𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣ *_UK (LONDON)_* ........Kwance yake rai-rai a madaidaicin gadon nasa da mutanen Nigeria ke kira da 6-by-6. Sai dai wannan yaji katifa mai shegen laushi da bedsheet fari tas shima mai laushin gaske da ko'a ido ka kalla zaka shaida hakan. Yanda yake ɗan furzar da numfashi sama-sama da huttai ga zufa da tai ma jikinsa jagab zai tabbatar maka da ga training ya fito. Dan wandone na jc ƙarami da ya tsaya masa a fin rabin cinya da rigarsa. Sai takalma da aka san ƴan ƙwallo da su a ƙafarsa. Jikinsa ne a saman gadon ƙafafun zube a ƙasa. Iska mai nauyi ya sake furzarwa tare da buɗe idanunsa da launinsu ke a surke. Sam babu fara'a a tare da shi, dan fuskar nan ɗam take fiye da yanda kowa ya sanshi da rashin walwala acan baya....           Cikin kuzari da ke nuna cikakkiyar lafiyar gangar jiki ya tashi zaune da ƙyau, ƙaramin tsaki ya ja tare da yamutse fuska ya fara saɓule takalman ƙafar tasa. Anan ya zubesu tare da miƙewa gaba ɗayansa ya kama rigar jikinsa ya cire cikin kamar yanayin jin haushi ya jefar da rigar ƙasa. Dogon glass ɗin da ya kasance kamar bango guda a haɗaɗɗen bedroom ɗin nasa ya nufa. Ya kai hannu ya danna wani ɗan maɓalli green. A hankali glass ɗin ya shiga raba kansa biyu har ya bada ƙofa. Shiga yay nan ma kamar a ɗan fusace, lafiyayyen toilet ne ya bayyana da ni kaina na zama baƙauya a kallo, kai tsaye ƙarƙashin shower ya nufa ya sakarma kansa ruwa yana mai jan wata nannauyar ajiyar zuciya...        *_Aliyu Mika'il Idris Mawashi_* kenan da ke amsa sunan _Smart Mawashi_ a duniyar ƙwallon ƙafa. Duk da dai kwata-kwata watanninsa uku kenan da dawowa ƙasar ta UK a London yay signing a club ɗin Queen City. Du da kasancewar ƙaramin club ne muna fatan ya zame masa wani tsanin kaiwa inda ba'ai zato ba. A yanzu Smart da muka sani na baya mai shiru-shiru da rashin sakewa da jama'a ya sake zarce hakan. Dan yanzu ba shiru-shiru ba, har miskilanci ma ya koyo. Hakan kuma ta faru ne a sakamakon faruwar shuɗaɗɗun abubuwan da suka faru a cikin watanni ukun nan da suka wuce. A gaɓar da tafi kowace gaɓa muhimmanci a tarihin rayuwarsa. A lokacin da ya gama shiryawa da tsarawa kansa gina rayuwa mai ban sha'awa da birgewa tare da matarsa. A lokacin da yay shirin ɗaukar dukkan yarda da amanar kansa data rayuwarsa domin damƙa mata. Sai labarin ya canja da ga yanda ya rubuta shi a zuciya zuwa rubutun ƙaddara.. Matarsa ta kufce masa a yayinda da burinsa na zama ɗaya da ga cikin ƴan ƙwallo a wata ƙasa ya cika. A hankali komai ya dinga dawo masa a zuciya dalla-dalla tamkar a yanzu ne yake faruwa. _(Bayan fitarsa gida a waccan ranar ya nufi gidansu cike da damuwar halin da ya jefa Lulu a ciki. Ya samu Asma'u taje aikan da Ammah tai mata gidan Aunty Bilkisu. Sai Maryam kawai da Ammah. Ko zaman kirki baiyi ba a daddafe suka gaisa da mahaifiyar tasa ya sanar mata yazo ɗaukar ɗaya daga cikin su Maryam ne dan Mawaddat babu lafiya. Hankalin Ammah ya tashi, ko neman Abba bata tsaya yi ba tace ya ɗauki Maryam suje idan Abban ya dawo zata sanar masa, dan ita a nata zaton ko ciki Lulun ta samu. Cikin sauri Maryam ta kimtsa tare da ɗibar kunun gyaɗar da sukayi domin tafiya da shi can su karya dan itama ko karyawar basu yi ba. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso kasancewar safiya ce babu yawan go slow a hanya. Sai dai me tun a yanayin da sukaga ƙofar falon a buɗe da littafin da ya gani ɗazu a saman gadon Lulu yashe a ƙofar shiga falon alamar an yarda bisa kuskure gabansa ya faɗi. Amma sai ya dake cikin ƙarfin hali suka shiga, a falo Maryam ta zauna shi kuma ya nufi bedroom ɗinsa yana faɗa mata taje ɗakin Lulun yana zuwa. Maryam ta amsa masa da to, yayinda shi kuma ya nufi ɗakin nasa. Bai wani jima ba sai gashi ya fito. Ɗan turus ya tsaya ganin Maryam kamar a ruɗe tana kai kawo. “K lafiya? Ba canai ki shigaba ina zuwa”. Da sauri Maryam ta juyo gareshi tana bashi amsa da “Yaya ai Auntyn bata nan ciki fa. Har toilet na leƙa babu kowa a ciki, hakama kitchen, sai dai duk an harmutsa wadrobe ɗinta an ɗiba kaya harma da akwati guda da aka bari kamar sauri ya hana a ɗauka”. Wani irin duka ƙirjinsa ya dinga yi, sai kuma ya nufi ɗakin da sauri shima. Kamar yanda Maryam ɗin ta sanar masa haka ya gani, sai dai shi nashi idon ya ƙara masa ganin duk wani abu mai amfani a ɗakin ma babu shi. Ƙafafunsa ne suka fara rawa, sai dai cikin dakewa ya cigaba da ƙarfafa kansa. Takardar da idonsa ya sauka kanta a bisa gado ya ƙarasa ya ɗauka. *_Na tsaneka Aliyu, bana son sake ganinka a rayuwata, amma kaje na barka da ALLAH azzalumi. Ashe wa'azin naka duk na yaudara ne kaima baka aiki da shi. Ka manta da ni har abada, dan ko'a hanya nai maka tazara irin ta sama da ƙasa, gabas da yamma. Idan ka wahal da kanka a nemana kai ka so, dan babu wanda ya isa sakani sake zama da kai koda Uncle Yousuf ne._* jiyay jiri na nan ɗibarsa yay saurin kaiwa zaune yana ambaton sunan ALLAH. Ya jima a wajen zaune kansa na yamutsa masa har Maryam ta gaji da jira ta shigo ɗakin. Hankalinta ya tashi da ganin yanda Yayan nasu ya birkice cikin ƙanƙanin lokaci. Kansa tai tana ƙwala masa kira amma sai ya ɗaga mata hannu da ƴar tsawa-tsawa yace ta fita ta bashi waje. Ta tsorata dan haka ta fita da sauri. Kamar an saita batafi minti ɗaya da fita falo cikin ɗaurewar kai ba sai ga kiran Ahmad ya shigo mata. Da sauri ta ɗaya ta kai kunneta. Ko gaisawar kirki bata tsaya sunyi ba ta shiga faɗa masa abinda ke faruwa. Gaban Ahmad ya shiga faɗuwa shima da ga can, cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi a gidan. Tambayar duniya Smart yaƙi cemasa komai har sai da ya nuna fusata sanan a taƙaice ya ce masa, “Tabar gidan”. Duk da abin ya daki zuciyar Ahmad ɗin. Sai ya shiga kwantar masa da hankali akan yana zuwa ya tabbatar bazata wuce gida ta tafi ba. Wayar Uncle Yousuf yay kira, da ƙyar ya samu ta shiga. Bayan ya gaishesa bai wani tsaya kwana-kwana ba ya sanar masa halin da ake ciki. Hakan ya ɗan ɗimauta Uncle Yousuf ɗin shima amma sai ya yanke kiran yace yana zuwa. Gidansa ya fara kira Aunty Saliha dake tsaye itama cikin tashin hankali ta ɗaga wayar da sauri. Dan dama nemansa take tun ɗazun ta gagara samunsa. Kafin ma yay mata tasa tambayar ita ta jeho masa abinda ke bakinta. “Abban Ra'is wlhy akwai matsala babba. Yanzu nan Khadijah tai kirana akan na shirya naje gidan Mawaddat babu lafiya na lallasheta da kwantar mata da hankali, banyi ƙasa a gwiwa ba nai shiri dan na shiga tashin hankalin bayanin Khadijahn. Sai dai muna kan hanya sai ga text massege ɗin ta ya shigo wai karmu nemeta, dan tayi nesa damu, na faɗa maka a kira Aliyu ya bata sakinta ta arziƙi inba haka ba zata sashi ya bada ta wuya. Duk da saƙon ya bani mamaki nacema driver yay sauri mu tafi gidan nata. lokacin da muke shiga street ɗin mun haɗu da wata baƙar mota mai tinted glass suka wuce muka wuce. Mun samu gidan buɗe da wani makwafcinsu tsaye a bakin gate ɗin, driver na ƙoƙarin shiga ya dakatar da mu cewar aiko baijin gidan nan da kowa. Dan yanzu yaga wata mata ta rirriƙo matar gidan tana kuka sun shiga mota sannan a loda akwatina a Hilux ma, shima ganin sun bar gidan buɗe ne ya sashi fahimtar babu lafiya, shine fa naketa nemanka ka kira Aliyu koka turo min Number sa amma na kasa smaunka”. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un” Uncle Yousuf ya shiga maimaitawa. Nan ɗin ma baice komai ba ya yanke kiran. Mommy ya kira, itama bai tsaya sun gaisa da ƙyau ba ya jeho mata tambayar ko Lulu taje gidan. Da mamaki tace bata zo ba gaskiya, kuma batajin zatazo ɗin, dan yau tanada Shari'a. Jin haka Uncle Yousuf ya ɗan samu nutsuwa ya yanke kiran. Ahmad yay kira yace su maza court dan tana can zai turo Aunty Saliha yanzu su riƙeta. Da sauri Ahmad ya miƙe, shima Smart sai ya miƙe. Har Maryam basu bariba suka kulle gidan. Sai dai me koda suka isa can ɗin ma babu Lulu, an kuma basu tabbacin bata zo ba. Sosai yanzu kuma hankalinsu ya fara tashi, dan kowa yasan duk rintsi fa Lulu akaran kanta bazatai sakaci da aikinta ba, musamman idan akai la'akari da yanda take matuƙar son al'amarin. Sai dai yanda aka ɗibi kaya yayin barinta gidan na hargitsa ma kowa lissafi. Gidan ƴan uwa da duk aka san zata iya nufa aka fara bubbuga waya, gidan Alhaji Garko ne farko, amma sai cikin tashin hankali Dada tace batazo ba, ba cikin Kano ba har wajen Kano amma dai amsa ɗaya ce Lulu fa bataje ba. Tun kowa na ɗaukar al'amarin wasa harya fara shan hankali, zuwa yamma dole aka shigar da report police station. ALLAH sarki Smart, yini guda baici komai ba sai ruwa, dolene a kallo ɗaya ya baka tausayi, sai da Coach ya tsaresa bayan sallar magrib yasha shayi, yana gamawa kuma sai amai, sai zazzaɓi mai zafi. Dole ranar Ahmad da Abdull na gidansu sai anan suka kwana, dan suma dai tuni sun san mike faruwa Ammah duk kawaicinta a ranar sai da ta taka gidan Smart da ga ita har Abbah. Umma kam wani shegen daɗi takeji, dan a ganin ta in har wani abu ya samu Lulu iyayenta sai sun ɗaure Smart na tsawon rayuwa.          Al'amarin kamar wasa tuni ƙaramar magana ta zama babba, dan kwana ɗai-ɗai har uku babu labarin Lulu Daddy da Uncle Yousuf tuni sun wancalakar da ayyukan gabansu sun dawo Nigeria. Hakama su twins duk suna Kano. Smart yay wata irin zabgewa, bawan ALLAHn ko murmushi baka gani a fuskarsa, ya duƙufa kawai gayama UBANGIJI, dama Abba ya kai islamiyya da masallatai a taya addu'a, hakama ƴan sanda nata faman kai kawo da bincike. A cikon kwana na biyar ne fa Addu'a bata faɗuwa ƙasa a banza sai ga binciken ƴan sanda ya fara maida akalarsa kan Dada, ba komai ya kawo hakan ba kuwa sai dalilin ganin sanda aka fita da Lulu da maƙwaftansu yayi, dan ƴan sanda basu barshi ya hutaba shima. Yana ganin Dada yace ma ƴan sanda “A'a to ai wannan Maman ce na gani da yarinyar a waccan ranar, tare da wani saurayi haka mai ɗan kammani da su”. A take kowa ya dubi Dada da duk ta daburce, sai kuma ta hau borin kunya. Ran kowa a wajen sai da ya ɓaci idan ka cire Alh. Sulaiman da Tajuddeen da suka san komai. Smart kam wani irin kallo yakema Dada kawai, ji yake yau da ace bata da alaƙa da Lulu wlhy duk da tsufanta sai ya koyama matarnan hankali, dan sai ta tabbatar da ainahin Aliyu Hydar. Daddy ma dai da duk ya zabge a tsaye harda ciwo akan ɓatan Lulun a wani irin rikice yake kallon Dada da Alh. Sulaiman a karo na farko, shikam dama ya zargi Alh. Sulaiman, sai dai Uncle Yousuf ya kwaɓesa akan hakan. ALLAH sarki Uncle Yousuf sarkin dattako, da ya fahimci faɗan na cikin gidane sai ya sallami ƴan sandan kawai, da ƙyar suka tafi dan sun ce dolene Dada ta fuskanci shari'a. To abinka da manyan mutane, a take akai kiran cp ya basu umarnin tafiya. Bayan wucewarsu ne fa gida ya hargitse, dan Dada tace bazata taɓa faɗar ina Lulu take ba sai Smart ya saketa. Karan farko da tun faruwar al'amarin ya saki wani shegen murmushi mai ƙona zuciya a baɗini mai kuma hasala abokin gaba a zahiri........✍️ _Alhamdullah barkanmu da sake dawowa a book 2. Yanda muka fara a Sa'a ALLAH yasa mu kammala da nasarori. Ina godiya da jirana da kukayi tare da fatan alkairi 😘😘👏._ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣ ........Iyayensa ya kalla cikin nutsuwar data ratsashi a yanzu najin tabbacin ina matar tasa yake, cike da girmamawa ya ce, “Abba ku tashi muje gida kawai”. Abba da tausayin ɗan nasa ya ƙara mamaye masa zuciya ya ce, “Aliy ba tafiya gida ne masalaha ba, ka bari dai a sasanta muji miye dalilin aikata hakan”. “Abba bata da wani dalili face na son zuciya. Ina son cigaba da ganin girmanta a matsayinta na uwa kamar yanda kuka tarbiyantar dani girmama kowace irin furfura, tun farko ma ita ya kamata na zarga, amma banyi hakan ba saboda shi zargi bashi da amfani. Sai dai amsa ɗaya zan bada a yanzu har gaban Abada *_BAZAN SAKI MAWADDAT BA_*. Sai dai ayi ɗayan biyu. Ko na MUTU tamun TAKABA, ko ni na mata wanka na sallaceta zuwa kabarinta. Wannan dalilan guda biyu ne kawai zasu iya raba wannan auren da izinin ALLAH!!”. Ba su Dada ba hatta Abbah da Ammah sai da Smart ya girgizasu, dan magana yake a dake, a fusace, a kuma kausashe, hatta da Ahmad dake a matsayin aboki zai iya rantsewa bai taɓa sanin Smart ɗin yanada irin wannan zafin ba. Harara Dada ta watsa masa da faɗin, “Oh burinka kenan dama ta mutu kaci gadon dukiya. Sheɗani to ALLAH ya fika, sakin Mawaddat kuwa idan bakai ta arziƙi ba zakayi ta wuya dan bazamu taɓa haɗa zuria da jinin tsiya jinin talauci ba. dama koda ka aureta ai asiri kai ma iyayen nata matsiyaci”. Murmushi Smart ya saki da taɓe bakinsa cikin halin ko'in kula da zancen Dada. Sai ma ƙoƙarin barin falon da yake yi batare da ya bata amsa ba . Alh. Sulaiman da ya kai maƙura a kan Smart ɗinne ya miƙe a fusace yana nunashi da yatsa. Sai dai kafin ma yace wani abu Smart ya nunashi shima cikin gargaɗi, “Kai! Karka kuskura shiga ramin da zai bizne rayuwarka ta har abada ya barka da gangar jiki kawai da idanun kallo. Sunanka ƙanin uwa ne ba uba ko ƙanin uba ba. Ni da kake gani na nan Sulaiman na fika fiye da abinda ka iya wlhy. Idan kace zaka saka ƙafar wasa da ni sai na gigita rayuwarka ta yanda kai a karan kanka bazaka taɓa morarta ba balle waninka. Magana ake ta mutane ba irinku riɓɓaɓu ba okay...” da ga haka Smart ya sa kai yay ficewarsa kafin ma Alh. Sulaiman da jikinsa ke rawar ɓacin rai dana firgita ya iya furta komai, da gaskiyar Lulu idanun Smart sun cancanci kowane irin suna, musamman a yau da ransa ke a ɓace dan Alh Sulaiman idanun Smart na ɗaya da ga cikin abinda ya razana shi. Fitar Smart ɗin ta saka falon zama tsit, yayinda Alh. Sulaiman ke nuna ƙofa cikin rawar baki data hannu. Daddy ya sauke wata irin gajiyayyar ajiyar zuciya a karo na farko, sai kawai yaji hawaye sun cika masa ido, dan tunda Smart ya fara magana yake kallonsa harya fice. Uncle Yousuf ne ya tashi yabi bayan Smart, haka ma Ammah da Abbah. A gate suka sami Smart yana waya da Coach, dan a gobe ya kamata ya wuce dama, sai dai da yayi aniyar haƙura dan bazai iya tafiya wata ƙasa batare da anga Lulu ba. Amma a yanzu ya gama yanke shawarar wucewa babu fashi. Uncle Yousuf da ke kallonsa da murmushi yay masa nuni ya shiga mota inda Abba da Ammah suke, bai musa ba ya shiga. Har gida Uncle Yousuf ya kaisu, inda ya samu zama na musamman da Abba da Ammah. Shi ya lallashesu akan su kwantar da hankalinsu dan ALLAH a zubama su Dada ido aga gudun ruwansu, dan ya tabbatar sun aikata haka ne dan Alhaji Garko baya nan. Sosai Abbah ya gamsu da bayanin Uncle Yousuf ɗari bisa ɗari tare da ganin shawarar itace dai-dai. Bayan wucewar Uncle Yousuf Abba da Ammah suka sake zaunar da Smart sukai masa nasihar ya cigaba da shirinsa na tafiya kawai kamar yanda Uncle Yousuf ya faɗa da masa faɗan abinda yay ma Alh. Sulaiman da Dada. Haƙuri ya basu da alƙawarin bazai sake ba. Wannan shine sanadin tattara al'amarin Lulu ya haɗa kayansa a washe gari shi da Uncle Yousuf da Coach suka nufo ƙasar UK a London. Inda yay signing da wani ƙaramin team Queen City. Su Uncle Yousuf sun sake masa nasiha akan ya kwantar da hankalinsa kan al'amarin da kanta zata bijirema su Dada. Shi dai cikin dauriya da dakiya yake amsa musu da to kawai. Amma a cikin ransa shi kaɗai yasan irin ƙunar da yake ji da matuƙar kewar matarsa. Sai dai ƴan mazan sun ɗauki aniyar da jarumtar a wannan karon na sai ya tabbatar ma family ɗin Lulu gaba ɗaya da ita kanta shi ɗan halak ne, sannan talauci ba hauka bane ba. Duk da dai yanayin yaso taɓa shi da son maidashi sanyi-sanyi a watanni ukun daya samu kansa, sannan sam yanzu baka ganin fara'a a fuskar Smart, ya sake zama shiru-shiru a yanzu ma harda miskilanci zamu iya cewa ya ƙaro. Dan bai shiga sabgar kowa, abinda ya kawosa kawai yake yi sai bautar ALLAH. Baya zuwa ko ina da ga gida sai idan yana buƙatar sayen wani abu ya ɗan fita ya sayo ya dawo sai wajen training ɗinsu. Burinsa shine ya manta da komai kamar yanda Uncle Yousuf a koda yaushe ke bashi shawara, dan har yanzu Dada taƙi faɗin inda ta kai Lulu. Duk da yanda aka so yin ɓatacciya tsakanin Daddy da Alh. Sulaiman, dan Daddy yana ragama Dada kodan darajar sunan uwa, amma tunda ya fahimci da haɗin bakin Alh. Sulaiman akai komai sai hankalinsa yay masifar tashi, yasa a nemo masa Smart, Uncle Yousuf da ke nuna shi al'amarin bai damesa ba a zahirin dan yana son Daddy ya maganantu a wannan karon yace masa ai baya ƙasar. Zancen ya girgiza Daddy duk da bai san ina Smart ɗin yaje ba ko abinda ya tafi yi. Da ga baya ma sai Dada ta tattara ta bar ƙasar itama zuwa jiyyar mijinta....) Wannan shine abinda ya faru kafin tahowar Smart England. Ɗaure da guntun towel ya fito a ƙugu, sai ƙarami yana tsane jikinsa da sumarsa da ya jiƙe da ruwa. Mai ya shafa sama-sama tare da shiryawa ciki ƙaramin wando da riga armless. Gadon nasa ya sake hayewa yay kwanciyarsa dan barci yake ji sosai. Sai dai kafin barcin ya ɗaukesa tunani ya jasa tsahon lokaci.... Wannan kenan. ____________________★ *_CANADA_* Amai take sosai cikin galabaita da fitar hayyaci, a kallo ɗaya zaka fahimci yanda duk jikinta ya saki sai huttai take da ƙyar. Cikin tausayawa mai aikin da suka taho tare tun daga Nigeria ta ke jera mata sannu. Bayan ta gama aman ruwa ta sakarma kanta daga inda take zaune tana hawaye. Haka take tun can da ma bata da juriyar ciwo, a yanzu kuma da take jin ciwon tamkar ya bambanta da duk wanda ta sabayi ne ke sake galabaitar da ita da raunana mata zuciya, har tana jin anya bazata bijirema kakar tata ba ta bayyana kanta kota koma gida Nigeria. Tsahon watanni uku kenan da barowarta gida Nigeria bisa taimakon kakarta Dada. _(Dan a waccan ranar bayan fitar Smart da ga gidan ta fito toilet da taje yin fitsari, duk da tai masa kurarin barin gidan ba'a ranar tai niyyar hakan ba, sannan batai niyyar sanarma wani nata abinda yay matan ba kamar yanda aunty Khadijah ta bata shawara. Saman gado ta koma ta ɗauki book nata da take adana muhimman sirrikanta ta fara rubutu tana hawaye, bata kai ƙarshe ba ya cika dan haka ta buɗe sabo ta cigaba. Tana tsaka da rubutun ne taji sallamar Dada a bazata, kafin ma ta farga har ta shigo bedroom ɗin nata kai tsaye. Hawayen da Dada ta gani a fuskarta ya sata nuna tashin hankali da fara jera mata tambaya, sai taji zuciyarta ta ƙara karaya ta sakarma Dadan kuka kawai. Komai Dada bata tsaya tambayarta ba ta hau haɗa mata kaya, bayan ta kammala drivern da ya kawota ya shigo har ciki ya dinga kwasar kayan, yana kammalawa ita kuma ta ce Lulu ta tashi suje, da farko Lulu taso tirjewa akan ta bari Aliyu ya dawo, amma Dada ta balbale ta da masifa. Dole badan taso ba tabi umarninta ta sako. Sai dai tanayin taku biyu uku Dada ta rabga uban salati da antayo ashariya mai kawuna bakwai ta dire. Balbale Lulu tai da masifa irin wadda bata taɓa mata ba, tare da tambayoyi masu tsaurin gaske da suka saka Lulun ɗan jin nauyi harta gagara cewa komai. Sai da taga ta takura mata tace faɗuwa tayi. Hakan ya ƙara harzuƙa Dada ta fisgeta suka fita, sai dai zafin da take ɗan ji ya sata tirjewa dole Dada ta kamata suka fita cikin lallaɓawa. Anan ne makwafcinsu ya gansu, sai dai ita Lulu bama tasan maƙwafcin nasu bane ba. Lulu ta roƙi Dada suje Court akan case ɗin yarinyar nan da take so a ƙarƙare a yau, inda suka samu alƙali suka juye masa kuɗaɗe akan ya cigaba da riƙe mata mutumin a gidan yari zata bar ƙasar dan bata da lafiya. Da ga court hanyar airport suka ɗauka, suna isa basufi minti arba'in da biyar ba jirgin zuwa Abuja ya shirya tashi, dama Dada tasa a tanada mata ticket tun barowarsu gida. Ita kaɗai ta wuce Abuja Dada ta koma gida. Maimakon gidan Uncle ɗinta Khamil wata mata ce tazo ta tareta, tasan matar tare da Dada da daɗewa, suna kiranta Hajiya Shuwa. A ranar gaba ɗaya ta yini kwance ne da zazzaɓi a gidan Hajiya Shuwa, hakama washe gari dai duk gata nan ne dai babu isashen lafiya tare da ita. A kwana na uku Dada tai kiranta a waya ta tsara mata zance cewar ai Aliyu na nan nata zaginta da cewar wai ta tafi yawon banza ne, dan haka sun saka ƴan sanda sun kamashi a yanzu haka ma kotu zasu kaisa ya bata takardar sakinta. Ran Lulu ya ɓaci matuƙa dajin wai Smart na zaginta har da dangantata da karuwa, dan haka tacema Dada tana son ƴan sandan nan su ƙara wajiga rayuwasa kuma ya saketa. Kwana biyu bayannan da ke zama biyar da barowarta Dada ta kirata nan ma ta sanar mata Aliyu wai ya saketa. Duk da abinda take fata ke nan sai taji wani iri, daga ƙarshe ma ranar yini tai babu lafiya zuciyarta a cunkushe. A ranar ta sanarma Dada tana so tabar Nigeria zuwa America, amma sai Dadan ta bata shawarar taje gidanta na Canada tunda babu wanda yasan da shi, dan Uncle Yousuf yay ikirarin ɗaukarta da kansa ya maida gidan Aliyu ko tana suma tana mutuwa ne. Ran Lulu ya sake ɓaci, ta kuma sake jin ƙwarin gwiwar nisantar ahalinta baki ɗaya. Wannan shine dalilin tahowarta Canada tare da mai aikin da aka haɗota da ita mai suna Ummita. Sai dai tunda sukazo zuciyarta taƙi nutsuwa waje ɗaya, abubuwa da yawa tsakaninta da Smart a ɗan zamansu sun zame mata barazana a barci da ido biyu, wannan ya sata sake buɗe babin shaye-shayen ta sosai-sosai. Ko abinci bai dameta ba da ga shaye-shaye sai barci. A kwanakin da bazasu wuce sati biyun nan ba ne abubuwa suka fara canjawa, idan tasha kayan shaye-shayen ta tana kammalawa zatai amansu, tun tana ɗaukar al'amarin wasa har takai bata son warin kowane irin ƙwayar magani, amma cikin ƙarfin hali take daurewa ta sake gwada sha, ta kuma sake aman nasu. Wannan dalilin ya sata ɗaga ƙafa kwana biyu, sai kuma hankalinta ya fara dawowa jikinta har salla da lokaci yayi kamar wadda aka zabura sai ta tashi tayi. Kwana uku da suka wuce kuma sai zazzaɓi ciwon kai da kasala, ga yawan mafarkin Aliyu kamar wani magic a gareta. Sai duk randa tai mafarkin nashi takan tashi da ɓacin rai har taji buƙatar shan kayanta ko zata manta da shi. Sai kuma dai ta daure taƙi sha dan ko tunawa tai da su sai taji amai. Yau kuwa wayar gari tai cikin wata irin damuwa da kewar wani abu data kasa canka a ranta, sai zuciyarta daketa faman ƙuntata, cikin son kauda yanayin ne ta samu ƙwaya tasha amma ta rantse bata zama a cikinta shine take amayar da ita a yanzu).........✍️ Wannan kenan. 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣ .......Dole da taimakon Ummita mai aikin nata ta gyara jikinta ta kamota ta fito da ita bedroom. Cikin wando dogo da sweater ta shirya tare da Safa mai kauri sosai, ta haye gadon cikin rawar ɗari taja bargo har saman kanta. Tare da bama Ummita umarnin ƙara mata gudun room hitter ɗin ɗakin. Dan wani irin rawar sanyi take har haƙoranta na haɗuwa waje guda. Ga hawaye sun gagara tsayawa (yau fa an taɓo manyan mata🤣🙏). Yanayin da Lulu ke ciki ya tada hankalin Ummita, number da suke waya da Dada jefi-jefi ta lalubo ta kira, kamar baza'a ɗagaba ma sai kuma aka ɗaga, cikin ladabi Ummita tai sallama da gaida Dada, daga can ta amsa a gadarance da tambayar ina Lulu. Cike da damuwa Ummita ta sanar mata gata kwance babu lafiya, dama kusan kwanakin nan haka take ganinta sama-sama, sai dai rashin tabbatarwa yasa bata faɗa mata ba sai yau. Rai a ɓace Dada ta shiga zagin Ummita ɗin, duk ta rikice dan tana bala'in son Lulu, zamu iya cewa soyayyar mahaifiyarta ce ta dawo kanta. Ita dai Ummita haƙuri kawai take bama Dada kawai. Dan ta tabbatar masifar tsohuwar original ce. Ba'a rufa mintina goma da katse wayar Dada ba alerm ɗin gidan ya kaɗa, miƙewa Ummita da ke falo tai ta nufi ƙofar, bata buɗe ba kai tsaye ba, ta danna numbers dake jikin ƴar computer ɗin kusa da ƙofar dake manne a bango dan ganin wanene. Baturiyar mace ce tsaye, cikin nuna alamar tana ganin Ummitan da ga wajen itama ta ce, “Hy” cikin ɗaga hannu. Amsa mata Ummita tai itama da “Hy” ɗin. Cikin murmushi matar ta cigaba da magana cikin harshen nasara. “Sunana Doctor Olivia, Nazo nan ne bisa umarnin Mrs Garko”. Yanda ta kira kalmar Garko ɗin taso bama Ummita dariya, amma ta dake da ƙyar sai murmushi da tai mata tare da ɓuɗe ƙofar. Sun sake gaisawa da Dr Olivia, Sannan tai mata rakkiya ɗakin da Lulu ke kwance. Ganin yanda jikin Lulu yay zafi sosai yasa Dr Olivia cewa dole suje asibiti, a take tai kiran ambulance cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gasu. Lulu na rawar sanyi da faɗin su barta ita bazataje ko ina ba su Dr Olivia suka ɗauketa a ambulance ɗin tare da Ummita suka wuce. Suna zuwa babu ɓata lokaci aka shiga da Lulu ciki tare da rufuwa bata gudunmawar gaggawa. *_UK_* Hankalin Dada da ke jiyyar mijinta ya tashi sosai, amma tanata ƙoƙarin dakewa dan kar Alhaji Garko da ya fara samun sauƙin jikinsa Alhmdllh ya fahimta tare da sauran yaransu da sukan zo dubashi. Idan wannan tawaga ta wuce sai wata kuma tazo, abinka da masu hannu da shuni, kallon fita ƙasar ake kamar barin Kano a shiga Katsina ne. Alhaji Garko da bai san halin da ake ciki ba har yanzu dan babu wanda ya sanar masa saboda halin da yake ciki ya zubama matar tasa ido cikin tausayawa, dan shi ya fassara yanayin nata ne da gajiyawa musamman da yake akwai tsufa. Cike da kulawa ya ce, “Hajarah kina buƙatar hutu, ya kamata kije gida haka nan tunda jikina da sauƙi nima, har ma muna sa ran sallama nan da ƙarshen watannan”. “Haba dai Alhaji ya hankalina zai kwanta kana nan ina can, duk da dai jikinka Alhmdllh amma har yanzu kana buƙatar kulawa. Danni ko sallamarka sukayi bana son ka koma gida Nigeria yanzu har sai ka sake hutawa anan magana ta gaskiya.” Murmushi yay irin nasu na manya da faɗin, “Hajarah rigima kenan. Yanzu ni da abubuwa ke jirana tari-tari tunda ALLAH yasa da sauran kwanana a gaba mizai sa na kuma sake sabon zama anan ai gara na koma gida ko?”. “Humm Alhaji wlhy wannan gaskiya ce ba rigima ba. Gara dai ka sake hutawa dan muna komawa can hayaniya ma ta isheka musamman ta ƴan siyasar nan da ba gajiya suke ba. Dan haka dan ALLAH ka yarda kawai sai ka sake hutawa, nima yanzu inaga maimakon tafiya Nigeria bari na ɗan je Canada na huta na kwana biyu kafin a sallamekan ko.” Ɗan jimm yay na alamar tunani, sai kuma cikin nuna fahimta ya ce, “Shike nan idan hakan kike so uwar garke na. Yanzu yaushe zaki wuce Canadan?”. “Eh to ko zuwa yamma haka tunda ga su Khamil da iyalansa nan sun iso ko, auta ma yace min zai baro Saudiyya shi da matarsa gobe in sha ALLAH. Kaga dai ai ka sake samun masu kulawa”. Murmushi yay mata cikin nuna gamsuwa. Dan Dada kam a wajen bama miji kulawa jaruma ce, tsaye take kan abinta ta kankane ko ina tunda ƙuruciya har girma babu wata mace data taɓa raɓar mata miji da sunan kishi. Wannan tsananin kishin nata yasa hatta matan ƴaƴanta take jin kishinsu akan ƴaƴan nata da suma take matuƙar so da ƙauna tamkar ubansu. Babu ɓata lokaci ta hau shirin wucewa Canada, dan ji take kamar ta rufe ido ta isa taga hanlin da ƴar jikarta take a ciki, saboda a nata bahagon tunani babu abinda zuciyarta ke raya mata sai kodai Smart, ko Uncle Yousuf wani ya sakema Mawaddat asiri ne. Dai-dai lokacin da Lulu ke cika awanni goma sha ɗaya a asibitin su Dr Olivia Dada ke isowa ƙasar ta Canada. Tunda ƙuruciya an riga da an san lungu da saƙo na ko'ina, dan a duk ƙasar da suke yawan zama suna da gidansu na kansu musamman manyan ƙasashen nan masu ji da kansu irinsu England, America, France Chaina, Saudiyya, Dubai, dan da gasken gaske wannan family sunada dukiya, bayan wadda mahaifinsu ya gada a wajen nasa mahaifin ya kuma tara nasa na kansa, su kansu yaran kowanne ba ƙyalan bane wajen kuɗin, dan babu wanda ke zaune kaf ɗinsu a neman na kansu suke. Ko marigayiya Mawaddat mahaifiyar Lulu data kasance mace ɗaya tilo a cikinsu sanda tana raye tsaye take akan neman na kanta saboda haka aka gina musu rayuwa, duk da yana da dukiya kuma ya gada ne shima a wajen mahaifinsa bai yarda yaransa su zama cima zaune ba, suna ayyuka a cikin gwamnatin ƙasarsu da na wasu ƙasashe, suna kuma Business ƴaƴa da iyaye har ma da jikoki. Cab ta ɗauka tun daga airport zuwa asibiti kai tsaye, dan a ƙage take da son ganin halin da jikar tata ke ciki. Wadda har yanzu ana kan tafka rigima akan ɓoyetan da tai dan bayan ita sai Alh. Sulaiman kawai suka san ina Lulun take. Hatta da Tajuddeen sunƙi sanar masa. Ita Dada zuciyarta ɗaya ce game da ɓoye Mawaddat dan kawai ta rabata da Smart ne matsayinsa na talaka jikanta Tajuddeen ya samu. Yayinda shi Alh. Sulaiman ba haka kawai bane a tashi zuciyar, dan a yanzu haka bai fara aiwatar da plan ɗinsa bane akan Lulun sakamakon rasa inda Smart yake da yay shi kuma. Dan tun washe garin da Smart ya baro 9ja yasa malami binciko masa shi amma ƙasa ko sama babu labarinsa. Amsa ɗaya suke samu a bincikensu shine ya ɓoye kansa dan kar ya saki Lulu. Duk da dai suna zargi Uncle Yousuf ne ya ɓoyesa amma a ɗan tsukunnan sun ƙara tsananta bincike kasancewar har yanzu basu sami wani point ba akan hakan. Dan shi Uncle Yousuf ɗin ma ya sake baro Nigeria ɗin zuwa harkokinsa da ya bari bayan yayma Daddy tas da tabbatar masa da cewar ya zare hannunsa akan al'amarin Lulu, dan ya fahimci goyon bayan da Daddyn ke batane a baya ya bata lasisin biyema Dada tabar gidan aurenta. Saboda ya tabbar da babu haɗin kan Lulu Dada bazata taɓa iya ɗauketa a gidan aurenta ba harta ɓoyeta gashi ana neman wata uku kamar wasa. *_NIGERIA_* Sosai Daddy yana cikin wani hali na azabtuwar zuciya game da abubuwa da yawa. Na farko shine ɗan uwansa dake fushi da shi. Ƙaunar da yakema Yousuf a zuciyarsa daban ce a wannan duniyar, dan zai iya rantsuwa ko ƴaƴansa baya musu irin wannan ƙaunar har Lulun da ake kallo ya fifita. Na biyu rashin sanin inda Lulu take har yanzu, tun yana ɗaukar al'amarin wasa Dada zata dawo da ita bayan wasu kwanaki har lamarin ya fara bashi tsoro. Lokacin da yaje UK duba Baba Garko har roƙonta yay akan tayi haƙuri Lulu ta koma gida koda bazata koma gidan mijin ba, dan tabar aikinta da mutane ke matuƙar buƙatarta. Amma sai Dada ta murje idanu tai masa tas dole yaja bakinsa yay shiru dan yana ɗaga mata ƙafa kodan darajar sunan uwa da take amsawa. Sannan fa Daddy dama can Uncle Yousuf ya fishi zafi, shi dai barsa da zuciyar tsiya kamar ɗan kuturu. Abu na uku wani salon rainin wayo da Alh. Sulaiman ya ɗan fara kawo masa da nuna shi yanzu a shirye yake da shi akan komai, sai zuciyarsa ta fara bashi anya kuwa bada haɗin kan Alh. Sulaiman ɗin Dada ta ɗauke Lulu ba kamar yanda yay zargi tun farko. Idan ko haka ne to tabbas a wannan karon ya shirya duk wacce ma za'ai ayi shima. Wannan tunanin ne ya zaburar da shi yau daga gida daya fito yace driver ya wuce da shi office ɗin Alh. Sulaiman Sufi Garko. Sanda suka iso ma shi bai kai ga isowar ba, dan haka sukai zaman jiransa. Baifi mintina bakwai ba a tsakani sai gashi shima. Sai da ya shiga da kusan mintina huɗu drivern Daddy ya shiga ya nema musu iso. Alh. Sulaiman da tun shigowar Daddy cikin Companyn aka sanar masa, yana shigowa kuma ya shaida motarsa yay wata dariyar mugunta da bama sakatariyarsa umarnin shigo da shi. Tunda Daddy ya shigo Alh. Sulaiman da yay wata kishingiɗar iskanci a kujera yana jujjuya kansa ya saki murmushi mai ma'anoni da yawa. Yi Daddy yay kamar bai gansa ba, sai ma ya kai zaune duk da ba'a bashi damar hakan ba. “Ina fatan kana lafiya?”. Daddy ya faɗa a takaice. A gatsine Alh. Sulaiman ya amsa masa da “A office ka sameni ai ba'a gadon asibiti ba”. “Kuma haka” cewar Daddy a gatsine shima. Batare da ya jira cewar Alh. Sulaiman ɗin ba ya cigaba da faɗin, “Sulaiman ina kuka kai min yarinyata?”. “Ka shirya ganinta yanzu kenan?”. Idanu Daddy ya tsurama Alh. Sulaiman cikin ɓacin rai, sai dai kafin yace wani abu Alh. Sulaiman ɗin ya ƙyalƙyale da wata dariyar mugunta yana miƙewa tsaye. Takowa yay inda Daddy yake ya ja kujerar dake kallon wadda yake zaune shima ya zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya. Fuska ya tsuke ya zubama Daddy dake kallonsa cike da tsana idanunsa shima. “Isma'il Ibrahim Jiƙamshi! A da kana ɗaukar duk zantukana matsayin kurari ko? Kana tunanin bazan iya illata rayuwar Mawaddat ba dan kawai tana ɗiyar ƙanwata?. To kayi kuskuren sanin waye ni, dan zamanka da ni na tsawon shekaru bakwai bai maka amfanin komai ba kuwa. Bari kaji wlhy wlhy da ace na san da wannan sirrin a hannun Mawaddat ƙanwata kafin mutuwarta, ni da hannuna zan kasheta bayan na amsa, sai ALLAH ya taimaketa ta mutu a karan kanta kafin na sani ɗin, amma duk da haka bata tsiraba ta barma ƴarta gadon laifinta. Dan haka Isma'il ina maka gargaɗi na ƙarshe, ka bani camara ɗin nan, ka kuma saka a ranka baka taɓa sanina ba har abada, in ba hakaba, a wannan karon saina wargaza rayuwar kaf family ɗinka bata Mawaddat kawai ba. Dan haka zaɓi ya rage naka....” Murmushi Daddy yay mai ma'anoni da yawa duk da yasan duk abinda Alh. Sulaiman ɗin ya faɗa zai aikata fiye da hakan. Amma cikin nuna halin ko in kula idonsa akansa kyam ya ce, “Sulaiman kenan. Ka manta ni Isma'il ɗin wanene nima. Sannan banda haukarka a tunaninka baka camara na nufin gogewar abinda ka tafka da in kaf family naka sukaji sai sun maka tsanar da sai ka gwammaci mutuwa da rayuwa. To idan ka manta bari na tuna maka, bayan abinda Mawaddat ta ɗauka nima ai nasan komai, ko toshewar basirar taka takai ka manta cewar komai na sani tunda da bakinka ka kirani ka sanarmin abinda kayi kuma na gani da idona, hasalima tare dani ka ɗauki yarinyar ka kai ƙasan gotter ka jefar. ai ba abinda Mawaddat ta ɗauka bane kawai hujjar. Sannan na biyu Sulaiman kada ka manta a tafin hannuna kuke kai da su Alh. Baita, idan yanzu na sanarma duniya su waye ku a ƙasar nan wlhy wlhy ba dukiya ko matsayi ba sai anyi faca-faca da namanku da taimakon mahaifinka dan kafi kowa sanin irin tsanar da yay ma abinda kuke aikatawar. Ai dama na sanar maka tun a waccan ranar, sai na ɗan ɗana ma zuciyarka rayuwa cikin fargaba da zullumi fiye da yanda ƙanwarka ta ɗanɗana min a tsahon shekara ɗaya dana rayu da ita.....” “Nima ai na tabbatar maka sai dai mu rayu a tare cikin zullumin da fargabar ko ka manta”. Alh. Sulaiman ya faɗa a zafafe cikin katse Daddy. Sai kuma ya ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Isma'il kenan a tunaninka kaima ban san a yanda ka rayun bane, ko cakake ban san kaima kana rayuwa bane cikin irin yanda kake tunanin ka sani a tsahon waɗan nan shekarun. Ka gaya min inba tsoro ba miyyasa ka ɗauke ƴarka daga Nigeria da ga randa na tabbatar maka saina hukunta rayuwarta bisa laifin mahaifiyarta? Miyasa kaketa kaffa-kaffa da ita fiye da sauran ƴaƴanka?. Amsar itace Tsoro ne! Kana jin tsorona Isma'il!! Hhhhh tabbas wannan tsorone!!”. Da ƙarfi Daddy ya buga decks tare da miƙewa a zafafe.........✍️ Tofa fagen na manya ne yau🚴🚴🚴 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣ .......“Kai ɗin banza da zanji tsoronka Sulaiman. Ka sannni kaima ai, ni na wuce maka kanwar lasa, sannan ni ƙadangaren bakin tulune a rayuwarka data abokanka ta yanda kuka rasa yanda zakuyi dani. Ƙarshen target ɗinku shine ku kasheni dai, kuma na tabbatar muku a randa kuka kasheni wlhy ko minti ɗaya bazan cika ba da ɗaukewar numfashi kuma duniya zatai muku zafin da sai kun gwammace mutuwa kamar ni, dan sai mutanen duniyar sun san suwaye ku. Idan ba tsoro kuke ji ba miyya hanaku aikatawar a tsahon shekarun nan. Miyasa kuka kasa bayan kunada kowacce irin dama? Miyasa baku aikata bane sulaiman? Ku kashenin mana? Maza ku kashenin idan kun cika ku tsagerane dan ALLAH!!”.       Matuƙar razana Alh. Sulaiman yayi da kalaman Daddy, cikin ɓacin rai da zafafuwar zuciya ya nunashi da yatsa lips ɗinsa na rawa. “Haka kace ko?”.           “Haka nace Sulaiman, idan kuma bakaji ba na sake maimaita maka. Kuma wlhy na baka daga nan zuwa ƙanƙanin lokaci ɗiyata ta dawo gareni inba hakaba sai na sakaka nadama irin wadda sai ka gammaci mutuwa da rayuwa. Dan duk inda kasa ƙafa ka sani ni Isma'il ƙaddararka biye nake da kai. Plan ɗinku na gaba shine sakama Yousuf cocaine a kaya yayinda da zai baro ƙasar Chaina zuwa Nigeria. Bance ku fasaba dan ALLAH, amma ku sani wannan shine mabuɗin farko na kiran mutuwarku. Ni Isma'il kallon kitse kukema rogo kawai, dan ko poisining ɗin Baba da kukayi na barku ne kawai bisa wani dalilina na tarkon dana ɗanama rayuwarku. FURAR DANƘO NAKE, A SHEKARA ANA DAMU BANI FARAU-FARAU. Mawaddat kuwa bazan sake cemaka ina take ba, in dai har ita ɗin jinina ce da kanta zata maido kanta gida bisa bigiren bijire muku. Ku muje zuwa wasan a yanzu na shirya masa....”           Har Daddy yabar office ɗin Alh. Sulaiman da yay sumar tsaye bai iya dawowa a hayyacinsa ba. Sai da Daddyn yay banging ƙofar ne ya zabura wata zufa na feso masa a illahirin jikinsa. Bai ma san sanda ya since hular kansa ya hau fifita da ita ba jikinsa ma wata irin rawar shiga ruɗani da tashin hankali. Ji yake kamar mafarki yakeyi, shin Isma'il da ya sani ne haka wai shin ko canja shi ankayina? wagga al'amari haka kamar a mahwalki. Shiy yasan Isma'il nada zuciya kam tabbas batun yanzu ba, amma bai taɓa tabbatar da zai iya wani yunƙuri ba bayan kafiyar daya sanshi da ita kawai musamman da yaga tunda suka fara ƴar tsamar nan Daddyn nayi tamkar yana shakkarsa a koda yaushe, lallai ya yarda bakatsinan mutum abin tsorone yau. Da ƙarfi ya hankaɗa kayan saman table ɗin nasa da nuna ƙofa a kausashe ya furta “Isma'il You really are playing with fire!!!....”        (😂Daddy ni kaina ka shayar dani mamaki, ashe jinin katsinawan dai na aiki a jininka)                          *_CANADA_*        Sosai hankalin Dada ya sake tashi ganin yanda Lulun tai wani masifar ɗashewa ta ƙara haske sosai, ga komai nata ya ciko musamman ƙirjinta. Dan ma zazzaɓin daya tasota gaba ya ɗan saka jikin nata girgiza ƙasa kaɗan kwana biyun nan. Tambaya bayan tambaya Dada ta shiga jeroma Dr Olivia akan mike damun jikar tata haka. Kai tsaye Dr Olivia ta sanar mata Lulu na ɗauke da ciki wata uku da kwanaki biyu. Tamkar an fasa irin ƙaton dutsen nan mai girgiza yanki da gidajen wajen gaba ɗaya haka maganar Dr Olivia taima Dada saukar aradu a tsakkiyar ka. Cikin razani da zabura ta maimaita kalmar “Ciki!”  ɗin zuciyarta na bugawa. Dr Olivia ta sake tabbatar mata da hakane. Wata muguwar ashariya Dada ta lailayo ta dire akan Smart. Tare da faɗin, “ALLAH ya tsinema wannan shegen yaro dangin talauci dangin jaraba. Yanzu nan sai da dai ya ɗirka mata ciki. Amma Mawaddat kema ƴar banzar yarinya ce. Randa na ɗakkoki da ga gidan yaron nan har tambaya naita jera miki akan yanayin dana ganki amma kikace min faɗuwa kikayi ashe-ashe miƙa masa jiki kikai ya lalube”. Sai ga hawaye suna cika idon tsohuwar nan dan ɗaurama kai masifa. Kasancewar da Hausa Dada tai maganar duk sai hankalin Dr Olivia ya tashi ta shiga tambayarta ko lafiya. Rai ɓace Dada tace mata ba komai tana zuwa. Cikin rawar jiki ta fito tana neman lambar Alh. Sulaiman ɗanta...         *_LONDON_*        Iya ƙoƙari yana yi wajen ganin ya ajiye matsalolinsa gefe ya fuskanci rayuwarsa ta yanzu da cigaban da ya riskeshi. Sai dai hakan ya gagara matuƙa duk da akoda yaushe yay waya da Ammah ko Abbah ko Uncle Yousuf da Coach shawara suke bashi akan ya dai ƙara daurewa. Ammah kan masa nasiha mai ratsa jiki da tabbatar masa in sha ALLAH komai zai zama labari, kuma in har Mawaddat matar da zai rayu da itace duk abinda za'ai sai ta dawo garesa. Wannan ƙwarin gwiwar da mahaifiyarsa ke bashi kan ƙara ƙarfafa masa gwiwa. Sai dai hakan bai hanashi kasancewa cikin mafarkin Lulu ba a duk sanda zai kai kwance da sunan barci. Al'amarin ma har yana neman zame masa jiki akoda yaushe a koda yaushe cikin wanka yake. Ya kasa manta dare mafi daraja da muhimmanci da ya zama wani babban jigo a cikin zamansu na kwanaki ashirin da shidda. Tunashi kansa yay murmushi ko ƙaramar dariya harma da tausayawa. Duk da ashi kansa yasan darene da bazai iya tantance komai yanda ya kamata ba illa dai yasan a shi kansa yasha wahala balle ita. Amma sambatunta ko neman agaji zai ce na wannan dare ya kasa manta komai.          Yau ma kamar kullum cikin shiri fita wajen training ya fito daga dogon ginin estate ɗin da masaukinsa yake zaune mai hawa kusan ɗari da hamsin, a hawa na tamanin da biyar yake dan haka ya sakko ta lifter har zuwa block A, sanye yake cikin dogon wando na sport da riga mai dogon hannu itama dai irin wandon ce. Sosai ya canja gaba ɗayansa tamkar wanda dama tun farko yake rayuwa anan ɗin. Fatarsa ta sake gogewa ya sake yin haske da kwarjini da cikar kamala a cikin wata uku kacal tamkar wani baƙin bature. Yawan training da sukeyi ya sake buɗe masa halittun gaɓɓai da sake kasancewar sa tsayayyen mutum da za'a iya kallo a jarumi. Kunnensa manne yake da bluetooth yana magana a hankali kamar baya so alamar waya yake amsawa. Ba kowa bane face Ahmad da yay kiransa, duk da yanayin da yake a yanzu na sake zama shiru-shiru da rashin son magana idan Ahmad ɗin yay kiransa yakan ɗan sake suyi hira. Da ɗan gudu-gudu ya fara tafiya jefi-jefi yakan ɗagama wanda suke ɗan wucewa kamar shi a hanya hannu. Yayinda yake cigaba da magana da Ahmad ɗin. Da ga estate ɗin nasu zuwa inda suke training ɗin akwai ƴar tazara sai dai ba wata mai yawa ba sosai, amma duk da haka yakan jure tafiya a ƙafa koma cikin ɗan gudu-gudu kamar yanda yake yi a yanzu domin fara motsa jininsa kafin ya isa. Hakan na ƙara masa ƙarfi da zaburarwa a yayin da ya shiga fili sai karsashinsa ya ƙaru. Sosai sabon baturen Coach ɗin nasu ke yaba ƙwazonsa da jin cewar za'a mori yaron matuƙa idan aka ƙara tsayawa akan al'amarin sa zai zama babbar kaddara, shiyyasa akoda yaushe yake sake jan Smart a jikinsa da ƙara masa dabaru kala-kala dan Smart irin mutanen nan ne masu shiga ran mutane a komai nasu, ga shi baida hayaniya sam, yanayin da yake ciki ma ya sake maida shi miskili a yanzu duk da hakan ba halinsa bane a baya. Amma hakan bai hanashi zama abin so ga wasu ba hatta a cikin teammate ɗin nashi. Alhamdullah yana ƙoƙarin maida hankali tare da ajiye gyambon dake mamaye a zuciyarsa gefe domin fuskantar abinda yaje yi a yanzu, wannan ne karo na farko da zai tunkari babban wasa link na ƙasar da za'a fara, Yana alfahari da hakan duk da team ɗin nashi ƙarami ne. Cikin zafin nama ya iso inda sauran team mate ɗinsa suke. Babu ɓata lokaci suka shiga abinda ya tarasu, sosai yake nuna ƙwazo dake firgita al'amarin wasu a cikin abokan nashi bisa dalilai masu yawa. Na farko shi kaɗaine baƙar fata ɗan Africa a cikinsu, na biyu musulmi, na uku baƙon da har yanzu bai wuce watanni uku da kwanaki ba a cikinsu, amma yana taka leda da sunan training mai firgita zuciya. Ga yanda Coach ɗin nasu yay masifar maida hankalinsa kansa a ɗan ƙanƙanin lokaci na basu mamaki. Yau ɗin ma dai mamakin daya saba basu ya basun, dan har aka tashi babu alamun gajiyawar raunin jiki dana gaɓɓai a tattare da shi. Sai dai su a zahirine kawai suke ganin haka, shi a karan kansa can ƙasan zuciyarsa cike take da rauni. Ga wani irin faɗuwar gaba da ya tashi da ita yau tamkar wanda wani mummunan abu ke neman faruwa da shi. Amma yanayinsa na dakewa da rashin walwala yasa sam su basu fahimci komai ba.       Cikin huttai ɗai-ɗai irin na wanda yasha kai kawo ya samu waje ya kai zaune yana kwankwaɗar ruwan dake hannunsa. Sharkaf yake da zufa tamkar wanda yay wanka. Yanda yake shan ruwan kai a sama ya bama Adams apple ɗinsa damar motsawa cikin kaikawo haɗiyar ruwan da sauri-sauri. Sai da ya shanye ruwan tas ya sauke bottle ɗin yana furzar da nannauyar numfashi. A hankali ya zame jikin kujerar ya kwantar da bayansa yana mai lumshe idanunsa da kai hannunsa saman ƙirjinsa dai-dai zuciyarsa dake cigaba da bugawa ya dafe yana karanto addu'a da fatan koma minene ke tunkarosa ALLAH ya sauƙaƙa masa shi ya kuma bashi juriyar ɗauka..... *_NIGERIA_*      Alh Sulaiman na tsaka da kai-kawon tashin hankalin abinda ya faru tsakaninsa da Daddy kiran Dada ya shigo masa. Kasancewar wayar a hannunsa take yana son kiran Hon. Nakowa yaja ɗan tsaki. Kamar zai share kiran mahaifiyar tasa sai kuma dai ya ɗaga tare da kaiwa kunnensa batare da ko ya gaisheta ba a daƙile ya ce, “Dada ina ɗan wani uziri yanzu idan na kammala zan kiraki”.         Da sauri Dada ta ce, “Sulaiman muna cikin tashin hankali ka tsaya muyi magana dan wannan ma uziri ne babba”. Ɗan tsammm ya dakata da ga yunƙurin yanke kiran da yay yace “Uhumm” alamar saurarenta. Cikin rawar muryar ɓacin rai da tsufa Dada ta cigaba da faɗin, “Sulaiman ina Canada yanzu haka. Yarinyar nan dake tare da Mawaddat ce tai kirana wai gata babu lafiya tanata amai. Na ɗauka kawai normal fever ne nai kiran Dr Olivia ta dubata, amma sai ta kirani tana faɗa min zasu wuce da ita asibiti dan jikin yay zafi sosai. Hankali tashe na taho bayan nama Babanku dibara. Daga airport asibin kawai na is.....”       Cikin ƙosawa Alh. Sulaiman ya tare Dada da faɗin, “Dada bar wannan dogon bayanin kawai faɗi mike damunta?”.            “Wai tana da ciki har na wata uku”.        “What! To ubanwa yay mata shi?”.    “Sulaiman wazai mata banda ɗan iskan yaron nan”. Wata irin zafafaffiyar iska Alh. Sulaiman ya furzar ransa na ƙara dagulewa. Batare da wani tunani ba murya a kausashe ya ce “Zubar da shi za'ai Dada. Ki haɗani da Dr Olivia ɗin muyi magana”.         Ɗari bisa ɗari Dada ta amince da maganar ɗan nata, dan dama itama wannan shine a ranta. Alh. Sulaiman yay magana da Dr Olivia sun kuma gama ƙarƙare komai akan zubda cikin jikin Lulu kafin ma ta dawo hayyacinta tasan da shi. A wajen bature wannan ba komai bane ba, amma sai dai Dr Olivia ta tabbatar masa sai sunyi gwaje-gwajen da ya dace kafin cire cikin bawai zasuyi kai tsaye bane kamar yanda yake so shi. Yana yanke wayar Dr Olivia ta shiga yin abinda ya dace game da abinda zasuyi kan zubda cikin na Lulu ta hanyar gwada ƙarfin jininta da wasu abubuwa irin nasu na likitoci da su kaɗai suka san su.........✍️ 🚴🚴🚴🚴uhhhmmm bazance komai ba nidai. _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣ ........Basuyi mata allurar zubda cikin ba kamar yanda Alh. Sulaiman da Dada suka bada umarni har Lulu ta farka, an gama dai duk wani shirye-shirye har Dada ta saka hannu. A hankali ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi sosai tana bin ɗakin da kallo, sai da hankalinta ya gama dawowa jikinta sannan ta fahimci a asibiti take. Yunƙurawa tai da niyyar tashi sai hakan yay dai-dai da shigowar Dada ɗakin. “Sunahanallahi Mawaddat kin tashi?” cewar Dada tana nufota. Ita ta taimaka mata ta ƙarasa tashi, tare da kaiwa zaune a kusa da ita. Hakan ya bama Lulu damar kwantar da kanta a jikin Dadan tana hawaye. “Yaushe kika zo?”. Ta tambaya cikin raunin murya irin ta mara lafiya. Cike da kulawa Dada ta sake rungumeta a jikinta da faɗin, “Tun ɗazun dear. Ya kike jin jikin naki yanzu haka?”.       “Dada ko ina namun ciwo, ga yunwa ina ji sosai”.      “Ba dole kiji yunwa ba kina ɗauke da jinin yunwa. Shegen yaro da bai wuce saiti abu yi guda ya ɗiraka miki ƙunshi ya barki da jidali”.     Da mamaki Lulu ta ɗago ta dubi Dada saboda rasa gane ina zantukanta suka nufa. Dada ta ƙyaɓe baki cikin hasala tana yin ƙwafa. “Dada wai mi kike faɗi ne?”.            “Mtsoww ba komai tashi muje na kaiki ki wanke baki kizo kici abincin”. Duk da Lulu na son jin fassaran zantukan na Dada sai batai musu ba ta tashi a jikin nata, da taimakonta ta wanko bakinta da fuskarta suka dawo. Apple da tace tana so ta bata ta sha, takai kusan rabi ta ajiye ta ce ta bata yugut. Shi tasha sosai dan kaɗan ta rage a babbar robar da yake ciki. Sosai Dada ta saki baki tana kallon Lulun kamar wadda ke'a cikin yunwa. Ɗan gumin da ya tsatstsafo mata na ƙoshi ta kai hannu ta share tare da komawa jikin Dada ta lafe. Shigowar Dr Olivia ya sakata miƙewa zaune. Sannu Dr Olivia ke mata cikin fara'a da jin daɗin ganin ta tashi da daɗin rai, bayan ta ɗan tsokanarta ta ciro allurar da zatai mata. Lulu bata wani damu ba, dan ta ɗauka normal allura ce, dan haka babu musu ta yarda akai mata doctor na cigaba da tsokanarta.           Minti talatin dai-dai dayin allurar nan wani irin ciwon mara na azaba ya tasoma Lulu. A take jikinta ya fara vibration, tai wani irin dunƙulewa waje guda tana kiran “Wayyo ALLAH na Dada marata”. Yanda ta saki siririyar ƙararar sai da zuciyar Dada ta harba, hankali tashe tai amfani da wayar landline dake a ɗakin tai kiran doctor Olivia. Tamkar dama a kusa take babu jimawa sai gata ta faɗo, zuwa sannan jini ya ɓalena Lulu abin babu daɗin gani....       Iya wahala da azaba Lulu ta Shashi, inda da ƙyar aka samu jinin ya tsaya, akai mata allurar barci tare da gyarata, barcin wahala ne ya ɗauketa sai wata irin tagwayen ajiyar zuciya take saukewa a cikin barcin. Dada da duk ta shiga damuwa ta shiga tambayar doctor yanda ake ciki, Doctor ta tabbatar mata da aiki yayi ƙyau, dan yanzu haka dai ciki ya fita sai kuma ɗan jiyyar jiki da Lulun zatai na kwana biyu. Wata irin ajiyar zuciya mai nauyin gaske Dada ta sauke, a take tai kiran Alh. Sulaiman, a lokacin yana tare da su Hon. Misau suna tattauna batun Daddy. Kamar yaƙi ɗauka sai kuma dai ya ɗaga yana kaiwa kunne. A ɗan daƙile ya ce, “Dada nafa sanar miki inada uziri, mi kuma ya faru yanzun?”.          A ɗan ɗokance da ture maganarsa ta farko Dada ta ce, “Ai an kammala aiki yanzu haka ciki yabi gottern turawa kuma”. Ajiyar zuciya Alh. Sulaiman yayi da faɗin, “To maddala, na san zasu sallameku yau ku koma gida, zuwa anjima idan na samu nutsuwa zan kiraki”. Daga haka ya yanke wayar batare da ya jira tace wani abu ba. Hakan ya bama Dada haushi dan bata gama maganarta ba, amma sai batace komai ba bayan jan tsoki. Kamar yanda ya faɗa zuwa dare da Lulu ta sake farkawa aka sallamesu. Duk da Lulu najin jikinta cikin rashin ƙarfi kwata-kwata ga jiri na ɗinarta bata kawo komai a ranta ba. An basu magunguna suka hau cab zuwa gida. Sun samu Ummita ta gama gyara ko'ina sai tashin fresheners masu ƙamshi da gidan keyi, cikin ƙarfin hali Lulu ta ce ma Dada tana son tai wanka first, amma ta taimaka mata. Dada da kanta ta cuccuɗa Lulu tare da taimaka mata suka fito, kaya ma da taimakonta ta saka, tana gama sawa tasha tea ɗin da mai aikinta Ummita ta haɗa mata bisa umarnin Dada. Sosai ta sha shayin har ma abin yaso bama Dada mamaki, ita dai cikin sauke numfashi ta koma ta kwanta dan barci takeji har yanzun.        *_BAYAN KWANA UKU_*   Yau kawani uku kenan da zubar da cikin jikin Lulu da batasan da shi ba ba kuma tasan an zubar ba. Ta ɗan ƙarasa jiyyarta ta kwanaki biyu yayinda Dada ke kula da ita a duk motsinta. Yanda ta miƙe da wuri zai baka tabbacin zuwan Dada yay mata daɗi, dan akoda yaushe tana nane da ita. Duk da tana jin kewar ƴan gidansu musamman Daddy, Uncle Yousuf, Da Ammah sai take ƙoƙarin dakewa da sakama ranta haushinsu akan basa sonta. Ga kuma Dada a kaikaice tana sake cusa mata laifinsu hadda sharri. A duk sanda kuma Dada ta ɗakko zancen Smart sai Lulu taja tsaki da yamutsa fuska cikin shagwaɓa tacema Dada bata son ji, ita a daina mata koda zancensa. Hakan nama Dada daɗi da sake zaburar da ita cusa ma Lulu ƙiyayyar Smart a zuciya har ma da su Uncle Yousuf. Tun ma abin baya tasiri a ran Lulu har ya fara a randa take cika kwanaki biyar da samun lafiya a bazata sai ga Alh. Sulaiman da Tajuddeen. Lokacin tana kwance a falo tana kallo. A zahiri ta warke ragal. Sai dai tana jin wani irin kasala da son shan fruits, dan rigima ma yau sai cewa tai a mata kunun gyaɗa. Da Dada tace ina za'a samo wata gyaɗa anan sai ta sanya musu kuka na gaske. Dole Dada tai kiran wani saurayi ɗan ƙawarta da suma suke nan Canada ɗin amma asalinsu ƴan Nigeria ne ya bazama nemawa Lulu gyaɗa. Sai ko gashi ya samo, Ummita ta amsa ta haɗa mata kunun data buƙata sannan aka samu lafiya. Wannan kunu shine a gabanta har zuwa yanzu lokaci-lokaci takan zuba tasha abinta har sai taji yakai mata sannan ta ajiye. Sororo tai da ganin Uncle ɗin nata da Tajuddeen, dan ita dai ganin nasu yazo mata a bazata. Yanayinta babu yabo babu fallasa ta tashi zaune tana musu sannu da zuwa. Sai kuma ta ɗan dubi Tajuddeen a yatsune tare da balla masa hararar kallon ƙurillar da taga yana mata. Sanye take da doguwar riga kalar ja da tabi jikinta ta lafe, sai rigar sanyi data ajiye gefenta kasancewar gidan akwai hitter dake ɗumama ko'ina. Rigar ta fisga ta sanya tare da komawa kwancenta kamar yanda take da. Sai dai ta danna wani ɗan maɓalli dake gefen kujerar ya bada ƙara sai ga Ummita da sauri ta fito da ga wani ɗaki tana faɗin, “Aunty kina buƙatar wani abu n...” ta kasa ƙarasawa saboda ganin baƙi. Batare da Lulu ta kalleta ba ta ce, “Ki sanarma Dada anyi baƙi”. Ummita data zube tana gaida su Tajuddeen ta amsa da to tana miƙewa ta nufi ɗakin da Dada da Lulun ke kwana.      Ta wutsiyar ido Alh. Sulaiman ke kallon Lulu da nazartar ta, ba yau ya fara fahimtar girman kai da izzar yarinyar ba irin ta uwarta da ma shegen ubanta ce. Dan duk da yake amsa sunan yayan mahaifiyarta bata wani sakewa da shi, hasalima a duk sanda suka haɗu takan dinga acting like tana jin haushinsa. Hakan yasa yake zargin ko mahaigunta ya sanar mata wani abu a kansa ne. Wata ƴar ƙaramar ƙwafa yayi ciki-ciki a ransa yana faɗin (Zan dawo dake cikin hankalinki ai yarinyabke da ubanki dama duk mai daure miki ƙugu). Tajuddeen kam kai tsaye ya kafe Lulu da kallo, itako duk da tana jin idanunsa a kanta tai biris da shi tamkar bama tasan ALLAH yay zamansa a falon ba da ga shi har ubansan. Laifin Tajuddeen ne ya shafi mahaifinsa Alh. Sulaiman a wajen Lulu, dan bama shi ba, duk wasu ƴan gidan su Tajuddeen Lulu ta tsanesu a dalilin Tajuddeen ɗin ba kamar yanda shi Alh. Sulaiman ke tunanin Daddy ya faɗama Lulun sirrinsa bane.       Cikin nuna mamaki Dada dake fitowa ta ce, “A'a wai dama da gaske ne kuna tafen ashe dai?”.           Murmushi Alh. Sulaiman yayi da amsa ma mahaifiyar tasa da “Wlhy kuwa Dada ai na tabbatar miki babu abinda zai hanamu zuwa. Idan muka gaisheki sai mu wuce mu duba Baba kuma duk da shi Tajuddeen zai dawo nan Canada ɗinne akwai aikin da zaiyi”. Dada bata samu damar bama ɗan nata amsa ba saboda miƙewar da jikanta yay Tajuddeen yaje ya rungumeta. Lulu da duk ke saurarensu gabanta ya faɗi jin wai Tajuddeen yazo aiki ne nan Canada. To lallai dolene kam tabar ƙasar nan kenan a wannan gaɓar. Dan bataga haɗin kifi da kaska ba tsakaninta da Tajuddeen bazasu taɓa kasancewa a inuwa guda ba. Tsam ta miƙe cike da izzar nan tata sai dai rashin ƙarfin jiki na ciwo duk ya cinyeta a tsaye ta ɗauki flaks ɗin kunun gyaɗarta ta bar falon. Su duka da kallo suka bita kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa. Dada ta katse shirun da faɗin, “Bara yarinyar nan ta shirya muku abinci ko. Sannunku da hanya”.     Bakin Tajuddeen a washe yana sauke nannauyar ajiyar zuciya da ga dawowa hayyacin bin kallon Lulu da yay da ido ya kalli kakar tasu. Ido ya kashe mata tare da mata nuni da ɗakin da Lulu ta shiga da baki. Dada tai ƙaramar dariya da faɗin, “To Alhaji zumuɗinka kadai bi komai a hankali, dan bamu san wane kalar barbaɗe shegen yaron nan yay mata ba, maybe bata gama dawowa cikin hankalinta ba ta kuma butsare mana a karo na biyu kadai san halin taurin kai irin na Mawaddat da shegen fitina”.         “Karki damu Grandma, komai zai tafi dai-dai kamar yanda aka tsarashi. Indai ni ne a wannan gaɓar babu garaje. Bamma san tasan komai har sai an ɗaura auren”.      Ƙaramar dariya Dada tayi, yayinda Alh. Sulaiman ya kura musa ido kawai, sai dai baice dasu komai ba.......✍️ _🤔To an taɓa aure akan aurene? Yau naga lukutar masifa Dada da Alh. Tsule fa babu man kai zasu iya ɗaurawa...🚴🚴🚴_ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣ ........Lulu bata sake fitowa falon ba tana a ɗaki, sai in lokacin sallah yayi ta tashi tayi, dan tunda ta dawo asibitin nan kuma sai hankalinta ya dawo jikinta sosai. Da lokacin sallah yayi kamar wadda ake zabura sai Smart yazo mata a rai, miƙewa take cikin jan ƙaramin tsaki da son kauda al'amarin sa tai sallarta. Alhamdullah game da shan kayan shaye-shayen ta ma tunda suka dawo asibitin tamkar wadda aka tsawatar mawa bata sake sha'awar shan wani abu ba dan sun gagareta. Hasalima data tuna sai zuciyarta tahau tashi kamar wadda ta tuno wani abinci. Wannan dalilin ne ya zare mata duk wani tunanin ɗaukar wani abu tasha ya bugar da ita. Sosai wannan zuwa na su Tajuddeen da jin zaiyi zaman aiki anan yasata shiga dogon tunani, bata sha'awar tunkarar Nigeria sam, dan harga ALLAH wani sashe na zuciyarta na tsoron haɗuwa da Uncle Yousuf, sannan kuma bazata iya cigaba da zama a ƙarƙashin inuwa ɗaya da Tajuddeen ba. Dolene tasan mafita na barin ƙasar zuwa wata ƙasa daban ta karasa dogon hutun data ɗauro ɗammarar yi har sai sanda taso ta waiwayi gida Nigeria sannan. Kasancewar anan ba wani an damu da dare ko rana bane dan akoda yaushe ba fasa sabgoginsu suke ba sai in sanyin gari ya hana hakan yasa Lulu tunanin ɗan fita yau tasha iska. Miƙewa tai duk da yanayi rashin ƙarfin jikin da take ji ta sake sabon shiri cikin wando da riga da jibgegiyar rigar sanyi mai hula. Turare taɗan ƙarama jikinta ta ɗauki ƙaramin ledan chocolate ɗinta ta saka a aljihun rigar bayan ta ɗaure igiyar takalmanta ta fito. Tajuddeen kawai ta samu zaune a falo yana daƙilar waya. Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta. Shiko da sai da taɗan gittashi ƙamshinta ya dakar masa hanci ya sashi farga da ita da sauri ya ɗago. Ganinta da shirin fita ya sashi miƙewa da sauri yana faɗin, “Ƴammatan ina zuwa haka ba neman abokin rakkiya?”.        “Ba buƙata”.     Ta faɗa a daƙile tana ficewarta, kafin ya iso ƙofar ta maida ta rufe da sanya security ta baya tana hararar ƙofar da jan tsaki tai wucewarta. Sororo Tajuddeen ya tsaya bayan ya gama mummurɗa handle ɗin ƙofar ya tabbatar da ta kulle ta baya. Lips ɗinsa ya ciza da yanayin rashin jin daɗi ya koma ya zauna a inda ya taso. Itako Lulu cikin tura hannayenta dake sanye da Safa suma a aljihun rigarta ta fara tafiya bisa lafiyayyen titin street ɗin nasu a hankali dusar ƙanƙara na ɗan sauka mata a jiki ɗis-ɗis kaɗan-kaɗan. Duk da akwai sanyi sosai yanayin ya mata daɗi, dan rabonta da irin wannan fitar haka tun bayan gama jiyyar jikinta da Smart ya murza, tana kuma ɗan fara samun walwalar ta kwana biyu sabon yanayin ciwon nan ya sake kwantar da ita shima. Tayi nisa sosai da gidan ta samu wani shagon shan coffee ta shiga, coffee ɗin tasa aka kawo mata, sai dai tana kaisa bakinta taji zuciyarta ya fara tashi, a take ƴan cikinta suka shiga hautsinawa. Babu shiri ta baro gurin cikin tashin hankali bayan ta biyasu, duk yanda taso riƙe aman ya gagara dole ta koma cikin restroom nasu ta dinga sheƙasa har ɗan kunun gyaɗar da tasha a gida sai da ta zazzagar. Cikin galabaita ta samu ta wanke fuskarta ta fito dajan ƙafa. Can gefe ta samu ta sake zama tana maida numfashi ɗaɗɗaya zuciyarta a cunkushe da tunanin wai mike damunta haka ne?. Ita dai tunda take bata taɓa fuskantar kalar ciwo haka ba da amai. (Ni dai nace Hummm). Ta jima a shagon coffee ɗin kafin ta miƙe cikin ƙarfin hali ta sake nufo hanyar dawowa gida dan wani irin sanyi mai shiga jiki da ƙashi take jin na ratsata duk da yanda ta rufe duk jikinta da kariya harda su Safar hannu da facemask amma bata tsira ba. Da ƙyar ta iya kawo kanta gida, ta cire security ɗin data sakama ƙofar saboda Tajuddeen ta shigo cikin tangaɗi. Babu kowa a falon da alama Tajuddeen ya shige, gudun karma wani yazo ya sake damunta ya sata nufar bedroom ɗinta dan yau tayima Dada yaji akan bazata sake kwana a ɗakinta ba. Dan dama da nata zuwan Dadar ya sata komawa inda ta sauka kasancewar bata da lafiya. Gaba ɗaya hankalin Dada da Alh. Sulaiman da suka haɗe kansu a bedroom ɗin Lulun da tunanin bazata shigo nan ba koda ta dawo yanzu baya kan ƙofar, tattaunawa suke game da zancen cikin da suka saka aka zubar mata batare da tasan ma da cikin ba. Wani irin bugawa ƙirjin Lulu yay da ƙarfin gaske. Ta tsaya cak tamkar wadda aka dasa matsayin gunkin tarihi ba mutum mai numfashi ba tana cigaba da saurarensu. Kanta ne ya fara juyawa sannu-sannu ta fara ganin hajijiya babu zato sai jin faɗuwar abu sukai ƙasa yifff. A tare suka zaburo tare da kallon ƙofar cikin waro idanu.....         Bayan kamar awanni biyu ta dawo a hayyacinta, zuwa lokacin hatta da Tajuddeen na a ɗakin zaune a gefenta cikin damuwa dan har fuskarsa ta gagara ɓoyewa. Ɗaya bayan ɗaya ta gama binsu da kallo tamkar mai son tantancesu kafin ta maida idanun nata ta lumshe kawai batare data nuna alamar ta tashin ba. Hirar kakar tata da kawun nata ne suka shiga dawo mata dalla-dalla, ita Mawaddat ce keda ciki, ciki na haihuwar ɗan mutum, amma suka saka aka zubar da shi. To minene dalilinsu nayin hakan. Duk da a karan kanta bazatace son cikin take ko akasinsa ba, amma tanaji a ranta kamar ya kamata ace kafin su aikata zubar da shi a bari ta sani da kuma jin ta bakinta ai. Hannunta dake ajiye a saman cikin nata ta motsa a hankali, tare da sake matsar da shi ƙasa sosai ta shafa cikin. Wannan ne ya fargar da su Dada cewar ta farka. Gaba ɗayansu sukai kanta da sannu musamman Tajuddeen da Dada. Dan Alh. Sulaiman dai idanu kawai ya zuba mata batare da yace komai ba. Cikin damuwa Tajuddeen ke jera mata tambayar mike damunta? Ko zata tashi suje asibiti ne? Yanzu ina ke mata ciwo?. Idanun nata ta ɗan sake buɗewa ta kallesa, sai kuma ta maida abinta ta lumshe. Sake jera mata sannu da roƙon ta bari ya kaita asibitin yayi. Amma sai ta girgiza masa kanta kawai. Zai sake magana Alh. Sulaiman ya katseshi da faɗin, “Tajuddeen relax mana”. Shiru yay badan yaso ba, hakan yasa ɗakin komawa shiru. Lulu da gaba ɗaya take jin wani irin yanayi mai kama da jin zafi da ɗaci a zuciya ta sake buɗe idanunta da sukai ja akan Dada. Muryarta irin ta mara lafiya a dake ta ce, “Dada nice na samu ciki aka zubar?”. Ba Dada ba hatta Alh. Sulaiman sai da furucin nata ya razanashi. Kusan a tare suka kalli Tajuddeen da ya furta “Ciki kuma Mawaddat?!”. Maimakon amsa Tajuddeen ɗin Dada take kallo alamar jiran amsa daga gareta. Dada data ɗan daburce cikin inda-inda ta ce, “E... E... Eh hakanne Sweet heart. Mun...m...munji tausayinki ne da ganin halin da kike a ciki na wahalar ciwo. Sannan minene amfanin haihuwa da wancan sankaran shashashan yaron da ko kansa bai iya riƙewa ba sai baƙin talauci, ke akaran kanki ma baki isa haihuwar ba ai shekarunki nawa ma duka. Na biyu inaji a jikina bada yardarki aka samu cikin nan ba, sai dai in asiri yay miki tare da fyaɗe. Dan ke da bakinki kin tabbatar min baki taɓa bashi kan ki ba. Ki faɗa mana gaskiya, fyaɗe yayi miki ko?”.          Kai Lulu ta kauda tana mai lumshe idanunta batare data bama Dada amsa ba, dan wani irin zafinsu takeji kamar ta shaƙo ɗaya a cikinsu ta maƙure kawai, a mamakinsu sai ganin hawaye sukai na zirara ta gefen idonta yana sauka saman filon da take kai har a cikin kunnenta. Gaba ɗayansu babu wanda bai kasance a yanayin zama turus ba, musamman Tajuddeen da ke jin jikinsa na tsuma. So yake kawai yaji Lulu tace fyaɗe Smart yay mata, shiko ya ɗauki alwashin koda uwarsa yake yawo sai ya yagalgala masa rayuwa. Amma abin mamaki sai gashi iya lallaɓa Dada taima Lulu dan tace wani abu game da samuwar ciki taƙi tace komai. Da tagama zasu dameta sai taja bargo har saman kanta ta rufe kawai da faɗin “Not your business! Please live me alone”. Wannan abin da tai ya ƙara sakasu a wasi-wasi, amma sai Alh. Sulaiman yace su manta da batunta tunda dai an ɗauki mataki, yanzu kawai abinda zasu maida hankali shine binciko inda Smart yake ya saketa a ɗaura aurenta da Tajuddeen. Sun gamsu da hakan, sai dai daga ƙarshe Dada ta bada shawaran in har fa anƙi ganin Smart dole ne su nufi Nigeria su makashi a kotu ta bama Lulu takardar saki kawai ko su nemoshi su dole ga amsa kiran kotu yazo ya bada ai. Nan ɗin ma sun gamsu, dan haka suka tsaya a bisa shawaran nan guda biyu... Tun daga wannan magana Lulu ta koma musu shiru-shiru a gidan, dama ga yanayin rashin jin daɗin jiki da take fama da shi, wanda zuwa yanzu take kallon hakan a matsayin zubar mata da cikin da akayi ne. Su kuma su Dada ke fassarawa da asiri Smart yay mata kawai. Duk yanda Tajuddeen ke son shigema Lulu taƙi bashi fuskar hakan. Dole ya koma baya-baya da ita amma hakan na damunsa. Bama shi ba hatta su Dadan ta tattara ta watsar kamar bata san da su a gidan ba. Ummita kawai take kulawa dan yarinyar nada hankali da nutsuwa. (Ummita ta taɓa aure harda yara biyu, sannan zata iya girman Lulu kaɗan, wahalar da tasha wajen mijinta yasa bayan ya saketa iyayenta sukace bazata zauna musu a gidaba ta tafi wajen ƙanwar mamanta a Abuja. Karatu ta koma, bayan ta kammala rashin samun madogarar aiki ya sata amsar wannan aikin zuwa Canada ta hanyar Hajiyan Shuwa maƙwafciyar ƙanwar mamanta). Duk da abinda Lulu ke musu duk abinda tace tana so sai Tajuddeen ya fita neman mata shi a cikin garin koda yana tunanin bazai samu ba. Duk da dai ma babu abinda tafi nacemawa a yanzu kamar kunun gyaɗa da fruits. Ita kanta har mamakin kanta take akan shan kunun gyaɗar nan na ƙaddara daya sarfaceta. Dan ita a baya ba gwanar shansa bace ba, zama ta iya rantsewa a ɗan zaman datai gidan Aliyu ne ta koya shansa. Sunan Smart da yazo mata a zuciya ya sata jan ƙaramin tsaki. Ɓal-ɓal taji cikinta ya bada har sai da takai hannu samansa ta dafa. Sai kuma akai shiru. Bata kawo komai a ranta ba ta watsar da batun Smart gefe da kan faɗo mata a rai musamman idan tayi wani abu haka daya tuno mata da zaman nasu. Sannu a hankali jikinta kuma sai ya fara sauƙi, zuwa lokacin Alh. Sulaiman da Tajuddeen sun wuce wai duba Baba Garko, sai dai a baɗini shi Alh. Sulaiman nashi zuwan akwai manufa. Ganin Lulu ta samu sauƙi ta murmure sosai sai ma wata ƴar ƙiba da murjewar jiki da ta fara. Dan tayi wani irin ƙyau na farat ɗaya da haske tare da ƴar ƙiba. Zuwa yanzu babu abinda ke damunta sai ɗan zazzaɓin dare. Da zaran ance sha biyu tayi zazzaɓi zai rufeta, zuwa gabannin asubahi kuma sai ya sauka ta wayi gari garas tamkar komai bai faru ba. Shan kunun gyaɗa kam sai abinda yay gaba. Tana nan tana abunta. Tun Dada na maganar wannn shan kunun gyaɗa data laƙama suna na fitina har ma ta kawo ido ta zubama Lulun kawai.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣ ........Kwanan Dada goma sha ɗaya ta fara shirin komawa wajen mijinta. Lulu ko ta maƙale tace ƙafarta ƙafarta dan bazata sake zama ita kaɗai anan Canada ba ciwo ya halakata. Cikin lallashi Dada ta nuna mata bazai yiwu ba, ta kwantar da hankalinta ai Tajuddeen na dawowa nan ɗin duk da ba'a gidan zai zauna ba. Tsaf ta tubure cewar ai ita ko ƙasa ɗaya ma bazata zauna da shi ba. Tunfa Dada na lallashinta harta birkice mata da masifa cikin ɓacin rai. Amma hakan baisa Lulu ta yarda zata cigaba da zama a Canada ba. Sai ma cewa tai ita gida Nigeria zata koma to. Tofa babbar magana, hankalin Dada ya tashi, dan tasan taurin kai irin na Lulu sarai. Alh. Sulaiman tai kira ta sanar masa. Washe gari sai gashi ya sake dawowa Canadan. Shima balbale Lulu yay da bala'i tare da zageta tas ita da Daddy sannan ya saka Dada tattaro masa passport ɗin Lulun da komai da zai iya taimaka mata fita a ƙasar ya wuce da su harda na Ummita ma. Wannan abu ya tada hankalin Lulu, hakama Dada sai al'amarin ɗan nata ya fara bata mamaki kuma. Dan sai take ganin ya zafafa da yawa, miye na ɗauke passport kamar wasu masu son kidnapping yarinya?. Amma ta kasa iya masa magana dan harga ALLAH tana shakkar ɗan nata kasancewarsa ba kanwar lasa bane ba.            *_NIGERIA_*     Alh. Sulaiman ya koma Nigeria bisa matsawar Tajuddeen dole yakai kotu akan alƙali ya saki Lulu, amma sai ya bashi amsa da cewar sai ma'aurata duka sun gurfana a gabansa zai iya aikata hakan. Zancen ya matuƙar bashi haushi ya yayyaɓama alƙalin magana duk da kuwa suna mutunci. Shiko yay biris da shi dan yace bazai aikata abinda ya saɓaba, taya zai kama kashe aure ma babu masu alaƙa da auren kamar a garin da babu shari'a, to yace yamawa hukunci kenan. Kusan alƙalai biyu ya sake tunkara bayan na farko amma amsar duk iri ɗaya ce suma since sai ma'auratan sunzo, dan koda aka aika sammaci gidan su Smart sai akace ma nai kai takardar ai Smart bama ya ƙasar, bakuma asan randa zai dawo ba ma. Alƙalin ƙarshe ne ya bukaci ganin iyayen Smart. Koda Abba yaje sai ya nunama Alh. Sulaiman yafisa sanin takan duniya, dan cayayma alƙali ai yaron da matarsa suna tare acan turai, shi Alh. Sulaiman shirmensa kawai yake yi, yasa a kira masa Smart a waya, akayi kuwa sa'ar samunsa, sun tattauna sosai da alƙalin akayi sa'a kuma shima Smart ɗin yace yana tare da matarsa Alh. Sulaiman yana shirmensa ne kawai saboda yana son raba auren dan taƙi ɗansa. Alƙali kuwa ya samu Alh. Sulaiman yay masa tas tare da gagaɗin yabar wannan shirmen da zubda mutunci yara su rayu da juna tunda sunce suna tare, ɗanshi kuma yaje ya nema wata. Wannan makirci ya matuƙar ƙona masa zuciya, dan haka ya ƙullaci Abba a ransa da fara shiri na musamman....       Taƙaddamar Daddy da Alh. Sulaiman ta matuƙar sake ɗaukar zafi a wani yanayi shi da abokan haɗin kansa su Hon. Nakowa. Duk da dai Alh. Sulaiman ɗin bawai ya fito ya faɗa musu komai da komai bane a tsakaninsa da Daddy bayan wanda ya shafesu su duka ba, dan shi yana nuna musu TAKUN SAƘARSA da Daddyn dai iya tasu ce data shafesu. Bai kawo ɓoyayyen al'amarin dake a tsakanin su sam. Sun ƙara shirya sabon plan akan Daddy, tare da shiga kogin tunani da binciken ta yanda yake bibiyar al'amarin su. Musamman ma shi Alh. Sulaiman da yaji har poisoning ɗin mahaifinsa da yasa akayi wai Daddy ya sani. Wannan zance ya matuƙar tada masa hankali, dan daga ALLAH sai shi sai yaronsa Malami suka san wannan sirrin. Duk da dama gubar da suka bashin bata kisa bace, wadda zata kwantar da shi jiyyace kawai na tsawon watanni harya samu kammala shigo da abubuwansa wanda ya tabbatar da in har mahaifin nashi na tsaye akan ƙafafunsa za'a iya samun matsala a wannan karon. To Alhmdllh burin nasa ya cika, dan kayayyakinsa da suka taso daga ƙasar Mexico sun iso lafiya, inda cikin nasara yay hada-hadar rabawa customers ɗinsa shi da abokan Business ɗinsa da ayanzu sukafi ƙarfi a kudancin Nigeria. Bawai baya huɗa da hausawa ƴan arewa bane akan harkar, akwai su jefi-jefi a cikinsu, sai dai sunada tsoro matuƙa ba kamar ƴan kudancin ba, sunfi yarda su zama dilolin cikin gida bawai masu ɗakkowa daga wajen ƙasar ba. Sannan wasun su basa fito musu da kurwarsu a fili sai dai kawai ace business ne na kaya ko wani abu idan an haɗa sai a sakko kayan da suke shigowar da shi. Akan samu matsala idan mutum ya farga da wuri, dan mafi yawan hausawan da ake riftawa a ciki da zaran sun gane sukan zare hannunsu, sai ƙalilanne da ga ciki masu busashiyar zuciya da son dukiya ke afkawa a cigaba da harka kawai. Wasu kuma tsoro, dan daya zamana ka gane ka fidda kanka to lallai sai su Alh. Sulaiman sun kashe ka ta inda babu wanda zai gane su suka aikata. Hakan shine ya faru Da Daddy, dan kuwa dai Alh. Sulaiman yaja Daddy a jikinsa lokacin daya fahimci shine babban yaron mahaifinsu na gaban goshinsu da yake tsindum akan harkar shigar kuɗi da fitarsu, saboda duk wani babban business na ƙasashen ƙetare na Alhaji Sufi Garko Daddy shine tsaye akai. A lokacin Alh. Sulaiman yana buƙatar kuɗi masu yawa domin shigo da kayansa, sai dai kuma yana tsoron tunkarar mahaifinsa da batun dan bazai bashi ba kai tsaye sai ya bisa da tambayar ƙwanƙwanto. A hankali yayta hillatar Daddy da sunan abota har suka zama aminai ma sosai, kamar wasa ma sai shaƙuwa ta gaske ta fara shiga tsakaninsu ba kamar yanda Alh. Sulaiman ɗin ya tsara ba da farko. Tafiya tai zurfi sosai tsakaninsu har Alh. Sulaiman ya fara jan ra'ayin Daddy suka ƙulla alaƙar business na kawo motoci, sai dai kafin hakan sai da ya fara kafa masa tarko na musamman akan dukiyar mahaifin nasa, inda wasu manyan kuɗi suka dulmiye Daddy ya rasa yanda akayi, hankalinsa ya tashi matuƙa a lokacin, amma sai Alh. Sulaiman ya kwantar masa da hankali tare da maye gurbin kuɗaɗen da aka rasa ɗin yace Daddy ya dinga biyansa a hankali, wannan yasa Daddy sake sakin jikinsa da shi saboda rufa masa asirin da yake gani yayi akan abinda bai taɓa faruwa ba dan shi mutum ne mai takatsantsan da gaskiya shiyyasa Alhaji Garko ya yarda da shi matuƙa, shi kuma tsoron rasa wannan yardar daga mutumin kirki irin Baba Garkon ya sashi shiga a tashin hankali lokacin da kuɗin suka salwanta, iya bincike kuma bai iya gane komai ba. Sun fara business na safarar motoci daga waje zuwa gida Nigeria. Wannan shine silar buɗe *_JIƘAMSHI MOTO'S_* Kamar abin arziƙi Business ya fara tafiya yanda ya kamata, alhkairai suka ƙara buɗe hanyar shigoma Daddy tako ina. Cikin ƙanƙanin lokaci ya sake ɗagawa dukiya ta sake zama a hannunsa ya kuma biya Alh. Sulaiman kuɗinsa. Hakan ya saka Alhaji Garko a farin ciki, dan shi irin mutanen nan ne marasa baƙin ciki wana ƙasa da su. Maƙudan kuɗi ya sake bama Daddy akan ya ƙara a business ɗin, duk da kuwa dama can bawai ya barsa haka bane ba, yana masa alkairin tare da fidda masa hakkinsa na albashi mai tsoka. Amma sai wannan karon ya kasance na musamman, ba komai yaja ra'ayinsa dayin haka ba kuwa sai ganin yanda Daddy shima ya fara sanin ciwon kansa. Alh. Sulaiman da Daddy da sabbin abokan daya sani a dalilin Daddy su Alh. Misau sun cigaba da juya taro yana komawa sisi batare da Daddy yasan ainahin sirrin kasuwancin nasu ba bayan abinda aka sanar masa, dan ta ƴan bariki kawai ake masa da sunan shigo da motoci da babura, da wasu nau'o'in kayayyakin daban-daban. Sai da shekaru suka ka kusan huɗu a tsakani sannan ya farga a dalilin wani lokaci yaga cocaine da ga cikin kayan nasu da aka killace a store batare da su Alh. Sulaiman sun san yaya akai basu cireta ba sanda suke cire sauran.  Hankalin Daddy yay masifar tashi a wannan ranar, dan ya horu da ƙyamatar harkar shaye-shaye ma gaba ɗayanta a dalilin yanda ubangidansa Alhaji Sufi Ado Garko ya tsanesa matuƙar tsanar da sai da ya shiga ya fita da dukiyarsa cikin gwamnati aka kafa babbar hukuma da in ta kamaka da irin wannan kayan sunanka sorry kawai. Daddy baida yawan faɗa sam, sai dai mutum ne mai zuciya idan ka kaisa maƙura. Dan haka a wannan ranar ma ya tunkari Alh. Sulaiman cikin tashin hankali. Shima Alh. Sulaiman ɗin ya girgiza matuƙa shi da abokan huɗɗarsa, saboda suna kiyaye duk wani abinda zai iya kai idon Daddyn, amma sai gashi aiki ya buɗe a gaɓar da suke cin moriyar al'amarin fiye da baya. Da gaggawa sukai zaman meeting na musamman akan dolene fa a kawar da Daddy a duniya kamar yanda akema duk wanda ya nema bijirewa. Sai dai mi Alh. Sulaiman yay saurin ƙwaɓarsu akan karma su fara wannan taɓargazar, dan duk wani motsin Daddy a idon mahaifinsa Alhaji Sufi Garko yake, saboda yanda yake ƙaunarsa. Ya tabbatar musu idan suka taɓa Isma'il Jiƙamshi cikin ƙanƙanin lokaci komai zai buɗe musu, sudai jinkirta suyi tunani. Wannan furuci na Alh. Sulaiman shine ya kawo rabuwar kai, dan wasu na ganin ai yayi hakanne saboda Daddy abokinsa ne kawai, sannan yaron mahaifinsa. Amma inba hakaba su sauran da suka kawar ai akwai na jikinsu suma. Duk yanda Alh. Sulaiman yaso su fahimceshi hakan bata faru ba akai baran-baran. Wannan shine dalilin rabuwar Alh. Sulaiman da su Hon. Nakowa. Sannan yay amfani da wannan damar ya nunama Daddy goyon baya tare da tsarashi kan cewar shima bai san komai ba yaudararsa akeyi kamar yanda shima Daddyn akai masa, amma ya fita da ga wannan gaɓar. Hakan ya bama Daddy nutsuwa, inda ya yarda da Alh. Sulaiman ɗari bisa ɗari suka cigaba da amintakarsu tare da cigaba da business ɗin motocinsu kamar yanda suka fara. Sai dai fa a yanzu Daddy a ankare yake ƙwarai da gaske. Wannan ya saka Alh. Sulaiman canja taku. Shekara biyu da faruwar haka Mawaddat mahaifiyar Lulu ta dawo Nigeria daga karatu. Akwai shaƙuwa matuƙa tsakanin Mawaddat da Alh. Sulaiman yayanta, dan suna ɗasawa matuƙa duk da dai ita kowa a gidansu na sonta da ji da ita kasancewar itace mace sai autarsu, sai ƴaƴan ƴan uwa da Dada ta riƙa mata. Ƴar cikinsu dai su biyun ne kawai mata ita da auta Sultana. Akwana a tashi da dawowar Mawaddat Nigeria ALLAH bai haɗata da Isma'il Jiƙamshi da take yawan ji a bakin mahaifinta da ƴaƴanta ba sai a randa yazo gidansu game da kawo takardun matarsa da Alhaji Sufi yace a kawo. Wannan kuma shine karo na farko da ya shiga gidan shima dan duk iyakar huɗaɗarsu da Alhaji Garko da Alh. Sulaiman iyakarsu office ne da ma'aikatu, sai kuma gidan Alh. Sulaiman ɗin wannan Daddy yasha zuwa. So ne farat ɗaya ya shiga zuciyar Lulu, sai dai ta fahimci bazata taɓa samun kulawar wannan haɗaɗɗen guy ɗin ba (Sannan su Daddy anaji da ƙarfin samartaka ba'a ruɓe ba😂🙏). Ta nema shawaran Yayanta Sulaiman dan babu wani kunya ko shakku ta sanar masa. A lokacin dariya Alh. Sulaiman ɗin yayi da faɗin, “Anya kuwa zaki iya Kandala? Dan yanada mata da yara biyu twins sannan shi ba ɗan kowa bane face wanda Baba ya ɗaga darajarsa ta hanyar ɗaurasa akan dukiyarsa”. (Dan sukan kirata da sunan Kande ne saboda bayan haihuwarta ita ɗaya tilo a cikinsu mace Dada ta sake jimawa bata haifi mace ba sai a haihuwarta ta ƙarshe ta haifi autarsu mace mai suna Sultana, sai dai Sultana sikila ce ko isashen lafiya bata da shi yarinyar. Gata da wayon tsiya da shiga rai).........✍️ _Ayi haƙuri mu cigaba a next page muji sauran._ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣ ........Farrr Mawaddat tai idonta a lokacin irin na wayayyun mata shagwaɓaɓɓu kuma ta ce, “Yaya mizai hanani iyawa. Matarsa bata gabana dan na ita zan auraba ai, kasancewarsa ba ɗan kowa ba, yawan ƴaƴansa duk baya gabana shi dai ɗin nake so ni dai. Idan kuma ban sameshi ba zaku iya rasani. ” cikin sauri Alh. Sulaiman yace, “A'a rufa mana asiri Kandala, indai Isma'il ne ki ɗauka kin samesa an gama”. Taji farin ciki da jin furucin yayan nata ƙwarai da gaske, dan tasan zai mata ɗin kamar yanda ya faɗa. Sai dai mi koda Alh. Sulaiman ya tunkari Daddy da batun sai ya nuna shi sam baya ra'ayin ƙara aure, matarsa ƴar uwarsa uwar ƴaƴansa ta wadatar da shi”. Ran Sulaiman ya ɓaci, amma sai ya danne kawai. Bai so Mawaddat taji wannan al'amari ba sai dai tama riga taji su da kunnenta, wannan yasa ta tada hankalinta matuƙa. Tare da tunkarar mahaifinsu a wannan karon kai tsaye. Shi Alhaji Garko harga ALLAH yayi farin ciki, dan Isma'il Jiƙamshi yarone haziƙi mai hankali da tarin nutsuwar da kowane uba zai so haɗa zuci'a da shi, amma bazai masa dole ba zai dai masa irin na manya. Dan haka ya sallami Mawaddat akan cewar ta jirashi zaiyi magana da Daddy. Mawaddat tayi farin ciki, dan haka ta koma gefe sauraren mahaifinta, sai ma nemar aiki da tayi a inda Daddy yake dan kawai ta dinga ganinsa a kusa da ita. Alhaji Garko bai samu damar yin magana da Daddy ba har tsawon watanni kusan biyu saboda busy da yay da ga shi har Daddy ɗin. Mawaddat taso sake tunkarar mahaifinta da batun sai dai bata samu zama da shi ba saboda yay busy da yawa ƙasar ma ba sama yake ba. Amma tanata fakonshi. Ranar wata Lahadi data shiga a tarihin da Garko family bazasu taɓa mantawa da ita ba ta riskesu a ƙarshen wannan sati da ake saka ran dawowar Alhaji Garko daga dogon fatauci da ya tafi. Wato autar wannan zuri'a da kowa ke ma gata da tattali da ƙauna da tausayin halin da take a ciki mai kimanin shekaru tara a duniya Sultana aka wayi gari wani azzalumi yay mata fyaɗe, sai gawarta aka tsinta a can farkon layi ƙasan wata bishiyar dalbejiya na ƙofar wani gida. Wannan al'amari ya girgiza wannan gida tare da mamaki matuƙa akan tayaya Sultanar ta fita daga gida har hakan ta faru?. Dada dai tasan ta tafi islamiyya da ake kaita a mota a ɗakkota, ta kuma tabbatar da ta dawo gab da magrib, daga nan bata sake ganinta ba a tunaninta ta kwanta ne a ɗaki, dan yanayin jikinta na masu sikila yasa bata da kwaramniya sam. Sai da kusan sha biyu taje leƙata sai ta samu ɗaki wayam. Da farko bata damuba ta shiga kwala kiran masu aikinta da tambayar Sultana. Sai dai amsar ɗaya ce su basu sani ba, dan tunda ta dawo islamiyya basu sake ganinta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci Dada ta birkita lissafin kowa na gidan, dan gaskiya ALLAH ya jarabcesu da ƙaunar Sultana matuƙa, kodan tazo a ƙarshe ne batare da tunanin zuwan nata ba. Iya bincike babu Sultana a cikin gidan, dan haka nema ya koma har waje bisa zargin ko sanda ake sallar magrib ta silale ta fita duk da kowa yasan hakan ba halin yarinyar bane. Cikin amincin ALLAH kuwa sai ga ta an ganta, sai dai cikin jini kuma babu rai. Hakan bai hana a garzaya da ita asibiti ba, inda a gwaje-gwajen farko doctor ya tabbatar musu fyaɗe akai mata, amma ta farfaɗo daga doguwar sumar data tafi. Hankalinsu ya tashi, sai dai jin tana raye yasa sun ɗan ji sassauci. Alh. Sulaiman ne ya kawo police aka tattare duk ma'aikatan gidan zuwa police station. Harda kukansa kamar wani ƙaramin yaro, bayan lokacin har Auta an haifa masa Tajuddeen. Bin cike iya bincike ba'a gane komai ba, inda Sultana da ake tunani da murnar ta fara samun lafiya a wani dare tabar duniya. Dan haka kawai aka samu tana fisge-fisge da girgiza irin na firgitar wanda ya tsorata, duk da tana yin hakan dama tunda abin ya faru sai na ranar yafi na kullum. Da ƙyar doctor suka iya kwatanta ceto numfashinta, da ga ƙarshe dai tace ga garinku nan. Mutuwar Sultana ta zama kamar wata mutuwar babba a gidan, dan kowa ya koɗe ya jeme saboda kuka, sai dai halin da Mawaddat ta shiga yafi na kowa a gidan. Har asibiti ta kwanta na tsawon kwanaki kafin ta dawo dai-dai. Watanni sun ɗan sake shuɗawa har zukata suka haƙura da shiga dangana game da Sultana, yayinda jami'an tsaro ke cigaba da bincike, sai dai maimakon a cikin gidan sai hankalinsu ya fara karkata waje akan cewar ƴan hamayyane kawai sukai hakan. A ranar da Sultana ke cika wata biyu a cikin ƙasa Mawaddat ta tunkari Daddy da al'amari mai firgitarwa game da abinda ya faru da Sultana, inda ta nuna masa video data ɗauka a lokacin suna a cikin ɗaki tare da Alh. Sulaiman ga Sultana yashe cikin jini. Tare da ɗakko masa zancen da ya san bayan Alh. Sulaiman da shi sai UBANGIJI kawai suka sani, wato ɓatar maƙudan kuɗaɗe a hannunsa wanda yayanta Alh. Sulaiman ɗin ya ranta masa ya biya batare da sanin mahaifinsu ba har yanzu. Iya ƙoƙarin yayi danta fahimci gaskiyar al'amurin amma ta nuna sam bata da wannan lokacin, sai ma barazana data fara masa na in har bai aureta ba to lallai zata fallasa wannan video a gidansu dan kowa yasan yanda akai suka rasa Sultana. Hankalin Daddy ya tashi matuƙa, sai dai Mawaddat ta masa mugun ƙullin da yay imani da in har bai aikata yanda take so ba tofa lallai bashi da wata mafita. Dole badan yaso ba ya amsa mata, tare da tunkarar mahaifinsu Alhaji Garko da batun yana son aure Mawaddat. Alhaji Garko yayi farin ciki, yayinda Dada tai tsalle ta dire tace sam bata yarda ba. Ankai ruwa rana sosai game da wannan aure, dan an samu rabuwar kai wasu na goyon bayan Dada, wasu Alhaji Garko da Mawaddat. Inda dai daga ƙarshe bayan an cuɗa an cuɗo ALLAH yay wannan aure da babu wanda yasan manufarsa sai ALLAH sai kuma su ma'auratan. Mawaddat ta shiga gidan Daddy da gigiwar izza da gadara, inda daya motsa zai taka mata birki tamai barazana da wannan video recording da maganar kuɗaɗe. Hankalinsa a tashe yake, yayinda Mommy da Uncle Yousuf suka kasa fahimtar halin da yake a ciki lokacin duk da yanda yake son fahimtar da Mommy amma sai kishi ya rufe mata ido ta kasa fahimtar ba dukiya ko wani matsayi bane ya sashi aikata yin auren ma kansa balle biyema iskancin Mawaddat a gidan. (Wannan shine kuskuren Mommy. Mata ya kamata mu dinga sanin kowanne yanayi da mazajenmu suka shiga koda akan mace ne. Mu dinga sassauta kishi a wasu gaɓoɓin rayuwa dan wani abun kanzoma bawa ba yanda ake kallonsa ba.) Daddy yata gwada son sace camara ɗin nan daga wajen Mawaddat sai dai a ankare take da duk wani motsinsa. A magana ta gaskiya a zamanshi da Mawaddat bai taɓa jin sonta ba kona yini ɗaya, dan ko'a harkar auratayya ita ke kiɗanta ke rawarta game da shi. Sai dai yana yin dauriyar sauke hakkinta har ALLAH yasa aka samu cikin Lulu, sanadin cikinne ma yasa shi ɗan fara sassauta zuciyarsa. Hatta da son ƙyautatama Mommy idan yay niyyar yi Mawaddat kan masa barazana, ga shi Mommy taƙi fahimtarsa, a kullum kawai tana kallon yana cutar da rayuwarta saboda ya auri ƴar masu kuɗi ƴar ogarsa. Ana baifi sati guda a haifi Lulu ba a wani dare yana tsaka da barci Mawaddat ta tashesa. Hakan ba sabon abu bane da take masa, sai dai kuma bayan tashinsa cikin ɓacin rai ya fahimci tashin yau yasha banban da wanda take masa a baya. Dan a mamakinsa ma sai gata durƙushe gabansa a ƙasa tana hawaye da neman gafararsa akan duk abinda ta aikata masa. Ta ce, “Isma'il dan ALLAH ka yafe min, nasan na aikata abubuwa masu yawa a gareka tare da tilastaka aurena badan kaso hakan ba. Na kuma azabtar da matarka itama ta hanyoyi da dama. Ba komai ya jawo hakan ba sai ɗunbin so da ƙaunar da nake maka har ƙasan zuciyata. Duk da inajin kishin matarka banso shigowa cikinku ta wannan sigar ba. Sai dai komai ya canja a dalilin wannan video na fyaɗe da kukaima Sultana kai da Ɗan uwana Sulaiman da kuma kuɗin daka salwantar a Companyn mahaifina bisa son zuciya kamar yanda ma samu labari. A ranar da kukaima Sultana abun nan nayi kuka kamar zan mutu tare da jin tsanarku irin wanda ban taɓama wani mahaluki a duniya ba, na saƙa abubuwa daban-daban akan ku a ciki harda shafe numfashinku a bayan ƙasa. Sai dai zuciyata ta gargaɗeni da yin hakan tare da bani shawarar na dafaku da ranku cikin ruwan sanyi. Na fara da kai ne ta hanyar maka barazana harka aureni, tare da nisantaka da matarka da nasan kana matuƙar so da ƙauna. Da farko naso na haɗa harda Yousuf, sai dai nutsuwarsa da hankalinsa yasa naji tausayinsa nama tsaya masa akan ya tafi makaranta dan bana son yaga abinda na tanada muku. Burina sai na gama da kai sannan na koma kan rayuwar ɗan uwana Sulaiman shima, daga ƙarshe na fallasaku a idon duniya ku kunyata. Sai dai duk wannan lissafin nawa ƙaddara ta canjashi Isma'il a dalilin wannan cikin da ya shiga jikina a mistake, sau biyu ina yunƙurin zubar da shi amma hakan ya gagara, a karo na biyun ma sai likitoci suka tabbatar min idan na sake zan iya rasa kaina gaba ɗaya. Wannan yasa na haƙura na barshi badan naso ba. Sai dai kuma kana naka ALLAH na nashi, tashi kuma itace gaskiya. Wlhy Isma'il a ƴan kwanakin nan inajin kamar barin duniya ke gabatoni. Ji nake kamar bazan yi rayuwa mai tsaho ba. Shiyyasa na shirya faɗa maka gaskiya da neman afuwarka. Tare da baka shawarar kaima ya kamata ka fito ka sanarma iyayenmu gaskiyar al'amurin game da abinda kuka aikatama Sultana kai da Sulaiman koda bazaka faɗi maganar kuɗaɗe ba. Ku karɓi kowane irin hukunci hakan zaifi zama masalaha a gareku da zuri'arku gaba ɗaya”. Sosai jikin Daddy ke rawa a wannan lokacin, ya kama kafaɗun Mawaddat ya tadata daga durƙushen da take ya rungumeta a jikinsa. Sai kawai ya samu kansa da sakin kuka. Itama saita shiga tayashi. Sosai sukai kukansu kafin su zauna dan bata jurar tsaiwa yanzu. Suna zaune a tsakkiyar gadon suna fuskantar juna hannunsa cikin nata ya ce,........