta a bakin gate. Batako saurari mai taxi daya kawota ba ta afka ciki sai securitys ɗin ƙofa ne dake binta da kallo suna toshe hancin qarin kashin da take suka biya shi. Da ga Maash har Hayatu da Samraah da TJ dake jan motar da zasu fita da kallo suka bita suma. Nannauyan numfashi na sauke da faɗin, “To ita kuma wannan ƙalau take kuwa? Jibafa jikinta kamar wadda tai kashi, gashi sam bata a hayyacinta”. Hayatu ne cikin ƴar dariya ya karɓe da faɗin, “Babu tantama aikin Jaga ne wannan”. “Jaga kuma?”. Na faɗa ina kallon Maash da yay kamar ma bai san abinda ake yi ba. Yanzun ma bai tanka ba. Sai Hayatun ne dai ya bani amsa da, “Eh, ya kai musu ziyara ne. Kinga ko yanda suke tunanin ya mutu ganinsa a raye ai cakwakiya ce babba. Amma bari na taɓa Isma'il”. Wayar Isma'il ɗin ya kira. Yana ɗagawa da dariya ya fara daga can. Hayatu shima sai ya fara dariya. Da ƙyar dai cikin dariyar Isma'il ɗin ya bama Hayatun labarin duk abinda ya faru batare da yasan a Hansfree wayar take ba. Shi kansa Tj dariyar yake yi. Yayinda ni kuma nai ƙasa da kaina kawai inayin tawa can cikin maƙoshi. Dan yanzun ma mai gayya da aiki bai tanka ba bai kuma kulamu ba. Cikin ƙanƙanin lokaci muka iso gidan da yay matuƙar ƙayatar dani. Dan ya ginu iya ganin mai kallo, sai ma ka iya ɗauka gilashi ne kawai gaba ɗayansa. Ni dai a zuciyata naita santina har muka shiga ciki.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ......Da sauri saurayin da muka samu zaune a falon ya miƙe tsaye cikin nuna girmamawa. Sai budurwar dake ƙasan carpet bakinta a ɗaure da seletep hannunta ma a ɗaure. A kallo ɗaya da nai mata na gane Murjanatu ce. Sai da na ɗan waro idanuna waje ina kallon Maash. Amma sai ya ɗauke nasa cike da basarwa ya cema saurayin da ya kira da Muktar ya kwance mata abin hannunta dana bakinta. Kamar yanda aka bashi umarni yayi, sannan ya koma ya zauna yana mai dakawa Murjanatu data sanya kuka tsawa alamar taima mutane shiru. Shirun kuwa tayi tana hawaye da kallona. Duk sai naji ta bani tausayi. Murya a sanyaye na cema Hayatu su bata ruwa. Babu musu kuwa yaje ya kawo mata. Tako sha sosai tana sauke ajiyar zuciya. Sai da naga ta ɗan samu nutsuwa sannan na tashi na koma kusa da ita. “Murjanatu”. Na kira sunanta a taisashe. Amsawa tayi muryarta na rawa sosai da jikinta. Kafaɗarta na dafa da kulawa na ce, “Ki kwantar da hankalinki. Bamu kawoki nan domin cutarwa ba. Sai domin mu kuɓutar da ke. Kamar yanda kika sani na faɗa miki sunana a waccan ranar. Sannan kin mun sani na tsakanin mai jiyya da ma'aikaciyar asibiti a wancan karon.” “Hakane Aunty”. Ta faɗa muryarta na rawa. Kaina na jinjina da kallon Hayatu na ce, “Yaya Hayat ko zamu samu hoton matar can a wajenku”. Kai tsaye ya ce, “Abu mai sauƙi”. Tab dake gefen ogan nasa ya ɗakko, yay ɗan danne-danne ya miƙo min. Hoton Hajiya ƙarama ne rangaɗaɗau kuwa. Anci ado na fariyya kamar kai mata magana ta amsa. Janye idanuna nayi daga kan hoton na maida kan Murjanatu da har yanzu ta kasa nutsuwa da ƙyau. “Murjanatu ina son ki kwantar da hankalinki ki kuma amsa min dukkan tambayar dazan miki. Hakan da zakiyi shine zai kuɓutar da a halinki dan bamu kawoki nan ba sai da muka san komai a kanki”. “Dan ALLAH aunty kuyi haƙuri kada ku cutar dani, wlhy zan amsa muku duk abinda kuke buƙata. Bana son komai ya samu iyayena”. “Babu abinda zai samesu. Sai dai ki sani a yanzu haka suna a hannunmu. Idan kin amsa mana abinda muke buƙata babu gargada to tabbas zaki samesu cikin aminci harma mu fidda mahaifinki ƙasar waje yaga likita akan ciwonsa.” Da sauri ta jinjina min kai cikin ɗokantuwa. Hoton Hajiya ƙarama na nuna mata. Duk yanda taso dakewa sai da muka fahimci razanarta. Muryarta na ɗan rawa ta ce, “Shugabar asibitin da nake aiki ce. Sunanta Doctor Lawisa.” “Micece alaƙar dake tsakaninki da ita bayan wannan?”. Baki ta buɗe zata fara rantsuwa na girgiza mata kai da faɗin, “Gaskiya kawai Murjanatu. Dan da kunnena naji tana cin mutuncinki saboda kin sanar da wani cewar an cirema patient appendix. Wlhy kinji na rantse miki, idan baki faɗan gaskiya ba zan tafi na barki da su”. Na ƙare maganar ina nuna mata su Hayatu da Maash da yay wani zaman kasaita yanzu ya kwantar da bayansa da kujera ido a lumshe sai ka ɗauka ma barci yake. Amma ni nasan idonsa biyu mu yake kalloma. Cikin ruɗewa ta shiga roƙona akan karna barta da su zata faɗa. Zama na gyara alamar ina saurarenta. Sai da ta shaƙi numfashi da kukan da ke mata kai-kawo sannan ta ce, “Aunty zan faɗa miki komai dana sani. Amma dan girman ALLAH ki taimakeni da iyayena in ba hakaba wlhy zata iya halakamu. Dan akwai wani da yaso yin irin wannan kuskuren na fallasa sirrinta har yanzu bamu sake jin labarinsa ba. Hakama mahaifiyarsa wayar gari akayi ta ƙone a gidansu ƙurmis akace gobara ce. Again wata ta taɓa bijirema umarninta a gabanmu ta mata allurar poison ta faɗi a wajen ciwon ciki ranar batai kwanan duniya ba sai akace wai ciwon hanta ne ya kasheta dama ta daɗe da shi a jikinta. Still wata mata ta taɓa fahimtar an cutar da yarinyarta a asibitin tazo na rantse miki tana barin asibitin basu isa gida ba mota ta take napep ɗin da suke ciki sai gawarwakinsu aka dawo da shi asibitin.” Ba ƙaramin tashi hankalina yayi ba. Amma cikin dauriya nace mata, “In sha ALLAHU Murjanatu mun miki alƙawarin baki dukkan tsaro da kariyar UBANGIJI. Shiyyasa ma muka ɗauke iyayenki kafin ma mu kawoki nan ɗin”. “Shike nan aunty zan faɗa muku komai. Kamar yanda na faɗa muku sunana Murjanatu Usman. Teachen practice ne ya kaini asibitin kasancewar a bayyane duniya ta shaidashi da taimako wa talaka. Koda yake dama hakan shine burina. Dan a dalilin aikin ido da aka taɓama mahaifina ƙyauta a asibitin naji ƙarfin gwiwar yin karatu a fannin lafiya. Tare da alƙawarin neman aiki anan idan na gama domin hidima ga ƴan uwana talakawa nima. Hakan kuwa akayi, ana bamu zaɓin inda zamuyi practical ɗin na cike sunan asibitin. Na kumayi sa'ar aka turani can. A farkon farawa ban fuskanci kowace irin matsala ba, sai da na kusa cika watannin da suka kai gab da ƙarasa abinda ya kawoni, wani al'amarin daya gigitani ya faru. Mu huɗu ne baƙin masu koyon sanin makamar aiki, Dr Lawisa tai zaman meeting damu a satin kusan ƙarshe da zamu gama. Ta mana alƙawura masu yawa tare da ɗaukar mu aiki na dindindin da wasu abubuwa na ƙyautata rayuwa idan mun kammala karatun mu. Ƙarshen zancen shine tana son yin aiki tare da mu saboda ƙwazonmu. Harga ALLAH da farko bamu fahimci manufar aikin nata ba. Dan haka muka miƙa wuya. Rashin wayo kuma da jin ɓoyayyen aikin taimako ne da bata son kowa ya sani yasa data bamu takardar yarjejeniya akan da mun kammala karatu nan zmauyi bamuyi wani musu ba muka saka hannu itama ta saka tare da wasu mutane biyu da bamu san matsayinsu a wajenta ba. Tun daga nan muka fara aiki tare da ita. Sai dai a zahiri muna ma asibiti aiki ne kuma. Bayan kammala karatun mu muka dawo aiki gaba ɗaya, a kuma lokacinne aikin data buƙaci muyi taren muka fara shi. Tsagwaron tashin hankali muka shiga mu duka a ranar farko da muka fahimci minene aikin data kira na taimakon. Dan ba komai bane face cire ƙodar bayin ALLAH da basuji ba basu gani ba. Musamman ma talakawa da ke cikin matsanancin yanayin ciwon da ke buƙatar taimako. Sai ta katantance tace zata taimake su ta ɗakko wata cuta mai alaƙa da cikin ciki tace kana da shi sai an maka aiki. Idan aka saka kuɗin aikin ta yanke kaso biyu tace ka biya ɗaya asibiti zata biya sauran, sai ai amfani da wannan damar a cire maka ƙoda batare da ka sani ba. Nuna borenmu akan wannan al'amari yasa taima Safina allurar poison ta mutu. Ta kuma ɓatar da Pemi har yanzu babu wanda yasan inda yake. Kowa ɗauka yake ya mutu a gobarar data cinye gidansu. Ni da Sajida mun matuƙar razana, ta yanda har muka gagara iya nuna sake borenmu. A tsahon shekaru biyu kenan dana kasance a asibitin wlhy Ni kaina bazan iya faɗar adadin da matar nan ta cirema ƙoda ba. Tun daga kan yara ƙanana, manya, mata da ma tsoffi. Aikin kanso ya tashi wani lokacin asiri yay kamar zai tonu, sai dai tasan duk hanyar da zata bi ta daƙile komai ta cigaba da bizne mummunan aikinta. Badan muna so ba muke mata biyayya, dan wlhy yanzu haka Babana itace ta maida shi haka, hakama Yayan Safina ta maida shi gurgu. Dukkan motsin rayuwarmu tana biye da shi. Kusan mu goma ne ma'aikatan asibitin dake ƙarƙashin wannan mulki nata wanda dai na sani a bayyane, sai dai gaskiya sauran duk da amincewarsu sukeyi. Ni da Sajida ne kawai bama so. Rashin ƙarfi da hanya da tsoro ya hanamu fiddo zancen. Ba wannan bane kawai, hatta da mutun idan ya mutu akan yi saurin cire wasu sassan jikinsa sai dai wlhy ban san mi take yi da su ba. Hatta da ƙodar ban san wanda ake bamawa ba idan an cire. Sai dai akwai wata mata dake yawan zuwa wajenta Madam Jannifer, tana kawo yara itama ana cirar ƙodar tasu, a ɗan bincikena na gano itama tana safarar yarane daga arewaci da sunan aikatau. Sai dai idan ta kawosu sai ta saka wasu a karuwanci, wasu kuma ta rabama manyan mata ƴan lesbians. Wasu kuma a fita da su ƙasashen ƙetare. Ita ɗin matar wani babban soja ne daya rasu shekaru kusan goma sha bakwai. Tana da yara biyu amma duk basa Nigeria. Bayan mutuwar mijin nata ne tayi ridda daga musulimci ta koma kirista. Asalin sunanta Munnira ne, daga ita har mijin ƴan jihar Zamfara ne. A yanzu haka ma naga tana hannun hukuma an kamata da zargin kidnapping mijin ita Dr Lawisa. Sai dai abinda na fahimta tabbas da sanin Lawisa komai ya faru, dan shekaranjiya naji tana waya da ita sai dai ba komai na fahimta ba a zancensu. Sannan ana shigo da mugayen ƙwayoyi ana ajiyarsu cikin store ɗin asibitin nan da sunan kayan asibiti ne, ana kuma saida abubuwan asibitin masu muhimmanci suma. Wannan shine abinda na sani kawai Wlhy”..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_ .......Mu dukanmu salati kawai mukeyi da mamakin hatsabibanci irin na wannan mata. Sai kace ba mace da aka sani da taushin zuciya da tausayi ba. Lallai al'amarin na matar nan babbane. Tsahon lokaci babu wanda ya iya cewa komai hatta shi mai gayya da aikin. Sai da Jaga ya ce, “Humm ai dama na faɗa maka babban yaya. Akwai abinda take yi a asibitin nan shiyyasa ta bashi muhimmanci sosai. Dan matar nan ANGULU ce wlhy bata jewar banza. Shi kansa Commondo ɗin amfani kawai take yi da shi. Ai ko yanda kuɗaɗe ke shigar mata duk da tana ɓoyewa tuni ya kamata a zarge ta da hakan” Cikin jinjina kai Hayatu ya ce, “Tabbas maganarka haka take Jaga. Dan ko shi kansa Baba yanzu na fara tunanin anya matar nan ba itace ke amfani da shi ba”. “Zata yiyu bazata yiwu ba oga Hayatu. Saboda magana ta gaskiya shima tsohon nan hatsabibin kansa ne. Ko maganar saka yara a containers ɗin babban yaya na kwanaki wlhy ina da tabbacin yana da hannu a ciki. Dan ni na faɗa muku wannan Mr Paul fa abokin huɗarsa ne sosai. Sune ma suketa son jansa ya shiga siyasa yana ƙi, bakuga yanda aketa jan shari'ar ba ma. Yanzu dai gasu can na barsu a halin ruɗani da ƙaulanin kasa banbance ni fatalwar ne ko kuwa ina raye. Duk da dai nasan zuciyarsu tafi karkata ne a ni fatalwa ne. Amma a taron sunan nan na gobe zan tabbatar musu ni mutum ne. Ruɗanin da zasu shiga shi zai sa su fara neman hanyar tabbatar da gaskiya, babban Yaya kuma sai yay amfani da wannan damar. Ni wlhy so nake ma Babban yaya yasa a saki Commondo nifa nafi son na kashesa da hannun....” Ya kasa ƙarasawa saboda kallon da Maash ya masa. Murmushi na ɗan yi da girgiza kai. Hakama Hayatu sai da ya murmusa kaɗan. Sai TJ ne ya furta, “In sha ALLAHU bazaka sake aikata wani mummunan aiki ba Muntari. Na baya ma ALLAH ya yafe maka tunda Alhamdullah bama ka taɓa yin kisan ba dai”. “Hakane kuma Yaya Tijjani”. Jaga ɗin ya faɗa fuska a marairaice kamar zai yi kuka.. Ni sai ma abin nasa ya bani dariya...... 💦⭐💦⭐💦 Gaba ɗaya lissafin Baba prof ya gama rincaɓewa. Dan tunda Isma'il daya kawosa ya rakashi har Bathroom ya fita sai ma ya gagara yin wankan. Ga warin gudawar da yay a jikinsa na matuƙar damunsa. Amma ruɗanin ganin Jaga ya mantar da shi komai. Tabbas da farko zuciyarsa ta bashi Jaga fatalwa yay musu. Sai dai yanzu daya haɗa lissafi ya fahimci maganar Hajiya ƙarama gaskiyace kenan. Commondo na son cimma wata manufa shiyyasa bai kashe Jaga ba. Shiyyasa a yanzu ma da yake a hannun hukuma bai damuba, saboda yanada wanda zai masa aiki a waje. To amma Jaga sunan Awwab ya ambata ai. Ya ilahil alami. Shin ko dai Commondo shima ya koma ɓangaren Awwab ɗin ne? Tabbas idan hakanne zama fa bai gansa ba. Dole ne a gobe ayita ta ƙare kawai. Zaiyi amfani da taron da Nafisa ta sanar masa za'ayi a Mansion. Ƙasaitacen murmushi ya saki a hankali tare da sauke nannauyan ajiyar zuciya. Sai yanzu ne yaji ƴar nutsuwa na dawo masa. A gurguje yay wankan duk da jikinsa babu wani ƙarfi. Yau babu zancen shan barasa. Ɗakin sirrinsa ya shiga ya dinga haɗa duk wasu abubuwansa masu muhimmanci waje guda. Haka ya raba dare, sai da ya gama tsaff sannan ya bincika jirgin da zai iya tashi koma na wane ƙasa ne a gobe idan ALLAH ya kaimu ƙarfe huɗu. Yako samu mai zuwa Saudiyya, a take ya sayi ticket ta online ɗin. Bindigarsa daya jima bai yi amfani da ita ba ya ɗauka yayma zubin bullet taf sannan yay zaman yin dogon rubutu a takarda daban-daban kowanne da sunan ƴaƴansa. Suma ya kammala gab da asuba ya haɗasu ya ajiye. Sai lokacin ya samu giyarsa ya kwankaɗa son ransa sannan ya haye gado yay male-male..... 🌿✨🌿✨🌿 A lokacin da Baba prof ke wancan shiri anan Maash Mansion ma Hajiya ƙarama tunda ta samu ta sheƙama kanta ruwa akan batun Jaga sai ta fara samun ƴar nutsuwa. Ita dai tunaninta na nan akan Jaga fatalwa yay musu. Dan haka ta tabbatar ma kanta yin abinda ya dace kafin komai ya buɗe. Dan ta fahimci a yanzu Madam Jannifer da Commondo komai zai iya fita daga bakinsu. Hakama Baba prof a shirye yake da yin komai a kansu. Idan ko haka ne to batun ta kwanta a barci baima taso ba. Ita dama ta kammala dukkan shirinta game da kaf dukiyarta da harƙallolinta ta shirya ta yanda kota bar ƙasar zata cigaba da gudanar da komai a maɓoyarta. Hatta da sace Samraah ta gama da wannan matsalar, dan bazata taɓa barma Awwab ba, babu ruwanta da batun wani ƴar Abdul-wahab jirgin mota ce har yanzu tana sonta da kwaɗayin kasancewa da ita, ko cikin jikinta bai dameta ba zata zubar da shi da zarar sun bar ƙasar. Arwa kuwa da abarta zata tafi. Itama dai ticket ta siya ta online amma na ƙasar Dubai, daga can zata wuce ƙasar data gama tsarama kanta rayuwa da wani bazai taɓa tunanin tana a can ba saboda ƙasar ba wani wajen yawan zuwan mutane bane. Gaba ɗaya yaranta da ta gama shiryawa domin wannan yaƙi ta kira. Sai Marcel da shine uban tafiya. Abinda kawia ya banbanta shirinta da Baba prof ita sai nan da kwana biyu take shirin wucewa. Amma dai a gobe take son ai mata kidnapping duk wani wanda ke cikin list ɗinta. Saƙonta daga wajen Dr Khunal kuwa a daren yau zai iso Nigeria kamar yanda ya tabbatar mata. Dan tun ɗazu da sukai waya yace mata bazai ƙara minti goma da shi ba a hannu amma ya sake ninka mata kuɗin kuma a haka ta biya. Jirgin da ya taho da saƙon kuma da ayanzu haka yana a bisa hanya na tashi yay mata text da _Done_. Wannan ne ma ya bata ƙwarin gwiwar tunkarar Baba prof a ɗazun.... 🤍💫🤍💫🤍 A nan ɓangaren Fahad da Hafizzullah kuwa su shirin shagalin sunan gobe in sha ALLAHU sukeyi hankalinsu kwance. Dan su kawai a rakwashe a ƙwalle a girgije shine nasu shirin. Ga mutanen Kano su Abba da wasu a cikin ƴan gwarzo na a hanyar zuwa a goben domin ganin Falaq da kuma halartar bikin suna duk da taso ace itace ta fara ziyartarsu amma sun dai ce sune zasu zo domin neman afuwar mama Balki. Dan hakama suka kwaɓeta gaya mata, hatta da Samraah ma bata san da zuwan nasu ba. Amma Maash da Hayatu duk sun sani, a jirgi ma zasu zo. Abin da farko kamar wasa sai gashi dai gagarumin taron suna na niyyar haɗuwa. Dan daga abincin mutane ɗari da sukai niyyar yi sai Ummie tace a ninkashi ya zama na mutane dubu ɗaya za'a bada wani sadaka. Duk da ma bata san da zuwan baƙi daga Kano ba kasancewar har yanzu bata san alaƙar Hafizzullah da Samraah ba. Ba kuma tasan Samraah ɗiyar Jirgin Mota bace. Su Hayatu sun tsara sai a gobe zata sani in sha ALLAHU wajen taro. Koda Hajiya Mammah ta zagi Samraah da sunan ɗiyar driver a jiya kawai ta ɗauka hakanne amma hawai ta ɗauki abun da muhimmanci ba. Dan ko ɗiyar mai bara Awwab da Fahad suka kawo mata matsayin matansu zata goya musu baya kuma taso matan musamman idan sun kasance mutanen kirki masu tarbiyya. Bayanin likitanta akan ba komai zai dawo mata kanta lokaci ɗaya ba kamar da, ba kuma komai zata zurfafa nazari ko maida hankali akansa ba yasa yanda take ɗaukar Hafizzullah ɗan Mama Balki yasa suka barta a hakan kawai. Dama kuma bata tambayi kowa ba akan hakan ma..... 💙💢💙💢💙 Zazzaɓin dana fara ji yasa muka baro guesthouse ɗin nasa muka nufi gida. Muna shigowa gidan muka tadda wani bala'in kuma. Dan tun a compound muka samu ma'aikatan gidan cirko-cirko maza. Daga ciki kuma ihu da kurkurwa ke tashi kamar muryar Hajiya Mammah. Har Maash yaja hannuna alamar muje ciki na girgiza masa kai. Murya a marairaice nace muje muga muke faruwa. Yaso tirjewa na sake shagwaɓe masa kamar zanyi kuka. Mun girgiza matuƙa da abinda muka samu yana faruwa. Wai baƙuwa Hajiya Mammah tayi tun safe sai kuma ga ƙawarta Hajiya Rubayya da daren nan. Babu wanda yasan miya haɗasu aka jiyo hayaniyarsu. Tun sunayi a ɗaki har takai an fito waje tare da hankaɗo baƙuwar Hajiya Mammah waje tsirara. Ita ma Hajiya Mammah ɗin daga ita sai zanin gado data cikuykuye jikinta a ciki. Yayinda Hajiya Rubayya ke riƙe da wuƙa tana rantsuwar sai ta kashe Hajiya Mammah tunda taci amanarta. Cikin tashin hankali Maman Malika ke tambayar cin amana kamar ya. Babu ko ɓatan harshe Hajiya Rubayya ta saki baki tana kwarara bayanin aure sukai ita da Hajiya Mammah shekara biyar kenan. Amma sai gashi yau ta kamata da ƴar ƙanwarta da take riko a gado ɗaya. Babu wanda bai razana da wannan batu ba. Falon yay tsitt zuciyar kowa na bugawa da ƙarfi. Baka jin komai sai hayaniya da banbamin Hajiya Rubayya dana Hajiya Mammah da ke faɗin itama wlhy sai ta kashe Rubayya. Kafin kace mi sun farama juna fallasa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚_ .......Hajiya Rubayya ta shiga faɗin, “Amma dai kin san ke ƙaramar ƴar iska ce Nafisa. Sannan a tafin hannuna kike wlhy. Ko kin ɗauka nima zaki iya yimin irin asirin da kikayi ma Mu'azz da babanku na mallaka domin gidan nan da komai ya dawo hannunki ki dinga juya kowa na cikinsa. Kullum cikin bankawa Maash asiri kike dan ya auri ƴarki ku mallake dukiyarsa sai wanda kika so yaci. Da kikaga kinƙi samun damarsa akan auren kin buga kin buga ya gagaresa sai kikaje kikayo masa asirin da yayma ƴar mutane fyaɗe. Kika kuma shirya tozarta shi wa duniya sai da kikaga kin gagara samun hanya kika dakata. Dai-dai da ubanki asiri kike masa ko na miki ƙarya?”. Wani shegen zabura Hajiya Mammah tayi kan Hajiya Rubayya cikin kukan kura da wuƙa tsirara. Fashewa duk mukayi dan tsabar tsorata. Dan kowa ya gama sadaƙarwa za'ai kisan kai. Abunka da taron mata. Wani ihun da Hajiya Mammah ta sake saki da faɗin, “Ka sakeni Awwab ka sakan. Wlhy sai na kashe wannan matar yau”. Yasa duk muka fahimci shine ya riƙeta. Duk abinda taken kuwa bai sake ta ba. Yana tsaye cak itako tanata fisge-fisgen son ƙwace hannunta. Sam ba ita yake kallo ba. Sai da mukabi abinda ya kafe da ido muka fahimci Paah ne tsaye a wajen ashe. Tsabar mamakinsa da firgici sai kawai mukaji Hajiya Mammah ta ƙwalla gigitacciyar ƙara, koda muka dawo da kallonmu kansu hannunta daya riƙe mukaga ta riƙe da ɗayan hannunta tana ihu ga hannun na jale-jale alamar ƙaryata yayi. Ko kallon inda wani yake kuma baiyi ba ya keta ta tsakkiyarmu ya gitta Paah ya wuce a binsa. Sai da yaje fita a kausashe ya furta, “Hayat! Securitys su kwashe min matar nan da dukkan muƙarrabanta” yay ficewarsa. Razana matuƙa muka gani a fuskar Hajiya Rubayya. Ta zabura cikin masifa tana faɗin bataga ubanda zai kamata ba kawai securitys ɗin gidan suka shigo. Abinda ya ɗaure kan kowa da bada mamaki babu wanda ya musu bayani suka nuna Kubrah, Falilah, Afrah sai yarinyar da ake rikicin a kanta da Hajiya Rubayyar. Dai dai nan Hajiya ƙarama ke fitowa da alamun bata cikin nutsuwarta ko wadda ke cikin wani yanayi. Dan duk tayi wani firingai-firingai kamar wadda bata samu isasshen barci. Ƙoƙarin magana Hajiya Rubayya tai mata amma sai ta wani ɗauke kai. Wata muguwar ashariya Hajiya Rubayya ɗin ta lailayo, sai dai kafin ta dire securitys ɗin sunyi waje da ita. Baki ta taɓe kawai ta juya ta koma. Babu wanda hankalinsa ke kanta sai ni. Dan haka na sakama yanayin nata ayar tambaya. Cikin sauke numfashi na maida kallona ga Hajiya Mammah da aka rasa wanda zai ƙarasa gareta, sai ihu take abin tausayi. Sai naji kawai na sake girmama rashin mutuncin Ya Awwab ɗin, amma dai maybe yana da dalilin karyatan. Karo na farko Azizat da ƴar uwarta suka bani tausayi, dan sun haɗe kai can gefe suna faman kuka. Hakama Hajiya Mama hawaye take yi, da alama abinda ƴar uwar tata ke aikatawa ya ɗimautata kamar yanda ya ɗimauta kowa. Ummie da Paah da Mama Balki dake can gefe na kalla suma. Sai naga Ummie ta juya ta koma abinta, shima Paah ya take mata baya. Mama Balki kam babu wani alamun razani a fuskarta da alama tasan abinda Hajiya Mammah ɗin ke aikatawa tuni. Jiki a sanyaye na kalla Hayatu. Na ce, “Yaya Hayat ko za'a kaita asibiti ne dai. Kaga hannun har ya fara kumbura”. Ɗan jimm yay kamar mai tunani, sai kuma ya jinjina kai da faɗin, “Boss ya iya ɗori, ko dai kije ki lallaɓashi ko zai ɗorata, dan yanzu dare yayi ɗaya saura fa”. Cikin mamaki na ce, “Yaya Awwab wai kake nufi?”. Kai tsaye ya jinjina min kai alamar eh. Ajiyar zuciya na ɗan sauke da kallon Fahad da Hafizzullah dake latsa waya hankalinsu kwance suma. Sai bance komai ba na fita kawai ina addu'ar ALLAH ya sa a dace ɗin yazo yay ɗorin tunda dama shine ya karya... Sosai nasha mamakin samunsa zaune a falon ƙasa hannayensa duk biyu dafe da kansa. Gefensa na dama Paah ne zaune, haggu Ummie. Suma dai sunyi jugum-jugum. Juyawa nai da nufin komawa Ummie ta kirani. Dole na ƙarasa garesu kaina a ƙasa na durƙusa a gabanta. Hannuna ta kamo cikin mata, dole na ɗago na ɗan kalleta. Da ido tai min muni da shi. Sai na waro idanuna cikin marairaicewa. Kanta ta girgiza min tana sake lumshe idanunta alamar kar naji komai naje. Babu yanda na iya dole na rarrafa gaban nasa, kamar mai jin tsoro na ɗora duka hannayena biyu a saman nashi da ya dafe kai da su. Shiru babu alamar zai motsa ko nuna yasan da zamana. Sai naji na sake jin shakkar tasa. A marairaice na juya na kalla Ummie. Sake jinjina min kai tai cikin ƙarfafa gwiwa. Sai kuma ta miƙe, shima Paah miƙewar yay suka bar falon. Na ɗan ji sauƙi kaɗan dan ina jin kunyarsu. Dan haka na daure da rawar murya na ce, “Yaya Awwab!”. Shiru. Na saka faɗin, “My Lion!”. Nan ma shiru, ban gajiya ba na ce, “My hot please mana. Kayi haƙuri dan ALLAH kaje ka duba mata hannun kafa karyata. Bai kamata ba ko yaya ita ɗin uwa ce. Bai kuma zama lallai gaskiya bane abinda matar can ta faɗa, kama sani ko sharri aka ƙulla mata. Bai kamata mu yanke mata hukunci batare da wani bincike ba......” “Samrh leave me alone and get out of here!!”. Har tsakkiyar raina naji tsawar nan. Amma na dake na sake buɗe baki zanyi magana ya sake daka min tsawar. “I say leave!!”. Takaici yasa na saki masa kuka, miye nawa daga roƙon alfarma irin wannan tsawa haka kamar wata dabba. Abunka da mai ciki zuciya a kusa. Tsabar taurin kan mutumin nan har naci kukana na tsire bai kulanin ba. Bamma san lokacin dana tashi a fusace nabar wajen ba ina jin kamar zuciyata zata fashe. To irin wannan wulaƙanci har ina dan ALLAH. Idan ya gadama kar yaje ya ɗorata ai yayar babansa ce sunfi kusa. Haba bana son taurin kai wlhy. Ɗakina nai shigewata na kulle kaina ban kuma sake bi takansa ba. Wanka nayi nai kwanciyata sai zazzaɓin nawa na fama yay mun rijif kuwa. Da ga haka na koma takaina nima....... *_WASHE GARI_* Washe gari safiyar suna. Daga tashi sallar asuba da nayita da ƙyar na sauka ƙasa. Can ɗakin da Aunty Falaq take naje na kwanta dan zazzaɓi ne sosai a jikina. Tambayar duniya tamun na ganina anan da asubar nan nace mata ba komai anan kawai nake son kwanciya. ganin yanda nake rawar sanyi dole ta bar ni. Sai ma blanket data ƙara min. Kamar kuma yanda yake ga al'adar bahaushe an raɗama baby suna a masallacin nan Mansion Muhammad Awwab. Sama-sama naji su Fahad sun leƙo suna faɗama Aunty Falaq ɗin. Kasancewar basu shigo ba yasa basu san ina ciki ba. Sau biyu ina tashi yin amai kafin barci mai nauyi ya ɗaukeni. Na roƙeta kuma kada ta gayama kowa karma ta faɗama kowa ina a ɗakin. Shaƙiyancin da take min yasa na fahimci ita tana fassara yo yajin nawa zuwa nan da wani abune daban. Sai kawai na barta a hakan ne wai ina gudun Ya Awwab. Harda cemin itama farkon cikin nan haka ta dinga yi, sai da ya shiga wata uku sannan. Ni dai ban kulata ba.... ★ A sauran ɓangarori kam kowa ya tashi da shirinsa a yau ɗin. Baba prof, Hajiya ƙarama, Maash da muƙarrabansa. Sai su Fahad masu shagalin suna. Hajiya Mammah dai yau babu kanta. Dan Maash dai bai ɗorata ba a daren nan aka kaita asibiti, sai sune sukai mata ɗorin. Tsabar fitina kuma tace a sallameta zataje gida tai jiyya. Basu ƙi hakan ba suka sallamota. Wajen ƙarfe goma drivern ta da Maman Malika datai mata rakkiya suka dawo. Zuwa lokacin gida ya fara ɗaukar harama dan masu tsara decorretion a cikin garden har sun fara aikinsu. Dai-dai lokacin da su Hajiya Mammah ke dawowa Hajiya ƙarama ce daga can ta ɗakin da gen ɗin gidan yake da wani matashin saurayi dake aiki a gidan Baba prof matsayin mai shara da goge-goge. Wani ɗan akwati mai ƙyau ta buɗe tare da nuna masa cikin akwatin. Ƙaramar kwalbace ɗauke da ruwan allura sai syringe a gefenta. Fuskarta ƙawace da murmushi ta ce, “Kaga wannan allurar ita zakaje ka masa yanzu da gaggawa kafin giyar ta sake sa. Ka tabbatar a kan jijiya ka masa ita. Kada kai min wasa da abun nan. Idan ba haka ba, kaima kasan mizan iya yi Labaran”. “Babu abinda zai faru maa, dan har video ma zan miki ko kuma na kiraki ta WhatsApp video call dan ki tabbatar”. “Hakan ma idan kayi babu laifi, zan fiyin farin ciki ma.” tai maganar tana bashi akwatin. Da hannu biyu ya amsa ya saka aljihu, sai kuma ya gyara hiramin kansa da ƙyau ya fice. Sai da ya fita da fin mintina goma sanan itama ta fice ranta fesss. Tana komawa ɗaki Marcel ta kira akan karfa suyi wasa. Dan ƙarfe huɗu za'a fara taron. Ya kamata ace zuwa ƙarfe biyu sun gama da batun DJ ɗin da aka ɗakko su su maye gurbinsa yaransa su iso da kayan kiɗan. Ya tabbatar mata komai sun gama tsarawa. Nan ma ta yanke wayar tana Murmushi. Cike da nishaɗi ta shirya ta fita saloon. Dan yau so take ta fito a hajiyarta.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_ .......A ɓangaren Baba prof kam sai kusan sha ɗaya ya tashi saboda giyar da yasha. Zuwa lokacin yaron Hajiya ƙarama har ya zabga masa allura yama bar gidan dan ya gama nashi aikin kuma. Sai dai da yake ba take zata fara aiki ba, bai ji komai a jikinsa ba lokacin. Wanka yayi yay sallar asuba data suɓuce masa. Bayan ya idar break fast ya fara zaman yi sannan ya koma bedroom ɗin sa yay zaman yin waya da yaransa akan su kasance duk cikin shiri. Dan shi anayin azhar zai wuce Mansion. Suma sun tabbatar masa da komai done. Lokaci kawai suke jira. Amintaccen guard ɗinsa ya kira ya dinga kwasar kayyakin da yay packeging a daren jiya yana kaiwa mota. Sai da ya gama lodesu tsaf sannan ya faɗa masa inda zai kai masa su. Guard ɗin na wucewa yay kiran ma'aikatan gidan. Albashi ya babasu tare da sanar musu zaiyi tafiya, amma sai nan da gobe ko jibi. Su cigaba da kula da gida kamar yanda suka saba. Sun amsa masa da gurmamawa tare da addu'oin dawowa lafiya sannan ya sallamesu. Isma'il nakomawa kitchen ya turama Maash da Uncle Abdullahi dukkan bayanin. Shima ya fara shirya inasa-inasa dan yau ne aikinsa zai ƙare a gidan. Zai ma riga Baba prof fita... ★★★ Har ƙarƙashin zuciyarsa kewarta yake ji. Amma girman kai bazai barsa zuwa ya nemeta ba. Sosai yaji zafin damunsa da tayi jiya akan Hajiya Mammah. Har ma tana faɗa masa wai sharri akai mata bayan ga komai a bayyane gaban kowa akayi. Shi ya tsani aitama abu kwana-kwana bayan kuma ansan gaskiya ce a bayyane. Gefe kuma dama zuciyar ƴan mazan a tunkushe take. Dan ya gama samun dukkan bayanai ta kowanne ɓangare game da shirin Baba prof da Hajiya ƙarama tun a daren jiya. Hasalima bayan barowarsa karya Hajiya Mammah yana shiga sashensa aka kira wayarsa. Dukkan shirin Baba prof aka sanar masa. Dan haka hankalinsa ya tashi ya kai zaune cikin kujera shine ita kuma Samraah tazo ta damesa da wani batun Hajiya Mammah can. Yau kuma da safe aka bashi dukkan bayanan Hajiya ƙarama itama. Hatta da allurar data bayar akama Baba prof ya sani. Shi kuma a yanda yake jin zafin Baba prof ɗin baiga dalilin da zai sa ya hana ai masa allurar ba. Ai Hajiya ƙaramar ce dai-dai da shi. Suci kansu su sha baƙin ruwa. Makashin maza ai dama maza ne ke kasheshi. A ɓangarensa shima ya gama dukkan shiri da team ɗin sa da kuma su Uncle Abdullahi matsayin jami'in tsaro. Bai so wannan taron suna zai kasance a haka ba. Amma babu yanda zai yi dole sai an kai ga hakan dan ya gaji shi kansa. Yafi buƙatar komai ya fito ya kwashi iyalansa subar ƙasar nan suje su hutama ransu ko matarsa tayi rainon cikin nan cikin salama. Ummie ta huta daga gwagwarmayar da ga sha... Jin bazai iya daurewa ba kasancewar yasan a irin wannan lokacin tana a halin ciwo yasa ya nufi ɗakin nata, sai dai ya samu wayam babu ita. Amma dukkan alamu sun nuna anan ɗin ta kwana. Ransa ne ya ƙara ɓaci da tunanin ina ta tafi kuma. Dan har Bathroom ɗin ta ya duba amma babu ita. Ƙasa ya sakko ɗakin su Ummie nan ma babu ita, sai ma Paah ne kawai ke barci Ummie na bathroom alamar wanka take dan yaji motsin ruwa. Har zai nufi kitchen sai kuma ya fasa. Wayar Falaq yay kira a dake yace ta turo masa Samraah ɗin. Itako sai taji tsoro tace masa ai tana barci ne tun ɗazun. Ɓoyayyen numfashi ya sauke da yanke wayar kawai dan dama wayo yay mata dan ya tabbatar Samraah na wajentan. Daga haka ya sake haurawa saman a ransa yana raya sai ya hukuntata tunda har ta tafi inda bai aikata ba ta kwanta bayan ga ɗakinta ga nashi. Bata san dama yaji haushi rufe masa ƙofa da tai jiya ba. Sam baya son raini, dan shi abinda kawai ya ɗauki rufe ƙofan raini ne. Bai ƙara bi takanta ba yama shirya ya fita a gidan shi da Hayatu..... ✨✨✨✨ Kamar yanda zazzaɓin ya saba sakina gabanin azhar yau ma hakanne. Da ƙyar na tashi zuwa upstairs ɗin nai wanka nayi salla. Kasancewar Aunty Falaq ta faɗa min duk abinda ya faru har kiran da yay mata a waya yana nemana yasa bayan na shirya na nufi ɗakinsa. Kimtsashi na shiga yi duk da babu wani datti dan nawa dai an gyara, wannan aikin Mama Balki ne kullum takan zo da masu aiki su gyara ko'ina na sashen tana tsaye ɗakinsa ne kawai nake gyarawa ni dan babu mai shiga. Koda na kammala sai na ƙara ɗan jin ƙarfin jikin nawa. Komawa nai ɗakina na sake gyara jikina, dan sunan kamar wasa yanata tara mutane. Dangin Mama Balki sun zo suna sashensu, hakama na Baban su Hayatu da na mamansa. Saboda ma haka Aunty Falaq ta koma can babu wanda aka bari ya shigo nan sashen Ya Awwab ɗin. Ni kaina kwalliyar tawa sai naga ta burgeni, dan haka na tsaya ina kallon kaina a mirror harda yin hoto. Key na sakama ɗakinsa da nawa sannan na sakko dawn stairs. Na ɗan ji shock ɗin samunsa zaune a falon ƙasan shi da Ummie da Likitanta da Paah. Amma sai murmushin da Ummie tai min da miƙo min hannu alamar naje gareta ya sani sauke ajiyar zuciya. Yanda yay mun kallo ɗaya ya ɗauke kansa nima kallo ɗayan na masa na basar. Paah na fara gaidawa da girmamawa sannan Ummie dake riƙe da hannuna tana yaba kwalliyata. Batare dana kallesa ba shima nace masa ina yini sannan na gaida doctor ɗin shima. A haka Fahad ya shigo ya samemu likitan na cigaba da mana bayanin illar da aka so yima Ummie da alluran da aka dinga mata na birkita mata brain. Ya bata shawarar ƙoƙarin fidda abinda duk ke ranta koda ta hanyar faɗama wani ne, hakan zai sa nauyin da zuciyarta tayi ya ragu har ita brain ɗin ta samu rangwame. Haka dai ya dinga bayani dalla-dalla na matakan da za'a cigaba da bi domin tabbatuwar ingancin lafiyar Ummie ɗin. Tamkar an jeho Mama Balki sai gata ta shigo tana kuka. Mu duka duk miƙewa mukayi a razane. Ummie ta shiga tambayarta abinda ke faruwa. Da ƙyar cikin shaƙewar muryar kuka ta ce, “An ɗauke takwaran Alhaji ƙarami, an tare kuma ƴan Kano da akaje ɗakkowa airport kafin su ƙaras....” Kiran wayar Maash da akayi ne ya katseta. Uncle Abdullahi ya gani ɓaro-ɓaro. Ɗagawa yay, kasancewar akwai bluetooth a kunnensa saurarensa kawai yake. Daga can a rikice Uncle Abdullahi yake magana. “Awwab tabbas akwai matsala. Dan sun canja wasan da ga yanda ka sani. Sai dai ban san daga cikinsu ta ɓangaren wa aka samu canjin ba”. Komai Maash ƙin cewa yay sai yanke wayar da yayi kawai, ya wani fincike bluetooth ɗin kunensa yayi wurgi da shi. Gaba ɗaya kamaninsa sun canja jijiyoyin kansa sun mimmiƙe. Dai-dai nan Hayatu shima ya shigo a birkice yana tambayar Mama ina Falaq. Sake rikicewa mukai dan ita kanta Mama ma sai yanzu hankalinta ya kai. Cikin wani sabon tashin hankalin ta ce, “Ba kuna tare ba? Tun kiran da kai mata ai ta fito mafari kenan ma ta ajiye yaron.” “Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un. Wlhy ban kira Falaq ba ni. Tun yaushe kenan akai kiran?”. “Yau na shigesu ni Bilkisu. Wayarta fa na hannuna mun gama magana da Hafizzullah kiranka ya shigo na miƙa mata na tashi, bai fi minti ɗaya ba ta sameni da yaro a hannu tace kana kiranta shine ta bani shi ni kuma na miƙama Zaituna. Kwata-kwata bai fi mintuna talatin ba yanzu”. “Hafizzullah! To shi yana ina?”. Na faɗa cikin kiɗima nima, dan sai yanzu hankalina ya kai kansa. Kuka na fashe musu da faɗin, “Na shiga uku, aunty Falaq, Hafizzullah, da Baby kenan duk aka tattare. Dama sun faɗa, ashe sakacin da suka ambata sunyi naƙin bibiyar zuri'ar baban mu suna wani sabon shirin. Shin minene mahaifinmu ya aikata haka mai zafi garesu shi da Abie? Mi suka aikata musu Umm.....” na kasa ƙarasawa saboda wani irin kuka daya taho min ga jiri na neman kwasata... Rawa jikin Ummie ya farayi itama. Da kyar ta iya ɗaura hannunta akan kafaɗar Samraah dake wani irin kuka mai cin zuciya. Lips ɗin ta na kakkarwa ta ce, “Samraah mahaifin ku?”. “Yes Ummie, sun faɗa sunyi sakaci da basu bibiyi suri'ar jirgin mota ba kamar yanda suka bibiyi ta Abie.” “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Kina nufin kema jinin Abdul-wahab ce?”. Ɗagowa nai na kalleta, cikin kuka nace, “Ummie da ni da Hafizzullah da Yaya Musaddiq da Ya Awwab yakai ƙasar China karatu duk shi ya haifemu. Mu ƴan uwan aunty Falaq ne na jini”. Sake rikicewa Ummie tai ta juya ta kalla Mama Balki. “Dama bake ce kika haifi Hafizzullah ba?”. Kai ta jinjina mata alamar tabbatarwa. Tana hawaye ta ce, “Ɗayar matar Abdul-wahab ce ta haifesu, muma bamu san haka ba sai da Alhaji ƙarami ya auro Samraah.....” nan fa ta shiga bata labarin dalilin haɗuwata da Ya Awwab har zuwa aurenmu. Ai gani mukai kawai Ummie ta tafi zata zube ƙasa. Da sauri duk mukai kanta ALLAH dai ya bama Paah sa'a ya rungumeta a jikinsa. Wani irin kuka ta fashe da shi mai ban tausayi da cin rai. Sai kuma ta ture Paah ta miƙe. Wayar Ya Awwab ta ɗauka. Babu wanda yasan mi take yi ta shiga danne-danne sai kuma ta kai a kunne. Ɗan jimm tai har wayar ta shiga aka ɗaga, bata yi ko da sallama ba a kausashe ta ce, “Kai tsinannen matsiyaci maci amana butulu. Da ni kake TAKUN SAƘAR ka saboda nice jinin Ibrahim. Idan har kai ɗin ɗan halak ne kazo muyi gaba-da-gaba a yau ba kai kidnapping wanda basu da alaƙa da kai ba. Dan haka in har ka cika kai Adamu namiji ne ba mata maza ba. Ɗan halak ne ba ɗan shege ba kazo ka sameni”. Ƙitt ta yanke kiran tana mai wurgar da wayar. Kamar an saita kuwa Maash ya cafeta cikin hannunsa. Wayar shima ya kai kunensa yana wani makirin murmushi dake nuna tsantsar ɓacin ransa da fusata. Cikin tashi kakkausar muryar shima ya furta, “Nasan kaji mi tace. Dan haka ni Muhammad Awwab El-Mu'azz zan maimaita maka yanzu. In dai kai ɗin ba matsoraci bane. Shashasha lusari mai ɓuya a bayan mace. Kuma cikakken namiji ne ba mata mazan ba kazo ka sametan a cikin Mansion. Idan ba haka ba ni zan biyoka har inda kake, idan kuma hakan ta faru wlhy, wlhy sai kayi dana sanin kasancewata a cikin ZURI'ARKA tsohon banza!!”. Babu wanda jikinsa baya rawa yanzu kam a falon. Dan kaf ɗinmu ba yara bane. Mun kuma fahimci waye wannan da ake wayar da shi. Ko kallon inda wani yake Maash baiyi ba ya fice a binsa. Hayatu da Fahad suka take masa baya. Sai nima kawai na bisu dan bazan iya kallon yanda jikin Paah ke wani irin karkarwa ba........✍️ Tofa, yau fa ake yinta🤔 _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ ......Ganin sun tunkari motoci nima sai kawai na bisu. Yau kam da kansa ya buɗe mazaunin driver ya shiga. Dan haka na buɗe side ɗin gefensa nima zan shiga kawai mukaga an wangale gate. Abin mamaki motocin Baba prof ɗinne ke shigowa. Duk tsayawa mukai har suka kammala shigowar aka maida gate aka rufe. Kawai sai ƴan iska masu zubin shaiɗanu na dirgowa a motocin riƙe da mugayen bindigu tamkar sojoji sun tafi yaƙi. Harga ALLAH na tsorata, na kuma sake tabbatar da mutumin nan baƙin shaiɗani ne. Sai da yan barandar tasa suka gama zagayemu tsaf sannan shi ya fito. Sanye yake cikin manyan kaya harda hula kamar wani tsohon kirki. Ya kawo baƙin gilashi ya toshe idanunsa. Wani shegen tsaiwar ƴan iska yayi kafin ɗaya daga cikin yaran su kawo masa kujera tsakiyar compound ɗin alamar zama. Hannu ta ɗaga musu yana masa nuni damu ya wuce ainahin ƙofar babban sashen cike da takun ƙasaita. Dai-dai nan aka fara fito da mutane daga kowanne sashe na gidan ana maidasu sashen masu aiki mazansu da matansu. Ashe tuni ma yaransa sun gama zagayemu da sunan masu decorretion batare da an farga ba. Sai dai ashe nice mai tunanin ba'a fargan ba. Shi gogan yana sane da duk motsin su tunda suka fara aikin. Sai dai ya barsu a ƙarƙashin nasa shirin shima. Ganin ya nufi ƙofar falon shima a fusace muka take masa baya ni da Hayatu da Fahad. Zaune muka sameshi yay zaman ƙasaita, yayinda ƴan iskansa suka zagaye Maash. Muma muna shiga suka zagayemun. Su Azizat dake falon duk sun rikice suna kallon kakan nasu a firguce. Fito da duk wanda ke sashen yasa ayi. Kusan su Ummie sune ƙarshen fiddowa. Sai Hajiya ƙarama da tai sumar tsaye. Dan ta fahimci shirin wannan makirin tsohon ya danne nata kenan. Sai dai koba komai ta ribantu itama ai, sannan tanada tata nasarar. Ƙananun kukan da su Arwa keyi a wajen yasa ƴan iskan daka tsawa tare da yin harbi. Sake rikicewa falon yayi sai da ƙyar suka lafa. Ta gefen ido na kalla Maash da aka fi zagayewa da bindugun amma babu ko ɗar a tattare da shi. Sai ma tsaiwar ƙasaita ta yay bayansa jingine da bangon falon ya harɗe ƙafafunsa waje guda hannayensa duka biyu cikin aljihun wandonsa. Gefensa Fahad ne shima dai an zagayesan kamar yanda akaima yayansa. Sai Hayatu da ni ma da akaima ƙawanya tun a farkon shigiwarmu. Daga can ma Ummie sun zagayeta haka ma Hajiya ƙarama. Hajiya Mammah da itace ƙarshen fiddowa kasancewar tana ɗaki kwance tana jiyyar hannunta suna isowa wajen ihu ta fasa da faɗin, “Mun shiga uku Baba!”. Gilashin idanunsa ya cire yana mai binta da kallo. Bakin baya iya shiru cikin rawar laɓɓa ta sake faɗin, “Baba wai mike faruwa ne haka? Wane kalar bala'i ne wannan kuma ni Nafisatu Adams ƴan fashi da ranar ALLAH. Ni wlhy duk na ma rikice ko kidnapping ɗinmu akayi....” “Ko kuma yay kidnapping kansa ba”. Muryar Ummie ta ratsa kunnen kowa a wajen a bazata. Duk kallonta akayi dan dariyarta take hankali kwance idonta akan Baba prof.. da mamaki Hajiya Mammah ta ce, “Ummu-Hidaya! Ban gane ba. Baba ne fa taya zai yi kidnapping kansa kuma? Kina ganin mutane sun zagayemu da bindigu kamar babu hukuma a ƙasar”. Haɗe fuska Ummie tayi da watsa ma Hajiya Mammah ɗin wani kallo. “Kamar yanda kika gani mana Nafisa. Ai uban naku lusari ne ba jarumi bane. Sannan mata maza ne ba namijin gaske bane. Dan namijin gaske a filin daga baya riƙe garkuwa. Amma shi harda ƴan baranda ya zo. Adamu kenan, a tunaninka zuwa da waɗan nan wawayen dake hura hanci da bindigu a hannu zaisa ka amsa sunan NAMIJI a gabana? Ai kazo kai kaɗanka ne zan maka kallon ɗan rakkiyar mazan ma. Ka manta na faɗa maka, na faɗa maka in dai ni jinin Ibrahim ce da izinin UBANGIJI sai ka ƙare rayuwarka a ƙarƙashin ƙafafuna kamar yanda tun farko kake a ƙarƙashin ƙafafun mahaifina. Ai na faɗa maka dama bazaka taɓa tsira ba, kuma kafin ka mutu mutuwar wulaƙanci sai ka biya bashin CIN AMANAR da kayi ma mahaifina.....” “Ƙarya kike ƙaramar ƴar iska ni ba MACI AMANA bane. UBANKI shine ya fara CIN AMANATA. dan haka shine MACI AMANA, BUTULU, MARA ADALCI, mai son kansa kawai. Shekaru ashirin da shida na ɗauka ina masa bauta da durƙusawa ƙarƙashinsa, alhalin dukiyar da yake taƙama da fankama da ita dani aka tarata. NI!! NI!! nan Adams. Yazo ƙasarmu a matsayin matsiyacinsa faƙirin da baida banbanci da mabaratan kan titi kafiri mai bautar gunki. Mune muka tallafesa ya zama mutum, muka buɗe masa idanunsa ya fahimci a inda yake, musamman ma NI! NI ɗin nan. Uwata ta zama sanadin shigarsa musulinci. Babu irin wahalar daban masa ba, duk da shekarun daya bani ba wasu masu tazara bane haka nake kiransa YAYANA ko YALLAƁAI, idan ya buƙaci aikena jikina har rawa yake domin son ganin na cika masa fiye da yanda ya buƙata. Ko kallon banza wani ya masa zafi nakeji a cikin zuciyata har na ɗauki mataki. Nasha yin faɗa da abokan aikina idan suna gulmarsa. Idan yana ciwo nine tsaye a kansa har ya samu lafiya. Hatta da wankin kayansa da gyaran ɗakin barcinsa kullum nine keyi batare da jin komai ba a raina. Kafin ya furta yunwa na sayo abinci na ajiye masa, haka nake girmamashi a duk wani motsinsa tamkar yayana uwa ɗaya uba ɗaya. A duk lokacin da naga wani abun cigaba da zai ɗaga darajar Company bana baƙin cikin kawo masa shi. Kuma haka za'a gwada a samu nasara. Amma duk da wannan hidimta masan dana ƙare ƙuruciyata inayi a matsayi ɗaya yake kallona har a randa zai bar duniya. Wato YARONSA. Yaronsa da darajarsa kawai yayi aiki a biyashi sai idan wani ya taso a sake nemansa yayi ya biyashi da ƴan kuɗaɗe. Butulci na farko da tabbatar min shiɗin BAƘON HAURE ne mai rama ALKAIRI da SHARRI shine haɗa baki da budurwata ya turani karatu ƙasarsa bayan tafiyata sukayi aure saboda shi ɗin TSINANNE NE kafirin banza. Na danne zuciyata na ƙyalesa saboda dalilai biyu. Na farko ina masa kallon Yaya ne da zan iya sadaukar da komai a garesa kamar yanda nake tunanin shima zai iya sadaukar min. Na biyu yaci darajar mahaifiyata daya riƙe hannu biyu take masa kallon ɗa jininta. Sai dai nayima kaina alƙawarin komai tsahon lokaci sai na hukunta Rabi'ah da kaina da shi kansa. Dan a lokacin ita nafi kallo a mai laifi, idan shi bai san ina sonta ba ai ita tasan ina sonta. Idan kuma shi bai san ana barin halak dan kunya ba ita ai ta sani. Amma abin duniya ya rinjayeta. Koda yake banyi mamaki ba kasancewar ta ƴar KARUWA mai TUWO-TUWO kuma KARUWAR. Wasu irin hawaye ne masu zafi suka silaloma Ummie. Yayinda jikin Maash ya fara rawa na tsantsar fusata. Yana motsawa ƴan iskan nan suka sake attacking ɗin sa da bindugun. Amma duk da yasan zafa su iya harbin nasa ya mutu har lahira tuni ya watsar da su ta hanyar hankaɗe bindugun ya nufi mahaifiyarsa. Dan a duniya bai haɗa al'amarinta da kowa ba. Da sauri suka ɗana kunamin bindugun su da wanda ke zagaye da ita amma sai Baba prof ɗin ya ɗaga musu hannu yana murmushi. Kamo Ummie Maash yay jikinsa, maganar da babu wanda ke ji yake mata ƙasa-ƙasa cike da kulawa da tattali. Dariya Baba prof ya kwashe da ita kamar ba tsoho mai shekarun girma irinsa ba. Jinai zuciyata na ƙuna. Bamma san lokacin da nima na furta, “Wawa jahili”. ba Ai gaba ɗaya waɗanda ke zagaye da ni, da wanda ke zagaye da Maash ɗin sukayo kaina... “Duk wanda ya taɓa min MATA a cikinku wlhy! Why UWARSA ma sai tayi dana sanin HAIHUWARSA!!!”. Razananniyar muryar Maash ta ratsa kunnen kowa dake a wajen sai da muka firgita. Dan hatta da kamaninsa sai da suka sauya. Cikin nuna Baba prof da yatsa ya furta, “Kai kuma kafi JAHILAI JAHILCI tunda har kake iya maida FARI ya koma BAƘI. WULAƘANTACCE kawai da bai san girma da kimar HALLACI ba, mai faɗa da ƙaddara ɗan son banza. Kai har kana da bakin zaman yima mutane wannan surutan banzar naka soki burutsu. Duk abinda kake lissafin ka masan ai badan ALLAH kayi masa ba, kayine daman dan ka shiga jikinsa ka cimma wata manufarka baƙin annamimi. Idan kace duk ya maka wannan, inganta rayuwarka data ƴaƴanka da yayi fa. Bai kuma ji ƙyashin ɗaukar ƴarsa ɗaya tilo ya aurama ɗanka da ke a gurɓace ba. Sannan ya kama UWARKA ya riƙe da hannu biyu fiye da yanda ma kai kake riƙon nata. Sai ka gaya min UBAN mi kake so ya maka bayan duk wannan?”. “Ni kake zagi Awwab?”. “An zagekan, zan maka ma mafiyin wannan ɗin ne. Dan ni wlhy tuni na daina maka kallon MAHAIFIN UBANA. Na tsaneka” “Kamar yanda nima ban taɓa maka kallon ƊAN ƊANA ba tun ranar haihuwarka naji bana sonka”. “Alhamdullahi hakan yamun daɗi ai, dan ka taimaki kanka wajen gane abinda yafi ƙarfinka har abadan yafi ƙarfin naka. Kai ko kunya bakaji ba a duk wannan surutan naka ka faɗi ta inada Abie ya cutar da kai...” “Oh so kake kasan ta inda ya cutar dani mara kunya. To zakaji yanzun nan kuwa. Dan zan ko gaya maka idan ita uwarka ta gagara sanar maka. Ko aure da kake faɗin ya ɗauka uwarka ya bama Mu'azz ni na sakashi yin hakan ta ƙarfin tsiya ba hallacinsa bane ba........”✍️ Hummmmmmmmmm🏃 _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ ......Dukkan ƙuruciyata a wajen hidimtawa rayuwarsa na ƙarar da ita, amma da yake shi kansa kawai ya sani haka ya tattare dukkan dukiyar da aka tara da gumina a ciki ya rubuce sunan ƴarsa akai da naka, kai ɗin nan ɗan mitsitsinka dama baka san kanka ba balle waninka. Niko ya haɗani da wani tsohon companyn da ya gama mutuwa ya manna min ƴan kuɗaɗe wai ya sallaman naje na gyara. Tun daga lokacin na fara tunanin ta yanda zan mallake dukkan abinda ya handame ɗin nima tunda naga kowa kansa ya sani kawai. Haka na shiga na fita na kwaɗaita masa haɗa aure tsakanin Mu'azz da uwarka. Tsabar mutumin nan shi butulune nunawa ma yay kamar bai da wannan ra'ayin. Baya son wannan haɗin saboda Mu'azz baya jin magana. Rashin jinsa yayi yawa. Bazai iya riƙe masa Ummu-Hidaya ba miye-miye. Kai ko ga ƴar gwal an haifi a Nigeria. Komai bance masa ba a randa ya kawo min wannan zantukan banzar nashi. Na koma kawai gefe na shiga na fita shege a dawowa ta biyu baima san sanda ya amince ba jikinsa na rawa. Suma duk da akwai shaƙuwa a tsakaninsu na sake ƙulle zukatansu a waje guda suka nuna suna son junansu. A zatona wannan haɗin auren zai sa ya dunƙule dukiyar ya bama Mu'azz matsayinsa na mijin ƴar tasa tilo da yake taƙama. Kokuma ya tattara duka aikin ya bama Mu'azz ɗin. Ya cigaba da jagorantar companyn. Amma shegen mutumin nan sai ya ɗauki ƴarsa ya ɗorata akan komai. Tana wata ƙasar tare da ɗana da aka maida hoto amma tana juya kan dukiyar duk da ƙananun shekarunta. Wannan abu ya ƙara ƙona min zuciya matuƙa. Wato ni na ɓata ƙuruciyata a banza wajen hidimta masa ɗana ma zai koma ɗan amshin shata mijin Hajiya. Haba never. Tuni na je na kunno musu wutar da Mu'azz ya fara cin ubanta. Dan a lokacin data samu cikin farko ya jajibemu domin dubata da shirina naje. Na banka masa maganin da Malamina ya bani bamu baro ƙasar ba sai da ya zubar mata da cikin da ake ɗogafi da shi. Da matuƙar farin ciki na dawo a lokacin har kashi biyu kuwa. Na zubar da cikin da Mu'azz yay mata da ƙararshi data kawo min wai bata son ubanta ya sani ai masa faɗa akan neman matan da yake da dukanta da yake yi. A zahiri na amsa mata da to kawai, amma ko uhun bance masa ba. Yo neman mata sai na hanashi ya more ƙuruciyarsa ya ƙare kanta iya kaɗai kenan ma, ko kuwa tana matarsa bazai jibgi shegiya ba yanda yake so a kuma sanda yake so. A dawowar tamu ma dukkanin baya nai ina samu akan zaman nasu. Ubanta yake ci gwargwadon iko shine ma dalilin da yasa tana kammala karatun ta saka suka dawo Nigeria da zama. Duk da dai tana dojewa wai ta dawo ne tai aiki a kamfanin babanta. Ƙaryar banza kenan. Koda ta dawo ɗin nasan Mu'azz na aikata duk abinda yake acan bai fasa ba. Ban kuma tsawatar masa ba. Babban abinda ya fara saka min tsanar shegiyar yarinyar nan bayan wadda nake ma ubanta ta shafeta shine ɓoye zancen cikinka da tayi tare da wannan munafukar annamimiyar da mijinta. (Ya nuna Mama Balki) Ban tashi sanin tana da ciki ba sai da ya shiga watan haihuwa, shiyyasa ashe ubanta ya tura Mu'azz wata ƙasa aikin watanni har shida. Ni kaɗai nasan a halin dana tsinta kaina a wannan lokacin, dan haka na nutsu domin nemo mafita akan yanda ko ta haihu za'a maida abinda ta haifa lahira dan ubansa. Ƙawarta da naga tana yawan zirga-zirga a gidan ce tazo min rai. Dan haka na nemeta amma sai taƙi bani haɗin kai a lokacin da yake Lawisa shegiyar makira ce. Tata yawo da hankalina duk da barazanar da nake mata da kurari, sai da ta latsani da ƙyau har bayan an haifeka sannan ta yarda mukai magana. Wannan shine mafarin alaƙata da Lawisa duk da bata da wani ƙarfi sai idan dalili ya taso. Jawota jikina yasa na fahimci itama shegiyar tana kwana da tashi da baƙin cikin Ummu-Hidaya ɗin. Amma tana dannewa kullum tana jikinta. Kamar dai yanda nake ma ubanta wahala, itama tanata yima ƴar wahala. Duk da mun haɗe kai da Lawisa tako ina mun gagara samun nasara akan kauda kai a duniya. Dan koyaushe idon baƙar matar nan da mijinta na kanka. Ya nuna Mama Balki cikin tsana. Tako ina sun rufe komai sun katantane. Daga baya ma sai na fahimci shi Abdul-wahab kamar ya sakama motsina ido. Dan bawai ga Ummu-Hidaya ba hatta da uban gidan nasa wanni kaffa-kaffa yake da shi idan har ina waje. Rana ta farko dana zuba ma Ibrahim wasu ƙwayoyin da Lawisa ta samo mana ta kuma tabbatar min da in har Ibrahim ya shasu bugun zuciyarsa zai ƙara ƙarfi da ga ƙarshe ta buga ace heart attack ne ya kashesa bayan na gama wahalar zuba maganin a cikin shayinsa kawai matsiyacin yazo da wani salo ya ɓarar da shi as mistake. Ya kuma katantane shi da kansa ya haɗo masa wani ya bashi a gabana. Wannan abu yamun ciwo na fara ninka tsanar da nake masa a raina tare da saka masa alamar tambaya. A karo na biyu ma dana haɗa wutar lantarki a office ɗinsa kawai bamma san ta yanda akai ba kawai shi yaje ya kama wayar ya hana Ibrahim kamawa. Satinsa guda a asibiti yana jiyya a maimakon Ibrahim. Wannan ma ta wuce bance da shi komai ba na sake kafa wani tarkon a cikin gidansa da fetur nan ma Abdul-wahab ya wargaza min. Haka ya dinga bina kafa da kafa yana wargaza min ayyukana akan Ibrahim. Daga ƙarshe na fito ƙuru-ƙuru na masa gargaɗi da barazana. Amma da yake shi taurin kai ya masa yawa sai ma ya maida abun rainin hankali, har yana wani sanar min cikin gadara wai in ma ina wani tunani a kansa ne na canja dan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE shi ɗin ba kanwar lasa bane. Idan kuma zan shekara dubu ina ƙulla makircin kashe Ibrahim zai kasance a bashi kariya da izinin UBANGIJI. Kar kuma na ɗauka zai faɗa masa ne ya ɗauki matakin hukuma shi da kansa zai cigaba da bashi tsaro da tsarewar ALLAH batare da ya taɓa sanar da shi wanene ni ba har sai idan shine ya gano da kansa. Alwashi na ɗauka masa kan nima mu zuba ɗin, ni da shi ɗan halak ka fasa. Muka ko zuba ɗin ba tare da sanin Ibrahim ba. Tabbas Abdul-wahab ya nema zamenim bala'i a rayuwata. Dan haka na shirya shirin ƙarshe da shi a ciki dan ya cancanci irin hukuncin Ibrahim shima. “Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, Baba yanzu har wannan ya kai ka kashe Abie da ya inganta rayuwarmu. Shine fa sanadin barowarmu ƙauye”. Hajiya Mammah ce ke maganar cikin matsanancin kuka. Hakama Hajiya Mama da Paah kansu kawai suka duƙar suna hawaye. Cikin kaushin murya da zafin rai Baba prof ya daka mata tsawa da faɗin, “Oh dan yayi sanadin barowarku ƙauye bada wahalar ubanku bace Nafisatu. Ko a banza yasa na kawo kun badan ya cigaba da amfanuwa da ƙuruciyar mahaifinku bane. Kar wanda ya sake katseni ki bari nakai ƙarshen zancena mana kafin kiyi alƙalanci!!!”. Ya ƙare maganar a tsawace yana wani irin huci kamar bajimin sa. Kafin ya cigaba da magana a zafafen nasa. “Sai da na gama shirya komai sannan na tunkari Ibrahim da sigar neman alfarmar aron kuɗi da zan inganta bussines ɗina. Amma shi da yake butulu ne, kansa kawai ya sani sai shegiyar ƴar nan tasa da kai dake matsayin jikan da ni nama fisa matsayi da ƙarfi a wajenka domin ubanka na haifa. Haka ya nuna min baida waɗan nan kuɗin. Sannan ko yana da su ma bazai bani ba dan sunyi yawa. Naje na cigaba da juya na hannuna wai fara kasuwanci da kaɗan yafi albarka. Kuji min shegen makiri, shi bada manyan ya fara ba. Na zafafu ranar da ƙyar nai controlling kaina. Ban sake masa magana ba sai bayan wasu kwanaki na sake zuwa masa dai da wannan buƙatar amma na rabin abinda na nema a farko nan ma ya nuna min sam shifa bazai bani ba tunda ya sallameni. Idan ma dukiyar da nake kallo a hannunsa ce shima ba tashi bace mallakin ƴarsa ce da jikokinmu. Kam babbar bala'i kenan. Wai abinda aka tara da gumina ake min gadara da shi hahaha yaro bai san wuta ba kenan sai ya taka. Daga haka ban sake masa batun ba sai bayan kusan wata ɗaya naje masa da tayin sayen Shere a companyn nawa dan nayi amfani da kuɗin na tada companyn da ke neman durƙushewa. Abin mamaki wai azzalumin nan a wannan ɓangaren babu musu ya amince. Ya sayama ƴarsa kaso ɗaya bisa uku na Shere ɗin company na. Ya kuma biya akai duk abinda ya dace ya amshi takardu a gabana ya damƙa mata. Daga wannan ranar nai alƙawarin sai na ɗanɗanama Ummu-Hidaya azaba da wutar dalma a tafin hannunta. Matakin farko kuma shine kashe ubanta. Anyi haka da ƴan kwanaki kawai a bazata akace min wai tana naƙuda. Imagen matar ɗana nada ciki ban sani ba a karo na biyu. Hakan na nufin akwai abinda take shiryawa kenan itama ko ubanta ya kitsa mata a kaina, domin idan babu rami miya kawo rami? Ta ɓoye na farko na biyu ma haka........