03/04/2021 脿 15:04 - Les messages et les appels sont chiffr茅s de bout en bout. Aucun tiers, pas m锚me WhatsApp, ne peut les lire ou les 茅couter. Appuyez pour en savoir plus. 06/08/2021 脿 11:49 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *1* A nutse suke taka k'asar kowace da jakarta a hannu da dogayen hijab d'insu har k'asa, yanayin kamalarsu da fuskokinsu zai nuna maka sun samu tarbiya a zahirance dai, girgiza kai d'ayar tayi tace "Gaskiya yau ba zan je ba, dama ina shiga kallo ne a gidan idan ans s茅rie d'in da nake so, yau kuma ba'a yi dan haka ina gida." Wacce tafi tsayi da haske sosai ga kuma 'yar k'ibarta tace "Ni kam zan je, dan jiya mbc Bollywood sun yi tallar khabi kushi khabi gham, dan haka zan je nayi kallo." Tab'e baki tayi tace "Amma *Mimi* da dare ne fa, kinsan Abbanki ba zai barki fita ba." Kallonta tayi ita ma tace "Kinsan yau asabar yana tafiya babban masallaci wajen sauraren karatu, yana tafiya ni ma zan tafi, awa d'aya suke yi kafin su gama na dawo." Sake tab'e baki tayi tace "To yau *Mas'ud* ba zai zo bane?" Wani dogon tsaki tayi tace "Ina farin ciki zaki lalata min shi ta hanyar kiran sunanshi." Da mamaki ta kalleta tace "Mimi, Mas'ud fa shi ne iyayensa suka kawo kud'in gaisuwarki gidanku kuma iyayenki suka karb'a, sannan sun tsayar da magana cewa ana fara azumi zai kawo lefenki da sadaki, amma shi ne ba ki son maganarshi." Yatsina fuska tayi tare da cunno leb'enta na k'asa mai kalar pink sosai tace "Wa ya fad'a miki zan yarda ya kawo? Wallahi bana son shi." Da mamaki sosai tace "Ba kya son shi kuma kika bari manya suka shiga maganar?" Cikin rashin bawa abun mahianci tace "Eh, saboda kawai ya takura min ba yanda zanyi, sannan bani da wani tsayayye har yanzu da zai dinga d'aukar d'awainiyata, sannan kuma yana da wani abu da nake son namiji ya kasance da shi." Girgiza kai ta shiga yi da mamaki kafin tace "Mimi me yake damunki? Me yake da shi da kike so? Dama ba dan Allah kike kulashi ba?" Wani murmushi tayi da yasa kumatunta masu tudun gaske sake fitowa tace "Sam bai min ba ne *Asma'u*, sa'arshi d'aya ya iya d'aukar wanka." Jinjina kai tayi tace "Kenan kamar bankinki kike mayar dashi?" Dariya tayi da tasa hak'oranta fitowa farare tas tace "Kusan haka?" Cikin jimami tace "Allah ya shiryaki." Da dariyar mugunta tace "Ameen." Suna k'arasowa gidajen na su Mimi tace "To nasan dai saida safe, dan ke ko 'yar wayar nan baki da za'a dinga yin jira ta WhatsAp." Murmushi Asma'u tayi tace "Ke ma da kike da babbar wayar karki manta ba da sanin mahaifinki kike yi ba, kuma duk ranar daya sani zaki kad'e." Dariya tayi tace "Ba ma zai sani ba, kafin lokacin na yi aurena na tafi na barsu." Dariya Asma'u tayi tana girgiza kai tace "Mimi haka kika zama yanzu?" Fari ta mata da ido tace "Ah to! Zamu zauna rayuwa babu ci gaba ne, ke ma kina son kiyi auren ai rashin matsayi ne." Girgiza kai tayi tare da shigewa gidansu, ita ma shiga tayi tare da yakice hijabinta ta cire tana siririyar sallama, babu kowa a tsakar gidan sai mahaifiyarta dake zaune bakin murhu tana kad'a miya, yatsina fuska tayi tace "Mama yau ma dai na gadon ne?" Juyowa tayi ta kalleta, girgiza kai tayi ta yi banza da ita ta ci gaba d脿 abinda take, da sauri ta shige d'akinsu bayan ta duk'a kafin ta iya shigewa ciki, aje kayan makarantar tayi sai siket d'in data ja sama tayi d'aurin k'irji da shi ta fito, bokiti ta d'auka ta je gaban randa zata d'ibi ruwa uwar ta kalleta cikin muryarta kamar ta yara tace "Karki fara *uwa*, kar ki d'ibar min ruwa kinji na fad'a miki." D'agowa tayi ta kalleta da mamaki tace "Mama wanka zanyi fa." Cikin fad'a tace "Ruwan alwala kawai zaki iya d'iba, shi ma idan za kiyi sallah." Da mamaki tace "To me yasa? Babu ruwan ne?" Kai tsaye tace "Babu, kuma kinsan ai ke kinfi k'arfin d'ebo ruwan, k'annanki ne ke d'ebowa da k'yar suna kawo mana, amma ke kika fi kowa anfani dasu." Turo baki tayi tace "To yanzu dai bari na yi wankan, zan d'ebo miki gidansu madame *Maimuna*." Hararanta tayi tace "Ke d'in? Ke ce zaki d'auko bokitin ruwa?" Da sauri tace "Wallahi zan d'ebo." D'ibar ruwan tayi rabin bokiti ta shiga d'aki ta d'auko kwandon wankanta mai d'auke da rantsatsen sabulu mai tsadar gaske da samarinta suka siya mata tare da maclean da brush ta shiga ban d'akin. Ta jima a ciki tana gyara jikinta kafin ta fito rik'e da kwandon, bokitin kuma ta baroshi a can,da kallo uwar ta bita dan ita har ta gaji da mata maganar d'auko bokiti ma, idan ta tashi ta d'auko kawai. Buta ta d'auka tana sake zubawa k'afafunta ruwa tana fad'in "Gaskiya Abba ya daure a shafe mana ban d'akin nan da simitin, haba ban d'aki kamar wani filin dambe." Tana saurarenta ita dai har tayi alwala ta shige d'akin, mai ta fara shafawa tare da d'auko k'atuwar jakar kayan kwalliyanta, sanyayya kwalliya ta yi wa kanta mai birgewa kafin ta mik'e ta nufi wajen kayanta. Tabbas kayan dake cikin akwatinta kana kallonsu zaka san sun fi k'arfin 'yar wannan gida, k'arya da d'aukarwa kai ne kawai zai bata wannan suturu, dan duk girman akwatin nan na k'arfe shak'e yake da kaya, daga kallonsu a ido kawai zai tabbatar maka sababbi sun fi yawa kuma duk d'inkunan zamani ne masu tsada. Wani mahaukacin leshe ta d'auka ta saka riga da siket wanda aka cika gaban rigar da duwatsu masu k'yalli, dake tana da kumari sosai sai suka zauna mata d'ass a jiki musamman siket d'in daya fito da mazaunanta sosai, hijab ta saka ta fara gabatar da sallah magrib kafin ta gama ta d'aura d'an kwalin kayan, wani mayafi ta d'auka shara shara ta feshe da turare ta fito tsakar gidan. Kallon mahaifiyarta tayi dake tsaye tana sallah, hallitar Allah kenan, domin kuwa duk kyan *Maryam* da tsayinta da wannan baiwa da Allah ya mata, mahaifiyarta 'yar wada ce, ma'ana irin gajerun nan k'anana, dan da zata tsaya kusa da ita ba zata kawo mata a k'ugunta ba. Matsawa tayi kusan kwanukan data gani ta shiga bud'ewa, d'an tsaki tayi tace "Yunwa nake ji amma wallahi ba zan iya cin tuwo ba." Mik'ewa tayi ta koma d'akin ta d'auko 'yan canji a jakarta ta fito daidai da gama sallarta, kallonta tayi tace "Ina zaki je kika yi shiri haka?" Cikin turo baki tace "Babu inda zan je Mama, nan gidansu madame ne zan shiga." Girgiza kai tayi tace "Uwa bana son kowane lokaci kina zuwa musu gida, me yasa ba zakiyi hak'uri da kallon ba wai? Tunda Allah bai hore mana ba." Kamar za tayi kuka tace "Mama zan daina, yanzu ma wani film ne za'a saka mai kyau da ban tausayi, yanzu na dawo fa." Jinjina kai tayi ta d'auke kanta daga gareta tace "Idan ma baki dawo ba ke da mahaifinki ne babu ruwana." Cikin rad'a tace "Mama har sun tafi karatun ne?" D'aga mata kai tayi tace "Sun tafi tun kafin ki shigo." Murmushi tayi ta nufi hanyar fita tace "Yanzu zan dawo Mama." Da kallo ta bi k'ugunta dake bala'in juyawa sosai, tafiyar kuma a nutse take yinta amma dake Allah ya horesu, girgiza kai tayi tana fad'in "Allah ya shiryaki Mimi." Gidan yana kallon nasu ne babban gida ne mai d'auke da babbar k'ofa, kai tsaye ta shiga bayan sun gaisa da mai gadin, saida ta tsaya a farfajiyar ta ciro wayarta daga k'ark'ashin siket d'inta kusa da cibiya kafin ta shiga d'aukar kanta selfie, saida ta d'auki masu kyau kafin ta shiga WhatsAp ta d'ora wanda suka mata a statu tana wa jama'a barka da da dare, da sallama ta shiga babban falon yaran da matar gidan suna amsa ma ta, gaisawa sukayi a mutumce kafin ta nemi kujera ta zauna tana fad'in "Tanti mbc basu saka film d'in nan ba?" Lalaba kujerar da take kai tayi ta d'auki remonte ta mik'o mata tana fad'in "Gashi duba ki gani." Karb'a tayi inda Maimuna ke fad'in "Ni fa kallon ba damuwata yayi ba, idan ta ni ne ma saina wuni ban kunna tvn ba." Dariya kawai tayi sanda take nemo tashar, ganin ana tsaka da film d'in yasa ta gyara zama tace "Yawwa an fara." Tattara hankalinta tayi gaba d'aya ta mayar kan tvn, kallonta Maimuna tayi, yarinyar na birgeta sosai saboda iya d'aukar wankanta da saka kaya, kamar ba 'yar talakawa ba, dan ko ita dake auren mai kud'i bata kai ta saka kaya masu tsada da kyau ba, uwa uba jikinta dake d'aukar ido kamar na wata babbar yarinya. Mik'ewa tayi ta bar ta nan ta shiga k'arasa kimtsa gidan, tana kammalawa ta saka turaren tsintsiya kafin ta d'ebo abinci a plate, k'asa ta aje ta kalleta tace "Mimi sauko mu ci abinci." Kallonta tayi ta kalli plate d'in, kai har ga Allah ba zata ce a'a ba, macca ce fa da jar miya da naman kazi, ai duk rashin had'amarta tafi k'arfin cewa a'a tunda dama yunwa take ji, tasowa tayi a hankali ta zauna cike da kunya, ita kan ta Maimuna tayi mamaki dan gaske duk sakewar Mimi a gidan nan bata cika cin abinci ba, yanzu ma dan taga akwai yaran makwabta ne yasa ta zubo mai yawa idan ita bata ci ba su sun ci. Cikin nutsuwa suke ci suna kallon tvn saidai babu mai magana, basu ji tsayawar motarshi a k'ofar gidan ba sallamarshi kawai suka ji a tsakiyar falon tare da amsa gaisuwar da yaran mak'wabtan ke mi shi. Bayanta yake kallo dan tana fuskantar tv ne, saidai daga yanayin shigar yasan ita ce, ga k'amshin turarenta *pure love* daya gauraue d'akin duk da turaren wutar da aka yi, musamman data aje gyalenta a kan kujera saiya samu kan shi da k'urawa bayanta ido, d'inki ne kamar na yanzu bayan ya sauka sosai fiye da kafad'unta, rigar kuma a kan k'ugun take zaune har yana ganin zip d'inta da kuma zariyar da akayi a baya na salon d'inki. D'an lashe leb'enshi yayi tare da kallon gashinta data dunk'ule ta rufeshi da ribom, dan yanayin d'aurin d'an kwalin yasa tsakiyar data tara gashinta a bud'e yake. Murmushi ya saki yana k'arasowa yana fad'in "Sannunku, abinci ake ci?" Tunda ta ji sallamarshi ta tsaya cak saboda kunya, sunkuyar da kan ta tayi saida taji ya baro bayansu kafin tace "Ina wuni." Da sakin fuska ya amsa da "Lafiya lau Mimi, an wuni lafiya?" Sunkuyar da kan ta kawai tayi ba tace komai ba, mik'ewa Maimuna tayi tana fad'in "Sannu da zuwa? Yau ka shigo da wuri." Murmushi ya mata yace "Hakane, zan d'an fita ne shiyasa." Tsaye tayi gabanshi tace "Muje kayi wanka ko?" Jinjina kai yayi tare da mik'ewa, hakan yasa ita ma mik'ewa tana kallon Maimuna tace "Aunty ni zan tafi, saida safe." A tare suka kalleta da sauri yace "A'a Mimi zauna, ba jimawa zan yi ba kinji, zauna ki ci abincinki." Murmushi tayi sai lokacin ta kalleshi, a k'alla ba zai gaza shekara arba'in da bakwai zuwa da shida ba, yana da kwalliya saidai matsalar mutum ne mai k'iba. Girgiza kai tayi tace "A'a zan tafi, saida safe." D'aukar mayafinta tayi da wayarta duk da hannu d'aya hannu d'aya kuma a sagale saboda abincin daya tab'a ta juya, duk da yana gaban matarshi saida ya sake bin bayanta da kallo, lumshe ido yayi ya sake lashe leb'e yana ayyana a ran shi "Insha'Allah zaki zama matata ke ma, ina son ki Mimi, wannan surar taki zata zama tawa ni kad'ai, gidan hutu ne ya dace dake." Saida ya ga fitarta kafin ya kalli Maimuna data wuce gaba ya bi ta baya. Tana fita a farfajiyar ta wanke hannu ta sha ruwa a bakin panpon, yafa gyalenta tayi ta shiga latsa wayarta, tana kaiwa k'ofar gida kira na shigowa wayar, dubawa tayi ta ga an ruba *d'an wahala*. Tsaki tayi tare da d'auka dan bata tsallake kiranshi kasancewar mutum ne mai sakin hannu, a yanda ta wuni ba wadataccin kud'i zata so samun na kashewa. Cikin sanyayyar murya tace "... