[7/15, 1:18 PM] null:       ⚔️*🔥ƘARFE A WUTA🔥*⚔️ MALLAKAR AISHA ADAM (AYSHERCOOL) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION *BRIGHT PENS SECOND BATCH* Writer of Gaba da gabanta Ƙanwar maza Cutarwa Ruɗin ƙuruciya Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g *BISIMILLAHIRAHMANIRAHIM* *Labarin ƙarfe a wuta, ƙirƙirarran labari ne, idan yayi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata, arashi ne.* Ban lamunci a juya mini littafi, ta kowace irin siga ba, sai da izinina❗ Page 1 Tsit ƙaton falon yayi, ba ka jin sautin komai, sai ƙarar gudun AC. Sai mutanen falon da suke tsaye sun yi cirko-cirko, kamar masu jiran wani sakamako. Wata matashiyar budurwa ce, durƙushe a kan gwiwoyinta, fuskarta ɗauke da wani yanayi na tsantsar damuwa, da tashin hankali, fuskarta tayi sharkaf da hawaye. "Yanzu sakamakona kenan a wurinki? Irin wannan sakamakon shi na cancanta daga gare ki ko?" Cikin ƙulewa wata babbar mace ta ce "Dama wani sakamako ka ke saka ran samu daga tsintaccaiyar mage? Ai ba za ta taɓa mage ba, abun da na din ga ankarar da kai kenan, tun a shekarun baya, amma ka kasa ankarewa, yanzu ta nuna maka ita ƴar kunama ce" Budurwar ta yakice gumin da yake tsatstsafo mata, ba tare da nadamar abubuwan da suke gudana ba a ƙasan ranta, a zahiri ta ce "Ba mummunan sakamako bane ba, abun da ka tarbiyantar da ni a kai ne, gaskiya ita nake tsaye a kai, bani da niyyar cutar da kowa a gidan nan, kowa aikinsa yake yi, yakamata ayi mini adalci, ba a goyi bayansa a nuna ni ce nake kan ƙarya ba, a bari nima na yi nawa aikin" Cikin tsawa ɗaya matar ta ce "Har wata gaskiya ce da ke..... Dattijon ya ɗaga mata hannu ya ce "Ya isa haka, tashi ki je, ba na ko son ganinki, ki je ki yi abun da ki ke ganin ya dace da ke". Cikin rauni da tashin hankali ta ce "Abba, ba ka son ganina ka ce?" "Eh mana, idan har ki na gudun ɓacin raina da fushina, dole ki ba wa ɗan uwanki duk wani cikakken haɗin kai, domin gudanar da aikinsa yadda yakamata" Cikin matsanancin tashin hankali ta ce "Amma Abba ni kuma menene makomata...? Yakamata a ji ta bakina Abba" Bai tsaya sauraron mai za ta ce ba, yayi gaba zai bar falon. Cikin matsanancin tashin hankali, ta riƙe ƙafarsa ta na fashewa da kuka. "Haba Abbana, me yayi mini saura a duniya, idan har zan rayu ka na fushi da ni, ka yi haƙuri zan yi abun da ka ce in sha Allah" tuni hawaye ya cigaba da wanke mata fuska, tsantsar nadama da damuwa suka mamayeta, ta din ga kuka da sheshsheƙa kamar ta shiɗe, amma ya fizge ƙafarsa ya yi gaba. Yana barin falon, tamkar mutanen falon za su cinyeta ɗanya, haka suka yo kanta sa surutu, kowa da abun da yake faɗa. Tashi ta yi tsaye, ta goge hawayenta, cikin ko in kula, ita ma ta bi wata hanyar ta bar musu falon, cikin sigar kwa ci kanku. Ɗakinta, ta shiga ta buɗe drower, ta fito da wasu takardu ta zube su a kan gado, ta kunna system ɗin ta da take caji a gefen gadon, lokaci guda kuma ta ɗauki wayarta tana dannawa. Jin motsin mutum a bayanta, ya sanya ta waiwaya da sauri. A tsaye ta ganshi bakin ƙofa, fuskarsa babu walwala balle annuri. Mayar da hankali ta yi, za ta cigaba da danna wayarta, ya tako zuwa gabanta, ya tsaya ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Kin shirya aikata abun da aka umarce ki ko kuwa?" Cikin hanzari ta tari numfashin sa ta ce "Ban ce shirya ba, kuma ba zan shirya ba, daga nan har gaban abada, ka fita ka rabu da ni". Cikin matuƙar mamaki yake bin ta da kallo, "Yanzu duk kukan da ki ka yi, ƙarya ki ke yi kenan?" A hasale ta ce "Ina ruwanka, idan ma kukan ƙarya ne ko na gaske, ka yi aikinka in yi nawa, kar ka sake yinƙurin shigar mini aiki, idan ba haka ba komai yana iya faruwa, wallahi ba zan fasa abun da na yi niyya ba, idan kuma ka cigaba da takura mini, zan baka mamaki" Hannu ya saka, ya ɗagota daga kan gadon ya ce "Menene zai faru, wani irin mamaki zaki bani? Me zai faru nake son ki gaya mini. Kina da hankali kuwa? Kin san doka amma kina taka ta yadda ki ke so? Da me ki ke taƙama ne haka?" "Doka ko? Ni  iya takata na yi, kai kuma cin zarafinta ka ke ƙoƙarin yi, ka ƙyale ni babu ruwanka da ni, ka yi naka aikin na yi nawa duk wanda yayi galaba shikenan. Idan ka ga dama ka je ka sake gayawa Abba abun da duk yayi maka a kaina, wallahi babu gudu babu ja da baya, ban fara dan ina saka ran dainawa ba, ba tare da na yi nasara ba" hankaɗata yayi kan gadon, yana wani irin huci, zuciyarsa na yi masa zafi, yayi wata irin ƙwafa yana bin ta da kallo. Cikin hanzari ya fice ya bar mata ɗakin, saboda idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi mata abun da ba shikenan ba. Ta yinƙura ta tashi zaune tana haki, tana kallon ƙofar da ya fita. **** Tsaye take a gefen wani gini, tana ƙarewa harabar kotun ido. Yadda aka cika harabar da manya da ƙananan motoci ne, ya sake tabattar mata da manyan shari'oi za a gudanar a yau. Ta din ga kallon agogon hannunta, tana kallon gate shigowa harabar kotun. Motar gidan yari ce ta shigo, aka yi parking ɗin ta, sai dai tsayuwar motar babu daɗewa wata danƙareriyar motar, ta shigo harabar kotun. A ƙalla an kai mintuna goma da parking ɗin motar, sannan aka buɗe bayan motar, wata mata ta fito, sanye cikin coat. Mutanen da ke harabar wurin, suka nufeta, wasu suka karɓi jakarta, ana ta yi mata fadanci, cikin girmamawa. "Ya Allah kai ne Allah, kai ne buwayi gagara misali, Ubangiji da babu wani kafinsa, kuma babu wani a bayansa. Allah na san mutanen nan sun fi ƙarfina ta ko ina, amma kaine abun dogaro na, na san ba za ka bani kunya ba. Allah sun fi ƙarfina ka fi mini ƙarfinsu. Allah ka yi mini kunfayakununka a kan shari'ar nan, hasken gaskiya ya shafe duhun ƙarya, duk da ina da masu goya mini baya, amma Allah goyon bayanka nake buƙata" ta jima a tsaye tana karanto addu'a, tare da yi wa Allah kirari. A hankali ta furta "What a hectic trial, Ubangiji ka iya mini" cikin nutsuwa, ta fara taka takalminta mai tudu, ta nufi shiga cikin kotun, da takunta mai kama da na ƙasaita, shigarta ta lawyoyi tayi matuƙar yi mata kyau, tana tunkarar ƙofar shiga, zuciyarta na tsananta bugawa,tana fatan Allah ya shiga lamarin ta. **** Ƙofar famfo kano state. Ƙarfe goma saura mintuna goma na dare, tuƙi yake yi cikin sauri, saboda yadda fasinjar da ya ɗaukko take azalzalar sa. Duk saurin da yake yi, mita take yi masa, a kan ya ƙara gudu. Yanayin kwalliyar da ta yi, cikin baƙin material, fuskarta ta sha make-up, zai  tabattar maka daga wurin biki take. Ta kalli agogon hannunta, kamar ta fashe da kuka ta ce "Mai napep, ka yi wa girman Allah ka yi sauri" Ya ce "Wai dan Allah hajiya yaya ki ke so na yi ne? Haba babata duk saurin da nake yi, ki yi haƙuri mana mu tafi a sannu". A ƙule ta ce "Ban gane babarka ba, wani irin wulaƙanci ne wata babarka, na yi maka kama da tsohuwa ne?" Yayi murmushi ya ce "A'a, ai ku mata duk in da ku ke iyaye ne... Katse shi ta yi ta hanyar cewa "kuma sai aka ce na haifi kamar ka? Ai sai a bari na haifa tukuna, a yanzu na haifi kamar ka, ai tawa ta ƙare a duniya. Ko yayarka ka ce mini ka cuce ni, balle babarka. Ni dai ka ƙara sauri, yau na san kashina ya bushe, sai an yagalgalani da masifa a gida yau. Aikin banza, ƙawayen amarya ƴan wahala, mun gama wannan wahalar a ɗauke ta a mota an kai ta gidanta, mu muna fama a titi. Mu ma Allah ya kawo lokaci, ace ga miji ga mota" Ya waiwaya ya kalleta yana murmushi, a fusace ta ce "Lafiya malam?" "A'a Allah ya baki haƙuri". Kafin su ƙarasa in da zata sauka, ta ciro masa kuɗinsa, su na zuwa in da za ta sauka, ta miƙa masa, ta sauka tayi cikin layinsu da gudu a kan takalminta mai shegen tsini, ko wahalar gudun ba ta ji. Mayafinta da jakarta a hannu, ta tura gate ɗin ta shiga ta na haki. Wani matashin saurayi, yana tsaye a harabar gidan hannunsa riƙe da waya, ya kalleta ya ce "Daga ina ki ke?" "Biki" ta bashi amsa kai tsaye. "Za ki ci ubanki kuwa, Major yana nan ido biyu, tun ƙarfe takwas ya dawo yake tambaya ko kin dawo, gashi kin kashe waya ke ga ƙwararriya" Cikin ta yayi wata ƙara saboda tsoro "Allahumma inni as'aluka afuwa wal afiya, yau na kaɗe" ta ƙarasa maganar tana nufar cikin gidan. Cikin sanɗa ta shiga falon, sai dai tana shiga, ta fara tozali da dattijon zaune a kan kujera 3 seater, ya sanya ƙofar shigowa falon a gaba, da gani babu tambaya ta san ita yake jira. Tsayawa tayi ƙyam da takalmanta a hannu, da jaka da mayafi, kamar ta juya da gudu ta koma. "Daga ina?" Yayi mata magana cikin dakakkiyar muryarsa. Cikin rawar murya ta ce "Abba, wurin biki" "To juya ki koma in da ki ka fito" "Ai an tashi" tayi maganar kamar ta fasa ihu, dan tuhumar Abba babu daɗi. "Dama haka mu ka yi da ke? Ki fita ki je ki yi zamanki? Ki dawo mini gida bayan goma, sai ka ce ki na zaman kanki?, koma ki kwana a in da aka yi bikin" "Dan Allah Abb.." "Get out, kar ki kuskura ki yi mini magiya. Duk gidan nan babu mai bani ciwon kan da ki ke bani Arfa, koma in da ki ka fito ba ki da wurin kwana a cikin gidan nan yau" da gudu ta juya ta fita saboda tsorata da ta yi. Ta koma harabar gidan, a ƙasan zuciyarta ta ce "Na shiga uku, ni ake kora kamar wata karya, yanzu idan gidan mijina ne, ba sai dai ya gama bala'in in shige ɗaki na bar shi ba.. Ba ta gama tsinkewa da lamarin ba, sai da major ya kulle babbar ƙofar shiga cikin gidan. Ta zube kayanta, ta tafi famfon harabar gidan, ta dinga wanke fuskarta, ta wanke kwalliyar fuskar gaba ɗaya, ta koma ta zauna jiran tsammani ko Allah zai saka Abba ya buɗe mata ƙofa. Samarin gidan suka fara fitowa daga BQ, suna shimfiɗa a harabar gidan, za su yi kwanciyar zafi. Sai wulaƙanci suke yi mata, suna yi mata Allah ya ƙara, suna kyararta, kamar wadda ta aikata wani gagarumin abun kunya. Ganin ba ta da mafita, ta laluba ta samo tabarma ta shimfiɗa, ta yi kwanciyarta dan a gajiye take sosai. Tsakar dare, ta yi juyi, ta ji babu kowa a kan gadon sai ita kaɗai, mamaki ya kamata, ta kalli agogon wayarta, biyu da rabi na dare. Tasowa ta yi ta fito nemansa, sai dai ga mamakinta, ta tarar da shi a ventilation ɗin saman bene, ya zauna a kan kujera ya saka harabar gidan a gaba, hannunsa riƙe da ɗan ƙaramin Alqur'ani yana karantawa. "Lafiya dai?" Tayi maganar cikin mamaki. Ya waiwaya ya kalleta ya ce "Lafiya ƙalau" "Amma me ka ke yi a wurin nan, a wannan uban daren? Na zata tuni ka kwanta, na fito na duba falo baka nan" Cikin ko in kula ya ce "Kar ki damu, ki je ki yi kwanciyar ki, Arfat ke  punishment" Cikin takaici matar ta ce "To ta na punishment, sai kuma kai ka zo nan ka zauna, ka hana idonka bacci?" Yayi murmushi ya ce "Ko na kwanta ba zan iya rintsawa ba, ki yi kwanciyar ki kawai" tamkar ta yi tsaki, haka ta wuce shi ta ƙyale shi, tama tunanin yaushe ƙarshen wannan lamarin zai zo?. Haka ya kwana a zaune, yana gadin harabar gidan, duk wanda yayi juyi cikin mazan nan, yana kallon shi. Yana ganin yadda Arfa ke ta juyi, sauro ya dame ta, sai da ya ji tamkar ya sauka ya samu abu ya rufe ta, amma ya ƙyale ta. Asubar fari, ya yi alwala, ya sauka ƙasa domin tafiya masallaci. Samarin na jin takunsa, suka din ga tashi, idan ba haka ba, ya tashi mutum da carbi. Ya na zuwa in da take kwance tana bacci, ya tsula mata carbi a ƙafafuwanta. A razane ta tashi tana rarraba ido. Bai ce mata uffan ba, ya yi gaba ya fice. Tana ganin ya fita, ta tattara komatsanta, ta shiga cikin gidan, sai soshe-soshe take yi, saboda uban sauron da ya cije ta. Cikin ɗakinta ta shiga, ta watsar da jakarta da sauran kayan a kan gadonta, ta jona wayarta a caji. Ta tuɓe kayanta daga ita sai underwear. Wata matashiyar budurwa da aƙalla za ta ɗan girmewa Arfa ta fito daga banɗaki, ta kalle ta, ta ce "Arfa, ke kuwa a ina ki ka kwana? Har sha ɗayan dare ba ki dawo ba" banza tayi mata, ta taho fuuu ta kusa bangajeta, ta shiga banɗaki. Ta girgiza kai kawai ta shimfiɗa sallaya. Da ƙyar ta yi sallar asuba, sai soshe-soshe take yi, tana idarwa ta ɓingire ta hau bacci a wurin. Sosai take baccinta, dan ta gaji sosai, ga baccin jiya sam bai yi mata daɗi ba. "Nabila!Nabila!!" Tsaki tayi tare da jan "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, menene, wannan wane irin kira ne dan Allah?" "Abba ne ya ce, ace miki yana fatan kin ajiye aiki ne, da ki ka kwanta kina bacci haryanzu ba ki fita ba"da sauri ta buɗe idonta, gaba ɗaya ta manta yau Monday. Kamar korarriya ta tashi, ta afka banɗaki, a gurguje ta wanke bakinta, tayi wanka, ta fito ta shafa mayuka, da turaruka ta shirya cikin uniform. Ta saɓa coat ɗin ta a kafaɗa, ta ɗauki jakarta ta goyo, ta sanya takalminta, tayi waje tana kunna wayarta. Ta shiga kitchen, ta buɗe fridge ta ɗebi lemuka ta zuba a jakartab, da abun da ta ajiye da wanda ba ta ajiye ba, duk ta kwasa ta zuba, ta zuge jakar ta fito falo. A falon suka yi karo da wata matashiyar mata, matar ta kalli Nabila ta ce "Ma'aikaciya ko mahaukaciya, kalleki kamar korarriya Nabila, zaki fita aiki amma ki ka kwanta ki na kwasar bacci abinki". Nabila ta ce "Anty, the whole barrister ki ke cewa mahaukaciya?" "Yo banda shirme, kalleki kamar an hankaɗoki, ke wannan wane nutsatstsen ne ma zai ce ki tsaya masa shari'a?" Nabila ta ce "I will fill a lawsuit against you, what you did is deformation of character, the whole barrister Anty ki ka zaga" "Wuce ki tafi kafin na make ki ni? Idan suka kore ki daga wurin aikin, ai kya nutsu" Nabila ta sake kwasa da gudu a kan takalmanta kamar ba budurwa ba. Mai aikinsu ta tarar a famfon harabar gidan, tana wanke-wanke. "Shalelen Abbanta, yau kamar kin makara" Ɗaga mata hannu kawai Nabila ta yi, kowa ya ganta sai yayi magana, ta kalli hanyar benen Abba, kamar ta je ta gaishe shi, amma ta fasa ta san yadda ta makaran nan, sai ya zaunar da ita yayi mata faɗa, ga laifin jiya ga na yau, kuma ta san sai ya haɗa har da na waccan shekarar yayi mata, dan haka tayi wuf ta fice waje. Duk irin vibration ɗin da wayarta take yi, ba ta ɗaga ba sai da ta zauna a cikin adaidaita sahu, sannan ta ɗaga kai wayar kunnenta. "Wai Nabila wani irin wulaƙanci ne, nake ta kiranki ki ka ƙi ɗagawa?" Nabila ta ce "Ke ban son tijara, kin wuce aiki ne?" A fusace mai maganar ta ce "Ban sani ba" Nabila ta yi dariya ta ce "Sorry masoyiyya, ki fito titi gani nan" tafiyar mintuna sha biyar suka yi, suka iske wata matashiyar budurwar a titi, sanye cikin doguwar rigar abaya, ta kama adaidaita sahun ta shiga tana hararar Nabila. "Sorry sumy, kar ki fashe dan Allah" "Wallahi kin fusata ni Nabila" "Shiyasa na ce ki yi haƙuri ai, ya gidan ya su mama?" Sumayya ta ce "Suna lafiya ƙalau, meyasamu fuskarki? Na ga kamar ƙuraje" Nabila ta rausayar da kai ta ce "Ke bari, the whole me, jiya Abba ya saka na kwana a haraba, sauron nan na cikin flowers suka yi idi a kaina" Sumayya ta waro ido ta ce "Wai da gaske?" "Zan yi miki ƙarya ne? Wallahi dattijon nan ya ce wai na koma in da na fito ya rufe ƙofa. Aikuwa na din ga tsinewa amaryar nan, na baro ta a gidanta cikin nishaɗi da farinciki, ni kuma na afka tashin hankali, kamar ni degree holder, Abba ya rufewa gida. Yanzu dan Allah da a gidan mijina ne, da ba sai dai yayi masifar ya gama ba, babu wanda ya ji ya gani? Ai Abba ya tozarta ni jiya. Sai so ake a ga fuska a tuhume ni, ko ayi mini rashin mutunci a gidan nan, kin san gidanmu Allah ya wadata mu da munafukai, ni kuwa na haɗe rai" Sumayya ta ce "Allah ya ƙara, ke uwar gwaninta, har da kai amarya, banda uban anko da ki ka yi mata. Ina mai tabattar miki ke da ganinta ta tako gidanku, sai wani ikon Allah" Nabila ta ɗan yi shiru ta ce "Ku ma fa haka ne, kin san wani abu, ba hassada nake yi wa amira ta yi aure ba, amma kalli na fita kyau fa, na fita komai amma amira ta shige daga ciki, ohh ni Nabila, duk kyan nan da dirin nan yadda ki ka san na je na haye kan high table ɗin nan ayi da ni ranar dinner. Ba ma wannan ba duk wannan gayun da kwalliyar ban yi saurayi a bikin nan ba" Sumayya ta ce "Ki je ki ɗorawa ranki jarabar son aure, ki ƙi focusing a kan career ki, ni ko a jikina na san lokaci ne, kuma tun da ba yawon iskanci nake ba, duk wadda ta yi mini gorin aure sai na ci ubanta, shekarun namu nawa ne duka da za a addaba mana" Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ba haka ba ne Sumayya, we have a different backgrounds, ke kin san me nake nufi, wallahi ƴanci nake so Sumayya, ko ta halin ƙaƙa" Sumayya ta ce "Kar neman ƴanci ya kai ki ga halaka, duk ina samarin naki ne to?ba wanda zaki tsayar?" Nabila ta yi tsaki ta ce "Bar matsiyata, daga ƴan wahala sai ƴan iska. Sai dai duk wanda ya zo hannuna sai na ci rabona ayi baran-baran. Na daina wahalar son mutum, daga ƙarshe yayi breaking heart ɗina, ya ci bulus. And also haryanzu ban samu spec ɗi na ba kin dai gane" Sumayya ta ce "Au ke yanzu har wane zaɓe-zaɓe ki ke yi?" Nabila ta ce "To ana raba mai rai da motsi ne? Iya wuya akwai abun da zuciya take so, kuma ni na fi son namiji mai kumari sosai. Irin wanda zaki ganshi ingarman namiji mai cikar zati. Beside fuskar namiji ba gemu, ai sunansa sumayya, ni kuma daga dattijai, sai marasa gemu, sai kuma ƴan wahala, ni matashi nake so, ba kuma yaro ba" Sumayya ta ce "Au sunana ne ma abun kwatancen iya shegenki ko, to ki je dan kanki. Mai napep zan sauka a nan, za ta baka kuɗin" Nabila ta ce "Ke uban waye ya ce miki ina da kuɗi?" Tuni Sumayya ta sauka, ta bar Nabila. Nabila ta yi ƙwafa ta ce "Zamu haɗu ne, zaki ga wulaƙanci". *** A hankali yake buɗe jajayen idanunsa, a lokaci guda kuma yana lumshe su, tamkar mai shirin yin bacci. Sai mirgina kansa yake yi, yana sake lumshe manyan idanunsa da suka koma jajaye matuƙa. Tamkar an jefo shi, haka ya faɗo ɗakin, yana rarraba ido. A hankali ya ɗaga kai ya kalli wanda ya shigo ɗin, ya mayar da kansa ƙasa ya sunkuyar. "Allah ya taimaki oga..." Bai amsa ba kawai ya buɗe tafin hannunsa ya miƙa masa. Wata baƙar leda ya ciro, ya ɗora masa a hannun, sannan ya ce "Sai dai Oga ba a samu da yawa ba, ƴar kaɗan ce, cinnaku sun yi wa kasuwar ƙawanya, shiga da fitar kaya na bayar da wahala, da ƙyar na samu wannan wurin wani ɗan inyamura, ina ga wuri zan canza, saboda kamar ana son yi mini cune". Bai ce masa uffan ba, ya kwance ledar, ya fito da kwalin wata allura pack guda, mai ɗauke da ampoule na allura guda goma. Sirinji lamba biyar ya ɗauka, ya din ga fasa alluran yana zuƙa, sai da ya cika sirinjin, sannan ya miƙe hannunsa. Ya ɗaga kansa ya kalli matashin da ya kawo masa allurar, bai ce masa komai ba, matashin ya bar ɗakin. Ya mayar da idonsa kan hannunsa, ya yana kallon jijiyoyin da suka kwanta ɗoɗar a ƙarƙashin fatarsa, suka yi ruɗu-ruɗu, manya da ƙanana. Ya dubi guda ɗaya, ya huda ta da sirinjin hannunsa, ya fara bawa kansa allurar sannu a hankali. Sai da ya zuba ta duka, sannan ya yi jifa da sirinjin, ya sunkuyar da kansa ya na jiran Sakamakon hukuncin da ya ɗauka. Sai dai kusan mintuna goma sha biyar, bai ji abun da yake so ba, sai wani irin nauyi da kansa ya ƙara, idonsa ya din ga yi masa yaji, ya rintse idanunsa amma bai ji alamar abun da yake so ba. Abu kamar wasa kansa ya din ga wani irin sarawa, ƙirjinsa yana zafi. Ya dafe kansa da hannunsa bibbiyu yana jujjuyawa tare da rufe idanunsa. Ihu ya fara yi iya ƙarfin sa yana taƙarƙrewa, yana girgiza kansa, saboda yadda yake jin kansa tamkar zai yi bindiga. Da gudu suka shiga ɗakin, suka fara ƙoƙarin danne shi, amma ya yi ihu ya watsar da su baki ɗaya ya cigaba da kururuwa. Ayshercool. 08081012143 [7/16, 1:53 PM] null:           ⚔️*ƘARFE A WUTA*⚔️ MALLAKAR AISHA ADAM (AYSHERCOOL) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION *BRIGHT PENS SECOND BATCH* https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Arewabooks ayshercool7724 Watpad ayshercool7724 2 A ƙalla sun kai ƙarti uku majiya ƙarfi, suka riƙe shi, amma sai ƙoƙarin watsar da su yake yi, ga wani irin gurnani yana yi, kamar mahaukacin zaki. Da ƙyar suka haɗu suka kai shi ƙasa, suka daddane shi yana cigaba da ƙoƙarin watsar da su ya tashi. Ɗaya daga cikinsu da yanayin kamanninsa ya bayyana, ƙarara shaye-shaye ya huda shi, saboda yadda laɓɓansa suke baƙi ƙirin, ga wani irin ƙaton tabo a gefen fuskarsa. A hankali yake ɗan dukan bayansa cikin sigar rarrashi yana faɗin "Easy maza, easy, mun san ka na cikin damuwa da raɗaɗi, amma hakan ba mafita bane ba, ka yi haƙuri muna tare da kai ɗari bisa ɗari iya wuya" ya cigaba da maganar yana rarrashin sa. A hankali jikinsa ya saki, ya daina gurnanin da yake yi, ya lumshe idanunsa, ya rufe su, tamkar mai bacci. Sai da suka tabattar ya yi relaxing, sannan suka ɗaga shi. Major ne tsaye a gaban mudubi, yana ƙara kintsa jikinsa kamar wani matashi, ba dattijo ba, uwargidan sa na gefensa tana taimaka masa yana shiryawa, Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Arfa kuwa ta tafi aikin?". Ta yamutsa fuska ta ce "Ta ga dama ta tafi" Ya jinjina kai ya ce "Punishment ɗin da na yi mata jiya, shi ya hana ta zo ta gaishe ni yau kenan,'? zan gamu da ita ne idan ta dawo". "Dan girman Allah major ka ƙyale sabgar yarinyar nan, sai ka ce itakaɗai ce ƴa a gidan nan, komai ita su duk sauran ba ƴaƴa bane ba, da ba ka damu da lamarinsu ba?" Kallon da yayi mata ne ya sanya ta yin shiru, tare da sunkuyar da kai, bai sake ce mata komai ba, ya ɗauki mukullin motarsa ya fice. Cike da takaici ta sauka daga benen, ta fito main falon gidan tana mita. "Yaya ya dai? Meyafaru ne?" Duk da ba ta kasance mai sakarwa abokan zamanta fuska ba, amma haka kurum ta tsinci kanta da gaya mata abun da ya faru saboda takaici. "Major ne mana, gaba ɗaya ya tattara hankalinsa a kan yarinyar nan, kamar itakaɗai ce ƴa a cikin gidan nan, jiya kwana na ne, amma a barandarsa ya ƙare kwanan jiya, wai yana gadinta, abubuwan nan sun fara isata" Ɗayar ta taɓe baki ta ce "Ai ni na gaji, na zuba ido su ƙarata, abun da ba jiya aka fara ba, ba yau ba". Anty, wadda take ta uku, da take karyawa, duk da ba da ita suke ba ta ce "Amma dai an yi abun kunya, kishi zan ce ko baƙin ciki da ƴar cikinku" A fusace Uwargidan major, da ake cewa Mama ta ce "Asiya, da ni ki ke ko wa?" Anty ta ce "Duk wanda ya tsargu, sai menene dan ya nuna mata kulawa ta musamman, duk kulawar da yake bawa sauran yaran bai isa ba? Ƴaƴa nawa ne a gidan nan, kowanne ya na bashi kulawa dai-dai da buƙatarsa ne, amma da yake kishi ya zame muku bala'i, mussaman ma ke, da kowa ma yi ki ke, kin fi mu daɗewa da shi, amma haryanzu ba ki san halinsa ba" Mama ta ce "Ba zan yi musayar yawu da ke ba ƙanwar bayana, dan ba ki isa ba, da wanda ya ajiye ki zan yi". Anty ta ce "Idan ma ƴar cikinki ce, matsayinmu ɗaya matan major, kuma ni gaskiya nake faɗa" haka suka cigaba da ƴan faɗace-faɗacen su na kishi. Nabila kuwa da wasu lokutan a kan yi mata laƙabi da Arfat, tana zaune a katafaren office, itakaɗai sai aikin danna waya take yi, cikin nishaɗi kamar babu wani abu da yake damunta. Knocking ɗin ƙofar office ɗin aka yi, ta bayar da izinin a shigo. Nabila suka gaisa da matar ta ce "Nabila ko?" Nabila ta jinjina kai ta ce "Eh" "Ki zo Barrister yana kiranki" "Wane barrister?" Matar ta ce "Director. Dama ina son in yi miki magana. Kin ga wurin nan babbar organization ce, da muke dealing da mutane daban-daban, especially manyan mutane. Yana da kyau ki jajirce director baya son ragwanci ko harkar ko in kula da aiki, sai ku samu saɓani" Nabila ta yi murmushi ta ce "Na gane, na kuma fahimta na gode sosai" matar ta jinjina kai ta fita. Nabila ma tashi ta yi, ta fita ta tafi office ɗin da ake nemanta. Ta tarar da shi da wani babban mutum a zaune a office ɗin sa, ta gaishe su cikin girmamawa sannan ta kalli Director ta ce "Sir gani" Ya kashingiɗa ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Nabila, what is actually wrong with you ne?" Cikin mamaki ta ce "Ni kuma? Me na yi sir?" Ya gyara zamansa ya ce "Anya ke ki ke son zama lawyer ko choice ɗin major ne? Tun da ki ka zo wurin nan you don't care, sai dai ki zauna ki danna waya, ki yi ciye-ciye, sai kwalliya. Bama kya shiga cikin ma'aikatan ki ga yadda ake aiki, balle mu ga gogewarki, mu faa tura ki trials, dama zuba miki ido na yi amma na ga baki san zuru ba" Nabila ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa. "Ina buƙatar ganin canji a tare da ke, idan ba haka ba na fara kai ƙarar ki wurin Major, yanzu muna da client da yake son yin apeal, a kan wata shari'a da wasu mutane suka kai ƙararsa. Ki je na saka ki a team ɗin su barrister Habib, ki je ku tattauna yadda za ayi handling case ɗin. Effort ɗinki shi zai sanya na baki manyan cases to help your career" Ta risunar da kai ta ce "Ok sir" ta juya ta fara tafiya, sai dai mutumin da tarar a office ɗin, ya bi bayanta da kallo yadda ƙugunta ke juyawa, cikin skirt ɗin kayan jikinta. Office ɗin Barrister Habib ta je, aka sanar da ita suna ɗakin sirri, dan haka kai tsaye can ta wuce. Ta tura ƙofar ta yi sallama, suka amsa mata, ta nemi wuri ta zauna. Barrister Habib ya ce "Kin ga damar zuwa kenan?" Wani irin kallo ta yi masa, amma ba ta ce komai ba, su kuma suka cigaba da abun da suke yi. Shari'a ce a kan wani attajirin mutumin ya karɓe gonakin wasu ƴan ƙauye, ya basu diyya ya fara ginin kamfanin sarrafa shinkafa, sai dai suka yi ƙararsa diyyar da ya biya su, ta saɓawa yarjejeniyar da suka yi da shi, dan sam bai kai darajar gonakinsu ba. Ganin ba su da galihu, ya sanya bai damu da ƙarar da suka kai shi ba, sai da aka yanke hukuncin ya biya su, sannan ya ce zai yi apeal. Mamaki ya cika Nabila, irin maƙudan kuɗin da ya biya law firm ɗin su, a bashi lawyoyi su kare shi, ya isa ya ƙarawa mutanen nan, ya biya su haƙƙoƙin su. Nabila dai ta yi zuru da ido, tana kallon yadda ake harhaɗa hujjoji na halal da na haram, domin mutumin yayi nasara a kotu. Baƙin ciki da takaici suka isheta, sunan ƙauyen da abun ya faru kawai ya isa ka gane cewar masu ƙaramin ƙarfi ne. Dan galibi mutanen karaka da Allah suka dogara, da harkar noma suka dogara. Tashi ta yi tsaye ta ce "Excuse me please, na fara jin yunwa lokacin cin abincina yayi" Duka lawyoyin da shi kansa client ɗin suka ɗago suka kalleta. Habib ya ce "Ana tsaka da aikin?" Ta basar ta ce"Am sorry, am having a chronic ulcer, za a iya samun matsala, idan na cigaba da zama" daga haka ta ɗauki jakarta ta fice, tana mitar ba zata zauna a ƙulla wannan sharrin da ita ba, ranar lahira ta shiga uku. Ta koma office ɗin ta, ta yi alwala tayi sallar azahar, ta je ta samu Director ta sanar masa da tana da uzuri ta na son ta tafi, yayi mata iznin hakan. A hanya ta tsayar da mai napep, suka ɗauki sumayya, sannan suka tafi. Ta kalli Sumayya ta ce "Sumy, meyafaru ne? Na ga kina wani ɓata rai" Sumayya ta yi tsaki ta ce "Haushin kaina nake ji, da na karanci aikin jarida Arfa" Cikin mamaki ta ce "Amma meyasa, na ga shi ne zaɓinki?" "Wallahi duk ya fita daga kaina, hira aka yi da honorable Indabo, wai an yi borehole a ƙananan Hukumomin da yake wakilta, an raba kayan makaranta ga ɗalibai. An kai bencina makarantun firamare da na islamiyyu. Last week aka ce na je na tattauna da al'umman local government ɗin, na je ni ban ga ayyukan da aka yi ba, na tattauna da mutanen ƙananan hukumomin, sun ce ba ayi musu ba. Na kai recording ɗin, aka saka, wai lawisa ba ta tantance shirin ba, ba ta sani ba aka saka, kin ga cin mutuncin da aka yi mini, wai zan lalata musu business wai sai na je na samo mutanen da zan yi hira da su, su ce eh an yi ayyukan su yi godiya alhalin ba ayi ba. Na zama maƙaryaciya kenan me zan ce wa Allah? Wai har da idan ban yi wasa ba, sai honorable ya saka an ɗaure ni" Nabila ta ce "Ikon Allah, ashe duk kanwar ja ce sumy, yo nima hakan take ai, wani tasonon Alhaji ne ya zo yayi kirim a kan kujera kamar damin doya, ya biya uban kuɗi wai za a kare shi, ya cuci talakawa ko kunya bai ji ba, kuma director ya sakani a team ɗin lauyoyin, ni dai ba zan yi ba wallahi, sai dai ya yi ta gaya wa Abban. Haka kurum a cuci mutane ka je ka cewa Allah me?" "Wallahi Nabila, ba ki ji zuciyata ba, yanzu sai dai na je na tara maƙwabta na yi hirar ƙarya da su, a zo a sake sakawa, kuma wai sai na rubuta takardar ban haƙuri, ki ji fa" Nabila ta ce "Tirƙashi, wai ya ɗaure ki, to ya ɗaure ki shi ma ya hau da ɗaurin Allah " Haka suka cigaba da tattaunawa, har suka isa in da sumayya za ta sauka. *** Cikin tsananin tashin hankali, yake magana, kallo ɗaya zaka yi masa ka san hankalinsa a matuƙar tashe yake. Ya daki teburi ya ce "Kwamishina, dole fa ku nemo yaron nan, dole ku mayar da hankali a nemo shi a duk in da yake a ƙasar nan" Mutumin da yake zaune cikin kakin ƴan sanda ya ce "Honorable, ka kwantar da hankalinka, aikinmu baya buƙatar garaje da gaggawa, sai mun bi a sannu" "Haba Cp, wane irin bi a sannu? Rayuwata na cikin hatsari, yayi iƙirarin kashe ni, dole fa a nemo yaron nan, ko be kashe ni ba, idan ya buɗe bakinsa yayi wata magana a kaina kashina fa ya riga ya gama bushewa, na san fa waye yaron nan ciki da bai" Cp ya gyara zamansa ya ce "Amma honorable, wace irin yadda ko alaƙa ce tsakanin ka da yaron nan, da har ya sanka haka, zamansa a gari yake barazana a gareka" Tsaki mutumin yayi ya ce "Kai har ka tambayi alaƙar da ke tsakanin ɗan siyasa, da tantirin ɗan daba, ɗan iska? Ku nemo shi dillalin wiwi ne, da hard drugs. Da kun ganshi ma kawai a harbe shi, kuma a tuhumi controllern gidan yari, a kan dalilin sakinsa, bayan ko shari'a ba ayi masa ba tsawon lokaci" Ɗan sandan ya jinjina kai ya ce "Shi controller ya ce court order ya karɓa" "Ni dai ka yi mini wannan taimakon a nemo shi da gaggawa, dan yana cikin garin nan, tun da ga ayyukan ta'addanci yana ta yi yadda ya ga dama". CP ya ce "In sha Allah, ka kwantar da hankalinka za ayi duk mai yiwuwa, zan nemi zaƙaƙurai daga cikin mutanenmu, da suke dealing da criminal cases, very soon zai zo hannu, DSP Nasir na san zai yi abun da ya dace in sha Allah" "Yauwwa to shikenan, ko dai sanarwa za ku yi, ace duk in da aka gano shi a kamo shi, an sake shi ba bisa ƙa'ida ba" Da sauri ya ce "No ai ba haka aikin tsaro yake ba, ai wannan abun kunya ne ga hukumominmu, yanzu sanin in da yake shi ne babban target ɗinmu, dan yaron yana da wayo sosai, na bibiyi record ɗin sa, sai an yi taka tsantsan sosai wurin kama shi, sai an yi amfani da dabarun aiki, hatsabibi ne sosai" "To ayi ƙoƙarin hakan dan Allah". *** Gudu-gudu sauri-sauri ta ƙarasa gida, saboda azababben fitsarin da ya cika mata mararta, tana zuwa ɗaki ta watsar da komai a kan gadonta, ta shiga banɗaki. Sai da ta gama fitsarin, ta ji iska na shigarta, tayi wanka ta fito, ta tattare kayan da ta watsar, ta samu riga ta shan iska ta saka, ta shafa turare ta fita. Kitchen ta shiga dan zuba abinci, ta ci karo da fate-faten wake a cikin food flask ɗin ta. A ƙule ta ja uban tsaki, ta fito babban falo kamar ta fashe da kuka, ta hau ƙwalawa mai aikinsu kira. "Baba magajiya!" Daga can wani sashen ta amsa da "Na'am, Arfa gani nan" "Na ga faten wake yau?" "Eh, umarnin Hajiya babba ne, ita ta ce ayi faten wake". Cikin ɗaga murya arfa ta ce "Amma dai an san ba na ci ko? Kin dafa mini wani abun ne?" Magajiya ta ce "Wallahi har na ɗaukko doya na fara frayewa, na ɗan dafa miki, na soya miki miya, aka kuma sakani aiki". Nabila cikin kwakwazo take masifa "Saboda tsabar an tsane ni, so ake na mutu a huta, in je aiki in dawo a kasa ajiye mini abinci, sai a dafa abun da ba na so" "Ke Nabila meye haka ne, hajiya ce ta bayar da umarnin hakan, ki shiga kitchen ki dafa wani abun mana" Nabila ta kalli Yaya Sauda ta ce "In je in dawo yanzu, sannan in shiga kitchen in hau girki, bari in je in sha faten waken, duk abun da ya same ni, ku kuka kasheni, ai kun san likita ya hana ni cin wake" "To ki je ki ci ɗin mana, idan kin mutun sai ne? Banda gulma amma ai ki na cin ƙosai da shinkafa da wake, ko duk su ba waken bane ba" Kamar ƴar goye, Nabila ta din ga zirarar da hawaye ta na bala'i. "Kar Allah ya sa ki ci abun da aka dafa, kya mutu da yunwa agola ƴar wahala". Cikin tsananin fusata Nabila ta ce "Tun da dai ba shegiya ba ce ni da ubana, ai da sauƙi" Cikin son kunna Nabila, Sauda ta ce "Meye marabarki da mara uban?" Baba magajiya da ke tsaye ta ce "A'a Sauda, dan Allah kar ayi haka, ke fa babbace" Sauda ta ɗaga mata hannu tare da cewa "Babu ruwanki, ki wuce ki ƙarasawa mama aikinta. Ke kuma ki tsaya ki cigaba da hauka, banda samun wuri ina na taɓa ganin agola da miƙe ƙafa". "Ai gara ni, agolar ce, kuma iya wuya ni ƴar gari ce, ba baƙuwar haure ba, jikar yarabawa. Kuma ni ba dan albarkacin ubana ba, wallahi da na daɗe da barin gidan nan, gara na je na kama gida na yi zaman kaina, iyaka ace ina zaman kaina, ba ɗan iskan da zai takura mini" Sauda ta tsaya ta ce "To ki je ki kama ki yi zaman kan naki mana, ke dama banda Abba a tsaye yake a kanki, ai ƴar zaman kantan za ayi, kuma ƴar gagara". Nabila ta buɗe baki za ta yi magana, suka ji gyaran muryar Abba, daga saman bene. Tuni idon Nabila yayi jawur, saboda kuka da ɓacin rai. Ya ce "Magajiya" cikin sauri ta ce "Na'am ranka ya daɗe" "A gabanki kina tsaye yaran nan suke faɗa? Ki ka kasa tsawatar musu?" Ta risuna ta ce "Tuba nake ayi mini afuwa". Sauda ta ce "Wallahi Ab...." Ya dakatar da ita ya ce "Ban tambaye ki ba, kukan me ki ke yi ke kuma?" Yayi maganar yana kallon Nabila. "Faten wake aka yi, ba a dafa mini komai ba, kuma yunwa nake ji" Ya ce "Wannan abun kawai shi ne abun kuka kuma? Ke a rayuwarki ba zaki taɓa girma ba kenan?" Tayi shiru tana sheshsheƙar kuka, kukan da yake jin sa har zuciyarsa. "Magajiya, ko aikin wa ki ke yi, ki ajiye ki sama mata abun da za ta ci, ba biyanki nake dan a farantawa wani a ɓatawa wani ba, duk ƴaƴana nawa ne, babu banbanci a tsakaninsu" Ta risuna ta ce "In sha Allah Alhaji, za a kiyaye" "Ke kuma, ki cigaba da faɗa da yayyenki, zaki ga yadda zan yi da ke. Kuma na gode da furunciki Arfa, zaki yi zaman kanki ko? Tun ina raye ki ke wannan iƙrarin, ranar da na mutu ban san me zaki aikata ba, kin kyauta" bai tsaya jiran me za ta ce ba, ya wuce ya koma ɗakinsa. Sauda ta yi wa Nabila gwalo, Nabila ta ce "Ai ke yakamata na yi wa gwalo, ni na yi nasara, tun da an ce a ajiye aikin babarki ayi nawa, banza ƙatuwar kwabo" Nabila ta wuce ɗakin su, tana tunanin ko dan wannan tijarar, ya isa tayi fatan tayi aure ta bar gidan nan. *** Ɗan siririn matashi ne dogo, wankan tarwaɗa, sanye da kakin ƴan sanda, da ɗan hanzari yake bin wata doguwar baranda, wadda ta sa da shi da wata ƙofa. Ya buɗe ya shiga da sallama, ya sarawa wanda ya tarar a cikin ofishin, wanda da gani babu tambaya, ka san babba ne sosai a cikin rundunar jami'an tsaro, duba da yanayin ranks ɗin da ke maƙale a kafaɗar uniform ɗin sa, da kuma haɗuwa da tsaruwar office ɗin na sa. Ya ƙame tare da sarawa mai office ɗin, ya yi masa alama da ya zauna. Ya zauna tare da sake gaida wanda ya tarar a office ɗin, da uniform ɗin sa ke ɗauke da sunan ACP Solomon wada. ACP wada ya kalli matashin ya yi murmushi ya ce "CSP Nasir Yusuf" Nasir ya waro ido ya ce "Wane ni Yallaɓai, Dsp ɗin dai" "Au Csp ɗin ne ba ka so? Ba abun mamaki ba ne ba, ka ji gobe kai ne Cp na garin nan, kai koma IG gaba ɗaya" Nasir yayi murmushi yana sunkuyar da kai. "Ƙwazon mutum babu in da ba ya kai shi, kuma kar ka yi mamakin ƙwazonka ya kai ka in da ba ka zata ba. Yanzu ba karatunka da kuma ƙwazon ne ya kawo ka matakin da ka ke yanzu ba?" Ya jinjina kai ya ce "Haka ne ranka ya daɗe". Acp Wada ya ce "Good, wani aikin za'a sake baka, wanda mu ke buƙatar sa da gaggawa, direct order ce daga Cp,ya kuma ce a jinjina maka aikin office ɗin ka yana kyau" Nasir ya tattara hankalinsa ya ce "Ok sir, na gode sosai" Solomon wada ya ce "Nasir, idan ka mayar da hankali yadda ake so, ka gudanar da aikin nan, za ka samu cigaba a aiki sosai da sosai" Cikin girmamawa ya sake cewa "I will do my best in sha Allah". "Good" ya ɗaukko wani file ya ajiye masa, sannan ya ce "Kwanakin baya, akwai wani ɗan daba, da ya addabi garin nan, kai ɗan garin nan ne za ka fi ni sani, wai shi Aminu ana yi masa laƙabi da viper. Shekarun da suka gabata yana tsare, sakamakon laifin da ya aikata, kafin kwatsam mu samu sanarwar cewa an sake shi. So bayan sakin nasa, akwai kokwanto a cikin sakin da aka yi masa ba bisa ƙa'ida ba ne ba, duk da controllern gidan yari ya ce order aka bashi ya sake shi, bayan fitowarsa ya cigaba da aikata miyagun laifuka a ɓoye, na sayar da miyagun ƙwayoyi tare da ƙyanƙysar sabbin ƴan daba, da suka hana jama'a zaman lafiya a garin nan, wanda yaƙi da wannan a ƙarƙashin kulawar office ɗin ka yake, a zone ɗin. Abun da muke so da kai shi ne, Aminu ya shigo hannu, ko ta halin ƙaƙa." Nasir ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Ok sir, tabbas cases na dillancin ƙwayoyi da harkar daba, yana ƙara ta'azzara, amma laifin me yayi aka kai shi kurkuku? Kuma ya aka yi, aka sake shi ba bisa ƙa'ida ba?" "Wannan ba huruminka bane ba, duk ba shi ne a gabanmu ba, kamo yaron shi ne abun da muka saka a gaba, wannan abun da ya shafi shari'a ne, ɓarnar da yake aikatawa ta yi yawa. Kuma a zone ɗin ka yaransa suka fi yawa, dan haka ka je ka yi iya ƙoƙarin ka a kai. Yabawa da nustuwarka, da jajircewar ka ya sanya muka baka aikin nan, ina nan ina saurarenka, ba a buƙatar ɓata lokaci. Ka je ka duba file ɗin a tsanake, akwai sauran informations da za su taimaka maka wurin kama yaron, da duk wani record na criminal acts ɗin sa yana ciki. Nan da gobe in Allah ya kaimu zaka dawo mini da file ɗin. ba na buƙatar kuma ka yi wani abu sama da haka, kar ka ƙetare iyakar da na gindaya maka". "Ok sir, i will do mai best in sha Allah" ya ɗauki file ɗin, tare da sake sara masa ya fita. Ɓangaren Nabila kuwa, al'amuranta ba a samu sauyi ba, dan duk shari'ar da ba ta yi mata ba, ba za ta mayar da hankali a kai ba. Director kuma ya bar ta ne, saboda mutuncin mahaifinta Major Yusuf da yake gani, mutum ne na gari kuma akwai tarin alkhairai da ya yi masa, shiyasa ya ƙyale Nabilatake cin karenta babu babbaka. Nabila gaba ɗaya wasu lokutan sai ta ji tana danasanin karantar ɓangaren shari'a, yadda wasu abubuwan suke gudanawa sam ba sa yi mata daɗi. Hausawa suka ce sai hali ya zo ɗaya ake abota, ɓangaren ƙawarta sumayya ma haka, kusan ƙalubale ɗaya suke fuskanta, dan har gara ma Nabila tana da alfarma a wurin na ta aikin, Sumayya kuwa na ta babu sani babu sabo. Yau ganin motar Abba a gida bayan ta dawo daga aiki, ya sanya ta fuskanci yana gidan, dan haka da ta zuba abincinta, sai ta hau saman benensa. A falonsa ta tarar da shi da Yaya Nasir, suna magana, da alama magana ce mai muhimmanci suke yi, sai dai yayi shirin fita. "Abba sannu da gida" "Yauwwa" ya amsa a taƙaice. Sai dai ta na zama ya tashi ya yi wa Nasir sallama, ya fita ya bar falon. Nasir ya galla mata harara. A shagwaɓe ta ce "Dsp me na yi ne? Kwana biyu duk Abba ya canza mini, kai ma kuma kana hararata" "Ba dole ya canza miki ba, duk kin gallabi kowa a gida, bayan na dawo daga kaduna ake gaya mini wai kin je biki kin yi dare, ƙarshe a haraba ki ka kwana yayi punishing ɗin ki, ba ki zo kin bashi haƙuri ba. Law firm ɗin ku director ya kawo masa ƙara, daga danna waya sai kwalliya ki ka iya, ba kya son aiki, yayi ta bashi haƙuri ya ce a kula da ke a koya miki aiki, ko ba a biya ki ba, shi zai din ga biyanki salaryn. Kwatsam jin kunnensa ya ji ki na cewa ba dan shi ba, zaman kanki zaki yi, kin san kwana nawa ya ɗauka ba ya bacci saboda wannan maganar da ki ka yi? Duk cikinmu babu wanda Abba yake lelensa kamar ke, amma sai ba shi kunya ki ke ko ta ina?" Cikin sanyin jiki, da tashin hankali ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ban zaci ran Abba zai ɓaci har haka ba, to kuma ba ka bashi haƙuri a madadina ba? Yaya sauda ce fa take ce mini agola, ni kuma ba na son na gaya masa. Ba na son fushin Abba, dan Allah ka tayani ba shi haƙuri. Maganganun Sauda ne suka ɓata mini rai, na yi dana sanin abun da na faɗa, amma dan Allah Yaya Nasir ka bashi haƙuri" Ya girgiza kai ya ce "No ni ba ruwana" Kuka ta saka masa tana cewa "Wallahi ba zan ci abinci ba, sai yanzu na ji maganar da na yi, ta yi nauyi ban san abba zai ji ba" "Kin ga ya isa, kar ki saka ciwonki ya tashi na shiga uku, ya mayar da fushin da yake yi da ke kaina" ai kamar ya sake tinzirata, ta cigaba da sheshsheƙar kuka. Cikin tsawa ya ce "Ke wai dan ubanki meye haka? Am i your mate, ba magana nake yi miki ba?" Sai da ta razana, amma hakan bai saka ta daina kukan ba. Ya zuba mata ido, Nabila tun asalinta tun tana yarinya take fama da taurin kai na tsiya, yanzu ko dukanta zai yi, ba za ta daina kukan da take yi ba, balle ma yanzu ba wannan dan ta girmi duka. Har mamakinta yake yi, ƙatuwar budurwa ta kammala degree, kusan shekara ashirin da huɗu amma tana abu kamar yarinya ƙarama. Tsaki yayi, ya tashi shi ma ya fice, ya ƙyale ta, ta ci uban kukanta, ta kwanta a kusa da flask ɗin Abincinta ta hau baccin gajiya. A tsanake Nasir yake duba file ɗin da aka bashi, a kan Aminu viper, da aka ce lallai ya kamo. A record ɗin da ya duba, ya gano zuwan Aminun gidan yari, ba sau ɗaya bane ba, a kan mabanbanta laifuffuka da suke da alaƙa da harkar daba, da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi. Sai dai abun da ya ɗaure masa kai, ba a shigar da dalilin da ya sanya, aka kai shi prison na ƙarshe ba, an dai nuna ya aikata wani babban laifi ne, da ga cikin manyan laifuka da bai kamata daga lokacin faruwar abun zuwa yanzu ace an sake shi ba, haka zalika an cire wasu abubuwa masu muhimmanci da yakamata ace ya gani a cikin file ɗin, sannan ga shi solomon Wada ya yi masa umarni da ya yi amfani da iya abun da aka bashi. "To menene dalilin haka?" Ya tambayi kansa, a lokacin da kan na sa ya ƙara ɗaurewa. Sake duba file ɗin yayi yana tunani, kamar ya taɓa duba wani case, makamancin record ɗin da yake cikin file ɗin, sai dai kamar sunan ba haka yake ba. "Aminu Viper" ya sake maimaitawa. Ayshercool. 08081012143 [7/17, 1:25 PM] null: ⚔️*ƘARFE A WUTA ⚔️ AISHA ADAM AYSHERCOOL https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 3 Sama-sama Nabila ta ke jin hayaniya a kanta. Amma ta ƙi motsawa. "Ke Arfa" yayi maganar yana riƙe hannunta. Tashi ta yi zaune tana buɗe idonta a kan Abba, a sanyaye ta ce "Abba ka dawo?" "Na dawo, tun da na tafi ki ke kwance a nan, ko abincin ba ki ci ba?" "Abba Yaya ne ya ce kana fushi da ni, dan Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba" Major ya ce "Eh ya kira ni ya gaya mini, na haƙura tashi ki wanke fusarki ki zo ki ci abincinki" ta tashi ta shiga banɗakin falon, ta wanke fuskarta, ta zo ta zauna ta saka spoon ta fara cin abincin. Ya numfasa ya ce "Rashin ji ne, ya yi miki yawa arfa, duk yadda na so na yi haƙuri sai kin ƙure ni, ban bi daɗin abun da kunnuwana suka jiye mini ba, kina iƙrarin zaki yi zaman kanki" "Abba ka ce fa ka haƙura, ba zan sake ba" "To shikenan na ji, ci abincin" Umma tayi sallama da flask ɗin shayi, matarsa ta biyu, kasancewar yau girkinta ne. Ta zauna a kusa da shi, ta haɗa masa tea, ya karɓa yana sha ya na yi wa Nabila hira, kamar bai yi fushi da ita ba, har ta ɗan ware. Kiran sallar magariba ne, ya sanya ta tashi ta bar ɗakin, dan umma ta ji haushin zaman da Nabila ta yi, ita kanta Nabila ta so ba su wuri, amma Abba ya cigaba da jan ta da hira. Da ya dawo daga sallar magariba, kai tsaye ɓangaren mama ya wuce, tana zaune a falonta, da Sauda su na kallon tv. Gyaran murya yayi, sannan yayi sallama, suka amsa suna yi masa sannu da zuwa. Ba tare da ya amsa ba ya kalli Sauda ya ce "Sauda nan gidan waye?" Ta ɗan yi turus tana kallonsa. "Ki amsa mini" "Gidanka ne Abba" Ya ce "Masha Allah, idan ba zaki iya zama da ni, da tsarina ba, ko ki koma gidan tsohon mijinki, ko kuma ki fitar da miji ki yi wani auren" Cikin damuwa Mama ta ce "Major me yayi zafi haka?" "Baƙar aƙidar ki, da ta ara ta yafa, ba zan lamunta ba. Kun sani ba na ɗaukar duk wani abu da ya shafi Nabila da sauƙi, yadda na yi mata shamaki, da wanda ya zama katangar rayuwarta, dole na tsaya tsayin daka, na kula da ita kamar yadda na yi alƙawari. Ba zan lamunci a cigaba da wulaƙanta mini ƴa ba, har ta fara iƙirarin za ta yi zaman kanta. Babu wani ɗa da ya fi Nabila a cikin gidan nan, idan ki ka sake ce mata agola, to zaki fita ki bar mini gida ki nemi wani uban". Cikin takaici mama ta a ce "Amma da kunnenka ka ji ta faɗa mata haka? Ka san dai makirci irin na yarinyar nan ko?". "Kunnena ne ya jiye mini, ko zan yi mata ƙarya ne?" Suka yi tsur-tsur baki daya. Ya ja guntun tsaki ya bar falon. Yana fita sauda ta ce "Mama dan Allah sai yaushe Abba zai daina fifita yarinyar nan a kanmu, tun da aurena ya mutu bai taɓa yi mini gori ba sai yau, saboda ita?" "Ba ke kaɗai ba, ni kaina yadda ki ka san na yi mata kucciya, duk ita ce matsalar gidan nan, amma zan kawo ƙarshen komai da kaina, ki bar ni da su". Nabila kuwa na ɗakinta, itakaɗai, tana duba document ɗin shari'ar da director ya saka aka ba ta, sai dai gaba ɗaya ba ta da intrest a kan shari'ar, da ta gaji ma, ajiyewa ta yi ta hau waya da saurayi. Wata matashiyar budurwa ce ta shigo ɗakin ta ce "Wallahi Nabila abun da ki ke yi ba kya kyautawa" Nabila ta ɗan kalli Asiya, ta katse wayar ta ce "Da na yi me?". "Kin saka Abba ya yi wa mama da Anty sauda kaca-kaca saboda ke, sai da Anty sauda ta yi kuka". "To ai cewa zaki yi, Abba bai kyauta ba ni meye nawa a ciki?" "Amma ke ki ka gaya masa ta ce miki Agola, bayan yayi musu mu ma ya iskemu a babban falo, ya yi ta yi mana faɗa". Nabila ta ce "Ashsha, ai kin san ni bana kai ƙara, ko dai na ɗauki mataki, ko kuma Allah ya saka mini da gaggawa" Asiya ta ce "Ai shikenan, kowa yayi na gari kansa". Nabila ta ce "Allah ya yaye miki Aisya, ke ma fa matar nan idan ta tashi karta miki wulaƙanci, ba saurara miki take yi ba, daga ke har umman, amma ku yi ta bin ta kamar wata shugaba, ni dai ba mai takani ban ɗaga ƙafar na karya ba" "A'a ai ke ki ka ce, ke ki na da ma dogara" Nabila ta yi tsaki, tare da furta "Allah ka aurar da ni na huta da wannan kacaniyar gidan, Ya Allah dogo mai gemu" ta fita daga ɗakin tana addu'a. Bayan kwanaki takwas. A tsaye yake ƙyam, kamar ƙofa, kasancewar in da yake a tsayen ba a iya ganinsa sosai saboda duhu, sai dai inuwarsa ta nuna dogon mutum, kakkaura. Ya ɗauki ɗankwali, ya ɗaure kansa da shi, tare da naɗo ɗankwalin ya rufe fuskarsa sai idanunsa kawai ya bari a waje. Ya laluba hannunsa, ya ɗaukko wata irin doguwar wuƙa, ɓangare ɗaya zarto, ɗaya kuma kaifi, ga ta da uban tsini, a ƙalla za ta yi kamu uku, ya ɗaga rigarsa ya soketa. Ya sake ɗaukar wata ya soke a jikin wandonsa. Yanayin takun da yake kawai, ya isa ya tabbatar daƙaƙarfa ne, saboda yadda ƙasa ke amsa takun nasa. Bayan wasu awanni, duhun dare ya ƙara yi, sahu ya ɗauke, sai haushin karnuka ko ina. A ƙofar wani gida ya tsaya, ya din ga waige-waige, ya tabattar da babu kowa. Tamkar ɗan biri, haka ya cafke katangar gidan ya dira ciki. Ya saka mukulli, ya buɗe wata ƙofa a cikin gidan da duk ta yi ƙura, ya buɗe ta ya kutsa kai ya shiga ciki. Tsayawa yayi ya kunna fitilar wayarsa, yana haske ɗakin, take ya ji wani abu mai tsananin ɗaci ya fara kaiwa da komowa a ƙirjinsa, ya ji numfashin sa na barazanar barin ƙirjinsa. Jikinsa ne ya fara rawa, ya ji tamkar hankalinsa zai gushe, ya durƙusa a wurin yana wani irin haki, cike da wani yanayi na mai shirin fita hayyaci. Hayaniya ya fara jiyowa a waje, hakan ya saka shi miƙewa tsaye babu shiri. Cikin sauri ya fito daga ɗakin, ya kama katanga, ya leƙa, sai dai yana leƙawa ya ga ƴan ƙato da gora da miyagun makamai, sun fara taruwa a kewayen gidan, kasancewar akwai hasken farin wata, kuma akwai hasken ƙwayayen solar hakan ya bashi damar ganin makaman da suke hannun su. Babu tsoron komai, ya haye katangar, ya hau saman roofing gidan, ya dira ta wani ɓangaren, jin sautin dirarsa, ya sanya suka rufa masa baya, ta in da suke jiyo sautin gudunsa har da karnuka su na kururuwar a tare. Sai dai duk da wannan ƙira da Allah ya yi masa, ta siffar ƙarfi ba ya jin nauyin jikinsa, ya din ga dukan ƙasar da dukkanin nauyin jikinsa,  ba su ankara ba, ya ɓace musu ɓat kamar walƙiya. A bakin titi suka tsaitsaya suna haki, su na mayar da yadda aka yi. Ɗaya daga cikin su ya ce "Anya yaron nan, ba da layar zana yake amfani ba?" "Ba wata layar zana, tsohon hatsabibi ne kawai, ni na yi mamaki ma da ya gudu ai, da da ne fa, wallahi sai ya illata ku kan ya gudun. Ai kamar yadda na gaya muku ne, da na ji alamun ya zo, zan kira ku a waya na sanar muku, ai ba zan sake sukuni ba sai ya je hannu, na za ta ma zaku kira ƴan sanda ne" Ɗaya daga cikin jami'an sintirin, ya ce "Ko zamu kira ƴan sanda, mu yakamata mu fara huɓɓasa mu kama shi, sai mu miƙa musu shi, wannan gudun nasa yaushe muka kira ƴan sanda ma" "Amma duk da haka, yakamata su san yana zuwa ai" Shugaban su ya ce"Muddin suka sani, canza taku zai yi, ba zai sake zuwa ba". Malam lawan da gidan sa ne a jikin gidan da yake zuwa ya ce "In ji wa? Ba zai taɓa iya daina zuwa gidan nan ba, yadda ka san ya binne asiri a ciki, kodayeke sai ta yiwu ma asirin ya binne, wannan hatsabibancin nasa akwai lamarin sihiri a ciki, amma zan cigaba da saka ido, da ya zo zan kuma kiranku" "To shikenan malam lawan mun gode, yanzu ka koma gida, bari mu koma bakin aiki, ko kuma a raka ka ne?" "Ahha haba, kamar ba namiji ba, ba wani abu bari na koma, ai ya riga ya gudu" Suka yi sallama ya nufi layinsu. Sai dai yana daf da ƙarasawa gidansa, kawai ya ji an yi ball da shi, kasancewar sa ɗan ƙaramin mutum, sai jin sa yayi, ya yi sama ya dawo ƙasa kamar wani karmami. Ya tashi a gigice yana zaton ko gamo yayi da aljani, ya hau waige-waige. Haske shi ya yi da fitila, sannan ya ce "Kwana da yawa malam lawan, tsohon butulu, da na ƙyale ka ban yi maka komai ba, shi ne ka cigaba da yi mini bita da ƙulli?" Cikin kwakwazo, da tsananin razani ya ce "Na tuba, na bi Allah na kuma bi ka, dan Allah" kan ya ƙarasa, ya karya shi ɓaras, ta hanyar saka ƙafa, ya yi masa wani irin duka a ƙafarsa ɗaya. Malam lawan ya a kurma ihu, cikin tsananin zafin nama, ya cire hular kan malam lawan,, ya tura masa a baki, sannan ya ciro wuƙar ƙugunsa ya yanke shi a damtsensa, aikuwa jini ya ɓalle. Ya durƙusa a gaban sa ya ce "Yanzu ai ka ji daɗin bayar da rahoton zuwana, ragon maza kawai" ya tashi tsaye ya ja da baya ya ɓace a cikin duhu, ya bar shi a mawuyacin hali, ga karaya ga yanka, gashi kuma ya toshe masa baki. Ko da ya koma gidansa da yake zaune, ciro wuƙar da ya yanki malam lawan yayi, yayi jifa da ita. Ya tsaya yana haki, abun da ya yi alƙawarin dainawa, yau ya yi, ya zubarwa da wani jini. Ya dafe kansa yana huci cikin tsananin damuwa. ** Yau sumayya ba ta haɗa tafiya da Nabila ba, dan da wuri sosai ta fita, za ta shiga asibitin murtala ta duba wata yayar babansu da aka kwantar a emergency, za ta kai musu abinci. Su na tafe da mai adaidaita sahu, ta hango mutane na ta shiga su na fita a wani layi, duk da lokacin gari bai gama hasken da za ace, mutane suna wannan tururuwar ba. Da sauri ta tsayar da mai baburin, ta biya shi kuɗinsa, ta  sauka, ta nufi layin da mutane ke shiga su na fita. Wurin duk babu mata, sai maza, amma hakan bai hanata kutsawa da son gano abun da yake faruwa ba. Tsayawa ta yi ta tambayi wani magidanci, abun da yake faruwa. Ya sanar da ita, gawar wani yaro aka tsinta, a bayan maƙabartar unguwar, an yanke masa al'aura da wasu sassa na jikinsa. Jikinta na tsuma ta cigaba da kutsawa tana faɗin "Ku matsa, ni ƴar jarida ce" tare da nuna musu id card ɗin ta. Ta ɗaɗɗauki hotunan yaron, sannan ta tsaya tattaunawa da mutanen da suka fara zuwa su ka tarar da abun. Sai kiranta ake yi a waya, ana jiran ta kai abinci, amma sai da rana ta ɗaga sosai, aka gama komai ƴan sanda suka zo, sannan ta yi shirin tafiya, shi ma sai da ta karɓi lambar wayar wani ɗan sanda, da zimmar zai din ga ba ta update na sakamakon binciken da za su yi, a kan gawar. Ko da ta je asibiti ta sha faɗa,na rashin kai musu abinci da wuri, ko a jikinta, saboda ta samu rahoto, dan haka tana ajiye musu abincin, ta yi waje. Sai dai ba ta fito daga emergency ba, ta din ga jin ihun wani babban mutum, kamar mara gaskiya, haka ta koma tana leƙawa ta ga abun da yake faruwa. Magidanci ne, ake yi masa ɗinkin wani uban yanka a damtsensa, jikinsa yayi kaca-kaca da jini, duk da ana ta yi masa allaurar kashe zafi, amma sai ihu yake yi. Babu neman izni, ta afka ciki ta ce "Sannu bawan Allah, ka yi haƙuri Allah ya baka lafiya, ka daure" Duk sauka waiwayo su na kallonta, har da ma'aikatan, mutumin ya ce "Na gode sosai" Ta ƙara matsawa ta ce "Amma hatsari ka yi ne? Kodayeke wannan ai yankan makami ne ba hatsari ba" Ya ce "A'a wani ɗan daba ne, ya sare ni jiya cikin dare, dama hukuma ta daɗe ta na neman sa" Sumayya ta gyara tsayuwarta ta ce "Subhanallah, bawan Allah a wace unguwa ce haka? Ko rigima ku ka yi da shi ne?" Ƙanin malam lawan da yake tsaye a wurin, a fusace ya kalli sumayya ya ce "Dalla malama fita, mutum yana fama da kansa, kin zo ki na yi masa wasu surutan banza" Ta ce "A'a Allah ya baka haƙuri, ka sani ko akwai wani taimako da zan iya yi masa. Kalli saran da aka yi masa fa, idan ba za ka damu ba, zan naɗi muryarka, mu saka a radio, ko Allah zai saka, hukuma su bi maka haƙƙinka, barin su da ake yi suna cin bulus ya sanya suke cigaba da ɓarna". Malam lawan ya ce "Ke rufawa kanki asiri, hatsabibanci da ta'addanci yaron, ya wuce tunanin ki" Sumayya ta zaro wayarta, za ta yi magana, sai ga wasu mutane guda biyu sun shigo da wani kaki a jikinsu, da ba ta san na menene ba, suka mayar da ƙofar ɗakin suka rufe. Malam lawan ya kalle su, ba su ne ƴan sandan da aka kirawo suka tsaya masa, likitoci suka zo kansa ba ne. Sumayya ta yi tsilli-tsilli da ido,  ɗaya ya ƙirga mutanen da suke cikin ɗakin, da likita ɗaya, nurse ɗaya, sai ƙanin malam lawan da sumayya. Dan duk maƙwabtan da suka kawo shi, sun tafi wurin sana'oin su. ya ce "Ku biyar ne a ɗakin nan, idan ka sake mu ka ji labarin sunan wanda ya yi maka wannan raunin, to za ka maye gurbinsa da ya bari na gidan yari, dan haka ka ja bakinka ka yi shiru". Sumayya ta ce"Ban gane ba Yallaɓai, mutum mai laifi kuma ace kar a faɗi waye? Ba ka ga irin illar da aka yi masa ba ne, ga karaya ga rauni, da ya kashe shi fa?" Ya ba ta amsa da "Da ya kashe shi, bakinki zai iya sakawa, ki ɗauki hukuncin da za ayi masa na kisan" daga nan suka juya suka fice. Mamaki ya mamaye sumayya, ta ce "Kai kuwa bawan Allah, waye wannan shi kuwa, da har jami'an tsaro masu kaki, za su hana bayyana laifinsa, ana sane aka ƙi kama shi kenan?" Malam lawan ya ce "Ba zaki ja mini masifa ba, ki fita ki bar wurin nan, na ji da masifa ɗaya, bayan ɗinkin nan a karye nake wallahi" Cikin tsananin naci, da son samun rahoto, ta kwantar da murya za ta lallaɓa shi, ta samu labari, amma da likitan da ƙaninsa suka koreta daga ɗakin. Fitowa ta yi, tana ta mamakin abun da ya faru, yaya za ayi hukuma ta bawa mai laifi kariya, wane irin abu ne haka?. Ba ƙaramar makara ta yi ba, amma tunanin abun da ya faru, ya fi ɗaure mata kai. *** Sannu a hankali yake yi wa kansa allura, yana yi yana fatan samun abun da yake so, a hankali ya gama ɗurawa jijiyarsa ruwan allurar da yake fari tas a cikin sirinji, bayan ya kammala tsaf ya fara jin kansa yana yi masa nauyi. Take idanunsa suka yi mitsi-mitsi, ya soma lanƙwasa kansa, yana jin idanunsa kamar za su fito waje, suna yi masa yaji, a haka ya kunna sigari, ya kashingiɗa, ya na bawa sama hayaƙi,yana jin yadda jikinsa ke son bijirewa aikin allurar. Wayarsa ce ta fara vibrating, ya miƙa hannu, ya ɗaukkota ya duba, yana zaton ko a cikin yaransa ne, sai dai ya ga private number ce. Har zai ƙi ɗagawa, sai kuma ya ɗaga ya saka a kunnensa, amma bai yi magana ba. Daga cikin wayar aka ce, "Meyasa ba ka gajiya da neman magana ne? A wannan karon ma sai da ka saka na yi abun da na goge ɓarnar da ka yi, yakamata ka nutsu Aminu" Ya saki hayaƙi, tare da ɗan kaɗe tokar da sigarin ta tara, sannan ya ce "Waye kai? Sannan waye ya saka?" Mutumin yayi dariya, ya ce "Mutum mai ba ka kariya, domin cimma nasa muradin, yakamata ka sauƙaƙa mini aiki, ka daina aikata abubuwan da za su din ga barin trace a kan ka". "Ka yi muguwar kasadar ƙoƙarin cimma burinka da mutum irina, kar ka manta viper ake yi mini laƙabi da shi, macijin da ya fi kowanne hatsari, idan ka bari na sare ka, ka gama yawo" yana gama maganar ya cillar da wayar, ya ɓata fusaka kamar ya fashe da kuka. Cikin fusata ya ce "Ni again? wani ya kuma amfani da ni? Impossible zan watsa dafina a in da ya dace da in da bai dace ba, sai na tabattar da danganawa ga kunyar ƙarshe, ko da kuwa za ayi mutuwar kasko" ya yinƙura da nufin ya tashi tsaye, amma ya kasa sarrafa gangar jikinsa, hakan ya tilasta masa komawa ya nemi wuri ya kwanta. Duk da irin faɗan da sumayya ta sha a wurin aiki a kan makara, bai dame ta ba, jikinta sai tsuma yake saboda ta zo da rahotanni masu muhimmanci da ɗaukar da hankali. Ofishin head of news ta je, ta shiga da sallama. Matar ta ɗago ta amsa mata da ƙyar, ta ƙarewa sumayya kallo, ta ce "Yanzu ne lokacin shigowa aiki ko? Gaba ɗaya yaran yanzu ba kwa ɗaukar aiki da muhimmanci, kodayeke karatun ma ba wani na kirki ku ka yi ba, duk da satar amsa ku ke gamawa. Ki shiga hankalinki kafin na kai maganar nan wurin MD" Sumayya ta risuna ta ce "Afuwan anty, in sha Allah ba zan sake ba, na samu wasu rahotanni ne masu muhimmanci, da ya san na tsaya a hanya, shiyasa na makara na kawo miki a tantance ne ko za a saka su a news" A yamutse matar ta ce "Na menene" cikin farinciki da jin ƙwarin gwiwar ta yi abun arziki ta fara da gaya mata abun da ya faru a asibiti. Amma matar sai cewa ta yi"Amma ba ki da hankali ko? Ta yaya zamu saka wannan shirmen a news?" "Anty ai a rahotanni, ko a janyo hankalin hukuma.... "Dalla yi mini shiru, business mu ke yi a nan mu, ke fa iyayinki da rawar kanki yayi miki yawa sumayya. Meye hujjarmu idan aka tsutsiye mu, cewar hukuma na ɓoye mai laifi?" Sumayya ta ce "Wallahi a gabana aka yi, mutumin yana nan a emergency" "Kin ga idan ba ki da abun faɗa, fita ina da abun yi" Sumayya ta yi iya ƙoƙarin ta, ta danne abun da yake taso mata na fushi ta ce "To shikenan, sai kuma akwai abun da na gani, ina kan hanyar tahowa nan, a nan wajen gari, an tsinci gawar yaro an cire masa wasu sassan jikinsa". "Almara kenan, wa zai yadda da wannan zancen?" "Ba zance ba ne ba, na yi recoding ɗin maganar wasu daga mutanen da suka fara cin karo da abun". "Sumayya, ba irin wannan labaran mu ke buƙata ba dan Allah, je ki su murtala sun fita neman rahotanni, ki din ga kawo sensitive abubuwa" Summaya ji tayi wata irin ashar na kai komo a wuyanta, da take ƙoƙarin narkawa matar nan, ta rasa abun da ta yi mata, haka kurum ta tsane ta. Ta yi ta kyararta ba ta son ta ga tayi wani abu na cigaba. Sumayya ta fice daga office ɗin kamar ta yi kuka, ta koma reception ta nemi wuri ta zauna. Ba uwar da ta tsinana a aikin yau, tun da head of news department ta yi mata wulaƙanci. Kasancewar a makare ta je, ya sanya lokaci yayi gudu, Lawisa, wato head of news ɗin, ta din ga shiga tana fita, ta na kaiwa tana komowa, idan ta kalli in da Sumayya take sai ta haɗe rai. Wannan karon bayan ta fita, a tare suka shigo da managern director, sai karairaya take yi masa, tun da ya shigo ma'aikatan suke ta gaishe shi. Ban da sumayya da ɓacin rai ya saka ta cika ta batse. Sai da yayi gyaran murya ya ce "Wannan ba sabuwar staff ɗin mu ba ce? Ya na ganki a nan? Wane department aka kai ta ne?" Lawisa ta yi caraf ta ce "Sir ba ta da ƙwarewar aiki ne haryanzu, ana ɗan nunnuna mata aiki ne, kafin ta gama gogewa". Ya ce "Ok, babu laifi" sumayya kamar ta kwaɗawa lawisa mari, a fusakarta da ta sha uban bleaching, duk tayi taruwar jini. Ta daure ga gaida MD, sannan suka wuce gaba. Tsaki Sumayya ta ja, tana duba wayarta. Sai dai jin sallamar Nabila a reception ya sanya ta ɗago da sauri tare da amsa mata. "Ya na ganki a nan?" Nabila ta ce "Ke baki iya karrama baƙo ba ko?" Ta tsaya suka gaisa da admin ɗin da ke reception, sannan ta ƙarasa kusa da Sumayya ta zauna. "Arfa, ya na ganki yanzu ne? Lokacin tashi daga aiki bai yi ba?" "Kema ya na ganki a nan kamar mara galihu, ke baki da office ɗin da zaki zauna ne? Ki zo chambermu ki ga ofishin da aka bani hajiya, kamar wata sarauniya" Sumayya ta ce "Eh ofishin da baki damu da aiki ba ko, sai sun dawo da ke gadin chamber tukuna". Nabila ta yi dariya ta ce "Kin san wani abu, wai nan aikena aka yi, zan je na lallaɓa na zo da wata mata, ko in tattauna da ita, sannan in je shagari firm, zan haɗu da wani lawyer, kuma ni wallahi kaina ciwo yake yi" Sumayya ta kalleta ta ce "Ba zaki ba kenan?" "Ai faɗa ma ɓata baki ne, sumayya wurin nan naku mai kyau, tashi ki rakani na zaga" duk da ran sumayya babu daɗi, amma ganin Nabila ya sanya ta jin sanyi a zuciyarta. Suka shiga zazzagawa, ta kaita news room, sai dai su na buɗewa suka tarar da MD da lawisa a ciki, suna aiki. Sumayya ta risuna ta ce "Am sorry sir, ban san ku na ciki ba, Arfa mu je ki ga.... "A'a tsaya mana na ga nan ɗin, Nabila ta shiga cikin fara'a ta ce "Yallaɓai ina wuni?" Shima cikin fara'ar ya ce "Lafiya ƙalau, ya ki ke?" "Lafiya lau sir, ina fatan ba zan takura muku ba, ina son sanin abubuwan da ban sani ba a rayuwata, mussaman wanda ba field ɗina ba, sister ina wuni?" Tayi maganar tana kallon lawisa da ta yi bala'in haɗe rai. Lawisa ta takurawa Sumayya ne, saboda tana ganin ƴar gayu ce, ga ta baƙa amma baƙinta mai kyau ga ƙwazo, tana gudun ta ƙwace mata matsayin ta, kuma ita bazawara ce, a da a wurin babu wanda ya kaita gayu a wurin, amma yanzu sumayya ta fita. Yanzu kuma ga Nabila, ita da take da hasken fata ma sosai. Nabila ba ta san lawisa ta amsa ko ba ta amsa ba, ta ja kujera ta zauna, tana yi wa MD tambayoyi, a kan abubuwan da suke cikin news room ɗin. Lawisa ta ƙulu,ta din ga harar Nabila, amma ko a jikinta, ita kanta sumayya sai da haushi ya kamata abun da Nabilan take yi. Nabila ta ce "Yallaɓai, ko zaka saka mini lambarka, idan wani abu ya kama na aiki, zan iya taimakawa i am barrister Nabila Yusuf" Ya ce "Wow, what a very young and beautiful barrister, kin zama lawyer da ƙananan shekaru, ya karɓi wayar Nabila, ya saka mata lambarsa, ta tashi ta yi musu sallama. Sumayya kamar ta yi bindiga, su na fita ta din ga ɗurawa Nabila ashar, a kan abun da ta yi, tare da gaya mata alaƙar Lawisa da kuma MD. Nabila ta ce "Sumayya, dan Allah kar ki ɓoye mini, idan yana da kuɗi na ci rabona, na ga zai yi son mata" Ganin Nabila na neman mayar da ita mahaukaciya, sai ta canza maganar. "Ke kin san menene? wai ni zan kai rahoto har kashi biyu, sakaryar matar nan ta ce ba za a saka ba, wai ba sa buƙatar irin wannan labarin, MD ya tambayi me nake yi a reception ba na aiki, wai ta ce masa ban iya aiki ba, na rasa uban da na tsare mata ta tsane ni, dama ni na samu damar da ake baki, a wurin aiki, in yi wata shida ina aiki a wurin, wai ban iya aiki ba, da yake kwanan nan ya dawo daga ƙaro karatu, tun da aka ɗaukemu ya tafi". Maimakon Nabila ta tausaya mata, sai ta hau dariya, "Ai kawai ki fara soyyaya da MD ko ta bala'i, shi ne zaki rama". Sai da ta ga Sumayya ta yi fushi sannan ta ce "Sorry my sumy, maganar gaskiya babu daɗi, kuma kishi take da ke kuma tana ƙoƙarin kare abun da take so, shikenan" Idon sumayya ya tara hawaye ta ce "Sai kuma ta din ga daƙile ni a harkar aikina? Ta yi mini adalci kenan?" Nan ta ba wa Nabila labarin abun da ya faru, daga fitowarta daga gida, zuwa yanzu. Nabila ta ce "Na shiga uku, sumayya me ƙasarmu ke son zama ne? A zahiri an nunawa mutane ana neman mai laifi, a baɗini kuma hukuma na ɓoye shi? Duk yadda ake fama da ƴan daba da masu ƙwace a garin nan, tirƙashi ana maganin ƙaba kai yana daɗa kumbura, ke ba ki san sunan wanda ya yi laifin ba?". Sumayya ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, bai faɗa ba, korata ma suka yi". "Mu ƙarasa titi mu tari napep mu je asibitin, mu tattauna da shi mutumin, ni kin san ba na tsoron a mutu ko a yi rai. Sannan zan je na samu Yaya Nasir na yi masa maganar wannan ai abun kunya ne" Sumayya ta girgiza kai ta ce "A'a, na tsorata da kashedin da aka yi mana, a bar zancen kawai, ban san suwaye mutanen ba". Nabila ta ce "Wallahi sai mun je, akwai wata shashasha da ta isa ta hana ki cigaba a rayuwa, idan ma ba a saka radiyo ba, sai mu kwatsa a media ina da mabiya sosai a social media, sai ayi duk wadda za ayi.!!!" Ayshercool 08081012142 [7/18, 2:10 PM] null: ⚔️*ƘARFE A WUTA ⚔️ *AISHA ADAM (AYSHERCOOL) https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Page 4 "No Nabila, abun da ki ke yi is too risky, mutanen nan da gaske suke, they mean what they said, kar ki jefamu a matsala" Nabila ta ce"Karatunki ya tashi a banza kenan sumayya? Idonki har da hawaye saboda takaici. Wasu lokutan kin fiye sokwanci sumayya, da ni ce da tuni na ci buhun ubanta". Sumayya ta ce "Ni ce sokuwa ko? na gode amma ni ba zan iya kasadar da ki ke yi ba, na rasa aikina, but wait mu je na rakaki in da aka aike ki mana" Nabila ta ce "Wa? Taɓ tuni na kira MD na bashi uzuri, dama barrister Habib ne ya aike ni, yadda wannan matar ta wurin aikinku take, lawashi ko lotion take, haka yake yi mini, ba ya ƙaunata" "A'a, naki ya sha banban da nawa Nabila, shi taimakonki yake yi ai" Nabila ta kwaɓe fuska ta ce "Ke, idan fa kin ga ina zuƙewa a aikin nan, wanda za a kare ba shi da gaskiya ne, MD zan saka ya canza mini team daga na su Barrister Habib, na Barrister Bashir nake so, wata zazzafar shari'a za su kara, shari'ar manya ce, a kan kuɗi, zuwa zan yi na sha kallo, kuma an ce akwai yiwuwar na haɗu da masoyiyyata kwanan nan" Sunayya ta ce "Wa kenan?" "Anty Naja'atu Bunkure mana, kin san am die hard fan of that woman, Barrister Naja'atu duniya ce, ga gayu malam, harshenta akwai turanci, kamar wadda aka haifa royal palace ɗin Elizabeth" Sumayya ta yi tsaki ta ce "Aikin banza ƴar wahala, ita ta zama abun da ta zama a harkar aiki, har tana burgeki, ke kuma kina zaune kina shashanci, wallahi ƙarshe ki koma ƴar ɗaukar jakarta" Nabila ta ce "Kan uba, degree holder in yi dakon jaka, Kin ci mutuncina fa, Sumayya ta girgiza kai, haryanzu Nabila shirirta da yarinta na damunta. Ko da Nabila ta je gida, tun a tsakar falo take tambayar magajiya, ina DSP. "Bai dawo daga aiki ba, na ji ɗazu yana cewa ko za su je ringin" Nabila ta ce "Aikuwa ya yi ya dawo, sun bayar da maza, in mun zauna ya yi ta cewa police ya fi lawyer, yau zai sha kunya idan ya ji me suka yi. Yau zazzafan debate ne tsakanina da shi, har lemo zan yi mana aji daɗin yin musu" Anty ta ce "Ka ji mashirirciya, musun da za ku yi za ki haɗawa lemo?". "Eh mana, ɗan sanda sharri, lawyer kuma musu" tayi maganar tana dariya. Wani mugun kallo mama ta yi mata, yaran gidan nan har take suke yi wa Nasir da discipline master, saboda yadda suke jin tsoron sa, amma tsakaninsa da Nabila sam ba haka bane ba, suna good time sosai da Nasir, kuma duk gidan bayan Abba ba ta da abokin hira ko shawara sai shi. Nabila ta share mugun kallon da maman ke yi mata, ta tafi ɗaki. Misalin ƙarfe huɗu na yamma, Sumayya ta ga kiran lawisa, kawai ta basar ta cigaba da kallon tv, ta kira ya kai sau huɗu sannan ta ɗaga. "Ki na ji ina kiran waya ki ka ƙi ɗagawa?" "A silent take, bacci nayi ne". "Ki tura mini recodings ɗin nan, su murtala ba su sami wani samo rahotanni masu muhimmanci ba, kuma na ga su Mikiya radiyo duk sun wallafa labarin yaron nan, ki turo mini mu ga wanda za a iya tacewa a saka" Sumayya ta taɓe baki ta ce "To" Ta kashe wayar, ta ce "Allah ya ƙara, da mu muka fara sanar da labarin, kuma mu ka saka a internet, ai da ya fi, tun da ni ce ƴar jarida ta farko da ta fara zuwa wurin, amma ki ka ƙi" Ta lalubo lambar Nabila ta kirata, ta gaya mata abun da ya faru. Nabila ta ce "Amma baki da wayo sumy, ke yanzu sai ki tura mata, saboda ba ki da zuciya?" "To yaya zan yi mata?" "To amma kin san ko kin tura mata, sunanta za ta faɗa a mai rahoton ko wanda ya karanta ba ke ba ko?" Sumayya ta ɗan yi shiru ta ce "Kuma fa haka ne" "To tun wuri ki ce mata kin goge kawai, gobe ba za ta ƙara yi miki wulaƙanci ba". Sunayya ta ce "Haka za ayi, na gode sosai" cikin hanzari ta kira Lawisa, ta sanar mata da cewa ba ta ga recordings ɗin ba. Aikuwa ta hau ta da bala'i, Sumayya ta danna recording tana dariya ƙasa-ƙasa da niyyar ta turawa Nabila. Bayan sun gama wayar, ta turawa Nabila, suka din ga dariya, Nabila na ƙara bata ƙwarin gwiwar, kar ta sake ta ɗauki raini ko wulaƙanci daga wurin lawisa. Ta kuma cigaba da lallaɓa sumayya, a kan lallai ta koma asibiti, ta sake tattaunawa da mutumin nan, ko iya sunan mai laifin ta samo. Barrister Habib ne ya shiga office ɗin MD, ya zauna suka gaisa, cikin takaici Habib ya fara magana, "Barrister, ni fa na gaji da iskanci yarinyar nan, idan a team ɗi na za ta zauna, ta zauna, kuma dole ta yi biyayya ga abun da na sakata, idan wurin Bashir za ta koma, ta koma na gaji da iskanci da rashin mutuncin da take aikatawa, ba ta san aiki ba ko kaɗan" MD ya ce "Calm down Habib, na sani wallahi, na san ku na haƙuri da ita, wallahi nima nauyin mahaifinta nake ji ne, abun da yayi mini a rayuwa idan na kore ta ban yi wa kaina adalci ba, shi ma yana yawan bani haƙuri a kanta, marainiya ce kuma ba ta da cikakkiyar lafiya." "Mu ma duk marayun ne ai, waye yake iskancin da take yi? Ta zo lokacin da ta ga dama ta tafi lokacin da ta so, she's not serious at all" "Na sani, kuma nima ina gani, ka rabu da ita, duk wani abu da za ku yi ku daina sakata a ciki, ƙyaleta da bashir ɗin, shi ne daidai da ita, ku yi haƙuri dan Allah" MD ya din ga lallaɓa Habib, dan ba zai so rasa gogaggen lawyer kamar Habib a law firm ɗin sa ba, a kan Nabila da ba aikin ne a gabanta ba. Yau weekends ne, gaba ɗaya iyalan major na babbn falo, kowa ya ja nasa wuri yana karyawa, Nabila ce kawai babu a wurin. Tun yana jurewa ya kasa, yayi gyaran murya ya ce "Ina arfa ne?" Anty ta ce "Bacci take yi" Ya kalli walida ya ce "Tasota, ta fito ta karya, sai an cinye an bar ta, ta cikawa mutane kunne da kuka" Kusan mintuna goma da taso ta, sannan ta fito, kayan bacci ne a jikinta, dogon wando da rigarsa har gwiwa, kanta babu ɗan kwali. Nasir ya tsura mata ido, ko ƙiftawa ba ya yi. Abba ya ce "Ina kallabinki? Ki ka fito da wannan gashin ba kyan gani, kamar totuwar masara?" Ta saka hular hannunta ta ce "Haba Abba, dan daga bacci na tashi ne fa" "Tafi can ƙazama, kullum kai babu kitso, ba za a rasa kwarkwata a wannan gashin ba" dariya aka hau yi mata. Ko a jikinta, ta zauna kusa da Abba, ta kalli Nasir ta ce "DSP, yaushe ka dawo ba labari, ya hanya?" Ya jinjina kai ya ce "Alhamdilillah" Major da kansa, ya taya Nabila haɗa shayi, ga soyayyen dankali, ga bredin ta, amma tana buɗe bredin ta ce ba za ta ci ba, kwantai ne. Major ya miƙa mata nasa ya ce "Duba zaki iya cin wannan? Dankali kawai ba zai riƙe miki ciki ba" ta duba buredin Abban ta ce "Eh wannan sabo ne, Abba ka ƙara mini ƙwan, ni ba na son dankalin ma" Ya ce "To shikenan, ɗauki nawa da ma ni yanzu ƙwai bai dace da ni ba, a shekaruna" Idan da sabo, sun saba da ganin irin wannan fifikon da major yake nunawa, duk da mutum ne mai ƙaunar yaransa sosai da sosai, amma son da yake yi wa Nabila na musamman ne, amma fa hakan ba ya hana idan suka yi laifi, ya hukunta su kamar ba ƴaƴan cikin sa ba. Anty ta ce "Arfa ba zaki bari Major yayi ƙiba ba, kalli yadda ki ke tara mazaunai, saboda ci" Yayi murmushi ya ce "Tafi kowa girma a gidan nan" Nabila ta ce "Abba, Allah ya ƙara arziki, ka yi ta sayowa mu na ci" "Amin arfan Abba" Nasir ma ya juye mata nasa ƙwan, ta tattare tana dariya, dan ta na son ƙwai sosai. Mama kuwa kamar za ta yi bindiga, saboda baƙin ciki. Bayan an kammala cin abinci, su walida ne suka kwashe kwanukan da aka ci, Nabila kuma ta hau labartawa Nasir, abun da ya faru da sumayya da ta je Asibiti. Fafur Nasir ya ce ƙarya take yi. Ta haɗe rai ta ce "Yaya, wai meyasa a duniya jami'an tsaro ba kwa yadda kun yi laifi, ko wani ne daga cikinku yayi, sai kun ƙaryata, kun kare mutum" "Wa ya gaya miki hukuma tana laifi?" "Ba mutane ne hukunar ba? Ai mutane na laifi, kuma hukuma ma suna yi, wallahi da gaske nake, ka bincika ka ji kuma, koma na kira maka sumayyan" Ya ce "A'a ai ƙarya ki ke yi, ni zaki zauna kawai dan ki ƙure" Duk yadda ta so, ta fahimtar da shi, amma ya ƙi fafur. Abba dai kallonsu kawai yake yi yana dariya, ganin ba zai yarda ba, ya sanya ta ƙyale shi, ta koma wurin Abba. "Abbana" tayi maganar tana ɗan murmushi. Abba ya ce "Kuɗi zaki tambaya kenan?" Ta girgiza kai ta ce "A'a Abba, abu zan tambaye ka" "Ina jin ki" "Abba dama, wata amarya ce, suka kira ni a waya, zan je gida na yi musu make up, ita da ƙannenta na biki, za su biyani, VIP ne har gida" Haɗe rai yayi sosai sannan ya ce "Me na gaya miki a kan wannan sheɗancin? Kin san na hana ki sabgar banzar nan, ban da kalen sheɗanu jikinku, me wannan shashancin zai amafana miki, na fuskanci kin fi fifita wannan kwalliyar a kan aikinki, to babu in da za ki je". "Dan Allah Abba, wallahi zan samu kuɗi fiye da salaryna, dan Allah" "Ba in da zaki, tun da babu abun da ki ka rasa a gidan ubanki, ba matar da zaki bi gida ki na shafawa hoda, idan ta matsu tayi da kanta mana, banda shashanci ace mace ta zauna sai an bita gida shafa mata hoda da gazar" "Abba!" "Shut up" yayi mata tsawa, hakan ya tilasata mata yin shiru. Walida kuwa faɗan Abban dariya ya bata, wai idan sun matsu su yi da kansu, ba wadda za aje gida shafawa hoda. Nabila ta din ga jin ko a ɓoye sai ta je, tana son sana'arta ta kwalliya, Abba kuma ba ya so, wai shashanci ne da fatan aljanu, ita kanta idan tayi a fuskarta wasu lokutan, ya din ga faɗa kenan. Akwai ranar da za ta je biki, ta yi kwalliya ta saka eyelashes, ya kirata dan ya ga meya samu idonta, gashin idonta yayi tsawo haka, tun da ta ce masa sawa tayi, ba ta ankara ba, ya saka hannu, ya fige shi sai da ya haɗa da gashin idonta, ya ce ya kuma ganinta da shi sai ya zaneta. Har a gaban saurayi, ya taɓa korata gida, wai ta je ta wanke fuskarta, ba za ta cuci ɗan mutane ba, duk ta damalmala fuska da hauka, ta zama kamar wata bebin roba. Ta rasa meyasa Abba yake adawa da sana'ar nan tata. Nabila tun a weekend, take cigaba da zuzutawa Sumayya trial ɗin da za su je, kotu ranar laraba, farincikin ta ya kasa ɓoyuwa, wanda hakan ya samo asali ne, da yadda ta ga Barrister Habib ya ƙyale ta, ta koma team ɗin Bashir, kuma ta samu labarin barrister Naja'atu ma tana da shari'a ranar a kotun, dan haka za ta haɗu da ita. Nabila uniform ɗin ta, tamkar su yi magana, saboda ɗaukar guga, ita kanta a bar kallo ce a cikin kayan, ba fara ce tas ba, amma haskenta mai kyau ne da ɗaukar hankali, domin kuwa jikinta kamar ƙwai, dan tana kashewa Jikinta kuɗi ba kaɗan ba, ba ta da wata damuwa, ba abun da take yi da kuɗi, ban da sayen kayan gyaran jiki, ta samu kuɗi a aikinta, major ya bata, Nasir ma ya bata, ga wanda take tatsar samari, ga ƴan sana'ointa, dan haka kuɗi sam ba matsalarta bane ba. Barrister Naja'atu Bunkure matashiyar lawyer, mai dakawa maza gumba a hannu, karo da ita sai lawyern da yake jin kansa ya isa, dan abu ne mawuyaci case ya shiga hannunta ba ta yi wining ba. Ana yawan sanar da ayyukan alkhairin ta, a gidajen rediyo na taimako da tsayawa marasa galihu a kan shario'i daban-daban. Bakin Nabila ya ƙi rufuwa, ganin yau ga ta ga Barrister Naja bunkure, wata ƴar gayu da ita, yadda ta gabatarwa da kotu kanta kawai, ya isa ka tabattar da ta san me take yi, ga yaren nasara a harshenta wato turanci. Gaba ɗaya hankalin Nabila ba ya kan shari'ar, yana kan bunkure, da yadda take magana. Murna kamar nabila ta taka rawa, yau ga ta ga mentor ɗin ta. Sumayya ta samu damar editing news yau da kanta, kasancewar MD yana ta mitar, ta daina ware kanta, ta din ga shiga ana aiki da ita a haka za ta goge. Kiran Nabila ta gani, dan haka ta ɗaga ta ce "Kiran me ki ke yi mini ina aiki?" Sama-sama ta din ga jiyo numfashin Nabila, muryarta ƙasa-ƙasa ta ce "Kin tashi daga aiki ne?" "A'a menene meyafaru?" A galabaice ta ce "Na dawo chamber ne, na ɗauki kayana, ina hanyar komawa gida, ji nake kamar ciwona ne zai tashi, ina titi dan Allah Sumy ki zo" "Subhanallah, gani nan zuwa amma babu wani a wurin da zai kai ki gida?" "Ni ba na son damun kowa, dan Allah besty ki zo, kar na mutu a titi" Ganin ta gama abun da take yi, ya sanya a gurguje ta ɗauki jakarta, ta fita, ba ta tsaya ko ina ba, sai hanyar wurin aikin su Nabila, tana ta rarraba ido a titi tana kiran wayarta. A kan wani tudu ta hango Nabila, idanunta sun yi jawur, da alama tayi kuka sosai da sosai. Ta ce "Mai napep, bari na ɗauketa ka kaimu gadon ƙaya dan Allah, ba ta da lafiya" Ya ce "To shikenan" ta sauka ta rungumo Nabila, ta taimaka mata, ta shiga napep ɗin, sai dai babu baki, sai numfashi take sama-sama. "Arfa, meyafaru an ɓata miki rai ne?" Ta girgiza kai alamar a'a. "To menene? Haka kurum ciwon ya tashi" buɗe baki ta yi, da nufin yi wa sumayya masifar ta ƙyaleta, amma ta ji numfashin ta, zai gudu ya bar huhunta, hakan ya sakata yin shiru. Can kuma a hankali ta ce "Sumayya mu je gidanku, wurin umma" Sumayya ta jinjina mata kai, haka aka yi. umman sumayya na ganinsu hankalinta ya tashi, Nabila ta samu wuri ta kwanta. Umma ta ce "Sumayya, me aka yi mata ne?" "Wallahi umma ban sani ba, kawai kirana ta yi a waya, ciwonta ya tashi" Cikin kuka Nabila ta ce "Umma dan Allah ki yi mini addu'a, ki ƙyale sumayya" Umma ta ce "To shikenan" ta din ga tofa mata addu'a, har aka samu ta yi bacci. Bayan awa ɗaya da rabi, ta farka, har ta samu ta ci abinci ta yi salla, umma ta din ga tambayarta, ko wani abun aka yi mata, amma ta ce a'a. Ganin ta ware, ya sanya umman basu wuri, Sumayya ta sake kallonta ta ce "Ke, wallahi wani abu aka yi miki, yanayinki ya nuna mini, kin ga idonki kuwa, ki gaya mini menene?" Tayi ajiyar zuciya ta ce "Sumy, ashe haka ake ji, idan aka wulaƙanta mutum mussman a gaban jama'a, a dizaga ka" "Menene? Waye ya wulaƙanta ki?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Kin san Naja'atu Bunkure?" "Ba dole na santa ba, a wurinki na santa ai" "Ashe matar nan tsinanniya ce" Da sauri sumayya ta ce "A'uzubillahi, me yayi zafi, mentor ɗin taki?" Nabila ta ce "Zilwajahiani ce, abun da muke ji a kanta daban, yadda take daban. Yau muka haɗu a kotu, kin san ina cikin team ɗin barrister Bashir, tare muka je court yau. Bayan an fito, jiki na tsuma na bita, ƴan jarida sun baibayeta, na yi mata magana kin ga wulaƙantaccen kallon da tayi mini? Ba shi ne ya dame ni ba, duk da uniform ne a jikina, na cire girman kai na gabatar mata da kaina, a matsayin lawyer mai koyi da ita, amma still ban isheta kallon kirki ba. Abunka da zuciya da abun da take so, na matsa tare da miƙa mata wayata, a kan ta bani lambarta, sai ce mini ta yi ba za ta bayar ba, kar na isheta da kira. Na ce mata bakomai, a matsayina na mai koyi da ita, kuma mai ƙaunarta, dan Allah ko mintuna uku ta bani, na daɗe ina burin haɗuwa da ita. Ina son ta bani shawara a matsayina na lawyer mai tasowa, kuma ta bani tips da zan bi, na zama kamarta a rayuwa, dan ina son ta da irin ayyukan da take yi. Ta ƙare mini kallon baki isa ba, sannan ta ce 'Ki zama kamar ni kuma? Taka matsayin da na taka? Never! Don't even give a try, ba zaki taɓa zama ba, and leave my way please, ina da abun yi" Haka fa ta ce mini, a gaban mutane da masu yi mini dariya, da masu yi mini Allah ya ƙara wai neman suna da gidin zama ne ya janyo mini, wasu kuma su ka bani haƙuri wai haka halinta yake. Sumayya yau na tozarta, an wulaƙanta ni, duk yadda nake ganin ina da class, soyayya ta rufe mini ido, saboda ina ƙaunar matar nan fisabilillahi, wallahi da ƙyar na ƙarasa chamber, nan da nan na fara jiri, numfashina ya fara sama, kin ga dariyar da aka yi mini, wallahi na muzanta fiye da tunaninki" Sumayya ta ce "Nabila jikina yayi sanyi, ban taɓa zaton matar nan za ta aikata haka ba, wai meyasa mu mata, galibin mu ƴan baƙin ciki ne? Wato ba zaki zama kamarta ba, sai ka ce wayo da dabararta ne suka ba ta matsayin da take kai". "Wallahi sumayya, ko zan rasa raina, ko da kasada, sai na tabattar da na yi suna nima, sai dai idan Allah ya ƙaddara na mutu. Amma ina roƙon Allah, in sha Allah tana raye, sai na ɗaukaka fiye da tunaninta, kuma bibiyarta zan din ga yi, da bibiyar duk wani abu da ya shafe ta, sai na rama abun da ta yi mini. I will do a background check on her" "Ke fa baki iya ɗaukar abubuwa da sauƙi ba, ki ƙyaleta mana kanta ta yi wa, ni na ce me?, abun da nima ake yi mini, ni kusan kullum ake yi mini, ke yau ne kawai, kuma arfa matsayi na duniya ba na kiyama ba" Nabila ta girgiza kai ta ce "Wannan ke ki ka ga zaki iya, kuma ƙaramar alhaki ce ta wurin aikinku, wannan kuwa dizgin da ta yi mini, in sha Allah rabbi, sai na rama shi, dole na ajiye shirme, na mayar da hankali a kan aikina, ko dan fansar nan, kut wallahi matar nan ta gama cuta ta, kuma ba zan huce ba har sai na rama wallahi. Rakani titi in tafi gida" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin tashi tsaye. Sumayya ta danƙota ta ce "Nabila ki din ga sanyawa zuciyarki salama mana, kin fiye zafin rai, ki bi komai a hankali, kalli yadda ki ka kusa kashe kanki a banza. Idan Allah ya yi nufin ɗaukakaki fiye da ita, ita ɗin banza ta hana, dan Allah ki manta da ita, ki cigaba da rayuwarki". Ta kalli sumayya cikin takaici ta ce "Lallai ma sumayya, dan ba ki ga abun da ta yi mini ba, a gaban mutane har da masu yi mini dariya. Ni gaba ɗaya ma ji na yi ban yarda da ita ba, abun da ake faɗa a kanta daban, abun da na gani yau a kanta daban, akwai wani abu a ƙasa, and i will run a background check on her, for the first place ma, wacece ita? Idan ta kama har bunkuren zan je mahaifarta, meyasa abun da ake faɗa a kanta daban, ita kuma halinta daban". Sumayya ta ce "Na shiga uku, Nabila" kafin ta yi magana, Nabila ta yi waje, ta tarar da umman sumayya na salla, ta ce Umma na tafi, ta fice daga gidan. Sosai abun da ya faru ya tsayewa Nabila,da ta tuno abun sai wani irin takaici yakamata. Yau ba kowa ya san ma ta koma gida ba, dan yau babu surutu da hayaniya. Abu kamar wasa, har dare Nabila ta kasa walwala, ko fitowa daga ɗaki taƙi yi, gani take kowa yana kallonta zai gane an dizgata yau, duk iyayin na ta da jan ajin. Nabila irin mutanen nan ce masu saka abu a ran su, dan haka ko ta yi niyyar manta abun da ya faru, sai ta kasa. Ta ɗaukko wayarta, ta kunna data, ta tarar da messages ɗin sumayya, ta na ta yi mata faɗan ta yi haƙuri ta manta da abun da ya faru. Nabila ta yi mata reply da "You are not serious, ki saka ido ki yi kallo" Social media ta hau, ta shiga searching ɗin sunan barrister Naja'atu Bunkure, nan da nan sai ga hotunanta, da wasu daga cikin ayyukanta na jin ƙai, sai dai ba ta samu wani cikakken bayani da take son samu a kanta ba. Tsaki ta yi, bayan tuna yadda take mutuwar son matar nan a baya, har hotonta take sakawa a dp ɗin ta, saboda yadda take ƙaunarta, amma lokaci ɗaya a yanzu ji take yi, ba ta da wani maƙiyi idan ba ita ba. Har sha biyu da rabi na dare, ba ta samu cikakken abun da take son sani ba, sai ma zarge-zarge da suka din ga ɗarsuwa a ranta game da matar. Saukkowa ta yi daga kan gadonta, ta fice daga ɗakin, fita tayi can babban falo, ta nufi kitchen ta samu abun da za ta ci, dan yunwa take ji sosai. Fridge ta buɗe, ta samu ruwa mai sanyin gaske, da coc ta fito falo tana sha. Hasken fitila ta hango a baranda, ba a kashe ƙwan wurin ba, ga abba kullum sai yayi magana a kan rashin kashe kayan wuta, kafin a kwanta bacci. Wurin ta nufa, da niyyar ta kashe ƙwan, ta na zuwa ta leƙa, ta hango nasir a kan kujera, yana ta danna system. Ta window ta je ta zura hannu, tana taɓa masa kunne. Caraf! Ya riƙe hannun ba tare da ya ɗago ba. Tayi dariya ta ce "Shi ne ba ka tsorata ba" "Me ki ke tunanin zai razana ɗan sanda?" Ta ce "Ai dai ɗan sanda mutum ne, kuma na san ka ji tsoro mazewa ka yi" Yayi murmushi ya ce "Tsoro sai lauyoyi" Ta buɗe ƙofa ta fita ta zagaya in da yake ta ja kujera ta zauna sannan ta ce "Duk tsoron lauya bai kai ɗan sanda ba" Ya ɗago ya kalleta, sanye cikin kayan bacci pink, masu bargo kanta ko ɗan kwali babu, tayi parking ɗin gashinta" Murmusawa yayi ya ce "Ke kin san babu tsoro ga wanda yake riƙe makami, yayi yaƙi da ɓarna" "Hmm, yi dai a hankali, dan harshe ya fi makami dafi, kar lauyoyi su baka mamaki watarana" "Ina aiki kin zo zaki dame ni, ina nawa aikin, ina kallabinki?" "Yana ɗaki" tayi maganar tana lashe murfin jarkar lemon hannunta. "Kalli abun da ki ke yi kamar ƴar ƙauye, sai an yi magana ki fara ke barrister ce, ke degree holder " yayi maganar yana mayar da hankali a kan system. Ta numfasa ta ce "Wai aikin me ka ke yi ne?" "Wani aiki ne mai wahala, wanda nasara a kansa, na iya sawa na samu cigaba a aikina". Nabila ta ce "Haba dai, to Allah ya taimaka" "Amin" ya amsa ba tare da ya kalleta ba. Shiri ya wanzu na wani ɗan lokaci, sannan ta ce "DSP" "Na'am barrister" "Sannu da aiki" ya ɗago ya kalleta ya ce "Kin isheni fa, za ki tashi ki bar wurin nan" "Yi haƙuri, na daina magana" Ya cigaba da aikinsa, ta na shan lemonta, tana jin yadda iska ke kaɗata. Duk abun nan, Abba ta ɗakinsa ya na hango su, sai dai ba ya jin me suke cewa. Can ta sake cewa "DSP" A hasale ya ce "Ke! Meye ne? Tashi ki je ki kwanta dare yayi" "Ni na kasa bacci, raina ne a ɓace". "Ai dama kullum cikin ɓacin rai ki ke, tun da ke a rayuwarki ta duniya, baki da haƙuri tashi ki bani wuri" Ta marairaice ta ce "To ka tsaya ka ji me aka yi mini mana, dan Allah kafin na tafi, ka gaya mini me zan yi, wanda zai saka na yi suna, kowa ya sanni" tayi maganar very serious. Cikin gatse ya ce "Ki nemo in da Aminu Viper yake, ki taimaka mini na kama shi, kin ga sai ki yi suna, ni na samu cigaba a aiki" Ta fuskance shi sosai ta ce "Waye shi, a ina yake? Kamar na taɓa jin sunansa" Ya kalleta ya ce "Shi nake ta aiki a kansa, galibin aikin ta'addancin da ƴan daba suke yi, a wasu shiyyoyin da saka hannunsa, yaransa ne. An ce lallai na kamo shi, tun da yankin da ake ɓarnar ƙarƙashin kulawata yake akwai zarge-zarge a kan guduwa yayi daga prison" "Dan Allah idan na nemo maka shi, zan yi suna, kowa ya sanni?" Kallon baki da hankali yayi mata, ya cigaba da abun da yake yi. "Ka ga riba biyu kenan, na yi suna, kuma ka samu cigaba a wurin aiki, yes! Amma na ji ka ce akwai zarge-zarge a kan guduwa yayi daga prison how? Kun tabattar da hakan ko kuwa? Ka bani hints mana, laifin me ya yi a ka kai shi prison ɗin?". Takalminsa ya ɗauka ya miƙe tsaye ya ce "Tashi ki bar wurin nan, tashi maza" Da haka ya koreta, ta tafi ɗakinsu. Sai dai  da ga koma ɗakinta, ta dinga sintiri a cikin ɗakin, sosai ta ji maganar Yaya Nasir ta shiga ranta, ina ma hakan ta tabatta. "In taimaka masa ya kama ɗan ta'adda, in nemo haƙiƙanin dalilin barinsa daga gidan yari, idan guduwa yayi me ma'aikatan suke yi, idan sakinsa aka yi laifin me yayi, aka sake shi duk da hatsarinsa, na bankaɗo ainihin identity ɗin Naja'atu Bunkure, na gyara career ta, wai ma menene dalilin da ya sa ban zama ƴar sanda ba?, na zama wata lauya yau ka kare mai gaskiya gobe mara gaskiya. Ta yi wani irin shu'umin murmushi ta ce "Accepted DSP Nasir, zan nemo maka Aminu Viper, na bibiyi laifin da ya aikata, da yadda aka yi ya bar prison. Ayshercool. 