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ .......Banyi magana ba dai sai shi Mu'azz ɗin na samu na ci masa ƙaniya sai da ya koma yana rantsuwar shima wai bai san da cikin ba sai da ya kai watanni kusan huɗu. Ta kuma roƙesa kada kowa ya sani idan kuma ba hakaba zata gudu tabar gida har sai ta haihu ta dawo saboda ta fahimci baya son haihuwa shine ya zubar mata da cikin farko. Na Awwab ma shiyyasa ta saka mahaifinta ya turashi wani aiki na watannin rainon cikin nata da tayi bayan ta tabbatar mai idan wani abu ya samu cikinta sai ta kaisa kotu. Sosai raina yamun zafi da lusarancin Mu'azz. Dan a zahiri baya jin magana, sannan yana da zafin rai idan aka ƙuresa amma bashi da yawan hayaniya da kwaramniya tamkar ba mune muka haifesa ba. Kaf halayensa na mahaifiyata ne ya kwaso shi. Barshi dai da fitinar neman matansa kawai. Takaicinsa ya sakani korashi dan mun gama shirya kawai tafiya matakin ƙarshen ni da Lawisa. Sai dai dole sai mun sami point. Munata neman point bamu samu ba har sai da tafiyarsa jihar Katsina ta taso. Amma zaiyi landing a Kaduna ya ƙarasa Katsina ta mota. Hahaha wannan abu yay min daɗi matuƙa. Hakama Lawisa. Babu ɓata lokaci ta samar mana wanda zai mana aiki a kaduna. Abinda ya ƙara sakamu a farin ciki da tafiyar ta kasance da shegen makirin driver ɗinsa mai cika bakin zai iya ƙare rayuwarsa yana bashi kariya. Anyita ta ƙare, raina yayi sanyi FANSA ta tabbata akan Ibrahim da Drivern sa Abdul-wahab, sai dai wai Ibrahim bai mutu ba. Hakan bai wani ɗaga min hankali ba, dan nasan zan iya ƙarashi da hannuna abu mai sauƙi. Amma kuma zan iya bashi damar rayuwa koda a kwancen ne ta yanda yana kallo ina juya abinda ya cutar dani a kansa amma babu yanda zai yi dan ubansa..... “Wlhy kai jahili ne. Wato ɗauka ma kake rayuwarsu da mutuwarsu duk a hannunka take?”. Fahad ya faɗa a matuƙar zafafe yana kuka. Cikin tsawa Prof... Ɗin ya watsa masa harara da faɗin, “Nace a daina katseni sai naje ƙarshe. Kai yaushe ma aka haifi uwarka balle kai zaka katseni. Idan kai baka san rayuwarsa a hannun nawa take ba ita uwarku ta sani dan taga kaɗan daga abinda zan iya bayan tamun irin wannan gadarar. Haka shima uban nata. Ni ɗin dai daya wulaƙantar ni ne na shiga na fita aka kawosa Lagos ɗin yana a tsakanin rayuwa da mutuwa. Inda naso da tun a can zan kashesa amma ba haka nake buƙata ba alokacin. Ni na tsaya tsayin daka akai treatment ɗinsa har ya fara samun sauƙi. Kaga ko ai rayuwar tasa a hannuna take mara kunya (Wa'iyazubillah😭). Naje masa da jarabawar ƙarshe, wadda da ace ya cita da har yanzu yana rayuwarsa dan ba itace a gabana ba ni. Yana a gadon asibitin naje masa da batun duk halin da yake a ciki nine na sanya shi, na kuma gaya masa kuskurensa, tare da tabbatar masa idan har ya mallaka min abinda nake so a lokacin tofa zai tsira, hakama ƴarsa zata tsira. Hakama jikokinsa. Idan ba kuma ba haka ba, zan kashesa kamar yanda na kashe uwar matarsa da matarsa. Na kuma kashe ƴarsa da jikokinsa abinda ya hana nin ya dawo nawa gaba ɗaya dan babu mai cin gadonsa sai ni. Hhhhhh!!! Kun san miya faru? Da yake mutumin nan ƙasurgumin shegen Bature ne kai tsaye yace min bazai bayar ba. Har ma yana iƙirarin idan ya bar asibitin nan sai ya wulaƙanta rayuwata. Dan sai ya kaini hannun hukuma na faɗa masa dalilin kashe masa mata da mahaifiyarta. Hahaha ni sai ma ya bani dariya, dan haka na haɗa masa da abinda naso barinsa a duhu saboda wasu dalilai, amma tunda zai iya ɗaukar fansar matarsa da uwarta nashi iyayen fa?. Dan haka na fito na faɗa masa ai suma ni ne na kashesu. Nayi hakanne kuma a dalilin hukuncin auren budurwata da yayi, cikin sauƙi na shirya matsalar data zama gobara har yau ake ɗauka daga sune. Tofa wai wanda ke a gadon asibiti a tafin hannuna ke nuna fusata har gado na jijjiga. Sai famar hura hanci yake shi a dole sai ya ɗau fansa. Kaji Bature ɗan balaja'u. Kazo ƙasata kace zaka nunan gadara. Barinsa nai ya gama bige-bigen nasa sannan na siburbuɗa masa allurar poison. Hhhhh karfa kuga laifina dan alokacin bata mutuwa bace. Ina da makarinta a hannuna, na kuma nuna masa idan har yay min abinda nake so zan masa ita mu rabu lafiya ya cigaba da rayuwarsa zaɓinsa ne. Na koma gida ina jiran feedback. Washe gari kuwa na samu kira daga wajensa. Ganin ƴarsa da jikansa a wajensa har ma da lauyoyinsa yasa na fahimci gargaɗina ya amsu kenan. Dan haka na samu gefe naci dariyata son raina sannan na koma. Sai dai tun a farkon zaman meeting ɗin na fahimci baifa sallaman ba, lallai taurin kai baiyi ba, da ace mutumin nan yasan mizan iyayi da wlhy baiyi jayayya ba. Da bai zaman tattare komai da komansa a gabana ya mallakama ƴarsa da jikokinsa ba. Da bai ajiye shaidu akan hakan ba har kuma ya gayyaceni zaman. Dan wannan shine mafi girman kuskure daya taɓa aikatawa a rayuwarsa da shima yasan ya tafi yabar BAYA DA ƘURA. Dan nayi alwashin sai na tabbatar masa da TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE koda yana kwance a cikin kabarinsa. Yanda bai saka ni cikin zancen ba an ajiyeni ne matsayin hoto ko dan yamun gadara ne oho mas nima sai banyi magana ba har akai zaman meeting ɗin aka tashi. Abu ɗaya nai masa shine lokacin da zan fita a ɗakin nai masa kallon (Kayi kuskure) nai ficewata. Dan banda sauran kuma dil da shi wasan ya koma tsakanina da ƴarsa ne. Yes ni da ƴarsa dan allurar poison ɗin da nai masa kawai ta wadatar ta ƙarasa min rayuwarsa. Hakan kuwa ce ta kasance, washe gari aka shafe babin rayuwarsa. Ya zama tarihi. Alonso Ibrahim ya shuɗe kamar bai zo ba. Adalcina yasa na tsaya akan komai na jana'izar sa komai akayi yanda ya kamata. Ai koba komai baƙonka Annabin ka inji masu iya zance. Baƙunta yazo ƙasarmu, ya kuma tattara ya bar mana miya rage ai gaba ta ƙare kuma sai wadda aka barma JINI. Banyi ƙasa a gwiwa ba dan bana son na cigaba da jan al'amarin na samu Ummu-Hidaya da batun ta bama mijinta komai na dukiyarta ya cigaba da juya mata a matsayinta na uwa ta cigaba da tarbiyyar yaranta da kula da mijinta. Kun san buɗar bakinta mi tace dani kuwa? Hahahhhh!!! Kawai sai cewa tai wai (Baba karka damu, zan cigaba kamar yanda na fara wannan shine burin mahaifina). Banyi fushi ba na cigaba da nuna mata tayanda zata fahimta amma ina. Imagen like father like daughter. Kai harma tafi ubanta taurin kai da tsaurin ido. Koda yake ai jini biyu ta haɗa, Rabi'ah ma badaga nan ba a taurin kai. Iya son fahimtar da ita nayi cikin hikima amma ta tabbatar min da itafa tana akan bakanta, idan dai Mu'azz zai zo ya nema aiki ne a companys ɗinta yazo ƙofa a buɗe take, yayi kamar yanda kowa keyi a biyasa albashi, amma batun ta bashi ragamar komai ko ni ta bani sam bazatayi ba. Kai harma da fa su zagina ita ga BOSS LADY jinin Alonso da Rabi'ah masu kuɗi ko. To Rabi'ah ɗin ma dan ubanta saurana ubanta ya samu dan sai da na gama shanye romon a waje kafin shi ya aura abinka da karuwa ƴar mai tuwo-tuwo..... A zafafe Ummie ta ture Maash ta miƙe tana nuna Baba prof da yatsa, a matuƙar kaushin harshe ta ce, “Karya kake baƙin azzalumi annamimi. Oh surutun da aka barka kanayi taaa!! taaaaaa!! Tun ɗazun yasa kake jin kamar bakinka ne kawai ya iya magana har kake da kalmar yima mahaifiyata sharri. Ka kira Abie ɗina da maci amana, butulu, azzalumi, baƙon haure, kafiri da mine. Yanzu kana son aibanta mahaifiyata da zina. Ƙarya kake yi Adamu. Dan uwarka da bakinta ta faɗi mutunci da martabar da mahaifiyata taje da shi ga mahaifina. Idan kana gani bata raye yanzu ALLAH shine shaida kana da damar ƙaryatata dan dama ba daraja da mutuncinta ka sani ba ai. Sannan kana maganar na zageka, ai sai ka fito ka sanar musu dalilin da yasa na zageka bunsuru ɗan akuya wanda bai san mutunci da kimar kansa ba”. Ta share hawayenta da nuna shi.“Jama'a kunga wannan, in har bai tuba ba ya mutu, idan har wanda ya kashe basu dawo duniya ya nema gafararsu ba, idan har waɗan da ya zalunta ciki harda mahaifiyarsa da matarsa harma da ƴaƴansa basu dawo duniya ya nema anfuwarsu ba, to tabbas idan kuka gagara ganinsa a WUTA ranar sakamako maybe garwashi ne ya lulkuɓesa acan ƙasan wutar jahannama........✍️ *_“Ya rabba🙏😭. ALLAH ka rabamu da son zuciya. Wace irin rayuwace wannan ka ƙare rayuwarka a bibiyar ta wani. Mutane dan ALLAH mu canja, dan yanzu mafi yawanmu wannan itace rayuwarmu shiyyasa HASSADA take ƙara ƙarfi a zukatanmu wlhy🥲🥲.”_* _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ .......Bari na faɗa muku wani abu, duk da ya fito ya nunama mahaifina ainahinsa har yabar duniya bai nuna min wanene shi ba. Ko zaman meeting da mukai ana gobe zai bar duniya abinda kawai ya nuna min shine yana son ya tattara komai gareni, dan akwai wasu abubuwa daya ware na Muhammad da Fahad a cikin dukiyarsa. Sauran kuma nawane a matsayina na mai gadonsa. Ya ƙara da min nasiha game da kulawa da duk wanda zanyi mu'amala, ya tabbatar min dana tsaya akan gaskiyata, na kuma rungumi ƴaƴana na horar da su ta yanda sune zasu zama gatana kuma garkuwata koda anan gaba. Ya faɗakar da ni kada na cuci kowa, koda ma'aikaci na ɗauka mai hidimta min a cikin gida na sauke hakkinsa na kuma bashi darajarsa irin ta ɗan adam. Yace dani na cigaba da girmama wannan wawan, dan shi ɗin kamar ubane a wajena, yana kallonsa matsayin ƙani jininsa kodan riƙon da mahaifiyarsa ta masa da raino irin na uwa. Sannan mijina, duk rintsi kada na barsa, kada na masa ɗagawa, kada na ƙasƙantar da shi. Na ƙyautata masa, na masa biyayya matsayin sa na miji, shugaba, uban ƴaƴana, ta wani fanin tamkar yayana. Ya nuna min yasan halin Azz na neman mata, karna damu na cigaba da masa nasiha da addu'a watarana zai daina in sha ALLAHU. Daga ƙarshe ya bani amanar Bilkisu da Falaq tare da ɗora min nauyin nemo sauran iyalin Abdul-wahab na haɗasu na riƙe tare da ɗaukar nauyin rayuwarsu. Sannan ya danƙa min takardun Companynsa na robobi yace na bama iyalan Abdul-wahab ya mallaka musu duniya da lahira. Dan bazai taɓa iya biyan mahaifinsu abinda yay masa a rayuwa ba koda da dukkan abinda ya tara ne. Na amshi komai da hannu biyu, tare da masa addu'a da fatan samun lafiya. Daga nan mukayi zaman meeting komai lauyoyinsa suka saka hannu muma muka saka ni da Muhammad. Fahad kam da pinger print ɗin sa akai amfani dan bashi da wayon yin abinda ya kamata. Takardun Company daya mallakama zuri'ar Abdul-wahab akwai saka hannun Abdul-wahab ɗin sai dan ban san lokacin da ya sakashi yayi ba. Shima dai lauyoyi suka saka hannu na ajiye akan sai na samo sauran iyalan nashi sannan na damƙa musu. Nayi mamakin rashin cewar Adamu komai a wajen, da kuma yanda Abie bai sakashi a maganar ba ko sau ɗaya. Dan har muka gama cike-ciken takardun nan kallonmu kawai yake yi. Wannan abu ga tsaya mun a rai har na ƙudiri aniyar tambayar Abie idan mun kasance mu kaɗai. Amma sai labarin ya canja washe gari na rasa Abie na. Mai yankewa ta raba a gaɓar da nafi buƙatarsa.....” Kuka ya sarƙeta. Da yawan wanda suke a wajen suma hawaye suke najin tsananin tausayinta. A hankali na rarrafa inda take na rungumeta, sai shima Maash yazo ya haɗamu ya rungume mu duka. Ƙwacewa shima Fahad yay yazo ya rungume Yayansa. Haka mukai kuka sosai idan ka cire Maash da idanun ne kawai suka juye sai jijiyoyin kansa da suka tashi sosai. Hakan yasa na sake tabbatar da taurin kansa. Da ƙyar Ummie ta cigaba da faɗin.... “Na shiga ruɗani matuƙa na rashin Abie, amma haka nai tawakkali ina addu'a da fatan dangana wajen UBANGIJI. Badan zuciya ta saba ba, ba kuma dan gangar jiki da ruhi sun haƙura ba na fara dawowa dai-dai. Kwatsam sai ga azzalumin nan yazo min da fuskar yaudara akan na mallaka komai a hannun Azz yana kula da shi. A lokacin ban kawo komai a raina ba, sai dai ina akan nasihar mahaifina. Sannan bazan iya mallaka komaina ahannun Azz ba kodan halinsa akan mata. Za'a iya amfani da wannan damar a lalata komai dan nasan matan banza da dukiya basa taɓa rayuwa a muhalli guda. Dole wataran sai an rasa guda a ciki. Kodai dukiyar ta kakkaɓe a dalilin matan, ko matan su gudu a dalilin ƙarewar dukiyar. A zatona ya fahimceni zai bar ni, amma sai ya cigaba da kawo wasu hanyoyin cikin salon damuna. Kawai sai na fara shan jinin jikina, anya kuwa mutumin nan babu wani abu a ransa. Musamman idan na haɗa yanayinsa da zaman meeting ɗin da akayi na rashin cewarsa komai, da yanda ko wata mahaifina baiyi da rasuwa ba amma yake wannan kai-kawon na son na mallaka dukiya ga ɗansa duk da yasan hallayarsa. Kai akwai abinda ya kamata na sani. Na ɗauki ƙudirin wannan bincike kawai sai ma ya sauƙaƙa min ta hanyar fitomin da mummunar manufarsa. A wata ranar juma'a da na gama kammala shirin komawa office a litinin ɗin satin da zamu shiga ina falo zaune Muhammad na kusa da ni yana homework ina gyara masa, sai Hayat, Falaq, Fahad dake ta tsalle-tsallensu kawai sai gashi ya faɗo mana. Nayi mamakin hakan, babu neman izini babu sanarwar irin wannan shigowa haka. Duk da abin ya sosa raina sai na daurema zuciyata saboda Abie yace na masa biyayya tamkar ƙaninsa na jini, sannan koba komai shi ɗin mahaifin mijina ne. Hijjab dake ajiye a gefena kawai na ɗauka na saka ina masa sannu da zuwa. Bana jin ya amsa min yanda ya kamata, dan ko gaisuwar da su Muhammad sukai masa bai kulasu ba. Fahad ma da ya nufesa yana murna bai taɓa yaron ba ya waske. Nan ɗin ma dai bance komai ba, sai Muhammad nama magana akan ya tattarasu suje wajen Mamansu Fateema (Maman Hayatu) dan lokacin Bilkisu bata da lafiya. Yaran na gama fita na maida hankalina kansa. Cikin sauƙaƙa harshe na ce, “Baba lafiya dai kuwa? Yanzu nake zancen zuwa ni da yara gida mu muku barka da juma'a na sanar maka zan koma zuwa office in sha ALLAHU Monday”. Wani mummunan kallo ya jefeni da shi, cikin ɓacin rai ya ce, “Ummu-Hidaya kina son nuna min kema mai taurin kai ce kenan?”. Cikin nuna mamaki na ce, “Baba taurin kai kuma? Mizaisa na maka taurin kai. Kai fa uba ne a wajena. Ka cancanci sakani ko hanani akan abinda kaga zanyi ba daidai ba. Karka manta ko sanda Abie na raye yakan saka kamin faɗa ko gyara akan wani kuskure idan nayi balle yanzu da banda kowa sai ALLAH sai ku”. “Ƙarya kike Ummu-Hidaya, in da abinda kika faɗa haka yake da baki bijirema umarni na ba. Da baki nunama duniya ni ban isa ba. Idan ma wani abu ne a ranki to bara na fito miki a mutum. Baki da ƙarfin hanani abinda nayi niyya. Na biyo miki ta hanyar lalama ne domin na baki damar rayuwa cikin salama ke da yaƴanki. Dan haka zan miki gargaɗi ba ƙarshe da zai iya taimakonki. Kada kice zaki bijirema umarnina. Idan kuma har kikai hakan kiyi kuka da kanki akan abinda zai iya biyo baya. Ban kuma amince da komawarki office ba ranar litinin ɗin, idan har kallon uban kike min da gaske”. Sosai raina ya sosu da waɗan nan zantuka nashi. Bamma san fushi ya taso min ba na furta masa, “Baba ai baka da hurumin hanani zuwa aiki, inaga Azz ne kawai keda wannan damar matsayinsa na miji. Shima idan naga akwai tauye hakki a cikin al'amarinsa bai zama lallai na masa biyayya ba saboda tun farko ya ɗaukama mahaifina alƙawarin barina, nima kuma ya ɗauka min, idan har yasan hakkin alƙawari da muhimmancin sa kaga bazai bijire ba”. Dariya ya ɗan yi da mun kallon sama da ƙasa, cike da gadara ya furta, “Ga fili ga mai doki”. Yay ficewarsa. Wannan al'amari ya gigitani ya kuma ƙwaɓe min lissafi. Gaba ɗaya komai naji ya ƙwace min. Hankalina yay matuƙar tashi. Mutuwar Abie ta dawo min sabo fil a zuciyata. Nayi kuka irin wanda bazai misaltu ba a wannan yini. Dole na keɓance kaina daga kowa domin yin nazari. Sai ya zamto gaba ɗaya weekend ɗin ya koma min na bincike da nazarin manufarsa. Duk da gargaɗin nashi a monday ɗin haka na tashi da shirin fita aiki. Amma mi sai Azz ya birkice min a wannan safiya kan bazan fita ko'ina ba. Na tambayesa dalili yace ban isa ya faɗa ba. Fita dai office ya soketa har abada. Ko dai na bashi komai ya cigaba da kulamin da shi, ko kuma na bama Baba. Murmushi nayi kawai na takaici, dan na fahimci ɗora shi akai akan keken ɓera. Sai kawai ban kulashi ba na cigaba da shirina. Na gama zan fita ya hanani fita ta hanyar kulle ƙofa. Da farko roƙonsa na farayi da son fahimtar da shi kuskuren da yake neman yi. Amma yaƙi saurarena sai ma sake hawa da yayi. Hakan ya baƙantan rai da zuciya nima na hau sama muka fara rikici. Kamar yanda ya saba duk da tunda muka dawo Nigeria hakan bai sake faruwa ba ya ware ƙwanji ya hau dukana. Da ƙyar na shiga bathroom na rufe kaina ina kuka. Abinda yasa kowa bai sani ba saboda yaran duk sun fita makaranta. Bilkisu kam tana wajen mahaifiyarta saboda damuwar abinda ya faru na zuwanta can dangin Abdul-wahab suka ƙi saurarenta bata da lafiya ma. Abinda yasa a lokacin ban shiga maganar ba akwai shirin da nake yi ya kuma haɗa da nima ina a cikin damuwar ne. Ya cigaba da banbamin masifarsa akan na buɗe ƙofar na masa banza naci kukana sosai a toilet ɗin sannan na wanke ciwukan daya jimun. Haka ya gaji dan kansa ya fita ya bar gidan batare dana fito ba. Nima sai da naji fitar motarsa sannan na buɗe na fito. Bana son yarana su fahimci baƙar rayuwar da nake ciki tsakanina da mahaifinsu na tsawon shekaru, musamman ma Muhammad mai fushi da ƙin duk abinda zai taɓa ni. Dan haka na daure na gyara komai na gyara jikina nasha magani na fita zuwa office ɗin cikin ƙarfin hali kamar yanda nayi niyya tun farko.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ ......Wannan shine mafarin komai. Fita ta office kuma ta sake fusata shi ya cigaba da kunnomin Mu'azz da abubuwa iri-iri ya zamto a tsakanin nan sam babu zaman lafiya ko tausayi a tsakanina da shi. Duka, zagi, gori, har akwai wani dare da yazo min da w..... Kuka ya sarƙeta ta kasa ƙarasawa, sai da tayi sosai sannan ta cigaba da faɗin, “Da wata har ɗakin barci na, ya hanani fita a ɗakin sukai abinda suka so. Zan iya cewa ban kai wayewar gari da numfashi ba. Dan sume musu nayi tsabar tashin hankali, mijina da wata a ɗakina gadon mu na aure. Lokacin dana farfaɗo naga Fatima (Maman Hayatu) da Lawisa a kaina. Tambaya ɗaya na musu ina yarana? Suka bani amsa da suna lafiya kawai na maida idona na rufe. Wannan kuma shine ya zama tushen fara fitar damuwata. Daga kuka sai tasa yarana gaba naita kallo dan na fahimci a wannan gaɓar sune kaɗai gatana. Sune kaɗai abinda ya rage min na kalla naji daɗi kamar yanda mahaifina ya sanar min. Sai kuma matsanancin tausayin rayuwarsu da nake ji, dan bana jin nima zanyi tsawon rai batare da nabi bayan mahaifina ba. Saboda ina jin yanda ƙirjina da zuciyata ke mun nauyi. Bani da wata madafa, na rasa wanda zan fiddoma ainahin damuwata. Duk da kuwa bazanyi butulci ba Mahaifiyar Bilkisu tsaye take a kaina. Itama kuma Maman su Azz a ɗan tsakanin ta jani jikinta sosai. Kasancewar nayi shiru da bakina ban taɓa cewa kowa komai ba akan abinda ke damuna yasa kowa ke fassara al'amarin nawa da kasa yin tawakkali da rashin mahaifina da nayi. Ni kuma ni nasan ainahin matsalata. Bilkisu ta dawo saboda kwanciya ciwo da nayi a tsakanin, sai yazam ita da Lawisa da Fatima ke kula da ni da yaran, jin na yarda da su a raina saboda yanda suke nuna damuwarsu a kaina yasa na damƙa musu amanar yarana batare da su sun san dalili ba ashe Lawisa munafukata ce. Jiyyar kusan sati ɗaya na fara ƙarfafa kaina kodan ƴaƴana, bazan so na tafi na barsu a ƙananun shekarunsu ba. Lokacin Azz yayi tafiya, sai dai ban san takamaiman inama ya tafi ba, kamar mahaifinsa ya barni sai gashi ya dawo a kwanakin dana fara murmurewa. Ni yanzu ganinsa baya bani wani mamaki ko ɗar dan na gama sakashi a layin da ya dace da shi. Ashe ma ya wuce hakan dan sai a ranar yake tabbatar min. Banko kalli inda yake ba na gaisheshi da tambayarsa ko yau kuma miya kawoshi?. Kai tsaye yace dani cika alkawarinsa. Banji komai a kalmarba na ce, “Humm”. Shima Humm ɗin yace min tare da cigaba da faɗin, “Kin mun taurin kai da tunanin babu abinda zan iya gareki saboda baki san wanene Adams ba. To bari na fiddo miki da saninsa. Ni ba kanwar lasa bane ba yarinya. Dan shi kansa mahaifin naki ya buga da ni na kaisa ƙasa balle ke ƙaramar ANT. Na biki ta lallami da hanyar sulhu ta yanda zaki rayu cikin aminci da ƴaƴanki amma kin tabbatar min baƙya buƙata. To abinda na saka Mu'azz yake miki yanzu ƙarami ne. Ni nawa kashe ki zanyi kamar yanda na kashe uban naki, na kuma kashe uwarku da uwar uwarki da iyayen ubanki. Je kabarin Abdul-wahab drivern ubanki ki tambayesa labarin yaya karon battarmu da shi. Alwashi ya ɗauka zai ƙare rayuwarsa a kare rayuwar ubanki shiyyasa na haɗa da shi na kashe a randa nai shirin kashe uban naki. Sai ko gashi shine ya rigashi tafiya batare da ya karesan da ya ɗaukar min alwashi ba. Dan haka zaɓi ya rage naki, tattaro dukkan dukiyar ki danƙa min yanzun nan a hannuna. Ko kuma na ƙwata ta ƙarfin tuwo bayan na kashe ki, na kashe waɗan nan ƴan kuyi-kuyin yaran naki.” Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Harga ALLAH bazan iya ma fassara muku halin dana tsinta kaina a wannan lokacin ba. Dan kalaman wannan baƙin azzalumin ba ƙaramin dukan zuciyata sukayi ba. Duka mai girma da gigita brain da tarwatsa zuciya. Cikin rawar jiki na ce, “Kai ne ka kashe Mamana da mahaifiyarta? Sannan ka kashe mahaifina da iyayensa? Ka kuma kashe Abdul-wahab?”. Dariya ya bushe da ita harda buga ƙafa. Sannan yay min kallon sama da ƙasa ya ce, “Saura ma ke cikason su tare da yaranki biyu idan kika cigaba da mun gadara da taurin kai akan abinda aka tara da gumina aka bar miki da sunan gado. Da kike ganina cikakken ɗan hau ne wlhy, sannan gagararre ne a ƙauyenmu ki bibiyi tarihi na, taƙadaranci yasa na baro gida, samun ubanki yasa naji a raina kakata ta yanke saƙa amma ya nuna min shi ɗin ma shege ne kansa kawai ya sani. Ko karatu dana daure nayi nayine saboda na fahimci baka amsa sunan wane sai da shi. In da yay ma kansa adalcin bani abinda yake hakkina tun farko da yanzu yana rayuwarsa, amma ya nuna min shi wani kwallon shege ne. Hhhh yanzu yana ina? To kema kinada zaɓin rayuwa ko bin bayansa. Na baki daga nan zuwa dare na ga saƙo”. Ya ƙare maganar yana wata shegiyar dariya da miƙe.... Wani irin abine ya tokare min kafar numfashi, sai dai nayi jarumtar fisgoshi cikin azaba da ƙunar zuciya. Dai-dai yana saka ƙafa zai fita na dakatar da shi da faɗin, “Kai matsiyaci maci amana azzalumi, fasiƙi. Naji kaci nasarar kashe zuri'ata bisa dalilai daban-daban. Sai dai na maka alƙawarin ni Ummu-Hidaya Ibrahim ko zaka dinga yankan naman jikina wlhy bazaka mallaki wannan dukiyar da kake kwaɗayi ba. Kuma koda nima ya kasance ƙaddarar mutuwata a hannunka take sai na zamewa rayuwarka bala'i ta inda bakai zato da tsammani ba. Ka kira kanka taƙadari ko, to ai kan naka kawai ka sani, kuma na maka alƙawarin jinin zuri'ata daka salwantar bazai taɓa tafiya a baza ba sai ka biya da FANSA. FANSA a lokacin da baka da madafar dafawa, FANSA a gaban alƙalin alƙalai. FANSA a ranar da gangar jiki ke amsa tambayoyi ba baki ba. FANSA a ranar da ake roron ayyukan alkairi. FANSA a ranar da ake biyan bashi da aiki bada abinda aka karɓa a duniya ba. Idan babu aiki za'ai FANSA da zunubin mai hakki. Kamar yanda wannan dukiyar ta gagareka amsa a hannun mai ita duk da kanada damammaki da gadarar kai shege ne a hannun UMMU-HIDAYA ta ƙara maka nisa ne, nisa mai matuƙar tazarar da sai dai yaro da babba su hangi sararin SAMANIYA a samanta badai taɓawa da hannaye ba. Ai kai matsoracine ma tunda kashewa kake, cikakken namiji fili yake sharewa a gwabza yaƙin nuna ƙwanjin NASARA, Gwarzo na gaskiya ya ɗauki KAMBUN IKO!!!. Na faɗa, na kuma sake maimaitawa, zan kuma sake shelantawa. Ka kuma rubuta ka ajiye kona mutu a dalilin ƙaddarar mutuwata a hannunka take sai an maimaita maka hakan. Kuma koda bana raye wannan dukiyar tafi ƙarfin mallakar ka kai da kaf ZURI'ARKA baƙin TSINANNE, sai dai ku ƙare rayuwarku a ƙarƙashin ALFARMAR ZURI'AR MAHAIFINA”. “Hahhhhh!! Lallai yaro bai san wuta ba sai ya taka. Oh ya TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE kenan. To bari mu gani ni da ke waye shegen. Bazaki mutu ba. Zan barki a raye kuwa ta yanda sai na ɗanɗana miki azabar ruwan DALMA a tsakkiyar tafin hannu. Zakiyi rayuwar da gara mutuwa da ita. Zakiyi rayuwar da ke kanki sai kin tsani kanki da kanki. Zakiyi rayuwar da yaƴanki sai sunji sun tsaneki fiye da komai a rayuwarsu. Zan nisanta su da ke, na rainesu raino irin na bawa da uban gidansa. Fiye da irin rainon da UBANKI yay min. Dan sai na maida su KARNUKAN farauta ta da zan dinga jefama NAMA suna bi da gudu suna ɗauka tamkar wulaƙantatu. Dukiyar da kike gadara da ita ɗanki ne zai juyata ni da kaf ZURI'ATA muna kwance muna ci a cikinta. Sai ya ƙare ƙarfinsa da ƙuruciyarsa akan bauta min kamar yanda na ƙare nawa ƙarfin da ƙuruciyata akan naki uban. Sannan daga ƙarshe na miki alƙawarin zan shinfiɗe miki gawarwakinsu a gabanki bayan koman da kike taƙamar da shi ya dawo hannuna. Muje zuwa wasan ƴar Alonso”. Ya faɗa cike da gadara yana ficewa kafin nace komai. Bamma san yanda akai ba, yanke jiki kawai nayi na faɗi a wajen. Ban tashi farkawa ba sai bayan kwana biyu kamar yanda Bilkisu ta sanar min kwanana biyu a halin suma shiyyasa suka kaini asibiti. Halin da naga Muhammad a ciki ne ya ƙara ɗaga min hankali. Cikin kwanaki biyu duk ya fita a hayyacinsa. Dan haka na tambayeta shine take sanar min ai shima yana dawowa a makaranta lokacin ina sume kasancewar shi ya fara cin karo da ni sai ya ɗauka na mutu ne, shine ya yanke jiki ya faɗi shima. A tare ma aka kawomu asibitin. Sai dai shi bai jimaba ya farfaɗo. Tunda kuma ya farfaɗo basu sake gane kansa ba. Baya cin abinci sai ruwa kawai. Magani kam dama ya tsaneshi sai da ƙyar ake danna masa shi. Kamasa nayi na rungume ina hawaye. Shima yana kuka. A zancen nan da nake muku fa Azz baya gari, tun abinda ya faru na kawo min wata ɗakin barci daya gudu ban sake ganinsa ba har lokacin. Bamma san inda yake ba. Kuma har cikin raina ina son sani kodan jin abinda babansa ya faɗa da saka hannunsa yake mun komai tun farkon auren mu. Waɗan nan damuwar ta Muhammad da Azz ta sake ƙarfafa ciwona har nai jiyya kusan ta sati uku. Daga lokacin kuma komai ya canja daga yanda yake. Ummu-Hidaya ta gaskiya ta gushe. Ciwon HAUKA ya maye gurbi. Tun abin na buga min na ɗan dawo hankalina a wasu lokutan har komai ya rincaɓe ta yanda bana gane komai sai tsananin tsanar Muhammad. Gashi dai shine a mafarkina da ƙasan zuciyata. Amma a duk sanda ya tunkaroni ji nake tamkar na kasheshi na huta. Bana taɓa samun nutsuwa har sai na raunatashi... Kuka ya sarƙeta. Maash ta kamo ta rungume tsam a jikinta..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ .......Kowa a falon kuka yake fiye da zaton mai zato. Idan ka cire prof da muƙarrabansa sai Hajiya ƙarama da tai tagumi kawai. Sai Maash da ke kukan zuci dan babu ɗigon hawaye akan fuskarsa. Sai da kowa yay mai isarsa kafin Ummie ta cigaba da faɗin, “Kuji tsoron ALLAH duk da anan mafi rinjayenku zuri'arsa ne, kuyi alƙalanci na gaskiya. Minene laifin mahaifina ga wannan mutumin? Shin dama ALKAIRI kan zama SHARRI? Ta ina mahaifina ya tauye mutumin nan? Minene laifin su Muhammad idan yace ni na masa ko mahaifina ya masa. Adamu baka tunanin ALLAH yay maka talala ta tsahon rayuwa har zuwa wannan lokacin da kaci alwashi a kansa ba? Ko a tunaninka isarka ko gadarar taka ce ta jagiranceka zuwa yau? Lawisa mina miki a rayuwa? Wane mummunan abu na taɓa aikata miki da aka haɗa hannu da ke wajen cutar da ni. Ke ɗin fa ƴar uwa na ɗauke ki. Jawoki nayi daga rana a lokacin da kike matuƙar buƙatar hakan zuwa cikin inuwa. Na haɗu dake a secondary school first ranar da aka kaini nima kema aka kaiki. Yanda kike ƙazama daga ganinki anga jigatacciya yasa kowa a ajinmu baya son haɗa mu'amularsa da ke. Kin bani matuƙar tausayi dan koba komai rana guda aka kawo mu. Hakan yasa na janyoki jikina hatta da kuɗin break ɗina tare mike rabawa. A randa kika bani labarin aikatau aka kawoki garin Lagos kasancewar baki gane komai baki jin turanci gidan da kike aiki suka sakaki a makaranta yasa na ƙara jin tausayinki. Haka na kaima Abie kuka a kanki. Na roƙesa ya amsoki a gidan da kike ki dawo gidanmu. Soyayyar da yake min tasa bai musa ba ya amsa min ya kuma aiwatar. Sai dai wadda ta kawoki aiki ashe ƴar uwarki ce ta jini dan haka ta nuna bazata bamu ba dole mukai haƙuri. Amma Abie yace zai cigaba da ɗaukar nauyin karatun naki kibar aikatau ɗin. Haka akayi kuwa, duk abinda Abiena yay min a fannin karatu sai ya haɗa da ke, hatta da sutura a lokuta da dama idan aka siyamun nakance kema a saya miki. Haka zai saya miki batare da ƙorafi ba. Hatta da ƴar uwar taki yakan hidimta musu duk dan soyayyar dake tsakaninmu. Hatta da karatu da taimakonna kike yinsa dan baƙya gane komai ba gori ba. A haka muka kammala secondary. Duk da Abiena ya mun aure da Azz mun bar Nigeria bai daina ɗaukar nauyin rayuwarki ba. Kina zuwa masa da batun komawa karatu a fannin lafiya ya biya miki bayan ya tallafa miki kika fara. A haka na dawo na sameki kin zama ma'aikaciyar jinya. Abin ya birgeni na fara tunanin buɗe miki asibiti. Ina gayama Abie ya bani goyon baya ɗari bisa ɗari. Haka ya bani kuɗi na zuba aka gina ƙaramin asibitin shan magani da karɓar haihuwa kawai aka damƙa miki. Sai dai ƙarancin ƙwarewa yasa nai ƙoƙarin sake turaki ƙaro karatu, kafin ki dawo aka sake faɗaɗa asibitin. Ya zama kowa zai iya jiyya aka ƙara sabbin ma'aikata da kayan aiki da bako ina zaka iya samunsu ba aka shugabantar dake kula da komai na asibitin. Abubuwa da yawa kin sani a kaina Lawisa. Rayuwar aurena da sirrina da mahaifina ne kawai bana shering ɗin sa da kowa a rayuwata. Dan haka har mahaifina yabar duniya bai taɓa sanin a halin ƙuncin da nake a gidan aurena ba, na saka a raina watarana komai zai zama labari. Domin ina ƙyautatama mijina zato da fatan watarana girma zai sa ya ajiye wasu abubuwan kodan yaransa dake tasowa. Ko'a lokacin dana dawo a hayyacina na shakera kusan ɗayar nan na buɗe ido na ganki matsayin matar Azz ko sau ɗaya na taɓa canja miki fuska? Kona taɓa bincikarki yaya kika auri mijina? Gashi nan shima da ransa da lafiya Azz na taɓa tuhumarka ya akai ka auri Lawisa? Na taɓa nuna maka ba kayi dai-dai ba har na koma a halin ciwo?. Bama kuba ga ƴaƴana nan, ga Bilkisu nan da ake ganin inada kusanci da ita fiye da kowa akwai wanda na taɓa tambaya yanda akai Lawisa ta auri mijina?. Ba kuma dan banji zafi bane ko banyi mamaki bane, kawai na bar al'amarin matsayin ƙaddara kuma aurene ai ALLAH ya halasta muku dammi ni kuma zan butulce masa bayan yamun ni'imomi daban-daban a rayuwa da ban san adadinsu ba, sannan a halin da nake ciki dolene Azz yay aure ai. Zaman Lawisa da Azz matsayin ma'aurata bazai ƙaran da komai ba, ba kuma zai rageni da komai ba. Hatta da wannan yarinyar (ta nuna Arwa) dana buɗe ido na ganta akace ƴar Lawisa ce har yanzun ban sani ba Azz ne mahaifinta ko wani daban. Dan a sanina nasan gab da rasuwar Abie Lawisa tazo mana da zancen ta samu mijin aure acan garinsu. Sai dai har Abie ya rasu ba'ai auren ba ni kuma nazo na shiga halin dana shiga. To ban sani ba ko tayi wancan auren ko batayi ba, da kuma na dawo hayyacina ganinta matsayin matar Azz ban tambayeta komai ba. Lawisa a cikin wannan duk dana faɗa ta ina na cutar da ke? Minene laifina a gareki? Minene laifin mahaifina da har kika iya bada gudummawar aka halakar da shi akan abinda yake hakkinsa. Ki faɗa min Lawisa! Ki faɗa min....” Kuka yay bala'in sarƙeta har bata iya jan numfashi da ƙyau. A mamakin kowa sai muka ji Hajiya ƙarama na dariya. Babu wanda bai zuba mata ido ba a cikinmu dan mamaki. Sai prof ne ya wani taɓe baki da jan tsaki mai ƙarfi yana gyara zaman ƙasaitarsa shi a dole ga tantirin tsoho. Sai da Hajiya ƙarama tayi mai isarta sannan ta miƙe tana tafa hannaye da yima Ummie wani kallon zako ki sani yau. A gadarance ta ce, “Ummu-Hidaya kenan. Naji duk lissafinki da gorinki akan abinda kika min ke da babanki. Na kuma gode da gori. Dama kuma nasan irin wannan ranar zata zo, gata kuwa tazo. Dalili dai kike buƙata ko, to gashi zan faɗa miki yanzun nan. Komai ya faru ne a dalilin MAHAIFINKI. Tun a ranar farko da aka kaini makaranta kema aka kaiki na gansa son sa ya shige min zuciya sururuf....” Kaff falon nan hatta da Prof a wannan gaɓar sai da ya kalla Hajiya ƙaramar. Cikin halin ko'in kula ta ce, “Eh ku kalleni da ƙyau abinda na faɗa shine gaskiyata. So ne na gaskiya na aure ya shiga cikin ZUCIYATA a ranar farko dana fara ganinsa. Ban damu da zai iya haifata ba, danni ba shekarun na kalla ba NAGARTA da jin soyayya ta gaskiya. Sai dai abin kaico da tashin hankali a gareni ban san ta yaya zan mallakesa ba. Dan haka na shiga ƙulla ta wace hanya zan samu? Kwatsam sai kika shigo rayuwata kika jani jikinki. Nayi farin ciki da hakan domin son da nake ji inama mahaifinki kema ya shafeki. Ƙaunarki ta ƙara tasiri a raina a lokacin da kika kaini ga Mahaifinki matsayin ya taimaka min ga halin da nake a ciki. Bai kumayi musu ba ya amsheni, kinyi ƙoƙarin ganin na dawo gidanku da rayuwa amma innata ta hana hakan. Naji zafin abinda tai min amma na ƙyaleta da tunanin a hakanma zan iya mallakar babanki, idan ta hanani zama ai aure zai maidani zaman din-din-din. Na ɗan fiddo da hanyoyin nuna masa manufata duk da ƙarancin shekaru na amma ya nuna baima san minake yi ba. Banji haushi ba, na kuma ɗauka har cikin raina bai fahimta ɗin ba kasancewar Bature. Idan baki manta ba a cikin hikima nazo miki da labari makamancin irin namu gab da zamu gama karatu. Na nuna miki ƙawar na bala'in son baban ƙawarta amma buɗar bakinki sai kika ce wai bata da tarbiyya ne da kunya. Idan da kece kuma wannan ƙawar wlhy sai kin rabu da ita. Har misali kikai da ni da ke akan naga dai babanki baida mata ko, a misali nace ina sonshi wlhy sai kin rabu da ni har abada. Dan sam abun babu mutunci a ciki babu tarbiyya. A lokacin dariya kawai nai miki amma naji zafi har ƙasan raina. Na kuma fahimci aikine a gabana tuƙuru kenan. Daga ranar ban sake miki maganar ba har aka sha bikinki da Mu'azz. Nayi farin ciki matuƙa jin zaku bar ƙasar ne, a ganina damace agareni. Hakanne kuwa yasa kuna wucewa banyi ƙasa a gwiwa ba na fara aikama babanki sakwanin wasiƙu ta hanyoyi da dama. Amma bai taɓa amsa min ba. Ganin wankin hula zai kaini dare lokaci na wucewa na sameshi har office na fayyace masa sirrin zuciyata cikin roƙo da kuka. Ganin yanda ya shagala a kallona sai na ɗauka zai tausaya min. Amma ina gamawa ya balbaleni da masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Sai da yay mun tass da tabbatar min ai ko aure yake buƙatar yi bazai auri ƴar cikinsa ba, ƴar cikin tasa ma ƙawar ƴarsa da itama yakema kallon ƴa. Ya nuna min nama cire wannan tunanin daga zuciyata har abada kada na sake dawo da shi. Shi kallona yake dai-dai da Ummu-Hidaya, zai kuma cigaba da mun irin wannan kallone har abada. Dan haka idan inaso na shirya na koma makaranta, na kuma zaɓi kowacce nake so zai biya min............✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ......Ba wannan nake buƙata ba, dan haka na baro office ɗin cikin ɓacin rai. A tsakanin har jiyya na kwanta kusan na wata biyu. Da ƙyar aka samo kaina na dawo dai-dai. Na ɗauka nisantarsa da nayi zai canja komai, sai dai sam ba haka bane komai ma kamar ƙaruwar yake yi. Dan haka na yanke hukunci zuwa nace masan zan koma makarantar ko hakan zai sa ya koma fuskanta ta. Nayi mamakin daya amsan da hannu biyu ya kuma kaini makarantar yay min komai, sai zuciyata ta sake ƙarfafani akan zan iya shawo kansa wataran. Haka na cigaba da karatu ina cigaba da bibiyar rayuwarsa har kika dawo. Dawowarki taso canja wasu abubuwan dan na sake samu kusanci da shi fiye da sanda baƙya nan, na kuma sake fito masa da har lokacin ina kan bakana ya taimaka min ko bazai aureni ba yay tarayya da ni koda sau ɗaya ne. Amma sai ya karta min rashin mutuncin da yafi na farko, ya saka drivern sa yamun kora irin ta kare. Suka wulaƙantani mafi munin wulaƙanci da banyi zato daga garesa ba. Da yake so na gaskiya zuciyar take masa banyi fushi ba ko yanke mu'amula da ke har kika buɗen asibiti. A zatona lokacin kin mallaka min asibitin ne, wataran zaki mallaka min takardu matsayin nawa. Dan haka na ɗan ragema kaina damuwa akan mahaifinki. An kai matsayar da kika shawarceni da sake komawa karatu, ban musa miki ba na amsa da hannu biyu na tafi wata ƙasa karatu, ban kumayi wasa ba nayi karatun na dawo, abin farin ciki da kika fara tabbatar min da shi shine faɗaɗa asibiti, na takaici shine kawo wasu ma'aikatan matsayin wanda zamu haɗu mu kula wai da shi. Ni a lokacin zuciyata ta gama bani wannan asibiti mallakina ne, ba wai shugabancinsa nake buƙata ba. Ga soyayyar mahaifinki da maimakon raguwa kullum sake faɗi take a raina duk da inada masoyana gwargwado amma naƙi bama kowa muhimmanci. Anyi bikin buɗe asibiti a daren na bankama mahaifinki ƙwaya na kuma je garesa batare da kun sani ba kasancewar kuma duk barci na sakaku a gidan saboda anan na kwana wajenki. Sai da ya fara sakin jiki mukai nisa ga abinda nake matuƙar buƙata a garesa kawai ya tureni kamar wanda ya tuna wani abu. Ya jefeni da maganganu masu matuƙar zafi da ciwo, amma na danne na duka ina roƙonsa ko sau ɗaya ne ya taimakeni amma mutumin nan ya hankaɗoni waje bayan ya shashsheƙa min maruka da tabbatar min ya min mafi munin tsana a rayuwarsa. Ya kuma bani lokaci nayi gaggawar fita a rayuwarki gaba ɗaya idan ba hakaba zanga matakin da zai ɗauka a kaina. Na nuna masa kada yay wannan gangancin ni mai sonshi ce ta gaskiya, har tayin kashesa an kawo min ban amsa ba kuma wanda ke jikinsa ne daya yarda da shi. Amma sai ya nuna ƙarya nake yana sake wankeni mafi munin wanki ya sake saka Drivern sa a daren ya bar gidan da ni. Wannan zafin da ciwon yasa a washe gari na samu Adams da batun amsar tayinsa. Dan na fahimci bazan samu abinda nake so ba, to kuwa kema da yake komai domin ke sai kin rasa shi gwara ace bana ganinsa a duniyar gaba ɗaya. Wannan ne dalilin dunƙulewar mu da Adams, duk da ban wani saki jiki da shi ba shima sosai. Na kuma amshi umarnin iyayena akan mijin da duka zaɓa min duk da bana jin sonshi bamma taɓa ganinsa ba. Na kuma amshi tayin abokina da muka haɗu a karatuna mai suna Marcel. Na fara masa safarar yara mata kaɗan-kaɗan daga ƙauye mu, sai kuma yazo da buƙatar neman ƙoda. A tsakanin ne babanki yay accident, zan ma iya cewa da ƙodarsa muka fara a wajen treatment. Bayan mutuwarsa dil ɗina da Adams ya ƙare dan haka na buƙaci shere ɗina dan lokacin idanuna sun fara buɗewa da kuɗi. Amma sai ya sake kwaɗaita min batunki da kuma yanda kukayi da shi. Banyi mamaki ba dan ni nasan kina da taurin kai, zama ki iya faɗa masa abinda yafi hakan. Ko musu banyi ba da wannan sabon dil na amsa kuwa, mukai cinikin Shere ɗina akan zamuyi 60-40 muka fara aiki. Sai dai a tsakanin anyi aurena da Sabilu, mukai zaman shekara biyu da shi ya rasu. A randa kikai sumar farko na shock ɗin da kika shiga kan batun Mu'azz da budurwarsa ni na fara miki allura. Shi kuma ya bizne asirin daya amso akan ki tun daga ƙasar Togo. Daga baya kulawar da ɗanki ke baki ya nema wargaza mana aiki, dan duk wanda yasan Awwab tun yana yaro hatsabibin kansa ne. Shi kansa Adams ɗin wlhy yana jin shakkarsa da wasi-wasin karfa wataran ya zame maka ƙayar kifi. Dan akwai lokacin da yay niyyar ya kashesa na dai lallaɓashi akan koba komai zai mana amfani, dan yafi Fahad ƙarfin zuciya. Haka dai ya barshi badan yaso ba. Sai dai mun sake hanyar maidosa tafin hannunmu shima, muka saka ƙiyayya tsakaninku, hakama tsakaninsa da ɗan uwansa. Ni kuma na zama matar Mu'azz saboda aikinmu ya tafi yanda ya kamata, tunda mijina ya mutu na gama takaba. Sannu a hankali abubuwa suka kankama, maganar Adams ta fara tabbata, dan kuwa Awwab ya koma juya dukiyar, duk inda zai shiga ya fita ya sani akan kasuwanci. Har yama fi mahaifinki da ke zafin nama, ga shi da nasibi komai ya taɓa kafin wani lokaci ya zama kuɗaɗe. Tun muna ɗaukar abun ƙarami sai muka fahimci babbane fa, dan dukiya nata hanƙoro da bunƙasa. A tsakanin mukai tunanin warware asirin kanki domin gwadaki ko kin saduda ne, Adamu yazo da malaminsa na Togo, wanda shine yay ainahin asirin dama matsayin mai magani. Ya warware asiri a zuwan magani ya baki, kowa nata farin ciki lafiya ta samu gareki, yayinda mu kuma muke ta shirin kammala dil ɗin mu. Abin mamaki abin tsoro, koda bayan samun lafiyarki Adamu ya tunkareki sai gadararki tafi ta farko, kamar ma an ƙaro miki izza ne. Dan maimakon ki risina ƙaimi aka ƙara kunna miki. Kin saka ɗanki yin katafaren company a garin kano. Kin kuma fara wannan katafaren gidan dake a jerin gidaje na farko da ake alfahari da su a garin Lagos. A babbar anguwa irin wannan. Hakan ya sake haukatamu, dan mun sake tabbatar ba ƙananun kuɗi kika mallaka ba. Hankalinmu ya tashi, mun kuma fahimci idan fa har lafiyarki ta ɗore tofa mu wankin hula ne zai kaimu dare ne. Dan mun gano shirye-shiryen da kike akan Adams saboda shi kaɗai kika sani. Bamuyi ƙasa a gwiwa ba kuwa muka garzaya Togo, muka sake sabunta aiki, muka kuma canama mai maganin wajen zama dan mun san zaku nemeshi. Hakan kuwa akayi, kun nemeshin kamar yanda mukai zairgi, rashin samunsa kuma ya ɗaga muku hankali matuƙa. Ko'a kwalar rigarmu mukam. Bayan kun gama bige-bigen neman maganin asibiti da mutumin, dan babu kalar kai-kawon da baku sha ba daga baya dai kuka haƙora da tunanin mutumin ya mutu ne ma. Bayan shuɗewar watanni Awwab ya ƙarasa gina gidan nan, ɗakkoki ku dawo nan yasa abubuwa suka ɗan fara mana nisa. Dan sai dai kawai nazo sau ɗaya a rana da doctors ɗin ta damu sukema aiki kawai mu dubaki. Dan haka dole muka sake sabon lale musamman daya zama zuwa lokacin shi Awwab ya gama yarda da sakin jiki da ni, ta ɓangaren kakansa ma babu matsala. Shine ya masa magana da nuna masa muhimmancin dawowarmu kusa da su saboda al'amarinki. Da farko yaso ɗan tirjewa, sai daga baya kuma miya gani oho masa ya dai amince. Mun dawo Mansion, Nafisa ta dawo, Mama ma ta dawo, hakama Abdullahi da iyalansa, wannan duk cikin burin kakanku ne daman. Dan haka bai taɓa damuwa ba game da hakan duk da bashine yace duk sauran su dawo ba, saboda ya miki alƙawarin dama sai zuri'arsa sun zama suna kwance ya bautar da ɗanki wajen nemo musu suci su hutama ransu. Shi kansa baida aiki sai yawon bin ƙasashe yana hutawarsa duk da tsufar nan nashi da kike gani matsiyacin. Da kike maganar na auri Mu'azz ban taɓa sonshi ba. Ina zaune da shine kawai dan cika manufa.. Duk da a farko-farkon aure zuciyata ta fara karaya, amma bawai na miƙa wuya bane, soyayya ta gaskiya har yau har gobe mahaifinki kawai nake ma ita Ummu-Hidaya. Tabbas tako ina Mu'azz baida daɗin zama. Dan ko matan da yake bi a waje bawai suna jin daɗin mu'amula da shi bane saboda bai ɗauki mace da wata daraja ba. Kawai dai idan akace kuɗi to ƙarshen zance kenan. Suma kuɗin sukema biyayya. Shiko bin matansa mujarrabu ne a garesa ko nace hakkinki, dan akwai lokutan da sam baya so saboda tsoron Awwab da yake ji. Dan zan iya ce miki wannan ma shine dalilin fara shirina da Awwab, tun da ya gano halayyar sa sai ya fara tausaya min, dan ya fahimci nima bawai zaman daɗi nake da shi ba. Sosai shirinmu na tafiya yanda ya kamata, sai dai maganar buɗe Companyn Kano ne ya fara hargitsa mana lissafi. Dan na kula Adamu sam baya ƙaunar hakan a ransa da gaba ɗayan rayuwarsa. Ga kuma Awwab ɗin ya nuna masa taurin kai a bisa umarninki. Ban fahimci abinda yake jima tsoron ba sai da matashiyar budurwa ƴar jarida mara tsoro ta saka Awwab magana a karo na farko na rayuwarsa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ ......Koni na tsorita, dan duk wanda yasan Awwab yasan baya yarda yay hira da ƴan jarida. Hakan kuma nada nasaba da al'amarin ki, idan har kikaga yayi magana da yan jarida akan abinda ya shafi Bussines ne a kuma filin bussines ɗin kawai. Amma a wannan gaɓar bayan wani kallo da yama yarinyar irin wanda mu kammu shaida ne bayama mace irinsa koma ace bai yaɓa ba kai tsaye ya amshi gayyatarta. Hankali tashe nai kiran Adamu na tura masa faifan video ɗin dan yanata yawo, shine ma latest topic a wannan satin gaba ɗaya. Shima hankalin nashi tashi yayi, dan a ranar ya baro India zuwa Nigeria. Ko gida bai shigo ba daga airport yay Kano. Ba wannan bane kaɗai ya ɗaga mana hankali, akwai yaron Adamu mai suna Commondo dake masa dukkan ayyuka na sharri, kasancewar a gidan nan munada masu naɗar mana bayanai tako ina hatta Fahad dake ƙasar waje sai muka haɗa Awwab da wani yaron Commondo ɗin mai suna Jaga, Jaga irin mutanen nan ne masu wayo matuƙa. Ta duk yanda zasu shiga jikinka ka amince da su ya sani, dan haka duk rashin yarda irin ta Awwab sai da Jaga ya zama makusancinsa, muna murnar zamu samu nasara akan Awwab ta dalilin Jaga na jikinsa sai wasan ya canja, wasu halaye na Awwab suka rinjayi Jaga ya fara daina kawo mana bayanan komai akan duk motsin Awwab, idan ma muka takura sai ya dage mana akan shi bai samo komai ba. Dan haka muka fara sanya masa alamar tambaya. Commondo ya saka aka masa bincike akan al'amarinsa. Sai ko gashi an gano masa Jaga ya koma tsagin Awwab ne. Ya saka ko aka sato masa shi, dan kawai mun yanke shawarar a kashesa. Haka ɗin kuwa akayi, Ni da Commondo mukaje da Jaga har Kano a halin suma cikin companyn da Awwab zai buɗe a ranar buɗe Companyn, zan iya cewa ma har aka fara taron muna a cikin companyn a gabana da kansa ya caka ma Jaga wuƙa. Motsi da mukaji yasa muka shiga maɓoyarmu cikin ɗakin tarkacen machines da suka ajiye. Tacan muka fice dama mun tanadama kammu hanya ta dalilin sabon informer ɗin mu. Muka bar Jaga na shire-shiren mutuwa, mun kuma tabbatar kafin asan da shi ya mutu, idan aka ga gawar kuma a cikin companyn aiki ya tashi, dan dole ne Awwab ya shiga bala'i maganar fara aikin company ya tsaya, a shiga kai-kawon bincike mukuma muyi amfani da wannan damar mu cika burinmu dan mun fahimci abinda muke bibiyarfa sun nuna saura tsinka. Sai dai kuma me, har dare babu wani labari akan al'amarin, har jami'an tsaro mukai ma shune sukazo mana da batun babu wani abu daya faru makamancin wanda muke zargi, sai ma neman ɗora mana wani abu suke daban muka dai sha da ƙyar, ga kuma batun yarinyar nan dole Adamu ya shigo Nigeria. Koda ya isa Kano a can ya samemu, sai dai iya bincike bamu gane komai ba akan al'amarin yarinyar, hakama Jaga bincikenmu ya tabbatar mana ya mutu, Awwab ya saka an fidda gawa ta yanda babu wanda zai iya samun kafar zarginsa. Bamu so haka ba, amma ba komai ai akwai wata damar, koba komai kuma mun kawar da Jaga ɗin dake neman tona mana asiri. Mun cigaba da harkar gabanmu hankali kwance. Sai kuma shigowar yarinyar nan matsayin ƴar aiki ya sake wargaje lissafinmu. Kada kuyi mamakin da ban gane ta ba, saboda a wancan karon bawani kallo na mata sosai ba, akwai kuma facemask a fuskarta eyeglasses, hakama lokacin da tayi hira da Adamu da shi kansa Awwab ɗin ni ban wani maida hankali a kammaninta ba saboda zuciyata ba'anan take ba kuma lokacin ma dai da gilashi. Tabbas Samraah ta wargaza mana komai. Dan yarinyar nan kamar an karanta mata daki-daki ta dinga tafiyar da al'amuran har zuwa wannan gaɓar. Tabbas you are smart, I love you”. Taƙare maganar tana wani kashewa Samraah ido cike da salo... Harara na watsa mata cikin takaici na ce, “Ni kuma Kinga na tsaneki. Tsana mafi munin tsana da nake jin zan iya ɗaukar makami akanki wlhy. Jaka jahila butulu kawai. In sha ALLAHU ƙarshenku bazaiyi ƙyau ba. Ummie kuma ta muku nisa mai tazarar zango da har gaban abada bazaku taɓa iya kamota ba. Jinin iyayenmu kuwa daya rataya a kanku in sha ALLAHU bazai barku sake zaman lafiya ba a rayuwarku daga nan har ranar mutuwarku. Dan yana da nasaba da rashin nasarar ku kuketa wahala na shekara da shekaru har zuwa yanzu kun gagara cimma abu guda. Ciwon da Ummie tayi kuwa ƙaddararta ce wawaye, hakama rabata da ƴaƴanta ƙaddararsu ce. Yanzu da UBANGIJI yaso yaye musu ba gasu ba kukuma har yanzu kuna a ƙasan ƙafafunsu. Kai a tunaninka ka bautar da Ya Awwab yana nema muku duniya kuci kai da zuri'arka ko. Hhhhh baka fahimci ƙarshen labarin naka ba yanzu? Shi da kake tunanin ka bautar, da ku ƴan kwanciya a kawo muku kuci matsayin iyayen gida waye ta ƙaremawa? Waye ya faɗi ƙasa wanwar? Dawa ta ɓare? Da ku, ku ɗin nan marasa tawakkali ga UBANGIJI, marasa tauhidi da yarda da ALLAH ba abin wasan wani banza bane. Idan dai har ƙyautatawa zata iya zama wa irinku mutum bazai taɓa fatan ƙyautatama kowa ba. Dan kune kesa bayin ALLAH tsoron ƙyautata ma mutane a wannan ƙarni, kuke saka a gagara banbance na ƙwarai da butulallu irinku. Kaicon bawan da za'a ƙyautatama da tarin alkairi ya maida da sharri. Kaicon bawan da zai dinga kallon hidimarsa ga wani kamar ta fi ƙarfin ƙyautatawar da yake masa koda ya fitar da hakkinsa. Kai kana ganin kun tallafa ma Abie ya tashi saboda ya shigo ƙasarku matsayin baƙo. Ka hidimta masa, ka masa miye, ka masa miye, miye, ko. To amma malam mai hidima idan har da kunya a tare da kai kuwa ya dace ka zauna bamu wannan labarin ma?. A wannan hidimar da kai masa fa, shima shine ya ɗauki nauyin karatunka har zuwa wata ƙasa. Ya baro iyalanka daga ƙauye suma ya ƙyautata rayuwarsu, ya ɗauke su ya kai su ƙasar da kake ya inganta musu rayuwa da ilimi....” “Ilimi kodai ya lalata musu rayuwa, ta sanadin hakan ɗana ya lalace da neman mata....” A fusace na ce, “Ban gama magabata ba kada ka sake katseni!!!!”. Babu wanda bai kallan ba a falon, dan nayi magana ne fa like wata boss lady, ni kaina naga ƙarfin hali na. Fahad ya kwashe da dariya tare da faɗin, “Duk wanda ya ƙara katseki Aunty Sam ALLAH sai na kwashe miki ƙafafunsa. Cigaba da basu bayani.” Jinjina nai masa da satar kallon Maash, zaune kawai yake kansa a ƙasa ya dafe shi da duka hannayensa. Ummie kam kallona take tana murmushi. Murmushin na mata nima da cigaba da faɗin, “Abie bai lalata maka ɗa ko ɗaya ba. Baƙin halayyarka ce ta lalata su. Ko baka san masu iya magana kance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE ba. To ka binciki kanka da kanka kaine amsar tambayar abinda ke zagaye da zuri'arka. Abie ya baka gida bayan dawowarka, ya baka motar hawa. Ya ɗauki company guda sukutum ya baka tare da kuɗaɗen da zaka kafa Bussines. Ya ɗauki ƴarsa ɗaya tilo ya bama ɗanka aurenta. Duk da wahalar da take sha bata taɓa iya gaya masa ba ta shanye tai haƙuri, har ma tana tattali da fatan haihuwa da shi, a hakan da yake sonshi take. Duk da halin daka nunama mahaifinta na banza, ka kuma fiddo masa da ainahinka a sanda yake gadon asibiti bai gaya mata wanene kai ba saboda halin dattako. Bai ce ta rabu da ɗan ka ba. Bai ce ta tuhumeka da abinda ka aikata masa ba, sai ma cewa yay duk rintsi ta kasance da shi, duk rintsi ta maka biyayya a matsayin ƙaninsa na jini. Kaji halin manyan ƙwarai masu tauhidi. Dan ALLAH abin bai birgeka ba?. A lokacin da kazoma da Ummie baƙin halinka ɗanta nada wayon da zata sanar masa. Ya ƙullaceka a zuciya har kawo yau. Amma ka duba batace ma kowa komai ba har ka aikata abinda kake ganin damace ta baka ka aikata. Har warkewa tai a lokacin da shekarunsa suka kai yasan komai amma ta shanye bata faɗa masa ba. A hakan bata faɗa masa ba da ilimin da UBANGIJI ya bashi ya gano kai ɗin wanene? Amma duk da haka bai tunkareka ba ya barka da halinka shima. Baka tunanin talala suka maka na barinka da ƙarfin ikon ALLAH har azo irin wannan gaɓar da zaka fallasa kanka da kanka?. Ke ko baƙar tsinanna ai bani ma da abin faɗa a kanki. Dan ke baki da banbanci da dabbobin aladu masu cin kashi matsayin abincinsu. Kuma a cikinku duk ma wanda ya ɗauka min ƴan uwa ya dawo min da su. Idan ba haka ba ni ba Ummie bace da zata iya barinku da halinku, take a yanzu zan sakaku kuyi nadama wlhy, dan kunga wayar nan, komai da kuka faɗa ta kwashe a ciki, yanzu kuma zan tabbatar muku da sunana ƴar jarida ne. Bara kuma ku gani”. Kaf falon babu wanda bai waro idanu a kallona ba. Yayinda prof ya zaburo kaina jikinsa na rawa. Babu zato kawai mukaga Maash a tsakkiyar mu. Kallonsa yake kamar zai cinyesa da idanu. Cikin matuƙar fusata ya ce, “Mi zakayi”. A fusace shima prof ɗin ya furta, “Duk abinda zuciyarka take tunanin zan iya. Har yaushe aka haifi ubanta ma balle ita da take tunanin wani abu”.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑵𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚_ .......“Ai ko da kayi mafi girman kuskuren data faɗa zakayi, dan daka taɓa koda kayan jikin wannan wlhy Gara kaje ka ringume transformer kasan dama tsautsayi ya kaika. Oh kai da tunaninka zakayi duk wannan surutun naka ya tafi a banza yaranka su kashe mu ka fice salin alin zuwa airport ka hau jirgin zuwa Saudia daka gama shiri ko, daga can ka wuce ƙasar da kake so. To ai ka makaro. Dan wannan TSUTSAR NAMAN ITAMA NAMA CE. Idan taƙadaranci kakeji ka iya kada ka manta jininka ne ni, na ɗebo daga wasu ɗabi'unka, sai dai ina bi dasu ta hanya mai ƙyau domin maganin irinka. Idan kuma dattako ne, jinin Ibrahim nake, kaga ko gidan ka taras. Bari na faɗa maka abinda baka sani ba. Tun daga randa na gane kai wanene duk wani motsinka a tafin hannuna kake yinsa. Kaf ma'aikatan gidanka da kake gani aikina suke yi.” ya ƙare maganar da kallon ƙofa ya ce, “Bismillah”. Ba prof ba mu kammu sai da zukatanmu suka girgiza. Duk da ni Bama sanin ma'aikatan nai ba tunda ba taɓa zuwa gidansa nayi ba. Isma'il Kuku ne farkon shigowa. Sai maigadi, amintaccensa, drivernsa daya taɓa karyawa, bai san sanda ya bar hannun Commondo ba sai dai har yanzu akwai ɗaurin karaya a hannunsa. Amintaccensa, mai bayin filawa, masu share-share da goge etc. Taga-taga prof yay zai zube ƙasa sai da Hayatu ya taresa yana faɗin, “Hankali dai Baba hankali”. A yanda yay maganar kowa yasan akwai shaƙiyanci a ciki. Aiko Fahad ta bushe da dariya da faɗin, “ALLAH Yaya Hayat dama ka barsa ya ɗan sha ƙasa”. Mangare kan Fahad Ummie tayi kaɗan. Dafe ƙirji Baba prof ɗin yayi. Abin mamaki fuskar Maash da murmushi ya ce, “No no ai lokacin bugawar zuciyar baiyi ba da saura ɗan dakata min.” juyawa yay ya kalla masu bindugun dake zagaye da mu. A take suka sauke bindugun suna murmushi. Sai kuma suka haɗe hanayensu waje guda suka ɗan risina wa Ummie alamar ban haƙuri, nima suka juyo suka rissina min, sukaima Fahad da Hayatu ma haka... A razane Baba prof ya ce, “What?! Ozee. Ni zaku cima amana? Na ɗauki nauyin zuwanku tun daga ƙasarku kuce wani kuke ma aiki ba ni ba?.” “Dama can bakai mukazo yima aikin ba old man. Dan tun kafin kazo garemu shine ya fara zuwa”. Ozee yay maganar cikin nuna girmamawa ga Maash da harshen turanci. Idanu kawai ya lumshe musu ya buɗe su akan Prof da ya gama diriricewa yana kalle-kalle. Murmushi Maash yay da faɗin, “Oh Mr Paul daya ɗakko maka hayarsu kake nema. Hayat!”. Da sauri Hayatu yay salute ɗin Maash ɗin cike da girmamawa yana fita, sai ko ga Mr Paul bayansa da police biyu ya shigo. Maimakon ya kalla Prof sai ya rissina ya gaishe da Maash. “Kuturun bala'i, Yaya kana aljanna ina binka da addu'a wlhy, harma Ministar guda a ƙarƙashin komarka yake. Shegiya nera duniya ce”. Fahad ne da wannan maganar yana miƙewa zaram. Ba shi ba mu kammu abin ya matuƙar razana mu. Mr Paul fa da kowa ya sani Minister mai faɗa aji a ƙasar. Eh kam gaskiyar Fahad Naira maganin wata magana. Yanzu kam Baba prof sai da ya kai ƙasa yana nuna Mr Paul da hannu, murya da bakinsa na rawa ya ce, “Kaima munafukina ne dama Mr Paul?”. Cikin halin ko'in kula Mr Paul ya ce, “Professor magana ce ta kuɗi fa. Sannan magana ta gaskiya Maash yafi ƙarfina, ya wuce da sani na. Bani da zaɓin da ya wuce goya masa baya. Kadai san ni akan kuɗi Mamana ma zan iya badawa”. “Kutumelacy babarka fa? Shege Ministar yasan takarda hhhhhh!!”. Fahad ne da iskancin nan yanzu ma. Yanzu kam kasa daurewa nayi sai da na murmusa ina mai girgiza kaina. Yayinda Hawaye suka ɓallema Prof a bazata. Nan ma murmushin Maash ya sake saki da faɗin, “Inaa ai lokacin kuka ma baiyi ba. Hayat next level.” Sake fita Hayatu yayi sai gashi ya shigo da Jaga. Sai wani takun ƙasaita yake ana bubbuɗewa cikin tsadaddun suit Dan yanzu kam Maash ya ɗaure masa ƙugu. Baba prof zai zabura Jaga ya dafesa yana dariya da faɗin, “No tsoho kwantar da hankalinka ba Fatalwa bane JAGUS ne”. Kalmar JAGUS ɗin nan daya faɗa ita ta sakamu dariya. Dan hatta Maash ɗin sai da yay ɗan girgiza kansa. Cike da izza Jaga ya cigaba da faɗin, “Kun zata na mutu ko? To kwana basu ƙare ba old man. Kasan mu ƴan gidanmu ALLAH ya bamu tsahon rai. Kakana na goma ance shekara ɗari huɗu yayi a duniya, hakama na tara dana takwas dana bakai. Na shidda ne yay ɗari uku da uku, na biyar kuwa ɗari uku da arba'in. Na hudu yay ɗari biyu, na uku kuwa ɗari da hamsin, shine ya fara rage mana mudu. Wanda ya haifi ubanta ɗari da arba'in yayi, babana kuwa har yanzu yana raye ya kusan cika ɗari da hamsin shima. Ya kake tunani akan ni JAGA, ai maybe ma kakana na goma zan gado nayi four hundred inji turawa, larabawa kuma sukace أربعة مئة. Wani tsugunne gayu yay a gaban Baba prof ya kamo gemunsa yana wasa da shi fuskarsa da murmushi ya furta, “To ya kake ganin zaku kasheni tashi ɗaya na tafi tsoho? Abinda fa baku sani ba shi wannan bawan ALLAHn KAINUWA ne, sannan DUTSENE na rimi bashi fargaba ko ta ruwa. KWAI NE kuma CIKIN ƘAYA ajiyar ALLAH. Idan har munanan hallayarku zaku iya jan ra'ayinmu ku lalata mana rayuwa da bamu kuɗi da kayan maye, ta yaya kuke tunanin adali irinsa dake ƙoƙarin ƙyautata rayuwarmu bazai iya janye ra'ayinmu daga gare ku ba. Kai ka godema ALLAH a Muktar nazo nan ba Jaga ba, da wlhy sai na jajjage maka hanjin cikinka tsaf da wuƙa. Kasa a kasheni kai da yaronka da waccan ƴar iskar karuwar yar karuwa”. Ya nuna Hajiya ƙarama. Idanu ta waro waje da faɗin, “Ni ce karuwar ƴar karuwa?”. Muryarta na rawa. Murmushi Jaga yay yana miƙewa cikin wani ɗan iskan rangaji ya isa gabanta, sai da yay mata wani kallon sama da ƙasa sannan ya furta, “Oh maimaici kike buƙata kenan. To aike kin wuce karuwa ma. Matar datai aure kan aure jama'a miya kamata a kirata”. Yay maganar yana juyawa ya kalla kowa a farlon. Cike da shaƙiyanci Fahad ya ce, “Sai dai Uwar ƙaruwar Ya Muktar”. “Oh oh I love you my ƙani. Nima na zama babba”. Jaga ya bama Fahad amsa yana wani tsuke baki kamar zai yi kiss da girgiza kai like yanama ɗan yaro wasa. Dariya mafi yawanmu a falon mukayi, dan hatta Ummie sai da ta murmusa. Uban gayyar dai yanzu ma kai kawai ya ɗan girgiza. Jaga ya cigaba da faɗin, “Yawwa to kinji sunanki MAGAJIYAR KARUWAI. Bara na baku labarin wannan matar, dan nasan da yawanku baku sani ba hatta shi ogan nata kansa. A ƙauyenmu akan haifeta, kuma bata da uba, dan tsohuwarta a yawon tazubar ta samota itama. Bayan ta haifeta aka rirrima akama uwar aure da wani saurayinta da aka laƙama ƴar duk da shi ya rantse ba ƴarsa bace. Oho musu dai haka suka zauna taren ita lawisa na girma, tsangwamar mutane da hantarar da ake mata duk inda ta gitta ana kiranta ƴar shege, ko talla ta ɗakko babu mai saya yasa, a makaranta yara dunya dukanta kenan ƙanwar uwarta da itama take zaman tazubar ɗin anan Lagos ta ɗakkota ta taho da ita aka nema mata gidan aikatau. Tana fara aiki taga yaran gidan na zuwa makaranta itama tace tana so, haka mai gidan ya sakata amma da sharaɗin bazasu na biyan kuɗin aikinta ba. Tako amince, daga ita har ƙanwar uwar tata. Da yake tayi primary a ƙauyen namu, sai dai bata kammala ba. Amma shi mai gidan nan yay duk yanda yay aka sakata a aji ɗaya na sakandire. Daga nan ƙaddara da tsautsayi suka haɗata da Ummien mu ALLAH ya ƙara miki lafiya da nisan kwana. Ya rissina yana haɗe hannunsa wa Ummie. Murmushi ta sakar masa. Yayinda Fahad ya ce, “SARAUNIYA UMMIE ƳAR IBRAHIM MAMAN MUHAMMAD AWWAB DA SAMRAAH DA FAHAD ta amsa maka babban Yaya”. “Godiya nake my ƙani”. Cewar Jaga. Sai kuma ya cigaba da faɗin, kada na jaku da nisa. Tunfa Lawisa na aji biyu ta fara sanin maza, shiyyasa ma ta laƙema kakanmu Alhaji Ibrahim ALLAH ya gafarta masa. Sai dai bata samu nasara ba. Yawon tazubar ɗin nata ya fara yawa bayan ta gama makaranta. Wanda ya auri babarta tana zuwa ƙauye yace ya mata miji da Laminu, idan kuma har bata amince ba zai saki uwarta. Itako uwa bata son barin gidan miji, tacema Lawisa idan bata auri Laminu ba zata tsine mata. Da alama dai bata son tsiniwa, dan haka ta amshi Laminu da hannu biyu akan zata aure amma sai ta gama makaranta. Babu wanda yace a'a, dan a lokacin shima Laminu yana makarantar almajirci bai koma gida ba. Bayan kamar shekara huɗu sai ga Laminu ya dawo, lokacin Lawisa na nan Lagos wai ta zama a malamar asibiti, da akace tazo batun aure ya taso sai ta bijire, ai ko dai aka ɗaura mata aure da Laminu, sannan innarta ta ɗauketa da ƙarfin tuwo takai ƙauye. To abin mamaki kuma bamu san yaya akai ba Lawisa na zuwa ta faɗa soyayyar Laminu, wasu dai na ganin aikin asiri ne ba wani abu ba. Haka dai aka tarkatasu suka taho Lagos dan tace bazata bar aikinta ba. Abinda Lawisa da danginta basu sani ba shima Laminu shegen kansa ne, dan a inda yake ma ya addabi mutane matuƙa, aiko tana kawoshi Lagos idonsa ya buɗe ya fara mu'amula da manyan mutane a riga irinsu su Prof sai ya sake bushewa, dan kuwa wanda ya kashe yaje prison kamashi yay da Lawisa suna ikkanci a ofishinta na asibiti, shine ya bisa har can garinsu ya kashe aka kamashi aka kaisa kotu daga can aka wuce dashi magarƙama. To nadai takaice muku Lawisa taje ƙauye tace Laminu ya mutu a haɗarin mota. Haka akaita kuka da ƴan sadake-sadake musamman iyayensa harna kwana bakwai. Ita kuma ta shiga takaba wai. Bayan ta dawo ta cigaba da harkokinta daga ƙarshe ta auri ɗan oganta”. Ya nuna prof. “Abinda Lawisa da Prof basu sani ba shine. Laminu shine ya koma Commondo kuma yaron prof ne, ita kuma Lawisa mijinta ne uban ƴarta waccan”. Ya nuna Arwa. Wani mugun zabura kuwa Arwa tayi jikinta na rawa. Hannunta dafe da ƙirjinta ta ce, “Na shiga uku ni ɗin?”.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ .......“Tabbas ke kuwa. Da aka faɗa miki Ubanki ya mutu ƙarya akai miki, yana raye yana prison an yanke masa ɗaurin rai-da-rai a lokacin, ita a azaton Lawisa ya tafi kenan, tana son kumaa binne ainahinta ga wanda take tare dasu wato jama'ar wannan gida dake kanki ƴar tata shine tace ya mutu. Sai kuma ga oganta prof yaje ya cirosa a prison ɗin bayan wasu shekaru. A lokacin kuma tana auren ɗansa. Lawisa ta shiga ruɗani da ganin Laminu, yayinda shima hankalinsa ya tashi amma ya dake, sai da suka bar gaban prof ya buɗe mata aiki. Sunci uwar rikici sosai, daga ƙarshe ya barta ta cigaba da rayuwa a wannan gida amma tana bashi wata Share. Da kuma sharaɗin idan an samu abinda suke ma dakon wahalar nan ma zata raba abinda ta samu kaso uku ta bashi ɗaya. Duk dan ya rufa mata asiri ta amince. Sai dai har kawo yau shi Prof fa bai san da wannan alaƙa ba sam. Dan haka suka koma ta bayan fage suna cimasa dun-duniya.” Ai prof baima san sanda ya tafi zai kife ba a karo na biyu Isma'il Kuku ya taresa. Muryarsa na rawa ya nuna Hajiya ƙarama da faɗin, “Lawisa, dama duk zaman da nake da ku ke da Commando kun san juna? Ashe ma Ni dukan jaki kawai nake nabar taiki a kusa da ni. Na gode ALLAH da yasa nayi maganinki a gaɓar da ya dace”. Harara Hajiya Ƙarama da jikinta ya gama sanyi ta zuba masa itama muryar tata na ɗan karkarwa ta ce, “Daga baya kenan. Ji da abinda ke gabanka. Magani kuwa idan ma baka sani ba nine nayi naka”. “Mi kike nufi?”. “Abinda kake nufi”. Dariya Baba prof yay yana wani ɗan buga kansa ya ce, “Abinda ni nake nufi bazai taɓa miki daɗin ji ba wawuya. Ina fatan baki manta lemon da kika sha ba a jiya cikin mota ta kafin mu wuce wajen ɗan iskan mijin naki. To lemo ne mai ɗauke da gubar da zata dinga zagwanye jikinki a hankali bayan ya ruɓar da ke. Ai dama na faɗa kiki sai na kawar da ke, dan ba'a cin amanata a kwana lafiya, yanzu kin yarda ko hhhhh?”. Rawa jikin ta yake har sai da ta kai ƙasa. Sai kuma ta ƙyalkyale da dariya tana nuna shi da faɗin, “Tsohon banza ai TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. Naji ka bani lemo mai guba, nima kuma nasa an maka allura mai guba daka biya da hannunka zakaima Awwab. Kaga idan jikina ya zagwanye kaima naka zai kasance a kandare kar ka zagwanye ɗin wawan tsoho kawai. Ni da kai ai CUTA CE TA ƊAU CUTA ƁARAWO YA SACI AKWATIN MACIJI hhhhhhh”. Nan ma murmushi Maash yayi da katsesu ta hanyar faɗin, “Har yanzu dai ai ba'a gamaba, lokacin rikicin naku da aibanta juna baiyi ba. Kalla nan”. Ya ɗauki remote ya kunna television. Tar tar kuwa hoton Commondo ya fito, hannunsa sanye da Handcuff, gefensa Jannifer ce itama sanye da Handcuff ɗin. A gabansu akwai kayayyaki iri-iri na makamai da wasu kwaleye dake a rufe. Sai yara ƴammata a gefe zaune kawunansu a ƙasa an basu facemask sun saka. Sai ta gefensu kaɗan Marcel ne shima da nashi yaran gabansu zube da tarin makamai. Sai kuma yaran Hajiya ƙarama na asibiti. Ga su Rubayya a kusa da su ita da su Falila. Ba baba prof kawai ba, hatta da Hajiya ƙarama a firguce take gaba ɗaya. Ga Arwa tunda ta zube ƙasa ta kafa mata ido taƙi ta janye hannunta dafe da ƙirjinta. Sai da Commondo ya fara magana da jin ya ambaci sunansa da Commondo sanan Arwa ta juya tana kallonsa jikinta na rawa da lips ɗinta, alamar magana take son tayi amma ta kasa. Kan Commondo ƙasa aka fara masa tambayoyi yana amsawa. “Minene sunanka”?. “Laminu, amma anfi sanina da Commondo yanzu”. “Miye sana'ar ka?”. “Dabaru ne kawai”. “Kamar wane iri?”. “Akan sakani aiki kamar su kisa, fyaɗe, sai saida kayan maye da sauransu.” “Shekara nawa ka ɗauka kana wannan aikin?”. “A ƙalla ashirin da uku”. “Kana da uban gida ne?”. Ɗan jimm yay shiru kamar bazai amsa ba. Jikin prof nata rawa kamar idanunsa zasu faɗo cikin tvn. Sai da aka sake maimaitawa Commondo maganar sannan ya amsa da, “Eh inada uban gida”. Sai kuma yay murmushi “Shike sakaka duk waɗan nan abubuwan kenan?”. “Eh kusan hakan, wasu lokutan kuma aikina ne koma abokan huɗɗarsa”. “Minene sana'asa?”. “Sana'arsa kam bata da iyaka. Amma dai babban mutum ne a ƙasar nan mai faɗa aji. Yana safarar miyagun ƙwayoyi, yana safarar mata zuwa wasu ƙasashe. Yana kuma shigo da makamai. Yanada kamfanin sarrafa magungunan bogi. Sannan yana da alaƙa da manyan mutane da yawa da in na kira sunansu sai an razana. Kaɗan daga sana'oinsa na ɓoye kenan. Na zahiri kam rataye yake a bayan inuwar matar ɗansa da jikansa da yaci amanar mahaifinta bayan ya masa rana shi kuma yay masa dare. Idan zan buɗe muku aiki akan wannan mutumin zakusha mamaki. Amma kafin na ambaci sunansa zan baku sunayen wasu gurare yanzun nan jami'anku suje su yi binciken wajen in har aikin gaskiya zakuyi akansa awa ɗaya tayi yawa gareku, shiyyasa ma bazan faɗi sunansa ba sai kun gama binciken.” Cikin jinjina kai jami'in dake masa tambayiyin ya miƙe, inda ogansu yake yaje, suka ɗan yi magana ya sake dawowa. Takarda da pen aka bama Commondo, sai dai ya nuna musu bai iya rubutu ba. Dole jami'in ya bashi kunne ya gwargwaɗa masa abinda suke son ji. Murmushi Maash ya saki tare da ciro wayarsa a aljihu yay ƴan danne-danne yana kai hannu ya gyara bluetooth ɗin kunnensa alamar waya ya kira. Ana ɗagawa daga can kai tsaye ya furta, “Lokacinka”. Daga haka ya yanke... Zubewa kawai Baba prof yay a jikin kujera wata irin zufa na jiƙesa a dukkan illahirin jikinsa. Kamar yanda Commondo kuwa ya ambata in dai aikin zasuyi sai gashi basu wuce mintuna talatin ba kasancewar duk inda ya basu direct address ne ana zuwa ake ganin abinda ya faɗa ɗin. Na farko companyn Baba prof da Abie ya bashi, zuwa yanzu ya jima da faɗaɗashi sosai ana sarrafa magunguna, sai dai acan ƙarƙashin ƙasa ƙwayoyin mayene kawai iri-iri masu hatsarin gaske. Sai expire magunguna da ake loda ana kaisu arewa da drips, wasu ma ba expire ɗin bane basu da inganci sam. A wajen aka samo cocaine da yawa. Waje na biyu gida ne na marayu da kowa yasan Baba prof ɗin na ɗaya daga cikin masu bada gudumawa a cikinsa ashe yara ne ake safara zuwa ƙasashen waje. Wasu kuma anan ma cikin ƙasar ake kaisu wajen manya suna lalata musu rayuwa. Da yawan yaran da aka bincika akwai alamar daga arewacin ƙasar suke, ƙalilanne yaran kudanci. A dai cikin gidan marayun aka fitar da tarin makamai dake ajiye a cikin wani ɗaki. Hankalin mutane yay matuƙar ɗagawa sosai. Wannan wace irin masiface. Zuwa yanzu kafin ma aji ta bakin Commondo da yawan mutane sun gane prof ɗinne, kasancewar duk wajajen da akaje ɗin yanada muhimmiyar alaƙa da su ta bayyane. Kafin su dawo itama Madam Jannifer aka mata nata tambayoyin, ita kam babu kwana-kwana ta kwashe duk laifinta ta ɗora akan Hajiya Ƙarama da Baba prof ɗin. Ashe itama tana kawo masa mata daga arewacin, ita kuma Hajiya ƙarama ƙoda take sayar mata. Ta kuma tabbatar da Marcel uban gidanta ne ada, yanzu kam Bancy ne. An je binciken ina Bancy yake amma ya gudu. Sai yaran asibitin Hajiya ƙarama da suma suka buɗe aiki da tabbatar da cirar ƙoda da wasu sassan jikin mutane idan sun mutu, wasu turawa ke zuwa su saya. Sai su Falila da suka kasance yaranta. Itace ta kaisu Maash Mansion da sunan aikatau amma aiki suke mata. Ko mazajen da suka aura a gidan duk auren na bogi ne suma yaranta ne. Hasalima mijin Falila so yay ya bijire mata shine ta haɗa tarkon kasheshi a randa sukai kidnapping Paah. Ta sha sakasu abubuwa a gidan musamman ɗaure mahaifiyar Maash dake fama da rashin lafiya da sarƙa a toilet. Sai ta dai-daici zai dawo gida sai ta saka su kwanceta. Sukace ɗauri na ƙarshe da asirinta yaso tonuwa shine sanda matar Maash ɗin ta fara shiga sashen ta sameta a ɗaure har sarƙar taci jikinta. Shigar bazata tayi shiyyasa basu sani ba har sai da abin ya faru, a lokacin sunsha maruka a wajen Hajiya ƙaramar, ta kuma tabbatar musu idan bakinsu ya buɗe wlhy sai ta kashesu. Bayan dawowar jami'an da sukaje binciken sirrikan Baba prof aka buƙaci Commondo ko zai sake cewa wani abu. Murmushi yayi da jinjina kai, ya ce, “Kusan duk abin faɗa ya ƙare, sai dai ga saƙo zan bama professor Adams Isa K/Mashi, akwai wani ajiyayyen sirrinsa a hannuna da shine makasudin fara aiki na a ƙarƙashinsa. A lokacin da nazo Lagos ta sanadin aurena da matata Lawisa da iyaye suka haɗamu acan ƙauye mu. Abinda kowa bai sani ba mijin babarta ya haɗamu aure ne domin na binciko masa wani mutumi dake a jikin wani hoto. Wannan mutumi shine yay cikin Lawisa. Yaje ƙauyenmu ne yin aikin noman wiwi da ake masa a ɓoye. Ita kuma babar lawisa na kai musu tallan ƴar tsala a gonar, shine yay amfani da damar ya dinga amfani da ita har yay mata ciki. Lokacin daya gama harkar nomansa yabar gari ciki bai bayyana ba, sai bayan kusan wata biyu da hakan aka gane tana da cikin, maimakon ai bincike sai aka laƙama ƙanin babata dake matsayin saurayinta, shine aka sakashi dole ya aureta bayan an haifi Lawisa. Shi harga ALLAH yana sonta, amma yayi alƙawarin sai ya binciko wanda yay wannan aika-aika dan ya wanke kansa, wannan shine dalilinsa na sakani aurenta bayan ya samu tabbacin baban nata na anan Lagos ya zama babban mutum, kai tsaye ma ya bani inda zan sameta saboda akwai cikin ƴan garin namu da shi mutumin ya taho dasu nan birni suna masa aiki shine ma ya sanar da mijin babar ita lawisa ainahin gaskiyar yanda aka samu ciki. Sai dai yana jin tsoron bayyanawa ya saka kansa a damuwa dan ya tabbatar ubantan hatsabibine. Bari dai kada na kaiku da nisa. Da taimakon ɗan garin namu nazo jikin Prof.. ɗin, na kuma tabbatar da lallai shine na jikin hoton nan, a kuma cikin hikima na dinga bin hanyoyin dana tabbatar da shi ɗinne ubanta bayan ya fiddoni a prison saboda yana son na kashe masa wani babban ɗan siyasa a lokacin. Dan haka Lawisa ɗiyar Professor Adams Isa K/mashi ce. Idan kuma ya musa hakan inada cikakkun hujjoji bila adadin dazan iya kawowa akan hakan musamman daya kasance uwarta na raye wadda sukai abin tare, wanda akai komai a gabansu suma wasunsu suna raye. Hotonsa ma da aka samu bai san ita uwar lawisa ta ɗauka a cikin kayansa ba dan ita sonshi take a lokacin na gaskiya ta kuma zata shima son nata yake kamar yanda yake mata daɗin baki zai aureta. Sannan itama bata san mijinta ƙanin babata ya ɗauki hoton ba ya bani. Wannan shine saƙona. Sauran kuma tsakanin ni da shine idan mun haɗu a jail.......✍️ 🤔Bantan uban can kai. Kenan auren Hajiya ƙarama da Paah a wace matsaya yake? ALLAH ka rabamu da ruɗaɗɗiyar rayuwa🥲. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_ ......A yanzu kam kaf ɗinmu a cikin falon nan sai da muka miƙe tsaye. Mafi yawanmu jikinmu rawa yake yi. A kaf abubuwan nan saboda mu dai mun san wasu a cikinsu babu abinda yafi girgiza mana zukata irin wannan kalma ta ƙarshe daga Commondo. Hajiya ƙarama ɗiyar Baba prof ce. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Wata gigitacciyar ƙara kawai mukaji Hajiya ƙarama ta saki tana mai zubewa a wajen wanwar. Hakama Baba prof kifowa yay ƙasa daga kujera. Yayinda shima Paah ya zube a wajen sumamme. Hajiya Mammah ta daddage ta banƙara ihu da ambaton “Mun shiga uku baba! Ƴarka kuma???”. Hajiya Mama (Mashi'a) itama dai taga-taga tai zata zuben ta dai samu ya dafe kujera hawaye tuni sun wanke mata fuska. Uncle Abdullahi ne kawai ke tsaye ƙyam akan ƙafafunsa sai dai shima kansa a ƙasa yake. Da alama kodai kuka yake, ko kuma kan nasa ne ke juya masa. Fahad kam jikin Ummie ya shige yana wani bala'in waro idanu waje bakinsa a hangame kamar wanda yaga abin tsoro. Itama Ummien suman zaune tayi tana nuna Baba prof da Hajiya ƙarama dake ƙasa wanwar a sume. Yayinda Maash da ni da Hayat su Mama da ma sauran duk wanda ke falon duk mukai sumar tsaye kawai tamkar an dasa mu a wajen tsabar razanin jin wannan batu.. Gaba ɗaya gidan ya gama rincaɓewa. Hayaniyar zuwan jami'an tsaro da ƴan media ya dawo damu hayyacinmu. Burin ƴan jarida kawai su shigo gidan, sai dai jami'an tsaro dake zagaye da mu sun hana hakan. Ga Hajiya ƙarama na aman jini tana nuna Baba prof tana kuka. Shima kallonta yake da duk sauran ƴaƴansa yana kukan, musamman ma Paah da tunda ya yanke jiki ya faɗi shi baima farfaɗo ba. A haka aka fita dasu compaund aka saka cikin ambulance maimakon motar jami'an tsaro dan dukansu likita suke buƙatar gani. Muda aka bari gida zaune kawai muke jugum-jugum babu mai iya cema ɗan uwansa komai. Sai jami'an tsaro daketa faman kai kawo a lungu da saƙo na gidan da sunan bincike. Musamman ma sashen Hajiya ƙarama. Sun samo gwalai-gwalai ɗan kitt guda, sai ruwan allurar poison ɗin nan da taima Baba prof sauran ta ajiye da shirin yina Maash da Ummie. Sai magunguna da alluran data dingama Ummie nau'i daban-daban. Sai tarin wayoyi da take ɓoyewa da numbers ɗin abokan huɗɗarta ke a ciki. Bayan hakan akwai abubuwa da yawa da mu kammu da su kansu jami'an tsaron basu san ma'anarsu ba. Da ga ƙarshe dai aka tattare sauran yaransu dake aiki a gidan maza da suka rage su huɗu aka wuce da su. Maash, Hayatu, Jaga, Uncle Abdullahi suka bi bayansu dan har yanzu ba'a san ina su Hafizzullah suke ba, ana dai kan bincike. Dole ne a wannan gaɓar Hajiya Mammah, Hajiya Mama su baka matuƙar tausayi, kodan su ɗin mata ne shiyyasa Uncle Abdullahi ya fisu dauriya. Su Azizat kansu kuka suke iya iyawarsu. Dan tunda suke basu taɓa ganin tashin hankali makamancin wannan ba. Ni kaina ban taɓa gani ba. Ummie ce ma ta bani matuƙar mamaki, ko ɗigon hawaye babu a fuskar baiwar ALLAHr nan yanzu. Itace ma ta kamani ta tayar muka nufi sashen mu. Da taimakonta nayi sallar la'asar dan wani irin zazzaɓi mai zafi ne ya gama rufe ni. Mun idar mukaji hayaniya, sai ga Falaq ta shigo da gudu tana kuka. Duk miƙewa mukai kanta, cike da farin ciki. Koda muka fito waje sai muka samu har su Hafizzullah. Ga baƙin Kano da banyi zaton gani ba. Gwaggo Gudidi, Abba, Kawu Musa, Kawu Lurwanu sai Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain da yay musu jagora. Ashe bawan ALLAH har da shi aka ƙwamushe. Ai bamma san na kwasa zuwa jikin Gwaggo Gudidi ba. Kuka na sakar mata kawai, itama sai ta rungumeni tana sharar hawaye. Masauki aka fara kaisu dan su watsa ruwa suyi salla. Badan sun so hakan ba saboda matsuwar zama da Mama Balki suka je duk suka aiwatar. Badai a samu zama ba sai bayan sallar isha'i har su Maash sun dawo gidan. Dama suna asibiti ne wajen su Paah. Sai da suka ga komai ya daidaita sannan suka taho. Baba prof da Hajiya ƙarama na ƙarƙashin kulawar hukuma da likitoci. Sai Arwa da Paah da suke a kulawar asibiti dan su basu da alaƙa da jami'an tsaron. Har lokacin ina nane da su Abba. Sai tambayoyi nake zuba musu akan kowa da bayan tahowata. Cikin ƙarfin hali Abba ke amsa min, dan ya kasa kallona saboda kunya. Nima na fahimci hakan, amma sai ban nuna masa ba. Gwaggo Gudidi kam bakinta ya kasa rufuwa da yaba gidan ita da Kawu Lurwanu. Shi kansa kawu Musa na fahimci na manya kawai yake dan sai faman jinjina kai dai yake kasancewar yanzu duk muna a sashen Maash ne. Kallo ɗaya da nai ma Maash da suka shigo na fahimci a matuƙar gajiye yake. Koma nace alamominsa sun nuna tamkar ma bai da lafiya. Dan sai faman kai hannu yaje saman goshi time to time. A haka yay dauriyar zama suka gaisa da su Kawu Musa. Naji daɗin yanda ya girmama iyayena. Ga Ummie nata ɗawainiya da su itama kamar babu abinda ya dameta. Nan ko itama ɗazun ina kallonta tana sharar hawaye sai dai tana jin motsina ta goge fuskarta ta dake. Sai lokacin na fahimci ɗazun ma saboda mu take dakewar ashe. An gaggaisa da yima juna godiya da addu'oi kafin su Kawu Musa su bama Mama Bilki da Falaq haƙuri, sun amshi laifinsu da kuskurensu ƙwarai da gaske. Sun kuma nuna nadamarsu tun a wancan lokacin dan har Lagos ɗin sunzo nemanta rashin ina zasu kama yasa suka haƙura suka koma. Hatta gadonmu da aka raba da sunan Falaq a ciki, sun kuma tabbatar da yana nan ajiye basu ci ba. Wannan magana ta karyarwa Abba zuciya ya hau sharar hawaye shima. Haka ya shiga bamu haƙuri har Yaya Musaddiq da Maash ya kira a waya video call tun fara zaman. Yanda yake kuka yana faɗa mana wlhy duk Mom ce take cewa su sayar tunda shike wahala da mu, ko yaso bijire mata baya iyawa, wani lokacin sai sun ɗaga abu sun sayar ta dawo yayta kuka da ga baya a ɓoye. Baya jin daɗin abinda ke faruwa da mu a gidan musamman ma ni, amma bai san miyyasa baya iya tsawatar mata ba. Shi kansa yasan an zalunceni fiye da kowa a cikinmu, dan badan tsarewar UBANGIJI ba da kuma tsayawar Yaya Musaddiq akan tarbiyyata dana lalace kamar yanda Mom taso, sai dai shi ALLAH ba'ai masa dole, a ƙarshe dai gashi nan komai yana neman juyewa a kansu. Yanzu haka ba'a san inda Baby take ba. Sun je har dangin mijin nata satin da ya wuce suka musu korar kare akan sanda akai auren ai basu sani ba. Suje can su nema ƴar su suma tuni sun fidda mijin nata a cikin jerin ƴaƴansu. Ashe sauran matansa ma dake tare da shi zaman ƴaƴansu kawai suke yi tuni an raba aurensu tun sanda yayma amaryarsa fyaɗe ta baya ta tona masa asiri. Shine ya gudu yabar ƙasar, daga baya ya dawo ya auri Baby bada saninsu ba. Ƴan uwansa tsiraru da aka gani wajen bikin nasu na binsa ne saboda kwaɗayin abin duniya. Wannan al'amari ya ɗaga mana hankali. Yanzu haka Jalilah na asibiti yau kwana biyu kenan. Ga Abbas sun daki wani yaro a makaranta babansa babban mutum ne yasa an kamasu an rufe yau kwana biyar kenan shima. Munyi yawon bashi haƙuri babu adadi yaƙi sauraren mu ni da sauran iyayen yaran...” kuka ya sarƙe Abba. Daga ni har Hafizzullah da Yaya Musaddiq kukan muke muma. Yayinda gurin kowa yay tsitt, sai ma Ummie ce ke lallashin Hafizzullah dake kusa da ita da Fahad. Niko ina jikin Gwaggo ne da itama ke kukan. Hakama Falaq kuka take sosai ganin muna kuka. Maash ne cikin ƙarfin hali yay gyaran murya. Duk kallonsa mukai, cikin dakewar nan tasa ya furta, “Inaga kukan ba shine mafita ba. Addu'a ne kawai. Sannan in babu damuwa ina son sanin sunan shi mutumin dake tare da yarinyar”. Cikin kuka da zabura Abba ya faɗa masa. Kansa kawai ya jinjina yana miƙewa. Sai da yay ɗan taku biyu a hankali ya furta, “Sai da safen ku”. Daga haka ya haye sama. Da kallo duk muka bisa. Sai da ya ɓacema ganinmu Sheikh Muhammad ya ce, “Abubuwa sun masa yawa. Zuciyar ce kawai a tsaye. Inaga muma ya kamata duk muyi haƙuri mubar komai zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu. Dan ita kanta mahaifiyarsa likitocinta sunzo ganinta. Muma kuma muna buƙatar hutu. Ɗiyata tashi kije ga mijinki kinji”. Ya ƙare maganar yana nuni da ni. Ji nai kamar na nutse a wajen dan kunya. Sai da Gwaggo ta miƙar da ni. Sum-sum na wuce zan tafi Mama Balki Sarkin ƙarfin hali ta dakatar da ni. Kwandon data shirya abincin Maash ɗin ta bani, haka na amsa babu musu na haura saman nima da ƙyar. Na jima tsaye a bakin ƙofar batare da nasan miya kamata nayi ba. Komai da kowa tausayi suke ban a gidan. Hatta ni kaina tausayin kaina nake ji da kaina. Kusan mintuna biyu sannan nai ƙarfin halin buɗe ƙofar na shiga da sallama a bakina.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ ......A kwance na sameshi rai-rai saman kujera idanunsa a lumshe hannunsa dafe da kansa. Ƙafarsa ɗaya a ƙasa ɗayar a saman kujerar ya ɗan dogareta. Har na ajiye basket ɗin saman table na ƙarasa gabansa bai ko motsa ba. Babu alamar ma yasan da shigowata, dan kallo ɗaya zaka masa kasan ya mutaƙar yin nisa a cikin tunani. Gwiyawuna na kai durƙushe ƙasan carpet ɗin saitin inda fuskarsa take. Idanu na zubama ƙaramin pinkish lips ɗinsa da suka bushe na wasu sakanni. Kafin a hankali na kai hannuna saman nashi daya sa a kansa na janye. Har lokacin bai buɗe idanunsa ba, sai na ƙara jin gaba ɗaya zuciyata ta karaya. Mutum mai kaarfin hali irin Ya Awwab kaga yanayinsa ya canja haka ai ba ƙaramin abu bane ba. Bance da shi komai ba na ɗaura hannuna akan botiran shirt ɗinsa na fara ɓallesu. Har sai da na gama duka kafin na miƙe, saman jikin nasa na haye na kwanta gaba ɗayana na kwantar da kaina a ƙirjinsa. Sai kawai na saki masa kuka, dan jina a jikin nasa sai naji wani irin raunin zuciya ya sake mamayeni. Komai daya faru a ɗazun da yanzu ya zame min kamar yanzu-yanzu yake kan faruwa. Nafi minti ɗaya a hakan batare daya tanka min ba kafin naji saukar hannayensa a saman bayana. A hankali muryarsa can ƙasan maƙoshi sosai ya furta, “Miya faru kuma?”. Sai kawai na sake ƙanƙamesa nima, a hankali na furta, “Nayi kewarka”. Rungumeni ya sake yi da ƙyau shima yana wani jan nannauyan numfashi da busa min iskar cikin kunnena. Yanzu kam mun ɗauki tsawon lokaci a hakan da har mu kammu bamu san adadi ba, har na daina kukan na koma jan ajiyar zuciya kamar yanda shima yake yi. Muryata acan ƙasan maƙoshi na furta, “My Hot”. “Uhhyim”. Ya amsa min shima a ƙasan maƙoshin. Kaina na ɗago ina kallonsa. Idanunsa dake lumshe na shafa kaɗan. Sai ya shiga buɗesu a hankalin. Har cikin raina sai da naji tsoron ganin yanda suka canja, sai nai ƙoƙarin rissinar da nawan ina sauke ajiyar zuciya. Haɓata ya kamo ya maido da fuskar tawa, dole na sake kallonsa cikin idon. Alama yay min cikin yanayin ɗan ɗage kai da gira. Sai kawai na sake marairaice masa fuska zan saki kukan. Kansa ya girgiza min yana lumshe ido alamar kar nayi. Baki na taɓe hawayen na sakkowa da gudu. Sake rungumesa nayi na sakar masa shi. Motsawar ƙirjinsa naji kaɗan, sai kuma hannunsa daya tura a cikin gashina. A cikin kunnena ya furta, “Ni dai kar a haifa min yarinya mai saurin kuka”. A yanda yay maganar ne ya sani fara kai masa ƴan ƙananun duka, sai yay ƙoƙarin riƙe hannun nawa yana murmushi. Daga haka ya tashi zaune da ni a jikin nasa. Bathroom ya kaini, da taimakonsa mukai wanka muka fito. Mu duka mukai shafa'i da wutri. Ganin ya ɗauki Alkur'ani ya hau karatu nima sai kawai nayi amfani dana wayarsa. Sosai yin karatun Alqur'anin ya kawo mana sauƙi a zukatanmu. Harna ɗan samu ya sha tea da abincin Mama balki lauma kusan biyar. Nima na ɗan ci, da ga haka ya ɗan zauna dube-dubensa a laptop wanda nasan kawai yana yine badan hankalinsa na a wajen ba. Ni dai dake kwance a jikinsa tun ina kallonsa har barci ya ɗaukeni ban san sanda ya gama ta kwanta ba... Washe gari na tashi da zazzaɓina kamar yanda na saba. Nai ƴan amaye-amayena ya dai taimaka min nayi wanka na kwanta sai barci. Lokacin da nake farkawa rana ta ɗaga. Haka na kimtsa na fito neman abinci dan yunwa nake ji. Shi ko da'alama ma ya jima da barin gidan. Ina sakkowa su Ummie na shigowa da Mama Balki da Fahad sai Hafizzullah. Ashe daga asibiti suke duba jikin Paah da su Baba prof. Jikin Arwa dai kam babu daɗi, dan yarinyar nata aman jini. Wai da safen nan Commondo yake ta roƙon a kaisa ya dubata ta ganshi ya ganta koda sau ɗaya ne matsayin mahaifinta. Abin ƙaddara anama shirin sallamarta dan tun dare ta dawo hayyacinta ita sai kuka data kwana yi kawai. Tana yin ido huɗu da Commondo ɗin babu wanda ya lura ta finciki almakashin hannun nurse ɗin dake canja mata bandage ɗin goshinta sakamakon faɗuwar da tayi a jiya taji ciwo a wajen kawai ta cakamasa a gefen wuya. Ƙoƙarin riƙeta akeyi amma ina sake zarewa take tana caka masa tana kuka da yimusu ALLAH ya isa shi da uwarta. Da kƴar aka iya riƙeta aka ƙwace almakashin, shine kawai ta hau tari sai aman jini, yayinda aka kwashi Commondo zuwa taimakon gaggawa rai a hannun ALLAH. Shine fa akai kiran Maash ya tafi asibitin shi da su Ummie hankali tashe. Yanzu dai haka Commondo sakamakon abinda Arwan ta caka masa wata jijiyarsa ta tsinke. Ita kuma da ƙyar aka shawo kan aman jinin da take yi suka sakata barci. Baba prof kuwa tun a daren jiya allurar da Hajiya ƙarama ta masa ta fara nuna kanta. A yanzu haka daga ƙafarsa zuwa ƙugu duk sun sandare sun daina aiki. Dama Allurar bata mutuwa bace. Zata sabdarar da mutum ne ya zama babu inda ke motsi a tare da shi sai kansa kawai. Da yake gaɓa-gaɓa take bi yanzu haka ta sandarar da ƙafafun zuwa ƙugunsa. Itama Hajiya ƙarama data farka a barcin da suka sakata tana jin abinda Arwa taiwa mahaifinta ta sake rikitowa a gado batun da ake paralysis dai ta tabbata gareta bayan abinda Baba prof ya shayar da ita da bai fara nuna kansa ba dai ita. Al'amarin dai babu daɗin ji sam. Ƴan suna kam dama yau duk suka kama ganansu da safe. Ƴan Kano ne kawai dake shirin wucewa gobe idan ALLAH ya kaimu suma. Naso nace zan bisu, na dai daure saboda halin da gidan ke'a ciki. Ummie ta musu alƙawarin in sha ALLAHU da zarar Falaq tayi arba'in ita da kanta zata ɗaukemu da su Maash duka muje garesu dangi suga Falaq su kuma ga mazajenmu suma mazajen namu suga dangin namu. Gwaggo Gudidi taji daɗin hakan, tace maybe ma sannan Halime amaryar Abba ta haihu dan cikinta ya fara tsufa. Jin hakan Ummie tace to shikenan hakan ma yayi kawai. Suma dai washe gari suka wuce gida ya koma da ga mu sai mu. Hajiya Mammah dai wasan ɓuya take da kowa. Garama Hajiya Mama ta shigo sun gaisa da ƴan Kano har sau biyu. Yau kuma dana tashi jikina babu daɗi sosai dan har ruwa sai da aka sanya min shima ta shigo ta dubani. Sai dai daka ganta kasan bata cikin walwalarta. Duk ta zube a kwana uku kacal idanunta a kukkubure alamar taci kuka sosai. Bama su kaɗai ba mu kammu kowa ya kallemu yasan dauriya ce kawai, shiyyasa ko tattauna zancen abinda ya ke faruwar kowa ya kasa zama yayi da ɗan uwansa. Ga ƴan jarida na damunmu sai dai kowa yaƙi cewa komai a gidan dan uban gayyar bai kula ba. Ya Awwab ɗin ma kwata-kwata ya daina yini a gidan. Sai a yau ɗin da bani da lafiya daya kasance dani na fahimci shima bashi da lafiyar. Dan zuwa yamma duk dauriyarsa sai da ya kai kwance dai. Dole hayatu yazo masa da likitansa. ALLAH sarki Ummie duk ta damu. Shawara da likitansa ya bada akan ya kamata ya samu hutu gaskiya, idan dama hali yay nesa da ƙasar kona ɗan wata ɗaya ne dan jininsa ya hau sama sosai, har yanama zuciyarsa barazana. Hankalinmu ya tashi matuƙa. Duk da yace shi babu inda zai je bamu bi takansa ba Hayatu ya fara shirye-shirye bayan sun tattauna da Uncle Abdullahi. Ɗari bisa ɗari Uncle Abdullahi ya bada shawarar gaba ɗayanmu ya kamata mu wuce ɗin, batun Paah kuma a barshi a hannunsa dan yanzu kunya da tashin hankalin abinda Baba prof ya aikata ma Ummie da iyayenmu da wanda shima ya aikata yasa hatta da shi kansa ƙarfin hali kawai yake na fuskantar gidan. Amma idan akai ɗan nesa da juna zukata suka huta koba komai a tattauna wasu abubuwan. Da wannan shawarar Hayat da Ummie suka amince, cikin ƙanƙanin lokaci akai duk abinda ya dace musamman ga ni da Hafizzullah da Bahijja da Ummie ta amshe da bamu taɓa ƙetare ƙasar ba. Mama da Falaq da su sauran hakan ba komai bane. Haka kuwa akayi sati biyu ciff da faruwar komai muka ɗage zuwa ƙasar Spain kamar yanda Ummie ta buƙata, dan tana son kaima kufan mahaifinta ziyara, inda itama idan za'ace inane tushenta dole tace can ƙasar dan ba'a ado da ƙasar mahaifiya. Naso ace munje asibiti kafin mu wuce. Amma Uncle Abdullahi ya hana hakan. Hajiya Mammah ma bata yarda mun ganta ba. Ita ko Hajiya Mama dama ta koma a satin daya gabata.........✍️ _Ku ƙara hakuri dani dai kunji bayin ALLAH, ni kaina bana gane kaina saboda rikicin gidan Yayanmu maash😂😂😂🤪._ Barka da juma'a. Ina fatan kowa na lafiya. Fataken dare ga shi nan na baki ƙyauta🏃🏃 _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_ ........A randa suka wuce a ranar mahaifin su Azizat tsohon mijin Hajiya Mammah ya iso Nigeria shima. Ya zo da buƙatar amsar yaransa. Hankalin Hajiya Mammah yay matuƙar tashi, taita roƙonsa amma sai buɗar bakin Azizat ɗin da ƙanwarta sukace su gaskiya mahaifinsu zasu bi. Dama tunda abin nan ya faru suka koma sashen Uncle Abdullahi. Damuwa da kukan da suke sha ya sakasu shiga kamar a halin depression. ALLAH sarki ɗan uwa rabin jiki, sai Malika ce ke ƙoƙarin kwantar musu da hankali ita da mahaifiyarta. Ganin yanda suka tubure zasu bi mahaifinsu yasa dole Hajiya Mammah ta sallama. Tana ji tana gani suka tattara kaf kayansu suka bisa zuwa ƙasarsu, ko kallonta basuyi ba sai itace ke famar kuka. Bayan wucewarsu washe gari itama Maman Malika ta bama Uncle Abdullahi shawarar barin Mansion su koma nasu gida tunda aikinsa ya ƙare. Ta kuma bashi haƙuri bisa zargi data dinga masa da magana mara daɗi akan hakan. Dan sunsha tafka rigima akan dawowarsu Mansion batare da kowa ya sani ba. Saboda ita sam ba'a san ranta suka dawo ba a lokacin, sai dai da yake yafi ƙarfinta dole ta haƙura ta sallama ashe shi da tasa manufa. ALLAH sarki rayuwa, duk abinda ya sakaka dariya watarana sai ya saka ka kuka. Hakama wanda ya sakaka kuka zai iya sakaka dariya watarana. Yau ga Hajiya Mammah dake so da burin mulkar Mansion ita kaɗai ƙwallin ƙwal a cikinsa. Sai securitys da aka bari da wasu tsirarun ma'aikata maza. Amma kaf masu aikin nan mata sai da Uncle Abdullahi ya sada kowa da iyayensa da alkairi mai tsoka daga Ummie. Kuka sosai Hajiya Mammah tayi a wannan rana, ta dinga zagaya gida tana sambatu da surkulle kamar wadda ta zare. Kwana biyu dai ta fahimci kanta na neman kwancewa ta tattara itama ta nufi tsohon gidansu na gado inda Baba prof yake rayuwa, tunda shi bai kai ko kaso ɗaya bisa goman girman Mansion ba. Nan ɗin ma dai ba daɗin take ji ba sam. Dan kowa ya watse babu masu aiki ko ɗaya a cikinsa hatta maigadi ma. Ga jami'an tsaro sunma gida kaca-kaca saboda bincike. Haka dai ta raɓa ta zauna dan babu yanda zatayi. Idan ma tace zata bar nan ɗin ina zata je? Ita dai ƴan kuɗaɗen da take samu dama kullum cikin fallasar dasu take da lissafin ai Azizat zata auri Awwab su mallake dukiya. Shiyyasa ɗan abinda take da shi yanzu bawani ya taka kara ya karya bane ba. Dukiyar dake tsakanin Mansion da nan kuwa karo na farko a rayuwarta taji ko tsinke bazata iya taɓawa ba dan ba nata bane ba. Tana matuƙar jin kunyar tace zata koma gidan Uncle Abdullahi kuma kodan cin kashin data dinga ma matarsa da shi kansa. Saboda ita dama ba kowa ta ƙyale ba ko sanda suna Mansion. Tsanantar da jikin Paah yay ya saka Uncle Abdullahi zuwa ya sameta kan ko zataje tai jiyyarsa. Dan shi gaskiya yana matuƙar jin kunyar sanarma su Awwab halin da yake ciki. Balle ma shima Awwab ɗin yana can yana fama da jiyya. Ita kuma Ummue doctors na ƙara treatment ɗin ta yanda ya kamata. Batayi ko jayayya ba ta amsa masa. Haka ta shirya ya ɗauke ta ya kai asibiti batare da sun iya cema junansu komai ba. Dan su a karan kansu ma shakkar tada zancen abinda ya faru sukeyi. Sun fara shiga suka duba Hajiya Ƙarama da ɓarin jiki ke a shanye, sai Arwa da itama ke a kusa da ɗakinta yarinyar na cikin matsanancin depression abin tausayi. Sai Baba prof da komai baya motsi a jikinsa sai kai da idanu, ɗaki ɗaya suke shi da Commondo da Arwa ta tsinkema jijiya shima dai gashi nan ne kawai kwance sai idanun. A yanzu su duka huɗun suna a ƙarƙashin kulawar jami'an tsaro ne. Su asibiti ke kula da komai nasu shiyyasa ba'a buƙatar masu jiyya. Sai Paah ɗin ne kawai, amma duk da haka Uncle Abdullahi yana raba lokacinsa a tsakaninsu musamman Paah da Baba prof ɗin da suka zame masa dole... 🌿⭐🌿⭐🌿 A ɓangaren su Abba kam tunda suka isa gida Abba yayma Mom bayanin Maash ya amshi sunan mijin Baby yace zai bincika ta ɗan fara samuwa. Duk da dai a ƙasan ranta tana jin wani iri, dan koba komai dai Maash ɗin nan mijin Samraah ne. Yarinyar data ɗauka ba komai ba. Koda yake miye ma na ɓatama kanta rai, tasan dai matsayi irin na Maash da dukiyarsa mizaiyi da ita. Ƙilama ko ganinsa batayi balle ya mata kallon macen aurensa. Wannan batu na zuciyarta ta sata samun sassauci. A washe gari aka sallamosu asibiti. Suna zaune ita da Ummanta da Bibaa a falo Halime dake fama da ƙaton cikinta ta shigo tana ɗan hakki. Yanda cikin nata yay girma dole kayi mamakin kamar ba cikin fari ba. Da ga tsayen ta gaishesu da yima Mom ɗin yaya jiki dan bata iya zama sai da taimakon wani. Umma ce kawai ta amsa mata. Mom kam bama ta kalleta ba, yayinda Bibaa taja tsaki ta tashi ta bar falon. Ita kaɗai tasan zafi da raɗaɗin da take ji a zuciyarta a duk sanda ta kalla cikin yarinyar nan. Babu abinda basuyi dan ya zube ba amma ko gezau. Babu komai ai yanzu sun samo abinda zai musu maganinta. Dan teacher ɗinta ya tabbatar mata tayi ƙoƙari ta samo mahaifar Halimen a randa ta haihu. Shiyyasa yanzu ranar haihuwar kawai suke jira. Halime da yanzu ita abinda ma ya isheta shine ya isheta tana gama gaishesu ta fito abinta. Ɗakinta ta koma inda Abba ke jiranta dan yana gidan shima. Yau kuma ranar girkinta ne. Kamata yay ta zauna yana mata sannu. Cike da shagwaɓa ta amsa masa tana miƙa masa ƙafarta da tayi fushi. Amsa yay yana danna mata a hankali suna ƴar hirarsu. Hirar data saka Abban kwasar dariya dan Halimen nata zuba masa shirmen turancinta ne data dage tana koyo. Duk da ma dai a tsakanin nan makarantar ta gagareta saboda bata jin daɗi... Kullum sai Abba yayi waya dasu Samraah yanzu. Ƙoƙarin jawosu jikinsa yake yi domin ya kwaranye abinda ya cusa musu a baya. Su kuma sun saki jiki da shi da alama sun jima suna buƙatar hakan daga garesa amma ya gagara musu. Har dai ranar da su Samraah zasu wuce Spain Mom bata sani ba. Dan Abba ya daina sanar mata komai daya shafesu. Idan ma shawara yake nema Halime ce. Saboda zai iya cewa itace ta dawo dashi kan hanya akan batun su Samraah ɗin. Tunda ta fahimci komai kullum cikin masa nasiha take kamar ba yarinya ƙarama ba. Tun yana fushi da ganin ta shiga hurumin daba nata ba har ya fara fahimtarta. Sannu a hankali ya fahimci kuskuren da take ƙoƙarin nuna masa. Shiyyasa yanzu wani bala'in ƙara son yarinyar yake. Gata dai da ƙarancin shekaru sai hankali da sanin ya kamata. Fatansa dai ALLAH ya sauketa lafiya.... ✨🌿✨🌿✨ “Wai yaushe ne batun tafiya Lagos ɗin nan Daddyn Attahiru. Tunda abubuwa sun lafa inaga ya kamata muje muyima bawan ALLAHn nan godiya. Na kuma sake neman gafararsa akan kuskuren dana tafka. Wlhy gaba ɗaya ko'a zuciyata na tuna kunyar kaina da kaina nake ji”. Murmushi Dad dake zaune idonsa a television yayi, sai kuma ya ɗan kalla Mamyn tare da amsar kofin black tea ɗin da take miƙo masa. Sai da ya kai shayin bakinsa ya ɗan sha sannan ya sauke numfashi. “Karki damu zamuje, sai dai tama ƙara tsayi. Dan yau dana bincika ake sanar min shi da iyalinsa da mahaifiyar tasa duk sun wuce Spain. Dole muyi haƙuri har ALLAH yay musu dawowa.” “Tofa, ba kwana biyu daya wuce kake cemin kun gama magana da PA ɗin nasa ba zamu je a satin nan ba. Yaya akai hakan to?”. “Kin san manyan nan barin ƙasa tamkar zuwa bayi ne su fito suka maidashi. Balle shi Maash dake da jiragen kansa ma. Haka dai zamuyi haƙurin har ALLAH ya maidosu lafiya. Yanzu yaya batun shi Mansoor ɗin? Kin tuntuɓesa akan batun yarinyar nan ya amince? Dan so nake a haɗe bikin nan dana ɗan uwansa kawai a wuce wajen kowama ya huta naji da yarana mata suma”. Murmushi mai ƙayatarwa Mamy tayi, muryarta a sanyaye ta ce, “Ni kasan har yanzu baya wani sakin jiki da ni. Daga gaisuwa dai shike nan. Amma Attahir yace min yaga suna waya sosai da ita. Har yana cemata a weekend ɗin nan zai sake shiga Maidugurin su gaisa. Kaga kuwa idan bai amsheta ba ai bazai ce zai koma gidansu ba bayan zuwan da mukayi muduka ko”. “Eh gaskiya hakanne kam. ALLAH to ya ƙara daidaitasu. Haka zamu cigaba da masa addu'a ALLAH ya cire masa son ita waccan yarinyar. Dan ta masa nisa sosai sai dai haƙuri kawai. ALLAH kuma ya bamu ikon gyara kurakuranmu baki ɗaya”. “Amin” Mamy ta amsa muryarta na sake rauni. A haka Attahir da Mansoor suka shigo falon. Da alama daga wani wajen suke a taren. Kowannensu ledar hannunsa ya ajiye. Kafin su gaida iyayen nasu. Da kulawa suka amsa musu, Attahir ya cigaba da faɗin, “ALLAH duk mun gaji. Yanzu ni da ɗan gata ne Mamy sai ki bani shayin nan na Dad mai zafi nasha na more. Amma nasan ba'a sha miki shayin miji”. Dariya Dad da Mamy sukayi saboda yanda Attahir ɗin ya ƙare maganar abin tausayi. Yayinda Mansoor yay ɗan murmushi kawai dan yanzu ya koya miskilanci. Kofi Mamy ta ɗauka ta saka masa shayin tana faɗin, “A'a babana ai sai na baka. Nasan mika sayo min nima. Ai ba'a hana mai badawa. Man kaima zaka sha ko?”. Ta maida hankalinta akan Mansoor. Kai kawai ya girgiza mata alamar a'a. Sai ma ya yunƙura zai tashi Attahir ya kamasa ya maida yana harararsa. Badan yaso ba ya koma ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Cikin tsaresa da ido Attahir ya ce, “Yaya mukai da kai ne?”. Kai Mansoor ya ɗan sosa, sai kuma ya haɗe hannayensa biyu alamar ban haƙuri. Murya a karye ya ce, “In sha ALLAH zan gyara kayi haƙuri”. Kai kawai Attahir ɗin ya jinjina masa, shi kuma ya maida hankalinsa ga Mamy murya a sanyaye ya ce, “Mamy zan sha”. Murmushi ta sakar masa idanunta na cika da ƙwalla. Haka ta zuba musu kowa ta bashi cike da kulawa. Daga haka suka cigaba da hira. Tun Mansoor na jefa ɗaɗɗaya har dai ya fara sakin jiki. Harma hirar ta koma fannin shirin auren Attahir, daga haka shima Dad ya takalo masa nasa batun da Salimah. Da farko ya ɗan nuna shi ba sonta yake ba, sai da suka dinga masa nasiha da lallashi sannan yace zai ƙara nazari. Abinda ya yanke zai sanarma Attahir. Sun jin daɗin hakan, suka kuma bisu da addu'a su duka........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ .........Isowar mu ƙasar Spain bata zame mana cikin daɗin rai ba. Dan daga airport ma asibiti aka wuce da Maash. Abu kamar wasa ashe dai ciwo ke cinsa sosai yana dannewa. Sai ɗan jigatar tafiyar nan ta sake ruɓu-ruɓu da shi. Koni mai fama da ciki ban kaisa takwarkwashewa ba. Duk da nima dai sai da suka bani gado ba wasu awwani. Bayan komai ya dai-daita muka wuce gida aka barsa nan dan dokarsu babu mai jiyya. Dan nima ina buƙatar nutsuwar. Gida ne a cikin estate da ya amsa sunansa gida. Gida na farko muka shiga, hakan ya sakani sauke ajiyar zuciya, dan in ba haka ba wannan ai sai ka rikice saboda ginin duk iri ɗaya ne ya tafi reras abin sha'awa. Yay min ƙyau da tsari sosai. Ƙaton falone a farko sai gefen haggu da dama daya zama gidan kamar wani sashe biyu. Sai upstairs. Mun sami masu aiki biyu, mace da namiji, cikin girmamawa suke mana sannu da zuwa. Kafin su mana bayanin tsarin gidan. A take Hayatu yace ni na wuce sama, dan nan ne ɗakin Maash yake. Sai Ummie da dama tana da ɗakinta itama dan sun ɗan taɓa zaman jiyyarta anan ama lokacin ne Maash ɗin ya sai gidan. Itama ya rakata nata a side na hannun dama dake dauke da bedrooms huɗu, sama biyu, ƙasa biyu. Ita zata zauna a saman ne, ɗayan ɗakin kusa da ita tace Falaq ta zauna nan ita da Bahijja, dan tace cikakken wankan jego zata fara mata ta gaji da wannan gantallen jego nata kadama Ya Hayat ya saka ran zata bashi yanzu. Dariya muka saka sosai yayinda Hayat ke faman shafa ƙeya. Ɗakunan ƙasa kuma Mama Balki da Baba suma aka basu. Sai Fahad da Hafizzullah suma a side na haggun aka basu sama. Hayat kuma ɗakunan ƙasa koda dai Ummie ta bashi ƴar matarsa ga inda zai fake nan. Hakan yayi sosai. Dan haka babu wanda yaja zancen kowa ya tafi inda aka bashi. Sosai saman yay min ƙyau da ƙyatar da ni. Falo ne madaidaici sai bedroom guda ɗaya tal. Babu kuma ta inda muke da alaƙa da side ɗin bedrooms ɗin su Ummie da nasu Fahad. Komai tsaf yake kuma fari tas kamar kaci. Na dai samu nayi wanka na kwanta dan barci ne a idona sosai. Dama kuma likitocin sun ce a barni na huta sosai. Ban samu nutsuwar fahimtar gidan yanda ya kamata ba sai washe gari. Alhamdullah na tashi jikina yay daɗi ba kamar jiya ba. Sai kuma kewar mijina da son zuwa na ganshi amma ina jin kunya. Haka dai na daure a munafunce na tambayi Yaya Hayat. Shine yace na kwantar da hankalina zuwa anjima zai kaimu mu gansa. Naji daɗin hakan. Haka kuwa akai zuwa yamma muka je muka dubashi, yanama barci. Haka muka sakance kullum muna zuwa mu dubashi, wataran yana ido biyu wataran barci. Randa yake ido biyu ya dage nice zan masa komai, babu yanda na iya haka nake yi ina jin kunya har mu taho. Satinsa ɗaya aka sallamesa ya taho gida shima, dan ya matsa likitocin su sallamesa kin san ya tsani zaman asibiti. Murmushi kawai na ɗanyi lokacin da Hayatu ke sanarma Ummie ina mai jin daɗi a raina. Nima nafi son ya dawo gidan na bashi kulawa da kaina ai. Kamar ko yanda Hayatu ya faɗa da yamma sai gasu da shi. Kowa ya nuna farin cikin ganinsa. Bayan sun gaisa da su Ummie muma muka gaisheshi da masa yaya jiki. Da kai kawai yake amsa mana kafin ya tashi ya haura sama. Kasa tashi nayi dan kunyar idon su Ummie sai da Mama Balki tamin wayon maya tace na tashi ga abincinsa can an shirya na kai masa. A bakin gado na samesa zaune ya zubama ƙofar ido kamar dama ni yake dakon shigowa. Ina shigowar ya wani ɗan lumshe idanunsa da sake buɗesu a kaina. Hannu ya miƙa min alamar nazo garesa. Banyi musu ba kuwa. Saman cinyarsa ya ɗaurani tare da rungumeni muka dinga sakin ajiyar zuciya. Mun jima a haka sannan cikin raɗa nace masa, “Yaya jikin?”. Maimakon amsa min sai ya ɗagoni yana kallon fuskata. Tare da kai babban yatsarsa saman lips ɗina ya ɗan shafa. Idanuna na lumshe a hankali, dan yanda yake zagaya yatsar tashi sai nake jin tsigar jikina na tashi. Saukar hannunsa saman cikina ya sani buɗe idon. Muryarsa a ɗashe ya furta, “Yaya little Ummu-Hidaya?”. “Tana lafiya, tare da yima Abbunta addu'ar samun lafiya mai ɗorewa. Ta yi kewarsa kuma matuƙa”. Wani ɗan langaɓar da kai yayi gefe yana sake ƙanƙance idanu. Jinai sam bazan iya jurar kallon ba na faɗa jikinsa kawai na ƙanƙamesa tare da haɗe lips ɗinmu waje ɗaya.... Rayuwa a Spain wata irin rayuwace da kowa a cikinmu bazai manta da ita ba. Dan mun haɗu ne mun gina wani farin ciki a zukatan junanmu da har abada bazamu manta ba. Idan ka gammu bazaka taɓa ɗauka mu ba jini ɗaya bane. Mama da Ummie sun zama iyaye. Baba ya zama Uba. Maash da Hayat sun zama manyan yayye. Fahad da Hafizzullah sun zama garkuwa. Mukam ƙanne masu matuƙar biyayya gana gaba dasu. A cikin ɗakin mijina kam ni da shi sai sambarka da alhmdllh. Dan dukkan wata soyayya da kulawa ina samu daga garesa harma wadda banyi zato da tsmani ba. Hafizzullah da Bahijja sun koma makaranta. Yayinda Fahad aka fara shiga harkokin Bussines shima. Yaya Musaddiq yazo mana hutun sati ɗaya. Na shiga matuƙar farin ciki da wannan ziyara ni da ƴan uwana da su Ummie duka. A wannan zama ne Ummie ta bamu takardun Company da Abie ya bada a bamu. Munyi kuka munyi godiya sosai. Mun kuma tattauna abubuwa masu yawa da suka jima suna damun kowannenmu. Bayan wucewar Yaya Musaddiq Falaq ta koma ɗakin mijinta dan tayi arba'in. Little Awwab nata wayo Masha ALLAH. Ya Awwab ma jikinsa yayi sauƙi sosai. Kamar yanda Ummie ke sake samun lafiya yanda ya kamata. Dan yanzu haka itama zata fara cigaba da kula da wasu harkokin Bussines ɗin ne anan. Saboda Maash da Hayatu sun koma gantalinsu na ƙasashe. Har Nigeria ashe suna kaɗawa idan ta kama. Sai dai basu taɓa sanar mana ba. Cikina ya fara fitowa ɗan kif da shi, sai dai kunya tasa kullum bana rabo da hijjab in har zan sakko ƙasa wajen su Ummie, ko na saka riga mai burun-burun da ba'a ganewa. A hankali soyayya da shaƙuwa ta fara shiga tsakanin Fahad da Bahijja. Wannan abu yama kowa daɗi, sai dai ita Bahijja na dojewa saboda kunya. Ni da Aunty Falaq muna sake fanfata kuwa. A haka Jaga shima yazo yay mana hutu na sati biyu ya koma Saudiyya. Bayan wucewarsa bai fi da sati uku ba Abba ya kira yake sanar mana Amaryarsa ta haihu ƴan biyu duk maza. Murna sosai muka dinga yi dan mun san lokacin zuwa Nigeria yayi kamar yanda Yaya Awwab yay mana alƙawari. Gashi a ɗan tsakanin shima Yaya Musaddiq zai je ya musu hutun sati biyu. Sai abin ya sake mana dai-dai. Ganin har ana saura kwana uku suna babu Maash babu alamarsa a Spain jikinmu ya fara sanyi. Idan muna waya ko video call nai masa batun tafiyar kuma baya cewa komai sai ya basar ma. Dana fahimci hakan sai na daina masa batun gaba ɗaya. Mun daiyi ɗan gyare-gyaren muna jiran ikon ALLAH. Sai ana gobe suna da safe suka iso Spain shi da Hayat da Fahad. Munyi farin cikin dawowar tasu, amma harga ALLAH na fidda ran zuwanmu Nigeria a lokacin kam. Amma mi sai kawai yace mu shirya jirginmu zai tashi washe gari zuwa Nigeria. Tsabar farin ciki bamma san na rungumeshi agaban Ummie da Mama Balki ba harda manna masa sumba a lips. Sai da naji Hafizzullah da Fahad na dariyar shaƙiyanci sannan na farga. Ai da gudu na sakesa na bar wajen. Ummie na kirana cikin dariya ban waigo ba. Har ta gama haye stairs ɗin yana tsaye a inda ta barshi, ta kuma gefen ido yake kallonta. Ba yau ta saba rungumeshin ba. Sai dai koda kwatance bata taɓa yi a gaban Ummie ba. Sai ma idan shi yaso yin hakan ta doje. Jiyay gaba ɗaya ta saukar masa da kasala. Karo na farko sai yaji nauyi da kunyar Ummie da Mama Balki. Amma sai ya dake abinsa yama cema Hafizzullah ya bashi coffee. Tashi Fahad yay yabi Hafizzullah kitchen ɗin, sai da suka gama iya shegensu wai yayan nasu na borin kunya sannan suka kawo masa coffee ɗin. Yana amsa ya miƙe ya haura sama da shi a hannu. Ai ko suka gimtse bakuna suna dariya sai da Mama Balki ta korasu sashensu. Shigowarsa dai-dai da fitowata wanka. Dan ina shigowa bathroom na wuce dama. Alhamdullah yanzu kam laulayi yayi sauƙi sosai, dan tunda na shiga wata na shidan nan kam sai dai kwaɗayi da ciye-ciye nake. Amma ciwo-ciwon nan da jinin da nake gani duk wata kaɗan-kaɗan duk sun bari. Sai kuma ƙulafucin miji abin har kunya yake sakani. Yanda yake bina da kallon ƙurilla yasa na tura masa baki da kauda nawa idon a kansa. Murmushi ya saki kaɗan da laluba aljihunsa ya fiddo min chocolate ɗaya da indai yana gari ko yay tafiya ne ma zai shigo sai ya shigo min da ita. Bamma san nima nayi murmushin ba da nufosa. Kofin hannunsa ya ajiye yana mai ware min hannayensa duk biyu. Shigewa nai jikin nasa ya ɗagani cak yana juyi dani. Dariya na shiga yi ina ƙanƙamesa da faɗin, “Wayyo My Hot juwa. Juwa my Hot ka bari”. Saman gadon ya sauke ni tare da rungumeni da ƙyau shima yana murmushi. Nima ina ƙanƙame da shi ina faman sauke ajiyar zuciya. Daga haka lissafin ya canja. Tako wane fanni cikin nan baya hanani bashi dukkan kulawar data dace a zahirin rayuwa da shimfiɗarsa. Hakan ke ƙara saka shaƙuwa ta musamman a tsakaninmu da soyayya mai ƙarfi duk da har yanzu daga ni har shi babu wanda ya taɓa furtama ɗan uwansa kalmar (I love you) sai dai a aikace. Hakan kuma ya gamsar da mu ya kuma wadatar. Dan soyayya a baki ba'itace soyayya ba. Soyayya ta gaskiya ma ta wuce batun faɗi da bakin ai sai dai lokaci da yanayi su tabbatar.... WASHE GARI kamar yanda ya faɗa jirginmu ya wulla zuwa ƙasarmu ta haihuwa bayan barinta kusan watanni huɗu kenan. Mun sauka a Lagos inda motocinsa da guards ɗin sa na amana suka zo ɗibarmu airport. Da taimakonsu muka shige motocin dan ƴan jarida da bamu san ta yanda akai suka san zamu shigo ƙasar ba tuni sun kewaye mu. Ga jama'ar gari da muka zame musu ƴan kallo. Ni da shi mota ɗaya muje, dan tunda muka fito a jirgin yana maƙale da hannuna cikin nashi kamar za'a ƙwaceni. Sanye yake cikin ƙananun kaya da suka masa ƙyau sosai. Ni ko abayace a jikina baƙa data mun ɗas, tare da ɗan ɓoye cikina ɗan watanni kusan shida. Ni kaina nasan na ƙara ƙyau da cikar kamala ga ƙibar da ciki ya sani fatata sai ɗaukar ido take mai birgewa. Mun sha matuƙar mamaki da ganin yanda akai ma Maash Mansion gyara. An canja fentinsa da komai na cikinsa. Su Mama Balki an maidosu ainahin sashen da Ummie ta fara mallaka musu sanda take ginin gidan. Haka itama an gyara mata ainahin sashen da tayi da sunan nata. Sai Fahad shima da Hafizzullah, a kwai kuma ainahin sashen da in yayi aure zai zauna da matarsa. Sai Hayat da Falaq Ummie tace nan zasu dawo suma tafi son ganinmu a tare waje guda. Sai kuma mai gayya mai aiki muna dai anan nasa sashen na fil azal. Sai dai yanzu daga ni sai shi ne. An kawo sabbin masu aiki maza da mata. Kowa ya yaba Ummie harda hawayen farin ciki, dan Maash Mansion ya koma ainahin wanda ta tsara a rayuwarta. Bamu wani hutaba sosai a washe gari da safe jirginmu ya sake ɗagawa zuwa Kano ta dabo tumbin giwa.