✍️ _🚴🚴🚴🚴Dan ALLAH wazai tayani typing._ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 9️⃣ .........“Wlhy wlhy wlhy Mawaddat ban aikata komai ba wa Sultana, sannan ban san yanda akai muka rasa kuɗin nan ba a cikin Company, iya bincike kuma nayi amma ban gane komai ba har zuwa yau. Yanda kike kallon al'amarin ba haka yake ba. Kinƙi bani damar na warware miki ne tun farko shiyyasa amma yau zan sanar miki komai. Sai dai dan ALLAH ina son ki fahimceni, sannan kiyi bincike dan ki tabbatar da gaskiya ta. Ina zaune a gida tare da iyalina Sulaiman yay kirana hankali tashe yana kuka. Cikin sauri na shirya na nufi Garko house da yace min yana can a zatona ma wani abu ne ya faru da Baba wlhy, kasancewata ba baƙo ba a gidan yasa kai tsaye aka buɗen gate na shiga, hakan ya ƙara sakani sake shiga ruɗani, bayan nai parking nayi kiran Sulaiman ya sanar min na zagayo ta baya sashen masu aikin gidan yana acan. Na ɗan ji mamaki, amma sai bance komai ba nace masa ina zuwa. Wannan ne karo na farko danai ta wajen, da kwantace na shiga sashen dan alokacin duk masu aikin na can cikin gida suna aikinsu. Na samu Sulaiman zaune yana kuka ga yarinya gefensa kwance ya rufa mata bargo. A lokacin bansan matsayin Sultana a gidan ba, zamma iya cewa ranar ne nai mata ganin farko dan har sannan ba wani shiga gidan nake ba Sosai ai. Cikin tashin hankali da ruɗewar da nake a ciki nima na shiga jera masa tambayoyi. Da ƙyar ya iya sanar min fyaɗe yayma yarinyar. Kuma wlhy shi bada manufar hakan ba a zuciyarsa. Yazo ne wajen yarinyar mai aikinku dan sun saba kasancewa a tare kawai sai ya samu Sultana a ɗakin, kasancewar baya cikin hayyacinsa saboda abinda wai wani abokinsa ya yaudaresa ya basa da kayan maye a ciki kawai ya afka mata dan tana masa gizo ne like yarinyar da yake zuwa wajen nata sai daga baya ya fahimci abinda ya tafka ɗin. Kuka yake riris da roƙon na taimakesa, wlhy idan wani yasan wannan al'amarin to gaba ɗaya farin cikin family ɗin ku zai ruguje. Kai iyayenku ma zasu iya rasa ransu musamman ma Baba. Dan ya ɗauki son duniya ya aza akan Sultana kamar kowa na gidan gashi bata da isashiyar lafiya. Bani na aikata al'amarin ba amma wlhy na shiga matuƙar gigitaccen ruɗani a lokacin jin yarinyar ƙanwarku ce, dan wlhy bamma san sanda hawaye nima suka fara zubomin ba. Shine ya kawo shawaran yana son na taimaka masa mu kaita can waje ta yanda in mu ajiyeta kamar wani ne yay mata za'a fi saurin fahimta a kaita asibiti, muma kuma hakan zai fi bamu damar kaita asibiti da wuri karta rasa ranta. A ɗan gajeren tunanina a lokacin sai na fahimci hakan shine dai-dai saboda a ruɗe nake ni kaina bana iya gane komai dan tashin hankali, inba hakaba kafin a farga anan tabbas za'a iya rasata. Sannan su masu aikin zai zame musu tashin hankali. Ace a sashensu abun ya faru da ƴar masu gida dolene ace su nemo wanda ya aikata. Na biyu tashin hankalin daya tabbatar min Baba da Dada zasu iya shiga koma su rasa ransu. Wannan shine ya ƙarfafani muka ɗakko Sultana cikin duhun magriba muka saka a motata muka kawota ƙarƙashin bishiyar da aka ɗakkota. Bakuma mubar anguwar ba har sai da aka ɗauketa zuwa asibiti. Ban fahimci nayi kuskure babba a bama Sulaiman gudunmawa ba sai da na dawo gida nake bama Kareema labari kamar akan wani abun ya faru. Kalamanta ne sukai matuƙar rikitamin lissafi da zama nayi nazari nima. Matuƙar damuwa na shiga, har na yanke shawarar tunkarar Sulaiman da batun akan magana ta gaskiya mu fito kawai mu sanar da iyayensa gaskiya, musamman ganin yanda aka kama maigadinsu da wasu masu aikin gidan aka rufe kuma da taimakonsa ne koma nace shine ya saka akai hakan. Sai dai mi koda nai masa zancen sai ya shiga roƙona da kalaman da suka sake rikitamin lissafi, ina tsaka da neman mafita ke kuma kikazo da naki kalar salon..”        Kuka suka sake haɗe kai sunayi, sai da sukai mai isarsu sannan ta ɗakko masa camara ɗin ta bashi, hankalinsa ya tashi da ganin komai, dan tabbas duk wanda zai gani inba yasan gaskiya ba zai ce harda shi aka aikata, sai dai idan kai nazari a yanayin shi akwai sutura jikinsa saɓanin Sulaiman zaka iya fahimtar gaskiya. Laifinsa dai biyewa da yay aka fitar da Sultana a gidan. Roƙo sosai Mawaddat tai masa akan karya bar Sulaiman yasha ruwa a rayuwarsa akan wannan kuskuren har sai ya fito ya tonama kansa asiri, sannan maganar kuɗin Company ya binciki yayan nata sun salwanta ne da haɗin kansa, kuma kuɗin na hannunsa, dan taji suna tattaunawa da yaronsa Malami akan batun, sai dai ba komai taji ba da ƙyau gaba ɗaya. Wannan shine abinda take so ya mata koda bayan ranta. Ya tabbatar mata zaiyi amfani da shawaranta, dan yana son ya samu salama shima a ransa, hakan kuma bazata faru ba har sai ya fidda wannan ɓoyayyen sirrin da neman gafarar su Baba garko. Maganar kuɗi kuwa da tace ya bincika itama tai matuƙar girgiza masa zuciya, har ya fara shiga waswasi akan al'amura da dama game da abotarsa da Alh. Sulaiman ta rana tsaka. Kwana biyu da yin haka naƙuda ta tasarma Mawaddat, a lokacin daya samu Mommy na bata abu harga ALLAH a ruɗe yake, sannan ko Mawaddat ɗin ce tai mata haka a irin yanayin itama zai iya kawo hakan a ransa dan ya fahimci Mommy nada zafin kishi na masifa, shi da yake fuskantar ƙalubalen daga gareta shi yasan wannan saboda a zahiri da wahala ka gane tanada kishi a ƙanƙanin zama da ita. Dan ga wanda bai santa ba bazaice akwai ba, duk da yasan sun cuta mata, sannan tabbas tanada ƙyawawan halaye kishinne mai zafi kawai matsalarta, amma shi laifinta da yake gani shine kasa fahimtarsa da tayi tun farko. Lokacin daya ɗauki hanyar asibiti da Mawaddat cikin kuka dana azaba ta kamo hanunsa ɗaya ta ɗora a kan cikinta da faɗin, “Isma'il dan ALLAH ka yafe min, ka sake roƙamin matarka ta yafemin, ga amanar abinda ke cikina nan na baku, soyayya ta gaskiya daban samu daga gareka ba ina roƙonka dan ALLAH abinda zan haifa in har ya rayu shi ya samu. Kada ka bama kowa daga cikin ahalina abinda zan haifa ka riƙesa a wajenka ciki harda Dada. Idan da hali ma ka nisanta shi da su dan duk sanda Sulaiman yasan gaskiyar lamari kowane irin mataki zai iya ɗauka, kaima ka nisanta kanka daga al'amarin sa, inba hakaba wataran sai kayi dana sani, dan ƙarya yakeyi babu wani abokinsa daya bashi kayan maye da kansa yasha har cocaine yana sha dama, sannan ya jima yana lalata rayuwar masu aikin gidanmu, na taɓa tarar Dada da zancen amma bata yarda ba, sai ma balbaleni datai da faɗa akan idan taji batun a bakin wani saita ɓata min raina. Wannan dalilin yasa kaga na shige masa kamar munfi kowa shiri, amma ba haka bane ba, ina binciken abubuwa ne a kansa dan na jima ina zargin yana safarar miyagun kwayoyi a ƙasashe daban-daban musamman ƙasar Mexico, sannan yanabin hanyoyi daban-daban wajen ɗibar kuɗin baba. Na yi shirin idan na kammala bincikena na bama Baba bayanan ta hanyar gani da ido da zai tabbatar. Dan haka akwai abubuwa masu yawa da muhimmanci a cikin camara ɗin nan da suka shafesa sai kayi takatsantsan dan dama saboda shi na mallaketa...”        Wannan magana ta Mawaddat ta saka rayuwar Daddy sosai a wani hali bayan rasuwarta, shine dalilinsa na hana ahalinta jaririya daya maidama suna Mawaddat, tare da nuna mata soyayyar data roƙa garesa kuma yay mata alƙawari, wadda harga ALLAH bayan rasuwar tata kuma sai yake jin soyayya mai nauyi a kanta. Sai tausayin yarinyar da ya ringa ɗibarsa kuma shima. Dalilinsa na hana Mommy Mawaddat shawarar da yaji dangin mahaifiyarta na bata ne, hankalinsa ya tashi da jin abinda suka faɗa mata akan marainiyar ALLAH da batama san minene duniyar ba, sai dai ita Mommy bata san yaji ba. Yaso yay mata uziri amma jin itama ta karɓama ƴan uwan nata da cewar ai duk abinda Mawaddat tai mata saita ramashi akan Lulu ya saka zuciyarsa a razani lokacin. Dan baiyi tunanin kishin Mommy zaisa idonta rufewaba ta karɓi shawarar ƴan uwan nata. Wannan dalilan yasa ya sake tsayawa akan al'amarin Lulu ya hana kowa jingina da ita. Sai kuma ga abinda yafi na Mommy ya ɓullo masa, bai san yanda akayi Alh. Sulaiman yasan da camara ɗin hannunsa da Mawaddat ta bashi ba, kawai a wata rana ya samesa da batun a rikice, yace ya bashi camara ɗin Please. Amma sai shi Daddy kansa tsaye yace bazai bada ba har sai Alh. Sulaiman ya sanar masa gaskiyar al'amari game da harkar shigo da kayan shaye-shaye daya tsunduma shi, sannan ya faɗa masa gaskiya akan ya akai kuɗaɗen nan suka salwanta da kuma haikema Sultana a sashen masu aiki bayan kowa ya shaida bata zuwa can ɗin sai da ƙwaƙwƙwaran dalili. Wani banzan kallo Alh. Sulaiman yay masa tare da masa nuni da baida hankali. A kausashe ya ce, “Isma'il kai wanene da zaka titsiyeni? Yaushe ma ka kai inda kake tunanin ka kai ɗin? Kana almajirin gidanmu dan na jawoka kaci arziƙi har kake ganin idonka yay tsaurin sanin abinda ni kaɗai ya shafa. To daga yau ka kama kanka. Camara kuma idan baka bayar ta arziƙi ba zaka bada ta tsiya. Sannan ita wannan yarinyar ka shirya dan dolene na hukunta rayuwarta da laifin mahaifiyarta, dan ni bana yafiya bana kuma barin bashin gaba. Sannan sabo da kaza a wajena baya hanani yankata. Ba ita data zama ɗiyar ƙanwata ba, ko ita ƙanwar tawa da tana raye saina ɗan ɗana mata azabar sanin ainahin Sulaiman, amma duk da haka wannan ƴar tata zata fansheta ne”.       A lokacin tsawa Daddy ya daka masa, sai dai kafin yace komai Alh. Sulaiman ya bar wajen.       Wannan ne sanadin komai da zama mafarin ɗauke Lulu daga Nigeria Daddy ya maidata Garmany ya nema mata Nanny da tunanin ya kuɓutar da ita daga sharrin Alh. Sulaiman, shine kuma mafarin duk wani rikicin dake a tsakaninsu, dan har yanzu dai camara na a hannun Daddy duk barazanar da Alh. Sulaiman ke masa yaƙi bashi ita. Ya kuma kasa gayama kowa ciki harda Uncle Yousuf da Mommy dama Baba Garko....      Wannan kenan.                  *_★CANADA★_*     Zuwa yanzu wata irin nutsuwa ce ke saukarma Lulu maiban mamaki, yayinda girman da cikinta keyi ya fara ɗaukar hankalinta. Da farko ta ɗauka tunbi ta fara tarawa, hankalinta ya tashi ta fara tunanin ko kunun gyaɗar da take shane ya kawo mata haka. Ta yanke hukuncin fara fita motsa jiki kawai da alƙawarin daina shan kumun gyaɗa duk da tasan hakan bamai yiwuwa bane. Sai dai bata san yaya zatai hakan ba dan yanzu hatta security ɗin gidan na ƙofa Alh. Sulaiman ya canja shi, idan zata fita dole saita kira Dada ita kuma ta kirashi sai yasa a buɗe. Gefe guda ga cid ko bodyguard zata kirasu ma ita bata sani ba yasa suna bibiyar al'amarin ta. Ta fahimci hakanne a randa sukai fita yin wani shopping ita da Ummita. Hankalinta ya ƙara tashi, dan zuciyarta zuwa yanzu ta fara ayyana mata abubuwa da dama. Cikin harda tunanin anya kakar tata da kawunta basu da wata manufa a kanta. Wannan shine mafarin data fara natsar da zuciyarta waje guda da hankalinta domin fahimtar abubuwa a matsayinta na lawyer. Abu na biyu shine randa ta amshi wayar Ummita da nufin kiran Daddy a karo na farko. Dan ita nata wayoyin ma ta mantosu a Nigeria tun sanda ta taho, tanata ma Dada naci akan a kawo mata sai taita cewa ta manta. Koda Lulu ta saka number Daddy ta kira sai taji Alh. Sulaiman ya ɗaga. Hakan ya ɗaure mata kai akan miya kawo wayar Daddy hannun Uncle ɗin nata, amma sai ta tsinkayi Alh. Sulaiman ɗin na ƴar dariya da faɗin,........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 🔟 __________________ *3 DAYS CLASS* Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rararar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rararar kudinne sakamakon rashin neman scholarship da bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka canza kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni Class ze fara gobe jumaa insha Allah WhatsApp group 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/Ir0qcUHVd8VI3tTlCHPeIA WhatsApp 08144147273 _______________ ........“Karki cigaba da wahal da kanki wajen kiran kowa da wayar nan Mawaddat, koda kuwa Dada ce. Dan duk wanda zaki kira ni ne zakiji na ɗaga, dan lokacin da zasu san ina kiken baiyi ba”. Da ga haka ya yanke wayar ya barta da baki a sake. Na uku har gida ake kawo mata kayan shaye-shaye sai dai yanzu bata iya sha, kallon magani kawai ma tayar mata da zuciya yake yi, jima take ta tsani koda ganinsu. Na ƙarshe shine rashin dawowar Dada Canada tun tafiyarta kusan wata uku kenan. Idan sunyi waya kuma sai tace mata zatazo uziri ne ya riƙeta. Tajuddeen na zuwa gidan kusan duk bayan kwana biyu. Amma ko kallo bai isheta ba. Dan in yazo idan zai yini mata magana ko a bata furta masa har ya gaji ya tafi. Daga baya ma sai ta koma duk randa yazo kulle kanta take a ɗaki har yabar gidan baya ganinta. Duk da yanda waɗan nan abubuwan ke mata kai kawo a rai sai yanayin canjawar jikinta yafi komai ɗaga mata hankali. Da gaske fa komai nata ya canja, tayi ƙiba hallitun jikinta sun sake cikowa, ga wani mugun fresh da tayi kamar ka taɓata jini ya fito. Sai period ɗinta, duk da dama tun kan tai aure yana mata haka tai wata uku bata gani ba, idan kuma zai zo tasha wahalar ciwon mara. Tasha ganin doctors akan matsalar amma amsa ɗaya take samu shine yanayin halittar tane kawai haka lafiyarta lau. To amma a wannan karon idan fa zatai lissafi kusan watanta biyar kenan batayi ba, sai jinin data zubar na lokacin da su Dada suka zubar mata da ciki. Ganin al'amarin na neman sakata a wani hali ya sata saka Ummita ta kira mata Dada. Dada da har yanzu basu koma Nigeria ba sai dai suna shirye-shiryen hakan cikin mamaki take sauraren Lulu dake mata bayani akan rashin ganin period ɗintan. Amma ganin yanda Lulun ta tada hankalinta sai ta shiga kwantar mata akan ta bari zata turo mata Dr Olivia ko kuma ta shirya suje asibitin su sameta. Ɗan son fita da take ne yasata cewa gwara su sametan to. Sai Dadan tace to bari ta samu Alh. Sulaiman da maganar. Kasa shiru Lulu tai ta jehoma Dada tambaya akan miyasa yanzu komai nata sai Dada tace sai Uncle Sulaiman ya sani. Ita kanta Dada sai hakan ya tsikari zuciyarta, rashin sanin ƙwaƙwƙwarar amsa ya sata faɗin Lulun ta bari har sai tazo zasuyi wannan maganar. Badan Lulu taso ba tayi shiru.        Sunje asibiti sun sami Dr Olivia, inda akaima Lulu gwaje-gwaje da duk suka dace, babu wani wahala aka gano ciki ɗan watanni biyar a mararta sai dai kwanakin sa sun ɗan koma baya kaɗan, hakan kuma nada nasaba da yunƙurin zubar da shi da akayi kenan. Ba Lulu ba hatta Dr Olivia ta shiga ruɗani, dan al'amarine da bata taɓa cin karo da shi ba. Saboda tabbas ita shaidace sun zubar da cikin Lulu, sun kuma tabbatar da hakan, amma a yanzu ace musu kuma a kwai shi gashi yana rayuwa cikin ƙoshin lafiya. Dada ma da taji al'amarin hankalinta ya tashi, ta kira Alh. Sulaiman a rikice ta sanar masa. Tamkar wani sumamme haka ya daskare a waje ɗaya, har Hajiya Turai mahaifiyar Tajuddeen da suke tare a lokacin na tambayarsa ko lafiya? Bai iya cemata komai ba face furzar da wata irin iska mai zafi daga bakinsa ya miƙe ya fita. Kaɗan ta taɓe bakinta tare da binsa da kallo, gaba ɗaya kwanakin nan ta gagara gane kan mijin nata, iya tambaya da lallaɓa tayi shi kuma ya dage mata akan babu komai.....      Wani irin rikicewa da daburcewa Dr Olivia tai lokacin data juyo sukai ido huɗu da Lulu da bata san tana bayanta ba. A yanda taga Lulun kuma ya tabbatar mata taji wayar da tai da Dada. Cikin harshen turanci take ma Lulu magana harshenta na sarƙewa. Hannu Lulu ta ɗaga mata kawai alamar bata son jin komai, daga haka ta bar wajen cikin tangaɗin hajijiyar da take ji na kwasarta. Amma koda ta fito sai ta sauya yanayinta saboda bodyguard ɗin da Alh. Sulaiman yasa suke biye da su. Magana taima Ummita akan tazo ta rakata restroom. Ganin ɗaya daga cikin b.g ɗin na ƙoƙarin biyosu ta kallesa sheƙeƙe da faɗin “Can ɗin ma sai ka bimu. Ko an faɗa maka ma na gama abinda nake a asibitin!”. Tsayawa yay kansa a ƙasa dan ya fahimci masifar Lulu tafi tashi.          Tsaki taja da sake ɓalla masa harara sannan taja hannun Ummita. Ba restroom ɗin suka shiga ba, da ga can gefensa suka tsaya, karo na farko a rayuwar Lulu da taji ya cancanta ta sanarma wani damuwarta, dan zurfin ciki babbar ɗabi'arta ce shiyyasa abubuwa da yawa sukai mata nauyi a zuciya.      “Ummita so nake na gudu”. “Sosai Ummita ta waro idanu waje, sai kuma ta kalla inda Bodyguard ɗin nan da Lulu bata lura ya dai biyosun ba a laɓe, ƙasa Ummita takai kamar mai son gyarama Lulu takalmi, dan Ummita wayayyar mace ce da taga jiya taga yau, hasalima tashin ƙauye ce ita, daga baya ta dawo wajen yayarta a cikin Kano, sai dai matsalar data fuskanta ya sata komawa Abuja a yanzu.. “Aunty karki ruɗar da kanki dan munafukin nan ya biyo mu. Muyi tamkar takalmin nake gyara miki”. Lulu ta fahimceta dan haka hankalinta ya sake tashi. Amma sai Ummita ta ce, “Karki tada hankalinki zamu samu mafita. Aunty tsakanina da ALLAH nake jin ƙaunarki a cikin raina, saboda kin min abinda bazan taɓa yarda a cutar dake ba. Nima halin da kike a cikin gidan nan na tada min hankali. Na kasa tunkararki da batunne saboda ina jin tsoron karki kasa fahimta ta. Sannan ke kanki kin kasa gane tamkar anyi kidnapping ɗinki ne anzo an ajiye anan. Dan gaskiya akwai manufa a al'amarin kawun nan naki a yanda nake lure da shi, na fahimci hakanne tun sanda aka zubar miki da ciki da ɗauke passport ɗin mu da yayi”.      Lulu dake jin hawaye da wata matsananciyar tsanar Alh. Sulaiman ta cika mata zuciya ta ce, “Nima na fara jin haka a raina Ummita, sai dai gani nake mizaisa Dada a matsayinta na grandma ɗina ta aikata hakan, shiyyasa kawai nake hora zuciyata da ƙin yarda. Amma a yau zuciyata ta kasa karɓar al'amarin, cikin da suka zubar ashe bai fita ba”.       Da sauri Ummita ta ɗago tana kallonta. Lulu ta gyaɗa mata kai alamar tabbatarwa, “Yana nan Ummita, kuma wlhy naji ina matuƙar son sa. Idan har kakata nada manufa a kaina itada Uncles ɗina dama family ɗina duka ashe bani da babban abinda ya kamata na runguma sama da wannan cikin, yafi kowa kusanci dani a yanzu, banda uwa, banda ƙani, banda yaya. Daddy na da Uncle Yousuf sun fifita soyayyar wani a sama da tawa. Wlhy a yanzu-yanzu Ummita naji ƙauna da soyayyar abinda ke cikina harda zumuɗi da fatan zuwansa duniya lafiya, a wannan karon bazan bari su taɓamin shi ba, ina son na rayu da shi, bana son na rasashi ko shi ya rasani kamar yanda na rasa mahaifiyata”. Sosai Ummita taji itama hawaye na cika mata ido. Miƙewa tai tana murmushin yaƙe dan har yanzu munafukin na laɓe, sai dai bazai iya jin abinda suke faɗa ba. Hanya ta nunama Lulu alamar su koma tana ɗan murmushin yaƙe. “Muje restroom ɗin karsu fahimci wani abu, ina son ki kwantar da hankalinki ko'a fuska kada ki nuna musu kina son cikin balle yunƙurin guduwa. Na miki alƙawarin kozan rasa raina zan taimakeki. Dan nima kin min abinda bazan taɓa mantawaba, wanda shine dalilin amsar wannan aikin da nayi a lokacin da na ganki cewar kece wadda zan zauna da ita anan”. Sosai Lulu kema Ummita kallon mamaki, amma sai Ummitan tai mata murmushi kawai. Restroom ɗin suka shiga, Lulu ma sai tai fitsari sannan suka fito. Ganin sun nufo hanyar dawowa bodyguard ɗin nan yay saurin yin baya yana sanarma Alh. Sulaiman cewar gasu nan zasu dawo da gaske restroom ɗin suka shiga. Sarai Ummita taga waya a kunnesa, hakan ya sata sake gaskata zarginta. Sun koma wajen Dr Olivia wadda suka sameta tana waya da Dada. Dan haka Lulu ta laɓe tana saurarenta. Dr Olivia da bata lura da Lulun ba ita cikin harshen turanci ta cigaba da faɗin, “Idan akace sai an fidda cikin nan a wannan gaɓar akwai babbar matsala, dan za'a iya taɓa lafiyar ta ɓangarori da dama, koma a rasata baki ɗaya. Kawai Mrs Garko kuyi haƙuri ta haifi abinta. Amma dai har na mutu bazan daina mamaki da al'ajab ɗin wannan al'amarin ba, harma na sakashi a cikin manyan record namu na ban mamaki da suka faru a asibitin nan. Sannan zanyi bincike mai ƙarfi akai dan tabbatar da daga ina aka samu matsalar”.           Shiru alamar tana sauraren Dada itama, sai kuma ta nisa da cewa, “Shike nan sai kin shigo ɗin”. Daga haka ta yanke wayar. Haɗiyar zuciya Lulu ta dingayi cikin wani yanayi, kafin ta saita kanta da ƙyar ta nufi cikin office ɗin. Murmushin da Dr Olivia ta gani a fuskar Lulu ya ɗan sata jin relief, ta rubuta mata magunguna da abubuwan da ya kamata taci dan inganta lafiyarta data abinda ke cikinta. Lulu tai mata godiya ta fito akan zata cigaba da zuwa awo. Koda suka fito a asibitin sai da suka tsaya sukai ɗan shopping sannan suka wuce gida. Sun samu Tajuddeen yazo, amma kamar yanda Lulun ta saba kallo ɗaya ta masa ta kauda kanta tare da wucewarta ɗaki tana amsa masa gaisuwar da yake mata a taƙaice. Tajuddeen da yake jin kamar ya fasa kuka ya sauke numfashi mai nauyi tare da dafe saitin zuciyarsa dake harbawa da sauri-sauri, da gasken gaske yake ƙaunar Lulu, soyayya yake mata mai zafi wadda shi kansa wani lokaci yana jin abun na neman fin ƙarfinsa. Bai taɓa jin koda ɗigon sonta ya ragu masa a rai ba duk da cin kashin da take masa. Hasali ma duk abinda tayi sai ya zama shi birgeshi take yi tare da ƙara jin sonta a ransa. Burinsa ya mallaketa matsayin matar aure, ta zama uwar ƴaƴansa, randa yaji ta ɗauki cikin wani ba nasa ba har hawaye yayi, dan ƙarshe ma sai da ya ga likitansa.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣1️⃣ .......Kasancewar Tajuddeen a gidan ranar ya hana Ummita da Lulu sakewa, dan itama dai Ummitan irin mutanen nan ne masu tsantseni akan addini da rayuwa, balle kuma itama ɗin dai tanada tabo irin na Lulu, koma muce ya zarce na lulun tunda ita an riga an keta mata nata mutuncin a sanadin fyaɗen ma harta haifi ɗa sai dai a yanzu babu shi a raye, abin takaicin kuma mijin yayarta data riƙeta ne wanda ta taso tanama kallon tamkar uba ta aikata mata hakan. Sannan tanada matuƙar wayo da lura akan al'amura na rayuwa. Lulu data rufe kanta a ɗaki saboda kasancewar Tajuddeen ɗin tana shiga saman gado ta kwanta tai shiru cikin nazarin abubuwan da suka faru a yayin fitar tasu yanzu. Sai kuma kamar wadda aka tada ta tashi zaune zuwa gaban mirror ta nufa, kanta ta ƙurama ido na tsawon lokaci, kafin takai hanunta ta ɗage rigarta gaba ɗaya ta ƙurama cikinta da ya ɗan turo kaɗan idanu, sai kuma ta kai hannunta saman shi a hankali ta lumshe idanunta hawaye na ciko mata su, ɓul-ɓul taji ya harba tamkar abin shiri, da sauri ta buɗe idonta da hawaye suka cika taf tana kallon saitin daya motsa ɗin, sai kawai ta saki dariya mai haɗe da kuka. Dan abu uku ne ke mata kai-kawon. Wai ita Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi ce ɗauke da ciki na haihuwa, abinda bata taɓa kawowa a jerin tunaninta ba na rayuwa. Duk da kuwa tanada masifar son yara a rayuwarta, amma bata taɓa kwatantasu gareta anan kusa ba ace matsayin ga nata ba a dalilin tsanar maza da tayi a rayuwarta. Sai kuma wata hikima ta UBANGIJI da ikonsa gashi a yau itace aka tabbatarma zata haihu ɗan mutum matsayin mallakinta. (Mallakinku dai ke da ubansa) wata zuciya ta ayyana mata. Idanunta dake a rufe tai saurin sake buɗewa, dan abinda zuciyar tata ta tsikaro mata yay matuƙar dakar ƙirjinta. (Aliyu) ta sake ayyanawa a zuciyarta tare da kaiwa zaune a kujerar mirror ɗin tamkar cikin gajiyawa. Sai kuma a fili kamar wadda aka tunzuro ta furta, “Ai har abada bama zai san da cikin ba balle zuwansa duniya ko rayuwarsa Mtsowww!!” ta miƙe a ɗan hasale. Kokawa ta shiga yi da zuciyarta akan abinda take ta ƙoƙarin sake tsikaro mata game da Smart ɗin. Cikin tsawa-tsawa kamar zararra tace, “Please and Please bana son damuwa a beg”. Ta ƙara jan tsaki ta shige toilet. (Ni sai ma taban dariya sai kace wadda keyi da wani a gabanta😂🤳).           A haka Lulu ta ƙarasa wannan yini cikin wani irin yanayi mai wahal fassara a gareta ita kanta. Sai dai jaɗan-kaɗan hannunta na saman cikinta, yayinda zuciyarta ke cigaba da kawo mata al'amari mai nauyi dangane da kakarta da kawunta da sukaso rabata da shi batare da ko sau ɗaya sun taɓa tunkararta da batun tana da ciki ba ko tunanin zata so abinta. A ganinta wannan babban taka hakkin ɗan Adam ne ai, sannan bataga minene dalilinsu na zubar mata ɗin ba. Dole tana son tasan dalilinsu musamman ma Uncle Sulaiman data rasa dalilinsa na shishshigema rayuwarta a yanzu. Tunda a baya ita dai takan ma haɗa watanni bata ganshi ba. Ganin damuwa na neman cinkushe mata rayuwa ga kayan shaye-shaye sun gagareta sha a yanzu balle tasha ta manta damuwarta ya sata tattare tunanin ta ajiye gefe. Sai ma wani ɗan murmushin takaici ko damuwa za'a kirashi data saki, tare da shafa cikin nata a fili tace, “Wato kai saika nuna min daga jinin wanda ka fito ko?, abu na farko daka fara datse rayuwata da shi shine shaye-shaye, to ya isa a tsaya iya nan inba hakaba a sha ranƙwashi dan bana son shishshigi, shima uban naka yasan ba kanwar lasa bace niɗin tunda ban taɓa raga masa ba akan shiga min hanci daya dinga yi” ta duddungure cikin da yatsanta, zafin da taji ya sata ɓata fuska da sake faɗin, “Garama ka biyo halin Ammah dai zan iya fatan haka ba wannan mutumin mai fuska a turɓune ba uwa ta shanu” daga haka ta fito zuwa falo, dan tasan dai Tajuddeen ya wuce ai yanzu. Ilai kuwa Ummita kawai ta samu a falon tana ƙara gyarawa. Cikin ɗan murmushin da ayau ne ta fara yinsa ga Ummitan ta ce, “Ɗazun mun fara magana amma baki ƙarasa bani labari ba”. Ɗan kallonwa Ummita dake murmushi tayi, sai kuma cikin yanayin signal da idanu ta mata nunin tai shiru da bakinta. Sarai Lulu ta fahimta kuwa, dan haka ta waske da cewar, “Yanzu ni kuwa dama labarin ko dai film ɗin zan nema kawai na kalla da idanuna”.          Murmushi mai ƙayatarwa Ummita tayi tare da jinjina a kaikaice ganin uwar ɗakin nata ta  fahimci abinda take son ta fahimta ɗin cikin sauri, dan haka itama ta fara bata labarin wani Hausa film da take kallo a YouTube kawai. Sai daga baya Ummita ta ajiye mata ƙaramar takarda. Ɗauka Lulu tayi tana dubawa dan cikin littafi ta saka mata yanda ba za'a gane ba.         _“Aunty dole fa sai munyi taka tsantsan, dan inaji a jikina an saka mana recorder a cikin gidan nan da take recording duk wani magana da muke iyayi koda bata shafi komai ba, maybe ma harda cctv camara”._       Lulu ta jima tana kallon takardar da Ummitan ta ajiye tare da shiga dogon nazari akan abinda tace ɗin dama abubuwan dake faruwa. Wanda ya kamata dama tun farko ta nazarcesu a matsayin ta na Lawyer. Sai dai rashin fahimtar dalilan da zata iya hangar abubuwanne kawai yasa bata kai can ɗin ba, da kuma halin rashin lafiyar da take ciki shima. Zaram ta miƙe daga falon zuwa bedroom ɗinta, tamkar wadda akaima allura ta fara kaikawo tare da tsunduma cikin gidauniyar nazari. Komai take bi dalla-dalla, tun daga randa Dada ta ɗakko ta da ga gidanta har zuwa zamanta Abuja na kwana biyar a hannun Hajiya Shuwa batare da Dada ta barta ta nufi gidan Uncle ɗinta Khamil ba. Zuwansu Canada da kai-kawon da Uncle Sulaiman keyi anan ɗin shi da Tajuddeen. Yunkurin zubar mata da ciki da ɗauke mata passport da yayi daga ita har Ummita, bibiyar ta da taga anayi da canja security ɗin ƙofar gidan da akaiyi da bata isa fita ba daga ita har Ummita sai da izinin Dada, amma kuma ai shi Tajuddeen kai tsaye yake zo musu. Maganar da Dr Olivia tayi yau da Dada, zancen Ummita akan recorder da cctv camara da take hasashe. Tsaf Lulu ta haɗe waɗan nan abubuwan waje guda tare da tattara hankalinta a jikinta ta saka rigar lauyanci. Tana zaune a gado pen da book a hannunta tana rubuce-rubuce akan haɗa wancan da wannan ya bata ma'ana Ummita ta shigo ɗakin da sallama ɗauke da kofin kunun gyaɗa da ya zama abincin Lulu. Sai tururi yake da ƙyamshi mai daɗi. Ummita ta ajiye mata saman coffee table da ɗan kaiwa tsugunne a gabansa ta fara tsiyaya mata a ƙaramin kofi. Cikin raɗa-raɗa ta ce, “Aunty karfa ki tada hankalinki akan maganar nan da kikaga na rubuta tunda bawai mun tabbatar bane ba ko gani da idonmu. Amma ina son daga yanzu mu sake taku a gidan nan musamman akan wannan cikin na jikinki. Aunty duk da ban san miye dalilin son zubar da shi da ake ba ina son ki gane muhimmancinsa a gareki kamar yanda kika faɗa a ɗazun. Dan da ace bai kasance mai muhimmanci ba baza'aita kawo masa hari irin haka ba na san salwantar da shi gaba ɗaya. Sannan ina son ki nutsu a matsayinki na lawyer ki fahimci wanene kawunki da ɗansa da manufarsu, dan tabbas a nawa guntun nazarin na fahimci kamarfa suna amfani da Dada ne kawai a wannan al'amarin, kai shi kansa Tajuddeen ɗin kamar uban amfani yake da shi a kanki kawai wlhy”.        Tunda Ummita ta fara magana Lulu ta zuba mata idanunta ne kawai. Dan gaba ɗaya lissafin Ummitan yazo dai-dai ne da nata. A hankali itama ta furta “Ummita duk ya akai kika san wannan?”. Murmushi Ummita tayi da ya ƙara fidda ƙyawunta da gogewar data sake yi na zama a turai. Cikin nisawa ta ce, “Aunty kenan. A kanki zan iya yin fiye da hakan, dan ke wata madubi ce ta rayuwata data haska min kaina da ga ruɗanin munana zuwa na MACE MUTUM mai daraja”. Hannu takai ta share hawayen da suka sakko mata, sai kuma tai murmushi mai ciwo. “Aunty ki bari zamuyi magana amma ba'a gidan nan ba, sai dai ki yarda aikine tuƙuru a gabammu wlhy, amma bana son muyisa cikin gaggawa in har muna son kuɓuta da ga wannan tarkon cikin ƙoshin lafiya batare da an rasa wani a cikinmu ba.” ta miƙe a hankali ta nufi ƙofa. Da kallo kawai Lulu ta bita cikin wani irin yanayin sake shiga firgici, dan har wata ƴar zufa-zufa ke tsatstsafo mata a goshi. Sai kuma ta lumshe idanunta dai-dai sanda Ummita take ficewa a ɗakin gaba ɗaya ta zame ta kwanta. A karan farko ta saki lallausan murmushi irin wanda ke tabbatar da Lulu ƙamshi ta dawo kenan da ga barcin daya figeta na wucin gadi ba Mawaddat ta yanzu ba mai yawan karaya da yin sanyi. Dan tabbas a yau Ummita ta zame mata tamkar wata fitilar tochlight data haska mata wajen ajiye ƙafa da ɗaukewa, sannan allura mai ƙarfin gaske da ta zaburar da ita tare da wanke mata idanunta da ke lulluɓe a ɗan watannin nan cikin yanayin barci ruɗani. Laulayin cikinnan da daina shan abubuwanta ya so maidata wata sabuwar Mawaddat ba Lulu ƙamshi ba. Idanunta ta sake buɗewa a hankali ta ƙure p.o.p ɗin ɗakin da kallo. A zuciyarta ta ce, (Tabbas Ummita gaskiya kika faɗa, yanzu ba lokacin gaggawa bane ko burin guduwa. Lokacine na cigaba da kwantar da kai matsayin MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI har sai nasan SIRRIN DAKE ƁOYE. Dolene na fara sanin manufar Uncle Sulaiman a kaina tare da tantance Dada kafin a fara wasan) ta saki wata ƴar siririyar dariya da faɗin, “Mutanen nan wato har yanzu baku san wacece ainahin Lulu ƙamshi ba ko? Karku damu saura ƙiris ku sani har ma ku bama wasu labari. Hhhh” ta sake sakin dariya tana kai hannunta saman cikinta da cigaba da faɗin, “Idan na gama da su kaima zan dawo kan naka UBAN, dan ajiyarka da yay anan ta ƙarfin tuwo bai sha a banza ba duk da yamin sakin dana buƙata salin alin”. Wani ɓul-ɓul cikin yayi kamar ɗazun har sai da ta zabura alamar tsorata, sai kuma ta harari cikin da faɗin, “Idan ba kayi ko kikayi ba ai ba'a tabbatar min jinin gadararre bane. Dan haka a nutsu bana son iyayi okay”........✍️      _(😂Smart ɗanka ko ƴarka sun higa uku, duk tsiyar da ake maka da alama zata dawo kansu yanzu😂. Tofa dangin Smart kuma sai ku shirya MATA bisa kanku, dan akan cikinku zamu huce komai da kukai mana ehe🚴🚴🚴🥱)._ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣2️⃣ .........*_LONDON_*      A kwana a tashi ba wuya wajen UBANGIJI. A ɓangaren Smart komai na tafiya dai-dai da fatansa dama na duk masoyansa. Sosai ya ƙara canjawa a komai na halittar jiki, gogewar fatarsa da sake zamansa tsayayyen namiji ƙyaƙyƙyawan, ƙiba dai kam bai ƙara ba, sai ma canji wajen zama dana abinci da ya saka shi ɗan ramewa kaɗan dan yasha wahala kafin ya saba ci, yanayin ramar tasa sai ya sake fidda masa ƙuruciyarsa. Harma wani zai iya ɗauka shekarun da yake amfani da su a ƙwallon sune nasa na gaskiya. Kamar koyaushe Lulu na nan daram a ransa, sai dai ɗammarar da ya ɗaura akan tattara al'amarinta da duk wani wanda ke kusa da ita ya sashi dakewa tamkar a yanzu babu komai dake gaban nasa sai harkar ƙwallo da ibada da sam baya sakaci da ita. Abu ɗaya ke damunsa a kanta shine duk dauriyarsa a kowane dare kafin barci ya ɗaukesa daren nan mafi daraja daya ratsa a tsakaninsu ya dinga masa kai-kawon kenan, wataran har takan kaisa ga mafarkinta a wannan yanayin har sai ya kaisa ga wanka kafin sallar asuba. Wani lokacin kuwa har mafarkin gasu a tare yake da ciki a jikinta kotana shayarwa. Duk randa yay irin mafarkan nan yakan tsinta kansa a cikin nishaɗi duk da yana ganin abune mai wahala da yuwuwarsa ba lallai ba, bai kuma taɓa hasashen zata iya kasancewa da cikin na a haɗuwarsu ɗaya kacal, dan duk da ƙarfafashi da zuciyarsa da su Ammah keyi baya jin hasashensa zai iya tabbata akan sake kasancewar su inuwa ɗaya da ita balle har a kai ga haihuwa kuma. Dan ya jima da fahimtar Lulu nada taurin kai dana zuciya matuƙa akan abinda take ƙi ko take so....        A yanzu haka su Smart sun fara wasan da suka kwashe tsahon watanni suna training akai. Wasane da gaba ɗaya ƙasar Unitet Kingdom hankalinsu ke akansa, kasancewar ya shafi kowa-da-kowa. _Smart Mawashi no. 9_ da ya kasance wannan ne wasanshi na farko a cikinsu tun a wasan farko ya fara bada mamaki. Inda ya zama mutum na farko da ya jefa ƙwallo a raga. Ba'a ɗauki dogon lokaci ba ya sake na biyu. Babbar magana kenan, dan kuwa fa a wannan rana gidajen jaridu da na tabijin harma da rediyo da yanar gizo na ƙasar ta UK a duniyar ƙwallo ka-ce-na-ce ake akan wannan sabon yaro na Queen City, dan ya girgiza zukata fiye da tunani. Farin ciki da Coach ɗin su ya shiga tare da Teammate ɗinsa da fans a wannan rana ba'a magana. Shi kansa yana cikin farin ciki mara misali, dan daga ƙwallon farko har ta biyu da ya jefa sai da yay sujida wa UBANGIJI. Bayan gama Home mach da sukaci 3-1 sati mai zuwa suka tafi away mach, a wannan rana ma al'amarin sai godiyar ALLAH, dan ranar ma dai Smart ya zira ƙwallo sau ɗaya duk da dai ansha wahala matuƙa da gumurzu. Tofa, abinfa ya fara zama babban al'amari. Dan al'amarin Smart Mawashi ya fara ratsa zukatan turawan ƙasar England. Wasan link ya cigaba da tafiya fiye da yanda Smart ke fata, dan matuƙa team ɗin nasu na taka rawar gani, saboda sune na ɗaya a tebiri, dan sunada maki kusan talatin da biyu, sun kuma bama team dake bimusu tazarar kusan maki goma sha biyu. Suna taka rawar gani ta yanda a duk randa zasu buga wasa zakaga stadium ɗin ta cika maƙil fiye da kowace rana. Smart ya jefa ƙwallaye goma a wasa goma sha biyu da suka buga, sunci wasa goma, sunyi drow a biyu. Haka dai wasa ya cigaba da tafiya cikin nasarori daban-daban tare da ƙalubale. Ranar da za'a buga wasan daya kasance kamar na dabi ko hammaya tsakaninsu Model Unitet cika iya cika stadium ɗin tayi. Dan duk wani masoyin ƙwallo na ƙauye dana birni a wannan ƙasa dama maƙwaftan ƙasar sun taru domin ganin wannan wasa na da sabon ɗan wasan dake lokaci da Queen City zata buga da Model Unitet ɗin da kowa yasan akwai hamayya mai ƙarfi tun shekarun baya tsakanin team ɗin guda biyu. Bayan kammala al'adu irin na ƴan wasa su Smart suka shigo cikin fili. Bakinsa ɗauke yake da addu'a kamar kullum, yayinda yake sake jin wani irin karsashi da himmar ganin yanda ya tara masoya a ƙasar daba tashi ba. Wasa ya fara gudana yanda ya kamata, sai dai a mamakin kowa yau Smart sai wani jan jiki yake yi, gashi shine lamba tara da kowa zai iya taɓawa. Kaɗan-kaɗan masoyansa dama na team ɗin sa suka fara ƙananun maganar yau kuwa lafiya?. Shi kansa Coach nasu hankalinsa ya fara tashi ganin yanda Smart ke gara ƙwallon a kasalance, sai dai abin jin daɗin sun tare ko'ina har yanzu suma abokan hamayyar tasu basu zira ƙwallo ko guda ba, sunata dai kai hari. A haka har aka je hutun rabin lokaci babu wanda ya zira ƙwallon. Dabaibaye Smart da tambaya Coach yayi akan ko baida lafiya ne yau. Amma sai yay murmushi ya ce lafiyarsa ƙalau kawai dai a haka wasan yazo. Sake jan hankalinsu Coach yay akan karsu bari suyi wahalar banza bayan nasarorin da suka kwararo a baya, saboda in har suka bari Modal Unitet sukaci galaba a kansu zasu sanyaya gwiwar masoyansu ne, dan shi dai yau bai gane komai ga Smart ba. Tofa wasa ya canja salo, dan ana dawowa kowa ya nuna da zafinsa ya dawo. A mamakin kowa sai akaga Smart ya ware kamar bashi ba. Abinka da rainon gero da masara a tsaye yake kan ƙafafunsa babu jin gajiyawa ko nuna rauni, gara ƙwallo yake a fili da iyakar ƙarfin zuciya dana ƙwanji. Cikin mintuna biyu da dawowa su Smart suka zira ƙwallo ɗaya, sai dai bashine ya zira ba. Wannan zira ƙwallo ya sake saka wasan ɗaukar zafi suma Model Unitet team ɗin suka rama a mintuna goma da dawowa. Tamkar an tsirama Smart allura ne shi da Teammate na shi a wannan gaɓar. Bata kashi ake na gaske kowa nason ganin ya sake nasara da kai ɗan uwansa ƙasa, amma hakan bata samu ba sai a kusan mintuna ukun ƙarshe da za'a tashi cikin amincin ALLAH Smart ya saka ƙwallo a raga. Wani irin ihu stadium ɗin ya ɗauka tamkar garin London zai tsage kasancewar yau wasan na cikin gida ne, dan Model Unitet ɗin suma ƴan nan cikin London City ɗin ne. Sakanni ashirin da huɗu saura Smart ya sake jefa ƙwallo ta biyu uku kenan da ɗaya. Ya arrahaman zokaji yanda stadium ɗin ke girgiza saboda matsanancin ihu da masu kallo suka ɗauka. Yayinda teammate ɗin Smart suka wani irin rungumeshi a tsakkiya bayan ya ɗago daga sujidar daya zube ƙasa ga hawayen farin ciki sun wanke fuskarsa. Dolene yay farin ciki, a cikin mintina ukun ƙarshe saura a tashi kacal da kowa ya gama fidda ransa za'a tashi 1-1 amma ya zira ƙwallo har sau biyu, wannan abun yayi kukan farin cikine tabbas..           Wannan itace mafarin nasarar tabbatuwar cikar mafarkin Smart a harkar ƙwallon ƙafa. Dan gaba ɗaya ƙasar England da kafafen yaɗa labarai suka ɗauka. Tako ina ƙasar ta ɗauki zance akan wannan sabon yaro da Queen City ta samo a wannan karon. Wanda daga fara wasan link zuwa yanzu ya zira ƙwallaye ɗai-ɗai har goma sha uku kenan. Wannan nasara bata tsaya a iya ƙasar UK ba, hatta da sauran duniyar ƙwallo ma ta kurɗa a cikin labarai dama masu bibiyar wasanni. Inda masana ƙwallo keta ƙara fashin baƙi akan _Smart Mawashi_. Dan al'amarin ya girgiza mutane da yawa kasancewar wannan shine farkon wasan link daya buga a ƙasar ƙetare bayan na ƙasarsa Nigeria a baya. Coach Abdull-Hameed da takanas ya tafi ƙasar England ganin wannan wasa na su Smart yau saboda yanda yake ta nuna musu fargabar yinsa a dalilin jin labarin su waye Model Unitet ɗin shi da Uncle Yousuf da Ahmad harda hawayensa. Yana jin alfahari da kasancewar Smart rainonsa ne. Yayinda shima Smart kejin alfahari da hakan. Koda sukai waya da Ammah sai kawai ya sakar mata kuka. Ita sai ma abin ya bata dariya. Duk irin kafiya ta Aliyunta da taurin zuciya kaga yana kuka ai wannan al'amari ya kai babba a jerin farin cikin sa ko damuwa. Wannan dai tasan na farin ciki ne. Addu'a ta dinga jera masa daga ita har Abba duk da sudai ba sanin kan abun sukai ba.....          (To nima dai yau nace Smarty ina tayaka murna a madadin Lulu ƙamshin mu, harda ma tafin ban girma🥱👏) *_NIGERIA_* A yau wayar Smart da Abbah ita ta haskakama matan gidan mi ake ciki, dan Umma na tare da shi ne a sanda Smart ɗin ya kira sa kasancewar itace da girki yau ɗin. Ƙagara tai Abba ya gama wayar jikinta har karkarwa yake ganin numbar da aka kira Abban kuma taji ya ambaci Aliyu ta fara da +44.. yana gamawa cikin rawar harshe ta ce, “Alhaji wai wane Aliyu kuma ka samu da lambar wajen ƙasar nan haka?”. Kai tsaye cikin rashin damuwa Abba ya bata amsa da cewar, “Aliyu na ma. Ai yana can ƙasar turawa buga ƙwallo. Yanzu haka ma ya kirani ne yana faɗa min sunci wasan da tun kusan kwana biyar kenan yake faɗin mu tayasu da addu'a akai dan wasan nada ƙalibale sosai. To Alhamdullah sunci kuma shine ya saka kwallon har sau biyu bayan har sun fidda rai ga hakan”. “Tofa sabon zance, shi Hydar ɗin ne ya tafi ƙasar Turai ƙwallo amma mu da muke a gidan bamu da labarin hakan? To Alhaji wani sabon makirci ne yazo ake ɓoye mana hakan kamar wasu masu baƙin ciki ko mugun hali ko yaya ne!!?”. A hasale Umma ke magar har idanunta da suka kaɗa jajur na tara ƙwalla. Abbah da sai yanzu ma shi ya tuna cewar babu fa wanda yasan ina Aliyun yake bayan shi da Ammah da Bilkisu ya tsurama Ummah idanu da mamakin ganin yanda take kumfar baki. Sai dai maimakon ya mata masifa kamar yanda ta hayayyaƙo masan sai yay yinƙurin son fahimtar da ita dalilin ɓoyewar tasu cikin hikima. Amma abin mamaki Ummah ta birkice masa cikin ɗaga muryar data jawo hankalin jama'ar gidan gaba ɗaya zuwa sashen Abbah. Tun Umma na jidali da Abba a ɗakinsa har fa ta fito tsakar gida ta maida abin kan Ammah. Nanfa Mama itama ta ara ta yafa jin ba'asi, yayinda samarin gidan da sauran yaransu suma dai maganar tai mugun dukansu. Ammah dake da ga falonta zaune shiru kawai tai tana sauraren jidalin da Umma da Mama keyi, sai aunty Amarya dake basu haƙuri da faɗin ita bataga abin tada jijiyar wuyaba anan, kamata yay a kwantar da hankali aji dalilin su Abban nayin haka dan bazasu ɓoye ba ai da gangan dole suna da dalilinsu. Neman dawowa faɗan yay akan aunty Amarya, suna cewa itama ai munafukar ce, tunda tana naniƙe a jikin Ammah dan ƙwaɗayin ganin ƴaƴanta na auren masu kuɗi dole tace haka. Maybe ma tasan da tafiyar Aliyun amma taja bakinta tai shiru saboda makircinta da munafurci. Aunty Amarya kusan halinsu ɗaya da Ammah, itama bata da faɗa sai in an kaita maƙura, dan haka tai musu shiru da ga farko, sai da taga suna neman keta mata mutunci a gaban yaransu itama ta fara zazzaga musu nata masifan. Nan fa gida ya sake harmutsewa har sai da Abbah ya fito da ga ɗakinsa a fusace.......✍️ _🥱Shin Hajiya Yahanasu babu rami miya kawo rami ne?._ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* . 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣3️⃣ ........Cikin rufewar ido da nuna ɓacin rai Abba ya tsawatar musu. Ganin Umma na gunguni ya ce, “Wlhy duk wadda ta sake cewa tak sai ta bar min gida a wannan daren. Kuna son maidani wani shasha ne? Kuje an ɓoye muku tafiyar Aliyun kuyi duk abinda kuke jin zaku iya yi dan ALLAH marasa mutunci kawai”. Da ga haka ya koma ciki fuuu ya barsu da harare-harare. Duk abinda akeyi Ammah na jiyosu amma ko leƙowa batai ba, ta kuma hana har su Asma'u leƙowa wajen. A haka aka kwana cikin ɓacin rai wannan dare. Tun kuma a daren su Umma suka bazama sauran ƴaƴansu bayani ta waya cikin nuna hassada. Haka ma ƴan anguwa da rikicin ya ɗan shiga kunnuwansu musamman maƙwafta aka fara riƙe bakin mamakin jin Aliyu ashe baya Nigeria, duk ƙaryar da su Umma keta bazawa matan anguwa cewar ya gudu Lagos saboda dangin matarsa sun ce sai ya saketa ashe ƙarya ce. A wannan dare Umma bata koma ta kwana ɗakin Abba ba, washe gari sai ga yaran gidan na ma'auri nata zuwa musamman mazan tunda safe a cikin tashin hankali. Salim babban ɗan Umma da take ji dashi da fariyyar yafi kowa kuɗi a gidan shine tsageran tunkarar Abbah da maganganun rashin kunya wai yana nuna musu banbanci akan Aliyu. Sai da Abba ya gama saurarensa tsaf sannan ya zageshi ciki da bai da faɗi masa ashe sai yau ne suka san matsayin Aliyu da mahaifiyarsa a wajensa. To bari ya ƙara tabbatar musu da cewar Ammah ta daban ce a zuciyarsa, dan itace first love ɗin sa. Ta auresa a sanda baida komai, yayinda mahaifinta ya tallafi rayuwarsa batare da ƙyama ba a matsayinsa na almajiri, da ya nuna yana son ƴarsa ko sau ɗaya bai nuna ta fisa ba ya aura masa. Tun suna zama a gidan haya ɗaki ɗaya har ALLAH ya horo masa gidan kansa. Ammah tasha rufama rayuwarsa asiri da danginsa da abunta bata taɓa nuna masa isgili da hakan ba koda a cikin wasa. Tayi haƙuri da shi ita da iyayenta akan rashin haihuwa, har sai da uwarsa ta shigo da ƙarfin tuwo ta haifesa shi da ƙaninsa Sadiq kafin ALLAH ya bata cikin Bilkisu. Amma bata taɓa nuna baƙin cikinta ko hassada akan wata tazo a bayanta ta haihu ba. Uwar tasu da suke gani matsayin ƴar uwarsa shi bai taɓa jin sonta ba, da biye-biyen dangi ta kama ƙafa aka tilastashi aurenta... Wannan magana ta Abba taima Umma zafi matuƙa, har ta kaita da fashewa da kukan wai Abba naci mata mutunci a gaban kishiyoyi. Duk da Mama da ita aka fara fitinar sai gashi ta koma yima Umma dariyar ƙeta. Dan ba ƙaramin wankin babban bargo Abba yay mata ba a ranar. Har sai da ta kaita da kuka da hawaye. Da ga ƙarshe ta shige ɗaki ita da ɗiyanta suna zagin Ammah da jawa Smart mugayen addu'oin rashin nasara badan ya musu laifin komai ba sai hassada da uwarsu ta cusa musu kawai a ransu matsayinsa da ɗan uba garesu. Ɓacin rai ya saka Ammah tattara kowa a gidan ta watsar, inda cikin hikima ta nusar da aunty Amarya akan kada ta sake biyema su Ummar dan ALLAH. Tako ji maganarta dan itama ta kame kanta dana ƴaƴanta waje guda kamar yanda Ammah tayi.                  Tun a ranar Umma tai kiran Hajiya Naqiba ta sanar mata komai cikin ɓacin rai. Ran aminiyar cin mushen nata ya ɓaci itama. Inda ta balbale Umma da faɗan miyasa ta kasa riƙe kanta ne ta fito tai magana haka har miji na mata tonon silili a tsakiyar ƴaƴa da kishiyoyi maƙwafta na saurare. Cikin damuwa da hawayen da suka cika mata ido ta ce, “Rainane ya ɓaci wlhy Hajiya Naqiba. Kiga wahala da kashe kuɗin da nai akan yaron nan amma sai da ya tafi wannan shegiyar tamaular da na dutse ya tabbatar min itace silar arziƙinsa da bama gidanmu ba hatta ƴan anguwa nan sai ya riƙe da dukiyarsa. Wane irin koma baya ne ya sameni da har haka zata kasance. Wai yaushe ma ƙullin malam Na-zuru ya kwance akan yaron nan?. Haka fa zancen aurensa sai ji kawai mukayi, yanzu dan cin amana da makircin wannan shegiyar matar dake wani sim-sim kamar ta ALLAH za'ace wai yana Turai......”      Ƙaramar dariyar data katse Umma Hajiya Naqiba tayi, sai kuma tai saurin faɗin, “Yi haƙuri wlhy kece kika ban dariya da kikace sim-sim. Bayan kinsan Hafsatu ba sim-sim bace ba kawai dai tana kwasar ƙurarku ne ta watsar. Amma matar da in ta tashi muku wankin babban bargo sai kun kasa sukuni kike jinginawa da sim-sim, kawai dai shegen girman kai ne da ita kamar yanda ɗan nata ya gado saboda taga ta fiku komai. Ubanta mai arziƙi, tanada ƙyau, gata da ilimi kamar zai kasheta duk da ma bata son nunawa.....”        “To wai ni ban gane ba, yabonta kike ko minene?”.     “A'a rufamin asiri, wane yabo zanma kishiya nikuwa. Kinga mubar zancen tunda kin gagara fahimtata. Yanzu dai bamuga ta zamaba kenan. Dan na fahimci makircin da muka ƙullo a gidan Garko ba dukane yay tasiri ba ko kuwa yaya miya faru?”.              “Dan tasiri fa yayi tasiri, tunda gashi har sun ƙwace ɗiyarsu daga hannunsa. Abinda dai zamuyi shine shima fa makircin sai an haɗa mishi da ƙulli....”        “Ƙulli wane iri? bayan wanda mukayi”. Ummah ta katseta da sauri. Ɗan jimmm Hajiya Naqiba tai da faɗin, “Kai kuma fa haka ne, to kodai tsohuwar nan bata bama yarinyar nan rubutun nan ba ne? To aiko da sakel, dan dolene kiyi duk yanda zakiyi a satin nan mu shiga wajen Malam Na-zuru. Dan ba'a bori da sanyin jiki, dolene mu sake tashi tsaye akan wannan ɗan iskan yaron kuwa.”       “A yanzu kam da ya hau sama bana jin zai bar wata fita a gidan, sai dai ki taimaka min kije zan kirashi ta waya mu fara magana kafin kije”.       “Shike nan hakan ma yayi kuma dabara ce. Dan ko wani abu ya biyo baya ma baza'a zargeki ba kamar wancan sai dai suyita tunani cikin abokan tamaular tashi ne”.       Haka suka cigaba da tattauna mugayen ƙudirinsu akan Smart da Ammah iri-iri kamar basa tuna mutuwa mai gaggawa da kan iya ziyartar bawa a kowane lokaci a kowane irin yanayi mala'ikan mutuwa shi mai cika umarnin UBANGIJI ne.......      (ALLAH ka gafarta mana ka tsarkake mana zukatanmu, ka hanamu damar saɓa maka balle ta kaimu ga shirka ko cutar da wani mun akan abinda bazamu taɓa iya sakawa ko hanawa ba.😭🙏)                       *_CANADA_*      Dada ta iso ƙasar Canada kamar yanda taima Dr Olivia alƙawari, sai dai a ranar babu damar ganinta dan bata duty kamar yanda ta sanar mata. Kai tsaye gida ta nufa inda ta samu tarba a wajen Lulu ta musamman. Zuciyarta ta mata sanyi ganin yanda jikar tata ta saki jikinta a yau ba kamar yanda suka rabu ba. Sai dai duk motsin Lulun idonta na'a kan cikinta ne, amma batace komai ba dan Alh. Sulaiman yace mata kartace ma Lulun komai har sai ya iso. Tsaf Lulu na lure da ita amma ta basar sai ma tambayoyi data shiga jero mata akan yaya jikin Baba Garko. Dada ta amsa mata da cewar, “Ai jiki yayi sauƙi dan yanzu haka ma an sallamemu muna gida, har shi yana ma batun komawa Nigeria dan ya gaji da zaman turan”. Murmushi Lulu tayi cikin tsokana ta ce, “Dada kawai dai yana son ya gudu ne saboda tsoron kar sanyi ya ƙarasa rugurguza miki shi.” Ranƙwashi Dada ta sakai mata amma sai ta kauce da sauri tana dariya. Haka sukai hirarsu yau cikin nishaɗi har Tajuddeen ya iso. Anan ɗin ma Lulun ta basu mamaki dan bata tashi ba kamar yanda takeyi a duk sanda ya shigo gidan. Koda ya gaisheta ma sai ta amsa masa harda cewa “ykk?”. Duk da ataƙaice ta tambayi lafiyar tasa wani irin sanyi da shauƙi ne suka riskesa a lokaci guda. Ya saki wani irin lallausan murmushi da sauke ajiyar zuciya. Ƴar sakewar Lulun ya sashi kwana a gidan yau, washe gari sun wayi gari da zuwan Alh. Sulaiman tamkar a ƙasar ya kwana. Shima Lulu ta gaishesa sama-sama yana binta da wannan shegen kallon nasa ƙasa-ƙasa. Yayinda shima Tajuddeen ke ɗan binta da kallon mamaki musamman cikinta da yaga ya turo. Dukansu Lulu a hankalce take dasu, dan cikin ma ta saka rigar da zata bayyanashi ne garesu su gani da ƙyau saboda neman magana. Sai kuma wani salon yamutse-yamutse takeyi na ƙularwa ita a dole mai ciki (😂Lulu problems kenan🤣👏). Abinda Lulun keyi ya matuƙar sosa zuciyar Alh. Sulaiman, dan kasancewarsa gogaggen mutum mai huɗɗa da jama'a a fannoni da dama ciki harda matan banza. Ya fahimci da wani manufa yarinyar ke nuna musu ciki su tabbatar yana nan. Ya cije lips ɗinsa a hankali tare da miƙewa yana kallon Dada. “Zan ɗan je na wani waje na dawo Dada. Kai Tajuddeen ka jirani dan zamuyi magana”.        A tare suka amsa masa da adawo lafiya, yayinda Lulu da ke shan kunun nata na fama ta ɗan laɓe baki hankalinta a television kamar bata san mi suke ciki ba. Har ya fice bata tanka ba kuma, sai a zuciyarta take ayyana (Kuyi duk ku gama ƙulla makircin naku ina biye daku har a gaba danan dan inaji a jikina za'a samu canjin wajen zama in har akwai abinda kuke shirin)... Alh. Sulaiman na fita asibiti ya nufa wajen Dr Olivia, kusan a tare suka iso da ita cikin asibitin. Koda suka ƙarasa cikin Office cikin tsatstsareta da idanu ya ce, “Ya akai cikin yarinyar can bai fita ba? Bayan na baki duk abinda kika buƙata da ga gareni?”.       Ɗan murmushi baturiyar likitar tayi mai cike da ma'ananoni. Kafin ta ɗago tana kallonsa cikin ido. “Ciki kam na zubar da shi, kuma na saka amata wankin ciki da gwaji domin tabbatar da fitarsa. Sai dai in wani ta sake samu kum.....”           “You are vary stupid Olivia. Kalleni da ƙyau na miki kama da bakar fatar da zaki rainama hankali ko ki kalla wawa?. Niba likita bane, kuma banda ilimin likitanci, dan haka yaya akayi?!! Ciki bai fita ba!!?”.     Yanda yay maganar a tsawace da buga tebirin ya sata ɗan zabura kaɗan. Sai kuma ta watsa masa harara ta koma cikin kujerarta ta lafe. Sosai ransa ya sake ɓaci matuƙa, zuciyarsa sai zallo take da tuƙuƙi a cikin ƙirjinsa. Ya nunata da yatsa da faɗin,........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣4️⃣ .......“Look Olivia, kin san dai zan iya aikata miki komi ko? Ciki harda datse jijiyar numfashinki. Kin sanni na sanki ciki da bai, ki faɗa min yanda akai ciki bai fitaba?”.          “Mi kake so na sanar maka bayan wanda na faɗa?, Na faɗa maka iya abinda na sani ai, kasan irin haɗarin dana saka kaina wajen maka yanda kake so bayan kauce ƙa'idar allurar daya kamata nai mata. Kaifa ka kawo allurar nan kuma na cika umarninka nai mata, a gabanka komai ya faru kuma ko balle kace na yaudare ka”.      “Ƙarya kike Olivia, sai dai idan fakar idona kikai kika canja allurar dana baki. Dan babu macen da aka taɓa gwada wannan allurar a kanta hakan ta kasance kema kin sani. Sannan ƙarya kike bakuyi mata wankin ciki ba”.           Shiru tai kamar bazatace komai ba, sai hucin ɓacin rai takeyi kamar yanda shima yake yi. Wayar landline ta jawo tai kira, kai tsaye ta bada umarnin a sameta a Office. Mintuna baifi uku ba wani nurse baƙin fata ya shigo. Cikin girmamawa yayma Dr Olivia barka da shigowa tare da ɗagama Alh. Sulaiman hannu a taƙaice. Dr Olivia ta dubesa bayan ta zaro wani file a gefenta ta miƙa masa. Amsa yay cikin rashin sanin mizaiyi da shi.      Ta ce, “Buɗe”.    Babu musu ya buɗe tare da ɗan duddubawa, sai kuma ya ɗago yana kallon doctor. Kafin yace wani abu ta tareshi da faɗin, “Ban sakaka yima mai wannan file ɗin wankin ciki ba a ranar data samu miscarriage?”.          Ɗan jimm yay alamar tunani, sai kuma ya dubeta yana cewa, “Ƙwarai anyi haka doctor, sai dai kuma an samu akasi ai a ranar bamuyi mata ba saboda yanayin mahaifarta mukace bayan kwana biyu su dawo sannan ta huta saboda sun matsa a sallameta....”          A zafafe Alh. Sulaiman ya yunƙuro zaiyi magana Dr Olivia ta girgiza masa kanta. Ita ta ƙara fuskantar Nurse ɗin da faɗin, “Amma miyasa baka sanar min ba? Sannan da baki ka faɗa musu ko'a rubuce?”.         Kai tsaye yace, “Nazo sanar miki sai na samu kin fita. A rubuce kuma muka basu gaskiya, kuma ita muka bamawa ma a hannunta ai”.     “Okay zaka iya tafiya”.   Ɗan rissinawar girmamawa yay tare da ajiye mata file ɗin ya fice. Yana rufe ƙofar ya saki murmushin mugunta, a zuciyarsa yace (Ƴan iska ai dama nayi alƙawarin saina kuɓutar da yarinyar nan. Wankin ciki kuma ina kan sani naƙi yinsa bayan nai mata allurar tsaida jini da sauri ta yanda cikin bazai fita ba. Ina Musulmi baƙar fata bazan taɓa bari a cutar da wani musulmi ba in sha ALLAHU in dai ina asibitin nan. Tunda har naji hirarku dama nai alƙawarin taimaka mata dan na fahimci zaku cutar da ita ne bada saninta ba).          A ciki kuwa shiru Office ɗin ya ɗauka. Da ga Alh. Sulaiman har Dr Olivia kowa ya kasa cewa komai. Sai can ta nisa da ƙyar ta katse shirun da faɗin, “Yanzu ka yarda na maka aikinka ko? Sannan babu kuskurena a ciki na turata inda za'a mata wankin ciki, kaga kuma sun basu damar su dawo amma baku dawo ba, hakan na nufin yarinyar bata son rasa cikinne ko wani dalili daban.....”        Cikin wani irin baƙin ciki da zafin zuciya Alh. Sulaiman ya furta, “Dalilinta na banza. Ciki kuma dolene a zubar da shi”.      “Gaskiya bazai yiwu ba, inba haka ba kuwa komai zai iya faruwa kamar yanda na faɗama Mrs Garko. Ciki kuwa harda rasa ranta. Ni kuma bazan iya gangancin aikata haka ba a wannan gaɓar dan zai zama taka doka, cikin wata biyar da kusan sati biyu, taɓashi da niyyar zubarwa ai kowama yasan ganganci ne. Kawai ku barta ta haihu tunda tana son abinta”.        “Ashe zan kashe yarinyar nan kuwa!!” Alh. Sulaiman ya faɗa a wani irin kausashe jikinsa har ƙyarma yakeyi. Ita Dr Olivia ma duk sai tsoro ya kamata. Nurse ɗin nan ne yay knocking ƙofar ya shigo, cikin girmamawa ya aje wani file a gaban Dr Olivia a yanayin dafa tebirinta, hakan ya bashi damar zare ƙaramar wayar da ya ajiye batare da sun lura ba saboda rufewa da idanunsu sukayi. Daga haka yay ficewarsa yana ɗan murmushi....        Fitarsa kusan da mintuna biyar sai ga Alh. Sulaiman ya fito ransa a matuƙar ɓace tamkar zai kifa a cikin sassarfa. Nurse ɗin nan yay murmushi da biyo bayansa da sauri-sauri. Sun ɗan yi nisa a doguwar barandar yaji kamar ana binsa a baya. Jiyowa yay cikin sauri sai sukai arba da Nurse ɗin nan. Kamar zai yi magana sai kuma yay shiru sakamakon tare numfashinsa da Nurse ɗin yay cikin harshen Hausa. Mamaki ne ƙarara ya bayyana a fuskar Alh. Sulaiman, duk da kuwa hakan ba wani abun ai mamakin bane kasancewar matashin saurayin baƙin fata. Amma gaskiya bai tsammanin jin Hausa a bakinsa ba. “Sunana Usman B Sa'eed. Bahaushe haihuwar Nigeria girman Canada. Na biyoka ne nan saboda jin ina son taimakonka matsayin ƙabilata kuma addinina.”      Kamar Alh. Sulaiman zai yaɓa masa magana sai kuma dai ya haɗiye, yaga ya kamata yaji ƙarshen zancen. Usman ya cigaba da faɗin, “Dr Olivia bazata baka haɗin kai ba dama, dan kasan turawan nan da son bin ƙa'idar abu. Sannan gaskiya ta faɗa in har ta aikata sake zubda cikin aka samu matsala to akwai babbar ƙura da ku kanku zata iya shafarku. Karka manta anan sun san hakkin ɗan adam ba irin yankuna mu na Africa bane ba da zaka iya yin komai ba komai. Na fahimci cikin irin wanda mu mutanen Hausawa muke gudune wato na shege shiyyasa kuka matsu ku zubar. Dan haka zan taimaka muku ta yanda zaku salwantar da shi cikin sauƙi batare da kowa ya fahimta ba. Sai dai zai kai haihuwa, amma za'a haifesa ba'a raye ba, dan zan dinga mata allurar da yaron zaita ruɓewa a cikin nata batare da an fargaba itama kanta bazata fahimta ba dan na gane bata so a zubar da shi shiyyasa taƙi dawowa wankin ciki”.          Sosai Daddy yake nazartarsa, amma abin mamaki ya kasa hango yaudara a tattare da shi. Dan Usman irin mutanen nan ne masu maida abu serious ka kasa fahimtar gabansu da bayansu. Kai Daddy ya ɗan jinjina kawai tare da miƙa masa hannu. “Zan iya baka number ka sameni a gida bayan nayi shawara”.       “A babu damuwa ai Alhaji”. Cewar Usman cikin dakewa. A zuciyarsa kam sai dannama Alh. Sulaiman zagi yake kala-kala. Dan yana ayyana sune masu fita ƙasashen waje suna zubar mana da mutunci ana kallonmu wawaye creminal. Ya bashi number wayan suka rabu, da ga haka ya fice a asibiti ya samu taxi ya shiga dan anan baida lasisin tuƙi.  Maimakon gida sai ya nufi can wani joint a bayan gari kaɗan, wajene na sheƙe aya matuƙa dan mata na yawo ne babu sutura. A can ya samu ya huta zuciyarsa ta huce da samun damar yin tunani akan Usman Nurse. Ya fahimci wannan ita kaɗaice mafita kam a garesa. Dan yana son tabbas shegen cikin nan ya zube saboda shine sharar fage na farko da yake son ƙuntata rayuwar Smart da ita. Kafin ya tafi matakin farko akan Daddy da Smart ɗin harma da Uncle Yousuf, dan akan Lulu yake son ya musu tarko su ukun ta yadda zasu koma su kansu basu yarda da kansu ba. Wannan shine sabon plan ɗin da ya canja akan kowanne su. Tajuddeen kuwa lokaci yayi da zai kaɗa kansa ya bar Canada. Dan ya gama masa aikin da yake so, dama amfani kawai yake da yaron nasa a matakin dalillai biyu. Na farko manufarsa tun fil azal. Na biyu halin ciwo da yake ciki akan yarinyar shiyyasa yake biye masa kamar gaske dan ya samu kwanciyar hankalinsa. Dan gaskiya yana ƙaunar yaron fiye da sauran ƴaƴansa. Saboda kasancewar sa namiji ɗaya tilo a cikinsu. Yana ganin bayan ya tsigesa mataki na biyu da zaibi a kansa shine bin shawarar amaryarsa akan haɗashi aure da ƙanwarta, dan ya gamsu da bayanin datai masa ya kuma ɗauki shawararta. Sannan ita kanta Dada lokacin gama nata aikin yayi.       Koda ya koma gidan sai bai cewa Dada komai ba koda ta tambayesa ya batun zuwa asibiti. Sai da ta ƙara maimaita masane ya ce ta saurareshi yana nazari ne. Badan Dada taso ba dole tai shiru ganin ya haɗe fuska. Ummita dake laɓe tana jinsu, sai dai bata so jin Alh. Sulaiman yay shiru ba. A lokacin da duk wannan cakwakiya ke faruwa Smart na can cikin farin cikin samun nasarar cin ƙwallon da sukai tsakaninsu da abokan hamayyarsu ƴan Model Unitet a wannan ranar...... Bayan kwanaki biyu Alh. Sulaiman ya kammala yanke hukunci akan zancen Usman Nurse, sai dai bai nemesa ba sai da ya saka akai masa bincike a kansa tsaf. Inda aka kawo masa bayanai akan tabbatar da cewar karatu ne ya kawo mahaifinsa ƙasar Canada, amma asalinsu ƴan Nigeria ne. Anan Usman ya girma dan yana da shekara kusan goma iyayen nasa suka dawo Canada, sai dai fa yana yawan zuwa ƙasar haihuwar tasa. Usman dai a zahirance baya jin magana sam, dan duk wani ɗani'u na turawan nan yana zubasu musamman neman mata, kuma kamar yanda yake a turai hakan ba komai ba suma iyayensa basu ɗauke sa komai ba. Bai taɓa aure ba amma yanada ilimi mai dan babban Nurse ne shi ɗin. Wannan bayanai sun ƙawatar da Alh. Sulaiman, dan ya nazarcesu tsaf da fahimtar su a yanda makauniyar zuciyarsa ta tabbatar masa. Abinda bai sani ba Usman yarone mai matsanancin kishin ƙasarsa da ma yankinsa na Africa har ma da addininsa duk da waɗan nan rashin jin nashi. Wannan aƙidar tasa tasa ko kullum yake cikin yawo tsakanin Nigeria Da Canada kamar wani ɗan sama jannati. Dan ko aikin ma anan da ƙyar mahaifiyarsa ta samu ya yarda yakeyi, amma duk da haka sai da yaje ainahin ƙauyensu ya buɗe wani ƙwarya-ƙwaryan asibiti ya zuba likitoci da ke aiki a cikin kuɗi ƙalilan wa marasa lafiya. Koda Alh. Sulaiman ya gama tattare abinda yake buƙata sai yay ma Dada wayo akan ta koma wajen Baba, ciki Lulu kuwa su barshi ta haifi abinta kawai tunda dai Dr Olivia ta tabbatar musu akwai matsala. Ba haka Dada taso ba, sai dai bata iyayima ɗan nata musu, ganin kuma ya dawo da passport ɗin Lulun da Ummita ya basu ya sakata jin kwanciyar hankali, dan haka badan taso ba ta shirya ta koma wajen mijinta da al'amarin nata ya sashi fara tsarguwa shima. Sai dai baice mata komai ba tunda ta ce masa wasu kaya zata duba a Canada ɗin dama kafin ta wuce........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣5️⃣ ......Ko kaɗan Lulu bata nuna damuwa da tafiyar ta Dada ba duk da kuwa a ƙasan zuciyarta cinkushe yake matuƙa, amma plan ɗinsu ita da Ummita ya sakata dakewa abinta ta nuna komai ba komai har Dada ta wuce. Washe gari shima Tajuddeen mahaifin nasa ya janye ra'ayinsa ta hanyar tura sa Nigeria da saƙo. Ko kaɗan Tajuddeen bai kawo komai a ransa ba ganin shima Alh. Sulaiman ɗin yayi shiri wai zai wuce ƙasar Brazil ne yin wani business, sai dai ɗan nasa na wucewa yayo sau da baya. Sabon gurin daya shirya za'a kai masa su Lulu acan wani ƙauye ko yanki za'a kirashi ma ne oho ya wuce. Wajene tsibiri ne, dan a tsakkiyar wani irin makeken ruwa mara iyakar kallo tsibirin yake. Gidajene kawai na masu zuwa hutawa a wajen da yawon buɗe ido, sai jiragen ruwa ne kawai ke iya kaika cikin tsibirin. Wajen kam a kwai daɗin zama musamman ga wanda suka je hutawa, zaka tabbatar da hakanne ne idan kaga yanda mutane ke nishaɗi musamman ma masoya da masu kuɗi...... Kamar kullum yau ma bata fito ba har sai da Ummita ta kamma kimtsa gidan, yay tsaf abinsa sai tashin ƙamshi da ɗumi mai ratsa ɓargon jiki daya gauraye ko'ina. Wando da riga ne a jikinta marasa nauyi, dan haka matashi cikinta ya samu damar fitowa ɗas da shi. Yau gaba ɗaya kasala takeji, dan da ƙyar ta iya fitowa dan yunwa data addaba mata ya sata fitowa ta samu abinda zata ɗan ci. Kai tsaye kitchen ta nufa inda Ummita keta ɓuruntun dama mata kununta, koda tai sallama kafin ma Ummita ta kai ƙarshen amsawa ita harta isa ga freight, ruwa ta ciro mara sanyi ta sha, tana ajiye bottle ɗin da sauran wanda ya rage ta nufi Ummita. Fuskarta da murmushi take faɗin, “Har yanzu ƙarnin kifin nan da Dada tasa kika dafa mata a gidan nan ya ƙi fita wlhy Ummita”.          Da mamaki Ummita ta ce, “Kai aunty dan dai baki so ne kawai, amma wlhy ni banjin komai sai ƙamshin fresheners a gidan nan.”     Cikin ɗan yamutsa fuska da tsaki ta ce, “Wlhy Ummita yanzu ne dai bana so, amma da ai kafin na ci miki nama naci kifi, sai dai yanzu na rasa miya haɗani da shi haka ko ƙamshinsa bana so”. Da dariya Ummita ta ce, “Aikin Unborn ne ai Aunty”. Shiru Lulu tai tana kallonta kamar mai nazari kosan tuna abu, abinda ke ƙoƙarin tuna kam nasa ne a zuciyarta ya zo mata. Tabbas Aliyu bama yancin kifi kwata-kwata idan bata manta ba. A take ta haɗe fuska kamar a ɗan ƙufule ta ce, “Ni shikenan saboda wannan cikin duk abinda baya ci nima na daina ci koda ina sonshi, sannan abinda yake so dole sai na so shi kamar abin asiri?”.        “Wakenan Aunty?”.   Cewar Ummita cikin nuna mamakin furucin uwar ɗakin nata. Sai dai maimakon bata amsa sai taga ta juya tama fice a falon tana ɗan dafe kai. Bata kawo komai a ran nata ba game da dafe kan ta cigaba da zuba mata kunun gyaɗar a flaks ɗin da ake zubawa. Ta kammala idonta ya sauka akan sauran ruwan da Lulu tasha ta ajiye, ta san da wahala ta sake shansa. Dan haka ta ɗauka ta shanye ta jefa bottle ɗin a shara sannan ta ɗauki flaks ɗin da ƙaramin kofi tabi bayan Lulu. Ɗan turus tai na mamakin ganinta baje a kujera tana barci kamar ba yanzu ta baro ta a kitchen ba. Sai tai dariya da jin tausayin ta. Ta ajiye flaks ɗin itama da nufin komawa kitchen ta gyara kayan datai amfani da su a aikin itama kanta ya sara, da sauri ta dafeshi tana mai ambatar sunan ALLAH, jin hajijiya na neman yadda ta a ƙasa da bin bango ta fito falon itama, sai dai kafin ma ta kai ga kujera ta zube ƙasa, daga haka bata sake sanin ina hankalinta yake ba itama....        Duk abinda ke faruwa Alh. Sulaiman na kallo ta camera da ya saka musu kamar yanda Ummita ta zarga dama, wata shegiyar dariyar basanci ya saki sai kuma ya gimtse fuska duk a lokaci guda. Wayarsa ya jawo a gefensa tare da shaƙar cocaine ya wani girgiza kan nasa da wani irin style na ƙwararrun ƴan cocaine sannan ya kai wayar kunnensa. Cike da izza ya furta “Nan da awa ɗaya ku tabbatar su da duk tarkacensu suna a gabana” da ga haka ya yanke kiran batare da jiran an bashi amsa ba da ga can...       Matuƙa hankalin Lulu da Ummita ya tashi a lokacin da suka farka da ga nannauyan barcin da ya samesu suka ga kansu a inda ba'a nan suka kwanta ba. Cikin matsanancin firgici suke kallon juna kafin su miƙe duk a zabure su fara dube-duben inda suke ɗin. Falo ne madaidaici sai dai akwai komai a cikinsa sai bedrooms guda ɗaya mai ɗauke da gado biyu, sai kitchen. Ko ina a kulle yake ta hanyoyin waje sai dai suna iya hango makeken ruwan daya zagaye ko'ina da ina ta cikin gilashi. Basu iya ganin mutanen da ke kai kawo balle iya jiyo hayaniya saboda gilashin manne da ginin bullet proof ne. Yunwar da Lulu keji dan a yanzu sam bata da jimirinta ya sata fara jin yuuu-yuuu kamar jiri zai yadda ta. Da sauri takai zaune cikin rawar murya tace, “Ummita yunwa”. Hankalin Ummita ya tashi matuƙa dan haka ta miƙe cikin rawar jiki ta fara dube-duben ko zata ga abinci, cikin aminci ALLAH ta ganshi an ajiye a gefe kan ƙaramin dining table mai kujera biyu. Ɗakko mata tayi, jikin Lulu har rawa yake wajen karɓar abincin ta fara turawa, duk da baya mata daɗi haka takeci ko zata samu nutsuwa. Tan kammalawa ta fara sheƙa amai kamar zata fidda har hanjin cikinta. Ta jigatu matuƙa dan Ummita har da kukan ta, ita ta taimaka mata ta gyara jikinta ta canja kaya ta hau gado ta kwanta ta dunƙule a waje ɗaya cikin rawar sanyi, kafin wani lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufeta. Kuka sosai Ummita ta zauna ta dingayi, babban tashin hankalinta shine basu san wanene ya kawosu nan ba kuma. Duk da suna zargin Alh. Sulaiman sai dai zukatansu sun kasa zama waje guda. Sosai Lulu bata da lafiya gaba ɗaya a wannan daren, gasu a rufe balle Ummita ta fita ta nemo musu taimako. Sai da barcin wahala ya ɗauke Lulun ne Ummita ta samu damar tashi zuwa kitchen ta shiga bincike, ta ɗan samu nutsuwa ganin kayan abinci harda kayan tea, sai dai babu gyaɗa, ga shi a yanzu komai Lulu baci take ba da daɗin rai sai wannan kunun....        Kwanakin Lulu kusan uku tana fama da zazzaɓi kafin ALLAH ya bata lafiya ta dawo dai-dai, duk ta rame sai wani uban haske data ƙara. Kamar ance su dawo nan ciki ya fara girma, ga shi bata samun kunun gyaɗar da take so sai ɗan tea da take sha kaɗan-kaɗan, abincin ma Ummita kan zauna taita lallaɓata har sai taci ko yaya ne, duk da data gama take yin amansa. Wani bai taɓa zuwa musu ba, sai a randa suke cika sati guda ne suka wayi gari suka ga an ajiye musu kayayyakin abinci dana buƙata a falo, ciki harda gyaɗa abin mamaki. Kallon-kallo kawai sukeyi, a ransu sunajin tabbacin duk abinda sukeyi kenan ana sane da su. Murmushi Lulu ta saki a karo na farko, dan dama kawo su nan ya tabbatar mata da hasashenta akan kawun nata kenan. Basu da hurumin cewa bazasuci abinda aka kawo musun ba, sai dai Ummita kan zauna ta tofeshi da addu'oi sannan. Wannan abin da take ɗin ne ya sake sakama Lulu nutsuwa da ita. A hankali shaƙuwa ta cigaba da shiga tsakanin Ummita da Lulu, har takai yanzu Ummita na ɗorama Lulu karatun Alkur'ani da na wasu littattafan addini da take da su kamar yanda Lulun ta buƙata. Sannan cikin dare Ummita kan tashi tai nafilfilinta, tun Lulu najin damuwa da takurar hanata barci da Ummita keyi kasancewar bata saba da zama mutum biyu a ɗaki ɗaya ba har itama ta fara tashi tana sallar. Hakan ya saka Ummita a farin ciki sosai, haka itama Lulun wannan yanayin na sata jin farin ciki da jinta kamar wata sabuwar hallita, dan wata sabuwar nutduwa ce ta sake zo mata. Kullum sai Ummita ta mata addu'a ta bata a ruwa ta sha, sannan takan gaya mata wasu akan ta dingayi tana shafe cikinta da shi. A haka suka cika wata ɗaya a wannan juyayyen waje da basu san inane ba, sai dai hakan bai hana Lulu cigaba da tattara bayanai akan kawun nata ba, ranar da suka cika wata guda sai ga baƙonsu na farko daya fara ziyararsu. Wato Nurse Usman, babu wanda ya ganesa a cikin su Lulu, shi kuma bai nuna musu sani ba ya ce kawai yazo duba lafiyarta. Da taƙi sai yay kiran Alh. Sulaiman. Wannan ce ranar ta farko da su Lulu suka fahimci wanda ya kawo su nan ɗin duk da ita dama Lulu ta gama bama zuciyarta shi ɗinne. Al'amarin ya sake dilmiya Lulu a kogin mamaki game da abinda kawun nata ke yi akanta, sai dai batace komai ba ba kuma ta hana Nurse Usman ɗin yin aikinsa ba duk da tana ɗar-ɗar tana son a na duba mata lafiyar jaririnta kuma, shot note da Usman ya ajiye mata ya sakata sakin ajiyar zuciya. Shima sai yay mata ɗan guntun murmushi. Ya dubata tare da bata magunguna bayan ya tabbatar mata da lafiyar cikin nata. Tai masa godiya ya tafi. Sunyi mamakin ganin bayan ya kammala sai da ya kira akazo aka buɗe masa ƙofar sannan ya fita, hakan na nufin akwai wani a waje da ke gadinsu kenan ma kamar acan inda suka baro. Ganin Ummita zata saka damuwa a ranta Lulu tai mata murmushin kwantar da hankali. Note ɗin Usman ta miƙa mata, sai ga Ummita na murmushi da sauke ajiyar zuwa. Lulu ta lumshe idanunta a hankali ta furta “Yanzu kin fahimci wasan namu ne ko? Karma ki tadama kanki hankali yanzu lokacin tattara bayanai ne, dan haka babu buƙatar cigaba da shiga damuwa kuma farin ciki kawai domin kama tsuntsu mai wayo”. Ƙaramar dariya Ummita tayi, yayinda a ƙasan zuciyarta tamaji ta fara tsoron Lulu, dan fa ta fahimci atsabibiyar kanta ce ashe..... Tun daga wannan ranar Lulu da Ummita suka sake sakin jikinsu tamkar basu da wata damuwa, ga ciki nata haɓaka da bunƙasa cikin ƙoshin lafiya. Ganin yanda suka sake jiki da walwala ya saka Alh. Sulaiman bada umarnin a ɗan dinga buɗe su, sai dai yana son duk inda suka saka ƙafa a tsibirin nan yana sani. Dan ya zagayesu da mutanensa kusan goma batare da sun sani ba. A cewarsa yanzu plan zai fara. Kamar yanda itama Lulu take ji a ranta yanzu wasan zai fara........✍️ _🤣🤣Hahaha anayi muna cin gyaɗa mai gishiri🥱🥱🚴_ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣6️⃣ .......Tun a randa suka fara fitowa Lulu ta fahimci zagaye suke da idon yaran Alh. Sulaiman, amma maimakon ta razana sai ma tayi murmushi. Batace da tacema Ummita komai ba akan hakan, sai ma zunguran Ummita data shigayi game da sanin wacece ita? Da yanda akayi ta yarda ta biyosu Canada. Tuni hawaye suka cika idon Ummita. Bata hanasu zuba ba sannan bata sharesu ba, sai da ta jiƙe gaban rigarta sosai kafin cikin shashshekar kuka ta ce, “Sunana na yanka Fatima. Naci sunan kakata ne shiyyasa ake kirana Ummita. Asalinmu ƴan wani garine ɓagwai a ƙauyen bichi. Anan nai karatun primary ɗina, da ga baya aka kaini boarding school a wata makaranta da ake kira GGASS Ɗan/zabuwa. Naje har js 3 aka cireni na koma cikin garin Kano hannun yayata da ke aure acan sakamakon rashin lafiya data kwanta. Jeka ka dawo na koma zuwa ina kula da yayata a gidan mijinta tsahon shekara biyu harta fara samun lafiya. Tun ban wuce shekara ɗaya a gidan ba mijin yayata ke nunamin wasu abubuwan rashin ɗa'a, sai dai bana kulashi sai da naga abin na neman wuce gona da iri na nuna inason komawa gida dan ban son faɗama yayata na tayar mata da hankali. Amma sai iyayenmu sukaƙi yarda yayar tawa ma harda kukanta, acewarta idan na tafi wazai ringa kulawa da ita da ƴaƴanta biyu kamar ni. Tausayinta ya kamani sosai, dan haka na haƙura na zauna, sai dai na ɗauki matakan kare kaina tako ina har takai mijin nata shima ya daina shiga sabgata ya kama kansa. Ashe lumbu-lumbu yay min, dan sai da ya bari na shagala sannan a wani dare ina gab da kammala ss3 ya bankama yayar tawa maganin barci ya keta mun mutuncina. Maganin daya banka mata yay sanadin barinta duniya, na shiga tashin hankali irin wanda baida misali, sai dai na gagara faɗama kowa asalin al'amarin har akai sadakan uku. Ina murna zan koma gida sai babana yace na zauna tare da gwaggonmu mu kula da yaran harna ƙarasa jarabawar neco da waec da zamu fara. Naso tada hankalina amma akaita tausata, ganin akwai gwaggonmu ya sani jin zan daure ɗin. Mun fara jarabawa ina a cikin yanayin rashin jin daɗin jikina. Haka dai naita daurewa yayinda iyayenmu a bayan fage batare da sanina ba suke shirye-shiryen aurar da ni wa mijin yayata matsayin madadi waina riƙe yaranta. Da farko ya yarda sai dai a randa muka gama jarabawar ƙarshe na kaita a wahalce, tun daga makaranta aka wuce dani asibiti, inda a gwajin farko aka sanarma gwaggona da tazo inada shigar cikin wata biyu. Tashin hankali kenan wanda ba'a saka masa rana, babu bin ba'asi babana ya hau dukana Sakamakon zugar da mijin yayata yay masa akan dama ance ina yawon banza ai, baya son ya faɗa ne ace dan karya auranne yake son zamewa. Iya jijjiga kamalamansa sun jijjigani, yayinda ɓacin rai ya saka baba rantsewa bazan zauna masa a gida ba. Hankalin mahaifiyata ya tashi, amma sanin halin mahaifinmu ya hanata cewa komai, sai shawarar turani Abuja data yanke wajen ƙaninta. Matar ƙanin mamana na samu damar warwarewa komai da ya faru, ranta ya ɓaci matuƙa ita da ƙanin mamana, dan haka suka ɗaukeni muka juya Kano suka shigar da ƙara kotu tare da neman lawyer daya san aikinsa sai aka haɗamu da ke. A lokacin baki jima da dawowa Nigeria ba kamar yanda naji ance, dan hausanki ma ba wani sosai yake fita ba. Kin taka rawar gani a rayuwata ta hanyar tabbatarma mijin yayana MACE MUTUM ce (Rahma Abdull-majeed. Wanda bai karanta littafin nan ba wlhy anyi bashi🥱). Dan sai da kika turashi gidan yari har yanzu kuma yana can. Uncle ɗina bai saurari iyayena ba da suka shiga nadama sosai ya ɗakkoni muka sake dawowa Abuja. Inda ya nema min makaranta na fara. Ga rainon ciki inayi, cikin danai matuƙar tsana a rayuwata har ALLAH ya kaini ranar haihuwa. Sai dai alhmdllh jariri baizo da rai ba. Hakanne ya sani farin ciki na maida hankali a karatuna. Bana zuwa gida saboda gudun zunɗen mutanen ƙauye harna kammala karatu na na samu result mai ƙyau, ina cikin neman aiki ne sai ga Hajiya Shuwa a gidan mu kasancewar tana huɗɗa da aunty na, tana kawo mata turaren wuta. Jin ina neman aikin taimin tayin wannan aikin, sai dai tace aikin na shekara ɗaya ne kacal shiyyasa kawuna ya amince da sauri, ni dai bance komai ba dan banjin zanje ɗin, sai a randa na ganki matsayin wadda za'aima aikinne ya sani yarda da sauri-sauri domin rama alkairi da kikai min nima....”        Tuni hawaye sun jiƙe fuskar Lulu, jik 10inta har wani tsuma yake kamar wadda ake kaɗama gangi. Lura da hakan ne yasa Ummita kamata suka koma ciki batare da ma lokacin da aka basun ya cika ba.....                 _________★    A ɓangaren Dada tun a washe garin da Alh. Sulaiman yasa aka canjama su Lulu wajen zama yay kiranta cikin tashin hankali da makirci yake sanar mata baiga su Lulu ba, yazo gida ya samu sun gudu. Yasa ƴan sanda nemansu da ga baya suka fahimci sun bar ƙasar ne da taimakon wani dan har note aka bar masa. Hankalin Dada yay masifar tashi har takai ta kasa controlling kanta Baba Garko ya fahimta. Tambaya ya shiga jera mata wadda ta kaita da gaya masa cewar Lulu ta gudu da ga Canada, kuma suna zargin wani ne ya sace ta. Cikin matuƙar mamaki Baba Garko ya ce, “Canada kuma Hajarah, miya kai Mawaddat Canada ko ita da mijin nata ne?”. Wannan kalma ta Baba ce ta dawo da Dada a hayyacinta. Duk kuma sai ta daburce ta rasa abin cewa  har takai Baba Garko ya daka mata tsawa, tasan halinsa baya ɗaukar raini, idan ya juye mata takan rasa gane kansa, kafin yay hakanne akan jima shiyyasa take samun damar iskancinta. Waya ya ɗauka ganin bazata bashi gamsashiyar amsar da yake buƙata ba yay kiran Daddy. Sai dai wayarsa taƙi shiga, yasan hakan nada nasaba ne da yanayin network. Ganin zancen waya ma bazai bashi yanda yake buƙata ba a ranar ya saka autansa namiji da tunda yazo da iyalinsa bai koma Saudiyya inda yake aiki ba ya yanka musu ticket, dan yace yau bazai sake kwana a ko'ina ba sai a Nigeria, saboda ya fahim al'amarin babba ne. Hankalin Dada ya sake tashi, amma tasan a wannan gaɓar bata isa yi masa wani daɗin baki ya dakata ba, dole ta shirya suka wuce a tare.       Sunma Nigeria ƙasar haihuwarsu saukar dare, hakan sai ya sirranta dawowar tasu suka samu damar isa gida cikin kwanciyar hankali. Kowa ka gani a gidan Baba Garko ma'aikata cikin farin ciki yake da samun lafiyar tsohon abin son kowa. Mai tausayi da son ƙyautata rayuwar na ƙasa da shi, mai jan ɗan aiki jikinsa tamkar ɗan uwa ba bawa ba. Bayan albashinsu da ba'a taɓa tauyewa ba a koda yaushe cikin musu alkairin yake. Ko Zakka ya fitar sukan samu kaso mafi tsoka duk da Dada bata son hakan. Sannan duk abinda ya samu iyalansu ko lafiyar jikinsu yakance su sanar masa dan shine da hakkin wannan. Wannan yasa su jin ƙaunarshi da shiga a tashin hankali a duk lokacin da suka ga yana a cikin damuwa ko farin ciki. Sam hankalin Dada baya a jikinta, suna isowa sashenta ta wuce, layinta na Nigeria ta ɗora a waya sai dai kafin ya gama dai-daita duk ta ƙosa, hakan ya sata amsar wayar mai aikinta domin kiran Daddy. Amma abin mamaki sai ta samu number busy, bata kawo a ranta da mijinta Daddy ɗin ke kiran ba, dan haka ta cigaba da jera masa kira. Shiko Daddy dake waya da Baba Garko ganin baƙuwar lamba ce yasa koda ya kammala bai ɗaga ba, ganin ma za'a damesa ya sashi saka wayar a airplane mode kawai. Haukane kawai Dada batayi ba a wannan dare jin daga baya ma ta daina samun Daddy ɗin. Karo na farko da taji takaicin rashin riƙe number kowa na jikinsa da ga shi sai Lulu. Dan ko Yousuf ita bata da lambarsa. Matarsa kuwa (Mommy) dama ba huɗɗa take da su ba. Barcin kirki dai Dada bata sameshi a wannan daren ba sam. Tana sallame sallar asuba sai kuma ta fara jerama Daddy kira, sai dai har lokacin wayar bata shiga. Gaba ɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta kuma kasa zuwa inda Baba Garko yake. Dan gani take kamar yana riga ya gama jin komai da komai. Tayi kiran Sulaiman kuma shima wayarsa bata shiga ba sam... A ɓangaren Baba Garko ya gama fahimtar akwai matsala, sannan koma minene akwai saka hannun matar tasa a ciki. Yay kiran Daddy kuma dan yaji gaskiyar zance game da zuwan Lulu Canada sai ya samu numbersa busy. Akan Uncle Yousuf ya maida akalar kiran nashi, inda yaji komai da komai, yana gama wayar da Uncle Yousuf ɗin ne kuma kiran Daddy ya shigo masa. Maimakon ya tambayesa kamar yanda ya tambayi Uncle Yousuf sai ya canja kawai suka gaisa ya sanar masa yazo Nigeria, yana son da safe ya samesa a gida da wuri. Daddy yayi farin cikin jin Baba ya samu lafiya, sai dai ya shiga mamakin jin kiran gaggawa da yake masa. Wanda yasan koda bai kirashi ba tunda yaji ya dawo ƙasar da safen dole zaije gidan duba shi.           