[5/16, 5:50 PM] NANA: *_Typing📲_* *_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_* _{Gara rana dake}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_Da sunan ALLAH mai ramahama mai jinƙai_* *_Ya rabbi ina roƙonka da sunayenka ƙyawawa masu tsarki, ka bani ikon rubuta abinda zai amfaneni ni da al'umma. Ka tsareni rubuta abinda zai cutar dani da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W). Yanda muka fara lafiya ALLAH yasa mu kammala cikin farin ciki da kwanciyar hankali🙏🏻_*. *_Ya rabbi ka gafartama mahaifina, ka ƙarama iyayena biyu mata da suka rage lafiya mai amfani.😭🙏🏻_* _Littafin *BAƘAR INUWA* ƙirƙirarran labarine da baida alaƙa da kowa da komai. An yisane domin faɗakarwa, nishaɗi, ilimantarwa, harma da ban haushi ta wani sashe. Dan haka a wannan gaɓar ina son jan hankalin mai karatu, yayma kansa adalci yayma marubuci adalci._ *_A duk lokacin da mai rubutu ya kafa alƙalaminsa akan takarda ba yana nufin dole zai rubuta irin RAYUWARSA bane, ko irin RAYUWARKU. Malami yakan faɗakar ya tsoratar akan abinda ya dace. Haka shima marubuci yakanyi rubutu domin faɗakarwa ko nishaɗantarwa akan abinda rubutunsa yazo dashi. Idan yasa ƙyaƙyƙyawa, ba dole sai yanada irin wannan ƙyawun bane, domin kuwa kowa yasan a duniya akwai ƙyawawa. Idan yasa mai ƙarancin ƙyau (domin UBANGIJI bai halicci mummuna ba, kowa da irin ƙyawun da yay masa na halitta), ba dole sai yana a cikin wannan jinsin bane, sai dan rubutunsa a haka yazo. Idan yasa mai arziƙi, badan dole sai shima yanada arziƙin ba. idan yasa mai mulki, ba dole sai ya kasance jinin mulki ba. Idan yasa talaka, ba dole sai ya kasance talaka ba. Abinda kawai nasani alƙalamin marubuci zai iya taɓa kowa. Mai kuɗi, talaka, mai mulki, ɗan ƙauye, ɗan birni, musaki, mai ilimi, jahili, ƙyaƙyƙyawa, mai ƙarancin ƙyawu. Mai ƙyawun hali, mugu dama kowa da kowa. Duk kuma abinda ya taɓo idan zaka nutsu wajen zagaye cikin duniya koda ace da tunani ne sai ka samu mai kamanceceniya da LABARIN. Shiyyasa kuskure ne mai KARATU ya tsuke tunaninsa akan dole sai abinda ya sani MARUBUCI zai wallafa ko ya faɗa. Idan akasin hakan yazo kuma shi a gurinsa marubuci baiyi dai-dai ba. Karka manta ALLAH ya haliccemune yaruka daban-daban, jinsi daban-daban, yanki daban-daban, launi daban-daban, addinai daban-daban, yaruka daban-daban. Bai zama lallai sai abinda kai ka sani ko kake gani zai rubuta ba. MARUBUTA da yawa sun sha rubuta LABARANSU ko RAYUWARSU a littatafai daban-daban batare da kunsan nasu bane ba. Saboda basu fito sun sanarma duniya nasun bane ba. Dan haka ina roƙonku idan LITTAFI yazo muku, ku karanta kawai badan lallai sai yazama RAYUWAR wanda ya rubuta ɗin tazam dai-dai da abinda ke ciki ba. Kawai kadai duba darasin dake ciki ka amfana, akasinsa watsar, yi farin ciki da farin cikin da yazo dashi, dan wani abun akan rubutashine kawai domin ƙawata labari ko nishaɗantar da mai karatu wajen cire masa wata keɓantacciyar damuwarsa. Ina fatan za'a fahimceni_* _Banyi wancan dogon bayanin bane dan na canja kowa, nayi ne kawai dan ya zama dai-dai da fahimtar ka a ƙwaƙwalwarka da tuntar da kai wanene MARUBUCI a taƙaice. Domin kuwa KOWA masoyin Bilyn Abdull ne, amma bai zama kallai ita ta zama abin SON kowa ba._☺️ *_Alhamdulillahi ZAFAFA BIYAR sun sake dawowa gareku da sabbin salo daban-daban. Muna fata ALLAH ya baibayemu da alkairinsa mu da ku dake tare da mu. Sannan muna roƙon wanda ma basu tare damu, kodan sauke haƙƙi kuzo dan ALLAH ku saya da kuɗinku badan zamu iya furta kalma mara daɗi gareku ba. Dan kuwa koda wasa bama fatan jifan wani ɗan uwanmu musulmi da kalmar (ALLAH ya isa akan littafi). Masu saya ku fitar, dan girman ALLAH kuji tsoron ALLAH. Badan mu ba, badan mun isa ba. Kuyi haƙuri ku daina aikata mana hakan, domin UBANGIJI ya hana zalunci a tsakaninmu._*☺️🙏🏻 _Masoya kumuje zuwa, domin kuwa yanzu za'a far share filin wasan, dan wannan karon tafiyar ZAFAFA ta dabance😉⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️_. _____________________ *_Episode 1_* .............Tafe yake tamkar iska zata kwasheshi ya faɗi dan sauri. Yayinda yake ƙananun surutai kai kace sabon kamune a hauka. Ya sake cin tuntuɓe a karo na biyu, sai dai cikin sa'a ya dafe bangon gwaguyayyen gidansa saɓanin ɗazun da sai da ya kai ƙasa. Dogon tsaki yaja zuciyarsa na sake hasala da kumbura har cikin maƙogwaro. Cikin son huce haushinsa da takaici yasa ƙafa ya daki murfin gidan na sa da duk ya cinye da tsatsa tsabar daɗewar da yay, dan tunda aka gina gidan banajin an taɓa sauya ƙyauran saboda koɗewa da ciccinyewar da yay na tsatsa tamkar tsohon drom ɗin ƙarfe.         Ball ya fara da butar da ke a farkon shigowa, inda alamu suka nuna toilet ɗinsu ne a wajen. Ta tafi ta daki ƙarshen bango, murfin yay gefe itama tai gefe. Baba Nafi da ke alwalar magrib ta ɗago kai cike da nutsuwa da sanyinta ta dubesa. Sai kuma ta maida kanta ƙasa saboda uwar hararar daya zuba mata kai kace idanun nasa zasu zubo ƙasa ne.        “Kowanne shege da ke gidan nan ya fito!!”. Ya faɗa a kausashe yana dukan langa-langan da aka zagaye saitin inda yake tsaye matsayin kitchen ɗin girkinsu.           Cikin takaici da haushi aka bankaɗe labulen ɗakin tsakkiya, “Kai ko malam ka dinga sassauta ma zuciyarka mana dan ALLAH!, da wannan farar magriban da kowa ke ƙoƙarin kai abincin buɗa baki bakinsa maimakon a ganka bayan liman kana shirin gaida UBANGIJI sai ka lalace da neman masifa da tijarar hana iyalanka su susha ruwa cikin salama kamar yanda ka hana kanka?”.          Fici-fici yay da ido yana duban ta cikin ɓacin rai. Ya tattaro duka takaicinsa da damuwa zuwa cikin baki. Nunata yay da ɗan yatsa yana karkaɗa hannu cikin gargaɗi. “Larai ina rabaki da tararmun numfashi idan ina magana amma baƙya kiyayata. Na rantse miki da ALLAH idan ban sauke dukanin abinda na kwaso bisa kanki ba kice ba sunana DAUDA jikam mai ɗan-wake ba.”      Baki ta taɓe da sakin labulen, sai dai bakinta bai mutuba. Da ga cikin ɗakin take faɗin, “Can kaji da fitinarka ba'a kaina ba. Baka sauke haƙƙin bani abinda zanci a cikin wata mai falala ba bazaka sauken gangar ɗan bazakuɗa ba. Kai da ka kwaso abarka can ta ƙare maka ba Larai ba.”          Duk da ya jiyota sai bai tanka ba, ya cigaba da ƙwala shelar kiran kowa yazo gabansa. Shiru babu wanda yay tari tamkar kowa ya mutu a gidan. Wani ƙududun takaicin baƙin ciki daya taso masa daga tsakkiyar zuciya ya jawo da ƙyar zuwa maƙoshi ya fesar ta baki.         “Eh lallai ta tabbata an gama maidani ɗan iskan ƙasan gada, yo banda ana ɗaukata girman fadar karuwai harni dake amsa sunan maigida a gidan nan zanzo ina magana ku barni ina ɓaɓatu ga ƙwalon shege haihuwar tasha ko?..”         “Kayi haƙuri malam mudai salla muke wlhy, suma kuma nasan.....”       Wuff Larai tayo waje tana gyara zaninta dake neman ɓallewa saboda tsabar sauri, cikin harziƙowa ta tare numfashin baba Nafi mai maganar cikin sanyi da rashin son hayaniyarta “To annamimatu kinsan me? To muma sallar muke sai a maida sherin da ake son ƙulla mana cikin ciki ko?”.         “ALLAH sarki Larai nima ai abinda zance masa kenan bawai wani abu daban ba”. Baba Nafi ta sake faɗa a sanyaye.     Baki larai ta taɓe da juya ƙeya ta tura kallabinta disko gaban goshi, daddagaggiyar ƙeyarta ta bayyana. Murmushi kawai Baba Nafi tai da girgiza kanta ta ɗauke idonta gareta.       Duk abinda suke yana tsaye sai faman kumbura yake da harar ɗakin ƙarshe da ke jerin nasu baba Nafin. Sai dai baice uffan ba. Kusan mintuna biyar aka ɗaga labulen ɗakin aka fito. Mace ce ƙyaƙyƙyawa da bazata gaza shekaru talatin da biyar ba zuwa da bakwai. Daka ganta kaga ƴar duniya bugun farko. Sheƙeƙe ta dubesa shi da matan nasa ta watsar tana taunar chewing gum tamkar ba azumi aka kai ba yanzun nan.           “Wai Lafiya kaketa faman shela da farar magriba ko ruwa bamu kai bakinmu ba? Haba yadai kamata asan da da yanzu akwai banbanci, dan da kana juyamune muna haƙuri da tujaranka saboda kanada uwar kuɗinka a ƙugu, amma yanzu baka barinmu da cikinmu da hidimar ƴaƴanmu ka kuma haɗa mana da tijara da gadara *BAƘAR INUWA......”*        “Asabe! yanzu nan nine baƙar inuwar?”.        “Na tsakkiyar jeji ma kuwa, har gwara *RANA DA KAI”.*        Wata shegen dariya Larai ta bushe da shi, ta callara guɗa tana duban Asabe. “Kina birgeni amarya, idan mu latsamu a tauna baida wahala ke ai kin wuce kanwar lasa”.        Baki Asabe ta taɓe ta ɗauke kanta gefe. Wani irin ƙududun baƙin ciki ya sake kume Malam Dauda. Ya nisa tamkar bajimin sa dake a ganiyar tozon girma yana ballama Asabe ƙarfen ƙafarsa harara. Shikam ai auren bariki bai masa rana ba. Fuska ya sake tsukewa yana kai hannu ya kaɗo mutsiyar tuƙin tuwonsu dake rataye jikin kwanon kitchen ɗin.       “Matsalar mutum ce wannan kuma. Ina son naji wane shege ne tambaɗaɗɗe yaje wajen Jabiru mai shago ya amso lemon kwalba da cin-cin ɗin da matarsa keyi yace injini?”.       Kallon-kallo Nafi da Larai suka shigayi, sai dai komai babu wadda tace tunda sunsan shima yasan wadda zata iya wannan aika-aikar ai. Kuma shine ya bata wannan dama ɗin tun tana amarya, gashi yanzu tsahon shekaru goma sha bakwai har ƴan matanta na yawo galla-galla a gidan harsu huɗu komai ya gagara canjawa......        “Wai ba magana nake ba ne? Ko sai na maida ƙasan gidan nan zuwa sama ne!!?”.      Malam Dauda ya faɗa a matuƙar tsawace tsabar hasalar da zuciyarsa ke sake masa na baƙin cikin bashin da aka cimasa bayan baida ko sisi dana sharesan da akai yana magana. Nanma babu wadda ta tanka sai ƙarar taunar chewing gum ɗin Asabe kawai dake tashi ɗas-ɗas... Matashiyar budurwa da zata iya kaiwa shekaru goma sha shida zuwa sha bakwai a duniya ta fito da ga ɗakin da Asabe ta fito ɗazun. Sanye take da dogon jijjab har ƙasa alamar salla tayi. Tana tsananin kamanni da Asabe tamkar tayi kaki ta ajiye. Cikin ladabi da nutsuwa takai duƙe tana faɗin “Abbanmu barka da dawowa? Ansha ruwa lafiya?”.         “A gidan ubanwa nasha ruwan? ke kuma zaki sake ɓatan rai!”.       Ƙasa tai da kanta ƙwalla na ciko mata ido, dan tanada zuciya matuƙa, sai dai tana da ƙoƙarin dannewa musamman akan mahaifanta guda biyu da halinsu baida maraba da girman haihuwar ƙasan gada.       “Kayi haƙuri Abbanmu, dama zance maka nice na amso lemon a wajen jabiru”.       “Buhun bu*a'uban nan kayyasa (😨🙆🏻‍♀️🙊😆). E lallai na zama ɗan iska haihuwar ƙasan gada kuwa da gaske. To ubanwaye ya aike ki!!?”.         Yanda yay maganar a tsawace ya sata runtse idanunta da ƙarfi tana haɗe kukan dake neman taso mata. “Kayi haƙuri Abbanmu, babu wanda ya aike ni. Babu abinda zamuyi buɗa baki ne da shi shiyyasa na amso mana, nace masa kaine ka aikoni dan inba hakaba bazai bani ba”.         Sake maƙurewa yay jikin bango tamkar tsohon ƙadangaren da ciwon sanyi ya buge yake shaƙo ƙamshin mutuwa. “Ni DAUDA naga haihuwar jaraba jinin ladin ƙasan gada. Niko wai yaushe lalacewata takai har hakane a gidan nan ne wai? K dan uban uwarki har ni zaki laƙawa sheri ina fama da ƙishirwar azumi na? To wlhy ki rubuta ki ajiye sai kinyi nadamar hakan daga ke har uwar taki, dan nasan itace ta aike kin ta noƙe......”        “Kai Dauda sauraramin. To kodai dama dani ɗin kake bada itan ba da ka haifa? To wlhy ahir ɗinka wahainiyarka ta kiyayi ramata, inba hakaba kaima kasan na fika tsiya da tujara. Ka buga ƙafa kamar na karen mafarauta ka barmu cikin yunwa ga ruwa za'a sha saboda kafi kowa iya babbaku da tujara dan kawai an anso abin nera dubu guda injika shine zakazo tsakar gida gaban magauta da ƴan bani na iya kana zazzage min. To wlhy ina dai-dai da kai”.       “Tsssss!!!!” Kakeji wani irin gigitaccen mari mai ƙara da alamar zaiyi ɗan karen zafi ya sauka bisa kumatun budurwar nan dake tsugunne ranta a matuƙar jagule, ta amshi laifin ne dama dan gudun karsu raba halin da suka saba a gaban kishiyoyin mahaifiyar tasu. Amma sai gashi dabarar tata batai ba. Ta dafe kuncin jikinta na rawa. “Wannan marin na hanani zaman buɗa baki wajen Jabirunne da kikayi ke kuma. Saura na ƙaryar da kikaimun itama. Ke kuma Asabe yanzu banda lokacin mai lokacinki, amma ina nan tafe kanki..” ya ƙare maganar yana nuna Asaben.       Caraf Asabe tasha gabansa tana mazurai. “Wlhy ka sake taɓamin yarinya sai na rama mata. Kai barfa ganin uwa ban son ta, son kayana nake ras, idan kuma kaji ƙarya sake taɓata dai-dai nake da kai, danni a yanzu nake da naka lokacin. Banda kai dai kana cikin mazan da sai an tsoma kansu a wuta an ɗauraye musu zunibi ka fita baka ko bamu geron kunu ba dan mun samawa kammu mafita kazo har kana tara jijiyar wuya. To bara kaji ni ba matanka bane daka maida sakarkaru, idan kaji ƙarya kuma sake gwada bugunta ka gani, kaima kasan wacece Asabe autar hajiyar birni shalelen bahago dan mai.......”      Sai kuma taƙi ƙarasawa ta balla masa harara, ganin ya juya fuuuu zai sake ficewa. Taja tsaki da faɗin, “Da ka tsaya mana kaji ko zaka iya latsawa ka kwana lafiya ɗan gidan abun kwari mai yawo da tsinuwar uwa bisa kai”.         Wani irin kuka budurwar nan da har yau ke duƙe ta fashe da shi. Cikin masifa Asabe ta juyo kanta takai mata shiru dan tasan minene dalilin kuka. “Dan ubanki tashi anan kona huce kaf haushinsa a kanki mara mutunci. Ko dan dai nice jinin asara sai na zauna yana cin zarafina gaban kishiyoyi na masa shiru saboda ga jikar ta-salla wadda ta haɗiyi ƙur'ani dan haƙuri. K nifa bar ganina haka zan iya kakkaɓar daku nai gaba dama tausayinku ne yasa nake zaune a wannan gidan da tsiya taima katutu abincima sai anyi kwarakarsa a maƙwafta dan lalacewa”............✍️        *Tofa jama'a bana ina mukazo haka? Ina alƙalamin namu ya kwasomu ya kawo😹😹?.* _A cikakken Littafin BAƘAR INUWA kawai zamu samu wannan amsoshin. Naira ɗari uku me kacal, tare da duk zafafa biyar naira dubu ɗaya ne kacal. Karku bari ayi babu ku. Dan bakuga komai ba. Yanzu aka fara sharar filin wasan. Cakwakiyar sai wasan ya kankama😉. Dan duk wanda akayi babu shi ALLAH yayi missing🥺._ Taku _Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ___________________________ *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 *_TEAM ZAFAFABIYAR_* ________________________ *_BAƘAR INUWA..._* _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [5/18, 8:06 PM] NANA: *_Typing📲_* *_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_* _{Gara rana dake}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _“Kamar yanda na faɗa tun farko labarin, Littafin BAƘAR INUWA ƙirƙiraren labari ne, dan haka duk wani sunan gari da zai iya zuwa cikin labarin shima ƙirƙirarsa akayi, komai ma da zai iya shigowa cikin labarin ƙirƙirarsa akayi. Baida alaƙa da wata ƙasa ko wasu mutane. Koda kuwa kaji abinda ya shafeka ko yay kamanceceniya da kai to ka ɗauka kamarce kawai yayi bawai yana da alaƙa da kai bane ba. Dan Bilyn Abdull bata sanki/ka ba balle ta dasa alkalaminta akan ka. Rubutu ne kawai nayi dan nishaɗi, faɗakarwa, ilimantarwa, harma wani abun zai iya zuwa muku da ban haushi saboda wannan karon ma a haka alƙalamin nata yazo.😅🙏🏻_ ________________ *_Episode 2_* *_ƘASAR NAYA_* .........*_(DALLO STATE): HUTAWA L.G.A._* Da gudu budurwar ta miƙe ta shige ɗaki tana cigaba da kuka, ganin a yanda ta shigo ta wuce tana kuka, ƴammata biyu da za'a iya kira tagwaye kuma yayunta suka kwashe da dariya suna faman taɓe baki da ɗaga kwalbar lemonsu suna ɗaɗɗaka hankali kwance.       Sai kuma suka maida dubansu akan Asabe data shigo tana cigaba da zazzaga ruwan tujara.       “Kina wuta momyn mu!!👍🏼”. Ƴammatan suka faɗa suna mata jinjina da kwashewa da dariya a karo na biyu. Zama tai kusa da su taja kwalbar lemo guda tasa haƙori ta ɓalle murfin tana huci. Batare data cema ƴammatan komaiba ta ɗaga tasa a baki, kamar ƙiftawar ido sai gashi ta zuƙi kusan rabi sannan ta dire tana sauke ajiyar zuciya.        Wadda tafi hasken sosai dake kallon kwalbar lemon ta ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Mommy sunan wannan shan lemon naki shan huce takaici”.      Tsaki tayi tana gyara zama da ɗaukar tsokar nama dake gabansu ta danna a bakinta. “Yo wannan uban naku inba shan huce takaicin kakema ni'imar da ALLAH yay maka ba ai tuni yake tsotse maka ruwan jiki, ga waccan mara mutuncin dake abu uwa ba jinina ba.”         “Yo Mommy bayan kamanin da take dake ai sai muce muma  ko'an canja miki ita ne a asibiti? Muda yakamata muyo kamanin naki hegiyar mai taurin kan tsiya da kicifi duk an haɗa ita an bata.”        Duk abinda suke budurwar nan na jiyosu daga uwar ɗaka. Dan haka ta sake fashewa da kuka zuciyarta na mata ƙuna da raɗaɗin halin iyayen nata da ƴan uwanta. Tun tana ƴar ƙaramarta takejin ana zagi da la'antar halin mahaifanta a cikin layinsu, har gashi yau tsahon shekara goma sha bakwai bataji komai ya canjaba sai ma abinda ya ƙaru a dalilin ƴan uwanta guda biyu da kullum cikin janyo masu wata sabuwar maganar suke. Duk da dai itama ta fara rashin ji mai kama da nasu ALLAH ya tarota ta nutsu sanadin malamin islamiyarsu sayyadi Abubakar.             Hannu tasa ta share hawayenta da gyara kwanciyarta zuwa rufda ciki, duk da yunwa dake cinta saboda azumin data kai hakan bai dameta ba, ta lumshe ƙyawawan idanunta data gada wajen mahaifiyarsu Asabe a hankali Murmushi na suɓuce mata mai haɗe da hawayen tausayin kanta na rasa Abubakar. Tabbas zuwa yanzu ta yarda ta rasashi, ya tafi har abada bazai sake dawowa gareta ba kamar yanda iyayensa suka faɗa. Wannan ciwone a rayuwarta mafi muni da har abada bata tunanin warkewarsa, dan ya zama gyambo a ƙirjinta. A tsaye take da sunanta, amma a zuciya ta jima da mutuwa tun sanda iyayen abubakar suka saka ya fita a rayuwata. “Ya ALLAH ka ɗauka raina inhar zaifi zama alkairi a gareni”. Ta faɗa cikin kuka mai ban tausayi da tsum rai.                  Sunanta shine *_AMINATU_* sai dai ana kirana da *_RAUDHA_* sakamakon sunan kakarta da taci wadda ta haifi mahaifinta. Kamar yanda kukaji a bakin mahaifiyarta sunan mahaifinsu DAUDA, sai dai ana kiransa ɗan-azumi. Tun a ƙuruciyar mahaifinsu mutum ne marajin magana. Al'amarin nasa ya sake turewa a lokacin daya fara bin wani ɗan anguwarsu driver matsayin karen mota. Kamar yanda kakarsu ta taɓa basu labari tarbiyyar Abbansu da rayuwarsa ta sake gurɓacewa a dalin wannan bin mota, dan bai rufa shekara ba a hanun uban gidansa sai shima ga tashi motar. Tun yana jan ƙaramar mota harya koma babba irin ta company ɗin nan da ake ɗaukar kaya trailer. Fara jan motar trailer yasa albarka a hanunsa, dan babu wani tazara da hakan kuɗi suka fara zauna masa. Da ƙyar ya yarda ya auri matarsa ta farko Nafisa, wadda ɗiyar ƴar uwace ga kakarsu. Nafisa tanada matuƙar haƙuri, hakan yasa bata taɓa kai karan ɗan-azumi ba a duk gallazawa rayuwarta da yakeyi. Basu rufa shekara da aure ba ya auro sabuwar amarya mai suna Larai. Larai fitinanniyar mace ce mai kauɗi da rashin barin kota kwana. Yanda ta hana Nafi zaman lafiya haka ta hana Mal. Ɗan-azumi. Mahaifiyarsa tayi-tayi ya saketa yaƙi. Babu jimawa da auren Larai Nafi ta haihu, itama Laran bata cika shekara ba a gidan ta haihu. Zamansu ya cigaba da kasancewa babu wani daɗi, yayinda Mla. Ɗan-azumi ya cigaba da sake kutsa kai a yawon tazubar. Dan kuwa a kaso biyu bisa ukun kuɗin da yake samu suna tafiyane ga neman mata da ashararancinsa. Sune manyan ƴan duniyar duk wani gari na baɗala da ire-iren gurare na ashararanci da akasan direbobi na kakkaɓe dukiyarsu a wancan zamanin.      Nafi ce kawai ke damuwa da halin banza na maigidan nasu, Larai ko ko'a kwalar rigarta tunda akwai kuɗi, dan ita kam dama sune matsalar rayuwarta tunda itama acan ya kwasota a tashar ƴan tazubar ɗin. Suna da haihuwa hurhuɗu Nafi da cikin na biyar Ɗan-azumi ya sake sabon aure daga birinin Loss. Ba kowa ya auroba kuwa sai Asabe ɗiyar *Ɗahare (Hajiyar birni)* mai tuwo-tuwo a ƙarƙashin gada.        Ɗahare mace ce mara mutunci da duk wani shege daka sani ɗan yankin nan dake zaman tazubar a Loss ya san da zamanta. Asalinta a ƙasar saudia take tana TIKARI tsahon shekaru, a wani yaya da akayo alƙawarin ALLAH ya cika aka yayota zuwa ƙasar Ghana. Kasancewarta shaharriya acan ɗin ma yasata ko NAYA bata dawo ba ta sake komawa. Dan kuwa yaranta nacan su huɗu wanda ta haifa da wasu larabawa biyu, sai dai dukansu aure tai da su. Na farko rasuwa yay ya barta da yara biyu mata *Samiha da Hannah*, na biyu kuwa rabuwa sukai saboda Ɗahare ta wuce dukan tunanin mai tunani. Kwasotan ma da akai shine yay shunenta dan yana so ya sace yaransa dake hanunta su biyu. Sai dai kuma ta koma domin tanada hanya sosai. Komawar Ɗahare da biyu ne. Na farko da ƙudirin ɗaiɗaita rayuwar balaraben nan ne uban ƴaƴanta guda biyu, *Halima da Nasiba (Asabe)*. Na biyu ƙudirin rabo ƴaƴanta biyu daga hanunsa ne, dan labari yazo mata tana barin ƙasar yana zuwa ya kwashesu yabar wanda ta haifa da mijinta na farko. Kamar yanda ta tsara kuwa hakance ta kasance, dan kuwa dai duk da balaraben nan bawani mai shaharren arziƙi bane, dan kuwa baƙauyene ma. Sai dai yana da arziƙin dabbobi matuƙa na kiwo dana tatsar madara. Duk irin makircin da Ɗahare ta ƙware sai da tabi wajen ganin ta rabashi da wannan dukiyar, jin ana bincikenta a kama yasata tattaro duka ƴaƴanta huɗu ta baro saudia bisa taimakon wasu mutanenmu dake can masu ɗaure musu ƙugu. Koda ta dawo gida kuma babu inda ta yada zango sai tsakkiyar birnin jihar Loss. Inda ta fara tuwo-tuwo yaranta huɗu ƴammata zagaɗa-zagaɗa na taimaka mata.          Game da ƴaƴan nata tamkar kumbo kamar kafinta ne. Dan kuwa a kaf halayyarta babu wacce suka bari musamman ma Asabe mafi ƙyawun fuska da ƙyan sura a cikinsu. Dan kuwa ƙyaƙyƙyawar balarabiyace da kallo guda bai isar mai dubanta. Dan-danan alhazan birni suka fara wawarsu da sheɗanci, dan kuwa inma kace da aure kazo garesu to tabbas kuwa Ɗahare da sunanta ya koma Hajiyar birni ba daga maka kafa zatai ba. Zatai maka wankin babban bargo tace bata gama more wahalarta ba za'a tura mata ƴa cikin ɗaki, sam bata yarda ba.        Ko'a jikin ƴaƴan, dan suma basu buƙatar auren sai harkar neman kuɗin kawai, sai dai banda Asabe. Dan duk kauɗi da rashin mutuncin Asabe ita dai tafi buƙatar aure sama da rayuwar barikin. Bawai batayi bane, a'a bata cika sakin jiki tayi ɗin bane tamkar wata karya. A wannan halin ALLAH ya haɗata da Mal. Dauda ɗan-azumi, wanda yake tsaka da tashen kuɗi. Gashi shima masha ALLAH ƙyaƙyƙyawan bakatsine bafulatani. Dandanan ya fara sakar mata kuɗi na hauka, tare da zazzafar soyayya dan kwashi dai tunda ya ɗana sau ɗaya yaji bazai iya haƙuri yabarta ba sai ya aureta. Duk wani shigi da fici irin na ƴan bariki kwararru ɗan-azumi yayi ga malamsa na masa aiki, cikin ƙanƙanin lokaci ya rikita zuciyar Asabe tace inba shiba sai rijiya mai gaba dubu. Hankalin uwarta ya matuƙar tashi dan tafi kallon sa'arta jikin Asabe fiye da sausan ƴaƴanta saboda ƙyawu da ALLAH ya bata na larabawan asali da ko'a cikin ƙasar saudiyar abin kallo ce. Ganin Hajiyar birni zata bashi matsala itama ya rufe mata baki ruf. Babu ɓata lokaci aka shiga hidimar bikin daya bama kowa mamaki.       An ɗaura auren Asabe da Dauda, aka ɗakko amarya zuwa garin hutawa dake a jihar Ɗillo inda Dauda ke zaune da iyalansa. Ƙyawun Asabe yasa ake layin zuwa ganinta har wasu na faɗin ɗan-azumi ya auro aljana wadda zatai maganin sheɗancinsa. A zahiri ba aljanar bace, amma bakin mutane kam ya bisa dan Asabe ta zame masa *BAƘAR INUWAR..* daya gwammaci aljanar ya aura. Asabe ta take Larai rashin mutunci ta shanye. Dan ita ko kusa ko alama bata shakka ko kunyar tsige Dauda tas a bainar nasi ko gaban ƴaƴansa balle uwarsa. Inhar zai faɗa mata cuta saita mayar masa da mutuwa koda zata kaisu da dambe a tsakar anguwane. A haka ta samu ciki, inda ALLAH ya azurtata da haihuwar ƴaƴanta mata ƴan biyu masu tsananin kamanni da DAUDA. dan ko kaɗan basu biyo Asabe ba sai dai ace ko na jini dole ka gani a fisge. Ko kaɗan bata damuba, dan kuwa ƴaƴan soyayya ma take kiran ƴan biyun nata mata da sukaci sunan Faɗima da Fatisa. Bayan haihuwar su Fatisa ko wata uku bataiba ALLAH ya sake bata wani cikin, wanda shima ta sulluɓo ƴarta mace mai tsananin kamanni da ita a wannan karon. Dan kuwa ƴar nan duk da jinjirace duk wanda ya kalleta sai ya sake duba. Dan ta wani fannin za'ace ta hado ƙyawune na uwa da uba. Saboda ta ɗakko ɗan duhun fatar Dauda da hasken mahaifiyarta. Idan ka kalleta kai tsaye zaka kirata half cast kawai. Itako taci suna *Aminatu* asalin sunan inna kenan mahaifiyar dan-azumi. Sai dai kuma Asabe tace ana ce mata *Raudah* dan duk kishiyar data faɗar mata sunan uwar miji a gidan ranar za'aga ƙarshen bala'i da jidali. Bayan haihuwar Rauda Asabe ta sake haihuwar mace itama mai suna Yasmin. Itama dai kamanni biyu ta ɗakko na Asabe da Dauda. Sai dai itama baƙace sosai ba kamar Rauda ba.           Basai an faɗa makaba, dan kuwa batun tarbiyyar babu ita ga ƴaƴan Asabe a gidan, tasu ta fita daban data saura. (Ƴaƴanmu kan fara koyon ilimine daga ɗabi'unmu iyaye, dan haka sai mu kula dan ALLAH kodan gaba da zasu kai girma su gallabemu). Sam ƴaƴan Asabe ƴaƴane na rashin ƙwaɓo a gidan, duk taɓararsu babu ubanda ya isa nuna musu yatsa har a wajen Dauda. Dan har gori yakema sauran matansa akan basu taɓa haifa masa ƙyawawan yara ba balle mai kama da shi, dan su kam ƴaƴansu tamkar haɗin baki duk kamanninsu suka kwaso. Ko aike babu wanda ya isa aiken ƴaƴan Asabe sai ita, ita ɗin ma sai sun gadama suke zuwa. Hakan kuma bazaisa ta nuna ta damu ba. Hatta da Raudha ma haka ta taso a cikin nasu sai a hankali, dan itamadai halin ƴan uwan natane tsaf sai dai ma ace ta ɗarasu da shegen miskilanci da baƙar zuciyar tsiya da jan magana, dan kullum cikin faɗa take da yara harma da manyan. Sai dai kuma tanada ɗan sauƙin kai ta wani fannin kaɗan idan taso, ba komai ya jawo rashin jin Raudha fin na sauran ƴaƴan Asabe ba sai gatan da Mal ɗan-azumi ke mata a gidan fiye da kowa dan tana da sunan mahaifiyarsa.........✍️ 😉karfa ku bari ayi babu ku, dan ba'a far komai ba har yanzun😎🤙🏻. *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form din kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [5/20, 8:44 PM] NANA: *_Typing📲_* *_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_* _{Gara rana dake}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _Irin wannan katoɓara haka🤭, inda nasa *(Bakatsinen bafulatani episode 2)* an samu mishkilane ba haka bane. Dan babu sunan wannan jihar a ƙasar NAYA. ku ɗauka matsayin mistake Please🙏🏻😹_. ________________ *_Episode 3_* ..........Shigarsu secondary school ya ɗan fara canja wasu da ga halayen Raudha, taɗan fara rage kwaikwayon halaye irin na mahaifiyarsu. Bata da yawan magana, bakuma tason taga iyayen nata na faɗa tamkar karnuka a tsakar anguwa kowa na kallonsu yana ALLAH wadai. Hakan kuma ya farune sakamakon ƙulluwar soyayya tsakaninta da malamin islamiyyarsu sayyadi Abubakar.  Tun tana zama taita kuka idan suna raba hali harta koma tana nuna musu fushinta. A lokacin da suke ss1 farkon shigarsu wani faɗa da iyayen nata suka tafka har takaisu ga police station sakamakon yanzu Abbansu talauci ya masa katutu, takai ma nauyin gidan iyayen nasu mata ne ke ɗauka. Dan tunda kamfani ya kamashi akan satar kayan da yake jigila suka kafa masa kahon zuƙa, da yaga asirinsa zai tonu asabe ta zugeshi ya kwance tayoyin motar ya saida, motar takai shekara a ajiye, sai da komai ya lafa ya saidama ƴan gwangwan ita ya kawo kuɗin gida suka hau kai shi da Asabe da ƴaƴanta suka dinga cin daɗi sai ɗan abinda ake samma su baba nafi wataran. Acan kamfani kuma akace ya mutu. Ko shekara kuɗin basu ƙullaba komai ya ƙare, dan kuwa dai a ashararancin ɗan-azumi babu abinda ya canja na neman mata da busa sigari da caca. Tunda kuɗi suka ƙare zaman lafiya tsakanin Asabe da Dauda ya ƙaura. Kullum sune faɗa kamar kaji, taje ta nafko masa bashi dolensa ya biya ko bai ƙaunar ALLAH, idan yaƙi biya su tumu sama dan bala'i su dire bisa ƙasa. Dan kullum zancenta shine ya saketa bata halaka rayuwarta da ƙuruciyarta a ƙarƙashin runfar talauci. Shiko yace bata isaba tunda ta shigo ta shigo kenan. A randa taje ta cicciɓo masa wani bahagon bashi da har akazo aka saka wani filinsa kasuwa da yake ta burin gina mata aljannar duniya ta koma tun tana amarya ALLAH baiyiba ya sakasu yin faɗa na tashin hankali harda jima juna ciwo, shine aka kwashesu zuwa ofishin ƴan sanda daya saka Raudha tsananin baƙin ciki. musamman akan habaici da zagin da akema iyayen nasu akan sunyi dai-dai da juna kowa ɗan barikine ai, tunda dama a zauren dandi suka haɗu, wama ya sani koba zaman auren suke ba.      Wannan ƙananun magana sun matuƙar ƙona ran Raudha harta kaita da kasa kuka saboda bushewar zuciya. Kowa baije yay beilingn su ba, sai ita taje duk da ƙarancin shekarunta. Ƙyawunta da ganin ƙarancin shekarunta yasa d.p.o ɗin sonyin amfani da mutuncinta sannan ya sakar mata iyayenta. Da farko taso tai masa zagin ƙare dangi, sai kuma ta fasa saboda wani abu daya zo mata rai. A take ta amince masa akan ya sakar mata iyayen bayan kwanaki biyu zata kawo masa kanta. A tunaninsa bata da wayo, musamman da yay dubi da halin iyayenta na ƴan bariki. Kai tsaye ya sake su, tana ganin an fiddosu tai wucewarta gida ta barsu duk da magana da suka dinga mata. Ta rigasu zuwa gidan, dan haka kowa bai san itane taje ta fiddosu ba. Dama kuma tun a hanya suka taho suna hirarsu ta arziƙi tamkar basune aka amso hanun hukuma ba saboda tazubar ɗinsu.        Koda suka dawo gidanma sun kaɗa sun raya Raudha taƙi tanka musu, taƙi cin abinci ta kuma daina shiga harkar kowa a gidan. Tun suna ɗaukar al'amarin nata wasa harya fara cin ƙarfinsu, da ga ƙarshe dai suka haɗa baki da wani malamin islamiyyar su Raudha ɗin da suke yawan jin sunansa a bakinta da ganin tana tsananin girmamashi dan yana ɗaya daga cikin wanda suka gyara tarbiyyarta dake a bauɗe tunda farko sannan Raudha ta sakko harta nema gafarar iyayen nata (Sayyadi Abubakar). Dan Ya sayyadi Abubakar ya sanar mata su iyaye ba'a fushi dasu, ko wanne irin hali garesu lallaɓasu ake da ƙyaƙyƙyawan kalami. koda anji ciwo akan kuskurensu shanyewa akeyi ayi haƙuri. Saɓawa ALLAH ne kawai ba'a yarda kamusu biyayya akansa ba wannan haramunne.       Raudha taji wannan nasiha hartazo ta bama iyayenta haƙuri. Daga lokacin kuma ta dinga taka tsantsan da harshenta a kansu da fushinta. Idan ma taga abu zai basu saɓani ta gwammace ta amshi laifin ita koda zasu mata hukunci ne. Idan batasan tushen rikicin nasu ba kuma zatabi duk hanyar data dace ta sasantasu cikin hikima. Sai dai kuma kuka ya zame mata tamkar abokin rayuwa, dan sam bata ƙaunar halin mahaifan nata guda biyu ko kaɗan.        A yanzu haka Raudha da sauran ƴan uwanta na sauran ƴaƴan ɗakunan biyu sa'anninta suna akan zana jarabawar gama secondary school ne. A ƙalla shekarunsu Fatisa goma sha takwas, Raudha kuwa sha bakwai ita da Iklima da Binta. Kasancewar babu wani batun Noziri a karatun nasu yasa suka kammala da ƙarancin shekaru, musamman ma ita dasu Binta duk sun girme mata.           Halin talauci da fataran da suke ciki ga shegen son kuɗi na Asabe ya saka ƴaƴanta su Fatisa fara kaucewa hanya wajen biyema samari. Duk da kuɗin da yaran ke shigowa dasu na ban mamaki da kayan kwalliya basu sana'ar ko asi bai taɓa saka Asabe nuna damuwa ba balle tuhumarsu. Sai dai ma ta baje suci su sha mai daɗi tana kiransu masu farin jini. Tabbas *ZINA* tamkar sharri take, dan ƴar aikece komin daren daɗewa saita dawo cikin zuri'arka. Hakanne ya faru akan su Fatisa dama wasu a ƴaƴan mal ɗan azumi na sauran ɗakunan, dan kuwa cikin ƙanƙanin lokaci rayuwarsu ta ɗakko hanyar lalacewa Dauda naji na gani babu halin magana, duk da abun na ƙona masa rai da soya zuciyarsa. Dan ko yayi magana Asabe ta taresa da masifar cewar yanama ƴaƴanta sheri saboda shima aikinsane zina. Maƙiya masu baƙin ciki da hassada wa farin jinin ƴaƴanta na ɓoyewa bayan ƙofa suna musu dariya. Sai dai abinda Asabe bata sani ba na ƴaƴan ɗakintane ya fito, amma itama Larai nada Kangararru irin su Fatisa har su uku. Wani lokacin duk da gogewar ɗan-azumi a bariki, Asabe ta fisa bala'i, shiyyasa idan taja yaja sai ya sakar mata dan zuwa yanzu girma yaɗan fara kamashi, ga ciwo dake cinsa a tsaye na hawan jini wanda ko ba'a faɗaba asabe ce silarsa, gefe ɗaya taba ta gama cinye masa naman jiki sai ƙashi da jijiya da fata.      Halayyar su Fatisa na matuƙar ƙona ran Raudha, sai dai babu yanda zatayi dan ko tayi nasihar basaji. Ita kanta samarin na yawan kawoma rayuwarta hari, musamman daya kasance ta fisu ƙyau nesa ba kusa ba. Hankalinta yakan tashi matuƙa, shiyyasa akoda yaushe cikin suturta jikinta take da kayan mutunci harma da niƙab wani lokacin. Takan yawaita neman tsarin ALLAH daga ƙaddarar zina a gareta.          Rashin samo kuɗi da batayi yasa Asabe tsangwamarta a ɗakin fiye da kowa. Dan hatta Yasmin ta fita daraja duk da kuwa Asaben tafi son Raudha fiye da kowa acikin ƴaƴan nata. Sai dai lallaɓa da lallashin da take mata akan ta dinga kula samarin sai tafi su Fatisa samo kuɗi, amma Raudhan na bijirewa yasa ta ɗauka karan tsana ta ɗaura mata ita da su Fatiman. Kullum cikin caccakarta suke da magana mara daɗi. Da yake miskilace kuma bauɗaɗɗiya ko kulasu batayi ma balle ta nuna ta damu, fatanta kawai tai aurenta tana gama secondary school da ya-sayyadinta Abubakar da kowa yasan suna soyayya zuwa yanzun.                   A ɓangaren sayyadi Abubakar shima babban burinsa mallakar Raudha matsayin mata. Dan haka suna fara exam ya sanarma iyayensa akai kuɗi. Sunyi farin ciki da farko dan basusan ƴar waye ba a Hutawa. Dan haka suka tambayesa acewar mahaifinsa sai sun fara bincike tukunna. Abubakar ya shiga fargaba, amma sanin Raudha yarinyar ƙwaraice mai kamun kai, kuma da ita zai zauna yasashi jin ƙwarin gwiwa.        Bayan kwana biyu mahaifinsa ya kirasa shida ƙanensa sukai masa wankin babban bargo, tare da gargaɗinsa ya fita sabgar Raudha bata fito cikin gidan arziƙi da mutunci ba, su bazasu haɗa zuri'a da ɗan-azumi ba. Idan ma ƙyawun yarinyar ke ɗiɓarsa yaje akwai ƙyawawa da suka fita ya nemo. Idan kuma ya sake koda yima Raudha magana ne ALLAH ya isa basu yafe ba. Itama sunje har gida sun gargaɗi ubanta akan ta fita hanyarsa. Daga karshe suka hanashi cigaba da koyarwa a islamiyyar su Raudha ɗin baki ɗaya. Sukama maida rayuwarsa can cikin birinin Ɗillo wajen wani ƙanin baban nasa dake can da iyalansa.      Wannan shine sanadin raba Raudha da Sayyadi Abubakar. Tayi kuka kamar yanda shima yayi nasa. Kusan dukansu sai da suka kwanta a asibiti dan ba karamar shakuwace a tsakaninsu ba. Halin data shiga yasa ɗan-azumi da Asabe zuwa har gida sukaima iyayen sayyadi Abubakar tas. Wannan ya ƙara harzukasu suka kara jin tsanar tushen Raudha da ƙyamar haɗa zuri'a da su.      Sosai wannan lalacewar aure taima Larai daɗi, dan kuwa tana ɗaya daga mutanen da suka sake lalata zancen auren, mahaifin Sayyadi Abubakar nada ɗan hali, shiyyasa tun yana zuwa wajen Raudha takeji baƙin ciki da hassadar hakan. Sai dai tabi duk wata hanyar rabasu hakan bai samu ba, sai gashi cikin sauƙi komai ya lalace. Da wannan damar tai amfani wajen zuwa har gida ta sakema Asabe da ɗan-azumi batanci fiye da wanda iyayen Sayyadi Abubakar suka jiyo ga wasu mutanen. Sai ka rantse ɗan-azumin ba mijinta bane.      Raudha ta ɗanɗana azabar rashin Ya sayyadi Abubakar har batasan mi take rubutawa a jarabawa ba har suka kammala. Bayan kammalawar tasu ta sake dawowa gida zaman sabuwar jiyya, a dalilin hakan ciwon Asthma ɗinta da bai cika karfi ba ya sake ƙarfi har takai yana yawaita tashi yanzu. Gefe kuma ga azababben ciwon mara idan zatai period har suma take wani lokacin. Dama dalilin ciwon marar natane sayyadi Abubakar ya yanke shawarar data kammala secondary school suyi aure kawai, sai ta cigaba da karatunta a gidansa. Sanda suna tare saboda tsabar kiyaye yanayin nata da wata ya kama zai kawo mata magunguna da allura ta ajiye, da abin ya fara mata za'a nemo wani yaron makwafcinsu dake da kyamis yay mata allurar. Ta hakane take samun sassauci sai abun yazo da sauƙi.. _Wannan kenan😚👌🏼._ *_Mun dawo labari_*🏃 Kiran sallar isha'i ne ya sata miƙewa da ga kwanciyar kukan da tayi, ta fito daga ɗakin baki ɗaya batare data ko kalli inda su Fatisa ke zaune suna hira da shewa ba su da Mommynsu. Sai ma Yasmin ce data miƙe zumbur tana ƙwala mata kira da faɗin, “Aunty R zanje”. Dan tasan massallaci zataje sallar asham. Bata tanka mata ba, dan ƴan miskilancin na kusa ne, sai dai ta mata alamar tai alwala. Itama kuma ta ɗauka buta ta ƙarasa inda sukeyin duk wani hidimarsu na harkar ruwa a gidan tai alwalar sannan suka fice..........✍ *_Humm Sayyadu Abubakar Abubakar ya tafi, wa kuma zaizo? Ta ina zaizo? Yaushe zaizo AMINATU Raudha?. Dukkan amsarku na cikin BAƘAR INUWA ne, dan bazan gaji da faɗaba ba'a fara komaiba har yanzun masu karatu. Kar dai ku bari a baku labari😉⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️._* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form din kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [5/22, 11:14 PM] NANA: *_Typing📲_* *_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_* _{Gara rana dake}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ________________ *_Episode 4_* ..........Ruwa kawai tasha tunda aka kai azimin na yau na kusan ashirin da ɗaya, sai dai hakan baisa ta damu ba, duk da yunwa dake cin hanjinta dan koda asuba ma batai sahur ɗin kirki ba kasancewar tuwo sukai na sahur, itako a rayuwarta sam bata shiri da tuwo musamman miyan kuɓewa ɗanye. Sau da yawama idan taci gudawa yake sakata shi da shinkafa. Kai duk ma wani abu irinsu basu ciga damun Raudha ba. Tafi so da buƙatar abinci mai ruwa-ruwa irinsu fura, kunu, koko da sauransu. Suna fita Yasmin ta fiddo goran ruwa madaidaiciya dake ɗauke da kunu ta miƙama Raudha. “Aunty R gashi kisha”.         Cak Raudha ta dakata daga tafiyar da takeyi ta dubi Yasmin ɗin, ganin abu a leda yasata daka mata tsawa dan sam bata fatan abinda zai lalata rayuwar Yasmin ɗin itama. Cikin ruɗewa Yasmin ta fara rantsuwa. “Aunty R wlhy bani akayi, baba ce ta bani (Baba Nafi) sanda naje mata aika gidan kawu Rabi'u (Ƙanin Baba Nafi) na amso mata kunun batare da Mommy ta sani ba. Niko kinga banyi azumi ba shiyyasa na ɓoye miki shi dan karsu aunty Fatisa su gani su shanye ko Mommy”.      Ajiyar zuciya Raudha ta sauke da kamo yarinyar ta rungume a jikinta hawaye na ciko mata idanu. “I'm so sorry my little girl, bana son ki fara koyon hali irin nasu Aunty Fatisa ne shiyyasa. Dan ALLAH ki kiyaye karki bari wani ya yaudareki da abinda bamu da shi ya lalatamin rayuwarki kinji”.         “Inaha ALLAH Aunty R bazan yarda ba ai”.     Yasmin ta faɗa duk da ba komai take fahimta ba da ga gargaɗin ƴar uwar tata kai tsaye, saboda ƙarancin shekarunta. Dan Raudha ta bata kusan shekara shida a duniya, bayan haihuwarta Asabe ta jima kafin ta samu ciki, harma ta ɗauka haihuwar ta kare sai kuma ga cikin Yasmin ɗin..       Kama hanunta tai suka ƙarasa massallacin batare data amshi kunun ba, can gefe ta samu ta saka musu abin salla inda bazasu takura ba, dan sam bata ƙaunar zafi ita, sanyi ma idan yay yawa yana taɓa rayuwarta.      An gabatar da sallar isha'i da asham, bayan addu'oi da malam yayi tamkar yanda ya saba kowa yay ƙoƙarin kama gabansa. Raudha bata tashi ba, sai roban kunun da Yasmin ta ajiye a gabansu ta ɗauka ta buɗe murfin, duk da ya huce haka tasha kusan rabi ta miƙama Yasmin dake gyangyaɗin barci sauran dan tasha itama. Amma sai Yasmin ɗin tace mata ta ƙoshi. Sanin kunu bai damu Yasmin ɗin ba sosai yasa Raudha ƙarasa shanyewa sannan suka miƙe.       Sai da ta gama tattare musu kayansu sannan ta duƙa Yasmin tahau bayanta danta lura barci takeji. Yarinyar ta saki sassanyar ajiyar zuciya tamkar yanda Raudhan tayi itama. Koda suka iso gidan a tsakar gida suka iske kusan kowa a ƙofar ɗakinsa. Yaran nata hayaniyar surutu iyayen kowa na sabgar gabansa. Sannu kawai tai musu bayan sallama ta shige ta kai Yasmin ɗin ɗakin barcinsu da gaba ɗaya ƴammatan gidan kan kwana musamman idan ranar Babansu a ɗakin mamanka yake. Idan ɗakin wata yake daban zaka iya kwana a ɗakin mamanka ɗin. Fitowa tai tai ɗan uzirorinta batare data tankama kowa ba ta sake shigewa tai kwanciyarta dan su Fatisa a ƙofar gida ta barsu suna hira. *_WASHE GARI_* Raudha ta tashi da ciwon mara mai tsanani tamkar yanda takeyi duk wata. dama tun kusan jiya takejin alamarsa kaɗan-kaɗan, batai wani yunƙuri ba dan maganin da take sha ya ƙare. dama Ya-sayyadi ne ke saya mata shi kasancewar yasan lalurar tata. Idan har zatai period sai kowa ya sani. ba ƙaramar azaba take sha ba na ciwon mara dana ƙafa. Daga ƙarshe taita kwara amai. Idan ka ganta a irin wannan halin ma saika ɗauka yaron ciki ne da ita. Dan a farkon fara hakan tana jss1 secondary kowa a gidansu dama makaranta sun ɗauka ciki ne da ita, duk da lokacin batafi sa'ar Yasmin ƴar shekara goma sha ɗaya ba. Sai da aka dubata likita yace period zata fara sannan hankalin malaman ya kwanta har sukazo da ita gida akaima iyayenta bayani.       Duk murƙususun azabar da takeyi a ɗakin babu wanda ya sani, dan gidan shiru alamar yaran duk sun fice sabgogin gabansu, manyan kuma kowa barcinsa yakeyi. Sosai take cin azaba, dan tun tana kuka ma har kukan ya gagara, tsanani yay tsanani har takai Raudha da suma.         Kamar yanda ya saba shigowa gidan fagan-fagan babu ko sallama yauma haka ya shigo, dan tun fitarsa sallar asuba bai sake shigowa ba yana rumfar ƴan gulma kamar yanda ake kiran majalisarsu. Jin gidan shiru ya sashi fara ƙwala kiran Raudha, dan a rin wannan lokacin ita kaɗai zaka iya samu a gidan tana bautar gyarawa, data gama take wucewarta wajen tafsir sai sha biyu ta dawo.           Shiru babu wanda ya amsa masa, yabi gidan da kallo a harzuƙe, ko'ina kaca-kaca da kwanika da tulin tsummokaran kayansu kusufi-kusufi. Tsaki yaja yana nufar ƙofar ɗakin Asabe. “Asabe! Asabe!!” ya shiga ƙwala mata kira, dan har yanzu haushinta na jiya bai bar ransaba, musamman daya kasance yanzun nan jabiru mai shago ya sake masa maganar kuɗinsa, shine ma dalilin shigowa gidan da yay.         Cikin barci Asabe taji muryarsa bisa kai, ta miƙe a zabure tana yaye labulen daya saya falon nata matsakaici, komai babu a cikinsa sai ledar ƙasa dan duk ta siyar sun cinye kuɗin a ciki ita da ƴaƴan. “Wai wane kalar jidaline kuma haka da wannan farar safiyar? bazaka barni nai barcin dana gagarayi ba da asubahi!”.       Tsaki yaja yana turo kai cikin falon, yaci tuntuɓe da ƙafar Fatisa dake barci a gefenta itama, da sauri Asabe ta tarosa. “Gashi nan wajen gargajigarka ta masifa zakaima kanka lahani a banza, wai nikam mike faruwa ne?”.        Numfashi yaja da ƙarfi, batare daya amsa mata ba ya kai zaune a tsakar falon yana godema ALLAH a zuciyarsa da bai faɗi ba. “Asabe ina Raudha!?”.        “Raudha kuma? Wani laifin ta ƙara maka ne?”.        Kansa ya jinjina mata cikin tausasa murya tamkar bashine ya shigo da bala'i ba yace, “Laifi kam tana da shi a gareni kema kin sani, to amma abinda ya fara kaɗoni gida yasani yafe mata zan ma biya jafarun kuɗinsa insha ALLAH. Ina Alhaji Maude Dallatu uban gidan falalu mai shagon kayan ƙwalam ɗin can na bakin titi?”.       “Eh na gane!”. Asabe ta faɗa da sauri cikin ƙaguwar son jin inda zancen ya nufa. Fahimtar hakan ce ta sakashi cigaba da faɗin, “Wai shine fa ya aiko Falalu ɗin akan ya sameni ya faɗamin zaizo akan Raudha wajena.....”        “Ni bangane ina zancenka ya dosa ba wlhy ɗan-azumi, fito fili ka faɗamin kasan bana son wani kwana-kwana.”      Baki ya washe sosai cikin raɗa yace, “Inagafa cazai na bashi aurenta, idan ko haka ta kasance Asabe ai mun haye wlhy. Shiyyasa a koda yaushe bana gajiya da alfahari da ƴaƴanki ƙyawawa”.          Itama tuni fara'a ta baibaye fuskarta, nan fa suka shiga ƙus-ƙus akan batun wai kada magauta su jiyosu. Tun ma kan suji ta bakin Alhajin harsun gama yanke hukuncin tsaida ranar biki. Bisaga wannan shawara da suka tsaida cike da zumuɗi Asabe ta miƙe kiran Raudha.       Da sauri Larai dake laɓe tanajin komai ta afka ɗakinta har tana neman faɗuwa. Asabe kuwa da bata lura da itaba ta nufi ɗakin su Raudha.       Kururuwar ihun Asabe ne ya saka kowa fitowa a gidan har masu barci da Larai daketa faman kai kawo a ɗakinta ranta a dugunzume da zancen da taji.       Suna ƙoƙarin jin dalilin ihun nata suka hango Raudha a sanƙame tana girgizawa. A tsorace duk suka afka ɗakin, Baba Nafi tai dabarar ɗakko ruwa ta shafama Raudha ɗin. Sai gashi ta kawo wani nannauyan numfashi. Sai kuma ta ƙudundune jikinta tana ƙanƙame Asabe da sakin wani kuka maiban tausayi dako sautinsa baya fita saboda azabar da taci.        “Mommy zan mutu”. Kawai take iya furtawa da ƙyar tana sake ƙanƙame Asabe da itama tarasa ina zata saka kanta taji sanyi, dan sun fahimci ciwonta na marane ya motsa. Fatisa ce ta bada shawaran a kaita asibiti ko za'a iske Doctor Rufa'i abokin ya-sayyadi da wani lokacin shike kawoma Raudha magungunan da ga ya sayyadi Abubakar. Amma sai ɗan-azumi ya daka mata tsawa da faɗin, “A gidan ubanwa wani keda kuɗin asibiti anan gidan?, banda jangwaloma mutane masifa a samu ɗan libiya a jiƙa a bata tasha zai faɗa mata yanzun nan, sanin kanku ne maganin da yaron can ke saya mata Sule yasha faɗa mana tsadarsa ai. Sannan ba ko'ina ake iya samunsa ba ma a garin nan. Shima yana sayo mata ne a Ɗillo”. Fatima tai saurin cewa “Abba bafa ciwon ciki bane ba, kuma kasan kaima sai an bata maganin nan ko allura kawai take samun nutsuwa. Sai kuma last time da Doctor Rufa'in yay mata kalar sabuwar alluran nan shima da wuri ya daina mata”.      Zai fara hayayyaƙo mata itama tai saurin katsesa da faɗin, “Abba ni akaita ina da kuɗi”.        Jin haka yasa Mommy (Asabe) haɗiye maganar da take tattarowa domin fara zuba masa tujara. Amma duk da haka bawai ta barsa bane, zata dai jira taga lafiyar yarinyarta ta samu sannan ta cashe masa...........✍️ _😂Asabe ya Asabe, ɗan-azumi ya ɗan azumi. Wannan tujara da ƙauna sai ALLAH😆😹_. https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [5/22, 11:14 PM] NANA: *_Typing📲_* *_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_* _{Gara rana dake}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ________________ *_Episode 5_* ..........Bada son ran ɗan-azumi ba aka kwashi Raudha zuwa asibiti. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso, inda aka amshi Raudha dake a jigace har batasan inama kanta yake ba zuwa yanzun. Ko sisi Fatima bata da shi, tayi ƙarya ne kawai dan Abbansu ya bari a kawo Raudha asibiti. Tana ganin an amshi Raudha ɗin ta fito ta nufi ofishin Doctor Rufa'i, sai dai anyi rashin sa'a wai baya nan yamaje Ɗillo tun jiya. Dawowa tai inda Mommy da Abban ke tsaye a ƙofar ɗakin da aka shiga da Raudha ɗin. Zama tai itama tabi ayarin ƴan tagumi, a haka har doctor ɗin ya fito yana mai kwantar musu da hankali akan karsu damu komai zai dai-daita, dan zai rubuta musu wasu allurai da zasu sayo, da zaran anma Raudha ɗin inssa ALLAH zata samu nutsuwa. Cikin gamsuwa da rashin damuwa aljihunsa zaiyi tsuwwa ya miƙe yabi doctor ɗin, har yaje ya dawo mommy da Fatisa da Fatima bakinsu bai saɓa ba. Sai da ya dawo da takardar ya mikama Fatisa ɗinne ta ce, “Abba ya zaka bani kuma? Ba cayay a sayo ba?”.         Wani shegen kallo ya watsa mata ita da Fatima fuska a ƙwaɓe. “Kunci bu*a'ubaku, ƴan bu*a'uban yara da basa ko ganin mutuncina. Ni kikema magana haka kamar kina a gaban tsohon kwarto”.       Fuska Fatisa ta ƙwaɓe tana ƙunƙuni, zai sake magana Asabe ta katsesu.        “Wai nikam maganin zaku sayo a cetomin yarinya ko tazubar ɗinne ya motsa muku a bainar nasi?. Kai kullum bazaka ja girmanka ga yaran nan ba balle tauna harshenka da baiko da linzami wajen sakin magana”.         “Kar yayi linzamin mana. Banda shegantaka irin tata ba itace tace tanada kuɗi ba shine zata wani tsareni da idanu na rashin ta'ido. ai sai da nace ku bata ɗan libiya amma tace tanada kuɗi ko......”       “Ni dai ya isa da ALLAH. Ke Fatisa anshi kije ki sayo”.     “Mommy nifa wlhy banda ko sisi anan. Nace inada sune danya yarda akawota asibiti. Dan haka sai yaje ya nemo inma baida su, dansu dai likitocin nan bawai batun lamuni suka sani b.....”     Hannu yakai zai kwaɗa mata mari ta tashi ta fita a guje Fatima na take mata baya. Babu ko kunya ya rufa musu baya shima duk da kuwa tsufa ta fara kamashi, ga sigari duk ta gama cinyesa a tsayee....        “Subahanalillahi! Malam ɗan-azumi lafiya kuwa?”.          Cak yaja ya tsaya yana huci saboda jin an ambaci sunansa. Sai kuma duk ya diririce ganin Falalu mai shago tare da Alhaji Maude Dallatu, ya ɗan tura hularsa baya yana ƙaƙaro murmushi. “A'a Falalu kune anan? Ince dai lafiya ko?”.         “Ai kai ya kamata mu tambaya ko lafiya kuwa baba?”.     Cewar Alhaji Maude duk da kuwa zai iya girmar ɗan-azumin ko suyi sa'anni.             Fuska ya marairaice kamar zaiyi kuka, saboda hangen damar dake garesa ta ƙarshe da mafita kenan. “Alhaji wlhy Raudha ce babu lafiya muka kawo asibiti. Shine waccan ja'irar na bata ta sayo magani take shirin min ƙyuya irin nasu na yaran zamani”.        Fatisa tai saurin waro ido waje suna kallon juna ita da Fatima da gumtse bakunan su jin dariya nason kufce musu.      “Ai sai dai haƙuri baba. Inga takardar”.       Alhaji Maude ya sake faɗa a ladabce yana miƙa hannu ya amshi takardar hannun Abban. Kamar bazai bashi ba dai yana ɗan nannoƙewa sai kuma ya miƙa masa. Koda Alhaji Maude ya amsa bai wani tsaya dubawa ba ya kalli Falalu dake ɗauke da kaya niƙi-niƙi alamar duba wani mara lafiyan sukazo ko makamancin hakan. “Falalu ƙarasa ciki ina zuwa”.       “To ranka ya daɗe, amma daka kawo ni sai naje zai fi”. “No karka damu jeka ciki kawai zanzo yanzun”. “To a shigo lafiya”. Falalu ya faɗa cikin girmamawa yana ɗan murmushi.        “Baba ka jirani nan kaima ina zuwa”. Alhaji Maude ya sake faɗa yana tafiya da kallon mal. Ɗan-azumi. Kafinma yace masa wani abu har yayi nisa. Hannu ɗan-azumi ya ɗaga sama yana godema ALLAH daya kawo masa Alhaji Maude a lokacin daya dace, sai dai a ransa kuma ya ƙudira dolene kuɗin da duk zai biya na maganin sai Fatisa tayi kashinsu. Yana nan tsaye ko mintuna goma ba'aiba sai ga Alhaji ya dawo, da taimakon sa sukaje inda aka kwantar da Raudha ɗin. Babu ɓata lokaci doctor ya amsa dan dama su kawai yake jira.           Alhaji Maude na nane da su har kusan awa uku, dan sai da Raudha ta farfaɗo ta koma normal barci da allurar ta sakata sannan yace musu zaije ya dawo zuwa anjima. Godiya suka dinga masa kamar zasu gurfana ƙasa. Yana juya baya Asabe ta warce kuɗin daya mikama Baba tana faɗin. “Ɗan cin rabo, kaci naka zaka hau kan haƙƙina”.       Hannu yakai zai damƙota a fusace. “A gidan wane shege akace rabonki ne? Asabe anya zakiga ANNABI kuwa?”.        “Ai tare da kai zamu gagara ganinsa kwantar da hankalinka jemage maƙi jinin ƙasa sai samaniya..”       Cikin takaicinsu Fatisa tace, “Asibitine fa Mommy. Yanzu dan ALLAH idan ya dawo ya jiku kuma fa? Mudai wlhy kuna zubar mana da mutuncinmu”.       Baki Asabe ta ƙyaɓe. Batare data tanka ba ta zari dubu biyu ta miƙawa baba ta saƙe sauran a zane. Ƙin amsa yayi, sai dubanta da yakeyi cikin takaici da ɓacin rai. “Mikike nufi?”.       “Babu abinda nake Nufi sai haƙƙinka dana baka gashi nan. Tunda ALLAH kaɗai yasan abinda kaci kaima”.        Wata dariyar takaici da tafi kuka ciwo yayi ya ɗauke kansa. “Asabe kina wasa da lamarina wlhy. Ince dai nine silar haɗa auren ko? To wabilahillazi zan iya rusashi a gabanki kuma na bashi wata sai dai ki hangi arziƙin”.           Duk da taji tsoron zancen nasa dan tasan zai iya sai ta balla masa harara. Zatai magana likita daya ƙaraso ya katseta. “Baba zaku iya tafiya da ita babu damuwa”.      Gaba ɗayansu suka juya gareshi, kafinma suce wani abu Fatima da bata tanka musu ba tunda suka fara ta afka ɗakin da Raudhan take Fatisa biye da ita. Asabe ma ɗakin ta juya da niyyar shiga mal. Ɗan-azumi ya samu damar warce kuɗin data saƙe a cikin zani. A wani irin muguwar zabura ta juyo, sai dai kamar walƙiya ya ɓacema idanunta. Ranta yayi ƙololuwar ɓacin da har ma ta kasa bin bayansa balle yin magana har Fatisa da Fatima suka fito riƙe da Raudha. Yini guda harta sake ramewa, sai idanu zuru-zuru ga allurar da akai mata yasa barcin bai gama sakinta ba.       “Mommy mike damunki?”. Raudha ta faɗa a hankali idonta akan Asabe. Ƙwafa Asaben tayi tana magana cikin ɓacin rai, “Minene kuwa zai dameni idan ba ubanku ba, wanda ƙaddarar rabonku ta zama silar haɗuwata da shi. Wlhy a wannan gaɓar kuwa lallai zan shayar da Dauda zumar mamaki. Yanda yake jinsa tantiri nima tantiriyarce ta gaske, kuma zan tabbatar masa da hakan yau basai gobe ba”.         Dariya Fatima ta ɗanyi dan ita ko'a jikinta. Raudha kam hawayen da suka ciko mata idanu ne suka silalo a hankali. Hannu ta kai ta share da ɗan cije baki saboda kanta dake sara mata.           A haka suka hau mashin ko sisi babu a jikinsu. Sai da sukazo gida Asabe ta shiga ta kawoma mai napep ɗin masifa fal ranta..    Har aka sha ruwa Malam ɗan-azumi bai yarda ya dawo gidansa ba, dan yasan halin Asabe sarai. Ya tabbatar yau duk da azumin dake a bakunansu sai sun tara ƴan kallo a cikin anguwa, shi kuma baya buƙatar hakan tunda yasan shine mara gaskiya, shiyyasa ya zaɓi ƙin dawowa gidan har aka sha ruwa. Yadai samu gasashen naman kazarsa da fura mai sanyi yaci yay ƙat. Ya kuma ɗora da indomie da ƙwai da shayi wajen Bello mai shayi. Sannan ya ɗan zuƙa sigarinsa kara uku. Sai wajen sha ɗaya na dare ya lallaɓo a tunaninsa kowa yayi barci. Sai dai yayi rashin sa'ar cin karo da Asabe dake zaune dakaka tana zaman jiran shigowar tasa. Yanako shigowa tai caraf da rigarsa taci kwalarsa. Tun sunayi iya su har kowa na gidan ya farka. Dama Larai na laɓe tana kallon komai tun farko tana kwasar dariya, tunda taga Asabe zaune taƙi shigewa tasan akwai wata a ƙasa dama, balle itama akwai tsiyar data harbo, dan tun maganar da taji a ɗazun game da Alhaji Maude Dallatu mai son Raudha hankalinta bai kwanta ba, suna fita a gidan itama ta fice. Rigimace sosai ta harƙume a tsakaninsu harda doke-doke. Dan sai da maƙwafta suka shigo aka rabasu da ƙyar. Kuka sosai Raudha keyi tamkar numfashinta zai bar gangar jikinta. Dan ko leƙe bata leƙo ba dama tunda aka fara faɗan tana ɗaki kwance.          Abu kamar wasa har gabannin asuba wannan faɗa yaƙi rabuwa. Mutane har sun gaji sun koma gidajensu sun barsu. Ƴan gidan kam har yara sun farka dan kowa ya gagara barci. Duk suna a tsakar gida, Raudha ce kawai batako leƙo ba tana lafe a ɗaki tana faman dirzar kuka. Ko sahur ɗin kirki ranar babu wanda yayi a gidan. Kiran sallar asuba yasa Baba Nafi fara  roƙona malam Dauda akan ya fita massallaci shi dan ALLAH ko hakan zai kawo masalaha. Shawararta yasa shi fitar yana faman huci, duk da ba yaune karon farko da suke irin wannan faɗan ba, sai yakejin zafin Asabe a yau fiye da koyaushe. Ji yake tamkar ya saketa ya hutama ransa. Koda aka idar da salla maimakon yaƙi dawowa gidan sai shaiɗan ya dinga tunzurasa akan ya shigo yaga ƙarshen haukan Asaben. Yaran kawai ya samu suna kiciniyar alwala a tsakar gida. Dan Baba Nafi da su Fatisa sun lallaɓa Asabe da ƙyar ta shiga ɗaki itama bayan tayi alwala. Tana ɗaki zaune tana rusar kuka ya dawo, dan ko sallar ma haka tayita tana kuka. Wani irin ɗaci da zafin Malam Dauda takeji yau fiye da ko yaushe a rayuwarta.        “Haba Malam mi kuma ya dawo da kai gidan nan a yanzu?”. Baba Nafi dake tattare kayan wanke-wanke ta faɗa lokacin da malam Ɗan-azumi ke shigowa gidan zuciyarsa tamkar zata kama da wuta. Zuciyar tasa dama a kusa take, dan haka cikin masifa yace, “Na dawone dan naga ƙarshen isakancin Asabe yau a gidan nan!!”..         “Kai ɗin banza daka isa kaga ƙarshen iskancina Dauda. Kaima kasan ni nafi ƙarfin kanwar lasarka, dan ina dai-dai da wandama ya fika balle kai ɗin ƙaramin shegen bariki”.      Da wani irin rawar jiki malam Dauda ya cacimi taɓaryarsu ta daka yayi kan Asabe gadan-gadan. “Aiko yau zan tabbatar miki da ni babban Shege ne....!”         Baba Nafi datai saurin shan gabansa ta riƙe taɓaryar da sauri. “Haba Malam waini kam mike damunku yau haka ne? Yanzu akan ƙaramin abu dabai taka kara ya karya ba zance yaƙici yaƙi cinyewa domin ALLAH!”.       Hankaɗe Baba Nafi yayi, cikin matuƙar sake harzuƙa ya fisgi taɓaryar yana ƙoƙarin sake nufar Asabe da itama ta rarumo kujerarsu ƴar tsugunno ta nufosa, su Fatima suka riƙeta. Sake riƙesa Baba Nafi tayi dan taba duk ta gama cinyesa a tsaye ba wani ƙarfin kirkine da shi ba. Cikin matuƙar sake harzuƙa yake nuna Asabe da ɗan yatsa yana faɗin, *_“Kije na sakeki Asabe. Na sakeki saki biyun daya rage tsakanina da ke!!_* Bana son sake ganin fuskarki, Idan ba hakaba wlhy yau sai na kasheki a gidan nan da hannuna”.       Da sauri Larai ta shige ɗaki wani irin ɗan karen daɗi na saukar mata a rai da zuciya, har ji take tamkar ta daka tsalle ta dire dan yau burinta ya cika. Itako babu abinda zatace da malam ɗan-kande sai godiya. Gashi ya mata aikin da taketa kashe kuɗi tsahon shekaru a cikin ƙanƙanin lokaci. Gwatsar wayarta da tasha ɗaurin ƙyauraye ta ɗauka ta shiga laluben ƙanwarta Haƙila danta guntsa mata wannan daddaɗan labari haka da farar safiyar nan ta juma'a.        A tsakar gida kuwa duk yanda Baba Nafi take ƙoƙarin ƙwaɓar Malam ɗan-azumi yaƙi saurarenta sai sake maimaita kalmar saki yake ga Asabe da gaba ɗaya jikinta yay sanyi kuma a lokaci guda. Dan yana ambaton ya saketa duk zafinsa da takeji kuma sai taji ya kau baki ɗaya. Da wani irin sanyin jiki ta saki kujerar hannunta jin hajijiya na neman kadata ƙasa. Riƙota su Fatisa sukayi suma jikin nasu na rawa.          Raudha dake cikin ɗaki zaune tana karatun Al-qur'ani tai saurin miƙewa tana dafe ƙirji, dan kalmar sakin nan tajita tamkar sukar mashi a ƙahon zuciya. Tuni ta nema kukan da takeyi ta rasa. Da gudu ta fito tsakar gidan, taje gaban Mahaifin nasu ta zube gwiwa a ƙasa tan roƙonsa akan yayi haƙuri karya saki Mommyn su dan ALLAH. Duk hukuncin da yakejin zai mata ita yayi matashi dan ALLAH duk zafinsa zata ɗauka.      Hankaɗeta yayi cikin rufewar ido yay waje yana cigaba da kunfar baki. Raudha ta miƙe da gudu ta bisa tana kuka amma ko waiwayenta baiyiba.........✍️ *_Tofa yau dai da alama auren zobe ya ɓalle? Ko asabe zata yarda tabar gidane? Duk da kuwa saki uku ne a kanta idan aka tara da guda ɗaya na baya. Shin auren Raudha da Alhaji Maude Dallatu zai yuwu kuwa?. To minenen ma ma'anar BAƘAR INUWAr? Suwaye BAƘAR INUWAr? Mizai biyo baya a gundarin labarin BAƘAR INUWA? Dukan amsoshinku na cikin Littafin BAƘAR INUWA da nakeda tabbacin ya taɓo muku inda ke muku ƙaiƙayi. Karku ɗauka a gidan su Raudha kaɗai cakwakiyar zata ƙare. Sam ba haka bane, akwai wasu rikicin da gidajen a gaba. Sanin alaƙarsu da Littafin BAƘAR INUWA sai ka mallaki naka ankai har ƙarshe da kai. Masoya ba'a fara komai ba, dan kuwa a paidpages ne kawai zaku san minene gundarin labarin BAƘAR INUWA😉⛹🏻‍♀️🥰🥰🙏🏻_* _Ku kasance da ZAFAFA BIYAR domin karanta daɗaɗan labaransu guda biyar dake tafe da salo na musamman masu ƙayatarwa_. https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [5/30, 8:16 PM] NANA: *_Typing📲_* *____________________* *_ZAFAFA 5 NA MIKA GAISUWAR TA'AZIYYA ZUWA GA MARUBUCIYA UMMY AISHA, TA KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION, BISA GA RASHI NA MAHAIFIYAR TA DA TAYI. MUNA FATAN ALLAH YA JIKANTA DA RAHAMA, YA GAFARTA MATA, YA K'ARA MANA HAKURIN WANNAN BABBAN RASHI DA MA NA IYAYENMU BAKI ƊAYA (AMIN😭🙏🏻)._* *_____________________* *_Huuuuuum! Idan kaji hanci a sama yayin gittawar mata ƴan ƙwalisa ko shiga gidajensu kasan maganar ta ƙamshi ce_* *_Ina magana ne aka kayan ƙamshi ƴan gaske ba saka iska ta hure maka ba_* *_Ina mata ƴan ƙwalisa ma'abota so da ƙaunar ingantattun haɗin turaruka ƴan gaske? To kuzo maza ga dama a tafin hanunku cikin sauƙi da sauƙaƙawa._* *_Ana siyarda Turarukan Wuta na yan Maiduguri Set na amare. Ana bada sari kuma._* *_Sannan akwai kayan gyaran jiki. Akwai zumar qiba result cikin 1 week. Turaren daki, jiki, kaya, tsuguno, humra, colacca, turaren wanka, mopping scents, air freshener._* _Address Kano, Mariri Maiduguri Road. WhatsApp number 07068145252_. *Sai kunzo🤳🏻* *________________________* *_Episode 6_* ...........Da ga Asabe har ƴaƴanta hankalinsu a matuƙar tashe yake. Hakama Baba Nafi, duk da Asabe kishiyace a gareta aurota da akai a gidan ba ƙaramin alkairi ya zame musu ba ta wani ɓangaren. Dan koba komai Asabe kansaka Malam ɗan-azumi ya sauke haƙƙoƙin su dake kansa koda baiyi niyyar hakan ba. Dan kafin ya aurota sai ya gadama yakeyi, ya gwammaci yaje yay caca ko neman mata. Sannan duk jarabarnan tata da wahala kaga tana faɗa da kishiya, wani lokacin Larai kanso suyi, amma Asabe sai taƙi kulata. Mal. Dan-azumin ne dai ita da shi kamar suna kallon hanjin juna. Hatta da sauran yaran gidan duk sun zama sukuku, musamman ma da Inna mahaifiyar malam Dauda ɗin tazo ta sake zazzaga tata masifar ga Asabe saboda Larai taje ta sanar mata ƙarya da gaskiya, duk da kuwa ba ƙaunar laran take ba. Babu wanda ya tanka mata sai larain, dan harda kawoma Innar ruwa saboda tsugudidi. Saida ta gama zazzage masifarta tsaf da gorin Asabe tabar mata gidan ɗanta sannan tabar gidan, Asabe dai na ɗaki ita da yaranta duka cikin matsananciyar damuwa. Dan har Inna tayi ta gama babu wanda ya leƙo.        Gaba ɗaya wannan yini dai anyisa a gidan cikin rashin daɗin rai ga azumi. Idan ka cire Larai dakejin tamkar ta ciji sama dan farin ciki. Malam Dauda bai sake dawowa gidan ba sai dare bayan sallar isha'i. Tsabar jinsa yau a sama da sigari ya shigo gidan yana busawa, wayarsa mai shegen ƙara tana raira waƙar (marigayi Ali makaho)        Galala Baba Nafi tai tana kallonsa, dan duk iskancinsa bai taɓa shigowa gidansa yana shan sigari ba tunma yanaji da ƙuruciya a iskancin. Amma abin mamaki sai gashi a yau cikin watan azumin ramadana, a kwanakin goman ƙarshe da kowa ke dagewa da ibadar ALLAH, ya shigo gidansa dake cike da ƴaƴa a wannan yanayi.        Tsakar gida ya zauna akan rijiyarsu yana kaɗa ƙafa da kai yana zuƙar sigari da ƙwala kiran sunan Asabe tamkar zai tsaga bangon gidan. Ko tari bataiba ballantana ƴaƴanta, jin taƙi tankawar ya sakashi fara zazzaga ruwan masifa da jaddada mata ta bar masa gidansa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu baisan sake ganinta. Kuma ko Yasmin bai yarda ta ɗauka ba idan zata wuce, ta bar masa abarsa.      Nan ma ko tari babu wanda yayi sai Larai data fito daga ɗakinta ɗauke da tire ta jero kwanika. Dan duk da bai bada kuɗin cefane ba, ba kuma aikinta ba yau kuɗinta ta saka tai girki iya ita da ƴaƴanta da shi. Wani irin washe baki yayi yana gyara zama a lokacin data kai tsugunne gabansa tana dire tray ɗin.       “A'a! Larai na mina samu haka ne?”.    Cikin jin daɗin sunan daya kirata da shi ta buɗe tsohuwar kular dake sama, wadda ke cike da taliya da miyar kifi, sai kunun tsamiya a kofi da ƙosai data sayo masa a ƙaramin kwano. Albarka ya shiga kwarara mata da gyara zama ko kunya babu da tunanin bashi yay cefanen ba. Baba Nafi kuwa dake kallonsu tuni zuciyarta ta harba. Dan zuwa yanzu ta fara zargin Larai akan wannan fitinar dake faruwa tsakanin mijin nasu da Asabe. Dan lallai akwai wani abu a ƙasa gaskiya.       Cikin farin ciki Malam Dauda ya kwashi girki yana kwararama Larai kirari tamkar wani jikan maroƙa. Itako sai wangale baki take. ★★★      Washe gari sabuwar fitina ta sake tashi tsakanin Asabe da malam ɗan-azumi. Dan ya tabbatar mata sai ta bar masa gida a yau. Kuma bazata tafi masa da yaransa ko'ina ba. Ta bashi haƙuri sosai tana kuka amma yaƙi saurarenta, saima yi yake tamkar tana zugashi. Dan gaba ɗaya ya sake birkicewa, har mamakinsa mutane keyi musamman yanda aka san yana bala'in son Asabe, ba kuma yaune karon farko da suke irin wannan fitinarba a cikin anguwar, harma wadda tafi haka sunayi kuma su shirya. Ana tsaka da hakan kuma sai ga Inna yau ma. Komai sake rincaɓewa yayi har maƙwafta da suka taru domin bashi haƙuri akan ya maida Asabe kodan ƴaƴansa sai da ta shafesu. Dan Inna tas ta zagesu ta sake saka malam ɗan-azumi ƙarama Asaben saki ɗaya daya saura a tsakaninsu wanda ya mantama yayisa tun shekarun baya.       Wannan abu yayima su Fatisa zafi matuƙa. Dan haka suka shiga haɗa kayansu masu muhimmanci dana mahaifiyarsu. Cikin ɓacin rai Fatima taje ta jawo hannun Raudha da Asabe dake gurfane suna basa haƙuri, dan itama Asaben ta zama tamkar ba itaba yau duk masifarnan babu ita.       “Mommy dan girman ALLAH in har ba Abbanmu ne autan maza ba a duniya ki barsa kizo mu wuce tunda kema kina da dangi ba'a bola ya tsintoki ba, dan ALLAH idan ya tashi ya auri Innar dake zugashi ɗin...”       “K! fitsararriya!!”. Inna ta faɗa a tsawace. Ko kallonta Fatima batayiba taja hannun Raudha da Asabe suka nufi ɗaki.       Abinda Fatiman tayi ya sake hargitse gidan, Malam Dan-azumi da kansa ya shiga har cikin ɗaki ya fisgo Asabe ya kaita har ƙofar gida yana faɗin tabar masa gidansa, baya son ganinta ya tsaneta. Cikar da ƙofar gidan ta sakeyi ne yasa harsu Raudha suka fito da kaya malam Dan-azumi da Inna basu lura ba. Hakama Baba Nafi. Larai kuwa sarai ta gansu dan tana gefe tanata kwasar dariyarta.       Mota ƙarama suka fara samu da zata kaisu har jihar Bina shata, kafin wata makwafciyarsu da suke ƙawance da Asaben taje ta kamo hannunta ta kawota har wajen motar, dan itace ta hana su Fatisa komawa wajen gudun kar Malam Dan-azumi ya gansu ya hanasu bin Asaben. Itako bata fatan Asabe ta tafi tabar ƴaƴanta, gara duk rintsi ta tafi da abinta kafin abun yay sauƙi, dan da gani kasan malam dauda baya cikin hankalinsa sam. Tafiyar Asabe yasa akaɗan samu sauƙin hayaniyar. Sai mutane daketa yima Malam Dan-azumi ɗin ALLAH wadai da koran Asaben da yayi batare da wani ƙwaƙwƙwaran laifi ba, dan koda aka tambayesa ya rasa mi zaice tayi masa sai babbotan borin kunya yakeyi shida Inna da dama kowa yasan batan ƙaunar Asabe dama duk surukan nata sai baba nafi kawai, ita kanta wani lokacin baba Nafin baji da dadi take hannun innar ba. Na Larai da Asabe yafi zafi ne kawai dai dan ta kasa tanƙwara Malam Dauda ɗinne ya sakesu dole ta haƙura. Yanzu ko data samu dama shiyyasa tai tsayuwar daka wajen ganin ƙarshen Asaben da take kallo matsayin wani miki ga ɗan nata....        ★A Bina su Asabe suka yada zango gidan yayarta Halima da take aure anan. Sai dai kuma sunyi rashin sa'a bata nan wai tana jihar Loss kusan wata guda kenan ita da ƴaƴanta duka da mijinta. Sam Asabe bataso haka ba. Dan bata buƙatar zuwa babban birinin ƙasar Bingo dasu Fatisa wajen Gwaggo (Mahaifiyarsu hajiyar birni). Saboda ta tabbata idon hajiyar birni idon su Raudha to akwai matsala.       Cikin damuwa da sanyin murya Raudha ta kalli Asabe da sauran ƴan uwanta da duk suka jigata saboda azumi, ita kanta daba azumin takeba a jigace take dan babu abinda taci tun jiya da rana sai ruwa. Hawayen dake a idanunta ta share da faɗin, “Mommy nikam a ganina mizai hana mu wuce Bingo wajen su Gwaggo direct mana. Babu amfanin wani raɓe-raɓe a gareki damu a yanzu. Na tabbata Gwaggo ta canja zuwa yanzu, sannan zata amsheki hannu biyu tunda daman zamanki da Abbanmu ne bata so.”        Shiru asabe batace komaiba. Tasan maganar Raudha gaskiyane, sai dai tana fargabar zuwa dasu Bingo su lalace kuma. Su Fatisa basa jin magana tabbas, amma rashin jinsu bai kai inda masu karatu ke hasashe ba, sai dai ta tabbatar kusantasu da hajiyar birni a yanzu komai zai iya faruwa, saboda masifar son kuɗinta. Suma ƴaƴanta ta ɗorasu a hanyar banza dan kawai ta samu kuɗi, balle su kuma jikoki gasu kuma yaranta dukansu masha ALLAH, ba duk namiji zai kalla ya iya kauda kai ba......       “Mommy gaskiyafa Raudha ta faɗa wlhy, gara kawai mu tafi Bingo ɗin”.     Fatima ta faɗa cikin katse tunanin Asabe.       Numfashi asaben taja mai nauyi, “Banƙi ta taku ba, sai dai nima akwai abinda nake lissafawa. Amma kuma banida wata mafita saita tafiya Bingo ɗin a yanzu. Matsalar kawai dai itace bamu da isassun kuɗin motar da zasu kaimu ne mu duka”.         “Akwai kuɗi Mommy”.   A tare duk suka dubi Raudha datai maganar cikin mamaki. Cikin rashin damuwa da kallon da suke matan ta zaro kuɗi a cikin zani sabbi ƙal ƴan ɗari biyu ta miƙama Asabe. “Mommy jiya mutumin nan da yazo dubani a asibiti ya bani su. Nayi niyyar bakine dama idan munzo gida danki fara sana'a. Amma yanzu na tabbatar insha ALLAH zasu kaimu duk inda zamuje ko?”.        Hawaye ne suka ciko idon asabe. Dan bata taɓa tunanin Raudha haka ba. Ganin yanda take musu nuni dasu gyara yasa take tunanin sam Raudha bata ƙaunarta matsayin mahaifiya. Ashe ba haka bane ba. “ALLAH yayi muku albarka, ya kare min ku”.     Ta faɗa gawaye na silalo mata na nadamar sakaci da tasoyi akan tarbiyyar ƴaƴanta saboda ruɗin shaiɗan da son zuciya. Hannu Yasmin dake jikinta tasa ta share mata hawayen. “Mommy ki daina kuka, banason naga kina kuka kamar irin na Aunty R”.       Asabe ta rungume Yasmin tana murmushi da share sauran hawayen. “Na bari auta, itama bazata sake yin kukaba insha ALLAHU. Da ga yau zan tsaya akanku da inganta tarbiyyarku da muku addu'ar miji nagari ba irin mahaifinku ba da ni.”      Ba Raudha da ɗabi'ar iyayensu ke damunta a rai ba, hatta su Fatisa yau duk sai jikinsu yay sanyi ƙalau. Bayan asabe ta kira ƙawarta dake hutuwa sukai magana sai suka ɗunguma tasha duk da yamma tayi liƙis. Basu damuba dan tafiyar daren ma sai tafi musu kwanciyar hankali. Anan tasha sukasha ruwa dayin sallar magriba. Kafin motarsu ta tashi zuwa birnin Bingo. (Babban birnin ƙasar NAYA kenan. Dan yanzu hajiyar birni tana nan da zama ta baro jihar loss). ★★★          Ko bayan tafiyar Asabe Malam Dan-azumi bai farga da rashin su Raudha a gidan ba har yamma. Dan bayan lafawar komai sai zuciyarsa kuma ta sake shiga ƙuntata fiye da farko. Rasa mike masa daɗi yayi dan haka yabi Inna data jashi zuwa can asalin gidansu na gado. Barci ya kwanta yayi sosai dan har gab da magrib sannan ya tashi. Sai da ya fara shiga massallaci yay ramuwar sallar azhar da la'asar sannan yay zaman jiran magrib zuciyarsa duk babu daɗi. Koda aka idar da sallar magriba yau bai zauna shan kunun sadaka ba yayo gida fagan-fagan tamkar zai kifa ƙasa dan sauri. Da akuyar Larai dake bakin kwata ya fara bal. ta saki wani marayan kuka daya saka duk jama'ar fitowa daga ɗakunansu.       “Malam lafiya kuwa?”. Larai ta faɗa tana hararsa da nufar akuyarta dake kwance ta kasa tashi dan azaba. Bai tanka mataba, sai nufar ɗakin da yara ke kwana yayi ya leƙa, duk da kuwa duk sauran yaran gidan sun fito suma. Cikin sauri ya afka ɗakin ya hau leƙe-leƙe duk da babu wani lungu da zai iya ɓoye mutum a ciki. A zabure ya sake yo waje, nan ma bai kula sauran yaran dake masa barka da shan ruwaba ya nufi ɗakin Asabe dake garƙame da ƙwaɗo.        Wata muguwar ashariya ya lailayo ya dire yana duban Baba Nafi. “Ina yarana?”.      Duk da sarai tasan su Raudha yake nufi sai ta haɗe rai itama. A ɗan zafafe tace, “Gasu nan tsaitsaye ai”.         “Mtsoww! Su Raudha nake nufi!!”.      Yanda yay maganar a tsawace ya saka kowa zabura banda Larai data laɓe baki tana hura hanci. Cikin jin zafin yanda ya nuna damuwa da rashin ganin ƴaƴan na Asabe ta ce, “Tunda ka kori uwarsu mi zasu zauna kuma su mana anan muma. Kaima kasan sun bita”.       Wata muguwar shaƙa ya kaima Larai ido a rufe, ya maƙureta jikin bango, “Ubanwa yace ta tafimini da ƴaƴa kuna gani kuka barta!!?”.       Cikin fisge-fisgen azaba Larai ta turesa tana kakarin shaƙa. Kafinma wani yay magana ya nufi hanyar fita ƙofar gida da sauri.       Kai tsaye gidan Malam Gambo amininsa ya nufa. Cikin sa'a kuwa yaci karo da shi a ƙofar gidansa. Ko sallama babu ya zube a tabarmar da Malam Gambo yake kai yana huci.       Malam Gambo dake dubansa yana murmushin ƙeta yace, “Mutumina lafiya dai ko? Badai Asaben bace ta sake dawowa kuma?”.       Harara ya zuba masa yana sake ƙwaɓe fuska. “Gambo gaba ɗaya shawararka ruguzani take nemanyi ba gyarani ba. Kai kace naima Asabe saki ɗaya zakasa ta dawo gidanka da zama har sai na gama hidimar auren Raudha da Alhaji Maude na jiƙu da kuɗi sannan na dawo da ita, amma har akaci aka tsire banma ganka a wajen ba. Gashi daga ƙarshe tama sace su Raudhan ta wuce da su”.        M. Gambo dake gimtse dariya yay ƙoƙarin dai-daita kansa da ƙyar. Cikin nuna ɓacin ran ƙarya ya miƙe zaune sosai. “Ya zakace banzo ba M. Dauda. Idonkane kai dai kawai ya rufe har bakaga sanda naketa ƙoƙarin ganin na saka Inna ta huce bata sakaka yin saki ukun nan ba.....”        Cikin ƙosawa M. Dan-azumi ya katse M. Gambo.       “Ni wannan duk bashi bane damuwata a yanzu M. Gambo. Babbar matsalata ta tafimin da yara. Shirina duk ya zama na banza kenan?”.        “Kwantar da hankalinka bai zamaba M. Dauda. Ai mugu shine yasan makwantar mugu. Badai kasan inda ka auro Asabe ba?”.         “Ya kake min wannan banzar tambayar. Idan ban sani ba daga sama akaimin wahayinta!”.      “ALLAH ya baka haƙuri ba haka nake nufi ba. Abinda nake nufi tunda kasan gidansu a loss mizai hana muyi shiri muje mu amso ƴaƴanmu”.       “Kai bazai yuwuba. Mahaifiyarta da ƴan uwanta jarababbune na bugawa a filin idi. Gashi basa ƙaunata ko kaɗan. Wannan ne yasa naje wajen malam na tsandu yay mata wani kafi da bata sake zuwa loss ba tun Yasmin na shekara uku. Yanzu ma uwar tata tabar Loss tana birinin Bingo....”        “A lallai likafa taci gaba, Bingo? to basai mu satosu ba kawai. Ai shiyyasa na faɗa maka mugu shine yasan makwantar mugu ai”.        Karan farko M. Dan-azumi ya saki murmushi dan gamsuwa da maganar M. Gambo. “Eh to kazo da magana mai ƙyau kuwa. Inko hakane dole na tsara wani abu a wannan gaɓar ma kodan na samu ƴan kuɗaɗe hanun Alhaji Maude Dallatu.”        “A wlhy ina bayanka M. Dauda. Tatsi ka more rabonka ɗan takarar ɗan-majalisa ba wasa bane. Kaga idan ALLAH ya taimakemu akai auren nan kuma yaci ɗin nan aimu mun haye wlhy. Kakarmu ta yanke saƙa rabajau zaka ganmu mutumina. Surukan ɗan-majalisa fa kenan, kai wlhy ƙilama ai maka Ministan kuɗi kona man fetur ni kuma kwamishina...”       “Minister kuma? Kai fa M. Gambo wani zubin kamar haka-haka kake. Minista ba shugaban ƙasa keyi ba?...”       “Af wlhy na shafa'a ne Dauda. Kasan maijin yunwa ko goruba aka bashi gani yake abinci ce”.         “Kai dai ka sani, ni kaga tafiyata shawararka ta faɗa. Zanje na ɓata daren yau wajen shirin yanda komai zai tafi har tafiyarmu Bingo ɗin ma”.     “Af to babu damuwa sai na jika. Amma sai bayan salla ko? Tunda naga kwana shida sallar ta rage kacal”.         “Ko gobe ta kama nidai tafiya zanyi na amso ƴaƴana”.     M. Dauda ya faɗa yana barin wajen.  Shaƙiyyar dariya M. Gambo ya saki yana kaiwa kishingiɗe. “M. Dauda kenan inka san wata ai baka san wataba. Badai ni ka raba da Ladi dandi ba muna tsaka da more duniyata. To kai gashi na rabaka da Asaben da kake ji da ita kuma zan koma ta bayan gida na aureta kai dai kaini gidan nasu kaga ikon ALLAH. Dan ba wani dawo da yaranka zai kaini ba hhhhhh”...........✍ 🤔Tofa, Larai ko M. gambo?. ALLAH dai ka tsaremu da abokai masu fiska biyu😥. ______________________ https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [5/31, 1:21 PM] NANA: *_Typing📲_* ________________ *_Episode 7_* ...........*_BINGO CITY_*          Kasancewar tafiyar dare da sukayi a tasha suka ƙarasa kwana, sai da safe suka fito domin shiga cikin garin Bingo. Duk da Asabe a tsorace take, hakan bai hanata tarar motar taxi suka shigaba. Kai tsaye anguwar data san su hajiyar birni na zaune a yanzu suka nufa. Sai dai har cikin rai tana tsoron haɗuwa da Gwaggon nata. Tana kuma tausayin ƴaƴanta akan tarbar da zasu samu ga mahaifiyar tata da sauran ƴan uwanta. Amma sai ta danne dan kar ta tada hankalin ƴaƴan nata da sukai zugum-zugum musamman Raudha.        Tun a farkon shigowa layin sukai tambayar gidan Hajiyan Birni (sunan da asabe tasan ake kiran Gwaggo a ko ina). Sananniyace a anguwar kodan katafaren shagonta na abinci da duk kewayan babu kamarsa a yanzu. Dan takai manya-manyan masu kuɗi da sanannun mutane ke zuwa wajen cin abinci da shan giya wajenta. Ta iya abinci kala-kala na ƙawa, gashi tana tsaftacewa. Ta samu kuɗi matuƙa shiyyasa ma ta baro geto ta dawo wannan anguwar da zama kodan customers nata ƴan ƙarya da sanannu wanda basa buƙatar shiga kowane waje.            Basu Raudha ba, hatta da Asabe mamakin ganin ƙaton wajen kuma lafiyayye take, itadai tasan Gwaggo bata da ƙarfin gina irin wannan wajen da sunan gidan abincinta. Kodai watace mai irin sunan Gwaggo itama......       “Mommy fitsari nakeji”. Yasmin ta katse ma Asabe tunaninta. Numfashi taja da ƙarfi tana ɗan waige-waige ko zataga inda Yasmin ɗin zata tsugunna. “Kinga jeki bayan dustbin ɗin can kiyi”.        Da sauri Raudha ta ɗan girgizama Asabe kai tana riƙo hannun Yasmin dake ƙoƙarin tsillawa da gudu. “A'a Mommy bai dace ba. Itafa mace ce, ya zata duƙa a titi yin fitsari? Mizai hana mu tambaya kodan guje mata ɗaukan wani cutan”.        Fatisa ta ballama Raudha harara tana yamutse fuska, “Raudha bazaki bar dai iyayi ba a rayuwarki? Miye idan tayi fitsari a can, duka shekarun Yasmin ɗin nawa a duniya da har za'a kirata mace”.       Kafin wani ya sake magana wata matashiyar budurwa sanye cikin wando baƙi da t-shirt pink alamun Uniform ɗin wajen kenan ta fito a cikin wajen cin abincin, cikin gurɓatacciyar hausanta tana faɗin, “Kai lafiya kuwa? Nan ba wajen tsayawa bane ba ku ƙara gaba”.         Fati zata fara magana cikin hasala Asabe ta dakatar da ita. “Yi haƙuri ƴammata ba haka nan muka tsayaba muma, muna neman wata ne anan ɗin?”.       “Wata kuma?” “Eh wata muke nema Hajiyar Birni. An kuma tabbatar mana tana anan wajen”.       Wani kallon banza budurwar ta sake musu sama da ƙasa. “Tabbas sunan mai wajen nan kenan. Sai dai ku kuma sam bakuyi kala da masu alaƙa da ita ba, da har zaku nemi ganinta haka kai tsaye”.       Asabe da ƙwalla ya cikoma idanu tace, “Hakane yarinya. amma ki taimakemu ki sanar mata Asabe ce da ga Hutawa”.       Kamar budurwarnan bazata motsaba tanata musu kallon banza. Sai kuma taja guntun tsaki. A yatsine ta ce, “Kunga kuɗan koma daga can”.     Nan ma Fati zatai magana Asabe ta hanata. Sai da budurwar ta juya ciki Asabe ta dubesu. “Dan ALLAH ku kwantar da hankalinku bana son wata fitina. Idan munga ba ita bace gaba zamuyi ai. Maida zance ga kowa ba namu bane a yanzu”.      Badan hakan ya musu daɗi ba suka ɗaga mata kai alamar to....... *★★★**★★**★★*        Kasancewar yau rana ce ta aiki kowanne ofishin gwamnati zaka samu ma'aikaci harma dana wanda ba gwamnatin ba ma'abota ayyuka a cikinsu. Baka ganin komai sai kaiwa da komowar ma'aikata a dukan ma'aikatu.         Sai dai a mafi yawan ma'aikatun gwamnati kamar yanda kowa ya sani ƴan siyasa ne mafi rinjaye a cikin yankin ofisoshin da suka shafi gwamnati. Kamar dai a yankin gidan gwamnati na babban birnin ƙasar NAYA (Bingo). Yawaitar ƴan siyasa a wajen yana da alaƙa da zaman taron meeting da shugaban ƙasa yayi har kusan sau biyu a safiyar ta yau saboda gabatowar watannin zaɓe da muka shiga shekarar ƙarshe na saukar duk wani mai mulki da ya ƙulla hawa biyu akan karagarsa.        A yanda alama ta nuna taron baima wasu daɗi ba. Dan lokacin tashi ma baiyiba shugaban ƙasa ya fita a wajen taro na biyu da aka zauna da wasu manyan dattijan jam'iyyar masu faɗa aji da mafi yawansu suka kasance masu sakawa da hanawa na wannan jam'iyya ne. Sai dai kuma bayan fitar shugaban ƙasa daga wajen taron da kamar mintuna goma sha biyar labari ya shigo kunnensu ya sake zama na musamman da ƙasaitaccen dattijon mai arziƙin nan kuma tsohon alƙali da kowa yakejin sunansa a ƙasar dama wajen ƙasar, har zamu iya cewa a yanzu ya zama tamkar wani shugaba dan ko masu mulkin babu abinda zasu layance masa na gwagwarmayar rayuwa da sanin muhimmancin talaka.         Kamar yanda basu fasa cigaba da ƙananun magana irin wadda akasan ƴan siyasa da itaba, haka ma shugaban ƙasa bai fasa ganawar sirrinsa da *_Alhaji Hameed Harith Taura_* ba.         Kallo ɗaya zakaima ƙyaƙyƙyawar fuskar dattijo Alhaji Hameed Taura dake ɗauke da ƙasaitaccen murmushin manya ka fahimci ɗunbin kamala da dattako tattare da shi. Yana zaune cikin luntsumemiyar kujerar da ke a ƙayataccen katafaren falon hutawa na shugaban ƙasa mai zaman mutum uku (three sitter). Zama ne irin na ƙasaita da dattijan taka, yana sanye cikin ɗanyar farar shadda harda malun-malun da suka ƙawatu da aikin surfani na maƙudan kuɗi. Ƙyaƙyƙyawane, duk da tsufa na farin gashi yama fuskar tasa shinge. Sai dai maimakon ya ɓata ta sai ya sake ƙawatata da kamala. Gefensa kaɗan shugaban ƙasa ne zaune shima cikin tasa ƙasaitar irin ta masu mulki. ba zasu iya zama shekaru ɗaya ba, sai dai yanayin jiki yasa Shugaban ƙasa yafi Alhaji Hameed ƙiba. Amma kuma kasantuwarsu cikin jin daɗi ya zaftare kaso mafi yawa na tsufan nasu gamai kallo.        Shugaban ƙasa dake magana cikin tsantsar damuwa ya sake gyara zamansa fuskarsa na nuna tsantsar damuwa da taraddadi. Cikin harshen turanci yake cigaba da faɗin, “Alhaji Hameed a wannan gaɓar da gaske nake bana buƙatar mulkin nan yabar hannunmu, dan na tabbatar maƙiyanmu na amsa tamkar mun bada sandunan rusa dukan tanadinmu ne a zahiri. Kai shaidane akan faɗi tashin da mukaitayi na ganin nayi shekaru goma bisa mulkin nan kafin yau. Miyasa bazaka amsa shawarata ba na fitowa takara kaima. Dan ni kai kaɗai idanuna ke iya hangomin zaka kawo kujerarnan a yanzun....”        Alhaji Haneed dake kallon shugaban ƙasa fuska ɗauke da murmushi na dattijantaka ya ɗan muskuta. Shima cikin harshen turancin ya fara magana da sigar rashin muhimmancin maganar ta shugaban ƙasa da rangwamen tasirinta a garesa. “Your Excellency badan a bakinka zancen nan ya fitoba dana kirasa da tarin wauta ƙwarai da gaske. Karka bari daɗin mulki ya kasa barinka ka dinga hango cewar ni Abdul-Hameed zan iya. Excellency ni sam bani da sha'awar mulki a ƙasarnan sam. Na zuri'ata da harkokin kasuwancina ma ya isheni gayya da takura. Sanin kankane dan na huta na tattara ayyukana na damƙa a hannun yarona tsahon shekaru goma kenan, iyakata a yanzu na taimaka masa da abinda bazan takura ba da ga gida. Ka ajiye maganata a gefe muyi mai muhimmanci. Kaine ka tilastani shiga siyasa saboda wasu abubuwa da muke iya hangowa zamu gyara koda bata hanyar mulki ba. Amma daka nuna sha'awar zakayi mulkin kai sai na baka goyon baya nima saboda nasan zaka iya. Kuma Alhmdllhi kayi ɗin an yaba. Ni yanzu inada shawara guda ɗaya zuwa biyu Excellency. Mizai hana mu duba a cikin yaran nan dake biye da kai ƙafa da ƙafa mu ɗora mai nagarta akan hanyar da mukeso, mu tallafa masa da taimakon UBANGIJI idan ya amince sai ya bashi mulkin tamkar yanda ya baka...”           Wani numfashi mai ƙarfi daya dakatar da Alhaji Hameed a magana Shugaban ƙasa yaja, cikin jin ɗaci da sukar da kalaman Alhaji Hameed ke masa a zuciya, ya haɗiye abinda ya tokare masa maƙoshi da ƙyar yana ƙaƙaro murmushi a saman fuskarsa. “Am sorry to say bana katseka bane ba Alhaji Hameed. Maganarkace tazo dai-dai gaɓar dataimin daɗi matuƙa. Harma a dalilinta wani tunani ya faɗomin a rai nima.”        “Masha ALLAH, wane irin tunanine?”.      Alhaji Hameed ya faɗa cike da yardar daya bama shugaban ƙasa matsayinsa na amini garesa shekaru aru-aru.          Shugaban ƙasa dake jin tamkar ya sokama Alhaji Hameed wuƙa ya sake ƙawata fuskarsa da murmushi. “Na yarda mu sami wani da muke ganin zai ɗora aikinsa bisa namu ɗin, sai dai a duk yaran dake tare da ni ɗin ban hango wannan nagartar ga kowa ba sai ga ɗanmu....”        Cike da mamaki Alhaji Hameed yace, “Ɗanmu kuma excellency!?”.        “Yes ɗanmu Alhaji Hameed. Basheer shi kaɗaine zai iya mana yanda mukeso batare da ya rusamu ba. Zamu tallata Basheer kuma inaji a jikina zai zama mai nasara insha ALLAH”.         (Dariya) karo na farko Alhaji Hameed yay dariya mai faɗi har haƙoransa na bayyana sosai. “Excellency baka rabo da wasa kai sam a rayuwarka. Banda ma dai iskar ac na busaka ta yaya kake tunanin Basheer zai iya siyasa harma takaisa ga mulki?. Idan ka manta bara na tuna maka. Bazan iya sakacin da Basheer zai ajiye harkokinmu ya dawo harkar siyasa ba, dan haka mubarma maganarnan Please, dan nasan bashi da interest akan hakan shi kansa....”         “Saboda ni ban isa da Basheer ba kenan Alhaji Hameed?”.       “Kash! Banso kai wannan zancen ba sam excellency, kaima ka sani kai ɗin mai iya zartar da hukuncine akan dukkan zuri'a ta. Sai dai kai baka hango ni abinda nake hangowa a wannan gaɓar. Dan haka ka sake shawara badai wannan ba”.        A take ɓacin rai ya gauraye fuskar shugaban ƙasa. Dan kuwa wannan itace dama ta ƙarshe da suke da ita akan Alhaji Hameed ɗin a wannan karon ma kamar yanda suke gani. Sun ɗauka tsahon shekaru suna shiryama Alhaji Hameed Taura tuggu iri daban-daban, amma yana tsallakewa, sai dai a wannan karon sun ɗauka alwashin bazasu taɓa bari damarsu ta suɓuce musu ba. Dole ne Alhaji Hameed ya amince da buƙatarsu ko yana so ko baya so......         Miƙewar da yay cikin fushi ya saka Alhaji Hameed riƙosa da hanzari. “Wai badai fushi kayi ba?”.       Cikin pretending shugaban ƙasa ya sake tsuke fuska yana son ƙwace jikinsa. “Mizaisa raina ya ɓaci tunda ka nunamin ban isa da jininka ba. Niko kaga komi ka zartar akan yarana ko tari bazanyiba balle ma na nuna maka inada alaƙa da sawarka ko hanawarka a kansu”.       Murmushi Alhaji Hameed yay yana girgiza kansa. “To naji zauna muyi magana. Dan nima ba ina nufin baka isa baneba. kawai dai akwai ƙurar da nake hangowa da tasowarta na dai-dai da guguwar da babu abinda zai iya tareta yayinda ta keto tsakkiyar birnin Bingo dama NAYA baki ɗaya”.        “Wannan hausan naka yayi girma da yawa ban fahimci komai ba”.       “Zaka fahimta ai”. Cewar Alhaji Hameed Harith Taura yana dariya....... ★★★*****★★★         Rai ɓace dattijuwar tsohuwar ta fito sanye cikin kaya na alfarma. Leshi ne daya amsa sunansa leshi mai tsadar gaske irin na jama'ar wannan yanki (masu hannu da shuni). Sai dai tana buɗe baki zatayi magana idanunta suka sauka akan su Asabe dake tsaye gefe har yanzu cikin alamun gajiya da buƙatar hutu. Turus ta ɗanyi a tsaye, sai dai fuskarta ta shanye tsoro da mamakinta. Asabe da jikinta keɗan rawa tun fitowar mahaifiyar tata ta fara takowa a hankali zuwa gareta hawaye na ƙoƙarin cika mata ido. Batun yanzu ba tasan mahaifiyar tasu ƴar gayu ce, sannan takowace hanya bi take domin neman kuɗi, tun ƙuruciya burinta tara manyan kuɗi ne, sai dai kota fara tarawar sukan rushe ne. Amma a bin mamaki a yau sai gata cikin yanayin da mai kallo kawai ya isa shaida lallai ta tara ɗin.....        “Wacece ke! Da ga ina kuma?!”. Muryar Hajiyar birni ta katse tunanin Asabe da bata san ma ta iso gareta ba. A firgice ta ɗaga kai ta dubi mahaifiyar tasu hawayen da take maƙalewa na sakko mata a guje.         “Dan ALLAH Gwaggo kiyi haƙuri, nasan ni mai laifice a gareki....”      Baki Hajiyar birni taɗan taɓe kamar zata juya. Da sauri Asabe ta riƙo hannunta tana sake fashewa da kuka. Sanin halin Asabe da abinda zata iya yasa Hajiyar Birni juyowa a tsawace tace, “Sakarmin hannu. Danni tuni nama fiddaki a cikin ƴaƴana. Na barma Dauda dandi dan na kula ya fini kima da mutunci a idonki ai.”        “Wlhy baiko kamo yatsan ƙafarkiba Gwaggo. Na tuba nabi ALLAH na biki dan ALLAH kimin rai. Kece komaina gwaggo, dan ALLAH ki tausayamin ni da yarana dan ke kaɗaice dolenmu sai ƴan uwana”.       Kamar hajiyar birni zata sake cewa wani abu sai kuma ta fasa saboda sanin a inda take, yanzu ko gab ma'aikata suke da fitowa cin abinci, bata fatan abinda zai ɓata mata rai. Gaba tai tanama matashiyar budurwar ɗazun magana da ido tai shigewarta ciki tabar Asabe nan tsugunne da su Raudha dake a tsaye cirko-cirko ransu a dagule matuƙa, duk da sun fahimci hamshaƙiyar matar data fito Gwaggo ce mahaifiyar Mommynsu. Dan rabonsu da ita tun suna ƙanana sosai. ★          Gida ne matsakaici mai rangwamen girma da ƙyawu budurwar nan ta kawosu. Wadda alama ta nuna umarnin hajiyar birni tabi. Basu sami kowaba a gidan, sai dai a kallo guda zaka fahimci mazauna cikinsa ya wuce mutum ɗaya kacal. Duk da budurwar tasan lokacin azumine hakan bai hanata ajiye musu abincin data taho da shi ba daga restaurant ɗin. Daga haka ta juya inda ta fito.       Asabe data fahimci nanne gidan mahaifiyar tasu saita bama yaran nata umarnin tashi su fara gyara jikinsu, musamman ma Raudha dake a yanayin buƙatar hakan matuƙa. Duk basuyi musun hakan ba, dan dama sunada buƙata suma.     Ɗaya bayan ɗaya suka dinga wanka a toilet ɗin dake a tsakar gidan bayan Raudha ta tsaftace sa, suna kammalawa Yasmin tai zaman cin abinci, Raudha ma ta ɗan tsakura tasha magani ta kwanta. Ganin Asabe ma ta kwanta Fatisa da Fatima suka faki idanunta sukacinye sauran abincin da Yasmin ta rage. A taƙaice dai suka karya azumin dake a bakunansu. Suma kwanciyar sukai suna sauke ajiyar zuciyoyi najin nutsuwar abincin da sukaci..... *_____________________________* *_FRIDAY EVERNING_*          DAREN juma'ar data kasance dai-dai da kwanaki biyar na wanzuwar wasu al'amura a ɓangarori biyar. Ya kumayi dai-dai da jajibirin sallar ƙarama da kowa ke saka ran kasantuwar ta lahadi insha ALLAH.    *_ANGUWAR SOBIA_*, Anguwace da ke ɗauke da manyan gidaje na alfarma. Basai an tsaya dogon bayani ba a kallo ɗaya ta isa mai buƙatar amsa cewar mazauna cikinta sun tara kodan hasken daya gaurayeta tako ina da keda banbanci da rana kaɗan. A wannan anguwa gida mai lamba goma sha huɗu shine mallakin dattijo Alhaji Hameed Harith Taura da zuri'arsa baki ɗaya. Katafaren gidane daya mallaki komai najin daɗin duniya. Ɓangarorin da suka kasance daban-daban a cikinsa ke nuni da ba Alhaji Hameed bane kaɗai ke rayuwa a cikinsa. Yana tare ne da dukkan zuri'arsa. Kamar yanda anguwar ke ƙawace da hasken lantarki, hakama cikin gidan yake tarwai da hasken da kake iya ganin shigi da fici na mutane ta kowanne sashe. Sai dai a kallo guda zaka fahimci masu yawan kaiwa da komowar ma'aikatan gidanne ba masu gidan ba ko ƴaƴan gidan.........✍               ________________________ *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/1, 11:58 AM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 8_* ............“Nikam dai nake ga kamar anzo gaɓar daya kamata ace nasan minene damuwarka?”.      Dattijuwar tsohuwa fara ƙal ta faɗa tana duban dattijon dake kishingiɗe a gefenta yana buɗe kwanikan data ajiye masa masu ɗauke da tuƙaƙƙen tuwo dawa daketa tashin ƙamshin kanwa. Duk da jin daɗi dake tattare da yanayinsu hakan bai hana bayyanar tsufanta ba ƙarara, sai dai jikinta nada ƙwarinsa musamman daya haɗa da cikar kamala da nutsuwar dake tattare da ita. A fuska kawai zaka fahimci ita ɗin bamai yawan wasa bace sam. Sai dai hakan bai hana kwarjininta bayyana akan fuskar ba.       Yanda ta tsatstsare sa da idanunta masu girma da haske duk da tsufan dake tattare da zagayen fatarsune ya saka Alhaji Hameed sakin murmushi yana tashi zaune sosai.       “Nifa kibar hukuntani da idanun nan naki Jannatu, tunda ko kwanikan nan da kika ajiye shaidane banyi wani laifi ba”.      Murmushi ta saki a karon farko tana girgiza kanta mai cike da furfurar gashi dake shan gyara. Ta gyara zamanta tana gyara kwanikan tuwon data zuba masa a gabansa. “Nima ba hukuntaka nakeba Dattijo. Kawai dai idaniyatace ta gaji matuƙa da ganin yanda kullum tunaninka keyin nisa da ni. Tun randa kukai zama da shugaban ƙasa na fahimci ka kasa sukuni. Daka zauna ko wani ya gusa a jikinka zakai nisa da duniyar mutane zuwa wata daban. Idan har ban shiga hurumin daba nawaba mizai hana na sani ko inada abin cewa dazai kawo mafita dattijo”.         Komai baiceba. Sai dai yayi murmushi mai sanyi da cigaba da cin abincinsa da yakeji a duk duniya babu abinda ya kaisa daɗi da nutsuwa a garesa. Itama ɗin bata sake cewa koman ba, dan ta fahimci ma'ana da dalilin shirun nasa. Sai ma ta maida hankalinta ga television ɗin dake manne a ƙayataccen bangon falon nasu kawai.              “Babu wanda ya shigo cikin yaran nan?”.         Alhaji Hameed ya faɗa dai-dai yana ture kwanikan abincin nasa alamar ya kammala. Hakan kuma yayi dai-dai da juyowar matar tasa garesa tana gyaɗa masa kanta. “Babu wanda ya shigo, kasan yau jajibirin salla, mafi yawansu suna can wajen gyaran jikin kwalliyar salla. Garama ja'irarnan Bilkisa data shigo ɗazun da hantsi tacemin can zataje sallar juma'a wajen uwarta Asma'u”.        Kansa kawai ya jinjina mata tare da ɗaukar ruwa yasha. Sai da ya ajiye kofin dayin hamdala ga UBANGIJI kafin ya gyara zamansa sosai da sake nutsuwa fiye da farko.       “Jannatu tabbas akwai abinda ke damuna, sai dai na barsane a iya ni da tunanin zan samo mafita mai ɓullewa kafin ki sani k da Basheer. Kamar yanda kikayi tunani damuwata nada alaƙa da zuwa ofishin shugaban ƙasa.” yaja numfashi, batare da ya bata damar cewa wani abuba ya cigaba da faɗin, “Ya buƙaci na fito takarar shugabancin ƙasar NAYA saboda rikicin da aketa tafkawa akan wanda zasubama takarar a wannan jam'iyyar. Dan kusan mutane biyar ne suka nuna sha'awar hakan, sannan dukansu sun cancanta a fuskar gudunmawar da suka bama jam'iyya da shi Excellency ɗin. Kai kawon daketa wanzuwa ya sakashi ganin duk su huta shi ya ɗora wanda yaga ya cancanci ɗorawa daga ayyukansa. Shine bai tunkari kowaba sai ni”.        (Murmushi) ta saki murmushi mai faɗi tana sake fuskantarsa. “UHMM!! That's a salient point Dattijo. Sai dai kai wace amsa ka bashi?”.        “Ban san dalilinki na jingina tatsuniyar tasa da muhimmiya ba. Sai dai na yarda dake wajen warware matsaloli cikin sauƙi. Amsar dana basa ɗayace wadda nasan kema zakiyi tunanin hakan, shine ba zanyiba, banga dalilin dazai sakani yin mulki a wannan shekarun nawa ba na tsufa. Kai ni bamma taɓa sha'awar hakanba shima ya sani. Siyasar kanta ma sai da kukayi yaƙi sosai kafin na shiga domin bada shawarwari badan tana cikin tsarina ba. Sai dai bijirewata baisa ya ƙyaleniba. Ya kawo dalilai masu yawa da yake ganin Basheer ya cancanta....”         “Shima bai cancanta ba”. Ta katsesa tana kallonsa da murmushi yanzu ma.     “Miyasa kikace haka Jannatu?”. Ya tambaya cikin mamaki da taraddadi.           “Dalilai masu yawa dattijo. Sai dai ba kowa zai iya kallonsu a dalilan ba, amma nasan kaima zaka fahimci wasu a hakan”.      “A dalilin fahimtar wasunne ma yasa kai tsaye nace shima ɗin bazaiyiba Jannatu. Tayaya ma excellency ke tunanin zanbarma duniya Basheer alhalin shine kawai inuwar hutuna a yanzun. Shine kaɗai ɗan da muka haifa, a kuma wannan gaɓar dukkan wani kaiwa da komowa na abinda ALLAH ya azurtamu da shi a hannunsa yake, hasalima bana tunanin yanada interest akan mulki shima”.         “Wannan gaskiyane dattijo. Naji daɗi da tunaninmu yazo iri ɗaya. Duk da dai ni da kai akwai banbancin hange a tafiyar. Rashin cancantar Babangida ko kai a siyasa bashike nufin zamuƙi amsar wannan damar ba da ALLAH ya matso da ita a tafin hannunmu, domin taimakon talakawa da ƙasarmu ta NAYA.”        “Ban gane mikike nufi ba? Mizai amfanar damu a cikin amsa bayan munsan babu mai riƙewa to?”.       “Akwai!”. “Akwai?! To wa kenan?”.        *_RAMADHAN!”_* A take dukkan Murmushin da ke shimfiɗe a saman fuskarsa ya ɓace ɓat. Wani abu mai kama da fushi da ɗaci ya bayyana. Kansa ya kauda gefe tamkar bazaice komai ba, dan ita kanta ma harta fidda rai da ga jin wani abun a bakinsa. ★★★__________★★★   A lissafi yau kwankinsu biyar kenan cif da shigowa cikin birnin na Bingo, inda a cikin kwanaki biyar ɗin nan Asabe tasha matuƙar fama wajen neman yafiyar mahaifiyarta data turje cewar bazata riƙe su Raudha ɗin ba. A cewarta ita kaɗai ta haifa, ita kaɗaice dolenta da idan Dauda ya koro zata amsa. Amma ƴaƴansa su shirya ta basu kuɗin mota su koma gidan ubansu suma.      Hankalin Asabe yayi matuƙar tashi harma dasu Fatisa, dan haka suka dage wajen roƙo da taya Mommynsu magiyar ganin an barsu sun rayu a kusa da ita. Sai dai ga Raudha sam abin ba haka yakeba. Dan gaba ɗaya zubin kakar tasu da ɗabi'unta basu mataba, domin tun ba'ai nisa ba ta auna ta ɗora abubuwa da yawa na kakar tasu a mizani da ya cire mata sha'awar rayuwa anan ɗin. Duk lalacewa gara gidan mahaifinta, tunda dai acan babu mai takura maka akan tilas sai kabi wata hanya mara tushe. Abinda ya ƙara tada hankalin Raudha da zama cikin ƴan uwan mahaifiyar tata shine.... *Halayensu*, dan a kallo ɗaya idan kai musu da wahala ka ɗorasu a mizanin mutanen kirki kai tsaye. Kamar yanda kukaji tun a farkon labarin su Asabe su huɗu ne a wajen hajiyar birni, Asabe kuma itace auta, sannan itace ta fara bijirewa wajen ganin tayi aure. Sai dai bayan auren nata yayarta da suke uba ɗaya wadda itace ta uku a gidan itama ta sake ɓallewa tai aurenta a birnin Bina. Yayinda hajiyar birni ta cigaba da zama da sauran ƴaƴan nata biyu suna neman arziƙi ta kowacce irin hanya.      Sai dai kuma bayan shuɗawar wasu shekaru da adadinsu bai wuce uku zuwa huɗu ba itama babbar yayarsu tai aure anan cikin Loss ɗin.  Amma kuma sai aka samu matsala auren bai wani yi ƙarko ba ya mutu sakamakon mijin data aura baisan haihuwa. Ta fito da ciki inda ta haifi ƴan biyu, suka kuma cigaba da zama anan wajenta, dan duk bushewar zuciya irin na hajiyar birni bata amince ƴaƴanta suyi nesa da itaba. Duk inda zaka kaje da rana ka dawo ka kwana a gida. Koda babbar yayar su Asabe ta yaye yaran nata sai ta sake wani auren duk da hajiyar birni bata so. A wannan karon tayi auren ne a jihar Dokato, inda shima auren bai kai ko'ina ba ya ƙare sakamakon jarababbiyar kishiya data samu. Nan ma ta fito da yaro, duk da shi sai da akai kicimilli kafin ubansa yabar mata akan tilas. Bayan fitowar tata kuma ƙanwarta mai bi mata itama ta auri wani ɗan siyasa mai faɗa aji anan Loss (Aunty Hannah), sai dai a nan Bingo suka zauna.      Itakam ta zauna harda yarinyarta guda data haifa da shi, sai dai sheka guda kenan auren ya mutu ta dawo gida da zama itama, ta kuma faɗa harkar siyasa dalilin sanin manyan mutane da tayi tun tana gidan tsohon mijinta ya taimakama nasarorinta ƙwarai da gaske. Dan a yanzu haka tana kusa sosai da matar shugaban kasa harma da shi shugaban kasa ɗin kansa, duk da dai bata fito da hakan a fili ga mutane saboda tsohon mijinta. A taƙaice dai a yanzu haka hajiyar birni duk tana tare ne da yaran nata da jikoki huɗu a wannan gida. Sai kuma ƴarta ta uku dake aure a Bina itama da yaranta uku. Sai Asabe mai yara huɗu, kuma sune za'a kira kamar manya a jikokin na hajiyar birni duk da uwarsuce ƙarama.      Bayan magiya da roƙo da aka dinga mata tare da yayun Asabe biyu da suka kasa zaman aure suma sai ta amince. Sai dai ta amince ne da sharaɗin zasu tashi su nema na kansu dan bazata iya ciyar dasu har su huɗu ba. Kai tsaye Asabe ta amince bisa shawarar yayun nata da suka kwaɗaita mata wani abu daban ba wanda zuciyarta take ƙyamata ba a yanzun.       To ayanzu dai haka gasu a zaune bisa sharaɗin neman nakan nasu, wanda a dalilinsa hajiyar birni tace su Raudha su shirya bayan salla zasu fara mata aiki a restaurant ɗinta. Dan zasu iya samun wasu ayyukan a dalilin zamansu wajen, tunda masu hannu da shuni ne ke dabdala akoda yaushe.                 Kamar koda yaushe tunda suka zo garin yau ma ta buga uban tagumi bayan kammala aikin gidan da a yanzu ya zame musu tamkar wajibi ita da sauran ƴan uwanta. Sai dai halinsu na rashin son moriya kesa duka aikin ya dawo kanta sai abinda Yasmin taɗan iya tsakura a ciki ta rage mata. Duk da azumi ne haka take dagewa ta gyara komai tsaf, hakan ya saka gidan canjawa cikin ƙanƙanin lokaci, da'alama dama rashin zama a gyarashine ya sashi canja kamanni......       “Raudha!”.    Asabe ta kirayi sunanta da ɗan ƙarfi a karo na biyu. Firgigit ta juyo ta kalleta dan sam bataji na farko ba.       Hannu Asabe ta shiga tafawa na taraddadi tana salati. “Oh ni Asabe Raudha wai mi kike son maida kanki ne? Duka shekarunki nawa da zaki jefa kanki cikin masifar tunane-tunane mike damunki?”.       “Mommy babu komai fa, kawai na zaunane naɗan huta Yasmin ta fito wanka nima na shiga”.       “Ƙarya kike Raudha, ki faɗamin gaskiyar abinda ke damunki tun kafin mu saɓa.”       Ajiyar zuciya Raudha taja da ɗan ƙarfi tana haɗiye ƙwallar data cika mata ido. Cikin yunƙurowar dukan damuwar dake akan ƙirjinta ta fara magana. “Mommy so nake na koma islamiyya, kinga dai rayuwa bazata tafi da ƙyau ba babu neman ilimi, tunda babu tabbacin samun cikar burin yin makarantar gaba da sakandire (secondary) inaga ya dace ace mun maida hankali akan na addinin matuƙa, a ƙalla dai mun mori wani yanki na arziƙin duniya dazai amfanar damu har a lahira. Amma idan na ɓata miki rai a zancena kiyi haƙuri”.          Sosai zuciyar Asabe ta karye da tausayin ɗiyar tata. Ta sani duk cikin ƴaƴanta babu mai nutsuwar Raudha. Yarinyace mai hankali da sanin yakamata. Ya rinyace abar alfaharin kowaɗanne irin iyaye. Sai dai yarinyace mai murɗaɗɗen hali da wuyar sha'ani. Ba komai take kallo dai-dai da ra'ayin mutane ba, ta rasa inda ta kwaso wannan bauɗaɗɗen halin nata da taurin zuciya. A ido zakai mata kallon mai sauƙin kai, amma sam ba haka baneba, wanda ya nutsu ga fahimtar halin Raudha ɗinne kawai zai gane ra'ayinta yasha banban dana mutane.......       “Mommy kiyi haƙuri..” Sassanyar muryarta ta katse tunanin Asabe. Guntun murmushi ta saki tana kaiwa zaune kusa da ita, tare da kai hannu ta kamo nata. “Karki damu indai islamiyya ce zan sakaku Raudha, sai dai ki sani bazai zama dai-dai da yanda kike zuwa ta gida ba har sau sama da uku. Saboda kinga nan zaku ringa zuwa wajen aiki, kinga dai yanda sauran ƴan uwana ke tsaye bisa ƙafafunsu, babu wanda ke zaune yana dogaro da Gwaggo. Kowa neman na kansa yake yi ta yanda nima bazai yuwu na zauna na zuba ido Gwaggo ta cigaba da ɗawainiya damu ba”.            “Hakane Mommy, sai dai ina roƙon dan ALLAH komi zamuyi ya kasance bisa ƙyaƙyƙyawar hanyar da bazamuyi dana sani ba watarana mu da ke. Bazan ɓoye mikiba Mommy wlhy sam rayuwar gidan nan batamin daɗi, nafison hutawa....”         Harara Asabe ta dalla mata da ture hannayenta a cikin nata, rai ɓace tace, “Uban hutawa kikafi so mara mutunci, Raudha bar ganin ina lallashinki wlhy zan ɓata miki rai. Duk da buhun wulaƙanci da tozarci da ubanku yay min har kike iya kallon cikin idona kina faɗamin baƙya son nan kin fison Hutawa. To dan ALLAH ga hanya nan koma Hutawar mtsoww mara mutunci kawai”.       Hayaniyar Asabe ce ta fito da Hajiya Mama babbar yayar su Asaben da yau bata fita ko'ina ba tana gidan tana barci.      “Asabe lafiya? Wa kikema ihu haka?”.      “Wannan mara mutuncin yarinyar Raudha mana.”     Ta faɗa a hasale tana harar Raudhan datai ƙasa da kanta hawaye na gangaro mata bisa kumatu. Cikin ɓacin rai Asabe taima yayar tata bayani kamar ta rufe Raudha da duka dan taji zafin maganar datai sosai a ranta. Itama Hajiya Maman faɗa tahau Raudhan da shi sosai har tana mata gorin ubansu bai iya komaiba sai bin mata kamar tsohon bunsuru da busa sigari. Ba Raudha kaɗai ba, hatta su Fatisa wannan furuci na Hajiya Mama ya zafesu a rai matuƙa. Ana tsaka da wannan kicimilli ɗayar yayar Asaben da suke kira Aunty Hannah ta shigo gidan. Da alama fita tayi, dan sanye take da kaya na alfarma sai bula ƙamshi take. Babu yanda za'ai mai kallo yace daga wannan gidan ta fito duk da shima gidan nada ƙyau gwargwadon iko. Sai dai shigar tata tafi kama data hamshaƙan mata da duniya ke kan ganiyar ƙaunarsu da rungumarsu a jikinta. Ta ajiye key ɗin motar ta bisa centre table ɗin falon tana kaiwa zaune.         “Nikam lafiya kuka rufe yarinya ƙarama da ihu tamkar wasu kishiyoyinta?”.        Sanin halinta na rashin son ganin ana takurama yara Hajiya mama tai saurin faɗin, “Hannah bar wannan ba abar goyon baya baceba....” nan itama ta shiga zayyana mata abinda ya faru da Raudha ta faɗa harya fusatasu.        Saɓanin su ita murmushi tayi tana gyara zama saboda wani abu daya cuɗanya tunaninta da zancen Raudha ɗin cikin ƙanƙanin lokaci, har takai ƙwaƙwalwarta ta haska mata wani nasara a ƙananun daƙiƙu, dan yanzu haka daga government house take.        “Raudha badai islamiyya kike so ba? To zakije islamiyya”. Ta faɗa murmushinta na sake faɗaɗa tare da shafa kan Raudha a hankali. Su Asabe na buɗe baki da nufin yin magana ta girgiza musu kanta tana miƙewa. Dukansu binta sukai da kallon mamaki harta shige cikin ɗakin barcinta. Bawai amsa buƙatar Raudha ɗin bane abin mamaki a wajensu, dan sun san itaɗin mace ce mai son yara sosai, sannan ma tun zuwan su Asabe gidan kowa ya fahimci irin son da take nunama Raudha, dan ko abu zata saka ai mata kafin ta saka su Fatisa ta saka Raudha, sannan har zama take suyi hira da Raudha ɗin. Abinda ya basu mamaki ta shigo a yanayin damuwa sosai, amma dagajin abinda suke ɗauka laifi ga Raudhan sai saɓanin hakan ya bayyana a fuskarta, dan a zahiri tamkar abinda Raudhan tayi ne ya warware dukan damuwar data shigo da shi cikin gidan.........✍ _Tofa minene a ran aunty Hannah da har yay dai-dai da burin Raudha kuma?🤔_ ___________________ *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/1, 11:46 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 9_* ..............*_GOVERNMENT HOUSE_*         Sosai jam'iyya mai mulki ke shirin kamawa da wuta a wannan ɗan tsukun a dalilin shirun party Chairman da shugaban ƙasa game da batun ɗan takara. Bakajin komai sai tsugunne-tsugunne da kace nace. Dan a wannan gaɓar ba wai jinta bakin su party Chairman ne kawai keda amfani ga jamiyya ba. Hatta manyan jam'iyar an zuba musu na muzurune game da kaiwa da kawowa da suketa famanyi cikin duhun dare.       Wasu a cikinsu na goyon bayan shugaban ƙasa ne kai tsaye, yayinda wasu ke kaiwa da komowane akan nasu ƴan takarar da suke fatan a tsaida domin cancanta ko wani burinsu na daban tamkar yanda shima shugaban ƙasa keda tasa manufar shi da muƙarabbansa na bayan fage, harma da wanda suke a cikin tafiyar mulkin tsundum. *_01:32am_*          Agogo ya nuna a sirrintaccen falon dake fadar shugaban ƙasa ke ganawa da shaƙiƙansa na siyasa masu faɗa aji a bayan fage dama a zahiri ga jam'iyyar. A zahiri su ɗin manyane na ƙasa da ko kwatancen arziƙi sukai da kai idan da rabo sai ka haye. Da taimakonsu shugaban ƙasa ke mulki bayan UBANGIJI ya ƙaddara hakan, duk da dai akwai wasu gwasaken ɓoyayyu. Inda yay biyayya ga dukan tsarinsu ya mora suka mora. Daɗin hakan yasa basa buƙatar kuɓucewar mulkin a hannunsu, gudun kar wanda zai faɗa a hannunsa ya gagara zama ƙarƙashin mulkin mallakarsu da faɗa aji. Hakan yasa su yanke shawarar sake ɗora wanda zai iya binsu sau da ƙafa, sai dai sun hanga sun hango matsalolin dake cikin hakan ga dukkan waɗanda suka hasaso ɗin kai tsaye. Da ga ƙarshe bayan wasu dalilai suka yanke shawarar bama tsohon Alƙali kuma shahararren ɗan kasuwa Alhaji Hameed Taura takarar, da shirin bayan anyi komai an gama mulki ya samu zasu salwantar da rayuwarsa wanda zasu bama mataimakinsa ya maye gurbinsa. Sunyi wannan tunanin duk da cewa Alhaji Hameed Taura ɗayane da ga cikinsu, sai dai sam baisan akwai wata alaƙa a tsakaninsu su huɗu da suka killace kansu da itaba wadda babu shi. Sannan baisan ɓoyayyar manufarsu mummuna akansa ba tun shekaru masu yawa da sukasha auna rayuwarsa ba'a dace ba, saboda kwanansa basu ƙareba dan a hannun ALLAH suke. Babban dalilin zaɓarsa domin sake kawo kujerar shugaban ƙasa yanada alaƙa da farin jinin da ALLAH yay masa ga al'umma saboda ɗunbin ƙyautatawarsa ga talaka. Bashi da ƙyashi balle wulaƙanci. Ya cicciɓa mutane da yawa talakawa da sukai arziƙi a ƙarƙashin dukiyar da ALLAH ya mallaka masa. Bashi da girman kai, bashi da izza. Sannan baya ɗaukar raini ga dukkan wani maiji da kansa koda ace ya fisa arziƙi ne. Bai taka kowa bai yarda a takashiba shima.       Su kansu kusan kaso biyu bisa ukun dukiyoyinsu kaso biyu na Alhaji Hameed Taura ne. Wannan yana ɗaya daga cikin manyan dalilan da yasa zukatansu suke jin tsoron kar wataran ya amsa su koma baya. Shiyyasa suka sha auna halaka rayuwarsa amma ALLAH baisa sun dace ba. Hatta ɗansa *Basheer Hameed Taura* sunsha kai masa hare-hare ALLAH na kareshi. Rashin nasarar hakan ta sakasu komawa kan jikansa namiji tilo shima guda ɗaya a cikin ƴaƴa goma sha shidda da ɗan nasa Basheer Hameed Taura ya haifa mai suna *_RAMADHAN B. HAMEED TAURA_*. Sun so tsunduma rayuwar Ramadhan a harkar shaye-shaye tun yana secondary school ALLAH ya tsallakar dashi. Dan kuwa bai jima da farawaba ALLAH ya fargar da Uwargida kuma amarya ga Alhaji Hameed Taura, *Hajiya Firdausi Amin Taura* kenan. Mace ce jajirtacciya kuma tsayayya akan ahalinta. Sam bata da wasa koda akan fuskane. Mace ce mai addini matuƙa da son taimako. A hannunta Ramadhan ya girma tun daga yaye, duk da kuwa suna gida ɗaya mahaifiyarsa sam bataso hakan ba, musamman da taga bayanshi bata sake haihuwar wani ɗa namijinba a cikin ƴaƴa shidda mata data sake haihuwa da Basheer Hameed Taura. Bama itaba kaf sauran matan Alhaji Basheer Hameed Taura ɗin guda biyu duk basu da ƴaƴa maza sai mata. Sai dai babu yanda ta'iya, dan sam Anne ba sakarar uwar miji bace da matar ɗa zata taka koda da kirsane. Babu ruwanta da rayuwarsu bare harkarsu, dan bata taɓa sakama matan ɗan nata idoba balle damuwa da mi suke ciki. Dan da ace ita ɗin sakaraice da tasha matuƙar wahala a hannun Gimbiya Su'adah. Gimbiya Su'adah mace ce mai izza da tsananin taƙama kasancewarta ɗiyace ga sarkin jihar Bina. Sannan ƴar gata kuma sangartacciya mai ji da mulkin gidansu. Mace ce mai shegen girman kai da ƙyamar talaka, dan sam bata biyo ƙyawawan halayar mahaifinta ba. A ƙasar amuruka suka haɗu da Alhaji Basheer Hameed Taura yayin karatu, inda soyayya mai ƙarfi ta ƙullu harta kaisu ga aure kasancewar su ƴaƴan ƙwarya tabi ƙwarya.            Bayan ceto rayuwar Ramadhan da Anne tayi daga faɗawa shaye-shaye suka sake harar rayuwarsa akan neman mata. Sai dai anan ALLAH ya karesa, dan baima saka matan a gabansaba balle su damesa. Musamman daya kasance yanada ƙananun shekarune dama a wancan lokacin. Abokan banza suka ƙirƙirar masa da sukaso fara jansa yawon dare, tunda ya farga da halayensu ya janye jikinsa. Dan Ramadhan mutumne daya gado halayen iyayen nasa ta ɓangarori biyu. Akwai halin mulki na ɓangaren mahaifiyarsa tattare dashi. Akwai kuma halin dattako na ɓangaren kakansa dake yawo a jikinsa. Hakanne ya sakashi zama mai murɗaɗɗen hali tun daga yarinta har girma. Bazamu ce dashi miskili ba. sai dai zamu kirasa mutum mai tsananin girman kai da ɗagawa. Ba komai yake so ba, ba komai ake saka yaso ba, sai idan shine yaso a karan kansa. Da yawan lokuta Anne ce kawai ke iya tanƙwarashi ta ƙarfin tsiya saboda itama tanada zafi sosai.        Su *Alhaji Wali Bajau* basu daina bibiyar rayuwar iyalan Alhaji Hameed Taura ba musamman Ramadhan da suke kallo matsayin zuciyar gidan har yakai girma. Da tsiya-tsiya da makirci Alhaji Haladu Gwandu ya ƙulla soyayyar ɗiyarsa da Ramadhan har takaisu ga aure a shekarar daya kammala karatunsa akan lauya. *Amnah* yariyace ƙyaƙyƙyawa kuma ƴar gayu kamar yanda Ramadhan ke buƙata. A shekaru kaɗan ya ɗarata hakan ma dai-dai da ra'ayinsa ne, dan sam baison auren yarinya ƙarama yace sun cika shirme da ƙuruciya wa miji. Soyayya ce ta haɗa Amnah da Ramadhan a zahiri, a baɗini kuwa su Alhaji Gwandu sun shirya hakanne da manufa, dan ta bayan fage suka dinga amfani da Amnah suna cutar da Ramadhan. Burin Ramadhan aikinsa na lauya, tare da faɗaɗa karatunsa na Addini dan tun yana shekara sha bakwai ya sauke alkur'ani mai girma ya fara hadda, saboda Anne bata da wasa, ga shi ALLAH ya bashi ƙwalwar karatun shima. Sai dai burin mahaifiyar Ramadhan gimbiya Su'adah ba haka bane. Burinta duk dukiyar Taura Family ta dawo hannun Ramadhan ne, dan haka taita ƙoƙarin jan hankalin mijinta harya amince da jawo Ramadhan ɗin cikin babban kamfanin (company) na taura aka ɗaurasa matsayin oga kwata-kwata. badan ya so ba ya amsa, dan shi hakan baya cikin burinsa. Amma nasihar tsoho Hameed Taura ya sakashi amincewa akan tilas ya fara musu aiki. Lokaci-lokaci kuma yana taɓa aikinsa na lauyanci a ɓoyo dan gudun ɓacin ran mahaifiyarsa mai zafin zuciya da son nuna gadara ga kowa.         Suna shekar ta uku da aure Amnah ta haihu ƴarta mace, sai dai kuma an haifeta sikila ne tamkar uwar tata data kasance sikilar ce dama. Ko kusa hakan baisa ubanta ƙin son kayarsa ba duk da sam gimbiya Su'adah basan auren takeba. Amma kasancewar itama uban Amnah ɗin ba koma baya bane akan juya kuɗi ya sata ɓoye ƙiyayyar auren a ƙasan zuciyarta, sai idan abin nata ya motsane taita azabar masifa.      Hawan Ramadhan MD a Taura company matsaloli sukaita faruwa na ɓatan kuɗaɗe da wasu asarori da aka rasa musabbabinsu. Tun su Alhaji Hameed na kawaici hartakai shida mahaifin Ramadhan Alhaji Basheer Taura sun zaunar dashi sun masa ƙorafi da tambayar mike faruwane haka company keta baya maimakon gaban da suke fita da nasarori?.      Amsa ɗaya ce shima baida masaniya. Amma yana kan bincike da ƙoƙarin daƙile komai. Tun ana tattaunawa iya su uku harta kai Anne ta shigo tafiyar, hakama sauran matan gidan sun sani. Kowa yana ɗaura zarginsa akan Ramadhan da tunanin ko yana wata harkar banza ne ta kuɗi a ɓoye?.     A ranar da su Alhaji Balarabe Gizo suka shirya kai rayuwar Ramadhan ƙasa yayi dai-dai da ranar birthday ɗin ƴarsa Haseenah ƴar shekara biyu cif a duniya. An shirya liyafa ta gani ta faɗa tare da gayyata ta mutanen arziƙi Alhaji Haladu Gwandu ya baiwa Amnah ruwan addu'a da aka gauraya da guba akan ya amso ma Ramadhan ɗinne saboda ciwonsa na diabetis, Ramadhan nada diabetis sakamakon ya zame musu tamkar gado ne. Alhaji Hameed Taura nada shi, hakama Alhaji Basheer Taura, shima Ramadhan ɗin haka da wasu daga cikin yara matan gidan. Sam Amnah batai tunanin mahaifinta zai iya cutar da Ramadhan ɗinta ba. Dan haka ta ɗauka ruwan addu'a da ƙyaƙyƙyawar zuciya takai masa. Sai dai an samu akasi bayan gama birthday party lafiya an watse ta buɗe fridge a gajiya ta ɗauka goran da ruwan addu'ar yake da tunanin ruwa ne saboda fitilar kitchen dake a kashe saita falo data ɗan hasko kaɗan ta sha. Tana sha Haseenah najan hannunta da mata gwarancin ruwa ruwa. Sai da tasha sosai sannan ta bata tasha itama.      Wannan magani da Amnah tasha da ƴarsu Haseenah ya zama sanadin barinsu duniya. Dan kuwa azababben ciwon ciki ne ya baibayesu ita da ɗiyar har sai da aka kaisu asibiti, inda tunkan suje ma Haseenah ta rasu saboda ƙarfin gubar, Amnah kuwa sai kusan asuba itama tace ga garinku nan. Likita ya tabbatar musu hanjinsu ya kakkatsene ita da ɗiyarta saboda ƙarfin gubar da suka sha.        Kwatanta irin tashin hankalin da Ramadhan ya shiga a wannan lokaci ɓata bakine. Bama shiba kowama da ke da alaƙa dasu wannan al'amari ya taɓa masa zuciya. Dan kowa dai ya fahimci guba aka ajiye musu. Sai dai ba'asan kowa ya ajiyeba saboda Amnah ita babanta yaba hannu da hannu batare da kowa ya sani ba. Ya kuma jaddada mata maganin diabetis ne kar Ramadhan yasha sai randa yake aiki musamman motsa jikinsa. Ita kuma ALLAH baisa ta bashi maganin ya sha da rana ba ta bari sai an tashi a birthday ɗin Haseenah. Ashe da rabon ajalinsune a ciki.      Sosai Ramadhan ya fita a hayyacinsa. Dan yana mayuƙar son matarsa da ƴarsa duk da lalurar dake tare da su ta sikila. Iya bincike anyi a gidan babu wani bakin zare da aka samu sai tunanin cikin masu zuwa birthday ne suka ajiye gubar kawai. Tsabar yanda Ramadhan ya tada hankalinsa akan son gano wanda ya aikata ya saka su Alhaji Haladu Gwandu da abin yay matuƙar taɓawa da tunzurawa sakawa aka kai Ramadhan ƙasar Ukraine wai ganin likita. Sune suka tsarama likita ƙaryar da yace kar a sake yarda Ramadhan yay zaman NAYA sai bayan wasu shekaru harya manta da abinda ya faru. Sunyi hakanne domin su nisantashi daga bincike ko bibiyar ainahin gaskiyar lamarin da suka san reshe ya juye da mujiyane. Dan haukane kawai Alhaji Haladu Gwandu baiyiba a dalilin rasuwar shalelensa data bar duniya a dalilinsu.     Ƙura ta lafa, abubuwa sun canja, shekaru sunyi gudu har kusan biyar da faruwar komai. Ramadhan yayi jiyyar zuciya data gangar jiki harya warke, amma anyi-anyi ya dawo NAYA yaƙi. An kaɗa dambu da takiya yace shi da NAYA har abada. Babu irin roƙo da lallaɓa da basu masaba musamman gimbiya Su'adah da take kasa ɓoye ɗunbin soyayyar da take masa koda a idanu ne amma ya kafe akan bakansa. Da ga ƙarshe ma sai ya koma U.S da zama. Kafiyarsa da murɗin hali yasaka kakansa Alhaji Hameed Taura yin fushi yace su barsa ya dawwama acan dan ALLAH karya dawo. Ya kuma saka sharaɗin koda wasa kar wanda ya sake zuwa dubashi har Mahaifinsa da gimbiya Su'adahn. Inko ba hakaba zai saɓama mutum a gidan.     Wannan shine dalilin da yasa Alhaji Hameed Taura baya son ko maganar Ramadhan ai masa a gidan, duk da yana tsananin kewarsa a kusa da shi da begensa shima. Dan shi kaɗai ke zuwa dubashi a ɓoye batare da shi kansa Ramadhan ɗin ya sani ba.      Yayinda Ramadhan kuma har yanzu zuciyarsa ke cike da burin binciko koma wanene da alhakin kashe masa iyalinsa, dan haka a tsahon shekarun nan babu abinda yake saƙawa da kwancewa bayan kasuwancinsa daya maida hankali dayi shi kaɗai sai hanyar dazai yi binciken yanda rayuwar matarsa da ƴarsa ta salwanta. A cikin wannan halin kuma Anne ta kawo shawarar Ramadhan B. Hameed Taura ya maye gurbin kakansa a kujerar shugaban ƙasa da akai masa tayi. Inda dudu shekarun Ramadhan B. Taura 36 a duniya. Ya rasa iyalansa yanada shekaru 31. Yanada ashirin da bakwai yay aure. A yanzu shekaru 5 cif da faruwar komai kuma.      A hasashe ba'a taɓa samun wani shugaban ƙasa mai adadin shekarunsa na ƙuruciya ba a ƙasar ta *NAYA* ba sam. ★         “Kana nufin dole kenan mu amince da zancen Alhaji Hameed Taura indai muna buƙatar cikar burinmu Your Excellency?”.      Monday Mazier ya faɗa a ɗan hasale.      Shugaban ƙasa da Alhaji yaro glass suka kalli juna suna murmushi mai kama da takaici suma. Yayinda Alhaji Haladu Gwandu ya dafa kafaɗar Monday Mazier ɗin yana faɗin. “Mr MM cool down abeg. Muma duk irin zafin da kakeji munjisa a lokacin daya tabbatar mana ya amsa tayinmu, amma kuma jikansa ne zaiyi bashi ba. Ƙwarai da gaske ya shammacemu, shammata maiban mamaki. Dan yayi hakane dan mu janye buƙatarmu kodan kasancewar jikan nasa yaro, tunda yana ganin ba'a taɓa shugaban ƙasa mai ƙarancin shekarunsa ba a wannan ƙasa ta NAYA. Sai dai kodana zauna nai zari sai banji komai ba, domin Ramadhan baida maraba da hoton bango da kowa zaizo ya kalla ya wuce manne a falo batare daya amfana masa komaiba. Shine surikina da yarinyata ta rasa ranta a dalilinsa, yana can U.S tsahon shekaru biyar tamkar zararre. A ganina wannan damace a garemu mai sauƙi, duk da naji a raina Taura yayi hakane danya dawo da hankalin yaron gida kamar yanda sukaita fata a shekarun baya yaƙi hakan. Amma idan Taura yasan wata ai baisan wataba, Idan muka fitar da yaron matsayin ɗan takara zamu kawo wani sabon abu a ƙasar nan da ba'a taɓa yiba, sannan matasa zasu yarda da gaske muna tare da su. Babu tantama mulki zai cigaba da kasancewa a hannunmu ne”.         “Woow exactly my man”. Mr MM ya faɗa yana bama Alhaji Haladu Gwandu hannu suka tafa bakinsa washe da dariya tamkar yanda shugaban ƙasa da Alhaji Yaro glass da Alhaji Balarabe Andu keyi suma alamar hankalinsu yaɗan fara dawowa jikinsu.      Alhaji Yaro glass ya gyara zama da faɗin, “Tabbas nima sai yanzu na fahimci manufar Taura na yarda cikin sauƙi, kuma hakan yamin daɗi, dan mu idan bai saniba wata damace ta ɗaukar fansa sau biyu akan abu guda. Ramadhan zai hau mulki na tsahon shekaru biyu kacal, sannan zai mutu sau biyu......”       “Sau biyu kuma?”. Shugaban ƙasa ya katse Alhaji Yaro glass cikin rashin fahimta.      Alhaji Yaro dake murmushi yace “Ƙwarai kuwa sau biyu, dan dole ne mu ɗauka fansar Amnah data mutu dominsa, sannan mu kashesa adalilin taurin ran kakansa da ubansa. Na farko zai kasance cikin nasararsa da jin daɗin mulki a shekarar farko, a shekara ta biyu zai fara ciwo a dalilin guba da zata zagaya jininsa zuwa ɓargo da jiki. A shekara ta uku muyi bikin mutuwarsa da biznesa vice president ya hau kujera ya shekara biyu biyar cif kenan. Shekar ta ƙarshe a sake sabon zaɓe wannan shine amsar mutuwa biyu”.      Ya ƙare maganar yana ƙyalƙyalewa da dariya, suma sauran suna tayasa kamar wasu zararru. Sai da sukai mai isarsu kafin suyi shiru suka koma shan shayi da cigaba da ƙulla tsiyatakunsu........✍ 🤔🤔Hummm wani lokacin ma rasa abun magana ake. *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/2, 11:37 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 10_* .............*_WASHE GARI_* shugaban ƙasa yay waya da god father nasu na siyasa dake faɗa aji a ƙasar baki ɗaya, sai dai a siyasance babu mai iya jin sunayensu. Ya sanar musu dukanin tsare-tsarensu. Sosai nasu tsarin yay masa shima harya yaba musu, dan yasan komai sai dai suna bayan fagene, ya kuma tabbatar musu komai zai tafi dai-dai dan Alhaji Hameed Taura a tafin hannunsu yake.       Cikin farin cikin yabon da shugaban ƙasa ya samu yace, “Na gode ranka ya daɗe. ALLAH ya ƙara girma da ɗaukaka. Badan ku ba babu mai ganin koda hotonmu a ƙasar nan. Shiyyasa muke addu'ar tsahon rai a gareku domin muyita cin karenmu babu babbaka”. (Ashe kasan shi mai mutuwane, rayuwarsa mai ƙarewace excellency. Inhar kuwa zai mutu to bai isa amfana maka komaiba face wanda yazo cikin ƙaddarar duk wanda kuka hara. ALLAH ka bamu shugabanni na gari🙏🏻🤦🏻).      Bayan ya gama masa kirari da yabon dake sake buɗa masa kai ya ɗora da bayanin...       “Ranka ya daɗe a yanzu haka mun gama yanke shawarar ganawa da shi yaron kawai muji ta bakinsa shima”.       “Tunani mai ƙyau, sai naji ku”. Daga haka ya yanke wayar. Shugaban ƙasa ya cireta a kunnensa yana jan kakkauran tsaki da ballama wayar harara. Cikin ƙunƙuni yace, “Mugu ƴan hana ruwa gudu, ALLAH dai ya kusa kasheku muma mu babake ko'ina, daga sama har ƙasan ta zama tamu. Dan badan kuba da mune taurarin duniya ta kowanne fanni.”       (Kai jama'a kamar bashi bane ya gama masa ƴar murya yanzun🤣, siyasa shegiya😂). *_TAURA HOUSE_*         Kamar yanda al'adun ƙasashen da  hausawa yake dama musulinci baki ɗaya, irin wannan lokacin ko nace wannan ranar ranakune masu muhimmanci na shirye-shiryen bikin salla. Tamkar kowanne gida dake shiri haka Taura family house ma keyi ƙwansu da kwarkwata. Danko duk ƴammatan gidan zaka gansu da zanen lalle baƙi ko ja. Wasu sunyi kitso wasu gyaran gashi kawai. Hakama matan Alhaji Basheer Hameed Taura babu koma baya dan duk ɗinsu ƴan gayu ne kuma ƴaƴan manya, dan kowacce tana alfahari da irin gidan data fito ne.       Misalin ƙarfe tara na dare da yay dai-dai da sanarwar ganin jinjirin watan shawwal daga bakin mai girma sarkin musulmi ƙararrawar dake sanar da taron meeting na iya manyan gidan ta kaɗa. Ba sabon abu bane hakan a duk daren kowacce salla, sai dai a wannan karon taron meeting ɗin yazo da banbanci. Sakamakon manyan gidan kawai ake buƙata banda yara.      Cikin tunani da taraddadin lafiya duka matan Alhaji Basheer Hameed Taura suka kimtsa kawunansu zuwa sashen surukan nasu domin amsa kira. Sai tsoffi guda biyu da suka kasance ƙanne ga Alhaji Hameed Taura da suma suke zaune a gidan a halin yanzun. Sai ƙanin Alhaji Hameed Taura ɗin autansu da ya iso da iyalansa daga ƙasar Dubai a daren jiya domin halartar bikin salla da sukanzo a kowacce shekara...                       Duk wani wanda ake buƙatar gani a katafaren falon na alfarma da an tsarasane kawai domin gudar da meeting na ahalin gidan ya iso. Kowa ka gani zaune yake cikin mutuntawa ga dattijo Alhaji Hameed Taura da matarsa Anne. Dan dukan matan Alhaji Basheer kansu a ƙasa yake kasancewar suna gaban surukai.     Bayan an buɗe taro da addu'a Alhaji Hameed Taura da ahalin gidan ke kira da suna Bappi yay gyaran murya da tasaka kowa sake nutsuwa a wajen.       “Da farko dai ina tayamu murnar ganin wannan wata na shawwal da rai da lafiya. Ina roƙon UBANGIJI ya amshi ibadunmu da mukayi, ya yafe mana kura-kuranmu. Yasa muna da rabon ganin na gaba da rai da lafiya.”      A tare suka amsa da (amina).     Ya cigaba da faɗin, “Nasan zakuyi mamakin canzawar zaman meeting ɗin yau, dalilin hakan kuwa ya dangantane ga Ramadhan kacokal”.      Da dauri Gimbiya Su'adah da yaran ke kira da (Maa) ta ɗago jin an ambaci sunan gudan jininta mafi soyuwa. Yayinda firgici da taraddadi ya bayyana cikin ƙyawawan idanunta. Dan batason mi kuma ya samu Ramadhan ɗin ba koya aikata. Tunda yau kusan satinsu biyu rabon da suyi waya sakamakon ta masa maganar ya daure yazo musu salla gida......         .... ya katse mata tunani da cigaba da faɗin, “Wani babban al'amarine ya tasoma gidan nan, sai dai mun ɗaukesa kacokan mun rataya ga shi Ramadhan saboda wasu dalilai. Na farko yin hakan zaisa ya dawo kusa damu dole. Na biyu zaisa yazo shima yay aure. Na uku ya isar da abubuwan da muka kasa isarwa ga sauran mutane bisa ga abinda ALLAH ya azurtamu da shi.”      Duk da a dunƙule yay dukan bayanin hakan bai hana farin ciki bayyana a fuskar Maa ba. Ji take tamkar Bappi ya mata albishir ne da wani yanki na farin cikin samun ƙyaƙyƙyawar makoma. Tana matuƙar burin ganin yaronta a kusa da ita. Tsabar jin daɗin hakan harta gama yanke masa matar aure a ranta. Dan wannan karon tanason zaɓama yaron nata matar aure ko hakan zaisa ta sanadin matar ya dawo gareta ba wajen Anne ba....”        Dogon tunanin da gimbiya Su'adah ta tafi yasa har Bappi ya kammala jawabinsa ma bata ƙarasaji wasu abubuwan ba. Sai murmushi take wanda ya kasa ɓoyuwa bisa fuskarta. ★       Ana tashi da ga taron tun kan ta ƙarasa sashenta ta fara kiran wayar gimbiya Asma'u yayarta da suke uwa ɗaya uba ɗaya (Adda Asmah). Su baƙwai mahaifiyarsu gimbiya Naja'atu da ake kira fulani ta haifa, sai dai sauran duk mazane su biyune kacal mata, kuma sune manya. Hakan yasa musu wata shaƙuwa da son juna na musamman dan sun tashine tamkar tagwaye. Kasancewar kuma irin gidansu gidane na tsantsar ƙabilanci da ƴan ubanci yasa kowa da nasa yake shaƙuwa.        Dai-dai tana saka ƙafarta a ƙawataccen falonta na alfarma da yaji kayan more rayuwa har zaman musaltashi zai iya zama ƙauyanci gimbiya Asma'u ta ɗaga wayan. Itama tayi aure tuni, anan cikin garin Bingo ma take, rana ɗaya ma akai musu aure. Sai dai ita tayi kusan shekara biyar bayan aurensu kafin ta samu haihuwa. Yaranta biyu kuma kawai. Mace da namiji.       Batare data dubi su Zuhrah dake zaune a falon kowa na harkar gabansaba ta shige tana mai zolayar yayar tata da faɗin, “Haba ƙasa badai har kin fara barcin naki ba ko?”.       Amsar da aka bata daga can ta sata sakin ƴar dariya tana tura ƙofar glass na corridor ɗin bedrooms ɗinta ta shiga. Ta kan wani tattausan carpet dake a tsakkiyar corridor ɗin ta taka zuwa ƙofar tsakkiya. Ɗaki ne da musaltashi ɓata lokacine. Dan haka kowa ya musalta da kansa. Ƴar sarki matar Alhaji Basheer Hameed Taura. Ta kai zaune tana sake ƙawata murmushin fuskarta da faɗin, “Amin Adda Asmah. Dama albishir na kiraki nai miki”.       Tai dariya saboda zumuɗin Adda Asma daga can. “Oh god hajiyar ruɗu kwantar min da hankalinki. Bafa wani abu bane yaronkine kawai zai dawo NAYA, dalilin kiran naki kuwa maganar aure da mulki da ya sakko a ciki ne. Inaga lokaci yayi da zamu cika burinmu na haɗa auren Ramadhan da Aina'u tunda ta kammala karatunta”.      Dariya ta kuma saki wadda inba Asma ɗin ba babu mai iya ganinta a saman fuskar Gimbiya Su'adah saboda izzarta da girman kai. A take a wajen suka gama yanke hukunci komai game da auren ƴaƴan nasu, batare da gimbiya Su'adah tayi wani dogon tunani ko bincike akan mike a ran Bappi ba. *_★★HAJIYAR BIRNI HOUSE★★_*                 Tun shigowarta ɗakin kwance kawai take tana faman murmushin samun mafitar damuwar data shigo da ita cikin gidan. Dan tabbas da damuwa ta shigo kamar yanda hasashen ƴan uwan nata yake, damuwar da keda nasaba da zuwanta wajen first lady.       Ita ɗin mace ce ƙyaƙyƙyawa kuma gogaggiya, inda a dalilin harkar barikinta ta haɗu da Alhaji Yaro glass babban ɗan siyasa dake riƙe da babban muƙami a ƙasar ta NAYA. Tun a haɗuwarsu ta farko taji sonsa a ranta, inda akai dace shima ya kamu. Dan haka sukai aure cikin ƙanƙanin lokaci. Sai dai abinda bata saniba Alhaji Yaro glass a ƙarƙashin mulkin mace yake a cikin gidansa. Dukkan faɗa ajinsa iyakarta waje ne. Daya taka gate ɗin gidansa sunansa mijin hajiya Fanta. Tabbas ta fuskanci ƙalubale kala-kala a zamanta da Hajiya Fanta da bazasu musaltu ba, har takai sai da ta tsigeta a gidan hankalinta ya kwanta. Ta kuma kauda hankalin Alhaji Yaro glass da ga gareta baki ɗaya, duk da ƙulafucin son komawa garesa da takeyi musamman saboda ƴarsa ɗaya tilo da suka haifa tare dake wajenta. Tun farkon zuwanta gidan suke ƙawance da Hajiya Bushira hamada, wadda sam bata shiri da Hajiya Fanta duk da kuwa mazajensu abokaine shaƙiƙai. Koda yake ance ada ƙawayene suma na amana, sai dai ƙawancen ya watse ne a dalilin ƴaƴansu. Mafari kenan Hajiya Bushira taita tunzura Alhaji Yaro glass ya ƙara aure, tun baya biye mata har yaji sha'awar yin hakan lokacin daya haɗu da Aunty Hannah.      Bayan fitowarta a gidan hajiya Bushira tayi iya ƙoƙarinta na ganin Aunty Hannah ta koma gidan Alhaji Yaro glass amma hakan ya gagara, har suka samu nasarar ɗarewa kujerar mulkin ƙasar ta NAYA. Inda Prof... Usama D. Hamada ya samu nasarar zama shugaban ƙasa bisa ƙoƙarin su Alhaji Hameed Taura. Su kuma su Alhaji Yaro glass suka koma gefe matsayin manya sunacin karensu babu babbaka. Dan ko muƙami ɗaya basu amsaba a bayan fage suke nasu mulkin su.      Hankalin aunty Hannah ya sake tashi dan tana son Alhaji Yaro glass sosai, amma sai Hajiya Bushira Hamada (First lady) ta kwantar mata da hankali akan karta damu, inhar tana raye sai ta koma aure gidan Yaro glass. Aunty Hannah tana cikin manyan ƙawayen first lady da suke mata ayyuka a ɓoye, amma tana ɓoye kantane saboda Alhaji Yaro glass.         A yau ma first lady ce ta buƙaci ganin aunty Hannah ɗin tun daren jiya akan wani aikin sirrinsu, a hirarsu ne first lady keɗan tsoguntama aunty Hannah batun wanda su shugaban ƙasa suke son tsaidawa takara, tare da burinsu na salwantar da rayuwarsa daga baya Alhaji Yaro glass ya maye gurbinsa, dan shine sukeso ya zama mataimakinsa. Wannan al'amari ya matuƙar saka Aunty Hannah a farin ciki matuƙa. Har takejin zata iya bada gudunmawarta akan wannan al'amari. Sai dai maganar data biyo bayan hakan ce ta sakata a damuwa, dan kuwa first lady ta sanar mata sun tattauna da shugaban ƙasa akan suna son samawa yaron matar auren da zata dinga musu aiki a kansa batare da sanin kowa ba, amma suna tunanin ta yadda zasu ɓulloma Alhaji Hameed Taura game da hakan. Dan samawarwa Ramadhan matar aure daga ɓangarensu ne kawai mafita da hangen nasararsu a tafiyar. Hakan yasa tacema aunty Hannah taje ta tayata tunani da nazarin mafita dan tana son ita ta fara kawoma shugaban ƙasa mafita koda ƙara samun ɗaukakarta na mata garesa, sannan ita kuma ta zama first lady kodan cusama hajiya fanta baƙin ciki. Dan ba hawan Alhaji yaro glass bisa kujerar matamakin shugaban ƙasa ko zama shugaban ƙasa bane matsalarta ita. Hajiya Fanta ta samu muƙami dai-dai da wanda ta taka shine damuwarta kawai. shiyyasa take so ta shiga ta fita wajen ganin ta nakasa Hajiya Fanta kafin lokacin Aunty Hannah ta koma gidan ta zama tauraruwa a mulkin da Alhaji yaro glass zaiyi.          