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_ ......Motocin da suka ɗakkomu daga airport na shigowa gidan da suka kawomu na ganesa. Kallonsa nayi kawai, ganin ni yake kallo shima yasa na ɗan hararesa kaɗan. Sai ya saki mun ƙaramin murmushi. Murya can ƙasa ya ce, “Kin gane gidan ne?”. “Hummm taya zan mance sa. Gidan da akayi kidnapping ɗina”. “Harda sharri abun”. Kwantar da kaina nayi a jikin hannunsa ina murmushi. Na ce, “Babu wani sharri sai gaskiya. Ai kaida Yaya Hayat ko humm”. “Miza'a mana?” Ɗan far nayi da idanu na, cike da shagwaɓa na ce, “Sai na bama yaranku labarin rashin jin da kukayi”. Murmushi yayi kam yanzu sosai har haƙoransa na bayyana. Yayinda na shagala da kallonsa dan in yay irin murmushin nan ba ƙaramin ƙyau yake masa ba. Kaɗan na kaima kumatunsa sumbata. Kafin yace wani abu na buɗe motar na fice abuna. Ashe ma kowa ya fito mune kawai a mota. Duk sai naji kunya ta kamani. Haka dai na dake. Shima fitowa yay fuskar nan a haɗe kamar ba shi ya gama murmushi ba yanzu yana ƙoƙarin gyara rigar suit ɗinsa. Ido muka haɗa nai saurin ɗauke nawa na maida ga little Awwab dake hannun Hafizzullah. Duk da gidan ba wani ƙatoto bane ba dan ko kashi ɗaya bisa takwas ɗin Maash Mansion bai kaiba shima dai yayi ƙyau. Kuma yana da nasa girma gwagwado da zai ɗaukemu mu dukanmu. Duk a falo muka zube kowa na maida numfashin gajiyar tafiya duk da ba wani nisa bane. Amma kasancewar ta jiya bata gama sakinmu ba sai duk gamu nan dai. Shi dai uban gayyar bai zauna ba ya shige bedroom ɗinsa. Sai TJ da Hayatu ne keta ɗawainuya da mu. Bamu wuce mintina goma ba aka kawo mana abinci daga gidan su Bahijja. Hameed ne da wannan aikin. Ya zauna an gaisa aka ɗan taɓa hira yace zai wuce. Aiko Bahijja ta maƙale masa dan tana kewar gida. Ba'a hanata binsa ba dan tayi ƙoƙari ma. Muma dai abincin kawai mukaci na marairaicewa Ummie kan zamu fara gaba ni da Falaq da Hafizzullah kafin su taho anjima. Dan har yanzu tara ma batayi ba. Hanyar bedroom ɗin da Maash ya shiga Ummie ta nuna min. Ta ce, “Maza jeki mijinki ne da wannan ikon. Idan ya amince ni nawa addu'a ne daughter. Kema tashi ki gayama naki”. Tai nuni da Falaq. A kunyace duk muka tashi, yayinda Fahad da Hafizzullah ke faman mana dariyar shaƙiyanci. Samarin nan sun ishi kowa. Bare mu da suka sama ido ALLAH ya aurar da su mu huta dai. Idan kuma da mai so a fans ɗinki bily yazo na sayar masa😂. Banyi mamakin samunsa yana barci ba hankali kwance. Dama nayi zargin hakan tunda naga ya shiga bai fito ba kusan awa ɗaya da rabi. Ashe shi barcinsa yake sha hankali kwance. Kayan daya cire ya zube a kujera yana cikin duvet abinsa ya ƙure ac ya rage fitilar ɗakin kamar dare. Kusa da shi na ɗan zauna dan harga ALLAH na matsu naje naga ƴan uwana bazan iya haƙura har sai ya tashi dan kansa ba. Sai da na ɗan zubama fuskar tashi ido na kusan mintuna biyu kafin na kai yatsana saman girarsa mai cike da baƙin gashi na shafa. A hakankali na gangaro har saman hancinsa na sauka kan mitsitsin bakinsa. Sosai barcin ya masa nauyi dan bashi da alamar motsawa. Sai kawai na rankwafa na sumbaci lips ɗin nasa. Ina ƙoƙarin janyewa caraf aka riƙe nawan. Idanu na waro sosai dan mamaki. Ashe idonsa biyu yay likimo. Mintsini na dinga kai masa amma kota kaina baibi ba, sai ma jawoni da yay saman gadon ya sakani cikin bargon. Duk shagwaɓa da roƙon da nake masa yay kunnen uwar shegu dani ya shiga yin yanda yaso dani. Bamma san na bada kai bori ya hau ba. Dan mutumin nan ku barni da abuna kawai ni nasan sirrin kayana. Cike da shagwaɓa nake kallon agogo tamkar zanyi kuka. Shiko ko'a kwalar rigarsa gashinsa yake tsanewa tamkar bai san inayi ba. Haka na ɗauka mai na shafa na gyara fuskata inata faman kumbure-kumbure. Rasa yaya ma zanyi nayi, dole na ɗauka waya na kira Aunty Falaq nace ta taimakeni da akwatin kayana. Dariya ta dingamin da tsokana, sai da taji zan mata kuka tace gashi nan a kofar ɗaki ta ajiye. Haka na leƙo na ɗauka. Shiri nayi cikin siket da rigar lass da duka min ƙyau sosai na fito a matar Maash ɗina. Shi dai yana zaune yana kallona. Sai da na gama nazo inda yake, cikin sanyin murya na ce, “Yaya to waye zai kaimu?”. “Ina?”. Ya tambaya cikin halin ko'in kula. Idanu na waro ina kaiwa zaune kusa da shi. Cikin sake marairaice wa nace, “Dan ALLAH my Hot kada kasa na maka kuka. Kafa san gidan Abba zamuje yaufa ne sunan. Ɗazu ma tambayarka Ummie tace nazo nayi shine.. shine kai kuma...” Na kasa ƙarasawa. “Uhhm Ni kuma! Ni kuma mi?”. Ya faɗa cike da salon ɗage gira sama. Hannayena duka biyu na saka kan fuskata na ce, “Ai ba saina faɗa ba. Dan ALLAH kace muje ALLAH so nake naje naci shinkafar sunan irin saukewar farko ɗin nan kaga fa har sha biyu saura”. “Ohhh kice kwaɗayi ma zaki je ashe?”. “ALLAH Yaya Awwab bazaka gane ba. Tunfa muna Spain nake sha'awar cin shinkafar suna, kaga tunda yanzu ga dama ai sai naje naci ko”. Idanunsa da ya kafeni da su ya ɗan jaa luuu yana jinjina min kansa. Sai kuma ya kalla agogon ɗakin. A saman lips ya furta, “Sai yaushe zaku dawo?”. “Lah Yaya bacan zamu kwana ba wai?”. Kansa ya girgiza min alamar a'a. Sai kuma ya miƙe ya nufi akwatin ya ɗauka kaya. Sai da ya kammala sakawa sannan ya dawo inda nake da wani ƙaramin kit a hannunsa. Sarƙace ya ciro a ciki da kansa ya saka min harda ƴan kunnenta da zobe da abin hannu. Tayi ƙyau sosai daka ganta kaga diamond. Kallonsa nayi idanuna cike da ƙwalla. Sai ya ɗauke kansa tare da faɗin, “Let's go”. Baki na buɗe zanyi magana ya ce, “Shiiiii!!! Bana son surutu”. Daga haka yaja hannuna muka fice. Falaq da Fahad da Hafizzullah kawai muka samu a falo wai suna jirana. Sai Hayatu dake waya a gefe Little Awwab a hannunsa. Gaisheshi suka shiga yi, ya amsa musu da kai, kafin ya tambayesu su Ummie. Falaq tace sun kwanta suna hutawa wai kar a tashesu sai lokacin tafiya gidan suna. Murmushi kawai ya ɗan yi da maida kallonsa kan Hayat daya gama wayar ya nufo mu, sai da ya amshi little Awwab a hannunsa sannan yay masa nuni da mu. “Waɗan nan ya za'ai da su?”. Murmushi Hayatu yay da amsa masa da “An gama shirya motocin tafiyar tasu. Hafiz da Fahad sunce zasu iya kaisu sai guards da zasu musu rakkiya, idan sun ajiyesu sai su dawo”. “Okay yayi hakan ma”. Daga haka yaja bakinsa yay shiru. Sai Hayat yace muyi himma. Sosai dukanmu farin ciki ya kama mu. Musamman ma su Fahad da aka samu ƙafar gantali, dama a matse suke tun ɗazun. Banyi zaton zai biyomu har wajen ba. Amma a mamakina sai naga ya miƙe riƙe da little Awwab ɗin ya kama hannuna muka fito. Har jikin motar da zamu shiga ya buɗe min da kansa yay min nunin na shiga. Tsayawa nai kawai ina kallonsa kamar yanda shima yake kallona. Sai da mukaga hasken camara kammu sannan muka dawo hayyacinmu. Duk juyawa mukai, Hafiz da Fahad ne ashe ke ɗaukar mu hoto. Da sauri suka shige mota suna shafar kawuna. Nima sai kawai na shiga inda ya buɗe min ɗin na zauna. Ɗan duƙowa yay ya gyara min gyalena da ya ɗan sauka sannan ya saka mun little akan cinya ya sumbaci gefen kumatuna. Cikin kunne ya raɗa min, “Banda rashin ji babyna bata gama ƙwari ba”. Kafin ma na ɗago na kallesa ya janye jikinsa ya rufe ƙofar. Kallonsa nayi idanuna a narke. Kafin na motsa lips ɗina a hankali na furta, “Zanyi kewarka”. Wani ɗan iskan Murmushi ya sakar min da ƙanƙance idanunsa ya ɗan ɗage min gira ɗaya. Sai kawai na duƙar da nawa kan nima ina murmushi ganin Hayatu na kallonmu. Sai da muka fita a gate ɗin Fahad dake gefen Hafiz dake driving yay gyaran murya da faɗin, “Gaskiya mudai Aunty a dinga sassautawa kar a ƙona mu”. Daga ni har Falaq kallonsa mukayi, duk da nasan baya cema Falaq aunty. Yayinda Hafizzullah ke dariya ya ce, “Faɗa musu dai. In ba haka ba ALLAH ban komawa school sai da mata”. Dariya Falaq ta saka, yayinda na riƙe baki ina kallon Hafizzullah ɗin ta mirror. “Lallai yaron nan zama da Fahad yasa kaima ka fetsare ko? Aiko duk zanyi maganinku. Bari mu dawo zan faɗa masa duk abinda kukace a motar nan”. Da sauri har hada baki suke wajen bani haƙuri. Falaq dai nata dariya... Mun iso anguwarmu lafiya. Ban san nayi kewarta ba sai da muka shigo cikinta. Komai yana a yanda na barsa. Ɗan cigaban da aka samu a shekara ɗaya da wasu watanni da bana nan ba wasu masu yawa bane. Murmushi kawai nake saki har motocinmi uku sukai parking a ƙofar gidan Abba. Ta farko data bayanmu duk guards ɗinsa ne. Sai mu a motar tsakkiya fara tass dako makaho ya laluba yasan an sayeta da kuɗaɗe masu tsokar gaske. Tunda muka shigo anguwar aketa kallonmu. Barema cikin layinmu wasu har biyowa sukai suga su wanene a ciki. Kafin Hafiz da Fahad su fita guards ɗin har sun fito. Sune suka buɗe mana ni da Falaq, kamar yanda suka buɗema Fahad da Hafizzullah........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ ......Jinai ma hawaye na neman cika mun ido. Amma haka na daure na dake abina dan yanzu fa ba da bace. Matar Muhammad Awwab El-Mu'azz Maash nake. Amsar handbag ɗina guard ɗin ɓangaren da nake yayi da sauri, yayinda ni kuma na saka little Awwab a kafaɗa na zuro ƙafata dake sanye cikin takalmi mai ƙarancin tudu silver sai sheƙi yake, ya wani masifar haska ƴar ƙafata da tai cas a ciki. Cike da ƙasaitar da ban san ta fara bin jinina irin ta matan manya🤪 ba na fito. Ni kaina a yanda nai action ɗin fitowar nasan nayi barazana a wajen Bily. Dan a take shock ɗin mutane da yawa ya bayyana saman fuskokinsu. Aunty Zakiyya dake tsaye tare da wasu mata da alama rakosu tayi kota tarosu ce tai wani masifar zabura da ƙwala kiran sunana cike da farin ciki tazo ta haɗa ni da little ta rungume. Kafin kace mi yara sun fara cillawa da gudu cikin gida suna faɗin ga Samraah. Ya ALLAH da ƙyar muka samu shiga cikin gidan. Hafizzullah riƙe da handbag ɗina daya amsa hannun guard ɗin nan. Mu huɗun duk muka shiga har Fahad. Cikin lokaci kaɗan gida ya yamutse, na ɗaki nata fitowa. Ni dai ina rungume jikin Gwaggo Gudidi da itama ta fito. Hango Mom da tai kamar mutuwar tsaye yasa na saki Gwaggo Gudidin na nufeta na rungume. Dan harga ALLAH wani irin kewarta nake ji, na yarda da batun masu iya magana da sukance sabo akewa kuka ba mutuwa ba. Farin cikin da nake ciki da ƴan uwa da suka lulluɓeni yasa sam bamma fahimci halin da Mom ɗin ke ciki ba. Da ƙyar aka sarara min saboda Gwaggo Abu datai maganar su barni na zauna bani kaɗai bace ina fama da kaina sai jagwalgwala ni suke. Kai tsaye kowa ya fahimci inda ta dosa, dan koba'a fada ba duk mai hankali ya ganni yasan inada ciki. Anan tsakar gida muka zauna a tabarma dan na samu damar gaisawa da kowa. Ƴan uwan, maƙwafta dama yara nan fa aka shiga gaisuwa. Yayinda yaran keta shigowa da kayayyaki. Ashe Hayatu ne ya lodosu a motar bisa umarnin uban gidan nashi batare da saninmu ba. Cike da shaƙiyanci abokan wasa ke tambayar wai cikina wata nawa ne. Harararsu kawai na dinga yi naƙi faɗa, da naga zasu takura min ma sai na gabatar musu da aunty Falaq. Ai ko nan take aka koma murnar ganin ƴar uwa, dan akwai dangin ɓangaren babanmu da yawa da sukazo daga Gwarzo kasancewar dai akwai zuminci a tsakaninsu da dangin mahaifiyar tamu su Abba. Sai kuma aka koma koke-koken yima iyayenmu addu'a. Kiran sallar azhar ya taimakemu muka samu sararawar mutane. Sashen Mom da ban sake gani ba tunda na rungumeta ɗazun muka shiga. Babu mutane sosai dan wai bata gayyaci kowa ba. Hasalima tun ɗazun tana ɗaki ihun zuwane ya sa ta fito har mutane suka ganta a yau ɗin. Zaune muka sameta ta zabga tagumi. Zama nai kusa da ita na sake rungumeta. Koba komai dai ita muke ma kallon uwa dan itace ta rainemu. Sai da na ɗan jima a jikinta sannan na ɗago cike da kulawa da girmamawa na gaisheta. Muryarta na rawa ta amsa min, ban damu ba na tambayarta ina su auta naga banga kowa ba sai ita kaɗai sai Ummanta da itama na gaisar. Umman tata ke sanar min ai sun ɗan fita ne. Kaina na jinjina da faɗin, “Mom bari muyi salla yau akwai labari, so nake ki bani labarin duk abinda akayi bana nan nayi kewarku sosai. Hanun Aunty Falaq naja muka wuce tsohon ɗakina dan Little Awwab na hannun su Gwaggo an goyesa, su Hafizzullah kam tuni sukai gaba abinsu. Mun ɗauro alwala zamu fara salla Aunty Falaq ke faɗin, “Sis... Matar nan kamar batai murna da ganinki ba. Da fa muka shigo kamar kuka take”. Murmushi na mata da faɗin, “Kai aunty maybe na murnar ganinmu ne. Kin san fa itace ta riƙemu”. Humm kawai tace badan ta yarda ba ta kabbara sallarta. Nima sai na kabbara tawan. Bayan mun idar na ciro wayata a jaka dake ruri. Ganin Yaya Awwab ke mun video call da sauri na ɗaga. Tar-tar kuwa ya fito akan screen ɗin kamar na taɓashi na kama. Ganinsa zaune kamar a bedroom yasa na ɗan waro idanu. A shagwaɓe na ce, “Salla fa?”. Sai da ya ɗan kalla agogon hannunsa tare da lumshe idanun ya buɗesu a kaina sannan ya motsa lips ɗinsa ya furta, “Yanzu kikayi naki ke kenan?”. Kai na jinjina masa. Shima ɗan taɓe bakinsa yay da jinjina kansa ya ce, “Yayi. A ina kike nan?”. Back camara na maida na haska masa ɗakin kaf sannan na maida ta gaba fuskata da murmushi na ce, “Tsohon ɗakina ne munyi salla da aunty Falaq”. Zaune ya tashi da ƙyau yana faɗin, “Sake haskawa na gani”. Babu musu na tashi tsaye ina haska masa da nuna masa wardrob ɗina na bango ni da su auta, inda nake ƙwana. Harma da wasu abubuwa nawa da har yanzu ba'a fita dasu a ɗakin ba. Maido da camaran nai kaina ina murmushi, shima sai ya murmusa da silent muryar nan tashi ya furta, “Ɗakin matar Maash ya ƙayatar da ni, zanso wataran nima nayi barci a cikinsa tana jikina”. Sosai na waro idanuna, sai kuma na kalla inda Aunty Falaq take. Wayam ta fita, na ɗan sauke ajiyar numfashi da kallonsa. Gira ya ɗan ɗaga min alamar miye ɗin nan. Nima sai na tura masa baki na ce, “Aunty Falaq fa na nan, a gidan namu kuma zaka kwana harma na kwanta a jikinka”. “To minene? Kuma zan ƙi magana da Matana saboda Falaq na nan? Yanzu dai yashe zaku taho. Ina buƙatar ɗumin matata”. “Kai Yaya ko awa biyu fa bamu yi a gidan nan ba. Bammaga Abba ba? Kuma su Ummie zasu zo idan anyi la'asar. Kai bazaka zo ba?”. Shima fuska ya ɓata, da ƴar shagwaɓa ya ce, “My Tiger ana ga ƙura kina ga yaƙi, ni mizan zo nayi taron mata, sai gobe in sha ALLAHU zamu zo mu duka gaida Abba sai muga babys.” “To Please mu kwana nan. Kagafa ƴan uwa duk suna nan sunzo da yawa musamman ƴan gwarzo. Ga shi duk basu san Falaq ba”. Kai ya girgiza min alamar a'a yana lumshe idanunsa. Idanuna cike da ƙwalla na ce, “Miyasa?”. Kamar bazai ce komai ba sai kuma a hankali ya furta, “Sabida mijin Samrh bazai iya barci ba sai da Matarsa a jikinsa”. “Kaida kake tafiyanka fa sai ma kai sati ban ganka ba”. Murmushi ya ɗan yi kawai yana kallona hannayensa harɗe a ƙirjinsa. Ganin yaƙi magana na sake tura baki da faɗin, “Shike nan amma fasa hiran da kai, kuma namayi yaji yau anan zan kwana”. Na katse kiran. Nayi hakan ne saboda shigowar su aunty Zakiyya da suka kasa haƙuri. Dole na biye musu muka fita. Babu su Mom a falon yanzu, dan haka muka fice tsakar gidan dake ta sake cika da ƴan suna. Sashen amaryar Abba muka shiga mai jego kenan. Haka kawai naji tamun a rai, gashi dama bazamu wuce sa'anni ba. Daga ita har ƴan uwanta sai haba-haba suke damu. An zagayemu da kayan ciye-ciye kamar mune kaɗai baƙin sunan. Yara na hannunmu Masha ALLAH daga gani dai sun kwaso ƙyawunta. Muna a sashen Abba da Kawu Jafaru da abokansa suka shigo. Shima kasa ɓoye farin cikinsa yayi, babu kunya ya dinga yima abokansa bayanin ga ƴarsa dake aure a Lagos tazo. Tuni sun ɗau haske. Niko da Falaq munata gaidasu da girmamawa. Anan muke jin ai walima zasuyi, nima sai na sanar masa ai Yaya Awwab ɗin ma na zuwa idan anyi la'asar harda mahaifiyarsa. Kasa rufuwa bakin Abba yay dan farin ciki. Ganin yanda yake ta farin cikin na ɗauka waya na turama Yaya Awwab ɗin roƙon dan ALLAH ya biyo su Ummie. Sam banyi tunanin zai zo ɗin ba. Bayan la'asar gida ya gama cika matuƙa mun zama abin kallo tako ina sai ƙusƙus mata suke da nuna ni, ta wajema anata shirin fara walima wasu ma har sunje sun zazzauna sai ga wasu zuƙa-zuƙan motocin har huɗu. Biyu dai na guards ɗinsa ne da suka rakomu ɗazun suka koma. Biyu kuma ɗaya Ummie ce da Mama balki da uwargidan Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain ce. Sai ɗayar Tj da Hayatu a gaba, uban tafiya a baya. Ina da ga bakin gate muna magana da wasu ƴan islamiyyar mu da aka kaima labarin zuwana dake nan layinmu sun zo tabbatar wa na ɗan rakosu akan gobe zamu haɗu yau taro yasa bazamu gaisa da ƙyau ba motocin suka tsaya. A take kallo ya koma kansu kamar sanda muma muka iso. Number motocin yasa na gane nashi ne, sai nai tunanin su Ummie ne kawai. Su na nufa cike da murmushi zan tarbi su Ummie sai kawai aka buɗe masa. Fitowarsa ta saka mutane da yawa ambaton Masha ALLAH. Dole nima na tsaya cak ina kallonsa kallo irin na mamaki. Dan sanye yake da bugaggiyar shadda data ji ɗinki ɗan ubansu da yay masifar zauna masa a jiki tamkar dan shi kaɗai aka halicci shadda a duniya (Tofa namu mazan fa🤔😏) ga wani arnen takalmi da hula daya murza a sama. Yana masifaffen ƙamshin nan nasa daya mamaye wajen gaba ɗaya yama danne namu. Karo na farko dana ganshi sanye da manyan kaya a rayuwata. Kullum daga suit sai ƙananu kawai. Gira ya ɗan ɗage min da kashe ido ɗaya cike da salon nan nasa na isa da ƙasaita. Sai kuma yamun alamar wai nazo garesa. Kafaɗa na maƙe masa da nufar Ummie na rungume. Hannu biyu ta riƙeni itama tana murmushin da masa daƙuwa dan kowa a wajen kasancewar idanu na kanmu yaga abinda ya faru a tsakanin namu. Kansa ya ɗan rissinar da kai hannu ya shafo wuyansa. Tuni kuwa waje ya fara ɗaukar ƙusƙus. Yayinda su Abba suka taso cike da farin cikin tarbar babban mutum irinsa kuma surukinsa. Yanda yake ƙoƙarin girmama iyayena sosai yake ƙara saka min ƙaunarsa da kgirmansa a zuciyata. Nima sai naja su Ummie muka shiga cikin gidan da tuni har an kai musu labarin mijina da iyayensa ne suka zo. Shigowar su Ummie ya saka gidan ɗaukar tsitt, kowa na yaba sunan UBANGIJI a ransa. Dan duk wanda ya kalla Ummie yaga cikakkiyar baturiya a kayan hausawa. A falon Mom Gwaggo Gudidi sukai musu masauki. Babu wani alamar wulakanta kowa ga Ummie. Kowa yazo cikin girmamawa da mutuntawa take gaishesa. Kamar yanda suma suke mata gaisuwa irin ta girmamawa.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ .......Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama shirya musu abincin suna kala-kala a farlon Mom ɗin data fito ta gaishesu cikin dauriya da dakewa. Da alama dai mahaifiyarta ta kwakwkwafeta ne. Dan kallo ɗaya zaka mata ka fahimci a susuce take. Bare ma ganin su Ummie ta sake firgicewa. Bata ma ida susucewa ba sai da Maash suka shigo shi da Hayat da Abba har cikin gidan a falon da muke na sashen nata. Da ga can tsakar gida Abba yabar bakin kowa buɗe dan kai tsaye ya sanar musu wannan mijin Samraah ne, wannan kuma Falaq. Anan kuma tsabar neman magana irin na Yaya Awwab Ummie ta bani Babys na miƙa musu kawai ya haɗa da hannuna ya riƙe yaƙi kuma saki dole na kai duƙunne gabansa hannayena da nashi tallafe da Babys ya ɗaura saman cinyarsa a haka. Niko ina ta duƙunne a gabansa like na dafa gwiyawunsa. Cikin ɗan iskan salon kallon nan nashi dake kashe min jiki ya kallan fuskarsa da ɗan murmushi muryarsa very soft da kowa baya ji sai ni ya furta, “Kamar ace namu ne ko My helf”. Tamkar zan nutse dan kunya, danni gani nake kowa na jinsa na marairaice masa fuska. Cikin magana ƙasa-ƙasa na ce, “Yaya Awwab su Abba fa da Ummie, ka saki min hannu na tashi Please”. Ɗagowa ya ɗan yi da alama shima dai ya shagala da mantawa da su ɗin, fiiii ya ɗan kalla kowa sai kuma ya dawo da kallonsa kaina. Cikin sake maida muryarsa Low ya ce, “Ya Rabba. My tiger dama bamu kaɗai bane?”. Hararsa na ɗan yi, sai kuma nai ƙoƙarin janye hannayena dan nama fara gajiya da durƙuson. Ina samu na zaresu na miƙe a wajen batare dana kalla kowa ba. Kamar munafuka sum-sum na koma kusa da Mama balki na zauna kaina a ƙasa. Har aka gaisa aka gama ban sake kallon kowa ba. Sai da Abba yace nazo na amshi yaran a hannunsa zasu tashi sannan na miƙe dan dole. Koda naje sai ya bani ɗaya wai na bari zai tayani da ɗaya. Ya zanyi dole na bisa a yanda yake so muka fito a falon dan na ƙara fahimtar yana matuƙar son yara. Kamar an saita sai ga su Fahad da mai hoto. Ai kawai taremu sukai mu tsaya a mana hoto a haka. Yau dai naga takaina, dan dole na tsaya aka ɗaɗɗala mu babu ko kunyar taron mata dake cike da gidan nan ga su Abba Yaya Awwab ya rungumeni ni da Babys ɗin aka mana hoton nan. Ina samu wani ya amsa na nufi fecewa a wajen amma ya damƙe hannuna dole a haka muka fito har ƙofar gida. Sai da yaga matasan anguwa da abokan Abba dama magidantan sun zagaye motarsa sannan ya barni na koma ciki badan yaso ba. Naji daɗin hakan dan na fahimci take-takensa so yake ya gudu dani gida wai hayaniya namun yawa ga babynsa. Cikin gidan na koma aka cigaba da hotuna. Sai ga yara na shigowa da labarin wai mijin Samraah da ƙaninsa (Hayatu) nata rabon kuɗi wa matasa da magidantan anguwa a ƙofar gida. Kamar wasa ana haka sai ga Hafizzullah da sukai kira a waya shima ya shigo shi da Fahad suka farama matan cikin gidan rabo. Zo kaga gyuɗa, wasu ma kaina sukazo sunayin gyuɗar ana zuba min kirari. Humm kuɗi! Kuɗi! Jama'a kuɗi dabbane. Badai zance komai ba, na bama kowa damar ya auna a cikin ransa kawai.... Suna kam dai Alhamdullah, dan yayi matuƙar armashi fiye da zato da tsammani. Dan daga ƙarshe dai su Maash basu tafi ba sai da akai sallar magrib muka tafi tare akan gobe in sha ALLAHU zamu dawo a gaisa sosai gobe idan ALLAH ya kaimu Yaya Musaddiq ya shigo sai mu shiga gwarzo. Badan naso ba na bisu muka tafi. Ni da shi a mota ɗaya ina jikinsa inata faman fushi an hanani kwana. Nan ko jikina harda su zazzaɓi abinda na jima banyi ba. Nasan wannan hayaniyar ce da daƙunar dana sha wajen mutane. Gwaggo Gudidi harda bani tofi nasha wai maganin baki. Ni har dariya ta bani dan har ɗaga rigata tayi ta shafe cikin da shi. Kafin mu isa gida nayi barci, sai kawai jinai kamar an ɗaukeni ana tafiya dani, sanda nake buɗe ido har mun iso falo gasu Ummie da kowa sai kawai na fuske naƙi buɗe ido dan bazan iya yarda na haɗa ido da kowa ba a wannan yanayin wlhy. Sai da ya shiga ɗaki dani ya dire a saman gado na buɗe idanuna. Tsayawa kawai yay a rankwafen yana kallona cikina ido, irin dama kin tashin nan ashe kikai likimo. Kaina na kauda gefe ina murguɗa masa baki. Sai ya saka hannu ya dawo da fuskar yanda take cikin ɗage gira da motsa lips kaɗan ya ce, “Naga wannan”. Zanyi magana kawai ya rufen baki ruff da nashi. Daga haka salon wasan ya canja sai tsintar kaina nayi a ruwan wanka. Ai ban sake cewa komai ba dan nasan dai da gudunmawata akaje inda akaje ɗin.... Washe gari ɗan zazzaɓin dana tashi da shi yasa na tashi a kasalance. Da ƙyar na iya taimakawa Falaq da Ummie da Mama balki mukai break fast, duk da Yaya Hayat yace mu bari za'ai order muka ƙi, sai da muka kusa kammalawa sai kuma gashi an kawo daga gidan Sheikh ma. To baiyi yawa ba, tunda dama akwai guards da securitys ɗin gidan, sai hakan yasa abincin ma ya sake wadatar mu sosai. Sai da akai zaman ci wasu ma sun fara sannan mai gayya da aiki ya fito. Dan barcin daya hanamu yi jiya yay ramuwa da safen bayan sun dawo daga jogging shi da su Hayatu. Da kayan barci ya fito jikinsa alamar ma ko wanka baiyi ba. Kujerar kusa da ni Fahad ya ja masa ya zauna. Batare da ya kalla kowa ba yace “Ummie, Mama good morning”. Da kulawa suka amsa masa. Yayinda muma muka shiga gaishesa. A fakaice ya amsa mana sau ɗaya ya ɗauka tea ɗin gabana ya fara sha. Ummie ce tai magana tana kallonsa. “A'a Muhammad ya zaka shanye mata tea, ba gashi zata haɗa maka ba.” Cikin langaɓe kai da marairaice murya ya ce, “Ummie yunwa. Rabona da abinci fa tun jiya da dare”. Kanta ya ɗan girgiza da faɗin, “Ai laifinka ne. Ace mutum bazaicin abinci ba sai yunwa ta cimasa ciki ta cinye. Shiyyasa gaka nan ko ɗan tumbin nan na matasa bakayi sai uban ƙirji kamar zaki. Ni Ulser ma nake tsoritar maka”. “Humm Ummie ai ta jima da kamashi fa”. Cewar Hayat cikin damuwa. Hararar Hayat ɗin ya ɗan yi da ɗaukar tea spoon ya jefa masa. Sai ko a saman kansa. Dafe wajen yay da faɗin, “Ummie shike nan ya fasa miki kan ɗa”. Yanda Hayatun yay maganar da yanda Ummie taima Maash ɗin daƙuwa da jifa masa tea spoon ɗin itama ya cafe yasa muka hau dariya. Sai da ya ɗan harare mu musamman su Fahad sannan muka gimtse. Sai Ummie da Mama ke kayarsu da su babu damar a hanasu dai. Haka dai muka ci abincin cike da nishaɗi, yaƙi yarda na zuba masa wani dole a plat ɗaya muka ci ni da shi. Duk da bama wani na kirki yaci ba, shine ya fara tashi wai ya ƙoshi. Duk lallaɓawar da Ummie ta masa sai ya marairaice wai a hakan ma yayi over feeding cikinsa zai fashe. Ni tausayi ma ya fara bani, na fara jin ya kamata likita ya dubashi ko hanjin nasa sun naɗe ne shin. Falo ya ɗan zauna har lokacin da muka fara kammalawa muma. Kafin ya tashi ya sake komawa bedroom ɗin namu. Muma bamu zauna a falon ba kowa ya tafi ɗakinsa domin kimtsawa. Dan Yaya Hayat yace fita zamuyi mu dukanmu.... 💢🌟⭐🌟💢 “K yanzu kina ganin wannan kukan zai fisheki Jalilah? Tun fa jiya kike abu ɗaya bayan na kwana takwas da suka wuce. A gabanki kuma likita ya sanar mana idan fa baki nutsu ba zaki iya yanke jiki ki faɗi ƙarshe da paralysis ce.” Hawayen da suka cika idon Mom ɗin ne suka sake sakkowa a guje. Bata iya ta share ba. Sai magana data farama mahaifiyarta muryarta na sarƙewa. “Umma yaya kike son nayi, miya rage mun idan ba kukan ba. Ki duba fa ki gani komai neman ƙwacewa yake yi kamar a mafarki. Mun gagara samun mahaifar shegiyar yarinyar can ƴar ƙauye amma tazo ta addabemu. Tsabar munafunci mun rasa a ina tsohuwar can takai ta bizne. Muna ji muna gani munga samu munga rashi. Bamu gama fita a wannan magagin ba sai ga wannan shegiyar yarinyar. Kiga fa, ƙamshinta ma kawai abin firgitarwar ne a garemu. Ki kalla lass ɗin jikinta wlhy irin na miliyoyin kuɗin nan ne. Sarƙarta ta diamond ne Umma. Diamond da muke ji a labari, dan Gara zinare kanzo hannayenmu koda na ƙaramin kuɗi. Umma handbag ɗinta da mayafi da takalmar ƙafarta ba kannanun kayan kuɗi bane. Ga ciki a jikinta, kiga yanda yaron nan ke mata kamar ita kaɗaice mace a duniya ko kunyar uwarsa baya ji kai tsaye yake nuna mata kulawa da tattali. Itama uwar kuma ko'a jikinta ko irin ɗan kishin nan na uwar miji babu a tattare da ita. Ƙamshin turarenta kawai ka shaƙa kasan irin na manyan turaren nan ne da talaka sai dai yaga hoton kwalayensu a net idan yay searching. Why Umma why hakan ta kasance ne? Umma Baby da Bibaa na naima tanaji da fatan irin wannan rayuwar ba sakaran yarinyar nan da ko hasken kirki na fata bata da shi ba. Ina ganin Mansoor yafi ƙarfinta ashe wanda ya takesa ya shanye ne zai maye gurbinsa. Umma taya hankalina zai kwanta ni ko sanin inda tawa ƴar take banyi ba ma. Ga Abbas na hannun ƴan sanda. Gaba ɗaya Imam bai damu damu ba yanzu. Yanda yake rawar jiki akan ƴaƴan nan da aka haifa masa sai ki ɗauka ba'a taɓa masa haihuwa a gidan nan ba. Umma wlhy ji nake kamar na kashe kaina na huta kawai da ganin wannan baƙin cikin. Wai waɗanda ke ƙasan ƙasan ƙafafuna, na fisu da komai na rayuwa a da sune suke kokawa da turareniyar hayewa can sama ƙololuwar ƙurewa suna shirya alamomin zubar da ni da mun ɗagawa. Kamar ni Jalilah Ummie. Ni ɗin nan dai Jalilarki......” Kuka mai ƙarfi ya sake sarƙeta. Kamota Umma tayi jikinta ta rungume itama idanun nata cike da hawaye. Dan abinda ƴar tata ta faɗa duk gaskiya ne. Ita kanta dauriya kawai take ta manya amma jiya ko wani barcin kirki batayi ba saboda tunani da damuwa. Zuwan yarinyar nan Samraah ba ƙaramin hargitsa musu lissafi yayi ba. Ga lissafin Halime da basu gama ba. Ganin wanene ai nahin Maash ɗin a zahiri yau ba hoto ba, da yanda ya dinga ɓarin kuɗi kamar ba nemansu yake da wahala ba ya sa komai ya ƙwace mata ma. Ga yarinyar da ciki itama, idan ta haifi Namiji fa shike nan ta gama mallakar komai. Har zuwa yau da safe ta gagara komawa dai-dai yanda ya kamata........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ ......A tsare motocin da muke ciki suke tafiya saman titi tamkar an zana su. Duk ta inda muka gitta sai kaga idon mutane na binmu. Ni dai ina kwance a jikinsa ina game da waya yana kallona hannunsa a saman cikina yana shafawa. Jakin babangida da muka ɗan hau ya sa na cije baki da miƙewa zaune da ƙyau saboda motsin da cikina yaya babu shiri, ƙoƙarin tambayata yake lafiya ni kuma hankalina nakan mai agwalina dake bakin titi cike da barrow da idona ya hango min. Har mun ɗan gota nace ma TJ ya tsaya. Tsayawar kuwa yayi, ni kuma na kalla ogan nasa daya zuba min ido. Batare da damuwa ba na ce, “Ya Awwab Please bara na sayi Agwalima ɗin can”. Nai maganar ina zaro 1k a handbag ɗina. Ƙoƙarin buɗe ƙofar motar nake ya riƙo hannuna. A marairaice na juyo na kallesa kamar zanyi kuka. Baice komai ba ya ɗauke kansa tare da sakin hannuna ya buɗe side ɗin da yake ya fita. Cikin rawar jiki TJ ya fita shima yana faɗin ya bari ya sayo amma ya ɗaga masa hannu. Hakama Hayat da su Fahad ganin ya fito duk suka fito suma amma sai bai kalla kowa a cikinsu ba ya tsallaka wajen mai agwalima ɗin. Tashin bal, gaba ɗaya mutane sun zuba masa ido musamman ganin yanda yaje gaban mai agwalima ya tsaya. Shi kansa mai agwalima duk ya rikice dan duk wanda dai ya kalla wannan ɗan gayen yasan baiyi kalar shan abun titi irin wannan ba, barema wai agwalima. Hannu ya bama mai agwalima alamar busabaha. Jikinsa na rawa ya waro idanunsa waje zai ɓoye hannun, amma sai bai damuba ya riƙo hannun nasa shi kuma. Cikin dakewar nan tasa da silent voice ga hausa bai cika ba ya ce, “Ina son shi duka saka a leda”. “Agwalima ɗin ranka ya daɗe?”. Mai agwalima ya faɗa cikin waro idanunsa waje fiye da ɗazun. Cikin halin ko'in kula ya jinjina masa kai. Sake ruɗewa mai agwalima yayi ya shiga kwasheta yana zubawa a bako. Yayinda masu wayoyi aka samu abin ɗauka kasancewar wani ya ambaci sunan Maash ɗin a wajen. Yana gamawa ya laluba aljihun farar shaddarsa da yau ma Samraah ta dage sai ya saka ya zaro kuɗi. Bai wani damu da dubawa ba ya ajiyema mai agwalima ya ɗauka bako ɗin zai wuce. Cikin sauri TJ da Hayat, Fahad, Hafizzullah suka zo dan su amsa amma nan ma ya hanasu sai da ya kawota har mota ya saka a sit ɗin gaba ya cira guda biyu ya buɗe side da nake ya ɗauka roban ruwa ɗaya ni dai ina binsa da kallo kamar wata sakara ya wanke a gwalimar fes sannan ya miƙo min. Kasa koda motsawa nayi, sai idanuna na ne da suka cika da hawaye ke binsa da kallo, ɗan duƙowa yay ya hure min idanun tare da kamo hannuna ya ɗaura a gwalimar sanan ya rufe murfin ya zagaya nasa side ya shiga. TJ na gama rufewa na faɗa jikinsa kawai na ƙanƙamesa hawayen da nake riƙewa na gangaro min. Ku gane bawai yayi abinda maza da yawa bazasu iya bane ba ko basu taɓa yi ba, kawai dole ne abin ya bani shock musamman da na sani kuma da kuke biye da labarin nan kuka sani Maash yayi makamancin hakan abun mamaki ne. “Shagwaɓa ba”. Naji saukar soft muryarsa cikin kunnena dai-dai yana ɗagoni zaune da ƙyau. Ɗagowa nai na kallesa idanuna na sake cika da hawayen zanyi magana. Kansa ya girgiza min tare da kai yatsarsa ya ɗauke hawayen. Sai kuma ya ɗago hannuna dake ɗauke da agwaliman ya ce, “Ya ake ci?”. Murmushi na sakar masa ina ɗan langaɓe kai na ce, “Bafa ci ake ba sha, bari ka gani”. Ban jira amsarsa ba na luguyguyta agwalima ɗin yay ruwa sannan na sha shi, wani irin lumshe idanu nayi dan jinai tamun daɗi fiye da koyaushe. Jin an riƙo hannuna yasa na buɗe idanun, kan bakinsa ya kai agwalimar dana sha ɗin shima ya sha. Da sauri ya saki hannun nawa yana dafe bakinsa. Cikin ɗan waro idanu na ce, “Miya faru?”. “Tsami”. Ya faɗa fuska a yamutse kamar zai fasa ihu. Bamma san dariya ya kwace min ba. Sai da ya dungure min kai yana faɗin, “Mugunta ba”. Sannan na tsagaita. A haka muka iso gidan Abba. Tarba muka samu fiye data jiya. Dan yau iya danginmune kawai sai na Aunty Halima amaryar Abba dake shirin tafiya gida, dan har suyar namansu sun kusa kammalawa. Cike da farin ciki auta yazo ya ƙadandaneni harda kukansa yana faɗa min yayi missing ɗina, miyyasa na tafi na barsa Bibaa nata dukansa. Bata masa homework bata masa wanka. Murmushi nayi ina mai lallashinsa, na kalla Bibaa da tai sumar tsaye kawai tana kallonmu. Hannunta na kamo itama na rungumeta a jikina. A mamakin kowa sai kawai ta saki kuka da babu wanda yasan dalilinsa. Haka dai bayan an nutsu a falon baƙi iya manyan damu aka gaggaisa ni da Falaq muka fito, dama su Fahad basu shigo ba suna ɗakin Yaya Musaddiq abinsu. Sashen Mom muka shiga gaisheta. Dan tunda ta fito taga mune ta koma. Tana kwance a kujera ta juya ma ƙofa baya. Koda muka gaisheta Ummanta ta amsa wai barci take. Dariyama abin ya bani ni kam. Dan na fahimci bata san na ganta ne kawai, alhalin sanda muke shigowa suka fito suma, daga baya ne suka koma dakin. Ban wani damu ba muka fito. Sashen Aunty Halima muka shiga. Nan ne kam muka baje anata shan hira har ƙanwar mijin Aunty Zakiyya da tai min ƙunshi biki tai mana ƙunshi ni da Aunty Falaq. Sai ga Hafizzullah ya shigo da waya a hannu ya nuna mana wai mutane sun yi video ɗazun wajen sayen agwalimar da Yaya Awwab yayi gashi nan yanata tranding anata comments. Ni abun ma sai ya bani mamaki irin wannan rashin aikinyi haka har ina. Kowa yaji da sabgar gidansa amma sun zauna damuwa da abinda bai shafesu ba. Wannan nunawa ta Hafiz tasa ƴan uwa da basu san abinda ke faruwa ba suma duk suka gani. Nanfa abokan wasa suka tasani da shaƙiyanci aunty Falaq na kare ni da Aunty Halima. Sosai kasancewa a gidan Abba yau ta sakamu a farin ciki, bayan sallar azhar sai ga Yaya Musaddiq ya iso. Fahad da Hafizzullah sunje airport sun ɗakkosa. Sosai gidan ya sake rikicewa da farin ciki, sai lokacin ma nasan ashe su Yaya Awwab meeting sukayi akan batun auren Yaya Musaddiq ɗin. Shi Abba da bai san Yaya Musaddiq nada budurwa ba yace ya bashi Bibaa. Sai da Yaya Musaddiq ya iso aka tambayesa kafin a sanar masa batun Bibaa yace ai yanada matar aure. Gaba ɗaya sai jikin Abba yay sanyi, Gwaggo Gudidi zatai batun Bibaa yay mata alamar ta bari. Haka dole tai shiru. Bayan la'asar muka bar gidan. Companyn sa mukaje. Daga inda labarin Muhammad Awwab El-Mu'azz Maash da Samraah Abdul-wahab Gwarzo Sam-G ya fara kenan. Sai da naji hawaye sun cika min ido. Dan komai dawo min ya dinga yi tamkar yanzun ne yake faruwa, barema da muka shiga hall na meeting aka saka mana footage na ranar taron. Hatta da inda nake ɗaukar video a wajen gawar Jaga da bai mutu ba. Rungumeni Ummie tayi tana hawaye. Yayinda Maash ya haɗamu gaba ɗaya ya rungume shi kuma. Bamu baro cikin company ba sai goma da kusan rabi na dare. Muna fitowa daga Company tafiyar tamu ta rabu. Su Ummie akai gida da su mu kuma wata hanyar daban. Ƙoƙarin tambayarsa nayi ya hana, dole naja bakin nai shiru har muka iso. Wani irin mugun waro idanu nayi ganin gidan da aka fara kawoni amarya matsayin matar Maash, ni kuma ina ɗauka matar Mansoor. Rasama abinda zance masa nayi, na saki baki da hanci kawai ina kallonsa. Ido ya ɗan kashe min tare da jan mayafina ya rufe min fuska sannan ya ranƙwafo ta bayana hannayensa duk saman kafaɗata cikin kunne ya furta, “Idan za'a kawo amarya rufe fuskarta akeyi”. Ban iya nace masa komai ba. Face murmushi dana saki ta cikin mayafin. Hannuna ya kama har ciki, bai ajiyeni a falo ba ya kaini har bedroom ɗin nan da tarihi bazai taɓa mantawa da shi ba. Sai da ya zaunar da ni a saman gadon sannan ya furta, “One minute” ya juya ya fita. Mayafin na ɗaga ina bin bedroom ɗin da kallo idanuna cike da hawaye komai na dawo min tamkar yanzu yake faruwa. Sai da naji motsin zai shigo mai maza na maida mayafin yanda yake. Abinda ya shigo da shi ya ajiye, na fahimci hakanne saboda ƙamshin daya cika ɗakin. Cikin nutsuwar nan tasa ya kai zaune kusa da ni, batare da yayi magana ba ya kamo hannayena cikin nashi, kaɗan ya murza yatsun da suka sha lalle yau wajen ƙanwar mijin aunty Zakiyya, sai kuma ya ɗagosu duk ya kai mitsitsin bakinsa ya sumbata. Hannayen ya saki ya kama gyalen ya buɗeni ya saka kansa ciki shima, sannan ya sake maidawa ya lulluɓe mu. Cikin wata irin murya mai taushi da sanyi ya furta, “Mrs Muhammad Awwab!”. Har cikin tsakkiyar kaina naji wannan kira. A wani irin slowly na ɗago manyan idanuna da ruwan hawaye ya jiƙe na zubasu cikin dara-dara ɗin cat ɗin nasa da blue ɗin ya fito sosai da ɗigo-ɗigon gold. Idan har kaga idanunsa haka to yana cikin matuƙar farin ciki ne babu wata damuwa a tattare da shi........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑯𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅_ Kai jama'a 100 fa 😭 .......Kallon juna muke tsakkiyar ido tamkar zamu cinye kanmu. Ga numfashin juna muna shaƙa a lokaci guda. Cikin matuƙar sanyin murya ya furta, “Samrh! Kece ALJANNAR DUNIYA TA”. “Nima haka Yaya Muhammad”. Na bashi amsa cikin karyewar murya. Kamoni yay gaba ɗaya na ya saka cikin jikinsa ya rungume tsam-tsam. Kafin ya shiga laluben lips ɗina ya haɗe da nashi. Wani kalar salo yake min mai gigita zuciya da matuƙar nuna sallamawa ga abinda ka yarda kake kuma matuƙar so da bege. Ban wani zauna ɓata lokaci ba na bashi dukkan amanna nima. Sai da ya tabbatar da kansa ya samu yanda yake so kafin ya barni muka sake rungume juna muna mai sauke ajiyar zukata a jere. Munja tsahon lokaci a haka kafin ya ɗagoni yana kallona. Murya a dasashe ya furta, “ALLAH yay miki albarka kinji”. “Amin ya rabbi, tare da kai Yaya Muhammad”. Idanu kawai ya ɗan lumshe min ya buɗe murya a ɗashe ya ce, “Salla”. Ban musa masa ba muka shiga toilet. Yanda nake ganin ko'ina ƙal nasan sakawa yay akazo aka gyara. Alwala muka ɗauro kawai muka fito. Kamar yanda ya ambata muka gabatar da salla har raka'a huɗu. Addu'a ya mana sosai dana sake tabbatar da yanada ilimin addini. Bayan mun idar ya buɗe ledar nan daya ajiye. Sai ga gasassun ƴan shila da akaima gyara na musamman a cikin takeaway. Kun san Sam-G ɗin taku yanzu babu abinda ta iya sai kwaɗayi, ai ƙagara ma nayi a fara ci. Da kansa ya dinga bani, shima yana ci, sai da mukai ƙat barema ni (Su Sam-G anga banza🤪). Fuskarsa da ɗan murmushi ya ce, “Na biya bashin kazan al'ada ba?”. Idanu na lumshe ina murmushi na furta, “Harda gyara ma”. Sai kawai ya jinjina kai yana sake faɗaɗa murmushin sa shima. Taimaka min yay na cire kayan jikina shima haka muka tafi bathroom wanka. Dan na fara hamma barci kuma yazo. Baya wasa da hakan dan Doctor ya tabbatar masa ina buƙatar dinga samun isasshen barci a ƙalla na awa goma sha ɗaya kowace rana. Bayan munyi wanka da brush mun fito ya ciro kayan barci a wardrobe ya saka min, sannan shima ya fita. Babu wani jimawa ya dawo cikin nasa kayan barcin harna kwanta ma ni. Fitilar ɗakin ya rage shima ya hawo saman gadon yana mai kwantar da kansa a saman filon da nawa yake. Tare da rungumoni jikinsa sosai. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, dai-dai lokacin da yake kai hancinsa saman wuyana yana busa min numfashinsa da shinshinar wajen. Da sauri na ƙanƙame hannunsa dake saman cikina. “Kin fara barci ne?”. Kaina na girgiza masa. “Bayan an kawo amarya ɗakinta, angonta ya bata kazan al'ada. Sunyi sallan godiya ga UBANGIJI miya rage kuma?”. Jinai gaba ɗaya na daburce musamman yanda yake maganar a cikin kunnena da shinshinar sa yana kuma busa min numfashi duk a lokaci ɗaya. Muryata na rawa na ce, “Ba komai sai suyi barci su huta gajiyar biki”. “Faɗi gaskiya dai?”. A shagwaɓe na ce, “Da gaske”. “Bashin kazan shi fa?”. Ya sake faɗa cikin salon ruɗa min jiki. Da ƙyar na iya furta, “Ai ba bashi bane ƙyauta ne na tarba”. “Ni dai nawa bashi ne a biyani”. Ya bani amsa yana birkitoni jikinsa gaba ɗaya. Bamma san na shige ba kawai na ƙanƙamesa ina masa kukan shagwaɓa da faɗin wannan ai wayone kawai.... 💙🩸💙🩸💙 Tari ne ya hanata sukuni cikin dare, ga barci ta kasa saboda abubuwa sunma zuciyarta yawa matuƙa gaya. Gashi yau Ummanta ta wuce gida, tayi zaton Abba zai shigo ya kwana anan sai dai har yanzu babu shi babu alamarsa. Tashi tai ta shiga bayi, kawai sai tarin ya sake sarƙeta. Sai da tayi sosai hannunta a saman bakinta. Tana samu ya tsagaita ta janye hannun mi zata gani. Jini a cikin hannun nata. Wani irin tsargawa zuciyarta tayi. Tai tsai tana kallon jinin al'amarin kamar a mafarki. Jini fa? Mike nan? Mi hakan ke nufi?. Jitai gaba ɗaya tana neman susucewa ma. Tuni ta zame jaɓar ta zauna a ƙasan bayin wani zufa na keto ma illahirin jikinta dake tsumar rawa. Ta jima zaune a wajen batare data san makama ba. Kafin tai ƙarfin halin tashi ta wanke hannunta da bakinta da fuskarta ta fito. So take ko kuka tayi kam yanzu amma hakan yaƙi yiwuwa. Haka ta ɗauki waya batare da duba ƙarfe nawa ba tai kiran Ummanta. Cikin alamun mai barci ta ɗaga daga can, sai kawai ta sakar mata kuka. Hankali tashe Umma ke tambayarta lafiya. Da ƙyar ta iya mata bayanin abinda ya farun. Ita kanta Umman daga can duk ta gigice. Sai maimaita kalmar, “Jini! Jini fa da Jalilah. Miya kawo jini kuma daga tari. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un na shiga uku ni Larai. Kinga yanzu dai ki kwantar da hankalinki dare ya riga yayi, kuma ko mijinki kada ki faɗawa da sassafe zanzo muje asibiti kinji ko”. Mom na sharar hawaye ta ce, “To Umma sai kinzo”. Koda ta yanke wayar sai ta faɗa saman gado kawai ta saki kuka, dan bata da abinda ya rage mata kuma sai dai kukan kawai. Al'amarin yaran nan su Samraah da Haihuwar nan ta Halime yayi masifar tsaya mata a zuciya fiye da komai. Dan shi kansa Musaddiq yaron gaba ɗaya ya sauya ya canja tamkar bashi ba. Sai ka ɗauka ama can ƙasar wajen yake rayuwa ba watanni kawai yay da tafiya ba. Hafizzullah ƙaraminsu na baya-baya da bama ta damu da shi ba shi kansa yaron baka gajiya da binsa da kallo yanzu. Balle kuma babbar giwa. Yarinya ƙarama jiba yanda take gara kan babban mutum irin Maash da manyan ƙasa ma ganinsa garesu aiki ne babba. Ai dolene ma a wannan al'amarin akwai aikin asiri. Bata yarda da tsohuwar nan ba Gwaggo Gudidi. Akwai abinda suka nemawa yarinyar nan ta mamaye Maash da danginsa. Kuma wlhy sai ta tona mata asiri dan sai inda ƙarfinta ya ƙare auren nan sai ya tarwatse. Bari dai tasan inda Baby take tukunna”. Sai kuma hawaye sharrrrr..... Hummm Mom! Mom!! Mom!!!!!!🤨 ❣️❣️❣️❣️ Barci na sha sosai da safe dan tun bayan sallar asuba dana koma ban tashi farkawa ba sai sha ɗaya. Nayi mamakin ganinsa gefena shima yana barcin. Sai duk ya bani tausayi. Babu wanda baya buƙatar hutu a rayuwarsa. Sai dai kawai dan babu yanda za'ayi dole a haƙura. A gefe mutane sha'awarsa suke ya tara, a rayuwarsa kam cike take da ƙalubale da buƙatu kamar kowa. Na tabbatar inda zai samu dama zai kwanta a gida ya huta koda na tsawon sati ɗaya ne. Amma sam bashi da wannan damar. Koda ya gwada yin hakan bashi yiwuwa garesa, ni kaina matar tasa lokacinsa ƙayyadajjene a gareni. Numfashi na sauke a hankali, tare da kai lips ɗina saman small nashi na sumbata. Sai kuma na shige jikinsa kawai na rungumesa sosai. Saukar hannunsa a saman kaina, da yanda ya tura yatsun cikin gashin yasa na sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Muryarsa a raunane cikin yanayin wanda ya tashi a barci ya furta, “Kin tashi?”. Kaina na jinjina masa tare da sake shigewa jikin nasa na ce, “Amma kai bana son ka tashi yanzu”. “Why?”. “Saboda ina son ka huta Please. My Hot wlhy jikinka na buƙatar hutu sosai. Ka duba hanlin daka shiga wata huɗu da suka wuce saboda stress. Shike nan kullum kai ina zaka neman kuɗi, ina ka dawo neman kuɗi. Daga jirgi sai zaman mota. Ko lokacinka bana wani samu. Please kuna hutawa mana, duka rayuwan nawama yake wai. Mu gama nema da tara dukiyar mutuwa ta zo ta tsamemu a cikinta mu tafi kamar ba'a taɓa yinmu ba. Sai ma mun dace da haihuwar ƴaƴa na ƙwarai ne zamu tafi mubarsu da dukiyar su mana addu'a, wasu bishashar gabansu kawai itace damuwarsu. Please mu kasance tare kawai ni basai kaje ko ina ba”. Na faɗa ina sake shigewa cikin jikinsa sosai. Shima sake ƙanƙameni yay yana sauke wasu irin ajiyar zuciya a jajjere. Kamar yanda nai tsammani baice komai akan batun ba. Sai taimaka min da yay mukayi wanka. Bayan mun gama kimtsawa falo muka dawo, banyi mamakin ganin an kawo mana abinci ba sai dai naji kunya dan daga gani daga gida ne. Haka na zauna muka karya koma nace ni na karya dan shi kam bana ɗaukar cin abincinsa cin abinci. Yanda bai nuna zamu bar gidan ba nima sai nake jin daɗin zama a cikinsa. Salla kawai ke fitar da shi. Ina ganin kiran su Aunty Falaq naƙi na ɗaga dan nasan tana can ta haɗa kai da Fahad iya shege zasu min. Hafizzullah dai gida muka barsa yaga Yaya Musaddiq ya nane masa. Ba ƙaramin farin ciki na tsinta kaina a ciki ba da zaman gidan nan na yau. Sai la'asar muka fita, nazata ma gida zamu koma sai naga mun nufi wani waje daban. Ashe gidan Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain muka nufa. Acan muka samu su Ummie. Aiko sai naji duk na daburce. Ga Aunty Falaq ta sakani gaba da tsokana. Ummie dai da Mama murmushi kawai suke. ALLAH ya taimakeni Fahad ya shigo tare da Bahijja sai tsokanar ya koma kansa. Har dare muna a gidan Malam, koda muka baro can gidan dai muka koma ni da shi su Ummie kuma suka wuce can. Yau kam a ɗakinsa muka kwana, katifa ce kawai a cikinsa ƙatuwa. Nan ɗin ma mun kasance cikin farin ciki sosai. Washe gari babu barcin safe mukai shirin tafiya Gwarzo. A gidan Abba muka haɗu da su Ummie, nayi mamakin ganin harda Mom, sai dai daga gani bada son ranta bane ba. Dan ina ganin Abba na mata masifa, ga Ummanta tsaye galala tana bin Abban da kallo. Mota duk muka shiga, dama shi Maash tunda ya fito ya gaida Abba ya koma ciki abinsa. Su Ummie kam bama su fito ba. Wajensu Gwaggo ta shiga. Aunty Falaq da mijinta sai Yaya Musaddiq. Hafizzullah da Fahad motarsu daban. Ni da uban tafiya sai TJ dake jan mu. Abba shi da Mom da su Bibaa sai Kawu Jafaru da muka ɗauka a hanya. Gaba da bayanmu motar guards ce. Ɗan kwanciya nayi a jikinsa dan shi yanata aikinsa ne a laptop. Tun ina kallonsa ina cin chocolate ɗin hannuna harna fara barci. Sai da ya ɗan motsani zai gyara min kwanciya na ɗan buɗe ido. Lumshe mun nasa yayi ya sake buɗewa da faɗin, “Sleep” akan lips ɗin sa. Maida idanun mai kawai na rufe dan barcin nake ji sosai.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑯𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒐𝒏𝒆_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ ......Mun iso tushe asali abin alfahari. Tarbar da muka samu ya sake tabbatar min da ansan da zuwanmu. Dan mun sami gidan Kawu Musa cike da dangi ƴaƴa da iyaye kamar ba safiya ba. Bayan gaishe-gaishe da ƴan koke-koken tuna mahaifinmu suka sake neman gafarar Mama Balki da Falaq. Kai tsaye sukace su sun yafe komai ya wuce. Suka kuma nuna farin cikin kasancewa a cikin ƴan uwa da yanda aka musu tarba ta mutuntawa da nuna ƙauna. Falaq nata kuka dan ita kaɗai tasan a kalar farin cikin da take a ciki yau ɗin nan. Abinda ta gama fidda rai da samunsa yau gata tsundum a cikinsu wato dangin mahaifinta, kuma kowa na nuna mata soyayya da ƙauna kamar za'a cinyeta dan kulawa, hakama little Awwab kowa nata ma yaron addu'a. Su Kawu sun damƙa mata gadonta a hannu, yayinda Ummie ta damƙa mana alƙawarin mahaifinta. Sai zuciyar Abba ta sake karaya yau ma harda kukansa yana bamu haƙuri akan kuskuren da yay na salwantar mana da namu hakkin dake a hannunsa na mahaifinmu dana mahaifiyarmu. Dan gona ɗaya ta rage itama dan tana a hannun Kawu Sabi'u ne yana nomata shiyyasa Abban bai sayar ba, Mom kuma bata san da ita ba. A gaban kowa ya faɗi Mom ce duk ta dinga saka shi yin hakan, shi kuma a lokacin wlhy baya gane komai sai bin umarninta da sabon faranta ma zuciyarta. Kuka ta sanya masa wai ya kawota cikin danginsa dan ya tozartata ashe su sake ɗaukarta a wulaƙance. Babu wanda yabi takanta dama tunda muka zo duk ta kasa sakewa saboda da can ba zuwa take cikinsu ba, ba barin ƴaƴanta take su zo ba. Idan kuma su sunje ta wulaƙantasu da nuna musu ƙyama. Dangin su Mamanmu ma da mukaje kasa sakewa tayi. Can ma mun samu tarba ta mutuntawa da girmamawa. Haka muka kasance cikin farin ciki a tsakkiyar danginmu. Sai naji kamar a barmu muɗan kwana amma nasan uban gayyar ba yarda zaiyi ba. Dan koda naima Ummie magana sai tace nayi haƙuri idan na haihu ita da kanta zata tsaya har sai nazo nayi sati da ga ni har Falaq. Na ɗan ji sanyi da jin hakan, falaq ma nata murna dan tana son zuwa ta kwana ɗin ko dan sanin kowa yanda ya kamata. Yini guda muna a can, dan sai bayan sallar la'asar muka barosu suna kewarmu muna kewarsu. Ga uban alkairi naban mamaki da Maash yay musu. Ni kaina sai da naji hawaye sun cika min ido da alkairin nasa. Gashi an tsaida magana gobe idan ALLAH ya kaimu su Kawu zasu zo akai komai na Yaya Musaddiq dan Abba yaje yayi magana da iyayen Ruƙayya sunce su babu wata damuwa suzo kawai tunda dama sun san da maganar Musaddiq ɗin. Sai da muka raka su Abba har gida sannan muka wuce muma. Yau dai kam wajen su Ummie muka wuce. Gajiyar da kowa ya kwaso yasa ba'a zauna falo ba duk muka shige ciki. Ni wankan ma sai da tainakonsa nayi, dan barci kamar zan zube ƙasa nake ji.. WASHE GARI muka samu baƙuncin abokan aikina su Ruƙayya. Abin mamaki harda MD da kansa. Hayatu ne ya saukesu a falon baƙi. Aka kai musu kayan tarba kafin na kimtsa na fita tare da boss. Naji daɗin hakan da yay min, gashi maƙale da hannuna har muka shiga falon ko kunyarsu bai ji ba. Har su Ruƙayya sun miƙe da nufin zuwa su rungumeni suna ganinmu tare sukai surrender. Murmushi na musu cike da nuna jin daɗin ganinsu. Mutuniyata dai sai sinne kai take nasan kunya ce ta isheta. Niko sai na basar na haɗa su duka na nuna jin daɗin ganinsu. Cike da girmamawa MD da su Usman suka gaida Maash, nima muka gaisa harda cemun wai ranki ya daɗe. Ɗan harararsu kawai nayi bance komai ba. Kada na tanka cibi ya zama ƙari dan kafin mu fito harda gargaɗi a kan na kula yanzu ba da bace kada naje ina musu murmushi tunda harda maza. Ni dariya ma ya bani, amma dai na amsa dan a zauna lafiya. Mun ɗan taɓa hira da duk dai mai alaƙa da aiki ce. Shi dai baya saka mana baki sai idan yaso dan kansa. A hirar ne suke sanar min ashe MD yanzu baya wajen, an ɗan samu rikice ne ya ajiye aikinsa. Station ɗin ma yanzu neman durƙushewa take saboda sabon MD ɗinsu bashi da aiki sai wulaƙanta mutane. Ga son yaɗa labaran sirrin mutane, yanzu haka muma wai akan video da yake yawo a media na sayen agwalima da Yaya Awwab yayi yana nan yana shirya abu a kansa. Shiyyasa ma sukai azamar zuwa su gammu tun kwana biyu da suka wuce amma basu samu damar hakan ba sai yau. Maimakon Maash ya tanka akan batun sai ya shiga yima MD tambayoyi akan ainahin masu companyn. Cike da girmamawa ya dinga bashi amsa. A mamakin mu da zasu wuce sai kawai yace MD ya fara shirin komawa aiki on Monday. Ba su ba hatta ni sai da na kallesa. Amma sai ya basar. Bayan wucewarsu naso muyi maganar sai bata yiwu ba saboda zuwan Yaya Musaddiq. Shi kuma suka fita shi da Hayatu. Bayan la'asar koda suka dawo ya shigo ɗaki na biyosa da ruwa sai na samu ya shiga wanka. File ɗin daya ajiye a side drawer na ɗauka ina dubawa dan haka kawai yaja hankalina ganin tambarin gidan TV ɗin mu. Ba ƙaramin razana nayi da ganin sunana ba matsayin mamallakiyar gidan tvn. Zufa naji tana keto min, da ƙyar na iya controlling kaina na maida na ajiye yanda ya ajiye abinsa. Koda ya fito ban nuna masa na gani ɗin ba sai taimaka masa da nayi ya kimtsa muka fito falo dan yace zai ci abinci. Koda ya kammala cin abincin kuma hira da su Ummie dake falon ya ɗauke hankalinsa. Sai kuma ga kiran Uncle Abdullahi yana sanar musu ai ALLAH yay ma Arwa rasuwa yanzu babu jimawa. Ashe yarinyar jiyya take sosai zuciyarta ta kumbura. Sunƙi sanar mana ne saboda kunya da nauyin abinda mahaifinsu ya aikata mana da nata iyayen. Shi kuma Maash ko shigowa yay ƙasar baya zuwa asibitin ta yanda zasu gansa. A ɓoye yake zuwa ya duba Paah kawai ko shi Paah ɗin ma bai san da haka ba. Harga ALLAH bai taɓa maida hankalinsa kan yarinyar ba dan shi yama manta da ita sam. Iyayenta kuwa dama bai yaɓa sha'awar dubasu ba da Kakansa. Paah ɗin ma dan ya zame masa dolene yana kuma fatan sauke hakkinsa dake kansu matsayin mahaifi. Shiyya dukkan ɗawainiyar asibitin shike ɗaukar nasa batare da shi kansa Uncle Abdullahi ya sani ba. Dan bai hana a amshi kuɗinsu ba, amma yace su ajiye duk randa aka sallami Paah ɗin su basu abinsu. Wannan rasuwa ta shigemu. Dan haka a ranar muka fara shirin wucewa dan Ummie ta roƙo Uncle Abdullahi da a jinkirta jana'izar har zuwa safiya ayi a Mansion. Ita yarinya bata da laifi, bata san komai ba akan abinda ya faru itama tsintar kanta tayi a tsakanin hakan. Idan ma za'azo dubi ta wani fannin ita aka cutar Haka kuwa akayi bayan sallar isha'i jirginmu ya wuce Lagos badan mun shirya hakan ba. Dan sati guda muka zo da niyar yi a Kano. Sai dai kana naka ne ALLAH yana nashi. Daga airport dai duk gida muka wuce, kowa kuma makwanci ya nema domin hutama rayuwarsa. Sai washe gari bayan sallar asuba aka kawo gawar Arwa gidan. Dangin iyayenta guda biyu sun iso daga ƙauyensu kasancewar tunda wancan zancen ya fasu ashe sunzo dama. Sai dai Uncle Abdallahi ya hanasu zuwa Mansion, da suka dawo kuma a lokacin mu mun wuce Spain. Mama Balki tai mata wanka da kakarta data haifi Hajiya ƙarama. Aka shiryata aka kaita makwancin ta na gaskiya. Duk da Arwa yarinya ce sannan uwarta kawai ta sani a gidan mutuwar ta shigi su Mama Balki sosai. Ita Ummie ba wani shaƙuwa sukai ba amma taji rasuwar. Ni kaina da ban taɓa damuwa da shirgin yarinyar a gidan ba sai da rasuwar ta dakeni. Hakama Maash bai dai ce komai ba face yimata addu'a amma nasan koyaya zai ji, dan yarinyar harga ALLAH tana masa kallon ɗan uwane kamar uba ɗaya. Duk da itama ya jima da fahimtar take-takenta na son shi. Abin mamaki sai ga su Azizat sun zo daga Niger suma a washe gari. Azizat tayi kuka sosai dan kowa yasan a gidan suna shiri matuƙa da Arwa. Duk da shirin nasu baya wuce akan a ƙuntatama Malika ko yanda za'a shawo kan Maash dai. To koma dai yayane ita dai ta tafi ta huta kuma. Sai fatan ALLAH ya gafarta mata kurakuranta da namu dana iyayenmu baki ɗaya... Rasuwar Arwa tayi matuƙar jijjiga iyayenta. Musamman ma Hajiya ƙarama. Dan a wannan ranar likitoci kwana sukai kanta tanata wani irin kuka da aman jini. Ɗayan ɓarin jikin ya ida mutuwa. Dama ga allurar poison ɗin da Prof yay mata ta fara aiki kaɗan-kaɗan kamar yanda wadda tai masa shi tuni ma ta gama masa illa. Haka dai aka sakata barcin dole har washe gari da aka bizne Arwa bata farko ba. Shima dai Commondo yaci kuka rurus. Dan duk da bai taɓa nuna damuwarsa akan ƴar tasa ba yana matuƙar sonta da ƙaunarta. Yana gani ko wahalar da ya sha a rayuwa zata tafi a banza a ƙalla dai ya bar mai masa addu'a. Dan koda ta masa abinda ya sakashi shiga a wannan halin bai taɓa jin soyayyarta ta ragu masa a zuciya ba. Ashe itace zata fara tafiya ta barsu, inama shine ya tafi ba ita ba. Kaicon wannan mummunar rayuwa tasu mara ƙyaƙyƙyawan tarihi da alƙibalar gani a koya........