Zuwa ƙarfe bakwai da rabi duk wanda Baba Garko ya buƙaci gani a gidan nasa ya iso. Dan harda ƴaƴansu ƙannen Alh. Sulaiman ɗin. Uncle Khamil da auta da suke kira Uncle Sadiq ne kawai babu dan shi sun barosa acan, sai kuma Alh. Sulaiman da shima dai fushin da Baba keyi da shi yasa bai saka shi a cikin meeting ɗin gaggawar ba. Sosai kowa ke cikin farin ciki da ganin yanda mahaifin nasu ya samu lafiya kamar bashi ba. Zamansu babu jimawa ƴan sandan dake bincike akan case ɗin sa suka iso gidan. Ya ce suyi haƙuri suje zuwa anjima zai nemesu yanzu yanada muhimmin uziri ne da iyalansa.......✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣7️⃣ ______________ *3 DAYS CLASS* Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rararar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rararar kudinne sakamakon rashin neman scholarship da bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka canza kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni Class ze fara ranar jumaa insha Allah WhatsApp group 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/Ir0qcUHVd8VI3tTlCHPeIA WhatsApp 08144147273 _________________ ........Bayan anyi gaishe-gaishe da taya juna murnar samun lafiyar Baban kai tsaye ya jehoma Uncle Yousuf tambaya kamar jiya. Uncle Yousuf da tunda suka shigo bai kalli inda Daddy yake ba, ko gaisuwa sama-sama yay masa kansa tsaye ya fayyace komai kamar yanda ya faɗama Baba Garkon a dare jiya. Jikin Dada tuni ya jiƙe da zufa, amma tsabar makirci sai ta fashe da kuka wai Uncle Yousuf ɗin ya haɗa mata harda sheri dan ya baƙantata kawai. Ita koda ta ɗakko Lulu dan bata da lafiya ne ta ɗakkota.....” tsawa Baba Garko ya daka mata da cewar, “Yima mutane shiru mutuniyar banza da kullum bata sanin ta girma a rayuwarta. Bance miki ki fita cikin al'amarin auren yaran nan ba tun farko? Rashin lafiya shi mijin nata ne yay dake bazai iya kula da ita ba? Ko kin fishi sanin abinda ya dace yayi akan iyalinsa?!.”.         “Ka gaya min. Kuma ni naga shi ba wani kuɗin da zai iya kulane da ita ga resa ba”.     “Mtsoww zancen banza kenan. To raini ne da son tozarta ni da nunama duniya ban isa ba ya saki zuwa ki ɗakko yarinya a ɗakin mijinta har ki kaita wata ƙasa?”.     “Bafa haka bane sam Alhaji ka fahimceni, yarinyarfa da bakinta ta fayyace min gaskiyar manufar auren .......” nanta ta kwashe komai da komai da Lulu ta sanar mata ta faɗa musu. Karo na farko Uncle Yousuf yay murmushi, yayinda Uncle Muneer ɗanta dake bima Alh. Sulaiman cikin son danne ɓacin ransa da taushin murya kamar yanda ya saba girmamata matsayin mahaifiya ya ce, “Amma Dada duk da a ta gaya miki haka a matsayinmu na wanda muka fita hankali nazata zamu taimaka mata ne ta hanyar kwantar mata da hankali ta haƙura ta zauna a ɗakin mijinta dan yaron nan mutumin kirki ne da duk wasu iyaye na ƙwarai zasu so haɗa zuri'a da shi”.       Harara Dada ta ɓalla masa, yayinda Baba garko ya amshe da “A'a ina zatayi haka ga matar ƙaruna ƴar ƙaruna kuma da hankali bai gama game mata jini ba, ai Mawaddat ɗin ma ta fiki hankali. Wai Hajarah mi kika ɗauki rayuwa ne? Mi kika ɗauki dukiya ne? A zatonki dan ALLAH ya yomu a haka mun zama mafifitane a cikin mutane har a wajensa? Kamar yanda talauci yake jarabawa itama dukiyar da kike gani jarabawace. A wani fanin ma babbar fitina ce ga bawa. Shekara nawa ya rage miki a wannan duniyar da har kike jin wai dukiya har zata cigaba da zame miki abin tinƙaho. Ba tonon silili ba naga ai kema ɗiyar talakawance amma na aure ki, ƙarewa ma mahaifinki masinja yake ga mahaifina mutuncinsa da sanin Yakamata yasa mahaifina cewa na auri ƴarsa. Ban yi musu ba kuma na aureki nake zaune da ke har tsawon shekarun nan matsayin ke kaɗai matata Ashe albasa batai halin ruwa ba....”          Sosai Dada ta daburce dajin kalaman mijin nata irin wanda koda kwatance bai taɓa yinsu gareta ba tun aurensu. Su kansu yaran sai da sukaji shock su dukansu. Dan basu taɓa sanin wannan tarihin ba kasancewar a sanin da sukaima mahaifin mahaifiyar tasu hannunsa a jiƙe yake, sosai Baba kema Dada cin mutunci da ya sakata kuka rurus, agaban ƴaƴan nata ya kuma turketa saita gaya masa inda suka kai Lulu koya bata mamaki da hukuncin da bata taɓa zato ba. Ganinfa ruwa ya ƙarema ɗan kada dole Dada ta fayyace komai game da kai Lulu Canada ita da Alh. Sulaiman harma da yunƙurin zubar mata da ciki da sukayi amma bai fitaba sai da ga bayan nan kuma suka gane hakan, sai kuma kiran da Sulaiman yay mata a jiya cewar ya nema su Lulu ya rasa wai wani ya sacesu, amma yasa ƴan sanda na bincike. A yau da safe kuma yake turo mata text message akan yana zargin Yousuf ne da Smart. Da matuƙar mamaki Uncle Yousuf ke kallonta cikin nuna kansa ya ce, “Ni Yousuf ɗin ko wa?”.          “Inba kaiba waye Yousuf anan, munafuki algungumi. Ai dama kana biye damu tunda muka ɗauke ta kai da shegen yaron nan mara kunya dan bakinku ɗaya ne dama. Dan haka saiku fito da ita tunda ankai ga yanda kake so”.       Tuni fa falo ya hargitse, dan sai kawuna kuma suka nema rabuwa. Yayinda Daddy da tunda ya shigo falon baice komai ba ya zuba musu ido kawai. Hakama Baba Garko. Cikin ɓacin ran yin shirun Daddy Uncle Yousuf ya tashi ya fice a falon dan zuciyar ƴan maza ta motsa da gaske a yau. Ganin bazasuyi shiru ba Baba Garko ya katse hayaniyar tasu da faɗin, “Hajarah kije na sakeki saki biyu, kuma ki barmin gidana a yau har sai kun maido Mawaddat idan da yiwuwar ki dawo sai ki dawo”.        Waɗan nan kalmomi masu dukan zukata na Baba Garko ne suka saka falon yin tsitt, yayinda ya miƙe abinda ya shige cikin bedroom ko waiwayen su bai yi ba. Dada kam da taji kanta na juya mata sai ganinta kawai sukai a ƙasa babu numfashi. Cikin tashin hankali sukai kanta. Duk hayaniyar da ake Baba na jinsu amma har suka kwasheta zuwa asibiti bai ki leƙo ba.      Wannan shine sanadin kwanciya Dada a asibiti na tsawon sati biyu tana jiyya, dan hawan jininta ne yay masifar motsawa. Koda ta samu sauƙi kuma Baba yace duk wanda ya kawo masa ita gida a cikin ƴaƴan nasa wlhy sai ya kwashe masa albarka. Duk kuma wanda yazo yay masa maganarta a gidan nan ma sai ya kwashe masa albarka. Wannan ya saka yaran tsorata matuƙa dan sun san wanene mahaifin nasu akan zuciya, balle yanzu ya sake birkice musu irin yanda basu taɓa gani ba. Gashi sunata kiran Alh. Sulaiman dake matsayin babba garesu kuma silar wannan tashin hankali amma sam sun gagara samunsa. Dole dai aka wuce da Dada gidan Uncle Muneer aka gyara mata sashen baƙi....                  *_CANADA_*     Labarin Ummita da Lulu taji ya ƙara musu shaƙuwa matuƙa, yayinda Lulu ta fara tunanin buɗe ƙungiya domin taimakon yara marasa zuwa makaranta dan al'amarin yaron nan data taɓa amsar Number a wajensa bisa titi har yanzu yana ranta bata manta ba, tana jin babu daɗi kuma da bata sami ziyartarsa ba. Ƙungiyar zata riƙe abubuwa uku ne. Karatun yara da rashin galihu ya hanasu yi, sai harkar fyaɗe da kuma shaye-shaye. Ɗari bisa ɗari Ummita ta bama Lulu goyen baya game da wannan ƙyaƙyƙyawan ƙudiri nata. Dan haka suka hau tsare-tsaren su kamar waɗanda akacema gobe zasu bar wannan wajen. Lulu ta cigaba da rainon ciki yayinda Usman ke zuwa dubata da bata magungunan ƙarin lafiya ita da abinda ke cikinta. Alh. Sulaiman kuwa na tunanin allurar gubar da zata ruɓar da tayin cikin Usman ke mata. Akwai fahimtar juna sosai a tsakanin su Lulu da Usman, dan shi ke kawo musu duk wasu bayanai akan Alh. Sulaiman, sai dai a rubuce yake basu, a zahiri kam babu wata alamar dake nuna ko kallon arziƙi sunaima junansu. A haka a haka dai har ALLAH ya kai cikin Lulu haihuwa. Inda ta koma zama da ƙyar tashi da ƙyar. Gaba ɗaya ta canja kamanni saboda kumburin da taɗan yi, dan ma Ummita baiwar ALLAH tsaye take a kanta yanda ya kamata, bata gajiya da yima Lulu da abinda ke cikinta addu'a. Ga Usman na iya bakin ƙoƙarin sa akan komai nasu ciki harda fara shirya musu hanyar guduwa daga tsibirin. Lulu bata taɓa kiran lambar kowa ba tun sanda ta gwada Alh. Sulaiman ya ɗaga. Tunda aka kawosu gidan bai zo ba ko sau ɗaya, hakan ya sasu fahimtar kodai duk cikin takune ko kuma baya ƙasar ne.....    *_UK (LONDON)_*       A ɓangaren Smart wasannin link sun cigaba da tafiya cike da nasarori harma da ƙalubale, inda ALLAH ya ɗaga darajar team ɗin su suka ƙare da maki tamanin da shida, Smart ya jefa ƙwallaye ashirin da bakwai. Hakan ya sashi zama best player na wannan kakar wasa ta bana a ƙasar England, inda ya samu ƙyautar takalmin zinare, team ɗin su kuma ya samu damar shiga babbar gasar premier link na england. A randa su Smart sukai wasan ƙarshe ne ya kasance dai-dai da randa Lulu ta wayi gari da naƙuda. Hankali tashe Ummita tai kiran layin Alh. Sulaiman, amma sai ya amsa mata a daƙile cikin halin ko'in kula. Sai da yaga Lulu na neman rasa ranta sannan yay kiran Usman akan yazo ya dubata, a kallo ɗaya Usman da yay mata ya tabbatar da Alh. Sulaiman cewar dole fa akai Lulu asibiti, dan theatre ya kamata ai mata tilas. Da farko Alhaji Sulaiman ya ɗauki abun babu wasa, sai da fuskanci zai iya rasa damarsa sannan ya amince aka a wuce da Lulu asibiti can cikin gari dan shi tunaninsa mutuwar ɗan a ciki ta jawo hakan. Dai-dai ana shiga da Lulu ɗakin theatre Smart da gabansa keta faduwa ya zira ƙwallo a minti ɗayan ƙarshe da ya rage a tashi wasan. A take garin ya ɗauki ihu, yayinda ya kai ƙasa yay sujida hawayen farin ciki na ziraro masa. Gaba ɗaya teammate ɗinsa sukazo kansa aka rungume juna, suna mai ɗunbin farin cikin shiga a jerin manyan team na duniya da zasu buga primier link kenan, abinda ko'a mafarki ba'a taba kawo musu ba. Amma Alhamdullah sai gashi a dalilin ɗan baiwa kamar yanda suka sakama Smart sun shigo cikin jerin masu nasara. Sosai London City take a hargitse yau anata selebration, su Smart na cikin wata irin doguwar mota mai masifar ƙyau da ɗaukar hankali hannunsu rike da kofin da suka ci suna ɗagawa masoya. Wasu a cikin teammate nashi har cire riguna sukai suna jefama fans. Shi kam dai murmushin sa yake mai ƙayatarwa cike da nutsuwa yana mai ɗaga hannayensa duk biyu, yayinda idan idonsa yakai kan yara yakan ma hannun nasa kiss ya hura musu, sai kaga yaran na maido masa da kisa ɗin suma, jin farin cikin yake tamkar ya zarce na cin ƙwallo a zuciyarsa yau, dan fargabar ɗazun nan da faɗuwar gaba duk ta gudu saboda addu'oin da yake ta yi. Haka suka dinga zagaye cikin London City a wannan mota, inda ta ko ina suka gitta imasoyane ƴaƴa da iyaye harma da kakanni da suka fito domin kallonsu. Sunan Smart Mawashi yasha kira a wannan rana tamkar zai ƙare duk da yanda suke kiran Mawashin abin dariya, sai yaji har hawaye na cika masa ido da wannan al'amari da rahama ta UBANGIJI. A rayuwa ai babbar rahamace ma kaga mutum ɗan uwanka na nuna maka irin soyayya balle kowa yasan Bature akan ƙyamar baƙin fata a zahirance.         Wannan fa nasara ta Smart ta saka hankalin manyan club na ƙasashen turai gaba ɗaya irinsu Italy, Spain, Germany France etc... dawo wa kansa, yayinda aketa kaikawo da cecekuce akan al'amarin yaron a wannan yini, kowacce kafar yaɗa labarai kaje a ƙasar ta England musamman a fanin ƙwallon ƙafa zancen kenan dai Smart Mawashi, Smart Mawashi.. Al'amarin kamar busa usir na alƙalin wasa. Cikin ƙanƙanƙanin lokaci manyan clubs ɗin suka fara ƙwaɗayin nuna zawarcinsa ta ƙarƙashin ƙasa........✍️ _To insha ALLAHU dai mun kusa zuwa gaɓar da komai zai cigaba da tafiya a buɗe, ina zazu ɗin nan ne ɗan can mu samesa yanda muke so🥱 dan nasan kunfi kauri acan😜🚴🚴🚴_ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣8️⃣ .........*_CANADA_*    Sosai Lulu ta riga ta sakama ranta tsoron haihuwar ne, duk yanda su Usman suka so ta haihu da kanta hakan na neman gagara. Ga naƙudar tata da gani mai zafi ce, dan tayi wujiga-wujiga a ƙanƙanin lokaci. Tun ma tana hawayen har idanun sun bushe, Ummita dai nata maimaita mata addu'a tana faɗa. Har ALLAH ya isa sai da tama Smart cikin fitar hayyaci😜, akace kuma sai anyi Shari'a da shi yayi jail😂. Abin yaso bama Usman dariya ya dai danne da ƙyar. Dr Lameer yaja Usman gefe cikin damuwa ya ke faɗin, “Ussy inaga fa muyi mata CS ɗin nan kawai, ta riga ta saka tsoro a ranta ga shi kuma jinjirin yayi girma da yawa sosai saboda ciye-ciye data dingayi. Sannan an taɓa taɓa cikin hakan ya raunana mata mahaifa. Amma da ace bata saka tsoro a ranta ba wannan bakomai bane zata iya haihuwa da kanta. Yanzu kam ina tsoron kar wahala tasa mu rasa abinda ke cikinta”.        “No no Doctor bana fatan a rasa babyn nan wlhy, inaga kawai ayi mata cs ɗin”.            “Shike nan babu damuwa, wazai saka hannu a cikinku?”.       “Bara na saka hannun kawai ni”.     Alhamdullah an samu nasarar zaro baby boy a jikin Lulu ƙamshi. Lafiyayyen yaro ƙyaƙyƙyawa da bai baro komai na ubansa ba, ga shi ƙaton gaske masha ALLAH. Dan hatta wani tawadan ALLAH da Smart ke da shi a gefen kunnensa babba shima jinjiri na da shi. Ankai Lulu ɗakin hutu, yayinda Ummita ta rungume yaro tana mai jin ƙaunarsa a ranta kamar jininta. Shi kansa Usman yaron ya shigar masa rai. Bai kira Alh. Sulaiman da ke can yana jiran ace Lulu ta haihuwa ɗa a ruɓe ba, dan yau shine target ɗinsa akan kuɓutar da su Lulun dama. Shi yay duk wani tsare-tsarensa na nemawa Lulu transper da taimakon Dr Lameer zuwa wani ɓoyayyen ƙaramin asibiti a Derby city. A wannan daren aka fita da Lulu cikin ambulance da Ummita, abinka da turai tsaro kaca-kaca hankalinsu kwance suka iso Derby city zuwa gabannin asubahi. Sanin Alh. Sulaiman zai iya bibiyarsu komai ya tafi ne akan tsari da kulawa. Dan wani gida ne a kusa da asibitin aka ajiyesu, acan gefen gari wajen ana noman fruits, sai gidan abinci da ke gaba kaɗan kasancewar babban hanya ce, sannan bature shi babu ruwansa da daji duk inda yay masa alƙarya ce. Komai da Lulu zata iya buƙata na kulawar lafiyarta su Usman ya tanada a gidan, dan bashi da damar barin ƙasar da su a yanzu kasancewar passport nasu na hannun tsule, fita dasu kai tsaye zai zama mai wahala.        Kusan ƙarfe takwas Lulu ta dawo hayyacinta, inda cikin amincin ALLAH ta farka bakinta ɗauke da addu'a. Da sauri Ummita da ke zaune a gefenta rungume da jariri dake ta barcinsa tai saurin kallonta da faɗin, “Alhamdullah aunty kin farka?”. Idanu kawai Lulun ta zuba mata ita da jaririn, sai kuma ta sauke numfashi a hankali da motsa lips ɗin ta tana mai bin ɗakin da kallo. “Ina ne nan Ummita? Miya faru da ni?”. Cike da farin ciki Ummita ta ce, “Aunty an miki C'S ne ga baby boy mun samu, nan kuma sabon wajene da Usman ya kuɓuto damu da ga hannun kawunki.” Lulu batace komai ba sai idanu data zubama jaririn hannun Ummitan, da sauri Ummita ta miƙe zuwa gabanta da jaririn, Lulu ta zuba masa ido zuciyarta na wani irin harbawa na masifa. Dan duk da yaron da sauran ɗanyantakarsa ta kasancewa jinjiri kamaninsa da mahaifinsa a bayyane suke. A hankali ta lumshe idanunta tana sakin wasu irin ajiyar zuciya a jajjere, sai kawai ta samu kanta da sakin kuka. Hankalin Ummita ya tashi, ta shiga jera mata tambayoyi akan ko wani waje na mata ciwo ne? Bata iya bata amsa ba har su Usman suka shigo, Dr Lameer ya dubata yayinda Usman ke faman lallashinta da tabbatar mata ta kwantar da hankalinta, insha ALLAH sun kuɓuta kenan, zai kumayi duk yanda zai yi na ganin sun koma gida Nigeria. Ummita ita ta bada shawaran ya kamata ama jaririn huɗuba fa, dan haka suka tambayeta wane suna take so a saka masa. Ita kanta batama san lokacin da ta furta, *_“ALIYU”_* ba. Usman da ya saki wani ɗan murmushi ya ɗauki jinjirin yaymasa huɗuba da suna ALIYU HYDAR ZAKIN FAMA. tare da masa addu'a dan duk lalacewar Usman yanada iliminsa na addini. Kawai zama a waje ne ya sashi zama mara jin magana.         Lulu da idonta ke a lumshe a zuciyarta ta furta (ALLAH ya albarkaci rayuwarka *_Aliyu Aliyu Mika'il Mawashi_*) sai kuma ta ɗan yamitse fuska kamar wadda take jin hakan banbarakwai a zuciyarta...       _(To muma dai munce ALLAH ya raya Aliyu Aliyu Mika'il Mawashi. Dangin Smart kar ace bamuyi Barka ba🥱🚴)_                      *_NIGERIA_*     Sosai Daddy ke fama da ciwo a tsaitsaye, sai dai yanata dauriyar ganin bai bari ko Mommy ta fahimta ba. Sai dai ya gagara ɓoye damuwarsa akan halin da suke ciki tsakaninsa da ɗan uwansa Yousuf. Yousuf nada matuƙar muhimmanci a garesa ta yanda baki bazai iya furtawa ba. Su fa kaɗaine ƴan uwansa shi da Mommy sai zuri'ar da suka tare a yanzu. Tunda yake da ɗan uwansa bayan rikicin Kasancewar Mawaddat (Maman Lulu) a rayuwarsu baya jin akwai wani saɓani daya taɓa shiga a tsakaninsu kamar haka da Yousuf ɗin ya ɗauki zafi da shi. Ba wai baya son fitowa ya faɗa masa gaskiyar al'amari bane, bai son tada masa da hankaline kawai ko sakashi a matsala. Shiyyasa ya zaɓi shanyewa shi kaɗai a tsahon rayuwa. Amma yana gani a wannan gaɓar in har yana son ɗan uwan nasa ya fahimcesa dolene ya buɗe masa sirrin nan dai da yake ta faman biznewa a tsahon shekaru badan tsoro ba sai don dalilai guda biyu. Na farko baya son tarwatsa farin cikin family ɗin mutum mai mutunci da daraja a rayuwarsa irin Alhaji Sufi Ado Garko. Ya taka rawar gani a rayuwarsa da har a yanzu ake iya kallonsa a nuna a matsayin wane. Duk da yasan wannan rubutaccene daga UBANGIJI ko babu shi ɗin komai zai iya tabbata. Amma UBANGIJI ya sakashi zama matsayin sila. Idan ya kasance mai tarwatsa farin cikin wannan ahali yana jin kamar ya rama sharri ne da alkairi. Na biyu shine kare rayuwar yarinyarsa duk da yasan shi bai isa hana komai ba daga ƙaddarar ALLAH. Tunda gashi nan a sanadin hakan har Lulun ta faɗa shaye-shaye batare da ya iya bata kariya akan hakan ba. Hasalima bai taɓa sanin tanayi ba sai a shekarar nan. Tun daga ranar jikinsa yay sanyi matuƙa da sake tabbatar da wayo ko dabara bata kare maka abu sai UBANGIJIN talikai masanin sirrin fili da ɓoye. A hankali ya kai hannu ya ɗauke ƙananun hawayen da suka ciko masa idanu. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi da ɗaukar wayarsa ya rubuta gajeren text message wa Uncle Yousuf ya tura masa, duk da yasan a gajiye yake dan jiya ya dawo daga UK kamar yanda yake ji a bakin Mommy dan shi dai Uncle Yousuf ɗin bai sanar masa ba sam.        Uncle Yousuf na tsakiyar iyalinsa suna kallo, yayinda Deen da Ra'is ke home work text ɗin Daddy ya shigo masa. Kamar zai share sai kuma dai ya ɗauka ya duba ganin kallon da aunty Saliha tai masa. Shiru yay yana kallon text ɗin da bai wuce layi biyu da rabi ba. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya dan shima harga ALLAH yana azabtuwa da rashin ɗan uwan nasa a kwanakin nan. Dauriya kawai yake yi. Tunda ya san kansa bai taɓa wayar gari da yini harda kwana baiyi waya da yayan nasa da yakema kallon kamar mahaifi ba. Dan ko baya ƙasar sukan yi waya sama da sau uku a rana. Dan ƙa'idarsa ce duk safiya ko suna a ƙasa ɗaya ko basa nan zai gaishesa, sannan da dare kafin ya kwanta zai kirasa yay masa sai da safe. Idan ma bai kira ba bisa wani uziri na yau da gobe shi daddyn zai kirashi da kansa. Bayan wannan wayoyin biyu na ƙa'ida wasu wayoyin kan shiga a tsakaninsu game da Business ko wani muhimmin abu da ya shafesu. Jin zuciyarsa ta kasa nutsuwa waje guda ya miƙe yana kallon aunty Saliha. “Sweetheart ɗan bani key Please”. Da mamaki ta ce, “Key kuma?. Ina zakaje kaiko a daren nan kamar wanda ke a tarkon mace?”. Karan farko yay murmushin da bai niyya ba. Dan tun a kallon da tai masa sanda text ɗin ya shigo yasan akwai magana a bakinta. Komai baice ba sai wayar da ya miƙa mata. Dan tsakanin shi matarsa akwai yarda mai ƙarfi da fahimtar juna. Duk inda ƙofar zargi ta nema buɗe musu sukan yi saurin tosheta kafin a samu ɓaraka. Cikin sanyin jiki ta miƙa masa wayar da faɗin, “I'm sorry dan ALLAH, ALLAH ya bashi lafiya”. Murmushin kwantar da hankali ya mata da nuna mata hanya alamar taje ta ɗakko masa. Babu jimawa kuwa sai gata ta dawo. Ta miƙa masa tare da ɗan rungumesa. Bayanta ya ɗan bubbuga yana faɗin, “Thanks” daga haka ya saketa ya fice yanama su Deen bye bye. Duk da dariyar dake tasoma Daddy ganin yanda Uncle Yousuf ɗin yazo a ƙanƙanin lokaci yay ƙoƙarin danneta. Sai ma sake langaɓewa da yay. Cikin sassarfa da ruɗani Uncle Yousuf ya ƙarasa garesa. Sai faman jera masa tambayoyi yake a jajjere. “Yaya mike damunka? Dama baka da lafiya? Tun yaushe kake a kwance? Kasha magani? Miyasa baka kirani munje asibiti ba?”. Cikin murmushi Daddy ya kamo hanunsa dai-dai yana kaiwa zaune kusa da shi a bakin gadon nasa. “Irin wannan tambayoyi haka a jere auta wanne zan amsa a ciki?”. Kai Uncle Yousuf ya langaɓe gefe kamar mai shirin fasa kuka, dan da gaske yaga yayan nasa ya rame masa a idanunsa sosai. Daddy ya sake sakin murmushi tare da lumshe idanunsa. Sai kuma ya yunƙura da niyyar tashi. Da sauri Uncle Yousuf ɗin ya taimaka masa ya zauna da ƙyau. Shima sai ya zauna gab da shi sosai hannayensu cikin na juna. Cikin tausasa murya Daddy yace, “Kana fushi dani saboda ɗiyarka ko? Kayi haƙuri Yousuf kaji. Yayanka ba son zuciya bace ta lulluɓe masa ido. Idan ma a kwaita to ajizancine kawai irin na ɗan adam. In sha ALLAH yau zan fiddaka a cikin duhu tun daga lokacin da kuka fara tuhumata kai da Kareema har zuwa yau ɗin nan. Amma dan ALLAH ina son kai min ƙyaƙyƙyawar fahimta kaji.”        “Insha ALLAH Yaya”. Uncle Yousuf ya faɗa a sanyaye.......✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣9️⃣ ........Murmushi Daddy yay masa tare da sake damƙe hannayensu cikin na juna sannan ya fara da faɗin, “Tun ranar dana wayi gari da salwantar maƙudan kuɗaɗe a cikin Company hankalinna yay masifar tashi, nabi diddigi tako wane fanni amma ban fahimci komai ba akai. Na shiga ruɗani matuƙa da tunanin ta ina zan iya samun waɗan nan kuɗi haka, dan ko za'a saida duka ƙaddarar dana mallaka a wancan lokacin bazasu biya ko kaso biyu bisa goma na abinda ya salwanta ba. Ina cikin wannan ruɗani da ɗimuwar Alh. Sulaiman ya shigo rayuwata.........” kaf ya kwashe labari ya sanarma Uncle Yousuf da jikinsa ke wata irin tsuma, ga hawaye shaɓe-shaɓe kaca-kaca da fuskarsa kamar wani ƙaramin yaro. Shima dai Daddy ɗin hawaye yake, ya jawo Uncle Yousuf jikinsa ya rungume yana ɗan bubbuga bayansa alamar lallashi. Sai da yaji ya bar kukan sannan ya ɗagoshi. Zama Uncle Yousuf ya gyara cikin dasashiyyar muryarsa ya ce, “Yaya miyasa ka iya barin wannan babban al'amarin masu nauyi irin haka a ranka. Miyasa baka taɓa sanar damu ba dan ALLAH? Haba yaya har wanene Sulaiman da makircinsa da zai maka irin wannan ƙullin haka ka zauna kallonsa?”.         “Yousuf ka fahimceni hakan dolene a gareni saboda dalili masu yawa. Sannan ma lokacinne bai yiba shiyyasa, maybe UBANGIJI yay masa talalane da kuma hukuntani akan kuskurena nima. Na farko na yarda da shi da kallonsa da siffa irin ta mahaifinsa na mutumin kirki kasancewar a haka yazo min. Sannan bazan so maida sharri da alkairi ba a yanayin riƙon da mahaifin nasa yay min. Sannan dolene nayi komai domin kare ku a matsayinku na ahalina, dan shekarunka a lokacin sunyi ƙanƙantar da bazaka iya fahimtata ba yanda ya kamata. In da ban shanye komai ba za'a iya cutarmin da ku tako wace irin siga musamman ma kai, dan ko ita Kareema na hanata fita aikine daga baya bisa wannan dalilin, amma duk sai kuka fahimci cewar saboda Mawaddat ne. Eh saboda itane, dan ita ta ƙirƙiri hakan dan kuɓutar da Kareema daga sharrin Sulaiman batare da koni na fahimci hakan ba sai daga baya. Sai kuma lokaci da baiyi ba kamar yanda na faɗa, dan kasan komai na ALLAH ne sannan yanada lokacinsa.”        “Hakane Yaya na kuma yarda dakai. ALLAH sarki Maman Mawaddat munata zarginta akan abubuwa da yawa. Ciki harda tunanin ko asiri tai maka a farko, sai daga baya nima na fahimci ba haka bane saboda wasu dalilai. ALLAH ya gafarta mata ya yafe mata.”     Cikin lunshe idanu Daddy yace, “Amin Yousuf, ai shiyyasa zargi bashi da amfani. Akoda yaushe da ace munama duk wanda ya shigo rayuwarmu uziri akan al'amuran rayuwa damun zauna lafiya da samun salama a zukatanmu”.              “Hakane Yaya. Amma duk da haka akwai abinda kayi da har yanzu basu wanke a zuciyata ba. Na farko akan Mawaddat daka nisantata da samun karatun Addini dama sakaci akan tarbiyyarta. Na biyu nuna mata goyon baya akan duk abinda tai dai-dai ne harda nuna ƙyamar talaka a matsayin mijinta. Why Yaya? Bayan nasa wannan ba ɗabi'un da iyayenmu suka horar da kai bane ba”.        Ɗan jimm Daddy yay cikin tsantsar damuwa. Kafin ya ɗago idanunsa da suka kaɗa sukai jajur ya zubawa Uncle Yousuf. “Tabbas Yousuf wannan shine babban kuskuren da nai da cutar da rayuwar Mawaddat a rayuwata da bazan taɓa yafema kaina ba. Da farko halin Sulaiman ya rufemin ido da abinda naji dangin mahaifiyar Kareema na faɗa mata. Sai nake ganin nisantata da ƙasar kamar yanda mahaifiyarta ta roƙan tun farko kamar shine masalaha agareni da ita. Namanta shi UBANGIJI shine mai tsarewa a duk inda kake. Na tauye rayuwar Mawaddat akan rashin ilimin addini da kaita wata ƙasa da kafirci yafi ƙarfi a gaɓar da komai idan ta gani bazai zama abin ƙi ba a gare ta. Wannan itace jarabawata ni da ita. Maybe hakkin yarinya da Sulaiman yayma fyaɗe na ɓoye ne bayan nasan gaskiya UBANGIJI ya jarabceni da hakan, shaye-shaye kuwa a dalilin haɗa hannu da nai da su Sulaiman da bamu san iya adadin yaran da wannan safarar tamu ta gurɓatawa rayuwa ba duk da ban sani ba inaga shine nan UBANGIJI ya jarabceni akan ta. Sai kuma soyayyar da na dinga dana sani akan ƙin nuna ma mahaifiyarta har sai da ta roƙa gareta bayan ita ɗin jinina ce shima ya taka rawar gani. Sai tausayi da ya zama jagora Da silar zama komai. Ban taɓa ƙin Aliyu a zuciyata ba game da alaƙarsa da Mawaddat. Hasalima a kullum cikin tashin hankali nake kar adalilina su Sulaiman su cuta masa. Saboda har sacesa sun taɓa yi Sulaiman ya bashi aiki akanmu ni da ita. Amma yaron nan ko sau ɗaya bai taɓa gwada cutar damu ba. Yousuf baka san irin kalar ƙaunar da nakema yaron nan bane. Wlhy a duk sanda ya kawo Mawaddat gida nakan laɓe naita kallonsa da sanya masa albarka. Ko kuɗi da gida da mota dana bashi na bashine bada wata manufa ba sai don nima na ƙyautata rayuwarsa kamar yanda UBANGIJI NA ya ƙyautata tawa da silar Baba Garko, sai dai idan na fito da sigar da za'a kalla a masalaha komai zai iya faruwa da shi. Saboda yanda ya tsunduma kansa a al'amarin Mawaddat wanda na tabbatar zai iya cutuwa har sakawa nai ƴan sandan farin kaya na bin sa batare da ya sani ba. Inaga bayan aurenka ban taɓama wani aure kukan farin ciki ba sai na Mawaddat, dan a randa aka ɗaurashi na kwana yima ALLAH godiya, hakama randa ta tare na kwana roƙon ALLAH yasa gidan zamanta ne. Amma sai Kareema take ganin al'amarin nawa a juye. Ko nawa auren na farko dana biyu duk sunzo da dalilai ne, dan haka ban jisu a jinin jikina ba kamar wannan auren, ni kaɗai nasan irin addu'oi da nake maka a zuciyata. A randa na kirashi game da barinta ta fita aiki nayi hakane dan na tunzurashi da kai ku hanata fitar, dan hakan da zanyi ne kawai zai sake tabbatar min da yaron zai iya abinda nake fata akan Mawaddat. Sannan zai iya juyata a yanda kowane namiji ya kamata ya juya gidansa bawai ita a matsayin mace ta juya shi ba. Sosai na dinga dariya akan maganar da ya faɗa min, na yini raina fes, sai dai a fuska kowa ya gagara gane kaina har Kareema. Yousuf ina son Kareema sosai dan matar ƙwarai ce, sannan ita ɗin jinin jikina ce, zuciyata na mata uziri akan abubuwa da dama. Soyayyarku a gareni ta dabance Yousuf, ku nakema kallo tamkar iyayena, dan kuna iya gayamin gaskiya duk ɗacinta. Garama Khareema tana jin shakkata, wasu lokutan takan haƙura ta shanye”         Shiru kawai Uncle Yousuf yay yana kallon Yayan nasa da murmushi a fuskarsa mai ƙayatarwa, a zuciyarsa kam sai ayyana (Namijin duniya) yake. Tare da jin nadamar abubuwan da ya dinga yi game da ɗan uwan nasa musamman zargi. Cikin ƙarfin hali Daddy ya katseshi da tambayar ina Smart yake a yanzu?. Kai tsaye Uncle Yousuf ya sanar masa komai akan Smart daya sani da ga wajen Abdull-Hameed Coach. Sosai Daddy yaji tausayin yaron ya ratsa masa zuciya, tare da ƙaunarsa ta haƙiƙa na sake ratsashi...       “ALLAH ya bashi nasara akan burinsa ya kuma yimasa albarka” Daddy ya faɗa yana miƙawa Uncle Yousuf wayarsa. Uncle Yousuf dake amsa addu'ar Daddyn ya amshi phone ɗin ya tsirama hoton ƙyaƙyƙyawan jaririn ido, tunani yake ina ma yasan wannan fuskar?. Kasa hasasowa ya sashi faɗin, “So cute Yaya, yaron wanene haka da nake jinsa a raina tamkar jininmu”. Murmushi Daddy yay mai haɗe da ƴar dariya, sai kuma ya dafa ƙafaɗar Uncle Yousuf ɗin da faɗin, “Jininka ne Yousufa. Dan ka zama Grand father yanzu”.        “Grand father? Ta yaya Yaya? Ni da bayan Mawaddat ɗina ban aurar da kowanne ɗa ba, duk da itama an sanar mana tana da ciki, sai dai rashin sanin ina take yasa bama musan yaushe ne haihuwarta ba”.      Sake faɗaɗa murmushin Daddy yay da tsare ƙanin nasa da ido dan san ganin irin reaction ɗin da zai nuna. A hankali ya furta, “Ai Mawaddat ɗin taka ce ta haihu jiya ɗin nan...”           “What!!!!”.      Uncle Yousuf ya faɗa da ƙarfi cikin wata irin zabura da ta saka jikinsa har yana karkarwa. Cikin rawar murya ya ce, “Yaya Please karka min wasa irin wannan dan ALLAH. Wlhy zan iya maka kuka”.      Dariya sosai Daddy keyi masa, kafin ya jinjina masa kansa alamar tabbatarwa. “Babu wasa a maganata Yousuf, bakaga ɗan na maka kama da ƙanin naka Aliyu ba.”              “Ya subahanalillah! Yaya dan ALLAH mafarki nake ko ido biyu? Idan a barci nake jin wannan zancen ka taimakeni karka bari na farka. Idan ko a zahiri ne ka faɗamin dama kasan inda Mawaddat take duk wannan kaiwa da komowar da nake yi”.         Daddy dake murmushi har yanzu ya kamo hannun Uncle Yousuf ya sake zaunarwa a kusa da shi. “Please relax sweet heart. Ai ina sane da duk wani shigi da ficinka, na Barka ne har zuwa irin wannan ranar ta yau sannan kasan gaskiyar al'amarin. Dan na sanka da rashin haƙuri farin ciki zai iya sakawa ka buɗe min aiki. Ai tun a randa Dada ta tabbatar min Mawaddat na'a wajenta na ƙara tsananta bibiyar Sulaiman. Saboda na tabbatar duk inda Dada zata kaita sai da gudumawarsa. Nace maka na tafi Hong Kong ne kawai dan na ɓatar da kowa a lissafi, da ga can na bibiyi Sulaiman ƙafa ya ƙafa har zuwa ƙasar Canada da ya nufa shi da ɗansa. Ban wani sha wahala na a bibiyar tashi ba na gano inda Mawaddat take. Sai dai ban zauna ba na kamo hanya na dawo, tare da jin ƙarfin gwiwar barinta cikin ƙudirar UBANGIJINA. Sai dai na saka wani yaro Usman ɗan Alhaji Bashir Sa'eed dake Canada cigaba da bibiyar min al'amarin su dama na gidan gaba ɗaya. A bakinsa naji Mawaddat na ɗauke da ciki, har ma da kaita asibiti da sukai domin yunƙurin zubar da shi, da ceto cikin da yay har zuwa yau........” kaf ya kwashe komai da ya sanar masa. A abin mamaki sai ga hawaye share-share Uncle Yousuf na sake zubarwa. Daddy ya cigaba da faɗin, “Ina kan sani na barta can a wajen nasu duk da nasan Sulaiman zai iya cuta mata, sai dai kasancewar Usman na sanar min duk wani motsinsu ya sani sake samun ƙwarin gwiwa. Nasan hakan shine kawai zai sake koyama Mawaddat sabuwar rayuwa ta fahimci mi ake nufi da gundarin rayuwar ma kai tsaye. Ta kuma san wanene Sulaiman ta yanda duk sanda za taji komai game da shi abin bazai zo mata a bazata ba balle harta cutu. Sannan zata sake sanin muhimmancin mijin da darajarsa tare damu family nata gaba ɗaya. dan a yanzu haka Dada ta sanar mata mijinta ya saketa”.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣0️⃣ .........Ji Uncle Yousuf keyi kamar yay ta kuka, ga wani jin zafi da takaicin Dada da Alh. Sulaiman na cimasa zuciya. Sai sake kallo Jaririn yake a hotuna harda ɗan gajeren vedion. Uncle Yousuf ya rungume Daddy jikinsa na tsuma. Babu wanda ransa ke hango masa kamar Smart a yayinda zaiji wannan labari mai cike da al'ajabi da mamaki. Dan koda Dada ta sanar musu samuwar ciki da kasancewarsa basu faɗa masa ba saboda yana kan gaɓar da kwanciyar hankali yafi buƙata, ga shi su kuma ba sanin inda zasu samo Lulun sukai ba a lokacin balle su ƙarfafa shi.       “Yaya yanzu yaushe zata dawo gida? Dan tana buƙatar kulawa a yanzu sosai”.      “Ya sake kwashe musu passport ɗinsu ne shiyyasa, amma ina kan ƙoƙarina na son ganin an dai daita musu komai sun baro ƙasar. Sai dai ba Nigeria nake so ta dawo ba, dan ina son nai amfani da wannan damar ne wajen ɗaure Sulaiman da jijiyoyin kansa sannan na ɓata abinda na gyara akan Mawaddat.”                “Wannan tunani ne mai ƙyau Yaya, inaga kawai ta wuce wajen mijinta to”.          “Zan so hakan Yousuf, sai dai zai iya zama matsala. A yanzu yaron yana a wata gaɓa ne da kowa zai iya kai masa hari ya kumayi tasiri a kansa cikin sauƙi. Bai kamata mu bada gudunmawar maida shi baya ba bayan al'amura sun ɗakko hanyar warware wa. Su Sulaiman shu'umai ne ta yanda komai zasu iya aikatawa. Sannan suna huɗɗa da manyan ƴan iskan duniya a fagen cinikayyar kayan shaye-shaye. Wannan babbar dama ce a hannunsu da akowane ƙasa mutum yake, ko wane irin matsayi ya taka zasu iya ƙulla masa. Abinda kawai ya dace muyi yanzu shine mu rufe bakunan mu ruf zuwa wani lokaci, amma mahaifinsa da mahaifiyarsa su san da wannan haihuwar. Shima kuma na aika a sanar masa yanzu hakan. Daga iya mu huɗun nan kar kowa yasan inda Mawaddat take Please”.         “Na fahimceka ƙwarai da gaske Yaya. Kuma insha ALLAHU a yanzu bakai kaɗaine zakai wannan aikin ba. Ni da kai ne zamuyisa dan na fara ji a jikina Sukailan ne ya koyama Mawaddat shaye-shaye”.      Sosai Daddy yaji daɗi da farin ciki, duk da yana tsoron kar a cutar masa da ɗan ƙanin nasa ɗaya tilo kuma. Amma ya bar komai a hannun UBANGIJI, sannan idanunsa a buɗe suke a yanzu kam kowane irin ƙalu bale ya shirya masa. Zancen Alh. Sulaiman ne ya koyama Lulu shaye-shaye kuma shima kansa yana wannan tunanin, a yanzu haka kuma yana kan bincike ne sosai har ma da yanda akai Nanny ɗin Lulun ta mutu duk zuciyarsa na masa zargin Sulaiman. sai dai a yanzu bai cema Uncle Yousuf ɗin komai akan hakan ba....         *_CANADA_*     Sosai Alhaji Sulaiman da ya iso Canada yau ɗin nan ke a cikin tashin hankali. Dan duk iya bincikensa yayi amma babu Usman babu su Lulu. Har asibitin da aka kaima Lulun cs yaje sai suka ce masa su basuyi wata theatre wa mai sunan ba. Neman haukace musu yayi, daga ƙarshe akasa security fiddashi tare da warning ɗinsa mai ƙarfi na in ya sake dawowa yay musu hayaniya zasu saka jami'an tsaro kamashi. Baya haɗa sabga da jami'an tsaro ko'a Nigeria, dan kun san mai kaza a aljihu baya jimirin ass. Balle ya samu labarin mahaifinsa ya saka a bincika a nemo inda yake tun kusan wata uku da suka wuce. Shiyyasa ma yaƙi zama waje guda yaƙi kuma shiga Nigeria kwata-kwata duk da labarin da ya samu har na sakin mahaifiyarsa Dada da Baba Garkon yayi. Yana tsaka da kasancewa a haukacensan saƙo ya iso masa. A birkice ya saka hannu a littafin ɗan saƙon, tun kafin ya koma cikin gida ya buɗe, inda ya fara cin karo da hotunan ƙyaƙyƙyawan jariri har kala uku. Hoton ƙarshe da ke ɗauke da rubutu ya juya cikin tsumar jiki. *_Zakaran da ALLAH ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai yayi. Aliyu Aliyu Mika'il Mawashi ya iso duniya lafiya_*       “What!!” Ya faɗa cikin bugawar ƙirji da rawar hannu. Sai kawai ya saki wani irin ihu mai ƙaraji tare da yin watsi da hotunan. “Usmaann!!” ya sake ambata da ƙarfi. Sai kuma ya ƙyalƙyale da wata irin dariya mai ƙona zuciya, tare da faɗin, “Yaro baka san wuta ba sai ka taka. Ka taro babban match ɗin da kaf family naka basu isa zamar maka defenders ba. Sai na tarwatsa rayuwarka ta inda zaka dawwama dana sanin yaudara ta da ka shirya yi. Yarinyar kuma da hannunka zaka maidota gareni”. Da ga haka ya fisgi rigar sanyinsa da ke a hanger ya fice gidan.....           *_NIGERIA_*         Tun randa taji Smart baya Nigeria ta kasa zaune ta kasa tsaye, ko kaɗan zuciyarta da gangar jikinta sun gagara hutawa. Ba ita kaɗai ba, hatta ƴaƴanta ta cusa musu hassada da ƙyashin da ya ingizasu fara bibiyar al'amuran Smart har suka gano irin cigaban da yake samu a yanzu haka, duk da dai a farko dariya suka fara da ganin Smart ɗin ai a ƙaramin team yake ma. Sai dai kuma a hakan ma dai UBANGIJI sake bayyana shi yake ga duniya a bisa kowane matakin nasara koda akwai ƙalubale a cikinsa. Abu na biyu yanda Abba ya fara jiƙewa a ƙanƙanin lokaci, dan bai iya ɓoye alkairin da Smart ɗin ke turo masa. Duk da ba wasu maƙudan kuɗi bane na tashin hankali, sai dai suna riƙesa ta yanda a yanzu haka baima fita kasuwa sai yaran. Duk da aikin da Malam Na-zuru ya sake mata a kan Smart ɗin hankalinta ya kasa kwanciyar jiran nashin kaɗai. Tuni sun bazama ga wasu malaman harma da bokayan babu inda Hajiya Naqiba bata zuwar mata. Wani lokacin kuma suje tare ma.         Ammah ce ta fara fuskantar al'amarin na Umma a randa ta kamata tana bizne abu a bayan windown ta ga sunan Smart tana kira. Hankalin Ammah ya tashi matuƙa a wannan ranar, amma bata yarda Umma ta ganta ba harta kammala. Bayan barinta wajen tai kiran ƙanwarta Gwaggo Sa'adah ta sanar mata komai cikin tashin hankali. Gwaggo Sa'adah ta kwantar mata da hankali akan tana zuwa, sai dai karsu taɓa abinda Umman ta bizne tunda akwai jinin Smart a jikinsu. Gwaggo Sa'adah ce tazo da wani almajirinta, inda cikin hikima ya tone abinda Umman ta bizne ɗin. Layune da wasu sirkulle a kwalba an ɗaure. Koda aka kunce layun abinda ke rubuce a ciki su dukansu ya daga hankalinsu. Amma sai almajirin nan ya ce su kwanatat da hankalinsu addu'a tafi gaban komai ai. In sha ALLAH tunda an farga da wuri babu abinda zai faru, zai je da su ya lalata. Gwaggo Sa'adah taso a ajiye a nunama Abban. Amma sai Ammah tace a'a a ƙyaleta a rufa mata asiri idan halintane zata ƙara ai har Abban ya gani da kansa wataran. Har Gwaggo Sa'adah taji haushi sai kuma da ga baya ta fahimci hikimar Ammah.       Tunda ga faruwar wannan al'amari Ammah ta sake dagewa da addu'a akan ƴaƴanta gaba ɗaya. Tare da sadaka akoda yaushe. Duk inda taga maraya tana ƙoƙarin taimaka masa. Suma yaran kullum cikin ƙara ƙarafafasu take da ibada har Smart. A duk sanda sukai waya sai ta sake nusar da shi. Alhmdllh yana fahimtar ta sosai, kuma dama baya sakaci akan ibadarsa duk da wataran gajiya kan hanashi iya tashi sallar daren daya sabama kansa yanzu. Amma a koda yaushe bakinsa bai rabo da ambaton ALLAH.      Yau ma kamar kullum gidan yana ruɗe da hayaniyar yara da jikoki kasancewar juma'a ce ta ƙarshen wata. Dan an sakko massalacin kenan sai ga Abdull ya shigo yana sanarma Ammah Abbah yace a bada ruwa anyi baƙi. Kasancewar itace da girki babu wanda ya damu. Ta haɗa ruwa harda zoɓon da Maryam tayi domin zuwan Ahmad ɗinta kasancewar duk juma'a yake zuwa hira bayan sallar la'asar (Kun san fa Ahmad da Maryam an jone🥱). Har Abdull zai wuce Ammah ta sake dakatar da shi, dan tunda taga Abbah ya aiko a amshi ruwa da alama baƙin masu muhimmanci ne. Masar da tayi matsayin abincin rana ta zuba ta ce Asma'u ta ɗauka ta bisa da shi.          Sosai Uncle Yousuf ya tsirama Asma'u da ta kai har ƙasa tana gaishesu idanu, dan sosai tana kama da Smart, sai dai kawai dan shi namiji ne ita mace, ta kuma fishi haske sosai. Murmushi yayi domin tuna wani abu. Daddy na lure da shi sai dai baice komai ba har Asma'un ta fita. Mikewa Abba yay da nufin barinsu suci abinci, amma sai Daddy ya ce yayi zamansa ai ruwama kawai ya wadar. Ɓata rai Abba yay da faɗin, “Saboda abincin namu ba irin naku bane Alhaji Isma'il?”.       Cikin ɗan daburcewa Daddy yace, “Wlhy ba haka bane Malam Mika'il. Amma aimana afuwa bara muci.” dariya suka ɗanyi cikin barkwanci, da ga haka suka shiga buɗe abincin, ganin masa tasha manshanu ga lafiyayyen zoɓo bama su san sanda suka shiga cin ba har sai da suka tada abincin tas. Daddy na tsokanar Uncle Yousuf ne ya cinye, shima yana tsokanarsa shine ya cinye. Shi dai Abba dariya yake musu cike da sha'awar wannan zuminci tamkar wasu abokai. Bayan sun kammala Uncle Yousuf yace ya kamata Ammah tazo dan suji miya kawosu a tare. Abbah ya jinjina kansa cikin gamsuwa, sannan ya ɗaga waya yay kiran Ammah. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gata, tayi mamakin ganin ashe baƙin su Uncle Yousuf ne, amma sai batace komai ba ta zauna suka gaisa cikin girmama juna. Uncle Yousuf ya zaro hotuna a aljihunsa ya miƙama Abbah. Amsa yay yana murmushi, sai dai yana kallon jinjirin dake a hoto sai da zuciyarsa ta harba. Dan haka ya ɗago da sauri ya na duban Ammah data tsira masa ido, sai kuma ya dubi su Daddyn da ke kallonsa da murmushi. Itama dai Ammah gabanta ne ya faɗi lokacin da taga abinda ke jikin hoton, muryarta na rawa ta ɗago tana kallon Abbah. Abban Salim wannan ai Hydar ne yana jinjiri, sai dai ban san sanda aka ɗauki hoton ba gaskiya, dan kayama na manta da su.”       Daddy da ya kasa riƙe dariyarsa ne yay gyaran murya, dan haka suka dubeshi su duka har Uncle Yousuf dake danne tasa dariyar shima. Daddy ya ce, “Anya Aliyu ne? Kudai sake kallon hoton Malam Mika'il”.        Kallon juna Ammah da Abba suka sake yi, sai kuma suka sake maida hankalinsu a hotunan. Abba ne ya sake cewa, “Gaskiya Aliy ne a hotunan nan Alhaji Isma'il. Ba mu da muka haifesa ba ma, duk wanda zaka tambaya in har yasan Aliy yana jariri wannan amsar zai baka”. Ammah dake jinjina kai tace, “Wannan gaskiya ne Abban Salim. Dan Hydar ne yana jariri”.         “Wannan jinin Aliyu Hydar ne a yau ba Aliyu yana jinjiri ba”. Cewar Uncle Yousuf cikin murmushi. Cikin haɗa baki Abbah da Ammah sukace, “Jinin Aliyu! Tayaya?”.        “Ta hanyar matarsa Baba. ALLAH ya albarkaci matar Aliyu da haihuwa jiya, wannan shine albarkar da ALLAH ya azurtamu da ita mu da ku da shi”.        A hankali hawaye suka ziraroma Ammah da jikinta har yake tsuma.  Muryarta na rawa ta ce,.......✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣1️⃣ ........“ALLAHU akbar, ALLAH mai rahama mai jin kai, Sarki gagara misalin masu misalai. Isashe mai iko da koman da ke iya kallon kansa a iko. Dama anga ɗiyar tawa?”.          Kai Uncle Yousuf ya jinjina mata, da ga ita har Abbah da farin ciki ya sashi jin yama kasa motsawa, sai sunayen ALLAH yake ambata a jajjere. Cikin nutsuwa Uncle Yousuf ya zayyane musu komai ta yanda zasu fahimta. Wato gano inda Lulu take dama abinda ya faru akan cikin har zuwa haihuwarsa a yanzu. Sai dai suna roƙonsu da su ɓoye wannan sirrin dan basa son asan inda Lulu take a yanzu har sai abubuwa sun dai-daita domin koyama Alh. Sulaiman da Dada hankali bisa kuskurensu. Da ga ƙarshe suka sanar musu sunan yaro Aliyu kamar yanda Lulun ta saka aka masa huɗuba da shi. Sosai su Ammah sun gamsu da wannan dabara, tare da mamakin wannan baƙin hali na su Dada. Ga kuma Umma a gefe itama tana nata yaƙin, duk da dai Ammah ce kaɗai tasan da wannan. Yaro yasha addu'oi shi da mahaifiyarsa Lulu na fatan samun lafiya a gareta. Da ga ƙarshe Daddy yace musu su shirya domin sama musu visa dan yana son suje su gano Jariri. Da farko Abbah yaso ƙi, acewarsa bazasu sakasu wahala ba. Duk randa suka dawo Nigeria ai zasu ganshi. Amma sai Daddy da Uncle Yousuf sukaita roƙonshi. Da ƙyar dai ya yarda ya amince. Inda tun a ranar suka fita da su domin yin passport. Abinka da harkar kuɗi, an gama musu duk abinda ya dace cikin ƙanƙanin lokaci saura jiran result kawai.      Kowa ya kalla Abba da Ammah a wannan yinin yasan suna cikin farin ciki mai tsanani, sai dai ba'a san kona minene ba. Dan hatta su aunty Bilkisu Ammah bata sanarmawa ba sai Gwaggo Sa'adah kawai saboda ita ɗin sirrinta ce, ai ko sai ga Gwaggo Sa'adah itama da hawayen farin ciki, da yammacin nan bata iya haƙuri ba sai da tazo gidan taga hoton jariri. Ita Umma dama bata gidan, tana can wajan biɗar baƙar tambayarta. Bata dawo gidan ba sai yamma lis. Sannan su Abba har sun dawo da ga fitar da sukai. Amma sai Mama ta sameta har ɗaki da gulmar wai yau surukan Smart sunzo gidan, kuma sun fita da su Ammah tana ganinfa akwai matsala. Sai dai kuma su Ammah tunda suka dawo sai faman washe haƙora sukeyi da ga ita har Abba. Dan Ammah harda su sadaka tayima yaran anguwa da maraicen nan. Sosai wannan magana ta tsayama Umma a rai, dan sabon malaminta da sukaje wajensa a yau ɗin nan dama ya sanar musu akwai wani babban al'amarin farin ciki da ya samu Smart ɗin, sai dai ya gagara gane ko minene anata nuna masa haske kawai babu komai. Amma taje gida duk abinda taji gobe ta dawo. Sai kuma gashi da ga dawowar tata taji sabon zance a wajen Mama macijin sari kanoƙe. Cikin matsanancin tashin hankali tai kiran Hajiya Naqiba suka tattauna, sai dai duk iya hasashensu sun kasa canko komai ilai tunanin ko Lulu zata dawo ne. Amma dai sun tsaida matsaya Umma taje ta zunguri Abbah akan batun. Wannan shawarar ta rika, dan haka a daren dan ta kasa nutsuwa ta nufi ɗakin Abba da nufin su gaisa tunda yau bata yini a gida ba. Lokacin Ammah ta baro ɗakin da kwanikan da yaci abincin dare. Zaman dirshen Umma tai suna hira da Abba bayan sun gama gaisawa, inda cikin salon makirci ta fara zungurarsa da batun Smart duk da bata fito fili ta ambaci sunansa ba. Dai-dai nan ALLAH ya kawo Ammah, tsaf ta fahimci manufar Umman, dan haka ta zauna a falon dan tasan halin maza wani lokacin sai addu'a musamman idan suka haɗu da makirar bace. Zuwan Ammah baima Ummah daɗi ba sam, dan tasan halin Ammah da shegen tsartar tsiya. Dan haka ta tashi ta fice cikin jin takaici tana ƙwafa. Da kallo kawai Ammah ta bita tana girgiza kai, inda bayan sunbar falon zuwa makwanci cikin hikima ta sake nusar da Abba muhimmancin ɓoye al'amarin haihuwar nan kamar yanda su Daddy suka roƙa, Abba ya fahimceta sosai, sannan bai zargi tayi hakane saboda Umma ba dan Ammah mace ce mai hikima da dattako. Kawai dai dan ba fitinanniya bace da lallai su Ummah sun kaɗe a gidan nan.....                *_UK LONDON_*    Sosai yake cikin farin ciki mara misali, yaso yay amfani da ɗan hutun da suka samu yazo gida Nigeria sai dai hakan na neman gagara saboda kara kainar da manyan clubs keyi akan al'amarin sa. Duk da dai abin bai fito fili duniya ta fahimta ba Coach ɗin sa shi da komai ke a garesa da Manager ɗin sa Uncle Yousuf suka ce ya dakata dai aga inda wasan zai tsaya. Wannan shine dalilinsa na haƙura da zuwa gida Nigeria ya cigaba da bama kansa hutu a gidansa. Sai motsa jiki da yakan fita da ɗan yawata gari idan yaso a wasu lokutan.      Yau ma yana gida kwance a binsa, sai dai idanunsa biyu yana zaune ne a falo idonsa a tv yana kallo sai popcorn da ke gefensa yana jefa ɗaya-ɗaya a baki (Su Smart an zama an gayu😂😜🚴). Gift da wani ɗan lutin yaro ke buɗewa a film ɗin yana tsalle ya sashi tunawa da saƙon da aka kawo masa jiya da yamma da ko buɗewa bai yi ba. Hasalima tunda ya amsa ya ɗora shi a inda takalmansa suke farkon shigowa falon bai sake bi ta kai ba dan yasan dai bai wuce irin gift da fans nasa kan kawo bane takanas garesa. Miƙewa yay a hankali zuwa corridor ɗin farkon shigowa, saƙon na'a inda ya barsa, dan haka ya ɗakko ya koma falon. Kiran Ahmad da ya samu na shigo masa a waya ya sashi ajiyewa ya ɗauki wayar. Kamar yanda suka saba cikin barkwanci suka gaisa da juna, Ahmad ya sake masa congratulations da tabbatar masa da next month yana tafe fa, dan yana son yazo ya masa hutu. Sun ɗan ja lokaci suna hirarsu cike da nishaɗi da ƙaunar juna kafin suyi sallama. Har ya sake shagala da batun saƙo zai koma ya kwanta sai kuma idonsa ya sake sauka a kai. Tashi yay ya jawo brown envelope ɗin ya buɗe tare da zira hannu a ciki ya zaro kayan ciki. Hotuna ne har guda biyar, sai flash drive guda ɗaya da kwalin haɗaɗɗen turare designer ɗan ƙarami sai masifar ƙamshi. Hotunan dake a kife ya fara ƙoƙarin dubawa, haka kawai ƙirjinsa na wani irin harbawa, saukar idanunsa akan hoton farkon sai da zuciyarsa ta motsa da ƙarfin gaske a cikin ƙirjinsa. Tsigar jikinsa ta shiga wani irin ya mutsawa. Tabbas wannan duk wanda ya sanshi a jinjiri yaga hoton nan yasan shine, sai dai shi da kansa yasan bashi ɗin bane ba saboda dalilai da yawa idan aka auna, musamman yanayin hoton da inda aka ɗauki hoton da suturar jikin yaron duk da yasan duk za'a iya editing, cikin tsumar jiki yaje ga hoto na biyu, nan ma dai yaron ne again. Hoto na uku ma haka, sai a na huɗu ne fuskar da bazai taɓa mantawa ba ko'a magagin barci ce rungume da yaron a saman ƙirjinta tana da ga kwance jikinta ɗaure da zanin asibiti, ga ƙarin ruwa a hannunta, sai rabin jikin mace da ke gefenta ta dafe mata yaron sai dai ba'a ganin fuskarta. Hajijiyar da yaji tana neman kwasarsa ta sashi komawa a kujerar daɓar ya zauna. Da ƙyar harshensa ya iya motsawa wajen furta, “Mawaddat da jariri ta yaya?”. (Ta yanda kowa ke samu mana) zuciyarsa ta bashi amsa kai tsaye. Rawa lips ɗinsa ya shigayi da illahirin jikinsa, dan sam ya kasa furta abinda ma yake son furtawar. A dai-dai nan kira ya shigo wayarsa. Da ƙyar ya iya juyawa ya duba wayar. Uncle Yousuf ya gani ɓaro-ɓaro. Cikin zallo kuwa ya caɓi wayar dan gani yake kamar mafitace ALLAH ya kawo masa na warwarewa da ga ruɗanin da ke neman zauta masa ƙwaƙwalwa tamkar a mafarki...       “Congratuletions angon ƙarni”. Kalmar farko da Uncle Yousuf ya furta masa bayan sallama da ta daki ƙirjinsa. Da ƙyar ya iya furta, “Angon ƙarni Uncle?”.      “Yes of course Son. Ka zama Daddy mana, na kuma san saƙon yaya zuwa yanzu ya isa zuwa gareka sai dai in baka duba ba”.          Wasu irin hawaye ne da masifar gudu suka shiga biyo kumatun Smart. Muryarsa na rawa ya furta, “Uncle kana nufin da gaske ne Mawaddat nada ciki kuma ta haihu? Sannan kun san inda take”. Uncle Yousuf da ke murmushi da ga can ya ce, “Hakane Aliyu, ALLAH ya azurta Mawaddat da samun ciki, kuma an mata cs a jiya an ciro yaro mai kama da kai, sai dai muma da ga baya duk muka san hakan. Tsaf ya kwashe labarin su Dada dana Daddy ya sanar masa har yunƙurin zubar da ciki bai ɓoye masa komai ba. Ya ɗora da bashi haƙurin cewar an ɓoye masa maganar ciki ne a lokacin dan kar a tada masa hankali tunda basu san takamaiman ina Mawaddat take ba a lokacin ɗin sai Daddy shi kuma ya ɓoye ne dan tsaron lafiyarsu, tare da manufarsu ta son a ɓoye yanzu har sai an wajiga rayuwar Alh. Sulaiman. Ɗari bisa ɗari Smart ya yarda da wannan shirin, yayinda zuciyarsa ke masa kai-kawo akan sakkowar Daddy da sauri haka. Sai dai baicema Uncle Yousuf komai game da wannan ba. Ya daiyi murmushi da cema Uncle Yousuf batun Alh. Sulaiman wannan wasan nashi ne. Jin wai Lulu kuma tace a sakama yaron sunansa ya sakashi sake yin murmushi da lumshe idanunsa, dan harga ALLAH baiyi tunanin hakan daga gareta ba. Irin farin cikin da Smart ke ciki yau da banne a rayuwarsa, dan ko randa sukaci nasarar cin ƙwallon nan baya jin farin cikin sa yakai koda kwatar haka. Ya kira Abbah da Ammah cikin zumuɗi, inda suma suketa tsokanarsa cike da farin ciki tare da masa barka da arziƙi. Ya ce, “Ammah shiyyasa kullum sai naita mafarkin yara, ashe takwarana yana isarmin da saƙon ya kusa zuwa duniya ne”. Dariya Ammah keyi, cikin tsokanarsa ta ce, “Oh ni Hydar ko irin ƴar kunyar ɗan farin nan babu ma?”. Dariya ya ƙyalƙyale da shi tare da rufe fuskarsa da fillon kujera kamar yana gabanta, ya ce, “Ammah sai anjima to nayi shiru”. Itama dariyar ta shiga yi masa sosai cike da jin shauƙi da tarin ƙaunar tilon ɗan nata namiji........✍️ _🚴🚴🚴Yau fa dangin Smart an cika mu da iyayi, to ɗa dai bara mu bada ba ehe dan zufarmu ce😏_ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣2️⃣ ........Koda ya ajiye wayar miƙewa yay zuwa cikin bedroom ɗin sa. Alwala yay domin gabatar da nafilar godiya wa UBANGIJIN talikai mai ƙyautar da kuɗi ko ƙarfin mulki baya badawa a duniya. Gaskiya tunda yake a rayuwarsa baya jin an taɓa masa wani suprice mai taɓa zuciya da jijjiga jinin jiki irin na yau. Bayan ya idar ya jima yana kwararoma ɗan nasa da Lulu kanta addu'oi, tare da fatan ALLAH ya kawo musu dai-daiton wannan al'amari da ƙarshensa cikin sauƙi su cigaba da rayuwa a inuwa ɗaya tamkar sauran ma'aurata. Wayarsa ya sake ɗauka ya dawo falon. A karan farko Smart yay kiran number Daddy yau tunda yabar Nigeria. Sun gaisa cikin mutunta juna da nuna jin nauyin juna musamman ma shi Smart ɗin. Daddy ne ya fara masa barka, shima Smart ɗin yay masa barkar. Da ga haka Daddy ya bashi haƙuri akan abinda duk ya faru a baya da masa bayanin akwai dalilin yin hakan, zai masa bayani amma ba yanzu ba sai sun haɗu. Sai batun ɓoye masa ciki da inda Lulu take nan ma ya bashi haƙurin kamar yanda Uncle Yousuf ya bashi da masa bayanin dalilin yin hakan. Cikin girmamawa Smart ke roƙon Daddy da ya daina bashi haƙuri shi bai taɓa riƙesa a ransa ba ko ganin laifinsa. Yana masa kallon uban ne da kuma uzuri dan yasan koma minene yanada dalili, ya kuma fahimci hakanne tun a randa Alh. Sulaiman yasa aka satoshi, shiyyasa ma ya haƙura da halayen Lulu ya sake komawa aikin gidan. A yanzun ma yana roƙon Daddyn da ya bar wannan wasan a hannunsa ya kwanta ya huta ya haifa masu masa yaƙin ai, fatansa kawai in har bai shiga hurumin daba nashi ba yana son jin tushen matsalar ne kawai. Murmushin jin daɗi Daddy yayi da ga can har Smart yana iya jiyosa. Da ga haka ya shiga sanya masa albarka da tabbatar masa in sha ALLAH zai sanar masa komai, sannan ya ɗauki kansa matsayin ɗa a garesa koda wasa ya daina jinsa daban a cikin family ɗin sa. Bama shi da suka haɗa jini ba a yanzu ko ahalinsa sun zame musu ahali ai suma. Sosai Smart yaji farin ciki da waɗan nan kalamai na Daddy, tare da sake jin kimarsa da mutuncinsa a zuciyarsa.. da ga haka sukai sallama cikin mutunta juna.     Bayan sun ajiye wayar Smart ya ɗakko laptop ɗin sa ya saka flash ɗin nan a ciki. Ba komai bane face videon yaronsa mai tsananin kama da shi sai Mawaddat ɗinsa da keta kallon jariri tana wani munafukin murmushi tare da motsa lips ɗin ta sai dai baya iya jin mi take faɗa, sai matashiyar matar da ke gefenta tana tofama yaron addu'a. A hankali ya lumshe idanunsa da sakin wata irin raunananniyar ajiyar zuciya ƙwallar ɗinbin farin ciki na sake cika masa idanunsa. Shi yama rasa mizaiyi domin nuna farin cikinsa akan wannan ƙyauta ta UBANGIJI mai tsadar gaske da kuɗi ko alfarma bata badawa a wannan duniya.. ji yake inama zai iya tauntsuwa ya gansa gabansu, kai shi koda muryarta ne yaji ma ta waya zai rage masa nauyin zuciya. Ƙasa haƙuri yay ya turama Uncle Yousuf saƙo akan neman number ta. amma sai ya samu reply cewar babu waya a hannunta amma akwai ta yaron da ya kuɓutar da su mai suna Usman zai tura masa. Duk da ya ɗan ji kishin nasa ya motsa sai ya danne...        *_NIGERIA_*    Sosai ta yi wata irin rama data sake bayyana tsufarta sosai gamai kallo. Ga shi bata da isashiyar lafiya sakamakon tsangwama da rashin kulawar da take fuskanta a hannun matar ɗan nata. Ba komai ya jawo hakan ba kuma sai gara rayuwar surukan nata data jima tanayi a shanun talla. Musamman ma ita matar Uncle Manner ɗin. Itama kuwa sai gashi ALLAH ya bata damar ramawa. Abinda yafi yima Dada ciwo a zuciya makircin Hajiya Aneesa, dan in har Uncle Manner na gida bai isa gane komai akan matar tasa ba, kulawa take bama Dada kamar uwarta mahaifiya, amma yana gusawa kashi ma ya fita daraja. Ta dinga gasa mata azaba da magana kenan masu zafi har sai hawaye sun cikama Dada ido. Ga shi ta hana ƴaƴanta raɓar Dadar sai ubansu na nan, daga bayama ko uban nasu na gida sai basa zuwa, da tayi magana kuma za'ace makaranta ce ta ɓoye su. Kaɗaici da damuwa sunma Dada yawa, ga kewar mijinta da rashin ƴancin data saba dashi na tsawon shekaru, babu irin kalar kiran da bataima Baba Garko da tura masa saƙo ba amma tamkar ma baya ganinta. Abinci kuwa sai wanda aka gadama ake bata dan nata daban ake dafa mata garo-garo su kuma suci lafiyayye. Idan Uncle Manner ya gani kafin ma yace wani abu matarsa ta fara zayyana masa zancen Dada ce tace ai mata, sunyi-sunyi kuma ta kafe harda musu tsiya. Sanin halin mahaifiyar tasa da yayi da irin hantara da ƙyarar da takema matar tasa tunba yanzu ba saya baya maida hankali ko ƙin yarda. Idan kuma ta saka masa kuka da nuna son ita dai a canja mata gida ko'a roƙar mata mijinta sai zuciyarsa na bashi son komawa wajen baban nasu ke damunta kawai. Yakan zauna yay mata nasiha da nuna mata illar biyewa zuciya da ɗan uwan nasa da tayi, yanzu gashi nan ya barta a halin ƙaƙa nakayi, tunda ko Nigeria ya ƙi zuwa, hasalima yaji ƙishin-ƙishin tattare iyalinsa da yake shirin yi su bisa inda yake a ɓoyen saboda tsoron umarnin mahaifinsu akan duk randa ya diro ƙafarsa Nigeria tun a airport a kamashi. Ga kuma tashin hankalin rashin sanin ina Lulu take a yanzu. Dan zuwa yanzu ta gama tabbatar ɗan nata nada manufa akan al'amarin da nasa. Ga Baba yasa an cafke Tajuddeen da ya shigo Nigeria a watan daya gabata, saboda bakinta daya furta cewar tare da shi ake komai ai. Iya binciken Tajuddeen anyi amma ya rantse shi bai san ina ubansa ya kai Lulu ba, ya dai san da su ake komai da farko amma shima kansa bai farga akwai wata manufa a ziciyar mahaifin nasa ba sai bayan na son ya aura masa ita. Sai a randa ya rabosa da Canada ya kwashe su Lulun. Ya kuma rantse a yanzu bai san ina yake ba, dan ya ɓoye kansa ne. Amma sam Baba Garko yace bai yarda ba, ƴan sanda su cigaba da riƙe Tajuddeen ɗin har sai Alh. Sulaiman ya miƙa kansa koya sako Mawaddat. Baba Garko yayi hakane kuma dan ya jima da sanin Tajuddeen shine zuciyar ɗan nasa. Kamar kuma ya sani dan hankalin Alh. Sulaiman na can a tashe game da kama masa yaro, dan haka ya baza mutanensa suketa shige da ficin ganin an saki Tajuddeen ɗin amma hakan ya gagara. Dan Baba ma da babansa, duk ƙarfin ikon da suke jin suna da shi da alfarma a ƙasar Baba Garko ya taka su ya shanye. Wani lokacin ma da bazarsa yake rawa.       Waɗan nan abubuwa marasa daɗi sunka haɗu suka tararma Dada a zuciya dan haka sam ta kasa lafiya. Ga shi a lissafinta wannan watanne na haihuwar Lulu in har Alh. Sulaiman bai salwantar da cikin ba kamar yanda yay niyya tun farko, sannan iddarta ta kusa cika, tana cika kuma hakan na nufin sun rabu kenan, dan tasan irin kafiyar Nana garko, sai idan da rabon su koma ne ma sai an sake ɗaura mata aure da mijin nata na auren tun jajayen sawu. Kwanciyarta asibiti kusan uku a tsakanin nan, a yanzu hakan ma tana asibitin tun shekaran jiya ƙarƙashin umarnin likita, sai banka mata allurar barci suke dan ta samu nutsuwa...        ★Tsaf Alhaji Garko na biye da al'amarin matar tasa, kuma ya maida aurensu tun a randa ya saketa kodan tausayin yaransu. Amma ya zaɓi yin biris da ita dan lamarin jikar tasa na ci masa zuciya. Ya kuma ɗauki alƙawarin hukunta ɗan nasa akan wannan al'amarin. A yanzu haka ya baza cid suna kan bincika masa inda yaje ya ɓoye kan nasa, dan yanaji a jikinsa a duk inda yake Mawaddat tana tare da shi....     __________★   Kamar yanda bokanta ya sanar mata ta koma sai da tai yanda tayi wajen hillatar Abba ya sake barinta fita yau suka koma ita da Hajiya Naqiba. Sun gurfana a gabansa suka gama masa bayanin komai, cikin jinjina kai da bugun ƙasa ya ce, “Tabbas akwai ɓoyayyen al'amari kuma iyayensa sun sani, sai dai an gargaɗesu da sanar wa kowa shiyyasa sukaja bakinsu sukai shiru. Kamar yanda na sanar muku tun farko bawai yaron zai gagaremu bane, kawai dai tsaye yake da ƙafafunsa wajen bautama ALLAH tamkar mahaifiyarsa. Bata gajiya kuma da nusar da duka ƴaƴanta ta wannan fannin. Shiyyasa cin galaba a kansa kamar baya abune mai wahala. Amma zamu gwada sa'armu mu gani a yanzun ma sai dai akan matarsa duk da itama tana nata ƙoƙarin . Sai dai maganar gaskiya ban gano abinda zai iya tasirin rabashi da nasarar da ke tunkarosa ba game da abinda yake yi ɗin. Dan lokacin hakanne yayi. Kunsan ance mai laya kiyayi mai zamani. Abinda kawai zan iya muku aiki a kansa shine nisanta shi da al'amarin matarsa itama kuma a nisantata da duk abinda ya shafesa, wannan zai iya zauta masa zuciya ƙila har al'amarin ƙwallon nasa ma ya iya taɓarɓarewa duk da dai abune mai wahala hakan ta kasance. Sannan kuma ko akan wannan farraƙun tsakaninsa da matarsa in ma anci nasarar sake nisantasun fa na gano akwai haɗari a ciki, kuma haɗarin zai iya dawowa ne matsayin ƙaiƙayi koma kan masheƙiya gareki. Yaya kika gani ayi ɗin?”.      Ɗan jimmm Umma tayi yayinda Hajiya Naqiba ta zuba mata ido da mata signal ɗin ta yarda kawai babu abinda zai faru ai sune masu nasara. Wannan ƙarfin gwiwar data hanga a idanun aminayar tata ya sata jin jina ma malamin nasu kai da faɗin, “Babu ma abinda zai faru malam in sha ALLAHU. Ni in sansamu ne ma har uwarsa da uban ai musu kalar asirin nan dan na tsani buɗe ido naga Hafsatu a gidan nan wlhy, sauran sakarkarun basu daman ba, dan babu wacce tasha gabana sai ita. Na rasa wane shegen boka ke mata aiki haka”.      Murmushi malam yayi kawai. Sai kuma zuwa can ya nisa da cewa, “Maganar iyayensa gaskiya bamai yiwuwa bane kamar yanda na faɗa miki. Dan matar nan a tsaye take fa wajen bautama ALLAH. Ke dai kawai ai miki na yaran ma zai baki duk nasarar da kike buƙata in har ba'a samu kuskure ba”.            “Bama za'a samu ba malam ayi kawai.” Hajiya Naqiba ce mai maganar. Malam ya amsa musu da to, tare da gaya masu adadin kuɗun da aikin zaici, babu musu ta ajiye masa duk da da ƙyar ta ƙwaƙulesu a hannun Salim, sai da tasha ƙunƙunai ma da ƙananun magana sannan ya bata. Amma da yake tana so haka ta amsa tana sanya masa albarka......        Koda ta koma gida dukkan yanda akace mata ta aiwatar tayi cikin kulawa da taka tsan-tsan, daga haka ta koma gefen kallon yaya wasan zai fara kuma.........✍️      _(Ni dai nace Hummm Ummah kenan🚴😵‍💫)._ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣3️⃣ .........*_CANADA_*        Kwanaki Uku kenan da mata cs ɗin, amma Alhamdullah da alamun fara samun lafiya tattare da ita kasancewar bata da ƙan jiki, sai dai kuma Lulu akwai raki. Mahaifiyar Usman da yake kira da Mamy tazo tana tare da su tun shekaran jiya. Hakan yasa take sake ƙara samun kulawa ita da jinjirinta. Ga Ummita na iya ƙoƙarinta itama tako wane fanni. Hakama Usman da Dr Lameer. Tayi mamaki matuƙa da ganin ɗunbin kayan baby da Mamy ta kawoma Aliyu ƙarami. Sai dai yanda matar ke kulawa da su cikin haba-haba ya sa Lulu kasa cewa komai akan hakan. Duk da wannan gata da kulawar da take samu wajen abokan arziƙi zuciyarta a cinkushe take da rashin ahalinta ko guda ɗaya a kusa da ita. Hatta shi kansa uban tafiyar yakan zo mata a rai, duk da a duk sanda yazo ɗin takan yamutse fuskar cikin nuna halin ko'in kula. Sai dai hakan babu alamar zai turesa a ran nata, dan data dubi ɗan jaririn nata zuciyarta kan harba mata, balle kuma idan tana shayar da shi takan zuba masa idanu da tafiya cikin tunani mai zurfin gaske akan al'amarin mahaifinsa. Kasancewar Mamy babbar mace ta jima da hango halin da Lulun ke a ciki, amma bata cewa komai saboda lokacin cewar bai isa ba...       A ranar da su Lulu ke cika kwanaki biyar da zuwan baƙon duniya su Abba da Daddy suka iso ƙasar Canada, tafiyar da tai masifar tada hankalin su Ummah dan Abba yace musu zasuje duba Smart ne zuwa ƙasar England. Jidali iya jidali rasar su Aunty Amarya sun gani wajen Ummah, dan su Asma'u ma basa gidan Ammah catai su tafi gidan yayunsu har sai sun dawo su dawo. Dan haka suka tafi gidan Aunty Bilkisu da shirin idan suka mata kwana biyu sai su koma gidan Hawwah itama su mata kwana biyu. Babu irin zagin da Ammah bata sha ba ranar har maƙwafta sai da suka shigo, inda mutane da yawa suka fara fassara al'amarin Umman da hassada. Dan sukam basu ga wani abin tada jijiyar wuya a nan ɗin ba...      Oho su Ammah ma basu san tana yi ba, dan suna can a hanya hankalinsu kwance. Ƙasar England su Abba suka fara yada zango wajen Smart. Wanda zuwan nasu yazo masa a bazata sosai, dan sam Uncle Yousuf bai sanar masa ba. Tsabar farin ciki baima san lokacin da ya rungume Ammah ba. Turesa tai cikin jin nauyi da faɗin, “Kajimin ja'irin yaro abinda ka koya a ƙasar turawan kenan kuma?”. Cikin dariya da shagwaɓa Smart ya ce, “Ammah nafayi missing ɗinki ne, ALLAH sai nake ganin kamar mafarki nakeyi”. Tsinguli ta kai masa da faɗin, “Bari na tabbatar maka idonka biyu”.      “Ouch!” ya faɗa cikin turɓune fuska yana kallon Abba a marairaice. Abba ya riƙo masa hannu yana hararar Ammah. Daddy da Uncle Yousuf dai dariya sukeyi, dan basu taɓa zaton Aliyun taɓararre bane a wajen iyayen nasa sai yau. Smart ya gaishe da Daddy cikin girmamawa, Uncle Yousuf kam ai baida maraba da aboki duk da yanzu ana ƴar kunyar surukuta kaɗan-kaɗan. Sosai mazaunin Smart ɗin ya ƙayatar da su Ammah, suka shiga godiya ga UBANGIJI a zukatansu da mamakin wannan rahama ta UBANGIJI. Sunci sun sha daga abincin da Smart ya tanada musu a cikin ƙanƙanin lokaci, dan abinci ne na ƴan Nigeria. Bayan kowa yaci ya ƙoshi suka ɗan tattauna, sosai zaman ya sanyaya ran Smart, inda ya fahimci surukinsa sosai a yanzu ya kuma sakko daga fushin daya tafi. Sun tafi zuwa masauki aka bar masa Ammah da Abbah nan. Hakan ya musu daɗi su duka, dan sun sami damar tattauna abinda ya shafesu sosai shi da iyayen nasa. Inda ya ƙara warware musu cigaban da ya samu da wanda yake fatan samu anan gaba. Ƴan uwansa kaf bai manta da kowa ba sai da ya tambaya, har maƙwafta da abokan arziƙi. Ranar dai ansha hira, dan duk rashin yawan maganar Ammah da Smart yau dai sun sha hira abinsu kamar suyita kasancewa a haka suke ji...        Washe gari da yamma suka wuce Canada har da Smart dake jin wani irin faɗuwar gaba lokaci-lokaci, yakanyi sauri ya ambaci sunan ALLAH. Wannan ziyara tazo ma Lulu a bazatar bazata. Dan bata san wainar da ake toyawa ba sai kawai ganin Usman tai da baƙi. Lokacin da suka shigo tana toilet ne ita da Mamy dake gasa mata jikinta da towel kamar dai yanda ake cikakken wankan jego a Nigeria duk da Lulu tasha maganin da ya dace Mamy bata barta ba kullum sai ta mata safe da yamma ita da ɗan jinjiri.         A hankali take tafiya Mamy biye da ita, tayi fayau da ita sai haske data ƙara da wani cikar ido irin na jego dan tana samun kulawa sosai irin ta malam bahaushe a wajen Mammy duk da cs akai mata. Alhamdullah kumburin ciki da tai duk ya saɓe amma baza'a kirata ramammiya ba kai tsaye. Sanye take cikin doguwar riga mara nauyi dake a buɗe sosai saboda yanayin inda aka yanka ta. Baya tai zata faɗi saboda firgicin ganin abinda idanunta suka gane mata, sai da Mamy ta riƙota tana faɗin, “Mawaddat yi a hankali kinji”. Daga lips ɗin Lulu har zuwa jikinta rawa yake yi, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo tun daga kan Daddynta har zuwa mutum na ƙarshe da ke tsaye ya ɗan jingina abango da harɗe ƙafafunsa waje guda. Sanye yake cikin Suit milk da sukai masifar masa ƙyau da fitar da cikar haiba da kamalar da ya ƙara, ga wani irin ƙamshi mai sanyi da daɗin shaƙa, gaba ɗaya ya canja da ga Smart na Nigeria zuwa wani baƙin bature mai aji a yanzu. Yanda yay tsaiwar ƙasaita da harɗe ƙafafunsa waje guda idanunsa a waya yana daƙila kamar baya a wajen saika rantse ba shine ke zumuɗin azo ba fiye da kowa. Sai da Mamy ta ambaci sunan Lulu ne ya ɗan ɗago idanun nasa a hankali da take kira na macizai kamar zai lumshesu sai kuma ya zuba mata su cikin shammata da bazata. Wani irin girgiza zuciyarta tayi ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri. Rashin mafita ya sata juyawa cikin tsumar jiki ta basu baya tana mai rumtse idanunta da masifar ƙarfi. Ammah ce ta taka a hankali zuwa gareta, cikin tausayawa da ƙauna ta kira sunanta. Kasa juyowa Lulu tayi sai jikinta da ke ƙara ƙarfin rawa. Riƙo hannunta Ammah tayi ta juyo da ita a hankali, sai kaiwa ta faɗa jikin Ammahn ta rungumeta tsam-tsam tare da sakin kuka mai tsuma zuciya. A hankali Smart ya sauke idanun nasa ƙasa yana wani irin haɗiyar zuciya da sauri-sauri. Dai-dai nan Ummita ta shigo ɗakin da sallama bayanta goye da baƙon duniya dake barci. Turus tai tana kallonsu itama cikin tsoro da mamaki, yayinda su kuma suka zubama jinjirin bayanta ido. Uncle Yousuf ne yay ƙarfin halin mata nunin ta kunto yaron. Sai ta kalli Mamy. Kai Mamy ta jinjina mata alamar ta kuntosa babu matsala, dan haka ta ɗan saki ajiyar zuciya tare da kunto yaron ta miƙama Uncle Yousuf ɗin. Kamar ko ya sani sai ga idanu ya ɗan buɗe yana motsa baki alamar neman abinci. Dariya Uncle Yousuf ya saki da faɗin, “Oh oh Aliyu dai kawai ne anan babu wani banbanci wlhy sai na shekaru”. Yay maganar yana ƙarasawa gaban Abba da Daddy cikin sassarfa. A hankali Smart da idanunsa ke kan yaron ko ƙyaftawa babu tun shigowar Ummita ya wani lumshe idanun da suka kaɗa a hankali yana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Jin al'amarin yake kamar a mafarki, shi Aliyu Hydar ne da ɗa na mutum matsayin mallakinsa a wannan duniyar. Ya arrahaman ALLAH mai alkairi. Furucin Lulu da ke faɗin, Ammah nayi kewarku cikin kuka ya sashi buɗe idanun nasa ya zuba musu su. Murmushi Ammah da ke sharema Lulu hawaye takeyi, kafin ta kama hannunta ta ƙarasa da ita a saman gadon da take jiyyar. Dai-dai nan Abbah ya ƙarasa da Jinjirin ga Smart, nannauyar ajiyar zuciya Smart ya ja tare da fesarwa, sai yaji ma duk ya sake daburcewa. Fahimtar hakan da Abbah yay ne ya sashi sakin ƙaramar dariya da sake miƙa masa yaron. A hankali ya miƙa hannayensa duk biyu Abba ya saka masa yaron a ciki, sai da yay masa kallon kusan sakanni goma kafin ya matsar dashi saman ƙirjinsa ya rungume tsam-tsam dai ga hawaye sharrrr. Uncle Yousuf dake murmushi ne ya ƙaraso gareshi, cikin tsokana ya ce, “A'a ƙanina kaga zauna karka zube mana a ƙasa majiyatan su sake ƙaruwa kuma”.       Furucin Uncle Yousuf ɗin ya sata sake ɗago idanu a karo na biyu ta kallesa, sai akai sa'a shima ita ɗin yake kallo har yanzu yaron na'a rungume jikinsa sai dai ya share hawayen. Harara ta balla masa da ɗauke kanta tana tura baki. Sai ya samu kansa da sakin murmushi yana wani ƙasa-ƙasa da idanu shima. Ammah da ke ankare da su su duka ta ce, “Babana zo mana naga sabon uba dana sake yi, danni kam kai da Mawaddat kun zama Kakannina yanzu kam tunda kun haifa mini Babana”.          A hankali ya tako gaban Ammah cikin yanayin nan nasa na nutsuwa da kasancewa jarumin namiji tsayayye. Maimakon ya miƙama Ammah babyn sai ya kai zaune a kujerar gaban gadon kusan da Mawaddat da hankalinta ke kan Uncle Yousuf da ke mata magana ƙasa-ƙasa..... Bayan an gaggasa Lulu ta gama ma Daddy da Uncle Yousuf shagwaɓa da koke-kokenta suma sukai mata faɗa akan barin ɗakin mijinta tabi Dada. Ta basu haƙuri da amsar kuskurenta. Sunji daɗin nuna nadamar tata kuwa a gaban kowa. Duk alkairin Ummita da Mamy da Usman gareta bata ɓoye ba. Su Abba sukai musu godiya sosai da wannan karamci duk da akwai sannaya tsakanin mahaifin Usman ɗin da Daddy. Bayan komai ya natsa an fahimci juna Usman yay ma su Abba jagora zuwa masauki, har lokacin kuma bakin Lulu da Smart bai saɓa ba, sai dai ƴar satar kallon juna, koda yake ma shike satar kallon nata, itako tayi biris kamar ta ma manta da shi a ɗakin take nunawa. Baiji komai a ransa ba game da hakan dan halinta kuma ai sai dai ya bama wani labari yanzu. Lulu akwai jan aji, koda wasa bata yarda ta zama a ƙasa ba akan al'amarinta. Lokacin da zasu wuce Usman ya ce ai shi Smart a barshi anan tare zasu wuce gida, suje su ya fara kaisu masauki sai ya dawo ya samesa. Mamy da Ammah kam dama tuni sun fice zuwa ɗayan ɗakin gidan. Itama Ummita sai ta zare jikinta cikin dabara wai bari ta wanke kayan baby data jiƙa ɗazun. Harara Lulu data fara tsarguwa da wannan ƴar zare jikin da ake ɗai-ɗai tabi Ummita da shi, sai dai batace komai ba dan Ummitan ta fita tana mata dariya...........✍️ *_😂Kar naji wani yace komai kuma ehe. Musamman ma dangi dangi Smart ɗinnan. 🙈Koda yake akwai su aunty fa🚴🚴_*       _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣4️⃣ .......Shiru ɗakin yay bakajin komai sai ɗan ƙarar room hitter kasancewar sanyin da ake zubawa. Zaune yake cikin kujerar nan cike da ƙasaita ɗansa rungume a jikinsa ya zuba masa idanu kawai tamkar mai son gama haddace halittar jikinsa gaba ɗaya. Yayinda ita kuma take zaune a gadon jiyyarta ta miƙe ƙafafunta dake cikin blanket hannunta riƙe da sabuwar tab da Usman ya siya mata jiya. A zahiri wayar take kallo da sarrafawa, sai dai a ƙasan zuciyarta mamakin irin canjawar da Smart ɗin yayi take har yanzu, tamkar fa ba drivern nan nata ba, ya wani goge ga tsadaddun kaya wanka iya wanka, koda yake tun ma yana a drivern sa ita shaida ce ya san sirrin saka kaya, sai dai na yau ɗin dabanne, dan ko faratansa ka kalla kasan ya samu canjin rayuwa. Dama can bamai hayaniya bane shi, amma yanayin nasa na yanzu ya sake sakashi a wani matsayin zafafan maza masu aji da jan ajin. Kai itafa ALLAH da'ace a hanya taga mutumin nan maybe bazata iya shaida shi ɗin bane ba duk da kamaninsa na nan a tare da shi, sai ƙyawu da kwarjininsa mai bayyana cikar kamala da haiba da ya sake bayyana. Numfashi taja a hankali ta fesar, sai kuma taja ƙaramin tsoki da ya sakashi ɗagowa a hankali da ga kallon babyn nasa da yake yi ya sauke mata firgitattun idanun nasa da take kira na macizai. Duk da bashi take kallo ba sai da tsigar jikinta ta tashi ta kuma ji kaifinsu a cikin jininta. Sai kawai ta sake ɗaure fuska. Cikin son ta kallesa da deep voice ɗin nan tasa acan ƙasan maƙoshi ya furta, “Ashe haka kika ɗauki darasin nan nawa da gaggawa ɗaliba ta? Ai ban san ke ɗin zaki kasance duka ɗauka ba haka, ga result na first class na gani kam”.        Sosai ta danne zuciyarta wajen nuna masa tamkar bama ta jisa ba balle ta fahimce shi. Amma duk da haka sai da ta ɗan saci kallonsa ta gefen ido. Wani murmushin ƙasaita ya saki tare da miƙewa ɗauke da babyn ya isa zuwa gareta, kafin tayi wani yunƙuri ya kai zaune a bakin gadon har jikinsu na gogar juna. Babu wanda baiji shock a jikinsa ba amma kowanne ya basar. Kaifafan idanun nasa ya zuba mata yana mai kai hannunsa ya ɗago haɓarta ta yanda zai kalla fuskarta sosai da ƙyau. Suna haɗa ido sai kawai ta lumshe idanun nata da ture hannunsa zuciyarta na wani irin harbawa, ita kaɗai tasan mi take ji game da shi, amma bata so tayi giving up, not now. Ƙoƙarin sake riƙo fuskar tata yake yi ta buge masa hannu a karo na biyu. Murmushi yayi mai sauti, tare da faɗin, “Baki son gani na ne?”. Ba tare data sake iya kallonsa ba a tunzire ta ja tsaki da faɗin,, “Aliyu bana son damuwa, wannan rayuwa ta ce, ka fita kamar yanda na buƙata tun farko please. In ma saboda wannan ɗan kazo kasa a ranka baka da alaƙa da shi, koma kana da ita to yafi ƙarfinka danni da ga yau da ga yanzu na datse alaƙar taku har abada.”         Wani irin murmushi ya saki mai ƙayatarwa tare da tsurama babyn ido, sai kuma ya ɗago yana kallonta cikin lumshe idanunsa da buɗesu duk a lokaci guda. Cikin murya mai taushi ya ce, “Mawaddatan'warahmah! Kin taɓa ganin inda aka raba jijiya da ƙashin baya aka cigaba da rayuwa akan ƙafafu? Duk wanda ya kalla wannan ajiyar ALLAHn yasan zufan Aliyu Hydar Mika'il Idris Mawashi ne ai. Shi ɗin jinin jikina ne, ke da kika haifa min shi kuwa jijiyar ƙashin bayana ce, taya kike tunanin zan rayu a lokacin da babu jini a jikina babu lakar ƙashin baya? Please ki kalla cikin ƙwayar idanuna ko sau ɗaya ne, maybe ki karanci abinda ke a cikin zuciyar Aliyu Hydar ɗin ki. So ɗaya yake miki tak da in sha ALLAHU wata mace bazata sake samun kwatankwacinsa ba. Ko so kike sai na kai ƙasa gaba ɗaya zaki yarda da ni?...”        Harga ALLAH kalamansa sukarta suke. Sannan yamutsa mata illahirin jinin jikinta sukeyi. Duk wani ƙwarin gwiwar ta a garesa neman suɓucewa takeyi. Cikin sanyin jiki da rauni ta ɗago idanunta cike da ƙwalla, sai dai bata iya kallon cikin nasa idanun ɗin ba kamar yanda ya buƙata ta maida su ta duƙar.            “pleaseee!”.      Ya faɗa a hankali cikin wani irin salon jan “e” ɗin ƙarshe data saka tsigar jikinta mimmiƙewa gaba ɗaya. Sai kawai ta samu kanta da sakar masa kuka da faɗin, “I say live me alone please Aliyu. Kace ka sakeni bayan ka keta min haddi akan abinda na bada tsahon shekarun rayuwata na hankali ina karewa, mi kuma ya rage da kake buƙata a gareni yanzu? Ko ɗan numfashin da ya sauramin kuma shima so kake sai ka rabani da shi zaka huta? Ka barni dan ALLAH, ka cigaba da zama a nesa da ni ni yafi min I beg you” ta ƙare faɗa cikin haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo🙏.        A hankali ya kwantar da yaron gefe ɗaya, tare da matsawa kusa da ita. Jikinta ta janye baya tana sake fashe masa da kuka. Ƙoƙarin riƙota yake tana buge masa hannu. Bai damu ba ya riƙota ya saka a jikinsa ya rungume tsam. Tana ƙoƙarin masa magana cikin kuka da fisge-fisge ya hanata kowacce irin dama ta hanyar manne lips nashi cikin nata. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya saki yayinda ita kuma ta sake sake masa kuka da san ƙwatar kanta. Sai da ya tabbatar ya saka jikinta yin laushin da ta daina ƙoƙarin raba jikinta da shi sannan ya saketa dan jikinsa ya fara karɓar al'amarin. Da sauri taja jikinta gefe ta dunƙule waje guda tana faɗin, “Mugu ALLAH sai ya sakamin”. Murmushi yay da lumshe idanunsa ya buɗe a kanta. A nutse cikin firzar da huci ya ce, “Muguntar mi nayi ni da halalina kuma. Mawaddat believe me duk wanda ya faɗa miki na sake ki ƙarya yay miki, har abada Aliyu bazai taɓa rabuwa da Mawaddat ba koda ana min azaba da bulalai ina tuɓe a tsakkiyar sanyin ƙanƙara. Har abada Aliyu zai cigaba da kasancewa matsayin mijin Mawaddat ne koda bazata cigaba da rayuwa da shi ba.”         “Aiko dole ka rabu dani, dan inada kalar mijin da nake so in ma auren zanyi amma ba irin ka ba”.      “Ohh just keep your mouth up Mawaddat! Idan ma mafarki kike to ki farka wlhy, kuma duk sanda kika sake ambatar min kalmar wani namiji na rantse miki sai na darje waɗan nan silly lips ɗin naki ta yanda bazasu sake buɗuwa da sunan magana ba”. Ya faɗa cikin hasala da birkice mata tamkar wani bajimin bahagon matashin zaki. Har Babyn da ke a gefensu yana barcinsa na ɗan zabura shima dan tsorata. Da sauri ya ɗaukesa ya mannasa da jikinsa yana mai lumshe idanunsa da suka kaɗa sukai jazur a ƙankanin lokaci. Duk tsaurin ido irin na Lulu ita kanta sai da ta firgita. Dan tsantsar tartsatsin wutar bala'in kishi ta hango a cikin birkitattun idanun nasa. Ta gefen ido ta saci kallonsa, dan ya miƙe yana jijjiga yaron saboda mutsu-mutsun da ya cigaba da yi. Ganin ya fara ƙushin-ƙushin ɗin kuka ya dawo gabanta cikin takun ƙasaita da hasala. Saman cinyarta ya ajiyesa babu alamar wasa a tattare da shi cike da bada umarni ya ce, “Shayar min da yaro abincin sa”.        Ɗago idanunta data ƙanƙance tai cikin hasala da mamakin ƙarfin halinsa. Sai dai hararar da ya wurga mata cikin tashi hasalar ya tabbatar mata wannan fa ba Aliyun baya bane data saba yima yanda taso. Sai ma duk taji tana neman daburcewa. Shiko ganin bata da niyar bama yaro abinda yace kawai ya kai zaune gab da ita kansa tsaye ya tura hannunsa a rigarta ya fiddo, zaro idanunta tai a wani irin razane, sai dai shi ko'a jikinsa dan kallo ma bata ishesa ba hidimar gyara yaron yake da ƙyau ya saka masa a baki. Shiko ɗan albarka ya cafke abinsa da sauri har sai da tai ƴar ƙaran jin zafi. Sai dai ta gagara ture uban da ɗan dan duk ya kanainayeta ga numfashinsa da ke sauka a jikinta wani irin harmutsa mata lissafi yake neman yi gaba ɗaya.  Da ƙyar ta iya fisgo kalmar, “Aliyu wai miye haka bana son wulaƙanci f.....”.           Fuskarsa ya matsar gab da tata ta yanda ta kasa ƙarasa abinda ta faro faɗar, ya wani busa mata iska a fuska da wata irin murya acan ƙasan maƙoshi ya furta, “Naga dai namu ne ai ni da shi. Dan haka bama son hayaniya karmu ƙware”.       “Takaici, haushi, kunya, duk suka kanainaye Lulu a lokaci guda. Ga wani irin neman rikita mata lissafi da kusancin nasu ke neman yi. Shima kansa a wahalen yake da kusancin nasu, dan da ƙyar yake danne zalamarsa da haɗiyeta..... Lips ɗinta da ke rawa-rawa ta buɗe zatayi magana sallamar Ummita ta katse ta, Ummita da ta shafa'a da kasancewar sa a ɗakin bata jira an amsa mata ba ta shigo, hakan ya sashi jan jikinsa baya da gyara mata yaron cike da basarwa. Ita ma Ummitan sai tai saurin juyawa zata koma cikin ruɗewa tana faɗi, “Ya ilahi dan ALLAH kuyi haƙuri, wlhy na shafa'a”.       Smart ne cikin ɗan furzar da iska mai nauyi ya furta, “Karki damu dawo abinki”. Badan Ummita taso ba ta dawo, sai dai kanta a ƙasa ta ajiye bowl ɗin data shigo da shi mai ɗauke da gasashen nama da yaji kayan haɗi da Mamy ke haɗama Lulun duk bayan kwana biyu. Zata juya Lulu dake hararar baby da babansa ta dakatar da ita da faɗin, “Ummita anko samo zam-zam ɗin?”.      Kanta a ƙasa ta ce, “Eh Yaya Usman ya sayo tun ɗazun ai, harma da zumar”.           “Yauwa dan ALLAH haɗo a fidarsa kin sanshi ba ƙoshi yake ba ya gado ci irin na ub....”      Sai kuma ta kasa ƙara sawa ta murguɗa baki kawai. Murmushi Smart ya saki, a hankali ya furta, “Ai dama ƙyawun ɗa ya gaji Ubansa. Baki ji har sunan bai bari ba ya gado. Ashe haka kike son sunan nan amma baki taɓa faɗa min ba?”.        Harararsa tai cikin takaici tana jin kamar ta shaƙurosa. Sai dai batai magana ba dan sai ma yanzu take jin haushin kanta da tace a saka mata sunan. Baki Smart ya taɓe kaɗan shima da ɗaukar bowl ɗin naman ya buɗe, guda ya cira da ɗan tsinken da aka sako a ciki ya kai baki yana lumshe ido. Hakan ya saka Lulu zuba masa nata idanun batare da ta lura da abinda take yin ba har ya buɗe nasa da suka wani ɗan shanye tare da yin luww kamar mai jin barci. (He looks so handsome) zuciyarta ta ayyana mata. A fili kam sai tai saurin fara janye nata tana wani taɓe baki. A kasalance shima ya janye nasan yana jan ajiyar zuciya.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣5️⃣ .......Sai kawai ya miƙe zuwa jikin window ya ƙurama waje idanu yana kallon shuke-shuken fruits da ganyayyakinsu ke sake ƙawata ƙamshin wajen. Da ƙyar ya iya samu ya dai-daita kansa a wajen har Ummita ta shigo ɗauke da zam-zam mai haɗe da zuma a ɗan wani kofi da ƙaramin spoon. Tana ajiyewa bata zauna ba ta fice. Nannauyar ajiyar zuciya ya sake sauke a karo na babu adadi da takowa ya dawo gaban gadon, komawa yay ya zauna a inda ya tashi tare da amsar yaron data janye a jikinta tana gyara riga. Amsarshi yayi yana goge masa baki, ita kuma sai ta miƙe masa ɗan cup ɗin. Cikin ɗan tura baki a ranta tana faɗin (Kaima ka ɗan ɗana wahalar da nake ci a kansa) A mamakinta babu musu ya amsa. Kamar kuma dama can wanda ya saba da rainon cikin nutsuwarsa ya ɗibo ruwan zam-zam ɗin mai haɗe da zuma ya zubama yaron a baki kaɗan sai gashi yana ɗan motsa bakin da yamutsa fuska. Hakkanne ya saka Smart sakin murmushi har ya ɗago ya kalli Lulu da itama dai kallon nasu take yi. Kauda idanun nata tai ta maida kan bowl ɗin namanta ta fara ci. Cikin ɗage gira ya ce, “Wannan dai ƙwaɗayinki ne ya gado Madam”.       Da sauri ta ce, “Wa ɗin? ALLAH ya sawwaka mi muka haɗa da shi da zai gado ni, haɗuwa a duniya rabuwa a cikinta”. Sosai maganar tata ta bashi dariya, amma sai baiyi ba yay murmushi kaɗan yana girgiza kansa. Ganin yasha sosai ya goge masa baki ya gyara masa kwanciya a ɗan gadonsa. Lulu ya kama tana kallonsu, amma yana juyowa ta kauda kanta gefe. Kusa da ita ya koma ya zauna gaf, batare da yayi magana ba ya amshi tsinken da take cin naman ya tsira shima ya kai bakinsa, sake tsiro wani ya kai mata baki, idanunta ta zuba masa batare data buɗe bakin ba, shima kallon nata yake a yanayin kasala, dan haka ya ɗan lumshe nasa idanun da kaɗa mata kansa alamar ta amsa. Kamar mai jin ciwo akan lips ɗin ta motsa su da ƙyar shi kuma ya saka mata naman. A kusan tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya su duka. Da ga haka ya cigaba da bata yana ci, sun ci kamar lauma uku a bazata ya jeho mata tambayar da ta sakata ɗan daburcewa, amma jarumar taku sai ta dake abinta.        “Mi yasa kika zaɓi yin rainon cikin nan ke kaɗai batare da ni ba?”.       Cikin basarwar nan tata da son dakewa batare data kallesa ba ta ce, “Miye haɗina da kai da zamuyi rainon ciki tare?”.               “Mai ciki da abunsa har ace miye haɗinsa da cikin. Serious banji daɗin haka ba Mawaddat. Naso ace Ni ne da kaina na kula da ke tamkar ƙwai a cokali a wannan gaɓar. Ban taɓa fuskantar minene ainahin ƙunci ba sai da na waiga babu ke a duniyata, nasan har yanzu zuciyarki na baki na aikata miki abinda ya faru a wancan ranar bisa son zuciya. Ko kaɗan ba haka bane, dan ina son kasancewa da ke basai na baki komai ba ai, domin ke ɗin halalina ce, mizai sa saina wahalar da kaina ta hanyar gusar miki da hankali kamar wani matsoraci. Kin taɓa ganin Aliyu Hydar a matsayin KURE ba ZAKI ba?”. Harararsa tai, sai dai ta kasa cewa komai, shima sai ya ɗan murmusa kaɗan da cigaba da bata naman yana faɗin, “Duk abinda ya faru a wannan ranar Ahmad ne ya ƙullasa bada sani na ba, sai dai karki damu zan rama miki ai kinji ƴar ƙanwata”.         Cikin suɓutar baki da harararsa akan ƙanwarsa daya kirata tana waro idanu ta ce, “Ahmad fa? Taya zan yarda hakane?. Sannan akan Maryam ɗin? Zaka rama?”     “To mata tafi mata ne? Shi ya jawo mata ai. Duk da dai ni ya biyani tunda ban wahala a banza ba ga AA Mawashi na a kusa da ni”. Karan farko tai kamar zata saki murmushi sai kuma ta hararesa ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Sai ka shirya amsa hakan a gaban alƙali ai. Dan sai an bimin kadin hakkina na fyaɗe”.            “Shima alƙalin koroki zaiyi da ga gabansa ai. Nidai yanzu nace magana ta wuce kawai, Aima Abbien AA afuwa bazai sake yin fyaɗe ba”. “Humm” ta faɗa tana mai lumshe idanunta. Shima sai ya zuba mata nasa kawai yana kallonta cike da shauƙi. Cikin motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Ke ƙyaƙyƙyawa ce Mawaddatan'warahmah”. Da sauri ta buɗe idanun nata a daburce, dan yanda ya furta kalmar sai taji kamar ya haɗa da jinin jikinta ne ya zuƙe har ma da numfashi, kafin ta samu damar cewa komai Usman yay sallama. Amsa masa yay yana mai dafe goshinsa da faɗin, “Gaskiya baka iya zuwa ba”. Ƙaramar dariya Lulu tai tana kauda kai, shi kuma ya harareta da bashi izinin shigowa bayan ya miƙa mata mayafin da ke ajiye gefenta da faɗin, “ALLAH yasa ma ba haka kike zama min a gabansa ba yana kallemin kayana”. Yanda yay maganar cikin ɓata fuska ya sakata sake sakin murmushi, cike da neman tunzurashi ta ce, “Mi kuma ya rage bayan shine mai karɓar haih....”        “Mtsoww! Shut up!”.      Ya faɗa a hasale yana balla mata harara fuska a gimtse. Dai-dai nan Usman ɗin ya ƙarasa shigowa, sama-sama ya bashi hannu suka gaisa, kafin ya ɗan juya yama Lulu tambayoyi game da yanayin jikinta. Ta tabbatar masa da Alhmdllh bata jin komai. Shima hamdalar yay yana ɗan duban Smart da murmushi, “Oga zamu iya wucewa masauki ko anan zaka kwana ka taya Madam jego? Dan itama lokacin barcinta yayi”.        “Kaga dana ɓarke ɗinkin sai ku tara min jama'arku na likitoci kenan”. Smart ya bashi amsa da ɗan barkwanci duk da da gaske maganar Lulu ta sosa masa zuciya amma ya danne. Ƙaramar dariya Usman yay da faɗin, “Ai kai oga ne zamu ɗaga maka ƙafa kodan Son ɗina AA”. Murmushi Smart ya sake yi kawai bai ce komai ba. Usman kuma ya matsa ga Lulu ya mata allura da duk sauran abinda ya dace sukai mata sallama, gaba Usman yay ya barsa. Ganin yanda Smart ɗin ya raka bayansa da kallo mai kama da harara yasa Lulu saurin faɗin, “Nifa wasa nake maka kada ka ƙullacin bawan ALLAH bayan ƙoƙarin sa a kammu. Kana dai ganin a yanda yay min allura ma cike da taka tsantsan”.       Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da ɗan lumshe idanunsa da launinsu har ya canja. Batare da yace mata komai ba a karo na biyu ya ƙarasa gareta ya rungumeta tsam-tsam a jikinsa ta yanda dai bai taɓa mata ciwo ba. Su dukansu babu wanda bai sauke ajiyar zuciya ba, yayinda Smart ya shiga laluben lips nata. Da sauri ta janye jikinta saboda jiyo takun tahowa, shima sai ya miƙe dan dai-dai nan Ammah tai sallama. Gaban gadon Babyn ya koma tare da kama hannayensa ya fara tofa masa addu'oi. Har saida ya kammala sannan ya ɗago yana kallon Ammah da ke taimakawa Lulu ta kwanta yanda zataji daɗi. Sun ƙara haɗa ido da Lulun ta kauda kai shima ya kauda da ɗan salon taɓe baki yana wani lumshe idanunsa..... *_NIGERIA_*      Sosai jikin Dada ya ruɗe a safiyar yau dan haka hankalin ƴaƴanta a tashe yake matuƙa. Cikin ƙanƙanin lokaci aka shirya mata barin ƙasar. Baba Garko na Abuja a lokacin Uncle Khamil ya kira shi a ruɗe yana sanar masa zai tafi Kano jikin Dada ya tashi sosai. Duk da ya ji damuwa a ransa sai ya danne cikin nuna halin ko'in kula ya ce, “ALLAH ya bata lafiya” ya kashe wayar abinsa. Abinda Baban yay ya sake tada hankalin yaran. Dan sun sake tabbatar da har yanzu ransa a ɓace yake akan mahaifiyar tasu. Haka suka shirya wasu a cikinsu suka wuce da ita gwiwa a sage. Wanda aka bari a gida kuma suka bita da addu'a kafin suma subi bayansu da ga baya. Matansu kam addu'a suke ALLAH yasa da ga can ta wuce ko zasu huta da samun sukunin zama da mazajensu cikin ƴanci kamar kowacce mace a gidan aurenta. Dan gaskiya surukar tasu ta musu kane-kane a cikin rayuwar aurarrakin nasu....         (To mudai munce ALLAH ya baki lafiya Dadansy).        __________★     Duk da zuciyarta a dagule take da wannan tafiya ta mijinta da kishiyarta da tafi tsana fiye da kowa a rayuwarta ta wani fannin hakan ya taimaketa, dan ta samu damar aiwatar da mugayen nufinta akan wanda suke wa taƙamar da tinƙaho. Saboda tayi alƙawarin kofa komanta zai ƙare ita sai taga bayan Smart da uwarsa. A haka ma dan bata san ainahin abinda ya kaisu UK ɗin ba kenan. Hankalin aunty amarya ya tashi da ganin kai-kawon da Umma ke yi, dan haka kawai zuciyarta ke ayyana mata kai-kawon bana banza bane ba. Su dukansu sun jima suna zargin Umma akan shige-shigen gidajen malamai. Dan a wasu lokutan sukan kasa gane kan mijin nasu ta koma sai ita kaɗai ce madubin dubawarsa. Sai sun dage da addu'a abin yay sauƙi kafin ta sake masa sabon aike. Wannan dalilin yasa a yanzu ɗin ma Aunty Amarya ta shiga damuwa. Sai dai ta rasa dawa zatayi maganar dan Mama ita ba gane kanta ake ba wasu lokutan sai a hankali ce. Ga shi su Maryam basa nan. Ganin abin nata cigaba da alamomi masu yawa ta ɗaga waya tai kiran aunty Bilkisu akan tazo dan ALLAH idan ta samu lokaci. Da sauri Aunty Bilkisu ta tabbatar mata da gatanan zuwa.           Da yamma ko sai gata, sai dai ta nuna kamar daga wani waje take ta biyo gaishesu. Sama-sama Mama da Umma suka amsa mata gaisuwarta, dan suna cike da takaici da kishin tafiyar Abba da Ammah. Aunty Bilkisu bata nuna ta damu ba ta shiga ɗakin aunty Amarya abinta. Tsakanin aunty Bilkisu da aunty Amarya suna abune kamar ƙawaye, duk da aunty Bilkisun ta girmeta kaɗan, bayan sun gaisa babu ɓata lokaci suka shiga tattauna abinda ya tara su. Sosai hankalin Aunty Bilkisu ya tashi da bayanin aunty Amarya, duk sai ta rikice. Cikin kwantar da hankali aunty amarya ta ce, “Bilkisu dan ALLAH karki ruɗa kanki, mu nutsu muyi tunanin abinda ya dace, dan kinga dai bawai tabbas garemu ba zargi ne”.         “Aunty wannan ai ya wuce zargi tunda har kinji tana ambatar sunan Hydar ɗin da matarsa. Wlhy nikam al'amarin Umma ya fara bani tsoro a gidan nan. Ko kin san kwanan nan sai da taje ta kaima kishiyata gulmar Ammah da har ta kaimu da yin faɗa. Alhaji ne ya tausheni da kar nazo gida na faɗa kamar zaimin kuka. Kuma ya tabbatar min da ai ta daɗe tana kai musu gwabsona dana Ammah kawai dai yanzu ne ALLAH ya tona asirinta. Akan wannan rigimar yanzu haka uwargidana na gidansu ya mata saki ɗaya”.             “Innalillahi. Itako Umman Hannatu mi take son zama ne? Wlhy al'amarin ta na bani mamaki”.       “Dolene abinta yake bada mamaki ai Aunty, ki duba fa yanda ta tada hankalinta a gidan nan tunda taji Hydar na ƙasar waje. Ni wlhy zuciyata ma har ta fara zarginta akan matsalar da yayta samun nan a baya. Kawai dai dan Ammah tace kar nayi magana ne”.           “Eh ai tabakin Yayar gara a barta, ita da kanta halinta zai tsangwameta kowa ya shaida. Amma yanzu idan akaji a bakin wani a cikinmu za'a ɗauka sharrin kishi ne kawai. Kin san kuma Yaya ita komai nata a nutse ne bata son gaggawa. Shiyyasa yanzu ma kikaga na nemoki dan kota dawo bana son na fara mata maganar, duk da nasan zata fahimce ni”.        “Hakane Aunty, yanzu to yaya zamuyi?”.       “Addu'a zamu dage da ita, mu kuma saka a cigaba dama Aliyu shima har sanda su Yaya zasu dawo miji nata shawaran”.     Aunty Bilkisu ta gamsu da shawaran aunty Amaryan, dan haka suka cigaba da tattaunawa. Bata bar gidan ba sai bayan sallar magrib........✍️ _Network kaje dan kanka. Na barka da ƙarfen da ake maƙalaka ehe🥱🥱🚴_. _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣6️⃣ .......Kamar yanda Daddy ya faɗi zasu tattauna da Smart tun a waya ya cika alkawari, dan washe gari tunda safe ya baro Abba da Uncle Yousuf ya sami Smart a gidan su Usman dan nan ya kawoshi. Sun gaisa cikin mutunta juna kafin su fara tattaunawa. A nutse Daddy ya fara ma Smart bayanin mafarin komai tsakaninsa da Sulaiman har zuwa yau da suke tare. Matuƙar girgiza Smart ya shiga, tare da jinjina ƙarfin halin Daddy da sake ganin kimarsa. Ya jure ɗaci da damuwa saboda kawai karya rama sharri da alkairi, saboda kare mutunci da lafiyar ahalinsa. Cikin zubda hawaye Daddy ya katse Smart da faɗin, “Abu ɗaya ne ke cimun zuciya a yanzu Aliyu shine cutar da matarka da nayi, kwarai da gaske na zalunci rayuwar Mawaddat dan rashin ilimin addini babbar naƙasu a rayuwar ɗan adam. Gara ace mutum bai san komai a limin boko ba dan wannan iya kar alfaharinka da shi shine duniya. Inajin kunyarta ta yanda a duk sanda na tunata nakanji hawaye na zubarmin tunda ba haka naima sauran ƴan uwanta ba. Wlhy alokacin idanuna ne suka rufe da iya tunanin kuɓutar da ita da ga sharrin Sulaiman ne kawai shiyyasa. Iya ƙoƙari Yousuf kuma yayi na ganin ta samu ilimin har malami ya nema mata a can Germany amma tsoron karda a haɗa baki da Malamin a cuta mata yasa na hana hakan. Ashe na manta UBANGIJI shine mai ikon tsarewa da killace bawa da ga sharrin masu makirci da ƙulle-ƙulle ba wai wayo ba. Domin nayi gudun gara na faɗa gidan zago. Dan ALLAH ka tayani bata haƙuri da neman gafararta, ka tayani gina mata sabuwar rayuwa, ka tayani horas da ita sababbin ɗabi'u, ka tayani ɗorata a hanyar tsira Aliyu kafin ɗan sauran lokacin da ya rage min ya ƙure mana ni da ita. Dan nasan da wahala na tsallake da ga tarkon Sulaiman saboda shu'umi ne na gaske. A yanzu haka ya ƙullaci mahaifinka akan maganar kotun nan, amma Alhamdullah babu abinda ya isa masa dan duk inda ya saka ƙafa na saka ƴan sandan farin kaya biye da shi, bama shi ba hatta ƙannenka dake gida dana ma'auri al'amarinsu na ƙarƙashin kulawar hukuma a duk sanda zasu bar gida. Kayi haƙuri kaima Aliyu na sakaka a rigimar da baku san mafarinta ba, shiyyasa raina fansa akan ganin wani abu bai cutar da ku ba a dalilina. Amma dan ALLAH ku yafe min duk laifina ne, da ace nayi nazari kafin na biyema Sulaiman tun farko maybe da duk bamu kai a irin wannan matakin ba.....”           “Daddy jarabawace kawai, bawa kuma bai isa tsallake ƙaddararsa ba. Ba kamana laifin komai ba sai alkairi a rayuwa. Babu abinda zan iya cemaka sai godiya da cigaba da maka addu'a har ƙarshen numfashina. Ba laifinka bane Mutumin nan hatsabibin ne na gaske. Na fahimci hakan tun a haɗuwata da shi ta farko. Dan haka na zauna na karancesa yanda ya kamata, sai dai rashin sanin abinda ke a tsakaninku yasa ban taɓa wani yunƙuri ba. Amma tabbas na jima da lura da duk inda nake ana biye da ni, hakama ƙannena, na shiga tashin hankali saboda a tunanina Sulaiman ne, sai daga baya na fahimci ƴan sanda ne, sai dai babu irin bibiyar da ban musu ba sunƙi gayamin wanda ya sakasu, sai nai tunanin ma ko Uncle Yousuf ne ko Coach a lokacin, shiyyasa na zaɓi musu shiru a ganina wataran ai zan sani. Kamar yanda na faɗa maka ina son ka bar wannan case ɗin a hannuna yanzu, sannan ina son na bada shawara....”        Cike da kulawa Daddy ya ce, “Ina jinka Aliyu, ka faɗi komi ke'a ranka kai tsaye tsakaninmu babu wani ɓoye-ɓoye”.      Kai Smart ya jinjina tare da furzar da iska mai nauyi. “Wato Daddy irin su Sulaiman da hatsabibancinsu yaƙin sunƙuru yake buƙata a farkon fara wasa. Kamar yanda ka ɗauki masa salon shekarun da suka gabata na nuna baka san mi yake ciki ba wannan salon zamu cigaba a yanzu har zuwa wani mataki. Domin idan har akace za'ai masa fito-na-fito a shirye yake da wannan tun ba yanzu ba. Jirace yake da kai kace kule yace cass. Sannan mahaifinsa da kai hallacin shanye komai daminsa zai iya samun bugawar zuciya wlhy in har yaji kasuwancin da yake yi da kuma ketama autarsu mutunci da yayi. Ko kuma shi da kansa ya shirya hanyar halakasu idan yaga zaka cimma burin tona masa asiri. Kaga anyi gudun gara kenan an faɗa gidan zagon dai. Dan haka mu ajiye batun fito-na-fito ɗin nan mu lallaɓa Baba Garko ya sakar masa ɗansa, ka cigaba da nuna masa kana shakkar tasa, sauran yaƙin ka bar mana zamu ƙarasashi ni da Mawaddat da Uncle Yousuf in sha ALLAHU”.       Idanu kawai Daddy ya zubama Smart, yama rasa abin faɗa akan wannan yaro. Lallai farar haihuwa tayi, dan shikam dole ya kira wannan yaro da farar haihuwa ga iyayensa. Smart ne da yaga kallon da Daddyn ke masa yay ƙasa da kansa yana murmushi kawai.... __________★    Yau kam Ammah da kanta ta wanke ɗan jikanta ta gyarashi ɗaras ɗas. Yayinda Mamy ta gyara Mawaddat ita kuma Ummita ta shirya abinci. Lulu da ke jin jikinta wani iri tunda garin ALLAH ya waye cikin damuwa take sanarma Ammah ta mata addu'a gabanta sai faɗuwa yake. Jawo hannunta Ammah tai ta zaunar kusa da ita cikin damuwa da kulawa ta fara mata addu'oi, a hankali Lulu ta dinga samun nutsuwa har ta ɗan sha tea ta kuma shayar da AA abincinsa. Sun kammala kenan Ummita na gyara mata gashinta su Smart suka iso niƙi-niƙi da kayan da ya siyo bisa jagorancin Usman. Da mamaki Lulu ke kallonsu su da kayan, Usman ya nuna Smart cikin ɗaga hannu yana ficewa acewarsa bari yay kiran Dr Lameer.          Lulu da ke jin faɗuwar gabanta na dawowa tun shigowar Smart ɗin ɗakin cikin dauriya ta ce, “Good morning” a takaice. Bai amsa mata ba sai da ya ɗauki AA tare da kaiwa zaune cikin kujerar dake a gaban gadon ya ɗan ma yaron kiss a goshi da kumatunsa sannan ya dubeta idanu ƙasa-ƙasa. Kamar wanda baya son motsa lips ɗinsa ya furta, “Haka ake gaishe da miji? Kamata yay kizo da gudu ki rungumeni da bani ƙyaƙyƙyawar sumba ki ce good morning rabin raina” yay maganar cikin kwaikwayon muryarta. Harara ta zuba masa da saurin faɗin, “ALLAH ya kiyasheni. Miye wani rabin rai babu ko daɗin ji.....”         “Ki rantse ni ba rabin ranki bane”.     “Kana buƙatar ganin likita kam”. Murmushi ya saki da ɗan lumshe idanunsa yana gyara AA da ƙyau. “To muje a hakan, idan tai wari maji ai. Ina fatan kun tashi lafiya ke da baban Ammah?”.       Cikin ɗan marairaice fuska ta ce, “Wane lafiya bayan ya hanamu barci, ka masa faɗa gaskiya ni bana son damuwa. ALLAH nima sai da nai kuka duk ya ruɗamu ga Ammah tayi tafiya ta gaji ya sata tanata faman jijjigarsa”.              Gaba ɗaya neman harmutsa masa lissafi take da salon nata. Ƙaramin gyaran murya yay saboda jin yawu na neman sarƙeshi. Hakan yasa Lulu zuba masa ido, sai yay saurin janye nasa da ke neman canja launi cike da basarwa ya ɗan lakace kumatun AA da faɗin, “My Grandpa miyasa ka hanamin Mata barci? To da ga yau karna sake ji kaji Sadaukina. Kuma ka bama Maah-maah haƙuri” Sai kuma ya ɗago ya dubi Lulu data zuba musu ido, a yanayin ɗan ɗage gira ya ce, “Koda yake ni ya kamata ma na bada haƙurin nan a madadinsa” ya ƙare maganar yana tasowa. Ƙoƙarin sauka tai a gadon tana faɗin, “Ni dai ban gayyaceku ba”.       Cikin ɗan murmushi ya ce, “Oh oh har ma takai gudunmu akeyi. Haƙuri da kawai zamu baki”.    “Na haƙura basai kunzo ba”. “Please mana Baby luv ko ɗuminki ki bari muji mana”.             Dama ta fahimci wayon nasa kenan, dan haka ta maƙe kafaɗa kamar wata ƴar baby da faɗin, “Naƙi ɗin. Kai koma kunya bakaji a gaban ɗanka sai kayi taɓara. Ka rage halin nan wlhy rashin jin magana zalla”.        Komawa yay ya zauna yana dariya da faɗin, “Kema ai rashin jin ne ya kaiki ga samo AA Mawashi. Haka kawai kin lalatama Ammah yaro, sai kawai ta ganki da yaro a hannu kuma dai tasan a inda kika samo.....”            “What!!”       Ta faɗa da sauri cikin daburcewa kamar Ammah na gabanta. Aiko ya shiga yin dariya a hankali. “Ni dai ai kowa yasan ni babu ruwana salihin ALLAH. Ina zaman zamana kikace sai anyi yaƙin ƙasa da ƙasa. Tsabar zalama baki fito a filin dagar ba sai da ganimar yaƙi wannan yarinya sai a barki kawai amma dai gaskiy....”         Fillon data ɗauka zata jefa masa ya hanashi ƙarasawa, cikin ɗaga hannaye sama da sauri alamar surrender ya ce, “Yi hakuri nayi shiru, ke kam akwai kawaici nine zalamammen ga shi ma AA ni yabiyo tabbacin haka”.          Hararsa tai da ajiye filon ta koma ta zauna. Sai kuma cikin damuwa da marairaicewa ta ce, “Da gaske dan ALLAH su Ammah suna ganin bani da kunya ko? Wata goma da kwanaki dayin aure na haifi yaro, wlhy nima abin na damuna, sai nake ganin abin yayi kusa da yawa kamar wata mayyar miji”.       Daƙyar Smart ya iya danne dariyarsa. Dan ya fahimci tsakaninta da ALLAH take tambayar. Cikin kaɗa kai ya ce, “Kai kai baza'a suce ba Madam. Sai dai ma a kiraki da jaruma mai matuƙar hazaƙar ɗaukar darasi a wajen malaminta. Ammah kam ai zata so nan da wasu watannin goma masu zuwa ki sake santalo mata wata baby girl ma again”.              Sosai ta waro manyan idanunta kamar zatai kuka. “Hydar wane fatan tsiyane kuma wannan dan ALLAH mutum ko gama dawowa hayyacinsa baiyi ba kamar wata akuya. Kasan miye rainon ciki da haihuwa kuwa?. Wlhy akwai wahala, ni da ga ɗayan nan ma na gama gaskiya”.         Tsam ya taso da ga inda yake zaune ya dawo kusa da ita. Cikin nuna damuwa ya ce, “Da gaske akwai wahala? Bani labari yaya kika kasance?”.       Lumshe idanunta tai a hankali tana mai ƙara shaƙar ƙamshinsa mai masifar daɗi, duk da dama dai tun ɗazun take shaƙar, kusancin da suka samu yanzu ne ya ƙara ƙarfinsa sosai a cikin han nacinta. Hannunta ya ruƙo tare da murzashi a cikin nasa a hankali. Idanun ta buɗe tsigar jikinta na tashi. Ta kalli hannayen nasu ta ɗan sake lumshe idanun nata da sake buɗewa. Cikin ƙara ƙasa da muryarta batare da ta farga da canja salon harshen nata ba ta furta, “Ai ya wuce kuma, share kawai”.         “Please ina son ji nidai”.       Ya faɗa yana murza mata hannu a ɗan marairaice. Hannun taso janyewa dan yana sata a wani yanayi salon nasa, amma ya hana hakan, sai kawai ta saki ajiyar zuciya a hankali ta furta,........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣7️⃣ .......“Humm akwai wahala sosai da bata da misali. Na ƙara jin ƙaunar mahaifiyata da jinjina mata wahalar da tai dani a dalilin wannan cikin. Ko abinci bana iya ci, da naci sai amai, ko wani abu na sha sai nayi amai. Gashi nan ko yanzu dana haihu magani ma ya gagareni sai dai allurai ake min dan in naga magani amai nake ji. Kunun gyaɗa ne kawai ya zama abincina kwana da yini. Gaba ɗaya dai abin babu sauƙi kawai dan ba'a iya misaltashi ma Aliyu. Balle naƙuda Hummm......”          Duk da a dunƙule ta bashi labarin ya fahimci dai ciki ya hanata shaye-shaye, sai kunun gyaɗa daya zamar mata abinci kawai. Cikin ƙara sanyaya murya da jin tausayinta da farin ciki ya ce, “Addu'ata dare da rana UBANGIJI ya tasirantar da itane atare da gudan jinina, ya ƙarasa min aikin dana fara kenan, sannan a kowane awa bayan awa yana tuna miki Abbiensa ne ta hanyar shan abinda yafi so fiye da komai.” yanda ya ƙare maganar da ƴar dariyar tsokana ya sata ɗan harararsa da taɓe baki, sai dai batasan hararar tata ba ta juye ne zuwa wani sassanyan kallon dake neman hargitsama Smart lissafi da hankali.        “Ita hararar nan tana son tada zaune tsaye ne fa. Zakuma ta iya takalo yaƙin ƙasa da ƙasa a taƙaice rigakafi yafi magani”. Ya faɗa a wani irin kasalance yana ƙasa-ƙasa da idanu. Ba fahimtar zancensa tai ba, amma salon da yay maganar da yanda yake wani narke idanu da murya ya sata janye jikinta a nasa cikin basarwa duk da saƙon nasa ya isa ga manyan mata fiye da yanda yay tsammani. Shima kawai sai ya basar cikin sauke ajiyar zuciya ya ce, “Yanzu miye shirinki akan suna gobe idan ALLAH ya kaimu?”.        Cikin mamaki ta ce, “Suna kuma? Da suwa za'ayi sunan to? Bayan naga idan za'ai suna a gida Nigeria taruwa dangi sukeyi da matan anguwa, in dai ban manta ba haka na gani a sunan Deen ɗin mu fa anyi, anan kuma mu yanzu wa garemu da zai zo?”.       “Mu mana, iya mu ɗin nan ma ai mun wadatar muyi suna bawai wajibi bane sai antarun kamar yanda kika gani a sunan Deen, in sha ALLAHU kuma za'a yanka masa rago kamar yanda ake yankama kowa. Ƙyautar da ban san da itaba ce ba fa a hannuna, taya bazan nuna godiyar ALLAH ba nikam. Sannan ni so nake daga nan mu wuce kawai basai kin koma Nigeria ba”.      “Hanyoyin nuna godiyar ALLAH ai suna da yawa ba sai ta hanyar yin taron suna ba. Sannan idan ban koma Nigeria ba ina kake son naje banda neman magana irin taka. Kuma ni nama faɗa maka na shirya cigaba da zama da kai ne? Auren contract akayi kuma ya ƙare it's ok”.         “Hakane kam, Alhamdullah suma waɗan can godiyar UBANGIJI ɗin duk na kamanta su, amma duk da haka dai ina son muyi shagalin suna. Kinga koda ƙannensa sun zo nan gaba suma shi bazaiga an musu ba'ai masa ba”. Ya ƙare maganar batare daya amsa maganartata ta ƙarshe ba.       Hakan ya bata haushi, dan haka a tunzire ta ce, “Miye wani ƙanne? Malam ka san abinda kake faɗa fa! Na gaya maka ni na gama auren nan”.     Dariya ta bashi ganin yanda tai maganar a gatsire, amma sai ya danne da ƙyar yay murmushi kawai da faɗin, “Naki tsarin kenan wannan ai”.        “Kamar ya nawa tsarin kenan?. Amma kasan dai ba haka akai da kai ba ko?”.        “Humm” yace kawai. Baice komai ba akan maganar tata yanzun ma, sai ma ya nuna mata ledojin da suka shigo da shi. “Kuyi haƙuri da waɗan nan babu yawa, sauran abinda ya dace duk na damƙashi a hannun Usman. Munyi magana da Daddy akan suna son a turaki Saudiya ki zauna a can na wani lokaci saboda Kawunki Sulaiman, dan bazai taɓa ƙyaleki ba zai cigaba da bibiyar al'amarin ku. Ke yaya kika gani?”.          “Ni babu inda zani, shi ɗin banza da zan cigaba da masa wasan ɓuya. Ko wannan ɗin ma da yaga yaci nasara saboda Dada ne wlhy, sannan ina kan sani na cigaba da biye masa bayan nasan manufarsa. Nayi hakkanne kawai domin sake tabbatar da shi ɗin waye. Amma har miye wani Sulaiman can”.        Murmushi yayi kaɗan, a zuciyarsa yana ayyana (ashe a wajen Daddy kika gado wannan taurin ran naki da kafiya) a zahiri kam sai ya nisa cikin ɗan cije lips ɗinsa ya ce, “Zamu iya tunanin shi ba abin tsoro bane ba, sai dai idan muka shagala da hakan zai mana illa a ƙanƙanin lokaci cikin salon duka ta inda bazamu taɓa iya sosawa ba balle mu rama. Mawaddat Kawunki ya wuce duk yanda kike tunani a kansa. Domin ya jima biye da rayuwarki tun kina ƙarama. Bana raba ɗayan biyu shine ya koya miki shaye-shaye. Kuma shine ya taɓa harar rayuwarki ta hanyar keta miki haddinki har kike firgita kika tsani maza....”        Da wani irin sauri ta kallesa, sai kuma jikinta ya fara tsuma. Dan danan annurin fuskarta ya ɓace gaba ɗaya. Cikin yanayin faɗa-faɗa ta ce, “Aliyu rayuwata ta baya ta zamar maka abar bibiyane ko mi?”.         “No ko ɗaya, mizai sa na bibiya bayan na gama fahimtar komai. Sannan Mawaddat nake so ba halayenta ba. Ruwana ne na maidata a irin halayyar da nafi buƙata kona barta da wanda na ganta a ciki. Mawaddat ki sani shure-shure baya hana mutuwa, duk yanda kike jin zaki iya ɓoye abinda ya faru a baya wataran zuciyarki bazata iya ɗauka ba. Kiyi haƙuri ba ina tilasta miki bane sai kin sanar min, kidai sani cigaba da riƙewar zai iya sake nakasaki akan shaye-shayen nan. Doctor ya jima da tabbatar da idan kika cigaba zaki cutu, sannan a yanzu ke ɗin Uwa ce Mawaddat, taya kike tunanin idan yaron mu ya taso yaji wannan ɗibi'ar koda a labari ne zaiyi farin ciki. Mahaifiyarki mutuniyar kirkice data shinfiɗama rayuwarta alkairai da dama da a yanzu sune ke bibiyarta da ke kanki har maƙiyanki da nata suka gagara cin galaba a kanki. Taya kike tunanin naki ɗiyan zasu samu irin wannan kariyar idan har baki zama uwa ta ƙwarai ba Mawaddat. Please ina so ki canja, canjawar taki kuma zata tabbatane kawai ta hanyar fidda abinda ke zuciyarki, dan shine yay miki nauyin da har kike jin abinda kike sha zai iya danne miki shi. Taya za'a gyara ɓarna da ɓarna banda wautarki......”          Wani irin kuka mai tsuma zuciyar da ta saki ne ya saka shi yin shiru, a hankali ya furzar da iska tare da miƙewa ya koma daf da ita, matsota yay ya saka a jikinsa ya rungume. Sai kawai ta sake sakin masa kuka da iya dukkan ƙarfinta da baƙin cikin dake cinkushe da zuciyarta da ƙwaƙwalwa. Bai sake mata magana ba ya barta tai kukan mai isarta dan haka zai rage mata nauyin zuciyar. Tako yi kukan sosai dan sun kai kusan awa guda tana abu ɗaya har sai da taji kanta na sara mata sannan tai shiru ta koma shashsheka. Cikin son kauda yanayin ya ce, “Uhm nace ba! Yau dai anan zan kwana ko? Naga ai gadon zai ishemu”.       Da sauri ta ɗago tare zuba masa harara da kumburarrun idanunta da suka sha kuka. Murmushi yayi da marairaice face yana shafa kai. “Nifa bance wani abu ba Madam. A wajen kwanciyar ma na yarda sai ayi kai da ƙafa AA a tsakkiyar mu. Kinga dai ai babu batun kawo harima balle ace da wata manufa nazo”.         Filo ta ɗauka ta maka masa. Ya shiga karewa shi kuma yana ƙyalkyala dariya. Dai-dai nan Usman yay sallama. Hararar ƙofar Smart yayi cikin dafe kai. Hakan ya saka Lulu dariya ta amsa da cema Usman bismillah shigo. Babu kunya yana shigowa Smart ya hararesa da faɗin, “Kai wai miyasa baka iya zaɓar lokacin zuwa bane ɗakin mutane?”.             “Oh ba'ai farin ciki da zuwana ba kenan na koma?”.       “Eh gaskiya koma anjima sai ka dawo, wannan ai shiga tsakanin masoya ne”.      Ita Lulu abin harya bata kunya tana kallon Smart ɗin a daburce, sai taji Usman ɗin cikin dariya yana faɗin, “To kama jama kanka yanzu ma anan ɗakin zan koma yini”.         “Uhm saboda ka sake tabbatarma da duniya kai ɗan Sa ido ne kenan?. To aiko addu'ar tsole ido zan fara da tsiyaye ido, ba sai naga da idon da zakai sa ido ba”.        Cikin mamakin yanda suka saki jiki da juna a ƙanƙanin lokaci bayan tasan Smart da shegen ɗaukar kai wa mutane ta ce, “Wai dama kun san juna ne kafin jiya kenan ko me?”.       Dariya Usman yayi, yayinda Smart ke murmushi yana harararsa. Cikin marairaice murya ya ce, “Inafa ya sanni Baby luv. Jiya fa daya rabani da ke a ɗakin nan ya tafi dani can ya dinga isa ta da surutu kamar rediyo. Har sai da ya nema sakamin ciwon kai”.           “Kinga laifina ne Momyn AA. Ni ban iya kurumta ba, naga ana neman maidani kurman ƙarfi da yaji bayan ga ɗan ƙasata na gani. Ni mamaki ma nake yanda yake miki hira ke ko mu ya raina kenan dai yake mana shiru-shiru”.        Murmushi Lulu tai da kallon Smart ɗin, dan tasan zaman Usman a ɗakin nan da saka musu baki da take dauriya kawai yake yi. Ita bata taɓa ganin mutum mai kishin tsiya irinsa ba kodan bata rayu a Nigeria ɗin bane oho. Ilai kuwa kafin ta gama tunanin nata ya miƙe tare da jan hannun Usman ɗin ya na faɗin, “Muje tunda dai ka rantse sai ka rabamu sa'ido master”. Da ga haka yaja hannun Usman suka bar ɗakin.          Ajiyar zuciya Lulu ta sauke da maida kallonta kan AA bayan ficewarsu da ganin Hararar da Smart yay mata sanda yake ficewa. A dai-dai nan Ummita ta shigo ɗakin da sallama. Harara Lulu ta sakar mata cikin wasa da faɗin, “Sai yanzu ake ganinki? Ɗan naki ma yayi fushi ai shima”.      “Oh oh karki haɗamu faɗa Aunty, my sweetheart, I'm sorry sorry naga kana tare da Daddy ai yau ko shiyyasa ban zo ba” Ummita tai maganar tana ɗaukar AA da manna masa kiss a goshi. Har zuciyarta take jin ƙaunar yaron, dan ya shigar mata rai sosai. Murmushi Lulu keyi, sai kuma takai kwance da faɗin, “Su Ammah barci sukeyi ne?”.. “A'a suna hira abinsu tun ɗazun. Amma gasu can tare da su Daddyn AA yanzu suna magana. Ashe gobe idan ALLAH ya kaimu shagalin sunan Yarona zamu sha?”.       “Ku kuma ƴan son bidi'a dama haka kuke so ko?”    Dariya Ummita tayi ranta fes......✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣8️⃣ ___________________ *3 DAYS CLASS* Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rarar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rarar kudinne sakamakon rashin neman scholarship da bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka canza kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni Class ze fara ranar jumaa insha Allah WhatsApp group 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/E8Lzqogsm1nAFy1feTwbmA WhatsApp 08144147273 👉 Masu bukatar tafiya da kudinsu ba scholarship ba, Muna yin study & work ko working visa, a takaitaccen lokaci, working visa Qatar munayi a sati daya, Canada study & working visa a 4 to 5 months, Oman working visa a 7 days insha Allah, Maxico Tour visa 1 month _________________ .......Har dare Lulu bata sake saka Smart a idonta ba. Suna can sunyi busy shi da su Usman. Sai ma zuwa yamma ne da kewarta ya ishesa ya sa Usman yay masa kiranta a wayar Mamy duk da tsiyar da yeke masa bai kulashi ba. Gaisuwa kwai sukai a wayar ya tambayi AA tana amsa masa cikin basarwar nan tata. Gajeren Murmushi kawai yayi da jinjina jan aji da son tsare girma irin na Lulu. Ya jima baiga mace mai ɗankaren basar da abu ba irinta. Shi kaɗai yake iya gane wacece matar tasa, shiyyasa yake sarrafata a salon da takan zurma ta saki masa jiki batare da ita kanta tana sanin ta zurma ɗin ba. Dan ita Lulu zuma ce, idan kace ma zaka bita da wutar maimakon cin nasara kai wutar zata dawo ta baibaiye ne. Shiyyasa yake amsar zaƙin nata da harbin duka gaba ɗaya sannan ya bita da feshin furanni masu ƙamshi...         Lulu tayi mamakin ganin irin ƙwarya-ƙwaryar liyafar da aka shirya cikin ƙanƙanin lokaci nan. Ba ita ba hatta su Ammah sunyi mamakin hakan. Sai dai Ammah taji daɗi sosai. Har dare suna abu guda. Bayan sun nitsa ɗin domin su huta ɗin ma gajiya ta hanasu zama a gidan. Lokacin da ya shigo ɗakin musu sai da safe Lulu ma tayi barci saboda alluran da ake mata. Yaronsa kawai yay ma addu'oi da kiss, idon Ammah kuma ya katangesa ga zuwa inda Lulun take sai dai kallo da ga nesa.       Washe garin cikar sati guda da haihuwar AA suka wayi gari da shagalinsu da kuma isowar Ahmad da Coach, dan Smart yace idan zai iya ɓoyema kowa banda mutanen nan biyu. Yaro yasha addu'a a wajen Coach da Ahmad, Lulu da Smart kuma sun sha sheri wajen Ahmad dan sai da Lulu ta koma ɓoyewa idan taji maganarsa. Duk da bawani yawane da su ba abin dolene ya ƙayatar da mai kallo. Kamar yanda Smart ya faɗa an yankama AA ƙaton ragon turawa, a take kuma aka gashe shi gashi mai ƙyau da tsafta ya shiga jerin abinda za'aci a wajen shagalin. Duk da Lulu na dojewa haka dai dole ta shirya a cikin kayan da Mammy ta kawo mata sabuwar doguwar rigar shadda babba sosai da bazata takura mata ba saboda ciwonta. A kallo ɗaya mai kallo zai san shaddar taja kuɗi, maiƙon da take ma kawai da stones work da aka zuba mata na azaba abin ba'a magana. Bawai an ɗinka kayan bane dan wannan taron, kayan Mamy ne ta ɗinka abinta sai dai bata taɓa sakawa ba. Tunda wannan ta taso sai kawai ta ce Lulu tai amfani da su. Karo na farko Lulu tasa kayan da ba fitet ba a jikinta. Amma sai tai ƙyau sosai musamman da Ummita ta mata ɗauri mai ƙyau sosai, ƙanwar Usman da sai yau suka fara ganinta tai mata kwalliya tana dojewa ta na komai sai da akayi. AA ma an shiryashi cikin wasu tsadaddun kayan yara masu taushi da ƙayatarwa da Abbiensa ya siya masa. Angon jego ma yayi nasa ƙyawun cikin lallausan farin yadi da ya zauna masa ɗas ya fito a cikakken bahaushen sa ɗan Nigeria dan harda hula. Ita kanta Lulu a kallo ɗaya data masa ta sake tabbatar da jiya fa ba yau bace, ƴan maza sun gama cika mazaje sai dai fatan tsahon rai kawai da gamawa da iyaye lafiya. Yanda yake satar kallonta haka take satar kallonsa. Sai dai in sun kama juna ta hararesa ta basar. Yakanyi murmushi ya ɗauke kansa kawai. A haka dai aka fara ɗan taron da iyakar sune sai Dr Lameer da iyalinsa da ƙanwar Usman da boy friend ɗinta data gayyato. Sai abokan Usman biyu da suna ganin Smart suka shaida shi kasancewar su masoya ƙwallo, sun kuma bibiyi wasan link na ƙasar England. Ɗaya ma ɗan can ƙasar ɗinne. Lulu dai tayi mamakin a ina suka kwasosu? Da yanda suke girmama Smart ɗin da wani tattalinsa duk ya ɗaure kanta dan kowa dai yasan waye bature. Sai dai batace komai ba dai ta bar abinta a zuciya tana taɓe baki. Gaba ɗaya taron nasu dai basu fi su ashirin ba. An kuma yisa cike da birgewa da ƙayatarwa, gashi babu wata hayaniya sai ɗan cool music da aka saka na waƙoƙin masoya, duk da dai Ahmad ya saka waƙar data shiga har cikin jini da ɓargon Lulu da Smart ta hausa. Wato (Labarina baya zama nawa ta Salim Smart da KEWA ta Auta Waziri). Amma da farko basu saka ba saboda su Abbah. Sai da sukai addu'oi wa jariri da mai jego dama uban jego sannan. Can cikin lambun Abbah da Daddy da mahaifin Usman suka koma abinsu suka baje suna hirarsu ta dattijai da tarin abinci da aka shirya musu. Yayinda Ahmad da Usman da hali yazo ɗaya a rawar kai suka warware sautin sai dai bamai hayaniya ba. Ansha hotuna kala da iri, sai dai a duk sanda za'ai Smart na naniƙe da Lulu, idan da namiji za'ai tana gefensa ta inda babu kowa bai yarda wani ya raɓar masa mata ba. Tunma su Usman basu farga ba har suka fahimci mutumin nasu fa akwai kishi. Sai suka kama kansu suma yanda bazasu takaloshi ba. Ahmad ne dai kam ya addabesa tako ina da ina, sai dai tunda ya iso AA na hannunsa ya kasa bama kowa. Har cikin rai ƙaunar yaron yake ji tamkar shiya haifa. Yace dai surukinsa ne dan shi da Maryam ɗinsa zasu haifa masa mata. Anyi dariyar zancen nashi, yayin da Smart ya ce, “ALLAH ya shiryeka kai dai. Kadai fara tara ƴaƴa sai ka fara canjawa”.         “To dama ance maka ban canja bane. Kana ganin har na fara furfura zuwan My Son duniya kuma surukina.” cewar Ahmad yana hararar Smart. Murmushi kawai yay masa da girgiza kai. Taro kam Alhmdllh, sai dai Lulu ana kammala hotuna ta koma ciki wajen Ammah da Mamy da suka basu waje suma saboda yanayin jikinta. Shima dai AA ba'a saki jiki da shi a wajen ba saboda sanyi. Sun ɗan samu gift dai-dai misali, zuwa dare taro ya tashi kowa ya kama gabansa. Gajiya ɗan kai da kawon da suka sha a yinin jiya yasa su Smart wucewa da wuri domin kwanciya.       Washe gari suka tashi Lulu nata rakin ciwon kai. Sai da Ammah tai mata addu'oi a ruwa tasha aka kama mata kan sannan. Lokacin da su Smart suka iso ya lafa mata. Tana cikin rubutu a littafinta Smart ya shigo da sallama su Ahmad biye da shi. Sai da ta saka mayafi yace su shigo. Sun gaisa da tambayar juna gajiyar taro Ahmad ya ɗan tsatstsokaneta sannan suka fito suka barsu. Smart da tun shigowarsa hankalinsa ke akan book ɗin da takema rubutu sanda ya shigo ta ɓoye. Suna fita ya kai hannu bayanta zai ɗauki littafin tai saurin buge masa hannu tana ɓata fuska. Idanun nan nasa ya kafeta da su babu walwala sam tare da shi. Duk sai taji ta daburce saboda mugun kwarijin ya mata da cika waje. Shima babu wasa a tattare da shi murya a dake ya furta, “Kinada wani abun ɓoyewa ne da kike ganin saninsa a gareni illa ne?”.       Fuska ta tsuke cikin cuna baki batare data amsa masa ba. Shima sai ya sake dakewa da koma mata Smart ɗin nan mai ɗaukar kai da manna mata hauka sanda yana drivern ta. A kausashe ya furta, “In ma baki son na sani kin makaro. Domin ɗayan littafin ai yana gareni. Banyi niyyar karantawa bane kawai dan nafi son jin komai daga bakinki ba'a rubuce ba.” Da sauri ta ɗago tana kallonsa, ya ɗauke kansa gefe kamar bai ganta ba. Sai kawai taji hawaye sun cika mata ido. Cikin rawar murya ta ce, “Da gaske kakeyi?”.        “Na miki kama da ɗan wasan kwaikwayo ne da zan miki ƙarya?. Mawaddat ɓoye-ɓoyen nan bazai kaiki ko'ina ba face cigaba da dasa miki damuwar da zata iya maidaki ga abinda kika baro. Mi kike ɓoyewa? Miye baki son a sani? A zatona ko zaki iya cigaba da binnewa kowa abinda kike kallo a sirrinki ni zan kasance ba'a cikinsu ba saboda kasancewata mafi ƙololuwar SIRINKI a yanzu. Amma bazan cigaba da takura miki son sani ba ki cigaba da riƙon abunki in dai nine bazan sake tambayarki ba”. Ya ƙare maganar kamar cikin ƴar fusata zai juya yabar ɗakin. Hannunsa ta riƙo da sauri, hakanne ya sashi tsayawa cak sai dai bai juyo ba, ya dai lumshe idanunsa da suka kaɗa sukai jajur. Itama batare data tashi ba cikin shashshekar kukan da ke sukar masa zuciya a hankali ta furta, “Aliyu ban san miyasa kake son ji ba? Babu wani abin sha'awa ko birgewa a son jin abinda ya shuɗe da ga tarihin rayuwata. Babu wani abin alfahari ko ƙayatarwa face baƙin ciki da takaici a cikin jiyana. Taya zan faɗa maka na taɓa kashe mutum da hannayen nan nawa ne?, kuma wlhy ban taɓa jin nadamar aikatawar ba har yau har gobe da ma ƙarshen numfashi na. Aliyu ban san taya kake son na faɗa maka na rasa Nanny na data raineni tamkar uwa ba a dalilin kisan da nayi ba, ta amshi laifin daba nata ba, ta rasa ranta a dalili na, Aliyu alhakinta bazai barni na rayu cikin salama ba...” ta sake sakin kuka mai tsuma zuciya.        Sosai shima yake haɗiyar zuciya, maƙogwaronsa sai faman kai kawo yake a cikin wuyansa. Idanun maza sun masifar kaɗawa. Da ƙyar ya iya controlling temper ɗinsa tare da firzar da numfashi mai nauyi ya juyo a hankali gareta. Har lokacin hannunta a cikin nasa ya zauna a kusa da ita. Jikinsa ya jawota ya rungume, hakan sai ya bata damar sake sakin kuka tana ƙanƙamesa kamar mai gudun a rabasu. Bai hanata ba, sai tambaya da ya jeho mata kai tsaye. “Taya akai kika aikata kisan kai? Dan nasan kinada dalili mai ƙarfi Mawaddat, bakiyi kalar masu aikata irin wannan laifin bisa son zuciya ba. Please faɗamin miya faru a shekarun baya a tsakaninki da Nanny ɗinki?”.          Cikin haɗiyar zuciya da shashshekar kuka ta furta, “Johanna itace Nanny na dana buɗa ido na gani a tare da ni tamkar uwa mahaifiya. Duk da dai kafin a kaini gareta na ɗan rayu a Nigeria hannun mahaifina da matarsa, sai dai babu abinda zan iya tunawa a wannan rayuwar saboda ƙarancin shekaru na. Nanny na da nake kira da Mah-mah Ta raineni ne tamkar zinariya, tana bani dukkan gata da uwa ke bama ƴaƴa duk da kasancewarta kafira. Bata taɓa cewa nabi addininta ba balle akai gata tilasta ni. Duk da na kasance mai tsiwa da rashin ji komai nai a gareta abin farin ciki ne, sai taga zan kauce da yawa ne take saurin gyara min duk da bata kasance muslma ba. Daddy na yawan zuwa gareni, dan haka nake ɗauka shi da ita duk iyayena ne, sai da na fara ɗan wayo na fara damuwa akan ƙin kwana da Daddyna keyi a gidanmu idan yazo Germany, ya yarda ya yini da ni a gida koma ya ɗaukeni mu fita yawo amma dare nayi zai wuce masaukinsa. Nakan masa ƙorafin hakan amma sai yay murmushi kawai. Itama idan na tambayeta miyasa Daddyna baya kwana tare da mu kamar sauran abokaina da iyayensu takance min aiki ne ke hanashi hakan.........✍️ NEXT PAGE PLEASE 🚴🚴🚴🚴 _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣9️⃣ ........Ban fara shan jinin jikina ba sai dana ga wani yana yawan zuwa wajen Mah-mah. Atake naji na tsanesa, ko yazo gidan bana kulashi duk iya maganar da zai min, ko abu ya kawo min bana amsa. Idan kuma ya ba Mah-mah ta bani indai nasan shine ya kawo bana ci. Yana shiga damuwa da yanda nake masan har ya kasa daurewa ya sanar da Daddy. A wani zuwa da Daddy yay ne yake sanar min ai Felix yaronsa ne na amana, duk wani kai-kawo akan business ɗinsa na Germany shine ke masa. Yana zuwa wajen Mah-mah Kuma saboda harkar business ɗinne, dan itama akwai abinda take riƙe masa. Wannan zance na Daddy ya sani ɗan sakin jikina da shi, a dalilin haka na gane ashe basu da wata alaƙa da Mah-mah ɗina, A duk sanda yazo suna tattauna harkar business ɗin ne kam da gaske. Hakan sai ya sani sake sakin jiki da shi har ina kiransa Uncle, yakan ɗauke ni randa ba makaranta ya fita dani yawo yayo min shopping kamar hauka. A wani zuwa da Uncle You yayi ne yaga wannan al'amari, cikin tashin hankali naji yanama Daddy faɗan mizai sa ya bar Felix ya shiga jikina har irin hakan a matsayinsa na namiji da Business ne kawai ya haɗa su, miyasa ma ya nuna masa wannan gidan. Shi ya yarda da Mah-mah na shiyyasa damuwarsa a kasancewarta mai kula dani ilimin addini da ake neman tauyeni ne kawai. Amma sam baiji ya yarda da Felix ba sam. Naji haushin Uncle You a lokacin, dan akwai shaƙuwa tsakanina da Felix, Kun san yaro dai. Har Uncle You ya gama min hutu a wannan karon ban saki jiki da shi ba, bai damuba bai kuma daina kulani ba. Tun daga wannan lokacin naga Felix ya daina zuwa gidan. Ba irin tambayar da bamma Mah-mah ba sai tace min yayi tafiya ne mai nisa. Akwana a tashi na fara mantawa da Felix a zuciyata, sai wataran katsam gashi, a lokacin inada shekaru goma sha kusan uku, dan kaɗanne ya rage na ƙarasa tunda har secondary na shiga, duk da dai su kasan karatun nasu bawai kamar namu ne na Nigeria ba, shiyyasa ma na kammala karatuna da wuri gaba ɗaya a ƙarancin shekaru. Zuwa lokacin na manta da shi, shiyyasa ban wani sake masa ba, ga shi kuma na fara hankali. Yaso jana jikinsa amma sam naƙi sake masa, idan ma yazo gidan ko fitowa falo bana yi sam. Ni ban san ashe wannan abun naci masa rai ba har yanama Mah-mah korafi, takanyi dariya tace masa na girma ne yanzu na zama ƴammata na fara kuma mantawa da shi.. A wata ranar asabar Mah-mah ta wuce wajen ibadarsu sai ni kawai a gida da mai aikinmu. Ina ɗakina na baza books na makaranta ina dubawa, jikina daga ni sai ɗan bomshot da best, kaina ko ɗan kwali babu sai jin mutum nai kawai ya faɗo min. Raina ya ɓaci ganin Felix. Dan ko sanda inada ƙuruciya baya shigamin ɗaki ai, balle yanzu da a iyayin tashi cikin jar fata yake sakani jin na zama ƴammata ni da ƙawayena. Cikin masifa nace mizaisa ya shigo min ɗaki, ya fita bana son shirme. Maimakon ya fitan sai ya tsaya kawai yana kallona, dan gaskiya inada tsiwa sosai tun da ƙarancin shekaru na. Dariya ya shigayi irin ta shaƙiyanci, batare da ya damu da masifar da nake masan ba ya murzama ƙofa key ya nufoni. Da farko na ɗauki al'amarin nasa wasa, sai da naga yana yunƙurin rungumoni jikinsa ne raina ya ɓaci, duka na shiga kai masa ina janye jikina, ganin bazan bashi haɗin kai a yanda yake so ba ya kamani ya ɗaure, hankalina ya tabbatar min da yana son wulaƙantamin rayuwa ne. Ina kuka da roƙonsa da magiya amma bai sauraren ba ya ciremin kaya kaf shima ya cire nashi. Aliyu wlhy ban taɓa sanin minene tashin hankali ba sai a wannan ranar, tsabar tsoratar da nai da ganinsa babu sutura ban san na suma ba, sai da ya ɗiba ruwan sanyi a Despenser ɗin ɗakina ya sheƙamin na farfaɗo. Zaginsa na shigayi cikin matsanancin tashin hankali bayan dawowa a hayyacina ina tofa masa yawu a fuska, shiko ya shiga marina yana dariya, da yaga na ƙi daina zagin nasa marin ma bazai masa ba ya cire belt dinsa ya dinga dukana da ita, tamkar ya samu wata babbar mace yay min duka na hauka, har yanzu da sauran tabbunan dukan a jikina wasu basu ƙarasa ɓacewa ba. Ga jini a sayin inda ya bugeni, ga kumburin fuska data sha mari da fashewar baki, ga haɓo da dukan da yay min a gefen ido duk bai duba wannan ba ya nema haike min. Na riga na suma saboda firgita dan ya na gab da cimma burinsa na suman, shiyyasa ban san yanda akai Mah-mah ta samu nasarar shigowa ɗakin ba, ita ce ta kuɓutar dani batare da ya samu nasara a kaina ba. Kiciniyar kwanceni da dukan da yake mata ya sani farfaɗowa, sai dai kafin ta ƙarasa kwanceni ya kaita ƙasa da duka itama. Ina kuka da zaginsa a saman lips dan ko magana bana iyayi dan wahala ya kekketa mata suturar jikinta ya ɗaureta kamar yanda ya mun, a gaban idona ya keta mata mutuncinta ta hanyar mummunan fyaɗe, ya kuma juyata ta baya nan ma ya wulaƙantata. Suma ta biyu ko a lokacin dan tashin hankali. Ban taɓa sanin ana suma a dawo a suma a dawo ba sai a wannan ranar. Kaina ya dawo yana wata ƴar iskar dariya da tabbatar min sai ya wulaƙanta min rayuwa fiye da yanda yay ma Mah-mah dake kwance cikin jini face-face bata ko numfashi sosai. Ban san yanda akai wani irin ƙarfi yazo min ba na halbesa da ƙafata a gabansa, azaba ta sakashi duƙewa, pen ɗina da nake aiki da shi kafin shigowarsa na ɗauka na buga masa a wuya, banyi tunanin zai iya mutuwa ba, a haukana hakan da zan masa ai zai tashi idan aka kaisa asibiti kamar yanda naga a film yana faruwa. A take ya saki razananniyar ƙara da zubewa a ƙasa hannunsa ɗaya riƙe da gabansa ɗaya ya riƙe wuyansa. Dai-dai nan mai aikinmu ta shigo, ashe matsiyacin aikenta yay kasuwa dan ya samu damar min illa ALLAH ya kawo Mah-mah ta dawo gidan. Ihunsa ya sata shigowa, koda ta shigo taga a yanda muke mu duka ukun sai itama ta fasa ihu da komawa da gudu, itace tai kiran ƴan sanda, abinka da inda akasan kimar ɗan adam, cikin ƙanƙanin lokaci sai gasu sun iso, a gaggauce aka tattaramu duka zuwa asibiti muduka ukun. Ban dawo a yahhacina ba sai bayan kwana biyu, a hakan ma ko yaya namiji yazo kusa dani na dinga firgita kenan harda ihu ina roƙon karya cutar dani, duk wanda ya ganni sai ya tausaya min sosai. Ashe nawa wasane, dan Mah-mah ita gaba ɗaya ma brain ɗinta ta birkice, ga wata irin jijjiga da jikinta keyi, a taƙaice dai kamar ta haukace ma kawai..... Felix Kuwa ashe abinda nai masa ya mutu. Ƴan uwansa sunce bazasu yarda ba tunda kashesa akayi, wannan dalilin ne ya saka aka maida hankali akan bama Mah-mah kulawa harta ɗan dawo hayyacinta, an tattara case zuwa kotu. Daddy bai zo ba, Uncle Yousuf bai zo ba har sai da muka samu kusan sati uku a asibitin, zuwa lokacin an miƙa case kotu har an ajiye ranar zaman shari'a. Ana gobe fara shari'ar Daddy ya iso Germany, ya shiga matsanancin tashin hankali da ɓacin rai akan abinda Felix ya aikata, a ranar bai zauna ba sai da ya samo ƙwararren lawyer, washe gari aka shiga kotu. Mah-mah, bata wani bari shari'ar ta ɗauki lokaci ba ta ce itace ta kashe Felix saboda yayi mata fyaɗe ta ƙarfi. Duk yanda naso faɗar gaskiyar abinda ya faru bani da dama saboda tun a daren jiya ta roƙeni akan kar nace komai, na rufa mata asiri kar Daddy yasan ni Felix ya fara hara, dan hakan zaisa ya kalli rainon da tai min a matsayin sakaci, koma ya ɗauka dama a haka take sakaci da al'amarina tun can baya. Kawai idan anje kotu zatace a wajen cetonta ne Felix yay min wanna dukan. Yanda ta tsara ɗin haka ta faɗa a kotu, bayan gama saurarenta da lawyer da dangin Felix suka kawo alƙali ya yanke hukunci, wannan yanke hukunci ne ya sake birkita ƙwaƙwalwar Mah-mah take a wajen ta shiga wani yanayi irin na masu taɓin hankali sosai, a gaggauce aka maida ta asibiti kamar yanda alƙali ya bada umarni, hakan bai wa dangin Felix daɗi ba, dan ba haka suka so ba, sai dai babu yanda zasuyi. Sashin masu taɓin ƙwaƙwalwa aka kaita, ana kula da ita yanda ya kamata bisa tsayawar Daddy. Hankalin Daddy ya tashi matuƙa game da halin da ya ga Mah-mah ta shiga ciki, sai dai rashin sanin yanda abin ya faru yasa shi bai yi tunanin da yanzu fa akaina abin zai faru ba, tunda Felix ni yaso ketama mutunci ba, ya ɗauka kawai wajen son ceton Mah-mah ɗin nawa ne kamar yanda ta faɗa na samu wannan mahaukacin dukan, wai dan ma na samu sauƙi sosai a lokacin. Kwanan Daddy uku da zuwa Germany Mah-mah ɗina ta mutu, ta bar duniya tana kuka da sunana bakinta....” Kuka ne yaci ƙarfin Lulu, ta sake ƙanƙame Smart da tun ɗazun idanunsa sun kaɗa sunyi jazur alamar yana kukan zuci ne. Sake ƙanƙameta yay shima jikinsa na wata irin tsuma, ji yake kamar zuciyarsa zata fashe, kukanta na sukar masa zuciya da ruhi. Tayi kuka sosai kafin ta cigaba da faɗin, “Wannan al'amari shine sanadin barowata Germany, na fahimci Daddy kamar yana tsoron maidani Nigeria ne a wannan halin saboda su Uncle You, ya maidani U.S, in da aka sake sama min sabuwar Nanny sai dai baƙar fata ce, asibiti aka sake kwantar da ni a can farko dan nima dai ina abu tamkar brain ɗin nawa ya taɓu. Na samu tsahon lokaci ina ganin likita kafin na ɗan rage firgita har Daddy ya saka ni a makaranta. Wannan shine ƙalubale na biyu, sannan sanadin abubuwa da yawa na rayuwata. Na ƙudiri niyyar yin karatu tuƙuru na zama lawyer domin kai ƙarshen irin masu halayyar Felix. Sannan kuma na kasa sakin jiki da kowa a yanzu ciki harda sabuwar Nanny ta. Banda aiki sai kuka, zaman ɗaki, a class bana shiga sabgar kowa. In har babu malami ma ina daga can gefe a takure. Duk yanda Daddy daya kasa tafiya ya barni ke lallaɓani da jana a jiki na kasa sakewa, depression yay min tasiri matuƙa. Wannan yanayin nawa ne ya jawo hankalin Alice da Luna gareni, tun bana kulasu har na ɗan fara amsa musu magana, ba komai ya jawo hakan ba sai ganin suna maida hankali a karatunsu, sannan suna nuna min suma suna cikin damuwa amma suna magance damuwarsu da wasu abubuwa shiyyasa ba'a ganewa........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣0️⃣ ........A hankali suka cigaba da shiga jikina da nuna kulawa har takai na amshi maganin da suke yawan kwaɗaitamun na sha wai zai min maganin damuwata, wannan shine sanadin komai, domin kuwa a randa na sha na farkon sai na fahimci na samu sassaucin damuwata, har takai bana iya tuna komai na wani ɗan lokaci, da ga haka aka fara, a hankali, a hankali al'amarin ya fara tasiri har aka farga damu. Malamai sun tsawata mana, saboda shekarunmu sunyi ƙaranci da shaye-shaye, sai dai babu alamar zamujisu, daga ƙarshe suka nema iyayenmu. Nanny na ce taje, amma koda muka dawo gida na tabbatar mata idan ta bari Daddy na ko Uncle You suka sani a bakin aikinta. Tasan zan iya, kuma Daddy na jin maganata, ga shi kuma ina nuna bana sonta dama. Dan haka taja bakinta tai shiru. Ni kuma sai na ɗauki matakin daina shan komai sai da dare, kafin safiya ya sakeni. Sai a week end ne nake sha da rana, wataran a gidan su Luna wataran gidan su Alice anan gidan dai bana taɓa yarda suzo ma balle musha wani ya gane, sai takai har week end ina zuwa gidajen su Alice da Luna. Sai da Daddy ya farga ne hankalinsa ya tashi, yayma Nanny na tas da tabbatar mata in fa har bata kula da aikinta ba zai sallameta. Ni kuma ya rufe ido yamun tas da faɗa dan ya fahimci na fara wasa da karatu, ya kuma haɗani da Uncle You shima yay nashi. Har lokacin babu ruwana da ko mazan ajinmu, ƙawayena biyun nan dai sune Luna da Alice. Faɗan da su Daddy sukai min ne ya dawo dani hankalina akan karatu sosai, sai kuma burin dake raina shima na ƙaramin himmar hakan matuƙa har muka kammala karatun. Mun samu damar shiga jami'a ni su Alice kamar yanda muka tsara, hakan ya sake bamu lasisin cigaba da shaye-shayen mu da yawon clubs. Sai dai inata taka tsantsan ta yanda babu wanda ke fahimtata har lokacin. Kula maza da su Luna suka fara ne ya fara sakamu fara samun matsala, sunyi-sunyi suja ra'ayina akan hakan amma ya gagara, sai ma saɓani da muka fara samu da su. Akwai wani yaro a depertment namu da ya takura min, duk da bashi kaɗai bane sauran dana karta musu rashin mutunci sukan kama kansu. Shiko naci yaƙi ya barni na samu sakat, har takai ya fara shiga jikin su Luna domin su shawo masa kaina. Amma hakan ya gagara. Ganin bazai samu nasara ba suka haɗa baki da shi aka bugar da ni, matsalar da aka samu ni ba komai ke sani buguwa irin ta galabaita ba, mukan sha abu tare da su su fita a hayyacinsu sosai amma ni ina normal sai dai ɗan yanayi, wannan yasa na fahimci manufarsu a kaina. Wannan shine sanadin daya sa na karta musu rashin mutunci irin wanda basu san zan iya ba, na kuma rabu da su dan su basu san nai mugun tsanar maza irin haka ba. Bayan rabuwa da su nasa Daddy ya canja min makaranta, naso barin shaye-shaye a lokacin sai dai hakan ya gagara dan ya shiga jikina matuƙa, sai dai ina kiyaye duk wani yanayin da wani zai iya fahimtar halin da nake a ciki, zuwa lokacin bani da Nanny, sai masu aiki, sai kuma wata yarinya da aka kawo da ga Ghana wai ɗiyar abokin Daddy ce tazo karatu. Babu ruwana da ita dan ko harakar ta bana shiga, sai mu kwashe sati biyu ban mata magana ba, koda tamun ma sai ma gadama nake amsawa. Duk ina mata wannan abunne saboda tsanar ƙawaye da nayi, bama na son ta shiga jikina da har zamuyi shaƙuwar da zata kaimu ga wani matakin kuma, sannan bana son ta san ina shaye-shaye. A haka na gama karatu da ƙyar, dan a wasu lokutan sai nayi kamar zan ɓaras saboda yanayin da nake ciki sai kuma dai na dawo hankalina da ƙyar na maida hankali. Alhamdullah na samu result mai ƙyau saboda inada kaifin basira, kuma na saka zuciyata ga abin. Na yi wasu courses da ban da ban da suka shafi karatuna har na tsawon shekara ɗaya da wasu watanni, da kaina na ce zan dawo Nigeria nayi service, dan haka kawai nake jin kewar asalina, na dawo Nigeria a tsagerata, dan bana iya ragama kowa sai Daddy Uncle Yousuf, Mommy ma rashin ɗaukar halina yasa nake shakkarta, Aunty Saliha da Aunty Naja'atu kuwa soyayyar da suka nuna min da kulawa tasani jin ƙaunarsu a lokaci guda. Dan naje Abuja ne gidan Uncle Khamil nai hidimar ƙasa ta, sai kakata Dada dake nuna min soyayya irin ta uwa, tana mun gata sosai da yimin duk abinda nake so. Case ɗin wata yarinya akan fyaɗe ne ya zama sanadin fara aikinna a Nigeria, raina ya ɓaci da abinda ya faru, har takai Aunty Naja'atu na sanar min ai wannan ba komai bane da ga cikin tarin cases na fyaɗe a Nigeria. Musamman ma a yankinmu dan gwara nan Abuja akwai wayewar kan da iyaye basa bari. Amma tacan wajen gida akan rufe zancen wai dan kada yarinya ta rasa miji ko ahalinta su tozarta sai dai iyayen baƙin ciki ya kashesu, itako ta ƙare rayuwarta a cikin ƙunci da baƙin ciki. Wannan al'amari ya tayar min da hankali sosai, sai ko na ɗauki ɗammarar zama kan ƙafafuna domin hana samuwar irin waɗan nan mata tasiri, da kuma kai duk wani shegen daya ce shi mace ce abar wulaƙantawarsa ta hanyar fyaɗe prison ya ƙare rayuwarsa acan ko ƙuruciyarsa.. Wannan shine jiyan na Aliyu. Banda baƙin ciki da takaici mi kaji a cikinsa? Babu wani abun birgewa ko ƙayatarwa”         Smart ya kasa magana, sai kukan zuci kawai, a ransa yana auna tsakanin Lulu da mahaifinta waye yafi wani zama a ƙalubale?. Sai dai duk da haka tabbas Daddy yayi sakaci da al'amarin ta, dolene a faɗi hakan, amma tunda har ya amsa laifinsa da tabbatar da kuskurensa shikenan. Lallai a yau ya koya darasin rayuwa a labarin Daddy da Mawaddat, bai taɓa tunanin ko hasashen za'a iya samun wanɗan nan al'amuran ba masu gogayya da juna. Sai dai shi fa har yanzu zuciyarsa na bashi dole akwai hannun Sulaiman akan al'amarin Lulu. Daddy bai farga bane a wannan gaɓar saboda yarda da kansa da yayi na ganin tako ina, ta kowanne motsi yana dabaibaye da al'amarin Sulaiman ɗin, ko kuma dama ya riga ya gama shirya hakan kafin shi Daddyn ya fara nashi shirin. Ya kuma haɗa da wannan itace ƙaddararta babu wata dabara ko tsaro da zai hana hakan. Duk da kuɓutar da itan da Daddy yayi hakan bai hanata fuskantar ƙaddararta da yake gudan mata a inda aka haife ta ba. UBANGIJI kenan, gagara misalin masu misali. Shi kaɗaine masanin gaibu a zahiri da baɗinin rayuwa.... Sai da ya firzar da nannauyar iskar bakinsa a kusan karo uku sannan ya ɗago Lulu da ke hawaye har yanzu a jikinsa a hankali. Sosai idanunta sun kumbura abin tausayi. Nasa juyayyun idanun ya zuba mata, tare da riƙe fuskarta a cikin tafukan hannunsa duk ya fara goge mata hawayenta da babban yatsun sa da faɗin, “Kalleni” cikin sarƙewar muryarsa da ke nuna tsantsar ɓacin rai da baƙin ciki.         A hankali ta ɗago nata Lulu idanun ta saka cikin nashi, a take gabanta yay wata irin masifar faɗuwa. Kanta ya sara. Yanayin da take jin kanta da jikinta tun a jiya ya shiga sake zafafa gudanar jinin jikinta da motsin numfashinta. Shi kam Murmushi mai sanyi ya sakar mata batare da ya fahimci halin da take ciki ba. Cikin ƙanƙanin lokaci kamaninsa suka juye mata zuwa wani abu daban kamar a mafarki. Baya taja jikinta daya fara ƴar rawa-rawa da sauri. Cikin mamaki Smart ke kallonta, kafin ya iya cewa wani abu a bazata kawai ta fasa wata iriyar gigitacciyar ƙara da ta saka su Daddy dake ƙofa na saurarensu shi da Uncle Yousuf shigowa a firgice. Hatta Abbah da Ammah da Mamy ma a ruɗe suka iso ɗakin. Riƙetan da Smart yayi sai take neman sume masa ma. Al'amarin ya bama kowa mamaki, Ummita na kuka tai kiran Usman, ya ce mata gasu nan shi da Dr Lameer ma a kusa. Ammah ce hankalinta ya kai da yanda numfashin Lulu keyi da yanda take son raba jikinta da na Smart ɗin. Da sauri ta ƙaraso garesu, hakan yasa Smart sakarma Ammah ita dan a rikice yake shima. A kuma dai-dai nan su Usman ke shigowa ɗakin. Zabura Lulu ta shiga yi a jikin Ammah da nuna Smart tana faɗin ya fita, bata son ganinsa ya fita. Yanda ta fita a hayyacinta cikin ƙanƙanin lokaci ga ciwo a jikinta yasa Abba jan hannun Smart ɗin suka fita, abin mamaki da al'ajab kamar ƙyaftawar ido sai ta koma laƙwas tana sauke numfashi. Cirko-cirko kowa yayi da mamaki, Dr Lameer ne yasa a maidata saman gado, yay ƴan dube-dubensa ya ce musu lafiya ƙalau take, dan jikinta ma Alhamdullah kaɗan ya rage. Wannan al'amari ya saka kowa mamaki, sai kallon Lulu dake sauke ajiyar zuciya sukeyi. Ganin an samu komai ya daidaita Abba da Smart suka sake shigowa. Zabura ɗaya Lulu tayi ta dire ƙasa tana neman kwasa a guje da ihun “Aliyu ka fita! Ka fita bana son ganinka, na tsaneka ka fita!”. Nanma sai da aka rirriƙeta, yayinda Smart yama kasa koda motsi. Ganin zata jima kanta ciwo akace Smart ya fitan. Yana fita abin mamaki sai ta sake komawa laƙwas. Ran Daddy ne ya ɓaci dan shi zuciyarsa bata kawo masa komai ba sai ganin da gangan Lulu keyi. Sai dai Abba ya riko hannunsa yana girgiza masa kai da faɗin, “A'a Alhaji Isma'il wannan ba abin faɗa bane abin dubawa ne. Sai dai idan shine yay mata wani abun tunda tun ɗazun suna tare a cikin ɗakin ko”.       Da sauri Daddy yace, “Babu abinda yay mata, dan duk abinda suke tattaunawa muna jiyosu ni da Yousuf. Baka san halin Mawaddat bane ba Malam Mika'il”.    Cikin damuwa Mamy ta ce, “Mawaddat wani abu yay miki ne?”. Kai Lulu da hawaye ke silalomawa ta shiga girgizawa a hankali. Sai kuma a hankali tace, “Mamy yana koma min wani irin siffa ne mara ƙyan gani daban tsoro. Dan ALLAH kuce kada ya sake shigowa bana son ganinsa”.          Babu wanda hankalinsa bai tashi ba da wannan furuci na Lulu. Ga kuka da AA kayi duk ya sake gigitasu. Dama kuma tun jiya da dare yake kukan sai da Ammah ta dinga masa addu'oi sannan suka samu yay barci gabannin asuba. Shiyyasa ma yake ta ramuwar barcin da safen nan ko wanka ana masa yana barci. Uncle Yousuf da gaba ɗaya ya gama ruɗewa ya ce, “Ko aljanune, dan gurin nan da suke ai baya rasa aljanu ba”.        Ammah da tun ɗazun tai shiru tana nazari ta ce, “Dama Mawaddat nada aljanu ne?”.........✍️ *_Lulu da Smart dole a kiraku da FURAR DANƘO kam....🥲 Sai dai in sha ALLAH maƙiya SU SHEKARA SUNA DAMU BAKU ZAME MUSU FARAU-FARAU 🤦😏🚶._*      _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣1️⃣ .......“A'a gaskiya, sai dai idan yanzu ta samesu”. Uncle Yousuf ya bata amsa. Iska Ammah ta ɗan furzar a hankali da cije lips sai dai ta kasa cewa komai. Duk yanda sukaso hasaso komai sun kasa, ga Smart yay masifar ɗaga hankalinsa da ƙyar su Abba suka baibayesa suna masa nasiha. Saurarensu kawai yake yi amma al'amarin na bashi matuƙar mamaki da tsoro. Wace irin masifa ce wannan suna ganin sun tsallake wancan siraɗin da ƙyar ace kuma ga wani abun daban dama yafi na baya muni. A wannan yini dai duk yanda akaso yin ɗan sauran shagalin da ya rage bai yiwu ba. Sai Daddy ne daya fita dan Ammah ta bada shawarar su wuce da Lulu Nigeria kawai. Sannan suka yanke shawarar a faɗama Baba Garko anga Lulu ɗin kamar yanda Smart ya bada shawara tun farko. Domin shi yana ganin Alh. Sulaiman ne yayo musu wani ƙullin kawai. Daddy da Uncle Yousuf da Abba ma tunaninsu kenan. Ammah ce dai keta wasi-wasi da tunani kala-kala sai dai batace wa kowa komai ba a zahiri. Ana tsaka da wannan cakwakiya kira ya samu Smart da Uncle Yousuf na gaggawa zuwa England akan harkar ƙwallonsa. Dole badan yaso ba suka wuce amma daka ganshi kasan hankalin ƴan mazan a tashe yake. Dan ma su Ammahn sun taru sun masa nasiha mai ratsa jiki da tabbatar masa matarsa na tare da shi in sha ALLAH. Nan da ƙanƙanin lokaci kuma zatazo ta samesa a inda yake. Hakan ya ɗan ƙarfafa masa gwiwa suka wuce....              Sanarma Baba Garko anga Lulu ya taimaka matuƙa. Dan cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙarasa abinda Daddy ya fara a washe gari da daddare suka wuce Nigeria a private jet. Suma su Mommy an sanar musu, da su Aunty Bilkisu. dan haka ahalin uku suka shirya babbar tawagar tarba. An yanke shawarar wucewa da Lulu gidan Abba zata zauna a wajen Ammah. Dan haka aka rankaya can kowa bakinsa yaƙi rufuwa da farin cikin ganin Lulu da jaririn da basu san da cikinsa na sai haihuwarsa. Dan farin cikin wannan Surprise Baba Garko ranar har ƙyaututtuka yayi na musamman. Abin tashin hankali na biyu tunda aka shiga da Lulu gidan su Smart ta juyo da gudu baya sai da aka rirriƙeta. Wannan al'amari ya sake hargitsa su Daddy yayinda sauran da basu san mike faruwa ba hankalinsu ya tashi. Umma da ke a birkice tunda labarin ganin Lulu yazo musu a kunne faruwar wannan abun ya sakata faɗawa dakinta tana dariya dan daɗi ji take kamar ta ciza uwauwanta. Ana can ana haya-haya na al'amarin tana nan tana kiran Hajiya Naqiba suna kwasar dariya. Sai dai fa batun haihuwar Lulu da sai a yanzu suka sani ya taƙaita musu farin cikin nasu...       Dole aka koma da Lulu gidan Daddy ita da Babynta hankalin kowa a tashe musamman Ammah da Daddy da Abbah. Dan sun sake tabbatar da lallai akwai matsala. Aunty Bilkisu da aunty Amarya da abu yayma tsaye a rai basuyi ƙasa a gwiwa ba suka ja Ammah gefe game da zargin su akan Umma da abinda ya faru bayan tafiyarsu. Mamakin wannan al'amari ya kashe Ammah tama kasa cewa komai sai kallon su Aunty Bilkisu takeyi. Itako mitaima Umma da zafi haka a gidan nan take mata irin wannan ƙiyayyar, duk da basu tabbatar ita bace dole ko suna so ko basa so tana cikin zarginsu tunda tayi abubuwan zargin ciki harda wanda aka gani da ido. Gwaggo Sa'adah da ranta ya ɓaci ce tace zatayi magana ita kam sai dai ayi duk wacce za'ayi. Da sauri Ammah sarkin dattako ta dakatar da ita da faɗin, “A'a Sa'adah ai magana ba tamu bace yanzun. Domin yinta kamar mun fargar da itane ta sake shiri tunda zuciyarta ta riga ta mutu. Fara magance matsalar ya kamata muyi kafin mu ɗauki mataki. Yaran nan na bani tausayi matuƙa, auren kusan shekara ɗaya amma basu taɓa zaman cikakken wata ba a ƙarƙashin inuwa ɗaya gashi harda rabon haihuwa. Muyi ƙoƙarin ganin al'amarin su ya dai-daita sannan muje mataki na gaba dan ita ba komai bace face baiwa ta ALLAH shine zai mana maganinta ta inda batai zato ba.”       Badan Gwaggo Sa'adah ta so ba ta haƙura. Amma ta ɗauki alƙawarin sai ta wajiga rayuwar Ummah itama....       A wannan yanayin akai taron suna mai ƙayatarwa, dan a zahiri Lulu normal take tsakaninta da Smart da duk abinda ya shafesa ne aka nisanta su, hatta da ƴan uwansa komai normal. Dan yanda ta dinga haba-haba da su aunty Bilkisu da ma duk wanda ya ɗan uwa na Smart abin zai baka mamaki da birgeka. Bama ita ba, hatta ƴan uwanta babu wanda ya wulaƙanta mata dangin miji. Umma ce ma taso kawo gutsiri-tsoma a wajen da ƴaƴanta akan abinda bai ko taka kara ya karya ba. A take Adda Mairo ta taka mata birki da faɗin, “Sufa basa son fitina da ƙananun magana. Alkairi da farin cikine ya kawosu akan gudan jininsu. Dan haka ta kama kanta gaskiya, tunda iya ƙoƙari mutanen nan sunyi da su a wajen taron nan”. Wannan abu ya ƙonama Umma zuciya dan ba haka taso ba. Bata bari sun taho tare ba tayo gaba, babu wanda yabi takanta sai ƴaƴanta. Dan ko Mama cewa tai wlhy bazatama kanta mugunta ba sai anci komai da ita, duk da acan gida ma da suka baro wani taron za'ai.        Bayan an gama taron suna da ya girgiza sukatan su Umma da har ta fara tunanin abinda tai ɗin kamar yama warwarene ganin ɓarin kuɗin da Smart yayi, dan hatta anan gidan suma Ammah tayi taron suna sai ma kace anan maijego take, yanda aka yanka rago da sa acan gidan su Lulu anan ma ƙaton sa da ragon aka yanka, a cewar Smart basai sun damu dana can gidan su Lulu ba balle a samu masu ƙananun magana duk da yasan su Lulun bazasu ƙi kawowa ba. Alhmdllh mutanen arziƙi sun taru tako ina fiye da zato da tsammani. Yayinda komai ya tafi cikin farin ciki da bajinta dai-dai misalin da baza'a taɓa kallonsa a almabazaracci ba ko nuna fariyya....         ________★   A washe garin gama taron suna Alh. Sulaiman ya iso Nigeria a hargitse. Dan a daren jiya labarin tabbatar da Lulu ta dawo Nigeria ya isa garesa. Kamar yanda mahaifinsa ya saka kuwa hakance ta faru, dan tun a filin jirgi jami'an tsaro sukai ram da shi. Wannan lamari ya girgiza zukatan Garko family sosai dama mutane da yawa da ke da alaƙa da uban da ɗan. Dan basu ɗauka Baba Garko bai haƙura ba tunda an samu Lulu. An saki Tajuddeen da ya share wata biyu a hannun jami'an tsaro yau, Baba Garko kuma yabar ƙasar sabgogin gabansa tamkar ba'ai komai ba. Ƴan ƙananun magana sun fara tashi kaɗan-kaɗan a tsakanin al'umma game da wannan cakwakiya tsakanin ɗa da ubansa. Kowa na faɗin albarkacin bakinsa, tun ƴan jarida nayi a ƙumshe har dai zancen ya fara fita a bayyane. Sai dai kowa da abinda yake faɗa akan al'amarin. Wasu suce sace ƴar ƙanwarsa yay ya ɓoye, wasu suce harda azabtar da ita yay saboda bata auri ɗansa ba. wasu suce aure yaje aka ɗaura mata akan aure da ɗan nasa. Magana dai barkatai gata nan, har abin ya fara shan kan Garko family musamman da sukaji ana neman saka waswasi akan AA wai ba'a ma san ɗan mijin Lulu na farko bane kona Tajuddeen.        Wannan magana ita ta tayarma da Daddy hankali. Ga Uncle Yousuf na tare da Smart acan England. Smart ne ya kwantar masa da hankali ta waya da tabbatar masa ai dama hakan zata faru dole, amma yayma kowa banza sai sun gama cecekuce ɗin nasu sai su san gaskiya. Abinda ke faruwar a yanzu yana cikin shirinsa akan Sulaiman ɗin. Hankalin Daddy ya ɗan kwanta ya samu nutsuwa. Amma yana mamakin wannan wane irin shirine haka da Smart da atashin farko ya ɗauki hanyar tallata abinda ke a ɓoye bayan da kansa yace yaƙin sunƙuru za'ayi. Koda yake bari ya saka masa ido yaga minene manufarsa. ai karan bana shine maganin zomon bana daman..... Ana tsaka da wannan dambarwa aka dawo da Dada gida Nigeria. Alhamdullah ta samu sauƙi sosai kamar ba itace aka fita da ita ƙasar raga-raga ba. Sai dai ta dawo ƙasarta da tagwayen al'amura biyu masu gogayya da juna zuwa uku. Na farko shine anga Lulu, sai dai tana baƙin ciki da haihuwarta da ɗan talakan nan dai, amma dai bata yarda ta furta ba gudun karta sake ƙullama kanta tsiya ga Baba Garko da tun a sibiti ƴaƴan keta faman kiransa suna bashi haƙuri ya maidata iddarta saura kwanaki ta cika amma yay biris da su. Abu na biyu shine fitowar Tajuddeen da kama Sulaiman kuma. Wannan al'amari ya sake ɗaga mata hankali. Ta kuma sake tabbatar da Baba Garko a shirye yake da kowa kenan, dan haka ta ƙara kama kanta.      Da ƙyar ta iya bari gari ya waye tasa Uncle Muneer ya kaita gidan su Lulu. Karo na biyu kenan da zata taka Jiƙamshi House a tsohon rayuwarta. Da ga lokacin rasuwar mahaifiyar Lulu sai yau saboda tsabar ƙiyayyar da takema Daddy a baya, koda yake har yanzu ma bawai ta barsa bane, kawai tana dannewa ne saboda Lulu ta nuna mata bazata ɗauki wannan ba ana zagar mata mahaifi. Duk da kasancewar gidane ginanne a tsaye, a kuma anguwar data amsa sunanta anguwa dan kosu da ke a kusa da gidan gwamna sun san a yanzu hotoro G.R.A ɗin ta basu baya. Amma haka tsohuwar nan ta dinga wani yamutse-yamutsen fuska har abin ya bama Uncle Muneer haushi da tabbatar da Dada fa bazata taɓa ta canja ba sai dai a barta da halinta kawai dan ya riga ya shiga jininta ne. Sun sami tarba tautuntawa da ga Daddy da Mommy. Duk da dai Dada na amsa musu gaisuwa sama-sama basu damu ba. Uncle Muneer ne dai ya ware abinsa sunata shan hira da Daddy cikin mutunta juna kamar yanda suka saba. A haka su Amrah dake maƙale da AA akoda yaushe yanzu, ko makaranta sai anyi jan ido suke wucewa suka fito. Yana goye ne a bayan Afrah yana barci, yayinda Amrah ke jiran time ya cika ta kunto mashi dan dole aka koma sakama kowa lokaci har su Naseer da ake korawa makaranta da ƙyar. Dan yau Suhaib harda kukansa shi sai da AA zai tafi kamar wani ƙaramin yaro. Basu ba dake ƙanana hatta Mubeen wataran faɗa ake da shi akan ɗaukar AA. Hakan na saka Lulu farin ciki da jin ƙaunar ƴan ƙannen nata matuƙa. Su twins kansu kullum sukan kirata sama da sau uku suna tambayar ina son ɗinsu. Hotunansa kam ƙa'ida akai masa wanka sai an tura musu. Ra'is da Deen kam ai sun ma dawo nan gidan saboda AA. Mommy kanta na ƙoƙarin gyara kuskuranta akan AA ɗin, dan itace a tsaye kan kula da Lulu da yaronta duk da Iya Tabawa na iya ƙoƙarinta. Dan ana cewa za'a samo tsohuwar da zata kula da Lulu ta ce ita dai a bata dama ta maida alkairi a wannan karon. Duk da dai a tsorace take saboda sanin halin Lulu ɗin. Amma dai ganin kamar ta ɗanyi sauƙi yanzu yasata cewa a bata dama. Bako a samu wata matsalaba kasancewar a yanzu ma ga Ummita kuma, sannan da gaske al'amuran Lulun sunyi sauƙi kam, duk da idan ƴan masifar na kusa takanyi abinta.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣2️⃣ .......Sai da Mommy ta harari Afrah sannan ta sakko AA a bayanta ta miƙama Uncle Muneer da yay magana. Dada ko tai muƙuy tana satar kallon yaron. Kamar dai kunya ce ta hanata cewa a kunnto mata shi. Amsarsa Uncle Muneer yay yana murmushi da tsokanarsa irin na wasar jika da Kaka Mommy na kare masa suna dariya. Cikin murmushi ya dubi Dada da faɗin, “Dada gafa baƙon duniya kinyi sabon ɗa”.      Murmushin yaƙe Dada tayi da faɗin, “Aiko ga shi nan bai baro gida ba, ALLAH yasa iya nan ya tsaya bai ɗakko sauran halayyar ba”. Kowa ya fahimci abinda take nufi, wato kamanin AA da Smart. Amma sai duk suka basar da ita. Ganin bata da niyyar cewa a bata ɗan yasa Uncle Muneer miƙa mata shi. A dai-dai nan Lulu da su Afrah suka kaima labarin zuwan Dadan ta fito. Babu kunya ta zabura gabansu ganin Uncle Muneer na miƙama Dada AA. Cikin sauri take faɗin, “Uncle kai dai ɗauki amma dan ALLAH kada ka bata ta faki idanunku ta kashe min yaro.”         Babu wanda furucin Lulun bai dakarma zuciya ba. Cikin faɗa Mommy ta ce, “Mawaddat mike damunki? Baki gane wacece bane? Dada ce fa!”.      Babu alamar damuwa ko sassauci da ga Lulun ta ce, “Mommy sarai na gane wace. Ko a cikin dubun mutane bazata layance min ba ai ba! Dada bace?. Kiyi haƙuri Mommy ki fahimceni, tayaya zan yarda ta ɗaukar min yaro bayan tun yana ciki aka haɗa kai da ita wajen nema ganin bayansa a gaɓar da daga ni har ubansa bamu san da shi ba saboda tsabar zaluncinsu. Dan haka barni da tsohuwar nan ni na dawo a rakkiyarta. Shin mima ya kawoki gidanmu? Keda kike zaginmu kuma kin rantse ƙafarki bazata sake taka cikinsa ba saboda Daddy da Mommy sun zalunce ki?”.        A daburce Dada ta ce, “Kina da hankali kuwa Mawaddat!?”.     “Sarai nake Dada, kinfi kowa sanin haka kuma. Ko a lokacin da nake shaye-shaye na san abinda nakeyi balle yanzu da nake a cikin hankalina. Yanzu dan ALLAH bakiji kunyar zuwa wai ganin abinda na haifa ba? Abin bai miki wani banbarakwai ba hakannan? Ai nazata ko'a hanya kika ga jinina dana Aliyu kya gudu dan kunya. Baku so ba ALLAH yayi, Aliyu ɗan Aliyu Mawashi ya tabbatar muku shi ɗan halak ne. Kuma ki sanarma ɗayan Mugun ni da shi wasa yanzu zai fara...”     Rawa jikin Dada ya farayi kamar mazari. Tuni hawaye sun cika mata idanu, muryarta na rawa ta ce, “Mawaddat ni kike ma irin wannan ɗibar albarkar haka? Saboda namiji? Namijin ma da bai damu da ke ba bai taɓa sonki ba sai da akai masa tallarki da sunan auren yarjejeniya. Kin bar gidansa bai nemi inda kike ba...”          Cikin ƙyaɓe baki Lulu ta ce, “Wannan gurgun tunaninki ne Dada. Shiyyasa kika zabgan ƙarya Aliyu ya sakan ko kunya baki ji ba saboda kina son na auri shashashan jikanki da baida freedom ɗin kansa sai na ubansa. Yo ai ko maza sun ƙare a duniya gara na mutu babu aure dana auri wannan shakatafin da ko ƙirrar mazan ƙwarai babu a jikinsa soƙai-soƙai kamar wani ɗan talo-talo. Aliyu ya soni ko karya soni wannan ba matsalarki bace ba, jeki fara gyara naki matsalar auren da ya rage saura kwanaki hope ɗinki ya kufce inba haka ba wlhy azumin bana sai mun buga miki gwauruwa tashi gari ya waye....”         “Mawaddat!!”.    Daddy ya faɗa da ɗan ƙarfi cikin tsawatarwa. Cikin girmamawa ta ce, “Na'am Daddy”.       Kansa ya girgiza mata alamar ta bari. Harara ta ballama Dada ta ɗauke kanta. Mommy da Uncle Muneer abin ai ya girmi kansu. Yayinda Dada ta saki kuka tana nuna Lulu. “Ni zaki cima mutunci Mawaddat saboda na zo gidanku ganin ɗanki. Ni kike nunama kin haihu kin san zafin ɗa?”.         Baki Lulu ta murguɗa mata da taɓe baki. Uncle Muneer ya sauke ajiyar zuciya yana sake gyara zaman AA a cinyarsa da yin gyaran murya ya dubi Dada. “Dada ya isa haka dan ALLAH miye abin wani kuka anan. Mawaddat yarinya ce ai, sannan irin wannan ranar nake gudun mana dama shiyyasa nake nuna miki ki daina biyewa Yaya da al'amarinsa. Yarinyar nan itace dai zata zauna da Tajuddeen, tun farko da aka ƙulla tace muku bata so, amma kika damu kanki, kuma godema ALLAH rabon yaron nan na namiji ne, da mace ne wlhy komai zai iya faruwa ciki harda iya rasa rai....”          “Yanzu dai Manneeru kana sake goyon bayanta ta cigaba da zagina kenan?”. Dada ta faɗa cikin kuka. Da sauri ya ce, “Sam ba haka nake nufi ba Dada. Taya zan giyama Mawaddat baya ta zageki kuma. Amma kuyi haƙuri. Ina son a gyara kuskuren nan ne saboda gaba. Yanzu badan ALLAH ya taƙaita ba yarinyar nan ta kuɓuta a hannun Yaya mi kike tunanin zai faru? Ko kuma data rasa ranta a wajen yunƙurin zubar mata da ciki. Yaya yayi amfani da ke ya barki a ciki. Sannan da mijin yarinyar nan fitinanne kina ganin zai ƙyaleku ne akan yunƙurin zubar masa da ciki har sau biyu? Ga shi kunje kunce mata mijinta ya saketa! Shin aure kan aure kukai shirin mata komi ma wai shin ni na kasa gane muku?”.        Tsigil Lulu ta ce, “Abinda suka shirya mun kenan Uncle, kuma wlhy a lokacin na ƙudiri aniyar suna ɗaurashi zan kashe Tajuddeen ɗin ne sai dai nima a kashe ni!”.      Babu wanda bai kalletaba yanzu ma a razane. Itako hankalinta kwance tama miƙe tana hararar Dada da cigaba da faɗin, “Kuma ko yanzu ba haƙura nayi ba. Dan bana barin bashin gaba. Sulaiman sai yamun bayanin alaƙata da shi da ya addabi rayuwata data mahaifina, dan haka ku jira sammacin kotu dan sai munyi shari'a, idan Aliyu ya iya muku haƙuri da kawai ci ni bazan barku ba”. Daga haka tabar wajen fuuuu. Dada ta zabura zata bita Uncle Muneer ya riƙeta yana girgiza mata kai. Sai ta ƙara fashewa da kuka ta maida faɗan a kan Daddy. Wai duk shi ya kitsama Lulu taci mata mutunci tasan Lulu bata da wannan wayon. Daddy dai ko tari baiyi ba, sai Uncle Muneer ne ya shiga mata magana cikin ɓacin rai akan shi da yasan abinda zatayi kenan da bai kawota ba. Yanda yake faɗa zai tabbatar maka ransa ya ɓaci, dan sosai take cima Daddy mutunci da masa gori. Amma ko tari bai mata ba balle aje ga batun ramawa. Su Amrah ne dai suka sake zuwa suka kira Lulu. Aiko sai gata a fusace. Ranta yafi na kullum ɓaci akan abinda Dada kema mahaifinta, atake na ƴan ƙwayar ya motsa ta rufe ido taima Dada tas har sai da ta gudu dan kanta saboda ganin buyagin Lulu fa ya haifi nata. Dan yanda Lulu ke ruwan bala'i zaka rantse bata taɓa sanin Dada ba a rayuwarta balle tuna qlaƙarsu. Uncle Muneer ransa ya kai matuƙar ɓaci, da yasan abinda Dada zatazo tayi a gidan mutane wlhy dabai kawota ba. Aiko ƙin kaita yay gidan Alh. Sulaiman da tace zata duba Tajuddeen shima.       Lulu kam da bayan fitarsu Daddy ya hauta da faɗa sai ta sakar masa kuka. Dole ya fice cikin ɓacin rai dan duk da yayi shiru kalaman Dada sun matuƙar zafar masa zuciya shima, amma bazai so Lulu ta cigaba da mata tsiwa ba matsayinta na kakarya. Ya danne ne kawai saboda dattako. Lulu na komawa ɗakinta kiran Uncle Yousuf ya shigo mata. Ɗauka tai kawai ta fashe masa da sabon kuka. Ƙirjin Smart yay wata irin harbawa. Dan dama kiran nashi ne bana Uncle Yousuf ba. Haka yake yi sai ya kirata da layin Uncle Yousuf ɗin yaƙi magana. Taita faman sallama yay shiru har sai ta gaji ta katse, wani lokacin tabi kiran wani lokacin ta share. Ko tabi baya ɗauka kuma sai dai ya bama Uncle Yousuf ɗin. Dama shi burinsa jin muryartane, wani lokacin ma yakanyi sa'ar jiyo AA na kuka musamman idan darene a Nigeria kasancewar AA ɗin ya dage da musu kukan dare yanzu. Da ance ɗaya tayi babu sauran zaman lafiya kuma sai anyi sallar asuba. Wani lokacin har Daddy fitowa yake ya ɗaukesa aita masa addu'a da rirriga amma yaron nan ko'a jikinsa. Mommy tayi, Ummita tayi Iya Tabawa tayi. Lulu kam sai dai tayi tagumi kawai yana kallonsu, wani lokacin ma ba'a tashinta sai idan kukan yayi nisa ne sosai ace ta tashi ta shayar da shi. Amma yaron nan ko'a jikinsa, wani lokacin ma dan zuciyar tsiya irin ta uban baya ko kamawa.       Kasa sauraren kukan nata Smart yayi ya yanke kiran, cikin tashin hankali da damuwa ya nufi Uncle Yousuf kamar zai fasa kuka ya ke faɗin, “Kuka takeyi, ka kira kaji mike damunta Please Uncle”.          Shima Uncle Yousuf hankalinsa ya tashi, dan yasan duk abinda ya saka Lulu kuka ba ƙarami bane. Wayar ya kira tare da saka Hans-free. Kamar bazata ɗauka ba kuma sai ta ɗauka. Tambayoyi Uncle Yousuf ɗin ke mata cike da kulawa batare da ko jiran sun gaisa ba. Bata ɓoye masa komai ba ta sanar masa. Smart ya sauke nannauyar ajiyar zuciya da lumshe idanunsa da suka kaɗa sosai. Shi dai tunda ba wani abu ne ya sameta ba ai da sauƙi. Lallashinta sosai Uncle Yousuf yay, sannan ya mata faɗa da nasiha akan rashin kunyar da taima Dadan. Ya ce karta sake babu ƙyau hakan. Dada tamkar mahaifiya take a gareta. Ta bashi haƙuri da tabbatar masa bazata sake ba. Amma a ranta fa tasan ita da Dada fa ai haihata-haihata (🤣😂 ALLAH ya ƙyauta su Lulu an san daɗin ɗa🥱🚴👏).          Cikin tsokana Uncle Yousuf ke duban Smart yana faɗin, “Darun matar nan taka sai kai Aliyu, ni dama nasan wlhy bazata ƙyale Dada ba. Kuma duk a wajensu ta kwaso wannan masifar ai dan mudai a family namu babu mafaɗaci”.       Murmushi kawai Smart keyi, a ransa yana sake jinjina hali irin na Lulu. Yasan tabbas yaransa sun bani da masifa tunda shima dai ba raga masa ake ba. Wani lokacin idan tana faɗa har mamakin wai kanta baya ciwo yake yi. Tana da tsiwa sosai, ga shi sam babu tsoro a idanunta. Ita dai kawai zaman lafiyarka da ita kada ka shiga gonarta ne kawai..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣3️⃣ .......Alhmdllh sosai jego yayma Lulu ƙyau, ga Iya Tabawa na mata wani sirrintaccen gyara irin na mutanen da cikakke da ke zama a jikin mace duk da bada kanta ta haihu ba. Gefe kuma Aunty Saliha ta sake kawo wanda sukai mata gyaran aure na nasu suma yanzu. Mommy ma na nata ƙoƙarin. Sai ruwan addu'oi wajen Malam na Yakasai da ake amsowa Lulu na tsarin jikin da yanayin da take ciki game da Smart. Wannan ƙoƙarin Ammah ne da Abbah. Dan ita kanta Ammah kan zauna da kanta tai mata addu'oi a cikin ruwa da ma ruwan zam-zam shima AA ana bashi.       Sai Daddy da ya kawo mata malama har gida tana ɗora mata karatun addini saboda Ummita zataje ganin gida itama. Da yake Lulu tasa abun a ranta hatta Mubeen zaunarwa take ko su Amrah su ƙara mata karatun. Gefe guda kuma tana ta ciku-cikun yima ƙungiyarta rigester shima da taimakon Daddy da Uncle Khamil na Abuja da shima ya bata goyon baya. Koda wasa bata son tuna Smart, dan ko AA ta kalla babansa yazo mata a rai kanta ya dinga wani irin masifar ciwo kenan dake tayarma kowa na gidan hankali. Inda aka yankata Alhmdllh yana sake warkewa, Aunty Khadijah matar Coach ce ke zuwa dubata kullum babu fashi, idan abinda ya kama taje asibiti ne kuma sai ta shirya Mubeen ya kaita suje suga likitan su dawo. Da Ummita zata wuce shatara ta arziƙi Daddy ya haɗa mata, itama Lulun ba'a barta a baya ba, Uncle Khamil ne da yazo ya wuce da ita duk da dai jirgi sukabi zuwa Abuja tare, dan Lulu ta gargaɗeta zuwa ɓagwai saboda gudun mutanen Alh. Sulaiman kar su cutar da ita ko iyayyenta.        ★A ɓangaren Ammah tsaye take wajen kaima UBANGIJI kukanta akan dai-daituwar zaman waɗan nan ma'auta. Tare da yawaita sadaka da azumi. Yaranta kaf basu zauna ba har ƴan uwanta kasancewar suna da haɗin kai. Yayinda itama Ummah ta kasa zaune ya kasa tsaye wajen sake lafto sabbin asirai kala da iri akan Ammah da Smart kai harma su Aunty Amaryar ba bari tayi ba. Dan a kwanakin nan da ƙyar suka samo kan Abba da aka nema juyarma da kai. Sai Alhmdllh al'amarin baiyi nisa ba ya sake shi, hakan ya tada hankalin Ummah kam sosai, dan ba ƙananun kuɗi ta kashe a aikin da akaima Abban ba, amma sai gashi ya tafi a banza cikin ƴan kwanaki ƙalilan....          *_UK LONDON_*    Hassada ga mai rabo taki ce, sannan duk abinda UBANGIJI ya ƙaddara shi a matsayin naka babu wani mahaluki a duniya da ya isa canja wannan ƙaddarar. Dan kuwa a lokacin da Ummah ke can tana faɗi tashi akan abinda bata iya jayayya da shi ba anan ƙasar England ƙaramin labari ne ke neman canja kansa akan Aliyu Mika'il Idris Mawashi, wato Smart Mawashi zuwa babban gaske gagarumi. Dan fa manyan clubs da ke zawarcinsa ta ƙarƙashin ƙasa sun fara bayyana kansu a fili yanzu. Wannan yasa aketa faman kai kawo da dambarwa tun barowarsu Canada shi da Manager ɗinsa Uncle Yousuf. Sosai ake ta kai ruwa rana da bata kashi a tsakanin Coach's ɗin mayan clubs ɗin. Shi dai Smart ya duƙufa gayama UBANGIJI da neman zaɓinsa. Dan bashi da wani zaɓi sai nashi. Yayi alƙawarin duk inda ya tsinta kansa zaiyi aiki tuƙuru in sha ALLAHU duk da a cikin zuciyarsa yana da club ɗin da yafi so da ƙauna kuma gashi a cikin masu zawarcin nasa. Amma sai bai Zafafa ba ya bar ma UBANGIJI komai sai su Uncle Yousuf da keta kaiwa da komowa shi da Coach ɗinsu na Queen City da duk manyan masu faɗa ajin club ɗin.      Sosai mahawara ta ɗauki zafi a tsakanin manyan clubs guda uku da suka riƙe wuta fiye da sauran, dan kowa ya gagara janyema kowa. Sannan duk sun zuba manyan kuɗaɗe akan Smart ɗin masu girgiza zuciya. Abu kamar wasa ƙaramar magana ta sake zama babba. Dan manyan gidan jaridu na duniya musamman a fanin ƙwallon ƙafa sunyi ƙur da idanunsu akan wannan batu domin ganin wazai ɗauki wannan lu'u-lu'un a cikin juji. An buga an turza an kai matuƙar kai ruwa rana kowa yaƙi sakarma ɗan uwansa, dole aka tafi mataki na biyu wato jin ra'ayin Smart game da wane team yafi sha'awa shi a ransa. Tun farko Smart nada ra'ayinsa dama, amma ya zaɓi barma UBANGIJI zaɓinsa. Har a yau da aka kai wannan matakin na jin ra'ayinsa bai ji zuciyarsa ta canja da ga abinda ta ke so ba tun yana da ƙuruciya. Dan haka bai wani basu wahala ba ya faɗa musu zaɓinsa wato *_ARSENAL FC_*. hankalin sauran clubs biyun da sukai gogayya da Arsenal ɗin ya ɗaga, a take suka ƙara kuɗi akan wanda suka saka a farko, amma dai Smart nakan bakansa Arsenal ɗin dai, dole suka haƙura dan aikin gama ya gama Arsenal tayi nasarar siyensa da kuɗi kimanin dala Miliyan arba'in.         