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:49 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *2* Cikin sanyayyar murya tace "Hello." Amsawa yayi da "Gimbiyata, ya kike?" A dak'ile ta amsa d'脿 "Lafiya lau." D'orawa yayi da cewa "Na ga statu d'inki na yi magana na ga ba kya en ligne (online)." Cikin yatsina fuska tace "Hakane." Cikin murmushi yace "To ki hau za muyi magana." A k'asan mak'oshi tace "Um um!" Da sauri yace "Me yasa?" Shiru tayi hakan yasa shi cewa "Ko babu mega (data) ne?" Yanzu ma a mak'oshin tace "Um." Wani murmushi yayi yace "Haba gimbiya Mimi, kuma shine baki kira kin fad'a min ba? To kinga bari na turo miki da kati yanzu saiki hau zamuyi magana." A dak'ile tace "Uhm! Nagode." Da fara'a yace "Haba ba komai, matar da zan aura ace babu kati a wayarta, ai abun kunyata ne." Yana kashe kiran taja tsaki tace "Aikin banza, ko me zanyi da shi? Wani k'azami dashi ko turare bai iya sakawa ba." Mayar da wayar tayi ta soke a siket d'inta kafin ta fita a gidan, canjin hannunta ta nufi bakin titi dan samun wani abu da za ta ci, dan da tana da kud'i isashi kayan shayi zata siyo, dan a rayuwarta tana son shayi sosai musamman da bred da soyayyen k'wai, a hankali ta taka har ta k'arasa bakin titin, babban birni kenan ba'a cika samun irin kayan soye soyen nan ba, a hakan ma wai dan suna unguwar marasa k'arfi, wani shago ta k'arasa kawai ta siyo sardine da bred ta juyo dan komawa gida. Tana ganin motar ta sunkuyar da kai dan ta gane shi ne, duk da haka saida ya tsayar da ita ya fito daga motar yana fad'in "Mimi daga ina kuma? Na d'auka ai gida kika shiga." Da ladabi tace "Na je nan ne bakin titi siyo abu." Murmushi yayi yace "Mama ce ta aikeki?" Da sauri ta kalleshi jin yace wai mama, bayan kuma tana da tabbacin ya girmema mahaifiyarta ma, d'an tab'e baki kawai tayi ba tace komai ba, hannu yasa aljihu ya ciro yan jaka biyar biyar gida biyu ya bata yace "Ga wannan kya siyawa su *Amir* abun kari da safe." D'an d'aga idonta tayi, a gaskiya ita kallon uba take masa da kuma mai taimakaonsu, ba kuma su kad'ai ba duka unguwar yana tallafawa gajiyayyu, haka yasa ta karb'a ba tare da tunanin komai ba tana fad'in "Angode, Allah saka da alkairi." Murmushi ya mata yace "Ki shiga gida kinji, bana son ganinki a haka ana kallonki." Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi amma kuma saita sunkuyar dan idonshi a kanta suke, jinjina kai tayi alamar to tare da takawa tana maimaita kalamanshi, saida tayi nisa kafin ta ji ya tayar da motar yayi gaba, da sauri ta sake kallon kud'in tana murmushin jin dad'i su ma ta sokasu a poshet d'in wayarta kafin ta saka wayar ta b'oye ta k'arasa gida. Daf da shiga gida wayarta tayi vibrations, tana dubawa tsabar kati ne ya turo mata har na jaka biyar, ko a jikinta dan ya turo mata fiye da na haka ma, shigewa tayi gidan da sallama tare da nufa wajen kwanuka dake cikin kwando a killace, k'aramin faranti ta d'auka na silba ta dawo ta aje kan tabarmar tare da ledar hannunta, d'aki ta shiga ta b'oye wayarta da kud'in kafin ta dawo ta zauna kan tabarmar ta mik'e k'afafu, uwar na kallonta ita dai har ta bud'e kifin ta juyeshi a ciki ta d'auki bredin, turawa uwar tayi tace "Mama ci." Girgiza kai tayi tace "Um um, a ci lafiya." Jawowa tayi ta ci gaba da cin abin ta tana fad'in "Mama har yanzu su Abba basu dawowa ba?" A sanyaye tace "Basu dawo ba, kinsan tafiya tare da su *Yaseen*." Cikin had'e fuska tace "To mama shi ma Abba ya dinga zaman shi a masallacin nan unguwar mana, yana wahala doguwar tafiyar nan fa." Da mamaki ta kalleta tace "Mimi d'aukar karatun da yake zuwa? Kuma kin fi kowa sanin shi d'in yana matuk'ar k'aunar karatun *Sheik Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif*, ba zai daina ba tunda yana so." Shiru tayi ba tace komai ba hakan yasa mahaifiyar ta sak茅 kallonta da kyau tace "Mimi, ni ko ki mayarwa da Mas'ud wayar daya baki?" Turo baki tayi tace "Na mayar Mama." Nunata da yatsa tace "Tsakaninki da Allah kin mayar?" Shiru tayi sai kuma ta kalleta kamar zatayi kuka tace "Wallahi mama gobe da ya zo zan mayar masa, ni dama wayar bata min ba." Jinjina kai tayi tace "Idan baki maida masa ba wallahi mahaifinki zan fad'a ma, ya fad'a miki baya son ki da waya yanzu Mimi, shiyasa ko da Mas'ud ya baki wayar nan nace ki mayar masa." Cikin turo baki tace "To naji zan mayar." Tuttura bredin ta dinga yi har ta mik'e ta wanke hannayenta da sabulu ta koma d'aki, kayan jikinta ta cire ta saka doguwar riga mai taushi ta yadi, tana fitowa tayi zaune mamarta tace "D'ebo ruwan fa sai yaushe?" Da sauri ta kalleta kamar zata fashe da kuka, saida ta turmuza k'afafunta alamar an takurata kafin ta mik'e bazar bazar ta d'auki bokiti tana gyara kallabin rigarta ta fita. Har zai wuce akan babur cikin sanyayyar murya tace "Ina wuni *Bello*." Tsayawa yayi tare da juyowa yace "Mimi, kina lafiya?" K'asa tayi da kanta tana murmushi kamar ba da hushi ta fito ba tace "Lafiya lau." Kallon bokitin hannunta yayi yace "Ya na ganki da bokiti? Wani wuri zaki tafi?" Cikin muryar shagwab'a da take da tabbacin tana kayar da mazan yanzu tace "Wallahi Mama ce ta aikeni d'iban ruwa, kuma kaga dare yayi yanzu babu kowa a wuri, shine nake tunanin shiga gidanku na d'ebo." Wani murmushi ya saki yace "Haba Mimi, kamar ki ace zaki d'ebo ruwa ki d'auko a kan ki bayan gamu a garin nan? Kinga koma gida ki zauna, dama gidan zan shiga yanzu idan na shiga zan saka yara su kai muku ruwan." Da farin ciki tace "Kai amma naji dad'i, nagode sosai." Murmushi ya mata yace "Ba komai." Juyawa tayi shi ma ya tayar da b芒bur d'in ya wuce gidansu da gida hud'u ne tsakaninsu, tana shigowa ta aje bokitin mamanta tace "Ina ruwan? Mimi ban san iskanci fa, yanzu cewa za kiyi babu ko kuma sun rufe gida." Dariya tayi tace "Mama ki zuba ido ki gani za'a kawo miki ruwa adadin da kike buk'ata." *Ahalin Aliyu Sharif* Babban masallaci ne da a k'alla yake d'aukar dubbanin jama'a, ana sallahr juma'a da sallah eid a ciki, ginin ya tsaru sosai ya k'awatu, a duk ranar asabar masallacin kan cika tantsam da mutane saboda babba kuma shahararren malamin dake tafsirin Alqur'ani a wannan ranar, mutane daban daban kan zuwa dan sauraren wa'azi daga gareshi, a ciki har da manyan yan siyasa dan dama masallacin a unguwarsu yake a cikin gidan *Gaddafi*, da kuma manyan attajirai manyan k'usoshi a gwamnati da saurensu. Ac dake wuri da panka ya hana mutanen gurin yin gumi duk da ba yanayin zafi a ke ciki ba. Teburin dake gabanshi tare da mai ja bak'i dake gefenshi a ciki yake da wayoyi manya da k'anana ana d'aukar recoding, sai d'an agaji guda a bayanshi da kuma wani mai tsaron lafiyarshi guda cikin bak'ak'en kaya da bak'in gilashi. A zahirance kyakyawa ne ajin da ba zai gaza hawa matakin farko ba, saidai kasancewarsa bafulatani yasa kana ganin zaka gane haka, a k'alla shekarunsa *arba'in da bakwai*, dan gemunshi ma har fari ke akwai wanda ya k'ara k'awatashi. Yanzu ma cikin raha da hankali da nutsuwa yake musu sharhin suratul *Noor*. Kiran wayarshi aka yi dake hannun mai tsaron lafiyarsa ya kuma d'auka saboda ganin lambar daga babban gida ce, yana d'aukar muryar Hajia cikin kuka tace "Sheikh, kana ina ne? Jikin *Ashraf* ya tashi fa, ga mu nan clinique de *gazobi*." Da sauri jami'in yace "Hajia muna tare da sheikh yana darasi, amma zan fad'a masa yanzu." Cikin tashin hankali tace "To dan Allah kayi sauri." Kashe kiran tayi hakan yasa jami'in matsowa ya sunkuyo kusan kunnenshi ya fad'a masa, da sauri ya kalleshi sai kuma ya sunkuyar da kan shi, ya jima haka kafin ya d'ago yayi gyaran murya, cikin nutsuwa da muryarshi mai taushi da sanyi da harshenshi mai gurgiri yace "A bisa wani babban uzuri daya taso min yanzu, zamu dakatar da darasinmu a nan saboda hali na ujila, da fatan zaku gafarceni, kira ne daga gida kan d'an uwana da baya da lafiya, muna barar addu'arku." K'ok'arin mik'ewa yayi yana jin yanda masallacin aka d'auki hayaniya ana jefo mishi addu'a ta fatan samun lafiya ga d'an uwanshi, ta hanyar baya suka nufa tare da d'an agajin da kuma mai tsaronshi, suna fita ta k'ofar wasu daga cikin mutanen har sun zagaye k'ofar, kowa hannu yake mik'o masa yana son sai ya jajanta masa baki da baki, wasu kuma lambarshi suke son amsa saboda a dinga kiranshi. Dake hakan ba sabon abu bane saiya shiga k'ok'arin zillewa amma ina dole saida ya gaisa da wasu, da k'yar ya samu ya shiga mota dreban ya ja shi zuwa asibiti. Suna zuwa asibitin kud'in clinique de gazobi suka fita a motar suna take mishi baya, saida aka fara fad'a musu d'akin da aka kwantar da shi kafin suka rankaya can, daf da zasu shiga ciki ya juyo tare da d'aga musu hannu alamar su jira shi, tsayawa sukayi suka hard'e a bakin k'ofar shi kuma ya shiga ciki. Su hud'u ne a d'akin, mahaifiyar Asharf da shi Ashraf d'in, sai kuma yayar Asharf d'in wacce mata ce ga Sheikh d'in sai kuma k'annan Hajia, amsa sallamarshi sukayi inda idonshi ke kan Ashraf dake bacci hannunshi d'auke da k'arin ruwa, cikin nutsatsiyar murya yace "Ya jikin na shi?" Cikin kuka Hajia tace "Jikinshi da sauk'i, sheikh wai yaushe ne za'a fitar da shi? Jikin Asharf ya fara bani tsoro fa, yanzu ciwon yana yawan taso mishi ba kamar da ba." A hankali ya matsa kusa da ita ya rik'o hannun yace "Kiyi hak'uri Hajia, insha'Allah zai samu lafiya, har yanzu a kan shirye shiryen tafiyarsa nake." Jinjina kai tayi tace "Allah ya sa." Da murmushi yace "Ameen, insha'Allah muna fatan haka." D'an juyawa yayi ya kalli uwar d'akinshi, sanyin idaniyarshi abar k'aunarshi, murmushi suka sakarwa junansu kafin tace "Sheikh mun d'aga ma ka hankali ko?" Girgiza kai yayi yace "Ba matsala, Allah ya bashi lafiya." Ita ma a sanyaye tace "Ameen." Saida ya saci kallon Hajia kafin ya kalleta da kyau, da hannu da kuma ido da girarshi ya mata alamar "Ya ajiyata?" Murmushi tayi tare da masa alama da motsa bakinta tace "Lafiya lau yake." Lumshe ido yayi alamar jin dad'i, sunkuyar da kan ta tayi ita kam dan kunya, shiru d'akin ya d'auka na wani lokacin kafin Hajia ta kalleta tace "Ki tashi ku tafi gida tunda jikin nasa da sauk'i ko?" D'an kallon sheikh tayi kafin ta jinjina kai alamar to, a hankali ya taka ya k'arasa daf da Asharf ya zauna bakin gadon, rik'o hannunshi yayi yana kallon kyakyawar fuskar Ashraf, duk da ba ciki d'aya suka fito ba amma yana bala'in son d'an uwanshi, sun shak'u sosai tun yana yaro, ladabinshi gareshi da kuma k'iriniyarshi suna birgeshi, kusan baya da aboki bayan yaron duk da kuwa ba tsaranshi bane, amma yanzu haka da zai samu sab'ani tsakaninshi da yayarshi na zaman tare, to shi yake ajiyewa tsakaninsu ya ja musu kunne. Lumshe ido yayi kafin ya sake bud'ewa, addu'a ya shiga karantawa yana tofa masa kusan minti talatin, su kuma kallonshi suke dan bai d'aga murya ba bare su ji su amsa da ameen, dan haka suna ganin ya sakin hannun Ashraf suka amsa da "Ameen." Mik'ewa yayi ya kalleta yace "Mu tafi." Kallonsu Hajia yayi yace "Saida safenku." A nutse suke takawa masu tsaron na gaba shi kuma suna baya tare da ita, suna fita mai tsaron ya kama murfin mota zai bud'e mishi, d'aga mishi hannu yayi alamar a'a, dakatawa yayi ya koma mazauninshi, da kanshi ya bud'e mata ta shiga ta zauna kafin ya rufe ya zagaya d'aya b'aren suka bar asibitin. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:49 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *3* Kasancewarshi malami zai sa kayi mamaki idan kaga tabkeken gidan da mai gadi ya bud'e musu suka shiga, amma idan kasan margayi Alhaji Aliyu Sharif zaka tabbatar wannan ba komai bane, dan tsohon shahararren d'an kasuwa ne daya tara mahaukatan kud'i kuma ya mutu ya barwa magadansu, haka na su iyayen suma suka musu suka bar musu suka gaji nasu kason, haka kuma sheikh Abdul Waheed ba malamin ci da ceto bane, d'an kasuwa ne haka kuma a cikin gwamnati ma shi d'in mai bawa gwamna shawara ne akan harkar data shafi ilimi. Shigarsu k'ayataccen falon yasa yara tasowa da gudu suna musu oyoyo, da murna shi ma ya d'auki k'ananan yana rumgumesu a jikinshi, babbar cikinsu kam a hankalce ta k'arasa kusa da mahaifiyarta tana fad'in "Momy sannu da dawowa, ya jikin tonton?" Da murmushi ta amsa mata da "Jikinshi da sauk'i, dan mun baroshi ma yana bacci." Da nutsuwa yarinyar tace "Allah ya bashi lafiya." Da fara'a tace "Ameen." Sauke yaran yayi yana kallon yarinyar yace "Uhm! *mamana* shi ne ko a kulani? Sai mamanki ko? To na yi hushi ma." Dariya tayi ta matsa kusa da shi ta kama hannunshi tace "Abu, kayi hak'uri, ina tambayar jikin tonton d'ina ne." Dafa kanta yayi yace "Ku masa addu'a kun ji, zai samu lafiya insha'Allah." Da kai ta amsa masa tare da fad'in "Insha'Allah Abu." Murmushi ya mata shi ma yace "Masha Allah." Kallon *Hafsat* yayi yace "Zan shiga ciki." Da ido ta masa alamar "Ina zuwa." Wucewa yayi yana murmushi tare da cire babbar rigarshi irin ta malamai da bata da wuya sai hannaye kawai, kallon *Aisha* tayi tace "Eesha, ku je d'akinku ki taimakawa k'annanki su watsa ruwa su saka kayan baccinsu, dare yayi kin ji." Da ladabi tace "To Momy." Kallon k'annanta tayi su uku tace "Muje." Mai bi mata ne ya kalli uwar yace "Momy, amma ai ban da ni ko?" Dariya tayi tace "Kai ai yanzu saurayi ne." Murmushi jin dad'i yayi tare da wuce suka haye sama inda d'akunansu suke, mik'ewa tayi da k'yar saboda k'afafunta da suka kumbura sakamakon cikin dake jikinta na wata biyar ta nufi d'akin sheikh, falo ne mai zaman kan shi dake zagaye da litattafai na ilimi daban daban da littafi mai tsarki kala kala anyi jere dasu, kai tsaye d'akin baccin ta wuce ta samu har ya shiga wanka, zaune tayi bakin gadon ta d'aga muryarta tana fad'in "Shi ne ka shiga ka barni ko? Ai zaka koma ne dan da kan ka zaka min wankan yau." Yana jin ta sai murmushi da yayi bai amsa mata ba, bai wani jima ba ya fito da rigar wanka a jikinshi, yana dariya, kama hannunta yayi yana fad'in "Muje na miki to, shikenan?" Turo baki tayi tace "To me yasa zaka tafi ka barni?" Murmushi ya sak茅 yi yace "A gafarceni to." Murmushi tayi ita ma tace "To na gafarceka sheikh nawa." Zip d'in rigarta ya ja zai cire tayi saurin cewa "A'a nagode, zan yi da kaina ai." Lumshe ido yayi ya girgiza mata kai alamar a'a yace "Ki barni, ina so na samu ladar, zanyi koyi da annabina ne manzon rahama, yayi wanka tare da matanshi yayi raha da dariya dasu." Jinjina kai tayi tace "To ai ni yanzu kunya nake ji, wannan abun fitowa yake sai nayi muni." Dariya yayi sanda ya kalli cikin data nuna mishi, shafa kumatunta yayi yace "A rayuwar aure babu kunya tsakanin ma'aurata, karki manta addininmu shine addunin da yafi kowane kunya hasalima ya koyar da mu jin kunya, amma a bisa haka ya fayyace mana komai game da rayuwar aure da yanda zamu tafiyar da addininmu, manzon Allah (S.A.W) yafi budurwar data fara k'irgen dangin kunya, yanda take jin kunya ta kasa sakewa da mahaifiyarta ma, a cikin gidansu ta kan zama kamar marar gata ko bak'uwa, amma a haka ya warware mana addininmu, kama daga yanda zaka samu najasa a jikinka har zuwa yanda zaka tsaftaceta, saida ya fad'a mana, dan haka wannan cikin kar ya sa ki cuceni ko ki cuci kan ki, kin ji Hafsat." Da kai ta msa alamar to, tana kallo ya cire mata kayan duk ya d'aure mata jiyoyin jikinta da k'aramin tambihinshi, hannunta ya ja zuwa ban d'akin ya shiga wankaceta soso da sabulu, saida ya gama mata suka fito, duk da d'akinshi ne amma a nan ya samu rigar baccinta ya saka mata, kwantar da ita yayi ya kalli fuskarta yace "Kiyi bacci kin ji, kin wuni ba kya jin dad'i yau hakan yasa na kai ki wajen Hajia, gashi alamu sun nuna a can ma baki samu hutu ba." Murmushi tayi tace "To, kai fa?" Murmushi yayi shi ma yace "Zan kwanta, amma zan fara dubo yaran nan na gani." Jinjina masa kai tayi ta bishi da kallo cikin doguwar farar rigarshi har ya fice a d'akin. *Maryam* Dake jiya saida Bello yasa yaran gidan suka cika musu kaf mazubin ruwa dake gidan yasa yau bata tsaya jiran ruwa ba, wanka kawai tayi ta shirya dan tafiya makaranta, fitowa tayi cikin hijabinta fari k'ar har k'asa rumgume da Alqur'aninta a k'irji, zaune tayi a kan tarmi tana kallon k'annanta dake cin d'umamen tuwo, yatsina fuska tayi tana ayyana ba zata iya cin shi ba, ta d'auko kud'in da mijin Maimuna ya bata Alhaji *Saminu*, idan ta je makaranta ta samu ko alala ta ci, fitowar mahaifinsu daga d'akin yasa ta saurin sauka daga turmin ta durk'usa kan ta a k'asa, saida ya tsaya gabanta cikin ladabi tace "Abba ina kwana." Da fuska a washe ya amsa da "Lafiya lau Maryam, har an shirya?" Jinjina kai tayi tace "Eh Abba." Kallon su Amir yayi dake cin abinci yace "Ku hanzarta to karku tsayar da ita." D'an satar kallonshi Maryam ta yi a ran ta tana fad'in "Su ba yara ba ace sai na jera tare da su mun tafi?" "Maryam." Mahaifinta ya kira sunanta, da sauri ta d'ago tana zuba mishi idonta, masha Allah, daga mahaifiyarya zuwa mahaifinta har k'annanta duk hallitarsu iri d'aya ce, dan kuwa mahaifiyarta ma har tafi mahaifin tsayi, dan shi ba zai wuce gwiwar Maryam d'in ba, k'annanta ma haka suke can cikin k'asa a haka kuma mai bi mata shekararshi goma sha hud'u, hakan yasa take matuk'ar kunyar tsayawa a tsaye idan iyayenta na tsaye, tana jin nauyinsu sosai da girmama halittarsu, shi ya sa bata iya tsayawa idan ba a hali na tafiya take ba. Cikin dattako *malam Adam* yace "Ku kula kinji, Allah ya tsare." Jinjina kai tayi tace "To Abba, ameen." Kallon mahaifiyarsu yayi yace " *Rabi'a* zan fita, da wani abu ne?" Shiru tayi kan ta a k'asa tana mai jin kunyar fad'a masa ba su da abinda zasu sarrafa da rana su ci, kunyar yaran yasa ta kasa yin maganar, lura da yayi yasa shi komawa d'akinsu, mik'ewa tayi ta bi bayanshi hakan yasa Maryam bin su da ido, saida suka b'acewa ganinta ta kalli k'annan nata, harara ta zabga musu tace "Wai sai yaushe zaku gama cin tuwon ne ku kuma? Sam ba kwa gajiya da had'iyar tuwo." Tsaki tayi ta mik'e tsaye tana ci gaba da kallonsu, cikin sauri suka shiga turawa dan kar ta fara d'imarsu da k'ulli, suna kammalawa suka mik'e suka wanke hannayensu suka sha ruwa, daidai nan suka fito daga d'akin y'a nufi k'ofa uwar da duka yaran suka bishi da addu'a, yana fita suma suka bi bayanshi suka fita, suna gaba tana baya tana takonta a hankali a haka har suka k'arasa makarantar dake bayan gidansu. *Asibiti* Saida suka gama gaisawa ya samu kujera ya zauna yana kallon Ashraf dake zaune yana kurb'an shayi, murmushi suka sakarwa juna inda sheikh yace "Ya jikin na ka?" Lumshe ido yayi yace "Jiki da sauk'i, ina so ma su sallami idan zai yiwu." D'an hararenshi yayi yace "Gaggawar me kake? Wani abu kake shiryawa ne?" Dariya Hajia tayi tace "Tambayeshi dai, ya manta jiya a some muka kawoshi nan." Yanda ya tsareshi da k'ananan idonshi yasa Ashraf cewa "Shekh ka fahimta mana, zaman a nan babu abin da zai k'ara min ko ya rage min, na ji sauk'i kawai su sallame ni." Rantsatsen rigarshi mai kama da alkyabba irin ta sarakuna ya d'an jawo daga gaba yana ci gaba da kallonshi, sanin ba zaiyi magana yasa Ashraf cewa "Wato kafi son nayi ta zama a nan ko? Saboda baka so na dinga zuwa gidanka ina damunka." Murmushi yayi cikin taushin murya yace "Da zasu rik'e min kai d'in ai da naji dad'i, dan na gaji da zaryar da kake min a gida kullum." Dariya Hajia da Ashraf suka yi inda ya kalleshi yace "To ba ga irinta ba, ni kam da zaka saka baki a sallameni, na rantse maka sai nayi budurwa gobe goben nan." D'aga girarshi d'aya yayi kamar wani gogaggen d'an duniya tare da murmushin gefen labb'a yace "Da gaske?" Saida ya had'e fuska yace "Ka sa a sallameni ka gani." Cikin dariya Hajia tace "Sheikh kasa baki to, idan haka ta faru ai zan fi kowa farin ciki, watak'ila Allah ya dubeshi ya bashi lafiya sanadiyar auren." Wata tattausar ajiyar zuciya ya sauke yana ci gaba da kallon Ashraf, d'an murmusawa yayi yace "Shikenan, amma idan sun ce da wata matsala ba zan takurasu ba." Babu wanda yace wani abu har ya mik'e yana gyara babbar rigarshi ya fita, ya d'an jima kafin ya dawo musu da takardar sallama, Ashraf na murnar zai tafi gida sheikh na mishi dariya da fad'in "Kamar wanda ya aje mata hud'u." Shi ma dariya yayi yace "Mata hud'u fa? Ai ni ra'ayina na yin mace d'aya ne, kuma ma me ya aikeni karambanin yinace hud'u? Bayan kai ma da ke ustazu d'aya gareka." Wani k'ayataccen murmushi yayi yace "Ni ma ina nan ina nema, zan k'ara ne ai dan samun wannan tagomashin na masu mata sama da d'aya." Da zolaya Ashraf yace "Kenan tare za muyi auren?" Sake d'aga masa gira yayi wanda hakan ya zama jikinshi yace "Watak'ila." Turo baki yayi yana hararenshi yace "Lallai ma sheikh d'in nan, wato zaka wa 'yar uwata kishiya kuma shi ne kake fad'a ma a gabana." Wani murmushi yayi ya juya ya kalli Hajia dake ta had'a kayansu dan tafiya bata kula da su ba yace "Na fad'a a gaban Hajia ma bare kuma kai." Hajia ce tace "Ni ai murna zanyi da faruwar haka, tunda arzik'i ne zai ci uban na da." Dariya sukayi sai sheikh daya sake sunkuyar da kai dan bai d'auka tana jin su ba, suna had'a kayan suka fito da sauri masu tsaronshi su biyu suka karb'i kayan hannunshi wanda ya karb'a a hannun Hajia, dake a mota biyu suka fito yau dan wajen aikinshi zai tafi yasa d'aya motar masu tsaronshi ne d'ayar kuma shi da su Ashraf da Hajia har suka isa gida, sai dai bai shiga ciki ba saboda lokaci ya tafi sosai. *Maryam* Hutun minti talatin aka fito dan mai buk'ata yayi buk'atarsa, a cikin ajin suke zaune tare da k'awayenta suna ta hira inda wasu ke cin abinci, ita ma robar alala ce gabanta inda Asma'u ke kallonta da mamaki dan bata d'auka zata iya cinye wanda ta siyo ba, saida ta ga ta ida ta d'auki ledar pure water ta tsotse ta jefar Asma'u tace "Masha'Allah, lallai yau na tabbatar Mimi ba matar k'aramin mutum bace ke." Harara ta wurga mata tace "Ban gane ba, me ya faru?" Saida ta kalli robar ta kalleta tace "Alalar dala arba'in fa kika cinye ke kad'ai." Tsaki tayi ta sake hararenta tace "Miye a ciki? Kud'inki ne ko nawa?" Girgiza kai tayi tace "A'a naki ne, Allah baki hak'uri." Tab'e baki tayi ta kalli wacce ke kusanta tare da zura mata hannu tace "In ga wayarki Jamila na tura vid茅os." Wayar ta mik'o mata tana fad'in "Ban da sababin vid茅os fa har yanzu, na wa'azi ne kawai aka turo min jiya." Saida ta fara dubawa kafin ta kalleta tace "Wai duk wa'azin shi ne kika turo?" Da murmushi tace "Eh, yana birgeni wallahi saboda ya iya wa'azi." Tab'e baki tayi tace "Shi ne ke birgeki? Ko kuma wa'azinshi? Ko kuma ilimin da Allah ya bashi?" Cikin rashin damuwa tace "Duka ma wallahi." Dariya 'yan matan suka saka inda Asma'u tace "Da alama dai Jamila da sheikh Abdul Waheed zai ce yana sonki da gudu zaki auresa." Da sauri ta kalleta tana dariya tace "Wallahi tsaf kuwa, ai ko bai fad'a ba da zan ganshi ido da ido ma ni saina rok'eshi ya aureni." Da mamaki Maryam ta kalleta tana nuna wayar tace " *Tsohon*? A hakan ma ke zaki rok'esa?" D'auke kanta tayi tace "Tabb'! Lallai da kin wulak'antamu." Jamila ce ta turo baki tace "Wallahi b芒 tsoho bane, dubeshi da kyau fa." Tab'e baki tayi tace "Na gani, amma akwai wa'azin da yayi yake bayanin wani abu daya faru, a lokacin ya ce yana da shekara ashirin da shida, ni kuma Abba na ya fad'a min yana neman auren mamana aka yi wannan al'amarin, a lokacin shi yana ashirin da shida shi ma, hakan na nufin shekarunsa *arba'in da bakwai* fa, kinga kenan tsoho ne tunda sa'an babana ne." Dariya sukayi sai wata dake kusa da Asma'u tace "Gaskiya indai hakane tsoho, fuskarshi ce dai bata cika nunawa ba." Asma'u kam cewa tayi "To ko ni dai da zai aureni wallahi zan amince, tunda yana da ilimi." Maryam kam tab'e baki ta sake yi tace "Allah ya rabani na rasa wa zan aura sai sa'an babana." Jefawa Jamila wayarta tayi ta mik'e zata fita dan wanke hannu tana fad'in "Wannan ai lalata k'uruciyarku kuke son yi." K'arar da wayarta tayi yasa Asma'u d'auka tana dubawa tace "Mimi Mas'ud ne ke kiranki." Shiru ta mata saida ta wanke hannayen ta dawo ta zauna ta karb'i wayar, datse kiran tayi tare da kashe wayar gaba d'aya, Asma'u dake kallonta tace "Me yasa kika kashe?" Kallonta tayi tace "Shi mahaukacin ina ne da zai kirani yanzu bayan yasan ina makaranta." Jamila ce tace "Watak'ila dan yaga lokacin hutu ne, wallahi ya damu dake mutumin nan Mimi." Banza tayi da su hakan yasa Asma'u cewa "An tab'o mata hirar data tsana a duniya, kuyi harkar gabanku kawai." Tab'e baki Maryam tayi tace "Da dai yafi kam." Wata hirar aka shiga saidai Asma'u kam ta damu sosai da abinda Maryam d'in ta fad'a mata cewa Alhaji Saminu ya bata kud'i, dan haka hankalin kowa na tafiya wani wurin ta sake gyara zamanta tace "Mimi, me yasa da Alhaji Saminu ya baki kud'in nan kika karb'a? Ba kya jin tsoro ke?" Kallonta tayi tace "Tsoro kuma? Na me?" D'an numfashi ta sauke sai kuma tace "Idan fa yace yana son ki?" Wata dariya ta kece da ita har da d'an bubbuga table d'in kafin ta tsagaita ta kalleta tace "Ya ce yana so na? To sai me? A gaban idonsa zan fad'a masa ba zan iya aurensa." Ba tare data d'auke idonta daga kanta ba tace "Me yasa? Amma naga mutumin kirki ne." Wawan tsaki taja tace "Ke yanzu dan ina mahaukaciya sai na yi soyayya da Saminu? Bayan kasancewarshi tsoho fa kin ganshi k'ato da shi, me zanyi da shi ni kam." Murya k'asa k'asa tace "To indai hakane ki daina karb'ar komai daga hannunshi dan Allah, ni wallahi tun rannan da muka je gidan naga ya cika kallonki da yawan kiranki na ji ina zargin akwai abinda yake nufi a kan ki." Yatsina fuska tayi tace "Wannan shi ya shafa wallahi, ni ko a jikina." Jin an busa usur d'in dake nuna lokaci ya k'are kowa ya shiga aji yasa Mimi sassauta murya tace "Malam yace da yamma wajen walimar sabka zamu tafi, da uniforme zamu je ko kayan gida?" Ita saida ta sassauta murya tace "Bari a tashi sai mu tambaya mu ji." Shigowar malamin yasa akayi shiru babu mai magana sai mayar da hankali a kan shi da kowa yayi, inda duk wani mai waya tuni ya kasheta dan an hana zuwa da ita, masu taurin kai ne ke tahowar da ita. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:50 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *4* A marairaice ya kalli Hajia yace "Dan Allah Hajia ki barni na fita, wallahi na fi jin dad'i idan ina waje." Ita ma a marairaice tace "Ashraf ba wai na hanaka fita bane, ka jira jikinka ya k'ara sauk'i mana." Kamar zaiyi kuka yace "Hajia na ji sauk'i fa, ba abinda nake ji a jikina yanzu." Da alamar tuhuma tace "Ka tabbatar?" Cike da tabbaci yace "Na tabbata Hajia, insha'Allah babu abinda zai faru ki kwantar da hankalinki." Jinjina kai tayi tace "Ashraf burina d'aya ne a duniyar nan naga ka samu lafiya, ciwon cikin nan naka yana d'aga min hankali fiye da tunaninka." Murmushi ya mata yace "Kenan Hajia baki da burin ganin nayi aure?" Turo baki tayi tana dukanshi a kafad'a tace "Dan na ga kayi auren har 'yan mata na dinga lissafa maka dake cikin ahalin nan, amma ka rufe ido ka nuna baka so basu ma ka ba." Jujjuyar da kan shi yayi yace "Hajia ai duk cikinsu ne babu wacce ta dace da kalar tsarina." Baki sake da mamaki tace "Iyeh! Wato har wata kalar tsarinka kake fad'a? To fad'i na ji ko zan iya samo maka." Dariya yayi ya gyara zamanshi yace "Hajia ni wayayya nake so mai ilimi, 'yar zamani da kuma tsafta wacce ta iya kwalliya, sannan wacce zata dinga kwantar min da hankali." Rik'e hab'a tayi tace "Ashraf matar sakawa a gaban mota kake nema?" Tintsirewa yayi da dariya ya mik'e ya fita har da d'an gudunshi har ya bar gidan a galleliyar motarshi. *Sheikh* A hankali yake juya kujerar kanshi na kallon sama amma idonshi rufe, hannunshi rik'e da katin gayyatar da aka kawo masa daga wata islamiyya da zasuyi sabkar Alqur'ani mai girma, jefi jefi ya kan sauke ajiyar zuciya saboda tunanin da zuciyarshi ke bijiro masa, dan gaskiya yana matuk'ar son ganin ya k'ara aure, ba dan Hafsat ta gaza ba ko baya jin dad'in zama da ita, kwad'ayin ladar da zai samu yake, yana son ganin shi ma kimarshi ta k'aru fiye da ta mai mace d'aya. Saidai abinda ke hanashi bai wuce tunanin 'yan matan yanzu ba, yaran da ko iyayen da suka haifesu basa iya tank'warasu, yaran da idonsu a tsaye a kai saman kai suke nuna maka baka waye ba, yaran da basa da hak'uri da juriya, yaran da waya da k'awaye suka fi komai mahimmanci a garesu, hakan yasa yake d'an dakatawa wasu lokutan, saidai kamar yanda yanzun zuciyarshi ke raya masa kawai zai rufe ido ne ya je ya nemi alfarmar malamin kan ya duba masa yarinyar daya yarda da tarbiyarta da nagartar iyayenta, idan ya masa haka shi da kan shi zaiyi yak'in neman k'uri'ar aurenta. A hankali ya bud'e idonshi tare da d'ora yatsanshi a kan kybord d'in na'urar ya turawa sakataranshi sak'on ya amince da gayyatar kuma zai je da kan shi da misalin 04:30 na yamma. *Maryam* 12:00 cif na rana suka taso, a hanya ma dai hirarsu bata fahimtar juna bace tsakaninta da Asma'u, dan akwai banbanci ra'ayi sosai a tattare dasu, tana cikin b'acin ran da Asma'un ta k'unsa mata a kan maganar wani saurayi da ita har ta manta da lamarinshi ma wai ta ci kud'inshi dayawa, bata tsoron ya k'i yafe mata? Shi ne fa ta hau take ta masifa take fad'in "Ai bani na ce ya so ni ba, kuma ni ban tab'a bud'a baki nace a bani ba saidai kai ne ka d'auka ka min." Mas'ud suka tsinkaya a kan dallelen mashin d'inshi yana danna wayarshi, wani uban tsaki ta kuma ja tace "Shi kuma me yake mana a k'ofar gida?" K'wafa tayi hakan yasa Asma'u cewa "Sai ma kin tambaya? Wurinki ya zo mana." Tab'e baki tayi tace "Duk da dama ina son ganinshi, amma ba zan ganshi yanzun ba, dan ni ba'a min haka wallahi." Rab'a Asma'u tayi zata giftata ta wuce tayi saurin rik'e hannunta tace "Ina zaki tafi Mimi? Karki masa haka mana." Tsaki ta kuma yi tace "Ke sake ni, shigewa zanyi na barsa mana." Da mamaki tace "Amma kinsan wurinki ya zo ko?" Fizge hannunta tayi tare da wucewa da sauri ta barta tsaye tana mamakinta, ai kam ko kallon kusurwar da yake ba tayi ba ta shige cikin gidan tana mitar ita zai wa dirar mikiya kamar wani ubanta? Shigewarta kawai ya gani hakan yasa shi tsayawa sagale da baki yana kallonta, saida ya tabbatar ita ce dai kafin ya d'an d'auke kan shi yana basarwa, kad'an daga aikin Mimi kenan, ya rasa gane wane irin so yake mata da har yake iya shanye komai daga gareta haka, ta masa wulak'anci ta ja masa aji ta yarfa shi fiye da kima, amma ya jure ya nace saboda tunanin ta kusa zama tashi, lokaci kad'an ya rage shi ma ya fara nashi salon mulkin, duk da dai ya tabbatar ba zai iya muzguna mata ba, amma saiya rama ko da na kwana d'aya ne dan taji idan da dad'i. Shi yasa baya nuna bai ji dad'i ba idan ta b'ata masa, ko ba komai Mimi ta yi, ta had'u iya haduwa da kowane namiji zai so samunta a matsayin ta shi, ga ta da wani siddabarun saurin dukan k'irjin namiji, indai kana da rai da lafiya sannan tsufanka bai kai k'adamin da baka sha'awar mace ba, to idan kaga Mimi zuciyarka zata amsa ma ka saidai kayi shiru da bakinka kawai, ba wai tsananin kyan da take d'auke dashi bane a'a, wata irin halitta ce da ita da kuma yanayin dake saurin d'ad'a namiji a k'asa warwas. Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi yana mai jinjina lamarin ubangiji, wai yarinyar data fito daga gidan nan na k'asa, sannan ta fito daga tsatson wadanni har take yagawa mutane rigar mutumcinsu? Lambarta ya shiga kira amma sam ta k'i d'agawa dan a lokacin ma wanka ta shiga yi. Tana fitowa ta saka riga da siket na atamfa ta feso turare kafin ta d'auki gyale ta yafa ta d'auko wayar ta cire layinta da card ta fito, a farfajiyar gida ta samu mamanta zaune ta zuba tagumi, tana kallonta tace "Mama lafiya?" D'agowa tayi ta girgiza kai tace "Ba komai, ina kuma zaki je?" Yatsina fuska tayi tace "K'ofar gida, Mas'ud ne a waje." Jinjina kai kawai ta yi ita kuma ta fita, cikin takonta mai birgewa ta k'araso ta tsaya tare da d'ora hannunta akan hannun mashin d'in ta juya mishi baya, kakkauran hannunta ya kalla wanda ya tabbatar zai yi matuk'ar kyau da awarwaron zinare kafin ya kalli k'eyarta yace "Ko dan sarauniyata tafi kowa sanin hushinta shi ne silar shiga damuwa shi ya sa take son tsokano damuwata?" Ba tare data juyo ba tace "Idan gaske ne me yasa kai ma za kayi abinda kasan baya daga cikin tsarina?" Murmushi yayi mai sauti yace "Na d'auki laifina da hannu biyu, a gafarceni ba zan k'ara ba, dama na zo ne saboda tun jiya nake kiranki, amma Mimi kin k'i d'aga min waya ban san me yasa ba? Shi ya sa na zo saboda ina da muhimmiyar magana da ke." A hankali ta juyo ba tare data d'auke hannunta ba tace "Wace irin magana kuma?" Leb'enta ya bi da kallo wanda bata shafawa komai ba, hakan yasa na k'asa tsayawa a kalar pink d'inshi sosai na sama kuma bak'i dashi, saidai na k'asa ya fi na sama girma da d'an tsayi daidai da fuskarta, numfasawa yayi yace "Dama akan maganar aurenmu ne..." Da sauri ta katseshi tace "Aurenmu? Aka ce me?" D'an zaro ido yayi yana mata murmushi yace "Mimi ko dai kema kin matsu?" Yatsina fuska tayi tace "Ina jinka." D'orawa yayi da cewa "Dama jiya malam sun had'u da Alhaji a wajen karatu, shi ne suka tsayar da ranar da za'a kawo kaya a saka mana rana, nasan malam ba zai fad'a miki ba sabida ke 'yar fari ce shi yasa na zo na sanar dake." Wani galala tayi ta bud'e idonta da kyau tace "Na ji dad'i daka fad'a min, dan kaga da sunyi kuskure." Da mamaki yace "Kuskure kuma? Na me?" Ba tare da damuwa ko d'aya ba tace "Kuskuren aurar dani mana ban shirya ba." Da wani sabon mamakin yace "Baki shirya ba kuma? Mimi sai yaushe zaki shirya?" Gyara tsayuwarta tayi ta mik'o masa wayar hannunta tace "Ga wayarka, kayi hak'uri Mas'ud a gaskiya ban tashi aure ba yanzu, idan ma na tashi ba zanyi da kai ba saboda wasu dalilai." Girgiza masa kai ta sake yi tace "Kayi hak'uri, Allah ya baka wacce ta fini." Da sauri ya shiga kakkarwa zai sauko daga mashin d'in kamar zai kifa ya fad'i, idonshi da suka rine sukayi ja ya shiga lumshewa yana fad'in "A'a Mimi! Mimi dan Allah tsaya kiji, Mimi..." Da sauri ya sha gabanta tare da durk'ushewa yana kallonta hawaye na sauka a idonshi yace "Mimi me na miki? Fad'a min wallahi zan gyara, bana so na rasaki Mimi ke ce rayuwata, dan Allah kiyi hak'uri kinji, wallahi idan ma auren ne ba kya so na janye, zan jiraki Mimi har sanda kike so sai ayi." Girgiza kai tayi tace "Mas'ud ka gane wani abu, idan muka ci gaba a haka zan yaudareka ne, shi fa aure ana ginashi ne da soyayya, ni kuma har yanzu bana jin sonka a cikin zuciyata." Tsam yayi tare da mik'ewa tsaye yana kallonta yace "Ba kya so na? To Mimi watannin da muka share muna soyayya fa? Duk murmushi da kalaman da kika min fa? Dan Allah Mimi ki ce wasa kike min." Idonshi ta kalla tace "Kayi hak'uri, dama gudun kar na wulak'anta ka yasa tun farko ban fad'a maka ba, yanzu ma nasan zaka d'auka yaudararka nayi, amma ba haka bane gaskiya ce na fad'a maka." Da mamaki ya girgiza kai ya juya ya kalli yanda idon mutanen dake kai kawo duk idonsu a kan su, sake kallonta yayi yana ci gaba da girgiza ai yace "Wulak'anci? Ai kin riga da kin gama wulak'antani, Mimi ki fad'a min wani dalilin da yasa kika guje ni, idan ba haka ba zan zargeki da cin amanata." Ajiyar zuciya ta sauke ta sake kallon fuskarshi tace "A gaskiya bana sonka ne." Rab'ashi tayi ta wuce tana fad'in "Kayi hak'uri." Juyawa yayi ya bita da kallo harta shige, ji yayi wasu hawayen sun sake taho mishi, d'an tsaki yayi na jin haushin kan sa, ji yayi kamar ya d'auki takalminshi ya jefa cikin gidansu, amma zuciyarshi sai b'ari take ga zazzab'in da yake jin zai rufe shi, haka ya juya yana saka wayar a aljihu ya hau mashin d'inshi y'a bar unguwar. Tana shiga ta kusa da mamanta ta zauna tana fad'in "... Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa. Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai. Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa. _Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._ _'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_ Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:50 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *5* Tana shiga kusa da mamanta ta zauna tana fad'in "Mama lafiya? Ya naga baki d'ora girki ba har yanzu?" Kallonta tayi tana sauke ajiyar zuciya, juyawa tayi ta kalli su Yaseen dake duba littafinsu suna karatu, girgiza mata kai tayi tace "Ba komai Mimi, zan d'ora yanzu." Da alamar tuhuma ta kalleta tace "Mama, ko dai babu abinda za'a dafa ne?" Da sauri ta kalleta sai kuma ta sunkuyar da kan ta, cikin k'aguwa Mimi tace "Mama ki min magana mana, idan baki fad'a min damuwarki ba wa zaki fad'a ma?" Kallonta ta sake yi a hankali tace "Hakane, Mimi ba tunani na abin da zamu ci yanzu bane, tunanin yanda zamuyi da dare nake, har malam ya bar gidan nan babu tabbacin zai samo mana wani abu, saidai abu na ubangiji kawai." K'ura mata ido tayi tana kallo, dafa kafad'arta tayi tace "Amma mama shi ne ba zaki fad'a min ba, har yanzu ina da canji a hannu na na kud'in da Mas'ud ya bani a ranar dana siyi kayan makaranta, bari na d'auko." Da kallo ta bita har ta shige d'akin, jim kad'an ta fito ta tsuguna gabanta ta nuna mata jaka guda tace "Kin gani mama, yanzu me za'a siyo sai naje da kaina." Girgiza mata kai tayi tace "A'a Mimi ba sai kinje da kan ki ba, kawo sai na ba Yaseen ya je." Ita ma girgiza kai tayi tace "A'a mama zan je, kinsan aikensu yanzu ba zasu dawo da wuri ba." Jinjina kai tayi alamar gamsuwa, dan haka tace "Mimi ko garin tuwo babu shi bare shinkafa, ki siyo mana wani abun da zamu iya sarrafawa da wuri kafin lokacin tafiyarku islamiyya." Jinjina kai tayi ta mik'e tace "To mama, bari na siyo mana ko ledar macca guda biyu." Bata jira me zata fad'a ba ta koma d'akin ta d'auko hijab ta saka ta fita, gungun yan matan unguwarsu ta wuce suna zaune a kan dakali suna hira, babu wacce ta kalla a ciki bare ta musu ko da sannu, hakan yasa suka kafa dandalin yi da ita dan dama haushinta dayawa ke ji. Tana zuwa ta siyo abinda tasan zasu buk'ata ta juyo ta dawo, tana kawowa daidai su suka bushe da dariya har da tapa hannu zabayar ciki na fad'in "Sarauniyar kuri, ji da kai da nuna isa, ka ganta a hanya tsabal tsabal gidansu kamar rudun tamtabaru." Cak ta tsaya tare da juyowa ta kallesu, gyara tsayuwa tayi ta tofar da yawu ta bisu da harara tace "Idan mutum ya na da k'arancin abun yi dama ya kan zama mai neman fitina, ni kuma a halin da nake ciki yanzu ban da lokacin masu abun yi ba bare marasa shi." Yatsina fuska tayi tare da takawa zata wuce, tsaki wata tayi tace "K'aryar banza da wofi, da bamu san asalin balbela bane da sai tace mana daga masar take." Wata ce tayi saurin cewa "Dan kawai Allah bai miki hallita irin ta iyayenki ba, shikenan kin d'auki girman kai da raina mutane kin d'ora a kan ki, sai ka ce wata 'yar shugaban k'asa." Sama da k'asa ta juyo ta hararesu taja dogon tsaki ta wuce ta barsu, hakan kuma zafi ya musu sosai dan sun so ta kulasu yanda zasu k'addamar da abinda suka tsara mata, da dukan tsiya zasu mata su mata baja-baja sai fatar nan ta canza kala, dan su har yau sun rasa gano dalilin da yasa fatar jikinta da surarta suka zama kala daban, idan ka dubi Mimi da gidansu da iyayenta, dole ka tuna da ayar da Allah mad'aukakin sarki yace *ya na fitar da duhu a cikin rana, kuma yana fitar da rana a cikin duhu, sannan yana fitar da rayayye a jikin matacce, kuma yana fitar da matacce a jikin rayayye, sannan yana azurta wanda ya so ba tare da hisabi ba*. *Sheikh* Tagumi ya buga yana kallonta yanda take ta cika mishi plate d'in gabanshi wanda tasan ba zai iya cinye abincin ciki ba, saidai har k'asan ranshi dad'i yake ji yanda Hafsat bata wasa da abincin shi, tunda ya aureta shi dai yayi hannu riga da yunwa, saidai ko baya gari amma yana gari kam yafi k'arfin nan. Zaune tayi tare da matso kujerarta kusa da shi ta d'auki cokali ta d'ebo ta nufi bakinshi, murmushi ya sakar mata tare da yin bismillah ya karb'a, sake d'ebowa tayi saiya nuna mata had'in kokombre da tayi da hannu alammar shi yafi so, yar harara ta cilla mishi ta d'ebo tana fad'in "Allah dai yayi walk'iya na ga mutum, domin kuwa nima nayi bincike na gano sirrin kokombre nan." Yar dariya yayi ya kanne mata ido d'aya yace "Kuma ai kinji dad'i da mijinki ya zama mai son kula miki da kanshi ko?" Cikin jin kunya ta sunkuyar da kan ta, d'ago hab'arta yayi yace "Bana so ki fara kallona a matsayin *tsoho*, shiyasa nake bin duk wata hanya data inganta dan na inganta miki lafiyata." Dariya tayi mai birgewa tace "Na ji dad'i, amma a baya na damu sosai da son sanin sirrin nan amma ka k'i fad'a min." Murmushi yayi yace "Ina rok'on Allah ya ma rayuwarki albarka, tunda na nuna miki ina son kokombre sosai da kabewa da kuma miyar albasa, baki tab'a gazawa ba wajen sarrafa min su, wasu lokuta abu daban kike dafawa dan ku ci, amma ni saikin d'ora min wanda na fi so." Murmushi tayi tace "To ai dan hidimarka nake zaune a gidan, idan ba zanyi ba miye anfani na?" Da sauri ya rik'o hannunta yace "Kina da, *Hassy* ko babu wannan ni zan iya zama da ke, karki manta ke fa 'yar uwata ce, mahaifinki da mahaifina ciki d'aya suka fito, kinga kuwa ko babu aure tsakaninmu zan iya rik'eki." Murmushi ta kuma yi tana sunkuyar da kan ta, karb'an cokalin yayi ya fara cin abincin yana bata ita ma yana fad'in "Ki shirya k'arshen wata zamu fita hutu insha'Allah." D'aga manyan idonta tayi ta kalleshi sai kuma tayi k'asa da idonta, ba sabon abu bane wannan kam a wurinsu, idan har kaga bai fita da ita k'arshen wata ba to baya gari ko kuma sabgogi sun mishi yawa, amma ya kan ware k'arshen wata ya d'auketa su keta hazo wani lokacina ita ke zab'ar inda zasu tafi, ba dan komai ba sai dan ita ma ta huta na kwana uku kawai ba tare da aikin gida ko kula da yara ba. Jinjina kai tayi tace "Insha'Allah, Allah ya saka da alkairi, Allah ya k'ara bud'i." Da murmushi yace "Madalla da *mata ta gari*." Da sauri ta d'ago tace "Ga *miji na gari*." A tare suka lak'aci hancin juna suna had'a baki wajen fad'in "Bisa koyarwa *addinin islama*." Cin abincinsu suka ci gaba da yi har ya kammala ya shiga dan shiryawa dan ana daf da kiran sallah la'asar ne. *Madarasatul darul tauhid* _(04:35 na yamma)_ Duk girman unguwar nan cike yake da mutane sakamakon sabkar nan, bak'i ta ko ina sun halarta bisa gayyatarsu da akayi, har yan makaranta sun zo kowane da kalar nasu uniforme, kusan makarantarsu Mimi sun zo a makare, dan ko da suka zo tuni an fara gabatar da karatu, gashi kuma ajin da aka ware dan sauke bak'i 'yan makarantar sai ta tsakiyar filin dole zasu bi su wuce. Mai kula da bak'in na ganinsu mata da fararen hijabai da siket bleue maza kuma farar hula da farar riga ya tarbesu, da 'yar bulalarshi a hannu ya shiga gaba yana bud'e musu hanya suna wucewa, ta tsakiyar filin suka bi suka wuce ta bayan babbar rufar alfarma dake d'auke da manyan bak'i. Sam Mimi bata kalli wajen ba dan daga nesa ta hango duk manya ne a wurin, daga kujerun da aka aza musu zuwa babban carpet d'in dake shinfid'e zaka gane haka. *Kamar tsautsayi* idonshi suka sauka a kan ta, kuma wani hukunci na ubangiji bai kalli kowa ba sanda kallonshi ya juyo a lokacin da 'yan makarantar ke wucewa, saida ta zo d'an nesa dashi wanda da a lokacin ta juyo zasu fuskanci juna ne ya kalleta da kyau, nutsatsiyar fuskarta ta kamala wacce babu d'igon kwalli a kai, tafiyarta ta wahainiya cikin sand'a da ladabi, hannunta jimk'e dana Asma'u suna takawa a hankali. Baisan lokacin daya furta " *Tabarakallah, masha'Allah, tabarakallah ahsanul kalik'in*." Wata nannauyan ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idonshi, a hankali ya d'ago hannunshi ya d'ora daidai zuciyarshi ya dafe sosai, wani k'ayataccen murmushi ya saki yana bud'e idonshi, a k'asan zuciyarshi ya furta "Hak'ik'a nan ya amsa da k'arfi, da fatan zaki zama *alkairi a gareni*." Mayar da hankalinshi yayi kan karatu amma ta wani b'angare tunanin yanda zai yi da sabo kuma bak'on lamarin yake, shin ya tuntub'i malamin makarantar a game da lamarinta? Ko kuma dai 'yan barandarshi kawai zai sa su nemo mishi gidansu ya gabatar da kan shi? Ko kuma dai ya fara shiga jikin yarinyar har ya fahimci *wacece* ita? Miye halayenta? Ya d'abi'arta take? Daga wane gida ta fito? Shin zata so shi ta zauna da shi? To amma ko zai san wacece ita dole sai ya fara sanin inda take rayuwa, dan haka yanzu wannan ne yafi mahimmanci a gareshi sanin *gidansu*. Sam bai samu halin da zai ci gaba da wulk'ita idonshi dan sake ganinta saboda tururuwar da jama'a sukayi a kan shi, kowa son yake su gaisa wasu daga nesa suna d'aukar hoto, da k'yar jami'anshi guda biyu da tallafawar 'yan agaji suka taimaka har ya shiga mota suka bar wurin. Tare da k'awayensu suka taho, amma sannu sannu duk suka rabu ya rage daga ita sai Asma'u kowace rik'e da ledar wainar da aka basu ta sadaka, suna karyo layin gidan taja wani birki ta tsaya tare da rik'e Asma'u suka koma baya, yanda ta zaro ido kamar an tsorata ta ne yasa Asma'u d'an juyawa sannan ta kalleta tace "Mimi lafiya? Me kika gani?" Cikin rashin gaskiya tace "Ke baki ganshi bane? D'an wahala ne fa." Da mamaki Asma'u tace "D'an wahala? Waye haka kuma?" Tsaki tayi tace "Ki gane mana, *Muttak'a* ne." Zaro ido tayi tace "Muttak'an ne d'an wahala?" Murmushi tayi tare da fad'in "Ya ci sunansa kam, dan kati ma na kud'i dayawa yake turo miki." Cikin rad'a tace "Asma'u ki bar wasa mana, bai san gidanmu ba fa, ya akayi ya zo nan?" Da alamar tuhuma tace "Idan ba ke kika fad'a masa ba ya akayi ya zo?" Hararanta tayi tace "Idan ni na fad'a masa kuma saina tambayeki?" Dafe k'ugu tayi tana feso iska a bakinta tace "Matsala kenan." Tab'e baki Asma'u tayi tace "Ke kika jawota da kan ki, duk da kin bawa Mas'ud dama ya kawo kayanki shikenan." Wata harara ta cilla mata ta jin haushi tace "Ana maganar arziki zaki sako min ta tsiya, Mas'ud d'in dana gama rufe babinshi ne zaki wani tado min zancenshi." Da maamaki tace "Ban gane kin rufe babinshi ba? Me kika masa Mimi?" Kallon idonta tayi tace "Abinda kike so mana, ba ke kika fad'a min idan nasan bana son mutum na fad'a masa gaskiya ba? To gaskiyar na fad'a masa." Girgiza kai tayi cike da jimami da rashin jin dad'i tace "Gaskiya Mimi baki kyauta ba, haba dan Allah." A k'ufule ta kalleta tace "Kinga ba wannan ba, fad'a min yanda zanyi na shiga gidanmu ba tare da mutumin can ya ganni ba?" Tab'e baki tayi tace "To shi banga aibunsa ba, ki tsayar dashi mana tunda kin kori Mas'ud." A hassale tace "Ke Mas'ud d'in banza, idan kina son shi ki fad'a min saina had'aku, shi kuma waccen lek'a kiga yanda yake mana, sam baya da tsari da iya ado wani sakarai da shi, kud'i ne Allah ya bashi amma babu aji." Da mamaki Asma'u tayi murmushi tace "Wasu ko mahaukaci ne suna so indai yana da kud'i, amma ke ko kana da kud'in sai ka iya d'aukar wanka, sannan ka zama mai k'ananan shekaru, dan na gama fahimtar kina gaba da duk wanda yake d'auke da shekaru arba'in da sama." Dariya ce ta kubce mata ta kalli Asma'u tace "Ba haka bane, ba gaba nake da masu shekarun ba tunda ubana ba shekarunsa kenan, kawai dai nasan a wannan shekarun babu abinda zan samu na soyayya a gurin mamallakinsu, mafi aksarinsu kuma zaki ga suna fama da shirgegen tunbi da nonuwa, sannan in k'ara tuna miki *sa'an babana ne*, ni kuwa me zai sa na auri sa'an babana a shekaru? Ai da kunya ma." Girgiza kai Asma'u tayi tace "Mimi ina jin tsoron ranar da zata zo kiyi nadama a kan wannan fariya da kike." Farr tayi da ido tace "Ba fariya bace." Jujjuyawa tayi da sauri ta k'arasa kusan dakalin dake k'ofar wani gida, zaune tayi tare da yaye hijabinta ta baya ta dawo dashi a gaba, Asma'u data k'araso ne tace "Ba zaki shiga gida bane?" Yatsina fuska tayi tace "Sai ya tafi." Da mamaki Asma'u tace "Mimi ko dai ba kya so yaga gidanku ne?" Da sauri ta kalleta tace "Saboda me? Ke tunda muke dake kin tab'a ji ko ganin na nunawa wani gidan da ba namu ba?" Kawar da kai tayi tace "Asma'u duk iskancina wallahi bana jin kunyar a ga gidan, hasalima alfahari nake a ga daga ina na fito, haka-zalika bana jin kunya nuna iyayena duk da zubin hallitarsu, ina son kayana a haka kuma duk wanda ya nemi raina min su wallahi zamu saka k'afar wando d'aya da mutum." Ajiyar zuciya Asma'u ta sauke tace "To in hakane ki shiga gida mana kar dare ya miki a nan." Tab'e baki tayi tace "Nasan waye Muttak'a, dan magriba ba zata sa ya bar k'ofar gidanmu ba, ni kuma haka kawai na tsani na ganshi kusa da ni." Ita ma tab'e baki tayi tace "To kinga ni tafiya zanyi, dan bana tsaya na biye miki ba har magriba ta mana a waje." K'ala ba tace mata ba sai binta da kallo tana d'an jujjuya ledar wainarta, wucewar su Yaseen yasa ta cewa "Kai ku zo nan." Da kallo ta bi gajerun k'fafunsu har suka k'araso, ledar hannunta ta mik'a musu tace "Ku kai wa mama ta ci ta baku sauran." Yaseen dake babba ne ya karb'a yace "Mimi ina kika samu waina dayawa haka? Mu fa hak'uri aka bamu aka ce bamu samu." Wani murmushin gefen labb'a tayi tare da girgiza kai, ita fa tana zaune aka biyota da wainar ma tare da Asma'u da ta ci albarkacin ta, wanda ya bata wainar abokin d'an ajinsu ne dake ikrarin wai yana son ta, kallo d'aya ta mishi ta d'auke kanta daga gareshi bata sake kulashi ba har yau, amma ko yanzu da zai ganta tsaye zata siyi pure water zaiyi tsal ne ya biya kud'i, ko da ba ita kad'ai bace yawansu ya kai dubunnai. D'an kallonsu tayi tace "Ku tafi gida." Juyawa sukayi sai kuma tace "Ku zo." Dawowa sukayi suna kallonta, cikin gargad'i ta kama kunnenta tace "Akwai wani mutum a k'ofar gida, idan ya tambayeku ina nake ku ce an rik'emu a aji muna hadda, sannan idan kun shiga gida ku fad'awa Mama na tafi duba jikin Iya Delu." Saida ta sake zaro ido tace "Kun ji ko?" Da sauri suka jinjina mata kai alamar to tare da juyawa suka wuce. *Alhamdulillah* munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa. Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai. Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa. _Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._ _'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_ Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:50 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *6* Saida ta ji kiraye kirayen sallah kad'ai ta mik'e ta sake lek'awa, ido ta zaro samakkon ganin ya fito daga motar shi yana alwala, girgiza kai tayi tace "Na shiga uku, wannan jaraba da me tayi kama? Na tabbata ya kirani baya samu ne shiyasa ya zo ya girke mana a k'ofar gida." Tana kallo ya kammala ya juya ya shiga kwanar da zata sadashi da masallaci, ai da sauri ta shiga takawa har ta k'arasa gida, tana shiga ko sallama ba tayi ba mamanta ta jefeta da harare tace "Daga ina kike?" Tsuru ta mata da ido tare da yin tsuguno saboda ita tana tsaye ne, a hankali ta kalleta tace "Mama Yaseen bai fad'a miki bane?" Cikin tsawa tace "Ke ba ruwana da shiririta, na tabbata k'arya kike dan daga yanda suka fad'a min ya tabbatar ke kika saka su fad'a." D'an sosa kan ta tayi tace "Mama ba inda naje fa, wani ne na gani a k'ofar gidan nan shiyasa ban shigo ba." Jinjina kai tayi tace "Ko da naji, Allah yasa ba wani abun kika masa ba." Girgiza kai tayi tana kallonta ta k'arasa saman tabarma ta saka hijab ta kabbara sallah, da sauri ta shiga d'aki ita ma bayan ta duk'a kafin ta shige, kayan ta canza a gaggauce ta fito tayi alwala ta kabbara sallah. Tana idawa bata tsaya yin azkhar d'inta ba ta mik'e da saurita saka takalmi zata fita dan ta samu ya bar k'ofar gidan nan, tana juyawa suka kwatse da mahaifinta yana binta da kallo. Da sauri ta duk'a tana fad'in "Abba gaisuwa." Saida ya k'araso yana gyara carbinshi a hannu cikin fad'a yace "Mimi waye a waje yake nemanki? Wanene shi da ban san shi ba?" Sunkuyar da kai ta sake yi tayi shiru, a zabure yayo kan ta yana sake fad'in "Ba dake nake magana ba? Mimi naga nema kike ki fi k'arfina ko? Kullum da kalar da zai zo nemanki gidanki." Daga tsugunnon ta ja baya tana fad'in "Abba kayi hak'uri, wallahi ba ni na fad'a masa gidanmu ba, bansan zai zo ba." A hassale yace "To ki je ki fad'a masa ya bar nan, kuma ya fita a sabgarki dan ni da mahaifin yaron nan mun tsayar da magana za'a saka muku rana." Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi sai kuma ta sauke idonta k'asa, jinjina kai tayi alamar to tare da mik'ewa jiki a sanyaye ta fita, da wayarshi a hannu yana dannawa ko da ya ganta ya sauke ajiyar zuciya, shi sam ba wai gidansu ko ganin mahaifinta bane ya dameshi, hasalima ba wannan ne a ganshi ba, ita d'in dai ita yake so kuma ya ji ya gani zai iya. Murmushi ya sakar mata yana fad'in "Mimi dama zan iya ganinki? Ai har na cire rai da zan tafi." Fuskarta a had'e ba alamar wasa tace "Me ya kawoka nan? Wa y'a fad'a maka gidanmu?" Murmushi ya sake yi ya rufe motar ya gyara tsayuwarshi yace "Tunda na turo miki kati jiya ina ta kiranki ba kya d'agawa, yau ma tun safe nake kiranki Mimi amma shiru, shiyasa na nemi gidanku aka fad'a min, dan dama na fad'a miki ni aurenki nake so nayi." Waina idonta tayi tare da sauke ajiyar zuciya tace "Kaga, dan Allah kayi gaggawar barin nan, kaga mahaifina bai sanka ba kuma sam bai ji dad'i ba, haka nima ban ji dad'in wannan ziyarar bazatan ba." Cikin rashin jin dad'i yace "Kiyi hak'uri kinji Mimi, wallahi na damu ne sosai shi ya sa, zan tafi amma ki d'auki wayarki zan kiraki." Cikin k'aguwa tace "Bana da waya yanzu, ta fad'i." Wani murmushi ya saki yace "Haba Mimi, yanzu dan wayarki ta fad'i har zaki yarda ki kwana babu waya a hannunki." Nuna mata wayarshi yayi yace "Wannan ta miki?" Kallon wayar tayi a tafin hannunshi, saida taji wani murmushi zai sub'uce mata, a ranta ta ambaci "IPhone." A zahiri kuma d'aure fuska tayi tace "Ta ya zan karb'i wayar hannunka? Bana so gaskiya." Murmushi yayi yace "Shikenan, yanzu fad'a min ina zamu had'u zuwa gobe da safe saina kawo miki wata." Kallonshi ta yi tana tunanin abun yi, ko ba komai ai zata iya siyarwa, idan kuma iPhone ya siya mata ta samu ta d'aukar kan ta selfie da vid茅o, bugu da k'ari duk k'awayenta idan aka cire *Salma* bbu mai iPhone, ita ma dan zata auri mai kud'i ne. Nulfasawa tayi tace "Zuwa goben na kiraka na fad'a maka." Juyawa tayi tana fad'in "Sai anjima." Shigewa tayi ya bita da kallo yana murmushi, a ranshi ya furta "Allah kai damo ga harawa." Saida ya soka wayar aljihu kafin ya shige motar ya bar k'ofar gidan. *Litini* Kasancewar yau zai shiga ofishin gwamnati ne yasa shi fita kan lokaci saboda bin dokar aikin da yake yi dan al'umma, saida ya fara biyawa ya ga jikin Ashraf kafin ya wuce, cikin ikon Allah kam yana zuwa aiyuka ya samu tari guda a gabansa da kuma bak'in daya bawa lokacin da zasu zo ganinshi, haka ma akwai wanda suka zo da fatan samun lokacinshi ko da ba yau d'in ba. Kaf wayoyinshi kashesu yayi idan ka cire fax d'in dake ofishin da kuma k'aramar samsung d'in da duk wani daya shafi aikinsa zai iya kiranshi ko sak'o. Sauri yake ya kammala ko ya samu damar barin ofishin da wuri, so yake ya yi yak'in da kan shi ta hanyar neman gidansu, amma abun ka ga babba sai ya zamana yana aiki ne kuma yana karb'ar bak'untar wasu manyan bak'in da sun fi k'arfin a sharesu, wasu kuma tausayinshi da karrama d'an adam ke saka shi tsayawa sauraren kokensu. Madadin sauka k'arfe 01:00 na hutu sai gashi har k'arfe 01:16 sannan ya tsaya cin abinci, yana tsaka da cin abincin sakataranshi ya shigo dan a lokacin waya ma ana yanke sadarwarta ne dan bashi damar hutawar yana fad'in "Yallab'ai, kayi bak'o." Lumshe ido yayi yana feso iska a bakinshi, bud'e ido yayi ya kalleshi yace "Waye?" Cikin ladabi yace "Ya ce a fad'a maka Muttak'a ne, wanda kukayi magana a kan passepord d'in nan." Da sauri ya kalleshi yace "Oho! Shigo da shi dan Allah." D'aga kai yayi alamar to tare da juyawa ya fita, aje d'an take away d'in yayi ya d'auki tissue yana goge jajayen leb'unansa, jim kad'an ya shigo da sallama yana fara'a, da ladabi kamar zai sunkuya ya shiga gaishe shi yana amsawa shi ma da fara'a, cikin fara'a sheikh yace "Ina so ne nasan tsarin fitar da marar lafiya a station d'in ku?" Da fara'a shi ma yace "Sheikh ai ba wani matsala bane, ana had'a visarshi ne tare da takardar shaidar rashin lafiyarsa da kuma asibitin da zai je gani, idan ciwon yayi k'amari da baya iya tafiya, ana iya tanadar masa wurin zama a vip, kamar yanzu ga mai buk'ata yana biyan kud'in vip ne, sannan zamu so sanin kalar rashin lafiyar, idan wacce bata da tsanani ne zata iya tafiya da yanayin jirginmu, awwanin da za'a d'auka a wajen tafiyar da kuma yanayin da marar lafiyar zai shiga idan jirgin ya tashi, idan akwai wata barazana dan mu sani da wuri mu kuma d'auki mataki." Ajiyar zuciya sheikh ya sauke yace "Nagode sosai, insha'Allah zan gabatar maka da duka abinda kuke buk'ata, ko ba ni ba zan iya aikawa." Da ladabi yace "Shikenan sheikh, ina jira." Lumshe ido yayi ya bud'e yace "Masha'Allah, insha'Allah." Da haka ya mik'e ya fita ya bar shi, har zai d'auki abincin shi ya kalli agogonshi data nuna masa 01:32, da sauri ya danna madannin da zai kawo masa sakarantashi a take, wanda dama dan kiran gaggawa aka yi shi, yana shigowa ya bashi take away d'in yana fad'in "Akwai bak'i ne a waje?" Da rusunawa yace "Eh yallab'ai, akwai wasu dattawa guda biyu da suka zo tun d'azu, sai kuma professeur *Yacoub Sumana* da ya zo yanzun." Sa茂da ya kalli gabanshi yace "Ka shigo da dattawan." Jinjina kai yayi tare da ficewa a ofishin, da irin haka fa aiki ya rik'e sheikh bai yi abinda yayi niyya ba, gashi kuma dolenshi ya halarci karatun *Umdatul ahkam* da yake gabatarwa duk ranar litinin da k'arfe 07:00 zuwa 08:00 na dare. *Maryam* Tun a hanyarsu ta dawowa ta rok'i Asma'u ta mata alfarmar da zata fita daga gida, da k'yar ta yarda tace za tayi amma ba zasu jima ba, suna zaune tare da mama a farfajiyar gidan tana gyara mata alaiyahu Asma'u ta shigo da sallama, har k'asa ta duk'a ta gaishe da mama dan haka ta ga k'awarta ma na yi, da sakin fuska ta amsa mata tana tambayarta mamanta? Da murmushi tace "Lafiya lau suke, sun ce na gaisheku." Da fara'a tace "Ina amsawa." Jim tayi tana satar kallon Mimi da ta sunkuyar da kai kamar bata ganta ba, kallon mama tayi tace "Mama, dama anjima zan tafi gidan aunty *Rayya* ne na ce bari in fad'a miki ina so Mimi ta rakani." Kallonta tayi sai kuma ta kalli Mimi, d'an jinjina kai tayi ta kalli Asma'u tace "Ba zaku kai magriba ba dai ko?" Girgiza kai tayi tace "A'a mama, nima haka mama ta ce kar na kai magriba." Jinjina kai ta sake yi tace "Shikenan Asma'u, na amince kuje Allah ya tsare, ko da mahaifinta ma ya dawo ya tambaya zan fad'a masa." Da fara'a tace "To mama mun gode." Kallon Mimi tayi tace "Mimi ki shirya da anyi la'asar sai mu tafi." Gyad'a kai tayi alamar to tare da fad'in "Na ji, nima dai da ina da aunty haka zan dinga jan ki muna tafiya." Dariya Asma'u tayi tace "Sai dai idan kinyi aure su Yaseen su je gidanki, ke kam sai hak'uri." Dariya Mama tayi tana girgiza kai har Asma'u ta fita a gidan, Mimi kam farin ciki kamar zata zuba ruwa k'asa ta sha dan murna, dan haka ta dinga aikinta da sauri amma ba yanda Mamar zata gane tana gaggawa ba. Suna kammalawa saida ta share gidan tas ta wanke ban d'aki kafin ta shiga wanka ganin la'asar ta gabato, kafin ta fito aka fara kiran sallah dan haka tayi alwala ta shiga d'aki, mai ta shafa da sauri ta d'auki wata watsetsiyar doguwar rigar leshe wacce aka yi ta sak da zubin bubu, gaban rigar zuwa wuya a tamfatse yake da duwatsu, hijabi ta saka ta shara yin sallah a nutse, tana idawa mama ma ta idar ta k'ara gyara zaman hijabinta tace "Mama zan tafi, sai mun dawo." Kallonta tayi tace "Ina d'an kwalin kayan kuma?" Nuna mata k'aramar jakarta tayi tace "Gashi nan ciki, mama kinsan leshe yana da cin rai musamman lokacin zafi." Jinjina kai tayi tace "Sai kun dawo, karki manta kuma ku dawo kafin magriba." Saida ta d'auko wasu takalmi confence da suka dace da kayanta da jakar tace "To mama." Fita tayi tana sake gyara zaman Jakarta a kafad'a. Gidansu Asma'u ta shiga ta gaishe da mamanta sosai kafin ta fito suka wuce, taxi suka shiga abun mamaki Asma'u sai taji Mimi tace a kai su *nouveau marcher*, ko da taji haka tasan gidansu Salma zasu je, dan haka kawai ta biye mata suna hira dan karsu fara fad'a yanzu yanzu. A bayan kasuwar aka aje su suka k'arasa cikin gidan, kyakyawar budurwa na zaune tana cin kwad'on dambu, tana ganinsu ta mik'e da sauri ta zo ta rumgume Mimi tana fad'in "Bestyna, daga ina haka?" Da farin ciki Mimi tace "Daga gida mana." Raba jikinsu sukayi inda suka shiga gaishe da matan gidan, wanda cikin sauk'i zaka fahimci yanayin zaman, dan da alama uwar Salma ita ke buga mulki a gidan, watak'ila yanayinta ko yarenta ya jawo haka, dan kuwa daga ita har yaranta fatarsu jajir take kamar wasu larabawa, sannan gata 'yar caras sab'anin guda biyun da suke da k'iba mai yawan gaske. Ciki suka shige inda ta musu masauki a d'akinta, suna shiga Mimi ta cire hijabin ta jefa kan gado ta cire jakarta ta zazzage kayan ciki, kallon Salma tayi tace "Besty taimaka min da kayan kwalliyarki, ni ban d'auko ba saboda mama zata gane." Dariya tayi ta juya ta d'auko mata jakar kayan tana fad'in "Muguwa, wani wuri zaki tafi shine baki fad'a min ba." Saida ta zauna da kyau ta kanta a madubi da alk'alamin zana ja-gira (crayon) ta shiga bin tsatsaren girarta da bata da yawa sosai kuma ba siririya ba tana zanawa, kallonta suka shiga yi inda Salma ke nuna mata sababin vid茅o d'in data samu na wak'ok'i, jin wata wak'a dake birgeta sosai ta wani mawak'i da suke gari d'aya da shi wato Niamey mai sunan *Auta mg boy* tayi saurin cewa "Besty bar min