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑯𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒐_ ......Har akai sadakar uku jikin kowa dai a sanyaye babu wani ƙarfi. Dangin su ma sukai shirin kama gabansu. Dan sun san anmusu halacci. ALLAH sarki Ummie, bata barsu haka ba sai da ta musu alkairi. Suka tafi suna mai sanya mata albarka da addu'oin fatan alkairi har ma damu kammu. Sun wuce da safe gidan ya sake komawa shiru. Dan su Azizat dama ba'a nan suke kwana ba can wajen mahaifiyarsu gidan Prof da safe su zo su koma can da yamma. Batare da mun sani ba washe gari akace mana sun wuce. Ita dama Hajiya Mammah tun randa akai jana'iza da tazo bata sake zuwa ba saboda kunya ne ko munene dai oho mata. Da yammacin ranar tafiya ta tasowa Yaya Awwab, haka ina fushi da kumbure-kumbure suka wuce shida PA ɗinsa da ƙandarariyar baturiyar nan dana tsana. Yanda take wani kwarkwasa da iyayi agaban Yaya Awwab na ƙona min zuciya. Bandai ce komai ba amma ALLAH idan bata kiyayeni ba sai na mata zanen yarabawa. Bayan wucewarsu gidan sai ya sake koma mana shiru, sai kawai na tattara na koma sashen Ummie dan bazan iya zaman sashen ni kaɗai ba. Ashe can ma Aunty Falaq ta gudo wajen Ummie ɗin. Dariya Ummie taita mana wai mu ragayen mata ne. Daga maza sun tafi sai mu gudo wajen Mamanmu. Shagwaɓa muka dinga mata tana biye mana. Ita dai Mama ido kawai take saka mana. Muna waya da ƴan Kano, Musamman Yaya Musaddiq da Hafizzullah da Abba. Sai aunty Halima sabuwar ƙawarmu. Dan yanzu mun ɗinke da ita kamar ba matar Abbanmu ba. Bahijja ma na Kano maƙale bata dawo ba. To batun dawowar tatama dai sai da aure a kanta. Dan an gama tsaida magana bikinsu za'ai kawai da Fahad a huta kafin mu koma. Sai yanzu ne ma nake jin batun komawar tamu Spain. Harga ALLAH na ɗauka mun dawo gida kenan. Kasancewar a gari ɗaya Abba ke cemin an saita bikin Yaya Musaddiq da na Fahad ɗin rana ɗaya. Nan kuma da kwana goma ne idan munada rabon kaiwa. Ba ƙaramin farin ciki na tsinta kaina ba da wannan labari. Na kira Ruƙayya naita mata tsiya, dan yanzu muna waya kullum da chart amma bata sanar min ba. Shima Yaya Musaddiq ɗin ya mun bayani duk yanda sukai da Yaya Awwab. Ya ɗauki komai na bikin ko naira ya yace baya son wani ya sanya. Harda hawayensa dan video call muke a lokacin, sai nima kawai na sanya masa kukan. Dole ya danne nashi ya koma lallashina. Kasancewar biki a ƙurarren lokaci mukai tunanin fara shirye-shirye ni da aunty Falaq. Dan ango dai Yaya Awwab ya tasa ƙeyarsa da shi aka tafi. Sai dai kwanansa uku sai gashi ya dawo. Maimakon Lagos sai ya sauka a Kano. Da daddare sai gashi tare da Hafizzullah. Mamaki ya kama mu dan munsan dai Hafiz na Kano. Sai cewa Fahad ɗin yay yaje ya ɗakkosa ne su fara shirin biki. Cikin harara nace “Wannan ɗan yaron? ina abokanka”. Sai kawai ya nuna Hafiz ɗin, wai ai shi shine babban abokinsa. Rasama abin cewa mukayi, sai Mama da Ummie ne ke mana dariya. Babu yanda muka iya dole muka shiga hidimar tsare-tsaren bikin tun a ranar. Washe gari da yamma Yaya Awwab yay kirana wai mu shirya za'a kaimu airport zuwa dare. Da mamaki na ce “Airport kuma Yaya Muhammad yin me?”. Kai tsaye ya bani amsa da, “Zaku same mu a Dubai ke da Falaq”. Rasama abin cewa nayi nikam. In ba masu abu da abinsu ba irin wannan yanke wannan hukunci kamar wanda ke Katsina zashi Kano. Babu yanda muka iya muka shiga shiri. Ummie nata faɗa wannan wace irin tafiya ce ni ina fama da kaina falaq ga ƙaramin yaro. Mama dai ta bata haƙuri akan tunda sunce muje mu tafi ɗin kawai. Haka dai Ummie ta barmu. Babu abinda muka ɗauka daga mu sai kayan jikinmu da handbags. Hafizzullah da Fahad suka kaimu airport. Fahad sai lallaɓamu yake wai mu zaɓoma matarsa kaya na kece raini. Muna isowa bamu fi mintuna talatin ba aka ɗauke mu. Banyi mamakin ganin mu kaɗai ba a jirgin sai wasu tsirarun mutane. Dan zuwa yanzu na sake fahimtar wanene mijina. Tabbas ALLAH ya musu baiwa ta dukiya, sai dai fatan ALLAH ya kaimu aljanna kuma... Mun iso Dubai lafiya. Sai dai ni naɗan jigata kaɗan dan banda juriya yanzu sosai, dama kuma tun jiya bana jin daɗi dauriyar kawai. Hayatu ne yazo ta ɗaukemu, sai naji haushin rashin ganin ogan nasa. Amma dai bance komai ba har muka iso gida. Gidane mai ƙyau sosai da yaji kayan more rayuwa. Shima Hayatun na ajiyemu yace zai koma wai meeting suke can ma ya bar ogan nasa kuma yana jiransa ne. Takaici yasa naƙi tanka masa. Sun san basu da lokacinmu suka kwasomu zuwa nan kara tsaye. Yanda nake kumbure-kumbure yasa Aunty Falaq tambayata lafiya. Cikin ɓacin rai na amsa mata da, “Aunty dan ALLAH wane kalar wulaƙanci ne haka. Sun san suna da abin yi suka kwasomu. Nifa ALLAH bazan jure wannan abun ba. Kayi aure dan ka kasance da mijinka akoda yaushe amma sam bashi da isashen lokacinka. Yau yana wannan ƙasa, gobe waccan, jibi meeting, gata taron ƴan kasuwa. Citta kaza, kanumfari kaza”. Dariya sosai ta sanya min, ta ce, “Oh oh little sis.. irin wannan lissafi haka. Lallai akwai aiki kenan. Ashe ke bazaki iya jure abinda na jure ba. To wlhy Yaya Hayat ko satin amarci bai cika mun ba suka bar ƙasar nan. Kwanansa biyar inaga. Da ya tafi ban gansa ba sai bayan sati uku. Nana ma sukai kwana ko huɗu ne da ƙyar suka sake tafiya. Nifa a ɗan zaman rikice-rikicen nan ne ma zance miki mun taɓa zaman sati ciff yana gida sai dai ya ɗan fita ya dawo sabgar wuni. Ya xamuyi tamu ƙaddara kenan, mata a waje gani suke mun gama morema duniya da komai na cikinta. Nan ko mu muka san ƙalubalenmu. Samraah kafin nayi aure babu abinda nake buri kamar naga koyaushe ina tare da mijina muna tattalin juna. Sai dai da safe na shiryashi ya ɗan tafi harkokinsa zuwa la'asar ace ya dawo mun kasance tare har wata washe garin, weekend kuwa ya zama salla ce kawai zata fitar da shi. Amma a satin farko na fahimci wannan burin nawa ya zama tarihi ba kuma mai tabbata bane. Tun ina damuwa da yawan fushi harma na haƙura dan bani da yanda zanyi. Dan haka kema haƙuri zakiyi, a hankali zaki saba da duk wannan rashin kasancewar tasu tare damu mu itace babbar ƙaddararmu a gidan aure. Muma godema ALLAH da ya kasance yanzu gamu a tare, ga kuma iyayenmu guda biyu ga Baba suna ɗebe mana kewa.” Ta ƙare maganar tana ja min kumatu na. Baki na sake tunzurawa, dan nikam gaskiya bana jin zan iya dauriyar nan. Kawai azo ayita da wajewa ga lokacin tafiya gana zaman gida. Amma dai bance mata komai ba. Wanka muka farayi muka ɗan tsakuri abincin da muka samu an kawo mana. Ni kawai ma sai na kwanta abina dan barci nake ji sosai. Ba ƙaramin ƙarin takaici naji a zuciyata ba sanda har na tashi naga babu shi babu alamarsa. Sai ma Aunty Falaq ce ta shigo tace na shirya wai Yaya Hayat ya kirata nan da awa ɗaya za'azo a ɗauke mu mu sameshi kasuwa. Baki na buɗe kamar zanyi magana sai kuma nai shiru saboda ƙwallar da suka cika min ido. jinake kamar nace babu inda zanje sai dai na daure kawai nai shirin cikin doguwar rigar data kawo min. Amsar little Awwab nai a hannunta muka fito, babu wanda yay magana a cikinmu bayan amsa gaisuwar Balaraben da yazo ɗaukar mu ya buɗe mana bayan motar muka shiga. Tafiya ce ta ƴan mintuna ta kaimu haɗaɗɗe kuma makeken shagon da baida iyakar labartawa. A can muka samu Yaya Hayat. Bayan mun gaishesa ya amshi Awwab a hannuna yana tsokanarmu. Murmushi kawai nayi ni dai bance komai ba, sai aunty Falaq ce ke kare mana. Saka Awwab yay a irin ƴar jakar goyon nan ta ƴan gayu a ta cikinsa, mu kuma muna biye da shi har cikin shagon. Bayan ya mana bayanin kayan lefen Yaya Musaddiq da Fahad zamu haɗa da wasu kuma daban aunty Falaq ke tambayarsa “Wai Yayana fa? Tunda muka iso bamu ganshi ba”. Cikin ɗan shafa kai ya ce, “Ai wlhy yama bar Dubai ɗin nan awa ɗaya data wuce. Amma dai zai dawo kafin mu wuce dan tare da shi zamu wuce Nigeria. Jinai hawayen da nake ƙoƙarin riƙewa sun zubo min, da sauri na kauda kaina gefe na share su. Komai ban ce musu akan batun nasa ba, suma kamar sun fahimci yanayina sai suka bar maganar muka fara abinda ya kawo mu. Yin komai nake zuciyata babu daɗi, yanzu na yarda da batun mutane da kance da zarar ka samu ciki mazan nan sun bar batunka, musamman masu kuɗin nan sunfi bama dukiyarsu muhimmanci fiye da matansu. Banda ma wulaƙanci irin na mutumin nan, ina cikin wannan halin ya raboni da ƙasata cikin gaggawa babu shiri, nazo kuma inda yake yana garin bawai baya nan ba, amma bai nema inda nake ba balle ya kira yaji yaya muka iso, bai kuma zo inda nake ba bayan ya gama uzirin da yake ya sake taka jirgi ma yabar ƙasar. Harga ALLAH na tsani wulaƙanci, ni mace ce mai son kulawa. Bawai dukiya da samun duk abinda nake so ne matsalata ba. Ina buƙatar tattali a koda yaushe da nuna damuwa ga abokin rayuwata, idan kuma abinda ya kamata na fahimta ne a fahimtar dani zanyi uziri. Munyi siyayya sosai, gajiyar da jikina ya nuna yasa Yaya Hayat yace mu bari haka sai gobe in ALLAH ya kaimu. Muna zuwa gida kobi takan abubuwan daya saya mana na ci banyi ba na wuce ɗaki na kwanta. Sai da aunty Falaq taga ban fito ba ta biyoni da shi. Ƙin motsawa nayi sai ta ɗauka barci nakeyi harda gyaramin blanket ta fita. Shigowarta biyu ina mata haka, daga ƙarshe dai ta haƙura ta kawo min duk abinda zan buƙata ta tafi itama ta kwanta. Har cikin dare sosai ina kallon waya da tunanin zai kirani ya bani haƙuri da faɗa min uzirinsa, amma shiru. Sai kawai na sanya kuka. Sai da nayi mai isata sannan na tashi zuwa bathroom nai wanka na fito, daurewa nayi naci abinda Aunty Falaq ta ajiye min dan yunwa nake ji sosai. Ina kammalawa na ɗauki wayar kamar zan kirashi wata zuciyar dai ta gargaɗeni na ajiye na kwanta. Sai kuma dai na ɗauka na kira shin har sau biyu ba'a ɗaga ba. Haushine ya sake ƙuleni na ajiye wayar.. Washe gari ma har mukai shirin sake fita babu kiransa. Na kai ƙololuwar shiga ɓacin rai musamman lokacin da muke tafiya a mota da naji Hayat na waya da shi. Wato nice mara amfani kenan. Shike nan zan nunama mutumin nan na haifu nima. A ranar muka gama sayyar duka. Yaya Musaddiq da Fahad set uku-uku na akwatina. Sai kuma set huɗu daban da bamu san kona waye ba. Sai muma muka ɗauki abinda muke so ko nace Aunty Falaq da Yaya Hayat suka zaɓa mana ni takaici yasa ma komai baya birgeni. Tun aranar sukam kayan aka wuce da su Nigeria. Mu kuma Yaya Hayat ya tafi damu yawo. Ni sam ba daɗin yawon nake ji ba. Nadai dake ne kawai ban nuna musu koda a fuska ba.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _Ina miƙa saƙon ta'aziyya ta ga ƴan uwa masoyan mu dake ƙoƙarin bibiyarmu ta rasa ƴar uwarmu da mukayi RAHAMA NALELE. Ya rabbi ka gafarta mata, ka yafe mata kurakuranta, kasa kabari ya zama wajen hutu a gareta, da iyayemu baki ɗaya. ALLAH ya raya abinda ta bari ka albarkaci rayuwarsu. Ka bama iyayenta da ƴan uwanta haƙurin rashinta da mu baki ɗaya. Ida tamu tazo muma ALLAH kasa mu cika da imani. Dan girman ALLAH, dan girman ALLAH, duk wanda yake ji a ransa ta taɓa masa ba daidai ba ko wani kuskure da ita bama tasan ta masan ba ko akan sani muna roƙonsa ya yafe mata. Ko sau ɗaya ne kuma a matsayinki na masoyiyar mu dan ALLAH ki mata addu'a a cikin sallarki, idan kin samu dama kiyi sadaka da fatan yaje gareta koda kaɗan ne 😭🙏. ALLAH ya gafarta mana baki ɗaya._ ........Yau ɗin ma a gajiyen muka dawo, dan ni harda ma ɗan guntun zazzaɓi na. Shayi kawai nasha na tafi na kwanta na barsu anan falo. Haka na tashi har washe gari zazzaɓin na damuna. Ban gaya musu ba, sai aunty Falaq ce data ɗan fahimci kamar bana jin daɗin take tambayata. Murmushi kawai naɗan mata da bata amsa da, “Kawai dai yanayin ne Aunty”. “Uhm yanayi, ko kuma Baby na ne dai? Ko Yayana ake kewa”. Murmushi kawai nayi yanzun ma ina ƙoƙarin kai fruit ɗin da ta yanka min sukai ƙyau a cikin bowl baki na. Dai-dai nan Yaya Hayat yay sallama. Itace ta amsa idonta a ƙofa, ni kam a zuciya na amsa ina mai gyara zaman gyalen dana yafa saman kaina ya sakko min har kafaɗa. Bai shigo ba sai da tace, “Bismillah”. Yana buɗe ƙofar ƙamshin turaren da ko'a barci nake najisa nasan na waye. Sai da zuciyata ta motsa. Amma na dake batare da na ɗago ba na cigaba da shan fruit ɗina. Yayinda Aunty Falaq ke masa sannu da zuwa da gaishesa. Amsa mata yay da kulawa, yana tambayar Awwab. Da girmamawa tace masa barci yake yi. Da ga haka ta miƙe ta nufi kitchen. Jin kaifin idanunsa a kaina yasa na kasa jurewa, kaɗan na ɗago sai na samu idon nasa ne kuwa a kaina. Yana sanye cikin wandon jeans navy blue da hi neck riga black data masa ƙyau sosai ta kuma kama masa jiki, sai black jacket ɗinsa a saman kafaɗarsa ya ratayeta da hannunsa. Cikin abinda bai fi sakan biyu na masa kallon ba a kaikaice ta yanda shi kansa bai zama lallai ya lura shi ɗin na kalla ba na maida kan Yaya Hayatu. Gaishesa nayi ya amsa min da kulawa yana tambayata gajiya nace Alhmdllh. A dai-dai nan Aunty Falaq ta fito da tray ta ajiye gabana, batare da tayi magana ba tabi bayan mijinta daya kama ƙarfen stairs zai haye. Tare suka haura, niko na cigaba da shan fruit ɗina kamar ban san da mutum a wajen ba, sai bayan kusan minti ɗaya da wucewarsu na ce, “Ina yini”. A mamakina sai kawai naji an gittani an wuce batare da ya amsa ba. Ta gefen ido na bisa da kallo wani irin tuƙuƙi na riƙe maƙoshi na, ɗakin da nake kwana ya shige abinsa. Ƙofar na ɗan harara na cigaba da shan fruit ɗina. Sai dai me, gaba ɗaya kuma sai naji ya fita a raina. Dangwarar da bowl ɗin nayi na zame a kujerar na kwanta. Tun ina ƙirga mintuna zai fito harna koma lissafin rabin awa. Jinai zuciyata ta ƙara yin ƙunci, lallai mutumin nan ɗan wulaƙanci ne. Amma bari naga iya gudun ruwansa dai kafin na yanke masa hukunci. Minti talatin ta zama awa guda, sai ma barci ya kwasheni a wajen batare dana shirya ba.... Ransa a dagule ya dawo Dubai ɗin nan kamar yanda ya barta cikin ɓacin rai. Dan akwai kayansa daya kamata tun six days ago ace suna Nigeria kawai ake sanar masa wai an riƙesu a ƙasar Camaroon. Yayi iya ƙoƙarin sa ta hanyar waya dan ganin kayan sun isa saboda muhimmancinsu da mabuƙata kayan dake jira amma sai wani banza ke raina masa hankali. Gashi anan Dubai ɗin ma abu mai muhimmanci yake yi. Ga matarsa na hanyar tahowa. Duk da yaso ace da kansa yaje tararta hakan bai yiwu ba, dan yayi zaman meeting da wasu manyan ƴan kasuwa na duniya akan wasu matsaloli. Yana cikin meeting ɗin ya samu saƙo wai ana neman juyar da jirgin kayansa inda ya fito an hanashi ƙarasawa Nigeria. Dole yay excusing kansa daga wajen Meeting ɗin cikin abinda bai fi awa ɗaya ba yabar Dubai ya nufi Camaroon ɗin. Tunda yaje can bai huta ba, yanata faman kaiwa da komowa shi da lawyers nashi dan ƙulli ne babba ake neman masa da gwamnatin ƙasar. Sai a yau ya samu kansa kayan suka wuce Nigeria, ko tabbatar da tashin nasu baiyi ba ya fallo ya koma Dubai ɗin dan hankalinsa duk hana kanta. Shine ya iso da ɗokin ganinta amma ko ɗaga kai ta kallesa ma batai ba. Yaso mata uziri sai yaga kawai ta ɗago ta gaida Hayatu batare da shi ko ma kallonsa tayi ba. Wane kalar wulaƙanci ne hakan, matarsa, da ya ɗauka dukkan kansa ya bata da kowane irin matsayin girmamawa. Kai ina baya son raini kuma sam. Koda wani laifi ya mata ya kamata ta haɗiye a gaban koda Ummiensa ne sai sun keɓe ita da shi ta faɗa masa ko ta nuna fushin da shi, idan ba ban haƙuri ne zai bata, idan na ya fahimtar da ita ne zai yi ƙoƙarin hakan. Amma har yanzu bata san wanene shi ba. Wankansa yayi ya haye gado yay kwanciyarsa. Dan kwana biyun nan sam baya ko isashen barci, ga wata yunwa da yake ji mai tsanani amma yafi buƙatar barcin dai first. Barcin kusan awa biyu yayi alerm ya tada shi, ganin lokacin salla yayi ya miƙe da ƙyar zuwa bathroom. Ruwa ya sake watsama jikinsa dan ya warware da ƙyau, yay alwala ya fito. Yana ƙoƙarin saka kaya ta shigo ɗakin, bai nuna yasan da shigowar tata ba kamar yanda itama ta nuna bata san da shi ba tai waucewarta bayi. Sai da ta shige ya zubama ƙofar cat eyes ɗinsa da suka sauya kala. Komai baice ba ya saka sallaya ya kabbara salla. Bayan ya idar tana daga gabansa tana tata ya ɗauka waya yay kira. Cikin harshen larabci yay magana da bata wuce ta sakan huɗu ba ya ajiye yana miƙewa. Bakin gadon ya koma ya zauna yana latsa wayar, mintuna kusan goma aka danna door bell ɗin gidan, tashi yay ya fita, babu jimawa ya dawo ɗauke da ƙyaƙyƙyawan kwando a hannu. Cikin set na kujerun da aka ƙawata bedroom ɗin dasu ya koma ya zauna, bayan ya mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa, dan har yanzu tana a saman sallayar bata tashi ba. Abincin da aka kawo masa ya ɗan tsakura kaɗan ya ture... Dai-dai nan na tashi daga zaman sallayar daya ishe ni. Veil ɗin kaina na warware, yanzun ma batare dana kala inda yake ba na nufi ƙofa zan fita amma sai na jita a rufe. Mamaki ya kamani dan nasan dana shigo dai ban kulle ba. Numfashi na ɗan furzar na koma kawai saman gadon nai kwanciyata. Ina kwance kamar mai barci sai dai idanuna ne kawai a lumshe naji alamar tsaiwar mutum a kaina. Sai ƙamshin turarensa daya cika min hanci matuƙa. Kamar zan share sai dai na buɗe idanun. A kansa na sauke su, ganin yanda ya wani kafe cikina da ido yasa na yamutse fuska. Kamar na balla masa harara sai dai na daure na sake maida idanun na rufe. A matuƙar mamaki naji saukar muryarsa a kaina wai yana da buƙata.. Kutumelecy ban taɓa sanin guy ɗin nan tantiri bane sai yau. Kasa jurewa nayi na buɗe idanuna a kansa jin ya kwanto gefe na. Sai kawai na yunƙura zan bar masa gadon. Ya maida ni ya kwantar. Ƙoƙarin turesa na shigayi sai dai ko gezau. Ƙarshe takaici yasa na sakar masa kuka. Amma hakan bai sakashi fasa abinda ya ambata ɗin ba. Sai dai duk yanda yaso ya samu haɗin kai daga gareni bai samu ba. Bai kuma fasa bina a cikin nutsuwa ba. Niko tunda ya barni sai na juya masa baya kawoi ina raira kuka. (Wato bily fushin mai ciki sai addu'a kawai, dan har cikin ƙasan raina haushinsa nake ji). Yanzun ma komai baice min ba ya ma tashi ya wuce bathroom abinsa. Aiko na sake hawa fummm... Haka yayo wankansa ya fito, sai da ya kammala gyara jikinsa cikin bada umarni ya da dakewar nan tasa a daƙile ya furta, “Five thirty zamu wuce”. Daga haka yay ficewarsa. Yau na sake tabbatar da rayuwar aure haƙuri ce kawai. Duk kuma daɗinka da miji sai ya baka wannan maɗacin. Nima ji nake ƙasar kawai nake son bari, sai kawai na miƙe na gyara jikina na shirya. Sai da nai sallar la'asar na ƙarasa kimtsawa na fito duk da da sauran lokaci. Babu kowa a farlon sai television, na wuce na ɗauka ruwa na koma na zauna a kujera. A haka su Aunty Falaq suka fito suka sameni suma cikin shiri. Damuwata na haɗiye na ɗauka Awwab dake ƙusha ƙushin kuka. Batare da mun zauna ba duk da saura kusan mintuna arba'in Hayatu yace muje anzo ɗaukar mu. Nayi zaton shi yana waje, amma sai naga mu kaɗai ne muka shiga motar, koda muka iso airport ma babu shi, sai da muka shiga jirgi bayan cikar lokaci mun zauna sai gashi ya shigo shi da Juliet. Dama a wuya nake, ga shi kuma da wannan shegiyar ƙandararriyar baturiyar. Su duka ban kallesu ba, sai da ya zauna a kusa da ni cike da iyayi ta ce min, “Good evening” tana ranƙwafowa da tab a hannu wai zata nuna masa abu.” Ai bamma san na buga mata wata tsawa ba cikin rufewar ido na furta, “Hy bar nan!!”. Ba ita ba har shi uban gayyar sai da ya kalleni. Na watsa musu harara su duka yayinda ita jikinta ma ke rawa. A daburce ta shiga bani haƙuri da ƙoƙarin mun bayanin abu zata nuna masa mai muhimmanci. Nima sai na sake fusata na ce, “Okay bazaki tafin ba kenan ko?”. Zata sake magana yay mata nuni data wuce. Sim-sim ta tafi har tana waigena. Na sake balla mata harara sai ta zabura da sauri ta ƙarasa ficewa a wajen. Ƙwafa nayi da faɗin, “Da ki tsaya mana. ALLAH da sai an fitar da ke a karye daga jirgin nan. Ki cigaba da shiga mun hanci karki fasa ramammiyan banza jiki duk ƙashi ko ƙyan kallo babu subi su nanewa mazan mutane da sunan aiki mayu”. Gyaran murya ya ɗan yi. A fusace na juyo ina harararsa. Na ce, “Oh ko zaka shigar mata ne?”. Kansa kawai ya ɗan jinjina min alamar a'a, idanunsa dake wani lullumshewa a kaina ƙyam. Cikin masifar dai nace, “Aida ka shigar mata duka zan iya daku”. Na ɗauke kaina nama kwanta ina wani buɗewa da ƙyau yanda zanji daɗi. Ta gefen ido yake kallonta sai yaji abin ma ya koma bashi dariya. Ya dai dake baiyi ba, sai ya ɗan murmusa kaɗan da girgiza kansa yana ɗaukar tab ɗin gefensa ya shiga daddanawa, dan akwai abinda yake son bincika a google.......✍️ _😂 ALLAH sarki Yayanmu Sarkin haƙuri. Dangin Sam-G magana ta gaskiya ku sake mata karatun aure, mu bama son Hayaniya da raini😌._ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒇𝒐𝒖𝒓_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ ........Har muka iso Nigeria ban shiga sabgarsa ba bai shiga tawa ba, koda yake ma ni barcina nasha sosai har muka iso. Su Fahad ne sukazo tarbar mu da Guards ɗinsa. Ɗan barcin da nayi yasa jikina duk babu wani ƙwari, dole na bari ya riƙo min hannu muka fito. Muna shiga motar ma idanu na rufe kawai har muka iso gida. Kafin kowa ya fito ni na fita, na shige jikin Ummie da Mama da suka fito tarbar mun. Faɗan yanda jikina ya ɗauki zafi amma suka taho da ni haka Ummie da Mama keyi. Falaq tace ai ban faɗama kowa banda lafiya ba fa, har Yaya Awwab bata tunanin ya sani. Kallonsa Ummie tayi cike da tuhuma. Sai maimakon yace wani abu akan hakan sai cewa yay, “Ummie good night”. Ya wuce warsa. Duk binsa sukai da kallo, na balla masa harara da murguɗa baki. Babu wanda yace komai Ummie tace muma muje mu huta kowa tasa an kai masa abinci bedroom. Ni dai badan naso ba na tafi sashen namu, ɗakina kuma na shige, komai fes an gyara min, wanka kawai nayi abuna nai shirin barci. Yunwa nake ji amma bazanje ɗakinsa ɗibo abinci ba dan na fahimci can Ummie tasa aka kai. Sai nayi kwanciyata. Ko minti huɗu banyi da kwanciyar ba ya shigo ɗakin, ƙin motsawa nayi balle yama san idona biyu. Babu zato kawai naji an ɗaukan camak an fice. Watsal-watsal nake da ƙafafu ina kaima ƙirjinsa ƙananun duka da faɗin, “Ni ka sauke ni, ALLAH zan maka ihu”. Ƙin kula ni yay yaƙi kuma cewa ko ci kanki har sai da ya kaini bedroom ɗinsa ya dire a gado. Kuka na fara masa yaƙi kulani sai abinci ma da ya ɗibo ya dire a gabana. “Ni banzan ci ba. Kuma ka buɗen ƙofa na koma ɗakina dan bazan kwana anan ba.” Ƙafarsa ɗaya dogare da gadon ɗaya a ƙasa ya kamo haɓata yana mai ranƙwafowa kaina. Cikin wani ɗan iskan salo idanunsa sarƙe da nawa a saman lips ya furta, “Garama kici, dan rashin cin bazai hana na nema hakkina ba. Ɗaki kuma na ɗaureki ne?”. Ya ƙare maganar cikin ɗage gira. Baƙin ciki yasa ni kaima hannunsa wawura zan ciza. Ai babu shiri ya janye jikinsa da waro idanunsa waje. Na balla masa harara da murguɗa baki na ce, “Da ka tsaya mana”. “ALLAH ya shiryeki”. Ya faɗa yana tura hannayensa duka cikin aljihun wandon pyjamas ɗin sa. Baki na tura da jawo abincin na hau ci ban sake kulashi ba. Ina jina nayi dam na sauka nayo brush. Gadon na haye nai kwanciyata ban kulashi ba. Shima baice min komai ba yana zaune yana kallona kawai. Cikin barci na jisa a gefena ya sakani a jikinsa. Sai kawai na sake shigewa nima. Da safe kuma ba kunya na ɗora da fushina nama bar masa ɗakinsa sai a sashen Ummie muka haɗu wajen breakfast... Shirye-shiryen biki sun kankama sosai. Muna shirin wucewa Kano saboda Ummie tace gara kawai muje can ɗin ayi komai tunda muɗin duk anguna ne. Hakan yamun daɗi sosai. Dan har gyaran jiki nake son muyi aunty Zakiyya ta gama shirya mana komai. Har yanzu ni da mutumina dai ana ƴar share juna. Sai dai shifa hakan baya hanashi zuwa yasha bidirinsa a jikina. Duk kukan dazan masa kuma bazai kulani ba. Randa su Ummie zasu wuce Kano sai ya nuna wai suyi gaba ni daga baya zamu taho tare da shi. Aiko na sanya kuka sosai. Harararsa Ummie tayi, amma ya fiske abinsa yaƙi cewa komai. Daga ƙarshe ma ya tashi ya fita a falon dama muna a babban falo ne mu duka. Zan ɗaga hankalina Ummie tace karma na damu kaina na barta da shi. Ban san yanda suka ƙare ba washe gari muka wuce da su Ummien. Mun isa Kano cikin aminci, bamu wani zauna ba muka hau gyaran jikinmu dan nan ƙanwar mijin Aunty Zakiyya tazo ta same mu. Ta kuma zuba mana wani shegen lalle daya amsa suna lallale tamkar ka cinyesa saboda ƙyau. Da dare sai ga su Fahad da ɗinkunanmu. Nayi mamaki sosai dan ni bamma san an kai ba. Ashe wannan aikin Ummie ne. A ranar da yamma dole naje can gidan Abba ni da Aunty Falaq. Can ma dai shirye-shirye sun kankama. Dan su Gwaggo Gudidi na gidan ita da aunty Halima ke komai. Wai Mom taƙi shiga tace tun farko ai ba'aso a ganta a ciki ba tunda ba'a sakata ba. Kobi takanta banyi ba ma ni kam yau dan al'amarin nata ya fara bani takaici. Muka zube musu kuɗaɗe masu yawa ni da Falaq domin amfani. Hakama Abba mun bashi isasun kuɗi da zai yi hidima, sai ya kama hawaye yana sanya mana albarka. Bamu baro gidan ba sai da muka tabbatar duk wata ɓaraka mun toshe kayarmu duk da Yaya Awwab yace zai ɗauki nauyin komai muma yana da ƙyau dai aga zabuwa da zanenta kawai. Yaya Musaddiq ma dai komai normal, dan shine ma ya dawo damu gidan tare da TJ ya gaida su Ummie da musu barka da zuwa. Gefe Ummie ta jashi da Mama Balki da Baba suka tattauna abinda bamu sani ba, ko faɗan aure aka masa kuma oho mudai an ware mu. Ummie ta kawo akwati guda ƙatoto na ɗinkunan biki data musu komai iri ɗaya sai color kowa da wadda yake so shi da Fahad nacin amarci. Jinai gaba ɗaya mutanen nan nama rasa mizan ce dasu a rayuwa... Washe gari gida ya fara amsar baƙi. Wasu a ɓangaren dangin K/mashi suka iso. Sai dangin su Mama Balki da suka nuna kara. ALLAH sarki Ummie duk da itama nasan tana son taga a irin wannan ranar a nuna wasu tawaga matsayin nata dangin na uwa da uba amma bazaka taɓa ganin damuwar hakan a fuskarta ba. Ta rungume duk wanda yazo a matsayin nata na jini. Can ma su Hafiz sun sanar min ƴan Gwarzo nacan cike da gidan Abba. A daren ranar su Yaya Awwab ma suka iso. Kasancewar isowar dare sukai ni har namayi barci, sai da asuba na ganshi. Idanu na zuba masa ya wani ɗage gira irin na kallon fa. Baki na taɓe da faɗin, “Miye ma abin kallo anan mutum duk tsufa ya taso masa”. Hannu ya kai zai cafkoni na fice da ɗan gudu ina masa gwalo. Ya jinjina kai alamar zan kamaki ɗin nan. Ban sake zuwa inda yake ba dan mun zama busy. A ranar muka kai lefen Bahijja, daga can muka wuce gidan Abba kuma zamu kai na Yaya Musaddiq tare da iyayenmu dake jira dan tun jiya da dare akwatinsa na gidan Abban. Mun samu cakwakiya a gidan, ashe kawo wannan kaya ya birkice Mom nata tsiya harda su gori. Abu kamar wasa har Abba ya mareta, kaɗan ya rage ai ɗanyen aiki ya saketa Gwaggo dai ta dakatar da shi ALLAH ya taƙaita. Shine ta shige ɗaki ta rufe kanta. Bata buɗeba sai da Ummanta tazo. Sai kuma sukaga an kawo likita alamar dai akwai damuwa. Amma ba'ace musu komai ba. Oho muma dai bamu matsawa kammu sai mun sani ba muka tafi kai lefe. Tarba muka samu acan ma ta girmamawa, yayinda gidan su Ruƙayya ya rikice da ganin lefen nan kamar yanda dangin Bahijja sukai murna. To da yake su sun fisu ƙarfi, itama kuma Ruƙayya irin rayuwarmu tayi a hannun kishiyar uwa sai abin nata yafi ɗaukakuwa. Dan can ɗin ma wata drama ɗin muka gani da tafi ta Mom. Matar baban Ruƙayya harda su suma sai da aka yayyafa mata ruwa. Kai jama'a kowane gida dai akwai irin waɗan nan ashe. ALLAH ya ƙyauta ya tsarkake mana zukatanmu. Haka dai muka barosu akan sai yamma kuma an haɗu, wajen kamu dan ranar za'ayi a hall ɗin da Ummie ta kama kasancewar dai komai za'ayisa a tare ne domin sauƙaƙama juna kai-kawon. Muna dawowa gida babu zama. Shirin kamu aka fara, ni da Aunty Falaq muka koma can gidan. Mun dai zama busy body abin tausayi. Acan ɗin ma ba zaman mukayi ba. Shirin tafiya kamun da ɗan abinda baza'a rasa ba mukayi kafin cikar lokaci. Bamu sami su Yaya Awwab a gidan ba. Ni sai hakan ma yamun daɗi, dan in yana nan wani abun zai iya cewa bazanyi na wahalar masa da yarinya ba. Sai da muka kammala shiri ne ina zaune a ɗaki ina shan complex ya shigo. Daga ni har bowl ɗin dana haɗa complex ɗin yake kallo. Ni dai na masa sannu kawai na cigaba da shan kayana dan har yanzu ba'a wani shirya bane gaba ɗaya. Kamar zai shareni shima sai kuma dai ya magantu. A daƙilen nan nasa yace, “Babu abinci a gidan ne?”. “Akwai mana”. “Shine kike shan wannan shiriritan bayan kin san bake kaɗai bace. Zama da yunwa ko. Aiko zaki nutsu waje ɗaya dan dama wannan kai-kawon ya fara isata. Gaba ɗaya kun maida kanku daga nan zuwa nan kamar kun manta ma akwai aure a saman kanku. Jiba fita zakiyi amma kin zauna har ana miki wani banzan makeup a fuska. Irin ma kin maidani shashashan nan da ban san ciwon kaina ba kowane banza idonsa akan matata......” Gaba ɗaya na zuba masa ido kawai dan ya rikice sai masifa yake. Fahimtar neman dalilin da zai sa ya hanani fitar nan yake yasa yau ni na sauke tawa zuciyar. Dan kishi tsababa a kan fuskar bawan ALLAH zai hau min bori. Haka dai yaci ya tsire ni dai na daure dan in ALLAH ya yarda bazai samu sanadin hanani rawar gaban hantsi ba. Ina ganin ya shiga bathroom sum-sum na kwashi abubuwana na gudu wajen su Ummie. Banko sake yarda mun haɗu ba har muka tafi. Sai a hanya naga ran aunty Falaq a ɓace itama nake tambayarta lafiya. Kamar zatai kuka tace, “Yaya Hayat mana. Su duk yawon da suke kana jurewa amma yau kishi ya rufe masa ido sai jaraba yake mun wai dan mi zan yi kwalliya haka alhalin fita zamuyi. Na masa bayanin wajen nan babu maza sam duk matane fa, hatta da masu video mata ne. Amma sam yaƙi fahimtata. Daga ƙarshe ma wai wlhy na damesa da tsari nabar ganin bikin Yayyena ne sai ya hana yaga abinda za'ayi. Shine kawai na masa shiru nidai ALLAH ya taimaka kikazo kika kirani na samu na fito”. Rasama mizan ce nayi, dan al'amarin nasu sai naga kamar wani haɗin baki. Shi wancan da bamma gudu ba ban san a wace matsaya nake ba yanzu. A hakan ma nasan yana can fam ALLAH yasa kada ya fanshe a gobe wajen walima da kuma dinner da sai anje Lagos za'ayita ita. Hakuri kawai na bata naja bakina nai shiru.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒇𝒊𝒗𝒆_ .......Wajen kamu ya matuƙar ƙayatuwa. Ya kuma tara mutane fiye da zaton mai zato. Dan ta kowanne ɓangare amare da angunan ƴan dangi ne. Babu wani hayaniya masu kiɗan ƙwaryane aka ɗakko sai mawaƙiyar nan khairat da taima amare da angunansu waƙar aure. Mufa mune amararori, tako wane ɓangare akwaimu. Shigowar amare hannayensu riƙe da juna cikin shiga iri ɗaya komai ya sake kankama. Bayan an kaisu har masaukinsu aka buɗe taro da addu'a kafin a fara abinda ya tara mutane. Dan so ake kafin magrib dai in sha ALLAHU a kammala kada a tauye hakkin kowa. Ko maƙiyi yaga wannan kamu yasan yay matuƙar ƙayatarwa. Alheri tv sun nuna komai live, sai wasu gidan tv da aka gayyato daban sai kuma masu ɗauka a wayiyi dan yanzu kowa ya zama mai ɗaukar hoto da video sai dai addu'a. (ALLAH ya hanamu ɗakko abinda zai zame mana damuwa wataran🙏). Tiɓis muka koma gida ga kaina na ciwo. Kai rainon ciki ma dai sai addu'a. ALLAH ya ƙarama iyayenmu rahama da gafara. Samun oga na gida ya sani jin shakkar shiga ɗakin, sai da ya fita Masallaci na lallaɓa na shiga. Kafin ya dawo har na kwanta. Koda ya dawo kuma saina lafe kamar mai barci, dan ni kaina nasan na taro Match. Washe gari aka tashi da shirye-shiryen ɗaurin aure. Tako ina gidajen a ɗinke suke da ƴan uwa. Duk da ina son tafiya cikin ƴan uwana haka na daure. Baƙin daketa shigowa daga sassa daban-daban dan gayyatar ɗaurin auren nan ta zaga fiye da inda ba'a zato, auren ƙannen Maash ba wasa ba, tun daga sallar asuba bai dawo gida ba sai kusan sha biyu. Ina ɗakin ina shirin ya shigo. Gaishe shi nayi dan da safe bamu gaisa ba. Ciki-ciki ya amsa kamar yanda yake yi ƴan kwanakin nan. Kamar na watsar da shi sai kuma na tambayesa na kawo masa tea? Dan nasan bai ci komai ba har yanzu. Idanu ya zuba min sosai yana kallona. Nima kallon nasa nake yi, sai kuma na janye ina ƙoƙarin wucewata. Cak na tsaya sakamakon riƙonin da akayi, kafin ma nace wani abu ya jawoni ya zaunar saman jikinsa ya rungume. Daga ni har shi ajiyar zuciya muka saki masu ƙarfi. Cikin kunnena ya furta, “Ni na gaji da wannan faɗan haka nan”. Maimakon bashi amsa sai kawai na sakar masa kuka. hawayen da suka cika min ido suka shiga gangaro min suna sauka saman ƙirjinsa. Murmushi ya ɗan yi da har naji alamunsa. Sai kuma muka sake ƙanƙame juna sosai. “Humm miyasa kike son bamu wahala. Gaba ɗaya kin zama mafaɗaciya.” “To ba kaine kake sakani yin faɗan ba. Kamun laifi kuma ka fini fushi harda ringa mun mugunta.” “Nima ai kin mun laifin, na shigo gida ina ɗokin zuwa na ganki kawai ki wani shareni kina gaida wani a gabana ni kamar baki san da ni ba. Kin san ko zafin da naji, da ƙyar na danne zuciyata ban hukuntaki ba”. “Amma kaifa ka fara min laifin, sai kuma ka fini jin haushi. Ina fama da kaina ka tasoni babu shiri zuwa wata ƙasa. Babu tarba, babu kiran waya, ban ganka ba, da ga ƙarshe ma akace min ka wuce wata ƙasar irin ma ni bana cikin tsarinka ɗin nan. Na kiraka a waya baka ɗauka ba, baka biyo kiran ba kace min koda uzirine ya riƙeka baki sanyi a raina. Ka dawo kuma kana wani shashasha min ƙamshi. ALLAH naji ranar kamar na baro ƙasar nan ko'a ƙafa ne”. “Ya rabba! Yanzu dai duk misunderstanding ne ya shiga kawai. Bayan Ummie na a duniyar nan kece mace ta biyu mai matsayin da babu mai irinsa a gareni Samrh. Gaba ɗaya abinda kike tunani ba haka bane ba......” tsaf ya zayyane min komai daya faru, tare da tabbatar min wayarsa lokacin a Dubai ya manta ta tsabar hankalinsa ya tafi ga wancan uzirin, shima sai daya dawo a randa ma zamu wuce yaje ya ɗauka wayar a office daya barta yake ganin miss calls ɗin. Yayi niyyar mun bayani a jirgi yaga na sake tunzura har inama Juliet masifa. Sosai na sake rungumesa da faɗin, “Kayi haƙuri, ni kawai na ɗauka tsabar muhimmancin harkokin ka ne suka fini. Ita kuma ALLAH bana sonta, taita maka wani iyayin banza. ALLAH wataran sai na karya mata ƙafafun nan kamar na sauro”. “Trouble maker, kawai sai ki karya mata ƙafafu?. Yanzu ni dai tashi time zai ƙure, idan na dawo ma ƙarasa faɗan”. Yay maganar yana ɗaukata camak zuwa bathroom. Da kansa yay mun wanka nima na taimaka masa yayi. Koda muka fito a gurguje na fara taimaka masa ya shirya dan su Uncle Abdullahi nata kiranshi ashe har sun iso tun ɗazun. Matuƙar ƙyau yayi a cikin manyan kayan dan yau harda babbar riga. Ga gyaran fuska mai ƙyatarwa yasha. Haka na gyara masa gashin nan na ɗauresa sannan na saka masa hula ta yanda ba'a ganinsa. Ni kaina bamma san lokacin dana furta masa, “Mijina kai ƙyaƙyƙyawane”. Wani silent murmushi yay da jan kumatuna ya kashe min ido ɗaya da faɗin, “Duk ƙyauna na kai wannan SARAUNIYAR MATAN”. “Uhm, saika sa mata sun zaneni ta ina na zama sarauniyarsu?”. “A fadar Muhammad Awwab mana”. Ya faɗa cikin soft murya da sumbatar lips ɗina. Ya kuma ɗan duƙa ya sumbaci cikina da ya fito sosai ɗan kif da shi. Hoto na masa a gurguje ya fice dan kiran su Uncle Abdullahi yaƙi daina shigowa. Yana fita nima nai nawa shirin inata faman sakin murmushi. Na yarda kam mata da miji sai ALLAH. Duk iya ƙololuwar fushin da za'a ɗauka da juna sai kaga na lokaci ne, da zarar an huce kuma an manta shike nan... A gurguje Please 🥺. ★★ Alhamdullah bayan sallar juma'a ɗunbin al'ummar MANZON ALLAH suka shaida ɗaurin auren Yaya Musaddiq da amaryarsa Ruƙayya. Yaya Fahad da Bahijja. Ɗaurin aurene da ya tara manyan mutane ƙasar da wajenta, ƴan siyasa, sarakuna, ƴan kasuwa daga ƙasashe daban-daban. Wasu ma dai suna Lagos suna jiranmu zasu halarci dinner ne. Shugaban ƙasa da kansa ya halarci wannan aure (Amma fa shugaban ƙasa Ramadhan nake nufi🤪). Ko garin Kano yasan yau ana ɗaurin auren masu hannu da manda. ALLAH sarki Paah ma da jiki ya fara sauƙi yazo, sai da za'a ɗaura aure Maash ya gansa. Tunda suka haɗa ido da Maash yay ƙasa da kansa bai yarda sun sake ba. Sai Maash ɗin ne ya danne zuciyarsa ya gaishesa da girmamawa. Bai kuma tambayesa yaya jiki ba. Uncle Abdullahi dai shi yay waliccin Fahad, Kawu Lurwanu kuma na Yaya Musaddiq. Bayan ɗaura aure aka ɗunguma ƙaton Hall ɗin da aka tanada domin ƙwarya-ƙwaryar liyafar da su Hayatu suka shirya domin ciyar da baƙinsu abinci. Anci kuwa ansha kowa ya godema ALLAH. Yayinda mu ma anan muketa namu hidima. Mansoor da Attahir da suma next week nasu bikin da Dad ɗinsu sun halarci ɗaurin auren. Bayan kammala cin abinci manyan baƙi suka fara kaucewa. Na jirgi na nufur airport na mota na nufar masauki, wasu kuma Lagos ma suke wucewa tun yau ɗin kasancewar can akai musu masauki. Sai bayan la'asar anguna suka shigo mana da manyan yayye. Ummie ta rungume Fahad tana hawaye, kowa yasan na farin ciki ne. Shima dai hawayen yake yi, mutane da yawa na tayasu. Koda ta sakesa Yaya Awwab dake tsaye kawai yana kallonsu shima ta kamo ta rungume tana mai sanya musu albarka. Daga haka akai hotuna, Paah dai bai zo gidan ba sai su Kawu Abdullahi. Dama matarsa da Malika suna nan tun jiya, Hajiya Mammah ce dai sai yau tazo a ɗarare, itama Hajiya Mama tana nan yau kwana biyu ita da duka yaranta. ALLAH sarki Ummie, ta dake zuciyarta komai daya shafi uba su take sakkowa gaba, tun Hajiya Mammah na nuƙu-nuƙu dai harta fara ɗan warewa. Ana hotuna Ummie na maƙale da ni da Aunty Falaq. Babu ko kunya shima uban gayya ya rungumeni aka mana, harda inda yake sumbatar goshina, hannunsa kuwa na saman cikina ko'a jikinsa. Bayan kammala hotuna anan muka ɗunguma can gidan Abba kuma. Cikin namu ƴan uwan da gayyar dangi. Nan ɗin ma dai anyi hotuna na kece raini, Mom dai taƙi ko fitowa. Tanama bedroom babu wanda zai ce yazo wajen bikin nan ya ganta daga jiya zuwa yau. Ita dai Bibaa da taga babu sarki sai ALLAH saita ware abinta cikin dangi. Auta kam yana nane da Yaya Musaddiq. Sai da aka ɗakko amarya Yaya Musaddiq sannan aka ɗakko ta Fahad, gida ne mai ƙyau da tsari aka kai amaren su duka anan anguwar da muke. Yaya Musaddiq a can sama, Fahad anan ƙasa. Duk da ba zama zasuyi ba su duka kowa yasan haka duka iyayen amaren sunma yaransu jere gwargwadon ƙarfinsu. Babu shiri daga gidan amaren na fito a ƙafa saboda babu wani nisa na koma gida. Dan ji nake kamar zan zube dan gajiya. Aiko ban nema kowa ba na shige nai wanka da ƙyar na kwanta. Bamma san lokacin da Yaya Awwab ya dawo gidan ba, sai cikin dare da yunwa ta sakani farkawa na gansa........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒔𝒊𝒙_ ........Washe gari tun safe wasu aka wuce Lagos da su, dan jirage uku na Maash aikin jigilar ɗaukar mutane sukayi🤪. Su Ummie suna cikin masu tafiyar farko, ni dai da Aunty Falaq da amare da angwayensu sai namu mazan dole sai yamma. Dan Fahad ya buɗe aiki. Babu ɗaya ƙafa a daren ya maida Bahijja amaryar gaske. Baiwar ALLAH tana ta ɓarzar kuka. Babu shiri Ruƙayya ta kirani tace nazo akwai matsala ta rasa yanda zatai da Bahijja itama duk ta firgice. A lokacin ina jikin nawa angon, cikin mamaki yake tambayar lafiya dan na roƙesa zanje can. Abinda ta gaya min na faɗa masa. Zai kira wayar Fahad dan shi bai ma fahimci komai ba na dakatar da shi. “Yaya karka kirashi, bafa wani abin tada hankali bane ba.” “Kamar ya kada a kira shi, kika sani ko wani shirmen ya aikata. Kin san fa Fahad baya jin magana”. Dariyama ni abin ya bani, na ce, “Ai wannan karon rashin jin nashi na manyanta ne. Kawai inaga ya angwance ne fa”. Idanu sosai Maash ɗin ya zaro da faɗin, “Samrh! Anya yaron nan nada hankali? Ya bari a gama bikin mana”. Dariya kawai na shiga yi. “Kai yaya mutum da matarsa. Nidai yanzu bara naje...” bamma gama rufe baki ba sai ga kiran Fahad ɗin ya shigo min. Muryarsa a sanyaye ya ce, “Aunty dan ALLAH kizo yanzu. Amma kada ki faɗama kowa nan zaki zo har Yaya Please. Wlhy ina cikin matsala”. Dakewa nayi ina ƙoƙarin danne dariya nace masa gani nan kada ya damu. Koda na yanke kiran sai Yaya Awwab da duk ke jinmu yay ƙwafa kawai. Ni dai na ɗan taɓe baki da faɗin, “Idan ma dai babu batun kwanciya asibiti da ɗinke-ɗinke irin na wasu ai da sauƙi. Shi yayi da ƙyau”. Harara ya zubo min kamar zai cinyeni da idanu. Na fita abina ina dariya dan nasan ya gane da shi nake dai.... Sosai Bahijja ta bani tausayi, kai maza dai duk sai abarsu. Ita kanta Ruƙayya duk tayi laƙe-laƙe. Haka na taimaka mata da ruwan zafi tanata faman kuka. Dole Yaya Musaddiq ya samo mana wata Nurse ƴar anguwar mu ta dubata. Alhamdullah dai tace ɗan ƙarin data samu baida yawa. Adai kula da shigarta ruwan zafi sosai wajen zai haɗe da kansa. Ta kuma bata magunguna. Ban baro gidan ba sai da taci abinci tasha maganin ta kwanta. Na fito na samu Fahad a falo ya zabga tagumi. Dariya nayi a zuciyata. Amma a zahiri fuskata a dake na ce, “Ta samu barci, ni bari naje na samu Yayanka dan dole tafiyar mu ta koma sai ko zuwa six ne. Idan ta tashi ka kula da ita ta shiga ruwan zafi yanda ya kamata”. Kansa dake ƙasa ya jinjina min, kafin murya a sanyaye ya ce, “Amma aunty babu matsala ko?”. Hararsa nayi. Ya sake duƙar da kai yana sosa ƙeya. “A yanzu dai babu, amma idan ka kuma batare data warke ba akwai. Ka kuma san duk yanda zaka lallasheta ta nutsu kar Ummie ko yayanka su fahimta, kaga dai wajen taro za'a shiga. In ba hakaba kai da su ne ni babu ruwana kaga tafiyata. Sai na shigo anjima”. Daga haka nai ficewata. A ƙofar gida na samu Maash jikin mota yana waya. Na ɗan tsaya ina masa kallon mamaki har ya kammala ya katse. “Lafiya kuwa na ganka anan? Ba barci kace zakayi ba?”. Fuska ya ɗan yamutse, “Na kuma kasa tunda kika fito. Idan akwai matsala inaga ki fito da yarinyar nan muje asibiti”. “No babu wata matsala fa. Ai shi bai jawo magana da yawa ba kamar wasu”. “Suwa kenan?”. Ya faɗa yana wani bina da kallo a dake. Kafaɗa na ɗan ɗage da taɓe baki na ce, “Ni dai ai ban faɗi suna ba a zancena ba ko”. “Kin san ALLAH yarinyar nan kina shiga mun hanci kwana biyun nan, amma zan kamaki ne. Zaki san ni kika tasa a gaba”. Dariya nayi da faɗin, “Oh oh kaji tsargar kai. My Lion kaji na ambaci sunanka a maganata. To kodai kaima haka kayi ne?”. “Zo muje sai na faɗa miki yanda nayi ni, dan har farkawa nayi aka ɗinke”. Yay maganar yana ƙoƙarin cafkoni. Da sauri na zille ina dariya nai hanyar gida. Tsaye yay kawai hannayensa duka biyu riƙe da ƙugunsa yana kallona harna buɗe gate zan shige. Sai da na saka ƙafata ɗaya na ɗan leƙo kaina na masa gwalo na ida shigewa ina murmushi. Kusan karo mukaci da Aunty Falaq a ƙofar falo. “Ke kuma daga ina haka?”. Dariya na saki da nuna mata gate. Nace, “Daga gidan amare. Na leka nemanki da zan fita naga kuna tare da Yaya Hayat a baya shine na wuce. Yayanki ne ya jiƙa aiki”. Idanu ta zaro sosai da faɗin, “Wanne daga ciki?”. Dariya na sake kwashewa da shi da kai bakina saitin kunnen ta na raɗa mata. Ta riƙe baki tana dariya da fadin, “Kai ALLAH ya shirya Yaya Fahad wlhy. Shi babu ɗan kawaici mu ƴan biki mu tafi sannan. Muje ni dama nemanki nake fa Aunty Maijidda ce ta kirani yanzun”. “Okay muje to”. 🏃A gurguje Please 🥺. 🌿🌿🌿🌿🌿 Bamu bar Kano ba sai shida na yamma. Abinka da jirgi mun isa akan lokaci, dan Alhamdullah sallar magriba ma a gida ta mana. Mansion fa yayi masifar cika ta ban mamaki. A hakama wasu suna hotels. Na ɗan ji sanyi ganin sashenmu babu wannan hayaniyar. Dan sai da ma ya buɗe sannan muka shiga. Bamufi mintuna biyar ba Ummie ta shigo ta samemu a falo dan bamu kai ga haurawa sama ba. Mun gaisheta cikin girmamawa. Ta amsa mana da kulawa tana tambayata babu dai damuwa ko? Babu inda ke mun ciwo kuma.. Nace mata eh babu komai. Sosai na waro idanu waje jin wai harda mu fa a wannan dinner. Dan Uncle Abdullahi ya dage akan dole mu kasance cikin anguna da amare tunda mu a namu bikin babu abinda akayi. Abubuwan da suka faru kuma Yaya Awwab bai taɓa magana ba ya kamata a wannan gaɓar duniya ta sake tabbatar da aurenmu. A marairaice na ce, “Amma Ummie ALLAH ai shine shaida. Idan ta mutane zamu bi ko UBANGIJI bazamu bautamawa ba yanda ya kamata. Kawai a barsu su cigaba da shirmensu watarana sa gane da kansu. Bayanin da Abba yay musu kuma a wancan karon mutane da yawa sun fahimta”. “Hakane Daughter. Amma ku fahimci zancen Abdullahi nakan gaskiya. Anji duk wancan ta wadatar, amma watarana ake gudu musamman ga masu tasowa da su bamu san wazai iya rarrabe musu gaskiyar ba. Sannan yaranku nan gaba wani zai iya amfani da wannan damar ya saka musu ruɗani a zukatansu”. “Hakane Ummie”. Na faɗa a sanyaye kaina a ƙasa. Jin shiru uban gayyar bai taka ba na ɗan ɗago na kallesa. Itama Ummie shi take kallon. Itace ta katse shirun namu da faɗin, “Muhammad bakace komai ba”. “Ummie toni mizance tunda kun gama magana. Duk hukuncin da kuka yanke ai dai-dai ne. Kawai dai kamar yanda ta faɗa ne maganar mutane ba abin biyewa bace. Tunda mu mun san kammu fine”. “Duk da hakan dai kawai ku shirya. Ga kayan da zaku saka can a ɗakinta an ajiye muku. Mai kwalliya zata zo ta mata”. Da sauri ya ce, “No Ummie abar batun kwalliyar nan. Kayan ma idan basu min ba zan iya canjawa”. “Kai kuma ka sani wannan uban ƴan kishin tsiya”. Ta faɗa tana miƙewa ta fice abinta. Shiru da ga ni har shi babu wanda yay magana. Sai ma wani kicin-kicin da yay da fuska alamar sam baya ra'ayin abin kawai yayi biyayya ne. Nasan dama bazai masa ba shiyyasa naso tun farko Ummie ta fahimta. Gudun karma ya juye bala'in a kai a sai na miƙe kawai ina faɗin, Bara nayi fitsari” na gudu abina. Nafi minti talatin da shiga sannan ya shigo. Ina kwance a gado kawai ina ƙullawa da kwancewa. Nasan mutumin nan da kishi kada ayi abun nan ya zame min baya da ƙura. Box ɗin da kayan ke ciki dako motsasu banyi a inda suke ba ya ɗauka ya shiga buɗewa. Sai da ya fito da kayan ciki tas ya gama kallonsu kafin ya zubesu a saman gadon ya kai zaune yana wani shafar fuska da furzar da huci mai ƙarfi. Shiru kusan na minti ɗaya kafin cikin sanyi nace, “Uhmm Yaya Awwab kodai kawai nacema Ummie banda lafiya. Nasan hakan zai sa tace nai zamana. Kaga shike nan an rabu lafiya”. Shiru kamar bazai tanka min ba sai kuma ya juyo ya kallani. Sai da ya ɗan lumshe ido ya buɗesu a cikin nawan kafin ya sake furzar da numfashi a slowly. Fuskarsa a yamutse ya ce, “Bayan ta tambayeki kince lafiya kike. Kawai ki tashi ki shirya ɗin”. Daga haka ya tashi ya fita abinsa..........✍️ 🏃🏃Mufa mun wuce airport. Wanda bai shirya ba sai ya taho a mota babu ruwana. Bikin Fahad guda ai sai mun zubar😂🤣🤣🤣. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ ......Ajiyar zuciya kawai na sauke nima na tashin. Sai da na fara yin wanka nazo nai sallar isha'i sannan na hau shiri. Lass ne ko material zan kirashi bamma sani ba nikam. Amma yayi masifar haɗuwa. Ga wani uban stones work yasha na musamman. Rigace doguwa har ƙasa fitet datai bala'in bin jikina ta fito da matashin cikina ɗas hannunta dogo sosai. Sai akai wani shegen flay jacket data sauka ta rufe har mazaunaina ta gaba kuma ta ɗan gota cikina ta yanda ba'a ganinsa sam. Sosai pitch and black color ɗin lass ɗin ya fita da fitarsa ta haƙiƙa. Ɗinkin kuma ya sake ƙawatashi. Tunda ya hana mai kwalliya dole ni na zauna naima kaina ɗan light makeup da na tabbatar yama fi wancan da za'a canja min kamanni. Dan nan a ainahina nake komai cif-cif. Ɗan ƙwalin kaina ɗauri daya sake ƙawata kwalliyar sannan na saka jacket ɗin da ɗan turare kaɗan na saka sauran tarkacen ƴan kunne da sarƙa da suka kasance zinari. Nasan nayi ƙyau koda ba'a faɗa min ba. Ya Arrahaman na faɗa a zuciyata ni kaina fa nake kallon kan nawa ta mirror. Kwalliya dai kam itace mace. Komai muninka indai zaka gyara sai an kalla an sake kallo. Bare kuma Alhamdullah muna da dai ɗan ƙyan nan dai-dai mu ma. Balle a yanzu da ciki ya sake ƙawatani da fiddoni fam. Flat shoes ɗin da aka haɗo da kayan na sakama ƙafata mai ƙawace da dan kyalli da baƙi. Kafin na haɗa ƴan tarkacena a handbag. Ina warware mayafin ya shigo shima cikin shirinsa. Shaddace baƙa data masifar fiddo da ainahinsa. Sai kawai na tsaya ina kallonsa kamar yanda shima yake kallona. Na buɗe baki zanyi magana sai shima ya buɗe zaiyi muna ƙoƙarin haɗa baki. Duk shiru mukai muna ma juna murmushi. Sai kawai nai ƙasa da kaina har ya ƙaraso inda nake. Kamar mai tsoron a jisa cikin silent voice ɗin san nan ya furta, “Anya kuwa zan barki fita a haka My Samrh”. Kaina a ƙasa ina murmushi na ce, “Sabida mi?”. “Kinyi ƙyau ne fiye da yanda kike tunani”. “Kaima ai hakan. Dan komai ka saka a jikinka ƙyawunka ƙawatashi yake yi”. “Ai ke kin mafi ƙyawun ƙyau My helf”. Ya faɗa yana rungumoni jikinsa. Ni dai addu'a kawai nake kada yace na cire ko yace an fasa. ALLAH dai ya taimakeni akai kiransa a waya kan mu ake jira kowa ya tafi har angwaye. Gyalen ya amsa da kansa ya yafa min. Batare da ta sake magana ba ya ɗauka handbag ɗina a hannunsa na haggu na damar ya kamani muka fita. Gidan shiru sai securitys kawai. Sai motar dake fake fara tass mai shegen ƙyau da kuma ta guards ɗinsa guda biyu. Da sauri TJ dake neman faɗuwa saboda kallonmu ya buɗe murfin da sauri, yayin da shi Uban gayyar ya zagaya da ni ta ɗaya side ɗin ya buɗe da kansa ya taimaka min na shiga sannan ya sake zagayowa inda Tj ya buɗe masa ya shiga.. kallona ya ɗan yi ya sakar min murmushi. Nima sai na sakar masa murmushin tare da kwantowa gefen hannunsa.... 