08081012143 [7/19, 1:11 PM] null:                                     *ƘARFE A WUTA* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION BRIGHT PENS SECOND BATCH. https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 5 Wurin shiru, ba ka jin motsin komai, hantsi yayi, yana zaune a kan wani dutse, yana jin yadda ɗumin ranar ke ratsa shi, dan ba ta riga ta yi zafi ba, hannunsa ɗaya ɗauke da taba sigari, yana ta zuƙa yana busawa, idonsa yayi jawur. "Viper" matashin  ya kira sunansa, yana ta sauke haki. "Ina jinka" yayi maganar ba tare da waiwayawa, ya kalli matashin ba. "An kama ɗan mama da kayanmu fa jiya da daddare, a chamber yamma da gari, yana tsaka da raba kayan ga mutane, kuma wadda aka kama da yawa" Ya saka yatsansa ya ɗan daki jikin sigarin, tokar jiki ta zube, ya ja numfashi ya ce "Wace hukumar ce?" "Masu ƙwaya ne" Ya miƙe tsaye ya ce "Shikenan, kar ka damu, ku bar shi a hannunsu" Ya waro ido ya ce "A bar shi, Ka manta a halin da ake ciki? Idan wani abu ya faru fa?" Cikin takunsa na ƙaƙƙarfan namiji, ya ƙarasa gaban matashin, ya riƙe kwalarsa a hankali sannan ya ce "Ba na butulci walid, ɗan mama ni yake yi wa aiki, dole na fito da shi. Ni ba zan kamu ba, da zan kamu da basu bari na fito ba. Kuma ko a yanzu suna sane suka bar guzuma, suke harbin karsana. Ni na shirya a kama shi, sannan ina son ku je dabar Madaki, ko wurin da yaransa suke, ku tayar da hayaniya, ku zubar da jini, kar ku raga musu ko kaɗan, ko da kuwa hakan yana nufin jami'an tsaro su kama ku" Yayi shiru yana kallon viper. Ya shafi sumar walid, da tayi cibiri-cibiri ya ce "Ya ka ke kallona kamar kana tantama a kaina?" Ya risuna ya ce "Tuba nake mai gida, duk abun da ka ce dole ayi shi, umarninka muke yi wa biyayya" "Good. Idan aka kama ku, ko da mutum ɗaya ne daga cikinku, ku ambaci sunana, ku ce ni ku ke yi wa aiki, ni ne na saka ku. Ina sake jaddada maka, kar ku ragawa kowa a cikin su. Amma ku kiyaye ƙa'idar aikina. Babu kisan kai, babu taɓa wanda babu ruwansa mata ko kuma ƙanan yara" Walid ya ce "An gama maigida" " Ɓace " ya furta a hankali. Yau Nabila ko karyawa ba ta tsaya yi ba, haka zalika ko sumayya ba ta jira ba, ta tafi aiki. Daga office ɗin ta, tana hangen harabar chamber, ta ga isowar motar Barrister Bashir. Bayan mintuna talatin ta bishi office ɗin sa, suka gaisa ya dube ta ya ce "Ƴar ƙwalisa ya jiki?" Ta ce "Jiki kuma, ba ni da lafiya ne?" Ya ce "Ranar da muka dawo daga court, kina ta tari har ki ka tafi gida, ko kin manta?" Ta ce "A'a na tuna, na ji sauƙi ai" "Wai meyafaru ne a kotun, bayan na je na ga abokina, da na dawo na tarar da ke gaba ɗaya ranki a ɓace, na tambayeki kin ce ba komai" Nabila ta ce "Da ma fa dan bana jin daɗi ne, ai ni ba zan manta da ranar ba, na ga masoyiyata kuma mudubina" Barrister ya ce "Wa kenan?" "Barrister Naja'atu, ina son matar nan sosai " Yayi murmushi ya ce "Bunkure ki ke nufi?, mace mai hatsari kenan" Ta waro ido ta ce "Hatsari kamar yaya?" "No, kin san ba ta da wasa da aiki, duk shari'ar da ta saka gaba, sai ta ga bayanta, ke kuma gashi ba haka ki ke ba, ba kya mayar da hankali a kan aikin". "Ai in gaya maka ganinta kawai da na yi, na ji wata irin ƙwarin gwiwa, na ji sonake na nutsu na mayar da hankali sosai a kan aikina. Sonake na bi footsteps ɗin ta, nima na yi nasara kamar ita. Amma me ka sani a kanta da zaka iya gaya mini?" Yayi murmushi ya ce "Nothing much, ki tambayi barrister Habib, ya santa sosai " sai da ta ji wani dummm! Yadda suke faɗa da barrister Habib, amma hausawa su ka ce ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake ba, dan haka ta ce "To shikenan, na gode sosai ayi aiki lafiya". Ta juya ta fita tana nanata "Dangerous woman, zamu gani ai". Ba ta zame ko ina ba, sai ofishin barrister Habib, ta tarar da shi da wasu client suna tattaunawa, ya ɗago ya kalleta ya ce "Meye?" A ɗan hasale dan a ƙule yake da ita. Ba tare da ta yi fushi ba, ta yi masa murmushi sannan ta ce "Wurinka na zo, amma bari na jira ka gama". "Idan na gama ina da abun yi" ya faɗa a taƙaice. "Dan Allah yaya habib ko mintuna goma ne" "Na gaya miki ina da abun yi, fita ki bani wuri" tsayawa ta yi tana kallonsa, tare da tura baki, babu alamar ma za ta fita ɗin. "Ba magana nake yi ba?" A shagwaɓe ta ce "Dan Allah" Ɗaya daga client ɗin ya ce "Barrister a taimaka mana, kar ta yi kuka" Ya ce "Ta daɗe ba ta yi ba, ba zaki fita ba?" Nabila ta ce "Ya ka ke korata kamar wata kare ne? Na san ina yin laifi, ka yi haƙuri na shiryu ai" Tsaki yayi, ya cigaba da rubuce-rubuce. Ta tura baki ta fice, a zuciyarta ta ce "Ai ko da me ka ke yawo, sai na samu abun da nake son ji a wurinka" Ta je ta samu MD, suka gaisa, sannan ta ce "MD, ka ga Barrister Habib ko, na je na bashi haƙuri, amma ya kore ni a gaban mutane". Ya yi murmushi ya gyara gilashin fuskarsa ya ce "Anya ba wani laifin ki ka yi masa ba?" "Ba laifi na yi masa ba, haƙuri na je ba shi fa, amma ya kore ni a gaban mutane" MD yayi murmushi ya ce "Ai ke ɗin ce ba kya ji, ya so ya koya miki aiki yadda yakamata, mussman yadda ki ke da faran-faran da mutane, amma ki ka ƙi ba kya so, idan ya saka ki aiki ki ƙi yi, dole ku din ga faɗa ai" Nabila ta ce "Na daina fa, so nake na zama ƙwararriya a kan aikina, ko dan farincikin Abbana, ku yi haƙuri" Ya jinjina kai ya ce "Shikenan, Allah ya sa, ki je ki bashi haƙuri" Ya ce "Bayan ya kore ni, yauwwa sir dan Allah ka san barrister Naja'atu Bunkure?" Ya jinjina kai ya ce "Yes, she's famous a tsakanin lauyoyi, har ma da jama'ar gari ma, ai sananniya ce sosai" Nabila ta yi murmushi ta ce "Wow ina yin matar nan sosai da sosai, yadda take gudanar da aikinta, ya ƙara jan hankalina a kan aiki, ai mun ganta kotu a lokacin da mu ka je kotu last, ni da barrister Bashir, ƴar gayu da ita" "Nabila, ke dai ki na son harkar gayu, amma ba gayun ba, ki mayar da hankali sosai a kan aiki, ki yi ƙoƙari ki kamo ta, ko ma ki fi ta". "In sha Allah, na yi maka wannan alƙawarin but i need your support" Ya murmusa ya ce "Kin samu, ɗari bisa ɗari, ƴar gidan major" "Yauwwa to ka bawa barrister Habib haƙuri, zan koma team ɗin sa dan Allah kar ya sake korata, mussaman a gaban mutane" "To za a bashi in sha Allah" Ta miƙe tsaye tare da faɗin "Godiya nake" ta fice ta bar office ɗin cikin nishaɗi. "Bunkure na ki zai zo mini da sauƙi, saura kuma Aminu Viper" *** Major ya ɗan tsurawa Uwargidan sa mama da ta tattare kwanukan da ya kammala cin abinci. Ta ɗago su ka haɗa ido, ta ce "Ya dai?" "Nasir" "Me yayi?" "Ki ja masa kunne, hawainiyarsa ta kiyayi ramata, na daɗe da gane in da ya dosa, amma tun da kin daƙile abun, to ya ƙara nesanta kansa da ƴa ta, kar ya kuskura in ji ko in ga wani abu da zai sosa zuciyata, kuma kar ya kuskura ya saka ta fara son shi, tun da ba ki amince ba, balle a jefa ta cikin yanayi mara daɗi". Cikin rashin fahimta ta ce "Amma major, wani abun ya yi ne?" "Bai yi komai ba,gugar zana dai nake yi, idan ma yana shirin yin, to ya shiga hankalinsa" cikin mamaki take bin sa da kallo, tabbas idan aka ji major  yana magana da kurman baƙi, akwai abun da ya gani, kuma ko me za ayi, ba zai fito yayi bayanin abun da yake nufi ɗin ba. **** Kamar ɓarawo haka yake zagaye tilon matsakaicin gidan, wanda can nesa da gidan, kamfanunnunka ne, sai gonaki. Cikin ƙasaita yake tafiyar, yana yi yana duba ƙaramar wayarsa mai madannai. Kamar korarre, haka wani matashi ya ƙaraso in da yake tsaye. Ya ɗaga kai ya kalle shi ya ce "Menene labari, yaya aka yi ka fito?" Cak matashin ya tsaya, ya ce "Wai dama ba kai ne ka fito da ni ba?" "Me zan tambaya idan na san komai?" Yayi maganar a ɗan hasale. "Wallahi master.... Cikin wata irin razananiyar tsawa ya ce "Kar ka sake kirana da wannan sunan" Cikin tsuma ya ce "Tuba nake oga, suɓutar baki ce, ban san waye ya fito da ni ba, kawai cewa aka yi na tafi" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Kuma ka tabattar da ka gaya musu sunana, cewar ni ne me kayan?" "Wallahi na faɗa musu" Ya jinjina kai ya ce "Shikenan" Ya ɗaga rigarsa ya zaro wata sharɓeɓiyar wuƙa, ya danƙa masa ya ce "Maza ka fasa cikin gari, unguwarmu, su walid sun tafi yaran Madaki zaku farwa babu sani babu sabo, idan an yi ram da wani daga cikin ku, ku ambaci sunana, ku ce ni ne jagoran aika-aikar, amma ku kiyaye ƙa'idar aikina" Ɗan mama ya risuna ya ce "Umarninka ne abun biyayya a gare ni, an gama za ayi yadda ka ce" ya soke wuƙar ya juya, ya tafi da sauri yana haɗa hanya.. Cikin ƙaramin gidan ya shiga, ya nufi ɗakin kwanansa, ya kunna fitilar wayarsa, ya kunna ƙwan solar, haske ya gauraye ɗakin. Ya saka mukulli ya rufe ɗakin, sannan ya zauna yayi shiru tsawon mintuna, daga bisani kuma ya ɗaukko wiwi ya naɗa ta, ya kunna ya fara zuƙa. Madadin ya ji ƙunci, da zafin da zuciyarsa ke yi masa, yana raguwa, sai ma wani irin baƙin ciki da matsananciyar damuwa da suka kawo masa ziyara. Wani abu mai tsananin ɗaci yake ƙoƙarin haɗiyewa, amma abu ya gagara. Ya ɗaga wiwin yana kallonta cike da baƙin ciki da takaici, yayi watsi da ita yana sauke numfashi. Kamar mahaukaci ya zabura ya buɗe wata akwati, ya ɗaukko kwalaben allura, ya farfasa ya haɗa, ya yi wa kansa, ya nemi wuri ya kwanta. Bai fi mintuna goma ba, kansa ya fara barazanar tsagewa, ya fara kakari yana rirriƙe kansa. Duk yadda ya kai ga ƙara yawan doses ɗin abun da yake sha, ba sa ɗaukarsa, su mantar da shi damuwarsa, sai dai su wahalar da shi, shi a yanzu babban fatansa ya samu abun da zai yi amfani da shi, da zai goge masa komai  na ƙwaƙwalwarsa ya yi bacci mai nisan gaske. *** Nabila ce tsaye a kitchen tana ta ciye-ciye, tana yi wa magajiya surutu. Baba magajiya ta ce "Dan Allah Arfa ki yi mini shiru na ji radiyona, wai ni ya aka yi, ki ka tashi da sassafen nan ma" Nabila ta yi murmushi ta ce "Baba magajiya kin gane mai muryar nan kuwa?" Baba magajiya ta yi dariya ta ce "Sumayya ce mana" "Ashe za ki gane ta" "Ka ji ƴa, yau na sanku da ke da ita, da zan kasa gane muryarta" "Ai in gaya miki baba magajiya, wata mata ce ta takura wa aminiyata, a wurin aiki, da iskanci kala-kala ga sumayya da son aiki, amma matar nan tayi ta taɗiyeta, ni kuwa na ce ta daina saurara mata wallahi,shi ne ma fa ake ba ta karanta rahotanni wasu lokutan, da experience ɗin ta da komai, wata sokuwa ta cuceta, ta hana ta cigaba" Baba magajiya ta ce "Ohh Arfa, ai mahaƙurci mawadaci, yawan faɗa ba shi da amfani" Nabila ta ce "A'a fa baba magajiya, ni ma ba faɗa ne da ni ba, wulaƙanci ne ba na so, duk wanda ya wulaƙanta ni, sai mun yi fito na fito da shi". Baba magajiya ta ce "A dai din ga haƙuri, tun da.... ba ta gama magana ba, Nabila ta yi wani irin tsalle ta ɗauki radiyon, tayi waje da gudu. Sashin mama ta faɗa, dan ta san tun da Nasir yana gari, lallai zai shiga sashen ta ya karya kafin ya fita. Aikuwa a sashen ta tarar da shi, yana karyawa, su na hira da mama, da kuma sauda. Ƙaro volume ɗin radiyon tayi, ta na yi masa nuni da ya saurara. Rahoto ne a kan rikicin faɗan daba, da ya gudana a cikin ɗaya daga manyan unguwannin kano, wanda tun goma na dare ake rikicin, har ƙarfe sha biyu ana rigimar, ƴan sandan sun yi nasarar cafke wasu daga cikin matasan, in da ɗaya daga wanda aka kama, ya ce Aminu Viper ne ya aka su Sai da suka kammala ji, Nabila cikin rawar jiki ta ce "Yaya Nasir, ba wannan ne wanda ka ke nema ba?" Ya jinjina mata kai ya ce "Shi ne" "Ka yi sauri ka tashi, ka je division ɗin da aka tsare ƴan daban, a baka su ka zurafafa bincike, gidan radiyon su sumayya ne, sai na biya can na sake samo rahoto". "Ke!" Mama ta daka mata tsawa, har sai da ta ɗan razana. "Tashi ki bani wuri, yaya ina magana da shi, ba sallama ba gaisuwa babu neman izini, kawai ki zauna ki na surutun banza" Nabila ta yi shiru ba ta ce komai ba. Sauda ta ce "Dama mama yaushe za ta gaishe ki, tana abu kamar mahaukaciya" Ta kalle su, ta kalli Nasir da yake wurin, ta haɗiye wani abu ta tashi, za ta fita. Nasir ya riƙo hannun ta ya tashi ya tsaya, ya ce "Sorry barrister, na gode sosai da wannan gudunmawa, zan je division ɗin, ki samo mini bayani a wurin sumayyan". Ya kalli mama ya ce "Haba mama, kin san tana gaishe ki, tsananin zumuɗin ta kawo mini labari ne fa ya sa ta manta, thank you Arfa ki shirya ki tafi aiki kar ki makara" A ƙule mama ta ce "Wai kai har abada ba zaka yi hankali ba, dan ubanka ya zauna yana cewa in ja maka kunne, a kan shishshigin da ka ke yi mata, amma ina magana kana dizagani a gabanta" Nabila ta yi gaba ta fice a fusace, dan idan ta cigaba da tsayuwa, za ta iya aikata abun da zai hana kowa wuni cikin farin ciki. Ya ce "Ni ɗin kuma mama?" "Kai ɗin fa, ko ka shiga hankalinka, ko kuma duk abun da ya biyo baya kai ka so". Sam sai ya ji maganar kamar maman ce, ta shirya kayarta dan ta saba, dan haka ya yi musu sallama ya fice. A gurguje ta tsaya ta gaisa da Abba, ta fice cikin zumuɗi, gidan radiyon su sumayya ta fara tsayawa. Sumayya ta yi mamakin ganinta, ta ce "Hajiya lafiya ki ka zo mana wurin aiki da sassafe? Talla ki ka kawo ko cigaya?" "Ƙaniyarki na kawo" Nabila ta ba ta amsa. Sumayya ta ce "Ai na san ke ungulu ce, ba kya jewar banza, ya aka yi uwar makara" Nabila ta ce "Yau da safe kan na fito, na ji baba magajiya na jin program ɗin ku na labaran ƙarfe shida, bayan kin karanto  naki, na ji wani rahoto na faɗan ƴan daba, jiya a kano" Sumayya ta ce "Eh meyafaru?" "Kin je wurin ne?" Sumayya ta zaro ido ta ce "In je in yi me?" "Na ji an ce wai yaran Aminu Viper ne" Sumayya ta ce "Eh to, ni ma haka na ji" "Dan Allah ki tashi mu je asibiti, an ce an kama wasu, wasu kuma da aka yi musu miyagun raunuka suna asibitin koyarwa na cikin gari" Sumayya ta ce "To wai ke duk menene haɗinki da hakan?" Kamar Nabila za ta yi kuka ta ce "Sumy ban gaya miki ba? Yaya Nasir ne incharge ɗin bincike a kan mutumin nan, kusan kullum sai an faɗi mugun aikinsa, ya tabattar mini da in dai na gano masa in da yake, ko na taimakasa ya gano zan yi suna sosai" Cikin matsanancin takaici Sumayya ta ce "Tashi ki tafi ko na ɗura miki ashar, ƴar wahala, shi yaya Nasir ɗin ne ya gaya miki haka? Ƴar sanda ce ke? Su ma ya suka ƙarke da su balle ke ki na mace, wallahi ba zan kai kaina ga halaka ba" "Sumy ki gane, this can all help our career ki zo mu je mana" "Wallahi ba zan shiga shirgin ƴan daba su kashe ni ba, idan kin yi sunan uban me zai ƙara miki, za a binneki da shaharar ne idan kin mutu?" Cikin ƙoƙarin son fahimtar da sumayya ta ce "Ba za a binne ni da shahara ba, amma atleast zan samu chances da zan iya fuskantar Naja bunkure" Wata uwar ashar sumayya ta yi wa Nabila, ta tashi ta ce "Mahaukaciya, ai sai ki yi, ke da bunkuren ƴan wahala" Nabila ta tashi a fusace, ta ɗauki jakarta ba tare da ta sake cewa sumayya komai ba, ta tashi. Sumayya ta girgiza kai ta ce "Arfa Allah ya taro ki ya shirye ki, ya yaye miki baƙin taurin kai" "Tun da kin ce ba zaki je ba, kar ki sake yi mini magana, kuma na gode" "Eh ba zani ba, haka kurum a kashe ni a banza, mutanen da ba tsoron Allah ne da su ba, mutanen da suke shan ƙwaya tana gaya musu gaibu, su ɓantarani biyu a banza ba da ni ba" Nabila ta yi mata shiru ta fice. Nabila ba ta yi tunanin komai ba, ta garzaya asibitin koyarwa, na cikin gari. Ba ta wani sha wahala ba, saboda tana zuwa, ta tarar jami'an tsaro sun kewaye sashen emergency, ba wanda yake shiga ko ya fita. Zagaye harabar wurin ta fara yi,tana neman hanyar shiga, da son tabattar da abun da yake faruwa a wurin, ta samu wata cleaner, ko meyafaru a in da ƴan sandan suke. Nan ta sanar mata da cewa, yaran da aka illata a wurin faɗan daba a daren jiya, aka kawo an hana kowa shiga ko fita. Nabila ta yi mata godiya, ta yi mata alheri, ta nufi wurin da aka hana shigar da fita.. Ta ƙarasa ta samu ɗaya daga cikin jami'an tsaro suka gaisa, sannan ta nemi shiga, suka ce ba za ta shiga ba. ID card ta nuna musu, amma ɗaya daga cikin su ya ce "Madam nan ba prison bane, kuma ba police station ba ne ba, nan Asibiti ne, ki bari idan aka kai su can, sai ki je ki yi aikin ki". Ta kwantar da murya ta ce "Dan Allah yallaɓai, ku bar ni na shiga, Ma'aikaciya ce nima" "Get out from here" yayi mata tsawa. Aikuwa ta hasala ta ce "A beg, don't shout at me, aikinka ka ke yi, nima nawa nake son yi, a kan me za ka yi mini tsawa?" Hankalin mutane ya fara dawowa wurin. Sake hayayyaƙowa Nabila yayi, amma cikin dakiya da taurin kai, take mayar masa da martani. Da ƙyar aka rarrashi police ɗin, dan cewa yayi sai sun tafi da ita station, wataƙila ma ƴar ƙunar baƙin wake ce, ko ta na da alaƙa da masu laifin. Nabila ta ce "Ni za ka yi wa sharri, ki in ƙunar baƙin waken zan kai, zan tsaya saurarku ne, da yanzu wani zancen ake ba wannan ba". Ana ta ƙoƙarin sasanta magana, amma Nabila ta ƙi yin shiru. Ta ciro wayarta, ta kira Nasir sai huci take yi. Yana ɗagawa ta ce "Yaya, ya ake ciki ne? Akwai wani labari ne?" Ya ce "No, wallahi arfa kin ganni, na zagaya station uku a yankin, duk ba a kai su ba, amma wata majiya ta tabattar mini da sakinsu aka yi, just recently" "Sakin su kuma? Saboda me?" "Ban sani ba, a kan abun da nake ƙoƙarin yin bincike kenan" "Ka hanzarta ka taho asibitin cikin gari, akwai waɗanda aka kwantar, police sun hana shiga sun hana fita, an hana kowa shiga, ko da kuwa kusa da ɗakin. Har da ƴan jarida ma an hana su" Cikin sauri ya ce "Ok shikenan, gani nan in sha Allah, hankalina bai kai kan in zo asibiti ba ma na duba ko akwai abun da zai taimaka mini, amma gani nan stay safe" Ta amsa da "Ok" Ta ajiye Wayar a jakarta, ta cigaba da kaiwa tana komowa, ƴan sandan suka saka mata ido, dan kar ta yi wani mummunan yinƙuri, dan ba su san manufarta na dagewa a kan son shiga wurin ba. Babu tsammanni aka fito da matasan, wasu ɗauke da raunuka, wanda ba za su iya tafiya ba, an turo su a kan gado, an nufi hanyar barin emergency da su. Nabila ta nufe su cikin sauri, amma ƴan sanda suka tare ta. Ta kalli ɗaya ta ce "Yallaɓai ina za a kai su? Na ga wasu a mugun yanayi, ya za a bar asibiti da su?" Babu wanda ya kula Nabila, aka saka matasan a cikin ambulance, har da iyayen wasu daga cikin matasan jami'an tsaron suka hana su bin su, suka rufe ambulance ɗin, su kuma su ka hau ta su motar ta ƴan sanda, suka bar harabar asibitin. Ƴan jaridar da suka yi ƙoƙarin bin su ma, aka dakatar da su, aka hana su ƙarasawa ma in da motar take har suka tafi. Tsayawa ta yi kamar wata shashasha, tana mamakin yadda abubuwa suke tafiya, kamar a film. Motar DSP Nasir ce ta shigo cikin harabar asibitin, yayi parking ya fito, yana ƙoƙarin kiran Nabila a waya,ya tambayi tana ina. Da sauri ta ƙarasa in da yake, tana kallonsa, amma ta kasa magana. Ya ce "Yaya dai? A wane ɓangaren suke, kin samu ganin na su kuwa?" Nan ta kwashe duk abun da ya faru, ta gaya masa. Cikin asibitin ya shiga, tana biye da shi, ya tambayi office ɗin incharge na A&E ɗin, ya gabatar masa da kansa, tare da yi masa tambayoyi, a kan dalilin da ya sa, aka sallami mutane da raunuka a jikinsu. Amma ya tabbattar masa da cewa, babu wanda yayi musu wani cikakken bayani, kawai ƴan sanda sun kawo musu yaran jina-jina tun a daren jiya, sun ba su kulawar da ta dace, daga bisani ƴan sandan suka ce asibiti za su canza musu, aka tafi da su. Nabila ta yi shiru, sannan ta ce "Akwai wata a ƙasa yaya Nasir, ko waye wannan Aminun, ya na da wanda su ke sponsiring ɗin sa. Shi an kasa kama shi, amma ya na saka yaran mutane ta'addanci, you need to put more effort, and i will hundred percent support you, everyone is equal before the law, dole a nemo shi a hukunta shi" Ayshercool 08081012143 [7/20, 2:02 PM] null: *ƘARFE A WUTA* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g. 6 Nasir ya ce "Sannu da ƙoƙari arfanmu, amma ki daina saka kanki a risk kin ji ko? Zan cigaba da ƙoƙarina in sha Allah sai na yi sanadin kawo ƙarshen ta'addanci da harkar daba a garin nan, domin kuwa yana ci mini tuwo a ƙwarya nima, but for now mu je na kai ki wurin aikinki" Nabila ta ce "DSP, dan Allah idan ka gano wani abu na rashin gaskiya, ko waye yake da hannu a ciki, ka tona masa asiri. Dan ina ga sumy zan yi wa magana, su faɗi abun da ya faru a gidan rediyo, an saki waɗanda aka kama, kuma wanda aka ji wa rauni ma, an hana kowa zuwa wurinsu, daga bisani kuma jami'an tsaro sun kwashe su daga asibiti, babu wanda ya san in da aka kai su, wannan wane irin abu ne?" tayi maganar cikin haƙiƙancewa. Yayi murmushi ya ce "Kar ki soma, ki na wasa da hukuma arfa, yanzu sai ki kwana a ciki ke, yanzu dai mu je mota" haka ya tasa ta a gaba zuwa mota, suna tafe tana mita. "Wallahi yaya na fara sarewa da lamarin ƙasar nan, anya kuwa gyaran ake so ayi da gaske, ta yaya za ace an gagara kama mutum ɗaya? Ana yekuwar ana nemansa, amma kuma ana kare laifukan da yake aikatawa, ni na kasa gane kan wannan lamarin. Ni fa muddin na gano wani abu na rashin gaskiya, sai na yi magana" "No Arfa, ba huruminki bane ba, ba kuma aikinki ba ne ba, kar ki kuskura ki saka kanki a hatsari, ƴa mace ce ke lamarin ƙasar nan ya wuce tunaninki, ba abu ne mai sauƙi kamar yadda ki ke hangensa ba" Ta yi ajiyar zuciya, sannan ta ce "Yaya garin nan yana kan gaba a garuruwan da ake ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, duk al'ummar da matasanta suka lalace da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi ba ta da gobe mai kyau, matasanmu su ne tushen al'umma mai kyau" Nasir ya ce "Na fuskanci abun da ki ke nufi, but is still not your field" Tayi shiru ta mayar da hankalinta kan titi, tana ta tufka da warwara a zuciyarta. Ko da ya kai ta wurin aiki, ta sauka suka yi sallama, ta shiga tana shiga office ɗin ta, sumayya ta fara kira. Sumayya ta ɗaga ta ce "Kin gama fushin ne?" "Ke ware ba wannan ba, matsoraciya da ba ki je ba ni na je, na samo labari, ina ga bayyana labarin ka iya janyo hankalin manya a cikin lamarin" Sumayy ta gyara zama ta ce "Labarin me?" Nabila ta gaya mata komai, yadda yaran da aka kama suka yi ɓatan dabo, da yadda aka fice da na asibiti ba tare da sanin ina aka kai su ba. Sumayya ta ce "Nabila lallai wannan magana ce babba, bari zan yi magana da MD na ji mai zai ce, gaskiya yakamata a zurfafa bincike a kan lamarin nan". Cikin zaƙuwa ta ce "Dan Allah sumayya ki ƙoƙarta, ayi a sanar, a ji mai hukuma za ta ce a kan haka, ko kin san shi kansa Aminu Viper ana zargin ko dai guduwa yayi daga gidan yari, ko kuma sakinsa aka yi ba bisa ƙa'ida ba, shiyasa ake tsananta nemansa yanzu" "Ke ya aka yi ki ka sani?" "Yaya ne ya gaya mini, akwai lauje cikin naɗi a lamuran mutumin, mutum kamar wani sheɗani". Sumayya ta yi shiru sannan ta ce "Bari, yadda mu ka yi da su zan gaya miki, amma maganar nan ta ɗauki hankalina sosai" "To shikenan, ina saurarenki, yadda ake ciki, ki sanar mini" suka yi sallama. Haka kurum zuciyar Nabila ta cigaba da azalzalar ta a kan lallai tana son sanin wanene wannan Aminun, akwai yiwuwar ta samu gagarumar nasara idan aka ce da saka hannunta wurin kama shi, shahararta ita zai ba ta damar yin gaba da gaba da Naja'atu Bunkure. Sai kuma ta tambayi kanta, for the first place, laifin me ya yi aka kai shi prison, har ake tunanin ya fita ba bisa ƙa'ida ba?. "Akwai ayar tambaya a kan abubuwa da dama" ta yi maganar a fili. *** Ƙurawa wayar gabansa ido yayi, yadda take ta vibration kamar ta tashi, a wannan karon ma private number ce, lambar da ko ta halin ƙaƙa yake fatan ganin ko waye mai ita ya bayyana a gare shi. Ɗan mama da ke kusa da shi ne, ya ɗaga wayar ya sanyata a hansfree, ya tura masa gaban sa. Daga cikin wayar aka ce "Manya gatan wasa, ko ka  tsorata ne ya sanya ka gagara ɗaukar wayata?" Yayi shiru bai ce komai ba. "Idan za ka kwana dubu kana ɓarna, zan kwana dubu ina goge ta, ina ɓatar da sahunka. Ka na ta cigaba da aikata ɓarna, saboda kana son lallai sai ka san waye ni ko?" "Wanene kai?" Yayi maganar a ɗan hasale. Mutumin yayi murmushi ya ce "Mutum, mai zuciya cike da muradai kamar ka. Ƴan kwanakin nan ka fi mayar da hankali a kan sanin wanene ni, fiye da abun da yake damun zuciyarka. Ka bi a hankali kar garin kallon ruwa kwaɗo ya yi maka ƙafa, kar ka saki reshe ka kama ganye, ya kai wannan maciji mai hatsarin gaske" Al-amin ya numfasa ya ce "Ni ba karen farauta bane ba, da za ka din ga wasa da ni, tamkar ɗan kwiwiyon da ka raina, ka yi a hankali da ni, ƙarfe nake cikin wuta, na fi ƙarfin ɗauka da hannu" Ya sake murmusawa ya ce "Ka huta mutumina, ka samu abun da zai ɗebe maka kewa, ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, ba za su taɓa rabaka da damuwa ba, matuƙar ba ka yi abun da zuciyarka ke gaya maka ba, haryanzu ka na da sauran ƙuruciyarka, zaka iya amfanar da al'ummarka" Kafin Aminu yayi magana, mutumin ya katse wayar. "Amma Yallaɓai, kana ganin wannan abun da muke yi shi ne dai-dai? Akwai abubuwa da yawa da yakamata ace mun mayar da hankali a kai, ba bawa ɗan daba kariya ba" Ya ajiye jaridar hannunsa ya ce "Kalle ni da kyau, ba na abun da babu manufa a kansa, dan haka kawai ka saka ido" Waya ce ta fara ringing, ya ɗaga sannan ya miƙo masa. Ya karɓi wayar tare da yin sallama. "Wa'alaikum Salam, barka dai ya ƙoƙari?" "Alhamdilillah sir, an yi clearing matsalar jiya, duk da an kusa samun akasi, yaron ba ya ji ko kaɗan, idan aka cigaba da tafiya a haka, kar asirinmu ya tonu fa, dan hakan tamkar yi wa doka karan tsaye ne, mu na saɓa ƙa'idar aiki" Yayi murmushi ya ce "Kar ka damu, doka ce ta fara yi wa yaron karan tsaye, shiyasa nake amfani da dokar, wurin bi da komai" "Haka ne sir, amma fa police suna neman shi ne ruwa a jallo, mu kuma muna kare shi, muna taka doka da yawa" "ASC, ko sun kama Al'amin, ba zasu bari doka ta yi aiki a kansa yadda yakamata ba, za su bar shi da masu son zuciya ne, su yi abun da suka ga dama da shi, ba wai hukumar ce kawai take nemansa ba, akwai lauje cikin naɗi ne a neman da ake yi masa" ASC ya numfasa ya ce "Shikenan, amma laifukansa sun yi yawa, duk wani ta'addanci da za'ayi a garin nan sai ka ji yaransa ne, slide mistake za'a iya kama shi, duk da wani abun kuma idan muka bincika, sai mu tarar ba shi ɗin ba ne ba" "Haka ne, amma idan an kama shi ma, sunana na ko naka, babu wanda zai fito, haryanzu bai san ko ni waye ba, kuma ba zan bari ya sani ba, kuma yana aikata wasu laifuka ne dan ya tilasta na ƙyale shi, ko kuma na bayyana kai na a gare shi, amma ka rabu da shi, komai cikin tsari nake yin sa, ka bar police su cigaba da neman sa, hukumarka kuma ta cigaba da aikinta, kamar yadda na ce maka" Ya amsa da "Shikenan sir, am always loyal to you, na gode" "Yauwwa ASC, duk halin da ake ciki dai, ina buƙatar ka sanar da ni" "No problem, sai an jima" bayan sun yi sallama, yayi wata irin dariya, da shikaɗai ya san ma'anarta ya ce "Wannan shi ne jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya" yayi maganar yana kallon yaronsa da yake tsaye yana kallon sa. Ya ce "Lallai, amma zan so in ji wani irin shiri ne haka ka ke yi sir" "Za ka gani a aikace, kai dai ka cigaba da biyayya ga abun da duk na umarce ka, nima zan yi amfani da ƙarfin iko da kujerata, na yi abun da ya dace". "Ok sir, in sha Allah". *** Misalin ƙarfe takwas na dare, wasu daga cikin manya na ƙungiyar ƙato da gora na unguwar suka tattaru suka zauna meeting a cikin ɗan madaidaicin office ɗin su. Duba da abun da ya faru, na faɗan daba da aka yi da yaran Aminu da na Madaki a waccan unguwa, sanin ya na shigowa unguwar lokaci zuwa lokaci, sannan kuma akwai yaransa a unguwar, ya sanya su zaman yin meeting, dan ƙara ƙarfafa tsaro a cikin unguwar su, kar su gama da can su dawo nan. Suna tsaka da tattaunawar, wasu zaratan matasa suka yi sallama, suka amsa suna bin su da kallo. Suka shiga cikin office ɗin, suka kewaye su, duk suka tsaya suna kallon su. A hankali ya sauke face mask ɗin fuskarsa, a take suka shaida shi. Kafin su yi magana ya ce "Awa ɗaya rak nake buƙata, zan gama abun da ya kawo ni na fita, muddin na kuma shigowa unguwar nan, ku ka sako ni a gaba, kamar kare za ku kama ni, wallahi sai na yi muku abun da na yi wa malam lawan". Shugaban ƴan sintirin ya ce "Dan meyasa zaka din ga shigo mana unguwa? Kai da hukuma take nema ruwa a jallo, ka san kai tauraruwa mai wutsiya ne, duk in da ka je sai ka yi fitina, tun da yaranka suka yi ɓarna jiya, na san cewa nan ma zaka shigo. Duk ka lalata mana yara ka tafi ka barmu da masifa, kuma yanzu ka dawo kana cigaba da bibiyarmu" Cikin tsawa Walid ya ce "Kai, ka iya bakinka, wallahi ko na ɓare maka shi har ƙeyarka". Cikin tamkakiyar fuskarsa Viper ya ciro zungureriyar wuƙar da take ƙugunsa, ya karta ta a ƙasa tayi wata irin ƙara, sannan ya ɗora ta a gefen wuyan mutumin ya ce "Ƴaƴanku za su cigaba da yi mini biyayya, sai na mayar da unguwar nan mafi munin sansanin ta'adancci da zubar jini, komai ya faru ai ku kuka so, yanzu dan Allah kai ba ka ji kunyar faɗar abun da ka faɗa ba? Duk in da zan je zuciyata na tsakiyar unguwar nan, kuma zan cigaba da shiga da fita yadda nake so, har sai na yi maganin azababbiyar ƙishirwar da ta addabi ruhina. Duk abun da na aikata muku na ɓarna, ku kuka so, mutanen banza masu butulci, kun taki sa'a da nake dakon alƙawari mai nauyi a kaina, ban da haka tun a fitowa ta, ɗaya bayan ɗaya zan yi muku kisan gilla. Idan na sake shigowa unguwar nan, kai da wannan mutanen, ku ka yi yinƙurin yi mini wani abu, duk wanda na kama, zai zama mutum na farko da zan yi wa yankan rago!" Gaba ɗaya suka zuba masa ido, suka kasa ko motsin kirki, saboda yadda suka zagaye su da miyagun makamai. "Ku karɓe wayoyinsu, ku rufe mini su, ku saurari order da zan bayar. Duk wanda yayi muku gardama ku karya mini ƙafarsa, ko ku tsarge masa cinya". "Angama boss" Yana fita daga office ɗin, suka mayar suka rufe, suka ƙwace musu wayoyi, sannan suka tsaya a kansu da wasu irin zabga-zabgan wuƙaƙe, kamar a abba tuwa. Babu wanda ya iya wani ƙwaƙwƙwaran motsi, dan a yadda matasan suke muzurai, kuma shaye-shaye ya huda su, duk umarnin da ya ba su za su bi. Sannu a hankali yake tafiya, har ya kawo cikin layin, ya tsaya a ƙofar wani gida, ya shafe tsawon lokaci kawai ya zubawa gidan ido, yana zancen zuci, daga bisani ya ƙarasa ya ƙwanƙwasa na kusa da shi, ya ja mask ɗin sa, ya rufe fuskar shi. Yaro ne ya fito ya ce "Waye?", ya cewa yaron "Ka je ka cewa babanka an zo duba shi" Mintuna kaɗan yaron ya dawo, ya ce ya shiga. Bai yi sallama ba, haka ya kunna kai cikin gidan, har tsakiyar falon maigidan, ba tare da an yi masa iznin hakan ba. Daga maigidan har matar gidan, da ƴan matan yaran, tsuma suka hau yi, ganin wanda ya shigo har cikin gidansu. Ya zaro wuƙarsa ya ajiye a gaban malam lawan, sannan ya ɗaga wani mukulli ya ce "Na rufe gidan nan da kwaɗo ta ciki, kuma duk wanda ya yi wani ƙwaƙwƙwaran motsi, zan zaunar da shi kamar yadda na zaunar da kai" yayi maganar yana kallon malam lawan. Ya durƙusa kama ƙafar malam lawan, da aka naɗe da bandeji, ya dudduba sannan ya ce "Ɗori yayi kyau, sai dai na yi mamakin yadda aka dawo da kai gida, maimakon ka yi jinya a asibiti" ya saita tsinin wuƙarsa a cinyar malam lawan ya ce "Waye ya ɗauko ka daga asibiti?" Cikin tashin hankali matarsa ta fara kuka ta ce "Dan girman Allah Aminu kar ka yi masa wan.... "Wallahi ki ka sake magana, sai na karya ɗaya ƙafar, ka gaya mini kafin na huda cinyarka" yayi maganar cikin razananiyar muryarsa. Cikin matsanancin tashin hankali ya ce "Wallahi wasu mutane ne, ban san su ba, su ne suka sauya mini asibiti, lokaci zuwa lokaci, suke zuwa da likitansu ya duba ƙafata, kuma sun gargaɗeni a kan muddin wani ya ji kaine ka yi mini haka, sai sun kashe ni" "Waye ya kai ka asibiti ranar da abun ya faru?" Cikin kyarma da rawar murya malam lawan ya ce "Wallahi kana barin wurin, ina wannan kakarin, wani ya zo yayi mini kashedin muddin na ce kai ne zai kashe ni, ya watsa mini wani abu, ban sake sanin in da kaina yake ba, sai da safe maƙwabta suka tsince ni, na ce masu masu ƙwacen waya ne suka yi mini" Aminu ya ware masa jajayen idanunsa sosai ya ce "Idan na samu labari  akasin abun da ka gaya mini, kar ka manta take na, maciji nake mai mugun dafi, sai na maka karayar da ba zaka sake taka ƙafarka ba a doron duniya. Zan cigaba da zagayowa zan kuma cigaba da sanya maka ido. Kar ka manta ka yi mini ganganci daban-daban, na kawar da kai, na riƙe biyu a raina idan ka yi na uku kasheka zan yi har lahira". Malam lawan ya jinjina kai, yana jin yadda mararsa ta cika fam da fitsarin tsoro. Viper ya a miƙe ya juya ya bi hanyar fita. Sai da suka tabattar da tafiyarsa, sannan matar malam lawan ta ce "Na shiga uku, baban su Amir dan Allah meya aike ka sake shiga sabgar mutumin nan? Daga ƴan sandan har ƴan ƙato da goran kar wanda ya ƙara tambayarka abu a kansa ka ce ka sani, kalli bala'in da ka jefa mu a ciki?" "Ke dalla rufe mini baki, tun da yanzu na tsira da raina shikenan, ina ga sayar da gidan nan zan yi na bar unguwar, idan ba haka ba wataran kasheni zai yi " "Ai koma menene Allah ya ƙara wallahi, abun da ka yi wa bawan Allah nan ka yi butulci da yawa" "Au so ki ke na rufawa mutumin banza asiri Haule? Ni ki ke gaya wa haka?" "Oho ai gaskiya ce" haka suka cigaba da faɗa, tana mita da ɗora masa alhakin janyowa kansa ko ma menene. Aminu kuwa, ta waya ya ce wa su ɗan mama, su baro ƴan vigilante ɗin, su bi shi gida. A gidan suka tarar da shi, ya dubi Walid ya ce "Ka yawaita survey a cikin unguwar nan, mutumin nan ya tabattar mini da cewa, wanda suka canza masa asibiti, suna zuwa da likta har gida yana duba shi". "To shikenan Oga, in sha Allah za ayi yadda ka ce" "Kuma na san mutanen nan ne, da mutumin yake kirana a waya, ya zama dole na san waye, da kuma manufarsa a kaina, da yake bibiyata har haka". Walid ya ce "An gama maigida" Nabila kuwa tun da ta shiga aiki tana office ɗin ta, suna communicating da Yaya Nasir. Wayar sumayya ce ta shigo ƙaramar wayarta, dan haka ta ajiye ta hannunta ta ɗaga da sauri ta ce "Sunayya yaya ake ciki?" "Kamar dai yadda na yi tsammani" ta bata amsa. "Me ki ka yi tsammanin? Yi mini gwari-gwari" "Ba irin labarin da suke buƙata ba kenan, hakan ka iya kawo musu naƙasu ga cigaba da kuma tasirin gidan radiyon su, kuma wai ba ni da cikakkiyar shaidar abun da na faɗa" "Haba Sumayya, ni ina da shaida fa, ga kuma yaya Nasir ma, kuma ya zaki tsaya a wurin wannan shashashar matar da ba ta son cigabanki? Ki yi wa Manager magana mana direct, nima ina da lambarsa, sai na yi masa magana". Sumayya ta ce "Nabila kenan, duk kanwar ja ce, shi ne ya jaddada mini hakan da kansa". "Allah wadaran naka ya lalace, Yanzu sumayya shikenan zuba ido zamu yi? Babu wani abun yi?" Sumayya ta ce"Idan na matsa zan iya rasa aikina, abun da ya nuna mini kenan, wai ba za su iya jayayya da hukuma ba, kuma na kawar da kaina a kan abun da ba zan iya jurewa ba, da ina da wata hanyar samun kuɗin, da ajiye aikin nan zan yi Arfa" "Shikenan, zamu yi magana anjima, see you later" ta ajiye wayar ta zauna ta yi shiru. Wani irin tsaki ta ja, tana mamakin yadda galibin private organizations suke buɗe wurare, for their personal interest kawai, kodayeke na gwamnatin ma menene, duk ɗaya. Ganin ɓacin ran ba zai amfanata komai ba, tana da abubuwan da yakamata ta yi, ya sanya ta fita ta tafi office ɗin Barrister Habib. Yana ta aiki a system, ya ɗago ya amasa mata sallamarta, ya cigaba da aikinsa. "Barka da aiki barrister". "Yauwwa" ya amsa a taƙaice. "Barrister wai haryanzu fushin ka ke yi, na shiryu fa na daina duk wani abu da nake yi, sonake na zama cikakkiyar lawyer abar koyi ga wasu, kamar gwanata Barrister Naja'atu Bunkure" da ɗan sauri ya ɗago ido ya kalleta ya girgiza kai ya ce "No wonder, shiyasa ba zaki cigaba ba" "Subhanallah, meyasa?" Tayi maganar tana ware ido. Maimakon yayi magana, sai yayi mata shiru. Wani irin kallo tayi masa, a zuciyarta ta ce 'Sai fa ka yi magana barrister' A zahiri kuwa ta ce "Ni dai haka kurum nake sonta, ayyukan ta na jin ƙai suna burgeni, ina son zama kamar ita. Amma tun da haka ne ma, na canza kamar kai nake son zama, daga yau kai ne mudubina" tayi maganar tana murmushi. "Ke da ba zaki iya zalunci ba, mu ne azzalumai ai" Nabila ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, waye ya faɗi haka? Wallahi ba haka bane ba, ni ban ce ba" "Idan har kina son zama shahararriya, dole ki yi iya yinki, a kan duk abun da ya zo hannunki, ko da kuwa babu tabbacin zaki yi nasara, idan ba zaki iya ba kuma, you can leave" "No, zan iya, ai na shiryu yanzu" Ya buɗe drower gabansa, ya ɗaukko wani file ya ajiye mata sannan ya ce "Wannan client ɗi na ce, a nan ƙofar na'isa gidanta yake, zan turo miki cikakken adress ɗin ta, ki je ku yi magana, sannan ki yi tunani a kan case ɗin nata" Cikin girmamawa ta ce "Na gode sosai, zan yi in sha Allah " Tana fita daga office ɗin nasa, ta gyatsine baki, ta ce "Kamar ni za a aika, gidan wata ƙatuwa, ba ma ta zo office ta same mu ba, hamshaƙiya saboda ga ƴar Nabila ƴar wahala. Amma bakomai da na zama abun da nake so, na fi ƙarfin kowane irin wulaƙanci" ta koma nata ofishin tana cigaba da ƙunƙuni. Da ta koma gida ma, ba ta bi ta kan aiken da barrister yayi mata ba, ta kwanta ta sha baccinta, bayan ta tashi ta shirya ta yi wanka, ta tafi gidansu sumayya. Sun jima suna tattaunawa da sumayya, a kan harkar aiki, har sumayya ta din ga ja mata kunne, a kan kasadar da take yi, tare da nuna mata illar hakan a matsayin ta na ƴa mace, ta kunnen hagu maganganun sumayya suka din ga shiga kunnenta suna fita, dan ba ta ji sun shigeta ba. Ta bawa Sumayya labarin aiken da barrister Habib ya yi mata. Sumayya ta ce "Kuma zaki ɗin?" "To ya zan yi?" Sumayya ta yi dariya ta ce "Ai na zata taurin kan yana nan?" Nabila ta yi murmushi ta ce "Na ajiye taurin kai, zan kama aikina yadda yakamata, ai sai burina ya cika sai na binciko wacece Bunkure kuma in sha Allah, sai sunana ya shafe nata a tarihin duniyar ma'abota shari'a". "Allah wadaran naka ya lalace, Nabila, wai ke wani irin taurin kai ne da ke ne? Ke abu ba ya wucewa a wurinki ne? Ki bar ta kawai, idan Allah ya so, tana raye zata ga nasarar da zaki yi a rayuwa" "Ina kwance nasarar za ta zo ta same ni kenan? Ke ƙyaleni, ina ga sai Allah ya kaimu friday da yamma, zan je waccan unguwar gidan matar, na ga bai turo mini contact ɗin matar ba tukuna, zaki rakani?" Sumayya ta ce "A'a gaskiya, wannan unguwar, ana ta fama, kamar ba kya jin radiyo, yadda suke fama da faɗace-faɗacen daba. Ki gayawa barrister ya ce  kawai matar ta je office ɗin ku, ko kuma ki bari komai ya lafa, dan kullum cikin faɗan daba suke" Nabila ta ce "So ki ke in kasa samun information ɗin da nake so daga bakinsa kenan? Ai lallaɓa shi zan tayi, sai na san wacece matar nan. Kodayake ma na saka Yaya Nasir ya rakani" sai kuma ta yi shiru, ta sake maimaita zancen Sumayya a zuciyarta. *Wannan unguwar ana ta fama da faɗan daba* Ta sake kallon sumayya ta ce "A unguwar ne aka ce yaran Aminu Viper sun yi sare-sare?" Sumayya ta yi shiru tana kallon idon Nabila. Nabila ta yi murmushi ta ce "Kar fa ki kawo komai a ranki, ba wani abun zan aikata ba, bari na tafi kan Abba ya dawo ya nemi ina nake" ta ɗau jakarta ta fita, tana jin kamar matsalarta ta zo ƙarshe. *Masu nema daga farko, ku yi joining link channel ɗina na saman page, idan kun shiga zaku samu daga farko* Arewabooks ayshercool7724 Watpad ayshercool7724 Ayshercool 08081012143 [7/21, 2:16 PM] null: *ƘARFE A WUTA* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION BRIGHT PENS SECOND BATCH https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 7 Katafaren falo ne, wanda girmansa ya ishi wani talakan gina gidan da zai rayu a ciki, talabijin ɗin da ke falon kawai ta fi rabon bango. Kujera set biyu ce a falon, kuma tsakanin kowane set da wani akwai tazara. Tinkis-tinkis haka ya fito cikin wata irin dakakkiyar shadda maroon, sai ƙyalli take yi, ba sai an faɗa ba ka san akwai tazara mai nisan gaske tsakanin sa da talauci. Ba wata ƙiba ce da shi ba, amma cikinsa yayi kurtsitsi a riga, har wani nishi yake yi. Ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga kujerun falon, ya kalli matasan da suke zaune a ƙasa a kan carfet. Dukkansu babu mai suturar kirki a cikinsu, kansu duk askin banza, yanayin shigarsu da fuskarsu kawai za ta tabattar riƙaƙƙun masu laifi ne. "Allah ya taimaki maigida" cewar ɗaya daga cikin su. "Ya aka yi madaki?" "Akwai ƙura ne, ƙurar kuma na neman zama gagarumar guguwa" "Ina jin ka" "Aminu Viper, haryanzu jami'an tsaro ba su kama shi ba, ya sa an kaiwa yarana mummunan hari, an yi musu miyagun raunuka, jami'an tsaro sun kama yarana sun saki nasa, wanda aka kai asibiti ma, an kwashe su daga asibiti babu wanda ya san in da aka kai su" Mutumin yayi tsaki ya ce "Ina mamakin yadda mutum ɗaya ya gagari kamun hukuma, ni anya ba raina mini hankali ma suke yi ba a kansa? Yanzu menene abun yi?" "Ka saka a sakar mini yarana, dan sai da su ayyukanka suke yiwuwa, kuma dole mu yi shiri sosai, idan da hali mu mu nemi in da yake mu kashe shi kowa ya huta" Mutumin yayi shiru yana kallonsa sannan ya ce "Aikuwa da na yi maka tukucin da baka taɓa tunani ba, zan saka a saki yaran nan anjima kaɗan, sai dai duk yadda zaka yi ka yi, a samo yaron nan, dama mugu shi ya san makwantar mugu ai" Madaki ya sauke numfashi ya ce "Zan shirya gagarumar ɗaukar fansa kan mai uwa da wabi a unguwar su, jinin yarana da suka zubar ba zai tafi a banza ba, dan shammatar su ka yi, suka mamaye su ba na nan" "Wannan ku ta shafa, ni babban burina shi ne Aminu, muddin yaron nan yana numfashi, kamar sarƙa ce a wuyana, dole a kawar da shi". Madaki ya ce "Ba kai kaɗai ba, ko kuma in ce da ni da kai kusan abu ɗaya ne a wurinsa, nima ka san akwai tawa ni da shi, tsohuwar gaba ce ta tsawon shekaru, wanda a kanta unguwanninmu suka kasa zaman lafiya har yau, ga kuma wannan al'amari da ya faru. Muddin ban kashe Aminu ba, ni zai kasheni" Ya jinjina kai ya ce "Ai Viper na fuskanci ƙarfe ne a wuta, ya fi ƙarfin ɗauka da hannu, sai dai da ɗan uwansa ƙarfe, kai kaɗai zaka iya maganinsa" "Ka bani lokaci kawai, zan kuma ƙoƙartawa, matsalar ko yaransa ba kowa ne ya san in da yake ba, amma na san dole Walid ya san in da yake, amma shi ma Walid ba lafiya ba ne taɓa shi, ka dai bani lokaci" "Babu isasshen lokaci, ka yi huɓɓasa kawai" Madaki ya jinjina kai. Mutumin ya ɗebo kuɗi ya bashi, ya sallame su, suka juya suka fita da shi da yaransa. Nasir ne tsaye a office ɗin sa, ya kalli matashin da yake zaune, da aƙalla zai yi sa'ansa ya ce "Mu'azzam lamarin ƙasarmu sai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka san da ƙyar na gano station ɗin da yaran nan suke, ba ma ta yankin da abun ya faru ba ce?" Mu'azzam ya yi murmushi ya ce "Haka ka ce mini" "Gaba ɗaya yaran under age ne, kuma duk cikinsu babu yaran Aminu, dan tuni an sake su, sai wani wai madaki, na ce dai a ajiye mini su, da yiwuwar mu kama madakin, zai iya sanin in da Aminun yake,tun da abokin faɗansa ne, amma da na yi magana da DPO ɗin division ɗin yankin, ya ce shi ma madakin ba ya kamuwa, kuma ya addabi yankin yana da yara sosai da sosai. Abun takaicin ma ba unguwar su ɗaya da Aminun ba, amma suke cigaba da tayarwa da mutane tarzoma" Mu'azzam ya ce "Harkar nan tamu sai fa Innalillahi wa Innalillahi raji'un, muna tufka manyanmu na warwarewa" Nasir ya ce "Bari kawai, zan yi iya ƙoƙarin da zan yi, ni zan kama Madakin, Arfa har asibitin da aka kai waɗanda aka yi wa rauni ta je, muka yi waya kafin na je wai an kwashe su, an bar asibitin da su, na fara zargin anya ba jami'an mu ne aka samu bara gurbin da suke mara masa baya ba" Mu'azzam ya ce "Ba abun mamaki bane ba, amma meya kawo Arfa cikin wannan lamari, ta bar aikin lawyern ne?" Yayi murmushi ya ce "Rigima mana, yarinyar nan ta zarce tunaninka, ba ta wasa da duk abun da ya shafe ni ko cigaba na" "Hmm Nasir kenan, wai yaushe zaka gayyacemu sabgar nan ne? Shekarun ka fa suna ja" Nasir ya rausayar da kai ya ce "Mama ce ta hana, ta nuna ba ta so, ban taɓa gaya mata ba, saboda tun kafin na furta maman ta gargaɗe ni a kan haka, kuma haryanzu ni ban ji ina son kowace yarinya ba, ita ɗin dai nake so. Ban san adadin samarinta da na kora ba saboda kishi. Yadda take son abun da nake so da son cigabana, na san da zan furta ina sonta, ba zata ƙi ba, amma na rasa yadda zan yi da mama". "A'a Nasir, dan Allah kar ka zalunci yarinya, haka zaku zauna shekaru na tafiya, kai baka aureta ba, kuma ba ka bari wani ya aura ba? Wannan ai mugunta ce, ka yi magana da Abba mana". Nasir ya girgiza kai ya ce "Manta kawai, abun ya wuce yadda ka ke tunani". *** Arfa na kitchen tana taya baba magajiya aiki, suna hira tana tambayar baba magajiya kwatancen cikin unguwar ƙofar na'isa, dan zuwa aiken barrister Habib, dan ita ba zuwa ta taɓa yi ba. Baba magajiya na girki, ita kuma tana wanke-wanke a sink. Siyama da take ƴa ta uku ga mama ce ta shigo kitchen ɗin, ta jefawa Nabila kwanukan hannunta maimakon ta ajiye. Nabila ta yi shiru, ta cigaba aikinta suna hira, duk da abun ya ɓata mata rai. Amfani ta kuma yi da kofi, ta wurgowa Nabila cikin sink, cikin zafin nama da masifa, Nabila ta ɗauki kofin ta jefa mata a fuska ta ce "Ai ba baiwar ubanki ba ce ni, da zaki din ga jifana da kwanuka" "Nabila ni ki ka daka?" "An dake ki ɗin?" Baba magajiya ce ke ƙoƙarin basu haƙuri, amma siyama ta shaƙe Nabila, Nabila ta rarumo wani kwano ta buga mata, dambe ya kacame. Baba uwani ta yi ƙoƙarin raba su, amma abu ya gagara. Ta fito falo da gudu, tana neman taimako. Dambe tun daga kitchen har falo, duk abun da Nabila ta rarumo sai ta kwaɗa mata, kamar wasu kuraye. "Mahaukaciyar ina ce ke? Ke kullum haka zaki ƙare ki zagi wannan ki ci mutuncin ƴaƴan gida kina ƴar karere" Cikin baƙin ciki Nabila take kallon mama, tana iya ƙoƙarinta wurin danne abubuwan da mama take yi mata, duk faɗanta da tashin hankalin ita da yaran gidan suke yi, amma sai mama ta shiga ta zaƙe ta shigarwa yaranta. Anty ta ce "gaskiya maman Sauda wannan ba girmanki bane ba, maimakon ki yi musu nasiha, sai ki din ga aibata Arfa, ai ba a haka" Siyama ta din ga zagin Nabila, zagi na cin mutunci, tsawar da Abba ya yi musu ne, ya sanya duk suka ɗago cikin tsuma. Ya nuna nabila ya ce "Arfa, ban isa na saka doka ki bi ba ko? Siyama ba gaba take da ke ba? Nake jiyo muryarki tun daga waje kina zaginta?" Arfa ta buɗe baki zata yi magana, amma ya daka mata tsawa ya ce ta yi masa shiru. Siyama kuma ta fashe da kuka tana gaya masa har dukanta arfa tayi. Aikuwa ta in da ya shiga ba ta nan yake fita ba, ya hana kowa magana ya yi wa arfa kaca-kaca saboda sanin ba ta ji, ga rashin haƙuri da taurin kai. Da sauri ta tafi ɗakinsu tana wani irin kuka, ta je ta faɗa kan gadonta, jikinta har rawa yake yi saboda baƙin ciki takaici ta din ga kuka. Cikin kuka ta ce "Ya Allah ka bani miji kowane iri ne, in dai zai zama alkhairi a gare ni, na tafi na bar gidan nan, na gaji Allah ka amsa mini dan girmanka, kowane iri ne zan iya zama da shi". Can falo kuma, jikin Abba ne yayi sanyi, ganin arfa na kuka ya san akwai wani abu a ƙasa, dan idan tayi laifi, wataran ko kasheta zai yi ba zata yi kuka ba, duk da tana da saurin kukan. Ya kalli Anty ya ce "Zainab je ki duba yarinyar nan, kar ciwonta ya tashi" Anty ta jinjina kai, ta bi bayan arfa. Mama kuwa a sashinta take yi wa Siyama mitar meyasa ba ta yi wa Nabila dukan da za ta kasa tashi ba. "Mama kin san yarinyar nan har aljanu take yi, haka kurum su tashi ni ta kashe ni, komai ta rarumo buga mini take yi, ba ki ji kafaɗuna ba" Mama ta yi ƙwafa ta ce "Na rasa yadda zan yi maganin yarinyar nan, wallahi bana sonta ba na ƙaunarta, gaba ɗaya ba kwa gaban mahaifinku sai ita, in sha Allah sai ta zame masa masifar da ba zai iya shawo kanta ba, sai ta kwaso abun kunyar da za ta kunya ta shi a idon duniya". Nabila kuwa ƙin saurar anty ta yi, ta sha uban kuka, Anty ta sanarwa Major kukan da take yi, ya basar kamar bai damu ba, amma ƙasan zuciyarsa sam babu daɗi. Tsakar dare suke waya da sumayya, take gaya mata abun da ya faru. Sumayya ta ce "Arfa, ke rashin haƙuri ne yake janyo miki wasu abubuwan, da kin yi haƙuri ba ki tanka mata ba, dama neman magana ta zo yi". "Sumayya kin san ba zan iya ba, ni ina wulaƙanta mutane ne?" Sumayya ta ce "A'a idan na ce kina da wulaƙanci Nabila na yi miki sharri, sai dai masifa da rashin haƙuri, ga jarababben taurin kai ba a gaya miki ki ji ko kaɗan" Nabila ta ce "Sai dai ayi haƙuri da ni a yadda nake, ni ba zan yadda da wulaƙanci ba" "Aikuwa zaki yi ta shan wahala dan ubanki" Nabila ba ta damu da zagin da sumayya ta yi mata ba, domin idan da sabo ta saba, dan wasu lokutan sumayya playing role take yi kamar na uwa a rayuwarta, ta kan ji maganarta idan ta ga dama. "Sumayya dan Allah ki yi mini addu'a, Allah ya bani miji kowane iri ne, in dai zai zame mini alkhairi a shekarar nan na bar gidan nan na huta" Sumayya ta ce "Ba ki da hankali, kowane iri fa ki ka ce" "Eh, wallahi idan ba haka ba, zan gudu na bar garin nan, na bar musu gidan, sumayya baki san me suke yi mini ba na gaji" ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa tana kuka. Sumayya ta san komai, dan haka cikin rarrashi, ta kwantar da murya, ta din ga yi wa Nabila nasiha, da rarrashin ta, har ta sassauta kukan da take yi. Da haka suka yi sallama, ta kwanta bacci. Sai dai ta kasa baccin, saboda yadda zuciyarta take zafi, ta rasa me ta tsarewa maman su Sauda a rayuwa, da ita da yaranta suka tsaneta haka, Nasir ne kawai suke ɗasawa da shi, da ƙyar bacci ya kwashe ta. Da safe ta shirya cikin wata abaya baƙa, tayi kyau ko karyawa ba ta tsaya yi ba, ta fito falo fuskarta babu walwala. Kallo ɗaya zaka yi mata, ka san ba ta samu isasshen bacci ba. Da kamar ta yi fuska tayi tafiyarta, amma ta haura benan Abba ta je ta gaishe shi, sai dai fuskarta babu annuri, babu raha da ta saba yi idan ta je gaishe shi. Ya ƙura mata ido ya ce "Kin karya kuwa?" Ta ce "Idan na tsaya karyawa zan makara, zan karya a wurin aiki" "Dan zaki makara sai ki fita ba ki karya ba, yaushe ki ka fara tsoron makara? Menene ma ya hana ki tashi da wuri?" Tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta, idonta yana cika da hawaye. Ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro kuɗi masu yawa, ya miƙa mata ya ce "Ga wannan na san wata yayi nisa, babu lallai ki na da kuɗi a hannunki, ki sai wani abun idan kin je ki karya, saura ki sai abun da zai ɓata miki ciki, ko ya cutar da lafiyar ki" Kamar ta ce ya bar su, amma ta saka hannu biyu ta karɓa, ta ce ta gode, yanayin yadda take tafiya kawai, zai tabattar mata da tana cikin damuwa ko rashin lafiya. Gaba ɗaya jikin Abba ya yi sanyi, a tsakiyar zuciyarsa yake jin zafi, idan ya ga Nabila a cikin damuwa, shiyasa wasu lokutan baya iya jure yi mata hukunci yake kawar da kai a kanta. Duk iya ƙoƙarin da Nasir yake yi, a kan yaƙi da harkar daba, abu ya ci tura, dan yaran da aka kama ya koma ya tarar da wai an yi umarni daga sama a sake su, abun ya ɓata masa rai sosai da sosai. ***** A farfajiyar wata bishiya suke zazzaune, suna ta shaye-shayen kayan maye, duk sun cika wurin da ƙaurin hayaƙi. Madaki ya karta wuƙa a ƙasa, ya kalli tarin matasan da sun fi ashirin a gabansa ya ce "Babu rangwame ko sassauci, babu mace babu namiji, ko babba yaro ko tsoho, duk wanda aka samu idan aka shiga operation ɗin nan a farmasa, ayi ɓarna ayi ta'adi a ɗauki fansar abun da Aminu yayi mana, jini ya din ga gudana ko ta ina, duk shagon wanda aka samu a fasa ku kwashi ganima, na yarje muku. Haka zalika duk wanda ya gano in da Viper yake, muddin ya kawo mini shi, a mace ko a raye, akwai tukuici mai tsoka" Suka fara shewa cike da maye, ɗaya daga cikin su ya ce "Aminu fa ƙarfe ne a wuta, duk wannan shewar kama shi ba abu ne mai sauƙi ba, da mai sauƙi ne na san da ka riga mu kama shi" Madaki ya ce "Rufe mini baki, ko na yi gunduwa-gunduwa da namanka, dole ne a kama shi, kai gobe duk wanda aka gani daga tsallaken unguwar su, ya shigo unguwar nan ma a sara mini shi kawai, a ɗauki fansa mafi muni na abun da ya yi mana, zan ga da ni da shi, waye zai sarara waye gaba da wani" Cikin haɗa baki suka dinga faɗin "An gama oga, gobe akwai ƙaramin yaƙi" misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe, a sannu take tafiya a cikin unguwar, tana duba kwatancen da barrister Habib ya tura mata. Kasa ganewa tayi, ta tsaya a wurin wani mai kanti, ta sayi ruwa ta sha, kuma tambaye shi. Tana tsaye tana duba wayarta a cikin shagon provision ɗin, wani matashi ya shigo, suka gaisa da mai kantin ya ce "Bani ƙulli biyu da ruwa uku" Mai kantin ya ce "Amma ka san ina binka sauran kuɗi ko?" "Zan biyaka, wannan yawa ne, ka bani na ware mana, caji zan yi kaina gaba ɗaya babu network,aljihuna kuma yayi gobara" "Ba zan bayar ba" mai shagon yayi maganar yana miƙawa Nabila ruwan roba. Nabila ta din ga satar kallon matashin, yadda bakinsa ya karkace saboda shaye-shaye take kallo, laɓɓansa duk sun zazzago. Tayi gyaran murya ta ce "Ɗan uwa ka bashi mana, tun da ya haɗaka da Allah, in sha Allah zai kawo maka, tun da ya yi alƙawari" "Rabu da shi, ba ya biyan bashi" Nabila ta yi murmushi ta ce "Nawa ne kuɗin nasa?" Mai kantin ya ce "Dubu biyu nake bin sa" Ta yi murmushi, tare da ciro kuɗi a jakarta ta ce "Dubu biyu ai babu yawa, Ga dubu uku, na biya masa kuɗin da ka ke bin sa, ka bashi wani bashin, ni kuma ka ɗauki kuɗin sayayyata" Matashin ya kalleta ya ce "Sai kin yi babbar yaya, Allah ya ƙara arziki" Ta amsa da "Amin ɗan uwa na gode sosai". Wani abu ta ga an bashi a nannaɗe a leda, da ruwa ya sake yi mata godiya, ya fice. Yana fita ta ce "Malam dan Allah menene wannan ya saya?" Mutumin yayi murmushi ya ce "Ƙanwata wiwi ce" waro ido ta yi ta ce "Wiwi kuma, ka ke sayarwa? Amma na ga kai kamar ba ka sha ko?" "Ki yi ƙasa da muryarki mana, ya zamu yi sana'a ce, ni ba abun da nake sha. ga canjinki" Cikin mamaki ta ce "Meyasa ka ke sayar da abun da ba ka sha?" "Kar ki tsananta bincike malama" yayi maganar yana haɗe rai. Ta jinjina kai ta ce "To Allah ya taimaka" Fitowa ta yi daga shagon, ta hangi matashin yayi nisa, ta rufa masa baya ta bishi da sauri. "Bawan Allah ɗan tsaya dan Allah" ta ƙarasa tana haki. Ya tsaya yana kallonta ya ce "Ya dai?" "Abu zan tambaye ka, amma kafin nan ka san abun da ka saya ɗin nan, yana da illa ga lafiyarka?" Tsayawa yayi yana kallon ta, tayi saurin cewa "Dan Allah taimako nake nema, wani gida nake nema, amma na kasa gane layin, ko zaka taimaka mini?" "Ina ne?" Ta gaya masa ya ce "Na san gidan, amma ba hanyar ki ka biyo ba nan" "Dan Allah kwatanta mini" "Mu je na kai ki bakin layin" Ta ce "Yauwa ɗan uwa, dan Allah mu yi wata magana mana, ka san wani mutum Aminu Viper?" Wani irin burki ya ci yana kallonta. "Yi haƙuri idan na ɓata maka rai, ɗan uwana ne shi, tun da Allah ya sa ya bar gidan yari, bamu sake ganinsa ba, kuma na ji an ce yaransa sun tayar da tarzoma a unguwar nan a satin nan, dan har asibitin da aka kai waɗanda aka yi wa rauni na je, na zaci zan ganshi, amma ban tarar da shi ba" Ya ware mata jajayen idanunsa ya ce "Ki ka ce ɗan uwanki ne?" Cikin ƙarfin hali ta ce "Eh, ina da alaƙa da shi" Ya ce "Na san shi, na kuma san in da yake" Da sauri ta ce "Dan Allah ka taimaka mini a ina zan ganshi?" Ya ƙare mata kallo ya ce, idan kin tashi, ki tambayi ina ne layin iraƙi a unguwar nan, idan ki ka je akwai wata babbar bishiya zaki ga wasu a zazzaune a wurin, ki tambaye su, za su nuna miki shi. Cikin tsananin farin ciki, ta din ga yi masa addu'a. Amma fa sai dai ta kasa tantance irin kallon da yake yi mata, hakan bai dame ta ba. Har ƙofar gidan matar ya rakata, ta kuma yi masa godiya, ta ciro kuɗi ta bashi, sannan ta shiga gidan matar. Matar ta karɓi Nabila hannu bibbiyu, bayan da Nabilan ta yi mata bayanin barrister Habib ne ya turo ta. Ta bawa Nabila duk wani information da take buƙata, tana gama abun da take yi ta tashi ta ce tafiya za ta yi. Babu yadda matar ba ta yi da ita ba, a kan ta zauna ta ci abinci ta yi salla, amma taƙi, ta tashi ta tafi. Babu tunanin komai, tana fita, ta tambayi wasu yara, ina ne layin iraƙi?. Duk sai da suka kalleta, ganin tana mace tana tambayar wannan layin da ƴan daba suka mayar mallakinsu, abunka da yara, babu tunanin komai suka sakata a hanya, ta yi musu godiya ta nufi kwatancen. Tana ta addu'a Allah ya sanya ta dace, duk tana da burin cikar nata muardin, amma za ta yi farinciki sosai idan aka ce Nasir ne yayi nasarar kama Aminu, koba komai likkafarsa za ta sake ɗagawa, ta nufi layin ba tare da ta san idan ta ganshin me za ta ce masa ba. Layin shiru babu kowa, babu gina-ginan kirki, sai kangwaye, sai da ta je tsakiyar layin, ta hango wata ƙatuwar bishiya, da mutane. Kamar ba mace ba, babu razani ko fargaba ta tunkari bishiyar. Gaba ɗaya suka zuba mata ido, har ta ƙaraso. Wiwi kawai suke busawa, ta ɗan tsaya nesa kaɗan da su, saboda hayaƙi. "Ina wuninku" Suka amsa mata da lafiya ƙalau, suna mamakin ganin mace a wannan chamber. "Dan Allah tambaya nake yi, wani nake nema, aka yi mini kwatancen nan aka ce zan sameshi". Ɗaya daga cikin su ya ce "Waye shi?" Ta ce "Amm, sunansa Al'amin, amma ana ce masa Aminu Viper, tun da ya fito daga prison ba mu sake ganinsa ba" Ɗaya ne ya miƙe tsaye ya ce "Ke, ba ki da hankali, a dabar madaki ki ke naman wannan ɗan iskan? Kai kan taba, sako su mass su rakata, tun kan oga ya zo ya saka ayi gunduwa-gunduwa da namanta" Sai yanzu ta fuskanci shigo-shigo babu zurfi wanda ya yi mata kwatancen ya yi mata. Cikin sauri ɗaya ya ce "Meyasa za'a bari ta tafi? Bayan ka san yau zamu fasa ɗaukar fansa, ta kanta ya kamata mu fara" yayi maganar yana ƙoƙarin zare makami. Sai dai tuni suka sako wa Nabila wasu irin murguza-murguzan karnuka, masu kama da zakuna. Cikin ihu ta kwasa da gudun tsiya, tana kururwar neman agaji, saboda yadda take ganin kamar karnukan za su cinyeta ɗanya, sai dai gudun da suke yi ya wuce hankali, ga takalminta mai tsini ne sosai, dan haka suka kusa cimma ta. Babu tsammani ta faɗi, saboda yadda numfashinta ya fara sama-sama. Ayshercool. 08081012143 [7/22, 1:49 PM] null:               *ƘARFE A WUTA* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g P8 Ta saka hannu, ta kare kanta, tana jiran su hauta da cizo. Wani irin fito ya yi wa karnukan, suka juya suka koma da gudu in da yake. Matashin nan ne na ɗazu, da ta biyawa bashi, ya kalleta ya ce "Kin san meyasa na taimake ki?" Bai jira amsar da za ta bashi ba ya ce "Ba na tunanin Aminu yana da wata ƴar uwa mace, dan haka ƙarya ki ke yi, akwai wata manufa a ranki da yasa ki ke nemansa. Sannan ya taɓa yi mini alfarma a lokacin da ya samu damar da zai kashe ni, kuma kin kyautata mini, alhalin baki sanni ba. Ɗan daba ba mahaukaci bane ba, shaye-shaye ne yake ruɗa mana tunani. Wannan shi ne kaɗan daga abun da ka iya samunki, idan ki ka cigaba da neman sa, ko bibiyarsa, wannan dabar babu abun da suke buri da fata, sama da su riga ƴan sanda kama aminu, mace ce ke ki kiyaye kanki, tashi maza ki tafi gasu can tahowa, idan suka cimmiki babu lallai na iya hana su illata ki" Da ƙyar ta tashi, ta yi gaba da sauri, tana cigaba da haki, adaidaita sahu ta hau, ta yi masa kwatancen in da zai kai ta. Kasancewar mai rabon shan duka, baya jin bari, suna tafe tana sauke numfashi, tana tunanin son sanin su kuma waɗan nan me yayi musu suke son su riga ƴan sanda kama shi, suna ƴan uwansa ƴan daba. "Ko wani ya kashe musu?" Ta tambayi kanta. "Yayi kisan kai, kuma a sake shi? Aikuwa sai na ga ƙwal uwar daka" ta furta a hankali. Ta so ta gaya wa Nasir, abun da ya faru yau, amma ta san tsaf zai ce zai zaneta, saboda kasadar da ta yi, dan haka ta bar wa ranta cewa sai ta samu wata gagarumar nasara, sannan za ta sanar da shi. Ko sumayya ma ba ta gaya wa ba, tayi shiru da bakinta, sai dai faɗuwar da tayi, duk ta goge gwiwa. Haka kurum tausayi, da tunanin makomar rayuwar matasan da ta gani, a harkar daba da shaye-shayen nan, ya dami zuciyarta ta rasa abun da yake yi mata daɗi, tana matuƙar son sanin me suke ji a cikin kayan shaye-shaye? Tabbas da ita wata ce, sai ta taimakawa rayuwar su, ko a mutum goma, idan biyu suka shiryu ai an rage. Kamar wadda ta sha kayan maye, haka yau tayi bacci da wuri, gudun da tayi jikinta duk ciwo yake yi mata, ga numfashi sai wahala yake ba ta. A wani ɗaki ta ganta, mai duhu sai haske kaɗan a ciki, ga karnuka duk a cikin ɗakin, sai haushi suke yi mata, an ɗaure su da sarƙa. Ihu take yi tana neman agaji, amma babu wanda ya san tana yi. Can sai ga wani mutum ya shigo, dogo sosai, mai cikar halitta, ba ta ganin fuskarsa saboda duhu, ya shigo ɗakin bai ce mata uffan ba, ya danƙo hannunta ya biyo tsakanin karnukan ya fito da ita daga ɗakin, ya ciro wuƙa zai caka mata a ciki. Wani uban ihu ta saki, tana kiran sunan Allah, da na Abba da Nasir. Tana buɗe ido, ta ga Abba a kanta, da Nasir, da su walida har da Anty da baba magajiya, ana ta tofa mata addu'a. Kallonsu take yi ɗaya bayan ɗaya, ta ce "Abba ya na ganku a nan? Meyafaru?" Nasir ya ce "Sannu" Abba ya ce "Arfa ba kya addu'a ko?" Ta girgiza kai ta ce "Ina yi Abba" "A'a ba kya yi, da kina addu'a babu yadda za ayi, ki kwanta kina yi mana ihu da safiyar nan, shiyasa nake hanaki wannan shegen fentin da bulbula turare a jikinki, dole sheɗanu su yi ayari, su yi ta binki" Nasir ya ce "Dan Abba ka yi haƙuri, haryanzu a tsorace take ma, a bari ta dawo hayyacinta gaba ɗaya, sannu Arfat, ki ɗauro alwala ki zo ki ɗauki Alqur'ani ki karanta". Abba ya miƙe ya ce "Aishikenan, zan yi waya da Barrister, su baki day off, ki samu ki huta" Nabila ta yi shiru tana rarraba ido, ta san lafiyarta ƙalau, tsabar tsorata ne da tayi. Tayi shiru ba ta faɗi abun da ya faru ba, suka din ga yi mata sannu. *** YALOKO ƘARAMAR HUKUMAR UNGOGGO Matashiyar yarinya ce, wadda dudu shekarunta ba su fi goma sha huɗu ba, take ta iza wuta a cikin murhu, gefe ga garin tuwo a cikin ƙwarya. Yaro ne ya yi sallama, ta ɗaga kai ta amsa masa. Ya kalleta ya ce "Ramma ki zo ana sallama" Ta ɗan waro manyan idanunta ta ce "In ji wa? Ko Habu ne?" "A'a, wani ne da mota" Ta miƙe tsaye ta ce "To mota kuma, ina zuwa?" Daga tsakar gidan ta ɗan ɗaga murya ta ce "Mama, wai ana nemana a waje, bari na duba waye, ruwan ya kusa tafasa" Daga cikin ɗaki matar ta amsa mata da "To ramma, hanzarta ki dawo, ina son zan fita ne" Ramma ta amsa da "to" ta ɗauki hijjabinta ta saka ta fice waje. Mintuna goma sha biyu ta dawo, jiki a sanyaye. Mamanta ta kalleta ta ce "Menene?" "Mama daga Kano ne, wai Anty mai jidda ce gidan da nake aiki, ta yi waya wai azo a ɗauke ni a mayar da ni, a satin nan za su dawo" Matar tayi sak ta ce "Da wuri haka, ba cewa aka yi sai bayan wata guda zaki koma ba?" Ramma ta ja ta tsaya ta ce "Jikina duk yayi sanyi, wai yanzu-yanzu zamu tafi" "To shikenan ai babu wani abu, ki yi haƙuri kin ji ramma, ni kaina ba a son raina ki ke barin gabana ba, da Allah ya sa mun tara kuɗin kayan gado, shikenan sai ki dawo ki yi auren ki. Maza mu je na tayaki haɗa kayan" Cikin abun da bai fi mintuna arba'in ba, suka haɗa kayan, suka yi sallama ramma ta bi direba zuwa gidan aikinta da yake Kano. Yana zaune ya zuba musu ido, suna haɗa masa tea, Walid ya zuba ƙwayoyi a cikin kofin, sannan ya zuba shayin. "Ƙara wannan ba zasu ɗauke ni ba" Walid ya ce "Amma boss, kai fa ka ke hanamu sha a baya, tayi yawa wallahi". "Ka ƙara mini na ce" yayi maganar a hasale. Ya ƙara masa ƙwayoyin yana kallonsa, saboda ƙwayar da suke yi wa laƙabi da raina kama, a baya sam baya shan irinta, saboda yadda take bugarwa, wasu lokutan rabi suke ɓallawa su sha, amma ya ce a saka masa kusan biyar yanzu. Ya ɗauki kofin ya kai bakinsa zai fara sha, Walid ya ce "Yau fa madaki za su je ɗaukar fansa cikin unguwa, daga majiya mai ƙarfi na ji zancen, daga jiya zuwa yau ya ce idan ɗan arearmu ya shiga ta su, a aika shi kawai" Ya cigaba da girgiza kofin ba tare da ya yi magana ba, ya sake yinƙunrin kai kofin bakinsa, walid ya sake cewa "Wata ta je nemanka a arear, aka kaita dabar madaki, Allah ne ya yi da kwananta a gaba, da kasheta za su yi" Duk da cikinsa yayi wata ƙara, jin an ce mace ta na nemansa. Wace mai tsautsayin ce wannan? Me take nema a wurina?, amma ya maze ya ɗago jajayen idanunsa ya kalli walid ya ce "Ni kuma?" Walid ya ce "Ba zan yi maka ƙarya ba, da gaske nake" Wani dogon tsaki ya ja, ya dungurar da kofin shayin, ya tashi ya ce "Ku ɗebo yaran nan na cikin unguwa, da na can wajen gari, ku sake dira a dabar madaki, ina son ɓarnar da za ku yi ta fi waccan, kar ku basu damar cutar da kowa. Ko kun gaya wa jami'an tsaro ƙudurinsu, babu abun da za su yi musu, ku far musu kawai, ka shirya komai, a bawa yaran na shan sigari" bai jira amsar walid ba ya fice. Walid ya yi ajiyar zuciya, ɗan mama ya kalle shi ya ce "Da gaske ka ke wata ta je nemansa, ko kuma ka faɗa ne, dan ka hana shi shan ƙwayar nan?" Walid ya ce "Duka, kai da ya sha abun nan, zai iya mutuwa fa" Ɗan mama ya ce "Ai rigimar da yake yi kwanan nan, ta ƙara yawa, sai an ƙara saka masa ido sosai, kashe kansa yake son yi wallahi, wasu lokutan bana son muke watsewa  mu bar shi shikaɗai a gidan nan". Walid ya girgiza kai ya ce "Ba zai kashe kansa ba". "Ya aka yi ka san hakan?" "Yana da abun da yake son cimma, kawai kayan ne gaba ɗaya ba sa ɗaukarsa gaba ɗaya yanzu, ka san yana cikin matsananciyar damuwa, duk kayan cajin nan kansa ba ya ɗauka kamar aljani, amma ina bincikawa, an yi mini alƙawarin wata zazzafar ƙwaya, daga kudu suke kawota. Yanzu dai wannan aikin da ya ce , maza-maza ka kira kwangila a waya, ya haɗa mana yara, a basu kayan caji, zamu fasa ƙofa, ai Madaki shi da ɗaukar wata fansa a kanmu, sai dai a lahira idan ana yi. Sai mun ga abun da ya turewa buzu naɗi. Ɗan mama ya miƙe ya ce "Ok, bari na hanzarta na fara haɗo su ta arear wajen garin nan". Walid ya ce "Nima fitar zan yi, wurin liti zani, zan shiga karɓar balance". Suka fice gaba ɗaya. Bayan tafiyar su Aminu ya koma cikin ɗakin, ya fara duba in da walid yake ajiye ƙwayoyi, amma ya dudduba bai gansu ba, ya zazzage ko ina, amma babu. Wani irin takaici ya tokare masa ƙirji, ya ja dogon tsaki, ya ɗaga gefen katifarsa, allurar sa saura kwalba biyu kawai, kuma ya san ba ɗaukarsa za ta yi ba. Haka ya zuƙe ta ya yi wa kansa, sai dai kamar kullum, yau ma ƙirjinsa ne ya fara da zafi, kansa yana juya masa. Wuƙar da take gefensa yake ta kallo, zuciyarsa na raya masa abubuwa daban-daban. Tun da Ramma ta suka isa cikin kano, gidan da take aikatau, kayanta kawai ta sauke a ɗakinta, ta hau aikace-aikace. Duk da akwai wata mai aikin, wadda ta girmewa ramma, sosai da sosai, amma matar gidan ita ta yarjewa ta shiga sashenta, har uwar ɗaka da na maigidan ta gyara mata, a cewarta ramma ta fi nutsuwa, kuma ba ta taɓa ƴar aikin da ba ta yi mata sata ba, sai ita. Matar gidan da ƴaƴanta gaba ɗaya sun tafi dubai hutu, shiyasa ta sallame ta, ta ce ta je gida ta huta, za su yi wata biyu kafin su dawo, kuma kwatsam yanzu sati biyu wai dawowa za su yi. Tana falon matar gidan, tana ta uban aiki, ɗan kwanakin da aka yi ba a taɓa wurin ba, duk ya yi ƙura. Ƙofar falon aka shigo, ta tashi da sauri, tana kallon mai shigowar, dan ba ta yi tsammanin ganin kowa a sashen ba, dai-dai wannan lokacin. *** Nabila kuwa kusan kwanaki uku curr, ta kasa nutsuwa da kwanciyar hankali, da ta kwanta bacci, sai mafarkin karnuka, tayi ta ihu. Haka Anty da baba magajiya za su danneta, su yi ta shafa mata man gelo da miski, ta ja bakinta, ta yi shiru, ba ta gaya musu abun da ta aikata ba. Yau kuwa gajiya ta yi da zaman gidan, dan baka cikin hijjabi ta shirya, ta ɗauki ƴar ƙaramar wayarta, ta fito falo. Umma ta kalleta ta ce "Ke da baki da lafiya, ina zaki je kuma?" Nabila ta ce "Wurin aiki, akwai buƙatar in je zan kai wani bayani ne mai muhimmanci" "Amma kin gaya masa, kar ya dawo ya tarar kin fita, ya yi ta faɗa" "Umma ba daɗewa zan yi ba" Saudat ta ce "Mhmm, a ma faɗi gaskiya, ko yawon banza za aje". Nabila har za ta yi shiru, ta ga idan tayi shiru, za ta cutu, dan haka ta ce "Idan fitsari banza ne, kaza ma tayi, idan yawon ma zan tafi, mai lasisi ne akwai riba, ke ki yi mana" Umma ta kalli Sauda ta ce "Sauda dan Allah ki din ga jan girmanki, Nabila fa ba sa'arki ba ce ba". "Na saka da ke ne?" Umma ta girgiza kai ta ce "A'a baki saka da ni ba, Allah ya taimaka". Sumayya tana ta aiki a news room, Nabila ta yi sallama ta shiga. Sumayya ta kalleta ta ce "Ina aikin?" "Ban je ba, ya aikin?" "Lafiya ƙalau, meyasa ba ki je ba?" Nabila ta ce "Ke ba wannan ba, yanzu na ga managern ku a waje muka gaisa" Sumayya ta ce "Good, ya aka yi?" "Rahotonki na last week, a kan case ɗin yarinyar nan da aka yi wa fyaɗe, na ji shiru baku sake cewa komai ba" Sumayya ta ce "Eh ya aka yi?" Nabila ta ce "ina da intrest a kai ne, ina son shiga lamarin, na ji shiru haryanzu babu wani update, na an ɗauki mataki" Sumayya ta ce "Dalla ware, kamar wata lawyer kirki, you are not even serious about the job" Nabila ta ce "Ke ban son wulaƙanci fa, am serious, na ji an ce wanda yayi laifin mai lasisi ne a garin nan, ina son sanin waye shi?" Sumayya ta ce "Nima ban sani ba" "Kamar yaya ba ki sani ba, am serious fa, da gaske nake sumayya ina son shiga case ɗin, free of charge na taimaka wa yarinyar, na ji tausayin su sosai da sosai, yadda uwar take kuka. Kuma daga ji ƴan karkara ne, masu ƙaramin ƙarfi". Sumayya ta galla mata harara ta ce "Sannu ambulance uwar taimako, manyan lawyoyi sun riga sun shiga case ɗin tuni, sai ki ja gefe" "Suwaye manyan lawyoyin? Kuma wai waye dan Allah, waye yayi fyaɗen?" "Ke! Nifa a rubuce aka bani, karantawa kawai na yi, hatta recording ɗin da aka saka, na muryar uwar da ƴar, tararwa na yi an yi, ban ma gansu ba, ban ga suwaye ba, balle na samu wani bayani. Case ma fa lamarin ya kusa zama a gidan nan, saboda saka muryar matar da aka yi, murtala ne dama ya yi recording ɗin ya saka, sai da aka kusa korarsu" Nabila ta ce "To fa, ina murtalan yake?" Sumayya ta ce "Ba zan nuna ba, kin ganki Nabila" "Ba wani abu zan yi ba, sonake kawai ya haɗani da matar da yarinyar". "Babu fa abun da zaki iya yi a kai, shi ma bai san waye wanda yayi fyaɗen ba, yarinyar aiki take a gidan, baƙo ne daga zuwa yayi mata. Dan Allah ki haƙura da case ɗin nan" A ɗan fusace ta ce "Saboda me?" Sumayya ta yi murmushi ta ce "Na ji an ce mutuniyar ki da jama'arta sun shiga cikin case ɗin, shiyasa na ce ki haƙura" Nabila ta ce "Wa kenan?" "Naja bunkure mana, antynki mudubinki, a bar ƙaunarki" Sumayya ta yi maganar tana dariya. A take annurin fuskar Nabila ya ɗauke, haka kurum jikinta ya bata babu gaskiya a lamarin nan. "Uban mudubin nawa, in dai wannan mudubin ne, Allah ya fasa shi na huta, wallahi sumayya tun daga abun da matar nan ta yi mini, kawai nake ji a jikina fuska biyu ce da ita, wadda take kallon jama'a da ita, da kuma wadda take ɓoyewa" "To ko ma dai yaya ne, sun shiga case ɗin, kin san kuma ba zasu tsaya su saurareki ba, mussaman da ta iya yi miki kallon ke ba komai ba ce ba" Nabila ta ce "Haka ne, amma rai dai an cire wa fara kai, lokaci ne, yana nan zuwa da zan bawa duniya mamaki, sai na saka ƙafa na bi ta kanta ko da halin ƙaƙa" "To ki bi a hankali, kar ke duniyar ta baki mamaki" Nabila ta yi shiru tana tunani. Sumayya ta ce "Ya dai?" Tayi guntun tsaki ta ce "Sumy zaman gidanmu babu daɗi, kamar in gudu wallahi". "Wai Nabila ba zaki daina wannan iƙirarin ba?" Ta girgiza kai ta ce "Ba zaki gane ba, faɗa muka yi da Siyama, har da Abba ayi mini faɗa, sauƙinta ɗaya ta ci duka da tukunya na din ga dukanta" "Haba Nabila, wannan ai yawa ne, degree holder da dambe?" "To yaya ki ke so in yi? In zuba mata ido ta yi mini duka? Ga uwarsu ta addabi rayuwata, ba ta san yadda ta tsane ni, nima haka na tsaneta ba, kawaici kawai nake yi mata ba. Duk uban ƴan matan gidan nan har da zaurawa, babu wanda duka sanyawa ido sai ni, da na motsa ayi ta janyo mini jafa'in karuwanci" ta ƙarasa maganar hawaye na cika mata ido. Sumayya ta ce "No dear, dan Allah ki ƙara jurewa, lokaci ne da kin yi aure zai wuce" "Yaushe zan yi auren? Dan Allah ni mummuna ce Sumy? Duk saurayin da ya zo, sai za a fara maganar aure, sai ya gudu kamar wata jaɓa" "Nabila kina da matsala, Babu wata halittar Ubangiji mummuna. Ga ki fara, ga gayu da ilimin addini da na zamani, kina da kwarjinin da ki ke bawa maza tsoro ne, ai ke kalar manya ce tawan, ba duk kai ba" Cikin takaici Nabila ta ce "Ba wasu manya, manyan da suka din ga yaudarata Allah ya isa da ba su aure ni ba suka ɓata mini lokaci, ni yanzu kowaye ma zan aura na bar musu gidan, ko ba na son shi. Idan ba haka ba wallahi wataran sai na gudu" Sumayya ga tausayin Nabila ga dariya, tabbas Nabila akwai farijinin samari, masu kashe mata kuɗi ma kuwa, sai dai Nabila ta fiye zaɓe-zaɓe, kuma ba ta fiye ba wa masu sonta da gaskiya muhimmanci ba. "Ki gudu ki je gidan uban wa? Gaki ga Abba nan maza ki gudu kar ki fasa" Sai kuma ta koma rarrashinta, har bayan azahar suna tare, sai da sumayya ta tashi suka fito tare. A reception suka tarar da wani mutum, ana ta yi masa fadanci, yana hura hanci cikin manyan kaya na alfarma, reception ɗin ko ina security. Sumayya ta risuna ta gaishe shi ya amsa, amma Nabila ko kallonsa ba ta yi ba, ta sunkuyar da kai, kamar alla-alla take yi, ta yi ta bar reception ɗin. Ɗan rikicewa yayi, ya ƙura mata ido, amma ta basar ba ta gaishe shi ba, sai so yake yi ta ɗago su haɗa ido, dan ya tabattar da abun da yake tunani, amma taƙi ta mayar da kanta gefe. Mamaki ya shiga yi, yana tunanin ko dai gizo idonsa yake yi masa? Sai dai ya rasa abun yi kafin ya yi wani yinƙuri, sun bar reception ɗin. Ɗaya daga cikin ma'aikatan ya kalla ya ce "Wannan mai hijjabin ma'aikaciyar ku ce ita ma?" Ya girgiza kai ya ce "A'a sir, she's just a guest here" Ya ce "She looks familiar to me, anyway shikenan dai" yayi gaba. Cike da takaici Sumayya ta ce "Kina kallon babban mutum ki ka basar ba ki gaishe shi ba, sai kallonki yake yi, ki ka sani ko shi ne mijin a dace a daidaita ko ƙyasawa yayi? Da irin wannan halin naki, ki ke korar samarinki na kirki wallahi". "Kin fi kowa sanin bani da baƙin hali, wasu lokutan ma cewa ki ke yi na fiye zaƙewa" "Haka ne, amma baki kyauta ba, ko dan kallon da yake yi miki, ai kya kula shi". Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ban taɓa jin na tsani wata halitta a kallon farko da na yi mata a rayuwata ba, sai wannan mutumin. Gaba ɗaya ya canza mini mood lokaci guda" Sumayya ta waro ido ta ce "Meyasa kun taɓa haɗuwa ne? Me yayi miki?" "No, ina ganin shi a poster dai, ba ɗan majalisa bane? Ban taɓa jin komai idan na ganshi a poster ba, sai yau da na ganshi ido da ido, bana fatan Allah ya sa na sake sanya shi a idona. Kin san me? ji nake kamar ya taɓa cutar da ni, cuta mai muni" "Arfa, kina hayyacinki kuwa? Tayaya mutumin da ki ka fara gani yau kawai, ki ce kin tsane shi, ya cutar da ke how?" "Ban san tayaya ba, amma haka nake ji a raina, kuma da gaske nake jin hakan" "Ki daina irin wannan wasan, kar ki saka a din ga yi miki mummunar fassara" "Forget, ba zaki gane ba" tayi maganar a daidai lokacin da suka ƙaraso titi. Tun ba ayi sallar magariba ba, walid ya riga ya gama tatara gayyar matasa zauna gari banza, wanda suka yi bankwana da fatan samun ingantacciyar rayuwa, suka kama makamai da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi. Kasancewar ba a cikakken hankalinsu suke ba, haka suka raraka kowa da kowa gida. Yaran madaki, na ta shirin shiga ɗaya unguwar sare-saren ɗaukar fansa. Labari ya iske su cewar, yaran Aminu sun rigasu yin dirar mikiya. Ba su yi zaton gayya guda, yaran aminun suka ɗaukko ba, dan haka suka fita domin su far musu. Kamar ba jikin ɗan Adam ba, haka suka din ga sara da sukar junansu, mutanen unguwa duk suka shiga gida suka rufe. Aka yi rashin sa'a madaki baya nan, ɗaya daga cikin yaransa, ya kira shi ya sanar da shi halin da ake ciki. Nasir yana zaune ya idar da sallar magariba yana lazumi, so yake ya tambayi ina arfa, ya ga ya jikinta, amma mama na babban falo, ya san da ya yi hakan, za ta yi masa faɗa, tare da sake gargaɗinsa a kan Nabila. Wayarsa ce ta fara ringing, ya shafa addu'ar, ya ɗaga tare da yin sallama. Da sauri ya tashi tsaye, yana faɗin gashi nan zuwa. Da sauri ya ɗauki mukullin motarsa, ya fito daga sashin mama, zuwa falo. Mama ta kalleshi ta ce "Ya dai? Ya na ganka a birkice?" Dai-dai lokacin Nabila ta fito daga ɓangaren ɗakinsu, hannunta riƙe da kofi, hakan ya sanya ya kasa ba ta amsa. Zuciyar sa ta tsananta bugawa da sauri, doguwar rigar material ce a jikinta, kanta babu ɗankwali, tayi parking ɗin gashinta. Wani irin kyau ta ƙara yi masa. "DSP yaushe ka dawo?" Tayi maganar tana kallonsa. "Da magaribar nan, yanzu nake shirin nemanki, in ga ya jikin naki? Wayarki ba ta shiga" Anty ta ce "Jiki yayi kyau, har fita tayi" "Fita kuma, ki ka je ina? Kuma da iznin wa?" "Dan ubanka ina yi maka magana ka shareni, maganarta ta fi tawa muhimmanci ne ko yaya?" A ɗan rikice ya ce "A'a mama, yi haƙuri kiran gaggawa aka yi mini, faɗan daba ya ƙara ɓarkewa, ƴan daba sun rufe unguwar babu shiga babu fita, yaran Aminu Viper ne da wani madaki, wai ƴan sandan da aka tura, sun kasa kwantar da rigimar, kin san am incharge of his case, shi ne zan je na ga abun yi" "To ka kula da kyau, ni wannan aikin ya isheni, shikenan kai ba hutu, ni hankali a tashe". Ya jinjina kai ya nufi ƙofar fita. Jin an ambaci Aminu, ya sanya jikin Nabila ya hau tsuma, ya bishi da gudu ta riƙo rigarsa ta ce "DSP, amma ba kai kaɗai zaka je ba ko?" "Eh, na yi waya za a ƙaro mini ƴan sanda" "Ko mu je tare?" Ya zaro ido ya ce "Ki yi me?" Sai kuma ta rasa me za ta ce "Kawai dai ko zan iya taimakawa" Murmushi ya yi ya ce "Ba fa kotu ba ce madam" "Zaki sake shi ya tafi ko kuwa? Wane irin iskanci ne haka, Meye haka ne Nasir?" Nabila ta saki rigarsa ta ɗan ɗaga murya ta ce "Take care, ka tsaya daga nesa nesa dan Allah, kar wani abu ya same ka, kar mu yi asarar ɗan ƙasa na gari" Dariya ya yi, ya fita da sauri. Mama ta hayyayaƙo mata "Wallahi ki kiyayeni da rashin tarbiyyar ki a kan ɗa na, na gaya miki" mama ta yi maganar tana nuna Nabila da yatsa. Nabila a ranta ta ce 'Ni yanzu ba ke ce a gabana ba, akwai abubuwan da suka fiki muhimmanci a wurina" Tayi gaba tana kiran lambar sumayya, ta sanar mata da halin da ake ciki, na rikicin faɗan daba. Sai dai kamar kullum, faɗa suka yi, sumayya ta gargaɗeta a kan ta fita sabgar harkar faɗan daban nan. Nabila tayi zuciya ta kashe wayarta, tare da jin da ita ƴar jarida ce, sai ta shiga unguwar nan, ta samo rahoto, tana matuƙar jin haushin yadda sumayya take ɗari-ɗari da gudanar da aikinta, sai dai ko ba dan sumayya ba,  ya zama dole ta taimakawa Nasir, kuma ta taimaki tata career, dan idan ba ta rama abun da Najar bunkure tayi mata ba, ba zata huce ba dan haka za ta cigaba da bibiya. Ayshercool 08081012143 [7/23, 1:37 PM] null:                                     *ƘARFE A WUTA* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) Follow this link, to join autar manya channel, domin samun litattafanta na baya da na yanzu. https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h Masu neman book ɗin ƘARFE A WUTA daga farko, su bi wannan link ɗin, su yi following channel ɗin, za su samu previous pages👇👇👇. https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 9 Har ƙarfe goma na dare, Nabila tana kiran wayar Nasir, domin jin ko yana lafiya, amma shiru wayarsa ba ta shiga, abu kamar wasa hankalinta ya fara tashi, zuciyarta ta din ga raya mata wani abun ya same shi. Da sauri ta tashi ta fita farfajiyar gidan, tana cigaba da kiran wayarsa. "Ke Arfa, me ki ke yi a wurin nan da daddare haka?" Ta ji muryar Abba babu tsammani. Cikin damuwa ta ce "Abba Yaya bai dawo ba, kiransa aka yi kwantar da tarzomar faɗan daba, kuma haryanzu bai dawo ba". Abba ya ce "Yana nan lafiya in sha Allah, da ki ka dawo nan kina sintiri,ai ba bin sa zaki yi ki nemo shi ba, harkar aiki ne yana nan lafiya in sha Allah" Abba yana rufe bakinsa, sai ga ƙarar motar Nasir, yana ta horn ba ƙaƙƙaitawa, gaba ɗaya suka nufi gate a tare. Suka tsaye har ya shigo yayi parking ɗin motar. Ya fito yana kallon su da mamaki ya ce "Abba lafiya na ganku a nan tsaye?" Major ya ce "Arfa ce ta fito tana jiran dawowarka, ya ya aka yi wayarka ba ta shiga gaba ɗaya?" "Tana cikin mota ne abba, ina ga network ne amma a kunne take" Cikin zaƙuwa ta ce "Yaya, komai lafiya dai ko?" Ya ce "Alhamdilillah, an sha artabu dai, yaran sun ninka yawan da muke tunani, mun kama wasu, wasu sun gudu, amma mun kama su da yawa". Mama ce ta fito ita ma, tare da su sauda, suna yi masa sannu da zuwa yana amsawa. Arfa ta ce "Amma dai ba su yi maka rauni ba ko?" Yayi murmushi ya ce "Da sun yi mini rauni, ai da baki ganni a haka ba" Nabila ta ce "To Alhamdilillah, bari na je na kwanta na yi bacci a nutse, tun da kana lafiya" Ya ce "Ki bar wayarki a kunne, za mu yi magana" Ta jinjina masa kai ta bar su a wurin ta tafi, mama kuwa kamar ta bi Nabila ta naɗa mata duka, ta kalli yadda Nasir yake wani sassanyan murmushi kamar shashasha, shi ma ji ta yi kamar ta kwaɗe shi da mari, duk ƙoƙarin da take yi a kansa na nesanta shi da Nabila, abu ya ci tura. Ta daure ta ce "Shiga ciki ka ci abinci, ka je ka nemi wuri ka kwanta". "No na tsaya na ci abinci a hanya ma, sai da safe, gajiye nake kwanciya zan yi" Major ya ce "To Allah ya tashemu lafiya" suka watse. A galabaice suka koma mafakarsu, domin kuwa sun sha artabu da jami'an tsaro, duk da an kama wasu, wasu kuma sun tsira da ƙyar. Sai dai sun yi wa su madaki mummunar ɓarna, dan ma Aminu ya yi musu kashedin babu ruwansu da cewa za su kashe madaki, saboda ya san hatsabibancinsa. Yana zaune suka faɗo ɗakin, suna ta mayar da numfashi, jikin rigar ɗan mama face-face da jini. Walid ya ce "Boss, an yi aika-aika amma kwaɓarmu ta so yin ruwa, dan an kama da yawa daga cikin yaran nan da muka gayyato, amma fa yaran madaki sun yi ɓarna, dan sun taɓa wanda ba su ji ba, ba su gani ba, duk da mun yi yinƙurin daƙile hakan". Maimakon Al'amin ya yi magana, kawai ya tashi tsaye ya shaƙo wuyan walid, ya haɗa shi da bango, ya ware masa idanunsa ya ce "Ina ƙwayoyin da ka kwashe a nan wurin?" Cikin takaici walid ya ce "In fita yi maka aiki, in dawo da ƙyar amma ka shaƙe ni?" Yayi maganar muryarsa na fita da ƙyar saboda shaƙar da ya yi masa. "Suna ina na ce?" "Na kwashe su na fita da su, dan ba zan bari ka kashe kanka ba, allurar da ka ke yi wa kanka ma, ba abun da take yi maka sai ƙara maka zafin zuciya" Fusata yayi da maganar Walid, ya ƙara shaƙe shi, Ɗan mama ya tashi da sauri yana yi wa Al'amin magiyar ya rabu da Walid. Walid ya ce "Idan ka kashe ni ma, ba zaka huce ba, ai na yi maka alƙawarin kawo maka sabuwar ƙwaya, amma wannan kashe kanka zaka yi, idan ka cigaba da sha, dan ba ta karɓe ka ba." A fusace ya hankaɗe Walid ƙasa, ya koma ya zauna ya dafe goshinsa. Wayarsa ce ta yi haske, ya ja wayar yana dubawa. "Aminu ka daina wannan gangancin da ka ke yi, idan ka sake shiga hannun mutanen nan, kar ka yi zaton za su hukuntaka da adalci, dai-dai da abun da doka ta tanada, ka nutsu ka daina wannan mugun wasan, ka mayar da hankalinka a kan burinka" iya ƙarfin sa ya saka wurin yin jifa da wayar, ta dagargaje a tsakiyar ɗakin, ya tashi zai fita. Duk da mugun ciwon da jikin walid yake yi masa, saboda artabun da suka yi, amma haka ya tashi ya sha gaban Al'amin ya ce "Ina zaka je ne?" Hankaɗe Walid yake ƙoƙarin yi, amma walid ya sanya ƙarfin sa, ya tura shi baya. "Ka rabu da ni walid, ya zan yi ne? So suke sai na haukace, waye wannan? Me yake nema da rayuwata? Wace manufarsa ce da su a kaina? Me kuma suke buƙata yanzu?" "Easy master" Cikin ƙaraji ya ce "Na ce kar ka sake kirana da wannan sunan" "Sorry boss, na san komai ai, ka kwantar da hankalinka" "How? Duk abun da suka yi mini bai ishe su ba, wai yaya zan yi ne? Kalli idona walid, ba na bacci fa, zuciyata kullum zafi take yi, ba na iya saka komai a bakina na ji ɗanɗanonsa,  ya zan yi ne?" Walid ya ce na sani, ya amsa yana yi wa ɗan mama inkiya da idonsa. Viper ya a sake cewa "Ka san kwana nawa na shafe ba na bacci? Ba kwanaki ban ba fa kawai, shekaru ne, ba na baccin da ya kai awanni biyar, ka san me nake ji kuwa?" Walid ya ce "Ban sani ba, amma na san da yawa daga abubuwan da ka lissafa" Jikinsa na tsuma ya ce "Wallahi zuciyata ci take yi da wuta, ka sani, wallahi idan na riƙe makami sai na yi kisan kai" yayi maganar yana rintse idanunsa, a lokacin da ruwan allurar da walid yake yi masa, ya fara ratsa jijiyoyin jikinsa. A nan take jikinsa ya saki, ya zubawa walid ido. Walid ya ce "Ko ba zaka yi baccin ba, ka rufe idanunka master, za ka samu releif" shiru yayi, domin ba zai iya motsa kowacce gaɓa daga jikinsa ba. Ɗan mama ya ce "Walid, anya ba zamu yi wani abu a kan lamarin nan ba kuwa? Ba za a kai shi ya ga likita ba? Kar ya haukace tuburan fa" Walid ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa alamar ɗan mama ya yi shiru. A hankali al'amin yake buɗe idonsa yana lumshewa, sai dai ya kasa ƙwaƙwƙwaran motsi. *** YALOKO ƘARAMAR HUKUMAR TOFA. Cikin tsananin ƙyanƙyami take ƙarewa ɗan ƙaramin ginin ƙasar kallo, rabin katangar gidan  ta zube, sai ciko aka yi da kara da buhu, aka rurrufeta. Abunka da mutumin ƙauye, cikin mutunci da girmamawa, matar gidan ta karɓeta, tana yi mata sannu da zuwa. Ta yi mata iso, har cikin ɗakinta, ta ba ta abun zama. Kamar ta zauna a kan kashi, haka ta ɗan ɗosana ta zauna, tana kame jikinta ta kalli matar ta ce "Baki gane ni ba ko?" Matar ta ce "Eh ban waye ki ba" "Ni ce barrister da na karɓi case ɗin ƴar ki, na zo mu tattauna ne, in yi magana da ita" Nan da nan hawaye ya cika idon matar ta ce "Tana banɗaki, bari ta fito" rufe bakinta ke da wuya, yarinyar tayi sallama a ɗakinta, muryarta ƙasa-ƙasa. Mahaifiyarta ta amsa, barrister kuwa zuba mata ido ta yi, yadda yarinyar take ɗingishi, take tafiya da ƙyar, har ta zo ta zauna. Ta kalli uwar ta ce "Kun kaita Asibiti ne?" Ta ce "A'a, tun dai a  can an kaita, maigadin gidan ne ya kaita, har aka yi mata ɗinki a goshinta, gashi nan in da aka ya ji mata rauni. Dan Allah baiwar Allah ki taimake mu, kamar yadda Allah ya taimake ki, a karɓar wa yarinyar nan hakkinta. Saura ƴan kwanaki aurenta, ya lalata mata rayuwa, idan zancen nan ya fasu a garin nan yaya zan yi?" Ta kalli yarinyar sannan ta kalli uwar ta ce "Baiwar Allah kuma hadda halinku, na son abun duniya duk yadda hukumomi ke jan kunne a kan kai yara aikatau meyasa ba kwa ji? Meyasa zaki kaita aikatau, maimakon makaranta?, a ƙa'ida fa kema sai an hukunta ki" Cikin rauni da damuwa ta ce "Baiwar Allah da ina da yadda zan yi yaushe zan kaita aikatau? An yi garkuwa da mahaifinta an ce mu kai kuɗin fansa, mun tattara dabbobi da gonaki mun sayar, mun bayar a kai a sako shi, sun rike ƙanin mahaifinta da ya kai kuɗin, sun haɗa su su duka sun kashe, gona ɗaya ta rage mana, ita ma wani mutum duk ya tarkata ya ƙwace, wai zai gina kamfani, an ce za a bamu diyya, gonar miliyan uku an bani dubu bakwai, abun da zan girka na basu su ci, ita da ƴan uwanta, bani da shi, nima ba cikakkiyar lafiya ce da ni ba, kuma ita ce babba, makaranta tana zuwa ajinta uku a sakandare, kuɗin da ake biya na makarantar ba ni da su, ya zan yi?" Tayi maganar kuka yana ƙwace mata. "Shikenan ya isa haka?, Amma kuma irin haka kin yi gaggawa zuwa gidan radiyo ki faɗa, ai wurin jami'an tsaro yakamata ki je". Maman ramma ta ce "Na je, dan da aka kira ni na je can birnin asibiti, da ƙyar aka karɓe ta wai ba ɗan sanda, daga can na je wurin ƴan sanda naga suna nema su cuce ni, wai ƙarya muke yi, babu yadda za ayi a ɗauki ƴa ta aiki a wannan gidan har ayi mata fyaɗe. Ba ki ga sintirin da na yi ba, na rasa abun yi shiyasa na kai wurin masu radiyo ko Allah zai saka a taimake mu" Ta jinjina kai ta kalli yarinyar ta ce "Ramma  ko?" Ta jinjina kai alamar eh. "Gaya mini yaya aka yi abun ya faru?" Ta ɗaga kai ta kalli mahaifiyarta, sai ta fashe da kuka ta kasa magana. "Hajiya ɗan bamu wuri mu yi magana" babu musu, ta tashi ta fita ta bar ɗakin. "Kin ga ki yi shiru ki kwantar da hankalinki, ki yi mini bayanin yadda abun ya faru, in ga ta ina zamu ɓullowa lamarin" Shiru ta yi tana tuna yadda lamarin ya kasance. "Ke!" Ya kirata cikin tsawa, bayan sun haɗa ido da ya shigo, ƙara razana ta yi, dan ba ta yi zaton wani zai shigo yanzu ba, a dai-dai wannan lokacin, da ta duƙufa tana ta aiki a falon gidan. cikin tsuma ta kalleshi ta ce "Na'am". "Ina masu gidan?" Yayi maganar yana ƙare mata kallo, matashiyar yarinya ce, da ba ta wuce shekara goma sha huɗu ba, irin farkon tashen balagar nan, ƙirjinta ya fara tasawa, wannan ne karo na biyu da yake ganinta a gidan. Tun a ranar farko yake jin wani abu na fuzgar shi a kanta. Cikin rawar murya  ta ce "Ai ba su dawo ba tukuna, gyaran gidan dai muke yi". "Ke kaɗaice a gidan kenan?" Cikin rashin wayo ta ce "Eh, amma zulai ta je sayo katin waya, zata dawo, tare muke aiki da ita, wai a satin nan za su dawo". Yayi wata irin ajiyar zuciya ya ce "Ɗaukko mini ruwa a kitchen zan sha" ta jinjina kai, ta ajiye duster hannunta, ta tafi da sauri har da gudu. Sai dai tana shiga kitchen ɗin, ya bi bayanta, ya mayar da ƙofa ya rufe. Turus ta tsaya tana kallonsa, jikinta yana rawa, taga ya fara tunkaro ta. Ta ja da baya ta miƙa masa ruwan, amma ya haɗa da hannunta ya riƙe. "Dan Allah ka sakeni, in ƙarasa aikina" Babu tausayi ko imani, ya ce "Nawa aikin zaki fara yi tukuna, kafin nata" Ganin akwai alamun ƙarfi a tare da ita, ba zata tsaya ba, ya sanya ya gaura mata wani lafiyayyen mari. A take hancinta ya fara zubar da jini. Ta ƙwala ihu, ya sake buga kanta da cabinet na kitchen, goshinta ya fashe, nan ma jini ya hau zuba, ga goshi ga hanci, dan haka ta kasa magana, jikinta ya saki. Haka ya keta mata haddi, ta hanya mai muni da rashin tausayi ya tashi ya fice ya barta. Idonta biyu, amma ta kasa taɓuka komai, ko ɗaga hannunta ta kasa yi. Zulai ce ta dawo ta tarar da ita cikin mummunan yanayi, a rikice ta fita ta kira ɗaya daga cikin masu gadin gidan, suka ɗauke ta suka kaita Asibiti. Aka ƙi karɓar su, sai da aka kira matar gidan aka sanar mata, suka yi magana da likitoci ta waya. Sai dai duk abun nan, ramma ba ta san ko sunansa ba, balle ta san ɗan waye shi. Kafin matar gidan ta dawo, ta aiko a bawa ramma kuɗi, a bata haƙuri su koma ƙauye, ko warkewa ba ta yi ba aka sallame su, shi ne mamanta ta ɗauke ta suka tafi gidan radiyo. Ramma ta bawa barrister labarin komai, tana kuka mai taɓa zuciya, goshinta ga ɗinkin da aka yi mata a asibiti, ga na ƙasanta da yake addabarta da raɗaɗi. Tayi ajiyar zuciya ta ce wa mahaifiyar ramma ta shigo. Bayan ta shigo ta zauna, ta kalle su ta ce "Baiwar Allah, dan cuta na san an cutar da ku, amma za ki sake jefa kanki a halaka, gara ku yarda ayi masalaha. Babu wata kotu, ko wani alƙali, da zai tsaya miki ya ƙwato muku hakkinku, saboda yaron nan ɗan gata ne gaba da baya, ubansa suke da ƙasar. Dan haka ki yi haƙuri, a baku wani abun, ki samu ku sai abinci, a kuma kaita asibiti, idan ta warware ta koma makaranta. A take ramma ta fashe da kuka, mahaifiyarta ta ce "Haba baiwar Allah, shikenan bawa dan talaka ne, ba zai samu adalci ba, kuɗi zasu ƙare, mutuncin ƴa ta fa? ni gaskiya so nake a karɓa mata hakkinta". Barrister tayi shiru tana zancen zuci "Ko yaushe mutumin ƙauye ya wani san ƴancinsa? Da matar nan take zaƙewa?' "Naira miliyan uku za a baku, kuɗi hannu, ki yi tunani zan sake dawowa. Idan kuma kun ƙi, zan cire hannuna, duk matakin da uban yaron ya ɗauka a kanku babu ruwana, ina sake gargaɗinki, babu ke babu magana da wani ɗan jarida ko makamancin haka, idan kunne ya ji jiki ya tsira" ta ciro kuɗi a jakarta, ta ajiye musu, ta tashi ta fice. *** Kamar zai tashi sama, saboda tsananin tashin takaici da haushi, ya ce "Madaki, wace irin shiririta ce wannan ku ka yi, ta yaya zaku bari, jami'an tsaro su sake kamaku?" Cikin muryarsa da ta riga ta fashe irin ta mashaya ya ce "Kai ka san ba laifinmu ba ne ba, wani banzan bakware aka kawo mana, kai zaka tsawatar, ka saka a sake su, dan idan babu su babu aikin nan" "Shikenan, na ji, ka saurare ni da kyau, zuwa hankali ya riga ya kwanta, mutane sun manta da abun da ya faru watan baya, ina son a cigaba da yi mini aikina, amma a wannan karon yankin yamma da gari zaku je, yaron kar ya wuce ɗan shekaru goma zuwa sha biyar, jininsa nake buƙata, a zuba a babban dam ɗin da yake rarraba ruwa a yankina, tun daga mazaɓata, sai ku kawo mini ƴan marainan yaron, da hanjinsa. Sa'ar aikin ranar laraba ce bayan al'muru. Idan kujerata ta cigaba da tabattuwa kuma zaku mora" Madaki ya ce "Wannan ba zai yi wahala ba, ka huta kawai, kujerar nan ko an so ko an ƙi, mai hawanta sai bayan ka mutu honorable" "Eh, amma ba yanzu zan mutun ba ai, sai an kwana biyu tukuna, zan aiko maka kuɗi, ayi abun da yakamata larabar tsakiyar wata za ayi, yaranka kuma za a sake su" "Sai da kai honorable, ka ci dubu sai ceto" "Yauwa yayi". Nabila kuwa sannu aka din ga yi mata a wurin aiki, ana tambayarta yaya jiki, ta din ga amsa musu da yauwwa. Ofishin barrister Habib ta je, ta gaya masa yadda suka yi da matar, da duk abun da ta yi documenting. Ya karɓa ya duba sannan ya kalleta ya ce "Yayi, amma me ki ke gani a kan case ɗin? Do you have interest on it?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Wani case na jiyo, na wata yarinya da aka yi wa fyaɗe,amma ana ta ɓoye abun, amma na ji an ce su barrister Naja'atu sun shiga case ɗin, hankalina ya fi karkata a can". "Wai ke menene haɗinki da wannan naja'atun ne? Ki kiyayi kanki da lamarin matar nan,tun da sun shiga case ɗin, ki ƙyale su, case ɗin wannan hajiyar ki tsaya ki mayar da hankali a kai ki yi" Ta marairaice ta ce "Amma barrister menene aibun hakan, tun da class mate ɗin ka ce, ka haɗa ni da ita dan Allah, ina son irin aikace-aikacenta na jin ƙai" Ya cire medical glass ɗin sa ya kalleta ya ce "Wai ke meyasa ki ke da taurin kai ne? Ke ma ki kafa naki harkar jin ƙan marasa gatan mana, dole sai kin zama ita, ke kin san wacece Naja'atu kuwa? Zahirinta ki ka sani, baki san baɗininta ba, go and work on this case now". Tsatstsare fuskar Barrister ta yi da kallo, a ranta ta ce "An zo gaɓar da nake so, hasashena ya tabbata, zan cigaba da matsa ka, har sai ka amayar da abun da ka ke ɓoye mini" A fusace ya ce "Ba zaki tashi ba, ki ka tsare ni da ido?" Miƙewa tayi tana zumɓura baki, ta ɗauki file ɗin ta fice. *** Kaiwa yake ta yi yana komowa, a katafaren office ɗin sa, hannunsa riƙe da waya a kunnesa, yana jiran a ɗauka. Har fitar da ran za a ɗauka, aka ɗaga. Cikin harshen turanci ya ce "Haba sir, kai fa nake jira kayan nan su iso, almost 2weeks, ayi ta ga kaya nan amma shiru, ni na riga na gama clearing road, a yankinmu na arewa, ka hanzarta na fara jin ƙishin-ƙishin canjin controllers na coustom, bana son a kawo waɗanda za mu yi ta fama" Daga cikin wayar mutumin ya ce"Sai fa ka yi haƙuri, kayan ne ba a gama loda su ba, kuma nima dole sai na gama da controllers ɗinmu na nan, kuma ka daina ɗaga hankalinka, babu wani wanda ya isa a ƙasar nan, ya sha abun da ba mu muka dama ba, ranar laraba kaya za su shigo, amma sample ce allurar, ba a shigo da ita da yawa ba, sai an ga yanayin aikinta tukuna, har da tablet ma" "To na ji, amma ka tabattar ranar larabar za su iso?" "Ko tantama babu" "To shikenan, godiya nake"ya katse wayar, cikin shauƙin irin ribar da zai mayar idan kayan suka tsira. Zaune take a ƙasaitaccen ɗakin baccinta, jikinta sanye da riga da wando na nylon, masu sauƙin zafi. Ta zauna ta nutsu, ta zubawa kayan kan table ɗin gabanta ido, tana ta saƙe-saƙe a kan ta sha ko kuma kar ta sha. Kwalabe ne na magunguna, da ƙwayoyi haɗi da allurai. Wata matashiyar mace ce tayi sallama, ta amsa mata, ta ƙaraso hannunta riƙe da cup ta na shan wani abu. "Sweetheart, ya dai na ga kin saka kayan nan a gaba kina kallo?" Tayi ajiyar zuciya ta ce "Tunani nake yi da zuciyata, in sha ko kar in sha" "So you are going to quit abusing drugs?" Ta girgiza kai ta ce "Is not that easy dear, jikina is resisting it, ba sa ɗauka ta sai na sha su in a very high doses, ba na son su huda ni, a fara ganewa. Mun yi magana da honorable a kan sabuwar allurar da suka yi order daga Mexico yana ta yi mini yawo da hankali" "Haba barrister, ke fa ta hannun daman honorable ce, ba zai yi miki yawo da hankali ba. An samu wani zazzafan malami fa" Ta ɗago idanunta ta kalleta ta ce "Wow, are you serious?" "Yes of course, aikinsa tested and trusted ne, amma kafin muje a kan buƙatarki, anya ba zaki duba a manyan mutanen nan, mu kai wani ba, ki yi aure yadda zai zama backup kar abubuwa su zo su taɓarɓare fa, ko ki samu wani kamar tsohon mijinki, ki aura" Ta taɓe baki ta ce "Ba zan iya aure ba, na riga na saba da rayuwar ƴanci, ba zan yi aure in zauna ƙarƙashin wani yana juya ni yadda yake so ba. Ai tun da na yi joining organization ɗin nan kin san in da na dosa". Ta ce "Na sani dear, amma duk da haka, religion da tradition yana da tasiri sosai da sosai a arewacin najeriya, ba na son wani ya gano wani lagonki, ayi amfani da shi wurin yaƙarki" Ta girgiza kai ta ce "Muddin ba zan samu wanda zan gindayawa sharuɗa ya bi ba, zan iya zamana a haka, i have so many ways to satisfy my feelings, when i need it, ba dai duk su ake yi wa a auren ba? Kin san komai ai ke. Ki saka mana time, mu je wurin mutumin, ba na son sunana ya ɓace, har sai na cika burina, na kammala aikin da na karɓo a wurin shugabannina, sai na tabattar da samun daidaituwar jinsi a tsakanin mutanenmu na arewa" Badi'a ta yi dariya ta ce "Ki huta baby, ki ɗan yi caji, sai ki kwanta, ko in fita da ke ne?" "No, ba na son na yi bacci da yawa, zan sake komawa wurin matar nan, a kan case ɗin ɗan gidan honorable, naga alamar za ta yi taurin kai, idan taƙi yadda kawai mu bi hanyar da muka saba bi" "Hmm, talaka akwai ƙi faɗi, kuɗin ne ba zata karɓa ba kenan? Sa yi biyu babu kuwa" "Manta da su, idan ki yi waya da journalist ɗin nan, manta sunasa nake yi, ki tura masa kuɗi, a cigaba da ɓoye wanda ya yi laifin, a sanarwa da duniya na shiga case ɗin, a sassaka a social media ma, a dai yi ƙoƙarin ɗauke hankalin mutane daga kai" ta ƙarasa maganar tana tuttula ruwan maganin da ke cikin wata ƙatuwar kwalba tana lumshe ido. Yau Abba kamar ya san Nabila so take ta lallaɓa ta fita, ya zauna a gida bai fita ko ina ba. Tayi iya tunanin ƙaryar da zata sharara masa, ta fita amma ta kasa tunawa, dan idan ya tsitiyeta zai gane ƙarya take yi, gashi weekends ne babu aiki. Cikin ikon Allah, aka samu tarzomar su madaki da Viper ta ɗan lafa, saboda an jibge jami'an tsaro a unguwannin. Nabila har alla-alla take yi, ranar Monday tayi ta fita aiki, daga nan ta tafi nata wuri. Ranar Litinin tun sassafe wasu daga cikin iyaye mata, suka fara sintirin karɓar belin ƴaƴan su da aka kama, a ofishin su DSP Nasir. Nasir yana zuwa ya tarar da su, an ce musu su jira sai ya zo. Tsakanin iyaye da ƴaƴa sai Allah, amma wannan rashin juriyar yana ɗaya daga abun da yake taka rawa, wurin sake sangarta yaran. Bayan sun gaisa da su, ya ce "Da farko ina mai baku haƙuri, domin kuwa ba za mu bayar da belin yaran nan ba, sai mun kai su gaban alƙali tukuna. Yaran nan ku kanku sun fi ƙarfin ku, ba kwa iya tsawatar musu, suna barazana ga zaman lafiyar al'umma, dan haka ku yi haƙuri a wannan karon babu sabo babu ɗaga ƙafa, sai dai na yi muku alƙawarin duk wanda muka kama ba shi da laifi, zamu sake shi, masu laifi kwai zamu kai gaban hukuma". Bai tsaya jin mai zasu ce ba, ya wuce office ɗin sa. Koke-koke wasu daga cikinsu suka fara, yayin da wasu suka din ga janyo masa jafa'i kala-kala, wai an zalunce su, an rufe musu ƴaƴa. A cikin office ɗin sa ya karya, kasancewar ya makara, bayan ya kammala, ya je in da ake tsare da yaran, tare da taimakon wasu daga cikin jami'an tsaro, ya fara tuhumar su, da ƙoƙarin zurfafa bincike akan su gaya masa in da viper yake. Wanda aka ritsa ɗin ana tuhuma ya ce "Wallahi Yallaɓai, da ne dai kafin ya je prison, na san in da yake, har gidansu na sani, muna yi masa aiki sosai da sosai, amma tun da ya fito bamu sake ganinsa ba, su Walid da tarago ne suka san in da yake, tarago kuma madaki ya kashe shi, walid kuma wallahi shima ba a ganinsa, muna yi masa aiki amma bamu san in da yake ba". Nasir ya ce "Ta yaya ku ke karɓar order daga wurinsa?" "Randomly, suke zaɓar mutum ɗaya su kai masa takarda, ko aje a ajiye takardar a in da muke taruwa shikenan" Nasir zai sake magana, wayarsa ta fara ruri, ya zura hannu a aljihunsa ya ɗaukkota, ya ɗaga ya saka a kunne, tare da yin sallama. "Kana ina ne?" "Na shiga wurin aiki sir" "Yaran nan da ka kama, ka sake su, kowa ya tafi, kuma ka janye jami'an tsaron da ka jibge a unguwar" cikin tsananin mamaki ya tashi tsaye ya ce "Sir, yarane da suke ɓarna fa, har kisan kai aka yi a ranar, yaya zamu.... "This is an order from higher up Nasir, ka saki yaran nan, nima umarni aka bani daga sama, Aminu Viper muka ce ka kamo mana, ba yaran unguwa ba" Ya taune lips ɗin sa na ƙasa cikin ɗacin rai ya ce "Amma sir, muna kan binciken wanda suka yi kisan kan ne". "Ka sake su nace, is an order" Nasir ya ce "Ok sir, as you wish"ya kashe wayarsa, jikinsa yana wata irin tsuma, ya tuna yadda a garin kamo yaran, sai da suka kusa kashe shi, a artabun da suka yi, ga kisan kai, ga miyagun makamai da suka kama yaran da su, amma an bashi order ya sake su, anya kuwa ana son kawo gyara da matsalar tsaro a ƙasar nan!? Ƙarfe a wuta paid book ne, few pages zan bayar free, masu buƙata za su iya contacting ɗi na, su fara subscribing, miƙaƙƙiyar tafiya ce, mai cike da sarƙaƙiya da ban al'ajabi. Ayshercool 08081012143 [7/24, 1:44 PM] null: *ƘARFE A WUTA* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) Ku yi following channel ɗin nan, domin samun littatafan autar manya. https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h Masu son ƙarfe a wuta daga farko, ku bi link ɗin nan ku yi joining channel ɗin https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 10 Gaba ɗaya zuciyarsa ta cunkushe, ya rasa me ma Yakamata yayi. Ya daɗe a zaune kafin ya tashi ya fita reception ɗin. Sai dai yana zuwa ya tarar da wani mutum a tsaye, baƙi ƙirin da shi, ya ɗaura ɗan kwali a kansa, ga wasu wulaƙantattun kaya a jikinsa kamar mahaukaci, idanuwansa jawur kamar an rina masa. Nasir ya ce "Lafiya kuwa? Wannan fa?" Ya dube shi ya ce "Kai ne Nasir ko?" Yayi maganar yana shagiɗe kafaɗa irin na cikakkun mashaya. Nasir ya ce "Ya aka yi?". "Na san ka samu saƙon ka sakar mini yarana, na zo na tafi da su ne" Wani irin ƙululun takaici ya tokare zuciyar Nasir, yayi ajiyar zuciya ya ce "Kai ne wa?". Yayi wani irin ihu, ya jinjina kai ya ce "Madaki nake, gumbar dutse, na san ko bamu yi gaba da gaba da kai ba, ka san labarina, ina son wannan ya zama gargaɗina da kai na farko na ƙarshe, babu kai babu shiga harkata da yarana, idan ba haka ba" Nasir ya tsare shi da ido, ban da lalacewa ace ɗan ta'adda ne zai shigo har office yana yi wa jami'in tsaro kashedi, saboda wasu masu faɗa a ji sun tsaya masa. Yayi murmushi mai ciwo ya ce sergent Iliya, ka fito da yaran nan gaba ɗayansu" Ya amsa masa da "Ok sir" Nasir ya zagaya, ya kama gefen rigar madaki, suka fita waje, ya kalle shi ya ce "Wanene Aminu? Ina zan same shi?" Madaki ya ce "Wane Aminun?" "Viper, na san ka san shi, tun da an ce abokin rigimarka ne" Madaki ya buɗe wawaken bakinsa, da wiwi duk ta dafar da haƙoran, laɓaɓansa sun zama manya, sun yi baƙi saboda taba, ya kwashe da dariya ya ce "Tabbas! Na san shi, ɗan zaki ne, da na yi sake ya girma yake neman gagarar kundila, dan da na kashe shi tun a wancan shekarun da haka ba ta faru ba. Nima neman sa nake yi ruwa a jallo, ko a raye ko a mace, dan haka idan ka same shi, ka sadani da shi. Sai dai ka bi a hankali wurin neman sa, jami'anku su suka masa sunan Viper, kumurci ne mai hatsari da idan ya sareka zai kashe ka" A dai-dai lokacin matasan suka fito harabar station ɗin suna ihu, suna sarawa madaki, wasu daga cikinsu kuma da ba yaran madaki bane ba suka fice. Nasir ba ya tunanin tun da ya fara aiki, ya taɓa cin karo da abun da ya ɓata masa rai kamar wannan, sai ya ji gaba ɗaya aikin ya fita daga kansa. Haka ya ja tawagar matasan suka bar harabar station ɗin suna iface-iface. Duk yadda Nabila ta so ta samu damar guduwa, daga wurin aiki yau, ta kasa samun dama, dan haka ba ta tashi ba sai ƙarfe uku, a lokacin ba ta da wani kuzarin kirki, babu abun da take buƙata wanda ya wuce ta tafi gida. Ba ta fi mintuna ashirin da shiga gida ba, Nasir ya dawo. Bayan sallar la'asar ya kirata a waya, ya ce ta fito yana son ganinta. Ba ta ɗauki lokaci ba, ta fita harabar gidan, wajen parking space akwai fararen kujeru. A can ta tarar da shi, sai dai yanayinsa ya tabbatar mata akwai damuwa "DSP, yana ga kamar ranka a ɓace ne?" Tayi maganar tana zama. "Damuwa kam akwaita, gagaruma kuwa arfa" Ta girgiza kai ta ce "Subhanallah, meyafaru yayana?" Nasir ya ce "An saki yaran nan fa, da muka kama shekaranjiya" Ta waro ido ta ce "Saboda me?" Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce "Saboda yaran ƴan siyasa ne, ina zuwa office aka kira ni daga sama, wai suma umarni aka yi musu, kar in sake kama yaran, aikin neman Aminu aka saka ni ba wannan ba, na daɗe ba ayi mini abun da ya ɓata mini rai irin wannan ba, kamar ni wai ni ɗan daba ya kalleni a cikin kakina, yake yi mini kashedi a office could you imagine. Sai an yi magana ace ba ma taɓuka komai, an janye jami'an tsaron da aka ajiye a unguwar ma" Nabila ta daki tebur tana huci, zuciyarta har wani tafasa take yi ta ce. "Shikenan, da wanda suka kashe, da kwanciyar hankalin mutanen unguwar, duk ba matsalar su ba ce ba? Personal interest ɗin su ne kawai a gabansu?" "Gashi kuwa kina gani, yanzu idan na matsa zasu iya raba ni da state ɗin nan ma gaba ɗaya, ni kuma bana son barin garin nan saboda, i don't want to miss you dear" Kamar za ta yi kuka ta ce "Wallahi Yaya gaba ɗaya aiki ya fita daga kaina, anya ba haƙura zan yi na kama kasuwanci ba, kai babu daɗi, sumayya ma haka, nima dan jan wuya ce, idan aka addaba mini ajiye aikin zan yi, gaba ɗaya ayyukanmu na taimako ne, amma ɓata gari sun yi kane-kane a ciki. Yanzu menene abun yi?" Nasir ya ce "Abun yi kawai na mayar da hankali, na yi musu abun da suka ce, shi kansa wanda suke son a kama ɗin, ina zargin wani abu ne akansa, ko tsakaninsa da wani ya sanya suke son in kama shi, ban da baka ya za ayi ace ɗan daba ya gagara kamuwa, alhalin yana cikin garin nan" Ta ce "To ka ce ba zaka yi ba mana, idan sun matsu su manyan su kama shi mana" Yayi dariya cikin takaici ya ce "Ba zai yiwu ba arfa" Ta kwantar da murya ta ce "Ka kwantar da hankalinka yaya, komai lokaci ne, sai dai duk ranar da Allah ya sa muka kai wani matsayi, mu yi iya yinmu, wurin ganin ana tsage gaskiya duk ɗacinta, lokaci ne ka yi haƙuri" Yayi murmushi ya ce "Idan ban yi haƙuri ba, ya zan yi, dolena ai, na san lokaci ne Ta ce "Yauwwa, in sha Allah, da ni da kai da sumy, zamu yi nasara a rayuwar aiki, and zan yi duk iya yi na, na ga ka kama aminu" Nasir yayi murmushi ya ce "How? Na yi amfani da techniques ɗina, na kama masu laifi, amma na kasa samunsa, akwai alamun shi ma yana da masu tsaya masa" "Mu ma Allah ya tsaya mana, zamu yi yaƙi da duk wani mai kawo cikas ga aiki da adalci" Dariya ta bawa Nasir ya ce "Ka ga ƴan ƙasa nagari" suka yi dariya gaba ɗaya. *** Sanye yake da gajeren wando, da riga armless baƙa, joint ne mai kyau sosai da sosai, yanayin matasan da suke shiga suna fita, zai tabattar da na masu hannu da shuni ne. Ya ɗora ƙafarsa a kan kujera, yana ta shan shisha, kusa da shi wasu matasan ne, suma suna ta nasu shaye-shayen. Sai matashi ɗaya da yake kujerar da take facing ɗin sa, yana shan sigari, ya kalli Abdul ya ce "Kai Abdul, wai wannan lumshe idon da ka ke yi, lafiya kuwa?" Ya sauke ƙafafuwan sa, ya tashi ya gyara zamansa ya yi wani murmushi ya ce "Ba lafiya ba" yayi maganar yana murmushi. "Ba lafiya ba kuma ka ke dariya?" Ya girgiza kai cike da shauƙi ya ce "Na rasa ya zan yi ne, tun ranar da na samu wata cika, under 18, na sarara na kasa mantawa da ita, duk matan da nake harkata da su, na kasa samun abun da nake so, kamar yadda na samu a wurinta. Ashe duk wahalar banza nake yi da nake biyewa manyan yaran nan" Saif ya ce "To ka koma mata mana" Abdul ya ce "I rape her" yayi maganar yana sake sakin hayaƙi a iska. "Rape kuma? How?" Abdul ya ce "I don't know, i was drunk, bai gama sakina ba kuma, na je gidan aunt maijidda, na tarar da yarinyar ashe ba ta gari ita da mijinta, duk yadda nake da ƙyanƙyami, nake son manyan mata, amma na kwaɗaitu da yarinyar nan, tun a ranar farko da na fara ganinta. I don't know why, but i still need her, na kasa samun yadda nake so, ita ɗin dai nake son sake kasancewa da ita. Warin da jikinta yake yi, make me more crazy on her, she was the first under 18 virgin i mate, i don't think... Saif ya katse shi ta hanyar cewa "Anya kana hayyacinka kuwa? Ko ka sha wani abun ne bai sake ka ba, ka ke yi mana surutun banza, ka yi raping ɗin under 18 old girl, kana vewa warin jikinta make you more crazy are you well?" Abdul ya gyara zamansa ya ce "Saif da gaske nake, i rape her, dad is even working on it, mamanta wai har sun shiga media sun kai ƙara. I don't care what so ever, i still need her, at any cost". "Abdul, ka ce dad ɗinka yana ƙoƙarin a rufe case ɗin, amma kana wannan zancen, ka san idan magana ta shiga media sai a hankali, da kai da dad ɗin abokan hamayya za su saka ku gaba". "Abu nawa na yi babu wanda ya fashe? I don't care, you will help me in nemo yarinyar nan, na ji dad ya ce naja ta shiga case ɗin, kuma ba wata ba ce ba, she's just maid da gani ka san yar talakawa ce" Cikin tsoro, Saif ya waro ido ya ce "Wannan barrister? Aikuwa ka kaɗe Abdul, an ya zaka sha wannan karon?" Abdul ya kwashe da dariya, har sai da ya janyo hankalin wasu kansu ya ce "You don't get sense, malam zaka taimake ni na sake nemo yarinyar nan, itakaɗai ce maganin ƙishirwata" yayi maganar yana cigaba da ƙyaƙyata dariya. *** Abun da Nasir ya gaya wa Nabila, ya ƙara azalzalar ta, akan son samun Viper, ta tabbatar da kama Viper zai iya zama silar cigabansa da ɗaukakar da take nema. Sai dai ta kawar da tunanin daga zuciyarta, a lokacin da ta nutsa, tana kallon hotunan Barrister Naja'atu a social media. Ayyukanta na jin ƙai, da makamantansu. Babu wani information da zai gaya mata haƙiƙanin wacece Naja'atu Bunkure, amma ta barwa zuciyarta lallai akwai wani abu a ƙasa a kan ta, kuma zata tono shi. Ranar talata da safe tana shirin fita aiki, sumayya ta kirata ta ce su haɗu, a in da suke saba haɗuwa, su tafi tare. Tun da Nabila ta ji haka, ta san akwai wani abu a ƙasa, dan haka ta amsa mata da to. *** Walid ne yake ta yi wa Al'amin lissafi, da bayanin ayyukan da ya saka ayi masa, amma sam hankalinsa baya kan abun da walid ɗin yake faɗa. "Viper" walid ya kira shi. Maimakon ya amsa sai ya ce "Haryanzu babu wani labari a kan masu zuwa gidan malam lawan?" Walid ya numfasa ya ce "Babu" Ya ce "Yaran nan gaba ɗaya aka sake su, tare da yaran madaki ko?" "Eh, ɗazu duk suka fita, an sake su duka". Yayi ajiyar zuciya ya ce "Zuciyata tana bani, kamar so ake a ɗauke hankalina daga abun da na ƙuduri aniyar yi, ni kuma wallahi muddin ina numfashi a doron duniya, sai dai ayi mutuwar kasko" "Amma tayaya haka zai yiwu, alhalin ka kasa sakin jikinka ka ɗauki ƙaddara, ba ka cin abinci, baka walwala, daga kwanciya, sai shaye-shaye, sai bayar da umarni, yakamata ka sakawa zuciyarka salama" "Walid!" Ya ambaci sunansa da ƙarfi. Ya amsa masa da "Viper" "Tashi ka fita" Cikin mamaki ya kalli Viper ya ce "In fita kuma? Ni ɗin walid ne fa?" "Eh ka tashi ka fita ka bani wuri" "Saboda ina bibiyarka, ina yi maka biyayya ka ke neman ka wulaƙanta ni? Ban da darajar ni ɗan halak ne da ba na manta alkhairi, kai ka san da tuni na daɗe da barinka" Aminu ya ce "Idan kai ɗan halak ne, a wannan karon ina son ka bar ni" Ya sake kallon viper ya ce "Ni ka ke kora?" "Eh bana buƙatar sake ganinka" Walid ya jinjina kai ya ce "Ok, na fahimta" ya tashi tsam, bai sake cewa komai ba ya fita. Aminu ya nemi wuri ya kifa kansa, ya dafe saitin ƙirjinsa. "Ni zaku mayar tamkar ƙwallon ƙafa, ku din ga bugani a tsakanin ƙafafuwan ku? Kun yi kuskure" ya furta cikin sanyin jiki. *** Tun da suka haɗu, sumayya na tsuma ta fara bawa Nabila labari. "Arfa kin san menene?" "Faɗi kar ta kashe ki" "Wannan satin, Honorable Ma'aruf indabo, zai yi program a gidan rediyon mu, kuma ni manager ya ce zan yi hirar da shi" Nabila ta yi murmushi ta ce "Wow congrats baby" Sumayya ta ce "Nabila, ba abun congratulations bane, indabo fa, wanda kwanaki aka ci mini mutunci a kansa, da na je mazaɓarsa ban tarar da ayyukan da aka ce yayi ba, shi ki ka gani a reception fa, da baki gaishe shi ɗin nan ba". Nabila ta ɗan waro ido ta ce  "Aikuwa sai ki rama, ki zaƙulo masa tambayoyi na tsitsiyewa, tambayar yaya uwarka ta haifeka, ke har waccan maganar ma ki ɗaukko, ki tutsuye ɗan bantan uba, ƴan siyasar nan wasu babu Allah a ran su" Ta ce "I wish ina da wannan damar, sai dai program ɗin ba live bane ba, kuma wai rubuto mini tambayoyin da zan yi masa za ayi mini, kamar dai karantawa zan din ga yi yana bani amsa" "Ban gane ba, interview zaku yi, ko kuma tattaunawa a kan cigaban da ya kaiwa mazaɓarsa?". Sumayya ta ce "Bari kawai nabila, dama murtala ne yake program ɗin, kuma baya nan aka ce na yi, ina ta murna amma gwiwata tayi sanyi, kuɗi ya biya sosai za ayi program ɗin, amma a ɓoye campaign kawai zai yi, kin san zaɓe ya fara ƙaratowa" Nabila ta ce "Taɓ abun tsiya, toshi da ƙosan rogo, wannan kawai tambaya da amsa zaku yi, haka yaya Nasir yazo yana gaya mini wai ƴan daban da ya kama, an kira shi daga sama wai ya sake su, abun babu daɗin ji, naga alamar sai mun zama jan wuya mun zage a kan ayyukanmu, yanzu dai ki ƙarasa, zamu yi waya zan shiga wata unguwa, muna da client zan duba wata shaida ne" Sumayya ta ce "To shikenan, mu yi waya ko kuma ni sai in zo gida" "Ok bye" ta tsayar da mai adaidaita sahun ya tsaya ta sauka. Wata adaidaita sahun ta tsayar ta hau, ta tafi unguwar ƙofar na'isa. Shagon nan da ta taɓa tsayawa ta sai lemo, nan ta tafi. Cikin mutuntawa, mai shagon ya karɓeta suka gaisa, da yake ya gane ta  ya ce "Hajjaju kin dawo unguwar ta mu kenan?" Ta ce "Eh malam, da wata alfarma na zo nema ne" Ya tattara hankalinsa a kanta ya ce "Ok, ina jin ki" Ta ce "Last da na zo, wannan mutumin da na tarar a nan, na ce masa ya taimaka mini ina son na haɗu da aminu Viper, amma ya kwatanta mini wani wuri, wai lungun iraƙi, suka kusa kasheni" Mai shagon ya zare ido ya ce "Viper kuma? Ke menene haɗinki da shi?" "Ɗan uwana ne, tun da ya fito daga prison, ban sake ganinsa ba" Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Allah ya rufa miki asiri da ba su kashe ki ba, kin san yadda suke nemansa ruwa a jallo kuwa? Idan suka riga jami'an tsaro kama shi, kashe shi za su yi. Kuma a iya sanina, babu wata mace da Viper yake da alaƙa da ita, dan haka ki rufawa kanki asiri, ko sunansa kar ki fiye ambata a cikin unguwar nan" Nabila ta waiwaya bayanta, babu kowa a wurin, ta ɗebo kuɗi ta ajiye masa ta ce "Waye shi, ko a taƙaice ne ka gaya mini wanene shi, a ina zan same shi" "Ki ka ce ɗan uwanki ne?" "Ka manta kawai, ni dai ka taimaka mini" Yayi ajiyar zuciya sannan ya ce "Hajiya, na tabatta kina da alaƙa da hukuma, gaskiya ina jin tsoro, ina da iyaye da ƙanne, da nake taimakawa, ko basu saka an kashe ni ba, sai an yi mini illa, muddin na gaya miki wani abu, daga baya su gano ni na faɗa" Nabila ta ce "Manta da batun hukuma, ba ni da alaƙa da ita, kuma babu yadda za ayi na bar wata ƙofa da zata nuna ka gaya mini wani abu, taimakona zaka yi, idan kuɗin sun yi kaɗan zan ƙara maka wallahi". Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Aminu sun taɓa zama a unguwar nan, bayan ya zama ɗan daba na iraƙi ake ce masa ko kuma mai dogon zamani, ƴan sanda ne suka saka masa Viper, saboda rashin tsoronsa, da azabar kwarjinin da yake da shi, gagararre ne sosai, kuma dealer ne na miyagun ƙwayoyi. Kuma matasan yaran nan marasa ji, suna jin maganarsa fiye da ta iyayensu, ba zan iya gaya miki sama da haka ba, amma zan kwatanta miki, in da zaki samu wani yaronsa, amma dan girman Allah, kar ki bari sunana ya fito, ki taimaka" Nabila ta ce "Na yi maka alƙawarin babu wanda zai ji". Ya ce "Idan magariba ta yi, ki je tal'udu, hannunki na hagu, akwai wanda yake zuwa a kan babur ya zauna yana sayar da katin waya, ya saka facemask. Ba katin yake sayarwa ba, balance yake karɓa na yaran da suke rarrabawa tabar wiwi, ƙananan dealolin su, da suke yi sayar musu da katan maye, yaron Viper ne makusantansa ne sosai, amma dan Allah ki riƙe alƙawari". Nabila tayi ajiyar zuciya ta ce "Zan riƙe in sha Allah, na gode sosai". Ta sake ƙara masa kuɗi. Fita daga shagon, tana jin kamar ta riski fiye da rabin matsalarta, idan Allah ya sa ta yi wa DSP hanyar kama aminu, atleast ta taimaka masa. Babu tsoro ko tunanin komai, ta ƙallafawa ranta ko ta halin ƙaƙa za ta yi nasara. Honorable Ma'aruf indabo, yana kashingiɗe a katafaren falon sa, hannunsa riƙe da waya ya kara ta a kunnensa, yana jiran a ɗaga. Muryar madaki ce ya amsa da "Sai mai gida" Indabo ya numfasa ya ce "An sakar maka yaran?" "An sake su mai gida" "Yayi kyau, ka fara ƙoƙarin yi mini aikina, zan shiga Abuja wannan satin, ka tabattar aikin nan ya kammala kan na dawo" "Baka da matsala oga" "Yauwwa, ya batun Aminu?" Madaki ya ce "Wallahi duk wata kafa da za a bi wurin samunsu, ya tsosheta, jiya wani ɗan sanda yake tambayata wai idan na san in da yake" Da sauri indabo ya tashi zaune ya ce "Waye shi? Meyasa yake tambayarka?" "Wallahi ban sani ba, amma dai shi ne ya kama mini yara, Nasir mai tama na gani a jikin kakinsa" Indabo ya jinjina kai ya ce "Shikenan zan bincika" Wata mata ce ta buɗe ƙofar ɗakin, ta shigo, hannunta riƙe da ƙaramin plate ɗauke da tuffa, ta ƙaraso kusa da shi ta zauna. "Ya dai na ganka kamar a tsorace?" Indabo ya ce "Madaki ne ya ce mini wai wani ɗan sanda yana tambayarsa Aminu jiya, dole na saka a bincika waye". Cikin takaici ta kalleshi ta ce "Au da kanka ka ke waya da ɗan daba, abun da ya faru tsakaninka da Aminu bai zame maka izina da darasi ba, kana ganin yadda ya zame mana barazana, ɗan tahaliki ɗaya ya hanaka sukuni". Ya ce "Na san abun da nake yi bilikisu, komai a lissafe nake yin sa, ai na yi kuskure na farko, ba zan yi na biyu ba. Aminu kuma ina da tabbacin akwai wani abu a ƙasa, kuma zan kawar da shi, kafin ya buɗe bakinsa". Ta ajiye trayn hannunta ta ce "Yanzu ya ake ciki da maganar Abdul, haryanzu Naja'atu ba ta ce komai ba?" "Nima ita nake saurare, na fiki damuwa ma da wannan lamarin, amma dole ki ja masa kunne, na fara gajiya da rashin mutuncin sa, ba zai ɓata mini siyasata a banza ba, ina ta fafatuka a kai, ya je ya yi abun da ƴan adawa zasu samu abun faɗa a kai ba". Ɓata fuska ta yi ta ce "Kai ma ɗanka ne ai, ka ɗauki matakin da ya dace da shi" ta ƙarasa maganar ta tashi ta bar masa ɗakin. Yayi guntun tsaki, ya ɗauki wayarsa yana kiran wata lamba. "Honorable, Allah ya taimake ka" "P.A ya turo muku list ɗin tambayoyin da zaku yi mini ko?" "Eh ya turo, mun kuma bawa mai gabatarwar da ka buƙata ta dudduba" Ya jinjina kai ya ce "Ina fatan yarinyar da na ce maka ce?" "Eh ita ce Yallaɓai" Ya ce "Yayi khau, ku turota gidana, ta zo ta yi recording ɗin a nan, ba zan samu zuwa nan ayi program ɗin ba" Cikin damuwa manager ya ce "Ina fatan ba wani laifin ta sake yi ba ranka ya daɗe?" Indabo ya ce "Da zan hukuntata, tun laifin da ta yi mini na farko, da tuni na hukunta ta, wani abu mai muhimmancin gaske na gani a tare da ita, da nake son tabattarwa" "Subhanallah, dan Allah yallaɓai ka yi haƙuri, idan laifi ta yi, ina nema mata afuwa ". "Jamilu, ka turo yarinyar nan gidana, tayi recoding ɗin program, kar ka sake yi mini musu". Ya kashe wayar ya ajiye. Yanayin yadda zuciyarta ke tsananta bugawa ne, ya sanya ta din ga karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. Sai dai ba ta ji za ta iya janye aikata abun da tayi niyya ba. Nesa kaɗan da in ya kwatanta mata ta je ta tsaya, sai dai tun kafin duhun magariba ya gama rufawa, mutumin da aka kwatanta mata ya zo ya kafa teburinsa na sayar da katin waya, ya nemi wuri ya zauna. Ta ɗan jima a tsaye, tana kallon sa, sannu a hankali ta fara tunkarar in da yake zaunen, tana addu'a a zuciyarta har ta ƙarasa in da yake. Kafin ta yi magana, wani matashi ya rigata ƙarasawa, suka gaisa ya miƙa kuɗi, aka bashi wata baƙar leda. Ta tattaro jarumtarta ta yi sallama ta ce "Sannu malam" ya ɗaga kai ya kalleta, sai dai kamar ya razana da ganinta. Ta sake cewa "Sannu malam" "Yauwwa" ya amsa da kakkausar muryar sa, yana cigaba da ƙare mata kallo. "Dan Allah kaya nake so" ya ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, ya ce "Wane irin kaya?" "Irin wanda ka ke sayarwa, amma ni direct nake son na din ga karɓa" "Jami'ar tsaro ce ke?" Yayi maganar yana cigaba da kallonta Nabila ta ce "Jami'an tsaron ai sun san da zamanka a nan, ina so ka haɗa ni da Aminu viper ne" Waro ido yayi ya kalleta ya ce "Ke! Yayi maganar yana zazzaro mata ido" Tayi ƙasa da murya ta ce "Kar ka ɗaga murya, ka taimaka mini, ɗan uwana ne, tun da ya fito daga prison ban sake ganinsa ba" "Ƙarya ki ke yi wallahi! Ban da ke mace ce, da namiji ce ke, wallahi sai na ciro hanjinki waje na zubar a titi, bar wurin nan, kafin na karya ki" Nabila ta marairaice ta ce "Ba ka da tabbacin ƙary..... "Ki bar nan, kafin na tsarga ki biyu da makami" ta ja da baya a hankali, tana kallon sa. "Ki bar nan na ce" ta juya da ɗan sauri, cikin tsoron yadda ya hayayyaƙo mata. Wayarsa ya ɗaukko ya kira Walid yana huci, cikin sa'a ya ɗaga. Walid ya ce "Maza ya ne?" "Wata yarinya ta zo neman boss, wai ƴar uwassa ce, anya ba a fara bibiyar sa ba? Idan ba haka ba, yaya aka yi ta san na sanshi". Cikin mamaki walid ya ce "Kar dai yarinyar da gagare ya ce mini ta je dabar madaki neman sa?" "Ban sani ba, amma zan so ka ganta, ka ga wani abun mamaki, mai ɗaure kai, dan na kusa guduwa wallahi" Walid ya ce "Kamar yaya?" "Ka ga, ina hangota haryanzu, zan bita na yi mata magana, zan ce ta dawo gobe da safe, zaka ga abun da na gani" Walid ya ce "Kai liti, ka tabatta ba matsala?" "Babu, kawai sonake ka ganta" "Shikenan, idan ka tashi yau, ka shiga area wurin dila, ya baka balance, idan na zo zan karɓa" "Sai da kai, an gama" Nabila na shirin hawa ɗan sahu, ta ji an yi fito a bayanta, ta waiwaya ta ga liti a tsaye. "Zo mana" yayi maganar yana kallonta. Kawai zuciyarta ta raya mata, ko wuƙa zai soka mata. "Ki zo mana" yayi maganar cikin tsawa. Cikin rauni ta ce "Dan Allah ba wuƙa zaka soka mini ba?" Ya ce "Ke da kashe ki zan yi, kin isa na bari ki bar wurin nan, shawara na canza, ban san alaƙar ki da shi ba, dan haka zan haɗa ku" Da sauri ta ɗan ƙarasa gabansa ta ce "Dan Allah, amma na ji daɗi na gode sosai da sosai". "Mu haɗu a nan, gobe ƙarfe biyar na yamma, zan haɗaki da wanda ya san in da yake, amma wallahi ki ka yi wani abu na rashin gaskiya, kin san sauran" Nabila ta ce "Babu wani abu na rashin gaskiya da zan yi, na gode yayana Allah ya saka da alkhairi" Ya ce "Ke ki nemawa kanki tsari, da na zama yayanki, ware ki bar nan" Hamadala ta yi, tare da jin kamar wata gagarumar nasara tana tunkarota. Ƙwas-ƙwas takalminta yake bayar da sauti a kan tiles ɗin wurin, sai sauri-sauri take yi ta ƙarasa ofishin manager. Da sallama ta shiga, ya ɗago ya amsa mata, ta ɗan risuna ta ce "Afuwan sir, na tsaya ƙarasa editing ɗin news ne, shiyasa ban zo kiranka da wuri ba". "Bakomai sumayya, sannu da ƙoƙari, ina yabawa ƙoƙarin ki da himmarki". Tayi murmushi ta ce "Na gode sir" "Ina sisternki, young barrister ne? Nabila ko, kwana biyu ba ta kawo mana ziyara ba" Sumayya ta yi murmushi ta ce "Ayyuka ne suka yi mata yawa, amma ko ɗazu muna tare" Ya ce "To Allah ya taimaka, yauwwa dama batun program ɗin nan ne, honorable ya ce ba zai samu zuwa ba, sai dai aje can gidansa ayi recording program ɗin, dan haka driver zai kai ki, a can badawa gidansa yake, za a kai ki ranar Friday, sunday zai yi tafiya ki yi recording program ɗin" Cikin mamaki da sanyin jiki, ta ce "Gidansa kuma sir? Amma ai yau murtala za su dawo, tun da su maza ne sai su je.... Ya ɗaga mata hannu ya ce "Look sumayya, ya zama dole ki je, murtala ba zai dawo yau ba, honorable ba wani abun zai yi miki ba, gidan da yake zaune da iyalansa ne, recording ɗin program kawai zaku yi. Idan kuma ba zaki yi ba, you know the consequences" Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta yi, ta ce "Allah ya kaimu" ta juya a hankali ta fice. ₦500 ne, via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank Special wanda ba sa son group 1k. Wanda za su jira document, idan an kammala 1k ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa wannan layin Sai a tura mini shaidar biya ta 08081012143 ko 07063065680 Ayshercool 08081012143 [7/25, 1:18 PM] null: *ƘARFE A WUTA* AREWABOOKS: ayshercool7724 Watpad: ayshercool7724 What's app: 08081012143 https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g 11 Bayanta manager ya bi da kallo, ta bashi tausayi sosai da sosai, sai dai yana addu'a Allah ya sa kar honorable ya cutar da ita. Kamar ɓarawo, haka walid ya diro a tsakar gidan, maimakon ya biyo ta ƙofa, ɗan mama yana zaune yana shan sigari a ɗan tsakar gidan. Bai kula shi ba, ya wuce ɗakin da viper yake, sai dai ya duba baya ciki. Walid ya dawo, ya kalli ɗan mama ya ce "Ina Viper?" Ɗan mama yayi dariya ya ce "Har ka gama fushin, ka dawo?" Walid ya ce "Kai ka san ba zan iya ba, ƙular da ni yayi ne, ina yi masa uzuri ne kawai na san kansa ya taɓu, yana ina?" "Baya nan" ɗan mama ya bashi amsa kai tsaye. "Kamar yaya? Ina yaje?" Ɗan mama ya zuƙi sigarinsa sannan ya ce "Ni na isa na hana shi fita ne? Ko kuma na ce sai ya gaya mini in da za shi? Da dai kai ne zai iya ɗaga maka ƙafa" A fusace walid ya ce "Dan me zaka bari ya fita?" "Au so ka ke na hana shi, ya karya ni, ko ya illata ni, kaɗaici ne ya dame shi, gidan babu kayan caji, sai na hayaƙi, shi ne ya fice. Yauwwa dama ina son gaya maka, ka daina kwashe kayan cajin nan gaba ɗaya, idan wani yayi rawa an bashi kuɗi, kai idan ka yi, na jaki zaka ci a hannunsa wallahi" Cikin takaici Walid ya ce "Wai so ka ke sai ya kashe kansa ne? Kana kallon allurar nan ba ta ɗaukar sa, farar ƙwaya ma fa ba ta yi masa komai, sai rikita masa ƙwaƙwalwa, idan ya haukace fa?" Walid gani yayi ɗan mama yayi tsuru-tsuru, yana rarraba ido, dan haka ya waiwaya bayansa, Al'amin ya gani a tsaye a bayansa. Bai kula su ba, ya zo ya raɓa walid ya wuce. "Master"ya kira shi. Al'amin ya waiwayo, fuskarsa babu annuri, idanunsa sun yi ja, jijiyoyin kansa suka miƙe ya ce "Me na ce maka a kan kirana da haka?" Walid ya ƙarasa kusa da shi, dai-dai kunnensa, ya yi masa raɗa. Viper ya kalli Walid ya ce "Kasheni ka ke so ka yi sannan hankalinka ya kwanta ko Walid?" Walid ya ɗage kafaɗa ya ce "Duk yadda ka gani" Viper ya hankaɗe shi gefe, ya wuce ɗakinsa, ya rufe ƙofa. Walid ya bishi ya leƙa ta taga ya ce "Me zaka yi ka rufe ƙofa?" Leda ya ciro daga aljihunsa, ya haɗa allura a sirinji, zai yi wa kansa. Walid ya ce "Al'amin, ba zaka daina yi wa kanka allurar nan ba ko? Ba za ta yi maka ba, ka haƙura mana" Al'amin ya tashi, ya je ya ja tagar ya rufe, ya bar walid a waje yana surutu. Sumayya kuwa tun da ta koma gida, mama ta lura da yanayinta, sai dai ta yi zaton ko gajiyar aiki ce, amma har dare ba ta walwala. Dan haka ta magantu, ta ce "Ƴar mama, wai ko babu lafiya ne?" Sumayya ta ce "A'a lafiyata ƙalau?". "To faɗa ku ka yi da mutuniyar ne?" "A'a bamu yi faɗa ba mama" Ba ta gaza ba ta sake cewa "To ko wurin aikin ne suka yi miki wani abun?" Sumayya ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Hajiya mama, bamu yi faɗa da ƴar ki ba, lafiyata kuma ƙalau, kawai kin san yanayin aikin namu ne, kayi ta ganin abubuwa na ban tausayi daban-daban". Mama ta ce "Ai baku ba sumayya, mu ma masu saurare, kusan kullum cikin zullumin kunna radiyon muke, sai dai ku ƴan jarida ku ne idonmu, ta bakinku kawai muke jin wasu labaran da jin halin da duniya ke ciki. Allah dai ya saka muku da alkhairi ya tsare mana ku baki ɗaya, daga ke har Nabilan aikin tainakon al'umma ku ke yi, Ubangiji Allah ya tsare ku ya kawo mazajen aure na gari" Sumayya kamar ta gaya wa mama, abun da aka umarceta a wurin aiki, amma ta san hankalinta tashi zai yi, zata iya hanata aikin ma, kuma Allah ne gatansu aikin nan ne gatansu, dan haka ta ja bakinta tayi shiru. *** Sannu a hankali barrister Naja'atu take bin titin ƙauyen, sai tsaki take yi saboda yadda garin yake babu kyakkyawar hanyar shiga. Sai uwar ƙura da kwazazzabai a hanyar. A hankali ta cigaba da tuƙin har ta ƙarasa in da take son zuwa. Sai da ta shiga tsakiyar tsakar gidan, sannan ta yi sallama. Daga cikin ɗaki a ka amsa sallamar. Daga baya matar ta fito daga ɗakin, ta ce "Waye?" Ganin barrister Naja'atu ya sanya ta ɗan saki fuska, ta bata damar shiga ɗakin. Shame-shame taga rammaa a kwance a kan katifa, ta nemi wuri ta zauna a gefe. Ta kalli in da ramma take, sannan ta mayar da idonta kan maman ta ce "Na dawo ne na ji me kuka tsayar, kuma na ga haryanzu ba ta da lafiya, anya ramma ba shagwaɓa a wannan lamarin? ya ci ace kin ware ai, da auren ma aka yi miki ai da kina gidan miji, ko shi ma hakan zaki yi ta yi masa". Fashewa da kuka ramma tayi, cikin tsananin baƙin ciki da takaici. "Meye kuma na kuka? Wannan abun da ki ke yi, sai mutane sun san halin da ki ke ciki?" Cikin sanyin jiki da damuwa, maman ramma ta ce "Tun da abun nan ya faru, take rashin lafiya, jiya mun je asibitin sha ka tafi, na garin nan, an ce ciki ne da ita" tayi maganar tana fashewa kuka mai taɓa zuciya. Sak Naja'atu tayi, tana kallon su. Ta numfasa ta ce "Wai wannan kukan na menene ku ke yi haka, kukan zai yi muku magani ne? Ai wannan ba abun ɗaga hankali bane ba" Cikin tsananin mamaki, maman rahama take kallon barrister Naja'atu. "Baiwar Allah, ce miki na yi fa, an ce mini ciki ne da ita, wanda ya dubatan ɗan garin nan ne, na san dole maganar nan ta fita, auren yarinyar nan ba zai yiwu ba, amma kina nuna bakomai bane ba, dan girman Allah a karɓowa yarinyar nan hakkinta". Naja'atu ta ce "Baiwar Allah, ko fa an kai yaron nan kotu yayi prison, abun da zai faru ya riga faru, ba kuma zai goge ba, ɓacin suna kuma ya riga ya ɓaci. Matsalar mutanen mu na Arewa, kuna giramama al'ada da addini a kan ƴancinku. Da in da aka cigaba ne, zata iya haife abun da ke cikinta, idan tana so, and rise him as a single mother, har ta iya neman ya din ga biyanta wani abu a kotu, shikenan. But for now, za a iya zubar da cikin ta cigaba da harkokinta sai me? Is an adolescent crises kowa ma zai iya faruwa da shi". Cikin mamaki maman ramma ta ce "Baiwar Allah kuma ke musulma ce?" "Ƙwarai kuwa, muslma ce ni gaba da baya, mafita nake baku da shawara. Zan je na yi booking a saka rana a can cikin gari, private hospital, a cire cikin lafiya ƙalau za a cire shi, yanzu an cigaba nesa ba kusa ba, ku karɓi kuɗin ku ku rage zafi". Rma ta fashe da kuka ta ce "Ni mama tsoro nake ji, an ce mutuwa ake yi, dan Allah ni dai a kai shi wurin alƙali, an ce kina taimako dan Allah ki taimaka mini, ji nake kamar na mutu na huta, ba a taɓa cikin shege a garin nan ba sai a kaina, dan Allah ki taimaki rayuwata, wallahi wanda zan aura ya ji labari ba zai aure ni ba, babu kuma wanda zai ce zai aure ni, cewa za ayi na zama ƴar iska" ta ƙarasa maganar kamar ta shiɗe. Barrister Naja'atu ta ce "And so what dan an fasa aurenki? Zaki iya zama duk abun da ki ke so a rayuwa ko da aure ko babu, waye ya ce muku aure shi ne limit na rayuwar ƴa mace ne? dan Allah ku fuskanci rayuwarku, ku daina bari ana cutar ku da addini da al'ada". Cikin baƙin ciki maman ramma ta ce "Kin ga ya isa baiwar Allah, idan bawa bai riƙe addini ba haka zai ta rayuwa kamar dabba a gari, babu ƙa'ida babu hukunci? Wannan ai salon bawa yaro damar ya je yayi zina ne, ko ni da nake jahila a cikin ƙauyen nan, sam maganarki ba ta da tushe balle makama a wurina, dan haka ki tashi ki tafi kawai, bana buƙatar taimakon naki, cuta ce an cuce mu Allah ya isa kawai" Naja'atu tayi wani irin murmushi ta ce "Ƙarshen abun fa kenan, ki yi Allah ya isa, na biyo miki da masalaha amma kin ƙi, shikenan idan kin ƙi ji ai ba kya ƙi gani ba, duk abun da ya biyo baya wannan shi ne abun da ki ka zaɓa. Sai dai ina sake yi miki gargaɗi da babbar murya, kar ki kuskura ki sake shiga kafafen watsa labarai ki yi magana, idan kuma ki ka sake, ba ruwana" Ta tashi ta sake ajiye musu kuɗi, da complementary card ɗin ta, ta ce "Akwai lambar wayata a jiki, na san zai iya yi muku amfani, idan ku ka ga babu sarki sai Allah, domin kuwa barin cikin nan, dai-dai yake da zama da ajalinta, dan kome zai ɗauka, uban wanda ya aikata laifin, ba zai bari ba" Gaba ɗaya bin ta suka yi da kallo, har ta tashi ta fita, ramma ta fashe da wani irin kuka, tare da jin ƙarshen rayuwarta ya zo. Mahaifiyarta ta kalleta ta ce "Ki yi haƙuri ramma, ina tare da ke in sha Allah, na san ko menene ya faru, ni ce sila, da ban tura ki aikatau ba, da haka ba ta faru ba, amma babu yadda zan yi ne, ki yafe mini dan Allah" tayi maganar tana kuka ita ma. Sumayya na ta aiki a kan computer, sai dai hankalinta baya kan aikin sam, kawai dai tana yi ne, amma ƙasan zuciyarta tsoro da fargabar dalilin da ya sanya, aka ce ta je gidan honorable Indabo ta yi hira da shi take ji, idan a kan laifin da ta yi wancan karon ne, ai ta bayar da haƙuri, kuma lokacin tana farkon zuwa ne. Sallamar murtala ce, ta dawo da ita hayyacinta, tayi murmushin yaƙe ta ce "Uncle murtala, saukar yaushe?" Ya nemi wuri ya zauna ya ce "Agogo sarkin aiki, yakamata a ƙara miki matsayi a gidan nan fa" Ta waro ido ta ce "Ni a wa?" "Ke a ma'aikaciya jajirtacciya mana, wai ya aka yi mutuniyar take ɗaga miki ƙafa yanzu, lawisa?" Sumayya ta ce "Hmm, Arfa ce ta ce na daina jin tsoronta, nima na nuna mata bani da kirki idan ta takura mini, shi ne fa ta sarara mini". "Ai matar nan ƴar bala'i ce lamba ɗaya" Sumayya ta sake tattara nutsuwar sa a kan sa ta ce "Yauwwa ncle murtala, akwai matar da ka yi recording, ta zo an yi raping ƴar ta, an ce Barrister Naja'atu ta shiga case ɗin, ina aka tsaya ne?" Da sauri ya ce "Rufa mini asiri, ni da aka kusa korata a kan case ɗin, kuma lawyoyi da masu kare hakkin ɗan adam, sun yi casa a kan case ɗin, sai dai tun da ta shiga cikin lamarin, kowa ya ja da baya" Sumayya ta ce "Ikon Allah, to ai haryanzu ban ji a ina aka tsaya ba, wai ɗan waye ne yayi?" "Taɓ ba zaki ji mutuwar sarki a bakina ba, nima ba ta faɗa mini ba matar, wai dai yaron ɗan masu kuɗi ne, wai ɗa ne ga wani ɗan majalisa, ba ta san sunansa ba, a gidan ƙanwar ɗan majalisar yarinyar take aiki, sun je gidan ta bi ba'asi, an hana su shiga, masu gadin da suka kai yarinyar asibiti ma duk an canza su" Cikin tausayawa Sumayya take girgiza kai ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shikenan akwai Allah, amma kana ganin ita Bunkuren za ta yi wani abun kirki a kai? Meyasa ba za a bibiyeta ba, a ji a ina aka tsaya a case ɗin ba, atleast a gurfanar da shi a kotu mana" Ya miƙe tsaye ya ce "Lallai ƙanwata baki san ƙasar nan ba, ai dokar ƙasar nan a kan talaka kawai take aiki, ko ɗan kansila ne, ba za su hukunta shi ba, ita kanta barrister nan akwai ayar tambaya a kan ta, duk da a zahiri ta Allah ce, amma yadda ake tsoronta komai tayi, babu wani mai challenging ɗin ta, akwai wata a ƙasa". "Gaskiya dai, Allah ya sa mu dace " Ya amsa mata da Amin. Nasir yana ta yi wa Nabila bayanin, irin cigaban da yake samu a neman viper, amma hankalinta ba ya kansa, jin sa kawai take yi, kawai ji take kamar ta gaya masa halin da ake ciki, amma ta fasa, dan ta san faɗa zai yi mata. Hankalinta bai dawo jikinta ba, sai da ta ji ya ce zai je Abuja. Ta kalle shi ta ce "Abuja kuma? Me zaka yi?" "Harkar aiki mana, a ƙalla sati zuwa wasu kwanaki" Ta kwaɓe fuska ta ce "Har sati?" "Eh mana, ko in tafi da ke ne?" Tayi murmushi ta ce "Wace ni, Allah ya bada sa'a" Kafin ya amsa, wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗaga ya saka a kunnensa, "To" kawai ya ce, ya ajiye wayar ya miƙe ya ce "Bari na shiga sashen mama, tana nemana" Nabila ta ce "To" Agogon hannunta take kallo, yau ko Abba zai jajjagata idan ya dawo bata nan sai ta fita, dan tuni ta ɓoye takalminta da hijjabinta a harabar gidan, za ta lallaɓa ta fice, yadda take ji a ranta, ko zata rasa rayuwarta, ba ta da wani burin da ya wuce ta ga an kama Aminu Viper, domin kuwa shi ne ƙashin bayan matsalar aikin daba da dillancin miyagun ƙwayoyi, gefe guda kuma ga dakon burin da take yi. "Nasiru sau nawa nake gargaɗinka a kan yarinyar nan? Ban isa in gaya maka magana ka ji ba ko?" Cikin son kare kai ya ce "Wallahi mama ba abun da ki ke tunani bane ba, magana muke yi kawai a kan harkar aiki" "Ni ka yi maganar harkar aikin da ni mana. Wai ma yaya muka yi da kai, ina alƙawarin mu?" "Mama dan Allah ki ƙara mini lokaci, sonake na kammala aikin nan na nutsu, kin san komai lokaci ne" A hasale ta ce "Zan kwaɗe ka da kai da lokacin, shekarunka nawa yanzu a duniya, me ka ke nema da Allah bai baka ba? Wato in saki jiki ka ce wannan shegiyar yarinyar zaka aura ko? To wallahi baka isa ba, idan ba ka kiyayeni ba, sai dai ka dawo ka tarar na aura maka duk wadda nake so" Yayi shiru ya sunkuyar da kai, shi bai ga aibun Arfa ba, kuma a zuciyarsa ji yake kamar zai samu chance ɗin da zata zama mallakinsa, rashin gaya mata abun da yake ji game da ita kawai, ba ƙaramin azabtuwa yake yi ba. Sanye take da face mask, tana rarraba idonta, ta ga ta ina zata ganshi. Liti ya kalli Walid ya ce "Ka ganta ko?" "Eh, amma bana ganinta sosai, ta rufe fuskarta da facemask". Liti ya ce "Bari na yi wa gali magana" Nabila na tsaye tana rarraba ido, wani matashi ya zo gabanta ya tsaya, ta ɗaga kai tana kallonsa. "Ki sauke takunkumin fuskarki". Cikin tsiwa ta ce "Ban gane ba, ina ruwanka da ni?" Wayar hannunsa ya ɗaga mata, da take a kan kira, muryar liti ta ji. "Ki sauke takunkumin fuskarki, ko kuma na fasa haɗaku" Waiwayawa take yi, ta ga ta ina za ta ga liti, ta kalli matashin ta ce "Da kai zai haɗani?" Ya girgiza mata kai. Ta din ga waige-waige ko zata ga daga ina liti yake ganinta, har ya san ta saka facemask. Kafin ta waiwayo, gali ya bar wurin. Ta sauke facemask ɗin, tana rarraba ido. Zabura Walid ya yi ya ce "Kai, a ina ka samo wannan yarinyar?" "Jiya ta zo ta same ni, wai ita ƴar uwar viper ce, in taimaka in haɗa su, na shiga area jiya na ɗan yi wuru-wuru, an tabattar mini ita aka kwatantawa dabar madaki, ta je nemansa, suka sakar mata karnuka, ban san waye ya kwatanta mata ni ba". Walid ya ce "Tabbas! Yakamata a haɗa su" Liti ya ce "Idan kuma haɗin baki ne, ko wata maƙarƙashiya ce aka shirya masa fa?" Walid ya ce "Zan kula da komai, amma yakamata su haɗu, ka ce ta dawo jibi da safe" "Kana ganin babu matsala?" "Babu matsala" Nabila ta fara gajiya da tsayuwa, matashin ɗazu ya sake dawowa, ya miƙa mata wayar. Ta karɓa ta yi sallama. "Ki dawo jibi, ƙarfe sha ɗaya za'a haɗaki da shi". Kamar Nabila ta yi zagi, dan haushi, amma ta danne ta ce "To shikenan, Allah ya kaimu" haka ta bar wurin jikinta a sanyaye, har ta fara tunanin ko dai raina mata hankali kawai zai yi. Haka ta koma gida, ba tare da ta ji za ta sare ba. Sumayya daga aiki gidansu Nabila ta je, dan su tattauna a kan umarnin da ta samu a wurin aiki. A ɗaki ta tarar da Nabila, tana bacci, dan daga wurin su liti da ta dawo, kwanciya ta yi. Tashinta tayi, Nabila ta tashi tana tsaki, saboda yadda ta tsani a tashe ta tana bacci. "Ke baccin uban me ki ke yi, bayan azahar, har kin dawo daga aikin ne?" Nabila ta yi miƙa ta ce "Ni ban je aikin ba ma" "Allah ya shirya ki, tashi ki wanko fuskar ki, mu yi magana akwai case Arfa". Nabila ta sake mayar da kanta kan fulo ta ce "Faɗi in ji" "Dalla ki tashi ki saurare ni" "Wai ba kunne ne yake ji ba?" Sumayya ta ce "Kin gane mutumin da muka gani a reception, ki ka ce kin tsane shi? Ɗan majalisa ne" "Yanzu takanas ki ka zo gaya mini ɗan majalissa ne? Ai na sanix Sumayya ta ce "Dalla ki tsaya ki saurare ni, Honorable Ma'aruf indabo ne ai" Nabila ta tashi zaune ta ce "And so?" "Shi ne wai ni zan yi hira da shi, a madadin murtala, amma ya yi waya, wai sai dai na je gidansa na yi recoding ɗin program ɗin, shi ba zai samu zuwa ba" Nabila ta waro ido ta ce "Saboda me?" "Wai ba shi da lokaci, Nabila tsoro nake ji, ko zaki raka ni? Jibi in Allah ya kaimu ne zan je,ba na son rasa aikina, kuma ina tsoron ya cutar da ni" Nabila ta ce "Kash, gashi kuma nima zan je wani aikin ne, da na raka ki aminiya. amma menene a ciki, ke zuwa gidan ɗan majalisa ba cigabanki bane?" A raunane Sumayya ta ce "Tsoro nake ji Arfa" "Sumayya, wani abun fa dole sai mun cire tsoro, tsoronki yayi yawa, ki yi addu'a, duk abun da ya same ki, gidan radiyon will be responsible, babu wani abu in sha Allah, ai mun riƙe addu'a" Yanayin fuskar sumayyan ya tabattar mata da gaske tsoron take ji. Sai dai ita ba ta ga abun tsron kamar yadda sumayya ta ɗaga hankalinta ba. Nan ta din ga jan ta da hira, har ta saki jikinta suka cigaba da hira, suka ci abinci tare. Sai daf da magariba ta raka Sumayya ta tafi gida. Duk da ƙirjin Arfa na tsananta bugawa, amma ba ta ji zata iya fasa abun da ta ƙudurta ba, domin kuwa sai ta ga ƙwal uwar daka, jibin nan za ta shirya ta sake komawa wurin liti. Paid book ne ₦500 via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank Sai shaidar biya ta 08081012143 Special 1k, wanda za su jira complete document shi ma 1k ne. Ayshercool 08081012143 [7/26, 1:37 PM] null: *ƘARFE A WUTA* Arewabooks : ayshercool7724 Watpad: ayshercool7724 What's app :08081012143 What's app channel https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Paid book ne ₦500 via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda ba ss som group akwai special 1k. 12 Yau ma ba ta sake zani ba, a yanayin da Walid ya iske Viper, ya sha duk abun da yake tunanin zai sha, ya bugu yayi bacci, amma jikinsa ya mutu murus, ya kasa baccin. Idanunsa sun yi jawur, tamkar ana iza wuta, jijiyoyin kansa sun kumbura, sai buɗe idonsa yake yi yana lumshewa. Walid ya kalli ɗan mama ya ce "Ɗan mama kai ka ke kawo masa kayan nan ko?" "Wallahi bani bane ba, da kansa ya fita ya samo abun sa, ban kawo masa komai ba". Ya mayar da idonsa kan Viper ya ce "Ka na ji na?" Ya ɗaga kai ya kalli Walid alamar eh. "Wai ba zaka daina fita ba, sai wani abu ya faru tukuna, ka sake sakamu a matsala?" Viper ya kalli walid, amma yayi masa shiru. Shikenan, ina son zamu fita da kai, zan nuna maka wani abu mai ban mamaki" Viper ya ce "Walid" ya kira sunansa da dakakkiyar muryarsa. Ya amsa da boss "Boss" "Meyasa ba ka da zuciya ne?" Yayi maganar cikin maye. "Na ce bana son sake ganinka" Walid ya ce "Saboda duk sheɗancina, ɗan halak ne ni. Ya zaka bi ni mu je?" "Ba zani ba" "Yakamata ka fara sanin dalilin da ya sa yarinyar nan ta matsa a kan lallai sai ta haɗu da kai, ina..... Cikin hargowa ya ce "Wai wace irin yarinya ce? Meye haɗina da ita? Wacece ita me take nema a wurina?" yadda ya firgice sai da Walid ya matsa baya da sauri. Ya cigaba da cewa "Kowacece, a kawar da ita, bani da alaƙa ta kusa ko ta nesa da kowace mace, kar ka kuskura kar kuma ka fara, idan ba haka ba duk abun da ya biyo baya kai ne sila" Walid ya ce "Na ji na fahimta, easy ka yi haƙuri". Ya ja tsaki, ya yinƙura dan ya tashi da niyyar ya fita, amma jiri ya ɗebe shi yayi baya, cikin zafin nama walid ya riƙe shi, ɗan mama ya taimaka masa, suka kwantar da shi. Ɗan mama ya ce "Da gaske ka ke wai sai ka haɗa shi da yarinyar? Kuma akwai alaƙar tsakaninsa da ita?". Walida ya ce "Shi nake son tabattarwa". "To ya ce baya so, amma kai ba ka tunanin ko ƙarya take yi?" Walid ya ce "Ƙaryar ma take yi, amma yakamata su haɗu" Ɗan mama ya sake cewa "Sai ka haɗa sun kenan, idan ya illata ta fa?" Walid ya ɗora yatsansa a kan leɓensa alamar yayi shiru, dan ya san Viper idonsa biyu kuma yana jin sa. *** A office ɗin su Nasir kuwa, hira ta yi hira, ake gaya wa Nasir, wani ɗan majalisa ne, yayi belin yaran madaki da aka kama, ya saka aka sake su. Cikin takaici ya ce "Allah wadaran naka ya lalace, muna tufka suna warwarewa, mun zama tamkar bayinsu, kullum cikin ganin gazawarmu ake, alhalin muna iya ƙoƙarinmu" Suka cigaba da tattaunawa, a kan yadda manyansu kan yi musu karan tsaye, a kan harkar aiki, da hana ruwa gudu. Ramma ce take ta murƙususun ciwon ciki, hankalin mahaifiyar ta a tashe, take ta ba ta jiƙe-jiƙen magunguna, da ta zuƙa kaɗan sai amai, ba ta iya cin abinci ga wani irin zazzafan zazzaɓi da yake damunta. Kullum ta na ɗaki, ko tsakar gida idan ba dole ba, bata fita, saboda yadda labarin cikin nan ya watsu ya cika garin su, dama ta san isa sai ya bayar da labari, tun da ɗan cikin garinsu ne, ku ma shi ne ya tabattar da akwai cikin. Cikin matsananciyar damuwa ta dubi ramma ta ce "Sannu ramma, na baiwa sani kuɗi ya sayo miki maganin zazzaɓi, kin ga haryanzu babu shi shiru bai dawo ba". Cikin kuka ta ce "Mama mutuwa zan yi". "Ki yi haƙuri ramma, ba zaki mutu ba, kina karya mini gwiwa, ki daure. Amma anya ba zamu yadda a cire cikin nan ba? saboda rufin asirinmu, kuma kema ki huta" Cikin sauri ta girgiza kai ta ce "Mama tsoro nake ji" Rasa abun yi ya sanya maman ramma, sakata a gaba suka cigaba da kuka tare, a zuciyarta ta din ga ja wa Abdul duk wani nau'i na masifa da jafa'i. Yau sumayya za ta je program gidan honorable Indabo, maimakon ta kasance cikin farin ciki, a dalilin zata shiga gidan babban mutum kamar sa, amma ta gaza nutsuwa da yin farinciki a kan hakan, sai wata irin fargaba da faɗuwar gaba da take fama da ita. Sai da ta fara shiga wurin aiki, ta gabatar da ayyukanta na ranar, sannan ta fara harhaɗa kayan aikin da za ta yi amfani da su. Gaba ɗaya jikinta babu ƙwari, sai tsananin tsoro da fargaba. Murtala ne yake ta kwantar mata da hankali, tare da nuna mata, hakan ma wani cigaba ne, ta sani ko daga program ɗin su daidaita da honorable ɗin. Jin sa kawai take yi, tare da murmushin yaƙe. Har bakin motar gidan radiyon da za a kai ta a ciki, yana ƙarfafa mata gwiwa, "Sumayya, abun da zan gaya miki shi ne, ki san iyakar ki a kan program ɗin nan, iya tambayoyin da aka rubuta miki, ki yi masa su zaki yi masa, kar ki ƙetare su ki jawo wa kanki matsala, ƴan siyasar nan ba kowa ne mai imani a cikin su ba" "In sha Allah uncle murtala zan kiyaye, na gode sosai" Ta shiga motar ta zauna, direban ya ja suka tafi. Nabila kuwa tana office tare da barrister Habib, dan yanzu ya saukko ya fara yaba mata, tana ƙoƙari, ya fuskanci kawai shiririta ce take damunta a kan aikin, da rashin mayar da hankali. Tana yi tana kallon agogo, kar ta saɓa lokacin da a ka bata. "Barrister" ta kira shi, ya ɗago yana sauraren ta. "Ban sani ba ko kana jin radiyo" Ya ce "Ina ji mana, meyafaru?" "Cases da dama, idan suka faru mussaman na masu ƙaramin ƙarfi, sai in ga barrister bunkure ta tsayawa mutane, wai ita ba dan kuɗi take aikin ba, dan barrister ce da ba kowa yake iya ɗauka ba, amma tana tsayawa marasa ƙarfi, ko kuɗi ne suka yi mata yawa?" Barrister Habib ya girgiza kai ya ce "Ke dai kawai ayi sha'ani" "Ka san wani abu kuwa? Akwai wani case da wata mata, ta je gidan radiyon su sumayya, ta kai koken an yi wa ƴar ta fyaɗe, an dawo mata da ita daga gidan aiki, ta je gidan da yarinyar take aiki, an hana su shiga, ta kai wurin ƴan sanda, amma ana ta yi mata yawo da hankali, wai yaron ɗan manya ne. To na ji an ce ta shiga case ɗin, amma haryanzu babu wani update, ka san da na so na jarraba sa'a ta, nima na shiga case ɗin ayi da ni, na tausayawa matar da yarinyar, amma na san ana babbakar giwa, wa zai ji ƙaurin zomo, na san ba za ta saurare ni ba ma". Barrister Habib ya tattara hankalinsa a kan Nabila ya ce "Nabila" "Na'am" "Just be yourself, ke dai ki kalli mutum a riga kawai, Naja'atu kura ce da fatar akuya, ba wata abar burgewa ba ce, da zaka yi koyi da ita ba. Yarinyar ƴan siyasa ce, babu wani taimakawa masu ƙaramin ƙarfi, ta fake da wannan ne, dan sunanta ya ƙara fitowa, kuma ya rinjayi ɓarnar da take aikatawa, ai mun yi karatu da ita tare, ƙwalluwar shegiya ce, ke abun bai baki mamaki ba, ace kowace shari'a idan ta tsaya maka, zaka yi nasara, ace komai kai ka ke nasara akwai ayar tambaya ai, dan haka ki yi ta kanki kawai. Duk da mu ma ɗin wasu lokutan, muna take gaskiya, amma yanayin aiki ne ya zo da haka, kuma nata ya ƙazanta". Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Biri yayi kama da mutum" Nabila a zuciyarta ta ce "Idan haka ne, ba gaba da gaba yakamata na yi da ke ba, tona miki asiri zan yi" Habib ya ce "Ya dai?" "Nothing sir, jikina ne yayi sanyi kawai na gode sosai da bayaninka" Ba tare da neman iznin kowa ba, ta ɗauki jakarta ta fita. A in da ta tsaya shekaranjiya, nan ta je ta sake tsayawa, tana fatan Allah ya sa ba jirgata za su yi ba. Ta shafe a ƙalla awa guda a wurin, har ta sare zata tafi, matashin da ya kai mata waya, liti yayi mata magana da ita, ta gani a gabanta. Bai ce mata uffan ba, ya miƙa mata wata takarda. Sunan wata unguwa ne a jiki,da dai-dai wurin da zata je ta tsaya, saboda tsabar wauta da rashin hankali, ta yi masa godiya ta tari abun hawa ta nuna masa takardar. Mai baburin ya gaya mata kuɗinsa, babu neman ragi, ta afka ciki ta ce su tafi. Lissafin da take ma a zuciyarta, na mamakin yadda Naja'atu tayi mata kallon ƙasƙanci ne, ta wulaƙanta ta alhalin ma ba wata mutuniyar arziki ba ce. Babban abun da ta fuskanta, ƙasar nan ba zaka taɓa samun wasu damarmaki ba, har sai ka taka wani babban matsayi na musamman, ka shahara sai dai hanyoyin bi a shahara ɗin ne, ko da kasada ko ka kauce hanya. Ta yi wa kanta alƙawarin, dole za ta bibiyi case ɗin yarinyar nan, ba naja'atu ba, ko a hannun ƙaramar hukumar bunkuren case ɗin yake, sai ta bibiya, ai da ƙananan kasada ake babba, ga kuma babban target ɗin ta, Viper, ta san idan aka kama shi, dole a sara mata, ta shiga cikin mata da suka kafa tarihi. Da wannan gurguntaccen tunani na Nabila, mai cike da wauta da rashin lissafi, suka cigaba da tafiya can ta ce "Malam, wai haryanzu ba a zo ba?" "Ba ki taɓa zuwa unguwar ba ne?" Ta ce "Eh, sai yau zan fara" Ya ce "saura kaɗan in sha Allah" Sai dai gabanta ya fara faɗuwa, tun bayan da ta ga sun bar cikin mutane, sun fita wajen gari. Dai-dai wani gidan gona ya ajiyeta, wurin duk shuke-shuke, da alama akwai mutane a daf da wurin, amma sai an yi tafiya kan a tarar da in da suke. Shi kansa titin wurin, babu ababen hawa da suke kaiwa suna komowa a wurin. Sai rukunin manya manyan kamfanunnuka a wurin, na shinkafa da na taki, wurin shiru sai ƙarar injinan da masana'antun ke amfani da su. Sai da ta sallami mai a daidaita sahun, sannan ta fara tunanin, to ina ma za ta nufa? Tsayawa ta yi, tana waige-waige, kawai ta hango wani mutum ya tunkarota, nan ta fara ja da baya, tana tunanin ko zurawa za ta yi da gudu. "Mu je" ya ce mata a kausashe. Ta turje ta ce "Ina?" "Ba ke ce baƙuwar Viper ba, mu je" A raunane cike da tsoro ta ce "A'a, ka kirawo shi mu yi magana a nan, ni dama kaya nake son saya a wurinsa" Cikin mamaki ya kalleta ya ce "Wani irin kaya?" "Wanda yake sayarwa" tayi maganar a tsorace tana kallon Walid. Ya gyaɗa kai ya ce "Baki san waye shi ba amma? Kin yi kasada nafi muni, wuce muje kafin na saraki biyu a wurin nan" Cikin rawar jiki ta ce "Dan Allah ka yi mini rai, ni ka kirawo shi nan kawai". "Wallahi zan saɓa ki a ka, wuce mu je" Salati Nabila ta din ga yi, dan tun da ta yo dakon kasadar nan, sai yanzu ta ga zunzurutun wautar da ta aikata. Ya sakata a gaba, suka nausa bayan kamfanunukan. A can gidan honorable kuwa, yana da office a cikin gidan sa, in da yake ganawa da mutane na mussaman. Hankalin sumayya ya ɗan kwanta, bayan da ta ga mutane na shiga suna fita a gidan, da alama ba shikaɗai ne a gidan ba, kuma gidansa ne da yake zaune da iyalinsa. A harabar gidan aka dakatar da wanda suka rako sumayya, aka ce itakaɗai za ta shiga. Wani security yayi mata jagora, zuwa wani sashe na gidan, ya kaita wani falo, ya ce ta jira a nan, ta samu wuri ta zauna, a kan kujera, tana zaune a falon office ɗin, tana ɗan kalle-kalle, tana jira kamar yadda aka umarceta. Cikin office ɗin kuma, Barrister Naja'atu ce suke magana da honorable. "Ni fa na yi iya ƙoƙarina, amma da alama mutanen nan, su na da taurin kai, juyin duniya sun ƙi saduda, sai iƙrarin a karɓar musu hakkinsu suke yi, ina ga kawai a ɗauki matakin da ya dace a kan ta". Indabo ya ce "Lallai dama haryanzu akwai masu ƙi faɗi a talakawa?" "Akwai su fa, ku kuna gefe, mune muke shiga cikinsu da rufe bakunanansu a kan ɓarnar da ku ke aikatawa, sai dai kan mage ya fara wayewa, babban abun damuwar sun gaya mini an tabattar musu tana da ciki" Yayi saurin ɗaga kai ya kalleta "Ciki kuma? Sau nawa yayi mata fyaɗen ne?" Ta ɗage kafaɗa ta ce "Wannan kuma shi za ka tambaya, ba zan iya cigaba da ɓata lokacina a kan wannan kucakan mutanen ba, ina da abubuwa masu muhimmanci kawai ayi abun da ya dace". Yayi ajiyar zuciya ya ce "Abdul, ban san lokacin da zai yi hankali ba, ina tsoron lokacin zaɓe, a samu wani ya fito da miyagun halayensa, in the next couple of years, sonake ya samu ref, ko deputy governor a tsayar da shi takara, saboda yarjejeniyar da muka yi, da jam'iyya kenan kafin na yarda na zauna a cikinta, amma al'amarin sa kullum ƙara lalacewa yake yi" Barrister Naja'atu ta ce "To, gara dai ka san abun yi" "Anyway, shikenan, ki tura mini address ɗin su ita yarinyar, za ayi abun da aka saba" ta miƙe tsaye ta ce "No problem" Ta buɗe ƙofar office ɗin ta fito, kallo ɗaya sumayya ta yi mata, ta gane ta, saboda yadda Nabila take ɗora hotonta a status ɗin ta a baya. Cikin son tabattar da abun da Nabila ta gaya mata, a kanta, ya sanya  ta tashi da sauri tana murmushi ta ce "Barrister Naja'atu Bunkure, baya goya marayu, dama zan ganki ido da ido?" Sumayya ta yi maganar tana murmushi. Kamar ta ga kashi, ta yatsuna fuska ta ce "Sannu". Sumayya ta maze ta ce "Na tsinci dami a kala yau, ni ƴar jarida ce, a cikin ayyukan da ki ke gudanarwa, zan so yi miki tambaya ɗaya zuwa biyu, na san masu sauraronmu, za su ji daɗin hakan, kasancewar ki abar so da koyi ga al'ummar mu, mussaman mata. Dan akwai sister na, die hard fan ɗin ki ce, ita ma lawyer ce. Cikin fusata Naja'atu ta ce "Ke saurara mana, daga ganina sai tsare ni ki hau zuba dan kina ƴar jarida, who permits you to do that?" Sumayya ta dake ta ce "No, barrister, ba as ƴar jarida ba kawai, as a woman and one of your fans, ko ƙorafi ne da ni, ta yaya zan same ki ki tsaya mini, atleast ko mintuna uku ki bani mana, dan Allah. Na san ƴan jarida wasu lokutan mu na da zaƙewa amma a duba roƙona" kamar ta zagi Sumayya, ta tsani baƙin naci irin na ƴan jarida, amma sanin halin su na yanzu sai su samu abun ɗorarwa ta ɓata mata career ya sanya ta danne ta ce "Ina jin ki" Fitowar honorable, ta sanya ta yin shiru, ya kalli sumayya ya ce "Mu je in da zaki ɗauki program ɗin" Tana ji tana gani, Naja'atu ta tafi. Can wani surƙuƙi ya ja ta, da sai da ta fara jin tsoro, sai dai duk in da suka ratsa, akwai ma'aikata. Sumayya ta sha mamakin, irin dukiyar da aka yi ɓarna, wurin gida wannan gida da kamar ba za a mutu a bar shi ba. Daga ita sai shi a ƙaton falon, mai ɗauke da ɓangarori daban-daban. Yayi mata iznin zama, yana ƙureta da idonsa, ta fito da kayan aikinta, ta fara saitawa, tana ta addu'a a zuciyarta, dan kaɗaicewar nan ta su kawai, hankalinta a tashe yake. Nabila kuwa, Walid sakata yayi a gaba, har suka zo ƙofar wani gida, a can bayan kamfanunukan nan, babu kowa a wurin, ba gida gaba babu a baya, sai ma wani uban dutse idan ka yi tafiya can gaban gidan, ba ta taɓa zaton akwai irin wannan wurin a kano ba. Ya kalleta ya ce ta shiga. Jikinta yana rawa ta ce ba zata shiga ba, sai dai ya kira wo mata shi nan waje, wanda har a lokacin idan ta ganshin, ba ta san me za ta ce masa ba, tsabar fitina ce da son ta ɗaukaka ko ta halin ƙaƙa ya sanya take wautar. Wani makami ya zare mata, mai kama da kibiya ya buga mata tsawa ya ce "Ki shiga na ce" sai a lokacin ta tabattar da ta tafka babban kuskure, haɗi da wauta mara amfani, idan suka illata ni fa?" Ta tambayi kanta cikin tashin hankali, haka ta shiga, yana bin ta da wuƙa. Ɗan mama yana ɗan matsakaicin tsakar gidan, yana wankin kayansu, jin kukan mace ya sanya shi ɗaga ido, cikin tsananin mamaki. Sai dai yayi wata irin zabura ya ja da baya, yana bin su da kallo. Yana cikin ɗaki a tsaye ƙyam, kamar an gina shi, ya bawa ƙofar baya, yana kallon bango. Ya sha ya bugu, amma bai samu yadda yake so ba, tunanin da yake son dainawa ya kasa, dan haka yana tsaye, yana ta nazarin abubuwa daban-daban a cikin ransa. Ɗan mama biyo su yayi, yana bin Nabila da kallo. Turus Nabila ta yi, duk da ba ta ga fuskarsa ba, amma yanayin suffar jikinsa, sai da ta ji tamkar ta zunduma ihu, kallo ɗaya zaka yi masa ka san madakin maza ne, ingarman namiji ne, da Allah ya yi shi da tsawo da kuma kakkauran jiki. Idonta ya sauka a kan miyagun makaman da suke ɗakin, kamar za aje yaƙin duniya, gefen katifar da take ɗakin kuma, sirinjai ne, da kwalaban allura a wurin, sai kuma satchets na magunguna da kwalabe da kwalayen sigari. Ban da warin sigari, da wani irin ƙauri da ba ta gama tantance ko na menene ba, babu abun da yake tashi. Tirƙashi! Ai ko lokacin da aka rufta ta, aka turata dabar madaki, ba ta ga abun da ya razanata ba, kamar yanzu ba, dan tarin ƴan dabar da ta tarar na su wasa ne, ba su firgita ta ba, tun da ta samu ƙwarin gwiwar yi musu magana. "Boss, ga ta na kawo maka ita, sai ka ji dalilin da ya sa take nemanka" Babban abun da ya ƙular da Viper, bai wuce watsi da umarninsa, da Walid yayi ba, tun da fari ya gargaɗe shi, a kan kawo masa wata mace, dan ba shi da alaƙa da su, amma ya yi burus da maganar sa. Kasancewar ya sha sai dai buguwar ta gagara yadda yake so, ya sanya ƙwayoyin suka taimaka wurin tunzura shi, ya waiwayo a fusace domin ya sauke wa Walid rashin mutunci. Sai dai gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa, adadin bugun zuciyar sa ya ƙaru da sauri da sauri, wani irin gumi ya fara tsatstsafowa ta kafafen gashin sa, jijiyoyin jikinsa suka kukkumbura. Shi dai ya san a farke yake, ba iya bacci yake mai nauyin da zai ɗauke shi, har ya sa shi mafarki yake, balle ya ce mafarki ne, kuma ya san a hayyacinsa yake, domin kuwa bai yi buguwar da hankalinsa zai gushe ba. Sai dai a zahiri, sam yanayin sa bai nuna irin halin da ya shiga ba, dan babu abun da ya canza a tattare da shi, ya zuba mata manya-manyan jajayen idanunsa. Tirƙashi! Jin ka ya fi ganinka! Nabila za ta iya cewa, tun da Allah ya sa ta buɗi ido a duniya, ba ta taɓa ganin mutum mai kwarjini da razanarwa kamarsa ba, kodayake ai ya wuce ta kira shi kwarjini, sai dai mai ban tsoro. Yadda ake faɗarsa a baki kawai, ta ɗauka wani ƙaramin alhaki ne kawai, sai dai yanzu ta tabattar da  ya wuce duk yadda ta yi tsammanin ganinsa sa. Ashe waɗanda take gani ƙaryar daba suke yi, ga ɗan daba na gaske yau ta gani,kamar ta fashe da kuka a cikin zuciyarta ta ce "Na shiga uku, wani tsautsayin ne ya kawo ni? Daga ni sai su idan suka kashe ni fa? Na san ko gawata ba za a gani ba, balle ayi mini salla, kamar yadda addini ya tanada" So take ta ɗaga ido ta kalle shi, amma abu ya gagara, saboda daga kallo ɗayan da ta yi masa, ba ta fatan sake yi masa na biyu, duk da zuciyarta na azalzalar ta, ta sake yin hakan, ba zata iya tantance abun da take gani a cikin idanuwanta ba, da kuma ma'anar irin kallon da yake yi mata ba. Ƙoƙarin sake satar kallonsa tayi, amma suka yi ido huɗu, tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa, saboda mummunar faɗuwar gaban da ta ziyarci zuciyarta, tabbas cikakken mashayi ne duba da yadda launin idanunsa suke, sai dai Allah ya yi shi da siffar girma da cikar zati, ya isa a kira shi da cikakken namiji. "Shi kuwa wannan meya haɗa shi da aikin daba, a irin ƙira da Allah ya yi masa, da aikin office ya dace, ko na tsaro, ya ɓata wayonsa, da ya ƙare a shaye-shaye da daba. Duk da ta sunkuyar da kanta, a tsakiyar ƙirjinta take jin kallon da yake yi mata. Walid ya zagaya saitin kunnensa ya ce "Ka ga abun da nake gaya maka?" Jinjina masa kai kawai yayi, taku ɗaya yayi, ba tare da Nabila ta ankara ba ya danƙi wuyanta. Ba wani riƙon kirki yayi mata ba, amma idanuwanta suka yo waje, jikinta ya hau kyarma, tamkar ana kaɗa mata gangi. Ta saka hannunta ta riƙe nasa, numfashinta na fita da sauri da sauri, cike da tsoro take ta gwagwarmayar ƙwatar numfashinta, saboda yadda take jin yana barazanar barin ƙirjinta. Ba ta ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da ta ji tsini a cikinta, ga wani irin azababben zafi da ya ratsa fatar cikinta. Ba ta san bata tsorata ba, sai da ya buɗe baki yayi magana. "Wacece ke? Me ki ke nema a wurina?!!" Numfashinsa ya sauka a fuskarta, warin sigari ya daki hancinta, jikinta ya hau tsuma. A rikice Walid ya ce "Boss zaka kashe ta fa, ka kalli abun da ka ke yi" Bai saurari walid ba, ya sake buga mata tsawa, tare da ƙara nutsa wuƙar da ya saita a cikinta. "Viper, jini ya fara zuba daga cikinta, ka dawo hayyacinka mana" yayi maganar yana ƙoƙarin kai hannu ya ƙwace wuƙar hannunsa. Idan ka taɓa ni, kai zan cakawa!" Yayi maganar yana kallon idon Nabila da suka yo waje, ga jikinta ya saki, sai numfashi da take yi da kyar. Buɗe baki tayi, da niyyar ta yi magana, amma jikinta ya saki, ta daina ganin komai sai duhu. "Viper kar ka kashe yarinyar nan" Amma kan walid ya yi wani yinƙuri, Viper ya watsar da ita a wurin, ta faɗi sumammiya. Ayshercool 08081012143                  *ƘARFE A WUTA* AISHA ADAM AYSHERCOOL Arewabooks : ayshercool7724 Watpad: ayshercool7724 What's app :08081012143 What's app channel https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g Paid book ne ₦500 via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda ba ss som group akwai special 1k. 13 Cike da takaici Walid ya nufeta da sauri, ya kalli Viper ya ce "Amma meyasa zaka yi haka? Da ka kasheta fa?" Aminu ya kalli saman tsinin wuƙarsa da take ɗauke da jinin Nabila, bai kalli Walid ba ya ce "Ban gaya maka kar ka kawo mini kowa ba?" Walid ya ce "Ka gaya mini, amma na tabatta ka ga abun da nake son ka gani, ai ko?" "And so, me hakan zai amafana mini? Ka ƙaddara ban ga komai ba, kuma gargaɗi na yi mata a kaina, dole na san tana da manufar son haɗuwa da ni, wataƙila wata ƙulalliyar ce, sai dai amafani da mace ba zai hana in illata ta ba, idan ta shiga gonata" Walid ya ce "Yanzu abun da ka gani, ba shi da muhimmanci kenan?" "Ko kaɗan" ya bashi amsa kai tsaye. Walid ya tsuguna a kanta, amma ya rasa abun da yakamata yayi. Wani irin numfashi Nabila ta fara fitarwa, mai sauti wanda hakan yake tabattar da, numfashin yana ba ta wahala. Ɗan mama ya ce "Mun shiga uku, wane irin numfashi ne wannan,ko mutuwa za ta yi ne?" Walid ya sake dirircewa ya rasa abun yi. Viper ya goge jinin Nabila da ke jikin wuƙarsa, a jikin rigarsa. Ya ɗaga kai, yana kallon yadda take jujjuya kanta, tana neman iska. Wata drower ya saka mukulli ya buɗe, ya ɗaukko wata ƴar ƙaramar akwati, ya ajiye, ya ƙarasa ya ɗauki jakar Nabila, ya zazzageta yana neman inhaler, amma bai gani ba, ya ja uban tsaki ya tashi, ya sake buɗe wardrobe, ya ɗaukko inhaler, sai dai sai da ya tsaya yayi ta kallon inhaler, yana kallon Nabila, sannan ya ƙarasa kanta, ya tsaya, ya ɗagota ya fesa mata a cikin bakinta. Kamar zata haɗiye inhaler, haka take sake buɗe bakinta, ya mayar da ita ya kwantar, ya ɗaga gefen rigarta, da wuƙarsa ta huda, ya saka auduga da spirit, ya goge jinin tsaf, ba wata huda ce ta kirki ba, kawai dai ta zubar da jini ne sosai. Gaba ɗaya suka zuba masa ido, ya zuba iodine a jikin audugar, ya saka a kan cikin nata, ya kawo plasta, ya saka. Dama ya saba yi musu dressing, idan suka je aka sare su, a wurin rashin jin su. Ya mayar da akwatin in da take, ya koma gefe ya kunna sigari. Mamaki yake da tunanin, uban me take nema a wurinsa, sai dai ya fi yarda da cewa, tarko ce ake son yi masa da ita. "Amma ya aka yi, aka samu wannan coincidence ɗin?" Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa. Duk suka koma gefe, suka zubawa sarautar Allah ido. Tari ta fara yi, ta yinƙura ta tashi zaune, ta kalli kayan cikin jakarta, da suke a watse, ta fara tattara abun ta, sai kuma ta dawo hayyacinta,bayan da suka yi ido huɗu da shi. A rikice tayi jifa da jakar, ta ƙwala wani uban ihu, nan take mafarkin da ta taɓa yi ya dawo mata, tabbas sai yanzu ta fuskanci inuwarsa take gani a mafarki. Ƙoƙarin tashi take ta gudu, cikin zafin nama, ya bar in da yake ya cafkota. Tausayinta ya kama Walid, tare da dana sanin kawo wa Viper ita, ko haɗa bakin aka yi da ita a cutar da shi, atleast ita macece ya ɗaga mata ƙafa, amma ya san in da ya matsa, sai Viper ya illata ta fiye da yanzu. "Waye ya aiko ki?" Yayi maganar a kausashe. Ta girgiza kai, amma ta kasa magana. "Waye ya turo ki na ce?" Yayi mata tsawa. A rikice ta ce "Wallahi ba kowa" tayi maganar tana zubar da hawayen tsoro. "Me ki ke nema a wurina?" "Dan Allah ka yi mini rai, na tuba na bi Allah, ba zan sake ba, dan Allah kar ka kasheni, wallahi ni marainiya ce, tayi maganar tana kawar da kanta gefe, ta kasa kallonsa, sai azabar bugu da zuciyar ta take yi, cikin tsoro da fargaba. "Look up kalleni" muryarsa ba a iya kunnuwanta take jin ta ba, a tsakiyar zuciyarta take yi mata amsa kuwwa, gashi ya matso daf da ita, warin sigarin da yake yi, ya fara hautsina mata ciki. "Kalleni" ya sake maimaitawa. Ɗan mama ya ce "Ki bi umarninsa, ba ya maimaita magana, kan ki farka a lahira". Cikin karkarwa, ta ɗaga kanta, da gefen idonta kawai ta kalleshi, amma ta fashe da kuka "Wallahi tsoronka nake ji, ba zan iya kallonka ba, idonka tsoro yake bani, dan Allah ka yi haƙuri kar...... Tsit tayi, ta haɗiye wani irin mugun yawu, da ta ji tamkar ta haɗiyi wuta, biyo bayan ganin ya saita  kaifin wuƙa a kwaroron maƙogwaronta. "Idan ki ka bari, na sake ganin fuskarki, ko a kan hanya, Wallahi sai na kashe ki!" Nabila ta gama saddaƙar da gumin da yake bin ƙafafuwanta, fitsari ne ba gumi ba, gashi tun daga goshinta, har cikin jikinta gumi ne kawai yake yanko mata ko ta ina. Ta jinjina masa kai, ya ja da baya, ya kalli Walid ya ce "Ta ƙara mintuna biyar a gabana, sai dai ka fita da gawarta" Walid ya kalleta ya ce "Zo in fitar da ke hanya" "To in ɗauki jakata?" Tayi maganar cikin tsoro. Walid ya ce "Hanzarta ki kwashe kayanki mu tafi" Sai dai ta kasa motsawar, ta ƙame a jikin bangon ɗakin, jikinta sai tsuma yake yi. A fusace Walid ya ce "Ki tattaro mu tafi mana" Nabila ta fashe da kuka, ta ce "Wallahi tsoro nake ji, kar in durƙusa ya kashe ni, dan Allah ka bashi haƙuri, kar mu haɗu a wani wurin ban sani ba ya kasheni, ya rantse sai ya kasheni". Walid ya ce "Na ji zan bashi, taho mu tafi" "Wallahi na kasa motsi" tayi maganar hawaye na cigaba da zuba daga idonta. Gaban wardrobe ya je ya tsaya, ya juya musu baya, ya saka hannayensa, ya kama ƙasan rigarsa zai cire ya canza wata, kamar wadda ya kwance daga ɗauri, dama idanunsa ne igiyoyin da suka ɗaureta, ta durƙusa ta kwashi kayan jakarta, da jakar ta fita da gudu, ta kwashi takalmanta, ta fyalla a guje, ta bar gidan. Dariya ɗan mama ya ƙyaleƙyale da ita, ya yi wata irin ashariya ya buga ƙafa, sannan ya je gaban Viper yayi wata irin kururwa, cikin sara masa tare da kambama shi ya ce  "Maza gumbar dutse, ina gwanin wani ga nawa, gaba salamun baya salamun mutumina, zaki ka ke sarki a gida sarki a dawa, ina mazan suke, ga fa uban ɗakina wanda ake kira namijin gaske. Sun buga da kai sun barka mutumina, Allah ya baka duniya lahirar ma ka samu in sha Allah. Mahadi mai dogon zamani. Kai idan ba namijin gaske ba, kalli yadda ka mayar da mai hankali zararre cikin ƙanƙanin lokaci, kalli yadda yarinyar nan ta firgice ta koma zararriya lokaci ɗaya, ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya tararka uban gidana, mahadinmu mai dogon zamani, Allah ya baka tsawon rai, ya kaimu ranar da zamu ba da jininmu domin ɗaukar maka fansa" Geɓare baki Viper yayi kamar zai yi murmushi, dan kirarin ya tuna masa wasu abubuwa da dama da suka shuɗe. Walid kuwa gaba ɗaya daga Viper har ɗan mama haushi suka bashi, kamar ya ɗura musu ashar, Nabila ko da cunen aka yi musu da iya, shi yaƙi ai ɗan zamba ne, kuma ko ba komai mace ce, bai kamata ya razanata har haka ba, tun da ya san mazan ma razana su yake yi. Takalmansa ya saka,  ya bi bayan Nabila, dan yadda ta fita a burkicen nan, komai zai iya faruwa, gashi ga dukkan alamu, ba ta da cikakkiyar lafiyar numfashi. Viper kuwa, rigar jikinsa ya canza, Ɗan mama ya ce "Boss, wai ka taɓa karatun likita ne? Na san dai ka iya wankin ciwo, to kuma na ga yau kayi aikin likita". Al'amin ya girgiza kai ya ce "Ko ɗaya, na zauna da mai irin ciwon ta ne" Ɗan mama ya ce "Na fahimta, amma dai ba fita zaka yi ba ko?" "Zaka hana ni ne?" Da sauri ya ce "A'a wane ni, ka san idan wannan jarababben ya dawo, ya tarar ka fita, masifa zai ta yi mini" bai saurari ɗin mama ba, ya bi ƙofa ya fita. Nabila kuwa tun da ta fita da gudu, ba ta tsaya a ko ina ba, sai da ta fita titi, shi ma babu ababen hawa, haka ta cigaba da tafiya tana waige-waige, sai a lokacin ta ji gefen cikinta, yana ta yi mata zugi, ta ɗaga rigarta ta ga plasta. Ga jikin rigarta da jini, a hankali ta furta "Na shiga uku" Addu'a ta din ga yi, tana cigaba da tafiya, cikin ikon Allah, Allah ya kawo mai a daidaita sahu, ta kama ta shiga, tana ta haki. Sumayya tamkar yau ta shiga harkar aikin jarida, haka tattaunawar ta su da honorable Indabo take kasancewa, saboda yadda ya tsatstsareta da manya-manyan jajayen idanunsa, yana yi mata wani irin kallo, gashi daga shi sai ita a wurin. Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Meyake damunki ne? Ki nutsu mana" Ta jinjina masa ta kai, ta cigaba da yi masa tambayoyin da su aka yarje mata ta yi masa. Sai dai ita kanta ta san amsoshin da yake bayarwa, na son zuciyarsa ne kawai, ba wani abu ba. Jin ta yi shiru, ya sanya ya kalleta ya ce "Ya dai?" Cikin girmamawa ta ce "Tambayoyin sun ƙare sir" "Kamar bakinki akwai magana, akwai tambayoyin da ki ke son yi mini ko? Mu je zuwa ina saurarenki" Ƙasan zuciyarta ta ce, ina ma da gaske ka ke, da ka ji ruwan tambayoyin da ko ka ƙi Allah, sai ka dangana da faɗar gaskiya, a zahiri kuwa ta girgiza kai ta ce "Babu sir" Ya kalli kofunan gabansu, ɗauke da shayi, wanda shi yana yi yana shan nasa, ita kuwa ko taɓawa ba ta yi ba. "Ya ba ki sha shayin ba? Ki sha mana" Sumayya ta sake risunar da kai ta ce "A ƙoshe nake ne" Ya ce "I see, amma na yi mamaki da ki ka ce mini baki da tambaya a gare ni, duk da yadda ki ka ƙaryata hirar da na yi kwanaki, ki ka ce ban yi ayyukan da na ce na yi ba, na ƙyale ki ne kawai saboda managernku yayi ta bani haƙuri, kuma ke mace ce yarinya ƙara ƴar cikina. Siyasa mu tamkar business take a wurinmu baby girl, we invest to make a profit, ita kanta gidan radiyon da ki ke aiki da su, nike hannun jari mafi tsoka a cikinta, dan haka abun da nake so shi ake yi, kuma domin yi mini campaign ya sanya na zuba kuɗina a harkar gidan radiyon" Sumayya dai ta yi shiru, ba ta ce komai ba. Ya miƙe tsam, ya zagaya ya zauna a kan kujerar da take kai, wanda hakan ya sanya ja da baya, tana maƙale jikinta. "Mun gama abun da ya kawo ki, sai kuma abun da ya sa na ce a turo mini ke" Da sauri ta ɗaga ido ta kalle shi, tana mamakin abun da ya faɗa. Ya ɗauki kofin shayinta ya sha, sannan ya ce "Yarinyar da na ganku tare, ranar da na yi zuwan ƙarshe, ita nake nema ba ke ba, amma ke ce tsanin da yakamata na taka na kai gare ta, wacece ita?" A tsorace take kallonsa, ya ce "Ki amsa mini mana". "Nabila ce, ƙawata ce, she's like a sister to me" ta faɗa a tsorace. "Ba wannan nake son ji ba" yayi maganar yana sunkuyowa daf da fuskarta. "Wacece ita?" Sumayya ta ce "Ƴar wani tsohon soja ce, dan Allah idan wani laifin tayi maka ka yi haƙuri, ba zata ƙara ba, idan ma dan ba ta gaisheka bane ranar, dan Allah ka yi haƙuri ba zata sake ba, ba ta da lafiya ne ranar" Ya girgiza kai ya ce "Ko ɗaya, tarko nake son na yi da ita, aiki za ta yi mini" Jiki na tsuma Sumayya ta ce "Wane irin aiki kuma?" Ya gyara zamansa ya ce "Kin san wani ɗan daba Aminu Viper?" "A'a ban san shi ba wallahi" Indabo ya ce "Kina ƴar jarida, ki ce mini ba ki san shi ba, jami'an tsaro na neman sa ruwa a jallo, na yi niyyar shafe tarihinsa, aka samu wani ya yi mini zagon ƙasa, ya rusa mini komai. Har a yanzu ana ta ƙoƙarin kama shi, kwatsam na ganku, kuma na ga tana da wani abu da zan iya yi masa tarko da shi ya zo hannuna, dan haka ƙawarki za ta yi mini aiki" Hankali tashe ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, mutumin da yake kashe mutane, tana mace ina ita ina ɗan daba, ba jami'an tsaro suna nemansa ba? Za su kama shi dan Allah ka ƙyale mu" Yayi wata muguwar dariya ya ce "Kin san waye indabo kuwa? Kama Aminu ya zama gawa ne kaɗai zai samar mini da nutsuwa da kwanciyar hankali, dan haka dole ƙawarki za ta yi mini aiki" Ta buɗe baki za ta yi magana, wayarta ta fara ringing, ta ɗauka ta duba, ta ga nabila ce take kiranta. Ya ƙureta da idonsa ya ce "Ɗaga mana, ɗaga wayarki" Jiki na rawa ta ɗaga, ta kara a kunnenta. "Sumayya kina ina ne?" Muryar Nabila ta fito raɗau a wayar. Sumayya ta ce "Ina nan ƙalau, lafiya kuwa? Na ji kamar kina numfashi da ƙyar, ciwon ne ya tashi" "Sumayya na kusa mutuwa yau" tayi maganar tana sauke numfashi. A rikice sumayya ta ce "Mutuwa kuma, lafiya" "Na haɗu da Viper, ya kusa kashe ni" Ras gaban sumayya ya faɗi, indabo ya ƙura mata ido, yayi mata alama ta cigaba da wayar. Jiki a sanyaye Sumayya ta ce "To maƙaryaciya, ni zaki jirga?" "Wallahi ba ƙarya nake yi ba, ya na ji muryarki kamar wadda aka ritsa, kin je hirar ne? Ko wani abun ya faru ne?" Sumayya ta ce "A'a, maƙaryaciya, mutumin da ake nema ruwa a jallo ki ka gani bai kashe ki ba?" "Ban sani ba, tun da kin ƙaryata ni ki je ki ƙarata, ina fatan dai mutumin nan bai yi miki wani abun ba, dan mutumin nan yayi ruwan ƴan iska" Kallonsa sumayya ta yi, sannan ta ce "Mu haɗu a gida" Nabila ta ce "Ai dole mu haɗu yau, akwai magana, zan biya asibiti numfashin zai ɗauke, ki kula da kanki dan Allah, jikina yana bani kamar akwai matsala a in da ki ke, idan da wani abu, ki sanar da ni" "Ke normal ne, sai mun haɗu" ta kashe wayar tare da kallon honorable Indabo ta ce "Wallahi ƙarya take yi, ba wani Viper da ta haɗu da shi, yayanta ne jami'in tsaron da yake bincikensa, amma wallahi ƙarya take yi" Cikin ko in kula, indabo yayi dariya ya ce  ce "Wato na yi zubin ƴan iska, wato a  rayuwata ni mutum ne mai sa'a, na tsinci dami a kala, yanzu ke zaki yi mini aikin ba ita ba. Dole ki tabattar idan da gaske take ko akasin haka ki sanar mini, duk wani aiki ko bayanai da nake son samu, ke zaki nemo shi a wurinta, idan ki ka saɓa umarnina kuma, zan saka a kawar mini da ke da ita baki ɗaya!" Sumayya gabanta ya faɗi, ta rasa abun yi, kamar ta kurma ihu, wannan wace irin ƙaddara ce, ace babban mutum kamar wannan da ake ji da shi a kujerun iko, na ƙasa da jihar nan, ya rasa wanda zai saka a gaba sai su ƴaƴan cikin sa. Ya ce "Buɗe wayarki ki bani" tamkar shashasha, haka ta cire password ta miƙa masa, yayi ƴan danne danne a jiki. Wani mutum ne yayi sallama, ya shigo, ya ce "Gani sir" "Wannan wayar zaka yi wa aiki" Ya ce "Ok sir" ya karɓi wayar yana daddanawa, sannan ya miƙowa Indabo. Ya ce masa "You can leave" Ya miƙa wa Sumayya wayar ya ce "Daga yanzu za ki din ga karɓar umarnin, abun da ake buƙatar ki yi, idan ki ka saɓa umarnin, zaki yi dana sani mara amfani, dan sai na fara da wulaƙanta rayuwarki, na tozarta ki, kodayeke dama wulaƙantacciyar ce. Dan ku ƴaƴan talakawa baku da wani amfani, kuma babu wani abu da zai faru idan na salwantar da rayuwarki, da kuma ta ta". Sumayya ta sunkuyar da kanta ƙasa, ƙirjinta na cigaba da bugawa. "Tashi ki je sakatariyata zata sallame ki" Sumayya ta tashi jiki babu ƙwari, ta bar ɗakin, tana tunanin wace masifar suke shirin shiga ita da Nabila. Allah wadaran bakin Nabila da bashi da saiti wasu lokutan. Shi kuma yana babban mutum, menene alaƙarsa da wani Viper, wai shi waye ma wannan vipern, da ya fi kuɗi wahalar samu? Tana fita sakatariyar ta miƙe tana murmushi ta ce "Har kun gama?" Sumayya ta ce "Eh" Ta miƙa mata envelope ta ce "Ga wannan ya ce "A baki" Sumayya ta karɓa ta duba, kuɗi ne maƙudai a ciki, gabanta ya faɗi, tabbas idan ta karɓi kuɗin nan, ta tabatta sai ta din ga bin umarninsa, gashi ba ta san wane irin umarni za a bata ba. Ajiye envelope ɗin ta yi ta ce "Ba na so" Ta nufi hanyar fita, tana tuna yadda ya kirata da wulaƙantacciya. Tana gaggawa ta kai ga ƙofar da zata fitar da ita waje, mutumin da ya karɓi wayarta ɗazu, ya sha gabanta, wanda hakan ya tilasta mata tsayawa. Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Kamar yadda honorable ya gaya miki, ke zaki yi mana aiki a zahiri, bama buƙatar ta san kina yi mana aiki, dan haka ko kin karɓi kuɗi, ko baki karɓa ba, baki da zaɓi dole sai kin yi komai kasadarsa, ko da kuwa yana nufin sanya rayuwar ƙawarki a siraɗin rasa ranta, zamu yi amfani da ita, idan kuma kin zaɓeta zaki iya rasa taki rayuwar" Cikin matsananciyar damuwa Sumayya ta ce "Muna mata, menene alaƙarmu da ƴan daba, wannan ba aikin hukuma bane ba?" Yayi murmushi ya ce "Shi zaki gayawa hakan ai tun a ciki, idan kuma zaki kai wa hukumar ne, ga fili ga mai doki" Wani abu mai ɗaci, ya tokarewa sumayya a ƙirji. Cikin ɓacin rai ta ce "Amma dai ba ku yi mana adalci ba, wannan tamkar rusa mana rayuwa ne, tayaya muna ƴaƴa mata zaku yi tarkon kama mutum mai irin wannan hatsarin da mu" "Ai ba ke aka ce ba, ƙawarki aka ce, dan haka ina kina son lafiyarki, da mutuncinki, kiyi abun da aka umarce ki, ita ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake ba. Ki yi ta kanki kawai, idan har ki ka yi abun da aka buƙata, babu wata alfarma da zaki nema a ƙasar nan ki kasa samu, zaki zama ɗaya daga cikin yaran honorable, za ki yi kuɗi, zaki ɗaukaka za kuma ki shahara, ki nutsu ki yi tunani da kyau, kar ki yi wawanci, ki je aikinki ya fara daga yanzu" Shiru ta yi tana kallonsa, har ya gama maganganun da zai yi, sai dai gaba ɗaya ta rasa wani tunani ma yakamata ta yi. Ba ga ce uffan ba, ta raɓa shi ta buɗe ƙofar ta fice. A cikin mota, direban gidan radiyon, da wanda suka rakota suke tambayarta, yaya program ɗin ya kasance?. Cike da basarwa ta ce musu lafiya ƙalau. Kafin su ƙarasa gidan radiyon, ta ce su sauketa, tana da uzuri, dan haka ta sauka, ta kira Nabila a waya. Tana kira Nabila ta ɗaga, "Yaya kina ina ne? Kina asibitin ko kin tafi gida?" Nabila ta ce "Ina can, wai sai bayan 2-5hrs za su sallame ni, idan na zama stable, haryanzu numfashi yana bani wahala" "Ok to gani nan zuwa" "To masoyiyya Allah ya kawo ki lafiya" Sumayya ta sauke wayar, kamar ta fashe da kuka, duk yadda take da Nabila, ace ta ha'inceta, ta saka rayuwarta a hatsari, anya amana ta ce haka kuwa?. A haka ta ƙarasa Asibitin, ta tambayi ɗakin da Nabilan take, aka nuna mata. Nabila na ganinta ta ce "Oyoyo sumyna" Sumayya tayi murmushin yaƙe ta ce "Ya jikin?" "Alhamdilillah da sauƙi" "Baki kira kowa a gida ba, na ganki ke kaɗai?" Nabila ta ce "Rabu da ni, ba wanda na kira, ƙarshe dai walida ko baba magajiya ne za su zo, dama da DSP yana gari ne, to shi ma wai ya tafi workshop ko me oho dai, Abuja ya tafi, dama da zai zo, to sai anty, ni kuma bana son takura musu, sai dai ba yadda na iya, na gaya wa Abba, kar su ji ni shiru. Amma ya na ga kamar kin yi kuka? yaya program ɗin?" Sumayya ta ce "Wani irin kuka ana zaune ƙalau, program lafiya ƙalau, ga recording ɗin ma ban kai ba, na ce bari na zo na  fara ganinki tukuna". Nabila ta haɗe fuska ta ce "Ki gaya mini idan wani abun yayi miki, mu san abun yi, na gaya miki ni gaba ɗaya mutumin nan bai yi mini ba, dai-dai nake da shi idan wani abun yayi miki, in yi fito na fito da shi, sai in da ƙarfina ya ƙare." Sumayya  ta haɗe rai ta ce "Ke da ya yi mini wani abu kya gannin a haka, ba wannan ba, maganar da ki ka gaya mini a waya, da gaske ki ke ko kuwa?" Nabila ta yi murmushi ta ce "Baki yadda ba ko?" "Yaya za ayi na yadda, mutumin da ake ta fafatukar yaya za a kama shi, ki ce mini kin haɗu da shi, kawai in yadda ta yaya?" Nabila ta kaɗa kai ta ce "Kusan watana guda zuwa na biyu ma,  kawai ina fafutukar yaya zan ganshi, na san dama zaki ƙaryata ni, ban gaya miki ba ma balle ki hana ni ko ki yi mini masifa. Amma cikin ikon Allah, viper ya bar mini shaidar da zai tabattar da  ya ganni" Cikin rashin fahimta, sumayya ta ce "Kamar yaya?" Nabila ta ɗaga rigarta, sai ga plasta a gefen cikinta, ta saka hannu ta cire plastan, sai ga rauni a wurin. Sumayya ta waro ido, tare da rufe baki, ta ce "Na shiga uku, Nabila kin haukace ne? Wai dama da gaske ki ke?" Ta saki rigar ta ce "Ai kafin yayi mini haka, rannan karnuka sun kusa yin watanda ta. Sunayya gayen nan ya wuce duk yadda nake tunani, ashe faɗar sunansa ne a baki kawai mai sauƙi, wallahi idanunsa sun kusa sakani fitsari a wando, sumayya yaya zan kwatanta miki yadda yake ne ki gane abun da na gani? Kwarjininsa ya wuce duk yadda zan kwatanta miki, wallahi da ya shaƙe ni, na ɗauka mutuwa na yi" "Har shaƙe ki yayi, kin ga Nabila ki rufa mana asiri, amma yaya aka yi ki ka samu in da yake?" "Na gaya miki kusan watanni biyu kenan ina nemansa, na san idan na gaya miki, hana ni zaki yi, duk ba wannan ne ya dame ni ba, yayi alwashin idan ya sake ganin fuskata, sai ya kashe ni, kuma mummunar kasada na kuma tafkawa Sumayya". "Ta me kuma?! "Wayarsa na sato, kan na taho!". Alhamdilillah, duka duka a nan mu ka kawo ƙarshen free pages, mu kasance a cikin paid pages, domin jin ainihin gundarin labarin *ƘARFE A WUTA*. ₦500 ne kacal ta wannan account ɗin, masu so ta private special group 1k zasu saka a wannan account ɗin. 0009450228 Aisha Adam jaiz bank Ayshercool. 08081012143 🔞 *PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143* *Ina masu buƙatar sayen nagartattun kayan magungunan mata, wanda babu cuta ko algus a ciki, ku yi joining link ɗin nan, domin samun nagartattun magungunan mata* https://chat.whatsapp.com/BLqFsnlyNf0B483RhoWq8v Tsoro Nabila ta fara ba wa Sumayya, "Are you serious? Nabila da ya kashe ki fa, ko kuma idan ya biyo ki fa? Meyasa ba kya tausayawa rayuwarki ne?" "Wallahi nima na yi tunanin hakan, amma ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, ai bai san in da nake ba, yadda zan ba wa DSP wayar nake tunani, ba tare da ya yi mini faɗa a kan dalilin da ya sa na yi ba, ko tuhumata" Ta ciro ƙaramar waya mai madannai, ta miƙawa sumayya, sumayya ta karɓa tana salallami, da sarawa sheɗancin Nabila. Nabila ta ce "Wayar babu caji, sai na je gida zan sakata a caji" tayi maganar tana karɓar wayar, ta sakata a aljihun ƙaramin wandonta na ciki. Ta sauka daga kan gadon, ta ce "Bari na shiga banɗaki na fito, na baki labari" ta sauka ta shiga banɗakin da yake cikin ɗakin. Sumayya tayi ƙuri da ido tana kallon ƙofar da Nabila ta shiga, tana tunanin yadda abubuwa masu karo da juna suka sakata a tsakiya. Wayarta ce ta fara ringing a cikin jakarta, ta ɗaukko taga baƙuwar lamba, ta ɗaga tayi sallama. Muryar namiji ce ya ce "Ya ku ka yi da ita?" Sumayya ta ce "Ita wa?" "Wurin wa ki ka je?" Aka tambayeta. Ta basar ta ce "Wa ke magana?" "Ya zama dole fa ki yi aikin da aka saka ki, ko kina so ko ba kya so, a in da taken nan idan aka so za a iya kasheta, ko a saceta ayi abun da ake so ta yi, yin abun da aka saka ki ne kawai zai tseratar da rayuwar ta. Ta haɗu da shi ko kuwa?" ta sunkuyar da kai ta ce "Wai dan Allah a tunaninka, tayaya mutumin da ƴan sanda ba su kama ba, ita ta haɗu da shi? Ƙarya kawai take yi dan ta raina mini hankali, Nabila tana da yawan wasa wasu lokutan, amma ƙarya take yi" Nabila ce ta fito daga banɗaki, ta ce "Da wani garan ake waya? Ko kin yi sabon kamu ne?" Sumayya ta katse wayar ta ce "Ba wani sabon kamu" "Sumy, ciwon nan na cikina ne yake yi mini zafi fa" Sumayya ta ce "Ai Allah ya ƙara, ni dama shegen duka ya yi miki, ya kakarya ki " "Ta Allah ba taki ba muguwa, wallahi sumayya da dukana yayi, zai iya kashe ni, kin ga ƙirarsa kuwa, kin ga tsawonsa?. Kin ga a yadda ya din ga kallona, na kasa gane wane irin kallo yake yi mini" Ta kashingiɗe kanta tana gwadawa Sumayya irin kallon da yake yi mata. "Wallahi sumayya ban taɓa ganin ido mai ban tsoron nasa ba, kin ji muryarsa, daga cikin ƙirjinsa yake fitar da ita, abun tsoro, ya ci sunansa viper". Wayar sumayya ta fara vibrating, ta tashi tsaye ta ce "Ina zuwa" Ta fita waje ta ɗaga wayar ta ce "Ya aka yi kuma?" "Idan har ba ta haɗu da shi ba, meye dalilinta na gaya miki ta haɗu da shi?" Kamar sumayya za ta yi kuka ta ce "Yayanta ɗan sanda ne, na gaya muku, a bakinsa da kafafen watsa labarai kawai take jin sunansa" katse wayar aka yi, ba tare da an sake ce mata komai ba. Ta koma ɗakin da Nabila take, sai dai abun mamaki taga Nabilan kamar matacciya. Da sauri ta ƙarasa ta taɓa ta, ta ga bacci kawai take yi, daga fitarta zuwa yanzu bai ci ace har ta yi wannan baccin ba. Message aka turo mata "Idan ki ka bamu bayanin da yake saɓanin gaskiya, abun zai wuce haka, ya zama dole ki bi duk wani umarni da zamu baki, muna bibiyarku daga ke har ita" Sumayya ta ajiye wayar, ta dafe kanta tana salati. Tsaye yake ƙyam a kan ƙololuwar dutsen, yana kallon yadda rana ta doshi faɗuwa, gari ya fara duhu sosai, a hankali ya ɗago hannunsa, ya kalli inhaler da take hannunsa, seretide inhaler ya din ga jujjuyata, yana sauke ajiyar zuciya. "Boss" ya ji muryar Walid a bayansa. Ya zagaya gabansa ya ce "Ka saukko haka dan Allah, magana nake son mu yi" "Bana buƙata kowace iri ce" "Na san na yi maka laifi, amma ka yi haƙuri, zan nemota duk in da take, kuma zan dawo maka da wayarka ina mai baka haƙuri" Ko motsawa bai yi ba, balle walid ya saka ran zai yi magana, daga bisani ya goya hannayensa a bayansa, ya cigaba da kallon rana. "Amma me ka ke tunani game da yarinyar nan? Anya babu wani abu a ƙasa da yakamata mu sani?" A hankali ya juyo, ya dafa kafaɗar Walid, ya matsa da ƙarfi ya ce "Hakan bai dame ni ba, koma wacece, Ma'aruf , madaki, da kuma wannan yarinyar da ka kawo, sai na tabattar da na kashe su gaba ɗaya, ko ta halin ƙaƙa". "A'a master, mace ce, wataƙila sakata aka yi, dan Allah ka yi haƙuri, zan yi maka bincike a kanta " "Idan ka kuma gaya mini wannan sunan, zan hankaɗaka daga kan dutsen nan" Walid ya yi murmushi ya ce "Baka girmama sunan ne viper, idan har ka damu har haka, yakamata ka bawa kanka da lafiyarka kulawa, ta haka ne zaka yi abun da ka ke so, yanzu ka taimaka ka sakar mini kafaɗata, wallahi kamar na karye" Ƙurawa walid ido yayi, Walid ya sunkuyar da kansa, ya san ya tunzuro zuciyar Viper, sakar masa kafaɗarsa ya wuce shi, ya fara sauka daga kan dutsen. Har bayan azahar Nabila ba ta farka ba, su kansu ma'aikatan asibitin, sun yi mamakin irin baccin da Nabila take yi. Hankalin sumayya kuwa yayi mummunan tashi, ganin Nabila ba ta farka ba. Bayan la'asar sai ga Abba, tare da Salim, wanda ƙani ne ga Nasir. A ɗakin da Nabila take suka tarar da Sumayya. Sumayya ta gaishe su, Abba ya amsa ya ce "Sumayya ke ce a wurinta?" Ta jinjina kai ta ce "Eh Abba" "Ai ni ce mini tayi, ba wani abun damuwa bane, ana gama yi mata abun da za ayi mata, za ta koma gida, sai da na koma na tarar ba ta dawo ba" Sumayya ta ce "Eh, ai ta samu bacci ma". Idonsa ya sauka a kan gefen rigarta, da take a huje ga jini, cikin mamaki ya ce "Ya nake ganin jini a jikinta?" Da sauri Sumayya ta ce "amm, dama wai faɗuwa suka a adaidaita sahu, shi ne ta ji rauni" "Amma ni bata gaya mini haka ba ai" yayi maganar cikin matsananciyar damuwa. Wata irin miƙa Nabila ta yi, tare da yin salati, duk suka yi kanta suna yi mata sannu. Suka din ga jera mata sannu, suna yi mata ya jiki. Sumayya ta kirawo likkta, ya zo ya ƙara duba Nabila, yayi rubuce-rubuce a file ɗin ta, ya sallame ta. Abba ya din ga yi mata faɗan meyasa ba ta gaya masa ta faɗi a adaidaita sahu ba, ta nunawa likitoci ciwon da ta ji. Sumayya ta kalleta, suka haɗa ido, sai ta fahimta, dan haka ta ce "Ai ba wani ciwo bane Abba, mu tafi gida na gaji". "Kin tabattar babu wani abu da yake yi miki ciwo?" Ta jinjina kai alamar eh, suka fito zuwa motar Abba, suka tafi tare da sumayya, su ajiyeta a gida. Sumayya ta kalli Nabila ta ce "Wai ya aka yi ɗazu daga fita ta, ki ka fara bacci, kusan awa huɗu ki na bacci?" Nabila ta ɗan yi shiru tana tunani, ta ce "Wani likita ne ya shigo yayi mini allura" "Ba Nurse ba, likita da kansa?" Nabila ta jinjina kai alamar eh, Sumayya ta yi shiru ba ta ce komai ba, a zuciyarta, take jinjina tsagwaron rashin imanin honorable Indabo, kenan idan ba ta yi abun da suke so ba, za su kashe Nabila kenan. Gabanta ya faɗi, ta kalli Nabila da ta kashingiɗa, tana ta lumshe ido, alamar baccin bai isheta ba. Tunani take da wa zata tattauna wannan maganar ne? ko wurin hukuma ta kai, ba ta da shaida ta zahiri, kuma ta san babu wani mataki da za a iya ɗauka a kai. *** Yana kwance a kan gadonsa yana kaɗa ƙafa, hannunsa ɗaya yana riƙe da waya, ɗaya kuma kan shisha, yana ta fesar da hayaƙi. "Hello" sautin muryar mace ya fito daga cikin wayar. Ya ce "Hello, how far?" Ta amsa da "Ya aka yi?" "Mun yi magana da tsoho, ashe kin gano in da yarinyar nan take?" "Eh, na gano, sai dai sun ce ba za su karɓi kuɗi ba, hakkinsu suke nema, dan haka sai ka san yadda zaka yi" Yayi murmushi ya ce "Ki san yadda za ki yi dai, ai kin san dolenki ki ɓoye laifin nan ma, kamar yadda ki ka saba". Cikin takaici ta ce "Ka ce dole?" "Ƙwarai dole, idan asirinmu ya tonu ai kema naki ya tonu, yanzu wane matakin ki ka ɗauka?". Tayi ajiyar zuciya ta ce "Yadda na lura, takamaimai, ba su san waye kai ba, daga ita bar babarta, dan haka zan je gidan ita Antyn taka, a bamu adress ɗin maigadin da suka kaita Asibiti lokacin da abun ya faru, duk da Yallaɓai ya gaya mini, an sallame shi daga aiki, amma dole za mu yi framing ɗin sa da laifin, in case wani zai tayar da maganar, sai mu ce mai laifin ya shiga hannu, abun da nake ƙoƙarin yi kenan" Ya kwashe da wata irin dariya ya ce "Daɗi na da ke akwai brain, anyway ina ne gidan su yarinyar, she needs to learn a lesson, da ita da babarta da ɗan jaridar da ya saka zancen". Da sauri ta ce "Kar ka kuskura, ba zaka ɓata mini aiki ba, na gaya maka ba su san kai waye ba, idan kuma ka yi wani yinƙuri, da ya samar da wata ɓaraka babu ruwana a ciki na gaya maka" Abdul ya ce "Na ji, ina son ganin yarinyar ne kawai" "Abdul, ina da abubuwan yi da yawa a gabana" "Naja'atu, kar ki katse mini waya, ki bani adress ɗin yarinyar". Kashe wayar ta yi, tare da jan tsaki, ta cigaba da rubuce-rubucenta. Nabila sai wajen sha ɗaya saura na dare, sannan ta ɗan dawo dai-dai, sai a lokacin ta samu ta yi wanka, a cikin ɗakinta ta tsaya tana kallon cikinta, da ciwonta, da haryanzu yake yi mata zafi. A haka ta lallaɓa, tayi shafe-shafen skin routine ɗin ta, ta fita kitchen ta haɗo tea, ta dafa indomie, ta koma ɗakinta, ta saka wayar Viper a caji. Ta ɗauki wayarta ta tarar da tarin missed calls ɗin Nasir, ta kira shi ta saka wayar a hansfree, tare da kashingiɗa. Ya ɗaga tare da yin sallama, ta amsa masa a hankali. "Arfa ko ki neme ni, ki ji ya na sauka ko?" A shagwaɓe ta ce "Am sorry, i got a little accident ne, a asibiti na wuni" A ɗan rikice ya ce "Subhanallah, garin yaya meyafaru?" "Don't mind, akwai labari ne" "Wane irin labari? Amma dai kina lafiya ko?" Tayi murmushi ta ce "Gashi muna magana da kai, lafiya ƙalau nake, ka ce Viper daga prison aka sake shi ko? Laifin me yayi aka kama shi?" Nasir ya ce "Ohhh my God, meyasa ki ka damu da lamarin nan ne har haka Arfa?" "Ni ka amsa mini Please" Ya ce "Yeah, amma ya shiga prsion, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, shigarsa na ƙarshe ne, ya ɗan daɗe, kuma da alama laifin da ya yi babba ne, sai dai ba wannan ne a gabana ba, kama shi nake son yi. Akwai jami'anmu suna yawo a farin kaya, suna neman bayanai a kansa" "Ka daina wahalar da kanka, na samo maka abubuwan da za su sauƙaƙa maka komai" Ƙasa-ƙasa yayi da murya ya ce "What do you mean? Ba na son wasa fa". Ɗan shiru ta yi, ta tabattar idan ta gaya masa gaskiya a yanzu, ba gwaninta za ta yi masa ba, dan muddin ta gaya masa ta san in da yake, zai ce ta je wurin ƴan daba, zaneta zai yi, kuma sai ya gaya wa Abba ta shiga uku. Dan haka ta ce "Da gaske nake, na je wurin wata client ɗin mu, a unguwar da yake, na samo labari, yana da yaransa da suke ƙananan dilallan tabar wiwi, amma ba su san in da yake ba, wai akwai wani guda ɗaya a tal'udu, yana sayar da katin waya bayan magariba, amma ƙwayoyi yake sayarwa, ya san in da yake". Ya ce "Look arfa, ba na son wasa, daga zuwa unguwar wurin client, har ki ka samu wannan rahotannin?" "Haba DSP, kar ka manta ni ma fa ma'aikaciya ce, wallahi ba ƙarya nake yi ba, daga majiya mai ƙarfi na ji labarin, na je wurin kuma na ga mutumin yana zaman sayar da katin wayar, idan baka yarda ba, idan ka dawo da kanka ka bincika" Yayi ajiyar zuciya ya ce "No, ba sai na dawo ba, zan aika a bincika mini, ina fatan baki gaya wa kowa ba?" "No, babu wanda na gayawa" Nasir ya ce "Good, amma kar ki kuskura ki yi wani abu, da zaki saka kanki a cikin hatsari kin ji ko?" Nabila ta ce "To, idan ka dawo zan baka wani abu mai muhimmancin da zai taimaka maka, amma sai idan zaka yi mini alƙawarin ba zaka dake ni ba, ko ka yi mini faɗa" tayi maganar tana kallon wayar Viper. "Menene abun?" "Sai ka dawo tukuna zan gaya maka, take care" "Shikenan, Allah ya kaimu na dawo ɗin, ki kwanta ki huta" "Ok bye-bye" ta kashe wayar ta ajiye, ta ɗauki ta Viper, da ta yi caji, ta kunna ta. Ta kai wayar hancinta ta sinsuna, ga warin sigari tana yi, ga ƙamshin turare. Ta fara shige-shige a wayar. Cikin call log ɗin sa ta duba, ga lambobi nan, sai dai duk kiransa ake yi ba ya kira, sai jerin private number da ake kiransa da ita. Ta duba cikin messages ɗin sa, babu komai a ciki, sai dai a cikin drafts ɗin sa, yayi saving ɗin wasu kwanakin wata. Tayi shiru tana tunanin yadda ta ɗaukko wayar ta sa, lokacin da take tattare kayan jakarta, da ta buɗe idonta ta gansu a tarwatse, ta ga wayar a gefe, ta haɗa da ita tana sane. Tayi ajiyar zuciya ta ce "Wani laifi ka yi aka kama ka, sannan aka sake ka, ba bisa ƙa'ida ba? Shi yafi cancanta ma in mayar da hankali in binciko, yadda ana kama ka, zan yi raising case ɗin nima, a hukunta waɗanda suka sake ka" tayi maganar tana sake mayar da wayar ta sa caji. "Ko ban ce na san in da ka ke ba, wayarka zata bawa jami'an tsaron damar nuna in da ka ke". Ta mayar da kwanukan kitchen, ta dawo ɗakin ta rufe ƙofarta ta kashe fitila za ta kwanta, sai dai tana kashe fitilar, sai ta ga kamar Viper ne a tsaye a gabanta, saura ƙiris ta kurma ihu, ta kunna fitilar tana zazzare ido, tana cigaba da ƙarewa ɗakin kallo, zuciyarta na saƙa mata ko ya biyo ta. Da ƙyar ta nufi gadonta ta kwanta, gabanta na faɗuwa, ba tare da ta kashe fitilar ba. Zumbur ta kuma tashi zaune, ta ɗauki wayar ta sa, ta sakata a cikin wardrobe ɗin ta, ta rufe ta ta dawo ta kwanta tana rarraba ido. Sai dai fa fafur ta kasa bacci, tsoro ya baibayeta, mussaman idan ta tuna ya ce idan suka sake haɗuwa sai ya kashe ta, sai yanzu ma ta fara tunanin da yaya zata miƙa wayar nan ga DSP Nasir, dan dolen dole sai ya tuhume ta, to idan ya tuhume ta wace amsar za ta bashi? Yaya aka yi wayar ɗan daba ta zo wurinta?. Sai kuma ta koma tunanin, yaya iyayensa suke ji, sun haifi ɗa ya zame wa mutane masifa a gari?. Tsananin zurfin da tayi a cikin tunani, ya sanya, wani ɓarawon bacci, ya yi awon gaba da ita, sai dai baccin bai je ko ina ba, ta din ga jin numfashi a fuskarta. A hankali ta buɗe idanunta, jin saukar numfashi a fuskarta, sai dai me, tayi tozali da fuskar Viper, ya kafeta da manyan idanunsa da suka yi jawur, dogon karan hancinsa yana taɓa nata, ko ƙiftawa ba ya yi. A firgice ta yi ihu, ta faɗo daga kan gadon, jikinta na wata irin kyarma, tana jejjera numfashi, sai dai ta buge wurin ciwonta, dan har ya fara zubar da jini. Sai da ta ɗago ta sake kallon gadon, sannan ta ga ashe filo ne yake taɓa mata hanci, sai ta ga kamar Viper. Ta rintse idanunta tana addu'a, tare da dafe gefen cikinta da yake ta yi mata zafi. Ɓangaren sumayya ma hakan take, dan kasa bacci tayi, dan ita kwanciyar ma gagararta ta yi, tayi dana sanin sha'awar fara aikin jarida, wace irin masifa ce haka tana zaman zamanta, ana neman mayar da ita ƴar ta'adda, saboda an fi ƙarfin ta. Alwala ta yi, ta tayar da salla, ta din ga addu'a, tana fatan Ubangiji Allah ya tsare su daga sharrin honorable Indabo, mussaman Nabila da ba ta san wainar da ake toyawa ba, gashi a yau kawai an yi wasa da rayuwarta, ba tare da ta san hakan ba, nan gaba ba ta san me za su yi mata ba, kuma ta san muddin ta gaya wa Nabila, akwai ƙura dan za ta iya aikata abun da zai sanadin su rasa rayuwarsu gaba ɗaya. Sai dai tana ta tunanin wace hanya Nabila ta bi ta ga Viper, tun da ta ce sun haɗu to lallai sun haɗu ɗin, hatsabibancin Nabila da taurin kanta, har tsoro yake ba ta. Tun da ta ƙududi aniyar yin sunan nan, idan ba wuƙa ta gani a maƙogwaronta ba, babu lallai ta haƙura. Honorable Ma'aruf ne a tsaye yana ta zazzagawa Abdul masifa kamar zai ari baki, shi kuma sai cika yake yana batsewa yana harare-harare. "Na fara gajiya da rashin mutuncinka Abdul, na gaji, gashi a banza ka nemo magana a wurin ƴar matsiyata, sun ƙi yadda a haɗa kai da su, a binne taiyar da ka shuka, dole sai na ɗau mataki a kai. In the next couple of years, kai zaka tsaya takarar deputy governor a garin nan, kamar yadda muka yi yarjejeniya da party, kafin na shiga, amma sai shashanci ka ke yi, so ka ke yi sai lokacin ya yi ƴan adawa, su ɓata mana shiri, na gaji da zubar da jini, saboda rashin hankalinka da wautarka, na ce ka yi aure ka ƙi, daga shaye-shaye sai neman mata, idan ma zaka yi yakamata ka san abun da ka ke ciki" Abdul ya numfasa ya ce "Ka yi haƙuri, ni yakamata na goge wannan ɓarnar da kaina, ka karɓar mini address ɗin yarinyar, zan san abun yi" "A baka ka je ka kuma yi wa mutane wani shirmen ko?" Ya girgiza kai ya ce "No, na yi maka alƙawarin ba wani shirmen zan yi ba, zan goge komai ne kawai" "Ɓace ka bani wuri" yayi maganar yana hakin baloƙoƙon da ya yi. Nabila fa abu ya zame mata ga ƙoshi, ga kuma kwanan yunwa, wayar Viper ta zame mata larura, ta rasa yadda za ta yi. Da safe Abba ya ce ta zauna a gida ta huta, saboda jikinta, amma ta ce masa ita ta ji sauƙi, fita za ta yi, da kansa ya ɗauke ta a mota, ya tafi kaita wurin aikin, suna tafe yana yi mata nasihohin da ya saba yi mata, amma da za a yankata, ba zata iya faɗar me yake cewa ba. A gate suka haɗu da Director, yana ganin major kamar zai dungura, saboda risunawa cikin girmamawa, ya gaida major. Ya amsa masa cikin girmamawa yana tambayarsa aiki. Director ya amsa da "Aiki Alhamdilillah, yau kuma da kanka ka kawo ta?" Major ya ce "To ya na iya, ƴar gudaliyata babu lafiya, kuma ta dage sai ta fito aiki. Ina fatan dai yanzu tana mayar da ka?" Director yayi murmushi ya ce "Alhamdilillah, ta rage shiririta, tana aiki sosai ranar Alhamis ma za ta fita trial ita ce incharge of case ɗin" Major ya ce "Masha Allah, idan ki ka yi wining, akwai special gift" Tayi murmushi kawai ta sauka daga motar, dan ba wani ganewa take yi ba. A wurin aikin ma, jin ta ta din ga yi tamkar wadda ta shekara tana amai da gudawa, gaba ɗaya gaɓoɓinta a sage suke, da ta motsa, sai ta ga kamar za ta ga Viper a gabanta. Layin Nasir ta kira, tayi sa'a ya ɗaga ya ce "Ya aka yi kuma?" "Ka aika a bincika maka maganar mutumin nan ne?" "Ki kwantar da hankalinki mana, ina sane zan aika". "Ai kar ka zo ka ce ƙarya nake yi ne" "Haba dai ni na isa ma" "Yaya" Ya amsa da "Na'am barrister Nabila maitama". "Wane laifi Viper yayi na ƙarshe ne, aka rufe shi?" "Ban gani ba a cikin record ɗin sa, waɗanda na gani dai, kawai rigima ce da mutane, da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi da kuma dillancin su". "Wace kotu da wace kotu aka taɓa kai shi?". "Arfa ban sani ba wallahi, wai menene akwai matsala ne?" Ta kashingiɗa ta ce "No, babu wani abu sai anjima" Ta kashe wayar ta ajiye, ta tashi ta tafi office ɗin Barrister Habib. Bayan ta yi sallama, ya amsa mata, yana ƙura mata ido, har ta ƙarasa ta zauna. Kai tsaye ya ce "Menene matsalar?" Ta ce "Na yi kama da mai matsala ne?" "Eh mana, yau ba kwalliya, ba ƙwalisa ba biscuit, ba sweet a hannu, duk yau dai sai a hankali" Tayi murmushi ta ce "Barrister ka bani dariya, saka mini ido ka ke yi kenan, ka san jiya a asibiti na wuni, shiyasa ban zo ba jiya" "Eyya, ai na zata mulkin ne ya motsa, ki ka ƙi zuwa, tun da ke ba tuhumarki ake yi ba, ba kya laifi" Sake sunkuyar da kai ta yi tana murmushi. Shi ma murmushin ya yi ya ce "Ina jin ki, meyafaru, dan ba kya zuwa office ɗin nan sai da dalili" Ta gyara zamanta ta ce "Barrister, na san ka san wani ɗan daba da ake nema ko? Aminu Viper" Yayi mata ƙuri da ido yana kallonta. "Dama wani labari na ji, wai wani laifi ya yi aka kai shi prison, kuma kawai sai aka sake shi ba bisa ƙa'ida ba, gashi sai ɓarna yake yi a gari" sai kuma ta yi shiru. Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ina jin ki" "To shi ne, sonake na san wani laifin ya yi, ban sani ba dan Allah ko zaka bincika mini, a wace kotun aka yi masa shari'a" "Meyasa ki ke son sani?" "Eh, sonake idan an kama shi, na bibiyi shari'ar da za ayi masa, kuma na binciki meyasa aka sake shi da" Wata ƴar dariya ya yi ya ce "Nabila kwanan nan na ga you are so much serious, amma kin san hakan kamar tarar aradu da ka ne ko? Amma let's see how far you can go, zan bincika miki in sha Allah, nan da 3days zan neme ki" "Na gode sosai babban yaya, Allah ya ƙare ka, na gode sosai da sosai" Yayi murmushi tare da jinjina mata da hannunsa ya ce "Ki huta little barrister " *** Can gidan su rahama kuwa, ta samu bacci, mamanta na tsakar gida tana ta shara, kasancewar ta mace mai son tsafta, jin motsi a bayanta, ya sanya ta waiwaya domin ta ga abun da yake faruwa. Matasa ne su uku, zabga-zabga cikin shigar banza a tsakiyar tsakar gidan. A tsorace ta ce "Lafiya kuwa? Meyafaru?" Ya ƙarewa gidan kallo ya ce "Dama a nan ku ke rayuwa, ƙasƙantattun matsiyata, amma har ki ke fatan ganin an kai ni kotu an karɓowa ƴar ki hakkinta? Har wani hakki ne da ita? Talaka yana da wani hakki ne ko ƴanci?" Cikin rawar baki ta ce "Waye kai malam?" "Na yi miki kama da malam? Ni na yi wa ƴar ki fyaɗe, da ki ka tafi nema mata hakkinta?". Sakin tsintsiyar ta yi, tana kallonsa, a ƙalla zai kai shekaru talatin da takwas, kallon idonsa ta yi babu mutunci ko imani a cikin su. "Yanzu kai ka iya samun ƙwarin gwiwar zuwa gabana, ka gaya mini ka yi wa ƴa ta fyaɗe? Bayan ka turo mini waccan bayahudiyar ta yaudaremu, ba ta yi nasara ba, shi ne ka zo gabana ka gaya mini ka keta wa ƴa ta haddi?" Ya fara takowa gabanta ya ce "Yes, na zo na ƙara kashe ƙishirwa ta ne, sannan in yaba wa baiwar Allah da Allah ya yi wa ƴar ki, kin iya haihuwa" Yayi maganar yana wata irin dariya, a fuskar maman rahama, da tuni idonta ya fara zubar da hawaye. Ya saka hannu ya riƙe ɗan kwalin kanta, haɗe da gashin kanta, ya tsuke fuska ya ce "Kin san ko ni waye, da ki ka saka na tako ƙafata wannan ƙazamin kucakin ƙauyen" Ihu ta saki, saboda zafi. Salim ya ce "Kai Abdul wannan yawa ne fa, ba wurinta mu ka zo ba fa" "Bar ni Salim, duk da hausawa sun ce abun cikin ƙwai, ya fi ƙwai daɗi, what if na wajen ƙwan ya fi?" Yayi maganar yana riƙe rigarta. Salim ya ce "No, kar ka yi haka, akuyanci kenan ai, dan Allah ka bari" Abdul zai yi magana, suka yi ido huɗu da rahama, a tsaye a ƙofar ɗakin su, tana kallonsa. Ayshercool 08081012143 🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143* *Ina masu buƙatar sayen nagartattun kayan magungunan mata, wanda babu cuta ko algus a ciki, ku yi joining link ɗin nan, domin samun nagartattun magungunan mata* https://chat.whatsapp.com/BLqFsnlyNf0B483RhoWq8v 15 A take ya hankaɗe uwar a gefe, ya yi wa ramma wani irin miskilin murmushi, ya nufe ta yana wata irin tafiya, irin ta riƙaƙƙun ƴan iska ya ce "Hi baby girl, long time almost 2months kenan fa ko?" Hawaye ne ya fara bin fuskar ramma, jikinta ya hau rawa. Ya sanya hannu ya dafa jikin bango, yana ƙare mata kallo ya shafi sumarsa ya ce "To ya ki ke, kin warke?" Shiru ta yi ta sunkuyar da kai, tana tuna waccan ranar, da irin yadda ya keta mata haddi cike da zalunci. Ya ce "Ohh, wai waccan ranar ce haryanzu ba ki manta ba ki ke kuka? Ya wuce ai wancan, kin bar ni da tsananin kewarki, duk ruwan da na sha komai sanyin sa, ya daina kashe mini ƙishirwa". Ya kai hannu ya ɗago fuskarta, ya shafi hawayen da suke ta ambaliya a kan fuskarta. Yinƙurawa mamanta ta yi da sauri, tana kururuwa ta ce "Kar ka taɓa mini ƴa, mugu azzalumi, wai babu wanda zai kawo mini ɗauki ne?" Ya kalli su Salim ya ce "Ku saka mini matar nan a silent" Haka suka rirriƙeta, suka ɗaure mata baki, suka shaƙa mata wani abu, a take jikinta yayi laƙwas. Ya sake kallon ramma ya ce "An ce akwai unborn ɗi na a cikin ki ko? da gaske za ki haife shi kuma?" Cikin kuka ta ce "Ban yafe maka ba, ka lalata mini rayuwa, ban sanka ban taɓa ganinka ba, ka biyo ni gida kana wulaƙanta mini uwa, dan bamu da kuɗi, Allah ya saka mini" tayi maganar tana fashewa da kuka iya ƙarfin ta. Salim ya sunkuyar da kai ya yi shiru, haka nan ya ji abun yayi masa wani iri a zuciyarsa, sauran matan da suke lalata da su, suke kai kan su, wannan kuma yarinya ce ƙarama. Dariya ya yi ya ce "Dan kin ce baki yafe ba, ba zai hana ni shiga aljanna ba, kun ƙuduri aniyar neman hakkinku, duk da an yi muku tayin kuɗi kun ƙi, zan nuna muku ƙarfi da izzar kuɗi a ƙasar nan". Ya danƙi hannun ramma, da jikinta ya ɗauki zafi sosai. Tana ihu tana kiran mama, ya ja ta suka fice daga gidan, suka sakata a mota suka tafi da ita. ***** Ɗan mama ne ya shiga ɗakin Viper, ya tarar da shi yana ta sintiri a ɗakin. "Ka daɗe ka yi ƙarko uban gidana" Viper ya tsaya cak, yana jiran ya ji me zai ce. "Na yi aikin da ka saka ni, ya tafi yadda yakamata " Ya kaɗa kai tare da yi masa alamar ya ƙaraso. "Ina labarin malam lawan?" "Kamar dai yadda ka ce, an kula da komai, sai dai babu wanda ya sake zuwa, gashi yanzu yana yawo a cikin unguwa". "Madaki fa?" "Shi ma kamar dai yadda ka sani, Honorable indabo yake yi wa aiki yanzu". "Ina buƙatar isassun kayan aiki, a kwanakin nan zan dirar masa, mu ɓalla ƙarfe, sai dai mu yi mutuwar kasko, ayi wadda za ayi". "Ba yanzu ba" suka ji muryar Walid. Suka mayar da hankalinsu kan sa. Walid ya ce "Viper da sauran lokaci, kai ka san madaki ba haka kurum yake daba ba, da zai kasu cikin sauƙi, da tuni mun kawar maka da shi, ka ɗan saurara tukuna" A hasale ya ce "Ba zan saurara ɗin ba tukuna" "Viper!" Ciki ƙaraji ya ce "Walid ka ƙyale ni" Walid ya girgiza kai ya ce "Da zan iya, da tuni na yi, mutumin nan ya fi ƙarfinmu ko ta ina, idan ka yi amfani da zuciya wallahi ba zamu yi nasara ba, ka bari mu bi komai a hankali mu lissafa, yadda ko mutuwar kasko ce mu yi" Cikin ƙaraji ya ce "Ba zan jira ba, na gaji, na gaya maka na gaji. Na so bin komai a hankali, meyasa ka kawo mini yarinyar saboda me? ka san ka ƙara tunzara zuciyata yaya ka ke so na yi, so ka ke sai na haukace tukuna? Kalli yadda na koma walid, kalle ni, abun da nake ta ƙoƙarin dannewa ka fama mini, dan me zaka kawo mini wannan yarinyar sannan ka ce na nutsu how? Ta ɗauki wayata ta tafi, ka na da tabbacin hannun wa wayata za ta shiga? Idan aka tashi kama ni, kana da tabbacin su waye za su kama ni, idan na ƙare a haka ban aikata abun da nake ƙuduri ba fa? Ko dai ka nemo duk in da yarinyar nan take na kasheta, ko kuma a yau ba sai gobe ba, sai na yi gaba da gaba da madaki ko na kashe shi ko ya kashe ni, amma kafin nan sai na fara gaba da gaba da wancan dabban" tuni gumi ya tsatsttsafo masa, jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, kafofin gashinsa ya bubbuɗe. Walid ya taka gabansa a hankali, cike da shirin ko ta kwana, dan ya san ƙarshenta sai ya ba shi gwale-gwale, ko ya mangare shi. Ya shammace shi, ya soka masa sirinji a damtsensa, kasancewar jikinsa babu riga, ya fara yi masa allura, sannan ya fara yi masa magana. Walid ya ce "Na san na yi laifi, amma ka bari na gyara laifina da kaina, na san abun da ka ke ji ɗan uwa, ba kai kaɗai ka ke ji ba Al'amin" Viper ya zubawa walid ido, ya rasa me zai yi, yana tsaye ya kashe masa jiki, ba zai iya komai ba, kasa tsayuwar yayi, ya tafi zai faɗi walid ya riƙe shi ya kwantar, ɗan mama kuwa dama tuni ya arce, dan yana tsoron a shaƙe shi. Barrister Naja'atu ce zaune a katafaren ofishin ta, tamkar na matar gwamna, yana ɗauke da duk wani kayan alatu da ake buƙata. Sannu a hankali take shafa screen ɗin wayarta, daga bisani ta saka wayar a kunnenta. "Honorable, ka isa Abujan ne?". Ya amsa da "Eh ma sauka" "Ok, yaya maganar yarinyar nan da Abdul ya yi raping?" "Yes, he handle the case himself, yayi maganin abun". Ta ce "Ok, ina fatan ka ja masa kunne, kar ya je ya aikata wani shirmen da ba zamu iya gyarawa ba". Ya ce "No, kar ki damu, zai yi abun da ya dace". Tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, dama ina tsoron ya yi wani shirmen ne, amma tun da ka ce haka, shikenan" Ta katse wayar, ta mayar da hankalinta kan sakatariyarta da ta shigo. Cikin gyatsine ta ce "Ke kuma ya aka yi?" "Kin yi baƙi ne ma" "Suwaye?" "Eh to, da alama dai ƙorafi suka kawo, ke suke..... "Ke bani da lokaci, ayyuka sun yi mini yawa, su ganki ko wani daban, hutawa nake buƙata, wannan jaraba a uzzurawa rayuwarka, london zan wuce ma ni this week na je na huta. Ki fita ki je ki sallame su" ta juya jiki a sanyaye ta bar office ɗin. Salim ya kalli Abdul da ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana shan giya a cikin wine cup ya ce "To wai yanzu ya zaka yi da yarinyar nan da ka kawo ka ajiye, Ga abun da aka tsara, kai kuma ga abun da ka yi?" Ya ɗan girgiza giyar a cikin kofin sannan ya ce "Gani na yi za ta ci bulus idan ta tafi a haka, sai na gama moreta zan aikata kawai" "Amma ba ka ganin, hakan zai iya kawo matsala, yanzu ko a nan gaba?" Ya girgiza kai ya ce "Ba wata matsala, na ɗan lokaci ne, zan gama abun da zan yi da ita, zaka iya tafiya ma kawai" Ya jinjina kai ya ce "To shikenan" Sannu a hankali ta buɗe idonta, ta din ga gani dishi-dishi, ta kasa tantance a ina take, dan ba ta taɓa ganin wurin ba. Ji ta yi an rufe ƙofa, ta ɗaga kai ta kalli mai shigowar, take gabanta yayi mummunar faɗuwa, duk da idonta bai gama washewa ba, amma sarai ta gane shi. "Kin tashi kenan? abun da aka shaƙa miki bai taka kara ya karya ba, amma ki ka yi wannan dogon zangon" yayi maganar lokacin da ya tsuguna a gabanta yana kallon idonta. Ƙirjinta ya din ga bugawa da sauri da sauri. Ganin ba ta ce komai ba, ya sanya ya tashi ya fita, babu jimawa ya dawo da plate a hannunsa, ɗauke da indomie da kifi a ciki, sai ruwan roba, hannunsa ɗaya kuma ledar magunguna ce. Ya tura mata plate ɗin gabanta, sannan ya fara haɗa alluran. Tayi shiru ta zuba masa ido, har sai da ya ce "Ki ci mana, allura zan yi miki" Cikin kuka ta ce "Dan Allah kar ka kashe ni" Abdul ya yi wani murmushi ya ce "Saboda me?" "Ni dai kar ka kashe ni, dan Allah ka mayar da ni wurin babata" Ya kalleta ya ce "Kashe ki fa sai na yi, ba dai ke taurin kai ba ke da babar taki, zan nuna muku cewa talaka ba komai bane illa bawa kuma takalmi ga masu kuɗi da dukiya, ba yanzu zan kashe ki ba, sai kin gama yi mini amfani tukuna. Yanzu ki ci abincin nan, zan yi miki allurai na zazzaɓin da yake jikinki". "Ni ba zan ci ba" ta yi maganar za ta tashi tsaye, amma ya daka mata tsawa ya ce "Wallahi idan ba ki ci ba, a yanzu zan kashe ki, ko gawarki babarki ba zata gani ba". Babu shiri ta fara cin abincin, sai dai a loma ta uku, ta hau amai, ta amayar da duk abun da ta ci. Cikin tsananin takaici ya ce "Ke mahaukaciyar ina ce zaki yi mini amai a nan? Nan yayi miki kama da wurin juye ƙazanta?. Tayi shiru ta sunkuyar da kai. "Tashi mu je in nuna miki in da duster da mopper suke ki gyara" Cikin tsoro ta tashi, tana jiri tana bin bango, haka ya saka ta gyara wurin da ta yi aman. Bayan ta gyara, ta shiga banɗakin tayi alwala, ta fito ta tayar da salla, ba tare da ta san ina ne gabas ba, da kuma adadin sallolin da ake bin ta ba, dan ba ta san adadin lokacin da ta shafe, ba a hayyacinta ba. Ya dawo ya tarar da ita a zaune, a takure wuri guda, bai kulata ba, ya ƙarasa ya sanya hannun sa a goshinta, ya ji shi da zafi rai. ɗaga ta ya ja ta ya dungurar da ita a kan gadon. Ya kama hannunta, ya saka sirinji, ya fara ɗaukar jininta. Bayan ya gama ɗaukar jininta, ya yi mata wasu allaurai duk a jijiyar hannunta. Ta zubawa saurautar Allah ido, dan kasa magana ta yi, tun yana allurar ta fara jiran jin alamar ciwonta ya ƙaru, dan ta sallama kashetan zai yi kamar yadda ya faɗa, amma bayan ya gama yi mata ya tashi ya fice, ya kulleta a ɗakin, ba tare da ta ji yanayinta ya sauya ba. *** Abun duniya fa ya ishi Nabila, wayar Viper ta zame mata wahala, dan kuwa kashe ta tayi gabaki ɗaya, sai dai duk in da ta zauna, musamman da daddare, idan ta shiga cikin duhu, Viper ne yake yi mata gizo, har abun ya fara tasiri a yanayin mu'amalarta. Tana toilet tana wanka, wayarta ta din ga ringing babu ƙaƙƙautawa, ta kammala wankan ta fito, ta ɗauki wayar tana dubawa. Lambar Nasir ta fara kira, ta nemi wuri ta zauna a gefen gado, tana jiran ya ɗaga. "Ina ki ka shiga ne? Ko kina wurin aiki ne?" Ta ce "A'a, yanzun nan na dawo gida" "Baki da lafiya ne?" "No, gajiyar aiki ce kawai" "To, aikin ki yayi kyau arfa, na yi waya da mu'azzam, gayen nan da ki ka faɗa mun kama shi, tare da tabar wiwi da ƙwayoyi" Sassanyar ajiyar zuciya ta yi ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, Allah shi ne abun godiya, what next?" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Na saka lallai su fara tuhumarsa, ya faɗi in da Viper yake". Zuciyarta ta din ga raya mata ko ta sanar masa kai tsaye, abubuwan da suke gudana, ta bashi wayar hankalinta ya kwanta, amma zuciyarta ta gargaɗe ta a kan aikata hakan. *** In da ya bar ta a kan gadon, nan ya je ya sake tarar da ita, ta tashi ta zauna ta dunƙule jikinta a wuri ɗaya tana bacci, sai ajiyar zuciya take yi. Wani irin murmushi ya yi, yayi miƙa lokaci guda, ya fara rage kayan jikinsa. Motsinsa ya sanya ta farka, fes ta buɗe idanunta, sai dai hankalinta ya yi mummunan tashi, ta ja da baya, ba ta ƙaunar ganinsa ko kaɗan. Ya hawo kan gadon ya nufota, ta din ga ihu tana kiran sunan Allah, ta na yi masa magiyar ya ƙyaleta, ya mayar da ita gida. Amma kamar ya kamo ƴar kaza, haka ya danƙota zai yi mata rashin mutunci, sai dai yana haɗa ta da jikinsa, ya ji kamar ana hura wuta a Jikinta, saboda zafin zazzaɓi, gashi sai wani irin ƙarni take yi, da warin man kaɗanya da take shafawa ya haɗe da ƙarnin koren sabulun da take wanka da wanki da shi. Ba wannan ya fi damunsa ba, rashin saukar zazzaɓin jikinta ne bai so ba, dan ko a yanzu a galabaice take. A ɓangaren ramma ma, warin giyar da yake yi, da ƙamshin turaren sa ya sanya ta fara yinƙurin amai, ba shiri ya cikata, ta sauka da gudu, ta tafi banɗakin da yake cikin ɗakin, ta din ga kwara aman, sai dai ruwa kawai take amayarwa, bayan shi babu komai a cikinta. Ta gama aman tana ta sauke numfashi, ta lallaɓa ta fito, tana bin bango, sai dai ta tsaya cak tana kallon sa yadda ya zuba mata ido. Cikin kuka ta haɗa hannayenta ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, ka mayar da ni in da ka ɗauko ni, hankalin mamana na san yana can a tashe, dan Allah ka yi mini rai ka yi haƙuri" ta ƙarasa maganar tana zubewa a kan gwiwoyinta tana bashi haƙuri". Strip ɗin gwajin ciki ya ɗago da yake hannunsa, wanda ya gwada da jininta da ya ɗiba ɗazu ya ce "Ke ce mace ta farko da ta fara ɗaukar cikina, kin kafa tarihi, tun da ki ka ce ba za a zubar ba, nima na ji ya shiga raina, ina son abuna, zaki haife shi kafin na kashe ki, kuma ba zan kashe ki ba sai bayan kin haihu" ta yi shiru tana cigaba da zubar da hawaye, wai ita ce ɗauke da ɗan shege a cikinta, a wani keɓantaccen wuri tare da ɗan iska, saboda kawai ba su da kuɗi, sai yau ta ƙara tabattar da illar talauci. Ya miƙe tsam daga kan gadon ya fice ya bar ta a ɗakin, ba tare da sanin makama ko abun yi ba. Sumayya ce a office ɗin manager, fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa. Ya kalleta ya ce "Sumayya yaya aka yi ne? Ko yayi miki wani abun ranar da ku ka yi program ɗin?" Ta girgiza kai alamar a'a. "To menene? Na ga kin yi editing ma kin tura mini, komai yayi normal, na ce a saka idan lokaci yayi kin yi ƙoƙari sosai, ina ga program ɗin hannunki zai dawo gaba ɗaya" Ta sauke numfashi ta ce "Sir" Ya amsa da "Yes ma" Sai kuma ta yi shiru. "Ki gaya mini mana idan da wani abu" ta girgiza kai ta tashi ta fita. Addu'a ya din ga yi a zuciyarsa, tare da fatan Allah ya sa ba wani abun indabo yayi mata ba, dan ya san halinsa sarai. Nabila tana office ɗin ta, tana aiki, barrister Habib ya buɗe ya shiga da sallama. Miƙewa tayi tsaye ta ce "Sannu da zuwa, da ka kirawo ni ai" Ya ƙarasa gaban teburinta ya ce "Babu damuwa, aikin da ki ka ba ni ne na yi" Tayi murmushi ta ce "Taimakon da na nema dai aka yi mini" Shi ma murmushin ya yi ya ce "Zan tura miki court ɗin da aka fara yi masa shari'a, da sunan wurin wanda za ki je ya binciko miki file ɗin, akwai dai wani abu a ɓoye". Cikin sauri ta ce "Ok, ai daga nan ma kana tura mini sai na tafi" Ya ce "Wait, ki tafi yanzu ba ki da aiki ne?" "Ai na kusa kammalawa saura kaɗan ne" Ya ce "shikenan, zan tura miki ta what's app, amma ki bi a hankali, fa kar ki je ki yi abun da ba shikenan ba" "In sha Allah, na gode sosai" Yana fita ta fara lissafi a ranta, tun kan viper ya je hannu, za ta bibiyi cases ɗin sa na baya, domin a shirye take da ta ƙalubalanci hukumar shari'a ciki har da alƙall da kuma hukumar gidan yari, kan sakin Viper ba tare da ƙa'ida ba, ta san ko ba ta yi nasara ba, za ta yi suna sosai. Tattara jakarta ta yi, ta fita bayan da saƙon barrister Habib ya shiga wayarta. Ba ta wani sha wahala ba zuwa kotun da ya bata adress ɗin, tun da dama sananniyar magistrate court ce a kano. Ofishin rijistra ta je, suka gaisa da mutanen wurin, sannan ta tambayi office ɗin mutumin da barrister Habib ya gaya mata. Aka yi mata iso, sannan ta gabatarwa da mutumin kanta, da wanda ya turo ta. Ya karɓeta da mutuntawa sannan ya ce "Baiwar Allah, gaskiya ta in da ki ka biyo, babu yadda za ayi na kasa yi miki alfarma, amma riƙe file ɗin nan, tamkar saka hannu ne ki ɗaukko ƙarfen da yake cikin wuta ne, dan Allah kar ki je ki yi wani abu da bai kamata ba, tun kan ki zo aka yi waya, aka ce a baki idan kin zo" Nabila ta ce "In sha Allah, babu wani abu da zan yi, ina ɗan yi wani bincike ne kawai". Ya ja ta suka tafi wani wuri a cikin kotun, suka shiga can wani office, da ba zaka ce akwai mutane a wurin ba, sai da suka shiga can ciki, suka iske wani mutum yana ta aiki a computer. Suka gaisa, wanda ya rakota ya ce "Oga, ga baƙuwa mun yi, Barrister Habib ne ya aikota, shi kuma daga top oga, ya ce a kawo ta file ɗin Al'amin viper zaka ɗaukko mata" Shiru mutumin yayi yana kallon ta sannan ya ce "Ya sunanki?" "Nabila yusuf maitama" "Me za ki yi da file ɗin?" Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Wani bincike nake yi ne" Ya mayar da hankalin sa kan mutumin da ya rakota ya ce "Ka gaya mata illar da ke cikin hakan?" "Na gaya mata, ko ma dai menene na gaya maka wanda ya ce a ba ta ai" Yayi ajiyar zuciya yana cigaba da yi wa Nabila kallon tuhuma, ya tashi ya shiga wani wuri. Ta kalli mutumin da ya rakota ta ce "Yallaɓai, meyasa file ɗin yake da hatsari har haka?" Yayi murmushi ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Yana da alaƙa da rashin gaskiya" Mutumin ya fito ɗauke da file ɗin, duk ya yi ƙura, hannu na rawa ta karɓa ta ja kujera ta zauna, ta fara dubawa. Sannu a hankali ta din ga bin bayanan ciki, da binciken rahoton ƴan sanda a kai, sai dai komai ba straight forward aka yi shi ba, gaba ɗaya kanta ya kulle, ba ta fuskanci wani abun kirki a ciki ba. "Amma sir, ina ƙarshen shari'ar, ai wannan ba a yanke hukunci ba, ranar ƙarshe da aka ɗaga shari'ar an ce sati uku za a sake zama, yanzu kusan shekara biyar, ba a sake rubuta komai ba" Mutumin ya ce "Eh yadda ki ka gani a haka yake" Cike da mamaki ta ce "Dan Allah wane alƙalin ne ya yi masa shari'ar?" "Yana abuja" suka bata amsa a taƙaice. "Wannan documentation ɗin, sam ba a yi shi ma yadda za a fahimta ba, amma dan Allah.... Wanda ya ɗauko mata File ɗin ya ce "Mu fa babu abun da za mu iya sake gaya miki, ba wanda yake da damar zuwa wurin nan sai staff ɗinmu, dan haka ki tashi ki tafi". Ta miƙe tsaye ta ce "Na gode sosai" Ta fito daga office ɗin tana mamaki, ta ja ta tsaya tana kallon office ɗin, a abun da ta fuskanta wuri ne da ake ɓoye files na musamman. "Yayi kisan kai!" Ta faɗa a fili. "Ba abun mamaki bane ba, da gani zai aikata abun da ya fi kisan kai, amma menene dalilin ajiye shi shekara biyar, ba ayi masa shari'a ba, an ɓoye file ɗin sa a wuri na musamman, ya shekara biyar a prison, kuma kwatsam an sake shi, babu document na wanke shi aka yi daga laifin ko kuwa, duk da an rubuta ya amsa laifin, amma wane hukuncin aka yanke masa? Wayyo Allah kaina zai fashe" ta yi maganar tana dafe kanta, da ya yi mata nauyi. *** A tsaye yake a kanta yana ƙare mata kallo, yanayin yadda take a kwance ya tabbatar masa da salla ta yi. Ruwan robar hannunsa ya fara zuba mata a Jikinta, hakan ya razanata ta tashi a gigice. Ya watsa mata sabulu da soso a jiki ya ce "Ki tashi ki je ki yi wanka, ba na son ƙazanta, kar ki haifar mini ɗa mai dauɗa" Ta yinƙura ta tashi da kyar, tana jiri, ga yunwa ga zazzaɓi ga kwana da ta yi amai, ta din ga bin bango, har ta isa banɗaki. Ta daɗe a banɗakin tana kuka, sannan ta yi wankan ta fito, ta tarar da shi a kan gado a zaune yana danna waya. Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Dalla cire wannan kayan, ƙazamar banza da wofi, har amai ki ka yi a jikin kayan amma ki ka mayar da su jikinki" kallonsa take yi, to tsirara yake son ta zauna? Ya buɗe wardrobe ɗin da ke ɗakin, duk kayansa ne a ciki, ya jefa mata wata shirt, ya ce ta ɗauka ta saka. Banza ta yi masa, ta kawar da kanta gefe, wanda hakan ya hasala shi, yana zuwa gabanta ya kwasheta da mari, abunka da jiki babu ƙwari, take ta faɗi ƙasa, ta riƙe fuskarta. "Ke kin isa ina magana ki yi mini banza, ƴar wahala mara amfani, ɗauki ki saka kan na tattakaki" Ramma ba ta ƙaunar duk da abun da zai taɓa lafiyar jikinta, haka ta zura rigar nan, ta zo mata har gwiwa, sai rufe jikinta take yi. Ya danƙota, ya fita falo da ita. A falon ya haɗa mata baƙin shayi, sai soyayyen dankali da ketchup ya ce ta ci. Gaba ɗaya a tsorace take, saboda kar ya kuma dukanta, haka ta din ga tsakura tana ci tana hawaye. Ta gama ci, ya ɗaukko alluran zazzaɓi da yake yi mata yayi mata. Ta lura yana da mai aiki a gidan namiji, har girki da gyaran gidan shi ne yake yi masa su. Ya kashingiɗa yana kallon tv, ita kuma tana gefensa a ɗarare, sai mutsu-mustu take yi tana share hawaye. Sahidar yatsunsa ya gani kwance a fuskarta, har ya ɗaga ya basar ya cigaba da kallonsa yana kaɗa ƙafa. *** "Allah ya taimaki maigida" "Menene labari?" "Na samu kiran waya ɗazu, wata yarinya ta je an kaita har ofishin secret files, an ɗaukko mata file ɗin viper ta duba" "Wacece ita?" "Yarinyar da ka ce ayi amfani da ita a kama Viper" Da sauri ya ce "What? Ya aka yi ta san da file ɗin ta je? Waye ya ce a bata?" "Wallahi ban sani ba, amma an tabattar mini da ga sama su ma aka ba su umarnin ba ta" "Sama ina, waye ya bayar da umarnin?" "Ban sani ba wallahi, kuma da gaske lawyer ce, idan kuwa haka ne, za ta iya yiwuwa da gaske ta haɗu da Viper, ƴar jaridar nan raina mana hankali ta yi" Indabo ya numfasa ya ce "Kar ku yi gaggawa, kar ta san mu na bibiyarta, ka bi ta hannun ƙawarta, ku samo me take son samu a kansa, idan ta ƙi, ku kamata ku azabtar da ita". Ya amsa da "Ok sir". Daga kotun, gida arfa ta tafi, tun daga shigarta, Sauda ta fara tsokanarta da faɗa, amma ba ta ita take ba, ɗakinta tafi ta cigaba da tunani da lissafi. Kamar wadda aka zungura, ta ɗaukko wayarta ta kira Nasir. Murya ƙasa-ƙasa ya ce "Arfa ya dai? Mun shiga meeting ne" Kamar za ta yi kuka ta ce "Yaushe za ka dawo?" "Zamu yi waya an jima, ki yi haƙuri" "Kar ka kashe mana dan Allah, ni ina cikin damuwa magana nake son mu yi, wani abu zan baka" Ya ce "Wani abu me?" "Abu ne mai muhimmanci a kan viper, amma sai ka yi mini alƙawarin ba zaka yi mini faɗa ba ko ka gayawa abba ba" Tattara nutsuwarsa ya yi ya ce "I hope, ba wata kasadar ki ka je ki ka aikata ba" Ta girgiza kai ta ce "Ba wata kasada da na yi, ni dai ka yi ka dawo, kan na mutu" A rikice ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, menene ki gaya mini" "Ka kwantar da hankalinka, kawai dai ka yi ka dawo, abun yana da muhimmanci, na san yadda zaka same shi kai tsaye" "Kin ga ba zan iya jira ba, gaya mini menene sai na aika su Mu'azzam, dama wanda aka kama ɗin nan ya ƙi magana" "Sai ka dawo gaskiya" ta kashe wayar gaba ki ɗaya, dan kar ya biyo ta, ta sake dafe kanta. Sumayya na news room, tana jiran lokaci ya cika, ta gabatar aka turo ƙofar aka shigo. Sak tayi tana kallon mai shigowar. Mutumin da honorable ya saka ya karɓi wayarta ne, ranar da ta je gidansa. Ya ja kujera yana kallonta, ya ce "Ya dai, kin yi mamakin ganina ne? Mintuna goma sha biyar suka rage miki, kan ki fara karanta labaran, zaki yi mini aiki". Ta zuba masa ido, amma ba ta ce uffan ba. "Meyasa ki ke yi mana ƙarya a aikinmu? Da gaske ƙawarki ta haɗu da Viper?" Cikin ɓacin rai Sumayya ta ce "Na gaji da amsa wannan tambayar, idan ba ku yadda da ni ba, ku nemeta ta amsa muku mana" Ya shafi sajensa ya ce "Zamu gani ai, yau ta je court ɗin da aka yi wa Viper shari'a, ta karɓi secret file ɗin sa ta duba, zaki kira ta, ki ji dalilin zuwan ta, da kuma abun da za ta yi da file ɗin" Sumayya ta girgiza kai ta ce "Nabila ba wani abu da za ta amfana muku, kawai na san ƴar rigima ce, so take ta yi suna ta ɗaukaka ta taimakawa yayanta shikenan" Yayi dariya ya ce "Za mu gani, daga yanzu zuwa azahar ɗin gobe, idan baki kawo rahoton dalilin bin diddigin shari'ar Viper da take yi ba, abun da ba kya zato zai faru" ya miƙe tsaye ya ce "lokaci ya cika, ki gabatar da aikinki" Sumayya ta dafe kai cikin matsananciyar damuwa, tana tunanin wannan wace irin rayuwa ce. Murtala ne ya shigo yana faɗin "Afuwan sisyna, mamager ya kira ni ne, na saita komai ki fara". "Ba ka ga mutumin da ya fita yanzu ba?" Ya kalli ƙofar ya ce "Ban ga kowa ba" Tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan mu fara". *** Ƙaramar wayarta ce isheta da vibration a ƙasan pillow, ta ɗaga ta ce "Bacci fa nake ki ke ta kiran wayata". "Haka dai, daga bacci sai kwalliya da cin abinci, ke har kin koma gida kin kwanta, ni tun 9 gani har 5 ban tashi ba" Nabila ta ce "Ke ba na samun bacci a ƴan kwankin nan wallahi" "Meyasa?" "Wallahi a tsorace nake, ba na iya bacci, gani nake kowane lokaci viper zai kashe ni, cewa yayi fa sai ya kashe ni, sonake Yaya ya dawo na danƙa masa wayar nan, na huta, wai da wayar wa ki ka kira ni ne?" Sumayya ta ce "Wayata ce ta ɗauke, ina ki ka je ne yau?" "Wurin aiki mana, amma da labari sosai, mu haɗu gobe in Allah ya kaimu" "Yakamata mu haɗu kam, dan na ga mutuniyarki bunkure, a gidan honorable Indabo" Daga kan gadon da Nabila take ta miƙe tsaye ta ce "Amma ba ki gaya mini ba sai yau?" "Na san halinki ne, uzzura mini zaki yi, ke bari na tafi gida ma yi magana" Ta kashe wayar, ta kaiwa murtala wayarsa, dan ta fuskanci mutanen honorable na bibiyar kiran wayar da take yi. Wuni guda ramma ba ta sake saka Abdul a idonta ba, sai dai kukunsa idan ya kammala girki, ya ƙwanƙwasa mata ƙofa ya ajiye mata abinci. Tayi kuka har ta gaji, ta koma addu'a, tare da fatan Allah ya kuɓutar da ita daga sharrin zaluncin Abdul. Tana zaune a ƙasan carfet, har wurin sha biyu na dare, ya shigo yana kokawa da ƙofar ɗakin, saboda a buge yake. Ta tashi tsaye cikin tsoro, sai dai ba tare da ta yi masa laifin komai ba, ya hau ta duka, ya din ga ball da ita yana taka ta da ƙafarsa, tun tana kururwa har ta kasa sai ajiyar zuciya, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta iya yi. Tamkar dabba haka ya afka mata, ba tare da la'akari da ƙarancin shekarunta ba, kodayeke ina tunani ga wanda hankalinsa ya gushe?. Bai farka ba sai kusan tara na safe, yayi miƙa ya tashi yana kallon ɗakin, da sauri ya kalli gadon bai ganta ba, ya kalli jikinsa, ya tashi yana mayar da kayansa, kawai ya ga jini a gefensa, har zuwa banɗaki, cikin hanzari ya nufi banɗakin, ƙofar tana buɗe dan haka ya shiga, ya tarar da ita a zaune ta jingina da jikin bath jini yana ta zuba daga jikinta, ga jikinta duk a kumbure saboda duka, idonta a rufe. Ya ƙarasa ya durƙusa ya ɗaga hannunta ya saki, ya ga ya koma babu alamar numfashi a tare da ita, rigarsa dake jikinta, tayi sharkaf da jini. Dafe kansa yayi yana tuna abun da ya faru jiya, kamar mafarki. 🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143* 16 Shi gashi ko sunanta ma bai sani ba, ya sake ɗaga hannunta, amma hannun ya sake dawowa ƙasa. Ya kai hannunsa hancinta, ya ji tana numfashi kaɗan-kaɗan. Ya haɗa ruwa a bath ɗin mai ɗumi, ya cire rigar jikinta ya ajiye a gefe. Ya ƙarewa jikinta kallo, ko ina shatin duka ne da ya yi mata, take wani abu mai kama da tausayinta ya ɗarsu a ransa, ya ɗaga ta, ya sakata a cikin bath ɗin, ga abun da ta yi ɓari nan daga cikinta a ƙarƙashin ta. Duk da ƙyanƙyaminsa, da yadda ƙarnin jinin yake hawar masa ka, haka ya din ga tarar ruwa, yana kwarawa a banɗakin, ita kuma ya din ga canza ruwan da take ciki, saboda yadda yake ɓaci da jini. Rigarta kuwa, wuri guda ya ware ta, dan kuwa yarwa zai yi, bai san yadda zai yi da ita ba. Ya fita da sauri, ya kira mai aikinsa solomon, ya rubuta masa abubuwan da yake buƙata ya ce ya sayo masa. Har solomon ya je ya dawo, yana ta ƙoƙarin ganin ya tsayar da jinin da take zubarwa. Ya ɗauke ta zuwa kan gado ya kwantar da ita kamar gawa, ya sake ɗiban jininta, ya yi bawa solomon ya ce ya kai kowane lap ne, idan ya kai ya kira shi a waya. Ya saka mata drip hannu biyu, ya sake su, yana yi yana duba vitals ɗin ta. Ƙofar ɗakin ake ta bubbugawa, ya tashi ya buɗe, ya ga saif a tsaye. Saif ya kalleshi ya ce "Ya na ganka kamar mara gaskiya? Lafiya kuwa?" Ya girgiza kai ya ce "Ina fa lafiya, yarinyar nan ce tayi miscarriage" Saif ya ce "Shi ne me to? Dama ba haka kake so ba, na ga ma fa kasheta za ka yi ka bar ta" Abdul ya ce "Haka ne, jiya daka sauke ni bayan ka tafi, ka san a buge nake, na dake ta sosai" "Lallai Abdul, yau ka fara yi wa mata haka to?" Ya girgiza kai ya ce "No, kawai su sauran su ne suke kawo mini kansu, shiyasa ban taɓa jin komai ba a kan abun da nake aikatawa, sai ta ji sauƙi sosai, zan kasheta na huta" Saif ya ce "Well mu je in ga jikin nata" Abdul ya tsaya a gaban ƙofar ya ce "No, ba zaka shiga ba" Cikin mamaki ya kalli Abdul ya ce "Lafiyarka kuwa?" "Ras nake, ba zaka shiga bane kawai" "Ka kashetan kenan?" "Idan na kasheta, zan kasa gaya maka ne, ko tsoronka nake ji?" Suna haka solomon ya kira shi, ya haɗa su da masu lap, ya gaya musu gwaje-gwajen da yake so a yi wa jinin ramma da ya bayar aka kai. Ya koma ɗakin da take, ya rufe ya saka mumulli, ta ciki, ya sake nufar gadon, ya hau yana tattaɓata ya ga ko ta na da rai. Ambaton Allah ya ji tana yi, tare da kiran sunan mama ƙasa-ƙasa, sai dai bai ma san sunanta ba balle ya kira sunan. A hankali ta buɗe idonta a kansa, ta yinƙura za ta tashi, amma ta kasa, duk jikinta ciwo yake yi, mararta ma wani irin ciwo take yi mata. Ya riƙe hannunta, yana tsareta da idanunsa ya ce "Sannu" Hawaye ya shiga ziraro mata ta gefen idonta ta ce "Me na yi maka jiya ka dake ni?" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "A buge nake ne ba abun da ki ka yi mini" Cikin ƙarfin hali ta ce "Allah ya saka mini, na barka da Allah" Ya amsa da "Tom" Ta sake yinƙurawa za ta tashi, amma ya riƙeta ya ce "Ina zaki?" "Salla zan yi" Abdul ya ce "Ki na zubar da jinin zaki yi salla?" Ta  ɗan gyara kwanciyar ta, cike da takaicin yanayin da take ciki, da kuma kallon da yake yi mata, cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah ka rufe mini jikina, ka daina kallona". Da idanunsa ya tsatstsareta, yana yi mata wani irin kallo, da ya ƙara ɓata mata rai, ta ɗaga hannunta da kyar, za ta ja zanin gado da ya rufe mata ƙafa, ta rufe jikinta da ko arzikin vest babu, amma ya riƙe hannunta, ya mayar ya ajiye wuri guda. Ya ce "Idan ruwan nan ya goce, mutuwa zaki yi, dan kin zubar da jini sosai, kuma bana fatan ki mutu yanzu, sai kin samu ciki, kin haifa mini ɗa, saboda zuciyata ta so abun da yake cikinki, ya zube". A hankali ta cigaba da sheshsheƙar kuka, tare da fatan ta mutu ta huta da wannan bayahudiyar rayuwar da ta faɗa, duk a silar talauci da rashin galihu, ta san Allah kaɗai ya san halin da mahaifiyar ta take ciki, na tashin hankalin rashin sanin in da take. Idonsa ya sauka a kan taruwar jinin da ya kwanta a gefen wuyanta, ya ƙara tabattar da ba ƙaramin duka ya yi mata ba. A karo na farko da ya ji waji abu mai kama da tausayin wani ya shiga ransa, she look very innocent and calm. *** Tun da Nabila ta shiga office ɗin Barrister Habib, take murmushi, shi ma murmushin ya yi mata ya ce "Ya ake ciki ke ƴar ƙwalisa" Ta zauna tare da faɗin "Godiya nake barrister, jiya ai na je, an bani duk abun da na buƙata, na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi" Barrister Habib ya amsa da "Amin ya rabb, ina fatan babu wani abun?" Ta ce "Akwai, abubuwan da na gani sun ɗaure mini kai, ashe kisan kai yayi" "Ba abun mamaki bane ba, dan mutum irin wannan ya yi kisan kai ai". Ta ce "Haka ne, amma shekara biyar ya yi ba a yi masa shari'a, kuma aka sake shi, ba tare da wani cikakken dalili ba, gaba ɗaya ma akwai abubuwan da babu a cikin file ɗin nasa ma" Ya ce "Nabila cases irin wannan ai da yawa, sai fatan Allah ya kyauta" Ta amsa da "Amin, yanzu saura alƙalin da ya yi masa shari'a, na ga an rubuta justice zakariyya, amma babu surname ɗin sa" Barrister Habib ya yi murmushi ya ce "Shi kuma me zaki yi masa?" "Kawai so nake na sani" "Ai an yi masa transfer ma daga kano, bama ya ƙasar ya je ƙaro karatu" Nabila ta ce "Kuma duk hakan yana da alaƙa da case ɗin viper?" "A'a ba na ce ba, na dai san shi ne before, bani da tabbacin yanzu" Ta ce "Na fahimta, na gode sosai da sosai, bari na je zan ga Sumayya, yanzu zan dawo, na yi mata alƙawarin haɗuwa da ita yau" Ya ce "Ok, Allah ya tsare" Ta tashi ta fita, dan kuwa yau ba ta da aiki sosai. Sosai take son ganin sumayya, domin ta ba ta labarin halin da ake ciki, a kan binciken da take yi a kan viper. Ta kira sumayya ta ce mata za ta shiga gidan radiyonsu, su haɗu a can. Tana fitowa daga gate ɗin, ta tarar da wani mai napep a tsaye, ta ce "Malam tafiya zaka yi?" Ya ce mata "Eh" "Yauwwa, mu je" ta kama adaidaita sahun ta shiga, tana ƙoƙarin ɗaga kiran da yake shigowa wayarta. Sai dai ba ta kai ga hakan ba, wasu matasa suka shigo napep ɗin, suka zauna a gefe da gefenta, suka rufe mata baki da ido, mai adaidaita sahun ya ɗauke kan babbar hanya ya yi wani wurin. Kusan awanni biyar, ramma ta ɗan samu ƙwarin jikinta, har ta samu ta yi wanka, sai dai ta kasa cin komai, ya sake ba ta wasu kayan a cikin nasa, duk da sun yi mata yawa, ta karɓa ta saka, ya ja hannunta zuwa falo. Solomon ya kawo abinci, da fruit, Abdul ya kalleta ya ce "Me zaki ci a nan?" Ta girgiza kai alamar a'a. "Wallahi ko ki ci abinci, ko na sake yi miki tsinannnen duka a wurin nan, bana son shashanci bar ganin ina lallaɓa ki" Cikin tsoro ta din ga cakalar abincin, tana ci tana kuka. "Ke, meye sunanki ne ma?" Jiki a sanyaye ta ce "Ramma" Ya yatsine fuska ya ce "Meye wani ramma, ba rahama ba?" "Eh rahama"ta amsa tana sunkuyar da kai. "Meye yake yi miki ciwo yanzu?" Ta ja majinar da take shirin zubo mata, ta goge hawayenta ta ce "Duka jikina" "Dukan da na yi miki ne, gama mu koma ɗaki, sai na yi miki tausa" Manyan idanunta ta kafa masa, tana kallonsa. "Ki daina kallona da wannan ƙwala-ƙwalan idanun naki, idan ba haka ba, na fita sai kin ganni". Ta din ga wasa da doyar, ta kasa ci, ta kuma rasa abun yi. Shiru-shiru sumayya ta din ga kiran wayar Nabila, ga wayar na shiga, amma ta ƙi ɗagawa har ranta ya fara ɓaci, gefe guda kuma ga mutanen honorable na ta kiranta su ji, yaya suka yi me Nabila ta yi da file ɗin viper da ta je nema. Nabila ta na ji aka sauko da ita daga cikin adaidaita sahun, bayan shafe lokaci ana tafiya. Babu bakin magana, an rufe mata baki, an ɗaure mata ido, sai addu'a kawai take yi a zuciyarta. Kwance mata idanu suka yi, ta yi tozali da Walid a gabanta yana yi mata wani irin mugun kallo, sai da hantar cikinta ta kaɗa. Wurin da suke kamar jeji, babu gida gaba babu a baya, sai shi da ƴan daban da suka kawota, ashe mai napep ɗin nan ma duk set up ne. Jikinta ya hau tsuma, sai dai ta kasa magana, amma duk da haka godewa Allah take yi, da ba wurin Viper suka kaita ba. "Yanzu abun da ki ka yi kin kyauta kenan?" Walid ya yi maganar yana tsareta da idanunsa. Ta sunkuyar da kai, ya daka mata tsawa ya ce "Tambayar ki nake yi, da ki ka saka a ka kama liti shi laifin me yayi miki, ina har in da Vipern yake kin sani, kuma kin je, meya hana ki tura kai tsaye a kama shi? Yanzu gashi ina ta fama da shi, ya ce lallai zai miƙa kansa ga hukuma, saboda a saki liti, ba zai sake bari wani ya wahala saboda laifinsa ba" Cikin dakiya Nabila ta ce "Dama haka ne ya dace da shi ai, mutumin da yayi kisan kai aka sake shi, kuma yake zubar da jinin mutane ai hakan yakamata yayi, ta haka ne zai wanke nauyin laifukan da ya aikata" Walid ya ce "Haka ki ka ce? Da ya yi kisan kai wa ya kashe?" Ɗaya daga cikin su ya ce "Me gida, ka bari mu cire mata ta yatsu ko za ta dawo hayyacinta, ji fa maganganun da take faɗa a kan master". Ya ɗaga musu hannu, ya dube ta ya ce "Shikenan, kin yi gaskiya yayi kisan kai, zan bar Al'amin ya miƙa kansa ga hukuma, amma ki sani duk hukuncin da aka yi masa, ke zaki ɗauki nauyin alhakinsa, idan ma amfani ake da ke dan cimma wata manufa a kansa, wanda suke amfanin da ke sun bar ki a duhu, amma kafin nan yakamata ki san waye Al'amin, meyafaru da shi, daga nan kuma duk abun da ki ka yanke ya rage naki!!!. GUNDARIN LABARIN. Tsaki yake tayi a jejjere, yana kaiwa yana komowa a matsakaicin falon, yana sauke numfashi. Matar da ke zaune a kan kujera ta kalleshi ta ce "Wai yanzu dan Allah wannan sintirin ne zai baka mafita?" Kamar mai jiran ƙiris ya ce "To yaya zan yi? Magana fa ake ta makomar siyasata, idan muka faɗi zaɓen nan akwai matsala, kuma malamin nan ya tabattar mini da na cika kowane sharaɗi, sai zubar da jini ranar zaɓe, kuma alamu sun nuna gwamnati da gaske take, za a tsaurara tsaro sosai da sosai a wurin zaɓen nan, kuma idan ba a cika wannan sharaɗin ba, komai fa ya rushe" Matar ta numfasa ta ce "Duk ina yaranka marasa jin nan ne, da suke yi maka aiki?" "Bilki duk suna hannu, kuma babu wani cikakken jan wuya da zai iya tarar aradu da kan nan, idan aka kama mutum da tayar da tarzoma a wurin, shekara sha biyar ne a gidan yari". "To sai me, kai zaka yi, ka biya su su yi aiki kawai". "To ai ki gane, duk sun tsorata da hukuncin ne" Bilki tayi murmushi ta ce "Ka fito da mai dogon zamani mana, kai ka san zai iya, Al'amin ba" Ya kalleta sannan ya nemi wuri ya zauna ya ce "Kuma fa kin kawo shawara, sai dai yaron ne hukuma ne sai da rarrash, ban taɓa ganin ɗan iska mai mulkin tsiya ba sai shi, tsaf zai ƙi yi, saboda kusan watanni shida yana tsare ban fito da shi ba" Ta ce "Amma ai yana jin maganar ka, zai yi ba ni da wata tantama" Ya jinjina kai ya ce "Hakan za ayi, zan saka a fito da shi" *** Sanye take da dogon hijjabi launin maroon, har ƙafarta hijjabin ya ɗauki guga, ƙafarta sanye da safa baƙa, sai sauri take yi tana ratsa lunguna har ta iso ƙofar gate ɗin makarantar islamiyyar. Sai dai duk wannan saurin da take yi, an riga an fara tarar makara, wanda idan da abun da ta tsana, shi ne a taɓa lafiyar jikinta. Kusan mintuna goma ya ƙara, bai shiga ajin ba domin yi musu ƙari, yana jira ya ga ta ina za ta ɓullo, yana ofishin malamai, yake hango yadda malam hamza ya zage ƙarfin sa, yana shimfiɗa mata murtukekiyar dorina a jikinta, sai kuka take tana bashi haƙuri. Sam bai ga fa'idar duka a cikin ladabtar da ɗalibai ba, mussaman mata, macen ma mai rauni kamar wannan baiwar Allah. Litattafan sa ya kwasa, ya tafi ajin nasu, malam Jamil kenan, ba ya duka ba ya zagi da cin mutuncin ɗalibi, amma ɗalibai na ganin girmansa da mutuntashi. Ana tsaka da tilawa ta shigo ajin, ta nemi wuri ta rakuɓe a gefe, ɗaya bayan ɗaya ɗaliban suke tasowa, suna zuwa gabansa da littafi, suna bayar da haddar Alqur'ani mai girma, idan ya kammala ji, ya rubuta maka making haddarka, sauran ɗalibai kuma na cigaba da tilawa, sai dai fiye da rabin hankalinsa yana kanta. A haka har aka zo kanta, ta tashi jiki babu ƙwari, ta je gabansa ta zauna, ta miƙa masa littafinta, ya karɓa yana dubawa, ba bu in da take da maki ƙasa da casa'in da biyar. Tayi bisimillah, ta fara karanto wurin haddarta, sai dai ba aje ko ina ba, muryarta ta fara rawa, kuka ya ƙwace mata, bai ce mata uffan ba, ya cigaba da kallon ɗaliban, tamkar haddarta yake ji. Sai da tayi sosai, sannan ta cigaba da karatun, tana yi tana share hawaye. "Ba kya son duka meyasa ki ka makara?" Maimakon ta bashi amsa, sai ta sake fashewa da kuka. "Kin ci abinci ne?" Ta ɗaga masa kai alamar eh. "Wani abun suka yi miki a gidan" ta girgiza kai alamar a'a. "To ni wannan haddar taki, ban ji ta sosai ba, dan haka sai kin sake wata, je ki zauna, kuma ki daina wannan kukan" ta jinjina masa kai, ta share hawayenta. Sai dai zamanta ke da wuya, sai ga malam hamza ya shigo da dogon littafi, yana muzurai. Yayi wa malam Jamil magana sannan ya ce "Duk wanda ya ji sunansa, ya tashi ya je gida, kar ya sake zuwa sai ya biya kuɗin term, tun da ba da yawun bakinmu zamu biya malamai ba, tun da iyayenku ba sanin darajar malaman addini suka yi ba, da dai na boko ne. Sunan farko sunanta ya fara kira, ya ce "Ke waliyiyya, duk term sai an kore ki, sai an yi ta artabu kan ki biya kuɗin term, duk wannan uban shirgegen gidan naku, dubu uku a wata uku sai an yi ta fama, tafi gida idan kin karɓo kuɗin kya dawo". Ba wannan ne karon farko da aka koreta saboda kuɗin makaranta ba, sai dai a duk lokacin da aka koretan, ta kan ji ta muzanta ainun. Haka nan ta ɗauki jakarta ta tafi gida, tana zuwa gidan ta tarar da wata babbar mace ta shirya za ta fita unguwa, ita da wata budurwa. "Me kuma ki ka dawo yi, an tashi ne?" "A'a mama, wai kuɗin makaranta aka turo ni na karɓa" Matar ta kwaɓe baki ta ce "Uban naki bayanan ai, tun da kin dawo dama unguwa zan je, maza ki ɗora girkin dare, bana son yin daren girkin nan" ta amsa da to. Budurwar ta ce "Yauwwa Jauhar, akwai kayana a kan gado, dama jibi zan koma school, tun safe nake jiran mai wanki, ya zo ashe ya tafi gida, kya wanke mini, har bedsheets ɗi na, bargona kuma na jiƙa shi, yana baya, idan ya so kan mu dawo idan sun bushe, ko gugar kya rage mini ki goge su". Ta sake amsawa da "To, sai kun dawo" Ta ƙarasa ɗakin da take kwana, ta hau cire uniform, ranta babu daɗi, duk ƴan gidan suna makarantun islamiyyar su, ita kuwa an korota daga ta su, kullum sai an kai ruwa rana kan a biya mata kuɗin makaranta, alhalin sauran har na term uku ana biya musu. Ta canza kayanta zuwa na gida, ta shiga kitchen ta kunna gas, ta tarar ya ƙare, ba ta jira komai ba ta ɗebi itace, ta fita garejin gidan, ta tayar da wuta ta ɗora girki. Ba ta fi shekara goma sha shida ba, amma yadda take sarrafa jikinta tana aiki, kamar wata babba. Tana girki tana wanki, a haka ƴan islamiyya suka dawo, kowa ya watsar da jakarsa, da uniform ɗin sa, masu ball suka tafi, masu wasa suka fita, duk suka sake ɓata gidan, ta bi ta sake tattarewa, ta haɗo kan kayan da suka watsar su ma ta zuba ruwa za ta wanke. *** Fuskarsa murtuk, kamar bai taɓa dariya ba, haka ya tunkari ƙofar gidan, yana wata irin tafiya, mai kama da ta ƙasaita, maimakon ya saka hannu ya buɗe ƙofar gidan, wani irin duka ya yi mata da ƙafarsa, ya shiga ba tare da ko sallama ba. "Wane mara hankalin ne yake dukar mana ƙofa haka, sai ya karya..... Shiru ta yi ta haɗiye sauran maganar, ganin wanda yake tsaye ƙerere a gabanta. "Yaushe ka fito? Ko in ce waye ya fito da kai?" Ko kallonta bai yi ba, ya cigaba da takun ƙasaita, ya je ya tura ƙofar wani ɗaki, ya shiga sai dai babu kowa a ciki, dan haka ya fito ya nufi kitchen. "Al'amin kar ka shigar mini kitchen, ban dafa komai da kai ba, na ga lokacin fitowarka daga prison ma bai yi ba, wannan jaraba da masifa Allah ya yi mini maganinka" ba ta gama maganar ba, ya fito daga kitchen ɗin, da kulolin abinci. Shan gabansa tayi ta ce "Kar ka taɓa mini abinci, abincin ƴaƴana ne da na mijina, bana son tashin hankali Aminu, ka je ka ajiye mini" Take ya juya idanunsa yayi mata wani irin kallo, a take ta ja da baya ta koma gefe, tana bin fulasan hannunsa da kallo. Wani irin fito ya yi, wani daga waje ya amsa masa da fiton, ya fita da fulasan abincin ba tare da ya amsa ko ɗaya daga maganganun da matar ke ta yi masa ba. Jauhar kuwa, kafin magariba ta kammala girkin nan, ta kawwame a flask, sai gyara gidan take yaran suna ɓatawa, da masu hankalik cikinsu da marasa hankalin duk babu mai taimakawa a gyara. Ta ɗauki abincin maigidan ta kai masa ɗakinsa. Tana idar da sallar magariba, ta shirya ta ɗauki jakarta, dan tafiya makarantar dare. Tana fita maigidan yana dawowa, yayi parking ya sauke glashin motar ya ce "Waliyiyya an fito?" Murmushi ta yi, sai da fararen haƙoranta suka bayyana ta ce  "Baba kai ma waliyiyyar zaka ce mini?" "Eh mana, ba haka malamanku suke ce miki ba, za a tafi makarantar ne?" Ji tayi kamar tayi masa maganar kuɗin term ɗin ta na islamiyya, amma ta kasa, mussaman da tuna gargaɗin mama da tayi mata. Ta ce "Eh baba, sannu da zuwa, na kai maka abincinka ɗaki ma, kana zuwa sai dai ka ci" Yayi murmushi ya ce "To Allah ya yi albarka, a kula sosai ayi karatu da kyau" Ta ce "In sha Allah" ta wuce makaranta shi kuma ya gyara parking. Gudun kar ta makara a makarantar dare, ya sanya ta fita ba ta ci abinci ba, duk da yunwar da take ji, ta ce idan ta dawo sai ta ci. Sai dai bayan dawowartata, ta tarar da an cinye komai. Cikin girmamawa ta ce "Mama an cinye abinci ne?" Mama ta kalleta ta ce "Au ba ki ci ba dama?". "Eh, na rana ma ban samu ba, na rufe nawa saboda kar na makara na tafi makarantar dare". "Eh to ai yayi kyau, al huda huda ina da littafi, to an cinye ki zuba ki ci kan ki tafi ba zaki iya ba, duk salon ace zaluntarki ake yi ba a baki abinci, kin wa kanki ai, ni ki hanzarta ki yi wa yara gugar uniform, tun da ga wuta, kar a ɗauke" Ran jauhar ya sosu rashin samun abincin nan, dan har ga Allah tana jin yunwa sosai da sosai, sai dai babu yadda ta iya, dole ta shiga ta kwaso tulin guga ta hau yi. Tana gugar nan zabga-zabgan ƴan matan gidan suna kawo mata karon nasu, har wurin sha biyu na dare tana abu ɗaya, ga cikinta sai ƙara yake yi tana hamma, ga bacci da gajiya, ga kuma yunwa. Bayan ta kammala guga, ta bi manyan ɗakunansu ta ba su, ta kai na sauran yaran ɗakin iyayensu, sannan ta koma ɗakinta, ta yi alwala tayi sallar isha'i, ta yi shafa'i da wuturi, ta nemi ta kwanta. Ba ta yi mintuna goma sha biyu da kwanciyar ba, ta jiyo ana ƙwala mata kira a tsakar gida. Haka ta sake yinƙurawa, ta fito matashin saurayi ne, tsaye hannunsa riƙe da leda ya kalleta ya ce "Kin fara bacci ne?" Ta ce "A'a yaya, idona biyu" "To ga indomie nan, faka-faka dafa mini dahuwar nan taki, mai muslmin daɗi, akwai gasashshiyar hanta a ciki da ƙwai, na san akwai attaruhu da alabasa a gidan, tayi yaji fa sosai" Ta karɓa ta ce "amma yaya da daddare nan ka ci yaji ka kwanta, ulcer fa" Zare mata ido yayi ya ce "Sai kin saka an yi mini faɗa ko, maza dafota ƙwan nan fa ya soyu shi ma" Tayi murmushi ta koma ta sake gangamin haɗa wutar da ƙanan itace, dan kuwa, ta riga ta kashe murhun, kuma ba ayi refilling ba. Kasancewar a gareji take girkin, sauro yayi mata rubdugu da cizo, sai da wutar ta kama sosai, hayaƙi ya kore su. Sai da ta gama tana juye masa, sai gashi ya shigo, hannunsa da leda ɗauke da lemon roba mai sanyin gaske. "Yauwwa waliyiyya, Allah dai ya tuttula miki albarka, ya baki miji nagari" ta sunkuyar da kai cikin jin kunya. Ya samu wuri ya zauna, ya ce "Samo plate ki ɗiba, sai ki jiye mini sauran" "A'a ni fa a ƙoshe nake, ka bari na lashe tukunya, ka san ina son romon indomie" Yayi murmushi ya ce "Ke ce romon ai" Ya zuba mata a tukunyar, ya datsar mata ƙwan, jikinta har tsuma yake yi, tana hannu baka hannu ƙwarya, ba tare da ta san tana hakan ba. Yadda ya lura tana ta suɗar kwanon, ya san babu lallai ta ci abinci yau, dan haka ya sake tura mata ta gabansa ya ce "Ungo na ƙoshi" Ta ɗan yi saroro ta ce "Yaya Saifu ba daɗi ne?" "Ina fa, ke kin san duk duniya, babu wanda ya kai ki iya dahuwar indomie, ƙoshi nayi kawai, ki hanzarta ki gama ki je ki kwanta, dare yayi" Ta karɓa ta yi masa godiya. Sai dai tana gama ci, wani matashin da zai girmewa saifu ya fito, ya zube mata kayansa na ƙwallon ƙafa, har da takalmi, sai tsamin rana da warin hammata suke yi, ya ce ta wanke masa kafin ta kwanta. Kamar saifu yayi magana, amma yayi shiru ya fasa. Ƙarshe ba ta kwanta ba, sai ɗaya da rabi na dare, shi ma ko da ta tuna, kwanaki kaɗan suka rage mata jinin al'ada ya zo mata, gashi ba ta da audugar tare jini, ga kuma kuɗin makarantar islamiyyarta, babu shiri ta fasa kwanciyar, ta ɗaukko kwanon da take zuba dutsen da take shiri da shi, ana biyanta, tana tara ƴan kuɗi, duk da shirin ba wata riba ce da shi ba, amma yana taimaka mata sosai. Tamkar mai shirin hawan aljanu, haka ta haƙiƙance, tana zuba masa bala'i, "Wallahi ba zai yiwu ba, dole ka zaɓa ko ni ko ɗan ka, idan har zai cigaba da shigowa gidan nan, to wallahi ni zan bar shi, dan ba zai illatani da yarana a banza ba, ko ya lalata mini ƴaƴa ba. Sanin kanka ɓaras ya karya mini ɗa, Allah ne yayi da sauran rabon Musa ya taka ƙafarsa a duniya, ga ni da yara mata, ya din ga shiga yana fita, ba ma wannan ba, yadda ya yi ƙaurin sunan nan a duniya, tsaf zai hana mini  ƴaƴa auruwa, to wa ma zai zo ƙofar gidan nan zance, yana tsoron a raba shi da rayuwarsa, ba zai yiwu ba gaskiya". Ya numfasa ya ce "Rahila, da wani idon ki ke so duniya ta kalle ni? Idan na kore shi na hana shi zuwa gidan nan, yana da in da ya fi nan ne?" "Idan ba shi da shi ka nema masa, ni fa ba zan cigaba da rayuwa da tantirin ɗan daba a cikin gida ba, ya sabauta mini rayuwata da ƴaƴana ba, Allah ya mayar da shi kurku ya dauwwama a can kowa ya huta, ina dalili za a hana ni rawar gaban hantsi, mutum ba tarbiyya duk na sangarta shi, an mutu an bar mutane da masifa da bala'i a bayan ƙasa, me ake da ɗa irin wanda zahra'au ta mutu ta bari, Aminu ai cikon asara ne a cikin al'umma, wallahi ta yi asarar haihuwa". Yana tsaye a bakin ƙofar shiga falon, yadda ta ɗaga murya, ya sanya ya ji komai, zuciyarsa ta din ga wani irin hanƙoro, wani abu mai masifar ɗaci ya din ga taso masa. Ya saka hannu ya danƙe handle ɗin ƙofar iya ƙarfin sa, saboda muddin ya shiga cikin falon, yadda yake jin sa a saman nan, ya cake da wiwi, babu abun da zai hana shi ɗaga matar nan, ya buga da ƙasa. Ya kasa gaba ya kasa baya, shi bai shiga ba, kuma bai bar wurin ba, kunnuwansa suka cigbaa da karɓar miyagun maganganun da take faɗa a kansa. Ƙarar da handle ɗin ya bayar ne, ya sanya su juyowa su kalli bakin ƙofar, ɓaras ya karya handle ɗin nan, duk ƙwarin sa, ya fara yi mata wani irin kallo, da ta kasa gane ma'anarsa. Ayshercool 08081012143 🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143* Da sauri ta ɓuya a bayan maigidan, hantar cikinta na wani irin kaɗawa. Ya nuna kansa da yatsansa ya ce "Haihuwata ce asara ko? Ni?" Cikin tsawa ya ce "Kai aminu, ya isheka haka, kar ka kuskura ka aikata wani rashin mutunci, ko ka ce zaka yi mata wani abu, koma menene ba kai ka janyo ba, ka nustu ka zama mutumin kirki mana, kalli yadda ka yi shuhura a shashanci da harkar sara suka, ni kaina ban so fitowarka ba wallahi, yanzu zaka zo ka cigaba da ɗaga mini hankali, ka hana ni zaman lafiya da iyalina, dan haka ka bar mini gida, kar ka sake shigo mini gida, ba na buƙatar ka". A hankali ya saki handle ɗin ƙofar da ya karya, ya kalli mahaifinsa ya ce "In daina zuwar maka gida, Abbu ina zani? Wurin wa zan je?" "Ka je duk in da ya yi maka, ko wurin ƴan iskan da suka ka ke jin maganar su sama da tawa, amma kar na sake ganinka a gidana" Yayi murmushi mai ciwo, ya ce "Shikenan, zan tafi zuwa lokacin da huce zan dawo" "Ba na buƙatar dawowarka, tun da ban isa da kai ba, ka je ka ƙarata" Tuni idanunsa suka rine, zuwa launin ja jawur "Ba a canza tuwo suna, ba ni da wanda ya kai ka ko ya fika, ba ni da gidan da yafi nan, dan haka ba zan daina zuwa gidan nan ba, amma idan ka matsa zan tafi, idan kuma na tafi na bar shi kenan har abada, wani aiki aka fito da ni na yi, da yiwuwar idan na gama aikin, na koma gidan yari, komawar da ba zan sake fitowa ba, sai ku huta da ganina" ya ƙarasa maganar kafofin gashinsa na mimmiƙewa saboda ɓacin rai. Rahila ta ce "Allah ya raka taki gona" Juyawa ya yi ya fice, har da sassarfa, dan yanzu abun da zuciyar sa ke raya masa, ba iya ya bugata da ƙasa bane, ya raba maƙogwaronta da wuƙar ƙugunsa haka yake ji. Tafiya kawai yake yi, yana tunani barkatai a cikin zuciyarsa, har ya ƙarasa in da yake son zuwa. Suna ganinsa suka mimmiƙe tsaye, sun risunar da kawunansu, tamkar dai yadda ake yi wa shugabbani, a wurin shugabancinsu, ba tare da ya ce komai ba ya zauna, yayi shiru. Liti ne yayi gyaran murya ya ce "Allah ya taimaki mai dogon zamani, menene damuwarka ne?" Al'amin yayi shiru, dan shi bai san me zai ce ba ma. Ba yadda ba su yi da shi ba, amma yaƙi magana. Liti ya miƙo masa wani satchet ɗin magani, ya ce "Ga wannan ka sha rabi, yanzu za ka ji ka ɓata, ka manta komai, wasu ƴaƴan matsalarka duk za su sauka, daga hau ka saukko za ka ji komai ya goge" Ya saka hannu ya karɓa, yana jujjuya satchet ɗin. "Ka saka ɗaya a ƙasan harshenka, shikenan". Ya ɓalli ɗayan ya saka a ƙasan harshen sa, ya jingina da bango, zuciyarsa na cigaba da tafasa. Sai dai bai fi mintuna sha biyar ba, idanunsa suka fara lumshewa. Yayi gyaran murya ya ce "Liti" Liti ya ce "Boss". "Chairman ya fito da ni saboda na yi masa aiki, ya ce na je yana son ganina, zai gaya mini aikin da zan yi masa, sai dai kafin na yi masa aikin zan yi nawa, ko da kuwa zan koma gidan yari ban yi nasa ba" "Allah ya taimaki maza, wane aikin ne, a shirye muke mu yi maka ko menene" Ya jinjina kai ya ce "Madaki zan kashe! Sai na kashe madaki!!" Liti yayi turus ya ce "Maza, duk lokacin da muka yi yinƙurin ɗaukar fansar nan, wahala muke sha madaki fa har tsafi yake yi wallahi, ya gagaremu" Ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa ya ce "Shhhh, ni bai gagare ni ba, zan kashe shi na koma gidan yari" Liti ya ƙura masa ido sannan ya ce "Maza ko ƙwayar ta fara yi maka aiki ne?" Ya buɗe idanunsa da suka yi ja, ya kalli liti, sannan ya mayar ya lumshe su a hankali, bacci yayi awon gaba da shi. *** Rana ta take sosai, ƴan makaranta na ta ɓullowa da ga lungunaa da titunan unguwannin. Sosai jauhar take sauri, ta je gidan da take yi musu shirin dutse, ta kai wanda ta yi, ta karɓo wani su bata ƴan kuɗaɗenta. Babban layi ne sosai, ababen hawa na kaiwa suna komowa, ta tabattar babu abun hawa, wata danƙareriyar mota, ta shawo kwana a guje, ba tare da ko yin horn ba. Gaba ɗaya ta ruɗe, ta kasa gaba ta kasa baya, kawai ta tsaya ta ɗora hannunta a kan ta, tana maimaita lahaula wala ƙuwwata illa billah. Da ƙyar ya iya cin burki, ya fito a fusace mutumin, babban mutum ne sosai, ya kusa sa'an Baba ma, ya hau ta da faɗa "Ba kya gani ne, wannan wani irin rashin hankali ne?" Ta kalleshi da fararen idanunta ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi na duba ban ga mota ba, ka yi haƙuri dan Allah" Mutanen wurin da suka saddaƙar sai ya buge Jauhar, suka taso suna salallami, sai dai aka rasa me nuna masa shi ne yayi kuskure, saboda uwar shaddar da ta bi lafiyar jikinsa ta kwanta. Sai kuma jikinsa yayi sanyi, ganin yadda take ta bashi haƙuri, duk da shi ne mara gaskiya, pressure da yake ciki da tension ne ya sanya shi hucewa a kanta. Sai kuma ya kwantar da murya ya ce "Ki yi haƙuri, ai ba ki ji ciwo ba ko?" Ta ce "Babu abun da ya same ni" daga haka ta tsallaka ta shiga layin da take son shiga. Kusan dozen biyar tayi na shirin, aka bata naira ɗari da hamsin, ta kuma karɓo wani tana lissafin saura ɗari biyu da hamsin, ta samu kuɗin pad, wanda magana ake ta saura ƴan kwanaki jinin ya zo. *** Al'amin ne zaune a kan kujera, yana wasa da zoben azurfar hannunsa, Indabo yana ta bayani, amma sam hankalinsa ba a kansa yake ba, dan bai san me ma yake faɗa ba. "Aminu magana nake fa" Ya ɗaga idonsa ya kalle shi ya ce "Ina jinka" "Yaƙin neman zaɓe da zan je, ina son a zubar da jini ne, a tayar da tarzoma ayi hatsaniya sosai da sosai, sai kuma ranar zaɓe" Ba tare da ya kalle shi ba ya ce "Shiyasa ka fito da ni, saboda zan yi maka aiki shi ne ka fito da ni ko?" "Eh saboda haka ne, kai ne ba ka ji, ka fiye rigima, na yi na yi ka fita sabgar madakin nan, ka haƙura, amma kamar annabi da kafiri, kullum cikin harin juna ku ke, kai ne faɗa a nan kai ne a can, wai fa har sayen rigima ka ke yi" Ya katse shi da cewa "Nawa zaka biyani?" "Zan baka dubu hamsin kai da yaranka". "Ɗaurin shekara biyar a gidan yari, shi zan yi a dubu hamsin ni da yarana, ka duba babbar kasada ce" Indabo ya yi murmushi ya ce "Baka da matsala in dai kuɗi ne" Ya tashi tsaye ya ce "Kamar yadda ka yi a wannan karon, ka neme ni kai tsaye, haka nake son ya cigaba da kasancewa, ba na buƙatar sanya wani P.A ɗinka ya neme ni, ya sanar mini da saƙonka" "Na fahimta, ka san mu ƴan siyasa dole sai muna yi, muna ɓad da sahu, baka da matsala". Al'amin ya jinjina kai, ya sa kai ya bar falon, cikin takun ƙasaita. ***** Saifu ne ya shigo gida, wajen ƙarfe uku da rabi, ya tarar da Jauhar tana wanki a tsakar gida, gidan babu kowa, yaran duk sun tafi makaranta. Ta ɗago ta ce "Yaya sannu da zuwa" Ya amsa da Yauwwa "Ina makarantar islamiyyar?" Shiru ta yi ta sunkuyar da kai, ba ta amsa masa ba. "Da ne nake fa" "Amm..dama ban biya kuɗin makaranta bane, sun ce kar na sake zuwa sai na biya" "Kuna kin gaya wa Baba?" Ta girgiza kai alamar a'a. Cikin takaici ya ce "To saboda me?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba. Saifu ya ce "Ke dai sokuwa ce wasu lokutan, dubu uku ne ko? Tashi ki saka uniform ki tafi" yayi maganar yana ciro kuɗi daga aljihunsa, ya miƙa mata dubu uku. Fuskarta ta faɗaɗa da murmushi, ta saka gwiwoyinta a ƙasa, ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode sosai da sosai yaya, Allah ya ƙara arziki". Ya ce "Amin, bar wankin, tashi maza" Ta ce "To kar maman su Hafsa ta dawo ban gama ba, labulayenta ne" "Ajiye, su hafsa idan sun dawo su wanke mata, maza ki tafi". Cikin murna ta tashi, ta tattare kayan wankin, ta shirya cikin uniform ɗin ta, ta tafi islamiyya. Duk da yau ma sai da aka zane ta, sannan ta shiga ta kai kuɗin makarantar tana ta kuka, dan ba ta ƙaunar duka sam. Sai dai duk da kukan da tayi, hakan bai hanata farincikin ganin ta koma makaranta ba. Sai dai bayan ta koma gida, Anty ta rufeta da bala'in ta tafi ta bar mata bedsheets ɗin da ta saka ta wanke mata. Jakarta kawai ta ajiye, ta hau wankin da aka sakata, bayan ta sha uban zagin tsamar nama, ita duk hakan bai dameta ba, ta kammala wankin sauran bedsheet ɗin, ta wanke kwanuka ta mayar da abincin dare. Duk ƴan matan gidan suna zaune, itakaɗai take aikinta a tsakar gidan, idan baƙo ya zo sai ya yi zaton mai aiki ce. *** Yau tun a makarantar boko, Jauhar ta ji period ya zo mata, gashi kuɗin pad ɗin nata saura ɗari da hamsin ba su gama cika ba, sai kame jikinta take yi, saboda tsoron kar jini ya ɓata ta. Da ƙyar ta isa gida, tana ta lissafin yadda za ta yi, gashi idan ta yi amfani da tsumma, lalata mata fata yake yi, ƙuraje duk su feso mata, ta rasa in da zata saka ranta. Haka ta wuni tana fama, ga uban ciwon mara, kamar tayi hauka, dan ma ta samu paracetamol a wurin Yaya saifu ta sha, ga uban aiki dan babu mai ɗaga mata ƙafa, haka nan ta saka tsumman, take amfani da shi, idan ba haka ba ta san haka za ta yi ta staining. Da magariba, tana zaune a tsakar gida, ta cinye ɗan abun da ta samu ta ci, wanda sam ba ta ƙoshi ba, duk da ita ta girka, sai lashe hannu take yi, Baba yayi sallama. Aka din ga jera masa sannu da zuwa, yana amsawa. Ya kalli Jauhar ya ce "Waliyiyya ya na ga kina suɗe hannu, ba ki ƙoshi bane?" Tayi murmushi ta girgiza masa kai ta ce "Alhamdilillah, na ƙoshi baba". Ya ce "To madalla, Allah shi ne abun godiya, akwai wani mutum da ya zo wurina yayi mini maganarki, ban sani ba, ko ke ki ka turo shi" Gaban juahar ya faɗi, ta kalli in da mama ke zaune a kan tabarma, ita ma tana cin nata abincin. Sau ɗaya saurayi ya taɓa biyota gida, mama ta ce idan wani ya kuma zuwa wurinta, ko ta bawa wani damar ya zo wurinta, sai ta kusa halakata, yayyenta ba su auru ba, ba za ta fara kawo musu maza ba, duk da dama shekarun nata ba yawa ne da su ba, haryanzu a SS2 take shekara goma sha shida, sai dai hasken fatarta ke ɗaukar idon samari ƴan bana bakwai, su biyota wai suna so, saboda kashedin mama ta koma saka niƙab. But Anty, babar su hafsa ta fito daga ɗakin ta, tana jiran ta ji ƙarashen maganar. Mama ta ce "Ba magana ake yi miki ba?" Jauhar ta girgiza kai ta ce "A'a Abba, wallahi ban san kowa ba, ban turo kowa wurinka ba" "Ƙarya ki ke yi, zaki aikata, ba abun mamaki bane ba kina halin kule-kule a waje, dan a zahiri kina da fuskar tsoron Allah, amma a baɗini ba kya ji" Anty ta ara ta yafa ta ƙarar da zancen. Baba ya ce "No, shi ma ya gaya mini, bai yi mata magana ba, ya zo ya fara samuna ne, na dai tambayeta ne kawai dan na tabattar, zan bashi dama ya fara zuwa wurinta, dan naga da gaske yake yi." Dumm ƙirjin Jauhar ya buga, ta fara zance yanzu, makarantar kuma fa, ga burinta na son yin karatu, duk da aure ba ya hana karatu, to amma idan wanda zata aura ɗin ba zai bari ba fa?. Da sauri mama ta tashi ta bishi ɗaki, tana yi masa magana "Yanzu aurar da jauhar ɗin zaka yi, ga yayenta duk a jibge, su kusan biyar babu wadda ka aurar?" Ya tsaya ya kalleta ya ce "To laɗifa, tara su zamu yi tayi ba zamu aurar ba? Tun da ita Allah ya fara kawowa sai mu fara da ita, ita ma ta huta" A take ta haɗe rai ta ce "Ban gane ita ma ta huta ba, na fuskanci duk lokacin da magana irin wannan ta tashi, sai ka nuna kamar bana ƙoƙari a kan riƙonta, kamar zaluntar ta nake ko?" Kamar yaronta ya ce "A'a bance ba" "To wallahi ba za ayi wa jauhar aure ba, ga su Sajida ba, wannan ai cin mutunci ne". Yayi mata shiru, bai sake cewa komai ba, ya ƙuduri aniyar, aurar da jauhar ko ba ta so. *** A tsakar gida ta tsaya tana ta kwaɗa sallama, daga cikin falon aka amsa mata, wata matashiyar mata ta fito. Suna ganin juna suka rungume juna, suna murna. "Zakiyya Bala, yau ke ce a gari?" "Wallahi kuwa Rahila". "Ya aka yi ki ka gane gidan nan? Kin san lambarki na rasa". Zakiyya ta ce "Ke wayata aka sace mini, tun da na canza layi na rasa lambarki nima, ai da Abba na haɗu a bakin titi, ya ce mini ai kun jima da dawowa unguwar nan, bamu da wani nisa bamu sani ba". Rahila ta ce "Allah sarki, shigo daga ciki, shegiyar ƙawata, na yi missing ɗinki fa" suka shiga suna dariya. Ta kawo mata ruwa da lemo ta ajiye, Zakiyya ta kalli gidan ta ce "Ikon Allah, nan ku ka dawo kenan?" "Wallahi kuwa, ai yanzu ba abun, tun da aka damfare shi ɗin nan, lamuran sai godiyar Allah, amma a hakan ma ai bamu tagayyara ba" Zakiyya ta ce "Gasakiya ne, Allah ya ƙara rufa asiri, ina su kursum?" "Duk suna makaranta, kin san tana level 3 ita yanzu, ina su hafsa, haryanzu babu labarin aure ko?" "Haba Rahila, yaushe za ayi auren su Hafsa ba ki ji labari ba, wallahi babu shiru, abu kamar saka hannu, har na fara zargin uwargidana, sai na ga ita ma ga nata nan biyu, Sajida da surayya, suma babu ana ta shige-shige shiru, dan ma ni da ita kar ta san kar ce, an daɗe ana gogawa taga babu riba, na sha gabanta shi ne ta sarara mini". Rahila ta ce "Subhanallah, kin ga nima ana ta fama, duk wanda ya zo kamar walƙiyya sai ya tafi, ni kuma ba zan bawa talaka aure ba wallahi" "Ba ke kaɗai ba Rahila, kin ga yaran nan, har mai suka shafa, sun yi ɗas sun zama farare, kwalliyar nan, supplements ɗin nan, na gyara dai, amma ba tsayayye duk sai shirmanmu" "Ki daina damuwa fa, lokaci ne" "Wallahi haka ne, ba ki san wani abun takaici ba, wai sai yarinyar nan, ƙanwar bayansu, jauhar ƴar bafulatanar nan da ya taɓa aura kwanaki, aka rabu tsiya-tsiya ƴar da ta mutu ta bari, wai ita wani ya ce yana so da aure, yarinyar nan sai da Laɗifa ta shiga ta fita, ko suturar kirki ba ta sakawa, wai amma a haka wani ya gani yake so, kin san ita ya bawa riƙonta" Rahila ta kwashe da dariya ta ce "Ai wasu lokutan maza ƴan wahala ne, ga in da ya dace su je, amma wani wurin suke kai kan su. Ni kaina ga nawa ɗan riƙon ya sani a gaba, ɗan gidan zahra'u tsinannen yaron da asiri baya cin sa, babu irin kurciyar dan ban saka ayi masa ba, amma abu ya gagara". Zakiyya ta gyara zama ta ce "Ke haba? Al'amin ko" "Shi, ai ya zame mini bala'i Zakiyya, ya zama riƙaƙƙen ɗan daba da shaye-shaye, za ki ji matasa suna mai dogon zamani shi ne fa" Zakiyya ta dafe kai ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ke ina jin labarinsa har a radio, dama shi ne, amma lokacin kina amarya kamar a nutse yake" "Ke rabu da ni oho masa, ni sonake ya bar gidan nan, kar ya hana mini ƴaƴa auruwa, ko ya illata wani, dan Abba da ki ke gani ɓaras ya karya mini ɗa kamar kara. Kina kallon halin da muke ciki, yanzu babu bushasha kamar da, ɗan abun da ta bari ya gada, ubansa ya fito da shi, ya ƙara jari, yaƙi wai ba zai taɓa masa kaya ba, kin ga da zai bar gida a neme shi a rasa ai ma samu mu ci, babu irin korar da ban saka ya yi masa ba, amma yaƙi tafiya". Haka suka cigaba da hirarraki, wadda galibi a kan rayuwar makaranta da suka yi, sai na iyalinsu hirrar take. Kusan sati biyu, da maganar da baba yayi, a kan wanda ya zo wurinsa a kan jauhar, yayi shiru da maganar kamar ta wuce, ya dawo da yamma, kasancewar juma'a ce, jauhar ta duƙufa tana ta shirin dutse. Kuɗinta da suka taru ba ta samu ta sai pad ba, sai ta sayo riɗi, ta ce zata soya ta juya kuɗin, idan suka taru ta saya da wuri. A tsakar gida baba ya tsaya, ya ƙwala mata kira, ta amsa ta fito ta tsuguna. Ya kalleta ya ce "Ki shirya, ki je ga baƙonki can a waje ya zo ku gaisa". Ji tayi kamar ta fyalla da gudu, ta tsaya da saurayi, ya ce mata me, ko ta ce masa me? Amma ta amsa masa, ta tashi ta shiga ɗakinta, jikinta duk yayi sanyi. Sajida ta shiga falo in da su surayya ke kallon Bollywood. "Kai kuna nan kuna kallo, baba fa da gaske yake auren jauhar zai yi muna zaune" Surayya ta ce "Kamar yaya?" "Kamar yadda na gaya muku, wallahi wai wani ne wai yake son ta" Hafsa ta ce "Da yardar Allah ba za ta yi aure ta barmu ba". Jauhar kuwa turus ta yi, tana kallon ƙatuwar motar da ke ƙofar gate ɗin gidan an yi parking ɗin ta. Zura kai ta yi tana lelleƙawa ta ga waye baƙon. Ya buɗe ƙofar motar ya fito, yana murmushi. Turus ta yi tana kallonsa, ya yi murmushi ya ƙaraso ya jingina da jikin motar, ya ce "Mayar da idon mana, kin yi mamakin ganina ko?" Da sauri ta durƙusa ta ce "Ina wuni?" "Lafiya ƙalau Faɗimatul Jauhar" Ya ɗan gyara tsayuwarsa ya ce "Na san dole zaki yi mamakin ganina, zuwa na yi na sake bayar da haƙuri, a kan incident ɗin da ya faru, na tsorata ki da na yi, na kusa buge ki da mota" Jauhar ta ce "Ai bakomai ya wuce, na ma manta" "Ai ni ban manta ba, dan sai da na koma wurin da muka haɗu, na tambayi ina ne gidanku, na samu baba muka yi magana, hankalina ba zai kwanta ba, har sai na aure ki, na kai ki gidana, na rarrasheki da kyau" Jauhar ta sunkuyar da kanta, tana jin abun wani banbarakwai. Ita gaba ɗaya ma ji take yi ya takurata. "Jauhar" "Na'am" ta amsa tana kallonsa da idanunta da suke farare tas, sai dai ba manya ne can ba. "Me ki ka ce? Ni aurenki nake son na yi, kuma nan kusa wallahi ba da nisa ba, na yaba da tarbiyarki fiye da yadda ki ke tunani". Kamar za ta yi kuka ta ce "Ai ban gama makaranta ba, ni yarinya ce kai kuma babba ne" Dariya yayi ya ce "Wow, ashe shagwaɓaɓɓiya ce har haka? To dan ni babba ne ba za a aure ni ba? Kar ki ce haka, zaɓin Allah ake nema kin ji sweetheart, ki yi ta addu'a Allah ya tabattar mana da alkhairi. Ina da mata ɗaya da yara biyar kacal, yaro ne ni haryanzu" yayi mata maganar yana kashe mata ido ɗaya. Ita kam gabanta ne ma ya faɗi, yara biyar ne kacal, ita duk wata harka da za ace kishiya, tsoronta take ji. "Kar in cika ki da surutu, bani lambar wayarki, a hankali zamu saba, kin shiga raina sosai, zan yi iya ƙoƙarina na baki kulawa dai-dai iyawa ta, kuma karatunki, in sha Allah sai kin ce kin gaji dan kanki" yayi maganar yana miƙa mata wayar ta saka masa lambarta. "Bani da waya ai" Ya ce "Ohh, ashe fa ƴar baby ce, ba ta isa riƙe waya ba, zan kawo waya in sha Allah" "A'a dan Allah kar ka kawo mini, ba ma za a bari na riƙe ba" "To ikon Allah, to ta ina zan din ga jin muryarki? Amma shikenan bai kamata na karya dokar gidanku ba, zan san abun yi na nemi iznin baba na kawo wayar. Amma baki tambayi sunana ba" Ita dai tayi shiru, tana mamakin yadda babban mutum kamar wannan, yake ta kashe mata murya. "Sunana Alhaji Mu'azzam. Ina dillancin kayan sawa, mussaman na mata, ina shigo da kaya daga ƙasashe daban-daban, kuma ni ɗan siyasa ne, yanzu haka ina da muƙmi a gwamanati, amma ba dai wannan ba, ni amincewarki nake nema, kar ki yi saurin rejecting ɗina ki yi mana addu'a kin ji zahrana" Jauhar dai ta yi gum, ita wannan tsayuwar ma kawai, kunya take bata kamar ta falfala da gudu. Haka ya gama surutansa, ba komai take fahimta ba, lissafi kawai take a zuciyarta, saura dozen nawa ta gama shirin dutse, ta kai ta karɓo kuɗin, ta cika ta soya riɗi. Kuɗin da ya miƙo mata, ya sanya ta ja da baya, tana girgiza kai. Ya kaɗa ya raya, amma fafur ta ƙi karɓa, sai haƙura yayi. Haka yayi mata sallama ya tafi, da sauri ta shiga gida, dan kuwa Alhaji mu'azzam duk ya cinye mata lokaci, ba ta ƙarasa shirinta ba, mugun kallon da ta tarar da ƴan matan gidan na yi mata a tsakar gida, ya sanya ta shan jinin jikinta, dan kuwa tuni yaran gidan suka kawo musu tsegumin irin motar da aka zo wurin Jauhar da ita. Sai jikinta yayi sanyi, ta hau tunanin laifin me tayi? Jiki a sanyaye ta ɗaukko aikinta ta cigaba. Sai dai suka din ga zaginta babu dalili, hafsa ta saka ƙafa tayi fatali da ɗan plate ɗin jauhar da take zuba dusten. Hankali a tashe ta ɗaukko tsintsiya tana tattarewa, ba tare da ta damu da son sanin dalilin da ya sa hafsan tayi mata haka ba, domin kuwa idan da sabo ta saba. Yaya saifu da ya fito daga banɗaki ne, ya ɗurawa Hafsa ashar, saboda ya ga abun da ta yi hafsa. Babarta ce ta fito tana yi masa masifa, tana kare hafsa, da mayar masa da zagin da yake yi mata. Aikuwa mama ma ta fito ta haushi da bala'in menene ruwansa da shiga abun da babu ruwansa, nan faɗa ya harƙe, sum-sum jauhar ta ja jikinta ta koma ɗaki. Da daddare bayan sallar isha'i, baba ya kira jauhar ɗakinsa, ya tambaye ta yaya suka yi da baƙonta, amma ta kasa magana, sai duƙunƙuna hannunta da ta din ga yi a hijjabi. "Jauhar" Kanta a sunkuye ta ce "Na'am baba". "Ba zan yi miki dole ba, ban bawa mutumin nan damar zuwa wurinki ba, sai da na yi bincike a kansa, na san makarantar ki ke tunani, ina mai tabbatar miki ya tabattar mini zai bari ki cigaba. Bana jin daɗin irin rayuwar da ki ke yi a cikin gidan nan, babu yadda zan yi ne. Amma idan ba kya son sa, ba zan yi miki dole ba, ki bi komai a sannu, ki yi istikhara da addu'a, na san ke mai yawan addu'a ce, da miƙa lamuranta ga Allah, ki ƙara dagewa sosai da sosai, ki nemi zaɓin Allah" "To Baba in sha Allah" "Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya yi miki albarka, ya sa naga jikokina ƴan farare masu kyau kamar jauhar ɗina" rufe fuska tayi ta ƙunshe fuskarta tana murmushi. Tun da ya shigo layin, wasu daga matasan layin ke darewa, suna ɓuya, ko a jikinsa, tafiyarsa yake yi cikin hanzari da ƙasaita, sumar sa ta cika masa kai, ya aske wani wurin ya bar wani, irin cikakken mara jin nan. Kai tsaye ya buɗe ƙofar gidan, ya kunna kai cikin gidan. Babu sallama ba komai, ya kutsa cikin falon in da suke zaune suna karyawa. Abbu ya ɗaga kai ya kalle shi, ya ce "Uban me ka zo yi mini gida? Me na gaya maka a kan zuwar mini gida?". Ya sunkuyar da kai ya ce "Ganinka na zo na yi na gaisheka" "Ba na buƙatar gaisuwarka Al'amin, ai tun da ka zaɓi watsewa a duniya, ka yi fatali da tarbiyarka nima na sallamaka, ka koma wurin abokanka ƴan wiwi da suka fi ni a wurinka. Kalli tsinannen askin da yake kanka, ka zo mini banda warin wiwi babu abun da ka ke yi, sanna ka ce ka zo gaishe ni? Ai ni na barwa duniya kai ka tashi ka bar mini gida" Yayi shiru yaƙi tashi, kuma ya ƙi magana, sai murza zoben azurfar hannunsa da ƙarfi da yake yi, zuciyarsa na zafi. Rahila ta ce "Dan Allah ka fita Aminu, wannan warin da ka ke yi, zan iya amai wallahi, kuma ni idan ina ganinka tsoro nake ji wallahi, tun da kullum a buge ka ke kar ka illatani ko yarana a banza" tamkar tana magana da dutse, haka yiyin gingirin gim, bai motsa ba. "Ba magana ake yi maka ba?" Yayi masa maganar cikin tsawa. Al'amin ya ɗaga idanunsa, da suka yi ja fiye da lokacin da ya shigo, ya ƙara matsawa kusa da mahaifiyar, ya zuba masa ido sannan ya ce "Na san ina wari, na san kullum a buge nake, a kowane lokaci zan iya ɗaukar makami na hallaka duk wanda ya yi gaba da gaba da ni, ko wanda bai ji ba bai gani ba. Wasu lokutan ma banbancina da mara hankali kaɗan ne, na san ba na jin magana ko kaɗan, bana tsoro ko shakkae aikata duk wani abu da zuciyata ta raya mini, amma idan ban zo wurinka ba wurin wa zan je? Da haka nake? haryanzu ban san laifina a wurinka ba Abbu, zan yi ƙoƙarin daina zuwa gidan nan kamar yadda ka buƙata, ko aka ce maka ana buƙata, amma idan na daina na daina kenan har abada wallahi! Ka huta lafiya" yayi maganar yana shafar saman hannun mahaifinsa. Yana miƙewa zai wuce, yayi ball da flask ɗin ruwan zafin da yake tsakiyar wurin, da kwanukan. Gaba sai da suka razana. Ta ce "Ka gani ko?" Shiru mahaifin Al'amin yayi, ya tashi da sauri ya bi bayansa, sai dai yana fitowa daga falon, ya ga an jefo Abba, babban ɗan Rahil, ƙaton saurayi amma kamar an watso shara. Ko ba a gaya masa waye ba, ya san aikin Al'amin ne, Abba kuwa bajewa yayi, ko shurawa ba ya yi, rahila ta fito tana kururwa. Abbu ya leƙa waje da sauri, a can ƙarshen layi, ya hango Al'amin, ya zare wuƙa yana ta zuba sauri. Ya rufa masa baya, yana ƙwala masa kira, amma ya ƙara sauri har da gudu, ya bar layin. Ayshercool 08081012143 🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143* Ganin Aminu ya ɓace masa, ya sanya ya koma gida da sauri, rahila sai kururwa  take yi, tana jijjiga Abba. Ƙannensa mata su azima, suka kewaye shi suka hau kuka. Abbu ya ɗebo ruwa, ya din ga zubawa Abba, har Allah ya sa ya buɗe ido. Cikin kuka take cewa "Ka gani ko? Ba zaka taɓa yadda da ta'addancin ɗanka ba, har sai ranar da ya kashe mini ƴaƴa, me yayi masa zai yi masa wannan ɗibar karan mahaukaciyar ya watsar? Wallahi na gaji, ina ga tafiya zan yi na bar maka gidan nan kai da ɗanka, na rasa uban me yaron nan yayi masa, ko dan ba kai ka haifi abba ba, ya tsane shi daga shi har nazifi ni ban sani ba. Ni ba abun na kai shi ƙara wurin hukuma ba, ba sa yi masa komai sai dai a sako shi, ni na gaji". Abbu ya ce "Dan Allah ki daina wannan maganganun, bari na samo mota, mu kai shi asibiti" Abba kuwa ko magana ya kasa, Nazifi ne ya taimaka aka fita da Abba zuwa mota. Al'amin kuwa da ya tabattar da ya tserewa Abbu, ya samu wani lungu, ya jefar da wuƙar hannunsa, ya samu wuri ya zauna, yana ƙoƙarin haɗiye wani abu mai tsananin ɗaci da zafi a maƙogwaronsa, ji yake kamar numfashin sa zai ɗauke, babu abun da zuciyar sa ke raya masa, banda ya kashe matar Abbu wato rahila ya huta. *** Gidan babu kowa, duk yaran sun tafi makaranta, mama tayi sallama a falon zakiyya. Ta amsa tare da fitowa daga bedroom ɗin, tayi miƙa ta ce "Lafiya kuwa?" "Au bacci ma ki ke yi? Lallai kam, to magana na zo mu yi" Zakiyya ta ce "Ok, bisimillah zauna mana" Ta nemi wuri ta zauna, ita ma ta zauna. Mama ta kalleta ta ce "Kin san waye yake son Jauhar kuwa?" "A'a sai kin faɗa". "Ɗan familyn mai atamfa ne" Waro ido Zakiyya ta yi, har tana neman faɗowa daga kan kujera, ta ce "Wani mai atamfar?" "Waɗanda dai ki ka sani,ba ma wannan ba shi zai tsaya takarar majalissar tarayya a yankinsu, jiya na tutsuye shi, yake gaya mini, ga kasuwancin atamfofi da lesuna da yake sayarwa, daga ƙasashe daban-daban yake order kaya, na din ga bugun cikinsa yana gaya mini, wai zata yi karatu idan tana so, idan business take so zai ba ta jari, idan ma zaman gida take so, ayi din ga yi mata komai, duk zai iya kuma nan kusa yake son ayi auren". "Bantan uba, namu ƴaƴan suna zaune za ayi hakan, muna me?" Mama ta ce "Hmm, ni fa na daɗe ina hana faruwar wasu abubuwan, rannan daga aikenta gidan Hajiyar lamin, wai ɗan wan maigidan ya ganta, ya ce ayi masa hanyar aurenta, uban yaron fa sanata ne a Adamawa, hauka nake? Na toshe na hana, na din ga aika su surayya, da walida amma ko kare a familyn babu wanda ya sinsuna su. Lokacin da suka yi sauka ma, babu kunya wai chairman yana son ta, tun ba ta kai haka ba ma, na ce ba za a lalata mata tunani ba, karatu take yarinya ce, na rasa wannan masifar". "Mun shiga uku, meyasa kowa sai ita? Kuma duk masu kuɗi, namu yaran fa?". Mama ta ce "Wannan shegiyar farar fatar suke yi wa ai" "Wace farar fatar? Su ma duk ba suna shafa mai ba, manyan zaratan ƴan mata, sun sha mai da kwalliya amma ace su duk shiru sai ita?" "Shiyasa tun jiya ban yi bacci ba wallahi, na saƙa wannan na kwance wancan, dole fa a rusa wannan maganar ma" Zakiyya ta ce "To yanzu menene shawara? Wallahi na rasa abun cewa, ko malamai zamu shiga ne?". "Babu lallai yayi tasiri, na fuskanci ƙashin masu arziki ne da ita, amma mu cigaba da shawara kafin faruwar abun". Zakiyya ta ce "In sha Allah " Mama ta miƙe ta ce "Sai na ji ki". *** Cikin ikon Allah Abba ya warware, babu abun da ya same shi, sai dai ya bugu, ya yi ta fama da jiri, sai da ya kwana uku a asibiti, aka sallame shi. Rahila ta cigaba da ɗagawa Abbu hankali a kan Al'amin, a kan lallai ya kai shi wurin hukuma, a san yadda za ayi da shi, kafin ya yi mata kisan gilla ita da yaranta. Gaba ɗaya maganganun Al'amin sun yi tasiri a zuciyarsa, amma kuma wani ɓangaren, Rahila tana da gaskiya, al'amin barazana ne a gare su, saboda yadda sunan mai dogon zamani, yayi ƙaurin suna a bakin mutanen unguwa, ba iya unguwar ba, har gidajen radiyo, duk wani faɗan daba da zai tashi a arear rukunin unguwannin to sai an ambaci mai dogon zamani wato Al'amin. Ƴan sanda har sun gaji da kama shi, idan an kama shi ma, ƴan siyasa sai sun saka an sako shi, daɗinta ɗaya ba ruwansa da taɓa kowa ko kayan kowa, sai ƴan daba da jami'an tsaro da su yake faɗansa. Bayan Jauhar ta dawo daga makaranta, mama da Anty suka sakata a gaba, suna sake yi mata tambayoyi a kan Alhaji mu'azzam, Jauhar ta rasa me za ta ce musu, dan ita ba komai ta sani a kansa ba, dan tun da ya zo sau ɗaya, bai sake zuwa ba, dan haka ta din ga ce musu ba ta sani ba. Aikuwa suka din ga zaginta, tare da kiranta munafuka. Suka gama zaginta, ta cigaba da sabgoginta. Yaya tijjani ya shigo, wanda shi ne babba a gidan, ya shiga wurin mama, jauhar ba ta san hawa ba, ba ta san sauka ba, ya kamata ya zane a yammacin nan, wai an ce masa kule-kulen maza take yi. Ihun jauhar ne ya sanya yaya saifu shigowa, ya tarar TJ yana mata bala'i, wai tana kula maza. "Haba yaya TJ, idan ba ta kula maza ba, kai za ta kula? Ko za a jiƙata a ruwa a sha ne? Da iznin baba fa ya zo wurinta idan ma a kan wannan mutumin nan" Mama ta ce "Rufe mini baki, kai da ba ka san me duniyar take ciki ba, yadda maza ke lalata yaran mutane yanzu, idan aka sake lalata ta kawai zai yi ya gudu, kuma fuska ya gani shiyasa ya biyota har gida, da ba ta bashi fuska ba ba zai zo ba. Idan da gaske yake auren zai yi, duk ga mata nan da suka fita komai sai ita. Saifu kawai ya girgiza kai ya fice, ransa ba ya yi masa daɗi, da irin riƙon da ake yi wa ƙanwarsa a gidan nan, shikenan maraici sai ha zama makamin cutar da bawa?. Har jauhar ta gama girkin dare, kuka take yi, dan ta daku sosai da sosai, fatarta duk tayi ja. Baba da ya dawo, bai san me aka yi ba, na dukan Jauhar. Ɗan autansu ne wato amir, ya shigo ya ce "Jauhar ana kiranki a waje, in ji wannan mai motar, kin ga har ya bani kuɗi dubu biyu". Anty ta ce "Ba zata je ba, je ka ce ba ta nan, ki mayar da kai ki gama sauran aikace-aikacen ki, idan kuma baki da abun yi, ki zo ina da shi ki yi mini". Baba ya fito da kansa ya ce "Amir, je ka ka ce tana zuwa, Waliyiyya, ajiye duk abun da ki ke yi, ki je ki sallami baƙonki". "Amma Alhaji..... "Amma me? A kan me zaku hana yarinya zance, maganar aurensu fa za a fara kwanan nan, da yaya za su fahimci juna?". Jauhar kamar ta ce wa Baba ba zata je ba, dan tana tsoron a sake saka yaya TJ ya dake ta. Amma ta kasa magana, ta zura hijjabinta, ta fita. Tun kan ta fita ta fara jiyo ƙamshin turaren sa, kamar wancan karon ta durƙusa tana gaishe shi. Sai dai bai amsa ba, ya ce "Na yi missing ɗinki Jauhar, sai dai na baki lokaci ne, dan kar na dame ki. Yaya ake ciki kin yi mana addu'ar? Kin fara so na?" Maimakon ta bashi amsa, sai ƙifta ido take yi, tana waiwaye kar TJ ya zo ya ce zai sake dukanta, tun da ta tsaya da wani ne ba sa so. Ya ɗora da cewa "Dama baba ne ya ce na ɗan baki lokaci, to kuma ga tafiya ta kamani babu cikkaken shiri, na ce a kawo mini kuɗin aure, kafin na tafi, amma na ga bari na ji ta bakinki, kar na yi miki shigar sauri" Tayi shiru kamar ba da ita yake ba. "Baby yangar nan tana yawa fa, dan Allah ki yi mini magana na ji nutsuwa mana" yayi maganar yana dawowa kusa da ita ya tsaya. "Jauhar ki yi magana mana" "Allah ya zaɓa mana abun da ya fi alkhairi" ta faɗa a hankali. Ya ce "Kin amince zaki aureni?" Ta ɗaga masa kai alamar eh. "Wow, anya ba zan  ce a ɗaura mu tafi chinan tare ba?" Ta ce "A'a, dan Allah a bari na gama makaranta, mun kusa yin WAEC". Alhaji mu'azzam ya ce "Na so ace zan iya yi miki hakan, amma ba zan iya jurewa ba, kar wani ya rigani, ko da na tafi ina can, iyayena zasu zo ayi maganar, da na dawo sai maganar bikinmu, i will be with my little baby amarya very soon in sha Allah" Tayi murmushi cikin jin kunya, tana murmushi. "Jibi in Allah ya kaimu fa zan tafi, babu tsammani tafiyar ta zo, me zaki gaya mini kafin na tafi, da zan din ga tunawa da ke, kin ƙi yarda na baki waya, balle mu din ga waya ina jin daɗi. Yanzu me zaki ce mini?". Ta ce "Duk lokacin da ka tuna ni, ka yi mini addu'a" "In sha Allah amaryar mu'azzam, zan din ga yi mana, daɗin auren mace mai addini kenan" Ya din yi mata hira, har ta ɗan sake tana yi masa murmushi. Ita dai ba ta sani ba tana son sa ko ba ta son sa, duk da ya girme mata, ya iya magana, ya sauke shekarunsa dai-dai da nata, ga ƙamshin turaren sa daɗi yake yi mata, dan a hakan yadda take fama, idan ta samu ƴan kuɗi, baka rabata da turare. Daga kan Surayya zuwa walida da hafsa, babu wadda ba ta fito ba, da niyyar za su fita yin wani uzurin, kuma babu wadda ba ta gaishe shi ba, sai dai gaba ɗaya hankalinsa da nutsuwarsa yana kan ƴar bainun gabansa wato Jauhar. Da zai tafi, sai da ya haɗe rai sosai, sannan ta yarda ta karɓi kuɗin da ya bata. Sai da ya tabattar ta shiga gida, sannan ya tafi. Ɗaki ta je ta bawa baba duk abunda ya bata, kuɗi masu yawa, mama ta din ga masifa, kamar ta ari baki, da sunan kula da tarbiyyar Jauhar. *** Al'amin yana kashingiɗe yana busa wiwi, yana kaɗa ƙafarsa ɗaya, yana jin sa a sama, dai-dai da kowa, sai dai busa hayaƙin yana bashi nishaɗi, yana jin daɗin hakan. Wuƙar gefensa ya ɗauka ya zauna sosai, ya karta ta a ƙasa, ya gyaɗa kai sannan ya ɗago ya ce  "zan shiga ƙofa, zan tayar da tarzoma, zan je ɗaukar fansa" "Wurin madakin dai?" Walid yayi maganar yana kallon sa. "Koma wurin waye, ka manta abun da suka yi mana kafin na je prison?" Walid ya girgiza kai ya ce "Ban manta ba" "Zamu ɗauki fansa, madaki kuma ban ce kowa ya taya ni ba, faɗana ne nikaɗai wannan". "Shikenan yaushe zamu shiga?" "Shammatar su zamu yi, zan yi muku magana" Ya koma ya kashingiɗa, ya cigaba da zuƙar wiwi. ***** Tun da Allah ya sa Alhaji mu'azzam ya tafi, Jauhar ta manta da babinsa, sai dai in mutanen gidan sun ɗaukko hirarsa, ita da yake zuwa wurinta ma ba ta zancensa kamar yadda suke yi. Babbar murnarta ita yanzu, ganin yadda kantunta yake ƙarewa da wuri, duk da ana yi mata mugunta a gidan, yaya saifu ya ƙara mata jari, ya bata dubu ɗaya. Ɗan kuɗin da take juyawa, da na riɗin, da na shirin dutsen, bai fi dubu biyu da ɗari biyar ba, amma murna take yi da hakan, jin kuɗin take da yawa, dan ƴar hamsin ɗarin da take bi na riba, ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, dan nan da nan ta tara kuɗin pad, har ta fara tarin kuɗin makarantar islamiyyarta, kan lokaci yayi ta zo tana nema. Yau an tashi daga islamiyya, ta sayar da riɗinta tsaf, dama da ɗaurin shirin dustenta, ta fito daga aji, tana lissafin tayi maza ta kai musu, ta karɓo wani. Ko da ta fito wajen gate ɗin makarantar, matasa suka gani suna guje-guje, wai faɗan daba ake yi, mai dogon zamani ya shigo ɗaukar fansa. Jauhar ko a jikinta tayi gaba, tun da daga in da ake gudun bayansu ne, dan haka tayi gaba abun ta, ta nufi hanyar gidan da take karɓar shirin. In da take bin shiru babu mutane ma, tana shiga layin gidan shirin, ta ɗaukko robar riɗinta, ta ciro kuɗin cinikinta, ta hau ƙirgawa murmushi ta saki, tana jin daɗi, ta fara tunanin tambayar kuɗin aya gwangwani biyu, ita ma ta din ga soyawa da gishir tana sayarwa. Hankalinta ne yayi mummunan tashi, bayan da tayi baƙin ganin da ba ta farga da shi ba sai yanzu. Hannunsa riƙe da wani mutum, da ba ta da tabbacin yana da rai ko babu, da wuƙa a gefen cikin mutumin, hannunsa duk jini, kuma shi ma da yake riƙe da mutumin da take kyautata zaton kashe shi ya yi ƙafarsa sai zubar da jinin take yi. Tun da ta shigo layin ta fara lissafa kuɗi, ya ɗaga kai ya ganta, amma ita sam ba ta ganshi ba, hankalinta yana kan lissafin kuɗin da yake hannunta, sai da ta je tsakiyar layin, ta kusa zuwa daf da shi sannan ta farga. Zuciyarta ce ta fara wani iri razanannen bugu, gashi ta kasa ko da motsa ƙafarta, balle ta cirata ta gudu, ba ta taɓa ganin mummunan tashin hankali ba tun da take a rayuwarta ba sai yanzu, ita ko film ne ta ga ana kashe-kashe, ko harbe-harbe bata kalla, kodayeke ita kallo ma bai dameta ba, amma sai yau gata ga gawa da jini. Ba tare da ta yi tsammani ba, wani irin ƙarfi ya zo mata, ta taƙarƙare iya ƙarfinta, ta kurma wani irin uban ihu, ta yinƙura da niyyar ta gudu, sai dai tsananin bugun da zuciyar ta take yi, ya sanya numfashinta kasa daidaituwa a ƙirjinta, kuma ta gaza ɗaukar nauyin jikinta, dan haka ta faɗi a wurin a sume, robar da cinikin, da jakar islamiyyar duk suka watse a wurin, gefen kwata. Duk da wannan uban ihun da tayi, babu wanda yayi ƙoƙarin buɗe ƙofarsa ya ga mai yake faruwa. Duk da dama, gidaje biyu ne kacal a layin, sauran duk bayan wasu gidajen ne a cikin layin. Tsaki ya ja, ya mayar da idonsa kan liti, da yake numfashi sama-sama. Ya kalli ƙafarsa da take ta zubar da jini shi ma, saboda saran da aka yi masa. Ya kwantar da liti, ya tashi ya tafi kan jauhar, ya kai hannun sa kan hancinta, ya ji tana numfashi. Ya kamo hannunta, ya riƙe tsintsiyar hannunta, ya ji zuciyarta na wani irin bugu, da saurin gaske. Kamar ya ɗauki tabarma, haka ya ɗauketa daga kan hanya, ya kwantar da ita a tsallaken kwatar, ya tattaro kayanta ya haɗe mata wuri guda, sai dai uniform ɗin ta, duk sun ɓaci da jinin da yake zubarwa. Wald ne ya ƙaraso layin da sauri, shi ma hannunsa riƙe da wata sharɓeɓiyar wuƙa tana zubar da jini, ya ƙarasa in da Al'amin yake harya fara ganin jiri, saboda jinin da ya zubar. "Subhanallah, waye yayi gangancin yankarka?" "Ƙyaleni, ka kira su baffan?" "Eh, suna bakin titi da ɗan sahun" Ya miƙe ya saɓa liti da yake zubar da jini a kafaɗarsa. Walid ya ce "Kawo shi, na ga kamar jiri ka ke yi mu ƙarasa". Ya ce "A'a bar ni da shi, zan yi wa honorable waya, ya aika mana ƴan sanda asibiti, waccan yarinyar, ka buga ɗaya daga gidajen layin nan, su fito su kaita Asibiti, ta tsorata ne, idan kuma ba haka ba za ta yi musu mushe a wurin, saboda zuciyarta na bugawa da sauri sosai" Walid ya ce "Wai wa yake ta wata yarinya, kai kaɗai zaku tafi asibitin, kalleku fa jina-jina" "Mai rai ce fa, idan ba su buɗe ba, ka haura gidan kawai, ka saka su buɗe, yanzu idan muka tafi da ita zai zama wani abun daban" daga haka yayi gaba, ya nufi barin layin. Walid ya yamutsa fuska, ya samu ɗaya daga gidajen, ya din ga wani irin bugu, kamar yaƙi. *** Cikin tsananin hanzari ta yinƙura, za ta diro daga kan gadon da take, tana faɗin"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah ku taimake ni, zai kashe ni" Cikin azama baba ya riƙe ta, ƙoƙarin ture shi take yi, ta saukko daga kan gadon. Baba ya ce "Jauhar, buɗe idonki, ki kalleni ni ne ki nutsu" sannu a hankali ta buɗe idonta, ta kalli baba, ta juya ta kalli su mama da Yaya saifu da suke wurin, sai malam jamilu da malam hamza. Jikinta ya hau wata irin tsuma, ta dinga fizge-fizge tana ƙoƙarin fizge robar ruwan hammunta. "Ke ki nutsu mana, meye haka ne ana yi miki magana" mama tayi maganar tana haɗe rai. Ta girgiza kai ta ce "Mama tsoro nake ji, wani ya kashe fa, dan Allah ku ɓoye ni zai kashe ni nima, ganinsa nake yi a idona, dan Allah baba ku tafi da ni tsoro nake ji" tayi maganar tana ƙoƙarin tashi tsaye. Baba ya ce "Wai shi wa?" Cikin kuka ta ce "Ban san shi ba, kawai gani nayi dai ya kashe wani yana kallona, nima na san zai biyoni ya kashe ni". Baba ya ce "To ai babu wani wanda aka gani an kashe, ke kaɗai aka gani a layin a sume". Anty ta ce "Uban me ma ya kai ki can, in da ba hanyar gida ba?". "Shiri na je karɓowa" "To ubanwa ya aike ki?" Baba ya ce "Dan Allah duk a daina wannan maganar, yanzu a bari ta samu nutsuwa". Ƙoƙarin kwantar da ita Baba yake yi, ta kalli jikin uniform ɗin ta, ta ga jini, ihu ta sake yi, tana faɗin "Meya same ni, baba kalli jini a jikina, na gaya maka nima kasheni zai yi, kalli jini fa wataƙila ma na mutu ne". A take wani abu ya ɗarsu a zuciyar mama, tayi wani shu'umin murmushi, yaya saifu kuwa likitoci ya kira, aka sake yi wa jauhar allurar bacci, dan gaba ɗaya nema take ta zare. Malaman islamiyyar suka yi wa su baba sallama, malam Jamil dama a kusa da layin da take zuwa karɓar shirin yake, yana yawan ganinta, wataran shi yake korata makaranta ko gida, tun da ya fuskanci halin da take ciki, yake ƙyaleta, dan watarn har gidansu take shiga, ƙannensa ƙawenta ne. Shi ya din ga bawa baba baki, da bashi tabbacin jauhar ba yawo take tafiya ba, kamar yadda mama ke ta iƙrari. Baba ya ce "Ni ma na san jauhar ba ta yawo, wannan abun da ya faru ma tsautsayi ne, Ubangiji Allah ya kiyaye gaba" suka yi sallama su malam jamil suka tafi. Kusan awanni biyu, jauhar ta sake farfaɗowa, sai dai wannan karon da sauƙi, ba cikin razani ta farka ba kamar da farko. Likita ya zo yana sake dubata, Mama ta ce "Likita kun dubata da kyau kuwa, wannan jinin na jikinta ba fyaɗe ƴan daban suka yi mata ba?" Dummm! Ƙirjin Jauhar ya buga, ba ita ba hatta baba sai da gabansa ya faɗi, suka kalli mama a tare. Likitan ya girgiza kai ya ce "No, bana tunanin hakan, razani ne kawai". "To amma meya kawo jini jikinta?". Likitan ya yi shiru yana kallon jauhar. Baba ya ce "Likita ka yi magana mana" Jikin jauhar ya cigaba da rawa, tana nanata fyaɗe a zuciyarta, amma kuma da gaskiyar mama, meyakawo jini jikinta?. Likitan ya ce "Zaki iya tuna abun da ya faru?". Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Na shiga layin kawai na ga ya kashe wani, da wuƙa a cikin sa, shi ma ƙafarsa tana zubar da jini" "Kin san shi ne? Kin taɓa ganinsa?" Ta girgiza kai alamar a'a Ya ce "Zaki iya tafiya?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya cire mata ruwan sannan ya ce "Saukko ki biyo ni" ta yinƙura ta sauka daga kan gadon, ta bi bayan likitan, zuwa wani ɗakin daban, ya kira wata nurse ya ce ta duba masa jauhar, amma jauhar fafur ta ce ba zata buɗe jikinta ba, sai ma ta hau kuka. Nurse ɗin ta din ga lallaɓata tana yi mata tambayoyi, ta saka ta ciro mata phant ɗin ta, ta duba ta ce wa likitan ba abun da aka yi wa jauhar ɗin mai kama da fyaɗe. Wataƙila da ta suma ya taɓa ta, tun da ta ce shi ma da rauni a jikinsa, amma ba dai fyaɗe ba. Likita ya koma ya yi wa baba bayani, baba ya din ga hamdala, mama ta ce likitan ƙarya kawai yake yi, babu yadda za ayi, ta samu jini a jikinta, idan ba fyaɗe aka yi mata ba. Likitan ya ce "Amma dai ba ƴar ki ba ce hajiya, da taki ce ba zaki yi mata wannan mummunan fatan ba, bani da wata riba da zan ci, idan na yi muku ƙarya, kuma babu yadda za ayi ayi mata fyaɗe ku kawota a haka, ba wani rauni ko alamu na fin ƙarfi, dan babu ɗan iskan da zai yi wa yarinya fyaɗe ya tsaya mayar mata da kayanta a tsakiyar layi, kamar yadda muka karɓi report" Baba ya ce "Doctor, a bar zancen ma gaba ɗaya, ni dai na gode sosai da sosai, na gode Allah da babu abun da ya sameta, za a iya sallamar mu yanzu?". Ya ce "Eh, yanzu zan sallame ta". Aka rubuta musu sallama suka tafi gida. Maƙwabta suka din ga shigowa yin jaje, saboda labari ya cika tsukin, faɗan daba ya rutsa da jauhar, an tsintota can a sume. Sai dai duk wanda ya zo, sai su mama sun bashi labarin, cewar cikin jini aka tsintota kuma jikinta babu rauni, ana kyautata zaton ko sun yi mata fyaɗe. Jauhar hankalinta ya kasa kwanciya, ta din ga tunani daban-daban, ko da ƙarancin shekarunta, a science class take ss2, kuma tana zuwa islamiyya ta san duk wadda aka yi wa fyaɗe sai ta ji wani sauyi a tare da ita, amma ita ba ta ji komai ba, babu wani abu da take ji na sauyi a tare da ita. Tun tana damun kanta, har ta watsar, sai dai ƙasan zuciyarta tana jin zafin abun da su mama suke faɗa, dan idan ta fita har tambayarta ake yi, wai da gaske an yi mata fyaɗe?. Har fita ta so ta fara gagararta. Sati biyu da faruwar lamarin, Baba ya zo ya sanar musu da cewa, iyayen Alhaji mu'azzam za su kawo kuɗin auren jauhar. Hankalinsu yayi mummunan tashi, daga su har ƴaƴan su. Suka ƙara tsananta tsangwama da kyarar jauhar. Duk da tana da matuƙar juriya, da kawar da kai, har abun ya fara effecting ɗin ta. Bai sanar da su lokaci ba, sai ranar da za a kawo ya sanar da su, hankalinsu ya ƙara tashi, sai dai ba su tsinke da lamarin ba, sai da aka kawo kuɗi masu yawan gaske. Anty ta kira Rahila, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali take gaya mata, tare da tambayarta ko akwai wani zazzafan malamin ta haɗa su, a samu a watsa lamarin. Rahila ta ce "Wallahi ni kaina a cikin matsala nake Zakiyya, yaron nan ya zame mini bala'i fiye da koyaushe, idan ya ga dama fa cikin gidan yake zuwa ya kwana a tsakar gida, gaya miki ne ban ba, sai da muka kwanta a asibi, ya ɗaga Abba ya buga da ƙasa saboda babansa ya hana shi zuwa gidan, gashi kamar ya fara jin tausayinsa, wallahi kamar na bawa tsinanne guba ya ci ya mutu" "Innalillahi, rahila menene abun yi? Ni fa sonake maganar ta watse, a dawo mutumin ya auri hafsa". Rahila ta ce "Aikuwa kin yi dabara, ina da wani malami, wurinsa nake son komawa, ina jin daɗin aikinsa sosai da sosai, duk da su ma malamn yanzu duk sun zama ɓarayi, su ci maka kuɗi babu biyan buƙata, amma nasa babu laifi". "Wallahi kuwa, saka mana rana, ko da tsiya da masifa, lamarin ya dawo kan hafsa". "Idan a shirye ki ke, kawai ki zo mu je, ba a bori da sanyin jiki" Suka yi sallama a kan haka, ɓangaren mama ma, tuni ta zari mayafi ta tafi nata wurin malamin, a kan lallai al'amarin nan kar ya yiwu. Haka ita ma anty ta shirya, ta tafi gidan rahila. Ita kuwa jauhar, addu'a take ta yi, Allah ya sa mutanen unguwar su manta da sharrin su mama da suka yi mata, na cewar fyaɗe aka yi mata. Maganar kawo kuɗin auren duk bai wani dameta ba, ita gaba ɗaya ba ta jin dadin rayuwar ma gaba ɗaya, gashi har a lokacin tana yawan tsorata, idan ta tuna abun da ta gani, haka take ganin abun a mafarki, sai dai tayi ta addu'a tana fatan Allah ya yi mata tsari da wannan mutumin mara imani. Malamin ya gama surƙullensa, ya kalli su zakiyya ya ce "Za a iya watsa lamarin amma fa kafin dawowarsa, muddin ya dawo, babu yadda za ayi". Zakiyya ta ce "Malam tayaya kenan?" "Ko dai a aura mata wani, ko kuma a kasheta" Tayi jimmm ta ce "Kisa kuma malam, a'a gaskiya ban da kisa, muguntar tawa ba ta kai nan ba, ni fa burina kawai ya auri ƴa ta". "Ta yaya zai aureta, alhalin yana ganinta?" Rahila ta ce "Sai a juya masa tunani mana malam". "Za a iya juya masa tunani, amma ba zai juyu yadda ake so ba, abun zai sake shi da wuri, dan su ma masu kuɗin ba da ka suke zaune ba, kuma maganin ba zai yi aiki a kansa ba, dole sai ya dawo ƙasar nan, zan haɗa laƙanin, ya manta da wannan ya auri wadda ku ke so, amma muddin ya dawo yayi tozali da wadda yake son ɗin, ƙasa ta nuna mini ba zai yiwu ba" Zakiyya ta ce "Tirƙashi! Ana wata ga wata, ga ƙoshi ga kwanan yunwa" Rahila ta ce "Malam mun gode, idan mun yanke shawara zaka ji mu, tashi mu je ki ji ina da shawara" Suka sallami malamin, suka tashi suka fito, ta kalli rahila cikin damuwa ta ce "Wace irin shawara ce da ke?" "Shawara ce mai kyau, amma ina ga mafita ce, tun da damuwar mu kusan ɗaya ce, me zai hana a haɗa ta aure da wannan fitinannen yaron na gidana, kin ga kun huta na huta, su je su ƙarata, ya bar ni da mijina da ƴaƴana". Zakiyya ta buɗe baki ta ce "Ta yaya? Babanta kuwa zai yarda?" "Ke dalla can, shiga zaki yi ki fita, idan ba haka ba wallahi daular da ki ke kallo ta gagareki, kin ga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya". "Wallahi maganarki gaskiya ce rahila, zan yi magana da matar gidan, ta fi ni iya sarrafa shi yadda take so a kan yarinyar, zan je mata da zancen, ayi a ƙarƙare kan wancan ɗin ya dawo". "Yauwwa, amma fa kar ki gaya mata wurin malami ki ka je" Zakiyya ta ce "Hauka nake zan gaya mata haka? Ke dai ki saurare ni kawai" "To shikenan, sai na jiki, yadda ku ka yi ki sanar da ni da wuri, nima zan wa babansa magana" suka yi sallama zakiyya ta tafi da ƙarfin gwiwar ta. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Cike da ƙwarin gwiwa, zakiyya ta tafi gida, tare da hasaso daular da za su shiga, idan hafsa ta auri Alhaji mu'azzam. Al'amin kuwa yana zaune ya miƙe ƙafarsa, da ta sha bandeji, hannun sa ɗaya riƙe da kofin shayi yana sha a hankali. Walid ya miƙa masa buredi ya ce "Wai yaya aka yi har yaran nan suka samu suka sareka ne? Ni fa haryanzu mamaki nake yi" Al'amin ya ce "Liti suka rufarwa da sara, shi na je karɓowa, saboda sun ga suna da yawa, shi ne nima suka yi tunanin za su yi mini taron dangi" yayi wani irin murmushi yana kallon walid. "Murmushin me ka ke yi kuma?" Ya ajiye kofin ya ce"swizalan ɗina ta sha jini sosai, wannan yankanma, ban lura yaron ya taho ba ne, yadda nake ji na anya ba wasan dambe zan fara ba walid. Idan na kwana biyu ban motsa ba, idan na tashi motsawar ba na iya riƙe kaina fa". Walid shi ma yayi murmushi ya ce "Ai ƙarfi ya yi maka yawa aminu, ka shiga dambe abun ba zai yi mana kyau ba, daga karate zuwa dambe, amma da sauƙi jikin ai ko?" Ya kalli ƙafar ya ce "Alhamdilillah, da sauƙi sosai, jibi za ayi aikin honorable, zai je campaign fa" Walid ya ɗan tsuke fuska ya ce "Akwai hatsari fa a aikin nan". "Ai ban ce wani ya tayani ba, nikaɗai zan yi abuna" Walid ya girgiza kai ya ce "Sorry, ba zaka yi kai kaɗai ba, amma da rauni a jikinka, ba ka warke ba". "Ba ruwanka da ciwona, zan yi abuna a haka" walid ya girgiza kai, dan ya san ko me zai ce, bai isa ya hana Al'amin abun da yayi niyya ba. *** Kamar zakiyya za ta tashi sama dan sauri ta ƙarasa gida, saboda rahila na bata shawarar nan, ta ji shawarar ta kama zuciyarta, kuma taga hakan ne kawai mafita, ayi ayi jauhar ta bar gidan kafin Allhaji mu'azzam ya dawo, wataƙila ita ke tsokanewa samarin kirkin ido, ba sa ganin nasu ƴaƴan sai ita. Ko da ta koma gida a can ta tarar da mama, ita har ta dawo tuni. Ta ja ta ɗakinta, ta ce "Na samo mafita fa, amma ban sani ba ko zata yi miki?" Cikin zaƙuwa mama "Wace mafitar ce, ina jinki" "Me zai hana mu san duk mai yiwuwa, a aurar da jauhar, kafin Alhaji mu'azzam ya dawo, tun da dama sai ya dawo, za a tsayar da lokacin bikin". Mama ta ce "To wa za a aurawa kafin ya dawo ɗin?". Anty ta ce "Ba zai gagara ba, sai dai shawo kan Alhaji ne aiki" "Wane irin aiki kuma? Babu wani aiki, ni a wurina ba aiki bane ba, wa ki ke gani yakamata ta aura". Zakiyya ta muskuta ta ce "Kin san dai muka bari ta auri wani mai danshi, daga ni har ke babu wanda za ta saurara, tun da bamu muka haifeta ba". Mama ta ce "Na sani" "To, kin san yaron nan da yayi suna a ƙofa, mai dogon zamani?" "Eh ina jin sunansa sosai" "To mariƙiyarsa, ƙawata ce tare muka yi boarding ai rahila shehu, kwana biyu bamu haɗu ba, kwatsam na je ƙofar na'isa na ga ɗan ta, ya rakani har gidan, to ita ma haka take fama da shi, ta rasa sukuni, kullum cikin tashin hankali take, neman maraba take da shi, uban ya kore shi, amma yaƙi barin gidan, kin ga idan aka aura mata shi, mun huta, a fake da fyaɗe aka yi mata, kuma dai ga tambarin da ki ka yi uwarta na maita, kawai dai ki lallaɓa maganar, kin san yadda zaki yi dai sabgar nan ta yiwu, wallahi muddin ba ta bar gidan nan ba, bana tunanin za a din ga kula namu, kuma wallahi ta auri mai kuɗi, kashinmu ya bushe, ai kin san riƙon da muka yi mata". Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Maganarki duka gaskiya ne, kar ki damu, wannan shawarar ta yi, kuma na aminta da ita, yadda muka kwashi baƙincikin uwatta, ita ma ba zata ji daɗi ba. Duk da wasu lokutan tana bani tausayi tana da biyayya, amma idan ba haka ba, namu ba zasu auru ga irin wanda muke so ba, ki gayawa ƙawartaki azo a nema masa aurenta, zan ji da komai" Anty ta washe baki ta ce "Alhamdilillah, magana ta ƙare". Jauhar kuwa, ba ta san me ake  ƙulla mata ba, ita lissafinta yadda za ta mayar da jarinta, dan tun da ta farka a asibiti, da ta dawo gida sai jakarta babu kuɗin cinikinta, dan ma mai shirin dutse ta yafe mata. Duk yadda take jin nauyin yin roƙo, haka ta cire kunya, ta tambayi yaya saifu ya taimaka mata da jari, ta cigaba da sana'arta, kuma cikin ikon Allah ya bata, saboda ta hannun daman sa ce sosai da sosai, aiki duk yawansa duk wahalarsa babu ƙyuya take yi masa, gyaran ɗaki, wanki guga idan baya nan tayi girki, ta zuba ta kai masa ɗakinsa, idan ya gama ci ya bar kwanukan a ɗakin, ta kwaso ta gyara masa, dan haka baya jin ƙyashin kyautata mata sam. *** Abbu yana daga kwance ya kammala azkar, ya juya zai yi bacci, rahila ta shigo ɗakin, ta nemi wuri ta zauna a kan gadon ta ce "Tun da idonka biyu tashi mu yi magana" Ya juyo ya ce "Ina jinki" "Magana ce mai muhimmanci, a kan Aminu". "Aminu dai Aminu dai, me kuma ya faru wannan karon?" "Menene ma bai faru ba, tun da an mutu an bar mini jaraba da masifa, kullum hankalina a tashe, nan aka zo ana bayar da labari, sun je ya tayar da tarzoma, har an yanke shi a ƙafa, rashin mutuncin sa kullum ƙara gaba yake yi" "To, na ji, maganar kenan ki sake maimaita mini abun da yake aikatawa? Wannan ai wani abu ne da na riga na sani". "Ba shi ne ba, magana ce a kan mafita game da abun da yake yi" Ya tashi zaune ya ce "Wace irin mafita?" Rahila ya gyara zama ta ce "Akwai wata ƴar ƙawata, yarinyar rashin ji take yi, tana neman fanɗarewa, gashi ba ta da wani tsayayye, na ce tun da shi gashi, kuma akwai wannan kangon gidan da ya gada, a gyara masa ka nema masa aurenta, ta je su ƙarata ko zai yi hankali idan ya ajiye iyali". Abbu ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Too, ikon Allah, banda abunki wane mai hankalin ne zai bawa Al'amin auren ƴar sa, yadda suanansa ya yi shuhura, a kan rashin ji". "To ai yarinyar na ce maka fitina take yi ita ma" "Kuma sai ayi gyaran ɓarna da ɓarna? Sai a aura masa wadda ba ta ji?" Rahila ta ce "To shi ɗin menene? Shi na kirkin ne?ko Jin yake yi? Sai su rufawa juna asiri, amma aka ƙyale shi a haka, nan da shekara ashirin, kana ganin zai yi nutsuwar da zai kula wata mace da sunan zai aura, tsabagin wauta da kayen maye ne kawai a cikin kansa" Abbu ya numfasa ya ce "Maganarki haka take, amma kamar yayi ƙanƙanta ma da auren shekara ashirin da bakwai, ga ba sana'a yake ba sai ɗaukar magana, da yaya zai riƙe auren? ga faɗa da faɗin rai". "Idan ya san ya ajiye mace, dole ya nemo ya ba ta ai, tun da morarta zai din ga yi, ko kuma kana tunanin zafin rai da faɗin ransa zai hana shi, mu'amala da ita ne namiji ne fa". Abbu yayi murmushi, har sai da haƙoransa suka fito, ya ce "Na san ɗa na kamar yunwar cikina, ban san meyasa mata ku ke tunanin maza, bamu da wani tunani idan ba wannan ba, Aishikenan". Ta kwanta ta ce "Aikuwa idan haka ne, da sai an dangana da nema masa magani, idan baya wannan tunanin" Ya kwanta a kusa da ita ya ce "Zuwa da safe in Allah ya kaimu, sai ki yi mini kwatancen gidan su yarinyar, na samu mahaifinta". Ta ce "Yauwwa Abbu ko kai fa" **** Jauhar ta dawo daga makarantar dare, ta tarar da Baba da baƙo a waje, ta durƙusa ta gaishe su, sannan ta shiga cikin gida. Baba ya nuna wa Abbu ita, ya gaya masa ita ce jauhar ɗin da suke maganarta, Abbu sam bai ga alamar rashin ji, a tare da jauhar ba sai ma nutsuwa da kamala, hatta muryarta mai sanyi ce, yayi mamakin da rahila ta ce masa wai ba ta ji, fanɗararriya ce, sai dai bai yi magana ba, suka cigaba da magana da Baba a kan nemawa Al'amin auren jauhar, ya sanar da baban jauhar Al'amin ɗin ba ya ji, sai dai bai gaya masa irin rashin jin ba, ya zata Baba ya san komai, saboda yadda rahila tayi masa bayani. Baba ya ce "Babu damuwa, Allah ya tabbatar musu da alkhairi, na san iyayen nata ba za su zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba". Suka taɓa hira, ya tambayi Baba ko akwai wani shiri da za su yi? Baba ya ce idan sun shirya kawai su kawo abun da suke da shi, ayi komai a wuce wurin. Suka gama magana, Abbu ya tafi gida yana farinciki, tare da fatan Allah ya sa ƙarshen matsalar Al'amin ce ta zo, Shi ma Baba ya shiga gida, can ƙasan zuciyarsa yana ta kokwanto da wasi-wasi, amma ya kasa ayyana hakan a zahiri.Sam  bai iya tambayar menene rashin jin da  Aminu yake yi ba, bai tambayi menene sana'arsa ba da sauran su, kawai shi dai ya tsinci kansa da amincewa, bayan da mama tayi ta jaddada masa idan har Alhaji mu'azzam ya dawo, ya ji ƴan daba sun yi mata fyaɗe za ta wulaƙanta, ba zai aureta ba, shi gaba ɗaya ma ya manta da batun ya karɓi kuɗin auren Jauhar. Abbu na komawa, Rahila ta tare shi, tana tambayarsa yadda suka yi, ya ce "Ya amince zai ba shi ita, amma ni da ya nuna mini yarinyar, ba ta yi kalar marasa ji ba". "Ban da abunka Abbu, dama a goshi ake gane marasa jin? Kai dai kawai ayi sha'ani". "Amma anya ban yi ganganci ba kuwa, ban sanar da shi ba na je na nema masa aure, idan ya bujire fa". "Au sai ma ya yarda? Ashe na kabari zai dawo duniya idan shi ne zai yadda, ka yi iya yinka a matsayin ka na uba, kar ma ka sanar masa, sai ka kai kuɗin, kuma ku saka lokaci kaɗan, kar ya tafka wata tsiyar, ba akwai gidan da ya gada na wurin babarsa a chiranci ba, aje a ɗan gyara masa, ya zauna". Abbu ya jinjina kai ya ce "Shikenan Allah ya yi mana jagora". Kwana huɗu, Abbu ya kira baba, ya ce za su zo, su kawo dukiyar aure. Ko da Baba ya sanar da wanda za su karɓi kuɗin Jauhar ɗin tare, sun yi mamaki, suka din ga tambayar sa, meyafaru da waccan saka ranar, ya ce musu matsala aka samu. Dubu ɗari uku da hamsin, aka kai kuɗin komai da komai, har da lefe da sadaki da kuɗin aure, wai bayan sati biyu za a ɗaura aure. Mama ta fito tsakar gida ta din ga rangaɗa guɗa, suna Allah ya sa za su gani, gaba ɗaya sai jauhar ta zama confused, wane irin abu ne haka? Alhaji mu'azzam ne ya dawo? Ko kuma yaya aka yi, aka kuma karɓar wani kuɗin. ta ji ana zancen wani Al'amin shi kuma daga ina? Ta tambayi kanta. Sai dai tsananin kunya, da kawaicin jauhar, bai sanya ta yi magana ko ta tambaya ba. Su surayya suka din ga yi mata dariya, wai ta ga samu ta ga rashi, from grace to grass. Duk wani shirin auren, Mama ce take yi, ita ke karɓar kuɗin a hannun Baba wani abun ta saya mata mai kyau, wani akasin haka, masu kyan ma tana saya ne, saboda kar a yi mata gori, ta riƙe yarinya shekara goma sha shida za a shiga sha bakwai, amma ba ta yi mata abun kirki ba. Aminu kuwa tun kan a kai kuɗin, yayi ɓatan dabo, dan rigimarsa ba ta ciwo shi ya zo gidan ba, dan haka tilas Abbu ya fara bin dabar da yake zama, da duk in da ya san zai ganshi, amma babu shi babu labarin sa, haka ya din ga bayar da cigiyarsa, kamar wani kuɗi, kowa ya tambaya sai ya ce masa bai ganshi ba. Rahila ta ce masa ya cigaba da shirin sa, duk in da ya tafi ma zai dawo. A gidan su jauhar kuwa, hankalinta ne ya tashi, da ta ji Anty na yi mata iƙirarin wai nan da sati biyu za a ɗaura mata aure, da angonta Al'amin. Saifu ya kasa jurewa, ya samu Baba ya tambaye shi, wai meke faruwa da auren jauhar ne?. Baba ya ce "Eh, nan da sati biyu za ayi" "Amma na ga kamar sau biyu aka kawo kuɗin, wancan an ce Alhaji mu'azzam, yanzu kuma an ce Al'amin wanne ne gaskiyar lamarin ne?" Baba ya ce "Maman ka da Antynku, ne suka yanke shawarar a aura mata wani, wancan za a iya samun matsala, ta ɓangaren zakiyya ma aka kawo wannan ɗin" cike da takaici yake kallon Baba ya ce "wace irin matsala kuma Baba? Meyasa wanda aka kawo ɗin ba za a haɗa shi da wata ba, sai jauhar? A ina yake, kuma menene sana'rsa? Yazo ya ganta ta ganshi, yayi mata?" Baba ya sunkuyar da kai tare da girgizawa ya ce "No, amma na san ba za su zaɓi abun da zai cutar da ita ba, kuma jauhar yarinya ce mai biyayya" Takaici ya ishi Saifu, ya tsani yadda matan gidan suke shirya wa Baba abun da suke yayi, kuma yayi babu musu mussaman a kan jauhar. Kawai ya tashi ya fita tsakar gida, ya tarar da ita, tana ta uban wanke-wanke, gefe ta jiƙa kayan wankin uniform ɗin ƙanan yaran gidan. Ya ja kujera ya zauna a kusa da ita ya ce "Waliyiyya, wai saura sati biyu aurenki?" Tayi yaƙe ta ce "Haka na ji, amma dai Baba bai gaya mini ba". "Wanda zaki aura ɗin kin taɓa ganinsa ne? Ki na son sa?". Ta sunkuyar da kai tana murmushi ta ce "Ko ban ganshi ba, tun da an ce su mama ne suka zaɓa mini shi, kuma Baba ya amince na san ba zai cutar da ni ba" "Baki taɓa ganinsa ba kenan?" Sai ta kasa amsa masa, ta cigaba da durza tukunyar hannunta cikin ƙarfin hali. Can kuma ta ce "Dan Allah yaya, ka roƙi baba, ya ce masa dan Allah ina son ƙarasa makarantata, ko WAEC na yi" Saifu ya girgiza kai ya ce "Ki kwantar da hankalinki, na san juriya kawai ki ke yi, amma in sha Allah, ba zaki ji kunya ba jauhar". Mama ce ta fito ta ce "Kai saifu, uban me ka ke gaya mata, hure mata kunne zaka yi?" Ya tashi tsaye ya ce "Ko na hure mata kunne, ba zai huru ba, kawai ina tausayin sauran ƴan matan ne, saboda komai nisan jifa ƙasa zai dawo" Ta ce "Saifu ni ka ke gaya wa haka? Me ka ke nufi?" "Mama kin san fa me nake nufi sarai, Allah ya haramta zalunci a kan kansa, babu wanda zai yi ya tsira wallahi" ya ƙarasa maganar yana ficewa. Cike da takaici da son hucewa, mama ta rarumi takalmi, ta jefi jauhar da shi a fuska, aikuwa ya tsokane mata ido. Ta zauna ta din ga mutsutsuka idon, sai da idon yayi taruwar jini. Ƴan unguwar su jauhar sai ganin invitation suka yi na bikin jauhar, suka din ga zuwa gulma da jin ba'asi, wane irin aure ne haka faka-faka ko lefe ba a nuna musu ba, da yake ba su san ma zancen kawo kuɗin auren farko ba. Mama da zakiyya, suka din ga cewa saboda ayi a rufa mata asiri, ake son ayi gaggawa a aurar da ita, sadakarta aka bayar babu ko kayan lefe. Saboda cin fuska a gabanta, suke faɗar hakan. A gabansu sai ta jure, tayi kamar ba ta ji ba, idan ta ɓuya kuma sai tayi ta kuka. Al'amin kuwa, honorable Indabo ne ya saka aka kai shi asibiti ta ƙarfin tsiya, saboda ciwon ƙafarsa an sake fama masa lokacin da ya tayar da rigima a wurin campaign, a haka yake lanjarata, ya tafi nasa wuri, saboda soyake Aminun ya warware sosai, kafin lokacin zaɓe kuma, yadda zai yi masa aikinsa yadda yakamata. Yana shiga arearsu, aka sanar da shi cewa, babansa yana ta yawon nemansa, mamaki ya kama shi, dan idan zai kwana nawa bai ganshi ba, babu ruwansa da in da yake, dan haka cikin gaggawa ya nufi gidan, domin jin dalilin neman nasa. Sai dai da ya je ya tarar da Abbun yana shirin fita. "Kai baka iya sallama bane Al'amin, sai dai mutum ya ga ka bayyana kamar wani shaiɗani?" "To meye marbarsa da shaiɗanin?" Tayi maganar ƙasa-ƙasa. Sarai ya ji ta, amma ya yi shiru, ya samu wuri ya zauna ya miƙe ƙafarsa ya ce "An ce kana nema na" "Ba an ce bane, nemanka nake yi, ka dawo daga gantalin kenan? Kodaye ba yau ka fara ba, ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni" Yayi shiru bai ce komai ba. "Daga nan ba kasuwa zani ba, Abba ne zai je ya buɗe shago, gidanka na chiranci, na gado zan je, za ayi masa wasu ƴan gyare-gyare, ba ni da kuɗi sosai a hannuna, za a yi masa abun da ya sauwwaƙa, kai ka ƙarasa gyarawa daga baya". Ya yi shiru yana wasa da zobensa, kamar yadda ya zame masa ɗabi'a, idan ba ya son yin magana. Abbu ya cigaba da cewa "Kuɗin aure na kai maka, next week za a ɗaura maka aure" Lanƙwashe ƙafarsa ɗaya yayi, ya koma wasa da yastun ƙafarsa, yana kallon wani wurin daban. Rahila ta ce "Taɓɗijan, lallai gagare". Abbu ya ce "Al'amin da kai nake fa" Ya ɗago idonsa ya kalli Abbu ya ce "Wai ni ko wa?" "A'a da ubanka nake ba kai ba, ni da waye a wurin nan?" Al'amin ya ce "Ni fa yau ban sha komai ba, garau nake balle ace a buge nake ban ji dai-dai ba, wannan kawai zance ne, ni da ake cewa gagarrare haihuwar asara, wa zai bani wani aure? Ni bana buƙata, idan kuma ba haka ba, duk abun da ya biyo baya ba ruwana idan na kashe yarinya, ko na yi mata illa, kar a zo ana yi mini ƙanan maganganu, ba na so bana buƙata". Ya yinƙura zai fice, Abbu ya riƙe shi ya ce "Umarni nake baka, ba shawararka ko ra'ayinka nake nema ba, dole ne wannan, aurenka wani satin, na kai kuɗin aure da komai, dole ka nutsu ka shiga hankalinka, idan ka illata musu ƴa ko kasheta kuma, zan sallamawa duniya kai, wannan shi ne hukuncin da na yanke" A fusace ya ce "Meyasa zaka yanke wa rayuwata hukunci, ba tare da amincewata ba bayan ka daɗe da sallamawa duniya rayuwar tawa? Ka yi hakan ne saboda farincikin matarka ko? Ta daina ganina na gusa na bar mata gidan nan ita da iyalinta. Da zan iya wallahi garin zan bar muku na ɓacewa ganinku ku samu cikakken kwanciyar hankali kamar yadda ku ke buƙata, amma ba zan iya ba. Ka sani ina ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, da gaske zan iya kashe ƴar mutane, ko na illata ta, sai dai ba na fatan na fi haka lalacewa, idan ka yi mini baki, zan ƙara lalacewa ne zan bi umarninka, amma duk abun da na yi mata da ni da kai zamu ɗauki nauyin zunubin. Saboda ni babu mata a tsarin rayuwata, miyagun halittu da babu Allah a ransu, bana fatan raɓar su, saboda yadda tasirin kaidinsu ya kassara rayuwata, kassarawar da ba za ta gyaru ba, mace ɗaya da nake wa kallon rayuwata, uwata kenan na rasata a yanzu babu wata mace mai sauran kima da mutunci a idona, nayi alƙawarin nesanta kaina da mata, nesantawa mai nisa ta har abada, amma ka karya mini alwashi, ta hanyar janyo mace rayuwata, ina sake nanata maka, duk abun da ya biyo baya, tare zamu ɗauki nauyin zunubin". Ya saka hannu, ya cire hannun Abbu da ya riƙe masa riga, ya saka kai ya fice. Har ya bar gidan, babu wanda ya sake magana, daga ita har Abbu. Gaba ɗaya aka hana jauhar fita daga gida, ana ta shirin biki, ita kuma tana rama kamar ana tsotseta, duk ta fiƙe sai farar fata da idanuwa. Maƙwabciyar su ta din ga cewa "Gaskiya mama ban so a aurar da jauhar yanzu ba, na so a bari maƙerin budurci ya gama ƙere mana ita, wannan kyawun da gidan wani hamshaƙin ya dace" Anty ta ce "Wannan ma hamshaƙin ne". A gida mama ta saka su surayya sa walida, suka dinga kwaɓe-kwaɓe suna murzawa jauhar da sunan gyaran jiki. Malam jamilu ya shiga matsananciyar damuwa, da samun labarin auren jauhar, dan har ga Allah yana matuƙar sonta, tsoron kar ta daina ganin mutuncinsa, ya sanya ya ɓoye mata. Gidan jauhar da aka je jere, yana da girma, sai dai tsakar gidan tsurar ƙasa ce, cikin ɗakuna babu floor, sai dai an yi plasta a ɗakunan, falo ɗaya da ɗakuna uku a ciki, kowanne da banɗaki, sai kitchen a tsakar gida da tsakar gida mai girma. An yi wearing ɗin wutar lantarki, a gidan. Sai buhunhuna, aka shimfiɗa a ƙasa, sannan cikin ɗakunan aka saka leda, falo kuma aka shimfiɗa carfet, saboda duk turɓaya ne. Tagogin duk babu na kirki, sai kame-kame da faci. Sai kujerunta, ƴan gida masu kyau, ɗaki ɗaya an saka furnitures, ɗaya kuma sai aka saka ƙatuwar katifa da wardrobe mai biyu, abun saka takalma. Duk da haka gidan ya yi kyau. Amarya ta din ga fargaba da tunanin, waye mijin nan, da haryanzu za ace, bai taɓa ganinta ba, kuma ba ta taɓa ganinsa ba? Kuma ya amince da zai aureta. Dogon gashinta baƙi, aka gyara mata shi, aka yi mata lalle ja da baƙi. Haka kurum take tuna Alhaji mu'azzam, a haɗuwarsu biyu, yadda yake nuna yana sonta, ba ta son ya zai ji ba, idan aka ce masa an yi mata aure. Kodayeke ita ba ta san dalilin fasawa da shi ba. Su liti suka lura da shirun Al'amin ya ƙara yawa, duk da ba mai yawan magana ba ne dama, sai ya zauna yayi shiru yana zancen zuci. Walid ya ce "Baaba, wai dan Allah kwanan nan meyake faruwa ne? Kamar ka na cikin damuwa" tabbas ba dan Walid ya tambaye shi yanzu ba, ba zai gaya masa ba. Ya karkace ya ɗaukko invitation a aljihunsa, ya miƙa wa walid. Wani irin ihu walid yayi, haɗi da kururwa, yayi katantanwa a ƙasa ya kuza uwar ashariya. Sannan ya ce "Allah dai ya biya maza, dama zaka afkawa sabgar nan, ka yi mana shiru haka? Ba ka gaya mana ba, balle mu shirya saura kwana uku fa". Sauran matasan da ke wurin suka miƙe suna tambayar Walid ko lafiya?. Ya miƙa musu invitation ɗin, take suka hau shewa suma, suna dara. Kawai ya dafe kansa, yayi shiru. Walid ya ce "Wai tsaya, auren dole za ayi maka ne? Na ga baka murna, kuma shi ne ba ka taɓa kai mu ehhh, mun gaisa da antyn namu ba, iya wuya mun samu mai dafa mana abinci" "Walid, Abbu ne ya shirya komai, ni ko ganinta ban taɓa yi ba, kuma ba na fatan na ganta, kuma ba kowa ne ya shirya wannan abun ba, sai wannan shaiɗaniyar matar ƴar haramun, ya ce umarni yake bani ba shawara ba, ni kuma na yanke guduwa zan yi, ba abun da zai haɗani rayuwa da wata mace, ba za a mayar da ni nusari ba, kalli yadda mace ta yi silar rushewar farincikin rayuwata gaba ɗaya" Walid ya zauna kusa da shi ya ce "A'a maza, duk lalacewar naka naka ne, kai ka san albarkar dattijan ke riƙe da mu, ka daina kallon abun da yake yi maka na rashin jin daɗi, idan yayi maka baki ƙara watsewa zaka yi. Duk da lokaci ya ƙure, dole ayi celebration, zamu gayyaci gayu a sha shayi a babbaka hayaƙi, abun farin ciki ya same mu" ya ƙarasa maganar suna shewa, ban da Al'amin da zuciyarsa kamar ta yi bindiga. Hatta kayan da Al'amin zai saka na aure, sai da Abbu ya saya wa Al'amin,  dan ko ganinsa bai sake yi ba, sai dai ya fita yawon neman sa. Ƙarfe goma na dare, su Walid suka shirya party, aka dafa shayi aka raba lemuka, da kayan shaye-shaye. Gogan yana gefe, yana zancen zuci, har ga Allah so yake ya gudu, amma ya san ya gudu alaƙarsa da Abbu za ta ƙara tsami. Kuma ya san ko ya gudu sai ya dawo, ba zai iya barin Abbun ba. Tunani yake kowace mai tsautsayin da ba a so, ce haka, aka zaɓi a aura masa oho. Ana tsaka da walimar hayaƙin, faɗan daba ya kaure, Al'amin kuma ya koma gefe ya ƙi magana, ƴan sanda suka yi wa wurin dirar mikiya, saboda rahoton da ƴan unguwar suka kai wa jami'an tsaro, ai kuwa suka kame su har da shi suka tafi da su ana gobe ɗaurin auren da bai san wacece matar ba. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Abbu kuwa hatta ɗinkin da Al'amin zai saka, ya yi masa, sai dai tun ranar da ya gaya masa, bai sake saka shi a idonsa ba. Yana zaune yana ta mitar rashin ganinsa rahila ta ce "Ba fa zama zaka yi ba, tashi zaka yi ka je ka nemo shi duk in da yake, kar ya kunyataka a idon duniya. Kana kallo yanzu na sauke mayafina daga gidansu amaryar, sun yi walima, duk sun gama shiri, na kai musu mukullin gida, har jere sun yi, fita zaka yi ka nemo shi ai" Haka Abbu ya shuri takalama ya bazama, aka sanar da shi, su na can wata unguwar, suna walimar aurensa. Ya bazama ya tafi, yana zuwa ya tarar da labarin ƴan sanda sun kama su duk sun tafi da su. Hankalin Abbu ya tashi, ya tafi division ɗin nan unguwar aka masa a station ɗin ma artabu aka yi da su, an kwashe su an kai su anti daba, ya ce wallahi ba za shi anti daba a daren nan ba saboda shi. Da ya koma gida kuwa, rahila kamar ta ari baki saboda mitar, meyasa bai je ba a sake shi, kar ya basu kunya, ya ce idan za ta iya, ta tafi. Jauhar kuwa su mama suka sakata a ɗaki, suna yi mata nasiha, fuskokinsu ɗauke da fara'a da jin daɗi, da nanata mata ba zasu zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba. Ita dai ta damu sosai ta ga waye wannan mijin, da har suka ga ya dace da ita? Har a ranar idonta da kwanciyar jinin jifan da mama ta yi mata da takalmi. Washegari ranar juma'a, za a ɗaura aure a babban masallacin juma'a, amma Al'amin yana tsare. Sha ɗayan rana, sai ga P.A ɗin Honorable indabo a anti daba da kansa, ya je belin Al'amin, wanda ya yi hakan ne, saboda aikinsa da yake son ya ƙarasa masa. Suka din ga sara masa, suka gaisa ya gaya musu wurin wanda ya zo, yake son ya yi beli, da wanda ya aiko shi" "Gaskiya malam  yaron nan ba zai ci bulus ba, state CID zamu kai shi" P.Aya ce "Ayi haƙuri, in anjima za a ɗaura masa aure, ko dan albarkacin wannan a sake shi mana" "Wai ka san me ya yi kuwa?" "Eh, an ce sun yi shaye-shaye sun tayar da tarzoma ko?". "Ai da wannan ne da sauƙi, ya saba zuwa wurin nan a kan haka, jiya ƴan sandanmu sun kamo su, saboda sun sha tana gaya musu gaibu, a tsakiyar harabar station ya ɗaga ɗan sanda ya buga da ƙasa, saboda yana ganin ya isa, ya na ji da ƙarfi. Kuma ya din ga yi wa mutane wani shegen kallo kamar kumurci, zai gane kurensa, CID zamu kai shi" Ana haka shugaban kula da sashen ya shigo da shi da wani matashin ɗan sanda, suka ƙame suna sara masa, ya kalli P.A ya ce "Lafiya kuwa?". Suka gaisa sannan ya ce "Honorable ne dai ya kuma aikoni ayi ban baki, a saki Mai dogon zamani " "Ba su gaya maka laifin da yayi ba? Jami'inmu fa ya daka, ba ya ji yaron nan ko kaɗan" "Sun gaya mini, amma kamar yadda aka saba, honorable ya bayar da saƙo" Ya numfasa ya ce "A fito da shi da sauran yaran da ku ka kama" aka buɗe Al'amin, da yaransa, ya fito yana ɗan jirga ƙafarsa a hankali, saboda taron dangin da suka yi masa jiya, suka yi masa dukan tsiya, daga jami'in ya tankaɗa ƙeyarsa, ya waiwayo a fusace ya saka ƙafa ya kwashe shi a wurin. Daga shugaban, har PA ɗin babu wanda ya kalla, ya kama hanyar ficewa daga cikin station ɗin. Ya girgiza kai ya ce "VIPER kenan, Allah ya shirya". PA ya ce "Viper kuma?" "Eh sunansa kenan a gidan nan, sunan da suka saka masa kenan, ban san sau adadin da muka kama shi ba, ban taɓa ganin mutum mai bala'in taurin kansa ba, mu daka mu daka wallahi ko gezau ba ya yi, ga wani sheɗanin kallo da yake yi wa mutane, kai ka ce kumurci ne zai kai sara, shiyasa nake yi masa sha'awar hakar tsaro, yana da girma da kwarjini na gaske, amma shi ba a saka shi ba a hana shi". P.A yayi murmushi ya ce "Ai tun da ka ga honorable ya riƙe masa wuta, ba ya wasa da lamarin sa, kai ka san ba ƙaramin mara ji ba ne". "Eh ai ku ne ke goya musu baya" "Ai sabgar tamu ce dole sai da su". Kafin PA ya gama sallamar su ya fito, tuni su Viper sun ɓace. Har gida walid ya je ya sanar da Abbu, an sako su, amma yayi yayi da shi, ya taho gida yayi shirin ɗaurin auren yaƙi. Abbu ya bi walid, har in da Al'amin yake, ya mimmiƙe yana bacci, jikinsa duk shaidar dukan da ya sha a station. Maganar duniya Abbu yayi, amma yayi burus ya ƙi tashi, sai da ya cire takalmi ya hau ƙwala masa, sannan ya tashi da ƙyar yana muzurai, Abbu ya tasa shi a gaba zuwa gida. Ba ƙaramin kyau manyan kayan suka yi masa ba, yayi wani irin kyau na mussaman, kwarjinin da Allah ya yi masa ya fito sosai da sosai. Bayan sallar juma'a aka ɗaura masa aure, bayan an saukko daga masallaci, babu wanda ya sake ganinsa. Jauhar kuwa gabanta sai tsananta faɗuwa yake yi, ƴan ƙawayenta na makaranta, suna ta tsokanarta, suna yi mata raha, amma ta kasa sakewa. Mama ta hau ta da zagi a gaban mutane, wai sai ta saka an ce aure dole za ayi mata, taƙi walwala ko wanka ba ta yi ta shirya ba. Jiki babu ƙwari, jauhar ta yi wanka, aka yi mata kwalliya. Tayi kyau sosai da sosai, dama dai-dai gwargwado tana da hasken fata da kyanta na fulani. Baba ne ya fara dawowa gida, gaba ɗaya jikinsa a sanyaye, ana ta yi masa Allah ya sanya alkhairi. Ya saka aka kira masa jauhar, zuwa ɗakinsa. Cikin tsananin tashin hankali da damuwa, Saifu ya shigo gidan, yana ƙwalawa baba kira. Mama ta ce "Saifu lafiyarka ka ke yi wa mahaifinka irin wannan kiran haka?" Bai saurareta ba, ya shiga ɗakin baban, mama da anty suka bi bayansa, 'yan biki kuma suka yi cirko-cirko. "Baba wane irin miji ka aurawa jauhar? Tun a masallaci nake nemanka ban ganka ba" Baba yayi shiru, ya ƙi bashi amsa. "Baba magana nake yi fa kayi mini shiru yanzu zaka yi alfahari da wannan zaɓin da ka yi mata?marainiyar Allah, ka rasa wa zaka aura mata sai tantirin ɗan daba? Laifin me tayi maka har haka, mutumin arziki ya fito yana sonta, amma ka hana shi ka bawa mutumin banza, yanzu wane mutumin kirkin ne zai so haɗa zuriya da mai dogon zamani" A gigice jauhar ta ɗago idonta, gabanta ya shiga faɗuwa, tana jin yadda sunansa ya karaɗe arear unguwannin, duk da ba ta taɓa ganinsa ba, amma ya shahara da rigima da 'yan unguwar su, da shi da madaki tana jin sunayensu, ta san dai madaki, tun da cikin unguwar su yake. Cikin zafin rai saifu ya sake cewa "Baba ka yi mini bayani, menene dalilinka na yin haka?" "Saifu, kai ma ka fara shaye-shayen ne? Uban naka ka ke gaya wa haka? Shi ka ke tuhuma? Ba 'yar sa ba ce? Zai zaɓa mata abun da zai cutar da ita ne?" Ya ce "Zai yi mana mama, ke da wannan matar menene ba zaku iya aikatawa ba, kuma na san ku kuka ƙulla komai, akwai Allah" Jauhar kuwa kuka ta fara, amma ta kasa magana, jikinta ya din ga tsuma, Hafsa kuwa fita tayi, ta kira yaya tijjani, wai ga saifu can yana yi wa baba rashin kunya. Aikuwa ya shigo cikin gidan da sauri, zuwa ɗakin baba, sai faɗi in faɗa yake da mama, baba kuma ya ƙi magana. Yana zuwa ya ɗauke saifu da mari, sai dai yana sauke hannunsa shi ma ya rama, take dambe ya kaure, sai dai jin hayaniya a waje ne, ya sanya suka yi saroro. Bushe-bushen 'yan tauri ne yake tashi daga ƙofar gidan, nan da nan warin wiwi ya din ga shigowa gidan, yaran Aminu sun cika layin, suka din ga busar 'yan tauri, suna yi wa Aminu kirari, sai dai babu shi a wurin. Su maman ma waje suka yi, domin zuwa su ga abun da yake faruwa. Nan 'yan biki suka dare, wasu kuma suka tafi kallo. Baba ya riƙo hannun jauhar, da take ta uban kuka, kamar shi ma zai fashe da kuka ya ce "Fatima, na yi miki laifi, ban san yaya aka yi wasu abubuwan suka faru ba, dan Allah ki yafe mini, in sha Allah ba zaki wulaƙanta ba, zaki yi alfahari da hakan, na san na daɗe ina zaluntar rayuwarki, ina cutar da ke, dan Allah ki yafewa baba jauhar, kar ki yi fushi da ni, in sha Allah sai auren nan ya zame miki alkhairi" Ta share hawayenta ta jinjina masa kai ta ce "In sha Allah Baba" "Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya yi miki albarka ya kare ki daga dukkanin sharri da abun ƙi, Allah ya kula mini da ke a duk in da ki ke.Na san dama ke mai haƙuri ce, zaki ci riba in sha Allah" ta jinjina masa kai tana ƙoƙarin haɗiye kukan da yake ƙoƙarin ciwota. Ba a rabu da bukar ba an haifi habu, ta san wannan auren wani sabon ƙalubalen ne a rayuwarta. Ƙawayenta tuni suka gudu gida, 'yan biki ma duk sun watse, ta samu wuri ta ƙule a ɗakinta, ta din ga kuka, tana neman agajin Ubangiji. Kwatsam! Yaran madaki suma suka taho layin, da niyyar tarwatsa yaran Aminu, dan kuwa ba sa jituwar da za su bari su shigo musu layi, su yi musu wannan budurin. Ba a jiyo komai, sai karafkiyar makamai, da zage-zage tamkar ana yaƙi. Suna daga cikin gidan, suka jiyo ana cewa tun da aka aurar da ƴar gidan ga maƙiyinsu, idan ta bar unguwar ta bar ta kenan, idan suka kuma ganin ta, sai sun sassarata. Mama ta ce "Zakiyya, kin ga wata tijara, ni fa hankalina ya tashi, ji kamar ana yaƙi". "To ke ina ruwanki, da an kaita ba shikenan ba, can su je su ƙarata ba" Suna cikin maganar, sai ga gwangwanin tiya gas, a tsakiyar cikin gidan ƴan sanda sun sake dira, su tarwatsa su. Jauhar ta ƙara takurewa tana kuka, saboda tsananin tsoro da tashin hankali, dan a kunnenta ta ji ana cewa, idan aka ƙara ganinta a unguwar ma, sai an sassarata. Unguwar ba ta yi dai-dai ba, sai bayan sallar la'asar, hatta sallar la'asar a gida aka yi ta a unguwar, saboda tashin hankali. Bayan Baba ya yi sallar la'asar, ya kira mama ya ce, ya shirya masa jauhar, ya kaita da kansa, tun kan yaran nan marasa ji su ce za su yi mata illa. Idanun jauhar duk sun kumbura, sun jawur saboda azabar kukan da ta sha. Mama tana dariya take cewa "Haba Jauhar, kowa da haka yake kafa nasa iyalin, da haka kowa ya saba" Jauhar ta kalli mama, iya wannan tashin hankalin bai isa ya sanya su gane sun jefa rayuwarta a garari ba, amma take yi mata wannan surutan? Haka ta yi alwala ta yi sallar la'asar, sai dai ta kasa addu'a ma. Ko kaya ba ta canza ba, mama ta ɗaukko mayafi, ta ce tare za su kaita ɗakin miji. Sun fito waje, Saifu ya kawo kai, yayi turus ya ce "Baba, yanzu wannan tashin hankalin da aka yi a unguwar nan, duk a kan auren nan, bai sanya ka saduda ba, ka haƙura? Baba ya yi masa shiru, ya yi gaba hannunsa riƙe da na jauhar, ya buɗe mata mota ta shiga baya, suka ja suka tafi. A can suka tarar da wasu daga danginsu Al'amin, a gidan suka din ga rangaɗa guɗa, da aka ce an kawo amarya, dan sun baro can gidan su Al'amin, a kan Abbu zai aika da motocin ɗaukko amarya, sai dai suna ganin Baba suka nutsu suka yi shiru. Har kan gado ya kaita ya zaunar da ita, ya riƙe hannunta, ya din ga yi mata addu'a, sannan ya sunkuya ya yi ƙasa da murya ya din ga yi mata nasiha, yana yi tana kuka, sai da ya gama ya din ga saka mata albarka ya ce mama ta wuce su tafi. Angon kuwa yana can dabar su, ban da bushe-bushen sigari, babu abun da yake yi, hatta dambarwar da aka yi a gidan su amaryar bai sani ba, shi dai ya san Walid ya ce za su gayyato 'yan gangi da 'yan tauri, ayi nishaɗi. Bai ma san a ina aka ya ba, balle ya san abun da ya faru. Sai wajen ƙarfe takwas na dare, Walid ya dawo, ya din ga ba shi labarin, abubuwan da suka faru, da yadda suka yi da 'yan sanda. A ƙalla ya kai mintuna goma sha biyar yana zuba, yana bawa Al'amin labari, amma bai tanka ba. Ya gaji ya ce "Maza, ka tashi mu shirya, mu raka ka gidan amarya". Sai a yanzu ya ɗago ya kalleshi, amma ya yi tsaki ya koma ya kashingiɗa. Walid ya ce "Wallahi ba ka isa ba, wai so ka ke sai Abbu ya yi fushi da kai? Dama na haɗa maka kayanka jiya, yau sai ka bar gidan nan, kai Allah ya ɗaga darajar ka, kana wasa da damar ka" walid ya cigaba da mita, yana ƙara haɗawa Al'amin kayansa a ghana must go, da masu dauɗa, da wankakku, har da takalma da brush, haka ya din ga danna su. 'yan uwan su Al'amin, babu yadda ba su yi ba, su ga fuskarta, amma fafur ta ƙi, ta din ga ƙudundunewa, suna nan tare da ita har tara na dare, suka gaji ga dare, masu zuwa ganin gida, duk suka gama, suka din ga tafiya, har ya rage saura itakaɗai aka bari. Nan hankalinta ya fara tashi, daga ita sai farar fitila mai batir, tana ta addu'a a cikin zuciyarta cike da fargaba da tsoro. Tana ta tunanin kar 'yan daba su lallaɓo su zo su kasheta. Ta gaji da zaman wuri ɗaya, ta ga ledar pure water, a ajiye a falo, da 'yan ganin gida suka zo da ita, ta ɗauka ta yi alwala, ta yi sallolin da suke kanta, ta zauna zaman dirshen tana tuna ƙalubalen rayuwa da ta haɗu da su kashi-kashi yanzu kuma ga ta kuma a wani mataki, mai hatsarin gaske. Har bayan sha ɗayan dare, sai itakaɗai a gidan. Fargaba da tsoron da take ciki, ya ninku a zuciyarta. Kasancewar bacci ɓarawo ne, haka ya yi awon gaba da ita daga nan in da take a zaune kusa da gado. Sai dai ba ta san adadin lokacin da ta shafe tana baccin ba, ta farka a razane, taga hasken wutar lantarki an kawo wuta. Ji ta yi kamar motsi a falon, ta lallaɓa ta leƙa cikin tsoro da tashin hankali bakinta ɗauke da addu'a. Wani dogon mutum ta gani a kwance a kan doguwar kujera, ya juya bayansa, ya duƙunƙune da babbar riga, da alama sauro ne ya dame shi, ya lulluɓa. Gabanta ya faɗi, ta koma ta zauna tana tunanin, wannan shi ne angon ko kuwa? Iya ƙoƙarinta ta dage kar ta kuma komawa bacci, saboda tsoron da take ciki. Al'amin kuwa, Walid ne ya taso shi a gaba, ya kai shi har gidan, daga shi sai shi, da ƙullin kayansa a ghana must go wajen sha ɗaya da rabi na dare. Suna tafe yana lallaɓa shi, sai da ya tabbatar ya shiga, sannan ya tafi. Ya shiga yana ƙarewa gidan kallo, shi dai ya san gidan kango ne, amma yadda aka jera masa kaya, yayi kyau. Yana shiga falon, bai bi ta kan ina amaryar take ba, ya tuntsurar da ƙullin kayansa ya haye kujera ya mimmiƙe kamar gawar sababi. An fara kiraye-kirayen sallar asuba, ta shiga banɗakin cikin ɗakin, tayi alwala ta din ga nafilfili, har aka yi sallar asuba. Bayan ta idar tana cikin azkar, wani irin nannauyan bacci, ya kwashe ta a wurin. Sai da gari ya yi haske, sannan ta farka, ta tashi tana salati, ta tashi tana ƙarewa ɗakin kallo. Yayi kyau sosai da sosai, duk ko fenti babu amma furnitures ɗin sun yi kyau. Ta fita falon gabanta na faɗuwa, domin gaida mai gidan da no nemanta bai yi ba, sai dai ba ta gan shi ba, ta leƙa ɗaya ɗakin, amma baya nan, sai ghana must go a falo. Ta fito tana ta lelleƙa gidan, abun ya burgeta, duk da ba ƙerarren gida bane, amma ta ji daɗin cewar gidanta ne ita ke da iko da shi, amma da ta tuna haryanzu ba ta yi ido huɗu da angon ba, sai gabanta ya faɗi, ta fara tunanin ko shi ma auren dolen aka yi masa da ita. Tunawa ta yi, da 'yan dabar Unguwar su, sun ce idan suka kuma ganinta a unguwar su, sai sun sassarata. Gaba ɗaya ranta ya ƙara dugunzuma. Ta zauna shiru a falo, tana ta jira, ko wani zai zo mata daga gida, amma shiru babu wanda ta gani, ga yunwa tana ji, dan wunin jiya ba abun da ta ci, gashi ta kwana ta wayi gari ba ta saka komai a cikinta ba. Can kuwa, Rahila kuwa kamar ta taka rawa, ta rabu da ƙaya, Aminu ya bar mata gida, ta ƙara sakewa da ita da yaranta yadda take so, fargabar ta zata ragu sosai da sosai, ta san yanzu dole zai tattara ya bar unguwar ya ƙara gaba. Dangin mahaifiyar Aminu da suka zo, daga can ƙauyen tofa, ta din ga wulaƙanta su, dan sai da ta yi wa Abbu masifar dan me za a gayyato su, sai dai a hakan gudunmuwar dubu ɗari biyu suka bawa Abbu na auren. Ban da uban kayan abinci da suka taho da shi, suka ce a ƙara a kan na biki. Sai dai har suka yi kwana biyun, ko sau ɗaya ba su ga Al'amin ba, sai kwasar takaicin rahila, yadda take wulaƙanta su, tare da aibata shi, tana an mutu an bar mata riƙon masifa da tsiya. Washegari da safe, waɗanda ba su je ganin gidan ba, suka ce za su je su ga gidansa, daga nan za su wuce su koma tofa. Da Abbu suka yi sallama, Rahila kuwa ko kallo ba su isheta ba. Har wajen sha ɗaya da rabi na safe, jauhar na zaune na rarraba ido,  ta ji sallma a tsakar gidan. Amsawa tayi, tana jiran ƙarasowar masu sallamar. Mata ne wasu 'yan dattijai, da matasan 'yan mata. Jauhar ta karɓe su hannu bibbiyu, suka shigo falon suka zazzauna, hannunsu da kaya. Suka gaisa da jauhar, ɗaya daga cikinsu ta ce "Tubarkallah, Aminullahi ya mori 'yar kyakykyawar yarinya Tubarkallah, ya sunanki?" Jin abun da suka ce, ya sanya ta gane 'yan uwansa ne, ta ce "Jauhar" Suka din ga maimaita sunan nata, suna cewa sunanta na 'yan birni. "Ina Aminullahin ne? Tun da mu ka zo, bamu ganshi ba, gashi daga nan can gida zamu koma" cewat wata dattijuwar. Jauhar ta ce "Ya fita" "Ohh, ji soko, daga kawo masa amaryar jiya, har ya saka ƙafa ya fice, to Allah ya kyauta. Kin ganni ni kakarsa ce, ga yayar gyatuma tasa, nan duk 'yan uwan mahaifiyarsa ne, amma ba ya zuwa in da muke. Dan Allah kya ɗan din ga saita shi a hanya, ki yi ta haƙuri kin ji, Allah ya baku zaman lafiya" Kunya ta saka jauhar kasa amsa musu. Suka yi ta yi mata hira, amma ta kasa amsa musu, saboda nauyinsu da ta din ga ji, sai dai kakartasa mace ce mai barkwanci, suka ba ta kayan da suka zo da su, su tsintsiyar laushi da ta kwakwa, kaskon turaren wuta, kayan miya har da kuɗi. Jauhar ta yi tayi musu godiya, sai dai ranta duk babu daɗi, ga baƙi amma babu abun da za ta basu. Zuwa azahar, suka yi mata sallama suka tafi. Har la'asar babu wanda ya sake zuwa, ta ji babu daɗi sosai, rashin ganin wani daga gidansu ko mutum ɗaya. Yaran maƙwabta suka ɗan shisshigo mata, shigowar ta su tayi mata daɗi, ta basu kuɗi, ta ce su sayo musu buredi. Suka sayo, suka zauna, suka ci tare da su, ta ajiye wani da niyyar idan mai gidan ya zo ta bashi. Mama kuwa bayan sun koma gida daga kai jauhar, duk 'yan biki sun watse, kowa tayi ta kanta. Suka ƙule a ɗaki ita da zakiyya ta ce "Zakiyya duk da gidan yarinyar nan babu gyara, amma yayi kyau sosai da sosai" "Eh ai hakan yayi, ma rage wani surutun, har ku ka taho kuwa kun ganshi ya je gidan shi angon?" Mama ta ce "Ina fa, itakaɗai muka baro, sai wasu 'yan uwan babarsa, su ma na san ba zasu jima ba zasu tafi ba. Nifa sunansa kawai nake ji, ban taɓa ganin sa ba". "Zaki ganshi ne, ba dai ya zama sirikinku ba? Ni na san shi, amma lokacin yana yaro, ai kin san daga baya suka dawo ƙofar na'isa da ba a nan suke ba, ni tsoro nake ji ma kar yaran nan su cigaba da kawo mana farmaki" Mama ta ce "Babu abun da za su dawo su yi mana, mun yada ƙwallon mangwaro mun huta da ƙuda, yanzu menene abun yi?" "Abun yi, shi ne mu jira dawowar wannan Alhajin, mu ga yadda za a ɓullowa lamarin ya haƙura gaba ɗaya da batun ta" "Haka ne, to Allah ya dawo da shi lafiya, sai ayi ta ta ƙare, jauhar dai an aurar da ita, sai mu jira mu ga yaya zai kasance da namu 'ya'yan. Gidan jauhar magariba na yi, yara suka watse suka bar ta itakaɗai kamar tsohuwar mayya. Sai fitila ta kunna, ta saka mayafinta ta din ga korra sauro daga ɗakunan, saboda yadda suke ambaliya kamar a barikin su. Ta rurrufe ko ina, tana jiran ta ga ta ina ango zai shigo, amma shiru. Har bacci ya kuma cin ƙarfinta ya kwashe ta. Wunin ranar kuwa, Al'amin zarya ya din ga yi, sai da aka sakar masa yaransa da aka kama a unguwar su madaki, har suka sanar masa iƙrarin da 'yan unguwar da suka yi, na idan suka kuma ganinta a unguwar sai sun sassarata. A ransa ya ce Allah ya ƙara, maganinsu kenan, da suka ga babu wanda ya dace su bawa 'yar su sai shi. Tare da su ya wuni yana shaye-shaye, Walid ya na son ya yi masa magana, amma ya san yana yi za su yi faɗa, dan haka sai dare ya sake lallaɓa shi, daga can unguwar ya goya shi a babur ya kai shi gidansa na ɗorayi chiranci. Sai dai kamar jiya, kafin gari ya yi haske, ya sake barin gidan, gashi ko brush ba ta da shi, ba ta da kayan girki, haka ta kuskure baki ta cinye biredin jiya, gashi ba ta son cigaba da taɓa kuɗin da aka bata, yakamata ta nuna masa kayan da aka bata, saboda 'yan uwan sa ne suka bata. Ta fito tsakar gida ta samu wani ɗan tudu ta zauna, tana tunanin yanzu haka za ta rayu, wanda ya ajiye ta baya ko ƙaunar ganinta, kwana na biyu kenan haryanzu ba ta ga kalarsa ba ma. Tana son yin wanka da sauran buƙatu, amma ba hali, babu ruwa, ga rijiya a gidan amma babu guga, babu sauran kayan masarufi. Ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi ya dawo da ita hayyacinta, ta tashi ta ɗaukko mayafi ta saka, ta buɗe a hankali. Saifu ta gani a tsaye, hannunsa riƙe da kaya. Ta washe baki ta ce "Yaya saifu" yayi murmushi ya ce "Na'am Waliyiyya" Ta bashi hanya ta ce ya shigo, ta karɓi kayan hannunsa, suka shiga har falo. Ya kalleta ya ce "Yaya babu wata matsala dai ko?" Ta girgiza kai ta ce "Babu" "Ina mijin naki yake?" "Baya nan, ya su baba? Ya su mama?" "Suna nan ƙalau, gida yaƙi kyau ba kya nan, duk 'yan matan nan an rasa wadda za ta yi aikin da ki ke yi" tayi shiru tana murmushi. "Ga sauran kayanki na kawo miki, na harhaɗo da na ɗakinki duk na kawo miki, muddin ki ga ya yi miki wani abu da baki gamsu ba, ki gudo gida kin ji ko?" Ta jinjina masa kai alamar to. Ya ce "Kina buƙatar wani abun ne?" Ta ce "A'a" Ya miƙe ya ce "Na san ba zaki faɗa ba ai" ya shiga kitchen ɗin ta yana dubawa, babu alamar an dafa wani abu. Ya ɗauki gas ɗin ta, ya fita da shi, ya yo mata refilling, ya yi mata sayayyar kayan shayi da 'yan kayan abinci, ya dawo ya kawo mata. Ya ce "Ki yi haƙuri jauhar, bani da kuɗi, amma zan sake dawowa in sha Allah, kar ki yadda da wani haƙuri, na san zaman aure haƙuri ne, amma kar ki zauna ana zaluntarki, ko ya ce zai dake ki, zan sake dawowa in sha Allah kin ji ko" ta ɗaga masa kai alamar eh, ya sayo mata guga, ya janyo mata ruwa ya tara mata, ta din ga yi masa godiya suka yi sallama. Bayan tafiyar sa, tayi wanka ta canza kaya, yaran maƙwabtanta da suka shgo, ta dafa musu taliya, suka ci ba ta gaza ba, ta ɗebarwa maigidan nasa ta ajiye. Sai dai yaran da wuri suka tafi yau, ta samu wuri tana wanke-wanke, ta ji kamar an wuce ta bayanta. Tashi ta yi a firgice, tana addu'a da tunanin ko gane-gane ta fara yi. Sai dai ta ga takalmi a ƙofar falon, kasancewar gidan akwai gate, kuma akwai ƙaramar ƙofa, ƙofar a buɗe take. Ta lallaɓa ta leƙa, ba ta ga kowa ba, ta shiga falon tana tambayar waye?. Fitowa ya yi daga ɗaya ɗakin, hannunsa riƙe da baƙar leda, kallo ɗaya ta yi masa ta gane shi, ƙwala ihu ta yi, ta ruga da gudu ɗakin da gadonta yake, ta rufe ƙofar ɗakin. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Hanyar da ta bi ya bi da kallo, yana tunanin a ina ya taɓa ganin fuskarta. A ransa ya ce "Mahaukaciya ce kenan, Shiyasa aka aura mini ita, haukana ya fi naki" ya fito daga falon ya saka takalmansa ya fice. Jauhar kuwa durƙushewa tayi, ta ɗora hannunta a ka ta ce "Na shiga uku" a take ta fashe da kuka ta ce "Allah ka sanya mafarki ne ba gaske ba, Allah ka sa ba wannan ne mijin nawa ba? A gabana ya kashe wani, Allah Ubangiji ka rufa mini asiri ka dube ni, ya Allah ka dubi maraicina da ƙangin da na baro, ka sassauta mini a nan, ya Allah ka sa ba shi ne mijina ba". Ta cigaba da addu'ar tana kuka, ta kasa fitowa sai ma ƙara sakata da ta yi a ɗakin tana kuka. A take komai ya dawo mata fes, yadda ta ganshi, ya yi kisan kai, hannunsa riƙe da mutum da wuƙa a gefen cikinsa. "Na shiga uku, ko biyoni yayi ya kasheni, me na yi masa wallahi ban gayawa kowa yayi kisa ba" tayi maganar ƙasa-ƙasa tana kuka. Ko da wasa ba ta yi yinƙurin, sake buɗe ƙofar nan, a banɗakik nan tayi alwalar magariba da ta isha'i, ta kasa addu'a komai, sai fatan Allah ya sa ba wannan ne mijinta ba. Ba ta sake fitowa ba, har garin Allah ya waye. Zaman ɗakin ya isheta, fitowa kuma ta gagareta, sai da ta leƙa ta ga babu kowa a falon, bakinta ɗauke da addu'a ta fito. Ba kowa, ta leƙa tsakar gida, ya rufe mata ƙofar, babu taklmansa kuma a wurin. Ta dawo falon, ya cinye taliya da man da da ta zuba masa tas, ya ajiye komai a wurin, hatta wadda ta ɗan zube a ƙasa bai kwashe ba, jug ɗin ma daban kofin jug ɗin daban. Ta kwashe komai ta fitar tsakar gida, ga sauran kwanukan da ta fara wankewa ta bar su a wurin, komai yana nan. Sai zuciyarta ta fara raya mata, ai ba shi ne mijin nata ba, ya shigo ne kawai ya tsorata ta, sai ta cigaba da addu'a Allah ya ƙara nesanta ta da shi. Ta yi 'yan gyare-gyaren ta na gida, yaran da suke shigo mata, yau ba kowa duk sun tafi makaranta, ga tsakar gidan wasu irin manyan ƙadangaru suna bin bango, dan haka fitowa tsakar gidanma wahala yake bata, saboda tsoro. Ta datse gidan, yadda babu wanda zai shigo sai ya bubbuga. A jere ta sake jera kwana biyu ba ta sake saka shi a idonta ba, akwai ranar da bai kwana a gidan ba. Bai sake dawowa da rana ba, sai cikin daren nan, idan ya tarar da abinci ya zauna ya cinye abun sa, kafin ta tashi ya fice. Abun ya fara damunta, ga tsoron gidan take ji, sosai da sosai. Wajen la'asar ta ji ana buga ƙofa, ta din ga tambayar waye, amma ta ji shiru. Har zata haƙura da buɗe ƙofar, ta zata ba kowa, aka kuma buga gate ɗin maimakon ƙofar da ƙarfin gaske. A tsorace ta buɗe, aikuwa ya hankaɗo ƙofar, ta kuma kurma ihu, ta kwasa da gudu, ta shiga kitchen ta rufe ƙofa. Sororo ya tsaya yana tunanin, ihun me take yi dan ta ganshi? Ya basar ya shiga ya yi abun da zai yi ya fice. Sai a yanzu ta fara gazgata lallai wannan ne mai gidan, shi ne mijin da aka aura mata. Cikin kuka ta ce "Allah komai ka yi dai-dai ne, Allah ka sanya shi ne mafi alkhairin da nake ta fata". Ta sanya wa zuciyarta za ta yi ƙoƙarin, danne tsoronsa da take ji, amma abun da ba ta gane na shi ne, ba iya abun da ya faru waccan ranar ne kawai yake ba ta tsoro ba, tsananin kwarjinin sa ne ke ƙara rikita ta. Suna dabarsu, Al'amin yana ta shan sigari, Walid ya ce "Maza, gaskiya abun da ka ke yi baya dacewa, an kai maka mata, amma kullum kana nan kana cakewa, akwai matsala ne?". Al'amin ya rausayar da kai ya ce "Yarinyar Mahaukaciya ce ashe" Cikin rashin fahimta ya ce "Mahaukaciya kamar yaya?". "Kamar yadda na gaya maka, ihu take yi itakaɗai" Walid ya ce "Ko dai tsorata ta ka ke yi? Ki tsaya kun yi magana kun gaisa?" Aminu ya ce "Da wa?" "Da amaryar mana" ya ja tsaki, yana mayar da sigari bakinsa. "Wallahi Aminu da ni aka yi wa auren gatan da aka yi maka da na more, haba baka kyautawa gaskiya " Yayi masa shiru, yaƙi ko kallonsa, dan ko zancen auren ba ya son ji, haka kurum ji yake yi kamar an yi masa dabaibayi. Saifu kuwa yanzu ban da gaisuwa, babu abin da yake haɗa shi da da mama da Baba, dama Babar su hafsa Zakkyya ba shiri suke yi ba, ko kallo ba ta ishe shi ba. Sai dai sun fara zancen a kawo 'yar aiki, dan duk yawan 'yan matan gidan nan, ba sa iya aikin gidan, girki sai dai a jagwalgwala, wani ya ciwu wani ba zai ciwu ba, gidan nan kuwa wasu lokutan kamar fadar mahaukaciya, dama jauhar ce ana ɓatawa tana gyarawa, yara na cire kaya suna zubarwa tana kwashewa, amma yanzu bata nan babu mai gyarawa. Baba kuwa ƙasan zuciyarsa yana nadamar auren da ya yi wa jauhar, amma ba zai iya nuna hakan ba, ya duƙufa yana yi mata addu'ar samun kwanciyar hankali a gidan aurenta. Cikin dare da ya dawo, ya ji gidan a rufe, bai tsaya jiran komai ba, ya kama katanga ya dira kamar ɓarawo. Gaba ɗaya jauhar a zatonta, itakaɗai ta kwana a gidan, saboda ba ta ji bugun ƙofa ba, ta fito tana ta share-sharenta, ta ɗora ruwan zafin dafa makaroni, saboda su yaya saifu ya sayo mata, taliya makaroni, mai maggi sugar da sauransu. Ta fara bin ɗakunan tana gyarawa. Sai dai ta din ga jin warin taba, ta rasa daga ina take jin warin. Kawai ta nufi ɗakin da yake ciki, ba tare da ta san yana ciki ba, ta afka, a zatonta ita kaɗaice a gidan. Yana kashingiɗe yana zaune yana kaɗa ƙafa yana shan tabarsa, ya zazzage kayansa a kan katifar ɗakin, ghana must go ɗin, ya cillar da ita a tsakar ɗakin. Har da takalma a kan katifar, soson wanka da brush duk suna kan katifar. Ba wannan ba kawai, har da ledoji da kwalayen taba, ga tokar maganin sauro ko ina. Kamar mahaukaciya haka ta juya, ta ɗiba da gudu, sai dai a wannan karon, rufa mata baya ya yi, ya cimmata, tana ƙoƙarin rufe ƙofar ɗakin da ta shiga, ya hankaɗa ƙofar ta faɗi jikinta na wata irin tsuma. Ya zuba mata ido, wanda ya haddasa mata tsuma da karkarwa cikin razani da matsanancin tsoro. Bai ce mata komai ba, sai cigaba da kallonta da yake yi. "Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ban gayawa kowa ka kashe shi ba, dan Allah ka yi haƙuri, ni matar aure ce, ka daina shigo mini gida" tayi maganar wani irin gumi na tsatstsafowa daga fuskarta. Ya sunkuyo saitinta, warin sigarin da ya sha, tana dukan hancinta, sai a lokacin ya gane ta, ya gene a in da ya taɓa ganinta. "Kin ganni na kashe shi?" Ta jinjina kai alamar eh. "Mahaukaciya ce ke? Ki na da taɓun hankali ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a, tana ja da baya. "Idan ki ka kuma ganina, ki ka gudu kina ihu" ya zaro wuƙa a ƙugunsa, ya nuna mata. Sannan ya ce "Sai na yi miki abun da ki ka ga na yi wa wancan mutumin, wato in kashe ki" Ta girgiza kai ta ce "In sha Allah ba zan sake ba" ya miƙe, ya mayar da wuƙarsa ya fita ya bar ta. Wani irin numfashi ta din ga saukewa, cike da tsoro, ta ƙara gazgata cewar, shi ɗin ne dai mijinta ba wani ba. Ta jima a wurin tana kuka, sannan ta tashi a hankali, ta sake komawa ɗakin da ta gano shi. Ɗakin yana nan, kamar mahaukaciya ta buɗe dealer, ya watsar da komai, sai warin sigari ɗakin yake yi. Ta ɗaɗɗaga labulaye, ta zo ta durƙusa ta fara ware kayansa, wankakku da masu datti, ta kwashe takalmansa, ta jera masa a bayan ƙofa, wankakkun kayansa, ta shirya su a cikin wardrobe, marasa wankin ta fita da su, ta share ɗakin tsaf, ta ɗauki brush ɗin sa da toothpaste, ta kai masa banɗakin cikin ɗakin, da bokiti da buta. Kayanta akwai turarukan wuta, da aka bata na gudunmuwa, sai dai ba ta da gawayi, dan haka ta kunna na tsinke, ta sassaka a ko ina, saboda korar warin sigarin nan. A cikin kayan sa ta ga wata Mp, ta ɗauki mp ta kunna ta ji tana yi, ta kunna radion jiki, ta ji tana yi, ta fita tsakar gida da ita, tana ta aikace-aikace, da zummar kan ya dawo ta kashe ta ajiye masa, ta ɗan ɗebe mata kewa, ta manta ko sallama baya yi kafin ya bayyana. Gidan su jauhar, akwai maƙwabciyar su Anty lubabatu, tana tausayinta sosai, suna mutunci da juahar, dan idan ta haihu, jauhar ta yi ta zuwa gidanta, dan ta ɗauki yaranta, ita ce ta haɗata da 'yan gidan su, take karɓar shirin dutse tana yi. Tun washegarin kai jauhar, ta shiga gidan ta ce wa su mama, a bata mutum ɗaya ya rakata gidan jauhar, amma suka ce ba wanda ma ya san gidan. Jauhar kuwa, ta gama aikinta tayi wanka, gidan babu komai na abinci, sai taliyar nan da macaroni da yaya saifu ya saya mata, gashi sun isheta, sai dai babban abun da yake yi mata daɗi, tana da damar ta dafa ta ci yadda take so, saɓanin idan a gida ta girka, sai ta gama wahalar a sanmata. Tunani take yi, idan ta dafa taliya yau ma ko zai ci, tana tunanin ko shi ma sun fara isar shi. "Karfa ya ce ko ban iya girki bane, shiyasa kullum nake dafa taliya. To ai gidan bakomai sai su" Ta ɗan yi shiru, tana tunanin yau bari ta aika a sayo mata kayan miya, tayi da miya, so take ma ta nuna masa kuɗin da kakarshi ta ba ta, amma tsoronsa take ji. Tana ta tunani, ta ji ana buga ƙofa, cikin murna ta tashi, ta san baƙi tayi sa ɗebe mata kewa. Anty lubabtu ta gani, maƙwabciyar su, da ƙanwarta wadda take karɓar shirin dutse a gidanta, cikin murna tayi musu maraba. Allah ya sa tana da ruwan pure water, ta basu. Ta ce "Anty lubabatu shi ne sai yau zaku zo ko? An barni nikaɗai, ba wanda yake leƙo ni". "Ki yi haƙuri jauhar, tun washegarin kawo ki, nake sintirin neman mai rako ni a gidanku, wallahi fafur 'yan gidanku da 'yan tsukin nan aka rasa masu zuwa su rako mu, wai tsoro suke ji, 'yan gidanku ma wai ba za su rakomu ba, mijinki ɗan daba ne, ni kuwa na ce ko menene zamu zo, sai kwatance suka yi mana". Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Shikenan bakomai, yaya saifu ma ya zo, daga ni sai yaran maƙwabta, ni kaɗai nake wuni". Samira ta ce 'Allah sarki, mma dai jauhar ba wata matsala dai ko?" Tayi murmushi ta ce "Babu anty samira, ya shiri kin zo mini da shi?" "Taɓ kina amarya, kawai sai na kawo miki shiri?" Jauhar ta ce "Eh mana, zai din ga ɗebe mini kewa ai, dan Allah idan an samu mai zuwa, ki bayar da yawa a kawo mini, na din ga yi" Anty lubabtu ta ce "Jauhar iyayen neman kuɗi". Samira ta ce "Bar ta ta nema, rayuwar nan ba a zama haka" Miya lubabatu ta soyawa jauhar, mai yawa ta sha naman kaji, da shinkafa da 'yan kayan buƙatu. Jauhar ta ji daɗin hakan sosai da sosai, ta din ga murna, suka wuni tare har la'asar, sannan suka tafi. Suna tafiya ta aiki almajiri, ya sayo mata salak da kayan haɗin sa, ta zauna ta shirya salak ɗin nan, ta juye miyar a tukunya, ta ƙara soyata tayi mata gyare-gyare ta ƙara mata su maggi da kayan ƙamshi ta kammala komai. Ta ɗebarwa yaran da suke shigo mata abincin ta basu, ta ɗebe wani ta rufe, dan abincin da yawa, ta sake turara shinkafar ta zuba a wani flask mai kyau kamar a lokacin ta dafa ta. Tana aikinta, tana jin radiyo a mp. Ta bawa yara kuɗi, suka sayo mata ruwa da lemo mai sanyi. Ta gama aikin, ta share kitchen ɗin, ta kwaso sharar abun da ta ɓata, ta fito kawai ta ga Al'amin a tsakar gida, aikuwa ta razana ta saki abun kwashe sharar tana ihu, ta zubar da sharar a wurin, har zata gudu sai kuma ta tuna kashedin da yayi mata, ta tsaya jikinta yana rawa ta ce "Yi haƙuri, tsorata nayi, ban san ka shigo ba" tayi maganar tana kare jikinta, saboda babu hijjabi a jikinta, bai jira ta gama maganar ba ma, ya shige falo. Ta daɗe a tsakar gida, ta kasa shiga falon ma, ta lallaɓa ta shiga zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, gaba ɗaya falon ya gauraye da warin wiwin da yake yi. Ba ya falo, ta shiga ɗaki ta sako hijjabi ta fito, sai dai ta kasa zuwa ɗakin da yake. Wanka yayi ya fito, ya tarar ta ajiye masa sabulun wanka, a cikin wanda ta zo da shi, banɗakin ta kai mas bokiti da ruwa, ga buta ita ma cike da ruwa. Ya gama wankan, ya ɗora soson a kan sabulun yayi fitowarsa, da zai canza kaya kuwa, duddubawa ya din ga yi, da ya gan su a cikin wardrobe, sai da ya watso su gaba ɗaya ƙasa, sannan ya zaɓi wanda zai saka, ya bar su a wurin ba tare da ya gyara ba. 'yar siririyar muryata ya ji a bakin ƙofar ɗakinsa, tana ta sallama. A fusace ya ce "Meye ne?". Ta razana ta ɗan shigo daga bakin ƙofa ta tsuguna, ta ce "Dama tun washegarin kawo ni, wasu sun zo, da kakarka hajiya da wasu, suna nemanka na ce baka nan, suka bani kaya da kuɗi dubu goma, amma na sai maggi da ashana da omo, a ciki baka zama a gida, ban nuna maka ba, shi ne na kawo maka" Ɗan shiru ya yi, jin ta ce hajiya ta zo, ya ji babu daɗi da bai haɗu da hajiyar ba, dan rabon da yaje ya ganta har ya manta. "Ga kuɗin" muryarta ta dawo da shi daga tunanin da yake yi. "Bar nan wurin kafin na yi ball da ke, ba ruwanki da shiga sabgata na gaya miki, tashi ki ware" ta tashi ta ce "Kuɗin fa" banza ya yi mata, ya tsaya yana kallon fuskarsa a mudubin ɗakin. Ganin ba zai kulata ba, ya sanya ta ajiye masa kuɗin, ta tashi za ta tafi, cikin tsawa ya ce "Ke!" A razane ta waiwayo. "Kwashe kuɗin nan ki bar nan" jiki na rawa, ta ɗauka ta ce "To bar mini ka yi" mugun kallon da ya yi mata ya sanya, ta juya da sauri ta bar ɗakin. Ta je kitchen, ta shiryo masa kwanukan abinci a kan tray, amma ta tsaya tana wasi-wasi, kar ta kai masa ya kuma korarta, ta shiga falon tana taradaddi. Ta na shigowa yana fitowa daga ɗakin, take hannunta ya hau rawa, ta ji tana neman ta saki farantin da kwanukan, ta ƙarasa tsakiyar falon, ta ajiye ta ce "Fita zaka yi, ga abinci" ta juya ta koma kitchen ta ɗaukko ruwan roba da lemo, da ta saya masa ta ɗora a kan wani plate ɗin ta kawo. Tana zuwa taga ya zauna ya kame zai ci abincin, kasancewar yana girmama cikinsa, Al'amin yana son abinci, dan haka ba kowane tayi yake wucewa ba. Maimakon ya ɗebi abincin, ya zuba a plate, kawai ya buɗe flask ɗin, ya juye salad ɗin a ciki, ya ɗaga flask ɗin miyar ya girgije a kai, ko kallon cokalin bai yi ba, ya zura hannu ya kama kai loma. Duk da wani irin mugun tsoronsa take ji, amma haka cikin tsoron, ta tsiyaya masa lemo a kofi ɗaya, ɗaya kuma ta zuba masa ruwa. Satar kallonta ya yi, yadda take komai a nutse, sai dai hannunta rawa yake yi, saboda tsoro, mamaki yake yadda take wani zuba masa ruwa kamar ya sakata. Ya din ga tunanin ita kuwa wani zunubi ta aikatawa 'yan gidansu, suka zaɓa su aurar da ita ga shi? Gaba ɗaya yanayinta kalar 'ya'yan hutu ce, irin wanda ba sa son wahalar nan. Sai dai yadda yake auna loma, yana basarwa ba zaka ce, ita yake satar kallo ba. Ta koma can gefen kujera ta zauna ta yi tsuru, gabanta na cigaba da faɗuwa da zarar ta kalleshi, sai dai duk da haka, a ranta ta ji tana son yi masa magana a kan kakarsa, da sauran tambayoyi, duk da miskila ce, amma idan ta samu wuri akwai hira. Sai dai ko kusa ko alama, ba ta ga wannan fuskar ba. Kan ta ankara ta gama zancen zucin, ya kawar da abincin cikin kula 'yar tsakiya, shanye ruwansa da lemo tsaf, ta zuba masa ido, duk da ba abun mamaki bane ba, ta saba ganin maza da shegen cin tsiya, dan tsaf Yaya Saifu zai iya cinye cikin babban flask, dan akwai ranar da suka din ga musu da surayya, ya ce zai iya cinye shinkafa rabin kwano a zama ɗaya, dama taliya leda guda yake cinyewa. Dan haka ba ta yi mamakin yadda ya cinye abincin ba, ya dubi carfet ɗin ta, milk mai haske, ya goge hannunsa a kai ya tashi tsam ya bar mata wurin da kwanukanta a wurin. A hankali ta ce "Na shiga uku, miya a kan carfet ɗina" da sauri ta kwashe kwanukan, ta ɗebo ruwa da omo, ta goge wurin da ya goge mata hannu a carfet, ta koma ɗakinsa, ta sake kwashe kayan da ya zubar. Ya watso su duka gaba ɗaya, ya cire na jikinsa duk ya watsar ya ƙara gaba. Ta sake gyara masa, ta kwaso wanda ya cire, da wanda ta kwashe na wanki ɗazu, ta fito ta jiƙa su zata wanke. Ta koma ta sake sharo falon, sai dai ta ga leda a in da Ya tashi, ta ɗauki ledar, ta taɓa ta buɗe, tana tunanin ko ita ta ajiye wani abun, amma ta ga wani abu kamar ganye a ciki, ta sinsuna ta kasa gane ko menene, kuma a iya tunanin ta, ba ta ajiye ba. Ta samu wani wurin ta ajiye, ta cigaba da aikinta. Sallama aka din ga rangaɗawa a ƙofar gida, ta wanke hannunta ta ce "Waye" Ya amsa da "Ni ne" ta saka mayafi, ta fita ta leƙa. Wani jibgegen ƙato ta gani, jiki duk a murɗe, duk bai kai girman Al'amin ba ba. A ɗan tsorace ta ce "Sannu" Ya ce "Yauwwa, matar gidan tana ciki ne?" Ta ce "Eh meyafaru?" "Ɗan je ki ce mata ana sallama da Boss" Ta yatsuna fuska ta ce "Waye hakan?" "Mai dogon zamani nake nufi, ba shi ne maigidan ba?" Jauhar ta ce "Ba wani mai irin sunan nan a gidan nan, ba sunansa kenan ba" Ya ce "Kee, ni fa nake rako shi har gidan nan, ki ce mini ba sunansa kenan ba?" Ta tsuke fuska ta ce "To shikenan idan ba ka yadda ba"ta mayar da ƙofa ta rufe. Walid ya koma gefe ya kira Al'amin ya ɗaga ya ce "Ya mai laya". Walid ya ce "Na kiyayi mai zamani, maza na zo gidanka wata 'yar cika, ta leƙo ta raina mini hankali, na kusa kwarfeta, na ƙyaleta ne kar na kwafsa" "Wacece ya aka yi?" "Kai na zo nema, ina ta jiranka, yaran nan za su karɓi kaya su rarraba, ba ka zo ba, na biyo ka gida, wata jar yarinya nunar rana mai kama da 'yan china ta ce mini wai ba mai irin sunanka a gidan, na ce mata mai zamani wai ba gidan ba ne" Al'amin ya ce "Ita ce matar gidan fa" "Kai haba maza, wannan ɗin?" "Yarinyar da ta suma, na ce ka saka a kaita Asibiti" Walid ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, maza ka sha kwana wallahi, dama ita ce, kaga rabo, wata 'yar caras beauty ka ji muryarta". "Kai dalla malam, ka buga mata ƙofa, ka ce ta duba in da na tashi, na bar leda ta baka, ka tsaya shirme". Walid ya ce "To meye na yi mini masifa kuma, na ga dai auren dole aka yi maka" katse wayar walid ya yi, yayi ashar ya ce "Ina da wannan, ai kan a ganni a ƙofar gida, sai an sha wuya, kai Aminu kamar ba biladam ba" yayi maganar yana bubbuga ƙofar gidan. Kamar ba zata buɗe ba, ta sake buɗewa cikin mamaki ta ce "Malam lafiya?" "Ya ce ki duba in da ya tashi, ya manta leda ki bani" "Shi wa?" Cikin mamakin yadda take neman raina masa hankali ya ce "Maigidan" "Dan Allah ka yi haƙuri, bai bar mini wannan sallahun ba" Ya ce "Saboda bai bar miki sallahu ba, ba zaki bayar ba?" Ta marairaice ta ce "Idan na baka ya dawo, ya ce mini ba shi ya aikoka ba, kaga bani da abun da zan ce masa". Ya ce "Gaskiya ne, shikenan" ya juya ya tafi, ta mayar da ƙofar ta rufe. Duk da kayan suna da nauyi, haka ta zage ƙarfinta a kan kayan nan, ta wanke su. Sai a lokacin ta kalli window, ta ga mpn da ta ɗaukko masa ta ce "Na shiga uku, da ya ganta fa me zan ce masa?" Ta ɗauka ta mayar masa ɗakinsa Al'amin kuwa duk in da ya juya, sai dai ya yi gyatsa saboda yadda ya ƙoshi. Walid ya je ya samu Al'amin, ya  din ga yi masa mitar yadda jauhar fafur ta hana shi saƙon nan. Yayi ya gama, bai ce masa komai ba, sai sakace da yake yi, yana cigaba da jin ƙamshin miyar da ya ci a hannunsa. "Yanzu mai zamani shikenan yau b za a sayar da kaya ba? Saboda ka yi aure 'yar yarinya ta hana aiki yau?" Al'amin ya kalle shi ya ce "Ƙila" Yayi tsaki ya ce "Yauwwa, na haɗa maka da mp ɗina a kayanka, ka kawo mini kayata kafin ita ma ta ce taka ce ba zata bayar ba" Al'amin ya tuna ya ganta a kan window, kuma ya ga yadda ta gyara masa ɗakin, ya tabattar ɗauka tayi ta kunna. A ransa ya ce 'Ashe ba tsoron ki ke da gaske ba' "Malam magana nake yi maka, a kawo mini mp ɗina. Yunwa ma nake ji, ko zamu je cin garau-garau ne?". Aminu ya miƙe ƙafa ya ce "Sai ka dawo" Walid ya fice yana tunanin asarar da za su yi, na rashin sayar da kayan nan yau, ya san ko zasu dambace da Al'amin, ba zai koma gidan nan ya ɗaukko kayan ba. Ƙarfe tara na dare ya shiga cikin unguwar, tare da su liti, da Walid, sai dai ba su shiga cikin gidan ba, suka zauna a barandar kusa da gidan, suka din ga hira suna shaye-shaye. Jauhar kuwa kamar a cikin falonta suke shaye-shayen, saboda yadda duk gidan ya gauraye da wari. Yau da gari yayi haske ta fito, a falo ta tarar da shi, a kwance a kan doguwar kujera. Ta durƙusa ta ce "Yaya ina kwana" waiwayowa yayi ya kalleta ya kawar da kansa, sai dai ba ta tashi ba. Har ta fitar da ran zai amsa ya ce "Lafiya" Ta miƙo masa leda ta ce "Ga abun da ka manta jiya, wani ya zo ya ce ka aiko shi, ni dai ban bashi ba. Na ga kamar ganyen shayi ne, ko na ɗiba na dafa mana tea?" Afujajan ya kalleta, tashi ya yi zaune ya ce "Da me zaki dafa tea ɗin?" Ta nuna masa ledar tana sunkuyar da kai ta ce "Naga kamar ganyen shayi ne, sai na dafa mana ko jallof ɗin taliya ce?" "Wiwin zaki dafa a matsayin shayi, saboda mahaukaciya ce ke?" Da sauri ta kalleshi ta saki ledar da sauri, sai dai ba ta ji daɗin mahaukaciya da ya kira ta da ita ba. "Dan Allah ka yi haƙuri, ban sani bane". "Jiya mai laya ya zo, ya ce miki yana neman mai dogon zamani, kin ce ke baki san shi ba, to ni ne mai dogon zamani, idan kuma jami'an tsaro ne suka ce miki Viper ni suke nema, idan ki ka cigaba da yi musu rashin kunya kuma, za su sassaraki ne a banza su bawa karnuka namanki" Shagwaɓe fuska ta yi zata yi kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah ka bashi haƙuri, ba zan sake ba, dama ban san me zai yi maka bane, shiyasa na ce masa ba kai bane ba shiyasa" Ya saka hannu ya ɗauki ledarsa ya tashi zai fita ta ce "To karin kumallon fa" ko waiwayowa bai yi ba, ya fita. Bayan fitarsa, ta je ta kwaso kayansa da ta wanke, ta ninke su tsaf, ta shiga ɗakinsa, tana shirya masa kayan, ta fito masa da guda ɗaya da zai saka, ta ɗaukko bedsheet tana canzawa katifarsa, kawai ta yi karo da wata irin zabgegiyar wuƙa. Gabanta ya faɗi wuƙar kawai abun tsoro ce. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, jikinta na rawa ta hau kuka, ta kai hannu za ta ɗauka" "Idan ta ji miki rauni, ke ki ka sani". A razane ta ɗago jikinta na tsuma. "Fita ki bar mini ɗaki, bincike ki ke yi mini ko?" Ta girgiza kai ta ce "A'a wallahi, bedsheet zan canza maka na ganta, ba bincike nake yi maka ba" "Fita to" Ta ce "To, ga kaya na fito maka da su, wanda zaka saka". Ya sake tsuke fuska ya ce "Ki fita na ce" Ta zo fita, ta kasa saboda yana tsaye a wurin. Yayi tsaki ya bata hanya, ta fita har da tuntuɓe, a tsakiyar falon ta ga ledar buredi, da sugar da madara da Lipton. Ta lallaɓa ta fita ta kunna gas, ta ɗora shayi. Buga gate ɗin gidan ake yi da ƙarfi, ba shiri ta tafi ta buɗe. Wani matashin magidanci ta gani, a tsaye ya kima uwar hula, ya rufe kunnuwa. Ta gaishe shi cikin ladabi, ya ce "Ina matar gidan?" Mamaki take yi, meyasa mutane suke neman matar gidan idan suka ganta. "Lafiya?" "Eh, megidan muke nema? Sunana malam lawan, ni ne mai wannan gidan na kusa da ke" Jauhar ta yi murmushi ta ce "Allah sarki, baban su halimatu? Ai suna shigo mini". "Eh, mai unguwa yana neman mijinki, ƙararsa muka kai" Ta ce "Subhanallah, laifin me yayi muku?" "Au jira zamu yi sai ya yi kan mu ɗauki mataki, an ce mana mutumin banza ne, kuma da ya zo bai yi mana sallama ba, bamu san da wani irin mutum zamu zauna ba, jiya an hanamu sukunk da warin wiwi, ya tara mana 'yan iska a layi. An gaya mana gawurtaccen ɗan daba ne da ya addabi in da yake, aka yi masa aure mu aka kawo mana bala'i. Gara aje a zauna da mai unguwa da 'yan sanda, ko ya tashi, ko ayi yarjejeniyar zaman lafiya da shi". Jauhar ta ce "Haba malam, bai yi muku komai ba kuma sai a kai shi wurin 'yan sanda, ina laifin mai unguwar ma, in sha Allah ba zai sake sha muku komai a layi ba, kuma ba zai cutar da kowa ba ma. In sha Allah wataran sai labari zai daina". "Ke rufe mini baki kan na kwaɗe ki, nasiha zaki yi mini, ba zamu zauna da mutumin banza da wofi ba wallahi, ya lalata mana yara haka kurum ba" Motsi ta ji a bayanta, tana waiwayawa ta ganshi a tsaye, ashe duk ya ji abun da malam lawan ke faɗa. Da sauri ta leƙa ta ce "Ka tafi kar ka bari ya ganka"ta waiwayo ta rufe gate ɗin tana kallonsa. "Ya tafi kar ya bari na ganshi ko? To ke bari na yi miki abun da zan yi masa". Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Kafin ta yi wani yinƙuri, ya janyeta daga jikin gate ɗin, sai dai kasancewar ba ƙwari ne da ita ba a kansa, sai da ta kai ƙasa. Ya buɗe ƙofar ya lelleƙa, bai ga kowa ba, tuni malam lawan ya ɓace. Ya dawo ya kalleta, ta sunkuyar da kai, sai murza yatsan ƙafarta take yi, da yake yi mata zafi, saboda faɗuwar da ta yi. Ƙwafa ya yi ya wuceta, ta lallaɓa ta tashi, ta shiga kitchen ta ɗora tea, ta ɗebi miyar nan da su Anty lubabatu suka kai mata, ta ƙara gyarata ta zuba ta kai masa falo. Ya wani maze yana basarwa, nan kuwa jira yake yi, tayi ta kawo masa ya ci. Sai dai yadda yake cin abinci ya goge mata a jikin kujera, ko carfet yana damunta, sai dai idan ya gama ya tashi ta goge. Dan haka ta sayo toilet paper, take haɗo masa da ita, amma ko kallonta ba ya yi, idan Allah ya taimaketa ne, wani lokacin sai ya goge a jikin kayansa kamar wani ƙaramin yaro. Da daddare kuwa kullum, sai ya cika gidan da warin sigari, wasu lokutan ba zai dawo ba, sai sha biyu na dare, ya shige ɗakinsa yayi ta shaye-shaye, da safe kuma idan ta ajiye abinci zai ci, idan ba ta ajiye ba ba zai tambaya ba, kuma ba zai sayo ya kawo ba. Idan za ta gyara masa ɗaki sau goma a rana kuwa, muddin ya shiga sai ya watsar da komai ya ɓata, yayi shaye-shayensa ya bar mata toka da sauran karan sigari duk a ɗakin. Wasu lokutan sai su shafe kwana biyu ba su haɗu ba, gashi zai kwana a gidan, amma ba zai shigo ba sai ta yi bacci, duk da wataran ba ta baccin sai ta ji shigowarsa, asubar fari kuma sai ya fice, ranar da ya ga dama kuma, sai ya bari gari yayi haske, ko za ta bashi abinci, dan sai yanzu ya fuskanci abincin waje wasu lokutan ga ƙaurin hayaƙi gashi ba sa jin sinadaran ɗanɗano, nata kuwa har cikin kansa yake jin su. Yau ma dawowa ya yi rana tsage-tsage, walid ya sayo musu abinci, yana fara ci ya ji babu daɗi, ya ajiye ya ce gida zai tafi. Walid ya ce "Da ranar nan tsaka zaka fi gida?" "Eh" ya amsa a taƙaice. "Lallai, na fuskanci lamari yana ta daidaita to Allah ya sa mu ji alkhairi ya kawo zuriya ɗayyiba" Ya haɗe rai ya ce "Mai laya" Walid ya ce "Sorry maza, na kiyayi mai zamani" ya fice ya tafi gida. Jauhar tana ta lissafin kuɗin hannunta, sun kusa ƙarewa, girkin ma duk da dabaru take yin sa, ga gogan babu ruwansa sai dai ta dafa ya lashe. Da 'yan dabaru take yin ɗan wake yau, ta aiki almajiri ya sayo mata kabeji da cucumber, tana jiran dawowarsa, Al'amin ya dawo, a duk lokacin da za ta ganshi sai ta razana, gashi ba sallama yake yi ba, ya hangota da tukunya a kan gas, ya yi ajiyar zuciya ya san zai ci abinci. Ya shiga ɗakinsa, ya tarar ta sake wanke masa kaya, ta gyara ɗakin tsaf. Tsaki yayi ya ce "Ita dai wannan an yi 'yar wahala" Ya daidaici lokacin da ta gama girki, ya dawo falo ya zauna, aikuwa sai ga ta abinci bakinta ɗauke da sallama. Bai amsa na sai Alla-alla ta kawo ta ajiye, saboda yadda ƙamshin manjan, ya cika masa hanci. Ta ajiye masa ya haɗa abun sa ya fara ci. Ta zauna a gefensa, cikin fargaba ta ce "Yaya" shiru ya yi mata, yana haɗiye ɗan wakensa da hurhuɗu biyar-biyar. Ta sake cewa "Yaya magana nake dan Allah abu zan tambayeka". "Malama sunana Aminu, kar ki sake ce mini wani Yaya" a ranta ta ce 'Ai na san a rina' A zahiri kuma ta ce "Ai ba zan iya faɗar sunanka ba, ya za ayi na faɗi sunan mijina kamar mara ɗa'a" sai ya ji abun wani banbarakwai wai mijinta. "To me zan din ga ce maka?" Ba ta jira amsar sa ba, dan ta san ba zai amsa ba, ita kuma zaman kuramen nan da suke yi ba son sa take yi ba, ace kana zaune a ƙarƙashin mutum, amma ba zai kulaka ba. "Na ji abokanka suna ce maka boss, ni kuma sai na ce maka master, idan na ce master zaka amsa, ko nima boss zan ce? Tun da ba ka son yaya?" Ta tambaye shi tana murmushi ba tare da ta kalli in da yake ba, saboda kwarjinin da yake yi mata, yanzu haka ma ƙarfin hali kawai take da take yi masa magana. Kallonta yayi, tana murmushi dimple ɗin ta na side ɗaya ya lotsa, ya gane dakiya kawai take yi, amma a tsorace take yi masa magana. Duk da bai bata amsa ba, amma matsern da ta ce zata din ga kiransa da shi, ya so yayi murmushi, amma yaƙi ya sha kunu, yana suɗe kwanon ɗan wakensa. Cikin hikima ta ce "Da da sauran garin ɗan waken nan, da na dafa maka wani, ko na ƙaro maka?" "A'a" ya ajiye kwanon, cikin sauri ta miƙa masa wani tsumma mai kyau, ta ce "Gashi ka goge hannunka, manjan yana da kamu, sai mu je waje na zuba maka omo ka wanke sosai" ya karɓa ya goge, ya koma ya kashingiɗa yana duba wayarsa mai madannai. "Na ce, dan Allah sonake na shiga maƙwabta na yi musu sallama na tare, wai haka ake yi, ka ga mu bamu cewa kowa mun tare ba" "Sauka lafiya" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. "Yauwwa na gode sosai master, bari ayi la'asar, sai na je. Yauwwa mutumin ɗazu ya ce wai mai unguwa na nemank..... Ba ta ƙarasa ba ya tashi, dan surutunta ya fara isar sa. Bayansa ta bi da kallo, 'Da sannu wataran zaka tanka mini ne, ni ba zan iya rayuwar zaman kurame ba' tayi maganar a hankali. Huɗu da rabi, bayan ta yi la'asar, ta leƙa ɗakinsa ta ce masa za ta fita, ta tarar yana salla. Wata irin ajiyar zuciya ta yi, tare da hamdala a zuciyarta, ba ta taɓa tsammanin yana kai goshinsa ƙasa ba. Ta zauna a bakin ƙofar tana kallonsa, duk da shaf shaf yake yi, kuma azahar da la'asar ya haɗa a lokacin, amma ta ji dadin ganin yana salla. "Master bari na je, idan ka idar ka sani a addu'a, Allah ya sa ka daina jin haushina, ban san me nayi maka ba" dama ta san ba amsawa zai yi ba ta fita. Matasan 'yan mata ne su biyu a gaban rahila suna cin abinci, da alama daga makaranta suka dawo, domin kuwa bayansu jibga jibgan akwatuna ne, na 'yan makaranta. "Umma, nifa haryanzu na kasa daina mamaki, wai yaya ne yayi aure? Wai dan Allah ya aka yi aka samu aka bashi 'ya a yadda yake? Kuma ba a bari mun dawo ba aka yi bikin?" Rahila ta ce "Ke dallacan, waye ya ce miki abun na shiri ne shahida? Neman mafita nake ba shiri faka-faka na saka aka samo wata yarinya ya je can ya ƙarata, ya ƙara sako mini yaro a gaba, irin kallon da yake yi mini, tsaf zai halakka ni, cikin ikon Allah tun da aka yi auren, ban sake ganinsa a gidan nan ba, ya samu mace yayi luf" Shahida ta ce 'Ni wallahi mai tsautsayin da aka aurawa nake jin tausyai, yaya za ta yi da shi dan Allah dan Annabi?" Amira ta ce "Ke ina ruwanki ne shahida, ina ruwanki da ko ma wa ce ta aure shi, ba dai an samu ya tafi na, case close". Shahida ta yi murmushi ta ce "Ina ne gidan nasa ne?" "Yana can gidansa na ɗorayi, ba kuma cewa na yi ki je ba, kar abun da ya kai ki gidansa, balle ya lallaɓa ya dawo mana nan ya je can su ƙarke". "Ahh haba umma, sai mu yanke alaƙa da shi duka kenan? Yayi aure muna school kuma mun dawo ba zamu ganshi ba?" Amira ta ce "Wallahi a garin shishshigin nan da ki ke masa, zai kassara rayuwar ki, ki yi ta shige masa yana yarfaki" "Wallahi ki ka je gidansa ma sai na ci ubanki shahida, na gaya miki, ke baki san sai ku kasa auruwa ba saboda mugun halinsa da mummunan tabon da yake da shi ba a unguwar nan?" Shahida ta ajiye cokalin hannunta ta ce "Umma, shi fa jini ya fi ruwa kauri, the only male brother i have, sai ki ce sai na yanke alaƙa da shi?" "Au jayayya zaki yi da ni? Shi Abban uban meye idan ba yayanki ba?" Ta tashi ta ce "Ai ba babanmu ɗaya ba, Yaya Al'amin kuma babanmu ɗaya, kowane ina son sa" Rahila ta ce "La ila ha illalahu Shahida " Amira ta ce "Dan Allah umma bar shashasha, za ta gane kurenta ne" Rahila ta cigaba da salallami, a kan yadda ke adawa da ita wasu lokutan a kan Al'amin. *** Juahar gidan malam lawan ta fara shiga, wato gidansu halimatu da walida, yaran da suke zuwa tayata hira, suka gaggaisa da maman, sannan su halimatun, suka rakata sauran gidajen maƙwabta, tayi musu sallama. Har wurin masu kayan miya, da masu shaguna suka nunnuna mata da wurin makarɗe. A bayan gidan suka je har gidan wata tela, da har da yaranta, su na shigarwa jauhar, suka gaisa jauhar ta tarar da yaran suna stone work a jikin ɗinki, har ta karɓa tana taya su, saboda a rayuwarta tana son sana'oin hannu suna matuƙar burgeta. Take cewa matar, idan an samu stone work ta din ga aika mata da shi tana yi mata. Matar ta ce 'To nawa zan din ga baki, dan kuwa ina samun aikin su sosai da sosai" Cikin tsananin murna, da jin cewa ta samu abun yi, ta cewa matar, ko nawa ne ta bata, tana son za ta din ga yi, nan hira ta ɓarke, take gaya wa matar, ta iya shirin dutse, har adon da ake yi da shi a jikin ɗinki, duk zata iya, suka yi yarjejeniyar matar zata din ga bata ta yi mata. Ganin hadari ya fara haɗowa, ya sanya ta yi mata sallama, ta koma gida, sai dai tana komawa, ya zura takalmansa zai fice, ta ce masa kar ya fita, hadari ne a garin, amma ba ta gama rufe baki ba, ta ji ya buɗe ƙofa ya fice. Ta kawar da abun da zata kawar, ta rurrufe ko ina, ta laluba ta ɗauki mp a in da ta ajiye, ta tarar ya ɗauke kayarsa, ta ce "Da sauƙi, tun da ba ka yi mini faɗa ba". Ruwan sama aka yi, kamar da bakin ƙwarya, ga wata irin iska da ta jefa jauhar, cikin razani da tashin hankali, yadda kwanon yake ƙara ji take tamkar zai kwashe ne, saboda ƙarfin iskar da ruwan. Ta takure wuri guda, tana ta addu'a, kasancewar lokacin da ake ruwan sama, lokaci ne na karɓar addu'a, mafi yawan addu'arta a kan Al'amin ne, da take masa fatan shiriya. Ko da ruwan ya tsagaita, ta fito falonta, ruwa ya shigo sosai, ya jiƙe ɗakin, ta buɗe ƙofar falon, rashin kyakykyawan magudanan ruwa, ya sanya kwatocin layin yin ambaliya, duk suka shigo mata gida, gashi ba ga da rariyar kirki, sai ta banɗkuna, dan haka babu wurin da ruwan zai fita, tsakar gidan ya shafe da ruwan kwatami, falonta ma duk ruwan ya shigo, gashi idan aka yi ruwan, tsigar jikinta tayi ta tashi. Haka ta samo kwano, ta din ga ɗibar ruwan tana zubarwa, ta naɗe carfet ɗin ta, ta jingine, sai zallar buhun da aka shimfiɗa a ƙasa, ta din ga kwarfe ruwa a falon nan. Ta je ta yi sallar magariba, Allah ya sa ruwa bai shigar mata bedrooms ba. Ana sallar isha'i sai gashi ya dawo, ya tarar da ita, fitilarta babu batirin kirki, duk tayi duhu, sai kwashe ruwa take a falo. A ransa ya ce "Iyayenki ne suka ja miki" tayi masa sannu da zuwa, ta cigaba da aikinta, har zai wuce ya dawo ya karɓi kwanon, ya haɗe mata kujerunta wuri guda, ya kunna fitilar ƙaramar wayarsa, ya ƙarasa kwashe ruwan. Shi kansa ya san gidan nan kango ne, yana buƙatar gyara sosai, bai ci ace har an saka mutum a ciki ba, amma da iyayensa da na ta, ya rasa wannene uban garajen da ya saka aka yi haka. Ya ɗaɗɗaga labulayen, saboda ɗakin ya sha iska, daga nan ya tafi makwancinsa, ta tafi nata. Da safe ruwan duk ya tsane, amma sai ƙanƙame jikinta take yi, ƙarnin ruwa da ya kwanta ya din ga damunta. Haka nan ta daure, ta gyara gidan, ta zuba miya ta yi jallof ɗin macaroni, kasancewar falon a jiƙe yake, da danshi, da sauran Lipton ɗin jiya, ta dafa shayi har da su citta ta yi sallama a ƙofar ɗakinsa, bai amsa ba dama labulen a ɗage yake ta shiga. Ta ajiye masa ta ce "Ina kwana?" Ba ta jira ya amsa ba, ta haɗa masa tea, ta tashi ta fita. Aka jima ta dawo, ta shiga banɗakinsa ta wanke, ta ɗauki bokiti ta dawo, ta haɗo ruwan zafi na wanka, ta kai masa banɗakin ta ce "Master ga ruwan wanka nan na kai maka, mai ɗumi ne" idan ta ce mastern nan, sai ya ɗaga kai ya kalleta. Ta ce "Yauwwa, master zan kafa ƙusa a toilet ɗin ka, idan ka gama wanka, ka dinga saƙale soson, idan ba haka ba sabulun narkewa yake yi, sai ka ga ya ƙare da wuri" Ta zagaye shi, ta fara tattare kayan duk da ya watsar a ɗakin kamar ƙaramin yaro. Ya gama cin abincin sa, ya fara shan tean, yana jin yadda ƙamshin da yajin citta yake ratsa shi yana yi masa daɗi. Yana zaune ta gyare ɗakin, ta kukkuna masa turaren wuta, sai dai kafin ta ƙarasa, ya kunna sigari a ɗakin. Sai da ranta ya sosu, akwai sauran warin ta jiya da daddare ma da ya sha, ta gama aikin ɗakin, ta kunna turaren wuta, ya kuma kunna wata sigarin. Ta maze ta ce masa "Ruwan wankanka, kar ya huce fa, na ga garin da sanyi haryanzu, idan ka yi wanka da na sanyi, zaka yi mura" A hasale ya ce "Ke, fita ki bar mini ɗaki, kin gama tsegumin ai, kin sakani a gaba kin ga abun da nake yi, to fita ki bar min ɗaki, ba zan wankan ba" Ba ta sake cewa komai ba, ta juya ta fice, ta cigaba da ayyukan ta, tana tsaka da wanke-wanke, ya fito da sauri, hannunsa riƙe da waya yana cewa "Kar ku raga musu, gani nan zuwa" ta miƙe tana kallonsa, amma ta kasa yi masa magana. A haka yana ƙaurin sigarinsa da komai, ga kayan da su ya wuni jiya, ya wayi gari da su, amma bai canza wasu ba, ya fice cikin matsanancin sauri. Ta koma ta cigaba da aikinta, tana addu'a Allah ya sa ba wani rashin jin zai je yayi ba. Baba yana gida, aka aiko ana sallama da shi. Yana fita ya tarar da 'yan uwan Alhaji mu'azzam da suka kawo kuɗi. Suka gaggaisa, ƙanin mahaifin Alhaji mu'azzam ya ce "Gamu mun dawo, ɗanka ne ya dawo da mu, ya ce a bayar da haƙuri, kar a ji mu shiru, ayyka sun yi masa yawa, ba zai samu dawowa nan kusa ba, shi ne ya ce mu zo ayi magana, a ƙarasa shirye-shirye kawai, ayi auren a tura masa ita can". Gaban Baba ya faɗi jikinsa a sanyaye ya ce "Alhaji dama ko da baku zo ba, zan neme ku ni na zo, an sami matsala ne, zan dawo muku da kuɗin aurenku". Suka yi turus gaba ɗaya suka ce "Wace irin matsala ce haka?" "Yarinyar nan, yau ta kusa sati biyu, ina mai baku haƙuri, a bashi haƙuri dan Allah. Zan kawo muku kuɗin aurenku" "Amma wani abun yayi ne, ko wani laifin shi mu'azzam ɗin yayi?". Baba ya ce "Ko ɗaya, ka san matar mutum kabarinsa, mu'azzam bai yi mini komai ba, dan Allah a bashi haƙuri" Suka ce "To shikenan, Allah ya tabattar mana da alkhairi". Suka amsa da "Amin" Baba ya ce "Ku bani account number, na mayar muku da kuɗin auren" Ɗaya daga cikin su ya ce "A'a, a bar wannan maganar sai ya dawo tukuna, Allah ya basu zaman lafiya" Ya amsa da "Amin". Bayan la'asar yara duk suna islamiyya, babu 'yan aike, ta ce bari ta fita ta sayo maganin sauro, idan ya dawo sai ta gaya masa. A ƙofar gida suka haɗu da maman su halimatu a waje da wata maƙwabciyar su, suka gaisa ta ce "Maman halimatu, ba ku shigo mini mun gaisa ba haryanzu". "Wallahi Amarya, ba ƙi muka yi ba, kin sa yanayin mijin naki sai a hankali, abun da tsoro, kar wani abu ya faru". Ranta bai yi mata daɗi ba ta ce "Haba dai, ina ruwansa da ku? Kawai dai a shigo a gaisa, shikenan a gaida su halimatu" tayi gaba zuciyarta babu daɗi, a duk lokacin da ta ji an aibata shi, sai ranta ya sosu. Har dare ba ta sake ganin Al'amin ba, gashi ita ba waya ba, wasa-wasa har dare yayi babu Al'amin babu dalilinsa har garin Allah ya waye, bai kwana a gida ba. Sai abin ya fara damunta, gashi ba ta san a ina za ta ganshi ba. Abu kamar wasa, aka sake shafe wuni, aka shiga kwana na biyu, babu shi babu labarinsa, nan fa hankalinta yayi mummunan tashi, gashi ba ta san wa za ta nufa ta gayawa ba. Maman halimatu ce tayi sallama, Jauhar ta saka hijjabi ta fito tana murmushin yaƙe ta ce "Maman halimatu, sannu da zuwa shigo" "A'a ba shigowa zan yi ba, abbansu yana nan bai fita ba, bai san ma na shigo ba na ce kin kuwa san an kama mijinki?" Gaban Jauhar ya faɗi ta ce "Yaushe? A ina? Waye ya gaya miki?" "A bakin Abban su halimatu na ji, cune suka yi masa aka kama shi, amma dan Allah kar ki gaya masa wanda suka saka aka kama shi ɗin dan Allah, na gaya miki ne na san baki sani ba". Tuni idon Jauhar ya cika da hawaye ta ce "Eyya, meysa abban su halimatu yayi haka? Wallahi babu abun da zai yi wa wani, ba ruwan shi da kowa idan ba taɓa shi aka yi ba, ina aka kai shi? Dan Allah ki gaya mini, ina gidan ban san ina zan nufa ba ma". Tayi ƙasa da murya ta ce "Yana anti daba can aka kai shi". "Menene anti daba kuma? Ina ne?". "Can in da ake kai 'yan daba, ki shirya ki je ki duba shi". Ta ce "To na gode" bayan tafiyar maman halimatu, take ta ji haushin malam lawan ya kamata. Tayi tunanin ko gidansu za ta je, ta faɗa, amma sai ta ga idan tayi hakan, kamar ta tozarta kanta ne, dan haka ta fasa ta ɗora girki, ta gama ta shirya, ta zuba a flask, ta bi kwatancen da maman halimatu tayi mata. Su kansu yanayin jami'an tsaron wurin, tsoro suka bata, ba ta taɓa zuwa police station ba, ta gaishe su cikin girmamawa sannan ta ce "Dan Allah wani nake nema" "Wa kenan?" Wani ya tambayeta. "Al'amin sunansa" Ɗan sandan ya ce "Anya, babu wani mai irin wannan sunan da muka kama". Ta ce "Dan Allah nan aka ce mini an kawo shi, dan Allah officer ka duba mini" Na kusa da shi ya ce "Ko viper take nufi?" Ta ce "Eh shi, mai dogon zamani" "Ya aka yi me zaki yi masa?" "Wurinsa na zo, maƙwabciyata ta ce mini cune aka yi masa aka kama shi, wallahi bai yi komai ba". "Ke ya aka yi ki ka san bai yi komai ɗin ba? Wacece ɗin sa ke, ni tun da muke kama shi ma, ban taɓa ganin wani ya zo wurinsa ba, idan ba ire-iren sa ba ko yaran ubangidansa ba" Ta ce "Mijina ne" Saroro suka yi suna kallon jauhar, kyakywar yarinya ƙarama da ita. "Ke kuma auren soyayya ku ka yi? Jama'a kun ga matar Viper, yaushe ne kuwa zuwansa na ƙarshe aka fito da shi aka ce aure yayi" waiwayowa suka yi suna kallonta, ta sunkuyar da kai tana fatan Allah ya sa su bar ta ta ganshi. Ɗaya daga cikin su ya ce "Ku fito da shi, ta ganshi, amma dai Viper yayi asara, daga aurensa ya saka 'yar mutane fara sintiri saboda shi". Saroro yayi da ya hangota cikin hijjabi, 'yan sandan suna yi mata tambayoyi. Tana ganinsa tayi ajiyar zuciya, ya ƙaraso gaban kantar ya kalleta ya ce "Me ya fito da ke?" "Kwana biyu baka nan, ban san in da ka ke ba, sai yau ban san kama ka aka yi ba" Ya sake kallonta ya ce "To ware ki koma" Jauhar ta ce "To in koma, kai fa ba sakinka za su yi mu koma ba?" Al'amin ya ce "Ki tafi na ce, kuma kar ki sake zuwa wurin nan kina mace, ware" haushi ne ya kamata, yadda yake korarta, shi ba ayi masa abun arziki sai hantara. Ta ɗora leda ɗuake da flask ɗin Abinci ta ce "Gashi abinci ne na kawo maka" sai da ya ɗan yi shiru yana kallonta. Tun da ya fara rashin jin sa, babu mai tunawa da shi, ya kawo masa ziyara ko abinci, idan ba su walid ba, sai kuma ita yanzu. "Ahh yau zamu ci girkin amarya, amma hajiya sai kin fara ci kafin ya ci" Bai saurari ɗan sandan ba, ya ɗauki abincinsa ya koma gefe. Ya buɗe, ta yi sauri ta zagaya, ta huda ruwa pure water, ta ce masa "Ka fara wanke hannunka" Kamar ya shareta, sai kuma ta zuba masa ya wanke, ya saka hannu ya fara cin abincin. "Akwai sauro ne wurin? Na ga kamar ya cijeka, jikinka duk cizon sauro?" "Mmm" ya amsa yana cigaba da cin abincin. "To yaushe zasu sake ka, kar ka yi rashin lafiya, saboda cizon sauro" shi dai yayi shiru yana cin abun sa. Ya gama ci ta bashi ruwa, ya karɓa ya zuƙe, ta ƙara masa wani ya shanye. Ta ce "Officer, to zaku sake shi? Bai yi komai ba" "Ke, da wiwi muka kama shi da ƙwayoyi, sai kuma ki ce bai yi komai ba? NDLEA zamu kai shi". Jauhar ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah ku yi haƙuri, ba zai ƙara ba in sha Allah, Master ka basu haƙuri su ƙyaleka mu tafi" miƙewa yayi tsaye, ya nufi hanyar komawa cikin ceil. "Officer to, idan na sayo maganin sauro da ashana, zaku bar shi ya kunna?" Gaba ɗaya sai ta basu tausayi, ya ce "Sayo" Ta juya ta fita da sauri, shi kuma ya tsaya ya waiwayo ya bi bayanta da kallo. "Viper, wai dan Allah ka bamu labari, wurin wani bokan ka kai 'yar mutane da iyayenta, suka aura maka 'yar su?" Shi dai ya ƙarasa ya koma cikin ceil, yayi zamansa, ba a jima ba, sai gata da maganin sauro, da ashana. Suka karɓa a nan kan kanta, suka ce ta tafi. "Dan Allah ku bari na sake ganinsa" "Ke wuce ki bar nan, da ki ka samu ma aka bari ki ganshi?" Ba ta karaya ba ta sske cewa "To ana bashi abinci? Ko ina kawo masa na dare ma" "Au uban wa ki ka ajiye da zai bashi abinci a nan? Ware ki tafi" Jiki a sanyaye ta ce "To, zan tafi ga wannan dan Allah officer ko buredi ku bashi" ta ajiye musu ɗari biyar sannan ta ce "Dan Allah kuma ku yi haƙuri, kar ku kai shi NDLEA, dan girman Allah in sha Allah zai daina, ba zai ƙara ba ma dan Allah" "Ki je ki kawo dubu hamsin, sai mu sakar miki shi" Tayi shiru, har ga Allah ba ta da ita, ba ta da dalilinta amma ta ce "To zan kawo, amma dan Allah kar ku kai shi, zan kawo muku in sha Allah" Ta fito daga wurin, tana tunanin ina zata nufa ta samo dubu hamsin a sake shi. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Tun da ta hau adaidaita sahu, tunani take yi, yaya za ta yi ta samu dubu hamsin ta kai, a sako shi. Ta san muddin aka kai shi NDLEA case ɗin tsayi zai yi, ba zata musa an ganshi da kayan maye ba, tun da yana sha. Ta koma gida tayi salla, amma abun duniya ya isheta, ta kasa ko cin abinci, tausayinsa duk ya cika mata zuciya, jikinsa yayi ruɗu-ruɗu da cizon sauro, gashi almu sun nuna ba abinci ake ba shi ba. Baba kuwa abun duniya ya dame shi, yadda ya ji kunya a idon iyayen Alhaji mu'azzam, ace sun kawo kuɗi sun gama magana, amma ya aurar da ita ga wani, ko gaya musu bai yi ba, ya rasa me yake yi masa daɗi, har sai da zakiyya ta fahimta ta ce "Baban su Saifu, wai lafiya kuwa? Tun da ka yi baƙi jiya, gaba ɗaya ka rasa nutsuwar ka" Ya sauke numfashi ya ce "'yan uwan Alhaji mu'azzam ne, suka zo suna bayar da haƙuri a kan jin su shiru da aka yi. Wai za ayi mata visa ayi auren a tura ta can" Waro ido tayi ta ce "Sai kuma ka ce musu me?". "Na aurar da ita" yayi maganar a sanyaye yana sake jinjina wautar da ya yi. "Ba a haka fa, sai ka ce musu Allah ne ya ƙaddara a hakan, amma akwai yayyenta, ko hafsa ba sai a maye gurbinta da ita ba, hafsa ba ta fi jauhar komai ba ma? Ai bai kamata a bari ya tafi haka ya tsallake gidan nan ba". "Zakiyya, kun saka na yi abun da yake damuna, na cuci 'ya ta ba gaira babu dalili, na aurar da ita ga mutumin da ba na kirki ba, na rasa yadda aka yi, lamarin nan ya faru, kunyar haɗuwa da jauhar ma nake yi, na kasa komawa gidanta, zuciyata zafi take yi mini" Zakiyya ta ce "Jauhar fa an gama babinta, sai a fuskanci 'yan uwanta, bai kamata a bari mutumin nan ya tafi haka ba" "Zakiyya, dan Allah ki bari na samu nutsuwa, ni ban san ma meyake damuna ba, dan Allah ki bari na ji da abun da yake damuna" Ta kwantar da murya ta ce "Babu wani abu fa da yake damunka, kai ne ka ke neman ɗorawa kanka matsala, amma komai mai sauƙi ne, idan ya dawo ba sai a lallaɓa shi a bashi Hafsa ba ya aura". Baba ya ce "Na ji, amma dai yanzu ki ƙyaleni" ya ɗauki hularsa ya saka ya fita. A tsakar gida ya tarar da su surayya, aiki duk ya kacame musu, aiki ba aiki, wanda da jauhar na nan, ita kaɗai take yi suna mimmiƙe kamar kifi a fridge. Suna ta yi masa a dawo lafiya, ya dawo da baya ya tsaya, ya kalle su ya ce "Surayya, kun je gidan ƙanwarku kuwa kun ganota?" Duk suka yi shiru, suka kasa amsa masa. "Yakamata ku je ku ga in da aka kaita, ita ma ta ji daɗ". Mama ta fito daga kitchen ta ce "A'a fa, ka san dai yadda mijinta yake, ba zuwa gidanta ne ba za ayi ba, kar mutum ya je ya illata shi". Yayi shiru bai ce komai ba. Jauhar kuwa kasa nutsuwa tayi, har sallar nafila tayi mussaman tana fatan Allah ya sa kar a kai Al'amin NDLEA. Duk yadda ta kai ga tunani, ta rasa mafita, bacci ya gagareta, a gidanma ya ta ƙare da sauro, ina ga shi da yake can, ta yi ta fatan Allah ya sa su saya masa buredin nan su bashi, sai kuma ta tuna ba ta bayar da kuɗin da za a saya masa ruwa ba, gaba ɗaya ta shiga damuwa, haka har garin Allah ya waye. Ta ji ƙarar babur ɗin malam lawan alamar ya fita, tana ta tunanin ko shiga za ta yi gidan, ta yi wa maman halimatu magana, ko akwai taimakon da za ta iya yi mata. Tana cikin tunanin, maman halimatu ta shigo, suka gaisa jauhar ta ce "Yanzu nake tunanin zuwa gidan wurinki". Maman halimatu ta ce "Yaya kin same shi ɗin?" "Eh yana can, sun ce na kai dubu hamsin a bayar da belinsa, amma wallahi bani da ita" "To yanzu ya za ayi?" Jauhar ta ce "Wallahi ban sani ba, shi nake ta tunani" "To ki kira gidanku mana ki faɗa" ta girgiza kai ta ce "A'a, daga yin auren sai na fara kai musu complain, a'a gara na rufa masa asiri na samu ya fito" "Aikuwa Jauhar sai ki yi tunanin in da zaki samo kuɗi". Tayi saurin cewa "Dan Allah ko akwai wanda zaki haɗa ni da shi, ya sai carfet ɗina?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Eh akwai wata dillaliya, kusa da titi gidanta yake" Cikin ɗoki jauhar ta ce "Mu je ki rakani maman halima". "Shikenan, amma Jauhar kina me ki ka auri mutumin nan, gashi daga aurenku kin fara wahala, da kyanki da ƙuruciyarki, kin auri wanda zai wahalar da ke". Jauhar ta yi murmushi ta ce "Maman halimatu ku daina aibata shi dan Allah, ku din ga yi mana addu'a" "To Allah ya kyauta" Jauhar ta saka hijjabi, suka tafi gidan dillaliya, sai dai bata nan, aka kirata a waya, ta ce sai yamma zata dawo, zata biya gidan maman halimatu, su je gidan Jauhar ɗin. Wunin ranar jauhar kamar ta yi hauka, saboda dillaliya ba ta zo ba, sai tunanin halin da yake ciki take yi. Sai wajen ƙarfe biyar sannan ta zo, ta ga carfet ta ce zata saya dubu goma. Maman halimatu ta ce "Haba sahura, wane irin dubu goma, bai fi sati biyu ba ca carfet ɗin sabonsa dubu kusan sittin ne fa". "To ku ɗauka ku mayar kasuwar mana, tun da an shimfiɗa ai ya zama taoho". Jauhar ta ce "Bakomai na yadda" ba ta da burin da ya wuce ta ga Al'amin ya fito. Sahura ta ce 'Saboda kin ban tausayi, na saya dubu sha biyu, bari na baki kuɗin. Maman halimatu ta ce "Wallahi sahura shiyasa da yawanku ba kwa arziki dillali, duk cuwa-cuwar ta ku, a tsiyace ku ke mutuwa" Sahura ta ce "Oho miki dai" Ganin ta fito da kuɗi da yawa, ya sanya jauhar shiga kitchen ɗin ta, ta ɗauko blender da set na tukwanenta masu kyau, ta cewa dillaliya su ma ta saya. Maman halimatu ta ce "Jauhar, idan 'yan gidanku suka gane kin sayar da kayanki fa?" Sahura ta ce "Wallahi uwar su halimatu ke 'yar baƙin ciki ce, ke kika saya mata?". Jauhar kamar ta yi kuka ta ce "To ya zan yi maman halimatu, bana son zamansa a wurin nan, sauro ma kawai ya ishe shi" Sahura ta ce "Allah sarki yarinya, Allah ya mayar da alkhairi, idan an tashi sayar da wasu ma ki kira ni" Da ƙyar ta bawa Jauhar dubu ashirin da huɗu gaba ɗaya. Wanda a ƙalla sun kai kayan dubu ɗari da wani abu. Ƙoƙarin nemo wani abun take, maman halimatu ta hanata, ta ce ta bari gobe ta je station ɗin, ta basu haƙuri ta ce musu abun da take da shi kenan. Jauhar ta ce "Ki na ganin za su karɓa kuwa?" "Za su karɓa mana, ai kin yi ƙoƙari" kamar ta janyo wayewar gari, ta din ga addu'a Allah ya sa su karɓa su sake shi. Da wuri ta gama komai, wurin ƙarfe goma da rabi ta fita, shi ma maman halimatu ce ta hanata fita da wuri, ta ce mata ba da wuri suke zuwa ba. Suna ganin Jauhar suka ce "Madam ya aka yi ne? Kin sake dawowa ganinsa ne?" Ta ciro kuɗin ta ce "Gashi dan Allah yallaɓai ku sake shi, sukaɗai na samo dan Allah ku yi haƙuri" Ya zuba mata ido ya ce "Shekarar ki nawa ne?" Ta ce "Na kusa shiga sha bakwai, dan Allah ku yi haƙuri" "To ai ba zamu iya baki belinsa ba, kin ga mace ce ke, kuma yarinya, Allah ya sa ya daina abun da yake ko dan saboda ke, karɓi kuɗinki, ba zamu sake shi a kan wannan ɗan kuɗin ba, kotu ma zamu kai shi" Kawai ta saka kuka, "Dan Allah ku yi haƙuri, ba zai ƙara ba dan Allah kar ku saka a kai shi prison" Ɗaya daga 'yan sandan ya ce mata "Yi haƙuri ki daina kuka, da wasa yake yi miki, an zo belinsa ma, ke ki ke tayar da hankalinki, ko mun kama shi zamu sake shi" Kasa daina kukan tayi, hannunta riƙe da kuɗin, wani ɗan sanda ne ya fito, da alama babba ne, bayansa kuma walid ne da Al'amin da wani mutum. Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta zubawa fuskarsa ido, da take a ɗaure babu walwala. Walid ya ce "Kai Viper, wannan ce yarinyar da na tarar a gidanka, tayi mini rashin mutunci" "Wannan fa me aka yi mata take kuka?" "Sir, matar Viper ce" ya kalleta ya ce "Hajiya me aka yi miki ki ke kuka?". "Ce mini suka yi na kawo dubu hamsin za a sake shi, na kawo kuma suka ce mini wai kotu za su kai shi" ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka cike da yarinta. Ya kalli 'yan sandan ya ce "Waye ya ce ta kawo dubu hamsin" "Sorry sir, dan ta daina zuwa aka gaya mata haka" Nan ya hau yi musu faɗa, suka din ga bayar da haƙuri, Al'amin kamar bai santa ba, yayi gaba. Da sauri ta bi bayansa, tana ta yi masa magana yayi shiru. Walid ya ce "Haba mai dogon zamani, ka tsaya ka saurareta mana" A fusace ya waiwayo ya hau ta da masifa "Ban ce miki kar ki sake zuwa wurin nan ba? Kin san suwaye ake kawowa wurin nan? Mutuncinki ne a ganki a nan?" Sai da ta ja da baya a tsorace ta rufe fuskarta, saboda razana da masifar da yake yi mata. "Wai Aminu meyasa ka ke yin haka? Da uban waye ya damu da kai, yake ta taka? Macen kenan haka zuciyarsu take, ko dan matar gidanku ba ta da kirki kowa ma haka yake?" Tsaki ya yi yayi gaba. Walid ya ce "Yi haƙuri mu je, rabu da shi ya ƙarata, kar ki sake tayar da hankalinki saboda shi" suka tari a daidaita sahu suka tafi gida. Da suka je gida, ta shiga gidan ta bar shi da Walid. "Aminu, dan girman Allah ka rage jaraba, kalli yadda duk ta rikice saboda kai, kar ka yi wasa da damar da ka samu, ka saka ta tsaneka dan Allah" Ya tsaya ya ƙarewa ƙofar gidan malam lawan kallo, yayi ƙwafa ya shiga gidan, ba tare da ya tanka Walid ba. Jiki na rawa ba tare da ta yi fushi ba, ta kawo masa tea da buredi. Ya gama baccinsa ya tashi, ya yi wanka, ya gama ya ga ta kafa masa ƙusar rataye soso a banɗakin, har zai rataye yayi tsaki ya yar da soson a kan sabulun ya fito. Ya canza kayansa ya fito falo, Satar kallonsa take yi, kamar ya ƙara kyau, kwana biyun da ya yi a tsare ba ya shan komai, kamar ya yi kyau sosai. Sai murna take yi ya dawo gida. "Ke!" Ta ɗago ta kalleshi. "Meye sunanki ne?" "Jauhar" Ya kalleta ya ce "Me? Angela?" Murmushi ta yi ta ce "Angela kamar wata mage,  sunana Jauhar" Guntun tsaki ya yi ya ce "A saka muku normal suna, sai dai a saka ƙaƙale-ƙaƙale da iyayi, ni ba zan iya ba" "To ka kirani da fatimata fatima zahra" wani irin zirrrr ya ji a jikinsa, fatima zahra, sunan mace mai girma da daraja a idonsa, Ummansa abar ƙaunarsa, duk da ba ta duniyar, amma idan ya ji sunan har wata tsuma yake yi. Ya maze ya ƙarewa falon kallo, ya fita tsakar har zai wuce ya kalli kitchen ɗin ta sannna ya ce "Zo nan" Ta fito ta ce "Gani" "Wa ki ka sayar wa carfet ɗinki da kwanukanki?" Gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, yaya aka yi ya gane ko ya sani? Sai ka ce aljani? Ya ƙare mata kallo ya ce "Ina jinki, ya aka yi ki ka samu wannan kuɗin da ki ka kai? Ina kuma abubuwam da na tambayeki? Ki ka yi mini ƙarya kuma jikinki ya gaya miki" Kamar munafuka, haka ta zayyane masa komai. Bai ce mata komai ba, ya fita. Sahura na tsakar gida, tana hira ita da wasu coustomominta, kawai ta ga wasu irin zaratan matasa su uku, a tsakiyar tsakar gida da manyan gorori kamar za su farauta. Ta tashi ta ce "Lafiya malam? Me ku ka zo yi mini a gida. Wannan ai.... Haɗiye maganar tayi, da ya sako ƙafarsa cikin isa tsakar gidan. Yana shigowa idonsa ya sauka a kan carfet ɗin, a shimfiɗe a falonta. Ya ce "Liti, ku naɗo mini carfet ɗin nan" Ta waro ido ta ce "Malam lafiya?" Walid ya zaro wuƙa ya ce "Ki ka kuma magana, sai kin ɗaware daga sararin nan yanzun nan" daga ita har sauran matan, suka hau tsuma. Kamar abun banza, suka din ga yi mata cilli da kujeru, suka naɗo carfet. Viper ya ce "Dubu sha biyu ki ka saya ko?" Ta jinjina masa kai. Ya ce "Ɗaukko mini sauran kayan da ki ka karɓa a wurinta" jiki na tsuma ta shiga ta kwaso su. Ta ajiye masa a tsakar gidan, ya ce "Ɓarauniyar zaune, daga yanzu ki san abun da zaki din ga saya, ban da a nutse na zo miki, sai na saka an zana miki awarwaro a hannu, yadda gobe ba zaki sake zalunci ba. Liti ba ta kuɗinta". Liti ya zaro kuɗi zai bata, Al'amin ya ce "Wait, ta riga ta shimfiɗa a ɗakinta, ka cire dubu uku a kai, sannan ka sake cire dubu biyu zan cika ku wanke mini carfet ɗin ku kai mini gida. Haka kuwa aka yi, suka cilla mata kuɗi, suka kwashe kaya suka tafi. Jauhar ta na yi wa wasu stone work, dan kuwa matar ta fara kawo mata kayan tana yi, hakan yana ɗebe mata kewa. Ba ta yi aune ba, ta ganshi a tsakiyar falo, hannunsa da kaya, ya dungurar mata da su a tsakiyar wurin ya ce "Daga yau, ko cokali ki ka kuma sayarwa, saboda ni sai na ɓata miki rai, fiye da yadda ki ke tunani" Baki buɗe ta ce "Master, karɓowa ka yi, kuɗinta suna wurina fa, Allah zai kaman..." "Na ba ta kuɗinta, ko tsintsiya ki ka sake sayarwa, zan gane kuma ranki sai ya ɓaci". A hankali ta ce "Na shiga uku". *** Matasa ne a ƙalla su biyar, dukkanin su, babu wanda ya gaza ko ya wuce shekaru ashirin da biyu, suna sanye da tufafi masu nuna datti, gashin kansu da yanayin fuskarsu kuwa, babu tambaya sun bayyanar da tsantsar rashin ji a tattare da su, sai bushe-bushe suke yi, suna shewa. Wani matashin ne ya diro ta saman katanga, gaba ɗaya suka nutsu, suna yi masa sannu da zuwa. "Kai gayu akwai matsala wallahi" gaba ɗaya suka tattara masa hankalinsu suna sauraren sa. Ya ce "Kaii, wai ashe mai zamani ne ya tare a unguwar nan kusan sati biyu bamu sani ba?" Ɗaya daga cikin su ya miƙe ya ce "Ƙarya ne wallahi, me yake yi mana a unguwa". "Nustu, ni ma ban sani ba sai ɗazu, mai unguwa na ji yana maganar, sai za su je police station, ko a sasanta ayi zaman lafiya da shi, ko ya bar unguwar nan". Ɗayan ya yada sigarin hannunsa ya tashi ya ce "Guduma gaskiya kar dagus ɗin ka ya janyo mana matsala, ya san waye mai dogon zamani kuwa?". "Guys mafita ɗaya ce wallahi, kun san ba a sarki biyu a zamani ɗaya ko?" "Me ka ke nufi?" Guduma ya ce "Dole ɗaya ya bi ɗaya" "To waye zai bi wani?" "Kwanciyar hankalinmu da nustuwarmu, shi ne mu yi mubayi'a, samunsa ma a unguwar nan wani security ne, zai sa a din ga jin tsoranmu" Wani matashi ya ce "Ƙarya ne wallahi, babu wanda ya isa ya zo unguwarmu mu yi masa mubayi'a ba a isa ba". "Kai Kwano, bari na yi maka wani lissafi, duk sarkin da ya zo garinka ba da ziyara ba, ya shafe awanni arba'in da takwas, a irin harƙallarmu, to ɗayan biyu, ko dai ɗaya ya bi ɗaya, ko kuma a yaƙi juna, a kama sarki ɗaya da mutanensa a matsayin ganimar yaƙi, mu rayu a matsayin bayinsa, harƙalar da Mai zamani yake yi, ta ci uban tamu, ba sa'anmu bane ba, mu yi abun da ya dace, idan kuma mu ka bari rigima ta ɓalle, wallahi a unguwar tamu, zamu rayu kamar bayi ne amma ku yi tunani". Can Al'amin kuwa yana zaune a station, ga mai unguwar da yake da sauran mutanen unguwa. Yana zaune yana kallonsu, suna ta ɓaɓatun gaskiya ya tashi ya bar musu unguwa, saboda bad record ɗin da suka samu, a kansa daga in da ya baro, kuma nan ma ya zo yana yi musu shaye-shaye kar ya ɓata musu yaran unguwa. Suka yi suka gama, yayi shiru kamar mai zancen zuci, suka yi suka gama, D.P.O ya ce "Malam Aminu, ka ji abun da mutanen unguwar da ka tare suka ce, me za ka ce?" Sai da ya ja wasu seconds, sannan ya ɗaga kai, ya kalle su da jajayen idanunsa masu matuƙar kwarjini, duk suka yi shiru, suna sauraren sa, ya ce "Haryanzu ban ji an ce ga abun da na yi ba ai. Ba zan ce komai yanzu ba, gobe in Allah ya kaimu, mu haɗu a nan ƙarfe huɗu na yamma, zan faɗi abun da na yanke". D.P.O ya ce "Ina fatan ba wata ɓarnar zaka yi ba?" "Ba na sara sai an zo ramina" daga haka bai kuma cewa komai ba, ya tashi ya fice, ba tare da ya jira iznin hakan ba. D.P.O ya ce "Abun da nake so da ku shi ne, ku bi yaron nan a sannu a samu maslaha, kar ku yi wani abu da zai tunzura shi, ya fara yi muku fitina a unguwa, ku bari mu bi a hankali mu sasanta, ɗan ƙasa ne yana da damar zama a in da yake so, ku bi a hankali ayi musu sulhu". Shi kuwa yana fita, ya kira wayar liti, bugu biyu ya ɗaga. "Liti, nan da mintuna arba'in zuwa awa ɗaya, ina son ka tattara mini, duk wasu yara marasa ji a arear unguwar nan da nake da kewayenta, duk wanda ya yi gardama, ayi masa ɗaurin igiya da swizaland gaba da baya, a layin gidana nake son su taru". Liti ya amsa da "An gama shugaba" Sahura kuwa, sai da ta je har gidan maman halimatu ta ƙare mata cin mutunci, a kan yadda Al'amin ya je har gida, ya ƙare mata tanadi, a kan ta sai kayan matarsa, maman halimatu ta din ga ba ta haƙuri, ta ce su shiga gidansa su yi magana da jauhar ɗin, amma ta ce ai ba mahaukaciya ba ce ita, da zata shigar masa gida ya ritsata ya kashe. Jauhar tana ta aikin stone, ta ji ana wata irin busa a unguwar, kamar da ƙaho ake yin busar, irin bushe-bushen da aka din ga yi, ranar ɗaurin aurenta, dan haka gabanta ya faɗi ta shiga cikin tsoro. Sannu a hankali, hayaniya ta fara cika layin nasu, da surutan matasa, ɗaki ta gudu ta rufe ƙofar falo, dan tunani ta fara yi, ko yaran madaki ne, gashi ba waya ce da ita ba, balle ta kira Al'amin Kafin ya ƙarasa layin gidan, liti ya kira shi a waya, ya sanar masa sun fara taruwa matasan, dan haka bai bi ta cikin ba ya bi ta baya. Jifff! Ta ji dirar abu a tsakar gida, ta katanga ya diro gidan, ya fara ƙoƙarin buɗe ƙofar falon, amma a rufe ya jijjiga ya jijjiga amma ya ji a rufe. Ya shiga bugun ƙofar kamar yaƙi, ƙulewa tayi a ɗaki, ta hau addu'a, tare da tunanin ta ta ta ƙare, yaran madaki sun zo neman Al'amin, ko sun zo sassarata. "Ke malama ki zo ki buɗe mini ƙofa" sai da ta ji muryarsa, sannan ta fito ta buɗe, ta kalle shi, ta leƙa tsakar gida ta ce "Ai ban san kai ba ne, biyoka aka yi ne?" Wani irin kallo ya yi mata, ya ce "Matsa ki bani wuri" ta matsa ta bi bayansa tana surutu "Master ka daina dirowa ta katanga dan Allah, gaba ɗaya na tsorata wallahi, na zata madaki ne, suka zo nemanka na ji sai busa ake yi ga warin kayan shaye-shaye...... Haɗiye maganar tayi, da ya waiwayo yana yi mata kallon warning. Ta ce "Yi haƙuri, ka ga abokanka sun dawo da carfet ɗin, wai wanke shi suka yi, amma dai yakamata na je na bawa dillaliyar nan haƙuri, ai ka ga an shiga hakkinta, har gida ta zo tayi wa maman halimatu masifar abun da ka yi" ɗakinsa ya shiga, ya kulle ƙofar ya saka sakata ya bar ta a bakin ƙofa. Sai abun ya bata dariya, kafin awa ɗaya matasan nan sun kusa cika layin nan, sai hayaniya suke yi. Malam lawan kuwa, a waya matarsa ta kira shi, ta ce kar ya kuskura ya dawo yanzu, 'yan daba sun cika layin nan. Jauhar na ɗakinta, tana aikinta, ta ji yana buɗe gate, a razane ta fito saboda yanayin bushe-bushen da ake yi, ya tabattar mata da akwai matsala. Yana fita wurin yayi tsit, kamar ba su ne suke hayaniya ba da. "Sai da kai sarki, ƙaramin dodo magajin babban, ko ma in ce ka ɗara shi. Mu na yi maka maraba da zuwa wannan unguwar, mun fito ƙwanmu da kwarkwata domin yi maka mubayi'a". Cewar guduma yana geɓare baki, yanayin yadda yake maganar kawai a buge yake. Viper ya goya hannunsa a bayansa, ya ce "Manyanku sun kai ƙarata a kan yarjejeniyar zaman lafiya, sai dai ni da ku zan yi wannan yarjejeniya. Abu goma a cire bakwai a tara da ɗaya zan gaya muku, a bi iyaye, ayi caji kaɗan saboda lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa, a kiyayi taɓa kayan wani. Babu zubar jini a tsakanin ku, ko duk wani wanda yake unguwar nan, abu na ƙarshe mafi muhimmanci da fari salin alin na so zama a unguwar nan, wataƙila na ɗan lokaci na baku wuri, amma tun da abun ya zo da haka, sarki biyu ba zai yi sarauta a zamani ɗaya ba. Ko dai mutum ya yi mubayi'a ko ya bar unguwar nan. Kar kuma a kuskura a matsi ramina idan ba haka ba, zan yi ɓarna. Mu haɗu da shugabannin dabar Unguwar nan da kewayenta gobe a station ɗin unguwar nan, domin yarjejeniyar zaman lafiya. Kuna iya samfewa" Su ka din ga yi masa kirari, yana jin kansa yana sake fashewa. Bayan sun watse, maman halimatu ta shigo, tana ba ta labarin abun da sahura ta zo ta yi mata. Jauhar ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri maman halimatu, dan Allah ki bata haƙuri, ba yadda zan yi, na so mayar mata ma da kayan, ya ce idan na sake sayar da wani abu, zai ɓata mini rai. Wallahi yana ankare da komai, ko cokali na sayar zai gane, ni har tsoro yake bani, bari na baki dubu goma a kuɗin, ki kai mata ta ƙara ki bata haƙuri dan Allah" Maman halimatu ta ce "To shikenan, Allah ya kyauta" ta bata dubu goma ta kaiwa dillaliya, ita kuma ta bata kyautar dubu biyu, sauran kuɗin kuma ta ɗan yi musu cefane dan kuwa shi babu ruwansa. Washegari tun ƙarfe biyu, su mai unguwa suka koma police station, suna jaddada dole a kori Al'amin, dan jiya kafin su je gida ya rigasu zuwa, ya tara musu dandazon 'yan daba a unguwa. Al'amin bai je ba, sai ƙarfe huɗu tare da rakiyar su walid, da kuma matasan yara 'yan shaye-shaye da sun kai ashirin da wani abu. D.P.O ya ce "Lafiya, waɗanan fa?" Al'amin ya kalli mai unguwa, ya nuna masa guduma ya ce "Ka san wannan? Ko ba ka bani amsa ba ɗanka ne, meyasa ba ka kore shi daga unguwarka ba? Ko dan shi ɗanka ne?.  