wak'ar nan." Aje mata wayar tayi gabanta tace "Besty kinsan da jibi za'a kawo kayana kuwa?" Da sauri ta kalleta tace "Dan Allah? Da gaske?" Cike da tabbaci tace "Allah kuwa." Cikin farin ciki tace "Kai amma dole na yi waya kafin ranar, dan wallahi ni zan zama farko da zata fara had'a hotunan kayan lefenki." Dariya tayi tace "To ina wayarki?" Yatsina fuska tayi sanda take saka conciller tace "Dama ai na fad'a miki bana son Samsung d'in nan, ya rasa wayar da zai bani sai Samsung ? Samsung d'in ma duos." Tab'e baki tayi sai Salma da tace "To ai ke besty ba'a gane gabanki ne wallahi, kin ga fa har abokin 'ya'yana yace yana sonki ki fad'a min na fad'a masa ya ma fita harkarki, wallahi dan baya son raini ne amma har yanzu yana son ki, ke nan fa saida 'ya'yana ya fara min mad'e a kan ki yana nuna min son ki yake, ko da na fara tuntub'arki da lamarin kika kalli idona kika ce bai miki ba." Wata shak'iyar dariya tayi sai Asma'u dake saurarensu tun tuni tace "Tsakani da Allah? Yayanki fa?" Kallon Asma'u tayi tana gyara yaloluwar rigarta data fito mata da 'yan tsirarun nonuwanta tace "Wallahi haka ya faru, bansan wane irin namiji take so ba?" Tab'e baki Asma'u tayi tace "Ai indai Mimi ce namiji zai tsallake jarabawar tantancewar fara kula ka ne idan ka haye wad'anan matakan, na farko ka zama dogo ne da ka iya d'aukar ado da tsafta, na biyu ka zama wayayye d'an zamani da zaka iya aje ta gaban mota ku zaga gari, idan ta kama har k'asar waje ka dinga fita da ita dan shak'atawa, na uku ya zama matakin karatunka mai zurfi ne yanda zaka iya cireta kunya a ko ina kuka shiga, na hud'u ka zama mai d'an abun hannu da zaka iya d'aukar d'awainiyarta, ko da baka kasance d'an babban gida ba ita wannan bai dameta ba, na biyar kuma shi ne ka tabbatar *shekarunka daga talatin* ne k'asa da haka, dan ita a tunaninta a wannan k'adamin ne yake ganiyar k'uruciyarsa, duk zai iya yin wad'ancen abubuwan dana lissafa ne idan wannan ne adadin shekarunshi, sama da haka tana ganin ya jima da tsufa a duniya, ita dama bata damu sai kyakyawa ba, indai kana da wancen to an wuce wajen a wurinta." Wani nauyayyen numfashi Salma ta sauke ta kalli Mimi da har tayi nisa a kwalliyarta tace "Lallai besty burinki babba ne, ko ni da zan auri mai kud'i ban saka ran ya dinga fita da ni ba." Jinjina kai tayi sai kuma tace "Indai hakane kenan duk sanda kika ganni tare da alhaji na dariya kike min?" Mimi kam bushewa tayi da dariya dan gaskiya abin da ke faruwa ta fad'a mata, ganin haka yasa Salma hararenta tace "Allah indai hakane zan hanaki halartar bikina." Tsagaitawa tayi da dariyar tace "Haba besty wa ya fad'a miki? Ni na isa na wa mijin da zaki aura dariya." Hararanta tayi tana turo baki tace "Allah yasa gaskiya kika fad'a." Dariyarta kawai ta ci gaba da k'yalk'yalawa can kuma saita kalli Salma sanda take shafa man leb'e tace "To wai besty me yasa zaki aureshi? Dubeki ki dubeshi, wallahi wannan tsaf zai kasheki da tumbinshi a daren farkonku, kuma fa zai kai hamsin mutumin nan." Waro ido Salma tayi tace "Ke Mimi bansan wulak'anci, wallahi arba'in da hud'u yake, haka ya fad'a min da bakinshi sanda na yi shagalin murnar k'arin shekarata." Asma'u dake ta dariya ne tace "Wato Mimi ke dai idan kika k'i abu kina da hanyoyi dayawa na kusheshi." Salma ce tace "Gane min hanya dai yar uwa." Kallon Salma tayi tace "Baki yarda ba kenan?" Shiru tayi sai kuma ta kalli Asma'u tace "Yar uwa fa tayiwu dan baki san shi bane, gaskiya ta fad'a indai zan cire son zuciya, ina jin fa Allah ne yayi ni d'in matarshi, dan nima da fari babu yanda ban yi ba dan mu rabu, dan gaskiya idan na tsaya kusanshi yanda kika san gwiwa ce da kaza." Wata dariya suka kuma tintsirewa da ita har Asma'u, hakan yayi daidai da mik'ewar Mimi ta shiga kashe d'aurin d'an kwali kamar wacce ke koyar da kwalliya, kuma a haka duk ta koya ne ta hanyar kalle kalle a waya da saka kai, hakan yasa k'wandalarta bata shiga hannun mai kwalliya ko mai lalle, indai tayi niyya zata zauna tayi abun ta, kitso ma ta iya tsaf kan ta dai ne bata yi wa, kuma a haka bata d'aukeshi sana'a, a ganinta ajinta ya wuce nan gaskiya, tun mama na mata fad'an tayi har ta daina, mama kawai take ma sai Iya Delu sai kuma k'awayenta idan ta so. Sassauk'an d'auri tayi ta d'auki gyalenta ta rub'ashi biyu ta d'ora a kafad'a d'aya, turarenta ta d'auka ta fesa sosai kafin ta kalli Salma tace "Besty kira min lambar Muttak'a." Yatsina fuska Salma tayi tace "Shi ne dama zai zo kika d'au wannan wankan?" Kallonta tayi tace "Zaki d'aukeni hoto ne, idan ya kawo min wayar na ga kalata saina rik'eta na d'ora hotunan a statu na gaishe da mutane." Girgiza kai Asma'u tayi ita dai ta zuba mata ido kawai, wayar Salma ta d'auka ta kira lambarshi da tasan ta saka sunan mace dan kar ta samu matsala da na ta alhajin ta kira, tana jin an d'aga ta mik'a mata wayar ta karb'a, saida tayi kamar ba za tayi magana ba kafin tace "Ina gidansu Salma, minti ashirin gareni na komawa gida, idan na tafi gaskiya ba zamu had'u nan kusa ba." Da farin ciki yace "Gimbiya Mimi an gama, gani nan zuwa cikin minti goma." D'inn? Ta yanke kiran tare da mik'awa Salma wayar tace "D'aukeni." Sauka tayi daga kan gadon da take ta shiga snapchat ta fara d'aukarta, duk da rigar dake gareta haka ta matsa mata suka d'auka tare, Asma'u ma da k'yar ta iya tsayawa suka d'auka guda uku da hijabinta a jiki, har hoto mai motsi saida ta mata abun kamar na hauka ko gajiya basa yi. Tsawon mintuna suka d'auka saida ya kira yace gashi ya zo ta kallesu tace "Ina zuwa 'yan mata, ku tayani da addu'a Allah yasa IPhone zai bani." Dariya Salma tayi tace "Zai zaki iya fasa mishi da kai da duk wacce ya baki idan ba IPhone d'in b芒 ce." Dariya sukayi ita kam ta juya ta fita a takonta d'aid'ai, da kallo Asma'u ta bita tana jin ina ma Mimi zata kimtsu ta rumgumi halin da suke ciki, tana tsoron wata rana ta jawo musu abinda zai fi k'arfinsu, idan wani ya maka kyauta dan Allah wani ba haka bane, idan wani ya yafe maka sanda ya maka wani neman hanyar fanshewa zai yi, wani kuma zai iya bin kowace irin hanya dan ya fanshe wahalarsa a kan ka. Gata dai yanzu sun fito daga gidan babu kwalliya a fuskarta, ta zo gidan k'awa ta cab'a ado na d'aukar hankali, sassauk'ar kwalliya tayi amma da za'a tambayeka *wacece ita* sanda ka ganta a kan titi, ko shakka babu zaka ce k'aramar autar shugaban k'asar ne baki d'aya, sabida yanda kayan suka karb'eta ta haska tayi matuk'ar kyau, ka rantse da Allah yar babba ce zata je wani babban taro na manyan mutanen da ke fad'a aji a k'asa baki d'aya, amma kuma a gidansu nan suna can ta barsu sun yi faten tsakin masara da alaiyahu, ta tabbatar sanda Mimi ta baro gida basu da abinda zasu ci na gode da safe kawai, amma ita ba wannan ne a gabanta ba rayuwarta take yi mai cike da burirrika da saka kai a uku. Gaba d'aya gigicewa yayi ya shiga sakin baki yana kallonta, a matsayinsa na sojan jirgi sai yaji ina ma wata 'yar hatsaniya ta faru a yanzu yanzun a layin nan, da zaiyi ram da ita ya saka a motarshi ya tafi da ita a zuwan cikin rububi ne na tashin hankali, kai shi a gaskiya zai iya rayuwa da Mimi ko babu aure, a yanda yake ji zai iya tarben tsinin wuk'ar da aka turo dan illata ta shi ya tarwatsa rayuwarshi, a kan baiwar Allahn nan zai iya yin komai. Hakan yasa bayan ya damk'a mata ledar mai kyau ya ciro kud'i yan jaka goma goma (Kwate馃槹 kin ga almubazzaranci) guda uku ya bata wai ya siye kwalliyar nan, bata yi k'asa a gwiwa ba kam ta sa hannu duka ta karb'a tana mishi godiya, yatsina fuska tayi saboda tsarguwa da kallon da yake mata na wuce k'a'ida tace "Ni zan koma ciki zamu tafi gida." Tangale hab'a yayi yace "Mimi bana so ki tafi, kamar nayi ta kallonki." Wulwul tayi da idonta tace "Sa茂 anjima, kaga idan mu kayi magriba za'a mana fad'a, kuma dan had'uwa da kai kawai na zo nan." Jinjina kai yayi yace "Shikenan Mimi ta wa, sai anjima ba dan raina ya so ba." Juyawa tayi zata koma cike da jin haushin Mimi ta shi da yace, tsayar da ita yayi yace "Mimi sai yaushe zaki bani dama na fito ayi maganar aurenmu?" Juyowa tayi ba wani d'ard'ar tace "Sanda na shirya." Marairaicewa yayi yace "Kamar yaushe kenan? Mimi ba kya so kiyi aure ne?" Fuskarta a had'e tace "Ina so, amma ba yanzu ba." Lura zaiyi magana yasa ta saurin juyawa tana fad'in "Sai munyi waya." Shigewa tayi ya bita da kallo har ta shige, d'an lashe leb'enshi yayi na k'asa daya bushe tare da shiga mota ya bar unguwar. Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa. Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai. Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa. _Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._ _'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_ Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:51 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *7* Tana shiga cikin sauri ta ciro kwalin wayar daga ledar, saida ta daka tsalle ta rumgume Asma'u tana murna ganin IPhone duk da k'aramar tashi ce, amma dai taji dad'i sosai da ganin wayar, Asma'u kam mamaki ne ya hanata magana sai kallonsu suna ta murna har da yin zaune tasa Salma turo mata abubuwa da dama har da hotunan data d'auka yanzu, suna idawa a gaggauce sukayi sallama da cewa sai sun zo ranar da za'a kawo kayanta, suna fita suka samu taxi ta nufi dasu unguwar yayar Asma'u. Ko da suka je gidan basu wani jima sosai ba sai sak'on da Asma'u ta bawa yayar ta ta wanda uwar ta bata ta kawo sanda ta ji zasu taho, 05:50 suka baro gidan suka shiga takawa a k'afa dan isa bakin titi, dama idan aka kawoka ne kake samun mai kai ka har k'ofar gida, amma idan ba haka ba masu taxi basu cika kai kawo a layin ba. Cikin fad'a Asma'u ta kalleta tace "Gaskiya Mimi kina ban haushi wasu lokutan, wai ke ba kya tsoron abin da zai je ya dawo ne?" Yatsina fuska tayi tana d'an goge zufar data tsatsafo mata a hanci, kallonta tayi tace "Ba ma zaki kulani ba ko?" Kallonta tayi ta sake yatsina mata baki tare da d'an mata gwalo ta sake d'auke kanta, jinjina kai tayi tace "Ba komai ki ci gaba, Allah na gani nayi iya k'ok'ari a kan ki Mimi, bana so k'awance na da ke ya zama irin k'awance da aka ambata ranar lahira mu had'u ni da ke muna zagin junanmu, ko kuma na rok'i da ki haska min gabana dan na tsallake sirad'i ko ke ki rok'i hakan, na fi so mu wuce a tare cikin aminci." Wata bak'ar Prado ce ta sha gabansu ta tsaya wanda dole su ma suka tsaya cak, da sauri Asma'u ta rik'e hannun Mimi tana fad'in "Shikenan, Allah ya taimaku yasa ba cikin samarinki bane wani zai sace mu." Kallonta Mimi tayi, saidai kafin tayi magana Ashraf ya zuro farar k'ararshi mai d'auke da takalmi k'afa ciki irin na matasan da suka san kansu wayayyu yan zamani k'irar polo, kafin suyi wani yunk'uri ya gama fitowa gaba d'ayanshi ya tura murfi da k'arfi ya rufe, a sanyaye ya shiga takowa gabansu yana cire bak'in glass d'in fuskarshi, gabanta ya tsaya cak yana mai k'arewa duk ilahirin jikinta kallo, faffad'an bakinshi mai d'auke da tsararun hak'ora ya bud'e ya nunota da yatsa kamar zai tsokale mata ido yace "Ke wacece da zaki wuce ta nan baki gaishe dani ba?" Mimi da tun fitowarshi ta saki baki tana kallonshi, a take ta tambayi " *Wanene wannan*? Yaushe ya zo garin nan?" Dan kam ita daga tsarinshi zuwa fatarshi da gyaran kanshi ya bayyana mata ba mai jin yaren hausa, zabarmanci, barbarci, tubanci, fulatanci ko buzanci bane, tunda take bata tab'a jin namiji ya birgeta a kallonshi ba sai yau, hasalima samarinta kallo d'aya take musu bata sake sha'awar kallonsu. Amma wannan sai take jin zata iya zaunawa tayi ta kallonshi ba zata k'osa ba ita kam. Sanda ya shiga nuna ta da yatsan nan a karo na farko a rayuwarta da taji a ranta zata shanye wulak'anci ta kuma had'e, dan wannan ba guy da zata ma rashin kunya bane, yanayinshi ma ya nuna mata zai iya tsinka mata mari, babbar asarar da zatayi kuwa bata wuce su rabu ba tare da yace yana son ta ba, dan gaskiya ita duk ajin shi da yanda ya birgeta ba zata tab'a sauko da k'anta k'asa tace tana son shi ba, ina! Ba zata iya ba, gwara idan sun rabu tayi takaicin rasashi a gaba kuma zata samu wani