🤍❤️🤍❤️🤍 A ɓangaren anguna da amaransu kwalliya ce ta kece raini da ko makaho ya kalla yasan naira tayi aiki a wajen. Dan rigunan amare da suka kasance pitch sun musu masifar ƙyau. Hakama angwaye dake sanye da fararen suit kamar ka sace su ka gudu dan ƙyau. Manyan motocin da aka sakasu sabbi ƙal ko ledojinsu ba'a ɗaye ba sunyi matuƙar sake ƙawatasu. To magana ake ta aljihu da manda fa. Ƙannen Maash sunfi gaban wasa a wannan gaɓar. Hall ya cika iya cika taban mamaki duk da kuwa duk wanda ya shiga wajen yana da lasisin hakanne. Harka ce ta manyan mutane da ƴaƴan manyan. Ga ƙawayen amare sun fito cikin nasu kalar ta musamman da nunama tsara. Kamar yanda al'adar biki yake bayan sanar da isowar anguna da amare ƙawayen amarya da abokai suka jagoranci shiga dasu cikin tsari da nutsuwar data ƙayatar da kowa. Yaya Musaddiq shine babba. Dan haka yana a gaba shi da amaryarsa Fahad biye da shi maƙale da tasa amaryar da makeup ya ɓoye yanayinta na gumurzun da tasha a jiya hannun angon nata. Dan yanda tafiyarta ma bata gama daidaita ba Falaq ta canja takalmanta zuwa flat gudun matsala. A hakanma dai dan hannunta na cikin nashi ne ya taimaka mata da rufa asirinta. Babu wanda zai ce waɗan nan angwaye da amare basu birgesa ba. Ga shi an musu ɗinki na mutunci da sam bai fidda tsiraicinsu ba. Hasalima maimakon naɗa ɗan kwali a saka net su rolling ɗinsa akai musu ta yanda ya sake mutuntasu matuƙa. Wajen hawa steps Bahijja ta kasa saboda azabar data ratsata. Dan tun takun farko ta tsaya cak. Ai kawai Fahad na fakar ido ya ɗauka kayarsa camak ya ƙarasa da ita har saman kujerar da zasu zauna. Miko za'ai inba dariya ba. Dan yanda yay ɗin dole ya burgeka kuma ya baka dariyar. Shiko ko'a jikinsa fatansa dai asirinsa ya rufu a gama harkar nan lafiya Ummie ko Mama ko Hajiya Mama wani bai ramfosa ba. Dan Hajiya Mammah ma shi zaima iya gaya mata da bakinsa har yanzu ba wani mutunci take da shi a idonsa ba. Wajen zama uku aka tanada. Su suna gefe da gefe na tsakkiya na babban yaya. Sai dai ba kowa ya sani ba, ana daita mamakin ma rashin isowarsa akan lokaci wajen dan har aka gabatar da addu'a da ɗan wasu abubuwan bai iso ba. Sai bayan kusan mintina talatin aka sanar da isowar tashi. Anan fa wanda basu san Maash ba suka fara baza ido domin ganinsa. Wanda kuma suke wasi-wasin batun aurensa na son tabbatarwa da gaskiyane ko kuwa. Saboda an san dai babu yanda zai ya halarci wannan dinner babu matar. Bayan mc ya gama kirari da wasa shi ya shigo cikin gakun nan nasa na ƙasaita da rakiyar bajiman guards ɗin sa abin zabbirgewa. A gefensa ƙyaƙyƙyawar matarsa da suka gama dacewa a gefensa hannunsa sarƙe a cikin nata ɗayan hannunsa ɗauke da handbag ɗinta. “Masha ALLAH”. Kalma mafi girma data dinga fita a bakunan mafi yawan mutanen wajen kenan, dan duk iya hassadarka kasan wannan haɗi ya haɗu. To sai muce mai abu da abunsa ne ya shigo. Dan kuwa dai bakin mc ya gagara rufuwa sai washi yake iya washi kamar zai haɗiye garshensa. Abu mafi birgewa ga anguna guda biyu kuma ƙanne da duniya ta shaida ga MAASH yana taka step ɗin wajen suka miƙe domin girmamawa a garesa. Sai kawai ya tsaya kallonsu shima da murmushin da mutane da yawa zasu iya rantsuwar basu taɓa gani akan fuskarsa ba. Dan har cikin rai yake jin alfaharin kasancewarsu ƙannensa, tare da cika burin kakansa da har ya koma ga ALLAH bazai taɓa mantawa da shi ba. Sai kuma ƙyau da sukai masa matuƙa dan da kansa ya bada design ɗin kayan da ke jikin nasu musamman ma suit ɗinsu. Nuni yay musu da su zauna kafin ya ƙarasa shi da tasa zinariyar mazauninsu. Kamata yay da kansa ya zaunar sannan shima ya kai zaune ya kuma jawota jikinsa da ƙyau tamkar za'a ƙwace masa ita. Aiko abokansa sai kawai suka hau salute nashi. Farin cikin Ummie baya musaltuwa a wannan rana. Sai da ta share hawaye ta sake sharewa sau babu adadi. Yayinda ita ke kukan farin ciki anan acan asibiti Baba prof na ƙunar zuciya yake yi shi da ƴarsa Lawisa. Dan kuwa saboda su Maash ya ɗauki nauyin gidajen tv masu yawa suke nuna wannan dinner live. Ya kuma saka aka saka musu tashoshin dan su gani kamar yanda kowa ke gani. Wani irin zafafa da hanƙoro zuciyar prof keyi a cikin ƙirji. Sai dai babu damar motsa ko ɗan yatsa dan shi da dutse basu da banbanci a yanzu ƙasancewar sai an motsashi dan haka yake turum. Rashin makama ya sakashi fashewa da kuka kawai. Hawaye masu azabar zafi da ƙona zuciya suka dinga bin fuskarsa. Yayi kiran azo a kashe masa tvn amma babu kowa a kusa. Sai faman taunar lips yake yana fasasu da gaƙori tare da antayi ashariya manya-manya kamar ba tsoho ba. A ɓangaren Commondo kam dariya ya dinga yi, dan shi ba taron bane ya zame masa abin kallo prof ne. A kwanakin nan dama a tsakaninsa da shi sai dai ƴar tsinema juna da yin ALLAH ya isa. Prof ɗin yayi-yayi a raba musu ɗaki anƙi ko kulashi. Daya damu mutane ma dan bakinsa ras na magana da ga shi har commondo ɗin. Sai securitys ɗin dake tsare da su sukace bashi da wannan isar ai a yanzu. Kalmar nan ta masa masifar ciwo. Ai ko ya dinga surfa musu zagi a wannan rana amma babu wanda ya kulashi... ★★ A wajen dinner bayan mc ya gabatar da isowar Maash da tashi amarya aka sake addu'a. Kafin aunty Mama ta fito ta gabatar da kanta matsayin ƙanwar mahaifin anguna. Ta kuma buƙaci nutsuwar kowa dan acewarta tana da bayani mai muhimmanci da babban saƙo ga duk wanda ke a hall ɗin dama wanda ke gani a wajen ta hanyar television. Tsitt kuwa hall ɗin ya sake yi fiye da da. Itama sai ta sake nutsuwa da juyawa ta fuskanci Maash dake gyarama Samraah mayafinta suna magana ƙasa-ƙasa. Cike da kulawa ta kira ainahin sunansa.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ ........Dara-dara ɗin cat eyes ɗinsa ya ɗago ya kalleta. Tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya amsa mata da girmamawa. Da sauri mc ya kawo masa mic dan kowa na buƙatar jin abinda zai faɗa. Hakan ya sake gamsar da mutane. Hajiya Mama ta cigaba da faɗin, “Muhammad Awwab wacece a tare da kai?”. Juyawa yay ya kalla Samraah da tai ƙasa da kanta. A hankali ya ɗaura hannunsa saman haɓarta ya ɗagota. Kallon juna sukai cikin ido kafin a hankali ya kai mic ɗin saitin small pinkish lips ɗinsa ya motsasu cike da ƙasaita idanunsa a cikin na Samraah ɗin itama nata a cikin nashi har lokacin ya furta, “Aunt! Ita ɗin MATATA CE!”. Ya Arrahaman, irin wannan salo haka mai kashe zuciya. Sai kawai hall ɗin ya ɗauki tafi. Da ƙyar aka samu ya lafa. Hajiya Mama ta sake faɗin, “Yaushe ka fara sonta?”. Yanzun kam idanunsa ya lumshe tare da sake juyawa ya buɗe su akan Samraah da ita kanta wannan tambaya ta sakata jin zumuɗi tana kallonsa. Cikin tsakkiyar idonta ya sake saka nashi. Cikin wani irin soft voice ya furta, “Ranar dana fara GANINTA”. “Yaya akai haka bayan kowa yasan Maash ba ma'abocin shiga sabgar mata bane?”. “Saboda ita ta kasance ta MUSAMMAN”. “Uhmmm Masha ALLAH ta musamman kam. Muma shaida ne. Amma zamu so musan yaya akai haka da sauri?”. “Saboda tayi abinda wani bai taɓa kwatanta yi ba a sunan ma'aikacin jarida harda Mazan. _(“Sir a matsayinka na matashi da za'a iya shiga mamakin ganin yanda ka gina katafaren kamfani irin wannan da ya zama na farko a Africa, a duniya na uku kuma bama shi kawai ka mallaka ba, akwai wasu manyan cibiyoyi daka kafa a ciki da wajen Africa ma ba Nigeria kawai ba, ko nace duniya, shin ko zaka iya jan hankali matasa irinka dake tasowa dangane da neman na kai da asalin tarihinka dan su san kaima ba daga kwance ka kai wannan matsayin ba, sai da kai aiki tuƙuru, tare da tsallake ƙalubale masu yawan gaske kuma duk kai haƙuri ka jure har gashi a yanzu ka zama wani babban ginshiƙi tauraron duniya dake haska yankinsa da ƙasarsa, yarensa harma da addininsa?)_ Sune kalmomin data furta masu girgiza zuciya da rarrabesu suka zama masu wahalar gaske da sanya razani, tare da jan hankalin Muhammad Awwab El-Mu'azz Maash gareta. Dan shine lokaci na farko, kuma karo na farko da naga tsantsar JARUMTA da iya aiki da ƙwarewar iya sarrafa harshe na ƴan jarida a tare da yarinya ƙarama kamarta. Idan nace muku TSORONTA naji, har na amince batare dana shirya hakan ba karki musanta min” Kutumaddu-madu. ai wani irin sowa da ihu da hall ɗin nan ya ɗauka na matasan samarin dake wajen dama abokan uban gayyar su kansu kai kace wata gagarumar ƙwallo da duniya ta dasa ma idanu gaba ɗaya ce a kaci. Ya ilahil alamin. Maash ya gama buɗe aiki yau. Ita kanta Samraah jikinta tsuma yake yi. Babu shiri ta shige jikinsa ko zata samu nutsuwar fuskantar mutane. Sai da aka samu hall ɗin ya lafa bayan mc ya warware sautin waƙar da aka rairama Maash ɗin da Samraah sannan tambaya ta koma kanta. Cikin tsareta da ido Hajiya Mama ta ce, “Daughter Samraah wanene wannan tare da ke?”. Kallonsa na ɗan yi sai kuma na duƙar da kai ina murmushi. Mic ɗin ya kawo gab da bakina, a hankali na furta “Mama Miji”. “Oh Woow Masha ALLAH. A ina kuka fara haɗuwa?”. “Wajen taron buɗe Company naje a matsayin mai ɗaukar rahoto.” “Kenan kema tun a ranar ki ka faɗa a soyayyarsa?”. Shiru nayi kamar bazance komai ba. Hakan yasa hall ɗin yay tsitt sosai. Sai da Hajiya Mama ta sake furta, “Muna sauraren Mrs Maash”. Ɗagowa nayi na ɗan kallesa sai naga ya wani tsareni da shanyayyun idanunsa. Ɗan hararsa nayi kaɗan na maida kaina na rissinar. Kamar mai koyon magana na ce, “Mama kawai dai....” Sai kuma nayi shiru. Sai da na sake jan wasu sakanni da saka ƙaguwa a zuciyar kowa na kuma ji a raina ajin da naja ya jawu. Dan shi kansa uban gayyar a ƙagare yake sannan na furta, “Addini, nagarta, Ƙyawawan ɗabi'u, kama mutuncin kai, yakana sune suka fara jan hankalina bayan aure. Aduk wanda ke gefe idan akace masa Maash abinda zai faɗa ko ya fara kawoma ransa, ko ya kallesa a bangon mujallu ko jaridu da fuskar television matsayin matashi da ake makallo da wasi-wasin dukiyarsa ko ta halak ɗin ce ko kuwa akwai wasu dabaru. Tantiri da baya jin magana, mai izza, fariyya da dukiya. Mai tsananin ɗagawa da girman kai wanda baya son arewa da mutanen yankin. Sai dai kuma sam ba haka bane, na fahimci hakanne nima a lokacin da muka kasance kusa da juna. Maimakon waɗan can halayen da ake masa kallo da ga nesa. sai naci karo da kishiyarsu a tattare da shi. Hasalima da matasanmu zasuyi koyi da halayensa da sun matuƙar ribantuwa. Mutum ne mai addini da kula da shi fiye da yanda muke zato. Yana da ilimin addinin sosai. Mutum ne mai sauƙin kai da son sauke hakkin na ƙasa da shi cikin tausayawa. Mutumun ne jarumi ba malalaci ba. Akoda yaushe ƙoƙarin neman nakansa yake ta hanyar HALAL da kuma guminsa. Sannan ba arewa bace baya so manyan arewan ne da ya kamata su jawosa jikinsu arewar ta amfanu da shine ruɓaɓɓu. Dan ta aljihunsu kawai suke yi su. Wannan nagartar tasa itace tushe kuma mafarin komai. Idan har za'aso MAZAN da basu da ko quarter ɗin waɗan nan halayen nasa shi mizai hana a so shi”. Na ƙare maganar a hankali ina mai ɗago idanuna na kallesa. Shima ɗin kallona yake, dan haka na ɗan kashe masa ido ɗaya kamar yanda yake min ina wani sassanyan murmushi. A hankali na motsa lips ɗina idanun nawa a cikin nasa na ƙarasa furta, “Dan haka shine ALJANNAR DUNIYA TA”. Sosai hall ɗin ya kaure da tafi, yayinda dj ya saki cool music na masoya mai ratsa zukata. Shiko jikinsa kawai ya jawoni ya rungume sosai. Tare da faɗin, “NIMA ITACE ALJANNAR DUNIYA TA”. Sake hargitsewa hall ɗin yayi kuwa. Kusan mintuna goma kafin komai ya nutsa. Aunty Mama ta cigaba da faɗin, “Nasan wasu dayawa zasu ce muda mukazo taron sabbin amarya da ango mun ƙare kuma ga tsaffin aure. To ayi haƙuri, suma wannan taro harda su. Dan nasan mutane da yawa kafin sanin Maash yayi aure sukan saka a ransu duk ranar da zata kasance ta bikinsa sai ya nema fasa Nigeria da wajenta na ban mamaki. Sai kuma komai ya faru batare da an sani ba, hakan yasa daga baya da abin ya fito wasu suka shiga ruɗani. Shiyyasa mukai amfani da wannan damar domin tabbatarma da mutane gaskiyar da suke son sani. Muhammad Awwab El-Mu'azz Maash dai mijin Samraah Abdul-wahab Gwarzo ne. Wadda akafi sani da Sam-G. Muna musu fatan alheri da zuri'a ɗayyaba tare da dawwamammen farin ciki. Yanzu zamu dawo kan angunanmu da amarensu suma. Mc bissmillah”. Taro ya cigaba da gudana cike da birgewa da ƙayatarwa. Tarihin angwaye biyu dana amarensu sai san barka. Yayinda aka warware sautin mawaƙa da aka gayyato daga arewaci da kudancin ƙasar. Kai da kaga yanda ake zuba liƙi da manyan kuɗaɗe zaka san bikin na girma ne. Su Alhaji Fahad babu yakana babu ɗaga ƙafa yasha rawarsa. Yayin bada cake ya tsotse lips ɗin Bahijja tsaf dan sai da ya saka a nashi bakin sannan ya bata. Lokacin da Ummie tazo tana musu liƙi su dukansu bayan an saka mata waƙarta ta girma itama Mama Balki da Hajiya Mammah biye da ita Maash da Samraah sukazo suka fara liƙeta da daloli🤪 itama. Ai tuni suma aka zo ana zuba musu nasu. Yayinda Ummie ta juyo garesu suma. Hakama Yaya Musaddiq da Fahad da amaren biyu suka fara zuba musu. Falaq da Hayatu da Jaga Hafizzullah suma ba'a barsu a baya ba. Waje dai kam sai sambarka kawai. Duk fa wannan al'amari dake faruwa a idanun su Mom ne da tun ɗazun da suka iso taci karo da Mansion illahirin jikinta ya dakata da aiki. Sai hawaye, wani abu daya dinga yunƙuro mata a ƙirji yasa babu shiri ta bukaci shiga toilet. Toilet ɗin kusan neman gigita mata lissafi yayi, ta hau tari sai ga jini. Kuka sosai taci a bayin tana kallon jinin data tara a cikin hannunta. Ita kaɗai tasan abinda take ji a zuciyarta. Wannan wane irin al'amarine haka mai ban ruɗani. Shiyaysa tacema Ummanta bazata zo ba. Amma ta takura akan su zo kodan suga tsiyar da za'ayi. Damunta da Umma tai da knocking yasa dole ta buɗe bayan ta wanke fuskarta ta fita. Data fito ɗin ma ta samu an baje musu tarin abinci na alfarma da sai a gidan girma. Sai abinda kake so zaka ɗiba kaci, ga Halime sai dai zuba santi take ta kasa zuane ta kasa tsaye. Ashe ba'a nan abun ya tsaya ba, aka kwaso su kuma zuwa wajen nan daya ida gigita tunaninta. Harda matar shugaban ƙasa fa. Bama wannan ba, yanda aka ɗaukaki al'amari Samraah na bata mamaki da tsoro, koyaya ta motsa Maash na ankare da ita. Hakama mahaifiyarsa. Yaya Musaddiq kam duk abinda sukema ɗan su Fahad basu babbanta shi ba. Suna ɗaya ake kiransu da shi, ƙannen Maash. Ana cikin taron mahaifiyar Maash taje har inda su Samraah suke ta kamo hannunta ta dinga zagayawa da ita wajen manyan matan dake wajen suna gaisawa. Tsabar wulaƙanci tana ata gefen wata matar Minister amma ko kallonta Samraah batai ba kamar ma bata ganta ba, alhalin har haɗa ido sukai. Sai kuma can ta hangosu inda Halime take har Ummie na ɗaukar yaro ɗaya a cikin yaran suna dariya cike da nishaɗi. Akazo wajen liƙa kuɗi, Samraah da Maash fa daloli suka liƙa su. Akazo kuma aka lulluɓesu suma da liƙin. Ga kalaman da Maash ya dinga zubawa akan Samraah ɗin kansa tsaye cikin tsananin kulawa da tattali. Itama kuma ta zuba a kansa. Jitai ma gaba ɗaya idan ta cigaba da lissafin zuciyarta zata buga. Sai kawai ta tashi ta fice a hall ɗin idanunta har kamar ma basa ganin hanya da ƙyau... Ba Mom kawai ba, acan asibiti jikin Baba prof da Hajiya ƙarama rikicewa yayi. Dan shi jijjiga ya fara kamar irin na mace mai naƙuda ya dinga taune lips suna jini kumfa na fita ta bakinsa ta hanci. Ga idanunsa ƙyam akan television. Itako Hajiya ƙarama kuka take iya ƙarfinta tana jama mahaifin nata ALLAH ya isa. Itama dai daga ƙarshe sai da doctors ɗin suka mata allurar barci.......✍️ Kuce dani ina Paah🏃🏃🏃?. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒏𝒊𝒏𝒆_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ ......Paah na gida yana kallon komai shima. Dan tunda suka dawo ɗaurin aure can gidan Prof Uncle Abdullahi ya kaishi inda Hajiya Mammah take zaune kasancewar an sallamesa asibitin. Babu yanda Uncle Abdullahi baiyi da shi yaje dinner ɗin ba amma yace bazai iya ba. Wlhy bazai iya haɗa ido da Ummie ba, balle Muhammad da Fahad kuma. Dama ɗaurin auren da ƙyar ya iya dake zuciyarsa ya je. Dan kawai yana son ya halarta ne tunda bai samu zuwa na Maash ba a wancan lokacin. Haka dole Uncle Abdullahi ya barsa. Amma sai yace masa ya kalla to ko'a tv ne. Shine yay zaman kallo shima. Gaba ɗaya murmushi ya ƙi barin fuskarsa. Ga hawaye sun gagara tsayawa. Ji yake inama ya dawo da baya ya goge dukkan abinda ya aikata ya zama kamar ba'ayi ba. Yasan ya tafka kurakurai masu yawa a rayuwarsa da shi kansa baya jin zai iya yafema kansa balle Ummu-Hidaya. Ya mata abubuwa da yawa a rayuwa da ya kamata ace ta yanke alaƙa da shi tuni amma ta jure ta cigaba da zama da shi har zuwa gaɓar da mahaifinsa ya aikata mata abinda bai taba sani ba, bai taɓa zato ko tsammani ba. Tabbas bama ita ba su kansu mahaifinsu ya zalincesu, ya cutar da su da rayuwarsu. Ko'a mafarki bai taɓa tunanin zai iya kwatanta abinda ya aikata ga mutum irin Abie ba. Wannan wace irin cin amana ce mai saka ruɗani da barazanar keta zuciya. Kuka mai ƙarfi ya sarƙeshi. A cikin wannan halin Uncle Abdullahi ya shigo a rikice yake sanar masa ya tashi suje asibiti jikin baba ya rikice. Ji yay tamkar yace bazai je ba. Amma dai ya daure dan yana son yin tambayoyi ga mahaifin nasu kafin shi ko shi wani ya bar duniya. A wannan gaɓar har cikin zuciyarsa yana fatan barin wannan duniyar ne.... 🌿🌿🌿🌿 Alhamdullah taro ya tashi lafiya, anguna da amare sun kasance tare da juna. Washe gari baƙi da yawa suka kama gabansu. Ƴan Kano ne kawai suka rage. Sukam sai sunga wucewar Yaya Musaddiq da matarsa shiyyasa. Zuwa yamma manya suka yima anguna da amare nasiha da addu'a. Musamman ma Yaya Musaddiq da zasu wuce a ƴau China. Bayan sun kammala Yaya Awwab ya zauna da mu. Yaya Musaddiq, Aunty Falaq, ni sai Hafizzullah. Ya fara da mana nasihar riƙe junanmu da gaskiya. Tare da ɗaukar nauyin mu ya danƙa ga Yaya Musaddiq a matsayinsa na babba garemu a yanzu kuma uba. Ya nuna masa tarbiyyar daya bamu itace zamu haɗu mu gina family da har ƴaƴanmu zasuyi alfahari damu anan gaba kodan ƙoƙarin mahaifinmu. Daga ƙarshe yay maganar company da Abie ya bamu. Ya bamu shawarar za'a raba companyn bisa tsarin shari'a garemu matsayin gado. Sai kuma mu dunƙuleshi waje guda mu ginashi da ƙarfin ikon ALLAH. Abinda dai yake so mu gane anan ya kasance kowa yasan hakkinsa da kuma abinda zai dinga shigo masa koda anan gaba ALLAH ya ɗauke wani a cikinmu bazai zame mana rikici ba ko ya zame wa ƴaƴanmu. Mu duka mun gamsu da shawararsa. Mun kuma masa godiya. Daga haka kuma kamar yanda ya faɗa aka ɗunguma tare da manyan iyayenmu zuwa wannan company. Ashe ma ana abubuwa cikinsa. Sai dai ba wani ƙato bane amma watarana in sha ALLAHU idan mun jajirce ALLAH ya kuma amsa zai kai ma inda ba'ai zato ba. Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain ya mana rabo na adalci, kowa yasan tsaginsa, ya kuma mana nasiha shima dan yau zai wuce... Muna dawowa gida su Yaya Musaddiq sukai shiri. Rakkiya mukai musu airport. Bayan zaman mintuna kusan talatin jirginsu ya ɗaga shi da amaryarsa Ruƙayya. Baiwar ALLAH tanata kukan rabuwa da iyayenta. Haka dai suka tafi kowa na musu fatan alheri. Yayinda na koma sukuku ni kuma. Dan mun bar Mom a gida tanata aman jini. Su Hayatu dai suna shirin tafiya da ita asibiti. Daga nan asibitin muka wuce muma. Mun samu Alhamdullah jinin ya tsaya har sun sakata barci. Nan dai akai mata addu'ar samun lafiya muka wuce gida. Banyi mamakin samunsa a gidan ba harma ya kwanta wai kansa ke masa ciwo. Nasan harda wannan hayaniyar. Wanka na farayi sannan na haɗo masa shayi. Da ƙyar na samu ya tashi ya sha. Magani kuma yace bafa zai sha ba. Iya lallaɓa yaƙi, dole ba haƙura na masa addu'a kawai muka kwanta dan nima takaina nake. Washe gari mutanen Kano suka wuce suma da Mom a haka. Aunty Halime ta tafi ta barmu da dariyarta. Gidan ya koma shiru da ga mu sai mu. Sai masu aiki da keta ƙoƙarin saita komai. Ango da Amarya dai ko ƙeyarsu bama gani. Suna sashensu ana shan amarci. Sai dai a aika musu abinci a koma a ɗako kwano (Da gaskiyarka Fahad🤣😂). Labarin rikicewar jikin Prof ta samemu a bakin Hajiya Mama da bata koma ba. Da farko dai babu wanda ya tanka. Sai daga baya Ummie tace mu shirya zamuje asibiti. Babu wanda baiyi mamakin jin batunba. Dan ko Maash da baya nan yaje Abuja yana dawowa dana faɗa masa kasa yin magana yay, sai idanu kawai daya zuba min. Sai kuma can ya miƙe ya fita. Ban san miya faru ba naga ya dawo dai ransa a ɓace. Bai gaya min ba ban tambayesa ba. Bayan sallar isha'i muka fita bisa umarnin Ummie. A asibiti mun samu duka yaransa tare da shi. Numfashi ma yanzu sai da abin shaƙar numfashi. Tunda muka shiga ɗakin jikin Paah har rawa yake. Sam ya kasa haɗa ido da kowa a cikinmu. Ko gaisuwa da akayi da tambayar yaya mai jiki shi kam bai iya amsawa ba. Ni sai ma duk ya bani tausayi, ga ac a ɗakin amma shi zufa yake yi. Prof ma idanunsa a kammu ya ƙura ma Ummie su, da Yaya Awwab da tunda muka shigo yay tsaye a bakin ƙofa abinsa yana danna waya kawai. Bana jin ko gaisuwar da akai ma shi yayi. Baima kalla kowa ba. Miƙewa mukai da shirin tafiya prof ya shiga jujjuya kansa da shi kaɗai ne ke aiki. Uncle Abdullahi ne yay ƙoƙarin dakatar da mu, tare da matsawa gaban gadon ya cire masa oxgyen ɗin. Wani irin jan numfashi yay da ƙarfi har sai da muka tsorata, dan da sauri Bahijja ta shige jikin Fahad da ke kusa da ita. Cikin wani ƙarfin ya sauke numfashin idanunsa akan Ummie. Rawa lips ɗinsa suke alamar sonyin magana, sai da ƙyar ya iya tattaro abin faɗar muryar ma sam babu daɗi. “Ummu-Hidaya kina gani kinci nasa ko?”. Murmushi Ummie tai masa da gyara tsaiwa, batare data yarda ta kalla kowa ba ta ce, “So kake na tisa maka da bakina naci NASARAR ne? Dan nasan kai a karan kan ka kasan naci nasarar”. Hawaye ne suka zubo masa, ya shiga jinjina kansa yana murmushi dake tabbatar da tsantsar takaicinsa da yanda zuciyarsa ke ƙuna. “Hakane Ummu-Hidaya. Na yarda kinci nasara, amma bazan taɓa karɓar FAƊUWA ba ni kuma. Domin kema baki ci nasarar ba sai da ƙarfin ikon ƊANKI”. “Humm in dai har ka yarda naci nasarar ai Alhamdullah, domin idan ma ɗan nawane yaci ai kai da kaya duk mallakar wuyane. Saboda kaima yanzu daka tashi kiransa ƊANA kace.” “Ɗanki kam, amma da jinin nawa ɗan nima. Shiyyasa ma ya iya irin NAWA salon. Domin TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. Jinin ubanki bashi da ƙarfin da zaki samu wannan ZUMMAR ko shi ɗan naki ya samu”. “Oh ashe akwai jinin ɗanka a jikinsa. To ai ban sani ba saboda ni kaina kawai nake kallo a matsayin mahaifiyar waɗan nan BARADEN. Idan kana tantama gasu nan ka tambayesu. Shin suna da wani ne bayan ni a matsayin wadda ta haifesu....” Kafin ma ta rufe baki a kausashe Fahad ya amshe da, “Babu Ummie. Ke kaɗai muka sani, ke kaɗai kuma muke kallo. Kece DUNIYAR mu. Bayan ke daga ni har ɗan uwana ko DANGIN UBA bamu da su balle UBA. Kai ko tsohon BANZA ashe bazaka risina ba har sai kaji kanka a KABARI kenan? Ai kaima kasan dama itace mai nasara a kanka tun kafin yanzu. Kamar yanda Abie yake mai nasara a kanka dun kafin ita. Bakaji dama mita faɗa maka ba a wancan lokaci, kamar yanda ka ƙare rayuwarka a ƙarƙashin ƙafafun Abie. Haka zuri'aka zasu ƙare a ƙarƙashin ƙafafunta. Shin tsohon najadu baka fahimci wannan ayar bane ba a yanzu? Ko dai an maka filla-filla ne?. Gasu nan ka tambayesu. Su dukansu a ƙarƙashin ALFARMAR wa suke a da da yanzu. Ko kana tunanin badan ALLAH da MAZANTAKAR ɗan uwana ba da tuni kana bara a titi, su kuma suna can gidajen karuwai da ƴan maɗigo. Wlhy da ace akwai inda zanje a zuƙe jinin ɗanka a jikina da tuni na jima da tafiya. Ka iya bakinka kodan ka mutu a hannun ƴaƴanka, dan wlhy ina ɗaga maka ƙafa ne saboda Aunty Mama da Uncle Abdullahi. Amma ka sani wannan da kake gani tafi ƙarfinka. Shari'ar duniya kuma bata da lokacin yi da kai shiyyasa koda akace za'a kai ku kotu tace bata ra'ayi, muma kuma muna goyon bayanta. Wannan halin da ƴar shegen da kaje kayo ta saka ka ciki ya isheka. Ummie kumuje, ni banga amfanin ma ɓata lokacin yin magana da wannan wawan tsohon alakwan-kwan ɗin ba.” yaja hannun Ummie da Bahijja yana faɗin, “Aunty kumuje Please”. Gaba ɗayan mu kamar an sagar mana gwiyawu. Sai dai ganin Yaya Awwab bai motsa ba duk muka kallesa. A mamakin mu Paah ya ƙure da idanu shi. Tsahon sakanni kafin ya sauke ƙafarsa daya dogara jikin bango, murya a dake ya furta, “Idan akwai igiyar auren Ummie a kanka, ina son ka yanke ta ta hanyar shaidar hakan. Idan kuma kaƙi zamu haɗu a court”. Daga haka ya kama hannun Ummie shima ya fice.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒆𝒏_ .......Mun iso gida babu mai iya cewa ko uffan. Ni dai harga ALLAH banji daɗin abinda sukai ma Paah ɗin ba. Koba komai mahaifinsu ne. Anji yayi kurkure, babban kuskure kuwa da magana ta ALLAH yafe masa ga ɗan da yasan zafin mahaifiya abune mai wahala. Sai dai kuma idan duk aka tattara akai haƙuri sai komai ya wuce. Koda muka kasance daga ni sai shi naso na masa maganar su ɗan sautama Paah ɗin, su kuma bashi damar neman afuwar Ummie, idan ta yafe masa suma suyi haƙuri su yafe masa. Tunda dai babu hannunsa a cikin manyan laifukan. Koda yake shima nashin babban laifi ne. Amma sai naji tsoron hakan. Dan kallo ɗaya kaima fuskarsa ta isa sakaka ka shiga hankalinka. ★★ A asibiti sun wuce sun bar cakwakiya. Dan Prof dai bakinsa yaƙi rufuwa sai tsinema su Fahad yake. A fusace Paah ya furta, “Ƴaƴana ba tsinannu bane ba baba. Kuma in sha ALLAHU bazasu kasance hakan ba. In dai kai baka kasance da tsinuwar ALLAH a kanka ba su mi sukai maka da kake aibanta min su?. Baba ka cutar da mu. Ka wulaƙanta rayuwarmu ta hanyar kasa godema ni'imar da UBANGIJI yay maka. Abie ya maka dukkan gata na rayuwa batare da kun haɗa komai ba. Ya tallafeka ya tallafi mahaifiyarka, ya tallafi matarka damu ƴaƴanka. Amma ka zaɓi sakashi a rana kai ka maye gurbin inuwarsa. Shin baba kai wane irin mutum ne? Bakaji komai ba a yayin salwantar da rayuka har shida saboda buƙatar DUNIYA mai yankewa? Bakayi tunanin kaima wataran zakaje inda suka tafi ba? Bakayi tunanin sune da nasara ba kai ne mai faɗuwa koda ace ka mallaki kuɗin daka salwantar da rayukansu a kansu. Kaicon mahaifi irinka, kaicon jini irin naka, kai cin zuciya irin taka Bab.....” kuka mai cin rai ya sarƙe Paah, hakama su Uncle Abdullahi kuka suke sosai a wannan gaɓar. Su dukansu suna maimaita masa inama ace ba shine mahaifinsu ba. Inama zasu iya canja ƙaddararsu. Wani irin ratsa zuciyar Baba prof kalaman yaran nasa sukeyi matuƙa, kodan basu taɓa haɗe kai sun masa hakan ba a tare ne oho. Komai fa yayi ne domin su, domin jin daɗinsu, amma a ƙarshe ma gashi suna kaico da kasancewarsa mahaifinsu. Kokuwa anzo gaɓar da shima zai ɗanɗani ɗacin hakanne oho. Sai kawai ya fara jijjiga kamar ɗazun, dole dai aka sakasu suka fito likitoci suka ƙara rufuwa a kansa. Kafin wani dogon lokaci abin ya rincaɓe matuƙa. Sai aman jini ta hanci ta baki. Haka suka kusa kwana a kansa, sai dai kuma babu tsumi babu dabara. Lokaci yayi. Prof an tafi ba'a nema gafarar kowa ba, zuciyar ma batayi nadama da yarda ta aikata ɓarna ba. Hatta ƴaƴansa kaico suke da kasancewarsa mahaifinsu, babu kokarin da ba'ai ba na ya kama kalmar shahada da suke karanta masa sai ma saɓanin hakan ke fita a bakinsa. Su kansu likitoci da jami'an tsaron dake tare da shi jikinsu yayi sanyi. Yayinda kowa ke jifansa da ALLAH wada rai. Babu wanda za'a ambatawa mutuwarsa ya faɗi alkairi ko nema masa rahama. Sai dai a ce halinsa ya bisa. Wasu ma cewa suke sai kuma aje a tarar da abinda aka shuka. Cikin matuƙar kuka Uncle Abdullahi ya ce, “Kaicon mu ƴan uwa, Kaicon mu. ALLAH yasa muyi dawwamammen tuba kafin mu koma garesa. Wlhy ƴan uwa ba'ata yaya rayuwarka ta ƙare ba ko yaya ƙarshenka ya kasance ne abu mai sauƙi. Ka cutar da mutane ka kwanta jiyya ko fuskantar wani iftila'i na rayuwa ne sakamakon ba ko ƙaddarar laifunka. Babban tashin hankali da bawa zai fuskanta a rayuwarsa bayan shuka mugayen ayyuka shine ya bar duniya batare da neman gafarar kowa ba kamar yanda mahaifinmu ya kasance a yau. Ya bar duniya ZUCIYARSA na mai kasancewa a bushe batare da rinisa ga UBANGIJI ba. Ya bar duniya jama'ar dake zagaye da shi a kusa ko nesa suna mai jifansa da ALLAH wadarai da murnar an rage musu mugun iri irin. Yabar duniya kowa naji a ransa shari'ar UBANGIJI tafi wadda za'a kwatanta yimasa anan duniya. Ya bar duniya ana ALLAH wadai da gagara nema masa gafarar UBANGIJINSA😭😭. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ƴan uwa mun san minene raɗaɗin FITAR RAI kuwa? Mun san MINENE KWANCIYAR KABARI KUWA? Mun san MINENE TASHIN KIYAMA kuwa? Munsan MINENE WUTA DA ALJANNA kuwa? Ƴan UWA ni da ku duk bamu sani ba fa😭. Amma UBANGIJI ya mana nuni da su a cikin littafinsa mai tsarki a ayoyi daban-daban, MANZON ALLAH ya isar mana da saƙon tabbatattu ne kuma zamu kai garesu ko mun shirya, ko bamu shirya ba. Ko mun yarda, ko bamu yarda ba. Mi muke kallo ƴan uwa? Mi muke jira? Mi muke tsammani? Mi muke hange? Ina muke tunanin kaiwa?. Itafa duniya sunanta kawai DUNIYA. Ribarka da ita kawai ka BAUTAMA UBANGIJI, kayi biyayya ga MANZON ALLAH. Sai UBANGIJI ya baka ƙyaƙyƙyawar makoma domin RAHAMARSA da GAFARARSA. Dan ALLAH, dan ALLAH, dan girman ALLAH ƴan uwa mu tuba mana. Mu zubda mugayen ayyukanmu mu koma ga ALLAH. Kin san kina bin Bokaye domin biyan buƙatar duniya mara amfani a gareki, akan KISHIYA, ko Mallakar MIJI, ko Mallakar abokan zama, ko Mallakar ƴan uwanki, mahaifiyarki, oganki a wajen aiki, ogarki a wajen aiki ko kasuwa, family ɗinki ko na mijinki. Kin san kina ZINA, kin san kina MAƊIGO, kin san kina amfani da kanki wajen biyama kanki buƙata, kin san kina shaye-shaye, kin san kina gulma, kin san kina annamimanci, kin san kina zunɗe, kin san kina muguwar kissa wa miji dan ya tozarta abokiyar zamanki, kin san kina yaudara, kin san kina zamba cikin aminci, kin san kina cin bashin mutane, kin san kina kawalci, kin san kina cin amanar mijinki, kin san kina sata, kin san kina sakaci da tarbiyyar ƴaƴanki subi maza dan su samo miki kuɗi, kin san kina cutar mutane ta hanyoyi da dama, kin san kina! Kin san kina! Kin san kina😭. Ya kai ɗan uwa aikinka shine ɓata tarbiyan ɗiyan mutane. Kana matashi ko mai aure kasan yanda zaka yaudari yarinya da kuɗi ka aikata ZINA da ita. Ko ka bita ta ƙarfi, ko yara ƙanana da bama su gama sanin kansu ba. Kasan kana bin bokaye domin asiri yara su bika su soka. Kana bin bokaye dan oganka na office ko kasuwa. Kana bin bokaye dan neman mulkin duniya. Kasan kana LIWAƊI, kasan kana gallazama matarka a cikin gidan aurenka. Duk hakkin da ALLAH yace ka sauke nata kana tauyeta, bata isa kuma tace ka tauyeta ba sai kaci zarafinta. Kasan kayi sakaci da tarbiyyar ɗiyan da ALLAH ya baka matsayinka na mahaifi. Kasan kana sata, kasan kana gulma, munafunci, annamimanci, zunɗe, fallasa sirrin gidanka a majalisa, zamba cikin aminci, durƙusar da makwafcinka na kasuwa ko wajen aiki saboda kai ka tashi. Amsar cin hanci da rashawa ka bama wanda bai cancanci aiki ba ka hana wanda ya cancanta. Shaye-shaye, siyar da kayan maye, kawalci, neman matan mutane a social media, kune munafukan anguwa anzo neman auren yarinya ku ɓata saboda son zuciya, aboki ya kawo muku damuwar gidansa dan ku bashi shawarar banza ku ɗora shi bisa mummunar aƙida. Duk wani munafunce-munafunce a harkar siyasa kana gaba-gaba. Kaine! Kaine! Kaine. To kafa shirya, akwai babban aiki a gabanmu wanda baka san ranar da zai zama MAFARI gare ka ba. Akwai ɗan ɗanar raɗaɗin zafin fitar RAI. akwai kwanciyar KABARI da amsa tambayoyin cikinsa. Akwai tashin alƙiyama, akwai HISABI, akwai makoma mafi girman tashin hankali. Sune guda biyu, dole, dole, dolene a cikin biyu sai kin/ka kasance a cikin ɗaya. Wato WUTA ko ALJANNAH😭😭. Zaɓi ya rage tsakanin ni da kai. Dan haka mu kasance masu sassautama zukatanmu. Mu guji duk wasu mugayen ayyuka da ruɗanin duniya fa shaiɗan ke ɗibarmu garesu komai ƙanƙantarsu. Mu zauna da mutane lafiya dan bamu san randa malaki'an mutuwa zai ƙwanƙwasa mana ƙofofinmu ba. Mu sauke hakkin na ƙasa da mu, mu kiyaye cin hakkin koda iyalanmu ne. Mu bama ƴaƴanmu tarbiyya ta ƙwarai, mu nema daga hankalinmu, muyi haƙuri da kaɗan, wataran sai UBANGIJI ya bamu mai yawa ta hanyar da bamuyi zato ko tsammani ba. Ba sai munyi shirka, ko tauye hakkin wasu zamu samu arziƙi ko ɗaukakar duniya ba. Daga ɗaukaka har dukiyar ba masu amfanar damu komai bane idan har bamubi ALLAH da MANZONSA ba. Domin ita DUNIYA ba nan bane gidan GUMURZUN. LAHIRA itace kankat, sai mai RABO kuma ke samun tagomashi da ROMON dake can. Mu yawaita istigfari, mu yawaita istigfari, mu yawaita istigfari. ALLAH ka gafarta mana ka gafartama iyayenmu. Ya rabbi kasa muyi dawwamammen tuba kafin mu koma gareka. Ya rabbi kasa ranar mutuwar mu ta kasance ranar farin cikin mu, ya rabbi kasa kwanciyar kabari ta zama hutu a garemu, ya rabbi kasa mu kasance a cikin tawagar da MANZON ALLAH zai ceta yayi kuma alfahari damu ranar TSAIWA matsayin al'ummarsa. Ya rabbi kasa duniya a tafukan hannayenmu kada ta kasance a cikin zukatanmu. Ya rabbi kasa kar muje da arziƙi gaban UBANGIJI, hakkokin MUTANEN da muka zalunta a duniya ya cinyesu mu koma MATSIYATA. dan arziƙin DUNIYA ɗan uwa, ƴar uwa ba shine arziƙi ba. Arziƙin tashi da ayyuka ƙyawawa a ranar sakamako, amma haƙƙokin mutane ya cinyesu bayan an gama biyansu mu tashi taskarmu babu komai sai zunubansu da namu shine babban talauci😭. To ALLAH ka bamu ikon sauke hakkin mutane da ke a kammu, mu kuma nema gafararsu kafin mu koma garesa. Ya rabbi kasa mu karɓi LITTAFINMU da hannun DAMA😭😭. Ya UBANGIJI, ya RABBI, ya ALLAH kasa ALJANNA ta kasance makomarmu ni da ku da iyayenmu baki ɗaya 😭😭😭🙏”......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒆𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_ .......A safiyar yau kam ko ina da ina labarin mutuwar prof ta karaɗe. Uncle Abdullahi yazo har gida ya sanar mana. Shiru kawai falon yayi babu wanda ya iya cewa komai. Dama tun jiya da muka dawo daga wajensu kowa sukuku yake. Banyi zaton Ummie zatace muje ba. Amma sai tace muje. Yaya Awwab da Hayatu ma sun fita amma tace su dawo gida. Haka ta tasamu gaba mukaje can gidansa da za'ayi jana'izar sa. A yanda ya shahara, yay kuma suna a tsakiyar manyan ƙasar nayi zaton jana'izar sa sai tayi kamar ta fasa garin Lagos da kewaye. Amma sai me sam munje ƙofar gidan babu kowa. Sai tsirarun masu gadin gidajen maƙota dake tsaitsaye daga ƙofar gida. Sai ƴan sandan da suka kawo gawarsa suma dai nasan kunyar Uncle Abdullahi ne ya sakasu tsayawa. Sai mijin Aunty Mama. Sai kuma mu da mukaje, dan ko mu a cikin gidan iyakar mune kawai, Hajiya Mammah, Aunty Mama, Ummie, Mama Balki, Maman Malika, Malika, Ni, Bahijja, Aunty Falaq. Ba wannan bane kawai abin kuka. Ko sanda za'ai masa salla gaba ɗaya nakan sahu mutum tara ne. Paah, Uncle Abdullahi, Baban Hayatu, Mijin Aunty Mama, Hayatu, Awwab, Fahad da sai da Ummie ta masa dole sai wani mai gadin makwaƙwafcinsa. Sai TJ drivern Maash. Amma sauran mutanen wajen duk zare jikinsu sukayi cikin dabara ana fitowa da gawar tasa. Wannan abu ya matuƙar saka Ƴaƴansa kuka. Mu ma ya tayar mana da hankali. ALLAH dai ka rabamu da mummunan ƙarshe. Ana dawowa daga kaisa makwancinsa Yaya Awwab ya aiko wai mu fito zamu wuce gida. Hakan yay matuƙar saka Paah kuka na tashin hankali. Ya riƙe hannun Ummie yanayi. Yayinda Fahad ke riƙe da ɗayan hannunta yana janta su tafi. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, wannan abu ya sake taɓa zuciyar kowa. Duk yanda Yaya Awwab ke gudun shigowa gidan sai da ya shigo. Kallo ɗaya yayma Paah dake durƙushe riƙe da hannun Ummie yana kuka ya ɗauke kansa. Jimmm yay a tsayen kafin ya tako a hankali zuwa garesu. Fuskarsa a gefe ya kama hannun paah ya cire daga cikin na Ummie. Batare da yace komai ba ya kama ta suka fita da ita. Sai Uncle Abdullahi da Baban Hayatu ne suka zo suka kama Paah aka shiga da shi ciki. Dan wani irin jan numfashi yake da ƙyar tsabar yanda yake kuka da kiran sunan Ummie. Haka muka tafi muna kuka muma. Dole salon tafiyar kam ya canja yanzu. Ummie da Fahad da Yaya Awwab ɗin suka tafi a mota ɗaya, mu kuma mika shiga sauran motocin muka bisu baya... Sam gidan babu daɗi, dan tunda muka dawo Ummie ta kulle kanta. Hakama Yaya Awwab rufe kansa yay a ɗaki, duk yanda na dinga roƙonsa ya buɗe ina kuka ƙiy yayi. Itama Ummie Mama Balki nata lallashinta ta buɗe amma bata buɗe ba. Ashe shima Fahad nacan ya rufe kansa a Garden. Haka muka kasance da su har dare. Sai wajen ƙarfe ɗaya aka samu da ƙyar Ummie ta buɗe. Da ga ni har Falaq jikinta muka shige muna kuka. Itama sai ta rungumemu tanayi. Tunda abin nan ya faru babu wanda zai ce yaga kukan Ummie irin yau. Idanunta sun matuƙar kumbura luhu-luhu. Haka muka koma wajen Yaya Awwab amma shi kam bugun duniya yaƙi ya buɗe. Har gabannin asuba ana abu ɗaya. Haka aka ƙyalesa dole dan kowa ya tabbatar bafa zai buɗe ɗin ba. Wannan yanayin ya haifar min da tashi da ciwo nima. Dan har washe gari dai Yaya Awwab yaƙi buɗe kansa. Su Uncle Abdullahi ma sun zo shi da Aunty Mama da Hajiya Mammah suna roƙonsa ya yafe musu ya buɗe amma ina. Haka dole aka taso Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain daga Kano. Dan Hayatu da yasan Maash ɗin zai iya abinda yafi ma haka yana gani sha biyu tayi yaƙi ya buɗe kawai ya tattara ya tafi Kano. Ƴar matsalar ma da suka samu a airport ce ta sakasu kaiwa Magrib kafin su iso. Lokacin da suka iso mai ɓalle ƙofa nata iya ƙoƙarin sa amma abu yaƙi yiwuwa saboda security ya saka ga ƙofar, gashi ba anyhow ƙofa ba. Ta windows ma kuma duk ya rufe babu ta yanda za'a ganshi. Da wa'azi Malam ya fara, sannan ya koma nasiha, ya koma lallashi da ban baki. Da ga ƙarshe ya rufe da tsoratarwa akan in fa har ya bari zuciyar Ummie dake cikin damuwa. Ko ni dake matarsa da tsohon ciki tawa zuciyar ta buga, ko Paah ɗin da suke ganin sun sallamashi saboda laifin da yayima mahaifiyarsu tashi zuciyar ta buga yabar duniya batare da ya yafe masa ba shi kenan sai ya shirya amsoshin da zai bama UBANGIJI kuma. Daga haka muka bar wajen. Har mukai sallar magrib ana jiran ko zai buɗe, akai isha'i shiru, sai wajen ƙarfe tara sannan ya buɗe. ALLAH sarki uwa. Jikin Ummie har rawa yake taje ta rungumesa a jikinta tana kuka mai ban tausayi. Ya matuƙar galabaita dan haka dole likita ya fara ƙoƙarin duba shi. Ba kuma kamai ya jawo masa hakan ba sai rashin natural iska da abinci, sai rashin isashen barci saboda idanunsa sunyi lufu-lufu shima, dan ruwa kawai yake sha a ciki. Sai dai akwai Alkur'ani a ajiye da sallaya alamar dai abin alkairi yake yi a ciki ba fushin kawai ba. Wlhy nayi zaton idan ya buɗe zamuga ya fasa komai na ɗakin. Amma sai ba haka ba. Yana a cikin nutsuwarsa sai dai ya gama jigata da galabaita. Kowa yaji daɗin hakan, Malam kansa yanata sanya masa albarka da baiyi fushi irin na yahudanci ba. Faffasa abubuwa ko neman kashe kai, ko zama cikin matsanancin bakin ciki babu ambaton ALLAH ko miƙa lamura garesa..... ⭐⭐⭐⭐ Har ranar addu'ar uku babu wasu mutane ko ƴan zaman makoki. Hatta masu irin zuwa gaisuwar nan babu sam. Sai ma hotunan prof ɗin dake yawo a media kowa na faɗar albarkatun bakinsa marasa daɗi a kansa. Da wahala kaji wani ya masa addu'ar neman rahama. Sai sake tono mugayen ayyukansa da ALLAH wadarai, ya kuma zama abin yima mutane ishara... A ɓangaren mu muma dai sai muce Alhmdllh. Dan kowa dai ya dawo cikin hankalinsa. Sai dai babu wani armashi a gidan sai oga Fahad dake cin amarcinsa. Sai kuma Malam dake ƙoƙarin haɗamu yay mana nasiha kullum da tunatar da mu muhimmancin iyaye da haƙuri da su. A hankali nasihar ta dinga ratsa kowannenmu har washe garin da akai addu'ar uku na prof dai Malam yazo da Paah gidan da duka ahalin prof ɗin. Ummie da yaya Awwab har sun miƙe Malam ɗin ya dakatar da su. Haka dole suka koma suka zauna badan sun so ba. Sai dai sun ƙi sake kallon ko sashen da Paah yake sam. Ni dai cikin ƙarfin hali na gaishesa, hakan da nayi sai Aunty Falaq ma da Bahijja suka gaishesa. Miƙewa mama Balki tai tana mana nunin mu tashi mu basu waje, amma sai Malam ya dakatar da ita yace duk mu koma mu zauna ai zaman namu nada amfani. Komawar mukai muka zauna jikinmu duk a sanyaye... Shiru na kusan minti ɗaya kafin malam yay gyaran murya yayo addu'a. Sannan ya fara karanto hakkin mata akan mijinta, hakkin miji akan matarsa. Hakkin uba akan ƴaƴansa, hakkin ƴaƴa akan mahaifansu. Daga ƙarshe ya rufe da faɗin, “Kun san miyyasa na fara muku da wannan foundation ɗin?”. Amsawa mukai mu duka da a'a. Ya jinjina kansa da cigaba da faɗin, “Saboda tun farko idan aka gagara kiyaye wannan haƙƙokin suke ruguza gida dama al'umma gaba ɗaya. Shiyyasa a mafi yawan lokuta zaka samu gidajen mu babu wani ginshiƙi dake riƙe da su. Maganar gaskiya ce ta taramu anan, mu kuma gyara abinda muka ɓata saboda munada sauran dama tunda muna a raye, bamu sani ba kuma ko sakan ne ya rage mana, minti ko awa ko kwana, sati, wata, shekara ko shekaru duk bamu da wannan ilimin. Shiyyasa a duk sanda ka aikata kuskure ka fahimci kuskure kayi yimaza kai Istigfari ko neman gafarar wanda ka zalunta ka kuma yi tuba na gaskiya da cikakken alƙawarin dainawa dan baka sani ba ko iya wannan damar ce kake da ita. Dan ko yana raye kaima kana raye sai ma ka dace da ya yafe maka ne fa. Ga shi kuma UBANGIJI shi baya yafe laifin wani akan wani. Alhaji Mu'azz zan fara da kai. Tun farko kaine baka gina gidanka a yanda ya dace ba, ba kuma ka sauke hakkokin da ya kamata ace ka sauke ba. Tabbas a dukkan abinda ka faɗa min kayi kuskure, kuskure kuma mai girma. Babu wanda baya kuskure a rayuwa, mu kuma maza mukan aikata fiye ga haka ga abokan rayuwarmu mata. Sai dai wasunmu kan ɓoye suje can suyi a gefe matan basu sani ba, ai ko laifi kake aikatawa ana ganin kayi alkunya ka kuma mutunta kanka idan ka ɓoyesa. Amma bayyana shi tamkar izgilanci ne ma UBANGIJI. Na tabbata ga Ummu-Hidaya ta riƙe ka a raine saboda girman kuskurenka na ƙarshe, abinda tayi kuma shine dai-dai, suma kuma yaranta basuyi laifi ba a dalilin juya maka baya da sukayi, hakan shi ya nuna suna kishinta, da mutunta ta dan koni nan abinda zanyi kenan akan mahaifiyata........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆_ *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ .......Amma sunyi kuskure da suka manta kai sunanka mahaifi, har abada kuma wannan sunan na nan a tsakanin kai da su na mahaifi da ƴaƴa bazai taɓa ya canja ba, dolene ka sauke hakkokin su, suma dolene su sauke hakkokinka. Domin idan UBANGIJI ya tashi hukunci zai hukuntaka ne da kuskuren da kai masa, su kuma bazai zama hujja a garesu ba wajen kare kansu suce ai saboda wancan dalilin ne suka gagara sauke hakkokinka. Wancan kuskuren daban, wannan ma daban. Dan haka ina kira a garemu gaba ɗaya, da mu gyara kuskurenmu tun kafin guri ya ƙure mana. Ruwan Ummu-Hidaya ne ta yafe masa laifunkasa, wannan tsakaninsu ne. Amma ku dai ku nema afuwarsa ya yafe muku, sannan shima ya nema afuwarku ku yafe masa dan ku duka kun tauye juna ta fuskokin kasa sauke hakki. Abinda ya faru kuma a baya ya rigada ya faru, ku daina kallonsa shi da ƴan uwansa da laifin da mahaifinsu ya aikatama marigayi Ibrahim da Abdul-wahab dama sauran mutane. Wancan shima tsakaninsa da sune, tsakaninsa kuma da UBANGIJISA ne. Nasan abine mai wahalar gaske, dan magana ta gaskiya ya kai girman da idan cewa Ummu-Hidaya tai ku fita a rayuwarta gaba ɗaya batayi laifi ba. Adam yayi kurakurai masu yawan gaske da kawai dai sai abar ma ALLAH ikonsa. Domin shine ke rahama, kuma shine ke jinƙai. Ina tayaku jaje da kasancewar sa mahaifi a gareku, ina kuma tayaku addu'ar ALLAH ya hanaku gada daga ayyukansa da kuma halayensa. Dan shi jini ba ƙarya bane, ɗabi'ar iyaye na naso a jikin ƴaƴayensu. Shiyasa masu iya magana suke cewa TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. Saboda haka iyaye mu kula, mu kula, mu kula da gyara ayyukanmu kodan ƴayanyenmu masu tasowa kada ɗabi'unmu na banza suyi naso a jikinsu. Uba kasan irin uwar da zaka auroma ƴaƴanka, uwa kisan irin uban da zaki sakarwa ƴaƴanki. Ina muku fatan ku tsarkake zukatanku, ku cigaba da gyara halayenku, ku guji ayyukan ɓarna, in sha ALLAHU sai UBANGIJI ya nisantaku da irin waɗan can halaye, wanda muka san kuma munayi a ɓoye muyi ƙoƙari mu gyara. Sannan shi kuma ku cigaba da masa addu'a, sadaƙa mai gudana, ba'a yanke ma bawa hukunci tsakaninsa da UBANGIJIN sa. Amma kuyi haƙuri ku yafema juna, ku dunƙule waje ɗaya kuyi haƙuri da juna, ku manta baya hakan shine zai saka muku salama a cikin zukatanku domin fa babu yanda zakuyi, jini ya riga ya haɗu tunda har an haihu. Idan ke Ummu-Hidaya kin yanke alaƙa da su matsayin ƴaƴan Adam daya aikata laifi mai girma a gareki, su kuma su Muhammad yaya zasuyi a matsayinsu na dangin mahaifinsu kuma ga mahaifin nasu a raye. Dole suma sunada nasu hakkoki a kansu. Idan ku kunce kun janye daga gareta saboda mahaifinku ya mata laifi kuma jin kunyarta, a ganinku yin nesan da ita shine mafita a gareku. Su kuma waɗan ƴaƴan da suka kasance jininku a tsakaninku fa. Wanda sunada hakkoki a kanku kuma. Ita rayuwa duk inda akaje aka dawo tanada sarƙaƙiya, duk ƙoƙarin ka na toshe can dole zaka samu can yanada amfanin da idan ka toshe nan ɗin zaka iya dana sani wataran. Shawarar kawai dazan iya baku shine kuyi haƙuri, kuyi haƙuri, kuyi haƙuri. Waɗanda suka haɗa yau duk sun tafi, sun kuma barku da gwagwarmaya mai wahala gaskiya. Wahalar da haƙurin nan ne kawai zai iya ɗorar da ku matsayin ahali. ALLAH ya farta mana, ya kuma shiryemu baki ɗaya. Yasa hakan ya zama izna a garemu dama na bayanmu masu tasowa.” A tare duk muka amsa da Amin. Yayinda Paah ya miƙe zuwa kusa da Ummie ya zauna. Kansa a ƙasa hawaye na sauka masa ya ce, “Tabbas Ummu-Hidaya ni mai kuskurene a gareki mai girma. Nayi abinda ban cancanci duniya ma ta yafe min ba balle ke dana zalunta ko yaƴanmu. Ke ɗin jarumar mace ce da samunki a wannan duniyar sai an sha matuƙar wahala. Kin shanye, kin kurɓe daga zaluncina. Dan nasan tun daga sati ɗaya na aurenki baki sake jin daɗi daga gareni ba. Kuma hatta da mahaifinki baki taɓa faɗa masa wanene ni ba, sai da ya gano da kansa. Saboda dattako da mutunci na wannan bawa ya sameni batare da saninki ko mahaifana ba yamun nasiha da nuna min illar abinda nake aikatawar. Bai tozartani ba, bai ce na sakar masa ƴarsa saboda ni ɗan iska bane ba. Bai kuma samu mahaifina da zancen ba. Bai kuma gaza wajen cigaba da jawoni jikinsa yana nasiha ba. Badan bashi da ƙarfin ɗaukar mataki a kaina ba. Badan bashi da ƙarfin cewa na sakar masa ke ba. Sai dan kawai shi ɗin jarumin mahaifine mai ƙyaƙyƙyawar zuciya. Wlhy ina ji inama ace Abie shine mahaifina tun a wancan lokacin, inama ace naji nasiharsa naji tsoron ALLAH, kai inama ace mutuwa nai tun ina ƙanƙanina.....” kuka ya sarƙesa. Itama Ummie kanta a ƙasa tana nata kukan. Muma kukan mukeyi, shugaban taurin zuciya ne kawai babu ɗogon hawaye a nasa idanun sai dai sun juye gaba ɗaya alamar dai ana na zuci. Da ƙyar Paah ya ciga da faɗin, “Ummu-Hidaya bamma san ta ina zan fara baki haƙuri ko neman gafararku ke da ƴaƴana ba. Sai dai wlhy ku sani duk duniya ban taɓa son wani abu ba sama da ku ɗin nan ba. Ina muku so da baida iyaka. A yawan lokuta nakan aikata abu gareku batare da ni kaina nasan ta yaya akayi ba, sai daga baya nazo na shiga tashin hankali amma bana iya neman afuwarku. Wlhy ban san irin yanda zan kwatanta miki tashin hankali da ruɗanin dana shiga a waccan ranar ba sakamakon abinda ya faru. Kuma wlhy abinda kike tunanin ya faru bai faru ba, kina faɗuwa kika suma hankalina ya tashi, sai dai tsoro yasa na kasa tsayawa a gidan nima na gudu. Ummu-Hidaya dan girman ALLAH basai anyi tone-tone ba ki yafe min, na roƙeki ko bazaki cigaba da zama dani ba kamar yanda ƴaƴanmu suka buƙata ki yafe min. Dan ALLAH ki yafe min na roƙeki. Muhammad da Fahad kuma ku yafe min dan ALLAH, ku tayani roƙon mahaifiyarku ta yafe min. Bilkisu dan ALLAH ku tayani roƙon ƴar uwarki ta yafe mun. Ƴaƴana Falaq da Samraah da Bahijja ku tayani roƙon mamanku ta yafe min. Na tuba nayi nadama wlhy”. Kuka ya sake sarƙeshi. Itama Ummien kuka take mai ban tausayi da taɓa zuciya. Yayinda illahirin mu muke tayasu. Su duka dole ne su baka tausayi, matuƙar tausayi. Tashi Ummie tayi ta haye sama. Da sauri Paah shima ya tashi ya bita yana kiran sunanta. Suna shiga ɗakin ya zube a gabanta gwiyawu a ƙasa, tare da riƙe ƙafafunta yana kuka sosai. Kukan take itama kanta a gefe har numfashinta na shiɗewa. Haka ya cigaba da mata magiya kusan fin ta minti talati. ALLAH sarki Ummie, zuciyar babu duhu, ita ɗin mai tausayi ce, ta gada daga ƙyawawan halaye na mahaifi. Sai kawai itama ta durƙushe ƙasan ta shiga marin Paah ɗin hannaye bibbiyu suna kallon juna su duka suna hawayen. Tayi masa yafi goma dan harda ƙirjinsa take kaima dukan amma daga marin har dukan ba masu zafi bane ba. Kafin ta faɗa jikinsa tana sake fashewa da kuka. Shima amsarta yay hannu biyu ya rungume yana nashi kukan da sake bata haƙuri.... Acan falo ma su Uncle Abdullahi da Hajiya Mammah da Aunty Mama haƙuri suke bama Maash da Fahad. Tare da neman afuwarsu. Musamman ma Hajiya Mammah da tasan tayi abubuwa a gidan. Ba kuma ta ɓoye ba komai da tayi ta sanar musu. Hatta abinda ta saka a abinci ta bama Samraah takai masa yaci da ga ƙarshe abinda ya faru ya faru, ta sanar musu da manufarta tayin hakan. Ashe hatta su kansu su Uncle Abdullahi ba ƙyalesu tai ba. Tayi musu na mallaka ta yanda duk abinda zatai a gidan zasu kasance cikin shakkarta. Sosai al'amarin nata ya sake bama kowa mamaki, amma tunda dai komai ya wuce batun neman gafara ake yi sai suka yafe mata, tare da fatan ALLAH ya yafe musu baki ɗaya. Daga ƙarshe suka bata shawarar ajiye ɗabi'arta ta je ta roƙa mijinta yafiya shima ta koma wajen ƴaƴanta. Ko kuma ta samu miji tai aure dan shine babban mutuncinta da kimarta. Ta kuma dukufa neman gafarar ALLAH tayi tuba na gaskiya da alkawarin bazata sake aikata abinda ya aikata a baya ba. Daga nan malam ya mana nasiha tare da shawarwari akan muma tamu rayuwar da namu mazajen. Suma mazajen namu ya musu a kammu. Har dai aka rufe taro da addu'a Ummie da Paah basu fito ba. Babu wanda yace komai a kan hakan. Amma fa Yaya Awwab ficewarsa yay a gidan bayan wucewar su Malam... ★Har dare bai dawo ba. Tun ina ɗaukar al'amarin da sauƙi har na fara shiga tashin hankali. Gashi na kirashi yaƙi ya ɗauka. Sai na nema Yaya Hayatu. Kwantar min da hankali yayi, ya tabbatar min na shirya dan yanzu dama ya kira shi yace ya kaini inda yake. Banyi mamakin hakan ba, dan na fahimci Yaya Awwab akwai taurin kai. Sai dai ta wani ɓangaren bana ganin laifinsa. Yana ƙaunar mahaifiyarsa ne sosai. Sannan duk wani ɗa na ƙwarai irin abinda zai yi kenan, ko nice ma abinda zanyin kenan magana ta gaskiya. Shiryawar nayi dan ina matuƙar buƙatar ganinsa nima. Abinda zan iya buƙata kawai na ɗauka, koda na fito sai na kasa tafiya sai na nufi sashen su domin sanar ma Ummien. Nayi mamakin samunta a falo ita da mama Balki. Ganin yanda nake sim-sim ta miƙomin hannu cike da kulawa tana faɗin, “My darling miya faru? Zonan naji”. Hummm yanda Ummien ke treating namu mukanji kammu like babys ne, ƴan shagwaɓa a gaban iyayenmu, musamman ma ni da ban tashi da uwa ba. Ban samu irin wannan gatan ba. A hankali naje gabanta zan durƙusa, amma sai ta jawoni kusa da ita ta zaunar. Sake tambayar tawa tayi, a ɗarare na sanar mata. Murmushi tayi da sake shafa kaina, sai ka rantse bata da wata damuwa. Amma ko makaho ya kalleta yasan tana cikin ta, dan idanunta sun yi bala'in kumbura saboda kuka. Har ina jin sake karyewar zuciya da kallonta a yanayin. Cike da dakiya ta ce, “Karki damu kinji Baby na. Kije wajen mijinki, ki lallashesa ki tausa masa zuciyarsa. Nasan yayi hakane domin samun daidaituwar kansa. Dan Muhammad bai iya fushi ba, idan yana cikin fushi baya iya controlling harshensa ma. Shiyyasa na koyar da shi yin hakan tunƙuruciya, dan idan yabar inda akai masa kuskuren sai kiga ya huce. ALLAH yay muku albarka, ya kuma saukeki lafiya kema dan na ƙagu naga wannan miji na Bilkisu ko Kishiya ne ma dai to”. Dariya Mama Balki tayi, nima na ɗan murmusa kaɗan. Haka nai musu sallama na wuce batare dana iya kallonsu ba........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DsaV9faJPfULbIJBU7TS72 https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ _ ......Ina a baya kaina jingine da kujera na lumshe idanu, yaya hayatu na daga gaba yana driving dan shine zai kaini. Muryarsa a sanyaye ya ce, “Auntynmu dan ALLAH ki lallaɓa Yayanmu ya yi haƙuri komai ya wuce Ummie da Paah su cigaba da kasancewa tare. UBANGIJI ma muna aikata masa laifuka da sukafi wannan girma, ko mushiriki ka kasance ka dawo ka tuba garesa tuba na gaskiya yana yafe maka duk da ƙin shirka da yake balle mu mutane masu fatan gafara daga UBANGIJIN. Paah yayi laifi, amma yayi nadama, al'amarin sa kuma ya ta'azzara ne bisa jagorancin zaluncin shaiɗanin tsohon can. Amma wlhy Ummie na son shi, shima kuma yana sonta sosai. Koyaya Ummie na buƙatar abokin rayuwa a wannan gaɓar, tana buƙatar mai ɗebe mata kewa da tausasa damuwarta ta tsahon shekaru. Sannan batai tsufan da zata gagara wani auren ba. Ba kuma zasu bari ta auri wani mijin ba saboda dole kishin mahaifinsu na nan a tare da su. Kinga ita ai an tauyeta, sannan ko doctor ya bada shawarar mijinta ya kasance da ita yanda ya kamata hakan zai cigaba da daidaita matsalarta komai ya koma dai-dai game da abubuwan da suka dinga bata, in ba hakaba ta cigaba da shiga damuwa wataran brain ɗin nata zata sake birkicewa ne. Nasan duk son da Ummie kema Paah in har Yaya Awwab bai yarda su koma tare ba itama bazata amince da shi ba. Haka ma Fahad, amincewar Yaya Awwab ce kawai zata rissinar da shi ya haƙuran. Ke kuma rissinar Yaya Awwab a yanzu kamar tana a hannunki ne. Kinada tasiri matuƙa da rawar da zaki taka a wannan gaɓar komai ya koma normal. Mu dawo full family har ƴaƴanmu su taso suma su mora haƙuri da juriyar mu”. Hawayen dake zuba min na share. Cikin jinjina kai na ce, “In sha ALLAHU zanyi ƙoƙarin hakan Yaya Hayatu, amma kaima sai ka tayani da su Mama kuma. Dan wlhy ina tsoron fushinsa matuƙa. Yaya Awwab nada murɗaɗen hali mai ban tsoro. Amma yanzu dan ALLAH ina Paah ɗin?”