Duk wani masoyin Smart a wannan rana yana a cikin matuƙar farin ciki mara misali, Ammah duk dauriyarta sai da tai hawaye lokacin da Uncle Yousuf yay kiransu yake sanar musu al'amari fa ya kai girman da aka daɗe ana fata. Sai kuma addu'ar cigaba da samun nasarori ga Smart ɗin. Amma wannan tsanin kam an haye sama ƙololuwa.      Sun ɗanyi zaman meeting meeting da ƴan cike-cike na tsarabe-tsaraben da aka san ƙwallo da shi su da Manager ɗin sa Uncle Yousuf da shi kansa Smart ɗin. Kafin dai a ƙarƙare ya saka hannu a ƙarshe. Da ga haka akaje matakin duba lafiyarsa ciki da bai. Alhamdullah nan ma normal an samesa da cikakkiyar lafiyar jiki dama ta sassan jiki. Bayan kammala waɗan nan ya ziyarci Arsenal camp domin yin hotuna da gabatar da shi ga teammate ɗinsa. Ya samu tarba fiye da yanda yay zato da tsammani ga teammate ɗinsa. Dan tunda suka shiga cikin camp ɗin bakinsa bai bar ambaton ALLAH ba. Kwarjininsa da hasken musulunci ya sake ƙawatashi a garesu da girmama mutuncinsa. Sunyi hotuna da duk abinda ya dace a wannan ranar kafin a wuce mataki na gaba. Wato gabatar da Smart Mawashi ga fans.       Duk wani masoyin Arsenal ya halarci babban stadium ɗinsu da ke a cikin birnin London. Wasuma da ga ƙasashen ƙetare suka zo domin ganin sabon yaron na Arsenal da za'a gabatar saboda soyayyar da sukema club ɗin. An cika matuƙa da har sai da Smart ya dinga jin kansa na sara masa. Ga kuma masu kallo a television. Amma ya daure bakinsa na cikin ambaton ALLAH ya fuskanci masoya. Wani irin ihu da stadium ɗin ya ɗauka lokacin da yake shigowa fuskarsa ɗauke da sassanyan murmushi yana mai ɗaga musu hannayensa biyu yay dai-dai da wanda su Mubeen suka ɗauka suma a cikin falon gidansu da Lulu ce kawai babu tana can ɗakinta tana barci. Hatta AA na a hannun Daddy dan har shi ake wannan kallo. Fitowa tai a ruɗe, sai dai ganninsu duk suna kallon ƙwallo a tv kuma duka gidan ya sata tsayawa turus cikin dafe kai da jan tsaki. Babu ma wanda yasan tanayi dan hankalinsu bama ya wajen. Cikin jin haushi ta juya ta koma duk da tayi mamakin ganin harda Daddy da su Iya Tabawa wai ake kallon ƙwallo yau a gidan. Abu ne ita dai da bata taɓa gani ba. Ta dai san Mubeen nayi da su Hussain idan sun zo. Amma kosu Amrah ta sha jin suna faɗa da Mubeen idan zai kalla ƙwallo ya hanasu su kalla film. Amma wai yau sai gashi ƙwai da kwarkwatar gidan ta gani. Abinda ma Lulu bata lura da shi ba shine harda masu wanki duk suna a falon, dan suna da ga ƙasa ne zaune yasa bata gansu da ƙyau ba... Kamar yanda a gidan Daddy suke kallo a gidan su Smart ɗin ma hakane. Dan su Mubarak ne suka cika gidan da abokansu da samarin anguwa. Yayinda ba'a bar Abba a baya ba da ga shi har Ammah da sauran yaran gidan sun cika a falonsa danƙam dan shi yasa a tattaro kowa yazo. Ran Umma da Mama a mutuƙar ɓace yake. Zuciyar Umma bata nema fitowa ta baki ba sai da aka nuna Smart na shigowa cikin tsakkiyar tarin tawagar turawan nan yana ɗan wasa da ƙwallo, stadium ɗin ya ɗauki ihu kamar zai tsage. Sai kuma sanda aka ɗaga rigarsa mai lamba tara yanda suka ɗauki ihu mai jijjiga kunne ita zuciyarta suke jijjigawa, dan a bazata kawai sai ta fashe da kuka. Da farko babu ma wanda ya lura da ita sai da Huwaila ta ce, “Ummah ke kuwa miya sakaki kuka? Ko duk farin cikin ganin Yaya Hydar ɗinne?”.      Lokacinne hankalin kowa ya koma kan Umma. Sai dai kafin ma wani ya iya cewa wani abu ta miƙe cikin rangaji kamar wadda tasha tai marisa ta nufi ƙofar fita. Ƙayataccen murmushi Abba da Ammah suka saki kusan lokaci guda. Yaranta dama duk wanda ke wajen zasu ɗaga hankalinsu su bita Abbah ya ce kowa ya koma ya zauna, idan kuma wani ya bita sai ransa ya ɓaci. Dole sukabi umarninsa. Da ga baya ma abinda ke faruwa ya ɗauke hankalinsu kowa ya manta da batun wata Umma can.... Sosai Smart ke jin farin ciki a ransa mara misali dan harda hawayen farin ciki ganin yanda waɗan nan ɗunbin al'umma suka amshesa da taruwa domin shi. Bakajin komai sai ambaton sunansa a wajen, _Smart Mawashi, Smart Mawashi_ dai. Yanda ma suke ambaton Mawashi ɗin abin dariya. Abinda ya ƙara tabbatarwa da mutane Smart Mawashi ya amsu yanda a yinin ranar kawai an saida copy na rigar JC mai ɗauke da sunansa kawai ta kai kimanin dubu hamsin. Wannan al'amari ya matuƙar ɗaukar hankalin mutane da gidajen jaridu. Yayinda masu fashin baƙi akan harkar ƙwallon ƙafan keta nasu aiki. Gida Nigeria musamman arewaci kuma garin Kano sun shiga matuƙar alfahari da ganin ɗan su yau a wani mataki na rayuwa da sai ɗan baiwa mai Sa'a kawai ne ke takawa. Hatta da social media babu abinda ke kai kawo sai hotunan Smart Mawashi da tarihin rayuwarsa. Hatta da hotunan bikinsa ranar sai da suka dawo sabbi a yawon media. Sai a lokacin ne Lulu tasan wainar da ake toyawa. Ita kasa ma fassara al'amarin tayi sam. Cikin sauri ta shiga bincike-bincike a media. Sai ko gashi ta ga duk abinda take buƙatar. Tsabar yanda al'amarin ya dakar mata zuciya bata iya furta komai ba. Dan datace ma zata tsananta tunani ko maganar Smart ɗin matsanancin ciwon kai da tsanarsa da take ji ke dawo mata sabuwa. Dan ma Alhmdllh zuwa yanzu akwai ɗan sassauci a a al'amarin kasancewar addu'a da aka duƙufa yi babu dare babu rana. Yau ɗin ma dai ta yini da ciwon kan, dan har dare tana kwance tana fama har sai da Daddy ya shigo yay mata addu'oi.... Bayan Smart ya fito da ga stadium hirarsa da ƴan jarida ta zama abu na biyu da ya sake zama babban topic a kansa a wannan yini. Ya bada tarihin rayuwarsa da yay matuƙar taɓa zukatan mutane harda masu hawaye, dan ma ya ɓoye kaso tara cikin goma ya bayyana abinda yake da buƙatar duniya ta sani ne kawai. Ya bayyana irin yanda ya tashi da son ƙwallo a zuciyarsa da taimakon da Abdull-Hameed Coach yay masa a rayuwa da matsalolin da ya samu da ga baya. An masa tambaya akan dalilinsa na zaɓar team ɗin Arsenal duk da sauran clubs biyu da suka riƙe wuta a zawarcinsa sun sake ƙara kuɗi amma yace Arsenal ɗin dai. Sai yay murmushi da faɗin “Arsenal club ne da tun yana yaro yake matuƙar so, sannan club ne mai ɗunbin tarihi da kuma ya ajiye tarihi da tarin masoya a duniya, sannan club ne one of the best in the world. Sannan yana da ƴan wasan da yake matuƙar so da kallo a matsayin madubinsa a cikin club ɗin irinsu Terry Herry. Patrick Vieira da sauransu.......”✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣4️⃣ ........A ɓangaren Ummah tana shiga ɗakinta ta sake tsagewa da kuka, a haka ta hau neman layin Hajiya Naqiba.       “Na shiga Uku Aminiya Abban Salim ne ya mutu?”. Cewar Hajiya Naqiba a rikice jin Umma na ɓarza kuka.     “Ba garama mutuwar ba zan haƙura dole Aminiya. Ashe malamin nan yaudarata yake shima duk irin maƙudan kuɗin dana zube masa. Gonata ta gado fa na ɗaga na sayar na bashi kuɗin aikin nan amma ace wai duk a banza nayi, yau sai ga shegen yaron nan mai taurin ran tsiya a tsakkiya Turawa kamar zasu cinyesa dan soyayya. Wai wani ƙungiya na kwallo asinal yake ko uwarmi ne ma oho musu suka sayeshi da wani uban kuɗi da har yanzu ma zuciyata da ƙwaƙwalwa ta sun kasa haɗawa dai-dai, wai zai musu ƙwallo na shekara biyar. Shike nan na mutu Aminiya, duk wahalar da nake akan yaron nan dai abanza take cigaba da tafiya”.         “Tofa babbar magana, wai shi Hydar ɗin ne yakai wannan matakin na shiga ƙungiyar Arsenal? Shin ko shine ma ɗazun Maheer ke ban labari cikin zumuɗi wai wani matashi Smart ɗan Kano ya zama babban gwaska a duniya, yanzu hakama yana nan gidan Alhaji Sammani wai suna kallo ko ana nunashi”.               “Matsiyaci haihuwar asara shine. ALLAH ya tsinewa uwarsa ma bashi ba. Na tsani matar nan fiye da yanda na tsani mutuwata, duk irin wahala da kai-kawon da nake a kanta da faɗi tashi kullum abbanza suke tafiya. Narasa wace irin baƙar tambaya ke ga Hafsatu”       “Humm Aminiya kar kice haka, kin manta nasarar da kikaci ta tsahon shekaru yaron nan ko filin ball bai iya shiga, ga tsanar da Abban Salim yay masa. Sannan a yanzu haka fa akwai asirin dake jikinsa wanda ya gagara zama da matarsa waje ɗaya....”            “Na fara ji a raina asirin nan bai kama shegen yaron nan ba, matar tasa kawai ya kama dai kamar, kuma mayen yaƙi sakinta. Malam yana ɓoye mana ne kawai”.      “Tunda dai har ya kama matar tasa ai ya wadatar damu. Ki kwantar da hankalinki dan ALLAH yanzu ma bamu makara ba. Wajen Na-zuru zamu koma tunda dama shine yay masa wancan ƙullin goron na farko, irinsa zai sake mana ko ya shiga filin ya yanke jiki ya faɗi basai muga ta ƙafafa ba. Sannan kisa ranki a inuwa, wannan maƙudan kuɗi da kikaji ba nashi bane ba, haka naji Maheer nacewa da nake masa faɗan shi miyyasa bazai zo ya koya ƙwallon ba.”         “Kai dan ALLAH wai da gaske kike? To kudin na waye?”.     “Ni ban sani musu ba, kamar dai yace wai ko kungiyar daya bari ne ai da kuɗin, shi za'a yanka masa nasa albashinne.”                “Kai amma har na ɗan jin sanyi, shegiyar uwarsa sai muga ta hura hanci, ashema kuɗin na wasu ne shasha ɗan ya koma bawan turawa bata farga ba”.      Dariya suka kwashe da shi kamar suna kusa da juma....      Niko na ce, “Hummm!”.   ★Sosai abinda Umma tayi ya tsayama Abba a rai, har ya shiga dogon nazari akanta. Sai dai baicema kowa komai akan hakan ba. Itama baice matan ba. Ya dai ɗauki ɗammarar saka ido a lamarinta domin tabbatar da abinda ransa ke raya masa...            ★Ammah kam ko'a jikinta, dan ita zuwa yanzu lamarin Ummah bai wani damunta sosai. Face dagewar da tai da addu'a ita da zuri'arta domin kariya da ga sharrinta. Dan duk yanda Gwaggo Sa'adah taso ɗaukar mataki ta hanata, acewarta su jira sakamako na zuwa akan kowa.....          *_6 MONTH'S LATER_*                 Abubuwa da yawa sun faru masu tafiya da nasarori da kalubale a cikin waɗan nan watanni da suka kasance kusan tara da haihuwar Lulu. Ƙalubalenta na farko mai kuma girman gaske shine shiga tsakaninta da mijinta uban ɗanta da akai ta hanyar sammu mai ƙarfi. Nasararta ta farko komawa islamiyya neman ilimin addini tuƙuru tare da maida hankali matuƙa duk da ta koma bakin aikinta. Sai wannan gaɓar ta kuma samu nasarar kafa ƙungiyar da take buri data samu tallafin ƙarfafa gwiwa da ga iyayenta da kakanta har ma da ƴan uwan haihuwar makaifiyarta. Nasara ta uku kafa business ɗinta data jima tana buri na turare, tana kawosu daga ƙasashe daban-daban, ana kiran ƙaton shagonta da suna *_LULU's ƘAMSHI_*. Nasara ta huɗu ƙyaƙyƙyawan yaronta da kamaninsa ke ƙara fitowa dana mahaifinsa nata ƙara wayo gashi cikin ƙoshin lafiya da kuzarinsa. Alhamdullah kuma yana a cikin kariyar UBANGIJI shikam. Dan duk da irin hare-haren da su Umma suke kawo masa ALLAH ya kiyaye abinsa yaron nan ko gezau. A yanzu haka ya fara miƙewa ya ɗan dafa kujera alamar dai yana son taka ƙafa. Ana kaisa wajen Ammah ya yini abinsa, kasancewar yana shan koko kuma gashi baida damuwa akwai haƙuri yasa sai ya yini lafiya sannan a maidosa. Itama su Asma'u kanzo su yinin mata anan. Su aunty Bilkisu kansu kan zo suga AA da gasiheta lokaci-lokaci. Itama kuma tana zuwa gidajensu har ta yini. Can gidan ne dai bata iya zuwa. Dan kota gwada hakan baya yiwuwa. Wannan abu na cimata rai dan tana so da ƙaunar Ammah a ranta. Wannan soyayyar da ga ALLAH ce. Shiyyasa itama Ammahn kan leƙosu lokaci-lokaci musamman idan ance AA na mura haka ta haƙora. Sosai shaƙuwa ta shiga tsakaninta da dangin Smart. Dan hatta samarin su Mubarak sukan zo gareta a ɓoye batare da sanin iyayensu mata ba. Duk watan duniya kuɗi kan shigo account ɗinta da ga Aliyu, sannan akan kirata da number ƙasar England. Sai dai kota ɗaga ba'a magana, sai ita zata dinga hello-hello da ga ƙarshe a yanke kiran. Takan ji haushi tace bazata sake ɗagawa ba. Amma da an kira bata iya haƙuri sai ta ɗaga ɗin...       ★A gidan su Smart kam nasarori da ƙalibalen suma dai basu tsallake su ba. Sai dai Alhmdllh a ɓangaren Ammah babu abinda zata cema UBANGIJI sai godiya. An tsaida Ranar auren Maryam da Ahmad. Yayinda ɗaukakar da ALLAH ya bama Smart ta sake fiddota a cikin ƴan uwa dama jama'ar gidan har da dangin Abbah. Smart ya dakatar da Abbah fita kasuwa duk watan duniya ya yanka masa albashi shi da Ammah a cikin albashinsa da ake biyasan duk sati-sati. Sannan Ahmad zai kawo kayan abinci bisa Umarnin sa.          Wannan abu na ƙara ɗaga hankalin Umma har ma da Mama. Sai dai banbancinsu ita mama kan balbale nata yaran da faɗa ne akan suma su san ciwon kansu su dinga ma mahaifinsu in ba hakaba smart zai ƙwace dukkan power ɗin su, sannan ita bata bin malamai, kishi ne dai irin na matan bahaushe da jin ƙyashin cigaban kishiya. Itakam Umma tsantsar hassada da baƙin ciki sunbi sun kanainaye mata zuciya da ruhi. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Duk ɗan abinda ta samu suna a yawon malamai da bokaye ita da Hajiya Naqiba aminiyarta. Aikin suke iya ƙarfinsu amma basu sake jin wani sabon abu ba bayan zaman Lulu gida. Ga malamin nata ya tabbatar mata akwai fa matsala idan aikin bai kama Smart ba shi. Dan su duka biyun akai musu ai akan su tsani juna. Wannan dalilin yasa take ta faman bibiyar al'amarin Smart dan taji shi ya wajensa yaya akan matar tasa amma ta kasa samun kowacce irin mafita. Ga lamarin Huwaila na caja mata kai. Dan ta girmi Maryam amma har yanzu babu tsayayye, saka auren Maryam kansa ya hargitsa mata lissafinta. Balle da taji cewar itama mai hannu da maiƙo zata aura. Wayyo ina wuta ta saka Ammah ne. Ta rasa wane irin sirri keda Ammah ɗin da dukkan ƴaƴanta suke auren ƴaƴan masu kuɗi. Yanzu dai abu biyu ta saka a gaba. Wato tarwatsa rayuwar Smart da rusa auren Maryam. Duk ta fige ta lalace a tsaye saboda saka wa kai musiba. Itace kullum faɗa da ƴaƴa akan su bata kuɗi, musamman ma Salim dake nuna mata shi fa ya gaji da wahalarta, mitake da kuɗi wai kamar wata ƴar caca..       Duk abinda take a yanzu idon Ammah ƙyam yake a kanta, dan haka ta dake dagewa da addu'oi da sadaka.. Tare da kiyaye duk wani abinda Umma zata basu koda abincin gidanne yanzu ranar girkin Umma sai suka daina ci, miya Ammah ke musu mai yawa tasa a freight, duk ranar da Umma tai girki sai tayi musu abinci a a ɗaki suci, na Ummar a fitar waje aba mutane cikin hikima.. A tunanin Ammah Abbah bai san mike faruwa bane, sai dai idonsa na akan komai yana dai biye yaga iya gudun ruwan kowannensu musamman ma Ummah..         ________★   A garko family kam abubuwane keta ƙara tsamari. Abu na farko shine Baba Garko dai tunda ya tsallake bayan kama Sulaiman bai sake dawowa ba, sai labarin a washe garin da Dada taje gidan su Lulu suke jin cewar an ɗaura masa aure matar ma ta bisa. Ranar sunga abinda ya girmesu a wajen Dada. Dan zaman ƴan bori tayi a gaban surukai ta saki ƙaƙƙarfan ihun da ya nema girgiza ginin gidan. Ba ita ba su kansu yaran hankalinsu ya tashi, a ganinsu mi mahaifin nasu zaiyi da wani aure a shekarunsa haka, kuma abin mamaki wai ma budurwa ya aura sa'ar ƴaƴan cikinsu. Matansu kam dai wannan al'amari yay musu daɗi, sai dai suna ƙoƙarin dannewa a gaban mazan nasu.. sai an koma gefe asha gulma da dariyar Dada..         Sai da Baba Garko ya kwashe watanni kusan shida da amaryarsa suna yawan hutawa a ƙasashe sannan suka dawo Nigeria da cikinta da ya fito kowa na gani. Ƙyaƙyƙyawar mace ƴar gaye mai tarin ilimin addini dana boko. Sannan gata yarinya ƙarama, dan bazata wuce sa'ar Lulu ba ma. Da gani dai kasan kuɗi ta gani ta shige, duk da dai Baba Garko ba baya ba wajen ƙyau amma tsufa ai ya ƙwace komai sai godiyar ALLAH kawai. Wannan ciki ya saka ƴaƴansa jin matuƙar kunya, sai dai babu damar yin magana ya maka wankin babban bargo, dan shi ko'a jikinsa. Kuma yace dole su girmama masa mata. Suna son sake bashi haƙuri akan mahaifiyarsu suna jin tsoro, dole sukai gum da bakunansu.       Washe gari Daddy da Uncle Yousuf sukaje gaishesa suma da masa murnar aure anan ne su dai suka fidda kunya da tsoron suka roƙesa akan yay haƙuri itama Dada ta dawo. Ai an mata gargaɗi. Shima Alh. Sulaiman ai masa afuwa dan ALLAH ya dawo cikin iyalinsa. Bai tanka musu ba dai, sai sakawa da yay Uncle Yousuf ya kira masa Smart a waya. Yako kira masa shi suka gaisa. Yana jin ƙaunar yaron matuƙa yanda yake bashi girma. Yay masa faɗa akan rashin kiransa su gaisa, tare da tayasa murnar cigaban rayuwa da ya samu. Yace shi ai bai sani ba sai kwanan da ya gansa ana hira da shi ya shiga mamakin kamannin har yay kiran Daddy shine fa yake tabbatar masa da shi ɗinne. Haƙuri Smart ya bashi cikin girmamawa da tabbatar masa zai gyara insha ALLAH. Cikin gamsuwa Baba Garko ya sake saka masa albarka. Sai kuma ya tambayesa yaushe ne zai zo ya ɗauki iyalinsa. Ɗan jimm Smart yay na wani ɗan lokaci, kafin ya firzar da numfashi yana jan ajiyar zuciya. Cikin tausasa harshe ya ce, “Baba yanzu ni lokacin nawa ne sai a hankali, dan gashi ana tsaka da fara buga wasan premier link ne. Sannan kuma itama bana son a takura mata har sai idan itace da kanta ta yarda zata nemeni nake ganin hakan zai fi zama masalaha, itama bazataga an takura mata ba kamar farko”. Murmushi irin na manya Baba yayi. Tare da cewa, “Shike nan shawaranka yayi sosai”. Daga haka suka ajiye wannan maganar Smart ya koma bashi hakuri shima akan maida Dada da sakin Alh. Sulaiman. Acewarsa shi ya yafe komai ya wuce a tari gaba........✍️      _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣5️⃣ ........Wannan roƙo nasu Smart da Daddy da Uncle Yousuf harma da Abba da shima yazo masa murnar ƙara aure akasha hira da barkwanci na tsoffin abokai bayan sati biyu Dada ta dawo. Dawowar data zame mata matsanancin jin zafi. Gashi ba abun tace bazata dawo ɗin ba ta rasa sauran damarta. Ga muzantatan da surukanta keyi na sake ɗaga mata hankali. Ta samu gida fa komai ya sauya. Hatta masu aiki kowa dai Aunty Amarya dai aunty amarya dai. Dan yarinya ta kwantar da kai tana cin garar arziƙi abinta. Ta kuma kame kowa na gidan da ƙyautatawa bayan uban gayyar Baba Garko da taima ram da zuciya yake jinsa kamar wani ɗan shekara talatin, dan more tsufansa yake hankali kwance ya manta da batun wata aba Dada... Ganin cikin amarya da Dada kejin wai-wai a bakin mutane ya sake ɗaga mata hankali ta ɓarke da kuka. Wai itace yau tsofai-tsofai da kishiya, kishiyar ma sa'ar jikokinta kai jama'a wane irin cin zarafine wannan Alhaji Sufi yay mata ne ita kam a duniya, duk wahalar da tai a ƙuruciya na hana wata shigowa gidanta sai a wannan gaɓar za'ace wai ga ɗan uba a cikin zuri'arta. Ga shi Baba Garko yaƙi ko saurarenta tunda ta dawo, duk ranar girkinta fa zai yi kamar suna tare amaryarsa bata zuwa inda yake, amma kuma bai barin itama Dadar tazo. Ko kuma ma ya ƙirƙiri tafiya. Bayan wata ɗaya da dawowar Dada yasa aka saki Alh. Sulaiman shima.....        ______★ A ɓangaren uban gayya kam al'amura sai dai Alhmdllh. Dan komai yana tafiya fiye da yanda akai fatansa. Ya zama cikakken ɗan wasan Arsenal da yanzu duniya ke kallo ta faɗa da kiransa *_GWARZON ZAKI_* Sunan Smart Mawashi sake dilmiya yake a duniyar ƙwallon ƙafa. Dan a yanzu haka ya fara taka sabuwar rawa a sabon team ɗin nashi na Arsenal. Duk da kuwa wasanni uku kenan suka buga kacal. Sai dai aduka wasan babu wanda bai saka musu ƙwallo ba. Wannan ya sake jawo hankalin al'umma kansa tako ina a duniya. Ya zama ɗaya daga cikin matasan yara masu tashe a duniyar ƙwallon da ake faɗa ake ma kan faɗa a kowane yini. Al'amarin matarsa bawai baya damunsa bane, ya miƙama UBANGIJI al'amarinsa ne kawai da fatan cinye waɗan nan jarabawoyi kashi-kashi. Shi kaɗai yasan abubuwan da yake jurewa a irin wannan tsukun. Amma yana matuƙar begen matarsa a kusa da shi har ma da gudan jininsa takwaransa.....         ____________★   Yau ma a gajiye ta dawo gidan kamar kullum Ummita biye da ita da tarkacenta. Tunda aka kammala bikin buɗe ƙungiyar nan tata bata huta ba. Ga aikin kungiya gana office ga karatun islamiyya ga shago. Dan rainon AA dai bazatace komai ba kusan Mommy da su Afrah ne keyi da Iya Tabawa. Tsakaninta da shi kawai ta shayar da shi. Kasancewar ma yana shan tea da koko hankali kwance bai cika damuwa ba. Shiyyasa ma bata fita da shi ko'ina. Ba kuma ya kuka dan shi ɗin mai iyayene da yawa. Itada kanta ma wani lokacin har tausayi yake bata da rashin samunta yanda ya kamata. Amma yaya zatayi.        Tunda sukai sallama AA da ke a bayan Suhaib na masa doki ya fara zillo. Saukesa yay suna masa dariya. Ya rarrafo da saurinsa zuwa gareta. Kamar yanda suke dariyar itama dariyar takeyi. Daukarsa tai ta jefa sama ta cafe tare da rungumesa tai masa kiss. Shima yay mata a kumatunta biyu. Lakace masa hanci tayi cike da farin ciki da jinjina wayonsa. A kullum kamar ana ƙara masa wayo ne. Baya magana dai sannan tafiya bata nuna ba, amma idan ka gansa bazakace watansa tara ba. AA akwai zafin nama da ɗankaren wayon tsiya. Shiyyasa ɓarna babu kama hannun yaro. Idan aka kaisa hira wajen Daddy har korosa yake saboda ɓuruntu. Hakama Mommy sunta faɗa kenan.      Cikin zubewa a kujera Lulu ke faɗin, “Wayyo ALLAH ku bani ruwa kafin na shiɗe Please”. Amrah na dariya ta miƙo mata ruwa da kofi, kofin ta ture ta ɓalle murfi goran ta kafa kai kawai. Neman ƙwacewa AA yake tana buge masa hannu, bata kulashi ba sai da ta kusan shanyewa ta bar masa ɗan kaɗan sannan ta bashi.            “Wai lallai aunty Lu.. kinji ƙishi fa”.      Cewar Mubeen dake ƙoƙarin ɗaukar AA da ke miƙa masa hannu. Dan shigowarsa kenan shima da ga makaranta. Tace, “Ka bari kawai broth wlhy yau munsha wahala ne. Ai bazan iya driving-driving ɗin nan ba a nema min driver please. Sai dai mai hankali dan ALLAH ban son mai surutu da ƙazanta”.          Dariya Amrah da Afrah da Mubeen suka sanya. Mubeen ke cewa baki son irin su Dallatu yake ko wa ma mai shegen ƙaryar nan ga yalalen haƙora”.      Itama dariyar tayi, dan ta tuna da wanda suke maganar, shine ta kora aka kawo Smart. Akwai shegen surutu da son fafa amma ba tsafta. Aiko yasha marukanta babu adadi. Haka kawai sai Smart ya zo mata a rai. Taɗan lumshe idanu da jan ajiyar zuciya, gaba ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke. Tsam ta miƙe tabar falon suna cigaba da hirarsu bama su farga ba. Dan Ummita suka shiga bama labarin direbobin Lulun da akasha kala-kala a gidan. Tana shiga ɗakin nata da ke tsaf-tsaf yana ƙamshi mai daɗin gaske dan yana nan a yanda kowa ya sanshi da tsafta, iya Tabawa bata wasa da gyaransa saboda Lulu sam bata son ƙazanta. Abayar jikinta ta saɓule, wando da rigar data saka a ciki suka bayyana. Suma zaresu tai ta shiga wanka. Tana fitowa ta gabatar da sallar magrib da aketa yi. Alkur'ani ta ɗauka tai karatu gwargwadon abinda ya sawwaƙa kamar yanda ta saba a yanzu, kafin ta ɗora da azkar na yamma da bata samun damar nutsuwar yi sai irin iyanzu ɗin. Koda Ummita ta shigo mata da takardun ta da Laptop bata katse abinda take ba, sai ga Iya Tabawa ma da tea da Lulun kesha duk dare AA goye a bayanta. Tea ɗin ta fara ajiyewa a inda Lulun ke zama yin ayyukanta sannan ta matsa gaban gado ta sauke AA ta kwantar a hankali. An masa wankansa an masa shirin barci sai ƙamshi yake yi kamar ba dare ba. Fita sukai gaba ɗayansu suka ja mata ƙofar, dan babu kuma mai sake shigo mata kenan, itama da wahala ta sake fita in ba Daddy ne bai shigo gidan da wuri ba taje su gaisa. Kamar dai yau da suka samu baya a gida bai dawo ba.       Bayan kammala addu'ointa tsam ta miƙe ta maida komai a inda yake tare da zare abayar sallarta ta maidata a inda take ajiyewa. Doguwar riga mara nauyi da bata kai mata har ƙasa ba ta saka mara hannu. Ta ɗan rage gudun acn ɗakin saboda AA mai saurin ɗaukar mura sannan ta nufi gadon nata. Zama tai a hankali gefen da yaron yake da ga can ɗan tsakkiya tana sauke ajiyar zuciya da ɗaukar wayoyinta. Ɗan dudduba massages tayi da miss calls da akai mata ɗazun bata samu amsawa ba. Ta kira wanda zata iya ta share sauran. Sakwanin ma amsa wanda suke da muhimmanci tayi sauran ta barsu. Tana ƙoƙarin ajiye wayar kira ya shigo. Number nan ce dai da ko ta ɗaga ba'a magana tayi masifar har ta gaji, har blocking tayi amma tarasa yanda ake cigaba da kiran nata. Har ta tsinke bata daga ba, aka kuma sake kira. Tasan idan bata ɗaga ɗin ba dai ba dainawa za'ai ba koda za'a jera mata kira hamsin ne, dan haka ma take ɗagawar ta samawa kanta lafiya tunda bata san wane aljani ne ba kuma. Kamar kullum shiru anƙi ace komai, sai dai tana iya jiyo saukar numfashi da fitarsa a hankali. Itama yau sai taƙi yin magana. Haka sukai shiru kusan na mintuna uku kamar ba kuɗi ake ci ba.        “Hummm koma waye dai ALLAH ya shiryesa”. Ta faɗa cikin jin haushi da yanke kiran tana jan ƙaramin tsaki. Wayar ta jefar gefe tare da kai hannu ta gyara ma AA kwanciya, sai ta samun kanta da zubama yaron ido kamar yau ne ta saba ganinsa. Ta ja tsahon mintuna biyar tana ma yaron kallon ƙurillah tare da cakuɗa abubuwa da yawa da ke cimata zuciya. Ganin zata zurfafa tunaninta yay yawa ta sumbaci goshin yaron da sauke ajiyar zuciya mai nauyi ta masa addu'a ta gyarashi. Miƙewa tai zuwa inda take zaman aikinta ta zauna, sai da ta haɗa shayi sannan ta kunna laptop tare da rage hasken ɗakin, bakajin komai sai motsin keyboard da na ac. Ta kwashe tsahon lokaci a wajen kafin ta tashi tana faman miƙar gajiya, toilet ta shiga tai uzirirrikanta ta fito tai shirin barci ta haye gado kusa da gudan jininta ta kwanta.....        Washe gari kamar yanda ta saba da wuri tai shirin fita. Dan ma tana ta fama da AA da ya maƙale mata yau shagwaɓa yake ji, sai da Ummita ta shigo ne ta ansar mata shi ta samu ta ƙarasa gyarawa tana faɗin, “Yaro zaka gane kuranka yayeka zanyi ai a cikin watannan”.            Cikin waro idanu waje Ummita ta ce, “Kai aunty wasa kike amma dan ALLAH?”.      “Oh wasa ko zakuga wasa”. “Kai aunty wata tara fa, baima cika cif-cif ba. Banda ma yanada kirinki da zafin nama ai bai kai a fita a barsa ba”.         “Uhm Ummita kanku fa akeji, wlhy jira kawai nake ya taka na yayesa. Tunda yana cin abincinsa ba wani ya damu da nonon bane sosai ai gara na hutar da kaina ko.”     “Mudai aunty kiyi haƙuri to ko shekara ɗaya mu cika dan ALLAH mun tuba”.              “Ummita kenan, wai baki tausayina ne ma dai ko. Da wanne zan ji?”.       “Aunty damu mana, ai mune farko kafin komai. Dan kulawar mu da ta Abbienmu itace farko”.      Shiru Lulu tai bata sake cewa komai ba. Dan a duk sanda Ummita zata ambaci Abbien AA ɗin takanji zuciyarta na mata nauyi, shiyyasa bata sakewa hirar tai nisa a kansa take basarwa. Ficewa tai a ɗakin tana faɗin, “Bari na duba Daddy zanyi breakfast a wajensa ki yi maza ki shirya kin san munada aiki yau”.         Cikin girmawa Ummitan ta amsa mata da to tare da Binta da kallo tausayi. Sosai ma'aurata ke matuƙar bata tausayi, bata taɓa ji ko labarin irin aurensun nan ba. Auren kusan shekara ɗaya da fin rabi kaɗan babu a biyu amma zaman wata ɗaya cikakken ba'a samu ba, dan ma UBANGIJI mai hikima da ya saƙa zare mai girma na azurtasu da ɗa. Tana ma kanta addu'a, amma gaskiya Lulu na ɗaya daga cikin manyan addu'ointa a kowacce rana. Fatanta ALLAH ya kawo iyakar komai ta koma wajen mijinta da ayanzu duniya ke faɗa da saurara a fanin ƙwallon ƙafa. Ita tasan duk da Lulun bata nunawa tanada damuwa sosai. Dan tasha kamata tana kallon AA kallo mai harshen damo kasancewar sa tamkar photo copy na mahaifinsa. Sannan shi kansa yaron soyayyar da take nuna masa mai kallo yasan ba tashi bace shi kaɗai harda ta Abbien nasa........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣6️⃣ ........A wajen Daddy ta karya kamar yanda ta faɗa. Sunata hirarsu cike da nishaɗi. A cikin hirar ne yake cemata yana son ya je ya ɗan huta kwana biyu da ga nan zaiga doctor ɗinsa da kuma wani business da zai yi a England. Batare da ta kawo komai a ranta ba dan harga ALLAH bata san a ina Smart yake ba yanzu, ta ce, Daddy badan ina akan gaɓar wani case ba ALLAH nima dana bika na ɗan huta kona 1week ne. Da ga nan ina son na shiga U.S ma duba wasu takarduna a gidan can”.        Da ƴar tsokana Daddy ya ce, “To ko na jiraki ne Sweetheart. Kin san fa na daɗe bamuyi tafiya tare ba ina jin kewar hakan”.       Dariya tayi da faɗin, “Daddy karka sa Naseer ya ɗauka na ƙwace masa fadarsa ta autanci fa.”    Shima darawar yay cike da nishaɗi yana faɗin, “Ai yace yanzu shi ba auta bane. AA ne Auta. Banda ƙarfin hali an taɓa ƙwace ɗan wani gida a bama wasu.”           Murmushi Lulu tai da cewa, “Nakune ai Daddy, wake da iko da shi sama da ku?”.       “A'a fa Mawaddat son kai da maida ɗan wani naka. Da haka ne ai da kema na haƙura na barma su Dada. Mahaifinsa na sane da abinsa kafin ya waiwayone kawai. Yanzu dai ki duba idan kinada dama zuwa hutun sai na jirakin, dan nima zan shiga U.S ɗin insha ALLAH. Nanny ɗinki ma ta kirani wai bata da lafiya sosai zata koma ƙasarsu Gambia tai jiyya. Amma nace ta ɗan jirani har naje sai ta wuce”      Sosai Lulu ta nuna tausayawa da mata addu'ar samun lafiya. Da ga haka suka cigaba da hira har lokacin fitarta yayi. Tare suka fito da Daddy ɗin har da Mommy data samesu itama. Ta samu Ummita na jiranta, dan haka bata ɓata lokaci ba ta ɗan tattaɓa AA da masa kiss tana jaddada ma su Amrah su ɗauki saƙon Ammah a ɗakinta idan zasu wuce kai AA ɗin yini can yau kasancewar juma'a ce duk sati can ake kaisa dama. Sun amsa mata da to ta shiga mota suka wuce....      ________★   Kamar koda yaushe Ammah tayi farin cikin ganin jikan nata. Dama gashi juma'ar ƙarshen wata ce yaran gidan duk zasu zo. Shima cike da ɗokin ganinta ya maƙalƙaleta dan ya saba da kakarsa kasancewar ana kaisa. Da yaga Asma'u ma haka ya dinga zallo dan ɗan lelenta ne. Su Amrah basu jimaba suka wuce duk da ba haka Asma'u taso ba. Sai dai zasu wuce school ne dole babu yanda zasuyi. Itama yau bazataje bane saboda tun jiya tana kwance babu lafiya. Maryam kuwa tana gidan aunty Bilkisu saboda makaranta tafi mata kusa da ga can yasa tafi zama a can yanzu sai weekend ake ganinta anan gida tunda an zama ƴan jami'a bisa tsayawar Smart, da. Yaran Abba mata basa shiga jami'a sai a gidajen mazansu. Itama ganin an kawo kuɗi yasa Smart cin ƙarfin Abban da ƙyar dai ya amince ta fara. Shi kuma Smart yayi hakane saboda yasan dangin su Ahmad ƴan boko ne na gani kasheni, baya son ƴar uwarsa ta shiga cikinsu ta koma baya. Yanzu ko koba komai taci ƙarfin kusan shekara biyu kafin bikin tunda gashi yanzu tana da shekara kusan ɗaya. Bikin kuma shekara ɗaya aka saka.     Koko Amma ta fara bama AA sai ya ƙi sha ya fara bultso mata shi. Cikin dungure masa kai da faɗin, “Ɗan nema yau kuma kokon ne bazaka sha ba. Kaima dai tsurfa irin ta Babangida yana yaro duk ka iyata.”        Dariya Asma'u da ke kwance take musu. Ta ce, “Kai Ammah yayan ne yay tsurfa?”.      Ammah ta ce, “Tab har ma ana magana. Ai Hydar al'amarin sa daban ne dana kowa. Kinga tashi haɗa masa tea ko zai sha”.          “To Ammah. Amma ƙilafa baya jin yinwa ne.”      “Eh to da wannan kuma. Sai dai kum....” dai-dai nan kira ya shigo wayar Ammah ɗin. Tashi Asma'u tai ta ɗakko cikin zumuɗi take faɗin, “Ammah Yaya Hydar ne”. Murmushi itama Ammah tayi, dan haka Asma'u ta ɗaga tana gaishesa cikin farin ciki da girmamawa. Da ga can ya amsa mata da kulawa tare da tambayarta jama'ar gidan tace kowa lafiya yake. Ya tambayeta miyasa bataje makaranta ba ta sanar masa tun jiya bata da lafiya shiyyasa Ammah tace yau kar taje sai monday.”        “Okay” ya faɗa a taƙaice cikin rashin son hayaniyar nan tashi. Har zata miƙama Ammah wayar ya sake faɗin, “Kinje asibiti ne?”.        Amsa ta bashi da cewar, “A'a Aunty Mawaddat ta turomin Doctor ya dubani da dare”.     Da mamaki ya ce, “Gidan tazo?”. “A'a Yaya ai bata iya zuwa har yanzu, ta kira Ammah ne suka gaisa shine taji Ammah namun faɗan shan magani. Tace mata ta barni bari doctor yazo ya dubani sai yay min allura idan ban son maganin ne”.          “Yayi”.       Ya faɗa a taƙaice. Da ga haka yay shiru. Ita kuma sai ta miƙama Ammah wayar. Ya gaida Ammah cike da girmamawa. Ta amsa masa da kulawa. Dariyar wasan da Asma'u kema AA ya jiyo. Ya ce, “Wake dariya haka?”.       Ammah ta ce, “Babana ne Asma'u kema wasa.     “Yau kuma anan ya kwana kenan?”. Da ƴar dariya Ammah tace, “Banda abinka Hydar ina mai shan no-no zai kwana wani waje bada uwarsa ba. Yanzu su ƴan biyu suka kawoshi dai. Sai kuma dare sai Mubarak ko Abdull su maida shi. Sai dai nasan yanda baida da rigima kwana nan ma zai iya yi batare da ya damu ba, badai a taɓa gwadawa bane. Da har haƙurinka ya biyo bai bar komai ba shikam”.             Ɗan murmushi kawai Smart yay da ga can da faɗin, “Hummm”.        Sanin halinsa na rashin amsa komai dalla-dalla yasa Ammah fahimtar abin cewar kenan. Dan haka ta ɗora da faɗin, “Hydar baka ganin ya kamata kayi magana su taho haka nan ko ALLAH zai sa a dace komai ya daidaita, duk da dai bata iya shigowa gidan nan har yanzu kuma tana son hakan. Ko tazo sai dai ta tsaya waje shima da ƙyar ake sha dan sai ta tafi da ciwon kai. Amma ƴar albarka kullum bata gajiya sai ta kirani safe da yamma taji lafiyata. Kayan shayi da su sabulu zuwa kayan buƙata irinsu-irinsu sai dai na bama wani. Ai duk wanda yay wannan shiga tsakani na kai da iyalinka bazan yafe masa ba a wannan karon” hawaye suka cika mata ido.           Cikin rauni da sanyi Smart yay murmushin ƙarfin hali da faɗin, “Ammah dan ALLAH ni bana son kina damuwa. Komai lokaci ne ai, ALLAH dai ya bamu ikon cinye jarabawa. Wlhy ni kuma ina jin nauyin su Daddy ban san taya zan taresu da maganar nan ba. Ina ga kawai mu cigaba da zubama sarautar ALLAH ido komai zai wuce. Yanzu ya batun ganin naki likitan ne? Kodai nan zaki taho. Dan ina son itama aunty Bilkisu tazo nan ɗin saboda matsalarta, akwai wata ƙwararriyar likita anan da nake fatan insha ALLAH ta ganta za'a dace”.          “Hydar kai dai na kula baka jin kisan kuɗi sam. Wannan ƙoƙarin naka yayi akan ƴar uwarka. Amma ni dai ka barni anan ai akwai likitoci ƙwararru in sha ALLAH zasu dubani. Dan ma ka damune kawai amma ai ƙafar ba wani tanayi sosai bane yanzu tunda ka aiko min maganin nan”.       “Ammah ai lokacin abu a yisa. Da banyiba ai da bani da shi. Yanzu kuma Alhmdllh. So nake ma muyi magana da Abba dan ina son gyara gidan nan tunda naga baya son barin anguwar”.           “Tab kaima kasan mai raba Abbanku da anguwar nan ai sai dai mutuwa. Gyaran dai shi yafi kam”.       Cike da gamsuwa ya ce, “In sha ALLAHU hakan za'ayi kawai”. Da ga haka suka cigaba da hirarsu tsawon lokaci kamar yanda yakanyi duk sanda ya kira. Har sai da aka kaima su Umma suma su gaisa. Kamar ko yaushe sai da Umman ta bugi cikinsa akan komawar matarsa. Shi dai yay murmushi kawai kamar yanda yakanyi a duk sanda tai masa tambayar saboda nuna kunya. Sai dai hakan na ƙona mata zuciya da jin ƙarin tsanarsa. Cikin rashin daɗin rai ta miƙama Asma'u wayar batare da ko sallama sunyi ba. Mama ma ankai mata sun gaisa da aunty Amarya. Lokacin da ta maida ma Ammah wayar take sanar mata “Yau ma Ummah sai da ta tambayi Yaya wai yaushe zai zo ya maida Aunty Mawaddat ne? Ko baturiya zai kawo musu wannan karon?”.       Murmushi kawai Ammah tai da girgiza kai tana mai mamakin halin irin na Ummah. Tana rakata ne kawai zuwa gaɓar da take buƙatar bata amsa. Shiyyasa a yanzu take cigaba da shanye komai, dan ta gama ji a ranta da hannun Ummah a al'amarin su Smart ɗin...... ________★   Tunda ya fito a prison da mahaifinsa ya sa aka kaisa jiyya ya kwanta kusan ta wata guda saboda wahalar da yaci a wajen. Da ga ƙarshe ya ɗauki amaryarsa suka wuce Mexico. Watanninsa biyu kenan sai yau ne ya dawo Nigeria. Ya murje abinsa tamkar komai bai faru ba. Sai ƙiba da ya ƙara abinsa mammokaɗewar da yay duk ta ɓace. Tafe yake cikin izzar nan tashi da ƙasaita yana faman hura hanci. Abokan cin mushen nasa ne su Hon. Nakowa sukaje tarbarsu. Sai Tajuddeen da shima baifi kwanaki uku da dawowa ƙasar ba. Shima dai ya murje abinsa kasancewar hankalinsa kwance yake akan zaman Lulu a gida. Gani yake auren ya mutu suna ɓoyewa ne. Acewarsa ta gama ɓoye-ɓoyen ya fito a ɗaura musu aure. Shiyyasa ya ajiye makaman yaƙinsa da mahaifinsa ya ɗorasa tsakaninsa da kakanninsa ya je suka dai-daita da Baba Garko. Dan ya bashi haƙuri sosai da tabbatar masa shi baya tare da mahaifin nasa, sannan bai san manufarsa akan Lulu ba. Baba Garko yaso korasa amaryarsa ta lallashesa da tausashi akan ya jawo Tajuddeen ɗin a jikinsa, hakan zai sa ya canja masa ra'ayi akan dagiyar soyayyar Lulu harma ya haƙura. Ya fahimci manufarta, dan hakan da zai yi ne kawai zai barranta halin jikan nasa da ubansa kar shima su rasashi.        A kallo ɗaya zaka ɗauka babu komai a tattare da Alh. Sulaiman ɗin sai farin ciki, nan ko zuciyar tsatstsage take da mugayen nufi musamman akan abubuwa da dama. Dan wannan karon kam ya dawo da shirinsa shiyyasa ya bada ƙafar ja baya. Acewarsa ja baya ga rago ba tsoro bane shirin faɗa ne.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣7️⃣ .......Cikin ɓacin rai abokin nasa ke kallonsa. Dan gaba ɗaya a watannin nan MM Atik ɗin ya sake birkicewa. Ɗan sauƙin da aka samu wani aiki da mahaifinsa ya haɗashi da shi ne zuwa Chaina shine dalilin ɓuyansa. Sai a watan jiya yake dawowa gida Nigeria. Abinda ya farayi shine neman Nadia. Sai dai ya taki rashin Sa'a wai tana kwance babu lafiya. Dan cikinta ya kumbura sosai tana fama da ciwon hanta da ƙoda sakamakon shaye-shaye. Ga ciki ta samu wanda taita faɗi tashin ganin ta zubar da shi amma ya gagara zuba, tayi ƙoƙarin ganin Alhaji Baita domin cikin tasan nasa ne, amma ta kasa samun kowacce irin dama. Daga ƙarshe mahaifinta ya korota da ga gidansa.       Yana gama jin abinda ke faruwa da ita a wajen yarinyar shagonta yaja tsaki da faɗin, “Mtsoww bata da wani amfani a gareni yanzu”. Da ga haka ya kaɗa kansa yay tafiyarsa. A sabon bincikensa ya gano Lulu na gida amma ta haihu, yaji baƙin ciki da jin ciwon jin kalmar haihuwar nan har ya nema susuta kansa. Dan giya ya dinga ɗorawa da cocaine yana sambatu. Da ƙyar su Asim abokinsa suka samu ya dawo dai-dai. Sai dai ya rantse yana akan bakansa sai ya mallaki Lulu koda ta ƙarfi ne dan sha'awarta zata iya kashesa. Saboda a ganin da yay mata ranar bikin ƙaddamar da ƙungiyarta sai yaji kamar ƙarya ake masa ta haihun. Dan tana nan fes da ita babu alamar wani koma baya ko tawayar haihuwa tattare da itan. Sai ma ƙyau na musamman da yaga ta ƙara masa da cikar kamala duk da yanzu dai bata shigar wando da riga ko matsatstsun kaya ta fita haka zuwai sai da abaya a sama. Wani lokacin ma da facemask, sai kuma wai yaron nan mai tashe da shi kansa yake matuƙar so wai shine drivern nan nata data aura. Wannan abu shima ya jijjigashi, ya jima yana mamaki a ransa. Amma dan ƙarfin hali har yanzu a hakan baya jin zai janye dan kullum kamar ana ƙara rura masa wutar buƙatar Lulu ne. Ko neman mata ya rage yi yanzu dan kowacce ta bar burgesa, sai ma idan ya ɗanga kina yanayi da Lulun ko idan yasha cocaine ɗinsa na faɗa masa banza wofi ya jajubeki, yana dawowa hayyacinsa kuma a ƙare da bala'i maybe ma ki samu tsabar duka...        Ko sau ɗaya bai kula Asim ɗin dake fece shi game da nacinsa akan Lulun ba. Sai ma miƙewa da yay yayi shigewarsa toilet ya bar Asim ɗin na cigaba da masa hayaniya....       __________★     Sosai abubuwa sukama Lulun yawan da har tace bazata bi Daddy ba ta fasa. Lallaɓata ya dinga yi har taso fara tsarguwa sannan ya taƙaita. Daga ƙarshe dai ta ce zataje ɗin kodan takardun nan da take son ɗakkowar. Taje gidan Uncle Yousuf suke maganar da aunty Saliha. Murmushi kawai aunty Saliha tayi dan tasan da tafiyar dama a bakin Uncle Yousuf da baya ƙasar. Wasu abubuwa ta haɗa ma Lulu wai na gyaran jiki. Bata kawo komai ba ta amsa dan yanzu ta dage da irin abubuwan gargajiyar nan ganin sun amshi fatarta da ƙyau. Ga kamshin da yanzu ya kama jijinta kuma duk dai irin haɗin su khumra data raina a da ne. Koda ta dawo gida batayi wasa da su ba, yayinda Mommy ma a kaikaice take ta bata nata sirrikan. Hatta da iya Tabawa ba'a barta a baya ba. Da ga ita sai AA zata wuce. Taso suje da Ummita amma Daddy yace ta bari sai da ga baya, idan ma harda iya Tabawa take so duk zai haɗo mata. Dariya tayi da faɗin, “Haba Daddy sai kace wadda zataje zama. Su bari kawai mu dawo danni ko Aliyu da zaku bari a gida zan barsa”.         “A'a bazai yiwu ba kije da shi shima ya huta. Tafiya babu abokina ai bazai mun daɗi ba”. Yay maganar yana lakace hancin AA dake tsale-tsalle a jikinsa. Murmushi kawai Lulu tayi daga haka suka cigaba da shirinsu musamman ma shi AA da komai sai an masa.        *_UK LONDON_*       Tafe yake a nutse kan ƙafafuwan sa. Da ka gansa kaga tsayayyen mutum mai cike da jatumta da lafiyar gaɓai. A komai nashi babu hayaniya babu ɗagawa duk da wasu kan fassara shiru-shirunsa da girman kai tun bai zama wani ba. A duk sanda yake da uzuri na fita ya kanfi buƙatar takawa da ƙafarsa in har wajen da yake son zuwan babu nisa. Kamar dai yau da ya fita zuwa shopping na ƴan abubuwan buƙatarsa. Ya riga da ya kai wani matsayi a yanzu da fuskarsa ta zama ba ɓoyayya ba musamman a cikin birnin London. Hakan yasa a duk sanda yake da buƙatar irin fitar nan yakan sakaya fuskarsa da abinda zai ɓadda masa kamanni. Kamar dai yau, ya saka facemask da glasses, ya kuma ɗaura p-cap duk dai cikin son kaucema idanun jama'a dan yaje ya dawo batare da kowa ya damesa ba. Alhmdllh har ko yaje ya dawo babu wanda ya ganesan, garama a cikin mall ɗin da yaje biyan kuɗi kasancewar dokace sai anga fuskarka da yaja nurse mask ɗin ƙasa mai cire kuɗin ɗin ta wani zaro ido bakinta a washe zata ambaci sunansa yay mata murmushi da mata alama zip abaki. Dole tai shiru amma murmushi da farin ciki yaƙi barin fuskarta, har da ɗan leƙensa da zai wuce, sai da ya fice gaba ɗaya take faɗama sauran ƴan uwanta da ke wajen harda masu cewa basu yarda ba. Wasu kuma suka biyo bayansa. Ya riga ya zargi za'a iya yin hakan dama sai yana fitowa ya canja hanya. Wannan yasa suka sake tabbatar mata basu yarda ba. Ba komai ya sasu jin basu yardan ba sai dan mall ɗin nasu ƙarami ne, a ganinsu Smart Mawashi yafi ƙarfin zuwa nan yin shopping. Irinsu ma sunfi son yin online shopping a manyan mall ai.          Ɗayan hannunsa da babu kaya ya fiddo da ga cikin aljihu wandonsa ya saka security ɗin ƙofar. Sai da computer ta ambaci sunansa sannan ƙofar ta buɗe kanta a hankali. Numfashi ya ɗan furzar yana tura kansa cikin gidan bakinsa da sallama duk da yasan shi kaɗansa ne a gidan nasa. Tuni ya samu canjin wajen zama. A inda yake nan gida ne shi kaɗai a ciki madaidaici mai ƙyau da tsarin birgewa, dan yana ɗauke da abubuwan more rayuwa da ɗan adam kan buƙata koda da sha'awa ne. Ya cire takalmansa a inda yake ajiyewa yasa slippers na zaman gida, tare da hanging rigar sanyinsa sannan ya ƙarasa shiga. Ya ɗan bi falon da kallo ganin fitila a kunne ga wani baƙon ƙamshi, sai dai bai kawo komai a ransa ba ya ɗan ɗage kafaɗu da taɓe bakinsa tunda yasan dai bayan Uncle Yousuf da yasan security ɗin gidan babu wanda zai iya shigo masa, sai ko Ahmad, maybe ya manta ne da zai fita bai kashe fitilan ba. Kayan shopping ɗin nasa ya kai duk inda ya dace sannan ya nufi bedroom ɗinsa hannunsa riƙe da jacket ɗinsa da ya zare ya ɗan sagalota a kafaɗa. Tafiya yake a hankali kamar cikin kasala da gajiya yana latsa waya da alama akwai abinda yake sonyi ko kira. Cikin rashin maida hankali ya tura ƙofar ɗakin da ƙafa ya shiga tare da sake turata da ƙafa ya rufe. Dai-dai nan take fitowa daga Bathroom sanye cikin rigar wanka pink da tazo da abinta. Sosai gabanta ya faɗi da ganin mutum ya shigo mata kai tsaye a inda batai tunanin ganin wani ba, duk da tun shigarta bathroom ɗin ta shiga halin tsarguwa amma ta dake. A bedroom komai need yake babu tarkace babu abinda aka bari a waje da zaisa ka zargin akwai mai amfani da ɗakin sai a toilet ɗin ne, sai dai wani tunani da yazo mata ya sata gamsuwa tai wankanta hankali a kwance.         “Who are you Man?!”.      Ta faɗa cikin faɗa da son dake razanar da tayi. Shi kansa gabansa ne ya faɗi, ya ɗago da sauri dan yasan bai bar kowa a gidansa ba shi dai, amma sai ga muryar mace a tsakkiyar kansa a cikin ɗakin barcinsa bama falo ba. A karo na biyu ƙirjinsa yay wata irin jijjiga ganin wadda bai zato ko tsammani ba, wayarsa da ke neman suɓuce masa a hannu yay saurin damƙewa, sai kuma ya ɗan ja baya kaɗan gannin tayo kansa da masifa hannunta ɗauke da wani deco.. da ke ajiye a bedside drawer ɗinsa. Duk da yana a cikin yanayin ruɗani sai da ta so bashi dariya amma ya dake, yo abinda ta ɗakko ɗin ko buga masa tayi mizai ji duk da glass ne. Tana gab da zuwa ina yake ya ce, “Please Relax Ladyy”.      Cak taja ta tsaya zuciyarta na harbawa da masifar ƙarfi dan ko'a magagin barci wannan deep voice ɗin bazata layance mata ba. Cikin rawar lips da ta murya ta furta, “Aliyu!”.          Idanu kawai ya zuba mata ta cikin glasses ɗinsa na kusan sakanni talatin, kafin a hankali ya kai hannu yay ƙasa da mask ɗin fuskarsa tare da zare glasses ɗin. Idanun ya lumshe a hankali tare da sake buɗewa yana mai kamo gefen lips ɗinsa da haƙori. Kallon nasa da yanda gaba ɗaya ya canja fiye da ganin datai masa a lokacin haihuwar AA a Canada ya sata jin kamar jiri na neman kwasarta zuwa ƙasa ne ma. Shima yana jin fiye da abinda take ji ɗin, sai dai ƴan mazan a tsaye suke banda a ƙwayar idanunsa bata iya hango komai da zata iya bama fassara. Son tabbatar da ba aljana bace ko mafarkin da ya saba harta fara masa gizo ya sashi kauda idanunsa a kanta ya fara waige-waige. A saman gadonsa ya hango abinda yake neman a kwance yana barcinsa da alama ya gaji dan yayi wani baje-baje da ƴan kafafu da hannuwa yana zuƙar iskar sabuwar ƙasar Babansa da fesarwa cikin kwanciyar hankali. Karo na farko ya saki murmushi ganin wanda ya bari a jinjiri ya fara zama mutum, dan girman jikin AA yafi watanninsa yawa kasancewar ya ɗakko har tsawo irin na gida. Duk wanda ya kallesa yasan su ɗin jini ɗaya ne dan kamaninsa sun sake bayyana kansu matuƙa a tattare da yaron. Lulu da ke jin wani yamm-yamm kamar zata zube ƙasa a hankali ta furzar da iska mai nauyi tare da jan jikinta baya a hankali ta koma bakin gado ta zauna cikin dafe kai. Wato ta fahimci Daddy da Uncle Yousuf wayo sukai mata kenan kawai. Shiyyasa taita fama da shi su fara zuwa U.S amma ya dage su fara zuwa UK yana da abinda zaiyi mai muhimmanci. Takun sawayensa ya sata kallonsa ta gefen ido, ganin kamar inda take yayo ya sata ɗagowa sosai tana masa kallo mai kama da harara. Sai kawai ya basar ya wuceta zuwa inda yaronsa yake.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣8️⃣ ........Tattaɓa shi ya shigayi idanunsa na cika da kwalla, sai kuma ya rankwafa da ƙyau daga zaunen da ya kai ya manna masa kiss a goshinsa da kumatu duk biyu. Kamar AA yasan mi ake ya wani juya abinsa ya kwanto a hannunsa. Murmushi yay mai kama da ƴar dariya, sai shima kawai ya kai kishin giɗe ya rungumesa a jikinsa sosai yana sakin ajiyar zuciya masu nauyi da shafa lallausar sumar kan yaron da Lulu ta hana a aske, sai gyaran fuska ake masa. Yaja kusan mintuna biyu a haka kafin ya ɗago idanunsa ya dubi Lulu da ke satar kallonsu. Kanta tai saurin maidawa gefe cikin taɓe fuska. A karo na farko yay magana cikin ɗan sakin murmushi. “Irin wannan bazata haka Madam?”.        Mikewa tai tamkar bata jisa ba zuwa inda akwatin kayansu yake, dan ɗaya ta ɗakko jal ita da AA, kayansa ma sunfi yawa dan nata basu wuci kala uku ba sai kayan barci. Sai da ta zuge zip ɗin tana ƙoƙarin ɗaukar kaya sannan ta bashi amsa da “Sai yanzu kasan da ni?”. Bata jira amsarsa ba ta wuce closed ɗinsa hannunta riƙe da kayan data ɗauka taja labulen da aka sa a wajen wai dan karya kalleta. Da ƙyar ya iya danne dariyarsa yana mai lumshe idanu, ya dai fahimci kishi ake da AA ɗinsa kenan. Mintuna kaɗan ta fito sanye da wando da riga marasa nauyi, sai dai yanda suka bi jikinta da fidda mata surarta fes ya saka zuciyar ƴan maza motsawa. Ga Lulu hakan normal ne, ita batayine dan wani birge miji ba, tun fil azal wannan shine dressing nata. Batare data kallesa ba ta wuce gaban mirror ɗinsa dake cike da turarruka da mayukan gyaran gashi sai abinda ba'a rasa ba. Gashinta taƙe ƙoƙarin tifkewa. Kwanciya ya gyarama AA tare da miƙewa, dai-dai tana tattare gashin cikin hannunta bayan ta zare ribbon ɗin data ɗaurosa da shi sukai ido huɗu da shi a bayanta. Yay wani tsaiwar ƙasaita irin na isassun maza yana kallonta da mayatattun idanun nan nasa. Sosai ta ƙara jin ƙirjinta ya motsa, tai azamar janye idanunta tamkar bata ganshi ba. Idanun ya rufe ya buɗe a lokaci guda yana ɗan ƙara matsawa jikinta daf ya mata runfa, sai kuma ya ƙarasa rungumeta a hankali tare da ɗaura kansa a kafaɗarta. A tare suke ja numfashi da sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Yanda yake wani bin wuyanta da shinshina idanunsa a lumshe ya sata jin tana neman zubewa a ƙasa, saurin riƙo hannayensa duk biyu da ke zagaye da ita a saman cikinta tai, hakan ya sakashi sake ƙanƙameta tsam-tsam kamar za'a ƙwace masa ita ya wani busa mata numfashi a cikin kunne....      Harga ALLAH bazata iya ɗaukar wannan salon nasa ba, dan haka tai ƙoƙarin jan jikinta da saurin faɗin, “Wai nikam minene haka?” cikin rawar murya data lips. A cikin kunnenta ya raɗa mata “Saƙon barka da zuwa mana. Haka ya kamata ki tarbi mijinki _My Final Choice_”.     Kanta ta matsar gefe tana taune lip ɗinta na ƙasa, cike da basarwar nan tata cikin son janye jikinta ta ce, “Kama nemo Final Choice ɗin naka bana son iyayi”.          Sake ruƙota yay sosai yana murmushi. Idanunsa ƙyar a kanta ta cikin mirror ɗin ya ce, “Kowa yasan na nemo abita ai tuni. Dan duniya duk ta san Mawaddatan'warahmah ce Heart controller ɗin Aliyu Hydar Mika'il Mawashi”.     “Kai dai ka sani”.   Ta faɗa tana janye jikinta a nashi. Bai hanata ba ya saketa tare da harɗe hannayensa a ƙirji. Kallonsa tayi ta ɗauke kai da rusinar da idanunta. A hankali ta ce, “Malam matsamin na wuce”. Dan ya tsare mata ko ina. Bai matsa ɗin ba, bai kuma daina kallonta sama da ƙasa ba. Kallo irin mai haka mutum sukuni ɗin nan da ji iska ma na maka wahalar shaƙa. Ƙoƙarin raɓasa tayi ya tare, ta sake komawa ɗayan ɓangaren, nan ma ya tare, ta koma tsakkiya nan ma ya tare. Sai kawai ta zabga masa harara tana tunzura baki. Hannayensa ya warware da ƴar murmushi har sannan a fuskarsa ya ɗan matsota, baya ta matsa ta manne da mirrorn. Shima sai ya dafe hannayensa a mirror ɗin ta gefe da gefenta ta koma tsakkiyarsa, ya ranƙwafo sosai yana busa mata numfashinsa a fuska. Ga son su haɗa idanu da yake faman yi. Cikin daburcewa ta furta “Aliyu!”.        “Uhmyim Mawaddat!”.     Ya amsa mata kafin ma ta gama rufe bakinta, sai taji ma ta sake daburcewa dan yanda yay kiran sunan nata da amsawa acan ƙasan maƙoshi da busa mata numfashin yasa ƙafafunta ma suka fara rawar son kasa ɗaukarta. Ɗago idanunta da suka tara ƙwallar da ita kanta bata san dalili ba tayi, hakan ya bashi damar ɗaura lips ɗinsa akan nata kamar dama abinda yay target kenan. Kafin tai wani yunƙuri ya tallafi kanta da ƙyau da hannun damarsa, ɗaya hannun kuma ya saukesa akan bayanta. Sam bata da wani sauran ƙarfin yin wani yunƙuri, dole ta haƙura dan tasan wani buyaginta bazai sa ya fasa ba in dai shi ne, sannan ita kanta kawai ƙarfin hali ne tana buƙatar mijinta. Jin tsaiwar na neman gagararsu yay ƙoƙarin tattarota zai ɗaga. Da sauri ta tattaro nata ɗan hankalin waje guda itama ta kai masa ɗan duka a gefen cikinsa....         “Ouch!”.     Ya faɗa yana sakinta yana dafe wajen. Sai kuma hankalinta ya tashi ganin yanda ya duƙe, cikin rikicewa ta ruƙo hannunsa dake riƙe da inda ta bugesan duk da dai ita tasan kaɗan ta masa. Muryarta har rawa take wajen faɗin, “Please kayi haƙuri ALLAH ban san zai maka zafi ba, wayyo ni”.          Sake langaɓewa Smart yay kamar gaske, ta kamashi ta jinginar da mirror ɗin tare da ɗan daga rigarsa tasa hannunta a wajen tana murza masa a hankali. Sake langaɓe murya yay yana faɗin, “Wayyo zafi Ammah kizo ta targaɗa miki ni”. Harga ALLAH Lulu ta ɗauka da gaske yake, dan haka ta sake ruɗewa har idanunta na tara ƙwalla, duk yanda yaso riƙe dariyarsa hakan na neman gagara, dole ya saketa dai-dai tana kwantar masa da kai a kafaɗarta.       Galala tai tana kallonsa ga hawayen da suka cika mata ido na neman fara zubowa. Cikin son danne dariyar da ke ƙara tunƙuro masa ya ce, “Dama haka kika damu da Aliyu? Madam!”.        Hararesa ta ballara masa da raɓawa ta gefensa ta wuce tana jan ƙafa da ƙyar dan ji take tamkar zata zube ƙasa ma. Shima sai yaja nasa jikin yana murmushi zuwa ƴar ƙyaƙyƙyawar kujerar dake gefe da ɗan table mara tudu dai-dai ita da zaka iya miƙe ƙafa a kansa ya zauna yana sauke numfashi da ƙaramar dariya. Sai da ya bada kusan mintuna biyu hankalinsa ya dawo jikinsa sannan ya tashi zaune da ga kwantar da bayansa da yay ya buɗe idanunsa a kanta. Tama kwance kusa da AA ne idanunta a lumshe ta wani dunƙule jikinta waje guda kamar wata baby. Ƙaramin murmushi ya saki da miƙewa ya fara zame kayan jikinsa da faɗin, “Ya kamata ki fara cin abinci kafin ki kwanta barcin ko”.      Shiru kamar bazata amsa masa ba, sai can a takaice ta ce, “Ba buƙata”.    Bai sake cemata komai ba ya nufi bathroom. Da kallo ta bisa, sai kuma rashin sake cewarsa koman ya bata haushi ta wani tura baki da hararar bayansa tana murguɗawa ta maida idanunta ta rufe. Ya ɗan jima kafin ya fito ɗaure da towel yana goge jiki da ƙarami. Kai tsaye wayarsa da ke ring ya nufa yana ɗan yamutsa fuska da kallon agogo. Bai niyyar ɗauka ba, sai dai ganin Ahmad ne ya sashi ɗagawar tare da ɗaukar bluetooth ya manna a kunnensa ya cigaba da abinda ke gabansa da alama Ahmad ɗin yake saurare.        “Ka kira dai kayi gulma ɗan sa ido”.     Dariya Ahmad ɗin ya kwashe da shi da ga can. Ya ce, “Ai kai dama ba'a maka abin arziƙi. Ni yarona na kira naji yaya yazo bai jigataba dai ko?”.             “Ga shi nan na samesa yana kwasar barci dan sun shigo gidan na fita. Yaya kun gama da mutanen?”.       “Har yanzu dai ana cuɗawa, naga sun ɗauki burin duniya sun ɗaurama wajen. Amma dai za'a dai-daita in sha ALLAH dan naga da Yaya yace zamu haƙura kuma kamar sun damu.”    “Oh kuma dai?”. “Ai kasan dama irin wannan matsalar ba daga masu kayan bane masu sayarwar ne”.            A hankali ya ɗan furzar da iska da faɗin, “To duk yanda kukai dai?. Ya batun wancan aiki? Yaushe ne kuma shigowar taka?”       “Ai maybe ma na fasa, dan business ɗin bai faɗa ba har yanzu, kasan abinda ma lura da shi komai suna fara yinsa ne a tsare kafin su sakeshi a kasuwa, amma dai shi guy ɗin nan ya tabbatar min zai haɗani da ogan nasu saboda nace masa ni dila ne, sannan pharmacy ɗin nan ya kamata aikinmu ya fara ta kansu dan na sake zuwa da takardar nan still sun saida min jiya. Kaga tabbacin maganarka kenan ta fito”        “Hummm aina faɗa maka dama. Sai dai inaga kafin hakan ya kamata musan mai pharmacy ɗin. Sai Companyn da yafi kawo musu kaya. Dan ina son mu fara da mutuminka ne”      “Uhm wannan ma tunani ne mai ƙyau, sai dai kuma kamar abin zai mana wahala nake ga. Kasan fa kai ka fini dabaru ta irin waɗan nan fannin”.           Murmushi Smart yayi yana ɗan lumshe ido. Cikin ɗan furzar da iska yace, “Kaima zaka iya Ahmad. Ka nutsu na maka bayani, yaro zamu samar da zai nema aiki a wajen, ta silar yaron ma zamu samu abinda bamu hasaso ba ma. Plan a kenan, idan wannan zai ja mana lokaci plan b muja yaro ɗaya dake pharmacy ɗin a jiki, ta hanyar masa alkairi kasan dai yanda mutanenmu suka ɓaci da wannan karɓar na goran, a cikin biyun nan zamu dace da ɗaya”.           “Yess boss na fahimce ka, kuma tabbas wannan dabaran yayi, shiyyasa nake sonka”.      “Ɗan iska waye boss ɗin naka?”.   Dariya Ahmad ya sanya da faɗin, “Kai mana. Zanyi ƙoƙarin nan daga nan zuwa next week, Dan Cameroon ma nake son zuwa kawo shanun nan dai. Ya kamata ka shigo ayi harkar nan da kai ALLAH, dan na hango za'a samu alkairi a ciki.”      “ALLAH mutumina! Kaifa nasan baka wasa dama da harkar ƴan canji. Yanzu yaya za'ayi?”.             Cikin dariya ya ce, “Masheranci, kaima naga ai bawasan kake da su ba. Muyi magana kawai idan ka samu time, yanzu karna shiga lokacin Madam tana amaryarta. A huta lafiya tsohon ango”.        Kafin Smart yace wani abu ya yanke kiran. Ya ɗan lumshe ido da girgiza kansa yana furzar da iska. Yana ƙoƙarin cire bluetooth ɗin idonsa ya sauka akan Lulu ta mirror da ke kallonsa.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣9️⃣ .......Sai dai yana waigawa ta rufe idanun ita a dole barci take. Nasa idanun ya rufe da sakin guntun murmushi ya ƙarasa shiryawa ya miƙe. Wando yasa 3quater da ƴar riga armless yasa turare. Baice da ita komai ba ya fita domin duba mima zai bata taci ne duk da yasan halinta bawai ta damu da abinci bane. Ganin babu wani abinda zata iya so sai kawai yay mata order na gasashen kifi da abinda yasan zata iya so. Cikin abinda baifi mintuna ashirin da biyar ba aka danna bell ɗin gidan. Tashi yay zuwa ƙofar dan yasan abinda yay order ne aka kawo. Shi ɗinne kuwa. Mai kawo saƙo ɗin na ganin shine ya wani washe baki, cike da zumuɗi da farin ciki ya ce, “Smart Mawashi”.     Murmushi Smart yay masa. Shi kuma ya zaro wayarsa yace Please ya bashi dama suyi hoto ɗaya. Kai ya jinjina masa alamar babu damuwa. Ya gyara sukayi sai farin ciki yake yi. Shi kuma ya amsa kayan ya koma ciki. A falon ya ajiyesu ya nufi bedroom ɗin.....        *_NIGERIA_*    Kamar yanda ta saba a ƙarshen kowane wata take sake ƙulla silin zare ɗaya a jikin battar da malamin ya bata game da asirin da taima Smart da Lulu. Yau ma cikin nishaɗinta ta jawo battar hannunta riƙe da farin zaren kirtani tana ɗan raira waƙarta ta barmani coge alamar dai tana a cikin nishaɗi. Dan bayan Aunty Amarya da Ammah ta sanar mawa babu wanda yasan yau Lulu ta koma wajen mijinta a gidan.. Wani irin kwance-kwance ƙirjinta yay ya yanka lokacin da take jawo battar idanunta ƙyar akan zararrikan data ɗaura zube ƙasa a warware. Battar ta tukunyar ƙasa ƴar ƙarama ta wani tsage daga sama har ƙasa. Tana ɗagata ta rabe biyu tsokokin nama biyu da suka wani tsotse a waje guda tsire da allurai suka zube a ƙasa. Ƙara ta daddage ta fasa na tsananin fita hayyaci da tashin hankali batare data farga da ɓaranɓaramar da take neman yi ba. Su Huwaila dake falo suna kallone farkon shiga a ɗakin nata a gigice. Ganinta kwance wanwar a ƙasa babu numfashi ga wata ƴar tukunya-tukunyar tsafi zube a ƙasa harda allurai a jikin tsokar nama ya sasu suma fasa ƙararar data ankarar da su Ammah. Kusan a tare suka afko ɗakin tare da gayyar yaran gidan. Babu wanda idonsa bai gane masa wannan tarkacen tukunya ba idan ya shigo, har Abba da ya shigo a ƙarshe dalilin kiran da Salis yaje yay masa akan tarkacen ya fara sauke ido kafin Ummah dake kwance wanwar ana sheƙa mata ruwa amma babu alamar numfashi tattare da ita.       Wani irin harbawa ƙirjinsa yayi tare da jin kansa ya sara. Yana sake maida idonsa akan Ummah ya ga ta koma masa wata irin mummunar hallita. Da sauri ya kauda kansa yana mai ambaton sunan ALLAH. Yanda yay baya zai faɗi sai da Ammah ta tarosa tana faɗin, “Ya Salam Abbansu yi ahankali”.       Hannun Ammahn ya riƙe yana jujjuya mata kai, muryarsa na rawa ya ce, “Hafsat fiddani a ɗakin nan kaina zai fashe”.          Furucin Abba yasa gaba ɗaya hankalin sauran yaran da su Aunty Amarya dawowa kansa. Sai kuma hankalin kowa ya sake tashi ganin halin da Abba ke a ciki. Amma mi abin mamaki yana fitowa ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya da sakin kan. Kallonsa Ammah tai da faɗin, “Yaya dai Abbansu?”.      Kamar bashi ya gama cewa kansa kamar zai fashe ba ya ce, “Wlhy Hafsat kinji kuma ya saki kamar ba'ayi komai ba.” Sosai abin ya ɗaure kanta. Bata gama fita a mamaki ba kuma sai ga yaran na fitowa da ɗaɗɗaya hannayensu dafe da kansu. Wasu ma a guje suke faɗin, “Dodo! Dodo!!”. Cikin ƙanƙanin lokaci gida ya gama rikicewa. Kowa ya fito a ɗakin Ummah, da kuma sun fito sai su jisu sakawai kamar an zare musu komai. Umma da hayaniyarsu ta sakata farfaɗowa cikin tashin hankali tabisu da kallo ganin yanda suke fita a guje. Ganin babu kowa sai taga damace ta sameta ta tattare kayan nan. Da sauri ta tattarasu jikinta na mazari ta ɗaure a ɗan kwali ta tura ƙarƙashin gadonta. Sannan ta fito cikin ƙarfin hali. Tana sakko ƙafarta waje yaran suka shiga yanka ihu suna kwasa da gudu zuwa ɗakunan iyayensu da faɗin, “Wayyo Umma ta zama dodo! Ummah ta zama dodo!”. Ba yaran kawai ba sai ga su Aunty Amarya suma duk sun rufta ɗakunansu. Abba ma har tuntuɓe yake na barin wajen sai Ammah ce ke kallonta da ambaton addu'oi a bakinta. Dan itama kam yanzu a wata irin mummunar siffa mara ƙyan gani tane kallon Ummahn.  A nutse ta nufi nata ɗakin itama aka bar Umma ita ɗaya a tsakar gida cikin tashin hankali da mamaki. Sai kallon jikinta take taga minene sukema gudu amma bataga komai ba. A take jikin nata ya kama rawa. Ɗakinta ta koma ta jajibi waya tai kiran Hajiya Naqiba....            *_★UK★_*      Cikin mamaki Smart ke kallon Lulu da ta buɗe gasashen kifin ta maida ta rufe da sauri fuskarta a ɗan yamutse. Dan shi dai a sanin da yay mata tana son kifi sosai. Shi kam baya so, dan ko a yanzu haka dauriyar shaƙar ƙamshinsa kawai yake yi. Da farko yayi tunanin halin nata ne ya motsa, sai ya so ɗauke kansa. Amma ganin yanda ta tura baki da faɗin, “Nifa bana cin kifi yanzu” ya sakashi zuba mata idanunsan nan.           Cike da shagwaɓa ta ce, “Ni ka daina kallona da wannan idanun”. Ƙaramin murmushi yayi da janye idanun nasa, da kulawa ya furta, “Yaushe kika daina cin kifi kuma Madam?”.      Harararsa tai saboda Madam ɗin da ya kirata da shi, sai ya riƙe kunnuwansa alamar sorry. Mikewa tai tana ƙara tura bakin. Hannunta ya riƙo da sauri dan yasan kaɗan daga aikinta tace zata koma bedroom ɗin da da ƙyar ya samu ta fito. Saman cinyarsa ya zaunar da ita, cikin lallashi kamar wata ƴar yarinya ya ce, “Faɗa min yaushe kika daina cin kifi?”.           A ɗan tunzure ta ce, “Da cikin ɗanka”.      “Woow really?!”.    Kanta kawai ta jinjina masa da yunƙurin tashi ya hanata damar hakan yana dariya ƙasa-ƙasa da faɗin, “Oh oh like father like son. Babie luv anya akwai wanda ya kaini sa'ar nasara a ƴakin ƙasa da ƙasa kuwa?”.           “Kamar ya?”.       Ta faɗa tana kallonsa a karo na farko. Gira ya ɗage mata tare da kwantar da kasa a kirjinta ya ce, “Aliyu ɗan Aliyu a suna. Aliyu ɗan Aliyu a kamanni. Aliyu ɗan Aliyu a hallaya. Ya kamata ki bani Award na gwarzon shekara ALLAH kuwa.”         Ƙoƙarin ture masa kai take ya riƙe hannun, cikin mamaki ta ce, “Wai dan ALLAH yaushe ka lalace haka Aliyu? Ko abinda zama cikin turawan ya koya maka kenan kai?”.      Idanunta da suka canja launi ya ɗago yana mata wani irin narkakken kallon da ya sanya jininta da tsigar jikinta yamutsawa a lokaci guda. Cikin motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Kece kika lalatani fa Mawaddatan'warahmah.”         Da sauri ta waro manyan idanunta a cikin narkakkun nashi. “Ta yaya?”.      Bakinsa ya kai dai-dai kunnenta ya raɗa mata maganar data sakata jin inama kasa ta tsage ta shige kawai. Dan a take ta wani daburce ta shiga kai masa ƙananun duka a ƙirji. Hannayen ya shiga ƙoƙarin riƙewa yana dariya. Har sai da ta kai shi da kaiwa kwance a kujerar, bata barshi ba ta bisa tana a saman jikinsa ta cigaba da mintsininsa shi kuma yana tarewa da faɗin, “Wayyo fatana da zafi fa ban san mugunta baby luv”. Yanda taga yana ɓata fuska alamar zafin dai yake ji da gaske duk da bada wani ƙarfi take masa ba ya sata fara dariyar itama. Abu mai wahala ga Lulu kenan, kaga tana dariya haka tab ɗin, ai ko murmushi sai a inda taso ga kuma wanda taso. Gaba ɗaya ma sai ya shagala ma shi yana kallonta tamkar ya samu television.          Dariyar ta daina yi ganin yanda ya zuba mata mayatattun idanun nasa da gaba ɗaya suka canja launi da ƙanƙancewa, sai dai murmushi bai bar fuskarta ba, ta ɗan lakace masa hanci da ɗage gira ta ce, “Kallon fa?!”     Idanun ya lumshe a hankali da sake buɗesu a kanta, “Dariya na miki matukar ƙyau my heartbeat”. Ya faɗa cikin wata irin murya mai laushi da sanyi. Samun kanta tai da lumshe nata idanun itama tana ɗan kauda fuskarta gefe da ƙoƙarin sauka a jikin nasa. Hannunta ya riƙo ya dawo da ita ta kwanto jikinsa fiye da farko, fuskarsu gab-gab da juna suna musayar numfashi. A hankali ya sake faɗin, “Kada ki sake barina dan ALLAH. Ina azabtuwa matuƙa Mawaddatan'warahmah. Wlhy kece farin cikin Aliyu, kece bugun zuciyarsa, kece sanyin idaniyarsa, bayan mahaifiyata bana jin na taɓa jin wata mace a cikin jinin jikina da komai na sama da ke. Ki bani dama koda ƴar karama ce domin tabbatar miki da hakan Pleassseee!”.          Wani irin luuuu tayi da idanunta ta lumshesu, sai kuma ta sake buɗesu a kansa. Cike da basarwa ta kai yatsanta saman lips ɗinsa ta fara zagayawa. “Dama kai ɗan ƙwallo ne?”. Ta faɗa cikin basar da zantukansa. Idanunsa da ke rufe ya buɗe a kanta. Jan ajinta na sake rikita masa lissafin rayuwa, ya ce, “Humm!”.        Gira ta ɗaga masa kaɗan tana wani cije lips da jan hancinsa. “Miye wani Hummm amsa nake so da baki?”.         Kauda fuskar tashi ya ɗan yi gefe yana murmushi, kafin ya sake maido idanunsa a kanta da ɗan juyasu alamar tunani. Sai kuma ya ɗan ɗage kafaɗu da taɓe baki kaɗan ya furta, “Tun ina yaro ma”.            “Uhhyim! Shine ka zama kuma driver?”.       “Ƙaddarata ce wannan”.    “Bani labari to”. Cikin ɗan ɓata fuska ya ce, “Ba yau ba amma?”.     “Miyasa?.” “Saboda ina da abinda yafi labarin muhimmanci. Ango fa nake ki tausayawa min? Niba ɗan jarida ba na ƙare da bada labari haba ai ace min ma shakatafi”.       Kalmar shakatafin ta bata dariya, dan haka ta murmusa har haƙoranta na bayyana. Ta ce, “Miye shakatafin? Ni Bama gane manya-manyan hausar nan naka suna yin girma da yawa”.         “Oh kefa na manta rabi da rabi ce baki cika bahaus”.     “Kai ka rabani ɗin ko?”. “Inba ni ɗin ba waya isa kaiwa ga wannan aikin”. Ya faɗa cikin fassara maganar tata da wata siga daban.              “Kai kana da matsala ba'a hirar arziƙi da kai. Sakeni naci abinci na fara jin yunwa”.          “Sorry na daina ayi hirar arziƙin. Abinci kam nan kawai ya isheki ƙoshi yau ai”. Ya ƙare maganar da nuna lips ɗinsa.       “Lips ɗinne kuma ya zama abinci?”.     “Sosai kuwa, kona gwada miki”. “A'a na yafe girmana bai kai can ba”. Ta faɗa tana ƙoƙarin sauka a jikinsa.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣0️⃣ .......Ƙaramar dariya yayi da ɗage gira sama ya ce, “Nima naga alama ƴar ƙanwata babu abinda ta sani sai cin abinci da barci”. Ya ƙare maganar da lakace mata hanci. Hannunsa ta buge da sake yunƙurin tashi tana faɗin, “ALLAH dai ya shiryaka kai kam”. Sakin nata yay yana dariya da tashi zaune shima cike da shaƙiyanci.             “Miye na dariyar to”.        “A'a babu komai ƴar ƙararrama, ai ko cikin AA ma a ruwan madara kika sha ni shaida ne.”    “Kaji da shi dai. Fitinanne”. “Kema zaki zama fitinanniyar”. “ALLAH ya tasreni wlhy”.    “Sai dai na gaba wannan dai ya faru tunda ga AA a duniya”.           Da sauri ta miƙe cikin ɗage kai tana faɗin, “Oh kama tunamin, yaron nan zai iya tashi ya ce zai sakko wlhy”.      Miƙewar yay shima da cewa, “Yi zamanki ina zuwa, bari na duba shi.” bata Musa masa ba ta koma ta zauna. Sai dai har ya gama haye ɗan steps ɗin hanyar bedroom ɗin nasa tana binsa da kallo, sai da ya shige ta sauke nannauyar ajiyar zuciya da lumshe idanu tana sakin wani ɗan murmushi mai sanyi. Babu jimawa sai gashi ya dawo ɗauke da AA kuwa a hannu, sai zillewa yaron yake da ɓata fuska irin na ƙiwa, shi adole bai sanshi ba. Yana ganin Lulu ya wani zabura wajenta yana ɓare baki. Dole ta amshesa dan ya cika mata kunne, yana ganinsa a hannuta sai yay shiru yana kallon Smart da sauke ajiyar zuciya. Zaune Smart ya kai kusa da Lulu cikin damuwa da ɗan murmushi, ya zubama yaron idanu da faɗin, “Kayi fushi da Papa ko Sweet heart? Kayi haƙuri Papa yayi laifi da baizo ya ganka ba tsahon lokaci. Please ka daina min ƙiwa kaji my sweet friend ɗina”. Ya ƙare maganar yana ɗan lakacema yaron hanci. Da sauri AA ya sake lafewa jikin Mamansa ya zata ɗaukar yasa zai sake yi. Murmushi ya sake saki da girgiza kansa kaɗan. Sai kuma ya dubi Lulu dake saurarensu da kallo kawai. “Yana cin abinci ne?”.         Cikin ɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki tana kallon yaron ta ce, “Da ga Kunu sai tea kawai yake sha, sai biscuits haka da ɗan sweets suma wani lokacin ko an bashi bai sha”.      “In dai ya biyo Babansa kam bazai sha ba, dan bana shan zaƙi nikam. Bari na haɗa masa tea ɗin maybe yunwa ce ta tashesa”. Kai kawai ta iya gyaɗa masa. Har ga ALLAH wannan halayyar tashi na saka mata ganin girmansa da kimarsa. A haka idan ka dubesa sai ka ɗaukesa a wani mutum mai jin kai da girman kai, amma sai ka zauna da shi kaga baida damuwa akwai sauƙin kai. Babu jimawa ya dawo da cup ɗin tea, zama yay a gabansu yana fuskantarsu, ya ɗan ɗebi tea ɗin a spoon ya kai bakin AA. A mamakinsu sai sukaga yaron ya ɗan kallesa kamar zai yi kuka sai kuma ya amsa. Dariya suka sanya su duka. Smart ɗin ya ɗan dungure masa kai da faɗin, “Ana son kayana amma ana guduna”. Ita dai Lulu dariya take musu. Tun yana amsa daga cinyarta harya zamo ya rarrafo jikinsa.        “Oh ashe ƙiwar bamai nisa bace Sweetheart”. Smart ɗin ya faɗa yana ɗaukarsa zuwa jikinsa. A haka ya cigaba da bashi tea ɗin suna hira da Lulu duk dai akan yaron ne da yanda yake samun soyayyar ƴan uwanta da nashi. Sosai Smart kejin ɗari a ransa, dan kuwa maganar nan ce dai ta malam bahaushe da kan ce mai ɗa wawa shima ke ɗawainiya da shi.... *_NIGERIA_*      A karo na farko tun bayan sakinsa da dawowarsa ƙasar yau sukai zaman meeting na farko da abokan cin mushen nasa. Wato Alh. Baita, Hon. Nakowa. Da Hon. Misau. Sai yaronsa Malami da aka dakatar daga waje kafin lokacin tasa shigowar yayi, dan akwai abinda ya ke son su fara tattaunawa da ba dole bane sai malamin yaji duk da kuwa a cikin sirrikansa babu abinda bai sani ba. Wani abu ma daya sani su su Alh. Baitan basu sani ba. Sun ƙara jajanta masa abinda ya faru cikin nuna ɓacin rai da tattara laifin gaba ɗaya akan Daddy da ɗan ka-ce-na-ce akan yanda akai suka san inda Lulu take. Shi dai shiru yay kawai yana saurarensu har suka gama bai ce uffan ba. Sai ma ya ɗakko musu batun kayan da yayo order da lokacin da yake ganin zasu iya shigowa Nigeria. Sun ɗan tattauna sosai akan hakan sannan suka dai sake komawa batun Daddy. Duk wani tsare-tsare a kansa sun yisa ne a wannan ranar harda ita Lulu da Smart suna a cikin plans nasu. Hatta da Abba wannan karon shima ya shigo lissafinsu..... *_UK_*     .....Tunda suka dawo bedroom ɗin domin kwanciya sai tsoro ya shigi Lulu saboda ganin take-taken Smart ɗin a kanta. Sai dai tana ta ƙoƙarin basarwar cike da ƙarfin jali. Alwala tayo zatayi shafa'i da wutri yace ta jirashi. Jitai kamar zatai kuka, ta ɗan kai dubanta kan AA da ya haɗa da tarkacen kwalaben turarensa. Babu jimawa ya fito shima da alamar alwalar yayo. Kayan jikinsa ya canja zuwa jallabiya, cikin umarni ya jasu jam'in salla raka bibbiyu har sau uku, da ga ƙarshe suka rufe da shafa'i da wutrin. Juyowa yay gareta ya ɗaura hannunsa na dama saman kanta ya karanto addu'a. Zuwa yanzu tana da ɗan iliminta na addini gwargwadon iko, dan haka ta fahimci sallar da sukayi, duk da kuwa ita bawai ankawota bane matsayin amarya, sai dai a wancan lokacin ma ai sunyi irin sallar a randa komai ya shiga tsakaninsu. Sai ko ga shi shi da kansa yana faɗa mata cikin tsokana da murmushi ya ke cewa, “Kin san ke yau a amarya kike, dole ai miki tarba irinta amarya”. Bata iya cewa da shi komai ba, sai dai tuni taji zuciyarta ta fara gudu a cikin ƙirjinta tuno da wahalar da tasha a waccan ranar da sakamakon abinda ya biyo baya na samuwar cikin AA. Sai ma taji ta gagara tashi a wajen. Ganin ya tashi shi ya koma saman gado waje ɗansa hankalinsa a kwance jiki a sanyaye ta jawo handbag ɗinta ta fiddo Alkur'ani itama ta fara karatu. Ta wutsiyar ido Smart ke kallonta yana jin wani irin farin ciki mara misali har tsigar jikinsa na tashi, sai dai baice komai ba dan a ganinsa lokacin cewar baiyi ba. Ya cigaba da yima AA wasa har yaron ya sake ɓingirewa barci. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali da kwashe kayan ya gyara masa kwanciya, dan tunda suka shigo Mamansa tai masa wanka da canja masa kayan barci, sai ƙamshi yake mai daɗi. Kwanciyar yay shirin yi shima abinsa bayan ya shiga bayi ya gama uzirinsa ya fito ya canja kayansa zuwa na barci da feshe jikinsa da turarruka ya haye gadon harda yin addu'ar barci. Hakan ya saka Lulu ɗan jin nutsuwa, ganin har ya ja bargo ya rufama kansa ta saki ajiyar zuciya. Mintuna kusan goma sha huɗu baya ta rufe Alkur'anin ta miƙe itama. A tunaninta Smart yayi barci. Toilet ta shiga ta ƙara gyara jikinta kamar yanda aka koyar da ita salo-salo a wannan fanin duk da ita batayi da manufa ba, dan bata ma fatan a kai ga hakan saboda tsoro yake ji sosai. Ta jima tana kallon kanta a mirror kafin tai ƙundunbalar fitowa. Ta ƙasan ido Smart da yay likimo yake kallonta, gaba ɗaya tsigar jikinsa ta shiga tashi dan rigar barcin da ke jikinta ba wata ta kirki bace, sai dai a gareta ita bawai tasa da wata manufa bane dan dama can tana sakawar a ita kaɗanta. Gadon ta nufa zuciyarta dai na kai-kawo, dan haka data ɗan kai zaune a bakin gadon ta tsurama Smart ɗin ido. Ganin bai ko motsa ba ta sake yarda yayi barci, sai kuma ta dubi a inda ya kwantar da AA, da ga gefensa sai dai ya kakkaresa da filos ta yanda ko juyi yay bazai faɗi ba, shi kuma ya kasance kamar a tsakkiyar gadon ya bar mata ɗayan gefen nashi. Sai da ta ɗan hararesa duk bata san yana kallonta ba sannan ta tura baki tana kaiwa kwance a hankali, tasan idan tace zata ɗakko AA ta maido tsakkiyasu Smart ɗin zai iya farkawa, koma yaron ya farka shi ya sanya mata daru duk da dai yanzu ya bar kukan dare, dan haka ta haƙura akan zuwa da safe dole a nema mafita, tunda dai taga ba ɗaki ɗaya bane a gidan ita zata koma wani ɗakin ta bar masa ɗakinsa, tun ma ɗazun da ace tasan nashi ne bazata yarda ta sauka anan ɗin ba. A hankali ta ɗan ɗaga bargon kaɗan ta yafama jikinta tana wani rumtse ido da cije lips, harda waigawa ta dubi Smart sai taga yana a yanda yake dai ko. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sake saki da lumshe ido ita a dole tasha da ƙyar.         Dariya Smart ke dannewa da ƙyar, sai da ya tabbatar ta gama dabarun nata sannan ya mirgino jikinta a hankali ya rungume ta tsam. A firgice ta juyo jikinta har yana rawa. Sai ya sakar mata murmushi da kashe mata ido ɗaya. Muryarta har rawa take wajen faɗin, “Dama idonka biyu?”. “A'a yanzu na farka” ya bata amsa cikin gimtse dariya. Kallonsa take cikin rashin yarda da cewar yanzu ya farka wai. Zatayi magana ya ɗora yatsansa saman lips ɗinta da faɗin, “Shiiii!!!”.      Dole ta haɗiye maganar idanunta na kawo ruwan ƙwalla. Juyota yayi da ƙyau suna fuskantar juna, murya ƙasa-ƙasa yake magana yana busa mata iska a fuska. “Amarya mai tsoro da fa ƙyar take sha a hannun ango. Karki zama raguwa mana Nooru Nisa”.            Fuska ta ɗan ƙwaɓe kamar zata sakar masa kuka. Sai kuma cikin rawar murya ta ce, “Aliyu kaga dai ALLAH ni har yanzu wajen da akai min aikin nan bawai ya gama warkewa bane, sannan ma banda wani isashen lafiyar jik.....”      “Irin wannan sharhi haka Madam. Ni nace zanyi wani abu ne?”. Ya faɗa cikin katseta da kai yatsarsa saman lips ɗinta yana zagayawa. Sai kuma duk taji kunya ta lulluɓeta, irin wannan kama kai har ina. Shima murmushi yayi dan ya fahimci ya rufe bakin maganar, abin faɗar sun maƙale. Idanunta ta maida ta rufe a hankali tana haɗiyar zuciya, daga haka ta fara ƙirƙiroma kanta barcin dole. Jin numfashinsu ya sake kusanta da juna ya sata buɗe ido da sauri, sai dai kafin tayi wani yunƙuri lassafin ya canja, dan Smart ya rantse yau fa a angonsa yake, ya barta ne kawai ta gama kame-kamen nata..........✍️ Hummm🚴🚴🚴🚴 _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣1️⃣ .......Al'amarin Umma kamar wasa ƙaramar magana ta fara zama babba. Dan ita kanta tun tana ɗaukar abun matsayin ba komai ba sai gata ta fara hawaye cikin tashin hankali. Dan kuwa dai ƙawarta Hajiya Naqiba tazo, amma tana shiga ɗakin nata itama da gudu ta dawo tana ihu mai firgitarwa da yafi na jama'ar gidan. Hankali tashe Umma ta biyota tana faɗin, “Na shiga Uku ni Yaha, Aminiya kema ɗin abinda suke min zaki min? Wai mina muku ne haka kuke irin wannan firgita da ni? Dan ALLAH ki faɗamin Aminiya kar ki min yanda suke min kema”.      Ina Hajiya Naqiba ba sauraren Umma take ba. Ihu kawai take kwarawa da iya ƙarfinta har maƙwafta da mutanen waje na iya ji, daga ƙarshe ma ta yanke jiki ta faɗi a sume dan Ummah taƙi daina binta. Cikin tashin hankali Umma ta isa gareta ta na jijjigata, a dai-dai nan mutane suka fara shigowa gidan da ga waje hankali a tashe. Ai sai ga maza na dafe huluna suna juyawa a guje. Duk wanda ya shigo yana tozali da Umma rungume da Hajiya Naqiba sai ya afa da gudu ya juya. Ba matan ba ba mazan ba ba yaran ba. Cikin ƙanƙanin lokaci zance ya zagaye anguwa. Masu ƙarfin hali na cigaba da shigowa domin tabbatar wa. Sai dai fa babu fashi duk wanda ya shigo zai juya a gujensa yana ihu da faɗin “Wayyo Dodo!! Wayyo dodo!!.”        Umma da ke zubama hajiya Naqiba ruwa tana kuka dan ganin abin da bana lafiya bane ta zabura jin aminiyar tata ta sake fasa gigitacciyar ƙara. Dan tana farfaɗowa taci karo da ita a kanta. Yin ƙurin da zatai domin ceton ranta ƙafa ta gurɗe jikake ɓass kamar an ɓalla katako ba ƙashi ba. Sai ta sake zubewa a ƙasa cikin wata irin wahalalliyar ƙarar azaba ta sake sumeya. Duk da abinda ke faruwa kaf ƴan gidan na maƙale ta windows suna kallo har ƴaƴanta da suka rarrabu. Wasu a ɗakin Ammah wasu na Mama. Ita dama aunty amarya da yaranta ɗakin Ammah suka afka suma. Ammah da al'amarin ya jijjiga ma zuciya na zaune a kujera tana cuɗawa da kwancewa. Dan in har lissafinta yayi dai-dai ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya fa a wannan karon. Tukunyar da suka gani tarwatse a tsakar ɗakin Ummah itace asirin da taima su Aliyu matarsa ke ganinsa da mummunan siffa irin wadda suke ganin Umma da ita a yanzun. Abba ne yay hikimar kiran yaranta na ma'auri da su Salim yace suzo babu lafiya. Dan shikam yama rasa ina zai kama a wannan lamari. A yau dai ya sake tabbatarwa Umma na bin bokayen tsubbu, kuma tabbas akwai ƙamshin gaskiya mai kamanceceniya da juna akan al'amarin Aliyu da matarsa da wanda Umma ke'a ciki yanzu. Yau matar Aliyu ta koma wajen mijinta, hakan na nufin komai ya daidaita tsakaninsu asirin ya dawo inda aka aikashi. Dama ai sharri ɗan aike ne, idan ya isar da saƙonka sai ya dawo ya tabbatar maka yaje. Har zai kira Smart sai kuma ya fasa cikin girgiza kai dan a yanzu ya tabbatar dare ne a UK.       Yaran nata ma koda suka iso duk wanda yay tozali da Umma sai gudun ceton rai. Umma ta fashe da kuka da tun ɗazun take irinsa har muryarta ta dishe. Ga aminiyarta kwance ƙafa sai kumbura take kowa ya kasa zuwa a taimaka mata saboda Umma da ke a wajen. Al'amarin dai sam babu daɗi, Umma na cikin tashin hankali fiye da wanda al'umma ke ciki akan ganinta a mummunar halittar da kowa ke ganinta. Ita kuma lafiya Lau take kallon kanta, dan har ɗaki ta nufa ganin kanta a madubi babu wata damuwa ko tawaya tattare da halittar ta sai fuskarta datai kace-kace da hawaye har idanunta sun kumbura. Kafin ta fito ne aka samu aka ɗauke Hajiya Naqiba dake kwance bata da banbanci da gawa. Dole asibiti aka wuce da ita a gaggauce dan ƙafar tayi masifar kumbura damm abin zattashin hankali......            *_UK_*            Wahala iya wahala Lulu tasha a wannan dare hannun Smart. Dan zata iya rantsewa ita kam bata ga banbancin sa da daren farkonsu ba, kodan ta saka ma ranta tsoron al'amarin ne oho. Amma tabbas ko a yarda da ita ko kar a yarda Smart namijin gaske ne da ko'a cikin mazan ma zai iya amsa sunan mazaje ne. Sai dai bata sani ba ko ragwantakarta yasa take masa irin wannan kallon ko kuma dan shi ta sani bata san sirrin sauran mazan ba.          Shi kansa sai da ya koma tausayinta, dan magana ta gaskiya fa bai raga mata ba, wahalarsa ta kusan shera ɗaya da wasu watanni sai da ya fanshe abinsa tsaff. Sai dai kuma shi a karan kansa bashi da zaɓin da ya wuce hakan. Bai sani ba ko tsananin begenta da yake a cikine ya sashi jin yau ɗin babu bambanci da wancan daren da ya kasa goguwa a zuciyarsa, amma ako ina kam zaiyi alfahari da baiwa irin ta matar tasa. Dan a wancan dare shima sabo yake, yau kam ya banbance tsakanin aya da tsakkuwa. Ya kuma zaɓi yimata mai gana ɗaya ne dan cire mata tsoron nan da ya lura yay mata tasiri. (Humm gyaran su iya Tabawa bai faɗi a banza ba kenan🥱🤣🚴).         Langyare iya langyare, raki iya raki yasha shi. Kuka kam muryarta har bata fita. Tun ana bashi haƙuri da roko da magiya har dai aka koma kiransa mugu. Yaƙushi da cizo duk ya samu rabonsa kafin duk wani ƙarfinta na neman ceton kai ya ƙare ta koma zallar hawaye da jiran mala'ikan mutuwa (acewarta🥱😜😂).        Shi ya fara farkawa lokacin da alerm ɗin da ke tadashi sallar asuba ya kaɗa. Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa da ke jingim da barci dan basu wani jima da kwanciyar ba. Hannu ya kai ya kashe alerm ɗin gudun kar AA ya tashi shima. Tunda ALLAH ya taimakesa dai har ya gama bidirinsa na daren jiyan yaron bai farka ba. Idannunsa ya zubama fuskar Lulu dake barci kamar a wahale, shi sai ma ta bashi dariya, dan haka ya ɗan murmusa da kai hannu ya shafa fuskar tata. Baki fal tsiwa da rashin ragiya amma sai tosoro da ragwantaka uwa farar kura. Ɗumin da yaji a fuskarta ya sashi jan bargon kaɗan yasa hannunsa a wunyanta. Zazzaɓine sosai a jikin nata kam kamar yanda yaji. Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe da sumbatar goshinta yana sake matseta a jikin nasa cike da tausayawa.       “I'm so sorry Final Choice. Aliyu bazai sake baki wahala ba da ga yau kinji”. Ya sake kai mata sumba a saman hanci yana mai sake jinta sama can ƙololuwa a zuciyarsa. Da ƙyar ya iya samu ta tashi sai faman langyare take masa da kukan shagwaɓa. Shi dai biye mata yake yana binta da lallashi. Dan ko a wancan karo na farko ba'ai masa wannan langwai ɗin ba. Koda yake wancan ana bori yaushe ma ya samu kanta. Dan haka yau kam ya ƙudiri aniyar rama mata dukkan tattalin da bata bashi damar yimata a waccan ranar ba. Yanzun ma taimaka mata yay ta sake ɗan gaggasa jikinta, duk da dai yasan taimakon da yay mata jiya kawai ya wadatar, yasan kam harda raki da ragwantaka dai koma yace shagwaɓa. Shine ya jasu salla yanzu ma, suna idarwa ya miƙe ya fita, bai jima ba ya dawo ɗauke da kofin tea da soyayyen ƙwai. Da ƙyar ya samu ta sha tea ɗin, kwan ko bata ko kallesa ba balle ta ci, sai maidashi yayi. box ɗin magungunan sa ya ɗauko ya bata na zazzaɓi tasha da rage raɗaɗi. Sai da ya ga ta sake komawa barci ya sauke ajiyar zuciya. Yasan koyaushe AA zai iya tashi shima, dan haka ya haƙura da fita ko'ina motsa jiki ya ɗan yi a gida. Ilai ko bai jima da farawar ba AA ya farka. Rarrafawa yay kan Lulu yana kuka. Hakan ya sakata farkawa. Harararsa tayi, itama kamar zata saki kukan ta ce, “Ni bazaku kasheni ba kai da ubanka wlhy. Kai tayi idan ya jika yazo ku ƙarata”.        