Wannan shine dalilin shigowarta da damuwa gidan. Sai dai kuma abinda ta tarar na boran Raudha ya kawo mata mafita cikin sauƙi da take tunanin first lady zatayi matuƙar farin ciki da ita har itama ta samu cikar burinta na komawa gidan Alhaji Yaro glass matsayin matar vice president.      Ta saki murmushi mai ƙayatarwa tare da jawo hamshaƙiyar wayarta 1phone ta shiga sarrafata. Kai tsaye number first lady ta laluba. Harta tsinke ba'a ɗaga ba, dan haka ta yanke shawarar sake kira dan tasan saƙon da take shirin kaiwa mai matuƙar muhimmanci ne.      Cikin sa'a kuwa tana gab da tsinkewa first lady ta ɗauka. “Hannah am sorry ina amsa wani call ne. Ina fatan har an samu mafitar ne da gaggawa haka?”.        “Sosai ma kuwa your excellency. Zumuɗin hakanne ma yasa na kasa haƙurin bari sai nazo nace bara na kiraki”. Aunty Hannah ta faɗa cikin washe haƙora kamar tana gaban first lady. Itama daga can first lady ta amsa ne cike da zumuɗin son jin yaya akai? Dan haka kai tsaye aunty Hannah ta fara jero mata bayani....         “Akwai yarinyar ƙanwata dake aure acan jihar Ɗillo. Sai dai a wani ƙaramar hukuma suke mai suna hutawa. Yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce son kowa ƙin wanda bai samu ba. Gata ƙarama sosai sweet 17. Tanada yanayi irin na mutane masu haƙuri da komi zatai baza'a zargeta ba. Sannan inada yaƙinin zata shiga ran Alhaji Hameed Harith Taura cikin ƙanƙanin lokaci. Kai harma da uban gayyar kansa dan da gaske yarinyar ta haɗu your excellency......”         “Ban katsekiba Hannah, amma mu minene alaƙar shirinmu da ƙyawunta ko sanyin halinta? Mufa wadda zatai mana aiki kawai muke buƙata batare da matsala ba”.        “Hakane your excellency amma bara na kaiki. Alhaji Hameed Taura mutum ne mai son mu'amula da mutanen kirki, a dalilin hakane mazajenmu suka ɓoye masa ainahin fuskarsu suka aro ta mutuntaka suka yafa ma kansu har takai abotarsu yin tsaho zuwa yanzun. Dan haka bazai yuwu mu samo yarinya mai rawar kai ba akan wannan shirin. Dole ta kasance mai irin suffar Raudha, sannan ƙyaƙyƙyawa. Abu na biyu dole ta kasance ɗiyar masu ƙaramin ƙarfi da basu da wata power ɗin zamtowar yarinyar mai buɗaɗen kai da komai zata iya fahimta idan an sakata tayi, sannan kuma zamu iya juyata ita da iyayenta yanda muke buƙata muma cikin sauƙi dan batasan komai ba sai abinda muka ɗorata a kai”.          First lady ta ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Kai Hannah shiyyasa nake bala'in sonki wlhy. Dan kuwa kanki na ja matuƙa. Sai dai matsalar ɗaya zuwa biyu ce. Matar shugaban ƙasa ƴar 17years, kuma mai kwalin secondary school kawai. kuma ɗiyar ƴar uwarki bayan kinsan shirinmu shine itama idan ta kammala mana aiki rayuwarta zata iya salwanta”.           Aunty Hannah tai ɗan murmushi tana sake damƙe filo a jikinta. Dan ita inhar buƙatarta zata biya salwantar rayuwar Raudha ba komai bane ba a gareta. “Your excellency matsala ta farko ba matsala bace ba. Dubi da shima ɗin yaro ne matashi da zai zam na farko bisa kujerar mulkin ƙasar NAYA. Karatu kuwa ko tana gidansa za'a iya sakata ta fara badan zai amfanemu ba sai dan kawai zai bada kariya ga masu ƙorafin matar president iyakarta secondary. Na uku kuwa karki damu, dan mun rasa iyayenmu ma munyi haƙuri balle ƴaƴa. Ko Samha ce zan iya sadaukar da ita domin samun cikar burinmu (ƴarta fa😱, anya kuwa gsky aunty Hannah ke faɗa🤦🏻). Abinda kawai zamu maida hankali yanzun shine koya mata rayuwar manyan mata da abubuwa.”        “Okay na gamsu da bayaninki, sai dai kuma taya zamu haɗa alaƙar su kuma?”.       “Wannan shine dalilin kiranki your excellency...........”✍ _(Tofa, su Aunty Hannah kumafa🤔🚶🏻)._ *_Yaya kuke gani masu karatu? Shin Ramadhan zai amince ya amsa kiran Alhaji Hameed Taura kuwa zuwa ƙasar NAYA? Harma da tayin zama shugaban ƙasa?? Kokuwa ƴan ƙasar ta NAYA zasu yarda da wannan sabon al'amari na hawan matashi mai jini a jika irin *_Ramadhan B. Hameed Taura_* ne matsayin  shugaban ƙasarsu ne?. koba shekaru ba karku manta akwai matsalar sauran ƴan jam'iyya, akwai ta shekaru, akwai!! Akwai akwai da yawan gsk. Muje zuwa donjin shin yaya zata kaya ne?🚶🏻_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/3, 1:00 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 11_* ............*_SALLA BIKI ƊAYA RANA_*          A duk wanda ka duba yau inhar musulmi ne na ƙwarai zaka fuskanci farin cikin zagayowar wannan rana ta salla bisa fuskarsa. Rana ce da mafi yawan al'umma suka ganta suka kuma sake ganinta. Sai dai hakan baisa ta gunduresuba. A kowace shekara murnar zagayowarta ake yara da manya tamkar lokacin suka fara riskarta.     Ƙarfe goma na safe tawagar ɗunbin al'ummar musulmi dake a sassa da dama na babban birnin ƙasar Bingo da ke a NAYA suka kammala sallar Edi. Bakin kowa a washe yana gaida ɗan uwansa ko aboki. Yayinda irin su Raudha baƙi a garin keta ƙoƙarin ganin sun fito da ga harabar babban masallaci idin domin samun abun hawansu. Dan kuwa dai aunty Hannah ce da kanta ta kwaso ƙwai da kwarkwatar yaran gidan ta taho dasu filin na idi.     Duk da a ƙurarren lokaci su Raudha sukazo Bingo tsaf Aunty Hannah ta haɗama kowansu kayan salla na gani na faɗa. Wanda a zahirin gaskiya first lady ce ta bada maƙudan kuɗaɗe domin yin hakan. Su dukansu matan sanye suke cikin baƙaƙen abayoyi ƙirar Egypt, sai dai ta kowa ta banbanta da kalar adon da yafi buƙata. Kasancewarsu ƙyawawa jinin ƴaƴan larabawa duk da ba kowanne a cikinsu ya biyo iyayen nasu ba sai gasu ɗas tamkar wasu ƴaƴan manyan mutane.       Tafe suke Yasmin da twins na surutu da bada labarin yaran da suka zauna kusa da su basu iya salla ba su Fatisa na dariya. Sai Raudha da kusan ke ƙarshe a bayansu tana tafiya a nutse dan sam bata iya sauri ko garaje ba. Kanta a ƙasa yake tana ɗan kallon yara daketa kaikawo cikin shigar malam bahaushe abin sha'awa. Kamar ance ta dubi gefenta idanunta karaf akan wani matashin saurayi da kallonsa kawai baida daɗin yi. Duk da ranar salla ce kuma shigar farar jallabiya yayi fara ƙal a jikinsa saita banbanta da jikin nasa. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci baiyi kama da mutanen kirki ba.        Gabanta ya faɗi ganin yana gyara wata ƴar wuƙa dake a hannunsa sai ƙyalli takeyi. Abinda ke manne a kunnensa ya kai hannu ya gyarama zama alamar magana yakeyi da wani, dan bakinsa sai motsi yake yayinda idanunsa ke kallon saitin inda yake tunkara. Juyawa tai da ƙyau itama tana duban wajen. Zuciyarta ta ɗan harba sabida yin tozali da wani kamilallen dattijon tsoho ƙyaƙyƙyawa. Duk da shekaru sunja garesa hakan bai hana bayyanar cikar kamalarsa da jin daɗi ba. Tsaye yake akan ƙafafunsa cikin ɗanyar shadda fara ƙal da ko ba'a faɗaba kasan an narka kuɗi wajen ɗinkata.      Ya sake damƙe hannun mutumin da suke tare fuskarsa na sake ƙawatuwa da murmushi alamar gaisuwa sukeyi irin wadda take nuna an daɗe ba'a haɗu da mutum ba. Sake maido kallonta tai ga saurayin nan daketa sake tunkararsu. A take jikinta ya fara rawa, tanaji a ranta akwai abinda saurayin ke ƙullawa mara ƙyau a zuciyarsa game da kamilallen tsohon da takejin nutsuwa a zuciyarta game da shi. Badan ta sansa kota taɓa ganinsaba sai ɗazun da suke shigowa massallacin idin da wani tsoho daya fisa tsufa sosai ya kusa faɗuwa. Dakaga tsohon na ɗazun kasan talakane, amma sai ga wannan dattijo ya zaburo har shima yana shirin faɗuwa ya tare tsohon a jikinsa yana masa sannu, kasa ɗauke ido tai a kansu a ɗazun har suka shige cikin massallaci yana riƙe da shi. Kwarjininsa da cikar kamalarsa da shekarunsa na girmane kawai sukaja hankalinta da zuciyarta nason taimakonsa, (sai dai ta yaya?). Ta ambata a zuciyarta batare da tasan amsa ba. Farga da saurayin na gab da kaiwa garesa ga shi zai juya baya ya sakata zabura ta nufesa. Kusan a tare suka ƙarasa ga dattijon ita da saurayin.       Cikin ƙwarewar aiki na iya kisa saurayin ya kaima Alhaji Hameed Harith Taura yanka da kakkaifar wuƙar hannunsa gayama jini na wuce yanka ta gefen ciki. Inda ya tabbatar idan ya yanka sai ya mutu kuma. Sai dai kash, wuƙar na gab da kaiwa kansa batare daya fargaba dan yayi kamar zai wucene Raudha tazo ta tare yankan ya sameta a cinyarta sakamakon ɗan tsallen da tayi nason cimmasa.         Wata irin ƙara ta saki da damƙe cinyarta da hannu guda ɗayan kuma ta damƙo rigar jazuga dake son sake kaima Alhaji Hameed Taura wani yankan ganin wannan Raudha ta tare. Kusan duk wanda ke a kusa da su a wajen sai da ya juyo, a take kuma duk akayo kanta. Inda Alhaji Sammani yay azamar janye Alhaji Hameed Taura dan bashi kariya daga yunƙurin saurayin a karo na biyu. Hakanne yasa saurayin fincike rigarsa daga hannun Raudha datai ƙasa zata faɗi ya arta cikin na kare (gudu).        Da sauri Alhaji Hameed ya kai hannu ya riƙo Raudha jikinsa na rawa. Dan duk mai hankali ko ba'a masa bayanin komaiba zai fahimci abinda yay shirin faruwar. Sai dai kafin ma kowa ya nema ba'asi wani yaro da bazai gaza shekaru goma sha uku ba yake faɗin duk abinda ya gani. Dan kuwa akan idonsa Raudha taima Alhaji Hameed Taura garkuwa daga suƙar wuƙar saurayin.      Cikin ƙanƙanin lokaci ahalin Alhaji Hameed Taura suka zagaye wajen, ga securitys da ƴan agaji suma duk sun iso. Duk mai tausayi sai ya zubarma Raudha hawaye ganin irin mugun yankan da saurayin yay mata a cinya, dan ma ansa abu an yane ƙafar dan har rigar ya tsarge. A sume take jikin Alhaji Hameed Taura dake cikin matsanancin tashin hankali. Musamman yanda Yasmin tazo ta faɗa jikin Raudha tana kuka da girgizata.       Isowar Ambulance ɗin da ake jirace tasa mutane darewa ma'aikatan asibitin suka iso wajen da keken ɗaukar mara lafiya. Da taimakon Alhaji Basheer Hameed Taura da shima jikinsa ke rawar tashin hankalin abinda yaso samun mahaifin nasa aka ɗora Raudha bisa keken har cikin Ambulance ɗin. ★       Daga ahalin gidan Taura har su aunty Hannah kaiwa da komowa kawai suke na tashin hankali a ƙofar ƙayataccen asibin na musamman da aka kawota. Wanda tabbas badan dalili ba ko katangarsa bai zama lallai Raudha ta taɓa taɓawa ba harta ƙare rayuwarta. Da farko ƴaran gidan Taura hankalinsu yafi tashine akan jin kakansu aka kawoma harin ALLAH ya tsaresa. Sai da sukaga hankalin Pa ɗinsu da kakan nasu su kuma akan Raudhan yake sannan suka ɗan koma jimantawa. Koda za'a kawo Raudha asibitin badan securitys da ke biye dasu har nan ba da gida zasuyi wucewar su. Har mamakin yanda Bappi da Pa suke a ruɗe sukeyi, sun san yarinyar tayi ƙoƙarin kodan jarumtar da tayi na tarar wannan azaba. Sai dai mafi yawansu sunaji a ransu tayine dan neman suna ko kuɗi ko wani abu daban koma tare take da saurayin. Dan sun san haka kawai dai mutum bazai tarema wani mutuwa ba babu dalili, ballema ƙaramar yarinya irinta. Wasu ko a cikinsu gani suke koma bakin saurayin da Raudha ɗaya ne, maybe akasi aka samu kawai, ko kuma ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya.      To koma dai miye Alhaji Hameed Taura da ɗansa Alhaji Basheer Hameed Taura su ba haka bane a nasu zuciyar. Ɗunbin tausayine na Raudha da jinjinama ƙundunbalarta a ransu, sai fatan ALLAH ya bata lafiya da taraddadin wanene ya aiko saurayin ga wannan aikin? Dan kuwa dai cikin hayaniyar mutane ya ɓace ɓat, har suka baro wajen securitys na nemansa ne amma babu alamar zasu gansa.        Aunty Hannah da su Fatisa na rakuɓe a gefe suma rayukansu fal mamakin abinda ya faru. Dan sam babu wanda ya kula da sanda Raudha ta tafi bama Taura kariya sai ƙararta sukaji, sai ko sauran bayani a bakin mutane da suka tsinta. Yasmin dake kuka Alhaji Hameed Taura yazo ya durƙusa gabanta, duk da tsufansa da matsayinsa bai dubaba. Yasa hannayensa biyu yana share mata hawayenta. Cikin lallashi yace, “Minene sunanki?”.        “Yasmin!”. Ta bashi amsa cikin shashshekar kuka.       “Oh mai sunan larabawa to kukan ya isa haka ok? Kima aunty addu'a zata tashi lafiya kinji!”.      Kanta ta jinjina masa tana jan tagwayen ajiyar zuciya. Tausayinta ya kamashi matuƙa. Ɗunbin kamannin daya gani tsakaninta da mara lafiyar ya sashi hasashen ƴar uwartace. Hannunta yaja ya zaunar a kusa da shi yana kai kallonsa ga Muneera data koma can gefe tana waya kamar bataso a jita, da alama dai wani take sanarma abinda ya faru. Ya san kuma bazai wuce mamansu Gimbiya Su'adah ba. Dan tun ɗazun yakejin kira na shigo masa waya ya tabbatar Anne ce amma bai ɗauka ba. Yasan dai zuwa yanzu labarin abinda ya faru ya karaɗe kowacce kafar yaɗa labarai abinka da babban mutum.        Ko wane gidan tv ka kalla daga nuna sallar idi sai zancen an kaima Alhaji Hameed Harith Taura hari a filin idi. Yayinda hoton Raudha na kwance cikin jini a hannunsa shima keta kai kawo.       Babu yanda Alhaji Basheer baiyi Bappi ya koma gida ba amma yaƙi, ya tabbatar masa bazai iya barin wadda ta fansar da lafiyarta a gareshi cikin wannan halin ba ya iya komawa gida ya samu nutsuwa. Dole ya ƙyalesa har lokacin da doctors ɗin dake tare da Raudha suka fito suna sanar musu Alhmdllh ta farfaɗo. an kuma mata ɗinki a wajen tare da alluran kariya daga gujewa wasu cututtukan. Domin a bincikensu sun gano jikin wuƙar akwai dafin maciji.       Wannan abu ya sake tayarma da Alhaji Hameed da zuri'arsa hankali. Dan tabbas da an samesa babu makawa zai iya rasa ransa kodan yanayin jikin tsufa dake tare dashi.. *__________________________*             “Sai da nace maka yaron nan bazai iyaba Mr JK amma ka dage akan ƙwararrene ta hanyar wannan aikin”.     Ɗan takarar shugaban ƙasar NAYA a jam'iyyar adawa ya faɗa cikin ɗunbin tashin hankali da ruɗani yana nuna mutumin dake daura dashi a ƙayataccen falon na alfarma. A tsakkiyar falon kwanikane barbaje na abincin salla, sai sauran mutane uku dake ta gefen hannun haggunsa suma bisa kujerun rayukansu duk a ɓace.      Wanda aka kira Mr JK ya girgiza kansa cikin takaici shima yana faɗin, “Karkaga laifina Engineer. Ku kanku kunsan badan yarinyar can data bashi kariyaba babu shakka sai aikin yaron ya tafi dai-dai, sai yanzu na sake tabbatar da Alhaji Hameed Taura ya wuce ifiritu sai dai hatsabibi. Duk yanda muke tunanin cimmasa cikin sauƙi abune mai wahala”.        Cikin sauran mutane ukun ɗaya ya amshe da faɗin, “Tabbas abune mai wahala, sai dai ya kamata musan yarinyar nan ƴar uban wacece ne? Sannan minene dalilinta na bashi kariya?.”         “Wannan yanada muhimmanci Alhaji Sale Sukini, sai dai babban mai muhimmancin shine Alhaji Hameed. Domin wannan abun daya faru babu abinda zai ƙara masa sai farin jini ga jama'a. Ka duba kaga cikin ƙanƙanin lokaci kowacce kafar watsa labarai data yanar gizo ta ɗauka. yaya kuke tunani idan rana tsaka ya fito da manufarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar NAYA kuma?”.                  “Kuma gaskiya fa maganarka nakan hanya Alhaji Badamasi. Domin barin Alhaji Hameed Taura a raye tamkar hana yuwuwar nasararmuce. Babu yanda zamu haɗa takara da shi a dubemu a ƙasarnan, su kansu abinda suka fahimta kenan shiyyasa suka jawoshi ya hau kujerar dan sauran da suka nuna sha'awa a jam'iyyar tasu duk ruɓaɓɓune, babu wanda zai iya kawo kujerar. Shiko duk da bawai siyasar ya bama ƙarfi ba suna cewa gashi jama'a zasu amsa”.        Duk da ac dake aiki a falon hakan bai hana Engineer zame hularsa ya hau fifita ba, dan wata irin zufa ce ta ruɗani ke karyoma duka sassan jikinsa. Ya tabbatar duk abinda abokan nasa suka faɗa shine gaskiya. Shiko a yanzu babu abinda yake buri da fata sama da shugabancin ƙasar NAYA. yayi shekaru goma cif yana mulkin bisa muƙamin gwamna. Yaji daɗi sosai ya koma a kujerar majalissa itama shekaru biyar kenan, yanzu kuma burinsa yakai ga kujerar daga ke babu wata. A da hankalinsu kwance yake da hangen nasara saboda waɗanda suke hasashen jam'iyyar mai mulki zata bama takara duk bazasuyi armashi ba. Sai dai labarin daya zo musu sati kusan guda kenan akan zaman shugaban ƙasa da Alhaji Hameed Taura da kowa ke tunanin takara sukeson bashi ya ɗaga musu hankali. Domin kuwa a majiya mai ƙarfi sukaji hakan daga bakin wani munafikinsu dake cikin mulkin na shugaban ƙasa a yanzun. Sun yarda da shine bisa dalilin ba yaune karo na farko daya kawo musu labariba kuma ta tabbata daga fadar shugaban ƙasar na NAYA.      Zaman sake sabon ƙulli sukai akan Alhaji Hameed Taura da baisan sunayi ba ma.... *_Tofa maƙiya ta ko ina🤔_* *_GOVERNMENT HOUSE_*            Kamar yanda abokan adawa kecan suna tattaunawa anan fadar ta shugaban ƙasar NAYA ma hakanne. Dan kowannensu na kallon abinda ya farunne ta fuskar siyasa. Alhaji Hameed Taura mutumin kirkine da kowa ke yabon halayensa tun ƙuruciya. Dan ko lokacin daya ɗan fara bayyana kansa a siyasa mutane ƙalilanne suka soki hakan.      Su kansu rayuwar Alhaji Hameed Taura bawai damuwarsu bace. Sai dai basa buƙatar rasata a yanzu har sai sun cimma nasu burin sannan. Dan haka zasu sake tsayawa tsayin daka wajen ganin sun bashi kariya har su tsallake. *_(ya ALLAH. Siyasa batai ba😱🚶🏻)._*          Duk da tare shugaban ƙasa yay salla da Alhaji Hameed Taura a babban masallaci kuma har abin ya faru bai koma gidaba hakan bai hanashi sake sabon shiru shi da tawagarsa suka nufi asibitin da aka kai Raudha ba. Dan labari ya samesu cewar Alhaji Hameed Taura na asibitin. Dolene suma suje su nuna jimaminsu da bama al'amarin muhimmanci tunda shima ya ɗaukesa da girma. *_TK SPECIAL HOSPITAL_*         Cikin ƙanƙanin lokaci asibitin ya ƙara samu tsatstsauran tsaro a dalilin isowar shugaban ƙasa da tawagarsa. Hakan bai bama kowa mamaki ba saboda sanin amintakar dake tare da shugaban ƙasar da Alhaji Hameed Taura. Dole aunty Hannah ta ɓuya dan bata buƙatar shugaban kasa yasan tanada alaƙa da Raudha a yanzun.     Bayan sun duba Raudha dake cikin ƙyaƙyƙyawar kulawa shugaban ƙasa ya tilasta Alhaji Hameed fitowa suka ɗunguma zuwa Taura house tunda jikin nata Alhmdllh. Da wannan damar suma sauran yaran duk suka gudu gida tunda daman zaman kakansu sukeyi anan ɗin. Sai dai anbar Raudha cikin tsananin tsaro da kulawa ta kowanne fanni. Ga ƙyaututtukan maƙudan kuɗaɗe da waɗanda suka rako shugaban ƙasa duk sukai mata. Sai a lokacin su Aunty Hannah suka sami damar shiga suka dubata da ƙyau suma. Dan ɗazun Alhaji Hameed ne kawai ya shiga da Pa.      Sun tausaya mata ƙwarai da gaske, dan ƙafar tata ta matuƙar kumbura sai ma ratayeta akai jikin wani ƙarfe. Barci takeyi ga jinin data zubar ana ƙara mata. Kusan mintuna sha biyar akace su fito dan ba'a buƙatar kowa ya zauna da ita saboda gudun abinda zaije ya dawo. Hakan yasa dole Aunty Hannah ta kwashi su Fatima suka koma gida suma. Dan tun ɗazun dama Asabe ke kira da wayar hajiyar birni tana kuka akan su sanar mata idan Raudha ta rasu ta haƙura kawai. Dan duk wanda yaga Raudha a hoton dake yawo babu tantama zai ce ta mutu ne, musamman yanda jini yay faca-faca a jikinta cikin ƙanƙanin lokaci. Danma baƙar rigace a jikin, sai dai adon farin zare da akai mata yasaka jinin bayyana ga idanun mutane..........✍ *_Tofa wannan fa shine ake kira ƙaddara ta riga fata. Su aunty Hannah na neman ƙulla hanyar dalili, ga dalilin wanda ya fisu sanin gaibu shi ya ƙulla ta hanyar da basuyi zato ko tsammani ba. Masu karatu yaya za'a kwashe kenan to?🤔_*      *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/3, 11:33 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 12_* ..........Duk yanda ƴan jarida suka so ɗaukar wani rahoto bayan wanda aka gani a filin idi hakan ya gagara. Dan an toshe ko'ina da zai basu damar ma sake ganin Raudha ɗin. Koda Alhaji Hameed da shugaban ƙasa kuma suka fito anso jin ta bakinsa akan wannan al'amari amma ya nuna bazaice komaiba a halin yanzu. Dole suka barsa ya shige dan kowa yasan shiɗin kaifi ɗaya ne. Idan yace e to lallai e ɗin ce. Idan kuma ya ce a'a baya canja ra'ayi daga a'a ɗin tasa.. Sosai sallar tazo a wani yanayi ga wasu mutane ta ɓangarori huɗu.     Na farko gidan Taura. Dan duk yanda suke baje kolin farin ciki da gagarumin biki a shagalin kowace bikin salla wannan karon sai armashin nata yay ƙaranci saboda jimami na abinda ya kusa faruwa.     Ɓangare na biyu gidan su Raudha musamman Asabe da ƴan uwanta su Fatisa. Duk da suma dai su Hajiyar birni hankulansu ya tashi, sai dai wani sashe na zuciyarsu abin ya musu daɗin. Dan koba komai suna kallon abinda Raudha ɗin ta aikata tamkar wani silar samun arziƙinsu ne a wannan gaɓar. Daga hajiya mama har Hajiyar birni sai wani nannan suke da Asabe da ƴaƴanta a wannan yini. Ana kuma lallashinta akan ta kwantar da hankalinta ta cire damuwa Raudha na samun dukan kulawa.     Ɓangare na uku shine su Mr. JK da rashin nasara ya jefa rayuwukansu cikin ɓacin rai da taraddadi na ƙaulani. Sai faman tsugunne-tsugunne sukeyi na sabon shiri duk da kuwa bayan azhar suna cikin tawaga ta farko data isa gidan Taura domin kai jaje kamar yanda manyan ƙasar da ƴan siyasa keta faman yi. Wasu kuma ta waya suke kira suna jajantawa sakamakon ba cikin Bingo suke ba.        Na ƙarshe shine gidan gwamnati da al'amarin nasu ya rabu biyu. Kason farko shugaban ƙasa da abokansa su Alhaji Yaro glass. Kaso na biyu first lady da aunty Hannah da komai ya basu mamaki. Sun riga sun gama tsara yanda haɗuwar Raudha da Alhaji Hameed Taura zata kasance sai gashi ALLAH ya sauƙaƙa musu ta inda basuyi zato ko tsammani ba. Duk da abun ya ɗan ruɗasu sun shiga matsanancin farin ciki dan gani suke komai zaizo da sauƙi. First lady zata ƙarasa sauran aikin na ɗora shugaban ƙasa akan hanyar da zai fargar da Alhaji Hameed haɗa alaƙar auren Raudha da Ramadhan.... (Tofa masu karatu. Yaya kuke ganin hakan zata farune bayan shi uban gayyar da aketa wannan tsugunne-tsugunne dominsa ma yana can wata ƙasa hankalinsa kwance batare da ya sani ba? Kumuje zuwa dai muga yanda zata kasance🏃.) *_AMERICA (NEW-YORK CITY)_*             Duk wani cikakken musulmi wannan ranace da bata ɓoyuwa a garesa a duk inda yake a faɗin duniya. Sai dai ƙarancin yawan mabiya addinin musulinci a wajen ya rage masa armashi da jin daɗin wannan ranar. Amma dolene zuciyarsa ta kasance cikin shauƙi da godiya ga UBANGIJI daya sake zagayo masa da ranar.          *Broadway street* anguwace dake a cikin birinin new york dake ƙasar amuruka. Layine mai tarin abubuwan birgewa da ƙayatarwa kamar yanda mai karatu yasan turawa da gyara muhalli. A katafaren block dake ɗaya daga cikin gine-gine na musamman a broadway street gida mai lamba goma sha tara Ƙyaƙyƙyawan farin mutum amma baƙar fata mai tarin kwarjini da cikar kamala ne zaune bisa sofa a falo. Falo ne haɗaɗɗe da bai cika yawan tarkace ba ko hargitsi.         A kallo ɗaya zaka iya kiransa da tuzurun saurayi dan shekarunsa a ƙala zasu iya tasarma 35. Sanye yake cikin farar ɗanyar shadda data samu aiki na musamman da bazaka iya mata kallo ɗaya ita da mamallakinta ka ɗauke kai ba. Sai dai duk da tsadarta da ɗaukar idon da takeyi bai hanata yamutsewa ba saboda a yanyin dayay zaman bisa sofa. Gaba ɗaya hankalinsa kacokan ya tattara ne ga television ɗin dake a falon, inda yake kallon tashar dake da alaƙa da ƙasarsa ta NAYA. Bakomai ya sakashi nutsuwa ga tvn ba sai bikin salla da na idi da aketa nunawa na ƙasar tasa dama sauran ƙasashen duniya.        Duk da fuskarsa bata nuna shauƙin kallon ko zumuɗi ba kwayoyin idanunsa sun gama fallasa asirin zuciyarsa baki ɗaya. Dan yanda ya tattara dukan hankalin nasa ya isa shaidar komai na ƙayatar da shi. Basai ance maka ƙyaƙyƙyawa bane, fatarsa kawai ka kalla kasan shiɗin mai ƙyaune. Dan mutane da yawa kan kira mai irin yanayinsa da suna black american duk da kuwa a ƙasarsa fari yake kai tsaye. Yana da yanayi mai sanyi a fuska tare da duk wani ado dake ƙawata fuskar gayun wannan ƙarnin. Abu mafi ɗaukar hankali dake tattare dashi gyararriyar sumar kansa da tasha wani salon aski na musamman duk da kai tsaye bazamu kirata mai taushi da laushi irin ta larabawa ko turawa ba. Dan kuwa a tsaitsaye take cunkus kamar yanda akasan sumar baƙin mutum, sai dai ɗunbin gyara da kuɗaɗen da take lashewa yasa tazam mai ɗaukar hankali da birgewa ga mai kallo. Sai girarsa ta haggu da akai mata wani salon tsagu da kan iya saka mara fahimta ɗaukar gayune yasa shi tsagawa, sai dai sam ba haka bane tabon raunine a wajen da ya samesa tun yana primary. Sai ga tabon har girmansa bai dishe ba. Batun yanzu ba mutane da yawa sunsha ɗauka an kwashe gashin wajen ne tamkar tsagar kitso kawai dan gayu. Kowa yasan abune mai sauƙi yanzun kaga lips ɗin gayu pink kodan abubuwan da ake tu'ammali dasu domin yin hakan.        Baza'a kirashi siriri ba, ba kuma za'a ce dashi mai ƙiba ba. Kawai dai mutum ne tsaka tsaki musamman daya kasance yana tu'ammali da inginan motsa jiki.         Karon farko ya sake waro manyan idanunsa da ada suke a ɗan lumshe bisa television ɗin sakamakon abinda ya gani. Cikin sassanyar muryarsa mai ɗan kauri da buɗewa ya furta “What?!!” yana zabura gaba ɗayansa tsaye bisa ƙafafunsa. Dan ba ƙaramin harbawa ƙirjinsa da ƙwaƙwalwar kansa sukaiba a lokaci guda saboda tozali da abinda ya faru ga kakansa a filin idi.       *_Ramadhan B. Hameed Taura_*. Ya matsa gaban television ɗin da sassarfa dan ji yake tamkar idanunsa basa gane masa komai daƙyau. Tabbas babu tantama hakanne, dan kuwa ganin mahaifinsa da ya iso wajen a kiɗime da sauran ƴan uwansa mata ya sake tabbatar masa da komai gaskiyane. Da sauri ya koma gaban sofa ɗin da yake zaune a da ya sungumi ɗaya daga cikin wayoyinsa uku dake a saman table. Cikin ƙwarewa ya far sarrafata tare da kutsawa cikin shafukansa na sada zumunta.     Duk da ya daka barkono daga ƙasar haihuwar tasa duk da begen da ahalinsa ke masa yaƙi saurarensu hakan bai hanashi dinga bibiyar al'amuransu ba batare da sun sani ba. Dan kuwa ya ɓoye kansa daga yanda zasu iya ganosa kai tsaye, ainahin shafukansa da suka sani kuma duk yayi blocking nasu babu mai ganin abinda yakeyi sai dai da salon sabon suna da bazai gane ba.      A babban shafin sada zumunta na watsa labaran ƙasar ya fara cin karo da ainahin bayanin abinda ya farun, harda gajeren video a shafinsu na istagram. Wani irin tsuma jikinsa da zuciyarsa keyi dan kuwa tamkar an tuna masa da wata rana data kasa shuɗewa a tarihinsa.  Ranar da tsayawar numfashinsa ce kawai shima zata iya ɓaddata a cikin jerin abubuwan da suka zauna masa raɗam a cikin ƙwaƙwalwa. Kakarsa (Anne), kakansa (Bappi), Mamansa (Gimbiya Su'adah), Babansa (Alhaji Basheer Hameed Taura) duk suna raye a duniya. Bai taɓa ɗanɗana ɗacin mutuwar wani makusanciba a duniya sai akan matarsa masoyiyarsa da ƴarsa gudan jininsa. Shiyyasa yake matuƙar jin ɗunbin raɗaɗi da zafin gusawarsu a duniyarsa ta hanyar da bazai taɓa yafema wanda ya ƙirƙiretaba duk da yasan tana cikin ƙaddararsu.       “Bappi!!”. Ya faɗa cikin yanayi najin ƙaimi da tasowar mazantaka. Haka kawai zuciyarsa ke raya masa wanda ya halaka masa Amnah da Haseenah ne suke farautar Bappin sa. Sai ma ƙasan ransa ke tunzurasa da koma dai an samu galabar cutar da bappin ne aka ɓoye. Karon farko da tun bayan barowarsa ƙasar NAYA shekaru biyar kenan yakejin tamkar ya rintse ido ya gansa a ciki. Duk da halittarsa ta nutsuwa da cikar kamala hakan bai hana idanunsa nuna birkicewar da ƙwaƙwalwarsa ke neman yi ba. Da sassarfa yay jifa da phone ɗin tasa bisa sofa ya nufi dogon glass ɗin da aka raba tsakanin falon da bedroom ɗin barcinsa. Kasancewar yaja labulen gefe da gefe yasa ake iya hango gadon ɗakin da ya gama haɗuwa shima.      Da wani irin gudu ƙofar glass ɗin ta zuge kanta gida biyu saboda yanda ya danna maɓallin makunnar da ƙarfin tuwo tamkar itace tai laifin....        Wani irin ruri ɗaya daga cikin wayoyinsa keyi na neman agaji alamar kira, sai dai duk da jinta da yakeyi baiko nuna alamar zai fito daga bedroom ɗin ba dan yasan wanene ke kiran nashi.     Still kira ya sake shigowa a karo na kusan biyar. Ɓaro-ɓaro sunan A.J ya bayyana a kan screen ɗin. A.J abokine ga Ramadhan wanda shima mazaunine aƙasar ta amuruka. Kamar yanda suka saba haɗa liyafar cin abinci a kowanne ranakun bikin salla babba da ƙarama wannan karon ma hakane. Maƙudan kuɗaɗe suke haɗawa su ƙayata zaman nasu da shi batare da jin hakan a jikinsu ba dan kowa ya tara.     Mafi yawansu sunada mata da ƴaƴa. Harma da masu manyan ƴan mata da samari. Dan kuwa akwai sa'oin Alhaji Basheer a ciki harma da tsoffi da ƙaddarar zama ta zaunar a ƙasar tsahon shekaru. A irin wannan zaman ƴammata da yawa sunsha yima Ramadhan tallar kansu amma baya kulawa. Dan ko fuskar a tunkareshima baya basu balle suyi tunanin dacewa. Manyan ciki kuma kan dunga kwaɗaita masa maganar sake aure amma baya kulawa nan ma.        Tunda ya fara riskar bikin salla a ƙasar bai taɓa missing wannan zaman ba, dan yana matuƙar ɗebe masa kewa sosai akan ahalinsa. Hakan yasa rashin isowar tasa ta dami kowa har A.J ya fara danna masa kira a jajjere. Sai dai kuma ana tsaka da haka dattijo alhaji sufyan harɗo yaci karo da labarin abinda ya faru ga Alhaji Hameed Harith Taura a filin idi yau. Dan haka yay azamar fargar da sauran ƴan uwansa maybe labarin ya riski Ramadhan ɗinne shima.      Dukansu sun nuna jimami, yayinda A.J da Mufeed yanke shawarar zuwa gidan na Ramadhan da suke kira da suna Top gee dansu gani. Fitowa Sakai a cikin garden ɗin Sultana biye dasu, basu hanata ba dan kowa yasan irin ɗunbin so da ƙaunar da Sultana kema Ramadhan ɗin duk da baya kulata. Cab suka tara tare da sanar masa inda zai kaisu....       Fara danna ƙararrawar gidan yayi dai-dai ne da fitowar Ramadhan daga bedroom ɗauke da madaidaiciyar bag daya haɗa abubuwansa masu muhimmanci da zai iya buƙatar amfani dasu. Ya canja kayansa zuwa ƙananun kaya daya ɗora jibgegiyar rigar sanyi daketa maiƙo da santsi tamkar leda kalar light blue. Sai hularta mai gashi a cin bakin baƙi tamkar kayan ciki t-shirt mai gajeren hannu da black jeans wando. Ƙafarsa sanye cikin baƙaƙen takalma boot.       Duk da ba kwalliya yay ba hakan bai hanashi yin ƙyau ba. Baibi takan doorbell ɗin da aketa bugawaba ya cigaba da karkashe komai na na'urar lantarki dake a cikin falon kamar yanda ya kaso na bedroom.                  Da ga A.J har su Sultana binsa suke da kallon mamaki dai-dai sanda ya buɗe ƙofar. Bakinsa da gashin gemunsa kawai suke iya gani zuwa rabin kumatunsa, dan yaja hular rigar ne ya rufe masa rabin fuska tare da toshe idanunsa da glass mai nuna blue a jiki.        “Mr R kana lafiya kuwa?”. Mufeed ya faɗa yana ɗan kai hannu ya dafa kafaɗar Ramadhan ɗin dake ƙoƙarin fitowa batare da ya damu da hanin nasu ba.        Ƙarasa fitowa yay yana zuge zip ɗin bag ɗin hannunsa mai kama da school bag da faɗin “Zan wuce NAYA? Akwai matsala”.        Atare suka haɗa baki wajen ambaton “Matsala kuma? Miya faru?”. Dan sunfi son suji idan da gaske ne kar suyi katoɓara. Hannunsa na haggu ya ɗora saman kansa ya zame hular tai baya ya saketa bisa dokin wuyansa yana ƙoƙarin saka lock jikin ƙofar duk da baya tunanin zai jima acan inhar ya iske komai lafiya.          Ƙoƙarin sake maimaita tambayar tasa A.J yayi, bai tankashiba yanzu ma sai da ya kammala rufe ƙofar ya rataya hannun bag ɗinsa ɗaya a hannun haggunsa, hularsa yaja saman kansa tare da ɗan bubbuga kafaɗar A.J ɗin. “Na riga nayi Booking flight, kuma gab yake da tashi zamuyi waya”. Daga haka yay gaba a binsa.     Hankali tashe ganin yanda yake komai cikin zafin nama yasa Sultana ƙoƙirin binsa zata kira sunansa Mufeed ya riƙo hanunta. Kansa yake girgiza mata alamar karda ta tsaidashi ta barsa. A take hawaye suka ciko mata idanunta da take bin Ramadhan dake ƙoƙarin shiga cab daya tsayar da kallo. Kamar walƙiya cikin ƙanƙanin lokaci cab ɗin ta ɓacema ganinsu abinka da lafiyayyen titi duk da dokar ƙasar akwai ƙa'idar da driver kanbi yayin tuƙi... *_ƘASAR NAYA. (Taura house)_*          “Ya kamata ka ajiye komai gefe kaci abinci hakanan dattijo”.     Anne dake zaune gefen Alhaji Hameed ta faɗa cikin tausasa harshe da nuna kulawa. Ganin baida alamar tankawa ta cigaba da faɗin, “Mu godema ALLAH da ƙudirin koma wanene bai cikaba duk da wani ya cutu a dalilinmu. Haka rayuwa take cike da jarabawa. Talaka mai nema cin yanzu da anjima yana cikin jarabawa babba dake taka rawar gani wajen iya wargaza komansa. Sannan ni'imar arziƙi ga masu arziƙi a lokuta da dama ɗaukakar a garesu itace gagarumar jarabawarsu. A koda yaushe cikin ɓoye kansu suke, badan komaiba sai don gudun a cutar dasu ko makamtan hakan, dai-dai da masoyansu na gaskiya taka tsantsan suke wajen kokwanton neman tabbaci koda kuwa sunada yaƙini masoya da maƙiya zasu iya shiga a jarabawarsu. Dattijo bamu isa canja ƙaddara ba, dan haka kalmar da tafi cancanta a bakunanmu a yanzu itace *_Alhamdulillahi_*. Sai fatan ALLAH ya bama yarinyar lafiya itama”.           Sosai kalamanta suka sanyaya masa ransa. Yaja numfashi mai nauyi da sakin guntun murmushi. Baki ya buɗe da niyar cewa wani abu maganar tasa ta maƙale a maƙoshi saboda abinda idanunsa suka hango masa a bakin ƙofar katafaren falon nasu. Saurin maida idanun nasa yay akan agogo tamkar wanda akaima shune da mummunan abu. Ƙarfe goma na dare da wasu mintuna. Tunda suka samu gidan nasu ya lafa da ƴan jaje da masu zuwa yawon salla sai kowa ya nutsu a sashensa saboda hadari da garin ya haɗa na alamun saukar ruwan farko na damuna da kowa ke fata.      Sake maida idanun nasa yay ga ƙofar ransa fal tunanin gizon da idanun suka saba masa ne na tsananin bege da kewar jikan nasu duk da fuskarsa a rufe take da hular rigar sanyin jikinsa hakan bai hanashi ganesa ba. Hakan yasa itama Anne duban inda ya ƙurama idanun baki wagame tayi........✍ *_iyakata Hummmm!! A wannan gaɓar😜_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan🔥😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/3, 11:36 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 13_* ...........A hankali Ramadhan dake a bakin ƙofar ya cigaba da tako tsaftataccen marble's ɗin falon, dan ya cire takalmansa tun a corridor ɗin daya raba falon farko da wannan falon, sai safa baka kawai. idanunsa akan kakannin nasa. Tafiya yake dai-dai da hurowar iskar hadarin dake kaɗa labulolin falon tare da walƙiya tamkar yana taku a saman kaɗawar tata ne. Harya ƙaraso gaban Baffi basu iya sun motsa ba, ya durƙushe gaban bisa gwuyawunsa tare da sauke jikkar kafaɗarsa. Hannu ya kai bisa kansa a hankali yay baya da hular nutsatstsiyar fuskarsa mai cike da kwarjini da cikar haiba ta bayyana.        A hakan ma bai iya dubansu ba, dan har yanzu idanunsa sakaye suke da gilashinsa mai nuna blue. Maimakon ya zaresa sai matsawa yay ya ɗora kansa bisa cinyar Bappin yana sakin wasu tagwayen ajiyar zuciya da lumshe idanunsa masu nauyi da fargaba.         ★    A ɓangaren Pa ma yau tare yake da gimbiya Su'adah dan girkintane. Tsananin gajiyar dake tare da shi ta kaiwa da komowar da yayi yau kashi-kashi ya saka shi yin wanka da ruwa mai ɗumi da taimakon gimbiya Su'adah. Fitowarsu kenan a toilet ɗin tana tsane masa jiki da towel ƙarami. Ya kai dubansa ga labulen windows da aka ƙawata adon bedroom ɗin nasa da su. Yanda iska ke kaɗasu abin sha'awa ga mai kallo. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke batare daya ɗauke kansa a jikin labulen ba ya fara magana a hankali.       “Da ace Bappi zai yadda da ya bar maganar nan ta takara. Saboda na tabbatar abinda yaso faruwa a yau yanada alaƙa da wannan siyasar da bana hango wani amfaninta a garemu ko kaɗan....”      Wani irin bugawa ƙirjin gimbiya Su'adah yayi. Domin ba ƙaramin ƙwallafa rai da ƙara jin alfahari takeba akan batun fitowa takarar tilon ɗanta namiji da Bappi ya kwaɗaita musu tun daren jiya. Zata iya cewa dukkan farin cikinta na yau da murmushinta yana da alaƙa ne da hakan kai tsaye. Idan ko mijin nata ya cigaba da nuna adawarsa akan hakan ko kokwanto lallai tana cikin ɗunbin rashin nasara kenan. Dan kuwa Bappi zai iya saurarensa akan hujjojinsa inhar ya samesa da batun........       “Su'adah kinyi shiru”. Pa ya faɗa cikin katse mata dogon tunanin data faɗa. Numfashi taja mai ƙarfi a ɓoye da ƙaƙaro murmushi tana kaiwa zaune a gefensa. Maɓallan rigar barcinsa dake ajiye gefe take ɓallewa bayan ta ɗakkota a hannunta.      “Ba shiru naiba Daddyn Ramadhan, nima wani tunani nakeyi game da maganarka. Tabbas zancenka nakan gaskiya, dan ni kaina harna fara jin tsoro. Idan har za'a iya harar mana Bappi irin haka akan wannan batun shi kuma Ramadhan dazai tsaya takarar yaya zata kasance kenan?”.          “Abinda nake hangowa kenan Su'adah. An illata mana yaro a baya batare da mulki ba, har takai ga ya nisancemu a yanzu saboda tabon da aka bar mana a zukata ya kasa barin ruhinsa. Inaga yanzun da ake son ɗora masa nauyin abinda ya girma shekarunsa. Suma da suke manya masu shekaru basu tsira ba balle shi da dudu shekarunsa talatin da biyar. Ko'a tarihi babu wani shugaban ƙasa a wannan ƙasar ta NAYA da akayi mai ƙarancin shekarunsa fa....”        “Ƙarancin shekarunsa basu bane damuwar Dadyn Ramadhan. Dan kuwa koba komai anzo da wani sauyine da al'ummar ƙasar NAYA zasuyi farin ciki da shi. Mun cancanci mu damu da gudun abinda zaije ya dawo, sannan kuma ta wani ɓangaren yanada ƙyau muyi dubi da talakawa masu buƙatar irin Ramadhan ɗin a yanzun, domin da gaske ƙasar NAYA irin Ramadhan take buƙata da shekarunsa. Badan shugabannin baya sun gaza ba, a'a suma sun taka irin rawarsu kuma munji daɗin ƙoƙarinsu da yaba musu, dan mulki ba abune na wasa ba. Wanda ke gefe bai isa sanin wahalarsa ba sam. Dan shi daɗin kawai yake hangen maiyinsa na ciki yake, sai dai abunda bamu saniba wahalarsa itace kaso 99. Kaso ɗaya kacal ɗin nan shine kawai jin daɗin ga ma'abota mulki. ALLAH ya sakama shugabanninmu da alkairi, ya yafe musu kurakuransu yay riƙo da hannayensu. ALLAH kuma ya basu ikon sauke nauyin al'umma dake kansu”.         Numfashi ya sake saukewa da faɗin, “To amin ya rabbi. Amma duk da haka ina jin tsoro Su'adah”.       “Karkaji tsoro Dadyn Ramadhan. Addu'a kawai zamu duƙufa yi, tare da tunanin ta hanyar da zamu maido Ramadhan gida a yanzu batare da mun sake ɗorama Bappi wani nauyin ba”.         “Eh kema kinyi batu na hankali. Inko hakane barama na leƙa bappin dan na manta ma ban sanar masa batun kammala fidda komai na zakkar ba yau, duk mun wuni cikin rashin kwanciyar hankali ba'a fitarba kamar yanda aka saba”.        Miƙewa tai tsaye tana taimaka masa ya saka jallabiya fara bayan ta ajiye rigar barcin gefe, dan tasan bazaije sashen su Anne da kayan barci ba. Hakan al'adarsace da girmamawa ga mahaifan nasa batun yanzu ba. Turare taɗan fesa masa sannan ya fice.             Gimbiya Su'adah ta sauke nannauyan numfashi a ƙasan ranta tana godema ALLAH daya kasance yau girkintane har taji batun nan taima tufƙar hanci da wuri. Taya zata amince maganar nan ta koma ciki bayan ta fito. Da farko bataƙibama ace shi Alhaji Basheer ɗinne zai hau shugaban ƙasar ba. Dan koba komai darajarta zata ƙaru, ta fito daga gidan mulki mafi daraja da kima, gata tana aure a gidan dukiya sahun farko a ƙasar NAYA dama yankin Africa baki ɗaya. A ƙarshe a kirata first lady. Lallai data amsa sunanta *_SARAUNIYA SU'ADAH_* ba gimbiya Su'adah ba. Amma ko'a hakan ma ba komai baneba, dan samuwar mulkin ga gudan jininta wani abune mai girma da za'ayi ƙarnuka da zamanai da bazai mantu ba. Sannan dole ne a kirata uwar shugaban ƙasar NAYA. Dan haka itace da kanta zata zaɓa masa matar aure dai-dai da ra'ayinta. A wannan karon bazata sake sakaci irin na farko ba akan matar da Ramadhan zai aura. (“Mulki! Mulki!! Mulki!!😣🚶🏻” ). ★         Turus Pa yay tare da ƙoƙarin haɗiye sauran sallamarsa a maƙoshi duk da ta kusan gama fita a harshensa. Ba komai ya jawo hakan ba sai tozali da yay da gudan jininsa zaune gaban Bappi da Anne. Gaba ɗaya fuskar tsoffin nasa babu alamun fara'a, yayinda Ramadhan ɗin yay ƙasa da kansa yana magana a kausashe mai cike da ɗaukar alwashi.        Kai tsaye ya fahimci kausasa harshen nasa nada alaƙa da abinda yaso samun bappin a yau. Sarai ya sani basai an faɗaba, ɗansa Ramadhan mutum ne mai zafin zuciya ainun, abu kaɗan ke fusatashi ya hargitse tamkar baisan wani abuba wai shi sauƙin kai. Amma idan ka kallesa a fuska bazaka taɓa ɗauka ma yana magana mai alaƙa da masifa ba saboda fuskar mutane masu haƙuri da rashin son hayaniya garesa. Sometimes idan yay abu mutanen da basu san ainahinsa ba sukance bashi bane ba, dan a zatonsu ko yatsa ka sakama Ramadhan bazai taunaba saboda haƙurinsa da rashin son magana. Girman kai ne dai kam kowa na masa kallon mai shi kai tsaye, koda sau ɗaya ka fara ganinsa.       Sai dai su duk sun san ba hakan baneba, Ramadhan bauɗaɗɗen mutum ne mai zafi da tsananin ɗaukar kai (girman kai inji bahaushe😎). Tabbas baida yawan magana badan yana miskiliba, tsabar jin kai ne kawai ke hanashi magana a lokuta da dama koda ace ya dace yayi ɗin. Tabbas anan ɓangaren ya biyo mahaifiyarsa ƙwarai da gaske, dan saima ace ya ɗarata izza dajin mulkin a cikin jininsa fiye da ita da aka haifa a gidan mulkin. Sai dai kuma ta wani ɓangaren yanada wasu halaye kishiyar waɗan can da zama dashi ne kawai zai iya fiddoma wanda ya sanshi da waɗan can ɗin su.....         “Ramadhan!”. Pa ya faɗa cikin wata irin murya mai kaushi-kaushi da ɗaci. Dan haka kawai daya tuna yanda suka dinga bin Ramadhan akan yay haƙuri ya manta komai ya dawo ƙasar NAYA amma ya nuna musu bazaibi maganarsuba ya shiga dawo masa a rai.     Da ga Ramadhan har su Anne juyowa sukai suna kallon Pa ɗin, dan sam basuji shigowarsaba balle sallamarsa saboda tasowar iskar hadari dake ƙaruwa.      “Pa!”. Ramadhan ya faɗa da sauri yana miƙewa idonsa akan mahaifin nasa.        “Miya kawoka gidan nan!!”. Pa ya faɗa yana ƙoƙarin dakatar da Ramadhan daya miƙe da alamar ɗokin ganin mahaifin nasa da zumuɗin isowa garesa, dan jikinsa har tsuma yake.       “Pa!......” Ya sake buɗe baki zaiyi magana Pa ya dakatar da shi.       “Karkace komai a gareni!!, zo ka fita a gidan nan yanzun nan!!”.      Yanda yay maganar babu wasa ya saka Ramadhan duban su bappi, kafin ya sake kallon Alhaji Basheer Taura.       “Pa.......!”. “Ramadhan!! Nace ka fita a gidan nan yanzun nan!. Bana son sake ganin wannan fuskar taka!!”.      Alhaji Basheer Taura ya faɗa a tsawace yana nunama Ramadhan hanyar falon.      Wata irin muguwar hajijiyace ta fara ɗibar Ramadhan. Dan dama can shi bayason ihu, musamman idan yana akan gaɓar bacin rai tuni ake samun matsala kansa ya nema juyewa saboda tsananin yanda ƙwalwar kansa ke kasa ɗaukar tashin hankali mai shallake tunani. Lokacin da yana yaro idan hakan ta faru ansha cemusu yanada aljanu ne masu ƙarfi sosai. Sai dai basu taɓa yarda ba dan su sam basu cika ɗaukar waɗan nan abubuwan da muhimmanci ba (kamar yanda kowa yasan ɗan boko🙏🏻), sai dai hakan baya hana duk lokacin da abu ya faru makamancin matsalar ta biyo baya Anne ta zauna tai masa addu'a a ruwa da saman kansa har sai ya samu nutsuwa sannan. Amma abin mamaki zai iya yini yana ajiyar zuciyar wannan ɓacin ran, ko kuma ya yini a ɗaki yana barci. Sannan sai ya haɗa kwanaki biyu zuwa uku baiyi magana da kowa ba. sai dai ya samu wajen ruwa ya zauna, ba kuma zaici abinci ba duk da kasancewar sa ma'abocin son abinci sai Anne ta takura masa shan abu mara nauyi kamar su fura yogurt, fresh nonon shanu ko na raƙumi da makamantansu. Dan yana tsananin son madara da dukkan nau'ikanta a rayuwarsa. Bayan aurensa da Amnah idan ransa yay irin wannan ɓacin yakan hucene a kanta ta hanyar yin tarayya da ita yanda zata jigata har sai an kwantar da ita a asibiti abinka da sikilla. Dan likitocin kance ko mai lafiya akaima irin wannan kamun babu shakka zataji a jikinta balle Amnah ɗin. A duk lokacin da fushin ya sauka yakan shiga damuwa idan ya kalli yanda ya fiddata hayyacinta. kai wani lokaci ma har saida akai mata ɗinki tsabar lamarin Ramadhan yana bukatar addu'a🤦🏻. Amna kam tana jin jiki da shigar Ramadhan irin wannan yanayin, sau biyu yana sakata ɓarin ciki. da tana raye na tabbatar zatace hakan shine mafi girman tashin hankali a rayuwar aurenta da Ramadhan ɗin, shiyyasa duk wani fushinsa take gujewar wanzuwarsa a karan kanta.        Yanda ya fara juya kai jijiyoyin na tashi sama da maƙogwaronsa dake kai kawo a wuyansa, gashin kansa na mimmiƙewa yasa Bappi fahimtar mike shirin faruwa. Yasan Ramadhan bazaice komaiba, dan shi mutum ne mai tsananin tsoron saɓama iyaye, shiyyasa daya dage akan bazai dawo NAYA ba a shekaru biyar ɗin nan abun ya basu mamaki matuƙa, dan duk rintsi baya ƙetare maganarsu.     Da sauri Bappi ya girgizama Alhaji Basheer kai yana miƙewa ya riƙo hannun Ramadhan daya fara ƙoƙarin ɗaga ƙafa yana jujjuya kansa cikin tafukan hannunsa daya riƙe kan nasa. Tuni idanunsa sun rufe ruf saboda wata baƙar hajijiyar da yake gani falon na juya masa da wani irin shegen gudu.       Babu abinda ke maimaita kansa a kwakwalwar Ramadhan da zuciyarsa sai *_“Ramadhan!! Nace ka fita a gidan nan yanzun nan!. Bana son sake ganin wannan fuskar taka!!”._* da Pa ya faɗa.       “Zan tafi Pa, bazan sake nuna maka fuskar nan ba nayi alƙawar.....”      “Shut up!!”. Bappi ya faɗa da ƙaraji shima yana katse Ramadhan ɗin bayan ya fisgosa ya zube a saman kujerar kusa da shi. Juyawa Alhaji Basheer Taura yay a fusace yabar falon, shi kansa wani irin jiri-jiri na neman fara ɗibarsa. Sai hakan yasa yakejin yana tafiya tamkar akan iskar dake kaɗawa har zuwa sashen nasa. Bai iske gimbiya Su'adah ba. Da alama taje shirin barci. Dan haka yay kwanciyarsa, koda ta shigo bayan kusan mintuna talatin da kwanciyarsa bai motsaba. Hakan yasa tai tunanin ko yayi barcine. Sai kawai taja bargo ta lulluɓa masa bayan ta rufe wasu a murafan windows ɗin dan iskar ta fara yawa. *_WASHE GARI_*          Da mamaki kowa ya tashi yaga Ramadhan a gidan. Sai dai a yanayin da yake na hawa saman dokin zuciya yasaka bakin yaran gidan rufewa ruf. Dan ko kallonsa kayi bakaso sake ganiba fuskar tamkar zatayi aman wuta😜.          Gimbiya Su'adah ce kawai ya iya tankama tambayarta itama a taƙaice, dan ita firgitama tayi da ganin nasa. Har zuciyarta na raya mata kodai da gaske Ramadhan ɗin nada aljanune wai?.      Ko amsa ɗaya bata samu daga tarin tambayoyin da take jera masa ba, sai ma miƙewa yay yana sanar mata cewar zai koma America.       “America!”.   Ta maimaita da yanayin ruɗani da tashin hankali. ita dake murna ɗanta ya dawo gareta kuma. Kafin ta sake cewa wani abu yayo waje. Dan dama a bedroom ɗinta ya sameta kasancewar ta duba an kammala shirya abincin breakfast na Pa tazo dan ta shirya, sannan taje ta tadashi a barcin daya ɗan koma na safe bayan dawowarsa masallaci.      Har ya fice a sashen baki ɗaya bata dawo hayyacinta ba. Dan da alama sumar tsaye tayi kawai.      ★ “Shiga mota muje”.       Bappi ya faɗa idonsa akan Ramadhan daya fito daga sashen iyayen nasa a wani irin yanayi. Duk da alamu sun nuna yayi wanka ya canja kaya hakan bai hana fuskarsa bayyana yanayinsa na jiya ba. Sanye yake cikin wani tattausan tissue yadi da basai ance komai game kallo ba wajen hasashen irin kuɗin daya lasa na sayensa dana ɗinkinsa. Duk da simple style ne a jikinsa hakan bai hana bayyanar tsadarsa da fitar ɗinkin ba a bisa ƙyaƙyƙyawar ƙirarsa ta mazantaka da ƙuruciya ba, ga shi baƙi sai farar fatarsa ta sake haskawa. Babu alamar sumar kansa ta samu gyara yau tsabar yanda ta hargitse, sai dai hakan bai hana ƙyawunsa bayyana ba harma ya ɗauka hankalin wasu mutane koda ba kowaba.        A tunaninsa airport ɗin zasuje, kamar yanda ya sanarma Bappin yau zai koma bayan sun fito da ga sallar asuba. Dan haka babu musu ya shige inda M. Adamu ya buɗe masa kusa da Alhaji Hameed Taura (Bappi). A wata jiƙaƙƙiyar mota data gama haɗuwa. A tsammaninsa ƴan kayan buƙatarsa dake cikin bag an riga an fiddo masa tuni.........✍ *_Tofa ina Bappi zai kai mana wannan young tiger ɗin mai kama da barkonon noman ranin😎🏃?._* [6/6, 5:24 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 14_* ...........Sai da motar ta tsaya a harabar asibitin sannan Alhaji Hameed Taura ya dubi Ramadhan da ke kwance jikin sit ido a rufe. Sai faman jan numfashi yake a gwame alamar ransa har yanzu a ɓace yake. Sumar kansa yayma kallon second goma ya sake ɗauke kansa, batare da yace komai ba ya miƙa hannu a booth ya ɗakko ledar dake ajiye da huluna a ciki ya duba wadda yake zaton zata dace da shigar Ramadhan ɗin ya ɗakko. Dama shekaran jiya ya sayesu domin Ramadhan ɗin, sai dai ya mantasu ne a motar bai kuma sake shigartaba sai yanzun.      Kari yay mata sannan ya ɗaura masa akan hannu, hakanne yasa Ramadhan buɗe idanunsa da suka ƙanƙance da canja launinsu.     “Saka hular nan muje”. Komai baice ba ya ɗauka hular ya ɗora saman kansa kawai batare da duba tayi ko bataiba. Kai Bappi ya ɗan girgiza da riƙo hannunsa ganin zai fita. Batare da shima yace masa komai ba ya gyara masa ita ta zauna ɗas tamkar dan shi akayita. Sosai ya fito asalinsa na bahaushe cikakke. Wanka na ɗaukar jikin Ramadhan ko wanne irine. Sai dai a duk lokacin da ya saka manyan kaya yakan zama babban mutum da cikar kamalarsa ke daɗa fitowa a zahiri ga masu kallonsa. Sai kaga yayi maka wani irin kwarjini dake saka mutane jin shakkarsa da bashi girma koda basuyi niyya ba.      Duk da ya fahimci asibiti sukazo bai tanka ba har suka shigo ɗakin da Raudha ke jinya, police ɗin da president ya bamma Alhaji Hameed Taura biye dasu tamkar jela. Ko'a dacan da ƙuruciya Alhaji Hameed baya son bodyguard tare da shi balle yanzu da tsufa yay masa kamun kazar kuku, yake ganin rayuwar ƙiris ta rage masa ma.         Bappi ne kawai yay sallama a zahiri duk da yasan babu kowa a cikin. Ramadhan kuwa a saman laɓɓansa yayi yana biye da Bappin tamkar dole. Ɗaki ne babba dake ɗauke da komai na buƙatar mara lafiya ɗan gata. Sai Nurse ɗaya dake tare da Raudha data farka tun asubahin yau. Tun ɗazun doctor ya shigo yay mata dukan abunda ya dace tare da dubata. Aka kuma bata abinci taci tare da magunguna. Yanzu haka idanunta biyu tana kallon television ɗin ɗakin da ake nuna wani wasan salla na yara daya ɗauke hankalinta, yayinda Nurse ɗin ke zaune tana faman latsa wayarta.       “Barkanku da zuwa ranka ya daɗe”. Nurse ɗin ta faɗa cikin ɗan rawar jiki tana miƙewa zaune. Ranta fes kamar an bata ƙyautar kujerar makka yau gata ga babban ɗan kasuwar nan daya gawurta a ƙasar NAYA da ƙetare a gabanta. Tare da young millioner grandson ɗin sa a gefensa. Dan fuskar Ramadhan sananniyace ga mutane sakamakon rawar da yake takawa shima akan dukiyar tasu wajen juyata da kuma nuna bajintar taimakon talaka akan aikinsa na lauyanci. Babban abinda ya sake bayyanama duniya fuskar tasa lokacin daya rasa matarsa sakamakon shan guba da sukai, dan labarin babu gidan jarida da redio da yanar gizo da bai zagaya ba. Hatta da Raudha taga labarin duk da a lokacin tana jss 2 ne a secondary.     Dan in bata manta ba alokacin har gulmar tsarin halitta da iya ɗaukar wankan Ramadhan ɗin tayi a ranta, duk da kuwa a jikin jarida ta gani ita a wajen wata ƙawarta Rahma Salisu.....       “Masha ALLAH, Alhmdllhi ya rabbi”. Bappi ya faɗa yana duban Raudha murmushi na sake faɗaɗa akan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa.     Murmushin ƙarfin hali itama tai masa, dan haka kawai ita dai dattijon ya shiga mata rai. “Abba ina kwana”.     Ta faɗa da dasashshiyar muryarta tana satar kallon Ramadhan da ko kallon ɗaya a cikinsu baiyi ba balle ɗakin. Tunda suka shigo ya jingina da bangon farkon shigowa ya tura hannunsa a aljihu ya fiddo wayarsa dake tsuwwa yana dubawa. Hakan yasa Raudha bata ganin fuskar tasa da ƙyau yanda ya kamata. Sai dai ƙamshin turarensa da yanda kayan suka zauna ɗas a halittarsa yay mugun fisgar idanunta daga kasa barin kallonsa da son tuno a inda ta taɓa ganinsa......        “Lafiya lau ƴar albarka, yaya jikin naki?!”. Bappi ya sake katse mata tunani a karo na biyu yana kallon ƙafarta da akai hanging jikin wani ƙarfe, har yanzu a kumbure take sosai abin tausayi.      “Alhamdulillahi naji sauƙi Abba”. “Zadai kiji soon insha ALLAH. ALLAH yay miki albarka. Ya cigaba da baki kariya a duk inda kika shiga a faɗin duniya. ALLAH ya share hawayenki ya azurtaki da zuri'a ta gari da zata zama lulluɓin nagartacciyar inuwa ga ƙaddarorinki”.       Hannu Raudha ta kai ta share hawayen da suka silalo mata tana amsama bappi. Zuciyarta sai sake faɗaɗa take da ƙaunar tsohon.       Magana da Bappi yayma Ramadhan ne ya sakashi ɗan matsowa gaban gadon, a karon farko yayma Raudha kallo guda yana tura wayarsa a aljihu, tare da ɗauke idon nasa da ya saka tsigar jikin Raudha tashi. Ƙafar yaɗan kalla, sai kuma ya watsa mata harara. Tun a jiya daya karanta abinda ya faru kafin ya iso ƙasar, da kuma bayanin da Bappin yay masa akan yanda abin ya faru sai zuciyarsa ke raya masa akan wani dalili Raudha ta aikata hakan. Dan in babu dalili babu yanda za'ai ta bada jikinta a raunata saboda kakansa. Na farko kodai akwai shiri a lamarin, ma'ana tanada alaƙa da makashin. Na biyu ko tayi hakanne domin kuɗinsu ko wani abu makamancin hakan. Na uku tanada alaƙa da waɗanda suka halaka masa mata da ƴars......       “Ramadhan!”. Bappi ya ambaci sunansa a nutse ganin kallon banzar da yake yima Raudha a kaikaice. Fuska ya sake ɓatawa da jan ƙaramin tsaki a ransa. Harya buɗe baki zaiyi magana ya maida abunsa ya tsuke ganin Bappi ya ɗan ja baya yana kai wayarsa da aka kira cikin kunne alamar amsawa.          Tuni Raudha ta ɗauke idanunta daga kallonsa. Saboda kallon banzar da taga yana binta da shi ya saka zuciyarta yin ɗaci. Tanada haƙuri, amma tana da zuciya. Sannan ta tsani wulaƙanci koda ga wanda ya girmeta ne......       A hankali cike da ƙasaitarsa da jin eh ya isa ya taka gaban gadon sosai fiye da farko, ƙamshin turarensa ck one ya sake sirɗaɗawa cikin hancin Raudha yana keta cikin jininta zuwa ɓargo, saboda ƙarfinsa da tasirinsa ga ma'abocin shaƙansa. Ƙarfen gadon ya dafa saitin kanta tare da ranƙwafowa har tana iya jin fitar sautin numfashinsa. Ya saki wani sihirtaccen murmushi mai ɗauke da ma'anoni da yawa dai-dai gaɓar da yake cafke ƙwayoyin idanun Raudha da mamakinsa ya sata ɗagowa ta kallesa cikin nasa.       “Ki daina yaudararsu, ki kuma tabbatar musu ke *_BAƘAR INUWA ce_*. Idan kikai wasa da gargaɗina ni zan zame miki *_BAƘAR INUWAr_* da sai kin gwammaci *_GARA RANA DA NI!_*.             A kausashe furucin ya fita daga harshen Ramadhan, cikin ƙasaitacciyar muryarsa mai faɗi da kauri ya shiga dodon kunnen Raudha. Da ace ba kusa gab yake da kunnuwanta ba, ita da kantace zata ƙaryata cewar shine ya faɗa ɗin, dan duk wanda yaga yanayin nasu zai ɗauka wata maganace mai daɗi a sanadin tausayawa.       Kafin ta iya ce masa wani abu ya fincike idanunsa a cikin nata cike da tabbatar da gargaɗinsa. Ya ɗan dubi Bappi dai-dai yana ɗagowa ya miƙe akan ƙafafunsa da ƙyau. Ganin Bappin su yake kallo sai ya sakar masa murmushi yana ɗan kai hannu ya shafo ƙeyarsa...        Tabbas wani abu da Ramadhan bai kawo a ransaba a wannan gaɓar ya shiga ran Bappi a bazata. Tun a daren jiya yake cuɗawa da kwancewa wajen laluben nemo hanyar da zai kwatantama Raudha da iyayenta alkairinta, amma sai ya gagara samowa. Dan gani yake kuɗi, gida, ko makamantansu dan ya bama Raudha bai biyata ba. Saboda ita ransa ta fansa. Sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci ALLAH ya haska masa wata hanya da yake ganin ko bai saka mata ba, zai kwatanta kusantata gareshi harya samu alkairi daga alkairinta a cikin zuri'arsa..... Ya saki wani ƙasaitaccen murmushi yana kai hannu bisa kafaɗar Ramadhan ya ɗan bubbuga cike da salon manya idan abu yay musu daɗi.         (Lallai sun dace) ya ayyana a ransa yana duban Raudha data kauda kanta gefe zuciyarta na luguden daka daga kausasan kalaman Ramadhan da zuciyarta ta kasama fashin baƙi. Sai kawai nan ma Bappi ya fassara kauda kan nata da tunanin jin kunya duk da baisan wane furuci jikan nasa ya furta a gareta ba.         Ramadhan da shi sam baima kawo abinda Bappin ke ayyanawa ba a tunaninsa sai kawai ya nufi hanyar fita dan gaba ɗaya ya gundura da zaman asibitin. So yake yabar ƙasar nan a daren yau dan tuni ya kammala booking flight. Sai dai zai tashi ne ta jihar Loss shiyyasa yake son barin Bingo da wuri yaje can ya ɗan huta kafin daren.        Nanma da kallo Bappi ya bisa yana murmushi, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga Raudha da har zuwa yanzu ruɗani bai bar tunaninta ba... *_TAURA HOUSE_*       Tun fitarsa take ƙame a tsaye, sai da ta fahimci jinin jikinta sulalewa yake zuwa ƙasa sannan tai jarumtar jawo numfashin dake neman barin ƙirjinta yana bin jininta dake sauka a ƙafafunta. A ƙa'idar kowanne ranakun bikin salla na babba da ƙarama washe gari a masarautarsu take yinta ita da dukan iyalanta dama ahalin masarautar garin ta Bina. Shiyyasa a yanzu haka jirgin da zasu bi a shirye yake tsaf zuwa jihar BINA fitarsu kawai ake saurare.       Waya ta jawo da sauri dan bazata iya jira har sai ta isa garin Bina ba zuciyarta zata iya fashewa. A yanda take ƙoƙarin dialing numbern na ƴar uwarta Asma zai baka tabbacin a ruɗe take. Ta saka wayar a hansfree dai-dai shigarta. Bugun shigar kiran na bugawane dai-dai da bugun zuciyarta. Sai dai abin takaici harta tsinke ba ɗagaba. Sake kira tai nan ma babu amsa. Sai da ta jera kusan kira biyar amma ba'a ɗaga ba. Lallai babu lafiya, dan a ƙa'idar gimbiya Su'adah daga kira ɗaya bata sake yima mutum ko yaya suke, mai-martaba ne kawai keda wannan alfarmar da arziƙin a gareta. Amma a yau sai gata da jera har biyar batare da taji ta gundira ba.      Da sauri ta maida akalar kiran nata ga mai-martaba saboda zuciyarta ta ayyana mata shine kawai maganin kukanta a yanzu bama Asma ba. Cikin sa'a kuwa tana gab da tsinkewa a ka ɗaga, domin kuwa abune a bayyane kowa yasan gimbiya Su'adah ƴar gaban goshin mai-martaba ce saboda sunan wadda ta riƙesa da yakema kallon uwa aka saka mata.     Cikin girmamawa tamkar tana a gabansa ta rissina tana gaishesa. Daga can ya amsa da sakewa cike kuma da ƙasaita irin ta masu mulki.       “Mamana kun iso ne?”.   Cikin girgiza kai da sake raunan murya ta ce, “A'a Abi bama mu taho ba. Dama Ramadhan ne yazo NAYA jiya, bamma san da zuwan nasa ba sai a safiyar yau. Koda ya shigo gaisheni yayiminne tamkar maƙiyarsa ba mahaifiyarsa ba. Daga ƙarshe yake sanarmin a yau zai koma America. Nama tabbatar yanzu yana gab da barin ƙasar..” ta ƙarasa faɗa tana sakin wani kuka mai ban tausayi gamai saurarenta.      Mai-martaba ya saki ƙasaitaccen murmushi yana gyara kishingiɗarsa. “Ni ban san randa Mamana zata girmaba har yanzu. Yanzu dai akan   Ramadhan kike ɓatamin hawayenki? To sharesu ki kwantarmin da ranki. Yanzu babu jimawa mukai waya da Alhaji Hameed akan zasu ƙaraso nan tare da shi, suna airport ma a yanzu haka”.      Wani irin wawuyar ajiyar zuciya ta saki da murmushi lokaci guda. Sai hawayenta data kai hannu ta share da faɗin, “Nagode Abbi”.       “Godema ALLAH”. Ya bata amsa yana yanke wayar. Tuni ta manta da hawayen fuskarta ta hau sakin murmushi. Koda Addah Asma ta kirata batabi takan kiran ba dan tasan yanzu zasuje su haɗu ai.... *_TK SPECIAL HOSPITAL_*           Ita ɗin yarinyace mai kaifin basira da hangen nesa. Hakan yasa tun bayan barin su Ramadhan ɗakin ta shiga cikin zurfin tunani da fassarar kalamansa. Sai dai kafin ta samu damar samo amsar sallamar ƴan uwanta da su Asabe harma da kakarsu Hajiyar birni ya katseta. Taji daɗin ganinsu dan dama tunda ta farka take tambayar likita ina suke. Dan da farko ta tsorata da tsadajjen asibitin da taga kanta a ciki.       Rungumeta Asabe tai tana kuka, dama shi ta kwanayi a daren jiya. Dan gani take Raudha ta rasu ne su aunty Hannah na ɓoye mata. Hakama Yasmin tana kallon ƙafar Raudha ɗin ta fashe da kuka, kukanta kuma yaja hankalin su Samha suma dake ƙananan yara suka fara.        Sai da hajiya mama ta ɗan musu tsawa ne ganin aunty Hannah na lallashinsu sunƙi su nutsu. Yanzu kam tsit sukayi sai Asabe ce ke nata tana jerama Raudha addu'oin samun lafiya....    ★     Kasancewar Alhaji Hameed Taura ba ƙaramin mutum bane cikin ƙanƙanin lokaci zancen sake ziyararsa asibiti tare da jikansa ta baje kafafen yaɗa labarai dana yanar gizo. Harma abin ya bama Bappin mamakin tunda yasan baici karo da ɗan jarida ko gudaba. Sai dai tunawa da cewar yanzu waya ta maida kowa ɗan jaridar kansa ya sashi watsar da kokwanton.       Yabo dai kam yana samu akan ƙoƙarin tsayawa tsayin daka ga Raudha. Dan yanda kowa yasan wanene shi ba'ai tunanin zai bada lokacinsa gareta ba. *_JIHAR BINO PLACE_*           Duk da Ramadhan nata ɓata fuska a cikin jirgi hakan bai hanashi jin daɗiba a ransa sanda suka iso cikin masarauta. Dan suna sauka a airport ƙayatattun motoci na alfarma guda huɗu wanda uku ke tare da hadimai, ɗaya ta ɗaukarsu suka iso filin jirgin.         Alhaji Hameed Harith Taura kowa yasan abokine ga Sarki Abdul-wahab tun da ƙananun shekaru. Dan kuwa tarihi ya tabbatar da sunyi karatun degree na farko tare a jami'ar Bino. Sannan harkokin kasuwanci sun sake haɗasu a wasu fannoni kafin mai-martaba ya haye karagar milkin jihar ta Bino. Sai kuma gashi sun zama surukai a dalilin auren ƴaƴansu.        Yau ranace da masarauta ke cike da baƙi tako ina. Amma hakan bai hana a samarma da su Ramadhan tarba ta musamman ba. Ramadhan na gama gaisawa da mai-martaba daketa tsokanarsa akan ya'akai kuma ya baro masu jajayen kunuwan?. Ko sun gaji sun koroshine da kansu. Shi dai murmushi kawai ya dingayi dan ba kasafai irin wannan wasar ke shiga tsakaninsa da kakannin nasa ba. Daga su Bappi har su mai-martaban sunyi trianing nashi ne like iyayensa ba kakanni ba. Garama Fulani takan ɗan tsokanesa. Sai dai kuma shi ɗin bawai ya iya wasan baneba iyakarsa murmushi ko ada can ma balle yanzun.      Fahimtar magana su mai-martaba kesonyi ya sashi zame jikinsa zuwa cikin gida domin ya gaisa da kakar tasa da iyaye da ƴan uwa. Yako karancesu da ƙyau, dan yana fitar suka hau tattauna dalilin zuwan Alhaji Hameed ɗin dan awa ɗaya kacal suke da ita saboda mai-martaba na amsar baƙuncin manyan mutane masu barka da shan ruwa da barka da salla.      Abubuwa masu muhimmanci guda biyu suka tattauna. Wanda ya shafi auren Ramadhan da Bappi atake ya sanar ma mai-martaba har yayi masa mata. Da kuma batun fitowa takara da zata bayyana nan da ƙanƙanin lokaci.    Duk gaba ɗaya mai-martaba yayi farin ciki ya kuma sanya albarka da fatan alkairi a cikin lamarin, tare da bada goyon baya dan a ganinsa ai babban cigabane jikan nasu ya samu. Daga haka ya ƙara da nasa shawarwarin shima...........✍ *_Barkanmu da dawowa._*😘😘👌🏼      ________________________ *mg's skincare* Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩 Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️ Shin kinafama da Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata? Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫 Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind Bridal kit:18k Beauty kit:11k Student package:7k Herbal whitening soap:3k Chat 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Facebook: mg's skincare Instagram:glow_with_mgs Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝 Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩 Then @mgs skincare gat you covered 💯 Now is time to glow😍 Pamper ur skin🦵 Shine like bride👰🏻‍♀ Glow🧖‍♀️ 💯 tested nd trusted🤝 Guarantee Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166 _____________________ https://arewabooks.com/chapter?id=629a77b967809ad6daab2109 *_Chapter 13_* *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/6, 11:46 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 15_* ..........Su Bappi basufi mintuna talatin da isowaba Gimbiya Su'adah da tawagar ƴaƴanta mata suka iso suma. Anan ne ta samu damar haɗa hannu da fulani (mahaifiyarsu Uwargidan sarki) da Adda Asmah suka rufe Ramadhan da faɗa sosai akan abubuwa da dama, ciki harda batun zamansa babu aure, duk da dai basu fiddo maganar zaɓa masa mata ba.      Shiko dai ya cinkushe fuska yana saurarensu kawai. Sai da sukayi mai isarsu ya basu haƙuri kawai yay fitowarsa. Dan Bappi ya kirasa akan ya fito su wuce. Idan kuma ya barsa anan to?. Da sauri yacema Bappi a'a zai bisa, dan so yake yaje ya wuce loss, sai dai bai faɗama bappi ƙudirin nashiba kai tsaye. Yanzu kam ya iske mai-martaba tare da Bappi da Pa da suka iso da Gimbiya Su'adah. baiyi mamakin ganin Pa ɗin ba, tunda tun yana ƙarami yasan a irin wannan ranar ta washe garin salla suke zuwa gaishe da mai-martaba ɗin daman. Zama yay gefen mai-martaba daya nuna masa yana satar kallon Pa da fuskarsa ke a haɗe alamar har yanzu yana kan fushinsa na jiya. Koda yake har suka baro Bingo dama baiko kallesa ba duk da har falonsa yaje ya gaishesa.        Sai da suka tabbatar da nutsuwarsa sannan Bappi ya fara magana cikin nuna alamar babu wasa tattare da shi.          Ramadhan ya ɗago a firgice yana duban mai-martaba. Kafin ya maida dubansa ga Pa da baice uffan ba.      “Bappi!”. Ramadhan ɗin ya faɗa cikin rawar harshe.        Bappi dake kallonsa cike da tausayawa a can ƙasan ransa. A fili kam ya dake ya jinjina masa kai. “Umarnine wannan ba shawara ba Ramadhan. Domin nasan zaka iya insha ALLAH. Zaka kuma kawo cigaban da muke fata wa ƙasar nan ta hanyar basira da ƙuruciyar da ALLAH yabaka. Domin NAYA irinka take buƙata, tabbas irinka take buƙata.”         Miƙewa Ramadhan yayi yana girgizama su Bappi kansa. Ya kai hannu ya tura hular kansa baya saboda zufa dake ɓillowa a kowacce ƙofa ta gashinsa. Babu abinda zuciyarsa ke ambata sai sunayen ALLAH. Ya sake buɗe baki zaiyi magana Pa ya dakatar da shi....         “Biyayya ga iyayena dole ne a gareka, domin bazasu taɓa jefaka a hanyar halaka ba. Tunda har su Bappi suka amshi tayinsu, dolene kaima ka amsa da ga garesu kayi biyayya. Idan ba hakaba babu ni babu kai da ga yau da ga wannan likaci....”        “Pa Please yayi girma da yawa....” “Baiyi ba Ramadhan. Domin kaima kayi abinda kakeso a shekaru biyar muka kuma ƙyaleka, duk badan kafi ƙarfinmu ba. Dolene yanzu kaima kabi abinda mukeso dan lokacinmu ne.”         “Ya ALLAH”. Ya faɗa cikin sake shiga tashin hankali yana komawa baya ya sake zubewa a cikin kujerar da ya tashi. Gaba ɗaya ƙwayoyin idanunsa sun sake canja kala a lokaci ƙanƙanin. Ɗan sassaucin daya samu na damuwar jiya wadda ta fita ta sake maye gurbinta. Gaba ɗaya gashin jikinsa ya mimmiƙe sai faman tura yatsun hannunsa yake cikin sumarsa dan son control ɗin abinda ke taso masa...        Duk da Bappi ya san Ramadhan ɗin yakai maƙura gab yake da birkice musu bai sassauta masa ba. Dan a ganinsa gara ayita baki ɗaya ta ƙare kawai. Hakan yasa kai tsaye ya ɗora da faɗin, “Sai kuma batun aure, shima mun riga mun maka mata dan ko munce ka nemo ba kawowa zakai ba. Bakuma zai yuwu ka hau mulki babu mace ba, idan har ALLAH ya ƙaddara zaka hau ɗin. Dan haka mun gama yanke hukunci mu zamu nema maka aur.....”       Kafin ma Bappi ya ƙarasa numfashin Ramadhan ya fara fisga. Ya shiga laluben hanun bappin dake kusa da shi, da ƙyar ya samu ya riƙosa ya damke. Cikin sauri Bappi ya miƙe ya ya rungumesa a jikinsa da kiran sunansa yana girgizashi.       Su dukansu ɗunbin tausayinsa ne a cikin ransu. Wannan yanayi da yake shiga idan ransa ya ɓaci yana tada musu hankali, babu irin likitan da basu gani ba, amma iya bincike akan sanar musu lafiyar ƙwaƙwalwarsa kalau. Sai dai maimakon su maida hankali gana musulinci sai suke sakaci, dan tabbas al'amarin nasa yana kamanceceniya da nai mai iska ko sihiri, ga diabetis kuma da shima ya zame musu na gado. Dan shi kuma Bappin ne ke dashi, shima Alhaji Basheer ɗin nada, hakama Ramadhan ɗin da wasu a cikin yaran gidan ƴammata.       “Ramadhan relax, calm down Please”.     Bappi ya faɗa yana shafa kafaɗarsa da ɗora masa kofin ruwa a baki. Babu musu ya sha kusan rabi, sai kuma ya miƙe ya sake rungume Bappin. Murmushi Bappi yayi da sake rungumesa da ƙyau shima yana shafa bayansa.          “Please Bappi a sassauta mini koda maganar auren a janye”. Ya faɗa lokacin da Bappi ke ɗagosa da ga jikin nashi.       Murmushi Bappi yayi mai ƙayatarwa da shafa sumar Ramadhan ɗin yana girgiza masa kansa. “Babban sassauci kawai bin umarninmu Ramadhan. Idan kayi hakan sai ALLAH ya albarkaceka da nasarori a rayuwarka ok?”.        Maimakon amsa sai ya sake faɗawa jikin Bappin ya ƙanƙamesa har takai mai-martaba da baice komaiba har yanzu sakin murmushi. Shi kansa Pa gefe ya maida kansa yana nasa murmushin dan yasan mai shiga tsakanin Bappi da Ramadhan sai ALLAH. Shi kansa ya buɗe masa wutane dan yasan sa sarai akan kafiya da dagiya kan abinda bayaso. Shiko bazai taɓa yarda mahaifinsa yaji kunya ba tunda har ya riga ya amshi tayin su president ɗin.... *_GOVERNMENT HOUSE_*         Tarba ta musamman Alhaji Hameed Harith Taura ya samu shi da Ramadhan a fadar ta shugaban ƙasa, kasancewar tun a daren jiya Bappi ya sanarma mai-girma shugaban ƙasa zuwan Ramadhan ɗin NAYA ta hanyar text Message.         Duk da tarin liyafar da aka shirya domin Ramadhan hakan bai wani birgesaba, dan tunda suka baro masarautar Bina zuciyarsa bata tare da gangar jikinsa duk da nasiha mai ratsa jiki da mai-martaba da Pa da Bappi sukai masa.       Sai kuma Raudha dakan faɗo masa a rai. Sai yanzu yake ƙara yarda da hasashensa kan dalilin Raudha na bama Bappi kariya. Dan haka kawai bazata bada ranta akan wanda bata saniba ko rashin dalilin, zuciyarsa na sake tabbatar masa a yanzu abinda tayi nada alaƙa da wannan batun na fitowarsa takara, lallai akwai wani shiri a ƙasa da su Bappi basu fahimtaba. Sai dai wanene ke shiryawa? Akan mi? Akan wane dalili? Duk bai saniba shima.       A zuciyarsa yake ayyana. (Inko hakane dolene nabi dukkan hanyar daya dace dan na sani koda kuwa hakan na nufin zai iya rasa raina).       Taro ne daya tara manyan jiga-jigan jam'iyyar tasu, sai dai gaba ɗayansu sunada masaniya akan son tsayar da Ramadhan takarar. Amma kowa yanada manufarsata ta amincewar kuma. Wani yanki a cikinsu kamar su Alhaji Yaro glass sune suka san ainahin manufar. Sauran kuma suke kallon hakan bisa ƙyaƙyƙyawar niyyar manyan jam'iyyar na kawo dai-daito akan rabuwar kawuna dake neman shiga tsakaninsu a dalilin yawan ƴan takara. Sai dai kuma duk da haka wasun su zukatansu a ƙuntace suke da rashin son Ramadhan ɗin musamman da suka gansa yaro ƙarami saboda mafi yawansu sun haura sittin su, kawai dai basu da ƙarfin faɗa ajine sai ya zam dole suka zuba ido wajen bin gangar yarima asha kiɗa.       Bayan anci an sha da ga abinda aka tara wanda Ramadhan ko ruwa bai sha ba a wajen suka fara gudanar da abinda ya tarasun. Shugaban jam'iyya da sauran jiga-jigai sukayi bayanai da welcoming ɗin Ramadhan cikin su, tare da fatan zai basu haɗin kai wajen yin aiki tuƙuru da ƙara ɗaga darajar jam'iyya.      Ba wani fahimtarsu yake ba, dan sam hankalinsa baya a tare da su. Amma magana da ido da Bappi yay masa ta tilasta masa miƙewa yay bayani shima. Bayan godiya da jinjina a garesu ya tabbatar musu zasu sameshi fiyema da yanda suke buƙata.      Jin kalmar (fiye da yanda suke buƙata) a bakinsa ya sasu ji a ransu zasu iya juya Ramadhan duk yanda sukeso domin biyan buƙatunsu..... *_JIHAR ƊILLO. HUTAWA_*                            Tunda Asabe tabar gidan gaba ɗaya sai ya koma tamkar wani zararre. Duk masifarta da gantalin faɗansu da baya ƙarewa itaɗin ta daban ce a gareshi. Dan a gidan Asaben ce kawai zata samu abunta ta bashi batare da baƙin ciki ba. Amma ko baba Nafi duk haƙurinta akwaita da halin banza a wani fannin itama. Sai dai nata da sauƙi akan na Larai.      Da farko Larai tata ƙoƙarin ganin neman auren da Alhaji Maude Dallatu Kema Raudha ya dawo kan ɗiyarta ne Zabba'u. Dan tata lallaɓa M. Dauda akan hakan tare da banka masa rubutu da magungunan malam. Ance tsafi gaskiyar mai shi, dan ta ɗan fara samun kansa harma da manta Asabe da ƴaƴanta da taso yayi, sai dai kuma ba'aje ko inaba aikin ya watse.        Dan a ranar salla tunda labarin abinda ya faru da Raudha yazo kunnensa sai ya rikice harda kukansa. Ya dinga tsinema Alhaji Hameed Taura akan yaja an kashe masa ɗiyarsa saliha mai addini. Dan kuka rurus ya zauna yanayi a bakin masallaci. Mutane suka taru a kansa anata bashi haƙuri da lallashi amma M. Dauda sai sake ɓare baki yake yana fyatar majina.       Daga ƙarshe yace inhar anaso yay shiru sai a haɗa masa kuɗin motar zuwa Bingo inba hakaba yata kuka kenan har sai Alhaji Hameed Taura yazo Hutawa. Mutane sun san halin M. Dauda ƙwallon ɗan is.... Ne shiyyasa basuyi ƙasa a gwiwa ba wajen fara haɗa masa wasu ƴan kuɗaɗe. Yai kwanaki biyu kenan kuwa ana haɗa kuɗin a masallaci. Ba wani kuɗin kirki bane suke badawa. Mai hamsin mai ɗari ne kawai, shiyyasa haɗa kuɗin yaɗan ja lokaci duk da sun san zuwa yanzu ya samu fiyema dana motar.     Ilai kuwa a daren jiya aka tattare kuɗin naira dubu bakwai aka bashi harda canji a sama. Daɗi ya sakashi fara godiya yana kuka, harda cewa baisan ana ƙaunarsa a anguwar tasu ba har irin haka. Sudai mutane dariya suka dinga gumtsewa kawai. Shi ko ko'a jikinsa, ana idar da sallar asuba ma ko wanka baiyiba yaje gida ya canja babbar riga kawai, rigar duk ta fita hayyacinta da tsufa da dauɗa amma bai damuba. Dan itace kawai rigarsa ta arziƙi ta ganin shugaban ƙasa. Ya dakwarra wata shegiyar hula da ko wanki babu tare da ita balle sitatin kirki.      Duk jarabar da Larai taita masa da ƙirƙirar suyi rigima ta lalube kuɗin bai kulata ba, sai ma ɗakko bakko ɗin kayansa data gama shiga uku dan tsufa yay yayi fitowarsa. A ƙofar gida yaci karo da malam Gambo abokinsa. Yay wani gaba kamar zai kifa sai kuma ya dawo baya ya dafe bango yana hangame baki da haɗe fuska.         “Kai kuma lafiya na ganka anan harda malum-malum?”.     Baki M. Gambo ya washe yana miƙewa tsaye da leda viva ɗinsa a hannu, shi kansa ba ƙaramin a harmutse yake ba, dan har gwarama m. Dauda ɗin ta wani fannin. “Kai abokina ya kake magana haka kamar ka manta ni abokinka ne na amana. Ai bai kamata na barka kaje kai kaɗai ba babu kara. Dole ne na bika muga halin da yarinyarmu ke ciki tare. Mu kuma san matakin da zamu ɗauka akan tsohon nan Taura”.        Da farko ƙanƙance idanu M. Dauda yayi yana harar M. Gambo Ƙasa-ƙasa. Sai kuma tunawa da yay M. Gambo ya fisa tujara ƙila idan sun sami ganin Taura zaifi ƙwato musu ƴanci. Dan yayi alƙawarin idan Taura bai sauraresu ba gidan redio zai dawo ya masa terere duk da a yau yaji a labarai an sake cewa Taura da jikansa sunje sun sake duba Raudha a asabitin da aka ɓoyeta ana bata tsaro na musamman. Ciwon Raudha ya damesa, amma a ƙasan ransa gani yake silar arziƙinsa ce a wajen. Dan yasan dai baza'a nakasta masa ɗiya a dalilin Taura ba Taura yaƙi jiƙashi da kuɗaɗe. Wannan yanada ɗaya daga son zuwan nasa Bingo...       “Abokina daina tunanin nan muje da-ALLAH kar rana tayi”.     “A'a ai ba tafiyar bace matsalata M. Gambo, ka sani duk fa abinda muka samo sammaka zanyi ba raba dai-dai zamuyiba. Dan nasan badan ALLAH kake son mini binbinin nan ba.”       Kamar m. Gambo zaiyi magana sai kuma ya fasa, dan yasan halin buyagin M. Dauda. Lallamashi kawai ya shigayi harya haƙura suka tafi tasha neman motar Bingo..... *_BINGO CITY (TAURA HOUSE)_*          Komai ya ƙwace masa, babbar damuwarsa hanashi komawa da Pa da Anne sukayi America. Dan Bappi dai yaƙi yace masa komai tunda suka baro gidan gwamnati. Shima ɗin bai yarda ya zauna da kowa ba ya shige ɗakinsa dake a sashen na su Anne. Koda yake bazamuce ɗaki kawai ba. Dan shima tamkar wani part ne na musamman a wajen. Falone har guda biyu ƙarami da babba, ƙaramin an shiryasane kawai dan hutawa, inda glass ne kawai ya rabasa da babban sai labulaye. Sai bedrooms biyu, kitchen, store, dining, da ƙofar da zata sadaka da backyard inda akai wani haɗaɗɗen ƙaramin garden da yasha tsirrai masu ni'ima, ga madaidaicin swimming pool a gefe da akai masa wani style da ruwa ke fitowa ta wani dutsuna tamkar ƙorama. Daga can gefe keɓantaccen wajene da akayi da glass an cikashi da kayan motsa jiki ().      Duk gidan bamai shigowa wajen sai idan aikosa akai, dan ko baya nan mai kula da shine kawai ke shigowa saiko Bappi idan yanason kaɗaice kansa. Idan kana hango wajen daga cikin falonsa saboda glass ne a bangon saika ɗauka bama cikin NAYA kake ba, dan daga falon kana jiyo ƙamshin furanni dana saukar ruwan dake fita a dutsen nan, ga grass carpet ta ko'ina lamarin ba'a cewa komai.        A yanzu hakan ma dai a cikin garden ɗin yake kwance bisa kujera irin wadda akan ajiye gaban ruwan nan domin hutawa kawai, ƙafarsa ɗaya a ƙasa ɗaya tana kan kujerar, yayi kwanciyar rigingine ne fuskarsa na kallon sama, yay filo da hannunsa ɗaya yayinda ɗayan ke riƙe da gorar ruwa, ya ƙurama sama ido tamkar yana irgen gajimaren dake yawo ne a cikinta.      Abu biyune sukafi komai masa kaikawo a yanzun. Maganar siyasa da su Bappi keson tsundumasa batare da shi ya taɓa ra'ayin hakan ba. Sai ɗunbin zargin Raudha da yake ganin tayi komai ne da wani dalilinta kona sakawar waninta. Na ƙarshe ma tana ɗan sukarsa sai dai ba sosai ba, wato maganar aure, babu zancen ƙara aure a budget ɗinsa, dan haka koma ƴar wacece ake son aura masan shi zai gargaɗeta ta bijire ma su Bappi. Dan haka baya ɗaukar wannan babbar matsala........✍ To Ramadhan B. Taura bara mugani koba babbar matsala bace kamar yanda ka ɗauka😜🏃🏃.                    https://arewabooks.com/chapter?id=629a77b967809ad6daab2109 *_Chapter 13_* *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/7, 5:07 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 16_* ..........Tunda mai-martaba ya sako zancen Ramadhan a cikin meeting da yakeyi da ƴaƴansa da matansa a duk irin wannan ranar hankalin Gimbiya Su'adah da Fulani da Adda Asmah yake a tashe. Ba komai ne ya tada hankalin nasu ba kuwa sai jin mai-martaba yace har Alhaji Hameed Taura yayima Ramadhan ɗin mata. A cikin satin nan ma zasu tuntuɓi iyayenta dan baya buƙatar abun yay nisa.     Duk yanda gimbiya Su'adah taso daurewa saboda ƴan uba dake a wajen kasawa tai. Ta ɗago a firgice tana kallon mahaifin nasu. Cike da ƙasaita yace, “Mamana kinada magana ne?”.     Kowa yasan irin son da yake mata saboda sunan wadda taci, dan haka suka shiga ɗan taɓe baki suna maida kawunansu gefe rayukansu fal hassadar jin Ramadhan zai fito takarar shugabancin ƙasar NAYA a dalilin kakansa.       “Abi maganar yimasa matar ne sai naga kamar anyi gaggawa, tunda kaga abinda ya faru a baya kamar ya kamata a bari ya nutsu kafin a sama masa wadda zata dace da shi da matsayin da muke fata zai hau”.        Mai-martaba da ke kallon television kamar bazai ce komai ba sai kuma ya ɗan murmusa. “Mamana banda abinki wace nutsuwa Ramadhan ke buƙata bayan wadda ya samu a shekaru biyar da faruwar rasa iyalinsa. Kece fa kike damuwa da rashin aurensa har kike damuna, yanzu kuma an sama masa kina jayayya?. Alhaji Hameed bazai taɓama Ramadhan zaɓen matar banza ba, sannan yanada iko akansa irin wanda ni bani da shi matsayina na kakansa ta ɓangaren mace. Inaga addu'a da fatan alkairi ya kamata mu masa, dan bazasu taɓa zaɓa masa matar da bazata dace da matsayin da kike kallon ba”.      “Amma Abie....” Kansa ya girgiza mata. Kafin cikin ƙasaita ya ce, “Na gama magana Mamana”.      Dole tai shiru, sai dai zuciyarta tafasa take tamkar zata kama da wuta. Fulani da bataso Gimbiya Su'adah yin maganar anan ba ta ɗan harareta ta wutsiyar ido itama. Dole tai shiru har aka tashi taron kowa ya koma sashensa. ★★       “Ammi wlhy bazan amince ba a wannan gaɓar, wai taya za'ace ni da Basheer dake mahaifin Ramadhan bamu isa yanke hukunci akan ƴaƴanmu ba musamman ma Ramadhan sai dai tsoffin nan dake matsayin kakanninsa.”     Gimbiya Su'adah daketa kaikawo a cikin falon hutawa na Fulani ta faɗa cikin tashin hankali. Kafin Fulani tace wani abu Adda Asmah ta amshe rai ɓace.      “Maganar gaskiya wannan fin ƙargine Ammi. Amma ni ina ganin tun farko harda sakacinmu. Taya zaki sakar musu ragamar ɗanki bayan shi kaɗai ne tilon ɗa namiji a gidan. Daɗin daɗawa shine kuma babba.....”      “To Adda ya kike so nayi?, bayan kinsan tun daga yayen Ramadhan suka riƙesa suka hanani, wane kalar abune banyiba amma sukai kunnen uwar shegu dani tsoffin nan”.       “Amma ai basai ta wannan hanyar ne zaki dawo da Ramadhan jikinki ba. Tun a lokacin ya kamata kiyita jan ra'ayinsa cikin hikima shi da kansa zai dawo gareki batare da kin nuna musu koda a fuska ba. Amma ai wannan ƙarfa-ƙarfar tayi yawa. Dan wlhy yanda yakejin maganar waɗan nan tsoffin da mutuwa ke gab da su bayajin taki ma”.         Tsaki Fulani tayi, hakan ya sasu kallonta su duka. Ta gyara zamanta na ƙasaita tana hararsu.        “Kunfa dameni da surutan banzarku. Ku miyasa a komai baƙwa nutsuwa kuyi abun hankali sai shirme. K Su'adah yanzu kamata yay ki lallaɓa musan wacece zasu aura masa. Ni yanzun zan tuntuɓi mai-martaba da batun ƙudirinmu na haɗa auren Aynah da Ramadhan ɗin naji mizaice, duk dai abinsa ai bazaiƙi jikarsa ba ko?. Indai Ramadhan ne a wannan gaɓar zai dawo garemu, dan bazamu amince ya samu mulki su Firdausi su cigaba da juya manashi yanda suke so ba. Shine babban jikana na farko, dan haka nima inason abina”.        Sosai shawarar mahaifiyar tasu ta ɗan basu nutsuwa, dan haka gimbiya Su'adah ta zauna tana sauke numfashi da ajiyar zuciya.... *_TK SPECIAL HOSPITAL_*          “Kai wlhy idan sama da ƙar zata haɗe yau sai na shiga naga halin da gudan jinina ke a ciki, kajimin mara mutunci. Bar ganin kasa waɗan nan kayan kai tunanin zanji tsoronka, kai fa ba komai bane sai mai gadin gate ɗin asibiti mun sani, ni da kake gani na anan ba ƙaramin tantiri bane, duk wani gidan shege da shegiya dake ƙasar NAYA da mu akai taron bikin buɗesa saboda gawurtarmu a iya shege. Idan kaji ƙarya cigaba da nunamin yatsa kaga idan ban karya shege ba naga miza'ayi min”.     M. Dauda ne ke zuba ruwan bala'i a gaban gate ɗin Tk special hospital. Dan security ɗin gate ya hanasu shiga ciki, shine suka tafi da kokawa akan sai fa sun shiga ɗin. Ganinfa da gaske suke security ɗin ya ɗaga waya ya kira ogansa. Jin hayaniyarsu ta cikin wayar ne ya tilastama Dr Shamsu fitowa da kansa dole har wajen gate ɗin.          “Kaga matsa masa Daniel”. Dr Shamsu dake ƙarasowa wajen gate ɗin ya faɗa cikin ɗagama security ɗin hannu ganin su M. Dauda na neman ɓalla masa kunkuru. Dan sun haɗu su biyu sun ƙadandanesa adole sai sun ɗagasa. Ga Daniel ɗin kuma yayi huɗunsu dan su taba duk ta gama ragaɗe naman jikin nasu.     Cikin bin umarni security ɗin ya janye jikinsa yana ƙwafa da hararsu. Suma harar tasa suke da cigaba da kumfar baki har sai da Dr Shamsu ya dakatar dasu.         “Kunga Baba ya isa haka dan ALLAH, mike tafe da ku?”.     Da farko M. Dauda shima kallon sama da ƙas ɗin yay masa zai yaɓa masa bagaƙar magana M. Gambo ya dakatar da shi ta hanyar zungurinsa, shi ya fara magana da sauri.      “Ranka ya daɗe dama munzo duba yarinyarmune da aka jima ciwo a dalilin Alhaji Hameed Taura. Wannan mahaifintane, ni kuma abokinsane kuma ɗan uwansa na ƙut-da-ƙut”.       Dr Shamsu ya ɗan rumtse ido dan shi surutun M. Gambo hawar masa kai yake, a ƙasan ransa yana auna Raudha da wanda aka kira mahaifin natane. Tabas M. Dauda ƙyaƙyƙyawa ne, sai dai taba duk ta gama cinyesa ta sake sakashi komawa baƙi. Idan mai nazari ya nutsu tsaf a kallonsa zai ɗanga yanayi na jini dake tsakaninsa da Raudha, sai kuma kamanin su Fatisa da shi tafi rinjaye duk da suma sun fisa ƙyan gani da ƙuruciya a yanzun.      “Maganar gaskiya bazai yuwu na yarda daku kai tsaye ba, saboda dalilai masu yawa. Yarinyar nan kowama zai iya basaja yanzu domin farautar ranta ko nuna dangantaka da ita domin idasa mugun nufinsa akan Taura. Dan haka kuyi haƙuri idan an sallameta zaku ganta. Dan a yanzu dai babu mai ganinta saboda tana ƙarƙashin kulawar ƴan sanda”.        “Kutt... Bantan uban can kayyasa. Kai awa da zakace bazanga ɗiyata ba. To wlhy yau an taɓo bala'i, ai dama nasan za'a rina shiyyasa na shirya tsaf dan yin kayayatu a gidan redion jaharmu. Zan tafi bazanƙi ba, amma Taura ya saurari saƙona, dama ba'ance mana anji ƙishin-ƙishin ɗin takarar shugaban ƙasa zai hito ba, to wlhy nine zan fara masa ƙafar angulu ni Dauda uban Raudha mijin Asabe baban Ɗanjuma da Garbebe.........”        “Ya ALLAH”. Dr Shamsu ya faɗa yana ɗan ja da baya danjin kansa na sara masa bisa surutun M. Dauda. Su Malam Dauda na ganin haka suka faki idonsa suka kwasa da gudu zuwa cikin asibitin. Securitys ne suka rufa musu baya. A taƙaice dai cikin ƙanƙanin lokaci suka nema harmutsa asibitin, sai securitys sukai kama-kamar ɗakkosu zuwa waje. Ganin abun nasu bana masu hankali bane ga marasa lafiya da basa son hayaniya yasa Dr Shamsu ɗaga waya ya kira Bappi batare da tunanin zai ɗauka ba. Sai dai Alhmdllhi tana a ringin na uku aka ɗaga. Cikin girmamawa Dr Shamsu ya gaishe da Alhaji Hameed Taura, tare da jero masa bayanin abinda ke faruwa duk da shima daga can yana iya jiyo hayaniyar.        “Oh ALLAH waɗan nan wane irin mutanene haka? Doctor Please saka wani ya kawomin su gida yanzun nan”.        “Okay Ranka ya daɗe yanzu insha ALLAH ”.      Bayan ya yanke wayar ya dakatar da hayaniyar su Malam Dauda da ƙyar yay musu bayani, amma sai suka ƙi yarda a cewarsu raina musu wayo Dr Shamsu zaiyi dan su bar asibitin. Anyi-anyi amma sunface basu yardaba, babu inda zasuje. Idan gaskiyane shi Tauran yazo ya samesu a asibitin inyaso sai su bisa.      Sosai zancensu yasa mutane sake musu kallon mahaukata. Yo inba mahautaba taya zasuce Taura da kansa, mutum lamba na biyu a masu kuɗin africa, na ɗaya a NAYA yazo nan domin su kawai.     Shidai Doctor Shamsu rasama yanda zaiyi yay, sai dai cikin ikon ALLAH yana tunanin miye mafita sai ga Bappi ya kirashi. Cikin rawar jiki ya ɗauka, ya kora masa bayanin halin da ake ciki. Murmushi kawai yayi da cewa, “Karka damu ina zuwa”.     Idanu Dr Shamsu ya ɗan kwalalo da hangame baki na mamaki, sai dai kafinma yace wani abu Bappi ya yanke wayar. ★       Bappi ya ajiye wayar yana duban Ramadhan dake gefensa yana shan furar da Bappin kesha shima, tun wayar farko da yayi Anne ta tambayi lafiya ya mata bayani, amma duk da Ramadhan ɗin na'a wajen ko tari baiyiba, furarsa kawai yake sha yana sarrafa lap-top ɗinsa kamarma baya a wajen.           “Ramadhan!”. Bappi ya kirashi a hankali.      Ɗago nutsatstsiyar fuskarsa yayi mai ƙarancin hayaniya yana kallon Bappin, kafin yace wani abu Bappi ya taresa da faɗin, “Tashi muje ka kaini TK hospital”.         Tuni ɗan sakewar fuskar tasa ya ɓace, sai dai kuma babu damar yin gardama, dan shima Bappin ya tsuke tasa fuskar. Cikin marairaicewa ya maida dubansa ga Anne tamkar zai fasa kuka.       “Ni miye nawa kake kallona. Koni nace ka kainin?”.     Ɓata fuska ya sakeyi da janye idanunsa, batare da yace komaiba ya kashe lap-top ɗin ya miƙe, jacket ɗinsa baƙa mai ƙyalli dake ajiye saman kujerar gefensa ya ɗauka ya ɗora saman baƙin wandonsa da baƙar t-shirt, yanda t-shirt ɗin ta kama jikinsane yasa ƙyawunsa da yanayinsa na mutum mai tu'ammali da motsa jiki ya bayyana. Sosai sumar nan tasha gyara yau sai ƙyalli takeyi. Ɗan corridor ɗin dake hanyar bedrooms ɗin Anne ya nufa, ya buɗe wani ƙaramar drawer na glass da aka saka domin ado kawai ya ciri key batare daya duba na wace mota ya ɗauka ba. Dan duk keys ɗin motocin da suke amfani dashi anan sashen nanne wajen ajiyarsu.      “Furar fa!?”. Anne ta tambaya lokacin da Ramadhan ɗin ke ɗaukar p-cap ɗinsa zai ɗora saman kai, dan yasan Bappi sai yayi magana akan gashinsa.        Hular ya gyara ta rufe masa fuska sosai, ciki-ciki yace, “Na ƙoshi”.     A yanda yay maganar Anne tasan a ƙufule yake, dama yaya lafiyar giwa. Tunda akai masa zancen mulkin nan da aure ƴar sauran fara'ar fuskar tasa ta ɓace ɓat duk da shi ba mutumne miskili ba, maganarce dai sai ya zaɓa da wanda yay niyyar yi saboda jin kansa da yay gado gurin uwa. Gaba ɗaya a kwanaki biyun nan daga gaisuwa babu ruwansa da kowa a gidan. Gashi kuma Ramadhan yayi mugun tsanar driving a rayuwarsa, ita da Bappi ne kawai ke shigar masa hanci akan ya tuƙasu ko yanaso ko bayaso. Amma daya tuƙa mota ya gwammaci ma ya hau mashin, shiyyasa mashina ɗinsa kusan uku a gidan.       Duk da yanda yaga bayan motar daya ɗakkoma key tayi ƙura haushi ya hanashi komawa ya canjo key. Sai Alu ya ƙwalama kira akan yazo ya fidda masa ita daga runfa. Lokacin da Bappi ke fitowa cikin jallabiya dan bai canja kayaba hula kawai ya sanyo saboda yamma ce garin yayi luf da alamar hadari. Ramadhan dake amsar motar a hannun Alu ya miƙa hannu ya buɗema Bappin gefensa, dan yasan in har shine zai tuƙasa a mota baya zama baya.      Koda Bappi ya shigo komai baice masa ba ya ɗaura belt tamkar yanda Ramadhan ɗin ke ƙoƙarin saka nashi, dan shi ƙa'idarsa indai zaiyi tuƙi baya ƙin saka belt ɗin, dan mutum ne mai tsananin son bin doka koda ace sauran ƴan ƙasa na mata riƙon sakainar kashi.                          ★       Tunda motar ta shigo Doctor Shamsu ya fahimci su bappi ne, sai ya zare jikinsa da ga wajen hayaniyar ya nufesu. Shine ya buɗema Bappi ƙofa ya fito, zai risina domin gaisheshi Bappi ya hana ta hanyar riƙo hannunsa. Cikin kunya da girmamawa Dr. Shamsu ya yarda suka gaisa, kafin yace, “Ranka ya daɗe sun riga sun tara mutane, ina ganin muje daga ciki sai na shigo da su”.       Bappi baiƙi hakan ba, dan daga inda yake yana hango yanda M. Dauda da abokinsa ke zazzaga masifa ga mutane da securitys ɗin asibitin zagaye da su. Wasu na musu kallon mahaukata wasu na dariya, wasu najin daɗin abinda sukeyi na yaɓa magana ga Alhaji Hameed Taura.       Ramadhan da baida niyyar fitowaba sai ya kwantar da kujera ma abinsa ya lumshe idanu tare da ƙara ƙarfin a.c dan garin yay luf-luf dayin dumm alamar hadarine, sai ɗan zafin ya bada yanayin jinsa a cikin jiki kawai.                Da ƙyar Dr. Shamsu ya lallaɓa su M. Dauda zuwa office ɗinsa. Sai dai duk wani iya shegen da suka shigo da shi suna cin karo da fuskar kamala ta dattijon arziƙi Alhaji Hameed Harith Taura ya gudu. Cikin ɗan rawar jiki suka zube a ƙasa tun daga ƙofar office ɗin. Ɗan murmushi yay musu yana girgiza kansa. “A'a haba kutashi ku ƙaraso Please”.       “Ranka ya daɗe nan ma ya isa”. Suka faɗa cikin haɗa baki.    “Bazai yuwu ku zauna anan ba, kuyi haƙuri ku ƙaraso.”          Dole suka miƙe domin cika umarninsa. Bayan sun zauna Bappi ya tura musu ruwa da lemon da Dr. Shamsu ya ajiye masa. Suna ƙwaɗayin sha sunajin kunya, dan haka suka dai daure da ƙyar suka haɗe yawunsu na ƙwaɗayi. Hannu Alhaji Hameed ya miƙa musu, nan ma suka shiga nannoƙewa sai da yay da gaske suka yarda suka bashi nasu hannayen suka gaisa. A zukatansu sai yaba laushin hannun wannan tsoho suke, koda yake gidan kuɗine fa da kansa.          “Alhmdllhi Doctor ya kirani yaymin bayanin komai game da zuwanku nan, kuyi haƙuri ba'a hanaku shiga gareta bane dan baku isaba, kawai dai saboda tsaro ake taka tsantsan, gashi kuma bamu da tabbacin abinda kuka faɗa ɗin...”       “Wlhy ranka ya daɗe ni mahaifinta ne, ama ɗauka hotona a nuna mata”. M. Dauda ya faɗa cikin zillo yana katse Bappi.      Murmushi Bappi yayi, dan shima dai yaga yanayin jini, sai dai taba data cinye M. Dauda ɗinne ya ɓadda ainahin kamanin nasa da Raudha.      “Ai bama sai ankai ga nan ba. Yanzu bara muje ɗakin kawai”.     Kafin ma Bappi ya miƙe su har sun fice, ya ɗan girgiza kansa yana murmushi dan dariya suke bashi. Suna abune tamkar wasu firgitattu...........✍ https://arewabooks.com/chapter?id=629a77b967809ad6daab2109 *_Chapter 13_* *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/8, 6:03 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 17_* ............★Raudha na zaune yau an cire ƙafar tata a jikin ƙarfen dan kumburin ya sauka sosai, maimakon tayi ramar ciwo sai ta ƙara haske da ƙyau saboda samun canjin waje, ga abinci mai ƙyau ga a.c.      Idanu taɗan waro saboda mamakin ganin mahaifin nasu, cikin rawan baki tace, “Abbanmu!”.     Wannan kawai ta isa amsa ga bappi, dan cike da zumuɗi shima M. Dauda ya nufa gadon yana ware hannuwa wai zai ringume Raudha irin na turawa kar Bappi ya rainasu yaga su ƴan ƙauyene basu iya tattalin ƴaƴa ba. Sai dai kuma tunkan ya ƙaraso Raudha tai saurin ɗaukar filo ta tareshi tana faɗin, “Abbanmu lafiya?”.      Sosai dariya ta nema kufcema Bappi, yay ƙoƙarin kauda kansa yanayi ƙasa-ƙasa. Dan M. Gambo ya matsa da sauri ya ɗirkama M. Dauda dundu a baya. “M. Dauda ka nutsu mana miye haka zaka zubar mana da mutunci”.       Harararsa M. Dauda yayi, cikin yin ƙasa da murya yace, “Kai baka gane ba, idan ba'ayi hakan ba ai sai attajirin nan ya ɗauka bama kula da ƴaƴanmu, kasan su haka sukema ƴaƴansu kamar larabawa da turawa. Ko so kake yay tunanin dan munga sun raɓesune muka fara son su”.      “Eh kumafa hakane kayi gaskiya, sai dai kasan Raudhatu ustaziya ce bazata yarda ba fa, karma kaja ta bamu kunyar datafi wadda muke gudu”.      Duk zancen nasu sarai Bappi najinsu duk da a hankali sukeyi, dan shi ALLAH ya bashi ƙarfin ji, zama a iya cewa a wajensa Ramadhan ya gado ƙarfin ji, ko yaya kai magana kusa da su sai sunjika da izinin ALLAH, dan haka yay saurin katsesu dan karsu kasheshi da dariya. Ya gyara tsaiwarsa dayin gyaran murya yana faɗin, “Ya kamata ku dubata sai muje muyi sallar magrib, na kuma san masaukinku......”      Kafinma ya kai ƙarshe M Gambo ya katsesa da faɗin, “Ai bamu da wani masauki yallaɓai, dan shi M. Dauda ya rabu da gyatumar tata shiyyasa ta taho nan ita da yaran wajen tata gyatumar. Dama yanzu haka munzo biko ne da duba jikin Raudhatun”.         Raudha dake jin tamkar ta fasa ihu dan takaicinsu ta kauda kanta gefe idanunta na tara ƙwalla. Tana son mahaifinta, tana kuma fatan ya nutsu ya bar duk abinda yakeyi na ashsha, sannan sam bata baƙin cikin nunasa matsayin uba dan bata da kamarsa..      Bappi yay saurin dakatar dasu, “Ok ok babu damuwa muje muyi sallan first dai yanzu, sai musan abunyi kamar zaifi”.     Badan sun so ba suka bisa. Dan gaba ɗayansu idonsu nakan Haɗaɗɗun kulolin abincin dake gefen gadon Raudhan. Sai haɗiyar yawu suke tunkan suga abinda ke a ciki.      Suna fita doctor na shigowa. Hakan yasa Raudha roƙonsa aron waya dan gara ta kira Mommy ita kam bazata iya da halin Abba ba. Shima Dr Shamsu ya gamsu da hakan, dan haka babu musu ya bata ta saka number Mommyn, cikin sa'a kuwa bugu ɗaya aka ɗaga. Wani daɗi ya kama Asabe saboda jin muryar Raudhan Alhmdllhi, duk da dai da safe sunzo asibitin dubata ita da Aunty Hannah ma.       “Mommy dan ALLAH kizo asibiti wlhy Abba ne yazo shida baba Gambo”      Zumbur Asabe ta miƙe har tana neman yadda zani. Shi dauda ɗinne yazo Bingo harma asibitin da kike?”.      “Wlhy kuwa mommy gasu ma tare da baba alhaji (Bappi take kira haka). Yanzu ya jasu suka tafi massallaci”.      “Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un. Ashe kuwa zanci kaza kazan ubansu a garin nan. Ni yanzu babbar matsalata baza'a barni shiga asibitin ba....”         “Mommy dan ALLAH ki kwantar da hankalinki banga abin faɗa anan ba. Kizo asibitin Doctor zai shigo dake yace. Amma mommy dan ALLAH karki tayasa kuyi rikici Please”.     Tai maganar tamkar zatai kuka. “To” kawai asaben tace mata ta yanke wayar, badan tasan zata iya bin maganar Raudha ɗin ba. *_BINA STATE PLACE_*            “Ranka ya daɗe bakace komai ba”.    Fulani ta faɗa a hankali cike da ƙasaita tana duban mai-martaba dake kishingiɗe a tsakkiyar falon hutawarsa da ko iyalan nasa ba kowacce keda ikon shigarsaba sai Fulani kawai.        Bai motsa ba, sai dai ya saki wani murmushin ƙasaita irin na manya, masu kuma ji da girman mulki. Kafin ya ɗago idanunsa ya ɗan dubeta ya ɗauke kansa.       “Wai miyasa ku mata a koda yaushe baku da hangen nesa ne? Yanzu banda dai son neman magana miya kawo zancen haɗa Aina'u da Ramadhan aure? bayan kunji Alhaji Hameed ya zaɓa masa mata...”         “Humm mai-martaba kenan, ni a ganina ai hakan ba wani abu bane, ƙara danƙon zumincine, ka tuna fa Ramadhan shine jikanka na farko namiji a gidan nan, da ace shi ɗin ɗane da namiji ya haifa ba mace ba shine kamarfa magajinka a yanzun, amma sam yaron nan baya son zama cikinmu, akoda yaushe sai dangin ubansa saboda Firdausi ta gama shanyesa su kaɗai yake gani ita da mijinta, amma idan muka haɗashi aure da Aina'u ta tayamu yaƙin jawosa jikinmu ai muma ka.......”         “Ya isa dan ALLAH. Yanzu nan Wasila bana hanaki irin wannan zancen ba? Yanzu miye abin asiri dan Ramadhan yafi buƙatar ya rayu a gidan su?. Karfa ki manta can ɗin shine adonsa, kuma shine tunƙahonsa, to bana son ƙara ji, hakama maganar haɗasa da Aina'u inhar ba sune suka sasanta junansu ba bana buƙatar sake jinta. Dan har abada Alhaji Hameed bazai saka doka na karya masaba koda akan ƴaƴana ne balle jikansa da yake da iko da shi tamkar yanda yake da iko akan mahaifinsa. Kuyi masa fatan alkairi kawai ku tsaya matsayinku”.        Fulani ta taune lip ɗinta da ƙarfi da haƙora kamar zata hudashi, sai dai sanin halin mijin nata yasata sakin ɗan murmushin yaƙe da cewa, “To shikenan ranka ya daɗe, yanda kace ai haka za'ayi insha ALLAH anbar zancen. Dama can rashin zama nayi nazarine akan batun shiyyasa ban fahintaba.”         “Haka nakeso ki kasance. ALLAH yayi muku albarka baki ɗaya”.      Da ƙyar fulani ta daure ta amsa tana haɗiyar zuciya. A ranta ko abubuwa masu yawa take kitsawa gameda kowacce shegiyar yarinyace zata aure mata jika sama taka. (Hummm Fulani kina kaka inaga gimbiya Su'adah uwar miji. To maji yaya za'a kwashe to😜🏃). ___★____★___          *_BINGO CITY_*          Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Asabe da M. Dauda lokacin da akai kici-ɓus. Dan kuwa dai doctor Shamsu da kansa ya shigo da Aunty Hannah da Asabe, shigowarsu babu jimawa kuma Bappi da su M. Dauda suka dawo ɗakin domin yin sallama da Raudha.        Asabe ce ta fara janye idanunta tana jan tsaki, hakan yasa M. Dauda da jikinsa ke tsuma da sabuwar ƙaunarta matsowa kusa da ita cikin ɗan rawar jiki. “Haba Asabe nine fa Dauda ɗinki, dan ALLAH karkiyi fushi dani wlhy sharrin shaiɗanne”.         Hannunsa dake neman taɓata ta buge tana faɗin “Kaine sheɗan ɗin kanka ai macuci kaw......”       “Mommy Please!!.....” Raudha ta faɗa tana fashewa da kuka dan tasan komai zai iya faruwa akan iyayenta na raba hali. Asabe zata sake magana Bappi daya fahimci su ɗinne iyayen Raudha ɗin yay saurin dakatar da ita.             “Inaga nan ba wajen magana bane, kamar zaifi muyi haƙuri muje daga waje ko masaukinku ko? Ko kuma mu bari zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.....”        “A'a dan ALLAH ranka ya daɗe gara ayita yau ta ƙare, idan ta bar nan bazata sake yarda na gantaba, zama ta iya sace Aminar daga nan ɗin itama”.      Harara Asabe ta balla masa, sai dai riƙe hannunta da aunty Hannah tayi ya sata yin shiru ta haɗiye abinda taso faɗa. ★      A tare suk rankaya gidansu Asabe, sai dai Bappi motar Dr Shamsu yabi yace Ramadhan ya koma gida, dan sanda suka fito barci ya samesa yanayi a cikin mota, ya sanshi da barcin wuri, dan shi ƙa'idarsa da tara na dare tayi to ya kwanta kuma. Sai dai kwana biyun nan daya tsinta kansa a NAYA hakan bai kasanceba, shiyyasa daya ɗan kaɗaice sai ya kama barci saboda tsabar buƙatarsa da yake yi.       Rikicewa sosai Hajiyar Birni tayi da ganin Alhaji Hameed Harith Taura har cikin gidanta. Mutumin da bata taɓa tunanin koda ganin motar hawansa ba a hanya balle shi kansa. Babban abinda zai birgeka da shi babu wani damuwa ko tsantsamin gidan tare da shi, hasalima da aka kawo ruwa shine ya fara sha tare da godiya.      Su M. Dauda dai an nutsu saboda hararar da Hajiyar Birni ke antaya musu tamkar ƙwayar idonta zai fito.        “Kuyi haƙuri da lattin zuwan gareku matsayin wanda ƴarku tai kasadar bama kariya. Da farko dai naso ace sai ta samu lafiya zanzo da kaina na kawota gareku nai muku godiya na kuma baku haƙuri. Sai dai an samu akasin hakan a dalilin zuwan waɗan nan bayin ALLAH da ayanzu na fahimci shine mhaifin *Raudhat*. Duk da dai na haɗu da ita mahaifiyarta a aaibiti tun randa abun ya faru, hakama ku da bansan matsayinku garetaba har yanzun. Zanyi amfani da wannan damar domin neman afuwarku, ku gafarceni, da nasan Raudhat zatayi wannan kasadar domin ni tabbas zan dakatar da ita, sai dai masu iya mafana kance ƙaddara ta riga fata, sai muce ALLAH ya bata lafiya ya albarkaci rayuwarta. Ku kuma kuyi haƙuri ku koma tare dan na fahimci baƙwa tare da juna, kuma Raudhat batajin daɗin hakan”.           Kafin kowa yace wani abu hajiyar birni ta amshe zancen cikin washe baki. “Ai muke da godiya ranka ya daɗe, ALLAH ya saka da alkairi bisa kulawar daka nuna akan Raudha, dan bamu taɓa zaton hakan ba. ALLAH ya kara lafiya da nisan kwana. Suko babu sauran aure a tsakaninsu dan saki uku ne yallaɓai......”         M. Dauda yay wata zabura tare da fashewa da kuka. “Ni wlhy ina son matata kuma a bincika ba'a cikin hayyacina na saketaba ranka ya daɗe...”        “Eh wlhy wani malami yace asiri Larai ta maka ai”. M. Gambo ya amshe zancen yana matsar kwalar ƙarya shima. Dan dukansu kowa da abinda ke ransa tsakanin shi da M. Dauda ɗin.          Hajiyar birni ta amshe zancen da faɗin, “ALLAH yayama wannan malami albarka tare da Larai, dan sun taimakeni da suka aikata wannan asiri matsiyaci”.      Kuka M. Dauda ya sake fashewa da shi yana fyatar majina da tsohuwar babbar rigarsa tare da matsawa zai duƙa gaban hajiyar birni ta daka masa tsawa. Itama Asabe miƙewa tai cikin masifa sai dai duk Bappi yay azamar dakatar dasu dan shikam baisan hayaniya a rayuwarsa.         “Inaga dan ALLAH ayi haƙuri tunda dukanmu nan ba yara baneba. Kamar wannan magana tana buƙatar nutsuwa kuma tsakaninku ne. Dama nima akwai abinda ke tafe dani game da Raudhat. Dan tayimin abinda wani mahaluki bai taɓa minba a rayuwa, bani da abinda zan sakanka mata da shi amma ina buƙatar irinta a kusa dani. Ma'ana inason ku bani aurenta dan ALLAH ko ta hanyar hakan zan samu damar kwatanta mata kwatankwacin alkairin data min nima...”        Gaba ɗayansu suka waro idanu a kansa, tare da auna shekarunsa dana Raudha. Cikin rawar baki Asabe tace, “Alhaji kai da kanka?”.         Karon farko ya saki ɗan murmushi domin ganin yanda duk sukai diri-diri, gasu dai a mu'amulat tamkar mutanen banza, ƴarsu kuma nutsatstsiya kamila, amma ashe sun san abinda ya cancanta, amma bara ya sake gwadasu. Numfashi yaja ya fesar da gyara zamansa.       “Eh ni da kaina”. “Wlhy na baka ranka ya daɗe” M. Dauda ya faɗa cikin zallo da rawar jiki yana sake gurfana gaban Bappi tamkar mai neman gafara. Da sauri Asabe ta amshe da, “Nidai dan ALLAH ka gafarceni Alhaji ban amince ba, Raudha bazata auri tsoho sa'an kakanta ba. Son zuciyar da naso tafkawa a baya na biye maka Dauda kan alhaji Maude Dallatu ya kaimu ga zuwa wannan matsayin, yanzu ko na gane gsky mutuncin ƴaƴana da ƙyautata rayuwarsu yafiyemin komai a duniya dan sune gatan wata rana. K....”         “K! Yima mutane shiru!!”. Hajiyar birni ta faɗa cikin daka tsawar data saka Bappi toshe kunne tilas. Aunty Hannah ma da illahirin jikinta ke rawa tun fara mganar Asabe saurin fincikon Asaben tai baya da faɗin, “Asabe kina da hankali kuwa? Kinsan wanene shi a ƙasar nan?”.        Kuka Asabe ta fashe musu da shi. Cikin matsar kwalla tace, “Adda ni babu ruwan da koshi ɗin wanene. Ina duba rayuwar ƴaƴana ce, bana fatan su tashi a irin tamu rayuwar, fatana suyi ƙyaƙyƙyawar rayuwa bawai ta kuɗi ko son duniya ba. Dan haka ku gafarceni, ko ni akace na auresa yamin tsufa balle Raudha”.         A tare suka hayayyaƙo mata har M. Dauda dake jin a yanzu baya buƙatar lallaɓa Asabe, dan zata masa ƙafar angulu ta kaisa ta barosa. Ganin suna neman harmutsa falon Bappi ya dakatar dasu cikin roƙo. Sai da suka nutsu ya fara magana cike da dattakonsa da kamun kai.         “Lallai wannan baiwar ALLAH ta fiku gaskiya, dan kuwa tayi ƙyaƙyƙyawan hange da iyaye da yawa kan kasayi harma da ƴammatan wannan zamani akan auren wanda yake da manyan shekaru. Lallai ke ɗin uwace ta gari, kuma na gode da yanda kika nuna mutuncin ƴarki da farin cikinta shine gaba a ranki fiye da kuɗi ko wani matsayin da rayuwa ke bama bawa mai ƙarewa. Banzo nan dan na koma da buƙatata ba. Dan haka zan sake roƙonki a karo na biyu. Ina son ki yarje mijinki mahaifin ƴarki ya bama jikana auren ƴarku dan ALLAH badan wani matsayi namu ba ko abinda muke da shi. Domin Raudhat a yanzu tana buƙatar ta samu tsaro kodan rayuwarta dake a cikin haɗari, to zamanta anan tare daku kuma komai zai iya faruwa harya shafeku. Badan mu zamu iya kareta ko hana wani ƙaddara sauka gareta ba, domin muma bayin ALLAH ne kamar ita, kamar kuma ku. Alkairin da taiminne yasa nakejin kwaɗayin ɗaukarta ta zama ɗaya daga cikin family ɗina. Ta kuma haifamin jikoki daga tsatsonta da nake fatan suyi koyi da ƙyawawan halayenta wanda tarihi bazai taɓa gogewaba daga abinda ta aikata na alkairi a gareni”.       A kusan tare duk suka sauke ajiyar zuciya, tare da zubama Asabe ido. Zukatansu har zallo suke nason jin amsar da zata bama Bappin.      Taja kimanin wasu dogayen mintuna tamkar mai nazari kafin ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi.       “Amma dan ALLAH Baba miyasa bazaka duba akwai tazarar rata tsakanin jikanka da ɗiyata ba.....”        “Babu wani banbanci ɗiyata, domin kuwa dukanmu ALLAH ne ya haliccemu, ya kumace mu bauta masa shi mai rahamane ga duk wanda yayi biyayya ga hakan, sannan mai azaba ne ga duk wanda ya bijire masa. Dan haka ki sani babu wanda yafi wani a gun ALLAH sai wanda yafi jin tsoronsa. Ni da ku da Raudhat duk abu gudane. Mutanene masu barci, masu kashi, masu mantuwa, masu shagala, masu... Masu.... Masu..... Da yawa.”        “Hakane ranka ya daɗe. Na gamsu da bayaninka, zan kuma iya amincewa da buƙatarkane idan har Raudha ta amince da auren jikan naka”.           Babu wanda baija ajiyar zuciya ba a falon, kafin suɗan ƙara tattaunawa da Bappi, daga ƙarshe yay musu sallama suka rakasa har wajen Dr Shamsu dake jiransa a mota dan shi bai shigo ba. Tare da su M. Dauda suka tafi, dan yace zai kama musu masauki tunda nan babu wajen kwana.      Aiko sai murna suke tamkar su ciza uwawunsu dan daɗi😂😝.........✍ https://arewabooks.com/chapter?id=6299deaa67809ad6daaa6509 *_Chapter 11_* *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742👌🏻 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/8, 6:04 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 18_* ............Tun bayan wucewar su Alhaji Hameed Taura Aunty Hannah keta faman kai kawo a ɗakinta da kiran number First lady. Sai dai kuma tayi kira yakai biyar amma ba'a ɗagaba. Ta sake duban agogo ƙarfe goma da mintuna ashirin da huɗu. Tasan yanzu first lady batai barci ba, da wahala kuma ace tana tare da president, sai dai idan wayar ta bari a wani waje. Wannan tunanin ya sata canza akalar kiran ta tura mata guntun saƙo, da ga haka ta ajiye wayar ta faɗa wanka zuciyarta fal wasiwasin ta yanda zata ɓulloma Raudha da Asabe su amince da auren nan cikin sauƙi.        *_WASHE GARI_* first lady ce ta tada Aunty Hannah a barci, dan ko sallar asuba bata tashi tayi ba har kusan 7am. Da ƙyar ta lalubo wayar takai kunnenta tana faɗin, “Hello waye?”.       Amsar da first lady ta bata ya sata wartsakewa babu shiri ta tashi zaune. “Ranki ya daɗe sorry barka da safiya! Wlhy barcine a idona”.           Kanta ta jinjina saboda amsar da first ladyn ta bata tana faɗin, “Okay to babu damuwa gani nan zuwa yanzun nan insha ALLAH”.        ★    Su Asabe na a falo suna karyawa aunty Hannah ta fito cikin gayu na ɗaukar hankali. Fatisa da Fatima dake sanye da Uniform ɗin wajen abincin Hajiyar Birni suka fara gaisheta da yaba ƙyan nata. Tai murmushi tare da musu alamar love da yatsunta. Kafin ta ɗauka doya guda a cikin plate ɗin Asabe. “Ƴar uwa barka da safiya”.        Duk da Asabe tayi mamakin gaisuwar saita share ta amsa mata. “Barka dai Adda fita zakiyi ne?”.          “Eh wlhy zan ɗanje wajen aiki ana nemana ne”.      “Aiko da zakibi ta wajen asibiti ne dana biki sai na sauka dan inason yin magana da Raudha game da zancen nan na jiya karma suje su yaudareta abun yay nisa gara na sani”.         Hajiya mama dake fitowa daga kicin a masife tace, “O ke Asabe wai mike damun kanki ne dan ALLAH? Ƙiri-ƙiri kina neman mana baƙin ciki da arziƙin dake tinkaromu!. Alhaji Hameed Harith Taura fa akace. kinsan wanene Taura kuwa a ƙasar nan dama Africa gaba ɗaya?”.        Kafin Asabe tace wani abu aunty Hannah tai murmushi da amshe zancen tana ƙyaftama Hajiya mama babbar yayar tasu ido. “A'a Hajiya Mama karkiga laifin Asabe. Tana da gaskiya wlhy, ya kamata muji ta bakin Raudha mu kuma binciki halin yaron, dan aure ba abin wasa bane. Tunda ba kuɗin zata aura ba mai kuɗin zata aura”.               “Yauwa Adda dan ALLAH ki fahimtar dasu. Dan naga su dukiyar waɗan nan mutanen kawai suke kallo har shi uban nata da dama kwaɗayayye ne. Yanzu idan ta auresa bata son sa, ko taje tana shan wahala fa? Ai kunga mun tauye mata rayuwa”.          Hajiya Mama ta danne ɓacin ran maganar Asabe da ƙyar tana ƙaƙaro murmushi. “Hakane kuma Asabe yanzu na fahimceku. Ki bar Hannah kawai ta wuce maje wajen Raudha ɗin tare tunda dama jiya banje ba”.     Badan Asabe taso hakan ba ta amince. Aunty Hannah tai musu sallama ta fice kusan tare da su Fatisa da zasu hau keke napep dan hajiyar Birni tuni ta jima da wucewa ita. *_GOVERNMENT HOUSE_*             Tun tattaunawar da sukai da aunty Hannah ɗazun da safe ta kasa zaune ta kasa tsaye, dakon shigowar shugaban ƙasa kawai take gidan, amma har zuwa yanzu ƙarfe goma sha biyu na dare babu shi babu labarinsa. Duk da dai tun kusan tara na daren ya shigo gida, sai dai sun shiga meeting ne shi da su Alhaji Yaro glass, kuma har yanzu basu fitoba. Tai ɗan gajeren tsaki tana tura hular kanta baya ta faɗa saman kujerar, duk da sanyin ac dake gauraye da falon wata irin zufa takeji mai mannewa iya fata da jini. Ta zame rigar sama ta kayan barcinta dan itama nauyi take mata saboda tsabar ƙaguwa. Rashin mafita ya sata zamewa ta kwanta a kujerar, dan ta ɗau alwashin ko zai kai asuba tana nan tana jiransa.        “Gimbiyata kina lafiya kuwa?”. Shugaban ƙasa da ya shigo a matuƙar gajiye ya faɗa lokacin da yake zubewa saman kujerar gefenta. Zumbur ta miƙe zane tana ware idanunta a kansa, sam bataji motsinsaba, duk da dama tasan shi bai damu da sallama ba dan zai shiga waje.        “Lafiyar nan da sauƙi wlhy tun ɗazun zaman jiranka nakeyi anan excellency ”.       Fuska ya sake ƙwaɓewa yana ture hularsa. Cikin tabbatar da matuƙar gajiyar dake tare da shi da barci yace, “Bushira kiyi haƙuri babu abinda nake buƙata a yanzu irin barci da wanka”.          “Shiruna bazai yuwu ba, inko nayi to zai iya cutar damu baki ɗaya. Dan maganar ta shafi shugaban ƙasar da kuke son ɗorawa na wucin gadi” Bata bashi damar yin magana ba ta cigaba da tata maganar saboda ganin ya bada hankalinsa gareta. “Tunda ka sanarmin ƙudirinku akan Alhaji Hameed da jikansa daya kawo a maimakonsa naketa nawa ƙoƙarin nima. Dukanmu munsan Ramadhan a yanzu baida mata, tunda kune kukai sanadin rasa matar tasa, shiyyasa nake ganin a yanzu ma inhar kuna buƙatar mutuwarsa kamar yanda kuka tsara (wa'iyazubillah 🤦🏻) to dolene sai mun haɗa da matarsa, dan itace mafi kusanci da shi da zatai mana aiki batare da wani zargi ya shiga ba. Kaga kenan mune ya dace mu bashi mata a karo na biyu”.         “To amma.....” “Karka katseni excellency ”. Ta faɗa tana murmushi.       “Nasan tambayarka itace bai wuce ina zamu samu ba? To na gama da wannan matsalar, yarinyar data bama Alhaji Hameed kariya a filin idi ɗiya ce ga ƙanwar Hannah tsohuwar matar Alhaji Yaro, kuma a yanzu haka Alhaji Hameed ya buƙaci su bama Ramadhan auren yarinyar, sai dai mahaifiyarta na neman bijirewa dan tace sai idan yarinyar naso. Amma babanta ya yarda saboda shegen ƙwaɗayi, hakama hajiyar birni da su su Hannah ɗin, duk da dai ita Hannah muna tare, dan itace ma ta tabbatar min inhar Asabe ta nunama yarinyar bataso itama bazata amince ba saboda tanada kafiya da son uwar sosai......”        “Bushira sorry na katseki, ni abinda ban fahimtaba anan, ribarmi zamuci na shiga maganar tunda sun gama ƙulla zancen auren? Inhar kuma yarinyar zata iya bijirema auren muma zata iya ƙin amsar buƙatarmu ai. Sannan karki manta Hannah zata iya yin komai danta rama korar kare da Alhaji Yaro yay mata. Imagine ma ace kina tare da Hannah har yanzu batare dana sani ba”.         “Duk yanda kuke tunanin Hannah ba haka take ba, tana son Alhaji yaro har yanzu, kuma ta san ba laifinsa bane laifin Fanta ne. Amfanin auren yarinyar nan a garemu Hannah zata iya sakata tai mana aikinmu cikin siyasa batare da ita kanta tasan ita ta kashesa ba, kai koda ta sani ko muna tunanin zata sani itama zamu iya kashetan dan mulkin dai ya koma hannun Alhaji Yaro. Kasan kuma inhar zaka taimaka Hannah ta koma gidan Alhaji yaro zata aikata komai har mutuwar yarinyar, dan da arziƙi a garin wasu gara a naku, a garin wasunma gara a gidanku, a gidankun ma gara a ɗakinku, a ɗakinkun ma gara a kanka. So zataima kanta yaƙine itama”.          Karon farko ya kwashe da dariya yana kamo hannunta. “Oh woow gimbiyata! yanzu dai na fahimci komai wlhy. Gaskiya kinada kai tawan. To amma mu yanzu wace rawa zamu taka?”.        “Yauwa yanzu kai magana shugaban ƙasar NAYA. Abinda zakuyi shine ku samu mahaifin yarinyar ku jikesa da mahaukatan kuɗaɗe. A bashi gidan zama, itama uwar a jiƙeta tare da mahaifiyar su Hannah ɗin, dama duk wanda keda faɗa aji akan auren. Sannan ku samu Alhaji Hameed ku nuna masa goyon bayanku akan auren da nuna cewar yayi hallaci ya cancanci yabo, kar kuma ya yarda yarinyar ta suɓuce ga Ramadhan dan irinsu akeso ga mulki zasu taimaki talaka. So ko yarinyar ta bijire bataso bazata taɓa samun haɗin kan kowaba ita da uwar dole su amince”.       Tashi yay kawai ya rungumeta, ji yake tamkar ya haɗiyeta dan daɗin wannan shawara tata. Tun a daren ya turama su Alhaji Yaro glass saƙo da ɓoyayyar number ɗinsa da su kaɗai keda a laƙa da ita akan gobe akwai mitin ƙarfe 6 na safe kafin ya fita office. *_BAYAN KWANAKI UKU_*           Dukan shawarar da First lady ta bada su Alhaji yaro glass sun aiwatar da ita ta hanyar nuna cewa sunyine dan Alhaji Hameed Taura da kuma Ramadhan dake matsayin surukinsu a da, dama zamansa haka babu aure na damunsu. Hundred percent Alhaji Hameed Taura ya yarda.       M. Dauda kam da su Hajiyar birni haukacewa sukai dan farin ciki, dan manyan kuɗaɗe da aka mallaka musu. M. Dauda, hajiyar birni. Asabe, Hajiya mama. M. Gambo. Kuɗaɗene da zasuja jari. Koda Asabe ta nuna hakan bai mataba hajiyar birni masifa ta dinga mata, harda rantsuwar inhar bata yarda Raudha ta auri Ramadhan ba wlhy sai ta tsine mata, kuma sai dai ta ɗau Raudha subar garin dan bazata zauna inuwa guda da mai mata baƙin ciki ba.      Kalaman hajiyar birni yay matuƙar tada hankalin Raudha da aka sallamo daga asibiti yau, dan Alhmdllhi ƙafarta tayi sauƙi sosai saboda kula da take samu da ingantattun magunguna gashi bata da ƙan jiki. Bazataso a sanadinta a tsinema mahaifiyartaba. Sannan idan sun bar nan ina zasuje, tunda babu wanda ke garesu sama da su a yanzun. Dan haka tace ita ta amince zata auresa duk da batajin son Ramadhan a ranta ko kaɗan, sai dai a gani guda datai masa har zuwa yanzu tanajin kwarjininsa cike da idanunta, yayinda kalamansa ke zaune daram cikin ranta shiyyasa takejin matuƙar tsoro. Amincewa aurensa na nufin tabbatuwar kalamansa gareta, sai dai kuɗi ya rufe idanun iyayenta sun kasa fahimtar ni'imar da suke ganin suna ciki *_BAƘAR INUWA..._* ce, gara ranar da suke ciki da ita. Zata amince domin gujema hawan tsinuwa akan mahaifiyarta, zata kuma amince dansu samu farin ciki koda ita zata rasa nata farin cikin. Dan duk wanda ya dubeta ya dubi Ramadhan ya tabbatar shi ba tsaran aurenta bane ba, kawai dai kakansa ya kalli abinda tai masane da tunanin zai mata tukuyci da auren alhalin bazai zame mata irin inuwar da shi yake hango mata ta jin daɗi ba.          A lokacin da waccan cakwakiya ke gudana a gidan su Raudha anan fadar shugaban ƙasa shugaban jam'iyya ne ya fitar da sunan ɗan takara a yau a zaman taron da akayi yau ɗin na manyan jam'iyyar. Inda kamar dai yanda aka saba wasu suka nuna jayayya akan Ramadhan ɗin kodan ƙarancin shekarunsa, tare da kawo hujjar bai san siyasa ba, bakuma zai iya ba tunda bama zaman ƙasar yake ba, bai san komai na wahalar talaka ba.         Idanu Ramadhan ya rumtse da ƙarfi saboda wani irin sarawa da kansa yake masa a dalilin hayaniyar da ɗakin taron ya kaure da shi. Dama da ƙyar Bappi ya sakashi zuwa wajen taron har sai da ya nuna ɓacin ransa shi da Anne da Pa. Koda ya shigo yaga mutanen dake wajen daga sa'an Pa sai sa'annin Bappi baiji ko ɗar ba, a lokacinne ma yaji kibiyar son yin mulkin ta soki ƙirjinsa. Dan yana ganin yakamata sumafa matasa ace anayi dasu a ƙasar NAYA dan sune ƙasar.      A yanzu kuma boren nasu ya sake harzuƙa zuciyarsa dajin eh lallai zai amince ya amshi mulkin ƙasar NAYA inhar ALLAH ya saka hakan a cikin ƙaddarar rayuwarsa. Da ƙyar shugaban jam'iyya ya tsawatar akai shiru, kafin ya yanke hukunci akan gobe za'ai primary election duk da a ransa yasan dolene candidate nasu ya tsallake. Duk sun amince da hakan, daga haka kuma taron ya watse wasu ransu ɓace wasu ransu fal murna, sai dai masu murnar zukatansu sun rabu gida biyu akan dalilin murnar.     Wani meeting ɗin su Alhaji yaro glass suka sake shiga iyakarsu kaɗai akan batun, kafin kuma da yamma shugaban ƙasa da shugaban jam'iyya su sakeyin wani zaman da wasu jiga-jigan jam'iyyar. *_JIHAR DILLO. HUTAWA L.G.A_*          Koya ya shiga matuƙar mamakin yanda M. Dauda ya dawo garin hutawa a jiƙe da kuɗaɗe shi da abokinsa, dan maimakon su rufe sirrinsu sai sukazo sunama jama'a fankama da kuɗi da nuna sumafa sun kai yanzun. bama shi ba abokinsa M. Gambo ma dai ajiƙen ya dawo. Nan take aka fara ƙananun magana da dangantasu da ɓarayi saboda hankalin jama'a ya tashi musamman da suka san dai ba ko sisi su M. Dauda ke magani ba, dan inhar ba sata ba ko wannan kidnapping da akeyi ba babu ta yanda za'ai daga barinsu gari na kwana uku su dawo haka. Aiko nan take manyan anguwa suka haɗa kai suka kai ƙararsu gidan hakimi, hakimi baiyi ƙasa a gwiwa ba ya aika a ka kira masa su M. Dauda daya saka innarsa da iyalansa haɗa ƴan kayansu dan so yake a gobe ya fara gyaran gidansa. A gefe kuma yana tunanin sake sabon aure da lallaso Asabe ta dawo (bayan saki uku ne tsakaninsu🙄).           Hakimi da ƴan fadarsa babu kalar binciken su M. Dauda da basuyiba amma sun dage akan sufa basu kuɗin nan akayi. Ganin kamar suna son rainama fada hankaline saboda ambatar sunan manyan mutane da sukayi yasa hakimi saka ƴan sanda suje da su. Haka kuwa akayi, a ranar a police station suka kwana, washe gari hakimi kuma ya kai magana fadar mai-martaba sarkin Dillo. Bako a ɓata lokaciba wajen yayubar su M. Dauda sai cikin birnin Dillo fadar sarki.         Nan ɗin ma dai amsar da suka bama hakimi ita suka bama sarki akan inda suka samo kuɗi, sai dai shima bai gamsu ba saboda sunayen da su M. Dauda ɗin suka ambata na manyan mutane. Sai ma hankalinsane daya sake tashi dan gani yake kamar su M. Dauda nason yin amfani da sunan manyan ne dan ɓata musu suna. Baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen fara neman waɗanda yakeda kusanci da su ciki harda Alhaji Hameed Taura da tarihi ya nuna karatu ya taɓa haɗasu a jami'a.          Da ƙyar ya samu damar magana da shi a ranar ta hanyar P.A ɗinsa, bayan sun gaisa cikin mutunta juna matsayinsu na manya da ƴar tsokana ta tsoffin abokai mai-martaba yayma Bappi bayani game da su M. Dauda. Da farko sam Alhaji Hameed Taura bai gane ba saboda baiyi tunanin su M. Dauda sun koma ba, kuma shi har yanzu ma bai basu ko sisi ba su shugaban ƙasa ne sukai musu ƙyauta. Sai da aka haɗashi da M. Dauda, yana ko jin muryarsa ya gane, amma duk da haka sai yasa aka tura masa hotunansu ta email.       Yana gani kuwa ya gane, dan haka yayma mai-martaba bayanin da zai iya fahimta. Jin alaƙar dake shirin faruwa tsakanin su dan babu wanda baisan abinda yaso faruwa da Alhaji Hameed ɗin ba ran salla sai shima mai-martaba ya shiga mamaki, harma yake cema Alhaji Hameed anya kuwa baya ganin tun farko dama akwai dalilin daya saka yarinyar masa garkuwa.      Alhaji Hameed Harith Taura mutum ne mai sauƙin kai da tsarkake abu koda ace yazo a yanayin daya kamata a zargesa, hakan yasa shekaru aru-aru su Alhaji Yaro glass keta cutarsa yana ƙyautata musu zato dan bai taɓa damuwar zama ya zargesu ba. Cikin nutsuwa ya fahimtar da mai-martaba shi dai zaiyi ne bisa ƙyaƙyƙyawar niyya, kuma baijin yarinyar zata aikata haka dan yarinyace ƙarama kuma nutsatstsiya.      Cikin ƙanƙanin lokaci mai-martaba ya yarda dan shima mutum ne mai fahimta, harko yay alƙawarin za'a dama dashi a harkar bikin shine ma uba ga Raudha tunda dai a ƙarƙashin mulkin jiharsa take. Alhaji Hameed yayi matuƙar farin ciki yayi kuma godiya.      Wannan shine ya wanke su M. Dauda wajen hakimi da sarki, sai dai ga jama'ar gari sun ƙara gaba wajen ƙananun magana musamman da akaita dawo da zancen abinda Raudha tayi da kuma dalilin rabuwar Asabe da M. Dauda ɗin da ba'a wani jima ba. Kafin kace kwabo zance yaje bakin ƴan jarida da yanar gizo harya fara yawo...........✍ https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/9, 8:02 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 19_* ............. *_BINGO CITY_*   Ƙananun magana da surutan dake faruwa a gari dama wasu manyan kafafen yaɗa labarai dana yanar gizo baisa Alhaji Hameed Taura ya damu ba ko janye maganar auren Raudha da Ramadhan. Dan cecekucen jama'a yayi dai-dai ne da cin primary election da Ramadhan yayi zancen tsayawarsa takara ta fito fili. Aifa jama'a da ƴan siyasa ƴan bani na'iya suka samu nayi, yayinda magoya baya keta faman murna. Ƴan jam'iyyun hammaya kuwa tuni suka fara cece kuce akan sam Ramadhan bai cancanci fitowa takarar shugabancin ƙasar NAYA ba. Saboda dalilai masu yawa.      Ɗan jarida dake hira da wani riƙaƙƙen ɗan siyasa a jam'iyyar hamayya ya gyara zama da faɗin, “Ranka ya daɗe miyasa kuke ganin bai cancanta ba bayan shiɗin matashine mai jini a jika da ba'a taɓa ko kwatanta shugaban ƙasa mai ƙarancin shekarunsaba a ƙasar NAYA? Sai nakega kamar wannan wani al'amarine daya kamata kowa yay murna da shi tare da yabama jam'iyya mai mulki data kawosa dan sunyi abinda ba'a taɓa yiba suma. Sannan Ramadhan B. Taura kowa yasan gidansu akwai kuɗi, a cikinsu ya tashi babu yanda za'ai ya handame kuɗin Al'umma tunda ba baƙonsa bane kuɗin”.      Wata ƙasaitacciyar dariya Alhaji Andi ƙaura ya sake. Kafin ya haɗe fuska da faɗin, “To ai kuɗin daya tashi a ciki suna ɗaya daga cikin abinda yasa bazai iya ba. Banda matsala da ƙarancin shekarunsa dan koba komai muma muna buƙatar matasan ayi dasu. Sai dai kuma Ramadhan B. Taura bai cancantaba saboda baisan komai ga wahalar talaka ba. Idan baka saniba bara na faɗa maka. Shekaru biyar da suka wuce an kashe matar Ramadhan B. Taura da ƴarsa ta hanyar kai musu guba har gida cikin fridge sukasha suka mutu. Idan har wanda bazai iya bama iyalansa tsato da za'a halakasu har gidaba, tayaya zai bama ƴan ƙasa? Maimakon fa a tsaurara binciken gano wanda ya aikata sai ma yabar ƙasar gaba ɗaya ya koma America da zama. shine bai tashi dawowa ba sai yanzu wai shi yazo yay mulkin ƙasa. Inama laifin ya fito kansila ɗin anguwarsu ko ƙauyen Taura, amma ba NAYA ba dan babu abinda zai iya. Kai kana gani ko primary election ɗin nan ba kuɗi daliget sukaci ba da sauran ƴan takarar da suka janye masa tunkan fara jefa kuri'a?. Hutu da jin daɗi ya iya, yaje yayi kayarsa yabar wanda suka san wahalar talaka suyi mulkin ƙasar NAYA”.         “To amma ranka ya daɗe sai nake ganin kamar jama'a zasuce kana faɗar duk wannan ne saboda kaima ana zargin takarar zaka fito a jam'iyyar hamayya?”.       (Dariya). “Dan kawai zan fito takara sai a danganta zancena da ita. To nabama duk mai saurarenmu damar zuwa ya binciki, shin a zancena akwai ƙarya kuwa?”.          “To amma ranka ya daɗe idan za'a duba a yanzu haka Ramadhan B. Taura yana shirin angwancewa ne da ɗiyar talakawa, wadda kowa ke ganin halaccine garesa bisa itama nata hallaccin data nuna akan kakansa wanda taima garkuwa aranar salla a filin idi. Shin wannan bai kai a yaba masa ba kuma a ƙara tabbatar da yasan kishin talaka da darajarsa ba?”.         “To ai wannan maganar auren nasa ga kowa ma abayyane take. Dama sunyine domin duniya tai irin tunaninka, inba hakaba taya kake tunanin yaro kamar Ramadhan B. Taura young millioner da tun yana ciki ake tara masa kuɗi a accaunt zai auri ɗiyar talaka mai wahalar neman na masara a kullum. Kai ita kanta yarinyar ma a majiya mai ƙarfi tayi abinda tayine dama saboda an biyata. Sune suka sakata tayi hakan domin ayi irin tunanin da kayi. ka auna mana, dayin abun da fitar sunansa matsayin ɗan takara gaba ɗaya sati biyu kenan”.         Ɗan jarida ya jinjina kansa yana kallon fuskar camara man. “To jama'a kuna dai jin tattaunawarmu da Alhaji Andi ƙaura acikin shirin SIYASA RIGAR ƳANCI dake zuwa muku anan gidan tv na G tv. Gashi mun kwararo bayani kuma lokaci ya ɗaga mana hannu, amma ku mana afuwa sati mai zuwa zakuji ƙarashen wannan fira insha ALLAH, zakuma kuji amsoshin zantukan Alhaji Andi ƙaura daga bakin makusancin ko nace jam'iyya mai mulki shima insha ALLAH”.             Ɗauke hotunansu ya saka Raudha cusa kanta cikin ƙafafu ta fashe da kuka. Tun farkon fara hirar ta zauna kallo sakamakon cin karo da hotonta da tayi tare da na Ramadhan. Da farko rikicewama tayi dan bata gane shi bane, sai da hajiya mama dake zaune a falon tana kallo ke faɗin, “ALLAH dai ya kaimu randa zanga wannan zuƙeƙen surikin namu ya zama shugaban ƙasar NAYA ɗiyata first lady, ɗiyata da zakimin baƙin cikin zama uwar first lady”.       Cikin rashin fahimta Raudha ke duban hajiya maman, sai kuma ta maida hankalinta ga tvn dan itako batama san wanda ake kira da mijin nata ba ya fito takarar shugaban ƙasa. Sosai hankalinta ya sake tashi dajin wannan hira musamman abinda Alhaji Andi ƙaura ya faɗa akanta. ALLAH shine shaidarta batayi dan a yaba mataba. Hasalima batasan wanene Alhaji baba ba alokacin. Amma gashi nan ta shiga bakin duniya yau harda masu fassara al'amarin da cewar an biyatane dan tayi, wasu na faɗin neman suna da neman gindin zama ne dama. Wasu na faɗin dan kuɗi tayi.      Surutu dai iri-iri gasu nan marasa daɗin ji, ita kanta zuwa yanzu harta fara ganin gaskiyar zantukan mutanen, dan tana da tabbacin Ramadhan yafi ƙarfinta. Musamman da zancen fitowarsa takarar shugabancin ƙasar NAYA ya bayyana. Sannan ita tun da ake maganar auran nan batajin ma shi ya sani, tunda tun randa yaje asibitin nan bata ƙara ganinsa ba. Sai ma hannunka mai sanda dayay mata akan zame mata *_BAƘAR INUWA_*  inhar bata faɗi dalilinta na bama kakansa kariya ba. Idan har shi zaiyi irin wannan tunanin dan jama'ar gari sunyi mizaisa ta zargesu.......       “Raudha!”. Asabe ta sake kiran sunanta a karo na biyu. Ɗagowa tayi tana dubanta dan bataji na farkon ba. Cikin tausayin ƴar tata tasa hannu ta ɗagota ta rungume. “Haba Raudha kukan nan ya isa mana. Kina sake tayarmin da hankali wlhy. Ni nasan bakison auren nan, bansan miyasa kika amsa musu ba.....”       “Wlhy ko bataso saita yisa”. Cewar Hajiyar birni dake fitowa daga ɗaki a fusace. Dan yau da wuri ta baro shago saboda tana shirye-shiryen daina zuwa wai dan zata zama kakar matar shugaban ƙasa (🤔😝😂lol).        “K dan ubanki saketa kitsaya da ƙafafunki!!”.      Raudah ta saki Mommynta da sauri saboda gigitacciyar tsawar da Hajiyar birni tai mata. A take hajiyar birni ta haɗasu su duka ita da Asaben ta zage tas Hajiya mama na tayata. Sai da Aunty Hannah ta shigo gidan kusan goma na dare sannan tasa baki dan har lokacin sunata mita. *_TAURA HOUSE_*      A ɓangaren Ramadhan ma da duk ƴan gidansu sunga hirar da akai da Alhaji Andi ƙaura, hakan kuma yasa Gimbiya Su'adah jin wa ɗanta zai aura. Dan tayi-tayi Pa ya sanar mata dama yaƙi. Sai gashi yau taji a shanun ƴan talla.          Cikin lokaci ƙanƙani ta birkice, su Lubnah na tambayarta amma bata sauraresu ba. Da suka cigaba da damunta ma tsawa ta daka musu tai wurgi da wayar da take neman Fulani taƙi shiga ta fice zuwa sashen Pa duk da yau ba itace da girki ba. Zaune ta iskesa shi da Hajiya Mufida sunata hirarsu. A kallo ɗaya da sukai mata suka fahimci babu lafiya. Dan kowa a gidan yasan shegen girman kai da isar Gimbiya Su'adah. Duk da tanada tsananin kishi kishiya bata isa fahimtar komai daga garetaba. Dan batayin wani abu da za'a samu kafar rainata, ko kallon banza bata amince zamanyi da kishiyaba dan tace zubar da mutunci ne. Hakan kuwa da takeyi yayi tasiri, dan kame kan nata yasa ko shirmensu suke yakan tsayane iya su biyu, ballema suma ɗin kowa ji take da kanta abunka da kowa ubanta ya tara kuma akwai ilimi, dama hayaniyar tasu bata wuce ta harara ko rainin wayo anama juna yatsine-yatsine ko ɗaukar kai.       Tsam hajiya Mufida ta miƙe tana tattare wayoyinta, cike da kulawa ta dubi Pa. “Bara nayo shirin barci kafin ku kammala”.     Kansa kawai ya ɗaga mata idonsa akan Gimbiya Su'adah datai zaman ƙasaita a gefensa fuskarta tamkar zatayo aman wuta. Sai da ta tabbatar Hajiya Mufida ta bar sashen saboda akwai cctv da ake ganin shiga da fitar kowa daga nan falon sannan ta dubi Pa.        Kafinma tai magana yace, “Lafiya?”.          Idanunta da suka kaɗa zuwa ja ta zuba masa, cikin son nuna isar tata tace, “Abban Ramadhan ban yarda da wannan auren na Ramadhan ba”.       Kansa ya ɗan girgiza ya ɗauke ya maida ga tv. sai da yaja numfashi ya fesar kafin yace, “Komi yasa?” batare da ya sake kallonta ba.           Bata damu da yanda yay ɗin ba, cikin kaushi da nuna a wuya take tace, “Saboda bata dace da shi ba. Taya za'ace duk ƴaƴan sarakunan ƙasar nan dana attajirai da masu mulki arasa matar da za'a bashi ya aura sai wannan?! Wad......”       Cikin sauri ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Su'adah bana son hayaniyar banza. Shin ɗanki aure bautar ALLAH zaiyi? Ko auren kuɗi ko mulki?. Sannan ma ina zuwa, kina nufin Bappi bai isa zartar da hukunci bane a kan ɗayanmu? Ita yarinyar kuma kinsan ƴar waye da kike wannan hanƙoron.”       Zatai magana ya sake dakatar da ita. “Karma ki ɓata lokacinki a banza. babu abinda zai hana wannan auren sai idan Ramadhan ne ya mutu, ko ita yarinyar insha ALLAH”.        “To ashe kuwa lallai zata mutun”. Ta faɗa a harzuƙe tana miƙewa zata fice batare data san katoɓara da suɓutar bakin da tayiba. Wadda ta saka Pa binta da kallo ƙirjinsa na bugawa. (Gimbiya Su'adah ta manta har yanzu akan binciken wanda ya kashe matar Ramadhan da ƴarsa akeyi, tun kuma a wancan lokacin an tabbatar musu wanda ya ajiye gubar suka sha sai dai idan yanada alaƙa dasu ne tunda duk wanda yazo birthday ɗin Haseenah makusancinsu ne. Sannan kafin wancan auren ma ta nuna borenta na ƙin Amnah saboda tanada sikila).         “Ya ALLAH mi Su'adah keson faɗa ne?”.     Pa ya faɗa a razane yana miƙewa zaune sosai. Zuciyarsa fal fargaban kar dai Su'adah nada alaƙa da kisan Amnah. Da sauri ya girgiza kansa. Dan a halayenta babu mai kamanceceniya da iya kisan rai. Barta dai da gadara da girman kai wannan kuma ya tabbatar jinin mulki ne ke yawo a jikinta. To amma miye ma'anar furucinta na yanzu? Anya kuwa babu lauje cikin naɗi.       Hankalinsa ya tashi matuƙa da wannan tunane-tunanen, harta kaisa ga fitowa daga sashen zuwa sashen iyayensa. A falo ya iske su harda ƙannen kakannin nasa su Inna sunata hira hankalinau kwance. Yanayinsa ne ya saka Yafendo tambayarsa ko lafiya?.       Da ƙyar ya iya haɗiye kaso sittin cikin ɗari na tashin hankalin daya shigo da shi, ya ƙirƙiri murmushin dole ya aza a fuska yana girgiza kansa. “Ba komai Yafendo, dama nazone akan batun Ramadhan”.        Bappi ya sauke ajiyar zuciya a hankali, “Dama muma shi muke tattaunawa anan, dan munga dukan hirar da akai da Alhaji Andi ƙaura, nasan kuma itace kaima ta hargitsoka. Karka wani damu, dama wannan itace siyasar, duk wani abu da zasu masa yarfe damu kanmu yanzu bazasu gajiya wajen bincikosa ba. Sai dai mu mun riga munsan kanmu, addu'a kawai za'a dage da ita. Insha ALLAH a cikin satin nan za'a kai kuɗi a tsaida magana, sai a ɗaura auran bayan an gama zaɓe hankalinmu ya kwanta.”         “Bappi haka shine dai-dai amma idan son samune dama a ɗaura auren kawai yanzu, sai ta cigaba da zama a gidan nasu bayan zaɓen sai ta tare ɗin”.      Ɗan jimm Bappi yay yana tunani, kafin yay magana Anne tace, “Ya kamata ku fara jin ta bakin iyayenta dai, ku basu haƙƙinsu har sai sun yanke muku lokacin da sukaga ya dace da su. Da campaign da zaɓe har zuwa rantsarwa inaga watanni uku ne zuwa huɗu ai. To idan kunji ta bakinsu kunga yayi nisa sai ku roƙi alfarma. Kokuma shi uban gayyar ku tuntuɓesa ko yanada wani lokaci daya tsara”.           Bappi yace, “Masha ALLAH hakan yayi kuwa. insha ALLAH zanyi magana da Ramadhan ɗin da safe idan ALLAH ya kaimu, na tabbatar yanzu yay barci. Ni bammasan yanda za'a kwashe da shi akan wannan barcin wurin ba yanzun. Dan kuwa ba nasa bane ba barci inhar da gaske ƙasar NAYA zai riƙe da ƙyau”.      Ƴar dariya suka ɗanyi su duka. __________________________________         Alhmdllhi kamar yanda su Bappi suka yanke shawara an kai kuɗin auren Raudha Hutawa, dan Bappi ya dakatar da M. Dauda sake zuwa Bingo da yay niyyaryi akan son lallaɓa Asabe ta koma aurensa, yace yay haƙuri suɗan kammala wasu abubuwan. Shima M. Gambo ya bashi shawarar ya zauna su taya Ramadhan campaign anan daga baya sa san dabarar lallaɓa Asaben, sai shima ya gamsu.       An amshi kuɗin auren Raudha harda hakimi, hakama dangin M. Dauda kowa so yake ace da shi akayi. Anba M. Dauda zaɓin tsaida lokaci, babu wani tunani ya yanke watanni huɗu. Duk da ba haka Bappi yaso ba sai baice komaiba sukai fatan ALLAH yasa haka shi yafi alkairi. Dan shima Ramadhan ɗin koda ya tuntuɓesa cayay wata huɗun, dan yafi son maida hankali akan wannan maganar campaign ɗin, ya kuma kawo hujjar idan akai auren yanzu za'aga kamar yayine dan amfani da Raudha wajen campaign. Sai dai abinda Bappi bai sani ba Ramadhan so yake ya zamewa auren, so yake kafin wata huɗun ya samu wani ya aurama Raudha ɗin batare da sanin su Bappi ba.   ★★★     A ɓangaren ƴan jam'iyya babu ɓata lokaci aka hau campaign ta kowanne ɓangare bayan an bada damar hakan ga ƴan takara ta kowanne fanni. Duk wani ɗan uwa da abokin arziƙi ya fito domin tallata *_ Brr Ramadhan B. Hameed Taura (Young millioner)_* kamar yanda matasa ke kiransa. Ta ko ina posters nashine ke yawo. Matashi na matasa kenan.        Duk wani ƙarfin halin Ramadhan da tunanin zai iya sai abin ya koma bashi tsoro, lallai siyasa ba wasa bace ba. Ƙoƙari yake yaga ya hana duk wani ɗora matasa akan ta'addaci na basu ƙwaya da makamai da wasu manya keyi amma hakan ya gagara. Dan su Alhaji Yaro glass sun rigada sun kammala shirinsu tsaf a bayan fage. Hasalima Ramadhan baida maraba da hoto game da kowanne irin tsari nasu. Sai dai duk wani tsari nasu mara kyau sun binne iya su. Mai ƙyawunne kawai suka fiddo garesa. Hakan yasa yake cigaba da musu kallon mutanen kirki.       Tabbas an kaɗa gangar siyasa. Mutanen ƙasa kuma sun amsa. sannan Alhmdllhi ta ko ina Ramadhan ya samu karɓuwa musamman a wajen matasa ƴan uwansa. Dan suna ganin wannan karonfa yaƙin nasune bana kowaba. A gefe kuma ƴan siyasa nata yarfe ga abokan hamayya. Musamman Ramadhan da tako'ina aka sakashi tsakkiya akan bai cancantaba. Ta yaya wanda ko aure baida shi zai iya riƙa ƙasar NAYA. Taya mai ƙarancin shekaru irinsa zai iya riƙa ƙasar NAYA? Taya ɗan gata irinsa zai iya riƙa ƙasar NAYA? Taya... Taya... Tay.... Dayawa suketa faman lissafi.           Sai dai kuma masu iya magana kance _zakaran da ALLAH ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho sai yayi_. To hakanne kam ga Ramadhan, dan tako ina bakajin sunan kowa sai na _Young millioner_ ga ƙuruciya ga kuɗi ga gayu ga ƙyawu.       A ɓangaren ƴammata suma ba'a barsu abaya ba wajen yaƙin ganin sun ture gwamnatin Raudha sun maye gurbinta. Wasuko gani suke koda ita babu abinda za'a fasa fatansu dai Ramadhan ya amshi tayi kawai. Dukan saƙonsu da shishshiginsu yana hankalce da shi. Sai dai kuma basune agabansaba yanzun. Ita kanta da aka saka masa ranar auren da ita bata gabansa. Dan yakanma manta da wata saranar aure dake a kansa gaba daya. Shi hatta sunan Raudha sai abakin ƴan siyasa ma ya fara jinsa. Kuma bazaice ya riƙeba duk da ana yawan ambata saboda yarfe da ake masa akan batun aure dama auren nata da mutane kan fassarasa a siga kala-kala.         Kallo ɗaya zakai masa ya baka tausai, duk ya rame yayi duhu saboda wahalar campaign da rashin barci. Duk ƙoƙarinsa nason ganin kowa ya fahimcesa hakan bai hana wasu jifansa da kalmar *Mai girman kai ba* susukance ya cika girman kan tsiya da izza. Duk lokacin da kalmar nan ta fito a bakin wani ɗan siyasa yakanyi murmushi, dan shi dai wannan girman kai nasa da aketa faɗa har yanzu bai ganinsa..........✍ *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/10, 7:45 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 20_* .............★A ɓangaren gimbiya su'adah da fulani da Asmah suna akan bakansu na ganin sun hana auren Ramadhan da Raudha suma. Sai dai kuma hayaniyar campaign ta sakasu ajiye wannan batun gefe. Kowa fatansa a yanzu Ramadhan ya haye mulki kawai, daga nan koma miye zai biyo baya sai ayi. Dan sun ɗau alwashin yaronsu bazai auri ɗiyar talakawa ba. Zuwa yanzu sunyi bincike mai tsanani akan Raudha har Hutawa, shiyyasa suke tunanin karya lagon su Bappi da wannan sirrin a haukarsu. ★★★        Raudha kam tun kwanaki biyu da kai kuɗin aurenta aunty Hannah da First lady suka yanke shawarar ɗauketa anan gidan, tare da kafama hajiyar birni hujja da kar Asabe ta zugeta, aiko tai azamar amincewa dan ita kanta lamarin Asaben tsoro yake bata duk da tasanta da kafiyar tsiya tunba yanzu ba. Tunda itama haka tayi ga masu kuɗi na sonta a wancan lokacin amma ta dage sai M. Dauda, itako a yanzu bazata yarda Asaben tai mata baƙin cikin samun abubuwa da damaba a dalilin auren Raudhan. Sun maidata wani gida keɓantacce wai ana koya mata dabarun mulki irin na first lady. Bawai suna mata hakan danta ƙaru ba, sunayine kawai danta saki jiki dasu har idan buƙatar sakata musu aiki ya taso anan gaba tayi babu musu.         Kasancewar an haɗota dasu Yasmin kuma harda aunty Hannah duk da bata cika zama ba saboda yawon campaign sai hankalinta bai tashiba sosai, ga wata dattijuwa da sukace tana aikine a fadar shugaban ƙasar shekaru goma kenan cir na mulkinsa mama tambaya, sai ƙarin mutane biyu ƴan gayu sukuma masu koya mata abubun daya shafi gyaran jiki da dai sauransu. Sai shahararriyar mai kayan gyaran jikin nan dake gyare Raudha ɗin lungu da saƙo da ingatattun kayanta kayan ƙamshi dana sanyi *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* _(guys ku garzaya dan zaku samu duk abinda kuke buƙata ga amaryar kb, daga kayan ƙamshin jiki, gida, kayan mata, maganin sanyi ingantacce😋😘😍🤗)_           Kuma akwai wata islamiyya dake anan kusa da gidan saboda matsawarta yasa suka sakata ita dasu Yasmin. Sai dai bata fita sai da dogon hijjabin Uniform ɗin makarantar harda niƙaf. Ba'a dabarun mulki kawai aka tsayaba har gyaran jiki dasu saka kaya, girki duk koya mata akeyi, dan ma Alhmdllhi dama ta iya abubuwa da yawa na aikin cikin gida sai dai bana ƴan gayu irin haka ba, ba kuma sosai take girki ba a gida saboda icce suke amfani da shi ita kuma Asthma.        A gefe kuma damuwar auren nata na nan daram a ranta. Musamman yawan ganin Ramadhan da takeyi a tv saboda campaign yanzun. Hakama idan ta fita islamiyya duk da anguwace ta manya tana ganin posters nashi. Ita kanta tasan ƙyaƙyƙyawane, yanayinsa da kwarjininsa dole ya shiga ran mai kallonsa da hanzari, sai dai ko kaɗan batajin sonsa a ranta, kamar yanda tasan itama bazai taɓa ya sota ba. ita da kanta kuma tana tilastama kanta saka ƙinsa a ranta saboda wasu dalilai        ★Al'amarin campaign ya miƙa, kowa yana hangen nasara tattare da Ramadhan duk da masu iya magana kance siyasa kamar mace mai ciki ce, ba'a san mi zata haifa ba. Abubuwa da yawa masu daɗi da marasa daɗi sun faru a wajen campaign ɗin nan, wasu sun wuce an manta, wasu ko bazasu gogu a zuciyaba sai bayan mutuwa.      Da gaske Ramadhan ya manta da batun wata Raudha saboda hargitsin campaign, sai idan wani ya ambaci sunanta ko zancen auren nasa ya fita a bakin wani yake tuna wata sa rana dake kansa ta aure. Sai dai ga Bappi da Pa da Anne ba haka bane, dan sunata shirye-shiryensu na biki duk da hatsaniyar campaign ɗin da kowa ke a ciki. Ga gimbiya Su'adah kuwa tunda ta gama binciki tushen Raudha hankalinta ya sake tashi ta birkicema Pa. Ko kulata baiyiba balle ta samu amsa. Hakan ya kuma ɓata ranta ita da su Fulani, batare da sanin kowaba suka shiga ƙulle-ƙullen yanda zasu ɓadda Raudha, sai dai sunbi duk wata hanya data dace amma basu sameta ba saboda ɓoyeta da akayi. Wannan dalilinne yasa gimbiya Su'adah tun karar Pa ana gab da rufe campaign.         “Wai nikan nakega ya kamata ko sau ɗayane ai matar da Ramadhan zai aura a ganta wajen campaign, kar mutane su fassara rashin ganin nata da wani abu kuma ai”.       Shiru kamar Pa bazai amsaba duk da tasan ya jita sarai, sai da ya gama kallon rahoton da akeyi a tv game da taron campaign daya faru na Alhaji Andi ƙaura a jihar Sato sannan, cikin fushi dajin ɗacin kalaman da Alhaji Andi ƙaura yay amfani dasu a wajen da yarfen da yayma Ramadhan yasa muryarsa kausasa.         “K dake matsayin uwarsa tunda aka fara campaign ɗin kinje ne?”.      Fuska ta kumbura, cikin zafinta tace, “Miye alaƙar ganina da ganinta a wajen? Kuma ni ai inada masu zuwamin”.       “To itama ai danginta sunje sun wakilceta, dan mahaifinta campaign ɗin da yayi a yankinsu bana tunanin wani a gidan nan yayi kwatankwacinsa ma.”       “Tunda ko yana neman gindin zama da shegen kwaɗayi ai dole yayi. Imagine yarona kamar Ramadhan dake da kowane irin gata na duniya ya ƙare da auren ƴar karuwa da ɗan duniya. Jikar mai tuwo-tuwo tikari a saudia. Miyasa idan dan alkairin da tayinne baza'a bata kuɗi itada iyayen nata ba tunda su sukafi buƙata. Sai an wani ƙaƙabama yarona? Idan kuma auren nata dole ne basai a samu wani a bashiba a ma'aikatan gidan nan”.        Pa yasan ya cigaba da saurarenta zai iya mata abinda duk yazo masa a rai, dan haka ya miƙe tsam ya bar mata falon. Hakan ba ƙaramin sake ƙona mata rai yayiba, dan harda ƙwalla suka taru mata a ido, zuciyarta na ƙarajin tsanar Raudha da duk wanda ya shafeta. Tayi alƙawarin koda sunfi ƙarfinta anyi auren nan wlhy sai Raudha ta gwammace mutuwa da rayuwa.         Da wannan ɓacin ran ta yini ranar, da daddare ta buƙaci ganin Ramadhan, duk da yanda yake a matuƙar gajiye dan yau jihar Nobama sukaje campaign haka ya daure ya amsa kiran nata. Tunda ya shigo take kallonsa, duk ya rame yayi duhu saboda wahalar kai kawo, sai dai hakan bai dametaba, dan tasan yana samun mulki zai koma normal harma yafi da.         “Barka da dare Maa!” Ya faɗa cike da girmamawa yana kaiwa zaune kujerar dake gefenta. Tab.. ɗin hannunta ta ajiye cike da ƙasaitarta tana dubansa. “Baka dai, lafiya ne na ganka sukuku?”.        Numfashi yaɗan furzar, cikin muryarsa mai ɗan faɗi yace, “Kaina ke ciwo, nasan hayaniyarnan ce kawai”.          “Basai kasha magani ba, ya za'ai mutum ya zauna da ciwo”.      “Bana son na cika yawan shan maganinne, nasan da nayi barci zan ware”.          Baki kawai ta ɗan taɓe, ta sake harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya da tsuke fuska. Dan tana so ya fahimci ba zancen wasa bane. “Ina muka tsaye game da auren wannan yarinyar da aka ƙaƙaba maka?”.         Baya ya ɗanyi da jikinsa ya kwantar a kujerar, ya lumshe idanunsa tamkar baiji mitace ba. Kusan sakan biyar sannan ya furzar da iska batare daya buɗe idanun ba. “Babu wani abu da zan iya yi akan auren nan tunda Pa da Bappi da Anne sun dage, kawai na yanke zan auretan daga baya zan san abunyi”.           “Jikar tikari mai tuwo-tuwon zaka yarda ka aura? To bara na faɗa maka idan ma baka saniba. Uwarta kanta sai da tai karuwanci, a barikinne ma ta haɗu da uban yarinyar dan shima ɗan duniyarne na bugawa a magazine, daga kakarta har ƴan uwan uwarta duk karuwai ne har yanzun. Idan ma barci kake ka farka, duk yanda zaka zame ka zame kafin cikar waɗan nan kwanakin da suka tsaida”.       Harga ALLAH maganganunta sun sokesa. Kuma dama tayi amfani dasu ne dansu soke-san tunda tasan yanda ya tsani karuwai tun yanada ƙarancin shekarunsa balle yanzun. Idanunsa dake kumbure da ɗan ja a cikinsu saboda rashin samun isashen barci ya zuba mata. Sai kuma yaɗan janye cikin taune lips. “Maa waya faɗa miki?”.         Harara ta danƙara masa tana miƙewa, “Kaje ka bincika tunda na saba maka ƙarya...” Tana faɗa tabar wajen.        “Maa Please.....” Ya faɗa da sauri yana ƙoƙarin ganin ta tsaya amma tai masa banza ta shige. Jagwab ya koma ya zauna a kujerar yana dafe kansa daya ƙara ƙarfin gudun ciwo. _(Ƴar karuwa, jikar tikari mai tuwo-tuwo. Ubanta ma a yawon duniya suka haɗu da mamarta sukai aure, sannan duk ƴan uwan uwarta karuwaine har yanzun)._  “Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un”. Ya faɗa a fili yana dafe kansa da ya sake wata irin sarawa kamar zai faɗo ƙasa. Duk yanda yaso miƙewa a wajen kasawa yay. ALLAH ya taimakesa sai ga Rafi'a ƙanwarsa ta uku ta shigo falon da shayi a hannu da waya a kunne alamar magana takeyi.       Cikin sauri tace, “Subahanallahi Yaya!”. Wayar da kofin shayin ta dire bisa centre table tayo kansa, duk yanda taso taimaka masa ya tashi ta kasa, dole ta fita ta kira Pa da sauran ƴan uwanta dake can babban falo kowa na harkar gabansa. Waɗanda ke a cikin ɗakunan barcinsu kuma suka firfito suma saboda yanda take kwakwazon kiran Pa.        Komai Pa baice masaba, sai taimaka masa da yayi ya miƙe, da kansa ya kaisa har sashen su Anne su Rafi'a biye da shi hankali tashe, wasunsu ma hawaye sukeyi duk da bawai ya suma bane ko yanayi yayi tsamari. Kawai dai idan ka kallesa kasan babu lafiya tare da shi.      Suma su Anne hankalinsu ya tashi, a take aka nemo doctor duk da yace su barshi shi lafiyarsa ƙalau, amma basu sauraresa ba. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga doctor Shamsu. Koda ya dubasa sai yace musu gajiyace da ƴar damuwar data saka jininsa ɗan haurawa. Sai kuma sugar ɗinsa yayi low sosai da alama kwana biyu baya kula da shan maganinsa.         Da ƙyar Ramadhan ya yarda aka saka masa drip, sai da Bappi yay masa jan ido ma, ALLAH ya taimaka bai jima da fara shiga jikinsaba barci mai nauyi yay awon gaba da shi. Su duka tausayinsane ya kamasu. Dan sun san yana matuƙar ƙoƙari akan abinda bai saba ba. Duk da yana zirga-zirgar kasuwanci ba irin wannan bace. Dan ko hayaniyar campaign ɗin nan tashin hankaline. Balle kuma akwai ƴan kunji-kunji kala-kala a gefe ga abokan hamayya dama abokan tafiyar.        Duk fita sukai suna masa fatan samun lafiya ganin yayi barci. Sai dai ran Pa a ɓace yake sanin Gimbiya Su'adah ce ta sake saka Ramadhan ɗin cikin wannan yanayin, kuma duk abin nan da akeyi babu idonta a wajen.         A ɓangaren gimbiya Su'adah kam duk taji komai, taƙi fitowane danta sake jaddadama Ramadhan fushinta ya tabbatar da zancen bana wasa bane. Dan taji daɗin yanda taga zancen yayi tasiri a ransa. Hakan yasa babu ɓata lokaci ta kira Asma data bata shawarar ta sanar mata. Cikin jin daɗi adda Asmah tace, “Su'adah ai dama na faɗa miki hakanne kawai zaisa Ramadhan yay mana biyayya. Ni yanzu ina ganin mu haɗa wani shiri da zai sake sakashi tsanarta. Suma kakannin nasa susan mike faruwa idan ma basu sani ba”.      “Okay ina saurarenki wace idea ce”.        Idanu sosai Gimbiya Su'adah ta zaro bayan ta gama jin yayar tata adda Asma. Cikin rawar harshe tace, “Anya Adda Asmah wannan shawaran yayi kuwa? Karki mantafa mulki Ramadhan ke nema. Koyaya abu yake yanzu zai ita taɓa kujerar da yake neman. Abokan hamayya na masa yarfe da ƙazafi inaga wannan ta fito......”        “Su'adah ki kwantar da hankalinki, babu ta inda wannan zai shafi Ramadhan. Sai ma ɗaga darajarsa da zai ƙara”.      “Uhm-uhm Adda kedai bari sai mun sanar ma Fulani”.        Wani irin takaici ya baibaye Adda Asmah daga can, ji take kamar ta jawo ƙanwar tata ta hau duka. Amma a fili sai tace “To hakan yayi”.       Koda Gimbiya Su'adah ta kira Fulani ta sanar mata zaginta ta hau yi. Duk da ta yabama ƙoƙarin ta na farko akan sanarma Ramadhan su waye dangin Raudha ɗin. Amma maganar fita da tsiraicin suce Raudha ce da wani wannan gangancine. “Ku miyasa baku da hankali. a tunaninku dan kunyi video na bogi kunce itama yarinyar karuwace zai hana mutuncin Ramadhan taɓuwa ne. To idan baku san siyasa ba ko mulki ku farka. Wannan abun zai iya ruguza duk wata nasarar da muka samu a campaign duk da kuwa bai aureta ba, idan ma baku sani ba zancen auren nan nata shi kansa wani mutunci ya ƙara masa ga al'umma har a wajen campaign. Idan zamu kaudashi kuwa zamuyine a sirrance bawai mu nuna wa duniya ba marasa tunani kawai. Ku fitar da video ɗin abokan adawa sujuyar da shi akan tare take da Ramadhan ɗin a ciki shashashu kawai”.       Shiru gimbiya Su'adah tai da waya a hannu dan Fulani na gama faɗa ta yanke wayarta. Itama irin wannan tunanin tayi tun farko shiyyasa ta bijirema Addar tata. Inko hakane gara ta tattara zancen Raudha gefe tukunna, dan duk abinda zai hana ɗanta hawa mulkin nan zata kwana ta yini yaƙi da shi ne. ______________________________      Badan Ramadhan ya warke ba ya miƙe ya koma filin daga, amma Alhmdllh ɗan ƙarin ruwan da akai masa yasa jikinsa yin daɗi. Ranar wata juma'a bayan sakkowa massallaci yay campaign nasa na ƙarshe a ƙauyensu Taura. Inda ɗunbin jama'a suka taru har abin ya bama mutane tsoro musamman abokan hamayya irinsu Alhaji Andi ƙaura. Su president kam ji suke kamar su goya Ramadhan a baya dan daɗi. Dan kuwa sun san burinsu na dawowar mulki garesu ya gama cika. Sai kuma fatan kauda Ramadhan a shekaru biyun da suka ɗiba masa (wa'iyazubillah. Sun manta ran kowa a hannun ALLAH yake. Sannan shike bada mulki ga wanda yaso a kuma lokacin da yaso).           Muslata irin farin cikin da Ramadhan ya shiga a yau ɓata lokaci ne. Dan kuwa ya tsorata da yawan mutanen da suka taru dominsa. Har yanaji a ransa kodai akwai aljanu kamar yanda wasu ke faɗa ne. Sai dai farin cikin nasa bai hana jin ɗacin da tsanar Raudha da ahalinta ba. Duk yanda yake turesu a ransa sun kasa gushewa. ______________________________ *_RANA BATA ƘARYA SAI DAI UWAR ƊIY TAJI KUNYA_*       A faɗin ƙasar NAYA da kewaye yau itace daren zaɓen shugaban ƙasa. Dan haka ta kowanne sashe akwai abinda ke gudana ga kowa. Wasu fatan nasara, wasu shirye-shiryen kota kwana, wasu addu'oi. A cikin masu salla da addu'a a wannan dare harda Ramadhan, Anne, Bappi, Pa, Yafendo, Inna da wasu a cikin ƴan uwan ahalin Taura. A masarautar Bino ma dai Mai-martaba ya kwana raya wannan dare. Yayinda irinsu Gimbiya Su'adah sukejin mulki kamar sun samesa ne.     Duk da Raudha bata jin son Ramadhan ta masa fatan alkairi, harta kwanta kuma zuciyarta taita zingurinta akan ta tashi tayi salla ko raka'a biyu ne. Tabi shawarar zuciyarta tayi kuma ta roƙi ALLAH samun shugaba na gari bawai Ramadhan ba. *_WASHE GARI:_* kusan tara na safe Feena ta shigo ta sakata shiga wanka. Batare da tasan dalili cewa tai wankan ba tace ai yanzu tai wanka ita. Fita Feena tayi, babu jimawa ta dawo da kaya a hannu da makeup kit. Sam Raudha batason wannan ƙaƙale-ƙaƙalen, amma saboda Aunty Hannah ta shigo ta mata magana dole ta amine akai mata light make-up ɗin. Sannan ta saka kayan da aka kawo matan. Tabbas tayi ƙyau, sai dai bazata iya fita da gyalen da aka haɗo kayan da shi ba. Dan haka ta ɗakko gogaggen hijjab ɗinta daya shiga da kayan ta saka. Duk jarabar aunty Hannah dole ta barta dan kuka ta sanya musu.            Tana zaune fuska a kumbure tana shan tea ɗin da aunty Hannah ta tilasta mata sha Yasmin ta iso da saƙon “Mom wai ga baƙon yazo inji mama tambaya”.       Cikin sauri aunty Hannah ta amshe kofin shayin hannun Raudha ɗin. “Sai ki tashi tunda dama haka kike so ki fita bakici komai ba. Sai ki tashi ya iso kuje ku jefa ƙuri'a muma zamuje tare da tawagar shugaban ƙasa”         Sosai gaban Raudha ya faɗi, ta ɗago da sauri ta dubi Aunty Hannah. Sai dai kafin tai magana Feena ma ta shigo.       “Hajiya suna jiranta fa”. Da sauri Aunty Hannah ta miƙar da Raudha, bag ɗin da zata riƙe mai ƙyau ta saƙala mata a hannu, hakan sai yay matuƙar sake fito da tsarin kwalliyar tata musamman da hijjab ɗin ke iya cinyarta kawai, gashi mai hannu, ya kuma ɗau guga ya kwanta luf da haska ƙyaƙyƙyawar farar fuskarta kasancewar blue color ne, sai hakan ya ƙara bama skirt ɗin nata fitowa sosai ya buɗe. Kamar zata fasa kuka ta zura takalman da aka ajiye mata masu ɗan tudu da suka sake fidda ƙyawun ƙafarta.........✍      *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _A AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account. *Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks. *Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku. A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant). -------- Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar: *Bank Transfer* *Airtime Transfer* Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance. *Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks. _Account No_ - *1220077999* _Account Name_ - *Arewa Books Publishers* _Bank_ - *Zenith Bank* Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din: Amount Paid: - Nawa aka tura? Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa Transferred time: - lokacin da aka turo Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi Deposit date: - ranar da aka turo Sai ayi SUBMIT. *Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar: MTN, 9Mobile Glo Airtel Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance. *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/10, 7:45 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 21_* ...........Cikin girmamawa baba Adamu driver ya buɗema Raudha jibgegiyar motar yana faɗin, “Barka da safiya ranki ya daɗe”.      Sosai kunya ta kama Raudha, dan baba Adamu ba yaro bane ba, cikin ɗan murmushi tace, “Baba ina kwana”.         Amsawa yake cike da girmamawa da jin ƙaunarta, dan duk yanda kake kanaso a girmamaka a mutuntaka. Yaran gidan su Ramadhan kuwa ƴammatan nan yanda suke masa har ƙwalla yakeyi wataran. Sai dai idan Pa ya gani ko Bappi ko Anne su tsawata musu. Dan Ramadhan shima yana bashi girma sosai. Samun kansa yay da taya Ramadhan murnar samun mace tagari, tare da binsu da addu'ar fatan alkairi a zuciya.       Tunda motar ta fita a gidan Raudha na kallon titi ne kawai da shaƙar ƙamshin motar mai neman sakata barci. Ga wani sanyi dake ratsa jiki a hankali. Da farko a tsorace take, amma ganin babu kowa a motar sai zuciyarta ta samu nutsuwa.       Tafiyar da bata gaza mintuna sha biyu ba suka iso, abinka da lafiyayyar mota akan nagartaccen titi. Wani irin tsargawa cikin Raudha yayi ganinsu a *airport*, inda bata taɓa zuwa ba sai dai ta gani a tv. Zuciyarta ta shiga tsinkewa lokacin da take fitowa idanunta sukai arba da gayyar jama'ar Taura Family ƙwansu da kwarkwatarsu. Jitai ƙafafunta na hahharɗewa. Cikin sauri ta shiga ambaton addu'ar da duk tazo bakinta a zuciya. Anne da fuskarta ke faɗaɗe da murmushi ta riƙo hannunta tana faɗin, “Masha ALLAH wannan amarya kam da gaske zata iya ture gwamnatina”.        Raudha dake jin kamar zata nutse ta rissina tana gaida Anne. Sake riƙota Anne tayi ranta fal da jin ƙaunar yarinyar, harga ALLAH shigar mutunci da Raudha tayi na hijjab ya matuƙar burgeta. Bappi ne na biyu data gaida kasancewar shine kusa da Anne, shima kuma yanata zuba mata murmushi tare da sake tambayarta ƙarfin jiki tace Alhmdllhi.         Sauran ƙannen Ramadhan duk sun sake yarda Raudha ƙyaƙyƙyawa ce ƙwarai da gaske, wasun su ta shiga ransu, wasu ko sunajin ƙinta a rai badan ta musu komai ba. Bayan ta gaida Pa ta gaida su Gimbiya Su'adah badan tasan matsayin kowanne ga Ramadhan ɗin ba. Kawai dai yanda ta gansu manya matsayin iyaye yasa ta risina kamar yanda ta gaida Pa suma ta gaishesu. Su Hajiya Mufida sun amsa mata da fara'a musamman ma hajiya Shuwa da dama haka take da sakewa. Gimbiya Su'adah kam bana tunanin tama amsa mata. Sai wani kallon ciki da bai take mata fuska a yamutse.     Oho Raudha bama tasan tanai ba dan taƙi yarda ta kalli kowa. Sai ma juyawa datai ta gaida su Zainab ƙannen Ramadhan ɗin. A take Rumaisa da Fadila da Basma suka riƙota sun murmushi, zasu iya zama sa'anninta a shekaru, sai dai jin daɗi da hutu yasa sun fita girman jiki.        Sai yabata suke da faɗin yayansu yayi sa'ar ƙyaƙyƙyawar mace, ita dai ta kasa cewa komai sai ɗan murmushi, dan duk a takure take. Bata sake tsurewa ba sai da zasu shiga jirgi da batai tunanin nan ɗin zasu shiga ba, dan sanda suka fara taka steps ɗin sai da Bilkisu ta riƙota saboda tuntuɓe da taci zata faɗi. Tambayar zuciyarta ta dingayi ina zasuje ne haka? A ɗayan gefen kuma tsoro ne fal da fargaba.          Can aka kaita sashen vip ba inda sauran suka zauna ba. Duk da kuwa duk cikin jirgin Taura family's ɗinne da ma'aikatan gidansu. A taƙaice ma jirgin nasune. Duk da ba gama tantance ƙamshin turarensa tai ba lokacin da suka iso hanunta cikin na Basma sai da gabanta ya faɗi saboda wani shegen ƙamshin turaren daya daki ƙofofin hancinta. Ta sake waresu da ƙyau tana zuƙa da yin tazbihi ga UBANGIJIN daya azurta ƙwaƙwalwa da gangar jiki akan son ƙamshi da banbance wari.       Sallamar da Basma tayi ne ya sakashi ɗago idanunsa da kallo guda zakaima cikinsu kasan yana matuƙar buƙatar son hutu, yay mata duba ɗaya ya janye ya maida ga magazine ɗin da yake karantawa.        “Yayanmu dama Anne ce ta ce na kawo aunty Raudha ta zauna anan acan zata takura”.              Cak ya tsaya da karatun, sai dai bai janye magazine ɗin daga fuskarsa ba. Tsahon mintuna biyu kafin yayma Basma nuni da kujerar dake kallon wadda yake kai batare da yace komai ba. Bai kuma kallesun ba har yanzu. Duk wannan abu Raudha na laɓe a bayan Basma ne. Sai da Basma ta juyo ta kamo hanunta tana murmushi.       “Bismillah auntynmu ki zauna anan, dan ALLAH ki saka yaya yay surutu, dan tunda aka fara hargitsin campaign ɗin nan ya sake zama shiru-shiru”.     Kasancewar a cikin kunne tai mata maganar yasa Raudha saurin duban gabansu, sai dai kafin ta iya furta wani abu Basma ta kamata ta zaunar a kujerar har gwiwarta na ɗan gogar ƙafarsa daya harɗe ɗaya saman ɗaya. Kamar walƙiya kuma Basma ta ɓace a wajen.          Zan iya ce muku a wannan lokacin zuciyar Raudah ce kawai zata iya sanar muku halin da take ciki, dan faɗa da bakima ɓata lokaci ne. Ta kasa dubansa balle ƙwaƙwaran motsi, abinda ta iya ƙarfin halin yi kawai shine faɗin, “Ina kwana”.      Bata damu da amsawarsa ko akasin haka ba, dan koya amsa bata tunanin ƙwaƙwalwar kanta zata iya banbance da wane yare ya amsa ɗin. Magana da na'ura ta farayi na a ɗaura belt ya sashi janye magazine ɗin daga fuskarsa a hankali. Akan Raudha idanunsa suka sauka. Harya janye idanunsa daga kallo guda dayay mata yana ƙoƙarin ɗaura belt ɗin sai kuma ya sake dubanta. Harga ALLAH yana matuƙar son blue color, shiyyasa duk inda yaga kalar da wahala bai nutsu a duba ba. Balle wannan daya haɗu da farar fata da cute face ɗin Raudhan. Motsin da zuciyarsa tayi a cikin ƙirji ya sashi janye idanun nasa gaba ɗaya daga gareta, harya sake ɗukar magazine ɗin zai buɗe sai kuma ya fasa ganin bata motsaba balle tai yunƙurin saka belt ɗin, ga jirgi ya fara ƙugi alamar zai tashi.         Cikin yatsine fuska da sake ɗaureta ya matso da jikinsa. ganin ya matso da hanunsa da gargasa suka ɗan bayyana a white skin nashi yasata saurin dubansa, sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska ya sata saurin rumtse idanun ta matse jikinta.       Lip ɗinsa ya taune na ƙasa da balla mata harara yana girgiza kai, sai kuma ya taɓe baki lokacin daya zugo belt ɗin yabi ta cinyoyinta da shi batare daya taɓata ba ya sakashi a ɗayan gefen. Wani shegen numfashi dake fita da sassarfa ta saki ganin ya koma ya gyara zamansa kamar yanda yake a da. Sai taji kamar ta saki kuka kawai ta huta ita kam.      Bai sake bi takanta ba har jirgin ya ɗaga duk da yaga yanda ta dafe kai lokacin da jirgin ke shillawa cikin gajimare. Karatunsa ya cigaba dayi duk da ƙamshin khumra ɗinta ta mugun addabar hancinsa, amm ya fuske kasancewar sa gwanin jin kai.             Gaba ɗaya Raudha a birkice take bata samu nutsuwa ba har sai da jirgin ya sauka, dan kwata-kwata tafiyar mintuna ashin da uku ce ta kawosu jihar Bino. Ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya lokacin daya miƙe yana ajiye magazine ɗin, komi baice mataba ya kwashi phones nasa guda uku da wani ɗan leda. Sai da ya ɗaga labulen wajen zai fita sannan ta tsinkayi tattausar muryarsa mai faɗi da ɗan buɗewa cikin kunnenta.       “Zaki cigaba da zama ne anan?”. Da farko bata fahimci da ita yake ba, sai da ta waiga taga dai ita kaɗaice a wajen sai ta miƙe tan ɗaukar bag ɗinta ta sakala a kafaɗa a sanyaye. Sai a yanzu ta samu damar iya kallonsa. Sanye yake cikin wani skay blue yadi mai shegen taushi, dan yanda ya ɗauka guga da ɗaukar idon mai kallo kawai ya isa kasan an sayesa da kuɗaɗe masu nauyi. Ga telan daya ɗinkasa ya fidda komai yanda ya kamta dai-dai da jikinsa kuma. Rigar iyakarta cinyarsa, hakama hanunta gajere ne iya gwiwar hannu, sai hula daya murza black da takalmansa suma black half covers. Sai agogonsa omega, fuskrsa tayi fayau saboda ɗan ramar da yayi da kuma gyaran fuska da Bappi ya takura masa yay jiya da yamma.        Da sauri taja da baya ganin ya juyo a bazata lokacin da suke gab da fitowa, ledar hanunsa na facemask guda biyu ya ɓare ɗaya ya miƙa mata. Ɗan ɗagowa tai, sai dai tai azamar janyewa kasancewar idanunta da suka faɗa cikin nasa a bazata. Karon farko da taji wani abu ya tsarga mata daga ƙwaƙwalwa zuwa yatsan ƙafa mai kama da tainkewar jini, taji tamkar ta saki fitsari lokacin da taji hanunsa a gefen fuskarta, tanaso ta ɗago ta kasa, sai rumtse idanu da tai da ƙarfi jin ya tura yatsunsa biyu ta cikin hijjab ɗin ya saƙala igiyar a kunnenta, kafin ta farfaɗo ya ja facemask ɗin zuwa ɗayan gefen haggunta ya saƙalo nan ma.      (Ya rabbi) ta iya ambata a ranta. Bata iya motsawaba duk da rawar da jikinta ke mata sai da taji alamar ya juya sannan ta iya binsa da kallo.        Yanada tsayi gwargwado, sannan ga jikinsa a murje kasancewar yana cin ƙarfe ga kuma jin daɗin rayuwa. Jin kansa da ƙasaita da mutane d yawa ke fassarawa da girman kai suna ƙara masa wani ƙyau da girma a idon mutanen. Musamman masu son kawo masa wargi duk da ƙananun shekarunsa kuwa. Duk da kasancewarsa ba miskiliba bashi da yawan fara'a. Bakuma dan baya yin dariyar bane, a'a kawai sai ya zaɓa wanda yaso yake iya ganin haƙoransa.           Tunda suka fara sakkowa. steps ɗin jirgin hasken camaras keta walainiya a kansu, dan su Bappi duk sun sauka har suna ƙoƙarin shiga motocin dake jere da aka kawo dansu. Sake ruɗewa Raudha tayi duk da ya zartata da step ɗaya, dan yana gaba ne tana biye da shi.      Ƴan jarida nason ji daga garesa amma securitys sun musu zobe. ganin yanda wani keta son kutso kai yasa Ramadhan ɗan dakatawa ya ɗagama securitys ɗin hannu. Dole suka ɗan janye hannayensu suka bama ƴan jaridar dama suna antaya musu harara.          “Ranka ya daɗe gaka a jiharka ta Bino domin zuwa tushenka ka jefaa ƙuri'a. Ko zamu iya sanin ya kakeji a wannan ranar kuwa?”.          Wani ɗan murmushi ya saki dakai hannu ya shafi gashin daya zagaye bakinsa, “Inajina tamkar kai, kamar kuma kowa, domin banda banbanci da kowa”.        “Amma ranka ya daɗe duk wani mai irin matsayin da kake kai na ɗan takara a yanzun musan hankalinsa nakan zaiyi nasa ko bazaiyiba. Miyasa kai kakejin kanka kamar kowa irina?”.        “Saboda nayi imanin ALLAH shine ke bada mulki ga wanda yaso, a kuma lokacin da yaso. Idan ni ba alkairi bane ga ƙasar NAYA ALLAH ya hanani damar samun wannan kujerar, ALLAH ya bamu wanda ya fini alkiri”.       A take wajen ya ɗauki tafi, fuskokin mutane cike da fara'a. Yayinda wasu suka shiga masa kirari da suna *_DOGARO GA ALLAH JARI_*.      Harya ɗaga ƙafa zai wuce wani ɗan jarida yace, “To amma ranka ya daɗe baka ganin mutane zasuga kamar basu da galihu musamman dasu suka kasance a rana tun daga fara campaign amma ko sau ɗaya ba'a taɓa ganin budurwarka ba a wajen, gashi kuma yau ranar zaɓe ma babu alamar zata fito jefa maka ƙuri'a?”.      Ɗan tsura masa ido Ramadhan yayi na sakanni uku, sai kuma ya janye yana sakin murmushi. Shi lauya ne, yanada sauƙin karanta da fassara kalman mutane, dan haka ya ɗan dubi Raudha da kanta ke ƙasa, a ranta tana jera godiy ga ALLAH ga kuma Ramadhan daya bata facemask ɗin nan, dan da batasan yanda zatayiba.      Sarai ya fahimci ɗan jaridan yayi wannan magana ne saboda son tabbatar da Raudha matsayin wadda ake ta raɗe-raɗin zai aura. Sai kuma ya janye ya maida ga ɗan jaridar tare da kai hannu ya ɗora kan kafaɗarsa ya ɗan bubbuga. “Duk da hakan ba huruminka bane zan baka amsa, Ganin wadda zan aura a wajen campaign ba shine ya kamata kai da ire-irenka su maida hankali ba. addu'a da neman zaɓin ALLAH na samun shugaba na gari ya kamata mu maida hankali. Ƙuri'a kuma insha ALLAH zanje na jefa tare da my wife to be insha ALLAHU yanzun”.      Ya ƙare maganar da juyowa ga Raudha yana ɗan ranƙwafawa da maida hanunsa ɗaya baya ɗayan kuma ya nuna mata hanya. Wannan respect daya nuna ga Raudha ya matuƙar ɗaukar hankalin mutane da ƴan jaridar dake a wajen, dan take aka shiga zuba musu ruwan camaras tare da darewa aka basu hanya suka fito daga zoben da akai musu.       Wata irin nannauyan ajiyar zuciya Raudha ta saki lokacin data shiga motar da aka rage domin su, dan sauran kowa ya shiga. Shigowarsa gefenta ya sakata ɗauke numfashi, bata sake ƙwaƙwaran motsi ba har suka iso cikin Taura.        Garin ya matuƙar burgeta, dan an gyarashi titi ta ko ina, ga fitulun solar ma birjik. Cike garin yake ta ko'ina da mutane saboda masu jefa kuri'a. Wani wajen kuma sifiku ne aka warware kiɗa na tashi da waƙokin da aka rerama Ramadhan iri-iri na campaign, wani gefen kuma na abokan hamayya ne. Dan duk da nan ɗin tushensane wasu basa ra'ayinsa magoya bayan Alhaji Audi ƙaura ne da sauran ƴan takara.       A jere motocinsu da tun shigowarsu garin ya ɗauki sabuwar hayaniya suka isa ƙofar ainahin family house ɗinsu dake tamkar masarauta a garin saboda ginine na ƙawa da aka narka kuɗi wajen yinsa. Sai da suka fito Ramadhan ya miƙama Raudha katin zaɓenta da batasan dashi ba. Amsa tayi kawai tare da faɗin “Nagode” a hankali batare da tunanin yajita ba.         Bappi da Anne ne suka fara jefa ƙuri'arsu. Sai Pa da matansa uku, sannan *_Ramadhan B. Hameed Taura_* da *_Raudha Ramadhan B. Taura_*. Har cikin rai taji haushin jin cire mata sunan Abbanta da akai aka ɗora na wanda baima zama mijin nata ba tukunna. Daga haka Yafendo da Inna ma suka jefa, sai sauran al'ummar gidan suka biyo baya.        Cikin ƙanƙanin lokaci hotunan jefa ƙuri'ar ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyya mai mulki da matar da zai aura ya fara yawo a yanar gizo da kafafen yaɗa labarai. Sai dai wasu har sun fara ƙananun magana akan facemask da Raudha ta saka. Har ƴan yarfen siyasa da abokan hammayya na faɗin, _Matan wasu na wahala shi yana ɓoye tasa da bai riga ya mallaka ba ma..         Duk wanda ya jefa tasa ƙuri'ar yana shigewa cikin gida ne, dan haka ita da shi tare suka shiga katafaren gidan na Taura Family da za'a iya kira da masarauta. Kamar yanda tai tunani kuwa akwai mutane sosai a ciki, sai dai ta gagara ɗaga ido ta kalli kowa da komai duk da tarba ta mutuntawa data samu ga mutane. Sai dai cikin nutsuwa take gaida kowa da girmamawa batare data kalleka ba.         Da alama anan zasuyi breakfast ma, dan an haɗa tarin abinci kala-kala a katafaren falon da suke zaune, wanda tunda suka zauna bata sake jin muryar Ramadhan ba. Batasan a yaya ma yake amsa gaisuwar mutane ba dan ita dai a ƙasa ta zauna kamar sauran yaran kuma taƙi kallon kowa. Babu yanda ba'ai ta hau kujera ba amma taƙi, hakan datai sai ya birge Anne da wasu tsoffi na ahalin gidan, dan wannan dai alama ne na tarbiyya.       Bayan shigowar kowa aka ɗunguma dogon dining table ɗin dake can gefe gari guda domin karyawa. Sai dai gaba ɗaya Raudha ta kasa kai ko lauma guda bakinta. Basma sai zungurinta take ita da Rumaisa dan sune suka sakata tsakkiya. Ramadhan kam nacan falo ma bai taso zaman cin abincin ba yana waya ne..........✍ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account. *Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks. *Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku. A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant). -------- Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar: *Bank Transfer* *Airtime Transfer* Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance. *Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks. _Account No_ - *1220077999* _Account Name_ - *Arewa Books Publishers* _Bank_ - *Zenith Bank* Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din: Amount Paid: - Nawa aka tura? Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa Transferred time: - lokacin da aka turo Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi Deposit date: - ranar da aka turo Sai ayi SUBMIT. *Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar: MTN, 9Mobile Glo Airtel Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance. *WANNAN SHINE BAYANAN* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/10, 7:47 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 22_* ...........Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci karo da wata wulaƙantacciyar harara data saka zuciyarta da hanjin cikinta tsargawa da ga gimbiya Su'adah. Saurin maida kanta tai tana amsawa Anne da rawar murya. Babu wanda ya lura da hararar sai Pa da Hajiya Shuwa. Dan haka Pa shima yay ɗan gyaran murya da sakin murmushi yana faɗin, “Ɗiyata ki saki jiki kici abinci kinji, munan family nakine na biyu insha ALLAH. Dan haka kar kiji komai kici duk abinda kike buƙata, kema mai baiwa wanine”.      Kai Raudha ta jinjina. Muryarta a risine ta ce, “To Abba nagode”.       Kiran da Ramadhan yayma Bilkisu ya hana kowa sake magana, ta miƙe tana amsa masa. Babu jimawa ta dawo ta fara zuba kunun gyaɗa a kofi. Anne ce tace mizatai da shi.      Cikin ɗan tura baki tace, “Yayane yace na haɗa masa nakai masa can”.           “Kunun kawai?”. “Eh Anne shi kaɗai yace”. “Bazai yuwu ba haɗa masa abinci, ni bansan mike damunsa ba yanzu bai son cin abinci duk ƙaunar dake tsakaninsu ada, yanzu babu ita.”       Bappi da tun ɗazun baice komaiba ya ɗan kalli can cikin falon inda Ramadhan yake yana faɗin, “Wannan hayaniyarce kawai ba wani abu ba, bara kiga ya samu nutsuwa zai koma cin kayansa.”       “Hakane” Anne ta faɗa cikin tausayawa.      Raudha kam duk abinda ake tanaji kamar kowa, sai dai tana tsakurar abincinne da satar kallon yanda aka loda masa uwar madara a cikin kunun da bai gaza rabin kofi ba. A ranta take gulmar kunu zai sha ko madara?. Bata da mai bata amsa dan haka ta haɗiye gulmarta a ciki.      Koda Bilkisu takai masa kunun kawai ya ɗauka da farfesun kan rago, sauran kuwa ta dawo dasu. Adalilin dawo da kayanne take jin Yafendo na faɗin, “Ai kunga dai bazai cin ba, amma ya ɗauka masoyinsa Nama da madara, dan wancan kunu dai madarace kawai ba kunu ba”.       Dariya suka sanya, yaran nayi ƙasa-ƙasa. Anne tace, “Ai Ramadhan da nama sai kace wani kure, shi dai yaci nama. Bansan irin wannan ƙauna ba. Ko rai aka ɓata masa baya ƙin cin nama saboda son shi da yakeyi”.      Nan ma dariyar suka ɗanyi, ita dai Raudha nata murmushi ne kawai.      ★★★ Da zasu koma batare da shi da Pa da Bappi ba, su sun wuce cikin masarauta ne, su kuma direct airport. Hakan ya saka Raudha jin daɗin komawar, dan sai ita kaɗai a vip ɗin. Sai dai tanata kallon tarkacensa daya bari a wajen da shaƙar ƙamshinsa tamkar yana nan, ta sake rimtse agogonsa dake cikin hannunta wanda da zasu fito daga falo a Taura Anne ta lura da shi ya manta a inda ya zauna, shine ta sata ta dakkosa. Koda ta ɗakko ta bama Anne cewa tai ta ajiye a wajenta ta bashi da kanta. Wannan shine dalilin tahowa da agogon har cikin jirgi tunda bata gansaba har suka baro Taura, yanzu kuma sai take ganin kamar bai dace ta ajiye anan ba gara ta bari ta bashi hannu da hannu. Sai dai kuma a ina? Yaushe kuma?. shine ke mata kaikawo a zuciya har jirginsu ya iso Bingo city batare da ta yanke kwakwarar shawara ba. Daga ƙarshe ma sai ta turashi cikin bag ɗinta batare da tasan dalilin yin hakan ba..      Koda suka sauka Anne sawa tai a maidata gida direct. Tai godiya batare data iya kallon kowa ba. har mota su Fadila suka mata rakkiya da nacin ta basu number ɗinta. Fuskarta ɗauke da murmushi tace musu itafa bata da waya.       A tare suka waro idanu waje. Rumaisa tace, “Kamarki matar Yaya guda baki da waya? To miyasa? Dami kuke gaisawa da Yaya kuma?”.      Cikin son kauda musu zargi tace, “Dokar Abbanmu ne sai kayi aure zaka riƙe waya”.        “Woow imagine! Dama akwai masu biyayya irinku har yanzu game da waya?”.        Basma ta faɗa da mamaki, dan su tun suna jss 1 ma sunada wayoyi, koda Ramadhan ya ƙwace a wancan lokacin basu ƙulla wata gudaba iyayensu mata suka saya musu wasu sukace su dinga ɓoyewa kar Ramadhan ɗin ya gani. Kuma haka akai har suka shiga ss 1 bai san sunada waya ba. Sai da ya saya da kansa ya basu.        Murmushi kawai Raudha tayi, yayinda Rufaidah ke faɗin, “Ai yanzu an saka miki ranar aure ya kamata Abba ya barki ki riƙe, zan faɗama Yaya kuwa”.       Kafin Raudha tayi magana har sun ɗaga mata hannu sun bar wajen saboda kiran da Sumayya ta ƙwala musu. _______________________       Alhmdllhi an kammala zaɓen shugaban ƙasa, duk da dai a wasu sassa an samu ƙananun hatsaniya na matasa da kuma sace akwatin zaɓe. Sai dai Alhmdllh abun bai tsamari ba jami'an tsaro suka tsawatar. Zuwa yanzu babban fatan kowa shine hayewar wanda ya zaɓa. Inda wasu ko barcin kirki basayi musamman ga ƴan takarar idonsu kyam a tv, wasu kuma a redio ana sauraren sakamakon zaɓuƙan jihohi.     Sai dai abin zai baka mamaki idan nace ga Ramadhan ba haka bane, dan shi tamkar ma an basa lokacin samun damar yin barci ne. Ko sau ɗaya bai taɓa zama kallon sakamakon zaɓe ba balle damuwa da yaya komai ke tafiya. Lokaci-lokaci dai yakanji ihun yaran gidansu na faɗin Yayanmu ya haye jihar kaza. Daga haka bazai iya ƙaras da komaiba kuma.          A randa ake tsumayen jin sakamakon zaɓen kuwa ƙasar tayi tsitt kowa ya kasa kunne, inda masu shirin kota kwana ke shirye tsaf na tada tarzoma ta kowanne sashe. Dan dayawan sauran ƴan takarar sunfa fahimci wanda zai iya kai labari kai tsaye. Dan haka suka shirya sai dai kowa ya rasa. A sashen su Alhaji Yaro glass duk da sunga alamun nasararsu hakan bai hanasu shirya nasu ƴan tada zaune tsayen ba suma, dan a cewarsu ko da zata kwaɓe sun shirya.      To suma dai jami'an tsaro sun shirya tsaf dan bada kariya ga al'umma kamar yanda Ramadhan yasa Bappi kiran I.G da General da sauran manyan shugabannin hukumomin tsaron ya nema alfarmar su tsaya da ƙarfinsu wajen ganin wani harmutsu bai tashiba dan ALLAH...           ★A ranar talata ƙarfe huɗu da mintuna talatin da bakwai na yamma shugaban zaɓe prof. Rabilu S Barde ya sanar da sakamakon zaɓe ga wanda ya lashe kujerar shugaban ƙasar NAYA.       Sabon shugaban ƙasa da komai nasa yazo da mamaki da sabon sauyi. Matashi na matasa, *Barr Ramadhan B. Hameed Taura*.             A hankali kofin fura dake hanun Ramadhan da fitowarsa kenan daga kitchen ɗin Anne yaje ya ɗebo furan dan yasha saboda barci daya tashi a makare yay sallar la'asar a ɗaki ya sulale ƙasa ya tarwatse saman Mable's ɗin da aka ƙawata falon da shi. Babu zato babu tsammani jikinsa ya kama rawa, dan harga ALLAH sakamakon zaɓen yazo masa a bazata, bai taɓa saka ran zaici ba dan yasan akwai manya a gabansa, duk da shike da ɗaurin gindin masu mulkin ƙasar da manya. Wasu irin hawayene masu ɗumi suka silalo masa a saman kumatu, ƙafafunsa da suka nema gaza ɗaukar gangar jikinsa sukai ƙasa ya durƙushe akan gwiwoyin sa biyu har ɓallin ƙofi na ji masa ciwo. Amma sai bai kulaba duk da zafin daya ratsasa sai ya tafi sujdah.       Anne da Bappi, Yafendo, Inna, Pa Siyama, Bilkisu ma dake falon duk Sujudan suka tafi kamar yanda yayi. Kafin su ɗago su bilkisu su cika falon da ihu saboda shigowar sauran ƴammatan gidan da gudu suna ihun murnar yaya ya haye.        Duk wannan ihu dake faruwa Ramadhan ya kasa ɗagowa daga sujida sai da Pa yazo da kansa ya kamashi ya ɗago da shi. Sai kawai ya fashe da kuka ya rungume Pa ɗin.      Pa dake murmushi shima idonsa cike da ƙwalla ya shiga shafa bayansa a hankali. Tsit falon yayi suna kallon yayan nasu, dan da yawansu zasu iya rantsuwar basu taɓa ganin kukansa ba kamar haka. Garama irinsu Mardiyya dake bimasa a yanzu kuma duk suna gidan aurensu.      Taɓa kafaɗarsa da Bappi yayi ya sakashi sakin Pa ya juyo ya rungume Bappin. Anne sai tazo dukansu ta rungumesu. Hakan yasa yaran gidan duka zuwa suka rungumesu su duka suma.      A ɓangaren gimbiya Su'adah kam ai tsabar farin cikin ta zama uwar shugaban ƙasa jitai tamkar ta ciji uwawunta. A take ta fara amsa wayoyin taya murna ga ƴan uwa da abokan arziƙi. Yau sam babu ɗaure fuska sai farin ciki. A ɓangaren Raudha ma shujuda tayi lokacin da aka sanar da Ramadhan matsayin wanda yay nasara. Batayi domin shiɗinne taso yaci ba dan dole. Tayine saboda fatan ace shine ahugaba na garin da suketa fatan samuwar mulki a hannunsa.      Su aunty Hannah kam gidan suka cika da ihu ita da ma'aikata. Ganin haka su Yasmin suka tayata suma. Farin cikinta uku ne a yau. A gobe za'a maida aurenta da Alhaji yaro glass kamar yanda sukai mata alƙawari. Na biyu zata zama matar vice president, na uku nan da shekar biyu itace matar president ɗin. A fadar shugaban ƙasa ma da duk wani dake tare dasu ransa fal farin ciki. Hakama jama'ar gari magoya bayan jam'iyya da Ramadhan. Dan tuni an fara bikin murna ta ko ina saboda jami'an tsaro sun taka rawar gani na hana kowacce irin fitina yin tasiri. Yaran su Alhaji Audi ƙaura duk wanda ya fito ram ake da shi. Ta ko'ina ka zaga kiɗe-kiɗe da bushe-buahe ke tashi a ƙasar NAYA birni da ƙauye. A lokacin da wasu ke murna wasu kuka sukeyi, dan da gaske irinsu alhaji Audi ƙaura ƴan takara wasunsu suma suka dingayi sai da aka zuba musu ruwa. Yayinda magoya bayansu da iyalansu ke cikin tsantsar baƙin ciki. Baƙin cikinsu bai sake ninkuwa ba sai jin cewar Jami'an tsaro sun kafa sun tsare ko'ina domin hana kowacce irin tarzoma tashi. Idan ma tsautsayi ya fiddo mutum kamesa sukeyi. ★★-★★      Bazamuce hankali ya kwanta a ko'ina ba. Sai dai Alhmdllhi masu tada tarzomar basu sami yanda suke so ba. Jami'an tsaro ta kowanne fanni kuma sunyi ƙoƙari, sai dai ALLAH ya saka musu da alkairi. Shi kansa shugaban ƙasa duk da akwai manufarsa ta ɗora Ramadhan akan mulkin yayi ƙoƙari sosai wajen jadadama jami'an tsaro harkar tsaron. Shine ya fara kiran Ramadhan ya tayasa murna. Sai kuma alhaji Yaro glass dake matsayin vice president a yanzu.      Alhaji Audi ƙaura ne na huɗu bayan mai-martaba kakansa, saboda shawarar da god father ɗinsa ya bashi na kiran Ramadhan ya tayasa murna. dan shine babban abokin hammaya dake bi masa a ƙuri'a, ido zai fi yawa a kansa fiye da sauran ƴan takarar.     Hakan kuwa akai, ya kira Ramadhan ya tayasa murna. Ramadhan dake kwance a doguwar kujera ya ɗora kansa bisa cinyar Anne an lulluɓesa da bargo saboda sanyi da yace yanaji ya amsa masa cikin muryar dake nuna rauninsa a yanzun. Duk da halin da yake a ciki ya cigaba da amsa kiraye-kirayen waya har sallar magrib, koda aka idar ma bai huta ba. Dan duk da zazzaɓi daya rufesa har kusan sha biyun dare yana amsa wayoyin taya murna daga sassa daban daban na duniya.     Abokai, yan uwa. Da iyaye, ƴan siyasa da shugabanin gargajiya. Wasuma bai sansu ba sai a yau.       Duk yanda Ramadhan dai yaso samun nutsuwa a ranar bata samu ba. Hasalima da zazzaɓi ya kwana da ciwon kai mai tsanani. Da safe har sai da doctor yazo ya duba shi. Duk da halin da yake ciki dole ya cigaba da amsa kiraye-kirayen taya murna a wannan yinin ma.. ********      Kwanaki huɗu bayan faɗar sakamakon zaɓe ƙura ta lafa, sai shirye-shiryen zaɓen gwamnoni kuma da akeyi ta ko ina. Dan tsakaninsa dana shugaban ƙasa sati biyu ne. A kuma wannan tsakanin su Bappi suka sake zuwa Hutawa aka tsaida ranar ɗaurin auren Ramadhan da Raudha. Suka kuma ajiye komai har sadaki.         Mal. dauda baki har kunne ya zama surikin shugaban ƙasa. Dama tunda ya dawo da ƴan kuɗaɗensa sai ya zaɓi dawa zaiyi magana yanzun. An bige gidansa ana sabon gini, gefe kuma yana neman aure batare da sanin su baba Nafi ba. Dan Larai anata hura hanci sune da gida yanzu, duk da ta shiga ɗunbin baƙin cikin jin daga inda tushen kuɗin suka fito. Sai dai abinda malaminta ya faɗa mata game da watsa auren na Raudha da Ramadhan yasata shiga walwala ta maida komai ba komai ba. Yanzu sakamako kawai take jira na fasuwar auren a haukarta (😹😹).        *____________★_____________*     SANNU-SANNU bata hana zuwa, a na gobe zaɓen gomnoni aka maida auren Alhaji yaro glass da aunty Hannah. Duk da ba wani taro sukaiba aure kawai aka ɗaura ƙawayen aunty Hannah sun ɗan haɗu a gidan, ciki kuwa harda first lady. Wadda a ranar kowa ya sake tabbatar da alaƙarta da Aunty Hannah ɗin. Su Asabe ma dai nan gidan sukazo suka kwana, hakan yasa Raudha da mominta samun damar keɓewa da ƴan uwanta. Kuka ta dinga rusa musu akan wlhy bata son auren nan dan mutanen nan sunfi ƙarfinta. Duk da wasu sun nuna soyayyarsu gareta wasu ƙuru-ƙuru a ƙannensa da wata babbar mace da take ƙyautata zaton mahaifiyarsa ce saboda kamanni da suke ɗanyi suka nuna mata tsana da gargaɗi. Nan dai duk ta basu labarin abinda ya faru ranar zaɓen shugaban ƙasa.      Hankalin Asabe ya tashi, ta shiga yima Raudha faɗa akan miyasa ta amsa a wancan karon, dama irin wannan take guje mata tun farko. Maba danginsa ba ko shi bata ƙyautata zaton zai so ta. Mutumin da tun yana ciki ake ajiye masa kuɗi a asusun banki, ya girma yasamu ingantaccen ilimi, babu kalar ƙasar da bai zagaba yaga mata ƙyawawa ƴaƴan manya irinsa, amma tai tunanin zai iya dubanta matsayin mace. Kawai dai kakansa ke son wannan haɗin saboda alkairin datai musu.        Lallashinta su Fatisa suka dingayi da bata baki harma da shawarwari, dan harga ALLAH suma suna son ƴar uwar tasu ta auri shugaban ƙasa. Koba komai zasu fantama matsayin yayyen matar shugaban ƙasa. Zasu huce gajiyar wahalar da sukasha a hutawa a baya.        Sosai Asabe ta kasa zaune ta kasa tsaye, ji take kamar ta gudu da ƴaƴanta daga Bingo. Dama tasan idon Gwaggo idan yaranta sai wanu abu ya biyo baya. Dama wannan taita fargaba tun farko. Tunanin inda zataje da su ne ya sakata sake shiga damuwa. Har aka ɗaura auren aunty Hannah bata da wata walwala. Kowa tunaninsa aunty Hannah zata tare ne acan gidan Alhaji yaro kamar auren farko, sai sukaji saɓanin haka wai anan zata cigaba da zama tukunna. Hankalin Asabe ya sake tashi, dan tasan kuma babu danar sace Raudha kenan.        A ranar dai ko leƙe ango bai leƙo gidan ba, washe gari akai zaɓen gwamnoni. Wannan karon babu inda Raudha taje, hasalima wuni tai murƙususun ciwon mara har sai da suka dangane da asibiti. A asibitin ta kwana, washe gari suka dawo gida. Haka kwanakin suka cigaba da shuɗawa batare da Raudha ta ko sake jin labarin wani Ramadhan ba sai a tv kawai idan an ambaci sunansa ko an nunasa. Sannan Asabe ta kasa samo mafita game da auren na Raudha. Sai da auren aunty Hannah da Alhaji yaro ya cika wata guda cif suka fara ganinsa a gidan. Dan zuwa yanzu an kammala duk wasu zaɓuka sai jiran rantsarwa kuma. A ranar gyaran da ma'aikatan sukaima gidan ma na musamman ne, bai isoba kuma sai wajen tara na dare.       Raudha ta haɗo kan su Yasmin sukazo suka gaishesa. Baki ya saki da hanci yana kallon Raudha ɗin yana haɗiyar yawu. Dan harga ALLAH baisan haka yarinyar take ba. Bai taɓa ganinta ba sai a hoto, sai dai kuma a yanzu canji waje data samu ya sake fiddo mata da ƙyawunta da cikar budurci. Dan tana akan shekarunta ne na girma.      Harga ALLAH Raudha ta tsargu da kallon da tsohon ke mata, dan haka ta shiga ambaton sunayen ALLAH da jifansa da addu'oi. Tunda ta samu ta gudu ɗaki kuwa bata sake leƙo waje ba harda safe. Tanaji Yasmin tazo tana tashinta wai tazo a karya inji sabon Abba tai mata banza. Dole ta koma tace barci take.       Har Alhaji Yaro yace Yasmin ta koma ta tasota Aunty Hannah ta hana cikin kissa. Acewarta a barta tai barcin batajin daɗi, kuma anjima sunada wani trianing akan Raudhan. Badan yasoba dole ya haƙura, sai dai a ransa yana fatan ALLAH yasa kafin yabar gidan ta fito. Sai kuma akai rashin sa'a addu'arsa bata karɓu ba harya fitan batako leƙo waje ba.........✍       *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _A AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account. *Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks. *Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku. A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant). -------- Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar: *Bank Transfer* *Airtime Transfer* Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance. *Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks. _Account No_ - *1220077999* _Account Name_ - *Arewa Books Publishers* _Bank_ - *Zenith Bank* Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din: Amount Paid: - Nawa aka tura? Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa Transferred time: - lokacin da aka turo Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi Deposit date: - ranar da aka turo Sai ayi SUBMIT. *Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar: MTN, 9Mobile Glo Airtel Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance. *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/10, 7:47 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 23_* ............A ɓangaren Ramadhan kam yama manta da wani batun aurensa balle Raudha. Harkokin gabansa kawai yakeyi na shirye-shiryen rantsarwa da zaman meeting-meeting da suke yawanyi da ƴan jam'iyya a gidan gwamnati. Shi kansa ma haushi meeting ɗin ke basa a mafi yawan lokaci, dan wasu yakan rasa gane kansu balle inda suka dosa. Sai dai yana nutsuwa dai wajen maida kansa yaron da suke kallonsa yana karantar komai da nanufofinsu.      Sai dai abinda Ramadhan bai sani ba a garesa ne kawai ya manta da abatun aure, ga jama'ar gidansu da masu so da masu ƙi duk abin na ransu. Domin shiri su Anne keyi na musamman akan auren, lefe ya kammala haɗuwa tsaf, hakama abubuwan da duk za'a buƙata ga taron biki.           A ɓangaren su gimbiya Su'adah ma dai suna nan akan bakansu na hana tabbatar wannan aure, sai dai kuma tun randa Pa ya ritsata tana waya da Asma yaji kuma mi suke faɗa yaja mata dogon gargaɗi, tare da alwashin inhar wata matsala ta shigo a auren nan ta shirya amsar matsala a nata auren itama. Wannan ne ya tada mata hankali ya kuma ja mata birki, sai ta koma zungurin Ramadhan akan auren. Sai dai kuma rashin zamansa a gidan ya taimakesa da masifarta.     A yanzun kullum cikin ƙulla yanda zasuci uban Raudha suke inhar ya tabbata sai anyi auren. Tare da ɗaukar alwashin aurama Ramadhan Aina'u koda daga baya ne.      A hutawa ma dai Mal. Dauda ya shirya tsaf, dan gyara na haƙiƙa yayma gidansa tamkar bashi ba. Ya baza ɗinkuna yayma kuma kowa na gidan. A yanzu haka Innarsa da ƙaninsa da iyalinsa suma sun dawo nan gidan da zama. Hakan yasa Larai ta rasa kataɓus dan Inna cin uban surukai take babu ɗaga ƙafa. Balle ma yanzun da take ganin ɗanta yay arziƙi, ai koda wasa babu wanda ya isa zagin Asabe a gabanta duk da bata nan. Takance Asabe ai farar uwa ce tunda gashi sanadin ta haifi Raudha suna hutawa. Takanji takaicin saki ukun da ta saka Mal. Dauda yay ma Asabe a yanzun. Inama ɗaya ne ko biyu da yanzu sai ta dawo abinta.         To anan ma dai shirinsu suke tsaf duk da babu amarya har anko an fitar ma.        *_SATIN BIKI_*   Shiga satin biki ya saka ango da amarya dawowa cikin hankalinsu. Dan kuwa sun tabbatar yanzu kam da gaske ake ƙwarai. Ta ko ina sanar da wannan ɗaurin aure ake a kafafen yaɗa labarai dana yanar gizo, yayinda wasu baƙi dake ƙasashen ƙetare suka fara sauka ciki harda su Sultana daba taron bikinne ya kawotaba kai tsaye. Dan tunda akace Ramadhan ya fito takarar shugabancin ƙasar NAYA take son zuwa, sai kuma ga batun aurensa da yay matuƙar tada hankalinta har takaita da kwanciya asibiti. Halin data shiga yasa Babanta yarda su Mufeed suzo da ita taga Ramadhan ɗin.      Sai dai kuma tun jiya suka iso amma ganin Ramadhan yay musu wahala saboda yana can suna shirye-shiryen zancen rantsarwa. Za'a ɗaura auren ne juma'a, asabar ayi rantsuwa, lahadi su tare gidan gwamnati tilitin shugaban ƙasa ya fara shiga office. ______      Ga amarya kam itama ta yarda dai auren nan babu fashi, tunda aka shiga satin bikin aka sake ninka yanayin gyaran jikinta da akeyi, tayi ƙoƙarin toshe duk wata hanya bata sake haɗuwa da Alhaji yaro glass ba duk da yana yawan zuwa gidan yanzun. Ana saura kwanaki biyu ɗaurin aure daren da washe gari za'a maidata Hutawa kusan sha biyu yunwa ta addabeta, dan duk yinin yau bataci wani abincin kirki ba saboda damuwa. Bata son auren nan ko ɗigo a ranta, gefe ga tsoro da fargabar tsantsar ƙiyayyarta data hanga a cikin idon Gimbiya Su'adah da wasu a ƙannen mijin nata. Jin har kamar zuciyarta na tashi dan yunwa ya sata fito da nufin zuwa kitchen ko tea ta haɗa.      Da sauri taja birki jin kamar ana magana ƙasa-ƙasa dai-dai tana ƙoƙarin sanyo ƙafarta a falon, ta ɗan laɓe tana leƙe daga corridor ɗin ɗakunan barcinsu ita da su Yasmin. Aunty Hannah ta hango da wasu mutane uku, babu wanda ta gane a cikinau sai Alhaji Yaro glass kawai. shima dan rabin jikin aunty Hannah nakan nasane. Dan tana zaune kusan a jikinsa ne ko kunyar sauran mutanen bataji. amma sauran ukun babu wanda ta sani.      Jin an ambaci sunanta yasa gabanta faɗuwa. taɗan sake matsowa daf da hanyar fita corridor ɗin ta kasa kunne taji da ƙyau.       Wanda yake a kujerar ƙarshe mai sanye da jallabiya baƙa ya ƙara fuskantar aunty Hannah yana faɗin, “Hannah kinga dai mun matuƙar yarda da ke, dukkan wani shirinmu a yanzu tamkar ya rataya a wuyanki ne. Bama son kuskure ga yarinyar nan, dan idan aka samu kai tsaye ke zamu ɗaurama alhakin hakan”.         Kanta ta jinjina masa tana tashi zaune sosai. “Alhaji Wada karkaji komai, na riga na ɗaura Raudha bisa kowacce irin hanya da bazata iya bijire mana ba. Ku ɗauka tamkar yaron nan ya mutu ya gama a shekara biyun da kuka ɗeba masa. Adai ɗaura auren jibi, da zarar sun tare za'a fara bata maganin tana saka masa a abinci, ko abin sha kamar yanda first lady ta sanar min..”         “Hakan shine dai-dai, dan munaso ya fara masa aiki a hankali yanda ko bayan mutuwarsa za'a ɗauka diabetis ɗinsa ce ba wani ba, tunda dama maganin zai ƙara ƙarfin diabetis ɗinne ya kuma haifar da hawan jini mai ƙarfi. Sannan a yau da safe duk wani poison an sakashi a cikin ac ɗin falonsa da bedroom dan a hankali mukeso ya fara ratsa jininsa shima ta yanda zai zama bashi da wani kuzarin nutsuwa yay aikin ma, dan cikin idon yaron nan ka kalla kasan bazaiyi mutunci ba. Yana gama gane kan mulkin nan mukanmu ba ɗaga mana ƙafa zaiyiba wlhy.”          Alhaji Yaro glass ya karɓe da faɗin, “Ai dama shegene yaron nan, yanda kaga kakansa da taurin kai haka shima yake. Ni gani nakema mizai hana ita Raudha mu fito mata ƙuru-ƙuru akan aikin da muke son tai mana kawai dan yarinyace sai yanda mukai da ita.”       “A'a wannan ganganci ne, idan kuma aka samu akasi ya faɗa sonta fa? Ko kuma itama tana sonsa yanzu haka? Dan yaron nada qualitys ɗin da mata zasu so sa a ƙanƙanin lokaci. Giyar soyayya kuwa zata iya janta ta sanar masa. Kawai muyi yanda muka tsara ayi amfani da ita”.           Cikin zafin rai Mr MM yace, “Idan ma mun sanar matan tace zata tona mana asiri halakata zamuyi itama a banza....”       “Ai ko yanzu ɗin ba tsira zatai ba. Kana tunanin zata dinga shaƙar gubar nan ta cikin ac ta tsallake itama. Yanda zata dinga masa illa a hankali itama hakanne zata kasance. Sai dai akwai wata allura da za'ai mata wadda gubar bazata yi tasiri a jikinta da wuri ba kamar shi”.        A tare duk suka kalli Aunty Hannah bayan sun ɗauke idonsu ga Dr Bonba daya gama bayanin.      Kanta ta kaɗa musu tana watsa hannaye baya. “Miye na kallon nawa?, kun san dai Raudha ɗiyar ƙanwata ce. Duk da kuwa ina son zama first lady bashike nuna bana son abata ba. Nasan bai wuce kuce ya shawarar ta canja ba game da allurar riga kafin guba. Ku zauna kuyi tunani da hankalinku, babu ta yadda za'ai mu bari gubar tai tasiri a jikinsu lokaci guda, dan komai zai fito ne. Amma idan bayan ya shi ya mutu ne itama ta mutu za'a iya cewa zuciyartace ta buga saboda rashinsa itama tabisa”.        “Woow!”. Suka faɗa a tare suna tafawa. Shugaban ƙasa mai sauka yace, “Hannah kinada basira, anya kuwa idan mutumina ya zama shugaban ƙasa bake bazaki koma juya ƙasar ba kuwa?”.         Wata shegiyar dariya tayi tana juya idanu, Alhaji Yaro glass ya sake rungumota jikinsa da manna mata kiss a kumatu. “Inaga shugaban ƙasa biyu kam zakuyi”. Ya faɗa cikin raha. A can ƙasan ransa kuwa yana ayyana ashe kuwa itama zata mutu nan kusa, dan Hannah bata isa shiga masa hanci bai fyatota ba duk da take matarsa.........      Zuwa yanzu sosai hajijiya ke neman yadda Raudha a ƙasa. Tai azamar dafe bango jin zata zube a ƙasa. Laɓɓanta sai faman rawa sukeyi amma sun gagara furta komai, dan ko tace zata furta ɗin batasan mi zata furta ba. Da ƙyar ta cigaba da laluben bango ta koma ɗakinta, batasan a yaya ta zube saman gadon ba harda jan bargo ta lulluɓe, jikinta ya shiga wani irin karkarwa na rawar sanyi         Yanzu ta fahimci ba ahalin Ramadhan bane zasu zama BAƘAR INUWAR ta ba, ba Ramadhan bane BAƘAR INUWAR ta ba, aunty Hannah itace BAƘAR INUWAR ta. Shi kansa Ramadhan sun tittiɗashi ya hau kujerar mulki ne badan ya ni'imtu ba, badan ta zame masa INUWA da irinsu talakawa suke hangen masu mulki na ciki ba. bai san sun kaisa BAƘAR INUWA bane, gara ace a rana yake da shiga cikinta. ta sake fashewa da kuka.        ALLAH sarki talaka. A kullum gani yakeyi shi a RANA YAKE, mai mulki shike cikin Ni'imtacciyar inuwa, ashe baisan da wata BAƘAR INUWAR MUKIN gara ranar da shi yake a ciki ba. Yau gashi saboda mulki yayar mahaifiyarta ta ɗauketa da hannunta ta kaita BAƘAR INUWA. Shiyyasa suka dage ashe, shiyyasa suka hana mahaifiyarta nuna ƙin auren, shiyyasa suka babbake ko ina da ina. Miye mafita? Zata bijirema auren ne ta hanyar guduwa ko zata haƙura ta zauna ta ceci rayuwar wanda a yanzu take kallo da fatan ya zama adalin shugaba madubin al'umma kamar yanda talakawa suka ɗora yaƙininsu a kansa da ƙwarin gwiwarsu?.      A take kanta ya fara sarawa, dan tama rasa kalar tunanin da zatayi saboda ƙarancin shekarunta. Ga wani irin tausayin Ramadhan ɗin da ahalinsa na dirar mata a zuciyarta, dan ta taɓajin cewar kakansa Baba alhaji aka bama takarar shi kuma ya bashi saboda yace bai ra'ayin mulki a shekarunsa. Ashe baisan ya kai jikansa BAƘAR INUWA bane. Tabbas bazata iya fahimtar komaiba a yanzu dole saita san komai, sanin komai kuma bazai yuwu a gareta ba sai ta yarda da auren Ramadhan. Sai dai kuma tana buƙatar shawara wajen na sama da ita, wazata tunkara? Hajiyar birini! (Kai a'a gwaggo sai a hankali ce) Hajiya mama (kai itama a'a duk tafiyar ɗaya ce) Mommynsu! (Ina bazai yuwu ba zata sake tada mata hankali) Su Fatisa! (Ina basu da hankalin da zasu iya fahimtarta ta wani fanin ma gara ita). Take wani irin zazzaɓi mai zafi ya rufeta, sarawar da kanta keyi ya ƙara ƙarfi..        Koda suka wayi gari da safe Raudha babu lafiya aunty Hannah bata kawo komai a ranta ba sai tunanin fargabar aure da akasan kowacce amarya da shi. Tunda sassafe suka nufi can gidan dan yau zasu wuce Hutawa su duka har Hajiyar birni. Su Fatisa kam tun jiya suka wuce harda su Yasmin.          Asabe ce kawai ta damu da ganin halin da ɗiyar tata take ciki. Suko hankalinau nakan kuɗaɗen da aka aiko daga gidan su Ramadhan injisa aba amarya na hidimar biki, sai tarin kayan rabo. Ko irin ɗan faɗa da nasihar da akema amarya babu wanda yay mata a dangin mahaifiyar tata. Sai ita Asaben ce ta jata gefe taita lallashinta da mata nasiha. Tare da ƙarfafa mata gwiwar ta ɗauka Ramadhan shine zaɓin ALLAH a gareta. Maybe shine kuma mafi alkairi. Dan ita kanta tayi addu'a tayi sadaka akan rushewar wannan aure amma babu alamar zai rushe ɗin.       Raudha ta yarda da maganar Mommy takuma ɗauki aniyar haƙuri, dan ita kanta tayi addu'ar sosai akan zaɓin ALLAH game da auren komai kuma bai canja ba, tunda gashi har gobe idan ALLAH ya kaimu ɗaurin aure.        Ƙarfe kusan sha biyu suka bar Bingo zuwa jihar Dillo a ƙaramar jukumar hutawa. Kasancewar lafiyayyar motace kuma drivern yasan aikinsa zuwa huɗu na yamma sun iso. Asabe tayi mamakin yanda aka tarbesu, ga gidan nasu data sani duk ya cinye a baya ya zama wani haɗaɗɗe yanzun. Dan harda su gate aka saka.      Kowa burinsa yaga Raudha matar shugaban ƙasa. Dan haka maƙwafta da ƴan anguwa sukaita tururuwar shigowa ganin amarya. Sai dai kuma ita amarya Raudha ta ɓoyewa ganinsu saboda zazzaɓi dake damunta har yanzu. Abu biyu ke tayar mata hankali. Zancen su Aunty Hannah da tsarin auren nasu daya sha banban dana saura. Babu wani jituwa tsakaninka da ango balle wani maganar biki ma ya shiga. To gaba daya ma sau biyu ta taɓa ganinsa a zahiri, babu kuma wanda wata maganar kirki ta shiga tsakaninsu a ciki.           Duk yanda taso cigaba da zurfafa tunanin nata dole ta haƙura saboda hayaniya da gidan ya ɗauka. Kai kace yau ne ɗaurin aure. Ga dj ya warware kiɗa tun da safe dan su Fatisa suka ɗakkosa tun daga Bingo. Tun kuma a daren jiya aka fara raƙwashewa duk da amarya bata iso ba. Shiko Mal. Dauda dama babu ruwansa, dan shi kansa yana gefe da abokansa yana ɗan rausaya ƙafa saboda yanda kiɗan ke shigarsa tsumin baya na neman motsawa.        Kowa ka gani a cikin farin ciki yake a gidan, ƴan uwa da wandama kalan dangine duk bakuna a washe. Musamman Inna dake nuna cewar yanzu tafi son su Raudha fiye da kowa a duniya. Larai ce kawai take cikin tashin hankali, dan ta koma gidan malaminta yafi sau shurun masaƙi yana cemata ta dai jira ai ba'a ɗaura auren ba ko. Kowace daƙiƙa ta agogo dake matso da lokcin ɗaurin auren na bugawane da bugun zuciyar larai. Duk ta fita hayyacinta tsabar rashin nutsuwar zuciya. A daren jiya har faɗa sukai da Mal. Dauda ya shashaheƙa mata mari da tabbatar mata idan ta ɓata masa farin ciki a taron bikin nan zai yanka mata jan ticket ɗin komawa gidansu dan bazai zauna da mai masa baƙin ciki ba.     Wannan shine dalilin daya sakata kama kanta sai idan ta shiga ɗaki taita haɗiyar zuciya. Baba nafi kam babu ruwanta. ta shige cikin dangin Asabe dana mijinta anata harkokin arziƙi da ita. Hakama ƴaƴanta na ma'auri da wanda basuyi auren ba. Yanda take ɗin yasa Mal. Dauda mata ƙyautar kuɗi masu tsoka wai itama ta tarbi baƙinta.        A daren ranar duk yanda Raudha taso maƙalewa taƙi fita ƙofar gidan inda su Fatisa suka tara ƙawayensu dama wanda ba'a gayyataba hakan bai yuwu ba. Acewarsu yaune sukai taronsu na ƙawaye. Dole aunty Hannah ta matsa mata shiryawa cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar Material a cikin akwati guda da aka kawo mata na kayan fitar biki. dan ba'a kawo lefe ba Ramadhan ya hana. Yace idan an ɗaura zai bata da hanunsa. Su Bappi sun goya masa baya dan auren Amnah ma haka yayi. Shiyyasa aka kawo mata kayan fitar biki kawai da aka ɗinka akwati guda da duk abinda zata buƙata na ado.        Light makeup Feena da suka taho tare saboda kwalliyar amarya tai mata, aka gyara mata dogon gashinta data gada wajen Asabe tare da naɗa mata ɗauri mai ƙyau. Kanta ke matuƙar ciwo ga zafin zazzaɓi amma haka ta daure ta fitan. Nanfa ƙawaye suka shiga mata hotuna duk da dare ne harma da jama'ar gari. Burin kowa ace ga hoton matar shugaban ƙasa a wayarsa ya samu na fafar faɗama wasu yanada alaƙa da ita koda anan gaba idan ganinta ya musu wahala. Wasu ko a take suka shiga watsashi a media dan hannayensu na ƙaiƙayi.       Wajen ya sake ƙawatuwane lokacin da Hajiyar birni tazo ta farke ƴan ɗari biyar-biyar ta hau yima Raudha liƙi. Sai itama aunty Hannah ta farke ƴan dubu-dubu. Sai ga Mal. Dauda ma da kansa ya farke nasa dubu-dubun. Nanfa yaran dj da mutane suka shiga wawaso. Abu kamar wasa sai ya zama gasa akaita shigowa anama Raudha liƙi. Wasu ma ƴar dubu ɗaya ce suke canzowa goma-goma ko biyar-biyar suyi dan dai ace suma sunyi.      Alhmdllhi dai sai ga taron ya zama wani ƴar ƙwarya-ƙwaryar wasa. Amarya ce kawai zuciyarta ke a ƙuntace da damuwar data dameta. Suna mata kallon wadda zata shiga Ni'imtacciyar INUWA basu san BAƘAR INUWA bace, gara ranar da suke ciki ta fita kwanciyar hankali.       Jirin da tace tanaji yasa Hajiya mama maidata cikin gida, aka bata tea da magani tasha ta kwanta. Kasancewar maganin naɗan saka barci aka dace barcin yay awon gaba da ita dan dama akwai bashinsa a kanta. *_WASHE GARI_*          Tunda farar safiya motocin jami'an tsaro kala-kala suka fara shigowa garin Hutawa suna masa zobe. Al'amarin tuni ya fara tsorata masu tsoro suka nutsu a gidajensu. Zuwa ƙarfe sha biyu garin ya fara ɗaukar haramar baƙi. Babu abinda ke danno kai cikin garin sai jibga-jibgan motoci da suka ƙoshi. Kai harda su helicopters. Tuni gidan hakimi daya amshi ɗaurin auren ya cika ya tun batsa da manyan ƙasa dana baƙin ƙetare. Dan babu kalar fatar da bazaka samu ba. Tunkan shugabanci gidansu Ramadhan babban gidane sannne, sai ya zam samun mulkin ya sake haskesu.        Ƙarfe sha biyu da rabi dai-dai tawagar shugabn ƙasa kuma ango *_Ramadhan B. Hameed Taura_* ta dira cikin garin hutawa. Dan tun a daren jiya nasa baƙin ta kowanne ɓangare ke danna kai birnin Bingo, yau kuma suka ɗungumo a motoci zuwa Hutawa, duk da kuwa su Alhaji yaro glass sun so hanashi ya tabbatar musu bazaibi jirgi ba zaizo a mota saboda wani dalilinsa.      Ta ko'ina garin ya sake harmutsewa. yayinda wasu a abokan nasa ke matuƙar mamakin inda Ramadhan ɗin ya ƙwaƙulo matar aure a wannan garin da idan ka ɗauke ɗai-ɗaikun manyan gidaje da lafiyayyen titi babu komai a cikinsa sai hayaniya da tarkacen talakawa (🙄🤗ALLAH mun gode maka daka yimu a talakawa).........✍ *_Sai ku shirya. Dan bai kamata ayi bikin nan babu mu a wajen ba gskiya. Zafafa biyarma duk zasuje. Dan suna nan suna sallar dare shugaban ƙasa Ramadhan ya haɗasu da muƙaman ministoci😹😹👩🏼‍🦯_* *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _A AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account. *Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks. *Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku. A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant). -------- Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar: *Bank Transfer* *Airtime Transfer* Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance. *Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks. _Account No_ - *1220077999* _Account Name_ - *Arewa Books Publishers* _Bank_ - *Zenith Bank* Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din: Amount Paid: - Nawa aka tura? Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa Transferred time: - lokacin da aka turo Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi Deposit date: - ranar da aka turo Sai ayi SUBMIT. *Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar: MTN, 9Mobile Glo Airtel Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance. *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/13, 8:47 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 24_* ............Kusan tare tawagar ango da tasu Bappi ta iso tare da forma president. Sai wasu gwamnoni masu sauka dama wanda sukaci zaɓe. Dama wasu tuni sun iso, dan a kaf jihohin ƙasar NAYA arba'in da ɗaya babu gwamnan da baizo ɗaurin auren nan ba da sarakunan gargajiya. Sai waɗanda lalura ta hana kuwa, suma sun bada wakilai. Hakama masu ƙananun muƙamai irin members na majalisa dama na jihohi da cabinets na tsohon shugaban ƙasa dana gwamnoni, attajirai da manyan malamai, kai harma da jama'ar gari da aba'a gayyata ba. Dan a cewarsu dole suzo su kashe kwarkwatar ido, ɗurin auren shugaban ƙasa guda ba wasa ba.        Tsabar cikar da garin yayi sallar juma'a wasu har akan tituna, motoci kam har an rasa wajen fakin. Badan jami'an tsaro dake zagaye da garin ba ma da ba'asan yaya zata kaya ba.      Ango yayi shar cikin wata muguwar ɗanyar shadda da zaman neman addin kuɗin da aka sayeta ma ɓata lokacine. Takalma da agogon hanunsa zuwa hula kuwa dole a kirasu na musamman. Yayi fayau dashi saboda ƴar ramar campaign da har yanzu bai gama cikowa ba.. Ga gyaran fuskar da ya sha da tsagar kan gashin girarsa na tabon ciwo sun sake ƙawata fuskar tashi. Ƙamshi yake na musamman, ga securitys zagaye da shi, kai kace zasu iya karesa daga cika aiken mala'ikan mutuwa ne (😕🤕).       A kusa da kakansa Bappi yay salla a sahun farko, ɗayan gefen haggunsa Mal. Dauda ne hakimi a gefensa. Sai can ɓangaren shugaban ƙasa mai sauka tare da mai-martaba da sarkin Dillo. A yau sarkin musulmi ne ya jagoranci sallar juma'a. Bayan idar da salla aka gudanar da ɗaurin aure kamar yanda shari'a ta yarda. Jikin Mal. Dauda sai rawa yake, dan harga ALLAH a firgice yake ganinsa tsakkiyar manyan mutane da bai taɓa tunani gani ba koda a mafarki. Daya sani ya bari ƙanin nasa ya karɓi auren kamar yanda Inna tace. Amma sai ya bijire dan kar wasu su zata ba shine mahifin Raudha ba. Ko wani yayima Sabilun alkairi saɓanin shi daya cancanta.       A hankali shugaban ƙasa Ramadhan ya lumshe idanunsa lokacin da ake sanar da ƙulluwar auren nasa kamar haka. *_(Alƙawarin ALLAH ya cika. Domin kuwa Aminatu Dauda Haladu ta zama mata ga Ramadhan B. Hameed Taura. akan sadaki mai daraja. ALLAH ya bada zaman lafiya da zuri'a mai albarka)_*.       Annan take waje ya ɗauki gungunin faɗin amin, yayinda irin su Alhaji Yaro glass ke faɗin (Ba amin ba) a zukatansu. Gefe kuma daga can wajen masallaci aka shiga busa algaitu daga sarakuna domin girmamawa ga shugaban ƙasa. Yayinda maroƙa suka shiga kirari da yabo ga ango kuma shugaban ƙasar NAYA.        Wani irin iska ce mai shiga jiki da sanyi tamkar na tsakkiyar hunturu suka shiga ratsa Ramadhan batare da yasan dalili ba. Tabbas bayajin sonta, yayi biyayya ne kawai ga iyayensa. Shiyyasa ya rasa dalilin yanayin daya shiga a yanzun. Dan lokacin aurensa da Amnah tsintar kansa yay kawai da zumuɗin ganinta a lokacin da aka shafa fatihan aurensu. Saɓanin yanzu da yake jin tamkar an sake aza masa wani nauyine bisa kansa bayan wanda yake ɗauke da shi. Ya shiga sauke ajiyar zuciya a hankali lokacin da Bappi ya rungumesa yana musu addu'ar zaman lafiya da fatan alkairi. ★★★      A can gidan su Raudha ma taƙe yake da mutane har wani baya iya jin zancen wani. Amarya na maƙure jikin Asabe dan zazzaɓi ne mai zafi a jikinta har amai tayi ɗazun saboda takura mata taci abinci da Hajiyar birni tayi. Kwalliya kam sai da hajiyar birnin da Aunty Hannun sukai tamkar zasu halakata dan bala'i sannan ta amince akai mata.      Cikin ƙanƙanin lokaci ta fito tamkar tauraruwa cikin taurari. Tayi ƙyau harta gaji, musamman da sarƙan gold ɗin wuyanta tai mata wani irin masifar ƙyau da haska fatarta. Duk yanda akaso ta fita tsakar gida ƙi tayi, dan har aka fara guɗe-guɗe a cikin gidan na jin an ɗaura auren bata leƙo ba, sai ma fashewa da tai da kuka mai ban tausayi, dan tasan tata ta kare. Wannan auren tamkar mabuɗin buɗe hanyartane na zuwa lahira ita da wanda ta aura ɗin.      Tana daga kwance tanajin labarin taron mutanen da aka tara wajen ɗaurin auren nata. Sai taji komai ya kuma kwance mata a ƙwaƙwalwa. ★★★        An kammala ɗaura aure mutane suka fara kama gabansu. Wasu garuruwansu suke komawa, wasu Bingo. Kafin la'asar sai yazam tsirarun mutane suka rage sai tulin jami'an tsaro. Shi kansa angon ana idar da sallar la'asar jirgin helicopter yazo ya ɗaukesa. dan tawagar da yazo da ita ta abokansa da abokan kasuwanci tuni sun kama hanyar Bingo. Ibrahim babban abokinsa tun na ƙuruciya ne kaɗai anan tare da shi. Duk yanda Ibrahim ɗin yaso yaje yaga amarya tare da sauran abokai ayi hotuna Ramadhan bai bada fuska ba. Dole suka haƙura tunda sun san gobe idan ALLAH ya kaimu dole ne su ganta a wajen dinner da kuma rantsarwa ranar lahadi.       Ɗagawar jirgin ango babu jimawa jerrrun motoci  talatin cif suka sake shigowa garin Hutawa. Sai na jami'an tsaro dake biye da su kai kace shugaba ƙasar akazo ɗauka, sai dai kuma ko basuzo ɗaukar shugaban ƙasa ba sunzo ɗaukar mata kuma amaryar shugaban ƙasa. (😜😜 wayaga Mino first lady. Lol)         A yanzun kam ma kukan Raudha ta kasa, dan anan ɗin ma babu wanda ya zaunar da ita yay mata faɗa balle nasihar aure ko lallashinta. Damuwarsu kawai karsu rasa motar zuwa kai amarya. Andai kira Mal. Dauda sunyi sallama. koda yazo shima ɗin sai ya ɓige da matsar ƙwalla yana jaddada mata inhar bata zauna lafiya gidan mijinta ba harya sakota tai masa baƙin cikin wannan NI'IMTACCIYAR INUWAR da ALLAH ya tsundumasa sai ya taine mata. Kuma babu shi babu ita. Ko kasheta kullum Ramadhan zai dingayi ana sake busa mata sabon numfashi baice ta nuna masa damuwarta koda a fuska ba.      Jikin Asabe ya ƙara sanyi da kalaman tsohon mijin nata da ayanzu takema kallon wanda baisan ciwon kansa ba. Yayinda tausayin ɗiyarta ya ƙara mamayeta. Sai dai babu yanda zatayi dan su Hajiyar birni sun hanata kowane irin ƙarfin iko na uwa, komai sun mamaye.        Zuwa ƙarfe biyar da wasu mintuna kowacce mota ta ɗauki iya adadin mutanen da zata iya. Yayinda suka fita cikin garin Hutawa a jere motar amarya a tsakkiya. Gaba da baya jami'an tsaro ne.       Wani irin sarƙewa numfashin Raudha ya shigayi alamar Asthma ɗinta zai tashi, dan kuka. ALLAH yasa Hajiya mama dake a motar tai saurin fahimta taja hand bag ɗin Raudha da sauri tana laluben inhaler ta. Da ƙyar ta samota aka shaƙama Raudhan. Sai da numfashinta ya dai-daita suka shiga sauke ajiyar zuciya ita da Hajiya Zuhrah dake tamkar ƙanwa ga Pa. uwa ga su Ramadhan. Dan kuwa Yafendo ce ta haifeta. Itace babbar ɗiyarta, sai dai tana Australia tare da mijinta dake matsayin ambasada a can. A yanzu ma biki ne da bikin rantsar da Ramadhan ya kawosu ƙasar. Komi na kammala kuma zasu juya.         Tuni tausayin Raudha ya sake mamayeta, dan tunda ta ganta ƴar ƙarama take mamakin yanda iyayenta suka amince suka mata aure (kusan su irin manyan nan wayayyu ƴaƴan sai sunci boko sun ƙoshi, wani lokacin ma ba bokon ke hanasu yin auren ba, ra'ayine kawai da tunanin za'a yanke musu jin daɗin rayuwar ƴammatanci ko samartaka. Shiyyasa suke ganin masu aurar da yara 17years zuwa 20 tamkar ganganci sukai🤧). *_______________________*        *_BINGO CITY_*   Kamar yanda aka nuna ɗaurin auren shugaban ƙasa Ramadhan live a gidajen tv haka aka nuna tahowar amarya da isowarta bingo ma. Inda duk da ɗunbin mutanen nan dake cike da Taura house da wanda sukayo ma amarya rakiya hakan bai hana Anne da ke fama da tsufanta ba fitowa tarbar amarya ita da su yafendo. Fulani na zaune tare da su suka fito amma batako motsa ba. Dan tona irin baƙin cikin da suke ciki game da auren nan ita da Asmah da gimbiya Su'adah ɓata lokacine. Abinda kawai suka sani shine sun tanadama Raudha bama-baman bala'in da sai ta gudu gidansu da ƙafafunta. Dan shi kansa Ramadhan ɗin jiya ya sha masifarsu saboda yace suyi haƙuri shi bazai iya bijirema Pa da Bappi akan maganar auren nan ba.     Aiko sukai masa ca gimbiya Su'adah harda kuka wai Anne ta asirce mata shi bayajin maganarta baijin ta mahaifiyarta da ƴan uwanta. Shi dai bai sake ce musu komai ba, da ga ƙarshe ma kiran wayarsa da akaine tai bailing sa ya samu ya gudu musu. Har zuwa yanzu kuma basu sake ganinsa ba, dan koda ya baro Hutawa kai tsaye wajen meeting ɗin da zasuyi da shugabannin jam'iyya na jihohi ya wuce.        Sosai ahalin Raudha sunji daɗin tarbar da akai musu. Tun daga kan shimfiɗar fuska har zuwa ta wajen zama da abinci dana sha koma Alhmdllhi. Mafi yawancinsu kuma ba ƙaramin rikicewa sukai da ƙaton mansion ɗin na Taura ba. Har takai wasunsu ma sun gagara bakin magana.        Babu wani event a yau, dan Bappi ba mai son yawan bidi'oi bane, shiyyasa da wahala kaga anyi taron biki a gidan ana wannan events ɗin na almubazaranci da dukiya, komai yana tafiyane gwargwado, sai abinda ya zama wajibi kamar abinci wannan kam har sai kaci nama ka gaji duk haɗamarka da zura...😜 WASHE GARI ma babu wanda yaga idon ango har kusan azhur, dan jiya bai dawo gidan ba sai kusan 3am. Hakan ya sakashi maƙalewa a part ɗinsa yaki fitowa. Ko sallar asuba a gida yayi saboda makara da yay. Masu kiɗan ƙwarya sunyi wasa daga safe zuwa azhar ɗin anan cikin gida. Abin kuma ya ƙayatar da mutane dan kowa yayi farin ciki. Inda amarya tasha ƙyau harta gaji. Dan nasiha da lallashin da Anne tai mata a daren jiya yasaka mata nutsuwa ta daure tabar kuka kasancewar a ɗakin Anne ta kwana tare da ita. Takoji daɗin kasancewa da tsohuwar, tare da ƙarajin ƙaunarta a zuciya da ɓargo.      Ansha ɗinkuna an kuma sha liƙi, abun mamaki harda gimbiya Su'adah da Adda Asmah a masu liƙi, dan Fulani ce ta basu shawarar suma suje suyi tunda su Hajiya Mufida sunyi. Karta yarda kishiyoyi su fita nuna iyayi ga auren ɗanta. Irin wannan sakacin tayi tun farko har Anne ta mallake mata shi a matsayinta na kaka.           Adda Asmah ta rungume Raudha da kanta ke a ƙasa bayan ta gama mata ruwan ƴan dubu-dubu. “Kinci nasarar shigowa cikin zuri'ar Taura ƴar *_KARUWAI_*”.      A bala'in firgice da rawar jiki Raudha taso janye jikinta. Sai dai Adda Asma ta sake matse a cikin nata jikin kasancewarta mace mai ƙiba. A kausashe ta cigaba da faɗin, “Sai dai hakan ba shike nuna Ni'imtacciyar inuwar da kike kwaɗayi keda Karuwan danginki bace kika shigo.....”     Ta saketa tana miƙewa tsaye da ƙyau, ƙasa Raudha tai da kanta jikinta na wani irin rawar tashin hankali. Adda Asmah ta saka hannunta dake cike da zabban gold da bangles ta ɗago haɓar Raudha. Idanunta ta tura cikin na Raudha da ƙarfin tsiya tana murmushi, wanda ya gansu daga nesa sai ya ɗauka wani maganar alkairi da yaba Raudha take. A kausashe da salon murmushin makircin tace, *_“BAƘAR INUWA_* ce da gwara ranar da kika baro da ita yarinya”.      Ta ƙare maganar da sakin fuskar Raudhan ta sake rungumeta sannan ta saketa. Ko tari gimbiya Su'adah batai ba. Sai dai fuskarta da ɗan murmushin ƙasaita. Kowa yasan halinta na girman kai shiyyasa babu wanda ya damu da yanayin nata, dan likin ma data fito taima amarya ya bama wasu mamaki. A haka dai taron ya tashi ƙwaƙwalwar Raudha a harmutse a kuma cushe. Dan tun kalaman Adda Asmah sai kawai ta koma ambaton sunayen ALLAH dan shine kawai zai iya zame mata mafita a zuciyarta yanzun.         Tana ɗakin Anne bayan ta idar da salla Fatisa da Fatima zaune kusa da ita suna magana take jiyo ƴar hayaniya ambaton sunan shugaban ƙasa dake amsa sunan mijinta a yanzun. Idanunta ta ɗan rumtse a hankali tana jan numfashinta zuwa tsakkiyar ƙirji. Buɗe ƙofar ɗakin na Anne da shigowar mayen ƙamshin turarensa cikin hancinta ya sata saurin buɗe ido. Ƙirjinta ya ɗan harba saboda haɗa ido da sukai, dan tuni su Fatisa sun miƙe daga kusa da ita suna gaishe shi. A taƙaice ya amsa musu yana janye idonsa akan wadda har yanzu bama gama tantance kamanin nata yay ba. Indama ace su Fatima kama suke da ita to da wahala ya iya ganeta a yanda ya shigo ya samesu.         Tuni Raudha ta janye idanunta tai ƙasa da kai, sai dai jin fitar su Fatisa a ɗakin yasa taji kamar ta miƙe ta zura da gudu ta bisu su fita tare.         “I..ina y..yini”. Ta faɗa cikin rawar harshe da in'inar da batasan daga ina ta samota ba lokacin da take jin tamkar takunsa na kusantota, duk da kuwa akwai lallausan Turkey carpet da ƙamshin daya yake fitarwa ma na musamman ne tamkar ba ɗakin tsohuwa ba.      “Assalamu alaikum”. Muryar Anne da buɗe ƙofar suka katse sauraren Raudha da ga jiran amsa gaisuwarta gareshi. A hankali ta saki numfashin data riƙe a tsakkiyar ƙirjinta tamkar mai jiran ace ar ta haɗiye abinta cikin ciki.      Shugaban ƙasa Ramadhan dake ƙoƙarin ƙarasawa saman ɗaya daga kujera biyun dake a bedroom ɗin na Anne ya kai zaune yana amsa mata sallamarta. Yayi matuƙar ƙyau cikin shadda ash color data wadatu da jiƙaƙen ɗinki da ƙyawun surar da ALLAH yay masa. Da gani basai an faɗaba maiƙonta kawai ya isa amsa ga mai hasashen kuɗinta.         “Wai sai yanzu ake ganinka a gidan nan Ramadhan?”.   Anne ta faɗa tana kaiwa zaune bakin gado gab da Raudha dake a ƙasan carpet. Dan ko Anne tace ta hau gadon bata iyawa saboda kunya.        Ɗan murmushin daya tsaya masa iya kumatu yayi yana duban tsadadden agogonsa _Breitling_ dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa Silver. “Anne barci ne naji zai halakani shiyyasa na kulle kaina kawai”. Ya faɗa cikin muryarsa mai faɗi da kauri. Sai dai a hankali yake maganar tamkar baya so.          “To ALLAH dai ya rabamu dayin ragon shugaban ƙasa anan, Aminatu sai kin dage da addu'a kam”.      Yanzun ma gajeren murmushi kawai yayi, sai dai ambaton sunan Raudha da tayi ya sakashi ɗan dubanta ya ɗauke ido. A ransa ko rayawa yake (a haka dai tamkar mutuniyar kirki, sanin gaskiyar al'amarinta sai ALLAH). Dan shi tozali kawai da yay da Mal. Dauda jiya ya sake gaskata maganar su Maa.        “Abinci fa?”. Anne ta katse masa tunani. Agogon nasa ya sake kallo yana ɗan furzar da iska. “Idan da fura kawai a bani ya isa Anne”.         “Fura kam tayi kaɗan ga wanda baiko karya ba. Banajin ma kaci wani abu daren jiya”.       “To Anne ya zanyi”. Ya faɗa a yanayin nuna rauni kamar na shagwaɓa. Kasa daurewa Raudha tayi sai da ta saci kallonsa. A ranta tana faɗin (humm). Oho baima san tanayi ba. Dan telephone dake kan table Anne tai amfani da ita wajen sakawa a kawo masa abinci. Babu jimawa kuwa ɗaya daga cikin amintacciyar ma'aikaciyar gidan ta kawo masu damammiyar fura datasha haɗi da gasashen naman rago mai romo, sai shawarma.           Babu ko jin nauyin Raudha dake zaune ya zare agogo ya gyara zama. Anne ta duba Raudha da keta wasa da zoben hanunta cikin kulawa. “Aminatu kema ai ba abincin kikaci ba, tashi kije kuci ko ƙyaji ƙarfi”.       Da sauri Raudha ta girgiza kanta. A ranta tana faɗin (tab ɗi ni zanci abinci da shi?) a fili kam sai tai saurin faɗin, “Anne na ƙoshi wlhy”.      Lallaɓata da lallashinta Anne ta shigayi amma ta dage ta ƙoshi, harda ƴar ƙwallarta da taso bama Anne dariya ma.       Duk da a kunnensa suke duk zantukan nasu ko nuna alamar yama san sunayi baiyi ba. Furarsa da nama yaketa ci a nutse hankali kwance. Hakan yasa Anne taɓe baki tana dubansa, cikin ɗan tsokana tace, “Da yake mai abincin ma marowacine Aminatu ai kinga yayi shiru dan kar aci”.       Yasan da shi take, dan haka ya ɗago idanu yakalli Annen. Cikin yamutsa fuska yace, “Kai Anne, kunzo kunce zakuci ne na hana?”.        “Ko bakace ba ai baka nuna alamar kana so aci ba”.      Murmushi kawai ya ɗanyi ya cigaba da cin abincinsa batare daya ƙara magana ba. Yan kammalawa kuma bai ƙara ko mintuna uku ba ya miƙe wai zaije su Ibrahim na jiransa a masaukinsu. Dan in baije yanzu ɗin ba da wahala ya sake samun dama. Bai kamata kuma ace sunzo dan shi ba amma yay musu wahalar gani duk da sun san yanzu da da akwai banbanci tunda shiɗin sunan shugaban ƙasa yake amsawa.        Addu'ar dawowa lafiya Anne tai masa, hakan yasa itama Raudha a hankali ta furta ALLAH ya tsare batare da tayi tunanin shi da Annen zasu jita ba. Sai dai kuma amsawar da Anne tai da “Amin ya rabbi Aminatu” ya sata fahimtar tajita. Shiko bata tunanin ya amsa harya fice abinsa.........✍ *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09 Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/14, 1:17 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 25_* ..........*_8:15pm_*        Gagarumar dinner ɗin da su Alhaji yaro glass da Shugaban ƙasa mai sauka suka shiryama su Ramadhan ɗin ta fara gudana. Ƴaƴan manya ne da manyan ƙasar kansu kawai kake gani a wajen. Amarya da ango sunsha ƙyau har sun gaji. Dan zaman bayyana ƙawatuwar shigarsu da docration na wajen ma ɓata lokacine. Anci ansha daga kayan daɗi kamar babu gobe. Yayinda ango ya hana amarya tashi daga inda suke zaune ko sau ɗaya. Dan haka wanda sukai musu liƙi ma anan suka iskesu wajen zamansu sukayi. Cake ma nan aka kawo musu suka yanka a zaunen basu tashi ba. Humm sabon salo kenan wai rawa agaɓar gacci. Dan kuwa ƴan jarida da masu jiran ayi suce tuni sun sami abin faɗa.      Sai faman cece kuce suke na cewar wai mi Ramadhan ɗin ke ɓoyewane da ya hana a ga matar tasa yanda ya kamata. Dan kuwa duk da kwalliyar da taci yau fuskarta sanye take da facemask, kuma shine da kansa ya sanya mata sanda suke tahowa a mota. Ita kanta ta kasa fahimtar minene dalilinsa na son ɓoye mata fuska a duk sanda suka haɗu? Shin *_BABU SO! MIYA KAWO KISHI?!_* (Wannan littafi na nan tafe a gareku ba babu so miya kawo kishi? Insha ALLAH😉🤗😄). Bata da mai bata amsa dan haka ta haɗiye a ranta.         Ƙarfe sha biyu dai-dai aka tashi, bayan mawaƙa kala-kala sun baje basirarsu tunda daga kan na hausa har zuwa na turanci. Hakama masu wasan barkwanci. Kamar sanda suka taho yanzu ma sun koma gidane bisa tsaron na musamman daga jami'ai. Kamar kuma ko yaushe har suka iso ɗin ko kallo bai haɗasu ba ita da shi balle magana. Yay mata rakkiya har ɗakin Anne da basu riga sun iso ba su yay wucewarsa nasa part ɗin ya barta da sakin numfarfashin data tara a ƙirji. Duk da ko sau ɗaya bai wani taɓata ba, dan ko hannunta bai riƙeba a wajen dinner ɗin ƙamshin turarensu ya cakuɗe dana juna har baka iya banbance wanda take yi saboda ƙarfin nasa, ta kwanta lamo a gefen gadon Anne batare data iya cire ko zobe a yatsanta ba. Batasan mi zatai tunani ba a yanzu, girman mijin nata a mulki, ko auren nasu da baida alƙibilar kwatantawa?. Rabuwa da iyayenta ko shiga BAƘAR INUWAR da su suke hasashen Ni'imtacciyar inuwa ce a gareta?. Manufar su aunty Hannah a kan kashe su, ko tsananin ƙiyayya da ƙyamar da take hange a idon uwar mijinta da sai a yau wajen dinner tasan matsayinta na mahaifiya ga Ramadhan ɗin?. *_“Ya ALLAH kaji tausayina. Nayi tawassali da sunayenka ƙyawawa masu tsarki. Da kai na dogara dan bani da kowa sai kai ɗin tun farkon fari. ALLAH ka ƙyautata ni'imarka garemu a ƙarƙashin wannan BAƘAR INUWA da kowa kema kallon Ni'imtacciyar inuwa a garemu.”_*     Hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanunta zuwa kumatunta har saman facemask ɗin fuskarta da ta gagara cire koda shi ne. A wannan yanayin gidan ya fara ɗaukar hayaniyar mutane alamar an dawo dasu gida suma. Dole ta miƙe ta fara zare sarƙa da tarkacen jikinta gudun kar Anne ta zargi wani abu. Duk da kuwa a ranta yanzu hankalinta yafi karkata da kwanciya akan ta tunkari Anne da batun da taji a bakin su Aunty Hannah. Sai dai kuma bata son tozarta yayar mahaifiyar tata dan koba komai bata da kamarsu a duniya, tunda gashi har ana aibantata da halayensu da suka aikata tunkan haihuwarta. ★★★      WASHE GARI aka gudanar da rantauwa ga shugaban ƙasa da gwamnoni. Kum harda Raudha shugaban ƙasa Ramadhan yaje wajen. Sai dai tana cikin dogon farin hijjab da facemask yau ma. Abin ya sake burge jama'a musamman talakawa. Da kuwa idan akai dubi da yanda mafi yawan matan gwamnonin suka cakire cikin shiga ta rashin mutunci da kece raini a yau ɗin. Ga gwalagwalai dake ƙyalli da walwali a jikinsu tako ina. Hatta da Hajiya Fanta da aunty Hannah matan vice president shigar tasu ba'a magana. Sai dai a kallo guda zaka gane ran Hajiya Fanta a ɓace yake saboda kasancewar aunty Hannah a wajen bayan mijin nasu yace mata da ita kaɗai zaije banda Hannah. Dan tunda aka maida aurensa da aunty Hannah suke tafka rigima har yanzu kuma babu daɗi a tsakaninsu, tace sai ya saki aunty Hannah ɗin. Shiko ya tabbatar mata hakan bamai yuwuwa bane dan Hannah nada muhimmanci a tafiyarsa ta yanzun.        Ga ƴan siyasa kuwa sai suka fara takale-takale da zungure-zunguren batun saka facemask da amaryar ta shugaban ƙasa ke yawan yi, dan tunda ya far bayyanata wa duniya ranar zaɓe ba'a taɓa ganin real face nata ba sai da facemask. To yau ma al'amarin yaci uban na da, dan farin siririn gilashi da Raudha ta saka a idonta saboda kumburin da ya ɗanyi na kuka da rashin isashen barci ya ƙara mata wani ƙyau da burge mai kallo. Ga facemask da ya saka ba'a ganin ainahin face nata kuma. Sai haka ya zam ba'a ganin komai nata a waje sai tafukan hanunta kasancewar hijjab ɗin data saka mai hannu ne.     Uban gayyar shima fararen kayane a jikinsa na wani haɗaɗɗen boyal ɗinkin babbar riga. Ya kawo hularsa tangaran data fita a fice ya murza. Bayan kammala Rantsuwa suka wuce wajen bikin da aka shirya gudun mawa da ga Mai-martaba. Ƙarfe biyu aka tashi aka dawo da Raudha kawai gida, shugaban ƙasa Ramadhan kuwa gidan gwamnati aka tafi masa rakkiya. Bayan idar da sallar la'asar aka gabatar da walima da addu'oi daga manyan malamai har zuwa ƙarfe shida na yamma. Daga haka taro ya tashi lafiya kuma zuwa anjima za'aima amarya rakkiya gidan gwamnati insha ALLAH tunda angonta ya tsufa acan.          ★★★_______★★★      An yima amrya shiri na musamman domin miƙata gidan gwamnati da zasu zauna insha ALLAH. Ba wasu mutane masu yawa bane zasuyi rakiyar, dan haka da wuri aka kaita ga gimbiya Su'adah da su Adda Asmah da sauran matan Pa su Hajiya Mufida.        Duk da a lulluɓe fuskar Raudha take da golden color na veil hakan bai hana gimbiya Su'adah jefa mata kallon tsana ba. Da ƙyar ta iya dauriyar cewar “ALLAH ya bada zaman lafiya”. Daga haka ta tsuke bakinta. Sai su Addah Asmah ɗinne keta karaɗin kwarara addu'oi ga amaryar da ango. Abinda gimbiya Su'adah tayi yasa mutane da yawa fara tsarguwa, dan kuwa basuji daɗin yanda ta sallami surukar tata matar ɗanta na farko ba kuma namiji tallin tal.         Raudha da dai ba sanin mi ake ciki tai ba. Dan kanta a duƙe kuma a lulluɓe. Tunda ba wani farin sani tai musu ba bata iya tantance muryoyin da sukai magana ba. Daga part ɗin Gimbiya Su'adah part ɗin Hajiya Shuwa aka nufa da ita. Itako ta mata ƙyaƙyƙyawar addu'a harda ƙyauta da babu wanda yasan minene a cikin dan an riga anyi packaging nashi da leda mai ƙyalli alamar gift. Hakama Hajiya Mufida tarba ta mutuntawa taima amaryar da doguwar addu'ar zama lafiya harda fatan nan da baɗi a sake taron suna. Itama dai tayima amarya ƙyautar cheque na kuɗi da babu wanda yasan adadi tunda a ninke takardar take. Sai wani ɗan box a cikin ƙaramar bag.        Bisa jagorancin Hajiya Mufida aka kai Raudha ga Pa. Inda shima yay masu doguwar addu'a da nasiha ga Raudha tare da ƙyautar key na mota galleliya. Sai sashen su Yafendo inda can ɗin ma tasha addu'oi da kyauta ga dangin su Ramadhan ɗin. Daga haka aka sake maidota wajen Bappi da Anne suka sake musu addu'oi, Bappi ma yay mata ƙyauta a dunƙule wadda babu wanda yasan minene. Hakama Anne, koda yake gara na Anne da alama harda kayan turare dan ƙamshinsu tuni ya addabi hancin kowa. _Sisters turarurrukan *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* daban suke dana saura. Zaka tabbatar da haka ne kawai yayinda ka mallaki naka. Ba turare kawai take saidawa ba. Harda kayan gyara amarya galla-galla na musamman da sai an gwada akan san na ƙwarai. Sirrinsu daban ne, idan nace na daban, ina nufin na daban dana saura😉😘😘🤗_.        Har cikin mota Anne ta kawota, tare da sake musu addu'a domin tuni ango shi ya shiga fadarsa. Amaryarsa kawai yake jira a kai masa.           Har suka iso a tafiyar da bata gaza mintuna a shirin ba saboda jiniya da aka sakama motocin yasa akaita basu hanya, wannan yasa suka iso cikin ƙanƙanin lokaci. Amarya dai bata buɗe ido ba yanzu ma. Sai dai kunnuwanta naji mata yanda ƴan rakiyar tata ke ta yaba wannan katafaren gida first class. Tsirarun ƴan uwanta kuwa da akazo dasu rikicewa sukai. Bataga laifinsu ba, dan masu shiga ƙasashen duniyar ma da kuɗin ƙugunsu sun yaba balle su.        Ita dai babu komai a ranta sai addu'oi, dan zuciyarta sai faman tsinkewa takeyi musam da kalaman su aunty Hannah ke dawowa a cikinta tamkar bitar karatu, sai dai Alhmdllhi mafitar data samu a safiyar yau da matakin data ɗauka tana fatan zuwa yanzu an kauda matsalar farko da takema fargaba kafin masu zuwa. Kamar yanda Anne ta gargaɗeta da yin addu'a haka ta dingayi a duk takun da zatayi har suka iso ainahin cikin babban falon farko na gidan.       Gaban Raudha yay masifar faɗuwa. Tai azamar rumtse idanunta tana ambaton sunayen ALLAH masu tsarki, daga haka bata sake fahimtar komai ba har suka iso inda aka sanar mata falonta. Kamar yanda Hajiya Zuhrah da suka iske gidan suna jiransu ta ambata, ita da ƙanen Ramadhan biyu dake aure Mardiyya da Safina, sai wata cousin ɗin su Pa itama mace mai kirki hajiya Mariya, tun sanda za'ai rakkiyar shugaban ƙasa suka shigo tawaga akai masa rakkiya tare da su.           “Inaga mu barta iya nan kawai, shi mijin nata idan ya shigo da kansa sai ya kaita ɗakin da yaga ya dace su zauna ko?”.     Cewar Hajiya Mariya. A tare su hajiya mama suka nuna gamsuwa. Sai dai aunty Hannah ta taɓe baki dan tasan sun riga da sun zaɓa musu ɗakunan da zasu rayu ta hanyar saka ƙaramin symbol a saman ƙofar bedrooms ɗin ta ciki bisa shirinsu. Dan haka cikin kwantar da murya tai magana tana duban hajiya Mariya da murmushi. “Amma auntyna ayi amarya a falo? Kodai muyi haƙuri a kaita nata bedroom ɗin yazo ya sameta kamar kowacce amarya shima, koba komai zai tabbatar shima a yau ba shugaban ƙasar NAYA kawai yake ba, ango mai amarya fil a ledarta ne”.      Yanda ta ƙare maganr da ɗan shakiyanci ya sakasu sakin dariyar manya. Hajiya Mariya mace mai sauƙin kai da fahimta. tace, “Kumafa kin fini gskiya ƴar uwa, dan gara ya tabbatar da gaske muke yau muke son jika da izinin ALLAH”.      Nan ma dariyar suka sanya, tare da kama Raudha da kanta ke lulluɓe har yanzu, dan sam bama fahimtar zantukan nasu take ba ita kam. Har bedroom ɗin da suka zaɓa mata aka kaita, sai dai kuma an samu akasi ba wanda su aunty Hannah suka tanada dominta bane. Amma batace komaiba, ta barwa ranta zata dawo da kanta tasa Raudha komawa can ɗin cikin sauƙi.       Anan ma dai su Hajiya Mariya Nasiha suka sake mata mai ratsa jiki, kafin su tattara su fito suna mata sai da safe.       Sai a yanzu Raudha ta samu damar rushewa da kuka. Ta zame ta kwanta kan katafaren gadon da tasan ko bata kallaba ya haɗu harya gaji. Ji take inama ba'a haifeta tazo duniya ba, inama Abbansu bai saki momynsu ba har sukazo Bingo. Inama ranar batazo idi ba har ƙaddara ta sakata shiga hurumin Alhaji Hameed Harith Taura. Inama... Inama.... Inama. Sai dai bakin alkalami ya bushe, bushewa irin wadda idan akace sai an tausasashi karyewa kawai zaiyi yabar tawada dabin yatsun hannu.      Kuka taci sosai a wajen har kusan rabawar dare, Ba kuma tako ɗaga mayafin nata ba balle ta kalli wani abu daya shafi ɗakin kamar yanda bata kalli falon da gidan ba sanda zasu shigo, wani wahallen barci da zazzaɓi suka fara fisgarta, duk da kuwa kafin yau tasan tana da burin ganin fadar shugaban ƙasa tamkar kowane ɗan ƙasa. Har lokacin babu angon nata babu alamarsa, ta riga da ta fidda rai da shigowarsa, duk da dama bata sanya ran hakan ba tun farko. Tasan bata kai kodarajar ma'aikatan gidansu ba. Ya amshi aurentane kawai saboda halacci ga kakansa. Bazai sota ba, kamar yanda itama batajin son sa ko kaɗan a ranta. Sai dai tana tausayinsa matsayin shugaban ƙasarta dake cikin wani tarko mai wahalar sha'ani da nazari ga wanda baida yawan maida hankali akan abu. Harga ALLAH tana cikin razanin zantukan su Aunty Hannah har yanzu. Dan ko maganar aunty Hannah taji a kwanaki ukun nan ji take kamar ta saki gudawa a wando saboda razana da mamaki. Yanzu miya kamata tayi a wannan ranar da tasan shugaban ƙasa zai fara kwana a ɗakin da take da tabbacin an haɗa Poison da suka ambata cikin ac ɗin tunda bata da tabbacin saƙonta ya kai ga Bappi zuwa yanzun? Zata fito ta sanar masa ko zata jira taga idan saƙon nata yay nasarar kaiwa, ko yaya zatayi?. Wa zata tunkara da sauran batun ya bata shawara ne? Idan ta samu nasarar daƙile wannan ta poison ɗin ac?. Wane damar yunƙurine da ita a wannan dare na farko a gareta na shiga BAƘAR INUWA tare da shugaban ƙasarta?, idan tayi yinƙurin faɗa masa ya tuhumeta da a ina ta sani wace amsa zata bashi?, idan ta iya faɗa masa komai tanada tabbacin zai yarda ba turotan sukai ba kamar yanda su can yake a garesu zasuyi amfani da ita ne wajen cutar da shi. (“Ki daina yaudararsu, ki kuma tabbatar musu ke *_BAƘAR INUWA ce_*. Idan kikai wasa da gargaɗina ni zan zame miki *_BAƘAR INUWAr_* da sai kin gwammaci *_GARA RANA DA NI!_*) furucinsa a randa ta fara ganinsa a TK special hospital tare da kakansa, cikin halin ciwo take amma ya rumtse ido ya faɗa mata waɗan nan kalaman da tasan sune gaskiyar abinda ke a ransa. Inaga yanzu kuma da take cikin mugun ƙullin da bashi kaɗai ba, mutane da yawa ma idan suka ji bazasu fahimceta ba. Dan kuwa ba kowa ya gama yarda domin ALLAH ta bama dattijo Alhaji Hameed Taura garkuwa ba ranar idi, ciki kuwa harda mijinta, shugaban ƙasarta kuma a yanzun..      Da wannan tunanin barcin yay galaba a kanta.........✍ *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/15, 1:23 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 26_* ............A ɓangaren shugaban ƙasa kuwa yana cikin gidan lokacin da aka kawo Raudha, sai dai yana tare da wasu manyan mutanen ƙasar NAYA da sukazo masa gaisuwar barka da shigowa gidan gwamnati. Daga haka suka cigaba da tattauna wasu abubuwa da suka shafi ƙasar tare da shi. Zaman saurarensu kawai yayi da tankaɗa da rai-rayar dukan kalamansu. Alhmdllhi zaman kuwa ya masa daɗi duk da yana buƙatar son kwanciya ya huta, dan ya fahimci abubuwa da dama wanda ada bai kawosu cikin ransa ba.       Bai samu shigowa ba sai kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare, a galabaice yake da son kwanciya da kuma jin yunwa, dan haka ido rufe yashigo ciki batare da tunawa da wanzuwar Raudha matsayin mata kuma amarya a gidan ba. ★★        Hasken ranar daya leƙo ta cikin labulen window ya haske fuskar Raudha ya sata fara motsa idanun da gyar, dan kanta har yanzu ciwo yake mata har a cikin barci. Idanun ta buɗe da ƙyar kuma a hankali, sai dai hasken ya sakata sake maidasu ta rufe sannan ta kare fuskar da hanunta. Sake buɗewar tai duk da nauyin da yay mata. Da ƙyar ta yunƙura ta tashi, tare da bin jikinta da kalllo zuwa ɗakin, ganin time ya sata tashi a zabure ta diro ƙafafunta bisa tattausan lafiyayyen carpet dake gaban gadon. Bata da nutsuwar cigaba da kallo da mamakin ɗakin, ta nufi ƙofar da zuciyarta ke tabbatar mata toilet ne. Ilai kuwa tayi sa'a dan ta dace da hasashenta. Nan ma bata damu da zaman yima komai kallon ƙurilla ba, duk da akwai abubuwan kallon kuwa bila adadin, tai alwala ta fito.        Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin data idar da salla. Tsami da ciwon zazzaɓi dake cin ƙashinta ya sata yanke shawarar sake komawa cikin toilet ɗin tayo wanka da ruwa mai ɗumi. Sosai taji daɗin jikinta, sai da ta fito kuma idonta ya raina fata, dan babu kaya ko ɗaya a ɗakin sai na jikinta. Jiri da takeji da rashin mafitar inda zata nema kayan sakawa ya sata faɗawa gadon ta sake kwanciya tare da jan bargo ta ƙudundune. Rawar sanyi ta fara a hankali kafin wani zazzafan zazzaɓi da yafi na daren jiya yay mata rijib. ★★          Tun kammala tsaftar lungu da saƙo na gidan da farar safiya da ma'aikatan gidan sukai shugaban ma'aikata ya tattaro kowa sukai zaman dakon fitowar first lady dinsu domin gabatar mata da kawunansu. Sai dai kuma har kusan goma na safe babu ita babu alamarta. Shugaban ƙasa ko tun bakwai na safe yabi ta sirintacciyar ƙofar da bai zama lallai kowa na gidan ya gansa ba inba wanda suke a harabar gidan ko aiki ta sashen ba ya fita zuwa office.     Basu gaji ba suka cigaba da zama har kusan sha ɗaya, wasu a cikinsu dai sai ƙunkuni suke a zuciya da sukar wulaƙancin first lady, waɗan da suke a gidan tun zamanin tsohon shugaban ƙasa na ayyana (ita kuma da salon wulaƙancin da tazo kenan). Wasu ko masu ɗan hankalin ciki na ayyana maybe ango ya angwance ne har first lady ɗin kuma amarya ta gagara fitowa. Haka dai sukaita tunani barkatai kowa da irin nasa hasashen har su aunty Mariya da sukazo kawo akwatinan lefen Raudha suka iso gidan.          Kusan a tare suka iso da su aunty Hannah da sukazo domin amsa. Sai dai halin da suka iske Raudha a ciki ya sakasu mantawa da wani karɓar lefe ko badawa. Aunty Mariya da tunaninta ya tsaya akan shugaban ƙasa Ramadhan yayi angwancine amma ya tsallake Raudha ya fita sai faɗa takeyi. Dan duk wanda ya dubi yanyin Raudha ɗin, da idanunta da suka koɗe saboda kuka dole kai tsaye ransa ya basa abinda aunty Mariyan ke zargi.          Duk falo suka koma bayan sun mata sannu, aka bar aunty Hannah kawai tare da ita, acewarta zata taimakawa Raudhan ta gyara jikinta. Dan tasan yaran yanzu da son jiki yanzu haka bata shiga ruwan zafi ba.       Kalaman aunty Hannah ba ƙaramin ƙona ran Safina ƙanwar shugaban ƙasa dake bi masa a haihuwa da Aina'u da tazo kallon ƙwaf suke ba. Dan koda akace bara a kimtsa Raudhan Safina ta dubata tunda likita ce, ca tai bata iya duba patient na gida.         Tsaf aunty Mariya ta fahimceta, dan kaf ƴaƴan gimbiy Su'adah idan ka cire Bilkisu da Basma babu mai ƙaunar auren Raudha, saboda gimbiya Su'adah ta gama fallashe musu sirrin asalin Raudha ɗin kaf da cusa musu ƙinta. Su Basma ne kawai basu ɗauki abin da muhimmanci ba. Acewarsu ma ai ba Raudha ɗince ta aikata karuwancin ba. Talauci kuma ba'a goshi yake ba balle a gane wanda ya fito a cikinsa, su dai sun son Raudha kodan taimakon kakansu da tayi wanda da yanzu labarin wani ake bashi ba.         Aunty Mariya tasan yanzu Ramadhan zai musu matuƙar wahalar gani musamman a wannan ranar daya fara shiga office, dan haka tai kiran Anne ta sanar mata suna buƙatar doctor yazo ya duba Raudha ɗin. Anne da zuciyarta ke mata hashe irin na Aunty Mariya cikin damuwa tace, “Ya cutar musu da yarinya ko Mariya?!”.      Cikin jin nauyin Annen Aunty Mariya tace, “Anne sai dai haƙuri, ƴaƴan nan namu na yanzu sam basu da tausayi. Komai yinsa suke da ƙarfin tuwo da tunanin abari ya huce.....”         Ƙwafa Anne tayi cikin takaici ta ballama Shugaban ƙasa Ramadhan da ake kan gaɓar nunawa a television zaune a office suna gaisawa da vice ɗinsa Alhaji Yaro glass harara. “Kai gaka anan hankali kwance kabar ƴar mutane a wahale ja'irin kaya”.     Oho baima san tanaiba, hasalima shi har yanzu bai tuna da wata Raudha ba a ransa. Musamman da tunda yazo office ɗin suna tare ne da vice ɗin nasa, bayan yayi zaman mintuna talatin da wasu manyan mutane. Yayi ƙyau matuƙa cikin shadda kalar ruwan ƙasa mai ɗan duhu kaɗan sai maiƙo take da ɗaukar idanu. Ɗinkin babbar rigane daya kara masa kwarjini da girman shekaru ga mai kallonsa. Fuskarsa tayi fayau saboda ramar da yayi, sai dai wasu kai tsaye suke fassara yanayin cikar haiba da kamalar fuskar tasa da ya sha angwanci ne kawai. Ga hularsa tangaran dake ta ɗaukar idanu na sake fiddo ainahin ƙyawunsa kai tsaye.      Anne ta ɗauke kanta daga kallonsa dai-dai sanda aka sake nuno yana musabaha da Alhaji yaro glass, tsintsiyar hannunsa dake sanye da baƙin agogo da baƙin link mai brown stone suka bayyana. sai zabba na azurfa biyu dake a yataunsa wanda duk itace ta saya masa su a saudia.         “Lafiya wai kiketa sababi ke kaɗai Janna?”.     Dattijo Alhaji Hameed Taura ya faɗa lokacin da yake fitowa daga toilet ɗin bedroom ɗin nasa da Anne ke zaune. Cikin sake ɓata fuska tace, “Da jikanka nake mana”.      “Oh-oh mi yayi ɗan bawan ALLAH ”.      “Kaface haka mana. Yanzu Mariya ta kirani wai a tura musu likita. Yaje ya farma ƴar mutane babu tausayi balle duban ƙarancin shekarunta. Bai kuma tsaya neman mai taimakonta ba ya tsallake ya fita sabgar gabansa shi a dole ga shugaban ƙasa”.      Murmushi mai faɗi Alhaji Hameed yayi yana kaiwa zaune kusa da matar tasa ƴar daru. Ya kamo hanunta cikin nasa idanunsa na yawo a fuskarta. “To amana afuwa dan ALLAH. Insha ALLAH bazamu sake ba”.      “Ko jikina kunne ne ba yarda zan bazaku sake ba. Amma ina gargaɗinku da ku kiyayeni”.      Tai maganar tana tashi da cire hanunta cikin nashi dan ta ɗakko ɗayar wayarta a ɗaki ta kira Doctor. Binta yay da kallo yana dariya ƙasa-ƙasa. Banda dai daru irin nata mutum da matarsa sai a hanashi yin yanda yaso. Shekarar Ramadhan nawa babu aure, kuma shi shaidane Ramadhan baya neman mata tun yana saurayi balle yanzun. Dole kuwa ya damƙi mace a samu matsala.       Bata daɗe da fitaba ta dawo tana sabuwar mitar ƙin samun Doctor Hauwa'u, dan haka ta sake kiran Aunty Mariya taji yaya.      Koda aunty Mariya ta ɗaga saita ce tama kwantar da hankalinta an samu doctor da tazo zata dubata. dan aunty Hannah ta kira wata ƙawarta dake nan kusa da fadar shugaban ƙasar.        ★     Duk da aunty Hannah ta lura zazzaɓi ne kawai da damuwa ke damun Raudha babu wani taɓata da ango yayi saita zaɓi yi musu ƙarya da zaunar dasu akan hasashensu na cewar ai ta gasa Raudha a ruwan zafi, dama batayi bane da ƙyau shiyyasa. Shi kuma shugaban ƙasa yana sauri yaje office bai sake taimka mata ta shiga ba da safen nan.       Kalamanta sun sake baƙanta ran su Safina har Aina'u najan tsaki da hura hanci, zuciyarta kam kamar ta ɓallo ƙirji ta fito dan takaici. Aunty Hannah najin za'a kira doctor daga Taura house tai ruwa tai tsaki akan akwai ƙawarta anan kusa zata kirata basai an saka kowa wahala ba. Ilaiko haka akai, Doctor Farhat tazo ta duba Raudha, ta kuma bata magungunan zazzaɓi harda allura da ledar ruwa ɗaya. Sai suka haɗa baki koda su aunty Mariya suka shigo nuna musu sukai dai har ciwo shugaban ƙasa Ramadhan ya jima Raudha, amma basai anyi ɗinki ba zai warke.         Sosai mamaki ya kashe Raudha a kwance, dan kuwa tanajin lokacin da suke ƙulla zancen a toilet da suka shige, ita kuma ta bisu ta laɓe dan ca take allurar mutuwa zasu mata ma tunda yanzu aunty Hannah ba'abar yarda bace ba. Sai matuƙar kunya ta hanata iya buɗe ido ta kalli kowa a cikinsu duk da addu'oin da suke jera mata na samun lafiya da albarka. Ga wani takaicin aunty Hannah da mamakinta. To miye nayin ƙaryar dan ALLAH anan? Koda ma hakance ta faru sai an fallasata ma duniya da dangin miji.              Har suka bar gidan ran adda Asmah da su Safina a ɓace yake. Aina'u kam ai ba'a magana. Dama can batazo bikin ba jiya ta iso Bingo saboda bikin rantsar da shugaban ƙasa. Yau ko tazo ne danta gansa duk da akwai shakkar hakan tare da ita a dalilin wasan ɓuya da sukeyi ita da shi game da wani al'amari daya faru a america kusan shekara huɗu kenan. Lokacin yana farko-farkon shiga ruɗanin rasa Amnah da Haseenah.      Bayan wucewar su aunty Mariya, Aunty Hannah da aunty Halima suka buɗe akwatunan lefen suka gani. Har cikin rai sai da aunty Hannah taji hassada ta soketa, dan ko ita data ɗauka tsahon shekaru tana kutsetseniya cikin manyan mutane bata taɓa ɗaura wani zanin ba. Kayane masu tsada da ƙyau. Ita kanta gimbiya Su'adah da wannan takaicin masu kawo lefen suka barota. Aunty Halima dai daɗi taji ta kumayi addu'a, dan koba komai uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da Asabe. Ballema ita mace ce mai zafi da sauƙi, tana da kirki kuma da son dangi. Gata ƴar gaskiya da gaskiya. Dan tun bayan auren Asabe itama ta fahimci aure shine mutuncin ƴa mace ba rayuwar da mahaifiyarsu ta ɗorasu a kaiba. Batai shawara da kowaba ta nutsu ta tuba, wanda ta tuba dominsa kuma sai ya kawo mata mijin aure cikin sauƙi bisa rahamarsa.         Duk yanda aunty Halima ta hana karsu ɗauki komai aunty Hannah bata saurareta ba. Kowa a gidansu sai da aka ɗaukar masa wani abu a lefen sannan suka wuce bayan sun damƙa Raudha hannun Tambaya wai ta kula da ita idan ta tashi a barci. Aunty halima dai ba haka taso ba, taso suyi haƙuri har Raudha ta farka suji ko tanada buƙatar wani abu, amma babu yanda ta iya tunda aunty Hannah na gaba da ita. *_TAURA HOUSE_*         A Taura house kuwa sabuwar fitina su Adda Asmah suka sake kunna gimbiya Su'adah. Wani irin zogi takeji a ƙirjinta da jin mai rabata da Ramadhan sai ALLAH......       “Wlhy Ramadhan yaban mamaki, banyi zatoba daga garesa, bansan mi yarinyarnan ta mallaka ba da har ya ruɗesa da kusantar ta....”        A hasale Fulani dake shirye-shiryen komawa masarauta saboda kiran da mai-martaba ya mata tazo ta tare gidan surukai ta katse Adda Asmah mai maganar a hasale. “Aiko yayi na farko yayi na ƙarshe dan ubansa. Bandama namiji duk inda yake maye ne (ba ni na faɗaba fulani ce😱) har miye a jikin yarinyarnan na bibiya. Yayta wani ɗaga kai da izzar banza a waje ashe shashasha ne”.        Cikin taɓe baki Addah Asmah tace,  “Ammy shiyyasa tun jiya nace a fara bata maganin nan na hana ɗaukar ciki ai, shima muyi masa gargaɗin karya raɓu yarinyarnan dan nidai nasan yanda Ramadhan ya jima babu mace koda bai son yarinyarnan zaiyi ruwan kashe gobara da ita. Amma sai kukace babu abinda zaiyi da ita. A tunaninku yanda take ƙyaƙyƙyawa ɗin nan zai iya kauda kansa gareta tunda ma ba tabbacin baya sontane damu ba......”       Gimbiya Su'adah ta haɗiye wasu hawayen baƙin ciki dake neman zubo mata. Cikin kaushin murya da jin tsananin sakejin sabuwar tsanar Raudha ta katse yayar tata, “Aiko zaiyi aman abinda ya taɓo dan ubansa. Itako sai na maida rayuwarta abin tausayi a ƙasarnan itada karuwan dangin uwarta da faƙiran dangin ubanta. Shiko zaiyi nadamar haɗa shimfiɗa da ita da yay, zaizo ya sameni ai”.      Kuka Aina'u ta sake fashewa da shi dan duk suna zaune a falon ita da su Safina. Basma da Bilkisu ne kawai babu. Lubnah dake bima Safina kam tafi kowa ɗaukar zafi, dan halinta kaf irin na gimbiya Su'adah ne dama. Rashin son Raudha ya hanata zuwa fadar shugaban ƙasar tun jiya.      Cikin takaici Munirah dake bima Bilkisu ta harari Aina'u. “Wlhy aunty Aina kina bada mata. Miye abin kuka dan Yaya Ramadhan ya kwanta da waccan wawuyar yarinyar. Nifa kune kuke ganin laifinsa Maa. Karfa ku manta jinin karuwaice, wama ya sani ko itace taja ra'ayinsa ga hakan tunda iyayenta sun koya mata. Kuma koba komai ya mora sadakinsa da wahalar da aka sakashi yakeyi na yawon zuwa ƙauye da kisan kuɗi. Ni dama ya farka shegiya yanda bazata ɗinku ba mtsoww!!”.          Duk da kasancewar Muneera ƙaramar yarinya a cikinsu sai maganarta tai musu daɗi, dan daga Yusrah sai auta Basma a ɗakin Gimbiya Su'adah, a yanzu hakan shekarun Muneera gaba ɗaya bai wuce ashirin da ɗaya ba zuwa da biyu. Amma har take iya waɗannan zantukan.         Safina ta ɗanyi dariya, “ALLAH kumafa zancen Muneera haka yake, baima kamata muga laifin Brother ba. Dan haka kibarma fushi da shi Maah. Yarinyar zamu cima ƙaniya kawai. A kuma ɗorata akan maganin hana daukar cikin nan da lalata mahaifarta. Sannan tunda Muneera ta kammala karatunta ta koma can da zama ita da Lubnah, sune zasuci mana ubanta cikin sauƙi kuma suna kawo miki abinda duk ke faruwa a gidan.”         “Shawararki yayi dai-dai Safina”. Fulani ta faɗa cike da isa da ƙasaita. batare da ta basu damar cewa wani abuba ta cigaba da faɗin, “Harma da Aina'u. Tsakanin Bilkisu da Basma ma wata taje su haɗu su zauna”.       Adda Asmah tace, “Eh hakan yayi Ammy. Sai dai kinsan Halin Ramadhan zai iya cewa sunyi yawa. Kodai su Bilkisun su zauna su”.        “Aiba lokaci ɗaya zasu tafi ba, da daɗɗaya kodan waɗan can tsoffin suma da basa iya gani su ƙyale. Amma zuwa Basma ko Bilkisu nada nasa amfanin. Su nuna suna sonta suke, zatafi sakin jiki da su har su san komai nata. Su kuma su Lubnah ta hanyarsu zasu dinga sanin wasu abubuwan ai ko”.        Cikin gamsuwa suke jinjinama Fulani kawunansu. Banda gimbiya Su'adah da har yanzu zuciyarta ke a matuƙar ƙuntace. Dan ko magana bata iya sakeyi ba. ____________________      A can bangaren su Aunty Hannah ma suna zuwa rabon ganima aka fara, sai dai banda Asabe da tausayin ɗiyarta ya rufeta game da labarin da aunty Halima ta bata dan itama batasan ba gaskiya bane tunda aunty Hannah bata sanar mata ba. Taji inama Raudha nada waya yau data kira taji ko muryartane taji sanyi. Dan rabonta da ita tun randa aka ɗakkota da ga Hutawa. Ita nan gida tayo dama ita da hajiyar birni. Su aunty Halima ne kawai suka je kai amarya.........✍ *_Hummm🚶🏻_* ________________________ Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗 Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali Ina masu pimples Tabo(spot) Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻‍♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself 100%tested nd trusted Soap price:3k Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free Maiso kindly message 08062991549 07046881166 Call 08064532391 Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏 Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝 Mg's skincare _________________________ *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/16, 8:18 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 27_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKK👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62aa07dd3992cc4a44aaa7a4 ________________________ Assalamualaikum lovely brothers and sisters. Please support our YouTube channel *sudais kura* for Allah sake our channel is all about Qur'an recitation and other Islamic studies 🙏🏼 I am not perfect, but I'm a mother who love to see kids Recite Qur'an. I'm trying my best with the little I know to install the love of the holy Qur'an into sudais heart at this young age. Please support our journey by subscribing to *Sudais kura* YouTube channel 🙏we are planning to start some simple craft and art work too on the same channel insha Allah. Just subscribe and you will not regret❤️ the channel link 👇🏻 https://youtu.be/g6BGEBv-X8Y ________________________ ...........*_GOVERNMENT HOUSE_*       Barci sosai tayi har taji babu daɗi. A kowanne motainta Tambaya kan leƙa ta tabbatar tana lafiya. Bata farkaba sai bayan la'asar. Taji daɗin jikinta sosai dan magunguna masu kyau Dr Farhat ta bata. Wanka ta farayi mama tambaya ta gyara mata ɗakin tunda dama aikinta ne. Bata tambayeta wacece ita ba tunda tasan a irin wannan gidan dama dole a samu ma'aikata. Bayan ta gasa jikinta da ƙyau ya sake warwarewa tayo alwala ta fito. Ɗakin ya sake komawa tsaf sai ƙamshi yake. Batabi takan komai ba ta gabatar da sallolin dake a kanta sannan ta miƙe ta buɗe akwatinan da aka zube matan. Cikin sa'a ta samu ɗinkakkun kaya kala kusan biyar da sai daga baya aka amso a wajen tela dan bai kammala mata na fitar biki ba da a aka kai wancan ranar. Riga ne da skirt na atanfa less Onion color. Sai ratsin milk kaɗan a jiki da stones da aka kawata ɗinkin da shi. Kayan sun mata ƙyau da fiddo kalar fatarta musamman data ɗan rame kwana biyun nan.        Duk wanda ya ganta yaga amarya kodan gyaran jikin da tasha na nagartattun kayan *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* da duk amaryar da akaima gyara da su dole tazama abar kallo. (Amare dama mata ƴan ƙwalisa dake buƙatar kayan gyaran jiki na musamman, tun daga kan ƙamshi na turarurrukan gida dana jiki, har zuwa gyaran fata da kayan mata ingantattu ku garzayo ga *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* domin samun naku kuma. Masu iya magana kance siyen nagari maida kuɗi gida😘😋🤗), ga lallin ƙafarta da hanunta raɗam tamkar bazai fita ba. Mama tambaya ce tazo ta sanar mata an shirya mata sabon abinci tunda breakfast ya huce, anma fiddashi tuni. Ta amsa cikin mutuntawa ga mama Tambaya dan koba komai zata iyama jika da ita.      Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, amma tanajin yunwa. Dan haka tai dauriyar fitowa falon saman inda mama tambaya ta saka kuku ya shirya abincin. Sosai mamaki ya cikata ganin table ɗin a cike, dan babu wani zancen ƙauyencin gidan ko tsarin abubuwansu tattare da ita kasancewar an mata lectures na koma kafin ta shigo. hasalima ta shigo ɗin tun kafin a kawota matsayin matar gidan. “Mama wannan abinci duk suwaye zasu cisa haka?”.       Kan mama Tambaya dake tsaye a ƙasa tai murmushi. “Ranki ya daɗe ke da shugaban ƙasa ne kawai, duk da bamu da tabbacin shigiwarsa gida a yanzun”.      Mamaki da takaici ya kume Raudha a rai. dan kai tsaye ta danganta hakan da almazarancine kawai. Talakawa nawane suke wahala babu ko ruwan kunu da zasu sha a yau, amma an shirya abinci fin kala huɗu a dining ɗin gidan shugaban ƙasa wai dan shi kawai da matarsa. Tabbas ta sake yarda mulki BAƘAR INUWA ne kawai. Dan hakkin mutane kawai aka barka da shi ka shiga uku. Ta rumtse idanu da haɗiye ɓacin ranta, cikin saisaita murya tace, “Mama yayi yawa ai, ya kamata a dinga dafa iya wanda za'a iya ci kawai ya wadatar. Dan ALLAH daga yanzu a dingayin dai-dai misali. Idan kuma ansan ma shugaban ƙasa bazai dawo yaci ba adaina girkawa da shi har sai idan shine ya bukaci hakan”.        “Amma ranki ya daɗe haka tsarin yake tun a wancan shugaban kasar mai sauka dana sani nidai.”        “To mama inaso a canja yanzu danni dai bana buƙata sam”.       “Insha ALLAHU za'a gyara ranki ya daɗe, dan dama dai tun ɗazun duk ma'aikatan gidan nan suka gama taruwa domin gabatar da kansu gareki”.       Duk da gaban Raudha sai da ya tsinke ya faɗi dan fargaba tausayin kanta sai ta dake tace, “Ba damuwa sai a sanar musu na tashi to”.      “An gama ranki ya daɗe. A fito lafiya”.             Kai kawai Raudha ta iya ɗaga mata, dan babu abinda ƙirjinta keyi sai luguden daka. Ita Raudha, ɗiyar Mal. Ɗan-azumi da Asabe na Hutawa ce a wannan ajin na ƙaddara. Itace akema wannan girmamawar duk da ƙarancin shekarunta. Itace matar shugaban ƙasa wadda kowa zai iya kira da first lady a ƙasar NAYA da ƙetare a yanzun. Itace matar shugaban ƙasa *_Ramadhan B. Hameed Taura_*. Ɗan ƙwalisar gayen nan maiji da giyar kuɗi da lokaci, ƙyaƙyƙyawa mai girman kai da jan aji wa manyan mata. Wannan wace irin ƙaddara ce haka mai kama da almara ko hikayoyin marubuta. Badan tayi imani babu mai iya ja da ikon ALLAH ba da tace kodai ta mutune ko barci take har yanzu komai nazo mata a mafarkine ba gaske ba. Wannan ƙaddara ta mata nauyi da yawa a zahirin rayuwa da baɗini. Gaskiya mahaifiyar Ramadhan ɗin ta faɗa ita ba kowan kowa bace, sannan Ramadhan yafi ƙarfin yafi ƙarfin kowa nata. Sayyadi Abubakar ma da bai kama ko ƙafarsa ba iyayensa suka tabbatar da ya fita balle shugaban ƙasa.      Waɗan nan tunane-tunanen suka hanata sakin jiki taci abincin kirki har mama Tambaya ta sake dawowa ta isar mata da saƙon taruwar kowa. Tambayar mizai hana su shigo nan tayi. Cikin girmamawa mama Tambaya tace, “Ranki ya daɗe basu da wannan hurumin sai mu huɗu kawai. Ni da Chief kuku da mai gyaran ɗakin shugaban ƙasa sai mai gyaran falon nan kuma.”       Ɗan jimm Raudha tayi tana dubanta, sai dai komai bataceba ta miƙe da ɗaukar milk gyalenta data fito dashi ta yafa har saman kanta sannan suka fito. Tana gaba mama Tambaya na take mata baya ★Falo ne babba da za'a iya kiransa mafi girma a duk falukan gidan. Komai na cikinsa kalar tutar ƙasar NAYA ne. Ya ƙawatu matuƙa da kayan more rayuwa. Ma'aikatan da adadinsu zai kai kusan hamsin suka rissinar da kai domin girmamawa. Gareta suna miƙa gaisuwa. Duk da ba kabilarta bane su duka haka ta amsa musu cikin mituntawa dan babu wanda bai kere shekarunta ba a cikinsu.     Shugaban ma'aikata na sashen nata ne ya fara gabatar da kansa, sai shugan kuku's da sauran kukus ɗin, sai Mama Tambaya da mai gyaran ɗakin shugaban ƙasa. Kafin sauran su cigaba ɗaya bayan ɗaya. Tun ma Raudha na fahimtarsu har da daina tunaninta ya tafi wani wajen da ban. Cikin nutsuwa ta ɗaga musu kai da fara faɗin,        “Masha ALLAH naji daɗi, ina kuma fatan zaku riƙe amana dan nasan babu wani addini dake goyon bayan cin amana ko zalunci. Bazance karku cutar damu ba ko a haɗa baki daku wajen cutar damu. Sai dai zance kuji tsoron ALLAH karku zaluncemu da son zukatanku ko biyewa ruɗin kuɗi. Idan kun kiyaye kuma ALLAH zai kiyayeku ya ɗaga darajarku zuwa wani matsayi da baku taɓa zato ba. A duk lokacin da bawa ke tsoron rasa wani abu wani nacan ya samu yayi shi. Idan murna da farin cikin samu kake wani nacan shi kukan rasawa yayi. Sai musa a ranmu duk zamu iya zama ɗaya daga cikin wannan matsayin. Dan a duniya babu mai wahala sama da _mai buƙatar abu a lokacin da abun baizo ba. Da kuma mai ƙin abu bayan ana tsaka da samuwar abun_. ALLAH yasa mu dace, ya bamu ikon sauke nuyin juna bisa bigiren tsoron ALLAH da cire son zukatanmu ko yanke hukunci akan umarnin zuciya”.       Sosai sunji daɗin kalamnta, wasunsu da zamansu nada alaƙa da kalamnta na son cutar dasu sai jikinsu ya fara sanyi. Gata dai ƙaramar yarinya amma tanada cikar kamala da kwarjinin manya. Uwa uba iya sarrafa harshe cikin taka tsantsan da mutunta kowa. Wasu kuwa da yake zuciyar ta bushe ko'a jikinsu, a ganinsu ma ta cika iyayine da son nuna ita mai addini ce.      Sun shiga mata godiya bayan ta sallamesu. Daga haka ta koma ciki abinta. Zaman ɗaki ta cigaba dayi har ƙarashen wannan yini babu shugaban ƙasa babu alamarsa. Maganinta da tasha ya sata barci da wuri ma batare da ta damu da yanda wanda ya aurota ya banzatar da ita ba. *_BAYAN KWANKI BIYU_*          Yau kwankin shugaban ƙasa da amaryarsa biyu kenan a gidan gwamnati, sai dai tunda suka shigo gidan babu wanda yaga ɗan uwansa. Dama Raudha bata saka a ka ba, sai dai duk sanda za'a nunasa a television takanji wani iri a ranta tamkar mai ganin laifinsa. A gefe kuma tana yaba iya tsara adonsa da kyawun haiba da ALLAH ya bashi. Shi mutum ne da ko yaya yasa sutura ko badan kwalliya ba saita nuna kanta a jikinsa, koda bamai muhimmanci bace da rashin tsada. Abu mafi ɗaukar hankalinta shine ƴar tsagar kan girarsa dake nuna tamkar irin ta gayun zamani, tunaninta ya tsayane kawai akan ya bada wanzami yay masa hakane saboda gayu. Bama ita ba, mafi yawan mutane haka suke fassara tsagar dake kwance da wani salon style tamkar an tsara bisa girarsa ta dama. Da ace tanada dama da saita masa tambaya akan tsagar.      Ba komai yake mata daɗi ba a gidan, musamman abinci da kaɗaici suna sukar ranta. Sam girkin su kuku baya mata ɗan ɗanɗano a baki, ga kewar momynsu da ƴan uwanta musamman Yasmin da suka shaƙu matuƙa. Kai har ƴan hutawa kewarsu takeyi sosai. Sai kwaɗayin karatunta na islamiyya.       A tarewar tasu sau uku tai baƙi manyan mata masu ji da kansu da zasu iya haifarta har jika da ita ma, wai matan gwamnoni ne sunzo gaisheta. Sai wasu kuma matan manyan ƙasar ne ƴan siyasa. Ita dai nata gaisuwane a garesu da godiya. Dan duk da ƙarancin shekarun Raudha nasihar sayyadi Abubakar ta jima da maidata mai halin manya. Tanada nutsuwa da zuciya, ga miskilancin tsiya. shiyyasa takeda takatsantsan akan abubuwa masu muhimmanci. Ba komai takema garaje da rawar kai ba har saita nutsu ta fahimcesa. Hirarsu Aunty Hannah na taka rawar gani wajen bude mata ido da sanya ido ga duk wanda zai raɓeta a yanzun. Dan zuciyarta ta kasa yarda da kowa da komai na gidan. Kullum kuma cikin yin nazarin ta yaya zata kuɓutar da shugaban ƙasa take.      A ɓangaren shugaban ƙasa kuwa yayi matukar zama busy ne. Sam baya samun kansa yanda ya kamata a kwana biyun nan da fara shigarsa office. Wani abu daya faru randa ya fara zuwa office ya sakashi fara binciken wani abu akan jerin sunayen cabinet ɗinsa da suka tattauna akan zai naɗa. Sai dai kuma yana gabatar da su ga mashawartan nasa  wasu a cikin manyan jam'iyyasa sukayo masa ca akan akwai tsarin da sukebi wajen naɗa cabinet na shugaban ƙasa. Shi kuma a take zuciyar maza ta motsa yace bai yarda ya hau kujerar dan ya zama a ƙarƙashin mulkin mallakar wasu ba, dolene a barsa da zaɓinsa ya samu abokan aikin da zai sauke nauyin talakawan ƙasa. Ja'inja ta ɓarke sosai a tsakaninsa da su wannan shine ya ƙara ɗauke hankalinsa ga Raudha har ma da su Gimbiya Su'adah data cika tai fam da tunanin ɗan nata na can na rugurguzar amarci da holewa a gidan gwamnti ya manta da su.      Tayi kiransa har sau uku amma bai daga ba. Daga karshe kuma tama bar samunsa kuma bai biyota ba. Abun nan ya sake harzuƙa mata zuciya dajin tsanar Raudha. Sai dai UBANGIJI shine kawai masanin gaibu akan abinda zuciya ke hasashe babu tabbaci. Abinda gimbiya Su'adah bata sani ba shine shugaban ƙasa baima da lokacin kansa. Dan cikin kwana biyu kawai su Alhaji Yaro glass sun gama hargitsa shi, harya fara hange da saka inuwar mulki a jerin BAƘAR INUWA ce kawai ga wanda ya tsinci kansa a cikinta. Wayar da duk family contacts nasa ke ciki a gida yake barinta, hakan yasa taketa kira ba'a ɗaga ba bakuma a bita ba. Daga karshe ta mutu saboda karancin caji. Shugaban ƙasa bai luraba kuma sai yau da kewar su Anne ta ishesa yaga ya dace ya kira. A gefe kuma yana buƙatar yin magana da kakansa akan wannan rikicin nasu na fidda sunayen cabinet ɗin dake faruwa tsakaninsa da ƴan jam'iyya. Dan bai tunkaresa da zancen bane a tunanin zai iya shi kaɗai, yanzu ko yana buƙatar shawarar sa.        