. “Paah ya koma can gidan wajen su Uncle Abdullahi. Amma ki kwantar da hankalinki in sha ALLAHU muma zamuyi ta ɓangaren mu.” “To ALLAH ya taimake mu Yaya. Amma mizai hana ka fara kaini naga Paah ɗin”. “A'a kiyi haƙuri kada kije yanzu. Zan dai iya saka miki number sa ki kirashi a waya. Amma batun ku haɗu a wannan halin Yaya Awwab bai gama sakkowa ba akwai matsala.” “Shike nan na fahimta, hakan ma yayi ka tura min number ɗin tashi.” Koda muka iso gidan a falo muka sameshi zaune yana karatun Alkur'ani. Yaya hayatu baima shigo ba ya juya. Nima sai na samu waje na zauna ina sauraren muryarsa dake raira karatun cikin nutsuwa. Har ma barci ya fara rinjaye idanuna na zame na kwanta. Sai da naji ƙamshinsa gab da hancina sosai sannan na buɗe idon. Kallonsa nake kamar yanda take kallona. Baiyi magana ba ya ɗaukeni camak zuwa bedroom ya kwantar. Shima kwanciyar yayi ya sakani a jikinsa. Mu duka ajiyar zuciya kawai muke saukewa a jajjere har barci ya ɗauke ni, ashe shima barcin yayi sai da na farka na gansa.... Kwanaki biyu kenan muna tare da ga ni sai shi a gidan. Babu dai yawan magana dan ya koma min Maash ɗin dana sani a baya. Sai dai dukkan kulawa yana bani dan sai nima na kasance duk bana jin daɗin jikina abinka da mai ciki. Abinci safe, rana, dare Mama Balki na ƙoƙarin aiko mana da shi. Yaya Hayat ne mai kawowa. Abinda yake burgeni da shi ya matuƙar maida al'amarin sa ga UBANGIJI. dan a zaman nan ibada ce kawai sai kuma kasancewa da ni. Duk wasu harkokin Bussines ya ajiyesu gefe guda kawai. Hatta phones ɗin duk ya kashe. Tsahon kwana huɗu sannan mukayi shirin komawa gida. Bayan sallar magrib ya shigo yana min maganar na shirya muje sai ga Hayatu yay kiransa, ban san miya ce masa ba naji kawai ya kama faɗa. Sai kuma ya yanke wayar. A fusace ya nufi ƙofa zai fita. Nai saurin tafiya na rungumesa ta baya nima. Kaina kwance a faffaɗan bayansa, na zagayo hannayena ta saman shafaffen cikinsa. A hankali na ce, “Miya faru Zaki na? Ban sanka da faɗa cikin hayaniya haka ba, Please cool down”. Shiru yay sai ajiyar zuciya da yake faman saukewa a jajjere. Cikin sake tausasa harshe na ce, “Please ka faɗa min miya faru? Maybe na iya baka shawara”. Nan ma shirun yayi a binsa, sai da ya mula dan kansa ya furta, “Miyasa zai kawoshi nan. Nace na haƙura, mi kuma ya rage”. “Wanene?”. “Mijin Ummie”. Ni dariya ma maganar tasa ta bani, wai mijin Ummie. Yau Paah ɗin ma baza'a kirashi ba kenan. Amma sai na danne tare da sake tausasa harshe na zagayo ta gabansa. Hannayena duk biyu na ɗora akan kafaɗunsa duk da ya mun tsaho ina kallon cikin shakkiyar idanunsa da gaba ɗaya sun jirkice. Na ce, “Haba my Hot, kenan baka hakura ba? Ba kaji nasihar Malam ba. Yanzu kana son kayi min wani kuskure wataran abinda ke cikina ya dinga maka yanda kakema Paah a yanzu. Kai ma fa yanzu uba ne, sannan bamu san mi yau da gobe zatazo mana da shi ba. Kasan kuwa matuƙar wahalar da mukasha a rayuwa saboda rashin iyaye? Amma ku kuna son raba naku dake a tare. Yaya a mafi yawan lokuta nike girka abincin da za'aci a gidanmu, amma ni bazan cisa ba. Wani daga cikin ƴan uwana bazai cisa ba. Badan bama so ba fa ko babu wadatar abincin. Ka gaya min da Baba na darai ko Ummyn mu zasu barmu da yunwa ne? Government school mukayi, amma yaran gidanmu private masu tsada. Ana musu ɗinki sau biyar mu ba'a mana sau ɗaya ba. Shin da ace iyayenmu na raye ko guda ɗaya ne zamuga wannan rayuwar ne. Duk inda zasu faɗi su tashi zasuyi domin mu. Ku godema ALLAH naku duk suna raye, har gamu muma muna jingine jikinsu suna mana gatan da muka rasa a baya. Paah yayi kuskure, ya kuma yarda yayi kuskure, muma kuma bamu wuce kuskuren ba. Shi da Ummie suna son junansu, kada ku ƙi basu haɗin kan cigaba da zama a ƙarƙashin inuwa ɗaya. Ku tausaya mata kodan bayanin likita, yanzu kunfi son ta rabu da Paah ta auri wani banza can da maybe ma dan dukiyarta zai aureta ne kawai? Kai ne babba, idan har kayi mubaya'a Fahad shima zaiyi wlhy. Please ka saki ranka komai ya wuce”. Na ƙare maganar cikin sanyin murya da marairaicewa kamar zanyi kuka. Ganin ya zuba min idanu kawai na sake faɗin, “Please mana”. Naja kumatunsa. Hararata yayi, niko na sanya dariya da sake ja masa hanci. Sai ya dungure min kai shima yana ɗan lumshe idanunsa a slowly. Cikin farin ciki naja hannunsa muka fito. Ganin Paah a falo zaune nai saurin sakin hannun nasa na koma bayansa na laɓe. Ƙaramar dariya Paah ɗin yayi mai ɗan sauti da faɗin, “Oh oh my daughter please fito mana.” Fitowar nai kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hannuna. Sum-sum nazo gabansa na durƙusa cikin girmamawa na gaishesa. Ya amsa min da kulawa tare da sanya albarka. Cikin jin daɗin addu'ar da yay ma iyayena na miƙe zuwa kitchen. Ruwa na ɗakko masa da yogurt, sai snacks dan bamu da wani abinci. Yanzu kam zaune na sami Yaya Awwab ɗin kansa a ƙasa. A gaban Paah na ajiye tray ɗin zan bar wajen ya ce dani “Daughter dawo”. Dole dawowar nayi, ya nuna min gefen Yaya Awwab ɗin ya ce, “Zauna kusa da mijinki”. Ban musa ba na zauna kaina a ƙasa. Sai da ya ɗauka ruwan dana kawo masa ya sha tare da sanya min albarka sannan yay gyaran murya da gyara zama. “Muhammad! Kayi haƙuri ka sake yin hakuri kaji. Ni dai koda bazaka yarda na cigaba da zama da mahaifiyar ku ba, ka yafe min. Namaka alƙawarin zanyin nesa da ku na har abada dan nafi so da fatan kuyi farin ciki a rayuwarku, hakan shine ƙaddarar mu...” Shiru babu alamar zai ce komai. Ganin haka yasa ni na magantu. Murya a sanyaye na ce, “A'a Dady duk ma ba'aje can ba. Babu inda zaka tafi in sha ALLAHU kana tare damu har abadan. Na tabbata shima kansa yana jin nauyin abinda ya farune shiyayasa kaga haka”. Na ƙare maganar ina mintsinin yaya Awwab ɗin dan so nake yace wani abu. Ganin na damesa ya nisa. Muryarsa acan ƙasa ya furta, “ALLAH ya yafe mana baki ɗaya. Kamar yanda ta faɗa kuma ni banga amfanin tafiyar ba. Tunda kun daidaita kanku mu miye kuma namu face mu muku fatan alheri. Kawai dai magana ta gaskiya ya kamata kaje asibiti a tabbatar mata da lafiyark.....” Da sauri na zaro idanu waje, tare da kai hannuna saman bakinsa na rufe. Cikin rawar baki data murya na ce, “Yaya Please kada kai magana haka”. Katseni Paah ɗin yay cikin murmushi ya furta, “Daughter gaskiya mijinki ya faɗa, kuma hakan shawarace me ƙyau shine kuma abinda ya dace nayi. Naji daɗi kuma da amincewarsu akan cigaba da zama da mahaifiyarsu, ALLAH yay muku albarka Muhammad”. Murya a sanyaye na amsa da Amin. Yayinda shi kuma ya amsa a saman lips kawai........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒇𝒐𝒖𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ .......Daga ƙarshe dai tare da shi muka fito bayan mun kashe komai. Da kansa ya buɗe mun mota ya taimaka min na shiga, Paah na kallonmu da murmushi. Sai da ya maida ya rufe sannan ya buɗema Paah ɗin shima. Ya shiga ya zagaya mazaunin driver. Yanda Paah ɗin ke janmu da hira yana ɗan amsa masa yasa naji sanyi a raina. Nima yana sakani a hirar cike da kulawa. Murmushi kawai nake iyayi da bashi amsa a kunyace. Dawowarmu gidan tare da Paah ya saka kowa farin ciki, musamman Ummie data kamani ta rungume tana sanya min albarka. Shima Yaya Awwab ta rungumesa. Fahad na tura baki zai wuce Paah ya jawosa ya rungume shi shima yana murmushi. Alhamdullah ita rayuwa komai akai haƙuri sai ya zama mai sauƙi cikin rahamar UBANGIJI. Ranar kowa zaka samesa cikin cikakkiyar walwala da rabonmu da ita tun a hidimar bikin nan. Duk da haka Paah bai kwana a gidan ba. Ya koma can gidan ya kwana. Sai dai ya sanarma Ummie duk yanda mukayi. Ya kuma mata alƙawarin zaije ya binciki lafiyarsa. Idan har akwai matsala zai sawwaƙe mata. Idan kuma babu shike nan. Amma dan ALLAH kada ta sanar ma su Awwab. ALLAH sarki Ummie haka kuwa tai gum fa bakinta duk da tana a cikin fargaba da damuwa. Haka shima Paah ɗin yana cikin tashin hankali. Washe gari suka haɗu a asibiti, Yaya Hayat tasa ya kaita. A gabanta akaima Paah komai aka basu kwanaki uku zuwa amsar result. Daga nan ne suka dawo gida. Suun samu baƙi daga Kano, Attahir yayan Mansoor da Mansoor ɗin, sai Mahaifinsu ne suka kawo ma Yaya Awwab invition ɗin aurensu takanas domin girmamawa. Tare da zuwa su masa godiya akan abinda yay game da Mansoor a dubai. Ni bamma sani ba sai da ya shigo yake sanar min akwai baƙi a gidan naje na sanarma su Ummie zai shirya sannan. Ban tambayesa su waye ba naje na sanarma su Ummie ɗin. Kasancewar a falon baƙi aka saukesu dan danan na shiga kitchen da kaina ina tsaye masu aiki suka haɗa komai suka tafi kai musu. Dan naga yanda ya ɗauki batun baƙin da muhimmaci. Kusan mintuna talatin da kai musu abinda na aika ɗin ya shigo ya samemu a babban falo yake sanar mana gasu zasu shigo. Magana Ummie ke son yi amma bai bata dama ba ya fita. Sai mukaita kallon kallo. Waɗan nan waɗanne irin baƙine haka masu muhimmanci a wajen Yaya Awwab. Shigowarsu ya katse mana tunaninmu, ina ɗaga kai wazan gani. Mansoor da fa babansa da yayansa. Sunan ALLAH na ambata zuciyata na rawa, dan na rasa ma ina zan kamo al'amarin nikam. Ashe bani kaɗai ba, ta ɓangaren Ummie ma ta daskare a tsaye ta zubama Dad ɗin su Mansoor ɗin ido. Yayinda shi kuma Dad ɗin ya kafe ƙaton black & white ɗin hoton Kakar Ummie da Mahaifiyarta kakar su Yaya Awwab kenan da kallo. Shi kuma Mansoor ya ƙure ni da ido. Gyaran Muryar da Yaya Awwab yayi ne ya dawo damu hayyacinmu mu duka. Cikin rawar baki data jiki Dad ke nuna hoton da yake kallo. Kamar wanda ke koyon magana idonsa akan Yaya Awwab ya furta, “Son ina kasan wannan matar?”. Yay nuni da kakar Ummie. Kallon Ummie Yaya Awwab yayi, sannan ya kalla Dad ɗin cikin nutsuwarsa ya furta, “Uwa take a wajena, domin ɗiyarta gata nan a kusa da ita itace ta haifi Ummie na”. “What!? Kakar tawa? kasan mi kake faɗa kuwa?”. Ya faɗa a matuƙar birkice yana kallon Ummie da itama jikinta ke rawa sosai. Matsawa Yaya Awwab yay jikin hoton sosai ya kamashi ya sauke. Tare da takowa gaban Dad yana mai jinjina kansa. Ya furta, “Tabbas Maimoonatu itace ta haifi Rabi'ah, Rabi'ah ta haifi Ummie na tare da wannan” ya ƙare zancen da juyawa ya nuna kakansa Abie. Birkicewa Dad yay gaba ɗaya. Yayinda Attahir ya furta Dad wlhy kamar Mammi, dan ALLAH Mansoor kalla da ƙyau basa kama da Mammi? Ni sai nagama kamar akwai irin hoton nan a cikin hotunan Mammi da muka taɓa ɗauka ta kwace har tana kuka”. Amsa Masoor ya bashi da, “Tabbas Yaya wannan hoton Mammi na da shi, kuma ta faɗa mana sunan ta jikin hoton Maimoonatu Addarta ce. Har alƙawari tama akan zata bamu tarihinta wataran ka manta. amma sai bamu samu zama ba saboda abubuwa”. Kamar zancen su Mansoor ya ƙara zaburar da Dad tuni ya lalubo wayarsa a cikin aljihu. Danne-danne yayi ya kai kunnensa. Baima ko amsa sallamar da ake masa daga can ba ya furta, “Kawu, dan ALLAH zan tura maka wani hoto yanzu ɗan nunama Mammi, duk amsar data baka akan hoton ka kirani yanzun nan”. Bamu san mi akace masa daga can ba ya dai yanke kiran. Hoton ya ɗauka a waya ya tura, muna nan tsaye kusan mintuna biyar sai gashi an kirashi. Ɗagawa yay da rawar hannu ya saka a hansfree. Raɗau muryar ƴar tsohuwa ta fito sai dai cikin kamar mai son fashewa da kuka ta furta, “Abubakar ina ka samo wannan hoton? Da ga ina ka samo min hoton Adda Maimoona? Waya baka shi? Dan duk duniya daga ni sai ita keda shi a yanzu, kuma na duba nawa na tare da ni. Ban taɓa nunama kowa ba kuma sai Mansoor da Attahiru naka. Suma a jaye-jayensu na tsiya suka ɗakko kuma a take na ƙwace balle nace sune suka sata suka kai maka....” kuka ya sarƙeta. Cikin tashin hankali da kulawa Dad ya tareta da faɗin, “Kinga yi haƙuri Mammi, in sha ALLAHU duk zan miki bayani. Bari nayi magana da Kawu Sulaiman daga yanzu zuwa ko yaushe zai kawoki inda nake”. “Ba ita ya kamata ta zo ba. Nice zanje Muhammad. Dan ALLAH ku kaini inda suke ina son naga tsohuwar nan”. Ummie ce ta faɗa cikin kuka. Rungumeta Yaya Awwab yay yana lallashi. A take ya juya ga Hayatu yace ya bincika musu airport akwai jirgi mai tashi yanzu ne zuwa Kano. Da girmamawa Hayatun ya amsa. Bai kuma ko gusa a wajen ba yay kira. Ankoyi sa'ar samu. Sai dai sai nan da awa uku zai tashi. Sam Ummie tace sai dai fa a tafi airport a jira jirgi. Amma ko minti goma bazata sake yi a Mansion ba. Haka dole kowa ya shiga shiri muka fice a gidan aka bar masu aiki kawai. Harda Paah da Yaya Awwab yay kira ya sanar mawa. Zama mukai na awa biyu ciff a airport kafin jirgi ya tashi, cikin ƙanƙanin lokaci kuma muka iso. Mun samu motoci ma na jiranmu. Dan haka babu ɓata lokaci muka dunguma. Gidane madaidaici mai ƙyau. Mota uku ce kawai ta iya shiga ciki, ukun sai a waje suka tsaya. Sai da muka firfitone na tuna tabbas mun taɓa zuwa gidan ni da Mansoor. Kuma lallai anan ne nake tuno nasan mai kamannin Kakar su Yaya Awwab ɗin. Haba nayi-nayi na tuna, har shan zaman bincike da hasashe nake da zuciyata amma sam na gagara tunawa saboda abin yamun nisa ne sosai ashe. Kafinma mu gama fita a mota tsohuwar ta fito wani mutum mai tsananin kama da kakar su Ya Awwab ɗin riƙe da hannunta. A tun sanin danai mata dama tsohuwa ce, sai dai yanzu ta ƙara tsufa fiye da da. Duk kuma da kasancewarta a hakan tana tafiya da ƙafafunta, dan irin tsoffin nan ne da ALLAH ya bama ƙaramin jiki sannan bata da tsaho sosai kuma ALLAH ya bata lafiya. ALLAH sarki Ummie jikinta har rawa yake ta ƙarasa gare su. Bata san kakarta ba sai a hoto, hakama mahaifiyarta. Amma ko makaho ya kalla hoton Mama Rabi'ah da mahaifiyarta ya kalla na tsohuwa Mammi da wanda ke riƙe da ita yasan sun haɗa jini. Dan kamace sosai a bayyane dan ma tsufa ya cinye wani abun na iya Mammi, shima dai namijin ya manyanta sosai. Rungumeta kawai Ummie tayi ta fashe da kuka tana faɗin, “Tabbas koda ba'ace min kuna da alaƙa da Mamina ba da grandma ni nasan ku jininsu ne. Miyasa kuka ɓoye min? Miyasa?”. Hannu tsohuwa takai saman kan Ummie tana shafawa tana hawayen itama da faɗin, “An sanar mana Adda ta jima da rasuwa tun kwana biyu da barin Kano, hakama Rabi'ah dan haɗarin mota akace mana sunyi, kuma anje har inda haɗarin ya faru motar ta ƙone, an bincika tasha dan a tabbatar motar dai suka shiga aka sake tabbatar da hakan. Amma taya kika san Addata bayan ke ɗin baturiya ce..” kuka ya sake sarƙeta. Paah ne ya matsa garesu cikin lallashi shi da Dad sukace suje ciki tsaiwa a hakan babu daɗi. Haka kuwa akayi muka shiga ciki. Kasancewar falon babba ne sai duk ya kwashe mu batare da wani ya matsu wani ba sam. Har lokacin dai su Ummie kuka suke yi. Mammi kuma na riƙe da hannun Ummie ɗin kamar za'a ƙwace mata ita, yayinda ɗayan hannunta ke riƙe da hoton su Mama Rabi'ah. Gefenta dattijon nan ne da shima dai hawaye take ta faman sharewa yana ta kallon Ummie.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏_ ........“ALLAH sarki Adda ALLAH ya gafarta miki. Shiyayasa mahaifinmu har yabar duniya yana maimaita shi yana ji a jikinsa kina raye keda Rabi'ah. Ni kaina a lokuta da dama sai naita jin hakan a cikin raina. Har nakanji fata da ɗokantuwar inama ace zamu sake haɗuwa. Tabbas Marka ta cucemu, ta zalunci rayuwarmu. Mun barta ga ALLAH kuma shine zai miki sakayya da mu ahalinki. Uwarmu ɗaya ubammu ɗaya da Adda Maimoonatu. Ita iyayenmu suka fara haifa, sai kuma haihuwar ta tsaya musu cak tsahon shekaru basu sake samu ba. Harma sun fidda rai da hakan duk da matsin lamba da mahaifiyarmu ke samu wajen dangin mahaifinmu Babanmu bai taɓa kwatanta ƙara wani auren ba. A haka Adda ta kai shekaru goma sha uku. A tsari dai ta isa aure na wancan lokacin, dan haka wani abokin baba mai suna Kabiru na fitowa baba ya bashi. Duk da anata surutu akan hakan baba bai kula ba. Dan kuwa shima baba Kabiru shekararsa goma sha shida matarsa bata taɓa ko ɓatan wata ba. Haka dai akai biki aka kai amarya, sai me ba'a ƙulla wata biyu ba sai ga mahaifiyarmu da ciki itama Adda da ciki. Ikon ALLAH kenan, wannan al'amari ya matuƙar girgiza mutane. Yayinda Marka matar Baba Kabiru tai matuƙar tasar hankalinta. Kullum fitina ita da miji, ta kuma dinga gallabar Adda kenan amma ita bata kula mata. Da ga ƙarshe ma da akaga fitinar na neman yawa, wataran zata iya salwantar mata da ciki sai Adda ta dawo gida kusa da mahaifiyarmu suka ƙarasa rainon ciki tare. Mahaifiyarmu ita ta fara haifarmu ƴan biyu ni da mahaifiyar Abubakar” ta nuna Dad. Itace Hassana nice Usaina. Murna da farin cikin duk wani masoyan iyayenmu bai ɓoyu ba, dan sosai akai shagali na nuna tsara. Bayan suna Adda ta cigaba da rainon ciki mahaifiyarmu na wankan jegonmu. Sai da tai arba'in biyu kamar yanda akeyi da sannan Adda ta haihu mace itama. Itama anyi farin ciki, yayinda Baba Kabiru ya rikice dan daɗi, shima haka ya dinga ɓarin kuɗi a ranar sunan yarinya da taci Rabi'ah. Bayan suna anan gida ta cigaba da zama har tai arba'in. Baba Kabiru ya matsa Adda ta koma ɗakinta, sai dai halin Marka na saka iyayenmu tsoro. Dan a hakanma da take gida ba ƙyaleta tayi ba. Shi kansa Baba Kabirun ba daɗin zama yake ji da ita ba. Dan kullum cikin tashin hankali suke. Shi kuma ya kasa sakinta saboda mahaifinsa ne ya aura masa ita cousin ɗinsa ce. Ya kuma cemasa idan ya rabu da ita bai yafe masa ba. Ga mahaifin nasa ya rasu yanzu. Haka dai badan mahaifiyarmu naso ba aka maida Adda gidan Baba Kabiru. Adda nada matuƙar haƙuri, shiyyasa ta iya jure halayen Marka na tsawon lokaci batare da ta taɓa zuwa gida ta faɗa ba. A haka Rabi'ah ta isa yaye aka kawota nan gidanmu, sai kuma ga Adda da wani cikin. Bamma san yanda zan musalta muku bala'i da masifar da Marka tai a wannan gaɓar ba, ta kuma ci alwashin sai Adda bata isa sake haihuwa a gidan ba, Rabi'ah ma data haifa sai ta koma. Zancenta ya tada hankalin mahaifiyarmu, har tace ita dai Baba Kabiru yay hakuri kawai ya rabu da Adda. Amma sai babanmu ya hana. Haka aka cigaba da rayuwar kullum Rabi'ah na nan gidanmu, sai dalili mai ƙarfi kesa a kaita gidansu. A haka ALLAH ya sauki Adda lafiya, sai dai ɗan baizo da rai ba. Tsabar jahilci na Marka ta dinga dariya wai alhakinta ne. Babu dai wanda ya kulata Adda ta sake zuwa tai wanka, dan lokacin sai mace tai haihuwa uku tana zuwa gidansu wanka. In dai takaice muku sai da Adda tayi haihuwa uku bayan Rabi'ah amma yara na zuwa babu rai. Kai tsaye kowa ya dinga faɗin Marka ce. Shi kansa Baba Kabirun ya sakama ransa ita ɗince, cikin rufewar ido yay mata saki uku. Abinda bata taɓa tunani bane, aiko ta gigice matuƙa ta kuma dawo tana bashi haƙuri da tabbatar masa zataje ta karya asirin da tayi ƴaƴan Adda ke mutuwar. Tashi hankalinsa ya sake yi, kenan dai gaskiya ne itace ke kashe masa ƴaƴa. Aiko sai ya sake harzuƙa ya lakaɗa mata uban duka. Haka aka kwasheta zuwa ƙauyensu. Wannan abu shine ta saka Marka ɗaukar alwashin sai ta ɗau fansa akan Adda. Babu wanda yabi takan batunta aka cigaba da sabgogin rayuwa. ALLAH bai sake bama Adda wani cikin ba sai da muka kai shekaru goma sha uku ana ma batun mana aure mu harda Rabi'ah ƴarta. Kwatsam sai ga ciki. Tayi rainonsa cikin aminci da salama dan yanzu hankalinta a kwance yake ita da mijinta da ƴarsu. Har dai ALLAH ya sauketa lafiya ta samu ɗa namiji, ranar suna aka saka masa Sulaiman”. Ta nuna dattijon ɗaya kamota ɗazun mai kama da grandma. Dukanmu babu wanda bai kallesa ba cikin maɗaukakin mamaki, kenan dai shi ɗin ƙanin mahaifiyar Ummie ne uwa ɗaya uba ɗaya. Mammi ta cigaba da faɗin, “Ranar sunan Sulaiman komai ya canja daga yanda yake, domin kuwa da yamma a wajen taron suna aka nema jariri aka rasa. Hankalin kowa ya tashi Adda harda sumanta, sai dai ko sama ko ƙasar babu jinjiri babu alamarsa. Ana cikin wannan taraddadi kuma itama Adda da Rabi'ah aka nemesu aka rasa. Ai sai ma hankali ya koma kansu aka manta da batun jariri. An bazama nemansu tako ina. Nema iya nema babu ta inda aka dace, anata yawo da hotonsu har cikin tashoshi. Sai a kwana na biyu a wata tasha ake tabbatar mana lallai sunzo nan sun shiga motar zuwa Lagos, amma kuma ana raɗe raɗin motar tayi haɗari ma a jiya da dare mutanen ciki sun ƙone ƙurmus. Sake tashi hankali yayi, baba Kabiru da baban mu suka tafi garin da motar tai haɗin. Tabbas sun samu anyi haɗarin, kuma an tabbatar musu babu wanda ya tsira a motar. Suma kuma da idonsu sunga wajen sai kufan wuta da gwangwanin ƙarfen motar. Ko yaro akacema mutum zai rayu a ciki bazai amince ba. Haka suka dawo mana da wannan tashin hankalin da damuwa. Baba kabiru kuwa ya yanke jiki ma ya faɗi, tun daga nan bai sake tashi ba har ya rasu. An yima Adda da Rabi'ah sadakar uku data bakwai, a ranar ne shima Baba Kabiru ya rasu. Hankali ya koma akan al'amarin Sulaiman da shima ba'a da tabbacin yana raye, sai kuma hukuncin ALLAH wata ƴar uwar Marka tazo mana da labarin Sulaiman a binciki Marka, itace ta saka aka sace shi, kuma itace sanadin salwantar su Adda. Dan kurciya ta musu. Ɓacin rai ya saka Baba aika ƴan doka suka kamo Marka har ƙauyensu, sai gashi da taga wuya ta faɗi kamar yanda ƴar uwarta ta faɗa. Ta kuma faɗi inda ta kai Sulaiman ta yarda. Haka aka sake bazama nema cikin amincin UBANGIJI sai gashi an samo Sulaiman a gidan mai garin ƙauyen, wani ne ya tsinta Sulaiman a gonarsa shine yaje ya kai gidan mai garin. Matarsa kuwa ta kama ta riƙe ta adana. Dan da ƙyar ma ta yarda ta bada Sulaiman ɗin. Mahaifiyarmu ce ta cigaba da kula da shi, yayinda dangin baba Kabiru suma ke iya ƙoƙarin su na ɗawainiya da shi. A haka akai bikinmu ni da Hassana ta. Itama bata tsallake wata ukun farko ba ALLAH ya bata ciki. Sai dai ni ALLAH bai kawo ba harta haihu ɗanta Namiji. Shine Abubakar”. Ta nuna Dad ɗin su Mansoor. Bai shekara biyu ba sai ga wani cikin ta sake samu. Na fara shiga damuwa, dan ni mutum ce mai son yara sosai. Dan haka innarmu ta kwantar min da hankali da Hassanata. Na kwantar da hankalina sai dai na roƙi a bani Sulaiman na cigaba da riƙesa. Babu musu Baba yace hakanma yayi, dan suna ganin riƙon Sukaiman ɗin zai bani nutsuwa. Ya kuwa bani, dan tuni na manta da damuwar rashin haihuwa. Hassana ma ta sauka lafiya mace, aka saka mata Maimoonatu. Bayan haihuwarta babu jimawa ALLAH yay ma Baba rasuwa. Mun shiga matuƙar ruɗani, daga baya dai zukata suka haƙura akan dole. Shima bai shekara ba Innarmu ta bisa. Shike nan muka koma babu uwa babu uba kuma. Sai ni sai ƴar uwata da ƴan ƴaƴanmu. Bayan Maimoonatu da muke kira Adda Hassana ma bata sake haihuwa ba sai bayan kusan shekaru goma sha, sai ga ciki. Na tayata murna sosai, da mata fatan sauka lafiya, dan yanzu kam ni zuciyata ta dake. Abubakar ma kusan a hannuna yake shima. Wannan ciki ashe shine sanadin ajalin Hassana, dan kuwa a wajen haihuwarsa itama ALLAH yay mata rasuwa ita da abinda ke cikinta. Bamma san yaya zan fasalta muku halin dana tsinta kaina a wannan lokacin ba. Amma dai lallai na jigatu, kowa ya tafi ta barni kamar labari. Dole na tattare duka ƴaƴan ni da mijina muka cigaba da riƙewa, duk da dai dangin mahaifinsu Abubakar sun so tayar min da hankali akan amsarsu nafaƙi aminta sam. Dole suka haƙura suka barni da kayana. Rana ɗaya na aurar da su su duka ukun. Adda ta auri Sulaiman, Abubakar ya auri ɗiyar ƙanin mijina uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Daga baya shima mijin nawa ALLAH yay masa rasuwa, muka koma daga ni sai su gasu nan. Sun riƙeni uwa mahaifiya, koda wasa basu taɓa gazawa wajen min hidima irin ta ɗa da mahaifi ba. Nima kuma ban ƙara kukan rashin haihuwa ba, dan duk abinda mai haihuwa zai buƙata na samu fiye ma da hakan a wajensu. Dan haka ina son sanin tayaya aka faɗi a ragaya? Bayan dukkan alamomi sun tabbatar mana Adda da Rabi'ah mun rasa su”..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_ ......Paah ne cikin girmama al'amarin UBANGIJI ya shiga jinjina kai. Tare da faɗin, “Wannan hikima ce ta UBANGIJI Mama, mai rayawa a sanda yaso, ya kuma ɗauki rai a lokacin da yaso. Mu dukanmu anan babu wanda zai iya amsa wannan tambayar taki ta yaya akai su Mamie suka tsira har suka kasance a Lagos. Sun shiga motar, basu shiga bane, tsira sukai ALLAH shi kaɗai ya barwa kansa sani sai kuma su. Dan duk waɗanda zamu iya sanin ainahin zancen daga bakinsu ALLAH yay musu rasuwa babu ko ɗaya yanzu a raye. Kaɗan daga abinda muka sani dai ita Grandma Maimoonatu taje da Mamie Lagos ne suke abinci anan kusa da companyn mahaifin Ummu-Hidaya. Sai sabo ya shiga tsakani har ake zuminci. Daga baya kuma ya auri Mamie Rabi'ah kenan shi Abie mahaifin Ummu-Hidaya. Shine suka haifeta, ALLAH ma ya ƙara bada wani cikin wajen haihuwarsa ne ALLAH yay mata rasuwa. Itama kuma Grandma ɗin saita rasu a dalilin haɗarin mota da aka.....” Saurin riƙe hannunsa Ummie tayi dan ta fahimci ɓaranɓaramar da yake shirin yi. Ta share hawayenta da cigaba da faɗin, “Haɗarin mota tayi kafin ma rasuwar Mamie na. Amma a tsakaninsu babu wani nisa sosai. Tabbas mahaifina ya taɓa sanar min Mamiena har ta bar duniya tana naci da ƙishirwar son sanin ina ahalinta suke, dan kamar dukansu an juyar musu da tunani ne sun manta komai musamman ma ita Mamie ɗin. Amma ita Grandma bata son faɗa mata. Idan ma ta dage da tambayarta sai ta nuna mata ɓacin rai. Sai dai tana yawan ɗaukar wannan hoton taita kallo tana kuka”. Ta miƙama Mammi hoton data ciro a handbag ɗinta. Amsar hoton Mammi tayi, aiko ta saki kuka mai ban tausayi. Iyayensu ne a jiki, sai ita Adda ɗin da cikinta da su a ranar suna su. Ta share hawayenta da faɗin, “Wannan mune da iyayenmu aranar bikin sunanmu ni da Hassana ta. Sannan tana da tsohon cikin mahaifiyarki. ALLAH ya jiƙan Adda da Rabi'ah. Ashe sallamar kenan mukayi. ALLAH ya saka mana, in sha ALLAHU Marka sai kin girbe abinda kika shuka tun a duniya. Amma ina son naje daku har wajen Marka ta tabbatar da UBANGIJI ya fita. Idan tana ganin ta salwantar da rayuwar Adda da Rabi'ah to ga baya nan sun bari”. “Tabbas Mammi zamuje. Kinga wannan shine babban ɗan Ummu-Hidaya, sunansa Muhammad Awwab, ga matarsa nan da ciki. Sai wannan ƙaninsa ne Fahad, ga tashi matar nan satin daya gabata akai bikin nasu.” Kuka Mammi ta sake fashewa da miƙa mana hannu tana faɗin, “Duk kuzo gareni ƴan albarka, kuzo naji ɗuminku kunji”. Garetan duk mukaje, ta kamamu ta rungume tana kuka. Matuƙar farin ciki yau muna a ciki, Ummie taje kusa da kawunta Sulaiman ta zauna. Kuka yake sosai tun ɗazun, hannunsa ta riƙe cikin nata itama tanayi. Abin tausayi. Babu ɓata lokaci akai kiran su Mami a waya ta taho da ƙannen su Mansoor. Itama Adda matar Uncle Sulaiman akace ta taho da tawagarta. Cikin abinda bai gaza awa ɗaya ba gida ya gama hallara. Duk da Mami yanzu tasan babu matsala tsakaninta da Maash sai ta kasa haɗa idanu da shi har jikinta na rawa. Ta dinga satar kallon Samraah. Sai da aka musu kuma bayanin abinda ya faru sai ta sake firgicewa. Nan fa sabon kuka ya tashi. An sake gabatar da su Awwab matsayin yaƴan Ummie da mu matansu, sannan ƴaƴan Dad su huɗu suma da matarsa. Sai Uncle Sulaiman da Adda da nasu ƴaƴan shida ALLAH yay ma ɗaya rasuwa. Baza uku mata uku. Ashe a cikinsu ne ma Attahir zai auri ɗaya.. A gurguje Please 🥺 💢🌟💢🌟💢 Batun dai komawa Lagos ranar bata yiwu mana ba. Dole zuwa dare muka wuce can gidan gashi ma'aikatan gidan basu san da zuwanmu ba. Sai da muka isa aka hau gyarawa, sauƙin ma bawani dattine yayi ba tunda bamu daɗe da barin garin ba. Ummie dai can gidan Mammi muka barta. Dan tana nane da kakarta. A falo muka baje munata tattauna wannan iko na ALLAH mai ban al'ajabi da mamaki. Duk rashin son magana ta Yaya Awwab sai da ya saka mana baki. Ballema da nake basu labarin ni tun randa naga hoto a office ɗinsa nake laluben inda nasan mai kamannin. Sai dai da yake nima sau ɗaya na taɓa ganin Mammi ɗin na kasa tunawa. Shi kuma Maash yace a jikin Dad yaga kamannin, ashe ƙarfin jinine kawai. Ashe shiyyasa ma yace su shigo dan suga hotunan itama Ummie taga Dad ɗin. Mun jima muna hirar har Paah da Baban Hayatu kafin kowa ya nema makwanci. Kamar yanda tsohuwa Mammi ta faɗa washe gari suka kwashemu sai ƙauyen su Marka. Ni dai wannan tafiya bata min daɗi ba dan naci ƙaniyata gwargwadon iko. Saboda hanyar bata da ƙyau, sauƙina ma daga ni sai shine a motar, ina kuma jikinsa koyaya nace wash zai ce minene. Bama ni kaɗai ba kowa ya jigatan ashe. Haka dai muka fito yara da manya sun zagaye motocinmu suna kallo. A ƙofar wani ruɓaɓɓen gida da duk katangar ta cinye ana hango komai na cikinsa, ɗakin kansa wasu ɓangarori sun rushe an saka langa-langa ne da tsummuna harma da itace. Haka muka bi bayan Mammi kowa na yamutse fuska. Sai da muka shiga sosai mukaga yamushshiyar tsohuwar da tafi gidan gajalewa zaune acan ɗan lungu ta zuba tagumi tana kallon waje ɗaya. Sallamarmu ce ta sakata dawowa firgigit ta juyo tana kallonmu. Da alama ganin Mammi ya saka jikinta fara ɓari. Mammi dake tsaye ta dogare jikin sandarta da tana riƙeta ne badan ciwo ba fuskarta da murmushi ta ce kwantar da hankalinki Marka Hussaina ce dai ba wata ba. Tare da dukkan zuri'ata.” ta juyo tana nuna mata mu. Binmu da kallo Markan take jikinta na ƙara ƙarfin rawa. Zeenat babbar ɗiyar Uncle Sulaiman da autansu Ahmad suka shimfiɗa tabarma. Batare da an bamu izini ba muko duk muka zauna. Sai Yaya Awwab ne kawai a tsaye da Hayatu da Attahir. Dama nasan shikam bazai zauna ba, dan wani ɗan iskan kallo ma yakema Marka. Dama Ya faɗa min sai fa yaci ƙaniyar matar a daren jiya. Amma naita bashi haƙuri tunda ance ma ta tsufa miya rage mata kuma. Bai dai ce min ya haƙura ba, bai kuma cemin zai aikata ɗin ba. Tiryan-tiryan Mammi ta dingama Marka bayanin mu. Dan hatta shi Uncle Sulaiman ɗin ta jima bata gansa ba. Tunda ta samu Baba mahaifin su Mammi yasa ƴan doka suka saketa bata sake gigin zuwa ko hanyar Kano ba. Ana sanar mata Ummie ɗiyar Rabi'ah ce ta fashe da kuka da kiran ta shiga uku. Ballema da aka nuna mata su Maash kuma sai fitsari kawai mukaga yana binta. Bature matsayin jikan Rabi'ah da Maimoonatu ai kasheta ma kawai zaiyi yau. Da ƙyar aka samu ta nutsu. Yayinda Maash yaja tsaki cikin gurɓatacciyar hausarsa ya ce, “K mima za'a kashe anan ƙazama kawai. Ki jira mai miki hukunci yana nan a madakata ke da ire-iren ki yana jiranku. Ganinmu anan ma kawai ya isa miki aya tunda wayonki ko dabaranki da baƙin halinki bai hanamu zuwa duniya ba. Harma ga ƴaƴayenmu nan tafe in sha ALLAHU”. Daga haka yay ficewarsa a gidan. Attahiru da Hayat suka bisa. Yayinda Fahad ya ƙare mata tanadi shi da Jabeer ɗan Uncle Sulaiman. Dan shima kusan halin nasu ɗaya da Fahad ɗin. Gashi basu wuce sa'anni ba. Haka dai muma muka fito muka barta tana kuka da faɗin ta cuci kanta, ga shi nan kowa ya gujeta, sai ta kwana ta yini bata ci abinci ba, ba'a bari yara su shiga inda take ance ita mayyace ta cinye yaran kishiyarta. Babu wanda yafi yakanta sai Ummie ce dai harda ajiye mata kuɗi.... Koda muka koma cikin kano tattare komai akai aka ajiye gefe aka kuma shiga hidimar bikin su Mansoor da har yanzu ni da shi bamuyima juna magana ba. Sai dai nakan kamashi yana kallona lokaci-lokaci. Ɗauke kaina kawai nake tamkar ban gansa ba. Kasancewar Ummie gaba-gaba a bikin ya tilasta mana kasancewa muma. Dan ita tana can ma ta tare cikinsu ko sau ɗaya batazo nan ta kwana ba. Ina son zuwa gidan Abba na gaishesu amma sarakin nawa ya hana. Wai duka yaushe aka rabu, ya kuma hanani na kira kowa na sanar musu muna gari. Sai Hafizzullah da yazo nan ya samemu, sai da ya sanarma Hafizzullah ɗin ma kada ya faɗama kowa. To bama can ɗin kawai ba, ranar kamun amaren su Attahiru ɗin ma hanani zuwa yayi, sai washe garin ɗaurin aure shima da ƙyar har sai da na masa kuka. Abin ya konan rai amma na sharesa.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ .......Ana kammala ɗaurin aure kuma sun shigo gidan nace wai na zo mu wuce gida. Aiko bai ƙwalƙwal da idanu zan masa kuka Ummie tace ya barni mana. Ransa a ɓace ya ce, “Ummie tazo kawai mu tafi, itada bata da isashen lafiya ma. Bana son nayi wani abinda za'ace banyi dai-dai ba a dangin nan naki”. “Ban gane ba, Muhammad mi dangina suka maka?”. “Ni basu min komai ba, wannan yaron ne duk inda matata tai idonsa a kanta. Bana son na tsiyayar masa da ido ace nayi ba daidai ba. Idan kuma aka cigaba da tafiya a haka ALLAH zan aikata”. Cikin mamaki Ummie ta rasa wama yake nufi, Ni kuma sai yanzu na harbo jirgin nasa. Oh ALLAH kishi da Mansoor kuma. Mutumin da ko magana ma bamuyi ba. Hayatu ne dai yama Ummie bayani a taƙaice, sai kawai ta girgiza kanta tana faɗin to ALLAH ya shiryeka Muhammad, kadai tuna yanzu shi Uncle ɗin ka ne, dan ƙanina ne. Ni dai wannan kishi naka ban san ina zai kaika ba. Sai kuyita tafiya”. Babu kunya kuwa ya jani muka tafin, ganin haka sai aunty Falaq ma kawai tace ma Yaya Hayatu itama zata koma. Da dare akai dinner, sai dai ni bamma je ba, shima kuma hakan babu inda yaje. Washe gari ma yake sanarma Ummie abu ya taso masa zai wuce. Yana ganin kuma har dani. Ɗan jimm Ummie tai kafin tace, “Amma dai Muhammad yarinyar nan dake fama da tsohon ciki ina zakaje da ita hakane?. Sannan jibi Hafizzullah da Fahad da Matarsa zasu wuce. Haka zaku barmu gida shiru dan ALLAH”. “Ummie Please mana. Ba kince da Mammi zaki tafi ba da kuma yaran Uncle har su biyu, ga kuma yaran nan suma ƙannin Attahir. Na miki alkawarin zan kula miki da ita. Da watan haihuwar ya kama zan dawo miki da ita. Bafa nisa ma zan miki da ita ba nan Dubai ne kawai Please”. Badan Ummie nazso ba ta barmu. Harga ALLAH nima naji daɗin hakan, dan ina son Ummie da Paah su more abinsu. Hakan kuma bazata kasance ba sai idan mun gusa daga gidan. To ashe Hayatu ma ɗauke Aunty Falaq zaiyi su wuce. Zasu je can China akwai aikin da zasuyi shi da Yaya Musaddiq.. A randa muka dawo Lagos a ranar Paah ya kawo result ma Ummie. Alhamdullah komai lafiya lau, babu wata matsala da zata hanasu kasancewa tare. Ummie harda kukan daɗi, uban gayyar dai bai tanka ba. Garama Fahad ya ce ALLAH ya kiyaye gaba, daga haka ya tashi ya fita abinsa. Mun san duk sai a hankali zasu manta da komai, dan bazai yiwu a lokaci ɗaya ba dama. Shi dai Paah ɗin ma murmushi kawai yayi. ★Rayuwa ta sake canjawa daga wani aji zuwa wani. Dan kuwa kasancewata daga ni sai Yaya Awwab a Dubai wani ajine na karatu mai faɗin gaske. Wataran daɗi wataran saɓaninsa, dan mun sake fahimtar halayen juna kamar kowa waɗanne ma'aurata. Kulawa dai Alhamdullah ina samunta daga garesa. Hakama yaron cikina. Dan akwai aikin companyn da yake yi anan Dubai ɗin shine ALLAH ya taimakan ya kasance waje ɗaya. Sai da mukai sati biyu nama damesa da ko zai kawo min Bibaa saboda idan ya fita gidan kuma babu daɗi. Da yaga na damu sai aka samo min wata mai aiki balarabiya. Alhamdullah sai nake jin daɗin zama da ita. Dan mutuniyar kirkice ga amana da addini. Sannan tana bani shawarwari sosai akan rainon cikin nan. Muna waya da mutanen Nigeria, musamman ma su Ummie kullum ne babu fashi sai nayi waya dasu fin sau uku ita da Mama balki. Hakama su Aunty Falaq da Yaya Musaddiq da Aunty Ruky kuma ƙawa. Sai aunty Halime, Abba da Gwaggo Gudidi suma dai duk ana gaisawa. Ta ɓangaren Fahad da Bahijja da Hafizzullah ma dai hakanne. Dan har an gumtsa min gulma Bahijja na laulayin ciki. Itama dai Ruƙayya Aunty Falaq tace kamar taga an gamu fa. To muna dai zuba ido... A gurguje Please 🥺 💦❤️💦❤️💦 Alhamdullahi na shiga watan haihuwa. Gaba ɗaya kammani sun canja. Kullum wayyo tako ina babu daɗi. Na mugun ƙibewa ko nace na kumbure. Ga masifaffen cin abinci ko cikin dare na farka sai naci. Tun yana mun dariya akan cin abincin har ya koma tausayina. Duk uzirinsa idan biyar tayi yakanyi ƙoƙarin ya dawo gida dan mu fita na ɗan tattaka. Idan kuma yayi busy da yawa ne sai Nasreen ta fita dani. Ta gefe guda Ummie ta damesa akan ya dawo dani gida. Hakama Mama da Mammi da har yanzu tana tare da Ummie. Itama dai Gwaggo Gudidi kullum ƙorafinta kenan. Ita bata son na haihu a ko ina sai Nigeria. Dan wanka zata mun cikakke na jego. Ni dai nasan tana faɗane kawai dan Yaya Awwab ba yarda zaiyi da batun tafiya wankan nan ba. Amma kada nayi magana tace nayi rashin kunya shiyayasa dai nayi shiru kawai. Matsin lambar da yake samu a wajensu yasa ya fara dai-daita abubuwansa dan mu wuce gidan. Sai dai kuma muna namu ne ALLAH yana nashi. Nashi ne kuma gaskiya. A safiyar yau na tashi duk dai babu daɗi, ga wata irin zufa da nakeyi kamar mai wanka da ruwa. Haka dai na daure na fita kitchen duba Nasreen dan mu haɗa masa breakfast. Saboda idan ban saka hannu ba bazai ci ba. Komi zatai gwanintar dafawa baya ci. Sai yace ya ƙoshi. Sai idan ya tabbatar nice nai girkin koda da taimakonta ne sannan zai ci, duk fa ma cin abincin nashi duk shiririta ne. Amma da yake yanzu ina dagewa ina kulawa yana ci fiye da da daya maida chocolates abinci. Itama ina shiga ta zuba min ido. Sai kawai na kauda kaina gefe ina tambayarta mi take ƙoƙarin haɗawa. Idanun nata har lokacin dai a kaina tace bata haɗa komai ba dama tana jiran fitowata ne. Shine nace mata kawai muyi abu mai sauƙi. Mun fara girkin dai ta kasa daurewa. Cike da kulawa take tambayata kodai banda lafiya ne? Taga inata zufa alhalin kuma bamma fita motsa jikin ba yau. Dan taga ogane kawai ya fita. Murmushi yaƙe na mata kawai nace babu komai. Kawai dai ina jin zafi ne, maybe kuma dan muna a kitchen ne. Badan ta yarda ba ta barni muka cigaba da aikin. Can dai naji fa abin bana wasa bane ba, dole naja kujera na zauna ina cemata ta cigaba bari na huta. Haka na kife kaina a table ɗin ina ambaton sunayen ALLAH. Dan wani irin juyamin cikin keyi. Nafi mintuna goma a hakan sai ga door bell na ƙara. Nasan shine ya dawo, ni kuma ke zuwa buɗe masa a ƙa'idarsa. Amma sai na kasa, da ƙyar ma nace mata taje ta buɗe masa. Da to ta amsa min ta fita. Bata wani jima ba sai gasu ita da shi sun shigo, shi ya fara shigowa ita kuma tana biye da shi. Nasan ganin bani na buɗe masa ba ya tambayeta, ita kuma ta sanar masa. A ɗan rikice ya ke faɗin, “Samrh kina lafiya kuwa?”. Kaina na jinjina masa ina murmushin yaƙe. Ya ce, “Ban yarda ba. Diba yanda koke zufa kamar mai aikin ƙarfi. Tun fa ɗazun naga kikeyi amma kince babu komai. Gashi har kin kai zaune kimma kasa aikin. Kinga tashi muje asibiti”. Da ƙyar nace, “Maybe fa juyi ne kamar na wancan karon”. “Ba wani juyi oya tashi”. Ya faɗa cikin bada umarni babu alamar wasa a tare da shi. Fuska na marairaice masa zanyi magana ya katseni da faɗin, “Karma kice komai ta shi”. Baima jira cewata ba ya ɗagani, a haka muka fita. Munje tsakkiyar ƙaton falon ƙafa ta riƙe. Tun ina ɗagata da ƙyar ina cije baki har da na gagara. Dole na tsaya cak ina hura hanci. Sake rikicewa yay, ai sai kawai ya ɗaukeni cak yay waje da ni yana sanar ma Nasreen ta same mu a mota. Kamar jira yana kaini mota kuwa na fara murƙususu. Cikin tsawa yace ma driver ya shiga mota mu wuce. Shima bayan ya shiga ya rungumeni a jikinsa, Nasreen da driver na gaba. Kafin ma mu gama barin anguwar na rikice musu. Yayinda shima ya rikima driver wai baya gudu. Dole fa driver ya ƙara gudun ma da ya wuce ƙa'ida. A hakan dai ALLAH ya kawomu lafiya asibitin. Tun a waje aka tarbemu, amma yaƙi bari a shiga da ni ni kaɗai, duk haƙurin da suke bashi sai da ya bimu labor room ɗin. Dan kai tsaye sukace ai haihuwa ce gata ma gab gab sosai. A ciki da kyar suka samu ya fito bayan ya canja min kayan da suka ɗakko zasu canja min.... Alhamdullah duk da bazan ce na haihu salin alin ba, dan ansha gumurzu babu laifi. Sai dai gaskiya haihuwan tazo da sauƙi dan banyi doguwar naƙuda ba. Amma fa mata sunji a jikinsu. Dan ina samu abinda ke cikin nan ya fita sai kawai na shiɗe, sai da suka shafa min ruwa na kawo numfashi mai ƙarfi. Da kukan baby daya cika ɗakin na fara cin karo. A hankali na sake jan numfashi tare da ambaton “الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ . Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat. اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ. Alhamdu lillahi ala kulli halin.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏_ ......Tunda ya fito ya kasa zaune ya kasa tsaye. Nasreen da Driver ma dai na zaune jugum-jugum. Ya ciro waya yafi sau biyar da zummar kiran su Ummie sai kuma ya fasa. Gara dai ya bari ta sauka sanan. Yana nan dai yana kai-kawonsa da addu'a a bakinsa aka buɗe ƙofar. A tare shi da su Nasreen suka zabura. Tuni Nurse ɗin data fara fitowa mai ɗauke da Baby na laɓe a bayanta ta saki murmushi mai ƙayatarwa da faɗin, “بَارَكَ اللهُ لَكَ فِي الْمَوْهُوبِ لَكَ، وَشَكَرْتَ الْوَاهِبَ، وَبَلَغَ أَشُدَّهُ، وَرُزِقْتَ بِرَّهُ. Barakal lahu laka fil mawhubi laka, wa shakartal wahiba, wa balagha ashuddahu, wa ruzikta birrahu. Congratulations da samun Baby girl ƙyaƙyƙyawa kamar kai da mahaifiyarta” Sai kuma ta matsa mai ɗauke da Babyn ta bayyana. Wani irin nannauyan numfashi Maash ya sauke tare da zubewa ƙasa yay sujda. Kafin ya ɗaggo hannayensa a sama cat eyes ɗinsa na yin ƙyalli kamar mai shirin sakin kuka ya furta, “الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ . Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat. اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ. Alhamdu lillahi ala kulli halin”. Sai kuma ya miƙe ya amshi Babyn ya rungumeta a jikinsa yana sake miƙa godiyar sa ga UBANGIJI tare da yimasa kirari a bayyane. Dan shine kawai mai bada irin wannan ƙyautar da dukiya ko mulki bata badawa. Ɗago babyn yay mai kama da shi sosai ya zuba mata ido yana sakin murmushi mai matuƙar ƙayatarwa da yakan jima bai yisa ba. “Dadaa na miki fatan alkairi da zuwa duniya mai cike da gwagwarmaya UMMU-HIDAYA. أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ. O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah.” Ya kai lips ɗinsa saman goshinta ya sumbata tare da sake tungumeta a jikinsa. Yayi kusan minti biyu a haka duk suna kallonsa. Bakin driver da Nasreen yaƙi rufuwa. Sun ƙagara a basu baby a hannunsu suma su gani. Sai da Nurse tai gyaran murya sannan ya farga da su. Miƙa musu Babyn yay yana tambayar Nurse ɗin matarsa fa. Cike da girmamawa ta sanar masa itama tana cikin ƙoshin lafiya. Suna kammala gyarata ma zai iya ganinta. Daga haka ta karɓi Babyn a hannun su Nasreen ta koma da shi ciki. Shi kuma ya ciro waya ya koma gefe. Paah ya fara kira ya sanar mawa. Dan zuwa yanzu kam tsakaninsu Alhamdullah, suna waya ko yaushe da mahaifinsu. Sun kuma cire komai a ransu hatta sauran dangin baban nasu suna kira. Farin cikin da Paah ɗin ke ciki har babu misali, haka ya yanke wayar yana murmushi yay kiran Ummie itama. Sai akai Sa'a suna tare da Mama balki da Mammi ma. Aiko suma dai can suka kaure da murna. Daga haka yay kiran Abba sannan Yaya Musaddiq da Hayatu sai su Fahad. Shi kansa yanda kowa ke farin ciki da zuwan Babyn tasa sai yake jin farin cikinsa na ƙara nunkuwa. Bare kuma da aka fito da Samraah zuwa ɗakin hutu. Bai ko ɗaga musu ƙafa ba yabi bayansu. Haka dole suka fito suka barsa suna dariya. Dan tuni ya rungume kayarsa yana bata kisses tako ina da sanya mata albarka. Ban iya nace masa komai ba dan barcine sosai a idanuna saboda alluran da sukai min. Tun ina jinsa da ƙyau har na koma sama-sama barcin ma yay awan gaba da ni. Sai da nai barcin awa takwas cif sannan na farka. A lokacin kam baby na kusa da ni itama tana barcinta hankali kwance. Sai Nasreen a gefe zaune cikin kujera tana danna waya. Ta na ganin na motsa ta taso inda nake tana mun sannu. Kaina kawai na iya jinjina mata da tambayarta Yaya Awwab. Bakinta yama kasa rufuwa ta ce yanzu ya fita tarbo baƙi airport shi da driver. Sunzo da ga Nigeria. Nayi mamaki, su waye ya taso haka kuma tun daga Nigeria, muda ya kamata muyi shirin wucewa kuma tunda ALLAH ya ƙaddara anan zan haihu. Nurses ɗin ta kira min, suka taimaka min na ƙara gyara jikina, sai lokacin naga Baby. Idanu kawai na zuba mata hawaye na sakko min. Ni Samraah Abdul-wahab Gwarzo, Sam-G ce yau da ƴa ta mutum matsayin mallakina, tare da mijin da ban taɓa mafarkin samu ba a rayuwata. Dan ban taɓa koda kwatance tunanin Maash zai iya zama mijina ba. Tabbas tun a ganin farko dana masa jikin Magazine naji wani abu a raina game da shi, shiyayasa ma na dinga ƙoƙarin kushesa dan kar abinda najin yay tasiri a zuciyata. Saboda ina gani Mansoor ne kawai ya cancanta a lokacin, babu ma wani abu wanda zai tabbata makamancin abinda ƙasan zuciyata ya ke ji. Ashe shi UBANGIJI ya gama nasa tsarin. Ƙaddara ta jima da rubutuwa a cikin littafi. Sosai na rungumeta ina mai sake godiya ga UBANGIJI daya azurtani da wannan ƙyauta. A hankali na furta, “Ina neman miki tsari da kalmomin ALLAH cikakku daga dukkan shaiɗan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa. ALLAH ya raya mana ke, ya albarkaci rayuwarki, ya sa ki zame mana ɗiya abar alfahari, yasa ki amfanar da kanki da addininmu da zuri'armu da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W). ALLAH ya hanaki aikata shirka, ALLAH ya hanaki aikata zina, ALLAH ya hanaki aikata Maɗigo, ALLAH ya hanaki aikata sata, ALLAH ya hanaki cutar da kowa, ALLAH ya hanaki shaye-shaye da dukkan miyagun ayyuka. ALLAH ya tsarkake zuciyarki ya wadata ta da imani da tsoronsa, da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W) mara yankewa ke da ƙanneki masu zuwa idan hakan na cikin ƙaddararmu” “Amin ya rabbi ALJANNAR DUNIYA TA”. Aka amsa min daga baƙin ƙofa. Idanuna dake lumshe na buɗe, shi ɗin ne dai tsaye kamar yanda na sani kodan muryarsa data ratsani da kuma ƙamshinsa da sai yanzu na farga. Takowa yay a hankali zuwa garemu. Ya zauna kusa da ni yana mai rungumoni jikinsa ni da ita. Sai kuma ya kaimin kisses a wuya tare da raɗa min a cikin kunne, “Madalla da samun Uwar ƴaƴa ta gari abin alfahari miji da ƴaƴanta. Sannu da ƙoƙari Samrh. ALLAH yay miki albarka”. “Amin tare da kai mijina. ALLAH ya bamu ikon bata tarbiyya kamar yanda iyayenmu suka bamu”. Da Amin nan ma ya amsa. Kafin ya sanar min Ummie, Mama Balki, Paah, Baba, sai Mammi sun iso suna gida. Cikin zaro idanu waje na ce, “Kai My hot muda ya kamata ace mune zamu tafi mu samesu ma yanzu. Amma shine ka barsu suka wahala suka taho”. “Sunce bazasu iya haƙuri bane ba. Yanzu haka ma da ƙyar na samu suka wuce gida nace musu za'a sallameki yanzu tunda sunce dakin farka ne. Kuma lokacin da suka tabbatar zaki iya farkawar har ya gota. Little Ummu tazo da farin jini”. Murmushi kawai nayi ina mai girgiza kaina. Haka ya taimaka min shi da Nasreen muka kimtsa. Da taimakon Nurse ɗin nan mukaje mota. Suna mana addu'a da fatan alkairi muka wuce muka tafi. Mun samu iyayen namu kam zaune sunƙi ko cin abincin da aka taresu da shi suna jiran isowarmu. Ai motarmu na shiga suka firfito. Tun a haraban gidan suka tarbemu. Ummie ta rungumeni tana hawaye da sanya min albarka. Yayinda Baby na can hannun su Paah suma suna sanya min albarka da mata addu'a. A haka muka shiga cikin gidan. Dandanan fa tsohuwa Mammi da tazo da guzirinta na kayan wanka ta fiddo ta bama Mama Bilki akan a ɗora. Haka kuwa akayi, dandanan aka dafa Mama Balki tai mun cikakken wankan jego ina shagwaɓa ina wash tana lallaɓani. Yayinda tsohuwa da kanta ta sulluɓe baby tas ita kuma. Kafin kace mi mu duka an shiryamu tsaf. Ummie kuma ta dama min kunun kanwa da duk suka taho da kayansu, sai gasashen naman rago da yaji haɗi na musamman 😋🥱 sai uban ƙamshi gidan yake yi. Aka kuma baɗesa da yajin daddawa da suka taho da abinsu dai. Haka Ummie ta zauna cikin kulawa ta sakanni a gaba naci naman nasha kunun wai kuma sai ga tea, aiko na fara mata kuka wlhy na ƙoshi. Dole aka barni haka. Sai lokacin na samu mukai gaisuwa da su. Sunata ƙara jerama Baby addu'a da ni kaina. Kasancewar su a tare da ni ta ƙara min farin ciki da walwala. Haka mukai shirin kwanciya cike da kulawarsu. Baby dake barci tun ɗazun ta farka. Haka aka tsareni nai feeding ɗinta dan sunce yunwa ce. Na dai sha zafi, to amma yaya na iya tunda muma haka iyayenmu sukai haƙuri da mu a lokacin tamu haihuwar da rainon. Ga kiran waya tako ina shigowa yake kamar wayata zata tashi aiki. Kowa ya kira ɗaga masa nake. Dan masoyi na gaskiya ne ma zai tayaka farin ciki idan abin farin cikin ya sameka. Ya kuma tayaka kuka idan na jajen ya sameka. Nasha mamakin ganin harda Hajiya Mammah a masu kira, cike da farin cikinta kuma tanatama Baby Addu'a kuma dan tuni hotunanta sun kai garesu. Hakama Maman Malika da Malikar duk sun kirani. Suma zuwa gobe in sha ALLAHU sun ce suna tafe. Ƴan Kano ma harda wanda bamma yi zato ko tsammanin suna da number ta ba duk sun kira. Aunty Halime ce ke sanar min da aka faɗama Mom na haihu kuka wai ta fashe da shi. Gata babu isashshiyar lafiya. Kullum bakinta nakan Baby yanzu. Duk ta bushe ta lalace a tsaye. Ummanta kuwa wajen neme-nemen asirinsu taje mai mashin ya kadata a hanyar wani ƙauye ta karya ƙafa har waje biyu. Cinya da gwiwa. An ɗaura baiyi ba aka sake har sau uku. Ga ƙafar nan tana neman zame mata jangwam. Dole sai ƙanwar Mom ɗin ce tazo tana kula da ita. Ita Mom ɗin taƙi wai abarta ta kanta takeyi. Abinda ya dameta shi ya dameta. Umman tata dai har ranta ya ɓaci taita kuka akan furucin Mom ɗin tana ja mata ALLAH ya isa da faɗin ai duk ta dalilinta ne komai ya faru da yaƴanta, amma shine zata mata sakayya da halin ko'in kula........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ .......Washe gari su Maman Malika da Hajiya Mammah suka iso suma. Hakan sai ya sake bani mamaki. Na tambayesa wai ba gida zamu tafi ba. Dan ina jin kunyar tambayar su Ummie. Shine yake sanar min ai batun tafiya babu shi. Babu mai kwasarma yarinyarsa sanyin jirgi. Za'ai suna anan kawai. Hankalina ya tashi, ta ina zan yarda da hakan. Idan shi danginsa na da ƙarfin tahowa nan ni kuma nawa fa? Ai ni za'a cuta kenan. Bamu ƙarasa maganar ba ya fita saboda kiran da akai masa a waya. Dama ya shigo ne mu gaisa da safen nan bayan Mama Balki ta mun wanka Mammi tama Baby. Da wannan damuwar na yini a rai dan bai dawo gidan ba har su Hajiya Mammah suka iso. Ummie ce ta ɗan lura da yanayina shine take tambayata mike damuna. Har nayi niyyar ɓoye mata sai naga bayan ita inada wata uwar ne. Sai kawai na fito na sanar mata ina hawaye. Murmushi tayi da rungumeni, cike da kulawa ta ce, “Karki tada hankalinki kinji yarinyata. Nima ina bayansa, dan ba baby kawai ba koke bazan yarda kisha iskar nan ba. So nake ki samu jego mai ƙyau da kulawa. Shiyayasa ma muka taho nan. Tunda kuma kikaji ya faɗa nasan yanada nashi shirin shima a ƙasa. Dan yanzu haka bamu jima dayin waya da Gwaggo Gudidi ba ma. ALLAH ya ƙaddara anan ɗin za'a haihu, sai kawai ayi haƙuri a ƙarasa komai” Kaina na jinjina mata ina godiya. Daga haka muka cigaba da sabgogin mu. Bai dawo gidan ba sai dare. Koda ya shigo muka gaisa ban masa maganar ba. Sai ma zancen isowar su Yaya Musaddiq da Hayat gobe idan ALLAH ya kaimu yay min. Tare da nuna min wasu kaya wai idan ina son su zasu taho dasu ne. Idan kuma bana so su barsu kawai. Cikin farin ciki na sanar masa ni komai ransa ya biya masa yayi basai ya bi takaina ba. Daga haka mukai ƴar hira yana rungume da ƴarsa sai da Ummie tazo ta korashi. Dan tare da Mama balki muke kwana anan. Washe gari kamar yanda ya faɗa da yamma sosai sai ga ƴan China sun iso. Basufi awa biyu ba sai ga kuma ƴan Spain suma. Hafizzullah, da Fahad da Bahijja. Aiko gida ya sake kacemewa. Dan har ma ya fara mana kaɗan. Sai da aka buɗe na kusa da mu ban taɓa sanin nashi bane ba sai yau. Ina dai ta ganin gidan a rufe koda yaushe sai nayi tunanin masu shi banan suke zama bane maybe zuwa suke time to time yin hutu kawai. Wannan taron ya sa naji a raina dama ya shirya abinsa fa. Dan tabbas-tabbas a haka yaso al'amarin ya kasance. Shiyayasa ya dinga min wayo da su Ummie ɗin kansu wai sai na shiga watan haihuwa saboda doctor yace ina son kulawarsa. Kai ya Awwab sai a barsa dai kawai. Yanda kowa kenan nan da Baby nece lallai kam naga haihuwar dangi. Dan daga Fahad har Yaya Musaddiq, aunty Falaq da Yaya Hayatu uban kayan da sukazo da shi na baby sai kawai nai tagumi ina kallonsu. Bayan ma anan shi uban gayyar ya loda wasu, saboda har ɗaki an haɗa mata. A ɓoye kam sai da nayi kuka Bily, dan sai nake jin kamar soyayyar ma ta mana yawa. Mammi dai ta kafa ta tsare, duk abinda ake mun na jegon nan irin na mutanen da ne. Tsohuwar nan da uban guzirinta ta taho na kayayyakin itatuwa. Ga Hajiya Mammah nata ƙoƙarin ganin ta goge laifinta, sai dai fa masifar tana nan, wannan kam sai haƙuri dan kowa yasan halittarta ce. Itama Aunty Mama a yau ta iso da nata yaran. Sai fa aka sake kacamewa. Jikina duk ya fara yin sanyi, ƴan uwana uku ne fa sai matar Yaya Musaddiq a cikin duk wannan taron. Ina zaune a ɗaki nayi tagumi na saka Baby da nake feeding gaba da kallo ya shigo da sallamarsa. Ganin yanda ya tasamu gaba da kallo idanunsa ƙyam a kammu yasa naji kunya, janyeta nai na gyara jikina na miƙa masa ita. Ɗan murmushi yay da faɗin, “Oh baki so naga kina mun feeding Mamana?”. Nima murmushin nayi ina ɗan girgiza kai, na ce, “Kai yaya kunya kuma. Kawai dai naga baka ganta bane tun safe shiyayasa. Ka dawo lafiya?”. “Alhamdullahi, kuyi haƙuri na kasa baku attention ɗina yanda ya kamata. Ni kaina ina son ko yini ɗaya nai a gidan ayi jegon da ni amma uziri yamun yawa”. Cikin ƴar dariya na ce, “Namiji kuma da jego? Kayi harkokinka mu zamu maka jegon”. “Kin tabbata?”. Na jinjina masa kai alamar tabbatarwar. Murmushi yay shima tare da ɗan jamun hanci. Sai kuma ya ɗan bata fuska da faɗin, “Duk sun saka min ke kinyi duhu. Nace ma Ummie a daina miki amfani da wannan ruwan zafin ga wani traditional medicins a ciki dani ko kallonsu ma bana son yi amma Ummie tace babu ruwana. Kema baƙya so ko?”. Fuska na marairaice masa ina kwanciya a jikinsa da faɗin, “Yaya bawai fa ina sha bane ba. Kuma suna da amfani sosai. Duhun nan kuma wanka da ruwan zafi ne yasa ba wani abu ba. Zamu washe ne. Ni yanzu ma ba wannan ba, wai taro zakayi ne naga invition card a hannun su Hafizzullah?”