Kaf a kunnen Smart dake shigowa, dan haka ya saki murmushi yana ƙarasowa ciki. Tana jin motsinsa ta maida idonta ta rufe kamar barci take. Nanma murmushi yayi kawai da ɗaukar AA dake neman yimasa ƙiwa kamar jiya. Tsaff yama yaron wanka duk da dai da ƙyar akasha, dan sau kusan biyu yana neman suɓuce masa ALLAH dai ya kiyaye baisha ƙasa ba. Ganin kamar yunwa yaron keji yay zaman fara bashi tea da dama ya haɗo ya ajiye tun ɗazun kafin ya shiryashi yana nishi da ƙyar dan bai iyaba. Pampa's ma da ƙyar aka iya sawa sai da ya duba a net.. yaga yanda akeyi. Duk kuma abinda sukeyi Lulu na kallonsu dariya kamar ta kasheta amma ta zaɓi yin likimo wai ya ɗanɗana yaji shima idan da daɗi. Shiko a zatonsa barci takeyi, sai da ta kasa riƙe dariyarta dai tayi sannan ya farga idanunta biyu. Cikin kalar tausayi yake kallonta da faɗin, “Yanzu nan idonki biyu aketa wannan dambarwar amma babu ko taimako Baby luv?”.          “Ku ƙarata nima ta kaina nake”. Ta faɗa tana masa gwalo da jan bargo ta rufe har kanta. “Haka kikace ko? Ba komai zamu rama ne ai”. Bata sake magana ba tai luf a bargo abinta tana dariya har suka kammala ya hawo gadon da yaron yana sauke numfashi ɗaɗɗaya. Sauka da ga jikinsa AA yay zai haye kan Lulu ya riƙoshi yana faɗin, “A'a Sweet heart abar Momy ta huta kaga Papa ya koya mata karatu duk ta jikata”.        “Yaushe ka koyamin karatun?”. Lulu da bata fahimci inda ya dosa ba ta faɗa tana buɗe kanta da sauri harara idonta kamar zai faɗo. Gira ya ɗaga mata da kashe ido ɗaya ya ce, “Yanzu ma malamin a shirye yake in har za'a barsa ya ƙara ɗora sabon darasi”. Yanzu ne ta farga da inda zancensa yaya dosa. Bargon taja ta sake rufe kanta da faɗin, “ALLAH dai ya shiryeka Aliyu. Ni kutashi ku fita barci nake son yi kun daman”.        “Amin ya rabbi tunda addu'a aka min. Amma fa babu inda zamuje muna nan tare da ke”.      “To ku koma ƙasan carpet kun ishan ALLAH”.              “Anƙi ɗin”.         Harararsa tai shi da ɗan nasa ta matsa can ƙarshen gado ta sake jan bargo dan da gaske jikinta ciwo yake mata sosai, ga zazzaɓi. Murmushi yayi da binta da kallo, dan yasan da gaske bata da lafiyar, yana mata hakane danta saki jikinta dai ne kawai. Wasa ya cigaba da yima AA dake son shi kawai a saukesa yayi ɓarna, sai da ya tabbatar tayi barci ya ɗan janye mata bargon da ga kan fuska danta samu iska. Goshinta ya taɓa yaji da ɗan sauƙin zafin, sai kuma ya maida kan wuyanta. Shima dai alhmdllh ya fara sauka. Sai ya samu kansa da sauke ajiyar zuciya........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣2️⃣ ______________ *3 DAYS CLASS* Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rarar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rarar kudinne sakamakon rashin neman scholarship da bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka canza kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni Class ze fara ranar jumaa insha Allah WhatsApp group 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/E8Lzqogsm1nAFy1feTwbmA WhatsApp 08144147273 👉 Masu bukatar tafiya da kudinsu ba scholarship ba, Muna yin study & work ko working visa, a takaitaccen lokaci, working visa Qatar munayi a sati daya, Canada study & working visa a 4 to 5 months, Oman working visa a 7 days insha Allah, Maxico Tour visa 1 month _______________ ........Kuka take sosai a gaban mijin nata da ayanzu al'amuransa ke bata tsoro matuƙa. Gaba ɗaya ya sauya mata, sauyawa irin wadda bata taɓa zato ko tsammani ba. Kai koda a mafarki ko lissafin rayuwa bata taɓa tunanin itada Sufiyanun nata zasu kasance a irin wannan ajin ba. Amma a yau sai gashi wai harda mata kishiya sa'ar jikokinta da wannan shekarun nata tsofai-tsofai. Kuma ko kunyarta baya ji yake soyayyarsa kamar wani ƙaramin yaro.         Baba Garko da tunda ta shigo ta zauna bai ko ɗaga kai ya dubeta ba sai ma wayoyinsa da yake hankali kwance. Daya gama wannan zakaga wata ta shigo. Cikin jin gundura da kukan da take rera masa ya ce, “Amma dai kin san kina damuna ko? Please bana son damuwa idan kukanki zakiyi zaki iya bani waje”.     Sake ɓarkewa tai da sabon kuka kamar wata ƙaramar yarinya. A dai-dai nan akai knocking ƙofar falon, ɗan jimmm yay yana kallon ƙofar kafin ya ce, “Ko waye ya shigo”. Mai aikin amaryarsa ce ta shigo a rikice, amma hakan bai hanata kaiwa tsugunne da ga bakin ƙofa ba ta gaisheshi cikin girmamawa sannan ta ɗora da faɗin, “Alhaji aunty amarya ce bata da lafiya, tun ɗazun kuma ta hana azo a sanar mak...” ai mai aikin ma bata ƙarasa rufe baki ba ya miƙe zaram ko nauyin tsufarsa baya ji. Ƙofar ya nufa a hanzarce, Dada da kanta ya nema tarwatsewa ta bisa da kallo galala, wani irin tuƙuƙin baƙin ciki na sake turniƙe mata zuciya. Ba'a ko rufa minti huɗu ba sai gashi ya shigo a rikice, ko kallon inda take baiyi ba ya shige bedroom ɗinsa. Cikin ƴan sakanni ya sake fitowa ya fice hannunsa riƙe da key ɗin mota ya canja zuwa jallabiya. Kasa motsawa tayi a wajen har sai da taji ƴar hayaniya na tashi ta miƙe jikinta na rawar ɓacin rai ta leƙa ta window. Akan Baba garko da ke rungume da amaryarsa ita kuma tana faman yarfe hannu tana kuka idanunta suka fara sauka. A take zuciyarta ta ayyana mata haihuwa. Sake dugunzuma zuciyarta tayi har tana jin jiri na neman kwasarta, batama san sanda ta sulale a wajen ba ta zube saman kujera jaɓar wasu zafafan hawaye na wanke mata fuska, sai kuma ta ɓarke da kuka. Tunda take a rayuwarta, bata taɓa shiga matsanancin baƙin ciki da tashin hankali irin na wannan gaɓar ba. A tsahon rayuwar ƙuruciyarta ko firar kishiya bata so, kai ko ƙawa ko cikin ƴan uwa akaima wata kishiya daina zuwa gidan mutum take saboda yanda ta tsani kishiya. Amma a yau sai gata da ita a wannan shekarun nata, harma da ciki na haihuwa.....        (🤣🤣🤣🤣🤣 Kar kuce dariyar mugunta nakema Dadaras😜)          ____________★      Tun Ummah na ɗaukar al'amarin ta ƙarami harta fahimci ya wuce da saninta. Kuka ma da hawaye yanzu ta kasa yinsa. Ƴan gidansu sunzo sai dai me suma ƙarewa sukai da fita da gudu harda masu faɗuwa. Wajen Abba suka koma kowa na maida numfashi, yayanta cikin damuwa ya ce, “Anya ba aljanune suka shigi Yahanasu ba Yaya Mika'il”.     Cikin ɗan taɓe baki Abba yace, “Idan ma sune wajen biɗar baƙar tambayarta ta kwaso su. Ballema bana jin hakanne. Nafi ƙyautata zaton ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya. Ni yanzu jibirin ban san yanda zanyi da wannan matar ba. Gaba ɗaya ta firgitamin iyali sun kasa sakewa kowa sai zaman ɗaki”.       Cikin damuwa Jibirin yace, “Amma yaya bai kamata kace haka ba. Ƙilama cikin matanka wata taimata haka kasan dai mata akan kishi”.     “Wane matan nawa? A'a ƙarya haramun. Ai duk cikin iyalina babu fanɗararre irin Yaha. Nasan halin kowacce a cikinsu da abinda zata iya. Na jima ina zarginta dama da shigen-shigen nan kawai dai ban taɓa gani da idona bane shiyyasa ban kafa hujja ba. Amma a yanzu na gama fahimtar komai. Ko wannan halin da kaga tana cikin sihirin da taima Aliyu da matarsa ne ya dawo mata...”            “Aliyu kuma Yaya? Aliyu Aliyu dai namu na nan?”.        “Shi ɗin fa”.    “Ikon ALLAH! To shi Aliyu dake matsayin ɗanta kuma zatama asiri. Miye ribarta kenan?”.              “Oho mata, ita ta sani”.         Sosai al'amarin ya girmi kan kowa. Cikin ƙarfin hali Zaidu ya bada shawaran to ko za'a samo malamai suyi addu'a ne. Dan wannan yanayin nata abin tashin hankali ne ga kowa tunda gashi hankalin kowa a tashe, shi wlhy yanzu haka baya jin yau ɗin nan zai iya barci lafiya saboda ganin wannan mummunar halitta da Ummah ta koma. Abba dai yace shi babu ko sisinsa a nema mata lafiya. Hasalima ya kirasu ne su wuce da ita dan bazai iya ba. Hankalinsu ya tashi matuƙa, dan sukam bazasu jajibi wannan halittar ba sukai cikin iyalinsu suna zaune ƙalau. Dan haka suka dage bashi haƙuri da roƙo da magiyar ya barta a ɗakinta cikin ƴaƴanta harta samu lafiya sai aji dalilinta na wannan mummunan al'amari, idan ma matakin sai ɗauka sai ya ɗauka. Anfi ƙarfin Abba ne kawai, dan haka yay shiru. Su suka fita suka zo da malamai, da ga tsakar gida suka tsaya aka kwala mata kira ta fito. Su kansu malaman sai da suka zabura da ganin mummunar halittar dake tunkarasu, ganin tana yo kansu gadan-gadan sukaji fa dauriya ba tasu bace. Ai tuni suka dafe kawuna kowa ya ara cikin ta kare yana jan kula'uzai. Bayan su an sake kawo wasu malaman amma fa kowa yazo yana tozali da Umma sai dai a tsincesa waje ya dafe ƙeya. Al'amari kamar wasa sai ƙara faɗi yake. Dan takai ƴan jarida daga gidajen rediyo har sun fara zuwa neman labari. Sai dai suma fa suna shigowa sukai ido huɗu da Umma labarin bai ɗaukuwa garesu sai ƴar reren gudu...       Tsabar tashin hankali da hawan jini Umma ta koma ko gani batayi da ƙyau. Barci kuwa ya ƙauracema idanunta gaba ɗaya. Cikin ƙanƙanin lokaci tai wata irin muguwar rama mai ban tsoro. Babu abinda ke ɗaga mata hankali sai ganin ƴaƴanta suma gudunta suke da mijinta da ta ɓata tsahon shekarun rayuwarta tana faɗa da faɗi tashi a kansa. tana son jin halin da Hajiya Naqiba take amma babu hali. Rayuwa ta mata duhu, duhu irin wanda ko tafin hannunka baka iya gani, duhu irin wanda zuciya kanta bata iya tuna komai sai ƙunci da ciwo mai raɗaɗi. Hatta salla yinta kawai take amma bata ma sanin mitake yi a cikinta. wanka kam bama'a maganarsa dan tashin hankali. abinci dama yanzu ƙofar ɗaki Abba ke zuwa ya ajiye mata saboda kowa tsoro yake ji, shi kansa dai tausayin rai ne ke sakashi yin ƙarfin halin ajiyewar kawai dan an hanata fitowa.....         *_★UK★_*     Sosai tasha barci, dan ko da lokacin salla yayi da ƙyar ya iya tashinta tayi ta sake komawa. Bata tashi ba sai gab da la'asar. Yana falo suna kicimilli da ɗansa ta fito. Tsaye kawai tai tana kallonsu har bata san tana murmushi ba. Mayataccen ƙamshinta ya fargar da Smart kasancewarta a wajen. Zaune ya tashi da ga kwancen da yake yana ɗaga AA dake sukuwa a saman cikinsa. Cikin lumshe ido da sakar mata murmushi ya ce, “Kin tashi?”. Cikin falon ta ƙarasa takowa tana marairaice fuska. Hannunsa ya miƙa mata alamar tazo garesa. Babu musu ta ƙaraso, ya riƙo hannunta ya zaunar gefensa yana mai rungumota ta gefen jikinsa kanta a saman kafaɗarsa. AA dake neman haye mata jiki ta dungurema kai batare da tayi magana ba. Smart dake kallonsu da murmushi ya shafo fuskarta da faɗin, “Yaya jikin naki?”.        “Ba sauƙi”.     Ta bashi amsa cikin tura baki. Sosai ya waro idanunsa waje. “Ba sauƙi fa Nooru Nisa”.       Fuska a gimtse ta ce, “Eh mana dan ni dai jikina ciwo yake mun har yanzu”.      “Kai Madam bansan ragwantaka fa. Ni da nake shirin yanzu a sake tafiya yaƙin ƙasa da ƙasar again.”            “Dawa?!”.       Yanda tace dawa ɗin cikin waro idanu da ƙwaɓe fuska kamar zatayi kuka ya sashi kwashewa da dariya. Mintsini mai zafi ta sakar masa tana miƙewa. Ya riƙe wajen da sauri yana yamutse fuska da faɗin, “Wai ALLAH na! wannan zalincin fa? Kefa kin iya mugunta”.     Gwalo ta masa tana dariya, ta ce, “Mugayen ai da yawa kai ne malamina”. Tai wucewarta kitchen Dan yunwa takeji.         “Haka kika ce ko? Ba komai zan rama ne”.     Dariya ta shige tanayi, babu jimawa ta fito ɗauke da apples data yayyanka a ƙaramin bowl. Ƙasa ta zauna dan taji daɗin miƙe ƙafa. Smart dake binta da kallo ya ce, “Badai wannan ne abincin ba?”.         Muryarta a marairaice da shagwaɓa ta ce, “ALLAH bakina babu daɗi, ina son naci kozai washe. Sannan wannan ɗin ma ni kam ya isheni”.      Idanu kawai ya tsira mata yana kallonta. Ta ɗan hararesa da faɗin, “Kallon fa?”. Murmushi yayi da janye idanun nasa cikin yin luuu da su. Sai kuma ya sake zuba mata su cikin yanayin kasala. “Yarinyar nan anya kuwa?”.              “Anya kuwa mi?”.         “A'a ni bance komai ba. Kawai dai dama sai nake ga kamar fa wannan karon ma kin amshe ne, kin san fa ni bana saɓa saiti a zahirin fili wasa da na ɓoye”.      Da farko bata fahimci mi yake nufi ba. Sai da tai ɗan shiru sai kuma ta dago ta hararesa. Dariya ya ƙyalƙyale da shi, zai sake magana ta tura masa Apple ɗin data tsiro a bakin tana sake harararsa. “Kai dai ALLAH ya shiryeka wlhy”.          Murmushinsa ya cigaba da yi shi dai, koda ya shanye apple ɗin data saka masan sai ya sake matsowa da buɗe baki wai ta ƙara masa. Kafaɗa ta maƙe alamar anƙi ɗin. Ya bata fuska cikin yanayin shagwaɓa. “Kina sha, kina bama AA ni kuma sai a wareni. ALLAH sarki nima da Ammah na kusa da banga haka ba. Bari na kirata na faɗa mata”.       Da sauri ta fisge wayar ta tura ƙasan ƙafafunta. Sannan ta tsiro apple ɗin ta tura masa abaki tana harararsa. “Mai kwaɗayi, kai yanzu in an barka saika faɗa?”.          “Sosai kuwa. Harma da Daddy da Abba duk zan kira, ince tunda kika zo baƙya kula da ni.”      “Sharri Master kenan. Daka kasheni dan ina jin kunyar Abba sosai ALLAH.”      “Ni kuma baƙya jin kunyata ko?”. Murmushi tayi tana sakama AA da ke tsaye jikinta yana wasa da gashinta apple ɗin a baki. Cikin basar da zancensa ta ce, “Da kai Daddy ya haɗa baki kuka kawoni nan ko?”.             Kwance ya kai yana ɗora kansa a saman cinyarta, sai da yay ƴar dariya da tsokano AA ya ce, “Nikam babu ruwana. Daddy ne yay miki wayonsu na manya saboda yana jin tausayina. Shekaranjiya dai muna magana da shi yake cemin akwai saƙo da zai aiko min da shi, idan kuma ya samu shigowa London to, dan zaije Manchester city ne”.      “Lallai ma Daddy nice saƙon yake nufi ko mi! Sai kace wata kayan wanki”.    Dariya sosai Smart ke ƙyalƙyalawa har AA na faɗawa jikinsa shima yana tayashi. Sai kawai Lulu ta zuba musu ido tana kallo. Sai da sukai mai isarsu ya jiyo yana kallonta. Ganin yanda ta zuba musu ido ya ɗan ɗage gira da faɗin, “Kallon fa Madam”.             “To ba dole na kalleku ba naga kun zare. Wai nikam dama kana dariya har haka? Amma da kaita tsuke fuska kamar wanda akaima saƙon mutuwa!”.      Kansa kawai ya shafa yana murmushi baice mata komai ba. Itama sai ta share ta cigaba da shan Apple ɗin ta. Lokacin-lokaci tana saka masa a baki shi da AA da ke saman jikinsa yana wasa da ƙasumbarsa.......✍️ _🚴Ya kamata mu taya Ummah da Addu'a 🥱🥱🥱_ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣3️⃣ .......Haka suka cigaba da kasancewa cikin farin ciki da nishaɗi a wannan yini. Sai zuwa wani lokaci yayi kiran Ammah kasancewar su a Nigeria ba daren bane. Sun gaisa sai yake jinta kamar cikin damuwa. Cikin kulawa ya shiga jera mata tambaya. Sai cewa tai babu komai ya haɗata da Mawaddat. Kafin ya bama Lulun ne take tambayarsa babu dai wata damuwa kowa?. Ya ce Alhmdllh yanzu haka ma gasu nan AA ya ishesa da ɓarna. Murmushi Ammah tayi har yana iya jiyo sautinsa. Ta ce, “Ai wannan baban nawa yana ji da ƙarfi da lafiya ne, nima ɗakina ya huta da ɓarnarsa ai yanzu, ga shi nan duk yamun fashe-fashe kala da iri. Dan Babana ne kawai yasa bance a biyani ba”.       Cikin dariya Smart ya ce, “Ai ba'a shiga tsakaninku da Baban naki kam Ammah. Sai dai nayi mamakin yanda yay girma haka, ashe hoto na rage min girman nasa.”          “Ai duk kai ya kwaso Hydar. Babu wani abu naka da yaron nan ya bari. Yanzu dai Alhmdllh komai ya zama labari, sai ku sake dagewa da addu'oi dan ita matsalar rayuwa da jarabawa basa ƙarewa. Idan wannan ta wuce watace kuma zata iya kutso kai a kowane irin lokaci. Abinda dai kawai ake buƙata shine bawa ya tsarkake zuciyarsa kada ya nufi kowa da sharri, domin shi ɗan aike ne duk inda ka aikashi sai ya je ya dawo ya tabbatar maka yaje. A zauna da mutane lafiya dan ALLAH, kar a zalunci wani koda da ganganci ne, idan kaima mutum kuskure ka bashi haƙuri ka kuma nema afuwa, sannan ka gyara wannan kuskuren. Ga matarka nan dai ta dawo gareka, sai aji tsoron ALLAH ka sauke hakkokinta da ALLAH ya ɗaura maka, karka zalunceta saboda kana amsa suna Namiji shugaba ita tana mace kai rauni, karka ce akoda yaushe dole kaine a sama da ita, shi aure ƙauna da haƙuri da kawaici ke jagorantarsa yay ƙarko. Sannan shi babba shi aka sani da shanye komai daga na kasa da shi, idan laifi tai maka kayi nazari da bincike kafin yanke hukunci, karka yarda ka yanke hukunci cikin fushi, karka yarda kace zaka zagi iyayyenta a bisa kuskurenta, kada ka aibantata ko hantararta dan kawai ta maka abinda bashi kake so ba. Nasiha da jawowa a jiki shike saka zuciyar waninka maka biyayya komai taurinta, a duk lokacin da ka kasance mai adalci da tattalin rayuwar mace da ƙyautata ma da yin haƙuri da ita ba sai kace ta kiyayeka ba, ita da kanta zata dinga jin shakkar maka laifi ma, bakuma zata taba samun nutsuwa ba idan ta ganka cikin damuwa. A duk kuma sanda tai kuskure ka tsawata mata zata fahimceka fiye da yanda kake buƙata. Ka yabama matarka a duk sanda tai abu mai ƙyau, ko kwalliya ta maka kwarzantata ka nuna mata duk duniya babu ƙyaƙyƙyawa a wajenka sama da ita, idan girki ta maka nuna mata tafi kowa iyawa, babu kuma wani abinci dake maka da ɗi sama da nata. Idan tana magana da kai ka bata hankalinka da ɗaukar kowane furucinta da muhimmanci koda kai a wajenka bamai muhimmanci bane. Ina mai tabbatar maka Aliyu matarka saita maidaka tamkar sarki, zaka zama ɗan lelenta, zaka zama amininta, zaka zama mata ɗan uwa, zaka zamar mata jarumi, zataji babu wanda take so ta birge a duniya sama da kai. Komai iyawar waninka za taga taka itace a sama da kowa. ALLAH ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka. ALLAH ya kiyaye gaba”      “Amin ya rabbi Ammah, in sha ALLAHU zaki sameni mai biyayya akan shawaranki da umarninki. Nagode sosai, ALLAH ya ƙara muku lafiya da tsohon rai mai albarka. Ga Mawaddat ɗin dan naga ta ƙagara kamar ta kwace wayar”.  Dariya Ammah tayi, yayinda shi kuma yake mannama Lulu wayar a kunne yana dungure mata kai. Alamar zan rama tai masa tana faɗin, “Ammah na” cikin zumuɗi. Cike da farin ciki itama Ammah da ga can ta amsa mata da “Na'am Mawaddat ɗina. Kun sauka lafiya ko?”.       “Lafiya lau Ammah ina yini?”.    Da kulawa Ammah ta amsa mata da tambayarta AA. Tai murmushi kawai batace komai ba dan sosai take jin nauyin Ammah akan al'amarin AA ɗin. Ta rasa miyasa hakan. Saboda ita kaɗai take iyama wannan karan. Garama Mommy itama akan ɗan ɗaga mata ƙafa wasu lokutan. Hira sukayi da Ammah sosai, itama tai mata nasiha tamkar yanda taima Smart, dan tana jinta babu bambanci da ƴaƴanta ne, sosai Lulu taji daɗin shawarwarin Ammah, harda ƴar ƙwallarta. Sun cigaba da hira har takai kunnen Lulu ya jiyo ihu da hayaniya. A tsorace take cema Ammah suwa ke ihu haka?. Rasama mi Ammah zatace mata tayi, shima Smart jin an ambaci ihu ya amshi wayar yasa a hansfree. Cikin ƙarfin hali Ammah ta ce, “Babu komai yara ne ke wasa”.      Haka kawai Smart yaji bai gamsu ba. Amma sai baice komai ba har sukai sallama. A yanayin damuwa Lulu ta ce, “ALLAH kamar Ammah na cikin damuwa”.         Kai Smart ya jin jina mata. “Tabbas akwai abinda take ɓoyewa. Kuma tunda kikaga taƙi faɗa mana bamai daɗi bane. Ina zuwa bari na kira Aunty Bilkisu”.      Wayar ta miƙa masa, yana kira kuwa aka ɗaga. Bayan sun gaisa ya tambayeta yaya jikin ta. Ta amsa masa cewar da sauƙi. Sai dai jiya mai gidanta yayi maganar cewar wai zai kaita Egypt, “Amma ina zargin dan Abba yay masa maganar cewar kace zanzo wajenka naga likita ne. Dan tunda matarsa ta dawo na kasa gane kansa a gidan nan Aliyu. Ni wlhy zaman nan yama isheni. Hatta yaran nan baya shiga harkarsu, jiya dan Sadiq yay faɗa da yarinyar wajenta bakaga dukan da babban yaronta yay masa ba, wai nayi magana shine yake faɗin banda haƙuri akan yara da kawaici.”       Sosai ran Smart ya ɓaci, amma sai ya shanye cikin danne zuciyarsa ya shiga bata haƙuri da lallashinta akan karta damu. A yanzu haka ma yana nan yana mata shirin tahowar cikin satin nan Ahmad zai zo ya kaita tayi visa, shi kuma mijin nata ta share batunsa kawai. Yaran kuma ta kaisu wajen Ammah daga can a dinga kaisu makaranta. Taji daɗin shawararsa sosai. Da ga haka take tambayarsa ina Mawaddat. Shekaranjiya abinda ke faruwa a gidan nasu yasata ɗan taƙarƙarawa taje shine Ammah kece mata ai sun komo wajensa. Har take tsogumin basuje musu sallama ba shine Ammah tace ai tafiyar ta shamattace akai babu wanda ya sani..        “Wani abu ya faru a gidan ne?”.    “Ammah bata faɗa maka bane? Ai mugun abin waccan azzalumar matar data muku ne ya koma kanta. Dan yanzu bakaga yanda ta koma wata irin mummunar halitta ba wlhy Hydar. Kowa fa bai iya zuwa inda take yanzu gidan nan cika yake da ƴan kallo harda ƴan jarida. Ai Umma taga ƙarshenta”.           “Ni duk kin sake dilmiyar dani wlhy Aunty. Please kimin dalla-dalla miya faru da Ummahn?”.       Tsaff aunty Bilkisu ta zayyane masa labarin abinda ya faru tun jiya da Lulu ta taho. Sosai suka girgiza da jin wai Ummah ce ta musu asirin nan, kuma yanzu haka ma kowa ita yake zargi akan abinda ya dinga faruwa da shi lokacin da yake faɗuwa idan ya shiga filin ball. Komai bai iya cewa ba sai ALLAH ya ƙyauta ganin yanda Lulu duk ta ruɗe harda su kuka. Dole yay sallama da aunty Bilkisu ya rungume matarsa a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya. Gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa sunyi jazur. Ganin yanda Lulun ta tsorata ya sashi ɗan sakin jikinsa shi. Fuskarta dake cikin tafukan hannunsa ya ɗago suna kallon juna. Ya ɗan ɗaga mata gira cike da tsokana. Sai kawai ta sake fashe masa da kuka. Dariya yayi a karo na farko. “Wai anya kuwa keda AA kunada maraba kuwa?. Shagwaɓanki yayi yawa. Yanzu minene abin kuka anan?. Ko kina jin haushin an rabaki da mijinki ne harna wata kusan goma bakiji ɗuminsa ba. To yanzu ba gaki tare da ni ba barci sai inda kika zaɓi kwanciya a jikina”.          Hararsa tai tana ture masa hannu. Shi kuma ya cigaba da dariyarsa yana kai mata kiss a fuskar. Bai barta ba sai da ya ga ta saki jikinta har tana dariya. Cikin sakin ajiyar zuciya a jajjere ta ce, “ALLAH naji tsiro ne Aliyu. Ni dama matar nan haka kawai bana sonta. Ashe muguwa ce. Kenan fa tana cikin wani ƙungiyan secret ne?”.         “Secret kuma?”.    “Eh mana tunda gashi tana iya turama mutane Dodo”.     Fuskarsa da murmushi ya ce, “Ba wani ƙungiya. Kin san a ƙasar hausa mata sun ɗauki kishi wani babban al'amari. Wasun ku zasu iya aikata komai saboda wannan kishin nasu. Bansan dalilin Ummah na aikata min hakan ba, dan ni taimawa ai. Amma nasan koma minene yana da alaƙa da kishi. Na jima da fahimtar ta tsani Ammah da mu kammu. Dan lokacin da akace na aureki baki ji yanda ta tada hankalinta wai na auri ƴar gidan masu kuɗi. Hakama aurarrakin su Hawwah”.         Cikin mamaki Lulu ta ce, “Oh dan gidanmu da kuɗi ka auran shine matsala kuma?”.      “Su haka suke gani. A tunaninsu ƴar masu kuɗi sai ɗan mai kuɗi. Idan ma za'ai irin wannan auren bisa ƙaddara ɗan mai kuɗi ya auri ƴar talaka yafi ƙayatarwa suke gani. Amma idan ƴar mai kuɗi ta auri talaka kamar zai zama ƙarƙashin mulkin mallakarta ne. Koda yake mafi yawa hakan ce ke faruwa shiyyasa tunanin duk mutanenmu yake a iri ɗaya.”           Baki Lulu ta taɓe kawai. Kamar bazatace komai ba sai kuma can tace, “Ni wannan abin ban ɗaukesa wani abu ba. Kowa bada yanda ALLAH ke son ganinsa ba. Talakawa nawa ne keyin arziki, masu ƙuɗi nawa kuɗinsu ke ƙarewa su koma abin tausayi. ALLAH da Daddy na bani tarihinsu shi da su Mommy da Uncle You har kuka nayi, kaga suma da basu da komai, amma yanzu fa. Kuɗin da duk mutuwa kowa zaiyi ya barsu ma”.         Kallonta Smart yake cike da jin ƙaunarta, bai taɓa sake tabbatar da tanada hankali ba sai yau. A hankali ya jawota jikinsa ya rungume tare da kai mata kisses tako ina a jikinta. Batai yunƙurin ƙwace jikinta ba kamar yanda ta saba. Sai da taga yana neman sakin layi ne ta shiga turesa, sai dai shi ya riga ya kai inda baya jin kira, dan haka ya ɗakko sabon salon kashe mata jiki har ya ɗauki hanyar cimma burinsa. Sosai ta rikice masa dan a tsorace take da al'amarinsa. Shi kuma ya tabbatar mata da babu gudu babu ja da baya. Duk da yau bata sha wahalar waɗan can matakan ba yanzun ma dai taji a jikinta. Shi kuma yasha raki da langaɓe. Lallashi yay tayi shi dai kam tunda ya samu yanda yake so. Bai kuma wani ja dogon lokaci ba ya sake nuna muradinsa, sai ta sanya masa kuka harda cewa ita Nigeria zata koma bazata iya da shi ba gaskiya. Dariya yayta dannewa, bai kuma ƙyaletan ba sai da ya samu yanda yake so. Aiko yasha baƙar magana a wannan yini, harda cewa sai ta gaya shi da Uncle Yousuf da Ammah. Ya ko miƙo mata waya cikin gyatse ya ce ta kira. Amsa tayi zata kira ɗin kuwa. Yanzu ya sake tabbatar da wautar ɗiyan madara, dan sai fisge wayar yay ya ɓige da cema Uncle Yousuf ya kira ne su gaisa. Dariya Lulu ta koma yimasa harda gwalo, dan ita wasa take masa, yo hauka take tacema Uncle Yousuf ɗin mi ma. Ta kula kallon yarinya Smart yake mata, shiyyasa take zuba masa taɓarar yaran aje a hakan........✍️ _Kiyi son ranki Dan lokacinki ne ta wajen mu🥱😂😂🚴🚴_ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣4️⃣ .......Smart ya samu zama da Daddy da ya shigo London a ranar da Lulu ke cika kwanaki biyar. A ranar sun buga wasa a cikin London ɗin ne, bayan sun tashi ne sukai zaman tattaunawa su uku harda Uncle Yousuf da ya shigo domin kallon wasan shima. Daddy ya damƙa masa camara, tare da tabbatar masa Sulaiman yana shiri na musamman a kansu. Dan a yanzu haka akwai wata yarinyar baturiya da ya gano an turota ta shiga jikin Smart ɗin. Shiyyasa ma yay azamar kawo masa matarsa kusa da shi saboda gudun kar'a samu akasi. Murmushi Smart yayi da firzar da iska. Kansa a ƙasa ya ce, “Karka damu Daddy in sha ALLAH babu abinda zai faru. Kafin na mallaki iyali nafi ƙarfin kaina ma balle yanzu da na tabbatar da har zuri'a na fara tarawa. In dai al'amarin Sulaiman ne yabar damunka, dan a yanzu haka a tafin hannunmu yake. Abinda nake buƙata a wajenka kawai yanzu bayan wannan camara ɗin shine list ɗin abokan huɗɗarsa. Sannan ka sa su Hassan subar Abuja su koma Kano gabanku. Dan Sulaiman ya fara kai musu hari ta hanyar aboki, a yanzu haka ana gab da jan ra'ayinsu da wani kasuwancin da nake ƙyautata zaton irin shigo-shigon da akai maka ne”.       Sosai hankalin Uncle Yousuf da Daddy ya tashi, dan sam Daddy hankalinsa bai kai wajenba saboda wani babban business da ya dauki hankalinsa kwana biyun nan. Smart kuma bai sanarma Uncle Yousuf ba dan yakan ɓoye wasu abubuwan gudun tada musu hankali. Muryar Daddy har rawa take wajen faɗin, “Aliyu yaya akai kasan wannan kai da kake anan?”.     Murmushi Smart yay masa, cikin shafa kai ya ce, “Daddy koyarwarka ce ai. A yanzu idanuna a buɗe suke akan duk wani motsin su Sulaiman da tawagarsa. Sannan Usman ya sake zame min cctv camara. Dan yanzu haka yana Nigeria yin wani aiki da ya shafi hakan ma. Sannan Uncle Yousuf shine jagoran tafiyar,..”      Da sauri Daddy ya dubi Uncle Yousuf. Murmushi yay masa ya kauda kansa shima. Smart yay dariya shima da cigaba da cewa, “Mu yanzu fatanmu Daddy kaje ka kwanta abinka ka huta. Karka damu da duk wani ƙulle-ƙullensu dan biye muke da su. Yanzu haka a daren jiya sunyi zama kanka harma da Abba. Sannan akwai kayansu dake hanyar shiga Nigeria. Kayane masu nauyin gaske da suka haɗa kusan kaso bibbiyu na dukiyarsu domin kawosu, dan mugayen kayan shaye-shayen ne kawai a cikinsu da in har suka samu shigar da su zasu samu maƙudan kuɗaɗe. Target ɗin mu yanzu muna zargin Sulaiman nada Company na sarrafa magunguna a ɓoye, sai dai bamu san a ina Companyn yake ba, shine muke bibiya domin mu tabbatar...”         Ji Daddy yay kamar ya saki kuka, hannayen Smart da Uncle Yousuf ya kamo a cikin nashi, sai ma ya rasa mizaice da su. Sai ga hawaye kawai na gudu a fuskarsa. Da ga Uncle Yousuf har Smart rikicewa sukayi. A take suka shiga jera masa tambayoyi. Sai ya sakar musu murmushi yana goge ƙwallar tasa da faɗin, “Kunga bafa wani abu bane. ALLAH yay muku albarka. Ban taɓa tunanin zanga irin wannan ranar ba a gareni. Domin na ɓata tsahon shekarun girmana a tunanin yanda zan ɓulloma wannan al'amarin ne. A duk sanda nayi hangen sako su Hussain a ciki sai zuciyata ta ƙi aminta da hakan, saboda su sunada rauni. Sannan har yanzu suna a kan dokin ƙuruciya ne ba komai suke kallo a mai muhimmanci ba. Aliyu kai ɗan halak ne, nagodama ALLAH da yasa ka zamo mijin Mawaddat, na kuma godema ɗan uwana da yay wannan haɗin alkairi. ALLAH yay muku albarka. Ya kare rayuwarku da ta ahalinmu gaba ɗaya. ALLAH ya ƙara ɗaukaka ku, ku zama abin alfahari da babu irinsu a wannan zamanin. ALLAH ya albarkaci rayuwar Aliyu ƙarami da takwarana Isma'il (Ra'is) da Kamaluddeen, yasa suji ƙanku fiye da yanda kuka jiƙanmu”.         Cikin rauni Smart da Uncle Yousuf ke amsawa da Amin. Smart na ƙara jin ƙaunar surukin nasa na ratsashi. Ga Uncle Yousuf Daddy ya juya. A hankali ya furta, “Nasha gaya maka Yousuf kaine babana a wannan matakin, narasa baba ne kawai a suna, amma ga babana a kusa dani.....”      Cikin katseshi Uncle Yousuf ya ƙyalƙyale da dariya. Sai kuma ya rungumesa da faɗin, “Oh oh Yaya ni Wlhy kunya kake sakani, ni dai ba sai kace komai ba. Karka manta fa kaine na tashi nakema kallo a matsayin mahaifi kai da aunty Khareema. Kun raineni tun bansan kaina ba. Kun gatantani tun baku san minene daɗin ƴaƴa ba. Wlhy raina fansa ne a wajen kare ku daga duk wani maƙiyi da zaice kune abin harinsa. Ni dai fatana ka cigaba da kwantar min da hankalinka kawai da mana addu'a. Sannan ka janye mana ra'ayin su ƴan biyun kamar yanda Aliyu yace shine kawai aikinka.”      Kasa cewa komai Daddy yayi, Smart dake saurarensu yana murmushi ya ɗan fesar da numfashi yana ɗan jujjuya camara ɗin. “Inaga a wannan gaɓar ya kamata Mawaddat ta fara aikinta. Dan haka zan duba abubuwan cikin camara ɗin nan tare da ita. Sai dai ina jin tsoron al'amarin ta dan bata da haƙurin kawaici ma abu, zata iya buɗe mana aiki da wuri wlhy”.        Yanda ya ƙare maganar cikin marairaicewa ya saka Daddy da Uncle Yousuf kwashewa da dariya. Dan kuwa suko suka san wacece Mawaddat. Daddy yace, “Aliyu kamar kasan abinda nake tunani kenan ALLAH. Dan Mawaddat yanda kasan zawayi haka take. Ballema ta ƙullaci Sulaiman ɗin a yanzu, dan bakaga yanda taima Dada bane ba ma fa. Abinda kawai zamuyi shine da zarar kun gama gani sai mu samu lokaci mu zauna da ita mu duka kafin na wuce. Sauƙin ma ga babanta da ya san matakan bida ita yanda ya kamata sai kaga tayi abinda ake so”       Murmushi kawai Uncle Yousuf ya keyi shi dai. Yace “Ku gama gulmarta duk sai na faɗa mata ai, dama kun mata wayo kun kawota nan. kai kaine za'a hana tuwo”... Yau maganar yana nuna Smart.       Dariya Smart da Daddy keyi, Daddy yace, “Sauƙin abinma kaine gaba-gaba wajen ƙullawar dan nayi recording.”     Smart ya kasa daina dariyar waɗan nan mutane. Komai nasu a sauƙaƙe cike da ƙauna da soyayyar juna. Suna ƙara masa ƙaimi akan ƙaunar ƴan uwansa shima.....       _______★      A ɓangaren Lulu tun fitar Smart itama ta fice a gidan. Asibiti ta nufa saboda maganar Smart dake cimata rai akan shi baya saɓa saiti. Haka kawai take jin tsoro a ranta, ita yanzu ta samu ciki kuma ai taga bonu. Yaushe ma yaronta yay ƙwarin hakan. Bawai bata son yara ba, amma dai tafi son ko zata sake haihuwa sai AA ya kai irin 5years haka. Yanzu kam tana ina zata fara haɗama kanta cakwakiyar nan, ga business ga rainon AA, ga fitinar ubansa, ga rainon ciki da hidimar ƙungiya dana aikinta. Ta samu ganin likita, babu wani kwana-kwana tace planning zatayi, amma su fara tabbatar da babu wani abu a jikinta, duk da dai a ganinta haɗuwa uku bai zama lallai a samu wani abu ba, to amma idan tai la'akari da farkon haɗuwar aka samu cikin AA sai hankalinta ya sake tashi taji ta kasa yarda da kanta. Doctor dai ta mata dukkan abinda ya dace sannan ta bata magani, acewarta a iya bincikensu mahaifarta fresh take babu komai. Amma ga magani tasha koda ma an samu akasi marar zata sake wankuwa fass. Daga haka suka saka mata abu a jiki ta dawo gida tana jin hankalinta a kwance. Ta iske har lokacin Smart bai dawo gidan ba. Dan haka ta ƙirƙiri aiki dan zama waje ɗaya ya isheta. Tsaff ta gyara gidan tare da musu girkin Nigeria yau. Tana kammalawa tai wanka, kayanta da ya rage ɗaya tak ta saka ta dawo falo ta zauna dan AA tunda suka dawo barci yake abinsa. Ta shagala a kallo ya shigo gidan da sallama hannunsa ɗauke da kaya. Bata motsa da ga inda take ba ta dai zuba masa ido, shiko nashi idanun na kallon gidan ne da yanda aka gyara shi, aka canja zaman abubuwa da yawa. Gyaran mace dabanne. Ya ayyana a zuciyarsa yana ajiye kayan hannunsa a hankali. Kusa da ita ya kai zaune cikin yanayin gajiya ya ke faɗin, “Madam ya gidan?”.         Baki ta tura da faɗin, “Ni ALLAH idan baka daina cemin Madam ɗin nan ba zamuyi faɗa ko kaima na saka maka suna. Sai kace wata tsohuwa?”.      “Oh da yarinya kike ɗaukar kanki, ai kin tsufa tunda gaki da AA. Nan da shekara ashirin zaki ga anzo fara miki gaisuwar uwar miji”.          Dariya ta ƙyalƙyale da shi, ta ce, “Kai kuma Baban miji ko”.      Murmushi yayi yana ɗan girgiza kansa. Sai kuma ya lunshe ido ya sake buɗewa a kanta. “Ina boss ɗin gidanne naji shiru?”.         “Barci yake, shiyyasa nake hutawa ta ai.”     “Ai yanzu ga baban shi ya dawo hutu ya ƙare”. Yay maganar yana kissing kuncinta da kwantar da kansa a kafaɗarta. A hankali ta sauke numfashi da lumshe idanunta itama. Dan zuwa yanzu duk yanda taso cigaba da riƙe kanta salonsa na barazanar tonata ne. Ƙarfin hali ne kawai da taurin kai irin nata. A hankali ta ce, “Yaya wasan?”.         “Alhamdullah bakin ƙi zuwa kallo ba”.       “To ni Wlhy ban iya kallon ƙwallo bane”.    “Sai ki fara koyo ai”. “Zan ƙoƙarta in shan ALLAH kodan kai. Ni yanzu ma maganar da nake son maka shine jibi fa ya kamata mu koma”.          Batare da ya buɗe idonsa da ga rufen da suke ba ya ce, “Ina kenan?”.      A shagwaɓe ta ce, “Nigeria mana”. “Uhhyim yin me?”. Idanu ta zuba masa da mamaki, “Ya zakace yin me bayan kasan ayyuka na baro na taho nan, kuma ni da shirin sati ɗaya na taho ko kwana goma. Wlhy inada abubuwa masu yawa acan”.        Kaɗan ya buɗe idanunsa yana kallonta, tsahon mintina kamar bazaiyi magana ba sai kuma ya firzar da numfashi. Cikin deep voice ɗin nan nashi da babu wasa a cikin fitar sauti ta ya ce, “Mawaddat! Ke yanzu idan ance miki ki ƙara tafiya kibar mijinki sai ki tafi? Kiyi lissafi shekarar aurenmu ɗaya da wattani takwas kenan fa. Amma bamu taɓa zaman cikakken wata guda ba har yanzu. Idan ke baƙya jin damuwa da hakan ni gaskiya ina ji. Sannan haƙurina ya ƙare ina buƙatarku a kusa dani yanzu. Shekarunmu tafiya suke bakwai komawa baya ba, ko sai ƙarfina ya ƙare sannan zaki fiskanceni a gaɓar da bazan iya komai a gareki ba. Na waiga ma na ganku a kusa da ni farin ciki nake ji. A yanda nai wasa a fili yau kowa yasan ina cikin farin ciki mara misali, aure ibada ne fa bawai son zuciya ba ko ra'ayin kanka a yanda kaso tafiyar da shi. Dan haka maganar komawa na soke shi, ba yau ba, ba gobe ba babu ma rana kawai at all. Dan haka karma ki sake mun maganar data shafi hakan ranmu zai ɓaci ne kawai”. Ya miƙe fuska a tsuke ya bar falon zuwa bedroom........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣5️⃣ .......Da kallo kawai ta bishi zuciyarta na wani irin rawa da mamakinsa. Gaba ɗaya ya juye mata a kammanin da ta sanshi tun farko na dakewa da rashin son ɗaukar raini. Gaba ɗaya sai taji ma shakkarsa ta shigeta. Kusan minti uku tunaninta ya fara zurfi sai kuma ta miƙe, dan ganin ɓacin rai a tare da shi kuma duk sai take jin itama nata zuciyar babu daɗi. Bedroom ɗin ta shiga da sallama ƙasa-ƙasa, inda yake tsaye yana saka bathrobe a jikinsa ta nufa, dan har ya cire kayansa. Sallamar kawai ya amsa mata batare da ko kallonta yayi ba harta iso gabansa. Fuskarsa da ke kicin-kicin ta zubama ido, ganin bazai kalletan ba yasata kai yatsanta manuniya ta ɗan takaleshi a kafaɗa. Kautar da jikinsa yay, ta ƙara lakatoshi a hannu, ya sake kaucewa kamar wani ƙaramin yaro, sai kawai ta matsa ta rungumeshi ta baya ta ɗora kanta a saman bayansa tare da zagayo hannayenta saman cikinsa tana wasa da igiyar bathrobe ɗin kamar zata kwance. Idanunsa da ya lumshe saboda jinta a jikinsa ya ɗan ƙanƙame jin ta zagayo hannunta saman cikinsa, a hankali ya firzar da iska yana cije lip ɗin sa na ƙasa kaɗan da ƙoƙarin yana ƙoƙarin zame hannun nata amma sai ta sake ƙanƙamesa.        “Fushi kayi?”.     Ta faɗa a hankali. Shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya ɗan sake sauke numfashi da kama hannun nata ya zagayo da ita gabanshi. Mayatattun idanunsa ya zuba mata kamar yanda itama take kallonsa cikin tsakkiyar ido. Gira ta ɗan ɗaga masa tare da kanta, “Fushin dai?” ta faɗa tana kai yatsarta ƙirjinsa a saitin zuciyarsa ta shiga zagayawa da faɗin, “To ki huce hajiya zuciya”. Harararta yay da buge mata hannu yana sake ɓata fuska kamar wani AA. Sai kawai ta ƙyalƙyale da dariya da faɗawa jikinsa ta sake rungumesa.          “ALLAH in kana shagwaɓa kamar AA najin yunwa fa”.     Duk yanda yaso cigaba da riƙe kansa ya kasa. Murshi yayi yana ɗan lumshe ido da dungure mata kai, sai dai baice komai ba. Dan haka ta fara masa cakulkule. Dole ya fara dariya da ƙoƙarin janye jikinsa amma taƙi barinsa, sai ma baya yake tana binsa har suka faɗa saman sofar ɗakin. Bata daina ba duk rokon da yake mata sai da ta tabbatar ya jigata sannan ta barshi tare da faɗawa kansa suna dariya su duka.         “ALLAH ke muguwa ce”.     Ya faɗa yana ja mata hanci. Amsa ta bashi da “Ai kai ka koya min dan kaine malamin koya mugunta ma”. itama tana dungure masa kai. Sai suka sake ƙyalkyalewa da dariya.             “Kin fara nauyi ALLAH, ɗaga ni karki fasa min ciki”.          Fuska ta ɓata da duban kanta, sai kuma ta hararesa da faɗin, “Ta ina na ƙara ɗin? Ni ALLAH bana son sharri”. Kallo ya bita da shi irin a ɗan ɗagen nan, sai kuma ya nuna mata yana gimtse dariya. Inda ya nuna ɗin ta kalla. Da sauri tace “ALLAH zai saka min” tana kai masa duka da filo. Ƙoƙarin riƙewa yake tana dariya da faɗin, “Daga faɗar gaskiya. To shikenan na yarda baki ƙaraba. Ƴar ƙanwata na nan yanda take ƴar sawalwala abinta cas-cas”. Sauka tai da ga jikin nasa ciki nuna irin nayi fushinnan, shima sai ya miƙe da sauri ya riƙota tare da ɗagata gaba ɗayanta suka fice a ɗakin. Tana zille-zille da faɗin ya sauketa bai kulata ba ya fita ta baya inda swimming pool ɗinsu yake. Direta yay a bakin ruwan ya cire bathrobe ɗin jikinsa yay hanging a kan ɗan ƙarfen da aka saka domin hakan kawai dama. Da sauri ta kauda idanunta da ga kallonsa, dan har yanzu ta kasa iya daina jin kunyarsa, duk da bawai haka nan yake ba akwai ƙaramin boxer jikinsa bazata iya jurar kallon nasa ba kai tsaye a haka. Shima komai baice mata ba sai murmushi da ya saki kawai, cike da kwarewa yay tsalle da sufa irin na masu wasa da ruwa cikin ruwan. Yanda ya fantsama ciki sai da ruwan ya tarwatso mata a jiki har a fuska. Fuskar ta kwaɓe tana kallonsa kamar zatai kuka, shi baima san tana yi ba sai da ya kai ƙarshe zai juyo ya kula. Dariyar mugunta ya kwashe da shi, sai kuma yay ƙasa cike da kwarewa ya sake dawowa gabanta ya miƙe tsaye yana dariyar da ɗibar ruwan a hannu ya sake watsa mata a fuskar. Lulu ba haƙuri idan akai saita rama. Hannu takai itama zata ɗibo danta rama ya fisgota ta faɗo ciki. Kokawa suka fara a ruwan yana kunnata da dariya, sai kuma yay mata gwalo yay ƙasa cikin ruwan. Itama da sauri ta nutse ciki ta bisa saikace wasu kifaye...       Sun jima a cikin ruwan suna nishaɗin su kafin suka fito saboda tunawa da AA shi kaɗai a ɗaki. Bathrobe ɗin da yazo da ita ta saka, sannan taje ta ɗakko masa wata shima. Tun shigarta ɗakko masa rigar ta samu AA ya tashi, dan haka bata zauna jiransa ba ta juya ciki. A ɗakin ya sameta tana cirema AA kaya, yana ganin shi ya shiga miƙa masa hannu dan yanzu ya daina masa ƙiwa. Shima cikin farin ciki ya ɗauki abunsa yana mai sumbatarsa da faɗin, “Oh oh Baban Ammah ya tashi kowa ya ɓoye kayansa kafin a cika musu aiki”. Cikin dariya Lulu tace, “Aikam dai, dan yanzu zai fara haɗa gwaramar tasa”. “Ai ke ya gado, dan Uncle Yousuf ya cemin kema kina ƙarama hummm”. A shagwaɓe ta ce, “Shi Uncle You ɗin ya faɗa, ni dai ALLAH babu ruwana salaha da ni, sai dai kai dan dama Ammah tace tasha rashin jin ka”. Shima fuskar ya ɓata da faɗin, “Sharri ba haushi zanji ba ai” daga haka ya nufi bedroom da AA a kafaɗa domin yimasa wanka. Dan yanzu in har yana gida kusan komai shikema yaron, acewarsa yana koyane koda ta haifo ƴan uku basai sunje neman Nanny ba. Takan hararesa kawai idan yace hakan.....       ★ Zaune suke a wajen cin abinci yana cin abincin da tai masan idanunsa a lumshe alamar dai yana jin daɗin sa, itako sai murmushin farin ciki takeyi. Dan a yanzu babu abinda ke sakata a farin ciki sama data gansa cikin farin ciki. Batai zaton zaici abincin haka da yawa ba, sai gashi ko yaci sosai har yana faɗin jikinsa yay masa nauyi. Bayan ya kammala ta gyara wajen suka koma falo. Zama yay yana wasa da AA ita kuma ta kwashe kayan da ya shigo da su zuwa ciki, na kitchen kuma takai kitchen. Sosai taji farin cikin ganin kayan sakawa ne ya siya mata, sai turarruka na mata masu daɗin ƙamshi duk da tazo da su khumra da turarrukanta abinta. Sai kayan kwalliya da batazo da su ba, shima AA an saya masa nasa. Tana cikin kwashe kayan taci karo da camara. Tsai tai tana kallo da jujjuyata a hannu, sai kuma ta ajiye cikin taɓe baki ta cigaba da gyara kayan. Sai da ta kammala tsaff ta ɗauka camara ɗin ta koma falo da ita. Kwance yake a ƙasan carpet yana waya da Ahmad, AA na gefensa yana wasa da kayan wasansa, yanda ya nutsu sosai ya tabbatar mata da magana suke mai muhimmanci, dan haka ta kai zaune Camara ɗin a hannunta tana kallonsa shi da AA ɗin cike da jin farin cikin su ɗin duk nata ne fa. Abinda ya ɗan fara jan hankalinta ga wayar tasa shine kalmar daya ambata cikin yanayin ɗan ƙaraji har yana tashi zaune. Sosai ta zuba masa idanu, yayinda shi kuma ya cigaba da faɗin, “Kaga Ahmad relax please. Karka ruɗar da kanka, ni dama nasan dolene wannan binciken ya tono mutane da yawa a ciki, aiba abin mamaki bane ba hakan karma ka tada hankalinka a banza. Yanzu abinda zamuyi shine dole mu tafi mataki na biyu, wato plan B.”         Cikin matsanancin ruɗani da ga can Ahmad ya ce, “Dole ne hankalina ya tashi Aliyu. Mahaifin aunty Khadijah fa! Kasan kuwa yanda nake ganin mutunci da kimar mutumin nan, amma ace har da shi a cikin mutanen nan. Kasan kuwa irin muggan miyagun kwayoyin da yaron nan ya sanar min ana saidawa a pharmacy ɗin nan! Ban taɓa sanin haka ƙasar nan tamu ta lalace da rashin doka da bin ƙa'ida ba sai yau. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un”.         “Humm Ahmad kenan kana wasa da mutanenmu. Abinda yasa kake ganin irin waɗan nan abubuwan abin mamaki saboda rayuwar daka tashi ne. Amma mu da aka haifa a getto eria muka rayu a ciki munsan irin waɗan nan abubuwan fiye da yanda kake zato, kawai dai mutum dan baida ƙarfin ɗaukar matakine shiyyasa. Ni dai abinda nake so da kai yanzu dolene fa ka sake ƙara ɓoye kanka, dan ko Yaya Hameed da Uncle Yousuf ban san susan da hannunka a ciki, shiyyasa ma kaga nace Uncle Yousuf ɗin yabar komai a hannuna shima saboda suma suna huɗɗa da mafi yawan manyan ƙasar, zamu iya zuwa gaɓar da al'amarin wani zai girgizasu su buɗe mana aiki”.         “Hakane Smart na fahimceka yanzu, kuma in sha ALLAHU zamu basu mamaki, tabbas mune matasa ya dace muyi hanƙoran gyara ƙasar nan tamu akan wannan mummunar safarar dake cigaba da yaɗuwar gurɓatamu tamkar wutar jeji a kasarmu, in ba haka ba sai anzo lokacin da babu wani matashi da zai iya amfanar kansa balle wani ko ƙasar, zasu cigaba da mana illa ta hanyar dafe madafin iko su barmu da raɗaɗin shan miyagun ƙwayoyin da suke mana safara mu kuma muna sha da tunanin rage raɗaɗi, wlhy Smart naji na tsanesu, natsanesu, su azzalumai ne.....” Kukan da ya tahoma Ahmad ya hanashi ƙarasawa, shiru kawai Smart yay yana saurarensa shima zuciyarsa na ƙuna. Tuni idanunsa sun gashe zuwa jajur. Yana jin raɗaɗi fiye da wanda Ahmad yake ji, tun yana yaronsa ya tsani shaye-shaye, baya son yaga anayi, yana jin ciwo matuƙa idan yaga matashi ya lalata rayuwarsa da shaye-shaye, shiyyasa cikin ƙanƙanin lokaci al'amarin Lulu yay tasiri a zuciyarsa. Da ƙyar ya iya furta, “It's okay Ahmad. Kuka bashi ne magani ba, aiki tuƙuru domin ganin mun karya su. Sannan inaga dolene zamuyi amfani da ƙungiyar Mawaddat a wannan gaɓar domin tattarro hankalin matasa dan wannan aikin yana son taron dangi ne. In ba hakaba zaƙulosu da muka ɗauka ɗammarar yi bazai magance mana matsalar ba tunda zasu iya sayen hukumomi da kuɗi kasancewar wasu a cikinsu suma ruɓaɓɓune”.         “Tabbas haka ne nima nayi wannan tunani, kuma na yarda da shawarar nan naka. Sai dai yanzu ban san yaya zamuyi ba tunda kaga ita tana nan”.     Cikin ɗan ɓata fuska da kallon Lulu ta gefen ido ya ce,,......✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣6️⃣ .......“Ni kuma gashi gaskiya bazan iya baku Matana ba yanzu dan kaima dai kasan ango nake”.          Dariya Ahmad ya kwashe da shi da faɗin, “Ɗan iska shegen sama. Banza ta faɗi ko anata kwasar romon dimakuraɗiyya. Sai kaita riƙo ai ko tana nan zata mana aiki”.      “Shegen sa idon ka dai a kanka zai ƙare. Sai dai fa daga nan ɗin dan mai kawo min mata Nigeria yanzu ban gansa ba”. Ya ƙare maganar yana kashema Lulu dake kallonsa ido. Kanta ta ɗauke tana ɗan murmushi da harararsa. Dan ita ta ƙagara ya kammala wayar ya mata bayani. Sun sake tattaunawa sosai da Ahmad ɗin kafin suyi sallama. Yana yanke wa kiran Uncle Yousuf na shigowa. Tashi yay yabar falon ma gaba ɗaya, Lulu ta bishi da kallo cikin jin tsarguwa. Bai jima ba sai gashi ya dawo. Ganin yanda ta turɓune fuska ya sashi zuba mata ido.         “Lafiya kuwa Madam?”.    Baki ya taɓe da ɗauke kanta gefe. A hankali ya kai zaune kusa da ita yana mai kamo fuskar tata. “Please miya faru kar kiyi fushi mana.” harara ta sakar masa da buge masa hannu tana son tashi, yay saurin riƙota ta faɗo jikinsa. Rungumeta yay da ƙyau ta yanda bazata iya tashin ba. Cikin tallafo kanta da ɗaura goshinsa a saman nata ya ce, “Please Baby luv, kin san fa da fushinki gara kawai a tada yaƙin duniya na uku. Faɗamin minene?”.          “Ba kai bane kake ta wani ɓoɓɓoye abu dan kar naji”.      “Haba ni na isa. Kikama san Aliyu ciki da bai ɗinsa balle abinda ke a zuciyarsa. Dama fa zan yi maganar dake”.      “Babu wani ban yarda ba. Bayan tun randa mukazo kaketa wani magana da Ahmad a cuccure, hakama idan Uncle Yousuf ya kiraka sai ka koma gefe ko Daddy”.             “To yi haƙuri bazan sake ba. Bani ɗan lokaci yanzu zan miki bayanin komai dan kema kina daga cikin tawagar ai. Dama ba'azo gaɓar da naki aikin zai fara bane kawai shiyyasa. Haɗamin coffee yanzu ina zuwa”.       Babu musu ta miƙe zuwa kitchen, ya bita da kallo har sai da ta shige sannan ya tashi yana sauke ajiyar zuciya. Bedroom ya shiga, babu jimawa ya fito ɗauke da laptop a hannu da Flash drive kusan huɗu. Centre table ɗin falon ya jawo gabansa sosai yana kaiwa zaune da zube kayan hannunsa, sai lokacin idonsa ya sauka akan camara ɗin data ɗakko. Ɗauka yay ya ajiyeta a gefe yana girgiza kansa, sai gata ta fito ɗauke da ƙaramin tray da coffee 2cups sunata turiri.. gefensa ta zauna tana ajiye masa nasa gabansa itama ta ajiye.       “ALLAH yay miki albarka”.   Ya faɗa yana ƙoƙarin saka flash a jikin Laptop ɗin. Cikin jin daɗi da farin ciki ta amsa masa. Dan a duk lokacin da yace ALLAH yay mata albarka tana matuƙar jin kanta on top ne. Sai da ya gama saita komai ya kalleta. “Ina son ki nutsu sosai dan maganar da zamuyi mai matuƙar muhimmanci ce”.          Kanta ya jin jina masa da sake maida hankali garesa sosai. Cikin nutsuwa shima ya fara mata bayani ta yanda zata fahimta tun daga randa Daddy ya fara aiki a maikatar da Alhaji Sufi Garko ke shugabanta, wanda a dalilin haka ne ya ja Daddy a jikinsa, a maimakon aikin gwamnati ya maidashi akan harkokin kasuwancinsa. Yanda abubuwa suka dinga tafiya har zuwa sanda kuɗi suka ɓata da shiga jikinsa da Sulaiman ya farayi ta hanyar nuna masa zai taimakesa da kasuwancin da suka fara tare har zuwa sanda ya fahimci abinda ke cikin business ɗin da haduwar Daddy da mahaifiyarta, da abinda ya faru a dalilin aurensu, fyaɗen da Alh. Sulaiman yay ma Sultana da yanda Daddy ya tayashi ɓoye sirrin zamansa da mahaifiyarta, rasuwarta, mutuwarta, ɗauketa a Nigeria har zuwa girmanta, shigowa rayuwarta da yayi dama kamun da Alh. Sulaiman yay masa har zuwa aurensu da buɗe musu ciki da Daddy yayi akan komai da dalilinsa na ɓoyewa. Yanayi yana nuna mata abubuwa a laptop ɗin nashi, yawanci duk wayoyin barazana ne, da wasu harƙalloli tsakanin Daddy da Alh. Sulaiman ne, dama hotunan abokan da sukai huɗɗar kasuwanci da Daddyn ya adana matsayin hujjar da ya dinga tsorata su Alh. Sulaiman da tawagar su Nakowa da ita. Tunda ya fara Lulu ke kuka na tashin hankali, har takai AA ma ya fara kuka sai da Smart ya ɗaukesa ya ɗaura a cinya. Jikinta tsuma yake matuƙar tsuma, idanunta sun masifar kumbura saboda kukan da taci. Cikin damuwa ta ce, “Na cikin camara ɗin ma dan ALLAH ka nuna na gani”.        “Ba yanzu ba”.    Ya faɗa yana jawota jikinsa ya rungume cikin lallashi. Sai ta sake tsage masa da kuka. Muryarsa a raunane shima kamar zai saki kukan ya ce, “Please mana ya isa kukan haka kinji, mugodema ALLAH tunda babu abinda ya faru da shi. Duk da ina ji a jikina da saka hannun Sulaiman a zuwan Felix gareki, hakama su Alace da Luna da suka koya miki shaye-shaye ina zargin sakasu akayi mawaddat duk da dai bani da tabbaci.”       Kanta ta sake turawa a jikinsa tana kuka mai cin zuciya. Duk sai hankalin Smart ya sake tashi. Dole ya rufe laptop ɗin ya maida hankali a lallashinta da bata baki. Duk yanda taso suga abinda ke a cikin camara ɗin a yau yaƙi yarda. Da yaga ta damu sai yace mata dole sai an kwashe abinda ke cikinne zuwa flash shiyyasa. Badan ta yarda da shi ba ta haƙura, sai dai ta ɗauka waya tai kiran Daddy. Yanda yaji tana kuka shima sai hankalinsa ya tashi, cikin ruɗewa ya shiga lallashinta da tabbatar mata tayi haƙuri zuwa gobe zai shigo birnin London shi da Uncle Yousuf. Hakan ya ɗan sakata jin sassauci, dan babu abinda tafi buƙata a yanzu sama da taga Daddyn a kusa da ita. So take ta sake tabbatar da babu abinda ya samar mata shi. Uncle Yousuf ma ya amshi wayar ya lallasheta, hakan ya ɗan ƙara saka mata jin sauƙi, bayan ta yanke wayar ta shige jikin Smart tana hawaye. Murmushi yay yana mai ɗagota, cikin zuba mata idanu ya kai lips ɗinsa kan nata a hankali. A nutse ya canja yanayin nasu zuwa wani abu daban, babu kunya a falon akai yaƙin ƙasa-da-ƙasa, sai dai ƙura ta lafa kuma ta koma jin nauyi. Shi kuma yana mata dariya da tsokana wai dama abinda take so kenan ashe. Itama dai yanzu ta zama babbar mayaƙiya. Tashi tai ta bar masa falon bayan ta gama mimmitsinesa da bubbuga masa filo. Da kallo ya bita yana mai jin ƙarin ƙaunarta mai faɗi da girma na sake mamaye sa tako ina. Da ga ƙarshe ya miƙe da ƙyar ya bita bedroom ɗin. Bathroom ya nufa inda yake jinta sukayo wankan tare. Shine ya koma falon ya ɗakko AA da ke barci. Suma dai kwanciyar sukai domin hutawa ransu.....          *_NIGERIA_*     Sau biyu ana ɗorata amma ƙashin ya gagara zama saboda tanada ƙiba, gashi a cinya ta karye. Su kansu malaman asibitin lamarin neman fin ƙarfinsu yake. Ƙaninta dake tsaye kan lamarin nata ne ya yanke shawarar su nemo masu ɗorin gargajiya. Dan mijinta tunda yazo zuwan farko asibitin yaji irin sambatun da takeyi da tona ma kanta asiri ita da aminiyar tata da ayanzu kowa ke kira da Dodo ransa yay masifar ɓaci. Ashe itace ta rabashi da matarsa mai sonshi dan ALLAH tun bashi da komai, sannan ta rabashi da manyan ƴaƴansa da sam yanzu ko kallon arziki bai musu da ma danginsa. Hatta da karatunsu bai saka hannu ba gashi yanzu duk ALLAH ya tallafesu sun samu ayyukansu. Ranar yayi kuka da hawayensa da yin dana sani. Yana zaune da matarsa lafiya ƙyale-kyalen Naqiba da suka haɗu a wajen aiki ya kwashesa har yana kushe matarsa akan bata iya komai ba sai gidadanci saboda kawai batai zurfi a ilimin boko ba. Shagalin biki akai na alfarma lokacin ya zubda kuɗi tare da sakata a danƙareren gidansa da ya gama gini. Itace ta gaban mota idan zai fita, itace ta zuwa jahohi idan aiki ya kaisa, acewarsa itace mai ilimi. Duk da bawai wani mahaukacin kuɗi ne da shi ba yanada rufin asirinsa dan har Saudiyya yaje kusan sau uku, kuma duk tare da matar son nasa Naqiba. Yakan je Dubai kuma saro kaya a yanzu haka, dan yanada manyan shaguna a cikin kasuwar kwari. Yakan yima Naqiba abu sau sama da goma kafin yayma matarsa da ƴaƴansa, a haka har suka haihu ɗaya da ita, dan Maheer kawai ta haifa sai mace ita kuma ta rasu tun tana 3years.... An sake ma Hajiya Naqiba ɗorin gargajiya da taci uwar azaba harda sumanta. Bayan farfaɗowarta ne ta cigaba da sambatu kamar zautacciya. A wannan halin su Abba da sukazo dubata saboda a gidansa ta samu matsalar, yana ta son zuwa sake dubata tun randa suka kawota asibiti tashin hankalin Ummah ya hana shi. Sai yau ne yaga ya dace yazo kar ai abin kunya shine ya kwaso su Abdull suka zo. Anan ne kunnensu ke jiye musu sambatun Hajiya Naqiba da ke fallashe sirrinsu. Ba Abban kawai ba hatta su Mubarak ji sukai ƙasa na neman kasa ɗaukarsu. Bakin Hajiya Naqiba bai mutu ba sai da akai mata alurar barci mai ƙarfi. Tuni Abban ya baro ɗakin ko sallama bai iya yima danginta dake cike da ɗakin suna faman mata ALLAH wadai ba. Cikin sauri yaransa suka take masa baya. A wannan tashin hankalin suka dawo gida, sun iske Yayan Ummah Jibirin ya sake zuwa da wasu malaman yau ma. Sai dai suna jira Abban ya dawo a tunkari Ummhn.           Duk hayaniyar da akeyi Umma na jiyosu da ga falonta, sai dai furucin Abba yasa a yanzu bata iya fitowa ko tsakar gida, dan ya tabbatar mata idan ta sake fitowa ta firgita masa iyali batare da shi yace ba a bakin aurenta. Wannan kalma na ɗimautata a duk sanda ta sake maimaita kanta a ƙwaƙwalwarta. A cikin abinda bai wuce sati guda ba duk tayi wata irin firingau-firingau da ita. Tai muguwar rama kamar mai cutar sida. Kuka kam idanu sun daina sai dai na zuciya. Tunda take ko'a labari bata taɓa sanin akwai makamancin irin tashin hankalin nan nata a duniya ba. Ita a yanzu ma neman hanyar zuwa ga malamin da yay aikin take ya karya shi amma babu hali, tsakar gida ma ya gagari mutum balle ƙofar gida har akai ga shiga mota. Abincin tana cinsa ne kawai dan tsoron mutuwa. Amma badan yunwa ba. A duk sanda ta jiyo muryar Ammah dai ta fashe da kukan baƙin ciki na tsananin jin kishi. Tana jin raɗaɗin tayaya za'ai ace Ammah taci nasara a kanta kenan? Itace fa Yahanasu mai yawan ƴaƴa maza a gidan fiye da kowa, ƴar uwar mai gidan jininsa, tafi kowa yawan ƴaƴa, ita ta fara haihuwa a gidan, tanada power ɗin juya miji a tafin hannunta koda daga baya zai suɓuce mata zata sake nemo hanyar riƙosa. Kowa a waje gani yake itace ke juya gida da miji, amma a kullum sai Hafsatu ta zama sanadin rusa mata plans nata. A kowace safiya tana ji kamar ta kashe matar nan ko zata ji sassauci na zafin tsanar da take mata. Kuka irin mai ƙona zuciya ɗin nan ya suɓuce mata, sai dai babu ɗigon hawaye a cikin idanun sai zafin zuciya da gwara ma kaita hawayen........✍️ _🥱🥱Jiya kunji shiru ko. Ina nan na dage muku da typing ne nima na ƙagara mu gama🚴🚴._ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣7️⃣ .......A gidan Alhaji Garko kam ALLAH ya sauki amarya lafiya, ta silloɓo ƴan biyunta duk maza har guda biyu masu kama da Baba Garko da ƴan uwansu. Farin ciki a wajen Baba Garko da ma'aikatan gidansa ba'a magana. Babu ko ɗar balle jin kunya ya ɗaga waya yay kiran Dada a farko. Rabon da ya kirata a waya harta manta a rayuwarta, duk da halin da take ciki jikinta har rawa yake wajen ɗauka. Dan addu'a take a ranta ALLAH yasa baƙar dagar ce ta mutu ita da cikin. Sai dai me tana kaiwa kunne kalma ta farko da ga bakin mijin nata, abin sonta da sukai ƙuruciya ga su a tsufa tare itace, “Alhamdullahi ALLAH ya sake azurtani da yara biyu MAZA masu kama da ni kamar sauran ƴan uwansu. Sai ki shirya kayan tarbar sabbin ƴaƴa Hajarah”. Da ga haka ya yanke kiran kamar dama da gayya yayi, hakan yay dai-dai da tsayawar numfashin Dada da tunda ya fara maganar yake fita dama a fisge. Yaraf ta sulale a wajen ta zube babu numfashi..... (🥱DADA team sai ku kai ɗauki🚴).        _________★     Kamar kullum pharmacy ɗin cikin hada-hada da kai-kawon mutane yake. Dan babban pharmacy ne da duk kalar maganin da kake nema ko kayan anfani da ya shafi lafiya zaka sameshi. Ga shi akan babban titin da mutane ke yawaita kai-kawo sosai kuma. Ba sayen ɗai-ɗai kawai suke ba har sari suna badawa wa ƙananun camix ma. Banda ɓoyayyun masu amsar miyagun kayansu da ko yaran shagon ba kowa yasan ana harƙallar ba sai amintattun ciki da masu lura, sai dai kosun luran babu damar magana dan anfi ƙarfinsu.           Duk da safiyace akwai mutane sosai musamman masu sari. Basu wani damu da jin dirar motocin ƴan sanda ba a ƙofar pharmacy ɗin kowa ya cigaba da abinda yake yi. Sai dai me motocin ƴan sandan na gama dira ta NDLEA suka dira suma har mota uku. Sai a lokacin hankalin mutane ya fara dawowa jikinsu, sai dai kafin yin wani yunƙuri jami'an gaba ɗaya sun rufe ƙofar pharmacy ɗin. Sauran kuma sun afka ciki. Gaba ɗaya mutanen ciki an tattaresu zuwa mota, hakama ma'aikatan an tisa ƙeyarsu cikin store ɗin wajen wasu kuma cikin pharmacy ɗin. Duk tambayar da suke akan su mi sukayi babu wanda ya basu amsa. Jikin Manager ɗin wajen har rawa yake wajen ƙoƙarin kiran layin oga kwata-kwata ya sanar masa.      Duk da hankali Alhaji Sadi Dikko Baduku ya tashi da jin wai NDLEA a pharmacy ɗin nasa sai cikin rashin damuwa da gadarar masu arziƙi ya buƙaci yaron nashi ya bama ogansu waya. Cikin jin ƙwarin gwiwa Manager ya nufi wanda yake ƙyautata zaton ogan nasu ne ya kai masa wayar. Kallon sama da ƙasa mutumin yay masa tare da daka masa tsawar da sai da ya zabura. Ba Manager ba hatta shi kansa Alhaji Sadi Dikkon sai da ya zabura. Mamaki da al'ajabin wane ɗan iska ne wannan ya sashi yanke kiran, da sauri ya shiga neman shugaban hukumar NDLEA na Kano baki ɗaya, sai dai har wayar ta gama ring ba'a ɗauka ba. Sake kira yay aka danna masa busy alamar an yankesa. Anan ne fa hankalinsa ya fara tashi, da sauri ya shiga neman number Hon. Nakowa.....          *_UK_*     Kasancewar yau bashi da wasa suna nane a gida suna zubama juna taɓara. A yanzu haka zaune Lulu take gaban Mirror Smart tsaye a bayanta wai yana mata gyaran gashi. Yayinda AA yay busy a ƙasa da kayan wasansa cikin kuzari da lafiyar da ALLAH ya bashi. Dan yanzu haka Alhmdllh yana miƙewa har ai taku ɗaya zuwa biyu musamman idan idanun iyayen basa kanshi. Idan ma sun gansa sai ya koma ya zauna kamar dai yanda akasan yara masu koyan tafiya kanyi na rashin son a musu ihu yayinda suka miƙe. A hankali Lulu da ke kallon hotunan Smart a waya ta ɗago idanunta jin kamar ya daina motsa hannun nasa a saman kan nata. Cikin mamaki ta ɗan waro idanunta da faɗin, “Lafiya kuwa? Tunanin mi kakeyi haka?”.     Shiru babu alamar Smart ya jita, dan sosai yayi zurfi a tunanin nasa. Wayar ta ajiye tare da juyowa tana fuskantarsa, sai da ta riƙo hannunsa cikin nata ne ya sauke ajiyar zuciya. Hannun nasa taja zuwa wajen gado, babu musu ya bita. A bakin gadon ya kai zaune, ita kuma ta tsugunna a tsakanin ƙafafunsa hannayenta dafe a cinyoyinsa suka zubama juna idanu. “Mike damunka haka kake irin wannan tunanin Mr A?”.       Murmushi yayi a karo na farko, dan ya fahimci a kwana biyun nan bata iya kiransa da Aliyu kamar yanda take yi, ya ɗa furzar da iska kaɗan da kai hannu ya gyara mata gashin da ya sakko mata a gefen ido. A hankali ya furta, “Ba komai fa tunaninki kawai nake yi”.            Hararsa ta ɗan yi cikin girgiza kai, sai kuma ta marairaice fuska kamar zatai kuka. “Ina kusa da kai ne zakai tunani na. Ni ban kai na san matsalarka ba ko?”.       “Ke kikafi kowa cancantar sanin matsalata ai Baby luv”.    “Ban yarda ba tunda gashi ka kasa gaya min. Ni kuma duk sirrina babu wanda baka sani ba”.        Murmushi ya sake sakin mata da ɗan lakace hancinta. “Nima ai duk kin sani. Dan babu wanda ya kaiki sanin Aliyu a yanzu ciki da bai ɗinsa.”             “Ni ban yarda ba”.        “To mi kike son ji?”.    “Damuwarka”. Hannunta ya kama tare da ɗagota ya zaunar a saman cinyarsa. Sai ya rungumeta sosai yana sauke ajiyar zuciya. Kusan minti ɗaya suna a haka sannan ya sassauta mata yana kwantar da kansa a kafaɗarta. “Baby luv abubuwane suna neman yin yawa a tsakanin nan. Na fahimci sam gidanmu babu kwanciyar hankali ga kowa musamman ma Abba da Ammah. Suna ɓoyemin ne kawai amma lamarin Ummah na damunsu. Nima da nake anan ɗin yana damuna, shiyyasa nake jin da inada dama zanje Nigeria a tsakanin nan gaskiya. Ga batun mutumin nan, nasan hatsabibine bana wasa ba, zai iya bin hanyoyi da yawa dan ganin ya cuta mana.”          Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, sai kuma ta saki murmushi da shafa fuskarsa, wasa ta cigaba da yi da gashin ƙasunbarsa a hankali. “Humm ni dai ka kwantar da hankalinka. Na farko dai batun wata Umma ma ka ajiyesa gefe ita ta jama kanta damuwa da ita baida wani amfani. Na biyu mune ya kamata mu kwantarma da Abba hankali shi da Ammah dan suna damuwa ne saboda abinda duk ya faru a kammu akayisa. Sulaiman kuwa shi ba komai bane a yanzu takansa ma yakeyi. Amma kamar yanda ka faɗa kam zai iya yin komai da ga sanda ya farga ruwa ya ƙare masa. Dan haka komai yana buƙatar ayisa cikin gaggawa a yanzu gaskiya”.         “Kema kinzo da shawara kam. Sai dai kin san kamashi a yanzu kai tsaye bazai yiwu ba duk da muna da hujjoji”.      “Eh hakane, muna buƙatar gaɓa. Ma'ana a kamashi cikin wani laifi dumu-dumu irin wanda baida mafitar nan. Wannan shine zai sa a cigaba da zaƙulo laifukansa na ɓoye. Shiyyasa ka daure ka barni na koma Nigeria. Aikin nan yana buƙatar fuska da fuska ne fa”.             A take fuskarsa ta tsuke, babu alamar zai ce komai. Kansa ta ɗaga da ga kafaɗarta tana mai zuba masa idanu. “Wai kai ance maka zan gudu ne. Ina fa gama abinda nakeyi zan dawo ALLAH kuwa. In dai gudu ne kasa a ranka ka ƙaremin nawa yanzu babu sauran wajen ɓuya. Idan ma nace zan barka ai Uncle Yousuf da Daddy sai sunyi farfesuna koma su tauneni ɗanya. Kasan irin matsayin da kake da shi kuwa yanzu a gidan mu. Ai ko Ummita dana sani a baya-bayan nan defender ɗinka ce ta gani kasheni.”         Kallonta kawai yake shi dai, kafin ya samu damar cewa wani abu kira ya shigo masa waya. Ita ta miƙe zuwa mirror ta ɗakko. Gannin Daddynta ne ta ɗaga tana kaiwa kunne.     “My Son!”. Daddy ya faɗa daga can. Cikin ɓata fuska tamkar tana gabansa ta ce, “ALLAH ya soni nima ina da Ammah da Uncle You da Abba da Mommy, ga Baba Garko”.         Sosai Daddy ke dariya. Ya ce, “Oh oh irin wannan gori haka Mawaddat. To ai ALLAH yasa ma Baba Garkon nawa ne ɗan sammiki nayi. Kinga sai ki ƙarata da iyayenki nima ki barmin nawa da kuma yaro na”.      Dariya tayi itama da faɗin, “Ai nafa bar maka Daddy ku ƙarata.”    “To shike nan ƴar albarka. Ki faɗawa mijin naki gamu nan tafe in sha ALLAH. Ina fatan dai yana gidan?”.          “Lah Daddy wai nan zaku zo? Dama kana London”. Ta ƙare maganar cikin shagwaɓa. Murmushi Daddy yayi da ga can har tana iya jin sautinsa. “A'a yau dai zamu shigo, ina Manchester.”      “To Daddy ALLAH ya kawoku lafiya, mizan dafa muku?”.       “Basai kin dafa komai ba ƴar Daddynta. Muda bazamu jimaba ma. Bye bye sai munzo”. Ya yanke wayar kafin tace wani abu. Bata damu ba ta zauna kusa da Smart da ke kallonta tana murmushi. “Mr A dama Daddy zasu zo shine baka sanar min ba?”.           Murmushi kawai yay mata baice komai ba. Itama sai ta dungure masa kai tana miƙewa. Fita tai a ɗakin zuwa kitchen ta barsa shi da ɗansa.....       ★Tarba ta mutuntawa Daddy da Uncle Yousuf suka samu, shi Daddy wannan shine zuwansa na farko, Uncle Yousuf kam ɗan gida ne. Sun ci abinci a tare cikin farin ciki. AA na nane da Daddy dan akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu. Kasancewar ba wani jimawa akai da rabuwa ba bai manta kakan nasa ba. Bayan sunci sun sha sukai zaman abinda ya tarasu. Tsakanin Lulu da Daddy sun ɗan ƙara tattaunawa akan abinda ya faru tsakaninsa da Sulaiman da Mahaifiyarta. Yanzun ma sai da tai hawaye. Ashe babban kuka na gaba, dan lokacin da suka fara kallon abinda ke cikin camara ba Lulu ba hatta Smart da Uncle Yousuf sai da sukai hawaye. Daddy kam ƙasa kawai yay da kansa yana mai jin kewar matar tasa. Kuka sosai Lulu keyi na fitar hankali da ganin mahaifiyarta. Smart na son lallashinta yarasa yanda zai yi ga surukai. Dole ya hakura ya zuba mata ido sai tissue da yake faman miƙa mata na share hawaye, sai Daddy ne ya sakata a jikinsa ta gefe yana lallashinta. Yau jinta take kamar gata ga mahaifiyarta. Ashe dai haka suke tsananin kama, dan duk wanda ya ganta yasan mamanta yasan itace ta haifi abinta. Suna kama matuƙa tamkar tayi kaki ta ajiye ne. Ƙuruciya kawai Lulun zata fita. Ganin waɗan nan tsiyataku na Alh. Sulaiman ya sa Lulu cewa tanada shawara. Su duka idanu suka zuba mata alamar saurare. Zamanta ta gyara cikin dasashiyyar muryarta da kuka ya ɗasar ta ce,.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣8️⃣ .......“In dai muna son kama mutumin nan ya zama mai ƙarfin da bashi da mafita dolene sai mun haɗa hannu da Baba Garko, inba hakaba ko yazo hannu zai zama a banza ne, kai koda an kaisa kotu ne zai iya kuɓuta ma fa, idan ma an tsallake nan alƙali ya yanke masa hukunci to abokan huɗɗarsa zasu iya cireshi saboda yana huɗɗa ne da manya-manyan shegu na duniya bawai na Nigeria kawai ba. Duk da dai abu ɗaya dana sani ga manyan dilas na waɗan nan kayan a duk sanda sukaga zata kwaɓe musu ko zaka ci amanarsu zasu iya kashe juna. Ma'ana kamar yanda sukeyi akan duk wanda ya so bijire musu, shima ya koyo wannan ɗabi'ar ne a hannun turawan nan. Dan haka dolene zamuyi amfani da matakai uku na salon yaƙin kuma duk masu kamanceceniya da juna. Matakin farko shine Baba Garko, sai kuma kama duk wanda suke zagaye da Sulaiman ɗaya bayan ɗaya, hakan zaisa mu ruɗa masa hanjin ciki da jigata masa rayuwa mu sabautashi a tsaye. Hikimar saka Baba Garko anan itace yanada ƙarfi, sannan a fannin safarar miyagun kwayoyi shi maƙiyinsu ne, zai iya yin komai akan duk wanda hukuma ta cafke ta yanda bazasu taɓa kuɓuta ba. Mataki na biyu zamu ƙullama Sulaiman talala tsakaninsa da abokan huɗɗarsa musamman turawan nan na ƙasar Mexico. Kunsan duk wani shege akan harkar waɗan nan kayan yana ƙasar Mexico, saboda wannan matsalar na zagaye da rayuwarsu fiye da kowa a duniya, kuma nanne Sulaiman yafi safarar kayansa. Na uku dolene mu ɓoye kammu mu duka ta yanda idan muka kunnamasa wuta Daddy zai fara hara har zuwa wani mataki, saboda shi kaɗai yasan yana da camara ɗin nan, mu kuma zamuyi amfani da wannan fusatar tashi ne muyita fidda laifinsa waje ta yanda wasan zai zame masa gaba kura baya sayaki...”         Su duka babu wanda murmushi bai bayyana a kan fuskarsa ba, domin gamsuwa da shawaranta ɗari bisa ɗari. Albarka Daddy ya dinga saka mata, yayinda Uncle Yousuf ke tayashi. Smart dai na murmushi da binta da kallo ƙasa-ƙasa. Dan ya sake tabbatar da lallai matar tasa ƙwaruwace a lauyanci ashe tasan mutakeyi. Daddy ne yace, “Ni yanzu gaskiya bawani sanin kowa da kowa na cikin kasuwancin nayi ba, inma komai zai mana wahala sai dai wannan”.       “Shima bazai mana wahala ba Daddy, karka manta lungu da saƙo na sani, nasan manya da yara masu wannan business ɗin, kuma duk da haka zan nemo Nadiya itama, duk da bana jin zata bamu haɗin kai ta ciki sauƙi saboda abinda nai maita a last rabuwarmu, amma zan ƙoƙarta naga na ta dawo gareni saboda nasanta zata iya komai akan kuɗi, dan wannan ita ido ce a garemu tamkar google. A yanzu haka zan iya bada list na wanda wasan zai fara a kansu”.          Anan ma duk sun gamsu da zancenta, a take kuma ta zana musu sunaye da adireshin wajajen da take sayen kayayyakin, tun daga hannun ƙananan ƙwari har zuwa manya-manyan dila data sani a dalilin abokan huɗɗar nata. Ba kuma wai a wajen Kano kawai suke ba, a faɗin Nigeria gaba ɗaya harma da kasashen ƙetare dake maƙwaftaka da Najeriyar. Sosai Daddy yasha mamakin ganin waɗanda ta zano ɗin, har ma da Uncle Yousuf. Shi dai Smart ba kowa ya sani ba sai ɗaidaiku irin su Hon Nakowa suma dan sun kasance sanannun ƴan siyasa ne. Sai dai ganin sunan MM Atik Kumo ya sashi kallonta. Ta fahimci mi yake nufi, dan haka ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Shima Dila ne ai, ko'a ranar daka ɗakkoni a gidan nan tare da tsoffin nan gidansa ne, sannan shine ya sayar mana da kayan”.        “Shi wannan ɗin da nake gani simi-simi?”.      Lulu ta ce, “Humm bakaga komaiba ma, wasu ma dan ban san yanda zan misaltasu bane ku gane saboda sunan banza na sansu da shi, wasu kuma haɗuwar club ne kawai”.    Babu wanda ya sake iya magana dan sun san a zancen Lulun kam babu tantama...        A ranar su Daddy suka koma Manchester, dan washe gari suke son tafiya Nigeria su duka biyun, a Abuja kuma zasu sauka domin wucewa da su Twins, dan har Daddy ya nema musu transper zuwa Kano, duk da dai sun so bijirewa ya nuna musu basu isa ba. Har Mommy sai da ta kirashi akan hakan ya nuna mata babu ruwanta, ƴaƴansa ne, yanda yaso haka zai tafi da rayuwarsu. Dama dai da amincewarsa suke aiki a Abujar yanzu kuma yace su dawo gida suyi a gabansa. Jin ya buɗe mata wuta dole ta kama kanta, dan Daddy nada haƙuri, idan aka ƙuresa kuma akwai hayaƙi.      Tunda su Daddy suka wuce Lulu ta maida Camara ɗin nan abar kallo, sai da Smart ya ga kukan nata yayi yawa ya kwace ya ɓoye, duk roƙon datai masa akan ya bata ƙi yayi. Da ga ƙarshe ma ya ɗauketa suka fita. Wannan ɗan yawon da sukayi ne ya rage mata raɗaɗi da damuwar da take a ciki sosai. Dan basu dawo gidan ba sai da dare ya tsala kasancewar su daren da rana duk babu ruwansu bai hanasu hidimar gabansu. Washe gari ya kwasheta suka sake fita, sune har wajen gyaran jiki da wajen wasan yara aka kai AA duk da shi ba fahimtar komai yake ba. Wannan ɗan busy ɗin ya saka mata nutsuwa ta cire komai a ranta, sai sake duƙufa yima mahaifiyarki addu'a kuma.       Ahmad yay kiran Smart akan pharmacy da jami'an tsaro dana hukumar NDLEA sukaima dirar mikiya. Inda babu wani shan wahala aka gano na mahaifin aunty Khadijah ne dai, ta kai ma har an kamashi shi da yaran pharmacy ɗin gaba ɗaya. Duk da wasu sun rantse su basu san ana wannan baƙin kasuwancin ba. Sai dai ba'a sauraresu ba an ce sai abinda bincike ya tabbatar... Sosai Smart da Lulu suka tausayama Aunty Khadijah, dan Ahmad yace ana faɗa mata yanke jiki tai ta faɗi a asibiti, yanzu hakama tana can, bama ita kawai ba, zuri'ar gidansu gaba ɗaya suna cikin tashin hankalin al'amarin, dan abunne da babu wanda ya taɓa kawowa a ransa..... *_NIGERIA_*    Tako ina komai a hargitse yake. Musamman ma a fanin iyalan Alhaji Sadi Dikkon da aka wayi gari da labaran kamashi, tare da yima babban pharmacy ɗin da sai yau mutane da yawa suka san nashi ne tsirara. Inda aka dinga nuna miyagun kwayoyin dake danƙare a cikin pharmacy ɗin da yanda ake kasuwancinsu a tsawon lokaci batare da hukumomi sun fargaba balle jama'ar gari da basu taɓa kawoma ransu ba. Gaba ɗaya Kano a rikice take da kace nace, saboda Alhaji Sadi babban mutum ne da ke a cikin jerin ƴan kasuwar da ake ji da su a Kanon dama ƙasar ta wani fannin. Sannan sam a fuska bazaka taɓa kawoma kanka zai iya aikata irin wannan ƙazamin kasuwancin ba.                   Alh. Sulaiman na kwance a gidansa hankali kwance, yana ma tsaka da jin daɗin duniyarsa shi da amaryarsa kira ya shigo masa a waya kusan ƙarfe biyun dare. Rai a ɓace ya ɗaga duk da yaga Hon Nakowa ne a kan layi. Sai dai yana ɗagawar furucin Hon. Nakowa ya sashi zabura yana ture matar tasa gefe da lailayo wata gawurtacciyar ashariya mai kawuna goma sha biyu ya dire. Har neman taune halshensa yake wajen faɗin, “Tayaya hakan ya faru? Shi wane sakaci ne ya kaishi ga haka?”.          “Babu fa wanda yasan yanda akayi, Garko kaima kasan Alhaji Dikko na cikin mutane masu taka tsantsan matuƙa. Kawai dai akwai abinda ya kamata musani, sannan muna buƙatar zaman meeting na gaggawa dan nasan zuwa safiya zasu iya cewa zasu kamashi”.       “Wane zaman jira zai tsayayi ayi meeting da shi, a daren nan ya sayi ticket ya bar ƙasar nan kawai, idan kuma ya bari suka kamashi to tabbas zai mutu, dan mutuwarsa tafi rayuwarsa muhimmanci a garemu yanzu. Sauran aikin zamu ƙarasa a rufe zance. Dan haka kai kiran su Baita yanzun nan mu haɗu, dan muna buƙatar ganin shugaban NDLEA da IG ma kansa”.       Cikin gamsuwa Hon. Nakowa yace “Hakan yayi”.          Alh. Sulaiman na yanke waya idonsa ya sauka akan amaryarsa data zuba masa ido. Wani irin dafe kai yayi da faɗin, “Oh shiitt” dan harga ALLAH ruɗewa tasa ya manta bashi kaɗai bane a ɗakin ya zauna yana sakin zance har haka. A wani irin fusace ya nufeta, babu zato taji ya mata wata irin tsawa da nunata da yatsa. Har sai da ta zabura.      “Me kika ji?!!”. Ya faɗa a gigice. Kanta ta shiga girgiza masa jikinta na rawa. “Banji komai ba wlhy Alhaji. Kwata-kwata banji komai ba”.            “Idan ma kin jin ki ɗauka baki ji ba, idan kuma kikace zaki nuna kinji kiyi kuka da kanki”. Da ga haka ya wuce fuuu zuwa toilet domin tsarkake jikinsa. Tashin hankali na haƙiƙa ta shiga, dan jikinta har rawa yake yi, zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta ta fito. Gaba ɗaya kalaman mijin nata sun ɗimautata, so take tabar ɗakin ko zata samu iska, sai dai babu dama, dan fitar tata zai iya sawa ya zargi wani zataje ta faɗawa. Bata taɓa sanin atsabibancin mijin nasu ya kai haka ba, karo na farko a rayuwarta da taji ashe garama da ALLAH bai bata haihuwa a gidan nan ba..       Tana a kwancen ya fito, jikinsa duk laima bai damu ba ya saka jallabiya tare da zarar wayarsa da key ɗin mota ya fice. Da kallo kawai ta bishi kamar matacciya, dan ko dogon numfashi bata iyayi saboda tsabar tashin hankalin da take ciki..         ★A lokacin da su Alh. Sulaiman ke nufar inda zasu haɗu meeting a lokacin jami'an tsaro sukai dirar mikiya gidan Alhaji Dikko dake ƙoƙarin sulalewa ya bar gidan batare da sanin ko iyalinsa ba. Aiko a take sukai ram da shi. Jiniyar motocin jami'an tsaron ne ya fargar da iyalinsa dama ƴan anguwa. Hankalin kowa a tashe, yaran sai kuka suke suna kiran yayunsu a wayoyi, ta hakane Aunty Khadijah da batasan mike faruwa ba tun safe da aka fara tone-tone a pharmacy ɗin mahaifin nata da ita kanta bata taɓa sanin nasa ɗin bane labari ya risketa daga bakin ƙaninta. A wajen ta yanke jiki ta faɗi tana tsaka da duba mara lafiya. Tun a daren Coach da Ahmad suka nufi asibitin cikin tashin hankali. Shine ma ya samu damar kiran Smart suka tattauna bayan aunty Khadijah ta farfaɗo an mata allurar barci mai ƙarfi. Zuwa safiya labari ya ƙara karaɗe ko'ina da ina, yayinda shugaban NDLEA na Kano dama na ƙasa gaba ɗaya suka ƙi ɗaga kiran su Alh. Sulaiman. Hakama IG da CP basu ɗaga musu kira ba. Abinda basu sani ba shine akwai wata ƙullaliya tsakanin gwamna da Alhaji Dikko, yana samun labarin abinda ke faruwa yay kiran CP da shugaban NDLEA na jiha yay musu gargaɗi. Tare da tabbatar musu in suka bari Alhaji Dikko ya ƙuɓuce musu a bakin aikinsu. Sannan Baba Garko ogan Gwamna ne na amana, dan haka yay kiranshi shima akan su IG da shugaban NDLEA na ƙasa. Shi baba Garko dama abune daya tsana a rayuwarsa, yake kuma yaƙi da masu alaƙa da shi, amma sam bai san akwai alaƙa tsakanin ɗansa Sulaiman da Alhaji Sadi Dikko ba sam...      Matuƙar tashin hankali sun shiga jin an cafke Alhaji Dikko, a take meeting ɗin su ya canja akala zuwa shirya yanda zasu kashe Alhaji Dikkon kawai. Dan sunci alwashin bazasu taɓa barinsa ya tona musu asiri ba. Sai dai dolene suyi komai ta ƙarƙashin ƙasa saboda gujema idon mutane a kansu. Sun nema amintattunsu dake cikin jami'an tsaron, kai tsaye suka basu umarnin kashe Alhaji Dikko ta hanyar guba. Kasancewar suma abokan cin mushen nasu ne sukai na'am da hakan. Dan in dai aiki ya buɗe suma nasu ya buɗe ai........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣9️⃣ .......Kowa da abinda ya damesa. Duk da abinda ke faruwa a jihar ta Kano ya girgiza Abba hankalinsa a rabe yake gida biyu a dalilin halin da Ummah ke ciki. Duk da ma dai malaman da aka kawo a wannan karon su sunyi jarumtar tsayawa, sai dai daga kallo ɗaya da sukai mata sukace ta koma cikin ɗaki kawai. Sun tattauna da Abba akan dolene asan mushurikin da yay mata wannan aiki. Cikin nuna rashin amincewa Abba yace shi babu ruwansa. Babu inda zaije neman wani akan aikin da bai aiketa yi ba. Babu irin lallashin da ba'ai masa ba yace babu gudu babu ja da baya. Da ga ƙarshe dole ƴaƴanta ne suka nufi wajen Hajiya Naqiba da ke gida, dan asibiti sun sallamesu kamar yanda suka buƙata akaje akai mata ɗorin gida. Sun sami Hajiya Naqiba a yanayin daya tada musu hankali, dan ƙafarta tai wani irin mahaukacin kumburin da har tafi gangar jikinta girma. Kuka take sosai da ihu na azabar zogi da raɗaɗin da ƙafar kemata. An kira mai ɗori ya tabbatar musu ta sake gocewa, ma'ana dai ɗori baiyi ba. Ya kuma tabbatar musu da shi gaskiya bai san yaya zai yi ba, sai dai su nema wani kuma ya gwada sa'arsa. Daga haka yay tafiyarsa ma shikam. To shine fa ƴaƴan Umma suka samu ana shawarar neman wani mai ɗorin dan an tabbatar musu na gargajiyar dai yafi kar su maidata asibiti. Ga mijinta ya nuna kamar ma abin bai damesa ba duk da irin kiran sunansa da take famanyi shi da ɗanta Maheer. Shi Maheer ɗin da farko ya zauna, da ga baya yay ficewarsa acewarsa shi gaskiya ihun da take ya ishesa, yana fita suka haɗe da abokansa sukai tafiyarsu wajen ƙwalewarsu da kayan shaye-shaye. Dole yaran Umma suka dawo gida jiki a sanyaye. Sun sake iske tashin hankali Umma dake wani irin nishi a ɗaki amma kowa ya kasa shiga ya dubata, Ammah ce ma ta nuna zatai ƙarfin hali Abba ya tabbatar mata idan ta shiga sai ya ɓata mata rai, dole ta kama kanta cikin damuwa. Suma ɗin dai babu wanda yay yinƙurin shigar saboda tsoro....      Har yamma babu wanda yasan halin da Ummah ke ciki, sai yayanta Jibirin ne ma yay ƙarfin halin bada shawarar a sake kiran malaman nan koda taimakon da zasu musu. Kowa ya bada goyon bayan hakan. Dan haka akai kiransu. Babu jimawa suka iso kasancewar akwai sanayayya tsakaninsu da Jibirin ɗin. Addu'oi sukayi da ƙarfin halin cusa kai a ɗakin, sai gasu suna rige-rigen dawowa a guje. Har yaran gidan dake tsakar gida na tayasu da afkawa ɗakunan iyayensu. Sun tabbatar da gaskiya bazasu iya ba, wannan mummunar halitta ganinta ai tashin hankaline ma. Sun tabbatar da shawararsu kawai ya kamata a bi aje a nemo mutumin da yay musu wannan aiki zaifi sauƙi fa. Wannan al'amari ya sake tayarma da kowa hankali. Dole ƴan uwanta suka tattaru neman mafita su da ƴaƴanta. Dan Abba dai da gaske ya juya musu baya.....      ________★   Al'amari kamar wasa Dada sai da ta kwanta asibiti na kwana biyu, randa aka sallamonta ta samu surukanta cike da gida sunata harkokin arziƙi akan zaman bakwai. Wannan abu ya sake dugunzuma mata zuciya. Baba Garko ya shigo dubata da daddare ta sanya masa kuka. Kallonta kawai ya tsaya yanayi, bawai baya jin tausayinta bane, ba kuma baya sonta bane. Ya riga ya ɗaura ɗammarar horatane kawai. Dan ko auren nan nashi yayisa ne da gayya danya ƙona mata rai tunda yasan babu abinda ta tsana a duniya irin kishiya. Kuma ya samu nasara. A yanzun ma cikin ɓacin rai yaja tsaki da faɗin, “Ni al'amarinki kam ya fara bani tsoro Hajara. Shin wai baƙin ciki kike da ƙaruwar dana samu ko yayane? An faɗa miki haihuwa kin yanke jiki kin faɗi sumammiya, yanzu kin sakani a gaba kina kuka. Kin ganni nan ni bana son damuwa ina cikin farin ciki a ɓata min shi. Idan kinga zaki sakama ranki dangana ki saka, idan kuma kinga wannan halin da kike neman jefa kanki ne abin burgewa sai ki cigaba. Dan bakin alƙalami dai ya rigada ya bushe. Takardu sun jima da rubutuwa babu wata cleaner ɗin gogesu. In sha ALLAHU nan da wata shekarar ma wasu biyun zata sake zubomin a gidan nan, sai ki shirya sake suma. Na barki lafiya”. Da ga haka yay ficewarsa. Sama da ƙasa numfashin Dada ya ringayi, jininta yay masifar hawan da har idanunta na koma mata dishi-dishi, ALLAH ne ya taimaketa Uncle Muneer ya shigo ya sameta a lokacin, da tabbas zuciyarta zata iya bugawa komai ma ya faru....       (To Baba Garko ALLAH ya raya ƴan biyu. Koda yake kace nanda baɗi ma wasu kake so. Kaga tsoho da rigima🥱😂😂🤣🚴🚴)       *_★UK★_*   Alhmdllh a ɓangaren ango da amarya komai na tafiya dai-dai. Basu da wata damuwa sai cilin ɗinsu sukeyi. Duk abinda kuma ke faruwa a 9ja a cikin kunnensu yake. Dan suna samun information sosai ta hanyar Ahmad da su Daddy da suka koma gida. A yanzu haka tarko na biyu suke shirin ɗanawa. Dan sun gama shirya komai tsaff lokaci kawai suke jira.          Soyayya suke zubama juna mai tsayawa a rai da zuciya harma da gaɓɓan jiki. Duk da Lulu na dojewa da ɓoye nata sirrin har yanzu ta gagara furtawa a baki sai dai Smart ya gani a aikace. Dan zuwa yanzu kam karatun malamin nata tsaff ta haddacesa tama koma ruɗa masa tunani da salo-salonsa. A ranakun da yake da wasa koda ba'a cikin London bane bata iya zama, binsa take su tafi ga ɗan yaronsu da kowa ya gani sai ya tanka. Dan haka Smart ya dage da tofe abinsa da addu'a itama yana cemata tai masa saboda baki.      Lulu aja rigima bayan ta kira Baba Garko sun masa barka ita da Smart, ta kuma kira maijego da zuwa yanzu sun ƙulle sun zama ƙawaye dan kawai ta turama Dada haushi. Waya ta ɗaga tai kiran Dada. Bayan su. Gaisa Dada na zaton Lulun ta sakko ne daga fushin da take da ita zatai mata yaya jiki sai taji ta fara mata barkar haihuwar gidan. Dada ma bata san ta lailayo ashariya ta makawa Lulu ba. Aiko ta kwashe da dariyar ƙularwa tana mai yanke wayarta. Murmushi kawai Smart da ke zaune yana saurarenta yayi. Dan shi rashin jinta zuwa yanzu tsoro ma yake bashi wlhy. Baice mata komai ba sai da zasu kwanta ya mata faɗa. Tadai nuna masa taji, amma yasan batajin ba. Dan a ɓoye ta haɗa kayan jarirai na gani na faɗa ta bada aka wuce da su Nigeria wai a kaima maijego da jinjiraye....       Ana kwana na biyar da kama Alhaji Sadi Dikko Aunty Bilkisu da Iya tabawa suka iso Unitet Kingdom tare da Ahmad. A ranar Smart baya gida sunje buga wasa. Sai Lulu ce taje tarbarsu duk da Ahmad yasan gidan. Sosai aunty Bilkisu da duk take a tsorace ta samu nutsuwa da ganin Lulu, cikin farin ciki suka rungume juna. Hakama Iya Tabawa yau Lulu harda rungumeta, yayinda Ahmad ya caɓe yaronsa a hannu shima. Cab suka shiga har gida, dan Lulu bata driving anan kasancewar bata da lasisi. Sai Smart kawai. Daga Aunty Bilkisu har Iya Tabawa gidan ya birgesu sosai. Sunata santi da jera addu'a ga Smart. Abincin da Lulu ta shirya musu sukaci, bayan sunyi nak Ahmad yace zai wuce can ya samu Smart. Zuwa gobe sa dawo tare ɗan ba'a ranar Smart ɗin zai dawo ba. Tafiyar Ahamd ta sake basu damar ɓararrejewa, dan ma Aunty Bilkisu ba daɗin jikinta take ji ba sai ƙarfin hali kawai. Sun ɗan taɓa hira kafin Lulu ta kwashesu zuwa asibiti dan a yau take son aunty Bilkisu ma ta fara ganin likita. Kuma ko Smart baisan da hakan ba, dan shi nashi shirin kawai sai ya dawo ya kaita da kansa.     