Sai da yay ma wayar caji kafin ya kunnata, da saƙon gimbiya Su'adah ya fara cin karo. Yay ɗan tsamm kafin ya buɗe ya duba. Tun a layuka ukun farko na saƙon zuciyarsa ta tsarga da abinda ya ta rubuto, ya ɗan dafe kai yana rumtse idanunsa da cije baki, sai kuma ya buɗe idanun ya ƙarasa karantawa. Missed calls ɗin nata ya duba, kafin ya ajiye wayar yana jan numfashi da ƙyar. Yasan Maihaifiyarsu mutum ce mai saurin fushi, sannan tanada yanke hukunci akan abu batare data bincika ba. To amma a wannan gaɓar maganarta ta tabbatar masa da cewar tana da hujja, dan kuwa ko Anne idan bai manta ba a ranar ta turo masa wani guntun saƙo itama mai nuni da faɗa akan abinda yay ma yarinyar da shi tunma da aka kawota gidan bai ko ganta ba. Leɓensa na ƙasa ya tura cikin baki yana ɗan taunarsa kaɗan-kaɗan. Tuni idanunsa da gaba ɗaya sun koɗe saboda rashin isashen barci da samun hutu suka sake rinewa da takaici. Mi yarinyarnan ke nufi da abinda tayi? Itace ta faɗa musu ya aikata wani abu da ita kenan? Maganar mahaifiyarsa ta wancan daren ta shiga dawo masa a cikin kai, sai dai kafin tunanin nasa yakai ko ina kira ya shigo a wayar. Tun kan ya ɗaga yasan Anne ce, dan ita da Pa da Bappi da Maa duk ya banbanta musu ringtone. Cikin furzar da fushinsa ya ɗaga yana kaiwa kunne.         Daga can Anne ta ɗan sauke ajiyar zuciya, cikin damuwa tace, “A tunaninmu dawowa ka mulki ƙasar NAYA zai kusantamu da kai ne? Sai gashi yana sake nisantamu Ramadhan ”.      Murmushi ya ɗanyi mai sauti, cikin tsokana yace, “Ba kune kuka jawo hakan ba Anne.”       “Uhm hakama zakace dan gidanku”. Murmushi ya sakeyi mai faɗi, ransa fal ƙaunar tsohuwar. “Am so sorry sweet Anne na, wasa nake miki”.          Itama murmushin tayi da ga can, har yana iya jiyo sautinsa. Ta cigaba da faɗin, “Shike nan ko waya ma ta gagara muyi da shugaban ƙasar NAYA, sai dai mu gansa a television”.      “Kuyi haƙuri Anne, ni kaina tausayin kaina nakeyi, babu komai a mulkin nan sai baƙar izaya. Wanda ke nesa damu ne suke hangenmu cikin wata ni'imtacciyar inuwa, amma wlhy Anne mulki BAƘAR INUWA ce kawai...”       “Asha Ramadhan! Asha. Karna sakejin hakan kaji, komai na rayuwa jarabawace kawai da rubutacciyar ƙaddara. Ka zama jarumi mai magana ɗaya kawai, sannan jajirtacce wajen tunawa da ɗunbin talakawan da suka dage rana da dare wajen ganin ka zama shugabansu. Ka kuma zama mai haƙuri da juriya kamar yanda na sanka kaji”.      Numfashi ya sauke mai nauyi, cikin ƴar nutsuwar da kalamanta suka bashi yace, “Inaha ALLAHU Anne nagode sosai ”.        “Babu damuwa. Ina Aminatu? Yanda kai wahalar ji itama tayi, har yanzu ban samu damar jin yaya jikinta ba haɗani da ita”.      Ɗan jimm yayi na alamar ɗaukewar numfashi, sai kuma ya shiga lalubo abinda zaice domin kare kansa. Sai dai ƙarya ba halinsa bace, dan haka harshemsa ya suɓuce wajen faɗin, “Tana ɗakinta”.        Kamar Anne zatace wani abu sai kuma ta share, sai kawai tace, “Daure ka haɗani da ita naji yaya take?”.      Baida wani zaɓin daya wuce bin umarninta. Dan haka ya amsa mata da cewar, “To Anne zan kira”.       Komai bata sake cewa ba ta katse kiran. Miƙewa yay cike da nutsuwarsa, ya ɗauka t-shirt mara nauyi baƙa ya sanya, tare da baƙin 3quarter na wando. Ya shigo gidane da wuri saboda burin yin barci, dan ko sallar magrib da isha'i ma a massalacin gidan yayi su. Slippers masu taushi baƙaƙe ya saka a ƙafarsa ya nufi ƙofa, sai kuma ya tsaya cak riƙe da handle ɗin ƙofar, dan haka kawai ya samu kansa da buƙatar sanya turaren da bai sakama jikin nasa ba, sai dai duk da haka yana ƙamshin sabulan wankansa, suma kayan suna nasu ƙamshin na kaya da yakan ajiye a Wadrobe, tun yana ƙaraminsa Anne ke masa haka, koda ya girma abin ya zame masa jiki koda yaushe zaka samu turaren kaya a Wadrobe ɗinsa.      Komawa yay da baya-baya yana ɓata fuska tamkar wanda akaima dole, ya sako turare kala biyu masu sanyin ƙamshi sannan ya fice. Duk wanda ya kallesa ya kalli yanayinsa dolene ya dangantashi da mutum mai girman kai, dan ko a tafiya abinda ke gabansa kawai yake kallo, sannan ba kowa bane yake ganin ya isa ya saka a sabgar rayuwarsa koda ta magana ce. Ko abokai sai ya gadama yake kula wasu. Ba kuma wai dan baya magana bane ko dariya, dan ko kusa baya kama da miskili. Mutum ne shi mai surutu a inda yaso ga kuma wanda yaso..........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/17, 1:36 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 28_* *_BAƘAR INUWA👉🏽 AREWABOOKS👇🏾_* https://arewabooks.com/chapter?id=62aafdab52e2996a61a92f3d ...........Tun bayan idan da sallar isha'i take ƙara jin zuciyarta a matuƙar ƙuntace, kewa da kaɗaici na damunta. Tana so koda a waya ne taji muryar mahaifiyarta da ƴan uwanta. Kuka taci sosai kafin ta miƙe ta shiga bayi, daga ƙudirin wanke fuska sai ta zarce yin wanka. Sosai ko taji daɗin wankan, dan sai faman sauke ajiyar zuciya take. Fitowarta kenan ɗaure da guntun towel, sai ɗan ƙarami tana goge fuskarta zuwa kunne da ƙeya inda hular wankan bata rufe mata gashi ba harya jiƙe. Murɗa handle ɗin ƙofar yayi dai-dai da ɗora hannunta saman hular wankan data rufe gashinta da shi gudun jiƙewa ta zare, da sauri ta waigo dan tasan babu wanda ke shigo mata, ko mama tambaya tun ranar bata sake shigowaba, gyaran ma ita tace ta bari zata keyi da kanta. Akan gashinta daya tarwatse bisa dokin wuyanta zuwa baya saboda waigowar da tai a fisge ya fara sauke idanunsa.      Ƙirjin Raudha ya buga da ƙarfi tamkar yanda nasa ma ya harba. Sai dai ya dake kasancewar gwani akan jin kai. Gaba ɗaya jikin Raudha tsuma yake dan bata taɓa tsammanin cin karo da shi ba, tama rasa wace tambaya zataima kanta. “Miya kawosa nan? Mi yake so? Mi zaiyi? Mi akayi?.....” haka suka dinga turereniyar fitowa daga ƙwaƙwalwarta zuwa zuciya. A gefe kuma waige-waigen abinda zata iya rufe jikinta takeyi cikin tsananin kunya da tashin hankalin ganinta a haka tamkar tsirara. Sai dai a zahiri bazaka fahimci hakan ba sai ɓata fuska ma da tai.       Shugaban ƙasa Ramadhan yaso ya juya ya koma, sai dai zuciyarsa taƙi aminta da hakan saboda sanin fitinar Anne daba ƙarewa take ba. Idan har bai cika umarninta na haɗata da ita ba to lallai kam ya takaloma kansa wani sabon abune kuma.        Idanunsa ya ɗauke tare da cigaba da takowa cikin ɗakin a ransa yana juya yanda ta wani haɗe fuska, har a zuciya ƙamshin da ɗakin keyi da sabulun da tai wanka ya masa daɗi. Dan shi mutum ne mai girmama kamshi. Kan sofar dake a ɗakin guda ɗaya tal ya kai zaune, sai sake tamke fuska yake shima kamar wanda aka aiko Pa ya mutu. Ya fara sarrafa wayar da ke hanunsa alamar neman Anne.      Da wannan damar Raudha tai azamar nufar hijjabin sallarta ta ɗauka ta saka tana ƙunƙuni. Ta sauke ajiyar zuciya duk da bawai taji nutsuwar bane dari bisa ɗari ta harari inda yake. Tabbas bata son shi, amma tana tsananin ganin girmansa da kwarjini a idanunta. Yana matuƙar cika mata ido irin wanda wani ɗa namiji bai taɓa mata ba a rayuwa. Taga girma da kimar sayyadi Abubakar a baya. Amma akan shugaban ƙasa Ramadhan sai takejin hakan na musamman ne. Cikin ture tunaninta da ƙara aro nutsuwa kan harshenta tace, “Ina yini”.       Maimakon ya amsa mata duk da yajita sai ya miƙo mata wayar hannunsa. Baiyi magana ba, amma tasan hakan na nufin ta karɓa. Jitai jikinta ya sake komawa sanyi ƙalau tunda batai tsammani ko hasashen wanene ba. A hankali ta ƙarasa takowa gabansa, cikin risinawa ta amshi wayar har yatsun hanunsu na gogar juna.        Cikin rashin sanin wanene takai wayar kunnenta. A nutse kuma tai sallama da muryarta mai sauƙin ƙarfi. Daga can Anne ta amsa mata da kulawa dan haka kai tsaye Raudha ta ganeta. A karon farko murmushi ya suɓuce a fuskar Raudha har tana nuna ɗokantuwa.       “Anne barka da dare”. Amsar da Annen ta bata da ga can ya sata sake faɗaɗa murmushinta tana ɗan girgiza kai da faɗin, “A'a Anne ba haka bane. Kawai dai....”     Sai kuma tai shiru bata ƙarasa ba. Murmushi ta kuma saki mai sauti daya sa har shugaban ƙasa Ramadhan ɗan dubanta daga zaman ƙasaitar da yay bayansa jingine da kujerar, yanda take magana a sake da kakar tasa ya sashi ɗan taɓe baki.. wanda bai saniba zai ɗauka barci yake saboda idonsa a lumshe suke, sai dai ras yake kallo dasu dan ya kaisu ƙasane kawai kamar ya lumshe ɗin.      Ƙwayoyin idanun nasa ya janye a kanta, sai kuma ya ɗan yamutsa fuska saboda abinda zuciyarsa ta raya masa. Da ga haka bai sake yarda ya kalleta ba hartai sallama da Annen ta miƙi masa wayar tana faɗin, “Nagode”.         Bai tanka ba, bai kuma nuna alamar zai amsaba balle miƙewa. Ganin bai motsaba kuma idonsa a rufe sai tai mamaki da tunanin ko barcine ya ɗaukesa? Rashin amsa yasata miƙewa da wayar ta ajiye a table ɗin gaban sofa ɗin. Wadrobe ta nufa, ta buɗe box ɗin da aka zuba mata kayan ƴan kunenta masu muhimmanci ta ɗakko agogonsa da taketa faman ajiya tun a waccan ranar a Taura.      Inda yake ta sake dawowa ta zauna ɗofane a stool ɗin gefen kujerar, kafinma tayi magana sai taga ya miƙe, ɗan duƙowar da yay domin ɗaukar wayarsa a saman table ɗin ya sasu samun kusanci sosai. Babu shiri ta ɗauke numfashinta tsam tamkar zata shiɗe saboda kusancin nasu ya bama kamshin turarensa da fitar numfashinsa damar bugar juna da nata numfashin.        Komai baice akan agogon ba, bai kuma amsa ba ya ɗauka wayarsa zai juya.        “Ga agogonka”. Ta faɗa da ƙyar batare da tunanin zai jita bama, dan haushi shariyar tasa ta bata. Dakatawar da yay daga yunƙurin  fitar ya bata damar cigaba da faɗin, “Ranar da mukaje jefa ƙuri'a Taura ka mantashi a falo, sai Anne tace na dauka maka, kuma yazam ba tare muka taho ba dan haka na cigaba da ajiyesa a wajena”.       Karan farko yayima agogon kallon tsaf da ita kanta mai maganar, tana da yanayin sanyi a fuska, amma sam babu tsoro ko shakka a muryarta, kai tsaye take magana. Agogone mai tsadar gaske, sannan mai matuƙar muhimmanci a garesa. Dan Amnah ce ta bashi as gift ɗin anniversary ɗinsu na cika shekara ɗaya da aure. A bazata taji ya ɗaura yatsun hanunsa kan nata ya ɗauka agogon yana faɗin, “Thanks”.          Da kallo ta bisa harya fice yaja mata ƙofar, taɗan sauke numfashi da miƙewa zuciyarta na ayyana mata abubuwa masu yawa. Ta kula mutumin nan wutar kara ne sai da izo, komai da ƙarfin hali take yinsa kawai.       ★   Koda ya isa ɗaki wayar ya tilla saman lafiyayyen gadonsa, ya ɗago agogon yan ɗan murza fuskarsa tamkar mai son ganin lokaci, sai kuma ya ɗan saki guntun murmushi mai ciwo da ɗaci. A saman laɓɓansa ya furta “ALLAH ya gafarta muku”. Daga haka ya tura agogon cikin aljihunsa tamkar ba kwanciya zaiyi ba. A kuma wani gefe yarinyar dake matsayin matar tasa a yanzu ce ke masa kaikawo a rai.       _________________________________        Tun daga wannan ranar Raudha bata sake saka shugaban ƙasa Ramadhan a idonta ba sai dai a television ko ƙaton hotonsa dake a gidan tako ina. Baƙi kam har yanzu tana yinsu jefi-jefi yayinda damuwarta da kaɗaici na nan a ranta daram. A ido ta ƙara ƙyau ga mai kallo, fatarta ta sake gogewa a cikin ac da rashin fita rana. Ga lafiyayyen abinci duk da baya mata wani ɗanɗano. Bata aikin komai da ga ci sai kwanciya.       A yanzu fatan gani ko Aunty Hannah ne take, danta roƙa alfarmar a kawo mata koda Yasmin da su Noor ne su dinga ɗebe mata kewa. Sai dai tsit kakeji babu alamar wani nata zai tuna da sun kawota nan. Hakama da ga ɓangaren Shugaban ƙasa babu wanda ya sake leƙosu har yanzun. Gashi suna a cikin sati na biyu da kawota gidan. Takanji motsin shigowarsa wani lokacin, kai harma fitarsa da safe. Sai dai bata taɓa gigin koda leƙawa ba balle su haɗu. Shi da ya ajiyeta ya nuna ya manta balle ita.      Dan yau ma tanajin fitarsa yana waya kamar cikin faɗa-faɗa, dan muryar nan tasa mai faɗi da amo na fitane a kausashe har tana iya jinsa da ga ɗakinta. Ajiyar zuciya ta sauke da ɗaukar Al-qur'anin ta ta hau karatu. Dama a yanzu bata da abokin hira ko ɗebe kewa sai shi. Yanda take yawan karantashi yasa har tayi sauka ta ƙara ɗakkowa daga farko, dan Raudha ta sauke alkur'ani mai girma. Tana akan yin haddane ma da wasu littafan. Babban burinta a yanzu cigaba da karatun ta harma dana boko. ____________________________         A kallo ɗaya zaka fahimci tsannin ɓacin ransa da ma duk wanda ke a cikin ɗakin taron. Su biyar ne kacal, kuma dukansu manya-manyan jam'iyyarne dake da ƙarfin faɗa aji. Wanda suna ɗaya daga cikin waɗanda suka taka rawar gani akan ganin Ramadhan ya zama shugaban ƙasa. Da farko bashi yay niyar zuwa meeting ɗin ba wakili ya naɗa, sai dai shawarar Bappi ta sashi janye wakilin ya halarci meeting ɗin da kansa.           Chairman party da yafi kowa shiga ɓacin rai ya sake duban Shugaban ƙasa Ramadhan B. Hameed Taura. Cikin son tausasa harshensa da haɗiye fushinsa yace,       “Amma ina ganin ranka ya daɗe kamar ya dace a dinga bin dokokin jam'iyya da tsare-tsaren dake shimfiɗe a cikinta tun usil. Dan duk shugaban daya hau mulki a ƙarƙashinta sai ya bisu”.           Shugaban ƙasa Ramadhan da babu abinda zuciyarsa keyi sai tafasa ya haɗiye wani ƙududun abu mai ɗaci daya tokare numfashinsa, kamar bazaiyi magana ba sai kuma yay wani munafikin murmushin takaici. “Ƙwarai da gaske dokar Jam'iyya nada muhimmancin daya dace kowa yay biyayya a kanta, kuma shaidane kuma inayi, amma abinda nake nuna muku anan ya dace muyi biyayya ga jam'iyya ne bisa ga abinda ke huruminta. Bance karku kawo zaɓinku a cikin jerin sunayen cabinet ba, sai dai ina tabbatar muku bazai yuwu nayi 70-30 da jam'iyya ba. Dan ina buƙatar waɗanda zasu tallafamin na sauke nauyin al'umma dake a kaina. Taya kuke tunanin zan aminta da waɗanda zasu juyani bani zan juyasu ba....”         “Ranka ya daɗe saboda a haka tsarin yazo”.       “Ni kuma gashi bazanbi tsarin ba”. Shugaban ƙasa Ramadhan ya faɗa a matuƙar hasale yana watsama Mr MM daya jima da lura baya ƙaunarsa wani mugun kallo da manyan idanunsa da babu abinda kake hange a cikinsu yanzu sai tsagwaron fushi da hasala.        Ƙasa Mr MM yay da kansa zuciyarsa na suya da sake jin tsanar Shugaban ƙasa Ramadhan. Mafi yawancinsu suna takaicin ɗan yaro da shi sa'an ƴaƴansu yana jayayya ga duk abinda suka kawo. Wanda a baya duk shugabannin da jam'iyyar ta kawo bisa kujera babu wanda ya taɓa ƙetarewa.        Alhaji Balarabe kwano ya ɗan risinar da kai yana fuskantar shugaban ƙasa Ramadhan, cike da ladabin munafunci yace,  “Ranka ya daɗe ALLAH ya huci zuciyarka. Inaga ya kamata duk mu kwantar da hankulanmu a sasanta. Yau kusan sati guda kenan ana maimita zance ɗaya. Tun anayi a takarda har takai yau an zauna meeting face to face, amma babu wata masalaha”.       Nan ma shiru Ramadhan yayi tamkar bazai amsaba. A ransa yana jin wani irin tsanar mulkin da takicin kansa na amsa batare da binciken sanin yanda abubuwan suke ba. Ashe mafi yawan lokuta ana zagin shugabanin ƙasa ne kawai batare da hakkinsu ba. Dan tun a washe garin daya fara zuwa office ya fahimci ba shugaban ƙasa ke mulki ba, wanda ke zagaye dashi keyi. A mafi yawan lokuta baida maraba da hoto a katako kawai. Sai dai rashin sani yasa kowa ya yayo zaginsa sai ya sauke akan shugaban ƙasa saboda shi kaɗai akema kallon mai hakkin sauke hakkin al'umma alhalin ba haka bane sam.        Yaja numfashi da ƙyar yana gyara zamansa. “Zan iya yarda da 50-50 akan Cabinet amma bisa sharaɗi guda”.       Da sauri duk suka maida hankalinsu gareshi cikin takaici. Dan 50-50 ɗin badan ta musu bane. Amma wasu har fuskarsu ta washe da murmushi tunda koba komai za'a rage.        Ya sake jan numfashi dayin rubutu kaɗan a takardar gabansa ya tura tsakkiyar table ɗin yana bin fuskokinsu da kallo a ransa dariyar mugunta yake musu. “Zan yarda bisa sharaɗin nine zan zabi speaker na majalissa. Idan kun amince kuyi singing, nima zanyi”.        “What!!”. Suka faɗa kusan su dukansu suna waro idanu dayin zallo.     Cikin ɗage kafaɗa na I don't care ya miƙe abinsa, guard nasa yayi saurin ja masa kujera baya.       “Duk shawarar da kuka yanke ina saurarenku”.     Ya faɗa yana nufar ƙofar da zata sadashi da office ɗinsa kai tsaye batare da yabi hanyar fita ɗakin meeting ɗin ba ta waje..       Kallon-kallo kawai aka komayi kowa ya kasa magana, dan kuwa shugaban ƙasa Ramadhan ya dakesu ne a kan jijiyar wuya dake kawo numfashin kila wa kala.         Shigarsa office ɗin baifi da minti biyu ba kiran Gimbiya Su'adah ya shigo masa. dole ya danne ɗaci da fushin dake a zuciyarsa har maƙoshi ya karɓa mata da girmamawa. Har yanzu haushinsa takeji, dan haka cikin kaushin murya ta sanar masa su Lubnah zasu zo musu hutu. Ba zuwansun bane ya bashi mamaki koya damesa. Jin har su biyar zasu zo da sunan hutu, bayan a cikinsu akwai wanda ke aiki da karatu.         “Okay Maa, amma kuma su su Lubnah aikinsu fa? Sannan Basma duka yaushe ta fara zuwa school da zata fara sakaci da shi?”.       A zafafe gimbiya Su'adah tace, “To sai akace maka bazasu iya zuwa daga nan ba ne? Zanje ganin likita na ne london, idan kuma baka buƙatar suzo ɗin sai su wuce Bina”.      “Am sorry Maa ba haka nake nufi ba. Insha ALLAH nima zan shigo gidan cikin weekend ɗin nan”.     Bata amsashi ba, sai ma yanke kiran da tayi. Ya rumtse idanu da ƙarfi, tare da tura lip ɗinsa na ƙasa cikin baki ya hau tauna da ɗan ƙarfi. Waɗan nan takaicin ya hanashi yin komai yau a office, duk da dai dama aikin bawani mai tsauri bane duk tsare-tsarensane akan ayyukan da yaga ya dace ya fara shimfiɗawa kodan tukuyci ga talakawan da suka tsaya a rana domin zaɓensa. *______________________________*         Tun bayan tashin shugaban ƙasa a meeting ɗin wasu a cikin yaransu suka sanar musu da sharaɗin daya kawo na yarda da 50-50 akan cabinet saɓanin 70-30 da suka tsara. Ransu ya ɓaci suma matuƙa, basuyi ƙasa a gwiwa ba wajen miƙa zancen ga nasu god fathers ɗin. Suma da ga can hankalin nasu a tashe yake, kuma ransu a ɓace yake. Duk da kasancewarsu a mabanbanta gari a wannan ranar suka nufo Bingo gaba ɗayansu suka haɗu domin tattaunawa. Sai dai zaman nasu bai samu akan lokaci ba sai wajen sha ɗaya na dare. Tsabagen ƙwarewa a siyasa kuma kusan ƙarfe huɗu na yamma sai da suka kaima shugaban ƙasa Ramadhan gaisuwa har office.        Yayi farin ciki da zuwansu, ya kuma girmamasu matsayinsu na manyan ƙasa kuma kakanni a garesa, dan dukansu zama su iya girmar Bappi, wasu kuma sa'anni da shi. Su ɗin kowa yasan manyan mutanene a ƙasar kuma dattijan arziƙi da sukai hidima ma ƙasa shekaru masu yawa da suka shuɗe. Sannan mutanene masu dattako da bazaka taɓa jin bakunansu akan mulkin ƙasar ba har sai idan ta ɓaci. Sai dai abinda ƴan ƙasa dama shuwagabannin basu sani ba, waɗannan dattijan lulluɓin biri ne kawai a jikin kuraye, sune ke juya ƙasar NAYA bisa table tamkar mulmulallen ƙarfe bisa ƙarfe. Duk wani shugaba da zai hau a gwamna ko shugaban ƙasa sai da yardarsu, sannan duk wani mai taimaka masa da zai naɗa sune da kaso mafi yawa a ciki, shiyyasa a kowanne mulki, a kuma kowacce jaha yaransu ne akan madafun iko.       Kamar gaske shawarwari masu daraja suka bama shugaban ƙasa Ramadhan. Wanda yaji daɗinsu kuma yay farin ciki dasu, barin office ɗinsa kuma bai wuce da awa guda ba har zuwansu gareshi da shawarwarin da suka bashi sun watsu kafafen yaɗa labarai dama yanar gizo. inda kowa ya samu damar tofa albarkacin bakinsa. A mafi yawan Comments ɗin kuma ya ta'allaƙa ne ga yabonsu da jinjina mutuncinsu a idanun al'ummar ƙasar NAYA. *11:00pm*         Su dukansu biyar zaune suke a cikon falon gidan ɗaya daga cikinsu mai ƙarancin haske kasancewar an kashe mafiya yawan fitulun. Sai yaransu huɗu irin su shugaban jam'iyya, da Alhaji Yaro glass sai shugaban ƙasa mai sauka Usama S. Hamada da Mr Mike Bando vice president ɗinsa.       Bayan sun gama sauraren ƙarin bayanai daga bakunan yaran nasu oga kwata-kwata mai shugabantar tawagar dattijan ya ajiye kofin shayin hanunsa yana wani shegen murmushi da faɗin, “Da alama yaron nan bazaiyi tsahon ran cika 2years ba, kamar yanda mukai masa fata”.      Sauran dattijan huɗu sukai ƴar dariya, yayinda su su Alhaji Yaro glass basuga abin dariyarba anan. Dan har cikin rai sun fara jin fargaba akan taurin kan shugaban ƙasa Ramadhan.        “Amma ranku ya daɗe kenan zamu yarda da sharaɗinsa?”. Forma Vice president Mike Bando ya faɗa cikin jin ɗaci.          Wanda ke kusan tsakkiyar dattijan zaune ya ɗan taɓe baki da faɗin, “Well! Zamu iya yarje masa zakuma mu iya jayayya da shi. Sai dai ku sani dukansu biyu sunada haɗari. Yarje masan, da kuma yin jayayyar”         Cikin takaici Alhaji Yaro glass yace, “Kenan ranka ya daɗe wannan ƙaramin alhakinne zai zamar mana ƙadangaren bakin tulu, ya ringa juyamu yanda yake so? Wai mizai hana ya mutu ne a wata shida?”.        A tare dattijan suka kwashe da dariya. Sai kuma suka gimtse fuska. “Haka tunaninsa ke ayyana masa, shiyyasa har ya sharɗanta abinda ke a zuciyarsa. Shi yaro ne, baisan siyasa ba, bai san komai nata ba, bai san wahalar rayuwa ba dan cikin dukiya ya tashi. Dan haka wannan ba tunaninsa bane...”        Da mamaki suka dubi oga kwata-kwata da yay maganar. Murmushi ya sakeyi batare da damuwa da kallon da suke masan ba. Yakai yatsunsa biyu ya ɗan ɗalli bowl ɗin gabansa mai ɗauke da fruits. “Tabbas ba tunaninsa bane, wannan tunanin Alhaji Hameed Taura ne. Dan haka shine zai fara mutuwa kafin yaron”.     Ya ƙare maganar cikin kaushin murya da ɗaure fuska. A take su alhaji yaro glass suka shiga kallon-kallo. Dan su kam bama su hasaso hakan ba a ransu, tunda sun san shima Ramadhan ɗin gwanine na taurin kai da rashin mutunci. Har cikin rai wannan abu yay musu daɗi, kuma sunyi na'am da shi. Dan kuwa mutuwar Alhaji Hameed Taura suma shine burin ransu..........✍ *_(Hummm🚶🏻🤦🏻)_* *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/17, 1:36 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62aafdab52e2996a61a92f3d *_Episode 29_* ...............*_GOVERNMENT HOUSE_* Tattaunawar sa da dattijan ya bashi ƙwarin gwiwa sosai. Dan yaji matuƙar daɗin shawarwarinsu. Da wuri yau ya shigo gida, dan haka yana ɗan watsa ruwa ya fito falon upstairs ɗin domin yin wani ɗan aiki. Da kansa ya buɗe fridge ya ɗauka fresh furarsa da Anne bata gajiya da aiko masa duk bayan kwana biyu. Da ga can gefen falon kujerune guda biyu dake gab da wawakeken glass ɗin dake tamkar matsayin window, sai dai shi zaka iya fita ta cikinsa zuwa barandar upstairs ɗin, daga nan cikin falon kuma zaka iya hango kai kawon kowa dake a ƙatuwar harabar gidan. table ne tsakkiyarsu, sai fitila doguwa dake tsaye wadda zaka iya amfani da ita idan baka buƙatar hasken falon da yawa. Zama yay da bismilla kafin ya buɗe furansa da kilishi dake a cikin kwali. Daga haka ya kunna apple lap-top ɗinsa ya fara aiki a nutse cike da ƙwarewar iya sarrafa keyboard. Sosai ya shagala a aikin dake masa matuƙar dadi, dan tsare-tsarene da suka shafi ayyukan da zai ɗora cabinet ɗinsa a kai. Lokaci-lokaci yakan ciri kilishi ya kai bakinsa koya ɗan zuƙa fura. Cak yatsunsa da ɗan sakewar fuskarsa suka dakata sakamakon jin kamar shashshekar kuka. Sai dai kuma bai ɗagoba har kusan sakanni talatin. Tabbatar da da gaske kuka ake a kusa da shi ya sakashi sake nutsuwa yana sauraren inda sautin ke fitowa, kafin ya ɗago da ƙyar tamkar an masa dole ya kai dubansa ga inda sautin kukan ke tashi. Babu yalwataccen haske a falon, amma hakan bai hanashi hango Raudha dake zaune can steps na sauka downstairs ba, ba dukanta yake hangowa ba, iya kafaɗarta ne kawai zuwa kanta, saboda tana zaune ne a steps ɗin kusan tsakkiya ta masa ƙasa da yawa. Ɗauke idanunsa yay da ga kanta, ya maida ga agogon dake jikin lap-top nashi, ƙarfe ɗaya saura na dare. Cigaba yay da aikinsa tamkar abin bai damesa ba, sai dai acan ƙasan zuciyarsa kukan nata na sukarsa. Bai cika san kuka ba, musamman irin nata mara sauti sai jan ajiyar zuciya. Duk yanda yaso cigaba da aikin cikin shauƙin daya fara sai hakan ya gagaresa, dole ya ɗauke hannayensa ya gyara zamansa a kujerar tare da harɗe ƙafafunsa ɗaya kan ɗaya ya jingina bayansa da kujerar ya lumshe ido yana cigaba da sauraren fitar sautin kukan nata mai haɗe da jan ajiyar zuciya. Tun yana lissafa sakanni ya koma mintuna, har takaisa ga kusan mintuna talatin babu alamar zatai shiru. Takaicin tsayar masa da aiki ya sakashi jan siririn tsaki ya buɗe idanunsa. A ɗan harzuƙe ya miƙe zuwa makunnar wutar falon ya dannasu baki ɗaya. Warr haske ya gauraye ko'ina. A matuƙar tsorace Raudha tai saurin miƙewa tare da juyowa. Gabanta yay matuƙar faɗuwa saboda tozali da tai da shugaban ƙasa Ramadhan tsaye jikin ƙarfen benen hannayensa duk biyu zube cikin 3quarter wandonsa. Fuskarsa kicin-kicin yana watsa mata wani irin kallo da batasan a wane aji zata fassarashi ba. Saurin maida kanta ƙasa tai da ga barin kallonsa, yayinda ruɗanin da kunyar kayan dake a jikinta suka hadu suka dabaibayeta, ta naɗe duka hannayenta a ƙirjinta tana shafa damtsen hannunta dan son bawa jikinta kariya. Kayan barci ne masu santsi da taushi baby pink color. Wando iyakarsa gwiwar ta, hakama rigar mai kamar best sai dai hanunta nada faɗi, ba wata babba bace, dan ta mata ɗas a jiki tamkar saida aka gwadata akayita, sai gashin kanta dake ɗaure a tsakkiya da ribbon yana reto. Raudha tanada gashi mai ƙyau, duk da kuwa bawai yanada tsaho kalar da za'a ce masa irin na indiya ko turawa ba. Sai dai a cikin mutane irinmu dole ne a kirata mai baiwar gashi musamman a yanzu da ya samu gyara na musamman da kulawa wajen Feena a gidan aunty hannah lokacin training ɗin da akai mata, sai ya kara ƙyau da zama abin kallo dalilin halittarta nada alaƙa da jinin larabawa, dan kafin auren bata taɓa sakama kanta relexer ɗin ba. Kokawa yake da zuciyarsa da idanunsa da ga barin kalonta amma ya kasa, damin kuwa ALLAH ya azurtata da abinda yake matuƙar so ga diya mace. Tun Ramadhan na yaro yana matuƙar son gashi, dan yana ɗaya daga cikin abinda ya ƙara shaƙuwarsa da Anne cikin ƙanƙanin lokaci a wancan lokacin. Anne nada gashi sosai, haka zai zauna yayta jagwalgwala mata shi wai yana mata kitso ko tsifa. Har ya shiga secondary school bai daina zaman taya Anne tsifar kai ba dan kawai ya samu damar wasa da shi........ “In... Ina yini”. Raudha ta katse shi da ga shagalar kallonta. Komai baice mata ba, sai dai ya janye idanun nasa a kanta. Bata taɓa jin ya amsa mata gaisuwa ba, dan haka yanzu da bai amsa ɗin ba bata damuba ta fara hawowa steps ɗin cike da tsoro da kunya da nufin komawa ɗakinta. Tazo gab da shi zata gitta a bazata taji saukar muryarsa cikin kunnenta babu zato. “Mike damunki?”. Duk da ahankali yay maganar bata hanata jin tasirinta cikin zuciya da ɓargon jikinta ba. Kanta dake ƙasa ta girgiza masa, cikin ƙoƙarin danne kukan dake taso mata tace, “Babu komai”. Komai bai sake ce mata ba, sai ma raɓawa da yay ta gabanta ya koma inda ya baro. Bata cigaba da tafiyar ba har sai da yakai zaune da kusan minti biyu. Sum-sum ta nufi hanyar bedroom ɗinta batare data yarda ta dubesa ba hawaye na rige-rigen sake sakko mata saman kumatu. Daga inda yake zaune, ƙwayar idonsa ta bita da kallo harta shige. Idanun ya maida ya lumshe tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya ya lafe jikin kujerar yana kokawar danne abinda ke taso masa.... ★★★ Tun daga wannan ranar Raudha da shugaban ƙasa basu sake haɗuwa ba. Sai dai kamar kwankin baya, takanji shigarsa da fitarsa gida. Dan takan jima batai barci ba. Takai ko dare ya raba bai shigoba sai taji shigowar tasa. A haka suka kuma shanye satin ya zam satinau uku da aure da kuma shiga gida gwamnatin. A safiyar juma'a kusan 12pm na rana sai ga su Aunty Hannah a bazata harda Hajiyar birni sun kawo mata ziyara. Harga ALLAH taji matuƙar daɗi da yin farin ciki, duk da tsananin tsoron al'amuran aunty Hannah a yanzun. Sun samu tarba ta mutuntawa a gareta dama ma'aikatan gidan. Dan Mama Tambaya ce tsaye kan komai har sai da taga kuku ya wadata gabansu da abinci na musamman da abin sha. Bakin Hajiyar birni har kunne tanata zuba santi yau gata a fadar shugaban ƙasar NAYA. Kuma jikarta ke amsa sunan matar gidan, ƴarta matar vice president, kai wannan daɗi ya mata yawa. Ta kama Raudha ta rungume tanata saka mata albarka ko damuwa da ramar datai babu wanda yayi. Raudha taji daɗin ganin Yasmin da yayunta su Fatisa. Har su fatisan ke faɗa mata aunty Halima zata wuce da su gidanta a Bina su koma makaranta. Hakan ya mata daɗi, dan dama bata son zaman su Fatisa a Bingo hannun su Hajiyar birni gudun kar a saka rayuwarsu a garari kodan rawar kansu, saboda mummynsu bata da wani ƙarfin iko akan komai. Babu abinda zaman nasu zai amfana musu sai ƙara lalacewa duk da taga kamar sun ɗan nutsu yanzu tun sakin da Abbansu yayama Mummy. Batai ƙasa a gwiwa ba wajen roƙon Hajiyar Birni a bar mata Yasmin anan. Babu wanda yace mata komai akan hakan, sai ma hajiya mama data wani taɓe baki da hararta. “Oh saboda ita kaɗai kuka haɗa uwa da ita? Yanzu Raudha har idonki yayi buɗewar raba ɗayan biyu tsakanin Yasmin da su Noor?”. Kai Raudha tai saurin girgizawa, “Lah a'a wlhy Hajiya mama ba haka bane, dama so nake naji idan za'a barmin Yasmin ɗin sai nace itama Noor a bani tunda Asim shi namiji ne”. Hajiya Mama zata sake magana aunty Hannah ta katsesu. “To inaga mubar maganar haka sai munje gida ma tattauna. Sai itama Asabe a kirata idan ta amince”. Badan Hajiya mama taso ba tai shiru. Daga haka suka cigaba da hirarsu har lokacin salla yay Raudha ta kaisu ɗakinta dan suyi. Wasun su sunyi alwala wasu na ƙoƙarin yi Asim yace mata zai ƙara shan lemo. Da to ta amsa masa tana ɗan murmushi. Taja siririn gyalen jallabiyar jikinta ta yana ta fito domin ɗauka masa. Yau ne karon farko da tun zuwanta gidan ta nufi hanyar kitchen, badan ta tabbatar nan ɗinne kitchen ɗin ba. Sai dan taga tanan kuku ya dinga fito musu da abinci ɗazun. Tana ƙoƙarin ɗaura hanunta a handle ɗin ƙofar dake a rufe taji kamar ana magana a hankali, kuma kamar muryar Aunty Hannah data fito a ɗaki tun shigarsu tana amsa waya. Nutsuwa tai ta kasa kunnenta, sai ko tajiyo aunty Hannahr na faɗin, “Waɗan nan sune kalolin abubuwan da yafi sha kenan?”. Kuku ya amsa mata da faɗin, “Eh ranki ya daɗe. Amma kamar yanda na sanar miki har yanzu bai taɓa cin abincin gidan nan ba. Amma kullum akayo sharar sashensu nakanga alamar kwalayen anci nama musamman kilishi, sai kuma fura da naga yana shigo da ita da kansa duk bayan kwana biyu”. “Fura kuma?”. “Eh ranki ya daɗe”. “Okay hakan ba matsala bane. Zamuji daga ina ake kawo masa furan da naman ba damuwa. Yanzu dai daga yau duk bayan sati za'a dinga kawo waɗannan kalolin drinks ɗin zuwa nauyin kowanne milk cikin cefanen gidan nan idan zakayo. Sai ka kula sosai wajen zubasu a iya fridge ɗin da yake mu'amula da shi. Maganar abinci kuma zan saka matarsa ta kula da shi akan cinsa dan muna buƙatar ya dingaci ɗin, dan muna buƙatar waɗan nan abubuwan su dinga tasiri a cikin jininsa a hankali yanda babu wani likita da zai iya fahimta da wuri sai dai a ɗauka diabetis ɗinsa ce”. “Okay Ma baku da matsala da hakan, dan ɗazuma nayi magana da Aunty (forma first lady, ƙanwar mahaifiyarsa ce, uwa kenan take a wajensa, kuma tun yana ƙarami itake tsaye kan karatunsa saboda mahaifiyarsa ta rasu wajen haihuwarsa, a hanun mamarsu first lady ɗin ya tashi ma. Aikine dake buƙatar sirri, shiyyasa ta ɗorasa akai gudun kar aci amanarsu ko a samu matsala. A haka ma akwai abinda ya sani da ita aunty Hannah ɗin bata sanshi ba). Ta ƙaramin bayani sosai dama akansu ɗin da yanda zai dinga amfani da shi a abincin nasa musamman ma shayi. Amma na mata complain akan matarsa, tace babu damuwa itama koda taci”. Ɗan jim Aunty Hannah tai, sai kuma ta ɗan ɗaga kafaɗa da taɓe baki alamar ko'a jikinta inhar burinta zai cika na ganin mijinta a kujerar shugaban ƙasa wataran. “Ba damuwa idan tacin itama kamar yanda first lady ɗin ta faɗa. Sai dai ka kula, ba kowanne ma'aikaci bane namu a cikin ku, sannan wanda suke namun ma da ga kai sai Tambaya kuka san sirrin aikin da kukeyi”. “Okay Maa. I promise bazaku taɓa samun matsala daga gareni ba kuma kun sani, Aunty Bushira tamin komai a rayuwa, miye amfanina idan ban saka mata da buƙatarta ba.” Da sauri Raudha taja da baya wani irin kuka na neman kufce mata, jitai bama zata iya ƙarasa ji ba, babu abinda kanta keyi sai sarawar tashin hankali. Bayan poison na ac bai ishesu ba sai sun haɗa da matakan ingiza ciwonsa, ya kamata tasan wane ciwo ne ke damunsa ma. Bata da tabbacin yunƙurin da tai akan matsalar ac ta karɓu, amma tana addu'a da fatan hakan dan tasan ta tura saƙonta inda da wahala a ɗaukesa shirme. Jin za'a buɗe ƙofar kitchen ɗin tai azamar rugawa karkashin ƙafar bene ta lafe har sai da aunty Hannah ta shige bedroom ɗinta na ƙasa da ta kaisu dan suyi alwala. dan bata kaisu upstairs ba sanin nan ɗin kamar sirrine na shugaban ƙasa. Sai da tayi ɗan kukanta mamakin aunty Hannah da dalilinta na son aikata duk wannan abubuwan na ƙara kumeta. Dan a iya hasashenta tarasa minene alaƙar aunty Hannah da shugaban kasa da har take gaba-gaba wajen yin haɗin gwiwa da wasu domin kashesa. A gefe kuma zuciyarta na ƙara ninƙaya wajen tunanin zancen farko na sakama shugaban ƙasa poison a cikin ac. Ga wani zasu dinga basa a abinci da drinks? Kai mutanen nan sam basu da imani wlhy. Amma insha ALLAHU ALLAH bazai taɓa basu nasara ba. Zatai iya bakin ƙoƙarin ta na ganin burinsu bai cikaba akan shugaban ƙasa kodan kyakywar zuciyar kakanninsa. ★ Da ƙyar Raudha ta iya danne komai dake a ranta har lokacin tafiyar su yayi, shatara ta arziki ta haɗama kowannensu daga kayan lefenta. Dan sune kawai take takama da su a gidan matsayin nata. Hakama Mummy da Aunty Halima ta haɗa musu tasu tsarabar. Ta rakasu har harabar gidan tana sharar hawaye. A dai-dai lokacin da motarsu ke fita a harabar farko na gidan motocin shugaban kasa da securitys nasa ke shigowa. Ko ba'a faɗa ba tasan shi ɗinne, dan haka tai shirin juyawa cikin gida tana ƙoƙarin amsa gaisuwar wasu a hadiman gidan da sai yanzu suka ganta. Shugaban ƙasa Ramadhan da tun tsayuwar motar tasu idonsa ya ganta ya bita da kallo a kaikaice batare da waɗanda ke a wajen zasu iya gane hakan ba. Zuciyarsa ke masa wasuwasi da tambayar su waye ɗin waɗancan da har zata fito rakkiyarsu har harabar gida?. Rashin mai amsa masa hakan ya sashi ɗauke idonsa a ƙofar data shige ya maida ga agogon hanunsa. Ƙarfe huɗu na yamma da wasu mintuna. Ya dawo gidane saboda yana son su fita ita da shi zuwa Taura house gaishe da su Anne. Wannan lokacin kawai ne da shi, gobe idan ALLAH ya kaimu zai bar ƙasar wani taron shugabannin Africa da za'ai a ƙasar Nigeria. Buɗe ƙofar ne ya saka Raudha dake kwance ɗagowa da sauri har gyalen kanta na zamewa ya faɗi, duk da shi ɗin ta tsammaci gani sai kuma duk ta ruɗe. Cikin in ina take masa barka da dawowa da gaishesa. Kamar kullum yauma bataji ya amsa ba, sai dai idonsa na kanta da har ya sata kasa kallonsa. “Nanda mintuna talatin zamu fita can gidan gaishe su.” Daga haka yaja jikinsa baya zai rufe ƙofar, dan dama tsaye yake a jikinta riƙe da handle ɗin. Yana gab da rufewa kuma sai ya sake buɗewa, da sauri ta ɗago sai suka haɗa ido. Cikin azama ta janye nata, yayinda shi kuma ya sake tsuke fuska da faɗin, “Karna sake ganin wannan gashin dokin a kanki ki ciresa” Babu shiri ta sake ɗagowa, sai dai harya maida ƙofar ya rufe. Hannu ta kai bisa kanta ta damƙo jelar gashinta dake ɗaure da ribbon, a fili tace, “Gashin doki kuma?”. Tai maganar da ɗan waro idanu waje tana miƙewa zuwa gaban mirror. Ribbon ɗin ta zare gaba ɗaya, ta shiga kallon gashinta da tattaɓashi kamar yau ta fara ganin nasa itama, kai kace so take ta tantance na dokinne ko natan?. Ta ɗan girgiza kai tana sakin murmushi, dan harga ALLAH ma dariya ya bata. Yayta wani cin fuska ashe idonsa nakan gashinta. “Kajimun mutum, kawai daga ganin gashi sai kace masa na doki sa'idiniyya”. Ta sake faɗa a fili tana murmushi. Maganar fitar da yace zasuyi zuwa Taura house ya sata maida ribbon ɗinta da sauri ta nufi hanyar toilet, dan ya kamata taɗan watsa ruwa. Harta shiga kuma sai ta fito dalilin qani tunani da yazo mata arai. Tare da tuna Mummynsu (Asabe) duk da kakarsu Inna ba cika son mahaifiyarsu tai ba a duk sanda zasuje wajenta ko ita wani abu ya kama zataje wajenta koda tare da su Larai ne sai ta sayi wani abun takai mata. Tun tana mata irin wannan ƙyautar tana rainawa da kiransa neman suna har kowama ya fahimci hakan yana daga cikin kyawawan halin Asaben duk da kuwa take tujararriya. Raudha tai murmushi dajin ƙara son mahaifiyar tasu a cikin ranta. (Haka rayuwa take, duk mugun halin bawa sai ka samesa da wani ƙyaƙyƙyawan halin tare da shi koda baida yawa. Hakama duk ƙyaƙyƙyawan halin mutum sai ka samesa da mummuna. ALLAH ya bamu ikon yin ƙyawawan halaye da ƴaƴanmu zasuyi koyi). A cikin sauran kuɗin data rage ta ɗauka wasu ta fita. Duk da zuciyarta ta gama raya mata daina yarda da duk ma'aikatan gidan hakan bai hanata fita neman mama tambaya ba. Cikin sa'a ma sai ta sameta a falon farko zaune tana kallo. Da sauri ta miƙe ta nufota tana faɗin, “Ranki ya daɗe in buƙatar ganina kike ai basai kin sakkoba, sai ki kirani ta telephone kawai”. Komai Raudha batace ba sai ɗan murmushi datai mata da miƙa mata kuɗin hanunta. “Mama zan iya samun kilishi mai ƙyau nan da mintuna sha biyar?”. “Insha ALLAHU ranki ya daɗe zaki samu, dan kuwa sana'ar yarona ne, kum anan yake gab damu ba nisa”. “Yauwa to Alhmdllhi, gashi yaymin kashi kamar.....” ta ɗanyi jimm tana hasahenshen yawan manyan gidansu Ramadhan ɗin. “Yauwa bakwai. Sai kuma wannan idan za'a samu goro mai ƙyau shima a siyamin”. Mama tambaya ta amsa tana faɗin, “Insha ALLAHU duk za'a samu ranki ya daɗe”. Har cikin rai Raudha taji daɗin hakan, ta jiya cikin da sauri. Maimakon ta shiga wankan sai ta buɗe akwatinan lefenta. Duk da tasan sune suka haɗo hakan bai hanata zaɓo turaruka masu ƙyau da daɗin ƙamshi kala biyu ba. Ko ba'a faɗaba tasan zasuyi tsada matuƙa. Ta ajiyesu saman mirror sannan ta koma wajen kayan khumrah ɗinta dake cikin ɗan show glass tana kallo. Taja kusan sakan talatin kafin ta far ɗaukarsu tana dubawa. Aunty Halima ce tai matasu dukansu, Haɗi ne na musamman da ga *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* ƙamshinsu kawai ya isa sanar da mai shaƙa an kashe ingantattune kuma nagartattu. masu ƙyau da daɗin kamshi ta ɗiba kala uku-uku, sai dai kowanne da kalar kamshinsa, sai turaren wuta kala biyu shima ta ɗiba kashi-kashi duk ta ajiye. Ganin kamar lokaci ya ɗan ja ya sata saurin faɗawa bayi, a gurguje ta gyara jikinta ta fito. Tana cikin shiryawa taji ɗan ƙarar bell ɗin dake tabbatar da ana jiranta a ƙasa. Hijjab tasa ta fita dan tana ƙyautata zaton mama tambaya ce. Ilai kuwa itace da ledoji riƙi-riƙi. Raudha ta amsa tana mata godiya tare da ajiye mata kuɗin data fito da su a hannu. Godiya mama tambaya taitayi duk da ba wasu masu yawa bane............✍ *_Mu mun tafi Taura House. Dan kunsam nice zan zama cos ɗin shugaban ƙasa. Idan aka hananu kuma hummm basai na faɗa ba dai🤧🚶🏻_* *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/17, 1:36 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62aafdab52e2996a61a92f3d *_Episode 30_* .........Cikin sauri-sauri Raudha ta sake packaging ɗin komai yanda ya dace. Sannan ta ƙarasa shirinta tare da saka hijjab ɗinta mai hannu daya je har gwiwa, yasha karin guga sai ɗaukar ido yakeyi. Duk wanda ya kalleta yasan tayi ƙyau kodan shigar mutunci da tayi, duk da tasan da ga mota sai gida. Ɗauke da manyan souvenirs bags guda uku ta fito a hannu, sai ƴar side bag ɗinta dake rataye a gefen kafadarta. Bata saka turare mai karfi ba, dan sai kazo gab da ita zakaji sanyin ƙamshin khumrah ɗinta da na turaren da tasa.         Kusan a tare suka fito daga corridors ɗin bedrooms ɗin nasu, shugaban ƙasa Ramadhan dake sanye cikin shadda blue ɗinkin half jamfa yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Har cikin rai yaji daɗin ganinta da Hijjab, duk da gashinta da batasaka ɗan kwali ba ya fito ta gaba kaɗan saboda zamawa da hijjab ɗin yay baya. Baiyi magana ba, duk da yana da bukatar ta ɗaura ɗan kwalin, sai dai girman kan nasa da ganin idan yay mata magana kamar zubar da kai ne ya sashi zaɓar yin shiru, cigaba yay da takowa cikin falon cike da mazantaka da salon tafiyarsa da mutane da yawa suke fassarashi da mai girman kai. Hular kansa ya ɗan sake gyarawa dai-dai yana gittawa ta gabanta. A tare ƙamshin junansu ya dinga rige-rigen shiga hancinansu.      Maimakon Raudha taga sun fita ta ainahin downstairs ɗin da zai kaisu ƙofa sai gani tai yabi ta hanyar da yake shigowa gidan, nanma kuma dai benan ne yay ƙasa zai kaika ƙaton faluka har biyu kafin ka fita baki ɗaya, sai dai a gefe akwai wani ƙarami na hutawa shima. Bayansa tabi, koda ta fito sai taci karo da falukan da sukafi waɗan can da take gani kullum haɗuwa. Wajen ya matuƙar kayatar da ita, hakama harabar wajen dan tana ganinsa ta windown ɗakinta. Sai dai bata taɓa gigin ko tunanin zuwa ba, tunda batasan ta ina zatabi ba. Da alama fitar tasu ta sirri ce, dan mota biyu kawai ta samu a tsaye alamar suna jiransu. Kuma driver ne kawai sai securitys biyu. Cikin matuƙar girmamawa suke gaishesu ana buɗe musu ƙofofin bayan security ɗaya ya amsa kayan hanunta ya nufi booth. Shi ya fara shiga sannan itama ta shiga cike da fargabar ganin duk a baya zasu zauna kenan.       Fitar ma ta karamin gate dake wajen sukabi, kanta dake ƙasa yasa batasan taya suka ɓullo kan titi ba. Tafiyar mintuna ƙalilan ta kawosu katafaran gidan na Taura house. Kai tsaye motocin a ƙofar sashen su Anne suka tsaya, kasancewar ana kiraye-kirayen sallar magrib ita kaɗai ta shiga ciki, shi kuma suka fita massallacin ƙofar gidan.          Sosai Anne dake ƙoƙarin fita da ga kitchen zataje ɗakin don gabatar da salla tai mamakin ganin Raudha, dan yanzu babu jimawa ta gama waya da Ramadhan. Sai dai sanin halinsa na zurfin ciki ya sata ture mamakin ta maye gurbinsa da farin ciki. Dan sosai taji daɗin ganin Raudha ɗin har fuskart ta kasa ɓoyewa.        A tare suka gabatar da sallar magrib a bedroom ɗin Anne. Bayan sun idar suka sake gaisawa. Sosai Raudha kejin daɗin zama da tsohuwar. Mutum ce ita mai cikakkiyar kamala da dattako, ga tsafta da mutunci. Ko kaɗan rashin sakin fukar Anne bai damun Raudha, dan ta fahimci anan Ramadhan ya ɗakko rashin walwala da sake fuska, da kuma wajen mahaifiyarsa, dan itama ta lura gwanar ɗaurewace.        Fitowarsu falo tayi dai-dai da shigowar Bappi riƙe da hanun Ramadhan. A kallo ɗaya zaka fahimci ɗunbin shaƙuwa da ƙaunar dake tsakanin jikan da kakan. Shima Raudha ta gaisheshi cike da girmamawa. Amsa mata yake da fara'a da ƙauna. Sai sanya musu albarka yake tare da addu'oin zama lafiya da zuri'a ɗayyiba. Daga haka suka ɗan cigaba da taɓa hira har aka kira sallar isha'i.          Bayan sun dawo daga masallaci mai aikin Anne ta shirya musu abinci a dining. Tuwon shinkafa da miyar kuɓewa ɗanya da man shanu. Sai gasashiyar hanta da taji kayan lambu. Anne dake duban Shugaban ƙasa Ramadhan daya ɓata fuska tai murmushi. Tasan hakan nada nasaba da ganin miyar ƙubewa dan bayaso.         “Anneee!”.   Ya faɗa a tunzure. Sai da taɗan gintse fuska tace, “Lafiya!”.       “Ki bani fura”. “Saboda anyi maƙiyarka kuɓewa”. Sake cuɗe fuskar yayi fiye da farko. Bappi ya kauda kai gefe yana murmushi.        Kujera yaja baya zai miƙe Anne tace, “Malam koma ka zauna”.      Yanzun kam tamkar zai fasa kuka, ba Bappi ba hatta Raudha dariya ya bata, to ashe ba ita kaɗaice ta tsani miyar kuɓewa ba tanada ɗan uwa. Sai dai ta kula nashi har yafi nata. Salamar mai aikin Anne da sauke tiren da take ɗauke da shi ya saka Ramadhan dakatawa da ga maganar da yay niyya. Tana barin gurin Anne ta tura trayn gabansa. “Kure uban ƴancin nama sai kaita kaya gashi nan”.            Kamar bazai kula ba sai kuma yakai hannu a nutse ya buɗe kwanikan guda biyu. Ɗaya gasashen kaza ne a ciki, ɗayan kuwa farfesun naman kai. Zaman Raudha a wajen ne ya hana bakinsa buɗewa. Amma duk da haka sai da yay ɗan ƙunƙunin da Anne tasan mi zai iya faɗa. sai dai bata kulashi ba ta maida hankalinta ga Raudha.           “Aminatu zuba abinci mana”.    Cikin jin kunya Raudha tace, “Anne na ƙoshi ALLAH”.       “Tab anan gidan? Aiko bazai yuwu ba. Inma tuwonne bakiso ai ga nama nan. Ko kuma ki faɗi abinda kike so a girka miki”.        Da sauri Raudha tace, “A'a Anne wannan ma yayi”.         “To Alhmdllhi, kinga juya kuci naman gashi nan wajen mijinki, dan nasan kema dai kwanan nan zai koya miki kurancinsa.”         Ƴar dariya Bappi yayi yana kallon Ramadhan ɗin da tuni ya fara kai laumar naman duk da akwai zafi. Ita dai Raudha batai gigin saka hannu ba. Sai dai ta zuba tuwon leda ɗaya. Maimakon miyan ƙubewan saita ɗan saka gasashen hantan a gefe ta dingaci da shi a haka. Ko tari shugaban ƙasa Ramadhan bai sakeyi ba, sai da yaji yayi nak da naman kazar nan sannan ya turama Raudha ƙasusuwa da fiffike sai wuya. Duk yanda taso daurewa kasawa tai, ta ɗago tana masa kallon mamaki, a bazata ya wani kashe mata ido ɗaya ya ɗauke kansa.      Wani irin muguwar ƙwarewa Raudha tayi, dan harga ALLAH salon nasa yazo mata a bazata da sakata a wani yanayin ruɗani. Anne ce ta bata ruwa, shiko sai ya ɗauke kai ma. Ko sannu da suke jera mata shi baiyi ko guda ba. Anne na niyar masa magana Bilkisu ta shigo falon. Haka take kullum tana nane da tsoffin, shiyyasa bayan Ramadhan itace ta biyu da suke matuƙar so da ƙauna a jikokin nasu.         Da sauri tazo ta rungume Raudha tana farin cikin ganinta. Sai kuma ta koma shagwaɓan miyasa Anne bata kirata ta sanar mata Yayan nasu yazo da Raudha ba tun ɗazun.       Anne tai mata daƙuwa da faɗin, “Kinci gidanku, tunda nice bbc uwar magana ko? Yanzu da kikazo bagasu kin gansu ba. Kimaje da ita ta shishshiga ta gaida iyayen naku”.         Bilkisu ta amsa mata da “to”. Bayan Raudha taba Anne da Bappi tsabansu ta ɗauka sauran ita da bilkisu suka fita. Sashen su Yafendo suka fara zuwa. Inda tsoffin sukai mata tarba ta mutuntawa. Basu wani jimaba sosai ta basu tsarabansu suka fito.          Sun shiga sashen Gimbiya Su'adah suka tarar tana salla. ƴammatanta kuma duk suna ɗakunansu. Dan haka Bilkisu ta bata shawaran su je su gaida su Ammy to. Bata musaba suka fito zuwa sashen Hajija Mufida. Itama dai ta tarbesu kadaran kadahan. Raudha bata damu ba suka ajiye mata tata tsaraban suka fito. sashen hajiya Shuwa suka shiga, sai dai sun iske tana wajen Pa dan itace da girki. Can ɗin suka nufa suma. Pa ya tarbi surukar tasa da kulawa. Yayinda itama takai duƙe gabansa tana gaisheshi da girmamawa shi da Hajiua Shuwa dake gefensa.      Shima dai addu'ar zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba yay musu, yayinda Hajiya Shuwa ke tayasa da Amin da murmushi yaƙe. Dan harga ALLAH matan na Pa na matuƙar jin kishin duk abinda ya shafi Ramadhan a gidan bisa dalilai masu yawa. Sun kusa mintuna goma sha biyar kafin su fito domin komawa sashen Maa.         Da sauri Lubnah dake dakon fitowar tasu ta koma ciki tana sanarma gimbiya Su'adah. “Maa gasu nan yi maza ki zuba tsakin kukar a burner, shegiya mayya zamuyi maganinta yau ai. Idan ma shi Yayan ta lashe masa kurwa mu tamu bazata lasu ba”.           Dai-dai gimbiya Su'adah na rufe murfin burner ɗin Raudha da Bilkisu sukai sallama. Gimbiya Su'adah bata amsa ba, sai Lubnah ce ta amsa cike da isa tana wani yamutse fuska kamar maijin warin kashi.       Raudha takai tsugunne tana gaida surukar tata, yayinda hayaƙi mai haɗe da yaji-yaji ke sake tasowa cikin hancinta. Cikin ƙarfin hali da dauriya ta juya tana gaida Lubnah duk da a yanda gimbiya Su'adah ta amsa mata. Tsaki Lubnah taja mata. Bilkisu tace, “Kai Aunty Lubnah gaishekifa tayi”.        “To dan uwarki bazan amsaba ko dole ne? Shegiya uwar shishshigi, ki cigaba da nane mata ta lasheki”.          Raudha da tuni numfashinta ya fara fisga saboda hayaƙin tsakin kukar tai ƙoƙarin jan bakin hijjabinta zata toshe hannci amma ta kasa. A take jikinta ya fara rawa. Maimakon ganin yanayin nata yasa gimbiya Su'adah fahimtar akwai matsala sai zuciyarta ta raya mata yanayin Raudha na tabbatar da itaɗin mayyace kamar yanda lubnah ta faɗa. Murfin burner ɗin ta buɗe ta sake matso dashi gaban Raudha.          Raudha ta miƙe tsaye da sauri tana ƙoƙarin buɗe baki tayi magana sai ta kasa, da sauri-sauri numfashinta ke ja, laluben bag ɗinta data manta ma tana sashen Anne ta shigayi a ƙoƙarin ta na ɗaukar inhaler ɗinta, amma ya gagara. Sai ma baya datai luuu. Tabbas taji ta faɗa jikin mutum, da ga haka bata sake sanin mike faruwa ba....        Shigowarsa ɗakin yayi dai-dai dayo baya da Raudha tayi zata zube ƙasa saboda numfashinta daya dunƙule a ƙirji ya kasa isa huhunta balle yazo maƙoshinta ta fitar kota shaƙa. Mamaki ne ya kamashi, amma sai yay dauriyar tallafota da ƙyau jikin nasa saboda jin yanda take ɗin tamkar kokawa da numfashinta.         Kafin yayi wani yunƙuri Bilkisu da tayo wani uban tsalle ta dire a gabansu cikin rawar jiki take faɗin, “Ya ALLAHU. Aunty Raudha lafiya?!”. Kakarin azabar jan numfashi da Raudha keyi cikin ficewar hayyaci ya saka Bilkisu saurin faɗin, “Yaya kodai tanda Asthma? Tabbas Asthma ne, kuma ina ƙyautata zaton wannan abunne ta faɗa tana nuna burner ɗin itama tana kare hanci” shi kansa daba Asthmatic ɗin ba yana shigowa abun ya fara hawa masa kai. Dan haka bai jira wani ƙarin bayani ba ya ɗauka Raudha dake gab da rasa numfashinta ya fice da ita a ɗaki.         A rikice Anne da Pa da Bappi dake falo suna hira da cin kilishin da Raudha ta kawo musu suka miƙe suna tambayar lafiya!. Bai samu damar amsa musu ba, ya shimfiɗe Raudha bisa doguwar kujera. Bag ɗinta dake ajiya ya fusga ya fara zazzagewa. dan yasan inhar asthmatic ce ita baza'a rabata da yawo da inhaler ba. Ilai kuwa sai gata ta faɗo. dan itace kawai a ciki ma sai turare da sweets.       Girgizawa yay sannan ya tallafo kanta ya matsa mata a baki. Da ƙyar ta iya zuƙa kaɗan, sake matsa mata yayi, ta shiga da ƙarfi kasancewar numfashinta da ya fara fisgowar dawowa. Matsowa Anne tai ta zame mata hijjab ɗin gaba ɗaya, sai Raudha ta samu damar sauke numfashi da ƙarfi.          A hankali Shugaban ƙasa Ramadhan ya kai zaune a kujerar kusa da ita yana dafe kansa da rumtse idanu, ya huro iskar bakinsa. Shi kansa sai yanzune ya samu damar sauke kakkauran numfashi.      “Garin yaya haka ta faru? Dama tanada Asthma?”.         Maimakon Ramadhan ɗin ya bama Anne datai tambayar amsa sai Bilkisu ce ta ɓige da bada amsar. “Wlhy Anne Accident ɗin ya faru a sashen Maa ne. Saboda wani turaren wuta da suka saka. Yanayinsa zaisa dole mai Asthma ya samu attack gaskiya.”        Babu wanda ya sake cewa komai, sai sannu da suka shiga jerama Raudha ɗin. Shiru babu wanda ya biyo bayansu daga sashen gimbiya Su'adah har kusan mintuna arba'in. Hakan ya bama su Anne mamaki, sai dai basuyi magana ba. Pa da yasan ƙiyayyar da matar tasa kema surukar tasu ransane ya ɓaci. sai dai komai baiceba. Ganin Raudha ta dawo normal harta tashi zaune sai ya sake miƙewa ya nufi sashen mahaifiyar tasa somin gaisheta.         Yanayin sallama a falon sukai shiru daga taruwar zaman zagin Raudha da sukai, Lubnah na sake tabbatar musu mayyace ai. Tunda gashi ansa tsakin kuka a wuta ta kasa zama. Basma ce kawai babu dan tana ɗaki tamayi barci batasan bidirin da akeyi ba.       Komai baice musu ba, duk da baiji akanmi suke ƙus-ƙus ɗin ba ya wuce bedroom ɗin mahaifiyar tasu. Itama acan tararwa yay tana waya da Adda Asmah tana sanar mata sun tabbatar Raudha mayyace yau. Sallamar tasa baisa ta dakata da wayarta ba sai da ta kammala. Sama-sama ta amsa masa gaisuwarsa kafin ta rufesa da masifa, tare da jadada masa su Lubnah zasu dawo zama tare da su domin su saka mata ido akan Raudha karta lashe mata shi dan yau ta sake tabbatar da Raudha ɗin mayya ce. Tunda gashi nan ta saka tsakin kuka a wuta Raudha ta kasa zama a sashenta. Komai baice da itaba har tayi ta gama. Ya bata haƙuri sannan yay mata sallama ya fito.     Koda ya dawo sashen su Anne bai zauna ba yace Raudha ta tashi su wuce. Sabuwar gasassun kajin da Anne tasa aka gasa aka kawo musu tare da fura da farfesun naman kai da shugaban ƙasa Ramadhan yace a saka masa a cooler zaije da shi.       Har bakin mota Bilkisu da Anne sukai mata rakiya, itako tanata musu godiya. Shiru motar babu wanda yake ko ƙwaƙwaran motsi har sukai ƴar tafiya. Shugaban ƙasa Ramadhan dake lafe jikin kujera idanunsa a lumshe yace, “Dakata anan”.       Gangarawa drivern yay gefen titi kaɗan, yayinda Raudha ta ɗan dubesa a sace dan catake barcima yakeyi. “Malama bada kuɗin nawa kilishin”.      Sam Raudha batai tunanin da ita yake ba, amma sai ta ɗan juyo ta dubesa. Dai-dai ya buɗe nasa idanun shima da ɗan karkato kansa gefenta suka haɗa ido.           “Kina zaton zaki sayama kowa ne ni na haƙura”.       Ƙasa tai da kanta mamakinsa na neman hakalata. sai kuma tai saurin cewa, “To ai ban fito da kuɗi ba ALLAH”.      Kamar bazai tanka ba, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ya kwantar yana lumshe ido kamar yanda yake da. “Ba damuwa zan ara miki, idan munje kiban abina”.      Yanzun ma dai sai da ta sake kallonsa saboda al'ajab. Bata ida narkewa da al'amrin nasa ba sai da taga ya miƙama driver atm ɗinsa batare da ya buɗe idon nasa ba.           “Na nawa zaki siyamin?”.    (Ya ALLAHU, mutumin nan so yake ya kasheni). Raudha ta faɗa a cikin zuciya. Kafin a fili cikin fisgar numfashi tace na “10k”.      Yasan driver yaji kuɗin, dan haka ya faɗa masa pin ɗin atm ɗin har yanzu yana a yanda yake. Shiru motar ta sake ɗauka Raudha nata juya al'amarin a ranta har driver ya dawo da kilishin.       Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan, kamar yanda suka fita ta barauniyar hanya tanan suka dawo. Raudha ce ta amshi ledar kilishin, shi kuma ya ɗauki saƙon Anne, duk da driver yaso dauka amma ya hanashi. Suma securitys ɗin sun gwada amsa ya hana nan ma. Suna shigowa ya miƙa mata hannu alamar ta bashi. Babu musu ta miƙa masa. Ya ajiye mata na Annen. Ciki-ciki yace, “Raba ki ɗau naki, ki kuma kawomin kuɗina”.         “Na bar maka”.    Ta faɗa kanta a ƙasa ganin zai wuce riƙe da kilishin da aka sakata saya dole.         “Oh nice”. Ya faɗa a daƙile yana dawowa baya ya ɗauka kulolin biyu. Sai da yaje gab da corridor ɗin ɗakinsa ya sake faɗin, “Wannan ƙyautar bashike nufin zan yafe kuɗi na ba fa”.          Karon farko da lamrin nasa ya sakata sakin murmushi, ta ɗan girgiza kai tana nufar nata hanyar ɗakin itama. Tana shiga batai ƙasa a gwiwa ba ta ɗakko sauran kuɗin da suka rage mata. 10k ta irga ta fito. Karo na farko a zamanta gidan ta nufi corridor ɗin da bedrooms nasa suke. Rasa gane wanda yake a ciki tayi, taita canki canka. Daga ƙarshe dai ta yanke shawarar yin knocking ɗin na ƙarshen. Tayi knocking kusan sau uku babu alamar akwai mutum, har zata juya na kusa da shi sai kuma aka buɗe ƙofar.             Saurin yin ƙasa tai da kanta gabanta na faɗuwa ganin da gashi sai guntun towel. Jikinta naɗan karkarwa da tsuma ta miƙa masa kuɗin. Komai baice mata ba ya amshe abinsa ya maida ƙofar ya rufe. Da sassarfa tabaro corridor ɗin zuwa nata bedroom ɗin, tana shigowa ta zube a gado dan jitake kamar numfashinta na sizing..........✍          *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* [6/20, 8:00 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62ac32dac3c5aa93405acd94 *_Episode 31_* ..........*_WASHE GARI_* koda Raudha ta farka a barcin safe data koma ta samu Ramadhan ya wuce. Cikin mamaki takebin kulolin jiya da Anne ta zubo musu nama a ciki da kallo. Ta miƙe da ƙyar tana cire hijjabin sallarta dan akan sallaya barcin ya kwasheta tana azkar. Kulolin ta nufa. Ya cinye farfesun naman kan tas sai ƙasusuwa. Kazar kuma kusan ɗaya da kwata. Sosai mamakin hakan ya rufe Raudha, shiko wane irin kuren nama ne haka? Sai kace ya haɗa iri da mayu (😱😝 Raudha ta rama bani ba). Ta ɗan girgiza kanta zuciyarta na raya mata da alama dai ba shikaɗai bane akwai aljanun cin nama tare da shi. Da wannan tunanin ta nufi toilet. Wanka tayo da brush, bayan ta fito ta kimtsa jikinta da ɗakin. Itama kular sauran naman ta ɗauka da nufin ci duk da yayi sanyi kaɗan sai taci karo da takarda guntuwa da ATM card. Ɗauka tai ta ƙarasa kan sofa sannan ta buɗe takardan. Pin ɗin atm ɗinne a farko. Sai gajeren rubutu da bai wuce words goma sha biyu ba. *_(Anne zata aiko da sabuwar mai aiki, tare da masu zuwa miki yawo)_*. Shike nan abinda ke jiki, sai wani ɗan zane kamar emoji data gagara gane ma'anarsa.            Saƙon ta dinga maimaitawa a zuciyarta, haka kawai take jinsa da girma. Tasan dai Anne bazata kawo wadda zata cuta mata ba, sai waɗanda zasu zo mata yawon ne take ɗar-ɗar, dan inhar yaran gidan ne akwai matsala kenan.       Duk yanda taso samun nutsuwa ta gagareta, dan hankalinta bai tashi ƙololuwa ba sai dai baƙin nata suka iso har su biyar. Aina'u, Lubnah, Basma, Bilkisu, Muneera. Ta gane Lubnah ta kuma gane Aina'u. hakama Basma da Bilkisu da sukazo cike da murna suka rungumeta.. Su Aina kam suna mata wani kallone kamar trash. Dan Lubnah harda faɗin, “Kurwarmu dai ɗacine da ita, kar aga mun dawo kusa ai tunanin nama yazo. Wlhy mutum yace zaici ya taɓoma kansa mutuwa ne kawai”.        “Tuna mata dai”. Cewar Muneera. Komai Raudha batace musu ba. Sai gaishesu da tayi. Duk da basu amsa mata ba sai ta danne. Falon tsakkiya ta nufa inda tacema mama tambaya a gyara musu ɗakunan ciki. Mama Tambaya tai ɗan jimm kafin tace, “Amma ranki ya daɗe kodai ɗakunan falon farko zaifi, dan falon tsakkiya dana karshe da upstairs ke ce kawai keda hurumin yin huɗɗa da shi. Sai ko idan kunso kai baƙi masu muhimmanci ”.      Murmushi Raudha tayi, “Mama waɗan nan ma ai sunada muhimmanci, dukansu ƙannen mai gidan ne”. Daga haka ta juya ta koma ciki.        Sai dai kuma mi, koda aka gyara ɗakunan tsakkiyar sai su Lubnah sukace bazasu zauna anan ba sama suke so. Kobi takan Raudha da roƙon da Basma da bily ke musu basuyi ba suka nufi saman. Corridor ɗin ɗakinta suka nufa, duk bedrooms ɗin sai da suka buɗesu kowa ya zaɓi ɗai-ɗai. Da Aina ma na Raudha ɗin tace tana so, sai da Lubnah ta jata gefe ta raɗa mata wani abu a kunne sannan ta canja dana kusa da ita. Dama 4bedrooms ne, dan haka su uku kowa ta ɗauka guda.       Mama Tambaya zatai magana Raudha ta hanata, dole tai shiru. Koda Basma ta kira gimbiya Su'adah ta sanar mata sai ta hau banka mata zagi akan ina ruwanta, tunda can ɗin sukeso basai a barsu ba, daga ƙarshe taja mata gargaɗinta bayan ita takira wani ta sanar masa sai taci ubanta. Kuka sosai Raudha ta shiga ɗaki tayi, sai dai a gabansu bata yarda murmushi ya bar fuskarta ba.          Abinci da kansu suka bama kuku umarnin abinda za'a dafama kowannensu, Raudha dai batai ko tari ba, hasalima tunda ta shige bata fitoba sai da Mama Ladi ta iso. itace Anne ta aiko ta zauna da ita. Tayi hakane kuma domin ta dinga koyama Raudha abubuwa masu muhimmanci dan ta kula ba komai Raudha ta iyaba kasancewar mu ƴaƴan talakawa munada ƙarancin wayewar wasu abubuwan irin na masu hannu da shuni. A wahalar rayuwa da ilimin zaman cikinta kuwa duk da Raudha nada ƙarancin shekaru tanada wayo saboda irin rayuwar data tashi a ciki.       Mama Ladi mace ce wayayya dan tayi iliminta na addini dana zamani gwargwadon iko. Ƙaddarar rayuwa da jarabawar iska yasa bata zaman aure. Tayi aure yafi sau uku mazan na rasuwa. Wannan yasa ake gudunta a garin Taura. Harta kai ko gittawa tai ta waje sai a dinga gudu. Abin ya isheta ta tattara kayanta zata gudu a garin tsautsayi yasa Alhaji Basheer Taura (Pa) ya bugeta da mota lokacin yazo Taura ɗin. Taji ciwo sosai, dan haka ya kaita asibiti, bayan tayi jiyya ta warke sarai yaji matsalarta. Daga nan ya kaita family house ɗinsu na Taura ta zama shugabar ma'aikatan gidan tana kula da komai da kowa. Amanarta da iya mu'amula yasa suke ƙyautata mata sosai. Wanda ma bai sani ba yakan ɗauka ƴar uwarsuce a yanzun.         Maimakon sashen ma'aikatan gidan a falon farko Raudha tasa aka bata ɗaki. Hakan yasa su Lubnah basu san da zuwan mama Ladi gidan ba. Duk da ba wani damuwa sukai da ita ko a Taura ɗin ba. Hasalima yanda suke ƙyarar masu aiki da hantararsu haka sukema mama ladi itama                          ★Ranar da su Basma sukazo government house gimbiya Su'adah ta nufi masarautasu dake a jihar Bina. A can ta samu Adda Asmah na jiranta, dan dama haɗuwar tasu akan Raudha ce dai da suke kira karamar alhaki ta kuma zame musu damuwar zukata. Bayan sun samu shiga sashen mai-martaba suka gaisheshi sai suka ɗan shiga sashen tsohuwar kakarsu dake fama da jiyya kusan shekara bakwai kenan. Sun duba jikinta itama kafin su koma sashen fulani. Dan a tsarinsu sauran matan sarki basu ishesu kallo ba balle gaisuwa. Shiyyasa sam babu haɗin kai tsakanin yaran gidan tunda suna kallon su gimbiya Su'adah dake amsa sunan manya basu mutunta iyayensu da jansu a jiki balle su ƙanana.         A babban falon kusa da fadar fulani suka yada zango, bayan sunci sun sha gimbiya Su'adah ta labarta musu yanda sukai da Raudha akan turaren tsakin kuka.        Adda Asmah taja tsaki cikin ƙyaɓe fusaka da takaici take faɗin, “Kuji makirar yarinya, to ai tasha a no-no ke kuwa ai dole. Jinin karuwar gogaggun duniya ai dole tayi makirci irin haka wai Asthma ta tashi..”       “Humm ki bari kawai Adda. Babban abinda ya ban takaici da ƙonan zuciya yakema bisa kan sake ƙonamin har yanzu wai ko kunyar idona Ramadhan bai gani ba ya ɗauka yarinyarnan cikin rawar jiki ya fita da ita saboda shi fitsararrene...”       “Karkiga laifinsa Su'adah. Ke kina ganin zasu barsa hakane babu wani ƙulli? Kinsan kuwa wacece hajiyar birni? Gogaggar karuwa uwar karuwan manyan ƙasar nan. Yo uwar karuwan manyan ƙasa mana, tunda kuwa ƴaƴanta harda uwar yarinyar sune hajarta a wajen manyan ƙasar. Dan an tabbatarmin harda aurensu bin maza sukeyi”.         “Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un. Wlhy Adda sake firgitani kikeyi”. Gimbiya Su'adah ta faɗa cikin nuna razana da tashin hankali.      Kafin Adda Asmah ta sake cewa wani abu Fulani dake waya tun dazun ta ajiye wayar tana maida hankalinta garesu. “Ita hajiyar birnin har wacece ita, har mi akai akayita. Ai wlhy lokacin da kuka kawomin labarin tushen yarinyar ma sam ban kawo Hajiya Ɗahare bace hajiyar birnin, da ko aurenki zai mutu Su'adah bazan yarda da wannan kwamcalar haɗin ba. Dan nasan baku manta wata shegiyar karuwa da mukaita kicimillin raba mai-martaba da ita ba shekara ashirin da ɗaya kenan”.        Cikin zaro idanu waje su duka har haɗa baki suke wajen faɗin, “Ammy wai kina nufin matsiyaciyarnan data like masa a loss lokacin ana shirye-shiryen basa mulki”.      “Ƙwarai kuwa ita fa, to itace hajiyar birni kakar wannan shegiyar yarinyar da aka mannama Ramadhan.”       Sosai tashin hankali ya bayyana a garesu, dan su ɗin shaidane akan wahalar da iyayensu mata musamman mahifiyarsu taci a wancan lokacin. Ko randa kakansu ya rasu mutane nata raɗeraɗin da karuwa mahifinsu yazo da ga loss. Sakamakon acan yake aiki. Ba kowa bane kuma face hajiyar birni. Bayan an bashi sarauta ma tasha kawo masa ziyara a ɓoye kamar yanda sukeji, harma ya furta cewar zai aureta shaƙiƙan dattijan masarauta sukai masa kacaca, aka kuma saka masa ido matuƙa har sai da aka rabashi da ita.      (Kowa yasan mahaifinsu mai-martaba na yanzu mutum ne da dama bayajin magana tun ƙuruciya, dan ita kanta fulani dake wannan babbotan adai rufe rufau, akwai babban akasin daya faru tsakaninta da mai-martaba ɗin tun tana ss2 secondary, bayyanar abin kunyar daya ƙunsa mata yasa iyayenta saurin zubar da shi aka rurrufe akai musu aure ya wuce da ita ƙasar waje sukaci gaba da karatu a can. Dan dama shi acan ɗin yake, wani zuwa hutu da yay ya ganta daga haka yayta jan ra'ayinta da soyayya har ya ƙunsa mata ciki. Gashi kuma ƴar uwarsa ce, dan kuwa ɗiyace ga ƙanwar mai martaba mahaifinsa kenan, kuma ƴar waziri ta wancan lokacin. Amma sai gashi yau duk sun manta da waɗan nan ta murje ido tana faɗin munin wani harda nuna ƙyamarsa.          Wannan tunani na Fulani akan hajiyar birni kakar Raudha ya sake tada hankalin su gimbiya Su'adah. Duk da dai ita Addah Asmah tanayin komai ne dan ƴarta Aina, gefe kuma ga tsananin hassadar ƴar uwarta da take fama da ita shekaru aru-aru na finta da mijin nunawa sa'a. Dan kuwa Taura family sunfi family ɗin da take aure komai, shiyyasa take son ƴarta ta shiga gidan kodan su mallaki abinda ƴar uwar tata ke taƙama da shi, musamman daya kasance Ramadhan shine jika ɗaya namiji tilo a zuri'ar Alhaji Hameed Taura. Wanda ko a yanzu ALLAH kaɗai yasan iya abinda yake mallakinsa kodan kasancewarsa ɗan gaban goshin kakanin nasa. A gefe kuma shima ba azaune yake ba yana kan neman na kansa ne. Adda Asmah tasha saka gimbiya Su'adah a hanyar banza, sai dai ALLAH ya timaketa tana saurin gyara kuskurenta saboda samun tsayayyen miji irin Pa da tuni ya gama gano wacece yayar matar tasa. Sai dai bai taɓa gaya mataba gudun shiga tsakanin ƴan uwan juna.       A take anan Adda Asmah ta gama tsara musu dolene wannan al'amari a haɗa da malamai gaskiya, Fulani ta amince, Gimbiya Su'adah dai tana ɗan janjeni, dan kuwa ita dai barta da ƙasaita da isa harma da rashin mutunci, amma bata yarda dabin malami ba. Shiyyasa anan ɓangaren kam basa shan inuwa ɗaƴa da adda Asmah ɗin..       “Su'adah kinyin shiru! Ko baki amince ba ne?. Idan baki aminceba bawaifa dole bane, sai dai fa ki tabbatar Ramadhan ya sake miki nisa na har abada. Dan a baya gwara tunda a gida ɗaya kuke kina ganinsa yana ganinki, sai dai kawai an rabaki da shi bai miki kallon uwarsa sai kakanni ya ɗauka iyayensa. A yanzu ko ku dukane zaku rasa harsu karuwar su ɗauka. Dan kuwa dai sune masu amfana tunda ƴarsu yake aure.....”         Wani dogon numfashi da ya katse Addah Asmah a magana Gimbiya Su'adah taja da ƙarfi, tuni idanunta sun kaɗa sunyi jazur saboda damuwa da ɓacin rai. Ji take tankar ta haɗiyi zuciya ta mutu dan baƙin ciki. “Adda dan ALLAH kibar wannan mugun fatan, dan wlhy inhar ina raye har gaban abada babu su babu wannan nasarar akansa. Ni kin sanni kawai dai bana son harka da maƙaryatannan, dan bokaye da malmn tsubbun nan mafi yawanci lokaci abinda suke faɗa ƙaryace kawai, sai dai aci maka kuɗi a barka sakarai”.        “Bazan musa miki akwai irinsu ba, amma kema kinsan namu ba irin waɗan nan bane. Kuma ni da Ammay dai bazamu cutar da ke ba balle Ramadhan. Mu dama hausarmu anan muje musa a masa roƙon ALLAH ya karesa daga sharrinsu. sannan muɗau mataki kar yarinyarnan ta samu ciki, mu kuma dawo da hankalinsa kan Aina'u dan ɗanmu ya dawo hanunumu baki ɗaya”.       Numfashi gimbiya Su'adah ta kuma ja a hankaki, kafin tace, “To shikenan na amince aje ɗin, amma gaskiya sai dai a samu wani amintacce yaje ni dai bazanje ba dan Abbansu ba yarda zai ba”.      Fulani dake matuƙar jin takaicin ƴar tata Su'adah ta balla mata harara. “Tunda ke ɗin shashasha ce sanar masa zakiyi zakije wani waje. Wai nikam Su'adah yaushe zaki san ciwon kanki? Anya kuwa Basheer haka ya barki kuwa? A haka dai duk wanda ya ganki sai ya ɗauka wata jarumar gaske ce, sai dai basu san ƙatotuwar shashasha bace ba”.        Ƙin cewa komai gimbiya Su'adah tayi, sai dai ta sake ɓata fuska alamr maganar mahaifiyar tasu bai mata daɗi ba. Haka suka sake ƙulla abubuwa daban-daban harda maƙudan kuɗaɗen da za'a kaima malaman wanda kaso biyu bisa uku Adda Asmah duk cutarsu tayi kawai. *_BINGO. GOVERNMENT HOUSE_*           Gaba ɗaya zaman gidan ya sakema Raudha tsanani tun zuwan su Lubnah, ga damuwar zancen aunty Hannah da kuku da taji shima ya kasa barin ranta. A wajen su Bilkisu kawai take samun sauki. Su kuma suna fita school tunda safe sai yamma suke dawowa. Duk da suma dai su Lubnah ɗin na fita aiki, Aina'u ce kawai bata aikin uwar komai sai kallon series kullum a lap-top. Sai ko gantalinta da samari dan a yanzu haka duk hanyar da zatabi ta sani na zuwa club da dare. Shiyyasa bata sakewa. gidan su Ramadhan idan tazo, saboda su dokane da 6 na yamma tayi aka kwaso yaran gidan daga islamiyya babu mai sake fita sai safiyar gobe. Kuma duk inda zaka sai dai driver ya kaika ya dawo da kai.                 Kwanan Ramadhan biyu ya dawo NAYA daga taron da suka gudanar a ƙasar Nigeria. Duk da dawowar rana yayi bai shigo gida ba, kai tsaye office ya wuce su Raudha ɗin ma a labarai sukaga dawowar tashi. Har kuma suka kwanta barci bai shigoba alamar wani abun ya tsayar da shi wanda bazai wuce zaman meeting ba.       Ilai kuwa hasashen haka yake, dan kuwa dai zaman meeting ɗin sukai da su forma president anan cikin gidan akan son sasantawa game da batun cabinet daya sharɗanta yarda da 50-50 akan zaɓin shugabannin majalissa. Sai dai kuma a yau ɗin ma babu nasarar, dan kuwa dai Ramadhan yana akan bakansa. Da ga ƙarshe rai ɓace aka watse babu abinda aka cimmawa. Shima kansa rai ɓacen ya dawo gidan, dan haka baibi takan kowa ba yay shigewarsa ɗakinsa.       Sai dai kuma kamar koyaushe dawowar tasa ta wanzu ne a kunnen Raudha dake zaune tana karatun Al-qur'ani bayan ta idar da salla. Agogo ta kalla, ƙarfe biyu saura. Taja numfashi zuciyarta na mamakin yanda al'amrin ke tafiya. Dama haka mulkin yake mutum ko lokacin kansa baida shi?. zata iya rantsewa tunda suka tare a gidan nan sau uku kacal taga ya dawo gida kafin takwas na dare. Sai ko randa suka fita ɗin nan daya shigo kusan biyar na yamma. Bakinta ta ɗan taɓe ta cigaba da karatunta zuciyarta na raya mata *_BAƘAR INUWA_* kennan. Gara rana da ke. Dan zama a ƙaton gida da cin mai daɗi da sunanka babba a ƙasa ne kawai jin daɗin. Talakan dake cikin waccan ranar yama fi mai mulkin jin daɗin duniyar. Tunda koba komai shi zai shigo ya huta a gidansa kan lokaci. Yaci yasha hankali kwance tare da iyalansa. Amma gasu anan kullum cikin haɗa tuggun yanda za'a halaka rayuwarsu akeyi. Bashi dake mulkin ba ba ita ƴar karoro ba dake amsa sunan matarsa.        Koda ya kimtsa jikinsa duk yanda yaso kwanciya kasawa yay, dan yunwa yakeji sosai. Rabonsa da abinci tun breakfast na bankwana da sukayi a Nigeria shi da sauran shugabanin ƙasashe da suka halarci taro. Ga kansa na ciwo ga ɓacin ran da aka ƙara masa yanzun. Siririn tsaki yaja yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa, kafin ya tura lip ɗin nasa cikin baki ya fara tauna a hankali har sannan idonsa na a lumshe. Dan kwance yake a saman katafaren gadonsa da yaji lafiyayyun shimfiɗu na alfarma. Ƙafafunsa a ƙasa suke yana rigingine, sai filo da yay da hannayensa. A hankali ya buɗe idanunsa dake cike da gajiya da barci. ganin agogon na ƙara gudu ya sashi miƙewa ya fice a ɗakin, dan yafi buƙatar abinci mai nauyine baya son shan kowanne juice ko milk.      Yasan bai dace yace zaije kitchen nema abinci ba, dan haka ya nufi ɗakin Raudha kai tsaye duk da zuciyarsa batason aikata hakan kuma.........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/21, 11:49 AM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62b0ba6cf0deac225fe20185 _________________ KWANGILA COLLECTION 🌺🌺 Assalamualaikum tallah maganin watarana komi ake buqata da akeso asiya ku kira lambarnan kaway inshallah zakusamu,07046881166 Shin kinshafa Mai kinyi duhu har kinajin kunyar duban kanki a madubi? Kokuma sokike kiyi haske kiyita walwali kowa yadinga santinki?ga hadin set dinmu me bala'in kyau inkikayi amfanidashi kinrabuda kowani irin matsala ta fata insha Allah chat 07046881166. Matsalarki t zamantakewar aurene kinkasa gamsar d miji? Infection ne matsalarki ko budewar gaba kokuma,bushewa,kimin mgana yar uwa,07046881166. Uwargidaye d amare kinaso duk Wanda yazo dakinki yatafi yana zancenshi da fadin allahunma arzuqni? Munayin frames tsala tsala n daki da madubai donsawa a falo bbu ruwanki d (nunamin daki inga fuskata) kede kira wannan number 07046881166 Munada kayan Yara masu kyau masu inganci duk kushewarki d Kaya namu bazaki iya tafiya kivarsuba,kisawa yaro/yarinya sufito kmar dangin ashwariyya nemeni t wannan number 07046881166 Sekuma duk abinda kikeso d bamu lissafaba zaki iya turomana mu Nemo maki mesauqi dakuma qarko, Duka kayanmu suna zuwane a farashi sari kayanmu nada arha matuqa kizo ki kwashi garavasa,mesiyan daya daya ko sari duk muna marhabun daku, 07046881166 nagode senajiku🥰 _______________________ *_Episode 32_* ..........Buɗe ƙofar ya saka Raudha saurin juyowa dan batai tunanin ganin wani ba a wannan lokacin. Su Bilkisu ne dama dai ke shigo mata a kwana biyun nan, tasan kuma yanzu sunyi barci. A bazata ta ɗan waro idanu waje, domin ganin abinda batai zato ko tsammani ba. Tunda bai taɓa mata hakan ba...       Ɗauke kanta tai da ga garesa da sauri, ganin ya cigaba da takowa cikin ɗakin kuma idonsa a kanta ko ƙyaftawa bayayi. Kayan barci ne jikinsa farare tas, wandon har ƙasa, hakama rigar mai dogon hannu ce. Ko ba'a faɗaba kallo da ga nesa zaisa ka fahimci zasuyi taushi kayan. Duk da kasancewarsa farin mutum kuma badan kwalliya ba sai da suka masa ƙyau. Sai da ya ƙaraso gaban gadonta ya dauke idanunsa a kanta ya koma bin ɗakin da kallo kamar yau ya fara shigowa ciki, hannayensa dake zube cikin aljihun wandon pyjamas ɗin nasa ya zare sannan yakai zaune a bakin gadon.        Mamakine ya sake turnike Raudha, sai dai babu damar yin magana ko neman dalili. Sosai fuskarsa ke a cinkushe babu ɗigon fara'a, wanda yay masa ma farin sani yana ganinsa zai gane ransa a ɓace yake.          “Sannu da zuwa”. Raudha ta faɗa a hankali kamar mai raɗa. Sai dai hakan bai hanashi jinta ba. Amma maimakon ya amsa mata sai jeho mata furucin data kasa jurewa sai da ta ɗago ta dube...      “Bani abinci”. Shine abinda ya fito a bakinsa batare da ya damu da girman mamaki da maganar zata zo wa Raudhan ba. Bawai dan bai isaba, sai dan ba haka ya saba ba. Batama tunanin ya taɓa cin abinci a gidan kamar yanda kuku ya faɗa.      “Kallona zaki tsaya ko abincin zaki bani?”.      Tsam ta miƙe har tana bige ƙafa da gado. Ta matse ido raɗaɗin na ratsata ta fice zuciyarta na gudu-gudu fiye da takun kafafunta. Ita yanzu ina zata nemo abinci 1 harya gota? Tasan dai kuku yayi barci. Ƙwalla suka cika mata idanu, amma sai ta haɗiyesu tana ƙoƙarin sauka downstairs.       Turus ta ɗanyi ganin Bilkisu zaune a falon duk da dai babu haske mai yawa, iyakar lamp ne na gefen kujera kawai. Amma hakan bai hanata ganinta ba. Ta baje books da takardu saman centre table da taja gaban kujerar da take zaune. Itama Bilkisun a ɗan firgice ta ɗago, sai kuma taja ajiyar zuciya da ɗan shafa ƙirjinta. Da'alama da farko tsoro taji, farin glass ɗin idonta ta zare tana faɗin, “Aunty lafiya bakiyi barci ba?”.      Raudha ta ƙarasa takawa inda take, “Ke ya kamata na tambaya aunty Bilkisu, ko tsoro bakiji ke ɗaya anan?”.       “Karatu nakeyi aunty, cikin ɗaki Basma ta hanani yi a nutse da gurnanin barcinta. Shiyyasa na dawo falon. Kuma banji tsoro dan securitys ma ai gasu nan sunata kai kawo a compound”.     Kai kawai Raudha ta gyaɗa mata, dan tasan gsky aunty bilyn ta faɗa. Haka securitys ɗin gidan ke kwana tsaye kamar zasu iya tare mala'ikam mutuwa ɗaukar ran wani a gidan.....        “Aunty ko baki da lafiya ne?”. Bily ta katse tunaninta.      “A'a lafiyata ƙalau. Abinci yace zaici shine zan duba. kitchen”.      Ɗan jimm Bilkisu tayi dan da farko bata gane wa Raudha ke nufi ba, sai kuma ta ce, “Oh ko Yaya ya dawo ne?”.        Kai Raudha ta jinjina mata cikin ɗanjin nauyi, dan Bilkisu ta girmi su Fatisa ma ba itaba. Bilkisu tai ƴar dariya. “Oh yanzu a daren nan kuma?. Amma bana tsammanin abinci a gidan nan. Ya kamata kema dakin ajiye masa tunda kinsan komi dare zai shigo”.      To kawai Raudha tace. Dan bayan hakan bata da abin faɗa. Taya zata zauna fadama Bilkisun ɗan uwansu bai taɓa cin abinci a gidanba. Ita huɗɗa makamanciyar wannan ma bata taɓa haɗasu ba. Kitchen ɗin ta nufa, ganin hakan yasa Bilkisun bin bayanta. Komai sun buɗe babu wani abincin arziki da zasu bashi ya ci, dan haka Bilkisu ta bata shawarar su dafa masa wani abu kawai mai ɗan sauƙi. Ba musu Raudha ta amince, abinka da na'urorin dake sauƙaƙa aiki, cikin abinda bai ƙulla awa guda ba suka haɗa masa abinci mai sauƙi da Bilkisu tasan bazaiyi ƙorafi ba. Raudha ta haɗa komai a wani ɗan basket mai ƙyau ta ɗauka suka fito. Sama ta nufa, Bilkisu ma sai ta hau tattare komatsanta domin komawa ciki ta kwanta haka nan...          Saɓanin yanda ta barsa zaune yanzu a kwance ta samesa saman gadon, sai dai ƙafafunsa duka biyu na a ƙasa cikin tttausan slippers ɗinsa bakaƙe da suka sake haska ƙafar tasa. Yaja karamin filo ya saka kansa, amma duk da haka sai da ya tallafe kan da hanun haggunsa. Na damar kuma nakan cikinsa riƙe da hisinil Muslim ɗinta daya kifa saman cikin. Kamar yanda Raudha ta zarga barci ne ya fara figarsa, sai dai tana buɗe ƙofar ya farka dan dama bai nisa ba. Amma sai bai motsa ba harta ƙaraso gabansa taja table dake can gaban sofa ta ɗora basket, duk da bata da tabbacin anan ɗin zaiyi zaman ci.       Sai da ta kai durƙushe sannan tace, “Ga abincin”.      Shiru kamar bai jita ba, harta fara tunanin ko barcin nasa yayi nauyine. Tana shawarar yanda zata tadashi sai taga ya motsa hanunsa, littafin ya ajiye gefensa kafin ya tashi zaune da kyau. Fuskar ta ƙara tsukewa fiye da farko alamar dai yunwa nacin bawan ALLAH da ba wasa (😹🤭😝lol).          “A zuba?”. Ta tambaya cike da taraddadi. Mai makon ya amsa mata sai ya zuba mata hararar da ta sakata fara buɗe bowl ɗin da suka zubo abincin babu shiri. Ya ɗauke kansa kamar bai lura da yanda hanunta ke ɗan rawa ba. Ji yake ma kamar ya mangareta, ga takaicin kansa ya ishesa. Dan sai yanzu yake ganin kamar ya zubar da ajinsa ne. (Malam shugaba da baka san da ajin ba sai da kaga girki a gabanka🙄😝😂?).          Yana ganin tanata zubawa bai tsaidata ba, sai dai ta zuba mai isarta da take zaton zai cinye sannan ta mike zuwa karamin fridge dake a ɗakin nata ta ɗakko bottle water ta buɗe ta tsiyaya a karamin glass cup data haɗo da shi ta ajiye masa ta miƙe. Shi dai tuni ya fara cin abincinsa ma.       Har ya kammala cin abincin natsuwa na saukar masa bai sakejin motson Raudha mai ƙarfi ba. Shi yama zata kwanciya tayi, sai da ya ɗan waiga ya ganta a inda ya shigo ya same tana cigaba da karatun Al-qur'aninta. Sai dai kuma harga ALLAH barci takeji, amma batasan taya zata kwanta yana a ɗakin ba.     Koda yaji uwar hanjinsa ta ɗauka baiyi yunƙurin barin ɗakin ba, sai da ya sake share kusan mintuna ashirin a zaune yana cigaba da karanta hisunil Muslim ɗinta da ya sake ɗauka. Hammar da yaga ta jera kusan sau uku a jere ya sashi mikewa riƙe da littafin. Ta bishi da kallo dan ko inda take bai kalla ba har yaje ƙofa. sai da ya kama handle ɗin zai murɗa ya furta kalmar “Thanks ”. Tamkar mai ciwon baki.        Ƙincewa komai tai itama, dan Raudha badai zuciya ba. Hakan ya sashi waigota lokacin da yake saka ƙafarsa ɗaya waje. A mamakinsa sai yaga kanta duƙufe akan Al-qur'anin duk da kafin ya waugo ɗin yana jin idanuntane a kansa. Lip ɗinsa na ƙasa ya kamo da haƙori ya tura cikin baki tare da cijeshi da ƙarfi, kafin ya galla mata hararan ‘Wannan abar ko’ ya fice yana ƙwafa.       Tanajin ya rufe ƙofar itama ta sake ɗaggowa ta dallama ƙofar harara da murguɗa bakinta. Kafin ta rufe Al-qur'anin ta cire hijjab ta haye gadonta bayan ta kashe filar ɗakin gaba ɗaya tabar lamp na gefe side drawer ɗaya kawai. Dan kayan da yaci abincin ma batabi takansu ba tunda tasan bata da ƙarfin kaisu kitchen. ★★            Tun da ga wannan ranar Raudha bata sake sakashi a idonta ba, sai dai ta gansa a television, kai ko ƙannensa dake a gidan bata tunanin yama san da zamansu. Oho ita ina ruwanta, a ganinta wannan matsalarsa ce shi da su.         Kamar ko yaushe tana yawanyin baƙi, dan yau data kasance alhamis ma ta samu baƙuncin wasu matan gwamnoni guda huɗu. Dukansu manyan mata ne da zasu iya haihuwarta koma yin jika da ita, amma yanda suke mata kalamai cikin girmamawa da kwantar dakai batasan ta dinga tsinewa da tsige mulki da siyasa a zuciyarta bama. Yo banda mulkin babu ta yanda waɗan nan natan zasu iya ko kallonta. ƴar aikisun ma sun fita shekaru, ilimi, wayewar rayuwa, da ma ta siyasar. Amma dan abun kunya sunzo gabanta suna damunta da wani your excellency da ranki ya daɗe. Taja tsaki a ranta tana ƙarajin takaici da bama inuwar muliki suna BAƘAR INUWA.      A ɓangaren shugaban ƙasa kuwa ya sake komawa matuƙar busy. Dan abubuwane birjik saman kansa musamman na talakawansa da suka zuba ido da kunen sauraren farajin naɗe-naɗen muƙamai, tunda sunsan wannan hanyarce kawai shimfiɗar fara musu aiki. Anan kuma cikin gida gasu tsohun shugaba ƙasa sun tasashi gaba akan tursasashi amincewa buƙatunsu kamar yanda god father's nasu ke control nasu suma a bayan fage. Sai dai taurin kai da tsaurin ido na Ramadhan ya sashi jajircewa akan maganarsa ta farko na yarda da sharaɗin 50-50 amma ragamar zaɓin speaker na hannunsa. Sukuma sanin tasirin speaker ɗin a garesu yasa sukace sam bazata saɓuba. Ga list ɗin shugaban ƙasa na cabinet ɗin da suka kasance zaɓinsa duk yarane matasa da basu wuce talatin da biyar, arba'in zuwa ƙasa ba. Ma'ana duk sa'aninsa ne. Waɗan da zasu ɗara shekrunsa ƙalilanne.           Tabbas jayayyar ta fara gundurar manyan jam'iyyar, domin kuwa ta wani fanin a tsorace suke da dagiyarsa. Ba komai ya jawo hakan ba sai zuwansa ƙasar Nigeria. Dan bayan zaman tattaunawa da sauran shugabannin Africa da sukai a Nigeriar shugaban ƙasar Nigeria yayi zaman na musamman kuma na sirri da shugaban ƙasa Ramadhan ɗin. Kuma har zuwa yanzu babu wani bayani daya fita akan tattaunawar tasu ta ko wanne fannin na ƙasashen biyu.           Daga can bayan fage kuma god father's nasu na cigaba da shirye-shiryen tsara ta yanda za'a halaka dattijon arziki alhaji Hameed Taura da suke kallon shike bada gudunmawar kafiyar Ramadhan kai tsaye.      To bayan dai an turza an kuma turzo dole su Alhaji Usama suka amince suka sakarma Ramadhan tashi jayayyar badan yafi ƙarfinsu ba, sai dan akwai wata a ƙasa. Bayyi wani farin ciki ba, dan yasan a yin hakan da sukai kwai manufa mai ƙarfi. A cikin kwanki uku kacal da amincewar tasu akai zaɓen fidda gwani a majalissa. Dan sai da sune za'a gabatar da jerin subayen cabinet na shugaban ƙasa dama duk wasu muƙamai daya shirya tsaf.         Duk da akwai ɓoyayyen zaɓi hakan bai hana bama ƴan majalissa damar yin zaɓen fidda gwani ba akan speaker ɗin ba, daga ƙarshe dai dole aka nuna zaɓin bayan fage badan hakan shine fatan wasu ƴan ƙasarba da ma wasu a cikin ƴan majalissar, musamman da ya kasance babu wanda yasan da ainahin speaker ɗin sai da akaga sunayensu. Dan haka zaɓin ya bama kowa matuƙar mamaki da sanya mafi yawan al'ummar ƙasar NAYA farin ciki da sake ganin kimarsa. Musamman matasa da aka ɗakko matasa ƴan uwansu da ko'a wajen zaɓe ma ba'ai tunanin zasu kai labari ba amma aka aza a kujerun guda biyu da bayan kujerar shugaban ƙasa sai su a faɗa ajin ƙasar, dan kuwa duk matasane suma masu ƙwazo da aka zaɓesu da yaƙini tun daga jihohinsu. A ɓangaren manyan kuma da shugabannin jam'iyya hakan yayi matuƙar ƙona ransu da sakejin tsanar Ramadhan. Taya zai ɗakko yara ƙanana ya ɗora kan shugabancin manya, bayan ga wanda ma suka haifi ubanninsu a wajen ba'a su ba. Wannan zaɓin speakers yasa a ranar sau kusan uku jam'iyyar da shugaban ƙasa ya fito suna zaman meeting wanda ko guda a ciki ba'a gayyaci wani na jikin shugaban ƙasar ba kuma.       Raudha kanta da basanin minene siyasa ko mulki tai ba zaɓin ya mata ɗari bisa ɗari. Ta kuma sakasu a cikin addu'ointa sosai akan ALLAH ya cigaba da tallafa musu wajen ɗaura mutanen kirki bisa muƙaman da dole sai dasu ne mulkinsa zai tafi cikin nasara da sauke hakki.      Bayan fidda speakers shugaban ƙasa ya cigaba da wasu naɗe-naɗe da suka shafi office nashi da suka sake bada mamaki, masu bashi shawara akan fanoni da dama na mulkinsa da sauransu akwai manyan dattijai da akasan su akasan jajircewarsu wajen faɗar gaskiya da yin gaskiya akan ayyukansu da ma tsaurinsu. A zaɓin nasa ya kasance akwai matasa masu jini a jika irinsa ya muƙar sake ɗaukar hankalin talakawan ƙasa a kansa, har yanda wasu ke nuna masa ƙauna ma sai ya baka tsoro. Yayinda dattijan ƙasar NAYA musamman waɗanda suka ƙwallafa rai a mulkin suka fara shaƙa daga takun na shugaban ƙasa, dan suna masa wani kallone kamar na TAKUN SAƘAr nuna kishin matasan ƙasar da mayar musu murtanin sun babake komai a baya suma. Hakan yasa ba ƴan jam'iyyarsa kawai ba, har wasu ƴan jam'iyyun da sarakunan gargajiya suna zaman yin meeting da tattauna take-taken Ramadhan ɗin.       Sarai yana jin wasu abubuwan dake faruwa, amm sai yay biris kamar kunnensa a toshe yake, idanunsa kuma a makance. Yay matuƙar maida hankali wajen tsara yanda yake buƙata a tantance masa cabinet nashi da taimakon mayan mutanen dake zagaye da shi na kirki duk da akwai masu fuska biyu kuma a cikinsu dai suma harma a matasan, kafin su amshi muƙaman da ake burin bama kowannensu.. _________★_________          A daren yau manyan dattijan nan, da al'amuransu ke keɓantattu ga al'ummar ƙasa sukai zaman tattaunawa na musamman a tsakaninsu, dan gane da ganin bayan Alhaji Hameed Taura, da zukatansu ke raya musu komai shugaban ƙasa Ramadhan yanayine bisa umarninsa. Wato a zahiri dai Ramadhan shine shugaban ƙasar NAYA, amma a baɗini Alhaji Hameed Taura shike mulki. kamar dai yanda suke ga sauran shuwagabanin baya, wanda shima Ramadhan ɗin haka suka tsara a kansa. Sai dai tun kan aje ko'ina ga komai na shirin sukurkurce musu.       A cikin tattaunawar tasu ne. Oga kwata-kwata ke ambaton “A wannan gaɓar ya kamata matar shugaban ƙasa ta nema office nata”.     Cikin mamaki sauran duk suka dubesa, dan sam basu fahimci muhimmancin yin hakan ba a garesu. Ɗan murmushi ya saki tare da ɗaukar kofin abinda ke gabansa ya zuƙa ya ajiye. Cikin ɗacin rai yace, “Na fahimci a yanzu da kujerar first lady kawai zamu iya fara yaƙar wannan yaron tunkan al'amarin nasa ya ƙara nisan kiwon da bola sai ta fimu daraja”.       “Amma ranka ya daɗe, ko ka manta first lady sweet seventeen ce. Sannan girman ƙawai, iyakar karatunta o level ne. Babu abinda ta taɓa sani a siyasa balle sha'anin mulki, rayuwarma yaushe ta gama fahimtarta?”.           “Duk wannan raunin nata ne ya sani tunanin a bata office”.      Shiru sukai suna sake ninƙaya a nazari, dan har yanzu basuga wani alfanun hakan ba a garesu sam sai tsagwaron kwamacala da shirmen da ƙasar tasu ke tunkara. To amma sun san halin oga da shegen zakule-zakule. Sai dai duk sanda ya zaƙulo abu zaka samu mai muhimmanci ne a garesu daga baya.... ★★★             A lokacin da suke can suna tattauna yanda first lady Raudha Dauda Hutawa data koma *_Raudha Ramadhan Taura_* zata mallaki Office, anan Taura House Ramadhan dake ganawar sirri da kakansa ke zaune a keɓantaccen falon baƙi na Alhaji Hameed ɗin suna tattauna muhimman batutuwa. A cikin tattaunawar tasu ne kuma Alhaji Hameed Taura yay ma Ramadhan batun saka Raudha a makaranta ta cigaba da karatu, dan hakan nada matuƙar muhimmanci a mulkinsa da ita kanta.       Ramadhan dake kai yankan kilishi bakinsa yay wani ɗan guntun murmushi da baida maraba da takaici, kafin cikin tausasa harshe ya ce, “Bappi wannan shi naso nuna maka akan auren nan. Taya za'ai shugaban ƙasa da mata mai matakin o lavel a ilimi, sannan ƴar shekara sha takwas tayi yarinta da yawa?”.         “Wannan duk ba damuwa bane Ramadhan, sai ma kafi jin daɗin control nata yanda kakeso, zakace nina faɗa maka nan gaba idan idanunta suka buɗe akan abinda kake ganin kai bazata iya ba”.        “To amma Bappi ni a wannan gaɓar ma banga amfanin yin karatun nata ba, dan nidai yanzu bazan bari ta ƙetare ƙasar NAYA ƙaro ilimi ba, sannan bani da sha'awar iyalina shiga harkar siyasar nan”.          “Sosai tunaninka ya sani farin ciki, sai dai kuma baida nasaba da daƙile mata zancen cigaba da neman iliminta. Ba lallai saitaje ƙetaren NAYA ba. A cikin ƙasar nan dama ya kama tayi, kai kanka hakan kimace a gareka, da ƙara bama talakawa hope game da mulkinka. Zata iya shiga duk jami'ar da takeso a ƙasar nan, kokuma tayi online school na ƙasashen ketaren inma suke take so, amma zamanta babu karatu bazai yuwuba. Koda bazata shiga siyasa ba akwai abubuwa da yawa da suke bukatarta a mulkin koda kai da ita baƙwa buƙatar ta kasance a cikinsu”.      Ɗan jimm Ramadhan yayi, sai kuma yaɗan ɗage kafaɗa da cigaba da cin kilishinsa. “ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi”. Kawai ya faɗa ya tsuke bakinsa. Shima Bappi komai bai sake cewa akan hakan ba. Bayan murmushi da yay ma sai ya ɗakko masa wani zancen daya shafesu kuma..........✍ [6/22, 7:58 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62b0ba6cf0deac225fe20185 *_Episode 33_* ..........Yau ta kasance asabar, Ramadhan na gida bai fita ko'ina ba, dan yana buƙatar hutu saboda doctor ɗinsa ya tabbatar masa sugar nashi yayi low, sannan jininsa ya haura sama alamar hayaniya ta fara masa yawa. Shawarar doctor yabi, dan ayanzu yana matukar buƙatar ganin ingancin lafiyarsa fiye da baya, kodan ya samu damar sauke hakkin mutane a kansa. Barcin safe yayi sosai har takai su Raudha basuyi tunanin yana a gidan ba.          Kusan sha biyun rana su Lubnah na baje a bedroom na sama, wanda a tsari shugaban ƙasa da iyalansa ne kawai keda hurumin zaman cikinsu. Zaune suke a baje kowa na sabgar gabansa, ga kayan ciye-ciye da suka saka kuku ya shirya musu, wasuko anyi order nasune a wajaje daban-daban. Su duka ukun babu mai shigar mutunci, daga mai bomshot da best sai mai 3quarter singlet.        A can falon ƙasa, wanda shine na uku a jerin faluka uku da kai tsaye zai kawowa sashen iyalan shugaban kasa Raudha da Basma da Bilkisu ne zaune. Bilkisu na daga gefe tana aikin nata na karatu da bincike-bincike, Basma da Raudha na kallo a lap-top ɗin Basma ɗin cike da shauƙin film ɗin. Sai mama ladi da ke gefensu tana saƙar hannu, wadda alama ya nuna kayan sanyi ne na yara. Sai dai rabin hankalinta nakan television da ake nuna maimaicin labaran daren jiya.        Sanye cikin ƙananun kaya nashan iska ya fito, baƙin trouser dogo mai layin fari guda biyu a gefe da gefe, sai baƙar t-shirt. Kayan sun masa matuƙar kyau kasancewar sa mai hasken fata, sai dai fuskar sam babu ɗigon fara'a alamar barcin da yay bai gama sakinsa ba, duk da dai dama bawai ya cika yin fara'ar bane sai ga wanda ya gadama.       Tsaf falon yake a tsaftace, ga wani ƙamshi na musaman na tashi mai saka nutsuwa da kwanciyar hankali. Da ga can gefe cike tebirin dining yake da kayan breakfast kamar yanda kuku bai gajiya da shiryawa a kullum, duk da bai taɓa ganin alamar wanda akeyi da shi yaci ba sai matar gidan kawai.           Duk da yunwar dake cin cikinsa, maimakon ya nufi dining ɗin kai tsaye sai ya samu ɗaya da ga cikin kujerun falon ya zauna. Yana ƙoƙarin kunna television su Lubnah suka fito daga corridor ɗin bedrooms na Raudha suna kwasar dariya.          Turus sukayi a tsaye suna duban wanda basuyi tunanin gani ba zaune hakimce a falon. Yayin da Ramadhan yay tsam shima domin shigar muryoyin dariyar ƙanen nasa cikin kunnensa da shi sam baima san da zamansu a gidan ba ko yace ya manta da batun zuwansu.. Duk da kuwa Maa ta jima da sanar masa zasu dawo nan da zama kafin ta dawo. Amma jin Bappi da Anne babu wanda ya masa maganar ya sashi ɗaukar mahaifiyar tasa ta janye batun duk da a yanzu haka tana ƙasar England ita da Pa.           A hankali ya ɗago idanunsa ya zuba musu, tare da watsa musu wani irin gigitaccen kallo daya gama kiɗima su gaba ɗaya har fitsari na neman kufcema wasun su, dan a rayuwarsa yayi matuƙar tsanar shigar banza. Shi ko akan iyalinsa ne bai cika son ganin matarsa da ƙananun kaya ba anyhow.       Sanin dokarsa ya saka Lubnah da Muneera kwasa a guje suka koma hanyar da suka fito, yayinda Aina ta daburce matuƙa, dan tun randa ya kamata a U.S tana aikata abinda bai dace ba suke wasan ɓuya, ta kuma haramtawa kanta zama duk inda zasu haɗun tunda ya dawo NAYA. Ko maganar haɗata aure da ake da shi, tana matuƙar buƙatar hakan, dan tana mutuwar son Ramadhan tunba yanzu ba, sai dai tana fargaba da sanin mawuyacin haline ya amince da aurenta, shiyyasa tafi yarda da zuga mahaifiyarta (Adda Asmah) akan tarwatsa auren Ramadhan ɗin kawai.        Tun kafin abinda ta hango a cikin idanunsa ya fita a fatar bakinsa ya sake gigitata ta kai durƙushe ƙasa, sai kawai ta tafi da rarrafe dan batasan taya zata miƙe ma tayi gudun ba tsabar rikicewa..              Wani irin numfashi Ramadhan yaja na tsananin ɓacin rai, lip nashi ya tura cikin baki ya cija da ƙarfi, yayinda zuciyarsa ke ambaton sunayen ALLAH domin son yin controling fushinsa. Tsahon mintuna biyu ya buɗe idanunsa, tare da miƙa hannu ya ɗauka telephone ɗin dake bisa copy table na kusa da shi. Sai kuma yay shiru da tunanin wayar ina zai kira?.          Telephone ɗin ɗakin Raudha ya kira. Sai dai harta katse ba'a ɗauka ba. Siririn tsaki yaja, tare da maida akalar kiran zuwa ta falon ƙasa, dan iya nan yasan zata iya zama inhar bata bedroom da nan falon upstairs                Da sauri Mama Ladi data ɗaga kira ta mikoma Raudha da suka maida dukan hankalinsu a kallo ita da Basma kan wayar. Ta ɗago da sauri tana duban mama ladi dake miko mata kan wayar, suma su Bilkisu ita suke kallo. “Ranki ya daɗe inaga daga sama ne kiran nan dan ba'ai magana ba”.       Komai Raudha batace ba ta kai wayar kunnenta da tunanin kosu Lubnah ne.           “Ameenatu! Ki sameni yanzun nan”.         Duk da ba kowa ke kiranta da wannan sunan ba hakan bai hana gabanta faɗuwa ba tai saurin duban Upstairs ɗin a ɗan firgice. Jin ƙarar ajiye wayar da yay ya saka Raudha mikewa har tana cin tuntuɓe da ƙafar Basma ALLAH dai ya hanata kifawa Bilkisu ta tareta.        “Yi a hankali aunty Raudha karki ji ciwo”.       Kai kawai ta iya jinjinama Bilkisun tai ƙoƙarin fara haura steps ɗin da ɗan gudu-gudu, duk da hakan bai hana bayyana nutsuwarta a tafiya ba, wadda ta zame mata halitta tun bayan da sayyadi Abubakar ya saita mata rayuwa.        Ramadhan dake zaton ganin bullowarta dama daga downstairs ɗin ya shiga watsa mata kallon da tunkan ta karaso hanjin cikinta suka fara barin jikin sauran kayan ciki suna kaɗawa. Tana masa kallon mutum mai ƙarancin kirki amma kallon da yake jifanta da shi a yau yayi tsanani da yawa, gashi batasan akan mi yake yi ɗinba kuma. Dan koda wasa bata taɓa kawoma ranta tunanin zaman su Lubnah a saman zai iya fusatashi ba tunda taga dai ƴan uwansa ne ai.               Bilkisu ta ture books ɗin gabanta ta miƙe da sauri tana gyara gyalen jallabiyar jikinta. Dan bata raba ɗayan biyu su Aina'u ne. Upstairs ɗin ta fara haurawa da sauri-sauri itama. Dan haka Basma ta miƙe tabi bayanta.             Hawowar su Bilkisu saman yayi dai-dai da ƙarasawar Raudha daketa ambaton sunan ALLAH gabansa, dan bata taɓa cin karo da irin kallon muzanci da yake mata ba a wajen wani mahaluki......        Turus Basma da Bilkisu sukai ganin wanda basuyi zaton gani ba suma. Dan duk zatonsu su Aina ne ai sukai kiran Raudhan ta landline. Ganin fuskar yayan nasu ya tada hankalin su Bilkisu dan kowa yasan idan yay fushi fita hayyacinsa yakeyi. Duk da dai basu san dalilin kiran Raudhan ba, amma tsoron da suka gani akan fuskarta ya sakasu shan jinin jikinsu suma. Cikin ƙarfin hali Bilkisu ta ambaci sunansa cike da ladabi da shakka.        “Yaya!”.   Wani shegen kallo ya watsamata itama, sai dai kafin yace komai wayar jikinsa ta hau ring. Yasan Maa ce, dan haka ya ɗaga yana jan numfashi da ƙyar tsabar ɓacin rai, baya raba dayan biyu su Muneera ne sukai kiranta. Ba wata magana ta bari sukai mai tsayi ba, dan bata bashi damar cewa komai ba ta yanke wayar.        Ransa ne ya ƙara ɓaci, Yana ajiye wayar Bilkisu data fahimci wadda ta kirasa saboda sunanta daya ambata a farkon wayar takai zaune gabansa a ƙasa. Cikin tausasa harshe ta ce, “Am so sorry Yayanmu. Wlhy ba laifin Aunty Raudha bane ba.....” tsaf ta zayyane masa komai a randa sukazo. Komai baice ba, sai dai ya tura hanunsa cikin gashinsa, tare da jingina bayansa da kujerar ya wani lumshe ido. Tsahon minti ɗaya kafin ya buɗesu a hankali suka sauka akan Raudha da Basma ta riƙema hannu gam-gam saboda lura da yanda jikinta ke rawa ɗazun. Tasan dolene taji tsoron yayansu a irin yanayin nan tunda ba taɓa gani taiba maybe, kosu da suka saba gani a duk sanda ya birkice irin haka tsananin tsoronsa suke.          Janyewa yay ya maida ga Basma. “Kiramin su”.      Kanta ta jinjina masa, kafin ta zare hanunta da cewa “To”.      Da hannu ya nunama Raudha kujerar gefensa. Zama tai a ɗarare tana cigaba da ambaton sunayen ALLAH.      Babu wani jimawa suka fito su duka kowacce da zabgegen hijjab kamar matan liman. Gabansa duk suka ƙarasa suka zube kowacce kai a ƙasa. Hakan ba ƙaramin mamaki ya bama Raudha ba. Duk da halin da take ciki itama a ranta al'ajabin yanda suke tsoronsa takeyi, gasu dai manya da su suma. Ita dai tana zaune a inda take, yayinda har Basma a yanzu take a gabansa duƙe.          Bai wani tsaya tambayarsu kojin ta bakinsu ba ya fara magana a nutse amma muryansa a kausashe. “Na baku mintuna goma kacal ku tattara komatsanku ku koma sashen baƙi. Idan kuma har na kuma ganin wata da ƴan iskan kaya a jikinta wlhy-wlhy bazata sake taka ƙafarta gidan nan ba harna barsa ƴan iska kawai. Matata kuma karku fasa mata duk abinda kukai niyya tare da kai magana wa Maa ina dai-dai da ku”.       Daga haka yay musu nuni da su miƙe su bar wajen. Sosai Raudha tai mutuwar tsaye akan furucinsa na ƙarshe. *_“Matata kuma karku fasa mata duk abinda kukai niyya da kai magana wa Maa ina dai-dai da ku”_*. (Minene dalilinsa?). Bata da mai bata amsar nan, dan haka taɗan saci kallonsa ta gefen ido. Ta janye a hankali saboda wani shegen nishin takaici da taji an saki a kusa da ita. Muneera ce, ta watsa mata wani irin kallo na zaki san komu su waye tabi bayan su Lubnah da tuni sun nufi ɗakunan nasu tattare kayansu.          Dafata Basma tayi ganin kamar ta tsorata da abinda Muneera tayi, cikin raɗa yanda Yayansu bazai ji ba tace, “Karki wani damu kanki babu abinda suka isa miki, dan wlhy duk tsoron Yaya suke kamar mutuwarsu. Iyakar iskancinsu na bayan idonsa ne. Kuma tunda muma muna gidan ko kallon banza suka miki sai yaji”.       Kanta ta girgizama Basmam a hankali itama tace, “A'a dan ALLAH karku ƙara faɗa masa Basma. Wannan ma da kun bari na masa bayani yanda bazai zargesu ba”.         “Tab wai tsoronsu kike ji? To wlhy kima cire, dan su aunty Lubnah wutar karane sai da izo. karki yarda suga rauninki zakisha wahala. Gara ki fito musu a mara kunya kema dan nan gidankine kowa yazo zai zaunane karƙashin ikonki. Yanzu dai ki samu Yayan ki bashi haƙuri, dan yana son idan yay fushi koda baka da laifi ka bashi haƙuri”.       Duk da maganganun Basma sunyi tasiri a ranta sai bata nuna ba. Harga ALLAH kuma tanajin daɗin zama da Basma da Bilkisu a gidan       Ganin kowa ya fice a falon harsu Aina riki-riki da akwatina yasa Raudha yanke bin shawarar Basma. Sai da ta ɗan ƙara jan sakanni da fitarsu kafin ta dubi inda yake kamar kazar da ƙwai ya fashema a ciki. Duk da yaji alamar idonta a kansa bai motsa ba, Raudha dake a zaune kanta a ƙasa ta ƙara damke bakin ɗankwalin atamfar jikinta data yafo a kanta sannan ta ɗan zamo jikinta a kujerar kaɗa. Zani da rigane sun mata matuƙar ƙyau dan anyi ɗinkin dai-dai jikinta.        “Dan ALLAH kayi haƙuri baza'a sake ba”. Tai maganar a hankali kamar kuma zata fashe da kuka.       Anan ɗin ma baiko motsaba. Sai dai yajita sarai dan shi mutum ne mai ƙarfin ji shiyyasa Anne ko gulmarsa batayi indai yana gidan. Tsawon mintuna biyu, har Raudha ta sake buɗe baki zata sake bashi haƙurin sai tai shiru saboda ɗagowar da yay daga ɗan jingina jikinsa da yayi da kujera yana sauke mayatattun idanunsa a kanta. Zata iya jure zama wajen da yake, amma bazata iya jure kallon da birkitattun idanunsa suke mata ba. Saboda sunada wani irin kaifi da kwarjini a gareta na musamman.          Kallonta yake sosai kuma kai tsaye wanda ta rasa mi yake kallone a jikin nata. Dan ta kasa dubansa ita. Tsabar kunya ji take kamar ta nutse a wajen ta huta. Sai da yay mai isarsa ya janye idonsa ya maida ga agogon dake a tsintsiyar hanunsa. Batare da amsa ban haƙurinta ba ya ce, “Ina bukatar abinci”. Daga haka ya sake ɗauke kansa ya maida ga television ɗin dake ɓaɓatu a katafaren falon da yafi kowanne falo haɗuwa da tsaruwa a gidan.            Numfashin daya toshe mata maƙoshi taja da karfi ya wuce cikin ciki ta fesosa a hankali tan mikewa. Sai kuma wani irin fargaba ya ɗarsu mata a zuciya dan tasan dai akwai breakfast ɗinsa a dining, tana shakkar nuna cewar zata haɗo wani bata san amsa mizai biyo baya ba. Rashin mafita ya sakata nufar dining ɗin ta shiga buɗe abincin wajen kusan kala uku. Sam hankalinta bai kwanta da su ba, dan haka ta sake dawowa inda yake zaunen tana kai durƙushe gabansa yay mata nuni da kujera.      Babu fuskar yin musu, sai kawai takai zaune a ɗofane kamar ɗazun. “Dama zance ko a duba lunch dan wancan sun huce”.       Shiru bai amsa ba, hakan ya sata ɗan ɗago ido ta saci kallonsa, sai taga ita yake kallo, sai dai tana ɗago ido ya janye nasa cike da basarwa.       “Duk yanda kikai yayi”. Ya bata amsa tunkan tace wani abu. Tsam ta miƙe a wajen ta nufi downstairs. Shi kuma ya cigaba da kallonsa zuciyarsa na kissima masa wani abu daban akan Raudhan. Baya buƙatar ɓuɗewar idanunta da yawa, sai dai a matsayinsa na shugaban ƙasa yana bukatar matarsa ta zama mai buɗaɗɗen brain kodan mu'amula da mutanen dake a cikin gidan dama masu shigowa. Bai cika son macen aurensa mai ƙarancin shekaru ba, amma shawarar Bappi tasa hakan baya damunsa yanzu kuma.       Cikin sa'a Raudha ta iske kukus ɗin gidan na shirin tsara abincin lunch ogansu tsaye akan mai shirya abincinsu duk da dama wannan kitchen ne da iyakar su da wanda ya shafi sashen kawai akema girki, dan haka ta dakatar da shi akan a tattaro breakfast dake sama, zataima shugaban ƙasa lunch da kanta. Kuku yaso yin magana sai dai babu fuskar hakan, sai ya miƙa mata book ɗin dake ɗauke da tsare-tsaren abincin da Ramadhan ke ci saboda yanayin lafiyarsa.         Tana tsaka da dubawa Bilkisu data wuto a falo ta shigo, dan iya su Lubnah kawai aka maida sashen baƙi da ke a falo na biyu. Cikin ƴar tsokana Bilyn dake hawa saman cabinet na kitchen ke faɗin, “Uhm yau da alama amaryarmu da kanta zataima babban yaya ango girki kenan?”.        Murmushi da kunya ne suka lulluɓe Raudha lokaci guda. Tasa book ɗin ta ɗan kare fuskarta. Littafin Bilkisu ta amsa tana dariya itama da sake faɗin, “That's good my sweet aunty. Dama naso na baki shawarar nan tun randa mukai na dare ɗin nan. Inaga yana da ƙyau ragamar girkin mijinki ya dawo hanunki bawai ki barma kuku ba tunda ke special first lady ce data banbanta dana baya, tunda naga Yaya yafi bukatar ganinki a gida kawai ko muryanki baison fita.”          Murmushi nan ma Raudha tayi kawai. Bilkisu taci gaba da faɗin, “Yaya mutum ne mai tsantsami, shiyyasa baya cin abincin kowa sai na Anne. Dan na sashenmu ma yasan ƴan aiki keyi.”        Cikin jin daɗin shawarar Bilkisu da ganin mafitace ma ga fargabar shirin su aunty Hannah data rasa yanda zata ɓullo masa yasa Raudha faɗin, “Insha ALLAHU zanyi ƙoƙarin hakan Aunty Bily. Nagode sosai”.         “A'a mune ai da godiya tunda za'a kula mana da yayanmu”.      Nanma Murmushin kawai Raudha tayi. Daga ƙarshe Bilkisun ce ta taimaka mata sukai komai yanda ya kamata. Sai kuku ya zama ɗan kallo, dan bilkisu gwanace wajen sarrafa girki. sai kuma tambayoyi da sukan masa akan na'urar da basu gane ba ko idan suna buƙatar wani abu da basu san inda yake ba.        Basu wani ɓata dogon lokaci ba komai ya kammala. Suka bama kukus daketa aikin haɗa sauran abincin waje.... ............Kasancewar an kwashe abincin breakfast dake a dining ɗin ɗazu ya bama Raudha damar shirya wanda suka shigo da shi ita da Bilkisu da Basma. Har yanzu yana a inda suka barsa. Sai dai saɓanin ɗazun da yake kallo yanzu yan aiki a system ne. Har sukai suka gama bai ɗago ya kallesu ba. Sai da su Basma suka sauka Raudha ta ƙaraso inda yake.      Bata mance abinda yay mata ɗazun ba, dan haka takai zaune akan kukerar dake facing nashi a ɗofane. “Ga abincin an shirya”. Ta faɗa cikin sanyin muryarta dake da matuƙar tasiri ga Ramadhan batare da ita ta san hakan ba.      Kansa kawai ya ɗan jinjina mata batare da ya ɗago ba. Sai da yaja kusan mintuna uku sannan ya miƙe ya nufi dining ɗin. Itama Raudha baya ta dafa masa tana mai satar kallon yanda yake taku cike da ƙuruciya da mazantaka irin ta masu shekarun da basu gaza nashi ba, alamar akwai lafiya da ƙarfin jini a tattare da su.          Duk yanda Bilkisu ta bata shawara haka tayi, duk da ya ɗanyi mamakin yanda tayi komai kai tsaye bakamar waccan ranar ba da dare sai ya danne, cikin nutsuwarsa ya fara cin abincin bayan ya kalli agogon dake ɗaure a hanunsa. Raudha tai ƙoƙarin barin wajen dan a matuƙar takure take dama.        “Ji mana”.   Wani irin tsargawa cikin Raudha yayi, dan a tunaninta ko abincin ne bai masa ba. Ta dawo da baya tana ƙoƙarin haɗiye fargabarta. Abincinsa ya cigaba da ci tamkar bashine yay kiranta ba. Sai da yaja kusan mintuna biyu a hakan.        “Ba'a ajiyemin abinci a wuce a barni a wajen sai kace mara gata har sai na kammala”.        Idan ta fahimci zancensa yana nufin dai dole ta zauna a wajen har sai ya kammala. Kai mutumin nan zai illatata, shi bai san a takure take da hakan ba? Nasihar Bilkisu data Anne ta sata komawa ta zauna, a ƙasan ranta tana ƙara ganin laifin su hajiyar birni da ko nasihar yanda zata rayu da miji basu mata ba. Sudai kawai farin cikinsu zata auri shugaban ƙasa ɗan babban gida.          Ita dai tunda ta koma ta zauna kanta a ƙasa, shiko laokaci-lokaci yakan ɗago ya kalleta, sai dai komai baice mata ba harya kammala. Shiru wajen ya sake ɗauka, shi bai tashi ba shi bai mata magana ba har kusan mintuna uku da wasu sakanni. Sai dai kaifin idanunsa dake kanta ba karamin kassara duk wani ƙwarin gwiwa na Raudha yake ba. Ji take tamkar ta fasa ihu ta huta.         “Na fahimci komai sai na koya miki shi a gidan nan?”. Ya faɗa a hankali tamkar bada ita yake ba. Da sauri ta ɗago ta kallesa dan furicinsa yazo mata a bazata. Ya kaɗa bata ƙwayoyin idanunsa masu rikita mata lissafi. “Miye burinki a rayuwa?”. Babu shiri ta maida kanta ƙasa zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Ganin baida alamar sake maimaita tambayar balle ta tabbatar da abinda tajin a farko ya sata ƙarfin halin faɗin,        “Karatu. Na addini dana boko”. Karan farko a duk yinin yau ya saki murmushi, sai kuma ya ɗan kauda kansa a kanta ya maida ga ƙaton hotonsa dake manne a falon, irin wanda a duk wani office dake ƙasar NAYA shi zaka gani manne.         “Wane mataki gareki duka a yanzun?”. Ya faɗa batare daya ɗauke idonsa ga hoton ba.      Sai da ta juya maganarsa sau uku kafin ta fahimci inda ta dosa. “Nayi saukar Al-qur'ani watanni bakwai da suka wuce. na haddace littafin arba'una hadith tun shekaru uku da suka wuce, a yanzu haka akwai hadithai sama da talatin da bakwai a kaina bayan arba'una hadith, sai sauran littatafai suma wani na ƙarisa wasu ina gab. A fanin boko secondary na kammala, sai dai ko result ban amsa ba”.         A hankali ya janye idanunsa daga kan bakinta dake motsin masa lissafin cike da nutsuwa. Ya ɗan haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙoshi tare da kai hannunsa ya shafi gashin dake kwance a fuskarsa. Jin baice komai ba itama sai bata sake cewa komai ba. Miƙewa yay kamar zaibar wajen sai kuma ya ranƙwafo kanta. A ɗan rikice taja kanta baya jin saukar numfashinsa kusa da ita. Cikin magana irin ta masu raɗa yake magana saitin kunenta. “Shiyyasa kike zubamin ustazanci a gida ashe”. Yana gama faɗa ya janye jikinsa baya yabar wajen, dariyar yanda ta diririce na cinsa. Da ƙyar Raudha ta iya sauke numfashi tare da nannauyar ajiyar zuciya da kai hannu ƙirjinta dai-dai saitin zuciyarta ta dafe.       Shin mike damunsa ne wai? Mike son faruwa da ita ne? Ta taɓa so a baya akan ya sayyadi, sai dai akwai banbanci da abinda takeji a yanzun game da Ramadhan. Mike nan hakan?. (Yana miki kwarjini ne kawai, da abunda bakiyi tunani daga garesa ba) wani sashe na zuciyarta ya faɗa cike da tabbatar wa.       ★Tun daga wannan ranar Raudha bata sake jin ɗuriyar Ramadhan ba tsahon kwana biyu, kota shirya abincin safe da Bilkisu ke tsaye kanta kullum yanda suka aje haka kuku ke kwashewa. Dama dai basa shirya lunch tunda sun san yana office. Na dare ma ba'a taɓawa haka ake kwashesa. Raudha bata sanin sanda yake fita balle shigowa.      Yana ɗan bata tausayi, dan ta fahimci sam bashi da lokacin kansa. Gaskiya mulki ba wani daɗi bane ba. Da wahalhalun cikinsa yafi daɗin yawa. Musamman ma irin na Ramadhan dake zagaye da maƙiyansa batare da ya sani ba.       Addu'a ta cigaba da masa, tare da maida hankalinta ga abubuwan da Bilkisu ta duƙufa koyar da ita, wanda take matuƙar jin daɗinsu har tanajin canji a al'amuranta. Duk da ba baƙinta bane, saboda kusan duk irinsu ne su aunty Hannah suka koyar da ita a wancan lokacin. Banbancin kawai tana maida hankali a waɗan nan saboda fahimtar lallai zaman gidan bazai yuwu mata ba sai ta zama mai buɗaɗɗen brain irin na manyan mata. Ba komai ya sata irin tunanin nan ba sai ziyarce-ziyarce da matan manyan mutane irin ƴan majalisu da gwamnoni ke kawo mata cikin gidan. Kallonsu kawai wajen iya tsara ado firgitata suke. Balle a magana da sauransu.           Bata taka kowanne irin mataki da yay kamanceceniya da nasu ba, sai suttura kawai a yanzu da zata iya fin wasu saka masu tsada ma saboda Anne tsayin daka ta tsaya ita da Hajiya Mariya wajen haɗa lefen Raudha da kayayyaki na alfarma saboda hangen irin hakan.         __________★★_★★__________          A ɓangaren Ramadhan ayyuka ne sukai masa yawa sosai, dan a wannan gaɓar suna tsaka da tantance sunayen mutanen da ya kamata su sami mukamai. Sai dai a zahiri bazaka taɓa jin baki ko cewar shugaban ƙasar ba. Sai dai daga bakin mai magana da yawunsa ko mai magana da yawunsa akan yaɗa labarai.        A ɓangaren majalisa kuwa bayan zama da kaikawo akan jerin sunayen cabinet na shugaban ƙasa da aka fitar aka sake dawo da sunayen ofishin shugaban ƙasan. Yayinda shi kuma ya sake maida sunayen ga majalisa a rubuce kan a tantance daga dukiyar kowanne na jerin sunayen. Ma'ana duk suzo su bayyana abubuwan da suka mallaka, hukumar bincike da yaƙi dacin hanci da rashawa kuma ta tankaɗe ta rairaye ta ajiye duk wani documents nasu. Wanda ba'a yarda da nashi details ɗin ba a ajiye sunansa gefe guda baya cikin jerin wanda za'a bama muƙamin.         Tofa wannan magana data fito da ga kakakinsa mai tabbatar da yawun shugaban ƙasa ne ta tada hankalin manyan jam'iyya. Ba komai ya kawo hakan na kuwa sai sanin cewar a cikin waɗan nan mutanen musamman wanda sukai bayar akwai masu kashi a ɗuwawu da yawa. Dan haka Jam'iyya ta bada sanarwar taron gaggawa tare da gayyatar shugaban ƙasa.        Wannan ne karo na farko da jam'iyya ta gayyaci shugaban ƙasa a bayyane tun bayan hawansa kujerar mulki, dan duk bata kashin da akai akan sunayen cabinet da zaɓin speakers na majalisu a rubuce ne data hanyar zaman sirri. Lokacin da kakakin shugaban ƙasa ya isar da wannan takardar gayyata ga Ramadhan ɗagowa yay yana dubansa. Yay ɗan murmushi yana sake maida dubansa ga takardar batare da yace komai ba.        Chief of staffs ya sake risinar da kai cike da girmamawa yace, “Ranka ya daɗe, na riga na shirya saƙon maida musu akan bazaka samu damar zuwa ba, nasan zaman bai wuce akan binciken dukiyoyin sunayen cabinet ba. Gashi a ranar ma kanada tafiya zuwa ƙasar China”.        Ramadhan da har yanzu idanunsa ke kan takardar ya cigaba da nazarinta tamkar mai bita. Sai kuma ya ɗago yana duban cos a nutse, sai dai yanzu babu wannan murmushin na ɗazun. “Tunda zama ne a bayyane zanje, sai dai ka canja musu lokaci”.        “Amma....” Hannu Ramadhan ya dagama Cos, dan haka ya haɗiye abinda yake son faɗa. COS baiso hakan ba ya jinjina kai kawai. Daga haka suka cigaba da tattauna abinda ya dace har zuwa iya adadin daƙiƙun da zai iya ganawa da shugaban ƙasar ya cika ya fito.         Bayan fitar COS. Da wasu sakanni Ramadhan ya ɗauka ɗaya da ga cikin wayoyinsa ya shiga danna-danne. Babu jimawa aka ɗaga kiran da yay. Cikin girmamawa ya fara gaisawa da Bappi, kafin ya zayyano masa batu akan takardar gayyata da jam'iyya tai masa.     Murmushi Bappi yay da ga can. Kafin yace, “Naji daɗi da kai tunanin zuwa ɗin, domin wannan shine kira na farko da jam'iyya tai maka a bayyane, duk zaman da kukai baya na sirri ne. Amma inaga a wannan gaɓar kar kai jayayya da su, duk umarnin da suka baka koda na janye batun bincike akan cabinet ɗinne kayi hakan”.          “Amma Bappi hakan ai tauye hakkin talakawa ne? Sannan zamu iya ɗaura ruɓaɓɓu a lulluɓe suzo suna ruguza mana tsari”.        “Zancenka yana kan hanya, sai dai ka sani Ramadhan bazai yuwu ka samu komai na ra'ayinka hundred percent ba, har sai ka nutsu ka fahimci mutanen man a to z. Dan zuwa yanzu zuciyata ta fara faɗamin akwai manufa a ɗoraka wannan mulkin musamman idan mukai la'akari da saƙon da muka samu daren ɗaurin aurenka da bincike ya kuma tabbatar mana da komai...”       Wani irin kakkauran numfashi Ramadhan yaja, sai kuma ya jinjina kansa cike da nutsuwarsa yace, “Babu damuwa Bappi duk yanda kace haka za'ayin”.          “Thanks you my dear, adai sake dagewa da addu'a, kar ai sakaci da ibadar ALLAH. Duk abinda yazo a nema zaɓin ALLAH, a kuma zartar dashi bisa gaskiya da amanar talakawa da tunawa da rantsuwar da akayi.”        “Insha ALLAH Bappi, ALLAH ya ƙara lafiya da tsahon rai mai amfani”.     “Amin ya rabbi”. Daga haka suka ajiye kan wayoyin kusan lokaci guda. Yayinda kowannensu ya tsunduma a tunani ta ɓangarensa.    ★★     Kamar yanda Bappi ya ƙara masa ƙwarin gwiwar amsa kiran jam'iyya a yau koda ya baro office kai tsaye falon da zasuyi zaman anan cikin fadarsa ya nufa. Su huɗu ne kawai. Party Chairman da wasu manyan masu faɗa aji a jam'iyyar su biyu. Cikin mutunta juna suka gaisa, domin dukansu sai dai a kirasu iyaye ga Ramadhan ɗin, ballema ta wani fanin duk suna tare da kakansa ne.        Kamar yanda Ramadhan yay hasashe akan maganar cabinet ne hakanne kuwa, dan haka bayan ya gama saurarensu bai wani ja maganar tayi tsayi ba ya nuna ya gamsu da abinda suka faɗa ɗin. Duk da acan ƙasan ransa wani irin ƙuna zuciyarsa ke masa da takaicinsu.       Tabbas sunji daɗin yanda yay musun, dan har fuskokinsu sai da suka nuna hakan, tare da yaba masa na bama jam'iyya girmanta a wannan karon. Daga haka suka cigaba da tattauna wasu abubuwa muhimmai bayan an bama ƴan jarida damar sanin wani abun. Basu tashi a zaman ba sai kusan ɗaya da rabi na dare. Dan haka a matuƙar gajiye Ramadhan ya ƙarasa cikin gidansa. Dole kuma ya dakata ya saurari COS na mintuna biyar kafin ya shige. COS kuma shima ya nufi nasa gida. ______________________________        Kwanaki sun ɗan ƙara shuɗawa da adadinsu ya kai kusan goma sha,  Ramadhan ya ziyarci ƙasar China na tsahon kwana huɗu ya dawo, an kumayi naɗin cabinet da yasaka wasu farin ciki wasu ɓacin rai. Babban farin cikin talakawa a zaɓin matasa da suka shigo tawagar sosai a wannan tsarin ma. Darajar shugaban ƙasa ta sake ɗaukaka a idanun matasa dama ƴan ƙasa, domin abubuwa na zuwa da ba'a taɓa gani ba a ƙasar NAYA. A gefe kuma ana cike da fargabar wasu a cikin cabinet ɗin, domin kuwa ansansu, sun riƙe wasu muƙaman an gani, inda ake yawan zarginsu da handama da baba kere wa dukiyar talaka. Wannan ya kawo ƴan kananun magana ga talakawa ga ma masana akan harkar mulki da siyasa tare da ƴan jam'iyyar hamayya da dama suke jiran ƙiris su hau suka. To komadai miye shi talaka ɗaukarsa a kullum shugaban ƙasa ne keda ikon mulki da zartarwa ga ƙasa, sai dai baisan zagaye yake da masu tilastawa da hanawa ba a zahiri da baɗini, takan kai ma wani lokaci shugaban ƙasa bai isa bayyana ra'ayin kansa ba koda yana buƙatar hakan.          A washe garin da akai naɗin cabinet bai fita office ba sakamakon hutawa na kwana biyu da likitansa ya buƙaci yayi, dan jininsa ya hau sama. Baiso zaman ba sam, sai dai babu yanda ya iya saboda Anne ta saka baki.      Hutune da basai ƙasa ta san zaije ba, domin zai ɗan iya zartar da wasu ayyuka muhimmai da ga cikin gidansa. A ranar yinin farko Raudha batasan wainar da ake toyawa ba, tunda rabon ma ita data gansa tun randa ya dawo China, shima ta fito ne da dare ɗaukar ruwa sakamakon ruwan fridge nata ya ƙare ta shafa'a bata saka an zuba ba sukai kiciɓus da shi a falo yana haurowa daga stairs ɗin fadarsa. Taɗan daburce a lokacin, dan bataso ya ganta da kayan barcin jikinta ba. Ta shiga masa sannu da zuwa aɗan daburce, dan ga kunyar kaya gata tsareta da yay da idanu. Kusan mintuna biyu suna a hakan kafin yay wucewarsa bedroom ɗinsa ita kuma ta saki ajiyar zuciya ta koma ɗaki da sassarfa, ruwan da bata ɗauka ba kenan. Daga ranar kuma basu sake haɗuwa ba sai dai ta gansa a television.         A ɓangaren su Basma kuwa washe garin daya dawo daga China duk suka koma gida saboda gimbiya Su'adah ta dawo, hakan sai ya saka Raudha a tsananin kewarsu da damuwa fiye da farko, dan tanajin daɗin zama da bilkisu da Basma ɗin. Su Lubnah kam tun randa ya maidasu sashen baƙi dama sai ta so ma suke ganinta, hakan ya kawo mata sauƙi sosai da cin zarafinsu.        Bayan tafiyarsu sai ta koma bata da abokin zama sai Mama ladi, tun bata sakin jiki da mama Ladin sosai harta fahimci ƙyawawan halayenta itama. Dan cikin hikima take ɗorata akan abubuwa masu muhimmanci da suka shafi aurenta da zamantakewar mutane fiye ma da yanda Bilkisu ke mata. Kuma Alhmdllhi tana fahimta sosai tare da ɗaura ɗamarar ɗaukar komai.        Kusan sha ɗaya na safe tana bedroom ɗinta Mama Ladi ta shigo bayan ta nema izini, dan tunda mama Ladi tazo gidan aikin mama tambaya ya koma iya falon ƙasa, dama aikinta kula da ɗakin Raudha da zama mai kusanci da ita fiye da kowa. Kawo mama ladi kuma ya nuna Raudha ta sake ta, hakan yama mama tambaya zafi, har takai ƙara wa iyayen gidanta su aunty Hannah. Amma sai suka lallasheta akan karta damu zasuyi wani abu.          “Mama akwai matsala ne?”. Raudha dake duba littafi ta faɗa fuskarta a sake tana duban mama Ladi data shigo bayan ta bata izini.      Cikin girmamawa tace, “Ranki ya daɗe dama naga su Hajiya Anne ne gaba ɗayansu a gidan nan sai nake tunanin kamar dai babu lafiya”.         Sosai ƙirjin Raudha ya buga, a ɗan tsorace tace, “Suna ina?”.       “Basu shigo ta nan sashen ba. Ta can fadar shugaban ƙasa naga anbi dasu”.       Tunda suka shigo gidan gwamnati bayan wanda sukai mata rakkiya da kawo lefenta su Lubnah ne kawai suka taɓa zuwa gidan a kaf zuri'ar Taura, dan haka Raudha ta tabbatar lallai babu lafiya da gaske. Tun lokacin da yabi da ita ta fadarsa lokacin da zasuje Taura house bai sake ba, amma tsabar ruɗewa batasan ta fita kai tsaye zuwa can ba bayan ta zumbula hijjab har ƙasa da yay mata matuƙar ƙyau kasancewar yanda komai na jikinta ya sake canjawa a yanzu saboda canjin waje da abinci.        Tana kai ƙafarta step ɗin farko ta tsaya cak sakamakon riƙota da akai. Tsabar bugawa da ƙirjinta yayi batasan ta juyo gaba ɗayanta ba. Kasancewar yana gab da ita sai ta faɗa a jikinsa gaba ɗayanta.      “Ya ALLAH”. Ta faɗa a rikice tana son jan jikinta baya...........✍ *_Tsabar gata pags 2 na haɗe muku waje guda👩🏻‍🦯🥹🥹_* *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/23, 8:36 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62b35fdfcfb019e4836d06fe *_Episode 34_* ..........Bai bata wannan damar ba, sai ma saurin riƙota da yay ya tallafe da hannunsa da ƙyau, dan ya tabbatar dabai mata hakan ba zata iya zamewa a samu matsala. Karan farko, a kuma lokaci na farko da hakan ta faru.      “Relax”. Ya faɗa cikin wata irin muryar data nema gusar da hankalin Raudha, maimakon ta samu nutsuwar daya ambata. Ganin ba nutsuwar zatai ba ya juyata ya jingina da jikin glass da akai kwalliyar stairs ɗin da shi. Sai dai har lokacin tana a jikin nasa. Numfashi taja da ƙyar, ta haɗiyi kakkauran yawun daya kasa gusar mata da bushewar maƙoshin data riski kanta a ciki, tsahon minti guda da wasu sakanni bai sake magana ba yana kallonta kawai, sai da ya ɗanga numfashinta ya dai-daita ya janye jikinsa a nata ya matsa baya kaɗan. Hannayensa ya zura cikin aljihu duka yana furzar da ƙaramar iska shima a bakinsa.        “Miya faru?”. Ya faɗa idanunsa na cigaba da yawo akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da har yanzu take a ɗan firgice. Kanta ta girgiza masa, ta lalubo amsa da ƙyar da ga ƙwalwarta zuwa harshe.       “Ba komai, kawai naji ance su Anne sun zo ne”.           Shiru baice komai ba, sai dai har yanzu idonsa kafe a kanta. Jin shirun ya sata ɗan ɗagowa da tunanin ko baya tare da itane? Duk da kuwa tanajin tasirin kaifin idanunsa a kanta. Janye idanunsa yay cike da basarwa ya maida downstairs duk da baya iya hango su Annen sai hayaniyarsu sama-sama.         “Ni sukazo dubawa”. Ya faɗa har yanzu idonsa a downstairs.       Cikin subutar baki da waro idanu Raudha tace, “Baka da lafiya ne?”.      Yanda tai maganar kanta tsaye, da waro idanunta farare tas ya matuƙar tada tsigar jikin sa. A gefe kuma taso bashi dariya amma sai ya gimtse. Takawa ya ɗan ƙarayi gabanta, ta matsa baya tana sake mannewa da glass ɗin. Hannunsa ɗaya ya ɗaura jikin glass ɗin gab da ita, ɗayan na cikin aljihunsa bai cire ba. Ya ɗan ranƙwafo kanta yanda har tana iya jin saukar numfashinsa a saman fuskarta.      “Kin damu dani ne balle ki sani?”. (Ya ALLAH) Raudha ta ambata a cikin ranta, dan kaɗan ya hana zuciyarta yin tsalle ta fito ta bakinta daga ƙirji.      “D...dan ALLAH kayi haƙuri”. Ta faɗa kamar zata fashe da kuka, duk da idanunta a rumtse suke.     Karon farko Ramadhan ya saki wani ɗan guntun murmushi da lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta, tare da sake kusanta fuskarsa da tata. A bazata ya sauke lips nashi a kan nata ya sumbata. Gaba ɗaya ta waro masa idanunta baki a hangame jikinta na tsuma. Wata ƴar shaƙiyyar dariya yayi yana sake maida lips ɗin nasa saman nata ya tsotsa. Sai kuma ya janye ya ɗan ɗallesu da yatsansa manuniya har yanzu fuskarsa ƙayace da murmushin da bata taɓa sanin ya iya ba “Ustaza ana so ana kaiwa kasuwa” Ya faɗa cikin raɗa da ɗan rungumota jikinsa. Jin numfashinta kamar yana barazanar ɗaukewa ya sashi sake sakin murmushin mai faɗi ya janye jikinsa ga baɗaya ya bata iska. Aiko sai ga Raudha da sakin wata wawuyar ajiyar zuciya da ita kanta sai da taji kunyar kanta.     Bai sake cewa komai ba ya nuna mata hanyar downstairs ɗin alamar suje. Kasa kallonsa tayi, bakinta kuma ya gagara furta komai balle tace masa wani abu, kai ji take ma kamar ta zama matatta dan bata gane komai😹🤭...         Kusan gaba ɗayansu suka zubo musu ido lokacin da suke sakkowa. Duk da kan Raudha a ƙasa yake sai da taji kaifin idanunsu a jikinta. Dama gashi mai gayya mai aikin ya gama sukurkuta mata rayuwa a sama. Dan har yanzu zuciyarta bata bar luguden daka akan abinda ya faru ba.        Anne, Bappi, Pa kallo guda sukai musu suka ɗauke zukatansu fes da farin ciki, hakama fuskokinsu ɗauke da murmushi. Gimbiya Su'adah ma dai a kallo gudan ta ɗauke idanunta cike da takaici da sakejin tsanar Raudha, dan ji take kamar ta kunna mata wuta ta babbaka banza. Hajiya Mufida da Hajiya Shuwa kuwa tsantsar kishi ne sosai a ransu. Yayinda sauran yaran mafi yawa babu komai a ransu sai ɗan abinda ba'a rasaba na ƴan ubanci da shakkar Ramadhan ɗin a tare da su. Sai ko su Lubnah dake zubama Raudha kallon tsantsar tsana a kaikaice.       Rufaidah da Basma and Fadila suka taso suka rungume Raudha bakunansu kamar gonar audiga....        Cikin nutsuwa Raudha ta kai duƙe gaban Bappi da Anne ta gaishe su. Fuskokinsu cike da fara'a dajin ƙaunarta suke amsawa. Suka ɗora da tambayar ya jikin mijin nata?. Kanta a ƙasa ta amsa musu kafin ta koma gaishe da Pa shima, shima dai ya amsa mata da kulawa yana tambayar jikin Ramadhan ɗin. Nanma dai kanta a ƙasa ta amsa fuskarta dai da ɗan murmushin girmamawa wanda yake sukar zuciyar gimbiya Su'adah matuƙa. Dan koda Raudha ta gaishe ta da ƙyar ta amsa. Bakuma ta tambayeta jikin Ramadhan ɗin ba. Dan a ganinta Raudha bata isa ba.         Raudha dai ba kallonta take ba, sai dai a ranta tanajin shakkar uwar mijin nata da take hango ɗunbin tsana da ƙyamar da take mata ƙiri-ƙiri. Ta gaishe da su Hajiya Shuwa ma. Sukam cike da bariki suka amsa ma Raudha ɗin da kulawa suna tambayarta jikin Ramadhan. Sauran yara kuwa ta gaida wanda suka girmeta, yayinda su Lubnah suka basar da ita itama sai tayi kamar bata gansu ba ta wayance da amsama Anne tambayar da ta jeho mata akan Ramadhan ɗin na kula da shan maganinsa dai ko?.         Raudha ta ɗan saci kallon inda ya ke zaune cikin kujerar dake gab da Bappi. Ido suka haɗa, tai azamar janye nata tana fafutukar nemo amsar data dace ta bama Anne.        “Oh Anne, har yanzu dai kina ɗaukata wani baby doll na lura?”.       Yanda yay maganar a ɗan narke ya saka Bappi da Anne darawa. Pa yay murmushi kawai, dan kowa yasan ƙaunar dake tsakanin Ramadhan dasu Anne sai dai ALLAH yasan iyakarta. Hanunsa Bappi ya kamo cikin nasa har lokacin fuskarsa da murmushi mai faɗi. “Gaskiya ka girma kam, kai da ke shugabantar babbar ƙasa irin NAYA ai ka wuce doll”.        “Yauwa Bappi na dama nasan yanzu munfi shiri” Ya ƙara faɗa a narke.               Mikewa Raudha da abin ya nema girman kanta tai, karon farko na rayuwarta ta koma sashenta domin bada umarnin shirya abinci. Amma rashin sanin yanda tsare-tsaren suke yasata neman mama tambaya. Mama tambaya ce tai mata bayanin wannan alhakin shugaban ma'aikata ne. Shine yasan tsarin aikin na kowanne ɓangare a gidan.      Babu jimawa aka nemo mata shi. Ya iso gabanta cike da girmamawa duk da kuwa babban mutum ne. Amma mulki sha'aninsa daban ne ai. Ta masa bayanin abinda take buƙatar ayi. Ya tabbatar mata cikin girmamawar da harga ALLAH kunya take bata. Sai dai babu yanda zatayi tunda ga'a inda ta tsinci kanta bisa alƙalamin ƙaddara.      Cikin ƙanƙanin lokaci aka kammala cika umarnin Raudha da tuni ta koma wajen su Anne. Duk da tasan basuzo da yunwa ba dai ta saka an shirya musu abubuwan motsa baki kala-kala domin karramawa. Sai fruits da kayan sha. Dan danan falon ya kaure da ƙamshin abubuwa. Har cikin rai Ramadhan yaji daɗin abinda tayi, hakama Anne ta sakejin ƙaunar yarinyar a ranta matuƙa.       Kowa ya ɗan taɓa wani abu, idan ka cire gimbiya Su'adah dako ruwa bata kurɓa ba. Sai ma sake miskile fuska da tai tanta harare-harare. Sam Ramadhan baiji daɗin yanayin nata ba, gashi yasan haushinsa takeji tun akan abinda yay ma su Lubnah dan bai yarda sun haɗu ba tunda suka dawo da ga London. Sannu da zuwa ma ta waya yay mata duk da yaje Taura house ɗin har sau biyu a sirrance. Dan na farko ko Anne ma batasan yaje ɗin ba.         ★★   Bayan wucewar su Anne Raudha da tai musu rakkiya ta dawo, bata sameshi a falon ba, dan haka ta haura sama itama, a ranta tana ganin ya kamata shima ta haɗa masa wani abun tunda taga baici komai a abinda aka ajiyema su Anne ba. Tsaye ta samesa a falon saman yana amsa waya, ɗan dakatawa tai ya kammala sannan. Kanta a ƙasa dan har yanzu matsananciyar kunyarsa ce ke dawainiya da ita.        “Naga bakaci komai ba, ko kana bukatar wani abu?”.         Mikewa yay batare da yace komai ba. Dan hankalinsa ma gaba ɗaya yana kan waya da alama akwai abinda yake nema. Sai da ya ɗanyi nisa da ita yace, “Biyoni da shi ciki”.      Ƙirjin Raudha ya harba ganin ya nufi hanyar bedroom ɗinsa, dan tunda randa ta kai masa kuɗin nan bata tunanin ta sake ko kallon sashen, balle tai sha'awar shiga ɗakinsa wataran. Cikin dauriya da bin umarni ta amsa da “To” tana mikewa ta wuce downstairs ɗin dan sama masa abinda zaici ɗin. Samun kuku da tai tare da mama ladi ya bata ƙwarin gwiwar haɗo abinda ya dafa na lunch wanda tasan zai masa daɗin ci matsayin mara lafiya, tasan dai mama ladi bazatayi sakacin da za'a cutar da shi ba a gabanta.        Ɗauke da basket ɗin data shiryo abincin ta shigo falon, kai tsaye tabi bayansa duk da zuciyarta na lugude har yanzun. Sai da tai knocking sau biyu ta ɗan dakata duk da bataji motsi ba. Lokacin da'aka murza handle ɗin ƙofar sai da ta rumtse ido hanjin cikinta na juyawa. Ta ɗan zabura baya tare da daburcewa ganin da ga shi sai towel alamar wanka ya fito ma. Komai baice mata ba ya saki ƙofar ya juya ciki. Sam kasa shiga tayi, ta cigaba da tsaiwa a wajen har sai da yay magana.      “Akwai dodo ne a ɗakin?”.    Da ɗan rawar baki ta ce, “Am sorry”. Bai sake tankawa ba hakan yasa cikin sanɗa kamar wata ɓarauniya ta shigo kanta a ƙasa. Wani irin mayatattun ƙamshin turare kashi-kashi suka fara rige-rigen afka mata cikin hanci. Ta ware manyan idanunta laɓɓanta dake motsawa a hankali na ambaton kalmar “Masha ALLAH”. Dan kuwa duk haɗuwa da tsaruwar ɗakinta da take gani sai ta gansa ba komai ba akan wannan, dan ma ta kasa kallon ko'ina yanda ya kamata. Amma duk da haka ɗaki ne kam da zaman lissafin tsarinsa ma ɓata lokacine. Abinda kawai za'a iya faɗa shine ALLAH ka gafarta mana ka azurtamu da aljanna maɗaukakiya.        Da ƙyar Raudha ta iya ɗaga ƙafa ta ƙarasa ga wasu haɗaɗɗun royal chairs farare tas da adon pitch kaɗan-kaɗan ta ajiye basket ɗin saman centre table dake tsakkiyarsu. Ga wani lumbutsetsen Turkish carpet da laushinsa ba'a magana.        Ramadhan dake tsaye gaban mirror yana gyara jikinsa duk yana kallonta, a duk lokacin daya ganta a yanayin kunya irin wannan sai zuciyarsa tai ta kaikawo akan tambarin karuwanci da akace ahalinta na da shi. Yana son mace wayayya kuma mai shekarun dake gab da nashi, dan haka yake kallon mace mai ƙarancin shekaru ba'a tsarinsa ba, sai dai akan Raudha zuciyarsa ta fara kokwanto da saƙa masa kalmar wauta a ra'ayin nasa, duk da kuwa shi bazai iya cewa komai game da wani abu akan Raudha na so ko makamancin hakan ba.         Ya ɗan yatsine fuska da ɗaukar t-shirt fara ƙal da ya ajiye ya saka a jikinsa, sai wando three quarter da baima gama kaimasa gwiwa ba shima ya saka cike da rashin damuwar Raudha na ɗakin. Kodan yaga ta juya masa baya ne oho masa.         Sayun takowarsa wajen ya saka Raudha dake bin ɗakin da kallo har yanzu ɗauke idonta ta sake nutsuwa. Ya kai zaune a kujerar dake facing wadda take zaune, yanda baiyi magana ba itama batai ba, sai sakkowa da tai ɗan gabansa ta fara cire kwanikan da ga basket ɗin. Bayan ta bubbuɗe ta nema zaɓinsa akan abinda zai ci.     “Duk wanda yay miki saka”. Ya bata amsa a taƙaice hankalinsa nakan canja tasha a television. Ƙundunbala tai ta zuba masa wanda yay mata ɗin, bayan ta kammala ta koma ta zauna inda ta taso saboda tunawa da dokarsa ta ranar. Sai da ya shanye kusan 2minutes sannan ya ajiye remote ɗin ya ɗauka spoon yana mai ƙurama abincin ido kamar mai son gano muninsa ko daɗinsa.       Ramadhan mutum ne mai tarin nutsuwa akan komai. Girman kai da yawan mutane ke kallonsa da shi yasa komansa zaka iya masa kallon yanayinsa da isa ne irin ta waɗanda suka isa. Cin abincin yake tamkar bayaso, duk da ma yafi maida hankalisa ga nama. Sai da yay nisa da cin abincin harma ya kusan gamawa da naman ciki (wayaga kure🤣), sannan ya ɗan ɗago ya dubi Raudha da hankalinta ke akan tv.       “Bismillah”.    Ya faɗa a daƙile kamar an masa tilas.       Juyowa Raudha ta ɗanyi ta kallesa, dan batai tunanin da ita yake ba. Da ido ya mata nuni da abincin, hakan ya sata itama kallonta ya sauka akan kwanon naman. Batare da tasan tayi ba ta ɗan tura baki gaba alamar sai da ka cinye naman.      “An gaya miki duk mutuncin da nake da mutum ina masa ƙyautar nama ne”.        Raudha tai saurin janye idanunta jin ya mata fassara daban, ga dariya data taho mata a bazata tanata ƙoƙarin kare bakinta da hannu, domin son kore tunaninsa tai sauri cewa, “Ni ama ƙoshe nake, nagode”.        Kafaɗa ya ɗan ɗaga da taɓe baki irin na I don't care. Daga haka ya ɗan ƙara abincin ya ture yana goge bakinsa da tissue da ambaton Alhmdllhi.     Bayan Raudha ta gama tattare kwanikan da nufin kama gabanta ya dakatar da ita.      “Ɗauka min abu a cikin bedside drawer ɗin can.”     Babu musu tabi umarninsa. Bedside ɗin da taga ya kalla ta nufa. Ta buɗe drawer ɗin wajen, takardu kawai ta gani, dan haka ta kwasosu ta dawo. Koda ya amsa sai ya buɗe file ɗin da suke ciki ya zaro guda ɗaya ya turota gabanta akan centre table ɗin. Ɗan dakatawa tai da ga kwashe kwanikan da take, ta kalli takardan sannan ta ɗan ɗago ta dubesa dan neman ƙarin bayani. Hankalinsa akan sauran takardun yake. Ƙundunbala tai ta ɗauka ta duba, jikinta ne kawai ya kama rawa, ta ɗago ta kallesa, ta sake maidawa ta kalli takardar. Tayi haka yafi sau biyar, dan ta rasa abin faɗa. Ruɗani ta shiga ko farin ciki ne yay mata yawa?, abinda ta daɗe da fidda ran samu, abinda zuciyarta ta daɗe da jaddada mata yay mata nisa... Cikin wani irin slow ta zamo a kujerar ta durƙushe gabansa hawaye na sakkowa saman kumatunta a hankali. Tabbas da ace bashi ɗin bane yau a gabanta babu abinda zai hanata daka tsalle ta rungumesa...           Ƙafafunsa dake harɗe ya ɗan motsa yana mai zuba mata mayatattun idanunsa. Farin cikin data tsinta kanta a ciki ya hana tasirantuwar kallon nasa gareta.        _“Ina roƙon ALLAH ya azurta zuciyarka da tarin farin ciki fiye da wanda ka sakani a yanzu. ALLAH ya baka ikon sauke nauyin al'umma dake kanka, ya kareka da duk wani abin ƙi na zahiri dana ɓoye. ALLAH ya ɗauraka a saman maƙiyanka kai da zuri'arka baki ɗaya. ALLAH ya cika maka burikanka na alkairi ya ƙyautata maka da sakamakon aljannah a ranar da ita kaɗaice abar kishirwa ga kowanne irin rai”._       Tunda yake, tunda yazo duniya, ko yace tunda ya mallaki hankalin kansa a rayuwa, wani mahaluki bai taɓa masa makamanciyar addu'ar nan ba. Saboda shi mutum ne da idan yay alkairi baya taɓa zama a wajen dan jiran a gode masa ko a yabesa. Baya son yawan yabo a gaban ido, yayi imani da yana iya sakama mutum fara aikin riya, dan yabo na saka shauƙi a zuciyar wanda akaimawa da tunzurawar shaiɗan a wani lokacin. Ya lumshe idanunsa a hankali na kusan mintuna biyu. Sai kuma ya buɗesu a kanta. Komai baice ba sai nuni da yay mata da hannu alamar ta koma saman kujera. Batai musu ba ta miƙe ta koma, kwalin tissue dake a centre table ɗin yasa ɗan yatsa ya turashi gabanta.         Anan ɗin ma bata musaba ta zara ta goge fuskarta tas tana haɗiyar zuciya. Tsahon wasu mintuna ɗakin ya ɗauka shiru, sai jan numfashinta kaɗan-kaɗan irin na wanda yay kuka. Tsam ya miƙe daga inda yake zaune, hakan yasa Raudha sake maida kanta ƙasa saboda kunyar wandon jikinsa. Duk da ya fahimci hakan sai bai maida kai ba, ya taka a hankali ta bayan kujerar da take zaune, kamar zai wuce sai kuma ya tsaya a dai-dai saitinta.          A bazata, cikin rashin tsammani Raudha taji saukar numfashinsa ta gefen fuskarta, alamar ranƙwafowa yay ta bayan kujerar. Sosai ta daburce, jikinta ya fara tsuma dan tun asali ta riga ta sakama ranta tsoron kusanta kanta da wani namiji saboda kare kanta daga faɗawa tarkon lalacewa, ta wani gefen kuma mamakinsa na sake dilmiyata a ruɗani, dan abubuwan da yake matan basu tai tsammani ba, basu ta hanga cikin idanunsa kafin aurensu ba, bata tunanin shima ɗin su yay mata tanadi, to miya canja shi? Kodai yana zargin akwai masu son amfani da ita domin cutar da shi? Kodai?.. Kodai?... Harma ta rasa lissafin da zatayi saboda tasirin da saukar numfashinsa ke mata a dokin wuya yana tada mata tsigar jiki da yamutsa jinin jikinta.          Ramadhan da ke lure da yanayin nata, ya basar abinsa, dan kuwa da gaske tunanin Raudha na kamanceceniya da wani ƙulli dake a ransa tun farko. Koya faɗa ko karya faɗa tabbas zuciyarsa bata yarda da ita ba kafin yau, shiyyasa yake binta matakin da ya tsara domin tabbatarwa (Humm da alama wajen gwaji za'a gwaje shugaba ƙasa😉lol).       Cikin magana kamar raɗa yace, “Miye tukuyci na?”.        Hannayenta ta matse cikin juna, dan yanda yay maganar cikin kunnenta tsigar jikinta ba ƙaramin yamutsawa tai ba, ga yawu kaɗan ya rage ya sarƙe mata numfashi. Taso jan jikinta gefe sai dai ya hana hakan ta hanyar zagayowa gefen damarta, kasancewar har yanzu a ranƙwafen yake sai yay mata runfar da ko numfashi ta kasa saki da ƙarfi. Gara ɗazun kujera ta musu katanga, yanzu ko hanunsa ma ɗaya idan tace jikin kujerar zata manne a kansa zata kwanta, ta gaba kuma ya tare ko ina. Sai kawai taji ƙwalla sun sake ciko mata ido. Maganar take sonyi amma ta kasa, sai laɓɓanta ke ɗan motsawa kaɗan-kaɗan.........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/24, 7:59 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62b5bb45fa0b02c20d2788dd *_Episode 25_* .........Shi dariya ma ta bashi, amma sai ya dake abinsa, duk da ya fahimci kusancinsu ne matsalarta yaƙi kuma janye jikin nasa.       “Kin zama kurma ne?”. Da sauri ta girgiza kanta, tana ɗan matse jikinta waje guda..    “Mikake so?”.        Ta faɗa da rawar harshe. Karan farko ya saki wani guntun murmushi dashi kansa a ƙarjinsa kawai yaji abinsa. Sai kuma ya miƙe da ga kanta ya taka zuwa kujerar gefenta ya zauna. Wayarsa dake faman vibration ya ɗauka, a yanda yake magana zaka fahimci mai muhimmanci ce, sai dai kuma ɗan walwalar dake kan fuskar tasa ya ida ɓacewa gaba ɗaya. Sunan Maa da taji ya ambata ya tabbatar mata da gimbiya Su'adah ce, kusan mintuna uku ya ajiye wayar batare da ta bashi damar yin wata kwakwkwarar magana ba.      Lip ɗinsa na ƙasa ya tura cikin baki da ƙarfi ya shiga taunarsa, yarasa miye manufar Maah ɗin na zuwan su Lubnah gidan su zauna. Abin takaicin ma a yanzu harda sharaɗin kar'a kuskura a ajiye mata yara a sashen baƙi. Dolene yaci uban yaran nan gwargwadon iko a wannan karon, dan zai saka musu ido sosai tare da abinda ko tace suzo zasuce a'a                          ★Ganin yanda yanayinsa ya canja zuwa ɓacin rai sosai ya saka Raudha da zuciyarta har yanzu ke kai kawo ɗan duban agogon ɗakin. A ɗan ɗarare ta ce, “Zanje nayi salla, magrib tayi”.             Komai baice mata ba, sai dai ya kafeta da ido tamkar mai son gano maganin takaicin da Maah ta cusa masa yanzu a jikinta.        Kanta ta duƙar ƙasa, wani ɓangare na nasihar Anne da Mummynsu na mata kaikawo a zuciya. _(Idan kin gansa cikin fushi, koda bake kika ɓata ransa ba ki faɗa masa magana mai daɗi da zata kore fushin nasa koda bazai saurareki ba. Idan har kika gusa a wajen zai maida hankali ga maganarki kuma fushinsa ya kwaranye, kimarki ta sake girma a idanunsa har yaji wataran kece kikafi kowa cancanta daya tunkara da matsalolinsa)._ Ɓoyayyen numfashi taja a hankali, zuciyarta na sake tunzurata akan gwadawa koda bazai kulatan ba. Kallonsa taɗan sata, ganin yanda ya lumshe idanu yana faman taunar lip data fara fahimtar ya zame masa ɗabi'a yasata haɗiyar busashen yawun da ya tokare maƙoshinta.        _“A kowanne lokacin haƙuri shike kwaranye abinda zuciya bataso ba. koda ɗacinsa yafi ƙarfin ƙwaƙwalwa”._         Raudha ta faɗa cikin matuƙar dauriya da ƙundunbala. Bakuma ta jira amsa ba ta kwashi kwankan da admission latter ɗin da ya bata ta kama hanyar fita a ɗakin cikin sassarfa, zuciyarta na luguden daka kamar zata fito. Dan sam batai tunanin zata iya faɗa masa maganar data faɗa ɗin ba yanzu sam.          A hankali ya buɗe idanunsa da suka canja launi ya zuba mata, harta fice a ɗakin bai iya koda motsawa ba. Abu biyu ke masa kaikawo a rai. _Mamakinta_ da kuma _Ƙarfin halinta_.          Raudha kam koda ta koma ɗaki bayan ta idar da salla admission ɗin ta sake ɗauka ta duba sosai, sai lokacin ta sake samun damar fara tsallen murna dariya na suɓuce mata da hawaye a lokaci guda. Inama tanada waya ta kira Mummy ta sanar mata, kai harsu Fatisa da Abbansu ma da duk saita faɗawa.      Bata sake bi takan Ramadhan ba, sai dai ta kasance cikin ɗunbin farin cikin daya bata a wannan dare. Washe gari batai ganda ba ta shiga kitchen da taimakon mama Ladi da kuku suka shirya breakfast, dan bata san yau ma ba fita zaiyi ba. Ɗaki ta koma tai kwanciyarta dan murna bata bari tai barcin arziƙi ba jiya da dare. Sosai tasha barci, dan sai wajen sha biyu ta tashi. Wanka ta shiga bayan ta kimtsa ɗakin, tana tsaka da shiryawa ta samu saƙo daga mama ladi cewar tanada baƙi. Yin baƙi yanzu ba baƙon abu bane a gareta, dan haka ta canja akalar shirin nata datai niyya da doguwar rigar jallabiya ta sanya lass.         Tuni Mama tambaya ta musu masauki da tarbar data dace da su, dan kuwa aunty Hannah ce matar vice president da wasu hamshaƙan mata su kusan shidda. Tabbas duk sun girmeta da finta wayewar rayuwa. Amma itama zama da Mama ladi da Mama tambaya ga huɗubar Bilkisu Da Anne data samu, ga wadda su aunty Hannah suka saka a mata tunkan ta shigo gidan yasa zuwa yanzu indai dressing ne baza'a nuna mata komai ba. A ɓangaren nutsuwa kuwa dama kowa yasan Raudha Alhamdulillahi bata da matsala tanan. A gefe kuma duk abinda ya haɗa da aunty Hannah *_TAKUN SAƘA_* take masa, dan karku manta a fuska Raudha yarinyace mai haƙuri, sai dai su aunty Hannah basu taɓa tunanin murɗaɗɗen haline da ita a baɗini ba.           Da sallama suka shigo falon guards ɗinta da mama tambaya da mama ladi na take mata baya. (Tabbas Raudha first lady ce da jinta yafi ganinta). Ta kai zaune fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi, ƙasan zuciyarta ɗauke da addu'a.        “Mom barkanku da zuwa”. Ta faɗa idonta akan Aunty Hannah dake mata kallon mamaki. Dan wani ƙyau da cikar kamala Raudha ta sake mata har da ƙiba. Ga wani buɗewa da taga idonta ya ƙarayi. (Da alama yarinyar nan tasan namiji zuwa yanzun) Aunty Hannah ta rayama ranta dan a tunaninta sanin namiji ga ɗiya mace shike sake buɗe kanta da idanu. Murmushi ta saki na basarwa ta amsa Raudha ɗin cike da tsantsar kulawa.       “Oh my baby kodai nayi jika ne? Irin wannan ƙyawu haka?”.     Kunya ce ta kama Raudha, amma sai ta dake ta saki murmushi kawai batare da tace komai ba. Sauran matan dake ɗan darawa suka shiga faɗin ashe munada gagarumin biki kuwa. Nanma dai komai Raudha batace ba, sai murmushin dake fuskarta da har yanzu bai gushe ba. Har suka taɓa ɗan barkwancinsu kuma bata tsoma baki ba, dan dukansu a haife sun haife ta, mutum ɗaya a cikinsu zata iya kira da yaya dan ita bata kaisu shekaru ba.         Bayan sun ajiye barkwancin nasu a gefe aka gaisa a mutunce, Raudha bata bada wata ƙofar da wani aciki zai amfani da ƙarancin shekarunta ya kawo mata raini ba koda a magana ne. Aunty Hannah ce tai mata bayanin dukansu matan ministoci ne, sunzo ne domin yin godiya a gareta da miƙo gaisuwa ga shugaban ƙasa.      Raudha ta ɗan jinjina kanta, cike da nutsuwarta da salon jin kai da aunty Hannah ke ganin kamar Raudha ta fara take binsu da kallon ƙasan ido. Sai da taja kusan mintuna biyu kafin ta fara magana.       “Muma muna godiya da ziyara, ALLAH ya bar zuminci. Shugaban ƙasa kuma zaiji saƙon gaisuwarku”.        A kaikaice aunty Hannah ta ɗan waro ido waje, ta shiga ƙyaftama Raudha idanu amma sai Raudha ta basar da ita tamkar ma bata lura ba. Ganin haka aunty Hannah ta miƙe tana faɗin, “Ya kamata kuɗan taɓa wani abu ko, bara uwa da ƴa su zuge labule”.        Murmushi duk suka saki, dan tuni ta riga ta gama baza musu alaƙar dake tsakaninta da Raudha, kuma kamanin da suka gani tsakaninta da Raudhan ma ya sake tabbatar musu da haka. Kamar Raudha bazata miƙe ba, sai kuma ta tashi a nutse suka nufi ɗaya da ga cikin bedroom ɗin dake a falon.         Suna shiga aunty Hannah ta damƙi hanun Raudha ta maida ƙofar ta datse. “K kinada hankali kuwa? Kinsan su waye waɗan nan matan?” Kafin Raudha tace wani abu ta cigaba da faɗin, “To ki saka hankalinki a jikinki waɗan nan duk zasu iya sayen garinku hutawa ne da kayan cikinsa. Kin wani zauna kina musu yatsina da jan aji dan sunce suna son ganin shugaban ƙasa”.       Raudha da ke binta da kallon mamaki ta ce, “Amma Mom shugaban ƙasa dake office yanzu ta ina zan kaisu wajensa? To ko a gida yake ma ganin shugaban ƙaramin abune Mom?”.      Aunty Hannah dake hararta ta ce, “K wawuya kina kwana da mutum a gida ɗaya amma baki san komai nasa ba. Abban Samha ya sanarmin sai monday zai fita office yana gida. Wai kuwa ma kina aikin da muke buƙata a gidan nan ko zaman samun canji waje da canja kayan da Asabe bata taɓa saka makamantasu ba kika tsaya”.      Sosai maganar aunty Hannah na ƙarshe ya soki Raudha fiye da komai, amma sai ta danne tama saki murmushi. Takuma ƙi cewa komai.       Wani irin takaici ya turniƙe zuciyar aunty Hannah, jitai kamar ta shaƙe shegiya ta huta. Dan ita ba hangen Raudha zata iya cin amanarsu take ba, zuciyarta kawai tana bata dan Raudha ta shigo daula ne take son fara raina mata wayo da tunanin tana dai-dai da ita.....          Ganin aunty Hannah ta lula duniyar tunani Raudha tai tunanin maido da ita, dan ta fahimci fiddoma aunty Hannah ainahin kanta a yanzu ba nata bane. Cikin murmushi da nuna ɗoki tace, “Mom dama fa wlhy inata son ganin wani a cikinku, ya samarmin makaranta fa”.        Firgigit aunty Hannah ta dawo hayyacinta, sai kuma ta saki murmushi da faɗin, “Kai Alhmdllhi da wannan labari, naji daɗi dan yayi abinda ya dace. Dama da batun nan nazo a raina, dan ya kamata ace kema zuwa yanzu kin fara fiddo kanki wa jama'a sosai, bawai ki kume cikin gida ba kamar kowace mace. Karfa ki manta ke first lady ce, ki masa maganar ya baki office ki fito duniya tasan ƙoƙarin ki...”       Cikin mamaki Raudha tace, “Mom office kuma?”.       “Eh office! Ko kina nufin haka zaki cigaba da zama ƙumshe a cikin gida ne, k wai kuwama kinsan mike miki ciwo? Kina matsayin matar shugaban ƙasa amma ko waya baki da shi?. Ina karatun da su Feena suka koya miki badai a banza ya wuce ba?”              Raudha taja ajiyar zuciya kawai batare da tace komai ba, hakan ya sake tunzura zuciyar aunty Hannah, cikin takaici tace, “To wlhy inma zaki dawo cikin hankalinki kiyi maza ki dawo. Bazai yuwu ki zauna kina mana ƙauyanci ba da shirme, kinsan nawa first lady ta narkar na kuɗi akan a koya miki abubuwan can kuwa? Amma Raudha gaba ɗaya kina nuna ma komai bai shiga kanki ba......”        “Mom nifa bawai bai shiga bane ba. Kawai dai duka yaushe na shigo gidan. Kofa wata biyu ba'a cika ba. Yanzu dan ALLAH idan yaga ina rawar kai da wuri ai saima ya gane komai. Shifa ba irin yanda kuke tunani bane ba, mutum ne mai lura da saurin fahimta. A yanzu haka bawai ya gama yarda banda alaƙa da wanda yaso kashe Bappi a filin idi bane ba......”         “Kusun uban can, kujimin ɗan iskan yaro. Duk yankan da kikasha bai gani ba zaima dinga ɗaukar haka?  To aiko zai gane kurensa wlhy. Yanzu abinda zan faɗa miki shine komi zai baki na magani karki sha, ko shi ko danginsa. Dan na kula waccan shegiyar uwar tasa zamu dama da itane, kaɗan daga aikinta tabi duk hanyoyin da zatabi danta daƙileki ga ɗaukar ciki. Ni kuma babban burina yanzu na ganki da ciki, dan koba komai kema ya kasance kinada wani kaso a dukiyar Taura. Sannan shima shugaban ƙasar komansa yazam namu ne. Abu na biyu ki fito ki nuna masa kina son fita fa kema a dama dake a harkar mulki, dan haka a baki office naki. Kuma wlhy ki nema waya bana son wawanci, ko kina nufin duk sanda nake buƙatar magana dake sai na dinga tako ƙafa nazo nan a matsayina na matar vice president?”.        Kai kawai Raudha ta jinjina mata, a takaice tace, “To duk zanyi”.       “Karma kiyi mana”. Cewar aunty Hannah a ƙufule.       Koda suka fito tsaf aunty Hannah ta canja yanayinta kamar komai bai faru ba. Itama Raudha dai bata bada wata ƙofa na fahimtar komai ba. A zaman nasu ne daga cikin matan ta ke kawo shawarar ya kamata first lady ta buɗe musu office. Ma'ana dai irin ƙorafin aunty Hannah. Atake kuwa duk sukai na'am. Raudha dake ɗan murmushi tace insha ALLAH zatayi shawara. daga haka ta tsuke bakinta. dama can ba komai take saka musu baki ba.       Wasu a cikinsu suna ɗauka dan tana ganin kanta sa'ar ƴaƴansu ne kawai shiyyasa take girmamasu da ƙin cewa komai. sai dai kuma hasashensune wannan, Raudha tana karantar kowa da lafazinsa ne kawai.      Bayan wucewarsu baifi da mintuna goma sha bakwai ba sai ga su Maneerah. Ko kaɗan Raudha batai farin ciki da zuwansu gidan ba. Musamman ganin babu Bilkisu da Basma a wannan karon. Amma sai ta danne ta musu tarba ta mutunci duk da kallon banza da suke mata suna wani dariyar iskanci.         Cikin dauriya ta bama mama tambaya umarnin a gyara musu ɗakin da zasu zauna. Amma sai Aina ta katseta. “Talaka bai iya cin arziƙi ba idan ya samu waje”.      Lubnah ta doka tsaki tana ma Raudha wani shegen kallo. “Shi wanda ya ajiyeki a gidan bai miki bayanin inane masaukinmu ba ne?”. Kafin Raudha tace wani abu Manirah ta ajiye wayar hanunta tsakkiyar centre table. Saukar maganar gimbiya Su'adah kawai taji a cikin kunenta a bazata....          “Bata wayar.” “A wlhy Maa wannan trash ɗin bazata taɓamin waya ba. Gashi nan nasa hansfree yi mata magana”..      Munirah ta faɗa tana harar Raudha da tura wayar gabanta. Cikin kaushin murya da ga can gimbiya Su'adah ta cigaba da magana a kausashe, dan kuwa warning mai ƙyau taima Raudha cikin kausasa harshenta, ta kuma tabbatar mata a wannan karon idan tai wani abinda Ramadhan harya dawo da su Ainah sashen baƙi wlhy itama sai ta ɗanɗana kuɗarta sannan tabar gidan. Daga karshe ta bita gorin kasancewarta ƴar talaka jinin karuwai kuma mayya.        Waɗan nan lafuzza na Gimbiya Su'adah sun yima Raudha zafi da ɗaci mai tsanani, harta kasa iya riƙe hawayen da suka ciko mata idanu sai da suka zubo. Batama jira Munirah da suke dariya ta ɗauka wayarta ba ta bar wajen zuwa upstairs da ɗan gudu kuka mai ƙarfi na ƙwace mata.. Babu zato taci karo da mutum har goshinta na buƙagar ƙirjinsa. Da sauri taja baya tana ƙoƙarin maida kukan nata ta haɗiye, sai kuma tasa hannu biyu ta goge hawayen da suke rige-rigen sakko mata.       Shugaban ƙasa Ramadhan dake tsaye hannayensa duka cikin aljihun wandonsa ya kafeta da ido batare da yace komai ba. Cikin muryar wanda ke son yin kuka Raudha ta ce, “Ina yini ya jiki?”.        Bashi da niyyar amsawa, sai cigaba da kallonta da yakeyi kansa tsaye, kusan mintuna biyu Raudha ta fahimci ba amsa mata zai ba, ga shi kukan da taketa dannewa son kwace mata yake, raɓashi tai ta wuce hawayen na ƙwace mata. Komai zata iya ɗauka daga Ramadhan da danginsa. Sai dai kalmar karuwanci da ake jifan iyayenta da shi yana taɓa mata zuciya. Tasan gaskiya suke faɗa, amma kalmar na mata zafi, zafi irin wanda ke ƙona zuciya.            Tsaiwa ya cigaba da yi a wajen kunnuwansa na sauraren darerakun su Aina'u da ke downstairs da maganganun banza da sukeyi akan Raudha ɗin. Iska ya ɗan furzar da tura lip ɗinsa cikin baki kaɗan yana ciccizawa. Sai da wayar jikinsa da ke ring na gab da tsinkewa sannan ya cirota a ljihu, ya haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa kafin yay dialing no ɗin dan kiran ya riga ya katse.      “Barka da yamma”. Ya faɗa a tausashe dan son danne ɓacin ransa. Da ga can gimbiya Su'adah ta amsa masa a gadarence cikin kaushin murya da ragowar fushin Raudha dake a muryarta. Shima dai ɗin gargaɗin tai masa akan su Lubnah. Ta kuma jaddada masa idan taji wani abu yaje kunnen su Anne ransa sai ya ɓaci matuƙa. Da ga haka ta yanke wayar batare da jiran cewarsa ba.        Karon farko ya saki guntun murmushi yana kai hannu bisa sumarsa ya shafota da tura wayar a aljihu tare da hanunsa duka. Kamar yanda bai furta mata komai ba, a yanzun ma data yanke komai bai ceba duk da akwai abin cewar a bakinsa. Tsaiwar wasu ƴan mintuna ya karayi a wajen tamkar mai nazari, kafin ya nufi hanyar ɗakin Raudha cikin tafiyarsa da babu garaje, wadda da yawan mutane ke kallon girman kai ne ke sashi salon takun kawai da nuna shiɗin wani ne. Sai dai sam ba haka baneba, halitarsace hakan kawai...           Koda ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga tsaye yay kawai yana kallonta batare da ya shigo gaba ɗaya ba. Tana kwance a saman gado rubda ciki tana kuka, ya shaida hakane saboda yanda shashshekar kukanta ke tashi a ɗakin. Sam bai cika son ganin mutum a damuwaba a tayuwarsa, saboda ya ɗanɗani ɗacin damuwa baiji da daɗi ba, kai zai iya cewa har yanzu tana ƙunshe da ciwon damuwa, baya tunanin kuma zai samu waraka har sai randa ya koma ga ALLAH.     Ƙarasa shigowa yay ɗakin yana ɗan bin ko'ina da kallo. A ɓangaren tsafta ya jima da bama Raudha lambar yabo, ba komai yasa haka ba sai kasancewarsa mutum mai tsananin son tsafta da ƙamshi. Zamansa a bakin gadon ya fargar da Raudha shigowarsa, tai saurin share hawayenta da miƙewa zaune har kafarta na ɗan shurin jikinsa. Bai juyo ya kalleta ba, bai kuma ce mata komai ba duk da yana kallonta ta wutsiyar ido.     Hawayen da ke cigaba da sakko mata take sharewa da ƙoƙarin ganin ta tsayar da kukan. Tsahon wasu sakanni kafin ta samu nasarar danne hawayen da ƙyar.      “Kana buƙatar wani abu ne?”.      Ta faɗa cikin girmamawa da tausasa harshe a garesa tamkar yanda ta saba. Sai lokacin ya ɗan juyo yana dubanta, ya kafeta da shanyayun idanunsa da ke nuna alamar bai jima da tashi a barci ba, ko kuma dai akwai abinda yake saɓanin barcin a cikinsu.        “Karfa ki zata lallashinki nazoyi yarinya”.      A yanda yay maganar batasan murmushi ma ya suɓuce mata ba. Ta kauda kai gefe tana sake share hawayen nata. Kishingiɗawa yay yanda zai iya kallon fuskar tata sosai. Shima fuskar tasa da ɗan murmushi dake iya laɓɓa. Cikin kafeta da idanunsa ya ɗan leƙa fuskar tata, “K kuka baya miki wahala ne? Ko dama haka ustazan suke saboda tsabar ƙarfin imaninsu?”.        (Kai jama'a wai miya shiga kan mutumin nan ne kwana biyun nan?) ta ambata a zuciyarta tana kai hannu saman fuskarta ta rufe murmushinta na ƙara faɗaɗa. Hannunsa yasa ya buge hannayen nata data rufe fuska.       “Gulmammiya nasan kinanan kinajin daɗi kamar ki taka rawa shugaban ƙasar NAYA yazo lallashinki kina kuka”.        “Ni Aminatu yaushe nace?”. Ta faɗa cikin waro masa manyan idanunta gaba ɗaya da ɓata fuska cike da shagwaɓa...........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/24, 7:59 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62b5bb45fa0b02c20d2788dd *_Episode 36_* ...........“Ki rantse bakiji daɗi kamar zai kasheki ba? Nasan dai ustazai basa ƙarya Ustaza!”.       Dariyar da tazo mata a bazata ta ƙyalƙyale da ita da sake rufe fuska saboda a yanda yay maganar.   “ALLAH nidai ba ruwana”.         Murmushi ya saki mai ƙayatarwa. Sosai yaji sanyi a ransa ganin damuwarta ta kwaranye ta sanadinsa. Bazai iya cewa komai a kanta ba, sai dai bazai so a wulaƙantata ba domin ɗan adam ba abin wulaƙantawa bane, wannan karatune daya samu daga kakaninsa tun ƙuruciya. Sannan bayaso Raudha tai tunanin akwai wani banbanci a tsakaninsu dan kawai tana ƴar talakawa....         Duk tunanin da yake idannsa na'a kanta ne. Bazai ɓoyeba cute face nata na matuƙar birgesa tare da sumar kanta data kwanta har saman goshinta sosai. Sannan a ɗan zamansu ya fahimci tanada haƙuri da juriya. Shiko yana son mutum mai waɗan nan halayyar musamman mara riƙo. Yanda ta saki jiki da shi lokaci guda duk da tasan ba haka yake mataba a baya ya masa daɗi matuƙa da sashi nutsuwa gareta.             “An taɓa faɗa miki k ƙyaƙyƙyawa ce?”.        Ya faɗa cinkin suɓutar harshe da ƙan-ƙan da murya yna sake shanye idanunsa suka koma ƙanana.           Wani irin dummm taji a kunenta saboda furucin nasa. Bazata iya jurewa ba, dan haka tai azamar maida kanta ƙasa tana wasa da zanen less ɗin jikinta. A ranta mamakin yanda baijin ko kunyar ƙureta da ido a lokuta makamantan haka takeyi, ta matuƙar tsanar kallo a rayuwarta, sai dai ta rasa dalilin da yasa nashi baya mata zafi ko gundurarta sai dai sakata a wani yanayi da yake yi.......         “Uhhmm?!”. Ya buƙaci jin ta bakita cikin wani yanayi.           Fahimtar amsa yake buƙata daga gareta ya sata saurin jinjina masa kanta tana murmushi.       Basar da zancen yay ya ɗakko wani yana furzar da numfashi.      _“Kuka yana sake raunana raunin mai raunine a duk sanda yake yinsa. A tunaninki kukanne zai iya canja ƙaddararki? Ki zama mai juriya sai ki kasance cikin masu nasara. Ki ɗauki ƙaddara matsayin jarabawa sai zuciyarki ta dawwama a farin ciki. Ki amsa a duk lokacin da aka jehoki da sharri ko alkairi, sai dai zaɓin inda zaki ajiyeshi yana daga karfin imaninki ne. Bana bama mai son ganin kukana dama a duk lokacin da yaso hakan, domin in tabbatar masa da damarsa itace nasarata a yau da gobe na”._       Ya ƙare maganar da miƙewa zaune sosai ya ɗan leƙo fuskarta da hawaye ke sauka saboda nasiharsa ta shigeta. Tissue ɗin daya ɗiba a side drawer nata ya ajiye mata saman cinya yana miƙa mata yatsansa ƙarami.       “Zamu iya zama abokai”. Yanda yay maganar da abinda ya faɗa ya sata kasa jurewa saida ta ɗago ta kallesa. Idanunsa manya da suka canja launi ya kaɗa mata.          “Ustazah bana son gulma fa, da kika samu ma zaki zama ƙawar shugaban ƙasar NAYA?”. Yay maganar da ɗage gira sama yana ɗan ɓata fuska.     Murmushi tayi da miƙa masa nata yatsan suka ƙulla.           “A rage gulma ƙawata Ustazah”. Yay maganar da juyawa zai fita....       _“Nagode, ALLAH ya dawwamar da farin ciki da nasara a rayuwarka data ahalainka baki ɗaya, ya cika maka burinka na alkairi”._       Cak ya tsaya saboda tasirin da  addu'arta yay a dukanin zagayen ɓargonsa zuwa jini. Ya saki wani lalataccen murmushi daya kawata ƙyaƙyƙyawar fuskarsa, sai kuma ya juyo a hankali gaba ɗayansa yana fuskantarta tamkar mai tsoron hakan. Har yanzu tana a yanda ya barta, sai dai hawayene sabbi ke faman mata gudu a kumatu. A hankali ya tako ya dawo zuwa gareta. Saukar numfashinsa a kanta ya sata ɗagowa da sauri, ƙoƙarin jan jikinta tai baya saboda kusancin da suka samu yayi yawa. Amma sai ya hana hakan ta hanyar riƙo haɓarta ya sake kai fuskarsa gab da tata. A hankali ya ɗan hura mata iska a saman idanunta data rumtse, sai kuma yay sama kaɗan ya ɗora tausasan laɓɓansa saman goshinta. Harga ALLAH jitai kamar numfashinta zai ɗauke gaba ɗaya, dan kuwa a bazata taji saukar laɓansa saman goshin nata, cikin yanayin kasala ya sake sakar mata kiss a goshi idanusa a lumshe kamar yanda ta ƙara matse nata tanajin kamar ta saki fitsari kawai ta huta.      “I like you my Friend”. Ya faɗa a kunnenta cikin wata irin muryar raɗa batare da yasan sanda kalmar ta suɓuto daga ƙirjinsa zuwa harshen ba. Kamar yanda kalmar ta suɓuto masa batare da ya shirya ba haka tari ya subucema Raudha har yawu na sarƙe ta. Sosai jikinta ke tsuma yanzu kam har mai kallonta zai iya ganin hakan. Ramadhan da tuni ya kai ga ƙofa batare da ya juyo ba saboda abinda zuciyarsa ke ayyana masa ya furta, “Kisha ruwa”. Cikin tattausar muryarsa sannan ya fice ko waiwayenta baiyi ba.         Raudha da tari ke neman halaka mata numfashi, dan har ya fara fisga kamar Asthma ɗinta zai tashi ta silmiyo a gadon zuwa fridge, bama tasan a yanda ta ɗakko ruwan ba ta ɓalle murfin kawai ta kafa a baki. Yanda take shansa yana wuce mata a maƙoshi da gudun tsiya haka hawaye ke rige-rigen sakkowa da ga idanunta zuwa fuska. Tas ta shanye ruwan, ta zube ƙasa ita da robar tana maida numfashi.        Sai da taja kusan mintuna biyar a wajen tana kokawa da zuciya da tunaninta kafin hankalinta ya ɗan fara dawowa jikinta. “I like you”. Ta maimaita kalmar daya faɗa a saman laɓɓanta batare da zuciyarta ta amince da sakata a irin gurbin da takejin wasu na ambata ba ga abokan rayuwarsu.      “Tabbas ba haka bane, tashi nada banbanci da tasu”.   Ta sake faɗa a zahiri cikin yarda da kai, dan sam bata yarda da abinda ɗayan sashen zuciyarta ke tabbatar mata ba. Saboda son kauda hakan ma sai ta miƙe ta faɗa toilet kawai maybe idan ta sakarma kanta ruwa zatafi dawowa a hayyacinta fiye da haka. A wani ɓangaren kuwa mamakinsa take matuƙa. Ina ɗaɗɗaure fuskar tashi ta tafi ne da shan ƙamshi?. Kalaman Anne suka shiga dawo mata a safiyar da za'a kawota nan government house. _Ameenatu nasan zaki iya fuskantar ƙalubale kala-kala a cikin auren nan har ga Ramadhan dake amsa sunan miji gareki. Sai dai ina fatan ki zama mai haƙuri da juriya wataran zaki cimma nasarori. Bar ganinsa haka yana wannan ɗaure-ɗauren fuskar da tsumewa yanada sauƙin kai sosai musamman ga abinda yake so. Ɗan karan surutune da shi sannan yana dariya fiye da zatonki. Sai dai bazaki san duk waɗan nan abubuwanba sai kin zama jaruma sannan mace. Kar kiji nace mace ki zurfafa tunani. Mata da yawa sukan koma muna mata a wasu lokutan a gidan aure koma a waje. Amma duk macen data amsa sunanta *MACE* zaki sameta jaruma sannan duk tsanani bata raki. Mai haƙuri, mai juriya, mai tiƙe sirri, mai bama mijinta farin ciki, mai mantawa da duk wani ɓacin rai bayan ya fuskanceta koda a baya ya cutar da ita, mai kula da tarbiyyar ƴaƴanta dama duk wanda zai kasance a ƙarƙashinta koda ma'aikacin gidanta ne. Karkiyi sakaci da yima mijinki addu'a idan yay miki alkairi koda na murmushi ne, karkuma kiji shakkar bashi shawara ko sauke fushinsa koda bazai fahimceki a lokacin ba koya saurareki. Domin mata dayawa tsoron baza'a fahimcesu ko baza'a ɗauka shawarsu ba kesa watsar da miji idan yana cikin wani hali koda sun fahimci hakan. Wannan ba dai-dai bane ba. Bashi shawara koda baya ganin kimarki, wlhy Ameenatu wataran da kansa zaizo miki da damuwarsa domin yasan a wajenkine kawai zai samu mafita. kuma inhar kikaima miji shawara ta farko ya dace akanta ya kuma fita a damuwa, shima bazai ƙara yarda ya ganki cikin ƙunci bai ƙoƙari ganin ya fiddaki ba koda ace shine ya sakaki sai ya damu ya dawo yana lallashinki da son maye gurbin ɓacin ranki da farin ciki......_ Ƙwallane suka cika mata ido, dan kuwa tabbas taga haka, ta kuma yarda da batun Anne. Dan tana ƙyautata zaton canjinsa nada alaƙa da abinda ya faru ranar. Fatanta ALLAH dai yasa ya ɗore. (Uhm su Meeno aiki ya fara ci za'a mallake ɗan gimbiya Su'adah🤥😏🤕🚶🏻). ____________★★★★_____________              Su Lubnah sun sauka a ɗakin kusa da ita, sai dai saɓanin wancan lokaci ɗaki guda aka haɗesu yanzu. Sosai Raudha ta sake kame kanta da ga garesu, dan taci alwashin zata kiyaye gargaɗin Maah. Sai dai bazata sake bada fuska gasu Muneera suci zarafinta ba duk da kuwa sun girmeta.          To Alhmdllhi, tattarasu datai ta watsar ya taimaka mata matuƙa wajen saka shakkarta a zukatansu. Dan bama ta yarda ta fito inda suke balle su ganta. Ɗakinta kuwa da sun so dinga binta har ciki suyi mata cin kashi, gargaɗin da Ramadhan yay musu ya sakasu kame kansu dan sun san halinsa. Idan ransa ya ɓaci ya kama mutum ya ɓalla ya ɓalla banza babu mai ce masa baiyi dai-dai ba.      Bayan kwanaki uku da zuwansu data kama monday bayan sallar isha'i Raudha na ɗakinta kwance a gado cikin dauriyar ciwon mara data ɗan fara ji sama-sama telephone na ɗakinta tai tsuwwa alamar kira. Ɗagawa tai da tunain Mama Ladi ce ko Mama Tambaya ko Kuku. Dan sune kawai ke kiran layin idan tayi baƙi ko suna sonjin abinda zata ci ko take buƙata.        “Assalamu alaikum”. Ta faɗa a nutse cikin sanyin muryarta data sanyaya sakamakon ciwon da takeji na ɗan taso mata musamman ƙafafunta, tunda tazo gidan batai period ba. dama yakan mata haka wata biyu uku wani lokacin kafin yazo. Ramadhan dake acan falonsa na ƙasa ya ɗan lumshe ido yana sake lafewa jikin kukerar da yake zaune. Sai dai idonsa na kan COS dake daga ɗan gefensa.         “Wa'alaikassalam”. Ya bata amsar da ta ɗan sata zabura tana cire kan wayar a kunnenta ta kalla da mamaki. Sai dai maganar da taji kamar yana sake yi ya katse mata tu'ajibbin nata ta sake maida wayar a kunnenta.         “Ki sameni a downstairs”. Wani irin kakkauran numfashi Raudha ta fisgo daga ƙirjinta ta fesar, sai kuma tai tagumi tana jujjuya abun a ranta dan ji take kamar mai mafarki. (Itako mi zata masa yanzun? Yau fa tsahon kwana uku bata gansa ba ma. Kai ko motsinsa bataji ba). Rashin mai tayata zancen ya sata miƙewa kawai. hijjab fari ta ɗauka ta saka a jikinta har ƙasa, sai ta ɗan ƙara turare kawai a jikinta saboda tunawa da shawarwarin Bilkisu.      Sanin downstairs na fadarsa yake nufi ya sata nufar can kai tsaye, dan tunda take dashi bata taɓa ganinsa a falukan da zai kawoka sashen nata ba. Ta can yake shiga tacan yake fita. Inba dare ba bazaka taba ganinsa ko'a falon upstairs ɗin ba ma sai dai na downstairs din. Itako sau biyu kacal ta taɓa zuwansa.          Tun kafin ta gama sakkowa ta ƙare masa kallo shi da COS, kayan data gani a jikinsa jallabiya baƙa da adon golden ya sata tabbatar da ba yanzun ya dawo ba. Koma bai fita a gidan yau ɗinba ma oho masa. Duk da a nutse take tafiya hakan bai hana flat shoes ɗinta ɗan bada sautin ƙarar da ta saka Ramadhan duban stairs ɗin ba ta wutsiyar idanu.  Ganin sanye take cikin kayan mutunci ya sashi ɗan furzar da numfashi ya maida hankalinsa ga sakama takardun da COS ya kawo masa hannu.         Da sauri cos ya mike tsaye domin girmamawa a gareta, ya ɗan risinar da kansa yana faɗin, “Barka da fitowa ranki ya daɗe”.       Raudha da taji abin gingiringin ta haɗe yawu da ƙyar tana aro jarumta ta yanama kanta. A tausashe ta ce, “Barkan ka ya ƙoƙari?”.         “Alhmdllh Ranki ya daɗe”. Cos ya sake faɗa cike da girmamawa. Ramadhan dabai ɗago ba duk da yana saurarensu yay mata nuni da kujerar gefensa da hannu kafin ya ɗan dago ya dubi cos bayan Raudha takai zaune zuciyarta sai faman gudu take a ƙirjinta.          “Barka da dare”. Ta faɗa yanda take da tabbacin shi kaɗai zai iya jin gaisuwar tata. Bai amsa ba, bai kuma daina abinda yake ba har tsahon minti guda da wasu sakkani. Ya miƙama cos file ɗin da ya gama dubawar sannan ya dubi Raudha data fidda rai da zaton zai amsa matan.        “Kina lafiya?”. Ya faɗa shima a hankali yanda ita kaɗai zata iya jinsa. Ɗan ɗagowa Raudha tayi tana amsa masa a tunaninta har yanzu idonsa akan takardun yake. Ido suka haɗa, tai ƙoƙarin janye nata ya hana ta hanyar cafko yatsun hanunta da take ɗan murzawa a hankali alamar a takure take. A dolenta ta ɗan ware idanunta cikin nashi, shi kuma yay amfani da damar wajen kashe mata ido ɗaya cike da salon da ya nema birkita mata lissafi. Sai dai kafin ta dawo hayyacinta ya ɗauka envelope ɗin saman table ɗin gabansa ya aza mata bisa cinya.          “Ki duba a cikinsu ki zaɓi guards biyu da zasu dinga kasancewa da ke”.     Tamkar mai koyon magana ko mai tsoron buɗe laɓɓa tace, “Amma....”         “Shiiii!!” Ya faɗa a hankali yana ɗaura pen ɗin hanunsa saman lips ɗinsa tausasa kalar pink. Dole ta haɗiye yawu a hankali dan har yanzu idonsa na cikin nata tace, “Thanks”.         Wani tattausan murmushi yay mata yana wani lumsha idanu da janye yatsun hanunsa dake murza nata ya maida hankali ga cos da yay ƙasa da kansa tamkar hankalinsa nakan takardar da yake dubawa. Sai dai kuma a munafunce yake satar kallon wannan soyayya ta Mr president da first lady. Sai da ya ga Ramadhan zai juyi ne yay saurin maida dukkan hankalinsa ga takardun sosai.        Oho daga Ramadhan har Raudha basu san yanayi ba. Dan tuni Raudha ta zaro hotunan cikin envelope ɗin tana dubawa. Ƴammata ne cikin shigar uniform na aiki, wasu kuma suit na mata. Dukansu bazasufi shekaru ashirin da biyar zuwa da bakwai talatin ba. Sai da ta duba duk hotunan guda biyar sannan ta zaɓa na mutum biyu dake sanye da baby hijjab alamar musulmai ne, maybe ma yarenta ne duka.         Kamar mai jin tsoron maganar yanzun ma tace, “Waɗan nan sunyi”.      Kai kawai Ramadhan ya jinjina mata batare da ya ɗago ba.  Dan rabin hankalinsa na ga abinda yake dubawa a file ɗin hanunsa. Kusan mintuna uku sannan ya ɗan duba cos da alamar ɓacin rai a fuskarsa... “Jafar! Abinda ke rubuce anan kuwa gaskiya ne? Ko idona ne?”.            “Tabbas gaskiya ne ranka ya daɗe. Dan duka mutane goma sha ukun nan daka gani akwai kwangilolin ayyuka a kansu, wasun su sun fara basu ƙarasa ba, wasuma ko niyyar farawar basuyi ba. Kuma munada tabbacin kuɗaɗen aikin sun fita a bitalmani harda saka hanun shugaban ƙasa mai sauka. Waɗan nan sune evidences na fitar kuɗaɗen duka”.      Yay maganar da miƙa masa wani file ɗin. Sosai Raudha ta ɗago tana kallonsu yanzun kam, dan zancen nasu haka kawai ya ɗauka hankalinta. Ta ɗan kafama Ramadhan daya dafe kansa bayan duba takardun idanunta.        “Cos!!”. Ya faɗa a kausashe.        “Yes your excellency!”.     “Ina buƙatar a tura ma dukansu takardar gayyata, ku zauna da su kai da minister Abubakar Gandu Ku tattauna dasu domin bibiyar gaskiyar lamarin. Bayan kun tabbatar da gaskiyarsu ku basu kwanaki biyu kacal su dawo da kuɗaɗen kafin mu miƙa sunansu ga hukuma”.         “Okay sir!”.      Ɗan murmushi Raudha ta saki daya ƙawata fuskarta, cike da ƙarfin halin danne ciwon marar dake tsinkulinta, sai hakan yay dai-dai da ɗagowar Ramadhan suka haɗa idanu. Harara ya sakar mata yana sake tsuke fuska. Sai kawai murmushin ya sake suɓuce mata batare data shirya hakan ba. Idanu ya ɗan ƙanƙance ɓacin ransa na sake bayyana a fuskarsa, tai saurin girgiza masa kanta da kama kunuwanta dake cikin hijjab alamar “Am sorry”.        Baya ya ɗanyi da jikinsa yana lumshe idanu da furzar da huci. Hakan da yay ya saka Raudha cikin dauriya tace, “Ranka ya daɗe idan babu damuwa nace wani abu dan ALLAH?”.          Babu shiri ya buɗe idanunsa dan baiyi zaton jin hakan daga gareta ba. Ta marairaice fuska kamar zata fasa kuka. “Dan ALLAH abokina”        Tai maganar cike da marairaicewa. Sai yanayin yay kama da wadda shaƙuwa ke tsakaninsu sosai take masa shagwaɓa. Harga ALLAH sai da zuciyar Ramadhan ta motsa. Domin shima dai mutum ne tamkar kowa, sannan zuciya gare a ƙirji ba kuma dutse bane....     Kafin ya gama dawowa hayyacinsa ta ce, “Ranka ya daɗe maimakon a damu da zancen su dawo da kuɗin kuma su sake faɗawa hanun ɓata gari kafin su koma a bital mali, mizai hana a zaman da zakuyi dasu, mizai hana ku tilastasu ƙarasa aikin da suka fara, waɗanda basu faraba su fara kawai. Idan da buƙatar ƙarin wani abu da zai inganta aikin fiye da farko ko zai kammalashi sai ku daɗa musu. Koba komai hakan zai sa talakawa su tabbatar aiki kukazo yi da gaske......”      Yanda ya kafeta da idanu ya sata haɗiyar yawu da ƙyar. Cikin ɗan shakku da ganin zaƙewarta ya sata faɗin, “Ban faɗi haka dan ganin gazawar maganarku ba. Sai dan kawai a nawa hasashen shari'a da su tamkar zaman ɓata wani yanki na lokutankune masu muhimmanci ga alƙawran da akaima talakawa. Dan fallasasu zai ɗauke hankulanku ne kacokan ya maida can, aikin da kukai burin yi lokacinsa yayta tafiya. Bai kuma zama lallai su da suka basu kwangilar ba su yarda su tozarta kai tsaye tunda maybe akwai ƴan uwansu ko abokansu a ciki da makamantan hakan. Ƙila kuma dalilin hakan da zaku musu su shiryu su koma mutanen kirki wajen gyara halayyarsu har na ƙasa dasu masu tasowa suyi koyi idan kun ɗorasu akan irin wannnan matsayin. Idan na shiga hurmin daba nawa ba a gafarceni ranka ya daɗe”.          “Raf! Raf! Raf!”. Cos ya fara sakin tafi bakinsa a washe da murmushi.       “Oh my god uwa garemu. Ranki ya daɗe wannan shawara ce mai daraja data warware kowanne irin tarnaƙi cikin sauƙi ai. ALLAH ya kara girma da nisan kwana masu albarka.”         A ɗarare Raudha tai murmushin yaƙe. Dan bata da tabbacin mai gayya mai aikin shi ya amshi zancen kamar yanda taga cos ya nuna jin daɗinsa kai tsaye ba.       Cos da ya sha jinin jikinsa ga yanayin shugaban ƙasar shima yay saurin dakatawa yana faɗin,  “Ranka ya daɗe m....”      Hannu shugaban ƙasa Ramadhan ya ɗaga masa yana buɗe idanunsa da furzar da iska mai nauyi...........✍        *_Humm su Ustazah kai ya fara buɗewa fa, an fara samun kan😹😹😜🚶🏻_*      *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/27, 8:50 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62b6073efa0b02c20d2ac11e *_Episode 37_* ..........“Vary interesting”. ya faɗa a hankali, batare da ya basu damar maganaba ya cigaba da faɗin, “Inaga zamubi exactly idea ɗin nata, sai ka shirya muku zama a tura musu invitation ok”.         “Yes ranka ya daɗe. ALLAH ya ƙara lafiya da shekaru masu albarka.”       Raudha ce kawai ta amsa da amin tana sauke ajiyar zuciya kusan sau uku a jere. Harga ALLAH tayi matuƙar yin ƙarfin hali ne kawai wajen faɗa. Ba komai ya sata kawo hakan ba sai tunawa da su tsohon shugaban ƙasa. Dan tabbas zasu iya bin kowacce hanya domin ganin anƙi hukunta su waɗan nan ƴan kwangilar, sannan yanda suke ɗane da shi a tarko fara fiddo manufarsa kai tsaye ga duniya cutarwa ce garesa. Dan ta tabbatar bazasu ƙyalesa ba yay aikin shekara biyun da suka ƙudiri aniyar bashi damar yi ɗin. (Duk da tasan su basu isa hana zartar da ƙaddarar da babu wani hannu daya ƙirƙiri rubutata a doron duniya).....         Hotunan dake saman cinyarta da ya ɗauka ya sata dawowa a hayyacinta. Bayan ya duba waɗanda ta zaɓa batare da yace mata komai ba ya mikama cos.       “Okay sir an gama insha ALLAH. Za'a kaima Chairman ɗin zuwa safiya zasu fara aikinsu.”.      Kai kawai shugaban ƙasa ya jinjina masa tare da tura masa sausan files ɗin dake ajiye saman centre table ɗin. “Babu yuwuwar zan duba waɗan nan ɗin a yanzun. Inaga ma ƙarasa a office idan ALLAH ya kaimu, idan na fito ina buƙar fara ganawa da vice president”.        “Okay ranka ya daɗe, ALLAH ya huta gajiya ya ƙara lafiya. A huta lafiya ranki ya daɗe”. Cos ya faɗa cikin rissinar da kai alamar respect sannan ya mike da takardun daya tattare ɗin ya tura a bag ɗin da ya shigo da su. Raudha na ganin ya fice itama ta yunƙura da nufin miƙewa dan mararta ta takura mata dauriyarta neman fara ƙarewa takeyi. Jitai an cafko mata hannu.          Da ƙarfi ta rumtse idanu dan harga ALLAH wannan sabon salon nashi na harmutsata. Abune da shi kaɗai ya fara mata su a rayuwa....        “Nace na gama da ke ne?”.    A hankali ta girgiza kanta tana faɗin,  “Kayi haƙuri” ta koma ta zauna tana ƙoƙarin cire yatsun hanunta a nashi. Gaba ɗaya yanda yake murzasu ɗin harmutsa mata jinin jiki yake yi. Sakinta yay shima, ya koma jikin kujerar ya lafe yana ɗan furzar da iskar bakinsa. Sai dai yanda maƙogwaronsa ke kai kawo zai baka tabbacin magana yake da zuciyarsa. Dan harda ɗan matse idanu yayi lokacin da yake tura lip nashi a baki yana ɗan ciza. Sai kuma ya buɗe idanun a kanta da alamun kore tu anin dake bijiro masa ya ɗan tsuke fuska                         Takardun da ke gefensa ya ɗauka ya miƙa mata, “Komai ya kammala akan school naki. Akwai sabon driver da zai dinga kaiki yana maido ki.”       Hannu biyu tasa ta amsa tanajin kamar ta tashi taita tsallen daɗi. Amma sai ta daure ta shiga masa godiya da addu'a cikin dauriyar danne ciwon da ke taso mata.      Gyaran murya ya ɗanyi cikin kausasa harshe ya cigaba da faɗin, “Barinki kije makaranta bashike nufin zaki iya duk abinda ranki ya so ba. Ki kama kanki dan a yanzu kinada banbanci da baya. Akwai aure a kanki banason shigar banza. Sannan ki sani ke matar shugaban ƙasa ce, komai naki a yanzu abin tallatawa ne ga mutane koda bai kai ya kawo ba. Ya rage naki ki riƙe wannan darajan ko kiyi sakaci da shi komai zai iya faruwa. A waɗan nan takardun akwai na bank a ciki, ki cika komai kiyi musu singing za'a maidasu can. Karatu nada muhimmanci a gareki matuƙa a wannan gaɓar, saboda ƙarancin shekarunki da matsayin da kike kai a yanzu, ya rage naki ki maida hankali kiyi abinda ya kaiki kokiyi wasa da damarki.”       Ganin yanda yake magana serious ya sata sake nutsuwa itama. “Insha ALLAH zaka sameni mai kiyayewa. Bazan gaji da maka godiya ba da fatan alkairi a rayuwarka. ALLAH ya baka ikon sauke nauyin al'umma ka gamawa lafiya cikin farin ciki tamkar yanda aka zaɓeka cikin farin ciki. ALLAH ya saka maka da alkairi kai da zuri'arka baki ɗaya”.        “Amin, thanks”. Ya faɗa yana miƙa mata leda mai tambarin apple ƴar madaidaiciya. Sai kuma ya marairaice fuska cike da salon tsokana ya fara faɗin,      “A duk lokacin da zaki fita a gidan nan ina son na dinga sani Ustazah. Dan bana bukatar matata na rayuwa tamkar akuyar sake da ko'ina zata iya jefa ƙafa a lokacin da take so. Kinada damar canja driver ko securitys ɗin da za'a kawo miki idan halayensu basu miki ba. Karkiyi tunanin yin amfani da matsayin da ALLAH ya bamu wajen taka wani, idan haka ta kasance hukunci zai iya bi ta kanki kamar kowa. Idan kinada buƙatar wani abu zaki iya faɗa”.          Murmushi mai faɗi Raudha ta saki har haƙwaranta na bayyana a waje. Ramadhan dake kallonta yay azamar lumshe idanunsa da jan numfashi a fisge. Raudha da batasan murmushi nata ya zama wani abu daban ba ta ɗago idanunta taɗan kallesa tana jera masa addu'ar fatan alkairi a rayuwa.        Kansa kawai ya jinjina mata batare da ya buɗe idanun ba. Wani irin murɗa mata maranta yayi, tai saurin kife kanta a hanun kujerar jikinta na rawa. Sunan ALLAH take ambata a zuciyarta da damƙe hanun kukerar da iyakar ƙarfinta.       Shurun da Ramadhan yaji ne ya sashi buɗe ido da nufin sallamarta dan yana son zuwa shima ya hutama ransa. A gajiye yake matuƙa sakamakon motsa jiki da yayi yau sosai da yammar nan. Dan ya fita a keke, sai dai securitys na biye da shi a mashina da mota ɗaya badan yaso haka ba.          “Zanje ciki, kije abinki kema”. Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa. Sai dai ganin taƙi ta ko motsa ya sashi sake dubanta dai-dai yana tsayawa kan ƙafafunsa. “What happend?”.     Ya faɗa yanabin hanunta data matse hanun kujera da kallo, ga kuma kamar jikinta ma na rawa. Duk yanda taso ɗagowa ta amsa masa kasawa tai, sai ma ƙoƙarin zamowa da take akan kukerar alamar abin ya fara tsauri. Shi tsoro ma abin yaso ɗan bashi, amma sai yay dauriyar matsowa ya tareta ganin zata kai ƙasa. Birkitota yay a jikin nasa, amma sai yaci karo da uban zufan data haɗa cikin ƙanƙanin lokaci. Ta ƙanƙamesa da iya ƙarfinta cikin azaba.....        “Ya ALLAH. K! What's wrong with you?”.         Ina batama san yanai ba, dan hankalinta ya fara nisa da duniyarta. Ganin yanda ta matse cikinta da hannu guda ya sashi kai hannu wajen ta saman hijjab ɗin. Sai kuma ya furzar da iskar bakinsa yana miƙewa ɗauke da ita gaba ɗaya. Dan ya fahimci yana buƙatar zuwa ɗaki da ita ya bincika da ƙyau.       Hawowarsa cikin falon yayi dai-dai da fitowar su Aynah da ga ɗakinsu zasuje ƙasa cin abinci. Turus sukai cikin al'ajab. Sai dai tun kallo guda da sukai musu kowanne yay ƙasa da kai dan sun san halinsa. Shiko baima ko kalli inda suke ba ya nufi bedroom ɗinsa ɗauke da Raudha da zuwa yanzu ma numfashinta ya fara nisa da ƙirjinta.        “What!”. Munirah ta faɗa lokacin da ya ɓacema ganinsu.        “What! Ko what sisto. Amma dai wannan tsinanniyar yarinya anyi makira dai. Ɗauka fa? Lallai an gama shanye kurwar Yah Ramadhan a wajen nan”.         Cikin takaici Lubnah ta juya bedroom ɗin nasu batare data tanka musu ba tana ƙoƙarin kiran Gimbiya Su'adah.         A can ɗakin Ramadhan kam lokacin da yake shinfiɗe Raudha a gado sai ya fahimci ma ta suma ai. Mamaki abun ya bashi tamkar almara ko wani shirin film. Suma fa. Duk da abun ya bashi tsoro sai baiyi wani irin nuna rikicewa da ruɗani a zahiri ba dan mutum ne shi da bai iya gaggawa ba akan komai. A nutse ya zare mata dogon hijjab ɗin jikinta. Sai ga kayan barcinta wando iya gwiwa da mitsilar rigar best sun bayyana. Ruwan dake ajiye a side drawer nashi ya ɗauka ya shafa mata a fuska. Na farko ko motsi batai ba, sai da ya zuba mata da yawa ta kawo nannauyan numfashi. Sai kuma ta fashe da sabon kuka tana kiran sunan ALLAH da kira Mummy.        Hanunsa ya ɗan kai a goshi ya murza hanunsa ɗaya riƙe da ƙugunsa yana kallonta, sai kuma ya kai zaune kafarsa ɗaya a ƙasa ya tanƙwashe ɗayar a saman gadon ya ɗan tallafo fuskarta.        “Please relax mike damunki ne Ameenatu?”.   Duk da ta jisa bata iya bashi amsa ba, saima damƙo hanunsa da ke ƙoƙarin riƙo nata tayi cikin rashin fahimtar manta dawa take tare ta ɗora saman mararta tana jan wahalallen numfashi.        Duk da akan rigane sai da tsigar jikinsa ta tashi. Ya ɗan lumshe idanu sa sakamakon jin wani irin ɗumi da marar ta ɗauka. “Oh my GOD ”. Ya ambata akan laɓɓansa. Da ƙyar ya samu ta barshi ya janye hanunsa a wajen, ɗaya a cikin wayoyinsa ya ɗauka ya fara neman layin Anne. Dan shi dai baisan wata doctor mace ba bayan kanwarsa Safina da zai nema tazo ta dubata a yanzun. Bugu ɗaya kuwa Anne ta ɗauka saboda wayar na hanunta ne tana duba abu.        “Kai lafiya kira a daren nan Ramadhan?”.        Hannu ya kai saman goshinsa ya murza da tura lip ɗinsa a baki ya ɗan ciza kafin cikin damuwa yace, “Anne akwai damuwa ne. Bata da lafiya ko zamu samu doctor ne?.”         “Ya ALLAHU, waye baida lafiya? Aminatu?”.       Yanda tai tambayar ta kuma bama kanta amsa ya sashi sakin ɗan murmushi duk da damuwar da fuskarsa ta nuna.....        “Kaga ina zuwa bara na nemo Doctor Shamsu......”       “A'a Anne i no need him. Mace nake bukata”.        “Naji uban ƴan kishi”. Anne ta faɗa tana yanke kiran. “Kishi!!?”.       Ya maimaita kalmar yana janye wayar a kunensa cike da mamaki. Dan kalmar tazo masa a bazata. Baki ya ɗan taɓe da ɗage kafaɗa irin (I don't care) Ɗin nan. Sai ma ya dire wayar a gefe kawai ya kamo Raudha dake cigaba da murƙususun ya ɗaura kanta bisa cinyarsa. Ai kamar jira take ta kife kanta a cikinsa ta zagayesa da hannayenta biyu ta ƙanƙame dan azaba.        Harga ALLAH kaɗan ya rage ya saki ƙaramin ihu, amma sai ya dake ta hanyar rumtse idanunsa gam da tura lip ɗinsa cikin baki ya taune da ƙarfi kamar zai hudashi ko shi yay laifin.       Cikin abinda bai wuce mintuna 30 ba doctor Hauwa ta iso tare da Bilkisu datai mata rakkiya. Sai dai basu samu damar shigowa ba sai da mama ladi taje tai magana kai tsaye. Yanda suka samu Raudha a jikinsa tanata murƙususu ya saka Bilkisu jin nauyi ta juya ta fita bayan ta gaida shi. Kai kawai ya iya ɗaga mata, kafin ya dakatar da ita daga ƙoƙarin fitar.       Dole ta dawo kanta a ƙasa ta taimakama Dr Hauwa'u ta dubata kamar yanda ya buƙata. Dan shi ya samu ya zame Raudhan a jikinsa da ƙyar ya tashi ya basu waje saboda Dr Hauwa'u maƙwafciyarsu ce. Hasalima babbar mace ce sa'ar su Maah. Yana mata kallon uwa ne kodan dalilin ɗanta da suke tare tun ƙuruciya. Sai dai koda ya koma gefe ya zauna cikin sofa ransa fal wasiwasin mike damunta haka?.         Dr Hauwa'u data ɗan duba Raudha da a yanzu take a jikin Bilkisu ta juyo ta kalli Ramadhan da idonsa ke kansu shima. “My son gaskiya tana tare da babbar matsala na ciwon mara yarinyar nan.  Da ace ma a asibiti muke ina buƙatar mata gwaje-gwaje kafin nasan miya kamata na mata...”       Cikin girmamawa yace, “Mom to yanzu yaya za'ayi kenan?”.            “Eh to ba damuwa, zan mata wata allura insha ALLAH zata samu sauƙi, sai dai bayan ta samu lafiya ina buƙatar ganinta a hospital kar kuyi wasa”.        “Insha ALLAHU Mom”. Ya faɗa nan ma da girmamawa a gareta. Raudha ba wani tsoron allura take ba, dan haka cikin sauƙi Dr Hauwa tai mata allurar, mintuna goma ba'a cikaba ta fara yunƙurin amai. Cikin sauri Bilkisu ta taimaka mata zuwa bayi                  ★★★     A can ko ɓangaren su Munirah tuni ta dannama Gimbiya Su'adah kira. Cikin sa'a kuwa ta ɗaga a bugun farko dan tana bedroom ɗinta tana shirin wucewa turaka. Cikin tashin hankalin bayanin da Munirah tai mata a kausashe tace, “K ban san shashanci wace irin magana ce wannan?”.       “Wlhy da gaske nake Maah! Yanzu haka ma ga Aunty Bily tare da Momyn Ya Suraj nan sunzo gidan da alama zata dubata ne. Kinga ko inba ciki ba taya za'a taso Momyn Ya Suraj a yanzu duk da bawani dare ne yayi ba. Dama tun ɗazun nake lura da ita tanata wani yamutse-yamutse, da kuku ya shirya lunch ma bataci ba catai ya samo mata farfesu mai yaji”.       “What! Impossible hakan ta kasance ina raye. Ramadhan!! Ashe zan tabbatar maka da ni wacece idan ka manta”.      Gimbiya Su'adah ta faɗa a matukar tsawacen da har ta firgita Munirah mai kai gulmar. Cikin daka tsawa ta ce, “Maza jeki haɗani da shi!!”.      Idanu sosai Munirah ta zaro kamar tana gabanta. Hankali tashe ta ce, “Abeg Maah. Taya zan kai masa waya ki masa wannan maganar bai ɓallani ya zubar da banza ba. Dan ALLAH ki rufamin asiri, zamowar Yaya shugaban ƙasa bawai yana nufin yayi laushin da zan iya kai masa wargi bane Maah. Please na roƙeki ki kirashi a layinshi”.       Tsaki gimbiya Su'adah tai tare da ɗaga wayar tata ta dasa da ƙasa. ALLAH ya taimaka akan gado ta faɗa da lallai saita tashi aiki a yau. Ita Su'adah har tana raye ɗanta yayma yarinyar data fi tsana fiye da komai a duniya ciki batare data farga ba, ita yaron nan zai cima amana ya haɗa shimfiɗa da jinin karuwai bayan ta masa gargaɗi. Wlhy bazai yuwuba, bazata taɓa haɗa zuri'a da yarinyarnan ba. sai dai komi zai faru ya faru. Kuma lallai sai taci mutuncin Ramadhan fiye da yanda yake zato ko tsammani).     Ita kaɗai taketa surutanta a zuciya tana kaiwa da komowa a tsakiyar katafaren ɗakinta tamkar mai dawafi.       ★★★       Ramadhan da bai san anai ba tuni Dr Hauwa ta bama Raudha duk wani taimako da ya dace, ta kuma tabbatar masa da Raudha zata samu barci mai ƙarfi da zai taimaka mata wajen samun nutsuwa. Amma kar suyi wasa bayan ta samu lafiya ta sameta a asibiti. Da ga haka sukai masa sallama zasu wuce bayan Bilkisu taje ɗakin Raudha ɗin ta ɗakko mata part da pant data fahimci tana bukata. Sai dai a ranta tana jin daɗi da mamakin yaushe Raudha suka ɗinke da Yayan nasu haka har da kwana a ɗakinsa. Koma dai miye tayi farin ciki ita kam dan tana ƙaunar wannan haɗin har cikin ranta.       Sosai Raudha da barci ke ɗibar idonta taji daɗin abinda Bilkisu ta ɗakko mata. Tana son tace zata koma ɗakinta ta kasa ɗaga baki saboda barci. Dole ta haƙura ta lumshe idanun bayan ta sake cusa pant da part ɗin cikin hijjab ɗin jikinta wai kar Ramadhan ya gani.       Ya jima zaune bai motsa ba a inda suka barshi har Raudha tai nisa a barci. Abubuwane birjik a cikin kansa da UBANGIJI kaɗai yake fatan yay masa tallafi a kansu. A hankali ya miƙe ya nufi gadon saitin inda Raudha ke kwance a baki-baki, dan a nufinta ta ɗan kwanta ne idan su Bilkisu sun tafi itama ta koma ɗakinta.      Tsaye yay a kanta ya zuba mata idanu kawai tamkar mai son gano matsalar tata a kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta. A hankali ya turo iskar ƙirjinsa zuwa baki ya fesar dai-dai lokacin da yake kai hannu ya ɗage hijjab ɗin jikinta da nufin cire mata gudun karya cutar da ita.........✍           *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/27, 8:50 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62b6073efa0b02c20d2ac11e *_Episode 38_* ..........Hijjab ɗin ya ajiye gefe idanunsa akan hanunta data matse pants biyu da ledar part da Bilkisu ta ɗakko mata. A hankali ya kai zaune gefenta, sannan ya kamo hanun nata ya zare abinda take ɓoyon. Kai tsaye ya gane ko minene, ya ajiyesu gefe da ɗan sake tsura mata ido. Yanda ta ɓata fuskar alamar batajin daɗi har a cikin barci ya sashi sakin ƙasaitaccen murmushi yana kauda idanunsa. Sai kuma ya miƙe ya gyara mata kwanciyarta batare da yace uffanba ya nufi toilet bayan ya lulluɓeta da lallausan duvet nashi dake ta tashin ƙamshin turarurrukan sa.         Kusan ƙarfe goma na dare Ramadhan ya kai kwance bisa katafaren gadon nasa bayan kammala komai na al'adar rayuwarsa kafin kwanciya. Addu'a yay, harya shafe iya jikinsa zai kwanta sai kuma ya ɗan dubi Raudha dake gefensa. Miya tuna oho masa ya karanta mata addu'ar itama ya tofa mata sannan ya kwanta zuciyarsa na masa wani irin kaikawo na son tuna baya. Amnah tamkar mage take a wajen son jiki, a duk sanda yake gida zaka sameta manne da shi. Tun hakan na takura rayuwarsa har ya saba. Shiyyasa bayan rasuwarta ya jigatu matuƙa da kewa. Taunar lip ɗinsa ya shigayi da ƙarfi idanunsa na tara ƙwalla, a hankali ya shiga ambaton sunayen ALLAH dan yasan zurfafa tunanin wani motsawar ciwone daga zuciya zuwa ƙwaƙwalwa. Cikin amincin ALLAH batare da ya farga ba sai barci yay awan gaba da shi.      Kasancewar allurar da akaima Raudha yasa barcinta yin nauyi harya tashi yay salla bata farka ba. Bai tadata ba tunda yasan bata salla. Barcinta ta sha sosai har kusan bakwai da wasu mintuna. Ta buɗe ido a hankali tana ambaton addu'ar tashi a barci. Taja ƴan mintuna kafin ta tashi zaune, ta riga bin ɗakin da kallo a ɗan firgice dan tama manta a ina take. Duk abinda take Ramadhan na'a ɗakin zaune bakin gado ta bayanta yana dalle-danne a lap-top da alama aiki yake mai muhimmanci.       Sam bata lura ba, dan ta juya masa baya. Ji take tamkar jikinta ya ɓaci, dan haka ta fara laluben kayanta na jiya da bilkisu ta ɗakko mata. Ganinsa zaunen a bazata ya sakata waro idanu waje tasa hannu tana kare jikinta kunya tamkar ta nutse. Zuciyarta har wani gudu take kamar zata fito. (Na shiga tara ni Amina ina zanga Hijjab ɗina?) ta faɗa a zuciyarta tana ɗaga duvet ɗin da sauri-sauri.         Duk abinda take bai ko nuna yasan tanai ba, amma kuma yana lure da ita ta gefen ido. Abinda yay tunanin tana nema dake a gefensa ya turo mata da hannu batare da ya ɗago kansa da ga lap-top ɗin ba. Wani irin takaici da kunya suka sake lulluɓe Raudha taji tamkar taita tsala ihu kawai. Da sauri tasa hannu ta kwashe, tsabar rikicewa batama san ta nufi hanyar fita ba.       Yatsunsa ya murza suka bada sautin ɗas-ɗas da ya tilastata tsayawa ta juyo, har yanzu kansa naga lap-top, amma sai yay mata nuni da hanyar toilet ɗin ɗakin batare da yayi magana ba.        (Wayyo ni Aminah na shiga uku na) ta faɗa a zuciyarta kamar zata fashe da kuka. Dole ta nufi hanyar toilet dan bata da zaɓin daya wuce hakan. Bazata iya bijirema umarninsa ba, sannan bazatama iya fita da kayan jikinta ba. Ɗazunma ruɗewa ta sata nufar can da rashin zaɓi.       Yau kam ba kamar jiya ba, tsaf ta zauna ta kalle toilet daya lashi kuɗaɗe, da ga ƙarshe ta fara wanka zuciyarta cike da mita dole shuwagabanni su shagala da son mulki da mantawa da talaka. Sai da ta kammala wankan tana ninke kayan barcinta taci karo da jinin daya ɓata mata wando, cikin rumtse ido ta dafe kai dan ta tabbatar ta ɓata masa gado kenan.. Ita kam taga takanta yau da a gidan nan. Duk da kunyar da take na fito ɗaure da towel haka ta daure dan gara fitowa da towel tunda ta yafo wani akan yaga jinin data ɓata masa gado.       Saɓanin ɗazun yanzu tsaye ta samesa saitin inda ta tashi yana ɗage-ɗagen duvet. Kai tsaye zuciyarya ta ayyana mata yana dubawane kota ɓata masa gado. Sosai Raudha tama manta waye shi a wajenta. Dan batasan tai tsalle ta dire ba a gabansa ta damƙe duvet ɗin hanunsa ta cikuykuyesa a hannu. Mamaki ya sakashi dubanta daga sama zuwa ƙasa. Sai dai kuma baice komaiba ya kai zaune da miƙa hannu zai sake amsar duvet ɗin dan bai buƙatar yawan magana yau ransa a ɓace yake. Tsam ta matsesa a jikinta kamar zatai kuka....         “Ni wlhy bansan hakan ta faru ba”...      Mamakinta ya sashi sake ware idanunsa a kanta.     “Are you okay?”. Kanta ta jinjina masa kawai tana sake matse bargon a jikinta. Dan koba komai yana sake bama jikinta kariya da towel ne kawai. sannan bata son yaga yanda ta ɓata masa gadon.      Shi saima abun ya girmesa da bashi dariya amma ya gimtse. Cikin takaicin ɓata masa lokaci da take ya kama bargon zai fisge saita biyoshi itama, kawai sai gata a cinyarsa ɗare-ɗare zaune.       (Ya ALLAH yarinyarnan kuwa tanada lafiya?).      Ya ayyana a ransa da mamaki jininsa na yamutsawa da sauri-sauri. Tuna abu zaiyi mai muhimmanci da wayar da yake nema ya sashi ƙoƙarin fisgar bargon batare da ya cemata komai ba a zahiri, amma kuma ya harɗe mata ƙafa da tasa yanda ta kasa tashi a jikin nasa duk da tanata ƙoƙarin hakan. Wajen fisgar bargo towel ya kwance. Ai bama tasan ta fasa ƙara ba da ƙadandanesa gaba ɗaya. Dan duk hannayenta ta harɗo wuyansa da su ta kife ƙirjinta a nashi jikinta na rawa. Babu shiri ya saki bargon ya toshe kunnensa.          Jin yanda take sake matsesa tana neman harmutsa masa tunani ya sashi cire hanun a kunnensa. Sai kuma a bazata ya saki murmushi jin ɗumin hawayenta a jikinsa alamar kuka takeyi. Yay ɗan gyaran murya idonsa akan gashinta dake ɗaure cikin ribbon duk ya sukurkuce wani ma ya jiƙe a gaban goshinta. So take ta ɗagashi amma bazata iyaba.        (Oh oh yau naga takaina). Ya ayyana a ransa, a fili kam cikin raɗa yace, “Ustazah jikina kar yay ciwo kin cika nauyi”. Yana maganar ne yana kama jelar gashin nata dan ya tabbatar dai nata ɗinne ko sakawar take kamar yanda yake zargi. Tabbatar da natane ya sakashi tura yatsun hanunsa duka cikin sumar ya zare ribbon ɗin....         Saurin sakinsa Raudha tai baki ɗaya jin wani kuma baƙon lamarin daga garesa, ta fisgi bargon ta cukuykuye jikinta a ciki. Da ƙyar ya iya danne dariyarsa, yanda ta cukuykuye ɗin ya bashi damar ganin wayarsa da yake nema, sai dai tana kusan rabin kanta. Gyara murya yayi, ta buɗe idanunta kaɗan sai suka haɗa ido. Ganin zata maida ta rufe ya sakashi mata nuni da wayar da ɗan yatsa. Wajen ta kalla dai-dai yana miƙo hanunsa zai ɗauka. Ta ɗan ɗaga jikinta tana tura baki. Duk yanda yaso dannewa ya kasa sai da murmushi ya suɓuce masa har haƙoransa na bayyana.          (Masha ALLAH) ta ayyana a ranta ganin yanda murmushin yay masa bala'in ƙyau. Shi dai tuni ya ɗauka wayarsa ya bar wajen. So take ta tashi taje ɗakinta amma ta kasa, haka ta cigaba da kwanciya a wajen nannaɗe a bargo harya kammala shirinsa cikin ɗayar shadda milk color datai masa ƙyau sosai. Ya murza brown hula mai kwalliyar milk kaɗan-kaɗan.           Ƙaruwar ƙamshin turarensa _Sauvage dior_ cikin hancinta ya sata ɗan buɗe ido. Tsaye yake a side drawer ɗin gefen da take yana ƙoƙarin saka link ɗin hanu. Duk yanda taso janyewa kafin ya kamata ta kasa, haka ta cigaba da binsa da kallo harya juyo hanunsa ɗauke da takardu suka haɗa ido. Saurin rufewa tai shi kuma ya ɗan taɓe baki yabar wajen dan tun ɗazun dama yake ji a jikinsa ana kallonsa.          “Ni na wuce office kinsa na makara yau. Saura ki batamin gado da wannan abun naki”. Ya faɗa yana ƙoƙarin barin ɗakin. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana ɗan harar bayansa, yana ƙoƙarin murɗa handle ɗin ƙofar tace, “ALLAH ya tsare ya bada nasara”.        Bataji ya amsa ba, sai dai tasan zai amsa ɗin saboda da wuya tai masa addu'a yaƙi amsawa balle yanzu da suke ɗasawa kuma. Yauma ta fahimci kamar akwai abinda ke damunsa ko kuma ƴan girman kanne a kusa. Gaisuwa ce dai sai ya gadama. Bayan ficewar tasa taja kusan mintuna 2 sannan ta miƙe, ita kanta sai yanzu abinda ya farun ke bata dariya. Taita sakin murmushi tana ƙoƙarin gyara masa gadon bayan ta nema towel ɗinta daya koma gefe ta saka.      Tsaf ta gyara ko ina har toilet. Ta tattara kayanta ta fice bayan ta saka hijjab. Tayi mamakin cin karo da su Aynah a falon, sai dai ta ɗauke kanta kawai da niyyar wucesu batare data nuna tasan da zamansu ba.         “ALLAH dai ya rabamu da karuwanci ni Aina'u. Tsabar jaraba baza'a iya riƙe kai ba saboda an saba da maza tun a titi tamkar uwa da danginta. Ni ALLAH ma yasa cikin na Yaya Ramadhan ɗinne ba wani yayisa ba tun kan a shigo.”         Har cikin rai maganganun Aina'u sun soki Raudha, amma sai ta wuce abinta batare data tanka  mata ba. Kai ko kallon inda suke batai ba ma balle ta nuna tasan da zamansu tai shigewarta ɗakinta.          Sai da ta kammala shiri  tana ɗan kimtsa ɗakin nata maganganun Aynah na ƙarshe ke mata kaikawo a rai. (Ciki? Wa take nufi nada cikin?) ta tambaya a zuciyarta batare da tunanin lalubo amsa ba. Haka dai ta ƙarasa aikin da wannan tunanin tai zaman cike takardun jiya dan ta jona wayarta a caji tunda ta shigo.      ★★★★       A office kam murmushi ya kasa barin face ɗin shugaban ƙasa Ramadhan. Dan babu abinda ke masa kai kawo a rai sai hidimarsa shi da Raudha na safiyar yau. Shigowarsa office da cos ya fara ganawa akan tsare-tsaren abinda zaiyi a yau. Amma shi kansa cos sai satar kallonsa yake ganin yau babu ɗacin ran nan sam tattare da shi. Hakama a zaman meeting da yay da sabbin ministers fuskarsa ƙawace da fara'a tamkar bashi ba. Bayan sallar azhar ya samu hutun awa biyu shi kaɗai a office. Jiyay tamkar ya kirata a waya. Sai dai zuciyarsa na gargaɗinsa akan idan ya kirata mizaice mata to? Karma ta ya yake rikitata duk da dai yanzu Alhamdulillahi sun saki jiki da juna sosai. Yau ma sama-sama yake jin kansa shiyyasa bai biye mata ba. (Humm🤳🏻). *_TAURA HOUSE_*                  Tun wayar da tai da su Munirah ranta yake a ƙololuwar ɓace. Koda ta kira Adda Asmah ta sanar mata itama ɓacin ran ta nuna sosai, hakama Fulani. Kai tsaye shawarar Adda Asmah sukabi akan zubda cikin jikin Raudha kota halin ƙaƙa ita da fulani.        Tana gama waya da su ta kira Safina.         “Maah lafiya kuwa kira a wannan lokacin!?”.       Tsaki gimbiya Su'adah tai idanunta na sake rufewa da ɓacin rai dan ba ƙaramin fanfata Asmah ta sakeyi ba, ita kuma ta riga ta yarda da ita tsakani da ALLAH. “Maganin zubda ciki nake so mai tsananin ƙarfi da zai rikito a cikin mintuna goma”.       “Na shiga uku Maah waye da ciki?!”. Ta faɗa a cikin tashin hankali da tunanin cikin ƴan uwantane wata ta yayo musu abin kunya.       “K dalla ba abinda kike tunani bane. ALLAH ya tsari zuri'a ta da fasiƙanci. Wannan ƴar iskar yarinyar ƴar karuwai ce, wai harni Ramadhan zai yaudara Safina ya lallaɓa yay ma shegiya ciki”.       “Innalillahi... Anya Maah kun tabbatarma nasa ne? Kinsan fa yanda Brother yake da taurin kai akan abinda bashi yaso ba. Kuma kowa yasan Bappi ne ya manna masa auren nan bawai yana so bane, ƙilama asiri sukai masa wlhy inhar ya kasance cikin nasa ne ma.”      Sosai maganganun Safina sukai tasiri a zuciyar gimbiya Su'adah. Takai zaune tanajan numfashi mai nauyi. “Safina maganarki kuma nakan hanyar wlhy. Da harna ƙullacesa a raina. Tabbas inhar cikin nan ya kasance nasa yarona baya cikin hayyacinsa sun masa asiri. Nasan wacece kakar yarinyarnan komai zata iyayi dan tayi a baya akan mahaifina”.       “Humm kin gani ko Maah. Nidai nasan Brother bazai taɓa son yarinyarnan ba. Idan ma ƙyau ne ai yanada shi, sannan akwai tarin mata dake binsa wanda suka fita ƙyawun amma bai kula ba sai ita banza ƙaramar alhaki sa'ar Basma fa. Autarmu, inagama Basma ta girmeta wlhy”.               “Aiko zataci ubanta, zan tabbatar mata damu asiri baya cinmu, dan na kula saka mata idon da nayi ban ɗauka wani mataki a kanta bane ya kawo hakan. Yanzu ki aikomin da sunan maganin”.       “Indai magani ne kwantar da hankalinki, zansa doctor Wali ya kawo miki ma har gida. Sai ma nakejin dama kar a zubar da cikin mu nuna kawai bana Brother bane mu kunyata ƴar iska nasan zaima iya sakinta....”       Ɗan jimmm Gimbiya Su'adah tai tana nazari, sai kuma ta girgiza kai kamar Safina na ganinta. “Ina bazai yuwuba baki da hankali. Idan kuma yace cikinsa ne fa? Ramadhan da shegen kafiya kema kin sani. Sannan tsoffin nan zasu iya cewa bazataje ko'ina ba ta zauna a wajensu har sai ta haihu anyi DNA test. Ke dai kawai mu ɓarar da ɗan iska mukuma san matakin ɗauka da zai hanata damar ɗaukar wani”.      “Okay Maah duk yanda kikace haka za'ayi. Bara na kira Dr Wali ɗin. Amma ya za'a bata maganin?”.        “Wannan mai sauƙi ne ba su Lubnah nacan ba, ai na sake maidasu zama can bayan na tsara tsoffin nan akan zasuje suɗan dinga ɗebe mata kewa injisa. Bayan na masa gargaɗi shi kuma”.       Safina tai ƴar dariya daga can tana faɗin, “Kai wannan shegiya ta zame mana *ƘARFEN ƘAFA*”.        “Nikuma zan zame mata *BAƘAR INUWA* kuwa da sai ta gwammace zaman ranar data baro dani dan ubanta”.         “Shiyyasa nake sonki Maamana”. Kashe wayar Gimbiya Su'adah tai tana murmushi.          Mintuna arba'in ba'a cika ba Dr Wali ya iso da maganin, tsabar muhimmancin maganin har falon baƙi gimbiya Su'adah tasa aka saukesa taje da kanta suka gaisa ta amso. Tafiyarsa babu jimawa Munirah da zata amshi maganin ta iso. Duk yanda Dr Wali yay mata bayani haka taima Munirah. Tai mata gargaɗi akan su lura da abinda zasuyi.       Munirah ta tabbatar mata da sai tayi alfahari da su insha ALLAH. Da ga haka ta shiga mota driver da tasa ya kawota ya juya da ita government house. *_GOVERNMENT HOUSE_*       ALLAH sarki Raudha batasan mike faruwa ba. Bayan ta kammala cike takardu ta nemo littafin data ajiye numbers na Mommynsu da ƴan uwanta ta loda a sabuwar wayarta da har credit cart sai da Ramadhan yasa aka loda mata a layin nata. Cikin farin ciki tai kiran number Mommynsu. tana ɗagawa taji muryarta sai ta sa kuka dan daɗi. Ita Asabe ma sai abin ya bata dariya. Amma tunanin ko Raudha na cikin wani ƙunci ne data guda tun farko yasa dariyartata kasa fitowa ta hau jera mata tambayoyi. Da ƙyar Raudha ta haɗiye kukanta ta tabbatar mata da babu komai jin daɗin jin muryartane ya sata kukan kawai.       Ajiyar zuciya Asabe ta saki, sai kuma ta hau saka mata albarka. Sunyi hira sosai ta sanar mata zancen makarantarta ta tayata murna. Daga haka ta gaisa da sauran ƴan uwanta har hajiya mama da hajiyar birni da yanzu ta daina zuwa shago sai su Fatisa. Sai dai tana zuwa taga yanda komai ke tafiya ta koma gida.      Bayan kammala wayar ne taji yunwa na ƙara damunta dan bata karya ba. Mikewa tai ta fita da fatan ALLAH yasa akwai abinci table. Addu'arta kam ta karɓu, dan haka babu ɓata lokaci tai zaman cin abincin da tunanin idan ta kammala ta ɗan sauka downstairs dan duk yau basu haɗu da su Mama ladi ba.       Wani irin cafkewa su Munirah dake laɓe sukai lokacin da Raudha take haɗa shayi. Sun tsiyaye ruwan flask ɗin duka suka bar dai-dai kofi guda suka saka ƙwayoyin maganin fiye ma da yanda akace su bata. Maimakon 2 sai suka saka har 6 dan basu da hankali. Wai yanda cikin zai rikito da wurwuri kowa ya huta.        Tsaf Raudha ta shanye shayin ta ɗan sha farfesu saboda bakinta babu daɗi. Dama ita idan tana period tata kwaɗayi kenan tamkar mayya. Ko abinci bata cika so ba tafi son nama a irin wannan lokacin. Riƙewar da mararta tayi ya sata ɗan dakatawa da ga shan farfesun kamar mai hasashe. Kirjinta yay wani irin yankewa tamkar ana kiɗa a kan zuciyarta. A take kanta ya fara juyawa cikin ficewar hayyaci ta kife fuskarta akan kwanon farfesun tana ambaton sunan ALLAH. Ba tare data fahimci mike faruwa ba taji abu na ɓulɓulowa ta kasanta da gudun tsiya yana sauka jikin ƙafafunta...........✍ 🤦🏻      *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/28, 8:28 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62b9f997e1f6b1b5d98322a0 *_Episode 39_* ..........Sai da suka tabbatar ta fita a hayyacinta sannan suka fito a inda suke ɓoye fuskokinsu washe da fara'a tamkar ba mata ba. Ba imani babu tausayi duk da ganin jini na gudu a ƙasan Mable's ɗin dining ɗin, har yana gangarowa cikin falon da gudu.          Shigowar kuku da yazo kwashe kwanika da tunanin an kammala da su ya saka Lubnah da ta farga da shi sakin wata irin ƙara tana nufar kan Raudha da tayo ƙasa zata faɗi cikin fita hayyaci. Munirah zatai magana itama ta farga da kuku sai ta sanya nata ihun itama. Ihunsu ya rikita falon gaba ɗaya har Mama ladi da Mama Tambaya dake falon ƙasa jiyosu suka hauro babu shiri. ★★      Dole akai gaggawar mika Raudha clinic na cikin gidan. Dan duk wanda yaga yanda take zubda jini abun sai yayi matuƙar firgitashi. Doctors ɗin kansu ruɗewa sukai, haka suka rufu a kanta kusan su uku domin ƙoƙarin ganin sun tsaida jinin sun ceto rayuwarta, dan tuni numfashinta ya bar gangar jikinta.        Mama Ladi da duk ta gama ruɗewa ce ta kira Anne ta labarta mata abinda idonsu ya iya gani. Haka ma Mama Tambaya ta kira Aunty Hannah ta sanar mata. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga aunty Hannah ta iso saboda ta ɗanfi kusa da Anne. Itama Anne ba'a haɗa mintuna talatin ba ta iso harda Yafendo da Inna duk da suna fama da tsufansu.        Har kusan azhar doctors ɗin gidan na gwamnati basu ce komai ga su Anne ba, dan Dr Hauwa ma da sukazo tare da su Anne itama ta ƙaru cikin doctors ɗin. Kowa yay jigum-jigum cike da fargabar abinda suke tsoron ji. Bama su ba shaƙiƙanta hatta da ma'aikatan gidan duk wanda al'amarin yaje kunnensa a tsorace yake. Gaba ɗaya sai gidan yay tsitt.       Ramadhan baisan halin da ake ciki ba sai da suka fito salla COS ya samesa a office yake sanar masa kiran da ya samu da ga Chief security na gidan game da Accident ɗin da Raudha ta samu wanda har yanzu ba'a san musabbabin sa ba. Sosai hankalin Ramadhan ya tashi, amma a fuska bazaka taɓa tabbatar da haka ba, sai nanata kalmar cos ɗin yake a cikin ransa tamkar karatu. Gashi yana da shiga meeting a dai-dai lokacin kuma mai matuƙar muhimmanci. Haka dai ya dake cikin dauriya ya shiga meeting ɗin badan ya fahimci komai da aka tattauna a wajen ba. Baima haɗa mintuna talatin ba ya fito ya barsu su ƙarasa.      Ya sake ganawar sirri da wani babban mutum da ga ƙasar Nigeria akan wani aikin haɗaka da suke sonyi da ƙasar ta Nigeria ɗin. Sai dai zaman nasu bai wani armashi ba saboda hankalin shugaban ƙasa rabi yana cikin gida. Awarsu guda suka kammala ya fita sallar la'asar. Abubuwan da suka rage masa na sauran awoyin ba wasu masu tsawwalawa bane idan ka cire ganawa da vice ɗinsa Alhaji Yaro glass, dan haka yasa cos sokesu sai gobe idan ALLAH ya kaimu shi kuma ya shiga gida.       Iske su Anne da yay a gidan ya sake tabbatar masa da al'amarin babbane. Gashi sun sanar masa har zuwa lokacin basuji da ga doctors ɗin ba. Zama yay kawai cikin kujera ransa duk a dagule. Gaba ɗaya yama rasa wane kalar tunani zaiyi shi kam, yasan jiya ta shiga wani hali, amma lafiya lau ya fita ya barta yau ai.         “Anne har yanzu basu ce komai ba? Kuma babu wanda yasan miya faru daga nan ciki?”.         Cikin jimami da damuwa Anne tace,, “To ALLAH kaɗai dai yasan musabbabin gaskiya. Amma su su Lubnah sunce tana cin abinci ne abin ya faru, suma sai ganin jini sukai malale a ƙasa, shine ma suka shiga ruɗanin da har ya fargar da su Ladidi”.       Iska ya turo daga ƙirjinsa ya fesar ta baki a hankali tare da kai hannu saman goshinsa yana ɗan murzawa. Cikin jimamami Yafendo ta karɓe zancen da faɗin, “Shi dama cikin fari na mai rabo ne, sai dai fitar nata yazo da haɗari. Dan tsinkewar jini irin wannan kam tashin hankaline babba ga mai ɓari, sai kace wadda aka ba wani abu”.        Aunty Hannah da tun ɗazun batace komai ba sai satar kallon shugaban ƙasa da takeyi, dan yau ne ta fara ganinsa ido-da-ido itama a cikin gidan tunda take zuwa. “Da alama cikinne ma dai baiyi wani ƙwari ba shiyyasa. Amma al'amarin yayi kama da wadda tasha wani abu kam gaskiya”.        “Ciki?!”. Shugaban ƙasa ya firta cikin kasa ɓoye al'ajab nashi. Kallonsa sukai gaba ɗayansu duk da kuwa yayi maganar ne a hankali. Anne tace, “Ikon ALLAH, kai bama kasan da cikin ba kenan? Amma jiya ba Hauwa'u tazo ta dubata ba?”.         Kansa ya ɗan jinjina mata sai kuma ya haɗiye dukan abinda ke masa kaikawo a cikin rai. “Itama sai yau zata bamu sakamako dama Anne”.     Yay ƙoƙarin danne gaskiyar zancen saboda wasu abubuwa da ke masa kai kawo a rai da zuciya. Shiru falon ya sake ɗauka na wasu mintuna. Kafin ya miƙe da kansa ya fita da ga falon zuwa Clinic ɗin.         Koda ya fito securitys sukai masa caa hana kowa binsa yay, sai dai duk da haka odilan ɗinsa bai yarda ya barsaba duk da dai a cikin gida ne. Ba wata tazara bace mai yawa tsakaninsu da clinic ɗin. Zuwansu yayi dai-dai da fitowar doctor Sambo da ga ɗakin ya baro su Dr Hauwa dake ƙarasa gyarata. Cikin ɗan rikicewar ganin oga kwata-kwata da kansa ya fara miƙa gaisuwa. Hannu kawai Ramadhan ya ɗaga masa, sai kuma yay masa nuni da office alamar su koma ciki..     Suna shiga Aynah na Munirah dake laɓe suka kaima bango duka. Tunda suka kira Gimbiya Su'adah suka sanar mata ta basu umarnin zuwa su sami likitan su masa maganar komi za'ai kar bakinsa ya faɗi cewar da safe tasha maganin nan. Ya nuna tun jiya ta sha shi da yamma kuma ba yau ne na farko data sha ɗin ba. Shine sukazo fa, suna gab da isa ga doctor Sambo da suke zaman jira tun ɗazun sai kuma ga yayansu da kansa. Hakan ya saka su ɓuya dan kar ya gansu..       “Wane issue kuka samu?”. Ramadhan ya tambaya kansa tsaye dan shi baya son ɓoye-ɓoye ko jan rai a magana”.       Cikin in-ina da fargaba Dr Sambo ya fara magana. “Ranka ya daɗe zuwa yanzu dai munyi nasarar ceto rayuwarta, mun kuma tsaida jinin. Sai dai ta zubar da jini sosai a yanzu haka muna ƙoƙarin samun wanda za'a ƙara mata ne. A binciken da mukai kuma mun gano magani ta sha wanda ya wuce ƙa'ida ma shine ya kawo tsinkewar jinin kamar haka. Badan anyi azamar kawota ba ma zata iya rasa ranta saboda maganine mai ƙarfi kuma abinda aka sha dominsa ma babu shi...”         “Maganin miye?”. “M...maganin abortion ne?”.      “Abortion?”. Ya maimaita maganar ta sigar tambaya.     “Yes sir, sai dai kuma ma babu cikin, bincike ma ya tabbatar mana mahaifanta bai taɓa ɗaukar ciki ba sam. Hasalima a cikin yanayin perio....”        “Ya isa haka..” Ramadhan ya faɗa cikin ɓacin ran bayyanar kishinsa ƙuru-ƙuru daya kasa ɓoyuwa. Da ƙyar ya danne takaicin taɓa masa mata da sukai da sanin sirrin da basu dace da sani ba daga gareta ya fara magana mai kama da gargaɗi.        “Wannan maganar ta tsaya iya ni da kai. A wajen kowa yazam cikinne ya zube da gaske. Kar a ƙarama matata jinin kowa a ɗiba nawa. Da ga nan zuwa gobe ina son sanin sunan ƙwayar data sha.”      “Okay ranka ya daɗe insha ALLAH. Sai dai da zai yuwu zanso ganin abinda taci na ƙarshe dan kamar daga nan matsalar take”.       Ɗan tsura masa ido Ramadhan yayi kamar mai nazari, sai kuma ya kauda idonsa yana miƙewa, “Muje ka ɗiba jinin, sauran aikin kayi magana da Chief security na gidan”.       “Okay sir ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana. Ya kareka a duk motsinka da rayuwar iyalinka baki ɗaya”.      A saman laɓɓa ya amsa yana ficewa daga office ɗin.       Ba ƙaramin tashin hankali zuciyar Ramadhan ta shiga ba lokacin da yaga Raudha. Cikin ƙanƙanin lokaci ta zube ta sake haske mai ban tsoro alamar dai da gaske babu jinin a jikinta. Cikin cije lip dinsa da masifar ƙarfi ya kai hannu saman kanta ya shafa gashinta lokacin da yake kaiwa zaune a kujerar da Dr Sambo ya ajiye masa. Sai kuma ya sinkuyi kanta ya kai bakinsa saman goshinta ya sumbata. ALLAH sarki Raudha, inama ace idonta biyu taga wannan al'amari. Na tabbata jininta zai iya daskarewa ma baki ɗaya.      Kamar yanda ya hana a saka mata jinin kowa nasa aka saka mata, dan kuwa dagewa yay sai da aka ɗiba leda biyun da suke buƙata ɗin. Sai bayan an saka mata ne su Anne suka samu damar shigowa suka dubata, zuwa lokacin har Ramadhan ya koma cikin gidan dan shima yana ɗan buƙatar kwanciya ya huta. Ya bama Chief security damar binciko duk abinda suka tattauna da Dr Sambo. Dan haka babu ɓata lokaci Chief security ya fara aikinsa akan sauran abincin breakfast da Raudha ta ci.          Ba'a samu wani tangarɗa ba wajen gano Raudha tasha maganin zubda ciki ne ta hanyar ruwan shayi da yay saura a flask ɗin. Wanda a zahiri Raudha ta shanye sa tas, sai dai lokacin da Ramadhan ke sanarma Chief security aikin da zaiyine zancen ya shiga kunnen Lubnah. A firgice taje ta matsa ruwan zafi da ga dispencer ta jefa sabuwar ƙwayar magani a ciki jikinta na rawa. Batafi mintuna biyar ba kuma Chief security ya iso falon dan ALLAH yasa ma ba'a kai ga kwashe kwanikan ba saboda halin da Raudha ta shiga ya ruɗa kowa.         Kuku bai farga da abinda ke faruwa ba sai da Chief security yasa aka kira masa shi. Gaba ɗaya ya rikice ya ruɗe, dan zuwa yanzu labari ya fara karaɗe gidanne first lady ɓarin ciki tayi, ana kuma zargin an saka mata wani abune ta ci a abinci.       Su kansu su Anne a rikice suke da jin wannan al'amari musamman ma aunty Hannah da tasan suna da alaƙa da kuku. hasalima yaronsu ne su yakema aiki a gidan. A gefe kuma ta shiga mamaki da ruɗanin mizaisa kuku ya zubdama Raudha ciki? Saboda koba komai suma suna buƙatar cikin matsayinsu na jinin Raudha mafi kusanci. (To koma dai miye, wannan wata sabuwar cakwakiyace kuma🤥🚶🏻 Aunty hannaty). ★★★        Ramadhan bai sake cewa komai ba akan batun duk da yaji cewar Raudha tasha ƙwayar ne da ruwan shayi. Hakan na nufin kuku's ne da aika-aikar, a yanzu haka kuma shugaban kuku'e ɗin dake da alhakin kula da abincinsu yana hanun securitys na gidan.        Bayan sallar isha'i su Anne suka wuce gida har aunty Hannah. Sai dai zuwa lokacin Ramadhan yasa an dawo da Raudha cikin gidan tana ma ɗakinta. Alhakin dubata ya koma wuyan Dr Hauwa'u a yanzun gaba ɗaya, sannan Mama Ladi aka bari a ɗakin zata cigaba da kula da ita.         Ramadhan ya nunama Dr Hauwa'u yana son kowa ya cigaba da ɗaukar hakan har su Anne cewar cikinne da Raudha kuma ya zube. Batasan dalilinsa ba, amma kuma ta karɓa alfarmarsa dan ta fahimci akwai ƙulli a cikin al'amarin mai girma. Badan ma ALLAH ya taƙaita ba komai zai iya faruwa da mahaifar Raudha ɗin, a yanzu hakama basu da tabbacin komai zai iya zama normal. ★★           Washe gari da safe ya tashi babu wani damuwar jinin da aka ɗiba masa. Dan har massallaci ya fita sallar asuba. Bayan dawowarsa massallaci ya jima zaune cikin sofa yana ƙullawa da kwancewa akan al'amarin. Wajen shidda aka kawo masa tataccen haɗin shayin lemon tsami da wasu ganyayyaki na shayi da yake sha a duk safiya dan shi ba ruwansa da wani coffee.         Har kukun dake kula da shayin nasa ta kammala ta fita bai motsa ba. Baima amsa ko gaisuwarta ba. Hakama bayan fitarta bai sha shayin ba dan tunaninsa ma baya tare da duniyar mutane. Bazai so ya zama silar hana wani cin abinci ba, amma dolene ya ɗauka wani mataki game da wasu ma'aikatan gidan musamman kuku's dake da alhakin basu abu suci.              A hankali ya furzar da iskar daya tara a ƙirji yana miƙewa batare da yabi takan shayin ba. Ba tsoron an zuba masa wani abu yake ba, kawai dai yau bama shi da ra'ayin shan komai ne kawai. Wanka yayo yay shirin office, tamkar kullum yau ma yayi ƙyau matuƙa yana ta baza ƙamshin turarurrukansa da suka amsa sunansu turare. Koda ya fito ɗakin Raudha ya nufa, kowa bai samu ba a ɗakin ba sai dai an gyara shi yanata ƙamshi. Raudha kwance a gado cikin bargo babu alamar ta farka. Tsaye yay akanta ya tsurama cute face nata ido, ta sake haske sosai, ta kuma rame. A hankali yakai zaune bakin gadon tare riƙo hanunta dake saman cikinta ya riƙe cikin nasa. Kasa jure abinda ya ratsa sa yayi, sai kawai ya rumtse hanun da ƙyau a cikin nashi har sai da taɗan motsa.        Tabbas ya yarda ita ɗin ƙyaƙyƙyawa ce, sai dai a ganinsa tayi yarinta da yawa. A zuciya yake wannan tunanin, a zahiri kam ido kawai ya tsura mata. Yanada meeting da shuwagabanin tsaro baki ɗaya, dole ta sashi miƙewa yana ƙoƙarin zare hannunsa a cikin nata sai dai ta riƙe nasa ita kuma. Tsamm ya tsaya yana kallon hanun nata yanda ta matse yatsun nasa biyu tamkar tana ido biyu. A bazata murmushi ya suɓuce masa, sai dai komai baice ba ya zare yatsun nasa yana ɗon furzar da huci.        ★    Koda ya fita kafin yaje office ma wajen meeting ɗin ya fara zarcewa, dan ya makara, kuma zama ne mai matuƙar muhimmanci. Harkar tsaro da lafiya da ilimi sune sahun farko da yake burin fara shimfiɗawa al'ummarsa kafin komai. Dan haka yasa aka shirya masa zama da shuwagabanin jami'an tsaro ta kowanne ɓangare, dana lafiya takowane nangare, dana ilimi takowane ɓangare. Zai fara zama da jami'an tsaron ne kafin sauran suma.       Meeting ɗin ya jasu lokaci saboda muhimmancin sa. Dan a ƙalla sun sami good 3hours. Koda ya shiga office bai iya taɓuka wasu abun arziƙi ba. Yadai gana da vice president Alhaji Yaro glass akan wasu muhimman batutuwa. Sanda suka kammala lokacin salla yayi. bayan dawowarsa massallaci ya gana da COS daga nan ya tafi hutun awanni biyu. Maimakon zaman hutun sai yay zaman yin waya da Bappi.       Ƙarfe biyar na yamma ya shigo gidan yau. Sai da ya fara zuwa ɗakinsa yay wanka ya kimtsa cikin ƙananun kaya sannan ya fito domin duba jikinta. Bai samu kowa a ɗakinba yanzu ma. Motsin ruwa da yaji ya tabbatar masa tana toilet, agogon dake a tsintacciyar hanunsa ya kalla tare da ɗan bin ɗakin da kallo. Saukar idanunsa akan hoton dake saman bed side drawer ɗinta ya sashi takawa a hankali garesa hannayensa duka cikin aljihun wandon jeans ɗin sa, hoton ya tsurama ido duk da bawani fitaccen hoto bane, hasalima ya ɗau shekaru, dan mace ce da mijinta sai yara huɗu, ɗaya jaririya a hanun mijin, sai ƴar shekara 7 da kamanin Raudha ke tare da ita tabbacin dai itace ɗin. Sai biyu da bazasu wune shakara tara ba da alama twins ne.       Kiran da akaima wayarsa ne ya katse sa da ga kallon hoton, ya zarota a aljihu yana mai janye idanunsa a hoton gaba ɗaya. A kuma dai-dai lokacin Raudha ta fito da alamun wanka tayi.        A hankali take takowa cikin ɗakin dan da farko bata lura da shi ba. Sai dai kuma yanda ƙamshinsa ya cika ɗakin ya sata tsarguwa harta kasa ƙarema ɗakin kallo. Sallamar da yay lokacin da yake kai wayar a kunnensa ya sata tsayawa cak daga takowar da take, gaba ɗaya jitai ta daburce, gashi ta riga da tazo kusan tsakkiyar ɗakin tasan dai ya riga ya gama ganinta kuma. Kallonsa ta ɗan sata kaɗan, ya ɗan zuba mata idanu tamkar mai shirin gano wanda ya aikata mata abun a jikinta.       Da sauri ta maida idanun nata ƙasa. Shima ya janye nasa yana cigaba da sauraren masifar da gimbiya Su'adah ke masa ta cikin wayar, shi gaba ɗaya ma ya rasa dalilin faɗan nata shiyyasa saurarenta kawai yake batare daya fahimceta ba har tayi ta gama ta katse kiran bayan ta bashi umarnin ganinsa.       Kansa ya ɗan girgiza kawai yana sauke numfashi, a zuciyarsa mamakin daru irin na mahaifiyarsa yake. A zahiri kam idonsa ya maida ga Raudha datai tsaye tamkar an dasata     “Ƙaraso mana”. Ya faɗa a hankali tamkar baya so.             Duk da bathrobe ce a jikinta gaba ɗaya kunya ta dabaibayeta. Amma saita daure ta ƙarasa bakin gadon dan jiri take gani ma. Tana gab da isa jirin ya kwashe tai tamkar zata faɗi ALLAH ya taƙaita sai jinta tai jikin mutum............✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/29, 8:46 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62bb08b56a04a27945e24a2b *_Episode 40_* ..........Ba sai an mata wani explanation ba tasan shine. Dan mayataccen ƙamshinsa tuni ya ƙara ƙarfi a ƙofofin hancinta. Kasa buɗe ido tayi ta kallesa dan kunya, ga shi bata da ƙarfin da zata ƙwace jikinta a nasa.       “Kina ganin jiri ne?”.    Ya faɗa a hankali yana tallafo fuskarta cikin tafin hanunsa. Bata yarda ta buɗe idanunta ba, sai ta jinjina masa kanta, zuciyarta babu abinda take sai luguden daka kamar zata fito waje, ga tsigar jikinta sai yamutsawa take. Dan wannan shine karo na farko da ya taɓa mata irin wannan riƙon a cikin jikinsa sosai kamar haka. Shi kansa danne yanayin kawai yake a zuciyarsa, yay ƙoƙarin kaita zaune a bakin gadon....           Dai-dai lokacin Mama Ladi da batai zaton samunsa a ɗakin ba ta turo ƙofar da sallama ta shigo saboda tasan Raudha ɗin ma ta barta ne tana wanka batai tsammanin ta fito ba. Shigowar tata baisa ya janye jikinsa da ga na Raudha ba, sai ma itace data ɗan dabirce har ta samu ƙarfin yin mutsu-mutsu amma sai ya shareta. A ɗan rikice Mama Ladi ta juya zata koma ya dakatar da ita       “A gafarce ni ranka ya daɗe wlhy bansan kana ciki ba”.      “Is ok”. Ya faɗa tamkar baya so yana matsar da jikin nasa daga na Raudha ya zaunar da ita da ƙyau ya miƙe akan ƙafafunsa, nuni yayma Mama ladi data ajiye kayan hanun nata. Cikin girmamawa ta ƙaraso ta ɗora tray ɗin saman table da alama abinci ta haɗoma mata.          “Babu dai wata matsala zuwa yanzu ko?”.        “Eh ranka ya daɗe Alhmdllhi. Likitama da tazo ɗazun tace komai ya dai-daita sai dai a cigaba da kula da maganinta, ta kuma dinga cin abinci sosai dan ƙarfin jikinta ya dawo”.       Baice komai ba sai kallon Raudha da yayi. Sosai ta rame, ƴar ƙibar da tayi duk ta zube. Idanun ya janye yana ɗan furzar da iska. Sai kuma yace, “ALLAH ya ƙara lafiya”.         Mama Ladi ta amsa da “Amin”. Raudha ma data kai kwance saboda rashin ƙarfin jiki ta amsa a laɓɓanta.         Bai sake cewa komai ba ya fita a ɗakin ya barsu, dan Taura house yake son zuwa amma a ɓadda kama zai fita gidan. Ɗakinsa ya koma ya ɗaura jacket saman kayansa da p-cap ya fita, odilan ɗinsa dake jiransa dan dashi kaɗai zasuyi fitar yay saurin risinawa yana masa barka da fitowa. Kansa kawai ya jinjina masa.        “Saifu muje lokaci yaja”.    “Okay sir, odilan Saifudden ya faɗa da sauri yana buɗe masa back sit. *_★★TAURA HOUSE★★_*         Gaba ɗaya ranta a ɓace yake tun jiya a gidan, tsabar bala'in dake cin ranta ko barcin kirki batayi ba da daddare. Yinin yau kuwa babu wanda zai ce yama ganta a gidan har ƴaƴanta, sai Adda Asmah data shigo da yamma ta ƙara fanfata matuƙa saboda cikin nan na Raudha ya matuƙar tsaya musu arai duk sun san ya zube kamar yanda sukaji bakin su Lubnah da Anne. Ɗazun da rana Hajiya Shuwa da Hajiya Mufida sunje har government house sun duba Raudha. Koda Anne taga babu gimbiya Su'adah batace komai ba, saboda ɗaukar hakan matsayin kawaici ga abokan zaman nata.         Knocking ƙofar bedroom ɗin nata ya katse mata wayar da takeyi da Fulani. “Ammy zan kiraki inaga gashi nan ma yazo mara mutuncin”. Daga haka ta yanke kiran da miƙewa ta buɗe ƙofar dan a kulle take kasancewar bata buƙatar kowa ya shigo mata.           Barin wajen tai, Ramadhan da yaga tsantsar ɓacin rai a yanayin nata ya ɗan furzar da iskar bakinsa yana ambaton sunan ALLAH a zuciyarsa. Ko ɓangaren su Anne bai shigaba ya wuto nan. Koda ya kai zaune yana gaisheta bata amsa masa ba, sai kawai ya saki ɗan murmushi da zame p-cap ɗinsa ya ajiye shima yay shiru.        Tsahon mintuna uku ɗakin ya ɗauka shiru, sake ɓaci ranta yayi fiye da wanda take ciki. A zafafe ta watsa masa harara tana magana a kausashe, “Yanzu ai ka fara ganin abinda muketa nuna maka akan wannan shegen auren, matarka tayi yanda take so na zubar da ciki saboda ta fito a gidan marasa tarbiyya. Tunda ta nuna bata shirya haihuwa ba kasani ni bazan amince ba. Dan haka dole ne ka ƙara aure nan da wata ɗaya, kuma Aina'u zaka aura.....”        “Maah!. Aina'u?”.    “Eh ita, idan kuma ban isa ba kamar yanda ubanka da kakaninka suka isa har suka aura maka zaɓinsu ka amsa ba tare da bijirewa ba sai naji.”        Iska ya furzar da ƙarfi yana ɗan rumtse ido da buɗewa lokaci guda. “Maah Please calm down. Kibar zancen wata Aina'u a beg. S.......”       “Anƙi a bari ɗin, kai yanzu Ramadhan dan baka da mutunci har kana da bakin faɗamin nabar zancen ɗiyar ƴar uwata akanka? Aka saka kama auri karuwa....”       (Ya ALLAH) ya faɗa a zuciyarsa yana rumtse ido da murza goshi. Cikin zafin rai gimbiya Su'adah ta cigaba da sauke masa takaicin Raudha da shi kanshi da dama take ƙullace da shi tun lokacin first night da suke tunanin ya faru tun a waccan ranar. “Ita ga ƴar iska mara mutunci, tasan bata shirya haihuwa ba miyasa ta yarda da kai dan ubanta, nama godema ALLAH data zubar ɗin kuma mahaifar tata bazata sake ɗaukar wani cikin ba. Bani da rabon haɗa zuri'a da jinin karuwai!!”.        Sosai ransa a dagule yake. Amma ya daure dan mahaifiya ta wuce wasa. Babu abinda yake sai haɗiyar zuciya. Babbar matsalarsa auren Aina'u da ta ambata, koma mizai faru sai dai ya faru babu auren Aina'u a cikin tsarinsa. Yariyar daya gani da idanunsa a cikin tsakkiyar club a America ana lesbians da ita, ƴan iska na ihu suna ɗauka a waya (Wa'iyazubillah). Ta rufe fuska da mask, shiyyasa tai tunanin babu mai ganeta, sai dai tayi rashin sa'a shi ya ganetan da idonsa. Dan ya tabbatar mata ya ganeta ɗin kuma ya cire mata mask ɗin. A wannan rana baiyi barci ba dan tashin hankali, dan koba komai itaɗin jininsa ce. Da uwarta da tashi fa uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Sannan mahaifinta shima ɗan masarautar su Maah ɗinne ɗan uwa na jini matsayin Uncle yake garesa. Amma itace yanzu Mahaifiyarsa ke tabbatar masa zai aura. Ji kawai yake ana ambaton Raudha da ɗiyar marasa tarbiyya amma shi har yanzu bai tabbatar ba tunda bai taɓa ganinta tana aikata wani fasiƙanci ba. Itako Aina'u da idonsa ya ganta ba labari ba.......           “Tunda ga ƴar iska ina magana kamin shiru ko!!”.      Gimbiya Su'adah ta faɗa cikin dawo masa da hankalinsa gareta. Ajiyar zuciya ya sauke yana gyara zamansa. Cikin tausasa harshe yace, “Maah Please relax. Ki bari ki huce sai muyi magana daga baya. Indai dan haihuwa ne insha ALLAH jikoki har sai kin rasa yanda zakiyi da su a gidan nan.....”         “ALLAH ya tsareni samuwarsu da ga wannan jinin karuwan da talauci. Dan haka karka sake min irin wannan maganar zan ɓata maka rai”.      “Ok. ok!. shike nan kiyi haƙuri Please”.     Tsaki taja tana ɗauke kanta gefe. Kaje dare yayi, amma ka tabbatar ka samu kakaninka da mahaifinka da maganar Aina'u dan wlhy babu fashi saika aureta, sai dai in mutuwa kayi ko ita ta mutu”.      (Oh oh, shikam yau ya zaiyi da tsohuwar nan) ya faɗa a ransa yana dafe kai. *_GOVERNMENT HOUSE_*         Tunda ya shigo ya zube a falon upstairs ɗin ransa duk a jagule. Kansa harya fara ciwo tsabar rasa ina zai kama. Magana da yake ji ƙasa-ƙasa kamar ana raɗa ya sashi sake nutsuwa da hasashen ta ina ne. Fahimtar da ga inda sautin ke tashi ya sakashi miƙewa. Kansa tsaye ya tunkari wajen, amma tsabar shagala da Aina'u tai a wayar da take yasa sam bataji motsinsa ba balle ƙamshin turaren sa.        “Amma naji daɗi Ummi da kika sake tunzurata, duk da dai wlhy a tsorace nake. Har zuciya ina son Yaya Ramadhan, amma nasan akwai matsalar da tai mana katangar danne zumuɗina. Gani nake kamar tursasawarku ma bazatasa ya amince ya aurenin ba......”      Shiru tai alamar an katseta daga can. Sai kuma ta sauke numfashi. “Wlhy zan jure Ummi, nidai yanzu burina ya amince ɗin, indai na zama matar tasa komai mai sauƙi ne. Sannan ƴar iskarnan nasan da wahala ta sake ɗaukar ciki kamar yanda doctor ya sanar mana. Kinga sanadin barinta gidan yazo kenan ƴar karuwai”.      Dariya ta ƙyalƙyale da shi sai kuma ta dumtse bakinta tana ɗan waige irin kar ajitan nan. Hakan yasa Ramadhan sauri ɓoyewa dan karta gansan. Janye hanunta tai a baki tana cigaba da faɗin. “Nifa harma mamakin yanda akai cikin nake Ummi, wlhy kinga wancan zaman har muka bar gidan nan bamu taɓa ganin ta shiga ɗakinsa ba ko shi ya shiga nata. Hakama yanzu banda randa muka gane tana da ciki datai pretending ya ɗakkota daga falonsa bamu taɓa ganinsu tare ba. Ni anyama cikin nan bada shi tazo ba....”         Shiru ta karayi na saurare. Sai kuma tace, “Wlhy Ummi komai zai iya faruwa. Ke dai ki cigaba da fanfa Maah dan ALLAH ayi-ayi nima na shigo wannan daular ta mulki a dama dani. Hhh Ummi nice nafi dacewa da first lady ba wannan ƙwailar yarinyar da ko ƙirar mata bata da shi ba”.        “Ok Ummi kije wajen Abban karya jimu kin sansa. Da safe ma karasa”.         Da kallo ya bita daga inda take tsaye harta shige lungun corridor ɗin bedrooms ɗin Raudha. Babu abinda ke masa turereniya a rai sai zantukanta da ya fahimci alaƙarsu da birkicewar mahaifiyarsu a yau. Wato Addah Asmah na tunzura Maah akan matarsa dan ya auri ƴarta. Wani murmushi ya suɓuce masa a bazata ya kai hannu ya shafo ƙeyarsa.          Maimakon ɗakinsa da ya kamata ya nufa sai ya wuce na Raudha kamar yanda zuciyarsa ke tunzurashi. Kansa tsaye ya murɗa ƙofar ya shigo. Mama Ladi da ke lallaɓa Raudha ta sha ko farfesu ne da shayi tai saurin kallon ƙofar tana amsa sallamar da yay a hankali. Tunkan ya karaso ta risina tana gaisheshi. Amsawa yay idonsa akan Raudha data dafe kanta saboda ɗan nauyin da yay mata.         “Wani abu ya sake faruwa ne?”.    “A'a ranka ya daɗe babu abinda ya faru, bayan fitarka ne ta sake komawa barci sai yanzu ta tashi. To tace tanajin yunwa ne an kawo abincin kuma tace ta ƙoshi. Shine nake lallashinta taci kodan ta samu ƙarfin jikinta kamar yanda likitar tace”.         Komai baice ba, sai alama da yayma mama ladin akan taje abinta. Cikin girmamawa ta risina da faɗin, “A fito lafiya ranka ya daɗe”.       Kamar zaiyi magana kuma sai ya fasa. Yana tsaye hannayensa duka a aljihu har Mama Ladi ta fice ta rufo ƙofar. Raudha da har yanzu hanunta ke dafe da kanta cikin rashin ƙarfin jiki tace, “Ina yini”?.        Karon farko taji ya amsa mata gaisuwarta da “Lafiya, yaya jikin naki?”.       “Alhmdllhi naji sauƙi”. Nanma baice komai ba ya taka zuwa bakin gadon ya kai zaune kusa da ita gab. Hanunta data tallafe kanta da shi ya janye da faɗin, “Oya ci abinci”.         Batare data yarda ta kallesa ba ta marairaice fuska kamar zata fasa kuka. “ALLAH na ƙoshi”.        “Ashe zan miki ɗura kenan ok! Bana son gardama maza ɗauka”.             Bata da zaɓin daya wuce bin umarninsa. Dan yayi kicin-kicin da fuska babu alamar wasa tattare da shi. Badan yana mata daɗi ba ko ɗanɗano ta fara tsakurar abincin, yayinda shi kuma ya ciro wayarsa a aljihu ya fara dannawa. Da wannan ƴar damar ta ɗanci tea ɗin ma kaɗan. “ALLAH na ƙoshi”. Ta faɗa a marairaice dan yaji tausayinta.         Wayar ya ajiye tare da ɗagowa yana kallonta. Yanda ya ɗan tsura mata ido kamar mai nazari ya sata fara wasa da zoben hanunta......       “Yanzu mike miki ciwo?”. Kanta ta girgiza masa. “Ba ko'ina, sai dai ɗan jiri shima ba wani mai tsawwalawa bane”.          “Kina sakaci da abinci ne shiyyasa shima bai tafi ba. Idan ALLAH ya kaimu gobe inada tafiya zuwa UK, zan samu kamar 4 to 5days kafin na dawo. So bayan na dawo inada sharuɗɗa na canja tsarin zaman gidan nan”.      Wani irin ƙuuuu cikinta ya bayar amma batace komai ba. Shima bai damu da cewar tata ba ya cigaba da maganarsa a kausashe babu alamar wasa. “Dole ne ki koma tsayawa a kan masu girkin nan inhar zasu mana abincin da zamu ci ni da k. Zaki koma kwana ɗakina dan Maah tana buƙatar jikoki saboda tana tunanin ta rasa wani ne a yanzun......”        Cak numfashin Raudha ya tsaya a aiki, cikin rashin fahimtar zancen nasa dan ƙwalwarta ma jitai ta toshe baki ɗaya ta ɗago tana kallonsa. Shima kallon nata yake cikin sarƙe idanun nata a nashi. A hankali ya kai fuskarsa gab da tata ya hure idanun nata. Saurin rumtsesu tai da ƙoƙarin jan jikinta baya amma sai ya ɗaura hanunsa a fuskar gadon kanta ya sauka akai. Jikinta ya sake matsowa a nata shima idanunsa na ƙara ƙanƙancewa. Cikin wani sautin murya da shi kansa baisan ta suɓuto da ga ƙirjinsa zuwa harshe ba yace,         “Idan kaka taso ganin jikokinta laifi ne?”.        Ruɗanin da Raudha ta shiga ne ya sata fara girgiza kai jikinta na tsuma. Ya kashe mata ido ɗaya da janye fuskarsa a tata ya maida saitin kunenta “To ki shirya bata madadin babyn da take tsamanin ta rasa a jiya”. Ya ƙare maganar da ɗan sumbatar gefen kuncinta ya miƙewa lokaci guda da ɗaga mata yatsunsa biyu “Good-night”.            Fitsari ne kawai ya ragema Raudha ta saki dan al'ajabinsa, amma hatta da kayan cikinta sai turereniyar dunƙulewa suke waje guda. da ƙyar ta iya sake numfashin data riƙe a ƙirji lokacin daya maida ƙofar ya rufe alamar ya fita. Gaba ɗaya kalamansa sai suka saka hajijiyarta sake dawowa sabuwa dan jinin daya batan ma ƙasa ya dinga zirarewa ta cikin jijiyoyi yabi numfashi ya fice fit. Hannu takai taɗan mari fuskarta dan gani take kamar a mafarki take dai, sai dai jin tabbacin a zahiri ne komai ya faru ba mafarki ba ya sata faɗin, “Inaga bashi bane aljani ne”. (🤣🤣saifa aljanin kam). ★★★★★       *_WASHE GARI_* kamar yanda ya faɗa kusan 8am ya shigo ɗakin nata cikin kwalliyar suit baƙaƙe da suka fiddo masa ainahin tsarin halittarsa da ƙyawun haiba da ƙuruciya. Duk ramar nan ta campaign ta ciko fatarsa ta sake fresh sai ƙyalli yake yi.         Kamar ko yaushe gaisheshi tayi sai dai taƙi yarda su haɗa ido dan har yanzu kalamansa na jiya basu bar bitar kansu a brain nata ba. Tsaf ya fahimci halin da take ciki amma sai ya basar. ATM card ya ajiye mata da wasu takardu guda biyu batare da ya mata wani bayani ba. Ya ɗan kalla agogon hanunsa yana furzar da iska a hankali....       “Zaki iya fara fita school idan kinji ƙarfi, idan kikaiwa gargaɗina ɗaukar wasa zaki iya rasa karatun baki ɗaya. Abota da wani namiji ko ɗan uban waye bana buƙata. Tarkacen ƙawaye bana ra'ayi. Kiyi abinda ya kaiki”.        “Insha ALLAH bazaka sameni da ƙinjin magana ba. Sai dai ina roƙon alfarmar securitys ɗin nan basai na dinga zuwa da su school ba, hakan zai iya nisanta idanu a kaina na zauna lafiya ga kowa dan ALLAH. Sannan ina son.....”      Sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa.       “Bana son kwana-kwana, idan zakiyi magana kiyita kai tsaye”.     Nanma kanta kawai ta jinjina masa. sai kuma ta ɗan ɗago a marairaice yanda zaifi tausayinta ta ce, “Dama ina son ne naje gyaran kai da kitso na kuma je naga Mummy i miss her”.        Miƙewa yay yana gyara necktie ɗinsa, a ɗan daƙile yake faɗin, “Well kina da damar hakan, sai dai bako yaushe nake buƙatar ganin kitso a kan matata ba. Idan nai buƙatar hakan zance ayi”.      Sototo tayi tana kallonsa baki buɗe har yaje ƙofa. (Oh dama yana mata kallon mata ne wai dama? Ba ƙawance yace kawai suy.....) ganin zai fice tai saurin katse tunaninta. “Dan ALLAH zuwa wajen Mummy fa to?”.           Yanda tai maganar cike da zalama ya sashi ɗan waigowa ya dubeta, sai kuma ya ɗauke kansa “Zamuyi waya”. Ya faɗa yana ficewa gaba ɗaya..............✍         *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*     [6/29, 8:46 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62bc34197660dfc79da0e14b *_Episode 41_* ...........Yau kwanan shugaban ƙasa Ramadhan da wasu mutanensa uku kenan a ƙasar UK. Zuwa yau kuma Alhmdllhi jikin Raudha yayi sauƙi sosai. Abin ƙarin farin cikin kuma a jiya Asabe da hajiyar birni da Hajiya mama suka zo suka dubata, jitai kamar karsu wuce, dan kuka rurus ta dinga ma Asabe da ta shagala a kallon fadar Shugaban ƙasa da ALLAH ya jeho ƴarta ciki. Ko'a mafarki, ko'a hasashe bata taɓa kawo kwatankwacin hakan a ranta ba. Wani iko sai ALLAH, shiyyasa masanin gaibu sai shi. Bawa karka takurama ranka da hassada da ƙyashi dan baka isa canja komai daga rayuwar waninka ko taka ba. Duk abinda ALLAH ya ƙaddara masa sai ya cimmawa a duniya ko kana so ko baka so. Sai dai baƙin ciki ya cigaba da zama abokin taka rayuwar. Dan kuwa ita ƙaddara ta riga fata inji bahaushe.          Gaba ɗaya sai taji ta sake tsanar kanta da abubuwan da suka faru a Hutawa ita da M. Dauda. Tasan ko bajima ko ba daɗe sai an dingama ƴaƴansu har jikoki gori da waɗan nan halayyar, dan ma Raudha bata sanar mata an daɗe da fara mata gori da su ba.          Zuwan Bilkisu da take kira da Aunty B yay mata daɗi a yau ɗin, dan tazo ne a gabar da take shirin fita wanke kai tunda ya nuna baya ra'ayin kitson duk da ta kasa gano dalilinsa na waɗan nan sharuɗɗan. Tare da Bilkisun suka fita wajen wani haɗaɗɗen gyaran jiki, kai dama dukkan buƙatun tsafta da ƙwalisa na mata. Wajene mai tsaro da sirri, dan mai wajen aminiyar Bilkisu ce. Tunkan su tafi kuma tai kiranta ta sanar mata cewar gasu nan zuwa da first lady tana buƙatar raguwar mutane a wajen.         Cikin rawar jiki miss xoxo ta sallami kaso biyu da rabi bisa ukun mutanen wajen saloon ɗin nata da kayan ƙamshi. Vip section ma ko empty ya koma dan first lady ba wasa ba. Ta zaɓo ƙwararrun ma'aikatan ta da tasan aikinsu babu wasa a ciki irin su Hafsat Rano, Mamu gee, Huguma, Bilyn Abdull. Ta sakasu shirya komai. (To Zafafa's kuma ba'a samu ministers ba an koma aikin saloon a *_YERWA INCENSE AND MORE_* 🚶🚶🏻😜)       Tarba ta girmamawa first lady Raudha Ramadhan Taura ta samu, duk da zuwane na sirri hakan bai hana wasu farga ba suka fara ɗaukar hoto a sace. Sai dai Alhmdllhi kasancewar shigace ta mutunci a jikinta hijjab har ƙasa da niƙaf ya taimaka ƙwarai da gaske wajen bata nutsuwa. Babu zancen zaman ɓata lokaci bayan gaisuwar girmamawa data dinga samu ga ma'aikatan wajen  da har ƴar ƙwalla tayi aka fara mata gyaran jiki tako ina. Dan kuwa Bilkisu ce ta lissafa duk abinda ya dace a matan.                Hummm lallai mace ƴar ƙwalisa ce kam. Dan kuwa gyaran da Raudha tasha duk da akwai na amarci a jikinta hakan bai hanata sake fitowa ba fes tamkar wata balarabiya, Bilkisu kanta babu abinda take sai yabawa. Batai ƙasa a gwiwa ba ta shiga ɗaukar Raudha hotuna dan wando da riga ta tilasata mata sakawa da zasu fito. acewarta basai tazo wajen saloon ɗin ana faman sakata rage kaya ba. Badan taso ba ta saka baƙin wandon jeans da top white anyi rubutu da Silver and black ƙyalƙyali a gaban rigar. *_I'm Beauty_*. Sai hijjab data ɗoro kawai a samansu.          Yanda hotunan sukai masifar ƙyau yasa Billy turama Yayansu a email ta kuma ɗaura wasu a status ɗinta tare da shafinta na twitter. Duk da babu wanda ya gane Raudha cikin ƙanƙanin lokaci ta fara samun Comments kamar banza da like. Harda masu cewa suna kamu. Dama ga shafin nata na sele... ne cike yake da followers kamar hauka, dan tana harkar business ɗinta da koya girki itama.      Tana ɗora hoton ta sauka da nufin sai dare zata duba Comments kamar yanda takeyi, suka kuma tattara da ga Saloon ɗin suka fito driver da securitys nata na jiransu. Raudha bata san Bilkisu tayi posting pictures nata ba, kawai dai yanda akai mata gyara na musamman harda jan lallale a yatsu ya sata farin ciki. Sai ɗan baƙi kaɗan da akai mata a bayan hanunta. Ga haɗin turarurruka na *_YERWA INCENSE AND MORE_* miss xoxo ta haɗo mata cikin leda babba.        Suna dawowa gida suka iske su Lubnah zasu fita gidan su Aynah. Batabi takansu ba dan manna musu hauka take yanzu bata shiga sabgarsu. Dan haka a matuƙar ƙulle suke da ita musamman ma Aina'u da takejin duk duniya a yanzu bata da maƙiyya sama da Raudha.        Salla suka farayi, barcin da take ɗan jine ya sata kwanciya tabar bilkisu na kallon wani series. *_ENGLAND (LONDON)_*           Tashin su kenan a meeting ɗin da shine na uku akan abinda ya kawosu ƙasar a kwanakin nan uku da sukayi. Tafe yake gwamnonin da sukai masa rakkiya su biyar biye da shi sai ministers uku da odilan nashi, babu abinda kake gani sai hasken camaras alamar hotuna yake sha da ga ƴan jarida da dama tun ɗazun suke tattauwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa. Hakama wasu a cikin gwamnonin da ministoci duk an ɗanyi hira da su.       A gajiye yake, yana shiga masaukinsa abinda ya farayi wanka, ya ɗan sha shayi sannan ya ɗan zauna domin duba abinda ya shafi family nashi da Business da rashin lokaci ya hanashi nutsuwar yi a kwanaki ukun nan. Cak ya tsaya da kofin shayi a baki zafin shayin dana kofin na ƙona masa laɓɓa. Ya dire kofin tare da fitowa a twitter ɗin da ya shiga cikin zafin rai. Haka yakeyi lokaci-lokaci yakan bibiyi shafin kaf ƙanensa na yanar gizo domin tabbatar da abinda kikeyi. Koda bai shigaba ma kika ɗora abu yakan gani. Idan kuma yaci karo da abinda bai masa ba zaka gane kuranka a hannunsa. Babu wani ɓata lokaci yay dialing number Bilkisu da yaga hotunan a shafinta, sai dai iya ƙoƙarin ya kasa samunta. Canja akalar kiran nashi yay zuwa ga number da tunda ya ajiyeta a wayar bai taɓa kira ba. Cikin sa'a kuwa ta shiga........ *_NAYA (BINGO CITY)_*          Cikin ɗan barcin daya ɗauketa takejin wayarta da ke a bedside drawer na faman vibration data sata. Babu wanda ta kawo a ranta sai Yasmin dan tunda tai wayar nan haka take damunta da flashing da wayar Mummysu ko tasu Fatima. Cikin jan ƙaramin tsaki ta miƙa hanunta ta lalubo wayar batare data tashi ba, da ƙyar ta buɗe ido kaɗan ta ɗaga ta maida kanta a filon da ɗora wayar bisa kunne tace, “Hallo Yasmin!”.       Wani irin tashi tsigar jikinsa tayi saboda jin yanda sautin muryar tata ke fita a mayen barci-barci. Cikin dakiya ya ture abinda ya tsikari ran nasa.           “Dama abinda kikaje yi a Saloon ɗin kenan?....”     Tuni idanunta suka watsatsake ta tashi zaune dakaka dan bata buƙatar fassara ta gama haddace mai muryar. Batare da ya bata damar yin magana ba ko amsa gaisuwar data fara masa irin na suɓul da baka ɗinnan ga wanda ya shiga ruɗani ya cigaba da magana a zafafe a kuma kausashe.        “Tunda ga ɗan iska wanda bai san abinda yake ba ko. Matata ta zama hajar da kowane kare da doki zai iya kalla har a yanar gizo. Tunda tallar jikin kike da sha'awar yi miyyasa baki zauna a gidanku kinyi ba, sai da aurena! Da aurena kike saka wando da riga ana miki hoto a ɗora a shafin yanar gizo! Jikin da ni ban taɓa gani a haka ba wasu dabbobi suke tururuwar gani  I hate you!! Na tsani ballagazar mace da bata iya kame jikinta stupid girl!.....”         Tuni hawaye sun wanke illahirin fuskar Raudha. Babu abinda jikinta keyi sai tsuma kanta harya fara sarawa saboda yanda yake mata magana a kausashe a kuma tsananin zafafe. Duk yanda take masa kallon mai tsauri ta fahimci ya zarce haka a yau. Dan babu komai a cikin kalamansa sai ɗaci da matuƙar hasala...         A hankali Bilkisu data shigo ɗakin ɗauke da roba ice-creem da kwalin pizza ta ƙaraso gareta bayan ta ajiye kayan hanunta kan table ɗin gaban sofa. Duk barkwancin data shigo da shi cikin ɗakin tuni ta haɗiye abinta ganin yanda fuskar Raudha ke wanke da ruwan hawaye ga waya a kunnenta. Wayar ta zare a hankali ta kashe batare da ta duba da wa Raudha ke waya ba.         Ta kamo hanunta sosai tare da jawota jikinta ta rungume. “Please aunty Raudha relax. Kibar kuka dan ALLAH na roƙeki. Ke da wanene haka da har zai saki kuka ta waya..?”        Ɗagowa Raudha tayi tana share hawayenta da hannu biyu. “Aunty B dan ALLAH kece kika ɗora hotunan da mukai a yanar gizo?”.        Cikin ɗan zaro ido Bilkisu tace, “What! Akansu ne kike kukan nan?”.        “Aunty shine fa ya kira yake faɗa akan ɗaurawan”.       “Wai kina nufin Yaya!”. Kai ta jinjina mata wasu hawayen na sake rige-rigen sakkowa. Da sauri Bilkisu ta ɗauka wayar tana ambaton “Ya ALLAH shike nan na mutu, shine na kashe masa kira”. Bata jira amsar Raudha da ba tai dailing number back. Ba'a ɗauka ba, dan yana can ya sake harzuƙa akan kashe masa wayar da akai. Ya riga ya gama fassara ƙarfin rashin kunya da rashin tarbiyyar Raudha. Har shine zata kashema waya? Kalmar mahaifiyarsa na ƴar karuwai danginta karuwai suka shiga masa kai kawo saboda kishi ya hautsinashi. A take kansa ya fara juyawa zuciyar ta sake tunzura da ɓacin rai ya fara huci.......         Kira ne ya sake shigowa a wayar tasa, tana gab da tsinkewa ya ɗaga da shirin yimata abinda bazata sake gigin kiran layinsa ba ma har abada.          Bilkisu da ƙirjinta ke luguden daga dan cike da ƙarfin hali ta sake ƙundunbalar kiran ta rumtse ido sakamakon cin karo da kausasan kalaman yayan nasu..... Ta rumtse ido itama da ƙarfi gabanta na faɗuwa dan ta fahimci a birkice yake. cikin rawar murya da ƙarfin hali tace, “Yaya... Am sorry Please nice. Wlhy ba laifinta bane laifina ne batama san na ɗaura pictures ɗin b....”        “Shut-up stupid!!!”. Ya faɗa cikin tsananin tsawar da tafi wadda yay ma Raudhan. Dan ya gane bilkisun ce ta amshi wayar.       “Na baki mintuna biyu ki saukesu wawuya kawai. Zan sauke miki abinda ke miki yawo a brain tunda media gidan ubanki ne da zaki ɗauketa hoto a haka kikai musu....”       “Dan ALLAH kayi haƙuri Yaya na tuba na san nayi kuskure”.       Ƙittt ya yanke kiran batare daya amsa ta ba..... *_ENGLAND (LONDON)_*          A kwanaki biyun da suka rage tawagar shugaban ƙasa Ramadhan sun fahimci bashi da walwala. Kai bama walwala ba gaba ɗaya a cikin yanayin fushi yake. Dan komai yana yinsa ne cikin faɗa-faɗa. Ko a wajen meeting da sukai na ƙarshe kalaman da yay amfani da su da suka nema tada ƙura a ƙasar NAYA ya sake tabbatar da zuciyarsa a wuya take.       Dan daga Bappi har Anne da Pa kai tsaye suka fahimci haka lokacin da suke kallon labaran. Sai dai mai magana da yawunsa ya sake faɗaɗa kalaman yanda zasu cire ƙulli a zukatan ƴan ƙasar musamman waɗan da suka ƙullacesa a rai. Wasu sun gamsu wasu ko sun riga sun hau da takaici matuƙa...     Oho shi baima san sunayi ba. Dan in yana a irin wannan yanayin bawai yana gane yaren kowa bane ba. Shi kansa baya gane kansa ballantana wani. Hatta da su Anne dan karsu kirasa ya kashe wayarsa ne. Sai dai hakan bai hana Bappi bin ta ɗayan layinsa ba shi ya kirashi. kamar bazai ɗaga ba ya dai daure ya ɗaga. Da ƙyar yake magana hakan ya sake tabbatar ma da Bappi akwai matsala...       Koda ya matsa masa da tabbaya bai ɓoye ba ya sanar masa abinda ya ɓata masa ran. Dan tun yana ƙaraminsa Bappi da Anne sune abokansa, aminansa, iyayensa, kakaninsa. Da wahala yayi wani abu batare da shawararsu ba ko bijirema umarninsu idan sun masa.      Dariya sosai ta kama Bappi amma sai ya gimtse ta da ƙyar sai murmushi yake. tsaf ya fahimci kishi mai tsanani ke ɗawainiya da Ramadhan. Ya daɗe da sanin jikansa nada kishi mai zafi irin nasa. Dan shima haka yake da tsananin kishi ga matarsa Anne. Kafin suyi aure yasha fasa bakin samari idan ya gansu tare da Anne koda ƴan family nasu ne. Kishinsa na ɗaya da ga cikin abinda yasa iyayensu aurar da su batare da sun jira sun kammala karatunsu ba.        “To ALLAH ya huci zuciyar maza”. Bappi ya faɗa murmushi faɗaɗe a saman fuskarsa idonsa akan matarsa data zuba masa ido da son jin mike faruwa da jikan nata.     Bappi ya cigaba da faɗin, “Bilkisu itace mai laifin bata ƙyauta ba sam. Amma ayi haƙuri a kori gaba. Na tabbata da Aminatu tasan zata ɗaura zata hanata tunda tasan baka so...”       “Amma Bappi wando da riga fa ta saka itama ta fita waje matsayinta na matar aure. Da bata sa kayanba ita Bilkisun zata ɗauketa hoton ne?...”          “Uhm itama tayi laifi anan, amma bilkisun ai ta girmeta ya kamata ta fita hankali tunda tare suka fita. Sai dai ina roƙa mata afuwa a tari gaba, idan ta ƙara ni kaina zance a hukuntata kaji babban mutum. Ayi haƙuri zuciyar ta huce haka nan dan ALLAH, dan naga muma ƴan ƙasa fushin ya shafemu har ana mana dogon gargaɗin da gashinan ya tashin hankalinmu baki ɗaya”.       Murmushi Ramadhan ya saki mai sauti yana kai hannu a goshinsa yana murzawa. “ALLAH Bappi bamma san na faɗa ba yarinyar nan ce duk ta harmutsani.”.         Dariya sosai Bappi ya ƙyalƙyale da ita da faɗin, “Ja'iri da alama dai kazo hannufa. Ni nasan Aminatu na ba kalar matan da za'a kira na cushe bane ai”.       Ramadhan ya ƙyalƙyale da dariya harda kwanciya a kujera. “Oh sweet bappi karda ku cika baki, dan nidai cusamin akai”.         “Nima naga alamar hakan kuwa yau”. Bappi ya faɗa yana dariya shima. *__________________________*          Wannan waya itace sanadin hucewar Ramadhan tun a london. Yayinda ita Raudha kenan NAYA cikin damuwa da fargabar karya hanata makarantar daya kwaɗaita mata tunda ya mata gargaɗi tun farko. Gashi gobe idan ALLAH ya kaimu zata fara zuwa monday kenan. Shi kuma yau Lahadi zai dawo kamar yanda ya faɗa kuma aka sanar a labarai. Bilkisu har yanzu tana gidan duk da sanin halinsa ta gwammaci zama harya dawo ta wanke laifin Raudha dan tasan itace da laifi ba Raudha ba. Bata son zama silar haɗa rikicin ma'auratan duk da bata taɓa zama ƙarƙashin inuwar aure ba. Ballema wannan auren nasu na ɗora ɗafini da take ganin matsala kala-kala baibaye da shi, dan duk ƙulle-ƙullen su Maah ta sani bata nunawane kawai tana musu fatan shiriya da ganewa.       Bilkisun ce ta ƙarfafa mata gwiwa suka shirya masa abinci mai ƙyau, ta kumaje ɗakinsa ta gyaro kamar yanda bily ta nusar da ita karta sake yarda wani yay mata gyaran ɗakin miji da ranta da lafiyarta. Sai kuma tai ƙoƙarin kwashe drinks ɗin da aka zuba masa a fridge duk da bata da tabbacin wannan ɗin akwai guba sakamakon har yanzu wancan kukun bai koma bakin aiki ba ana kan binciken ta yanda aka saka mata ƙwayar zubda ciki tasha kamar yanda taji a bakin Mama Ladi.        Da taimakon mama Ladi suke wannan ƙoƙarin na canja drinks ɗin a duk sanda aka zuba shi, sai dai ita kanta mama ladi batasan dalilin Raudha nayin hakan ba. Ko data sanarma Anne zancen catai “Bana tunanin yarinyar nan zata cutar da shi Ladi, anya kuwa babu wani abu a ƙasa data sani? Dan akwai wani saƙo da ya zo mana ana gobe ɗaurin aurensu kuma bamu san waye ya aiko ba, da kuma muka bincika mun samo abinda aka nusar damu akansa. Shiyyasa gaba ɗaya gidan gwamnatin nan a tsorace nake zamansu a cikinsa. Amma karki damu, insha ALLAHU munama Ameenatu ƙyaƙyƙyawan zato bazata aikata wani abu na cutar da Ramadhan ba”. A lokacin kai mama ladi ta jinjina tana murmushi kamar tana a gabana, cikin jin sake ƙaunar tsohuwar tace, “Insha ALLAHU Anne”  Daga haka ta yanke wayar, bakuma ta sake maganar driks da Raudha ke ƙoƙarin canjawa ba a duk sanda aka zuba a frighe ɗin sama dana bedroom ɗin Ramadhan.           Dan haka yanzu ma tare sukayi a sirrance tamkar koyaushe. Daga haka tai wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa da tai mata ƙyau sosai. Light make up bilkisu ta mata badan taso ba. Sai zuga ƙyawun datai takeyi da ƙarfafa mata gwiwar ya kamata ta koya kwalliya kuma ta dingayi dan tana ƙara mata ƙyau. Ita dai murmushi tayi kawai amma batace komai ba, dan kunyar Bilkisu takeji sosai, bama ita ba ko su Fatisa bilkisu ta girma, amma ita Bilkisun ba ruwanta ta saki jiki da ita sosai tamkar ƙawarta ma. A ranta tana faɗin, (wa zanma kwalliyar? Wannan birkitaccen yayan naku da bai iya komai ba sai jin kai da azabar masifar tsiya yaushe ma na ishesa abin kallo? Yau ka gansa normal gobe bajimin zaki kamar ɗan aljanu).       Har ɗauri sai da ta mata, ta kuma tilastata suka fito falo suka zauna dan su Lubnah tun randa ya suka fita basu dawo ba wai bikin ƙawar Aynah akeyi suna can gidan Adda Asmah.      Ita dai zaune take kawai amma badan tana fahimtar abinda suke kallo a television ɗin ba har aka nuna saukar jirgin tawagar shugaban ƙasa Ramadhan da shi kansa. Shine ya fara fitowa lokacin da aka buɗe jirgin. Kamar yanda ya tafi cikin suit haka ya dawo cikinsu sai dai na yanzu sky blue ne, rigar ciki light yellow. Bai sa necktie ba dan maɓallan rigar cikin ma guda uku a buɗe suke.           Fuskarsa ɗauke take da ɗan murmushi lokacin da yake gaisawa da masu tarbar tasu sai dai bamai tsawwalawa ba. A hankali Raudha ta sauke numfashi tana lumshe ido ganin fuskarsa da ɗan sakewa saɓanin yanda tai zaton gani, ita kanta ta yarda Shugaban Ramadhan ƙyaƙyƙyawa ne kuma ya iya ado, ba duk mace bace zata kallesa ta iya ɗauke kanta batare da taji wani abuba, ita kanta yana mata kwarjini da cika ido, badan ya ɗara sauran maza ko mutane ba. sai dai ita bata taɓa jin son sa ba.       Sake buɗe idanun tai tana kallon television ɗin, sai dai ranta cike yake da fargaba lokacin da ake nuna ya shiga mota ɗan jaridar na sanar da tahowarsa gida kai tsaye domin hutawa..........✍           *_Idan zanci duka a Zafafa yau, kuyo saurin zuwa ku kwaceni ALLAH. tsabar na hango irin dakuwar da zanyi har ji nake kamar nai hijira zuwa NAYA🤒🤕👩🏼‍🦯_* *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/30, 8:19 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62bcd9fd7660dfc79daa4337 *_Episode 42_* .........Ta najin shigowar motocin da suka ɗakkosa gidan ta miƙe a ɗan zabure wai zatai fitsari. Bilkisu da tuni ta gama fahimtar a tsorace take tai saurin riƙota tana danne dariyarta.      “Hi madam! sai fa Brother yaga kwalliyar nan ya shaƙi daddaɗan ƙamshin nan, dan haka babu inda zaki gudu”.     Fuska sosai Raudha ta marairaice kamar zatai kuka. “Aunty Please, kuma fa da gaske nak.......”       Sauran maganar ta maƙale sakamakon haɗa ido da sukai da abinda take tsoron gamuwar. Cak numfashinta ya ɗauke daga maƙoshinta har gangar jiki, sai da taji tana neman shiɗewa ne ta haɗiyi wani bushashshen yawu da ƙyar fuskarta na sake narkewa alamar dai da gaske a tsorace take, dan har yanzu ruwan masifar daya zuba mata shekaranjiya tana zaune daram a brain ɗinta, kowace daƙiƙa cikin bitarsu take a zuciya. Ga mai kallonta kuma a yanda tai ɗin babu maraba da shagwaɓa....       A hankali Bilkisu dake murmushi itama idonta akan Yayan nasu ta saki hanunta tana masa sannu da zuwa kafin ta ɗan zunguri Raudha ɗin alamar ta tashi ta tarbesa...          Ko gaisuwar bilkisun ma bai amsa ba, sai wata ƴar harara daya zuba mata na tabbacin har yanzu a ƙule yake da su yayi da idanunsa da sukai ɗan ja. Hakama saman hancinsa jajur yake da alamar murace ta kamashi.. wucewarsa yay zuwa bedroom ɗinsa jikinsa duk yay masa nauyi, saboda murar daya tashi da ita a safiyar yau. Gashi wahala mura ke bashi inhar ta damƙesa.       Nannauyan numfashi suka saki kusan a tare, sai kuma suka kalli juna suka ƙyalƙyale da dariya. Raudha da sosai ta saki jiki da Bilkisu a kwanakin nan tace, “Kai aunty B wlhy kema a tsorace kike fa”.        Dariya sosai Bilkisu tayi, cikin magana ƙasa-ƙasa tace, “Wlhy bazaki gane bane, Brother da kike gani ɗan daru ne bana wasa ba. Idan ya birkice babu mai iya tarosa sai Anne ko Bappi”.       Sake tsargawa cikin Raudha yayi har Bilkisu najin ƙara ƙulululu!!!, kasa daurewa tai sai da ta ƙyalƙyale da dariya. Yayinda Raudha kuma ta ɗan dafe cikin tana yamutsa fuska.         “Kinga tashi ki bisa da ruwa, naga ma kamar mai mura fa. Kuma mura na wajigashi idan ta kamashi”.      “Aunty B wlhy tsoro nakeji. Kinga kuwa harar daya bamu ko amsa sanun da kikai masa baiyiba fa”.     “Karki damu zai huce. Kedai kawai abinda zakiyi ko yayi magana yanzu karkice komai sai ban haƙuri. Ko bayani kar kice zaki masa za'a samu matsala dan ya tsani maimaita magana”.          Cikin tausayin kai Raudha ta jinjina mata kai tare da miƙewa. Dan koda bata son sa bazata taɓa son ace ta gagara sauke hakkin aure da ke a kanta ba. Idan ko ta tuno gargaɗin mahaifinta bazataso aurenta ya mutu ba har abada koda batajin daɗi a cikinsa. Ruwa da cup ta haɗa saman wani ƙyaƙyƙyawan golden tray mai yarfin fari kaɗan da fresh milk duk da tasan duk akwaisu a ɗakinsa. Ta gyara lulluɓin mayafinta har saman kai kamar wacce zata fita duk da ba wani babba bane ba. Yanda ta fahimcesa ma idan tace zata fita waje da mayafin ai zai iya halaka ta.       “Kimin addu'ar fitowa lafiya dan ALLAH aunty B”.    Ta faɗa cikin marairaicewa lokacin da tazo saitin Bilkisun. Cikin danne dariya Bilkisu tace, “Fatan alkairi aunty Babba. Insha ALLAH babu ma abinda zai faru sai alkairi da tsarabar kiss”.       Kunyar maganar ƙarshe ta saka Raudha saurin yin gaba tana ɗan tura baki. Bilkisu ta ƙyalƙyale da dariya har ranta tana sake jin ƙaunar yarinyar.          Tamkar wadda tazo sata a ɗofane tai knocking ƙofar batare da tunanin zaima jita ba. Jin shiru ya sata ƙara ɗan bugawa nan ma tsitt. Hannu ta kai zata sake bugawa a bazata aka buɗe ƙofar hanunta ya sauka saman kirjinsa da babu riga. Hasalima daga shi sai towel yana ta raɓar ruwa alamar wanka ya fito.      Da ƙarfi Raudha ta rumtse idanunta da ƙoƙarin janye hanunta daya haɗu da laushin fatarsa da laimar ruwan ɗumin dayay wankan da shi. “I...am sorry. ALLAH ban san ka taho ba”.      Ta faɗa kamar zatai kuka idanunta har lokacin a rumtse suke ji take kamar ta saki gudawa. Jin shiru ya sata ɗan buɗe ido ɗaya kaɗan. Wayam baya a wajen, gaba ɗaya ta buɗe tana haɗiye yawun da ya kasa wuce mata a maƙoshi da ɗan dafe ƙirji ta sauke numfashi. sai kuma tai saurin ɗago hanun ta kalla tare da kai masa duka da ɗayan hanunta tana cije baki kamar maiyi da wani (😂ba man kai ... Lol)         “Malama ki rufen ƙofa inba shigowa zakiyi ba”. Ta tsinkayi muryarsa da ke nuna tabbacin mura yake. Dan baima kai ƙarshen maganar ba ya saki atishawa a cikin tissue ɗin dayay saurin ɗorawa kan bankinsa.       (Masifaffe). Ta ayyana a ranta tana ɗaukar tray ɗin data ajiye a drawer glass da akai ado da shi gab da ƙofan ɗakin nasa. Koda wasa batai gigin kallonsa ba, dan shi ya fuske abinsa duk da kuwa daga shi sai towel. A ɗan table ɗin gaban sofa's ɗin ɗakin ta ɗora, kanta a ƙasa tace, “Ina yini? an dawo lafiya?”.       Sarai ya jita, amma yay banza yana cigaba da shafa mansa lokaci-lokaci yana atishawa, yabi ya tara uban tissue a ƙasa da yake tarewa da shi. Raudha na ƙoƙarin barin ɗakin cikin takaicinsa dan ta tsani wulaƙanci duk da bata da yawan hayaniya ya katse hanzarinta da faɗin, “Bani dustbin”.        (Yadai fi). Ta faɗa a ranta tunawa da wahalar da tasha wajen gyaran ɗakin nasa lungu da saƙo. Shi kansa lokacin daya shigo yaga ɗakin sai da yaji a ransa ba gyaran Tahir bane. Yanda bai tanka ba data gaishesa itama hauka ta manna masa taki tankawar ta fice. Kallo ya bita da shi cikin jin haushin bata amsa maganar da yay mata ba (ƙarfin hali😜 lallai wanzami baya son jarfa).      Guntun tsaki yaja da cirar tissue ɗin ya sake atishawa a ciki. Idanunsa sun kara kaɗawa da ja har suna tara ruwa a ciki. Jijiyoyin goshinsa kam duk a miƙe suke alamar ciwon kai.         Yana ƙoƙarin saka shirt mai ɗan kauri ta shigo, bata yarda ta kallesa ba, cikin ɗan yamutsa fuska da bata san tanai ba tasa yatsu biyu tana a yanayin ƙyanƙyami ta dinga ɗauke tissues ɗin daya tara a ƙasa tana jefawa a dustbin ɗin. Cak ya dakata da abinda yake yana kallonta, a ransa ya ce, (Da gaske yarinyar nan ta bala'in rainani, wai ni take ƙyanƙyami?) a fili kam sai ya taɓe baki ya ɗauke kansa. Ƙarasa shirinsa yay ya ɗauka misk zai ɗan shafa dan baya buƙatar saka wani spray turare saboda mura, dai-dai Raudha ta gama kwashe tissues ɗin sai wani kwaɓe fuska take hanunta a buɗe tabbacin ƙyanƙyami. Dariya yaji tazo masa tsabar muguntar daya shirya mata. Amma sai ya gimtse kayarsa bama zaka taɓa fahimtar hakan a fuskarsa ba. Raudha na ƙoƙarin gyara mayafinta kawai taji saukar atishawa a fuskarta har biyu a jere.       “Innalillahi.....” ta faɗa cikin subutar baki tana sakin dustbin ɗin ƙasa. Misk ɗin daya gama shafawa ya ajiye saman mirror yabar wajen tamkar baima san abinda yayi ba. Yaje saman sofa ya zauna ƙafa daya kan ɗaya. Cikin bada umarni da isar daya gada ga Gimbiya Su'adah ya ɗauka jaridar dake ajiye saman stool ɗin gefen kujerar yana faɗin, “Sai kiyi ƙyanƙyamin da hujja yanzu ai ko? Ina bukatar shayi kuma”.       Wani irin yamutse fuska Raudha tai, kai kace amai ne zai kufce mata. Sai kuma ta fashe da kuka ta ɗauki dustbin ɗin ta fice.       Da kallo ya bita ta saman jaridar, sai kuma ya saki guntun murmushi da taɓe baki lokaci ɗaya yana ɗage kafaɗa irin ko'a kwalar rigarsa ɗin nan.        Cikin sa'a Raudha ta samu bilkisu bata falon, kitchen ɗin dake falon ta shiga, kuka tayi sosai dan har cikin rai taji zafin abinda yay mata, yayinda wani gefe na zuciyarta ke ƙoƙarin nusar da ita abinda yayi ɗin ba komai bane, sai dai taƙi saurarensa. Sai da ta fidda duk wani takaicinta sannan ta wanke fuskar tas har kwalliyar tana faɗin “Anma fasa kwalliyar ALLAH bazaka sake gani ba”. Shayin da yace ta haɗa masa ta haɗa cikin flask mai ƙyau bayan taje ƙasa ta ɗibo kayan data san ana dafa masa shayi da su da yawa.          Maimakon a ɗaki data barsa sai ta iskesa a falo zaune yanzun. Bilkisu na daga zaune ƙasan carpet itama kusa da ƙafafunsa da alama haƙuri take bashi. Dan yanda tai kalar tausayi ya isa tabbatar da haka. Shiko yayi wani kicin-kicin da fuska har yanayin nasa yasa Raudha sake shiga hankalinta. Bayan ta ajiye a gabansa ta zuba shayin tare da saka masa sugar ɗinsu na masu diabetis da yake amfani da shi. Komai baice ba ya ɗauka abinsa ya fara sha.       Kanta a ƙasa tana ɗan wasa da yatsun hanunta tace, “A kawo abincin nan?”.         Cikin mamaki da al'ajab ɗinsa taga ya wani zuba mata idanunsa da mura ta gama firgatawa. Dan harsun kumburo fatarsu tai jaa ga ƙyallin ruwan a ciki, tsaf ya fahimci kuka tayi, sai kuma ya ɗanji babu daɗi. Amma a fuskarsa bazaka taɓa fahimtar hakanba. Dan wani yamutse fuskar yayi ma ya ɗauke kansa bayan ya zuba mata nunanniyar harara.        “Zan sha wannan, idan da buƙatar hakan daga baya na ci”. Ya faɗa bayan yaja wasu sakanni.      Baki ta taɓe zata bar wajen Bilkisu ta ƙyafta mata ido alamar karta tafi. Ta marairaice fuska kalar tausayi da alamar roƙo wa Bilkisun. Da ido Bilkisun tai mata nuni da Ramadhan da ya maida hankalinsa ga jarida... Sai kuma ta ɗauke kanta da faɗin, “Yaya dan ALLAH fa nace, i promise hakan bazai sake faruwa ba. Wannan ma kuskure ne wlhy kuma nice nayi banda Aunty Raudha dan batama san na ɗaura ba”.      Shiru kamar bazai tanka ba sai kuma ya ajiye jaridar yana furzar da huci kaɗan. A takaice ya ce, “Tashi kije”.      Ta san ya haƙura kenan, dan haka cikin jin matuƙar daɗi ta miƙe fuskarta washe da murmushi tana faɗin, “Thanks you Yaya. ALLAH yasa aunty Raudha ta haifa mana ƴan biyu”.       Hannu ya ɗaga kamar zai kai mata ranƙwashi ta kwasa da gudu tana dariya. Shima dai murmushi ne ya subuce masa a bazata. Yana matuƙar son Bilkisu a duk cikin ƙanensa. dan tanada hankali da nutsuwa. Gata da addini, wani lokacin akance halinsu na kamanceceniya da juna. Hakama a fuska suna matuƙar kama. Har lokacin da ɗan murmushi a fuskar tasa ya maida dubansa ga Raudha da mamakin dama yana wasa haka ya narkar da ita. Haɗa idon da sukai ya sata janye nata tai gefe da shi tana tura baki, dan har yanzu a fushi take. Sai kuma tai saurin yunƙurin barin wajen itama......         “Ina su Muneera?”. Tambayar tasa ta sakata tsayawa cak, sai kuma ta juyo kanta a ƙasa. “Inaga suna can gida, Yau kwanansu biyu”.       “Kinaga? Bamaki da tabbas kenan?”. Yanda yay maganar a dake ya sata ɗagowa ta ɗan kallesa. kasancewar idanunsa a kanta suke saita janye. Duk da zafi da zuciyarta ke mata sai ta danne. Banda ma ya raina mata hankali su Lubnah dake manyanta ne zai nuna kamar laifintane barinsu fita. A fili kam cikin sanyin murya da ɗan fushi-fushi tace, “Nasan can ɗinne kawai zasu je. Kuma ni da zasu wuce basuyi sallama da ni ba ai miye nawa”.        Yanda taɗan tunzura baki ya fahimci haushi taji. Batare da yace mata komai ba ya ɗauke kansa kawai gareta ya maida ga jaridarsa. Itama ganin haka ya sata barin wajen tai wucewarta bedroom.           *BAYAN SALLAR ISHA'I* tana zaune a ɗaki ita kaɗai dan bilkisu na ɗakin da su Lubnah suke tana waya da saurayinta ne. Yunwa takeji sosai shiyyasa tana idar da salla taje falo ta ɗibo abinci....       A hankali ya turo ƙofar waya manne a kunensa, kan agogon ɗakin ya fara sauke idanunsa kafin ya maida kan Raudha da mamakin shigowar tasa ya sakata shagala a kallonsa.          Takawa ya cigaba dayi inda take a hankali, tsabar yanda ta tafi wani tunani daban yasa harya iso gabanta bata sani ba. Firgigit ta dawo hayyacinta jin an hure mata idanu. Yanda ya ɗan ranƙwafo fuskarsa gab da tata har yana busa mata numfashinsa ya sata ƙoƙarin jan jikinta baya amma sai ya saka hannunsa jikin kujerar ya tokare. Koda ta matsar da kan nata sai ya sauka akan hanunsa. Saurin ɗagawa tai hakan kuma sai ya ƙara basu kusancin da take gudu. A haka ya cigaba da wayarsa cikin harshen turanci idanunsa cikin nata, yayinda yatsansa ke shafa girarta.         Fuska Raudha ta ɓata kamar ta fasa ihu da wannan dabaibayi nasa data gagara fassarawa, acan kuwa zuciyarta na liguden daka, sai dai duk yanda taso ɓoye firgicinta ya riga ya gama karantarta, dan duk ta daburce. Hatta cokalin da take shan farfesun gabanta ya suɓuce a hanunta ya faɗi saman table ɗin. Duk yanda ya fahimci takurata yay yaƙi janye jikinsa. Sai ma cigaba da wayarsa yay hankali kwance numfashinsa na sauka saman fuskarta itama yanajin nata a wuyansa, ta rasa yanda zata fassara lamarin nasa.       “Ina yini”. Ta faɗa kamar zatai kuka dai-dai yana sauke wayar a kunensa alamar ya kammala wayar, dan wannan kusanci nasu ya matuƙar sakata cakwalkwalin ruɗani. Kaɗan ya rage dariya ta suɓuce masa amma ya danne. Janye jikinsa yay da ga gareta ya kai zaune a kujerar gefenta cikin basar da gaisuwar tata.      Da ƙyar ta iya sakin numfashin data riƙe a ƙirji. Fitsari ne kawai ya ragema Raudha ta saki itakam dan al'ajabinsa. Bata gama dawowa hayyacintaba ta tsinkayi muryarsa still da wani furicin.        “Har yanzu kina ƙyanƙyamin nawa?”.       Babu shiri ta kallesa ido a zare. cikin marairaicewa ta ce, “Ni yaushe nace ina ƙyanƙyaminka?”.       Yanda tai maganar ya sashi tsura mata idanunsa da mura ta cika. Sai kuma ya janye yana sake tamke fuska. Kamar yanda itama ta ɗaure tata tamau.            Fuskarsa ya ɗan sake matsarwa gab da tata, still yanzu ma suna shaƙar numfashin juna. “Idan ma baki faɗa da baki ba ai sirrin zuciyarki ya fito, shiyyasa na baki numfashina naga idan kin ɗauka ke kuma yaya zakiyi da kanki?”.        “Ya ALLAHU!”. Ta faɗa cikin subutar baki da waro idanunta waje gaba ɗaya kansa. Yatsun hanunsa biyu ya ɗan kaɗa mata, sai kuma ya duba bowl ɗin gabanta mai ɗauke da farfesun kayan cikin da Bilkisu tai musu. Yunwa ce ta addabeta dan tun safe rabonta da abinci, fargabar dawowarsa da tuna azabar masifar da yay mata a waya ya hanata sake cin wani abu. Dama da safen Bilkisu ce ta takura mata........        “Ammafa wannan cin amana ne, aci nama ina gidan nan babu ni, wannan ƙawancen dake tsakaninmu kuwa na tsoron ALLAH ne Ustazah?”.     A yanda yay maganar ya sata kasa daurewa sai da ta kallesa. Ganin idonsa a kanta ya sata ɗauke nata da sauri tana tura baki. (Na shiga tara ni Raudha, ALLAH yasa dai da gaske ya huce kenan) ta faɗa a ranta, a fili kuwa sai ta ja kwanon namanta gabanta da faɗin, “Naji a kwance, idan na gama ci sai mu shirya”.          “Ko? to andai ji kunya Ustazai da rowan nama, idan kina son kanki da arziki muje ki bani nawa naci kokuma na ɗiba rabona a can” Yay maganar cikin ɗage mata gira ɗaya yana miƙewa. Batare da ya jira cewarta ba ya fice abinsa. (Uhm, su Ramadhana an fara zama ƴan is...😏🚶🏻) Filo Raudha ta ɗauka ta balla masa cizo tana matsesa a ƙirjinta. Sai kuma ta tillashi ƙasa tare da dafe kai tana faɗin, “Ni Raudha yama haukatar dani”.        Babu yanda ta iya dole ta miƙe ta ɗau mayafinta na ɗazun dan kayanne a jikinta har yanzun ma ta fita. Tsaye ta samesa a falo hankalinsa gaba ɗaya akan television da ake nuna labarai. Koke-koke da taji anayi a tvn ya sata saurin kallo gabanta na faɗuwa.  Jikinta ya kama rawa, domin kuwa rahotone na wani ƙauye a ƙaramar hukumar Gaman dake jihar Kuddo faɗa ya ɓarke a tsakanin ƙabilun dake ƙauyen. Gawarwakine zube na yara da manya harma da dabbobi, wasu jina-jina da raunika abin babu daɗin gani. Ga wasu nata kuka durkushe gaban gawarwakin ƴan uwansu da aka kashe ko aka raunata.       Kuka da Raudha ta fashe da shi ne ya maido Ramadhan da ga ɗaukewar numfashi da ya tafi na tashin hankali. Ya kai zaune jib cikin kujera hajijiya na neman ɗibarsa. Ba yau ne aka fara irin wannan rikicin a ƙauyen ba, sai dai bai taɓa gani ba kamar yau, ga shi yau ɗin daya gani kuma yana amsa sunan shugaban kasar NAYA ne da hakkin kowa ya rataya ne a ƙarƙashin mulkinsa..... Yanda jikin nasa ke rawa ya sakashi riƙo Raudha data kai dirƙushe a gabansa tana kuka ya rungume, itama ƙanƙamesa tayi kawai tana sakin wani sabon kukan.....       Wayarsa ya fara laluba da hannu ɗaya a aljihu, yayinda ɗayan ke tallafe da Raudha. Yana cirota kafin ma ya aiwatar da abinda yake shirin yi kira ya shigo masa. Da ƙyar ya iya controling kansa tsabar ruɗani ya ɗaga, da ga can hankali tashe cos ya ce, “Ranka ya daɗe kaga abinda ake nunawa a tashar Q-TV kuwa? Kodai halin ƴan adawa ne kawai....”          “No Jafar, karka kawo wannan, ka bincika yanzu abun ke faruwa ne ko tun ɗazun?”. “Okay sir ina zuwa”. Wayar ya jefa saman kujera, ya kai zaune shima har yanzu Raudha na jikinsa tana sharɓar kuka. Ji yake kamar shima ya fashe da kukan, amma ya daure ya ɗago Raudha, cikin dakiya yake faɗin, “Please Ameenatu relax mana. Kukanki sake tadamin hankali yake, bayan daga gareki ya kamata na samu ƙarfin gwiwa”. Hannu tasa tana sharar hawayen, “Kayi haƙuri”. Ta faɗa tana ƙoƙarin tashi daga saman cinyarsa da take zaune ɗare-ɗare gudun kar Bilkisu ta fito, kuma a karankanta ma dai da kunya ai. Komai baice mata ba, sai wayarsa data fara ring ya kai hannu ya ɗauka ganin cos ne.       “Ranka ya daɗe a yanda suka faɗa su dai yanzu ne. Amma dai yanzu I.G ya tabbatar min tun kusan magrib ne abun ya fara faruwa kamar yanda C.P ɗin jihar Kuddo ya sanar masa. Sai dai ka kwantar da hankalinka ya tabbatar min komai ya dai-daita zuwa yanz.......”            A matuƙar tsawace shugaban ƙasa Ramadhan ya katse cos, “Taya zan kwantar da hankalina Jafar? mutane na cikin irin wannan tashin hankalin!! Ka duba fa kaga mata ne da yara kanana a cikin jini saboda rashin imanii!!! Yanzu da akan familyna ya faru zakace na kwantar da hankalina ne? Na shiga uku ni Ramadhan!........”        A yanda yay maganar dole ne ya baka tausayi ya kuma tayar maka da hankali, dan abun al'ajabi sai ga hawaye na sakko masa. Wayar yay jifa da ita tare da dafe kansa yana yamutsa gashinsa da duka hannayensa biyu.       Sosai Raudha ta sake rikicewa itama, dan yanda yake birkita sumarsa yana hawaye da ambaton ya shiga ukun itama sai ta sake fashewa da kukan da zuwa gabansa ta durƙushe hannayenta duka biyu akan gwiwoyinsa............✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [6/30, 11:42 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62bd9379f0fb62def3120ded *_Episode 43_* ..........Su dukansu fuskokinsu washe suke da fara'a da farin ciki. Gasashshen naman rago ne a banƙare a tsakiyarsu. Sai lemuka masu tsada da daɗi ajiye gaban kowa. Gaba ɗayansu hankulansu nakan tv da ake nuna abinda ke faruwa a ƙauyen Kauci na ƙaramar hukuma Gaman. Cikin ƙyalƙyalewa da dariya Mr MM ya kai tsokar nama daya cako da pork spoon bakinsa yana faɗin, “Wato ranka ya daɗe dabarar nan taka tayi ɗari bisa ɗari, yaje ya dawo yana farin cikin samun na sarori sai yaci karo da ƙyaƙyƙyawar tarba ta musamman”.        Kwashewa sukai da dariya baki ɗayansu, Alhaji Haladu Gwandu dake dariya harda hawaye ya ce, “A to ba gani yake shi yanada dabarar shinfiɗa aiki ba ta hanyar ɗaura ƴan uwansa matasa kan manyan muƙamai, to sai yayi aikin mugani. Basai da zaman lafiya a ƙasar talakan zai ga aikin ba?”.      Wata dariyar suka sake kwashewa da ita. Sai dai banda oga kwata-kwata da yake murmushi kawai yana cin namansa shima. A cikin God fathers ɗin nasu ɗaya ya tsaida dariyarsa ya ajiye wuƙar daya yanko wani ƙaton nama ya ɗauka da hannu yakai baki. “Ai indai mune baima ga komai ba. Sai mutuwar fitinannen tsohon kakan can nasa ta tabbata nan da kwanaki uku, a kuma ranar plan B zai bayyana shima, yanda mutuwar Alhaji Hameed Taura bazatayi tasiri a zukatan mutane ba balle ya samu addu'a da nuna tausayawa”.         Dariyar suka sake tuntsirewa da shi. Forma president ya ce, “Wa yaga gaba kura baya sayaƙi. Bashi gani yake mulkin wasan yara bane ba, zai yabawa aya zaƙinta. Yanzu nan fa ina shirin fitowa ma nakejin wani ƙishin-kishin ɗin gulma, wai da yayi niyyar bincike akan kwangilolin da muka bada, sai dai ya dakatar dalilin wani abu da ba'asan tabbaci ba.........”         Vice president Alhaji Yaro glass ya karɓe zancen forma president da faɗin, “Wannan maganar kam tabbas ce, sai dai nima ina kan bincike miye dalilin hanashi fasa binciken. Dan yanzu haka ma gobe za'a zauna da masu kwangilan meeting tare da J.P.S”.           “What!! Alhaji Haladu Gwandu (Mahaifin Amnah) Ya faɗa aɗan razane. Dan kuwa akwai yaronsa a cikin wanda aka bama kwangilolin, kuma tabbas yau kusan kwanaki uku yana kiransa bai samu damar ɗaga wayar tasa ba saboda busy da yayi.....         “Wlhy da gaske haka zancen yake”.      Alhaji yaro glass ya faɗa a yanayin takaici da jin ɗaci. Waya Alhaji Haladu Gwandu ya lalubo a aljihun babbar rigarsa. Da sauri ya shiga laluben lambar yaron nasa. cikin sa'a kuwa bugu ɗaya ya ɗauka tamkar dama kiran nashi yake jira. Ko sauraren gaisuwar tasa baiyiba ya jeho masa tambaya. Sai dai amsar daya bashi tai matuƙar firgitashi ya saki baki da hanci yana saurare har yaron nasa ya gama bayanin saƙon da suka samu na kira da ga ofishin Minister.            A hargitse ya ajiye wayar bayan sun kammala yana faɗin, “To tunda ya fasa binciken kiran ubanmi yasa Minister ɗin yake musu?”.           “To wa ya sani”. Cewar Alhaji Yaro glass.     A harzuƙe Forma President ya ce, “Amma ya kamata ace irin waɗan nan abubuwan kana ƙoƙari saninsu Alhaji Yaro. Kasan kuwa wanene Ramadhan da Alhaji Hameed Taura?!!...”         “Haba Alhaji Usama ya zakaga laifina? Bayan kaima kasan yaron nan komai yinsa yake a ƙudundune, daga shi sai matsiyacin cos ɗin nan da nafi tsana fiye da komai yanzu a duniya. Sai ko shegen kakansa ɗin nan da ubansa da nasan sune masu bashi shawara sama da mashawartansa na mulki.....”            Mr MM zaiyo magana Oga kwata-kwata ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masu hannu. “Inaga wannan cece kucen ba shine mafita ba. Amma tabbas Alhaji Yaro akwai sakacinka anan. Sai dai muma munada laifi da bamu ɗoraka bisa hanyar data dace ka dinga sanin komai da komai ba. Amma ka sani matarka tana ɗaya daga ciki, dolene ta cigaba da kawo mana mike gudana a cikin gidan gwamnati ta hanyar matarsa tunda ƴa take a wajenta. Sauran magana kuma zamuyi daga baya idan na kammala nazari, amma a dakatar da kashe Alhaji Hameed Taura ba yanzu ba”.       Cikin gamsuwa duk suka ɗaga masa kawuna, duk da a ransu suna son sanin dalilin dakatar da kashe Bappin, sai dai babu damar yin jayayya........ *______________________________*          A matuƙar ruɗe Raudha ta kai hannu tana riƙo na Ramadhan jikinta na rawa. “Dan ALLAH kayi haƙuri, nasan wanda suka rasa ransu bazasu taɓa dawowa ba. Sai dai akwai mafita da zata taimaka a taimaki wanda sukaji raunika da tsananta tsaro ga wanda ba'a cutarba”.            Duk da bai ɗago ya kalleta ba yanda ya dakata da yamutsa kan ya tabbatar mata yana saurarenta. Sai kuma ya ɗago ɗin ya zuba mata idanunsa. Hawayenta tai saurin sharewa tana miƙo masa wayarsa data ɗakko. Sai kuma takai ɗayan hanunta ta share masa nasa hawayen shima da har yanzu suke sakkowa.          “Kasan yanayin ƙasarmu da ƙarancin kulawar da talaka yake samu akan harkar lafiya da tsaro. Lokuta da dama wasu a cikin jami'ai najin abu na faruwa sai dai tsoro da rashin kayan aiki na daƙilesu akai taimako, wasu kuma son zuciya ke hanasu yin kowane irin yunƙuri. To kamar hakane ga jami'an lafiya suma. Shiyyasa idan sakacin shugabanni ya haɗu da masu raunin taimako a jami'an lafiya ma yana ɗaiɗaita rayuwar talaka. Mafita itace yanzu ba wakili zaka saka ya bincika ba ko ya bama C.P na jihar umarni, kai da kanka ne ya kamata kai magana da I.G da C.P ɗin zasufi jin tsoron tashi suyi abinda ya kamata suma bawai su tura yara ba. Hakama asibitin da kanka ka kira Commissioner lafiya na jihar kai magana da shi dan ALLAH Ya Ramadhan......”         Ɗari bisa ɗari ya gamsu da maganarta, dan haka ya ɗago da sauri, wayar da take miƙa masa ya amsa yay dailing number cos. Kai tsaye yace, “Ka sameni”.       “Ranka ya daɗe yanzu haka ina cikin gidan nan ai”.     Cos ya faɗa da sauri gudun kar shugaban ƙasa Ramadhan ya yanke wayar. Duk da cos baya shigowa har nan yau dai ya bashi umarnin ya samesa. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai ga cos ɗin. Saurin janye jiki Raudha tai daga rungumar da Ramadhan ya sake mata bayan yayi magana da cos. Sai dai hanunta ya riƙo cikin nasa dole ta zauna a hanun kujerar da yake a zaune hanun nata rumtse a nasa.          COS ya rissina yana gaishe da Raudha data amsa a kunyace, dan yanda ya gansu da yanda yake bata girma har mamaki takeyi.       Cikin bada umarni Ramadhan yace, “Ina bukatar magana da I.G & commissioner of police na jihar, tare da commissioner lafiya”.         Kai Cos ya jinjina yana mai fara danna wayarsa. A taƙaice Cos yayma I.G bayani ya mikama Shugaban ƙasa Ramadhan wayar. Koda ya amsa bai wani tsaya sauraren gaisuwar ɗin ba da jikinsa keta ɓari da ga can shi zaiyi waya da shugaban ƙasa. Kamar yanda Raudha ta bashi shawara haka yayi, yana gama kora masa bayani cike da ƙasaita kamar bashi ya nema birkicewa ba yanzu ya miƙama COS wayar. Amsa yay da girmamawa ya sake kira masa C.P na jihar Kuddo da Commissioner ɗin lafiya. Daga ƙarshe yasa aka kira Gwamna ɗin jihar shima inda Shugaban ƙasa Ramadhan ya balbalesa da masifa jin tamkar ma shi babu wata damuwa tattare da shi.         ★Tabbas umarnin shugaban ƙasa Ramadhan yayi matuƙar tasiri, dan cikin ƙanƙanin lokaci dukkan abinda ya lissafa aka ninkashi ga jama'ar wannan ƙauye. Kafin wayewar gari tako ina garin jami'an tsaro ne har cikin dazukan yankin da sauran ƙauyikan, ga helicopters na sojoji sai yawo suke ta sama. Na asibitima suna samun ƙyaƙyƙyawar kulawa. Waɗan da sukai musabbabin fara haɗa rikicin da CP ya bada umarnin dankosu sai ga gawarwakinsu a cikin waɗanda suka mutu. (Dama haka fitina take, a mafi yawan lokaci wanda ya takalota shi take fara zubarwa a ƙasa. ALLAH ka zaunar da ƙasashenmu lafiya. ya gafarta mana kurakuranmu ka wadatamu da tsarkakakkiyar zuciya😰). ★★★          Da ga Raudha har Ramadhan idan sunyi barcin kirki a wannan dare sai dai ɓarawo. Ga mura ta mugun addabarsa da zazzaɓi mai zafi ma ya kwana. Yayi waya da Bappi yayi da Pa duk akan lamarin. Anne ma ta kwantar masa da hankali ta hanyar nasiha sosai da muhimmincin tashi tsaye akan addu'a .      Basu kaɗai ba hatta Bilkisu da damuwar ta kwana. Duk da dai nata tsananin tashin hankalin nada nasaba da halin da taga Yayansu da Raudha a ciki. Adalilin hakan ma yau a ɗakin Raudha ta kwana. Ita kuma Raudha a ɗakin Ramadhan suka kwana tare.                Da sassafe shugaban ƙasa Ramadhan yabar gidan batare da sanin su Raudha ba, dan ɗakinta ta tafi yin sallar asuba bayan ya fita massalaci shima. Sai da suka fito sukaci karo da shi a tv ana nunasa a cikin ƙauyen Kauci, abinda zai birgeka har da shi cikin tawagar masu zana'ida duk da karancin lokacin dake garesa. Ana kammalawa suka baro garin sai dai yabar jama'arsa suna sake zagaya ciki da bai ɗin ƙauyen. Tare suke da gwamnan jihar Kuddo ɗin. Daga ƙauyen asibiti suka wuce nanma shugaban ƙasa Ramadhan ya duba wanda suka sami raunika. Da ga haka bai ƙara ko minti biyarba a jihar Kuddo suka nufo Bingo dan da ƙyar yay squeezing time ɗinsa dama. Sai dai abinda yayi ɗin ya kara masa kima da daraja a idanun talakawan ƙasar NAYA. Gaba ɗaya a yinin nan babu abinda kakeji sai ruwan albarka da ake jera masa tako'ina.      Yayinda a ɓangaren su Alhaji Yaro glass kuma sukai yinin baƙin ciki da ƙunci dan basuyi zaton shugaban ƙasa Ramadhan zaije har ƙauyen ba domin nuna kulawa. Ba ƙaramin shiri ya wargaza musu ba akan hakan.        A ɓangaren mai gayya mai aiki kam Ramadhan yau ya yini ne cikin damuwa da ɗunbin fargabar wannan mulki mai cike da ƙalubale kala-kala. Tun ba'aje ko inaba fa kenan, inaga nan gaba kuma da shekaru huɗu da watanni kusan bakwai ke jiransa. Kai anya kuwa zaya iya?.       Da wannan tunane-tunanen ya yini a office ga mura da ciwon kai ga zazzaɓi ga kuma aiki. Yini gudan nan kuma bai ci komai ba ƙishi ma sai da yaji maƙoshinsa na neman fara yayyankewa sannan yasha ruwa, dan daya tuno jinin daya gano a Kauci sai tsigar jikinsa ta dinga tashi.           Duk da wannan damuwar hakan bai hana wakilan da yasa minister ya naɗa zaman mitin da masu kwangilar nan ba. Sun kuma gudanar da zaman tamkar yanda ya bada umarni. Yanayin zazzaɓi daya rufesa ya sashi barin office tun 2pm ya shiga gida.            ★Koda ya shigo gidan ya iske Raudha bata gidan, shi shaf ma ya manta da batun fara zuwanta school yau. Ɗaki ya shige ya kwanta, duk da abinci ya kamata ya fara ci ya sha magani hakan bai faruba, sai dai yaji ciwon kansa na ƙara tsanani ya ɗauka man zafi ya shafa ya sake lulluɓe jikinsa gaba ɗaya cikin duvet.          Duk da burin da taci akan wannan rana ta fara zuwanta makaranta abinda ya faru jiya sai ya rage masa armashi, Bilkisu ce ma da zuwan Ramadhan ƙauyen ya ɗan ƙarfafa mata gwiwa. Sai dai kuma kafin ta wuce ta ɗauka shawarar zuciyarta, so take tai karatu tankar kowane ɗalibi batare da ansan ita wacece ba. Hakan kuma bazai kasance ba sai idan bata tare da dogarawanta da aka tanada mata. Gudun karta aikata ba daidaiba ta sanarma Bilkisu shawarar data yanke a yau game da karatunta. Ɗari bisa ɗari Bilkisu ta yarda da tunanin Raudha, amma itama sai ta kira Anne ta sanar mata. Hakan ya burge Anne ta kuma bama Raudha goyon baya tare da yabama ƙyaƙyƙyawan tunaninta. Daga ƙarshe Anne tace zata turo mata Adamu driver ya kaita kafin a samu drivern da zai kaita. Idan kuma zata dinga tafiya da su Basma ne sai su na biyowa ɗaukarta inhar tanada lecture tare da su tunda makarantar tasu ɗaya ce.       Hakan yay mata, takumayi godiya sosai har sai da Anne ta ƙwaɓeta. Babu jimawa kuwa Malam Adamu yazo ɗaukar tata. Kasancewar securitys ɗin sun ganesa saboda yawan kawo family ɗin shugaban ƙasa da yake gidan yasa bai samu wata matsala ta shigaba. A ɓangaren Raudha shigar mutunci tayi dogon hijjab harda niƙaf, tafukan hanunta kawai kake iya gani hakan yasa bayan Mama ladi babu wanda yasan da fitarta.           Taji daɗin kasancewar ta a wannan makaranta da ta daɗe da fidda ran ganin kanta a ciki. Babban farin cikinta kuma department ɗinsu ɗaya da Rumaisa da Basma. Fadila ce kawai take daban dan abinda take karanta yanada banbanci da su Basma. Suturta jikinta ya matuƙar ɓoyeta ga kowa sai su Basma da suka sani. A nutse komanta ya gudana a wannan yani cikin kwanciyar hankali da farin ciki. Har a waya ta kira Asabe tai mata addu'ar fatan alkairi. Hakama M. Dauda ta kirashi sai dai Larai ta ɗaga cikin masifa tace baya nan. Ko jira su gaisa bataiba kuma ta kashe wayar. Murmushi kawai Raudha tayi dan halin matar baban nasu ba sabon abu bane a wajenta.       Ƙarfe huɗu da wasu mintuna su Basma suka kawota gida, sai dai basu shigoba suka juya. Yunwa takeji sosai dan har wani dishi-dishi take gani saboda ta fita ko karyawa batai ba. Kuma har taje ta dawo ruwa kawai tasan tasha. Sam batai tunanin samun Ramadhan a gida ba tunda tasan yana office, dan haka kai tsaye ta wuce ɗakinta. A daddafe ta watsa ruwa ta canja kayanta zuwa doguwar riga mara nauyi, sai hula data saka da Slippers ta fito. Ba komai a dining, ita kuma tacema mama ladi kar ai komai sai dare tunda itama bata gida hakama bilkisu. Taɗan riƙe ƙugu da hanunta dake riƙe da wayarta, ɗayan kuma tana murza goshinta dake mata ciwo ta ciki kaɗan-kaɗan tabbacin yunwa da rashin isashen barci na damunta.       Rasa inda zata kama ya sata kiran Mama ladi a waya ta sanar mata ta dawo. Sai kuma ta kai zaune cikin kujera cike da rashin ƙarfin jiki tana shafa ciki da ɓata fuska. dan da gaske yunwa takeji fa irin ta fita hankalin nan. Minti goma ba'a ƙulla ba sai ga mama ladi da basket na kayan abinci, ai tunkan ta ƙaraso inda take ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Wayyo mama gaskiya kina sona”.       Ƴar dariya mama ladi tayi tana ƙarasowa gareta. Cike da girmamawa ta ce, “Barka da dawowa ranki ya daɗe ai bansan kin shigoba wlhy”.      “Bamma jimaba mama, dan ko mintuna talatin bana zaton nayi, dan na fara wanka ne shiyyasa. Kamar kinsan da yunwa na dawo gidan”.        “Ai nasan za'a rina, tunda naga kun fita baki karyawar kirki ba. shiyyasa na tashi na haɗa miki wannan karki dawo ba'a kammala abincin dare ba”.      “Nagode sosai mama ALLAH ya saka da alkairi”.     Cike da jin daɗi mama ladi ta amsa mata. ta tsiyaya mata kunun tsamiya daketa ƙamshi dan ta fahimci Raudha naso sosai, zata zuba mata sauran abinci ta dakatar da ita. “Mama bara nasha wannan tukunna dai to”.      Cikin ƴar dariya mama ladi tace, “Yunwar dai bata kai ko'inaba ma kenan to”.      Dariya kawai Raudha tayi itama tana saka sugar. Mama ladi ta miƙe tana faɗin, “Bara na barki kici abinci naje kitchen muga mi za'a girka kar adalin shugabamu ya dawo da wuri. Amma mi za'a girka masa da kema kanki?”.         A cikin zuciya Raudha tace (shi wannan mina sani zaɓinsa inba nama da fura ba) a fili kam sai tace, ko tuwon alkama za'ai masa ne, sai a haɗa da farfesun kayan ciki asa yaji da ɗan yawa dan yana mura..... Kodaima mama ku jirani naci abincin zanzo kitchen ɗin kawai”.        “To shikenan a fito lafiya”.     A nutse Raudha ta cigaba da shan kununta hankalinta nakan wayarta tana karatun wani littafin hausa da Bilkisu ta tura mata. Bayi take ba, amma yanda Bilkisu ke zuga littafin ya sata fara dubawa shekaranjiya. Sai kuma kamar wasa labarin ya tafi da ita ta nutsu a karatunsa. Dan ita bama tasan bayan marubutan dake buga littafi ba akwai na online sai yanzu. Kodan bata da wayar ne shiyyasa. Kuma ko sanda suke hutawa bata damu da waya ba shiyyasa bata taɓa maida hankalinta ga nasu Fatisa ba, amma tasha jin suna sauraren littafi a waya ta zata na masu bugawa ne da ake karantawa a gidan redio.           Yunwa ce ta hana barcinsa tasiri shima. Duk da dai babu laifi ya ɗanyi tunda gashi har makara sallar la'asar yayi. Da ƙyar ya tashi zuwa toilet ya ɗan watsa ruwa duk da zazzaɓi dake jikinsa ga ciwon kai. A kallo guda zaka fahimci murar ta sake masa rugu-rugu dan saman hancinsa ya ƙara jaa sosai abinka da fari. Hakama idanunsa sun kumburo fiye da jiya fatarsu tai jajur. Ga shi dama baiyi wani barci isashe ba da daddare. Sama-sama ya shafa mai ya saka wando da riga masu ɗan kauri na kamfanin adidas harda hula a jikin rigar, sai dai bai ɗora hular a kansa ba ya saketa saman bayansa. Slippers ya zura cike da dauriya ya fito falon hannayensa duka a aljihun wandon, gara ya samu ko tea ya sha kozai samu nutsuwa ta wani ɓangaren. Tun daga nesa idonsa ke kanta, yayinda sam ita batasan dashi a wajen ba dan gaba ɗaya hankalinta ya tafine akan littafin da take karantawa mai suna *_SIYASA KO ƘABILANCI?_* na (marubuciya Bilyn Andull ƴar ƙasar Nigeria). Labarin ya matuƙar ɗaukar hankalinta saboda kamanceceniyarsa da tsarin da mijinta kamar yake kai a yanzun.         Tafiya yake a hankali kamar baya so, saboda rashin ƙwarin jiki harya iso inda take, ya kai zaune a kujerar 3seater ɗin da take zaune sam bata fargaba. Sai da ya kai kwance ya ɗaura kansa bisa cinyarta tai saurin ɗagowa a zabure dan tsabar firgitar ganin kan mutum bisa cinyarta a baza .        “Shut up!”. Ya faɗa da yanayin tsawatarwa ganin zatai ihu sai dai muryar a ɗashe take fita da sanyi-sanyin dushewarta a dalilin mura da damuwa. Hannu Raudha tai saurin ɗaurawa a bakinta, sai kuma ta lumshe idanunta zuciyarta sai lugude take a ƙirjinta kamar zata faɗo.        “Sai shegen tsoro”. Ya sake faɗa a hankali yana lumshe idanunsa da harɗe hannayensa a ƙirji ya miƙar da ƙafafunsa har bisa hannun kujerar da ƙyau. Raudha da sanin shi ɗinne baisa ta dai-daita ɗari bisa ɗari ba ta buɗe idanunta a hankali ta sauke bisa sumar kansa da ko ba'a faɗa ba kasan tana cin kuɗi kodan ƙyallin da takeyi duk da kasancewarta irin sumar baƙaƙen fata mai tauri da cika.       Cinyarta ta ɗan motsa cikin ɓata fuska, a ganinta adalilin miye wannan taɓara da zaizo ya kwanta mata cinya babu gaira babu dalili. Motsa ƙafafun nata ya sashi buɗe idanunsa sai suka shige cikin nata da take hararar masa kai. Da sauri ta kauda kanta gefe da gyara yanayin fuskarta tace, “Ina yini”.      Kamar koyaushe yanzun ma bai amsa ba, sai dai ya zare hanunsa guda daga saman ƙirji ya kamo haɓarta ya dawo da fuskarta yanda take. Cikin sake tsuke fuska ya ce, “Hararata kikeyi?”.       Idanu Raudha ta ɗan zaro. “Ka rufamin asiri, ni yazanyi na hahareka?”.      Kamar zaiyi magana sai kuma ya saki fuskar da maida hannayensa a ƙirji yana faɗin, “Inma kin hararenin ne iyakarki hararar, kuma duk matar dake harar mijinta dai kinsan aljanna sai dai ta gani dajin ƙamshi a maƙota”.........✍ *_🚶🏻🚶🏻🤣Da alama dai shugaban ƙasa Ramadhan ya koma wa'azi😂😜🤭_* *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account. *Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks. *Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku. A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant). -------- Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar: *Bank Transfer* *Airtime Transfer* Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance. *Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks. _Account No_ - *1220077999* _Account Name_ - *Arewa Books Publishers* _Bank_ - *Zenith Bank* Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din: Amount Paid: - Nawa aka tura? Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa Transferred time: - lokacin da aka turo Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi Deposit date: - ranar da aka turo Sai ayi SUBMIT. *Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar: MTN, 9Mobile Glo Airtel Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance. *WANNAN SHINE BAYANAN* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/1, 8:00 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62bd9379f0fb62def3120ded *_Episode 44_* .........Yanda yay maganar kamar bashiba yasa Raudha ɗan taɓe baki da marairaice fuska. “Ni dai tunda banyi ba ai Alhmdllhi”.       Bai tanka mata ba, sai dai ya sake buɗe idanu yana kallonta. Sosai zuciyarta ke gudu a ƙirjinta dan ta fahimci abinda yake kallon. (Oh ita Raudha taga takanta, mima ya kaita fitowa ba hijjab ko mayafi?) ta ayyana a zuciyarta a fili kamar zatai kuka.         “35, 32, 38... Uhhm da alama zaki iya....” Saurin buɗe ido tayi jin ta ɗan zama kanta na son ganin kuma mi yake ma lissafin numbers haka? Da cewa zata iya. Saurin son zame masa kai tayi a ƙafarta sai ya ɗan mintsini cinyarta. “Hi kokin manta sadaki na biya malama. Stay quite ko kiji a jikinki”.          Daina motsa ƙafafun tayi, sai dai tasa hannu ta kare ƙirjinta tana tura baki dan ta fahimci lissafin seize ɗinta na ƙirji, ciki, hips yake yi. Ji take inama ƙasa ta tsage ta shige kawai ta huta dan kunya. Ita kam al'amarinsa yanzu ya daina bata mamaki sai dai tsoro.         Ganin yanda ta kare ƙirjin nata ya sashi ɗan yamutsa fuska da taɓe baki. “Yarinyar nan anya kuwa bazaki lalatani ba. To banda son lalatani inda na dosa daban inda kika dosa daban tabbacin abinda ke ranki kenan”.              Ji Raudha tai mizai hana kawai ta saki kuka ta huta, kafin ta lalubo abinyi ya tashi zaune cike da ƙarfin hali yana gyara zamansa sosai a gefenta dab. Fuska a yamutse idonsa ƙyam a kanta yace, “Da alama yarinyar nan zaki tsufa da wuri, dan ƙiba zakiyi bata wasa ba mtsoww nidai an cucan..” ya ƙare maganar da ɗaukar kofin kunun da take sha. Zamansa ya gyara tamkar bashi ya gama zuba zancen ba ya kai kofin bakinsa bayan ya ƙarema abinda ke cikin kofin kallo ya fahimci kunun tsamiya ne da Anne nayi, kuma Alhmdllhi yana matuƙar son sa.           Yunƙurawa Raudha tai zata tashi dan ya gama dabaibaiyeta a cikin cakwakiyar kunya ya dakatar da ita. “Amma gaskiya baki da tausayi Ameenatu! Haka akace ki kula da miji idan baida lafiya!?...”       Yanda ya ƙarasa maganar da saki wata wahalalliyar atishawa da jin sunanta a bakinsa ya sakata dakatawa. Zuciyarta da ɗan fargaba ta dubesa dan tun dama yazo wajen ya fara magana da ɗumin dataji kamar a kansa daya ɗaura jikinta take tunanin yana lafiya kuwa? Sai dai tsokanar magana daya ɓige da mata yasata ture tunanin. Dubansa tai cikin ƙarfin hali, ganin yanda fuskarsa tai jaa musamman saman hancinsa, sai kuma idanunsa da ya buɗe suka haɗa ido suma sun sake koɗewa fiye da jiya alamar babu lafiya. Saurin kauda nata tayi tausayinsa na ɗarsuwa mata a rai, dan tun fil azal haka take da saurin jin tausayin mutum koda mugune (akwai lokacin da aka taɓa kama ɓarawo a makwaftansu, gashi dai itama haushinsa takeji saboda ya taɓa haurawa gidansu yay sata. Amma yanda aka dinga jibgarsa sai itama taita kuka tana roƙon a barsa ya tafi).       A bazata taji ya damƙi hanunta ya kai saman goshinsa da ya ɗauka zafi sosai har tanajin harbawar jijiyoyin wajen. Cikin tsoro da tausayinsa da ya bayya a cikin idanunta ta buɗe baki zatai magana sai dai ya rigata. Cikin taushi da sanyin murya da batasan yanada su ba.  “Ki bani abinci naci kiban magani”.         Tausayinsa sosai ya sake kamata. Cikin damuwa da sake sanyaya muryarta itama mai sauƙin faɗi tace, “Murance har yanzun?”.         Idanunsa daya ɗan maida ya lumshe ya sake buɗewa. Sai kuma ya kwanto kansa kan kafaɗarta yana faɗin, “Kin damu da nine balle ki sani? An baki amanata kin kasa riƙewa”. Nanma zafi taji jikinsa. Tai saurin rumtse idanu kunya na sake dabaibayeta da dariyar maganarsa (wai an bata amanarsa. Bama itace aka bashi amanarta ba) Tasan ya kamata tun a jiya data fahimci ya dawo da mura tabi shawarar Bilkisu na kai masa magani. Amma ganin kamar Bilkisu ta manta sai itama ta share batun dalilin abinda ya sake harmutsasu na faɗan ƙauyen Kauci. Dai-dai tana janye hanunta a goshinsa yace, “Kiramin Anne”.            A sanyaye tace, “Amma za'a tayar mata da hankali ai”.      Komai bai ceba ya ɗaura hanunsa saman cinyarta idanunsa a lumshe ya hau laluben wayarta. Saurin riƙe masa hannu tai a ɗan firgice jin yanda yake lalubeta kamar da gayya.         “Ki daina fassarani da abinda bashi nake nufi ba, ni waya nake nema”.        Duk da idonsa a rufe yay maganar hakan bai hana Raudha ƙyaɓe fuska ba da tsuke ta. Sai dai batace komai ba ta tura masa wayar ta dunguri hanunsa datai saurin saki a nata. Shima komai bai sake cewa ba ya ɗauka wayar ya ɗaura bisa hanunta. Murya babu wasa yace,       “Kiramin Anne”. Badan taso ba tabi umarninsa tai kira number Anne ɗin. Sau biyu tai wringing aka ɗaga, a hanunsa ta ɗora wayar dan ita kam bata san mizatace da Anne ɗin ba. Shima komai baice mata ba ya tashi da ga kafaɗarta ya kwantar da bayansa a kujerar yana kai wayar kunnensa. Dai-dai Anne na ambaton sunan Raudha cike da kulawa....        “Anneee!”. Ya kira sunanta cikin katseta. Ɗan jimm tayi kafin tace, “Ramadhan!”.      “Uhhyim” Ya amsa yana sakin atishawa cikin rashin ƙarfin jiki. A take Anne ta rikice, dama tun jiya ta tsargu a muryarsa da suna waya. Amma koda ta tambayesa sai ya nuna mata lafiyarsa ƙalau.        “Baka da lafiya ko! Haba Ramadhan abin nan kasa a ranka harya kwantar da kai haka?”.       “Anne cool down mura ne tun a uk nataho da shi”.    Sanin wahalar da shi da mura keyi ya saka Anne sake shiga damuwa. Cikin ƴar rikicewa tace “Haɗani da Aminatu”.         Maimakon bama Raudha da akace sai cayay “Anne ni dai kizo dan ALLAH, ko kuma na taho nan”.       Murmushi tayi mai sauti, ita kanta tasan badan raino irin na uwa taima Ramadhan ba tabbas a taɓare zai tashi. Sai dai batai sakancin masa rainon kaka ba ta tsaya kansa da tarbiyyarsa tamkar uwa, kai ko uwarsa batajin idan da a hanunta yake zai samu tarbiyya makamanciyar wadda yake a yanzu. “To naji bani Aminatu nace”.      Fuska ya tsuƙe yana ɗorama Raudha wayar a kunne sai kuma ya tashi zaune ya ɗauka kunun ya cigaba da sha badan yana masa daɗi a baki ba, saboda gaba daya baida appetite.  Gashi kuma yaji tasa sugar sai dai baiyi ƙarfi ba shiyyasa bai damu ba tunda yana ɗan sha wani lokacin duk da yana wahalar da shi idan akai rashin sa'a...          Cikin damuwa Anne take amsa gaisuwar Raudha. Kafin ta ɗora da roƙo akan Ramadhan ɗin. “Ameenatu kiyi haƙuri nasan bazaki barsa cikin ciwo ba amma dan ALLAH ki kula dashi sosai kinji. Ramadhan nada matuƙar rauni akan ciwo bai da juriya, ga rakin tsiya. Dan gaba ɗaya shafkewa yake tamkar yaron goye musamman mura da bata masa kamun wasa. Wajigasa take matuƙa ga wannan ma naji kamar ta masa ƙarfi sosai halan baisha ko magani ba tun jiyan?...”      Cikin ɗan in ina da kunya Raudha tace, “Eh Anne gaskiya inaga bai sha ba, dan yau tunda safe ya fita a gida”.        “Amma garin yaya haka ta kasance Aminatu?”.     “Uhm..uh...m Anne jiyanne ransa ɓace ya kwana saboda abinda ya faru a ƙauyan can, daga baya ma kulle kansa yay a ɗaki”.      Sosai Anne ta sauke numfashi mai nauyi tunda tasan halin kayanta idan ransa ya aɓaci. Alhmdllhi ma an samu canji bai sauke damuwar kan ƴar mutane ba, koda yake bawai komaine ke ɓata ran nasa ya aikata ba. Cikin katse tunanunta tace, “Ai mijin nan naki kam sai addu'a Aminatu, wani lokacin idan ya birkice tamkar mai iskoki a ka haka yake. Sai kinta haƙuri kinji. yanzu dai asamu kayan ƙamshi ai masa shayi da su citta ya fito sosai a ciki harda tafarnuwa. A abincin da yace yana so ma asaka yaji ya ɗan fito. Nasan sa da son wanka da ruwan sanyi ki hanashi, hakama ruwa mai sanyi karki bari yasha koda fura ne ko madara. Ruwan shansa ya zama da ɗan ɗumi haka, ƙafarsa ta kasance cikin safa. Yasha magani idan yaci abinci insha ALLAH zai taimaka masa hakan dan haka nake masa idan yana mura. Zuwa anjima zan kira, idan zazzaɓin bai sauka ba sai a turo Dr Shamsu.”           Raudha dake jin lisaafin kamar na ɗan goye ta jinjina kanta kamar tana a gaban Anne. “To Anne insha ALLAH yanzu duk za'ayi. ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana.”       “Amin Aminatu ALLAH ya saka miki da alkairi yay miki albarka.”     Cike dajin daɗi Raudha ta amsa mata kafin suyi sallama........            Wayar ta sauke da ga kunnenta tana sauke numfashi. Sai kuma taɗan kallesa ta maida kanta ƙasa da sauri ganin ita tsurama idanunsa kumburarru. “Mizaka ci to sai a girka kafin magrib insha ALLAH an kammala?”.        A hankali ya janye idanunsa a kanta batare da yasan ya shagala a kallonta ba tun tana waya da Anne. Shi kansa zuwa yanzu ya tabbatar yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce, sai kuma baijin zai..... Kasa ƙarasa abinda zuciyarsa ke son faɗa yayi badan yasan dalili ba. Cikin dasashshiyar muryarsa ya sake dubanta yana magana a hankali tamkar mai raɗa. “Koma miye ki dafa zanci”.      Kanta ta jinjina masa tana miƙewa. Ya bita da kallo harta nufi stairs. Sai da ta ɓacema idanunsa ya sauke numfashi da ƙyar yana ɗaukar remote ya canja television zuwa inda zaiga labaran shida na yamma.       Sanin maitarsa da nama ya saka Raudha haɗa masa farfesun da taimakon mama ladi. sai kunun gyaɗa, madarar shanu dake gidan ta tafasa itama ta juye masa a flask sai shayi. Aikin bai wani jasu da nisa ba tunda kaɗan iya cikinsa ne. Kuku kuma sukai sauran iya dai su dake sashen.        Da taimakon mama ladi ta hauro da kayan anata kiraye-kirayen sallar magriba. Ya tashi a falon, dan haka Raudha ta amshi sauran kayan hanun mama ladi tana mata godiya. Ɗakinsa ta nufa, tai knocking har uku bataji motsi ba, sai kawai ta tura ƙofar ta shiga da tunanin ko yana alwala. Ɗakin na nan tsaf yanda ta gyarashi da safe, sai dai duk ya watsar da kayan daya dawo office akan gado da ɗan stool ɗin jikin gadon zuwa ƙasan carpet. Kayan hanunta ta ajiye tana kwashe kayan, sai lokacin idonta ya sauka kansa a gado nannaɗe cikin bargo. Tausayi ya sake bata, ta ƙarasa ta gefesa, ɗan ranƙwafowa tai a ɗarare takai hannu taja bargon daya rufa har saman kansa, rawar sanyi ma taga kamar yanayi, yana ƙoƙarin ture hanunta da son hanata janye bargon sai hanun ya shiga cikin nashi, damƙewa yay da iya ɗan ƙarfinsa ya fisgota. Abinka da ba ƙarfi ɗaya ba sai gata gaba ɗayanta a kansa.         “Wayyo ALLAH na”. Ta faɗa cikin matse fuska saboda ƙirjinta daya bugi jikinsa, sauƙinma laushin bargon ya bata kariya sosai. Ƙoƙarin tashi take kamar zata fasa kuka, hakan ya bashi damar ɗaga bargon ya turata ciki. Rawa jikinta ya farayi, dan al'amarin yazo mata a bazata, ta shiga son fita da janye jikinta daya tura a nasa ya matse, duk da a halin ciwo da yake ciki hakan bai hanashi sauke ajiyar zuciya ba. Cikin rawar muryar da ke tabbatar da baida lafiya yake magana a kunenta cikin raɗa da sambatu na ciwo (Dan idan yana ciwo tofa akwai sambatu kamar su oh eh😂. bazan faɗi suna ba dai🤭 lol.)           “Anne sanyi nakeji ki ƙara min bargo, Anne kaina ciwo kamar zai fashe, wayyo Anne kaina jikina zafi Anne ko'ina ciwo”.        Dariya, tausayi, tsoro, mamaki, duk suka dira a zuciyar Raudha lokaci guda. Gata matse a jikinsa tamkar zai ɓalla mata ƙasusuwa ga zafin jikinsa na matuƙar ratsa nata jikin. Sosai ƙirjinta ke bada sautin fatt! Fat!! Da ƙarfi, da ace lafiya yake babu abinda zai hanashi da kiranta matsoraciya. Cikin rawar murya tace, “To ka bari na tashi na baka magani gashi magrib ma tayi”.        Jin muryarta saɓanin ta Anne da yake tsammanin ji ya ɗan buɗe ido, ba ganin fuskarta yake ba dan ya rufe musu har kai a bargon, “Kinada tausayi kuwa?”. Ya faɗa yana sake ƙanƙameta har saida tai ƴar ƙara saboda ƙirjinta. gaba ɗaya a birkice yake, “I'm sorry”. Ya sake faɗa a hankali cikin kunenta yana sassauta mata riƙon, sai kuma ya sake faɗin, “Kiyi shiru bana son magana kaina na ciwo”.        To yau dai Raudha taga takanta. Ɗan ƙwalisar nan Ramadhan mai shegen ɗaukar kan nanne haka. Shugaban ƙasar NAYA jinin Taura da ko kallon arziƙi sai ya gadamar wanda zai yimawa. UBANGIJI mai rahama, UBANGIJI mai jinƙai. Maiyin yanda yaso, ga wanda yaso. Cikin ƙanƙanin lokaci in yaso kamaka da ƙanƙanin abu sai ya firgitaka ka mance kai waye? Miye matsayinka?. Taja numfashi a hankali da shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa na REED. Zuwa yanzu ta nutsu a jikin nasa badan taso ba, babu abinda ke ratsata sai zafin jikinsa da sautin bugun zuciyarsa. Sai saukar numfashinsa a wahale. Magana yake a hankali bisa laɓɓa da bataji, sai dai tanajin alamar motsin bakinsa. Ta fahimci sambatune na ciwo kawai ke ɗawainiya da shi. Kusan mintuna talatin suka samu a haka, ganin lokacin salla na sake shigewa ta fara magana a hankali cike da lallashi.         “Lokacin salla nata sake nisa, ga abincin na kawo maka kuma da magani kayi haƙuri na tashi na baka kar mu makara salla”.        Sarai ya jita, dan idonsa biyu. Sai dai bai nuna alamar yajin ba har bayan shuɗewar wasu mintuna.        Da ƙyar Raudha ta samu ya rabu da ita ta tashi, toilet ta shiga tana sauke tagwayen ajiyar zuciya da taɓa jikinda da yay zafi kamar itama ta kamu da zazzaɓin. Ruwan ɗumi ta daidaitamsa domin yin alwala. Tayo tata sannan ta fito. Har yanzu yana cikin bargon ƙudundune. Cikin lallashi tace, “Ya Ramadhan ka daure kayi sallan sai kaci abincin da magani”. Kamar bazai motsa ba sai kuma taga ya miƙo mata hanunsa da ga cikin bargon, duk da kunya dake ɗawainiya da ita hakan bai hanata kamawa ba danta fahimci abinda yake buƙat kenan ta taimaka masa ya tashi. Da taimakon nata kuwa ya tashi, ganin kamar yana tangaɗi sai taƙi sakinsa sukaje ƙofar toilet, sai da taga ya shiga sannan ta sauke numfashi. Kasancewar akwai hijjab jikinta tasa abin salla tayi anan, tana raka'ar ƙarshe ya fito da alama ba alwalan kawai ya tsaya ba yayi wani uzirin nasa daban. A ɗayan abin sallar data saka masa ya tada sallar shima yana faman riƙe kai, kafin ya idan da sallar aka shiga kiran isha'i, hakan yasa Raudha komawa ta zauna domin gabatarwa.        Su dukansu sai da sukai salla har isha'i sannan ta haɗa masa abinci. abin mamaki yau yanka uku Ramadhan yaci na nama, sai romon farfesun kawai ya cigaba da sha. Raudha dake gulmarsa a zuciya ta shiga jinjina kai tana mamakin eh lallai magana ta girma kure na gudun nama yau. To ashe akwai ciwon da zai iya hana Ramadhan cin nama a duniyar nan?. Batace komai ba ganin ya ɗan sha ruwan kunun ya kuma sha romon nama. First aid box data gani a ɗakin ta ɗakko ta duba, cikin sa'a ta samu maganin mura data san yanada inganci tunda tasha amfani da shi itama. Da ƙyar ta samu yasha maganin yana yamutse fuska har yaso bata dariya, ta dai daure ta gimtse.      Koda ya koma saman gado da nufin kwanciya a ɗofane taɗan zauna. gadon da nufin gyara masa bargo kawai sai jitai ya ɗaura kansa a cinyarta, tare da riƙo hanunta yay filo da shi a kuncisa. Idanu Raudha ta ƙwalalo sai kuma ta ƙwaɓe fuska. Oho basai tanayi ba dan harya fara lumshe idanu, dole ta hakura da ƙudirin idan yayi barci ta zame jikinta ta gudu...........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/1, 8:00 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62bdf225f0fb62def3170d0f *_Episode 45_* ............Tun Raudha na irga sakanni harta koma mintuna, kamar wasa suka cinye rabin awa. Data yunƙura zata tashi Ramadhan zai sake ƙanƙame mata hannu, ga kansa bisa cinyarta. Fahimtar kamar barcin nasa baiyi nauyi ba yasata haƙuri ta sake bashi lokaci harda jingina da fuskar gadon, cikin rashin sa'a itama barci yay a won gaba da ita a wajen mai nauyi dan a gajiye take yau ga rashin barcin jiya cike da idonta dama.         A hankali ya fara buɗe idanunsa da sukai masa nauyi irin na mai farkawa a barci da rashin jin daɗin jiki. Alhmdllhi zazzaɓin ya jima da sauka. Hakama ciwon kan kaɗan-kaɗan yake jinsa shima yanada alaƙa da maganin murar da bai gama sakinsa ba dan barcine taf a idanunsa. Sabo da tashi sallar asuba akan lokacinta ya sashi farkawa. Hanunta da ke riƙe a nasa fuskarsa a kai ya ɗan tsurama ido, tun yana kallonsa dishi-dishi cikin ɗan hasken lamp har idonsa ya dai-daita. Zuciyarsa ce ta ɗan motsa na alamar mamaki, yay saurin ɗaga kai ya dubi sama. Itace kuwan da gaske, kuma akan cinyarta kansa yake. Ta ɗan zama kaɗan ta kwanta saɓanin da da take zaune. Sai dai a kallo ɗaya ya fahimci kwanciyar batai mata daɗi dan a matuƙar takure take a wajen.        Idanunsa ya dafe tare da cije haƙoransa ya tura yatsun hanunsa cikin sumar kansa. ‘Ya ALLAH’ ya faɗa a hankali cike da jin haushin kansa. Dan ya gama fahimtar lallai anyi abun kunya a daren jiya. Inhar irin sambatun daya san yanama Anne idan yana zazzaɓi yay mata itama to shikan dai yagama ganin takansa, raini kuma tsakaninsa da yarinyarnan ya samu gurbin zama. ‘Ni Ramadhan miya shiga kaina ne wai?’.       Ya sake faɗa a fili lokacin da yake tashi zaune hanunsa dafe yaɗan karkata yana kallonta. Duk da takaicin kansa da yake ji hakan bai hanashin jin tausayinta ba. Shi kansa ya sani idan shine bazai iya juriyar kwanciya haka ba dan kawai wani yaji daɗi shi. Jin za'a tada salla ya sashi miƙewa ya sakko a gadon da ƙyar, sai da Raudha ta tabbatar ya shiga bayin sannan ta buɗe ido a hankali. Tun motsawarsa itama ta farka, ta ɗaga hanunta da yay matuƙar tsami da ƙyar taɗan yarfar, wani irin azaba ya ratsata. Saurin riƙewa tai da ɗayan tana cije baki. Da ƙyar ta iya tashi dan kafaɗarta zuwa wuya suma duk a riken suke.          Cikin dauriya ta fita a ɗakin zuwa nata dan shima taji motsin ruwa alamar wanka yake. Itama da gasa jikinta ta fara, duk da ba saki hanun da wuyan sukai ba haka ta daure bayan idar da salla ta nufi kitchen. Tunda ta fito ma'aikatan gidan daketa fitowa domin tsaftace sashen ke zubewa suna gaisheta. Babu sa'anta a cikinsu, ta tabbatar kuma ko'a ilimi sun fita, dan haka take matuƙar jin nauyin wannan girmamawa da suke mata. Sai dai tana dauriyar dannewa da amsa musu a dake dan wani girman idan ALLAH ya baka dole kai haƙuri ka riƙe.         A kicin ɗin ma duk zubewa su kuku sukai suna gaisheta, sukam har sun tsaftace ko'ina sunama ƙoƙarin fara ɗora abinci ne. Tambayar mi zasu dafa tayi, suka sanar mata. Babu abinda ya kwanta mata da yanayin mara lafiya, dan haka tace suyi iya wanda za'aci kawai. Ita kuma ta fara ƙoƙarin haɗama Ramadhan da taimakon Agnes da ita kaɗaice kuku mace a cikinsu. Haka kawai nutsuwar Agnes ɗin ke burgeta. Gata dai ba muslma ba amma bata da rawan kai, kuma bazaka taɓa ganinta da shigar banza ba. Haka farce da ƙarin gashi duk bata sakawa.        Komai suke Agnes a girmame take tayata duk da ta girmeta sosai, amma tsabar girmamawa Mommy take kiran Raudha. Tsaf suka kammala komai, Raudha zata ɗauka basket ɗin Agnes ɗin tai saurin ɗauka cike da girmamawa. “No Mummy zan ɗauka”.      Cikin ɗan Murmushi Raudha tai gaba dan bata son gwasale Agnes ɗin. A tare suka haura saman, Agnes zata nufi dining Raudha ta dakatar da ita ta amsa da mata sannu. Kai tsaye ɗakin Ramadhan ta nufa, haka kawai murmushi ya suɓuce mata tunawa da abinda ya faru jiya dama abinda taji yana faɗa ɗazun, ta gama fahimtar baya ƙaunar raini sam. A zuciyarta take faɗin (karka damu, indai Aminatu ce har abada babu raini tsakaninmu).       A fili kam sai tai knocking ƙofar kaɗan dayin sallama. Bataji an amsaba sai kawai ta tura ƙofar tana ƙarayi. Duk abinda take yana kwance yana jinta, sai dai yay luf fuska a tamke dan kawai yasan tunda har jiya yay abun kunya ta gama samun hanyar rainasa. Raudha har zuciya bata kawo lanbo yay mata ba. Ta ajiye basket ɗin ta fita.         Da kallo ya bita harta fice.    ★★Sai da ta kammala shirinta na fita tsaf cikin kayan mutunci sannan ta fito tare da kulle ɗakinta dan tasan a koda yaushe su Lubnah zasu iya dawowa gidan. Koda ta koma ɗakinsa ta iskesa still kwance sai jikinta yay sanyi, duk zumuɗinta na son tafiya makarantar kuma sai ya fita mata a kai. Ajiye bag ɗinta da hijjab tai ta nufi toilet, tsaftacesa tai ta fito ɗakin shima ta gyara iya inda bazata takura masa ba. Daga haka ta ɗauka bag ɗinta ta koma ɗakinta dan ta haƙura da makarantar kawai tunda shima bazai fita ba.        Acan waje tuni securitys ɗinta da jiya ta gudumawa suna falon ƙasa suna jiran fitowarta. Hakama driver ya shirya tun da wuri dan gani suke jiya sakacinsu ne ya sata fita a gidan badasu ba. Basma ta kira ta sanarwa yau bazata shigo school ba. Daga baya sa nuna mata abinda aka kawai. Bata bama Basma damar yin ƙorafi ba ta kashe wayar gaba ɗaya itama ta kwanta, dama barcine taf a idonta ga ciwon da jikinta ke mata akan kwanciyar jiya.               Tunda cos ya ga takwas ta wuce shugaban ƙasa bai fitoba yasan murar jiya ta kwantar da shi kenan. Saƙo ya tura masa kawai ya cigaba da abinda ya dace dan Alhmdllhi ma yau abubuwan da Ramadhan ɗin zaiyi duk ba masu tsawwalawa bane. Zaman meeting ne sau kusan huɗu duka kuma an riga an tsara wanda zasuyi zaman. Abinda yake tilas saka hannu ne akan wasu takardu. _______________________________           Tunda su Basma ke bada labarin Raudha ta fara karatu a school ɗinsu zuciyarta ke a ƙuntace. Lallai ta sake tabbatarwa ɗanta baya tare da ita. Komai daya shafesa sai dai taji a shanun ƴan talla. Tana cikin wannan yanayi Mardiyya tazo gidan, ɗiyarta ta biyu dake bin Ramadhan. Daga office take taga ya dace ta biyo ta gaishesu dan rabonta da gidan tun bikin Ramadhan ɗin. Haka take ita bata da kwaramniya, ga haƙuri. Lokuta da dama mutanen gidan kan ɗauketa wadda bata ɗaukar abu serious, sai dai kuma ba haka bane. Ita irin mutanen nan ne da babu ruwansu da shiga sabgar daba tasu ba, muguwar ƴar I don't care ce ta bugawa a jarida. Halayyarta ya saka bata wani shiri na'azo a gani da Gimbiya Su'adah. Yaranta huɗu, tare da mijinta suke aiki a companyn su na kansu da sukai haɗin gwiwar ginawa ita da shi. Ba ƙaramin bala'i a lokacin taci ga Gimbiya Su'adah ba. Amma tai fumfurus ta shareta. Da farko robobi companyn ke fitarwa, a hankali abubuwa suka kara bunƙasa takai har designes na wasu abubuwan daya shafi kayan kitchen suna sarrafawa. Kamar wasa sai gasu sun bunƙasa suma ana kwatantasu a jerin manyan kamfanoni dake sarrafa abubuwa masu muhimmanci a ƙasar.         “Maah! Lafiya kuwa naga kamar ranki a ɓace?”.    Duk da tasan halin ɗiyar tata na rashin ɗaukar abu da muhimmanci hakan bai hanata fara zayyane mata cikinta ba rai ɓace.             “Miyema bai faruba Mardiyya. Yanzu a duniyar nan babu abinda ke cimun rai da ƙonan zuciya sama da auren ɗan uwanku. Na tsani yarinyarnan da duk wani mai alaƙa da ita a duniya. Ji nake zan iya kasheta da hannnuna wlhy.....”       “Wa'iyazubillah Maah miya kawo wannan maganar haka?”. Mardiyya tai saurin katseta.        “Humm Mardiyya kenan, yanzu ke tunda kike a duniya kin taɓa jin matar shugaban ƙasa mai shekara sha takwas? Jahila da ko karatun sakandire banajin ta kammala? Daɗin daɗawa ƴar karuwai marasa tarbiyya da kowa yasan aikinsu a bayyane yake.” hawaye suka silalo mata, ta kai hannu ta share da cigaba da faɗin, “Mardiyya na tabbatar a ƙuntace Ramadhan yake, biyayyar da yakema kakanninku ce kawai ta sakashi haƙura ya amshi raunanniyar yarinyar nan, wai dan takaici sai yanzu take shiga jami'a. Matar shugaban ƙasa fa daya kamata ta zama vary educational, wayayya ta nunawa a duniya, wadda duk inda tasa ƙafa zata fiddashi a kunya muma ta fiddamu. ALLAH dai ya tsinema wannan aure na Ramadhan albar.......”        “Haba dan girman ALLAH Maah wane irin furicine haka babu daɗin ji. Idan kin tsinema auren Brother tamkar shi kika tsinemawa dan zata iya yuwuwa yanzu haka an samu rabo tsakaninsu. Maah ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, ni wlhy banga wani aibu ga yarinyarnan ba. Inma iyayenta sunada wancan halin ai ba itace kedashi ba. ALLAH kuma yana fidda rayayye a cikin matacce, ya fidda matacce a cikin rayayye. Karatu ko karancin shekarunta normal ne ni a wajena. Miye amfanin ya auri wayayyar mai ilimin tazo ta zame masa damuwa shi da mulkin nasa damu kammu. Yanzu ko shi zai bama matarsa tarbiyyar data dace akan tsarin mulkinsa ta tashi akai kuma yay alfahari anan gaba Maah. Dan ALLAH ki cirema kanki damuwar nan ki musu addu'a sai kiga wataran komai ya zama yanda kike so. Kwana nawane zata kammala karatun ma, ina amfanin ya auri sa'arsa tazo ta rigashi tsufa........”      Hannu Gimbiya Su'adah ta ɗaga mata a fusace. Cikin zafin rai ta nuna mata ƙofar fita. “Tashi ki fitarmin kafin na saɓa miki Mardiyya. Nama manta tare nake da mara kishin kanta balle waninta. Shasha kawai da batasan abinda ke mata ciwo ba”.       Miƙewa Mardiyya tai ta ɗauka bag dinta da faɗin, “ALLAH ya huci zuciyarki Maah, amma nidai gaskiya na gaya miki, ita rayuwa bata da tabbas. Banga kuma aibun yarinyarnan ba, hasalima yanda take da ƙarancin shekaru idan kika jata a jiki zakisha mamakin ribar da zaki samu akan shi kansa Ramadhan ɗin da kike ganin kamar an nisantaki da shi. Ni na wuce dama zuwa nai na dubaku tunda ban samu shigowa gidan ba koda babbar salla”.       Ko kallonta Gimbiya Su'adah bata sakeyi ba. Itama saita fice a ranta tana nemawa mahaifiyar tasu shiriyar ALLAH da fatan ganewa. Dan tuni ta fahimci Adda Asmah na ɗaya daga cikin masu rikita lissafinta akoda yaushe. Su kansu wani lokacin haɗata ake dasu taita zuba musu tujara kamar ba ita ta haifesu ba.      Waɗan nan maganganu na Mardiyya sun sake harzuƙa gimbiya su'adah. Rai ɓace ta shirya bayan sallar zuhur ta nufi sashen Anne. Abinda takan haɗa kwanaki huɗu batai ba. Dan gaida surukai kullum baya cikin tsarinta duk da gida ɗaya suke rayuwa. Anne tayi mamakin zuwan nata amma sai ta danne ta tarbeta kamar yanda suka saba. Babu wani ɓoye-ɓoye gimbiya Su'adah ta sanarma Anne abinda ke a ranta.      Murmushi kawai Anne keyi jin bayanin surukar tata. Ita bazata hanata zartar da hukuncin aurawa Ramadhan wata matarba, sai dai bazata amince a cutar mata da jika ba dan ita kanta ta jima da fahimtar wacece Adda Asmah.       “Shike nan kije zan samu Dattijo da batun, zai kuma nema Ramadhan ɗin yaji tabakinsa. Idan ya amince da auren mu masu murna da farin cikine akan hakan. Fatanmu ALLAH ya basu zaman lafiya kawai.”          Duk da ranta ya ƙara ɓaci sai ta amsa da amin. Ta fice zuciyarta na ayyana mata maganin Ramadhan da zatayi. Dan bazata taɓa yarda ya nunama kakaninsa baya son auren ba. Tasan yana bijirewa shikenan bazasu bata goyon baya ba. *__,,,,___________,,,,__*          Barci ya sake sha sosai har wajen sha ɗaya. Ring ɗin wayarsace ma ta tilasta masa buɗe idanu da ƙyar. Ido a rufe ya kai hannu a side drawer da nufin kashe wayar sautin ring ɗin ya hanashi hakan dan yasan Maah ce. Komai bai kawo ransa ba sai tunanin taji baida lafiya maybe. Ya buɗe ido da ƙyar yay picking yana kaiwa kunnensa.         “Barka da asiba Maah!”. Gaban Gimbiya Su'adah ne ya faɗi, tai saurin cire wayar a kunenta tana kallo.....      “Maahhh!”. Daya sake faɗa cike da kasala da barci ya sakata gaskata zarginta. Da sauri ta latse wayar ta kasheta gaba ɗaya kanta na juya mata. (Har ita Ramadhan zai amsawa waya yana tare da mace. Innalillahi..... Shikenan yaronta ya gama watsewa hanun jikar karuwai).....       A ɓangaren Ramadhan kuwa tunanin network ne ya sashi sake dialing number ɗin tata da ƙyar yana kaiwa kunne da lumshe idanu. Sai dai switch up ma ake sanar masa. Yanayin rashin ƙarfin jikin har yanzu ya sashi ajiye wayar kawai da tunanin zuwa anjima zai nemeta. Sai dai ya sake jan ƴan mintunan a kwance kafin ya tashi zuwa bayi, sosai yunwa yakeji na ci masa hanji, badan haka ba baya tunanin zai iya tashi yanzun.         Shigarsa wankan baifi da mintuna biyu ba Raudha ta shigo hanunta ɗauke littafin data rubuta lecture ɗin jiya tana ɗan bitar abubuwan da bata fahimta ba, dama tun ɗazun take zaryar dubashi da ga falo zuwa bedroom ɗin. Jin motsin ruwa a bayi ya sata yanke shawarar gyara ɗakin a gaggauce ta fice kafin ya fito. Littafin ta ajiye a stool ɗin mirror batare data rufe ba. Cikin rashin sa'a tana tsaka da gyara kayan saman mirror ɗinsa dake a wargaje ya fito. Sosai ta diririce, tai azamar juya masa baya zuciyarta na luguden daka....          Duk abinda tai akan idonsa ne, har yayi kamar zai basar yanda ya saba sai kuma ya canja shawara. Inda take ya cigaba da takawa yana goge sumarsa da ruwa yaɗan taɓa kaɗan zuwa gefen wuyansa da kunne. Cak ya  tsaya sakamakon idanunsa da suka sauka akan littafin nata, ya ƙurama hand writing ɗin ido zuciyarsa na wani irin zillo, hatta da numfashinsa sizing yake wajen fita daga ƙirjinsa.....           Jin kamar tsayuwar mutum a kanta ya sata saurin juyowa saboda tsorata, dan bataji motsin ƙarasowarsa inda take ba. Yunƙurin barin ɗakin tai gaba ɗaya taji ya cafko hanunta tare da fisgota ta dawo baya, gaba ɗayanta ta faɗa masa har ɗayan hannunta na ƙoƙarin sauka akan ƙirjinsa dake nason ruwa. Ido ta rumtse da ƙarfi da son ɗage hannunta ta tokare tsakkiyarsu, sai hakan ya taimaka mata bata faɗa masa jiki gaba ɗaya ba. Sai dai kuma a bazata da tai niyyar jan jikinta baya cikin in..ina tana faɗin, “I'm sorry”.       Har yanzu idanunsa akan littafin suke, sorry data ambata ne ya dawo da zuciyarsa gareta, dan ya lula duniyar wani tunani daban, kamar yanda ya taɓa mata lokacin da ƴan gidansu sukazo dubasa ya ƙara matso da ita jikinsa dan bai saki hanunba dama. Mannata yay da jikin nasa duk da taƙi janye hanun nata. Kamar zata fasa kuka ta sake buɗe baki zatai magana dan ita hankalinta bai kai akan abinda yakema kallon ƙurulla ba saboda a rikice take...           ‘Shiyyy!!’ Ya faɗa yana maido idanunsa kanta da manna bayanta da jikin mirror. Kumburarrun idanunsa dake baibaye da mura ya sauke akan face ɗinta, ganin lips nata na rawa alamar sonyin magana ya girgiza mata kansa. Sake rintse idanu tai da ƙarfi. Murmushi ya saki mai ƙayatarwa idanunsa na cigaba da bin fuskarta da kallo, haka kawai yake shiga nishaɗi idan ya ganta a yanayin tsoron nan.         “Hy! Buɗe idonki”.     Yay maganar a dake kamar ba shi ya gama murmushi ba.     “Dan ALLAH kayi haƙuri..” Raudha ta faɗa cikin tsananin taraddadi kamar zatai kuka.               Sake matsar da fuskarsa yay gab da tata yana busa mata numfashinsa. Cikin wata iriyar muryar da badan a gabanta yake ba zata rantse bashi bane ya cigaba da magana.           “Kinsan ALLAH idan baki buɗe kin kalleni ba zan baki mamaki yau, ba ruwana da Ustazancin ki kaca-kaca zan miki”...........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*     [7/1, 8:00 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62be031cf0fb62def317f52f *_Episode 46_* ............So take tabi umarninsa ta buɗe amma ta tabbatar bazata iya kallonsa ba riga ba. Sai tayi kamar zata buɗe sai ta maida ta rumtse da ƙarfin tsiya. Tayi haka kusan 3times amma ta kasa. Cike da mugunta ya saki murmushi yana saka hanunsa guda ya janye nata data tokaresa da shi.      Wani irin ƙuuuu! Cikin Raudha ya bada sautin da har Ramadhan sai da yaji lokacin da taji saukar lips nashi akan nata daketa ƙyallin lipsgloss mai ƙamshin strowbarry. Shi kam da yayi da niyyar tsokana duk yanda yaso janye nasa lips ɗin sai yaji bazai iya ba, cikin rashin ƙarfin jikin da ke tare da shi ya sake manneta da mirror ɗin tare da rumtse ɗayan hanunta dake cikin nasa ya manne jikinsu waje guda yanda har numfashinsu ke fita da ƙyar....          Ya riga ya mata matsewar da rawar jikin nata ma baya tasiri, sai zuciyarta dake mugun gudu a ƙirjinta har yana iya jiyowa. Randa su Anne sukazo yayi kissing nata sai dai ba irin na yau ba. Na yau babu sassauci, kai tsayene, cike da salon daya sata shagala tuni tsoronta ya gudu saƙonsa ya fara shigarta ɓargo da jini. Itama tanada lafiya, duk da abinda takeji sabo ne gangar jikinta bataƙi amsaba, dan ta kai shekarun da zata iya buƙatarsa. Sai dai rashin sabo ya sake tabbatar da ruɗaninta, dan lokacin daya janye bakinsa kasa tsaiwa tai a kan ƙafafunta. Babu shiri ta sake ƙanƙamesa. Bazata iya ɗagowa ta kallesa ba, sannan ƙafafunta ma bazasu iya tsayawa akaran kansu ba, dan jikinta babu abinda yakeyi sai mazari.        Duka hannayensa biyu ya dafe kan mirror ɗin da suke jingine, kansa na bisa kafaɗarta, idanunsa duka a rufe suke saboda abinda ke faruwa a cikin nasa jikin. Lallai yasan ya takaloma kansa, ya kira ruwa yau. Yana zaman-zamansa da lallaɓa yanayinsa gashi nan ya takaloma kansa ruwa wajen neman tsokanarta ya tsokanoma kansa abinda ke kwance shekara da shekaru.        Sunayen ALLAH ya shiga ambata a zuciyarsa da son janye jikinsa da sauri, sai dai Raudha data dabaibayesa sam ta hana yuwuwar hakan garesa. Sai ma ƙara ƙanƙamesa tai dan bata fatan ya ganta a yanayin da take. Sake gwada janyewa yay itama ta sake ƙanƙamesa. Dole ta sashi buɗe ido yana kallon kansa da bayanta ta cikin mirror. Murmushi ne ya suɓuce masa, sake duban idanunsa da suka kaɗa sukai jajur yayi alamar fitinace kwance a cikinsu. Hannunsa ɗaya ya ɗaga da jikin miron ya kaisa kanta ya ture hular data saka, a take gashinta dake ɗaure ya bayyana. Yatsunsa ya tura ciki baki ɗaya ribbon ɗin ta fice duka.       Babu abinda ke fita a bakin Raudha sai kalmar innalillahi.... Har ƙarshe, ga hawayenta na zarya a kan ƙirjinsa. Murmushi ya saki da sake yamutsa gashin nata da yakeji kamar su yini yana wasa da shi. Cikin wata irin shaƙaƙƙiyar murya da bata taɓa cin karon ji da ga garesa ba ya fara magana... “Ustaza wannan ba mafita bace, idan kika bari naje matakin ƙarshe sam bazan saurarekiba sai na tabbatar da sadakina bisa kanki yanzun nan harda ribar baby insha ALLAH..”         Baima kai ƙarshe ba tai saurin sakinsa da son tureshi, sai dai hakan bamai yuwuwa ba, dan duk da halin da yake ciki ai goma tafi biyar albarka. Yanda tai ɗin ya bashi dariya, sai dai halin da yake ciki bana dariyar bane, yayi imani kuma da inhar aka cigaba da kasancewa a haka babu makawa a yanzun nan bazai iya ƙyale yarinyarnan ba, duk da ƙoƙarinsa na son yin hakan. Kaɗan ya matsa ta samu hanya, ai da gudunta ta fita har tana bigewa da ƙofa.... Shima zaune ya kai jagwab saman stool ɗin mirror bayan ya ɗauke book ɗinta dake a wajen. Ya dafe kansa zuciyarsa na matuƙar gudu kamar zata fito... (Mike damunka Ramadhan? Mikaje ka takaloma kanka wajen shegen tsokale-tsokalen neman ayi?) a zuciyarsa yake maganar, sai dai sam babu nadamar abinda yay tattare da shi. Sai ma a fili daya furta ‘Oh Ramadhan ka lalace, da sa'ar autarku kake wannan abun ko kunya babu.’        Sai kuma murmushi ya suɓuce masa, ya kai hannu a wuyansa, “Ni Ramadhana zazzaɓin ma ya dawo” yay maganar a marairaice yana wani langaɓe kai gefe cike da tausayin kansa.... Tuna abinda ya gani ya sashi saurin juyawa ga mirror ɗin, book ɗinta ya ɗauka ya buɗe, sai kuma ya miƙe yana bin rubutun da kallo. “Kai ina..” ya faɗa a fili yana girgiza kansa da miƙewa riƙe da littafin. Bakin gado ya koma, ya ɗauka ɗaya daga cikin wayoyinsa yay snapping rubutun, littafin ya ajiye ya cigaba da danne-dannensa. Tsahon mintuna biyu ya kai wayar kunensa.          Daga can cikin tsokana Bappi yace, “Ɗan gatan ALLAH ka warke kenan?”.       Murmushi yay yana sake ƙoƙarin control ɗin halin da yake ciki. “Oh Bappi nida nake kwance cikin ciwo kake kira ɗan gata?”.          Dariya Bappi ya karayi daga can. “Ɗan gatane mana tunda ciwon naka na ƴan gatane. Bakaji bahaushe yace _mura ciwon ɗan gata ba_”.          Dariya sosai shima Ramadhan ya sanya a wannan gaɓar Bappin na tayasa. Sai da suka nutsu Ramadhan ya fara magana serious. “Bappi wani abune ya ɗan rikitani yanzun nan. Amma na turo maka saƙo ta email ka duba yanzu dan mu tabbatar”.        Bappi ma daya koma serious ɗin yace, “To ALLAH yasa dai lafiya?”.          “Lafiya lau Bappi duba dai”. Bayan kamar mintuna uku sai ga kiran Bappi ya shigo, lokacin yana ƙoƙarin saka kaya a jikinsa. Dakatawa yay ya ɗaga wayar. “Ramadhan ina ka samu wannan hand writing ɗin?”.        “Iri ɗaya ne ko bappi?”. Ramadhan ya amsa tambaya da tambaya. Daga can Bappi yace, “Tabbas babu wani babbanci, kenan wanda ya turo takardar nan kamar yanda mukai hasashe yanada kusanci damu?”.         “Bappi kasan rubutun waye kuwa?”.      “Shi na ƙagu naji Ramadhan ”. “Ameenatu!”.     “Aminatu? Kana nufin Aminatu dai matarka?!”.         “Ita kuwa Bappi. Yanzu naci karo da shi a book ɗinta na makaranta, shiyyasa gaba ɗaya kaina ya kasa ɗauka nima dan na shiga ruɗani”.      “Uhhm to kaga wannan maganar bata nan bace ba, idan ka fita office gobe idan ALLAH ya kaimu zanzo kawai”.        “Bappi na sameka a gida mana anjima”.     “No Ramadhan akwai haɗari. Satar fitarka tayi yawa, ina tsoron magauta su fara fahimta su cutar da kai ta wannan hanyar. Dolene ka canja takunka”.     Fuska ya ɓata, dan gaskiya akace bazai dinga zuwa gidansu akai-akaiba an cutar da shi. Wannan takura har ina dan ALLAH.          ★Hajjaju Raudha kam tunda ta fice tana can ɗaki duƙunƙune a bargo. Ji take kamar ta tona tsakkiyar gidan kawai ta shige ta huta. Bawai bata san minene aure ba, domin tanada zurfi a ilimin addininta, shiko musilinci ya fiddo mana komai dangane da aure cikin hikima da rahamar UBANGIJI. Matsalar kawai shine komai yana zuwa mata baƙo ne. Bata saba ba, bata taɓa gani anayi ba. Bata karatun littafi sai ranar da Bilkisu ta bata, ko karatun tanayine cike da kunyar wasu wajajen idan tazo a lokacin. Gidansu na hutawa ko tv babu, wama yake da lokacin zaman kallo, yo fitinar Abbansu ma tasa idan rashin kuɗi ya ciyosa ya kwashe ya siyar kona wacece a gidan babu ubanda ya isa yace wani abu kuma. Bata da tarkacen ƙawaye, idan ma kika kasance mai rawar kai a aji bata shiga harkarki, sannan bata zaman fira in group daga boko har islamiyya, hasalima faɗa takema su Safara'u idan taga sunayi. Tasan dole ne ta shiga ruɗani da sabon yanayin da Ramadhan ke son jefasu a tsakanin nan. A wani bangaren kuma tanada gaskiyarta akan shiga ruɗani. Tun farko ta sakama ranta Ramadhan yafi ƙarfinta. Shima kansa ya tabbatar mata yafi ƙarfin nata. Mahaifiyarsa da danginsa harma da mutanen duniya sun tabbatar. A baya babu abinda take gani a cikin idanunsa sai saɓanin abinda take gani a yanzun, duk da dai harga ALLAH tasan bai taɓa muzantata da baki ba, bai taɓa hantararta ko wulaƙantata ba, kawai dai baya shiga sabgarta. Dolene canjawarsa a ƙanƙanin lokaci ta zama abu mai rikitarwa a gareta. Amma tayi alƙawarin hakan bazaisa ta taɓa saɓama umarni ko hani daga garesaba, zatai masa biyayya matsayinsa na miji inhar bai hau turbar sabama ALLAH ba. Zata yi biyayya ga umarnin UBANGIJI akan binyayya ga miji da dokokin aure kodan tabbatar da martabar tarbiyyarta data gidansu a idanunsa saɓanin wadda aka sanar masa da wadda duniya take kallon ahalinta dana iyayenta da shi......       Ƙarar landline ɗin ɗakin ta katse mata tunaninta, gabanta ya faɗi. Sai dai tunanin ko Mama Ladi ne ya sata buɗe kanta a bargon ta ɗaga.        “Ustazah! Haka aka koya muki kula da mijinne wai a islamiyyar?”.        Batama san bakinta ya suɓuceba wajen faɗin, “Wlhy Yaya Ramadhan zaka kasheni da raina!”.         Murmushi yay daga can, “Idan na kasheki Ustazah dawa zanyi angwancin?”.        “Na shiga uku”. Dariyar da batasan ya iyaba ya ƙyalƙyale da ita daga can. Tasa hannu ta rufe fuska tamkar tana gabansa. A zuciyarta ɗunbin mamaki da al'ajab ne danƙare. (Dama haka yake kokuwa yanzune ya canja.....?)      “Ina jiranki kizo ki bani abinci kar yunwa ta hallakani ga ciwo”. Ya faɗa cikin katse mata tunani yana yanke wayar.                  Baki buɗe Ramadhan dake zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya lap-top a cinyarsa alamar aiki yake ya saki yana kallon Raudha data shigo bayan tayi knocking ya bata izinin shigowa. (Lallai yarinyar nan kanta da motsi) ya ambata a ransa yana ɗauke idonsa gareta. Sanye yake cikin kaya masu taushi baƙaƙe. Duk da badan kwalliya ya saka ba sun masa ƙyau da sake fiddo hasken fatarsa. Idanunsa dake cike da abubuwa kashi-kashi ya janye yana maidawa ga aikin gabansa.         Gabansa Raudha ta ƙaraso bayan ta ɗakko basket abincin data shirya masa tun ɗazun, komai a cooler yake dan haka bata tunanin sun huce. Table ɗin ta kalla inda ƙafarsace fara tas a miƙe, ganinta da abincin kuma baisa ya sauke ba. Kallonsa taɗan sata a ranta tana gulmarsa ganin yanda ya tsuke fuska tamkar bashi ya gama mata abun kunya ɗazun ba (Humm da gaske mutumin nan dai yanada aljanu). A fili kam sai cewa tai “Ga abincin”.      Banza yay mata kamar baiji ba. Ta sake maimaitawa cikin marairaice fuskarta dake cikin niƙab data sako. Ganin yaƙi nuna yasan da zamanta a wajen sai takai durƙushe a gabansa tana dire basket ɗin a ƙasa. “Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy tsoro naji ɗazu ɗin”.      Nanma banza yay mata yana cigaba da sarrafa keyboard ɗin lap-top ɗinsa hankali kwance. Sai dai ya fahimci maganar tata nada alaƙa da tunanin gudun datai ɗazun ne.        “Dan ALLAH!”. Ta sake faɗa a hankali. Idanunsa da har yanzu jan yaƙi kwaranyewa a cikinsu ya ɗan rumtse, ga mura ga fitina da yaketa ƙoƙarin haɗiyewa taƙi hadiyuwa. Iska ya ɗan furzar dakai hanunsa saman goshi ya shafa, tunda tace ALLAH kuma ta gama da shi. Amma hakan bai hanashi yin magana a daƙile ba.        “Dan kin rainani ni zakizoma da wannan abun a fuska?!”.    (Oh ALLAH, dama akan niƙaff ne?) ta faɗa a zuciyarta tana lumshe ido. A fili kam hannayenta ta matse waje guda. Cikin sanyin muryarta dake tsumashi batun yau ba tace, “Dan ALLAH kayi haƙuri ALLAH kunyarka nakeji”.          (Kunya) ya maimaita kalmar a ransa yana ɗan bubbuga yatsansa bisa lips ɗinsa idonsa a kanta. “Okay! Naji ciresa to, inba hakaba kuma ni bashi zan cire ba, wancan zan cire”.        Kukane kawai ya ragema Raudha ta fashe da shi. Mutumin nan so yake kawai ya zautar da ita a gidan nan, dan sarai ta fahimci abinda yake nufin zai cire. Babu yanda ta iya dole takai hannu tana kwance niƙaff ɗin sai dai ta rumtse idanunta... Hararta yay ya ɗauke idanunsa dan ya tsani ganin hawayen nan. Jin bai tanka ba yasata satar kallonsa sai taga hankalinsa baya gareta. Saurin saka nikab ɗin tai ta goge hawayen. Kafin ta ɗaura basket ɗin saman table ɗin ganin ya sauke ƙafafun nasa. Abincin ta haɗa masa ranta cike da fatan ALLAH yasa ya barta ta koma ɗakinta. Sai dai addu'ar tata bata amsu ba. Dan bayan ya gama shan ƙamshinsa lap-top ɗin ya ajiye gefe tare da nuna mata gefensa fuska a tsuke.         (Nidai tawa ta ƙare) ta ambata a ranta tana miƙewa tabi umarninsa dan har tafara jin nutsuwa ganin ɗan sake mata da yakeyi kwana biyun nan, sam bazataso su koma ƴar gidan jiya ba. Duk da 2seater ce sai da taɗan takura sakamakon yanayin nasa zaman. Lap-top ɗinsa ya ɗauka ya maida a cinya yana faɗin “Ohya bani, dan hukun cinki kenan yau a gidan nan ciyar dani abinci daga nan har dare”. Ya matso da fuskarsa gab da tata. Cikin raɗa ya ƙarasa faɗin, “Inba hakaba kuma na rantse ni zan c....”       A zabure ta ɗaura hanunta saman bakinsa ta toshe, tsabar rikicewa harda tallafo ƙeyarsa da ɗayan hanunta”.         “Ni dai gaskiya-gaskiya to nama fasa abotar a kwance wlhy”.      Kaɗan ya rage dariya ta kufce masa. amma yay dauriyar dakewa yana bin fuskarta da idanun ke rumtse da bakinta dake maganar da kallo. Ga jikinta sai tsuma yake. Sosai yake jin nishaɗi idan ya ganta a yanayi na tsorata ko kunyarsa. Hanunsa yasa ya janye nata hanun daga bakinsa harda ɗan bugesa.         “Ustazah yaushe kika koma hakane wai? To ai mai raba wannan abotar sai mutuwa mun ƙulla kenan”.       “To an taɓa dole ne?”. Ta faɗa cikin waro idanu tana sake ƙwaɓe fuska. Hancinta ya lakata kaɗan da ɗage gira sama ya kashe mata ido ɗaya. “Abota dani dolene yarinya. Dama kika samu na zaɓeki zakimin iyayi”. Yaƙare maganar da wani salon taɓe baki kamar wani mace. Hakan sai yay bala'in saka Raudha dariyar da batai niyya ba. Sosai murmushin fuskarsa ya ƙara faɗi shima. Sai dai tana gama dariyar ta ɗago da faɗin, “ALLAH yanda kayi sai kace mace. Baba Laran gidanmu haka take idan tana faɗa”.       Fuska ya tsuke da kwaɓeta yana hararta. “Waye macen?”.            Dariyar dake yalwace da fuskarta ta sake ƙyalƙyalewa da ita tana kai hannu ta danne bakin. Yayinda shi kuma ya kai hannu ya mangare mata kai ransa cikeda nishaɗi. Ganin taƙi daina dariyar ya sake bata ranƙwashi....        “Wayyo Mommyna zai ɓararmin da karatu na”.     (Kan uban nan) ya faɗa a ransa dariya na kufce masa shima. cak ta tsaya da tata dariyar ta zuba masa ido batare data sani ba. Dan wani irin ƙyau dariyar tai masa. haƙoransa duka sun bayyana ba kuma yana yinta a haukace bane...       “Sharri kika koma kuma Ustazah?”. Ya faɗa da sake kai mata ranƙwashi yana dariyar har sannan sai ta duƙe kan nata ya sauka bisa cinyarsa hularta na zamewa ta faɗi ƙasa. Ƙoƙarin ɗagota ya shigayi amma taƙi yarda. cakulkulo ya fara mata a wuya, cusa kanta take sakeyi tana dariya da ƙoƙarin ture hanunsa.       Jinsa yake a wani irin nishaɗi daya jima baiyiba a rayuwarsa. Zai iya rantsuwa tun bayan rasuwar Haseenahr sa da Amnah bai sake farin ciki makamancin hakan ba da yake a kwanakin nan musamman yanzu. Yanda gashinta data ɗaure ke reto ya sashi kama ribbon ɗin ya zare gashin ya tarwatse. Da sauri Raudha ta ɗago dan batama san hulan ya zame kansa ba. Sai kuma kunya ta kamata jin ya tura yatsunsa a ciki. Tai ƙoƙarin matsawa ya riƙeta. Shiru tai tsigar jikinta na tashi, kamar yanda shima yakejin jininsa na haurawa da gudu a kowanne jijiyar jikinsa....        “Ina son gashin nan sosai”. Yay maganar yana matso da kansa a kafaɗarta da kamo gashin ya kai hancinsa yana shaƙar ƙamshin haɗaɗɗen turaren *YERWA INCENSE AND MORE...* da yakeyi. Sai kuma ya saka maida yatsun nasa cikin gashin ya tallafo kanta ya ɗaura goshinsa akan nata suna musayar shaƙa da fesawa juna numfashi... Murya a matuƙar shaƙe duk da akwai mura dama tattare da shi ya ce, “Ƙawata!”.        A yanda ya ambaci kalmar ba ƙaramin tada tsigar jikin Raudha yay ba. Da ƙyar ta iya faɗin. “Uhhyim”.       “ALLAH yay miki albarka”. Sosai taji daɗin wannan addu'a tashi da batasan dalilin yinta ba. Muryarta a raunane tace “Amin nagode”.       Kansa ya ɗan jinjina mata da cigaba da motsa yatsun hanunsa cikin gashin nata. “Ni kuma fa?”.        _“Kaima ALLAH yay maka rahama da rahamarsa. Ya kareka da kariyarsa. Ya baka ikon sauke hakkin ƴan ƙasa dake bisa wuyanka, ya baka nutsuwar ayyuka da har abada da baza'a manta da kai ba. Ya hanaka cin hakkin kowa koda bai kai girman ƙwayar gero ba”._         (Ya ALLAH yarinyar nan zata hakalani) ya faɗa a ransa yana mai rungumeta tsam a jikinsa. Wannan shine karo na uku da hakan ta faru tsakaninsu. Amma yau an samu cigaba dan itama tayi luf duk da jikin nata naɗan tsuma kaɗan-kaɗan.       “Insha ALLAH ke ƴar aljanna ce *_AMEENATU!_*”.      Murmushi mai sanyi da yalwa ta saki domin jin furicin nasa. Itama cikin rawar murya tace, “Tare da kai da iyayenmu baki ɗaya”.      Ɗagota yay daga jikin nasa yana ɗan murmushi. “Uhhm an samu jiki mai daɗi an lafe. Ƙawa kemafa naga kina buƙatar ɗumin mijinki gsky”.        Hannu tasa ta rufe fuskarta tana murmushi.     “Gulmammiya ni bani abincina. Kinzo kinatamin kwarkwasa yana hucewa”.        “Kai Yaya Ramadhan dan ALLAH”. “Kam kujimin yarinya da kalan dangi, yaushe na zama Yayanki nikan daga ƙawance kuma? Koda yake kije na yafe miki dai bani abinci cikina ya fara kiran Taura”............✍       *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _A AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account. *Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks. *Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku. A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant). -------- Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar: *Bank Transfer* *Airtime Transfer* Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance. *Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks. _Account No_ - *1220077999* _Account Name_ - *Arewa Books Publishers* _Bank_ - *Zenith Bank* Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din: Amount Paid: - Nawa aka tura? Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa Transferred time: - lokacin da aka turo Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi Deposit date: - ranar da aka turo Sai ayi SUBMIT. *Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar: MTN, 9Mobile Glo Airtel Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance. *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/1, 8:00 PM] NANA: *_Typing📲_* *_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_* https://arewabooks.com/chapter?id=62be031cf0fb62def317f52f *_Episode 47_* .........Duk yanda taso zamewa basa abincin fir yaƙi. Dolenta ta bashi kamar yanda ya buƙata, kunya kamar ta tsaga ƙasa ta nutse a ciki. Shiko ko'a kwalar rigarsa. Sai ma idan tayo ƙatuwar lauma ya harareta wai tafi ƙarfin bakinsa. Amma in namane dataso ragewa zai riƙe hanun da faɗin ‘Ban san mugunta Ustazah’.        A haka dai yaci ya ƙoshi itama ya tsareta sai taci. Fuska ta marairaice tamkar zatai kuka amma yace saifa taci babu ɗaga ƙafa. Dole ta ɗan tsakura dan a takure take sosai. Bayan ta kammala ta tattare kwanikan ta fita da su. Numfashi ya sauke a hankali da barin aikin da yake a lap-top ya kwantar da kansa jikin kukerar yana lumshe ido da furzar da numfashi. Sai kuma ya kai hannu a wuyansa dan har yanzu akwai zazzaɓi jikinsa dauriyace kawai. ‘Oh Ramadhan Taura ka zama ɗan cali-cali kuma?’. Sai kuma ya sake sakin murmushi da girgiza kansa kaɗan. Shi kansa baya sanin sanda yake biyema Raudha. Abinda ya sani kawai bai son ganinta cikin damuwa kamar baya. Sannan addu'arta a koda yaushe na bashi nutsuwa. Yayinda idan tana a yanayin tsoro da kunya take hana fitinarsa zama lafiya ya dingajin kamar kawai ya...... “Ya ALLAH” ya ambata da kai hannu cikin sumar kansa. Sai kuma ya tashi zaune sosai ya cigaba da sarrafa system ɗin cike da ƙoƙarin son ture abubuwan dake neman fin ƙarfin jarumtarsa...... _______________★★_____________          Alhmdllhi zamuce abubuwa sun fara daidaito tsakanin Ramadhan da Raudha, ta saki jiki dashi ba laifi suyi ɗan wasa da dariya. Idan kuma taga ya haɗe fuska ta kama kanta ta nutsu. kwana ɗakinsa dai bata sake yarda tayiba tun randa yay zazzaɓi. Amma yanzu tana ƙoƙarin tashi a kowace bayan sallar asuba ta haɗa masa breakfast da kanta. hakama abincin dare kafin ya shigo takai komai bedroom ɗinsa ta ajiye. Wataran ya leƙata da matsa mata tazo ta bashi abinci. wataran ya shareta yaci abinsa sai da safe idan tazo gyaran ɗaki ta tattare.           A washe gari Ramadhan da Bappi suka gana, ganawar data zama ta farko a zahiri da har ƴan jarida suka fitar. Sai dai babu wanda yasan mi suka tattauna a zaman nasu sai ni (Bilyn Abdull cctv footage ɗin ku😉😂). Sosai kansu ya tushe da mamakin ganin rubutun Raudha dai-dai da takardar da aka turama Bappi ana jibi ɗaurin aurensa da Raudhan. An musu nuni ne da karsu yarda Ramadhan ɗin ya tare a gidan gwamnati har sai an cire ac ɗin dake a bedrooms nashi da falukansa saboda akwai poison a ciki. Ranar sun shiga tashin hankali musamman Anne datace Ramadhan bazai tare government house a kashe mata shi ba. Shi da Bappi sukaita lallashinta da mata nasiha harta nutsu, inda basuyi ƙasa a gwiwa ba randa Ramadhan ya shiga gidan gwamnati kwana biyu da aurensa da Raudha suka canja duk ac ɗin dake sashen harma dana office ɗinsa. Hakama sai da suka bincike lungu da saƙo na ɗakin barci da falukansa na sirri gudun ko an saka camaras a ɓoye. amma Alhmdllhi babu alamar hakan sai iya ta inda ya dace kawai da dole a samu a kowane gidan gwamnati saboda tsaro. Dan wani yaron Aunty Zuhrah ne yay aikin. Sun sake tsintar kansu a tashin hankali lokacin da suka samu poisons a cikin ac's ɗin. Ranar har hawaye Bappi yayi. Daga haka kuma ya ɗarsama kansa zargin akwai boyayyen al'amari. Sai dai kai tsaye bai fito ya ambaci sunan kowa ba. Babban fatansu kawai susan wanene wannan mai turo saƙo. Hakan yasa ganin wannan hand writing da yay dai-dai dana Raudha yay matuƙar ɗaure kansu.         “Wannan ya sake tabbatar min yarinyar nan Alheri ce kuma akwai dalilin zuwanta garemu”. Bappi ya faɗa lokacin da suke ganawa da Ramadhan a office.      Cikin sauke numfashi Ramadhan yace, “Tabbas akwai abinda bamu saniba kuma ita take ɓoye mana. Abin ɗaure kan anan kawai shine a gaba ɗaya tarihin yarinyar dana bibiya babu wani alamun alaƙarta da wani sai danginta ko anan cikin Bingo. Sai dai sister ɗin mom nata tanada alaƙa da matar forma president, a yanzu kuma matace ga Alhaji Yaro glass Vice ɗina, dama kuma sun taɓa zaman aure ta fita. Bappi inhar hasashena yana kan dai-dai akwai boyayyar manufa tsakaninka da abokan nan naka gaskiya”.       Murmushi Bappi yayi yana ɗan jinjina kai. “Komai zai iya faruwa musamman idan akai la'akari da abubuwa masu yawa. Sai dai bana so zargin sunan kowa anan har sai muntabbar. Shawarata gareka anan lkawai ka cigaba da jan yarinyarnan Ameenatu a jiki, zaka iya jin fiye da abinda muke buƙata daga gareta. Amma tabbas ka shaida naji ƙarin ƙaunarta a raina da kimarta fiye da zaton mai zato. Dan zuciyata bata gayamin an haɗa kai da itane dan a cutar damu”.       A hankali Ramadhan ya sauke numfashi wani abu mai sanyi na sauka masa a cikin zuciya. Jiyake kamarma ya buɗe ido ya ganta gabansa. Jin yau ɗin yake daban da kullum a rayuwarsa. Sai dai me, yana zuwa gidan ya iske ɓacin ran su Lubnah da har takaisa ga marin Lubnah ɗin. A kuma daren yasa driver maidata gida. Sai dai abun ƙarin takaici washe gari Maah tasa aka maidota.       Wannan haushin ya sakashi tunda ya fita gida da safe bai dawoba sai dare. Washe gari kuma tafiya ta taso masa zuwa ƙasar faransa babu wani walwala tattare da shi sukai sallama da Raudha da ayanzu ta sake nutsuwa akan makaranta dan harta fara jin daɗin lectures din saboda taimakon da su Basma ke bata.     Ta ɗan shiga damuwa da canjawar tashi, sai dai daga baya ta watsar da komai dan indai dan abinda su Lubnah sukai matane ita ya wuce a gareta basa ma gabanta. Fatanta dai ALLAH ya bata kariya daga cutar da waninsu.       A washe garin daya wuce ta tashi da ciwon mara. Tasha azaba sauƙintama yasa Bilkisu dawowa gidan saboda ya fahimci suna ɗasawa da Raudha ɗin. Sai dai sunsha gargaɗi kamar babu gobe akan abubuwa da yawa. Hakama su Muneera sunsha nasu, dama tun marin da Lubnah tasha suka koma shiru-shiru a gidan dan sun san hali. Yanzu ko daya tafi sun ɗau alwashi kala-kala akan Raudha sai akai rashin sa'a Bilkisu ta dawo kusa da ita.       Bilkisu ce ta sanar masa halin da Raudha ke ciki ta hanyar massege. Hankalinsa ya tashi lokacin daya lura ta text ɗin. Sai kuma a lokacin ya tuna da zancen Dr Hauwa'u a wancan lokacin. Bai samu magana da Bilkisu ba sai dare bayan ya samu nutsuwa. Ta kwantar masa da hankali akan da sauƙi, dan Anne ta kira shine ta turo musu Maman Jabeer (Dr Hauwa) tazo ta dubata. Ta tabbatar masa tayi faɗa sosai akan ƙin zuwan Raudha ɗin bayan tun wancan karon tace taje bayan ta warke.         Yaji babu daɗi sosai, dan kuwa akwai sakacinsa tunda shine bai nuna maida hankali akai ba matsayinsa na wadda take a ƙarƙashinsa. Bai ce a haɗashi da Raudha ɗin ba, sai dai ya tabbatar ma Bilkisu tayi ƙoƙari idan Raudha ta samu lafiya suje asibitin Maman Jabeer ɗin.        Haka kuwa akai, bayan kwana biyu ta koma ragas kamar ba'ita ba. Dan haka sukaje asibitin da dare gudun idon mutane. Sai dai tana tare da dogaranta duk da hakan.       Sosai Dr Hauwa tai mata gwaje-gwaje na musamman yanda ya kamata. Cikin amincin ALLAH kuma ta gano matsalolin dake tare da Raudha ɗin harda imfection. Magunguna ta bata tare da wani bayanai a rubuce tace ta bama Ramadhan ba nata bane.          Kamar yanda akace shi ɗin zata bamawa kuwa bata buɗaba ta ajiye ta cigaba da sabgar gabanta. Tayi fes da ita, da alama kuma makaranta ta fara buɗe mata idanu da wasu abubuwan. Gashi bata wasa sam da karatu sosai take nuna ƙwazo dake bama su Basma dama class mate ɗin nata mamaki. Gashi taƙi yarda kowa yasan ita wacece, koda yaushe fuska a ƙunshe da niƙab. Bata shiga harkar kowa sai su Basma. Wasu na mata kallon girman kai wasu kuma tana ɗan birgesu duk da basu san wacece ita ba. Suma su Basma kuma sun kame bakinsu saboda gargaɗin Ramadhan da Anne.        ★Kasancewar yau juma'a da wuri ta dawo school.  Ta zube a falo Bilkisu na mata dariya. “Aunty ahaka za'ai karatun kuwa?”.       Dariya itama Raudha tayi tana ajiye ruwan data sha sosai. “Wlhy bazaki ganeba Aunty. Abunfa babu sauƙi sam. Dan masifa yau text har biyu mukayi ga submitting Assignment ɗin masifaffen malamin nan da nake gaya miki”.         Cikin dariya Bily tace, “Haka ake shan yaƙi ai Aunty har a cimma nasara. Fatanmu dai ki fito da first class duniya tasan firt lady ɗinmu bata wasa bace”.     Dariya Raudha tai tana miƙewa. “Uhhm Aunty Rabani da wata first lady. bara na watsa ruwa nazo naci abinci ko breakfast banyiba yau”.       Bayan tayo wankan anan suka baje a falon bilkisu na sake nuna mata aikin yau da mata ƙarin bayani. Salla kawai ke tadasu har magrib. Sam Raudha batasan yau shugaban ƙasa zai dawo ba dan tunda ta shigo gidan basu buɗe tv ba. Bayan sallar isha'i taɗan sake watsa ruwa. Fitowarta kenan a toilet ɗin ta samu wayarta na ringing. Cike da zumuɗi ta ɗaga ganin Fatima. Tun jiya suka sanar mata yau zasuje Hutawa duba Abba (Dauda) da baida lafiya. Taso zuwa amma babu dama har kuka tayi. Sai dai ta ƙudiri niyyar idan Ramadhan ya dawo zata roƙesa alfarmar zuwa itama. Bayan sun gaisa dasu Fatima har dasu Inna Fatisa ke sanar mata ga ƙawarta Zubaida da tazo duba Abban su gaisa.       Cike da mamaki tace “Zubaida fa? Dama bata mance ina duniya ba?”.      “Ni na isa first lady ɗinmu. Ranki ya daɗe kin wuce a manta dake ai a ƙasar NAYA ”.     Zubaida data amsa wayar ta faɗa. “Mara kirki bazaki canjaba dai?”. Cewar Raudha cikin dariya.       Dariya itama Zubaida ɗin tayi, kafin su gaisa a mutunce. Zubaida ƙawartace ta islamiyya. Itama yarinyace mai ƙwazo da sanyin hali kamar Raudha. So da yawama akance halinsu yazo ɗaya ne shiyyasa suke abota. Duk da abotar tasu bawai takai mai tsanani bace da har suka san sirrikan juna musamman ma Raudha da ba'a jin cikinta. cikin tsokana Zubaida ke faɗin, “Halan kin kusa sauke mana babynmu ranki ya daɗe”.         Raudha tai dariya tana ɗakko kayan da zatasa a Wadrobe. “Aiko gashi ma har yana motsi a ciki, ina fatan kun shirya zuwa suna”.     Dariya sosai Zubaida keyi. Itama Raudha haka. “Uhm matsoraciya keda rakin nan naki ace cikin ya tsufa za'aji muryarki haka ragal”.       “Tabɗi mi kika ɗaukeni. Ki shirya zuwa Bingo kiga yanda nake daram kuma ga ƙaton cikin ƴan biyunku tare dani. K cikinfa ba wani wahala kwantar da hankalinki ke huɗu zaki samo mana lokaci guda......”         “Idan ita bata samoba ke zaki samoshi yau ɗin nan”. A mugun firgice Raudha ta juyo har towel ɗinta na ƙoƙarin kwancewa jin muryar wanda batai zatoba balle tsammani. Sanye yake cikin kananun kaya tausasa gaba ɗaya baƙaƙe. Ya ƙara wani fresh abinsa harda ɗan tumbi alamar hankalinsa kwance yake. Ga sumarsa data sake samun kulawa na gyara. Sam batasan ya dawo gidan ba balle shigowa ɗakin dan ko shigowar motocinsa yau batajiba sam kokuwa hankalintane bai a wajen, ta diririce da rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi ganin ita yake nufowa. Har yazo gab da ita bata samu mafitar kare kanta da ko saka hijjab ba. Ta cikuykuyo wasu kaya zata yafa a jikinta ya riƙe yana mai zagayawa ta bayanta ya rungumota jikinsa.        Wayar ya zare da kallon screen ɗin, tuni dama ta yanke kiran, sai dai hakan bai hanashi ganin da Fatima tai wayar ba. “Ai bansan kina bukatar ƴan uku ba Ustazah da tuni na ajiye ƙawancenmu gefe na baki ajiyarsu”.      Innalillahi ina ƙasa Raudha ta shige ta huta. Ya sake kanainaiyeta jikinsa da kai hannun kan ɗaurin towel ɗinta zai kamar zai kwance. Da wani irin zafin nama ta wulƙito ta rungumesa jikinta na rawa sai ambaton “Innalillahi...” take har ƙarshe. Shiko mizaiyi inba dariya ba. Sai dai yay dauriyar gimtsewa abinsa ya sake kama towel ɗin data ƙanƙanme cikin hannu ta gaba ɗaya. “Dan ALLAH ka rufamin asiri karka cire Ya Ramadhan. Inba hakaba zan iya rasa numfashina”.        “Sai in baki nawa mu rayu tare ai”. Ya faɗa cikin raɗa da wata irin murya mai wahalar fassara ga Raudha.      Raudha ta sake ƙanƙamesa saboda yanda zuciyarta ke masifar gudu cikin ƙirjinta. Tunda suke bai taɓa mata kalar abun nan ba. Iyakarsa taɓa hanunta fuskarta ya dan sumbata ko laɓɓanta. Amma bai taɓa gwada ɗora hanunsa a wani sashe na jikinta ba sai yau. Dan kuwa a bazata taji saukar hanunsa kan ƙirjinta.       “Na shiga uku”.   “Baki shiga uku ba. Ai maganar kunya kuma ta kare insha ALLAH yau zamu neman ƴan huɗu............✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/1, 8:00 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 48_* MAGANIN SANYI SADIDAN.08046881166 Kashi 90% cikin 100% na matan wannan zamani basuda matsalar da take damunsu kwarai irin sanyi, Toga maganin sanyi kankat, Bazanmaki rantsuwaba domin batadakyau ga Sanaa,ama zanbaki tabbaci Koda infection aka haifeki d izinin Allah ze warke, Watakil kice kunyi magani harkungaji yaqi tfy to insha Allah ki jarraba wannan bi'iznillahi zaki dace.07046881166 Qulli ne guda daya tak zakisha d koko 2500 ne kudinshi,wlh zakibani lbr duk wani balain sanyi seyayi gudun fanfalaki y barki, Dan Allah Dan grman Allah serious buyers Dan Allah chat me up 08046881166 *_Episode 48_* .........Gaba ɗaya ya gama sabauta mata tunani da lafiyar jiki. Dan kuwa cak ya ɗauketa a karon farko na tarihi, bai direta ko inaba sai saman gado. Bai damu da rawar da jikinta keyiba da roƙon da take masa ya zame towel ɗin da taketa faman riƙo kai kace igiyar neman tsira ce. Batama san ta daka tsalle ta ruƙunƙumesa ba. Atare suka faɗa saman gadon.        “Haba hajjaju ki bini a hankali mana ai zanyi”.    Yay maganar yana danne dariya da ƙyar. Itako kuka ta fashe masa da shi da sake ƙanƙamesa. Burinta bai wuce karya kallar mata jiki ba. Tausayi ta bashi dan yasan wannan wani sabon al'amarine daga gareta. Yajawo bargo da hanu ya lulluɓesu yalwataccen murmushi shimfiɗe a fuskarsa. Jin bil haƙƙi kukan take kuma taƙi barinsa yay ko motsi ya sashi lalubar bakinta ya manne nashi. Cikin salon tsantsar zalama da yanayin da yake ciki ya fara binta da salon da batasan zai iya aikatawa ba.         A wannan lokacin tsabar firgici zamu iya cewa Asthma ɗin Raudha ma motsawa ta nemayi. Dan da gaske numfashin ta a take ya fara fita a rarrabe har tana sarƙewa. Bai barta ba sai da ya fahimci yana neman kama wani layin saɓanin wanda yay niyyar bi kawai.       Shiru yay bayan barinta yana sauraren yanda hawayenta ke sauka a ƙirjinsa har yana huda riga yana ratsasa. Yay tattausan murmushi hanunsa saman kanta da akai ma kitson da baisan anyi ba. Sai da numfashinsu ya gama dai-daita ya kai bakinsa kan kunenta yana magana cikin muryar da batasan ya mallaka ba. “Cutie! Yaufa babu fashi sai anje duniyar samo ƴan huɗun nan bazan iya ɗaga ƙafa ba”.      Sake ƙanƙamesa tai jikinta na rawa dan harga ALLAH tsoro ma yake bata. Kalamansa sake firgita rayuwarta takeyi. Shine na farko daya taɓa mata abinda wani namiji a duniya bai taɓa mata ba. Shine na farko daya taɓa ɗora hanunsa akan abinda wani mahaluki bai taɓa taɓawa ba. Shine na farko daya ganta a yanda wani bai taɓa gani ba sai yau, yau ɗin ma yanzun nan duk da bata da tabbacin ya kalleta ɗin...      Ring ɗin da wayarsa tai a jikinsa ya sashi furzar da numfashi mai ƙarfi. Sosai idanunsa suka canja launi hakama fuskarsa tayi ja abinka da fari. Yasan Maah! ce, ya kuma san abinda take buƙata. Dan ta tabbatar masa tana son ganinsa daya dawo akan zancen aurensa da Aina'u. Da ƙyar ya iya saita kansa yakai wayar kunensa bayan ya ɗaga. Da sauri Raudha dake duƙunƙune a jikinsa tai saurin barin jikjnsa ta dire saman gadon. Bai hanata ba harta sake duƙunƙunewa cikin bargon daya rufa musu. Murmushi yay ganin yanda ta yayesa ita kuma ta nannaɗe a ciki kamar an nannaɗe gawa a likafani. Sosai ya tashi zaune ko zai sake samu muryarsa ta saisaitu.         “Kiyi haƙuri Maah zanzo ALLAH amma sai gobe idan ALLAH ya kaimu. Inaga ma anan zamu yi hutun nan na kwana huɗu yanzu kaina na ciwo”.      Abinda ta faɗa ya sashi sake marairaicewa kamar yana gabanta. “Please maah i promise you bazan saɓa alƙawari ba”.       “Okay thanks you dear Mammah I love you”. Wannan kalma ta Ramadhan ta bala'in faranta ran Gimbiya Su'adah. Sai taji gaba ɗaya fushin da takeyi da shi ya kwaranye a zuciyarta. Sai dai hakan baisa taji zata janye maganar auren Aina'u ba, tana akan bakanta duk da suna kan rikici da Pa ne akan hakan ma. Dan kuwa su Bappi sunce su babu ruwansu indai Ramadhan ya amince su masu son hakane ai.         Mikewa yay yana kallon Raudha dake ƙudundune fuskarsa da murmushi. “Irin wannan nannaɗa haka Ustazah kamar wata shawarma?. Indai nine nayi nan ina jiran abinci da yunwa na dawo cikina kamar anmun sata”.    Ya ƙare maganar da shafa cikin nasa daya ɗan taso. Shi kansa ya fahimci ya ƙara nauyi, kwana biyun nan baya iya fita training, dole ya dawo kar azo yakai matsayin da ƴar rigimarsa zata kasa ɗaukarsa wata ran. Da wannan tunanin ya fice ya barta bayan ya gwada yayeta ta sake saka masa kuka.          Kallon-kallo Aina'u da Muneera kema juna ganin yanda Yayan nasu ya fito a ɗakin Raudha fuska ɗauke da ƙayataccen murmushi da sai dai su hanga yanama wani shi ko su Bappi. Wani irin zafine ya shiga ratsa zuciyar Aina da jin ƙara tsanar Raudha da duk wandama ke tare da ita. jitake zata iya kashe Raudha saboda Ramadhan a yanzu. Dan tun tana shakkar maganar auren nasu a yanzu abin ji take yana ƙara mata tasiri a rai da ɗokin kasancewarta matarsa kodan suma susha romon mulki, dan tasan dai ta auresa yanzu tabbas itace zata zama first lady bawai waccan kazamar yarinyar da ko tsarkin kashi batajin ta gama ƙwarewar yi. Momynta (Adda Asmah) ta gama tabbatar mata indai Ramadhan ne sai ya sota fiye da uwarsa ma a duniya da su Anne, dan zata mallake mata zuciyarsa yanda bazai sake tunawa da kallon wata mace da daraja a duniya ba sai ita. Tabbas tahau ta zauna. Ta kuma yarda. Dan ita shaidace Abbansu a tafin hanun Mom nasu yake. Sai abinda tace yake yi. (Hummm🚶🏻🤕. ALLAH yasa sanda za'aima wasu hisabi muna aljannah a fadan MANZON ALLAH (S.A.W).   ★★★       Da ƙyar Raudha ta iya daurewa ranta ta tashi. Sai dai gaba ɗaya a tsorace take da komai ma. Yau gaba ɗaya Ramadhan ya rikita mata lissafi. Tama rasa wane kalar tunani zatai. Shiryawa tai cikin doguwar rigar abaya baƙa. Komai bata shafa ba sai khurah da turare. Sai dai ta wanko fuskarta saboda kukan datai. Cikin ɗar-ɗar da zuciyarta keyi ta fito domin sama masa abincin daya buƙata. Cikin sa'a ALLAH ya taimaketa tai kiciɓus da Bilkisu a kitchen ɗin sama. Dan ƙamshin da taji da motsine ma yaja hankalinta tunda tasan bamai shiga inba itaba sai mama ladi dake gyarawa.      Ido taɗan waro kaɗan na mamaki. “La aunty Bilkisu..”      Bilkisu dake murmushi tai saurin cewa “Kamar kice komai. Kawai naga Yaya a bazatane shiyyasa na rugo kitchen ɗin tunda ba salla zanyi ba. Mun shagala kwata-kwata bamu buɗe television ba balle muga batun dawowarsa.”         Ajiyar zuciya Raudha ta sauke. Cikin danne abinda ke taso mata tace, “Wlhy nima nasha mamaki.”      Ƴar dariya Bilkisu tai. “Uhm ya miki surprise na masoyane kawai”.      Kunya zancen Bilkisu ya bama Raudah, ta kauda kai kawai tana murmushi. Hannu ta saka suka karasa aikin da aready dama Bilkisun tana gab da kammalawa. Sai da suna haɗa abincin a basket Bilkisu ke faɗin. “Niko idonki kamar wadda tai kuka”.      Da sauri Raudha tace, “Abune ya faɗamin a ido daƙyar na samu ya fita bayan nata zuba masa ruwa”.     Sannu Bilkisun ta mata dan har zuciya ta yarda. Raudha ta ɗauka basket ɗin tana mata godiya da addu'ar ALLAH ya kaisu ran aurenta da yanzu haka ana shirin saka rana kusan su biyar.          Da ƙyar ta iya kawo kanta ƙofar ɗakin nasa. Ji take kamar bazata iyaba amma ta daure matuƙa. knocking tayi kamar bataso. Tana shirin sake na biyu aka buɗe ƙofar. Bata yarda ta kallesa ba, dan tasan dai shine ɗin. Shiko idonsa a kanta ƙyam yana ƙaremata kallo yanda abayar tai matuƙar mata ƙyau. Matsawa yay ya bata hanya ta shige batare da yace komaiba. Sai da ta gittashi ta shiga ya maida ƙofar ya rufe. Saman kujerar daya tashi ya koma ya zauna tare da ɗaukar Tab.. Da ke a hanunsa kafin shigowarta. Ganin ya basar da ita ya sata daurewa tace, “Ga abincin”.      “Zuba” Ya faɗa a taƙaice batare da yabar abinda yakeyi ba. So yake yay dauriyar fasa abinda yay niyyar yi a gareta amma zuciyarsa taƙi amsar lallashin sam. Bai kalleta ba harta zuba masa gasashen naman ragon daketa ƙamshi, yaji haɗi na musamman. Sai kunun madara da Bilkisu tayisa a nutse saboda sanin yanda yake ƙaunarsa. Zata zuba abincin yay saurin dakatar da ita. “No bar nan kawai”.     Dakatawa tai ta maida kwanon ta rufe da tura table ɗin gabansa yanda zai samu nutsuwar ci. Sai da ya ɓata wasu sakanni ya ajiye tab.. Ɗin, dai-dai da miƙewar Raudha dake fatan samun hanyar guduwa dan yau bazata juri zama da shi a inuwa ɗaya ba. Caraf ya riƙo hanunta ya zaunar a gefensa.       “Na sallameki ne?”. Jitai kamar ta fashe masa da kuka kawai, amma ta daure dan kar yaga kamar ta cika rashin wayo. Hankalinsa ya maida ga abincin zuciyarsa na tunanin ta yanda zai ɓullo mata ta saki jikinta. Sai dai ya kai laumar nama baki yake faɗin, “Uhhmm Bestie kinji wani gashi na musamman kamar a birnin sin. K karfa ki zata santi nake naji abunne har cikin kai”.        Murmushi ne ya suɓucema Raudha. A hankali tace. “Uhhmm!”.            “Ai bakiji Humm bama sai kinci”. Ya ɗago gareta da tsoka daya ciro jikin dogon tsinken da Bilkisu ta tsiro guda uku. “Buɗe bakin kiji kar ayi babu ke”.       A kunyace tace, “ALLAH ni na ƙoshi”.      Fuska ya ɓata yana ɗan hararta. “Keni bansan gulma buɗe baki. Ni nasan tun kan ki kawo namannan kike addu'ar ALLAH yasa na sammiki”.           “Ya ALLAHU”. Ta faɗa da dasashshiyar muryarta dariya na suɓuce mata.  Shima murmushin yake tare da sake kai mata naman bakinta. Dole ta buɗe saboda cewarsa. “ALLAH sai na miki ɗura. Kuma saina tauna yayi laushi na juye miki a baki dole ki haɗiye”.      Fuska ta yamutse alamar ƙyankyami. Ya dungure mata kai da faɗin, “K yarinyarnanfa ƴar wulaƙancice wani lokacin. Wai ƙyanƙyaminama kikeji? Koda yake hakafa kikaimin kwanaki ina mura. Har shaƙa miki murar nai amma kikaƙi ɗauka saboda ɗan banzan ƙarfin jininki”.      Yanzu kam kasa daurewa tai ta sanya dariya. “Kai Ya Ramadhan ko tausayi babu?”.       “K nifa kibar wani cemin Yaya niba Yayanki bane bamsan kalar dangi. Nasan dai akwai abota tsakaninmu sai kumaaaaa......”        Ya ɗanja ƙarshe yana kashe mata ido batare daya ƙarasa ba. Ba shiri ta miƙe zaram amma yay saurin riƙeta ya maida. “Ustaza bansan fassara irin taku ta Ustazai fa. Kijira na karasa mana kafin ki kaini inda banje ba”.     Dole ta dawo ta zauna kamar ta ɓuya a kujerar dan kunya. Ya dungure mata kai yana kai nama bakinsa da taɓe baki. “Gulmammiyar yarinya nafasan kema kin kamu. A yanzu nan duniya bayan Mommy da Abba babu wanda kike so Kamar Ramadhan...”      “Ni yaushe nace!”. Ta faɗa cikin suɓutar baki tana taɓe fuska.               “Yo sai kin faɗa? Yanda kika kadandaneni ram ɗazu ke daɗi mijima ai ya isa shaida.”      “Innalillahi....” Ta faɗa kamar zata fasa kuka dan kunya. Dariya ke cinsa yanda tai wuri-wuri da idanu na kunya. Ya danne da ƙyar. “Oh kice baki son nawa mana kiga in gobe banje an ɗauramin aure da ƴammata uku ba galla-galla”.          Ji Raudha tai kamar ya kwaɗa mata guduma a tsakkiyar zuciya. A take fara'ar fuskarta ta ɓace ɓat. Tai ƙasa da kai zuciyarta na mata zafi da kalamansa.....      Wani daɗi ya baibaye Ramadhan kamar ya tashi ta taka rawa. Cikin shafa sumar dake zagaye da kumatunsa yace, “Oh su Ustazah ba kunya anga sumulmulin yaro ɗan jikan Anne an maƙale. Irin wannan kishi haka Ƙawata? To indai baki so nayo kishiyoyi yau kam dole naje farautar triple koda yake kefa huɗu ma naji kina faɗa saboda tsabar haɗama keda ma ko ɗan kiss ɗin nan na zamani sau ɗaya aka taɓa mik.......”         Ai bata bari ya ƙarasa ba ta daka tsalle ta guntse masa baki da hannayenta. Wayyo dariya kamar ta kashe Ramadhan. Yasan ya riga ya gama da ƴar darunsa yau. Sai dai wani farin ciki ke dawainiya da shi ganin kishinsa ƙuru-ƙuru tattare da ita. Koba komai yaji daɗi bashi kaɗai ke wahalar banzaba akanta ashe. Jikinsa ya jawota ya rungume. Cikin raɗa yace, “Na nayi shiru tashi kici abinci”.         “Kaci kayanka, ko kaje kuci da ƴammatan naka”.      “Wayyo Ramadhana anyi kasuwa. Uhm-uhm fa Bestie ALLAH karki tsaya kallon ruwa ƙwaɗo ya miki ƙafa. BABU SO MIYA KAWO KISHI?”.      Turesa ta shigayi da faɗin, “Wama zaice yana sonka ɗin. Abotarma an fasa”.             Nanma dariya kawai yakeyi yana sake riƙota dan ya fahimci so take tai amfani da damar ta tsere. Ya jima da gane tanada wayo duk da ƙarancin shekarunta. Matseta yay da ƙyau duk yanda taso ya hanata damar dole ta nutsu saboda abinda ya raɗa mata a kunne kamar ta nutse. tanaji tana gani ya tilasta mata cin nama da kunun wanda yay mata matuƙar daɗi. Dama da ƴar sauran yunwarta ta rana. Bayan sun kammala ta tattara kwanika zata fita da su ya hanata. Acewarsa ta tayashi salla ya bata labarin faransa tunda ita bata tambaya ba. Ganin ya zama serious doleta haƙura. Sai dai ta masa complain na rashin hijjab yace abu mai sauƙi yana da shi ai....          Raudha dai dauriya kawai take amma tabbas a tsorace take. Bayan sun idar da salla ya dafa kanta yay addu'a kamar yanda musulinci ya tanada ya kuma dace ace tun randa aka kawota gidan hakan ta faru. sai dai lokacin gogan nata na bisa gajimaren hayaƙi hakan bata faru ba. Sosai Raudha tai mamakin yanda taji yana kwararo addu'oi. Sam batai zaton yanada ilimin addini kamar haka ba. Sai taji ya sake birgeta zuciyarta ta ƙara nauyi game da shi.       Bayan sun idar ma ta buƙaci son zillewa ta gudu ya sake hanata. Ƙarshe ma kayan barci da batasan daga ina ya samosu ba ya bata wai ta saka. A matuƙar kunyace ta dubesa cikin marairaicewa amma ya nuna mata babu wani ɗaga ƙafa yau anan zata kwana. Shi ya gaji da raba musu makwanci da takeyi. Daga karshe ya haɗata da kunyar data sakata bin umarninsa dole.         “Ustazah a haka za'a samo ƴan huɗun kina gabas ina yamma. Gara dai kiba marasa ɗa kunya ki haifama Maah jikan da taketa fatan gani. Gashi ma kin ƙudiri surprising ɗinta har ƴan huɗu kika shirya.”        “Kai Ya Ramadhan magana wai bata wucewa a gunka”.     “Oh ikon ALLAH na kulafa kin fara bin hanyar rainani yarinyarnan. Ni miye nawa tunda faɗa kikai naji. Ai har Anne zanma albishir gobe”.        “Na shiga tara dan ALLAH ka taimakeni”.       “Hhhh taimako ɗayane zaki samu sai kin saka kayan nan”.      Wannan kandagarki nasa ya sata shiga toilet ta canja. Sai dai ta jima tana duban kanta a mirror ɗin toilet ɗin ta kasa fitowa. Sai kallon kanta take cike da kunya da ganin ƙyawun da tayi kamar ba itaba. Sai dai gaskiya bazata iya fita da rigarba gabans....       Maƙalewa tunaninta yay jin an buɗe ƙofar toilet ɗin. Tai mugun diriricewa ta ruɗe. Tama rasa mizata jawo ta rufama jikinta. Ramadhan da kamar suman wucin gadi ya riska a bakin ƙofar yana jan numfashi da ƙyar zuciyarsa na wani irin bugu da sauri-sauri. Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafa ya ƙaraso gareta. Sai dai a zahiri yanda yake a nutse bazaka taɓa fahimtar halin da yake a ciki ba. A bayanta ya tsaya idanunsa kafe akanta ta cikin mirror da suke fuskanta, sai dai ita ta duƙar da kai ta kuma kuɗindine jikinta da towel ɗin data sami nasarar jawowa.         Ta bayan nata ya zuro hannayensa duka biyu ya zare towel ɗin data rumtse a cikinsu. A wani irin tashin hankali taja numfashi a fisge da rumtse idanunta da ƙarfi tana ayyanawa a ranta. “Shike nan tawa ta ƙare ni Aminatu”.         Lallausan murmushi ya saki yana yaye towel ɗin a hankali saboda furicin zuci datai ya fito fili. idunsa kuma a kan cute face nata da hawaye ke silalowa a hankali. Tabbas matarsa ƙyaƙyƙyawa ce, mai kuma ƙyawun surar jiki abin buƙatar kowane irin namiji mai lafiya. Ya ja nannauyar ajiyar zuciya da kamo kafaɗunta duka ya juyo da ita tana fuskantarsa. Rawa jikinta ya farayi dan ƙafafunta bazasu iya riƙe nauyin gangar jikintaba a yau.           Tausayinta ya sake kamashi, sai kawai ya rungumota cikin jikinsa dan shi kansa ji yake jini na haura masa har saman ƙwaƙwalwar kansa. A tare suka saki kakkaurar ajiyar zuciya, sai kawai ya ɗauketa cak suka fice.         Cikin gadonsa da kullum Raudha ke ƙwaɗayin ganin an saki runmfar net dake jikinta ya nufa da ita. A hankali ya fara kai ƙafarsa ɗaya ya dire gwiwar sa akan lallausan gadon yana rankwafawa ya direta a gadon itama. Cikin wata irin murya mai tsananin sanyi da rauni yace, “To sakeni”.         Sam bazata iyaba. Dan hanun nata ma rawa yakeyi, ta ƙara ƙanƙame wuyan nasa da hannayenta data tallafo ƙeyarsa hawaye na rige-rige sakkowa.       “Ameenatu”. Ya kira sunanta da murya mai tsananin tsada da tsantsane.            “Uhhmyim!". Ta faɗa a shaƙe.     “Kiyi haƙuri na tashi zan canja kaya ne”.        Da sauri ta girgiza masa kai idanunta rumtse. “Ya Ramadhan tsoro nakeji”.     Murmushi ya saki mai sanyi, a hankali ya kai bakinsa kan laɓɓanta da goshinta ya sumbata. Cikin sake raunana harshensa yace, “Nima tsoron nakeji shiyyasa na gayyatoki ki tayani kwana kar ojuju ya kamani”.       Yanda yake mata magana a kunne ya sata sake ƙanƙamesa. Ganinfa ba sakinshi zatai ba sai ya kawai ya kwanto jikinta gaba ɗaya ya sakar mata nauyinsa.       “Mummy zan mutu”. Ta faɗa da ƙyar jin nauyinsa na fitar hankali. Murmushi kawai yayi ya ɗagata, baice komaiba ya fito a cikin gadon. Ita kuma ta samu damar nannaɗe kanta a bargon zuciyarta na gudu kamar zata faso ƙirjinta ta fito kawai kowa ya huta. Harya koma toilet ya kammala kimtso kansa bata buɗe kanta ba. A haka ya kashe fitilar ɗakin yabar lamps kawai ya shiga net ɗin shima. Bargon data ƙudundune a ciki ya ɗaga shima ya shige.. Murmushi yayi jin yanda ta ƙanƙame waje guda lokacin daya kwanto jikinta. A hankali ya kai lips nashi ya sumbaceta ta gefen kunne, ta ƙara curewa waje guda jikinta na rawa. “Haba Ustazah, tsoro fa na ragwayen mata ne, ko kina so masu zuwa Bingon suzo kuma babu cikin ƴan huɗun uhhm?”. Kasa cewa komai tai, sai hawayen tsoro dake mata gudu, babu abinda ke cin ran Ramadhan sai dariya. Musamman daya shafa fuskarta yaji hawaye. “Oh ni Ramadhana, ni kuma haka ALLAH yay dani auren raguwa. Yo raguwa mana, tunkan ace kule ke kin tafi cas...” Tsabar yanda zuciyarta taje maƙura kuka ta fashe masa da shi mai ƙarfi. Ya danne dariyarsa da ƙyar tare da mirginota ta juyo suna fuskantar juna. Sai kawai ya rungumeta yana shafa kanta murmushi ya ƙi barin fuskarsa. Sai da ya tabbatar ta nutsu ya dai-daita fuskarsu waje guda, cikin ɗan hasken dake a ɗakin yake kallonta, itako idonta a rumtse gam. “Kodai mu haƙura da farautar ƴan huɗun kawai Ustazah?”. Da sauri ta ɗaga mata kanta. Ya saki murmushi mai faɗi da ɗora goshinsa kan nata ya riƙo hanunta cikin nashi. “Tom naji, amma idan an haƙura minene tukuycina ni?”. “Wlhy zan maka nama da yawa da safe”. Raudha ta faɗa da sauri cikin rawar murya. Mi Ramadhan zai inba dariya ba. Wato yarinyar nan ta maidashi mayen nama. A fili kuwa sai ya cewa yay “Okay ALLAH ya kaimu Ƙawata ta amana”. Daga haka ɗakin yay shiru, jin kamar ya fara barci Raudha hankalinta ya fara kwanciya, itama sai ta lumshe na idanun. Idanu ya buɗe a hankali yana kallonta da murmushi. “Yaro yarone”. Ya faɗa a hankali da jan bargo ya lulluɓesu baki ɗaya. Can cikin barci ta tsinkayi abinda yafi ƙarfin saninta, sai dai mai girma shugaban kasa da shirinsa yake, dan cikin ƙanƙanin lokaci yay mata dabaibayin daya sakata shagala da miƙa wuya, sai da labari yay nisa ta raina kanta....... *_Bily kama bakinki iya nan🤐🚶🏻_*            ★Kallo guda zakai mata kasan taci uban kuka harta godema ALLAH. Duk da kasancewarta ba fara tas ba yanayin saida ya nuna a fuskarta. Gaba ɗaya ta jangwabe kamar ba Ustazah Raudha ta hutawa ɗiyar baba Dauda da Asabe ba. Lallai ba ƙarya daren jiya anci ƙaniyar sabada. Dan kuwa dai mai girma shugaban ƙasar Naya Ramadhan B Hameed Taura bai nuna yasan wata Raudha ƴar 18years ba balle ya bita a sannu. Babu da kalar yaren da bata roƙesa ba amma ya toshe jinsa da ganinsa ya nuna mata baya fahimtar kowanne yare saina cikar burinsa. Cizo da yakushi kuwa ya samu rabonsa gwargwadon iko har ba'a cewa komai. A ƴan gidansu babu wanda bata lissafo yazo ya taimaketa ba har maƙwafta da su Anne sun sha kira........✍    _Mace ƴar gatan ALLAH. mace ƴar gatan duniya. Mace sarauniya. Mace farin cikin duniya. Mace duniyar duniya. Mata ina miƙo gaisuwar ban girma amma banda ballagazaye wanda suka gama rabarwa a waje🙄🙄😏👩🏻‍🦯_        *_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/5, 11:13 AM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 49 & 50_* ..........Da asuba daya tadata suyi salla kuka ta dinga masa sosai. Duk sai tausayinta ya lulluɓesa. Shi kansa yasan ya tsaurara mata da yawa, dan dukan fushinsa na shekarun nan babu ƙwange sai da ya sauke shi tsaf. Bata wani yarda ya taimaka mataba tace zata iya.    Koda ya haɗa mata ruwa sai ya fita a toilet ɗin ya barta. Zafin ruwan ya sata harar ƙofar tana ƙunkuni ta surkeshi ya koma salaf. A haka ta gyara jikinta ta fito tana faman sinne kai. Ga dariya ga tausayi duk suna cin Ramadhan lokaci ɗaya. Amma sai ya gimtse dan karya sake tunzurata.       Da ƙyar ta yarda suka sake komawa barci bayan ta idar da sallar. Acewarsa su ɗan ƙara rage barcin idonsu dan anguwa zasuje. Taura house yake son suje hutun nan na kwanaki biyar da akai, amma bai sanar mata ba. Dan kuwa bazai yarda amarcin nan ya wucesa bai ɗana gadonsa na Taura house ba. (Mutumin nan ko😂😜)          ★Tun a daren jiya dama ya sanarma ƙanensa yau zasu wuce Taura house hutu gaba ɗayansu. Dan haka da safe ya turama Bilkisu text ta haɗama Raudha abinda duk tasan zatai amfani da shi su wuce su sai zuwa anjima zasu zo. Murmushi kawai Bilyn tayi. Sai dai kafin su fita tai ƙoƙarin haɗa breakfast ta ajiye musu. Mama Ladi kuwa ta zauna gadin abincin nan dan kuwa Anne ta kirata tun sanda suka gane Raudha ce ta aika musu takarda akan saka poison a ac ta ce mata ta dinga saka ido akan kowa na gidan kar'a cutar mata da su Raudha. Duk da tasan bata isa hana zartar da ƙaddarar UBANGIJI akansu ba.         Yanzu kam Raudha ce ta fara farkawa. Ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi matuƙa. Akan fuskar gogan nata ta saukesu. Idanunsa a lumshe, ƙyaƙyƙyawar fuskarsa tayi wani fayau. Duk da haushinsa na murzar da yay mata jiya babu tausayi da takeji haka ta shagala a kallonsa. Itama kanta tasan shiɗin ƙyaƙyƙyawa ne, ga yanayin jin daɗin rayuwa daya tashi a ciki, bai san wahalar komai ba sai ta karatu. Ahankali takai yatsanta saman girarsa data daɗe tana kwaɗayin taɓa tsagar wajen da zuciyarta ke bata wanzami yay masa. Sai dai me, koda ta shafa wajen sai taji santsi irin na tabon ciwo. Mamaki ya kamata, a zuciyarta tace, (Ashe ba tsaga masa akeba tabon ciwo ne) a fili kam mamaki ƙarara ya bayyana gareta da sake girmama sunan UBANGIJI, dan babu mai kallon wajen yace ciwone. Sosai tsagar ta fita da tsari kamar yimasa akai akan sani. A hankali ta sauke numfashi da maida gashin girar data yamutsa masa ta maidashi ya kwanta. Tana ƙoƙarin sake janyewa taji an riƙe hanun. Babu shiri tai saurin rumtse ido tana fisgewa amma yaƙi saki. Nasa lumsassun idanun dake cike da barci ya buɗe a hankali a kanta. Sai kuma ya sumbaci hanun nata daya riƙi ya turashi ƙasan kuncinsa yay filo da shi.  Ɗayan hanunsa kuma ya ɗaura a jikinta saitin ƙugunta.      “Good morning sweetheart”.   Wani bala'in kunyane da yafi na ɗazun da asuba ya lulluɓeta. Tai ƙoƙarin kauda kanta yay azamar tallafosa da hanunsa dake a ƙugunta ya hanata hakan. Cikin ɗan marairaicewa yace, “Ki amsa min mana Baby luv”.         Da ƙyar ta iya buɗe baki tace, “Ina kwana”.       Ahankali ya shafo kanta tun daga sumar gaban goshin har zuwa ƙeya yana ɗan murmushi. “Ya jikin ki? Duk da nima dai ya kamata a tambayeni nawa kodan yaƙushi da cizon dana sha”.       Ina ƙasa Raudha ta shige ta huta. Tai ƙoƙarin jan hanunta da yay filo da shi amma ta kasa. “Kibar wani gulma Ustazah, nasan kina son mijinki kar kiyi sake wata ta ƙwace miki ni”.       Kanta tai ƙoƙarin sinnewa a jikinsa. Yay murmushi yana riƙeta ya hana hakan. “Gara na faɗa miki gaskiya matsayina na abokinki babban amininki. Bazan so a miki kishiyaba kina ƙawata ta hanun damar, dan sai na fiki kishi kilama kullum dani zaki dinga cin dabe da ita a gidan ga muna lakaɗa mata duka ko ya kikace?”.        Duk yanda taso riƙe dariyarta ta kasa. Ta saki murmushi tana turesa. “Kai Ya Ramadhan....”       “K nifa bana wani kalar dangi ƙannena sun isheni, inama laifi da muke abota niba yayanki bane”.    “Toni ai bazan iya faɗar sunanka ba”. Tai maganar tana sake son cusa kanta a ƙirjinsa. Haɓarta ya riƙo ya ɗago fuskar tata da sumbatar laɓɓanta. Cikin sake ƙanƙan da murya yace, “To basai ki canjamin da wani ba. Amma sam bana son Yayan nan kamar wani zamanin iyaye da kakanni, bayan kuma jiya na gama turmusheki a gadon na....”        Dariya ta ɗan ƙyalƙyale da shi tana kaimasa ƙaramin duka a ƙirji. Shima sai ya rungumeta yana murmushi. Zuciyarsa fes da farin ciki.        Duk yanda taso zamewa kar suyi wanka tare bai bata damarba. Amma kuma taƙi sakin jiki haka ya gama nashi ya barota a bayin. Sanda ta fito yana zaune yana waya. Dan haka tai wuff ta fice a ɗakin bayan ta saka hijjab.        Ciwo take ɗanji kaɗan-kaɗan a ƙasanta amma ta daure ta shirya cikin wani material da yay mata ƙyau sosai da fiddo kalar fatarta. Tayi fayau da ita daka ganta kaga amarya, sai dai fuskar babu walwala sosai ga idonta duk wanda ya kalleta yasan taci kuka. Yunwa takeji amma batajin son cin abinci kuma. Bakinma ɗaci takeji yana mata kamar mai malaria. Tana fesa turare ya shigo, sanye yake cikin shadda ash color datai bala'in masa ƙyau. Sai maiƙo take da ɗaukar iadanun mai kallo. Ya murza hula baƙa data fiddo ainahin hasken fatarsa da ƙyallin angwanci. Duk da waya ya shigo yanayi hakan bai hana Raudha shiga jin kunya ba, ya ƙaraso inda take yana riƙe kwalban turaren da kunya tasata cigaba da fesa ƙasa-ƙasa dan karya tada mata asthma. Ajiyewa yay saman mirror ɗin ya riƙe hanunsa cikin nata idanunsa a saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta da yakeji kamar ya haɗiyeta. Ga ɗaurin datai ya sake fiddo ƙyanta kamar dai ya haɗiyetan ya huta kawai. Ita dai kanta a ƙasa tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa na _Dolce & gabbana_ daya gauraya da _burberry brit_. shiko yanata wayarsa da murza yatsun hanunta.       Tsawon lokaci harta fara gundura da tsaiwar kafin yay sallama da wanda yake maganar wanda ta fahimci kamar akan harkar kasuwanci ne. Saman mirror ya ɗaura wayar da kamo fuskarta cikin tafukan hanunsa ya sumbaci goshinta, sai kuma ya sakko a hankali ya sumbaci lips ɗinta dake ƙallin lips gloss. Shima ya duƙo kaɗan yana nuna mata nasa kumatunsa da goshi.        “Kai Ya Ramad......” Sai kuma ta kasa karasawa saboda ɗallin daya bama bakinta. “Dole na fara hukunta wannan bakin idan yaya ɗin nan bai fita a cikinsa ba”.      Hannu tasa ta rufe laɓɓanta da zafi ya maimaye idonta na cika da ƙwalla. Hannunta ya kamo ya zuba mata link ɗinsa da agogonsa _hublot_ dayay mata ƙyau sosai kalar ash. Batai musu ba, dan koba komai tasan aiki garesa lada ne. Links ɗin ta fara saka masa sannan agogon.      “Thanks bestie”. Ya faɗa a hankali idonsa a kanta. Sai kuma ya janye yana ƙoƙarin barin wajen mirror ɗin. “Ƙarasa mu wuce so nake na more gida sosai lokaci nata tafiya”.        Duk da batasan ina zasu ba cike take da ɗokin tafiyar. Ta ɗauka hijjab da zai shiga da kayanta ta saka tare da haɗa abinda zata iya buƙata a karamar handbag. Tana duba takalmi a akwatin lefenta ya sake shigowa. Bai yi magana ba yabi duk kayan wutar ɗakin ya kashe komai. Dai-dai tana gamawa yake faɗin, “Ko breakfast bazamu tsaya yiba mayi acan kawai”.      Kanta ta jinjina masa, sai dai har yanzu taƙi yarda su haɗa ido. A hankali ya matsa gefenta yay musu hoto bayan ya faɗi abinda ya sakata ɗagowa ta kallesa a ɗan tsorace. Sai hoton ya bada wani style mai ƙayatarwa kamar anyisane da shiri.         Bayan sun sallami su Mama Ladi suka fito compound inda jerarrun motocin da zasu fitan suke. Yau ce karo na farko da zasu fita tare da shi a bayyane. Sai gaisuwa ake miƙa musu cike da ɗunbin girmamawa wadda har Raudha takejin babu daɗi akanta. Dan kuwa da yawansu sun haifeta da girmarta. A motar da tafi kowace mota ƙyau da ɗaukar idanu ga tutocin ƙasar naya a jikinta suka shiga. Kafin wanda zasu musu rakkiya Taura house ciki harda cos da wasu ministers uku suma suka shiga. Ba wani tafiya mai tazara bace ba, amma ta fahimci an bama fitar muhimmanci matuƙar dan har a redion motar da driver ya kunna saiga sanarwar yau shugaban ƙasa Ramadhan B. Hameed Taura zaije hutun ƙarshen shekara gidansu a karo na farko tun bayan hawansa mulki na watanni kenan. Anan aka saka zantukan mutane daban-daban daketa masa addu'a shi da iyalinsa akan yasha hutu lafiya cikin farin ciki.      Sosai ya ƙara samun nutsuwa a ransa dan kuwa zuwa yanzun ayyukan daban-daban da suka faro na talakawa sun kankama matuƙa. Abinda zai matuƙar birgeka duk wani mai kwangilar gwamnati sunansa da aikin da zaiyi a bayyane yake ga al'umma. Hakan yasa yake ƙara samun addu'a ga talakawa dan kuwa babu wani ƙunshe-ƙunshe balle a cucesu a ƙiyi musu aiki kuma su rasa daga ina matsalar take. Kai hatta kuɗin da aka bama masu kwangilan da wanda sukebin bashi sai sun kammala a cika musu duk an sanar da duniya babu wani rifa-rufa. Hakan da yay ya matuƙar taimakawa da saka tsoro a zukatan masu kwangilar dan sun san kam inma basuyiba sune a ruwa tsundum. Gashi har adadin watanni ko shekarun da aikin zai ɗauka kowa ya sani a bayyane. Bashi kaɗaiba hatta da gwamnoni da ƴan majilusu, ciyamomi, kansiloli duk aikin da zakai ma ƴan yankinka a jihohin nan 41 dolene ka sanar da komai talakawa su sani.         Tarba ce ta musamman tawagar shugaban ƙasa ta samu a Taura house, dan kuwa wannan shine karo na farko da yazo gidansu a bayyane kuma da shirin kwanaki. Sosai bakin Anne da su Yafendo ke a buɗe, ganinsa ya musu wahala yanda suke buƙata tunda ya hau mulkin nan. Raudha dai gaba ɗaya a takure take. Jitake kamar kowa zai iya gabe abinda ya faru a tsakaninsu jiya. Ga anne da su Yafendo sai nan-nan suke da ita kowa na saka mata albarka. Bayan gaishe-gaishe da addu'oi Ramadhan da su Bappi suka fita salla dan tawagar datai masa rakkiya sun koma. Sai dai Taura house tako ina zagaye yake da securitys kai gaba dayama anguwar. Dole ne ka shaida shugaban ƙasa na nan koda matakan tsaron dake kewayen anguwar baki ɗaya, kai kace ko ƙuda bazasu bari ya gitta ba.            Da ƙyar Raudha ta iya tsarki da ruwan sanyi tsabar zogin da wajen ke mata zuwa yanzun. Har jin kanta take kamar wadda zazzaɓi zai saukarmawa. Anne na lure da yanayin nata sai dai batace komai ba dan zuciyarta bai kai ga zargin abinda ke faruwa da Raudha ɗin ba kai tsaye. Gashi tunda suka shigo dama yanayin idanunta na wadda taci kuka ya tsayama Anne a rai. A ɗakin Anne sukai salla duk da kuwa an gyara sashen Ramadhan ɗin tsaf domin su.       Bayan idar da salla gaba ɗaya gidan ƴaƴa da iyaye aka haɗu domin yin lunch a katafaren falon Bappi. Abincine mai rai da lafiya da gamsarwa a wajen iri-iri. Anyi hakanne kawai domin walimar zuwan Ramadhan ɗin da Raudha. Sai yanzu Raudha taga gimbiya Su'adah da sauran matan gidan, dan kuwa bata shiga gaishesu ba Anne tace sai zuwa yamma sun huta. Sai dai shi Ramadhan ya shiga ya gaida Gimbiya Su'adah ɗin kawai ganin bata a masu fitowa tarbarsa. Kasancewar salla zai fita yasa bayan gaisuwa babu wani abu daya shiga tsakaninsu ya fito suka fice massallaci.      Har ƙasa Raudha takai tana gaishe da iyayen. Kowa ya amsa mata cike da kulawa banda gimbiya Su'adah da ko kallon inda take bataiba. Ƙasan ranta wani takaicine da baƙin ciki da kishin yanda Raudha ta kara murjewa komai na halittar jikinta ya ƙara girma sai kace ƴar 25years. Ga tsadadden material ɗin dake jikinta wanda ta tabbatar za'a iya sayen abincin watanni na gidansu Raudhan da kuɗinsa. Ita saima taga kamar yarinyar tana wani jin kanta.      Oho Raudha batasan tanai ba. Ita abinda ya dametama ya isheta. Komai yinsa take cike da dauriya. Abincinma tana matuƙar bukatarsa amma ta kasa ci saboda bakinta babu daɗi. Sai juya spoon take a ciki tana ɓata fuska. Ramadhan na lure da ita. Kuma hankalinsa na kanta. Burinsa su haɗa ido amma taƙi kallon ko inda yake. yana zaune ne tsakkiyar Bappi da Pa. Sai Anne a gefensu da Yafendo da Inna. Ita kuma tana kusa da Bilkisu da Zainab ne. Su Lubnah sai faman jan tsaki suke ƙasa-ƙasa suma kamar su halaka Raudha sukeji musamman ganin suturar data sanya kosu da suka tashi gidan kuɗin basu saka ba. Tsadajjen agogon hanunta da zabba da bangles kawai duniyane. Balle ita kanta data kara wani kyau na musamman da su sam basa lura da shi sai yau duk da kuwa suna tare da ita.           Da gangan Ramadhan yay kamar ya sarƙe yaja gyaran muryar data saka kowa maida hankalinsa a kansa ana rige-rigen jera masa sannu. Bappi dake shafa masa baya kamar wani ƙaramin yaro ya kai masa kofin ruwa bakinsa yana masa sannu. Kaɗan yasha yana jinjina musu kai da satar kallon Ustazahr tasa. Sai dai bata yarda ta kallesa ba tun bayan ɗagowar datai kamar yanda kowa ya ɗago lokacin daya sarƙe. Ita sanun tatama a kan laɓɓa tai masa ta tsuke bakinta. Ganin dai ba samun yanda yakeso zaiyi ba sai ya haƙura. Takaici ya cika Aynah da duk hankalinta ke akansu. Hakama Muneera da idonsu akan yayan nasu da abinda yake yawan kallo. Jin hawaye na neman zuboma Aina'u itace ta fara mikewa wai ta ƙoahi. Babu wanda yace mata komai, hakan sai ya ƙara baƙanta ranta. Dan a ganin bai kamata aƙi bata kulawaba kodan mata ta biyu da take shirin shigowa ga ɗansu kuma ɗan uwanta.         Raudha da dama ba abincin take ci na kirki ba itace ta ukun tashi a wajen. Ramadhan ya ɗan bi yanda take tafiya da kallo. Hannu ya kai ya dafe goshinsa a zuciyarsa yana ayyana (Yarinyar nan zata tonamin asiri fa). Bayan sun kammala kowa ya tashi a wajen yaso janta sashensa dan ya fahimci mugunta taima kanta bata shiga ruwan zafin daya haɗa mataba da asuba, bayajin kuma da safe ta sake kula da kanta. Takaicin kansa yaji dabai tsaya akanta ya taimaka mataba duk boranta. Sai dai duk yanda yaso ya keɓe da ita ɗin hakan bata yuwuba dan su Basma na zagaye da ita a falon Anne suna hirar school duk da ba wani saka musu baki take sosai ba. Sai dai ganin Inna da Yafendo da Anne na wajen ya sashi haƙura ya shige shi acewarsa zai ɗan huta...........✍          _Ayi haƙuri da jina shiru, banda lafiya ne_. *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/5, 11:13 AM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 51_* ........Anne ta cigaba da maida hankalinta ga Raudha har zuciyarta ta fara hasashen abinda yake dai-dai. Sai dai ta danne komai batace ba har la'asar da aka tashi salla. Ramadhan ya fito sanye cikin ƙananan kayan daya canja suka sake fita massallaci da Bappi dan Pa na sashensa shima da iyalinsa. Har lokacin su Rumaisa na tare da Raudha harma sun kara samun yawan ƴan hirar su Sumayya. Magana kawai yay musu su tashi suje suyi salla ya wuce abinsa yana satar kallon Raudha da tun fitowarsa tai ƙasa da kai tana wasa da yatsun hanunta da jan lalle ya ƙawata dogayen faratanta.        Koda ya dawo bai samesu a falon ba, acan bedroom ɗin kusa da na Anne yaji hayaniyarsu. bai saniba ko Raudha na tare da su ko tana ɗakin Anne. Haka ya wuce sashensa ya buɗe garden ɗinsa dake a gyare tsaf da korayen tsirrai masu kamshi da ni'imar ruwa ya shiga. Tunanin kiran wayarta yayi, sai dai akashe ma akace masa. yaja guntun tsaki dakai hannu ya shafi sumar kansa. Duk saima yaji zuwa gidan ma ya gundiresa, dan ba haka yaso ba kwata-kwata. Ya riga ya gama tsara kasancewarsu a sashensa daga shi sai matarsa su huta yanda ya kamata, amma sai gashi hakan ya gagara.        Tun Raudha na daurewa dai har abin yaso fin karfinta. Dan da ƙyar ta iya dauriyar zagaya duka sassan gidan gaishe da matan Pa. Cike da takan tsantsan da faɗuwar gaba ta isa sashen Gimbiya Su'adah wannan karon, fatanta da addu'ar ta ALLAH yasa karta shaƙa mata tsakin kuka kamar wancan karon. Dan yau kanta shima wani azabar ciwo yake mata bayan zazzaɓi da ƙasanta da takejinsa kamar ana yankata ana watsa barkono a wajen.       Badai a mata turaren tsakin kuka ba, amma ta fuskanci cin zarafi wajen su Muneera dake zaune tare da Gimbiya Su'adah a ɗakin. A kuma nan suke tabbatar mata da auren mijinta da Ayna'u. Sosai hankalin Raudha ya tashi, da jin wannan zance sai dai ta bala'in dakewa kamar babu komai a ranta. Ta saki murmushi mai kayatarwa da faɗin, “ALLAH ya sanya alkairi”.         Dukansu kallon mamaki sukai mata dan basuyi zaton tanada bakin amsawaba musamman yanda tsoron gimbiya Su'adah baya ɓoyuwa a saman fuskarta.        “Idanma baki faɗa har zuciya ba dai sai anyi, nanda sati uku Aunty Aynah nakan karagar mulkin first lady ba illiterate irinki ba...”       Bumm kakeji Bilkisu da basu san da shigowartaba ta buge bakin Muneera dake maganar. “K dai baki da kunya sam Muneera. K har kina da bakin kiran wani illiterate? Koda kikai karatun ubanmi kika sani. Dan duk gidan nan kinfi kowa jakanta, badan Pa ba kin isa ki gama jami'a ne iyanzu kullum cikin daukar Cary over. Ina tausayin randa zaki ɗanɗani azabar gidan aure dan duk abinda kayi kaima sai an maka shi mtsoww”.       Tana gama faɗa ta kama hanun Raudha suka fice a ɗakin batare data saurari ihun da Lubnah da Ayna'u ke mataba. Gimbiya Su'adah kam uffan batace ba har bilkisun ta fice da Raudha. Hakama surutan su Aynah ɗin baisa ta tanka ba. Kafin su karasa sashen Anne Raudha ta tsaida Bilkisu tana bata haƙuri dan sai mita take da cewa yau saita sanarma su Bappi abinda su Muneera ke mata da ɗaurin ƙugun Maah. Roƙonta taitayi akan tabar zancen ita hakan baya damunta, kuma Maah mahaifiyace a gareta ai, ta isa ta mata komai. Amma Bilkisu ta dage akan saifa ta faɗa an ɗaukama abun mataki. Da ƙyar Raudha ta shawo kan Bilkisu ta haƙura suka karasa ciki Raudhan na tafiya da ƙyar. Dan har cije lips take da haƙori sannan bata iya haɗe ƙafafun.         Ramadhan dake bayansu batare da sun sani ba ya bita da kallo cike da tausayinta da wani ƙarin ganin girmanta. Koba komai yana son mahaifiyarsa, sai dai shima baya ƙaunar wasu halayenta amma babu yanda zaiyi yana ƙoƙarin mata addu'a. Suko su Lubnah lokaci yayi dazai ci ubansu gwargwadon iko.        Yafendo data kasa haƙuri yanayin na Raudha ce ta fargar da Anne cikin raɗa dan suna tare a falo suna magana akan meeting ɗin da zasu zauna yau iya su manya dangane da abinda gimbiya Su'adah ta kawo na auren Ayna'u da Ramadhan.       “Anya kuwa basai yanzu megidana ya taɓa Ameenatu ba? yanayinta yayi kama da hakan”.      Anne dake bin Raudha da kallo ƙasa-ƙasa itama tace, “Tun ɗazu na lura da hakan wlhy Yafendo, sai dai kuma idan na tuna abinda ya faru tun washe garin aurensu da ɓarin da tayi saina ture hakan a raina. Ƙila wata matsalace daban kuma”          “To lallai al'amarin akwai ɗaure kai, kodai akwai abinda bamu fahimta dai-dai ba tun a wancan lokacin, kokuma bai bar halin nasa na idan ya fusata ya sauke fushinsa kan mace ba?. Ya kamata a binciketa kam a bata kulawa dan yanayinta gaba ɗaya ya fallasa taji ciwo a wajen ko makamancin hakan”.       Numfashi kawai Anne ta sauke suka bar zancen suka kama wani. Suna wajen har aka kira magrib, a lokacin Raudha na can kwance zazzaɓi ya mata rijif. Da ƙyar ta iya tashi tai salla. Tana idarwa ta koma saman gado ta kwanta harda jan bargo hawaye na zubo mata. Tambayar duniya Bilkisu da su Rumaisa sun mata amsa ɗaya take basu (babu komai).       Bayan sallar isha'i suna falo zaune Raudha nata dauriya Anne ta fito daga ɗaki tai kiranta, da ƙyar ta iya dauriyar ganin ta saita tafiyarta amma hakan ya gagara. Har suka shiga ciki Anne batace mata komai ba, sai da ta zauna tana gaisheta ta haɗe fuska dan bata son Raudha tai mata gardama. Murya a dake tace, “Ameenatu faɗamin mike damunki tunda kukazo gidan nan naga baki da walwala kuma idonki ya nuna kinyi kuka?”.         Da sauri ta girgiza kai tana haɗiye hawayen dake neman zubo mata na zugin da take ji tace, “Ba komai ALLAH Anne. Kawai dai banajin daɗi ne”.       Shiru Anne tai cike da nazarinta. Sai kuma ta miƙe batare da tace komaiba ta nufi toilet ɗinta. Ruwa mai zafi ta haɗa yanda tasan zai taimaki Raudhan. Sannan ta fito ta kama hanunta suka shiga ciki. Duk yanda Raudha ke wani zame-zame ga kunya kamar zata halakata Anne bata saurareta ba. Babban towel ta bata ta ɗaura ta lulluɓa da gyalenta sannan ta sakata shiga cikin ruwan. Wani kuka maiban tausayi Raudha ta sanya har numfashinta na fisga kamar zata shiɗe. Ga kunyar Anne ga azaba, jikinta har wani karkarwa yake. Anne ta gama fahimtar matsalar Raudha amma mamaki ya hanata gaskatawa.       Haka ta sake canja mata wani ruwan har sau uku, sai ga Raudha taji wata irin nutsuwa na saukar mata. Anne ta fito tana bata umarnin tayi wanka da ruwan ɗumi kafin ta fito.        Ramadhan da tun shigar Raudha ruwan farko ya nufo ɗakin Annen ya tsaya cak jin ƙarar da Raudha ta ɗan saki sanda ruwan ya ratsata, ya dafe kai da riƙe ƙugu a fili yake faɗin, “Ameenatu kin kasheni, miyasa kikaƙi yarda na tainaka miki gashi nan kin gama tonemin asiri wajen tsohuwarnan da darunta baya karewa”.      Duk da Anne kakace renon uwa tai masa ba kaka ba. Hakan kuma baya hanashi yin wasa da ita wani lokacin. Dole ya fasa shiga ɗakin dan yasan rikicin Anne yanzu saita sauke masa na cikinta. Tun ɗazu itace a ransa. Duk abinda yakeyi hankalinsa na kanta, sai dai kuma haushin yanda ma ta wani sharesa na cinsa, dama sanda ya gansu da Bilkisu yaga kamar tafiyarta ba dai-dai ba, sai dai bai samu damar gama ƙare mata kallo ba suka shige. Falon ya koma dole wajen Bappi suka cigaba da hirarsu har Pa. Dama zai kira Anne ɗinne kamar yanda Bappi ya sakashi, koda ya dawo sai ya ce masa bai gantaba amma yaji ƙarar ruwa a bayi....        Babu abinda take sai sakin ajiyar zuciya a jajjere, Anne dake kallonta cike da tausayi ta nuna mata bakin gado tana miƙa mata shayi data saka aka haɗo mata, sai gasashshen nama da akaima haɗi na musamman dan zuwa yanzu ta tabbatar da abinda ke faruwa. Kokwanton da ranta keta mata yasata kiran Dr Hauwa tunda itace ta duba Raudha a wancan likacin da sukai zargin cikine da ita da kuma zubewar cikin. Dr Hauwa da take ɗaukar Anne matsayin uwa ta faɗa mata gaskiyar lamari akan kowancan karon ciwon marane kawai irin na period, hakama lokacin da akace tayi ɓari maganin zubda ciki tasha batare data sani ba, amma Ramadhan yace suyi shiru dan zaiyi bincike akan wanda ya aikata zuba maganin da Raudha tasha., kuma bayan shi Raudha ta karayi har sau biyu tama dubata akan hakan, itace kuma ta sanarma Ramadhan mafitar da zai iya dakatar da Raudha daga azababben ciwon marar da take fama dashi a kowanne period.      Godiya Anne tai mata ta yanke wayar, shiyyasa kafin ma Raudha ta fito Anne tasa aka kawo mata wannan abincin da tasan zai taimaka mata. “Maza kici kafin a samo miki magani”.      Yunwar takeji, amma sam bata son cin abincin. Sai ma wani irin barci dake fisgar idanunta. Haka ta daure taci abinda zata iya tace ta ƙoshi. A kusan tare Ramadhan da Anne suka shigo ɗakin. Sanye yake cikin kananun kaya da tun ɗazun ya canja. Anne ce kawai ta amsa masa sallamar da yayi cikin tsuke fuska. Raudha kam dake fama da kunyarsa dama bata yarda ta motsa ba, ba kuma ta ɗago ba.         Zama yay a ɗaya daga sofa's ɗin. Idanunsa akan matarsa da yakeji kamar yaje ya rungumeta, sai dai ya daure ya fuske dan tunda yaga yanayin Anne yasan fushi take da shi. Yanzun ma maimakon ta kirashi da wayarta Bappi tasa ya kirashi yana sashensa yana ƙullawa da kwancewa akan yanda zaizo ya tafi da Raudha can.         