. “Eh mana, ALLAH zai mun ƙyautar nan ne ban nuna farin cikina ba. Banyi na aure ba fa, dan ina kishin Matata. Wannan kuma ya kamata nayi dan kowa yasan Maash ya zama Baba shima”. Ya ƙare maganar da kashe min ido ɗaya. Murmushi kawai nayi da faɗin, “ALLAH to ya taimaka. Amma a ƙasan raina ina jin damuwar babu nawa dangin sosai a cikin sabgar. Ya jima a ɗakin sosai yau kam Hajiya Mammah tazo ta korashi. Ni saima suke ban dariya. Duk yanda suke tunanin rashin kunyar Yaya Awwab yana kuma fa da kawaici. Duk abinda kuma yasan zan cutu yana matuƙar ƙoƙarin kauda masa ido koda yana a buƙace da shi, dan ni kaina nasan a takure zai kasance a tsakanin nan. Amma idan bashine yaso ka fahimta ba bazai taɓa nunawa ba. Washe gari na tashi sukuku dan sabgogin bikin suna sun kankama a ƙasar da ba tamu ba. Sai kawai gasu Hafizzullah da Fahad suna shigo da kaya. Da mamaki nake kallonsu saboda a lokacin na fito zan nunama Aunty Falaq abu a kitchen basu ganshi ba. Ga Nasreen sun fita ita da yaran Aunty Mama kasuwa. Gaba ɗaya sai na saki baki da hanci da idanu ina kallon masu shigowar. Abba ne kan gaba. Sai Gwaggo Gudidi da aunty Halime Aunty Zakiyya a bayanta ɗauke da Babyn aunty Haline ɗaya. Sai Mom a ƙarshe Bibaa da Auta biye da su, sai Matar Kawu Musa da ta Kawu Sabi'u da Aunty Magajiya. Na zata sun ƙare sai ga Adda matar Uncle Sulaiman da yaranta sai Mamin su Mansoor da ƙannen su Mansoor ɗin biyu da matansu, sai uwargidan Sheikh, maman Bahijja kenan. (Ikon ALLAH, sai kace ba daga wata ƙasa zuwa wata bane) na faɗa a zuciyata wata irin ƙaunar bawan ALLAHn nan na ratsa ɓargo da jikina.. Gida kam ya amshi baƙi fiye da yanda nayi zato, tsabar farin ciki harda hawaye bayan na rungumesu ko nace nama rasa wazan rungume a cikinsu. Gwaggo Gudidi nata mun tsiya wai ko dai na suma ne. Ashe Ummie ma tasan da isowar tasu mune dai aka ɓoyema ko nace ni. Kowansu ya ɗauki Baby anata sanya mata albarka da addu'oi da kwarzanta kamanninta da babanta. Yayinda Mom ta zama wata abar tausayi, dan bata ma ɗauki Baby ba sai da Abba ya daka mata tsawa da faɗin, “Oh hassadar taki ce ta motsa nan ma kenan Jalilah”. Yanda yay matan sai ma ta bani tausayi, amma sai naga su su Gwaggo Gudidi ko'a jikinsu. Auta dai na nane dani anata bani labarin Nigeria. Bayan sun huta sunci abinci suma aka kaisu ɗayan gidan domin suyi wanka su huta. Abba kuma aka wuce da shi nashi masaukin shima inda su Fahad zasu kwana yau tunda an ƙara yawa. Koda ya shigo dubamu da dare kasa haƙuri nayi na rungumesa ina hawaye da jera masa addu'oin gamawa lafiya. Murmushi kawai yay da nuna min lips ɗinsa wai na masa kiss. Na maƙe kafaɗa da faɗin, “No Mammi ta hana sai nayi arba'in biyu”. “Ashe zan gudu dake basu sani ba”. Ya faɗa yana kaiwa zaune. Idanu na waro na ce, “Guduwa fa?”. “Sosai ma kuwa, su gwada su gani. One week kawai gashi na jigata ace har 80days haba kanwa na kawo duniya ma kenan. ALLAH sai dai su nemeki su rasa sace ki zanyi.” Ni dariya ma abin ya bani a raina nace lallai ashe da sabon tsalle. Ko na samu tsarki dole na kama kaina kada mutumin nan ya sani inba hakaba ya buɗe min aiki tsaff da laɓuɓuwar jaririya shi ba damuwarsa bace. A daren akai min ƙunshi da kitso, dan cikin yaran Uncle Sulaiman akwai wadda tai masifar iyawa harda su gyaran jiki. Duk wanda ya kalleni yaga maijego ɗanya jagab. Dan sosai gaskiya jego ya amsheni sai godiyar ALLAH.......✍️ A gurguje Please 🥺 _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ .........Washe gari da safe kowa yasan sunan Baby Ummu-Hidaya, dama hakan dai duk mukai tsammani. Su Yaya Musaddiq da Yaya Hayat da su Fahad sun kasa zaune sun kasa tsaye. Ashe gagarumar walima ake shiryawa batare da mun sani ba. Sai da Hayatu yake sanar mana ya kamata ace duk mu kasance cikin shiri basai anzo ɗaukar mu ba aita wane bai shirya ba wane bai kammala ba. Makeup artist aka kawo min data san aikinta. Wannan kam duk aikin Ummie ne dan da farko Yaya Awwab yaso yin bore tai masa jan ido da faɗa masa kwalliyar ma ba rufin asiri bace tunda tana ɓoye kammanin mutum. A irin wannan taron kowa ke sanin iyalinka idan ma da wani nufi a ransa yay tunanin aiwatarwa, amma idan ya gagara ma riƙe kammani ba shike nan ba. Yin wannan magana sai tasa yay kamar ya ɗan fahimta. Amma dai baice komai ba ya shige ɗaki. Dariya su Fahad sukaita ƙumshewa. Sai da Ummie tace, “ALLAH dai ya baku Sa'a ya jiku kunga ai sai ya huce kanku tunda nidai babu yanda za'ai dani.” Dariya su Mama Balki sukayi, yayinda Fahad da Hafizzullah ɗin suka fice da gudu. Haka dai badan fa yaso ba akai min wannan kwalliya. Ammafa magana ta gaskiya na haɗu ni kaina nasan nayi ƙyau. Kada fa kice na cika kuranta kaina Bily. Gaskiya nake faɗa miki. Bani kaɗai ba hatta Baby ta fito abinta kamar ka saceta ka gudu. Yayinda uban gayyar ya fito kuma sai kowa ya dinga faɗin, “Masha ALLAH Masha ALLAH. Ina ganin ƴammatan nan nata binsa da da ido harda Bibaa. A raina nace kwayi kwa gama in sha ALLAHU mijina yayi kenan. Koma akwai ƙaddarar ƙara auren a garesa bana fatan ace cikin ku ƴan uwansa gara ya auro bare da kowa zai goga sa'arsa. Haka dai Ummie ta tsayar da shi badan yaso ba ta mana hotuna, sai suka samu damar ɗauka suma. Sune suka fara yin gaba, ni da shi zamu taho ƙarshe. Aiko bawan ALLAH na ganin sun fice ya damƙoni ya shanye jambakin da aka samun tas. Fuska na ɗan ɓata da faɗin, “Kai Yaya”. “Kina sake cewa tak ALLAH sai ma na kwashe sauran kwalliyan.” ya faɗa a fusace. Bam na rufe bakina kuwa ban sake magana ba. Shima sai ya ɗau yarinyarsa yana mata wasa ya shareni. Oho, ai bani na kar zomon ba rataya aka bani nima. Haka har akazo ɗaukar mu ni da shi kowa na zumɓurar baki. Haka muka fita yana riƙe da Baby, amma koda mukaje wajen motar sai da ya buɗe min da kansa na shiga ya maida ya rufe da gyara min rigata sannan ya zagaya nasa mazauni inda shima aka buɗe masa ya shiga. A motar ma shareni yay yanata ɗaukar ƴarsa hoto, ashe hoton na wayone duk harda ni a ciki. Bandai tanka masa ba nima na maida hankali akan tawa wayar. Rikicewa nai sanda muka iso naga an cika hall fal da bayin ALLAH. Kai kace a ƙasarmu ta haihuwa muke. Kai Masha ALLAH. Dan waje yayi matuƙar ƙyau da ɗaukar idanu. Mun shigo kowa idonsa a kammu, ALLAH ma ya taimakeni shiga ce a jikina ta muntunci dan shigar cikakkiyar bahaushiya nayi ƴar Nigeria yankin arewa. Haka shima manyan kayane a jikinsa harda babbar riga ga hula kamar ba Maash ɗina ba. An mun gargaɗi yafi ashirin kafin mu shiga akan kada naje ina washe musu baki. Ni sai abun nasa ma ya bani dariya. Mun isa masaukin da aka tanada domin mu, aka fara da buɗe taro da addu'a. Da ga haka aka fara abinda ya zaunar da mutane. Ganin ya ƙi ajiye Babyn a gadon da aka tanadar mata nai masa magana, sai cewa yay shi bazai ajiye yarinyarsa ba a takura mata da ɗauka, yasan kuma kowa da niyyar da yazo wajen aje a masa kidnapping ƴarsa. Ikon ALLAH sai kallo na faɗa a raina. To in ba rigimar Yaya Awwab ba, duk uban securitys da aka zuba a wajen. Ga camaras tako ina, sannan gadon ma a kusa damu yake gab sosai taya wani zaiyi wannan ɗanyen aikin ni Samraah. To amma tunda ya sakama zuciyarsa haka sai na kama kaina kawai. Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain mahaifin Bahijja da wasu manyan malamai ne suka gudanar da wa'azi mai shiga jiki akan tarbiyyar ƴaƴan tun daga rainon cikinsu da rainonsu har kawowar girmansu. Sai lokacin nasan Malam ɗin yazo ashe harda Uncle Sulaiman da Uncle Abdullahi da Baban su Mansoor. Harma da su Mansoor ɗin da Kawu Jafaru. Bayan shi wasu malaman ma sunyi ƴan wasu ƙasashe daban-daban, daga nan aka fara cin abinci. Sosai Baby Ummu-Hidaya tasha addu'oi tare da ƙyaututtuka wajen abokan Babanta da har yau bai taɓa gabatar min da su ba matsayin abokai koni ya gabatar dani garesu matsayin mata. Sai na fahimci shifa komansa da tsari, akwai abinda yake alaƙantawa da aboki akwai wanda baya sakashi a wannan sabgar. Basu kawai ba ma'aikatansa ta fannonin kasuwancinsa daban-daban sun halarci wajen, sun kuma bama Babby gifts sosai kodan faranta ran mahaifinta kamar yanda suma yake faranta musu. Harda mutuniyata Juliet. Yau dai na ɗan sake mata fuska kaɗan kinsan ance mai ɗa wawa. Ansha hotuna sai dai kowa sai dai yazo inda muke ya samemu, kamar yanda ya faɗa kuma bai bar kowa ya ɗauka yarinyar nan ba sai dai a ganta a hannunsa ai mata addu'a. Ai yau dai naga fitina ta Yaya Awwab. Babu kuma damar ayi magana. Koda yake tsoffin nan namu naga sun goya masa baya da abinda yay ɗin. Walima kam sai san barka dan taro ya tashi lafiya. Sai a lokacin ya bama malaman da sukai wa'azi a wajen Babyn suka ɗauka suma. Sun sanya mata albarka tare addu'oi. Sannan suka ɗora da ƙara mana nasiha ni da shi akan tarbiyyarta da rainonta. A gajiye kowa ya koma gida. Sauran baƙi na'a masaukinsu. Wasu kuwa har sun wuce inda suka fito. Tsabar barcin da nake ji wanka ma da ƙyar nayi na kwanta. Koda ya shigo yimana sai da safe ma ni kam na jima a duniyar barci. Sai da Mama balki dake shirya baby Hidaya sukai ya fice. Washe gari muka tashi da ƙananun maganganun mutane da suka cika media, marasa aikin yi a Nigeria da wasu Malam suka dinga sharhi da caccakar al'amarin bikin sunan nan da malaman da sukai lectures wai kwaɗayi ya kawosu. Yayinda wasu suke ganin su basuga abin laifi ba. Maash dai ba aiki yakema gwamnati ba, ba wani muƙami garesa a gwamnatance ba, ba ɗan siyasa ba. Ɗan kasuwa ne da guminsa yake nema kowa ya sani. Ko mi zaiyi da kuɗinsa dan mi za'ai zaman masa sharhi tunda bana wani ya sata ba. Masu satar ma suke abinda suke so balle shi da guminsa ne. Dan kawai yaje wata ƙasa yay bikin sunan ƴarsa da ALLAH yay masa ƙyauta da samunta sai ya zama abin surutu. Kai mutanenmu sai a barsu. Harda masu faɗin almabazzaranci ne. Ga mabuƙata cike da ƙasarsa. Ai duk wanda yasan Maash yasan mutum ne dake taimako wa mutane kan jiki kan ƙarfi. Kuma sanda akai aurensa yayi ne. Sai kuma dan yayi na haihuwa. Kuma a wajen walimar nan ba wani shashanci akai ba, hasalima anyi lectures ne masu amfani ga iyaye, sai abinci da akaci. Abincinne ya tsolema wasu ido dai kenan da kuma mutanen da suka halarci taron. Kai koma dai miye su suka sani. Rai ɓace Fahad da Hafizzullah sukace zasuyi video suma su maida raddi, yayinda Hayatu ya tabbatar da sai ya saka an kama malam nan da masu fashin baƙin. Shi dai uban gayyar banda murmushi ma baice komai ba. Sai mune muka dinga basu haƙuri. Duk da dai nima raina ya sosu gaskiya. Al'amari kamar wasa akaita jan magana har fin kwana uku, wasu har suna ƙirƙirar comedy wai. Tab ɗin ai babu wanda yasan Yaya Awwab ya wuce Nigeria shi da Hayatu. Sai sakamakon abinda ya faru muka samu labari. Sai ga mutanen sun fito suna regretting abinda sukayin. Suka kuma faɗi gaskiyar sakasu akayi. Ashe wani abokin Maash ɗin ne ɗan tsohon shugaban kasa, kuma har taron ma fa yazo harda yima Hidaya ƙyauta ya biyasu suyi. Lallai yanzu ne na fahimci zancen Yaya Awwab ɗin na ranar walimar akan ƙin ajiye Baby. Idan ka kallesa a fuska bazakace zai aikata ba wlhy. Wannan bayyanar gaskiya yasa sabon zance sake tashi, ashe dai su maƙiya basa ƙarewa. An gama da batun su Prof da su Hajiya ƙarama dake can asibiti har yanzu tana fama da kanta jiki duk ya ruɓe ko inda take wani baya son zuwa. Ga Commondo da shima dai al'amarin nasa sai a hankali sai kuma ga wani shegen ya fito. Kuma tabbas akwai ire-iren sa da yawa damu bamu sani ba kuma suna a manne da mu ɗin. Wasu ma suna cine daga taskar sa. Haka rayuwa take, dama dole ne ka saka a ranka idan fa kama mutum alkairi a wannan rayuwar yanzu. Ɗayan biyu ne. Kodai ya amsa daga gareka d ƙyaƙyƙyawar zuciya ya gode maka da maka addu'a ya kasance na ƙwarai a gareka. Ko kuma ya kasance mai maka hassada da ya dinga raina alkhairinka garesa da ganin ya cutar da kai ta hanyar da zai mallaki fiye da abinda kake bashi, zaima iya haɗe kai da wasu a cutar da kai, ko ya dinga kusheka da aibantaka da munanaka a wajen wasu mutane. Ko ya gagara kareka a wajen masu aibantaka, da ance ga alkairinka yace ba haka bane ba. Shiyayasa muyi fatan ALLAH ya haɗamu da abokan huɗɗa masu sonmu domin ALLAH da zuciya ɗaya. ALLAH ka hana duk wani mai manufa a kammu raɓarmu ko jingina jikin shingen alfarmar dakai mana. ALLAH ka bamu ikon zama da kowa da zuciya ɗaya, ka hanamu cutar da su ko jingina jikin alfarmar da kai musu da mummunar manufa, ka hanasu damar cutar damu suma. Kwanansu biyu suka dawo, ƴan suna suka fara shirin komawa. Babu mai bani dariya da mamaki a wannan tawagar irin Mom. Haka zakiga tanata zagaye gidan nan tana kallo wani lokacin harda hawaye. Idan ko Yaya Awwab ya shigo ko taga yanda kowa ke bani kulawa sai ta tashi ta koma tsakar gida ta zauna. Daga baya na fahimci har yanzu tana wannan aman jinin musamman idan tayi tari. Haka naima Yaya Musaddiq magana ya ɗauketa suka kai asibiti aka dubata. An tabbatar musu zuciyarta ce ta yaɓu, idan kuma bata sassautama kanta ba to lallai tana gab da rasa ranta. Dan a yanzu haka ma sai an mata aiki a zuciyar dan ta samu matsala sosai. Sai dai kafin hakan sun bata magunguna na wata uku taje ta sha kafin ayi aikin. Da wannan suka wuce akan idan lokaci yayi za'a dawo da ita........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ ......Anan aka bar min Gwaggo Gudidi da auta, sai yarinyar Uncle Sulaiman ɗaya mai suna Fatima. Sai Mammi da zata ɗan kwana mana biyu itama dan zataga likita akan ciwon ƙashi dake damunta. Haka suka wuce suka barmu da kewa ana fatan kuma sai Bahijja ko Ruƙayya wani ya haihuwa a haɗu a Nigeria. Harda kukana dan nazata Ummie zatace tunda anyi suna muje can na ƙarasa wanka. Amma saita lallasheni nayi haƙuri uban tutsun ya hana. Dan itama taso hakan amma Paah yace ta barshi da matarsa tunda baya son na taho. Shine aka yanke shawarar bar min su Gwaggo Gudidi ɗin. Kasancewar Auta ya gama primary sai kawai na yanke shawarar sakashi makaranta anan. Dan in sha ALLAHU yazo kenan. Gara koshi Abba ya mora a cikin yaƴan Mom dai. Ban sha wahala ga Yaya Awwab ba. Dan ina sanar masa manufata akan auta ya bani goyon baya ɗari bisa ɗari, tare da sake min albishir ɗin suna gab da sanin inda mijin Baby yake. Dan tunda ya amsa sunansa a wajen su Abba yake ta bincike ta ƙarƙashin ƙasa. Saboda al'amarin sai da taka tsantsan, ƙungiyar da mutum yake babbar ƙungiyace ta ƴan luwaɗi, sannan sunada ƙarfi matuƙa da fito-na-fito da su ba ƙaramin abu bane. Wannan bayani nasa ya tayar min da hankali matuƙa, dan sai da nai kuka sosai ina mai taya ƴar Uwata da addu'ar ALLAH ya ƙwatota daga wannan makaunuyar ƙaddara da kwaɗayin abin duniya da son wuce wani ya jawo mata. Rayuwa ta cigaba da tafiya bisa ƙaddarorin dake rubuce a cikin littafin mu da alƙalaminsa baya ƙarya ko kuskure. Sosai Gwaggo Gudidi da Mammi ke kulawa da ni da Heedaya. Gyara suke min na haƙiƙa irin na tsoffi, nima kuma ina nawa dabarun a gefe da aunty Halime tazo min da su. A haka cikin amincin ALLAH mukayi arba'in. Yaya Awwab dai yayi haƙuri sosai a wannan gaɓar. Irin haƙurin da banyi zato ko tsammanin zai yi ba. Kodan aikin da yake ne ya ɗauke hankalinsa oho. Sannan yayi ƴan tafiye-tafiye dan har wajen su Yaya Musaddiq yaje yay kusan one week. Sannan yaje Nigeria ma. A dawowar ne ma nake jin batun mutuwar Hajiya ƙarama. Dan su Ummie duk da muna waya babu wanda ya taɓa sanar min. Ko basu sani bane oho. Washe garin da mukai arba'in ya dawo daga tafiyar kwana biyu da yayi, ranar dai kam ban tsallake ba a hannunsa. Dan murje idanu yay yama sauka a ɗakina ta yanda dole Gwaggo Gudidi ta janye jikinta. Aikam nako ji a jikina sosai. Dan sai da na dawo ina wayyo-wayyo na wahala. Ko tausayi babu ya ce ai yana kan sani yay duk abinda yayi, nima banji tausayinsa ba ai duk da nasan yana cikin wani hali na biyema su Mammi. Gobe ma na sake masa makamancin wannan horon. Baki kawai na tura masa bance komai ba. Ya fita yana dariya. Sati biyu da yin arba'in ɗina Bahijja tai ɓari. Tsabar Fahad baya ji haka ya kiramu yana rusar kuka wai ya rasa Babynsa. Kai al'amarin Fahad sai shi. Mudai mun jajanta tare da kwantar masa da hankalin ALLAH zai bada wani rayayye. Wannan ɓari sai da suka saka Ummie zuwa Spain dole. Satinta biyu acan ta biyo tanan wajenmu ganin takwararta. Kwana huɗu tai mana tai shirin wucewa. Aiko su Gwaggo sukace ƙafarta ƙafarsu. Babu kalar lallaɓawar da bamu musu ba musamman Mammi amma sukace ina su wannan zaman takura bada su ba. A gida sun saba shiga maƙwafta, barkar haihuwa, gaisuwar mutuwa da bakin aure da ziyarar dangi. Amma anan saika sati ma bakaga rana ba sai idan an fita damune sannan. Ya muka iya, haka Ummie ta wuce da su bayan Yaya Awwab ya haɗa musu shatara ta arziƙi. Aka barmu da Fateema da Auta. Wucewar tasu babu jimawa Fahad da Hafizzullah da Bahijja suka zo mana hutu. Zuwan nasu ya mana daɗi, nan fa Hafizzullah da Fateema aka ɗin ke. Tun bamu fahimta ba Bahijja ta tona. Nayi murna da hakan, dan al'amarin nasu zaiyi dai-dai insha ALLAHU. Itama dai Fateeman ba wata babba bace, yanzu ne ma ake nema mata makaranta anan dan ta kammala secondary a Nigeria. Shima Yaya Awwab da yaji yayi murna matuƙa, sai dai ya kiransu ya musu nasiha da tabbatar musu da ba yanzu ba sai shi Hafizzullah ya gama school sannan. Ita ko bata kammala ba ta idasa a gidansa. Hakan yama kowa, na kuma bisu da fatan alkairi. Suma satinsu uku suka koma inda suka fito. Haka rayuwar ta cigaba da gangarawa har ga Baby Heedaya da watanni takwas a duniya. Tayi ƙyau abinta kamanninta da mahaifinta da kakarta sun sake bayyana. Idan ka ganta sai ka ɗauka ma bani na haifeta ba. Dan sam bamu kamanni tako ina sai dai kawai ace dan jini. Tana rarrafenta ko ina, idan ma ta kama wani abu takan miƙe tana tafiya a haka. Amma ita kaɗai dai kota miƙe takan koma ta zube ne. Alhamdullah tana da wata goma ta miƙe, babanta daɗi kamar ya cija kansa. Ni harma mamakinsa nake akan soyayyar da yakema yarinyar nan. Idan yana mata wani abun nakan zauna ne kawai ina kallonsu. Sai na dinga jin kewar namu iyayen muma. Har kuka nakanyi watarana. Ai tunda ta cika wata na goma sha ɗaya ya fara tsirar yawo damu ƙasashe. Mune nan yau, mune can gobe kamar ƴan sama jannati. Idan nai magana yace gwara muyi yanzu dan da Heedaya ta isa shiga makaranta yawo ya ƙare. Amma yanzu muna da damar da zai zagaya da ni naga duniya nima. Da wannan sharhin nashi dole nake jan bakina nayi shiru. A wannan tsakanin ne Rukyn Yaya Musaddiq ta haihu, sai dai su sun koma Nigeria ne. Dole muma muka shirya muka nufi Nigeria. Tarba muka samu ta musamman a wajen Ummie da Mama Balki. Tuni an gyara mana sashenmu tsaf. Paah na maƙale da ƴar jikarsa. Sosai yake nunama Heedaya soyayya, dan yakance kama take da matarsa Ummie komai nata kamar ƙuruciyarta. Dan haka son da yake mata na musamman ne. Ummie dai takanyi dariya muma hakan. Kwanan mu biyu a Lagos muka wuce Kano. Nan kuma fa aka haɗu da ƴan uwa da abokan arziki. Rayuwa kenan, a yanzu kowa so yake mana bana wasa ba. Kowa so yake ma ace yana mu'amula da mu daga cikin ƴan uwa har ƙawaye. Babyn Yaya Musaddiq yaci sunan Babanmu, wato Abdul-wahab. Ban tsaya sanya ba a wannan suna na kishi kuɗi matuƙa. Dan bikin suna mukayi na nunama sa'a da ya sake birkice Mom da komai ya lalace mata. Ga Bibaa ta zame mata ƙarfen ƙafa yarinya bata jin magana sam. Dan washe garin sunan Abdull sai da Hafizzullah ya zaneta saboda yanda take zagin Mom dan ta mata faɗan yawo. Mukam sai abun ma ya girmemu. Yaya Abbas shaye-shaye har baya gane kansa. Dan haka mukai meeting akan kaisa Rihab ko za'a dace. Abba yay ta kuka yana sake neman gafararmu da sanya albarka. Muko mukace dan ALLAH ya daina bamu haƙurin nan haka mu komai fa ya wuce a garemu in sha ALLAHU. Kwana biyu da sunan mukai ziyarar dangi, mune har Gwarzo. Dole badan Yaya Awwab yaso ba yabar Ummie ta cika mana alƙawarinmu. Dan kuwa sati guda yace miyo. Farin ciki mukai sosai musamman ma Aunty Falaq da dama babban birinta kenan. Wannan ɗan hutu a gwarzo ya saka mu farin ciki matuƙa, dan mun zagaya dangi har cikin wasu ƙauyukan dake ƙasanmu da dangi ke rayuwa a can. Mun baza alkairi sosai inda muke ta samun sambarka da albarka da addu'oi wa mahaifanmu. Dan hatta abokan mahaifinmu na ƙuruciya bamu bari ba. Kowa ya samu alkairi daga garemu gwargwadon iko. Muma kuma da zamu taho sun haɗa mana tsaraba taban mamaki. Dan motocin da akaje ɗaukarmu banda biyun da aka barmu dasu dama saboda zuwa yanzu daga ni har Aunty Falaq kowa na murza tasa. Koda yake dama ita tana da mota, nice dai sai yanzu ALLAH yayi. Mun dawo Gwarzo da kwanaki uku muka sake komawa Lagos. Daga can kuma muka fara shirye-shiryen komawa inda muka fito. Amma sai Ummie tace ko zamuyi haƙuri kawai tunda ga bikin su Azizat ɗin Hajiya Mammah na tunkarowa. Dan baifi saura sati biyu ba. Kuma dai ya kamata ace mun halarta ai. Duk mun gamsu da hakan, amma mun roƙeta taima su Yaya Awwab ɗin magana da kanta. Musamman ma ni da nasan halin tutsun nawa. Ashe dai a hakan ma ba tsira nayi ba. Dan da daddare kamar yanda muka saba naga har zan kwanta bai kirani ba. Sai na sauke nawa jin kan ni na ɗaga wayar na kirashi. Kira biyu bai ɗaga ba. Sai nai tunanin ko yana wani uzirin ne idan ya kammala zai kirani. Amma mi har barci ya ɗaukeni shiru kake ji. Ina farkawa da asuba wayata na fara dubawa. Sai dai babu ko text message balle miss call. Haka nayi salla sukuku, bayan na idar nai azkar. Kasancewar mu muke haɗa break fast tunda mukazo muka hutar da su Ummie sai na tashi na fita zuwa kitchen.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ .......Muna aiki ina yawan kallon waya. Har dai Aunty Falaq ta kasa haƙuri ta magantu. Shine nace mata babu komai. Da ga ita dai har Bahijja basu gamsu ba. Sai da aikin namu yay nisa ne Bahijja ke cemana mu bata shawara. Tun jiya Fahad ke mata masifa akan zaman yin bikin nan. Yace shi bikin suna kawai ya turota ba zuwa biki ba. Iya haƙuri ta bashi da masa bayanin muma fa har damu amma yaƙi saurarenta daga ƙarshe ma ya kashe mata waya. Tuni hankalina ya tashi, dan tabbas nima kuwa inaga akan wannan matsalar ce nawa gwaskan ke shareni. To amma mu manya ne ai, sai na danne komai a raina muka shiga bata shawarar data nema. Gashi baiwar ALLAH tana fama da ɗan laulayin cikinta. Kai maza dai duk sai a barsu halinsu ɗaya wlhy. Harna koma sashenmu nai wanka na kimtsa dan a babban kitchen muke aikin na dawo bai kira ba. Heedaya dama tana wajen Mama Balki ne da Ummie ko Mammi, idan kin ganta a wajena tofa feeding ɗinta zanyi, da yake ma ta gado uban nata rashin damuwa da abinci sai na yini bata damu ba. Amma a hakan nace a yayata ya hauni da tujara wai karma ma nayi koda kwatance. Sai yarinyarsa tayi two years cif sannan. Ranar dan takaicinsu shi da ƴar har jinai hawaye sun cikan ido. Har muka gama break fast babu Yaya Awwab babu dalilinsa. Dole na zare jikina na koma sashenmu kamar zanyi wani aiki na sake kiransa. Yanzun ma ƙin ɗagawa yay, dan haka nai alƙawarin zanyi kiran ƙarshe. Idan yaƙi ya ɗaga ALLAH na barsa kenan. Yo ina dalili, naga dai bikin danginsa ne. Sannan Ummie tace mu tsaya ai bamu muka nema ba. Amma yake neman ɗaura min jakar tsaba. To na dai yi sa'a ya ɗaga, amma sai wani faman shashashan ƙamshi yake da tsuke fuska da yake video call na masa. Dan shi yafi son kira haka. Gaisuwar ma ciki-ciki ya amsa min daga haka yaja bakinsa yay shiru. Sai na daure na tambayesa ko baida lafiya ne. A gadarance ya ce, kin damu da hakan ne? Look Samrh kin san bana san raunin wayo, bikin suna na turoki yi, aka tilastani kikai tafiyar da ban niyya ba nai haƙuri na barki. Shine yanzu kuka sake tsarama Ummie magana ko. To ni bazance komai ba. Amma zaɓi ya rage naki, jibi Hafizzullah zai taho min da yarinyata, idan kin gadama kiyita zama ke kuma. Fateema da Mahaboob zasu dawo suma na barki lafiya”. Ya yanke kiran ƙitt. Shiru kawai nayi ina kallon wayar kamar mai son ganin ainahin cikinta. Kafin naji wasu hawaye masu zafi sun gangaro min. Dan ALLAH minene laifinmu anan Bily, wlhy halin maza na ban takaici. Su dai kawai abinda suka so shine dai-dai. Ga kuma gaskiya sai su taketa kai a ɗora maka laifi. Miyyasa da Ummien ta kirasu duk basu nuna mata basu amince ba. Sai su komo ta bayan fage mu suna ƙuntata ma. Dan dai mune kuka masu daɗin hawa. Cikin ɓacin rai na tashi na hau haɗa kaya. Sai da na gama tsaf na fita zuwa wajen Ummie. Cikin danne ɓacin raina nai mata bayanin abinda ya faru harma na Fahad da Bahijja. Ai bama ta bari nakai ƙarshe ba tai kiransu ta haɗa har Yaya Hayatu da bai ce komai ba ta zage tas. Ta kuma ce ba zamu koma ɗin ba sai anyi bikin, suma tana buƙatar gannin kowannensu a Niger ranar ɗaurin aure. Idan ba hakaba ransu zai fi haka ɓaci. Tofa Ummie ta ɓaro aiki. Dan daga wannan faɗa mu duka ukun suka ɗauke mana wuta. Muma sai muka haɗe namu kan kamar yanda Ummien ta bamu shawara muka tattarasu muka watsar. Haka muka cigaba da hutawarmu a Nigeria. Tun biki na sauran sati ɗaya Aunty Mama ta iso. Sai kawai Ummie tace mu shirya mu bita kawai suma zasu same mu. Haka kuwa akayi muka shirya mukabi Aunty Mama. Kasancewar jirgin dare muka bi mun isa batare da mun ƙaras da komai ba. An dai zo an ɗauke mu. Hajiya Mammah dama tana can one week kenan. Duk da saukar dare mukai na fahimci mahaifin su Azizat shima na da ɗan halinsa gwargwadon iko. Dan mai rufin asiri ne ba talaka tiɓis ba. Matansa biyu yanzu da ƴaƴa kusan goma sha uku harda su Azizat ɗin. Gidansu nada girma babu laifi. Azizat dai nata ɗan nuna kamar jin nauyin mu, da alama har yanzu wancan abun daya faru na a ranta. Mudai duk muka basar kamar bamu fahimceta ba harta gaji ta saki jikinta. Kwanan mu biyu su Malika suka iso suma da su Ummie. Kasancewar Ummie ta saka hannu sosai a bikin ita da su Aunty Mama bikin an masa shiri na musamman gaskiya fiye da ƙarfin mahaifinsu. Gashi kuma mijin da Azizat ɗin zata aura ɗan gidan sarauta ne. Sai kuma kasancewarmu ya sake kambama komai da armashi. Tun ana saura kwanaki uku ɗaurin aure aka fara bikin al'adunsu na buzaye daban-daban da suka matuƙar ƙayatar damu. Aiko Malika itama ta samo nata. Tana dojewa tana dojewa muka sakata a layi. Tuni ta bi suka ɗinke kuwa. Ranar ɗaurin aure babu zato babu tsammani sai ga Yaya Awwab, Fahad, Yaya Hayatu, yaya Musaddiq, harda su Mansoor da Dad ɗin su da Uncle Sulaiman sai Abba da Uncle Abdullahi. Tofa nan aka fara kallon kallo, musamman mu masu laifi a wajen mazan namu. Bahijja nata ɓakyatun tsoro muka dakar da ita. Muka ciskule muma kamar bamu san ina suka dosa ba. Dama ni rabona da waya da nawa gogan tun ranar da yace zai aiko a ɗauki su Heedaya. Yau kam sai yay kamar bai ganni ba. Yana manne dai da ƴarsa yana mata murmushi da wasa. Itako tana faman ɓangale baki dan akwai sabo a tsakaninsu kam da shaƙuwa mai inganci. A yanzu haka bata iya cewa komai ba sai Dadaa. Dadaa dai Dadaa dai iya maganar kenan. Da dare aka shirya zuwa dinner, anan ne kam dole suka tafi tare da mu. Dinner tayi ƙyau sosai, sunyi bajinta dangin ango suma. An gabatar damu a matsayin dangin mahaifiyar su, dan haka muka buɗe bakunan bags muka zuba liƙi muka fiddasu kunya. Daga nan za'a wuce da amare ɗakinsu. Dan su biyar ne cif. Akwai sauran ƙannensu da suke uba ɗaya suma. Kawai sai me bawan ALLAH ya gudu da ni hotel. Hankalina ya tashi dan na zata inda har su Paah da su Abba suke ne. Sai na samu ashe wani yaje ya kama ba inda akai musu masauki ba. Dana dage banzan shiga ba ɗaukata yay camak yay ciki dani, a ɗakin kuma ya hanani ƙwaƙwƙwaran motsi sai da yay min biji-biji da har sai da nayi kuka. Dan dole na shiga ruwan zafi sosai inajin kamar na masa ALLAH ya isa a zuciyata na dai danne. Koda ba fito daga bayin ban kulashi ba na hau shirin komawa can gidan, dan nasan dai an riga an kai amare yanzu. Amma sai ya ƙi kulani ma yamayi kwanciyarsa. Dama Heedaya na wajen Ummie. Kuka na fara masa amma ya shareni, haka dole na haƙura muka kwana anan. Washe garin ma bai maida ni ba sai yamma lis. Na je su Aunty Falaq suka tasani gaba da tsokana. Sai da nai musu bore suka barni. A daren ranar shi da tawagarsa suka bar ƙasar, mu kuma muka ƙarasa shagalin bikin washen gari. Sai lokacin nake jin ashe an maida auren Hajiya Mammah ɗin da Baban su Azizat jiya. Na tayasu murna gaskiya. Dan rabuwar kan iyaye damuwace. Muma a cikon kwana uku da gama biki muka koma Nigeria. Babu zama Ummie tai mana shirin na musamman bayan kwana biyu kowacce ta nufi mijinta. Mukaje kowacce kuma ta tadda nata sabon ɓacin rai. Da dai aka hau saman kuma sai aka dawo aka shirya kamar komai bai faru ba. Lamarin mata da miji sai ALLAH ai daman. ALLAH ya ƙara mana haƙurin zama da juna.. A wannan yanin ne kuma wani gagarumin cigaba ya tasoma Yaya Awwab. Planing ne na tsawon shekaru da yake yi sai yanzu ALLAH ya kawo iyaka. Haka ya kwashemu zuwa ƙasar saudia. Watanmu biyu a can har su Ummie suka zo suma suka samemu akai shagalin tare da su. Bayan munyi aikin Hajji muka wuce da su Dubai. Can ma zasu kwana biyu dan Paah na can yana wani aiki shima. A wannan ɗan tsakanin aka saka bikin Bibaa. Zuwa Nigeria ya kamamu dole kenan. Dama shi Yaya Musaddiq bai koma China ba tun haihuwar Aunty Ruƙayya. Akwai abinda yake yi mai muhimmanci a Nigeria ɗin sai ya kammala zasu koma dan yanzu ya kammala karatun nasa sai wasu courses da zai yi sai kuma Business da Yaya Awwab ya ɗaurashi a kai. Dan yanzu Yaya Musaddiq ɗin bana da bane ba. Ya zama komai Alhmdllh, ba nauyin iyalinsa kawai ba na ƴan uwa da yawa ma yanzu a kansa yake. Dai-dai gwargwado yana kamantawa. Sannan komai na gidan Abba yanzu ya koma kansa. Ya zama tauraro uba a cikin zuri'armu.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ ......Hidimar bikin Bibaa yayi dai-dai da haihuwar Bahijja da kuma sake haihuwar Aunty Falaq. Ta sake sulluɓo mana baby boy, yayinda Bahijja tai baby girl itama. Haka fa muka rankaya sai Nigeria. Sai da aka fara shan shagalin suna a Lagos da kusan sati ɗaya mun gyagije gajiya sannan muka ɗunguma zuwa Kano harda masu jegon. Sosai Mom bata da lafiya. Dan komai na fanin uwa Aunty Halime kema Bibaa, fannin Uba Yaya Musaddiq duk da Mom ɗin da Bibaa ɗin na nuna basa ra'ayin hakan. Babu wanda yabi takan su dan al'amarin Mom na bama kowa tsoro. Matar nada taurin zuciya matuƙa da girmama ƙiyayya. Ita har yanzu taƙi yarda nagaba yayi gaba fa. Muna isa muka sake maida biki namu dole kuma aka sakar mana. To itama dai mijin Bibaa ɗin sai a hankali. Dan ɗan kwalta ne irinta acan suka haɗu a tazubar ɗin su. Saboda a yanzu kam tsiyar da Bibaa ke tsulawa tacema Baby bata iya komai ba a sanda tai nata yayin. To koma dai miye tunda sun zaɓi zaman aure ai sai a taya musu suje can su ƙarata. Haka dai aka ɗaura aure muka sha dinner ta ƴan kwalta. Ango da kansa ya wuce da amarya gidansa. Mu sai muka koma gida. Sai washe gari mukaga gidan amarya. Gida dai na haya ne kuma ita ta kama da kanta. Kayan cikinsa kuma mune muka zuba su. Dama kuma bai mata lefe ba. ALLAH na tuba sadakin ma da yaya. To mudai munyi walima muka kamo gabanmu. Inda a daren Yaya Awwab ya kirani da sabon tashin hankali ko farin ciki zamu ce oho. Ya tabbatar min an gano inda mijin Baby yake. Ya kuma fahimci an ganosa yanzu haka ya sami issues mai ƙarfi cewar ya ɗakko Baby ya taho Nigeria da ita. Dan haka koda yaushe zamu iya ganinsu. Rasa dawa zanyi maganar nai. Sai kawai naja bakina nai shiru. Amma gaba ɗaya na kasa zaune na kasa tsaye nikam. Har safiyar washe gari kunnena a waje. Dan muna gidan Abba ɗin har yanzu. Dangi ma na Gwarzo duk basu wuce ba dan yanzu suna da ƴancinsu a gidan. Kwatsam bayan sallar la'asar mukaji hayaniya da iface-iface a cikin layi. Tun muna tunanin daga ina har dai muka fahimci anan gab da mune. Sai ga Hafizzullah ya shigo da gudu ya ɗauki taɓarya zai fita. Riƙeshi mukai muna tuhumarsa. Shiko yana fiffisgewa cikin fushi da faɗin mu sakesa. Wlhy da hannunsa zai kashe mutumin can. Tashi hankalinmu yay matuƙa dan bamu san wane mutum bane. Da ƙyar muka turashi ɗakinsa muka rufe. Yanata faman jijjiga ƙofa yana kuka da mana magiyar mu buɗesa. Bamu buɗesan ba mundai fita muma. Sai muka samu matasan anguwa sun ma wani jina-jina a kwance da alama ma baya numfashi sam. Tacan cefe ɗaya kamar mutum a kwance an lulluɓe da abu. Ga wari babu daɗi masu kallo nata toshe hanci. Wasu ma na kuka. Furucin makwafciyarmu da fasa kukan Baby data ambata yasa mukai wajen. Jikin Mom da itama ta taƙarƙara ta fito har ɓari yake wajen yaye mayafin da aka sakama Baby. Ai sai ta fasa gigitacciyar ƙara kawai ta zube a wajen sumammiya. Hankalinmu ya sake tashi muma dai muka isa wajen. Tabbas Baby ce kuwa ta rame matuƙa tamkar skeleton, sai idanu ɓulu-ɓulu babu ƙyan gani. Jikinta duk wasu irin ƙuraje, abin tashin hankali tsutsotsi sunata fitowa ta kamar bayanta. Ai dole aka maidata aka lulluɓe da sauri. Dai-dai nan jami'an tsaro suka zo. Mutumin da akaima kaca-kaca da jini suka ɗauka. Sai lokacin naji wasu na faɗin ai mijin Baby ɗinne. Kuma da alama ya mutu ma. Ashe zuwa yay kawai babu tausayi babu imani ya jefar da ita a ƙofar gidan tare da wurga uban kudi a kanta zai taka mota ya tafi matasan anguwa suka riƙeshi. Akaje wani shago akai kiran Hafizzullah. Ai yana zuwa yaga Baby da bayanin da akai masa ya kama jibgarsa. To yanzu Hafizzullah ɗin bana da bane. Ya zama cikakken saurayi ga ƙarfe yana ɗagawa duk ya wani buɗe. Ganin irin dukan da yake masa suma matasan anguwa suka tayashi. Ganin haka ya shiga ɗakko taɓarya wai sai kwankwatsesa. Shine fa har muka farga. Ana barin wajen da shi Hafizzullah ɗin na fitowa da alama ɓalle ƙofar yayi. Da ƙyar aka daddanesa ana bashi haƙuri da tabbatar masa ƴan sanda sun ɗaukesa da alama ma ya mutu. ALLAH sarki ɗan uwa, sai kawai ya zube a wajen yana kuka kamar yanda yaga munayi. A haka Abba da Yaya Musaddiq da aka kira a waya suka iso. Sai shima Abba kawai ya shiga kukan jikinsa na rawa har yana neman faɗuwa. ALLAH dai ya kiyaye Yaya Musaddiq ya riƙeshi. Ganin mutane nata sake cika wajen aka shiga da Mom da Baby da ke bin mutane kawai da idanu. Babu wanda zai san Baby a baya ya yarda itace wannan a yanzu. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Ya rabbi kasa mu gama da rayuwa lafiya. An sakama Mom ruwa ta farfaɗo, yayinda dole aka rufe gida fa aka hana kowa shigowa. Kuka Mom take na fitar hankali daban tausayi. Faɗi take ta cuci kanta, bazata yafema mutumin nan ba. Ummanta ta cuceta, ta zalunceta data ɗaurata akan wannan mummunar rayuwa. Ita inama ta mutu ta huta. Tana wannan sambatun akaga Baby dake hawaye itama na ƙoƙarin yin magana. Dole aka shiru tare da tsawatar ma Mom domin saurarenta. Dan Muryar bata fita da ƙyau. Cikin jan numfashi da ƙyar irin na mai kuka ta ce, “Mom ba Umma ce ta cutar da ke ba kece kika cutar da kanki sannan muma kika cutar damu. Dan ko tantama banayi alhakin su Samraah ne da Abba ke bibiyarmu. Kin sha sakama Abba kayan asiri a gaban idonmu cikin abinci ko ruwa ko ƙofar shigowa gida amma bamu taɓa sanar masa ko hanaki ba domin bama mahaifinmu kariya. Kin sha yima su Yaya Musaddiq asiri dan su koma ƙasan mu. Kin sa Abba ya cinye dukiyarsu ta gado, dan hatta gidan nan da muke ciki ainahin gidansu kika saka ya sayar ya siyamana wannan. Kin hana Abba ya sakasu a makaranta mai ƙyau. Shi Yaya Musaddiq ma daga secondary bai cigaba ba. Kullum fatanki ALLAH ya bama Samraah mijin da zai wahalar da ita, talaka, hatsabibi shaiɗani koma a mata cikin shege a titi. Kina hanasu abinci, duk wanda yazo domin taimakonsu sai kin rabashi da gidan nan. Daga ƙarshe ƙwaɗayinki ya sakaki haɗani aure da wannan mitumin da sam baya jin tsoron ALLAH. Tun a zuwan farko kuka baɗesa da asiri ke da Umma wai a riƙeshi da ƙyau saboda ya muku alƙawarin zuwa Saudiyya. Bakuyi bincike a kansa ba kuka hana Abba yayi kika aura min shi kuna murna. Ga sakamakon hakannan, ya kaini wata ƙasa yana luwaɗi da ni, abokansa nayi. Idan ban yarda ba su dakeni su ɗauri suyi ta ƙarfin tsiya. Ba kuma mutum ɗaya ba su da yawa. Wani lokacin har suma nake dan wala suna ciyar dani abinci mara ƙyau. Suna shan magani domin kare kansu daga cututtuka amma ni basa bani. A haka na fara ciwo. Yau wannan gobe wancan har aka tabbatar musu da na kamu da ƙanjamau da ciwon hanta dana ƙoda. Hakan ma kamar daɗi yay musu. Sai suka daina min komai suna saka karnukansu nayi da ni a madadinsu......” kuka sosai ya sarƙeta. Muma kukan mukeyi, sai da tayi sosai ta cigaba da faɗin, haka zasu ɗaureni subama karnuka ni suyi amfani dani, har ciwon jikina ya fara bayyana ƙuraje suka fara fitomin. Ga tsutsotsi ta gabana da bayana. Shine yace zai maidoni gida dan ya bama iyayena kuɗin da suke ƙwaɗayi a wajensa gasu ya samu dani fiye da yanda yay fata. Dan burinsa ya cika na mallakar kuɗaɗe masu nauyi, samoni ya zame masa alkairi har an bashi muƙami a ƙungiya. Mom ki dubeni, miya rage mun, mi kuma ya rage banda jiran ranar mutuwa ta. Ni kaina nafi son na Mutu, bana son wannan duniyar Mom bana son ta. Inama ace baya zata dawo, dana goge abubuwa da yawa a rayuwata. Inama ace nice ke Samraah. Gaki nan kinyi aurenki, da alama ma har kin haihu dan Babyn hannunki na kama da Maash sosai. Babban tashin hankali na ƙilama makomata wutace, dan faɗar ALLAH ce wutar masu aikata abinda akai shekara kusan biyu anayi dani daban take. Kaicon na, kaiconki Mom, kaico da samun uwa irinki Mom. ALLAH ya isa tsakanina da ke bazan yafe miki ba ke da mahaifiyarki. Indai inada hakki a kanku ALLAH yay gaggawar saka min......” Kuka ya sake sarƙeta. Yayinda Mom damu duk muke kukan, sai dai tari ya sarƙe Mom ɗin ta fara aman jini. Tun yana fita iya baki ya koma harta hanci. Sai kuma al'amari ya rikice. Ai babu shiri aka kwashesu ita da Baby ɗin sai asibiti. Da ƙyar aka amshi baby, dan gaskiya al'amarin ta akwai tashin hankali ga duk mai imani. Ai dole shima Abba aka bashi gado. Muna cikin wannan tashin hankalin kuma sai ga jami'an tsaro wai sunzo kama Hafizzullah ance shine ya kashe mijin Baby ɗin. Sake tashi hankalinmu yayi, shiko ko gezau ya bisu yana kuma tabbatar musu ko yanzu aka kawo gawar mijin Baby gabansa sai ya sake mata raga-raga.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ .......Hankalinmu ya kasu kaso biyu. Ga Hafizzullah a station ga Mom ga Baby ga kuma Abba duk a asibiti. ALLAH dai ya taimakemu Yaya Awwab ya iso ƙasar a ranar. Ai jikinsa kawai na faɗa ina kuka. Ya rungumeni yana lallashi ta sigar shafa min bayana. Mun jima a haka kafin ya shiga ɗakin da Abba yake. Yafi mintuna talatin sannan ya fito. Shi da Yaya Musaddiq da Yaya Hayatu sai wani da ban sani ba suka fita. Kusan awa guda suka sake dawowa da police suka shiga ɗakin da Baby take. Sun ɗan jima suka sake dai fitowa. Mudai duk bamu san abinda ke faruwa ba. Dan har aka turo driver ya maidamu gida basu sake dawowa ba. Badan mun so ba muka koma, sai dai ba gidan Abba ba. Kusan sha biyu na dare ina zaune wanka ma na kasa na zuba tagumi Heedaya data gaji da tsalle-tsalenta tai barci na gefena ita da Awwab baban nasu ya shigo. Da sauri na miƙe ina hawaye da tambayarsa ina Hafiz?. Maimakon amsa min sai kawai ya jawoni jikinsa ya rungume tsam. Kuka na sake fashemasa da shi. A hankali ya fara hura min iska a kunnena, sai kuma cikin raɗa ya furta, “Calm down My Tiger. Mun amsoshi gashi can ma yana cin abinci wajen Falaq. Kema kin san ina gari, Musaddiq na nan, ga Hayatu bazamu bar Auta ya kwana can ba. Balle ma Yayansa Fahad ya iso yaje ya gwada musu halin nasa saboda harkar law ya karanta aikin ne kawai baida ra'ayin yi. Ko a wata ƙasa aka kama Hafiz sai ya kwana gidansu balle Nigeria ma kasarmu da muke da dukkan alfarma da karfi. Ni abinda yay min yayi dai-dai an rage mugun irin dan mutumin nan in ba kashesan akai ba yanda ya yaddata yay niyyar guduwa wani wajen zai sake tafiya ya yaudari wata itama yaje yayo mata hakan ya dawo da ita. ALLAH dai ya kare mana zuri'a. Kuɗi sun sa komai bawa na wannan zamanin zai iya aikatawa, sannan mata da yawa suna jefa kansu a irin wannan rayuwar saboda kwaɗayin auren mai kuɗi. Kaga mace tana maka tallan kanta babu kunya babu tsoron ALLAH a tattare da ita. Basu san dukiya daban ba, ƙyaƙyƙyawar rayuwa daban. Sannan ba kowace dukiya bace ke zama farin ciki”. “Hakane Yaya Awwab. Dukiya kam ta zame mana fitina a wannan ƙarnin, ga Mom nan ta jefa rayuwar Baby a masifa da har abada tabonta bazai gogu ba. Haka kuma zatai ta kallon al'amarin da ita ta jefata saboda itace ta kawo mata mijin. Sannan suka tausheta da asiri harta yarda da shi itama. Yaya Awwab ni dai inaga zan fita da Baby zuwa waje ko za'a dace, dan ba'a yankema bawa hukunci da rayuwa”. Numfashi ya sauke a hankali, tare da janye jikinsa a nawa ya matsa jikin gadon ya gyarama Awwab dake neman zuwa gaɓa kwanciya. Itama Heedaya ya sake matsar da ita sannan ya dawo ta inda nake ya zauna tare da kamo hannuna ya zaunar a cinyarsa. Cike da kulawa yana wasa da yatsun hannuna masu lallen biki raɗam ya ce, “Sweetheart kiyi haƙuri, batun fita da Baby bazai canja komai ba, dan yarinyar ta kamu da ciwuka masu haɗarin gaske da suka riga sukaci jikinta matuƙa. A yanzu haka su kansu doctors ɗin sun tabbatar mana bazasu iya mata komai ba sai dai jiran lokaci. Shiyayasa nai magana da wani ƙwarren likita akan irin wannan fannoni na ɗauka hoton Babyn na tura masa amma ya tabbatar min da gaskiya samuwarta dai yanda ake buƙata abune mai wahala. Sai dai ba'a yankema ALLAH hukunci akan rayuwa ko mutuwar bawa. Baga mahaifiyarta nan ba, shekara nawa tana ciwon zuciya tama ƙi yarda a mata aiki amma har yanzu. Akwai dai magunguna da zai turo zasu iso gobe insha ALLAHU sai a dinga mata amfani da su a samu su wannan tsutsan ya daina fita a jikinta.” “ALLAH ya bata lafiya to, amma gaskiya Mom ta cutar da rayuwar yaranta. ALLAH ya sa mu zama iyaye na kwarai akan ƴaƴanmu. ALLAH ya hanamu fifita ƴaƴanmu akan wasu ƴaƴa dan kawai bamu muka haifesu ba”. “Amin ya rabbi.” ya faɗa a hankali yana kissing lips ɗina. Yana neman sakin layi na shige jikinsa da faɗin, “My Hot yara fa”. Ajiyar zuciya kawai ya saki da shafo kansa. Sai kuma ya miƙe yana faɗin, “Muje wanka na gaji”. Hakan ya sakani sakin murmushi, shi babu ruwansa ɓacin rai bai hanashi biyan buƙatarsa. Wani lokacin ma idan yana cikin damuwar yafi ta'azzara min. Ɗakinsa muka koma acan mukai wanka ko nace ma ya taimaka min dan bani da wani ƙarfi sam. Tea ya haɗa mana da kansa muka ɗan sha da cake muka kwanta. Washe gari ganin Hafiz lafiya ya saka ni samun ƴar nutsuwa. Haka mukai shiri muka wuce asibiti da abincin da muka haɗa. Mun samu jikin Abba da sauƙi sosai, sai dai ya kasa daina hawaye da neman gafararmu dan yace hakkinmu ne ke bibiyar zuri'arsa. Mudai munta lallashinsa. Da yamma aka sallesa. Itama dai Baby an bamu ita za'a koma da ita gida dan magungunanta sun iso. Shansu kuma yafi zaman asibitin. Itama Mom ta matsa sai an sallameta duk da tana a cikin wani hali. Haka dai muka ɗunguma zuwa gida. Amma mi sai Abba ya ce ai Mom bazata sake shiga masa gida ba ya saketa saki uku. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Iya haƙuri an bama Abba ya barta taje tai jiyyar ƴarta ya ce ina ai ya gama kuma, shi zai yi jiyyar Baby da kansa. Ansha matukar koke-koke. Haka Mom ta tafi gidansu tana kuka da aman jini. Sai dai can ɗin ma Ummanta tace bazata zauna mata a gida ba. Sai yanzu ne tasan da ita a duniya kenan. Taje ma duk inda zataje ita ba damuwarta bace. Mutane sunta bata haƙuri ta rantse tace bata buƙatar Jalilah a rayuwarta har abada. Ko mutuwa tayi ma kar a bari ta zo kan gawarta. Wannan magana tata yasa Mom dinga zaginta tana tsine mata da faɗin ai koma mi ta zama ma sanadinta ne, dan itace ta ɗorata a layin son abin duniyar da har takaita da danne hakkin marayu. Aiko sai suka fara tsinema juna da zagi kamar ba ƴa da uwa ba. Mudai muna gida labari ya same mu. A gurguje Please 🥺 🤍🤍🤍🤍 Satin Baby ɗaya jikinta har ya fara ƙyau dan tsutsan da kurajen jikinta sunata lafawa sai kuma mai afkuwa ta afku. A wani daren talata ALLAH ya amshi kayarsa. Duk wannan bidiri da akeyi ko sau ɗaya Bibaa bata taɓa zuwa dubata ba sai yau data rasu ta shigo tana wani kukan iskanci. Ai tuni Abba ya korata da tabbatar mata baya buƙatar ganinta a gidansa. Ta koma can inda ta fito. Hakama Mom ya hanata shigowa sam ita duk danginta. Ashe yanzu tana a wani kango ne zaune tana jiyyar kanta. Ta sake lallacewa da fita hayyacinta. Sanadin wannan hanata shiga ta yanke jiki ta faɗi, sai ɗaukarta mutane sukai suka maida kangon jiki ya shanye. To koma dai yayane ALLAH ya gafartama Baby. Ita dai tata kuma ta zama labari. Addu'a kawai take buƙata. Naso taimakon Mom dan koba komai ita ɗin uwace a garemu, amma koda mukaje kangon sai tace bata buƙata. Ganinmu ma bata son yi sam a rayuwarta. Dan mune muka zame mata sanadin komai. Da iyayenmu basu mutu mun shigo rayuwarta ba da bata aikata abinda ta aikata ba har ake ganin laifinta. Hankalinmu ya tashi da kalamanta. Amma Hafizzullah da Fahad suka gaggaya mata magana sukasa muka baro wajen. Anayin addu'ar bakwai ɗin Baby ma duk muka kama gaban mu. A wannan komawar ne kuma na fahimci inada shigar ciki. ALLAH ya taimakan Heedaya ba wani damuwa tai ma da mama ba. Sai kawai nace masa zan yayeta tunda dai wata biyu ya rage ta cika shekara biyun da yake buƙata. Zai fara min tujara na sanar masa ina hasashen kamar cikine da ni. Ai tuni ya ajiye fushi gefe ya rungumeni cike da farin ciki. Haka ya kwasheni mukai asibiti. Tun a gwajin farko ma aka tabbatar mana da shi sai dai ƙaramine sosai. Munyi farin ciki sosai, Ummie tazo ta ɗauke Heedaya zata yayeta a can. Bai so hakan ba amma babu yanda zai yi, nasan kuma abinda yake tsoro kar Ummie ta riƙeta, saboda Awwab ɗin Yaya Hayatu tuni ta ƙwace. Ni nasan sai dai haƙuri, dan bana jin Ummie zata barmu da Heedaya kam daman. Alhamdullah haka naita rainon cikina cike da kulawarsa, inada wata na biyar muka wuce Nigeria bikin Hafizzullah da Fatimansa. Bikine na ƴan gata da akaima shiri tako wanne fanni. Dan duka ɓangarorin biyu mun shirya tsaff. Yayinda ango keta rawar kai da abokinsa kuma yayansa Fahad. Munsha biki kam Alhmdllh, dan mun haɗa taro na nunama tsara. Ummie da Mama balki ne iyayen ango kuma na amarya. Yayinda mu ko muke amsa sunan manyan yayye. Ana gama biki washe gari ba mutunci Hafizzullah ya ɗauke matarsa suka baro Nigeria, wannan kam duk shirin Fahad ne. Sai neman amarya da ango mukai muka rasa. Yaya Awwab ya turnuƙe Fahad da faɗa kuwa. Aiko yayta soshe-soshen kai wai wannan ta faru kam sai haƙuri.......✍️ *🤣🤣 ALLAH dai ya shirya yayan angon nan gaskiya. Har shima dai angon yana buƙatar addu'a 😂.* _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒇𝒆_ *_Nagode sosai ƴan uwa da ƙoƙarin following ɗina da kukai. ALLAH ya bar zuminci. A ringayi ana sayen kaya kuma to karku hanani zama Ɗangote 😂, Makka ina son zuwa. Sannan na zagaye kasashen duniya duk da wannan sana'ar 😂😂😂. Ina godiya love you all 😘😘😘✨._ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq *_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*. *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._ .......Ango da amarya sun fece mu miya rage mana. Sai mu haɗa kayanmu mu kama gabanmu muma yan biki. Dan haka Yaya Awwab yace sai mu wuce. Sai dai kafin hakan ya ɗaukeni zuwa Alheri tv. Inda aka sake faɗaɗawa da ƙawatawa aka zuba masa kayan aiki da samunsu kam bako ina ba. Sai da muka gama zagayawa mu duka dan har su Ummie muka je sannan ya kamo hannuna ya saka min takardu a ciki. Duk da na taɓa gani tun a sanda ya sayesan sai naji jikina yama kama rawa. Bamma san na faɗa jikinsa ba ina hawaye. Aiko su Ummie suka hau mun dariya da su MD. Yayinda Mansoor yay ƙasa da kansa kawai yana mai danne abinda ke cimasa zuciya daya gagara ajiyewa. ALLAH ya sani yana son Samraah har yanzu. Amma yana ƙoƙarin mancewa da bama matarsa kulawa da yaronsu. Fatansa kuma ALLAH ya cigaba da saka masa haƙuri da juriyar hakan. Dole dai tafiya ta ruguje dan Ummie tace sai anyi walimar buɗe wajen. Aiko walima aka shirya gagaruma ta nunama tsara. Aka gayyaci ƴan media sosai a wajen. Yau dai mutumina ya daure ya magantu, sai dai yace ni kaɗai zan masa tambayoyi. Hakan kuwa akayi, na tattauna da shi kamar yanda nima akai hira da ni da gaba ɗaya ma tawagar tamu. An gama samar da ma'aikata dama. Ni da Ruƙayya kuma zamu cigaba da aikinmu sai dai daga can ƙasashen da muke dan boss yace bazai taɓa yarda yana wani waje ba ni ina wani, hakama Yaya Musaddiq. Washe gari duk muka wuce. Ta tabbata dai Ummie ta kwace Heedaya da Awwab. Dole kuma mun bar mata. Garama su Yaya Hayatu su akwai wani a gabansu. Muko fa sai fatan ALLAH ya saukeni lafiya kawai. Mun koma gidan daga mu sai Auta, shima a mafi yawan lokuta yana makaranta. Sai kaɗaici ya fara damuna. Dan Fateema nan zasu dawo idan sun gama honeymoon ɗin saboda makarantar ta. Dole nasa Ummie ta samo min ƴammata guda biyu, duk da Gwaggo Gudidi bata so haka ta shiryo ta dawo nan dan takanas Maash yaje har Nigeria ɗin ya ɗakkota. Ita ta cigaba da kula da ni har ALLAH ya saukeni lafiya. Wannan karon ma anan na haihu. Na samu Baby Boy. Yaro yaci suna Abdul-wahab. Rikicewa nayi dan ban taɓa zaton hakan ba, nayi zaton sunan Paah za'a saka ko Abie. Rasama mi zancema Yaya Awwab nayi sai kawai na rungumesa ina hawaye. Shima dai wannan sunan anyi shagali, dan kamar da gayya ma Yaya Awwab ɗin ke komai. Yanda yake kashe kuɗi har tsoro abin yake bani. Kowa kuma ya fahimci murtani ya sake maidawa akan taron sunan Heedaya daya haɗa cece kuce. To koma dai miye ALLAH ya raya mana yaranmu ta albarkaci rayuwarsu. Itama dai Fateeman Hafizzullah da alama an gamu, dan sai zubda kananun yawu akeyi. A haka muka je Nigeria bikin Malika itama da aka kai Niger. Ta koma kusa da ƴan uwanta su Azizat da suma zuwa yanzu duk sun haihu. *_YEARS LATER_* Rayuwa makaranta, daga wannan aji zuwa wancan. Sam-G ta da yanzu ta koma Samraah uwa. Uwar yara biyar ciff dan Yaya Awwab ba ruwansa da wani ƙa'ida. Idan son samunsa ne ma na ƙara. Amma dai nace masa in sha ALLAHU nayi kenan. Bayan Abdul-wahab, nayi Ibrahim, Abie, nayi Paah Mu'azz. Sai Auta Hayatu. Heedaya ce kawai mace. Yaso da fatan na ƙara mace saboda na lura yana matuƙar son ƴaƴa mata, amma sai ALLAH bai ƙaddara hakan ba. Dan haka tuni ya rakito yarinyar Fahad da taci sunana da ta Hafizzullah suma first born nasu mai sunan Mamanmu. Sai ta Yaya Musaddiq itama mai sunana. Ni kaina naji daɗin hakan, dan Heedaya na hannun Ummie ita da Awwab ɗin su Aunty Falaq. Idan ka ganta wajenmu sai idan hutu sukazo. Shiko Hayatu ma basu da ƴa macen ko ɗaya yaransu biyar suma duk maza ne. Kasancewar yanzu suma suna nan kusa damu. To a hankali ma sai gidana ya zama matattarar yaran, dan da anyi hutu duk nan suke tattarowa su taho har Yaran Fahad huɗu, na yaya Musaddiq shima huɗu, Hafizzullah keda uku. Gida ya cika dam sai ranar tafiya aita kewa. Daga ni har shi hakan na sakamu farin ciki sosai. Kamar dai yanzu ma haka duk suna nan tare damu hutu suke yi. Hayaniyarsu tasa na haye can sama na rufe kaina da security dan akwai aikin da nake mai muhimmanci. Inba haka nayi ba bazasu barni nayi cikin salama ba musamman ƙananun. Jin ana taɓa ƙofar na ɗago da sauri ina jiran naga waye zai shigo, nama manta na saka security, ubangayyar ne kawai zai iya buɗewa. Sai da ya shigo na sauke ajiyar zuciya. Dariya yayi da faɗin, “Lafiya irin wannan sauke ajiyar zuciya haka?”. “Humm ALLAH bazaka ganeba my Hot. Yaran nan gaba ɗaya sun hanani aiki, shiyya na gudo nan ina ganin na tsira. Da farko na zata sune shiyyasa da naga kaine nai ajiyar zuciya.” Zaune ya kai kusa da ni yana murmushi, sai kuma ya zame ya kwanta a saman cinyata bayan ya ture lap-top ɗin gabana da takardun. Dama zaune nake a carpet na gaban gadon. Hannu ya kai ya shafi fuskata muna kallon juna cikin ido, fuskarsa da murmushin nan da nake matuƙar so a hankali ya furta, “To da' anan suke dindindin fa?”. Idanu na waro da ƙyau na ce, “A da wataran sai dai ku wayi gari kai da su na gudu wajen Ummie na kawai.” Sosai dariya ta kamashi, ya dungure min kai yana faɗin, “Matsoraciya kawai. Nima barci suka hanani su Auta kawo ƙara kawai shiyayasa na gudo nan dan nasan nan ne wajen ɓuyanki”. “Oh ashe muna da yawa matsoratan”. Dariya mukayi mu duka. Ya ce “Cigaba da aikinki bari nayi barcina”. “A hakan?”. Kansa ya jinjina min kawai yana lumshe idanun. Ganin haka sai nima nayi shiru dan na fahimci barcin yake sonyi da gaske. Idanunsa har sun nuna hakan. Wasa na fara masa da gashinsa, tare da fara masa labarin aikin da nake yi zan tura Alheri tv. Murmushi kawai yake yi idanunsa a lumshen har naji ya fara sauke numfashi. Sai kawai gasu auta a guje ana kiran Dadaa! Dadaa! Ammie!. Da sauri na dafe kaina. Suna zuwa ƙofa nai saurin zaro musu idanu da saka hannuna a saman lips nace “Shiiii!!!”. Duk cak suka tsaya suna kallona. Na sake musu nunin su koma Dadaa na barci. Saɗaf-saɗaf suka juya suka koma. Kaina na dafe ina faɗin, “Oh ya rabba, ALLAH ya shirya yaran nan sai da kuka gano mu”. Idanunsa ya ɗan buɗe ya kallan, sai kuma ya maida ya lumshe batare da yace komai ba. A haka ya ɗauka remote ɗin ƙofar dake a kusa da ni ya saka mata security. Zanyi magana ya juyo gaba ɗayansa ya manne lips ɗinmu waje guda. Daga haka labarin ya canja aka maida aiki gefe.✍️ To nima dai ya kamata na koma gefe ƴan uwa😂🤣. Dan magana ta ALLAH na gaji🥱. ALHAMDULLAHI ALHAMDULLAHI ALHAMDULLAHI. Godiya ta tabbata ga ALLAH (S.W.A) da ya rayani har zuwa yau na kammala wannan littafi. Ina roƙonsa kuskuren dake ciki ya yafe min badan halina ba🙏. Abinda nayi dai-dai ALLAH ya haɗamu a ladan baki ɗaya. Masoya! Masoya! Masoya!!. Ina godiya ta haƙiƙa a gareku da haƙuri da juriyar da kukai na bibiyata. Ina muku fatan alkairi a duk inda kuke. ALLAH ya kareku ya baibayeku da RAHAMARSA ku da zuri'arku baki ɗaya. Ni kaina ina muku so da ban san iyaka ba, musamman ƴan DANDALIN TSUTSAR NAMA kun sakani nishaɗi bana wasa ba❤️❤️😋😋🙏 Ya rabbi ka gafartama iyayenmu ka yafe musu kurakuransu damu baki ɗaya. Ƴan uwa musulmai dake fuskantar barazana ta rashin tsaro a yankunansu ya rabbi ka kawo ɗauki ka mana maganin waɗan nan matsaloli ta inda bamuyi zato ko tsammani ba. Bazan gaji da faɗa ba ina roƙon gafarar wanda duk nama kuskure ko ba daidai ba a wannan tafiya. Nima mutum ce kamar kowa zan iya maka abinda bai maka ba a sanina ko ba'a sanina ba. Maybe kuma shine littafi na ƙarshe da zan rubuta a rayuwata. Dan haka dan ALLAH duk wanda nama ba daidai ɗin ba ya yafe min. Idan labarin mutuwata ya riskeku kuyi min addu'a koda sau ɗaya ne a cikin sallolinku domin samun rahamar UBANGIJI na. Ku min sadaka koda da kaɗanne😭🙏. Inda na kuskure a labarin nan ko kai kake ganin ba haka kaso ya kasance ba to Amin afuwa. A haka labarin yazo, haka kuma UBANGIJI ya ƙaddara zan rubuta shi😀. Daga ƙarshe ina tallata muku kayan BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING masu ƙyau da rahusa akan farashi mai sauƙi😌. Karki bari a yi babu ke har adashen gata munayi, masu son zuwa Egypt ganin likita ko yawon buɗe ido duk zamu iya taimaka muku. 😘👌 Idan muna da rabon sake haɗuwa a wani littafin ALLAH ya haɗamu da alkairi❤️❤️❤️🙏 Taku har kullum Bilyn Abdull ce 👌❤️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*