A wannan ba wannan matasan wakilai ne da suke jagorantar wasu yaran a ƙarƙashin su, wanda duk a cikin unguwarka suke, kana nufin a sati biyu da zuwana duk ni na lalata su? Har na tare a unguwar nan, ba su san waye ni ba, sai jiya da na saka a tara mini su. Dama can kuna da lallatun yara, harƙallata nake, ba na lalata ɗan kowa, duk ɗan wanda ya lalace, dama lalataccen ne. Ina sake maimaitawa ba na harbi sai an matsi ramina ko in da nake. Ga mafita zan bayar, wadda ba zan ƙara ko rage wani abu daga abun da zan faɗa ba. Mafita biyar ce ba uku, ko dai a haɗa a kore ni, da ni da yaran nan, ko kuma ku yi wa gidana kuɗi ninki uku, yadda zai isheni na sai wanda ya fishi, na bar muku unguwa, idan ba haka ba....... Ba na ƙarasa magana sai dai na aikata. Duk sai suka yi ɗif D.P.O ya ce "Mai unguwa mai ku ka yanke?" Shiru suka yi ba su ce komai ba, D.P.O ya ce "Tashi ka ja zugarka ka tafi, babu wani abu in sha Allah". Ya miƙe ya ce "Galibi yaran nan secondary school drop out ne, wasunsu idan son zuciya ne ya kai su wannan halin, wasun su laifinku ne, ko dai ku nutsu ku gyara rayuwar matasan yaran nan, ko kuma su cigaba da lalacewa kuna rusa al'ummarku da hannunku" yana gama maganar suka fice da shi da su. D.P.O. ya ce "Yaron nan fa ya san abun da yake yi, jiya kuna barin wurin nan, daga can unguwar su, Aka kira ni aka ce a gargaɗe ku, babu ruwanku da shi, yaron 'yan siyasa ne, dan Allah ku lallaɓa ku zauna lafiya da shi. Bayan sun bar station ɗin, wani irin ɓacin rai ya din ga cizon zuciyarsa, a duk lokacin da aka samu matasa ire-iren sa, al'umma ba su da wani burin da ya wuce, yin watsi da shi, da nesanta kansu da ire-iren su, bayan su ne ƙashin bayar lalacewar ta su. Yau abun na sa ya fi na kullum, domin kuwa a buge ya dawowa jauhar, wajen ƙarfe sha ɗaya na dare, ya wuce ɗakinsa, ba ta kula shi ba ta koma gefe ta zuba masa ido. Washegari da safe shiru bai fito ba, ta leƙa ɗakinsa, ta tarar da shi a kwance yana bacci, gefensa ga kwalin ashana da na taba, ga kwalabe. Shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa, a hankali ta fara magana "Sun san da haka suka aura mini kai, Allah na roƙi ka bani mafita ka zaɓa mini shi, Allah ka kawo mini mafita, Allah ka shirya mini shi, Allah shiriya taka ce, Ni da shi duk bayinka ne, Allah bai gagari ikonka ba, Allah ka shirya min mijina. Allah ka sa ya daina abun da yake yi, Allah kar ka sa ya mutu yana saɓa maka" ta yi maganar tana kuka. A hankali ya yi juyi, satchets ɗin ƙwayoyi, suka zubo daga aljihun gaban rigarsa, ta saka hannu ta kwashe su, da kwalaben, ta hau caje ɗakinsa, duk wani nau'i na abun da ba ta yarda da shi ba, sai da kwashe daga ɗakin. A hankali ya motsa, ya buɗe idonsa, ita kuma ta fice daga ɗakin. Da ƙyar ya iya tashi, dama bayan sallar asuba, ya sake yin shaye-shayen. A yunwace, ba tare da ko wanke baki yayi ba, ya hau cin abinci, saboda kayan shaye-shayen sun rarake masa ciki, ji yaya ko tsayuwa ba zai iya yi a kan ƙafafuwansa ba, sai da ya gama ci ya dawo dai-dai. Ya shiga banɗaki, ya wanke bakinsa ya fito falo, ko ɗaga jauhar ba ta yi ba, balle ta kalleshi. Ya je gabanta ya miƙa mata hannu. Ta ɗago ta kalleshi. "Bani abun da ki ka caje mini ɗaki ki ka ɗauka" gabanta ne ya faɗi, mutumin da yake bacci ya aka yi ya san ta ɗauka?. "Bani mana" "Na zuba a shara an zubar!" (Yau juma'a mu yawaita salati, ga shugaba Sallallahu alaihi Wasallam) Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Duk da cikin matsanancin tsoro da tashin hankali ta bashi amsar, amma ta tattaro jarumtarta ta dake, ta ƙi kallonsa. "Ai ɗago kai zaki yi ki kalle ni, ki bani amsar da ki ka faɗa yanzu" Ta yi shiru, tana jiran yayi mata duk abun da zai yi mata. Ya ce "Dama ba ni na kawo ki gidan nan ba, kuma ba ni na ce a kawo ki ba, idan kin gaji ki tafi dama kin isheni, kuma idan ki ka kuma zuwa kaina ki ka tsaya ki na kuka, sai na ɓarar da ke". Gabanta ya faɗi, a buge ta tarar da shi yana bacci, ya aka yi ya san duk abun da ya faru, sai dai kalmarsa ta ƙarshe da ya ce a kawota ba, ta yi mata ciwo. Ta zata zai yi mata tijara, da ta ce ta zubar, sai kuma ta ga ya tashi ya nufi hanyar fita, kawai ta fara kukan da ba ta san na menene ba ma. Waiwayowa ya yi yana kallon ikon Allah, da ta samu bai casata ba, da ta ɗebe masa kaya,ta ce ta watsar kuma ya san ƙarya take yi ba ta zubar ba, shi ne saboda samun wuri har da ɓare baki tana kuka. Sosai yarintarta ta fito, yadda ta tura baki tana kuka, tamkar irin 'ya'yan madarar nan shagwaɓaɓɓu. Kawai ya girgiza kai ya fice, kafin ta fusata shi. Rahila da Zakiyya kuwa sai shewa suke yi, tare da farincikin yadda shawarar da suka yanke ta yi amfani. Zakiyya ta ce "Ni fa na zata yadda yake ɗin nan, ana kaita ya korota tun da ba son auren yake yi ba, amma dama na san ko zai daketa ya cinye abu ne mai wahala ta faɗa ko tayi yaji, juriya ce da ita kamar dutse shegiya". Rahila ta ce "Shi ɗin me? A duniya akwai namijin da zai ce ba ya son mace ne, ke ban da abun makirci wannan yarinyar son kowa ƙin wanda ya rasa, wa zai ce ba ya so, dan ma ƙarama ce, gashi ai sati biyu kenan sun yi luf daga shi har ita". "Wallahi na zata ba zai saurareta ba, ƙila ma ya korota, a yadda ki ke bani labarin yadda ya zama, da kuma rashin jin da yake yi". "Ba fa mahaukaci ba ne, idan ta iya zama da yaron nan, ba lallai ki ji kansu, ai duk wannan bala'in da nake yi da tashin hankali a kansa, wasu lokutan shi da 'yar uwassa yana yi mata abu, ke har magana shahida take gaya mini a kansa" Cikin mamaki zakiyya ta ce "Kai haba dai?" "Wallafa Allah, ba suna school aka yi auren ba, sai da na kusa dukan yarinyar nan, ƙiri-ƙiri wasu lokutan take nuna in daina takurawa ɗan uwanta, aikuwa ubanta nake ci". "Gaskiya kar ki zauna a kanta, ita ana neman mafita tana shirme? Ni kam yanzu menene abun yi ne? Ƴan uwan Alhajin nan fa sun zo, wai ayi aure ayi visa ta bi shi china" Rahila ta ce "Aikuwa sai dai a lahira idan ana zuwa". "Aikuwa, wai yanzu ya fasa dawowa nan da watan ɗayan ba, ina nan dai ina ta lallaɓa uban, a kan ya haɗa shi da hafsa". "Ai ba iya lallaɓa shi ba, malamai zamu cigaba da yi, in sha Allah sai abub nan ya tabatta, ita waccan ai an gama da babinta". Zakiyya ta ce "Haka ne kam, to Ubangiji Allah ya amince, ni dai ko nawa ne zan kashe, idan ta aure shi na san zan mayar da kuɗina". "Kar ki damu ai ba zama, za ayi duk mai yiwuwa, hafsa zata auri mutumin nan". *** "Ku yanzu a ganinku ya dace mu na ji mu na gani, baƙo ya zo unguwarmu ya saka mu yi masa mubayi'a? Baƙo ne fa, mu kuma a nan aka haife mu muka girma, muka kafa sabgar nan, kuma ace sai dai mu bi shi, ba dai ya bi mu ba?" "Wallahi nima dai haka na gani, abun yayi mini ciwo, guduma ya fi kowa bani haushi shege, ai wallahi sai dai a rabu biyu, ayi ta zubar da jini, har sai ya yarda ya bi mu, ba wani shege da zai shigo arearmu ya buɗe mana ido, mu zagaya mu ji ta bakin sauran, mu ji su waye suka bi, kuma suwaye za su yi tawaye". Ɗaya matashin, ya hurar da hayaƙin wiwi ya ce "Mu tabattar da suwaye a tare da mu tukuna, zamu yi masa sara na warning, idan ma ta kama, mu kawar da shi da ga sararin nan, ba wani ɗa da zamu yi wa biyayya, tun da muka yi wa iyayenmu ma tawaye". Suka cigaba da tattaunawa a kan yadda za su ɓullowa lamarin, su yi maganin Al'amin. ***** Kamar masu kasa gyaɗa, haka suka kewaye farantin wiwi, suna naɗawa a takarda. Suka mayar da wata ƙwaya garri, suka haɗata a cikin wiwin, ita ma suka ɗaura ta daban. Matasa ne suka din ga shigowa da ɗai ɗai, suna karɓa, suna zube balance, suna karɓar kaya. Liti ya shigo cikin ɗakin da Al'amin yake, da robar abinci, ya zauna ya ce "Taso ga abinci" Ya tashi zaune ya kalli miyar kan abincin, sai ya ji ƙyanƙyamin abincin, miyar sam ba ta ji mai ba, ga ta ba ta soyu ba, ba irin wadda waccan taɓararriyar yarinyar take bashi ba. Guntun tsaki ya ja, Walid ya ce "Lafiya?". "Na ƙoshi" "Meyasa?" Ya girgiza kai ya ce "Bakomai". "Ka ce mini kawai, abincin amarya zaka je ka ci, wai mu ko sau ɗaya ba zaka kawo mana abincin na ta mu ci ba? Sai dai ka yi ta ci kai kaɗai?". Kai tsaye ya ce "Ba zan kawo ba" "To ka ƙarata, ku ci ku kaɗai, dama ni naga kamar haushina ma take ji, ban san me nayi mata ba". Ya tashi yana fatan Allah ya sa ya je ya tarar ta yi abinci. Sai kuma ya tuna kukan da tayi kan ya fito, ƙila ma ba ta yi girkin ba. Sai dai kafin ya ƙarasa gidan, aka tsuge da ruwan sama, dan haka ruwa yayi masa duka, yayi ta sauri ya ƙarasa gida, ya san ƙarshenta ruwa yau ma ya shigar mata falo. Sai dai yau aka yi sa'a, ruwan bai shiga da yawa ba, sai dai tsakar gidan ya cika da ruwa. Tana ɗakinta tana salla, ya fara cire kayan da suka jiƙe, ta shigo da sallama, sai dai cikin matsanancin hanzari, tayi wani irin burki, ta juya. Shi mamakin ta yake yi, sam ba ta da zuciya ba ta fushi. Ba tare da ta waiwayo ba ta ce "Ina da ruwan zafi a flask, na kawo maka ka yi wanka, sai ka ci abinci kar ka yi mura saboda ruwan da ya dake ka?". "Kawo" sumi-sumi kamar mara gaskiya. Ihunta ya jiyo a tsakar gida, bai san ya aka yi ba, sai ganinsa yayi a tsakar gida, cikin hanzari yana zaton wani abun ne ya sameta, tayi jifa da flask ɗin a gefe, Allah ya sa na silver ne tana ihu, ta maƙale a jikin bango. "Ke menene? Meyafaru?" "Kwaɗo ne, zai riƙe mini ƙafa" Ji yayi kamar ya ƙarasa, ya kwaɗeta, wai kwaɗo take yi wa wannan ihun. "Zaki rufe mini baki ki zo ki wuce, ko sai na zo na tumurmusa ki?" Jauhar ta ce "Tsoro nake ji wallahi" tayi maganar tana ɗagowa, idanunta har sun yi ja. Sai dai mayar da kanta ƙasa tayi, da sauri, tana tsuma saboda babu riga a jikinsa, wani irin gashi ne a jikinsa, tun daga ƙirjinsa har saman cibiyarsa. "Ke ba na son gulma, miƙo mini flsk ɗin, idan ya so ki dauwwama a wurin" Cikin shagwaɓa ta ce "Wallahi da kwaɗo a cikin ruwan nan, tsoronsa nake ji" tayi maganar idanunta na bayyanar da tsantsar tsoro da tashin hankali. Cikin ruwan ya biyo, ya zo ya ɗauki flask ɗin, zai bar kitchen ɗin ya bar ta, ta saka hannu ta riƙe masa wando, tana ihu. Sai yanzu ya leƙa ya ga kwaɗon ne da gaske, amma girmansa ba wani ƙato bane take wannan ihun, shi bai taɓa jin wai ana tsoron kwaɗo ba, sai yau. A ransa ya ce 'Laifin iyayeki ne da suka zaɓa miki wannan rayuwar' Kwaɗo ya tsalla yayi waje, ita kuma jikinta sai rawa yake yi, cike da tsoro. "To ai sai ki cikani, tun da ya tafi ko?" Cikin tsananin jin kunya, ta sake shi, ta koma gefe. "A nan wurin zaki dauwwama kenan?" Ta ce "A'a idan ruwan ya bushe, na wuce, ka duba ɗakina akwai man zafi a kan mudubi, idan ka yi wankan ka ɗan shafa kar ka yi mura, abincinka yana ɗakinka" kallonta yake yi, yana son gane nature ta ce a haka, ko kuma iya shege ne, amma yadda take ƙifta ido a tsorace ya tabattar masa da gaske take. Ba ta yi tsammani ba, ya saka hannu ɗaya ya ɗago ƙugunta, hannunsa ɗaya kuma da flask taku kaɗan yayi, ya direta a tsakiyar falo. Kallonsa take yi da mamaki, shi kuma ya nufi ɗakinsa. Har ɗan tsalle ta yi, dan ta tabattar ta na da nauyi ne, ko ba ta da shi, da ya ɗauke ta kamar wata 'yar teddy. Ta fi mintuna sha biyar tana cigaba da mamakin yadda ya ɗagata kamar a bar banza. Tuwon shinkafa ta yi da miyar taushe, kamar ya cire kunne dan daɗi, ga katifarsa ta saka sabon bedsheet, ɗakin yana ta ƙamshi, amma hakan bai hana shi goge mata hannu a jiki ba, ya gama ya miƙe yana bacci, kayan na sa ma sai ƙamshi suke yi. Leƙawa ta yi ɗakin nasa, ya mimmiƙe a kan katifa, bai saka rigar ba yana bacci ta lallaɓa ta shiga da sanɗa zata kwashe kwanukan. Yanayin garin da sanyi saboda ruwan da aka yi, amma ya takure yana bacci. Ta fitar da kwanukan, ta ɗaukko bargo daga ɗakinta, ta zo zata rufe shi, ɗan ƙura masa ido ta yi. Al'amin ba shi da wata makusa, da yake baccin nan ma he looks very innocent and calm. Kasa rufe shi ta yi, ta tafi tunanin ya aka yi ya fara shaye-shaye, ya aka yi su mama suka samo shi ma, suka aura mata? A ina yake ina ne gidansu? Duk take tambayar kanta. Tashi ya yi zaune kamar aljani ya ce "Meye ne kin zo kin sakani a gaba kina kallona" Zabura ta yi ta ce "Yi haƙuri, na zata bacci ka ke yi, ba kallonka nake yi ba, na ga kamar kana jin sanyi ne, bargo na kawo maka" tayi maganar tana tsuma. Ya miƙa mata hannu, ta bashi bargon, ya ware shi ya lulluɓa, ta fita tana mamakin al'amin idan yayi wani abun mamaki yake bata, har da ajiyar zuciya ta ji yana yi alamun baccinsa yayi nisa, amma kawai ta ganshi a zaune. *** "Allah ya taimaki maigida" "An gaisheka, ya ake ciki?" "Komai normal, ba wani abu" "Yaya za ayi? An kama Ja'afar da kaya, hukumar nan sun ƙi sakinsa, ba zan matsa ba, amma ina buƙatar a musanya shi da wani" "Oga ba zan iya sakinsa kai tsaye ba, amma dole za'a samu wani a kama shi da kayan, sai a saki jafar a kama shi, ka san wannan karon shugaban namu, yana da sanya ido sosai" "Shikenan, ayi abun da yakamata kawai" "Ok sir". Cikin ikon Allah, matar nan tela, tana biyan jauhar, duk da ba wani kuɗin kirki take bata ba, amma tana jin daɗi sosai da sosai, ta sayi katin tara kuɗi, ɗan abun da tayi cefane, sauran sai ta saka a kati, kuma Allah ya saka mata albarka a ciki. Yaran maƙwabta idan sun shigo, tayi musu tsifa da kitso, babu ko sisin iyayensu. Ta duƙufa tana aikinta, ba ta ji motsinsa ba, sai jefo mata bargo yayi a ka. A razane ta tashi, bargon kuma ya cukuikuyeta. Ya ce "Zaki taka kwaɗo" Ihu ta saka ta samu ta cire bargon da ƙyar, tana dube-dube, yana tsaye yana kallonta, kamar ba shi yayi maganar ba. Ta ce "Ina kwaɗon?" Ya yi shiru bai ce komai ba. Ta kalli yadda stone ɗin ya zube kamar ta yi kuka ta ce "Kalli yadda ka saka na zubar da kayan sana'ata." Ta durƙusa za ta kwashe, sai kuma ta yi sauri ta hau kan kujera, ta maƙale ƙafafuwanta ta ce "Ina kwaɗon ya shiga ne?" Haryanzu shi dai bai daina mamakin yadda kwaɗo ya zama abun tsoro ba. Hanyar fita ya nufa, ta gane tsokanarta yake yi, nan ta ƙara jinjinawa ƙi faɗinsa, har ya iya ya tsokaneta, amma ya sha kunu ba fara'a. "Master" ta kira shi. Ya tsaya bai waiwayo ba. "Dan Allah idan Allah ya yassare, ka taho da omo, zan yi mana wanki". Yanzu ma bai yi magana ba ya fita, ta naɗe bargonta, ta cigaba da aikinta. Zakiyya kuwa, kamar zata zare, Rahila na ta janta wuraren malamai kala-kala, yadda za su samu, Hafsa ta auri Alhaji mu'azzam da zarar ya dawo. Har sha ɗaya na dare, jauhar na aikin jera stone ɗin ta a kan gadonta, dan tun tana jin tsoron zaman gidan, har ta saba, sai da ta ji bacci yana kama idonta sosai, sannan ta tashi ta ajiye kayan, tayi wanka ta fito tana shirin kwanciya. Ji ta yi ana buɗe ƙofa, dan haka ba ta damu ba, ta san mai gidan ne, sai dai bayan wasu mintuna ta ji kamar yayi jifa da wani abu a falo, yana ta haki mai kama da kakari, gabanta ya faɗi ta fito da sauri, ta tarar da shi ya riƙe hannunsa yana ta nishi, hannunsa an yanke shi, da ƙafarsa ta hagu, kasancewar da wuta, ya sanya ta ga yadda yake zubar da jini, a gigice ta ƙaraso cikin matsanancin tashin hankali ta ce "Master faɗa ku ka yi da wani? Ya aka yi ka ji ciwo haka?" Yayi shiru yana fesar da iska daga bakinsa. Da gudu ta shiga ɗakinta, ta ɗaukko zani ta danne masa na hannunsa da ya fi zubar da jini, ta rikice ta rasa me za ta yi, kawai ta nufi hanyar fita. Ya ce "Ina zaki?" Cikin tashin hankali ta ce "Maƙota zan je, a samo abun hawa a kai ka asibiti kar jininka ya ƙare". "A haka kuma zaki fita?" Sai a lokacin ta ga, ko hijjabi babu a jikinta, ta koma ɗaki, ta ɗaukko hijjabinta sai kuka take yi, tana dawowa falon ya ce "Kar ki fita" "Meyasa? Jini fa ka ke zubarwa" Ya ce "Ki ƙyale ni, zai daina zuba ne" Cikin kuka ta ce "Ni dai dan Allah ƙyale ni, sai wani abun ya same ka, idan jininka ya ƙare fa mutuwa zaka yi" ba ta ma jira me zai ce ba, ta kasa da gudu, tayi waje. Ta din ga buga gidan maman halimatu, malam lawan ya buɗe, ya tsaya yana tambayarta menene?". "Dan Allah baban su halimatu, ka taimaka mini, na ga kana da babur, mijina ne aka sare shi dan Allah a kai shi asibiti, sai zubar da jini yake yi" Ya waro ido ya ce "A daren nan, haka kurum garin taimakonku, wani abun ya same ni, shi ma idan ya samu wani haka zai yi masa, sai da safe" ya rufe ƙofarsa. Haka ta din ga buga gidajen layin nan, na ƙarshe ne mai gidan ya biyota, sai dai ba shi da abun hawa, suka zo ya tsaya a ƙofar gidan, ta shiga ciki. Yana zaune, ya kashingiɗa ya lumshe idonsa, yana jin yadda raɗaɗi yake ratsa wurin saran. "Master, taso mu je" Bai buɗe idonsa ba ya ce "Ina?". "Wai meyasa ka ke haka, asibiti mana" tayi maganar hawaye na ta ambaliya a fuskarta. Ya miƙe yayi waje, ya tarar da maƙwabcin na su a tsaye, suka gaisa Al'amin ya ce "Malam ka rabu da ita dan Allah, ka je ka kwanta, ba wani abu in sha Allah" Ya ce "A'a ga jini kana ta zubarwa, ni bani da abun hawa, na kira wani ƙanina, a nan titi chemist ɗin sa yake, ko taimakon gaggawa sai a baka" Tayi farat ta ce "Yauwwa mun gode Allah ya saka da alkhairi" Haka suka tafi, ya kira ƙanin nasa, ya buɗe chemist ɗin babban wuri ne sosai. Ya fara yi masa ɗinki, saboda raunin na hannunsa yayi zurfi sosai da sosai. Sai dai shi da ake ɗinkewa kamar ƙwarya ko a jikinsa, ita kuwa sai uban kuka take yi, tana yi masa sannu. Kawai bin ta yake yi da ido, har mamaki yake yi, yadda take nuna matuƙar damuwarta a kansa. Mai Chemist ɗin ya ce "Dan Allah ki daina kukan nan, ba wani abu, ba ki ga shi jarumi bane?" "To jininsa ba zai ƙare ba, ya zubar da jini sosai tun a gida" Ya ce "Ba zai ƙare ba in sha Allah, idan ma ya ƙare sai mu saka masa naki". "Ki daina yi mini surutu a ka kin cika mini kunne" yayi maganar a ƙule. Haushi ne ya cika masa rai, kamar ya kife mai chemist ɗin da mari. Ta ce "To na daina sannu" tayi maganar cikin kulawa. A ka gama ɗinki, ya ce zai ɗan saka masa ruwa, saboda ya taimaka masa ya zubar da jini sosai, amma fafur ya ce ba ya so. Ya haɗa masa magunguna, ya ce ya din ga zuwa ana wanke ciwon, jauhar ta ce "Sai dai ka bani kayan dressing ɗin, ba zai din ga zuwa ba". Mai chemist ɗin yayi dariya, ya haɗa ya bata, ta ce "Nawa ne kuɗin maganin? Da abun da aka yi masa?". Maƙwabcin ya ce "A'a kar ki damu, Allah ya bashi lafiya, ni zan biya". Jauhar sai da ta risuna, ta din ga yi masa godiya, sannan ta ce "Tashi mu tafi" ya miƙe tsam ta bi bayansa. Suka baro maƙwabcin na su a can, suka nufi gida. "Sannu, ka na jin jiri ne? Idan kana jin jiri mu tsaya ka huta, ko ka dafa ni" kallonta ya yi ya ga me zai dafa. Ya dai yi shiru bai yi magana ba. Suka isa gida, ya shiga ɗaki ya zauna, ta fito ta hau aikin wurin da ya ɓata da jini, dan a buɗe su ka bar gidan ma. Ya zauna ya ci abincin da ya tarar a ɗakinsa, ta ga ledar omo ce da sabulu da ta ce ya sayo, su yayi wurgi da su. Ta dawo ɗakinsa, ta tarar ya jingina ya lumshe ido, "Sannu master, yana yi maka zafi ne? Ga magungunan nan ka sha kan ka yi baccin". Ya girgiza mata kai alamar ta ƙyale shi, gumi ya fara tsatstsafo masa, saboda allurar ta sake shi, zafi ya fara ratsa shi. Saboda kar ta takura masa da surutu, ya kwanta ya hau baccin ƙarya. Ta fita ta ɗaukko mafici ta dawo, ta zauna a gefensa, ta hau yi masa firfita. Sai dai lokacin kusan ƙarfe biyu ne na dare, ta din ga zabga hamma, yana kallonta, har bacci ya ci ƙarfinta, ta saki maficin. Ya buɗe idonsa fes a kanta, har mamaki take bashi, yadda take nuna matuƙar damuwarta a kansa, kuma komai zai yi mata ba ta jin haushi. Hakazalika bai daina mamakin yadda aka yi, iyayenta suka yarda suka aura masa ita ba. Ya ciro wayarsa a aljihunsa, ya kira walid, uku sauran nan, ya ɗaga. "Walid" "Maza, ya aka yi ne?". "Ka san akuyancin da yaran nan suka yi mini?" Walid ya ce "Wane yaran, suwaye?". "Na baro chamber, na shigo cikin unguwa, kawai na ji sara a hannuna, sun kai su bakwai, suka hau ni da sara, kasheni suka so yi" Walid ya zabga ashar ya ce "Suwaye?". "Bari na yi wa ɗaya shaida, haryanzu ba su san waye ni ba, na karya biyu, sauran sun gudu, sun yi mini rauni a hannuna da ƙafata". "Yanzu kana ina?" "Ina gida, ni wallahi yarinyar nan ta fara takura mini, komai kuka, duk ta tashi hankalinta, iyayenta ba su yi mata adalci ba, ni fa ba zata hana ni rayuwata yadda nake so ba". Walid ya ƙyalƙyale da dariya ya ce "Mai dogon zamani, da uban waye ya damu da ka ji koma menene mana, tana da tausayi ne kawai da alama, ka dai daina yi mata muzurai da zare ido kawai" Yayi tsaki ya ce "Ka saka liti ya nemo mini suwaye yaran nan" "Shikenan, zamu faso gobe in ga jikin naka, sai da safe". Ya ajiye wayar ya kalli fuskarta, tana ta bacci a zaune. Hannunsa ɗaya ya saka, ya janyota ta kwanta a kan katifar, shi kuma ya jingina da bango ya cigaba da bacci. Kasancewar ba salla za ta yi ba period take yi ya sanya, tana ji ana kiran sallar asuba, ta cigaba da baccinta, sam ta manta a ina take. Ƙaurin da ya isheta ne, ya sanya ta fara tari, tayi juyi ta buɗe ido, da fuskarsa ta fara tozali, yana busa sigari. Ta tashi tana kallon ɗakin, sai yanzu ta tuna ta shigo tana yi masa fifita. Ta hau soshe-soshen cizon sauro. Ƙura masa ido ta yi, ya kawar da kansa gefe. A raunane ta ce "Master" Idonsa ya ɗago ya kalleta. "Dan Allah ka daina, ba na so zuciyata ba ta yi mini daɗi, kuma zaka cutar da kanka, kalli yadda ka je aka yi maka rauni, ka zubar da jini, haba master manya ba sa haka" tsuke bakinsa yayi yana sakin hayaƙin, a ƙoƙarin sa na hana maganganun ta yin tasiri a zuciyarsa. Ta girgiza kai ta ce "Shikenan, ya jikin?". Yayi mata banza, ya cigaba da busa sigari. "Dan Allah ko ba zaka daina ba, ka rage mana, lafiyar ka fa". "Ke, ki koma in da ki ka fito mana, ko na ɗaure ki na ce ki zauna ne? Tashi ki bar mini ɗaki". Ta gyaɗa kai ta ce "Abun har da gori, Allah ya baka haƙuri" ta miƙe idonta fal hawaye. Tana kitchen tana aikin karin kumallo, aka buga ƙofa, ta saka hijjabi ta buɗe ƙofar, ta ga walid d wasu matsa su biyu, suka gaisa suka ce mata, wurin mak dogon zamani suk zo. Ta haɗe rai ta ce "Sunan shi Al'amin, bari na yi masa magana". Tana shiga ta tarar da shi a falo ya fito. Ta ce "Ka zauna sai su shigo su ganka, amma ka ga da rauni a jikinka" tayi maganar tana sunkuyar da kai, tana jiran ya gaya mata baƙar magana. Idonta ya ɗan yi ja, saboda kukan da ta yi. Ya nemi wuri ya zauna, ba tayi tunanin zai yadda da hakan ba. Ta je ta leƙa ta ce musu su shigo. A falo suka tarar da shi, gida sai ƙamshi yake yi, gashi dai ba wani haɗaɗen gida ba, amma ta gyare gidan tsaf. Suka zauna a falo, Walid ya ce "Maza wallahi ka more, mu ma Allah ya tsamo mu, dan Allah ji wani ƙamshi kamar a gidan masu kuɗi". "Duba ni ka zo yi, ko munafunci ka zo yi?" Walid ya ce "Duka, amma dai ya jikin? Kut ka sha ɗinki kamar ƙwarya, za su ci ubansu yaran nan, kan yamma an gano su in sha Allah". Suna ta zuba, tana jiyo shi yana saka baki sama-sama, da ita ce dai ba zai yi hira ba, amma yana magana. Tayi sallama suka amsa, ta zo ta ajiye musu kofuna, da cokula da flask ɗin shayi, ta koma ta kawo jallof ɗin taliya a faranti, sai ƙamshi take yi. Liti ya ce "Allahu Akbar, sannu amarya, wannan hidima haka? Ai da mun sani tuntuni mun zo" Al'amin kallonta yake yi, da jinjinawa ƙarfin halinta, har ta ƙar sanwa, ta yi girki da su. Suka kewaye, suka din ga cin taliyar nan, liti ya ce "Kalarta kalar girkinta, abincinta mai daɗi, ita kuma 'yar beauty, wallahi maza ka more, ga gida mai ƙamshi" Ji yayi ya kasa haɗiye abincin, maimakon ya ji daɗin yabon suka yi mata, sai ya tsuke fuska ya tsame hannunsa daga kwanon abincin. Har suka gama santin, bai sake cewa komai ba, Walid kuma yana ankare da shi, dan haka da gayya, ya cigaba da kunna shi, suka gama abun da za su yi, suka fita tsakar gida suka din ga yi mata godiya. Walid ya ce "Wai ba zaka fito ka raka mu ba?" Tayi farat ta ce "A'a ba shi da lafiya ai" Walid ya ce "Au, to Allah ya baku haƙuri, Allah ya ƙara afuwa ya bar ƙauna". Bayan fitarsu ta kwashe kwanukan, ta wanke, tana ta aikinta, yana kan doguwar kujera a kwance, sai dai ba ta kula shi ba. Kusan kwanaki uku, jikin master yayi kyau, ba shi da ƙan jiki, ba zai sha magani ba sai ya ga dama, dressing kuwa cewa yayi ba ya so. A kwanakin nan jauhar na jin ciwon kai, da ciwon jiki, sai dai ba ta wani damu ba. Duk yadda ta so hana master fita, da 'yan dabaru sai da ya saka ƙafa ya fice, ya tafi nasa garari. Cin abinci ne yake dawo shi, ko sau ɗaya bai tambayi yadda take samun yin cefane ba, sai da ya zo ya ci. Tun da ya dawo gidan ya ji shiru bai ji motsinta ba, kuma bai ga abinci ba, sama da awa guda, saɓanin da, da ya shigo za ta fito. Kasa kwanciya hankalinsa yayi, ya nufi ɗakinta. A kwance take a kan gadonta, amma bai tabattar da idonta biyu ko bacci take yi ba. Ya ƙarasa gaban gadon, sai dai ya manta sunanta, Fatima zahra kuma yayi masa nauyin da ba zai iya faɗa a bakinsa ba. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Dukan gefen katifar da take kai yayi, amma ba ta motsa ba, ya zura kai ya leƙa fuskarta, ya ga bacci take yi. Duk da bai saba zuwa ya tarar da ita tana bacci ba. Ficewa ya yi, ya bar ɗakin, shi babban takaicin sa, rashin samun abun da zai ci. Jauhar kuwa, tun dare ta kwana ta na fama da matsanancin ciwon mara, ga ulcer ta tayar mata, sai gudawa take fama da tashin zuciya, ta samu ya lafa mata, ta kwanta ta hau bacci ga gidan yau babu abun da za ta dafa, ɗan kuɗin hannunta sam ba su da yawa. Ƙarshe dai buredi ya fita ya samo, ya dawo ya zauna a falo yana ci. Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba ya ga kiran indabo ne, kallon wayar ya cigaba da yi, yana cin buredinsa, sai da ta kusa katsewa ya ɗaga ya saka a kunnensa, yayi shiru. "Aminu" "Mmm" "Na dawo, kai nake jira, haryanzu ba ka zo ba" "Zan zo" "Yaushe kenan? Haba kai kuwa dan Allah, ba ka san kiran me nake yi maka ba fa" Al'amin ya ce "Na ce zan zo ai" "To shikenan, Allah ya kawo ka" Ya ajiye wayar, gaba ɗaya haushin buredin da yake ci ma yake ji, sam ba ya yi masa daɗi, har aka yi kiran la'asar, ba ta fito ba. Ya tashi yayi salla, ya fito falo ya sake zama, sai ga ta ta fito tana ɗan yamutsa fuska. Fuskar duk ta ɗan ɗaga tayi jawur. Ta zo ta nemi wuri ta kwanta, ba tare da ta ce masa komai ba. "Wai yau ba abinci ne?" Yayi maganar yana wani basarwa. Maimakon ta ce masa babu abun da za ta dafa ne, sai ta ce masa "Ba na jin daɗi ne" Ya taɓe baki, ya tashi ya saka takalmansa ya fice daga gidan, fitarsa ba kaɗan, ta ji horn da tsayuwar mota a ƙofar gidan, mintuna kaɗan ta ji ana bugun gate, ta saka hijjabi ta je ta buɗe. Baba ta gani a tsaye, cikin matsananciyar murna ta ce "Baba" yayi murmushi ta ba shi hanya ya shigo. Suka isa har falonta, ya samu wuri ya zauna ta ce "Baba meyasa baka kuma zuwa ba?" Tayi maganar hawaye na cika mata ido. Wani irin matsanancin tausayinta ya kama shi, har ya ji kamar shi ma ya yi kukan, amma ya danne ya ce "To ba gani na zo ba, Waliyiyya 'yar baba" "Baba babu wanda ya zo mini, sai yaya saifu da Anty lubabatu, kowa yaƙi zuwa in da nake, wai ba za su zo ba, mijina ɗan daba ne, kuma ba abun da zai yi musu, ba ruwan shi da su. Baba ya ce "Waliyiyya, ki daina saka irin wannan abubuwan a ranki, kar su dameki, ki yi haƙuri ke mai haƙuri ce, amma ki ƙara. Ya gidan ya mijin naki?" Cikin jin kunya ta ce "Yana nan lafiya, yanzun nan ya fita" "Jauhar, ina fatan dai babu wata matsala dai ko?" Ta girgiza kai ta ce "Babu". Turus yayi ganin takalma a ƙofar falo, amma ya ƙarasa ya shiga, ba tare da ya yi sallama ba. Kallo ɗaya ya yi wa mutumin, ya ga yana yanayi da jauhar ya ƙarasa cikin falon, hannunsa riƙe da baƙar leda. Durƙusawa yayi har ƙasa ya ce wa Baba "Ina wuni" hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa jauhar ba, dan tun da ta ji motsin shigowar sa, take fatan Allah ya sa kar ya yi wa baba wani abun na rashin ɗa'a. Baba ya ƙare masa kallo, kai ba ka ve mara ji bane ba, dan a cikin nutsuwarsa yake, ya ce "Lafiya ƙalau malam Aminu, yau dai Allah ya yi mun haɗu, ya gidan ya iyalin naka" Ya amsa da "Lafiya ƙalau". "To masha Allah, Ubangiji Allah ya yi muku albarka, ayi ta haƙuri, ka san ita rayuwar aure, zama da mace sai haƙuri, dole za ku saɓawa juna, ayi ta haƙuri. Ba yabon kai ba, na san Waliyiyya yarinyar kirki ce, amma duk da haka na san dole wataran a saɓa Allah ya yi muku albarka" Ya amsa da Amin, ya tashi ya bar wurin ya tafi ɗakinsa. Ta ce "Baba bari na dafa maka abinci"  ta faɗi hakan, dan kar baba ya fahimta wani abu. Baba ya ce "A'a, zuwa na yi dama na ganki, ni da ba a san da zuwana ba" Jauhar ta ce "Dan Allah baba ka tsaya" Ya ce "Gidanku ba zan tsaya ba, kira mini mijinki, zamu yi magana" Ta tashi ta shiga ɗakinsa, ta ce "Master, baba yana son ganinka". Ya jinjina mata kai, ya tashi ya fito, ya samu wuri a ƙasa ya zauna. Baba ya ce "Malam Aminu dan Allah alfarma zan nema, ka san jauhar ba ta kammala sakandare ba, an fara registration ɗin WAEC ne, shi ne na ce ina neman alfarma, zan biya mata tayi registration ta yi jarrabawa dan Allah". Aminu ya ce "Babu damuwa, Allah ya bada sa'a". "Amin Aminullahi, Allah ya saka da alkhairi" Baba ya miƙe ya ce zai tafi. Cikin rauni ta ce "Baba daga zuwanka sai tafiya kuma?". "To Waliyiyya ba dai na ganki ba". Kamar mara gaskiya, haka ta biyo bayan baba, a tsakar gida ya tsaya ya kalleta ya ce "Jauhar menene?" Ta girgiza masa kai alamar bakomai. Ya juya zai buɗe gate, ta riƙe rigarsa ta fashe da kuka. Ya ce "Subhanallah, gaya mini menene? Wani abun yake yi miki?" Girgiza masa kai ta sake yi. Ta cukuikuye rigarsa, ta cigaba da sheshsheƙar kuka, shafa kanta ya dinga yi sai dai ya kasa hanata cigaba da kukan. Sai ma hannu da ya sa, yana goge hawayen da suke ƙoƙarin zubo masa, ya san ba zata faɗa masa koma menene ba, amma yanayinta ya nuna masa tana da damuwa. Dan kanta ta cika masa riga, ta goge hawayenta ta ce "Ka gaida gida baba, ka ce ina gaida su mama da Anty da kowa da kowa" Yayi ajiyar zuciya ya ce "Za su ji in sha Allah, gashi ke ba waya ba, ranar talata ki je ki samu malam Hadi, a office ɗin su, zaki yi thumb print, yayi miki registration" Ta ce "To baba, na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi" ya fita ta rufe gate ɗin, ta jingina da jikin gate ɗin, hawaye na cigaba da zuba daga idonta. Duk yadda suka yi, Al'amin yana kallonsu ta window, ta goge hawayenta kafin ta dawo ɗakin, ya bar falon. Haka ta koma bedroom ɗin ta, ta kwanta tana ta tunani daban-daban a cikin zuciyarta. **** 'yan uwan Alhaji mu'azzam kuwa, ba su gaya masa cewar an aurar da jauhar ba, suka ce masa babanta ya ce yayi haƙuri idan ya dawo ayi auren, abun ya bashi mamaki, ga wata irin kewar yarinyar da yake yi, yana jin son ta sosai da sosai a ransa, ya din ga addu'a da fatan Allah ya sa ba wani abun ne zai faru ba, saboda jinkirin da ake samu ba. Kusan kwanaki biyu kenan, jauhar bayan ta gama ciwon mara, ta koma zazzaɓi, gashi babu abincin kirki, kuɗin da take tarawa a kati, ba ta son ta je ta ce a bata, a fuskanci akwai matsala, hakan kamar tonon asiri ne ga mijinta, 'yan unguwa su samu abun faɗa. Haka zata fita ya sayo gari, da gyaɗa ko suga babu ta sha, shi kuwa garujen ko a jikinsa, sai dai yana ankare da yanayin jikinta. Al'amin na zaune a katafaren falon honorable Indabo, yana jiransa. Babu jimawa ya iso falon, yana ganinsa yayi murmushi ya ce "Ango ka sha ƙamshi, da alama amarya ce ta ɓoye mana kai har haka" Shiru yayi, ya saka babban yatsansa yana sosa girarsa. Indabo ya zauna ya ce "Tun shekaranjiya na shigo, nake nemanka amma ka ƙi zuwa. Da farko dai ina yi maka murnar angwancewa da ka yi, ina Abuja aka sanar da ni an kama ka, ana gobe ɗaurin aure, na tura P.A . Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya" "Amin" ya amsa a ciki kamar an yi masa dole. "To yaya shirye-shirye? Ina fatan kana ƙara shirya mini yaranka, babban zaɓe yana gabatowa, idan aka yi nasara aka samu kujerar nan, Aminu zaku warwasa daga kai har yaranka, har da na kusa da ku ma, dan Allah kar ka bani kunya, duk da ba ka saba bani ɗin ba". "To" ya amsa yana kallon wani wurin daban. "Ka san meyasa na kira ka?" "A'a" "Akwai wani matashi, yana nan a social media, ba shi da wani aiki da ya wuce adawa da ni, da aibata mana jam'iyya,kuma hankalin matasa ya fara komawa kansa, na rasa yadda zan yi da yaron nan, duk wasu hanyoyi da zan bi a siyasance, na yi amma ya ƙi ganewa". "Me ka ke so ayi?". Ya jefowa Al'amin hoton matashin, an rubuta adress ɗin sa a jiki. Kallo ɗaya ya yi wa hoton, ba tare da ya ɗauka ba, ya ce "Me ka ke so ayi masa?" "Ire-iren sa suna da yawa, amma sonake ayi musu misali a kansa. Ina son yayi ido biyu da Switzerland ɗin ka, ka yi masa shaida alamar kun haɗu". Wani irin murmushi ya yi, ya fito da dogon harshen sa, ya lashi laɓaɓɓansa na ƙasa da suka yi duhu ya ce "Switzerland. Kamar ka ce idan aka samu kujerar nan, zamu warwasa da yarana da na kusa da ni, alƙawari ne ko zance?" "Wace irin magana ka ke haka ne, ba zance bane ba, da gaske nake yi mana". Al'amin ya ce "In ɗauke shi a matsayin alƙawari dai" Indabo ya yi turus, ya kasa bashi amsa. "Ba zan tura mota, ta tashi a bule ni da hayaƙi ba, ba senator ba wallahi ko shugaban ƙasa ka zama, ba za a bule ni da hayaƙi ba, dan haka maganar nan a matsayin alƙawari na ɗauketa" "Kai fa matsalarka kenan Aminu". "Menene sallamar aikina?" "Masu kauri ne, ga wannan ka fara rage ta" yayi maganar yana ajiye masa envelopes. "Ka san dai in da ka tura ni ko? Wallahi idan ka bani abun da bai yi mini ba, ba zan yi ba" Indabo yayi murmushi ya ce "Ai somin taɓi na baka, akwai ciko" Ya miƙe tsaye ya ɗauki envelope ɗin sa ya fice. Sai da ya je can dabar su, ya sallame su, sannan ya nufi gida. Da ya je gidan a buɗe ya tarar da ƙofar gidan, kai tsaye ya shiga ya tarar duk ta cika igiya da kayansa, ta wanke masa su. Mamakin jauhar yake, rashin sanin ciwon kai ne, ko me yake damunta, ta ce ba ta da lafiya, amma ta zage ta yi masa wanki, hatta ɗakinsa da ya bari kaca-kaca ta gyara masa. Ya samu wuri ya zauna a kan kujera, ya kunna sigari yana sha. Sallamarta ya ji a tsakar gida, bai amsa ba ya cigaba da shan sigarinsa. A hankali take takawa, ga yunwa ga ciwo, ta shigo hannunta riƙe da 'yar leda. Ta zauna a kan carfet jiki a sanyaye ta ce "Ka yi haƙuri, baka nan ne ban tambayeka ba na fita, magani na je chemist ɗin bakin titi na sayo" Sai da yayi wani munafukin tari, saboda tun ranar da mai chemist ɗin nan yayi masa ɗinki, ya din ga jan ta da hira, ya ji ya tsane shi, amma ya fuske yayi mata shiru. "Kar ka ga ban yi girki ba tun jiya, kuɗin hannuna ne suka ƙare, amma ga gurasa na taho mana da ita daga titi" ƙara yawan hayaƙin da yake fitarwa daga bakinsa yayi, ba tare da ya ko kalleta ba. Jin ba shi da niyyar kulata, ya sanya ta yinƙura za ta tashi, sai dai ta yi wani irin razanannen ihu, kallonta yayi da sauri, ya ga ihun me take yi, dan ya san ba zai wuce wani abun haushin ne ba, dan kamar gyare haka take da ihu. Ashe ƙadangare ne a ƙarƙashin kujerar da ta zauna a gabanta, tun shigowarsa ya ganshi, amma bai damu ba, ƙadangaren na ta neman hanyar fita, jikinsa yayi baƙi sosai, kamar an ciro shi daga kwata, yayi ba kyan gani. Tuni ta suma a wurin, dan kuwa hannunta ta ɗora a kansa ba ta sani ba. Maimakon ya tashi, sai ya zuba mata ido, cikin takaici, abu kaɗan sai ta suma, ko ta hau ihu. Kamar ba zai tashi ba, sai kuma ya miƙe. Ya saka hannu ya ɗauketa ya kwantar da ita a kan kujera, sai dai jikinta ya yi zafi sosai, sai yanzu yake tunanin zazzaɓi take yi kenan?. Ya duba ledar magungunan da ta sayo, maganin ɗaya mai hoton sauro, ɗaya kuma pcm ne. Ya kama gefen hannunta, ya ji bugun zuciyar ta yana bugawa da sauri, ya saki hannun nata yana kallonta, ita a rayuwata komai ma tsoro yake ba ta kenan. A hankali ta fara motsawa, ta yinƙura za ta tashi, ya ce "Koma ki kwanta" ta ɗaga idonta a hankali ta kalleshi. "Tsoro nake ji" ta faɗa muryarta na rawa cikin tsoro. Ya sake kama hannunta, yana jin bugun zuciyar ta, ya saki ya ce "Tashi" ta yinƙura ta tashi a hankali, kanta na sara mata ga jiri saboda yunwar da take ji. Tana daga kan kujerar a kwance, ya ɗage ɗaya kujerar da ƙadangaren yake ƙarƙashin ta, kawai ya saka hannu ya danƙi ƙadangaren ya jefa shi waje. "Na shiga uku master, ƙadangaren ka ke kamawa da hannunka" Tsaki yayi, ya wuce ɗakinsa, jikinta ya din ga rawa, tsigar jikinta ta din ga tashi. Ya dawo ya dire mata leda, ya ce "Ki ci ki sha magani" ya jefa mata wani kwali sannan ya fita. Kwalin ne ya fara ɗaukar hankalinta, ta ɗauka da sauri tana dubawa, sabuwar mp ce kar 'yar ƙarama mai kyau. Ba ta san lokacin da ta yi murmushi ba, ta hau kukkunata tana dubawa, sai da ta gama, ta ajiye ta buɗe ledar. Irin meatpie ɗin nan ne oasis manya kusan biyar, da ƙatuwar robar fura da nono. Kasancewar a yunwace take kuwa ta hau ci, ta ji babu daɗi kwana biyu tana ciwo, amma bai iya yi mata sannu ba, dama magani ba ta saka ran ya saya mata ba, mutumin da bai ba ta abinci ba wane magani zai bata, ashe yana sane, sannu ce ko ya jiki ba zai iya ce mata ba. Sai dai da tuna yadda ya ɗauki ƙadangare da hannunsa, sai tsigar jikinta ta tashi. Ana yin sallar isha'i ya dawo, mp ɗin ta har da fitila. Ta tashi tana yi masa sannu da zuwa, ya wani maze ya bata wata ledar, sannan ya zauna ya ce "Ki nemi wata ma'aikaciyar idan akwai a nan kusa, tayi miki, idan ki ka je wurin wancan ɗan iskan na bakin hanya kuma ni da ke ne" Ta saka hannu biyu ta karɓa, allurar zazzaɓi ce mai tsada ya sayo ya kawo mata, amma bai iya cewa ya jiki ba. "To godiya nake master, Allah ya ƙara arziki ya sa a fi haka, na ga saƙo ma na gode sosai da sosai Allah ya sa afi haka". "Amin". Ta ce "Ga naka na ajiye maka" Ya ce "Idan zan ci ba sai kin ce na ci ba, ki daina kuma wannan mugun tsoron, komai ya baki tsoro, idan ba haka ba ki kashe kanki a banza" Jauhar ta rausayar da kai ta ce "Nima ban san ina jin tsoron ba ne. Amma kai ba ka jin tsoron sa ka riƙe shi da hannu?" "Ban sani ba? Rannan kwaɗo yau ƙadangare, meye abun tsoro a jikinsu, har da suma saboda ƙadangare" tayi shiru ta sunkuyar da kai. Sai da ya gama sannan ta ce "Ka yi haƙuri to, ban san ya ake yi nake jin tsoron ba". "Idan ma kina sane ki cigaba da yi mini ihu a gida kamar gyare". Sai da ta yi murmushi ta ce "Zan koyi jarumta, zan daina jin tsoro in sha Allah. Yauwwa master yaushe zamu je ka kai ni na gaida su mama? Ba su taɓa ganina ba, ban taɓa ganinsu ba, su hajiya kawai na taɓa gani, yakamata ka kaini na gaishe su. Sai ayi girki mu je mu gaishe su, na ga haka ake yi". Shiru yayi, yana tuna Ummansa, tana yawan cewa Allah ya raya mini babana na ga aurenka, in ga mai sa'ar da zata auri ɗan autan mazana Jauhar ta ce "Ka yi haƙuri idan na ɓata maka rai ne maganar da na yi" Ya tashi tsam ya ce "Yauwwa, Ina sake jaddada miki, idan ba zaki iya zama ba, ko kin gaji zaki iya komawa gida, babu takura, na ga shekaranjiya kina ta koke-koke, idan da takura you are free to go" daga haka ya nufi ɗakinsa. Gabanta ya faɗi ta fara tunanin, me ta ce da zai ɓata masa rai har haka?. Haka nan ta ji ba ta fatan abun da zai sake mayar da ita gida yanzu, da sunan zawarci ko ace ta kasa zama, saboda ta san dama mugunta ce ta saka aka aura mata shi. A ranta ta ce 'Zan jure, in sha Allah zan bawa mara ɗa kunya, in sha Allah, Allah ba zai kunyata ni ba, ba zan tagayyara ba" Lokaci-lokaci yake leƙowa falo, sai ya hangota tana aikin stone ɗin ta, tana jin radio a mp. Yana so yayi mata maganar ta je ayi mata allura, amma ya fasa. Bacci ta fara, ji ta tafi ta je ta kwanta, har ta fara bacci aka kawo wuta, hasken lantarki ya hasketa, ba shiri ta tashi, sai a yanzu ta tuna ba ta kashe ƙwayayen ba, ta fita falo dan ta kashe, taga Al'amin ya fito daga ɗakinsa, yana soke wuƙa a ƙugunsa. Ta tsura masa ido tana kallonsa, bai san tana falon ba, yana ɗaga ido, suka yi ido huɗu, ɗaure fuska yayi ya zo zai fice. Ta ce "Master ina zaka je a daren nan, kuma?" Ai ko sake kallonta bai yi ba, ya nufi ƙofar fita. "Dan Allah kar ka je in da za a illataka, zuciyata ba ta yi mini daɗi in ga kana zubar da jini". Bai tsaya ba, sai da ya dangana da tsakar gida, ya kama katanga ya dira, ita kuma ta zauna a wurin ta fashe da kuka mai taɓa zuciya. Ko da ya fita titi, liti ya zo a kan babur ya ɗauke shi, suka tafi. Unguwar shiru, kowa ya shige gida, suka maƙale a wani wuri su na shaye-shaye. Can sai ga wanda suke hari, ya kwararo layin a kan babur, Al'amin ne ya fita da sauri, ya daki tayar gaban babur ɗin, aikuwa ya faɗi ƙasa da shi da babur ɗin. Suka rirriƙe shi, Al'amin ya zagaya dai-dai kunnensa ya ce "Tijjani Faruk ko? Gargaɗi aka ce ayi maka, a kan rubuce-rubucen da ka ke yi a dandalin sa da zumunta, da waɗanda ka ke suka, da Switzerland na so na yi maka warning ɗin, amma a yadda ka ke ɗin nan, zaka iya ɗayewa idan nayi maka da ita, ko iraƙi na saka maka a jiki ba zaka shura ba. Liti, duba bayana, ka ciro Russia ka yi masa rijiya a cinya, ka yi masa eleven da iraƙi a gadon bayansa". Tijjani yana ihu, yana kururuwa, yana komai, liti ya caka masa wuƙa a cinyarsa, ya yage masa riga, ya yanke shi sau biyu a baya, ya watsar da shi a wurin yana kururuwa. Can gida mama tana ta sintiri, har sha biyu saura, ba ta ji an ce Tijjani ya shigo gida ya ɗauki abinci ba, ta din ga kiran lambar wayarsa amma a kashe. Tana ta mita, aka kira baba a waya, aka sanar musu, an tsinto tijjani a hanyar dawowa gida, an yanke shi da makami, an tafi kai shi asibitin cikin gari, sashen bayar da agajin gaggawa. Ɗora hannu ta yi a ka, tana ihu tana ta shiga uku an kashe mata ɗa. Baba ya ce 'Ba cewa aka yi ya mutu ba, an yanke shi aka ce, ƙila masu ƙwacen waya ne ki bari mu je mu gani mana" Ya fita ya kira maƙwabcinsa, ya ce ya raka shi asibiti, domin su ga a halin da Tijjani yake ciki. Ala'amin bayan ya koma gida, a falo ya tarar da jauhar, sauro yayi dandazo a kanta yana cizo, sai ajiyar zuciya take yi ta ci uban kuka. Tsayawa yayi yana kallonta, tare da jinjinawa taurin kanta. Kamar ya tsallaketa ya wuce, ya durƙusa ya kwasheta kamar tsuma ya nufi ɗakinta da ita, yana zuwa ya kwantar da ita a kan gadon, ta buɗe idonta tare da ƙura masa ido. Tsaki yayi ya fita, ta mayar da kanta ta kwantar a kan pillow. Al'amin sawun keke ne, Allah kaɗai ya san in da ya dosa, ɗazu ya gama cewa idan ba zata iya zama ba, ta tafi gida, amma yanzu ya tsinto ta a falo ya kawota ɗaki. Da safe ta dafa tea, ta kawo masa da sauran meatpie ɗin da ya so jiya, yau bai yi rejecting ba ya karɓa ya fara ci. "Master" "Mmmm" "Na iya irin wannan meatpie ɗin fa, idan ka na so ka sayo mini kayan, na iya sosai mai daɗi". Ya ce "To". Da tana jin kunyar cin abu a gabansa, amma zuwa yanzu ta saba, ta gama cin nata, ta je ta kwaso kayansa da suka bushe, tana ninkewa ta saka zare da allura, tana ɗinke masa waɗanda suka yage. Yana kallonta tana yi, shi kuma ya karkace zai kunna sigari. "Master, shan sigari yana cutar da lafiya fa, ka din ga ragewa dan Allah, kar ka yi rashin lafiya". "Kin je an yi miki allurar?" "Zan sha magani, ba na son allura ne tsoro nake ji" Tashi ya yi zaune ya ce "Ƙadangare, kwaɗo yanzu kuma allura, sannu 'yar madara. Sai ki biyani kuɗin allurar da na saya" yayi maganar yana barsawa yana gyara gefen rigarsa. Tayi dariya, jin yau ya kulata, har ya ɗan yi doguwar magana da ita. "To nawa ne, sai na tara da kaɗan-kaɗan na biya ka" yayi shiru yana cigaba da sakin hayaƙi. Ta sake gyara zamanta ta ce "Master Mp nan fa tayi kyau sosai, Allah ya ƙara maka buɗi" Ya jinjina mata kai. Tijjani kuwa ba ma ya hayyacinsa, saboda ya zubar da jini sosai da sosai saran da su Viper suka yi masa, da ƙyar aka samu ya farfaɗo. Cinyarsa sun yi masa rami da ɗan buda, likitoci sai ƙoƙarin ceto ransa yake yi. "Sai oga" "Yaya na ji shiru fa, haryanzu kuna tsare da yarona". "Na sani, trape ɗin muke setting, idan muka yi gaggawa aikinmu zai kwaɓe" "Ok ina saurarenku". Jauhar sai murna take yi, zata je registration makarantar su, dama tun da aka kawota ba ta je unguwar ba. Da safe tana ta shiri, ya fito zai fita ya ajiye mata dubu ɗaya ya ce "Ki hau mota" "Na gode sosai da sosai, Allah ya sa a fi haka, ya ƙara buɗi, ya tsare mini kai" ba shiri ya kalleta, ya ga ba shi take kallo ba, sai jujjuya dubun take yi tana murmushi. "Da ina da wata ba zan kasheta ba, ina son sabon kuɗi sosai" tayi maganar tana ƙara faɗaɗa murmushin ta. "Sai ki ɗinka ta ki saka tun da riga ce" "Kuma zata yi mini kyau fa, adawo lafiya, Allah ya tsareka" Ya amsa da "Amin" Jauhar ta ƙarasa shirinta, ta tafi makaranta, kamar yadda Baba ya ce mata ta je tayi registration, a nan ta haɗu da 'yan makarantar su, ta din ga murna sun haɗu da 'yan makarantar su, da malaman makarantar ma. Ta din ga yi wa ƙawayenta mitar ba su je gidanta ba. "Jauhar wa zai zo gidanki kina auren ɗan daba? Ba ma za a bar mu mu zo ba" Jauhar ta yi murmushi ta ce "Ku daina fakewa da haka, ni da muke tare, ya aka yi bai yi mini komai ba?" "A'a ai ke matarsa ce, mu kuwa fa" Duk da ba ta gaya masa ba, haka kawai ta ji tana son ta je gida. Ganin ko ta fita ba hanata yake yi ba, ya sanya ta nufi hanyar gida. Gaba ɗaya sun yi mamakin ganinta, Anty ta ce "Yaya, ya na ganki yanzu meyafaru?" Jauhar ta yi murmushi ta ce "Lafiya lau anty, registration na zo na ce bari na biyo, tun da kun ƙi zuwa". Kallon jauhar suke yi, su ga ko akwai wani abu na tashin hankali a tare da ita, ko alamar duka ko makamancin haka, amma ba su gani ba, sai ma wata nutsuwa ta mussaman da suka gani a tare da ita. Mama ta ce 'm"Jauhar kin kyauta, wato miji daɗi, ki ka kasa zuwa ki duba ɗan uwanki, ya kusa mutuwa" Cikin tashin hankali jauhar ta ce "Subhanallah, mama ban sani ba ba shi da lafiya ne?" "Ina fa, ya dawo daga aiki, aka samu wasu suka sassare shi". Abun ya ɗagawa jauhar hankali, ta ce musu ba ta sani ba. Al'amin yana can wurin su Walid, kansa yana yi masa ciwo, ga yana jin yanayin jikinsa kamar zazzaɓi yana son kama shi. Yana jin wayarsa na ta vibrating yayi banza. "Viper wayarka fa ta cika mini kunne, dan Allah ka ɗaga" "Ƙyale ni, kamar zazzaɓi ne zai kama ni" "To ka kashe wayar mana". "Ba zan kashe ba" "Ka duba mana ko beb ɗin ka ce take nemanka, yarinyar nan ta na kula mana da kai yasin". Viper yayi tsaki, ya sake gyara kwanciyar sa. Walid ya miƙa hannu, ya ɗauki wayar ya ɗaga ya ce "Ya aka yi?" "Ka gaya wa uban gidanka, na ga cikarsa ta shigo mana arear, duk da kashedin da na yi kar ta sake zuwa, tun da ya kwasheta. Yayi ganganci mafi girma da muni, tun tun da ya bari ta shigo, ya zo ya ɗauki gawarta a dabata!. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Walid ya kalli Al'amin, ya lumshe idanunsa, wasu irin jijiyoyi suka fito raɗa-raɗa a goshinsa. Yayi shiru ya ƙi ko motsawa. "Mai zamani, ba ka ji me ya ce ba ne, matarka fa yake maganar ka je ka ɗauki gawarta" "Na aiketa ne?" "Ban gane ka aiketa ba? Kai kut....." Ya ɗura masa ashar. "Idan da gaske ya kasheta fa?" Al'amin ya tashi zaune, ya ɗauki wayarsa, ya danna ya kira wata lamba. "Yeah maza" Ya ce "Ina aikin da na saku?" "Ai ta gama ta tafi ma" Ya ce "Ba tafiya a ta yi ba, gidansu ta tafi, ba ka kira ni ka gaya mini ba. Wancan garan ya ce in je in ɗauki gawarta a dabarsa, wallahi ya kashe 'yar mutane sai na kasheka kai ma" "Haba maza, cewa ka yi mu saka ido, ta shiga ta gama abun da take yi ta tafi, kuma min bi ta ba ta sani ba, ta gama ta tafi ba ka ce mu bi ta mu ga ina zata tafi ba" "Wallahi liti ka bari muka haɗu sai na saka maka ƙarfe, ka ji na rantse. Ya ajjye wayar ya yinƙura, Walid ya ce "Ina zaka je, ka ce ba ka jin daɗi, ka zauna bari ni na je" "In zauna sai ya kasheta, sannan zan je?" Yayi maganar a zafafe. Walid ya bi shi da kallo, yana son gano haƙiƙanin in da ya dosa, amma bai gane ba,  Al'amin ya sake birkicewa ya ce "Ya kasheta ko ya bar ta da rai, ba shi ne a gabana ba, tun da ba ni na gayyato ta rayuwata ba, abu mafi muni shi ne ace madaki ya kuma yi mini illa, idan haka ta kasance, kan mai uwa da wabi, zan ɗauki matakin da ya dace". Ya fita da sauri, Walid ya bi bayansa, bai ma san ina ne gidan na su ba, sai da walid ya yi masa jagora, yaran madaki suna ganin Al'amin ya shigo musu unguwa da rana tsaka, amma aka rasa mai tunkararsa, dan ba su fiye galaba a kansa ba, sai sun yi masa taron dangi. Suna tafe a hanya, liti ya kira Walid ya ce masa "Ka ce ya kwantar da hankalinsa, na yi waya tana lafiya tana cikin gidan su, zamu fito da ita lafiya in sha Allah" Walid yana gaya wa Viper, ya ce "Ka ce masa bana so" ya yi maganar yana ƙara sauri. Jauhar kuwa na can, har ta ɗora musu girki, sai zungurarta suke yi, su ji a wani hali take ciki a gidanta, da irin zaman da take yi da Al'amin, amma ta dinga waskewa, taƙi gaya musu komai. Hafsa har da tambayarta, wai wuri ɗaya suke kwana?. Jauhar ta kwashe da dariya ta ce "To zai kwana a waje ne yana da mata?". Surayya ta ce "Iyee zama da maɗaukin kanwa, wato har bakinki ma ya buɗe haka?" Jauhar ta yi dariya ta ce "Kai Anty surayya tambayata fa tayi, bari na ƙarasa na je gida ma na yi girki, kar ya dawo". A tunaninsu za su ga jauhar cikin mawuyacin hali, amma sam ba su ga alamar hakan ba. Ta shiga suka gaisa da anty lubabatu,ta din ga murna yadda ta ga jauhar, babu alamar wahala a tare da ita, ta aika 'ya'yan anty lubabatu su je gidan kakannin su, su karɓo mata shirin dutse a wurin ƙanwar anty lubabatu. Da yake duk a unguwar ne. Anty lubabtu har da harhaɗawa jauhar 'yan kayan gyaran aure na mata, ita dai ba ta ce komai ba, ta karɓa ta ce ta gode. Da ta fito daga gidan, ta lura da wasu matasa da ba ta san suwaye ba, a layin amma ba ta damu ba ta shige gida. Walida ta tare ta ta ce "Me Anty lubabatun ta baki?" Suka karɓi ledar hannunta, suka ga kayan mata da turarukan wuta da humra masu kyau da ƙamshi. Suka din ga yi mata dariya cikin izgilanci surayya ta ce  "Wai nan ba ki yadda ba ke matar aure ko jauhar? Dan Allah ya ki ke yi ke kuwa da shi, ga 'yan shaye-shaye da ƙazanta, kuma har kiss ku ke yi?" Jauhar ta yi wani irin murmushi ta ce "Yaya surayya kenan" "Gaya mana man" "To ni me zan ce? Annabi ya hana faɗa, sirrinmu ne ai" Surayya ta ce "Lallai, yau na ga illar ƙani ya rigaka aure, ni ki ke gaya wa baƙar magana jauhar? "A'a ki yi haƙuri, ba baƙar magana ba ce" Ta karɓe kayanta, ta saka a jakarta, ta cigaba da aikinta. Ta zauna tana yanka salak, sai mita take yi ba ta haɗu da yaya saifu ba, kuma baba ma baya nan" Tijjani ya fito yana ɗan tattakawa, ta din ga yi masa sannu. Tun da ya shigo layin yake ganin yaran madaki tsilla-tsilla, alla-alla yake yi ya ƙarasa ya tabattar da abun da madaki ya faɗa gaske ne ko akasin haka, idan gaske ne bai san iya adadin haukan da zai yi masa ba. Walid ya ce "Ga gidan nan" dai-dai lokacin ɗan gidan anty lubabatu ya zo zai shiga gidan su jauhar, hannunsa riƙe da ledar viva, an zubo mata dutsen shiri da kayan yi kala-kala, babar anty lubabatu ta ce a bata kyauta a matsayin jari, shi ne gudunmawarta na biki. "Kai shiga nan gidan ka ce.... Sai kuma ya yi shiru dan ya manta sunanta, sai Fatima yake iya tunawa. Walid ya ce "Ka faɗa masa sunan" Tsaki yayi ya ce "Na manta sunan, sunan wani iri ne dai haka kamar Angela" Walid ya ce "Amma kuwa ka yi asara" Al'amin ya ce "Ka ce 'yar madara ta zo in ji Master" Walid na son yin magana, ya maze ya ce "Na san ƙarya fa madaki dama yake yi bai kasheta ba". Yaron ya shiga ya fara ba ta saƙon hajiya kakarsa, na bata kyautar dutse, ta karɓa tana murna da godiya, sannan ya ce "Wani a waje ya ce wai 'yar madara ta zo" take gaban Jauhar ya faɗi. Walida ta ce "Wace wata 'yar madara, babu ita a gidan nan, in ji wa ya ce maka?" Yaron ya ce "Wai in ji Master " Jauhar ta ce "Na shiga uku, master ne, ban gaya masa zan zo nan ba, waye ya gaya masa?". Ta ce "Bari na ɗaukko jakata" Anty ta fito ta ce "wannan aikin kuma wa zai ƙarasa shi? Ai sai yayi haƙuri ta gama, kai je ka ka ce masa aiki take yi, ya dawo an jima" Buɗe baki jauhar ta yi ta ce "A'a anty kar ya gaya masa haka, kaga haidar ka ce masa... Anty ta katse ta ta ce "Fita ka je ka gaya masa haka, waye shi ba gidan sirikansa ba ne ba". Gaban Jauhar ya tsananta faɗuwa, ba ta san me hakan ka iya haifarwa ba. Mama ma fitowa ta yi ta ce "Ba zaki zauna ki cigaba da aikin ba" Viper kuwa wani marurun takaici ne ya ƙule masa a wuya, jin irin saƙon da aka aiko masa da shi, kamar shi za a aikowa da wannan banzar maganar. kawai ya sai kai zai shiga gidan, walid ya riƙe shi ya ce "Mai zamani gidan sirikanka ne fa, dan Allah kar yi wani abu mara daɗi, ka zubar mata da mutunci" "Tun da suka zaɓi su aura mini ita, sai na tabattar musu da maganata ce gaba da ta su a yanzu" kawai ya saka kai cikin gidan. Cak ta tsaya, jikinta yana tsuma, ganinsa ya shigo yana wannan takun nasa, ya ƙureta da ido, tun kafin ya ƙaraso. Tsit suka yi suna kallon ikon Allah, ya ƙaraso, ta wutsiyar ido ya kalli yaya tijjani da ke zaune a kan farar kujera, ya sauke idonsa a kan mama, su surayya sannan Anty Zakiyya ta ƙarshe. Yana ganinta ya ƙara tabattar da Rahila ce ta saka aka yi masa aure, bai ga alamar akwai mahaifiyar jauhar a cikin su ba. Ya kalli Jauhar ya ce "Ni na aiko ki zo ki ka ce mini ba zaki zo ba?" Ta ce "Dan Allah Master ka yi haƙuri" "Shut up!" Yayi maganar cikin ƙaraji, tare da ball da bokitin da aka kawo markaɗe, da kwanon salak ɗin duk suka tarwatse a wurin, ta zabura ta ƙanƙame jikinta. Ai ba ita ba, har sauran matan gidan da 'yan matan. Tijjani kuwa ɗimaucewa yayi, dan kuwa ba zai manta muryar nan ba, duk da yana tantama amma kamar muryar wanda suka yi ma aika-aika. "Dama mun yi da ke zaki zo nan? Kin zata ƙarya suke yi da suka ce za su saraki idan suka kuma ganinki a unguwar nan?" Ɗago ido ta yi cikin tsoro tana kallonsa. Ganin yadda duk ta rikice ya sanya ya saki muryarsa ya ce "Zo ki wuce mu tafi" Ta ce "Bari na ɗakko hijjabina" Mayar da idonsa yayi kan Anty Zakiyya, ko ƙiftawa ba ya yi, babu shiri ta juya da sauri ta shige ɗaki. Jauhar ta fito, da jakarta da ledojinta, ya danƙi hannunta, suka yi waje. Suna fita Surayya ta ce "Bala'i dama wannan ne mai dogon zamanin? Jaraba jauhara na cikin bala'i". Hafsa ta ce "Ni kuma abun da na gani daban, kut wallahi na ɗauka zan ga wani gardin mummuna, ji mutum hanci har baka, kai amma yayi kalar tsoro da yawa, haka yake yi mata wannan tijara" Mama ta ce "Dalla ku yi mana shiru, kalli asarar da ya yi mana, abincin ranarmu ya mayar da mu baya" mama tayi maganar a ƙule. "To mama aikin gama ai ya riga ya gama, ni wallahi na zata dukanta zai yi ma. Anty har an gudu ɗaki, bayan ita ta bayar da saƙon da aka gaya masa" Daga ɗaki ta ce "Haka kurum in tsaya ya kasheni a banza, kin ga wani huci da yake yi kamar kumurci, gashi sai kallona yake yi, ya ƙara girma fiye da yadda na san shi". Jauhar kuwa suna fita, walid ya rufa musu baya, Viper ya din ga jan ta, gashi saurinsa ya ninka nata, kamar ta hantsila, Alla-Alla yake yi su ƙarasa titi ya saka ta a abun hawa, sai dai suka yi karo da madaki da yaransa. Wata irin muguwar dariya madaki yayi, wadda ta ƙara fito da ainihin muninsa, baƙi ne wuluk kuma gabjeje, yana da jajayen idanuwa, wanda yake rambaɗa musu farin kwalli, ga wani ƙaton sara a fuskarsa a kaikaice da ya raba fuskar in to two equal parts. Sai ta ga Al'amin ɗin ta nutsatstse ne mai kyan gani, a kan madaki, ta san gidansu ta san sunansa a unguwar su, amma ba ta sanshi a fuska ba. Jikinta ya hau tsuma, Al'amin ya sakata a bayansa, ya tsaya yana fuskantar madaki, Walid ya tsaya a gefensa. "Tun da aka gaya mini matarka ta shigo unguwar nan, na ce bari in auna adadin son da ka ke yi mata. Ka san bikin ma bana nan aka yi, labari na samu ban haɗu da kai na yi maka Allah ya sanya alkhairi ba. Ƙarfin halinka ya kai, tun da ka iya ratso cikin unguwarmu ka auri 'ya. Shiyasa na so ka zama ɗaya daga yarana tun a wancan lokacin amma ka ƙi. Ya leƙa ya kalli fuskar jauhar ya ce "Ashe 'yar gidan Alhaji faruku ce, rabona da ita tun tana 'yar mitsitsiya, ashe haka ta girma ta ƙara kyau, ka bani kunya ma, wannan ai ba ta wani gama nuna ba, wannan ai ka yi mata girma, kodayeke ba a nan take ba an danne bodari ta ka, bakinta mai kyau ɗan ƙarami zai yi daɗin sha, anya wannan ba.... Wani wawan mari Al'amin ya ɗauke madaki da shi yana huci, Walid ya riƙe shi ya ce "Viper ka san me ka yi kuwa?" Al'amin ya hankaɗe shi, ya kalli madaki cikin ido ya ce "Ka daɗe da kashe Al'amin ɗin da ka raina, ka mayar abun nishaɗinka, Kar ka sake ka shiga shingena, duk wala-walar da zaka yi, kar ka ƙetare iyaka". Yaran madaki suka yinƙuro, Madaki ya ɗaga musu hannu, ya ciro wata muguwar wuƙa a jikinsa, ya ce "Bari in nu na wa duniya kai rago ne, a gaban matar taka, da ka yi dan ka burgeta" Wani irin ihu jauhar ta ƙwala, ta rirriƙe Al'amin tana kuka ta ce "Dan Allah kar ka caka masa, zaka kashe shi idan ka caka masa, dan Allah ka yi haƙuri kar ka kashe shi". Viper ya ce "Kafin ɗayanmu ya bar duniya, za a ga waye ragon, ƙazamin kare kawai" Ya sake danƙar hannun jauhar, ya keta ta tsakanin yaran madaki yayi gaba, walid kuma ya tsaya a kan hanyar yana kallonsu, dan kar wani ya bi bayansu ya illata su. Madaki ya bi bayansu da kallo, ya din ga kallon wuƙar hannunsa yana murmushi, lallai yayi sake ɗan zaki ya girma, ya fara zama barazana a gare shi. Babban abun da ya ƙular da Al'amin, bai wuce yadda jauhar take ta rusa masa uban kuka ba a cikin a daidaita sahu, bayan koma menene ita ya janyo, kamar ya cillata kan titi ya huce, yana zaman zamansa an ƙaƙaba masa ita, yanzu dole duk in da zai yi sai yana tunanin kar a cutar da ita. Bai kulata ba har suka je gida,ga wani irin ciwo da kansa yake yi, ga zazzaɓi tun a hanya ya rufe shi. Suna zuwa gida, ya wuce ɗakinsa ya bar ta. Bin bayansa ta yi, cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah Master ka yi haƙuri, ban san haka za ta faru ba, nayi niyyar gaya maka dama idan na dawo, dan Allah ka yi haƙuri" Banza yayi mata, ya rufe idanunsa, saboda yadda sanyi yake ratsa shi, ga wani abu mai ɗaci da ya tsaya masa, ya ƙi wucewa, saboda yadda abubuwan da suka wakana a rayuwar sa, suke dawo masa cikin kansa a yanzu. Idan ya tuna abun da madaki ya faɗa a kanta, sai ya ji kamar ya kurma ihu, ya gama cutarsa, ko shi jai tsaya ya ƙare mata kallo, ya ga bakin nata ba sai shi. A marairaice ta ce "Master, Yaya Al'amin dan Allah ka yi mini magana, ka yi haƙuri ka yafe mini dan Allah, na san koma menene ni ce sila". "Get out from sight, ki tashi ki fita kafin ni na sassaraki a wurin nan" a tsorace ta tashi ta fita, tana waiwayen sa. Tana fita ya riƙe kansa, saboda yadda ya yi masa nauyi. Anty Zakiyya kuwa, Rahila ta kira a waya, bayan sun gaisa ta ce 'Ƙawata yau na ga tsiya da wasali" "Bani na sha meyafaru?" "Yau ɗanki ya zo gidan nan ai" "Wa kenan" "Sirikinmu mana, wai ashe yaran madaki ɗan dabar nan na unguwarmu sun ce idan ta sake zuwa unguwar nan, sai sun sassarata, ta zo gidan nan bai sani ba, a sukwane ya taho, yau mun ga bala'i, kin ga tijarar da ya yi ya ja hannunta suka tafi?" Rahila ta ce "Zai aikata fiye da haka ma, in dai Aminu ne ɗan banzan bawa kenan ake gaya miki" "Taɓ amma anya ba son yarinyar nan yake yi ba? Kin ga a yadda ya zo kuwa?". "To ke ina ruwanki, dama dai ba burinki ita wannan ta bar miki gida ba, shi ya sani ba mace ba ce ba? Luf zai yi ai, ni fa tun da aka yi auren ba mu sa shi a idonmu ba, na ce can ya ƙarata" Suka kwashe da dariya, Zakiyya ta ce "Taɓ amma ƙato ne, sai ka ce ɗan dambe, kuma wallahi ba wani abun gyara da muka yi mata, yau ne ma da ta zo maƙwabciyarmu ta bata, amma haka nan muka kaita" "Oho musu, in dai buƙata ta biya, ba shikenan ba, su ƙarata" Suka kwashe da dariya gaba ɗaya. Jauhar ta kasa zaune ta kasa tsaye, master ya ɗau fushi da ita, gashi ya ƙi fitowa, kuma ya korota daga ɗakinsa. Da canjin hannunta, ta haɗa ta sayo fulawa, ta kwaɓa alkubus, da wata irin miya ya 'yan dabaru, sai dai har ta yi ta gama bai fito ba. Sai ta kasa ci, ta sake lallaɓawa ta leƙa ɗakinsa, ta ga yana banɗaki, ta cigaba da tsayuwa ya fito, ta tsaya tana sallama a bakin ƙofa. "Idan ki ka bari na zo na sameki a wurin nan, sai na ɓata miki rai" Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri master, na tuba ba zan sake ba" Kwanciya ya sake yi, ya juyawa ƙofar baya. "To in kawo maka abinci?" Kamar ya ce eh, amma yayi mata shiru. Abun da ya ɗaure mata kai, bai wuce har dare kwanciya yake yi ba, yaƙi fitowa, cikin tsananin fargaba ta shiga da kwanukan abinci ta ajiye masa. Ƙamshin miyar da ya cika masa hanci, ya sanya ya buɗe idonsa. Gwiwoyinta ta saka a ƙasa ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ni ko wani hukuncin ka yi mini dan Allah ka daina yin fushi da ni, bana son na ga na yi laifi dan Allah" hawayenta ne yake ɗiga a kan katifarsa, ya gyara kwanciyar sa ya juya mata baya. Ya tsani kuka, ba ta san ƙara ƙular da shi take yi ba. Tashi ta yi ta sake zagayawa kamar mayya, tana yi masa magiya. Ya buɗe jajayen idanunsa yana kallonta, sai dai yaƙi magana. Yarrrr haka ta ji tsigar jikinta tana tashi, ba ta san kallon ma yake yi mata ba. "Ka yi magana Please, ka ce ka haƙura" tayi maganar tana jan majina. Ƙafarsa ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana kaɗawa, saboda ciwon da kansa yake yi, amma a zahiri abun da yake yin, kamar yana yi ne da gayya da nuna mata iko da izza irin ta ɗa namiji. "Kin cika mini kunne" yayi maganar a hankali, duk da buɗɗaɗiyar murya ce da shi irin ta jaruman maza. "To ka ce ka haƙura mana" tayi maganar cikin shagwaɓar da ba ta san ta yi ba. "Kai mini ruwa zan yi wanka" cikin sauri ta ce "To" Tunani yake yi daban-daban a ransa, ya ma rasa wanne zai yi, yana shiga wankan, ta sake gyara shimfiɗar katifarsa, ya yi wanka ya fito yanzu ma jikinsa babu riga, yana ƙoƙarin mayar da kayan da ya cire, da sauri ta ce "Ai kana da wankakkun kaya, na wanke maka ka saka wannan" ta yi maganar tana miƙo masa kayan da ta ciro masa. "Ɓace zan canza kaya" ta fita da sauri,mintuna goma da ta dawo, tuni ya kusa rabin abincinsa. Garin ta miƙa hannu ta ɗauki jug ta zuba masa ruwa, hannunta ya taɓa ƙafarsa ta ji zafi sosai, ta kalleshi ta sake kai hannunta ƙafarsa. "Master zazzaɓi ka ke yi?" Lomarsa ya cigaba da yi, cikin tsoro ta sake kai bayan hannunta ta taɓa hannunsa. "Na shiga uku ba ka da lafiya ai, duk ni na janyo ko?" Ya karɓi jug ɗin hannunta, ya cire murfin, ya kafa kai ya sha fiye da rabin ruwan, sai ka ce tsohon raƙumi. Ya gama ya jingina da jikin bango ya sake lumshe ido. "Master, akwai allurar nan da ka sayo mini ba ayi mini ba, mu je in raka ka ayi maka to" Gyatsa ya saki, maimakon ya yi hamdala, sai ita ta ce "Alhamdilillahilazi aɗa'amana haza, Ubangiji Allah ya ciyar da mu kullum, ya bawa wanda bai samu ba" "Amin" ya faɗa ƙasa-ƙasa zai kwanta, a sukwane ta ce "Dan Allah kar ka kwanta, mu je a duba ka, kar ka sha wahala, sauro ne yayi yawa a unguwar nan shiyasa muke ta zazzaɓi, dan Allah ka zo mu je a duba ka" "Kai wallahi kina addaba mini, kin dame ni" Jauhar ta kwantar da murya cikin sigar rarrashi ta ce "To na sani, amma ka yi haƙuri, na daina, dan Allah mu je a dubaka ka ji Mijin 'yar madara, ba ka ji yadda jikinka yayi zafi ba?" Ya kalli yadda ta dafe kafaɗarsa, tayi saurin sakinsa, ya ce "Sai an yi sallar magariba" "To mu koma falo, sai na saka maka maganin sauro a ɗakin, idan ka cigaba da kwanciyar jikinka mutuwa zai yi" Da ƙyar ta lallaɓo shi, suka dawo falo, ta kunna maganin sauro. Ana idar da sallar magariba, ta ɗaukko allurar, ta ce su tafi, ya ce ya fasa zuwa, shi ba zai iya tafiya ba. Da ƙyar sai ka ce ɗan goye, ta lallaɓa shi suka fita. Ta rufe ƙofar gidan, ta riƙe hannunsa ta ce "To mu je, kar ka ji jiri idan ka gaji ka yi mini magana sai mu tsaya ka huta". Kallonta kawai yake yi, ɗan hannun nata ɗan mitsitsi a cikin nasa. Suna tafe tana ƙara ba shi haƙuri, a kan laifin da ta yi. Nasiru mai chemist na ganinsu ya ce "A'a jauhar, kin warware shi ne shi ma ya kwanta" tayi murmushi ta ce "Allura na kawo shi, ayi masa mai sanyi dan Allah" Da jauhar ta san yadda yake ji a zuciyarsa idan ya ga tana tankawa mai chemist da ba ta yi ba, sai dai bai san dalilin hakan ba, kawai ba ya son ya ga wani yana kulata. Aka gama yi masa suka fito za su tafi, ta tsaya tambayar mai ɗanyen dankali nawa kwano. Al'amin ya zaro kuɗin ya bayar, suna tafe tana godiyar dankali. Da safe ta soya musu dankali da tea, ya gama karyawa, ya kalleta ya ce "Wannan matar da na gani a gidanku wacece?" Ta ce "Wacce?" "Mai baƙaƙen kayan nan" "Anty zakiyya ce, matar Baba ce" ya jinjina kai bai sake cewa komai ba. "Ka santa ne?" Yayi shiru bai amsa ba, daga haka ta ja bakinta tayi shiru. Babu yadda ba ta yi ba, a kan ya je a ƙarasa allurar nan, amma ya ƙi. Da ya ji ƙwarin jikinsa ma, fita ya cigaba da yi. Jauhar na zaune a falonta, tana tunanin ƙirƙirar sabbin styles na abun hannu da jigida, ta fara sayarwa. Aka bubbuga mata gate, ta tashi ta je ta buɗe, ta ga wani mutum da ba ta san shi ba, fuskarsa sanye da facemask ya ce "Mai zamani yana nan?" Ta girgiza kai ta ce "Ya fita" "Ga wannan ki ajiye masa". Ya bata leda mai baƙi da fari. Ta karɓa ta ce "In ji wa zan ce?". "Idan ya zo zai gane, ki ajiye masa a ɗakinsa, zan kira shi" Ta ce "To shikenan" Ta rufe ƙofa, kamar ta buɗe, sai ta fasa ta kai masa cikin drower sa, ta ajiye masa ta cigaba da sabgoginta. Kayan da anty lubabatu ta bata ta ɗauka tana duddubawa, ta ɗan ɗanɗana abun, tayi shiru tana tunani, ita sam abun da ake faɗa a auren, ba ta ga alamar sa ba, dan shi ba ta tata ma yake yi ba, ya ƙule a ɗakinsa yayi shaye-shayensa ya ci abinci ya fita yawonsa shi ne kawai a gabansa. Ta ɗan taɓe baki, ta ɗauki turaren wutar, ta tirara na gidan, ta turara na jikinta, ta ɗora girki. Da daddare da wuri ya dawo gida, gidan sai ƙamshi yake yi na musamman, giftawar farko da tayi, sai da ya ɗaga kai ya kalleta, ƙamshin har cikin ƙwaƙwalwarsa ya ji shi. Yau  faten dankalin ta yi, dan shi ne kawai da su, sai dai yayi masa daɗi bai taɓa sanin ana faten dankalin hausa ba, sai yau da ta bashi, har mamakin yadda take sarrafa abinci yake yi. Ya gama cin abincin ta ce "Master yanzu allurar nan dai ba za a ƙarasa ba ko?" "Eh" ya faɗa kai tsaye. "Ai shikenan, thank God tun da ka warke ai. Ka yi mini addu'a mun kusa fara WAEC, Allah ya sa result ɗina yayi kyau". "Sai ki yi karatu" "Ina yi ai" ya kalleta ya ce "A hakan, kina shirme dai" ta gane da kayan beat ɗin ta da stone yake, tayi murmushi jin yadda yau yake yi mata doguwar magana. "Ina karatu sosai da sosai fa". "Akwai kwaɗo a ƙarƙashin kujerar nan da ki ke" da sauri ta kalli kujerar, sai kuma ta yi dariya ta ce "Ai na daina jin tsoron" wai nan tsokanarta yake yi, amma fuskar nan a haɗe. Har wajen ƙarfe goma suna tare, yana ta danna wayarsa, mai madannai, ita kuma tana jin radio tana aikinta, ba hira suke yi ba, amma kasancewar su a hakan ma, daɗi take yi mata. Ya yi miƙa ya tashi zai tafi ɗaki ta ce "Tafiya babu sallama" Ba tare da ya yi Magana ba, ya ɗaga mata hannu, murmushi ta yi ta ce "Asuba ta gari mijin Angela" ɗan rausayar da kai ya yi kamar zai yi murmushi ya shiga ɗakinsa. Ya kwanta yana shaƙar ƙamshin da bedsheet ɗin sa yake yi, bai taɓa tunanin zai yi aure ba, dan babu wannan lissafin a gabansa, ba dan albarkacin auren ba, da a cikin tsummokara zai kwana a can gidan da suke tare da su Walid. Tsakar dare jauhar ta ji motsi, kamar ana watsi da kaya. "Malam kar ka shiga wannan ɗakin ba komai a ciki, mata ta ce a ciki, kuma babu in da shari'a ta baka damar shiga in da matata take" Jin muryar Al'amin, ya sanya ta saukko daga kan gadon da sauri, wata irin dalleliyar fitila aka saka ana haske gidan. "Shut up, kar ka sake magana, kar na sake jin bakinka" Cikin ƙaraji ya ce "Sai na yi magana, wallahi ka shiga ɗakin nan, zan illataka". Da gudu ta fito dan ta ga meyake faruwa, ma'aikata ta gani, har da jami'an tsaro, sun saka wa Al'amin ankwa sun durƙusar da shi a kan gwiwoyinsa. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Yallaɓai me yayi muku? Laifin me ya yi?" "Ki koma ɗaki Ki nemi hijjabi ki saka" yayi maganar cike da takaici. "Oya ku yi searching ko ina a gidan nan, kar ki motsa daga in da ki ke" Wani jami'in ne ya fito daga ɗakin Al'amin, da wannan ledar da aka kawo aka ce a ajiye masa, ya ce 'Ga abun da muka samu sir" Shugaban operation ɗin ya karɓa, ya zazzage sai ga ƙwayoyi, da allurai da wiwi da sauran tarkace sai kuma wata 'yar leda mai ɗauke da wani farin gari. Ya ce "Good, mu tafi da shi mun samu abar" "Yallaɓai, wallahi wani ne ya kawo su ɗazu, ba shi ya kawo su ba, dan Allah kar ku tafi da shi.  Ko kallonta ba su yi ba, suka tasa ƙeyar Al'amin. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Biyo bayansu tayi, tana wani irin kuka mai ban tausayi, tana yi musu magiyar su sake shi, ba shi da laifi, amma babu wanda ya saurareta a cikinsu. Maƙwabta na jiyo kukanta, amma babu wanda ya iya ko leƙowa ya ga abun da yake faruwa. Shi kuwa Al'amin ko a jikinsa, kukan da take yi ne kawai ba ya so. Suka saka shi a mota, ta ce "To Yallaɓai ina za ku kai shi dan Allah" "NDLEA, daga nan zamu miƙawa 'yan sanda shi, su kai shi gaban kotu". "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu dai sai kun kai shi NDLEA ɗin kenan? Wancan karon baku kai shi ba sai yanzu, dan Allah ku duba lamarin nan" Suka saka Al'amin a mota, suka tafi da shi, a falonta ta zauna, ta fashe da kuka, ta daɗe a wurin tana kuka, ganin hakan ba mafita bane, ya sanya ta tashi ta ɗauro alwala ta koma ɗakinta, tayi ta sallar da ba ta da tabbacin tana karanta ayoyin daidai saboda tashin hankali, ta ɗaga hannu tayi addu'a, amma ta kasa kawai ta mayar da kanta sujuda ta fashe da kuka. Har asuba ta yi idonta biyu, ta yi sallar asuba ta idar, ta zauna tana karanta duk abun da ya zo bakinta, wani abu mai nauyi ya tokare mata ƙirji, ta ji tamkar numfashinta zai ɗauke gaba ɗaya. Bayan sallar asuba magidantan layin suka tsaya suna salallamin, jiya da daddare ma'aikatan sun shigo layin, amma babu wanda ya fito. Malam lawan ya ce "Har kwa tambayi lafiya? Ai tun da ɗan daba ya tare muku a unguwa, sai abun da Allah ya yi, wurinsa suka zo, wataƙila ma wata ta'asar ya je ya tafka, suka zo suka yi masa ɗaukar amarya tsakar dare". Suka yi ta salallami da fatan Allah ya kyauta. Har rana ta yi haske, jauhar tana zaune a wuri ɗaya, idanun ta sun yi ja, duk sun kumbura fuskarta tayi ja ta kumbura saboda kuka. Maman halimatu da wata mata mai kallon gidan na jauhar suka shigo, sai da suka yi ta sallama, da ƙyar ta iya amsawa sam ba ta ji sallamar ta su ba ma, ta fito falo ta ce su shigo. Maman halimatu ta ce "Jauhar, lafiya kuwa? Wai meyafaru ne jiya mun ji hayaniya, babu damar mu fito. Take wasu hawayen suka ziraro mata ta goge su ta ce "Jami'an tsaro ne suka  zo suka tafi da shi" "Subhanallah, laifin me yayi?" Ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba" "To ki yi haƙuri, ki samu ki ci abinci,  sai ki nutsu a san abun yi, Allah ya kyauta ya kiyaye gaba" Ta amsa musu da to ta gode. Kai ka ce takaba take yi, duk ta fita hayyacinta, ba ta san wurin wa za ta nufa da maganar nan ba, kuma ba ta san ina hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyin take ba ma, balle ta je, ba kuma ta san ta tambaya a gano wani abun, gashi ko gidan su Al'amin ɗin ma ba ta sani ba, balle ta je ta gaya musu, ko da wani abu da za ayi a kai. Ta dudduba ta tattara ɗan kuɗin da take da shi, ta fita, ta samu mai napep ta tambaye shi idan ya san ina ne hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi. Ya ce mata ya sani, ya ɗauke ta ya tafi da ita. Ta din ga yawo a cikin hukumar, aka ce mata ba ya wurin, ba a kai shi ba, sai da ƙyar aka ce mata yana nan, amma ba zata ganshi ba, babu irin magiyar da ba ta yi ba, amma suka hanata ganinsa, ƙarshe sai gida ta koma a matuƙar galabaice. Ta rama salollin da suke kanta, ta din ga addu'a da fatan Ubangiji Allah ya fitar da shi lafiya, da ta san abun da zai faru kenan, da ba ta karɓi abun da ba ta san ko menene ba ta ajiye masa. Ɗaya maƙwabciyar ta ta wasila, wadda mijinta ya taɓa raka su wurin mai chemist ta shigo gidan. Ta ce "Jauhar yaya ake ciki, kin same shi kuwa, kin je wurin 'yan sandan?" Ta ce "Eh na je, ba su bari na ganshi ba" "Kuma ba su gaya miki abun da yayi suka kama shi ba?" Ta jinjina mata kai alamar eh, wasu hawaye masu ciwo suna zubo mata. "Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki jauhar, in sha Allah komai zai wuce kamar ba ayi ba, kuma in sha Allah zai fito" Ta ce "To Allah ya sa". Yau ma haka ta kwana salloli, da kai wa Allah kukanta, da fatan Allah ya saka mijinta yana lafiya ya kuɓutar da shi. Da safe ta sai ƙosai da buredi, ta dafa tea, ta kuma wanke ƙafa ta koma wurin nan, amma suka sake ce mata ba za ta ganshi ba, tayi magiyar har ta gaji, ta basu abincin ta ce su bashi. Ta koma harabar wurin, ta nemi wuri ta zauna, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, rabonta da abinci tun a jiya, gaba ɗaya tunanin halin da Al'amin yake ciki, da wanda zai shiga a nan gaba ya dame ta, ta gaji da zama ta tashi ta nufi gida. Ɗakinsa da suka shiga duk suka watsar da kaya ta shiga, dan damuwa ba ta bari ta shiga ta gyara ba. Duk sun watsar da komai na ɗakin, ta tattare masa kayan, tana cikin gyarawa ta gano wayarsa, ta ɗauka tana duddubawa sai ta ga tarin kiran walid da liti, cikin hanzari ta kira lambar walid. "Ya ne maza? Tun shekaranjiya ban sake jin ɗuriyarka ba, na zo gidanka ba kowa ka kuma ƙi ɗaga waya". "Assalamu alaikum" tayi masa sallama. Ya ce "Ahh madam ke ce ashe? Ya ake ciki yana ina?" Muryarta na rawa ta ce "Shekaranjiya da daddare jami'an tsaro sun zo sun tafi da shi" "Kamar yaya? Me yayi?". "Abu aka kawo aka ce na ajiye masa, su kuma suka zo da daddare suka ga kayan a leda, suka tafi da shi na je sun hanani ganinsa" tayi maganar cikin kuka. Walid ya ce "Ya isa haka yi shiru, bari na zo gidan gani nan" Sai ta ɗan ji sanyi a ranta, tamkar yana zuwa zai fito mata da Al'amin ɗin. Kusan awa ɗaya da rabi, ta ji ana knocking gate. Da sauri ta tashi ta je ta buɗe, liti ta gani da Walid, har ƙasa ta durƙusa ta gaishe su. Walid ya amsa ya ce "Ya aka yi, meyafaru?" "Yadda dai na gaya maka, wani ne ya kawo wata leda ya ce a ajiye masa, na manta ban nuna masa ba, kawai suka zo cikin dare suka tafi da shi, naje na je hukumar sun hana ni ganinsa" Liti ya ce "Ki yi haƙuri, ki daina kukan haka, kuma kin tabattar bai yi wani laifin ba?" "Ni dai a iya sanina bana tunanin yayi wani abun, duk da ba tare muke yawo da shi ba, amma dai sun ce a kan kayan da suka gani a gidan nan ne" Walid ya ce "Ki kwantar da hankalinki, in dai Viper ne, mutum ne mai sa'a koma menene zai fito, amma ki kwantar da hankalinki, yanzu idan muka je babu lallai su sauraremu, amma in sha Allah gobe in Allah ya kaimu da wuri zamu je mu ga yadda za ayi". Ta ce "To shikenan na gode sosai, bari na kawo muku ruwa" "Kar ki damu a ƙoshe muke, ki kwantar da hankalinki idan da wani abu ki kira lambata" Ta ce "To na gode" Ta rufe ƙofa suka tafi, liti ya ce "Ikon Allah" "Menene?" "Kawai rayuwar Mai zamani nake kalla, yadda yake gararambarsa da kamar babu mai so, idan muka faɗa cakwakiyarmu, iya mu muke warware kayarmu, babu wanda ya damu da mu, shi kalli Allah ya kawo masa mai kula da shi". "Haka ne, amma tausayi ta bani wallahi, yarinya ce sosai. Yana ta buyagi da rashin mutunci an yi masa aure, amma sai da ya mari madaki saboda ya tankata". Liti ya kwashe da dariya ya ce "Kai mace fa aka ce maka, na raba ka" Walid ya kwashe da dariya ya ce "A ƙi faɗinsa, da madaki ya ce ya kashe ta, mazewa yayi ba zai motsa ba, wai ba shi ya aiketa ba, amma ka ga wasu jijiyoyi da suka tashi a goshinsa, ga wani gumi da yake a iya karan hancinsa, bai san yana wasu abubuwan ba" suka sake kwashewa da dariya. Liti ya saka su guduma ɗan gidan mai unguwa, su din ga kaiwa sun komowa, suna ɗan zagaywa a layin gidan viper, idan suka ga wani abu da ba su yadda da shi ba, su sanar masa. Suka cigaba da kaiwa suna komowa a hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, amma su ma ba su samu ganin Viper ba, suka ce sai dai idan sun kai shi wurin jami'an tsaro su je can su ganshi. Hankalin Jauhar ya ƙara mummunan tashi, ta rasa in da za ta saka ranta ta ji daɗi. Ta sake amfani da wayarta, ta kira walid a waya, da yake sun ce kar ta sake zuwa hukumar, ta bari za su din ga zuwa su. Ta duba wayar kaf, babu sunan wani mutumin kirki a ciki, balle tayi tunanin akwai lambar wani ɗan gidansu,  ta kira duk sai sunayen su Liti da ire-iren su. Sai kuma ta fara tunanin ko ba shi da kowa ne? Amma da ba shi da kowa ai ba zata ga kakarsa ba, kuma an nuna mata Rahila ranar da aka yi bikinsu Anty Zakiyya ta ce mata wai babarsa ce, amma tana tantama tun da aka yi auren, bai taɓa kai ta gidansu ba, kuma babu wani wanda ya zo daga gidan. Walid suka Kuma dawowa suna rarrashin ta, a kan suna ta ƙoƙarin ganin ya fito, ta gaza haƙuri ta ce "Dan Allah to ina ne gidansu, yakamata ace sun sani" Walid ya ce "Taɓ ke 'yan gidan na su da suna ta tashi, da baki gansu ba, ki manta da maganar su kawai ki cigaba da addu'a". Ta ce "Amma kamar yakamata a gaya musu halin da yake ciki, ko ba za su yi komai a kai ba". Walid zai yi magana, liti ya ce "Bari na kwatanta miki gidan na su" yayi mata kwatance sannan suka yi mata sallama suka tafi. Liti ya ce "A irin wannan yanayin da take ciki, idan ba ka kwatanta ba sai ta tsaneka ai, idan ta je ta ganewa idonta shikenan" "Haka ne, amma ka san wannan matsiyaciyar matar gidan na su ba mutunci gareta ba, kar ta ƙara mata zafi". Suka cigaba da tattaunawa. Kusan kwanaki bakwai da kama Al'amin, idan ka ga jauhar sai ka ce tayi jinyar shekaru, duk ta ƙare ta fita hayyacinta. 'yan sana'oin ma ba ta iyawa, saboda tunani da damuwa. Liti ya zo da safe, tana falo tana karatun Alkur'ani, ta ga kiran waya a wayar Viper, ta tashi ta fita ya ce "Sako hijjabinki mu je, sun bawa 'yan sanda shi, idan Allah ya taimake mu, wataƙila mu ganshi" cikin tsananin zumuɗi, ta yafo mayafinta, ta rufe gidan suka tafi. Sai dai da suka je ɗin ma, tsugono ba ta ƙare ba, dan sun fi ƙarfin awa biyu, walid da liti suna safa da marwa, da faɗi tashin su ga Al'amin, Jauhar addu'a kawai take yi, tun da ta ga haka ta san lamarin ba ƙarami ba ne. Da ƙyar aka ce za su ganshi, aka tafi da wasu wani wuri, suka jira a reception ɗin sashen. Babu tsammani ta ɗaga kai ta ga yana tahowa, yana ɗingisa ƙafa, cikin hanzari ta miƙe tsaye ta zuba masa ido, kansa a ƙasa jami'an tsaro sun taso shi a gaba, su liti ma miƙewa suka yi tsaye, da ya kusantota sai ta ga jikinsa duk alamar duka, gefen fuskarsa a kumbure, haka wuyansa, shirt ɗin jikinsa tayi datti, duk busasshshen jini, take jikinta ya hau tsuma cikin tashin hankali. Ya zo ya nemi wuri ya zauna kamar basarake, gabansa ta ƙarasa cikin tashin hankali muryarta na rawa ta ce "Master, dukanka suke yi haka?" "Maza wai meyafaru ne? Me ka yi haka aka kawo ka nan?" Walid ya tambaye shi cikin damuwa. Jauhar ta ce 'Yallaɓai, dan Allah ku sake shi, dan Allah ku yi haƙuri ba zai ƙara ba, wallahi kayan da ku ka gani a gidan lafina ne, bai san da su ba, dan Allah ku yi haƙuri ku sake shi" Ɗaya daga cikin 'yan sandan ya kalleta ya ce "Yarinya yayanki ba ya ji, ba zamu sake shi ba, wanda aka kama da cocaine ki ke cewa a saki ba shi da laifi? For more than 7days ya amsa laifinsa yaƙi, ga kaya an kama shi da shi, yayi magana yaƙi kamar dutse" Gaba ɗaya sak suka yi suna kallon ɗan sandan. "Wace irin cocaine kuma? Ka ga malam ba ma son rainin wayo, haba kai tare fa muke sabgar nan da shi, a gidan uwar wa zamu ga cocaine ɗin?" Walid ya yi maganar a matuƙar fusace. Cikin tsawa wani ya ce "Kai ka san a ina ka ke?" "Na sani mana, ai ba lahira ba ce, balle ace mutum ta sa ta ƙare, ƙarshen abun dai ku kashe mutum, kai da muna harka da cocaine zaku ganmu a haka ne?" Jauhar ta yadda sai hali ya zo ɗaya ake abota, daga Al'amin har abokansa ba su da tsoro. Fashewa ta yi da kuka ta ce "Wallahi Yallaɓai zan iya rantsewa ba ya ta'amalli da cocaine, bai san ma in da zai same ta ba". "Yayi bayani da bakinsa mana" Cikin hanzari ta koma wurinsa, ta ce "Dan Allah Master ka yi musu magana ko zasu ƙyale ka mu tafi, ka gaya musu ba taka ba ce ba, laifina ne" Yadda ginin wurin ba ya motsi, balle yayi magana haka Al'amin yayi kirim a wurin. "Dalla malam ka yi musu bayani, ka gaya musu ba ka ta'amalli da ita kar su yi ta tila maka na jaki a banza su nakasa ka" Walid yayi maganar cikin ƙunar rai, dan ya san ƙage kawai aka yi wa Al'amin. Liti ya ce "Kai ma ka san ba zai yi ba, wasu lokutan zuciya in dai irin ta shi ce ba ta yi ba" Jauhar ta riƙe hannunsa za ta yi magana, sai dai jikinsa kamar wuta Saboda zafi, sai yanzu ta tuna bai gama warkewa ba aka kama shi, durƙushewa tayi a gabansa ta cigaba da kuka. "Lokacinku yayi, zaku iya tafiya" Liti ya ce "Ko ba ku ce ba zamu tafi, kowa yayi na gari dai kansa ya yi wa" Al'amin ya miƙe tsaye, ya saka hannu ɗaya ya ɗagata daga durƙushen da take, ya juya zai koma, ta saka ƙarfinta ta rirriƙe shi tana kuka. "Ke wai meye haka, da ki ka samu aka bari ki ka ganshi" ɗan sandan ya daka mata tsawa. "Wallahi sai dai ku rufe mu tare, ni ba zan tafi ba, wai ya ake so na yi ne? Ya zan yi ko ina babu daɗi, ni komai nawa ba sa'a. Na gaya muku ba shi da laifi, amma dukansa ku ke yi, tayaya hankalina zai kwanta idan na tafi? Ba laifinsa ba ne wallahi, laifina ne na karɓi abu daga hannun wanda ban sani ba dan Allah ku ƙyale shi" Matsanancin tausayin da jauhar ta bawa liti, ya sanya ya fice ya bar wurin, kuka take iya ƙarfinta, Al'amin har mamaki yake yi, tsakaninsa da ita ba wata shaƙuwa ko kulawa ta musamman amma idan abu ya same shi, gaba ɗaya sai ta rikice. Walid tsayawa yayi ya ga viper zai rarrasheta ko kuma ƙasaitar zai tsaya ya cigaba, da kuwa ko 'yan sandan za su rufe shi, sai ya zage shi. Ɗaya daga jami'an tsaron yayo kan jauhar, da nufin ya ɓanɓareta ta ƙarfin tsiya, su mayar da Viper, cikin hanzari ya ja baya da ita a jikinsa, ya ɗaga masa hannu yana ƙara tsuke fuska. Ya saka hannu, ya ɓanɓareta daga jikinsa, ya riƙe hannayenta, gaba ɗaya kammnin fuskarta sun canza saboda idanunta sun kumbura sosai ta koma pink saboda kuka. Ya sunkuyo dai-dai fuskarta ya ce "Kin kusa fara exam, ki yi karatu sosai, kar ki zauna zaman shiriritar nan, ki yi ƙoƙari ki yi karatu ki zama lawyer ko likita, ko dan saboda fitinannen mijinki, ki gaida mini da kwaɗinki da ƙadangaru idan kin koma gida" tana jin yadda jikinsa yake fitar da hucin zafi da warin datti, kwana bakwan nan babu alamar wanka ko wadataccen abinci a tare da shi. Ya kama kafaɗarta, ya saita ta hanyar fita ya ce "Kar ki sake zuwa wurin nan saboda ni" ya kalli walid ya nuna masa Jauhar, ya yi masa wata inkiya, ya juya suka mayar da shi. Suka fito tana kuka, liti ya girgiza kai ya ce "Wallahi Mutanen nan 'yan wuta ne" Walid ya ce "Kai wannan hurumin Ubangiji ne, amma ko dan hakkin yarinyar nan Allah sai ya kama su, a gidan uwasu zai ga cocaine ɗin, wallahi ƙila su suka zo da abar su suka saka masa" "Zasu aikata ai ba tsoron Allah suke yi ba" sun yi gaba suna ta surutu suna zage-zage da tsine-tsine. Suka nemi jauhar suka rasa, suka waiwaya, tana bakin ƙofar in da suka baro, ta zauna dirshan tana matsar hawaye. Liti ya ce "Taɓ lallai sabga da mata sai haƙuri, wannan ko mutuwa yayi abun da za ta yi kenan" Walid ya ce "Sai an yi mata uzuri, ba ta saba ganin wannan tashin hankalin ba, ina zuwa". Ya koma da baya wurinta, ya zauna ya din ga rarrashinta, tare da ba ta tabbacin Aminu zai fita. Cikin kuka ta ce "Ba ma fa shi da lafiya, zazzaɓi ne a jikinsa" "Ki yi haƙuri, Allah zai bashi lafiya" Ta sake cewa "To yanzu daga nan me za su yi masa?" "Wallahi ba mu sani ba, amma zamu cigaba da bibiya in sha Allah, sai mun ga abun da ya ture wa buzu naɗi" da ƙyar ta taso, suka kaita har gida, Walid ya ba ta kuɗi, ta ce ba zata karɓa ba, sai da ya ce mata Al'amin ne ya ce ya bata sannan ta karɓa. Har ta shiga falo, aka buga mata ƙofa, ta dawo ta buɗe, ta ga Malam lawan baban su halimatu a tsaye. Ta durƙusa ta gaishe shi, ya ce "Wato duk na san ke da mijinki, kuna jin haushina, amma ni duk in da gaskiya take sai na faɗa. Ke yanzu ki ji da halin da mijinki yake ciki, amma kin zo kina tara mana maza a layi, kusan kullum sai sun zo, shi fa aure abu ne mai daraja da muhimmanci". Jiki a sanyaye ta ce "Tara maza kuma?" "Eh mana, wannan da ku ke fita tare da su ku dawo, muharraminki ne?" Kalmar ta yi mata nauyi sosai, amma ta dake ta ce "Aboknsa ne, su ne suke taimaka mini a kan case ɗin sa" "To ke me yayi miko zafi? Ki koma gidanku mana, idan ya fito kya dawo, ko ma ki haƙura da auren, da kyanki da ƙuruciyarki nan da nan wani zai aureki, shi kuma ya cigaba da shashancinsa". Ta ce "To na gode sosai" "Ai gara dai ki san abun yi, ni Allah ya sa ma ba iyayenki ki ka bujirewa a kansa ba, Allah yake jarabatarki ba" gaba ɗaya sai ta ji kimarsa ta zube a idonta. Jauhar ta kama Alƙur'ani da da carbi, tayi ta Addu'a tana gaya wa Allah. Aka sake shafe kwana biyar, su liti suna yi mata yawo da hankali, suka kuma hanata komawa wurinsa, sai su ce mata sun je yana lafiya yana gaisheta. Haka kurum ta ji a ranta ƙarya suke yi mata, ba tare da sun sani ba, ta sake ɗaukar ƙafa ta tafi wurin 'yan sanda, har da abincinta ta tafi da shi, sai dai suka tabbatar mata sun kai shi kotu, har alƙali ya aike da shi gidan gyaran hali, zuwa lokacin da za a cigaba da shari'a. Cikin tashin hankali ta tambaye su, zuwa yaushe zai fito. Suka ce mata ta tafi kotun ta tambaya, suka din ga yi mata wasa da hankali, har da wanda suka biyota da maganar lalata. A ƙofar gida, ta tarar da su walid, sai jan ƙafa take da ƙyar, ta ƙarasa. Walid ya ce "Madam ina ki ka tafi ne, mun zo ba kya nan?" Ta kalleshi cike da karaya ta ce "Dama an kai shi prison ba ku gaya mini ba?" Liti ya ce "Komawa ki ka yi kenan, ke ana ta ɓoye miki, dan kar ki tayar da hankalinki, shi muka zo gaya miki, sai da muka tsara yadda zamu gaya miki, yadda ba zaki damu ba, amma kin tashi kin tafi kin jiyo wa kanki damuwa" Ta ce "To ya zan yi, na kasa jurewa". Walid ya ce "Yanzu dai tun da kin riga kin je kin ji da kanki, shikenan amma ki yi haƙuri zamu nemo wata hanyar mijinki zai fito in sha Allah" Jinjina musu kai kawai tayi, ta shiga gida. tuna da liti yayi mata kwatancen gidan su Al'amin, kamar korarriya, ta sake ɗaukar hanya, ta tafi unguwar su Al'amin tare da fatan Allah ya sa idan ta je gidan su Allah ya sa a dace a samu hanyar fitar da shi. Sai da ta haɗa da tambaya, sai dai gidan na su ba ɓoyayye bane ba, mussaman ma sunansa da ya riga ya shahara sosai. Sau biyu tana sallama aka amsa, mata wata matashiyar budurwa, da zata girme mata ta leƙo ta amsa. Ta ce "Ya aka yi?" Jauhar ta yi murmushi ta ce "Baƙuwa ce" Amira ta ce "Baƙuwa daga ina?" Rahila ta ce "Amira ki bari ta shigo mana" Ta bawa jauhar hanya, ta ƙarasa ta shiga falon da sallama. Rahila na ganinta ta washe baki, cike da duniyanci ta ce "Amrya ba kya laifi, ko kin kashe ɗan masu gida" jauhar ta zube har ƙasa ta gaisheta. "Lafiya ƙalau, zauna a kan kujera mana jauhar" ta sunkuyar da kai tare da girgizawa ta ce "Nan ma ya isa" "Amira matar Aminu ce fa, kawo mata ruwa dan Allah" kallon banza ta yi wa jauhar, ta gyara zamanta ta cigaba da danna waya. Rahila ta ce "Ke fa 'yar wulaƙanci ce amira". Jauhar ta ce "Ai a ƙoshe ma nake" "Allah sarki, ya mijin naki, tun da aka yi auren ba ki zo mana ba" tayi shiru tare da sunkuyar da kai tana murmushi. "Bari yanzu babansu zai shigo, sai ku gaisa". Amira ta saci kallon jauhar, kyakywar bafulatanar yarinya, daga muryarta kawai zaka san ba ta da hayaniya, ita aka aurawa Al'amin. Abbu ne yayi sallama suka amsa masa gaba ɗaya, ko da ya shigo sau ɗaya jauhar ta kalle shi ta mayar da kanta ƙasa, babu in da Al'amin ya bar kamanin mahaifinsa. "Abbu ga 'yar ka fa, sirikarka matar Aminu" Ya ce "Subhanallah" ya zauna yana faɗin "Yarinyar kirki, tuba nake yi yakamata ace na zo gidan naku, tafiya ta kama ni ne, ina ga yau kwanana huɗu da dawowa, kuma ina maganarku sosai wallahi, dan Allah ki yi haƙuri" "A'a babu komai, ai mu ne masu laifi, tuntuni yakamata ace mun zo, ban san gidan nan ba ne shiyasa shi kuma bai kawo ni ba" Rahila ta ce "Hmm, dama ya za ayi ya kawo ki, ai ko za a shekara sai idan rashin mutuncin sa ne ya kawo shi" yanayin maganganun da rahila tayi, ya tabattar mata da ba ita ce mahaifiyar Al'amin ba. Abbu ya ce "Ina fatan dai ba wata matsala, ba yayi miki wani abu na rashin kyautatawa?" Tayi ajiyar zuciya ta ce "Ba ya yi mini sai dai.." sai kuma ta yi shiru. Rahila ta yi farat ta ce "Sai dai me, ki faɗa ba wani abu, ai mu duk iyayenku ne". "Ƴan sanda ne suka zo mana cikin dare, suka kama shi suka tafi da shi, naje na kuma zuwa anƙi sakinsa, wai suna zarginsa da ta'amalli da hodar iblis". Rahila ta ce "Taɓ! Ki ce shi likkafa ce ta cigaba a harkar shaye-shayen har ya kai wannan matakin?" Jauhar ta ce "A'a ba ya amfani da ita, wani ne ya kawo ya ce a ajiye masa, ban san kowaye ba, su kuma suka zo amma wallahi ba shi da laifi, shi ne na ce bari na zo, dan Allah baba ko da hanyar da za a bi a sako shi, ba ma shi da lafiya wallahi, da na je dukansa suke yi, jikinsa duk shaidar duka" ta ƙarasa maganar tana kuka, duk yadda ta so riƙe hawayen amma abu ya gagara. Rahila ta ce "Au dama shi ne dalilin zuwan naki? Sai da matsala ta afku ki ka nemi gidan ubansa, in dai wannan ne ya saba, kina zaune 'yan iskan da suke bashi goyon bayan yin rashin mutunci za su saka a sake shi". Abbu ya ce "Ya isa haka rahila" ya kalli Jauhar ya ce "Ki daina kuka yarinyar kirki, case da ya haɗa da irin wannan case ne babba ba ƙarami ba, Al'amin ba ya jin magana ko kaɗan". "Wallahi baba ba shi ya kawo su ba, ban taɓa ganinsa da ita ba". "Idan ma yana ta'amalli da ita, ba gaya miki zai yi ba ai" Abbu ya ce "Ki kwantar da hankalinki, idan da wata matsala ki koma gidanku, zuwa lokacin da komai zai daidaita, zan je na ga abun yi" "Abbu ka san cocaine kuwa? Wallahi ka je suka fuskanci belinsa ka ke son yi, za su iya haɗawa da kai, ka dai koma gefe ka taya su da addu'a, duk masifar da ya janyo ta ƙare masa a kansa idan yana da rabo ya fito, idan babu ya ƙarata a can". Kalaman rahila suka yi wa jauhar zafi da nauyi, ba shiri ta tashi ta ce "To bari na tafi sai anjima". Rahila ta ce "Ki je gida ki yi ta addu'a, idan babu dama ki koma gida, amma shigar mahaifinsa wannan case ɗin ba mafita bane ba, kina zaune za a sako shi". Abbu ya ce "Ki yi haƙuri kin ji, zai fito in sha Allah, zan san abun yi" "Ka daina saka mata rai da zaka yi wani abu fa, haka kurum wani abu ya sameka gani ga 'ya'ya ka barmu" Bayan tafiyar jauhar, Abbu ya ce "Rahila, anya ban yi wauta ba da na biye miki aka aura wa yarinyar mutane Al'amin ba, kalli yadda take cikin tashin hankali da damuwa fa". "Wannan yarinyar fa da ka ke gani, ba a bar tausayi ba ce ba, ko ka manta kangarewa iyayenta ta yi suka nemi maraba da ita?" "Duk da haka rahila, ni fa tantama nake yi a kan maganar nan, gaskiya ina ga zan jagoranci raba auren nan, Al'amin ba zai yi hankali ba" "Abbu ina ruwanka, dan Allah ka bar maganar yaran nan" Jauhar kuwa bayan ta fita, ba tare da tunanin komai ba, ta nufi unguwar su, ta je ta samu baba, ko da wani abu da zai iya taimaka mata, ba tare da tuna haɗarin da hakan ka iya haifarwa ba, kodayeke wanda yake cikin ruwa ko takobi ka miƙa masa kamawa zai yi. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA Kina bukatar kaya masu kyau da inganci?? Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba?? Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta?? Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki. Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955 Sosai take sauri, tare da fatan Allah ya sa baba yana nan. Sai dai tayi iya ƙoƙarinta wurin daidaita nutsuwarta, kafin ta ƙarasa gidan. Yamma ta fara yi, yaran gidan sun dawo, sun yi kaca-kaca da shi, duk sun zubar da kayan makarantar su ko ina, ga uban wanke-wanke da aka rasa mai zaman kawar da shi daga wurin. 'yan ƙananan yaran gidan ne suka fara murnar ga jauhar, ɗakin mama ta shiga suka gaisa, ta kalleta ta ce "Lafiya na ganki yanzu? Wani abun ne?" Jauhar ta ce "Lafiya ƙalau wurin baba na zo". "In ce ko dai lafiya, kuma ya san kin zo? Ki tashi ki tafi kar ki saka makakken mijinki ya zo yayi mana tijara da tashin hankali" Anty ce ta leƙo falon ta ce "Jauhar ashe abun da ya faru kenan?" Jauhar ta kalleta ta ce "Anty dama kina nan ina wuni?" "Lafiya ƙalau, ashe kuma kama mijinki aka yi da hodar iblis, abu bai yi daɗi ba". Dammm! Ƙirjin jauhar ya buga, yaya aka yi anty ta san wannan zancen, mama ta ce "Kamar yaya?" "Yanzu muka yi waya da rahila, ta ce bata daɗe da barin gidan ba, ta je musu wai an kama shi". Wani abu ɗaci ya tsaye wa jauhar, kamar ta fashe da kuka, ta ce "Ba ya ta'amalli da hodar iblis, rigima ce kawai ta haɗa su da wasu, shi ne dai na je na sanar musu, kar ya zamana ba su sani ba" "Dan ubanki ni zaki yi wa ƙarya dan ki kare mijinki, ai rahila ba zata yi miki ƙarya ba" Walida ta ce "Taɓ, Allah ya kiyashemu taɓewa, hodar iblis abun ba arziki ai na zata a sara suka kawai ya tsaya ashe babban kai ne" Duk yadda ta so ta riƙe hawayenta ta kasa, ta fashe da kuka, suka din ga aibata Al'amin, gashi ba ta tarar da baba a gida ba, babu alamar za su tausaya mata, ko su rarrasheta, kawai ta tashi ta ɗauki jakarta tana kuka, ta fice. Hafsa ta ce "Allah sarki jauhara da tuni ana china ko gidan Alhaji mu'azzam ana shan A.C" suka din ga dariya. Ta kwashi ƙafa ta nufi gida, tare da ƙudirce wa ranta da yardar Allah, babu abin da zai saka ta sake zuwa gidan nan da matsalarta, ƙarshen ƙiyayya da tsana dai ana nuna mata a gidan nan. Kamar daga sama ta ji an buga mata tsawa "Ke bamu hana ki shigowa unguwar nan ba?" Sai a lokacin ta tuna abun da ya faru, cikin tsoro ta kalli mai yi mata tsawar, sai dai ta kasa magana, ta bishi da ido. "Ba magana nake yi ba" "Nawa ubanka ya bayar aka shimfiɗa unguwar da za a hanata shigowa mahaifarta?" Ta ji wata muryar daban. Ta kalli matashin yaron, guduma kenan ɗan gidan mai unguwa, da su Walid suka bawa ragamar kula da gidan Al'amin da shige da ficen jauhar, har ta je gidan su Al'amin ta taho nasu gidan yana biye da ita. Saroro ta yi tana kallonsa, dan ba ta san shi ba. "Waye kai? Meya kawo ka unguwar nan?" Guduma ya nuna masa Jauhar, ya ce "Wannan, wallahi kana taɓa ta zamu ɓalla ƙarfe a wurin nan, mu rabu salin alin" ɗayan ya ja da baya ya basu hanya, guduma ya ce wa jauhar "Mu je" Ita dai ba ta iya yi masa magana ba, ta cigaba da tafiya ita yanzu gaba ɗaya hankalinta da lissafinta yana kan halin da take ciki a yanzu. Misalin ƙarfe uku da rabi na dare, jirginsu ya sauka malam Aminu Kano international airport, direba ya zo ɗaukarsa. Duk da a gajiye yake, saboda doguwar tafiyar da ya yi, hankalinsa da lissafin sa yana kan, ya ƙarasa gida garin Allah ya waye, ya je ya ji ba'asin dalilin fasa aurensa da yarinyar da ya ƙallafa rai a kanta, kullum cikin tunanin ta yake, kuma tun da aka ce, an fasa bashi ita, ya ji ya ƙara ƙaunarta, ta shiga ransa fiye da yadda yake tunani. *** Kwanaki kaɗan ya rage jauhar ta fara jarrabawa, amma ba ta iya karanta komai, ga uniform ɗin ta, ga litattafanta sai dai ba ta da nutsuwar da za ta yi karatu, duk ta ƙare tayi rama ga rashin abinci dama damuwar da take ciki ba ta barinta ta ci abincin. Walid sai da yayi mata faɗa a kan zuwanta gidansu ba tare da saninsu ba, tare da jaddada mata mugunta da gaba mai tsanani da take tsakaninsa da Al'amin. Tana kwance a falo, maman halimatu ta shigo gidan, ta tarar da ita a kwance cikin damuwa ta ce "Jauhar, rayuwa za ta yiwu a haka kuwa? Yanzu da mutuwa yayi ba dole ki yi haƙuri ba, kin addabi kanki, kamar ko abinci ma fa ba kya ci" kamar ta soso mata wurin da yake yi mata ƙaiƙayi, ta hau rera kuka, ta zauna ta rungume ta ta din ga rarrashinta. Ta ce "Sako hijjabinki mu je gidana, kya ɗan sake ki sha iska, zaman kaɗaicin nan ba abun da zai amfana miki sai ɓacin rai" Haka ta bi maman halimatu, dan ba ta da wani zaɓi face hakan, ta zuba mata abinci ta bata, sai dai ta cakala ta bar shi ta ce ta ƙoshi. Halimatu ta zauna kusa da ita ta ce "Anty jauhar dan Allah ki daina kuka, zaki yi rashin lafiya " tayi maganar tana goge mata hawaye. Akwai shaƙuwa sosai a tsakanin jauhar da yaran layin, wasu ma ko iyayen su ba ta sani ba, amma su tana hulɗa da su, ta yi wa matan kitso, ta koya musu karatu idan tana da abinci ta ba su, ko 'yar alewa ko abun kusa da baka, shiyasa suna son taruwa a gidan idan master baya nan, sai dai rashin walwala da ba ta yi yanzu ya sanya duk suka watse suka daina zuwa. Baban su halimatu ya dawo, dama juahar na tsakar gida, ta gaishe shi ya amsa sama-sama, ya shige falo, ya fara ƙwalawa salamatu kira. "Baban halimatu sannu da zuwa " "Me matar mutumin nan take yi mini a gida? Haka kurum da tsinannen kwashe-kwashenki, ki janyo mana masifa muna zaman lafiya" Cikin takaici ta ce "Haba dan Allah, menene a ciki, tana zaune ita kaɗai cikin damuwa shiyasa na ce ta shigo, amma ka san haka kurum ba mai shige-shige ba ce ba". "Ke ki ka sakata a damuwar da zaki cirota, ambulance uwar taimako " Jauhar na jin su sama-sama, ta tashi ta ɗauki mukullin gidanta, ta fice ta koma gida. Jauhar ta kama addu'a iya yin ta, su liti fafur sun ƙi gaya mata kotun da ake yi wa Al'amin shari'a, kuma suka ƙi gaya mata prison ɗin da yake. Baba yana karyawa da safe, ya ga kiran waya da baƙuwar lamba, ya ɗaga ya ɗan yi gyaran murya yayi sallma. "Wa'alaikum Salam, barka da safiya baba". "Yauwwa barka dai, da wa nake magana?" "Alhaji mu'azzam ne baba, ina ƙofar gida na zo, na ce Allah ya sa ba ka fita ba". Jikin baba yayi sanyi, ya ce "Ahh ina nan ban fita ba tukuna, ashe ka dawo" "Eh baba na dawo" "To gani nan" Ya miƙe zai fita, mama ta ce "Ina zaka kuma kai da waye?" "Baƙo" ya bata amsa a taƙaice. Ya fita tsakar gida, hafsa ta shirya za ta tafi makaranta ya ce "Ke haryanzu baki tafi makarantar ba me ki ke yi?" "Ba ni da lectures ne da wuri, shiyasa yanzu zan tafi" "To Allah ya tsare" ta amsa da amin. Baba ya fito suka gaisa, ya ce "Malam mu'azzam ka dawo ashe?" Cikin girmamawa ya ce "Eh baba, na sameku lafiya?" "Alhamdilillah" "Masha Allah, baba tun ina china na samu wani labari, hankalina duk bai kwanta ba, na yi iya ƙoƙarina wurin dawowa, baba ko wani laifin na yi ka hana ni auren jauhar?" Baba ya girgiza kai ya ce "Wallahi ko ɗaya, kawai dai ka san matar wani ba ta auren mijin wata, Allah bai ƙaddara aurenku ba, ina mai baka haƙuri, na yi maka laifi ban kyauta ba, da kuɗin aurenka a hannuna na aurar da ita, amma ka yi haƙuri dan Allah" A razane ya kalli Baba ya ce "Aure aka yi mata?" Baba ya jinjina masa kai a sanyaye ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Hafsa kuwa har ta sako kai za ta fita, ta hango Alhaji mu'azzam, ta koma cikin gidan da gudu, ta samu mahaifiyarta a ɗaki ta ce "Anty, saurayin nan na jauhar ne ya zo, Alhaji mu'azzam gashi can da baba a waje" A sukwane ta tashi ta ce "Haba dai?" "Wallahi da gaske nake" "To maza ɗauko kayayyakin nan ki yi amfani da su ki fita kafin ya tafi" Can kuwa Baba sai haƙuri yake bashi, yana yi masa nasiha, dan shi bai san ma an yi mata aure ba sai yanzu, gaba ɗaya ya shiga damuwa, aƙalla zai bawa jauhar shekara ashirin da wani abu, ya girmeta nesa ba kusa ba, sai dai ta shiga ransa sosai da sosai, duk da ya sha yinƙurin ƙara aure a baya, amma matarsa tana hanawa, bai taɓa shiga damuwa na rashin wata ba sai jauhar, kamar ya zubar da hawaye haka yake ji. Jiki a sanyaye ya ce "Shikenan baba babu damuwa, na gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya basu zaman lafiya da zuriya ɗayyiba". Baba ya amsa da "Amin" Suka yi sallama, ya shiga motarsa amma ya kasa tuƙin, ya kifa kansa a sitiring motar, yayi shiru ya ji gaba ɗaya duniyar tayi masa wani iri, babu irin zargin da bai kawo a ransa ba, na dalilin hana shi auren jauhar. "Malam ya dai" da sauri ya ɗago kansa ya ce "Jauhar" "Ba ita ba ce, yayarta ce, tun ɗazu na ganka a nan baka tafi ba, lafiya?" "Yauwwa Alhamdilillah, dan Allah in tambayeki mana?" "Ok, Allah ya sa na sani" tayi maganar tana sake gyara tsayuwarta cikin iyayi. "Ko kin san dalilin da ya saka aka fasa bani aurenta, tun da kin ce ke yayarta ce" "Eh to, rashin ji ta fara yi, baba ya yanke shawarar aurar da ita kawai, tun da baka nan" Alhaji mu'azzam ya ce "Wani irin rashin ji?" "A tunaninka wane rashin ji mace za ta yi, a aurar da ita babu shiri?" Cikin matsanancin mamaki ya ce "Jauhar ɗin?" Hafsa ta ce "Ita fa, ko dan kana ganinta a haka? Dama ba sonka take yi ba, akwai wani saurayinta ɗan daba, da ta ƙallafa rai a kansa, ta fara rashin ji, kawai baba ya aurar da ita, ai ka ga ba zai gaya maka haka ba" yayi shiru yana kallon hafsa, kawai ya ji maganganun nata ba su shige shi ba, ya gyaɗa kai ya ce "Shikenan, Allah ya basu zaman lafiya" Ta ce "Amin, dan Allah ko zaka sauke ni a hanya, school zan tafi ko a titi ne sai na sauka na samu abun hawa?" Ya ce "Bakomai bisimillah" Jauhar ta idar da sallar la'asar, ta ga kiran walid a wayar Viper, ta tashi ta ɗaga da sauri, suka gaisa, ya ce "Wani tunani na yi, akwai uban gidansa da muke yi wa aiki, ɗan majalisa ne, sai dai Viper ne kawai yake iya samunsa kai tsaye, na ce ko wurin P.A ɗin sa zamu je, ki gaya masa dan ni ba shiri muke yi da shi, na taɓa marinsa idan mu ka je da ke wataƙila su saurareki". Cikin ɗoki ta ce "To shikenan, Allah ya sa dai su fito da shi ɗin" ya amsa mata da amin. Hafsa kuwa cike da salo da kisisina, da tasirin sihiri, sai da ta karɓi lambar Alhaji mu'azzam, har bakin department ɗin su ya kaita, sai dai idan zai yi mata magana sai ya kirata da jauhar, sai dai hakan bai dameta ba, lambarsa kawai da ya bata, ya sanya ta din ga jin kamar ta ma riga ta aure shi an gama. Tun safe jauhar ta shirya, ya din ga kiran wayar Walid da ta liti, amma ba ta shiga, tun tana saka ran za su zo, har ta fara sarewa, sai azahar walid ya zo, kamar ta yi masa kuka ta ce "Tun safe nake kiran wayarku, ina jiranka amma shiru ba ta shiga" Walid ya ce "Ai wayar nan ta sa ma kawo ta zaki yi" Cikin mamaki ta ce "Saboda me?" "Akwai dalili, yanzu idan kin shirya ki zo mu je can wurin P.A ɗin ki gaya masa, da mun je shiga zaki yi, mun gama magana da wani yaronsa" ta ce "To" Suna tafe tana yi masa magiyar, dan Allah ya kaita ta ga master, amma ya ce "Shi fa ya ce kar a kuskura a kai ki, yanzu idan muka kai ki tijara zai yi mana". Cikin damuwa ta ce "Haushina yake ji, ba ya son ganina ko?" Ya ce "Gaskiya ba na ce ba, ya ce dai kar a kuskura a kai ki, kuma ranar Litinin zaku fara jarrabawa, ki je ki fara" Mamaki ne ya kama ta, ya aka yi ya san lokacin da za su fara jarrabawa? Tayi ajiyar zuciya ta ce "To yaya jikin sa ya warware?" Walid ya ce "Eh ya warke" "Ina nan ina ɗan haɗa 'yan kayayyakin abinci, sai in baka ka kai masa" "Kar dai ki takurawa kanki" Jauhar ta ce "Ban takura kaina ba, amma dan Allah idan ka je ka ƙara bashi haƙuri, wallahi laifina ne ban gaya masa an kawo abun ba, kuma mantawa na yi" Ya ce "Manta kawai, dama Allah ya riga ya ƙaddara faruwar hakan". Suna zuwa ofishin, ba su wani sha wahala ba, aka shiga da Jauhar, ta gaishe shi ya amsa mata, ya ɗan ƙare mata kallo ya ce "Kamar na taɓa ganinki" Jauhar ta ce "Eh, akwai ranar da na je wurin mijina, na tarar ka je kai da yaya walid an fito da shi a police station". "Oh matar mai zamani ce, Viper?" Ta jinjina masa kai ta ce "Eh nice" Ya ce "Allah sarki, ya gida ya fama da rigimammen mijinki" Tayi murmushi tana wasa da yatsun hannunta. "Yaya aka yi?" Jauhar ta sauke numfashi ta ce "Dama, mijin nawa aka kama, har an kai shi prison an ƙi sakinsa, shi ne na ce bari na zo wurinka dan Allah ko zaka yi wa honorable magana, ko za a fito da shi" Ya girgiza kai ya ce "Al'amin ba zai canza hali ba, me kuma yayi a wannan karon?" "Ba laifinsa bane, abu aka kawo aka ce na ajiye masa, ban san ko menene ba, kuma na manta ban gaya masa ba, jami'an tsaro suka zo suka yi bincike cikin dare, suka kama shi, wai sun ga hodar iblis a cikin kayan" Cikin mamaki ya ce "Hodar iblis kuma? A ina ya sameta?" "Ai ba shi ne ya kawo ba, ba ya ta'amalli da ita" "Taɓɗijan, a wannan karon case ɗin babba ne, bari na kira honorable duk da ba ya gari". Ya kira honorable Indabo, ya sakata a hansfree tana jin duk abun da suke faɗa, suka gaisa. P.A ya ce "Honorable, mutumin ka fa ya janyo babbar jagwal ga matarsa nan a gabana ta zo a taimaka mata a fito da shi" "Wa kenan?" "Ma dogon zamani mana" Indabo ya ce "Kuma dai? Me kuma yayi?" "To wai hodar iblis ce, aka kama shi da ita?" "What! Coacine? Yaron nan yana da hankali kuwa, a ina ya samu coacine kuma?" "To ina zan sani, matarsa dai ta ce ba laifinsa bane ba" "Please count me out of this please, haka kurum na je fito da shi, 'yan adawa su sami na yi mini yarfe, ace nima safararta nake yi? Dama dai wani rashin jin yayi ba wannan ba, ni fa dama Saboda aikina na cin zaɓe siyasa dole sai da irinsu, shiyasa nake fito da shi, amma ban da haka meye haɗina da shi, zan nemi wani ya cigaba da yi mini ayyukana ni babu ruwana" P.A ya ce "A'a honorable, wani kaya fa sai amale, wallahi ba kowane matashi ne yake da ƙwarin da yake da shi ba, kar ka yar da shi wani ya ɗaka" "Ka san dai yanzu bana gari ko, dan Allah ka bar ni, ni yanzu lissafin siyasata na saka a gaba, idan ina buƙatar sa a gaba, na fito da shi" ya kashe wayarsa. P.A ya kalli Jauhar da jikinta yayi sanyi, mamaki ya cika mata kai da zuciya, wato yana amfani da jini da lafiyar Al'amin ne kawai dan cimma nasa burin, abun ya bata mamaki sosai da sosai. "Madam, kin ji abinda honorable ya ce, amma ki yi haƙuri zuwa ya dawo, mu gani zan cigaba da lallaɓa shi, kar ki damu da abubuwan da ya faɗa, kansa ne ya ɗauki zafi, amma shi da Aminu ba ta ɓaci, in dai wannan harkar ce, ba shi da sama shi". Ba ta ce masa uffan ba, ta tashi ta fita, yanayin yadda ta fito ne, ya tabbatar masa da akwia matsala. Ya ce "Yaya? Wani abun yayi miki ko maganar banza yayi miki, na shiga na ci ubansa" Ta girgiza masa kai alamar a a. "To meyafaru?" "Honorable ɗin ya ce babu ruwansa, ba zai shiga maganar ba saboda kar sunansa ya ɓaci" tayi maganar hawaye yana gangarowa daga idanunta. Walid ya yi shiru, tare da jinjina kai ya ce "Shikenan, bakomai mu tafi" Haka suka tafi duk jiki a sanyaye, ta ce "Yanzu shikenan babu abun da za ayi? Haka zai cigaba da zama?" "A'a zai fito, haryanzu ba a gama shari'ar ba ma, dole za a nemi wata hanyar". Jauhar ta ce "To shikenan, dan Allah ranar juma'a ka zo ka karɓi kayan da na tara, sai ka kai masa". Walid ya ce "Shikenan, in sha Allah, amma kar ki je ki saka damuwa a ranki, idan da wata matsala, ki kira ni a wayarki" Ta girgiza kai ta ce "Bani da waya" "To ki ara a ta maƙwabta, barinki da wayarsa akwai matsala, haka ya karɓe wayar Viper ya tafi da ita. Ta cigaba da faɗi tashi, wasila ta din ga aiko mata da abinci, sai dai sam jauhar ba ta son hakan. Aka fara exams, sai dai ba ta iya mayar da hankali wurin yin wani abun kirki, wataran kuɗin motar ma gagararta yake yi. Sai dai tana iya ƙoƙarin ta wurin aro jarumta, da ɓoye damuwarta, idan ta shiga cikin 'yan uwanta ɗalibai. Sannu a hankali ta fito daga harabar makarantar, ta tarar da yaya saifu. Murmushi ta yi ta ce "Yaya saifu, kai ne?" Ya ce "Eh, hau babur ɗin na kai ki gida" cikin murna ta ƙarasa ta rirriƙe shi ta hau, ta ce "Na zo gida sau biyu ban same ka ba". "Yau ai gani, mu je gidan naki". Ya ja babur ɗin, ta ce "Allah ya sa ba laifi na yi maka ba, na ganka kamar ranka a ɓace". Yayi mata shiru, suka ƙarasa gidanta, ta buɗe musu suka shiga. Ta kawo masa ruwa a jug, dan na rijiya yanzu take sha, ko kuɗin sayen ruwa ba ta da shi. "Waliyiyya" "Na'am yaya saifu" "Meyafaru da mijinki?" Tayi shiru ta ƙi magana. "Ki yi mini bayani ina jinki" Kawai ta fashe da kuka, yayi mata shiru tayi mai isarta, ya koma kusa da ita ya zuba mata ido ya ce "Jauhar, wani irin zama ki ke yi a gidan nan, na san akwai ƙalubale da ki ke fuskanta a gidanmu, amma atleast ai ko ni kya gayawa, sai ji na yi ana zancen an kama shi da cocaine, a tsakar gida ko baba ba ma bai sani ba, da yaya ki ke rayuwa ke kaɗai? Da yaya ki ke samun abun da za ki ci?" "Yaya saifu, ni cin abinci ko akasin haka bai dame ni ba, fatana da burina ya fito, ba shi da laifi, ko a yaya yake na yadda shi Allah ya zaɓa mini, ba ya dukana ba ya zagina. Ban san dalilin da ya sanya su mama suka zaɓi na aure shi ba, na karɓi ƙaddarata, na je gidan ai, amma yanayin karɓar da na samu na san ba zan yi nasara ba, kuma ban ma samu baba a gida ba". "Jauhar, a raba auren nan, ni ban ga alamar za a samu ɗa mai ido ba a auren nan ba, rannan fa cewa aka yi sai da ya zo ya tafi da ke, 'yan daba za su saraki, wace irin rayuwa ce haka? Ko khul'i ayi a raba auren nan" Tayi shiru ta sunkuyar da kanta. "Yaya ki ka yi shiru? Ko kina son shi ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "To kin amince a raba auren?" Nan ma ta girgiza kai. "Ki yi mini magana jauhar, idan kin amince in yi wa baba magana, a raba auren nan" "Dan Allah kar a raba, ni dai a fito mini da shi dan Allah" Saifu ya ce "Wai son shi ki ke yi ne?" Cikin kuka ta ce "Idan aka raba auren za ace mini bazawara" "To a kanki aka fara? Ba sai ki koma makarantar ki ki yi a tsanake ba?" Ta girgiza kai ta ce "Dan Allah ni dai yaya saifu kar a kashe mini aure, duk abun da yake yi zai daina a hankali, sharri ake yi masa ba ya ta'amalli da hodar iblis" saifu yayi shiru yana kallon ta, ya fara tunanin any ba son shi take yi ba, ya ma kasa gane me take nufi. "Shikenan, ƙyale baban ma, yanzu da an yi magana da shi, sai ya gaya wa matansa, wace kotun ake yi masa shari'a? Akwai wani baban abokina, sai na yi wa abokin nawa magana a san abun yi" Cikin murna ta ce "Na gode sosai yaya, ban san wace kotun ba ce ba, wai ya hana a kai ni, amma akwai lambar abokinsa, da tare muke up and down, ka ga daga nan ma sai mu je na ganshi". "No, tun da ya ce kar ki je, ba sai kin je ba, duk abun da ake ciki, zan din ga sanar miki, amma ki kwantar da hankalinki dan waliyiyya, tun da kin na ce, ke uwar soyayya Allah ya bar ƙauna, amma wallahi na tsani mijin nan naki" Ta ce "Dan Allah ka daina faɗa, ba zan ji daɗi ba, a din ga yi mana addu'a, ba na jin daɗi idan aka aibata shi" Ya ce "Iyee lallai waliyiyya baki ya buɗe, ki na so dai ki gaya mini ki na son mijinki maybe ma fiye da ni, to wallahi ki fi so na a kansa" Ta ɓoye fuskarta tana dariya ta ce "Wallahi yaya tausayi yake bani kawai, idan aka raba auren nan, akwai damuwa, kuma ina saka ran komai zai zama tarihi in sha Allah" Ya ce "Tafi can, kya ma faɗi gaskiya, kuma ko ba yau ba, kar ki sake wani ma ya san na shiga maganar nan, ai mu na da alfarma shige-shige yayi mana rana" jauhar tayi murmushi, ya bata kuɗi ya tafi. Kusan sati ba ta ƙara jin ɗuriyar saifu ba, ga babu su walid balle ta ji wani abu daga gare su, sai da ta ari wayar wasila, ta kira walid ta ce ya zo ya karɓi kayan da zai kai wa master. Ta saya masa maggi, mai, da sauran ɗan abun da ba a rasa ba, da prisoner zai buƙata. Ya karɓa tare da ƙara bata haƙuri, da ba ta tabbacin, yana nan suna ƙoƙarin fitar da Mijinta. Saifu ya sake komawa makaranta ya sameta, cikin murna ta hau tambayar sa, ya ake ciki?. "Ke mijinki abun da aka yi masa shiri ne kawai, na bibiyi abun ni da abokina, zaki sha mamaki idan na gaya miki an yi wani mugun sara a kan gaɓa, amma ba zan gaya miki ba, in je zaƙin soyayya ya ja ki ki gaya masa ba idan ya fito, ki haddasa husuma, baban abokin nawa yayi magana, sun ce ayi haƙuri ya ƙarasa wata ɗaya, kotu za ta wanke shi ya fito, ashirin da biyu ga watan gobe za a sake shi" "Wayyo Allah, yaya saifu kusan watanni uku fa kenan zai yi a prison?" "Au baki gode ba kenan?" Jiki a sanyaye ta ce "A'a na gode sosai yayana, Ubangiji Allah ya saka maka da gidan aljanna, to zaka kai ni na ganshi?" Ya ce "Amin ya rabb, yana prison na ciki gari, kuma ban ce ki je ba, kar ki kuskura ki je, kin ji na gaya miki" "Amma yaya meyasa?" Saifu ya ce "Saboda haka na ce miki, kuma ke ma kin ce ya ce kar ki je, kar kuma gaya wa wani gashi zai fito shi ma bai sani ba". Jauhar ta ce "To shikenan, na gode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi" "Amin ki koma gida, ki cigaba da exams ɗinki, idan da wani abu, ki neme ni a waya, kar ma ki sake zuwa gidan nan da wani batu a kan aurenki, tun da ki na son abun ki ki yi zamanki" Tayi murmushi ta ce "Ban san menene son ba dai yaya, ban san me ake ji ba, da farko dai na san ina jin tsoronsa sosai, amma yanzu kuma tausayin sa nake ji" Yayi murmushi ya ce "Ga kuɗin mota, ki sauka lafiya, yau ba zan je gidanki ba" Ta karɓa cikin murna tayi masa godiya, ta tafi gida. Ta ji sanyi a ranta jin cewar zai fito, sai dai tana cikin damuwa na rashin sanin halin da yake ciki, ya ji sauƙi ko kuwa, yana samun abinci ko kuwa?" Da ta samu kuɗi, take yin sayayya, ta ari waya ta kira walid, ya zo ya karɓa ya kai masa. Sana'a tuƙuru jauhar kamar tayi ƙwace, dama ga azumi yana gabatowa, ana samun ɗinkuna, dan haka tana samun aikin stone da beads, sai dai ba ta iya sakin jiki ta kashe kuɗin, saboda akwai abun da take son yi. Ita ce mayafai, har da su kantu da aya,  haka take saya ta soya ta ɗaura a leda yara na saya. Har guga take karɓar kayan maman halimatu, ta ta da ta yara tayi mata, ta biyata. Sana'oi kamar zata yi ƙwace, duk da ana yi mata mugunta a kan wasu abubuwan, mussman gidan mai ɗinki, da take yi mata aikin stone ta fara yi mata mugunta. Ta ƙara tsananta addu'a, da roƙon Allah, a kan Allah ya kuɓutar mata da mijinta, ya shirya mata shi. Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, saura kwanaki biyu Al'amin ya fito, jauhar ta yi ta gyaran gida, ta ƙara gyara masa ɗakinsa. Ranar da zai fito ɗin, ta yi girki, sai dai kuɗin hannunta ba su da yawa, duk mutane sun riƙe mata kuɗi, dan muɗin hannunta ba za su ishe su kuɗin mota ba ita da shi. Ta dafa ruwa ta zuba a flask, ta shirya tun ƙarfe tara, ta tafi prison ɗin, gashi damuna ta ja baya, an fara wani irin sanyi mai ratsa jiki. Ta nemi shiga cikin prsion ɗin, aka ce mata a waje za ta jira, idan yau za a sake shi, za ta ganshi ya fito. Tana nan zaune, wasu suna ta fitowa, 'yan uwansu suna ta murna, sai dai shiru-shiru ba ta ganshi ba. Nan hankalinta ya tashi, ta sake nufar wurin masu gadin ta ce "Wai haryanzu ban ganshi ba, kuma yau aka ce mini za a sake shi" "Waye ya ce miki za a sake shi?" Wani gandiroba ya tambayeta. "Yayana ne" "Yayan naki alƙali ne? Ko shi ya kawo shi nan ɗin, wanda zamu saki kenan yau sun gama fitowa" "Innalillahi na shiga uku" ta faɗa a raunane. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA Kina bukatar kaya masu kyau da inganci?? Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba?? Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta?? Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki. Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955 Da kallo suka bi jauhar, ganin yadda take yi musu kuka wiwi, wani gandiroba ya ce "Koma tsallake, idan ki ka gama kukan, sai ki tafi". Ta juya ta kama hanyar tafiya, tana ji a ranta kamar duk duniya, babu wanda ya kaita rashin sa'a. Sannu a hankali yake tunkaro gate ɗin fitowar, zuciyarsa cike da mamakin yadda aka sake shi, dan bai san ma zai fita ba, sai yau ɗin. Tsayawa yayi bayan ya fito daga cikin gate ɗin, ya lumshe idanunsa sakamakon hasken ranar da ya ji ya yi wa idanuwansa yawa, sannu a hankali ya cigaba da buɗe su, har ya ji hasken yayi dai dai da abun da idon nasa yake buƙata. Kamar an kira sunanta ta waiwayo, ta hangoshi a tsaye, shi ma ita yake kallo da mamaki, ba ƙaramin kashedi ya yi wa su liti ba, a kan kar su kuma ɗaukarta su kaita in da yake. Da sauri ta nufo shi, ta kasa tsayar da hawayenta ta na wata irin ajiyar zuciya ta ce "Har na ji daɗi, da suka ce mini, ba za su sake ka yau ba" Yayi shiru yana kallon ta. Ƙare masa kallo take yi, an yi masa aski an aske masa sajensa da gemunsa, sai ɗan kaɗan da ya fara fitowa, idanunsa sun washe yayi haske, saboda babu kayan shaye-shaye a nan, sai dai ya rame sosai. Kallonta kawai yake yi, kamar wata baƙuwar halitta, sai dai bai yi mata magana ba. Tayi ajiyar zuciya ta ce "Mu tafi?" Ya jinjina mata kai yayi gaba. Ta ɗaga ƙafarta kenan takalminta ya tsinke, ta durƙusa ta cire takalmin ta ce "Takalmina ya tsinke" ya kalli ƙafarta sannan ya dubeta, ƙafarta busu-busu, duk yadda ya santa da gayu, ko ba ta gaya masa ba, ya san tafiyar ƙafa ta yi. Ta tsayar musu da abun hawa suka hau, sai dai har suka je in da za su sauka, duk surutun da take yi, ko sau ɗaya bai tanka mata ba. A titi suka sauka, saboda kuɗin motar ba zai isa a shiga da su har ƙofar layin ba, har ta yi gaba, ya janyota ya cire mata takalmansa ba tare da ya ce komai ba. Ta ce "A'a ka saka kar ka taka wani abun". Kallon da yayi mata, ya sanya ta yin shiru, ta saka takalman kamar zata tashi sama a kansu suka shiga layinsu, kamar ta taka rawa, master ya fito. A falo ya zauna, ya kashingiɗa ya lumshe idanunsa, ta shiga banɗakinsa, ta haɗa masa ruwa mai zafi, ta ce "Master ga ruwan wanka na kai maka" bai yi mata musu ba, ya tashi ya tafi, kafin ya fito ta jera abinci a falo, ya yi wankan ya fito falo, ya tarar da abinci, yanayin yadda yake cin abincin ya tabattar mata da yana jin yunwa sosai duk da dama can acici ne. Yana so yayi mata magana, amma ya rasa me zai ce mata ma, ya gama ci ya tafi ɗakinsa ya kwanta, dan surutunta ya fara takura shi, duk da yayi kewar abubuwa da yawa a tare da ita, sai dai yadda yake jin zuciyarsa a cunkushe babu daɗi, ya sanya shi jin surutunta ya gundure shi. Allah ya taimaketa, ya wuni a ɗaki, bai fita ko ina ba, tun da ya dawo. Hafsa kuwa ta samu abun yi, dan tun da Allah ya sa ta mallaki lambar wayar Alhaji mu'azzam, take kiransa a waya, da sunan rarrashin sa a kan rashin jauhar, tare da ƙoƙarin sake ɓata jauhar ɗin a wurinsa. Mahaifiyarta ta sake miƙewa wurin shige-shige a kan Allah ya tabattar da lamarin aure tsakanin hafsa da Alhaji mu'azzam. Cikin ikon Allah, idan ta kira shi, yana amsawa ba ya yi mata wulaƙanci ko makamancin haka, hakan ya sa ta cigaba da ƙoƙarin cusa kanta cikin hikima da kissa. Sannan suka yi ƙoƙarin rufe wa mama duk wani abu da yake faruwa, ba ta san halin da ake ciki ba. Kasancewar Al'amin ya fito ya dawo gida, ya sanya jauhar yin isashshen baccin da rabonta da shi, tun kan a rufe shi, dan bayan sallar asuba da ta kwanta, ba ta farka ba sai goma saura. Ta fito tsakar gida da sauri, ta fara aikace-aikace, ta dafa tea ta soya dankalin hausa. Ta dafawa Al'amin ruwa a heater, ta je ƙofar ɗakin ta tsaya tana sallama. Ƙasa-ƙasa ya amsa, ban da yana da buɗaɗɗiyar murya ma ba za ta ji ba, ta shiga tana sake yin wata ta ce "Ina kwana master" "Lafiya ƙalau" "Ban san ka tashi ba, yau na makara da na fara kawo maka ruwan wankan ai, bari na haɗa maka" ta haɗa masa, yanzu ma bai yi musun yin wankan ba, ya tashi ya shiga banɗakin. Ɗakin fes yake, amma ta din da karkaɗe karkaɗe, da goge-goge, ta kunna turaren wuta, ta fito masa da kaya ta saka musu turare. Ya gama ya fito, jikinsa yana ɗigar da ruwan wanka, ya ɗauki dogon wando ya saka, ya zube mata wanda ya cire a kan katifa ya fito. Kallo ɗaya tayi masa ta kawar da kanta gefe ta ce "Ba ka saka rigar ba, na fito maka da ita ma". "Ba na buƙata, wandon ya isheni". Jauhar ta ce "To ai kar ayi sallama, a ganka a haka". "Ki koma ɗaki idan ba zaki iya kallona a haka ba" yayi maganar yana zama. Ya kalleta ita ma yau ba hijjabi a jikinta, doguwar rigar material ta saka, mamaki yake yi, yadda ta yi duhu, ga wani uban ƙashin wuya da ya fito mata, tayi rama sosai da sosai, ashe jiya dan ya ganta a cikin hijjabi ne ya sanya bai gane ba, sai ya ji ransa babu daɗi. Ta haɗa masa abincin ta miƙa masa, ya ɗauka zai kai baki ta ce "Bisimillah" a zuciyarsa ya maimaita sannan ya fara ci. "Askin nan da aka yi maka, ka yi kyau, sai dai ban so aka aske gemun ba gaba ɗaya" Idan ba gizo idanunta suka so yi mata ba, da murmushi zai yi ya shanye abun sa. Ta tanƙwashe ƙafarta ta sake cewa "Sannu master, a prison ɗin ma duka ake yi, na ga bayanka duk shaidar duka. Wallahi ba zan taɓa yafewa wanda suka yi maka sharri ba, ban taɓa shiga tashin hankalin da na shiga ba, na san baka ta'mali da wannan abar, sauran ma zaka daina wataran in sha Allah" tayi maganar hawaye na cika mata ido. "Kun kusa gama exams ko?" Jin yayi magana ya sanya ta saurin ce wa "Eh, cikin azumi zamu gama in sha Allah" "Allah ya taimaka" "Amin na gode, baka tambayeni kwaɗinka da ƙadangaru ba?" Ya rausayar da kai ya ce "Ai naki ne ba nawa ba" hakan yayi da kammala cin abincin. Ta ce "Alhamdilillahilazi aɗa'amana haza, warazaƙatana min gairi haulin minni wala ƙuwwa, Ubangiji Allah ya ciyar da mu na anjima" tayi maganar tana tattare kwanukan. Kafin ta dawo ya ɗauki pillown kujera ya kwanta. Ta je gabansa, ta durƙusa ta kai hannunta goshinsa ta ce "Wai haryanzu kana zazzaɓin ne?" Ya girgiza kai alamar a'a. "Master duk ka yi wani iri kamar an canza mini kai" duk lokacin da ta danganta shi da ita, sai ya ji wani abu a ransa da bai san Menene ba. Yana daga kwance ya din ga miƙa, yana ɗan banƙare kafaɗunsa zuwa bayansa. "Ciwo bayanka yake yi ne?" Ya gyaɗa mata kai alamar eh. "Bari na ɗaukko man zafi na shafa maka zaka ji daɗi, naga wani raunin bai gama warkewa ba". Ya jinjina mata kai, sai dai bai buɗe idonsa ba. Ta je ta ɗauko man, ta dawo ta zauna a bayansa, tana shafa masa a hankali. Ta ce "Juyo" ya gyara kwanciyar sa a hankali, jikinsa wasu wuraren duk shaidar yankan wuƙa, bayan tabon duka. Haka kurum zuciyarta ke raya mata, kai hannu kan gashin da yake kwance a ƙirjinsa, da sauri ta rintse idanunta ta kawar da wannan tunanin ta kira sunansa. "Master" "Mmm?" Ya amsa idonsa a rufe. Ta ce "Ka na jina?" "Mmm" A ɗan shagwaɓe ta ce "To ka kalle ni, magana zamu yi fa" Ya buɗe idanunsa a kanta, take ta sunkuyar da kanta, saboda wani irin nauyi da kwarjinin da idanun nasa suka yi mata, a tunaninta ta daina jin tsoron sa, ashe haryanzu da sauran rina a kaba, yayi mata shiru yana kallonta yana jiran tayi maganar, sai dai ta kasa. Gaba ɗaya sai ta diririce, ta kasa maganar sai cigaba da shafa masa man zafi a wuri ɗaya a kafaɗarsa. Hannunsa ya saka ya cire nata, ya karɓi man zafin ya ajiye, ya ce "Ya aka yi?" "Dama sonake na ce dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, na yi sanadiyar shigarka wahala, duk laifina ne da ban gaya maka an kawo maka saƙo ba, ka yi haƙuri mantawa na yi ka yafe mini dan Allah" "Idan naƙi fa" yayi maganar very serious. Cikin damuwa ta ce "Please dan Allah ka yi haƙuri" "Zan duba, ki je ki yi karatunki saboda exams" ta jinjina kai ta tashi, tsakar gida ta fita ta hau wanke-wanke, ta ɗaukko kayansa da ya cire, da wanda ya dawo da su daga prison, ta jiƙa su dan ta wanke. Wasila maƙwabciyarta ce tayi sallama, kasancewar ƙofar ba a rufe take ba, jauhar ta ce "Anty wasila sannu da zuwa ga kujera" "Yauwwa jauhara, ashe mai house ya dawo, jiya na ji halimatu ta ce ta ganku, na zata sharrinta ne ma, na zo ɗazu tun takwas da rabi, na yi ta bugu baki buɗe ba na ce bari na tafi, su jauhar ana can jikin miji an liƙe ba a tashi ba" Jauhar kawai ta yi murmushi tana fatan Allah ya sa bai jiyo ba, tun da yana falo a kwance. Ta ce "Jiyan ya fito, ban samu na shigo na gaya muku ba ke da maman halimatu". "Allah sarki jauhar, kin sha wahala shikenan kuka ya ƙare, ki daina anty wasila ba ki san me nake ji ba, zuciyata kamar ciwo take, Allah dai ya bar wannan ƙauna, zuciyar ya daina ciwo ko?" Dariya kawai jauhar take yi ta ce "Ta daina" "To ai da kamata yayi, da ki ka san zai fito, ki yi magana ayi gyare-gyare a gyara masa turaka, ki zo na baki kayan maman nihal Anty maryam, na sanmiki kayanta ki gwada ki ji, ai ba kya yi shiru ki zauna haka ba" (Ga mai buƙatar jarraba kayan maman neehal sai ya tuntuɓeta ta wannan lambar 0706 677 4630). Wasila ta din ga sakin layi, sai da jauhar ta ce "Anty wasila yana nan fa, yana falo yana jinki" Tayi ƙasa da muryarta ta ce "Na shiga uku, kuma ki ka bar ni nake ta zuba, amma baki kyauta mini ba". Ta durƙusa ta kwashi takalmanta cikin sanɗa, ta fice, jauhar ta din ga dariya, ta rufe ƙofarta, sai dai ita ma shiga falon ya gagareta, saboda kunyar abun da wasila ta din ga faɗa, dan ta san halinsa, sai ta sakankance, bacci yake yi, ta ga idonsa biyu. Ta jima tana raɓe-raɓe kafin ta shiga ɗakin, baccinsa yake yi, sosai take jin tausayinsa, yanayin yadda yake miƙa ma, kawai ya tabbatar mata da zaman gidan kaso bai yi masa daɗi ba. Tana ta dirzar kayansa, ta ji an yi wani irin fito a waje, sannan aka buga mata gate, ta saka hijjabi ta buɗe ta ga su walid. Ta ce "Yaya walid, ina wuni" "Madam dama mutumin nan ya fito baki sanar mana ba? Sai yaran da muka saka gadinki ne suka faɗa mana". "Dan Allah ku yi haƙuri, na san zai neme ku, bacci yake yi ne". Liti ya ce "Ko dai ki ka ɓoye shi ki ka hana shi fitowa" Ta ce "A'a na isa? Ban hana shi fitowa ba, ina dai roƙon Allah ku bar mini shi, na san dole dai zai zo in da ku ke". Walid ya sake wani irin fito, tana waiwayawa ta ga har ya zira riga ya fito. Saroro ta yi ta tsaya tana kallon sa, ya ƙaraso, zai raɓata ya wuce. Jiki a sanyaye ta ce "Fita zaka yi? Ban gama ganinka ba fa" Kallonta ya yi, ya raɓa zai wuce ta ce "Dan Allah Master kar ka sha komai, ko ka je in da ake aikata laifi, dan Allah" maganar da tayi, har hawaye ya cika mata ido. Bai kulata ba ya fita, gaba ɗaya sai ta ji garin yayi mata babu daɗi, duk da tana cikin shauƙi, da farincikin dawowarsa. Tana jin shewar su walid, da suka ganshi, ta ja jikinta, ta koma ɗaki, aikin ma ta kasa cigaba, kawai ta saka kuka, kasancewar shi ne kaɗai abun da take yi, ta rage damuwarta, sai kuma tsananta ambaton Allah. Tun wannan fitar da yayi, tun tana saka ran dawowarsa, har ta cire rai, dan har magariba ba ta kuma saka shi a idonta ba. Tayi ta addu'a a ranta, Allah ya sa yana lafiya. Har bayan goma na dare, ta kasa kwanciya, sai sha ɗaya da wani abu, ta ji yana rufe ƙofa, ta fito falo da sauri, ya shigo yana haska fitilar wayarsa, gaba ɗaya falon ya gauraye da warin wiwin da yake yi, jikinta yayi sanyi ta kasa yi masa magana, yadda yake tafiya ya tabattar mata da a buge yake, ya wuce ta ya tafi ɗakinsa. Ta nemi wuri ta zauna a wurin, ta haɗa kai da gwiwa, ta din ga kuka ƙasa-ƙasa, ta tashi ta nufi ƙofar ɗakinsa ta leƙa, ɗakin duhu, sai dai tana hango hasken wutar jikin sigarinsa, ta juya ta koma ɗakinta, ta ji tana neman sarewa, kamar Allah ba zai karɓi addu'arta a kan sa ba, da sauri ta din ga istigfari, ta nemi wuri ta kwanta. Da safe da ta tashi, ba ta ko nufi ƙofar ɗakinsa ba, sai da ya fito ya tarar da ita a falo, tana shirin dutse. Cikin girmamawa ta ce "Ina kwana" "Lafiya ƙalau" ya zauna a kan doguwar kujera, ta ce "Afuwan kar ka ga ban kawo komai ba, wallahi ba kuɗi a hannuna ban girka komai ba" Bai yi magana ba, sai kamar bayan mintuna goma, ya ɗauki wayarsa ya ɗan danna ya saka a kunnensa. "Kawo mini bredi da lipton, kayan tea dai na dubu biyu, kawo mini gida ka karɓi kuɗin". Ya ajiye wayar. Jin wayar da ya yi ya sanya ta tashi ta ɗora tea, kasancewar da wuta ta ɗora a heater. Tana cikin kwashe tea ɗin, ya fito ya je ya karɓo kayan shayin, ya ajiye mata a ƙofar kitchen. Ta ce "To, Allah ya saka da alkhairi" Ta ɗauka ta dudduba, da yabi ta ita, iya buredi da sugan ya isa, sauran kuɗin ko taliya sa saya, ta ɗauka ta soya ƙwan, ta kawo kayan karin. Shikaɗai ta haɗawa ta koma gefe, ta cigaba da shirinta. "Wannan shirirtar ta fi ki karya kumallo?" Ta girgiza kai ta ce "Ba na jin yunwa ne, zan karya amma". Gaba ɗaya ba ta walwala,  duk surutun nan ma da take yi masa, yau bakinta shiru, ta kunna mp ɗin ta, ta ajiye a gefe, tana saurar radio, ana ta zancen za a tafi yajin aiki, saboda tsadar rayuwa da rashin ingantacciyar rayuwa ga ma'aikata. "Amm Angela ki ke ko?" Tayi murmushi ta ce "Ko 'yar madara ba" tayi maganar cikin ƙoƙarin ɓoye damuwar da take ciki. "Koma dai wanne ne, magana ce da ni" Ta ce "To" ta ajiye kayan abun da take yi, ta fuskance shi, amma ba ta yadda sun haɗa ido ba. "Kalleni, idan ina magana na fi son ki kalleni, ki daina sunkuyar da kai" Kallo ɗaya tayi masa ta sake sunkuyar da kai ta ce "Ba zan iya ba ne, wani abu nake gani a cikin idon naka da yake bani tsoro" "Kin kusa daina gani, wata shawara na yanke a kan zamanmu, ni wannan yawan koke-koken da ki ke yi, da wahalar da ki ke sha ba na so, jin sa nake yi kamar wani nauyi a kaina, kuma ni gaskiya ba zan iya daina wasu abubuwan ba, ina saka ki a damuwa da matsala sosai, ga rayuwar ki a cikin hatsari, duk saboda ni. Kina takura rayuwata sosai da sosai, nima kuma ma san ina takura ki dan haka na yanke shawarar kawai na sauwwaƙe miki, ki koma gida Allah ya baki wani mijin ki yi aure, ni ba na buƙatar mace a cikin rayuwata". Tun da ya fara maganar, ta ji kamar an jona mata shocking, zuciyarta ta din ga bugawa da wani irin sauri, ta rasa me ma za ta ce. Sai da ya kammala tsaf, sannan cikin ƙarfin hali ta kalleshi ta kawar da mai ta ce "Wannan ne tukuicina kenan? Baka buƙatar mace a rayuwarka, nima ƙaddara ce ta kawo ni in da ka ke, na zata idan na jure na cigaba da yi wa baba biyayya, na yi biyayyar aure, komai zai wuce, zan ci riba, amma yanzu na fuskanci ni ce mara sa'ar, ko ina ba a buƙata ta,  yanzu tozarta maraicina shi ne ka ga ya dace da ni, har ya sanya ka ce ba zaka yafe mini ba jiya? shikenan ka bani a rubuce na kai wa baban, na gode master, amma duniya da ba a yafiya da mu zo i yanzu ba, na san nayi maka kuskure amma na baka haƙuri, amma ka sani idan ka sake ni, ka tozarta maraici" ji tayi numfashinta ya yi wa ƙirjinta nauyi, kawai ta tashi jikinta na rawa. Tsananin fargaba da tashin hankalin maganar da ya gaya mata, ya sanya period ya zo mata ba shiri, har jikinta ya ɓaci, dama sauran kwana ɗaya ya zo. Har tayi maganar ta gama, ba ta kalleshi ba ko sau ɗaya. A ransa ya din ga maimaita ;idan ka sake ni, ka tozarta maraicina. Ita a tunaninta abun da ya faru ne ya sanya ya ce zai rabu da ita? Marainiya ce kenan? Ya tambayi kansa a lokaci ɗaya ya bawa kansa amsa da no wonder. Sai kuma jikinsa yayi sanyi, shi wannan wahalar da take sha, ya ɗauka za ta yi murna da abun da ya ce, kawai ya basar ya kwanta. Sosai ta din ga kuka, a ɗakinta, tana tunanin wane irin baƙin jini ne da ita haka? Duk yadda take haƙuri tana lallaɓa auren nan, amma ya yi mata wannan sakayyar, take ta fara tunanin wane irin zama zata koma ta yi a wannan gidan na su, da suke nuna mata ƙiyayyarsu a fili? Da ƙyar ta shiga banɗaki ta gyara jikinta, ta fito zauna a ƙasa ta cigaba da kuka. Bayan ya gama abun da yake yi, ya fice ya bar gidan. Kanta ne ya fara ciwo, ga numfashinta da yake ta barazanar ɗaukewa, ga wani irin azababben ciwon mara da yazo mata da zazzaɓi duk a sanadin tashin hankalin maganganun Al'amin. Yaya saifu kuwa tun da ya dinga bibiya, aka tabattar masa da an saki Al'amin, hankalinsa ya kwanta, ya so ya je gidan nata ya tabattar amma har ga Allah ba ya ƙaunar shi, duk da sau ɗaya ya taɓa ganinsa, ranar ɗaurin auren a masallaci, kawai a jikinsa yake jin azabatar da jauhar yake yi, dan ba zata faɗa bane kawai. Al'amin kuwa, su walid suna ta hirar irin tashin hankalin da matarsa ta shiga, da aka kai shi prison, da irin aiken da ta din ga yi masa da kayan amfani yana prison. Gaba daya sai ya tafi lissafin yanzu idan ya saketa, to abinci fa? Amma shi duk da haka gani yake hakan ne mafita, wannan tashin hankalin da take shiga idan ya shiga cakwakiya, sai ya ga kamar yana shiga hakkinta da yawa, kuma a idonta yake ganin damuwa idan ta ganshi a halin maye. Da daddare da ya dawo, yadda ya fita ya bar kayan karin kumallo, haka ya dawo ya tarar da su, ba ta taɓa ba, sai yayi tunanin ko wani abun ta ci, dan haka ya ƙarasa hallake buredin da ƙwan, ya shige ɗakinsa ya cigaba da busa hayaƙi cikin nishaɗi. Washegari ya din ga zaman jira, ya ga ta fito ta yi abun karyawa, amma shiru, gashi bayan sallar asuba ya yi shaye-shaye dan haka yunwa yake ji sosai. Ganin har sha ɗaya ba ta fito ba, ya sanya ya fice, sai dai kuma yajin aiki ake yi, da ƙafarsa ya tafi unguwar su, wurin su Walid. Yau ko tsintsiya jauhar bata ɗauka ba, tana ta fama da kanta, da la'asar ya dawo, ya sake tarar da gidan yadda ya bar shi. Gaba ɗaya sai gidan yayi masa wani iri, ya kwashe kwanukan da ya karya da su jiya, ya fara tunanin ko fushi tayi, shi ne ya sanya taƙi yin shara a gidan. Yana tsaye yana kallon falon, ya ɗaga kai ya ga ta fito daga ɗakinta, kamar fuskarta ta kumbura. Ya tsaya yana kallonta, ya ga tana ɗaga ƙafa da kyar a hankali. Kawai ta yanke jiki ta faɗi a wurin, a sukwane ya yo kanta, ya ɗagata. ta motsa da ƙyar, hannu ya saka ya juyota jikinsa sosai, wani irin hucin zafi jikinta yake fitarwa, ta ɗaga idonta da ƙyar ta kalle shi, idanunta sun yi ja sosai da sosai ta mayar da su ta lumshe. Hankali tashe ya ce "Menene?" "Kaina ne zai fashe" tayi maganar hawaye na bin gefen fuskarta, kafin yayi magana, jikinta ya hau karkarwa, haƙoranta na karo da juna, idonta na neman juyewa saboda zafin zazzaɓi da matsanancin ciwon kai. Ɗagota yayi sosai ya ce "Ki na ji na?" Ta ɗaga masa kai da ƙyar. "Zan je in samo abun hawa, mu je asibiti" "Yajin aiki ake yi, ka manta?" tayi maganar a galabaice. Sai yanzu ya tuna, dan da ƙafa ya je yawonsa ya dawo, ƙungiyar ƙwadago na jagorantar yajin aiki da kuma zanga-zanga domin janyo hankalin gwamnati a kan wasu haƙƙoƙin 'yan ƙasa. "Na sani, yanzu zan dawo" Ba tare da ya san in da zai nufa ba, ya kwantar da ita kawai ya fita, a ransa yake jin idan ya bar yarinyar nan da ciwo, bai yi wa kansa adalci ba. A titin unguwar, ya ga wani ɗan adaidaita sahu, ya tsayar da shi ya ce "Malam mara lafiya zaka ɗaukar mini" Mai baburin ya ce "A'a yi haƙuri ba aiki na fito ba, ba ka san ana yajin aiki ba ne maigida?" "Ana yajin aikin amma ka fito da babur?" "Eh na yi wani uzuri ne, gida zan koma". A ɗan hasale ya ce "Mara lafiya zaka ɗaukar mini" Shi ma a hasale mai baburin ya ce "Na ce ba zani ba, ana dole ne? Ka nemi wani mana" A fusace ya daki tayar gaban adaidaita sahun, mai napep ya waro ido ya ce "Malam meye haka?" Kawai ya shiga bayan adaidaita sahun, ya zare wuƙa ya ce "Bi cikin layin nan, ko na zaro hanjinka yanzun nan da russia" tsit mai ɗan sahun yayi, ya bi layin tare da yin sarandar ƙwace masa baburin ma zai yi. A ƙofar gidan ya saka shi yayi parking, ya sauka ya ƙwace mukullin babur ɗin, ya shiga cikin gidan da shi. Ya ɗauko hijjabinta ya saka mata. "Master" Ya kalleta ba tare da ya amsa ba, ta ce "Yi haƙuri, na saka wahala" "Ki yi mini shiru" Ta ce "To" ya ɗaukkota kamar matacciya, ya shiga da ita napep ɗin. Ya ciro mukullin ya miƙa wa mai baburin ya karɓa yana cunkusa fuska ya ce "Megida amma ka san yajin aiki ake yi, ina zan kai ku? asibitin gwamnati babu aiki". Al'amin ya ce "Ko ma wane asibitin ne mu je" Kamar wata 'yar kyanwa, haka ta kwanta luf a jikinsa, da suka hau kwalta, sai sanyin da take ji ya ƙaru, dan haka ta ƙara shigewa jikinsa, jikinta na ta rawa. Wani Asibitin kuɗi ya kai su a gadon ƙaya, Al'amin ya cilla masa dubu ɗaya, ya rungumi jauhar ya shiga da ita. Ba a taɓa ta ba, sai da ya biya kuɗin file da komai, sannan aka fara yi mata abun da yakamata. suka shiga wurin likita, aka tambayi sunanta, ya manta surname ɗin ta da ya gani a invitation ɗin su, dan haka ya ce a saka mata Zahra Al'amin, shekaru ya ce bai sani ba, sai kintata akayi, aka tura su yin gwaje-gwaje. Bayan sun dawo,ikitan da ya duba ta, yayi ta mita malaria tayi mata mummunan kamu, ga ulcer kuma ga jininta ya hau. Al'amin ya ce "Malam ba lissafi ko masifa zaka yi mini ba, ayi mata abun da yakamata kawai" yanayin yadda yayi maganar, ya sanya likitan gane waye shi. Sai dai Al'amin yayi mamakin jin an ce jininta ya hau. Likitan ya ce "Tana da aure ne?". "Eh" Likitan ya ce "Ayi gwajin ciki, kar mu yi treatment da ka". Al'amin ya ce "Babu ciki" Likitan yayi saroro yana kallonsa. "Malam ni ne mijinta, babu wani ciki, ka yi sauri a fara yi mata abun da yakamata, tana ta murƙususun ciwo. Ko ba ka yadda ba? Al'ada take yi, ko kuna ganin cikin kwana ɗaya ne ko biyu?" Likitan ya ce "Ikon Allah" Jauhar duk da tana fama da kanta, wata irin kunya ta rufeta, ya aka yi ya san tana period ma. Tana ta yinƙurin amai, sai dai babu komai a cikinta, aka ce ya samo mata wani abun ta ci, kafin a fara treatment. Ya fita ya sayo uwar gurasa mai nama, da ruwa ya kawo mata. Ya zo ya tarar, an saka mata ruwa, da allurai. Ya kalli fuskarta, bacci take yi sosai, tana iya ƙoƙarin ta a kan sauro, kar ya cije ta, ba ita ba har shi, da magariba ta yi za ta hau rufe ko ina tana kunna maganin sauro. Abun da bai sani ba, tsananin damuwar da ta shiga bayan kama shi, da maganganun da ya gaya mata jiya ne suka haifar mata da ciwon. Sai dai babbar damuwarsa, hawan jinin da aka ambata. Sai wajejen magariba, ta ɗan samu afuwa. Wajen isha'i aka sallame su, suka yi mata wasu allauran, aka ce masa maza ya kaita gida, alluran suna kashe jiki. Duk kuɗin jikinsa sai da suka ƙare, suna fitowa harabar asibitin, jikinta ya saki ta tafi zata faɗi, ya riƙeta da ƙyar suka fita, sai dai gaba ɗaya titin babu ababen hawa. Ganin sai tangaɗi take yi, kuma bashi da wata dabara ya sanya, ya ɗaure ledar magungunan ta, ya ɗaga ta ya saɓa a bayansa, ya ɗauki takalmanta ya riƙe a hannunsa, ya zagaya ya bi lunguna. A din ga yi ana sauke hakki, idan baki saya ba 0009450228 Aisha Adam jaiz bank Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA Kina bukatar kaya masu kyau da inganci?? Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba?? Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta?? Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki. Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955 A ƙalla ya kai awa ɗaya da mintuna talatin, yana tafiya da ƙafa, bayansa ɗauke da jauhar, wani wurin idan da mutane, ayi ta kallonsa, tun da sauran sahun mutane, har ya zama saura ɗai-ɗai. A haka ya isa gida, ya buɗe gidan, ya shiga da ita ɗakinta ya kwantar da ita, zazzaɓin jikinta ya sauka, sai dai gaba ɗaya jikin nata ya saki. Ya kunna fitilar wayarsa yana haskata. Surutai take yi, wanda tun suna hanya take yi, sai dai ba ya gane me take faɗa sai yanzu. "Allah ka shirya mini mijina, Allah ka sa ya daina abun da yake yi. Ya Allah, Allah ka sa ya shiryu. Allah na san ba zaka kunyata ni ba, Allahumma inni as'alukal jannata wa na uzubika mina narr. Rabbana hablana min azwajina, wa zuriyyatuna ƙurattu a'ayunun waja'alna lil muttaƙina imama. Rabbigfir ummi wa abi, warahamhuma, kama rabba ya ni sagira" ta ƙarasa tana shafar fuskarta, da tafukan hannayenta, hakan ya tabattar masa da addu'aoin ta ne na salla, take maimaitawa. Ya lulluɓeta, ya tashi ya sake fita, sai dai abubuwa daban-daban suna ta cigaba da kai komo a zuciyarsa, ya ji ƙwarai yana son sanin wacece yake zaune da ita a matsayin mata, shi dai ya san ba shi da nagartar da uban kirki zai bashi auren 'ya, idan ba da wata a ƙasa ba. Cikin gari ya sake ninkawa ya tafi, bai zarce ko ina ba sai gidansu, ya tarar har sun rufe ƙofa. Bugawa ya fara yi iya ƙarfinsa, Abba ya zo ya buɗe, yana ganin Al'amin ya ruga da gudu ya koma, saboda yana bala'in tsoronsa. Ba tare da ya kula kowa ba, ya shiga kitchen, ya dudduba babu komai sun cinye abincin. Rahila ta fito, ta ce "Kai Aminu lafiya ka zo mana a wannan daren? Yaushe aka sako ka?" "Shahida" ya ƙwala mata kira, kasancewar ya hangota a falo. Cikin hanzari, ta fito ta ce "Gani yaya" Yayi mata alama ta shiga kitchen, ta shiga ya bi bayanta, ya ce "Dafa mini shayi cikin flask ɗin nan" yayi maganar yana nuna mata flask ɗin shayinsu, family size. "Wai Aminu me ka ke yi haka, dan me zaka sakata girki a wannan tsohon daren?" Bai kulata ba, ya kwaso ƙwai ya zube mata ya ce "Ki soya mini wannan ma". Rahila ta koma bedroom ta taso Abbu ta ce "Ta so, ga ɗanka can ya zo a wannan tsohon daren, kar ya yi mana ɓarna". Abbu ya taso ya fito, dan ya fara bacci ma. Ya fito yana faɗin "Kai Al'amin lafiya, ka zo mana a daren nan? Ina matar taka ina gidan naka?". Shahida ta ce "Abbu ka koma ka kwanta, ba wani abu, girki kawai ya ce na yi masa". "Kuma a daren nan, ina matar ta sa?". Abbu yana ta ɓaɓatu, Amma Al'amin bai kula shi ba, sai ma ɗaukko ledar viva, ya buɗe fridge ya kwashe lemon ɓawo ya zuba a ciki, kankana da sauran abubuwan da ya gani a ciki har da su madarar ruwa. "Ka yi masa magana, wannan kayan da yake ɗiba ina zai kai su?". Al'amin ya kalli rahila ya ce "Da kuka aura mini 'yar mutane, ai kun san bani da abun yi, in bari yunwa ta kasheta ko na fara satar kayan mutane ne na kula da ita? Ba ta da lafiya dan haka dole na fito na nemi abun da zan kai mata ta ci". "Da can kai da me ka ke riƙe kanka, ba sai ka nema ba, kuma saboda lalacewa da abun kunya, daga gidanku ne za a ciyar maka da mata? Al'amin ya waiwayo a fusace, ya nunata da yatsa ya ce "Ki kiyayi lokacin da haƙurina zai ƙare a kanki" Shahida ta ce "Yaya gashi na gama, ka ga akwai su maggi ma a nan, tayi maganar tana buɗe drower tana ɗaukkowa. Ta buɗe wata ta ɗebo su taliya da macaroni ta ce "Ka haɗa da su"ya girgiza kai ya ce "Ban da wannan, wannan sun isa" Ta sake cewa "Yaushe zan zo gidanka, ina son kan na koma school na zo muku ziyara, tun da ba ma nan aka yi bikinka, samu zo mu dubata" A taƙaice ya ce "Sai kin zo". Ta ce "Wannan ɗin sun isa, ko kuna buƙatar wani abun?" Ya ce "A'a, sun isa. zo ki rufe muku gidan" ya ƙarasa maganar yana kwasar kayan, ya nufi hanyar ficewa. "Al'amin" Abbu ya kira sunansa, ya tsya cak bai waiwayo ba. "A tunanin auren nan da aka yi maka nutsuwa zaka yi, ka daina wasu abubuwan da ka ke aikatawa, amma abu ya ci tura, ka sanya 'yar mutane a tasku da tashin hankali, meya kai ka ta'amalli da hodar iblis?. Lokaci yayi da yakamata ka daina wasu abubuwan, ko dan kare mutuncinka da na iyalinka. Ko dan ka ga ka sameta a ɓagas ka ke nema ka wahalar da rayuwarta" "Kaga Abbu dan Allah ka daina jan maganar nan, ya tafi kawai su je can su ƙarata, dama ai ba ji take ba ita ma, daidai da ita ne" Wani abu mai nauyi ya haɗiye, ya saka kai ya fice, ba tare da ya sake cewa uffan ba. Bayan ya tafi, Shaida ta ce "Mama dan Allah ki daina tayar da hankalinki a kan yaya, idan yana wannan abubuwan ki zuba masa ido, tun da ba kullum yake zuwa ya yi ba. Abu ɗaya kawai yake buƙata yayi iko da kayan mahaifinsa a matsayin sa na ɗa, kamar yadda muke yi, kin san fa ke da shi, ba kwa jituwa ki din ga kawar da kai a wasu abubuwan da yake yi, yana ɗaga miki ƙafa fa kar yayi miki wata illar". Abbu ajiyar zuciya ya yi, maganganun shahida gaskiya ne, amma shi babban takaicin sa, Al'amin ba ɗan da za a haɗu a rufawa kai asiri bane ba, miyagun halayensa ya sanya ba ya son ya zo ko in da yake. Gaba ɗaya auren da aka yi masa bai sanya ya nutsu ba, kodayeke da sauƙi tun da ya san ya fito ya nemi abun da zai bawa 'yar mutane. Ya koma ɗakinsa, Rahila ta bi bayansa, Amira ta ce "Ohh yau ni nake ganin tsiya, yanzu fa sai a ce ciki ne da ita ko?" Shahida ta ce "Ba abun mamaki bane" "Taɓ, a wannan muzuran da tashin hankalin nass har ta ɗau ciki, iko sai Allah" Al'amin ya sake ninkawa, ya koma gida ya shiga ɗakinta, ya tarar tana ta baccinta, kamar ya tashe ta, sai ya fasa, ya koma ɗakinsa ya kwanta. Bai farka ba, sai wajen tara na safe, a gaggauce ya yi sallar asuba, ya fito falo, ba ta nan ya shiga ɗakinta, tana kwance ta takure wuri ɗaya. "Kin tashi?" Ta jinjina masa kai almar eh. "To taso ki karya ki sha magani" Ta ce "To, bari na yi wanka nayi brush" A hankali ta lallaɓa jikinta, ta shiga ta yi wanka, ta canza kaya ta fito falon. Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Ina kwana?" "Lafiya ƙalau, bari na kawo miki abinci" Kitchen ya je ya ɗaukko kofi, da shayin da ya zo da shi a flsk, da uban ƙwan da ya saka shahida ta soya masa. Ya ajiye mata a kausashe ya ce "Gashi nan ki karya, ki sha magungunan da suka baki. Saura ki ƙi ci wani ciwon ya kuma kama ki" Ta na fara ci ta ji ta ƙoshi, amai ma take ji. "Wai ba kya so ne ki ke jagwalgwalawa?" Ta ce "Na ƙoshi ne" "A ɗan abun da ki ka ci ne har kin ƙoshi" ya taɓe baki, ya miƙa mata magungunan ta karɓa ta sha. Ya bata wayarsa ya ce "Saka mini lambarki, idan da wani abuk sai ki kira ni fita zan yi" Kallonsa tayi da mamakin yana sane ko wulaƙanci ne, ya sanya yake tambayarta lambar waya. "Bani da waya" ta amsa kanta a ƙasa. Ya mayar da wayarsa aljihunsa ya ce "Shikenan, maganar da nayi miki, ki yi tunani a kai, a ɓangarena ni ina ganin hakan shi ne mafita kawai, amma ki yi tunani abun da ki ka yanke, ki sanar da ni". Dummm ƙirjinta ya buga, kenan haryanzu yana kan bakansa? Ba ta ce masa uffan ba, ya fice. Rasa abun yi tayi, duk da ba ta da tsarki, tayi alwala ta zauna ta kalli gabas, tayi ta addu'a a kan lamarin rayuwarta. Can wurin su Walid ya tafi, in da suke zama su yi shaye-shaye, su naɗa wiwi. Walid ya kalli Al'amin ya ce "Maza lafiya kuwa? Yanayinka ya nuna kamar akwai damuwa". Banza ya yi wa walid, dan haka shi ma ya share shi, ya cigaba da aikin gabansa. Sai kuma can ya ce "Mai laya" "Na kiyayi mai zamani, ya aka yi?" "Dama yara matasa suna hawan jini ne, ba sai tsofaffi ba?" Ya ce "Eh to, na ji an ce akwai wanda ake haifar su da shi ma, amma hawan jini a matasa, maybe damuwa ce ko gado". Ya jinjina kai. Liti ya ce "Maza ko kai hawan jinin ke damu? Kana da 'yar madara, ai ba zaka yi hawan jini ba" Tsuke fuska ya yi, jin liti ya kira jauhar da 'yar madara. Gidansu Al'amin, Abbu ya shirya zai fita ya kalli rahila ya ce "Yakamta idan an janye yajin aikin nan, ku je ku duba matar yaron nan" Rahila ta ce "Taɓ haka kurum, su dai yaran su je ni in je ya illata ni a banza? Su dai su je" Abbu ya ciro kuɗi a aljihunsa ya ce "Amira, ga kuɗi nan ku hau mota, ga dubu biyar ku saya mata fruit ku kai mata, na ji an ce zuwa jibi in Allah ya kaimu, za a janye yajin aikin, sai ku je ku duba jikin nata, kafin na samu na je nima" Ta amsa da to Abbu. Sai dai bayan fitarsa Amira ta ce "Na samu na saka data, dan ba za ta ci 5k ɗin nan ba". Shahida ta ce "Wallahi kuwa da sai na gaya masa, ai ba haka ake yi ba" haka suka cigaba da faɗan su na sakonni. Jikinta ya ɗan yi sauƙi, sai dai ba ta daina ciwon kai ba, ga damuwar abun da Al'amin ya sake nanata mata, kenan yana nan a kan bakansa na rabuwa da ita. Kusan kwanaki biyu, ba ta bari su zauna wuri ɗaya, saboda kar ya sake tayar mata da maganar. Ya gama karyawa, yana kallonta tana ta shirin dutsenta, karyawar ma ba ta yi ba, kamar yayi magana kawai ya shareta, ya tashi ya fita. Su halimatu suka shigo, suka tayata aikace-aikace, sannan suka koma gidansu. Tana falo tana karatunta tana shirin dutse, aka yi sallama a tsakar gida. Ta amsa tare da bayar da izinin a shigo, 'yan mata ne da zasu girme mata su biyu, suka shigo falon. Jauhar ta faɗaɗa fara'arta tayi musu maraba. Suka gaisa da ɗayar, ɗayar kuwa sai hura hanci take yi. Shahida ta ce "Kin gane mu kuwa?" Jauhar ta ce "Na gane wannan ranar da na je gidan, mun haɗu da ita ai, ƙannensa ne ko?" Shahida tayi murmushi ta ce "Kin canka" "Sannunku da zuwa, baku taɓa zuwar mana ko sau ɗaya ba" Shahida ta ce "Ai da yake ba ma zama a gari saboda school, shekaranjiya ya je gida ya ce baki da lafiya, Abbu ya ce lallai mu zo duba ki kafin ya zo shi ma. Ya jikin?" "Jiki Alhamdilillah na warware" "To Allah ya ƙara afuwa, ko mu ce Allah ya raba lafiya, ya kawo mana baby lafiya" Shahida tayi maganar tana murmushi. Buɗe baki Jauhar tayi ta tashi da sauri ta ce "Bari na kawo muku ruwa" Ta kawo musu ruwa, lokacin ta hura gawayi, ta ɗora girki. "Wancan ba tea flask ɗin mu bane?" Amira tayi maganar tana nuna flask ɗin. Jauhar ta ce "Ina ga naku ne, shi ne ya zo da shi, ina ta so nayi masa maganar na waye, yanayin jikina ya hana, amma tun da Allah ya kawo ku shikenan". Suka cigaba da hira da shahida, yayin da Amira ke ta harare-harare itakaɗai. Shahida ta ce "Yaya muka ji da abun da ya faru da yaya na rufe shi da aka yi, Ubangiji Allah ya tsare gaba" Jauhar ta ce "Amin ya Allah, sharri ne ma aka yi masa, amma duk da haka a tayamu da addu'a dan Allah, duk zai daina wataran sai labari. Ina mama?" "Haka ne, ana nan ana yi, mama tana nan ƙalau, tana gaishe ki" Shahida ta sake cewa "Nikam wai dan Allah ya aka yi kuka haɗu da yaya ku ka yi aure, har ya taka ya je gida, sha biyu fa ta wuce, ya ce na yi masa girki matarsa ce ba lafiya na ce wace 'yar baiwa ce haka? Kin san a rayuwarsa ta duniya mata ba sa gabansa mu kanmu yadda ki ka san dodo haka yake a wurinmu". Jauhar za ta yi magana, Amira ta ce "Kin jiki da wata magana shahida, a ina kuwa za su haɗu?, Tallarta fa aka kawo masa ba ta ji, ta fanɗare a gida an rasa yadda za ayi da ita, aka haɗa su, aka jogana masa, da yake shi ma ba sanin ciwon kansa yayi ba, ko ke baki san zancen ba? Kin zauna kina ta zuba ni ina da wurin zuwa" ta ƙarasa maganar tana tashi tsaye ta ɗauki jakarta tayi waje. Gaba ɗaya jauhar ta yi sak, jikinta yayi shock, yayi wani irin sanyi da mamakin maganganun Amira. Cikin dirircewa shahida ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, wallahi ƙarya take yi, ina zuwa" ta lallaɓa ta ɗauki takalmanta cikin tsananin jin kunya ta bi bayan Amira. Biri yayi kama da mutum, duba da yadda aka yi auren cikin gaggawa ko wata guda ba a rufa ba, ashe abun da aka gaya musu kenan a kanta? A take ta ji ciwon kanta ya tsananta, ta fara tunanin wace irin muguwar ƙiyayya ce tsakaninta da 'yan gidansu har haka. Gidan su jauhar, Hafsa ta shigo daga zance, ta zauna a tsakar gida, Yaya saifu ya shigo, ya kalleta ya ce "Daga ina ki ke?" "Zance" ta bashi amsa kai tsaye. "Wurin wa?" Tayi shiru tana kallonsa. Ya ce "Wallahi kun yi asara, yanzu dama Saboda hafsa ta auri mutumin nan, da yake son jauhar shiyasa ku ka aurar da ita ga mutumin banza, wallahi ba ku kyautawa kanku ba, kuma da ikon Allah sai Allah ya saka mata". Mama ta ce "Saifu maganar me ka ke yi ne ban fahimta ba?" Ji yayi kamar ya gayawa mama baƙar magana, sa'arta ɗaya mahaifiyarsa ce, babu yadda zai yi da ita, kawai ya fice. Mama ta ce "Zakiyya, da gaske mutumin nan ne yake zuwa wurin Hafsa?" Ta haɗa rai ta ce "Ni ma ban san zancen ba sai yanzu" Mama ta ce "To meye abun ɓoyewa ban da abunki, ai abun farinciki ne a gare mu baki ɗaya. Dama ai jauhar ɗin ce ba ma son ya aura, wallahi nayi murna haƙanmu t cimma ruwa". Sai kuma ta ɗan saki ranta ta ce "Wallahi ina ta son na gaya miki, abubuwa ne sun sha mini kai, kuma ba gama daidaitawa suka yi ba" "Ai bakomai, Allah ya tabattar mana da alkhairi" suka gama maganar ta shiga ɗakinta, ta jinjina kai ta ce "Hmm zakiyya kenan, baki da wayo da ni ki ke zancen, duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, zaki gane kuskurenki". Yau tun la'asar ya dawo, kwana biyu ba ya yin dare, saboda rashin lafiyarta sai dai fa ba zai ce mata sannu ba. Ya kasa gane kan yanayinta, ta zuba masa abinci, ta koma gefe ta yi shiru. Ya gama ya tashi ya tafi ɗaki, zai ɗan kwanta ya huta, kasa jurewa ta yi ta tashi ta bi bayansa. Ta ssme shi, yana ta watso kayan wardrobe ɗin sa da ta gyara da ƙyar. "Master" "Yeah" ya amsa ba tare da ya kalleta ba. "Ƙanneka sun zo ɗazu baka nan" "Ok" kawai ya ce, amma ƙasan zuciyarsa mamaki yake yi, tun da ƙannensa ta ce, da ƙanwa ta ce ya san shahida ce kawai. "Dan Allah abu nake son tambayarka, na san kai ba ma'abocin ƙarya bane ba, na san ba zaka fara a wannan karon ba" bai amsa ba, dama ba tayi tsammanin hakan ba, ta ce "Da gaske tallata aka kawo maka, wai ba na ji na fanɗarewa iyayena shi ne aka aura maka ni?" Ya ɗaga rigar hannunsa yana kallo kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Eh, haka na ji" Cikin rauni ta ce "Kuma ka yarda?" "Kusan haka, dan na san ba yadda za ayi a aureni haka kurum babu dalili, a abun da bai wuce sati biyu ba" Yayi maganar yana ajiye rigar, ya ɗauki wata, sautin da tayi na ƙwacewar kuka ne, ya sanya shi ɗagowa a tsorace yana kallonta. Cikin kuka ta ce "Wallahi ni ba lalatacciya ba ce, ban fanɗarewa iyayena ba, dama kallon da ka ke yi mini kenan, kallon da 'yan uwanka da sauran mutane suke yi mini kenan" da ƙyar maganarta take fita, saboda numfashinta da ya fara sama. Ya ƙaraso gabanta ya ce "Wai ke ba kya gajiya da kuka ne? Komai kuka?" Hannunta take fifitawa kusa da hancinta, alamar numfashi yana bata wahala, da sauri ya ɗauketa ya fita da ita tsakar gida, ta lumshe idonta hawaye na bin gefen fuskarta, sai dai ƙirjinta sai ɗagawa yake yi yana sauka, alamar numfashin da ƙyar take yi. "Ko mu koma asibiti? dama sati ɗaya suka bamu mu koma" Ta girgiza masa kai. "Ba zaki daina kukan ba?" Maimakon ta daina, sai ma wata sheshsheƙa da ta zo mata, ga numfashinta yayi nauyi. Ya ciro wayarsa a aljihun wandonsa, ya kira liti. "Maza ya ne?" Viper ya ce "Kana ina?". "Na shiga area raba kaya". "Samo adaidaita sahu, ka zo gidana zan mayar da 'yar madara asibiti" "An gama mazaje" Zai ajiye wayar, ta fara vibrating, ya ɗaga bai yi magana ba. "Honorable ya dawo, akwai taron gaggawa da zai yi, yana son ganinka" "Na ji" "Dan Allah kar ka ɓata lokaci sosai, ka san zaɓe yana ƙara gabatowa" Ras jauhar ta gane muryar waye, muryar P.A ce, a take ta jinjina rashin kunya irin na ɗan siyasa. "Dan Allah kar ka je, idan ka tafi mutuwa zan yi" "Allah ya jiƙanki" A sanyaye ta ce "Amin, amma dan Allah ko na mutu kar ka je ba na son ka din ga zuwa wurin 'yan siyasa" "Ki yi mini shiru, idan ba haka ba zan tashi na bar ki" "Yi haƙuri" ta faɗa tana haki. A hankali take iya takawa, saboda numfashinta, ya sakata a napep ɗin da liti ya zo da ita, sannan ya shiga, liti ya zauna a gefe suka tafi Asibiti. File ɗin ta aka kai wa likita, shi da ita suka shiga, liti kuma yana can waje. Likita ya ce "Ka ƙi yadda ayi mata gwajin ciki, gashi tana ta fama da an duba dai" Ya ce "To duba" Jauhar ta ce "Ni bani da komai". "Shikenan, ki na da athma ne dama, wannan hakin da ki ke yi?" Ta jinjina masa kai ta ce "A'a allergy ne, shi ma kuma tun ina yarinya ne" Al'amin ya kalleta, likitan ya sake cewa "Akwai magani da ki ke sha ne? Ai kusan duk abu ɗaya ne, allergy ɗin da athma" Ta girgiza kai ta ce "A'a ai na daɗe ba na shan magani, addu'a nayi ta yi, ya  daina tashi, tun ina ƙarama sosai ban kum jin alamun sa ba" Likitan yayi murmushi ya ce "Masha Allah, ka ga 'yar baiwa, to a din ga sakamu a addu'ar mu ma, amma dai yanzu zan rubuta miki magani, sai ki kiyayi hayaƙi, ko kin shaƙi wani abun ne?" Ta ce "A'a kuka na yi kawai na ji na kasa numfashi sosai" Likitan ya jinjina kai, ya ce "Bari na duba bp naki na gani". Shi dai gogan bai ce komai ba, likitan ya duba bp ɗin ta sannan ya ce "Zahra kina shan magungunan da na baki kuwa?" "Ta jinjina kai alamar eh". "A iyayenki akwai mai hawan jini?" Ta ce "A'a" Ya kalli Al'amin ya kalli jauhar ya ce "Akwai abun da yake damunki ko?" Tayi yaƙe ta girgiza kai. "Zahra, ita rayuwar duniya haƙuri ake yi. Malam ka zauna da matarka ku tattauna idan a cikin aurenku matsalar take, a magance ta, idan ba haka ba, hawan jinin nan zai iya taɓa mata zuciya, idan wani abu ka ke yi mata da ba ta jin daɗin sa, ku tattauna dan Allah ku fahimci juna, amma tayi ƙanƙanta da wannan ciwon" "Zahra" likita ya kuma kiran sunanta, kamar yadda ya gani a jikin file. "Idan kun je gida, ki zauna da mijinki, idan damuwa ce da ke, ki gaya masa, ki cire koma menene a ranki, mijinki da kuma al'umma baki ɗaya muna buƙatar ki a raye" kawai ta sunkuyar da kai sai kuka. Al'amin ya ce "Rubuta mana magungunan kawai mu tafi" Ya rubuta maganin, ya bawa Al'amin yana kallon jauhar cikin tausayawa. Al'amin ya kalleta ya ce "Mu tafi? Ko yau ma goyakin zan yi?" A hankali ta tashi tsaye, ya ce "Kin daina hakin?" Ta ce "Ya ragu" Ya saka hannunsa ya riƙe nata, suna tafe a hankali har suka fito wajen asibitin in da pharmacy yake, ya saya mata maganin suka hau napep ɗin da ya kawo su zuwa gida. Shi dai bai iya rarrashi ba, bai ma san ta ina zai fara ba, amma gaba ɗaya yanayin da jauhar take ciki, bai yi masa daɗi ba, ya san fiye da rabin damuwar ta shi ne sila, ya ce su rabu kuma ta cigaba da kuka. Tana kwance a kan kujera, tayi lamo, shi kuma yana zaune a ƙasa, yana kaɗa ƙafa. "Master" "Mmm" "Kana ta ɗawainiyar asibiti da ni, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ya ƙara arziki" "Amin" Ta sake cewa "Master" Ya ɗago yana kallonta. "Dan Allah da gaske kallon mara ji wadda ta fanɗarewa iyayenta ka ke yi mini?" "Haka aka ce mini ai" Ta ce "Aishikenan, shiyasa ka ke so ka sake ni?". Ya ce "A'a kina takura mini ne kawai, kin isheni yanzu ina zaman zamana ba zan fita ba, sai dai na zauna kula da ke" Ta ce "To ka yi haƙuri, dan Allah kar ka fita yanzu, ji nake kamar kana fita zan mutu" idan tayi zancen mutuwar nan, gabansa faɗuwa yake yi, amma ya maze ya ce "To zan hanaki mutuwa ne?". "A'a, amma dan Allah ka daina yi mini kallon mutuniyar banza, dan Allah ka gaya wa 'yan gidanku, aje ayi bincike ma a kaina, wallahi ba mutuniyar banza ce ni ba" ɗago ido yayi yana kallonta, kenan zuwansu ne suka gaya mata wannan maganar, yayi shiru ya cigaba da latsa wayarsa. "Master" " 'yar madara" ya amsa bai kalleta ba. Likita ya ce "Ka daina yi mini abun da na so, ka tambaye ni abun da nake so ka daina yi mini" Ya ce "Tom" ɗan murmushi ta yi, yau tayi sa'a ana amsa mata ma. "Yaushe zaka sake nin?" Ya yinƙura ya tashi ya ce "Na fasa yanzu, sai an kwana biyu, idan aka yi yanzu ina ga warewa zaki yi". Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, ya shiga ɗakinsa. Cikin ikon Allah, washegari ta tashi jikinta da sauƙi, sai dai damuwar cewar ita fanɗararriya ce, ta kasa barinta. A tsakar gida ya taso, ya tarar da ita, tana aiki. "Ina kwana" "Kin warke ne?" Ta girgiza kai ta ce "A'a, bayan ba ka zauna mun yi maganar da likita ya ce ba" "Akwai abinci ne?" Ta ce "Eh shinkafa na dafa amma akwai sauran buredi in dafa tea" Ya ce "Zubo mini, ke ki sha tea ɗin" Ta zubo abincin ta kawo masa, ya kalleta fuskarta duk ta faɗa. "Amma yau ba zaka fita ba ko? Ka zauna ka kula da ni" Murmushi ya yi da gefen bakinsa, ta sake cewa "Idan ka gama cin abincin zan gaya maka abubuwan da nake son ka daina yi mini, ko sannu baka yi mini bama". Tayi ta zuba, amma yayi gum. Wayarsa da take ringing ya ɗaga ya ce "Ina sane zan zo yanzu" Ta haɗe rai ta ce "Amma ba fita zaka yi ba ko?" Ya ce "Fita zan yi" "Ni dan Allah ka zauna ka kula da ni" shagwaɓa da rikici kawai take yi masa tsakanin jiya da yau, kamar yau an cire mata tsoron sa. Ta tashi ta ɗauki kwanukanta, ta tafi kitchen cike da takaici. Ko ba zai kulata ba, tana son ganinsa a gida. Sosai ta ji ranta ya yi mugun ɓaci fitar da zai yi, ɗan tattalin da aka yi mata jiya zuwa yau yayi mata daɗi, duk da ana yi ana haɗe mata rai. Tana cikin ƙunƙuni, ya fito da sauri hannunsa da wayarsa a kunnensa, hannunsa ɗaya da makamin da yake kira da iraƙi. Ya ce "Gani nan, ka duba bayan nan, russiata da sweazland suna nan, ka ɗaukar mini su, kar ku bari su motsa, gani nan zuwa" hannunsa ɗaya yana soke makaminsa iraƙi a cikin ƙugunsa. Ya ce "Fitar gaggawa ta kama ni, idan nayi dare ban dawo ba, ki rufe ƙofa, duk wanda ya buga kar ki buɗe, idan na dawo na hauro" Banza tayi masa, ta cigaba da yanka albasarta. "Ke ba magana nake yi miki ba?" Shiru ta sake yi masa. Ƙoƙarin leƙawa yake yi, ya ga ko lafiya. Kawai ya ga ta jefo masa murfin tukunya, a zatonsa ko ba ta san me tayi ba, kawai ya ga ta sake jefo masa rariya. Saroro ya tsaya cikin mamaki, ta cigaba da zaro kwanuka tana jefa masa tana kuka, bai ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da suka haɗa ido ta jefo masa ludayin hannunta a ƙirji. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??     Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??     Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??     Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.      Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955 Tunani ya fara yi, ko tana da aljanu ne. Ganin idan ya ƙyaleta, fashe-fashe za ta yi, ya sanya shi takawa ya riƙo hannunta, amma sai ƙoƙarin fizgewa take yi. Kasancewar ba ta yi masa wahalar ɗauka, ya sanya ya danƙota kamar kazar cikin akurki, aikuwa ta cigaba da fizge-fizge da ƙoƙarin ƙwacewa, falo ya shiga da ita, ya tattara hannayenta ya riƙe, hakan ya sanya ta kasa cigaba da ƙoƙarin ƙwacewar. "Meye haka ki ke yi? Kanki ɗaya kuwa?" Kallonta yake yi, har ta fara kuka, shi bai ma san me yayi mata ta aikata hakan ba. "Me nayi miki ki ke jifana?" Cikin takaici ta kalleshi ta ce "Meye ma baka yi mini ba, ni bani da wani amfani a wurinka, bani da ikon roƙon alfarmarka, komai ma yi mini ka ke yi, ko yayi mini daɗi ko akasin haka, ba ka tausaya mini dama ka tsane ni, so kake yi na mutu ka huta". "To yanzu kuma me nayi miki?" "Wuƙa fa ka ɗauka zaka fita, idan aka yi maka wani abun ko ka yi wani laifin nikaɗai nake fama, sai su yaya walid da suke taimaka mini, amma kai gaba ɗaya baka tausayina, ba ka tausayin maraicina saboda da ma ba so na ka ke yi ba. Kodayeke ba laifinka bane, tun da sama ta ka aka aura maka ni, bayan an gama ɓata ni a wurinka. Ko hira ba ka yi da ni, in tayi maka magana kayi mini shiru, idan aka ga na mutu kai ne, sai ma na rubuta na bar wasiyya, idan na mutu kai ka ƙarasa ni da takaici" Yayi shiru ta din ga yi, tana faɗa tana kuka, sai da ta gama tsaf, sannan ya miƙe ya ce "Ki kula da abun da na gaya miki, kar ki fita kar ki bar gida a buɗe, idan na yi dare ki kwanta zan hauro". Ta ɗaga idanunta da suka yi ja ta ce "Sai ka fita ko?" "Ai na ce idan ba zaki iya ba, ki koma gidanku ko ban gaya miki ba?" Tayi shiru ranta na yi mata wani irin zafi, ya fita ya kwashe kwanukan da ta watso waje ya fice. Unguwar su ya nufa, faɗa ya haɗa ɗan unguwarsu, da ɗan unguwar su madaki, yaron ya kwaso 'yan daba yaran madaki, sun shiga unguwar su Al'amin su na ta faɗace-faɗace. Yana zuwa chamber su, ya ɗaukko wuƙaƙensa, ya fita, sai dai da ya je, yaran suka din ga darewa, saboda wanda suka taɓa karo da shi, sun san irin ƙarfin da Allah ya yi masa. Wani yaron madaki ne, da yake ji da tashen balaga da rashin mutunci, ya sha gaban Al'amin yayi yana zage-zage yana ƙoƙarin saran Al'amin. Ya jefar da wuƙarsa, ya nufi yaron, wanda suka san Al'amin suka din ga ce masa ya gudu, kar ya bari ya kama shi, amma kasancewar ya yi wa wiwinsa haɗin kauri da wata ƙwaya da suke yi wa laƙabi da 'yar fara, ya sanya yake jin kansa a sama, ko barikin sojoji zai iya shiga yayi rashin mutunci. Duk iya ƙoƙarin sa ya kasa saran Al'amin, saboda yadda yake da zafin nama, wurin kare saran, wanda idan ba professional athlete ne ba, babu lallai ya iya. Ya shammaci yaron, ya soka masa iraƙi a cinyarsa, a take ya kurma wani uban ihu, liti ne ya karyo kwanar, riƙe da nasa makamin yana ɗigar da jini, "Mai zamani yi haƙuri, kar ka karya yaron nan" sai dai bai rufe bakinsa ba, ya ga Al'amin ya fito da dogon harshensa, ya lashi laɓɓansa na ƙasa da su, idan har yayi haka sai aiwatar da muguntar da yayi niyya, kan liti yayi wani yinƙuri ya karya ƙafar yaron ya watsar da shi yana kururuwa. "Mai zamani, yanzu zaka sake janyo mana faɗa, madaki zai ce sai ya ɗauki fansa, da baka karya shi ba" Ya ɗago jajayen idanunsa a slow, yayi wa liti wani irin kallo ya ce "Ya zo ya ɗauki fansar a kaina, idan ya isa" ya wulwula iraƙinsa, ya cafe ya yi gaba. Kai tsaye gidan su ya tafi, da wannan wuƙar tana ɗigar da jinin da ya soki yaron nan. Yana shiga ya wuce falo, sai ganinsa suka yi a tsaye a kansu da makami tsirarsa. Salati suka fara yi da kururuwa, ya kalle su ɗaya bayan ɗaya, "Me ya kai ku gidana?" Yayi maganar yana kallon shahida. Cikin tashin hankali ta ce "Abbu ne ya ce Mu je mu duba matarka". "Shi ya ce ku je ku gaya mata cewar kangarewa ce ta sanya aka yi aurena da ita? Ku je ku ci zarafinta?" Cikin tashin hankali shahida ta ce "Ba ni na faɗa ba Amira ce wallahi". Rahila kuwa hankalinta ya dugunzuma, ta ce "Ka yi wa Allah da ma'aikinsa ka yi haƙuri, dan Allah kar ka yi musu wani abu" Ai kamar ta tunzura shi, ya saka wuƙa a wuyan Amira, "Ya zama na farko ya zama na ƙarshe, ayi duk cin kashin da za ayi a kaina, ban da 'yar mutane da ki ka haɗa kai ku ka cutar, idan aka kuma zan yi ɓarna, wallahi sai na saka wa mutum ƙarfe" Shahida ce ta iya cewa "In sha Allah ba za a sake ba" yayi ƙwafa ya fita. "Amira kin ga abun da ki ka ja mana ko? Da ya illatamu, da kin cuce mu" Amira kam kasa magana tayi, sai dafe ƙirji tana hakin tsoro. Al'amin wuni yayi ranar, yana partrol da yaransa a unguwar, saboda kar yaran madaki su zo su afkawa wanda bai ji ba bai gani ba. Cikin ikon Allah, har dare yaran madakin ba su sake shiga unguwar su Al'amin ba, duk da sun yi artabu sosai da wasu, dan sai da aka yi masa rauni a cikinsa, ya kama hanyar tafiya gida. Jauhar na falo tana karatun exam, duk da sun kusa kammala jarrabawa. Ta katangar ya diro kamar ɓarawo,s an samu cigaba, yanzu idan ya ga dama ya kan yi salama. Sallamarsa kawai ta amsa, ba ta sake kula shi ba, ya wuce ɗakinsa, mintuna goma amma ba ta biyo shi ba, ya fito ya ce "A kawo mini ruwan zafi zan yi wanka" Ta tashi ba ta ce komai ba, ta ɗaukki flask, aurensa da ita ta saba masa da wanka da ruwan ɗumi, saɓanin da da har a kuddudufi wankansa yake yi ya ƙara gaba. Yanzu kuwa kusan kullum, da an kawo wuta, take dafa ruwan a heater, ta saka a flask. Ta zo ta haɗa masa ruwan, sai dai ta ga kamar yana ɓoye wani abu. Kawai ta leƙa ta ga me yake ɓoyewa, yanka ne a gefen cikinsa, ya saka rigarsa yana ƙara goge jinin kasancewar ba mai zurfi bane ba. "Ka gani ko? Sai da ka je aka yanko ka ko? Abun da nake ta gudu, sai da ka zubar da jini ko, ba za kai daina zuwa wurin da za a cutar da kai ba ko master? Kodayake ma ni abun yake damu, kai ko a jikinka". "Na ce ya dame ki ne? Ba jikina bane?" Idan ba gizo idonsa yayi masa ba, hararsa ta yi ta fice. Shi mamaki ma take bashi, tun da ta yi rashin lafiyar nan, take rigima kuma kamar ta rage tsoron sa. Ya shiga ya yi wanka, ya fito ya tarar da ita da ɗan ƙaramin kwanon abinci, sai kuma kayan dressing, tun na lokacin da aka yi masa wancan raunin. Bai kulata ba, ya ja kwanon abincinsa ya cinye, awara ce da miya, ya sha ruwa. Ita ma ba ta kula shin ba, ta saka auduga da spirit tana goge, kan ciwon, tana gogewa tsigar jikinta na tashi, kamar jikinta take gogewa, shi kuwa kamar dutse latsa wayarsa ma yake yi. Haushi ya isheta, ta kalleshi ta ce "Wai ba zafi ne?" "Eh babu, idan ma dirzawa ki ke da ƙarfi, dan na ji zafi, ba na ji" ta tashi ta fice fuuu, tana yi masa fatan shiriya a ranta. Kusan awa ɗaya da rabi, ya shigo mata ɗaki, ta yi sauri ta tashi zaune, saboda ta san tsiyar da ta aikata masa. Ya kunna fitila ya hau yi mata bincike a ɗaki. "Me ka ke nema?" Ya tashi ya nufo ta, ya miƙa mata hannu ya ce "Bani kayana da ki ka sace mini yanzu" "Ni ba na sata" Ya ce "To baki nayi ki ka ɗauka? Ko kema kin fara sha ne ban sani ba? Kodayeke biri yayi kama da mutum, da ki ka iya kallona ki ka din ga jifana nan gaba ina ga swizaland zaki saka mini ina ga" "Ni ba na shan komai, kuma ban ɗau komai ba". "Ba ki ɗauka ba ya aka yi ki ka san a kan me nake magana?" Tayi shiru ba ta ce komai ba. Hankaɗata yayi, ya janyo ledar kayan shaye-shayen sa a cikin bargonta. "Na gaya miki idan kin gaji ba zaki iya zama ba, ban ɗaure ki ba, ki ƙara gaba" A ƙule ta ce "Ka ɗaure ni mana, zan tafi ba ka sallame ni bane, ka rubuta ka gani idan ban tafi ba. Tun da baka da tausayi idan ba mutuwa na yi ba hankalinka ba zai kwanta ba" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka. Ya kalleta, gaba ɗaya ko faɗan ba ta iya ba, voice ɗin ta sam ba na masu faɗa bane, shagwaɓa kawai take yi. Ya ce "Kin yanke hukunci kenan? Ai da kin gaya mini da duk ba a zo nan ba, zan rubuta na baki, dama na gaji". "Kuma wallahi idan ka yi shaye-shaye kai da Allah" Bai kulata ba, ya jefo mata kwalin sabuwar waya gal, ya ce "Gashi nan, akwai layi a ciki na yi rijista, idan kuma na yi wani laifin na gudu ke za a kama". "Bana so" ta faɗa tana kwanciya, duk da ƙasan zuciyarta tayi mamakin wayar. Ya saka hannu ya ɗauka ya ce "To kin huta" ya fice ya bar ɗakin. Ta kwanta ta yi shiru, sai ta fara tunanin ya aka yi ya ɗaga mata ƙafa ya ƙyaleta, sai kuma ta ga rashin kyautuwar abubuwan da ta yi masa. Bayan sallar asuba bacci ta koma, ƙarfe takwas da rabi ta farka, tana ƙoƙarin saukkowa daga kan gadon, tayi tozali da farar takarda da biro. Gabanta ya faɗi ta ce "Na shiga uku sakin nawa ya yi?" Ba ta taɓa takardar ba, ta saukko a sukwane ta tafi ɗakinsa sai dai baya nan ya fice. Gaba daya jikinta yayi sanyi, sai yanzu ta ƙara jinjina girman wauta da aikata. Yau rahila har gidan su jauhar ta je, suka ƙule a ɗaka ita da Anty Zakiyya suna ta surutu da shewa. "Zakiyya ina ga 'yar ku fa an gamu laulayi take yi" "Kai haba dan Allah" "Wallahi da gaske, ke 'ya mace shu'uma komai ƙanƙantarta, kin san yaron nan har gida ya zo da wuƙa ya gama ta'addancin sa tana zubar da jini, zai yi mini hauka a gida wai su Amira sun je masa gida sun yi matarsa ko me oho musu, na ga tashin hankali na ce iyee yanzu har ta samu wannan matsayin. Wallahi mamaki nake yadda ta iya zama da yaron nan" Zakiyya ta ce "Ba ki ganta ba kamar sokuwa, kafin ki ga ta yi fushi, ko tayi zuciya da abu za a jima, ko kuma kawai tsabar ƙarfin hali ne da ƙi faɗi ba" Rahila ta ce "Sai ta yiwu, ya ake ciki da maganar hafsa?" "Mu na nan ana ta murginawa, ana shirin kawo kuɗin aure, na ce lallai ta ce masa a haɗo da kayan lefe, ana sallacewa ayi auren, duk da wannan matar ta nuna bakomai na san tsohuwar muguwa ce, wataƙila wani abun zata kitsa, dan haka kan tayi wani yinƙuri ayi a wuce wurin". "Yauwwa kar ki kuskura ki sakankance ko ki yadda da ita, ni ban zaci lamarin ma zai zo da sauƙi haka ba, ku cigaba da tatsarsa kuna tarin kayan aure" Zakiyya ta ce "Ke kin ga hidima, ai ni dai Allah ya kashe ya bani, da yanzu sai dai mu ga ana yi wa waccan yarinyar jauhar" Rahila ta kwashe da dariya ta ce "Ga mijinta can suna fama, amma wallahi ya fara son yarinyar nan, kai amma ba ƙaramin haƙuri take yi ba bala'i Allah ya kyauta" suka cigaba da hirarrakinsu, da shirin biki. Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, suka fito daga taron meeting, daga ofishin jam'iyya, sakamakon gabatowar manyan zaɓuka da za a gudanar a cikin Nigeria. Yau bai san iya adadin meetings ɗin da ya yi attending ba, suka jero da shi da mataimakin firaministan jam'iyya na jiha, ya ɗan yi miƙa ya ce "Kai, yau na gaji over" "Kai honorable, da an yi babban zaɓe an wuce wurin, haka ne, ka san ban yi sati da shigowa daga Abuja ba, can ma wasu tarurrukan ne, abun duk babu sauƙi, ina ta ƙoƙari in sha Allah sai na kawowa excellency yankina, ina nan a satin nan zan yi empowerment na matasa, kuɗina duk sun tafi a campaign ɗin nan" "Kar ka damu honorable, hannun jari ka saya, da an wuce wurin sama zaka din ga kwashe ribarka, ka mayar da uwar da ribar ka ɓace ba zasu sake ganinka ba, sai bayan shekara huɗu" suka kwashe da dariya. Suka yi sallama, kowa ya nufi motarsa, ko da ya je gida, matarsa tuni tayi bacci, yayi wanka ya nemi wuri ya kwanta, dama ba yunwa yake ji ba, sai dai bacci ya gagare shi, ya din ga juyi a kan gadon, ga gajiya ga baccin yana ji, amma ya kasa ya ɓuge da lissafe-lissafe abubuwan da yake son yi idan ya dace ya samu ya ci zaɓen nan. Ji yayi kamar kansa zai fashe, saboda stress kawai ya tashi ya ɗauki mukulli, ko direba bai nema ba ya hau motarsa ya fice. Yamma da gari yayi, ya hau kan titin gwarzo road kasancewar dare ne, titin babu ababen hawa, ya sauke glas ɗin motar kaɗan, yana tafe a hankali yana shaƙa wani abu a hancinsa. Sai d yayi nesa da cikin gari sosai, sannan ya yi parking a gefen hanya, ya rufe glasan motar, ya cigaba da shaƙa abun nan, kusan mintuna talatin, sannan ya juyo kan motar ya nufi dawowa yana tafe iskar kan titin nan na ratsowa cikin motar, sannu a hankali har ya koma gida. Jauhar kuwa tun da tayi tozali da takardar nan ta kasa nutsuwa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, kuma taƙi buɗe takardar, da ta leƙa ta hangota ma, sai ta yi sauri ta fito daga ɗakin, ta din ga lissafa irin halin da za ta shiga idan ta koma gida, da irin dariyar da za su yi mata. Kuma yaƙi dawowa, har dare ba ta ganshi ba, hakan ya ƙara sanyata cikin tashin hankali, ba irin tunanin da ba ta yi ba, har ta fara tunanin ko da ya saketa, barin gidan yayi gaba ɗaya, sai dai kayansa suna nan, dan ita ta gyara ɗakin ya watso da komai ya bar mata a wurin. Sai sha biyu saura ya dawo, idonta biyu ya dawo ba ta yi bacci ba, sai da ta tabattar ya shiga ɗakinsa, sannan ta ɗauki takardar ta bishi ɗakinsa. Yana kwance a kan katifarsa, ya cika ɗakin da warin taba. Yanayinsa ya nuna a buge yake, saboda fitilar ɗakinsa a kunne take, ya haye katifa ya mimmiƙe idanunsa sun yi ƙanana da ƙyar yake ɗaga su, kallo ɗaya ya yi mata ya mayar da idonsa ya lumshe. "Master sai da ka rubuta takardar nan hankalinka ya kwanta ko?" Bai buɗe idonsa ba ya ce "Ke ki ka ce na rubuta" "Kuma sai ka rubuta ɗin ko? Saboda ina fargabar kar ka sake ni, bakomai maraici ne ya janyo mini, Allah ya gani na yi iya yi na, na yi biyayyar aure, amma kullum kallona ka ke yi wadda ta takura rayuwarka, ga takardarka nan, ban ma buɗe ba balle na san meye a ciki, kuma wallahi ban saku ba" ta dire masa takardar a jikinsa, ya ziro harshensa tare da naɗe shi ya mayar, ya gyara kwanciyar sa, har ta gama surutanta, bai kuma motsawa ba. Kasa bacci tayi, ta ɗaura alwala ta tayar da salla, ta din ga addu'a Allah ya sa ya fasa sakinta, saboda ita a ganinta gara ƙalubalen gidan Al'amin a kan na gidansu. Duk rintsi ba zai daketa ko ya ci mutuncin ta ba, ko yi mata sharri ba, sai dai miskilancinsa da gaya mata baƙar magana wasu lokutan da har daɗi take ji ya kulata, ciyar da su kuma da take yi mafi yawan lokuta baya damunta, sai ma yi wa Allah godiya da take yi da ko yaya ba ya hanata abun da zata sarrafa su ci, ko yaya ta kasa abun sayarwa za a saya dan ma ana yi mata mugunta. Bayan sallar asuba tayi shiru tana tunani, ta ga sam ba ta kyauta ba, wasu abubuwan da ta yi masa, tun daga jifansa da kwanuka, har zuwa tsiwar da ta yi masa, ita tayi mamaki ma da ya ƙyaleta. Yau ba ta iya komawa bacci ba, ta fito aikace-aikacen ta, tana yi tana leƙawa ko ta gani ko ya tashi. Tana falo ta jiyo motsinsa, ta tashi ta shiga ɗakin da sallama. Ya amsa mata, ba tare da ya kalleta ba. Jiki a sanyaye ta durƙusa ta ce "Master ina kwana?" "Lafiya ƙalau" "Ka tashi lafiya, ya ciwonka?" Sai a wannan karon ya kalleta sai dai bai ce komai ba. "Master dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri ka yafe mini, abubuwan da na yi maka kwanan nan ban kyauta ba, dan Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba, wallahi ni ba mara kunya ba ce, kawai na rasa ya zan yi da wasu abubuwan ne, damuwa tayi mini yawa, dan Allah ka yi haƙuri idan ka sakenin ma, ka yi haƙuri ka mayar da ni" tayi maganar cikin rauni. Ya lumshe idanunsa ya ce "Bani wuri zan kunna hayaƙi" Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri master, ka yafe wa 'yar madara ɓacin rai ne ba zan sake ba, na san ban kyauta ba, dan Allah ka yi haƙuri" "Sai fa kin tafi, kin isheni ne kawai takura mini ki ke yi" "Dan Allah ka yi haƙuri, na daina takura maka, har cincin na yi maka jiya, in kawo maka?" "Eh ki kawo mini, sai fa kintafi" "Da ka san abun da hakan ka iya haifar wa rayuwata, da baka sake ni ba, dan ka ga ina ta roƙonka shikenan, duk ranar da ka bari na bar rayuwarka na bar ta har abada lokacin da zaka so ka ganni da kuɗi ba zaka ganni ba". "Eh na ji, kafin ki fara ɗaukar makami, gara mu rabu, ungo takardarki tafi da ita" yayi maganar yana danƙa mata takardar da ya warware. Ta rintse idanunta, tuni ta fara kuka, ta buɗe idanunta ta sauke a kan kyakkyawan rubutunsa, dan ganin saki nawa ya yi mata. *Ba zan dawo da wuri ba, na bar kuɗi a kan katifata ki sai wani abun ki ci* Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, ta ce "Shi ne ka yi ta wahalar da ni? Dama ba sakina ka yi ba, ka sakani kuka?" Hamma yayi, yayi shiru ta ce "A'uzibillah" duk gurbin da ya yi wani abu, yakamata ya yi addu'a bai yi ba, sai tayi masa. Ta ce "Aishikenan amma dan Allah ka yi haƙuri abubuwan da na yi maka ka yafe mini" "To, ki bani wuri zan sha abu" Ta ce "To bani wayar da ka bani jiya" gefen katifarsa ya nuna mata, ta tashi ta ɗaukkota a kwali. Ta kalleshi ta ce "Yanzu dan Allah wannan ta wa ce master? To kai ina taka?" Ya nuna mata keypad ɗin sa. "Wallahi ko a mafarki ban taɓa tunanin riƙe waya ba, yaya saifu ya taɓa bani keypad mama ta ƙwace, Allah ya saka maka da alkhairi ya saka ka a aljanna, Allah ya nuna mini ranar da zaka daina shan komai, ka zama limami saboda salihancinka, Na gode master na gode sosai da sosai" tayi maganar tana tattaɓa wayar. "To excuse me, ina son yin caji" "To yi mana" Ya ce "Ki fita ki bani wuri dai, kar ki sume mini yau bani da kuɗin zuwa asibiti" Maƙale kafaɗa tayi, ta ce "Master, wai yaushe zaka kai ni na gaida mama ne? Da wurin hajiya ma?". "Wace maman?" "Mamanka mana, bamu taɓa zuwa ba, na san wadda na gani a gidanku ba ita ce mamanka ba" "In ji wa?" Jauhar ta ce "Babu uwar da zata zauna hankalinta a kwance, alhali an yi wa ɗanta sharri an tsare shi". "Mama ta mutu" ji tayi kamar ya soka mata mashi, ta kalleshi ta ce "Kai ma ka san pain ɗin master? Ka girma da ita ka santa?" Ya jinjina mata kai alamar eh. Jiki a sanyaye ta ce "Ni ban ma santa ba, ina yawan takura ƙwaƙwalwata, dan na tunota, da rayuwar da muka yi tare, amma bana iyawa, baba ne yake da hotonta, nayi-nayi ya bani, ya hanani, idan na shiga ɗakinsa zan gyara masa, sai na ɗauki hoton in yi ta kallo ina jin daɗi, duk da ina jin kewarta, ina son in san yaya take ya halinta yake, yadda su mama suke faɗa ne ko akasin haka? Kawai saboda Baba ya saka hoton a cikin wallet ɗin sa, ya ce zai kai a wanko wani ya saka a yi enlarging ɗin sa ya bani, mama ta ɗauki hoton ta yayyaga, ta watsar wallahi ji na yi kamar ta yaga zuciyata, bana riƙo idan an yi mini laifi mantawa nake yi, ana yawan cewa bani da zuciya amma haryanzu a raina, na kasa jin cewa na yafe wa mama abun da ta yi mini. Da farko da na taso, na zata mama ce ta haife ni, daga baya na gane ba ita haife ni ba, sai na fara tunanin ko kawai faɗowa na yi ko tsinto ni aka yi, kowa yana da uwa ban da ni, wataƙila a haka aka haifeni, daga baya na yi tunanin ko kawai 'yar aiki ce ni, na zata 'yan aiki duk ba su da iyaye. Daga baya na gane baba ne babana, uwa ce bani da ita, sannu a hankali kuma na gane ina da uwa amma bata duniyar. Sai dai ba na jin daɗin irin yadda su mama ke aibata mamana, duk da ba ta raye ban san ta ba, har suna cewa mayya ce ta taɓa kama su ma, amma baba yana faɗar cewa mamana mutuniyar kirki ce, irin halina ɗaya da ita, haka yaya saifu ma yana faɗa. Mama ce mariƙiyata, na so in tashi kamar ita ce wadda ta haife ni, amma ƙiriƙiri sai ta nuna mini banbanci ba ita ta haife ni ba. Ta saka aka cire ni daga makarantar kuɗi, aka mayar da ni ta gwamnati wai ba na gane karatu ni daƙiƙiya ce, kuma ni babu mai kula da ni, ko koya mini assignment komai ni nake yi wa kaina gashi baba ba ya iya magana a kan abun da ake yi mini. Ita kuma anty Zakiyya cin zali na zahiri, na daku a wurinta, duk ba wannan ba ni ya riga ya wuce, kawai haryanzu ina jin zafin yaga mini hoton uwata da mama tayi, da ƙazafin nan da suka yi mini, na fanɗarewa, na san zan yafe musu wataran amma ba yanzu ba. Ina son in ga mutum yana hira da mamansa, ko suna wasa irin na ɗa da uwa, abun yana burgeni, ko mutum ya din ga gaya wa mamansa damuwarsa da daɗi master, wataƙila kai ka samu wannan damar ni kuwa ban samu ba, maybe da mamanka ta yi tsawon rai wannan rayuwar za ta zo maka da sauƙi". Tana gaya masa raɗaɗin abun da take ji a zuciyarta yana raguwa, duk da kuka take yi. Ya ce "You are missing her?" Yayi maganar yana kallonta. Ta jinjina masa kai ta ce "So badly" "Ki yi mata addu'a" ta jinjina masa kai tana goge hawayenta, a take shi kuma ya tuna irin tasa rayuwar, duk da lokuta da dama idan ka haɗu da wanda ku ke da irin matsala ɗaya ku ka yi sharing ana samun releif, amma yanzu shi ba ya son doguwar magana idan ya fara ma gajiya zai yi, duk da kwanan nan jauhar na isarsa da saka shi magana, kuma muddin ya gaya mata shi nasa labarin, zata shiga damuwa dan haka ya ƙyaleta. Duk da kuka take yi, ta fara ɗaukarsa a hoto tana murmushi ta ce "Kai zan fara yi wa hoto da wayar nan, haryanzu mamaki nake yi, wai master ne ya saya mini waya, Allah dai ya sanya mini kai a cikin aljanna ya jiƙan mama, ya ja da ran wanda suka rage mana, Allah ya goyi bayanka ya yi maka jagora a cikin lamuranka. Kai master na rasa wace addu'ar ma zan yi maka, na rasa wace irin godiya zan yi maka ma" Har cikin ransa ya ji daɗin Addu'ar da take yi masa. Ya kuma amsa da Amin. "To mun gama ki tafi" "To me na yi maka ka ke korata?" Ya ce "Sigari zan sha" Ta ɓata fuska ta ce "Da sassafen nan ba ka ci komai ba, sai ka fara da hayaƙi, haba mai babban suna, idan a baya babu wanda ya damu da lafiyarka, ni ina son ka yi lafiya, ka rayu saboda ka ajiye 'yar madara, yau dai ɗaya ayi haƙuri dan Allah a ɗaga ƙafa kar a sha da sassafen nan" kamar shashasha haka yake bin ta da kallo, ta karɓe lighter da sigarin hannunsa, har da ta gefe ta cikin kwali ta tattaresu. "Bari na dafa mana shayi, cincin na yi jiya, amma na kasa ci saboda damuwa, ka yi brush sai ka fito ka karya, kuma zan din ga leƙowa saura na ga mutum ya sha wani abu" Sunkuyar da kai ya yi, yana murmushi da gefen bakinsa. Jauhar ta samu na yi, lambar baba ta kira, yana ɗagawa ko gaisawa ba su yi ba ta ce "Baba na yi waya" Baba ya ce "Masha Allah Alhamdilillah, ina tayaki murna waliyya" "Ka hau what's app mu yi video call" Baba ya ce "To shikenan waliyya" Al'amin ya kalleta ya maimaita waliyya a ransa, lallai ta ci sunan da mahaifinta ya kirata da shi. "Master, nan ne wurin video call ɗin ko?" Ya jinjina mata kai alamar eh. Tana kira baba ya ɗaga fuskarsa ta Bayyana a screen ɗin wayar. "Baba wayata touch screen ce mai kyau". Baba yayi dariya ya ce "Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi." "Amin, ina su yaya saifu su mama da Anty?" "Duk suna nan lafiya, baba dan Allah kowa da kowa a turo mini lambarsa, duk zan yi musu magana ta what's app, zan din ga kiran su kuma a waya" "To shikenan, a ina ki ka samu waya ne?" "Master ne ya saya mini" sai kuma ta ce "Au amm maigidan ne ya sai mini" Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar baba, ya ce "Allah ya saka masa da alkhairi, ya yi muku albarka baki ɗaya" "Amin baba" ta kaste wayar. "Master " ya ɗago ya kalleta. "Na gode sosai" ya ɗan tsuke fuska ya ce "Kin faɗa kin sake, ya isa haka" "Bar ni na yi yabon gwani ya zama dole". Tana cikin maganar hankalinta ya kai kan labarin da ake yi a radio, wata mata ce take kuka, take roƙon gwamna, sarki da kuma jami'an tsaro su kama Aminu mai dogon zamani bisa karya mata ɗa da yayi, ya soke shi da wuƙa, an kai shi asibiti rai a hannun Allah gashi ba ta da ƙarfi, tana neman a bi wa ɗanta hakkinsa. Cikin tsananin tashin hankali, jauhar ta kalli Al'amin, tamkar bai ji me aka faɗa a radiyon ba, sai tauna cin-cin yake yi ƙururus ƙurus ko a jikinsa an mari dutse. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??     Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??     Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??     Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.      Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955 Jinjina kai indabo yayi, ya ce "Za ayi ba zai gagara ba, zamu dawo idan an kammala aikin, kuma wa'adin da aka ɗibar mana ya cika". "Shikenan, nasara tana tare da kai, ba yaƙini muke da shi ba, tabbaci nake bakaz duk da akwai ƙalubale a gaba, sai da ba za su gagara ayi maganin ƙalubalen ba, amma a gaba kaɗan ɗin akwai dutse, da zaka yi karo da shi, na buga na duba, duk babu hanyar maganin dutsen nan, sai dai ayi ragas, ko ka kar dutsen ko ya kar ka" P.A ya ce "Kuma babu yadda za ayi da dutsen? Ko wata mafitar?" "A yanzu dai babu, Suka tashi suka fito, suna tafe a hanya Indabo ya ce "P.A" "Na'am honorable" "Bokan nan kullum cikin faɗin ayyuka masu hatsarin gaske yake, ina tsoron tonuwar asirina, kar mu je in sake janyo wa kaina jagwal kana kallon yadda yarinyar nan Naja'atu ta zame mini alaƙaƙai" "Mu bi komai a sannu sir, zamu yi nasara kuma samo yarinya ba zai gagara ba, ko cikin ƙauyukan nan aka bincika za a samu, ko kuma Naja'atu ta samo a irin mutanen da ke hulɗa da su" yayi ajiyar zuciya ya ce "Ba zan so ce a samo ta ɓangaren ta ba, amma kai na ɗora maka ragamar samowar" "Za a bincika in sha Allah sir" "Yayi, ina jiranka, ka ga idan lokaci ya ƙure, aikin da muka yi ya koma baya" "Haka ne, da yardar Allah ka ci kujerar nan ka gama, mu je injiniyoyin suna can gida suna jiranka, aje ayi lissafi" "Ok to, Aminu haryanzu ya ƙi zuwa ko?" "Wallahi yaƙi, Allah da wani wanda zai iya yi mana irin kasadar da yake ɗauka, da mun canza shi, ɗan rainin hankali ne, ko fushi yake saboda wannan karon ba ka fito da shi ba?" "Da fushi yake yi, ba zai ɗauki wayata ba, kuma ina son aiki da shi, ba ya jin kasada komai zafinta kuma ba shi da mgana ko kisan kai zaka yi a gaban sa, sai ya ga dama zai ɗaga kai, balle ka ji zancen a waje. Sannan babban abun shi ne, bokan nan ya ce nasarata tana tattare da wanda yake zubar mini da jini, na riƙe shi sosai, shiyas nake shanye iskancin sa". P. A ya ce "haka ne ya na da amana, ba shi da magana sam, amma shi ya san da hakan ne?". "Haba dai, hauka nake yi na bari ya sani, ba abun da ya sani, kawai aiki yake yi mini" Misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma, manyan injiniyoyi ne zaune a falon indabo, suna ta lissafin ginin plazarsa. Ga wanda zai tattauna da su a kan harkar yaƙin neman zaɓensa, suma su na jiransa. Al'amin yana cikin falon, ana ta lissafi, shikuwa yana hakimce yana kallon tv. Sai da aka gama lissafi, za ayi total ɗin kuɗi, Al'amin ya kalli shugaban engeneers ɗin ya ce "Kayi plusing da kuɗin siminti buhu shida, da tiles carton biyar" Ya ce "Na menene?" "Ina ruwanka, ka saka kawai". Injiniya ya kalli Indabo, Indabo ya ce "Kuɗi ka ke buƙata ne na baka?" "Gyaran gidana zan yi nima" Indabo ya ce "Engeneer a rubuta, a bashi" Al'amin ya sake cewa "Akwai yarana mutum biyar, da nake son a saka mini su a cikin aikin ginin nan, su yi su ma a sallame su" P.A ya ce "An gama mai dogon zamani" "Zamu zo tare da su, ni ne cikon na shida, da ni za ayi aikin a biyani" P.A ya sake cewa "Ba ka da matsala" Aka gama aka sallami injiniyoyi, 'yan jami'iyya suka shigo, duk yana zaune, aka gama meeting. Duk sai da suka gama, sannan Indabo ya mayar da hankalinsa da Al'amin ya ce "Mai zamani" ya ɗaga ido ya kalli indabo. "Akwai tafiya da zan yi ƙaddamar da takarata, a yammacin garin nan, ina buƙatar tawagar ka kai da mutanen ka, saboda ban san ya zata kaya a wurin ba, 'yan sandan nan gaibu ne wasu lokutan". "Yaushe ne?" "Nan da kwana goma" "Cikin azumi kenan?" Indabo ya ce "Eh" "Allah ya kaimu, baka da matsala" P.A ya ce "Allah ya ƙara maka nisan zango mahadi mai dogon zamani. Ina matarka kuwa?" Da sauri ya kalli P.A ya ce "Kamar ya ina matata, meye haɗinka da ita?" "A'a babu komai, lokacin da kana tsare ne, ta zo ita da Walid, ko da yadda za ayi ka fito, lokacin honorable baya nan" Viper ya yi shiru bai sake cewa komai ba. Wata ƙatuwar mage ce ta shigo, da matasan 'ya'yanta, fara tas kana ganinta ka san 'yar waje ce. Al'amin ya tashi ya nufi in da take, ya saka hannu ya ɗauki guda ɗaya ya ce wa P.A "Wannan mace ne ko namiji?" "Namiji ne" "Zan tafi da shi" P.A ya ve "Ka san kuɗin abun nan kuwa? Ya kai dubu ɗari shida fa, wannan ƙaramin". "Da gold aka yi shi ne?" Yayi maganar yana nuna ɗan muzurun da yake ta ihu saboda ya ji matsa. Indabo ya ce "A'a ɗan Germany ne" "Tun da ba daga aljanna ya zo ba shikenan, kai kawo leda na saka shi" yayi maganar yana kallon mai goge-goge. "P.A ya ce wace irin leda kamar zaka ɗauki masara, kwando dai za a baka. Yayi ƙerere, aka kawo masa kwando, ya saka muzurun ƙato da shi fari, jikinsa cunkushe da gashi mai kyau. Ya kalli Indabo ya ce "Zan tafi" Indabo ya yi murmushi ya ce "Ga abun kuɗi nan ka ɗauka a hannunka, ai ba sai an sallameka ba" "Za a sallame ni ko in tafi?" "P.A sallame shi" P.A ya buɗe jaka, ya ɗebo kuɗi ya miƙawa Viper. Al'amin yayi masa wani mugun kallo, indabo ya ce "Ƙara masa" "Ya ƙara ɗebowa, ya ƙara masa" Ya karɓa ya ce "Na karya wani yaro, yana emergency, babar yaron tayi maganar a kamani, a bi wa ɗanta hakkinsa, yana can a emergency asibitin tsakiyar gari, a kashe wutar, ko ta ƙone yiwuwar aikinka, hankakin nan suka yi ram da ni, ba zan yi aikinka ba" daga haka ya fice daga falon. P.A ya ce "Kai, honorable Mai zamani yana hawa kanmu da yawa wallahi, wai sai abun da yake so za a din ga yi yayi ta yi wa mutane tunƙaho?" Indabo yayi murmushi ya ce "Rabu da shi lokaci ne, bari a ci zaɓen, ai ka ga mutumin can ya ce akwai nasarar mu a tattare da shi, yanzu abun da za ayi, ka koma ka yi waya, ka saka a haɗa wata tawagar ta 'yan daba, da zasu far mana a wurin taron, yadda za a samu a zubar da jinin shi ma a can. Sannan ka tara mana 'yan media, idan hakan ta faru a ce abokan adawa ne suka yo hayar 'yan daba suka far mana". "An gama honorable, yanzu kuwa zan je na tara su na sanar musu tun yanzu" "Yauwwa, idan ka gama da su, a hanzarta ko aike ka yi wurin wanda ya karya ɗin, a rufe bakin babarsa" "Ok sir" *** Al'amin ya koma gida, ya tarar da Jauhar da maƙwabta, tana yi musu kitso. Yana shigowa hannunsa riƙe da ledoji, ta tashi tana murmushi, suka gaishe shi, babu wanda ya amsa sai sannu zuwan da tayi masa ya amsa. Ta miƙe hannu za ta karɓi kwandon, ya ce "Banda wannan" ya shiga falo da shi. Ta dudduba kayan, kayan abinci ne wata irin ajiyar zuciya ta sauke, tare da yi wa Allah godiya. Allah ya sa ta gama kitson, ta sallame su suka tafi, ta shiga falon hannunta riƙe da cup ta risuna ta miƙa masa. Ya karɓa ya ga zoɓo mai sanyi, sai ƙamshi yake yi. Ya kafa kai ya zuƙe ya miƙa mata kofin ta ce "Ba ka ce ba" Ya ce "Alhamdilillah" tayi murmushi ta ce "Sannu da zuwa" ya jinjina kai ta ajiye kofin, ya jefo mata muzurun nan a jiki, ta saki ihu tana tsalle, ta ce "Meye wannan?" "Shi ma wannan ɗin tsoronsa ki ke ji?" "Kamar kare fa?" "Mage ne, saboda ƙadangarun da suke damunki, ko shi ma tsoronsa ki ke ji?" Ta ce "Laaa, to ai bai yi kama da mage ba, masha Allah so cute" ta durƙusa ta ɗauke shi. "Master ina ka samo shi dan Allah, kamar ba ɗan nan ƙasar ba. Kai amma na ji daɗi sosai, wani sunan zamu saka masa" Ya ce "Muzuru" Ta kwaɓe fuska ta ce "Muzuru kuma? Sunan gayu za a saka masa, wane irin muzuru?". "Ba sunansa kenan ba?" "A'a, na saka masa suna mai zamani" "Ki ka kuma ko?" Yayi maganar yana kallonta. Tayi murmushi tana shafa kyakkyawan jikin muzurun. Ya ve "Da gaske kin je wurin P.A ɗin Honorable lokacin da aka rufe ni?" Ta kalleshi ta sunkuyar da kai. "Ki bani amsa" Ta jinjina masa kai alamar eh. "Ko wani irin hali zan shiga, kar ki sake zuwa wurin wani, mussman gidanmu da wurin 'yan siyasar da nake mu'amala da su, dan su fito da ni" Ta ce "In sha Allah, ba zan sake ba, amma dan Allah ka daina zuwa wurin da zaka cutu, kaga idan aka rufe ka, nikaɗai nake damuwa ba wanda yake taimaka mini, ni kuma ba zan iya jurewa ba ganinka a tsare" tayi maganar jikinta a sanyaye. Ya saka hannu a aljihunsa ya ciro kuɗi, ya ce "Ungo" Ta saka hannu ta karɓa ta ce "Na menene master?" "Ana zubar da kuɗi ne?" "Wai bani ka yi? Duka nawa ne?" "Mmm ki sha madara" Ta washe baki ta ce "Allah ya saka da alkhairi, Allah ya yi maka jagora, ya ƙara jan dogon zamanin nan" Ya ce "Za ki ga zamani, idan na kamaki" Tayi murmushi ta ce "Wannan kuɗin ya fi ƙarfin shan madara ai" Ta din ga kwarara masa addu'a, tare da nuna tsantsar farincikinta a kan abun da ya yi matan. A daren ya kira guduma a waya, ya sanar masa da batun aikin ginin da za ayi, ya kira Walid da su liti, da wasu daga cikin yaransa, sai dai sai da suka sha wiwi, suka yi bushe-bushen su, domin samun ƙarfi wurin gabatar da aikin. Sai dai tun da Allah ya sa Al'amin ya kawo ɗan muzurun nan, jauhar ta samu nayi, ta tattara nutuswarta da hankalinta a kansa. Duk ranar da babu aiki, sai guduma ya zo gidan Viper, ya tambayi jauhar ko ta na da aike ta kawo ya kai mata, tun ranar da ya ga zata kai markaɗe, ya karɓa ya kai mata, Anty sama Anty ƙasa, kasancewar ta mai kyauta, ya sanya take farinjini a wurin mutane, dan idan yayi mata aike, idan tana da Abinci ta na bashi, ba da abincin nan ba ƙaramin kankaro mata kima yake yi a. Sai guduma ya mayar da Al'amin kamar yayansa, bashi kaɗai ba, har 'yan sauran yaran da suke rashin jin, jama'ar guduma, idan suka ga Al'amin, tsakaninsu da shi girmamawa, idan da kuɗi a jikinsa, haka zai bi su mai ɗari biyar mai dubu, hakan ya sa suke yi masa biyaya sosai da sosai. Hatta layin gidansa, idan kwata ta cika, ko ciyayi suka fito, haka za su zo da kayan aikin su, su gyara tsaf. Sannu a hankali, Al'amin ya fara janye matasan, shi dai ba zai hana su shaye-shaye ba, sai dai akwai abubuwan da ya yi musu iyaka da sha. Da sharuɗan da ya gindaya musu, a kan in dai za su zauna da shi, sai sun kiyaye su. Jauhar tana makaranta jarrabawa, biyu suka yi ranar, ta dawo ta tarar an yi plasta a gidan gaba ɗaya, da shi da su Walid da guduma, sun yi kaca-kaca da gidan. Tana tsaka da mamakin ya dawo, ya tarar da ita ta ce "Master, aiki ku ka sha haka? Baka gaya mini ba, balle na kwashe kayan kuma ayi wa masu aikin girkin?". "Da su mai laya muka yi, ba wani abu". "Master wai a ina ka samu kuɗi haka? Amma ka yi haƙuri idan tambayar da na yi tayi tsauri". "Bana sata" amsar da ya bata kenan ya fita. Zata iya shaidar hakan, amma yakamata ace ta san in da ya samu kuɗi, tana tsoron ya ɗaukko musu rigima, sai dai gidan yayi kyau sosai. Da daddare ya dawo, sai dai sai wani share ta yake yi, dan ya ji haushin tambayar da tayi masa. "Master, dan Allah ka yi haƙuri, na san tambayar da nayi maka tayi tsauri, amma ka yi haƙuri dan Allah, Allah Ya ƙara maka arziki da wadata, ya tsare mini kai a duk in da ka ke" yayi mata shiru yaƙi amsawa. "Tuba nake, tare da dukkanin girmamawa kaina bisa wuyana, nake roƙon ayi mini afuwa, ayi haƙuri a yafe wa ƴar madara ranka ya daɗe, Allah ya ƙarawa zamaninka tsayi, ya kare ka ko a gida ko dawa ayi haƙuri ina ƙara bada haƙuri namijin mazaje" Ba ƙaramin fasa masa kai kalamanta suka yi ba, duk da ba yau aka fara yi masa kirari ba, amma sai ya ji nata ya zama na musamman, har cikin kansa ya ji kirarin. Amma kamar wani basaraken zaki, haka yayi shiru ya cigaba da kaɗa ƙafa. "To in dafa ruwan wanka na kai toilet ɗin tsakar gida? Na san an gaji da yawa yau. Ya kalleta ya ce "Ba na so" Ta sakar masa wani ƙasaitaccen murmushi ta ce "Ai na ce ayi haƙuri, manya ba sa fushi fa" ta yi maganar cikin shagwaɓa. A taƙaice ya ce "Kai mini" Bayan yayi wanka, suka zauna a falo, suka ci abincin dare, dama tun a hanya ta sayo wa magenta kifi, ta nutsu tana bashi, tana yi wa master hira. Kasancewar ɗakunan an yi sabuwar plasta, ya sanya suka kwana a falo, sai da ya tabattar ta yi bacci, sannan ya fice tsakar gida yayi shaye-shayensa. Gaba ɗaya washegari jauhar a gidan mai ɗinki ta wuni, ta tayata aikin ɗinki, saboda gidanta su Al'amin suna aiki, hatta ƙofar gidan sai da aka yi wa plasta, gyara ko yaya yake kyau ne da shi, sai ga gida yayi kyau sosai da sosai. *** Yau ɗaya ga azumi, ranar jauhar tana da exams, Al'amin ya ce ta zo ta hau babur ɗin sa ya kaita, babu abun da ta tsana irin yadda yake yawo da babur ɗin babu salansa, ga babur ɗin kamar na 'yan gwangwani,saman babur ɗin nan duk a ragargaje, kana kallon wayoyin da aka yi wearing ɗin nan da su. Amma dan kar ta watsa masa ƙasa a ido, haka ya karkato babur ɗin, ta rirriƙe shi ta hau, suka tafi. Ko da ta dawo a gida ta tarar da shi, duk idonsa yayi ja, wanda idan ba da ƙwaƙwƙwaran dalili ba, ba za ka ganshi a gidan ba. Ta kalleshi ta ce "Master na dawo" Ya ɗaga mata hannu kawai. Ta shiga ta canza uniform, ta dawo yana kwance yayi wujiga-wujiga. Ta fito ta shiga kitchen, dan ta ɗora musu abun buɗa baki da wuri. "Master wai duk azumin ne, ko magana ta gagara" yayi mata shiru. Kawai ta hau dariya "Wallahi master ranar da babu abinci ban san yaya zaka yi ba, wato ba ka ko azumin nafila, yau ɗaya duk ka fita hayyacinka har haka?" Hararta yayi, yayi mata banza. Ta din ga yi masa dariya, ƙarshe ya koma tsakar gida ya shimfiɗa tabarma, yayi shame-shame kamar gawar sababi. Ko da aka sha ruwa, ba yadda ba ta yi da shi ya tafi masallaci ba, ya ƙi ya shanye lemo jug guda, da uban ruwa kamar amale, kuma ya fara da cin shinkafa, maimakon ya fara da abu mai ɗumi yaƙi. Ta ce "Ohh ni matar master, ya Allah kar ka hanamu abun da zamu ci a kowane hali, ranar da babu abinci akwai matsala master magana ma ta gagara yau azumi ɗaya kamar zaka rasu?" Yayi mata shiru yaƙi kulata. A ɗan tarin da take yi, da kuɗin da ya bata daf da azumi, tayi musu sayyayar kayan tea saboda tanadin azumi. Sai da aka yi azumi biyar, sannan Al'amin yake iya fita idan yana azumi, ya je ya ɗan yi neman kuɗinsa, gefe ga black market ɗin su ta sayar da kayan maye. Yau ya dawo da la'asar ya sheme a falo, sai sauke numfashi yake yi. Ta kalleshi tana dariya, ya kalleta ya ce "Ki ka sake ki ka yi magana ni da ke ne". Jauhar ta ce "A'a ni ban ce komai ba" tayi maganar tana cigaba da dariya. Tana ta aikinta an kusa shan ruwa ya ce "Anya kina azumin nan kuwa?" Ta ce "Ina yi mana" "Gani nayi yau sha bakwai ga wata, ba kya azumi" Ta kalleshi ta ce "To meye da sha bakwai ga watan?" Al'amin ya ce "Period ki ke yi, dan banaba kya azumi" zaro ido tayi cikin mamaki, yaya aka yi ya san tana period, cikin jin kunya, ta ce "Ni ba abun da nake yi, ba wanann date ɗin bane" Kawai ya gyaɗa kai, ya ce "Ai da ki ka gama cin ƙosan a kitchen ki ka cika cikinki, ba ki goge bakinki ba, kuma lemon da ki ka sha ma cup ɗaya kin sha naki, tun da ba azumi ki ke yi ba, sai iya yi mini dariya" ai kamar ƙasa ta tsage ta nutse, ba ta sanin ya ake yi, yake sanin ta aikata wasu abubuwan ta hau goge baki ta ce "Sa ido ba kyau, azumi ka ke yi kar ka zobe ladanka, ko a kwashe ladan naka a bani" Yayi murmushi bai ce komai ba. A wurin shan ruwa faɗa suka yi ta yi, wai ba zata cika kofi da kunu ba, ba tayi azumi ba, kamar sako da sakuwa. "Wai master, dan ban yi azumi ba ai ni na girka, sai ka barbaɗawa duniya ban yi azumi ba? Haba master" Ya ce "Eh ai ba yi ki ka yi ba, dan haka nawa sai ya fi naki yawa, ƙara mini" Ta tura baki ta ce "Aikuwa da gobe in Allah ya kaimu sai dai ka karɓo kunun sadaka, da ƙosai ka ci, ba zan yi girki ba, tun da ni ba na azumi, ko ka girka abunka". Ya ce "Eh dan dai girki, ba wuya zan iya, ƙosan nan ma rago shi nan, gandiya ƙatuwa da ke ba kya azumi" "Bani da lafiya ne" haka suka yi shan ruwan, ya din ga jin kamar bai taɓa shan ruwa da nustuwa irin wannan ba. Ita kanta tsokanar da yake yi mata daɗi take ji, bayan sallar isha'i ya zauna a falo, ya ɗauka zata yi masa surutun da ta saba, sai dai hankalinta ba ya kansa, yana kan magenta da take cewa boti, tana bashi abinci tana shafa shi, haushi ya ishe shi, shi gashi ba iya hirar yayi ba, balle shi ya fara, kawai ya tashi ya tafi ɗakinsa. Bayansa ta bi da kallo kawai ta yi murmushi ta ce "Master kenan, hukuma sai da rarrashi". Bakwai ga watan azumi ya kama ranar da za su bi Indabo campaign, tun dare ya haɗa yaransa da wurin da za su haɗu su tafi. Da sassafe bayan Jauhar ta tashe shi yayi sahur, ta idar da sallar asuba ta kwanta bacci, ya silale ya fice. Wunin ranar ba ta ganshi ba, ba ta damu ba sai da ta ga an kusa shan ruwa, ta din ga kiran wayarsa, amma ba ta shiga, sai hankalinta ya fara tashi, dan ta san duk in da ya je da an kusa shan ruwa yake tahowa gida. Al'amin kuwa bayan sun dawo daga campaign, an yi sare-sare sun yi shaye-shaye, an yi wa indabo aikinsa yadda yakamata, Al'amin ya sallammi yaransa, shi kuma Indabo ya ce ya bishi gida, da shi da wasu 'yan jami'iyya su sha ruwa a gidansa, ya sanya an shirya abun shan ruwa. Al'amin ya ce sai dai su tafi tare da walid. Ƙaton falo ne na musamman, mai ɗauke da haɗaɗɗem dining, kayan abinci aka kawo, na ƙasaita aka din ga jerewa a kan dining ɗin nan, cikin fulasai na alfarma. Walid ya ce "Mu na cin albarkacinka mai zamani, wannan sabga haka?" Al'amin ya bari, aka gama jere abinci, ana ta rawar jiki a fara ci ayi buɗe baki, ya tashi, ya bubbuɗe fulasan. Wani irin farfesu aka yi na kajin gidan gona, ƙosassu, ga flask ɗin dankali dana ƙwai abincin ma har da na almubazzaranci. Al'amin ya ja flask ɗin kaji, ya janyo na dankali, ya haɗe kan kayan shayi madarar gwangwani da milo, ya kalli Walid ya ce "Dafe mini wannan mu ɓace". Indabo ya ce "Ina zaka tafi kuma, za a ci abinci?" "Gida" ya bashi amsa. "To kuma na ga kana harhaɗe kan kwanukan abincin, ya zaka yi da su ga mutane za su ci?" Kai tsaye ya ce " 'yar madara zan kaiwa" "A'a ya mage zata yi da wannan uban abinci haka?" Walid ya ce "Ba mage ba ce, madam za a kaiwa" Indabo ya ce "Haba mai zamani, sai ka ce a ɗibar mata, amma yaya za ayi mutane na zaune abincin mutum sha biyu duk ka kwashe rabi?". "Ba zai yiwu da ni da na saka rayuwata a hatsari, da wanda ku ka tsaya a cikin rumfa hankali kwance, ka yi mana sallama iri ɗaya ba, ai kana da kuɗi a dafa musu wani. Ka san son zuciya ba halina bane, a baya ban yi ba ba zan fara yanzu ba. Ba zan ci wannan abincin ita ba ta ci ba, kuma ai ga wasu nau'in abincin nan ku ci. Walid ɗaukko kwandon kayan marmarin nan ma" Indabo ya ce "To fulasan fa? Ka tsaya sai a juye maka a leda, na madam ne wannan" "Madam ba ta fi madam ba, sadaki bai fi sadaki ba. Ina fatan ka fahimci lissafin? kuma kuna da kuɗin sayen wasu, ko ba yanzu ba idan kun ci zaɓe zaku samu, dan haka har fulasan mun cinye" Indabo yana ji yana gani, Al'amin ya yarfa shi a gaban jama'a, suka kwashe abinci suka tafi. Jauhar ban da ruwa babu abun da ta sha, har bayan sallar isha'i sai yawo take yi a cikin unguwar tana nemansa, hankalinta a tashe. Ta gaji ta dawo gida da nufin ta kira Walid. Kawai ta dawo ta tarar da shi. "Master ina ka tafi, hankalina ya tashi tun safe rabonka da gida, ba ka gaya mini ina zaka je ba, gaba ɗaya tun da aka sha ruwa na kasa cin komai, ban san ina ka ke ba". "To kukan zaki yi?" "Baka gaya mini ina zaka je ba, hankalina gaba ɗaya ya ƙi kwanciya haba master dan Allah" "Ohh murya kamar tsuntsuwa, yenyenyen, ki din ga buɗe baki ki yi magana sosai" kawai tayi shiru cike da takaici, idonta kawai ya kalla, ya san hankalinta a tashe yake. Ƙeyata ya tura, zuwa ɗakinsa kawai ta tarar da jeren kwanuka, haɗaɗɗun fulasai, da uban kayan marmari. Tayi saroro tana kallon kayan. "Zo ki zuba mana mu ci, ba kayan wani bane, mun je campaign ne muka dawo aka shirya shan ruwa, na ce a gida zan ci na taho da shi". A ɗan tsorace ta ce "Master duk wannan kuma?" "Eh kwaso kwanuka" Iya kajin sai da suka tsorata ta, dan sun kusa goma, fulasai ne na alfarmar gaske. Ta ce "Ai ba zamu iya cinyewa ba". "Gasu nan dai, ki yi abun da ya dace". Duk son Jauhar da nama, sai da ya isheta, ta bawa maƙwabta, ta zuba wani ya kira guduma a waya, ya ce masa ya zo ya karɓa. Hatta magenta, sai da ya ƙoshi da ciye-ciye. Haka kurum ya din ga jin annashuwa a ransa, ganin ta ci ta ƙoshi, har abun ya gundureta. Bayan jera masa godiya da ta gama yi, kamar yadda ta saba, tare da addu'oi, ta ce "Master Alfarma zan nema a wurinka dan Allah" "Ina jinki" Ta saka hannu ta karɓi wayarsa ta ce "Dan Allah kar ka ce mini a'a, ko ba zaka yi ba". "To kar ki tambayi abun da ba zan iya ba". "Zaka iya mai babban suna, kaga naman nan yayi mana yawa, duk da an babbayar dan Allah sonake na ƙara gyara shi, ayi miya gobe in Allah ya kaimu, mu je yi wa su baba sannu da shan ruwa" A take ya tsuke fuska, ya ƙi magana. "Dan Allah Master, na neman albarka mu je mu gaishe su" "Wai ke wace iri ce ne? Tun da muka yi aure, bayan su hajiya, kin ga wani ya zo gidan nan daga ɓangarena? Ko Abbun kin ga ya zo? Dama maraba suke nema da ni, har gara mahaifinki ma ya zo" Jauhar ta ce "Kar ka ce haka, dama ba su yakamata su zo ba, mu yakamata mu je, ai su iyaye ba a fushi da su, kai fa ka yi wa wani faɗa a kan haka, bai kamata kai ace ka aikata haka ba, dan Allah ka yarda mu je" An kai ruwa rana sosai tsakaninta da shi, kafin ya amince. Washegari suka shirya, bayan azahar suka fara zuwa gidan su Al'amin. Suka fara zuwa gidan su Al'amin, suka yi sa'a Abbu yana nan, sai dai rahila tayi mamakin ganin Al'amin, yayi wani shar da shi, sai ƙamshin turare yake yi kayansa sun sha guga. Ashe Abbu zuwansa gidan su biyu, ba ya samun kowa, a gidan, gashi Al'amin ya wanke ƙafarsa ya daina zuwa gidan. Abbu baki ya kasa rufuwa, mamaki yake ganin Al'amin, a nutse da shi ya sako 'yar matarsa a gaba gwanin sha'awa, sai dai sai cika yake yi yana batsewa yana wani basarwa. Dan tun da suka gaisa da Abbu, bai sake cewa komai ba, jauhar ce take bashi amsa idan yayi magana. Rahila ma sai zuba take ta ce "Ikon Allah, anya ba a canzo wani Aminun ba, kun yi kyau abunku kun ƙara ƙiba, an ce kin yi rashin lafiya kwanaki, To na san dai ba zai wuce laulayi ba, Allah ya raba lafiya" Al'amin ya ce "Amin, tashi mu tafi rana tana yi" kawai ta girgiza kai jin Al'amin ya amsa, idan ma haka ne ai kamata yayi, yayi shiru kawai. Rahila ta sake cewa "To sai ayi ta kula da ita, ka san masu ciki sai ana lallaɓa su, ban da hantara da abun da zai ɓata mata rai, kuma ba zama zaka yi ba, ciki tun yana ƙarami ake fara sayayyar kayan jariri". Jauhar ta ajiye food flask, da leda ta ce "Mama ga wannan, kwa yi buɗa baki, a saka mu a addu'a" Abbu ya ce "Masha Allah, addu'a kullum cikin yin ta ake, Allah ya yi albarka" Rahila ta ce "Iyee har da su suga da kayan marmari?" Ta buɗe fulas ta ce "Abbu kaza ce fa a ciki, ikon Allah sana'a ka samu ne haka? Ko kuma haryanzu miyagun ƙwayoyi ka ke sayarwa, gara mutum ya san halaccin abun da zai ci". Al'amin ya kalli jauhar, irin kallon kin ga abun da nake gudu ko?. Ya ce "Ubana na zo gani, kuma banda 'yar madara ta matsa, da sai dai na je ƙofar masallaci, idan ya fito na ganshi kamar yadda na saba, dan haka ba sai kin san sahihanci da halaccin cin sa ba, tun da bani da alaƙa da ke" ya tashi ya danƙi hannun jauhar a gaban su. Abbu ya ce "Aminullahi tsaya mana"ya tsaya cak yana huci, jauhar sai ƙoƙarin zame hannunta take yi daga nasa, saboda kunya. Abbu ya ce "Allah ya saka da alkhairi, ya yi albarka. 'ya ta Allah ya saka miki da alkhairi, yayi muku albarka gaba ɗaya" Ta ce "Amin Abbu, a sha ruwa lafiya " A zatonta, zai ta yi mata masifa, sai dai ta ji bai ce mata komai ba, ya wuce da ita unguwar su, ya kaita har ƙofar gida. "Ki yi sauri ki fito mu tafi, mu koma gida" Ta ce "To* Ta sauka daga babur ɗin ta shiga gidan, suka gaggaisa, sai dai baba baya nan, ta ce "Dama ɗan abun sannu da shan ruwa na kawo masa, sauri nake yi na bar shi a waje, kar ya gaji da jirana" Anty Zakiyya ta ce "Lallai jauhar, shi mijin naki ya fi ƙarfin ya shigo ya gaida mu kenan?" "A'a ba haka bane Anty, kin san ba ya jituwa da 'yan unguwar nan, bana son wani abu ya faru ne" Mama ta ce "Haryanzu bai shiryun ba kenan? Sai labari muka ji wai ya fito ai, Jauhar wannan naman kajin, shi ya saya ko ke?" Ta ce "Shi ne" Suryaya ta ce "To a dai yi a hankali, Allah ya sa ba na sata bane ba". Jauhar ta ce "Allah ya tsare shi, Al'amin ba ya sata". Anty Zakiyya ta ce "Wato Jauhar ba zaki yi mana Allah ya sanya alkhairi ba ko, ko kishi ki ke yi?" Cikin rashin fahimta jauhar ta ce "Anty na me?" "Alhaji mu'azzam ya dawo, tun da kin yi aure yanzu hafsa zai aura, ya bayar da miliyan biyu tayi lefe, dubu ɗari biyar kuma kuɗin aure!" Ayshercool 08081012143. 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??     Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??     Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??     Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.      Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955 Abunka da zuciya, dumm haka ƙirjin Jauhar ya buga, da ƙarfin gaske, take wani abu da ba ta san menene ba ya taso mata. A ranta ta ce "Saboda haka dama ku ka aura mini Al'amin, dan rusa aurena da Alhaji mu'zzam?" 