A hankali ya janye idanun nasa a kanta yana jingina kansa jikin kujera ya lumshe su. Cikin ɗan furzar da numfashi yace, “Anne gani”.      Shiru kamar bazata kulashi ba, tanata ƙoƙarin sakama Raudha safa mai kauri a ƙafa bayan ta mulke ƙafar da wani mai da ita tasan amfaninsa. Sai da ta gama tsaf ta kamo hannayen Raudha suma ta shafa mata man ta saka mata safar hannu sannan tai magana batare data dubesaba tana rufe man. “Magani nake buƙata da zata sha”.       Idanunsa ya buɗe tare da ɗagowa. Sai ya saukesu akan Raudha da sam taƙi kallon ko inda yake har yanzu. Kafin cikin ƙanƙan da murya yace, “Waye baida lafiya?”.         Wani shegen kallo Anne ta zubo masa cike da harara kai kace idonta ne zai faɗo. Daƙƙuwa ta watsa masa a zafafe tace, “Ramadhan ungo wannan.”        Tattausan murmushi ya saki mai sanyi yana lumshe idanu ya sake buɗewa a lokaci guda. Fuska ya ɓata sosai cike da marairaicewa kamar ba shugaban ƙasa Ramadhan ba. “Waini Anne kamarma fa kinajin haushi na..”     Harara ta sake dalla masa tana janyo burner ɗin turare kamar zata jeho masa. “Oh saima yanzu ka fahimci haushin naka nakeji ashe....” ta ƙare maganar dayin kamar zata jeho masa har abin yaso bama Raudha dake kallonsu ta wutsiyar ido dariya. Amma saita gimtse yana sake kauda kanta dake mata tsananin ciwo gefe...         Hannu ya ɗaga mata alamar surrender. “Kinga yi haƙuri ajiye burner ɗin. Ina arziƙi ranar Monday a ganni da fasashen kai azata matata ce ta fasamin”.      “Oh to bara na fasa ɗin ai gara sumayi zaton hakane koba komai ta rage zafin muguntarka”.       Tasowa yay daga kujerar murmushinsa na sake faɗaɗa. Ya zauna kusa da Raudha a gefen gadon yana mai ruƙo hanun Anne ya amshe burner ɗin. “Yi haƙuri tagaba goshin Bappi yanzu mi akeso nayi?”. Yay maganar da juyawa yana ɗaura hanunsa a goshin Raudha da kunya ta dabaibaye kamar ta nutse saboda yanda ya zauna gab da ita sosai duk da baya taɓa jikinta dai.         Mikewa Anne tai tana mita ta fice. Ka tambayeta abinda ke damunta kasa a nemo mata magani kafin na dawo kuma ku tattara ku barmin ɗaki barci zanzo nayi”.      Gwalo ya ma bayan Anne, kafin ya maido dubansa ga Raudha. Jawota kawai yay jikinsa ya rungumeta baki ɗaya. Rawa jikinta ya farayi kaɗan-ƙaɗan har yana iya jin gudun da zuciyarta keyi. Ga zafin da jikinta ya ɗauka sosai na ratsa shi.     “I'm sorry Ustazah”.   Ya faɗa a hankali cike da tausayinta. Ita dai babu bakin magana, sai ma lafewa da tai duk da tsoron dake tattare da ita nashi. Kusan mintuna uku suna a haka kafin ya ɗagota daga jikinsa, hannu yasa ya share mata hawayen dake sakko mata a kumatu. “Yi haƙuri kukan ya isa haka Sweetheart, amma miyasa ɗazun baki shiga ruwan dana haɗa miki ba”.        A hankali yake maganar cike da nutsuwa. Da ƙyar Raudha ta iya buɗe baki tace, “Akwai zafi ne”.        “Ai zafin shine zai taimaka miki Ameenatu, gashi ƙinyin haka ya saka miki zazzaɓi har kin tone mana asiri wajen Anne dama duk mai hankali da zai lura da tafiyarki a gidan nan ɗazun”.       A ɗan tsoroce ta ɗago manyan idanunta a karon farko ta kallesa. “Ya Ramadhan kowa ya sani kenan?”. Tai maganar cikin rawar murya wasu hawayen na rige-rigen sakkowa. Dariya da tausayi ta bashi lokaci guda. Maimakon ya bata amsa sai ya sake rungumeta. Kusan minti biyu ya sake ɗagota. “Kinga tashi muje kisha magani dan tun ɗazu nasa aka kawo miki. Ga shi Anne dama ta koremu duk da nasan itama ba iya kwana zatai anan ba sai a bayan Bappi. Shiyyasa kema takeso kije jikin mijinki ki kwanta ki more..”      Hannunsa ta turo dan yanda yay maganar da abinda hanunsa ke mata sai kunya ta sake lulluɓeta. “Ni ALLAH ka bari”.        “Uhhm iyayi, nasan dai kinana daɗi ya rufeki bazaki kwana batare da mijinki ba.”      “Innalillahi... ALLAH Ya Ramadhan ka iya sheri”.              “Su Yaya anji jiki, wane Yayane zaiyi bidirin da nai a daren jiy.....”    Hannu tasa ta toshe masa baki da sauri kafinma ya ƙarasa. Da ƙyar ya iya danne dariyarsa yana janye hanunta. “To shikeman nayi shiru”.        Yasan ya kora su Basma tun ɗazu, Anne kuma tana sashen Bappi, sai kawai ya duƙa wai Raudha ta hau ya goyata. Ƙin yarda tayi itakam. Ganin zata cigaba da ɓata lokacinsa ya ɗauketa cak suka fice tanata mutsu-mutsu da roƙon ya sauketa bai saurareta ba. Dole tai saurin saƙalo hannayenta a wuyansa jin kamar zata faɗi. Ta lumshe idanunta da hawaye ke zaryar fitowa kunya kamar zata halakata, fatanta suje lafiya inda zasu batare da wani ya gansu ba..........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/5, 8:16 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 52_* ..........Sai dai addu'ar tata bataci ba. Dan suna shigowa falon daya raba sashensa da nasu Anne sukai kiciɓus. Sai dai Ramadhan ya ɗauke kai kamar baiga Anne ba dan shima dai kunyar yaji. Ɗan murmushi Anne tai tana binsu da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya da numfashi tana mai binsu da addu'oin zaman lafiya da samun zuri'a masu albarka.        Har ya isa ƙayataccen bedroom ɗinsa da komai na ciki yake kalar royal blue and golden bata yarda ta buɗe idanunta ba. Ya direta a saman lallausan gadonsa da yaji shimfiɗu masu inganci, anan ma da runfa ta net white color mai kwalliyar blue kaɗan-kaɗan.       “ALLAH nauyine dake Ustazah, wannan ai sai kisa na rame”. Ya faɗa cikin kunenta tare da sumbatar kuncinta na haggu. Ita dai bata motsa ba balle ta buɗe ido, sai da ta ɓata fuska da tura baki yace tana da nauyi. Murmushi yayi da ɗallin lips ɗin a hankali.        “ALLAH da zafi Ya Ramadhan”. “Ai dama dan kiji zafin nayi. Idan kuma wannan yayan bai fita bakinki ba ALLAH sai nazo na darje ciwon na banbanta miki tazarar dake tsakanin Yaya da ni”.       “Toni mizance dan ALLAH?”. “Oho ya rage naki tashi kisha magani kisa kayan barci kar wannan towel ɗin yasa mura kamaki”.         Da ƙyar ya iya sakata tashin tasha magungunan da tun bayan sallar magrib aka kawo masa su. Dan tun da yaga yanda take tafiya ya yanke shawarar nemansu. Kayan barci ya ajiye mata ya shige toilet, hakan ya bata damar sakawa da sauri-sauri tai amfani da designers turarurrukansa masu ɗan karen ƙamshi ta haye gadon da sauri tai kwanciyar kai da kafafu tare da yin addu'a kafinma ya fito taja bargo har saman kanta. Dan tasan kaɗan daga aikinsa ya fito da towel babu kunya a gabanta.           Ilai kuwa hakan ya fito kansa tsaye, ya ƙaraso har gaban gadon saboda wayarsa dake ring. Kasancewar ata gefen can ɓangaren Raudha ta kwanta shi kuma sai ya zauna a gefen gadon ta ɓangaren data bari domin shi. Yana goge ruwan fuskarsa da jikinsa yana wayar da A.J dake kula masa da business ɗinsa a can America yanzun. Cikin harshen turanci suke maganar cike da ƙwarewa, dan haka Raudha ta shagala a saurarensa dan yanda harshensa ya karye bama zakace yasan wani yaren Africa ba. Wayar taɗan jashi lokaci dan harya miƙe ya koma gaban mirror. Yana gyara jikinsa yana cigaba da wayar harya shirya cikin tausasan kayan barci, kafin taji ya sake zama a gefen nata. Kaɗan ta ɗaga bargon ta leƙashi, sai tagansa da kofin tea daketa turiri sai kuma lap-top da yake ƙoƙarin kunnawa har sannan wayar na maƙale a kunensa. Shagala tai a kallonsa ƙasan zuciyarta na godema ALLAH daya azurtata da samunsa matsayin miji. Banda ƙaddara ita tasan ko a ƴar aiki bazata ishi Ramadhan kallo ba. Sai dai UBANGIJI shi mai rahamane mai kuma jinƙai. Sannan mai ƙaddara abinda yaso ga waɗanda yaso koda akwai tazarar nisa ta rayuwa ko yare ko addini ko yanki a tsakanin bayinsa.        Yaja lokaci yana aikin sai dai ya ajiye wayar tuni, har barci barawo yay tashiri kan Raudha saboda maganin data sha.             Ramadhan da idanunsa ke faman raɗaɗin barci, ya kai hannu bisa goshinsa ya murza da furzar da iska mai nauyi. Ya gaji matuƙa, gashi abinda yakeyin mai muhimmanci ne. Dan kayan da zasu fitarne a sabuwar shekara A.J ɗin keson ya duba abinda baiyiba su ajiyesa gefe wanda yayi su fara packaging ɗinsa yanda ya dace da mikashi ga yan talla kafin a fitar.        A hankali ya rufe lap-top ɗin bayan ya kashe yana ɗan danna gefen wuyansa alamar riƙewa. kofin daya sha lipton da lap-top ɗin ya sauke kasa. kafin ya koma toilet ya ɗauro alwalar barci sanna ya hawo gadon da danna wani abu net ɗin ta buɗe gaba ɗaya ta lulluɓesu. Sai ɗan hasken fitilar cikin gadon daya kunna ya kashe ta ɗakin gaba ɗaya. Bargon da Raudha take ƙudundune a ciki ya ɗage, sai yaga ashe kai da ƙafa take kwance. Kansa ya ɗan girgiza kawai, yasan tadata yanzu wani aikinne kuma, sai kawai ya kwashi piilos ɗin shima ya maida inda tasa kanta dan bazai iya yarda da kwanciyar kai da ƙafa ba shida matarsa. Gara ace ɗaki suka raba ko gadon. Dan lokaci Amnah ko faɗa sukai da ita bai yarda da raba ɗaki ba. Dole ta kwana tare da shi ko zata kwana masa kukan baƙin cikin daya tusa mata. Inma itace tai masa laifin duk zafin da yakeji a ransa ya gwammaci su kwana waje guda ɗin, shi kuma yasan a inda zai fanshe haushinsa ai (🤣😂mugu ɗan masa🙊).         Sai da ya janye bargo gaba ɗaya ya karemata kallon yanda kayan barcin sukai mata ƙyau kafin ya saki wani ɗan guntun murmushi da iya laɓɓa ya tsaya masa. jikin nata ya taɓa yaji zazzaɓin ya sauka, sai kaɗan da bai ida hucewa ba dai. Filon da take kai shima ya ɗaura kansa suna fuskantar juna. Ya sumbaci goshinta da laɓɓanta sannan yay musu addu'a yaja bargo tare da rungumeta yana sauke ajiyar zuciya.         Da asuba ya rigata farkawa, sai dai yana motsawa itama ta farka. Gaba ɗayanta a jikinsa take lafe da alama hakan ya mata matuƙar daɗi, sai dai suna haɗa ido tai saurin ƙoƙarin janye jikin nata kunya kamar zata nutse. Riƙota yay ya hanata damar juyawar. Cikin ɗan daburcewa take ƙoƙarin faɗin, “Kayi haƙuri ni ALLAH ban san ma....”       Ruf ya rufe mata baki da nashi batare daya bari ta ƙarasa faɗa ba (😜ƙazanta ko brush babu🤕🙄). Duk yanda taso kwatar kanta bata samu damar hakanba. Dole ta nutsu ta barshi ya gama yamutsata san ransa tsoro kamar ya kasheta. Dan a tunaninta za'a tafi next level ne😖. Da ƙyar ya iya yakar ƙansa ya barta jin an sake kiran salla na biyu, ya sauka a gadon da ɗan zafin nama ya faɗa toilet. Ruwa mai ɗumi ya sakarma kansa yana mai sauke nannauyan numfashi da rumtse idanu. Sunan ALLAH ya dinga ambata dan yasan lallai akwai matsalolima ba matsalaba. Gashi da alama Raudha tamkar Amnah take itama zatai shegen raki duk da ita daba sickler ɗin ba. Dole ya haɗa harda wankan lada. Koda ya fito yay mata maganar ta tashi bata motsaba dan kunya harya zura jallabiya yasa turare ya fice. Sai dai ya gargaɗeta karya dawo ya sameta a kwance bata tashi tayi salla ba, ta kuma sake shiga ruwan zafi inba hakaba ya dawo da kansa zai sake gasata.           Raudha da gaba ɗaya a firgice take da Ramadhan ta miƙe da sauri bayan ta leƙo ta bargo ta tabbatar ya fita. Toilet ɗin ta afka itama. Ta watsama jikinta ruwa da ƙara gasa ko'ina duk da dai Alhmdllhi garas ta tashi yau sai dai rashin jin karfi na sabo.             Koda ya dawo a saman sallaya ya sameta tana karatun alkur'ani. Hakan ya masa daɗi sosai, sai shima kawai ya zauna suka cigaba dayi tare. Duk da mamaki ya matuƙar ɗaure kan Raudha jin yanda yake karatu a nutse cikin daddaɗar muryarsa mai faɗi da amo da gaba ɗaya ta danne ƙarfin tata siririya mai zaƙi. Sunyi karatun da yawa sannan sukai addu'a. Kanta a ƙasa tace, “Ina kwana”.     Bai amsaba, sai dai ya kafeta da idanu, ɗan dagowa tai kaɗan sai suka haɗa ido, zata maida ya riƙo habarta da hanun damarsa. “Karki kuskura ki rufe idanun nan”. Ya faɗa da sauri ganin tana niyyar lumshesu kuwa. Yanda taji babu wasa a furucinsa ya sata dakatawa. Sai dai taƙi yarda su haɗa ido....       “Ni bana son irin wannan gaisuwar ga matata shiyyasa ban taɓa amsa miki ba”.      Duk yanda taso jurewa kasawa tai, sai da ta ɗago ido ta kallesa sai karaf a cikin nashi da launinsu ya canja. Ƙwayoyin cikinsu bakaƙe masu ƙyalli ya juya mata cike da tabbatarwa. Ta risinar da nata tsigar jikinta na tashi dan ta rasa abin cewa kuma. Zuciyarta na tunanin (Banda gulma irin tashi wace gaisuwace kuma bayan wannan da aka banbanta tsakanin mata da miji da sauran mutane? Ita dai tunda ta taso a gidansu irin wannan taga anama Abbansu).       A bazata kawai taji saukar lips ɗinsa saman goshinta. Kafin ta dire numfashi ya saukesu kan lips nata ya bata light k.. Harya janye kuma ya sake maidawa ya cafkesu da ƙyau yana matse hanunta dake cikin nashi tsam.        A gwame ta dinga fidda numfashi kamar yanda nashi ke fita a harɗe, har saida yayi yanda yake so sannan ya barta dan kansa. Cikin rufewar idanu ya lalubi kunenta.      “Wannan itace nake buƙata a kowacce safiya idan mun tashi, da kuma idan na dawo aiki shine sannu da zuwana”.       (Tabb ashe kuwa akwai tsallen baɗake) cewar Raudha a zuciya. A fili kam yanda yay maganar babu wasa a ciki ya sakata jinjina masa kanta kawai batare da tace komai ba. Mikewa yay shima ya mikar da ita batare da ya sake cewa komaiba. Dolenta tabi yanda yakeso suka koma gado bayan ya cire mata hijjab ɗin ya barta da abayarta dan shima yana son kauda kansa ga abinda zuciyarsa ke bijiro masa.       Fargaba ta hanata barci har sai da taji yana sauke numfashi a hankali alamar shi ya fara sannan tai nata itama tunda taga ba abinda take tsoron bane zai faru..........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/5, 8:17 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 53_* ..........*_JIHAR ƊILLO (HUTAWA)_*            A Hutawa kam kowa yaga M. Ɗan-azumi yanzu sai yay matuƙar mamaki. Dan kamar yanda ya ƙudiri ƙara sabon aure ya auro dalleliyar budurwa sabuwa dal a kwali. Kai daka ganta kasan ƴan kuɗin ta biyo. Baƙaramin tashin hankali Larai ta shiga ba, dan saika ɗauka ma wani sabon haukane ya hau kanta. Data nema birkice masa sai ya aikata gida taje ta huta. Roƙo iya roƙo ita da danginta amma ya birkice musu ƙememe dama fitinarta ta isheshi, ga baƙin cikin rabasa da masoyiyarsa Asabe da har yanzu ko ɗigon sonta baibar zuciyarsa ba. Ganin haka Baba Nafi ta ƙara kama kanta da mutuncinta a gidan, dan tun dawowar Inna da ƙaninsa da matarsa dama gidan ya sake zama sai a hankali. Gadai jin daɗi yanzu a cikinsa amma kowa zaman haƙuri yake da ɗan uwansa saboda fitinar sirikarsu dabance a rayuwa, shi kuma M. Dauda na biye mata dan duk haukarsa yana ƙaunar Innarsa.           Tun auren Raudha alaƙar zuminci mai ƙarfi ke tsakaninsa da hakimi, hakama jama'ar gari sosai suke respecting nashi kowa burinsa ya zama abokin mu'amularsa (kaiko sirikin shugaban ƙasa fa ba wasa ba😝). Da wannan damar M. Dauda kan samu na hura hanci sai ya zaɓi wanda yaso ayi zumincin, shi da M. Gambo ne dai ana nan tif da taya, sai dai baisan M. Gambo nata masa zagon ƙasan ƙoƙarin kiran Asabe a wayaba kullum, wani lokacin harda mata ɗan text na soyayya dan ƴar sakandire ɗin nan dai shi da M. Dauda sunyita. Ita Asabe har zuwa yanzu batasan wanene ba. Dan tun tana sharesa da masa masifa idan ya kirata harta ɗan fara kulashi.        Hakimi daya fahimci rawar kan M. Dauda bata risinaba saima giyar kuɗi dake neman ɗorasa a wani layin bayan wanda yake kai yasa shi ƙara jansa a jiki yana masa nasiha, ya kuma bashi sarautar data tilastashi kullum zuwa gidan Hakimi ayi fadanci dashi. Koda yake mugun ɗagawa da faɗi yake da sarautar, inma ka kira sunansa baka haɗa da sauratarba to kuwa kaji barbaɗin jaraba daga sama har ƙar zai zugeka yana hura hanci da kiran shi ya wuce raini ai. Surikin shugaban mai ƙasar yake baki ɗaya, Baba sama baba ƙasa yake kiransa kuma saiya risina yake gaisheshi koda a wayane balle wani ƙaton ƙawai da talauci yayma katutu. (😂🤣ALLAH ya bar mana Man Dauda).       Ya sayi ƴar kwariɓar motarsa ana yanga da ita kwana biyu ta birkice, cike da masifa ya maidawa bakaniken daya saida masa yace wlhy koya dire masa kuɗinsa kokuma yasa azo daga Bingo a cukuykuyesa yasan dai uban matar shugaban ƙasa yake. Da farko makanike ya ɗau abin wasa, dan mahaukacima suka maida M. Dauda shi da yaransa. Saiko gashi ko mintuna ashirin baiyi da barin wajenba motar ƴan sanda har uku sunzo sun yayesu gaba ɗaya har yaran nashi. Dan kuwa M. Dauda yana zuwa police station d.p.o da ayanzu ya gama haddacesa shi da yaransa koda ɗunbin alkairin da suka samu a ranar auren ƴarsa da shugaban ƙasa sukai masa tarbar mutunci. Harda matsar kwallan munahinci wajen faɗa musu abinda akai masa a gareji. Rai ɓace d.p.o ya bama yaransa umarnin zuwa a kwasosu yana bama M. Dauda haƙuri.        “Baba ai kun wuce ko kallon banza yanzu a ƙasarnan, kunefa iyayen masu ƙasar. Gamu nan tunda ɗanku ya hau mulki albashinmu ma ninkashi akai tsabar adalci na wannan shugaba. Ai mu babu abinda muke sai fatan alkairi a garesa, mun kuma tabbatar lallai matasa masu jini a farce ƙasar NAYA ke buƙata irinsa.. ALLAH ya ƙara masa zaman lafiya da matarsa nan da watanni asake zuwa taron suna NAYA muci musha muyi warkan. Dan muna alfahari first lady tamuce wlhy”.      Daɗi kamar zai kar m. Dauda, ya dinga washe haƙwara yana sake baje babbar rigarsa dan ɗinkunan alfarma da Alhaji Hameed Taura yay masa na biki har kala goma sune suka zama na faɗi yanzu a gari. Lokacin da aka shigo dasu Gali a ɗage M. Dauda yake kallonsu da watsa hannaye gaba. “A rufeminsu har sai na manta da wanzuwarsu sannan a tunamin”.      Cikin roƙo da magiya kanikawan nan ke roƙon Alhaji Dauda (dan tunifa dama gargaɗi yake abar kiransa M. Dauda😂😜). Amma ko kallonsu baiyiba. Cikin takun ƙasaita ya buga babbar rigarsa aka fice dan d.p.o ya bada motarsa a maidashi gida.        Kwanakin kanikawan nan huɗu a ofishin ƴan sanda sannan ya bari aka sakesu da sharaɗin maido masa kuɗaɗensa nanda sati guda. Hakan kuwa akai sai gasu da kuɗaɗensa cif sun kawo, ya dinga antaya musu harara yana sake baje riga da hura hanci. Bayan ya koma gida ne ya nema kuɗin ya rasa da kwana biyu shine ya yanke jiki ya faɗi har saida aka kaisa asibiti. Wannan ne dalilin zuwa su Fatisa dubashi har suka sanarma Raudha, to ayanzu haka dai ya haɗa duk yaran gidan nasa da matan ya tabbatar musu idan kuɗinsa basu dawoba nera dubu ɗari bakwai wlhy suma cell zaisa a zubasu har sai sun magantu. (🤣😂To bara muga ta inda kuɗin Alhaji Malam Dauda surikin shugaban ƙasar NAYA zasu fito). *_BINGO CITY (TAURA HOUSE_*             Barci sukasha sosai kamar yanda Ramadhan yaso. Ga Anne daga falo na musu gadi dan koda su Basma suka taho wai anan zasuyi breakfast korasu tai duk da tasan da wahala hayaniyarsu takai ga sashen Ramadhan ɗin. Dama tunda ya shiga ya gaisheta bayan sallar asuba yace kar ai musu breakfast da wuri. Dan haka ba'a ɗora ɗinba kuwa sai kusan sha ɗaya na safe. Zuwa sha biyu an kammala komai an kawo falon part ɗinsa an shirya bayan an gyarashi yanata ƙamshi duk da bawani datti yayi ba.          A yanzu ɗinma kusan tare suka farka sai dai motsintane ya tadashi. Tai ƙoƙarin janye jikinta ya hana hakan. Cikin yanayin kasalar barci ya mika hannu ga side drawer ya ɗakko agogonsa yaɗan kalla time cikin lumshe idanu da buɗewa. Har sha biyu ta gota. Agogon ya ajiye da kai lips nashi a goshin Raudha da taƙi buɗe ido ya sumbata. Kafin ya saketa ya sauka baki ɗaya batare da yayi magana ba.      Bata iya motsawaba sai da taji ya rufo toilet ɗin. Ta miƙe da ƙyar itama dan barcine da bata sabayi ba ace tun sallar asuba har kusan 1. Gadon ta shiga gyarawa a ɗan gurguje, ta maida net ɗin yanda ta gansa, sosai yake birgeta dan ya sake kawata gadon da ɗakinma baki ɗaya. Har falo ta fito neman kayan shara, cikin sa'a ta samu a cikin kitchen bayan ta karema falon da kitchen ɗin kallo. komai akwai na buƙatar ɗiya mace har tana mamakin sai kace mai mata.      Shara ta gama tana tsaka da mopping ya fito. Bata yarda ta kallesa ba, sai shine dake binta da kallo ya nufi mirror yana faɗin, “Waya saki wannan aikin?”.       Amsa ta bashi batare data yarda ta kalla inda yakenba dai.      “Ba kowa”.   Komai bai sake cewaba harta kammala ta fita da kayan, taɗan jima kafin ta dawo da fatan ALLAH yasa ya saka kaya. Sai dai addu'ar tata bataci ba dan har lokacin ɗaure yake da towel tsaye a gaban Wadrobe da alama kaya yake nema. Kaita kauda cikin sauri ta faɗa toilet.      Baki yaɗan taɓe dan duk yana kallonta ta gefen ido. Ta jima bata fitoba, har sai da ta leƙo taga baya ɗakin. Da sauri-saurin tai shirinta cikin atanfa datai mata ƙyau matuƙa, ga ɗinkin ya fidda jikinta tsaf kamar ka saceta ka gudu. Ɗauri tai mai sauƙi amma ya mata ƙyar ta saka ƴan kunne kawai harda yafa mayafi sannan ta fito da nufin zuwa gaida mutanen gidan duk da kunya da nauyin ƙin zuwa akan lokaci na cinta. A tunaninta Ramadhan ma nacan, sai dai tana fitowa falo taci karo da gogan nata zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallon labarai a television da alama sallar azhar yaje yayo kawai ya dawo.      Tsamm tayi a ƙofar ɗaki kamar bazata karaso ba. Sai kuma cikin dauriya ta cigaba da takowa har inda yake. Kanta a ƙasa tana wasa da zobon hanunta tace, “Ya Ramadhan zanje naje na gaida su Anne”.     Maimakon ya amsa mata duk da idonsa ba'a kanta yakeba sai taji ya riƙota ya zaunar saman cinyarsa. Mutsu-mutsu zata fara ya dakatar da ita ta hanyar yaye veil ɗinta gaba ɗaya. “Banda ƙauyanci miye na zuwa gaban miji da veil?”.         Duk da maganar ta bata haushi sai ta dake. A sanyaye tace, “Wajensu Anne fa zanje”.       Wasa yake da jelan kitsonta idonsa a tv, “Sunce sun yafe yau ko ƙofar corridor ɗin can bazakije ba nayi gaisuwan da taki ai tun ɗazun”.       “Kai Ya Ramadhan wlhy bai kamataba ace banje na gaishesu ba. Gashi dama lokaci ya gama shigewa ai da kunya”.         Maimakon amsa mata maganar ko barinta tafiya sai ya ɗagata daga jikinsa shima ya tashi, dining ya nufa da ita dan shi ta yunwar cikinsa ma yakeyi. Dolo ta haɗiye komai dan yaci serious kamar bashi ba. Tsorone yaɗan fara kamata na gudun karfa mutumin nan ya juya mata baya bayan ya rabata da mutuncinta. Dan taga tun jiya ya koma sha mata ƙamshi irin yanda yakeyi mata a baya. Da wannan tunanin tai saving nashi komai, zata zuba nata ya hanata yay mata nuni data zauna kawai. Dole tabi umarninsa zuciyarta fal tsoron abinda ba haka bane. Shi Ramadhan yana ɗan ɗaurewa ne kawai dan gujema abinda zuciyarsa ke kwaɗaita masa game da ita. Dan tausayinta yakeji matuka. Amnah mai shekaru da suke gab da nashi duk da tanada lalura bata iya jure ɗaukarsa akoda yaushe balle ita. Dan sauda dama idan yaje gareta sai tayi kuka balle Raudha da yakema kallon jaririya. Shi kansa yasan yayi juriyaa shekarun da babu Amnah, amma ya tabbatar ɓacin rai da tashin hankaline suka girmama juriyar tasa, yanzu ko daya ɗan ɗana bayajin zai ɗaga ƙafa duk da ƙoƙarin hakan da yakeyi.       Tare sukaci abincin Raudha nata sinne-sinne. Shi dai bai kulataba. Daga ƙarshema ya amshe cokalin ya koma bata da kansa. Ina ƙasa ta shige amma babu damar gardama dan ya haɗe girar sama data ƙasa........✍     *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/5, 8:17 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 54_* ..........Koda suka kammala falon suka sake dawowa, ya kuma ɗaure fuska yanda bazata roƙesa fitar ba. Dole ta kama kanta dan kuwa koda ya zaunar da itama karshen 3seater sai ya kwanta shi ya ɗaura kansa a cinyarta. Ya kuma kamo hannayenta duk biyu ya ɗora a sumarsa sannan ya canja musu tasha.      Raudha babu bakin magana, tun tana cuna baki gaba har laushin sumar da takema kallon zatai ƙarfi saboda yanayinta na irin tamu ada ya fisgeta ta tura yatsunta a ciki a hankanli. Lumshe idanu Ramadhan yayi da sauke numfashi a hankali dan hakan abune da yake matuƙar so a rayuwarsa shima.       A hankali ta cigaba da wasa da yataunta cikin sumar cike da shauƙi harta shagala ta manta dawa take tare. Haka ta cigaba da wasa da sumar kansa cikin shagala tana kallon film, yayinda shi nashi idon ke'a lumshe ya lula duniyar tunani.       ★Kowa bai damu da rashin ganinsu a gidan ba har yamma, sai gimbiya Su'adah ce data cika tai fam da takaici, dan har Muneera ta aiko tai mata cid ɗinsu ta koma ta sanar mata ai duk yau ma bata tunanin Raudha taga rana. Gara Ramadhan kan fita yayo salla. Dama kuma shi yaje ya gaisheta da safe ma.. Har lunch ta shirya masa da kanta da maganin da Adda Asmah ta kawo waina fidda son Raudha a ransane ya tsaneta. Har sai ya mata korar kare a government house. Sai dai abinda bata sani ba na tsananin jan ra'ayinsa da mallakar zuciyarsane akan Ayna'u, malamin daya bata ya tabbatar mata Ramadhan yaci maganin nan sai ya manta har gimbiya Su'adah ɗin ma da kaf Taura family ya koma ƙarƙashin ikon ƴarta Ayna'u, hatta da mulkin ƙasar NAYA Aynah ce zata koma mai tsarawa da zartar da yanda za'ayi.       Sai dai kuma Ramadhan ya kwafsa mata baije sashen da rana ba. Washe garima babu wanda ya gansu, sai randa suka cika kwana uku yaje sashen nata shi da Raudha da rana. Hakan baisa ta gaza tanadin na dare ba a cikin gasashshiyar kazar da taji kayan haɗi na ban mamaki aka aika masa har sashen Anne da kunun madara da yasha zuma a ciki a wannan rana. Ita kanta Raudha basu ƙyaleta ba. A baki Bilkisu sukaji abinda tafi so, amma kasancewar guri ya ƙure aka haɗa mata zoɓo mai sauƙi aka barbaɗe da magani sanin Ramadhan baya shan zoɓo shi kuma.      Tunda Lubnah ta nufi sashen Anne da abinci sai kuma zuciyar gimbiya Su'adah ta shiga ƙunci, rasa mike mata daɗi tayi tanata faman kaikawo a bedroom ɗinta. Gaba ɗaya zuciyarta na nuna mata ƙiyayya da abinda ta aikata akan ɗan data haifa saboda tsanar matarsa. Sai dai kiyayyar da takeji akan Raudha nata ƙoƙarin danne gaskiyar dake son bayyana kanta ga kuskuren da idonta ya rufe ta kasa fahimta...        Sam Anne bata kawo komai a ranta ba ta haɗa kayan wajen gimbiya Su'adah a cikin dinner ɗin su Ramadhan. Taya ma zatai tunanin za'ai amfani da uwa wajen cutar da ɗanta? Ita bama ta taɓa kawoma ranta wani cikin surukan nata na bin malamai koda akan Pa ba. Tama shedesu akan hakan ɗari bisa ɗari dan bata taɓa ganiba gaskiya. Ita kuma mutumce da bata yanke hukunci akan abinda bata ganiba sam.           Raudha yarinyace mai tsarta, haka kawai taji gabanta na faɗuwa lokacin da sukai zaman cin abincin. ALLAH ta shiga ambato a zuciyarta, yayinda Ramadhan gashin kaza ya ruɗesa ya ɗan ɗiba da cokali mai yatsu ya kai bakinsa yana ambaton “uhhm”. Kallonsa tai kawai batare data iya cewa komai ba. Sai da zai kai lauma ta biyu ne ALLAH ya bashi ikon ambaton Bismillah. Ƙaramar ajiyar zuciya ta sauke, koda yace suci kazan catai ta ƙoshi, dan itakam idan tace zatai irin cin namansa ai matsala za'a samu. Bai wani ci da yawa ba ya tashi akan zaije wajen meeting idan an tashi yazo yaci. Amma ta tabbatar taci abinci inba hakaba ya dawo ɗura zai mata da kansa. Gimbiya Su'adah ce ƙarshen shigowa. Ramadhan ya gaidata cike da kunyar tun safe bai koma sashenta ba. Koda yake Anne ma da suke tare sai ya fito salla take ganinsa. Ya ɗanyi mamakin yanda ta amsa masa a sake, ta kuma gaida su Anne itama. Kowa zaune yake a kujera har su Yafendo, shine kaɗai zaune ƙasan lallausan carpet ɗin falon domin girmamawa ga iyayensa.      Ba Ramadhan ɗin kaɗai ba, hatta su Pa sakewar gimbiya Su'adah ya basu mamaki, duk da suna danganta hakan da abinda ta kawo take ganin zataci nasara. Su dai babu ruwansu, idan Ramadhan ya amince ya karɓa zasu tayasa so, idan baya so kam bazasu masa dole ba tunda yay musu biyayya akan Raudha kar su cika shiga hakkinsa.   Bayan an buɗe taro da addu'a Bappi ya bama Gimbiya su'adah damar faɗin abinda tazo musu da shi kafin yau. Tunda ta fara bayani Ramadhan ya ɗago a rikice yana duban mahaifiyar tasa. Fara'ar fuskarsa kuwa tuni ta ɓace sai dai komai baice ba harta kammala. Bappi ya jinjina kansa da maida hankalinsa ga Ramadhan da ya maida kansa ƙasa.       “Ramadhan kaji abinda mahaifiyarka tace. Tana buƙatar ka auri ɗiyar ƴar uwarta domin likita ya sanar matarka bazata sake haihuwa ba saboda ciki data zubar a kwanaki”.        Ramadhan daketa jera kalmomin innalillahi a zuciya ya nisa da ƙyar. Abinda Maah bata sani ba ya daɗe da kammala bincike akan yanda Raudha tasha magani, sai dai takamaimai wanda ya bama su Muneera maganin suka zuba mata dama yake nema ruwa a jallo. Sai gashi a cikin sauƙi ta tabbatar masa da itace, domin inba itace ɗinba taya tasan mahaifar Raudha zata lalace harta gagara haihuwa....?       “Ramadhan!”. Inna dake gefensa ta kira sunansa. Numfashi ya furzar da ɗago idanunsa da suka kaɗa ya kalleta. Sai kuma ya maida kansa kasa yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa.       “Kiyi haƙuri Maah bazan bijirema umarninki dan baki isaba. Sai dai zanyi hakane tare da tabbatar miki wannan BAƘAR INUWAr da kike hangemin gwara ranar da kike gudanmin da ita. Ban musa miki wasu a dangin Ameenatu nada tabo na ƙaddarar rayuwa ba, amma ina son ki sani wlhy Ameenatu yarinyace kamila mai addini. Sannan ta kawomin mu..tuncin...ta har gida. Idan zan faɗa miki wacece wadda kikema kallon mutuniyar kirkin a yanzu zakisha mamakin hakan. Maah laifin wani baya shafar wani ko'a wajen UBANGIJI. Sannan ALLAH na fidda rayayye a cikin matacce. yana kuma fidda matacce a cikin rayayye. Hauhuwa kuwa ta ALLAH ce, amma insha ALLAH akoda yaushe zaki iya ganin zuri'ata basai na auri wata ba”.      Dukkanin wata fara'a dake a fuskar gimbiya Su'adah ta ɓace ɓat, baka ganin komai sai ɗunbin ɓacin rai da azabar masifa. Gasu Pa kuwa gaba ɗaya murmushi ne kwance a fuskokinsu, bana bijirema gimbiya Su'adah da Ramadhan yayi bane. Na yabo da tabbatar da ingancin tarbiyyar Raudha da sukajine daga bakinsa. Wanda su sanin kansune Ramadhan baya iya boye abu inhar bai masa daɗi ba zai faɗa, hakama idan yayi masa zai yaba koda da murmushi ne. Koba komai hankalinsu ya sake kwanciya da yarinyar da suka jima suna kyautatama zato.       Babu wanda ya sake cewa komai har ita. sai Inna ce tai musu nasiha da gaba ɗaya take nufin da gimbiya Su'adah take amma sai ta haɗa kowa da kowa a ciki. Daga haka taron ya tashi babu wani armashi. Dan ko bikin yaran gidan da sukaso tattaunawa a yau ɗin shima bai yuwu ba dole aka barsa sai wani lokacin dan ana jiran sauran gidajen angunan su kawo kuɗi ne. Ƴammata kusan shidda za'a aurar a gidan nasu Ramadhan. Ciki harda Lubnah da Bilkisu kuwa. Sai Sumayya, Rufaidah, Ai'sha da Ummita. Dukansu sunyi karatu wasunsu ma na aiki, Ummita ce kawai take kan karatun saboda manemin nata ya takurane yasa za'a haɗa da ita amma sa'ar Muneera ce ma. Koda yake ita kanta Muneera ɗin ta isa auren ai kawai dai dan akwai yayuntane.        Babu wata walwala Ramadhan ya koma wajen Raudha, dan yasan ma'anar shirun mahaifiyarsa. Tuni ita har tayima shirin barci. Tana zaune ne a kan gadon tana assignment ɗin makaranta da aka basu na cikin hutu, sai dai sanye take da hijjab a saman kayan barcin nata. A kallo guda ta fahimci ransa a ɓace yake, cikin dauriya ta masa sannu. Bai amsa ba sai dai ya kwanta a gadon tare da ɗoro kansa saman cinyarta bayan ya ture takardun gabanta gefe.         “K dole kin zama ƴar boko ko?”. Ɗan murmushi tayi kawai dan yanda yay maganar kamar mai son huce haushinsa akan bokon nata ne. Cikin san kauda masa damuwarta tace, “Harka tunamin Abbanmu. Idan mukai masa laifi koya tashi baida ko sisi sai ya hana kowa zuwa makarantar boko ranar. Ya ringa faɗin, “Anma fasa bokon, daga yau bazaku sake zuwa ba, bandama shegantaka irin ta bature yabi duk ya katantane duniya ya hana kowa zaman lafiya, komai bazaka samesa yanda kake muradi ba sai kayi wani abu shege a.b.c.d kai nifa shiyyasa ma ana kaini ina tserowa a makaranta da ƙyar na haɗa sakandire ɗin ma”.       A bazata dariya ta ƙwace masa. Har haƙoransa na bayyana baki ɗaya sai dai ya kai hannu yana karewa. “ALLAH na lura Abba ɗan darune?”. Ganin yanda ya karɓi zancen ya saka Raudha dake nata ƴar dariyar itama faɗin, “Tab damma baka sanshi bane. Wlhy duk randa darun Abba ya tashi gidan nan ranar kowa sai yaji a jikinsa. Ko ruwa ka cika kofi zakasha sai yace ka ƙara masa talauci kana baƙin cikin ya zama mai kuɗi”.      Yanzu kam sosai yake dariya. Raudha da farin ciki ya cikata itama ta tura yatsunta duka a cikin gashinsa tana masa susa. Nan ta shiga bashi labarin M. Dauda sai dai na hankali wanda tasan mutuncinsa bazai zube a garesa ba. Cikin amincin ALLAH sai gashi ƙaunar mahaifinta ta sauka masa a rai har yanajin sassaucin takaicin halayyarsa tada da bincike yazo da ita.        “Ya kamata ma muje mu gaishe da Abba Hutawa gaskiya”. Cak Raudha ta dakata da susan da take masa a cikin gashi ta tsurama ƙyaƙyƙyawar fuskarsa ido idanunsa a lumshe suke yayin da hannayensa duka ke harɗe a ƙirjinsa yana kwance rigingine. Yanda ya nutsu zai baka tabbacin susar da take masa cikin gashi na masa daɗi. Ya buɗe lumsassun idanunsa da suka canja launi a hankali ya zuba mata su. Gira yaɗan ɗaga mata yana sassanyan murmushi. “Yadai naji kinyi shiru Ustazah?”.      Hawayen da suka ɗan cika mata ido ta haɗiye, cikin ƙaƙaro murmushin itama tace, “Nagode da karamcinka”.         “Cmon johre. An gaya miki Abban nakine ke kaɗai banson iyayi”.    Yay maganar yana dungure mata hanci da ƙoƙarin miƙewa zaune. Toilet ya shiga, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya da hawaye lokaci guda. Wani abu mai muhimmanci na sukar ranta. Koda ya fito wanka cayay ta kawo masa sauran namansa. Dan bacin ran daya shigo da shi ta riga ta gusar da shi. Kawo masa tai harda kunun, yako ci abinsa yay ƙat sannan ya koma bayin yayo brush, koda ya dawo assignment ɗin ta nuna masa inda bata gane ba.        “Ustazah! Kibar batun Assignment ɗin nan nima inada nawa Assignment ɗin mai kawo lada ma.”            “Please Ya Ramadhan dafa an koma hutu idan ALLAH ya kaimu zamuyi submitting”.      Gadon ya hawo yana ɗaure igiyar rigar barcinsa. Ya zare mata hijjab ɗin jikinta sannan ya ɗauka takardar data rubuta questions ɗin da amsar data rubuta daban na wanda ta gane. “Yarinyar nan kanki fa naja”. Ya faɗa cikin ɗage mata gira. Murmushi kawai tayi da maida kanta ƙasa. Shima hankalinsa ya sake maidawa ga takardun yana faɗin, “Ai gyaran ma kaɗanne”. Bayani ya shiga mata dalla-dalla harma akan abinda bata tambayesa ba, dan shima yayi course ɗin sanda yana jami'a. Sosai taji daɗin bayaninsa har tana sake zaƙulo masa wasu tambayoyin. Sai dai taƙi sakewa da jikinta sai faman karewa take da hannu kamar mai jin sanyi. Tsaf yana lure da ita amma yay kamar bai gani ba. Zata sake jeho masa wata tambayar ya turo kayan karatun nata ƙasa da jawota jikinsa yana faɗin, “K ni na gaji da aikin bautar bature zo kiji wata magana”.     Gabantane ya shiga faɗuwa. Sai dai ko saurarenta baiyiba yaja musu bargo ya matseta a jikinsa yana shinshinar wuyanta da kai mata kiss's..........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/5, 8:17 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 55_* ..........Yau ɗin ma dai kukan tasha sosai fiye dana ranar ma, a ganinta yauɗin ma babu banbanci da shekaran jiyan. Shidai aikinsa lallashi da jinjina ragwantakarta, duda dai yasan shi ɗin bana wasa bane. Bayan sallar asuba koda ya nuna sake ziyartarta kuka ta saka mishi iya gaskiyarta tana roƙonshi idan ya sake mutuwa zatai ita dai. Ta bashi tausayi ta bashi dariya kuma. Amma sai ya gimtse da nuna mata baifa san zancen ba a haka zata saba ai. Kuka sosai ta dingayi tana yarfe hannaye kamar wata ƙaramar yarinya. ALLAH ne ya taimaketa Bappi yay kiransa zasuyi magana, dan dama shirin office zaiyi daga Taura house can ya nufa. Ita kuma sai ƙarfe ɗaya zata wuce gaida su asabe daga can ta zarce gida.        Badan yaso ba dole ya miƙe ya zura doguwar rigar jallabiya ya fita batare daya kalli Raudha dake maƙure cikin labule ba tana sharar hawaye. Ganin ya fice ta faɗa toilet, wanka tayi da ƙara gyara jikinta dan ita dai harga ALLAH zafi takeji sosai. Yau dai anyi jarumta an shiga ruwan zafi tanata raki ita kaɗai. Koda ta fito harta shirya ta gyara ɗakin bai dawo ba. Dan haka ta saka hijjab ta fita gaida jama'ar gidan.      Kamar ko yaushe bata wani samu tarban arziki ga gimbiya Su'adah ba. Sai ma zageta tas da Lubnah da Aynah sukayi wai kwana uku batazo ta gaishe da Maah ɗin ba. Bata da abin faɗa dan tasan ita mai laifi ce. Yau ma da taimakon Bilkisu ta baro sashen bayan ta zage Aynah da Lubnah duk da kuwa duk sun girmeta. Masifa taitaima Raudha akan lokaci yayi da zata ƙarfafa ranta tabar zama su Lubnah na takata yanda suke so koda agaban Maah ne. Maah uwace, amma su ai ƙannene a gareta koda sun girneta tunda kanen mijinta ne. Murmushi kawai Raudha tayi amma komai batace ba.         Ƙin komawa tai part ɗinsu duk da Anne tace Ramadhan ya baro wajen Bappi, suna nan a falon suna taya Anne shirya table Ramadhan ya fito cikin shirin office. Ɗanyar shaddace golden yollow a jikinsa daketa maiko harda babbar riga, sai dai bata cika girma ba dai-dai irin ta matasan zamani da suke yayi. Sai baƙin takalmi _chukka boot_ da hula tangaran daketa ɗaukar idanun mai kallon. Ko kunya babu ya miƙama Raudha dake ƙoƙarin gyara mayafinta agogonsa _zenith_ wai ta saka masa. Sai wani faman ɗaure fuska yake. Sai da taɗan dubi sashen da Bilkisu da Anne suke taga sun ɗauke idanunsu kamar basu san mike faruwa ba sannan ta amshi agogon ta ɗaura masa kunya kamar ta nutse.       Kona gode babu ya raɓata ya wuce zuwa dining. Ta ɗan bisa da kallo ranta fes dan gara wannan fushin da azabar da tasan zata sake ɗanɗana a hanunsa. Anne ce ta sakata dole ta haɗa masa abinci, sannan suma suka zauna har Bilkisu da data karya anan.      “Yaya kamar bakajin daɗi?”. Cewar Bilkisu cike da kulawa. Anne da tun ɗazu hankalinta na kansa itama dai kallonsa tai. Ya ɗan yamutsa fuska da sake tsuketa. Sai dai komai baice ba. Anne ce ta sake maimaita masa tambayar Bilkisun. Cikin ɗan haushi-haushi yace, “Kawai bana son fitar ne”.      Ƴar dariya Anne da Bilkisu sukai da lallashinsa. Raudha kam da tasan ainahin fushin murmushi kawai tai taƙi yarda kuma su haɗa ido. Shi ya fara miƙewa. Harya gama sallama da Anne zai wuce ya faki idonta ya sakarma Raudha ranƙwashi akai.     Ba shiri ta saki karamar ƙara. Gaba yay abinsa ko waiwaye babu, Anne da komai ya faru akan idonta tace, “Mugunta dai babu ƙyau wlhy Ramadhan mita maka?”.       Ƙin tankawa yay, sai ya ɗagama Anne yatsunsa biyu alamar bye. Ita dai Bilkisu dariya kawai take ranta fal nishaɗi haƙarsu ta kusa cimma ruwa. (Batasan tuni tacin ba itace bata da labari). Bayan mintuna kaɗan suka jiyo jiniyar tafiyar motocinsa. Hakan ya bama Raudha damar bararrajewa suka daura hira da Bilkisu da Anne. Kusan ƙarfe goma baƙuwar Anne ta iso......          Sosai kunya ta lullube Raudha lokacin da hajiya take bayanin kayan da Anne tasa aka kawo mata nagartattu haɗin sakwattawa birnin shehu tun daga ƙasar Nigeria. Hajiya. Bata wuce ba sai kusan sha biyu, a lokacin Raudha ma ta mike taje tai shirin dan lokacin tafiyarsu ya gabato. Umarnin Anne ta bi na zuwa yima su Gimbiya su'adah sallama. Bayan ta kammala da kowane part harsu Yafendo ta nufi part ɗin surukarta a ƙarshe. Ita kaɗai ta samu a falo hakimce cikin kwalliya sai zuba kamshi take, duk da tasan bata kaunarta ta daɗe da bata lambar girma da yabo na iya tsara kwalliya da ado, dan sosai jikin gimbiya Su'adah ke ɗaukar wanka, ƙyaƙyƙyawa ce itama gata fara tas masha ALLAH, matsalarta kawai bata fara'a kamar wata sojiya😖.       Kamar ko yaushe data gaisheta bata amsaba. Ta watsar da ita a durƙushe tsahon muntina, Raudha data ga karta makara tai mata sallama zata mike amma saita dakatar da ita. Cike da gadara da tsanar data kasa haɗiyewa tata tace, “Kin dage sai kin zauna da Ramadhan duk da na nuna miki hanyar salama kin runtse idanunki. Okay fine, sai ki shirya shigowar Aynah ku goga kishi, mai sa'a ta haye”.      Wani irin dummm kunen Raudha ya ɗauka. Ta ɗan ɗago ido ta dubi gimbiya Su'adah. Sai dai wulaƙantaccen kallon data maka mata ya sata maida idanun ƙasa dole. wani irin abune yake sukar zuciyarta mai zafi da batasan ma'anarsa ba. (Kishi?) kai ina na kishi bane, domin *_babu so miya kawo kishi?_ maybe tsoro no kawai. To amma abinda takeji baya kama da tsoro sai jin ɗaci. Dan har wata hajijiya takeji kamar tana yawo da kanta a sararin samaniya. Sai dai ta danne a nutse taima Maah godiya da sallama ta mike ta fita duk da bata amsa mata ba.         Gaba daya Raudha bata fahimtar komai a gidan hajiyar birni. Babu abinda ke mata kaikawo a rai da zuciya sai furucin Maah na auren Aynah da mijinta zaiyi. Tabbas ko taƙi kota so ta yarda ta fara son shugaban ƙasa Ramadhan. Irin son nan kuma mai kama zuciya da baya saki cikin sauki, duk da ita har yanzu bata da tabbacin shiɗin yana son nata. Tun tana dauriya har saida hawaye suka dinga ziraro mata, saukintama akwai ba'a gaban Asabe bane. Kagara tayi ta koma gida dan bata son tayar musu da hankali, gefe kuma tana kwaɗayin yin maganar da Mommy ko taji sanyi a ranta dai.      Basu bar gidan ba sai bayan sallar la'asar. Driver ɗinta ta samu yana jiranta, dan hala tai sallama da su Basma da sukai mata rakkiya ta wuce. Kafin su karasa government house ma tasha kuka sosai a mota, suna zuwa ta danne ranta dai ta amshi tarbar da Mama Ladi da Mama tambaya sukai mata harma da sauran ma'aikatan sashenta da suka riski dawowar tata.      Duk liyafar da aka shirya musu ta abinci ita da Ramadhan ɗin da dinner bataji ta birgeta ba. Gashi shi baima shigo gidan ba har kusan tara na dare. Tana falo tsaye shayi take haɗawa koshi ta ɗan sha ta kwanata sai gashi. Tafiya yake a kasalance babbar rigarsa saƙale a hannu yana ƙoƙarin kunce agogonsa tunkan ya ida hawowa. Sai da taɗan rumtse ido ta karanto addu'a da fatan ALLAH ya bata ikon shanye halin da take ciki kafin ta juyo garesa.       Sannu da zuwa tai masa da nufarsa kai tsaye domin amsar kayan hanunsa. Babu musu ya mika mata komai sai dai bai amsa sanun datai masan ba. Sai ma yar harara daya sakar mata duk da a kasan ransa yaba ƙyawun da rigar jikinta tai mata yake. Rigace mai santsi sai dai sam babu nauyi tattare da ita kalar blue, sai dai an mata kwalliya da baƙi kaɗan-kaɗan, sai ta saka hula blue a kanta kamshin khumra mai sanyin daɗi na tashi a jikinta sama-sama. Cikin sauke ajiyar zuciya yabi bayanta ɗakinsa data nufa.          Kusan a tare suka shigo, ta ajiye kayan inda ya dace da nufar fridge dan bashi ruwa. Yayinda shi kuma ya hau zame kayan jikinsa da suka damesa sosai. Kanta a ƙasa ta tsiyaya ruwan ta mika masa lokacin da yake zaune bakin gado yana kunce takalnan kafarsa. Bai dago ba har saida ya gama cirewa, kafarsa dake cikin baƙar safa ta bayyana. Ruwan ya amsa nanma yana ɗan hararta, ita dai sai tayi guntun murmushi da ƙoƙarin danne zafin da takeji a ranta.       “Kayi hakuri dan ALLAH”. Ta faɗa cikin sanyin murya lokacin da yake miko mata kofin ruwan daya shanye gaba ɗaya. Mikewa yay kamar bazai tanka ba. Sai da ya nufi hanyar toilet ya bata amsa kausashe...       “Da kikaimin mi?”. Ita dai babu bakin cewa komai, da zai tausaya matama daya barta da abinda takeji a ranta. Mikewa tai ta fice kafinma ya fito. Ta koma falo ta karasa haɗa shayinta tai zaman sha a dining dan tasan dole zai fito nan abinci koya buƙaci takai masa can........       Shayin take sha, amma tunaninta sam baya tare da duniyar mutane. Tayi matukar yin zurfi a tunani har Ramadhan daya fito ya karaso dining ɗin bata sani ba. Yayi kyau cikin kananun kaya farare tas daga wandon har rigar. Sai baƙin Slippers daya kara fiddo hasken kafarsa. Idanu kawai ya zuba mata ransa fal mamakin mi take tunani haka da zurfi, dan shi a ganinsa yanda take da karancin shekaru kamar bata da wata damuwa da zata iya damunta a rayuwa. Hanunta da take zagayawa kan kofin ya rike cikin nasa ya matse da kofin. Zafi ya ratsata ta dawo hayyacinta firgigit. Sai kuma ta bata fuska da shagwabeta kamar zatai kuka. “Ya Ramadhan da zafi fa!”.      Bakinsa ya ɗan taɓe da faɗin, “Ai dan kiji zafin nayi. mi kike tunani haka?”.         Nannauyan numfashi taja a hankali, ji take kamar ta rushe masa da kuka. Amma sai zuciyarta ke tausarta akan ta daure har sai taji daga bakinsa tukunna. Cikin ƙoƙarin danne ainahin damuwarta tai ƙasa da kanta idanunta na tara kwalla. “Dan ALLAH kayi haƙuri ka yafemin, ALLAH inajin tsiro ne kawai shiyyasa. kuma akwai zafi wajen jinake kamar zan iya mutuwa”.       Idanu ya ɗan tsura mata na wasu mintuna. Sai kuma ya lumshesu ya sake buɗewa a kanta yana furzar da numfashi.        Jin yaki cewa komai ta ɗago ta ɗan dubesa fuska share-share da hawaye. Kauda kansa yay da rumtse idanu yana cizar lips. Sai kuma yaɗan murza goshinsa kafin ya zaro tissue dake a dining din ya miƙa mata.      “Bani abinci barci nakeji”.    “Baka haƙura ba dan ALLAH”.               Fuska ya sake tamkewa. “Nifa bana son nacin magana abinci nace ki bani ko”.      Da ƙyar ta haɗiye kukanta ta mike tai masa yanda ya buƙata. Sai dai abincin ma kaɗan yace ta zuba masa shima ta bashi shayi. Duk yanda ya buƙata haka tai masa. Kafin ta koma wajen zamanta ta cigaba da shan shayinta da duk ya huce da cokali. A haka Bilkisu da yasa ta dawo gidan da zama baki ɗaya har sai lokacin bikinsu ta fito ta samesu. Sannu da zuwa tai masa, sannan takai zaune itama dan dama bataci abincinba yau karatun alkur'ani tayi.          “Su Muneera fa?”. Ya tambayi Bilkisun batare daya daina cin abincinsa ba.      “Yaya ai muna isowa kayansu suka kwasa driver ya juya dasu kamar yanda Pa ya basu umarni”.      Kansa kawai ya jinjina. Raudha dakema Bilkisu kallon rashin fahimta dan batasan da barin su Aynah gidanba ta nuna mata Ramadhan da ido tana ɗaga mata gira. Kanta kawai ta maida kasa dan ta gane Bilkiaun na nufin ta tambayesa.        Haka suka kammala cin abincin kamar wasu kurame. Ramadhan ya koma falo ya ɗan zauna yana kallon labarai. Raudha kuma ta shiga tambayar Bilkiau miyyasa Su Muneera zasu koma gida?.       Ɗan harar wasa Bilkisun ta mata. “Aunty Raudha bansan jajibe-jajibe. Kedai kawai ki godema ALLAH an rabasu da gidan kawai suje can su karata da baƙin halinsu”.     Raudha zata sake magana ta dakatar da ita tana miƙa mata waya. “Kinga ni share waɗan can shashashun bani shawara. “Surukinkine ya turosa wai dole saina zaɓa kalar bags ɗin da nakeso”.     Cikin murmushi Raudha ta fara bin set na akwatinan da kallo. Sun haɗu iya haɗuwa. Da gani kuma daga kasar ketare aka turosu. “Humm ni wannan ai sai nai ruwan ido. Duk fa sun haɗu aunty Bilkisu”.      Yar dariya bilkisun tayi itama. “ALLAH nima tun ɗazun na kasa ajiye hankalina waje guda na zaɓa. Shiyyasa nace ya jira sai kin dawo kin zaɓa sai na bashi amsa.”      Har cikin rai Raudha najin daɗin yanda Bilkiau ta ɗauketa. Sai ta tuno da Queen Billy sabuwar ƙawar datai yau a school, a massallaci suka haɗu wajen alwala ta yarda wallet ɗinta batare data sani ba. Shine Raudha ta ɗauka ta bita massallaci da shi. Sai da suka idar da salla ta bata. Cikin jin daɗi ta rungumeta. Sai kuma ta saketa tana bata hannu. “Yi haƙuri dadine wlhy ya rufeni, dan duk abuna mai muhimmanci na cikin wallet ɗin nan sunana Bilkiau amma amfi sanina da  queen billy kefa?”.         Daga cikin niƙab Raudha tai murmuahi, dan ta fahimci queen Billy zatai ɗan karen surutu. Itama hanunta ta mika mata. “Nice name dear ni sunana Amenatu Dauda”.       “Sunanki mai daɗi zamu iya zama kawaye? Danni bakuwace yau kwanana biyar kenan da shigowa school ɗin nan har yanzu na kasa sabawa da kowa.”     Nanma murmushi kawai Raudha tayi, dan haka kawai queen Billy ɗin ta birgeta. Itama dai yarinyace kamarta dan bazasu wuce sa'anin juna ba. Gata ƙyaƙyƙyawa. Taso Raudha ta buɗe nata fuskarta amma taƙi, acewarta wataran zata ganine. Sun faɗama juna department sannan sukai sallama..........✍        *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/5, 8:18 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 56_* ...........“Oh oh wai duk zaɓen akwatinne ya saki tafiya tunani Mrs Ramadhan ”.    Firgigit Raudha ta dawo hankalinta. Sai kuma tai Murmushin da sauke ajiyar zuciya. Bilkisu tace “Uhm kodai mu bari sai da safe naga hankalinki nakan mijinki, nima gara na barki ki wuce kafin ya fara hararata”.       “Kai auntu Bily”. Raudha ta faɗa cike da kunya.     “To ai gaskiya na faɗa, gashi sai murmushi kike kina tunani, kwantar da hankalinki gashi can zaune ko'ina baijeba”.      Ita dai murmushi kawai Raudha tayi ta cigaba da duban akwatinan. Wasu Silver color ta zaɓa. Bilkisu tace, “Woow kinsan kala Auntyna wlhy ni kaina hankalina na kansu tun ɗazu. Sai ki ƙara biyu wai set uku yake so, dan da biyar yace nidai nace sunyi yawa gara ayi abin hankali sauran kuɗin aba mabukata.”.         Cikin zuciya Raudha ke jinjina masu kuɗi na abinda suke so. A fili kam sai ta murmusa. “Hakan da kikai yayi aunty, da ana samun irinku da almabazaranci da dukiya ya ragu ai. ALLAH ya sanya alkairi yasa damu za'ai”.          “To amin auntyna. Inshaa ALLAH lokacin kina fama da babynmu ma”.       “Kai aunty Rufan asiri”. Raudha ta faɗa tana mikewa. Itama Bilkisu mikewa tai tana dariya suka nufi falon inda Ramadhan ke zaune har yanzu yana kallon labaran...        A falon duk suka zauna. Bilkisu taima Yayanta sallama ta wuce ɗaki danta basu waje suma su shakata. Ganin hakama Raudha ta dubesa tana hamma. “Yaya baka bukatar komai naje nima na kwanta”.       Shiru bai tanka mata ba. Harta fidda rai da samun amsa taji yace, “Zo nan”.      Mikewa tai duk a tsorace taje gareshi. Tana koƙarin zama a kujerar gefensa ya riƙota ta zauna saman cinyarsa. Kusan tare suka sauke ajiyar zuciya. Matso da ita yay ta raɓu jikinsa har tana jin saukar numfashi sa a dokin wuyanta. Ya kama hanunta ɗaya cikin nashi yana murza yatsun a hankali. “Ameenatu baƙya tsoron wata ta ƙwace miki ni? Idan kinamin irin wannan riƙon na rashin kulawa tuni zan koma ba naki ba.”      A take idanunta suka cika da ƙwalla. Dan gani take yana mata ishara da aurensa ne kawai. Cikin rawar murya tace, “Dan ALLAH kayi haƙuri bazan sakeba. Ko zanji zafin zanyi juriya”.        Numfashi ya sauke a hankaki yana sassauta muryarsa. “Ni ba ina miki magana akan hakan bane. Ɗazu fa a gida ficewarki kikai sabgar da ba'a aikekiba kika barni ni kaɗai da shirin office, maimakon kizo muyi sallama ma sai kikaƙi. Dazan wuce ko addu'a bakiminba. Na dawo gida kuma na sameki babu wani tarba kin sake barina ni ɗaya a ɗaki kamar ba mijinkine ya dawo ba. Haka aka koya muku kula da miji a islamiyyar?”.      Kanta ta jinjina masa amalar a'a. Juyota yay suna ɗan fuskantar juna. Ya tsura mata idanunsa masu kaifi da ƙarfi. Har yanzu yatsun hanunta na cikin nashi still dai yana murzawa.           “Amma k miyasa kike son yima mijinki haka? Ko kina so wata tazo ta ƙwace ni?”.      Ai babu zato sai kawai ta rushe masa da kuka tana faɗawa jikinsa.           Murmushi ya saki mai faɗi, yasa hannunsa ya zagayo kugunta ɗayan yana shafa bayanta alamar lallashi. Sai dai baiyi maganaba tsahon mintuna har tagaji tai shiru da kanta. Ɗagowa tai tana goge hawayenta. shiko sai faman binta da ido yake.        “Ustazah kishi fa kenan? Anya wannan zuciyar bata kamu da son Ramadhan B. Hameed Taura ba mai tsanani?”. Yay maganar yana ɗora yatsansa manuniya saitin zuciyarta. Kunyace ta kamata. Amma sai ta ɓata fuska da ture hanunsa.        “Ni ba wani kishi”. Karamar dariya da rabonta da gani a garesa tun jiya yayi har haƙoransa na bayyana sosai. Ya shafa fuskarta da faɗin, “To shikenan naji ba'a son Ramadhan balle ai kishinsa. Sai dai ina bada shawara a gyara kafin naki ɗage kafar tafiya aljannar”.      Murmushi tayi cike da kunya ta sake sinne kanta a jikinsa. Daga haka suka shirya. Sai dai koda suka nufi ɗakinsa yayin kwanciya babu abinda yay mata sukai barcinsu lafiya.        ★_______★______★      Dauriya iya dauriya Ramadhan yayi akan kin sake kusantar Raudha, sai dai salon yanda yake mata abubuwa ya ƙara shaƙuwa a tsakaninsu. Ga Bilkisu na sake ɗaurata a layi sosai ita da mama ladi. Gefe kullum Asabe cikin yima yarta nasiha take akan abubuwa da yawa da abaya tasan ita ta tafka kuskure a kansu a rayuwar nata auren.     Karatunta na tafiya lafiya cikin aminci, randa Ramadhan bai gajiba idan ya dawo sukanyi karatu ya kara faɗaɗa mata bayani akan abinda bata ganeba. Hakama Bilkisu na iya bakin koƙarinta.  Acan school kuwa sun ɗinke da Queen Billy da batasan wacece Raudha ba. Har yanzu ma bata yarda ta nuna mata fuskarta ba. Duk da tasan kota nuna ɗin da wahala ta ganeta tunda dai babu wanda zaice ga ainahin fuskarta a duk hotuna dake yawo a media ita da shugaban kasa saboda facemask da take sakawa a koda yaushe idan suna tare. Su Basma ma sun karɓi Queen Billy, dan tanada shiga rai saboda barkwancinta da yawan fara'a. Ranar juma'a da take cika kwana biyar ciff batare da Ramadhan ya sake neman komai daga garetaba ta dawo school a gajiye da yamma lis. A falo ta iske Bilkisu da Ramadhan daya dawo gida da wuri yau. Dan shima Alhmdllhi komai yana tafiya masa dai-dai babu abinda gwamnatinsa keyi yanzu sai shimfiɗa manyan ayyuka da yan ƙasa keta sambarka. Irinsu Alhaji Haladu Gwandu da su forma president da God Fathers nasu kuwa na gefe sun shaka sunyi fam da takaici. balle kuma vice president da kamar ya zama hoto ga wasu al'amuran na gwamnati. Dan shegen mugun halinsa da Ramadhan ya fara fahimta ya sashi ɗan janye jikinsa da shi abubuwa da yawa sai dai ya gani a takarda. Ga kuma binciken da suke kanyi akan abinda suka fahimta game da alakar matarsa da Raudha.       Bilkisu ce kawai ta mata sannu, gogan ko ido kawai ya tsura mata yana kallonta ƙasa-ƙasa duk da fuskarta sakaye take da niƙab. Baki taɗan tura da kauda kanta daga garesa tace, “Ina yini”.      Shiru yay bai amsa ba, sai ma sake karkatar da kai yayi. Bilkisu dake musu dariya ƙasa-ƙasa ta miƙe cikin sanɗa tabar wajen. Ganin haka Raudha data yaye niƙab ɗinta tana kumbura fuska itama tabar wajen ta nufi ɗakinta. Idanu yaɗan lumshe da saki tattausan murmushi yana shafar kwantaccen gashin fuskarsa da yayma gyara ɗazun da safe san dan samun yin sallar juma'a cikin annuri da haiba.         Yana nan zaune a wajen har Raudha ta sake fitowa bayan kusan mintuna talatin. Sanye take da skirt da riga na atamfa, sun mata ƙyau sosai sun kuma kama mata jiki ɗam saboda ƙibar data ƙara. Dan sosai Raudha ke buɗewa ta ko'ina tana ƙara girma. Ga wani haske da tayi fatanta ya ƙara kwanciya luff da ɗan duhun da bazaka kirata fara ƙal ba.        Tsabar jan magana ta gaban Ramadhan tazo zata wuce kanta ko ɗankwali babu. Sai gashinta dake tsefe data ɗaure da ribbon yanata reto. Yi yai kamar bai ganta ba. Sai dai ta kusan gama giftashi ya taɗota da ƙafa sai gata a jikinsa. Ƴar ƙara ta saki mai cike da zallar shagwaɓa. yay saurin buge bakin da yatsunsa biyu.        “Wayyo Anne zai fasamin baki”. Ta faɗa hawaye na ciko mata. Zata tashi ya maidata, kamar gaske ya wani tsuke fuska. Cikin ɗage gira da hararta ya sake kaima bakin nata ɗalli ta kare. “Na kula kin fara rainani a gidan nan. Harni zakima ƙwalele da halalina”.       Idanu ta waro sosai sai kuma ta rufe fuska. “ALLAH dai yana gani ni babu ruwana. Kawai fa wucewa zanyi ni koma ganinka banyiba”.      “Oh really?”. Ya faɗa yana mikewa dauke da ita. Roƙonshi ta farayi tana wantsala kafafu akan itafa badashi takeba ALLAH yunwa takeji. Dan ALLAH yayi haƙuri bazata sakeba. Ko kulata baiyiba ya maida ƙofar ɗakinsa ya datse da key duk da yasan babu mai zuwa sashen. Cakulkulo ya fara mata daga kuka ta koma dariya da bashi haƙuri, bai ƙyaleta ba sai da suka dire cikin gadonsa. Salon daya fara bi da itane ya sata shagala da farko, sai da labari yay nisa a nanfa ido ya raina fata. Ta shiga magiya da roƙo akan abinda shi kuma anzo gaɓar da bazai iya ɗaga kafarba. Aiko taji ajikinta, dan har dana sanin shiga huruminsa tayi. Kuka kam ba'a magana.            Sun fito wanka yake dubanta da murmushi yanda ta lafke a gado tana sakin numfashi da ƙyar kamar wadda ke a cikin ciwo. “K kuwa yarinyanan an miki wankan jego kina jinjira? Shikenan da'an ɗan taɓaki sai ki sharɓema mutane a haka za'a haifa ƴan huɗun?”.        Shiru tai masa kamar tai kuka. Haka kawai yaji dariya ta taho masa. Bai iya dannetaba ya ƙyalƙyale kuwa. Haushine ya kama Raudha, a ganinta tsantsar muguntace ya gama wajiga rayuwarta ya dawo mata dariya. Sai kawai ta sakar masa kukan karya.      “Okay kukama kike? To bari kawai na sakaki mai dalili mana da kiyi na banza gara kiyi na lada.....”      Kafin ya rufe baki har takai ƙofa. Baki ya buɗe zaiyi magana gabansa yay wata irin masifaffiyar faɗuwa tare da kansa daya sara masa. Da sauri ya dafe kan yana ambaton sunan ALLAH. Raudha data zata wayau yake son mata tai tsaye kawai tana kallonsa da murmushi. “Ya Ramadhan na riga nasan wayonka ai. Shine harda pretending?”.       Jin shiru bai amsa mataba ga kujera ya dafe har lokacin hanunsa dafe a kansa kamar maijin hajijiya yasata daina dariyar ta tsura masa idanu. Da sauri ta ƙarasa garesa ganin ya tafi kamar zai faɗi. Tarosa tai, sai dai yanayin jiki ba ɗayaba yafi karfinta musamman da jikin nasa ya saki sai suka zube ƙasa ya faɗa kanta. Ƴar ƙara ta saki da ambaton sunan ALLAH saboda wani raɗaɗi daya ratsa mata hanunta da suka faɗi a kansa. Tai ƙoƙarin dannewa amma ta kasa dan azaba. Kuka ta saki tana son turesa sai dai ina. A take jikinta ya fara rawa, ta turashi iya karfinta yay ƙasa da ƙyar, sai dai kafin ya dire a bazata taji ya ɗauke fuskarta da mari.       “K! Baki da hankaline ni zaki ture?”.     Ya faɗa a matuƙar kausashe da muryar da ko sanda basa shiri bata taɓa ji daga garesa ba. Lallai ta maru, dan yay bala'in shigarta, zata iya rantsewa kuma shine na farko a duniya daya taɓa marinta, tsabar azaba har kifewa tai akan table sai ga goshinta ya fashe. Idanu ya waro a ɗan tsorace yay kanta yana ambaton “Ya salam Ameenat....”        Sai dai yana kai hannunsa jikinta ya sake tureta da ƙarfi ya sake dafe kansa dake juya masa. Duk yanda yaso yin addu'a bakinsa yay masa nauyi ya kasa furtawa. Duk da azabar dake ratsa Raudha a goshi da hannu haka ta sake nufarsa tana kiran sunansa a tsorace. Sai dai tana matsawa garesa ya sake hankaɗeta a matuƙar tsawace yace, “Fitarmin anan!!”.        “Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Ya Ramadh.....”       “Nace ki fitar min anan!!”. Ya faɗa a wani irin yanayi na fita hayyaci da tsananin ɓacin rai. Sosai jikin Raudha ke rawa kuwa yanzu. Ta fita a ɗakin da sauri kuka na kufce mata. Ga jini harya wanke mata fuska duk da taresa da tai da hanunta mai lafiya. Hanunta daya bugu kuwa wata azaba yake mata harya fara yawa da kumburi. Bata samu kowa a falon ba, sai dai karar buɗe ɗakinta da bugo ƙofar ta rufe ya fargar da Bilkisu dake gaban mirror tana kallon film a lap-top. Da sauri ta fito sai idonta yaci karo da ɗigon jini, a razane tabi jinin da kallo har ƙofar ɗakin Raudha, ai bama tasan kalar tsallen datai kawai ta ganta jikin ƙofar ba.............✍ 😥🙏🏻aimun afuwa. Jin daɗi baya dorewa sai da ƙaddara. A lokuta da dama jarabawa itace ke ƙara. kai mutum ga ajin nasara. Ba'a samun wannan nasarar kuma sai da haƙuri da juriya.🚶🏻    *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account. *Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks. *Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku. A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant). -------- Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar: *Bank Transfer* *Airtime Transfer* Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance. *Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks. _Account No_ - *1220077999* _Account Name_ - *Arewa Books Publishers* _Bank_ - *Zenith Bank* Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din: Amount Paid: - Nawa aka tura? Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa Transferred time: - lokacin da aka turo Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi Deposit date: - ranar da aka turo Sai ayi SUBMIT. *Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar: MTN, 9Mobile Glo Airtel Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance. *WANNAN SHINE BAYANAN* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/7, 1:31 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 57_* ..........“Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un aunty Raudha jini kuma?”. Bilkisu data shigo ɗakin a birkice ta faɗa tana ƙarawo gareta. Kamata tai suka nufi toilet, ta haɗa ruwa mai ɗumi ta taimaka mata ta wanke fuskar da hanunta, jinin dai bai tsaya ba. Sai dai sun tare da tissue. A bakin gado ta zaunar da ita, ta ɗakko first aid box ta shiga ƙoƙarin tsaida jinin, da ƙyar aka rufe wajen da audiga da bange. Ita dai Raudha babu abinda take sai sakin ajiyar zuciya.       “Aunty Raudha wai garin yaya? Ina Yaya kuma?”.    Komai Raudha kasa cemata tai, sai hawaye take sharewa kawai. Hankalin bilkisu ya ƙara tashi, sai dai ta barta bata sake maganaba. Tana niyar mikewa ta maida first aid box ɗin ma'ajiyarsa ta lura da kumbirin hanun Raudha kuma. Gaba ɗaya saita sake ruɗewa ta kamo hanun tana kallo. “Ya ALLAHU, nan ma ai ciwon kikaji Aunty! Kinga bara na kira Yaya da mama ladi dan ta iya gyaran ƙashi”.        Ita dai Raudha komai batace ba, babu jimawa suka dawo da mama ladi, bilkisu ta sake fita. Duk da ta fahimci akwai matsala ƙofar Ramadhan ta dingama knocking a ɗarare. Shiru babu ko motsi, sai ta ɗan tura ƙofar ta leƙa. Gabanta ne yay masifar faɗuwa hango Yayan nasu zaune akan tum-tum ya dafe kansa. Babu shiri ta shigo ɗakin da sassarfa. Muryarta har rawa yake ta durƙusa gabansa “Yayanmu dan ALLAH mike faruwa ne? Aunty Raudha taji ciwo sosai wlhy har a hanunta mi'akai mata”.         Da ƙyar ya samu damar fisgo kalmar innalillahi... A cikin zuciya. Ya ɗago jajayen idanunsa ya zuba kan Bilkisu datai matuƙar razana. Dan rabon da su gansa a irin wannan yanayin tun rasuwar su Haseenah. Baya taɗan ja jikinta na rawa. Shima sai ya cije lips sinsa da ɗago hanunsa ya kalla. Sai kuma ya dafe kansa dake matuƙar juya masa. Kusan minti ɗaya ya sake ɗagowa ya dubi Bilkisu da gaba ɗaya ta gama tsorata. Cikin yanayin damuwa yace, “Ina Ameenatun?”.        “Tana ɗakinta Yaya, nabar Mama ladi zatai mata gyara a hanunta dan harya kumbura, ga goshinta ya fashe da ƙyar na iya tsaida jini....”       Ai bama ta ƙarasa ba ya miƙe hankali tashe. Sai dai hakan bai hana bayyanar nutsuwarsa ba. Fita yay Bilkisu tabi bayansa. Kai tsaye ɗakin Raudha ya nufa, sai dai yana ɗaura hanunsa bisa handle ɗin ƙofar ya dafe kansa da yay masifar sara masa. Da sauri ya shiga girgiza kansa yana ja da baya. Barin wajen yay ya sake komawa hanyar ɗakinsa. Bilkisu ta bisa da sauri tana kiransa. Wata razananniyar tsawa data sakata jan birki ya daka mata, yay shigewarsa ya bugo ƙofar da ƙarfi har Bilkisu na zabura.           Kuka Bilkisu ta fashe da shi. dan kuwa ta fahimci lallai akwai matsala, sai da tayi mai isarta ta koma ɗakin Raudha. Ta jiƙe sharkaf da zufa kamar ba ac a ɗin saboda gyaran da mama ladi tai mata. Mama ladi dake naɗe mata hanun da bandage ta dubi Bilkisu. “Taji ciwo sosai, dan gocewar ƙashi ta samu. Garin yay hakan?”.         Kafin Bilkisu ta bada amsa cikin share hawaye Raudha tace, “A toilet ne na zame”.       Sannu Mama ladi ta shiga jera mata. Bilkisu dai wani irin tausayin Raudha ɗinne ya lulluɓeta. Dan ta tabbatar daga yayansu aka samu matsalar musamman da taga shatin yatsu a fuskar Raudha alamar marinta akai. Magani ta sha ta kwanta bayan tayi sallar magrib da isha'i, babu jimawa kuwa barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Bakajin komai sai ajiyar zuciyarta.         Tagumi Bilkisu tai zuciyarta nata kaikawo. tama rasa ina zata kama akan wannan al'amari. Kusan tara na dare sai ga kiran Basma ya shigo mata. Da farko kamar bazata ɗaga ba sai kuma ta daure ta ɗaga wayar na gab da tsinkewa. Wani irin dummm kunen Bilkisu yayi jin abinda Basma ta faɗa. Muryarta har rawa take wajen maimaita “Basma shi Yaya Ramadhan ɗin da kansa yace zai auri Aynah?”.       Daga can Basma tace, “Wlhy kuwa Aunty B. A gabana Maah tai waya da shi yanzun nan sai farin ciki take tana saka masa albarka. Ni nama rasa wanda zan tunkara da wannan abun al'ajab shine fa na kiraki naji ko wani abu ya faru anan”.      “Nan dai babu abinda ya faru, sai dai yana ɗakinsa. Amma dai wannan lamari da ɗaure kai. Basma anya Adda Asmah bata fara cin galaba akan Maah ba?”.         “Aunty Kamar ya?”. Saurin dafe kai Bilkisu tai jin zata saki layi. Ta manta ita kaɗai taji abinda Adda Asmah ta taɓa faɗa akan Mahaifiyarsu kwanakin baya sanda ake tsaka da rikicin auren Yayansu da Raudha. Kuma bata taɓa nuna ta saniba ko taɓa faɗama wani. Sai dai tana kallonta da abun kuma tun daga ranar taji bata sonta duk da yayar Maah ce. Hasalima tafi shiri da ita fiye da kowa a ƴaƴan gidansu, dan ita takan iya zuwa ta kwana gidansu Aynah ɗin ma ba kamar su Basma ba.            ★★★_____★_____★★★          Tabbas abubuwa sun kwaɓe a tsakanin Raudha da shugaban ƙasa Ramadhan. Ita gaba ɗaya tsoron haduwarsu ma takeyi, yayinda shi yasha gwada zuwa gareta da zaran ya iso kofar ɗakin sai yaji wani irin mugun tsanarta mai ban mamaki, dole yake juyawa ya fasa. Babu abinda Raudha keyi sai kuka, sai dai duk da haka tana ƙoƙarin zuwa makaranta. Bilkisu tayi-tayi ta faɗa mata ainahin abinda ya haɗasu taki. Takuma roƙota ALLAH akan karta sanarma su Anne. Rasa mi Bilkisu zatai tayi, sai kawai ta zubama sarautar ALLAH ido tana tayasu da addu'a.        A cikin kwanakin da basu gaza gomaba da faruwar komai Raudha duk ta fige ta rame. Sai uban haske datai ta ƙara tsayi. Kullum babu fashi zataje ta gyara masa ɗakinsa, duk bayan kwana biyu ta wanke masa under wears ɗinsa dan tafi gane wankesu da hannu ba Worthing machine ba. Idan ta gama sai tai drying nasu a machine ɗin. Komai dare kuma sai tayi zaman gogesu bayan ta musu turare na turaren wutarta na kaya mai daɗin ƙamshi sannan ta maida ɗakinsa ta jere masa.         Sam ya daina shigowa gidan da wuri, weekend kuwa har taci ta ƙare bai yarda sun gamu ba. Bata da aiki sai kuka da gayama UBANGIJI. Dan ta rasa wanema irin tunani zatai akan sauyawar tasa. Koda zuciyarta ta nuna mata dama sabbin halayyar daya fara mata yayine dan ya samu jikinta sai tai saurin ture tunani dayin a'uziyya. A haka suka sake cinye sati uku babu wani canji. *_RAMADHAN_*        A sashen Ramadhan shi kaɗai yasan tashin hankalin da yake ciki na tsananin son Ayna'u. Bashi da burin daya wuce mallakar Ayna'u matsayin matar aurensa. Kullum cikin yima su Bappi nacin akai kuɗi yake dan abun yanzu ya wuce Maah kawai har Anne da Pa da Bappi duk sun sani. Tun suna ɗaukar abun nasa wasa harya koma basu haushi. Dan ranar daya kai Pa ƙarshe akan lamarin ba karamin zagesa yay ciki da bai ba. Ya kuma masa dogon gargaɗi akan inya sake zuwa masa da batun Aynah sai ya matuƙar ɓata ransa. Dama kuma itama Maah yaja mata gargaɗi akan damunsa akai kuɗi da takeyi.        Wannan zagi da Pa yay masa ya matuƙar ƙona masa rai, dan kuwa dai a fusace ya dawo gidan. Abin tsautsayi Raudha na ɗakinsa tana gyarawa dan yau ta fita school da wuri tama rigashi fita, shiyyasa bata gyara masa ɗakin ba sai da ta dawo tunda shi bai dawo ba. Ba karamin firgita tai da ganinsa ba, dan rabonta da shi tun randa abin nan ya faru sai dai ta gansa a tv ko hoto. Duk ya rame mata a ido yayi duhu. Wata irin tsawa ya daka mata data nema wantsalo zuciyarta ta baki. Tai nufi fita masa a ɗaki ya shaƙota ya jefa saman gado.        Lallai Raudha ta tabbatar a baya wahalar da takesha a hanunsa ba wahala bace. Dan kuwa lallaɓata yake kuma cikin soyayya mai gusar da hankali. Amma a yau ta tabbatar da waye Ramadhan. Kuka take kamar ranta zai fita tsabar yanda ya wajiga rayuwarta. Daga ƙarshe ya korota a ɗakin. Da ƙyar ta iya kai kanta nata ɗakin, ALLAH ma ya sota Bilkisu bata gidan. Su mama ladi kuma indai ba ita ta buƙaci ganinsu ba babu mai hawo musu nan sai in zaiyi aiki. Ƙofar ta murzawa key sai dai bai rufu da ƙyau ba ta zube jikinta tana jan numfashi da ƙyar, tsabar kukan da taci har asthma ɗinta na ƙoƙarin tashi. Rarrafe ta dingayi hanunta rike da ƙirjinta, da ƙyar takai kanta jikin gado ta ɗauka inhaler ɗin akan bedside drawer. Tata ƙoƙarin ganin ta shaƙa hakan bai yuwuba, har takai numfashinta na neman fara nisa ALLAH ya kawo Bilkisu.        ALLAH ya taimaka ƙofar data rufe bata rufu ba. Da lallai zatama iya rasa ranta a wannan lokacin. Taimakon gaggawa Bilkisu ta bata, da ƙyar numfashinta ya dai-daita. Raudha dake magana a wahale ta roƙa Bilkisu ta haɗa mata ruwa mai zafi sosai. Bilkisu batasan mike faruwa ba. A tunaninta ko duk halin tashin Asthma ɗinne data shiga da kuma gajiyar makaranta. Bayan ta haɗa mata ta fito ta taimaka mata zuwa bayin, duk da dai yanda taga Raudha na tafiya a bubbuɗe ya ɗaure mata kai matuƙa.       Da ƙyar Raudha ta iya gyara jikinta, tai luff a cikin ruwan ɗumi tana hawaye da addu'ar ALLAH ya bata juriyar cinye wannan jarabawa. Amma tabbas zuwa yau ta fara fahimtar mijinta baya cikin hayyacinsa. Akwai abinda ke faruwa da shi da su basu sani ba. Zata tayashi da addu'a koma minene ALLAH ya yaye masa shi.        Kamar wasa sai ga karamar magana ta zama babba, dan kuwa dai ciwo sosai Raudha ta kwanta washe gari ko makaranta bata iya leƙawa ba ma. Kusan kwananta uku a halin jiyya kafin ta warware ta cigaba da harkokinta. Sai dai fa a yanzu babu wanda take tsananin tsoron haduwa da shi a duniya sama da Ramadhan. Ko maganarsa taji a tv sai gabanta ya faɗi. A haka rayuwa ta sake turawa suka sake cinye sati huɗu, sati kusan na bakwai kenan da shiga halin da suke ciki. Zuwa yanzu kuma har an kai kuɗin auren Aynah saboda birkicewar da Ramadhan yay musu.        Tuni Pa ya fahimci akwai sihiri tattare da yaronsa. Amma ya zaɓi barinsa a hakan dan yanaji a ransa dole sai Adda Asmah ta shayar da gimbiya Su'adah zumar mamaki sannan zata san ANNABI ya faku. Koda su Bappi ma suka fara irin wannan zargin Pa ɗinne ya gusar musu da zargin ta hanyar nuna musu babu wani sihiri uwarsa ke zugasa. Yayi hakane dan baya son suce zasu tashi tsaye akan Ramadhan ɗin, yafi son sai uwarsa taji a jikinta sannan. Amma kuma bai gaza da masa addu'ar kariya ba.       Abinda hankalinsu kuma ya gagara kaiwa akai su duka basuyi tunanin ko abin ya shafi Raudha ba. Dan ita dai ko sau ɗaya bata kawo wa kowa ƙararsa ba. Ta kuma hana Bilkisu faɗa duk da itama Bilkisun ba komai ta sani ba har yanzun. Kullum kuma Anne ta tambayi su Basma sukance Raudha na lafiya harma tana gaishesu tunda kullum dai suna tare a makaranta. Hakanne ya ɗan basu nutsuwa suke ganin shi kaɗai abin ke dawainiya dashi kenan.          ALLAH sarki Raudha, sai dai kuma abinda ba'a sani ita kaɗai tasan halin da take ciki, ga yanzu kullum da zazzaɓi take kwana. Ga kasala da batasan kota minene ba. Komai da ƙarfin hali take yinsa hatta karatun. Ita Bilkisu tana ɗaukar yanayin natane kawai da tunanin maganar auren Ramadhan ɗin. Dan haka ta maida hankali wajen bata shawarwari da nasiha.       Bazatace auren Ramadhan baya damuntaba, dan tasan wacece Aynah tasan kuma burinta akanta, dan tunda Ramadhan ya fara birkice mata Aynah da Addah Asmah suka kirata sukai mata zagin ƙare dangi saboda fahimtar ita sihirinsu bai kamataba. A tunaninsu itama bin malaman take shiyyasata ta tsira. Basu san ALLAH ne bai ƙaddara mata shan zoɓon waccan ranar ba kawai. Ranar taci kuka matuƙa dan zagine da cin mutunci da bazai taba goguwa a zuciyaba kai tsaye. A kalamansu kuma ta fahimci lallai akwai ƙullin dake kan mijinta da alama kuma sunada alaƙa da shi. Bata da abin faɗa, dan koba komai dai ƴan uwansa ne. Adda Asmah ma na amsa sunan uwane a garesa tunda yayar mahaifiyarsa ce da itama zata iya kiranta da uwa. Haka ta cigaba da masa addu'a da ita kanta abun na damunta.       Sai dai halin da take ciki na rashin jin daɗin jiki yafi kwashe kaso mafi yawa na damuwarta. Ko mahaifiyarta batasan halin da take a ciki ba. Sai dai a duk sanda sukai waya takance Mummy kimin addu'a. Idan asabe ta nuna damuwarta cikin tashin hankalin furicin Raudhan sai ta dinga kwantar mata da hankali akan babu komaifa saboda karatu take cewa hakan.      Ita dai Asabe hankalinta ba wani ya kwanta bane. Amma sai ta dage da bin ɗiyarta da addu'ar fatan alkairi. Itama kuma Raudha bata wasa. sosai take a kan ƙafafunta tana gayama ALLAH damuwarta akowanne dare. Wani lokacin ma tana salla tana rawar sanyin zazzaɓi, haka ta dage da azumin alhamis da litinin. Ta kuma dage da saka har Abba (M. Dauda) turama kuɗi akan ya bada sadaka yasa a mata addu'a ita da Ramadhan. Da yake shi kan babu notika ɗaurarru maimakon ya fahimci akwai matsala sai ya kama dariya yana yana faɗin.         “Ƴar nema taji daɗin gidan gwamnati bata son suyi shekara biyar kawai. Indai addu'a ce kin tara kin samu, yau kaf almajiran dake garin hutawa saina bisu kowacce tsangaya na tattare da malamansu sun saka rokon ALLAH, dan nima inason ku koma hawa na biyun ai. Amma Raudha ya kamata kima mijinki magana ko ministan bada kuɗin fansho ya bani mana. Zamannan ya isheni haka kinga wannan sarautar ba wani kuɗi ake samu ba sai uban fama da rawani da zazzare ido a fada. Ni badan ma kar hakimi yace na raina karamcinsa ba da wlhy tuni na ajiye. Ni kuma yan kuɗina kullum kasa suke, dan ma ALLAH ya taimakeni wanda Ƴaƴan Larai suka sata an ganosu ai da yanzu hawan jini ya shanye muku ni.      Murmushi Raudha tayi tana share hawaye. “Karka damu Abbah insha ALLAH zan san abinyi. Amma nidai gara kayi haƙuri ka cigaba da zuwa gidan hakimin”.      “To ai duk yanda kikace haka za'ai uwata farar haihuwa farar aniya your excellency. Insha ALLAH sai kunyi goma indai mulkin NAYA ne”.     Dariya ta ƙyalƙyale da shi babu shiri dan ya bata dariya sosai. Da ga haka sukai sallama ta ajiye wayar. Bargo ta kara ja har kanta dan wani irin sanyi mai ratsa ƙashi takeji. Ga ƙasusuwan ta kamar ana mata daka a kansu. Saboda zazzaɓin yau ko lecture ɗin karshe bata zaunaba ta gudo gida. Sai dai ta iske Bilkisu bata dawo ba. Haka shima mai gayya mai aikin da rabon dama ta sakasa a ido tun randa yay mata murzar ƴan bori. Dan ko zaune take a falo da taji shigowar motocinsa take shigewa. Ta katange duk wani abinda zai haɗasu a inuwa ɗaya saboda kare mutuncinta da nashi. Tun kusan satin baya take tunanin yanda zata fara masa addu'oin warware sihiri, idan ma shine tare da shi sai dai bata san ta hanyar da zata bashi yasha ba tunda baicin abincin gidan yanzu sai yaso. Hakan yasa ta haƙura ta barma ALLAH komai ya kawo musu mafita.      Barcine ya ɗan figeta da sam bama daɗi yake mata ba. Dan har a cikinsa tanajin ciwon dake nukurkusarta. Bude ƙofar ya sakata farkawa aɗan razane...........✍       *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/7, 1:31 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 58_* ..........A hankali ta saki numfashi tare da nannauyar ajiyar zuciya ganin Bilkisu ce ba wanda take fargabar haɗuwar da shi ba ko'a hanya bare a cikin ɗaki da ga ita sai shi. Zama Bilkisu tai kusa da ita tana kai hannu a goshinta. “Aunty Lafiya kuwa kika dawo da w....”      Maganar tata ta maƙale jin jikin Raudha da zafi. “Ya salam baki da lafiya yauma ko? Dan ALLAH ki yarda muje ko cikin clinic ɗin gidan nanne inma bazamu je wajan Mommyn Jabeer ɗin ba. Aunty wai zaki cigaba da cutar da kankine akan Yaya Ramadhan ne? Kin hana na faɗama kosu Anne halin da kuke ciki, ni kaina ɓoyemin abubuwa da yawa kikeyi wlhy. Harga ALLAH nidai na gaji da shurun nan da kika dabaibayeni da haɗani da ALLAH akan nayi”.        Murmushi Raudha tayi tana haɗiye hawayen dake son zubo mata. Ta tashi zaune cike da ƙarfin hali ta kamo hanun Bilkisu cikin nata. “Aunty B kiyi haƙuri dan ALLAH, ban hanaki gayama su Anne bane sai dan yanda kike kallon matsalar ba haka take ba. Aiki ne kawai yay masa yawa, sannan ni babu wani abu na rashin daɗi dake tsakanina da shi, kawai dan ba zaman gidan yake kamar da ba saboda ayyuka yasa kike ganin akwai matsalane. Kinga babu dalilin kai ƙara akan laifin da babu shi aunty. Nasan kina ganin kamar auren nan nasane cutarwa a gareni shiyyasa. Dan ALLAH kibar damuwa ALLAH ni banajin komai akan hakan duk da nasan dole ne naji kishi matsayina na matarsa. Amma karki manta Aunty ALLAH ya bashi damar yayi huɗu, a addinance ma da biyu aka fara, sannan uku, sannan huɗu. Sannan a yanayin da Ya Ramadhan ke ciki dama ya kamata ace yanada mace mai ilimi da zata jagoranci wasu abubuwa na mulkinsa bawai irina da iyakata secondary ba kuma mai ƙarancin shekaru. Karki manta aunty yanzufa nake shekara ta shatara kawai a duniya, koba komai kuwa Aynah nada kusan ashirin da tara ko talatin da ɗaya ko fin hakan ma, sannan tayi ilimi mai zurfi daga ƙasar NAYA har wajenta. Tako ina ta cancanci zama matarsa koda nauyin al'umma dake a kansa”.       “Humm Raudha sam ban gamsu da wannan bayanin naki ba. Babu ruwan hankali da ƙarancin shekaru, hakama babu ruwan sanin yakamata da ilimi. Mutane nawane a zamanin da basuyi ilimin boko ba amma sunada basirar tsara abinda ko professor na yanzu bai iya tsarawa ba. Kai har a wannan zamanin akwai wanda basuyi ilimin boko ba amma wlhy idan sukai miki wani abun sai kinsha mamaki. Hakama shekaru, shekaru baga kowa suke taka rawar hankali ba ga mai su. Zakiga mutum da shekarun manya amma idan yana tafka miki baranɓarama ke kyace ɗan goma sha ne. Kuma kiga karamin yaro na gyara masa. So ni a tawa mahangar banga ta inda Aynah zata taimaki Brother ba wlhy. Ƴar uwatace ita kuma jinina, amma bazan ɓoye miki cewar inaji a raina akwai manufa acinkin wannan al'amarin ba Raudha. kuma insha ALLAH bazan gajiyaba wajen ganin na daƙile hakan sai dai in ƙaddararsa ce zama da ita”.    Tana gama faɗa ta mike ta fita hawaye na sakko mata a fuska. Da kallo kawai Raudha ta bita sai itama ta fashe da kuka. Sai da tayi mai isarta sannan ta mike ta shiga toilet ta wanko fuskarta.... (ALLAH ka bamu ikon cinye jarabawa a duk yanda tazo mana🙏🏻😭). *______________★_____________*           A ɓangaren su Gimbiya Su'adah kuwa shirin biki suke na ƴaƴan gata, dan a wannan gaɓar ko auren Lubnah da Bilkisu bata bama muhimmanci ba kamar na Ramadhan da Ayna'u. Babu abinda zuciyarta ke raya mata sai cewar zata haɗa cikar birinta da maido ɗanta ƙarƙashin umarninta ta kuma rabashi da wadda ta zame mata ƙayar kifi a maƙoshi badan ta taɓa mata wani laifi ba ko kuskure.       Hatta da Ramadhan yanzu wani gata take masa na fitar hankali ita da su fulani da uwar gayya Addah Asmah. Baya iya jera sati baizo gidan ba a sace. Takai yanzu ko sashen su Anne baya shiga sai dai suji labarin yazo a bakin Basma. Hatta yin waya ya rage dasu, komansa gimbiya Su'adah. Ko abu ya shige masa akan harkar mulki maimakon kiran Bappi da yakeyi ko Anne a da sai ya kira Gimbiya Su'adah yanzun. A mafi yawan lokuta shawarar tata bata haifar da ɗa mai ido a garesa. Dan kuwa dai gadarace kawai da son nuna isa take ɗorasa akai, ALLAH ne kawai ke taimakonsa da in yay maganar da Cos sai yay saurin faɗama Bappi shi kuma ya gyara, wani lokacin idan Bappi ya kirasa yace kar ai kaza ɗin nan kaza ya kamata ayi har haushi yakeji, ya dinga ƙunkuni kenan yana cika yana batsewar fushi. Idan kaga haƙoransa a waje yanzu to tare yake da su gimbiya Su'adah. Aynah kam kamar yanda bokan Adda Asmah ya faɗa mata a ɓoyeta kar Ramadhan ya ganta har sai an kaita gidan gwamnati haka akai, sai suka fake da cewar gyaran jiki ake mata, amma a zahiri umarnin boka suke bi, dan ya tabbatar musu inhar Ramadhan yay ido huɗu da Aynah kafin aure duk wani sihirin jikinsa sai ya warware.     Game da Raudha kuwa a yanzu basu da lokacinta, dan su tunaninsu sun gama da shafinta lokacin komawarta gidansu kawai suke jira. Shiyyasa ko bibiyar lamarinta basa waniyi gaba ɗayansu.         Mutane har yanzu basu farga da halin da Ramadhan ɗin ke ciki ba, sai dai yanayinsa na kullum fuska a cunkushe yanzu kansa wasu yin kananun magana. Ƴan adawa kuma suka samu na suka a garesa da sake dawo da furicin nan na mai girman kai garesa.       Pa da duk abinda ake a gidan ya saka ido badan baya cikin damuwa da halin da ɗansa yake a ciki ba. Ya barine kawai azo gaɓar da gimbiya Su'adah zata gane kurenta. Sai dai a yanzu bita da ƙullin daya shirya musu akan shirin da suke gagarumi na auren ne. Dan ko events an haɗa yakai kala goma, sanin Taura family ba'a wannan almabazaranci sai suka fake da cewar duk a gidansu amarya aka ɗauki komai. Lokacin da gimbiya Su'adah tazoma Pa da zancen dariya sosai abin ya bashi. Amma sai ya gimtse kayarsa yace ALLAH ya bada sa'a.      Daɗine ya kama gimbiya Su'adah, dan gani take yanzu fa kamar ta fara samun kan Pa ɗin a dalilin turaren da Adda Asmah ta kawo mata tace tai amfani da shi a duk sanda zataje gareta. Dukan wata bukatarta sai ya amsa babu musu sai ma shakkarta da zai dingayi. Murmushi tai tana ficewa cike da tafiyar takama. A ranta kuwa sakama Addah Asmah albarka take da yaba mata. Dan ta tabbatar wannan turare shike taimaka mata wajen hawa kan Pa ɗin yanzu a yanda takeso. Amma da tasan bata isaba indai wannan uban kafiyar ne da taurin kai.     Bayan ficewarta nannauyan numfashi ya sauke da girgiza kansa, sai kuma ya saki murmushi tausayin ɗansa na ƙara ratsa masa zuciya. Mikewa yay ya fice sashen mahaifansa. Acan ya samu har su Yafendo suna hirarsu cike da farin ciki kamar yanda suka saba.      Bappi dake shan fura ya ɗan tsura masa idanu cike da nazarin ɗan nasa. Sai kuma ya ɗauke kansa. Ita kanta Anne idanun nata a kansa suke, dan tun shigowarsa ta fahimci akwai damuwa tattare da shi. Bayan ya gaishesu Inna ke faɗin, “Bashari lafiya kuwa na ganka kamar mai damuwa?”.      Ɗan murmushi yay mata yana furzar da huci. Sai kuma ya gyara zamansa sosai yana fuskantarsu. “Lafiya lau Inna, kawai nazo nayi magana da ku ne in ba damuwa”.     Yafendo tace, “Faɗi kanka tsaye Bashari mike faruwa?”.      Jin Anne da Bappi basuce komai ba ya sashi dubansu, sai dai yanda suka maida hankalinsu garesa suma ya sashi sauke ajiyar zuya. “Ba komai bane dama akan Ramadhan ne da wannan auren nasa.”        “Ba mun wuce wannan babin ba mi kuma ya faru?”. Bappi ya faɗa yana kallonsa fuska a tsuke.       “Kayi haƙuri Bappah, bawai na dawo da hanun agogo baya baneba. Kawai ina son muyi wani abune dan ALLAH saboda wani nazari dana zauna nayi.” batare da ya jira cewarsa ba ya cigaba da faɗin. “Ni da ku duk munsan waye Ramadhan da kuma kammu, amma jama'ar gari da Ramadhan ke mulka har yanzu basu gama sanin waye shi ba. Auren Ramadhan da yarinyar nan Ameenatu dududu watanni na bakwai muke a ciki yanzu, ko shekara bamuyiba. Aurene da yasha soke-soke da kace nace a idanun mutane da bakunansu dalilin tazarar da su suke hange da mu babu ita a zukatanmu. Shin ya kuke tunani idan akace yanzu an fiddo maganar ƙara auren Ramadhan wa duniya, kuma da ɗiya irinsa mai irin matsayinsa kuma ƴar uwarsa sannan mai dukkan kishiyar abinda akai cece kuce Ameenatu bata da shi a baya?. Dama ance munyi haɗin auren Ameenatune da Ramadhan saboda mu gyara masa siyasarsa ace yana son talaka gashi harya auri ɗiyar cikinsu. To yanzu wannan auren nasa da har yanzu bamu gama sanin kansaba ake masa shiri na tashin hankali bama tunanin cikkakkiyar amsace ga ƴan ƙasa da abokan hamayya?. Ba ina fargar damu bane dan tunanin kar Ramadhan ya rasa kujera a zaɓe nagaba. Ina fargar damune domun kare mutuncin kammu dana Ameenatu yarinyar kirki da batajiba bata ganiba, hakama ina kare kunyar da zamu daurama bayin ALLAH da suka goya da bayanmu suka kuma tabbatar da tsarkake abinda mukayin badan sakamakon mu a hanunsu yake ba, sai dan bana son mu cire hope ɗin mutane akan mulkin Ramadhan. A yanzu Su'adah tazomin da wannan invitation card ɗin” ya ajiye iv ɗin gaban Bappi. “Bappah ka dubafa ka gani, events kusan goma ne anan aka shirya wanda ake fatan duniya ta gani ta shaida za'ama Ramadhan auren gata bama ƙasar NAYA kaɗai ba. Bayan kuma mu a wannan gidan duk bama hakan tun auren ƴaƴanmu na farko, sannan ko'a yanzun ma bawai shine kaɗai auren da za'a ɗaura ɗin ba”.        Tsitt falon yay bayan Pa yayi shiru. Sai dai tsananin ɓacin rai ya bayyana ga fiskokinsu bayan duk sun ga katin da tarin bidi'oin dake a ciki. Anne da idanunta suka fara cika da ƙwalla tace, “Anya kuwa Ramadhan ma yana cikin hayyacinsa? Bana son zargi sam a rayuwata ballema dana san dai Su'adah mahaifiyarsa ce babu yanda za'ai ta cutar da shi....”       Murmushi Pa yayi, cikin kunar rai yace, “Idan ita bata cutar da shi ba ai anyi amfani da ita da son zuciyarta an cutar da shi Anne. Bara yau na fito na sanar muku gaskiyar lamari akwai sihiri tattare da Ramadhan, sam abinda yakeyi ba'a cikin hankalinsa yakeba..”         Salllami falon ya ɗauka da sautin kukan su Yafendo. Yayinda Bappi ya tsurama ɗan nasa ido duk da shima ya jima yana wannan zargin. Pa yaja numfashi mai cike da takaici. “Karku wani damu kanku ni hakan yamun daɗi ai, maybe a dalilinsa Su'adah zata dawo cikin hankalinta tasan abinda ke mata ciwo. Na jima da fahimtar hakan amma bana son kowa ya nemawa Ramadhan magani dan ALLAH har sai anzo gaɓar daya dace...”         Da sauri Inna ta katse Pa, “Baka da hankali Bashari. Taya za'abar yaro a baƙar inuwar sihiri? Kenanfa kusan duk abinda yakeyi baima san yanai ba! Kai nifa ina mamakin canjawar yaron nan lokaci guda. Har takai yanzu zaizo gidan nan amma bamu sani ba. Barinsa cikin wannan tashin hankalin ai matsalane, sai ya iya shafar mulkin da yake kai ko kai baka san hakaba”.      Karon farko Bappi ya saki murmushi, cikin takaici yace, “Sadiya kenan wannan na nawa kuma. Badan ALLAH ya bashi chief of staffs na ƙwarai mai amana da tsoron ALLAH ba ai da tuni halin da Ramadhan ke ciki ya bayyana a cikin mulkin nasa. ALLAH dai ya ƙyauta. Ni yanzu inaga kai Basheer faɗi dalilinka muji, idan mai yuwuwane saimu riƙe. Idan bazai yuwuba a sake shawara”.       Kai Pa ya jinjina masa. “Bappi abinda yasa na roƙeku kar'a nema masa magani saboda dalilai uku ne zuwa biyu. Na farko ina son Su'adah ta gane kuskurenta akan Ameenatu, na biyu ina son ta gane wacece ƴar uwarta Asma'u. Na ƙarahen da bakinta nake son ta bayyana dana saninta a kansa. Dan haka ina roƙonku yin wannan aure a sirrance. A ɗaurashi a sirrance iya wakilansa da wakilan yarinyar. Akuma hana kowanne biki da suka shirya da an ɗaura aure ya dauka matarsa su wuce kawai, sauran dokokina a kansa sai bayan ɗaurin auren ne”.      Shiru falon yayi kowa na nazari, bayan shuɗewar wasu mintuna Bappi ya fara jinjina kansa alamar gamsuwa. “Kamar hakan duk yayi gaskiya. Sai dai Jannatu mi kuke gani ku?”.        Anne dake ta danne kukan dake taso mata ta haɗiye da ƙyar. “Dattijo hukuncinka ai namune. ALLAH yasa haka shine mafi alkairi”.     Da amin duk suka amsa. Daga haka suka cigaba da tattauna abinda ya dace............✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/7, 1:32 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 59_* .........Bayan kwanaki biyar da wannan magana Bappi ya shirya da kansa yaje har masarautar Bina sukai magana da mai-martaba, sai dai bai sanar da shi ainahin dalilinsu game da sihiri dake tare da Ramadhan ba. Ya nuna masa suyi hakanne kodan gudun abinda zaije ya dawo ga mutanen ƙasa akan kallo da fasararar da zasuma al'amarin. Da yake mutum ne mai fahimta kuma yayi matukar yarda da Bappi a take ya amince ya kuma gamsu. Sai dai ya tsuke bakinsa ko fulani bai tunkara da zancen ba.     Haka shirye-shirye ya cigaba da gudana har biki ya rage baifi saura kwanaki takwas ba. Su gimbiya Su'adah nata shirye-shiryen fara sanarwa a gidajen redio da television Pa ya dakatar. Cikin ɓacin rai ta nema dalili yace idan lokaci yayi zata sani ai. Acan bangaren mai-martaba ma ya dakatar da Fulani da Adda Asmah, dan koda mijinta ya tsawatar shi da yake ya zama mijin tace batajiba, saima tujara data zuba masa gwargwadon iyawa shiko ya sanarma mai-martaba da dama shine ya bashi umarnin shima.      Wannan abu ya cuɗa musu zuciya. Babu kunya Gimbiya Su'adah harda kai karar Pa gaban su Bappi. Anne zatai magana Bappi ya girgiza mata kai, yace Gimbiya Su'adah taje zaiyo magana da Pa. Sai dai har yau da ya rage saura kwanaki biyar basuji komai daga bakin Bappin da suka san zai iya yiwa har mai-martaba magana ya janye sharaɗin daya sharɗanta akan duk wanda yay wani abu babu umarninsu a bakin auren Fulani ne. Tashin hankali kennan da ba'a saka masa rana. Domin kuwa wannan furuci na mai-martaba ya matuƙar birkita kowa a cikinsu har Ramadhan ɗin kansa da Gimbiya Su'adah ta kira a waya ta sanarma komai lokacin yana office. Da wannan ɓacin ran ya tabbatar mata zai shigo gidan da dare dama Bappi nata damunsa da son ganinsa ya sharesa.                      *_GOVERNMENT HOUSE_*.. Yau kam da wuri ya shigo gida saboda son zuwa Taura house da anyi magrib. Raudha najin shigowar motocinsa kuwa ta mike daga falo inda suke zaune suna tattauna tsare-tsaren bikin Bilkisu da ayanzu ta zame mata ƙawa dan dama bata da su sai school mate kuma ita iyakarta a gaisa babu aminiya. Saurin riƙota Bilkiau tai ta zaunar. “Ni banga amfanin wannan wasan ɓuyan da kike da shi ba, kiyi zamanki dan ALLAH karma ya samu kafar rainaki dan zai ƙara aure ko ya zata wani kishinsa kike ma”.      Kamar Raudha zatai kuka sai dai komai batace ba ta koma ta zauna ɗin. A haka Ramadhan ya shigo ya samesu. Akan Raudha ko ya fara sauke idanunsa, itama anyi sa'a kallon nasa take. Lokaci ɗaya zukatansu suka harba cikin bugu mai tsanani. Raudha da taga ya rame mata a ido sosai sai dai ya ƙara haske da ƙyau ta fara janye nata idanun fuskarta na nuna wani yanayi mai wajalar fassara. Shiko ido ya ɗan tsura mata tamkar mai nazari ko kuma yau ya fara ganinta. Sosai ya ga ta ƙara masa girma da cika. Dan duk da ciwo da take fama da shi a watan nan baki ɗaya saita kara buɗewa tai ƙiba da girma. Sannan komai nata ya ƙara girma ga haske tayi sosai mai tafe da wani sirrintaccen ƙyawu da duk hassadar mai hassada bai isa mata kallo guda ya ɗauke ido ba.        Kansa ne yaji ya sara masa. Yay saurin janye idanun a kasalance, sai kuma yay ƙoƙarin barin wajen kamar da ƴar sassarfa dan ko gaisuwar da Bilkisu ke masa bai amsa ba. Ƙofar ya maida ya rufe tare da jingina a jikinta lokcin da ya iso bedroom ɗin nasa. Ya ja ajiyar zuciya da sauke nanauyan numfashi idanunsa har sun kaɗa sunyi jajur. Ya jima a wajen tsaye kafin yaja kafafunsa da ƙyar zuwa toilet, agogon kawai ya cire ya sakarma kansa shower. Sai da yay sharkaf daga shi har kayan dake jikinsa sannan ya ragesu yay wanka....       Raudha da dama a cikin yanayi. dauriya take zaune a wajen ta miƙe da gudu tabar wajen hanunta toshe da bakinta. Da sauri Bilkisu ta bita har cikin toilet data shiga. Amai ta shiga kwarawa tamkar zata amayar da hanjin cikinta. Hankalin Bilkisu ya sake ɗagawa matuƙa ta riƙe Raudha. Sai da komai data ɗanci ya fita tas sannan aka samu lafiya. Bilkisu ta tamaka mata ta gyara jikinta da wajen suka fito tana jera mata sannu.       Cikin sauke numfashi a wahale tana kaiwa kwance ta ce, “Kai aunty B ƙamshin turare nan na Yaya babu daɗi”.        Sosai Bilkisu ta zaro idanu waje, sai kuma tace, “Kutt Aunty Raudha ƙamshin _Boucheron_ ɗinne baida daɗi? Anya kuwa kin shaka dai-dai?”.       “Ni wlhy lafiya lau na shaƙa, kuma dai tun yashe muke zaune a falon na ƙamshin komai bai dameni ba sai daya shigo ne ƙamshin turaren nan mai kama da ka.....”      Da sauri Bilkisu ta ruƙe mata hannu tana dariya, “Uhmm to lallai Taura grandchild bai zo da wasa ba.”     Sam Raudha ba wani fahimtarta tai ba. Bakuma tabuƙaci ba'asin mganar ba tama lumshe ido dan barci ke ɗan figarta ga kanta daya fara ciwo. *_TAURA HOUSE_*           Cikin matuƙar bayyanar tashin hankali Ramadhan ya ɗago yana duban Bappi da ya gama masa jawabi. A take idonsa ya rufe yama manta da wanda yake tare.       “Gaskiya bazai yuwuba Bappi, duk ma wada yake tunanin sharɗanta hakan ya janye dan ba yarda zanyi ba.  Tayama kamar ni za'ace a ɗaura aurena a sirri sai kace wani funafunci? Na muku biyayya na amince da zabinku kukai yanda kuke so nima dole a barni nai yanda nake so akan nawa zaɓin. Sannan maganar events banajin akwai ɗaya da za'a janye a ciki, ba sai kun dinga nuna hassadarku da adawa aka dangin mahaifiyata zan san kun isa da ni b.....”       Ji kake “tauuuu!!” Wani bazafaren mari ya sauka a saman kuncin Ramadhan har sai da ya kifa kamar zai faɗi. Pa da yake a fusace zai ƙara masa Bappi ya dakatar da shi. “No Basheer barsa barsa. Kai Ramadhan mu kake faɗama muna adawa da hassada da dangin uwarka!!”.        Har yanzu hanunsa a saman kuncinsa dan da gaske marin yay matuƙar ratashi. Cikin ƙanƙanin lokaci ya sake birkicewa gaba ɗaya, idanunsa suka rufe ruf. “Idan ba hassada ba a gayamin mi kuke musu? Kun rabani da su komai sai ku, tun ina 2years a rabani da uwata tayi kawaici ta bar muku amma hakan baisa kunga haƙurinta da kawaicinta ba. To wlhy daga yau ku sani ta ƙare, idan kuma kunce a'a to muzuba mu gani!!”.     Ya ƙare maganar cikin ƙaraji da nufar hanyar fita.           Da sauri Pa ya miƙe cikin wani irin fushi yay kansa shima. Sai da Bappi yay azamar riƙo hanunsa yana girgiza masa kai. Duk yanda Pa yaso yin magana Bappi ya hana shi, ganin yanda jikinsama ke rawa sai kawai ya rungumesa yana shafa bayansa murmushi na subuce masa na tsantsar zafin da yakeji a ransa. Da wahala kaga fushin Bappi. Mutum ne mai yawan fara'a da dattako, akoda yaushe fuskarsa ɗauke take da murmushi. Duk abinda kaga faɗansa akai an ƙuresane. *_GOVERNMENT HOUSE_*         Baƙaramin faɗuwa gaban Raudha dake zaune a gado tana karatu yayi ba. Babu haske mai yawa a ɗakin. ta zabi tai zaman karatu ne kafin lokacin da zata tashi ganawa da UBANGIJI ne. Ta zaro manyan idanunta akan Ramadhan daya shigo a tsananin fusace. “Innalillahi.....” har ƙarshe take ambata a jajjere harya iso inda take, wata irin muguwar damƙa yayma gashinta dake daure a tsakkiyar kai da hanunsa....        “K!! Har kin isa saboda aurenki a hanani yin yanda nakeso akan auren wadda zanyi? Wacece ke? Mikika taka?!.. Wato kinje kin kai munafunci garesu dansu hanani, to ai in gaya miki babu ubanda ya isa. Yau zan tabbatar miki ke ɗin ƙaramar mara kunyace kuwa wlhy...”       Kuka sosai Raudha keji jikinta na tsananin rawa. Ta shiga yarfa hannayenta duka biyu kuka mai ƙarfi na ƙwace mata ganin yana kunce belt ɗin wandon jeans ɗin jikinsa. Abu biyu ta kawo a ranta. Duka ko abinda yay mata ranar, dan haka tai yun ƙurin ceto rayuwarta sai dai hakan ya gagara. Dan tuni ya damƙota ya jefa saman gadon har sai da bayanta ya amsa dan azaba....... ★★★      Ihun Raudha ya matukar tada hankalin Bilkisu da ke ɗaki har barci ya fara daukarta. Ta fito a waje zuwa ɗakin sai dai ta samesa a kulle. Bugawa ta shigayi tana kiran sunan Raudha. Sai dai wata shegiyan ashariya da batasan Yayan nasu ya iyaba sai yau ya mulmulo mata daga ciki. Ai babu shiri tabar wajen a guje. Sai dai koda ta koma ɗaki wayar Anne ta kira. Tana dagawa ta fashe mata da kuka da fara zayyana mata abinda ta sani.      Sosai hankalin Anne da Bappi ya tashi, dan sun san ba kamar yanda Bilkisun ke tunanin Ramadhan dukan Raudha yake ba. Su sun san illolin daya dingama Amnah idan irin wannan ɓacin ran mai tsanani ya riskesa. sai dai suna ƙoƙarin rufe hakan ga kanensa idan ka cire Mardiyya da Safina dakan san wasu a wani lokutan.        Hankali a tashe tsoffi nan suka baro gida a daren nan tare da Dr Hauwa da suka taso itama ta waya suka nufo government house. Dan Dr Hauwa ce ma da kanta taja motar.      Lokacin da suka iso Ramadhan ya riga ya gama illata Raudha har jini ya ɓalle mata. Tunda ya fito a hargitse Bilkisu na son shiga tanajin tsoro. A durkushe suka sameta bakin ƙofar tana kuka. Tana ganinsu ta faɗa jikin Anne ta rungumeta.       “Anne ya kasheta, wlhy ya kasheta Anne!!”.      A tsawace Bappi yace, “Yana ina!?”. Cikin kuka Bilkisu ta sanar masa ya koma dakinsa. Hakan ya bama Anne da Dr Hauwa damar shiga. Bappi kuma ya tisa keyar Bilkisu ta nuna masa bedroom ɗin Ramadhan.        Hankalin Dr Hauwa da Anne ya tashi a yanayin da suka sami Raudha, dan haka babu wani kace nace Dr Hauwa ta fara ƙoƙarin ganin ta tsaida jinin. Tsahon lokaci ta ɗauka da taimakon Anne dake fama da tsufanta suka samu nasarar hakan.       “Anne bazai yuwu mu barta anan ba. Inaga muje da ita can wajenki dan tana buƙatar kulawa mai tsanani yarinyar nan a wannan gaɓar tunda Alhmdllhi cikin dake jikin nata mun samu ya tsaya. Da dai anyi dilay kam da labarin da ake ba wannan bane”.      Wasu hawayene masu sanyi suka sakko akan fuskar Anne. Farin ciki da cikin Raudha, da damuwar halin da jikanta yake sakamakon son zuciyar mahaifiyarsa.      A can kuwa ɗakin Ramadhan shigar Bappi tayi dai-dai da fitowarsa wanka, ya sauke towel ɗin da yake goge fusakarsa zuwa suma kawai yaji saukar mari haggu da dama. Gaba ɗaya wutar kansa ta ɗauke ganin wanda ya maresan. Bappi, abinda bai taɓa faruwa ba ko a tarihin ƙuruciya. Dan ko laifi yayi yana yaro sai dai Anne ko Pa su dakesa amma ba Bappi ba. A karshe ma Bappin ke komawa lallashinsa da masa nasiha. Amma sai gashi yau da girmansa. Shekara dai-ɗai har 36 a duniya kakan nasa ya rufe ido ya yarfata masa maruka har biyu bayan wanda Pa ya masa ɗazun....         “Ramadhan ka kiyayi haduwata da kai wlhy!!”. Bappi ya faɗa cikin gargaɗi da ke nuna tabbatarwa. Kafin yay wani yunkuri kuma ya juya yay ficewarsa.........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/7, 1:32 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode. 60_* .........*_TAURA HOUSE_*          Tunda suka baro government house a sirrance da Raudha kai tsaye Taura house suka nufo. sai dai anan ɗin ma dai babu wanda yasan da dawowar tasu kamar yanda kowa bai san da fitarsu ba. Sake dukufa Dr Hauwa tai akan Raudha har sai da ta tabbatar komai ya daidaita. Abin tausayi har ɗinki akai mata saboda bidirin da Ramadhan yay a jikinta. Hakan ya sake kona zuciyar Bappi da Anne sai dai babu wanda ya iya cewa komai har Dr Hauwa ta kammala aikinta ta wuce.      Barci Raudha take saboda allurar barcin da Dr Hauwa tai mata. Dan haka Bilkisu ta zauna ta zayyanema Anne komai data sani har wanda Raudha ma bata san ta sani ɗin ba. Anne harda hawaye tausayin Raudha mai tsanani na cin zuciyarta. Koba komai sune suka jefata a wannan masifar. Maybe dasun barta ta aura dai-dai da ita da duk hakan bai faruba. Sai dai kuma ƙaddara ta riga fata inji masu iya magana. Sannan kuma babu mai sawa ko hanawa daga abinda yazo a littafin ƙaddarar wani bawa koda yana kalon kansa matsayin SILA. *_WASHE GARI_*             Raudha ta jima bata farka ba har kusan tara, koda ta farka ɗin kuma Anne fidda kunya tai ta taimaka mata sosai kodan ɗinkin da akai mata. Ga Dr Hauwa ta tabbatar musu kar ai wasa da wani motsin Raudha mai karfi saboda cikinta a ɗofane yake. Hasalima bed rest shi tafi bukata fiye da komai a yanzun.            Tabbas abu biyu da Raudha tayi ya matukar birge Anne da Bappi. Na farko tambayar duniya sun mata akan abinda ke tsakaninta da Ramadhan ta keƙashe ƙasa ta dage akan babu komai. Tushen abinda ya faru tsakaninta da shi a jiya harya doke ta (dan duka suka danganta abun saboda alkunya da kawaici irin nasu) amma sai Raudha tace wai faɗuwa tai a toilet. Batasan su da idonsu sukaje sukaga halin da take a ciki ba. (Saboda sun ɓoye mata cewar Bilkisu ce ta kaita asibiti suma acan suka amso ta). Na uku tunda ta tashi babu wanda yaga ko ɗigon hawayenta alamar ta dake, wannan ya sakama Anne ƙwarin gwiwar cewar lokaci yayi da zatai training ɗin Raudha a bigiren da sai Gimbiya Su'adah da shaiɗanunta sunyi dana sani. Ramadhan kuwa zai matuƙar gane kuskurensa, ba ita zata hukuntashi ba Raudha ce da kanta zata hukunta shi. Hhhhh ashe akwai sabon show😋😉🤣. *____★____★_____★_____★_____*            Tsahon kwanaki uku Raudha na a Taura house babu wanda ya sani sai Bilkisu da Pa da su Anne. Koda Gimbiya Su'adah taga Bilkisu bataji komai ba tunda tasan dama tana shirin dawowa gida ai. Zuwa yau baƙi sun fara isowa daga masarautar su gimbiya Su'adah. Hakama a bangaren sauran matan gidan tunda kowa zai aurar da ɗa. Daga Taura ma dai wasu sun iso sai dai maza ne.     Babu wanda ya sake jin labarin Ramadhan babu kuma wanda ya bibiyesa, a kwanaki ukun nan ma ko a labarai sai dai kaji ance Shugaban kasa Ramadhan ya kaddamar da kaza da yawun wane. Amma shi ko sau ɗaya ba'a nunasa ba sai a yau da kowa yasan za'a tafi hutu na ƙarshen shekara da Christmas. Kuma kakakin shugaban ƙasa ya sanar a Taura house shugaban ƙasa zaiyi hutun nasa baki daya.         Hankalin Adda Asmah ya tashi matuka, musamman data kira bokanta yace sam karta yarda. Ita da suka gama cin burin kai Aynah government house kai tsaya ya Ramadhan ɗin zai musu haka, ya tabbatar mata ajiye Aynah a Taura house bazai taɓa haifar musu ɗa mai ido ba. Garama tayi duk yanda za'ai ta gyara barnar. Zuwa dare kuma tazo tare da Aynah zai mata wankan magani na ƙarshe da shine sirrin mallakar Ramadhan da duk ma wanda zai raɓesa, zai koma baijin magana ko umarnin kowa sai nata ita kaɗai Aina'u.         A rikice tai kiran Number Gimbuya Su'adah. Ita kanta gimbiya Su'adah ranta ya baci dan yau bata maida hankali akan television ba balle tasan da labarin. Tana can suna tafka rigima da Pa akan kofa dinner sai sunyi har guda uku idan ance sauran an hanasu. Shi kuma yace isar da bataiba kenan.      Ramadhan ta shiga nema, dan rabonta da shi yau kwana uku kenan tun randa ta kunna zuciyarsa akan kiran daya sanar mata su Bappi sun masa. Maimakon hankalinta ya tashi matsayinta na uwa ta nemesa sai ta share da cewar yana lafiya shiyyasa ko kuma aikin office ne ya rikesa.          A lokacin kwance yake yana barci, dan tunda aka baro Raudha daga gidan ya tsinta kansa a wani irin yanayi mai matukar wahalar fassara a garesa. Ya rasa mike masa daɗi mi kuma zai kama. Ransane a ɓace? Ko damuwa da halin daya jefa ƴar mutane? Kokuwa halin da ke shirin riskarsa na auren wadda shi kansa har yanzu baisan dalilin da yasa yake mata wannan mahaikacin son ba. Bisa lallabawar cos yake fita office. Sai dai baya wani jimawa yake dawowa gida. Kuma kullum ya shigo sai yaje ɗakin Raudha da mama ladi bata gajiya da gyarawa. Hatta jinin da Raudha ta zubar a wancan ranar idan bama faɗa maka akaiba bazaka sani ba. Yakanje ya kwanta a saman gadonta. Sai dai baya haɗa mintuna biyu kansa zai shiga sarawa da karfi har sai ya fito ya koma nasa.      Kunnawar da Ginbiya Su'adah tai masa yau ma ya sakashi tashi cike da fusata. Yay azamar dafe kansa dake juya masa da karfi. Sai kuma ya mike yana kallon agogo. Ƙarfe kusan sha ɗaya na dare. Amma tsabar yanda yake jin zuciyarsa tuni ya fice cikin ɓadda kama dan bazai iya jira sai gobe da zai huce Taura house ɗin ba ma, yanda yake komai saika ɗauka ana controling nashi da remote ne, dukya birkice, baya gane komai sai abinda su gimbiya Su'adah sukace yayi. Maimakon ma ko a motane yay fitar sirrin kamar yanda yakeyi, sai kawai ya fice da ƙafa ta karamin gate da taimakon odilan ɗinsa da baida ikon hanashi yin hakan saboda akwana biyun nan sam baya gane kan shugaban ƙasa, baya son yace wani abu kuma ga wani game da hakan saboda gargaɗi da Ramadhan yaja masa mai ƙarfi akan yanda yake fitar sirri inhar ya bari wani ya sani bayan shi duk hukuncin daya zartar a kansa yay kuka da kansa kawai. Cab ya tare sai taura house.                A dai-dai lokacin da Ramadhan ke nufar Taura house Adda Asmah ce da Aynah sun dawo daga gidan bokanta anyo mata wankan maganin mallaka. Sam batai tunanin haɗuwa da Ramadhan ba, shiyyasa ta yanke shawarar biyawa ta Taura House takai maganin da bokan ya bata akan gimbiya Su'ada tai turare da shi matsayin na rufa idon su Bappi akan events ɗin da suke sonyi. Sai dai a zahirin gaskiya ba hakan bane. Na rabata da Ramadhan ne baki ɗaya yanda zai koma karƙashin ikon ita Addah Asmah ɗin.        Kusan a tare Ramadhan da su Addah Asmah suka iso Taura house. Sai dai shi ya rigasu shigowa saboda an tsaya buɗe musu gate shiko yay wuff ya shige yanda ko mai-gadi ma bai lura da shi ba. Kai tsaye falon hutawa na gimbiya Su'adah ya nufa ta baya kamar yanda ta sanar masa ya sameta a can. Ko zama baiyiba Addah Asmah da Aynah suma suka shigo kamar yanda Gimbiya Su'adah ta sanarma Adda Asmah itama ta sameta anan. Adda Asmah bata san Ramadhan zaizo taura house ba. Haka zalika gimbiya Su'adah batasan Adda Asmah na tare da Aynah ba tunda tasan dokar dake tsakanin kar Ramadhan da Aynah su haɗu sai bayan an ɗaura aure....... *_Tofa dole na dara kafin na cigaba🤣😂🤣😂, wannan fa shine ana dara ga dare yayi🤣. Ga boka yace kar.....🤭😂bara dai kawai na tsuke bakina muga yaya wasan zai kaya to._*       ★Wani irin ihu Adda Asmah da Ayna'u suka fasa a tare cikin tsantsar tashin hankali. Dan kuwa sallamar Aynah dake gaban Addah Asmah tayi dai-dai da ɗagowar Ramadhan saboda ƙofar falon da aka buɗe batare da yayi tunanin wani zai shigo musu ba.       Ita kanta Gimbiya Su'adah dake ƙoƙarin kunna buner ta saka turaren hayakin magani da boka yace ta dinga sakawa a duk sanda Ramadhan yazo gareta ta saki tare da yin wani uban tsalle tana dafe ƙirji.          “Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un. Allahumma ajirni fi musibati.....” Ramadhan ya ambato a jere saboda suna haɗa ido da Aynah gabansa yay wani irin mummunar faɗuwar da har sai da kansa ya sara. Hannu ya kai ya dafe kan saboda yanda ihunsu ke shiga masa har tsakkiyar kwakwkwararsa. Duk da kunne sa daya toshe ihun bai fasa shiga ba. Kai bama shi ba, hatta duk wanda yake kusa da sashen gimbiya Su'adah dole ne yaji tagwayen ihun nan.       Pa ne ya fara shigowa a kiɗime. dan kamar yanda ya saba duk dare kafin ya kwanta sai ya zagaye gidan ya tabbatar da komai normal jininsa kuma ya motsa yauma hakance ta kasance. Yana ta wajen babban gate ɗin gidan baki ɗaya yaga shigowar Ramadhan. Duk da ya rufe fuskarsa da hular jacket ɗin jikinsa da facemask hakan bai hanashi shaidashi ba. Dan babu wata ɓadda kama da Ramadhan zaiyi bai gane abinsa ba. Shiru yay ransa fal al'ajab, bai gama dawowa hayyacinsa ba kuma sai ga motar su Adda Asmah ta danno kai. hakan ya sashi kiran Anne da Bappi da Yafendo a waya yace suzo dan ALLAH. Shi kuma ya biyo bayan su Addah Asmah ɗin.       Takan kowa Pa bebiba tsakanin Aynah da Adda Asmah data zube ƙasa kamar wadda ma ta suma. Yakai ga ɗansa dake jujjuya kansa cikin tafukan hannunsa alamar akwai abunda ke faruwa da shi. A dai-dai nan su Anne ma suka iso, suma duk kan Ramadhan ɗin sukayi hankalinsu tashe. Sai kawai sukaji ya fasa wata gigitacciyar ƙara da duk wanda ke a gidan nan ƙarya yake yace bai jita ba.     Innalillahi kawai suke ta ambato, Pa ya riko Ramadhan dake shirin kaiwa ƙasa ya ringumesa a jikinsa. Rawa sosai jikinsa keyi kamar mazari. Hakan yasa Bappi ma tallafawa suka riƙosa.         “Basheer kafin attention ɗin kowa ya dawo nan ɗin mu fita da shi”.      Shawarar Bappi Pa yabi, suka kama Ramadhan da har yanzu yake faman jujjuya kai sukai waje da shi, fitarsu kamar ƙyaftawar ido jama'ar gidan suka fara tururuwar shigowa falon a gurguje. Su kum ganin Adda Asmah kwance duk sai sukai kanta. Da wannan damar Anne da su Yafendo suka zame jikinsu suka bar falon.          ★★     “Ya ALLAHU miya faru? Suma yay?”. Cewar Anne dake shigowa falon Bappi idonta akan Ramadhan da suka shimfiɗar a ƙasan carpet Pa na kokarin shafa masa ruwa. Kai kawai Bappi dake zaune kan Ramadhan ɗin a cinyarsa ya ɗaga mata. Wani nannauyan numfashi Ramadhan ya ja a fisge sai kuma ya sake riƙe kansa zai fasa ƙara Bappi ya rufe masa bakki.       “Tabbas akwai matsala, inaga akwai lamarin azzaluman aljanun sihiri tare da shi”. Cewar Yafendo tana kuka. Da sauri Anne ta fita a ɗakin tana faɗin bara ta ɗakko alkur'ani. Bappi na kiranta tazo ta ɗakko na ɗakinsa bama taji ba harta fice. Zaune ta iske Raudha na karatun alkur'ani da alama sallar shafa'i da wutiri ta idar. Ai tama manta da batun bedrest da Raudha keyi ta kamo hanuntan.          “Ameenatu taso ga inda ake buƙatar karatun nan naki can.”     Hankali tashe Raudha ta dakata, ganin Anne a firgice yasa batabi ba'asi ba ta mike kawi ta bita. Sanye take cikin dogon hijjab fari har ƙasa. Dan haka baka iya ganin komai nata sai fuska da tafukan hannu.........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Gu :* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a t aikin bautar bature zo kiji wata magana”.     Gabantane ya shiga faɗuwa. Sai dai ko saurarenta baiyiba yaja musu bargo ya matseta a jikinsa yana shinshinar wuyanta da kai mata kiss's..........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 _[7/7, 1:32 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode. 61-62_* ...........Wani irin tsargawa kanta yay ganin Ramadhan shimfiɗe a ƙasa Bappi ya toshe masa baki, ga Pa a kansa yana karatun suratul baqara. Tuni jikinta ya fara rawa. Ta matsa da sasaarfa takai duke gabansa cikin rufewar idon manta waɗanda suke a falon. “Ya ALLAHU na shiga uku ni Raudha Ya Ramadhan mike faruwa da kai haka?”.          “Kinga Ameenatu yi hakuri baya cikin hayyacinsa yi masa karatun kawai”.     Ai Bappi baima kai karshe ba ta fara karatun itama cikin suratul baqaran. Wata muguwar zabura ya kara yunkurowa zaiyi saboda masu karatun sun zama biyu, ga zazzaƙar murya da ALLAH ya azurta Raudha da ita inhar tana karatu komai taurin zuciyarka saika nutsu a saurare. Tun sunayi yana fisge-fisge har ya fara lafawa a hankali. “Idan ma mu an koremu ai akwai wanda suke tare da shi tun yana yaro”.      Bakin Ramadhan ɗin ya faɗa a kausashe, amma a tabbaci bashi bane sai kuma ya fara sakin tari mai ƙarfi. Raudha da Pa basu dakataba suka cigaba da karatunsu sudai. Yayinda Anne ke duke gabansa tana rike da kansa ita da Bappi. Tsahon mintuna talatin suka sake kwashewa suna karatun kafin jikinsa yayi laƙwas. Duk da hakan Raudha bata dakata ba har sai da takai karshen suratul baqara lokacin agogo ke nuna karfe ɗaya da wasu mintuna na dare.       Ta matuƙar birgesu, sun sake jin kaunarta mai tsanani da taya gudanjininsu murnar samunta matsayin mata uwar ƴaƴansa. Bayan ta rufe da addu'a suka shiga sanya mata albarka. Ita dai kanta a ƙasa tana sharar hawaye. babban burinta tasan miya kawo mijinta gidan a wannan halin? Yama akai yazo? Miya faru da shi?. Waɗan nan sune jerarrun tambayoyin dake mata yawo bisa kai. Sai dai ta kasa furtasu ga kowa.        Anne da tasan lokacin barcin Raudhan ya gota cikin sanyin murya tace, “Ameenatu kije ki kwanta kinga kema fama kike da jikinki. Tunda Alhmdllhi da alama komai ya dai-daita barci ne ya ɗaukesa. Kamar Raudha zatace a'a sai kuma tay yunkurin mikewa domin bin umarnin Anne. Caraf taji an ruƙo mata hannu, bama ita kaɗai ba kowa a ɗakin sai da ya kalli hanun Ramadhan ɗin, kafin ya firta. “Ameenatu ruwa! Bani ruwa na sha inajin ƙishi”.       A hankali yake maganar amma hakan bai hanasu jinsa ba. Raudha duk kunya ta isheta. Amma saita daure ta dauka goran ruwan dake kusa da Anne, a sanyaye tace, “Ga ruwan to buɗe idonka”.       Bakinsa kawai ya buɗe mata yana ɗan girgiza kansa, kamar zata sake magana sai kuma Bappi ya dakatar da ita ta hanyar ɗago kan Ramadhan ɗin yanda zata iya zuba masa ruwan batare da ya cutar da shi ba. Duk da kunyar da takeji haka ta daure ta ɗora masa gorar a baki. Sai ko gashi yana zuƙarsa da yawa harya shanye. A hankali ta janye goran shi kuma ya ɗan buɗe idanunsa yana kallonta. “ALLAH yayi miki albarka”. Ya faɗa a hankali tare da maida idanunsa ya lumshe.      Kusan atare duk suka amsa da amin tare da sauke ajiyar zuciya. banda Raudha datai kasa da kanta ta amsa a kan laɓɓa. Bappi ne ya basu umarnin zuwa su kwanta, shi kuma zai kwana da Ramadhan ɗin sugani ko zuwa asuba zai dawo hayyacinsa su samu ya koma can government house kafin a farga. Dan sun tabbatar fitar ɓadda kamar daya sabayice yayo yau ɗin ma.      Badan Raudha taso ba ta mike. Koda suka isa ɗaki Anne wanka ta sakatayi, ta bata tea tasha kamar yanda ta saba turketa a duk dare kafin ta sakata kwanciyar dole. Sai dai ta lumshe idanune kawai badan barcin ba. Amma ita kanta tasan idan tace zatai barci a irin wannan halin yaudarar kanta zatai kawai...        A ɓangaren su gimbiya Su'adah kam kowa tunda baiga Ramadhan ba sai hankalinsa ya karkata akan Addah Asma'a da suka samu a kasa wanwar. Ruwa aka bata tasha, aka kuma dagata zuwa kujera sannan suka shiga mata sannu. Bayan numfashinta yaɗan daidaita Gambiya Su'adah ta sallemsu su duka falon ya rage daga ita sai Adda Asmah da Aynah.       “Adda inaga kuje gida zanzo da safe na sameku, dan zamanku yanzu anan akwai matsala zai iya fargar da jama'ar gidan wani abu. Su kuma ku barni dasu game da Ramadhan zanma tufƙar hanci”.       Addah Asmah da ba fahimtar komai takeba a yanzu gudun kar gimbiya Su'adah ta ɗagota ta jinjina mata kai ko maganin da suka kawo ɗin bata samu bata ba suka fice cikin taraddadin da ƙaulani. Numfashi gimbiya Su'adah saukewa, kafin ta nufi sashen su Anne. Sai dai tana tu karowa taji sautin karatun Raudha da Pa. Wani irin kunci da duhu zuciyarta ta sake shiga najin tsantsar tsanar Raudha da batasan yaya akai tazo gidanba ya riketa. Tunanin ko dama tare da Ramadhan sukazo ya sata juyawa ta fasa shiga baki ɗaya ta koma sashenta tana haɗiyar zuciyarta data cika kirjinta fam kamar zata fashe. ★_★★____________★★_★               Da asubar fari Bappi ya fita raka Ramadhan government house, kamar yanda ya fita ta barauniyar hanya yanzun ma tanan yabi da taimakon odilan nashi da shi kaɗai dama yasan da fitar. Tunda yaga bai dawo akan lokaci ba hankalinsa yake a tashe. Shi kansa yasan irin waɗannan fitar da shugaban ƙasar keyi akwai haɗari a cikinta. Sai dai shi ko'a jikinsa. Ko'an nuna masa illar fitar ɓadda kamar baya nuna damuwa ko hango wata matsala. Amma har cikin rai odilan ɗin nasa na tsoron randa wani zai farga a cikin gidan ko waje.          A taura house kam koda aka wayi gari babu wanda ya tada zancen. Musamman daga sashen Anne. Ita kanta gimbiya Su'adah tana son ma Pa magana tanajin tsoron a yanda ya tashi yau fuska kamar hadarin gabas. Amma har cikin rai tana buƙatar jin halin da yaronta ke ciki. Ta kira wayarsa amma ba'a ɗaga ba, ta rasa inda zata tsoma ranta ta huta har baƙi dai suka fara isowa irin su Safina da tawagar ƴaƴanta. Sai daga masarautar Bina kuma.      Zuwa Azhar gidan ya fara ɗaukar baƙi sosai. Hakan ne ya tilasta Gimbiya Su'adah fasa fita gidan Addah Asmah dan tun jiya da suka bar gidan bataji daga garesu ba. Ta kira duk wayoyinsu a kashe. Ta aika Muneera ta dawo ta sanar mata Aynah da Addah basa gida wai tun safe suka fita baƙi ma daketa isowa babu wanda ya samesu a gidan sai ma'aitan gidan keta saukesu. Wannan zance ya sake tada hankalin gimbiya Su'adah matuƙa dan haka ta kira fulani da suke shirin tahowa da yamma ta sanar mata. Duk da fulani tasan komai sai ta ɓoye mata akan ta kwantar da hankalinta zata bincika. Amma tasan Addah Asmahn bazataje wani waje ba daban. A sanyaye tace to.       Fulani ta sauke wayar tana taɓe baki. Dan yanzu sun ƙudiri aniyar daina faɗa gimbiya Su'adah komai akan shirinsu. A ganinsu sakacintane ya lalata komai a daren jiya kokuma akwai abinda take son gujemawa. Itako fulani burinta da alwashinta sai ta nunama Anne ba itace kaɗai keda iko da Ramadhan ba, yayinda Addah Asmah ke nuna itama shine burin nata. Sai dai acan kasan rai ba haka bane. Baƙar hassadar ƴar uwartace kawai ke cinta akan ta fita komai na rayuwa. A ganinta mallakar Ramadhan matsayin mijin ƴarta, zaisa abinda Gimbiya Su'adah ke takama da tinƙaho da shi ya dawo tafin hanunta ƙarƙashin ikonta.         Faruwar komai a jiya yasa Aynah kwana kuka akan bazata iya haƙuri da Ramadhan ba a yanzu. Ita duk ma yanda za'ai ayi ƙoƙarin gyara matsalar nan da suka tabbatar komai ya watse. Wannan shine dalilinsu na tafiya gidan boka bayan tun dare sun kirashi yanata faɗa akan abinda tunkan su sanar masa yace musu ya sani tunda aljanin daya turama Ramadhan yaci ubansa hanun Raudha da Pa da ayar ALLAH. Tun tafiyar da sukai da asubahin nan suna can har yanzu anata sake tsumo Aynah da shaiɗanci kala-kala akan Ramadhan kawai.... To bara muga wazaiyi winning anan kuma🚶🏻🤕. *_____________________________*               Ƙarfe biyar na yamma dai-dai tawagar shugaban ƙasa Ramadhan ta iso Taura house bisa rakkiyar jami'an tsaro da wasu na jikinsa. Kamar wancan hutun tako ina anguwar ta zama ƙarƙashin mulkin mallakar jami'an tsaro ne. Sauƙin ma dama can anguwar manyace bawai hayaniya ko yawan shigi da fici ake samu ba. Sai dai abin ya shafi masu tururuwar zuwa biki. Dan duk waɗanda suka iso yau dasunci karo da jami'an tsaron nan sai tsoro ya kamasu duk da sunsan yanzu Taura house yana da wani sabon girma bayan wanda kowa yasan gidan da shi.      Babu wanda yaga Ramadhan, domin motar da yake ciki har jikin ƙofar falon Bappi ta baya aka kaita, yana fita kuma ya shige ciki abinsa.       Raudha na bedroom ɗin Anne kwance ta gama ƙwallar shan kunu da Annen ta tsareta tayi Bilkisu ta shigo ɗakin da sallama. Wayar ta dake hanunta tana game ta ajiye, dan dama game ɗin kawai takeyi amma hankalinta naga mijinta da tunanin miyake ciki yanzun? Yana ina? Jikinsa da sauƙi ko babu?.         “Sai a daina mana shagwaɓa ga boss nan ya iso”. Bilkisu daba sanin abinda ya faru da Ramadhan ɗin tai jiya ba ta faɗa tana dariya bayan takai zaune kusa da Raudha. Murmushi kawai Raudha tayi da faɗin, “Kai aunty ni shagwaɓar mi nayi?”.       “Ai ba abun jayayya bane bara na lissafa miki yanzu kuwa ɗaya bayan ɗaya ta Brothe......”      Ta kasa karasawa saboda wanda ya shigo ɗakin. Da farko tsoro taji sosai ita kanta Bilkisun, sai dai yanda taga yanayinsa kamar a sanyaye ya sata ɗan sassautawa ta gaisheshi zata mike. Sai dai Raudha tai saurin riƙo hanunta idanunta na cika da ƙwalla. Sosai yanzu tsoronsa takeji, tsoro mai tsanani dan ita kaɗai tasan azabar da taci a hanunsa har sau biyu da bazata taɓa iya mantawa ba.        Raunanannun idanunsa ya sauke akan hannayen da Raudhan ta sarƙe. Sai yaji wani irin tausayinta mai tsanani yana dirar masa daga tsakkiyar kai har tafin kafa. Da ido yayma Bilkisu alamar ta fita. Dan haka tai saurin son zame hanunta cikin dabara tana faɗin, “Aunty Raudha bara na dawo tanan sai Yaya ya zauna nan”.      Sam Raudha bata yarda ba, saita ƙara ƙwaɓe fuska zatai kuka. Bilkisu da ita kanta tausayinta takeji tunda batasan ko yayan nasu bai dawo cikin hankalinsaba har yanzu ta zame hanunta ta gudu. Sosai jikin Raudha ya fara rawa ganin ya maida ƙofar ya kulle harda key. Babu shiri ta miƙe a kan gadon tana ƙoƙarin sakkowa. Sosai tayi ƙiba, tako'ina komai yayi zam, damma doguwar rigar jallabiyace a jikin nata baƙa. A hankali ya lumshe idanunsa tare da harɗe hannayensa duka a ƙirjinsa, sai kuma ya sake buɗesu ya zuba mata. Yanda take rawar jiki yasa ko'ina nata ke motsawa, ga rigar mai santsi ce, sai hakan ya ƙara taimakawa wajen motsawar jikin nata.      Murmushin takaici da tausayin kansu ya saki. Baiga laifinta ba, dan yasan dolene taji irin wannan tsoron nasa. Ya ɗan furzar na numfashi tare da warware hannayensa daga ƙirji ya fara takowa gareta cike da nutsuwarsa da kasalar yanayin rashin jin daɗi da yake a ciki........✍ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account. *Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks. *Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku. A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant). -------- Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar: *Bank Transfer* *Airtime Transfer* Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance. *Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks. _Account No_ - *1220077999* _Account Name_ - *Arewa Books Publishers* _Bank_ - *Zenith Bank* Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din: Amount Paid: - Nawa aka tura? Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa Transferred time: - lokacin da aka turo Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi Deposit date: - ranar da aka turo Sai ayi SUBMIT. *Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar: MTN, 9Mobile Glo Airtel Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance. *WANNAN SHINE BAYANAN* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/12, 10:50 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 63-64_* ...........Ƙasa takai durƙushe cikin rawar jiki. Ta haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo. “Ya Ramadhan dan girman ALLAH kayi haƙuri, na tuba kar kayi zan iya mutuwa yau. Wlhy wajen har yanzu yana ciwo”.        Kasa jurewa yay, sai da ƙwalla suka taru masa a ido. Matarsa ta sunna ke tsoronsa saboda yaje gareta tamkar karen farauta. Ya kusanceta tamar babu zuciya a ƙirjinsa. Maimakon abinda Raudha tai tunanin sai taga saɓanin hakan. Dan shima gabanta yakai durƙushe. Ya ɗora duka hannayensa kan nata ya riƙe. “I'm vary sorry Ameenatu ki gafarceni dan ALLAH”.      Ya faɗa cikin wata iriyar murya mai tsananin rauni da rawa. Da sauri Raudha ta buɗe idanunta dake rufe, danjin furucinsa da sautin muryarsa. Sosai ƙirjinta ya buga ganin hawaye a fuskar mijinta. Sai ta sake fashewa da kuka tana girgiza masa kanta. “Dan ALLAH Ya Ramadhan kabar kuka”.          Hanunsa dake cikin nata ya riko, ya jawota ta faɗa jikinsa, sai kawai suka saki kukan a tare abin tausayi. Tsahon mintuna uku suna a haka. Kafin Raudha ta ɗago tana share hawayenta tana magana. “Kaga dan ALLAH kabar kukan Abokina. Kaga nima na daina. Kuma ni ban taɓa rikekaba dama na yafe maka. Kai harma wanda zakamin a gaba na yafe maka Ya Ramadhan. Dan ALLAH ka daina kuka kar wani ya shigo, idan wani ya ganka a haka bazan yafema kaina ba”. Ta ƙare maganar tana kai hannayenta saman fuskarsa ta shiga share masa nasa hawayen.         Murmushi yay mata, wani irin kaunarta na ratsashi. Ya riƙo hannayen nata da take share hawayensa ya sumbata. Idanunta ta lumshe a hankali, saƙonsa na ratsa mata jini da ɓargo. Ciki disashiyar muryarsa yace, “Ustazah!”.       Idanun ta buɗe a hankali tana kallonsa. Ya kafeta da nashi dake cikin yanayin shauƙi da bege. *_“I love you!. Am serious I love you more than you can ever comprehend. Kinada muhimmanci a duniyata. Ina miki irin son da bayan mahaifiyata da Anne ban taɓa yima wata mace a duniya ba sai ke. Bazance miki ban taɓa so ba, sai dai inajin naki daban. Ga Ramadhan nan Ameenatu, Ramadhan B. Hameed Taura ya mallaka miki kansa da duk abinda yake nasa sai yanda kikai da shi, dan ALLAH karkici amana, karkiyi butulci, karkiyi amfani da wannan soyayya da dama ki cutar da shi......”_*       Gaba ɗaya jikin Raudha rawa yakeyi, gaba daya ya kashe mata jiki, ya sakata cikin taradadadi da kaulani. Ta fashe masa da wani irin sassanyan kuka mai tsuma zuciya.         “Nima ina sonka Ya Ramadhan, ina ƙaunarka da iya gaskiyata. Insha ALLAH bazan taɓa cutar da ko dabban Taura family ba balle kai. Har abada ko wanda zai ci amanarka bazan barsaba ma balle ni kaina. Ina fatan ko mutuwa ta ɗaukemu rana ɗaya, lokaci ɗaya, mu zama maƙwaftan juna a kabari sannan mu kasance ma'aurata a aljanna.....”        Fuskarta ya kamo cikin tafukan hanunsa ya haɗe goshinsu, sai kuma ya manna lips nashi akan nata tare da rungumeta a jikinsa.        Da sauri Anne da Bappi dake tsaye jikin window suna kallonsu suka ɗauke kansu. Anne tasa hannu ta share hawayen da suke saukar mata a fuska na ɗunbin tausayin waɗan nan ma'aurata. Tun fitowar Ramadhan daga falon Bappi Anne ta biyosa da shirin dakatar da shi, dan ta ɗauki aniyar saita wanashi akan Raudha. Biyota Bappi yay da hanzari shima da zummar dakatar da ita, sai dai tana ƙoƙarin gitta window ɗin ɗakin nata dake tabayan sashen Bappin ta tsinkayi roƙon da Raudha kema Ramadhan. Cak ta tsaya, a kuma dai-dai nan Bappi ma ya iso, ganin taja birki shima yaja ya kai dubansa ga abinda take kallo. Wannan yasa komai dake wakana a kan idonsu ne akuma kan kunnuwansu. Hannunta Bappi ya kama suka bar wajen.       “I need you Please”. Ya faɗa murya a sarƙe lokacin da yake janye lips nasa daga kan nata. kai ta shiga jujjuya masa cikin tashin hankali, har hawaye sun sake cika mata idanu.        “Please Ya Ramadhan forgive me wlhy akwai ciwo”.     Da ƙyar ya iya rumtse idanunsa da suka kaɗa sukai jajur, dan tabbas bukatarta yake mai tsanani, bakuma zaiso cutar da ita ba. Amma dole ya samawa kansa mafita ba kuma a ɗakin Annensa ba, dan akwai kunya a raka baƙo ya ruga...       “Shike nan naji, amma muje zan duba naga ɓarnar da nayi dan ALLAH”. Yay maganar a wani irin marairaicewa kamar bashi ba. Zatai magana itama ya girgiza mata kai tare da ɗora hanunsa kan lips nata alamar kartace komai. Dole tai shiru, ga tsoro ga fargaba. Haka ya kamata ya miƙar, batare daya bata damar cewa komai ba ya kama hanunta suka fito. Addu'a take a ranta ALLAH yasa babu kowa a falon, duk da tasan dai ta inda zasu ratsa ɗin ba falon da kowa ke iya shigowa bane sai iya ahalin gidan kawai.        Ta ɗanji sanyi da basu haɗu da kowa ba, sai dai mai aikin Anne dake ƙoƙarin shirya abincin dare a dining. Koda suka fito kam kasa tai da kanta tana gaida Ramadhan ɗin. Hannu kawai ya iya ɗaga mata suka wuce, dan yasan inhar yay magana kai tsaye za'a gane yanayin da yake ciki. Ko'ina ƙal yake a sashen nasa. Sai ma kamshi na musamman dake tashi dan Bilkisu da Basma ne sukai bautar gyaransa. Suna shigowa cikin ɗar-ɗar Raudha tace zanyi fitsari dan ALLAH. Sakar mata hannu yay kawai batare da yace komaiba. Sai ma ƙoƙarin rage babbar rigar shaddar jikinsa yake.       Babu wani fitsari da zatayi, tayi hakane danta kuɓutar da kanta daga garesa. Sai dai tasan hakan bamai yuwuwa bane. Amma tanada tabbacin yace zaiyi wani abu yanzu ɗinkin jikinta zai farke ne. Bayan kuma Dr Hauwa ta mata gargaɗi matuƙa akan ta kiyaye ta kuma kula sosai, shiyyasa Anne ke tsaye kanta kullum sau uku take shiga ruwan zafi.        Jin sautin kiran salla ya sata lumshe ido daɗi na matuƙar ratsata. ALLAH ya kawo mafita kenan. Jin kamar ana taɓa ƙofar tai saurin fara alwala. Kallonta kawai ya tsayayi sai kuma yay murmushi.        “Duk dai wayon Amarya Ustazah...”      Baki ta tura gaba lokacin da take ɗagowa bayan kammala alwalar, “Toni wane wayo nayi”. Tai maganar da kauda idonta a kansa dan ya cire har ƴar cikin da ga shi sai wandon shaddar da singlet baka.           “A'a ni minace kuma. Kefa daɗina dake fassara bawa a mizanin da bai kai ba. Ke dai jirani nai alwala kawai”.         Gwalo ta masa batare da tunanin ya ganta ta mirror ba. Sai dai yay shiru kawai dariya na cinsa a ciki. Bayan ya kammala suka fito, shine yay musu jam'i, dan duk nasihar datai masa akan zuwa massallaci nunawa yay ai lalura ce zata hanashi. Tasan ya bijirene kawai dan son ransa. Amma badan baisan hakan ba. Bayan sun idar ta ɗauka alkur'ani zata fara karatu ya riƙe.         “K ALLAH inaga zare miki ido zan komayi maybe zaki fara tsorona. Mai kan kwakwa kawai”. Ya kare maganar da mangare mata kai. Fuska ta kwaɓe tana shafa wajen. “Ni gasky ban yarda ba”.         Cikin ɗage gira yace, “Ko? To zoki rama mana”.       Tashin kuwa tai ta bisa, yana ajiye Alkur'anin zai ɗago ta bashi mintsini mai shegen zafi a damtsen hanunsa.      “Kamm lalai yarinyar nan kinci abinci, ni kikama wannan muguntar?”.       Dariya ta ƙyalƙyale da shi tana ƙoƙarin kwasa da gudu yay tsalle ɗaya ya cafkota. Jikinta ta fara fisga tana haɗiye dariyar dake cinta amma ina tazo hannu, gaba ɗayanta ya dauka cak yay kan sofa da ita. Duk yanda take watsal-watsal da ƙafafu bai saurareta ba. Sai ma dariya da yake mata harya direta. “Rama cuta ga macuci ai ibada ne yarinya”.          Yay maganar da kwashe hijjabinta gaba daya ya ajiye. Hannayenta dake kai masa ƙananun duka a ƙirji ya riƙe tare da kwantowa kanta, sai dai bai sakar mata nauyinsa ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ladabtar da zille-zillenta ta nutsu tana amsar saƙonsa. Sai dai acan kasan ranta a matukar tsorace take. Sai da ya tabbatar tayi laushi ya nema bin hanayar da take tsoro ta fara masa kuka da magiya. Dama ba zuwan zai ba. Amma ya tabbatar mata zai ƙyaleta idan tai masa abinda yace. Ko musu babu kuwa ta amince. Dan gwara hakan ita dai da abinda takewa tsoron.......       Luf take shiru a jikinsa tana sauraren yanda yake sauke numfashi a hankali da sanya mata albarka. Yayinda hanunsa ke cikin sumar kanta yana faman wasa da ita duk ya birkita mata ita. Murya can kasa a ɗashe tace, “Ya Ramadhan sallar isha'i fa akeyi”.       “Uhhm naji ai”. Ya faɗa a shaƙe idanunsa rufe. Shiru tai bata sake cewa komai ba har kusan mintuna biyar sannan ya miƙe. Kai tsaye toilet ya shiga, hakan yasa Raudha lumshe idanu da sauke ajiyar zuciya takai hanunta saman cikinta tana shafawa. Bata san yaya zaijiba idan yasan tanada ciki, ita kanta a duk sanda ta tuna akwai ɗa mai alaka da shi tanajin tsantsar farin ciki. Badan shi shugaban kasa bane, badan shi jinin Taura family bane. Sai dai ɗunbin soyayyarta da take hangowa a cikin idanunsa. Motsin fitowarsa a bayin ya sata dawowa hayyacinta daga dogon tunanin data lula.           Yanda ya fito yana goge sumarsa da jiki ya tabbatar mata wanka yayo, saurin ɗauke kanta tai ta maida gefe. Yay ɗan murmushi da ƙarasawa jikin Wadrobe ɗinsa domin duba kaya. “Madam tashi kiyi wanka muyi salla”.        “Ni alwala kawai zanyi”. Ta faɗa a shagwaɓe tana mikewa a gadon itama. Murmushi kawai yayi amma komai baiceba harta shige toilet. Sai dai kuma ashe cika bakinne kawai, dan itama dai hummm kawai............✍ *_Alhmdllhi barka da salla, ALLAH ya maimaita mana ya amshi ibadunmu baki ɗaya. ALLAH ya dawo mana da mahajjatanmu gida lfy, ya jiƙan iyayenmu, ya ƙara mana lafiya da zama lafiya. Inama kowa barka da salla ina kuma jiran naman salla dan nagafa sai nayi tuni za'a kawon kenan🤕👩🏻‍🦯_*. *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/13, 11:26 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 65-66_* ...........Fitowarta dai-dai da ƙoƙarinsa na kammala busar da sumarsa. Ya kalleta kawai ya ɗauke kansa baice komaiba. Dan rigartace dai a jikinta data shiga da ita ala dole babu abinda tayo. Sai da ya shimfiɗa abin salla ya miƙa mata wandonsa mai taushi na adidas da farar t-shirt. “Saka muyi salla lokaci na shigewa”.     Kanta a kasa batare data kallesa ba tace, “Bafa abinda ya sameta”.       “Humm Ameenatu kenan, karki manta na rigaki zuwa duniya. Bayan rigaki shekaru kusan goma sha takwas na baki, kinga a lissafi kuwa lokacin da nake a mizanin shiga shekarun girma na ɗa namiji aka haifeki”.       Kunya kamar ta nutse. Dan sam batai tunanin ya ganeba. Dama sotai ta masa dabara sai sun tada sallar ta gudu ɗakin Anne ta canja kayan tai salla.         “Hallo! Ko sai na nuna miki shaida ne dan rigar kanta ta tona miki asiri tare da wannan”. Ya tura hanunsa cikin hular kanta ya jawo silin jiƙaƙƙen gashinta a ciki. Da sauri ta kwashi kayan zata koma toilet”.        “Hii aini ba surukinki bane canjasu anan konazo na canja miki kina ƙara makarar damu”.      Babu yanda ta iya dole tabi umarninsa, bayan ta saka kayan suka gabatar da sallar. Suna idarwa wayarsa ta hau ruri, yasan Anne ce dan haka ya miƙe zuwa bedside drawer ya zauna a bakin gadon yana daukar wayar....         “Kai ka fita idona kawomin yarinya taci abinci tana fama da kanta”.       (Mutum da matarsa ƙarfin hali kenan) ya faɗa a zuciya yana sakin murmushi. A fili kam yace, “Okay Gimbiyar Bappi yanzu kuwa maida wukar”.                 ★Gaba ɗaya Raudha jitake kamar ta nutse dan kunya. Kanta a kasa ta risina ta gaida Anne da Bappi. Zata zauna kusa da Bilkisu dake tare da su yaja mata kujerar kusa da shi tare da kamo hanunta yanda su Bappi bazasu gani ba. Sai dai ya makaro sun gani ɗin. A kuma kallo ɗaya Anne ta fahimci wayo yaje yayma Raudha, sai dai addu'arta ALLAH yasa bai aikata abinda zai cutar da itaba tunda ɗinkin jikinta bai gama warkewaba. Tunda tazo ɗaki taga babu su tai niyyar kiransa a waya Bappi ya hanata. Acewarsa yasan Ramadhan na cikin hankalinsa bazai sake yarda ya aikata abinda zai cutar da Raudha ba. Gara su barsu su sasanta kansu da wuri kodan su Gimbiya Su'adah ma.         Bilkisu ce ta zuba musu abincin, dan Raudha dai ta kasa motsin kirki. Gani take kamar su Anne sun fahimci abinda duk ya faru tunda har abu yakai ga canja kaya. Kowa nacin abincinsa hankali kwance amma banda ita. Tsakura kawai take kaɗan-kaɗan.       “ALLAH in bakici abincin nan ba zan tonaki yanzu su Anne susan mikika aikato a ciki da hujja”.      Wani irin ƙululu cikinta ya bada. Harta kasa daurewa saida ta ɗan dubesa. Gira ɗaya ya ɗage mata da sakin wani munafukin murmushi daya tilastata maida kanta ƙasa da hanzari. Duk abinda suke su Anne na lure da su, sai dai kowa ya ɗauke kansa kamar bai san anaiba.          Farfesun kan rago Ramadhan yace Bilkisu ta zuba masa. Kamar jira tana buɗe bowl ɗin Raudha tai saurin toshe hanci da rike numfashinta. Babu wanda ya lura da hakan Bilkisu ta fara zubawa, kasancewar kusa da shi take tuni ƙamshin ya ƙara karfi a kusa da ita. Har takai amai na yunƙuro mata. Ta mike zaram zata bar wajen ya rikota.       “Lafiya kuwa?”. Kanta ta shiga girgiza masa da nuna masa ya saketa amma yaƙi. Anne ce ta fahimci abinda ya ɗaga hankalin Raudhan da sauri tace, “Ramadhan saketa”. Tai maganar tana mikewa.        Sam ya kasa fahimta, a zatonsa wani abune daban, ina kafin ya samu damar cewa wani abu ta kasa daurewa ta fisgi hanunta da ƙarfi. Sai dai kafin takai toilet na bayin ta saki aman a waje. Gaba ɗayansu sukayi kanta har Bappi, dama Ramadhan tunda ta fisge ya bita. Amai sosai takeyi a wahale. Shiko gaba ɗaya ya cimimiyota jikinsa duk a ruɗe. Sai tambayarta yake mike damunta?.           “Ramadhan ka barta taji da abinda ya dameta mana Please”. Anne ta faɗa cike da tausayin Raudha. Sai da ya tabbatar ta gama ya ɗagata cak ya nufi sashensa da ita. Anne zata bisu Bappi ya riƙo hanunta yana girgiza mata kai da murmushi a fuskarsa. “Barshi shi daya jawo yay aikin”.      Murmushi kawai tai da girgiza kai tana mintsininsa da nuna masa Bilkiau da ido. Yay karamar dariya da ita kawai tajisa. Mai aikin Anne ce tazo ta gyara wajen. Su kuma suka koma kan table suna karasa cin abincinsu kowa da tausayin Raudha a ransa      Bayan kamar mintuna goma sha biyar Ramadhan ya fito, a lokacin sun bar dining sun koma falo.       “Yaya jikin nata?”. Bappi ya tambaya cike da kulawa. Cikin damuwa Ramadhan daya koma duk wani kalar tausayi yace, “Bappi na barota kwance zan sama mata wani abincin a kuma kira Momyn Jabeer”.           “No kiran Mommyn Jabeer ba shine mafitaba ai. Da alama kamshin naman kan canne bataso. Taci abinci saita kwanta ta huta ALLAH ya raba lafiya”.          Wani irin yarrr yaji har saman kansa. Cikin rawar harshe yace, “Anne ban gane ba?”.      Hannu Bappi ya mika masa da faɗin, “Ajiye goro na ganar da kai”.     Ganin Bappi a serious sosai Ramadhan yay ƴar dariya yana shafa aljihu. Sai dai babu komai a ciki, hatta wayoyinsa na ɗaki. “Bappi na maka alƙawarin baka koma mi kakeso faɗi dan ALLAH”.      “Tabb ai an daina aikin banza a NAYA kai dai ajiye kasha labaru”.          Rasa mima zaiyi yay, sai kawai ya kwanto agogon hanunsa ya ɗora a hanun Bappin. Bappi ya ɗan juya agogon, sai kuma ya taɓe baki. “Ba laifi mai nauyine ai. Bilkisu bashi yasha”.      Bilkisu dake dariya cike da ɗoki ta nufi Yayan nata tayi ɗan hugging nashi, sai kuma ta sakeshi. “Yaya na kusa zama Mummyne fa, Aunty nada cikin wata biyu da kwanaki....”        “What?!!!”. Ai kafinma ta ƙarasa bayani ya juya da sauri ya bar wajen zuwa sashensa. “Na yafe miki sauran labarin”. Ya faɗa yana ɗago hannu sanda yake gab da shiga.         Mi su Anne zasuyi inba dariya ba. Pa dake tsaye tun ɗazu batare da sun sani ba yay murmushi kawai yana girgiza kansa. Ɗansa kenan abin alfaharinsa. Murɗaɗɗen mai wahalar fahimta ga wanda ke nesa da shi. Da yawan mutane akace musu Ramadhan mai sauƙin kaine a cikin gida zasu karyata. Domin shi mutumne mai yanyin mutanen da ake kira da girman kai kai tsaye. Dan kuwa tabbas magana ma sai yaso da wanda yay niyya yakeyinta. Dariya ko mutane da yawa kance basu taɓa gani daga garesa ba. Dan akan jima baiyi hakan ba sai a inda yaso. Sai dai ga wanda yaso kuma ya aminta shi mai sauƙin kaine da iya mu'amula matuƙa.         Cikin ɗan barcin daya fara figarta kawai taji an rungumeta. Tare da fara bata zafafan kiss's tako ina da ina a jikinta.         “Ya Ramadhan lafiya?”. Raudha ta faɗa a kasalance dan da gaske barci ya fara ɗaukarta. Bai bata amsa ba. Sai rungumeta da yay tsam a jikinsa yana jero addu'ar nan ga wanda abin farin ciki ya sama.        *الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .* *_Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat._*      _Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika._ *اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.* *_Alhamdulillahi ala kulli halin_*        _Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali._         Rigar dake jikinta ya ɗaga nanma yana sumbatar cikinta. Kafin ya kwantar da kansa akai wasu hawaye na tuna Haseenah na sakko masa. Ashe bayan Haseenah yana da rabon sake haihuwar ƙanen a duniya. Ɗagowa yay ya sake sumbatar cikin, sai kuma ya fara karanto addu'ar nemawa ƴaƴa tsari (iyaye dan ALLAH a dingayi, kai ko yaron cikine dake karanta ki shafe cikinki kafin ya fito ki ɗora dayi masa a zahiri😘😢. Domin kuwa MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu'ar: ).              *أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ.* *_O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah._*        _Ina neman muku tsari da kalmomin ALLAH cikakku daga dukkan shaiɗan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa_.         Raudha dake murmushi takai hannu ta shafa kansa. “Irin wannan security ba ɗaga ƙafa haka?”.       Tasowa yay gareta shima fuskar tasa da murmushi, ya kwanta kusa da ita tare da tokare kansa da hanunsa ya lakace mata hanci. “Uhmm barni gara na tofe abina tun yanzu kodan masu ƙarancin tsoron ALLAH. Yanzu nan Baby Luv kinsan da wannan abin farin cikin tun ɗazu kikaƙi sanarmin? Anya kuwa kina sona?”.      Dariya tayi tana mai saka tafukan hanunta ta rufe fuska. “Kai Ya Ramadhan kawai kuma saina kama faɗama inada cikin ɗan fari dan banda kunya”.         “Lallaima yarinyar nan”. Ya faɗa shima yana dariya da son zame hanunta. Ƙin yarda tayi, sai ma juyowa datai da sauri ta sinne kanta a ƙirjinsa. Idanu ya lumshe a hankali tare da rungumota ya kanƙame ta shima. ji yake kamar ya haɗiyeta kawai ya huta. “I love you sweetheart”.         “I love you too Noorullah”. “Nice name dear I love more. Na huta an daina kaƙabamin Yaya babu dangin gabas babu na yamma. Dolene yau nayi celebrations biyu kenan”.         Siririyar dariya ta saki tana mai ɗagowa ta sumbaci lips nasa ta sake maida kanta ta kudindine a jikinsa.       “Hummm wlhy yarinya ki bani kwana uku kacal saina maidaki mara kunya ta bugawa a jaridar duniya”. Yay maganar yana mai rungumeta sosai a jikinsa murmushi yaki barin fuskarsa.         Babu wanda ya karajin ɗuriyar Ramadhan da Raudha a gidan, kuma babu wanda ya nemesu. Garama ya kira Bilkisu daga baya ta kawoma Raudha sabon abinci taci ya busar mata da gashinta daga nan sukai kwanciyarsu............✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/13, 11:26 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 67-68_* ...........*_WASHE GARI_*           Washe gari babu kunya Gimbiya Su'adah tazo har sashen su Anne ta tuntuɓesu batun auren Aynah da Ramadhan. Dan Pa yaƙi bata haɗin kai kwata-kwata. Ramadhan ko taki cemasa komai duk da tasan yana cikin gidan. Hasalima har zuwa yay ya gaisheta. Yanda bata ɗaga masa maganar abinda ya faru ba a jiya shima baice komai ba. Yau ma bayan ya dawo sallar asuba yaje ya gaishetan. Nanma bataceba shima kumai bai ceba.       Koda Bappi ya gama saurarenta cewa yay taje zataji komi da suka yanke shi da su mai-martaba. Ranta ya ɓaci, amma ta danne ta tafi. Duk yanda sukai da Bappin ta kira Adda Asmah ta sanar mata. Itako daga can gurgun tunaninta bata yay aikin boka ya tabbata kenan. dan dama yace zai rufe bakin kowa ai. Shi kansa Ramadhan bai isa yin ko tari ba akan batun.        Hhh ALLAH sarki Addah Asmah. Batasan a yanzu matar Ramadhan da kakaninsa tsaye suke kansa ba. Dan a yau yini Raudha tai aikin karanta addu'oin warware sihiri dana kariyar ALLAH ita da Ramadhan suna tofawa a ruwa kamar yanda musulinci ya koyar damu. Suka kuma ajiye matsayin ruwan shansu. Yini guda suna a sashensu. Hatta abinci nan ake kawo musu. Yayinda Anne ta zaunar da shi ta sanar masa dokar Doctor akan Raudha na bedrest. Ya tabbatar mata babu damuwa zaiyi ƙoƙarinsa na kare hakan. Taji daɗi sosai tai masa nasiha ita da Bappi tare da addu'ar ALLAH ya kiyaye gaba.     Washe gari gida ya cika da baƙi taf tako ina. Bakajin komai sai hayaniya. Sai dai duk wannan hayaniya da gidan ya dauka babu mai ganin shugaban ƙasa da first lady. Dan suna can sashensu suna baje kolin shafukan soyayya kamar su kaɗaine a duniyar. Basu da aiki sai zaman garden ɗinsa dake matuƙar ɗaukar hankalin Raudha takeji kamar a wata sabuwar duniyar take. Abu mafi ɗaukar hankalinta tsuntsaye da ake kiwo a wajen da ruwan da aka kawata mai bulɓulowa cikin dutse kai kace ba tsarawa akai ba. Sau ɗaya ya barta ta shiga sukai wanka a pool ɗin wai bayaso Unborn ɗinsa ya ɗauka mura tun yanzun. Ita dai dariyama yake bata. Dan baida aiki saita idan ta haihu babynsa kaza kaza. Kokuma ya kwanta a cinyarta yayta hira da cikin da ko a jikinta bai nuna akwaishiba dan cikin a shafe yake kamar babu hanji balle ɗa.         A ɓangaren su Adda Asmah hankalinsu a tashe yake babu ango babu dalilinsa. Gashi har an fara event yau a cikin ukun kawai da mai-martaba ya basu izininyi tun a waccan ranar. Koda Fulani ta iso tasa a kira mata Ramadhan anƙi ganinsa. Gashi Bappi ya sashi kashe wayoyinsa duka sai mai muhimmanci kawai. Yo banda abin Fulani ma ganin shugaban ƙasa guda wasane kamar wani ganin Bilyn Abdull haka😏.      Aiko ta shaƙa. Tazo har sashen Anne amma ƙofar sashensa a rufe. Hakan yasata tunanin koma dai raina musu hankali ake baya gidan aka ajiye waɗanan zaratan securitys ɗin zagaye da anguwa kamar masu gadin wuta. to komadai miye Shugaban kasa Ramadhan ya zama gwal ma ya fisa arhar gani a garesu.      Dan ko kunshi da yace bilkisu ta kawo mai yiwa matarsa a sashen akai mata cikin garden, yayinda shi yake acan falon hutawarsa zaune shi da Ibrahim da A.J da sukazo biki suna shan hirarsu, dan Gimbiya Su'adah ta gama turama abokansa invitation kaf ta waya akan zaiyi amarya. Koda suka zo kuma baice da kowa komai ba akan hakan.      Koda aka kammala ƙunshin ya gani yayta santi. Kaɗan-kaɗan ya kamo ya sumbata. Harda labarta mata yanda ya dinga satar kallon kafafunta da hannayenta lokacin da akai mata na bikinsu. Aiko mi zatai inba dariya ba har saida ya ƙulu. Tako shiga masa gwalo da kiransa gulmamme.      Gyaran kai kam shi ya wanke mata da kansa ya gyara mata shi tsaf har taita mamaki. Yako tabbatar mata tsabar son da yakema gashine kawai ya sashi koya a wajen Anne. Harda cewa wataran zai mata kitso da sai tasha mamaki.       *_RANA BATA ƘARYA......_*        Lallai wannan zance haka yake. Dan kuwa a yau juma'a bayan sakkowa masallaci aka ɗaura aurarrakin yaran Taura Family har su biyar. Sai dai wanda suka kasa kunne suji da Ramadhan a ciki sukaji tsit. Sai da aka kammala a karshe aka ɗaura na Ayna'u Musaddiq da angonta Aminullahi Ashiru. Ɗa ga tsohon gwamnan jihar TANDAZA, ya jima yana sonta tana masa ikkanci, dan har kuɗi sun taɓa kawowa ta bijire. Da yake uban baida fus a gidan haka ya hakura duk da kuwa bokine garesa Alhaji Laminu Tandaza. Sai dai kuma masu iya magana sunce matar mutum kabarinsa. Gashi kuwa UBANGIJI ya tabbatar da hakan.       Gagarumar ƙurace ta tashi a gidan Adda Asmah jin sunan ango a bakin ƴan ɗaurin aure da ba haka suka saniba tun farko. A cikin kanƙanin lokaci ta hargitsa kowa. Zata taho Taura House ayi wacce za'ai ita da gimbiya Su'adah da take tunanin ta munafinceta Abban Aynah ya tabbatar mata ko gate ta tsallaka a bakin aurenta. Wannan tashin hankali ya saka Fulani hana Adda Asmah fita. Dan kowa yanda yaga Alhaji Musaddiq yau babu makawa zai tabbatar da abinda ya faɗa ɗin.       Amarya Aynah kuwa suma tayi a take sai da aka nemi likitan ceto ranta.       A Taura house kam babu wanda yasan mi ake ciki. Dan kuwa koda anguna suka shigo gaisuwa babu wanda yaji wani sabon abu da babu shugaban ƙasa Ramadhan da ganinsa dama bai zama lallai a idon kowanba.  Dan yanda ya fita tare da Bappi da mai-martaba wajen daurin aure haka suka dawo a mota ɗaya. Yana shigowa kuma ta ƙofar baya yabi zuwa sashensa dan ya tabbatarma Raudha kartaje ko'ina ana ɗaura aure gida zai dawo.       Duk da dai taji gargaɗinsa. Anne tazo da kanta ta tafi da ita ta gaisa da wasu aminanta na amana dan ba wani ganin Raudhan sukai sosai ba lokacin nasu auren. Komai cikin dauriya Raudha keyinsa. Amma jikinta a matukar sanyaye yake tunda tasan yau mijinta zai zama nasune su biyu. A kwanakin nan duka kullum sai ta buya tasha kukanta. Kuma tsaf Ramadhan na lure da ita batare data sani ba. Sai dai bai taɓa nuna mataba ya barta da lokaci kawai. Zai daibi duk hanyar data dace ya mantar da ita idan suna tare kafin ta sake samun dama.           Kasa ɗagowa tai ta kallesa lokacin daya shigo tana zaune ita da Basma da Rumaisa da Fadila a falo. Yayi kyau matuka cikin ɗanyar shadda data wadatu da jiƙaƙen ɗinki. Sai maiƙo da ɗaukar ido take gamai kallo. Gashi sosai babbar riga ke kawata adonsa da maidashi wani babban mutum. Sannu da zuwa su Basma sukai masa suna mikewa. Dama Anne ce tace suzo su ɗebe mata kewa kafin ya dawo tunda tasan babu mai shiga sashen nan da sunan yazo biki.            Bayan ficewarsu ya tako a hankali zuwa gabanta yakai dukunne. Hannayenta ya kamo cikin nasa tare da saka ɗayan ya ɗago habarta. Itama tayi ƙyau matuƙa cikin wani lass mai azabar kyau da nauyin kuɗi. Ga ɗinkin ya zauna mata ɗas a jiki saboda kibar da tayi da ƙara haske da fresh. Taci kayan ado na ɗan kunne da sarka da zabba da awarwaraye ga ɗauri daya amsa sunansa ɗauri kai kace itace amaryar.      Kukan da taketa riƙewa tun ɗazun ta sakar masa. Lumshe idanunsa yayi tare da mikewa ya ɗagata cak ya rungume a jikinsa yana murmushi.      “Haba ƴar aljanna. Kwantar min da hankalinki Ramadhan B. Hameed Taura na Ameenatu Dawood Hutawa ne ita jaɗai insha ALLAH. Badan bazan iya karawaba wataran idan kaddarar hakan ta shigo, sai dai ina fatan rayuwa dake ke ɗaya dan tun asali zama da mace ɗaya ne tsarin Ramadhan. Sai dai tsarin ALLAH yana gaba da nawa Ameenatu. Amma a yanzu nakine ke ɗaya babu wadda aka ɗaurama Ramadhan aure da ita”.        Ƙanƙamesa tai da sake fashewa da kukan da batasan na farin ciki bane kokuwa na minene. “I love you Noorullah”. Ta faɗa da ɗagowa lokaci ɗaya ta manne lips nata da nashi.       Tab humm, batasan kuka ta kawo gidan mutuwa ba. Dan kuwa bawan ALLAH caraf ya cafke tare da ɗaukarta cak sukai bedroom. Yako shiga yamutsata son ransa. Yama manta da wata kwalliyar biki. Sai da labarin ya canja salo kuma ta ruɗe. Sai dai batasan dama haƙuri yake yana ɗaga kafa ba dan dole. Aiko tilas ta bari ya rage zafi yanda ya kamata. Da ga karshe dole aka sake nemo su Basma suka kawo mai sake kwalliyar biki. Uhhm andai ji kunya😣😮🚶🏻.        ★Bayan sallar la'asar sai ga Aunty Hannah mata ga vice president da tawagarta sun iso gidan bikin. A ciki kuwa harda Asabe da Hajiyar Birni dasu Fatisa. Wayyo dadi kamar zai halaka Raudha. Ta rasa inda zata saka kanta taji daɗi. Ga Anne ta saka an musu kyaƙyƙyawan karamci da tarba ta musamman ta abinci. Su aunty Hannah anata faman ɗaga kai da hura hanci ana yatsine-yatsine kai kace itace ma firt lady ɗin tsabar yanda guards ke dogare a bayanta da mata ƴan siyasa.       Ina Raudha bata ita takeba. Farin cikin ganin Mummynta ya rufe mata ido ruff. Ko Hajiyar Birni da Hajiya mama sai da sukai mata tsogumi ta gaishesu. Anan suka kasance har bayan magrib. Da zasu wuce Anne ta haɗa musu shatara ta arziki musamman su Fatisa da sukaji kamar karsu rabu da ƴar uwarsu. Dan suma dai yanzu Alhmdllhi har sun kawo mazan aure ana shirin zuwa hutawa gaida Alhaji baba Dauda mai zamani surukin Mr president na ƙasar NAYA. Yaso zuwa daurin aure Inna ta tashi da amai da gudawa aka kwasheta asibiti a rikice tana can ana kara mata ruwa dole ya hakura. amma yasha takaici wai kallo ya wucesa daga shi har M. Gambo amininsa da shima ya gama saye zuciyar asabe batare data san shiɗin bane har yanzun. Dan yace bazai bayyana mata kansa ba sai ta yarda ya turo iyayensa. Itako tace su ba yaraba bata yarda da wannan ganganciba yazo gareta kawai su sasanta. To yanzu dai yace zaizo ɗin amma bai tsaida rana ba.      Bayan wucewar tasu ma zazzaɓi ne ya rufe Raudha. Koda aketa shirin tafiya dinner ita tana can duƙunkune a bargo. Dama kuma bata saka ran zuwan ba tunda tasan Ramadhan dai bazaije ba. Kuma babu tabbas zai barta taje itama.       ★Kafin a tafi dinner gimbiya Su'adah ta cigaba da neman number Fulani da Addah Asmah kamar yanda taketa fama tun bayan dawowar ƴan ɗaurin aure hakan baiyu ba. Dan duk kashe wayoyinsu sukai. Taso su Safina su leƙa gidan suyi ALLAH ya sanya alkairi hakan bata yuwuba dan Taura house yayi matukar cika kasancewar duka matan gidan uku sun aurar da yara.      Ta turama Ramadhan gargaɗi sosai akan ya tabbatar yaje dinner ɗin nan amma sai dai baima gani ba dan yau yayi busy da yawa. Babu wanda yasan ainahin abinda ya faru sai fa da aka isa wajen dinner sai su Bilkisu Amare kawai da angunansu amma babu Aynah babu Ramadhan babu duk wani wanda ya shafi masarautar Bina dake a gidan Addah Asmah dan dama biyu aka rabu. Wasu sukayo nan Taura House wasu can gidan a cewarsu duk za'a haɗe wajen dinner da walima dakai amare.        A sannan gimbiya Su'adah takejin mummunan labarin cewa ai kiɗa ya canja bada Ramadhan aka ɗaura aure ba. Ta matuƙar gigicewa a haukace ta shiga neman number Ramadhan amma har sannan switch up. Ta nufi sashen Pa ta iskesa da baƙinsa da basu wuce ba. Tsabar yasan miya kawota kuma yay kememe yaki tasowa. Haka ta wayance ta fito. Maida akalar kiranta tai ga Mai-martaba, shikam ta samesa. Sai dai yaja mata gargaɗi akan idan har tace wani abu yana cikin Taura house sai ya mata hukunci mai muni, tabar koma minene za'a tattauna bayan biki.       Wannan al'amari ya matuƙar sake rikita gimbiya Su'adah, dan kuwa a daren nan jininta ba karamin hawa yayiba har sai da Safina ta taimaka mata da maganin barci.       ★Wajen dinner kam bidirinsu suka sha kamar babu gobe. Dan gaba ɗaya anan aka haɗe amare da angwayen. An raƙashe an kwalle anci ansha sai dai Bily taji inama Raudha na wajen. Amma dai su Basma sun ɗauka komai a waya duk da anyi vedio recording. Su Ibrahim ne suka halarci wajen bisa wakilcin babban yayan amare shugaban ƙasa Ramadhan tare da cos. Hakama manyan mutane matan gwamnoni da ministers da ƴaƴansu duk sun halarta. Dan hatta da yaran su Alhaji yaro glass na nan anyi komai da su kamar babu wata a ƙasa. Karfe ɗaya aka tashi amare da tawagar jama'a yan biki sukayo gida. Masu gidaje a cikin Bingo suka nufi nasu muhalli anama angwaye da amare fatan alkairi da zaman lafiya da zuri'a masu albarka.........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/13, 11:26 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 69-70_* ............Washe gari Raudha ta tashi batajin daɗi sosai. Dan har saida Dr Hauwa ta shigo ta dubata har dasu karin ruwa. Sai hankalin Ramadhan ya rabu biyu ga meeting da za'a zauna duk da dai babu Raudha a ciki. Ga jikinta kuma.      Itako Gimbiya Su'adah tana can sun fice a sace ita da Safina zuwa gidan Addah Asmah, dan tana son tasan mike faruwa kafin a zauna zaman meeting duk da tasan har dasu Adda Asmah ɗin za'ayi. Lokacin da motar su gimbiya Su'adah ke shiga layin su Adda Asmah a lokacine driver daya ɗakko fulani zai kai Taura House shi kuma ke fita. Dan Addah Asmah tace fulanin tayi gaba suma zasu ƙaraso ita da mijinta da Aynah da kuma mijin Ayana ɗin da suke so ya saketa take a yau.       Saboda yanayin hayaniyar mutane yasa Safina bata tsaya da motar ko'ina ba sai ƙofar falon baya data san su Adda Asmah nada ita. Dan kafin tai aure idan tana son haɗuwa da Faisal mijinta tasha satar fita ta wajen taje ta dawo wani bai sani ba. Ta wajen babu kowa, sai daga ɗan bayansu ta backyard suke jiyo ƙananun hayaniyar masu wanke-wanke. Ginbiya Su'adah takai hannu zata buɗe ƙofar wani furici mai kama da saukar aradu yay azamar taka mata birki, tai kuma saurin damƙe hanun Safina dake shirin yin magana tana girgiza mata kai....      Su gimbiya Su'adah sun iso gidanne a dai-dai lokacin da Adda Asmah da Aynah ke tare a wannan falo, waya Adda Asmah keyi da bokanta akan abinda zasuyi idan anje wajen taro. Shine furucin ƙarshe data maimaita kamar yanda bokan ya faɗa ya shiga kunnen gimbiya Su'adah. Kasancewar sun gama wayar Adda Asmah ta ajiye a sanyaye tana duban Aynah data kafa mata ido.       “Mom wai yanaga jikinki kamar yayi sanyi?”.              “Tabbas dole jikina yay sanyi Aina'u. Sai dai zan iya aikata komai saboda ke. Kamar yanda malam yace na kirashi kafin muwuce wajen taron shine na kirashi, dan wannan dalilinne ma yasa nace Ammy (fulani) tai gaba zamu biyota. Yanzu har ita ta bar sanin sirrinmu tunda bazatace batason Su'adah kamar yanda take sona ba.....”        “Hakane Mom, amma nidai sanar dani mike faruwa kawai?”.     “Daɗina dake wutar ciki. Abinda kikaga ya girgizani da maganar malam ya tabbatarmin bincikensa na jiya ya nuna masa zasuyi taurin kai akan yarda da buƙatar mu, amma idan muka jajirce za'a iya samun nasa ƙila. Sai dai Ramadhan ɗin shine babbar matsala yanzu, saboda akwai yarinyar dake tsaye a kansa game da addu'a hatta azkar baya wasa yanzu safe da yamma, yace inhar tana tare da shi mawuyacine duk wani aiki namu yanzu yay tasiri a kansa dan tanada jajircewa. Hasashena ya bani tabbas shegiyar yarinyarnan ce ƴar karuwai. Maganarsa ta ƙarshe data firgitani itace zaɓin daya bamu akan Ramadhan ɗin, kodai akawar da shi kowa ya rasa shi da yarinyar, kokuma mu haƙur......”        “Ina bazai yuwuba Mom, wlhy bazan iya haƙura da Ramadhan ba. Idan nai haka ko to tabbaci ban cika mace ba. Har yaushe zuciyarki ta fara tausayine Mom?.”       “Nima ba tausayi nake jiba Aynah, domin zan iya komai a kanki, ciki kuwa harda kauda duk wanda ya tare min gaba. Tunda muka taso a gidanmu kowa yafi son Su'adah duk da kasantuwarta yarinya mai girman kai da ɗaukar kowa ba komai ba. Ba ƙyau tafini ba, amma ko kaya mukasa kafin a yabamin an yaba nata saboda ta iya tsara ado. Kullum a makaranta takan ɗauki maki na jarabawa fiye da nawa. A gida mahaifinmu yafi sonta fiye da kowane ɗa, dan hatta da shawararsa mai muhimmanci yakanyi da Su'adah baiyi da su Ammy ba. Mu duka ƴaƴan sarki ne amma ita kaɗai ake kira da gimbiya duk da nice babba. A koda yaushe wannan abu nacimun rai, taya zan fita komai amma yazam kullum itace da nasara sama da tawa? Hatta a shekarufa na fita. Abinda ya ƙara baƙanta raina da rayuwa lokacin da muke UK a school, tunda na fara ganin Basheer Hameed Taura na kamu da sonsa. Amma abin mamaki saina tsincesa tare da ƴar uwata Su'adah har sun fara soyayya ni ina nan ina ƙulla yanda zan tunkaresa da tawa soyayyar. Na shiga tashin hankali mara misali Aynah, har takai naji bazan iya jurewaba na tunkaresa da batun. Hummm karkiga irin korar kare da Basheer yamin tare da dogon gargaɗi, tun daga nan karatuna ya shiga hanyar taɓarɓarewa har muka dawo gida babu komai a result ɗina. Itako ta dawo da sakamako mai ƙyau cike da nasarori. Muna dawowa babu ɓata lokaci aka fara shirin aurar damu, ita aka aura mata wanda take so ni aka auramin mahaifinki batare da ina sonsa ba, dan iyayenmu ne suka ƙulla hakan. Watan Su'adah goma cif a Taura House ta haife ɗanta namiji santalele. Niko a lokacin ko ɓatan wata. Naji zafin hakan matuƙa amma naita ƙoƙarin dannewa. Bayan shekara biyu da yayensa ta sake Mardiyya, har lokacin ni babu labari. Nadai taƙaice miki sai a harhuwar Lubnah muka haihu tare, lokacin tanada yara har uku kenan niko 1 kuma mace ke. Na ƙara na biyu ma mace. Wannan ya ƙaramin tsanarta dan koba komai ta ɗarani da namiji kuma ƴaƴanta sunfi nawa. Daɗin daɗawa ɗanta shine ɗa tilo namiji agaba ɗaya Taura family. Nasha auna cutar da Ramadhan amma bai yuwuba saboda kakankinsa kullum nane suke da shi kamar sun san burina. Iyayi nayi Su'adah ta amshi Ramadhan a hanunsu amma sun hanata. Dan haka nasa akai aiki akansa aka tura masa wasu hatsabiban ajanu dakan maidashi tamkar wani mahaukaci. Sai dai mahaukacin ma naso ya koma baki ɗaya hakan bai kasance ba. Tun lokacin aurensa na farko naso ki auresa amma ya nuna baya ra'ayi, dan a yanzu babban burina shine ki auri Ramadhan ki ƙwato mana duk wani abinda Su'adah kejin tanada shi a hannu daya fini, amma kuma sai komai ya lalace bayan mun ɗakko hanyar nasara......”        “To amma Mom duk da waɗan nan abubuwan shine kike tunanin bazamuyi abinda malam yace ba. Ramadhan nada taurin kai, na tabbatar da wahala ya yarda da aurena, sai dai in uwarsa ce tace zata tsine masa. Idan ma tace hakan shi wannan jakin da aka auramin zai sakeni ne ta cikin sauƙi.....”         “Inko har duk abinda kika lissafo haka al'amarin zai zama to tabbas dolene Ramadhan ya mutu. Dan kawar da shine kawai zai sakama zuciyata salama akan Su'adah. Tunda bazamu samesaba to kowa ya rasa shikenan ƙurun-ƙus!!....…”      Wani irin banko ƙofar da akai ne ya dakatar da Aynah data fara dariya, atake sukai diri-diri, gimbiya Su'adah da kanta ke wani irin juyawa tanajin hajijiya ta shiga nuna adda Asmah da hannu sai dai abinda take son faɗa ya gagara fita. Safina datai wani tsalle ta shaƙo wuyan Adda Asmah ta buga da bango, hakanne yasa itama Ayna yin kukan kura a kanta ta shaƙeta. Ƴan biki ne suka fara shigowa a guje saboda ihun da Addah Asmah ta buga na azaba, har goshinta ya fashe jini na zuba...... *_TAURA HOUSE_*         Kowa ya hallara su kaɗai ake jira, mai-martaba da ransa ya gama ɓaci yana ƙoƙarin cewa a kirasu sai ga kiran daddyn Aynah ya shigo masa. Cikin tashin hankali ya shiga ambaton kalmar innalillahi.... Har ƙarshe, kafin ya ajiye wayar ya sanarma ƴan falon da duk hankalinsu ke kansa iya abinda Daddyn Aynah ya sanar masa. Zaram Ramadhan ya miƙe amma sai Bappi ya dakatar da shi.       “Ina zaka kuma?”.   “Bappi can gidan mana, kanajifa faɗa mizai haɗa Maah da Mom faɗa a duniyar nan?”.       “Koma miye ai zamu sani yanzu, ko kana mantawa da matsayinka a yanzune wai. Koma ka zauna Basheer yaje ya taho da su”.     Babu yanda ya iya ya koma ya zauna kamar zaiyi kuka. Zuciyarsa sai kaikawo take da tunanin mike faruwa? Miya faruwa? Mi akayi?. Hakama sauran kowa tunaninsa kenan sai dai babu mai bada gamsashiyyar amsa akai zaman jiran isowarsu.           ★Kusan awa guda suna zaman jira dan sai da Pa yay jan ido suka yadda suka taho dalilin ita gimbiya Su'adah na tsoron nata mijin, itako Adda Asmah ta raina nata. Wujiga-wijiga suka shigo musamman gimbiya Su'adah da sai da Safina ta bata taimakon gaggawa acan amma da yanzu labarin ba wannan ake ba kuma. Kowa hankalinsa ya tashi da yanayin nasu, musamman ma Ramadhan da cikin rawar jiki yaje ya taya Safina riƙo Maah dake tafiya kamar zata zube ƙasa sai hakki take sama-sama. Shidai Bappi uffan baiceba, binsu kawai yake da kallo hakama mai-martaba. Pa kuwa yanayinsa na nuna ko'a jikinsa dan dama irin wannan ranar yake addu'ar tazo duk da bai san mike faruwa ba shima har yanzun.       “Inaga muyi abinda ya taramu kamar zaifi”.    Cewar Pa da alamun ɗaci a muryarsa. Bappi zaiyi magana Mai-martaba ya katsesa.       “Gaskiya Basheer ya faɗa dan nima sonake na wuce akan lokaci”.      Bappi ya haɗiye abinda yay niyyar faɗa kawai yana girgiza kansa. Daga haka aka buɗe taro da addu'a sannan aka fara abinda ya tara ɗin game da sauya maganar auren Ramadhan da Aynah.        Bayan dawowar Ramadhan hayyacinsa, adare ranar Bappi ya sanar masa duk abinda ake ciki, amma sai ya dage akan shi bai taɓa jin son wata Ayna'u ba. Bakuma zai fara a yanzu ba bayan so na ƴan uwantaka dake tsakaninsu. Ya kuma tabbatar masa komi za'ai shi bazai aureta ba matarsa ta ishesa. Babu irin lallashin da Bappi bai masaba a wannan dare amma yace shifa yana akan bakansa.     Washe gari ma daya dawo gidan kafin yaje ga Raudha maganar da suka fara tattaunawa da Pa da Bappi da Anne harma da su Yafendo da Mai-martaba a waya kenan amma Ramadhan yace yana kan bakansa. Baice zai auri Ayna'u ba kuma ayanzu bazai amsa ba. Dagiyarsa ya sake tabbatar musu akwai sihiri tattare da shi sanda ya dinga musu hauka akan auren Ayna'u garda ɓatawa da su Anne. Wannan dalilin ya sakasu sallamarsa suka tattauna abinda ya dace a tsakaninsu. Mahaifin Aynah shine ya kawo shawarar a rufe komai iya su ranar ɗaurin aure yanada wanda zai aurama Aynah dan a raba gardama komai ya zama ƙarshe basai anta jan zancen ba. Wannan shawara tama kowa, dan haka suka rufe komai hatta Ramadhan baisan da haka ba sai da aka ɗaura aure da wani daban ba shi ɗin ba.         “ALLAH na gode maka da hakanma ta kasance, Ramadhan ka yafemin, duk halin daka shiga akan Ayna'u hardani a ciki, daban basu goyon bayaba da ba'a nema sabautamin rayuwarka har gashi yau ana iƙirarin kashemin kai ba...”      Gimbiya Su'adah ta faɗa cikin kuka hanunta riƙe dana Ramadhan. Tsitt falon yay cikin rashin fahimtar kalaman nata..........✍       *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*_________________ *_Typing📲_* *_Episode 71_* .........“K Su'adah wace maganar banza ce wannan kike haka?”.      Fulani ta katseta a harzuƙe. “Ammy karki wani rufe gaskiya da son zuciya. Dole ne sirrin ɓoye ya fito fili, ban taɓa zaton Asmah zata zamemin BAƘAR INUWA ba sai yau. Ashe gara ranar da nake gudu da ita. Asmah bazan taɓa yafe miki ba, kuma insha ALLAH haka zaki ƙare rayuwarki a rashin nasarar da kike gani kina ciki......”      A harzuƙe Adda Asmah ta yunƙuro zatai magana Fulani ta ƙatseta, hakan yasa mai-martaba bama gimbiya Su'adah damar faɗar duk abinda ke faruwa. Bako ta ɓoye ba, dan tun daga lokacin da riƙon Ramadhan ya koma hanun su Anne hanyoyin da Adda Asmah ta dinga sakata ita da Fulani har zuwa aurensa na farko, da kuma aurensa da Raudha zuwa son haɗasa da Aynah a yanzu da abinda suka jiyo ita da Safina yanzun. Bugu da ƙari dan ma kar Addah Asmah ta musa haka Safina ta ajiye wayarta da tayo recording duk maganganinsu kowa yaji.       Sallallami kowa ya shigayi a falon, yayinda Adda Asmah ta haukace musu akan ita ƙarya ake mata. Saharri ne kawai saboda gimbiya Su'adah na borin kunya ta hana ɗanta auren ƴarta. Idanma kuwa tayi wani abun ai tare sukayisa. Wannan magana ta Adda Asmah ta sake tada ƙura, dan ko ba kunya gimbiya Su'adah ta daddage ta yarfama Adda Asmah mari,        “Su'adah ni kika mara?!”. “An mareki Asmah, kaɗanma kika gani wlhy, na tsaneki, na tsani ganinki, nayi dana sanin saninki matsayin ƴar uwata ciki guda. Kuma insha ALLAH Ramadhan yafi ƙarfinki har abada yafi kuma ƙarfin ƴarki, sai dai ki mutu da baƙin cikina dana zuri'ata. Munafuka kita zugani akan su Anne da suka riƙemin yaro tsakani da ALLAH kina cemin macutane ashe kece azzaluma mai cin amanar zuminci. Da iznin ALLAH ƙarshenki bazai ƙyauba.....”       “K ce ƙarshenki baizai ƙyauba su'adah”. Adda Asmah ta faɗa tana kaiwa Gimbiya Su'adah mari, amma saita riƙe hanun ta murɗesa dan ko dai gimbiya Su'ada tafita ƙiba dama zuciya.       Idanu Ramadhan ya sake rumtsewa kansa na juya masa. Yayinda su Bappi keta faman musu magana amma sunƙi sauraren kowa. Dan wata irin hankaɗawa ma Gimbiya Su'adah taima Adda Asmah tai taga-taga zata daɗi Aynah dake kuka ta riƙota.        Nuna gimbiya Su'adah tai a kausashe. “Su'adah bakici bulus ba wlhy, ina matsayin yayarki kikaimin wannan abubuwan saboda kina auren mai kuɗi. Ni Asma'u nayi alƙawarin saina sabautar da rayuwarki data ahalinki baki ɗaya, dan wlhy sai kinyi dana sanin sanina. Sai kinsan na haifu cikin uwata da ubana, sai kin gwammaci daban kasance jininki ba!!”.      Tana gama faɗa ta juya zata fita cike da borin kunya. Ana dakatar da ita bata saurari kowa ba taja hanun Aynah suka bar falon tana mai jaddadama gimbiya Su'adah bazata yarda da ƙazafin da sukai mata ita da Safina ba da mari ta jiraci sakamako..        Wannan Al'amari ya firgita kowa ya kuma bama kowa mamaki. Mai-martaba da tun ƙuruciyar yaran nasa ya fahimci halin kowa ya share ƙwallar da suka cika masa idanu.             “Ni nasan wannan ranar zatazo. Bammayi tunanin sauƙinta zai kasance hakaba. Tabbas Su'adah nada halayen banza da takejin zata iya taka kowa da komai idan taso. Girman kai, ɗaukar kowa ba kowaba duk halayyartace. Sai dai abinda mutane da yawa basa saurin ganewa daga gareta shine, abin kowa bai dameta ba. Su'adah bazaka taɓa jinta ta zauna surutu akan damuwa da cigaban wani ba, sannan dan taga wani da abu bazakaga ɓacin rai daga gareta ba balle damuwar kishinsa. Itako Asma'u da kuke gani, tanada sauƙin kai da son mutane, sai dai tanada nunkufurci da hassadar bata yarda kowa ya fita ba. Waɗan nan halayen nasu sune suka banbantasu, dan ita Hassada na cinye ayyukan bayi, tana maida mai son yin nasara bayan wanda yake gani bai kai ya fisa ba. Sai kaga mutum da halayen banza. Kai kullum cikin ibada da sauransu amma yanata samun nasariri kai sun gagara zuwa gareka karasa yaya haka? Nafi wane komai a rayuwa mizaisa ya dinga bani tazara? Amsar itace hassada. Hassada na ƙwace nasarori, ga wanda baida ita tana bashi nasarori koda bai kaika ba. Wasu suna tunanin Hassada itace kawai naga wane da abu banji daɗi ba. Hassada na zuwa kashi-kashi a cikin ayyuka.          _Kaji kai kaɗai kake son kai nasara a rayuwa. Kaji kanajin zafin wanda kafi da komai na rayuwa ya samu wani abu kai baka samu ba. Ka dinga damuwa da yawan maganar cigaban wane. Mutum ya gina ƙyaƙyƙyawan abu ka ruguza masa. Misali mutanen da ke fidda mana littafi ko zuwa su saya dan su yaɗa hassada ce. Shiyyasa zasuga kullum suna wahalar banza da tunanin dakushemu mukuma munata nasara a rayuwarmu domin basu isa hanamu samun abinda ALLAH ya rubuto a ƙaddararmu ba._       Hassada na shigowa cikin ayyukan mutane daban-daban ƙarama ko babba, ka sani ko baka sani ba. ALLAH ya rabamu da hassada. Ka tsarkake mana zukatanmu akoda yaushe. Ka wajabta mana tsoronka da soyayyar ANNABINMU (S.A.W).      Nasiha sosai mai-martaba yayi a wajen harda Bappi, daga karshe aka sake rufe taron da addu'a kowa ya kama gabansa..           A ranar aka miƙa amare ɗakunansu zukatan wasu duk babu daɗi. Musamman ma gimbiya Su'adah dake kwance babu lafiya, dan jininta ya hau matuƙa sai dai gyaran ALLAH. Amma Safina da Mardiyya na tsaye a kanta harma da Fulani.     Raudha dai batasan mike faruwa ba. Dan koda Ramadhan ya dawo sukuku baice mata komai ba ita kuma bata tambayesa ba saboda ba daɗin jikin takejiba sam. Ko lokacin da aka kawo su Bilkisu har falonsa suyi sallama a taƙaice ya musu nasiha ya sallamesu. Bilkisu kuwa ta rungume Raudha suna kuka har abin ya bama wasu mamaki dan da'alama akwai shaƙuwa sosai a tattare da su. Ganin abun nasu bana wasa bane Ramadhan ya rabasu da ƙyar ya rungume matarsa duk da mutane dake wajen bai nuna ya san da su ba. Bayan wucewarsu ya jima yana lallashinta, daga ƙarshe ma yasata sukai kwanciyarsu.       Dan hatta da Aynah ta tare nata gidan bisa tursasawar mai-martaba. Hasalima shi da kansa yay mata rakkiya har gidan mijin nata ya kuma tabbatar ma mijin ko da wasa yaji a ransa zai iya rabuwa da Aynah duk abinda zatai, to lallai sai ya hukuntashi shima bawai ita kaɗaiba.     To Alhmdllh, mai-martaba ma dan bai san wanene Aminu ba, idan hatsabibanci Aynah takeji ya taketa ya shanye. Idan iskanci ne gidan ta taras. *______________________*           Har biki ya tashi lafiya kowa ya kama gabansa babu wanda ya sake tada maganar. Sai dai gimbiya Su'adah da jikinta keta sake tsanani duk da kulawar da take samu. Hakama Raudha ciwo ta kwanta sosai hakan sai ya raba hankalin Ramadhan biyu. Ga kwanakin hutunsu ya ƙare dama sati ɗaya ne kacal. Yanda jikin Maah ɗin keta ƙara tsanani ya saka Pa yanke shawarar tafiya taga likitan ta, dan haka randa su Ramadhan zasu koma government house aranar suma sukai shirin wucewa duk da Anne da taƙi yarda Raudha ta koma can gidan sai da Bappi ya lallaɓata. Aka kuma haɗata da su Basma.      Tasha kuka duk da ita shaidace a yanzu mijin nata ya dawo dai-dai, sai damuwar da take hange cikin idanunsa da bata san ta micece ba. Ba kuma ta matsa da tambayaba tanata masa addu'ar dacewa dai da warwarewar matsalar tasa...                    Abubuwa sun lafa sai dai bazamuce duka ba. Gimbiya Su'adah na can likita ya ɗorata a magani, yayinda anan NAYA Addah Asmah keta faman shigi da fici na son ganin an hakala mata rayuwar Ramadhan dama Gimbiya Su'adah kanta duk da ƴar uwartace uwa ɗaya uba ɗaya. Sai kuma auren Aynah da take son rabawa wadda kullum cikin kiranta take tana kuka da roƙon taimakonta tazo Aminu zai kasheta. Dan bashi da aiki sai na mata fyaɗe safe da yamma. Idan taƙi yarda ya naɗa mata ɗan karen duka yayi yanda yakeso kuma. Baijin nauyin shigowa gidan da ƴammata da abokansa susha giyarsu da cocaine. Ya kuma dinga basu labarin abinda tai a America a club, hasalima anan ya fara ganinta har yaji yana buƙatar kasancewa da ita amma ta maresa. Shine dalilinsa na ƙudira aurenta. Ya kuma ɗau alwashin sai ya gama morarta ya saki videon wa duniya.       Jin wannan zance Aynah tayi kuka tayi roƙo amma sam yaƙi saurarenta. Ta tabbatar masa komi yake so zatai masa akan karya tona mata asiri. Kota kanta bayayi saima ya zauna yayta kwasar dariya shi da abokansa.       *_GOVERNMENT HOUSE_*       Sukam matsalolin nasu da sauƙi Alhmdllhi, dan Raudha ma ta ɗanji ƙarfi harta koma zuwa makaranta ma. Idan akwai abinda ke damunsu a yanzu bai wuce ciwon gimbiya Su'adah ba. Sai dai kullum Pa na kwantar musu da hankali akan da sauƙi sosai. Hakan naɗan saka musu nutsuwa, har ma yake bama Ramadhan damar shan sharafin soyayyarsa. Duk da kuwa randa ya nuna buƙatar kasancewa da Ustazah ɗin nasa ansha daru. Kuka ta dinga masa da tsalle-tsalle dan ta kasa manta azabar data sha ta ƙarshe. Tunda suka dawo gidan daya tunkareta sai tace wajen bai warke ba ai. Ranar dai ya gaji da yawo da hankalin da take masa ganin zai cutu ya matseta ta ƙarfi ya duba.     Tuni ta warke abinta zaren ɗinkin ma ya warware da kansa saboda kulawar data dinga samu wajen Anne. Azabar data sha ne kawai yasa take gudunsa. To ranar dai kam duk kukanta bai saurareta ba sai da ya sauke nauyi. Sai dai ya bita a hankali matuƙa yanda har taji nutsuwa tsoronsa ya ragu a ranta bakamar kwanakin baya ba.      Daga ranar kuma suka sake dunƙulewa waje guda. Dan takai ma ita da kanta tana nuna so saboda cikinta yazo mata da wannan yanayin sosai. Cikin ƙanƙanin lokaci ta sake kara buɗewa tai ƙiba sosai da haske. Shi kansa har baya gajiya da kallonta da kiranta ƴar lukutarsa.      Da yace ƴar lukuta zata fara masa kukan shagwaɓa ita bata yardaba. Shiko yayta dariya da tsokanarta. Sukanyi waya da Bilkisu kullum, tana kuma cigaba da sake ɗorata akan abubuwa na musamman har gashi yanzu Raudha ta ɗauka sabbin ma'aikata. Mai mata kwalliya da kula da duk wani ado da zatayi musamman idan hakan ta kama akan wata fita ta musamman duk da har yanzu Ramadhan bai taɓa yarda yaje da ita wani taro ba. Sai mai mata gyaran jiki itama. Ramadhan bai hanaba tunda ya san duk abinda zai ƙaru da sune shima ai, to shinema mai ƙaruwar tun school dai kawai Raudha ke zuwa, sannan koda yaushe komanta a rufe.          Zuwa yanzu cikin Raudha ya shiga watanni na huɗu, ya fito mata ɗan duk da bawani ƙato can ba, wanda ma baida fahimta zai ɗauka tumbi ta fara ajiyewa saboda ƙibar da tayi. A kuma lokacinne gimbiya Su'adah ta dawo NAYA dan likitan riketa yay ta huta sosai acan.       Ita da shi sukaje mata sannu da zuwa a wani dare cikin fitar sirri. Har yanzu bazamuce Gimbiya Su'adah na ra'ayin Raudha ba. Sai dai akwai sassauci matuƙa a yanayin data amsheta. Harda tambayarta tana lafiya kuwa wannan ƙiba tata lokaci guda haka?. Ita dai Raudha komai batace ba sai ɗan murmushi kanta a kasa. Hakama Ramadhan bai saka musu bakiba dan a ganinsa bai kamata yacema Maah ɗin Raudha nada ciki ba taga rashin kunyarsa a fili. Sai bilkisu ce ta sanar mata Raudha nada ciki ai. Duk da gimbiya Su'adah ta danne yanayin data shiga na farin ciki ƴaƴanta sai da suka fahimta har shi Ramadhan ɗin da Pa, sai dai babu wanda yace mata komai akan hakan.       Raudha taji daɗin haɗuwa da Bilkisu da itama mijinta ya kawota duba Maah ɗin. Dan tanata son zuwa ma taga gidajen amaren laulayi ya hanata, Ramadhan kuma yace bazatajeba sai taji ƙarfi sosai. Makaranta ma yana barintane dan kar tai asarar abubuwa.      Sosai Anne ta bata dabarun rainon ciki da shawarwari, tare da mata addu'ar fatan sauka lafiya. Basu baro gidan ba sai kusan ɗaya na dare.........✍           *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_**_Episode 72_* .........Rayuwa ta cigaba da shuɗawa gwamnatin Ramadhan nata sakin manya-manyan projects naban mamaki. Ko'ina ka zaga a cikin ƙasa sai sambarka akeyi. Domin ƴan matsalolin dake shigowa tarin ƙoƙarin ayyukan da ake shimfiɗawa suna dannesu ƙwarai da gaske. Hatta da ƴan bani na iya abokan hammaya bakunansu sun mutu dan babu abin faɗa kuma, sai dai duk da haka sukan ɗanyi takale-takalensu a gidajen redio dana talabijin.      Suna dire zance masoyan Ramadhan ke basu amsa dai-dai da su, amsar da su kansu basu da bakin sake maida murtani, dan kuwa dai kowa shaidane ga Ramadhan tun bai cika shekara akan gadon mulki ba manya-manyan ayyukansa sun fito fili ma duniya. Ga tausayin talaka. Ayyukan yi ga matasa da matan aure harma da ƴan mata. Ɓangaren lafiya da wutar lantarki da ruwa duk Alhmdllhi. Duk da ba komai ne ya wadaci kowaba hundred percent anci kaso mafi yawa na gyara. Makarantu tsaye ake akan albashin ma'aikata da cire kowane irin bara gurbi da zai iya dakusar da ilimin ta hanyar alfarma ko cin hanci da rashawa. Babban abin birgewa a matsayinka na ma'aikaci idan an cireka a gurbin da baka cancantaba za'a kaika wani gurbinne daya dace dakai bawai korarka za'ai ba a aiki balle kaje ka kama wata sabgar mara ƙyau kuma.          A koda yaushe idan tunanin abu yazo masa yakan tunkari Raudha da shawara kafin ya fitar da shi ga abokan mulkinsa. Kasancewarta ta tashi ƴar talakawa, cikin takalawa da talauci yana taka rawar gani matuƙa wajen zaƙulo masa abubuwa masu muhimmanci na halin ƙunci da talakawa ke ciki a ƙasar. Idan kuma har yay bincike hakan yake samu. Wannan abu na ƙara saka masa ƙaunar matarsa mai yawa a zuciya, ko saɓani suka samu ta ɓata masa rai yakan rangwanta mata idan ya kalli hidimarta garesa....         Duk fa wannan ƙoƙari na Ramadhan yana a idanun su forma president da god fathers nasu. Sai dai sunyi likimo ne na nuna goyon bayansu gareshi ɗari bisa ɗari har ya cika shekara biyun da suka ɗiba masa tun farkon fari. A cewarsu daga nanne wasan zai fara kuma. Tunaninsu ya ƙara tsaiwa ne akan abinda ya faru game da zubama Raudha maganin zubar da ciki da sanadinsa har yanzu kuku ke a hanun security na gidan gwamnati. Sunbi duk wata hanya daya kamata susan wani abu game da case ɗin amma an rufesa ruf sun gagara jin komai. Hakan yasa zukatansu ke basu akwai wani abu aƙasa da umarnin Ramadhan kuma aka cigaba da ɓoye kuku tabbas. Domin a bincike ɗaya da suka samu kansa suka tabbatar da hakan. Akwai yaransu cikin masu kula da cctv room na gidan, kuma sune suka sakasu lalata camara ta cikin kitchen da koda aka bibiya ba'a samu komai ba, sannan falon sama da bedrooms na shugaban ƙasa da first lady ke ciki babu cctv saboda sirrinsu ne, a ganinsu tunda har babu waɗannan hujjojin bai kamata ace ancigaba da riƙe kuku ba amma sai gashi har yanzu babu labarinsa.      Waɗan nan dalilan suka sakasu tattara komai suka ajiye gefe acewarsu ya cika 2years ɗin da suka ɗiba masa tunda idan yasan wata ai baisan wata ba. Yana shaƙar poison a ac, yana sha a drinks wannan kaɗai ya ishesu. Kashe Bappi kuwa sun gama shirinsu tsaf akan hakan rana kawai suke jira.          Itama Aunty Hannah wannan shine dalilinta na rage zuwa wajen Raudha ɗin, sai dai tana nan tana shimfiɗa mulkin da ko first lady ɗin batayinsa, wandama bai sani ba ya ga yanda ake bata tsaro idan zata fita saika ɗauka first lady ce, ga matan ƴan siyasa da masu mukaman gwamnati tun ta tattare ta saka a aljihu tanayin yanda taso dasu.      Duk abinda take Hajiya Fanta naji kuma tana gani, sai dai ta bata lokacine acewarta ta gama nata kafin itama ta kammala nata shirin. Rashin sanin alwashin na hajiya Fanta kesa forma First lady Hajiya Bushira hamada da Aunty Hannah kejin duniyar da damar duka tasu ce a yanzu. Shiyyasa suke sake baje kolinsu yanda suke so. To bara mu cigaba da binsu muga yaya wasan zai kaya🚶🏻😮😖. *_TAURA HOUSE_*             “Nifa nata ƙoƙarin naga na danne amma yaƙi dannuwa, hakan ya tabbatarmin zuciyata akan gaskiyarta take ba wasa baneba”.        Pa dake kallon abokin nasa Alhaji Sageer Dogarai mai maganar yay ƴar dariya.       “Alhaji Sageer yau kuma labaran almara ka koma kokuwa zaka fara tsara littatafai ne na marubuta, danni dai banko fahimci inda zancen naka ya kama hanyar zuwa ba balle dosa”.      Dariya Alhaji Sageer yayi, tare da ƙurbar ruwan dake gabansu yana gyara zama. “Ko ɗaya Taura. Yanzu zan fiddo maka ainahin zancen dan na fahimci kai hausarma neman ƙwace maka take a harshe saboda yawon bin kasashe kamar ɗan sama jannati”.     Dariya sosai sukayi a tare. Kafin su tsagaita Alhaji Sageer ya cigaba da faɗin.       “Idan baka mantaba, a ranar ɗaurin auren yaran nan sanda muke shirin fita da kai bayan nazo na gaida Bappi, mun gamu da tawagar matar vice president”.     “Ƙwarai anyi haka”. “Yauwa Alhmdllh, matar da muka ɗan bigi juna har wayata ta faɗi itace tushen zancena. Sai dai zuciyata na cike da ruɗanin matar aure ce kokuwa?”.        Ɗan shiru Pa yayi na nazari, sai kuma yaja numfashi da tunano ko wacece hakan ta faru. “Dogarai tabbas ban sanka da neman mata ba ko wani abu makamancin hakan tun bayan rasuwar matarka kuma komai bai sauya ba, to amma bazance zuciyata bazatai hasashen wani abu game da hakan ba. Dan a yanda na sanka bazakaima matar nan irin son da nake tunain zai dace da ita ba”.         “Taura har yanzu ban canja ba, ina a yanda ka sanni wlhy. Ka ture batun yanda ka sanni akan son auren wayayyar mace mai zurfin ilimin boko, idan rawa ta canja dolene kiɗa ya canja shima a wasu lokutan. Ba wayewarta ko ilimnta na kallaba. Yanda naga kuna nuna jin kunyar juna kamar wasu surukai ne yaja hankalina sosai gareta, gata cikin shigar mutunci da kamala saɓanin sauran wanda ke tare da matar vice president. Wlhy har cikin raina sonta ya shigeni lokaci guda batare dana shirya hakan ba.”         A karan farko Pa yay murmushi, dan yasan wanene Alhaji Sageer Dogarai. Abokinsa ne tunna kuruciya koma muce amini. Shekarar matarsa huɗu kenan da rasuwa yaransu biyu. Tunda ta rasu kuma bai sake aure ba duk da matan nakai masa tallar kansu tare da cece kucen jama'a da dangi akan ƙin sake auren nasa tunda bawai ya wuce hakan bane. Pa ya ɗan ɗage kafaɗa. “Bazance ban yarda da kai ba. Sai dai zance inhar kasan ba hakan bane a ranka dan ALLAH karka aikata abinda zai zubar da kimarmu. Domin kuwa ita wannan mata da kake magana surukatace. Mahaifiyace ga matar Ramadhan kuma a yanzu haka bata da aure dan sun rabu da mahaifin matar Ramadhan ɗin tuni. Yaranta huɗu, ta aurar da ɗaya akwai uku gabanta, sai dai tana shirin aurar da biyu yanzu haka ma”.        “Alhmdllhi. Alhmdllhi”. Alhaji Sageer Dogarai ya faɗa yana kai goshinsa ƙasa domin yin sujudar shukur. Wannan ya sake tabbatar ma da Pa da gaske ne fa.         ★Kamar da wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai babu ɓata lokaci Pa ya tunkari Anne da Bappi da maganar. Sunji daɗi sun kumayi farin ciki, dan haka Bappi yace yabar komai a hanunsa.      A ɓangaren Bappi ma bai tsaya jan al'amarin ba ya tunkari su Hajiyar Birni da shi, sai dai kamar yanda yay hasashe Asabe ta nuna bijirewa su Hajiyar Birni sukai mata can. Murmushi kawai Bappi yayi, tare da basu shawarar su barta tayi tunani, amma ta bama Alhaji Sageer Dogarai ɗin damar zuwa gareta tukunna sai ta yanke hukunci. Ta aminta da hakan, babu kuma ɓata lokaci Alhaji Sageer yazo gareta washe gari.         Mutum ne kamilalle kuma mai tarin nutsuwa. Ba wani tsufa yayba dan shekarun nasa bazasu gaza dai-dai da Pa ba, ga iya magana dan a ƙankanin lokaci ya siye zuciyar Asabe har taji ta gamsu da shi. Sai dai bata amsa masa ba sai da ta garashi sosai. Shiko bai gajiya da binta ba har sai da ya samu amincewarta. Hajiyar birni kam ai likafa taci gaba burikanta nata tabbata bayan wahalar da taci a rayuwa da garari akansu. Wani lokacin bawa nayin gaggawa ne akan abinda baida masinaiyar UBANGIJI ya tanadesa cikin ƙaddararsa. Sai son zuciya ta sakashi tsayawa wajen nemansa koda ta hanyar data saɓama shari'a ne. Sai kaga yazo ya samu abin kuma daga baya.       Alhaji Sageer ya matsa shifa ayi aurenau kafin nasu Fatisa. Itako ta dage akan a'a sai anyi nasu Fatisa. Bai haƙura ba ya cigaba da jajircewa har hajiyar birni ta tabbatar masa yanda yakeso haka za'ai. Sam Asabe bataso hakanba. Sai dai bata ƙaunar yima mahaifiyarta jayya ko kaɗan, sannan Aunty Halima na ɗorata akan shawarar ƙwarai na gara tai auren ko bikin ƴaƴan nata ya ƙara mutunci a idon mazajensu da al'ummar da zasu halarci bikin. Tasan gaskiya Aunty Halima ta faɗa mata, dan haka ta tara yaranta ta sanar musu Raudha kuma aka faɗa mata ta waya. Kamar yanda su Fatisa suka nuna kishin Abbansu a fili haka ma Raudha. Dan kuka ta dinga rusawa akan ita bata yarda Mummyn nasu ta sake aure ba.        Shi dai Ramadhan ma da yaji tushen kuka. tagumi ma kawai yay yana kallonta. Sai da tayi mai isarta sannan yay magana.        “Oh ni Ramadhana naga takaina. Ni karma a haifamin yara masu kukannan fa? Yanzu ke Partner dan ALLAH ba abin farin ciki bane Mummy tai aure? Kinada ilimin addini fa, kin kuma san babu sauran aure tsakaninta da Abba taya zata cigaba da zama kuma a haka bayan har yanzu shekarunta basuyi nisan da hakan zai kasance ba”.       Baki ta tura gaba da juya masa baya zata kwanta ribda ciki ya riƙota. “K rufamin asiri, da wannan cikin zakiyi wannan kwanciyar?, ga Abba ya samu mai tayasa kishi ni ki halakamin nawa.”      Dama ba kwanciyar zatai ba. Dan yay magana tai hakan, ta sake tura baki da buge hanunsa dake riƙe da cikinta daya sake fitowa sosai yanzu kowama zai iya shaida akwaishi.         “Ni dai yi haƙuri karki cinyeni da baki, yarana suzo suga an gama gwaguyeni”.       Filo ta ɗauka ta shiga kai masa duka yana karewa da dariya, sai kuma ta mike daga gadon ta sauka tana daddaga kafa. Saurin riƙota yay ya zaunar a cinyarsa. Zata ɓare masa da kuka ya ɗaura lips nashi kan nata daga haka labarin ya canja.       Bai bartaba sai da ya tabbatar dukkan damuwarta ta gudu sannan suka shiga toilet suka tsarkake kansu tare. Bayan sun fitoma nasiha ya dunga mata har sai da ta fahimcesa ta sakama auren albarka. Suka kuma kira Asabe tare suka gaisheta da nuna mata goyen bayansu dan yanzu dama Ramadhan kanyi waya da Asabe da M. Dauda lokaci-lokaci. Hakanne ya ɗan ƙara sakama Asaben nutsuwar zaman Raudhan tare da shi.............✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/15, 8:33 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 73_* ..........A wata juma'a datai dai-dai da saura kwanki huɗu cikar shekarr Ramadhan guda a mulki aka ɗaura auren Alhaji Sageer Dogarai da amaryarsa Asabe. Aure ne daya tara ɗunbin al'umma musamman daya kasance juma'a ne mutane duk sun halarci masallaci. Aure ne daya saka wasu farin ciki wasu saɓaninsa musamman aunty Hannah da tun farkota nuna adawawta akai, sai dai kuma babu abinda ta isa ta hana daga hukuncin ALLAH.       Ƴar walima kawai akai amarya ta tare ɗakinta cikin aminci da mutuntawa. A kuma daren Ranar M. Dauda da abokinsa suka iso Bingo a haukace a dalilin M. Gambon ya samo labarin a shanun ƴan talla. Inda ALLAH ya taƙaita al'amarin ya kira Bappi ta waya kafin su tunkari ko'ina. Hakan yasa Bappi saurin taka masa birki yasa Malam Adamu zuwa ya ɗakkosu. Babu wanda yasan da zuwansu Taura House sai Anne da Bappi. Aka basu masauki mai ƙyau da abinci kafin safiya. Da farko M. Dauda ya nuna shifa ba wannan ya kawosa ba Bappi dai ya sake lallashinsa.      Washe gari da suka zauna akan batun fir ya nuna shifa sai Alhaji Sageer Dogarai ya sakar masa matarsa inhar ana buƙatar zaman lafiya a NAYA. Iya nasiha yaƙi har sai da Bappi ya bama Ramadhan Umarnin sakawa a kawo masa Raudha gidan. Tana makaranta M. Adamu yaje ya ɗakkota. Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake dan batasan mike faruwa ba. Gashi babu damar kiran Ramadhan ta damesa tasan yana office. Sai da suka iso taci karo da Abbansu ta sauke ajiyar zuciya. Yay sakalo yana kallonta da cikinta daya fito ɗas duk da ma hijjab ne a jikinta har ƙasa. Sai dai a yanda tai zaman sai da cikin ya fito.        “Oh ALLAH sarki Raudha ashe wannan irin arziki ALLAH yaymin naketa shirme ma? Dama ciki ne da ke?”.      Ina ƙasa Raudha ta shige dan kunya, Bappi yay murmushi mai faɗi da gyaran murya. “To kaga kariga ka fara zama babban mutum tunda ga jika kana shirin amsa duk da nasan bashi bane na farko. Ya kamata wasu abubuwan a ajiyesu hakanan kodan wasu dalilai Malam Dawood. Shi aure raine da shi, sannan ƙaddarace ta ALLAH. Ya riga ya ƙaddaro zaka zauna da mahaifiyar yaran nan na wani lokaci ku rabu, idan kuma da rabon sake zama sai kaga ta sake baro can ta dawo gareka ai”.      Hawaye malam Dauda ya share dan harga ALLAH yana son Asabe, so irin wanda bai tabama wata mace ba. Dan ko auren nan daya kara na budurwa dal a leda bai maye masa gurbin rashin Asabe ba a ransa. Nasiha sosai Raudha da Bappi sukai masa, sai dai M. Gambo nata zungurinsa akan karya yarda wai. Tsaf Bappi ya fahimci M. Gambo, ya kuma gane shine matsalar M. Dauda. Dan haka a ranar ya saka aka maidashi Hutawa bayan ya haɗashi da shatara ta arziki.       Sosai M. Gambo yaji zafin hakan, dan acewarsa ƙiri-ƙiri an nuna banbanci tsakaninsa da M. Dauda. hakan ya sashi ƙudirin abubuwan mugun abu da yawa cikin rai game da M. Dauda. Acewarsa in bai samu Asabe ba ai akwai hanyoyin ramuwa da yawa.          Kwanan malam Dauda biyar a Bingo, dan har gidan gwamnati aka kaisa ya kaso kwarkwatar ido wannan karon. Bappi kuma ya riƙesa akan ya zauna har sai anyi bikin cika shekara guda na Ramadhan a mulki. Hakan ya masa daɗi sosai, ya kuma sakashi farin ciki. Su Fatisa ma har nan Taura house sukazo gaida shi, har kuma zuwa yanzu bayan su Anne babu wanda yasan da zamansa a gidan. *_GOVERNMENT HOUSE_*           Sosai aka shirya bikin cika shekara ɗayan nan har abun ya ɗan so bama mutane mamaki, dan lamarin tamkar wani arashi. An shirya ɗakin da taron zai gudana cikin tsarin ado na tutar ƙasar NAYA. Duk da gwamnoni suma zasuyi nasu a jihohinsu hakan bai hanasu halarta ba. Hakama sarakunan gargajiya da abokan kasuwancin Ramadhan.         Su Alhaji yaro glass da muƙarrabansa harma da god fathers nasu kam sun halarci taron. Sai tarin manyan ƴan jam'iyya na kowace jiha. Kamar ko yaushe First Lady da mijinta shugaban ƙasar NAYA *_Ramadhan B. Hameed Taura_* suka iso wajen taron cikin shiga ta kamala ana take musu baya. Sanye take da hijjab har ƙasa fari ƙal mai hannu, sai kaɗan daga ƙasa ake iya ganin ƙasan doguwar rigarta mai kalar tutar ƙasar NAYA. Daɗin daɗawa akwai facemask a fuskarta tare da siririn farin glass iya hannayenta kawai ake iya gani da tsadajjen agogonta. Hakama shugaban ƙasa Ramadhan sanye yake cikin ɗanyar shadda fara ƙal daketa maiƙo da haska idanun mai kallo. Ta gaurayu da ɗinki na musamman daya ƙawatata ya kuma tabbatar fitar tutar ƙasar NAYA. Hakama hularsa zannah tayi matuƙar murzuwa. A kallo guda zaka tabbatar da tarin kwanciyar hankali da farin ciki tattare da shi. Yana riƙe da hanun matarsa har akai masa rakkiya wajen zamansa sannan mutane da suka miƙe dominsa na girmamawa suka koma suka zauna.       Kamar yarda shari'a ta tanadar malamai sun gudanar da addu'oi kafin a fara gudanar da abinda ya tara mutane a wajen. Inda bayanin shugaban ƙasa yay matuƙar birge mutane da ƙara darajarsa a idanusu. Lokacin da aka buƙaci cewar first lady.        Wata hamshaƙiyar mace ta miƙewa da takarda a hanunta ta tabbatar musu ga saƙon first lady ita  wakiliyarta zata isar bisa umarnin shugaban ƙasa amma matsayin miji ba shugaba ba basai tace wani abuba.       Hakan ya bama wasu mamaki, ya birge wasu. Wasu kuwa sun gumtsi gulma da sauya zancen a muhali na daban. Oho hakan bai damu Ramadhan ba, shidai burinsa tsare mutuncin iyalinsa da kuma kishinta da yakeyi. Bayanan da aka gudanar matsayin na first lady ma sun kayatar kuma sun birge mutane daban-daban. Daga haka taro ya cigaba da guna. Anci ansha anyi hani'an first lady da shugaban kasa babu wanda yasha ko ruwa a wajen.        Sai da ana gab da tashi a taron ne Raudha ta hango Abbanta tare da Alhaji Hameed Taura cikin shiga ta kamala tamkar bashi ba, dan kayan daya saka sun masa ƙyau matuƙa duk da jikin ya nuna ba'a saba sakawa ba. Taji daɗin yanda ya kame kansa a wajen har aka tashi lafiya.           Duk yanda Raudha ke ɓoyen cikinta a hijjab hakan bai hana wasu ganewaba, tuni kuma yan jarida suka hau yaɗa cewar shugaban ƙasa gab yake da zama angon karni kuma Baba dan firt lady na ɗauke da ciki. A fanin ƴan adawa kuma sun gama baza zance first Lady dai turancine bata iyaba shiyyasa Ramadhan ya hanata magana a wajen aka samo kwararriya aka fake da kishi.      Maganar tayi nisa sosai, sai dai cikin Raudha yaso danneta tare da manyan ayyukan da aka zano shugaban ƙasa Ramadhan ya shinfiɗa a shekara guda kacal.       A ɓangare. su Alhaji Yaro glass sunyi zaman meeting akan cikin nan, inda kai tsaye suka ƙalubalanci Aunty Hannah data ɓoye musu hakan. Ta nuna batasan Raudha nada ciki ba itama, amma hakan bashike nuna batai murnaba. Dan ita tanada manufa akan cikin koba komai zasu kasance da wani kaso na dukiyar Taura family musamman idan aka dace Raudha ta haifo namiji.     Wannan magana tata ta banƙanta ran su Alhaji Yaro glass, harya faraji a ransa Aunty Hannah bazatai dogon zangoba zai kawar da ita. Dan ya tabbatar shi ɗinma zata iya yin kalar tunanin da take furtawa akan dukiyar Taura family akansa kenan. Duk da kuwa Samha ce kawai a tsakaninsu har yanzun.      To komadai miye, mudai ƴan kallone ai.🤣 Kwanaki biyu da yin wannan biki na cikar masu mulki shekara ɗaya akan madafun iko Malam Dauda ya koma hutawa da shatara ta arziƙi. Dan kuwa kujerar makka har uku, tare da kuɗi masu yawa da galleliyar mota da alƙawarin buɗe masa manyan shaguna a hutawa da kuɗi zasu dinga shigo masa akoda yaushe. Wannan farin ciki ya sashi danne son Asabe daya san har Abada bazai iya dainawaba.         A randa M. Dauda yabar Bingo a ranar hoton wani video ya karaɗe yanar gizo da duk mai wayar da take iya buɗe data zai gani. Video ne daya kasance na Aynah a cikin club ana aikata masha'a da ita. Sai kuma wani shima a cikin ɗaki kusan su biyar duk mata. Abinda zai baka mamaki na club ɗin babu face mask kamar yanda Ramadhan ya sani.       Aminu ya saki wannan video ne bayan ya saka dukan abokansa sunyi amfani da Aynah a wannan dare wasuma harta baya (Wa'iyazubillah😭) yayi hakane a dalilin kawo mata ƴammatansa da yay gidan ta nuna itafa ta gaji ya sallameta hakanan kokuma ta tona masa asiri ga iyayensa da yake yaudarar nuna musu shi ɗin mutumin kirkine. Shiko ya tabbatar mata kafin tayi hakan shi zai fara tona nata a sirin wa duniya sai yaga nata da nashi wannene zaifi gawurta da kayatarwa. Tayi kuka ta roƙesa iyakar roƙo amma yay kunnen uwar shegu da ita sai da ya saki.       A lokacin da wannan video ya riski su Addah Asmah data haukata kanta a neman asirin hallaka Ramadhan da wulƙanta rayuwarsa data Gimbiya Su'adah har ƙasar China ta yanke jiki ta faɗi. Kwannta biyu kenan da dawowarta NAYA, wata kawarta ta rakata China wajen wani gagarumin masanin tsafi. Sun dawo zuciyarta cike da jin ɗunbin nasara saboda abinda matsafin ya haɗo musu, ta tabbatar idan har tai amfani da su Gimbiya Su'adah da zuri'arta sun zama labari kenan. Sai gashi a yau da take shirin zuwa Taura house da fuskar yaudarar roƙon gafarar gimbiya Su'adah danta aiwatar da aikinta wannan mummunan labari ya  baje ƙasar NAYA dama duniya tunda abune na media ako ina zaka iya ganinsa.      A firgice ma'aikatan gidan nasu da kanwar Aynah suka rufu a kanta sai dai babu alamar numfashi tattare da ita. Dole Zulfah tai kiran asibitin da suke ganin likita dan ta nema no na daddyn su ma bata samuba kasancewar shi bayama kasar.                 Hatta da gimbiya Su'adah da ayanzu babu wanda ta tsana a duniya sama da ƴar uwar tata abin ya firgitata, balle kuma Fulani da itama ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a sume dalilin tanada hawan jini.      Raudha ma ta gani kafin Ramadhan, amma ta kasa nuna masa sai zama datai taita kuka dan abun ya ɗaga hankalinta. Musulma ɗiyar muslmai gaba da baya itace a wannan halin duniya ke gani babu ko kunyar mahaliccinmu. Kaicon wata wayewar, kaicon wata dukiyar, kaicon wata damar dan da wata BAƘAR INUWA ce da ita gara rana ma.       Koda Ramadhan ɗin shima ya gani baiji abin saboba tunda a gabansa aka aikata, sai dai abinda ya bashi mamaki fitar videon bayan shekaru. Hakan na nufin dan kinyi barna ko kayi ka binneta da tunanin ta wuce mutane bazasu ganiba watarana UBANGIJI idan yaso sai ya tonota ta hanyar da kai bakai tunani ko tsammani ba. Sannan ya jiraka a madakata kazo ya hukuntaka dai-dai da laifinka dan shi bai kasance azzalumin sarki ba...........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/15, 8:33 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 74_* ..........Faɗuwar Addah Asmah ta jawo mata shanyewar ɓarin jiki, yayinda lokacin da Aminu ya kawo Aynah har gida da takardar saki uku bayan dukan daya lakaɗa mata ya sake ruɗar da jikin na Adda Asmah har sai da takai Zulfah ta kira gimbiya Su'adah tana kuka akan tazo ta taimakesu Mom ɗinsu zata mutu.      Jini ba wasa bane, dan duk yanda gimbiya Su'adah taso ignoring al'amari ya gagara gareta, har hawaye tayi itama ganin video na Aynah hawan jininta ya nema tashi. Tanda halayen banza ta wani fanin, amma tanada zuciya mai ƙyau kuma. Dama can zugar Addah Asmah ɗin ce da fulani ke sake kangarar da ita wani lokacin. Haka ta shirya Safina na roƙonta kartaje dan ALLAH Mardiyya tace danmi? Ita rayuwa ai ba'a maida sharri da sharri. Koba komai ai ALLAH ya nunama Adda Asmah ita ba komai bace ba, sannan duk makircinta a karƙashin hukuncin ƙaddara da jarabawa yake. Idan Maah taje gareta a yanzu Ai sake tabbatar mata zakaran da ALLAH ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi ne. Sannan babu hanun daya isa canja ƙaddarar ALLAH sai dai kai wahalarka ka ƙare a wahale wanda kakeyi dominsa yana ƙara zama sama da kai.      Da wannan zantuka na Mardiyya suka ɗunguma gidan Addah Asmah, inda suka isketa ita kwance Aynah kwance cikin jini na dukan da taci hanun Aminu. Da taimakonsu aka wuce da su asibiti, a kuma daren mai-martaba da fulani suka iso suma. Sunji daɗin ganin Su'adah da yaranta a wajen, suka shiga sanya musu albarka. A daren shima Daddyn Aynah ya iso, bai kumayi zaman ɓata lokaci ba akai shirin fita da su waje dan jikunan nasu su duka yayi tsamari sosai.       Da Fulani suka tafi, gimbiya Su'adah tai kememe tace babu inda zataje hakama ƴaƴanta. Babu wanda yaga laifinta anan, dan ansan an cutar da ita... ___________________________          Wannan hatsaniya na cigaba da yaɗuwa cikin Raudha na ƙara girma. Komai nata ya canja, idan kaganta sai kace ba ita bace. Auren su Fatisa hanata zuwa hutawa Ramadhan yayi, iyakarta nan Bingo sabon gidan Mummynsu da yake anan akai yinin biki kamar yanda Alhaji Sageer Dogarai ya roƙa. Anyi yinin biki laraba Raudah ma a kwance ta yini da zazzaɓi, amma dan jaraba tana a gidan ɓoye. Da dare Alhaji Sageer Dogarai da kansa ya maidata government house duk da kuwa anzo daukarta, kuma dama tana tare da guards nata. Ba kowa yasan Raudha na gidan ba ƴan biki, sai da zata wuce gida. Aiko abin ya bama kowa mamaki kodan yanda Aunty Hannah tazo ita tana baza mulki kaikace itace matar shugaban ƙasar ma. Washe gari Alhamis ƴan biki suka ɗunguma Hutawa, inda akai musu tarba ta mutunci dan yanzu M. Dauda Alhmdllhi, duk da dai ginin shagunansa ko muce super market bai gama kammaluwa ba har yanzun. Amm kuɗaɗen daya samu ba ƙaramin barje guminsa yake ba. Kujerar makka kuwa ya rike sirrin a ransa shi da Inna da Baba Nafi zasu.       Ranar Juma'a aka daura auren su Fatisa da mazajensu. Auren daya bada mamaki kasancewar shugaban ƙasa Ramadhan ya halarta tare da wasu gwamnoni da ministers. Hakama Alhaji Hameed Taura da Alhaji Basheer Hameed Taura. Ga Alhaji Sageer Dogarai da tasa tawagar dan a cewarsa su Fatisa shima ƴaƴansa ne. Saboda Asabe ta riƙe masa nasa da amana, duk da kalubalen data ɗan fuskanta ga yaran a farkon auren, sai dai halin kirki data dinga nuna musu da nuna rashin damuwa da abinda suke matan ita da Yasmin sai suma suka risina suka bata haƙuri ta haɗa ta rungume ta zame musu uwa.      Sam Raudha bata san Ramadhan zaije ɗaurin auren ba sai gani tai alabarai da aka nuna dalilin zuwansa wajen. Jitai fushin da take da shi ya kwaranye. Dan tunda yace bazatajeba take haushi da shi, ta kama matsar kwalla Basma na lallaahinta. Koda ya dawo gidan bayan la'asar kasancewar a helicopter yaje ya dawo saita rungumesa tana kuka da jera masa tagwayen godiya.      Murmushi yay kawai ya kama hanunta suka shige ɗakinsa. Ya zauna akan sofa tare da ɗoraya bisa cinyarsa duk da ƙaton cikinta bai damu ba.        Sai da ya ɗan sumbaci lips nata yake faɗin, “Partner yanzu kin lalace wlhy, komai kuka komai fushi kamar ba Ustazah ɗina mai haƙuri da juriya ba. Anya kuwa ranar shiga labour room ba akwai aiki gagarumi a gabana ba?”.          Kwanciya tai jikinsa tana murmushi da hawaye. “ALLAH Noorullah dan baka san wahalar bane. Cikin nan ya isheni ji nake kamar na cire na huta”.      Murmushi yayi mai kayatarwa, ya ɗaura hanunsa a saman cikin nata yana shafawa. “Kiyi haƙuri jarumata saura ƙiris insha ALLAHU. Kedai kawai mu cigaba da addu'a ALLAH ya saukeki lafiya ok”.      Kanta ta ɗaga masa da sumbatar kumatunsa. Kafin tace, “Shine ka tafi Hutawa ɗaurin aure koma ka sanar min”.        “Hhh haba ƙawata, ina sanar miki rigima zaki sakamin da shagwaɓa, ni banjeba ke bakije ba”.      “To amma tunda kasan zaka basai kaje dani ba da an ɗaura auren sai mu dawo tare”.           “Ke ɗin ce zaki yarda muje mu dawo a ƙanƙanin lokacin nan. Yi haƙuri ai dakin haihu insha ALLAH zakije ki kai musu baby su gani. Kimma san ya mukai da Anne?”.       “A'a”. Ta faɗa tana girgiza masa kai.       “Wai Taura house zaki koma da zama har ki haihu yaro yay ƙwari. Cikin farin ciki ta miƙe zaune sosai a jikinsa. “Kai amma naji daɗi ALLAH, koba ko....”     Baima bari ta ƙarasa ba ya mangare mata kai yana hararta. “Oh kinmaji daɗi kenan. To ai a take nace mata ban yardaba sai dai ita ta dawo nan”.      Baki ta tura masa gaba. “ALLAH wannan buƙulune kawai zakamin”.    Dariya ya ƙyalƙyale da shi mai kayatarwa. “Naji gara hakan, nida aka shirya yima buƙulun barina gaurofa. Muna nan tare ki haihu muyi rainon babynmu kamar yanda mukai na cikin”.        “Uhmm kaji wai mukayi, nadaiyi abina”.     Gira ya ɗage sama, yana mai kai bakinsa saitin kunenta. “To amma wake ƙarama babyn ƙarfi bani ba”.     Kansa ta ture da sauri tana ƙoƙarin tashi ya hanata. Haka ya cigaba da tsokanarta yana kunnata tana masa shagwaɓa. Daga ƙarshe suka koma gado sannan sukai wanka tare kamar yanda suka sabarma kansu a yanzu musamman irin wannan wankan na lada.            Kamar koda yaushe langyare masa tai, dan ba karamin jigata take ba a duk sanda hakan ta faru, sai takai ya mata tausa da lallaɓata tayi barci ake rabuwa lafiya. Yanzun ma bayan tayi barcin fita yay zuwa dinig yayi lunch dan yunwa yakeji sosai.      *____________________________*         A kwana a tashi babu wuya wajen UBANGIJI. Raudha ta cigaba da rainon cikinta cikin kulawar ALLAH da Ramadhan, duk da nauyin Al'umma dake a kansa yana iyakar ƙoƙarinsa gareta itama. Ga gimbiya Su'adah kadaran kadahan tsakaninsu, ba gallazawa babu nuna damuwa. Dan ko Taura House taje zata gaisheta ta amsa ba kamar da ba sai dai iyakar gaisuwarce. Bazata kulataba bazata kuma hantareta ba. Hakama tsakaninta da Aunty Hannah, takan leƙo gidan lokaci-lokaci su gaisa, wani lokacin da mutanenta ƴan siyasa, wani lokacin ita kaɗai sai guards nata. Sau uku tana zuwa gidan Mummynta Asabe. Hakama gidan su Bilkisu dake nan Bingo duk taje. Su Fatisa ne dai har yanzu bata leƙaba saboda ba'anan Bingo suke ba.       A haka cikinta ya shiga watan haihuwa raki da shagwaɓa ya ƙaru, dole kuma Aunty Zuhrah ɗiyar Yafendo ta dawo nan government House da zama dan Anne dai taƙi hakan duk da kuwa Ramadhan jikane. Tunda watan ya shiga kwanakin haihuwa ta daina zuwa makaranta, sai ta dai su Basma suzo su mata bayanin abinda akayi. Randa takejinta da lafiya ta fahimta, saɓanin hakan tace su barta karatunma baza'ayiba. Sukan mata dariya da tausayinta. Dan hatta uban gayyar idan ta birkice masa da rikici dariyarsa yake kwasa kafin ya koma lallashinta a shirya da ƙyar.         Tun dai ana saka ran haihuwar har kwanakin da aka bata a sibiti suka gota, koda Ramadhan ya nuna damuwarsa Dr Hauwa tace karya damu ana samun irin hakan ai ba komai bane. Adai cigaba da mata addu'ar sauka lafiya ..........✍ *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*       [7/15, 8:33 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 75_* ...........Alhmdllhi a wani dare na juma'a da yay dai-dai da cikarta watanni goma cif ta farka da gigitacciyar naƙuda. Rikicewa Ramadhan yayi, da ƙyar ya iya control ɗin kansa ya saka jallabiya sannan ya fito kiran Aunty Zuhrah. Da taimakonta suka ɗauki Raudha zuwa clinic ɗin gidan, yayinda tuni su Basma sun sanar ma Anne. Babu bata lokaci a daren Anne da Dr Hauwa suka nufo gidan, inda suka samu har wata Dr ta shiga da ita ɗakin haihuwar. Babu ɓata lokaci Momyn Jafar ta rufa musu baya itama, aiko ta tarar Dr Ingoze na niyyar halaka yaro dama uwar. wata irin muguwar bangaza takai mata tare da sauke mata tagwayen maruka, daga haka ta hankaɗota waje ta koma kan Raudha.     Kowa yayi mamakin yanda aka hankaɗo Dr Ingoze waje. Gashi Dr Hauwa tace security su rike mata ita har saita fito. Hakan kuwa akai zuciyar su Anne fal wasuwasi. Dama shi Ramadhan suna kawota ya koma ciki kamar yanda Aunty Zuhrah ta bashi umarni. Maimakon zama sai yay alwala ya fara nafilfili da nemawa matarsa sauƙin naƙuda da fatan sauka lafiya.      Tabbas Dr ingoze tama Raudha lahani, sai dai cikin amincin ALLAH an samu damar ciro jaririn ta hanyar theatre kamar yanda Dr Hauwa ta yanke shawara. Dan ƙarfin Raudha ya nema karewa saboda yanda Dr ingoze ta dinga danna kan yaron yana ƙoƙarin fitowa kafin zuwa Momyn Jafar.       Sai gabanin asuba suka fito, anci nasarar ciro santalelen yaro gashi ƙato alamar uwarsa taci ta ƙoshi. Sai dai babu damar ganin Raudha har sai ta samu isashen hutu kamar yanda Dr Hauwa tace. Atake murna ta gauraye gidan na gwamnati, kowa kuma nama Raudha fatan samun lafiya. Lokacin da jariri yaje hanun uban gayya Ramadhan hawaye yaji sun cika masa ido. Ya sumbacesa tare da rungume abinsa yana maijin kaunarsa na ratsashi. Wannan shine karo na biyu da ALLAH yay masa ƙyautar da kuɗi basa badata, hakama mulki da ɗaukaka. Ya bukaci ganin Raudha duk da Dr Hauwa taso dakatar dashi ya bata haƙuri, dole aka ƙyalesa ya shiga shi kaɗai ya dubata. Tausayinta ya kamashi, ya dinga jera mata tagwayen kiss's da addu'oi.      Zuwa wayewar gari labari ya karaɗe lungu da sako na ƙasar NAYA akan shugaban ƙasa ya samu ƙaruwa. Ga hoton Baby nata yawo saboda su Basma da sukaita turawa ƴan uwa da abokan arziki. Sai yazam kowa ƙoƙarin ɗorawa yake a shafinsa, wasu idan sun gani suma sai su ɗauka daga haka ya karaɗe wayoyin mutane. Yaro yasha addu'oi yayinda ƴammata da yawa suka koka dajin kishin inama daga jikinsu ya fita. Sultana dake ƙasar America kam harda kwanciya ciwo dan har yanzu ciwon son Ramadhan na zagaye da ita. Kawai dai babu yanda zatai ne tunda ya faɗa mata iya gaskiyarsa shi baya ra'ayinta tayi haƙuri ta samu mai sonta..      Karo na farko, lokaci kuma na farko da Gimbiya Su'adah ta kira waya tasa aka haɗata da Raudha data farka a washe gari da rana. Yajiki tai mata da fatan samun lafiya. Ita dai Raudha abun ma har hawaye ya sakata. Ramadhan dake gefenta yasa hannu yana share mata fuskarsa ɗauke da murmushi.      Ɗansa dake hanunsa yanata barci ya kalla. Ya shafi lips yaron jajaye yana faɗin, “Ba kuka zakiyi ba Partner. ALLAH zaki godemawa a wannan gabar, ni shaida ne Maah ta jima dayin nadamar abinda tai miki, ta shanye a cikintane kawai saboda nauyin tunkararki. A yanzu kam koda abinda ke faruwa da Lubnah a gidan miji ya isa sake tsoratata”.      Da mamaki Raudha ta dubesa. “Aunty Lubnah kuma?”.      Kai ya jinjina mata batare da ya kalletaba ya cigaba da wasa da sumar yaron. “Eh Lubnah. Tun satin da aka kai Lubnah gidan aure bata sake farin ciki ba. Kuskure kaɗan miji zai lakaɗa mata duka tare da ƙanensa. Ke hatta da uwar mijinma ba ƙyaleta taiba itama dukan nata take. Duk da dukiya irin ta gidan su Mansur ƙiri-ƙiri suka sallami kaso ɗaya bisa biyun ƴan aikinsu aikin ya koma kan Lubnah. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fita hayyacinta saboda azaba. Ameenatu, tun sanda Lubnah ta kawo Mansur garemu matsayin miji na nuna ƙin amincewata, saboda na jima dajin labarin mahaifiyarsa bata zama da sutukai. Hakama kanensa basu da isashen tarbiya. Amma sai Maah taƙi saurarena saboda Lubnah tace tana son sa akace ai nima wadda nake aure bata dace dani amma suka amsa. Dan haka Lubnah zata auresa ko ina so ko banaso. To ga sakamakonan sun gani, dan yanzu a dalilin dukan da surukar mijinne tai mata tai ɓarin cikin jikinta, maimakon Mansur ɗin yaji tausayinta sai ya maidota gida da takardar saki har uku wai yana zarginta da tarayya da drivernsu kiji sharri. Koda nai bincike uwarsace duk ta tsara hakan kamar yanda take koran matan ƴaƴan itama tai sanadin da za'a korota”.         Sosai abun ya taɓa zuciyar Raudha duk da zaluncin da su Lubnah suka dinga mata a baya. Ta jingina kanta da kafaɗar Ramadhan tana kallon babynsu hawaye na zubo mata. Shima rungumita yay da hanunsa cikin son kore mata damuwarta yace,         “Ustazah dawa yaron nan ke kama?”.       “Dani mana” Ta bashi amsa tana share hawaye. Ƙeyarta ya ɗan tallara kaɗan. “Son kanki yayi yawa madam. Kowa yaga Abdull-Hameed Ramadhan Taura yasan gida ya ɗakko, mufa jininmu ƙarfine da shi yarinya”.      Murmushi tayi mai ƙayatarwa da cewa, “Uhm nidai basan cika baki. Dama da Pa kace yana kama ko Bappi sai na yarda”.      Dariya yay yana mai sumbatar kumatunta. Hakama babyn ya sumbaci goshinsa. “Bakice komai akan sunan dana kirashi da shi ba”.     Murmushi tayi mai kyatarwa da shafa kumatunsa. “Saboda shine ra'ayina shiyyasa nima”.       “Woow sweetheart inajin daɗi idan muka kasance bisa tarayyar abu guda”.      “Noorullah! Idan duk yarana zasu kasance da sunan Bappi ko Pa ko Anne ko Maah ko kai bazan taɓa baƙinciki ba. Fatana dai ALLAH ya bani ikon sauke nauyinka dake kaina ka kuma zamemin miji har a gidan aljanna. ALLAH ya raya Abdull-Hameed Ramadhan Taura ya albarkaci rayuwarsa. Yasa yay gadon ƙyawawan halayen Bappin da Pa da kai kanka”.       “AMin ya rabbi sweetheart. ALLAH yay miki albarka ya ƙara miki lafiya. Yasa nan da wata shekarar mu sake dawowa labour room.....”       Da sauri ta rufe masa baki ƙwalla na ciko mata ido. “Wannan ai fatan tsiyane”.      Dariya ya kyaƙyale da ita yana ture hanunta. Miye na wani fatan tsiya anan ai nasan zaki iya Mrs Taura.     Haka suka kasance cikin nishaɗi har saida Aunty Zuhrah tazo ta korashi ɗakinsa sannan.          ★Sai da Raudha ta warke sosai aka fara shirye-shiryen taron suna, amma kowa dai yasan sunan yaron Abdul-Hameed anma Bappi takwara. Ramadhan yaso ayi suna a Taura house Bappi ya hana yace ayi a government house kawai. Badan yaso ba dole hakan aka shirya. Taron sunane daya haɗa manyan mutanen ƙasar NAYA lungu da saƙo, inda amaryar jego da baby sukaci ƙyau har suka gaji. Shi kansa angon jegon yayi tsaf dashi kamar yana shirin yin sabon aure. Anci ansha an kumayi bishasha, inda yaro ya samu ƙyaututtuka masu ban mamaki wasuma dan riya sukai badan ALLAH ba. Dan kawai wane yayi kar ace su basuyiba.. Hatta M. Dauda ba'a barsa a bayaba ya haɗo kayansa na jego harda saitin robobin wanka da saƙe saƙin wanka na icce da ƙatuwar garwarsa ya kawo. Wannan abu yasa su Aunty Hannah takaici duk da ba'a wajen taron ya bayarba. Sai dai ita Raudha farin ciki tai ita da Ramadhan.         A zahiri taro ya tashi lafiya, sai dai a baɗini wasu sun iso wajen taron ransu da ƙulli. Ba su kowa bane sai su Alhaji Yaro glass da ko Aunty Hannah yanzu batajin sirrinsu. Bayan taro ya tashi lafiya wajen ƙarfe biyar na yamma a tsakanin government house zuwa Taura house aka buɗema motar Alhaji Hameed Taura wuta. Harbi ne irin na kwararrun maharba da ko a nesa suka harbo harsashi sai ya isa ga wanda suka hara ɗin. Sai dai in ALLAH ya kaddara da kwananka a gaba ka tsalle domin ikonsa.                Tabbas masu harin sunyi nasarar kaima motar hari sai dai basu taki sa'a ba, amma duk da haka ɓarnarsu ta shafi Taura house. Bayan kammala walima Alhaji Hameed ya shiga mota shi da Anne da su Yafendo domin komawa gida. Sai dai kiran Daddyn Aynah ya riskesu akan rikicewar jikin Adda Asmah gashi ya kira Gimbiya Su'adah bata amsa ba. Hakanne yasa suna ɗan gota government house Bappi da Anne suka fita amotar suka shiga wata harda Yafendo, Inna kuma dake fama da ƙafa tunkan su tafi wajen walimar dama danta dagene Bappi yace a wuce da ita gida. Kasancewar motar da su Muneera ke ciki suka amsa ɗin yasa Muneera dawowa wajen Inna ita kuma. Su Alhaji yaro glass basu san da wannan canji da aka samuba suka sanarma yaransu tahowar Bappi da sanar dasu motar da yake ciki su shirya.        Idan UBANGIJI bai ƙaddara mutuwarka ga makiyiba, komai wahalar mai wahala sai dai ya dawwama cikin wahalar farautar zafin rana data ɗacin zuciya babu nasara. *_ALLAH ka shiga tsakaninmu da maƙiyanmu😭🙏🏻._*        Take a wajen ma ALLAH yay ma Inna Rasuwa, dan sai gawarta aka nufi asibiti da ita. Driver da Muneera ne kawai ke numfashi. Shima driver ko mintuna biyar basu cikaba ya rasu.     Karaɗewar labarin wannan hari da aka kaima Alhaji Hameed Taura cikin kanƙanin lokaci yasa ko zama basuyi a gidan Adda Asmah dake a mawuyacin hali itama suka taho. Hakama Raudha da Ramadhan da su Aunty Zuhrah duk sun rikice a government house. Dan kuwa babu abinda kake gani a yanzu akowane gidan tv sai harin da aka kaiwa Alhaji Hameed Taura. Amma abinda yaba mutane mamaki kamar yanda yan jarida ke faman shelantawa babu shi a motar duk da kuma daga government house kowa yaga motar ya shiga har shugaban ƙasa yay masa rakiya.      Zamu iya cewa a wannan dare gaba ɗaya NAYA a hargitse ta kasance. Dan ba'a samu damar bizne gawar Inna ba saboda jami'an tsaro sun rike. Kuka Raudha take tana sambatu da ambaton “Su din azzalumai ne. Dama sun ce sai sun kashemu, miyay musu, mi kai musu kaima mijina?. Na tsanesu, da ace sun samu nasara kan Bappi yau da kaina zan kashesu, amma ko yanzu karka ƙyalesu Ya Ramadhan. Na rokeka karka barsu suma su dukansu”.      Kalaman Raudha sun girgiza Ramadhan, dan haka ya tsareta ta sanar masa suwaye? Mita sani? Mi take boye musu. Shi tun sanda ta karema Bappi hari ya tabbatar tasan wani abu.      Cikin kuka ta shiga girgiza masa kanta. “Wlhy bansan komai a sannanba Ya Ramadhan, sannan bansan su wanene ba. Nayi hakane saboda shima ya taimaki wani tsohon daya fisa shekaru a filin idi. Amma badan na sanshi ba. Badan nasan komai daga garesaba. Sai dai zan faɗa maka abinda na sani nima, amma wlhy ka yarda dani, ban yarda da aurenka saboda su ba. Nayine kawai dan yima mahaifina biyayya da gujema mahaifiyata tsinuwa da Gwaggo tace zatai mata inhar ban yarda da aurenka ba...........”✍  *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*    [7/18, 8:24 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 76_* ..........Tsaf ta zayyane masa komai data sani na firar su Aunty Hannah da taji, har zuwa aikama bappi takarda, da batun canja driks nashi da ake kawowa cikin gidan.      Ya daɗe da bincike akanta game da drinks saboda yanda kuɗi ke yawan fita a accaunt ɗinta, wanda duk watan duniya ake saka mata kason kudi na Taura family da ake bama kowa. Bai mata magana ba ya shiga bincike akan son sanin mi take da kuɗi, cikin ikon ALLAH kuwa yay azamar ganowa saboda companyn da take aikama kuɗin. Ta hanyarsu ya gane ana kawo drinks gidan, baiyi ƙasa a gwiwa ba yasa akai masa bincike akan wanda take canjawa da wanda take sakawar. An gano wanda take cirewar wasunsu akwai guba a jiki mai shiga jiki a hankali, wanda take canjawar kuma lafiya lau yake. Tun a sannan yasan Raudha tasan wani abu, shiyyasa koda suka samu rubutunta yazama irin na wanda aka aika musu wasiƙa bai tada hankalinsaba. Burinsa kawai yasan asalin tushe da mafari, yau kuma ta zayyane masa komai.      Kyawawar runguma ya bata yana mai sanya mata tarin albarka. Sai dai hakan bazai hanashi kafa kwamitin bincike ba domin tabbatarwa. Badan bai yarda da itaba, sai dan haka dokar shari'a take shaidarta bazata wadatar ita kadaiba dole sai da wasu shaidun musamman da su forma president suka zama manyan kusoshin ƙasar. Dama Dr Ingoze dake hanun security na gidan ta tabbatar musu ita ba laifinta bane sanyata akai ta hakala Raudha da jaririnta inba hakaba itama za'a halaka kaf family nata. *_WASHE GARI_* akai jana'izar Inna da driver aka mikasu gidansu na gaskiya. Ciki kuma harda Shugaban ƙasa Ramadhan da yaje har makabarta. Bayan sun baro makabarta kuma ya wuce ya duba jikin Muneera da batasan ma ina hankalinta yake ba. Sosai ta canja kamanni saboda yanda motar ta kife ta dinga katantanwa da su a kan titi ga harbin data samu har biyu a ƙafa ɗaya da ƙugunta. Cike da damuwa da tausayin ƴar uwar tasa ya koma gida.        Sosai a wannan karon ma su Alhaji Yaro glass sukai baƙin ciki na rashin nasara. Har zukatansu suna sanar musu lallai Alhaji Hameed Taura na tsafi shiyyasa dukkan harin da suke kai masa sai ya kauce masa. Acewarsu to ai idan yasan wata baisan wata ba. Suna kusan sahun farko na zuwa yin jaje da ta'azziya Taura House. Sun kumaje har government house sunma Ramadhan shima dan ana gama jana'iza ya koma gida.      Randa akai addu'ar uku ranar Raudha ta koma government house tare da sabuwar mai kula da ita. Dama Anne nata faɗan zuwanta tun randa akai rasuwar acewarta tana riƙe da laɓuɓun yaro yawo ba nasu baneba ai. Duk da ba wankan jego take irin na mutanem da ba tana samun kulawa sosai dan babu ɗaga ƙafa Hajiya Mama ta dinga mata wankan towel. Yanzun ma koda suka dawo haka ta dinga kula da ita da ƙyau ita da Abdull. Dan Ramadhan ya hana a ɓoye masa suna. wasu kan kirasa Abdull wasu suce Abdull-Hameed ɗin. Shi dai Bappinsa yake kiransa, itama kuma takance bappi wani lokacin ko tace babban mutum.       A haka kwanakin jegonsu suka shuɗa duk da dai wajen da akai mata cs ya warke sarai Alhmdllhi. Ga gyara tana samu na musamman daga shahararriyar mai gyaran nan ƴar Nigeria dake jihar sokoto *_Maman Zara sokoto 07034251528_* (hummm kunga maman zarah ɗin nan karku bari kayanta su wuceku, ku garzaya domin kwasar rabonku, dan koda kuɗinka sai da rabonka kuwa) Gefe kuma Miss xoxo na kasheta da kayan gyaran jiki na musamman dana kamshi. Duk wanda yaga Raudha dole ya sake kallo, dan haihuwar ta sata buɗewa ta zama wata babbar mace da zaka iya bata shekaru ashirin da tara bawai sha tara ba. Shi kansa gogan nata haƙuri kawai yake da juriyar ɗauke kai. Amma inhar ya samu damar ritsata a ɗaki su kaɗai yana ɗan rage zafi ko rokonmi zata masa baya saurarenta. Dama aunty Zuhrah ce ke saka musu ido, ita hajiya Mama akwai kunyar surukuta shi kansa baya yi idan yasan tana kusa.       Ana saura kwanaki uku suyi arba'in Anne ta sanar masa ya kamata yabar Raudha taje hutawa, ta kuma je Bina masarauta duka tayo kwana bibbiyu. Fuska sosai ya tsuke kamar yana gabanta, sai da yaji ta sake maimaita masa sannan yay magana cikin marairaicewa.        “Amma Anne dan ALLAH...” Kaga Ramadhan ni bance tilas ba. Ina dai tunatar da kaine abinda ya dace. Kai yanzu kana ganin ya kamata ace har yanzu matarka bata taɓa takawa gaishe da mai-martaba ba? Sannan tunda akai bikinta bata taɓa zuwa gaida mahaifinta ba?. Nasan dole ne ai muku uziri saboda a yanayin da kuke yanzu, amma bashi ke nuna bazakuje ayi zuminci ba. Kodan kaga tanada haƙurin shanye komai batare data matsanta maka ba”.        Ajiyar zuciya yaɗan sauke, dan yasan tabbas maganar Anne gaskiya ce Raudha nada matuƙar haƙuri, kamar kuma hanata zuwa gaida mahaifinta tauyeta yayi tunda tasha nuna son hakan duk da bata taɓa tunkararsa ba.       Da wannan shawara ta Anne ya shiryama su Raudha tafiya cikin kwanaki biyu. Zatai tafiyar bisa rakkiyar su Hajiya Mama da tawagar securitys. Koba komai hakanma ai ya taimaketa tunda tana son zuwan. Hutawa suka fara zuwa, inda Mal. Dauda ya rikice ya rasa inda zai tsoma ransa dan daɗi. Hakama Baba Nafi da Inna da sauran yaran gidan. Amarya ma dai ba'a barta abayaba, tace dolene ta tarbi first lady kodan baƙanta ran Larai abokiyar hamayyarta. Aiko kamar yanda ta shirya kunna larai tako kunnuta harta kasa riƙe baƙin cikinta ta dinga sakin magana da aibanta Raudha harma da Asabe. Uban gayya Mal. Dauda dake ƙwaƙume da Abdull babu wani jan lokaci ya sauke mata maruka, tare da tabbatar mata yau tata ta ƙare a gidan taje ya saketa. Dan ya rantse duk wanda ya nuna baya son mai sunan Innarsa Raudha to shima bazai taɓa yasosa ba, domin Raudha dai farar haihuwa ce. Da farko Larai ta ɗauka abun wasa, sai da Inna tace “Idan bazata tafi ba ƙara mata guda Dauda”.       Haƙuri Raudha da Aunty Zulfah suka shiga badawa. Yayinda Hajiya mama ko'a jikinta. Take anan ma ta kira Asabe ta guntsa mata. Bawani daɗi Asaben taji ba. Dan acewarta saki koda kaine ka nema bashi da daɗi.       Sosai maƙwafta sun shigo gaishe da first lady, dan ma wasu tsoron securitys dake zagaye da gidan na mal. Dauda ya hanasu. Washe gari da safe taje har gidan hakimi takai gaisuwa da masa godiya. Shiko ya amshi Abdul yana mai sanya masa albarka shi da ƴan fadarsa da matansa. Sunbiyo ta super market ɗin M. Dauda da Raudha taji har ƙwalla ya cika mata ido dan babu abinda zatace da Bappi sai dai addu'a. Da zasu taho jitai kamar karta baro garinta, M. Dauda ya shirya tsaraba mai yawa wai duk na Abdull, ita Raudah abinma dariya ya bata. Yaushe Abdull ɗin yazo duniyarma dazai fara shan kayan zaƙin nan dana ciye-ciye. Da tace a rage cayay bai yarda ba. Itama Inna ba'a barta a baya ba tama Raudha tsaraba da kayan sirrinsu na tsoffi masu kyau da dama ta tanada tunda Raudha ta haihu. Dan ko lokacin suna da sukaje dama takai mata wasu.        Daga Hutawa Bina suka nufa cikin masarauta. To anan dai kam daga mai-martaba ta samu tarba ta ƙwarai. Fulani ce dai kadaran kadahan. Dan ko Abdull ƙin cewa a bata tai sai da Aunty Zuhrah ta ɗauka da kanta ta bata tace a sanya masa albarka. Sai kuma duk taji kunya. Mai-martaba kam acan suka baro masa Abdull, ba'a dawo musu dashi ba sai da ya fara ƙananun kukan yunwa.      Anan ɗin ma dai shatara ta arziƙi mai-martaba da sauran matan sarki suka bama Raudha dan Ramadhan yana girmamasu shidai. Babu ruwansa da wata aƙidar dake tsakanin iyayensa da su.. Ganin sunzo har Bina ta kira Ramadhan ta roƙesa zuwa gaida Aunty Halima itama. Bai hana ba, dan tun farko ma daya san Aunty Haliman a Bina take itama da kwanan akai mata. Sai dai gsky a matse yake da matarsa, burinsa kawai ta dawo. Aunty Halima taji matuƙar daɗi dayin farin cikin zuwan na Raudha. Hakama yaranta. Kasancewar Ramadhan yace sukai har dare sai su biyo jirgi yasata baje kolinsu sosai a gidan Aunty Halima. Dan sai kusan tara suka nufi airport jirgin 9:30 zasu bi.      Ƙarfe goma bataiba ma suka iso Bingo. Motocin da suka tafi tarbarsu da securitys suka kwasosu sai government house. A ranar ma dai Ramadhan yayi kawaicin kauda idonsa saboda yasan da gajiya tattare da su. Dan ko keɓewa bai yarda yayi da Raudha ba. A ɗakin da take jego ya shigo suka gaisa da su Aunty Zuhrah itama Raudha ta gaisheshi ya ɗauka Abdull ya fita. Kusan mintuna talatin yay kiran Basma a waya tazo ta ɗakko Abdull ɗin ta dawo da shi.        Washe gari su Hajiya Mama suka tarkata yan kayansu kafin Ramadhan haƙurinsa yakai karshe ya fara rashin ta ido. Shatara ta arziƙi suma ya haɗa musu suka tafi Raudha na matsar kwalla. Tsabar ya shiryama wannan weekend suma su Basma cayay zuje Taura house suyi weekend. Raudha zatai magana ya dinga zuba mata harara da mintsini. Doleneta tai shiru..........✍      Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulu mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd guess what😍munyi upgrading kayanmu gbdy domin jindadinku🥰bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida 💯 Natural/organic maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki komai da komai Akwai soap 3k Student package 7k Beauty kit 11k Bridal kit 18k Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏 [7/18, 8:24 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 77_* .........Bayan wucewar su Basma sai da ta tabbatar an gama shirya abinci a dining tabar sauran komai hanun mama ladi sannan ta shigo ɗakinta da yanzu ta dawo. Abdull dake a bayanta goye ta sauke saman gado, dan Anne ta gargaɗeta matuƙa akan ta dinga goyasa yanajin ɗumin jikinta batason wannan halayyar da matan yanzu keyi naƙi goya yaro ko ace za'a bama masu aiki suyita faman raino ke uwa kina hutawa. Wanka ta shiga, fitowarta babu jimawa tana ƙoƙarin neman kaya marasa nauyi ta saka Abdull ya farka ya fara ƙananun kuka.         “Oh oh babban mutum yi haƙuri ina zuwa. Nasan matsalarka yunwace acici”.        “Ai duk ke ya gado cin nan ba wani ba”.    Ta tsinkayi amsa daga bakin Ramadhan da bataji shigowarsa ɗakin ba. Ɗan juyiwa tai tana kallonsa, dai-dai yana karasawa saman gadon ya dauka Abdull yana sawa a kafaɗa. Murmushi tayi da ɗauke kanta tana cigana da ɗakko kayanta. “ALLAH ya Ramadhan kaima kasan banda ci, sai dai in kai”. Ta ƙare maganar tana nufosu kaya a hannu.      Kayan ya ɗanbi da kallo, cikin neman magana yace, “K har kina tunanin saka kaya a yau?”.      Cikin rashin fahimta tace, “Kamarya? Kana son na zauna da towel ne na kwashi mura?”. Murmushi yayi mai ƙayatarwa, ya sauke Abdull daya koma barci saman ɗan gadonsa ya gyara masa kwanciya. Tana ƙoƙarin saka riga ya riƙeta. “Idan ma kinsa zan ciresu ne, minene na wahal da kai?”.      Kunya ce ta kamata, cikin marairaicewa tace, “ALLAH ya Ramadhan ba kyau, kaifa yanzu ka girma sunanka Daddy”.       Kai ya dungure mata yana murmushi, sai kuma ya zare ribbon ɗin kanta tare da tallafo kannata ya manne goshinsu waje guda suna shaƙar numfashin juna. “K miyasa kin iya fassara mutum. Ni karki lalatani bankai can ba”.      Mintsini takai masa a gefen ciki, ya  janye jikinsa da sauri yana faɗin “Ouch yarinyar nan muguntar da kika koyo kenan a yawon arba'in ɗin”.     Dariya Raudha ta ƙyalƙyale da shi da masa gwalo. “Ai kaɗan ma kenan”.      Ƙwafa yay fuska a cuskule kamar gaske. “Haba yarinya zan rama ne idan kikazo hannu zaki gane kuranki”.      Juyowa tai da sauri garesa fuska a narke, dan tasan wanene mijin nata. “Please Noorullah sorry”.      “Ba wani sorry ai saina rama”.   Da sauri ta nufosa ta ɗane masa baya duk da ta zama lukuta yanzun, “Ya ilahi, yarinyar nan kin koma biri ne?”.     Ya faɗa yana juyota ta sakko suka faɗa saman gadon. “Gaba ɗaya kin zama ƴar lukuta amma ƙibar ta miki ƙyau”. Yay maganar a hankali yana busa mata numfashinsa a kan fuska. Kafin ta samu damar magana ya manne lips nashi kan nata. Itama a zalamen take, dan haka babu musu ta miƙa wuya ita shaidace mijin nata yayi haƙuri, kusan kwana hamsin ai ba wasa ba. Sai da taga zasu wuce hanyar da suka ɗakko ta fara ƙoƙarin janye jikinta. Amma ya nuna shifa sam bai yarda ba. Roƙon duniya da magiya ya nuna mata baiji bai gani. Dole ko ta miƙa wuya. Daga baya kuma ta shiga tsoro, dan tasan taji gyara babu ƙarya balle algus. Tafiya tai nisa Abdull ya sake farkawa yana kuka. Amma Ramadhan sam yaƙi nuna yama jisa, itako Raudha hankalinta duk sai ya koma kansa (uwa kenan. Uwa mafi uba koda uban sarki ne👍🏻).           Lokacin daya kai inda yake buƙatar zuwa Abdull yaci kuka harya godema ALLAH, da ƙyar ta iya dauriyar tashi ta nufi bayi, Bata ɓata lokaci wajen gasa jikinta ba ta fito dan har yanzu Abdull bai bar kuka ba duk da tabar Ramadhan na ɗan shillashi cikin ɗan gadonsa.      A yanzu ɗinma haka ta samesu, batace da shi komai ba ta yafa towel ɗin da take goge jiki a kafaɗarta ta ɗauka Abdull ɗin. Tashi yay shima batare da yace mata koman ba ya nufi bayin.       Lokacin daya fito tana shayar da Abdull ɗin idonta kan yaron nata da ɗan wasa da sumarsa. Ramadhan ya zauna kusa da ita da riƙe kafar Abdull dake motsawa. “ALLAH sarki kakan Dadynsa kaji yunwa da yawa. Mamanka ce ta cika zalama da wuri take son a farauto maka ƙanne”.    “Innalillahi... Kai Ya Ramadhan”. “Ba wani Ya Ramadhan anan. Inba azalame kike ba miye daga zuwana duba Bappina zaki wani kadandaneni sai da nayi”.       Ina kasa Raudha ta shige dan kunya. Ta ture kansa daga kafaɗarta, shiko ya ƙyalƙyale da dariya. “Uhhm tundafa kin samu kinmin kat aiƙyafa tureni, dama Ustazan nan shiru-shurunku aiba na lafiya bane. Yanzu haka nasa kina nan kina addu'ar a koma second r.......”      Hannu tasa ta rufe masa baki, idanunta har suna tara ƙwalla. Ta dangwarar masa da Abdull a cinya zata miƙe tabar wajen ya riƙota yana dariya. “Yi haƙuri wasa nake my Partner, duk fa nine zalamammen”.     Ita dai bata sauraresa ba, da ƙyar ya samu ya lallasheta cike da salonsa da yake kasheta da shi. Daga karshe suka ɗunguma falo sukai dinner aka sake dawowa filin daga....       Rayuwa ta cigaba da tafiya cike da farin ciki da jin daɗi ga waɗan nan ma'aurata, hakama mulkin Ramadhan kowa nata san barka. Bayan sun gama amarcin jegonsu ta tattara ta koma makaranta. Ramadhan ya sake maida hankalinsa ga harkokin mulkinsa. Yayinda a gefe ya naɗa kwamitin bincike akan harin da aka kaima Bappinsa.       Sai dai kuma mi a hankali rikice-rikice suka fara tashi a wasu yankuna na ƙasar NAYA. Ga yawaitar ƴan fashi a tituna da gidajen manya. Al'amarin kamar wasa sai ya dinga faɗi da gawurta harya fara fin ƙarfin jami'an tsaron dake a tsaye kan matasalolin. Sosai hankakin Ramadhan ke tashe. Tsabar ruɗani har wata rama yay yay duhu sosai. Ita kanta Raudha dake ƙoƙarin kwantar masa da hankali dauriya kawai take, dan zubda jinin ya fara yawan wuce hankali. Dan takai anabin manyan malamai ana musu yankan rago a cikin gidajensu. Komai daya shafi mulki sai ya fara tangal-tangal musamman manyan ayyukan da ake shimfiɗama talakawa. to ana ta rai waketa wani aiki. Mutane ma idonsu ya daina ganin ayyukan tashe-tashen hankulan kawai suke gani, akoda yaushe cikin zaman meeting ake tsakanin jami'an tsaro da masu faɗa aji, sai dai babu alamun samun wani sauyi.     Ba Ramadhan kawai ba, hatta su Anne hankulansu a tashe yake matuƙa, dan duk mai hankali ya kalla abubuwan da idon basira yasan ƙirƙirarsu akai da gayya.. Ramadhan na gab da cika shekara biyu a mulki Bappi ya bashi shawarar sauke duka manyan shugabanin tsaro, hakan kuwa akai, aka sauke su aka ɗakko wasu aka ɗora...       Hakan ya tada hankalin su Alhaji Haladu Gwandu matuƙa, dan shirine da babu wanda yasan dashi wayar gari kawai akai shugaban ƙasa ya zartar da hukunci. A gefe kum aka tara matasa takowane yanki aka basu aikin sakai sai dai gwamnati zata dinga biyansu albashi mai tsoka. Sannan aka saka maƙudan kuɗaɗe ga duk wani farar hula daya kawo sunan ɗan ta'adda uku ya tabbata kuma ɗan ta'addanne. Wannan shirifa ya zaburar da natasa da talakawa, burin kowa ya samu wani maraji ya kwafe sunansa a takarda da mafakarsa yakai hukumomin sirri da aka baza a kowace jiha ta ƙasar NAYA. Sai gwamitin bincike na musamman da aka ajiye su kuma a gefe akan son sanin ta inda makamai ke shigowa ƙasar ta NAYA.      Lallai wannan shiri ya zaburar matuƙa, dan ya maida kowa jami'in sirri mai himma. Takai har ƙananun barayi ma basu da wata sakewa yanzun, dan kan barci ne makwafcinka na maka minshari. Burinsa kayi kuskure kaɗan yakai sunanka a sauke masa kuɗaɗensa. Tofa inji masu jimamin fitar magana, bincike fa ya fara daukar hanya, dan wasu sunaye da ba'ai zato ko tsammani ba sun fara bayyana kansu ta hanyar yaransu da aka fara cafkewa. Bincike yanayin nisa firgici da ruɗani na sake bayyana ga su forma president. Har wani zama na sirri suka ƙirkira da Ramadhan, bai musaba ya amshi baƙuncinsu, ya kuma saurari dukkan soki burutsinsu daya sake tabbatar masa lallai sune ke ƙulla komai kamar yanda yake hasashe shi da Raudha. Ƙin cemusu komai yayi hakan kuma sai ya ƙona ransu.      Sunma rasa inda zasu saka hankalinsu suji daɗi dan sai tsinci ɗai-ɗai akema yaransu, abinda zai baka mamaki harda wanda suke cikin mulkin dumu-dumu. Ta ɓangare ɗaya suke ɗan jin sassauci idan suka tuna ta Ramadhan ta kusa ƙarewa tunda sunada tabbacin ya shaƙi gubar da suka shirya ya shaƙa ɗin ta shekaru biyu. Ya kuma sha a drinks sai dai ganin bai taɓa kwanciya ciwo ko canjawar jikinsaba na ɗan saka musu wasuwasi.     Sai dai a randa suka bama zukatansu salama da wannan madogarar a ranar jami'an tsaro suka cafke Aunty Hannah a dalilin maganar drinks da kuku ya tabbatar itace ke bashi. Ranar Raudha taci kuka sosai, Ramadhan yayta aikin lallashi. Ya tabbatar mata dama sun gama da kammala wannan bincike shiyyasa aka cigaba da riƙe kuku. A ɓangaren Hajiyar Birni ma hankalinsu a tashe yake, dan Raudha ta kira tana kuka saboda zuwa yanzu kowane kafar yaɗa labarai babu wani sabon labari sai na kama matar vice president da ake zargi da haɗa kai da kuku domin halaka shugaban ƙasa. Asabe ma ta kira Raudha, hakan sai ya sake rikitata har Ramadhan yama rasa ta ina zai lallasheta. Kukan da taci ya jaza mata zazzaɓi sai da Dr Hauwa tazo dubata, a gwajin farko kuma ta tabbatar musu Raudha nada cikin wata biyu.      Sake rikicema Ramadhan tayi, tayama za'ace tanada ciki bayan shekarar Abdull ɗaya da watanni huɗu. To shi dai abun yafi karfinsa. Ga rikicin mulki ga nata sai kawai ya haɗata da Anne............✍ Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulu mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd guess what😍munyi upgrading kayanmu gbdy domin jindadinku🥰bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida 💯 Natural/organic maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki komai da komai Akwai soap 3k Student package 7k Beauty kit 11k Bridal kit 18k Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏 [7/18, 8:24 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 78_* ..........“Tabbas dole Hannah ta mutu kafin a miƙata kotu”.     Forma first lady ta faɗa tana duban su Alhaji Yaro glass dake tare da ita harma da god fathers nasu a yau. Mr MM da duk yake a firgice yay saurin faɗin, “Ina bayanki your excellency maa”.        Gaba ɗaya falon dubansu suka maida ga Alhaji Yaro glass da tunda ya shigo baice komai ba, sai ma uban tagumi daya rafka. Numfashi yaja mai ƙarfi ganin sun dawo da kallonsu garesa alamar amsa suke nema. Yaɗan ɗage kafaɗa da yarfa hannuwa. “Ni a gareni babu matsala, da nasan ma wannan ranar zata zo da dakaina zan kashe Hannah tun kafin zuwanta. Dan tun randa case ɗin kuku ya shigo ya kamata a ɗauka wannan matakin, amma sai muka ɗauka hakan ba komai ba. Sai dai ku sani ba Hannah ce kawai zata mutu ba harda Kuku, dan kuwa Hannah da Bushira kuku ya sani ba Hannah kawai ba”.         “Amma kasan shi ɗin ɗanane jinina ko?”.     Cewar Forma first lady Bushira hamada a harzuƙe.        “Nima ai Hannah matata ce, cewa a kasheta bashike nufin bana sonta ba. Sannan idan baku manta ba matar Ramadhan jinin Hannah ce, amma da akace zata iya mutuwa a cikin shirinmu batai jayyya ba, ashe kuwa indai nasara muke bukata dolene mu ɗanɗani ɗacin rashin jinanannmu koda kuwa ƴaƴan da muka haifane”.      A take kowa ya goya bayan maganar Alhaji Yaro glass. Hakan yasa Hajiya Bushira hamada yin shiru. Oga kwata-kwata da baice komai ba sai da duk suka gama hayaniyarsu sannan yay gyaran murya. Dukansu hankali suka maida garesa.       “Idan har ta kisan wane da wane ne zamubi ta hanyar rufe sirrikanmu mutane da yawa zasu mutu a wannan gaɓar. Dan haka ba shine mafita ba, babbar mafita a garemu yanzu harin maƙiyinmu kai tsaye. Ramadhan shine kawai zamu hara kai tsaye mu sami nasarar daƙile duk wata damuwarmu. Amma dan mun kashe su Hannah kamar mun kashe macijine bamu datse kansa ba, domin kuwa kisan nasu tamƙar buɗe hanyar da masu bincike suke nemace kai tsaye muka bayar.      A take ɗakin taron ya ɗauka kananun hayaniya. Dan kuwa zantukan shugaba sun fargar dasu abinda basu hango a farko ba. Dan haka a daren yau basai gobe ba Ramadhan zai baƙunci lahira.....        “Idan shi bai baƙunceta ba, ku zaku baƙunceta ai”.  Cewar Alhaji Balarabe Andu daya daɗe tare da su da fuska biyu. Alhaji Balarabe Andu tsohon jami'i ne da tun komawar tsohon shugaban kasa Usama D. Hamada mulki na biyu ya shigo jikinsu. Koda yake zamu iya cewa tun a mulkin farko ma yana tare da su, sai dai basu sakin jiki da shi har sai lokacin mulki na biyu da suka tabbatat yana tare da tafiyarsu. Tun usul ya shigo tawagarne akan binciken wani gagarumin ƙulli da akai a wancan mulkin, sun buga sun buga suka kasa gane kansa. Shine yay shigar burtu ya zama ɗaya daga cikinsu. Yaso barinsu bayan kammala mulkin Usama D. Hamada, sai dai ƙullin da suka fara akan daura Alhaji Hameed Taura a mulki ya sashi dakatawa. Duk abinda suke yana biye da su, hatta da ac da suka saka poison a ciki na gidan gwamnati yaso zama silar da zai sa a cire sai Raudha ta rigasa, amma da taimakonsa su bappi suka cire batare da suma sun sani ba. Ya cigaba da tattara bayanan sirri akansu batare da sun sani ba, kuma ko ayanzu da aketa faman kama musu yara duk da saka hanunsa a ciki....      A firgice duk suke kallon Alhaji Balarabe Andu, dan wasunsu sun ɗauki abin wasa ne ko almara ko subutar baki,       “Alhaji balarabe kasan mi kake faɗa kuwa?”. Cewar Alhaji Haladu Gwandu.      Alhaji Balarabe yay wani murmushi tare da rausayar da kai gefe ya tafa hannayensa yana kallon Alhaji Haladu Gwandu batare da yace komai ba. A take jami'an tsaro suka shigo falon suka zagayesu su da makaman da suka tile a tsakkiyar falon wanda a yau ɗin nan aka iso da su ƙasar NAYA.....          ★Cikin ƙanƙanin lokaci ƙasar NAYA da kewaye ta ɗauki sabon labari na kama waɗan nan manyan mutane da wasun su ko'a hasashen zuciya bata taɓa kawo zasu aikata abinda ake zarginsu da shi ba. Bakin ƴan siyasa ya buɗe ta ko'ina bakajin komai sai kace nace. Abinda ma ya takaice kace nacen tsayawa akan jam'iyya mai mulki kawai waɗan nan mutane gaba ɗayansu suna tarayya ne a cikin mabanbanta jam'iyyu. Hakan na nufin kenan dama ƴan siyasa da yawansu a bayan fage kanwunansu a haɗe yake a zahiri kuma suyita gwara kan talakawan ƙasa da sasu luguden laɓɓa batare da sun hankalta ba. (Ƴan uwa idan zamuyi soyayya muyita dan ALLAH kuma saisa-saisa. Hakama kiyayya muyita saisa-saisa kuma domin ALLAH musamman irin ta siyasa. ALLAH yasa mu cika da imani).      A yinin wannan rana kawai hankalin al'ummar ƙasar NAYA ya dawo kan shugaban ƙasa Ramadhan. Aka dinga sanbarka a garesa da wanke laifukan da ake kallonsa da su. Yayinda wasu keta faman bankaɗe-bankaɗen abubuwanma da ba'asan da su ba sai yanzu.       A wani fanin Raudha na farin ciki, wani fanin kuwa tana baƙin cikin kasancewar yayar mahaifiyarta cikin tawagar waɗannan azzalumai. Ga laulayin ciki mai wahala da take fama da shi a wannan karon. Ga karatunsu ya ɗau zafi dan suna lavel 3 ne. har zuwa yanzu kuma bata taɓa kuskuren nunama wani ita wacece ba. Abdull bada shi take zuwa makaranta ba. Gida ake barinsa wajen Mama Ladi. Dama Alhmdllhi yana ɗan takawa zuwa yanzun, damma haƙora na maidashi baya idan yay zazzaɓi. Bayyanar cikin nan na Raudha kuma yasa Anne zuwa ta ɗaukesa a gidan ma baki ɗaya ya koma Taura House yaye. Sudai basu da ikon cewa komai, amma gimbiya Su'adah taji haushi dan ta ƙullama ranta itama abinda akai mata na ƙwace Ramadhan saita kwace Abdull, sai gashi Anne ta sake mata kwaf ɗaya kafin ta farga ta ɗauke ita (🤣😂Bashin gaba lol). ★★________★★★________★★            Rayuwa ta cigaba da shurawa su Alhaji Haladu Gwandu na cigaba da zama a tsare a gidan yari, a gefe kuma ana sauraren ƙararsu a kotuna mabanbanta saboda laifukan nasu sunzo daban-daban. Kowanne akwai babban laifin da yake shugabanta da ake tuhumarsa a kansa kai tsaye. Wanda sukai tarayya akai shine cin hanci da rashawa da shigo da makamai.      Ɓangaren shugaban ƙasa kam zamuce abubuwa sun fara dai-daita, domin ɓarnakun da tashe-tashen hankali ya kawo su akebi ana gyarawa kafin a ɗora sauran ayyukan da aka fara. A gefe kuma ya sake samun kwanciyar hankalin kasancewa da matarsa abar sonsa da alfaharinsa ƴar darunsa kuma dake fama da ciki. A haka ALLAH ya sake saukar Raudha lafiya, a wannan karon kam da kanta ta haihu yaronta namiji again, shima yaci sunan Pa wato Basheer. Suna kiransa Alhaji ƙarami. Duk da Ramadhan yaso kar ai taron suna dan bai manta abinda ya faru ana Abdull ba su Bappi sukace sai anyi. Haka dai akayi taro mai kayatarwa anan ɗin ma Raudha ta cigaba da shayar da yaronta.           Yankema su Alhaji Usama D. Hamada tsohon president hukunci dai-dai da abinda suka aikata yayi dai-dai da sake kaɗa tamburan siyasa. Dan hatta yunƙurin kisan Ramadhan da sukai tsautsayi ya koma kan Amnah ɗiyar Alhaji Haladu Gwandu sai da jami'in tsaro Balarabe ya fallasa. Wannan hukunci da aka yankema waɗannan azzalumai ya zama makamin campaign na Ramadhan a wannan lokaci, dan kuwa yanda abubuwa ke tafiya bama sai ance maka shine zaiyi nasara ba kowace alama ta nuna hakan.      Sai kuma wani babban abin farin ciki da Ramadhan ɗin ya aywatar a wannan lokaci shine hana bangar siyasa yin tasiri a ciki dabai na ƙasar NAYA. Duk ɗan siyasar da aka samu ya bama yara makamai ko kayan maye domin masa campaign ko makamancin hakan to takararsa ta ruguje bazaiyiba. Wannan al'amari shine ya saka ƴan siyasar shiga hankalinsu, matasan kuma dama mafiya yawansu sunda aikinyi wasu sabo dayine da kuma shegen kwaɗayi ke ingiza zukatansu.       Alhmdllhi campaign ya wanzu cikin nutsuwa da burgewa, inda har akai aka gama babu wanda yaga matar shugaban ƙasa ko da a poster. Sai dai Ramadhan yasha fita da Abdull da Alhaji ƙarami da shima yake neman cika shekara guda da haihuwa. Zuwa yanzu mutane da yawa sun fahimci shugaban ƙasa Ramadhan baya ra'ayin matarsa a harkokin siyasa ne kawai, yana kishinta yana killace abarsa matsayin tashi shi kaɗai. Hakan ya matuƙar birege mutane, harma a wannan campaign ɗin wasu ƴan siyasar sukai koyi da hakan musamman ƴan takarkaru.       Dan hatta abubuwan alkairi da Raudha ke shimfidawa a bayan fage bazaka taɓajinsa a bayyane wa duniya ba, acewarta tayine domin ALLAH badan wani ya sani koya yaba mata ba. Mijinta kuma ya bata goyon baya ɗari bisa ɗari.        Alhmdllhi an gama campaign lafiya ankumayi zaɓe shima. Yayinda sakamakon zaɓe ya tabbatar da sake zaman *_Ramadhan B. Hameed Taura_* matsayin shugaban ƙasa a karo na biyu a ƙasar NAYA. Duk wani masoyinsa ya tayasu murna da fatan sauke nauyin al'umma a kansu. Inda a wannan karon ya shigo sabon tsarin da sabon tsare-tsare da ƙudirirrika na musamman. Yayi sauye-sauyen wasu a cikin ministers da suka kasance zabin su Alhaji Yaro glass a wancan karon. Hakama vice president an sake sabo tunda su Alhaji Yaro ana can ana cin gabza a prison😝.          Rantsar da shugaban ƙasa baifi da sati uku ba su Raudha sukai GRADUATION a makaranta. A kuma lokacin ta bayyanama school mate nata ko ita ɗin wacece. Ansha mamaki, ansha al'ajab da kace nace ga ƙasar NAYA ma ba makarantar kawai ba. Gaba ɗaya hidimar bikin fitar tasu ita ta ɗauki nauyin komai. Ansha hotuna na tarihi kowa burinsa firt lady karta manta da shi duk da bata yarda ta buɗe fuskarta ba ko a wajen bikin kamar yanda Ramadhan ya bada doka. Yadai yarje mata ta sanar dasu ko ita wacece kawai..       A randa suka kamma bikin gama karatu a ranar ta sake fahimtar tana da ciki, taci kukanta tai gum da bakinta, sai dai batasan mai gayya mai aiki shi ya san da abunsaba tunkan ta sani. Sai ranar kawai yake bayyana mata ta gama boye-boyenta shi ya jima da sanin ya samo ribar farautarsa ai.     Galala tai tana kallonsa, shiko yay mata gwalo ya fice. Jitai kamar ta zauna taita kuka kawai. Ita wannan wane irin abune bata yaye yara sai sabon ciki. To babu yanda aka iya da hukuncin ALLAH, wasuma nema suke basu samu ba da kuɗi.      Tun tana zumbure-zumɓurenta harta ware suka cigaba da rainon ciki Mama Ladi ta yaye Alhaji Ƙarami. A randa Raudha ta haihu a ranar ALLAH yayma Addah Asmah dake fama da jiyya har yanzu rasuwa. Ba kowa yaji mutuwarba. Dan dama masu jiyyar tata sun matuƙar gajiya. Yanda bata nema yafiyar kowaba babu wanda yace ya yafe matan har gimbiya Su'adah da yanzu akai sanyi. Bata sakema Raudha dai bakuma ta takura mata. Babbar damuwarta ma yanzu zaman Lubnah a gida da Muneera da a yanzu ta koma sai wheelchair saboda ƙafarta ta samu matsala a wancan haɗarin. Har kuɗi da gida da mota aka saka ga wanda zai auri Muneera amma duk wanda yazo ya ganta saboda raunikan da tayi a fuska sun canja mata kamani sai ya gudu. Bilkisu kuwa tuni harta haihu abinta ita da su Fatisa. Yanzu hakama shirye-shiryen bikin su Basma akeyi.         A wannan karon dai Ramadhan ya dage baza'ai bikin suna ba, ya dai ɗauke matarsa bayan arba'in sukai tafitarsu America domin hutawa na sati biyu tare da yaransu uku vice president ya cigaba da riƙe ƙasar NAYA kafin ya dawo. Dan jinjirin shima yaci sunan Mal. Dauda. amma suna kiransa Dawood. Raudha da Ramadhan na cemasa Abbati.       Satinsu biyu suka dawo NAYA harkokin mulki suka cigaba da tafiya yanda akai fata...........✍               *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/19, 8:32 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 79_* ...........*_BAYAN SHEKARU BIYAR_*        Alhmdllhi abubuwa da yawa sun faru na cigaba a cikin waɗannan shekaru daga mulkin shugaban ƙasa Ramadhan. Ciki harda haihuwa da Raudha ta ƙara har sau uku. Bayan Dawood tayi ƴammata biyu tagwaye da sukaci sunan Saleeha da Zainab. Ta kuma sake Hauwa'u, sai auta da yaci sunan mai-martaba suna kiransa Saraki.        Babu abinda ƴan ƙasa zasuce sai sambarka. Dan kafin shekarun mulkin Ramadhan su kammala ya shimfiɗa manyan ayyukan da har abada baza'a manta da shugabanci irin nasa ba. Daɗin daɗawa bai saukaba sai da ya gyara wasu da yawa a dokokin kundin tsarin mulkin kasar NAYA. Ciki harda dokar shugabanci. Duk shugaban da ya haura shekara sittin bazaiyi mulkin ƙasar NAYA ba koda kansila ne. A kowace ma'aikata ana son kaso biyu bisa uku matasa su sami rinjayen samun aiki bawai lallai sai a manya ofisoshi ba. Kokai wanene kar'a baka aiki a gurbin da baka cancanta ba. Babu wani ɗan siyasa da zai tilasta ƴan ƙasa amsar zaɓinsa a kowace jam'iyya sai wanda takalawan kasa suka zaɓa. Duk ɗan siyasar daya tara matasa da kayan maye da makamai domin bangar siyasa bashi ba mulki har abada. Duk shugaban daya hau mulki dolene ya tsaya akan lafiya, tsaro, ilimin ƴan ƙasa da samar da aikin yi koda ta kananun hanyoyi ne ba lallai sai manya ba. Babu wani shugaba da zai gama mulkin gwamna ya koma mulkin majalisa. Daga mulkin gwamna kanada zaɓi na neman takarar shugaban kasa ne kawai koka koma gefe ka saka ido tunda mulkin ba dole bane.       Waɗan nan dokoki sun gamasar sun kuma saka jama'ar ƙasar NAYA farin ciki matuƙa. Aka dinga masa addu'a da fatan alkairi da sambarka. Wasu harda kukansu a randa ya miƙa mulki ga sabon shugaban ƙasa da yaci zabe wanda shima shekarunsa basu wuce arba'in ba kacal.       Ramadhan da Raudha sunyi bankwana da jama'ar kasar NAYA suna kuka da neman gafarar kowa suma harda Abdull mai shekaru tara a duniya daya fara zama ɗan saurayi abinsa. Hakama kanensa ganin iyayensu na kuka da yayansu sai suka dingayi suna dagama al'ummar ƙasar naya hannu alamar bankwana garesu. (Kai ALLAH sai naji kamar gaske nima sai da nai kuka😭😂🙏🏻)         Koda forma president Ramadhan B. Hameed Taura ya iso Taura house da tawagar masu rakiya talakawa da abokan mulki da iyalansa tarba suka samu mai girma daga su Anne da tsufa ya ƙara kamawa. Hakama kanensa dake gidan aure kaf suna gidan. Ya rungume su Bappi yana mai zubda hawayen farin cikin sauke nauyi da fatan ALLAH yasa bai taho da hakkin kowa a kansa ba. Sosai mutanen wajen suma suka sake shiga matsar kwalla duk da Ramadhan ɗin ya sakasu wani acan gidan gwamnati kafin su iso nan dama.       Anyi addu'oi godiya ga UBANGIJI, Ramadhan ya sake mika godiyarsa ga su cos da wasu manyan muƙarabbansa da alkairinsu bazai iya musltuwa da baki a garesa ba. Akaci akasha aka sake addu'ar bankwana kowa ya kama gabansa.       Daga Raudha har Ramadhan zazzaɓi suka kwanta har kusan sati, dan har Ramadhan na tsokanar Raudha kodai ciki ne tace ALLAH ya kiyaye tayi kenan. Ganin alhini yaƙi sakinsu Bappi ya bashi shawarar daukar iyalan nasa suje su huta.      Haka kuwa akai, Ramadhan ya tattara ƴaƴansa da matarsa suka wuce ƙasashen duniya shakatawa. Bayan sun ɗan zazzaga suka yada zango a ƙasar America inda yafi wayo. Sun sami tarba ta musamman ga abokansa da abokan kasuwanci ciki harda Sultana datai haƙuri yanzu haka itama yaranta biyu da A.J.       Rayuwar America rayuwace da Raudha da Ramadhan bazasu taɓa mantawa da itaba. Dan kuwa ta riskesune batare da hayaniyar komai ba kasancewar a baya harkokin mulki na yawan cinye lokutansu. Yanzu ko idan yaran suka nema shiga musu hancima tuni suke tattarasu su aika gidan A.J ko Mufeed ko Sultana. Babu abinda suke sai more ƙara'in amarcinsu da basu sami damar yi a baya ba duk da yanzu kam akwai nauyi na ƴaƴa da canjawar abubuwa da yawa na rayuwa. Dan kuwa dai da gaske Raudha ta koma yar lukuta (kamar bilyn Abdull😂😝👍🏻lol). Shi kansa mai gayya da aikin ƙibar yayi harda tumbi dake tabbatar da shekarun kuruciya sun fara nisa a garesa, dan kuwa arba'in da biyar yake tunkara yanzu. Yayinda Raudhansa ke tunkarar ashirin da takwas. Amma yanda ta buɗe ta zama babbar mace sai kace takai talatin da biyar. (Mace kenan ai, da zarar ka haihu kuma ai sai addu'a. Kai kobaka haihunba inhar akace an wuce shekarun nan na ƙuruciya sai sambarka, duk da dai akwai masu karamin jiki da zakagansu duf-duf abinsu masha ALLAH. Koma dai miye kowa da irin halittar da ALLAH ya tsara masa). _________________________      Watansu biyu kenan da baro gidan gwamnati, suna dawowa daga America suka sake dawowa Taura house dan Ramadhan baida sha'awar zama wani gida daban sai cikin family nashi, musamman da yanzu gidan ya koma iyayen sune kawai kasancewar kowa yayi aure kanensa dan Muneera ma dai ALLAH ya iyakance mata tayi auren zuwa yanzun, hakama Lubnah tayi itama. Sai jikoki idan sunzo musu hutun weekend. Shine namiji dole ƴaƴansane zasu kasance a gidan famanet, dan haka ko a yanzu bada wani ra'ayin gina gida ko saye balle tunanin komawa. Ita kanta Raudha nan ɗin yafi mata daɗi tunda tun usil ta rayune a cikin family house.       Wasu abubuwan sun canju, wasu ko ALLAH daya halicci bayinsa akansu kawai ne ka iya canjawarsu. Dan kuwa har zuwa yanzu babu wata shaƙuwa tsakanin Raudha da Gimbiya Su'adah. Sai dai tana nuna son su Abdull kam. Hakan yasa Raudha batajin komai a ranta tunda dai su Abdull jinintane ya wadatar sonsu ya zama ƙauna tsakaninta da surukar tata mai murɗaɗɗen hali.      Sosai Bappi da Anne tsufa ya sake baibayesu, dan Yafendo ma tana fama da jiyya a yanzu. Hakama Inna ta Hutawa ALLAH yay mata rasuwa, yayinda shima M. Dauda ke fama da ciwon hanta sakamakon shaye-shaye sigarinsa. Raudha tsaye take akan maganinsa amma al'amarin nasa dai sai addu'a kawai.          A ɓangaren su Hajiyar Birni itama dai tana fama da ƙafa sosai, dan takai yanzu ko'inama bata iya zuwa. Har ƙasar indiya Raudha tasa aka fita da ita taga likita. Sai dai an samu sauki amma ba'a warke ba abinka da harda tsufa.         Hajiya Mama ma ta koma gidan mijinta na farko, hakam Asabe na zaune lafiya da mijinta da ƴaƴansa. Dan a yanzu hakama shirye-shiryen auren babban ɗan Alhaji Sageer Dogarai da Yasmin akeyi saboda sun dai-daita kansu. Babu abinda Asabe zatace da ALLAH itakam sai godiya. Ga su Fatisa na zamansu lafiya a gidan aurensu suma da yaransu abin sha'awa. Taga ribar yin tuba na gaskiya da dogaro ga ALLAH da maida dukkan lamura garesa.      Ga yan prison kam sai muce ALLAH ya cigaba da rabamu da halayya irin tasu ta masu san zuciya, wasunsu baƙin ciki yasa zukatansu bugawa tuni sun bakunci lahira, dan kuwa da ransu ga Ramadhan na mulkin kasar NAYA amma basu da ikon ko ganinsa sai dai su karanta a jarida, wanda suka kai labari kuwa yanda ya sauka cikin salama ƴan ƙasa na kuka da begensa yay mugun haddasa musu ciwon zukata a dalilin hawan jini suma sukace ga garinku nan. Irin su Bushira Hamada da suka rage da rai rayuwar kawai ake cikin baƙin ciki dajin garama a mutu a huta da kallon wani takaicin da baƙin cikin rayuwar. dan a yanzu haka Aunty Hannah fama take da jiyya sakamakon zaftare kafa datai da fatanya wajen yin aiki cancer ta shigeta. Har prison ɗin Raudha takai mata likita na zuwa dubata lokaci-lokaci dan su Asabe kan kanje busting nata, itama Raudha ta taɓa zuwa sau ɗaya lokacin suna kan mulki. Bushira Hamada wai zata kashe Raudha aiko taci duka ranar hanun jami'an gidan prison ɗin. Daga lokacin Ramadhan ya hanata zuwa takuma bi maganar mijinta bata sake zuwa ba sai bayan saukarsu taje harda yara suka duba Aunty Hannah ɗin saboda jikin yayi tsanani sosai.            A hutawa ma dai komai Alhmdllhi, idan ka cire ciwon M. Dauda dake fama da shi, duk da dai yana samun kulawa Alhamdulillahi. Sai dai Rasuwar Inna data gitta ce ta girgiza kowa Har Raudha da Ramadhan dama jama'ar Taura Family duka sun mata halacci sunje harda Gimbiya Su'adah a karo na farko. Hakan yama Raudha daɗi, dan bayan sadakar bakwai data dawo har ɗaki taje taima gimbiya Su'adah godiya.      Rasuwar Inna baifi da watanni biyu ba Fulani ma ta rasu, nanma dai sun girgiza suka dunguma masautar Bina. Inda su Aynah dake zaune yanzu a masarauta itama dai tana fama da ciwo saboda abinda abokan Aminu sukai mata tun wancan lokacin yafi tabata, dan tasan dai Fulanin ce kawai ta rage gatanta kanwarta Zulfah tunda ta samu tai aure bawani zuwa takeba sosai sai hadimai ke dawainiya da ita saboda tsoron Fulani. Yanzuko babu fulani sai abinda ALLAH yayi kuma kenan tunda Hadiman ba tsoronta sukeba kamar da da idan tazo take takasu kamar itace ta haliccesu. Babanta ko tuni yayi aurensa yana zaune lafiya da matarsa dan harta haifa masa yara biyu maza kyawawa da yaketa alfahari da abinsa. Zulfah dai na tare da shi da matarsa dan ta ɗauketa uwa ita babu ruwanta.......✍ [7/19, 8:32 PM] NANA: *_Typing📲_* *_Episode 80 END_* ...........Cikin sauri-sauri take ƙarasa shirin nata. Tayi matuƙar ƙyau cikin ɗanyan shadda da taji wadataccen aiki. Sosai ta zama babbar mace da duk inda ta gitta dole ne a bata girma kodan yanda take cika idon mai kallo. Kwalbar turaren hanunta ta ajiye tana mai juyiwa jin an buɗe ƙofar ɗakin.       Batai magana ba, sai dai ta tsurama ƙyaƙyƙyawar yarinyar da bazata wuce 4years ido ganin yanda taketa faman tura baki gaba cike da shagwaɓa. Sanin halin ɗiyar tata ya sakata takowa a hankali gareta, ta amshi bowl ɗin hanunta tana kallon abinda ke ciki. “Zee miya faru?”.         Sake ɓata fuska yarinyar tai hawaye na ciko mata ido. A shagwaɓe tace, “Mamie ba Daddy bane da Saleeha suka cinye min”.       Kai Raudha ta dafe, a zuciyarta tana tunanin yaya zatai da Ramadhan a gidan nan itako akan cin nama, ƙoƙari take duk yanda zata hanashi ci kamar yanda likita ya saka masa doka. Shiko yasan duk hanyar da zaibi yacisa. Komai batace ba ta kama hanun Zainab suka fita. Kai tsaye falonsa ta nufa inda take jiyo ƙiriniyar Jiddah da Saraki. Dan su Abdull sun wuce Islamiyya. Zee ɗin ma dan bata da lafiyane bataje ba, itako Saleeha ganin Zee bazataba itama ta maƙale.             Kwance yake a tsakkiyar lallausan carpet ɗin falon, Jiddah da Saraki nata tsalle a kansa. Tun kan ta ƙaraso ƙamshinta ya sanar masa. Saraki ya sauka daga kansa da gudu ya nufeta. Ɗaukarsa tai tare da subatar kumatun autan nata. Shima ya sumbaceta da faɗin “I love you Mamie”.       “I love you too Darling”. Ta faɗa cikin shafa kansa tana murmushi    Fuska Jiddah ta ɓata tana hararan saraki, hakan yasa Ramadhan faɗaɗa murmushinsa tare da sumbatar goshinta itama yace “I love you sweetheart ”.       Dariya Jiddah ta sanya. Ta rungume Daddyn nasu tana faɗin “I love you too Daddyn mu”.         Raudha dake kaiwa zaune tai murmushi da girgiza kanta. Sai kuma ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Duk mai kishi da autana dai zai rame a gidan nan”.       Tashi zaune Ramadhan yayi sosai yana murmushi shima idonsa akan matar tasa, dan kwalliyar tata ta tafi dashi sosai. Kai kace wata anguwa zata. Ido ya kashe mata cike da salo yanda yaran bazasu gane ba. Itako ta hararesa tana nuna bowl ɗin hanun Zee daketa ɓata fuska.       Idanu ya waro sosai tare da miƙewa ya koma saman kujera idonsa akan Zee. “Zee yaushe kika fara gulma a gidan nan? Mi kikaje ki ka ce?”.         Cikin shagwaɓa Zee tace, “Daddy bakaine ka cimun dambun nama ba da Saleeha, kuma Mamie tace indai kaci na faɗa mata”.        Sake waro idanun yay akan Raudha, “Ustazah wannan haɗin faɗan fa?”.       Fuska ta marairaice masa sosai, a hankali tace, “Dan ALLAH ka daure kabi dokan Doctor, yaushe ka gama shan wahala, sugar ɗinka a shekaran nan kullum sama yake ba ƙasaba Please Noorullah”.       Murmushi yayi yana kauda kansa. “Ko naci ko banci ba zan mutune Partner. Mizaisa naita azabtar da kaina wajen ƙin cin abinda nake so. Komai inabin dokarsa ai amma bazan iya ƙin cin nama ba gaskiya”.       Ido kawai ta tsura masa kamar zatai kuka. Dan ita kam batasan taya zata masa bayani ya dinga fahimtarta ba. Su Pa nada sugar amma da yake suna bin doka nasu bai tsanani ba. Shiko sam yaƙi daina cin nama, gashi baya masa cin sauƙi, inhar ya samu zai masa cin tuwo ne. Kuma in zaici safe rana dare bazai gaji ba. Ganin yaƙi yarda su haɗa ido ta ɗauke kanta tana duban Zee da tuni ta ajiye bowl ɗin naman ta koma tsalle-tsalle tare da su Saraki.        “Zee ina Saleeha?”. Kafin Zee ta bada amsa Jiddah ta amshe da faɗin, “Taje wajen Granny Mamie”.         Kowa a gidan yasan a gidan Saleeha ƴar ɗakin Maah ce, dan ita da Dawood (Abbati) ma basa kwana ko'ina sai can, hatta kayan sakawarsu kashi biyu bisa uku nacan. Itako ji take da su kamar mi. Abdull kuwa na gaban goshin Anne ne kowa ya sani.         Cikin ɗan sauke numfashi Raudha tace, “Okay Zee ki ɗauka bowl ɗin can na saman dining kuje har auta a kaima Granny, ai an kaima Anne nata ko?”.        “Eh Ya Abdull ya kai mata da zasuje islamiyya”. Cewar Jiddah.   Suna fita Raudha ta mike ta koma kusa da Ramadhan daya maida hankalinsa akan labarai da ake nunawa a tv. “Wai fushi kake dan nace ka daina cin nama?”.       Hararta yayi ya ɗauke kansa. Da sauri ta taro fuskarsa cikin hanunta ta hura masa iska ganin zai lumshe ido. “Noorullah Please ka fahimceni, rayuwarka nada muhimmanci a gareni da yaranmu dama duk jama'ar gidan nan. Ina fatan yanda su Bappi sukaga yaranmu muma muga yaran su Abdul haka a duniya. Please sweetheart i love you more”.        Murmushi ya sakar mata mai sanyi, shima ya tallafo muskar tata. Shanyayyun idanunsa ya zuba mata, “My Heartbeat kinyi ƙyau”.         Ƙaramar harara ta sakar masa ganin zai kautar da wancen zancen. Ta buɗe baki zatai magana ya manne lips nashi. Idanu ta lumshe a hankali kamar yanda shima ya lumshe nashi, ta san kuma ƙarshen maganar kenan dan haka yake mata a duk lokacin data ɗakko masa irinta. Sunyi matuƙar nisa a faranta ran juna sallamar su Abdull ya ziyarci kunnuwansu.       A hankali Raudha ta janye jikinta, shima janyewar yay ya kwanta jikin kujera yana mai lumshe idanunsa da shafa kansa. Sai da ta saisaita kanta ta basu izinin shigowa kamar yanda suka horesu. A nutse matasan samarin uku suka shigo cikin fararen kayan Uniform.          A nutse suka gaishe da iyayen nasu, Abdull ɗan shekaru goma sha ɗaya da hankalinsa ke kan Daddynsu ya kai zaune gefensa cikin damuwa. “Daddy baka da lafiya ne?”.        Murmushi Ramadhan ya saki, a hankali ya shafa kan Abdull yana ƙoƙarin saisaita kansa. Muryarsa a dasashe kamar wanda mura take son kamawa ya girgiza masa kai. “Lafiya lau nake My son. Kawai dai inajin barci ne?”.       Abdull yay ɗan murmushi, cikin nutsuwarsa kamar wani babba ya ce, “Oh Daddy babu ƙyau barcin la'asar fa”.         “Ai bazanyi ba My dear. Kuje ku canja kaya kuyi alwala ku jirani muje Mosque. A kira Auta ma yana sashen Granny”.        Yay maganar yana shafa kan Abbati da Alhaji ƙarami da suka lafe masa a jiki suma.      “Okay Daddynmu”. Abbati ya faɗa cikin ƙiriniyarsa dan kam shi dai babu sauƙine. Yanzun ma shirun nasa nada nasaba da dukansa da Raudha tayi kafin su wuce islamiyya saboda yayi faɗa da Alhaji ƙarami.            Suna fita Ramadhan ya dubi Raudha yana murmushi. “Kinsa Abbana duk yayi laushi kamar bashi ba”.      Murmushi tai itama tana ƙoƙarin miƙewa. “Daban masa hakaba da yanzu da gudu zai shigo mana kuma faɗan har islamiyya za'aje anayi dan nacinsa. Nikam dai idan ya biyo darun Abba (Mal. Dauda) wahala zaici”.      Dariya sosai Ramadhan yayi, tare da kamo hanunta ya maidata ya zaunar. Rungumeta yay cikin raɗa da sakar mata kisses a gefen wuya. “Muje daga ciki kiji wani labari”.      Cikin ɗan waro ido da ture kansa “Kai Ya Ramadhan sallafa kacema yara zaku”.       “Wayo na musu ai, dan bazan iya sallar nan a hakaba kuma da sauran lokaci ai”.           “Wai miyasa kakemin hakane? Duk sanda nai kwalliyata saika bata”. Tai maganar murya a narke cikin shagwaɓa.        “Tukuyci nake badawa ai, tunda dama ni akaimawa ko”.      Zatai magana ya sake rufe mata baki ya hanata. Babu yanda ta'iya dole ta amshesa hannu biyu. Daga ƙarshe suka shige bedroom.✍ Hummmm bari dai na tsaya daga nan kar bin ƙwaƙwƙwafin yay yawa kuma😜. *_ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAHI!! ALHAMDULILLAHI!!!_* _Godiya ta tabbata ga UBANGIJI daya bani dama da rai da lafiyar rubuta wannan ɗan littafi. Abinda na rubuta dai-dai ALLAH ya bamu ladan baki ɗaya. Wanda nai kuskure ALLAH ka yafemin ni da ku da kuka karanta._ *Kamar ko yaushe ina neman afuwan duk wanda na ɓatamawa a yayin rubuta wannan littafin. A yafemin, a yafemin, a yafemin. Nima duk wanda ya ɓatamin na yafe masa, sai dai banda wanda ya zalinceni akan ganganci ko son zuciyarsa. Shima inhar yazo ya roƙa gafarata ya sanarmin zan iya yafe masa da fatan zai kiyaye gaba. Zata iya yuwuwa wannan shine littafi na karshe da bilyn Abdull zata rubuta a duniyar rubutu😭🙏🏻 babu ruwan mutuwa dauka take a duk sanda taso. *_Bazamu gaji da godiya a garekuba masoyanmu, kun nuna mana halacci kamar yanda kuka saba. ALLAH ya saka muku da alkairi ya bar zuminci, alkairin ALLAH yakai gareku a duk duniyar da kuke. Zafafa biyar na muku son so irin trillions ɗin nan wlhy. ALLAH ya saka da alkairi musamman wanda ke tare da mu tun farkon zafafa har zuwa yau. Kai harma wanda suka fara binmu yanzu duka mun gode sosai🙏🏻_* _Kamar yanda na faɗa BAƘAR INUWA ƙirƙirarran labarine. Idan kaci karo da abinda yay kamanceceniya da rayuwarka kayi haƙuri bakai din ake nufi ba. Sannan bazan gaji da sanar da mai karatu cewar littafi nishadi ne, faɗakarwa ce, harma da ban haushi. Idan kaci karo da nishaɗi kayi badan dole saika samesa ba ko ka nema. Idan kaci karo da ilimi ka amfana gwargwadon fahimtarka. Idan abin haushine ka ɗauka adon labari ne. Rayuwar novel bawai babu ita a zahiri bane, sai dai ba lallai kowa ya sameta 100% kamar littafin ba, idan ma ka samu kasa a ranka akwai ƙaddara da jabawar da zata iya banbanta da hikayoyin marubuta_. *Abinda kaso gani baka gani na rubuta ba amin afuwa ajizancine irin na ɗan adam da mantuwa. Wanda yazo ba'a yanda kaso ba shima kayi haƙuri ba komai ake samu a yanda ake son gani ba. ALLAH ya sadamu da alkairinsa a zafafa karo na 7 da zasu zo muku nan kusa insha ALLAH😘😘😘😘🙏🏻👍🏻* *Mallakin Bilkisu Ibrahim musa (Bilyn Abdull)* *_Yi ƙoƙari ka biya na kuɗi ne, kar kuci hakkin daba naku ba_* *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_* *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 __________________ *_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_* Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F *ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼 +227 95 16 61 77 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *_BAƘAR INUWA...👇🏻_* Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*