Kasancewar Usman da Dr Lameer ne suka haɗasu da likitan basu wani sha wahala ba na ganinta. A take aka bama aunty Bilkisu gado. Abinka da inda aka san darajar ɗan adam babu ɓata lokaci suka fara mata gwaje-gwaje da duk abinda ya dace. Koda Smart yay kiran Lulu bayan sun tashi a wasan bata sanar masa suna asibiti ba. Sun dai gaisa tai masa congratulations dan ganin sunci wasan suka ɗanyi hirarsu ta soyayya sukai sallama. Da yace ta haɗashi da su yay musu barka da zuwa Iya Tabawa kawai taba tace aunty Bilkisu na barci. Bai kawo komai a ransa ba ya yarda. Sallama sukai fan yana tare da Ahamd daya sameshi a can. Da ga haka itama ta cigaba da kai kawonta tare da Dr Lameer dake taimaka mata. Kasancewar mai jiyya ba zama yake a asibitin bayan ayi mata abubuwan da duk suka dace na wannan lokacin suka dawo gida, sai bayan wasu awoyi zasu koma dubata kuma...... *_★9ja★_*     A gidan Baba Garko suna akaci na kece raini da nunawa tsara. Dan ƴan biyu kam sunyi goshi matuƙa sannan sunzo da farin jini a wajen dangi. Kai da kaga taron nan kasan da gayya akayisa. Kasancewar su kansu dangin Baba Garkon ba daɗin Dada sukeji ba yasa a wannan gaɓar suke maida murtanin bashin gaba. Dan raƙashewa akai iya raƙashewa. Ga matan ƴaƴansa da jikoki cike taf da gida. Su kansu ƴaƴan dole sukazo kowa kuma da tsarabar suna. In ba haka ba kaci ubanka hannun mai gayya mai aiki. Alh. Sulaiman ne kawai babu, amma iyalinsa duk sun zo a sace batare da ya sani ba. Dan sukam dai basu yarda sun saka kansu a cikin faɗan iyaye da ɗansu ba. Hajiya Turai kuma tsaye take akan ƴaƴanta bata basu fuskar da zasu guji kakanin nasu ba. Tace babu ruwanta suma babu ruwansu. Ko Tajuddeen dake a cikin case ɗin tsundum cikin hikima ta dawo dashi ga kakaninsa tsundum. Dan tasan abinda take yi.      A yanda Dada ta koma laƙwas sai ta baka dariya ma da tausayi. Ba komai ya jawo hakan ba kuma sai kufcewar duk wata power nata. Gaba ɗaya ta fahimci komai fa ya gudu. Dan hatta matan ƴaƴan nata da take bama gwale-gwale yanzu kar suke kallonta. Bama sa shakkar dubar tsakkiyar idonta su yaɓa mata habaici a kaikaice. Karo na farko a rayuwarta datai kuka mai yawan gaske a dalilin tuna mahaifiyar Lulu. Tasha gaya mata gaskiya akan ta rage tsananin da takema matan ƴaƴan nata, in ba hakaba watarana sai sun nuna mata sun fita iyawa. Hakama dangin babansu ta daina musu wulaƙanci musamman marasa shi ɗin nan, kada wataran a auro wata a gidan ta riƙesu su rama duk cin kashin da take musu. Amma akoda yaushe saita hantareta harma da zagi saboda takaici da baƙin cikin ta kira mata kishiya, takance badan tana kama da Baba Garko ba itako da tace an mata misayarta a asibiti ne. Iya ƙoƙari Mawaddat tayi a kanta wajen gaya mata gaskiya akan abubuwa da yawa, yau gashi bata kusa da ita balle taji mata ciwon abinda ke faruwa. Dan ta kula ƴaƴa mazan nan fa ƴaƴansu da matansu kawai suka sani, tunda gashi kowa gani yake ta tsananta da kishin amaryar ubansu, ko kunyar faɗa mata hakan basa ji. Ko yau da safe Uncle Khamil da yazo sunan shi da nasa iyalin takanas da ga Abuja sai da yay mata irin wannan ƙorafin. Hakama autanta daya aiko da shatara ta arziƙi tun daga Saudiya. Gaba ɗaya saita fahimci goyon bayan mahaifinsu suke sam bata sonta ita yanzu. Babu abinda yafi ƙona mata rai da zuciya sama da saƙon Lulu, ita sai yanzu ma take sanin wai Lulu bata Nigeria tabi mijinta, bama wannan ba, shi kansa Smart ɗin bata san ya zama wani abu ba sai yanzu.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣0️⃣ .......Haka dai ta yini a ɗaki tana ƙulla wasikar jakai, sai wanda yaga dama yake shigowa gaisheta da jiki. Kowa yana tsakar gida yana raƙashewarsa hankali kwance harda su DJ suka saka Dan taro akai fa na gani na faɗa a harabar gidan. Ga abinci da kuɗi ana bishasha kamar ba gobe. Babu wanda ya damu dawai cewar Dada nada hawan jini bari a sassauta. To kowa sha'aninsa yake kamar ya manta da ita a gidan, sai ƴayanta ne kan ɗan leƙata time to time. A ƙarshe dole sai da likita yazo dubata. Washe gari da Uncle Khamil zai wuce ya roƙi Baba Garko ya bari ya wuce da ita Abuja ta ɗan huta. Cayay shi babu ruwansa duk ma inda zata taje. Wannan kalma ta sake sanyaya musu jiki. Yayinda Dada ta ɓarke da kuka akan ita babu inda zataje, ba komai ta tuna ba sai wahalar da tasha a hannun matar Uncle Manner. Babu yanda basu lallaɓata ba tace wlhy babu inda zataje garama idan mutuwa ce ta ɗauketa a ɗakinta yafi mata. Dole suka barta suka wuce.... (Su Dadancy anji gwale-gwale 🤣🤣🚴) _______★    Gaba ɗaya nutsuwa ta ƙauracema su Alh. Sulaiman. Dan sunbi duk matakan kawar da Alhaji Dikko al'amarin ya gagara. Duk wani babban ɗan siyasa da suke tare da shi a baya sun bisa amma kowa ya kife musu ciki akan case ɗin. Hakan ya sakasu fahimtar akwai wani babban ƙulli a ƙasa. Dan ko inda Alhaji Dikko ke ɓoye babu wanda ya sani a cikinsu har yanzu. Sun nema ganawa da gwamna amma hakan ya gagara, hasalima amsa ɗaya ake basu a koda yaushe shine yana Abuja. Tashin hankali na biyu a randa Alhaji Dikko ke cika kwanaki tara a hannun hukuma akai ram da babban yaron Hon. Nakowa. Da yamma sai ga labarin kama MM Atik Kumo shima. Kama MM Atik Kumo ya matuƙar ɗaukar hankalin jama'a fiye da na Alhaji Dikko saboda kowa yasan MM Atik Kumo dai ɗane ga tsohon gwamna M Atik Kumo, kuma ogane na gwamna maici a yanzu dan shine ma ya tallata shi ya kuma tsaida shi a takara. Wannan al'amari shiya ƙara maida hankalin mutane da yawa akan case ɗin, yayinda cecekuce ya ɓarke kasancewar kawunan jama'a na neman rabuwa. Wasu na ganin aikin gwamna na ƙyau, wasu na ganin al'amarin akwai lauje cikin naɗi dai. Sai dai yanda mahaifin MM Atik Kumo ya fito yay magana da nuna goyon bayansa akan aikin da gwamnan ya fara da kuma binsa da fatan alkairin kammalawa yasa zukata girgiza. Gwamna ya fara samun mafi rinjayen yabo ga mutane, suna ganin zuwa yanzu da gaske ake aiki za'ayi tuƙuru. Wasu kuma na ganin duk lumbu-lumbu ne kawai na ƴan siyasa musamman da ya kasance gab ake da yin zaɓe. Sai suke fassara abinda ke faruwar da kamar campaign ne kawai, komai na lafawa za'a saki duk wanda aka kaman.      To a baɗini zamu iya cewa kam harda hakan. Domin kuwa shugaban ƙasa shi abinda ke faruwa a Kanon yaja hankalinsa da ganin cewar in fa ya tallafa aka riƙe wannan makamin a ƙasar gaba ɗaya komawa kujerunsu babu fashi. Dan haka ya riƙe wuta shima tare da motsa sauran gwamnonin akan wannan aikinkin fa na kowa ne. Hankalin wasu a ciki ya tashi, kasancewar suma a cikinsu akwai ƴan safarar, wasu ma tsumu-tsumu suna cikin group ɗin na su Alh. Sulaiman ɗinne. Tuni suka fara kaima su Alh. Sulaiman labarin wannan fa al'amarin babba ne, dole akwai ta inda ake kunno wutar kuma dan shugaban ƙasa ma da kansa ya ɗauki lamarin da muhimmanci. Sun tabbatar da hakane kuwa a dalilin kame yaransu da aka cigaba dayi da customers ɗin su ƙananun diloli irin na anguwa da ƙauyuka. Gaba ɗaya duk sai suka sake susucewa da tunanin waye ke buɗe musu sirrika irin haka. A take fa aka fara zaman meeting meeting da bincike-bincike domin kamo bakin zaren. Duk wanda suke tunanin zasu iya buɗe musu aiki sun sakasu a faifai, Daddy shine na farko, dan haka suka zuba masa idanu. Sai dai me ta ko ina sun kasa gane komai, dan iya bibiyar Daddy da suka saka anayi babu wani motsi daga garesa a kansu. Hasalima wani business ya maidama hankali sosai. Al'amarin ya fara sakasu a ruɗani, suka cigaba da bibiyar duk wanda suke zargi amma basu gane komai ba. To dama hasashe ne kawai, domin sun tabbatar duk da wanda ke musu wannan illar ba ƙaramin sani yay musu ba. Sai kawai suka fara zargin junansu kuma. A randa sukai wani zaman da har ya jawo sa'insa a tsakaninsu suna barin wajen meeting ɗin aka cafke Hon. Baita. Al'amarin ya fara kaiwa intaha, dan lokacin da labari yazo ma Alh. Sulaiman harda cin tuntuɓe zai faɗi sai da yaronsa Malami ya tarosa. Hankali tashe ya shiga gida tamkar zai tashi sama. Yana shiga ciki kuma yaci karo da wani bala'in. To bala'i mana, dan ya samu kwali ne da aka nannaɗe da leda mai ƙyalƙyali kamar gift. Da farko bai maida hankalinsa akan abun ba sai da Hajiya Turai ke sanar masa ga saƙo nan ɗazun aka kawo wai a bashi. Kamar zai share sai kuma dai bayan ya gama bige-bigen wayoyinsa ya jawo abun ya hau farke ledar. Dan yanzu ya fahimci komai ma da zai iya zuwa musu ba abin yarda bane ba. Babu komai a ciki face envelopes guda biyu. Babba da ƙaramar. Babbar ya fara buɗewa, inda yaci karo da hotunansa har guda huɗu. Na farko shi da wasu mutanen kudu ne abokan huɗɗar kasuwancinsa suna tsakkiyar cinikayya, dan gabansu akwai cocaine har jaka uku a buɗe, sai jakkar kuɗi daloli a wata jakkar daban, a hannunsa na dama riƙe da ɗauri ɗaya na haggu riƙe da parcket na cocaine yana murmushin sa na basanci. Hoto na biyu tare yake da karuwarsa daga shi sai ƙaramin towel tana zaune a jikinsa itama da towel ɗin. Rawa jikinsa ya farayi, sai da ya wawwaiga falon ya sake tabbatar da shi kaɗaine dai sannan ya tafi hoto na uku. Tare da budurwar tasa ne dai suna shan cocaine a wani guri tamkar club. Da ƙarfi ya jimƙe hotunan cikin hannunsa illahirin jikinsa na wata irin tsuma, shin wanene da wannan aikin haka?. Zuciyarsa dake kumburowa take ayyana masa a hargitse. Tamkar wanda aka tsikara ya fisgi ƙaramar farar envelope ɗin itama ya buɗe. Takarda ce guntuwa a ciki mai ɗauke da gajeren rubutu, da words ɗin cikinta bazasu gaza 150 ba...         *_Da ace kasan ma'anar kalmar gidan rina da baka taɓoba, da ace kasan ma'anar fara takalo wasan da bazaka iya ƙara sawa ba da baka kalleni a matsayin birin wasanka ba. Abinda baka sani ba, ni idan na fara bana ajiyewa sai na kai ƙarshe. Haka nake kwanto nakeyi tamkar mage ta hango abin farautarta, saika gama sakankancewa dana ɓace sai na maka dirar mikiya. Wannan match ɗin sharar fage ne, na zahirin a tsakiyar filin da za'ayi yaƙin DUNIYA na uku zamu ƙarasa shi. Sai ka fara shirin saka sulken yaƙin, danni nawa sun jima a jikina. Ya rage naka neman bindiga, nokiliya, takubba, bomb, domin kare rayuwarka, dan kaima gab kake da bin sahun abokan naka zuwa jail......_*                 *_AMM✍️_* Wani irin gigitaccen ihu ya saki yana mai ɗaga Centre table ɗin falonsa ya wancalakar da shi gefe. “Wanene kai? Uban wanene kai? Dan uban wanene? Idan ka isa ka bayyana kanka mana. Nace ka bayyana kankaaaaa!!”. 🚴🚴🚴Da alama dai Tsule ya fara zarewa bari nayi nan🥱    ___________★         A ɓangaren Umma wahala da azabar ciwo ya sata fara sambatu. Tana kwance a ɗaki hawan jini na neman kaita lahira. Bata iya fitowa ba'a iya shiga inda take. Cikin ƙarfin hali tazo ƙofar ɗaki daga ciki ta zube tana kuka da roƙon a kira mata malam na kan tudu ya warware wannan asiri, su taimaka mata dama sai da ya faɗa mata in har asirin bai kama wani acikin Smart ko matarsa ba zai iya dawowa kanta. Batayi zaton hakan zata kasance ba shiyyasa ta amince. Da farko babu wanda ya fahimci abinda take nufi, sai da ta cigaba da kururuwa da ihu mutan gidan suka fara maida hankali a kanta. Aunty Amarya ce tai kiran Ammah dake ɗaki tana waya da Lulu. Duk da Ammah ta jima da wannan zargin a ranta zantukan Umma sun kiɗimata, amma baiwar ALLAH haka tai kiran Abba tana roƙonsa ya dazo gida. Kamar zaiƙi sai kuma dai yace gashi nan dama ba nisa yayi da gidan ba. Koda yazo yaji shima abinda Ummahn ke faɗi sai ransa ya sake ɓaci, wajen yay niyyar bari da tabbatar musu da shi fa babu ruwansa su kira ƴaƴanta. Sai da Ammah taita roƙonsa da magiya yaran gidan na tayashi sannan dai ya haƙura ya dakata amma yay kiran Yayanta Jibirin. Zuwansa yasa suka fara mata tambaya, da ƙyar take amsawa da basu adireshin inda malam na kan tudu yake. Anan ma Abba ya bijire bazashi ba, da ƙyar aka taru a kansa daban haƙuri dai, sai dai yace ba ranar ba dan bazaiyi tafiya cikin jeji da yamma ba. Dole suka barsa sai a washe gari aka shirya tafiyar a motar Salim da ya yarda zaije da ƙyar, dan shima sai ƙunƙuni yake akan tafiyar, damma dai Abba ba kanwar lasa bane. Su biyar sukai tafiyar, Abba, Salim, Kawu Jibirin da Kawu Idi shima ƙanin Ummah ɗinne, sai ƙanwar Hajiya Naqiba da suka taɓa zuwa wajen da ita, itama wai zata amsowa ƴar uwarta magani dan ƙafar Hajiya Naqiba ta rure tana jan ruwa ne. Sun sha wahala, yayinda motar Salim taci ubanta a hanyar jejin cikin sahara, da ga ƙarshe ma dole suka ajiyeta a wani waje suka cigaba da tafiya da ƙafa. Matuƙar mamaki ya kamasu da ganin inda wai su Ummah ke zuwa yin mugun abu, can wani ƙauyen Jigawa ne, bama cikin ƙauyen bane a bayan gari bokan yake sosai cikin tsakkiyar sahara a saman dutse (dan bama ce malami ba). Duk azabar zafi ranar wajen baya damunsa, dan ko bishiyoyin kirki babu saboda sahara. Da ƙyar suka iya hawa dutsin, Salim ya fasa hannu, cikin zafin azaba da ɓacin rai ya ce,.......✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣1️⃣ ........ “Gaskiya Umma kin cucemu, haka kawai kin saka mutane zuwa wannan azababben wajen”. Babu dai wanda ya tanka masa a cikinsu. Wani yabiɗaɗɗen tsoho suka samu a saman dutsen jikin bukkarsa. Surutai yake tayi kamar wani zararre, yana ganinsu ya kwashe da dariya. Turus sukai duk suna kallonsa, sai ƙanwar Hajiya Naqiba da tasan haka yake ne ta zube tana masa kirarin da suke masa. Hakan ya sashi yin shiru yana saurarenta, sai da ta kammala ya sake kwashewa da dariya yana ma kansa kirari shima. Sai kuma ya tsuke fuska yana kallon su Abba kamar bashi yay dariyar ba, “To asararru, ku bazaku zube ku kwashi gaisuwar bane wajen waliyyin ALLAH?”.        “Waliyyin shaiɗan dai. Ubanka ne zai gaisheka matsiyaci haihuwar asara” Salim da hanunsa ke masa azaba ya faɗa a fusace. Kaɗan ya rage Kawu Idi yay dariya ya dai daure. Kawu Jibirin ne ya ɗan girgiza kansa da fuskantar boka na kan dutse. Babu wasa a tattare da shi ya ce, “Muba neman wani abu mukazo wajenka ba. Hasalima baka da wata daraja a idanunmu face kasancewa a gafalalle abin ƙyama”. Ya zaro wayarsa yana nuna masa hoton Ummah, wannan matar tazo wajenka kayi mata aiki akan wasu mata da miji, tare da tabbatar mata asirin idan baici ɗaya a cikin ma'auratan ba zai iya komawa kanta anyi haka?”.       Dariya nakan tufu ya kwashe da shi harda ƙyakykyewa. Sai da yay mai isarsa kafin ya tsagaita da faɗin, “Shegiyar kaya ai wannan tasan takan mugunta. Dan koni uban gayyar da kaɗan na ɗarata. Sai dai a yanzu haka tana can cikin bala'i hhhhh. Dama mun faɗa mata ƙaiƙayi zai koma kan masheƙiya bata yarda ba hhhhh. Asirin bai kama mijin ba matar kawai ya kama, itama kuma ya saketa hhhh. Dan haka ya dawo kanta kuma bazata taɓa warkewa ba hegiya ta shiga kamun ɗan ƙallau.”       “Kaima yau zaka shiga kamun ALLAH ai matsiyaci. Ka tsufa har an yayyafa maka gishirin mutuwa a saman kai amma baka san Annabi ya faku ba” Salim ya faɗa yana ɗaukesa da mari. Kafin kace mi ya rufesa da duka. Da ƙyar su Kawu Idi suka riƙesa, zafin dutsen dana ranar yasa suka yayibosa zuwa ƙasa bayan Kawu Idi da Salim sun ɗaureshi. Abba dai ko sau ɗaya baice tak ba. Haka suka jefashi a mota duk da warin jikinsa ma ya ishesu suka ɗauki hanyar Kano. Da yamma liss suka iso, sun sami gida jigum-jigum baka jin komai sai nishin Ummah. Ganin boka na saman tudu ya firgita mutane da yawa. Duk da shi a cewarsa ba boka bane malami ne, dan hatta shigarsa dai ta malam ce sai dai dauɗa da warin rana ba'a magana. Ga Salim ya tunɓuke rawanin tun a can sai ƙwalelen kansa da yasha ƙwal a kwabo..... __________★    A bisa umarnin Lulu Ummita ta shiga binciken gidan su Nadiya ta hanyar yaranta na shagon saloon da yanzu ƙanwarta ke riƙe da shi. Da farko yaran nata sunji tsoro sunƙi faɗa saboda gargaɗin da akai musu. Sai da Ummita ta dinga musu magiya sannan suka faɗa mata gaskiyar a inda Nadiya take yanzu haka. Acan cikin wata tsohuwar makaranta ce da rufunta ya kwaye a ruwan bana. Hankalin Ummita ya tashi matuƙa da ganin Nadiya duk da bata santa ba kafin yanzu, sai hotonta data gani a wajen Lulu. Tayi baƙi ta lalace sai uban ciki haihuwa yau ko gobe. Wasu ƴan shaye-shaye dake zama wajen ke bata abinci da kayan shaye-shayen. Hankali tashe Ummita ta kira Lulu a video call. Da farko Lulu cewa tai bata yarda Nadia bace, sai da ta fashe mata da kuka cikin ƙarfin hali ta rantse mata cewa itace. Gaba ɗaya sai Lulu ta sake birkicewa da tashi hankali, itama ta fashe da kuka. Da ƙyar ta iya cewa Ummita sukai Nadia asibiti, amma ta kira Uncle Yousuf a waya. Koda Ummita tai kiran Uncle Yousuf ta sanar masa babu ɓata lokaci ya iso wajen shi da ƴan sanda da ambulance. An ɗauki Nadiya zuwa SHIRA'S HOSPITAL. Babu ɓata lokaci likitoci suka rufu a kanta, kamar jira cikin nata keyi dama sai naƙuda ta tashi. Doctors sun tabbatar bazata iya haihuwa da kanta ba, dole akai mata cs. Ana shiga da ita ɗakin theatre Uncle Yousuf ya nema gidan iyayenta. Sai dai koda yaje babu wanda ya sauraresa duk da ya sanar musu tana can a asibiti an shiga da ita theatre basu saurarensa ba. Haka ya baro gidan ransa a ɓace, sai bayan tahowarsa ƙanwarta ta biyosa asibitin a sace bisa umarnin mahaifiyarsu...... (ALLAH sarki Uwa kenan😭🙏).         *_★UK★_*        Fuskarsa ɗauke da murmushin zancen Iya Tabawa ya tura ƙofar bedroom ɗin a hankali ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, zuciyarsa cike da ɗokin san ganin sahibar ruhin nasa.. Cak kalaman bakinsa suka tsaya sakamakon tozali da ita zaune fuska share-share da hawaye ta zubama waya idanu...       “Mawaddatan-warahmah!”.   Ya kirayi sunanta cikin wani irin salon taushin murya mai amo da ratsa zuciyar mai saurare. A bazata ta ji saukar muryar tasa duk da a tsumayen isowar tasa suke. Dan hatta kwalliyar da taci yau a cikin skert da riga na atamfa da sukai mata ƙyau tayine da shi. Harda kwalliyar da hawayen tausayin Nadiya suka gama batawa. A hankali ta ɗago idanunta da suka kaɗa harda ɗan kumburowa. Sai ya samu kansa da lumshe nasa da sake buɗe su a kanta ya ware mata hannayensa alamar tazo garesa. Babu musu ta taso da ɗan gudu-gudu ta shige jikin nasa ya maida hannayensa ya naɗe a nata jikin. Wani kukan da ya sakashi runtse idanu da ƙarfi ta sake saki tare da ƙara ƙanƙamesa. Komai baice mata ba, bai kuma hanata tayi kukan ba har tsawon mintina biyu. Sai da ya tabbatar tayi ya wadaceta sannan ya ɗagata cak zuwa saman gado. Kwantar da ita yayi tare da kishingiɗa a gefenta ya tokare hannunsa da tallafo kansa ta yanda zai iya mata runfa. Ɗayan hannun kuma ya tallafo fuskarta ya zuba mata ido. Itama kallonsa take tana jan ajiyar zuciya. Karo na farko ya sakar mata murmushi mai sanyi da saka babban yatsansa ya ɗauke mata hawayen.        “Waya taɓa Final Choice ɗin Aliyu Mawashi? Maman Aliyu Mawashi? Kin san kuwa yanda nake jin ƙunar zuciya a duk sanda naga hawaye na sauka akan ƙyaƙyƙyawar fuskar nan taki. A gaɓa ɗaya kawai nake son naga waɗan nan hawayen da rakinki, amma ba'a banza haka ba okay”.       Hawayen ne suka sake ciko mata idanu, a hankali ya shiga girgiza mata kansa alamar kar tayi. Haɗiyesu ta shiga ƙoƙarin yi, sai kuma ta juya ta sake rungumeshi. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da ɗago fuskarta ya manna mata kiss a goshinta da hancinta ya sakko saman lips ɗinta. “In sha?”. Ya faɗa cikin raɗa yana nuna mata lips ɗinta da yatsa. Murmushi ta sakar masa a karo na farko da hawaye. Shima sai ya murmusa da kai nasa lips ɗin saman nata. A hankali suka lumshe idanu a tare kowanne na sauke ajiyar zuciya, daga haka tsarin ya canja zuwa wani fage daban...         Yana zaune a bakin gado yana goge jikinsa da ƙaramin towel ta fito itama sanye cikin bathrobe. Idanu ya zuba mata cike da jin ƙarin ƙaunarta da tausayi, suna haɗa ido ta ɗauke nata cikin jin nauyi. Wucesa tai niyyar yi ya riƙo mata hannu. Batare data juyo ba ta furta, “Zan shirya ne fa na haɗa maka abinci”. Murmushi yayi da jawota baya ya zaunar a saman jikinsa. Cikin kunneta ya raɗa mata maganar da ta sakata jin rikicewa dan kunya, shiko ya shiga darawa abinsa. Tashi tai zumbur a jikinsa ta gudu zuwa gaban mirror tana murmushi da faɗin, “Ni dai babu ruwana wlhy”.         “Daga baya kenan yarinya”. Ya bata amsa yana tasowa zuwa gaban mirror ɗin shima. Da jikin mirror ɗin ya jingina, hakan ya basu damar facing juna. “Miya sakaki kuka?” ya jeho mata tambaya dai-dai tana ƙoƙarin warware gashinta data naɗe a cikin ƙaramin towel. Numfashi ta ɗan firzar a hankali idanun nata na sake cikowa da hawaye, murya a raunane ta ce, “Nadiya ce”.     “Nadiya kuma? Who is she?”. “Ƙawata ce, sai dai bama tare yanzun”. “Ya akai banji sunanta a labarinki ba?”.       “A Nigeria na santa ai, kaima kuma ka santa ma. Dan ka taɓa kai ni shagonta saloon”.            Cikin ɗan yin jimm na alamar tunani ya ce, “Okay na gane, ba itace kikace zata taimakemu ba?”.     “Yes ita”. “Uhmum miya faru da ita?”. Wayarta ta ɗauka ta miƙa masa. Amsa yay ya duba. Recording ne na video call da sukayi ita da Nadiya. Shi kansa da farko bai ganeta ba. Al'amarin ya girgiza shi da bashi tsoro. Jiki a sanyaye ya miƙa mata wayar batare da ya iya furta komai ba. A bazata Lulu data sake fashewa da kuka ta ce, “Aliyu nagode da ƙoƙarin ka a kaina, bani da abinda zan iya biyanka da shi a duniyar nan face na dawwama ina maka addu'a har ƙarshen numfashi na kai da Uncle Yousuf. Yanzu nima da ALLAH bai taimakeni, kun tallafi rayuwata kun cireni da ga wannan mummunar ƙazamar rayuwar ba da hakance zata kasance da ni. Abinda nake sha ko rabinsa Nadiya bata iya sha fa. Amma kaga yanda rayuwarta ta koma, bata da maraba da mahaukatan kan layi masu wucewa yara na musu atire. Iyayenta sun korota a makaranta data lalace take kwana tsakkiyar kazaman ƴan shaye-shaye. Na shiga uku Hydar wace irin rayuwa ce muke jefa kammu ne haka?....”        Hankalinsa ne ya ƙara tashi ganin yanda take kuka na fitar hayyaci. Ɗagota yay ya rungumeta a jikinsa, tare da fara jera mata kalaman lallashi da nasiha. Sun jima a wajen tsaye ya karasa busar mata da kan nata ya ɗaure mata shi. Cikin son kauda mata yanayin ɓacin ran nata ya ce, “Ina auntyn taki wai, naga da Iya Tabawa kawai muka gaisa tana goye da AA”.        Murmushi ta ɗan saki kaɗan, sai kuma ta kallesa tana ɗan lullumshe ido cike da salon dake narkar da mutumin nata tace, “Tana asibiti ai, tun randa suka zo”.    Da mamaki sosai a fuskarsa ya ce, “Asibiti kuma Madam”.       Sai da ta ɗan hararesa saboda kiranta Madam sannan ta bashi amsa. “Eh ai abinda ya kamata ayi kenan, mizai sa na riƙeta a gida har sai ka dawo kuma. Yanzu kam kaga har sun bamu ranar da zasu mata aikin ma. Sai ka ƙarasa shiryawa muje ka ganta dama Doctor ɗin ta buƙaci ganin mijinta, sai dai nace mata baya kusa sai ƙaninta dai.”            Rasama mizaice mata yayi shi kam, sai kawai ya zuba mata idanu yana kallonta, yana jin tamkar ya haɗiyeta ya huta ma kawai. “Kallon fa?”. Ta faɗa tana wani tura masa baki da kashe masa ido ɗaya. Hannu ya kai zai cafkota ta zille tana dariya. Shima sai ya murmusa yana dimtse gefen lip ɗinsa da haƙori. Kayanta ta maida dan bata son Iya Tabawa ta zargi komai tunda ta ganta da su. Ta dawo gaban mirror ɗin ta maida ɗaurin ɗan kwalinta kamar yanda yake ɗazun da yin ƴar kwalliya. Shima sai ya nufi closed ɗinsa ya saka kaya. Tsaff suka fito suna zuba ƙamshi da annuri, ita sai yanzu ma ta san ashe tare yake da Ahmad. Amma yake komansa hankali kwance a ciki kamar bai bar kowa na jiransa ba, shiyyasa da zata fito ya sakata sanya abaya ashe. Sun gaisa da Ahmad yana faman tsokanarta kamar yanda ya saba. Ita dai nata murmushi ne musamman daya kasance boss ɗin nata ya watso mata kallon gargaɗi. Abincin da suka sha wahalar yi ita da Iya Tabawa ta gabatar musu. Sosai Smart yaji daɗin ganin tuwo, dan zai iya cewa tunda ya baro Nigeria bai sake ci ba. Kasa haƙuri yayi ya tambayi inda suka samo garin tuwo haka. Lulu ta bashi amsa da cewar su Aunty Bilkisu ne sukazo musu da shi. Bayan sunci sun ƙoshi kaɗan suka huta Lulu ta takura musu dole suka fice zuwa asibiti duba aunty Bilkisu, zuwa lokacin AA ya tashi yana hannun Babansa da yay kewa.......✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣2️⃣ ......Sosai Smart ya tsinta kansa cikin farin cikin ganin ƴar uwarsa, duk da tana kwance a gadon asibiti hakan bai hanasu yin hira ba. Anan ne take basu labarin halin da Ummah ke ciki a yanzu. Babu ɗigon tausayinta a zukatansu sai Smart kawai, duk da yana jin ɗacin rabashi da matarsa da tayi hakan bai hanashi jin tausayinta ba. Dan ko babu komai tunda ya taso kallon uwa yake mata, sannan jininsa ce ita tunda ƴar uwar Abba ce. Sun jima a asibitin, dan Smart ya gana da doctor sun tattauna, daya buƙaci yanda biyan kuɗi zai kasance sai ya samu Lulu ta biya komai har kuɗin aiki dana gaba ɗaya zaman da zatayi ma a asibitin. Kasa cewa komai yayi har suka dawo gida. Sai dai sun sauke Ahmad a masauki. A falo suka sake zubewa aka ɗaura hira, Iya Tabawa na basu labari suna kwasar dariya. Sun jima a wajen kiran wayar Smart da akayi ne ya sashi miƙewa ya shige bedroom, hakan ya bama Lulu damar bin bayansa bayan wani lokaci. Ta samesa har lokacin yana waya da Usman da ke bashi labarin irin halin ruɗanin da Alh. Sulaiman da abokan cin mushensa suke a ciki. Sai saƙon daya bada aka aika masa ɗin nan. Sosai Smart ke kwasar dariya har yana jin inama yana Nigeria yaga wannan ruɗani a fuskar Alh. Sulaiman. Sai dai babu komai yasan zai gani ta cikin direct camara ɗin da suka sanyama Alh. Sulaiman batare daya sani ba. Bayan sun gama wayar ne yake bama Lulu labari, itama dai dariyar tasha da jin inama tana 9ja ake wannan irin cakwakiya haka.           AA ya tambayeta ta ce ai ya koma kwana wajen Iya Tabawa. Da mamaki yace, “Abincinsa fa?”.     “Wane abinci kuma bayan wanda yake ci ya ƙoshi. Ai ni na yayesa”.    “Yaye a wata goma sha ɗaya? Wane irin rashin tausayine haka Baby luv”.               “Haba kai kam miye abin rashin tausayi anan. Nifa wlhy dama so nake ya taka kawai, yaron da dama ba wani ya damu da shan nonon bane ba.”         “Kin dai so yayesa saboda kina buƙatar wani babyn”.     “Kamar ya?”. “Kamar yanda kika ji mana”. Ganin kamar cikin ɗan zafi yay mata maganar ya sata jan bakinta tai shiru. Ita matsalarta da shi kenan saurin fushi. Abu kaɗan bazai fahimcesa ba sai ya hau kamar fulawar burodi, sai idan shi yaso shanyewa ya nuna kamar bai gani ba. Bata yarda ta sake magana ba. Shima sabgar gabansa ya cigaba da yi batare da ya kulata ba. Ganin abin nasa babbane ta fita ta bar masa ɗakin dan bata buƙatar wani ɓacin rai kuma a yanzu....        Bayan kwana biyu da dawowarsa akaima Aunty Bilkisu aiki. Duk halin da ake ciki jama'ar gida sun san komai. Dan haka kowa nata faman addu'ar nasara. Alhamdullah anci nasarar kuwa, dan anyi aiki har an kaita ɗakin hutu, basu sami ganinta a wannan ranar ba sai washe gari da safe. Sunji farin cikin samunta a cikin hayyacinta. A take kowa farin cikin sa ya gagara ɓoyuwa. Fatansu kuma yanzu ALLAH ya bata lafiya. Smart bai sake ma Lulu magana akan yaye AA ba, itama bata sake tayar masa da zancen ba har ya sake barin London ɗin a weekend daya zagayo. Sunje yin wasa, yayinda ita kuma take cigaba da zama tsaye akan al'amarin aunty Bilkisu daketa samun lafiya. Kullum sai sunyi waya dasu Ammah da kuma ƴan gidansu ta video call, musamman ma Ummita da ke tsaye akan al'amarin Nadiya dake a asibiti ita da Uncle Yousuf. Kwanan Smart uku ya dawo, yayinda Ahmad ke shirin komawa Nigeria. Taka tsantsan ta dingayi a ƴan kwanakin nan na ganin saɓani bai shiga tsakaninta da mijinta ba. Alhamdullah kuwa anci nasara, dan banda murzar juna babu abinda sukeyi sai zuwa asibiti wajen aunty Bilkisu da ɗan fita hutawa domin bama kansu farin ciki. Sosai kuma suna samu, dan yanda suka murje tsaff da su, ga tattalin juna da nuna kulawa kowa yasan hankalinsu ya kwanta. Sun kuma samu nutsuwa irin wadda duk wani mai aure ke buƙata a rayuwa. Sai ɗan saɓanin da ba za'a rasa ba na tsakanin harshe da haƙori dake zuwa yau da gobe. Duk yanda Lulu zatayi kuma takanyi na ganin abin baiyi nisa ba ta shawo kan abinta ya huce, shima kuma da yake bason ganinta a damuwa yake ki ɓacin rai ba baya barin abin yay nisa sam.....        *_NIGERIA_*   Alhamdullah an samu nasarar dawowar Ummah dai-dai, nakan dutse ya gama kunce ƙullin daya ƙulla su Salim suka miƙashi hannun ƴan sanda batare da sun saurari bayanin da yake musu akan bafa wai Ummah ta kuɓuta bane ba ɗari bisa ɗari, dolene sauran bala'oin data saka akai mata aiki akan Smart ɗaya bayan ɗaya zasu cigaba da dawo kanta. Sai ta shirya. Babu wanda ya sauraresa, sai yan jarida da suka kafa suka tsare har sai da suka samu cikakken bayani a bakinsa. A take fa al'amarin Umma ya shiga media da duniyar yanar gizo dana kafafen ƴaɗa labarai musamman irin na rediyo. Kafin kace mi mutane da yawa sunji kuma sun sani anata ALLAH wadai da al'amarin nata tare da mata irinta.      Ana wucewa da nakan dutse dole itama Ummahn aka kwasheta zuwa asibiti dan hawan jini ya mata biji-biji. A asibitin ma dai ƴan jarida basu barsu sun huta ba da jama'ar gari ƴan so da jin ƙwaƙwaƙwaf. Musamman ma da ya zam hotunan Ummah sun gama zagaye gari a suffar Dodo, saboda lokacin da nakan dutse ke ƙoƙarin warware asirin mutanen da suka samu shigowa musam yaran maƙwafta ɗauka suka dinga yi a wayoyi suna sakawa a shafukan su na sada zumunta. Dan danan fa sunan Ummah da Hajiya Naqiba yay amsa kuwwa a duniyar labarai da yanar gizo. Dan hatta Hajiya Naqiba basu bari ba sai da suka bibiyi al'amarinta.       (Su Umma an zama celeb.... sai ku tayata murna🤣😂).     A washe garin da aka wuce da Umma asibiti Smart ya buƙaci su koma gidan daya kama musu domin fara gyara wanda suke a ciki. Kusan dama a shirye suke da hakan, dan haka babu ɓata lokaci suka tattara zuwa can ɗin nan kuma aka bajeshi aka fara aiki bisa tsayawar Coach da manyan yaran gidan duk da Salim ya nuna hassadarsa a fili. (Nonon Ummah ba wasa ba ai🤣🙏).      Suko su Mubarak farin ciki suke abinsu ganin za'a gyara musu gida. Sai addu'a da fatan alkairi suke jerama Smart. Mazansu da matansu haka suka dinga kiransa suna godiya. Duk da wasu sun gagara hakan musamman a mazan saboda baƙin ciki. Dan Mama ita kanta a wannan gaɓar Hassadarta ta gagara ɓuya. Sai da taga Abba na neman birkice mata ne fa ta kama kanta. Sai ƴaƴanta mata da suka nuna mata karfa ta tafka kuskure makamancin na Ummah. Dole ta kama kanta ta koma yaƙe da addu'a a fatar baki. Ƙasan zuciyarta kam kamar zata ƙone, a ganinsu dai ƴaƴansu ne sukafi cancanta da wannan arziƙin.      Ni dai nace, “Hummm🥱🚴🚴”. __________★       A ɓangaren su Alh. Sulaiman suna tsaka da kukan targaɗe sai ga karaya ta samu. Dan kuwa dai al'amarin Nadiya ma ya bayyana wa duniya. Inda ta tabbatar da cikin jikinta na su Hon. Nakowa ne dan su duka babu da wanda bata mu'amula. Ta kuma tabbatar da cewar su ɗin manyan diloli ne na miyagun kwayoyi, dan ko ita sune suka koya mata shaye-shaye. Ta kuma tabbatar da in har sunce ƙarya ne su fito duniya su musa zancenta ita kuma zata bada manyan hujjoji a kansu. Tace bayan itama akwai yara da yawa da suka lalatama rayuwa ta hanyoyin shaye-shaye da zinace-zinace. Wasu sun jima da rasa ransu, wasu iyayensu sun koresu a gida sun shiga duniya. Wasu kuwa a gidan iyayen nasu ake lalata musu rayuwa batare da iyayen ma sun sani ba. Acewarta Bama su kawai ba, akwai manyan ƙasar da dayawa sukai suna da nisa a irin waɗan nan al'amuran, su suyi ƴaƴansu suyi. Ba kunya Uba da ɗa za'a haɗu a club ko da ƴa anama juna kallon kallo. Akwai wanda ake kaima yara ƙanana gida suyi musu fyaɗe, wasu ma harda maza sukemawa. Ta tabbatar da idan zata tona asirin mutane da yawa akan wannan al'amarin tofa manyan nan da yawansu bazasu sha ba a bisa madafun ikon da suke kai. Dan haka a rufe rufau kawai. Wannan video ya girgiza al'umma da yawa. Yayinda ya bama wasu da ke fuskantar irin raɗaɗin da Nadiya ke a ciki fitowa suma suyi magana. Fiye da yanda ba'a zato al'amari ya sake rincaɓewa. Dan kuwa a ranar kame na hauka jami'an tsaro sukayi, kuma duk yaran su Alh. Sulaiman ɗinne da Nadiya ta dinga lissafowa a faifai. Inda kuma duk akayi dacen kamasu dumu-dumu da abinda ta lissafa ɗin kasancewar dama sai da aka shirya musu talala aka saki video ɗin.      Zuwa yanzu kam su Alh. Sulaiman sun tabbatar da akwai mai musu zagon ƙasar nan. Duk da shi zai iya bugar ƙirji akan babu ruwansa da wata yarinya a cikin garin kwano. Iskancinsa a wajen Nigeria yakeyi sai ko Lagos. Dan budurwarsa ɗaya ce tak a Nigeria kuma a Lagos take zaune. Asalinta ma ba ƴar 9ja ɗin bace shine ya kawota ya ajiye. Sai dai kalmar fyaɗe da akace akwai masu yima yara kam ya girgiza shi, dan abune da anan kam baida tacewa. Dan haka idanunsa suka fara rufewa ya dannama Daddy kira dan ya fara ji a ransa anya Daddyn baida wata rawa da yake takawa a al'amarin nan kuwa. Duk da a yanzu haka ana tsaka da masa bincike akan *_AMM_* ɗin nan da ya aiko masa da takarda da hotuna, har yanzu kuma ya kasa hasaso kowa, ba komai ya jawo haka ba kuma sai kansa dake a birkice..... ★★ Daddy na a gidansa hankali kwance dan kallon wasan su Smart ma yake tare da su twins. Da farko kamar bazai duba mai ma kiran nasa ba sai kuma dai ya ɗauki wayar. Yasha mamakin ganin Alh. Sulaiman Garko. Har ya maida wayar ya ajiye da nufin sharesa sai kuma dai ya ɗaga tare da miƙewa ya shige bedroom ɗinsa.        Cikin wata irin gigitacciyar tsawa Alh. Sulaiman ya ce, “Isma'il mai kake tunanin ka taka ne?!”.      Daddy ya saki murmushi mai sautin da har Alh. Sulaiman na jiyosa. Kansa tsaye babu alamar ɗar a tattare da shi ya amsa masa da faɗin,.......✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣3️⃣ .......“Banda abinka Sulaiman Garko idan kaji makaho yace ai wasan jifa ai ya taka dutse ne. Toni a wannan gaɓar dutsina na taka bama dutse ɗaya ba. Sorry fa, inata son zuwa na maka jajen abubuwan dake ta faruwa amma nayi busy da yawa. Sai kuma naji yau ma wata yarinya ta ɓaro muku babban aiki, dan kaima banace bakayi ba. Wanda zai iya yima ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗaya fyaɗe ai abune mai sauƙi yayma sauran ƴaƴan jama'a ciki harda wanda ya haifa ma.....”          “Da hannunka kenan a ciki? Dama an tabbatar min da yarinyar ƙawar ƴarka ce ai. Isma'il karka manta ni zaki ne. Nakanyi farauta a duk dajin da yay min na kuma ci kowacce irin dabba na zauna lafiya batare da ko jin ɗar ba tattare da ni....”      “Banda Giwa, dan koda ka kadata namanta bai ciyuwa gareka sai da taron dangi Sulaiman Garko. Tabbas Nadiya ƙawar Mawaddat ce bakayi ƙarya ba, idan kuma kace zaka nuna wani giggiwa a wannan kadamin karan bana ne zai yi maganin zomon bana. Dan ka tabbatar da Mawaddat ce ta haifi Mawaddat, kasan kuwa tunanin zai iya zama duk iri ɗaya, hakama jarumtar. Ballema a yanzu da take a jingine a jikin matashin *_ZAKI_* na haƙiƙa ba arar suna ba irin ka. Gefenta ga *_DAMISA_* ƙi sabo. Sannan ga addu'ata biye gareta a dukkan motsinta. Ai nasha faɗa maka ni da ƴata da zuri'arta gaba ɗaya *_FURAR DANƘO_* muke, *_A SHEKARA ANA DAMU BAMU FARAU-FARAU_*. Idan kai acan ka wuni, ni kwana nayi. Maza ka sake shiri *_MAZAN_* ƙwarai da *_MACE_* mai kamar maza ne tafe bisa kanka ƙaramin biri......”         “Isma'illll!!!!!!”      Alh Sulaiman ya kira sunan Daddy cikin wata irin Mummunar tsawa mai razani. Kafin Daddy ya ce komai ya ɗora da faɗin, “Amma dai kasan zan iya karar da duk jama'ar asalin ƙauyen da ka fito bama kai kawai ba ko??!!!”.        Dariya Daddy ya ƙyalƙyale da shi tare da faɗin, “Ai ga fili ga mai doki nan Sulaiman Garko, zaka iya gwadawa idan har zaka iya, dan wlhy ba jama'ar garin jiƙamshi ba, koda ƙasar jiƙamshi ka taka da manufa saina karya ƙafafunka ta yanda bazasu ƙara ɗaukar gangar jikinka ba har gaban abada. Amma kafin ka tafi jiƙamshin ƙarar dadu ka tabbatar ka fara duba saƙo ga shi nan zai zo a hannun matarka shashasha ƙaramin biri abin wasan yara a tsakkiyar kasuwa”. Ya yanke wayarsa.     Haukacewa ne kawai Alh. Sulaiman baiyi ba da kalaman Daddy masu ƙona zuciya. A wani irin birkice ya ɗaga wayar ya naka a ƙasan tiles. Dai-dai nan amaryarsa ta shigo hannunta ɗauke da leda. A ɗan tsorace da ganin yanayin nashi ta ajiye ledar tana faɗin, “Saƙone aka kawo a baka, yanzu maigadi ya kaw....”     Yanda ya juyi a fusace ya hanata ƙarasawa. Har ya juya shima da nufin baida lokacinta sai kuma ya juyo tare da wani irin fisgar ledar. Zazzageta ya shigayi cikin tsumar jiki. Babu komai a ciki face Flash drive. Cikin rawar jiki data ruhi ya kai zaune daɓar yana mai janyo laptop ɗinsa ya saka flash ɗin jiki. Gaba ɗaya ya manta da kasancewar matarsa a wajen yay playing video ɗin da ke cikin Flash ɗin. Ba komai bane face fuskar mahaifiyar Lulu tana kuka da faɗin wannan shine kundin manyan laifuka na shi a ciki. Tana roƙon ko bayan babu ranta iyayensu su sani shine yayma Sultana fyaɗe....”       Ai bai ma kai ƙarshen video ɗin ba ya buga wata irin kuwwa da hankaɗa Laptop ɗin ƙasa itama ta kifu. Amaryasa data gama jin komai cikin firgita ta buga ihu itama tana neman hanyar fita a guje. Cikin tashin hankali yay tsalle ɗaya ya taɗota ta zube ƙasa. Idanunsa a rufe ya kai mata wata irin wariyar shaƙa. Tuni idanunta suka juye ta fara ƙaƙarin mutuwa.        “Mi kika ji?!! Na ce, “Mikika ji!!? Dan uban uwarki”.    Kanta take jujjuyawa alamar bataji komai ba. Wawan mari ya ɗauke fuskarta da shi ta bayan hannu da sake maƙureta. “Idan ma kinji ko kin gani wlhy wlhy wlhy ki zama kurma. Idan ba haka ba da hannuna zan kashe ki, na gina rami a tsakkiyar falon nan na bizneki. Kuma har abada babu mai sake jin labarinki ko tambayata ina kike. Baƙar mayya mai leƙe-leƙen masifaa!!”. Ya ƙare maganar da yarfar da ita ƙasa. Ya wuce bedroom ɗinsa a birkice. Babu jimawa sai gashi ya fito. Har lokacin tana kwance a wajen yabi takanta ya fice abinsa. Umarni ya bama maigadi akan kada wanda ya fita a gidan. Daga haka ya birka motarsa da kansa yau ya fice a bala'in guje....       *_★UK★_*   Cikin tashin hankali Lulu ke kallon Smart. Dan duk abinda ke faruwa tsakanin Alh. Sulaiman da matarsa akan idonsu ne kasancewar sun saka direct camara a jikin Alh. Sulaiman batare daya taɓa farga ba. Sun yi wannan aikinne kuma a lokacin da ya tafi jiyya bayan jami'an tsaro sun sake sa akan kidnapping ɗin Lulu da yayi. Sun haɗa baki da likitansa aka saka masa camara a gefen kunne ta wajen wuyansa a zuwan wani tabon theatre da akai masa ne a wajen wai na'urar na rike jijiyar kunnensa. Wannan aikin Uncle Yousuf ne, sun zaɓi saka masan ta yanda bazasu gansa ba sai dai suga abinda yake aikatawa saboda yanayi na yau da kullum irin na ɗan adam. Wanka da makamantan hakan. A kuma duk lokacin da zai shiga ɗaki da matansa ko aikata wata Masha'arsa da karuwansa sukan tsaida gani daga wajensu domin kiyaye dokar ALLAH. Ta wannan direct camara suke sanin duk wani motsin Alh. Sukaima batare da shi ya farga da hakan ba dan yana kallon abinda aka saka masan ne a yanda aka faɗa masa cewar tana riƙe jijiyar kunnesa da ta samu matsala.        “Wannan mahaukacin fa zai iya kashe matar nan. Ya kamata muyi wani abu”. Lulu ta faɗa cikin tashin hankali itama ganin yanda Kawun nata ya fita a hayyacinsa. Murmushi kawai Smart yayi yana ɗan lumshe idanu da zamewa ya kwanta. Kamar bazaice komai ba sai kuma zuwa can ya firzar da iska yana bata amsa da, “Babu abinda zai maita, wannan hargagin da kikaga yanayi na rashin mafitane kawai da ruɗanin da yake a ciki. Amma ba itace a gabansa ba yanzu Daddy ne da ke sai kuma mu da yake son sanin su wanene. Ina mai tabbatar miki yanzu haka gidan Daddy zai je”.         Da sauri Lulu ta ce, “What! Gidanmu fa kenan?” sai kuma ta fisgo computer ɗin gabanta ta sake buɗewa batare da jiran amsar Smart ɗin ba. Ilai kuwa sai ga Alh. Sulaiman na kwaɗa gudu a saman titi. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi a anguwarsu, a ma ƙofar gidansu. Sai dai ya gagara ƙarasawa saboda jami'an tsaro da ke zagaye da street ɗin ma gaba ɗaya musamman jikin gate ɗin gidan nasu. Wani irin duka ya kaima steering ɗin kamar zai fasa ihu. A haukace yay reverse ya koma ganin jami'an tsaron sun yo kansa.... Bata ma san lokacin data kwashe da dariyar data saka Smart buɗe idanu yana kallonta ba... ___________________★       Abubuwa tako ina suna cigaba da kwaɓema Alhaji Sulaiman Garko.  Domin kuwa da zaman meeting na maganin matsala da yayi musu. Dan kullum a cikin yinsa suke. Kowace hanya sunbi domin ganin sun cutar da Daddy ko zuri'arsa al'amarin ya gagara. Yanda Daddyn ke zagaye da jami'an tsaro lamari ba'a cewa komai. Sun kai hari gidan su Smart shima dai, sai dai anyi rashin sa'ar samun gidan a baje sai masu aikin gini. Iya bincike kuma kowa a anguwar sai yace bai san inda suke ba a yanzun. Fahimtar kamar raina masa wayo sukeyi ya sakashi komawa gida rai a ɓace neman mafita. Kowa bai nema ba a matansa ya nufi sashensa kamar zai tashi sama. Wani irin kallon ɓacin rai yabi falon da shi, ganin yanda ya barsa a harmutsensa haka ya dawo ya tadda abinsa. Abinka da mai zuciya a kusa, tuni ransa ya sake ɓaci. A dai-dai nan Hajiya Turai ke shigowa sashen nasa. Ganin ko'ina a harmutse ga shi yanata faman huci ya sata zuba masa ido. Sai kuma cikin dauriya ta ce, “Alhaji lafiya kuwa kake miya sameka haka?”.         “A'a a cikin turnuƙun yaƙi nake? Ke ban san iskanci fa da rainin wayo”.     “Ikon ALLAH, ALLAH ya baka haƙuri da ga tambaya”.   Bai sake tanka mata ba, itama saita fara ƙoƙarin tattara falon. Taɓa Laptop ɗin sa da tayi ya sashi tunawa da Flash ɗin dake jiki. Cikin tsawa ya ce, “K bani ita nan!”. Bata musa ba ta miƙa masa zuciyarta na sake shiga mamakinsa. A fisge ya amsa. Sai dai me babu Flash ɗin a jiki. “Ina Flash ɗin jiki yake?”.      “Flash kuma? Ni banga wani Flash ba, a gabanka fa na ɗaga ta”. Wani irin kallon zan kashe ki na binne anan ya shiga binta da shi. Hannu ya miƙa mata alamar bani. Sai duk ta sake dabircewa. “Wai Alhaji kana lafiya kuwa. Wlhy ban ɗaukar maka wani Flash ba. A gabanka fa na ɗaga Lap-top ɗin nan ba wani waje naje da ita ba balle kace.”         Babu zato babu tsammani taji saukar mari har biyu. Kafin ta gama dawowa a hayyacinta ya sake miƙa mata hannu da tsananin tsawa yace, “Turai!! Bani”.             “Wlhy tallahi Alhaji ban ɗaukar maka komai ba. Wai yau ka fara zama dani ne? Koka taɓa ajiye abinka ka nema ka rasa da har zaka ɗaga hannu ka maran!”.        “An mareki ko zaki rama ne?”.     “Bazan rama ba, amma zan barka da ALLAH”. Ta faɗa tana ficewa fuuu. Mutumin naku tuni zuciyarsa neman fitowa take ta baki, amaryarsa da ya bari a falon nasa ta kuma ji komai ce tazo masa a rai. A harzuƙe ya nufi sashenta, babu ko sallama ya banka ƙofar ya shiga. Baiko kalli ƙanwarta dake gaishesa a falo ba ya wuce bedroom ɗinta kamar zai tashi sama.         “Wlhy aunty ba ƙazafi bane ba naga komai fa da idona, kuma na faɗa miki ƙanwar nan tasu data rasuce ma fa a video ɗin, ɗayar kuma ƙanwar tasu ce ta ɗauka mahaifiyar yarinyar nan da ake cema Lulu....”    Waɗan nan kalamai da suka nema fasa zuciyar Alh. Sulaiman ne ke fitowa da ga bakin amaryarsa. Abinda kuma yaji na tabbatar masa taga komai da komai kuma ta faɗa ma wadda suke wayar. Ta buɗe baki zata sake magana idonta ya sauka a kansa. Zabura tayi, kafin ya iso gareta ta kwasa da gudu ta shige toilet ta banko ƙofar. Yana dannawa tana dannowa har dai ALLAH ya bata sa'a ta murza key. Wasu manya-manyan ashariya ya fara mulmula mata yana jijjiga ƙofar tamkar zai cireta. Itako duk da a tsorace take faɗi take, “Wlhy ko zaka kasheni bazan bada ba”.     Ashariya ya cigaba da ingiza mata da tabbatar mata wlhy sai ya kasheta.......✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣4️⃣ .......Hankalin ƙanwarta da ke jiyosu a tashe ta dannama mahaifiyarsu kira. Tana ɗagawa ta sanya mata kuka da faɗin suzo dan gida babu lafiya. Ga mijin auntyn ta nan zai kasheta. Wannan kalmar ta kisa ta ɗaga hankalin mahaifiyar tasu, babu ɓata lokaci kuwa sai gasu sun iso. Iya ƙoƙari iyayenta sunyi Dan ganin ya kwantar da hankalinsa an sasanta komai amma yaƙi sauraresu. Ya kuma babbake ƙofa yana jiran ta fito. Dole mahaifinta yay kiran Baba Garko. Baba Garko yaso ƙin shiga maganar, sai da ya jiyo manya-manyan ashariya da munanan kalaman bakin ɗan nasa ta cikin waya sannan ya shiryo yazo. Karo na farko kenan da suka haɗu tun bayan badaƙalar auren Lulu. Da ƙyar aka fidda amaryarsa a gidan bayan yasha mari a hannun Baba Garko. Sam bakinsa bai mutu ba, faɗi yake sai ya kasheta idan bata bashi abinda ke wajenta ba. Itako tana rantsuwar bazata bada ba. Ana tsaka da wannan rikici itama Hajiya Turai ta fito ƴan aikinta janye da akwatuna. Bayan ta gaida Baba Garko cikin girmamawa yake tambayarta mike faruwa a gidan haka. Tana kuka ta sanar masa iya abinda ta sani, harda marin da itama yay mata. A cewarta tasan itama amaryar tasa babu abinda ta ɗauka masa, ya jefa abunsa wani wajene kawai ya huce a kansu, dan haka ita gida Sokoto zata wuce. Baba Garko bai hanata ba dan shi yama rasa abin cewa gaba ɗaya..... *_★UK★_*     Watan Aunty Bilkisu ɗaya da sati uku cir aka sallameta da ga asibiti. A lokacin Lulu nada wata biyu da sati guda a UK. Doctor ɗin da ke tsaye akan lamarin aunty Bilkisu ce ta duba Lulu a ranar da tazo yin planing. Kamar wadda aka matsi bakinta a ranar sai take tsokanar AA dake ta tsale-tsallensa a ɗakin dan yanzu yayi ƙafa. Cikin ƴar dariya take cewa Lulu ta bata fine boy ɗin nan nata dan ita dai tana sonshi. Lulu tai murmushi kawai da faɗin cewa ta bata. Dariya ta sakeyi da cewar karfa daga baya tazo tace zata amshe, tunda taga ita matsoraciyace tana gudun samun wani cikin. Nan ma dai Lulu sai tai ɗan murmushi kawai ta basar gabanta ba faɗuwa dan Smart na a ɗakin sai dai waya yake yi. Likitar nan da neman magana ta sake cewa abinda ta saka mata bai dai bata matsala ko?. Da sauri Lulu takai dubanta inda Smart yake tsaye AA na jikinsa ya riƙe masa ƙafafu. Ido suka haɗa da shi, tai saurin janyewa zuciyarta na wani irin rawa, dan tunda ta yaye AA baida magana sama da ALLAH yasa ta samu ciki. Kanta ta dafe tana rumtse idanu, sai kuma ta ɗago ta kalla doctor ɗin da tuni ta maida hankali akan Nurse ɗin dake cirema aunty Bilkisu abu a jiki suna magana. Addu'a ta shiga yi a ranta ALLAH yasa kada parrot ɗin likitar nan ta sake magana. Yayinda take satar kallon Smart ta gefen ido. (ALLAH yasa mutumin nan bai ji ba) take ta ambata a zuciyarta. Lokacin da ya kammala wayar yana takowa inda suke jitake sayin takun nasa tamkar yana yinsa ne da bugun zuciyarta. Bai nuna mata yaji ba, duk da yanayinsa ya sauya. Dan ko kallonta baiyi ba ya ƙarasa gaban aunty Bilkisu rike da hannun AA. Tambayarta yake badai tajin komai ko. Ta tabbatar masa da Alhmdllh. Kansa ya jinjina cikin lumshe ido, tare da juyawa ga doctor yace yana son magana da ita. Cikin tashin hankali Lulu da ke kallonsu ta gefen ido ta ɗago gaba ɗayanta. Nan ɗin ma bai kalli inda take ba ya saɓi ɗansa a hannu sukabi bayan Doctor ɗin. Da sauri ta motsa zata bisu, aunty Bilkisu ta kirayi sunanta cikin katse mata hanzari. Dan ita sam bataji furucin Doctor ɗin ba lokacin hankalinta nakan Nurse. Dole Lulu ta dawo badan taso ba. Sai dai gaba ɗaya jitake komai ya tsaya mata cak, hatta iskar da take shaƙa da fesarwa bata gamsar da ita. Kusan mintina goma Smart ya dawo ɗakin, daga ƙofar ɗaki ya dakata yana faɗa musu su sameshi a waje. Aunty Bilkisu ce tayi ƙarfin halin amsa masa. Lulu kam jitai tamkar an ƙarasa zare mata jijiyoyin jikinta.         Sun samesa a inda yace ɗin, Nurses ɗin da sukaima aunty Bilkisu rakkiya biye da su. Suna tsaye har sai da suka shiga mota sannan suka juya ciki. Aunty Bilkisu ya kalla ta mirror yace ta saka belt, daga haka bai sake magana ba ya tada motar batare da yace itama Lulun ta saka ba. Hakan ya mata ciwo, dan in har zasu fita shi da kansa ma yake saka mata belt amma yau ko arziƙin ta saka ɗin ma bata da. Jiki a saɓule ta saka tana mai karanto sunayen ALLAH a ranta, zuciyarta fal tunanin mi yaje yayo a wajen doctor ɗin. Rashin amsa ya sata jan bakinta tai shiru. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan, ya ɗauki ɗansa yay shigewarsa. Sai itace ta taimakama aunty Bilkisu da Iya Tabawa data fito dan ita suka bari a gidan. Baya falo sai AA kawai da ya fara karakainar ɓarnar da yafi ƙwarewa a kai. Da'alama anan ya ajiyesa ya shige. Dole ta cigaba da daurewa suka zube a falon suma. Suna nan zaune ya fito cikin shirin fita, tayi mamaki dan tasan a irin wannan lokacin yana a gida baya fita ko ina. Tana son masa magana tana tsoron ya yaɓa mata mai zafi. Duk da dai bai taɓa kwatanta hakan a gaban wani ba. Aunty Bilkisu ya cema tasha magani ta kwanta, da ga haka ya ɗauki AA suka fice.          “Wai shi wannan mike damunsa? Naga tunda ya gama wayar nan ya wani canja gaba ɗaya kamar wanda ke'a cikin ɓacin rai?”. Aunty Bilkisu ce mai maganar tana kallon Lulu. Murmushin ƙarfin hali ta saki da faɗin, “Ƙila wani abu mara daɗi aka faɗa masa a wayar aunty, kin sanshi da zurfin ciki. Idan bashi yaso a sani ba ba faɗa zaiyi ba”.       “Aike naga ma da sauƙi Mawaddat. Amma a sanin da naima Hydar akan shiru-shiru banyi zaton zai iya sakewa da mace haka ba. Dan da idan yana abu saika ɗauka yana jin ƙyanƙyamin mutane ne ma. Ka faɗa masa magana ashirin ya baka amsar ɗaya sauran in zata kasheka ne ma ta kasheka babu ruwansa”.     Dariya zancen aunty Bilkisu ya bama Iya Tabawa. Lulu ma sai tai murmushin ƙarfin hali kawai....          Tsahon lokaci basu dawo gidan ba. Lulu ta kasa samun nutsuwa sau uku tana kiran wayarsa bai ɗaga ba. Sai da ta gama galabaita da rashin dawowar tasu sannan sai gasu. Iya Tabawa ce ta amshi AA da yay barci, shi kuma ya shige ciki abinsa bayan ya ajiye musu abinda ya shigo da shi ya shige da sauran ciki. Taja mintuna kafin ta tashi tabi bayansa, dan ita dai kam da wannan fisge-fisgen gara ayita ta ƙare kawai yamayi komi zai yi yafi mata sauƙi. Ta samu har ya shiga wanka, dan haka ta zauna bakin gado zaman jiran fitowar tasa. Zuwa can kuwa sai gashi ya fito da bathrobe a jiki yana faman goge kansa zuwa wuyansa da ƙaramin towel. Kallo ɗaya yay mata ya kauda kansa. Gaban mirror ya ƙarasa ya fara shafa mai, dan haka ta taso jiki a saɓule cikin dauriya tana faɗin, “Wai mike damunka ne? Gaba ɗaya ka canja ko wani abu ya faru? Idan abinda kaji doctor ta faɗa ne dan ALLAH ka saurare ni na maka bayanin da zaka fahimta”.          “Anyi wani abu ne?”.     Ya faɗa kamar a gatsine”. Rasama mi zatace masa tayi. Sai kawai tai tsaye ta zuba masa ido. Suna samun saɓani, amma bata taɓa ganin ɓacin rai a tattare da shi irin yau ba. Dan saɓanin da suke samu ƙaramine a take su shirya kuma. Amma wannan duk ya ɗaureta da jijiyar wuyanta. Harya kammala shafa man ya miƙe zuwa wajen kayansu bata sake iya cewa komai ba. Babu jimawa ya fito sanye da pyjamas masu laushi, turare ya fesama jikinsa ya haye gado abinsa tamkar ma ya manta da ita a ɗakin.         Da ƙyar ta iya furta, “Coffee fa?”. Dan yana shansa sosai. Batare da ya kalleta ba yana jan duvet jikinsa ya ce, “Naƙoshi.”      Zuciyarta tuƙuƙi take mata, dan haka cikin rawar murya ta sake faɗin, “Dan ALLAH ka tashi muyi magana, dan nasan wlhy abinda likitar nan ta faɗa ne ya ɓata maka rai, tunda kafin hakan ai cikin farin ciki muka fita, kuma ko'a can ma babu wani canji a gareka sai da akai maganar. Ni gask.....”                A wani irin fusace ya ɗago yana kallonta. Tuni idanunsa sun kaɗa jazur. Cikin kaushin murya da ɓacin rai ya ce, “Mawaddat bana son damuwa. Kinji nace miki wani abu ne? Kin tambayeni na faɗa miki babu komai, to mikike son nace miki. Please bana son hayaniya ki barni nai barci na. Idan kuma ɗakin kike so na bar miki ki cigaba da damuna”. Daga haka ya juya yay kwanciyarsa da sake jan bargo ya rufa. Jikin Lulu rawa ya farayi dan ɓacin rai. So take itama ta masa masifar amma ta kasa, ta rasa miyyasa take jin shakkarsa a yanzu har bata iya maida masa murtanin magana balle yin wani yunƙuri. Gaba ɗaya cika mata ido yake da wani irin kwarjini, girmansa take gani mai girman gaske da bayan mahaifinta da Uncle Yousuf bata ganin wani ɗa namiji da shi a duniya. Bata son ganin ɓacin ransa a yanzu balle ace itace ta ɓata masa. Ko yaya taga yayi fushi hankalinta tashi yake yi har sai taga sun shirya.... _____★         Sam babu daɗi a tsakaninta da mijin nata ɗan tsakanin nan, zai zauna yay wasa da yaronsa suyi hira da Iya Tabawa da Aunty Bilkisu amma ita banda ita. Ya ƙaurace mata a shimfiɗa, abinci ma idon su Aunty Bilkisu ke sakashi ya ci. Amma idan daga ita sai shine sai yace ya ƙoshi. Suna a wannan halin ya wuce Coventry wasa. Tafiyar tasa ta bata damar zuwa asibiti ta nunama doctor ɓacin ranta akan abinda ya faru da tambayarta su dama basu da sirri ne tsakaninsu da patient nasu, haƙuri ita dai doctor ta bata dan batai zaton al'amarin zai zama a haka da girma ba. Sannan ta faɗa mata bata san mijinta bai sani ba ai.       Kwanansa uku ya dawo. A ranar ne ta gama shirya sai dai suyi duk wacce zasuyi. Dan ta haɗa kayanta tsaff akan zata koma Nigeria. Kamar yasan shirin nata bai shigo gidan ba wannan karon sai dare. A yanayin gajiyen da yake yasa bai zauna ba suka gaisa da su aunty Bilkisu sama-sama ya shige ciki........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣5️⃣ ......... Da kayan data haɗa na tafiya ya fara cin karo. Yay ma kayan kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Har ya gama wanka ya kimtsa bata shigo ba, duk da yaji hakan babu daɗi sai ya daure. Ganin bata da niyyar shigowa shi kuma yana bukatar shayi ya sashi mikewa ya fita da kansa. A falo ya sameta zaune ta zubama tv ido. Ɗan tsai yay yana kallonta na wasu sakkani, sai kuma ya ɗauke kansa ya wuce kitchen. Babu daɗewa ya dawo ɗauke da cup ɗin shayi, wucewarsa yay nan ma ya barta da ƙamshin turarensa. Takaicinsa ne ya turnuƙe mata zuciya, taji kamar ta fasa ihu. Sai kawai ta ɓige da sakin kuka mai cin rai. Wayarta ta ɗauka, tai tsai tana kallo da tunanin wanda zata kira ta sanarma damuwarta, sai kuma zuciyarta ke kwaɓarta da yin hakan. Wani gefe na bata shawarar gara taje suyi duk wacce zasuyi ita da shi amma karta yarda sirrinsu ya zama abin kasawa a fai-fai. Sannan ba lallai ne ba ta samu goyon bayan wani, musamman idan tai la'akari da yanda mutanenmu suka ɗauki haihuwa abu mai matuƙar muhimmanci. Wayar ta yarfar a kujera wasu hawayen masu zafi na silalo mata. Ita da wannan shariyar da yake mata gwara ya balbaleta da masifa kawai, idan yaso ma ya haɗa harda duka yafi sauƙi. Batun yanzu ba ta tsani ta samu saɓani da mutum ya mata shiru, gara a sanar mata ayi hayaniyar da za'ayi komai ya wuce, saboda ita bata iya riƙo ba sam. Shiyyasa tafi yarda da da'an mata ta rama kawai a wuce wajen sai wata kuma ta taso.         Aunty Bilkisu da ke karance da yanayinsu a kwanakin nan leƙowarta biyu tana ganin Lulu zaune a falon. Ana ukun ne ta sameta tana kuka. Shiru tai tana kallonta cikin nazari, kafin ta ƙaraso cikin dakin ta kai zaune a kusa da ita ta zari tissue ta miƙa mata. Lulu bata musa ba ta amsa ta share hawayenta. Sai dai duk da haka basu daina zubowa ba. Lokaci sosai ta bata ta rage nauyin zuciyarta da kukan kafin ta fuskanceta. Cikin tausasa harshe ta ce, “Wannan shine auren! Shine kuma haƙurin da iyayenmu ke yawan jaddada mana akan muyi idan za'a kaimu gidan aure da bayan an kaimu. Su maza haka suke zuma ne ga zaƙi ga harbi. Zaka iya kuma cin karo da kowanne a garesu a kowanne irin lokaci koda babu wani ƙwaƙwƙwaran laifin da kai musu. Mawaddat kada ki kalleni a matsayin yayar miji, kalleni a matsayin yar uwarki mace da tasan zafinki da sanin ma'anar kalar raɗaɗin da kike ciki. Minene ke faruwa tsakaninki da shi?. Karki damu ki faɗa min, zan koya miki dabarun da zaki cimmasa, dan nasan Hydar nada zuciya, kafiya, da taurin kai akan abinda yake ra'ayinsa.”          “Aunty ni ban san mina masa ba. Na tambayesa amma yaƙi faɗa. Har roƙonsa nayi bai saurareni ba. Ni gaskiya ina son na wuce gida bazan iya ba....”       A bazata batare da sun san yana a bayansu ba suka ji saukar muryarsa a kansu, “Ai dama bazaki san mi kikamin ɗin ba, gida kuma ga hanya nan a buɗe tunda dama shine burinki tun ba yanzu ba!!”.          A zafafe itama Lulun ta ɗago zatai magana aunty Bilkisu ta jinjina mata kai tare da jimƙe hannunta cikin nata alamar kar tace komai. Shirun tayi sai dai ta fashe da kuka. Tsaki yayi da juyawa zai koma dan dama kofin da ya sha shayi ya fito maidawa kitchen, da sauri aunty Bilkisu ta dakatar da shi da faɗin, “Hydar dawo ka zauna”.           “Aunty ni mizan zauna na mata, kina jin fa abinda take cewa. Dan taga na ƙyaleta bance komai ba har tanada bakin faɗama mutane zata wuce gida. To zuciya take tunanin ta fini ko mi?...”      “Hydar Please cool dawn mana. Nace ka zauna. Idan kuma Ammah kuke son na kira muku nikam sai na kirata. Maybe ita kufi jin maganarta”.    Ransa a ɓace ya dawo ya zauna. Sai faman sauke huci yake. Yayinda ita kuma Lulu take kuka. Sai da aunty Bilkisu ta basu mintina kamar uku zuciyoyinsu suka ɗan risina kafin tai gyaran murya kaɗan tana fuskantar Smart. “Aliyu mike faruwa? Kasan dai Mawaddat amana ce a hannunka, sannan ni shaida ce tanada haƙuri da ƙoƙarin ganin ta ƙyautata maka a matsayinka na mijinta da kiyaye duk wani ɓacin ranka. Shin miya kawo wannan fitinar a tsakaninku haka babu daɗi? Kuna ganin kunmin adalci abu ya faru kuna irin wannan tashin hankalin ina a tsakkiyarku. Wane laifi ta maka? Miya faru kake fushi da ita? Tunda ita ta tabbatar min bata san abinda tai maka ba...”          “Ai bazata sani ba tunda ta ɗaukeni wawa da bai san ciwon kansa ba....”        Cikin kuka Lulu da ke kallonsa ta ce, “Toni ya kake so nayi maka ne Aliyu. Na tambayeka kace ban maka komai ba. Amma kana fushi da ni. Ko magana baka son kayi dani, idan ka gaji da zamanmu ne ka sallaman na wuce tunda ai ba dole bane. Ni dama bance inayi ba balle kaji su bini da tsatstsaga....”             “Oh nine kazar kenan? Ai ba sai kin faɗa ba dama nasan ba ƙaunata kike ba. Dan baki da yanda zakiyi da ni ne kawai kike zaune. Sai dai ban san ƙiyayyar da kike min ɗin takai girman haka ba, har ki guji haihuwa da ni. Na farkon dama ALLAH ne yayi maganinki ya samar da shi a lokacin da bakiyi zato ko tsammani ba, shine yanzu kika bi hanyar takaita ni. To sai ki sake ɗaura ɗammara dan wannan batai dai-dai da ke b.....”       “Ya ALLAH Aliyu...” Aunty Bilkisu ta katseshi cikin tashin hankali. Dole yay shiru shima yana hucin. Yayinda Lulu ke kukanta ita dai. Shiru falon yayi kusan mintuna biyu sai ajiyar zuciyoyinsu sannan aunty Bilkisu ta sake dubansa. A nutse ta ce, “Kai waya gaya maka bata son haihuwa da kai Hydar? Banji daɗi wannan furucin naka ba sam gaskiya”.            “Gaskiyar kenan ai aunty, inda tana son haihuwa dani bazataje tai planing babu sanina ba. Da haka zamuyita tafiya ni ina tunanin akwai matsala ita kuma tana cutar dani. Da yake bani da hakkinta sai gashi ALLAH ya sanar dani ta hanyar likitar da taje ta dubata. Ni na taɓa cemata bana son yarane? Gidanmu mu kusan talatin aka haifa, yanda na tashi na gammu nima haka nake fatan tara zuri'a. Amma shine zata zaluntan....”       “Niba azzaluma bace, kuma nima bance bana son haihuwar ba ai...”     “Ƙarya kike yi wlhy, idan ba zalunci ba mi kikayi? Da lafiyata da ƙuruciyata ki cutar dani ta hanyar katangeni da ganin jini na. Ke wlhy kika sake maidamin magana zan fasa bakinki ne har sai haƙoranki sun zuba. Bana son raini ki shiga hankalinki kar kiga ina ƙyaleki ki ɗaukeni wani banza can!!....”             A hargitse Lulu take dubansa. Zatayi magana Aunty Bilkisu ta hanata. Shiko sai huci yake yi dan ya gama kaiwa wuya. Abinda Lulu bata sani ba Smart ya tsani yana magana ana maida masa. Musamman idan shi akaima laifin yana sake harzuƙa ne. Duk yaran gidansu sun san wannan halin nasa, shiyyasa suke kiyaye wa. In ko kai kuskuren dagewa akan dole sai ka masa bayanin da zaka fidda kanka zai iya maka dukan hauka ne ya bar uwarka da jiyya. Wannan itace babbar matsalarsa, idan yay ƙololuwar fushi baya iya controlling temper ɗinsa sam. Shiyyasa yake da ƙoƙarin kauda kansa akan abubuwa. Ganin yanda ya fusata ya saka aunty Bilkisu cewa suje su kwanta da safe sa ƙarasa. Shi ya fara tashi fuuu ya wuce, dan haka ta hana Lulu tashi. Nasiha ta fara mata da sanar mata halinsa na son rashin maida murtani ko bama kai kariya. Dan shi idan akai masa laifi ko bayani wani lokacin baya buƙatar ai masa. Gara ka masa banza idan ya gama hawa da saukar zai huce da kansa ya dawo ya binciki gaskiya in ma hukuncinne ya maka. Ta nuna mata kuskurenta tare da bata shawarar taje ta cire abinda ta saka ɗin. Haihuwa ai komai na ALLAH ne. Ayi fatan kawai ALLAH ya bada masu albarka. Lulu taji daɗin nasiha da shawarar aunty Bilkisun, dan haka ta ɗan ji zuciyarta ta rage mata nauyi.         Koda ta shigo ɗakin kwance ta samesa. Batai magana ba ta shiga toilet tayi wanka ta gyara jikinta. Kamar yanda sukeyi a tsakanin nan kwanciyar kai da ƙafa haka ta kwanta yau ma. Ta lulluɓa da bargon data ɗakko. Duk abinda take yana jinta, amma ko motsawa baiyi ba. Sai can cikin dare sosai ya tashi yayo alwala ya zo ya kama salloli. Sai da ya ji zuciyarsa ta samu nutsuwa da karatun Alkur'ani sannan ya tsagaita. Ganin asubahi ta gabato ya haƙura bai kwanta ba har sai da yay sallar asubahi. Alerm ne ya tada Lulu, dama haka yake mata tunda suka samu saɓanin. Kafin ta fito bayi ya haye gadon yay kwanciyarsa...       Ranar yini yay barci, dan sai azhar ya tashi. Babu kowa a ɗakin sai shi kaɗai. Yay wanka ya shirya cikin ƙananan kaya marasa nauyi. Suna falo zaune Iya Tabawa na basu labarin sanda suna ƴammata Lulu na kwasar dariya kamar ba ita tasha kuka jiya ba ya fito, sam ita bata da riƙe abu, shiyyasa idan aka riƙeta take jin zafi. Da gudu AA dake wasa ya nufosa. Cak ya ɗaga yaron sama yana mai sumbatarsa cike da jin ƙaunarsa. A haka ya kai zaune cikin kujera suna dariya shi da AA ɗin da yakema cakulkule. Iya Tabawa ya fara gaisarwa sai aunty Bilkisu. Ya tambayeta yaya jikin tace Alhmdllh sai fatan komawa gida lafiya. Murmushi yay da faɗin, “Ai keda Nigeria sai nan da shekara ɗaya”.       Idanu ta waro sosai da faɗin, “Shi kuma mijin nawa kuyi yaya da shi?”.     Cikin kauda kai da taɓe baki ya ce, “Uhm su miji”. Kafin aunty Bilkisu ta sake cewa wani abu a fisge Lulu tace masa “Good Afternoon”. Kallonta yayi shima a karo na biyu cikin ɗauke kai yace, “Afternoon” a taƙaice. Daga haka babu wanda ya sake kula ɗan uwansa. Abinci ma sai da aunty Bilkisu ta zungureta ta tashi ta kawo masa. Batai zaton zaici ba, amma sai taga yaci sosai yana bama AA. Bata san yayi matuƙar kewar girkin nata ba ne. Basarwar da yake ɗin ma ta dole ce. Haka ya ƙarasa yinin nan a gida yau ko waje bai leƙa ba har washe gari. Washe garin ma sai zuwa yamma ya fita training center ɗinsu........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣6️⃣ .......Kwana uku ya ɗan fara hucewa a dalilin murar zazzaɓi da Lulu ke fama da shi. Duk da dai tana nuna ita ƙalau take. Sai da murar tai mata tsanani ne ta haƙura takai zaune. Mata da miji sai ALLAH sai gashi yana tattalinta da matsa mata tasha magani. Harda haɗa mata shayin kayan ƙamshi da kansa. Idan yaga AA zai takura mata ya ɗaukesa ya kaima Iya Tabawa. Ya bata kulawa sosai harta samu sauƙi. Da ga haka aka shirya kamar basu ba aka koma nunama juna soyayya da tattali. Sai aikinsu da suka saka a gaba. Ita aunty Bilkisu ma sai abin ya koma bata dariya. Shiyyasa dai akace duk wanda ya shiga tsakanin mata da miji ya matse. Dan zasu shirya ne su barsa a ciki. A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa mura na damun Lulu akai-akai. Ita abin har mamaki yake bata dan bata cika yawan mura ba a da. Sai dai ta danganta yanayin da sanyi da ake yi sosai harda dusar ƙanƙara.      Wasan su Smart na tafiya cike da nasarori da kalubale. Yayinda sunansa keta ƙara cigaba da amsa kuwa saboda yanda yake zura ƙwallaye a raga babu ko ɗar. In dai za'a kirayi sunan wani yaro mai tashe a wannan ƙarnin a harkar ball idan sunansa baizo na ɗaya ba dolene yazo ana biyu. Ballema ALLAH ya bashi farin jinin da akan ambacesan a farko. Sam baya wasa da addininsa. Sannan tsaye yake akan Lulu itama dan har yanzu shine mai ɗora mata karatu datai matuƙar maida hankalinta a kai. Wani lokacin kuma aunty Bilkisu ke ɗora matan.. A gefe kuwa sun matuƙar saka rayuwar Alh. Sulaiman a gaba, dan a yanzu haka ana tsaka da dambarwa ne tsakaninsa da amaryarsa akan Flash. Anyi-anyi ta bada taƙi. Yayi haukan yayi hargagin yayi kurarin duk da tana a gidan nasu tayi kememe. Hajiya Turai dai ce ƴaƴanta suka dawo da ita. Acewarsu sai da Mahaifin nasu ya bar mata gidan badai ita ta bar masa ba. Dan babu kunya suka dinga yaɓa masa magana musamman ma Tajuddeen, Alh. Sulaiman ranar harda hawayen baƙin ciki. Bai taɓa tunanin soyayyar da yakema Tajuddeen zai iya kallon tsabar idonsa ya masa rashin kunya haka ba, al'amarin ya girgiza zuciyarsa kam.. (Abinda kayi dole ai maka ai dama🚴🚴🚴😂).            *_NIGERIA_*    Watanni kusan huɗu kenan abubuwa na'a rincaɓe musamman a ɓangaren Alh. Sulaiman Garko. Dan anata musu tsinci ɗai-ɗai na masifa ta yanda gaba ɗaya kasuwar tasu ma ta tsaya cak. Ga manyan kayansu da ke gaf da zuwa Najeriya ɗin. Duk yay wani iri da shi duk da har yanzu ma shi bako a fara taɓashi ba. Dan ko'a cikin yaransa kaf babu wanda aka taɓa. Sai aminansa da Hon. Nakowa kawai ya rage sauran duk suna hannun hukuma anyi ram da su. Kullum cikin kiran Daddy yake yana masa barazana. Shiko Daddy na maida shi mahaukaci da naɗe komai a waya tare da kunnashi. A gefe ɗaya ga al'amarin amaryarsa da yaƙi ci yaƙi cinyewa. Burinsa kawai ya amshi Flash ɗin hannunta koda zai kasheta ne shi babu ruwansa. Tayi-tayi ya saketa kuma yaƙi. A randa yaje har gida ya cima mahaifinta mutunci ta tabbatar masa anzo gaɓar da take jira, dan haka a ranar ta aike ma su Baba Garko da video. Da kanta ta shirya taje har gidan ta danƙama Baba Flash. Har wulaƙanci Dada taimata saboda taje ta gaida amarya da duba yaranta. Ita dai bata tanka mata ba har Dadan tayi ta gama san ranta. Bayan wucewarta ne Dada ta nufi wajen Baba Garko. Ta sameshi da ƴan biyunsa da sukai kuɓul-kuɓul gwanin sha'awa. Takaici kamar zai tsayar mata da numfashi amma ta danne da ƙyar. Dama bata taɓa ɗaukar yaran ba tunda aka haifesa, dan haka yanzun ma kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta. Ko'a ƙwallar rigar Baba Garko, dan ya jima da fahimtar bakin ciki take da yaran. Sama-sama ya amsa mata gaisuwa ya cigaba dama yaransa wasa kamar ma ya manta da ita. Hakan ya sake Zafafa mata zuciya taji ta tsani yaran fiye da ko yaushe. A cikin tunzura ta ce, “Amma dai Alhaji bai kamata ka fifita rayuwar ƴar wasu akan naka ba. Yanzu yarinyar nan ta gama fetse mana yaro da iskance-iskanceta ta dawo tana mana barikanci. Ni na rasa mi Sulaiman yayi maka haka da zafi ne. Kabi ka tsangwamesa babu laifin tsaye babu na zaune. Idan ma maganar Mawaddat da Tajuddeen ce ya kamata ace ta wuce tunda dai tana gidan mijin da kuke son ganin nata da shi yanzu ai ko”.         Idan ɗakin ya tanka Baba Garko ya motsa, hakan ya sake harzuƙa Dada. Miƙewa tayi a fusace zuwa gabansa ta ɗauke Flash ɗin dake ajiye kusa da shi. Nan ɗin ma bai tanka mata ba harta fice, bai kuma nuna damuwa da ya bita akan flash ɗin ba ya cigaba da yima yaransa wasa. Hajiya Dada kam da masifa ta nufi sashenta. Harta ɗauki waya da nufin kiran Alh. Sulaiman akan yazo ya amsa sai kuma ta ajiye tana faɗin, “Bara dai naga wai ubanmi akema wannan tashin hankalin ne a ciki.” Ta ƙwalama mai aikinta kira. Jiki na rawa ta iso, a gabanta ta zube cike da girmamawa. Umarnin ɗauka mata tab.. a ɗaki ta bata. Babu jimawa ta dawo ɗauke da tab.. ɗin. Ita ta saka mata flash ɗin. Cike da gadara da ƙasaitar mulkin masu akwai Dada ta amsa ana wani gyara zama da busa iska tace mai aikin ta kawo mata lemo. Ita dai mai aiki umarni take bi.         Fuskar data fara bayyana ta saka ƙirjin Dada bugawa, jikinta ya fara tsumar kewa. Mawaddat ɗinta ce, yarinya mai hankali, mai sonta da ƙaunarta, sai dai ita kullum tana a cikin hantararta ne saboda tana ce mata kaza ba daidai bane kaza ne daidai. Kalaman Mawaddat suka cigaba da jan hankalinta kafin kace mi ta jiƙe sharkaf da zufa. Maimakon hasken ɗakin ta koma ganin duhu. Tun tana iya jin sauti da motsi har komai ya tsaya mata cak sai razanannen ihunta daya karaɗe kunnuwan duk wanda ke a kusa da sashen nata. Rige-rigen shiga masu aikin nata suka shiga yi inda take, sun sameta wanwar a ƙasa kofin lemon da aka ajiye mata ya kife da alama ma a kansa ta faɗa. Duk da hankalinsu ya tashi da ganin a yanda take sai da suka ɗauki tab.. ɗin suka kalla abinda ya razanatan. Yayinda mai tausayin cikinsu ta fita a guje kiran Baba Garko. Ai suma sai suka ƙare da ƙwalla ƙara a dai-dai shigowar Baba Garko da amaryarsa, dan tana tare dashi sanda mai aiki taje kiransa....         An ɗauki Dada babu alamar rai a tattare da ita ga jini na zuwa ta inda gilashin kofi ya jimata ciwo. Shi kansa Baba Garko a kiɗime yake dan bata taɓa kasancewa a irin hakan ba duk wannan rikicin da akeyi. Iyaka dai ta suma da'an zuba mata ruwa ta farfaɗo. Amma yau babu abinda basu gwada mata ba ko motsi. Da tab.. ɗin ya fita a hannunsa, dan yasan koma mi ya sakata a wannan halin bazai kasance ƙaramin ba.       Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya isa kunnen ƴaƴanta da jikoki. Kafin wani lokaci asibitin da aka kaita ya cika da Garko family, zuri'ar Uncle Khamil dake Abuja ne kawai babu suma suna tafe sai na auta dake a Saudiyya. Har zuwa washe gari ba'a samu kan Dada ba, dan haka hankalin kowa ke'a tashe. Hatta shi uban gayyar a wannan karon hankalin nasa a tashe yake. Dan koba komai fa yana son matarsa, sannan itace uwar ƴaƴansa. Tun shekarun ƙuruciya suke tare har zuwa tsufa da daɗi babu daɗi tana zaune da shi. Washe gari zuwa sha ɗaya na safe auta ya iso tare da nasa iyalinsa, tamkar shi Dada ke jira ya iso ta farfaɗo, sai dai fa numfashin farko da taja ta fesar da jini ta fesoshi. Wani sabon tashin hankalin kenan, dan likitocin ma sun kasa musu bayani, sai kai-kawo da shigi da fici sukeyi. Duk wanda suka tunkara sai dai ya zame da faɗin yana zuwa. Duk wannan abun da akeyi babu Alh. Sulaiman sai ƴaƴansa da uwar gidan sa. Karan farko da Tajuddeen yaji baƙin cikin halin mahaifin nasa. Shin wai minene na wannan gabar, a ganinsa mahaifiya ai tafi gaban wasa. Dada na a irin wannan yanayin har yace yanada wata hujjar cigaba dayin gaba. Duk wanda yaga Dada a jiya zuwa yau dolene ya tausaya mata. Shi kansa Baba Garko ya ajiye makaman yaƙinsa harda hawaye yake da sambatun ta tashi dan ALLAH kada ta tafi ta barsa. Cikin ɓacin rai Tajuddeen ya dannama ubansa kira. A lokacin yana ɓoyayyen Companyn sa suna tattaunawa da yaransa malami da wasu abokan cinikayyarsa mazauna Legos akan kayansu da suka iso Nigeria a daren jiya. Sai dai sun rasa yanda zasu fidda kayan daga bakin ruwa saboda kamar fa an saka musu ido... Yana ɗaga wayar Tajuddeen ya fashe masa da kuka cikin masifa yake faɗa masa “Yanzu nan Dad har kanada lokacin nishaɗi haka mahaifiyarka kwance ranta a hannun ALLAH tana aman jini likitoci tun daren jiya tsaye a kanta. Anya kuwa kana fatan gamawa da duniya lafiya Dad. Ace iyayenka ne abokan gabarka. In dai dan ni kakeyi toka ajiye dan nikam dai na haƙura da Mawaddat koda ace sonta zai zamar min ajalina. Duk ƴan uwanka gasu nan har wanda basa ƙasar kai kaɗai ne ka fita zakka a cikinsu saboda son zuciya. Idan ta mutu sai kazo zaman gaisuwa ai” ya faɗa yana yanke kiran wani irin kuka mai cin rai na kufce masa... *_★UK★_*     .....A dalilin wayar Tajuddeen da mahaifinsa su Lulu suka san halin da ake ciki. Domin suna tsaka da ganin zaman meeting ɗin Alh. Sulaiman da abokansa ta direct camara ɗin su. Hankalin Lulu ya tashi matuƙa, dan koma minene ya faru Dada ba abar yardawarta bace ba. Kuka ta fara cikin tashin hankali ta shiga neman layin ƴan uwa. Da kyar ta samu Uncle Amin ya ɗaga. Cikin kuka take faɗin yanzu nan Dada na'a irin wannan halin amma babu wanda ya faɗa mata. Lallashinta Uncle Amin ɗin ya farayi akan ta kwantar da hankalinta tai mata addu'a daga inda take. Amma ina Lulu taƙi saurarensa. Shima Smart ɗin ta matuƙar tayar masa da hankali, dole ya saya mata ticket dan bazai juri ganinta a haka ba. Sai dai ita kaɗai zata taho banda AA. Ta barsa wajen Iya Tabawa da aunty Bilkisu da har yanzu bata kammala ganin likita ba duk da tana a gida lokaci-lokaci dai take zuwa ana dubata asibitin........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣7️⃣ .......Uncle Yousuf da kansa yaje ɗaukar Lulu airport. Da ga airport ɗin kuma asibiti suka wuce kai tsaye. Ba ƙaramin girgiza zuciyarta tayi da ganin kowa da kowa na asibitin ba. Ashe ƴan Saudiyya ma har sun ƙaraso. Kasa haƙuri tai sai da ta leƙa Dada ta window. Dan an hana kowa shiga wajenta Baba Garko ne kawai ya shiga bayan likitoci sun sami kanta da ga aman jinin da take yi. Kuka sosai Lulu keyi da ya sake ɗaga hankalin duk wanda ke a wajen. Uncle Taheer Auta ne ya kama hannunta suka bar wajen, da ga gefe ya zaunar da ita yana lallashinta akan ta daina kuka addu'a Dada ke buƙata a yanzu. A hakama an samu kanta ba kamar da safe ba. Wannan ɗan lalashin da autan Dadan ya mata ne ya ɗan saka mata nutsuwa kaɗan ta rage kukan da take yi. Lokacin da zasu wuce gida tace ita a barta anan zata kwana. Hajiya Turai mahaifiyar Tajuddeen ce tai ƙarfin halin cemata, “A'a Mawaddat kema kulawar kike buƙata ai a wannan halin da kike ciki. Ga tafiya mai nisa kinyo”. Da yawan ahalin wannan family sun san ALLAH ya bama Hajiya Turai baiwar gane ciki koda ƙarami ne, dan haka kowa ya fahimci abinda take nufi akan Lulu ballema duk mai lura yaga Lulu yasan tana da ciki saboda illahirin halittun jikinta sun nuna hakan duk da kuwa akwai jin daɗi da samun kwanciyar hankali. Abinda bata sani ba hatta Iya Tabawa ta jima da fahimtar tana da ciki, tayi gum da bakinta ne kawai har ya bayyana kansa. Ita kanta aunty Bilkisu cikin kokwanto take magana ce kawai batayi ba. Amma har so tai ta tseguntama Ammah da ga baya kuma dai tai shiru dai. Lulu dai ba fahimtar Hajiya Turai tayi ba, sai dai babu yanda zatai ta yarda ta bisu. Kasancewar motar Hajiya Turai ɗin ta shiga sai kawai ta wuce da ita can gidansu (Gidan Alh Sulaiman kenan).         Alh. Sulaiman da tun wayarsa da Tajuddeen ransa ke'a ɓace yana zaune labarin zuwan Lulu Nigeria ya sameshi. Baida niyyar zuwa asibitin duk da baƙaƙen maganganun da ɗan cikin nasa ya faɗa masa sun kartar masa zuciya amma jin abar farautarsa a kusa da shi ya sashi niyyar zuwa. Sai dai bai baro Companyn nashi ba sai dare sosai saboda bada ƙafa. Sun riga sun gama shirya yanda zasu sace Lulu shida yaransa. Dan haka kai tsaye asibitin ya nufo. Sai dai ya samu kowa ya tafi sai ƙanwar Baba Garko kaɗai da ke tare da Dada. Inna Sadiya nada labarin komai na tsakanin Sulaiman da iyayen nasa, dan haka ta kallesa sheƙeƙe ta watsar, gaisuwar tasa ma sama-sama ta amsa masa. Duk yanda yaso jin wani abu daga gareta bata kulashi ba. Dole ya kama gabansa yana jan tagwayen ƙwafa da jin kamar ya make banza ya wuce. Yana fitowa yay kiran yaronsa Malami. Ya sanar masa su rabu zuwa gidan Daddy da Uncle Yousuf dan Lulu bata asibitin. Sun amsa masa da girmamawa, duk da sun san tsaron dake zagaye da gidajen daya faɗa ɗin, daga haka ya wuce gidansa shima. Koda ya iso bai nema matarsa ba kamar yanda itama ba shiga sabgarsa takeba a yanzun, dan tace zaman ƴaƴanta kawai takeyi ita kam dan ya gama fita mata a rai kasancewar amaryarsa ta sanar mata komai. Dan bayan dawowarta ƴaƴanta mata yayun Tajuddeen da ita sunje gidan su amaryar tasa domin lallashinta itama ta dawo ta nuna musu ai itakam tabar gidan nan har abada. Da suka matsa ne taja Hajiya Turai gefe ta sanar mata komai tare da nuna mata video ɗin nan. Hankalinta ya tashi matuƙa, dan itace ma ta bata shawarar ta kaima su Baba Garko videon inba haka ba mijin nasu zaibi duk wata hanya ya kwacesa a hanunta. Ba ƙaramin ruɗani Hajiya Turai ta shiga ba a week ɗin da ya gabata, da ƙyar ta iya tausar zuciyarta ko yaranta bata sanarmawa ba har yanzu.         Zuwa cikin dare jikin Lulu ya ɗume da zazzaɓi, kasancewar kwana biyun nan haka take fama sai bata damu ba. Ta dai sha magani ta kwanta duk da tana jin kewar mijinta ta taushi zuciyarta, sai gabannin asuba zazzaɓin ya saketa. Tana idar da salla kasa haƙuri tayi ta ɗora layinta na Nigeria akan waya. Smart ta fara kira. Bugu ɗaya ya ɗaga mata. A tare suka sauke nannauyan numfashi. Kafin a hankali ya fara furta, “Kin san ko yanda kika bar zuciyata cikin barazana da tashin hankali Baby luv. Tunda kika sauka nake jiran kiranki amma shiru har na fara jin nauyin yawan kiran da nakema Daddy da Uncle Yousuf.”         “Kayi haƙuri”.   Ta furta a hankali. Ajiyar zuciya ya sake saukewa da faɗin, “Ya zanyi, na haƙura. Ina dai fatan babu wata matsala ko? Dan wlhy gaba ɗaya na kasa nutsuwa duk da nasan wawan baiyi zaton kina gidansa ba”.     Murmushi Lulu tayi har yana iya jiyo sautinsa. Cikin ƙara tausasa harshe ta ce, “Bayan ka bashi ƙafa taya zai iya gano ka. Dolene na bama wanda ya saka maka suna Smart ƙyauta gaskiya. Mutum yana nemana ruwa a jallo amma ka turoni gidansa na kwana kuma. Sannan kada ka manta kawuna ne kake cema wawa”.          Ƙaramar dariya yayi shima. Ya ce, “ALLAH sarki masu kawu yi sorry. Sannan banda wata mafita sai hakan ai. Dan nasan bazai taɓa kawoma ransa zaki zo gidansa ki kwana ba. Yanzu dai sai kiyi taka tsan-tsan kuma.”      “In sha ALLAHU mijina. Jiya gaba ɗaya kewarka ta hanani isashen barci”.                “Uhm kamar da gaske. Ni ban san daɗin baki. Ina Aliyu yaga wannan matsayin. Ke dai kawai kice tsoro ya hanaki barci kina a gidan dodoki”.           “Oh hakama zakace ko? Shikenan ai zan rama. Bazan ma dawo ba sai bayan wata tara kama kanka”.      Dariya sosai yakeyi da faɗin, “Haba Baby luv ki tausayamin mana. Ni kaina kin ganni nan yanzu haka nama kasa kwanciyar sai lissafi nake da kallon hotunanki kawai. Na gayyato Baban Ammah ya tayani kwana ya addabeni da ɓuruntu.”           Cikin dariya ta ce, “Kai miya kaika wannan gangancin siyen gida a sama.”       “To yana iya kewar Mamansa ta isheni ne. Ni da ƙyar ma idan zan iya haƙuri ban taho Nigeria ɗin nan ba”.    Idanu ta waro sosai kamar tana gabansa. Ta ce, “Are you serious zaka iya barin wannan kwallon ka taho Nigeria?”.         “Humm yarinyar nan kina wasa da Aliyu ko? Zan baki mamaki”.     “A'a A'a nagode basai ka bani ba. Ai nasan zaka aika wlhy yi zamanka na yafe. Nima ba jimawa zanyiba ai. Yanzu dai ina son naje naga Ammah yaya za'ayi?”.     “Kefa rigimarki yawa gareta Mrs Mawashi. Keda ake ɓoyonki ina kuma zaki je yawo?”.             “Zuwa wajen uwata ne yawo. To nidai kasan yanda zakai dani gaskiya”. Ta faɗa cikin shagwaɓa har yana iya jiyo sautin yanda take buga ƙafa ƙasa.        “Kirufamin asiri Baby luv nayi barcina lafiya, kinga dai na sakama raina haƙuri tunda kika taho ko kuka banyi ba”.     Sosai Lulu take dariya. Ta ce, “Kuka fa?”. “Eh mana, na dai zama kalar tausayine kawai ko wanka yau ma bazanyiba. To in nayi wazan mawa baƙya kusa”. Dariya ta sake ƙyalƙyalewa da shi. Smart ɗinta kenan Zuma ga zaƙi ga harbi. Duk wanda kake buƙata za'a sayar maka akan farashin da ya dace. Sun jima suna hirarsu kafin ta tashi tayi shirin zuwa asibiti. Dan bazata iya sake komawa barci ba....       ★Yaran Alh. Sulaiman nacan sun kasa sun tsare a tituna jiran fitowar Lulu da ga gidansu ko gidan Uncle Yousuf. Anan ko su har sun fice gidan Alh. Sulaiman sai fitar motar matarsa ya jiyo. Ƙwafa yayi dan yayi alwashin koya mata hankali itama dan yasan ita ke zuga masa yara suna mai rashin mutunci. Ranar matan sun masa akan dawowarta gidan. Jiya kuma Tajuddeen ya masa akan Dada. Bai damu da fitar tata ba dan yasan asibiti ta wuce. A asibiti sun samu jikin Dada yau dai Alhmdllh, da sauƙi irin na malam bahaushe da ake faɗi. Amma dai har yanzu bata gane komai, sai ambaton sunan Sulaiman da take a hankali hawaye na ziraro mata. Duk wanda ya shiga dubata sai ya fito da mamakin yanda ta damu da al'amarin yayan nasu Sulaiman haka, bayan rashin mutuncin da yake zuba musu salo-salo. Sai da ta koma barci ne Baba Garko ya ce iyayen su sameshi gaba ɗaya a gida. Ganin haka sai itama Lulu tai kiran Smart kawai akan zuwa wajen Ammah. Sai da yay ɗan jimmm sannan ya amsa mata da “Naga dai kin matsa da ganin Ammahn nan, ɗan bani 10minut haka”.        Baki ta murguɗa masa tamkar tana gabansa....       *_GARKO HOUSE_*      Ƴaƴansa ne gaba ɗaya. Alh. Sulaiman da wanda suka rasu biyu mahaifiyar Lulu da Sultana ne kawai babu. Sunyi kusan zaman mintuna huɗu kafin ya fito. Bayan yakai zaune suka sake gaishe da mahaifin nasu. Da kai ya amsa musu yana gyara zama dan zuciyarsa sam babu daɗi. Sai da ya gama ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya kafin yay gyaran muryar da ta sakasu sake maida hankalinsu garesa.        “Na taraku anan ne a dalilin abinda yay sanadin kwanciyar mahaifiyarku asibiti duk da ni har yanzu ban san minene ba shiyyasa na buƙaci ganinku mu gani tare dan zata iya yiwuwa nima na tsinta kaina a yanayin da yafi nata ma...” cikin tashin hankali da ruɗani duk suke kallonsa. Bai damu ba ya cigaba da faɗin, “Nasan wasunku sun san rikicin dake tsakanin ɗan uwanku da matansa wasu basu sani ba. A watannin da suka gabata rikicin da bamu san tushensa ba ya ɓarke a tsakanin Sulaiman da matansa su dukansu har suka wuce gida. Sai daga baya uwar ƴaƴansa ta dawo amaryar da al'amarin yafi tsamari a kanta taƙi ta koma. Na barsu ne naga iya inda abin nasu zai kai sai kuma gashi jiya ta samemu anan gida. Flash drive ta kawo mana ta tace shine sanadin rikicin nasu. Da ga haka batai mana wani ƙarin bayani ba ta tafi. Bayan wucewartan ne mahaifiyarku tazo ta ɗauki Flash ɗin ta wuce da shi sai mai aikinta ta isarmin da saƙon gata can ta faɗi babu rai. Duk abinda zai saka mahaifiyarku a wannan mummunan yanayin bazai kasance mai sauƙi ba. Shiyyasa tun jiya na kasa dubawa ni kaɗai na zaɓi mu duba tare da ku”. Ya ƙare maganar yana jawo tab ɗin Dada da har yanzu flash ɗin ke a jiki. kusa da shi duk yay musu nunin su dawo. Haka suka zauna wasu kusa da shi a ƙasa wasu a kujera. Babu wanda zuciyarsa bata kaɗa ba a lokacin da fuskar marigayiya Mawaddat ta bayyana. Kafin sukai karshen videon babu wanda jikinsa baya rawa a cikinsu, ga hawaye duk ya cika musu idanu. Auta da yafi kowa shaƙuwa da Sultana a gidan baima san sanda ya fashe da kuka ba tamkar ƙaramin yaro. Kasa jurewa Baba Garko yayi ya miƙe jikinsa na karkarwa. Sai dai dole sukai saurin riƙosa saboda hajijiya dake neman zubar da shi a ƙasa, shima sai kawai ya fashe da kuka. Kukan mahaifin nasu ya sake tayar musu da hankali. Suma duk suka fara sharar hawaye..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣8️⃣ .........Kiran Smart ya saka Lulu tashi ta koma gefe. Kafin ma tace wani abu ya furta, “Akwai matsala fa Baby luv. Dan Kawunki ya baza yaransa sosai nemanki. Fitarki a asibin nan ma inaga sai da jami'an tsaro”.         Murmushi Lulu tai har yana iya jiyo sautinsa. Ta wawwaiga gefenta, tabbatar da babu kowa a kusa da ita cikin sake ƙasa da murya ta ce, “Karka damu zan tafi yanzu. Ka turo min address na wajen kawai kai dai”.     “Kin san mi kike faɗa kuwa. Taya zaki fita a gaɓar da wannan mara imanin ke nemanki ruwa a jallo. Ayanzu haka asibitin yake shirin tahowa dan ya samu tabbacin kina a ciki. Ga Uncle Yousuf nan zuwa shi da Daddy ma”.              “Ka kwantar da hankalinka zamu wuce plan E ne yanzu a kansa”.       “What! Plan E fa?. No no no Mawaddat. Bakya ganin halin da tsohuwar nan take ciki. Mu rushe plan E ma kwata-kwata bashi da amfani”.       “Shiko keda amfani musamman a wannan gaɓar Mr A. Dan babu abinda ya rage mana kuwa sai plan E ɗin. Dada ta riga taga video, shine ma dalilin kasancewar ta a wannan halin. A yanzu haka Grandpa da Uncles suna zaman meeting kuma nasan duk a kansa ne. So kaga abinda ya rage kawai mu ƙarasa sauran aikin. Dan haka yanzu zan saki....”        Da sauri ya ce, “Maw....” kafin ya ma ƙarasa sunan nata ta yanke wayar. Dan zuciyarta gaba ɗaya ta riga da ta gama kaiwa bango. Duk kiran da yake mata bata ɗaga ba. Cikin abinda baifi mintuna biyar ba ta gama sakin videon a ɓoyayyun shafukan data ɗauki tsawon lokaci tana raino da tara followers. Shafi ne da dama yake taka rawar gani akan harkar fyaɗe da shaye-shaye. Ta ginashi tun lokacin da su Dada suka saceta. Zuwa yanzu shafukan nada ɗunbin mabiya saboda abubuwan da ake posting a cikinsu. Sunasa kuma guda ɗaya ne a instegram, twitter, facebook, TikTok, da website. Sunan wanda ta saka, da abinda ta rubuta a saman video ɗin yasa cikin ƙanƙanin lokaci ya samu makallata masu ɗunbin yawa, kafin kace mi an fara shearing ɗinsa.       Yaron Alh. Sulaiman da suka kafa suka tsare a bakin asibiti na jiran fitowar Lulu ne ya fara cin karo da video ɗin, shima wani abokinsa ne ya tura masa yana tambayar ya duba wannan ba ogansa bane. Wani ihun tashin hankali ya fasa batare da ya farga ba. Har takai wanda ke ɗan wuwwucewa ta wajen suna kallonsa. Jiki na rawa ya shige mota. Kira ya dannama Alh. Sulaiman dake tsaka da yin online meeting shima a mota dan yana hanyarsa ta tahowa asibitin ya samu kira da ga Lagos. Sun buƙaci ya ajiye koma mi yake yi zasuyi online meeting na gaggawa. Hakan ya sashi samu waje yay parking hankali a tashe. Suna tsaka da tattaunawar akan batun kayansu ne dai kiran malami ya shigo masa. Bai yi niyar ɗagawa ba sai da yaga kira na biyar na sake shigo masa kuma duk da ga malamin ne. Yasan baya masa irin wannan kiran mafarautan, dan haka zuciyarsa ta bashi lallai akwai matsala. Dole yay excusing kansa ya ɗaga kiran.        “Oga ka duba na tura maka saƙo ta WhatsApp. Wlhy akwai matsala. Babbar matsala ma kuwa”.     Ba ƙaramin faɗuwa gaban Alh. Sulaiman yayi ba. Babu shiri ya shiga WhatsApp ɗinsa. Ai kawai sai ga mutumin waya na neman suɓuce masa. Duk da shi ya ga video ɗin amma tashin hankalinsa anan a ina malami ya samesa shi kuma? Ko amaryarsa da flash ɗin ke'a wajensa ce ta tura masa? Kai ina. Rashin samun gamsashiyar amsa ya sashi kiran malami. Muryarsa har harɗewa take wajen tambayarsa a ina ya samu video ɗin. Malami da gaba ɗaya yake a ruɗe ya ce, “Oga bama ni ba, a kowace waya zaka iya samunsa a yanzu. Dan an sake shi ne a wasu shafukan sada zumunta da ke a manyan apps da mutanenmu suka bama amanna. A yanzu haka wani abokina ne ya tura min wannan bayan na turo maka nima na shiga bincike wlhy tako ina videos ɗin trending sukeyi. Acikin abinda baifi minti arba'in ba miliyoyin mutane sun kalla”.      Karo na farko jikin Alh. Sulaiman ya shiga kakkarwa ta haƙiƙa. Bai gama dai-daita da wannan bala'in ba wani kiran ya shigo masa. Mai kula da ɓoyayyen Companyn sa ne na magunguna. Ruɗanin da yake ciki ya sashi ɗagawa batare da ya farga ba. Bai gama dai-daita wayar a kunnensa ba furucin Babban mai haɗa magunguna ɗin Companyn nasa ya daki kunnensa.            “Mun shiga uku Alhaji jami'an tsaro ne zagaye da dajin nan da Companyn nan. Gasu nan sun gama shiryawa da bindigu suna bamu umarnin mu miƙa kammu ta sauƙi kosu cinnama Company ɗin wuta. Yaya akayi haka Alhaji? Taya suka san da wannan wajen duk taka tsantsan ɗin da mukeyi na tsawon shekaru. Shike nan na mutu Alhaji kofa aure banyi ba balle na bar mai mun addu'a” ya ɓarke da wani irin kuka da ya nema fasa kwanyar Alhaji Sulaiman da gaba ɗaya ya gama jiƙewa da zufa. Ƙitt ya yanke kiran tare da tada mota a haukace. Wani kiran yaga yana shigowa, baida buƙatar duba wanene ma balle ya ɗaga. Kai tsaye gidansa ya nufa cikin wani irin mahaukacin gudu. Kaɗan ya rage ya take maigadinsa da ya gigita da horn. Baiyi parking na kirki ba ya fita cikin gudu-gudu daya firgita ma'aikatan gidan. Dan babu abinda babbar rigarsa keyi sai tashi sama bulummm-blummm-blummm. Yana gab da shiga falonsa ya nema yin wani uban tuntuɓe sai gashi ƙasa wanwar. Fuskarsa ta wani irin dunguruwa da ƙasa. Duk da azabar datake ratsa masa lips da goshe da kan hanci bai damu ba ya miƙe cikin ƙarfin hali. Sai ga jini na ɗiga yararara. Falon ya afka a ɗari uku da sittin, yana ajiye ƙafarsa ciki wayar da abokan huɗɗarsa ne kawai a ciki ta cigaba da ruri. Kamar zai fasa ihu ya ɗaga....        “Alhaji Sulaiman kayi takanka. Aiki ya buɗe wlhy yanzu haka an kame su Olu.....”      Wani irin kuka Alh. Sulaiman ya ɓarke da shi kawai tare da yakice babbar rigarsa da hular ya watsar. Sai kuma ya kwasa a guje zuwa cikin bedroom ɗinsa. (Gaskiya ka zare😂🤣😂🤣😂🤣😂🤣) Passport ɗin sa ya ɗakko, da gudu ya sake fitowa yana kai waya kunnensa. Malami yake kira yana ɗagawa ya ce masa ya siya musu ticket yanzun nan ta online nama kowacce ƙasane. Jirgin da zai tashi yanzu-yanzu dai yake buƙata. Yayi maza kuma su haɗu a airport.           Hankalin ma'aikatan gidan nashi ya tashi ganin gaba ɗaya kamar ya zare. A take sukai kiran Hajiya Turai suka sanar mata gida da babu lafiya. Dan sun gagara gane kan Alhaji gashi nan ya shigo a haukace, ya kuma fito ya shiga mota da alama sake fita zaiyi”. Kafin sukai ƙarshen wayar ma shi ya fice a gidan a haukace......          *_★UK★_*     Tun Smart da ke ganin komai na halin da Alh. Sulaiman ke ciki ta direct camara ɗin su yana dariya har al'amarin ya fara tada masa hankali. Jin da yay Alh. Sulaiman na shirya guduwa ya sashi saurin kiran Uncle Yousuf ya ce suyi report Immigrations office. Dan tabbas suka bari ya tsallake ƙasar yasha kenan. Dan a ƙasashen ƙetare yanada wanda zasu bashi kariya tunda bada kayan aka kamashi a hannu dumu-dumu ba. Cikin sauri Daddy ya aiwatar da hakan kuwa. Lokacin da Alh. Sulaiman da malami ke isowa airport har an fara shelar masu tafiya a jirgin Dubai su shirya. Sunyi farin ciki da samun hakan, dan Malami har ya siya musu ticket ɗin ta hanyar cuwa-cuwa ta hanyar wasu ruɓɓaɓun ma'aikatan da ke da alhakin hakan ta online. Restroom Alh. Sulaiman ya nufa domin canja kaya, yana fitowa har tuntuɓe ya nemayi wajen saurin nufar jirgin da har mutane sun fara shiga. Yana taɓa ƙofar ainahin inda hanyar zuwa wajen jirgin yake aka dakatar da shi duk da ya rufe fuska da facemask da glasses ga p-cap. Cikin masifa yake tambayar ba'asi. Kai tsaye ma'aikacin ya bashi amsa da yanzu-yanzu an tabbatar musu da karɓe lasisin fitarsa wata ƙasa. Sun samu saƙone kuma da ga immigrations office. Jiyay tamkar ya saki zawo a wando. Amma abinka da ɗan cocaine sai ya nema birkice musu har yana ƙoƙarin ture jami'in shi a dole zai wuce. Dai-dai nan aka sauke masa bindiga a saman kai tare da nuna masa handcuffs a kan fuska. A dake aka furta.       “You are under arrest Mr Garko..”    A wani irin hargitse ya juyo kunnensa na bada wani irin sautin tsuuuu!!! Kamar an doka masa guduma a kansa. Ido biyu yay da jami'an tsaro na ƴan sandan farin kaya wato DSS da na ainahin ƴan Sanda, dana immigrations sai na filin jirgin zagaye da shi kusan su hamsin. Kuma kowanne riƙe da bindiga. Gaba ɗaya airport ɗin tayi tsitttt baka ganin komai sai hansken wayoyin mutane dana ƴan jarida. Masu video nayi, masu hoto nayi, masu kallo nayi. Harda masu nunawa live a social media. Sai kawai ya rimtse idanunsa da sukai wani irin mahaukacin kaɗawa jazur, jijiyoyin kansa sun yi bala'in mimmiƙewa ruɗu-ruɗu. Bashi da zaɓin da ya wuce yin surrender kawai. Amma saboda ƙarfin hali da taurin zuciya irin na Tsule sai gashi da fakar ido ya hamɓari na gefensa bindigar hannunsa tai tsalle sama ya tare hannu ya cafe tare da ɗaurata saman kanta. A cikin abinda bai wuce sakan biyu ba hakan ta faru, shi adole sai ya tabbatar musu shi ɗin ƙwararren maharbi ne. Bindigar a saman kansa yana dariyar da tafi kuka ciwo da nunasu da hannu ɗaya ya ce, “Lusarai kawai. Da na miƙa kaina gareku wlhy Gara na kashe kaina. In ce dai shine ƙarshen abinda za'a iya min a duniya ko....”         “Karka aikata haka Mr Garko. Yin hakan kuskure ne ka miƙa kanka ga hukuma salin alin zaifi maka sauƙi”.     Shugaban NDLEA ne dake ƙarasowa yanzu ya faɗa daga inda yake tsaye. Wani banzan kallo Alhaji Sulaiman yay masa. Sai kuma ya kwashe da dariya yana ƙoƙarin ɗan kunamar bindigar. Tauuuuuu!!!! Kakejin sautin ya karaɗe airport ɗin da ya saka mutane fara kwasa a guje cikin ruɗewa da rikicewa.....         _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣9️⃣ .........Tana gama sakin videon da mintuna kaɗan Abdull na isowa asibitin shi da Asma'u. Da gudu tazo ta rungume Lulu cike da farin cikin ganinta. Basu wani ɓata lokaci ba suka shiga motar da Abdull ɗin ya tuƙo. Kai tsaye gidan da su Ammah ke zaune a yanzu kafin a kammala nasu da saura ƙiris suka nufa. Nan ɗin ma gida ne babba wadatacce da suke zaune babu takura. Duk zumuɗin ganin Ammahn da takeyi sai kuma ta ɓige da jin kunyarta. Ammah dake mata dariya ta rungumeta a jikinta tana mai farin cikin ganinta. Harga ALLAH ita tana jin Lulu a cikin ranta tamkar ƴar da ta haifa bawai suruka ba. Bata bari ta zauna ba sai da sukaje ta gaida Abba. Shima yayi farin cikin ganinta yana ta sanya mata albarka da mata ƙorafin rashin zuwa da AA bayan ya tambayeta jikin Dada. Duk da anan ɗin ma dai ya mata ƙorafin rashin faɗa musu da basuyi ba sai jiya suke sani. Haƙuri ta bama Abban da tabbatar masa suma basu sani ba sai da ga baya. Ta ɗan jima a wajen Abba suna hira sama-sama duk da ita duk a kunyace take kafin suka dawo ɗakin Ammah. Mama tayi ƙarfin halin zuwa mata sannu da zuwa kamar yanda taga aunty Amarya tayi. Bata nuna musu komai ba duk da dai taso taga idon Ummah, amma Asma'u ta sanar mata ai tana gidan yayanta ne sai an gama gini zata koma can da zama, sai dai Abba ya mata saki uku ma. Ko a jikin Lulu, sai ma zama data gyara tana shan kunun gyaɗa datace tana so Ammah da kanta ta dama mata. Dan a kallo ɗaya ta fahimci Lulu na ɗauke da ƙaramin ciki. Murnar kasancewa da su Ammah dan Maryam ma babu jimawa ta dawo daga makaranta ya mantar da ita wani batun Alh. Sulaiman. Sai dai tayi kiran Aunty Naja'atu ta tambayi ko Dada ta farka. Ta sanar mata bata farka ba ance sai bayan la'asar. Dan haka ta sake miƙe ƙafa har sai bayan la'asar ɗinne suka fito harda su Ammah da zasu je duba Dada. Sai a lokacin sukaji halin da garin Kanon ke a ciki. Abdull da Mubarak dake bibiyar komai suka shiga basu labari. Kwaɓarsu Ammah ta shiga ƙoƙarin fara yi wai saboda Lulu, amma sai sukaji lulun na ƴar dariya da faɗin, “Ammah barsu su bamu musha. Indai wannan ne baida maraba da wanda ban haɗa komai da shi ba a duniyar nan, dan inda akwai wanda ya tsanesa to nice farko kuwa.”     Shiru kowa ya kasa cewa komai a motar har suka iso asibitin dan furucin Lulun ya girgiza zukatansu.....       _________★         Ba jama'ar gari ba, hatta jami'an tsaron duk sun ɗauka Alh. Sulaiman ya kashe kansa ne. Hatta Smart da ke kallon komai ta can wani irin rumtse idanu yay da dunƙule hannaye ya kaima iska naushi da faɗin, “Ohhhh Shiittttt!!!!”.       Wahalalliyar ƙarar da Alh. Sulaiman ya sakice ta saka kowa ɗagowa da sauri. Dai-dai Alhaji Sulaiman na kaiwa ƙasa durƙushe akan gwiyawunsa bindigar hannunsa na faɗuwa ƙasa itama ya dafe hannun damarsa dana haggu dai-dai inda ƙwararrren maharbin jami'in ya sakar masa bullet. Kowa kallonsa ya maida akan jami'in, shiko ko'a jikinsa sai ma hura bakin bindigarsa da yay da baki ya turata cikin aljihun wandonsa yana ƙarasowa gaban Tsule. Wani irin fisgar hannuwan nasa duk biyu yay zuwa baya batare daya damu da jinin dake ɓulala a hannun Alh. Sulaiman ɗin da bullet ya ratsa ba balle jin tausayin maɗoɗowar azabar da yake yi ya saka masa handcuffs. Sai a lokacin mutane suka farga da ashe bai kashe kan nasa ba jam'in yay nasarar harbinsa a hannun bindigar ta faɗi.      Cikin ƙanƙanin lokaci zufa ta gama jiƙe Alh. Sulaiman. A haka aka taso ƙeyarsa zuwa wajen airport ɗin yayi wujiga-wujiga. Da ƴan uwansa ya fara tozali tsaye reras su huɗu mahaifinsu a tsakkiya cikon na biyar. Kallo ɗaya dayay musu bai sake marmarin ƙarawa ba saboda irin wutar bala'in da ya hanga a fuskokin nasu musamman ma autansu na maza dake wani irin huci kamar kumurcin maciji Uncle Taheer. A karo na farko yaji wasu irin hawaye sun sakko masa masu zafi da ɗaci. Babu zato babu tsammani yaji saukar wani irin gigitaccen mari maisa a gano ƙyallin kabari har saida ya durƙushe ƙasa. Bai gama dawowa a hayyacinsa ba aka sake sauke masa wani. Ba kowa bane da wannan aikin face auta da Uncle Amin. Har sai da sauran ƴan uwansa Uncle Muneer da Uncle Khamil suka rirriƙesu. A hankali Baba Garko ya ƙaraso gabansa hannunsa riƙe da ƙyaƙyƙyawar sandarsa ya zuba masa idanu na wasu sakkani. Sai kuma cikin ƙarfin hali ya saki murmushi mai ciwo. Cike da dattakon nan nasa yasa sandarsa ya ɗago haɓar Alh. Sulaiman da bai gama dawowa daga gigitar marin da yasha hannun ƙannesa na uku dana huɗu ba. Muryarsa da ɗaci sosai yace, “Sulaiman bazan maka baki ba. Sai dai ina baƙin ciki da takaicin saka maka suna mai daraja da kima irin wannan. Sannan ina jin raɗaɗin kasancewar ka jinina. Sai dai bazanma UBANGIJI butulci ba, domin ya bani huɗu gasu nan duk na ƙwarai, tare da biyu mata da basa raye duk da kaine kai sanadin mutuwar Sultana. Sulaiman kai ba mutum bane shaiɗani ne, dabbane tunda har zaka iya haikema ƙanwarka ƴar shekara tara kacal da lafiya bata isa ba. Kaiconka Sulaiman ka tabbatar asararre a wannan duniyar wlhy. Gashi nan kazo a banza zaka koma a wofi dan bana maka fatan shiriya harka koma ga ALLAH. Yau ina kuɗin daka tara ta hanyar haramun ɗin? Ina damar da kake ganin kanada ita ta lafiya da rayuwa da dukiya? Ka lalata dubban al'umma ta hanyar miyagun kwayoyi, kasa iyaye da yawa kuka! Kasa mataye da yawa kuka! Kasa mazaje da yawa kuka! Ina zaka da hakkin waɗan nan bayin ALLAH koda basu furta maka ALLAH ya isa ba. Kaiconka Sulaiman, wlhy bana fatan wani ya yafe maka akan wannan al'amarin koda mutum ɗaya ne. Kaje in dai duniya ce gaka nan a cikin tarkonta, ka gama wahala a cikinta kaje ka fiskanci hukuncin UBANGIJI kuma. Da ga yanzu na haramta maka sake amfani da sunana kona zuri'ata har bada”. Daga haka ya juya yana sharar hawaye. Yaransa dake bin Sulaiman da mummunan kallo suka take masa baya.      Wani irin durƙushewa Alh. Sulaiman yayi a wajen ya ɓarke da kuka. Dan kalaman makaifin nasu sunyi masifar shigarsa shiga mai tsanani da ƙarfi a cikin jini da ɓarko ta yanda baiyi zato ko tsammani ba. Da ƙyar jami'an tsaron suka iya ɗagashi aka jefa a cikin mota....       *_3 DAYS LATER_*                 A yanzu kam babu wani latest topic dake yawo a media da gari sama dana Alh. Sulaiman. Hatta maganganun da Baba Garko ya faɗa masa da marin da ƙannensa sukai masa sai yawo suke a social media. Hakama ɓoyayyen Companyn sa na magunguna sai da aka gayyaci ƴan jaridu sannan akai masa filla-filla. Baba Garko da ƴan uwansa sunje har Companyn suma. Sosai hankalinsu ya sake tashi saboda ganin ɗunbin aika-aikar da jinin nasu ya jima yanayi batare da sun farga ba. Harda jarirai a wajen da ake gwada magani a jikinsu kafin a fitar, wasu sukan mutu wasu su kamu da ciwuka al'amarin zattashin hankali dai. Ƴaƴansa kam kuka har suna rasa hawaye. Dan biyu da ga ciki harda saki mazajensu sukai musu.       Duk yanda Baba Garko ke ƙoƙarin danne komai ya cigaba da zama ba komai ba hakan ya gagara. Dan kuwa dai sai da takaisa kwanciya a gadon asibiti. Yayinda aka samu ita kuma Dada ta maro. Sai dai bata iya dogon magana sai kuka da jama Sulaiman kalaman ALLAH ya isa da faɗin, “Nayi dana sani ni Hajarah, dama Mawaddat tasha faɗa min Sulaiman na lalata yaran masu aiki kuma nima na sani amma son zuciya da son ƴaƴa ya hanani ɗaukar makaki sai da akaima Sultana fyaɗe. Ashe na rigada na makara tun a wancan lokacin, ashe shine ya wulakanta min mutuncin yarinya ya halaka min ita. Yarinyar da ko cikakkiyar lafiya bata da shi. Kaicona ni Hajara kaicona da irin son zuciyata. Gashi nan takaini ta baroni a gaɓar da bazan iya komai ba na dawo da baya balle na gyara. Wane irin abin kunya ne wannan da tozarci. ALLAH ya tsine maka Sulaiman. ALLAH ya ƙuntata rayuwarka tun daga nan duniya. Wlhy bazan yafe maka ba. Inama ɓarin cikinka nayi ko mutuwa naima gaba ɗaya a lokacin haihuwarka. Dama kin cemin zanyi nadama mara amfani idan ban gyara ba, kin faɗamin banji ba Mawaddat,, ban saurareki ba, da ace na saurareki da banga wannan mummunar ranar ba a rayuwata. Inama na mutu kafin zuwan wannan ranar. ALLAH ya isa Sulaiman.....” ta sake fashewa da kuka. Lallashinta aketayi akan ta daina tsine masa da muguwar addu'ar nan. Amma ina Dada idonta a rufe yake. Babu abinda take hangowa sai Sultana kwance cikin jini, yarinyar da har aka kaita makwancinta jini bai daina fita a jikinta ba. Haka aka sakata a kabarinta likafaninta duk jini.          Lokacin da Lulu dake kwana a wajen Ammah yanzu ta shigo Dada ta riƙota jikinta tana kuka. Itama sai Lulun ta kama kuka. Da ƙyar Uncle Khamil ya janye Lulu da ga jikin Dada saboda aman jinin data fara. Dama Doctor ya sanar musu zuciyarta ta taɓu sosai sai abinda ALLAH yayi kawai. Hankalin kowa ya sake tashi, dan Baba Garko ma hanawa akai a faɗa masa..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣0️⃣ ........Sai da suka tabbatar ya gama jigata da bullet ɗin da ke jikinsa sannan suka cire masa. Washe gari suka bisa da duka na hauka wanda ya kaisa harda karaya a ƙafa, suma kam yayita babu adadi suna farfaɗo da shi. Duk wanda yaga yanda ake wajiga rayuwar Sulaiman zai tabbatar da al'amarin da biyu ne. Inda ma aka ɓoyesa kawai tashin hankali ne. Dan da ƙyar Daddy da Lulu ta matsawa da son ganin Alh. Sulaiman ɗin sukaje aka barsu suka ganshi, ya samu wannan alfarmar ne kawai saboda taimakon da ya bama jami'an tsaro wajen cafke su Alh. Sulaiman ɗin. Daƙyar Alh. Sulaiman ya iya ɗaga ido ya kalla Daddy da Lulu data juye masa tamkar mahaifiyarta, saboda duka ya taɓa masa ido ɗaya. “Miya kawoka wajena?!”.       Ya faɗa da ƙyar muryarsa na karkarwa. Iska Daddy ya firzar yana mai ƙoƙarin maida hawayen da suka cika masa ido. Dan ganin yanda akaima Sulaiman ɗin raga-raga a kwana biyu kacal ya ɗaga masa hankali. Da ƙyar ya iya danne rawar lips ɗinsa ya furta, “Nazo ne na tabbatar maka wasan ya ƙare Sulaiman. Dama irin wannan ranar nake guje maka a baya amma ka kasa raurarena da fahimtata sam. Ka ɗauki tsawon shekaru kana tsula tsiyarka amma ka duba cikin abinda bai wuce awanni arba'in da shida ba ka koma tamkar bakai ba. Wannan fa kamun mutane ƴan uwanka kenan. Inaga kamun UBANGIJI kuma Sulaiman. Duk wahalar da kasha rani da damuna da sanyi, wahalar yawon ƙasashe domin tara dukiya kawai kallo a inda ka kasance yanzu. Talakan da bai taɓa riƙe dubu hamsin ba ya fika. Babu abinda yafi neman halak komai ƙanƙantarta sauƙi a wannan rayuwar. Koba komai zaka rayu cikin kwanciyar hankali ka kuma mutu cikin mutuntawar UBANGIJI. Mutane su ɗauki gawarka da girmamawa, a taya iyalinka kuka da jajantawa a tausaya musu. Amma ta irin hanyar da kuke bi fa? Zaka kasance cikin ALLAH wadai wa zuri'ar ka da al'ummar gari, kabar iyalinka da hantara wanda ma bai kai ya takasu ba ya taka su. Maimakon addu'a ga mutane sai ALLAH wadarai ke fita a bakunansu. Duk inda mutum ya buɗe a yanar gizo ciki da wajen Nigeria zancenku ne. Miye amfanin ɗaukakar ALLAH ya tsine irin wannan. Kasaka iyayenka a wani hali da iyalanka. Iyayenka mutanen kirki ne Sulaiman musamman mahaifinka, mutumne mai daraja da kima a wajen mutane, a duk inda ka zagaya alkairinsa ke fita daga bakunan mutane. Amma yau gashi kasa al'umma na ambatar sunanka a matsayin jininsa. Albasa batai halin ruwa ba Sulaiman......”       Kuka ya sarƙe Daddy mai cin zuciya. A mamakinsu sai ga Sulaiman na hawaye shima. “Maganganunka dukansu gaskiya ne Isma'il. Tabbas mun kasance masu son zuciya a rayuwarmu. Burin tara dukiya duk da wasunmu mun tashi a gidan dukiyar. Burin zama wasu abu a duniya batare da muna tuna muna mutuwa ba. Da'ace na saurareka tun a wancan lokacin Isma'il da ba'a kai wannan gaɓar ba. Yau gani a matsayin wanda ya rasa komai. Babu iyayen da suka sha wahalar haihuwata da bani tarbiyya da ilimi. Babu matan dana ɓata lokaci wajen neman dukiyar dan na birge su, babu ƴaƴan da nake zumuɗin tarawa domin a kirasu ƴaƴan wane. Babu ƙarfin da nake kai duk wanda ya bijiremin ƙasa. Babu ƙarfin da nake tunanin wataran zan iya sarrafa ƙasar dama wasu ƙasashe a hannuna. Komai ya ƙare Isma'il, komai ya kufce a gaɓar da nake gab da cimma nasara mara amfani. Komai ya tafi kamar bai taɓa zuwa ba.....” kuka ya sarƙe sa.       “Dan ma bakaji irin tsinuwar da uwarka ke maka bane ba! Da nadamar haihuwarka”. Lulu ta faɗa kanta tsaye babu alamar tausayinsa ko ɗigo a ranta. Dan itafa in dai ka kasance kayi fyaɗe to babu abinda zaisa taji tausayinka dan ta ganka a wani hali. Cikin tashin hankali Alh. Sulaiman ya ɗago yana kallonta. Ta wani ƙyaɓe baki da cigaba da faɗin, “Ai yanzu bakaga komai ba ma. Dan an gama wasanne saura yaƙin. Shi kuma yaƙin yanzunne aka fara shaiɗani. Wai kaine kake kuka nadama a cikin kwana biyu kacal. Ƙaryane ma na yarda da hakan makiri. Idan ma tunaninka Daddy na zai taimakeka ka fito ne ka cire hakan a ranka dan ka shiga kenan, kabarinka ma anan zasu gina maka shi su bizneka babu wanka babu sallar gawa. Wannan da kake gani yafi ƙarfinka kamar yanda ya faɗa maka tun farko, bama shi ba, mu dake ƙasa da shi munfi ƙarfinka dan gashi a ƙanƙanin lokaci mun sabauta rayuwarka tamkar ma ba'a taɓa yinka ba balle iyawarka. Nasan dai bazaka manta da wannan fuskarba ai”. Ta faɗa tana juya masa wayarta. Smart ne ya bayyana AA zaune a saman cinyarsa. Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗaga ma Alh. Sulaiman hannu da faɗin, “Hy ƙwaro”. Sai kuma ya saki ƴar dariya yana ɗage gira sama ganin yanda Alh. Sulaiman ɗin ya saki baki da hanci yana kallonsa. Nunasa ya shigayi wasu irin zafafan hawaye na rige-rigen sakko masa. Lips ɗinsa na rawa sai dai ya gagara cewa komai.         “Kwantar da hankalinka ai basai kace komai ba zan ƙarasa maka. *_Aliyu Mika'il Idris Mawashi_* ne dai naka. Yaron nan daka tura aiki jiƙamshi family. Idan baka manta ba na faɗa maka kada ka ƙulla wasa dani zan iya kaika ƙasa. Amma sai ka gagara ganewa saboda kana kallona yaro ƙarami ɗan talakawa da zaka iya hurewa tamkar silin gashin kanka a lokacin da kaso. Kayi kuskure Sulaiman dan ba'a raina maƙiyi koda na jinjirin sauro ne. Kamar yanda na faɗa maka ni kurari baya razanani hakanne, sai ma ƙaimi da yake ƙaramin. Da'ace baka kalleni a ba komai ba maybe da kaci nasarar tsallakewa da ga tarkona. Sai dai kash girman kanka da ɗaukar kanka sama da kowa yasa kai sake ɗan zaki ya girma yay gawurtar da ya wuce da saninka. Ka sani ni bani da wata matsala da kai dan babu abinda ya taɓa haɗamu kafin saninka. Kawai na ƙarasa aikin family na na biyu ne. Wato aikin surukina da surukata da kuma matata, dan duk wanda ya taɓasu kowaye shi bazan taɓa ƙyalesa ba saboda sunansu AHALINA suma a yanzu. Ni kuma ba'a taɓamin AHALI a zauna lafiya, sai nayi kaca-kaca da rayuwar mutum ta inda bai zata ko tsammani ba. Kamar dai yanda a yanzu muka shafe tarihinka da babinka. Ka sanar musu su cire maka camara ɗin dake gefen kunnenka dan aikina ya ƙare, bana buƙatar cigaba da ganin yanda kake cin ubanka a hannunsu bye bye Solomon”.         Dariya Solomon daya kirashi ya bama Lulu. Ta shiga ƙyalƙyalawa kuwa. Dai-dai nan jami'in ya shigo yake sanar musu lokaci ya cika. Ko'a jikin Lulu ta miƙe tana ɗagama Sulaiman yatsu biyu. Sai kawai ya bita da kallo wasu irin hawaye masu zafi na silalo masa. Dan babu abinda yake gani a tattare da ita sai mahaifiyarta. Gaba ɗaya ta juye ta koma masa Mawaddat ƙanwarsa. Duk da dama tana kama da ita mai tsananin gaske. Jiki a saɓule shima Daddy ya tashi ya fito.       Koda suka tafi a mota kasa cema Lulu komai yay sai da sukaje gida yace ta biyosa falonsa...... Wannan zuwa na Daddy ya tsayama Sulaiman a rai matuƙa. Zuciyarsa bata nema bugawa ba sai da aka cire camara ɗin da Smart yace a gefen kunnensa. Wani irin raɗaɗi yake ji a ransa da mamakin ta ya akai camara a jikinsa bai sani ba, har tsawon wane lokaci yaran nan suka ɗauka suna wasa da hankalinsa batare da ya taɓa farga ba. Sai yanzu ya gane Smart ne *_AMM_* da ya dinga turo masa saƙwanni. Tabbas yaron yayi gaskiya, ya ɗaukesa a bakomai ba, amma gashi ya zame masa komai. Ya kaisa ƙasa a lokacin da bai zato ko tsammani ba, ashe abinda suke zargin wani babban mai faɗa aji ke musu shine ke aikata musu shi. Yaron da basu taɓa kawowa a hasashen su ba. Shi baima taɓa kallonsa a jerin maƙiyan da zasu iya juya rayuwarsa haka ba. Ranar yaci kuka mai suna kuka da har sai da ya rasa hawaye. A rana ta uku aka ɗaukesa da ga Kano gaba ɗaya zuwa Lagos. A rayuwarsa bai taɓa sanin akwai azabar rayuwa irin wannan ba a duniya. Duk da yasan shi mugune, sun kuma kashe mutane da dama a dalilin harkar ƙwayar da sukeyi idan suka bijire musu. Amma wannan ɗin na musamman ne. Duk taurin zuciya da taurin kai irin na Alh. Sulaiman a wannan gaɓar sai gashi yana hawaye, shi kansa yasan anzo dai-dai wajen kuma. A randa aka isa da shi Lagos wahalar da yaci bai ma san ya fara kiran sunan Dada da Baba Garko ba akan suzo su taimakesa ya tuba, har Hajiya Turai da Tajuddeen da sauran ƴaƴansu sai da suka sha kira. Wannan itace nadama mara amfani, domin kuwa bakin uwa shine ke tasiri akansa tare da haƙƙokin mutane dana ƴaƴansu da suka zama sanadin lalatama rayuwa ta hanyoyi da yawa, gashi nan a kwanaki uku kacal rayuwarsa ta sauya a yanda ko maƙiyinsa ya gansa dolene ya tausaya masa, dan a yau ma sai da suka sake masa karaya biyu a hannu ɗaya. Bai san sanda azaba ta sakashi fara lissafo abokan huɗɗarsa ba. Wanda dama tunda aka kamashi hankulansu a tashe suke matuƙa suma, sau faman kai gwauro da mari sukeyi akan al'amarin shiyyasa ma aka ɓoye Alh. Sulaiman ɗin ashe..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣1️⃣ ......An cigaba da kame-kame a ƙasar mai ban tashin hankali. Inda harda sunan wani tsohon shugaban ƙasa, da wasu manyan ƴan siyasa a gwamnoni da ƴan majalisu ma dake ci a yanzu ya fito, sunayen manya-manyan ƴan kasuwar da ba'a taɓa zato da tsammani ba. Tare da manyan ma'aikatan gwamnati da tsabar yanda ake kallonsu iyayen ƙasa ake kiransu. Al'amari yakai intahar da mai gyarashi sai dai UBANGIJI. A cikin abinda baifi awanni a shirin da huɗu ba na cikar kwanakin Sulaiman a hannun hukuma sojoji suka sauke shugaban ƙasa tare da wasu gwamnoni. Hankalin mutane ya tashi matuƙa da tunanin ko juyin mulki ne, sai gashi bayan cikar wata a wa ashirin da huɗun an maye gurbin shuwagabannin da mataimakansu amma an maida shugaban ƙasar shima....        _____★   An wuce da Dada da Baba Garko zuwa ƙetare domin duba lafiyarsu. Hakan yasa Lulu shiryawa itama ta koma wajen mijinta bisa umarnin su Daddy. Taso ganin Ummah itama amma hakan bai faru ba saboda kai-kawon da tayi duk bata jin daɗin jikinta. Smart da kansa yaje tarbarta airport shi da ɗansa. Ta rungumesu su duka cikin ƙarfin hali da jin kewarsu duk da dudu kwananta tara ne kacal. Suna isa gida ta zube kwance a falo, hakan yasa kowa ya fahimci bata jin daɗin jikinta. Kiran Ammah da ya shigoma Smart da ke kallonta ne ya hanashi magana. Sai da ta katse ya kirata dan haka yake musu duk wanda ya kirashi koda a yaran gidansu ne. Bayan ya gaisheta da girmamawa take tambayar ƴan tafiya sun iso lafiya. Cikin ɗan damuwa yace, “Gata nan duk a galabaice muna shigowa ta zube a falo.”         “Ya salam, ai kuma dai kunyi ganganci ne. Dan ma ALLAH ya bata ƙarfin hali ne kawai. Amma a halin da take ciki ai ba kowa zai iya ɗaukar wannan kai-kawon ba da hayaniyar da aka sha. Sai kuyi ƙoƙari ku tafi asibiti dan a tabbatar da lafiyar abinda ke jikin nata da ita kanta”.      Cike da mamaki Smart da ke kallon Lulu ya ce, “Ammah abinda ke cikinta kuma? Wani abu tace miki yana damunta?”.          Cikin murmushi mai sauti Ammah ta ce, “Aiba saita faɗamin ba Babana. Duk wanda ya kalli Mawaddat ai yasan akwai ciki a jikinta”.        “Ciki fa Ammah?”.     “A'a kaini tsaya, wai ku baku san da cikin ba ne ko mi?”.   “Wlhy Ammah ni ban san tana da ciki ba. Itama kuma na tabbata bata san da shi ɗin ba”.         “Kai nikam yau naga sakarkarun yara. Yanzu ita Bilkisun dake tare da ku ga wannan tsohuwar ace suma duk basu lura ba. Aiko wannan cikin in bai kai wata huɗu ba ma to gab yake da kaiwa. Dan da alama ma babu jimawa da zuwanta nan ALLAH ya bada shi. Sai kuyi ƙoƙari dai kuje asibiti to”.       A sanyaye yace, “To Ammah insha ALLAHU”.     Yana yanke wayar Lulu ta miƙe cikin ƙarfin hali zuwa bedroom. Dan wanka kawai take sonyi. Da kallo suka bita su duka. Iya Tabawa ce ta katsesu da ƴar dariyar ta. A tare duk suka juyo suna kallonta. Tace, “Ai tun watan daya gabata na fahimci uwar ɗakina nada shigar ciki. Nayi shiru ne dai kawai saboda dambarwar da naji anayi”.        Dariya aunty Bilkisu tayi sosai tana kallon Smart daya rasa abin cewa. “Ka gani kunata faman fitina ashe ma ALLAH ya bada abinda ake ma rigimar. Nima sai gab da zata tafin nan na fahimta sai dai zuciyata bata tabbatar ba shiyyasa bance komai ba. Ashe Iya Tabawa ta mana na manya ne ma ita. ALLAH ya raba lafiya, ya bata lafiya ita kuma”.       A hankali ya amsa da Amin yana sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya miƙe yabi bayanta zuwa bedroom ɗin. Ya samu tana wanka, dan haka ya zauna a bakin gado yana zaman jiran fitowarta. Babu jimawa ko sai gata ta fito tana faman dafe kai. Miƙewa yay ya riƙota ganin kamar tana tangaɗi. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Miya faru kuma?”.     “Ina ganin jiri” ta bashi amsa a hankali. Kwantar da ita yay a saman gado ya rungumeta a jikinsa yana mai sauke tagwayen ajiyar zuciya. Idanunsa a lumshe yana shafa mata kai ya ce, “Dama kin san kina da ciki amma kika kasa sanar min?”.          Kanta ta girgiza masa a hankali da faɗin, “Wlhy ban sani ba. Duk da ina jin canji a jikina ba a yanda na saba ba na ɗauka kawai yanayi ne dan lokacin cikin AA ma sai da ya kai wata kusan huɗun na sani bayan ma anyi yunƙurin zubar da shi”.       Sake ƙanƙameta yay a jikinsa yana mai jin wani irin farin ciki mara misalin kwatance. Sosai yake son ƴaƴa a rayuwarsa. Kodan ta tashi cikin yawa ne a gidansu shiyyasa oho. A hankali ya shiga bata sumba yana mai sanya mata albarka. Ita dai riƙe kukanta kawai takeyi amma ita tasan mi take ji. Bawai bata farin ciki bane ba. Tana jin tsorone kawai dan ita kaɗai tasan irin wahalar da tasha a lokacin haihuwar AA da sanda cikinta ya tsufa. Sai dai a yanzu tana tsoron nunawa kuma ta takaloma kanta bala'insa. Haka ta cigaba da shanyewa da barma ranta kawai tunda dai mai afkuwa ta afku, sai dai tana mamakin ciki a jikin mace nayan tayi planing, gaskiya mutumin nan maye ne, itakam taga takanta kenan. Shi da kansa ya shiryata yana ta dai ƙoƙarin danne dariyarsa, dan daya tuna abinda tayi kuma ga cikin da take gudu sai yaji dariya na taso masa, haka dai ya daure ya kimtsata sannan ya fita ya kawo mata kunun gyaɗar da tace tana so yanata fan murmushi sai dai baice komai ba duk da bakinsa fal yake da zance. Kaɗan ta sha tace ta ƙoshi, daya matsa ma sai ta fara yunƙurin amai. Dole ya ƙyaleta suka wuce asibiti. An dubata tare da tabbatar musu baby na cikin ƙoshin lafiya. Gajiya ne kawai yay mata yawa, dan haka sukace taje ta samu hutu sosai a gida dan tana buƙatar bedrest. Sai magunguna da suka bata na ƙarin kuzari da ranakun da zata dinga zuwa ana duba lafiyarta suka kuma cire mata abinda ta sakama jikinta kamar yanda ta buƙata, dan bataga amfaninsa ba kuma. A haka suka kwaso suka dawo gida Smart na kwasar dariya dan a wannan gaɓar dai ya gagara daurewa. Itako sai kawai ta sakar masa kuka dan ta gane abinda yakema dariyar. (Mugu ɗan masa kenan😂😂)       A ranar dai duk ƙwaɗayinsa dole ya haɗiyesa saboda kwana tai babu lafiya, sai amai da take faman yi ko ruwa ta sha. Washe gari dole suka sake komawa asibitin. Kwantar da su sukayi suma dole. Gashi washe gari yana da wasa mai zafin gaske dan gab suke da kaiwa ƙarshen primier link. Alhmdllh Dan yana taka rawar gani sosai ga kuma team ɗinsu na gaba da kaiwa zagayen ƙarshe. Babu yanda zai yi dole ya shirya ya koma ya barta da su aunty Bilkisu....       ★Satin Lulu uku da dawowa aunty Bilkisu ta fara shirin komawa Nigeria. Alhmdllh taji sauƙi sosai sai fatan lafiya mai ɗorewa. Shatara ta arziƙi Lulu da Smart suka shirya mata. Haka ta wuce suna jin kewarta tana jin nasu dan Lulu harda hawayenta. Sai da Smart ya dinga lallashinta akan ta kwantar da hankalinta ba sun kusa tafiya bikin Maryam ba. Idan zasu dawo da Ammah zasu dawo in sha ALLAH. Hakan ya sakata jin farin ciki sosai.        Lulu ta cigaba da rainon cikin ta cike da kulawar mijinta da Iya Tabawa da ta zame mata tamkar uwa. A haka su Aunty Saliha sukazo hutu UK, kuma anan London sukai masauki kamar yanda Lulu taita naci. Sosai ta kasance cikin farin ciki mara misali. Balle ga ɗan lelenta Deen kuma da ya ƙara girma. Cikin jikinta daya fito sosai bai hanata yin hidima da su ba, dan kusan a gidan suke yini ma. Sai dare su koma masaukinsu. Wani lokacin kuma ita taje can.          Su Smart sun kai zagayen ƙarshe tare da ɗaukar kofi. Yayinda Smart ya taka rawar gani da sunansa keta sake zama abin ambato a zuciyar masoyansa. Ga ƴammata tako ina sun sakkoshi gaba. Sai dai shi ko kallo basu ishesa ba, dan yace ya rufe da ga Final Choice babu wata kuma. Kammala wasansu ya sashi fara musu shirin tafiya Nigeria dan ya samu hutu mai ɗan yawa. Ga kuma bikin Maryam da aketa shirye-shirye dan dama saboda shi aka ɗan ɗaga ƙafa....          *_NIGERIA_*    A Najeriyar ma abubuwa da yawa ne suka faffaru. Su Ammah sun koma gidansu da Smart ya gyara. An canja masa tsari mai birgewa da ɗaukar hankali. Yayinda Abba yace Ummah bazata dawo masa gida ba tunda ya saketa. Sai da aka taru a kansa anata bashi haƙuri akan tazo tai zaman ƴaƴanta. Cikin ƴan roƙo harda Smart. Da ga ƙarshe dai da ƙyar ya amince. Kasancewar itama da nata sashen ta dawo. Sai dai lokacin da zasu shigo gidan bata ma san ta ɓarke da wani irin kuka mai cin zuciya ba. Yanzu nan Aliyu ne ya gina musu wannan gidan. Duk faɗi tashinta dai ya tashi a banza a wofi an kai inda dai bata son kenan. Ranar kwana tayi tana kuka ita kaɗai a ɗaki. Wani tashin hankali kuma washe gari suka tashi da gobara a shagunan Salim. Komai ya ƙone ko tsinke ba'a fita da shi ba. Ana cikin wannan tashin hankalin ƴarta Hannatu ta dawo gida wai mijinta ya saketa. Gaba ɗaya Umma ta sake hargitsewa jiki ya koma ɗanye sharaf. Sai da aka kira Smart ana faɗa masa ne ya saka aka kaita asibiti. Satin ta ɗaya aka sallamonta. Gaba ɗaya Salim ya koma kamar zararre. Sai kuka yake yana jama Umma ALLAH ya isa akan itace ta ja masa. Ai dama nakan tudu ya faɗa duk bala'in data ƙulla akan Smart sai ya dawo kansu. Gashi nan kuwa. Ta cucesu ta zalunce su bazasu yafe ba. Ranar da matar Salim ta gudu da ƴaƴansa bayan ta saida gidan da shi ya kaɗai ya rage masa ai kaɗan ya rage a ɗaureshi a turu saboda tsabar zaucewa. Umma ta dinga kuka dan dama dai Salim ɗin ne abin tinƙahonta...........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣2️⃣ .......A ɓangaren Garko family ma dai ALLAH ya bama Dada da Baba Garko lafiya har sun dawo gida Nigeria. Sai dai Dada ƙarfin hali kawai take. Gaba ɗaya ta zama wata shiru-shiru. Sai da kaga ta tasa hoton Maman Mawaddat da na Sultana gaba tana kuka. A yanzu Baba Garko kan zauna ya lallasheta da mata nasiha. Hakama amaryarta takan ƙyautata mata duk dan dai ta kwantar da hankalinta, haka ma ƴaƴanta basa gajiyawa wajen tattalinta saboda an tabbatar musu zuciyarta idan har ta buga shike nan kuma. Dan haka kowa baya wasa da al'amarinta. Lulu kanta ba'a barta a baya ba wajen lallashin Dadan. Dan tana kallonta tamkar Mawaddat ɗin ta ne data rasa. Akoda yaushe cikin yin video call suke da ita....        __________★    Shirye-shiryen bikin Maryam ya kankama sosai, dan takowane ɓangare shiri kawai akeyi. Ana saura sati guda ɗaurin aure Smart da iyalinsa suka iso gida Nigeria. Ƙasar da yay kewa. Tarba ya samu maiban mamaki da ga al'ummar ƙasar tasa da ƴan uwa da abokan arziƙi. Dan da ƙyar suka iya baro airport sai da taimakon jami'an tsaro. Yayinda ya samu rakkiyar masoya har gida. Anan ma ya samu yaran anguwa da iyaye suna jiransa. Sai ga Smart na hawaye dan farin ciki. Ya tabbatar da mutane rahama ne. Duk wanda yace maka yana sonka da ƙaunarka ya gama maka komai a rayuwa. (Ya ALLAH ka barmu da masoyanmu. Duk wanda ya somu dominka ya rabbi shima ka soshi shi da zuri'arsa baki ɗaya. ❤️❤️❤️😘 wannan nakune masoyan alkairi 🙏).      Anan ɗin ma dai da ƙyar ya samu suka shiga gida saboda yanayin Lulu. Dan cikinta yayi girma sosai wannan karon fiye dana AA. Ga kuma kullum cikin laulayi take dan tunda ya fara tsufa bata da wani ishashen lafiya. Duk da dama dai haka taketa fama tun da cikin ya shiga watanni biyar. Babu kunya yau kam Smart ya rungume Ammah da Abbah a gaban jama'ar gidansu. Ya kuma rungume ƙannensa su Mubarak da yasan suna matuƙar kaunarsa. Kannensa mata nata kawo masa gaisuwar girmamawa harma da wanda suka girmesa kamar wani sarki. Tunda Ummah ta leƙo sau ɗaya ta gansa bata sake maimaitawa ba, ɗaki ta shige tana sakin wani irin kuka mai ƙona zuciya. Smart ya koma kamar wani baƙin bature. Ko makaho ya laluba yasan kuɗi da jin daɗin rayuwa da ɗaukaka sun zauna sai dai fatan gamawa da rayuwa lafiya.     Shiko sanin bata da isashiyar lafiya har ɗaki yaje ya gaisheta tare da duk sauran matan Abba har aunty Amarya. Ita kanta Mama a ruɗe take, kawai dai tana ƙoƙarin dannewa ne kar ai mata irin kallon da akema Umma. Dan ƙamshin Smart kawai rikita zuciya yake. Saboda kowa ya gama sanin hankalin Ummah fa a tashe yake. Wasu a cikin yaranta har abun nata na basu kunya.        Bayan yaci ya sha daga girkin mahaifiyarsa data musu girki da kanta dan Lulu bata iya cin komai sai kunun gyaɗa. Shi kaɗai taima sha na hauka dan motsi kaɗan taji yunwa yanzu. AA na hannun iyayensa wannan ya ɗauka ya ba wancan haka aketayi. Yaron birgesu yake gashi fes kamar ka lashe, komai na ubansa bai bari ba. Zuwa yanzu ya ɗan fara magana sai dai ba gane abinda yake nufi akeyiba ma sosai. Kwanciya Lulu tayi danta hutama ranta. Yayinda su Ammah da Smart suka buɗe shafin hira dan Gwaggo Sa'adah na gidan da su aunty Bilkisu da Hawwah. Daga baya sai ga Abba shima ya shigo duk da su Smart ɗin sun je sun gaishesa...      Washe gari aka kawo lefen Maryam daga gidan su Ahamd. Lefe ne na nunama tsara dan an nuna dukiya kam babu ƙarya. Ƙwaƙwalwar Umman neman zautuwa takeyi. Dan kasa jurewa tai yau ma sai kulle kanta tai a ɗaki. Ga dangin Ammah dana Abba nata zuba mata habaici batare da sun duba cewa ƴar uwarsu bace ba. Anyi komai cike da girmama juna da mutuntawa dan suma sun bada tukuyci mai tsoka. Bayan wucewar ƴan kawo lefe Smart ya ɗauki Lulu da AA da Asma'u suka nufi gidan su Lulun. Daddy da su Amrah sunyi farin cikin ganinta, duk da kuwa jiya harda su a ƴan tarbarsu. Basu koma gida ba sai dare. Mommy ma taji daɗin ganinsu. Tana ta tsokanar AA. Hira sosai Smart suka sha da Daddy, dan anan suka yini sai bayan sallar azhar suka nufi gidan Uncle Yousuf. Anan ɗin ma dai hirar aka sha, samun su twins da sukai can yasa Smart da Lulu fahimtar akwai wani abu tsakanin Hussain da Asma'u. Hakan yama Lulu daɗi sosai ita da Smart. Basu bar nan ba sai bayan la'asar. Sun nufi gidan Baba garko inda suka ƙarasa yinin. Itama dai Dada harda kukanta dan ta fahimci dai waɗan nan ma'aurata kainuwa ne dashen ALLAH. Sannan FURAR DANƘO ne damasu ace za'asha farau-farau abune mai wahalar gaske. Jiki luɓus suka koma gida dan Lulu tayi laushi. Ammah taita ma Smart faɗan miyasa bai barta acan ba yaketa yawo da ita haka. Shi dai murmushi kawai yayi yana kallon Lulu dake masa gwalo ƙasa-ƙasa. Washe gari yana tare da Ahmad da Coach, acan ya yini sukasha hirarsu da ubangidansa. Bai dawo gidan ba sai dare dan har Malam na Yakasai yaje ya gaidar bai manta alkairi ba nan ma....        Al'amarin biki ya kankama sosai, Smart ya haɗama amarya gidan mijinta da kaya na kece raini da nunawa tsara. Yayinda aka fara events da aka shirya wanda ya kafa ya tsare ya hana Lulu zuwa ko ɗaya saboda yanayinta. Daga ƙarshe ma da yaga hayaniyar gidan na mata yawa sai ya dinga janyeta zuwa masaukinsa. Acan suke kwana sai da safe ya dawo da ita nan ta yini cikin danginsa. Lulu ta amsa suna matar babban Yaya. Dan komi aka buƙata bata jin ko ɗar zata fidda a jakarta ta bada batare da tabi takan mijinta ba. Sai wasu a ƴan uwa suka fara tsogumin ai ta kankane komai sai abinda taso take badawa. Tun anayin ƙus-ƙus har zancen ya fito fili yakai kunnen su Ammah. A take Ammah ta nuna ɓacin ranta akan hakan, yayinda Smart da shima ransa ya ɓaci ya basu amsa da ai kai da kaya duk mallakar wuyane. Shi kansa a ƙarƙashin say ɗin Lulun yake bama dukiyarsa ba. Ballema ko sisi bai bata ba duk abinda suka nema ta basun kuɗinta ne. Wannan zantukan nasa yasa jikunansu yin sanyi, dama dai cikin dangin Abba ne da ƴaƴan Mama da wasu ana Ummah masu gulmar. Sai aka koma ƴar sinne kawunan jin kunya.     Ana gobe ɗaurin aure akai dinner. Ita kaɗai Smart ya bari Lulu ta halarta. Shima kuma yaje. Dan tare sukaje tana gefensa riƙe da hannunta AA daya maƙale masa da ga hannun su Abdull ɗauke a kafaɗarsa. Sun isa a lokacin da kusan kowa ya gama zuwa. Dan har biki ya fara. Dan haka gaba ɗaya attention na mutane ya dawo kansu musamman yanda mc ke kwarzanta wanene Smart ɗin da matsayinsa a wajen ango Ahmad da ma Amarya Maryam. Nan fa dangin Ahmad ɗin masu ɗan jijji da kai irin na dangin miji suka shiga hankalinsu. Dan sun fahimci abinda sukeji basu yarda ba ashe gaskiya ne. Dan kamanin Smart da Maryam a bayyane suke. Nan fa ƴammata suka ruɗe da ganin matashin ɗan ƙwallon da duniya ke yayi mai ji da kuɗi. Sai dai Lulu dake fama da cikinta tana nane da abunta. Duk yarinyar data kama tana kallar mata miji kuwa zatasha harara. Shiko Smart nata ƙunshe dariya dan yana sane da matar tasa. Amarya da ango sunsha ƙyau har sun gaji, yayinda bakin Ahmad yaƙi rufuwa. Liƙi sosai daya ruɗa hall ɗin Lulu da Smart suka dinga zuba musu harda AA da Ahmad ya ɗaga sama yana sumbatarsa da faɗama mc cewar a sanar kowa ya sani wannan surukinsa ne. In sha ALLAH yanda suka taru anan bikin aurensu haka wataran zasu taru bikin auren AA da matar da zasu haifa masa. Wannan zance na Ahmad yasa kowa dariya a wajen tare da addu'ar ALLAH ya tabbatar da hakan. Ba'a tashi ba Smart ya ɗauki matarsa suka gudu dan taje ta huta saboda bata jimirin hayaniya yanzu.... Washe gari aka ɗaura auren Ahmad Rabi'u Ƙoƙi, da amaryarsa Maryam Mika'il Mawashi akan sadaki naira dubu ɗari biyat bayan sakkowa da ga massalacin juma'a. Ɗauri aure ne daya samu halartar manyan mutane a dalilin gidajen biyu. Tare da ɗunbin masoyan Smart da ga jihohi daban-daban. Anyi walima da yamma. Zuwa bayan isha'i aka shirya kai amarya ɗakinta. Yayinda kaf yayunta harda su Sadiq ƙanana suka taru a falon Abba domin mata nasiha. Tasha kuka sosai har muryarta na dishewa. Dan yayun nata sun mata nasiha mai ratsa zuciya. Bayan an kammala Smart da Salim da Zubair da Kamal suka sakata a danƙarereiyar motar da Smart ya siya mata suka kaita gidan mijinta da rakkiyar mata iyaye guda biyar kawai. Da zasu taho ne ta rungume Smart tana kuka da jera masa godiya. Murmushi yayi a hankali yana mai lumshe idanunsa kafin ya ɗagota a jikinsa. Fuskarta ya riƙe cikin hannayesa yana girgiza mata kai alamar tayi shiru. Daga haka ya shiga gaya mata daɗaɗan kalaman da saida ta saki murmushi. Sannan ya kamo hannun Ahmad ya saka masa nata a ciki ya ɗan bubbuga kafaɗarsa ya fice yana maida hawayen da suka cika masa ido shima. Smart na matuƙar so da ƙaunar ƴan uwansa matuƙa a rayuwa. Akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu duk da bawani sakewa yake da su ba. Dama sauran duk sun fita harma sun shiga mota. Yana zuwa shima ya shiga kawai suka wuce........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣3️⃣ .......Washe garin da aka miƙa Maryam gidan miji Mawashi family suka tashi da tashin hankali biyu. Na farko shine gano Huwaila ɗauke da cikin shege na watanni biyar. Tashin hankalin bayyanar wannan ciki kuma yasa Ummah yanke jiki ta faɗi. Inda faɗuwar tata ta zama sanadin samun paralysis. Smart na masaukinsa yana barcin gajiya Lulu a jikinsa ya samu kira da ga Salim. Dole ya shirya ya nufo gidan da Lulu data dage bazai barta ita kaɗai ba. Sun sami gida a rikice. Ko Ummah ba'a ɗauka ba zuwa asibiti sai da yazo ya fara faɗa. Bayan ankai Ummah asibiti suka samu tabbacin ta samu shanyewar ɓarin jiki gida suka dawo da ita bisa shawarar doctor bayan anyi treatment ɗinta yanda ya kamata. Ummah dai an tafi, dan babu abinda ke motsi a ɓarinta na dama sai ido da kai. Amma daga wuyanta zuwa yatsanta ma ƙafa komai cak. Sai ɗayan ɓarin haggun kawai. Babu abinda take sai hawaye. Dan bakin ma idan tayi magana ba'aji sosai sai yawu ke fita babu ko ƙyawun gani.        Smart da Salim suka tsare Huwaila. Zata musu wani kwana-kwana tasha maruka a hannun Smart. Salim ya rufeta da duka da ƙyar aka tsaida shi saboda lalurar dake a jikinta. Wahalar da tasha yasata faɗin gaskiyar cewar saurayinta ne ya mata lokacin suna tare da Umma a gidan Kawu Jibirin, idan tace ta tafi makarantar islamiyya sai ya ɗauketa a hanya su tafi hotol ko ɗakin abokansa. Ran kowa ya ɓaci Abba harda hawaye yana jama Umma ALLAH ya isa da jin nadama bisa nadama akan aurenta. Dan bai tsira da komai ba sai baƙin ciki da tashin hankali tun daga ƙuruciya har zuwa yau. Garama yanzu da Smart ke ƙoƙarin dawo da su Salim a hayyacinsu. Dan a yanzu haka jira yake a kammala bikin nan ya gyarama Salim shagunansa da suka ƙone. Smart yasa an nemo wanda yayma Huwaila ciki tare da iyayensa. Da farko ya musa harda cewa shi baima taɓa ganin Huwaila ba, sai da Smart yay masa jan ido harda maruka biyu a gaban iyayensa babu ko kunyar idonsu sannan ya faɗi gaskiya, amma yace ai bashi kaɗai bane tana kaima wasu. Huwaila ta sanya kuka da rantsuwa da shi kaɗai take tarayya, hasalima shine ya fara saninta ɗiya mace, tana ma da shedar hakan. Ansha rikici sosai har sai da Huwaila ta kawo recording na wayar da suka dingayi da ta dinga ajiyewa sannan fa shegen yay laushi. Inda aka tsaida magana da zaran ta haihuwa za'a ɗaura musu aure. Sauran ƴamatan gidan kuma ya basu tabbacin nan da wata uku kowacce ta kawo mijin aure in ba hakaba shi zai zaɓo musu. Hakan ya saka iyayen jin kwanciyar hankali. Dan sai ga Mama sarkin ruɗiya yau na sakama Smart albarka. Saboda ba ƙaramin tayar mata da hankali batun cikin nan na Huwaila yay ba, dan itama tana da ɗaya a ɗakinta mai rawar kan tsiyar da giggiwa. Haka ta tasa ƴaƴanta gaba wanda basuyi aure ba tana roƙonsu ALLAH Annabi su taimaka mata su rike mutuncin kansu karsu kasheta tun lokacinta baiyi ba kamar yanda Huwaila ta zama sanadin Ummanta. Sun daiga yanda tarbiyyar ƴaƴan Ammah a gidan ta jawo musu alkairi.....      Samun lafawar ƙurar biki ta bama Smart nutsuwar fuskantar ƴan uwansa. Yayinda ya nutsu wajen nemawa ƴan uwansa maza da matan ma abinyi. Tare da zagaye dangin mahaifiyarsa dana mahaifinsa kaf yay musu alkairai masu tsoka da yaketa samun albarka shida zuri'arsa. Shine har dangin Mama dana Aunty Amarya, dan ita Umma danginta sune dangin Abba sai dai na ɓangaren mahaifiyarta. Gefe ɗaya kuma ya samu damar gina wasu manya-manyan mall guda biyu da kafa business daban-daban. Tare da yin amfani da ƙungiyar Lulu ya tallafama yara da ɗan yawa akan karatu. Masu shaye-shaye a ciki ya kaisu rihab. Dan Nadiya dake ta lallaɓa rayuwarta a yanzu tare da Ummita tsaye suke akan ƙungiyar. A cikin wannan halin bikin Ummita da Usman ya tashi suma. Haka Lulu taita ƙoƙari nan ma akayi komai da ita. Ta kuma bama Nadiya shawara akan ya kamata itama ta samu miji mai irin ciwonta suyi aure tunda yaron data haifa ya rasu. Ranar Nadiya tayi kuka sosai, tare jerama Lulu da Smart har ma da su Uncle Yousuf addu'oi. Dan yanzu ta koma gidansu a dalilin sanya baki da baba Garko yayi a zancen, babu kuma wanda take ganin mutunci da kima yanzu a duniya sama da Lulu da Smart. Amaryar Baba Garko ma ta shigo cikin tawagar masu kula da ƙungiya. Hakama Tajuddeen da a yanzu ya sakama kansa haƙuri game da al'amarin Lulu yana bada gudunmawa. Shima dai an saka bikinsa da ƙanwar amaryar mahaifinsa. Tunda ya lura yarinyar na masifar sonshi mahaifiyarsa da su Baba Garko suka bashi shawarar ya aureta kawai ya rufama kansa asiri, dan yanzu ba gida duka bane zai nema aure a bashi saboda tabon da mahaifinsu ya bar musu a cikin al'umma. Kowa ya zata Dada zataƙi. Sai gashi babu ko ja'in ja ta amince harda bada gudunmawar ta...        _______★ Hutun Smart ya ƙare zasu koma England sai dai Ammah tace bada Lulu ba. Dan a gida zata haihu wannan karon itama taga gatan da kowace ɗiya ke samu. Ba haka yaso ba dan haka ya dinga fushi. Ammah ko ta tattarashi ta watsar da faɗin yama fashe mana. Mawaddat ce dai babu inda zataje sai ta haihu tunda watan gobe ne haihuwar. Har kawo zancen AA zai shiga makaranta yayi amma Ammah tayi mirsisi da shi. Sai ma tace masa ya tafi da AA ɗin su zauna Lulu ce dai babu inda zataje. Babu yanda ya iya haka ya tattara rai a jagule ya tafi Lulu na faman masa dariya da gwalo. Dan ita farin ciki take da barinta a wajen Ammahn ta. Tana so da ƙaunar baiwar ALLAHr nan a rayuwar. Itama kuma Ammahn na nuna mata ƙauna mai tsayawa a rai. Idan ka gansu tamkar ba surukai ba. Wannan soyayyar tasu daga ALLAH ce kawai za'ace..      Bayan wucewar Smart babu jimawa aka ƙarasa masa ginin katafaren gidansa da mutane keta magana akansa duk da basu san kona wanene ba. Dan hatta Lulu bata sani ba. Ammah da Abbah da Ahmad da Coach sai Uncle Yousuf ne kawai suka san gidan na Smart ne. Kamar abinda Lulu ke jira kenan ta fara naƙuda. Hankalin su Ammah ya tashi dan cikin dare al'amarin ya tasar mata. Gashi Ammah ta fahimci Lulu nada masifar tsoro ga kuma ta da Naƙuda mai wahala. Dole suka wuce asibiti a daren nan bakunansu da addu'a. A wannan karon ma dai cs aka shirya yima Lulu. Tunda Asma'u ta kira Smart ta sanar masa hankalinsa ke'a tashe. Tun a daren nan ya fara neman mafita dan ya tabbatar bazai taɓa iya haƙuri ba sai yazo Nigeria. Da ƙyar ya samu aka masa alfarmar kwana goma. Aiko babu ɓata lokaci ya shiga shiri...       Alhamdullah an samu nasarar cirema Lulu yara biyu mata masu kama da mahaifinsu tamkar AA. Zokaga farin ciki da murna a wajen familyn nan guda biyu da suka zama tsintsiya maɗauri ɗaya a yanzu. Sai dai murnar tasu ta taƙaita ne kasancewar Lulu na cikin wani yanayi mai ban tashin hankali. Dan har Smart ya iso bata dawo hayyacinta ba. Hakan ya tada hankalin kowa da bada mamakin kasancewar a yanzu ansan cs ana yinsa ne ma idon mutum biyu. Koda Smart ya iso shi bata yaran yake ba, ta matarsa yake yi. Dan baiji nauyin kowa ba ya durƙushe a gaban gadon da take kwance samɓal kamar wadda ta mutu ya saki wani irin kuka mai ban tausayi. Yanda ya kife fuskarsa akan tafin hannunta yana kuka hawayensa suka jiƙe mata hannu. Haƙuri likitocin keta bashi dace masa addu'a take buƙata. In sha ALLAH kuma zata iya farkawa a kowanne lokaci numfashinta ne kawai yay nisa. Ba Smart kawai ba hatta Daddy hankalinsa a tashe yake. Dan yana tuna a dalilin haihuwarta ya rasa mahaifiyarta itama. Baba Garko da Abba ne suketa lallashinsu da basu baki. Har dare babu wani bayani akan Lulu. Ga Smart ya kafa ya tsare ko nan da can baya gusawa, salla kawai ke tada shi a ɗakin. Cikin amincin ALLAH gabannin asubahi Lulu ta farfaɗo. Rikicewa Smart yayi dan farin ciki. Ya rungumeta jikinsa na rawa ga hawaye..        Cikin ɗaga idanunta da kyar da shafo fuskarsa murya ƙasa-ƙasa ta furta. “Mr A!”.    Rikicewa yay da farin ciki yana tattaɓata da rungume hannunta a ƙirjinsa hawaye fal idanunsa ya amsa da “Na'am Mawaddatan'warahmah!”. Wani irin murmushi mai tsayawa a rai ta sakar masa tare da maida idanunta a hankali ta sake lumshewa, hannunta ya saki a hankali. Wani irin ƙara Smart ya saki yana mai girgizata da sambatun faɗin, “Dan ALLAH kar kimin haka Mawaddat, karki tafi ki barni, kece rayuwar Aliyu kece farin cikinsa. Ni nake fata na rigaki mutuwa bake ki rigani ba. Ki tashi dan ALLAH na roƙeki”.      Kukansa da sambatunsa yay matuƙar tada hankalin kowa a wajen. Dan Daddy ma luuu ya tafi zai faɗi sai da aka taroshi. Da ƙyar aka fiddo Smart a ɗakin likitoci suka rufu akan Lulu........✍️ 🙉🙉🙉Munga Boni _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣4️⃣ *SCHOLARSHIP, 3 DAYS CLASS* Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rarar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rarar kudinne sakamakon rashin neman scholarship da bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka canza kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni Class ze fara ranar jumaa insha Allah WhatsApp group 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/E8Lzqogsm1nAFy1feTwbmA WhatsApp 08144147273 👉 Masu bukatar tafiya da kudinsu ba scholarship ba, Muna yin study & work ko working visa, a takaitaccen lokaci, working visa Qatar munayi a sati daya, Canada study & working visa a 4 to 5 months, Oman working visa a 7 days insha Allah, Mexico Tour visa 1 month, Slovakia Job seeker visa ____________ .........Awannin da suka gabata sun tafine da sautin bugawar zukatan waɗan nan ahali. Kafin kowa ya samu nutsuwa a dalilin farfaɗowar Lulu. Ba'a bari an shiga inda take ba sai Smart kawai. Dan shikam a ranar ma tare suka kwana. Ko yaya ta motsa ya dinga tambayarta minene damuwarta kenan har saita sakar masa murmushi. Sai washe gari ƴan uwa da abokan arziki suka samu ganinta. Daddy ji yake kamar ya haɗiyeta dan farin ciki. Duk wani masoyinsu da uban gayyar sai yau suka samu nutsuwar kallon baby's. Yayinda aka koma kuma taya juna murnar samun ƙaruwa.     Salim shi Smart yasa yayma yara huɗuba a kasancewarsa babba. Itama Lulu sai a ranar ta samu ganin abinda ta haifa. Cikin ƙarfin hali da magana ƙasa-ƙasa take faɗin, “Mr A wannan karon ma kamin wayo, su duka kai suka biyo”.           Murmushi ya sakar mata yana wani ɗage gira sama da amsa mata da cewar, “Hakan na nufin na fiki jarumta a filin yaƙin ƙasa da ƙasa kenan. Next time ma ƴan uku zakiyi in sha ALLAH”.      Da sauri ta kauda kanta gefe tana faɗin, “Ai kai dama ba'a hirar arziƙi da kai. Mutum ko gama dawowa hayyacinsa baiyi ba kake wani kira masa haihuwar ƴan uku”.        Dariya ya sanya mata Nadiya na tayashi. Dan duk tana ɗakin suke wannan taɓarar... Dada da ciwo ya sake fidda tsufarta ta taƙarƙara da ƙyar tazo asibitin da duba Lulu. Lokacin da taga ƴan tagwayen nan sai da hawaye suka cika mata ido. Dole abubuwa su rincaɓe musu dan rabon yaran nan kaɗai ya isa ya zama sanadin kaudasu a duniya. Gashi nan cikin shekara biyu da rabi a auren nasu Lulu nada yara uku...        Alhmdllh Lulu ta samu kanta sosai kasancewar jikinta mai ƙyau ne baya riƙe ciwo. Kwananta shida aka sallamesu suka koma gida. Dan ta matsa akan ita a sallameta ta gaji da zaman asibitin nan bata son warin. Haka aka sallamota suka nufi gida. Sai dai maimakon gidan Abba sai taga an wuce da ita katafaren gidan da mijinta ya gina batare data sani ba. Duk da sun taɓa wucewa ta gaban gidan kasancewar a anguwarsu ta hotoro GRA ne har taita santinsa. Ashe wai nasu ne. Koda ta jiyo tana kallon Smart sai ya kama kunnesa yana wani ɓata fuska kamar AA na fushi. Murmushi kawai tayi tana mai sinne kanta dan suna a tsakkiyar mutane ne.       Gida bai sake rikita kowa ba sai da suka shiga cikinsa. Abun ba'a cewa komai kawai. Lulu na son keɓewa da mijinta sai dai babu dama. Dan gidan cike yake kasancewar su Ammah sunce fa sai anyi taron suna. Washe gari aka raɗama ƴan biyu suna. Inda sukaci sunan *_Ayshatul-humairah da Hafsatul-Ikram_*. Ƴan biyu Aysha da Hafsat sunyi goshi matuƙa. Dan kwai da kwarkwata na dangin Lulu da Smart musamman ƴan FURAR DANƘO C-BOX. AREWABOOKS, ZAFAFA FANS dama ƴan bayan katanga masu karatun bati sun zo a gayyar SOƊI🤣🥱 (A daure azo a biya 400 ne, duk 1k babu yawa bama son halin dangin Sulaiman Tsule ƴan bati. Dan nidai babu ruwana biyana za'ai🤪😜).  An raƙashe an ƙwalle a wannan taron suna yayinda amaryar jego da jariranta sukasha ƙyau har suka gaji. Shi kansa angon jegon badaga baya ba kam. Munci hinkafa iya hinkafa. Munha zoɓorodo harda kajin gidan gona masu tsokar gaske. Ga halawa da biskin duk an bimu da su a ledoji. Kai al'amarin dai ba'a cewa komai dan an nuna halin girma. Sai muce ALLAH ya raya Ayshatu da Hafsatuwa....          Har washe gari gidan nan cike yake da mutane. To su Xoxo anga hinkafar banza anƙi tafiya🥱. Huguma da Rano da Mamu kam harda rantsuwar su sai Lulu tai arba'in zasu wuce, yo anga gida ginin gilashi🤣. Nace kunji abin kunya Zafafa dai sai an nuna hali a ko'ina😏🚶, alhalin hinkafar nan fa dai kowa nada a gidansa, gilashi kuwa kowa akwai a windown gidansa. Amma dai bari mu bincika o'e da o'e kodai-kodai 🥱. (I love you Zafafa's😘😘😘❤️💞🙏).          Shatara ta arziƙi kam dai Lulu ta sameshi a wannan haihuwar. Dan Nadiya da Ummita da amaryar Baba Garko da Maryam amarya sune tsaye akan duk wani gift data samu. Tun a wajen hotuna bata sake saka mijinta a ido ba sai a daren na washe gari ya fidda kunya dai ya shigo har ɗakinta. Su Ummita dake baje suna buɗe gifts suka suka fara rige-rigen fita. Idanu Lulu dake da ga kwance AA na gefenta zaune yana fitinar a bashi Baby ta ɗago a hankali ta sauke a kansa. Shima ita yake kallo da yaransa guda uku dake gabanta reras. Lallausan murmushi ya sakar mata yana mai lumshe ƙyawawan idanun nan nasa da take kira na maciji tare da ɗaga kafafunsa a sannu-sannu ya cigaba da nufota cikin takun ƙasaita da kasala tamkar mai irga steps ɗin nashi. Dai-dai yana isowa ta yunƙura zata tashi zaune ya girgiza mata kansa yana mai kaiwa zaune a bakin gadon da kama kafaɗunta ya maidata ya kwantar yana kaɗa mata kansa. Bata da zaɓin daya wuce komawar ta kwanta. Baice da ita komai ba sai hankalinsa da ya maida kan AA. Cike da kulawa ya ce, “Waya saka Baban Ammah kuka ne?”.       Cikin shagwaɓa AA ya nuna Lulu, dan har yanzu shi maganar tasa sai a hankali ce. Dan ma ɗan zamansu a Nigeria ɗin nan ya fara samun bakinsa kasancewar gidan Abba gidan yarane. Balle shi da ko yaushe yana hannun yaran gidan kowa ji yake da shi saboda ƙyautatawar iyayensa. Kaɗan Smart ya ɗan waro idanu waje da faɗin, “Kai-kai Maah-maah ce”. Kai AA ya ɗaga masa yana wani sake ƙwaɓe fuska.. “Ayya Kakan Papa yi shirunka ƙyale Maah-maah kaji ko. Bazamu saya mata kayan daɗinmu ba ai ko?”. Nan ma AA ya ɗaga kansa dan yana jin magana sarai abinsa. Gyara masa zama Smart yayi tare da ɗaukar Hafsat dake a kusa da shi ya ɗauramasa a saman cinya, sai dai bai sakar masa ba tana a hamnunsa. A take yaron ya hau dariya yana nuna Aysha wai itama a ɗaura masa. Haka Smart ya biye masa itama ya ɗaura masan. Ita dai Lulu na kallonsu kawai, dan a yanzu tana sake fahimtar irin so da ƙaunar da mijin nata kema yara ta dabance. Sai da yaran suka ɗan jima a cinyar yaron sannan ya saukesu ya kwantar da su yace ya kwanta kusa da su ya musu wasa.        “Ni dai kada ya tsokale min idanun yara gaskiya. Har yanzu ban gama dawowa a hayyacina ba fa”. Lulu ta faɗa cikin shagwaɓa harda wani ɗan tura baki. Dariya ta bashi ma shi, dan haka ya juyo yana kallonta gira a ɗage ya ce, “Oh really?!”.     “Kai ne shaida ai, tunda kai kafi kowa shan kuka”.   Kansa ya kauda gefe yana murmushi da faɗin, “Oh ni Aliyu. Na shiga tara kuma da gorin yarinyar nan. Ke da baƙya raye a lokacin ya akai kika san haka?”.         Murmushi ta saki mai bayyana haƙwara. Ta ce, “Likimo nayi fa duk ina jinka. Dan na sake tabbatar da wanene mijina. Ashe ragone shi a kan lamurana”.    Yanzu kam dole dariyarsa ta fita da sauti. Ya zuba mata mayun idanun nan nasa yana sakar mata wani murmushi mai sanyi da fasa zuciya. A can ƙasan maƙoshi yana mai dimtse hannunta cikin nashi da ƙyau ya ce, “Kin san kuwa matsayin da Mawaddat Jiƙamshi ke da a zuciyar Aliyu! Wannan sirrin ALLAH ne kawai yasanshi Baby luv. Kin fa gama mamaye ko'ina da ina baki ragema wata koda ƙanƙanin fili ba. Har tsoro nake ji kada wataran ƙaunarki ta fasa zuciyar ɗan bawan ALLAHn nan ma”.      Tuni ƙwalla sun cika mata idanu, zaune ta tashi tana mai juya kwanciyarta zuwa jikinsa. A tare suka saki ajiyar zuciya da lumshe idanunsu suka buɗe duk a lokaci ɗaya. Akan yaranta ta fara sauke nata kafin ta juyo gareshi hawayen da suka taru mata na sakkowa a hankali bisa ƙyaƙyƙyawar fuskar ta. Da sauri ya wara idanunsa zaiyi magana sai ta sakar masa murmushi da girgiza masa kan alamar kada yace komai.         “Aliyu!”.     “Uhyim Mawaddatan'warahmah!”. “Kai ɗan aljanna ne da izinin ALLAH”. “Tare ai zamu shige in sha ALLAHU”.       “Da'ace wani ɗan adam nada damar buɗema ɗan uwansa nan dana buɗe tawa ka ga matsayin ka a ciki” tai maganar tana ɗaura hannunsa a saitin zuciyarta. Idanunsa da sukai rauni sosai ya lumshe da sake buɗewa a kanta. “Kin mallaki Aliyu Hydar da komansa Mawaddatan'warahmah. Na jima da sanin kema kin mallaka masa zuciyarki. Sai dai ban san miyyasa kika zaɓi ɓoyewa ba baby luv. Salonki na azabtar dani matuƙa”. Dariya ta ƙyalƙyale masa da ita tana ƙoƙarin tashi ya hanata. Sai ma sake matseta da yay cikin jikin nasa har sai da tai ƴar ƙara da faɗin, “Wash ciwona”. Da sauri ya saketa a rikice, ta ko kwashe masa da dariya tana masa gwalo. Sai ya ƙwaɓe fuska cike da shagwaɓa ya ce “Zan rama ne ai”.      “Sai dai wani karon wannan kam nayi winning”.    “Ba komai, ai da kai da kaya duk mallakar wiyane.” yay maganar yana mai lakace mata hanci. Ita kuma taja kumatunsa da faɗin, “Yaushe Aliyu ya fara ɓoyewa Mawaddat sirrikansa?” ta ƙare faɗa tana kallon ɗakin. Ya fahimci mi take nufi. Dan haka ya saki ɗan murmushi da kallon ɗakin shima. “Aliyu bai taɓa ɓoyema Mawaddat sirrinsa ba. Ya mata hakanne kawai domin supricing ɗinta, kuma Alhmdllh burinsa ya cika, wannan shine gidan Mawaddatan'warahmah da Aliyu da zuri'ar da zasu tara in sha ALLAH.”           Hawayene masu ɗumi suka gangaro a idanun Lulu dake kallonsa ko ƙyafta idanu batayi. Kallonta yay da sauri. Zai yi magana ta ɗaura yatsarta akan lips ɗinsa ta ce, “Shiii!!. Lokacin Mawaddat ne”. Yanda tai maganar cikin raɗa sosai ya sashi sakin murmushi.....✍️ 😁😁😁😁To nima bari na ɗan murmusa _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣5️⃣ ________ *_INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRAJI'UN 😭😭😭_* _ALLAH yayima *MARUBUCIYA FAREEDA ADO GACHI* rasuwa. Ya rabbi ka gafarta mata ka yafe mata kura-kuranta. Ayyukanta na alkairi su zama fansata domin rahamarka ya *UBANGIJI. MARUBUCIYA* ce data taka rawar gani a harkar rubutu da alƙalami da duniyar rubutu bazasu manta da ita ba. Tana cikin tawagar manyan marubutan nan na *MACE MUTU* a littafinsu mai suna *HANNU DA YAWA.....* da wasu ire-iren su. Ta rubuta littatafai ita kaɗai kamar haka._ *MEKE NAN?* *RAYUWAR MATA* *ƳAN UBA* *NI KO SHI* *RA'AYINA NE* *TUBALIN TOKA* *_ALLAH kai mata RAHMA damu baki ɗaya. 🙏🙏_* *_MADUBINA A HARKAR RUBUTU TA TAFI 😭😭😭🙏_* _____________ .......A bazata ya ji saukar lips ɗinta akan nasa. Daburcewa ya nema yi kasancewar anfa jima ba'a haɗu ba. Dama ɗan Ammah a wuya yake. Sai da ta gama rikita masa lissafi da salon da bai taɓa sanin ta iya ba sannan ta nema janye jikinta. Shi kuma a sannan yace bai san zancen ba. Dan ta riga ta ɓallo MAZAN FAMA. Murya a sarƙe yana ruƙota ya furta “Please Mawaddatan'warahmah”.       Murmushin mugunta ta sakin masa tana kai bakinta a saitin kunnesa ta furta, “Jego muke fa”.      “Bayan kin gama jigata ni”.   “Yada karaya haka MAZAN FAMA”. “Ki ɗauka kawai na zama rago ko MATAN FAMA”. Dariya Lulu ta kwashe da shi. Kamar zai saki kuka ya ce, “Ki kasheni ki huta kawai”.       “Idan na kashe Aliyu dawa za'a ganni a filin yaƙin ƙasa da ƙasar kuma ni Mawaddat”.     Harara ya ɗan sakar mata yana kaiwa kwance dan gaba ɗaya jikinsa babu wani ƙarfi. Yaransa ya zubama ido kawai dan AA ma yayi barci a kusa da twins.. Mintsini ta kai masa, yay shiru, ta sake ya sake mata shiru, ta sake kai hannu a karo na uku ya damƙe hannun tare da birkiceta. Rikitata ya shiga yi tare birkita mata lissafi da zazzafan salonsa. Sai ga Lulu na roƙonsa harda kukanta akan ya rufa mata asiri yau fa kwananta tara da haihuwa. toshe kunnuwansa yay kamar baya jinta, sai da ya tabbatar ta tsorata matuƙa sannan ya harareta yana komawa gefe. Sai kuma ya koma yimata dariya ganin yanda ta gama fita a hayyacinta da tsoro. ƙaramar ƙwafa yay da faɗin “Gobe ma ki sake takalata zaki sha mamaki dan sai kinga ƙarshen tsokala.” Baki ta tura masa tana harararsa, da sauri ya kai mata cafka, ta dire da gudu daga gadon. Dariya ya kwashe da ita harda hawaye itako tana harararsa baki a sama.....       Duk shagalin da aka sha sai da aka kaima Umma labari, hawaye kawai take zirararwa. Ga shi dai Aliyu yakai inda ta jima tana yaƙin, yayinda ita take kwance sai an kwantar an tayar. Miji ya saketa ƴaƴan nata ma sai wanda ya ga ALLAH yake tausaya mata. Gashi su dukansu sun koma ƙarƙashin alfarmar maƙiyin nata. Kallon Ammah kawai na ɗaga mata hankali. Dan daka ganta kasan Alhmdllh komai ya zauna dole a kirata uwar sarkin gida. Suna da matsayin data jima farautar samu. Huwaila harda nuna mata video ɗin gidan Smart. Nan ma saita ɓarke da kuka. Babu kunya Huwaila ta sanya dariya tana faɗin, “Su Umma dai ana kwancen ma baza'ai dana baƙin ciki da cigaban wasu ba”. Tana gama faɗa ta miƙe da cikinta tirƙai-tirƙai da ke saka jinin Umma sake hawa a duk sanda ta kalli Huwailar tayi wucewarta yayarta na mata faɗa bata ko saurareta ba.....     ★★★ Duk yanda Smart yake kwaɗayin zama kusa da iyalinsa dole ya shirya ya koma saboda cikar kwanakin da aka bashi. Ya tafi ya barsu da kewa kamar yanda shima ya tafi da kewarsu. Haka Iya Tabawa ta cigaba da kula da Lulu. Yayinda Asma'u ta dawo nan dan gidan yay masu girma duk da an zuba ma'aikata kamar su maigadi mai gyaran filawoyi mai wanki harma da driver da mai share-share da sauransu. Sannan Huwaila ma kusan tana anan ne ita da Nadiya. Hakan ya ɗan ragema Lulu raɗaɗin rashin mijinta a kusa da ita. Sai dai akoda yaushe suna maƙale a waya ana video call. Ammah na leƙosu akai-akai, hakama aunty Saliha. A haka sukai arba'in zuwa lokacin ta gama gyagijewa. Ga gyaran Iya Tabawa tana samu mai lafiya dan ita kanta tana jinta on top. Ta zagaye dangi itace har Abuja, kafin ta fara shirin komawa dan Smart ya ishi kowa da damuwarsa. Ammah dai data gaji da yawan ƙorafinsa ta ce ta shirya ta tafi wajen mijinta kozai barsu su huta. Kunya abin ya bama Lulu ma ita. Shiko ta fahimci ko'a ƙwallar rigarsa. Tare da Asma'u suka wuce da Iya Tabawa. Mai gayya da aiki ne da kansa yaje tarbarsu airport, da mamaki yake kallon Asma'u dan bai san da ita za'azo ba. Lulu bata taɓa sanar masa ba har taima Asma'u komai-da-komai na tafiyar. Bai iya cewa komai ba ya kwashesu suka wuce yana ɗauke da yaran duka, sai da Asma'u ta amsar masa AA dan taga sun masa yawa. Tsaff suka samu gidan nasu harda abinci ya tanadar musu. Dan haka babu ɓata lokaci sukayi wanka suka baje. Asma'u ce ma dai keta faman ƙauyanci da santin gidan suko suna mata dariya. Shi dai Smart na manne da yaransa kamar wani yace zai ƙwace masa su, dan gaba ɗaya hankalinsa na kansu ne.. Sai narkakken kallon da yake bin matarsa da shi lokaci-lokaci a kaikaice wanda ita kaɗai ta fahimci abinta. Dan haka taɗan shiga tsoro dan tasan yau kam saita ALLAH wai biri a hannun bamaguje. Gashi tasha gyara kala da iri da ita kanta tasan sai tayi bayani da yaran Jiƙamshi yau kam.       Kamar yanda tai hasashen kam ta ɗanɗana kuɗarta, yayinda Smarty ya rikice mata tare da sanya mata albarka babu adadi. Tattali kam ta shashi a wannan yinin, gashi dama babu inda ya fita dan haka suka yini a ɗaki da ƙyar yake barinta ta leƙa su Iya Tabawa kodan Asma'u dake fama da baƙunta. Yayinda ya barta da jin kunyar Iya Tabawa, shiko ko'a ƙwallar rigarsa. Bayan dawowarsu da sati uku ya fara nemawa Asma'u gurbin shiga jami'a ta fara, sai dai kullum tana manne da waya suna shan soyayyar su da Hussain ɗin ta, idan kuma ya bushi iska yakan shiryo yazo UK ɗin ya mata kwana biyu. Tayi farin ciki da hakan sosai dan ita mai son karatu ce dama. Shima AA an sakashi makaranta, sai dai ba boko bace ta addini ce da wani balarabe maƙwafcinsu ya ɗan buɗe domin yaran musulmai. Lulu ta cigaba da shayar da yaranta cikin ƙoshin lafiya da kuzari, yayinda suketa ƙara wayo da ƙyawu masha ALLAH. Kamaninsu da mahaifinsu da AA nata ƙara fitowa.... _________★         Sosai bashi da lafiya. Ya wani irin fita a hayyacinsa tare da yamushewa kamar wani tsoho dan ko Baba Garko bazai nuna masa tsufa ba a yanzu al'amarin zammamaki. Duk wanda yasan Sulaiman ya ganshi a yanzu zai iya dire rantsuwa da bada tabbacin bashi bane. Ya bushe a tsaye ƙwarai da gaske. Tunda aka gama shari'arsu aka kaisa wani mugun jail sau ɗaya Hajiya Turai taje dubashi, ba komai ya kaita ba ma sai amsar takardar sakinta. Dan amaryarsa ita ta samu nasarar amsa tun randa aka yanke musu hukunci. Da ƴaƴansa duka taje, duk da da ƙyar ta samu Tajuddeen ya bita. Ganinsu ba ƙaramin tayar masa da hankali yayi ba ya dinga kuka har suka taho. Sai Daddy dake dubashi duk bayan watanni biyu, amma ƴan uwansa da Baba Garko tun randa aka kamashi basu sake waiwayarsa ba.        Abinda Daddy ya gano a bincikensa saboda hankalinsa ya tashi da ganin yanda Sulaiman ɗin ya takwarkwashe a cikin watannin da basu gaza goma sha uku ba shine allurar guba akai masa da ke cinyesa a tsaye. Ba kowa bane kuma ya harba masa wannan tsiyar sai abokan huɗɗarsa turawan nan. Dan takanas suka zo Nigeria domin hakan garesa, acewarsa amfaninsa ya ƙare garesu kuma. Wannan allurar ce keta faman cin jikinsa a tsaye batare da kowa ya fahimta ba sai su waɗan da aka haɗa kai da su sukai masan. Tun ciwon na cinsa a tsaye har takaisa ga kwanciya a cikin asibitin jail ɗin. Watansa kusan takwas yana wahalalliyar jiyya kafin ALLAH ya amshi rayuwarsa. Rasuwarsa ta zagaya kowace kafar yaɗa labarai, wasu na masa addu'a wasu na ALLAH wadarai da faɗin sai aje kuma a fuskanci kamun ALLAH. Tsakaninsa da Rasuwar Dada wata biyu ne, dan tunda aka sanar musu sanadin mutuwar Sulaiman bata sake lafiya ba, da ga ƙarshe dai itama sai da ta bisa. Garko family sunji wannan rashi matuƙa. Dan Baba Garko yasha kuka shima har sai da ya kwanta asibiti. Lulu ma tazo, sai dai daga ita sai twins tazo. Satinta uku ta tattara ta koma.      (Sai muce ALLAH ya gafartama Dada da iyayenmu baki ɗaya 😭👏). *_YEARS LATER_*                     Barcinsa yake hankali kwance kansa a saman cinyarta. Yayinda ita kuma ta nutsu a masa gyaran kansa. Da farko hira sukeyi a hakan. Sai dai tunda taga barci ya ɗaukesa ta canja akalar gyaran gashin zuwa kitso kasancewar ya tara suma sosai a kan nasa. Sai dai normal askine a kansa ba irin na rashin mutuncin nan da aka san ƴan ƙwallo da shi ba. Tsaff tai masa kitso guda takwas tana kwasar dariya. Hakan bai mata ba ta zame kansa a hankali zuwa saman filo taje gaban mirror ta kwaso kayan kwalliya. A hankali ta zane masa fuska ya fito ras kamar wani mace. Sannan ta fara zuba masa hotuna. Kukan autanta da take jiyowa da ga falo ya sata ajiye wayar ta fita. Ilai kuwa shi ɗinne dan a hanya suka haɗu yana kuka.       “Kai kai waya taɓa min Ubana haka?” ta faɗa tana riƙosa yaron da bazai wuce shekaru uku ba zuwa jikinta. Cike da shagwaɓa ya ce, “Ba aunty Hafcy bace ba. Wai dan nace mata Hassatu shine ta mintsineni da rankwasar min kaina”.      Daƙyar Lulu ke danne dariya, dan kowa a gidan yasan masifar Hafsat ta dabance. Sam bata gado Ammah ba itakam. Gaba ɗaya a hallaya ita ta biyo. Sannan bata yarda a kitata Hafsatu ba. Tace sunan mutanen da ne ita Hafcy gayu take so.......✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗            𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣6️⃣ 🔚 .......Tun haihuwarsu sukaso ɓoye mata suna, Ammah tace a kirata da sunanta bata son wannan ɓoye-ɓoyen. Dole ake kiranta da hakan, itace dai bata iya faɗa sai tace mata Ammah. Smart kuwa shine ya laƙa mata Hafcy gayu saboda ƴar gayence ta gaske. Duk da shekararsu ta shidda kenan itada Hassanarta Aysha iyayi a wajenta ba'a magana kamar wata babba can. Ko shi Smart ɗin yace mata Hassatuwa fushi takeyi kota sanya kuka. Hannunsa taja zuwa falon, inda sauran yaran suke kowa da hidimar gabansa. AA shi dama boss ne (like father like son), komai na ubansa bai bari ba. Baya son hayaniya bayi da yawan magana. Idan kaji bakinsa a gidan nan to al'amari yakai intaha, ga jarabar son ƙwallo da kallonta. Shekararsa takwas kenan da ƴan watanni. Sai ƴan biyu Aysha da Hafcy gayu. Bayan su ta ɗan huta kusan 3years kafin ALLAH ya kawo cikin auta dan tace daga shi fa Alhmdllh ta gama duk da dai Smart yace akwai sauran Ahmad bata gama ba. Shi auta sunan Uncle Yousuf yaci. Shikam akwai fitina, dan halinsa da Hafcy gayu iri ɗaya ne, itama Aysha bajin magana take ba, sai dai nata wani lokacin takan zama irin AA ba ko yaushe ta damu da shiga hayaniyar ba sai idan ita taso.         “Wane ɗan jakar uba ne ya dakar min Babana?”.    Lulu ta faɗa babu alamar wasa a fuskarta. Da sauri Aysha ta nuna Hafcy. “Wlhy itace Maah-maah. Yarinyar nan ta fitini kowa a gidan nan, dan ALLAH a maidata Nigeria wajen Ammah”.      “Eh eh anji ɗin a maida nin, wake tsoron zuwa Najeriya ɗin ƴar iyayi kamar ma an kasa da ke”. Hafcy ce mai maganar cikin zaƙalƙalowa da tsiwa kamar su Lulu ana yarinya. Dan ita kam ko AA bata ragawa balle wata Aysha da suke kai ɗaya. A harzuƙe Ayshan ta miƙe tana huci itama da cewa, “Wai kaina zaki dawo halan. Kin san dai karanmu babu daɗi wlhy fasa miki baki zanyi bar ganin Papa mai goya miki baya yana gida ehe”.      “To gwada idan zaki iya”. Cewar Hafcy.     Tsaki mai ƙarfi AA da ke danna tab.. ɗinsa yana game na ball ya buga. Cikin jin haushi ya dubi Lulu da al'amarin yaran ya girmeta. “Maah-maah dan ALLAH kice ma ƴaƴanki su wuce ɗakinsu ALLAH sun isheni da hayaniya. Yaran nan suna bani ciwon kai ni gaskiya Nigeria zan koma. Gara naje wajen Daddy da Mamy”. (Ahmad da Maryam) dan kuwa ɗan gaban goshinsu ne. Ga kuma alƙawarin ALLAH ya cika sun haifa masa mata mai suna Rasheedah sunan mahaifiyarsa ana kiranta Nu'aimayah.      Cikin ɗoki auta da suke kira Uncle You ya ce, “Yaya nima zanje ka kaini wajen Mammah”. (Asma'u. Dan itama anyi bikinsu da Hussain yanzu haka tanada yaronta da yaci sunan Daddy). Fitowar Smart ya hana Lulu bama AA amsa. Gaba ɗayansu suka juya suna kallonsa saboda gyaran muryar da yayi. Aysha ce ta fara waro idanu waje. Yayinda Hafcy gayu ta dafe baki tana dariya. Duk rashin son hayaniyar AA sai gashi ya kwashe da dariya da faɗin, “Oh oh Papa waya maka kitso da kwalliya?”.       Cikin mamaki Smart ya kai hannu ya shafo kansa da dama yake jin duk ya ɗaure masa. Ilai kuwa sai ga kitso. Da sauri ya kalli sashin da Lulu take tana faman kwasar dariya. Su Aysha na tayata. Babu shiri ai ya nufi mirror dake cikin falon....      “Babbyyyy luvvvvvvv!!!” ya faɗa da ƙarfi ganin aika-aikar da tai masa. Mi yaran zasuyi in ba dariya ba kuwa. Yayinda Lulu ta arta da gudu zuwa bedroom shima ya take mata baya. Suko yara nata dariyar iyayen nasu dan ba yau suka saba gani ba, auta harda tsallensa duk da ba komai yake fahimta ba. Bedroom ɗin suka shiga zagayewa Lulu na dariya taƙi bari ya kamata. Cikin hakki da riƙe ƙugu ya ce, “ALLAH gara ki tsaya ma. Ni kikama wannan abun kamar wani ɗan daudu”.      Dariya ta sake kwashewa da shi da masa gwalo. Tuni ya sake yin kanta ta haye saman gado. Tsalle ɗaya ya cafkota suka faɗa saman gadon gaba ɗaya. Kanta ya haye yana mintsininsa. “Wayyo zaka fasamin ciki na banu na, nauyi fa gareka kamar Shari'a wlhy.”          “Sai dai ya fashe kuwa yau ba dai ni kikama kitso da kwalliya ba”.      “To bagaka nan ka fito a binka shar ba kamar wani ƴar budurwa. ALLAH da kai mace ne da su aunty Bilkisu sunci kuɗin samari”.     Cikin ɗage gira ya ce, “Sai kuma akai sa'a a namiji nazo ko. ALLAH kin gama da ni. Kigafa yanda yaran nan suke dariya. Yanzu wannan autan naki mai bakin surutu zai je yana bazani”. Ya ƙare maganar cikin shagwaɓa.           Dariya Lulu ta sake kwashewa da shi harda hawaye. Yayinda shi kuma ya zuba mata ido yana sake ƙwaɓe fuska. Kan nasa ta rungumo a jikinta cikin son sassauta dariyar tata take faɗin, “Sorry Babyna bazan sake ba. Ammafa ALLAH kayi ƙyau. Dan ALLAH ka yarda kullum na dinga maka kwalliya, kitson nan kuma ka barshi ai ba haramun bane ba dai tunda MANZON ALLAH ma kai ka faɗa min yanayi, mu dan ba al'adarmu bace ba dai shiyyasa idan mukayi lissafin baya dai-dai”.       “Anƙi ɗin” ya faɗa yana ture mata hannu da sauka a jikinta ya koma gefe yana faman kumbura fuska shi a dole yayi fushi. Dariyar ta sake kwashewa da shi ta tashi ta koma kusa da shi ta rungumesa ta baya. Da ƙyar ta iya haɗiye dariyar ta ce, “Sorry Babyn Baby luv ɗinsa.”          “Ban yarda ba, har zuciyarki ne?”.     “Eh mana, ai kasan ni da kai bata ɓaci”. Ta faɗa tana kai masa kisses. A hankali ya lumshe idanunsa da kamota ya juyota ta dawo saman cinyarsa. Cikin wani irin narkakken kallo da sauke murya ya ce, “I love you so much FURAR DANƘO na”.          “I love you too babyn baby luv. Amma kai ne FURAR DANƘO ba Mawaddat ba. Su Umma sun shekara sunan damawa har suka bar duniya baka zame musu farau-farau ba”.      “Ina ban yarda ba Baby luv. Ke da Daddy kune FURAR DANƘO har su Sulaiman suka faɗi baku zame musu farau-farau ba. Amma ni Ummah ai sanadin alkairi tamun, dan maybe da bata min abinda tai ba da ban zama driver na haɗu da Mawaddatan'warahmah Isma'il Ibrahim Jiƙamshi ba. Ke dai i love you irin mara ƙarewa ɗin nan har a cikin aljanna”. Ya ƙare faɗa yana wani ƙanƙameta a jikinsa ƙwalla na ciko masa ido na farin ciki da jin tamkar ya haɗiyeta. Itama ƙanƙamesan tayi tana hawaye. Kara rungumeta yay ajikinsa yana murmushi ya ce, “Kinsan abinda yabani mamaki kamar yanda su *NAWAFF* suka samu rashin jituwa atsakaninsu karshe ya rikiɗe ya koma soyayya sai gashi muma hakan ce ta kasance agaremu *RASHIN SANI* yasa muka zurfafama junanmu ƙiyayya amma ni nayi tunanin *WUTSIYAR RAKUMI* ce tayi nesa da kasa ne, ban taba tunanin zan sameki ba, na ɗauka aneman aure ma ana nuna *SIYASA KO KABILANCI*”. Ƙara gyara zamanta tai ajikinshi tana murmushi ta ce, “Ni kaina bantaba tunanin akwai yuwuwar aure atsakaninmu ba ganin irin *TAKUN SAKAR* Daya dinga shiga tsakaninmu, sai dai da yake ance *RAINA KAMA* kaga gayya, niba abinda zance sai dai in kara godema ALLAH daya mallaka min kai amatsayin miji kamar yanda *ABDUL MALEEK* (bobo) yayi, kuma ina kara godewa ALLAH daya baroni daga rayuwar *BAKAR INUWA* wacce gwanda rana da ita, kuma gwanda ni tawa rayuwar da irin rayuwar da zaka kasa tantance *KANWAR UWACE KOH KISHIYAR UWA*”. Kallanta yay ya ce, “Wannan ai ba *SABON AL'AMARI* bane in kikai duba da irin yadda mutanan yanzu suka kware da *SARAN BOYE*, sai dai sun mance shi *CIKI DA GASKIYA* wuƙa bata huda shi, kuma gwanda irin rayuwar da kikayi da wacce mutane suke jefa kansu *A SANADIN BIKIN SALLA*”. kallan shi tai itama cike da shauƙi ta ce, “Toh ai kasan su mutane basu *GUDU DA WAIWAYE*, sun manta cewa *MAKAUNIYAR KADDARA* duk inda kai tana tare da kai kamar yanda *NIDA AMINIYATA** aka haɗa baki da ita don amin fyade sai dai ta manta shi *KWAI CIKIN KAYA* wahalar fita gareshi, kuma shi *KUKAN KURCIYA* jawabine me hankali kadai ke iya ganeshi”. Murmushi yay yana shafa kanta ya ce, “Kamar yanda nima aure na dake nake  masa kallan *AURAN KADDARA KO BIYAYYA* a lokacin nayita tunanin naƙi amincewa saina tuna da irin wahalar da star din littafin *BAN SAKETA BA* yasha, shi ahakanma bai saketanba saboda rabuwa da abinda kake so balai ne wanda yafi *KARAYAR ARZIKI* zafi kidaina tuna abinda ya wuce domin duk wata *DAUDAR GORA* ciki ka shata”. Ƙara faɗaɗa fuskar ta tai da wani murmushin tace harkasa na tuna da irin soyayyar da Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul majeed Shahan-Shan na daular ruman yake nuna ma Fareedah Iffah, duk da alokacin suna cikin fuskantar tashin hankali da matsaloli, sai dai *MUTUM DA DUNIYARSA* ya dace ya gyara kansa.” Murmushi ya sake saki mai sanyi wanda ya kara fidda ainahin kyan fuskarshi yace duk da irin tarin kaunar da yake mata bata kai kwatan kwacin wacce nake miki ba domin kedin *FURAR DANKO* ce ashekara ana damu ba farau farau”. “Tabbas na yarda da irin son da kake min domin da *BABU SO* ba abinda zai kawo kishi Babyn Baby luv” ta ƙare maganar da manna masa kisses shi kuma yana lumshe ido da sake ƙan ƙameta. A haka yaran dake laɓe suna leƙensu da saurarensu suka shigo da gudu suma suna faɗin “Maah-maah!! Papa!! I love you so much.”✍️       *_Kai to nimafa I love you ɗin nan irin trillions wujiga-wujiga manya-manya nan masoyan amana🤣😂👏_* *_ALHAMDULLAHI YA RABBI👏😭_*       _ALLAH na gode maka daka kawoni wannan rana ta Friday/10/2023. Abinda nai kuskuren rubutawa ALLAH ka gafarta mini kuma da kuka karanta ya gafarta muku. Sannunku-sannunku da ƙoƙarin haƙuri kuma. ALLAH ya saka muku da alkairinsa ya bar zumunci. Yanda kuka so ni domin ALLAH ina fatan kuma UBANGIJI ya soku haka ku da zuri'arku baki ɗaya. ALLAH ya karemu ya tsaremu baki ɗaya. Ya sanya albarka da tarin alkairi a garemu. ALLAH ka gafartama iyayenmu da duk al'ummar musulmi da suka rigamu kwanta dama. Marasa lafiyarmu ALLAH ka basu lafiya. Masu ciki ALLAH ya saukesu lafiya. Ƴammata da zawarawa ALLAH ya baku mazaje na ƙwarai da sukafi mazan novels ƙayatarwa da nagarta. Mu da muke gidajen auren namu ALLAH ka cigaba da bamu zaman lafiya. Masu neman haihuwa ALLAH ka basu idan alkairine, idan ba alkairi bane ALLAH ka musanya musu da abinda ya fita alkauri. ALLAH ka shirya mana yaranmu, wanda suke shaye-shaye ALLAH ka yaye musu. Masu tasowa da basayi UBANGIJI ka cigaba da kare mana su. Ya rabbi ka kawo ma musulmanmu dake cikin wani hali a ƙasashensu mafita, ALLAH ka karya azzaluman kafirannan. Ya rabbi ka kawo ma bayinka ɗauki na halin da suke ciki.😭😭👏_    *Duk wanda naima kuskure a yayin rubuta littafin nan ya yafe min dan ALLAH. Dan zata iya yiwuwa wannan shine littafin Bilyn Abdull na ƙarshe a duniya. Zaku iya jin saƙon mutuwata akoda yaushe. Idan hakan ta kasance kumin addu'a da neman gafarar UBANGIJINA dan ALLAH 😭😭🙏*. Ta ku ce dai har kullum. Bilkisu Ibrahim Musa (Bilyn Abdull ce😘🤳)      _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR ‘KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*