'kul jauhar, Al'amin zaɓin Allah ne a gare ki, babu wanda yake da ikon canzawa wani ƙaddararsa, dama haka Allah ya tsara miki' Cikin sauri ta ce "Ahh haba, amma ba a gaya mini ba, ga shi muna waya, ina yi muku magana ta what's app, Anty ke ma ina da lambarki, amma ba a gaya mini, ko dan kar in haɗa lefen na zo na ɗauki kayan kwalliya ne ya sa ba a gaya mini ba?" Anty Zakiyya ta ce "A'a kar a gaya miki ki ji wani abu a ranki ne, dama Allah bai ƙaddara mijinki bane" Jauhar ta ce "Haka ne, mijin wata baya auren matar wani, idan an gama haɗawa ni dai zan zo a bani kayan kwalliya". Surayya ta ce "Au, ashe fa ba ayi miki lefe ba ke ko?" Jauhar ta girgiza kai ta ce "A'a kin manta an yi mini sayayyar kaya?" "Duk da haka wannan ai ba lefe bane ba" Wayar jauhar ta fara ringing, ta cirota daga jakarta ta ce "Master" "Fito mu tafi" "To gani nan" "Bari na tashi yana jirana, idan an saka lokaci sai a gaya mini" Hafsa ta ce "An saka bayan salla da sati uku ne" "To Allah ya sa zamu gani, a gaishe mini da baba, sai kuma Allah ya kaimu salla, Anty walida ku kuma na gaji da roƙonku ku zo gidana, ko sau ɗaya babu wanda ya taɓa yi mini kara ya zo". Hafsa ta ce "Ke fa babu wanda zaki gani a gidanki, muna yayyenki zamu din ga zuwa gidanki, ko so ki ke mu zo mijinki yayi mana illa?" "Haba dai, ba fa mahaukaci ba ne, da zai yi muku illa, da ban kawo yanzu tare da shi ba, sai anjimanku" Zuba mata ido yayi, har ta ƙaraso, sai dai ya lura da jikinta a sanyaye yake, bai ce mata uffan ba, ya kunna babur ɗin, ya karkata mata ta riƙe shi ta hau suka tafi. Sai yanzu ta ƙara gane dalilin yin amfani da yi mata sharri, wurin aura mata Al'amin, ba wai tana baƙin ciki da auren hafsa bane ba, ta san haka Allah ya ƙaddara kawai mamakin tsananin ƙin da suke yi mata take yi, ta san ko da kuɗi ba za su yadda su aurawa 'ya'yan su mutum irin Al'amin ba, saboda kar ta huta shiyasa suka yi mata wannan muguntar. Kallon bayan Al'amin take yi, a ranta ta ce "Kai Allah ya zaɓa mini, kuma in sha Allah sai na yi kyakywar rayuwar aure da kai master'. Da haka suka ƙaraso gida, sai dai yana ankare da yadda walwalarta ta gushe, take komai jiki a sanyaye babu kuzari. Ɗan muzurunta na ta kewayata, yana yi mata ɗan kuka, amma ta kasa kula shi, wanda da tana cikin walwala da tuni ta ɗauke shi tana yi masa rawa, da ma shi ba shiri yake yi da muzurun ba, dan dana sanin kawo mata shi ma yake yi, saboda yadda take tsananin ba wa muzurun kulawa, kamar ya jefar da shi haka yake ji wasu lokutan. Ya zuba mata ido, tana ta yi wa wani mayafi ado da beads, na kayan sallar mutane da take ta yi, sai dai a saɓule take  aikin. Muzurun ma ya gaji, ya koma gefe ya kwanta, saboda ta kasa kula shi. Har aka sha ruwa, ko surutun yau ba ta iya yi, abincin ma cakalarsa kawai take yi, ta kasa ci ta ajiye ta tashi tayar da sallar taraweeh. Ta cigaba da aikin beads. "Ssss, Ji mana" ta ɗaga kai ta kalleshi. "Zo mana"ta ce "To" ta yinƙura ta tashi, ta ƙaraso gaban sa, tana ƙoƙarin zama a ƙasa, ya nuna mata kusa da shi, ta zauna tare da sunkuyar da kanta. "Kin ga muna zamanzamanmu, ki ka kwashe mu, muka je wurin mutanen nan, gashi kin je an yi miki wani abun kin kasa sukuni, shiyasa tun farko na ce kar mu je, ki ka dage, kin dawo kin kasa nutsuwa, me aka yi miki?" Ta girgiza masa kai ta ce "Bakomai" Ya ce "Bana tambaya sau biyu" "Ka yi haƙuri dan Allah, babu komai, zuwa da safe zan wartsake in sha Allah". "Ba ki da juriya, kin fiye rauni, da wuri ake ganin gazawar ki, ki ƙara ƙoƙarin zama jaruma, ko dai ayi miki ki shanye ko shirya ramuwar gayya sama da abun da aka yi miki. Ki ajiye wannan abun da ki ke yi, ki tafi ki je ki kwanta" Ta jinjina masa kai ta ce "To master, na gode sosai" ta tashi jiki a sanyaye ta tafi ta kwanta. Sai dai bacci ya gagari idonta, ta din ga tunanin, meke damunta kishi ne ko hassada. Sai dai ta tabattar wa da kanta ba kishi bane ba, saboda ta riga ta zama matar wani, ko ba komai a yadda yake ɗin nan, ta fara appreciating yanayin zaman na su yanz saɓanin da, dan haka tana matar wani ba zata yi kishi a kan wani ba. Hakazalika ba hassada ba ce ba, ba ta ji ta damu dan hafsa zata shiga cikin daular da, da ita ce zata shiga, ta san wannan nufin Allah ne, kawai tana jinjina yadda suka shiga suka fita, suka aura mata Al'amin dan kawai kar ta auri Alhaji mu'azzam. Wannan gillin ɗabi'a ce ga zuciya, da duk yadda ɗan adam ya kai ga dannewa sai yayi tasiri, ta din ga istigfari da roƙon Allah ya sanyaya mata ranta, ta manta ta fuskanci Rayuwarta. Yanayin yadda Al'amin ya fara nuna damuwarsa a kanta, ya ke sanya wa ta ji tabbaci da ƙwarin gwiwar cewa wataran za ta ji daɗinsa, tun da dai babu duka ko zagi a tsakanin su, shaye-shayen sa da nema rigimarsa ne babbar matsalarta, gashi yanzu cefane ma yana yi ko ba kullum ba. A cikin kwanakin da ta dage da addu'a, sai ta fara jin sassauci ta fara mantawa, ta cigaba da mayar da hankali a kan sana'arta, da yi musu Addu'a babu dare babu rana. Al'amin ya fara rage yin shaye-shaye a gabanta, sai ta yi bacci, sai ya fita tsakar gida, ko ƙofar gida yayi, duk da wasu lokutan idan ta shiga ta tarar da shi yana yi, mazewa yake yi ya haɗe rai ya cigaba da shan abun sa, amma sosai yake rage abun da zai yi, wanda zai sanya ta shiga damuwa. Ya mayar da ita asibiti, likita ya tabattar da jininta ya sauka, kuma ya dakatar da ita daga shan magani, na wani ɗan lokaci. Saura sati guda salla, gidan jauhar mutane ne kawai ke shiga suna fita, masu mayafai, masu ɗinkuna da zata yi wa stone work, masu kitso da lalle, a haka kuma tana kasa kayanta, na shirin dutse, sarƙa abun hannu, jigida, ga kayan lemo, masu zuwa kitso suna yi mata ciniki. Ta zama very busy, idan yamma ta gabato, ga aikin abinci, sai dai garin Allah yana wayewa, ya fice ya bar gidan, saboda mutane. Sai dai ana shan ruwa take sallamar kowa, ta ce sai gobe, za ta kula da mijinta. Yana falo a zaune, ya gama shan ruwa ya kasa tashi, wata mata tayi sallama, tayi ta yi wa jauhar magiya, wai tana son ta turo yaran, ta wanke musu kai, tayi musu kitso, kowace yarinya ɗari da hamsin, su huɗu. Jauhar ta ce "Haba Maman Nana, ki bani ɗari bibbiyu mana, ga wanke musu kai, ga kitso?" "Taimakawa zaki yi jauhar, idan ki na son gobe mu kawo miki coustomers, kin san yadda garin yake, ubansu bai bani ko sisi ba, ni nake wahalata dan yaran su fito fes, ko hankici bai yi mana ba" Jauhar ta ce "To shikenan, bari na sallami master, gobe in Allah ya kaimu akwai mutane sosai, turo su yanzu a wanke musu kan, in dafa ruwa a heater tun da da wuta, gobe in Allah ya kaimu da sassafe sai ayi kitson" "Ke, na hana kitson, kwashi yaranki ki tafi wani wurin ayi miki" ta ji muryarsa a ƙofar falo. Jauhar ta ce "Master meyasa?". "Na hana kitson, duk wannan wahalar da ki ke wuni kina yi a ɗari da hamsin? Dama wuni ki ke wahalar banza, saboda aikin yi yayi miki ƙaranci? Get out malama kwashe yaranki ki fita, iyayen son banza". Kamar jauhar ta yi kuka ta ce "Master dan Allah... "Shhh" yayi maganar yana ɗora yatsansa a kan laɓɓansa. Matar ta fita ta kalleshi kamar za ta yi kuka ya ce "Na ga aiki ne yayi miki ƙaranci, mu je ina da aikin da zan baki ni, ki zauna ki wuni kina wahala, a ɗari da hamsin, ina zaki kai kuɗi ne wai? Duk kin rame saboda kin saka azabar son kuɗi a ranki" Yayi maganar yana kallon ta, tana tsaye tana tura baki. Ya fizgota gabansa ya ce ya kai hannunsa wuyanta ya ce "Wannan ƙashin na wuya da ki na shi? Duk kin yi wuri-wuri ga azumi ga wahala" da sauri ta ɗan kama jikinta, saboda unexpected ya saka hannunsa a wuyanta. Maimakon ya sauke hannunsa, sai ya miƙar da hannunsa zuwa kan maƙogwaronta, ya fito da dogon harshen sa har wurin haɓarsa, ya lanƙwasa shi, sannan ya mayar cikin bakinsa ya ce "Na ga kina motsa baki, me zaki ce?" Jauhar ta ce "Ai shikenan ka korar mini coustomer, kuma ka shaƙeni zaka kasheni ka huta. Kuma sai ka biyani kuɗin wanda ka korar mini, ɗari shida" "Bana son ganin wannan ƙashin, kwana uku kawai na baki ya koma" yayi maganar yana sake shafa wuyanta. Riƙe hannunsa tayi, tana kallon idonsa, da abun da yake yi matan ko a jikinsa. Ɗan muzurunta ne, ya yo tsalle yana yakushin ƙafar Al'amin, saboda riƙe wuyan jauhar da ya yi, yana kuka. Al'amin ya kalli muzurun, yayi cilli da shi, ya ce "Na kusa mayar da abun nan in da na ɗauko shi, ya fiye zaƙewa, zo ki yi mini aikina" Ta biyo shi tana mitar ya korar mata coustomer's , ya nuna mata kujera 3seater ya ce ta zauna. Ta nemi wuri ta zauna, ya kwanta ya miƙe ƙafafuwan sa a kan cinyarta ya kaɗa mata yatsunsa, alamar tayi masa tausa. Ta ji haushin yi mata asarar ɗari shidan da yayi, shi kuwa ko a jikinsa, sai dai ƙasan zuciyarta mamaki take yi, ashe yana kallonta har haka da ya gane ta rame. Iya ƙarfinta ta saka tana jan yatsun ƙafarsa, tana son yayi magana, amma ko a jikinsa. Tun tana yi da marmari, har ta fara gajiya, dama gashi wuni tayi aiki, tun tsakiyar azumi rabonta da baccin kirki. A take ta fara gyangyaɗi, bacci mai ɗan nauyi ya yi gaba da ita, kamar a mafarki ta ji abu yana taɓa cikinta, ta buɗe idonta ta ga menene, babban yatsansa ya saka yana taɓa cikinta. Da sauri ta ɗame cikinta, ta kalle shi, ya rufe idonsa kamar mai bacci. Ta riƙe ƙafarsa, ta sake kallonsa, amma ya saka ɗayar ya cigaba. Ta saka duka hannunta biyu, ta rirriƙe ƙafafunsa, tana ajiyar zuciya kamar mara gaskiya. A hankali ya buɗe idonsa, yana kallonta, ta sake ɗaga kai ta kalleshi, suka haɗa ido, tayi saurin kawar da kanta. "Dambe zamu yi ne ki ka rirriƙe mini ƙafa? Tausa fa na ce ki yi mini". Kamar ta yi kuka ta ce "Na gaji bacci nake ji" "Eh da aikin banzanki ne, ba zaki gaji ba ai, kin ga yanzu kya samu lada sama da ɗari shidan da ki ke yi mini ƙunƙuni a kanta" A shagwaɓe ta ce "Ni ba ƙunƙuni nake yi ba fa, ka yi haƙuri to" ya janye ƙafafuwan sa daga kan cinyarta, ta tashi da sauri, muzurunta ya bi bayanta, ta saka hannu ta ɗauke shi ta nufi ɗaki. Baba ya ji daɗin abun da ya tarar jauhar ta kai masa, ya din ga murna da sanya mata albarka, tare da yi mata addu'a iri-iri. Ganin hankalin Jauhar yana kan 'yan kuɗaɗen da take samu, na sana'ointa, ya sanya ya ƙyaleta, baya son yawan takura mata. A goman ƙarshen nan, haka ta din ga damunsa, a kan yawaita ibada, dan azumin kawai yake yi, ba sauran ibadu. Da ƙyar take saka shi yayi salla cikin dare ko raka'a biyu ce. Dama idan aka sha ruwa, ya ƙoshi sai ya je dabar su, sun yi shaye-shaye tukuna ya dawo gida. Ana jibi salla, ta saka shi a gaba da naci, da magiya, su je ayi masa aski saboda gabatowar bikin salla ƙarama. Ya ce na za shi ba, ƙarshe ita ta zauna, ta wanke masa kan, ta rage masa sumar da almakashi, tayi masa gyaran fuska da shaver, tamkar ɗa da uwa. Ana gobe salla, ta yi masa list dai-dai na talaka, ta ce ya sayo, za ta yi abincin salla, dan abubuwa da dama idan ba ta ce masa yayi ba, ba zai yi ba, idan kuwa ta ce ya sayo zai sayo, idan ba shi da hali kuma zai gaya mata ba yanzu ba. Da sassafe ƙarfe bakwai, ta shigo ɗakinsa da mp ɗin ta, an sako kabarbari da ake yi yayin tafiya idi, tana maimaitawa. *Allahu Akbar, Allahu Akbar la'ilahaillala* *Allahu Akbar, Allahu Akbar walillahil hamd* *Allahu Akbar kabiran* *Walhamdilillahi kathiran* *Wa subhanallah bukratan wa asila* "Master, kar mu makara sallar idi fa, ka tashi" ya motsa a hankali yana yamutsa fuska. Ta miƙa masa hannu ta ce "Barka da salla? Ina fatan ka yi sallar idi lafiya" Yayi miƙa tare da hamma, ta ce "A'uzibillah, Alhamdilillahilazi ahyana, ba'ada ma amanatana wa ilaihil nushur. Ga ruwa mai zafi can, ka zo ka karya mu shirya" "Sai na karya tukuna" "To taso ka yi brush, ko sai na ɗauke ka ne, sai ƙara maƙalewa ka ke yi a katifa" Kukan ɗan muzurun nan ne ya sanya Al'amin shi tashi zaune ba shiri, ya biyo jauhar yana yi mata ɗan kuka. Ta kalli muzurun ta ce "Sweetheart, mu je na baka abinci" Al'amin ya tashi ya bar ta da muzurunta, saboda zaƙewar muzurun ta fara yawa a kan matarsa. Ya fito daga wanka, ta shigo ɗakin da wata leda, ta saka dogon hijjabi light blue, sai zuba ƙamshi take. "Master yi sauri zamu makara" Ya shafa mai, ta buɗe ledar ta fito da ɗinkakkiyar shadda light blue, da hula, ga agogo sai takalmi soso na ta da nasa, iri ɗaya na ta na mata na sa kuma na maza. Turus yayi yana kallonta, cikin tsananin mamaki. "Ungo saka, bari na je na rufe ɗakina kan ka gama" Kamar soko ya kasa karɓar kayan. "Ko ba ka so ne?" Tayi maganar a sanyaye. "A ina ki ka samo wannan kayan?" Ta ce "Dama ana samo kaya ne? Neman kuɗin da ka ke cewa na saka a gaba ne, ka san wata nayi ina yi mana tarin nan? Hmm saka kayanka ina zuwa bari na ɗaukko wayata da darduma" ta ajiye masa ta fice. Kallon kayan ya din ga yi yana jujjuya su, har da aiki a jikin kayan, shi bai yi mata kayan salla ba tayi masa?. Ya saka wandon, ya tsaya yayi shiru yana kallon rigar, har ta dawo ɗakin. "Master saka mana" ta karɓi rigar tana ɓalle botiran jiki, ya karɓa yana sakawa ta ce "Alhamdilillahilazi kasani haza saub, waraƙatani min gairi haulin minni wala ƙuwwa" Ta saka masa hula, ta saka masa lence ɗin hannun rigar, ta ɗaura masa agogo, tare da saka masa farin glass na maza. Tayi wani irin murmushi ta ce "Tubli wa yuklifllahu ta'ala. Wallahi kana da kyau master, ka ga yadda ka yi kyau kuwa? Subhanallah saka takalmin mu ke falo na yi maka hotuna" gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, ashe matan ma sunan suka tara? Wace irin mace ce jauhar. "Master ka yi dariya mana, sai hoton ya fi kyau" Ta gama yi masa hotunan, ta riƙo hannunsa, ita ma ta saka nata gilashin fari, suka fita sallar idi. Musulunci mai daɗi, al'ummar musulmi na ta ɓarkowa ta kowane angle zuwa masallacin idi. Shi rabonsa da zuwa sallar idi ma, har ya manta lokacin, amma yau albarkacin auren mace ta gari, ta saka shi a gaba har zuwa masallaci. Aka idar da sallar idi, suka haɗu a wani gate ɗin daban, bisa koyi ga sunna, jauhar ta bawa wata wayarta, ta ce dan Allah tayi mata hoton first eid with habinbi. Ta ɗauka zai ce baya so, bisa ga mamakinta, sai ta ga ya saka hannu, ya dafo kafaɗarta jikinsa, yana kallonta, ta saka hannu ta zagaya a ƙugunsa kasancewar da kaɗan ta wuce ƙugunsa, ta kalleshi ita ma tana murmushi. Hotunan sun yi kyau sosai, banda wanda ya yi wa Al'amin kyakkyawan sani, ba zai gane shi ba, sai ya zama very decent and calm. Har suka dawo gida, hannunta na cikin nasa, cike da shauƙi da nishaɗi. Ya karɓi mukulli ya buɗe musu gida suka shiga, jauhar baba ta fara kira, ta yi masa barka da salla, ya ce mata idan mijinta na da account, ta tura masa ya saka mata barka da salla. Ta kira yaya saifu ma, haka ta din ga bin family tana yi musu barka da salla. Ta kalli Al'amin ta miƙa masa wayarta ta ce "Saka mini lambar baba, mu yi masa barka da salla" "Bani da ita" ya bata amsa. Ta marairaice ta ce "Dan Allah master" Ya ce "Sai kuma ki yi" Haka ta haƙura ta tashi ta ƙyale shi, ta tafi ɗakinta, ya din ga kallon kayan jikinsa, yana sake jinjina ƙoƙari da ƙarfin hali irin na jauhar, wai shi ta yi wa kayan salla. A status ɗin ta, ta yi posting "Alhamdilillah first eid with my amazing Habibi, Allah ya ƙara wa zamaninka tsayi, ya maimaita mana" Surayya ce ta fara ganin status ɗin, ta din dariya tana nuna wa 'yan gidan, suka din ga cewa pretending ne, na lallai sai ta nuna wa mutane tana cikin kwanciyar hankali, sai dai suna tsaka da gulmar, ta sake saka hotonsu riƙe da dadduma a filin idi, wanda hakan ba ƙaramin girgiza su yayi ba da ba su mamaki. Master ya kai mintuna goma sha biyar yana zaune, ta fito sanye da leshinta da ta saka ranar ɗaurin aure, ta shafa powder da jambaki, ta saka kwalli, ta kwantar da gashin gaban kanta, da gel, ta yi ɗauri mai kyan gaske, gashi ta kaiwa Suwaiba tela ta gyara mata ɗinkin, dai-dai jikinta. Har ya tashi zai shiga ɗakinsa, ya waiwayo ya ganta ta fito, mp ce a hannunta, tana bin waƙar da aka saka, a cikin nishaɗin barka da salla. Cikin waƙar m sharif *Farin gani kai ne tauraro, ko a cikin samari, mai ji da ni ba ka yin ƙwauro ka sa na wuce gori, na ɗau takarda na riƙe biro, kai na saka a fari, kai zan ba dawakai, kowanne da silkai, matsayinka ya kai ba zan yi ma kishiya ba....... Da haka ta ƙaraso gabansa tana rawa, tana yi masa fari da ido. Tsayawa yayi yana kallonta yana murmushi, sai dai bai tsinke da lamarin na ta ba, sai da ta ƙaraso gabansa ta riƙe hannunsa wai sai ya yi rawa. Karo na farko da ya buɗe haƙoransa talatin da shida yayi dariya. "Ba dariya zaka yi ba, ka yi mini liƙi ko ka yi mini rawa" ya buɗe baki ya ce "You are not serious" "Am serious mana, rawa ko liƙi, biyani ɗari shida ta ma da ka korar mini coustomer's" ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu da ɗari uku ya ce "Suke nan nake da su, uwar son kuɗi" "Ungo dubu ɗaya, sauran bari na bayar da ayata a markaɗo mini, na haɗa da snacks da tuwon salla na raba. Ba ka ce ma na yi kyau ba, ka taɓa ganin mace da tayi kwalliya tayi kyau kamar yadda na yi yau?" Yayi murmushi ya ce "Ni da ba kallon mata nake yi ba, ya za ayi na sani, ni dai ba ki yi mini kyau ba, kamar babyn roba haka ki ka zama" yayi maganar yana matsa kumatunta. "Daga Angela zuwa 'yar madara, yanzu kuma babyn roba?" "Eh, irin na wasan nan ba" Jauhar ta ce "Kyau nayi maka ne" Ta fice tsakat gida, tabbas tayi kyau kam, tayi fresh farar fatarta ta karɓi baƙin leshin sosai da sosai, kwalliyar ta yi mata kyau. Tana tsakar gida, wasila ta shigo ta kawo mata tuwon salla, suka gaisa tare da yi wa juna barka da salla. Wasila ta ce "Jauhar iyayen soyayya, mu matan layin nan, tare muka haɗa kai muka tafi idi, a hanya muka hango ku, an maƙalƙale hannun master ana yashe baki, kai jauhar a ji tsoron Allah" Jauhar ta ce "Anty wasila kina saka mini ido wallahi, ki sa ka in ta jin kunya" "Ke ba wata kunya, riƙe abunki wallahi, abunku gwanin sha'awa, kafin lokacin ya wuce, ba kowane namiji ne yake jure ayi ta soyayya ba". Al'amin ne ya fito, Wasila tayi tsit dan ba ta san yana nan ba, ta gaishe shi ya amsa ciki-ciki. "Master ina zaka? Kunun aya ka san baya daɗewa" "Nura ne a waje ya kirani, ba nisa zan yi ba" Ta ce "Ok to" Daga jikin gate guduma ya ce "Antynmu barka da salla". Jauhar ta ce "Yauwwa malam nura, ina fatan ka je idi?" "Eh na je, na biyo mu gaisa sannan ki bani tuwon salla". Jauhar ta ce "Aikuwa ka samu, amma sai ka kai mini markaɗen aya, ka sayo ƙanƙara sai na haɗa maka da tuwon" Ya ce "Ba case matar babban yaya" Al'amin bai sani ba, har gidansu jauhar ta aika da abincin salla, guduma ne ya kai ya kai na gidan su ita ma. Ta zuba wa Al'amin, ya tafi da shi, tun da ya shiga wurin na su, Liti da sauran yaran suke bin sa da kallo. Liti ya ce "Maza, wannan shuɗiyar audugar ruwan sararin samaniya fa, waye ya sayeka cikinta?" "Ban sani ba" Walid ya ce "Abun a tambaya ne, ni fa tun da na sanka sau ɗaya na ga ka saka manyan kaya, ranar da aka zarga maka uku, ina nufin igiyar sunnar ma'aiki da bint laban ɗin ka, wato madam 'yar madara" Ya tsuke fuska ya ce "Mai laya" Walid ya ɗaga masa hannu ya ce "Tuba nake, na kiyaya wannan ma'adanar abincin fa?" Al'amin ya ajiye musu kwanuka, suka dirarwa abincin nan da ci babu ji babu gani. Baba kuwa yaya saifu ya aiko, aka kawo mata fulasanta, da kuɗi dubu goma, kasancewar ba ta tura account number da ya ce ba a matsayin barka da sallar ta. Da daddare da ya dawo, yana shigowa ta ji warin sigari, dan da alama ma a cake yake, bai kulata ba, ya tafi ɗakinsa ya baje a kan katifa, ta bi bayansa har cikin ɗakin, cikin matsananciyar damuwa ta ce "Haba master, shi ne ka je ka sha da yawa, kalli a yadda ka dawo fa, gaba ɗaya ka ɓata mini ɗan farincikin da na tsinci kaina a ciki yau" yayi shiru yana sauke numfashi. Ta ƙaras ta ce "Tashi a cire kayan to, sai ka saka wasu" "Get out" "Ai zan tafi amma...... "I said get out" yayi maganar cikin tsawa. Ta tashi a razane, ta bar masa ɗakin, cikin azumi dai Allah ya taimaketa ya ɗan nutsu, saboda baki a rufe yake, ba ya shaye-shaye sosai, yau da ga sallacewa ya koma ruwa. Saboda tsabar takaici, ko baccin kirki ba ta yi ba. Da safe kamar ba shi ba, ya tashi ya fito abun sa, ya sayo abun karyawa, sai share shi take yi, amma ya nuna ko a jikinsa. Kasancewarta mai matukar raunin zuciya, sai kuma ta sake. Suna karyawa, Hafsa ta kira ta a waya, jauhar ta ɗaga tayi mata sallama ta ce "Amarya ba kya laifi" "Mhmm, dama anko ne mama ta ce sai an nuna miki, shi 'yan gida za su yi da bikina, zan turo miki ta what's app lace ne dubu goma sha biyar sai atamfar kamu dubu tara, na san ba lallai ma ki yi" Jauhar ta yi murmushi ta ce "Anty hafsa kenan, aikam dai kun san mijina talaka ne, zan sako dai abun da Allah ya hore mini na zo, in sha Allah" "Dama na sani ai, mama ce ta takura a turo miki kar abun ya zama surutu, a ga kin fita daban. Allah ya sauwwaƙe tisya" "Ba tsiya ba ce anty hafsa, idan ruwanka bai isa alwala bane sai ka yi taimama Allah ya kaimu bikin lafiya" ba shi aka gaya wa ba, amma sai ya ji maganganun hafsan tamkar direct da shi take, wani irin haushi da takaici ya kama shi. Sai dai ya basar ya cigaba da karyawa abun sa. Ya kammala ci, ta tashi ta yi aikace-aikacenta, yau ma wata kwaliyyar ta yi da abun da Allah ya yassare mata. Ya ce "Babyn roba" Ba ta kalle shi ba ta ce "Saura ta rodi" "Zaki gama kumbure-kumburen naki ki sace" Ta share shi, tana shafa muzurunta d take cewa boti. "Ina magana ki ka share ni, kina wasa da wannan abun da nake dana sanin kawo shi?" "To me zan ce maka? Kawai ka je ka sha abun da ka sha, daga yi maka magana ka hantare ni" tayi maganar idonta na cika da hawaye, saboda takaici. Maimakon ya damu, sai yayi murmushi ya saka hannu ya matsa kumatunta a hankali ya ce "Abun wasa na, you are like a toy to me, wani abu mai ɗan bani nishaɗi wasu lokutan" Galala take bin sa da kallo, ita ce ma abun wasan. "Kin daɗe kina yi mini abubuwa, abun da ki ka yi mini jiya ya tsaya mini a rai, ki ka ɗinka sutura sukutum ki ka bani, Allah ya suturtaki ranar da bayi za su tsaya a gabansa babu sutura. Na gode Allah ya baki miji nagari" Da sauri ta sake kallonsa, sakamon abun da ya faɗa na Allah ya ba ta miji nagari. "I still mean it, haryanzu ina kan bakana na rabuwa da ke a duk lokacin da ya dace, kina takura mini da yawa" A fusace ta saka hannu, ta buge hannunsa da ya riƙe kumatunta, ta waiwaya tana kallon gefenta. Ya ce "Idan ki ka kuskura ki ka jefe ni, yau ni da ke ne" tashi ta yi tana kuka, ta nufi ɗakinta. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??     Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??     Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??     Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.      Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955 Ba ta ƙara kula shi ba wunin ranar, dama kuma ficewa yayi ya bar gidan, ta rasa sai zuwa yaushe Al'amin zai yadda ya karɓeta su yi rayuwa, kullum ba shi da magana, sai maganar da zata tayar mata da hankali na zai rabu da ita, gaba Al'amin yayi hannun riga da duk tausayi. Abun da zuciyarsa ta raya masa kawai yake yi, ko ya yi maka daɗi, ko akasin haka ba damuwarsa bane ba. 'yan yaran da suka din ga shigo mata yawon salla, su ne suka din ga ɗebe mata kewa da rage mata damuwa. Sai bayan sallar magariba sannan ta sake ganinsa, tun da ta yi masa sannu da zuwa, ta ajiye masa abinci, ta koma gefe ta na danna wayarta. Sai da ya ci ya ƙoshi, ya samu wuri a kusa da ita ya zauna, ya ce "Abun wasan, ya dai?" Ta ɗaga kai ta kalleshi ta sunkuyar, ta hau wasa da yastun ƙafarta. Hannunsa ya saka shi ma a yatsun ƙafarta yana tayata wasan da take yi da su. "Master" "Mmm" "Meyasa ka ke son lallai sai ka sake ni ne? Saboda ka ga bani da makoma ko? Ban taɓa burgeka, duk ƙoƙarin da nake yi, ba ka appreciating kullum cikin tsorata ni ka ke, kana gaya mini abun da zai ɗaga mini hankali, me nayi maka ne?" "Baki dace da ni ba, da salihin mutum nagari ki ka dace. Da zan iya samun mutum mai amana da zai riƙe ki, zan iya rabuwa da ke ya aura, you  have an innocent soul, that doesn't deserve someone like me, shiyasa nake yawan gaya miki haka. Ko jiya a fusace nake, na yi miki tsawa sai da ki ka yi kuka, ina ɗaukar hakkinki" "To ni na ce maka bana son zama da kai ne? Ina yi maka addu'a, wataran zaka daina ai ko?" Tayi maganar tana kallonsa. Yayi shiru bai yi magana ba, "Dan Allah ka yi magana, zamu iya rayuwa tare, irin damuwar ɗaya, matsalar iyalan da muka tashi a tsakanin su, ba sai mu zama familyn junanmu ba, mu rayu cikin aminci da walwala. Amma master meyasa ka ke shaye-shaye bayan ka san yana da illa ga lafiyarka? Yana saka aikata abubuwan da bai kamata ba, kayi faɗa da mutane a zubar maka da jini, ko ka zubarwa wani, har kisan kai fa yake saka". "Wa na kashe?" Ta ce "Ranar da na fara ganinka, a unguwarmu, gawar wani na ganka da ita ka soka masa wuƙa" Yayi murmushi, ya haɗiyi wani abu mai ɗacin gaske. "Ban taɓa kisan kai ba, ranar ce haɗuwarmu ta farko ko? Ban kashe kowa ba" Cikin damuwa ta ce "Amma wuƙa fa na gani a gefen cikinsa, kuma meyasa ka ke shaye-shaye?" "Bana son silly question, rabu da ni" ta gyaɗa kai kawai ta ƙyale shi. Ranar hawan salla kuwa,  Jauhar ba ta san me ake yi ba, Al'amin ya haɗa yaransa, da miyagun makamai, da sunan tsaro kar wasu daga wani wurin su zo su fake da kallon hawan salla, su kawo musu farmaki su cutar da wani. Sai dai sun yi ba ta kashi da wasu marasa jin sosai da sosai, ciki kuwa har da yaran madaki. Sai da 'yan sanda suka yi kame sosai da sosai, daga wurin hawan Al'amin bai koma gida ba, ya wuce cikin gari, saboda kar jauhar ta ganshi da makami, da jini. A cikin garin ma, sai da suka yi wata fitinar, aka yi sare-sare da faɗace-faɗace. Sai bayan kwana biyu, jauhar take jin labarin abun da ya faru a wurin hawa, ganin Al'amin lafiya ƙalau ya sanya ta kwantar da hankalinta, tare da bawa kanta yaƙinin cewar babu shi a rigimar. Kwana na huɗu, tana kitchen tana girki, tana shirin kaɗa miyar cin tuwo, maman halimatu ta shigo gidan a gigice. Jauhar ta ce "Maman halimatu lafiya kuwa?" "Ke kina nan baki san abun da yake faruwa ba?" Cikin rashin fahimta ta ce "A ina?" "Wani ɗan daba ne wai madaki, daga can unguwar ku ya zo unguwar nan wai neman mijinki, wai ya illata masa yara, sai tarwatsa mutane suke yi, suna sara kan mai uwa da wabi a guje na ƙaraso" Cikin tashin hankali ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" take kanta ya sara, jikinta ya hau rawa, ta ɗauki wayarta ta kira lambar sa, sai dai tayi ta ringing baya ɗagawa. Hijjabinta ta ɗauka, maman halimatu ta ce "Ina zaki? Saran mutane fa suke yi, duk wanda suka samu duka ko sara". Ai ba ta ko tsaya bata amsa ba, ta fita cikin matsanancin sauri da tashin hankali. Ba ta san in da za ta nufa ba, addu'a kawai take yi da roƙon Allah, Allah ya tsare mata mijinta. Mutane na guje-guje ita kuwa kutsawa take tana duba ina zata ganshi tana kuka. A wani layi ta hango shi, ya riƙe wani matashi, idon Al'amin kawai ta kalla ta san a buge yake, babu alamar mutunci a idonsa, idanun sun yi jawur sai gumi yake yi, yanayin sa ya tabattar mata da ha tafka ɓarna, kafin ta ƙarasa, ya fito da harshen sa waje, kamar yadda yake yi, idan ya ƙudirci aniyar yin wani abu, ya ɗaga sweazland ɗin sa, babu tsammani ya ganta a gabansa, ta riƙe rigarsa tana girgiza masa kai cikin tsananin tashin hankali. "Idan ka kashe shi, rufe mini kai za ayi, ba lallai na sake ganinka, ka yi haƙuri kar ka yi kisan kai dan Allah" Jikinsa tsuma kawai yake yi, ya aiwatar da abun da zuciyar sa take raya masa, saboda yadda haɗin da yayi amfani da shi, yake fizgar kansa yake jin sa tamkar jinjirin doki, zuciyarsa kuma kamar an kunna wuta. Ta rirriƙe hannun da ya riƙe wuƙar da shi, da hannu ɗaya ya yi jifa da matashin gefe, shi kuma ya saki wuƙar, sai tangaɗi yake yi, ya kasa tsayuwa, sai gumi da yake tsatsafo masa ya furta "Madaki" kawai ya yanke jiki ya faɗi, sai a lokacin ta ga uban saran da yake gadon bayansa, ashe duk abun nan an sare shi a baya, rigarsa ta rine da jini. Wani irin gigitaccen kuka ta saki, ta ce "Na shiga uku, dan Allah ku taimaka mini a kai shi asibiti" tayi maganar tana girgiza shi. Ya kalleta da idanunsa, suka yi jawur, jikinsa ya fara rawa ga gumi ya jiƙa masa fuska. Ragowar mutanen da suke wurin, suka dare suka bar ta da shi, a wurin. "Master dan Allah kar ka rufe idonka, yanzu zamu tafi asibiti, Allah ka kawo mini ɗauki, Allah ka duba lamarin nan". Guduma ne ya shigo cikin layin da gudu, ya jefar da makamin hannunsa ya ƙaraso, wata irin ajiyar zuciya ta saki, yana zuwa ya jijjiga Al'amin ya ce "Master" sai dai idanunsa sun lumshe, saboda jinin da ya zubar. Yayi ƙoƙarin ɗaga Al'amin, ya saɓa shi a kafaɗarsa, amma abu ya gagara, ba ƙiba ce da shi ba, sai dai akwai nauyi. Ya kalli Jauhar da ta rikice, take ta kuka ya ce "Anty ki kwantar da hankalinki, in sha Allah yanzu zamu kai shi asibiti". Ya din ga wani irin fito, kan ka ce kwabo, wasu matasa suka din ga ɓullowa da ɗaya ɗaya, su ma suna fiton wasu suna fitowa. Suna zuwa suka yi tara-tara suka sunkuci Al'amin, guduma ya saɓa shi da ƙyar, da ƙarfin tsiya suka ƙwaci 'yar ƙurƙura a titi, suka ce mai ita ya bi si Asibiti su karɓa. Sai dai da suka je, ma'aikatan lafiya, suka ce ba za su karɓe shi su duba shi ba, sai da jami'an tsaro. Cikin kuka ta ce "Dan girman Allah kar ku yi mini haka, ku ceto ransa kar ya rasa ransa, dan Allah ku fara duba shi, kan a kawo 'yan sandan" ma'aikatan suka ƙeƙashe ƙasa suka ce, sai fa jami'an tsaro sun zo". Ta din ga rusa kuka a cikin emergency, guduma sai bata haƙuri yake yi. Ta kasa jurewa, ta tashi ta bi wani likita, ta riƙe rigarsa tana kuka ya ce "Dan girman Allah ka ceto rayuwar mijina, kar a rasa ransa dan Allah" Ya ce "Ba laifina bane ba, dole mu san meyafaru kafin mu taɓa shi". Kan kace kwabo, sashen emergency ya cika da 'yan daba, saboda an kawo al'amin. Babu tsammani ta ga shigowar liti tare da Walid, da wasu tawagar marsa jin suna take musu baya. Suka ƙaraso, in da jauhar ke zaune, da Al'amin a gabanta. Walid ya ce "Madam, ya aka yi haka ta same shi?" Ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, kawai ce mini aka yi ana faɗa, na je na tarar da shi, da zai cakawa wani wuƙa amma ya fasa, kawai dai ya ce madaki ya faɗi ashe an sare shi, kuma sun ƙi duba shi wai sai ƴan sanda sun zo, dan Allah ka saka baki yaya Walid. Ya kalli liti ya ce "Zan ɓallo ruwa, a toshe magudanan daga waje" liti ya jinjina kai, ya ja guduma suka fita. Wasu daga cikin matasan suka shigo, suka koro wasu daga majinyata waje, suka ritsa likitoci da makamai, sai sun duba Al'amin. Aka ce su kai shi kan gado, Walid ne ya ɗauke shi, suka kai shi kan gado, saran da aka yi masa ba ƙarami bane, yayi zurfi, hakan ya ƙara razana Jauhar. Liti ya ce "Wannan yankan madaki ne yayi masa shi, wannan shegiyar wuƙar da aka ce ta tsafi ce, da ita yayi masa saran". Jauhar ta ce "Na shiga uku, ba zai tashi ba kenan?" Walid ya ce "Zai tashi ki kwantar da hankalinki" Aka yi wa Al'amin ɗinki, kamar ƙwarya aks ɗinke bayansa, sai dai walid ba su bari an yi a gaban jauhar ba, aka ɗibi jininsa, dan dubawa idan sai an ƙara masa jini, sai dai baya buƙatar ƙarin jini, sai dai an saka masa ruwa saboda jirin da yake yi ya hana shi tashi. Sai dai ana tsaka da duba shin, jami'an tsaro suka iso, Walid ya ce kar matasan nan su bar su su shigo, sai an gama yi masa komai. Aka din ga artabu da 'yan sanda da dandazon, yaran da suka yi wa harbar emergency ƙawanya, da kyar 'yan sandan suka shiga. Da ƙyar aka tarwtsa tarin matasan nan, tana zaune ta ƙurawa fuskarsa ido, ƴan sanda suka ɗauki statement ɗin abun da ya faru. Jauhar sai addu'a take yi, tana fatan Allah ya sa ya farfaɗo. Ta riƙe hannunsa, tana shafawa a hankali ta ce "Allah ya shirya mini kai, ya baka lafiya master, inuwarka ce kawai nake tsaye a ciki nake saka ran samun farin ciki, dan Allah ka daina zuwa ana cutar mini da kai" Idonsa a rufe, ya ɗaga hannunsa a hankali, ya shafi fuskarta sannan ya buɗe idon a hankali ya kalleta sai dai bai yi magana ba. "Sannu master, an yi maka ɗinki a bayanka, akwai abun da yake yi maka ciwo ne?" Ya girgiza kai almar a'a. Ta shafi sumar kansa ta ce "Allah ya baka lafiya" Juyi yayi a hankali, ya kwanta a kan cinyarta, muryarsa ƙasa-ƙasa ya ce "Idan kina kuka ciwon ƙara zafi yake yi" ta goge hawayenta ta ce "To na daina, amma idan aka ji maka ciwo, zuciyata ce take kuka ba na so master". A hankali yake matsa hannunta, yana jin wata nutsuwa ta mussaman, da sassaucin zafin da zuciyar sa take yi masa. Zuwa magariba, ya miƙe ya ce sai sun tafi gida, Jami'an tsaro suka ce za su tafi da shi, sakamakon tayar da tarzoma a unguwa. Walid ya ce "Saboda hauka ake yi, master ku ware gida, ni ku tafi da ni mu muka je muka tayar da tarzomar" Ana fito da Al'amin, guduma ma ya taso, da sauri, Al'amin daga shi sai dogon wando, suka tari napep suka tafi gida. A wurin maman halimatu jauhar ta karɓi mukulli, ta buɗe musu gidan suka shiga. Ta saka yayi wanka, yayi alwala ya rama sallolin da ake bin sa, ta kawo masa abinci ya ci. "Master" ya kalleta "Dan Allah ka fita daga shirgin madakin nan, ba shi da imani, kar ya hallaka ka dan Allah" "Sai dai ɗaya yayi ajalin ɗaya ko ni ko shi, shari'ata da shi, Allah ne kawai zai rabata" Cikin rauni ta ce "Ina haɗaka da girman zatin Allah" "Shhhh, ki daina haɗa ni da Allah, kin san nauyin abun da aya aikata mini?" "Ban sani ba, amma ina da yaƙinin koma me zaka yi masa, ba zaka huce ba, ka yi haƙuri ka bar wa Allah mana, idan wani abun ya same ka ya zan yi ne? Yanzu kalli halin da ka sakamu a ciki, na san yanzu haka a cikin pain ka ke, ciwon a jikinka yake, amma a zuciyata nake jin raɗaɗin, haba master, haba dan Allah" tayi maganar wasu zafafan hawaye na gangarowa daga cikin idanunta. Ya miƙa hannunsa ɗaya da ba a side ɗin ciwon yake ba, ya janyota jikinsa, ba ta musa ba ko yi masa gardama, ta kwanta sosai ta cigaba da kukan, tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa sosai, kasancewar babu riga a jikin sa. "Ba zan ɓoye miki ba, ban taɓa tunanin zan yi wata alaƙa da wata 'ya mace ba, saboda ina yi musu kallon azzalumai, ke ki ka fara canza tunanina". Al'amin Ibrahim shi ne cikakken sunan Al'amin, mahaifinsa haifaffen garin kano ne, gidansu gidan yawa ne, baban Al'amin shikaɗai ne a wurin mahafiyarsa, sai tarin 'yan uba da galibinsu mata ne. Yayi karatu daga primary zuwa sakandare har yayi diploma, sai dai aikin yi ya gagara samuwa, akwai abokinsa sammani da suka yi karatu tare, tare suke yawon neman aiki, ya ja shi garin su tofa, aka samo musu gona, suka fara noma. A can ya haɗu da Zahra'u, ya ce yayi mata, da fari tsokanarta yake yi, saboda kwalliyar da take yi ta 'yan ƙauye ce take bashi dariya, daga baya soyayya ta ƙullu a tsakaninsu. Abu kamar wasa, har ta kai ga aure, duk da bashi da wata ƙwaƙƙwarar sana'a, sai kame-kame. Sun sha gwagwarmayar rayuwa tare, sun yi faɗi tashi, sun yi fama da yanayin rayuwa, kafin Allah ya buɗa masa ya fara samu. Lokacin da suke cikin wahala babu mai taimakonsa, daga shi sai ita suke wahalar su, ta samu ciki a lokacin ta haifi ɗan ta na fari, aka saka masa Abubakar Assidiƙ, sai lokacin da Allah ya fara buɗa masa, 'yan uwansa suka saka musu ido, da surutun yana zaƙewa da yawa a kanta. Komai ya samu ita, ya tashi daga tsakiyar cikin garin kano, ya koma gwauron dutse yayi mata gida mai kyau. 'yan uwansa suka fara tsangwamar ta, da cewa ta shanye musu ɗan uwa, Ibrahim ya mayar da ita makaranta ya samo mata admission a FCE, ta ke karantar English islamic. Kasancewar ta mace kyauta, da fara'a da sakin fuska ga mutane, ya sanya take da masoya sosai. Sai dai duk da kyautarta, da son mutane dangin mijinta ba sa ƙaunarta. A can gwauron dutsen, ta haɗu da wata mata rahila, maƙwabciyarta ce, tana yawan zuwa ta kawo mata complain a kan mijinta ba ya kula da ita da yaranta, hakan ya sanya tausayin rahila ɗarsuwa a zuciyar Zahra'au, kusan kullum cikin yi wa rahila aike take, na abun da zata kula da yaranta, kuɗi, sutura, abinci kayan masarufi, saboda Ibrahim yana sakar mata sosai baya yi mata iyaka da komai. Tana NCE 2, Sadik ya shekara biyar, ta samu ciki, tayi ta fama ga laulayi ga karatu, rahila take barwa Abubakar ta tafi makaranta, ƙarshen wata, take biyanta da kuɗi mai kauri saboda ita ma ta samu. Ta haifi ɗanta na biyu, aka saka masa Muhammad Al'amin, saboda haihuwar maza da take yi, dangin miji, suka ƙara yi mata caaa wai tana ta haifar maza, dan ta kwashe komai na gado idan ya mutu. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??     Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??     Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??     Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.      Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955 Ya saki Sadik a ƙasa bayan ya caka masa almakashin, cikin tsananin tashin hankali, Al'amin ya yi kukan kura ya danƙi ɗan daban, amma wani daga cikin yaransa, ya lallaɓa ya sake maka masa gora a baya, ya gantsare yana wani irin ihu, suka yi gaba suka bar su. Ya din ga dukan gate ɗin gidan, yana ƙwalawa Abbu kira, ya koma kan Sadik, ya rungumo shi, yana jijjiga shi. Sai da garin yayi shiru, sai kururuwar Al'amin yana kiran Yaya. Maƙwabcinsu ya fito, na kusa da shi ma ya fito, aka din ga buga gidan su Al'amin, har aka tafi nemo mota, sannan Abbu ya buɗe. Sai dai ya shiga tashin hankali, ganin Sadik a kwance kamar mara rai. Cikin tashin hankali Abbu ya tafi kici-kicin fito da mota, Al'amin ya zuciya ya ɗauki Sadik a kafaɗarsa, kawai yayi gaba. Da ƙyar aka riƙe shi, aka saka Sadik a mota. Al'amin sai zubar da hawaye yake yi, ya na kiran "Yaya ka buɗe idonka ka kalleni, ka tsaya yanzu zamu je asibiti" "A galabaice, Sadik ya motsa ya riƙa hannun Al'amin, sai kuma hannunsa ya saki. ko da suka je Asibiti, aka tabattar musu da Sadik ya koma ga Allah. Al'amin ya durƙusa a kan gawar, ya din ga rusa kuka, kukan da ko lokacin da umminsu ta mutu bai yi shi ba, maƙwabta na ta rarrashin Al'amin. Cikin kuka Abbu ya ce "Al'amin komai ya samu ɗa na kai ne sila, ka sa nayi rashin ɗa mai biyayya" "A'a Alhaji Ibrahim, kar ka sake ka ɗorawa Al'amin laifi, kai ne babban mai laifi, kana sane sarai unguwar nan babu kwanciyar hankali, ka bar su a waje, da ka buɗe musu sun shiga gida, koman dare ai da haka ba ta faru ba". A daren aka yi wa Sadik sutura, Al'amin gani yake yi kamar a mafarki, awannin da suka gabata suna tare amma a yanzu wai babu Sadik. Kodayeke Abbu yana da gaskiya shi ne sila, da bai ce zai bar gidan yayi tafiyarsa ba, da haka baya faru ba, dan kuwa Sadik ba ya yawon dare. Har jami'an tsaro sai da suka zo suka ɗauki bayanan abun da suka faru, sai dai Al'amin ya kasa magana. Sadik ya tara ɗimbin mutane, yara da manya matasa da dattawa wurin sallatar gawarsa, kasancewar sa mutumin kirki. Al'amin ya ji ina ma shi aka kashe, Sadik ya rayu, yayan nasa guda ɗaya tal da yake saukewa duk wata damuwarsa ya ɗauka babu ƙosawa ko gazawa, an kashe masa shi. Alhaji sammani, ya yi wa Ibrahim tatas, a kan yadda ya koma soko a kan gidansa, tare da ci wa Rahila mutunci tsaf, a kan abubuwan da take aikatawa. Ƙarshe ta shiga ta fita, ta raba abotar da aka yi shekaru ana ginata, suka rabu dutse a hannun riga, suka yi uwar watsi. Depression ya nemi ya kama Al'amin, babu wand yake ta tasa, gashi yanayin halayarsa idan ba wanda ya sanshi ya saba zama da shi ba, ba kowa zai iya masa ba, saboda miskili ne, ga nuƙufurci, ba zai taɓa cewa wani ga damuwarsa ba, shi ba abokai ba, haka ya din ga ragaita a layi, raɗaɗin mutuwar Sadik taƙi barinsa. Ya tafi wurin 'yan sanda ya tambayi, ko sun kama wanda ya kashe yayansa, suka ce masa bincike suke yi a kai, dan har a lokacin ba su tabattar da wanda yayi kisan kan ba, kuma a ranar ba Sadik kawai aka kashe ba. Al'amin ya koma gida, yayi ta addu'a Allah ya sa a kama wanda ya kashe masa Sadik, duk da dare ne, amma a ko ina ya ga wanda ya kashe shi zai gane, dan kuwa ƙofar gidan su akwai security light. Duk bayan kwana biyu sai Al'amin yaje, tun suna sauararsa har suka fara korarsa. Ga matsi ya ƙaru daga gidansu, babu in da zai samu abinci, ya yanke shawarar fara zuwa kasuwa ya duba ko dako ya fara, sai da ya je ya tarar ashe dakon ma sai ka san wani, sai an san da kai, duk sana'ar da yayi tunanin farawa sai ya ga dole sai da jari, gashi Rahila ta cigaba da ziga Abbu, ya ƙara tsanar Al'amin wai shi ne silar mutuwar Sadik. Al'amin ya fara gajiya da yunwa da take neman tagayyara shi, ya fara zuwa gida ya ɗauki duk abincin wanda ya tarar ya cinye, idan ya tafka wannan tsiyar, sai ya gudu ya kwana a kangwaye, gashi ya koma HND tun Sadik na raye, dama shi ne yake ta fafutukar tara school fees ɗin sa kan ya rasu, yanzu kuma ga yunwa da rashin kuɗin transfort dan haka ya daina zuwa makaranta gaba ɗaya. Gashi ko a maƙwabta aka rasa wanda zai yi wa Abbu nasiha, ko su din ga taimakonsa, saboda ana ganin babansa yana da rufin asiri. Yana can garin yawonsa, kawai ya hango wanda ya kashe Sadik, a tsallaken titi, da tawagar matasa 'yan daba, da gudun gaske Al'amin ya tsallaka titin, sai dai kan ya ƙarasa sun ɓace masa, cikin tashin hankali ya ƙarasa wurin wani mai ice ya ce "Malam dan Allah wanda ya wuce ɗin nan ina yayi?" Ya kalli Al'amin ya ce "Meye haɗinka da shi?" "Yayana ya kashe da almakashi, bai yi masa komai ba, 'yan sands suna ta nemansa" "Taɓ, ka raba kanka da wannan. Madaki kenan gawurtaccen ɗan daba ne, hukuncin kisa ma aka yanke masa a gidan yari, amma muka ga an sake shi, duk ya gallabe mu, ya hanamu sukuni mu ma, sai dai ka bar wa Allah kawai" Ai Al'amin bai tsya jin ƙarshen zancen ba, ya shiga cikin unguwar ya din ga yawo, amma bai ga madaki ba. Washegari da sassafe, ya koma wurin 'yan sanda ya gaya musu ya ga wanda ya kashe yayansa, su tafi tare da shi a nemo shi, an gaya masa sunansa madaki. Wani ɗan sanda ya kada baki ya ce "Ka san mutum nawa madaki ya kashe aka ƙyale shi?" al'amin ya ce "Ni ina ruwana da mutum nawa ya kashe, ku kama shi a kai shi kotu ni dai". "Ko an kai shi ma, za a sake shi, ka je ka yi haƙuri haryanzu bamu tabattar da shi ya kashe shi ba". Kasancewar Al'amin yana kan tashen balaga, ya sanya ya tsaya yana yi musu rashin kunya, aka saka wani sageant, ya zane shi aka kore shi. Hakan yayi matuƙar tunzura zuciyar Al'amin, ya din ga jin jinin ɗan uwansa ba zai tafi a banza ba. Ya din ga sintiri a unguwar da madaki yake, kasancewar ba su da nisa sosai, ya samu duk bayanin da yake son samu a kan madaki, da in da yake zama da shi da yaransa. Ya je gida ya shiga kitchen ya samo, wuƙa sabuwa gal, ya je ya ɓoye, ya saka a ransa shi ma sai ya kashe madaki, ko da kuwa za a kama shi a kashe. Sai dai aka yi rashin sa'a, Madaki bai fiye zama a unguwar ba, sai idan zai shigo yayi rashin mutunci, Al'amin ya din ga fakonsa, har ya yi wataran sa'a ya tarar yana nan. Gadan-gadan ya ratsa tarin matasan da suke ɗauke da makamai suna shaye-shaye, ya nufi madaki da wuƙa. Matasan suka mimmiƙe, amma madaki ya ɗaga musu hannu, a kallo ɗaya madaki ya gane Al'amin. Kafin ya ƙarasa gaban madaki, sani ya sanya ƙafa ya taɗiye Al'amin dan haka ya faɗi a gaban madaki, suka kwashe da wata irin dariya. Al'amin ya yinƙura zai tashi, madaki ya saka aka take masa kafaɗun Al'amin da ƙafa, yana ƙoƙarin tashi, amma cikin ƙarfin Al'amin ya tashi, madaki ya tako gaban Al'amin ya shaƙe wuyansa. Take Al'amin ya ji kamar an shaƙe shi da wata muguwar sarƙa mai nauyin gaske, a take ya ji numfashin sa na neman ƙwace masa. Al'amin ya saki wuƙar ya koma kokowar raba hannun madaki da wuyansa, madaki ya tsare shi da jajayen idanunsa da ya rambaɗa musu farin kwallin tsafi, yana ƙyaƙyata wata uwar dariya, daga bisani kuma ya tsuke rai tamau, ya ƙara tsananta shaƙe Al'amin, sai da ya ga ya daina motsi, sannan ya watsar da shi a wurin, ya kalli wani ya ce "Ku kai shi arear su ku watsar" "Ba za a saita ma hanya daga duniyar ba ya ci bulus kenan?" Madaki ya girgiza kai ya ce "Yana cikin tsananin ɗacin rashin ɗan uwansa, idan aka yage shi daga sararin nan, hutawa zai yi, sai ya gane kuskuren da ya aikata na yinƙurin da yayi" Suka ɗauki Al'amin suka kai shi unguwar su, suka jefar da shi a sume a gaban wani mai kayan miya, suka ce wa mutanen wurin "Gashi nan, ajiyarmu ne, zamu din ga bibiyar sa ku kira tsohonsa ya ɗauke shi idan yan buƙatarsa". 'yan unguwa suka ɗauke shu, suka kai shi gida, Abbu yana nan, aka kwantar da shi a tsakar gida, ana shafa masa ruwa, mai kayan miya ya gaya wa Abbu abun da yaran madaki suka ce, aka shawarce shi a kan ya kai maganar wurin jami'an tsaro, amma Abbu ya ce babu ruwansa, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, shi bai aike shi wurin 'yan daba ba. Tun daga nan madaki ya mayar da Al'amin kamar karen farautarsa, ya saka rayuwarsa a gaba, wataran har cikin unguwar su yake aikawa, a nemo masa Al'amin, a kai masa shi har dabarsa, su casa shi da zalunci kala-kala, wai sa ya saduda ya nemi afuwar abun da ya yi wa madaki, dan ba a taɓa samun wanda ya yi abun da Al'amin yayi ba, ya rasto har dabarsa ya nemi ya kashe shi, yana ƙanin ƙanin bayansa. Al'amin ya kalli madaki ya ce "Ka yi kaɗan na nemi afuwarka, baƙin kare kuma in sha Allah sai na zubar maka da jini, kamar yadda ka zubar da jinin ɗan uwana da bai yi maka komai ba" Ya durƙusa ya soka wa Al'amin wata kibiya a cinyarsa, cinyar sa na zubar da jini, amma saboda azabar taurin kai, ya datse haƙoransa ya ƙi ihu. "Na fuskanci zaka yi mini amfani, na saka ka cikin yarana daga yau, zaka din ga yi mini aiki" Al'amin ya girgiza kai ya ce "Ni fa kallon kare nake yi maka, da na bika gara na yi mutuwar wulaƙanci" Ya ce "Shikenan zamu gani, dafin ciwon da nayi maka na fili da na zuciya ya isheka ka saduda". Al'amin ƙafa taƙi takuwa, sai da kyar, ya din ga tagayyara a gari, yaran madaki suka matsawa unguwar su Al'amin, duk da suma suna da ƙasurguman 'yan daba, amma ba sa shiga harkar faɗan matasan 'yan daba. Al'amin ya ƙi ya karaya ya saduda, ga ƙafa yana ɗingisawa, ga yawon neman in da zai ci abinci, kullum rahiila cikin gaya wa Abbu take, Al'amin abubuwan da yake da yadda 'yan daba suke kawo masa farmaki, sun tabbatar da cewar shaye-shaye ya fara yi, dan haka lallai ya kori Al'amin daga gidan, ya daina zuwa kan ya kuma janyo musu wata masifar, ta ce a kama masa shago a cikin unguwa ya bar kwana a cikin gidan, duk da dama ba kullum yake kwana a gidan ba. Wata ranar juma'a da yamma, Al'amin yana tafe yana ɗingisa ƙafarsa, yaran madaki suka shigo, da wasu irin mahaukatan karnuka, kuma kai tsaye suka sakarwa Al'amin su, gashi ba zai iya gudu ba, saboda ƙafarsa, suka dirar masa da cizo, ya din ga danƙar karnukan nan yana jifa da su, manyan karnuka ne sun kai biyar, wannan ya yage shi ta nan, wancan ya kai masa cizo ta nan, sai da suka ga yana neman fara halaka karnukan, ko su yi mutuwar kasko da su, sannan suka nufi Al'amin suka fito da makamai. Dan madaki cewa yayi, su kai masa wani sashe na jikin Al'amin sun cire masa. Karnuka sun yi masa kaca-kaca da kayansa, da fatarsa da cizo da yakushi, jikinsa duk jini, amma ya yinƙura ya tashi, ganin sun tsaya a kansa da makamai. Ɗaya ya shammace shi, ya sara masa wuƙa a cinya ta baya, ya hankaɗa shi ya faɗi, yana faɗuwa suka ga ɗaya daga cikinsu ma ya faɗi ƙasa jini na zuba daga jikinsa. Gaba ɗaya suka ɗaga kai suna kallon wanda ya yi aikin. Wani gabjejen mutum ne, baƙi mai jiki sosai, da jajayen ido, a yaran madaki wani ya yinƙuro, amma ya caka masa wuƙa a ciki shi ma, ya faɗi. Ya durƙusa ya ɗago Al'amin, jikinasa jina-jina, ya kalli wanda suke tare ya ce "Samo abun hawa, a kai yaron nan asibiti" ya kalli sauran yaran madaki ya ce "Ku je ku gaya wa madaki, ya zo dabata ni dodo babban sarki, ina nemansa. Na ji labarin irin ɓarnar da yake shigowa unguwar nan yana yi, kasancewar bana shiga shirgin shirmen ƙananan matasa, ya sanya ban damu ba. Sai dai na wuce a mota, a wancan lokacin na ganku kuna dukan yaron nan, wannan karon ma na ganku kun saka karnuka na cizon sa, kamar ba ɗan adam ba awanni ashirin da huɗu na bashi, ya zo yayi mini bayani, idan ya bari na taka na je in da yake sai dai uwarsa ta haifi wani. Ku ɗauke mini wannan mushen, ku ɓace daga gabana" jiki na tsuma, suka ɗauki wanda aka cakawa wuƙar suka tafi da shi. A asibiti ɗan wando kawai aka bar Al'amin da shi, jikinsa sai tsatstsafar da jini yake yi, saboda cizon karnuka da yakushi, ga raunin da yake ƙafarsa, sai da aka yi dressing raunukan jikinsa, sannan aka yi masa rigakafin cizon mahaukacin kare, dan ba a san wane irin karnuka ne suka ciji Al'amin ba, aka saka masa ruwa, sannan aka kawo masa lafiyayyen abinci daga restaurant. Dodo babban sarki, bai sake bi ta kan Al'amin ba, sai bayan magariba, ya je Asibiti da shi da yaransa, aƙalla dodo ya kai shekaru arba'in da biyar, ya girmi madaki sosai, madaki kuma ya girmi Al'amin. Ya tarar da Al'amin a zaune, hannunsa ana saka masa ruwa, ya ƙarasa gaban gadon Al'amin ya ce "Sannu ka ji" Al'amin ya jinjina masa kai. "Yaron nan ba shi da imani ko kaɗan, tayaya zai saka a sakarwa yaro karnuka su je shi, zai ci ubansa da ni yake zancen, zan gani zuwa dare idan bai zo ba, sai na kashe shi wallahi" ya sake kallon Al'amin ya ce "Kai ba kai ne kuka tare a unguwar nan shekarun baya ba? Kuna zuwa islamiyyar dogon bene, kai da ɗan uwanka ba?" "Ni ne" "Ina ɗan uwan naka? Meya haɗaka da madaki kuma, na ga kai ba irin su bane" Al'amin ya yi shiru, sannan ya ce "Kashe mini Sadik yayi, ba abun da yayi masa, ni kuma na ga ba zan haƙura ba sai na kashe shi nima" Dodo ya ce "A'a dama yayanka ne aka ce mini an kashe a layin dawaki? Madaki yana fama da gigin daba, tun da ya samu masu tsaya masa, ya je prison ya haɗu da wanda suka fi shi rashin mutunci yake abun da ya ga dama. Zan ci ubansa kuwa yanzu me ka ke son ayi masa gaya mini" Al'amin ya ce "Kawai sonake shi ma ya mutu, in soka masa almakashi kamar yadda ya yi wa Yaya" yayi maganar cikin damuwa. Dodo ya dafa kafaɗarsa ya ce "Kwantar da hankalinka, yanzu dai fatanmu ka samu lafiya, za aje a sanar da babanka, ya zo asibiti ya duba ka, a samu mai jinyarka" Ya girgiza kai ya ce 'A'a kar a gaya masa, zan koma gida kawai" "Na ji ba za a gaya masa ba, amma sai ka zauna an kula da kai tukuna". Madaki hankalinsa ya tashi, jin an kashe masa yaronsa na hannun damansa, a hannun wanda ba zai iya ɗaukar fansa ba, dan gaba da gabanta. Yana tsuma, suka tafi in da Dodo yake zama, aka ce sai dai su bishi asibiti, baya nan. Asibitin gwamanti ne, Amma amenity dodo ya biya aka kwantar da Al'amin. Madaki cikin girmamawa ya ce "Na amsa kira ranka ya daɗe". "Ka san wannan ai?" Dodo yayi maganar yana nuna masa Al'amin. "Na san shi" "Daga rana mai kamar irin ta yau, idan kai ko wani daga cikin yaranka, ya sake taɓa shi, ko tsoratar da shi, wallahi sai na ƙarar da tarihin mutum a bayan duniya. Bana shiga harkar ƙananan dabarku, amma aka kuma ratso unguwar nan, aka taɓa shi, wallahi sai na yi abun da ba a zata ba. Ka durƙusa ka bashi haƙuri a kan cin zarafin da ka saka aka yi masa, ka sanya karnuka suka yi masa illa, yana ɗan adam ba dabba ba, sauran abun da ka yi masa kuma kai da shi ne". Madaki ya kalli Dodo ya ce "Ni zan bashi haƙurin?" Wani wawan mari, dodo ya ɗauke madaki da shi, da sai da ya kife ƙasa, "Ka shiga hankalinka, ka san da wa ka ke magana kuwa? Har ka mutu ba zaka yi iskancin da nayi ba, shekarata goma a ƙiri-ƙirin lagos, ba wani ɗan iskan da ban gani ba, ko ban sani ba, ka bashi haƙuri, ko na ciyar da macizaina namanka" Madaki ya kalli Al'amin, shi ma ya kalleshi, ya kalli dodo sannan ya ce "Ka yi haƙuri, bisa abun da na saka aka yi maka da karnuka". Al'amin ya ce "Ko ka bani haƙuri ko baka bani ba, gaba da ni da kai sai ranar da na rama zubar da jinin ɗan uwana da ka yi" sai da duk suka kalli Al'amin, Al'amin ba dai taurin zuciya ba. Madaki ya fice a muzance, a gaban yaransa aka saka ya bawa Al'amin haƙuri, an wulaƙanta shi ƙarshen wulaƙanci, dan haka ya ƙullaci abun a ransa. Al'amin har ya kwana huɗu a asibiti, Abbu bai neme shi ba, kullum abincinsa mai rai da lafiya yake samu ya ci, ga dodo shi ma kullum sai ya zo duba shi, ya yi ta yi wa Al'amin hira, har yaransa suka fara mamakinsa, dan Al'amin ba wani sakin jiki yake da shi sosai ba. "Al'amin da gaske kana son ka rama abun da madaki yayi maka?" Al'amin ya ce "Eh" "Tunani mai kyau, amma ka sani shi ƙarfe dole sai da ɗan uwansa ƙarfe, yanzu an sallameka, mu je mu kai ka gida, sai ka din ga zuwa dressing, na biya kuɗin dressing ɗinka, duk abun da ka ke buƙata zan baka adress ɗina, a nan cikin unguwar, ka je ka same ni" Al'amin ya jinjina kai ya ce "Na gode sosai" ya dafa kafaɗarsa ya ce "Kar ka damu Aminullahi" Da ya koma gida, babu wanda ya tambayi ina yaje, tsawon kwanakin nan, ga jikinsa duk raunuka,  amma babu wanda ya tambayi ya yake, sai ƙanwarsa shahida da suke uba ɗaya. Tun da dodo yayi wa madaki iyaka da Al'amin, ya samu sassauci, ya cigaba da sabgoginsa, bai kuma sake bi ta kan dodo ba. Da ƙyar ya samu aiki a wurin wani mai shayi, yake yi masa wanke-wanke da abun da ba a rasa ba, idan ba ya nan, da shi da ƙanin mai shayin ne suke riƙe wurin, hakan ya sanya ya fara rage damuwa da halin da yake ciki. Sai dai ƙanin mai shayin ya nemi da su haɗa kai da Al'amin, su ɗan din ga ɗaukar wani abu, Al'amin ya ce ba zai yi ba, ba a jima ba, yaron ya yi wa Al'amin sharri wai yana ɗebar masa kuɗi, kuɗi kusan dubu talatin, mai shayi ya kai Al'amin wurin 'yan sanda aka daka aka yi rarrashin ya ce shi bai ɗauka ba, ba kuma zai amsa yayi ba. Aka yi ta kai ruwa rana, da ƙyar case ya mutu, bayan ya shafe kwanaki a hannun 'yan sanda. Yamma liƙis, ya je ya samu ƙanin Habu mai shayi, har rumfar mai shayi, ya karya shi a hannun dama, aka kuma cafke shi zuwa wurin hukuma, aka nemi Abbu, amma ya ce ba ruwansa, tun da kangarewa ya ɗauka. Ɗaya daga cikin matasan da suke yi wa dodo aiki, wato Walid, shi ya gaya masa halin da ake ciki. Da kansa yaje station ya karɓo Al'amin. Ya saka shi a gaba, yana yi masa tambayoyi, a kan dalilin da ya sa, ya aikata abun da yayi. Ya kwashe komai ya gaya masa. Dodo ya ce "To daga yau, kar ka sake zuwa ka nemi wata sana'a, duk abun da ba ka da shi, ka zo na baka. Na fuskanci tsohonka baya yinka, ni kuma ehhh kawai ka kwanata mini a rai, tausayi kake bani, kana rayuwa da kai da wanda aka bugoku cikin samfurin jini ɗaya, an ɗaye maka shi, ta ƙarfin tsiya. Amma ba komai, zaka rama ne" Tun daga lokacin Al'amin ya zama yaron dodo, wurinsa yake zuwa ya karɓi kuɗin abinci, ya biya masa kuɗin registration, ya mayar da shi makaranta ya cigaba da HND, dama shekarunsa ba su kai shiga University ba, shiyasa ya fara zuwa poly. Dodo harkar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi yake yi, babban distributor ne, har garuruwa yake rarrabawa kaya. Bai damu da harkar daba ba, sai wannan sana'ar, Abbu bai taɓa tuhumar ya aka yi Al'amin ya koma makaranta ba, wace sana'ar ya fara duk bai tuhume shi ba. Dodo yana da manyan yara da matasa, ciki har da sa'an Al'amin mai suna Walid. Sai dai Walid ya tsani Al'amin ganin yana neman ƙwace masa fada a wurin dodo babban sarki. Ko aike babu wanda ya isa ya aiki Al'amin, dodo ne kawai yake sa shi ko ya hana shi, haka zai zauna a cikin su, su yi ta shaye-shaye suna ƙuƙƙula kayan maye, amma ba ruwansa da su, ko sigari bai taɓa gwada sha ba. Idan yayi dare a yawonsa, sai ya tafi gidan dodo, yayi kwanansa, dodo har safarar makamai yake yi, babban criminal sosai da sosai. Komai Aminullahi, komai Aminullahi, lokaci lokaci, ya kan tuntuɓi Al'amin, ko zai iya yafe wa madaki, amma ya ce har abada, har sai ya rama abun da yayi masa ya kan yi murmushi ya ce "Aminullahi kenan, in dai zaka zauna a haka, ba ka shirya ɗaukar fansa ba, ƙarfe dole sai da ɗan uwansa ƙarfe, roba ba ta tasiri a kan ƙarfe" baya gane mai dodo yake nufi, dan haka sai dai ya bi shi da to Al'amin ya ce masa dan Allah ya samo masa sana'a, ko wace iri ce zai din ga yi. Dodo ya ce masa zai duba. Duk abun da Al'amin zai yi, dodo bai yadda yaransa su yi masa wani abu na horo ko cutarwa ba, hatta kaya idan Al'amin ya cire, sai ya ce Walid ya wanke masa, wanda kan zuwan Al'amin shi ne na gaban goshi. Sannu a hankali, ya fara aiken Al'amin kai kayan shaye-shaye wasu wuraren, cikin dare idan motar kaya ta isao, haka zai ɗauke shi, su tafi su karɓo kaya. Wataran ya aike shi, hukumar hana sha da fataucin, suka kama shi, aka din ga tuhumar Al'amin, ya ƙi faɗan wanda ya aike shi da kayan, sai da aka kwana biyu ana nemansa, hankalin dodo ya tashi, aka bincika aka gano masa shi a hannun hukuma. Ya je ya karɓo Al'amin, sannan ya ce "A bashi kayan da aka ƙwace ayi musu kuɗi zai saya, idan suna da wasu ma a haɗa masa ya saya. Kuma hakan aka yi. Ya yi ta yi wa Al'amin faɗa, a kan dan me, ya zauna a hannunsu, bai saka an neme shi, ya fito da shi ba?. Ta kai ta kawo, Dodo yana tafiya da Al'amin wurin 'yan siyasa, dan a nan ne suka haɗu da Indabo, a lokacin baya shan komai. Duk da wannan abubuwan da suke wakana, Al'amin yana zuwa gida, ya ga Abbu, ko da kuwa zai yi masa faɗa ya kore shi, yana zuwa ya ganshi. Yaran dodo sun sha attempting koya masa shaye-shaye, amma ya ƙi, tun Walid yana jin haushin Al'amin, har ya haƙura, manyan yaran dodo suka saka masa mai zamani, ya kori gwamantin Walid dan haka idan yana son zaman lafiya ya kiyayi mai zamani" Dodo ya din ga dariya, ya ce "Kuma zamanin Aminullahi dogo ne a wurin dodo ba, bana tunanin akwai wanda zai ture gwamantin sa a wurina, dan mai dogon zamani dan haka mai laya" yayi maganar yana kallon Walid. Aka haɗa baki aka ce "Ka kiyayi mai zamani" suka yi abun da sigar raha. Al'amin ya je gida, domin ganin Abbu, amma ya tarar baya nan, Rahila kuma tayi baƙi, ya shiga kitchen ya ga an yi uban abinci, ya kwaso fulasan yayi gareji da su, ya zauna ya hau ci, duk da ya san na baƙin ne. Yana cikin ci, sai ga wata 'yar yarinya ba ta fi shekaru biyu ba, ta zo in da yake tana kallonsa, ta tsuguna ta saka hannu a kwanon, tana tsintar abincin tana ci. Ya kalleta, sai ya tuna jaririyar ummi da ta rasu, yanzu ga shi duk su ukun babu su. Sai ya din ga bata abincin a baki, amma hakan bai hanata saka hannu a kwanon miya ba, haushi ya kama shi, kamar ya kwaɗe ta, ya kama rigarta yana goge mata hannun, kawai ya ji salatin Rahila. Ya ɗaga kai ya kalleta ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku jama'a ku taimake ni, zai lalata 'yar mutane, Allah ya sa ba yi mata komai ba" Sai yayi saroro yana kallonta, ya rasa gane mai take nufi, wanda ta yi hakan ne, dan huce takaicin tozarcin da yayi mata, na cinye abincin baƙi. Shahida ta ce "Mama wanke wanke nake yi, ina hango su ba abun da yayi mata, abinci kawai yake bata" "Ƙarya ne rufe mini baki dan ubanki, ke kin taɓa ganinsa yana ɗaukar yara ne, balle ba da abinci a baki, ni na ga abun da na gani" dama 'yar ta maƙwabta ce, uwatta ta kawota ta fita. Ta tara wa Al'amin jama'a, wai ya saka wa yarinyar hannu a wando, da idonta abun da ta gani kenan. Duk dakiya da dauriyar Al'amin, jikinsa ya hau rawa, ya kasa ko motsi daga wurin, mutane suka taru a garejin gidan, Abbu dama sallar la'asar ya fita, a masallacin yana lazumi aka je aka kirawo shi. Cikin tashin hankali ya danƙo Al'amin, ya kwaɗa masa mari ya ce "Me ka yi wa 'yar mutane? Al'amin lalacewar taka har ta kai ga haka? Ni zaka zubarwa mutunci a idon duniya" Shahida tana kuka za ta yi magana, Rahila ta hanata, wata mata ta cire pampers ɗin yarinyar ta duba ta, ta ce "Wannan yarinyar fa babu abun da aka yi mata, lafiyarta ƙalau da ya taɓata ma, ba za a ganta a haka ba" Al'amin ya ƙwace rigarsa daga hannun Abbu, ya fice, yana jin zuciyarsa zata tarwatse, bai zarce ko ina ba, sai gidan dodo, suna ganin sa suka din ga tambayar sa, menene saboda yadda idonsa ya yi jawur, amma ya yi shiru ya ƙi kula kowa. Walid ya kira dodo a waya, ya sanar masa ga mai zamani ya zo, cikin ɓacin rai da tashin hankali. Ba a ɗauki lokaci ba, sai gashi, ya ce "Waye ya taɓa zuciyar magajin dodo, wa ya taɓa mini Aminullahi?" "Al'amin ya ƙi magana sai huci da ajiyar zuciya, ga wani gumi da yake yi" Dodo ya ce "Walid" "Allah ya taimaki babban sarki" "Narka jan tablet, ka bani" Walid ya narka ya bashi, ya miƙa wa Al'amin. Ba tunanin komai, ya karɓa ya shanye ya ajiye kofin, wani zuuuuu ya fara ji a kansa, ya fara ganin hazo-hazo, a hankali ya fara ganinsu bibbiyu, daga haka bai sake sanin abun da ya faru ba, sai sha biyun dare ya farka. Yayi sallolinsa, ya ci abinci, dodo ya ce "Magajin dodo, ba zan takuraka na ji menene ba, amma ya ka ke ji yanzu damuwar ta tafi gaba ɗaya?" Al'amin ya girgiza kai alamar a'a. "Duk wannan dogon zangon da ka yi? Bari na baka wani haɗin" Ya naɗa masa wiwi, ya kunna ya bashi, sai dai zuƙa ɗaya Al'amin ya hau tari, kamar zai shiɗe ya ce "Ƙara gwadawa, ba zaka yi ba" ya din ga zuƙa a hankali, tun yana tarin har ya daina. Ayshercool 08081012143 A din ga yi, ana sauke hakki ₦500 0009450228 Aisha Adam jaiz bank 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??     Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??     Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??     Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.      Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955 Tun daga lokacin, Al'amin ya fara shaye-shaye. Shiga layinsu ya gagare shi, saboda tsananin kunyar abun da Rahila ta yi masa na sharri. Sai da ya shafe wata guda bai sake takawa gidan su ba, sai dai kewar Abbu ta din ga damunsa, da asuba ya tafi masallacin da Abbu yake salla, ya yi sallar asuba a waje, ya jira ya fito, Abbu yana tafe ya ji kamar ana bin sa a baya, ya tsaya ya waiwaya, duk da gari bai gama yin haske ba, da sauran duhu, amma hakan bai hana abbu gane Al'amin ba. Ya tsaya, jiki a sanyaye ya ƙaraso, Al'amin ya risuna ya ce "Ina kwana" "Kai daga ina? Ina ka tafi tsawon kwanakin nan? Duk yawonka ba ka wuce kwanaki kaɗan, amma ban sake saka ka a idona ba" kallon Abbu yayi, yana tunanin da ma yana jin wani abu idan bai saka shi a idonsa ba?. "Ina nan" Abbu ya ce "Kana can kana shashanci, gaishe ni ma ba zaka iya zuwa ka yi ba ko?" Ya ce "Korata ka ke idan na zo" "Ba dole in kore ka ba? Tun da kai a rayuwarka ba ka gaya wa kanka gaskiya, kuma duk in da ka zauna sai an yi faɗa da kai. Ka yi salla ne?" Al'amin ya jinjina kai. "To wuce mu tafi" yayi maganar yana nuna masa hanya, sai Al'amin yayi ajiyar zuciya, tare da tuna masa baya, da yake ɗora shi a wuyansa idan suka dawo daga masallaci, har tsere suke yi da Abbu, duk yadda Abbu yake ji da shi, yanzu ya zama tarihi. Yana tuna abun da ya faru ƙarshe, sharrin da Rahila ta yi masa, sai ransa ya ɓaci, ya ƙi shiga layin ya tsaya. Abbu ya waiwayo ya ce "Ya ka tsaya kuma?" "Tafiya zan yi" "Zuwa gidan uban wa?" Al'amin ya ce "Da wani idon zan kalli sauran mutanen layin, bayan ga sharrin da aka yi mini, idan na ga matar nan, zan iya kasheta, sai anjima kawai na tafi, dama ganinka nake son na yi, tun da kana lafiya Allah ya ƙara lafiya" ya juya ya tafi, Abbu ya tsaya yana kallon Al'amin har ya ɓace wa ganinsa. Ko da ya koma gidan da suke, walid ya fuskanci Al'amin yana cikin damuwa, yayi masa tayin sigari, ya girgiza masa kai, can ya ce "Walid" Ya amsa da "Na'am" "Dan Allah ya aka yi ka fara Shaye-shaye?" Walid ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Wan babana ne ya cinye mini gado, nake ta wahala ina fama da rayuwa, matsin rayuwa ya isheni, kuma shi ba tallafa mini yake yi ba, kawai na fara dafar kan kayan mutane, kuma da nasa na fara, aka kama ni aka kulle, rodi ma na sata lokacin, aka ɗaure ni watanni shida, da aka kai ni prison ban saba ba, nake ta kuka saboda wahala, a can na haɗu da mai gida, sarki dodo, ya din ga kula da ni, bayan ya fita ya dawo ya biya mini tarar aka yanke mini, sake ni, kawai ya cigaba da kula da ni" "Ina mamanka?" Walid ya ce "Taɓ tana can tana fama da rayuwarta, kinko ya kanannaɗe rayuwarta, wannan tsohon auran wan baban namu, ya tattare gadonmu ya cinye, Sakandire kawai nayi, ita ma ba ganewa nake yi ba da kyar na kai. Tana fama da kula da ƙannena, ga bata da cikakkiyar lafiya, ni kuma bana iya tallafa mata, har gara yanzu mai gida ya kan bani kuɗi ya ce na je na gaishe ta" Al'amin ya jinjina kai ya ce "Ka cigaba da kula da ita, dan duk ranar da ka rasata, za ka yi kuka, kuma kar ka bari ta san irin rayuwar da ka ke yi" "Na nawa kuma, ai wancan tsohon munafukin tuni ya gaya mata, tana yi mini nasiha sosai da addu'a, ba ta taɓa fushi da ni ba" Daga haka Al'amin yayi shiru, yana cigaba da tunani. Da sannu Al'amin ya zama gawurtaccen mashayi, duk in da dodo za shi, da Al'amin. Ta kai ta kawo har kudancin Najeriya yake tafiya da Al'amin, ba fatauci ba, har wuraren sarrafa miyagun ƙwayoyi Al'amin ya sani, har manyan mutane a ƙasar nan da suke ta'amalli da su da kasuwancin su ya sani. Ya haɗa Al'amin da wani inyamuri, ya ƙara gogar da shi a kan harkar na'ura mai ƙwaƙwalwa, yadda ake amfani da ita a aikata laifuka daban-daban, suka sake danganawa da wani bature, ya ƙara koyar da Al'amin sarrafa computer wurin yin laifuka. Ya zamana kasuwancin miyagun ƙwayoyi, na ƙasashen da suke maƙwabtaka da Nigeria, Al'amin ke tafiyar da kasuwancin su ta online. Bai tsaya a nan ba, har cikin manyan 'yan fashi, dodo yake shiga da Al'amin. Dodo ba ya fashi da makami, amma zama a gidajen gyaran hali daban-daban ya sanya ya san masu laifuka kala-kala da yadda ake aikata su, bai fiye harkar daba ba, yafi gane wa safarar ƙwayoyi da makamai. Idan aka cewa Al'amin magajin dodo, sai dodo ya ce "Wannan dodon, da sauran imani a ransa, ɗan ƙaramin dodo ne, ba zai iya zama kamar ni ba, sonake ya horu, yadda zai iya tunkarar kowane ƙalubale, ciki har da babban burinsa na son ganin bayan madaki, dan kuwa madakin ma ya ƙwafe shi a rai, na cewar sai ya ga bayansa, tun da na saka ya sanya gwiwar sa a ƙasa wurin bashi haƙuri". Duk wani sirri na dodo, babu wanda Al'amin bai sani ba, kallon abu dodo yayi Al'amin ya san me yake nufi. Kai tsaye ya kan tura Al'amin wurin indabo, a lokacin yana fafutukar neman kujerar ɗan majalisa, sai dai wasu lokutan baya son dodo ya aika masa Al'amin, dan idan yayi masa abun da bai yi masa ba, tafiyar sa yake ya ƙyale shi, ba ya jure cin zarafi ko wulaƙanci, komai ƙanƙantarsa, ya yaɓawa indabo baƙar magana ya ƙara gaba, duk ba abu ne mai wahala a wurin Al'amin ba, Indabo ya kai wa dodo ƙarar Al'amin. Amma ya ce "Ina nema masa afuwa, ka riƙe Al'amin yaro ne mai amana, kuma duk cikin yarana babu wanda zai iya yi maka aikin da ka ke so bayan shi, yaro ne mai amana sosai da sosai, kuma ba shi da surutu, hakazalika yayi hannun riga da tsoro. Dodo ne ya nuna masa makamai kala-kala samfurin wuƙaƙe, da in da in ka sakawa mutum zaka kashe shi, da wanda za ka yi masa illa. Dodo yana yawan faɗar, Son da yake yi wa Al'amin daga Allah ne, bai taɓa son abu sosai da yake jin sa a ransa kamar shi ba. Ya san son da yake yi masa, ba zai kai na ɗa da uba ba, dan haka ya din ga mamakin yadda aka yi, mahaifin Al'amin ya wofantar da shi, duk da soyayya irin ta ɗa da uba. Ba yadda bai yi da Al'amin ya ɗora karatu ba ya ƙi. Ya ce "Aminullahi, harakar daba da shaye-shaye ba abune da nake yi maka fatan ka ɗore a kai ba, yakamata ka koma makaranta. Al'amin ya ce "Ni ma ba na fatan na ɗore, ina ɗaukar fansar abun da madaki yayi mini zan bar daba". Ya dafa kafaɗarsa ya ce "Ina maka fatan hakan, sai dai haryanzu ba ka kai ƙarfin da zaka tunkari yaron nan ba, dan kuwa shi har da tsafi yake yi, kai kuma na san komai za a yi maka, ba zaka yi tsafi ba, amma ba a shiga dawa dan ƙarya, ko na kare kai, zan nema maka". Duk da an ɗauki lokaci, yaran madaki ba su shiga unguwar su Al'amin ba, sai rana tsaka, suka shigo unguwar neman faɗa, a karon farko Al'amin ya ɗauki makami, jikinsa na wata irin tsuma, zuciyarsa na tafasa, wanda hakan ya faru ne a sakamakon abubuwan da yake ta'amalli da su. Dan shaye-shaye nasa, kala-kala ne, kowanne akwai lokacin amfaninsa. Idan wani aiki yake son yi, ba ya son gajiya da wuri, sai ya banki wiwi sai ya daɗe yana abun da yake so, ba tare da ya gaji ba. Idan kuwa rashin mutunci yake son yi, haka zai yi mata haɗe-haɗe na mussaman, haka ma idan so yake ya bugu. Bai fiye ta'amalli da ƙwaya sosai ba, ya fi ƙarfi ga wiwin. Ya je ya samu yaran, kan mai uwa da wabi, yayi musu ɓarna, sannan ya taka har dabar madakin, ya yi masa warning, "Ka gargaɗai karnukanka, a kan shigar mini area su nemi faɗa, idan ba haka ba, kan babban karen zan zo, na yi masa takunkumi, yadda haushi ma sai ya gagare shi" Madaki tun da dodo ya sanya ya bawa Al'amin haƙuri, ba su sake arangama ba, kusan shekara biyu, sai a wannan lokacin, sai da gabansa ya faɗi, saboda yadda kamannin Al'amin suka juye, ƙarara alamun shaye-shaye suka bayyana a tare da shi, yadda ya sake zuwar masa kai tsaye ba tsoro ko fargaba, ya sanya shi gane kuskuren da ya yi na barin Al'amin a raye. Tun da Al'amin yake tare da dodo, bai taɓa rashin kuɗi ba, kuɗi yake kamawa manya da ƙanana, kuma bai taɓa ci wa dodo amana ba. Har a cikin ma'aikata, ana samun ɓata gari waɗanda suke sayar wa dodo kayan maye, idan sun kama, duk wani salo na yadda ake sayar da kayan, ba tare da an gane ba, Al'amin ya goge, haka idan kana ta'amalli da su, kallo ɗaya zai yi maka ya gane. Yan kwamutin unguwa, suka kai ƙarar Al'amin wurin hukuma, a kan yana tayar musu da tarzoma, ba tare da la'akari da yaran da suke rashin jin tun kafin ya fara ba. Dodo ya je ya samu shugaban 'yan vigilant, ya ce masa "Wallahi duk wanda ya sake ɗaukar ƙafa, ya kai ƙarar Aminullahi sai ya ci ubansa, lokacin da aka kashe ɗan uwansa ku nawa ku ka tashi ku ka je wurin jami'an tsaro domin ganin an ƙwatarwa yaron hakkinsa, saboda ba yaranku aka kashe ba. Lokacin da yake ragaita ba shi da sana'a, mutum nawa ne suka mayar da shi makaranta? Ko suka bashi sana'a, dan mahaifinsa ya wofantar da shi, kuna 'yan unguwa ba ku ga dacewar ku nusar da shi kuskuren sa ba? Ai duk society da suka yi watsi da yaran su irin su Aminullahi muna nan muna jiran su, mu zamu karɓe su, mu mayar da su abun da ya dace. Gargaɗi nake yi, ni dai an san ba zan kamu ba, to haka Al'amin ma, ko bayan raina, ina da masu fito mini da shi idan ya shiga cakwakiya. Ku shirya Al'amin bai fara yi muku rashin ji ba tukuna" Ƴan unguwa suka rasa abun yi, yaransu da suke ƙanan rashin ji, suka fara bin Al'amin, yana ba su kayan wiwi suna sayarwa, yana ba su kuɗi, dama gashi da kyauta kuma ba shi da baƙin ciki. Duk yaran dodo, suna shakkar Al'amin, ko dan saboda masifar dodo idan aka taɓa shi, dama Al'amin ya fi yin faɗa da Walid, dodo ya kan ce masa Mai laya, ka kiyayi mai zamanin nan, idan ka ƙure shi, ba zan saka baki ba, idan ya tashi yi maka ɓarna ba. Su yi faɗa su yi daɗi. Tafiyar gaggawa ta kama dodo, zuwa kudancin Najeriya, sai dai ya ce wa Al'amin ya zauna, ya kula masa da harƙallarsa ta kano, ba zai tafi da shi ba. Abun da Al'amin bai taɓa yi ba, sai a wannan karon ya ce "Meyasa ba zaka tafi da ni ba?" "Aminullahi, tafiya ce mai hatsari, ka kula mana da harƙallarmu, sannan kar ka manta rules ɗin, a tafiyarmu babu BODMAS, idan ka ji wuta, ka wargaza komai ka ɓace" Al'amin ya jinjina kai ya ce "Allah ya taimaki sarki babban dodo" "Na gode, Allah ya ja zamaninka, zuwa in da ba ka zata ba, a cigaba da riƙe amana Aminullahi" haka nan Al'amin ya ji baya son dodo ya tafi. Kwana uku da tafiyar Dodo, suna zazzaune, suna shan sigari, aka jefo wata jaka ta katanga. Walid ya ɗaukko jakar, wasu daga cikin yaran wurin, suka fita da gudun tsiya, suna neman wanda ya jefo jakar, ba su ga wanda ya jefo ba. Al'amin ya ja jakar ya buɗe, kawai yayi tozali da kayan dodo a ciki, face-face da jini, har da takalminsa. Cikin ƙaraji Al'amin ya ce "Nooooo" ya tashi jikinsa yana tsuma ya girgiza kai ya ce "Impossible, ba zai yiwu ba, sarki yana raye, raina mana hankali kawai ake yi" Walid ya riƙe Al'amin ya ce "Al'amin ka nutsu mana, musulmai ne mu, idan ba a kashe sarki ba, babu yadda za ayi a ciro kayans jina-jina a kawo mana". Al'amin ya fara neman ya fita hayyacinsa, Walid suka danne shi, suka shaƙa masa wani abu, jikinsa ya saki ya hau bacci. Al'amin ya razana, ya shiga tashin hankali, ya ɗimauce sosai da sosai, da mutuwar dodo, ba zai manta gudunmuwar da ya bashi ba, duk da ba ta arziki ba ce ba, Al'amin kamar zai zare. Duk wata hanya da zai bi ya gano wanda ya kashe dodo, ya rasa, damuwa ta ƙara yi masa yawa. Ya ɗaukko makaman da ya saka aka ƙera masa, sweazland, Russia da kuma iraƙi, ya zuba musu ido, bai taɓa zaton ya shaƙu da shi haka ba. Mussman madaki ya zo ya sami Al'amin, yana ƙyaƙyata masa dariya, wai garkuwar da fake a bayanta, an samu wani gwanin saitin ya rusata, yanzu zai koma Al'amin ɗin sa matsoraci na ainihi. Sai dai cikin sa'a, Al'amin yana tare da sweazland, dan haka madaki ya fara yi wa rauni da ita ya ce "Dan an fasa garkuwata, ba ya nufin zaka cim mini,  *Ƙarfen cikin wuta nake* na fi ƙarfin ɗauka da hannu, ko da mariƙin roba, daga yau ka rubuta ka ajiye, ɗaya ya riski ajalinsa ne kawai zai kawo ƙarshen gabata da kai". Madaki ya kalli cinyarsa da ke jini ya ce "Meyasa ba ka kawo ƙarshen gabar yanzu ba, ka kashe ni?" "Saboda na fika sanin waye kai, akwai lokacin da ya dace da hakan". Yaran dodo, sun so Al'amin ya gaji harƙallar dodo, ba ita ba har manyan hada-hadarsa da manyan mutane. Amma Al'amin yaƙi, ya ce baya buƙatar duk wani abu da zai din ga tuna masa da dodo, kuma zai yi abun da zai Allah zai gafarta masa, ba ɗorar da laifukansa a bayan ƙasa ba. Da yawa sun so su ya basu sirrikan dodo, su cigaba da sana'arsa, amma Al'amin ya ƙi, ƙarshe ma suka bar wannan gidan gaba ɗaya, ya je ya kafa masa sansanin. Walid suna zuwa da Al'amin duba mahaifiyarsa, da ciwon Cancer ya kama, aka kwantar da ita a asibiti, kullum cikin neman jini ake, duk wani kuɗi na Al'amin, sai da ya ƙare a wurin kula da mahaifiyar Walid. Liti dama shi isaknci ne da abokai, suka saka ya lalace, dan har waje babansa ya kai shi yin karatu, bai koyo komai ba sai shashanci ya dawo. Kasancewar jinin Al'amin da na babar Walid iri ɗaya ne, ya bayar da jininsa sosai an saka mata, kullum cikin Kwantar wa da Walid hankali yake, tare da bashi tabbacin zata warke. Har zariya suke kaita Asibiti gashi, amma cikin ikon Allah ta koma ga Allah, abun nan da Al'amin ya yi wa walid, ya sanya ya sanya duk abun da zai yi masa baya fushi da shi, ko yayi sai ya huce. Suka koma ƙaramar harƙallar sayar da wiwi, idan kuma aikin ƙarfi ya samu su yi. Al'amin ya numfasa sannan ya ce "Ban kuma taɓa kashe kowa ba, duk rashin ji na, wanda ki ka ganni da shi, liti ne, yaran madaki suka soka masa wuƙa, kar ki sake cewa na yi kisan kai". Jauhar wani irin kuka take man ban tausayi, rayuwar Al'amin akwai tarin ƙalubale, sai ta ga ita tata rayuwar nafila ce. "Ki yi haƙuri, da yawan furta miki zan sake ki da nake yi, baki cancanci mutum mai tarin laifuka irina ba, wallahi ba zan iya yafewa madaki ba, da shi da wanda suka kashe dodo. Ban yi miki alƙawarin daina abun da nake nan kusa ba, binciken da na ƙara yi akan ki, na fuskanci kusan ƙalubale ɗaya muka fuskanta, dan na san duk wani abun alkhairi wannan shegiyar matar ba zata bari ya raɓe ni ba, dan haka na yi zaton ta shirya mini wata maƙarƙashiyar ne, dan haka ta aura mini ke, ashe wai wani mai kuɗi zaki aura, suka hana ita da wannan banzar matar ta gidanku, ban manta lokacin da take zuwa gidanmu ba ita ma. Haryanzu a shirye nake, mu rabu ki auri mutumin kirki, baki dace da ni da rayuwata ba, rayuwata ta riga ta gurɓace, kullum kina cikin tashin hankali bai kamata ba, duk a sanadina. Dama kin ga ke kalar matan masu kuɗi ce, in da zaki huta a kula da ke sosai. Ni kuma na gurgura na ƙarasa rayuwata" Jikinta na rawa, ta toshe masa baki, ta kalleshi, hawaye wani na bin wani a fuskarta, amma ta kasa magana ta cigaba da sheshsheƙar kuka iya ƙarfin ta. Ya sauke hannunta daga bakinsa ya ce "Lafiya kuwa? Wannan kukan fa?" "Zan zauna da kai a haka, na san wataran zaka daina, a lokacin da raɗaɗin kaɗaici da damuwar da ka ke ciki suka barka, a lokacin da ka fahimci wani zaluncin idan an yi maka wata shari'ar sai a lahira, ba zaka iya ɗaukar wa kanka mtaki ba. Zan zauna da kai har zuwa lokacin da komai zai zama tarihi. Ni ba zama da mai kuɗi ne damuwata ba, kwanciyar hankali nake so, in da za a ga mutuncina a kula da ni, dama miji nagari nake fata ba mai kuɗi ba". Ya lumshe idonsa ya buɗe ya ce "To ni na garin ne?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Murmushi ya yi ya ce "Tashi ki je ki kwanta, ɗaya da rabi yanzu. Ba zan manta ƙoƙarin ki a kaina ba, kina cikin mutane ma su muhimmanci da ba zan manta da su ba" da ta kalleshi, sai ta cigaba da zubar da hawaye, wani irin tausayin sa na ratsa zuciyar ta. Ya gyara pillow zai kwanta, ya kalli yadda take ta kuka, ya ce "Har mamki ki ke bani, yadda ki ke taƙarƙarewa ki yi ta kuka, ni fa da wayona, zan iya ƙirga sau nawa na yi kuka". Yayi maganar yana kwanciya amma ta cigaba da zama a wurin. "Idan ki ka bari na rufe ki a ɗakin nan, akwai ƙura" ta kalle shi ya ce "Ban taɓa ɗaga sweazland na fito da harshe, ba ta sha jini ba, sai a wannan karon da ki ka hana ni, ko ki tafi ko in sha naki jinin in huce". Wato shi gaba ɗaya labarin da ya bata ma, ko a jikinsa. Sai da ta gama koke-kokenta, sannan ta tashi ta fita daga ɗakin. Ba ta kwanta da wuri ba, ta daɗe tana salloli, da karatun Alqur'ani, a kan Allah ya shirya Al'amin, ya sanya tarayyar ta da shi, ta zama sanadin shiriyarsa. Sai da tayi sallar asuba, sannan ta kwanta, dan haka wani irin nannauyan bacci ya ɗauke ta. Sama-sama ta ji muryar Al'amin, yana faɗa da boti, ya zo tashinta yana jin yunwa, ya ga boti ya lafe a jikinta, shi ma yana tashi. Ya danƙo shi ya jefa ƙasa ya ce "Ware ka bar nan wurin dan ubanka" Boti ya tsaya, yana kallon Al'amin yana kuka. Al'amin ya mayar da idonsa kanta, bacci take sosai, shi kuma yunwa ta ishe shi, dan yayi shaye-shaye. Dukan katifar gadon yake yi a hankali, ta motsa kaɗan ta cigaba da bacci. Yaye bargon yayi gaba ɗaya, daga ita sai vest da gajeren wando, a razane ta tashi zaune tana kare jikinta. Ya riƙe bargon ya ce "Ki na ji na ki ka yi mini shiru? Ina son na karya na sha magani, kin ɗauki wancan abun kin kwanta kina bacci da shi". Cikin muryar bacci, mai haɗe da tsoro, ta ce "Na ji, amma ka bani bargon zan fito yanzu". Ya ce "In tafi ki cigaba da baccin, tashi mu je" To ka je ka jira ni, zan saka kaya. Taɓe baki ya yi ya ce "Da kin kwantar da hankalinki, ba na jin komai, ba abun da zan yi miki" ya miƙe yana ajiye mata bargon ta, ya danƙo kan boti ya yi waje da shi. A jejjere ta din ga ajiyar zuciya, tana maimaita maganarsa shi ba ya jin komai. Da ta fito kasa haɗa ido tayi da shi, ya kwanta ruf da ciki saboda raunin bayansa, yana jiran abinci. Bayan ya karya, ta ce "To wanka fa?" "Ba yanzu ba, gasa mini ciwon nan kai" Ta haɗo ruwan ɗumi, ta gasa masa, ciwon, tana yi yana raki, saboda yadda ya ga tana damuwa sosai, wai da zafi. Wayarsa ta fara ringing, ta hana shi ɗagawa, har ta katse, ta sake fara ringing, ta ɗaga ta ce "Assalamu alaikum, ba shi da lafiya bacci yake" "Ya jikin nasa?" Ta ce "Da sauƙi" "Masha Allah, ke ce matar ta sa? Al'amin ya karɓe wayar ya kasheta gaba ɗaya ya kalleta ya ce "Meyasa ki ka tsaya kina magana da wani?" "Na zata su yaya walid ne, yi haƙuri, amma yakamata ka kira shi ka ji, ko an sako shi" Al'amin ya haɗe ce "Wai ke kowa ma damuwa ki ke da shi ne?" "To ai gani nayi saboda mu ya shiga matsala, aka kama shi" "To ba ruwanki, da ni kawai zaki din ga damuwa" ta kwashe da dariya ta ce "To shugaba, in sha Allah. Juya in shafa maka man zafin a wurin" ya juya tana shafa masa a hankali, dan kar ya ji zafi. Wayarta ce ta fara ringing, ta ɗauka ta duba Ta ga lambar mama ce, ta ɗaga suka gaisa, ta ce "Yauwwa, dama kiranki na yi, ana ta shirin bikin hafsa, tun saura sati ɗaya biki yakamata ki dawo gida, akwai aikace-aikace da za ayi, saboda bikin. Ta ce "To shikenan mama, Allah ya kaimu lafiya" "Amin" ta kaste wayar. "Ba in da zaki" ya faɗa dai-dai lokacin da ta ajiye wayar. "Master meyasa, bikin Yaya hafsa ne fa" "Ko bikin wacece, ba zaki ba? Idan akwai mai neman dalili, sai a tuntuɓe ni". Jauhar ta ce "Master za su ga kamar wulaƙanci ne, ko baƙin ciki, ko ba zan yi satin ba, dan Allah ka bari na je bikin" Ya girgiza kai ya ce "No, bayan bikin kya je gidanta". Jauhar ta marairaice za ta yi masa magiya ya buga mata tsawa ya ce "Ina magana kina mayar mini, ba zaki je ba na ce" a razane ta ja da baya, ta sunkuyar da kai ta yi shiru, ya tashi ya bar mata falon. Yana ƙwafe da wayar da suka yi, aka ce ba zata iya sayen anko ba, yanzu kuma an ce ta zo ayi aiki, saboda baiwar su ce ita, ita kuma gaba ɗaya hakan bai dameta ba, wasu lokutan kamar ba ta da zuciya sam. Tun da Indabo ya ajiye wayar, yake jujjuyata yana jin yadda muryar jauhar, ke kai komo a cikin kwanyarsa, kana jin muryar ka san ta yarinya ce, haka kurum ya ji ya kwaɗaitu da son ganinta. Ayshercool 08081012143 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??     Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??     Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??     Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.      Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955 da Indabo ya cigaba da jujjuya wayar yana kallonta. Sosai jauhar ta ji babu daɗi, hanata zuwa bikin da Al'amin yayi, ba ta san dalilin sa na yin hakan ba, kuma bai gaya mata ba, ba ta san me za ta ce wa su mama ba, su yarda da ita. Kuma yayi fuska, ya hau hura hanci yana wani basar da ita, dan ma kar ta ce zata yi fushi da maganar hanata zuwa bikin da yayi, shiyasa yayi sauri ya rigata fara fushin. Haka ta wuni, idan ta tuna abun sai ta ji ba daɗi, da duk in da za ta je, ba ruwansa, amma yau bikin 'yar uwatta, ya ce ba zata je ba, Al'amin kenan. Sai dai tayi iya ƙoƙarinta, ta danne fushinta, ba ta canza masa ba, amma yanayinta kallo ɗaya yayi mata ya gane, a cikin damuwa take, kuma ya san hakan yana da nasaba da hanata zuwa biki da yayi. Can gidansu amarya hafsa, ana ta rawar kai, an sha gyaran jiki, magungunan mata kuwa ba a magana, fatar nan ta ƙara ɗashewa, tayi fara ƙal kamar aljana. Sai hura hanci ake yi, za a auri mai kuɗi, mama kuma sai yi musu lumbu-lumbu, kamar tana tare da su a komai. Suka din ga karɓar kuɗi a wurin Alhaji mu'azzam kamar ba gobe. Shi kuma duk abun da suka nema, haka zai ba su. Zakiyya ta saka hafsa ta tambaye shi, wai a ina za su je honeymoon. Murmushi ya yi da ta tambaye shi ya ce "Hafsa yawon ƙasashen duniya har sai kin gaji, dai ƙasar da ki ke so zamu je" hakan ya ƙara fasa mata kai, ta din ga jin cewa ta gama dacewa. Al'amin ciwonsa ya fara warkewa, kasancewar ba shi da ƙan jiki, ga kulawa da Jauhar take yi da shi sosai da shan magani. Ta ɗaura aniyar, fara ɗora Al'amin a turbar tafiya masallaci kuma, ya din ga salla a cikin jama'a, kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, ya kwaɗaitar da al'ummarsa, mussaman da ciwonsa ya kame, dan ya fara saka riga ya fita ma. Sai dai fa aikin ba na wasa bane ba, dan wasu lokutan idan ta tashe shi sallar, har a idar tana fama da shi bai tashi ba, mussman idan a cake yake, idan ta yi alwala kuwa ta zo tashinsa, ƙarshe sai ta ta alwalar ta karye, shi kuma bai yi ba. Sai dai ta tsananta addu'a da gaya wa Allah. "Ya Allah ga bawanka Al'amin, kai ka halicce shi, ka shirya wanda suka aikata laifuka fiye da nasa, Ubangiji Allah ka shirya mini shi. Allah ka sa ya shiryu a sanadin zamana da shi, Allah kar ka saka na ƙosa ko na gaji, Allah ka dubi niyyata ta son zama da shi da yin biyayyar aure kamar yadda ka umarta, Allah dan kunfayanunka ka shiryi wannan bawa naka" Duk in da jauhar ta ji Addu'ar biyan buƙata, irin su salatul haja, salla raka'a biyu, fatiha da sura, idan ta idar ta mayar da goshinta ƙasa, ta karanta la'ila ha illa ant subhanaka inni kunt mina zalimin. Ƙafa arba'in  da ɗaya, ba ta ɗagowa sai ta gaya wa Allah buƙatunta. Salatul tasbih, da sauran tasbihai haka take yi, tana yi wa Allah magiya da yin tawassuli da su, ta roƙi Allah ya shirya mata mijinta, ya haɗa kan su su zauna lafiya. Yau ta samu yayi sallar asuba ƙarfe shida saura da ƙyar, ta dawo dan ta saka shi yayi azkar, ta tarar har ya kunna sigari daga idar da sallar. Bai yi tsammanin za ta dawo ɗakin ba, kawai ya ji sallamarta ta shigo. Kamar yadda tayi tsammani, bai daina sha ba, kuma ya tsuke fuska. Ta ƙarasa gabansa ta zauna, ta zuba masa ido. "Kin san an hanaki shaƙar hayaƙi ko? Kin san ba cikakkiyar lafiya ce da ke ba" "Kai ma bai dace da kai ba, ina gaya maka ina son lafiyarka, su kan su masu kamfanin abar sun yi gargaɗi a kan haka, dan Allah ka ajiye magana zamu yi". Bai ajiye ba, yayi mata shiru yana cigaba da fesar da hayaƙin wani wurin daban. Tashi tayi ta zagaya, in da yake fesar da hayaƙin tana kallonsa. "Meye haka ne wai?" "Dan Allah ka ajiye mu yi magana" "Ina jinki ai" wani abu mai ɗaci ta haɗiye, kawai ta tashi ta bar masa ɗakin. Ta koma ɗakinta ta tsaya, kuka ya ƙwace mata, sai ta fara saito abubuwa, sai Al'amin ya sake burkice mata, tun da suka yi aure take yi masa addu'a, amma abun nasa sai a hankali. "Kul jauhar, kar ki yi saɓo, ko ki yi wa Allah butulci, Allah sami'ul alim ne, idan ka roƙa baka ga tasirin abun ba, lokacin ne bai yi ba, tun da shi ya ce mu roƙa zai amsa, kuma Allah ba ya sabon aiki' wata zuciyar ta gargaɗe ta. Istigfari ta cigaba da yi, ta nemi wuri ta zauna a tsakiyar gadonta, tana cigaba da tasbihi. Sai da gari yayi haske sosai, ta fita tana aiki, ya fito cikin takun ƙasaita, ya nemi wuri ya kame a kan kujera. Sai da ta kai zuciyarta, sanna ta iya ce masa "Ina kwana?" "Lafiya ƙalau" a ranta ta ce 'Ka yi laifi, kuma ka maze kana hura mini hanci, da ni ka ke zancen'. Ta ajiye masa karin kumallonsa, ta koma ɗakinsa, ta na gyarawa, yanzu ya rage watso mata kaya daga wardrobe, sai dai ya tara mata kayan wanki, a kan katifarsa. Tsayawa yayi a bakin ƙofa, yana kallonta. Yayi gyaran murya ya ce "Kin ce zamu yi magana, ta menene?" Ta kalleshi ta ce "Ka manta kawai" ta ƙarasa maganar tana kwaso kayan wankin za ta fita. Har ta gota shi, ya janyo ta kamar wata 'yar tsana, ya tsuke fuska ya ce "Gaya mini menene?" Ta sunkuyar da kanta, hawaye ya fara zubowa daga idonta, wani na bin wani. "Menene kuma yanzu?" Cikin rauni ta ce "Kai ne" "Na yi me?" "Kusan kullum sai ka sakani kuka mussaman kwanan nan, na ce dan Allah ka daina shan komai ka ƙi dainawa, haba master wane irin uba ka ke son ka zama idan Allah ya bamu zuriya? Ina son in ga ka daina shan komai ka daina abun da ka ke yi. Amma ƙir-ƙiri ɗazu ka ƙi daina sha". Ya ce "Ke, wai an gaya miki daina shaye-shaye kamar daina cin tuwo ne? Ina ƙoƙartawa fa, duk kin addaba mini, ina ji ina gani, asuba ina shan kara biyar zuwa sama, amma ɗazu uku kawai na sha amma ba kya gani, kuma yaushe na ganki, balle a tara wata zuriya? Shiyasa ma ban bari sun ƙaraso ba tukuna sai na gama abun da nake yi. yayi maganar yana basarwa. Wata irin kunya ta kama ta, jin abun da ya mayar da maganar. "Ki daina damuwa, ina ƙoƙari sosai, ba zan iya dainawa ba, sai na cika burina, mutum ɗaya kawai zan kashe, shikenan" Jauhar ta kalleshi ta ce "Kisa kuma? Ana ga ƙura kana ga yaƙi, idan an yi nan sai ka yi can" Dogon harshensa ya zaro mata, yayi wani irin murmushi, sai ta ga kamar ya canza gaba ɗaya, ya dafo kafaɗarta kamar ƙawarsa ya ce "Bar wankin, zan yi ki haɗo da naki ma, idan na gama zan yi gyaran kwatar layin nan, duk an bari ta cushe da shara, me zaki dafa mana da rana?" "Master ba ka da aiki sai zancen abinci ne?" "To idan ban yi zancen abinci ba zancenki zan yi babyn roba" "Saura ta katako, rana zata yi mini, ko wankin ka saɓa sai na yi mana ɗauraya" Al'amin ya ce "A'a ki yi aikin ki zan wanke" yayi maganar yana yi mata wani irin kallo tare da murmushi. Ita ma murmushin ta yi masa ta ce "Harshenka dogo ne, meyasa ka ke fito da harshe ne?" Ya ce "Rantsuwa ce, kowane specie ɗinmu, akwai irin ta su". Jauhar ta yi dariya ta ce "Wai specie kamar a biology?" "To in ce kowane ɗan daba?" Ta yi saurin girgiza kai ta ce "A'a ba na son wannan kalmar, babu daɗin ji" Ba tare da ta gane ba, yayi mata wayo, ta daina fushin da take yi, dan babban burinta ya kula ta, ya sakar mata fuska. Aka shiga satin bikin Hafsa, Anty Zakiyya ta kira Jauhar ta ce "Jauhar wai yaushe zaki zo ne? Ayyuka sun kacame, ko dai baƙin ciki ki ke yi da lamarin nan ne?" Jauhar ta ce "Haba Anty, ba haka bane wallahi. Kin ga maigidan ne ba ya jin daɗi, idan na taho babu mai kula da shi". "Kamar yaya? Au mijinki ya fi 'yar uwakki, kamar wani mijin kirki, da waye yake kula da shi idan ba shi da lafiyar?" "A'a Anty, ai miji duk in da yake miji ne, yana buƙatar kulawa ne, ba dan.... "Dalla yi mini shiru, har wani tinƙaho ki ke yi da wannan abun? Makakken ɗan wiwi. Ba tare da Anty ta sani ba, tuni ya karɓi wayar daga hannun jauhar, ya saka a kunnensa tana ta masifa "To ki zauna sai yadda yayi da ke, ai mutumin kirki mai kuɗi shi yake saka doka a bi, ba irin mijinki ba da har ki ke gaya mini wai ai miji miji ne ba". "Makakken ɗan wiwi yana godiya, kuma kun san da makakken ne, ku ka aura mata ni. Ni na hanata zuwa matata ba baiwa ba ce, ta zo ta yi muku bauta, ba zata zo ba, idan kun ga dama ku bar bikin kar ku yi" Jauhar tana girgiza masa kai, amma sai da ya gama maganar ya jefar da wayar. "Master, iyayena fa, ba a haka yakamata a gaya musu ba, da ka bi a hankali, na san yadda zan gaya musu". Al'amin ya ce "Kin san bani da tarbiyya, ban iya magana da manya ba" "A'a ba haka nake nufi ba" "Idan ma dai hakan ki ke nufi, idan kuma ban isa ba, ki shirya ki tafi " Jauhar ta ce "A'a ka ma isa, ai na fasa zuwan, amma ai ka yi mini alƙawarin zaka kai ni gidanta bayan bikin ko?" Tausayinta ne ya kama shi, ba dan haka ba da gidan hafsan ma ba zai bari ta je ba, amma ya tuna ɗan uwa duk in da yake daɗi ne da shi, kuma bai kamata ya hanata zuwa wurin 'yar uwatta ba, amma kamar ko a jikinsa ya ce "Zan yi shawara" Anty Zakiyya kuwa, sai da kayan cikinta suka yanutsa, saboda tashin hankali da ta ji muryar Al'amin a waya. Sai dai jauhar ta sha zagi a gidan, ana cewa baƙin ciki ne da hassada ya sanya ba zata zo ba. Yaya saifu ya ce 'm"Jauhara ba ta da irin wannan zuciyar, hankalinta na kan mijinta, wannan aure dai, in dai dan cin amana aka yi shi, ba in da zai je zai watse". A fusace Anty ta ce wa mama "Ki ja wa ɗanki kunne, kar ya sake aibata mini auren 'ya" An kai kwanaki huɗu ana events kala-kala na auren Hafsa, jauhar sai kallo da ta din ga yi, tana murmushi tare da jin babu daɗi rashin halartar auren yayarta, ga 'yan uwa da abokan arziki duk an taru. Ita ma ta ɗora hotunan, tana yi wa hafsan fatan alkhairi. Aka gama biki, aka kai hafsa gidanta, wanda suke haɗe da uwar gidansa, kowacce part ɗin ta daban. Aka yi sayen baki aka watse, ya tara su yayi musu nasiha, bayan Uwargidan ta fita, Alhaji mu'azzam ya ce "Bari na je na ɗan ƙara rarrashinta, na san tana cikin damuwa" haushi ya kama hafsa, dan a zatonta yana zumuɗinta, ba zai saurari uwar gidan ba. Sai dai har ɗaya na dare bai dawo ba, ta kira wayarsa a kashe, tun tana saka ran ya dawo, har ta gaji, bacci yayi awon gaba da ita. Da safe ma, ga yunwa ga gajiya, amma ba ta ganshi ba, sai sha ɗaya na safe. Ya ce "Jauhar am sorry please" ta kalle shi cikin takaici ta ce "Jauhar kuma?" "Afuwan Hafsat, wallahi madam ce nayi  ta faman rarrashinta, taƙi yin shiru kin san kishi babu daɗi, shiyasa na zauna da safen nan ma da ƙyar na fito, duk a cikin damuwa ta ke, yanzu haka kanta ciwo yake saboda kuka, ina ga da kaina zan fita nema mata magani" Tamkar hafsa ta zabga masa mari haka ta kalleshi ta ce "Ni bana buƙatar kulawarka kenan sai ita?" Ya ce "No ba haka bane ba? Ai ke sabuwa ce, sai ta fiki shiga damuwa, bari na je na sayo mata maganin na kai mata, na yi ordern abinci, idan ban dawo da wuri ba ki karya kawai. Abu kamar wasa, har wurin kwanaki uku, bai saurari hafsa ba, wai uwargidansa ba ta da lafiya, har ma ya ɗauki fushi da ita, wai ba ta je ta yi mata sannu ba, ta ɗauki waya tana kuka ta sanar da Anty, Hankalin Anty ya tashi, ta ce ta je ta dubata ɗin, za su sake shiri su ma. Baya nan hafsa ta shiga duba ta,  ta ce "Na ji an ce baki da lafiya, na zo duba ki" Ta ce "Ko ɗaya, lafiyata ras, kawai ina ƙoƙarin nuna miki ƙarfin ikon da nake da shi a cikin gidana da irin gangancin da ki ka aikata na shigo mini gida" Hafsa ta ce "Shigowar ai ita ce mai wuyar, tun da an ce hanawa ki ke yi, ni kuma na yi nasara na shigo, mu zuba da ni dake". "Lallai yaro bai san wuta ba sai ya taka, ga fili ga mai doki". Har hafsa ta kwana bakwai a gidan nan, ba su haɗa shimfiɗa da Alhaji mu'zzam ba, duk ɗokin amarcin da take yi, komai ya fita daga kanta, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ƙiri-ƙiri yake nuna mata shi ta matarsa yake yi ba ita ba, saɓanin abun da ya nuna mata a waje. Jauhar kuwa ta cigaba da yi wa master magiyar, ya taimaka ya bari ta je gidan hafsa tun da an yi bikin, kuma ta na son ta je gida ta gaida baba, ta bashi gudunmawar biki. "Ni fa nayi miki alƙawarin zuwa gidan yayrki, amma amarya ce, ya zaki je musu gida sati ɗaya da biki?" Cikin rashin fahimta ta ce "To ba a zuwa?" "Eh, idan sun shirya samun zuriya su, ai ba za so ki dame su ba, idan lokaci yayi zan kai ki". Anty da Rahila suka cigaba da yawon bin bokaye, ƙauye-ƙauye, dan su sake kama Alhaji mu'azzam, kuma ya saurari hafsa. Komai na buƙata gashi nan a zube, amma miji ya gagareta sai dai ta ganshi daga nesa. Tayi iya ƙoƙarinta, duk wanda ya zo, ba ta bari ya fuskanci tana cikin damuwa, ta baka abinci ka ci ka sha, idan zaka tafi ta baka na mota mai yawa, tayi ta hura hanci, saboda tana cikin gida na alfarma ga motoci a parking lot. Jauhar ta gaji da yi wa Al'amin magiya, ta ƙyale shi, dan kansa ya ce ta shirya, shi zai kaita gidan hafsan, su gaisa ya dawo da ita. Ta din ga murna tana yi masa godiya, amma ta ce "Dan Allah master a sakawa baburin nan salansar sa, idan muka fita fa saboda ƙarar da yake yi, sai kowa ya waiwayo ya kallemu". Ya ce "Ni fa na fi son abuna a haka" Ta kwantar da murya ta ce "Na sani, amma a taimaka mini, ko so kake kowa sai ya ɗaga kai ya kalli babyn robar taka?" "Zan duba" "Yauwwa master na" Yayi murmushi ya ce "Naki, waye ya baki?" Ta ce "Allah ne ya bani, kuma na karɓa hannu bibbiyu ina yi masa godiya" Ta kira hafsa a waya, hafsa ta ɗaga da ƙyar tana cika tana batsewa, Jauhar ta ce "Anty hafsa ina wuni, ina ta kiranki ba kya ɗagawa" "Bana kusa ne, shiyasa" "Adress ɗin gidan zaki bani, gobe in Allah ya kaimu zan zo in sha Allah" Kamar hafsa ta ce mata ba ta so, b tare da la'akari da su ba su taɓa taka gidan jauhar ba, amma sai ta ga ya dace jauhar ta zo ta ga daular da take ciki, dan haka ta bata adress ɗin. Bayan ta gama wayar, ta ce "Master ta bani adress ɗin, babu wuya ma gane gidan nata. Zo mu yi kallo a wayata" ta yi maganar tana zama a kusa da shi. "Ni kallon nan gajiyar da ni yake yi" Ta ce "Ahh haba dai, ko kaɗan nan, yana da kyau ka samu abubuwan da za su din ga ɗebe maka kewa" Al'amin ya ce "To zaɓi ɗaya, ko dai ki sauke wannan abun, ko kuma a haƙura da kallon" yayi maganar yana nuna boti, da yayi ɗare-ɗare a kan cinyar jauhar. Jauhar ta kwashe da dariya ta ce "Boti master ya ce ka tashi daga cinyar matarsa" kwanciya magen ya ƙara yi, yana lafewa. "Ban taɓa ganin abun da ya raina ni ba, kamar ke da magen nan ba" Jauhar ta din ga dariya, ita yadda ba sa ga maciji da botin ma dariya yake bata. Ta zauna a kusa da shi, tayi connecting da mp, ta saka musu film. Ta kalleshi ta ce "Ka ji ko? Baby ake cewa mace, kai baka yi mini irin wannan kalar soyayyar, sai zare mini ido da sakani kuka" Yayi murmushi bai ce mata komai ba, sai dai ta ji ya saka hannayensa ya riƙe nata. Mintuna goma da ta ɗaga kai ta ga yayi bacci. Ta zuba masa ido yana bacci, a ranta ta cigaba da yi masa addu'a. Ta kashe wayar ta ce "Master ka tashi ka je ka kwanta tun da kallon ne ba ka so" Yayi shiru bai motsa ba. "Master" "Mmm" ya amsa ba tare da ya buɗe idonsa ba. "Mu je na yi maka addu'a ka kwanta" Ya ce "Ɗauke ni, na gaji" Ta ce "Na ɗauke ka, ai kuwa da sai dai wata ba ni ba, aikin me ka yi ka gaji har haka?" "Ƙasa muka kwashe tifa biyar, ban sha komai ba kuma na yi aikin, ni da su Walid" Jikinta a sanyaye ta ce "Har tifa biyar master. Baka gaya mini ba sannu, amma dai sun biya ku ko?" Ya tashi zaune ya ce "Eh, har na kai wa mai solar kuɗin, ya zo ya saka miki solar, ya kawo miki fankar solar zafi ya fara yawa kuma ba wuta". "Solar kuma master? Da mun sai kayan abinci, zafi lokaci ne zai wuce, solar fa da tsada". "An ce masu asma, ba sa son zafi" ya yi maganar yana tashi tsaye, tashi ta yi ita ma, sai ta rasa me za ta ce masa, ya nufi ɗakinsa, ta rasa ta ina yakamata ta fara ma. Akwai abubuwa masu muhimmanci da yakamata ace yana yi da kuɗi, da solar da ya saya, kamata yayi ace ya sai musu kayan abinci, ya ɗinka sutura da ko ɗan takalmi ne mai kyau na kwalliya. Duk in da ya kwashi taklminsa soso haka yake ƙarawa gaba da su, kayansa ma ita ta ware masu kyan ta kai ɗakinta, sai idan za shi wani wuri na musamman ko juma'a ta bashi ya saka. Sai dai ta san bai kyautu, ta nuna ba ta ji daɗin abun da yayi ba, domin ko ba komai, yayi ne dan ya kyautata mata. Ya nemi wuri ya kwanta, ta zauna a kan katifar, ta ɗora hannunta a kansa, tare da karanto masa addu'oin kwanciya bacci. Abun da jauhar ba ta sani ba, bayan ciyar da shi da ta din ga yi farkon auren su, Addu'ar da ya ji tana yi masa cikin magagin ciwo, tayi matukar tasiri a zuciyarsa, Addu'a ce da idan ba uwa ba, ba kowa zai yi maka ba. Addu'oin da take yi masa idan yayi mata wani abu na kyautatawa ma, ba ƙaramin daɗi yake ji ba. Ga uwa uba kirarin da take yi masa wasu lokutan, da suke fasa masa kai. Duk wani abu da zai yi baya manta tarin alkhairin ta. "Allah ya saka maka da alkhairi, ya buɗa arzikin ka, ya wadata mu da halal ya nesanta mu da haramun. Na gode sosai da sosai Allah ya biya ka da gidan aljanna, ya jiƙan iyayenmu" Idonsa a lumshe ya ce "Amin 'yar aljanna, addu'ar ta yi daɗi" tayi murmushi ta tashi. Washegari da wuri ta shirya, tana ta murna za ta je gidan hafsa, ta wanke laifinta na rashin zuwa biki. Shi kuma ya ce zai kaita, amma ya din ga yanƙwanata. Ba su fita ba sai sha ɗaya saura, tiryan-tiryan, har gidan hafsa. Gida ne babba na gaske, Al'amin ya ce "Ba daɗewa zaki yi ba, da wuri zan dawo mu tafi" "To Allah ya dawo da kai lafiya, take care". Ya ce "To, ki shiga, sai na tafi" "Saboda kar in gudu?" "Idan kin gudu ma zaki dawo" yayi maganar yana tayar da babur ɗin sa. Juahar ta shiga har falon Hafsat, ta din ga bata haƙuri na rashin zuwanta bikin nan ta ce "Kin san halik maza wasu lokutan sai a hankali, babu yadda ban yi ba, amma ya hana, ba shi da lafiya lokacin" Hafsa sai ɗan fizgar kai take yi, wai ita dole ga matar mai kuɗi. Har la'asar tana gidan hafsa, bayan ta gama shan ƙamshin, ta saki jiki kuma suka hau hira, da yake ita ce sakuwar jauhar, daga ita sai jauhar. Ta din ga koɗa mata irin son da Alhaji mu'zzam yake yi mata, dan ta tura mata haushi. Jauhar kuwa ko a jikinta, ta ce "Wallahi yaya hafsa idan Allah ya baka miji mai sonka tsakani da Allah, duk wani ƙalubale mai sauƙi ne" Ta ce "Aikuwa shiyasa nake tausyinki, aure ba soyayya, ga miji sai a hankali" Jauhar ta ce "Aikuwa ke da ki ka yi na soyayyar ma, ba ki fi ni samun kulawa ba, da farko a tsorace nake da shi, tun da muka saba Alhamdilillah" "Taɓ, haryanzu yana safarar cocaine ɗin?" Duk da jauhar ta ji haushin maganar ta ce "Da safarar cocaine yake, ai mun girmi zaman Kano sai Abuja" Al'amin ya kira jauhar, ya ce ya zo ta fito su tafi. Ta leƙa ta window falo ta hango shi, a cikin harabar gidan. Ta ce "Ɗago kanka sama ka ga" ya ɗaga kai, ya hangota. "To ka tafi, ba yau zan dawo gida ba, sai gobe" "Wallahi idan ba ki fito ba, zan shigo har ciki" "Kaikaikai, gidan mutanen za ka shigo?" "Sai na shigo ɗin tukuna kenan?" Tayi dariya ta ce "A'a, rufa mini asiri, kar ka saka da ni da kai a zanemu, gani nan" Hafsa ta yi ƙuri da ido, tana kallon jauhar, tana leƙen Al'amin kuma suna waya, tana ta dariya. "Yaya hafsa, bari na tafi" Hafsa ta tashi ta ce "Mu je na raka ki". Suka fito harabar gidan tare, yanayin Al'amin a yanzu, akwai nutsuwa a tare da shi, ba kamar lokacin da ya je gidan su ya ɗauki jauhar ba. Hafsa ta ce masa "Ina wuni?" "Lafiya ƙalau" ya amsa idonsa a kan jauhar. "Ya ka ke hararata ne, ba gani na fito ba" Ya ce "Zaki yi bayani" motar Alhaji mu'azzam ce ta shigo gidan, yana hangen jauhar, ya ci wani irin wawan burki ya buɗe motar ya fito. Ya ƙaraso ya kalli Jauhar ya ce "Jauhar, dama kina nan?" Tayi murmushi ta ce masa "Eh, ina wuni?" "Lafiya ƙalau jauhar, sai dawowa na yi aka ce mini kin yi aure, na ce ko wani laifin na yi miki? Hafsa ta ce mini dama akwai wanda ki ke so, shi ki ka aura, ni kuma baki gaya mini ba lokacin da nake neman aurenki" Kallo ɗaya jauhar ta yi wa Al'amin, ta ga ya murtuke fuska, idonsa ya fara kaɗawa zuwa ja. Ta ce "Eh, gashi nan a gabanka mijin nawa, Allah dama ya ƙaddara yayata zaka aura. Yaya hafsa sai anjima". Ya ce "Tsaya na baki na mota" ya saka hannu a aljihunsa ya ɗebo kuɗin da bai san yawan su ba, ya miƙa mata ta girgiza kai ta ce "A'a na gode" Hafsa ta ce "Baby kawo ka ga" ta karɓi kuɗin ta turawa jauhar a jakarta, ta ce ba a mayar da kyautar manya, ku gaida gida. Tuni Al'amin ya juya ya fice, idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi wa Alhaji mu'azzam illa, da wuƙar da take cikin rigarsa a soke. Tun da suka tafi hanya, bai ce mata uffan ba, hakan ya sanya ta cikin matsanancin tashin hankali. Da ya ajiyeta a gidan ma, tafiyar sa yayi, bai ko shiga gidan ba. Ta din ga addu'a Allah ya sanyaya masa zuciyarsa. Duk yadda ya so ya sarrafa kansa ya kasa, sai da yayi shaye-shaye, domin rage raɗaɗin abun da yake ji, dan zuciyarsa har wani tururi take yi. Har sha biyun dare, idonta biyu tana zaune, tana jiran dawowarsa, ya koma mata Al'amin ɗin sa, dan ko sallama bai yi ba ya shigo, ya wuceta ya tafi ɗakinsa. Cikin fargaba, tana addu'a, ta bi bayansa, warin wiwi duk ya cik wurin. "Sannu da zuwa, nan zan kawo maka abincin?" "Fita ki bani wuri, kafin na kakkaryaki na zubar. Idan ba kya son zama da ni, ba sai kin wulaƙanta ni, ta hanyar kai ni wurin tsohon saurayinki ba, shiyasa nake ta baki zaɓi tuntuni a kan zama da ni, ba dan na sarrafa zuciyata ba, sai na kashe mutumin nan har lahira yau, fita ki bani wuri, bana ƙaunar ganinki ma". Ta marairaice ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, wallahi da na san zamu ganshi da ba mu je ba, ni saboda 'yar uwata na je". "Saboda 'yar uwakki, ko kuma saboda ki ganshi?" "Ya za ayi na je ganin wani, alhalin ina ɗauke da igiyar aurenka a kaina" "Ki daina wani kwantar da murya, na riga na gane abun da ki ke nufi, da in da ki ka dosa, if you still loves him zan iya sakin ki, ki iya koma wurinsa, tun kafin na illata ki, ba zan juri wannan cin fuskar ba, nan gaba ban san me zaki aikata ba" Cikin tsananin ɓacin rai ta ce "Idan ka sake ni, hakan baya nufin rayuwata ta zo ƙarshe, jaririn da ya zo duniya ma Allah ya na iya karɓar rayuwar mahaifiyar sa, kuma ya raya mata shi. Ka yi mini duk hukuncin da ka ga shi ya dace ni" ta fice daga ɗakin, cikin tsananin ɓacin rai da damuwa. Ransa yayi matuƙar ɓaci, jin yadda ta gaya masa maganganu, gashi dama a cake yake, ya nemi wata ƙwaya ya haɗiya ya kwanta, dan kar ayi ɓatacciya. Da asuba ya farka, ya saba ta zo tayi ta fama ta tashe shi, amma yau taƙi zuwa. Yayi sallar asuba, gari yayi haske ya fito, amma ba ta fito ba, ya gaji da zama ya fita. Da azahar ma, abincinsa ta ajiye masa ta yi zamanta a ɗaki, idan yana falo tana ɗakinta, idan yana ɗaki sannan zata fito. Ya shareta shi ma, yana jiran ta zo ta bashi haƙuri kamar yadda ta saba, amma taƙi, sai ya ji gidan yayi masa duhu babu daɗi. Kusan kwanaki uku, ba wanda yake shiga harkar wani. Yau har ya cire kaya ya kwanta, ya tashi ya zauna yayi shiru yana tariyo maganganun da ya gaggaya mata, sai ya ji sun ɗan yi nauyi da yawa. Ya tashi ya tafi ɗakinta, kasancewar babu wuta, ya kunna fitilar wayarsa, ya shiga. Tana banɗaki tana wanka, ta jingina fitilarta a kan mudubi, tana haska mata cikin toilet ɗin. Ya ƙarasa gaban mudubin, ya ɗauki wayar ya kashe fitilar. "Waye a nan?" Tayi maganar cikin tsoro, dan ba ta san ma ya dawo ba. "Waye?" Yayi shiru bai yi magana ba. Da sauri ta gama kwara ruwan a jikinta, ta fito sai dai ɗakin yayi duhu, ba ta ganin komai. "Wai waye ne?" Tayi maganar tana laluba hanya. Direction ɗin da yake ta nufo, cikin tsoro, kawai ta ji ya zaunar da ita a kan cinyarsa. Cikin tsananin tsoro ta ware baki za ta yi ihu ya tsohe mata baki ya ce "Shhhhh, Al'min ne" Ayshercool 08081012143