kamarshi ko wanda ya fi shi. K'yasta yatsunshi yayi daf da fuskarta hakan ya sakata lumshe idonta da suka fara kawo ruwa sabida jimawa tana kallon abu d'aya, daidaita nutsuwarta tayi ta saka idonta a na shi sosai, hakan ya bashi damar sakar mata murmushi yace "Wasa nake miki, kin tsorata ne?" Tarrr ta masa tana kallo inda a hankali ta shiga canza yanayin fuskarta daga shagala da mamaki har ta d'aure fuskar, kallo ne ta shiga yi masa irin na zuru d'in nan cikin jin haushi. D'an kallon Asma'u yayi da ita tayi galala take kallonshi yace mata "K'awarki bata magana ne?" Da sauri ta zabura tace "Tana yi mana." Kallon Mimi tayi ta sake jimk'e hannunta gam tana d'an motsa bakinta, a hankali ta sadda dubanta tayi k'asa da idonta tana sauke ajiyar zuciya, murmushi yayi mai sauti yace "Masha'Allah, dan Allah ya sunanki?" Da sauri ta sake d'agowa ta kalleshi, dan Allah ya sunanki? Kamar wata 'yar talla ko kayan miya? Sama da k'asa ta harareshi tare da kaucewa ta rab'ashi zata wuce, da sauri ya sake tare gabanta yace "Dan Allah ki saurareni, ko na biyo bayanku ne har na ga gidanku?" Asma'u ce tayi saurin cewa "A'a dan Allah ka rufa mana asiri, zaka sa a mana fad'a a gida." Kallon Asma'u yayi yace "To in hakane ki sa k'awarki ta min magana mana." Cike da tausayin kan ta ta sake kallon Mimi, numfashi kawai ta sauke dan bata ga abinda zaisa tayi maganar ba idan ba niyya tayi ba, sake matsowa yayi kusanta yana fad'in "Dan Allahana 'yan mata, ki taimaka ki fad'a min sunanki da unguwarku, nasan bai kamata na tsareku a kan hanya ba, amma babu yanda zan yi ne, ina ganinki naji zuciyata ta doka da k'arfi ta yanda ba zan juri ki sub'uce min ba." Kallon Asma'u tayi ta mata alama da ido mu tafi, zata taka k'afarta yace "Ki fad'a min abinda zanyi mana da zai sa ki min magana, dan Allah kada ki bari ki kubce min *Naana*." Kallon juna sukayi ido cikin ido, da sauri ta d'auke na ta saboda marayan kallon da yake mata, a marairaice yace "Ko sai na duk'a har k'asa ne?" K'asa ta k'urawa ido ba tace komai ba, a hankali ya nemi zemewa ya durk'usa k'asa yana fad'in "Wannan ba kom..." Ba ta barshi ya k'arasa ba tayi saurin kallonshi tare da fad'in "Maryam." Da mamaki Asma'u ta kalleta jin ta fad'i cikakken sunanta yau ga saurayi, a iya saninta saidai ta fad'a maka Mimi amma ba zaka ji Maryam a bakinta ba. Mik'ewa yayi yana sakin murmushi tare da fad'in "Alhamdulillah, *Mimi*, suna mai dad'i." D'an kumburo bakin da tayi yasa shi yin murmushi yace "Kina da aji, hakan kuma ya tabbatar min da na samu matar aure, fatana Rabbi ya dafa min kar ki k'i kulani a matsayin wanda zakiyi soyayya da shi ma bare aure." Hannu yasa aljihu ya jawo tartsetsiyar wayarshi ya mik'o mata yana fad'in "Zan iya samun agajinki ta hanyar rattab'a min lambobin da zasu sadani da inda kike?" Wani wallll! Tayi da ido tare da k'ura mishi ido, kunnenshi d'aya ya kama alamar ban hak'uri, fari tayi da ido hakan ya k'ara narkar dashi tare da fad'in "Ko na sake zubewa k'asa ne?" Har yayi haramar zubewa k'asa tayi saurin fizgo wayar ta shiga saka mishi lambarta, mik'a mishi wayar tayi a hannu suna kallonshi ya saka suna kafin ya kalleta ya sumbaci wayar, irin kallon firgitarwar nan ta bishi da shi, shi kam murmushi yayi yace "Yanzu musaya ta fara shiga tsakanina da ke, a sannu sannu wata rana zamu gauraya mu zama babban iyali da zai tsiro da kyakyawa kuma hazik'an yara." Kallon mamaki ta mishi shi kuma ko a jikinshi, saima rusunawa da yayi yace "Dan Allah zan iya saukeku inda zaku je?" Asma'u ce ta girgiza kai tace "A'a gaskiya, an hanamu." Kallonta yayi sannan ya kalli Mimi, cikin taushin murya yace "Hakan ne a ranki kema? Ba zaki shiga ba?" A hankali ta lumshe idonta wanda suka sha mascara suka yi tsayi sosai alamar eh, jinjina kai yayi yana jinjina al'amarin wannan mai kama da jinin sarautar, idan da za'a barshi da hasashenshi sai yace 'yar k'usa ce a gwamnati sun samu matsalar abun hawa ne, dan duk da baya da sani akan suturar mata yasan kayan dake jikinta ba masu arha bane, ko da akwai mai arha to sai dai ko 'yan kunnenta dake k'anana sosai mak'ale a kunnen. Saidai a wajenshi kam ko ta kasance 'yar babba ko ta kasance 'yar takala wannan bai dameshi ba, tunda ya karyo kwana idonshi suka sauka a kanta ya ji zuciyarshi ta fizga a guje ta rakito duk wani abu daya shafeta ta killace da jin cewa zata dage a kan ta ko ma wacece ita. Saida ya kalli k'wayar idonta ya daidaita gilashinshi da kyau ya manna mata shi a fuskarta, hakan kuma ba k'aramin kyau ya k'ara mata ba. Dariya yayi data fito da kyawunshi da kyau yace "Sai na kiraki, Mimi." Da kallo ta rakashi sai Asma'u da tace "Dama kasan inkiyarta ce Mimi?" Juyowa yayi yana shafa tarin sumar kanshi yace "Ban sani ba, amma duk mai sunan Maryam ina kiranta da Mimi, saboda sunan *mahaifiyata* ne." A tare suka saki murmushi ita da Asma'u, haka kawai ta ji abinda ya fad'a ya sata nishad'i, da kallo suka bishi har ya shiga motar ya barsu nan tsaye. Kallonta Asma'u tayi sai taga har yanzu idonta na kan shi, da sauri cikin jin haushi ta cire gilashin daya saka mata tana fad'in "Malama ya tafi to sai ki kama bakin." Da sauri Mimi ta kalleta sai kuma taja tsaki tare da k'watar gilashin ta saki murmushi ta kalleta tace "Dan Allah mutumin nan bai birgeki ba?" Girgiza kai tayi tace "Ko kad'an, tunda saurayinki ne." Cike da damuwa tace "Ke ba haka nake nufi ba, ina nufin tsarinshi, kalamanshi, kyawunshi da kuma yanda ya iya shiga zuciya lokaci d'aya." Galala Asma'u ta kalleta tace "To fa, da alama wannan kam shi ne *zakaran* da ya zubar da 'yan maza warwas a wajen Mimi." Kallon gilashin hannunta tayi ta sake mayar dashi ga fuskarta ta kalli Asma'u ta d'aga mata gira tace "Ya kika gani dan Allah? Ya min kyau?" D'aga mata gira tayi ita ma tace "Kinyi kyau kam sosai." Hannunta ta kama cike da jin dad'i suka fara tafiya tana fad'in "Asma'u a rayuwata ban tab'a tunanin zan had'u da irin wannan namijin ba?" Da mamaki ta kalleta tace "Me yasa? Naga ai burinki kenan samun irin wannan namiji." Saida ta saki hannunta tace "Hakane, amma ni ban tab'a tunanin zan samu kyakyawa haka ba ai, to wai wanene shi?" Ta fad'a tana kallon Asma'u, tab'e baki tayi ta d'aga kafad'a tace "Ina zan sani, sai ki bari idan ya kiraki ki tambayeshi." Wani murmushi ta saki tare da d'agawa wani d'an taxi hannu tana fad'in "Ba ni zan tambayeshi ba, shi ne zai fad'a min." K'ala Asma'u ba tace ba har suka k'arasa kusa da mai taxi, saida ta kalleta tace "Gida muka nufa yanzu ko kuma dai kina da sauran gurin zuwa ne?" Murmushi ta mata tace "Gida zamu koma mana ke ma, magriba ta kusa ai." Girgiza kai tayi ta kalli mai taxin tace "Tallague." Jinjina kai yayi alamar su shiga, bud'ewa sukayi suka shiga inda ya jasu, wayar ta ciro a jakarta ta shiga saitata zuwa yanayin da take buk'ata, saida ta tabbatar komai ya mata kafin ta ciro wani k'yalle a jakarta a hankali ta shige goge kwalliyarta na fuskarta tana kallon madubi, saida ta goge duka kafin ta kwance d'aurin d'an kwalin ta saka a jaka ta ciro hijabinta ta saka, sak yanda ta fito daga gidan hakan yasa ta kallon Asma'u tace "Zasu gane wani abu?" Girgiza kai tayi tare da juya mata baya tana kallon titi, tyab'e baki tayi tace "Asma'u kar kisa na fara tunanin ke 'yar bak'in cikina ce." Ita ma juya gabanta tayi daga kallonta, a zaman kuramen nan suka isa gida, babu wacce tayi wa yar uwarta sallama kowace ta shiga gida dan suna da tabbacin zasu shirya zuwa gobe a makaranta. *Sheikh* Sauri yake sosai dan ya fita masallaci da sunyi sallah a d'ora karatu kasancewar masallacin na shi ne dake manne da gidan, haka kuma ga asibitinshi dake kallon gidanshi wacce yake d'aukar nauyin ma'aikatan ana duba mutane kyauta, kawai zaka ciri kati ne da d'an abun da baiyi tsamari ba, amma daga maganar rashin lafiyar da zata kwantar zuwa mata masu haihuwa da yara k'anana duk kyauta ake dubasu. Suna alwala amma ya cikashi da surutu, har suka fito daga ban d'akin dake cikin falon zasu fita yana fad'in "Ustaz kana ji na? Wallahi da gaske nake fad'a maka, dama na ce maka zanyi budurwa yau ba? To na yi yanzu aiki ya rage naka ka nemo min aurenta." Hafsat dake jinsu tana neman tashi tsaye ne ta kalleshi tace "Wai auren wasa ne aka fad'a maka da za kace kayi budurwar yanzu kuma a nema maka aurenta?" Da sauri ya kalleta yace "Aunty Hassy bari maganar nan dan Allah kada kisa mijinki ya baud'e min, wallahi daga ganinta tana da hankali da nutsuwa, wai kin ganta kuwa? Ga mugun aji yarinyar na tabbata ba kowa take kulawa ba." Da sauri ya mayar da dubanshi ga sheikh zaiyi magana sai kuma ya yi shiru yana sunkuyar da kanshi saboda k'ura masa ido da yayi, a hankali cikin gyara ma hularsa zama da nad'in dake kanta na farin rawani yace "Kai yanzu har ka tabbatar da sahihancinta ne?" A marairaice ya kalleshi yace "Allah kuwa sheikh, yarinyar daga ganinta sam alamunta da yanayinta ba suyi kama da na wacce zata iya cutar da kowa ba." Juyawa sheikh yayi cikin takon hanzari ya nufi hanyar fita, da sauri shi ma ya bishi yana fad'in "Ustaz, indai kana so na kana son Hajia to ka nema min auren yarinyar nan." Ba tare daya juyo ya kalleshi ba yace "Ta fad'a maka tana sonka ne? Ko kuma dole za'a mata?" Da murmushi yace "A'a ba haka bane, dama amincewarka nake buk'ata kan zaka nema min auren na ta, idan na samu yarda daga gunka shikenan sai nayi yak'i dan k'wato zuciyarta." A daidai zasu shiga masallack suna cire takalminsu yace "Allah yasa alkairi, zan nema maka auren nata idan nayi bincike na gane yar manyan mutane ce, akasin haka kuma zaka hak'ura da ita *Asas*, ka yarda?" Jinjina kai yayi alamar to shikenan, shigewa sukayi cikin masallacin ana ta kiran sallah, lokacin tayar da sallah nayi ya shiga gaba dan jan su ba tare da mai jiyawar ba, da kan shi yake d'aga sauti yanda zai jiyar da kowa musamman daya zama ga lasipika. Suna kammala sallah aka shiga shirye shiryen karatu, cikin k'ank'anin lokaci aka had'a komai kamar yanda aka saba inda masu d'auka ma ana watsawa a kafafen sadarwa da gidajen tv da redio kowa ya shirya. A nutse sheikh ya fara bud'e katarun da muk'addima kafin su tashi a inda suka tsaya. K'arfe 08:10 suka kammala dan ma an amsa tambayoyi kenan, yana mik'ewa zai fita yan agaji da masu tsaronshi d'aya daga ciki suka shiga kakkareshi suna son mutane su gyara ya wuce, gashi k'ofar da zata fitar da shi ta baya kuma mai sadashi da cikin gida ne, gashi kuma yana son fita shi kad'ai ba tare da 'yan koren nan ba. Sosai aka rufe hanyar fitar masu tsaro na ta k'ok'arin a bud'a hanya ya wuce, musamman matasa sune a sahun gaba kowa burinshi su gaisa wasu kuma takardar tambaya ce da su suna son sai sun bashi hannu da hannu. Allah ne ya so shi ya rufe musu ido sanda ya kutsa ta cikinsu ya fice a masallacin ba tare da ma sanin jami'an ba, bai kuma tsaya komai ba yayi gaggawar fad'awa cikin gida, kai tsaye wajen motoci ya wuce inda ya d'auki wata jibgegiyar Honda crv ya danno hancinta waje sanda mai gadi ya bud'e mishi k'ofar yana bin shi da addu'a, har k'ofar gidan suka fito cigiya mmai gadi na fad'a musu sai hankalinsu ya kwanta tare da tunanin kuma ina ne sheikh zai tafi da baya buk'atarsu? A k'ofar gidan duk suka gyara tsayuwarsu da jiran ya dawo su tabbatar lafiya lau yake. *Maryam* Idar da sallarta kenan mahaifinsu ya shigo yana kiran sunanta, tasowa tayi daga kan tabarmar ta durk'usa kanta a k'asa tana fad'in "Abba gani." Cikin fad'a ya shiga fad'in "Mimi me mahaifin yaron nan yake fad'a ne? Me ya had'aki da shi da suka ce sun hak'ura da tura kayan? Wani abu kika masa na rashin kunya ko?" Girgiza kai tayi murya k'asa k'asa tace "Abba babu abinda na masa." A tsawace yace "To me yasa suka ce sun fasa? Yace ke da kanki kika ce ba kya son shi." Shiru tayi kanta a sadde ba tace komai ba, a zabure ya matso kamar zai daketa yana fad'in "Ba dake nake ba kina ji na?" Da sauri ta d'ago tace "Abba ni bana son shi ne." Baki sake ya shiga kallonta yace "Iyeeeeh! Ba kya son shi fa kika ce? Kuma kika kawo mana shi gidan nan har muka shiga maganarku." Turo baki tayi tana kunkuni, da sauri ya k'arasa duk'awa ya d'auki takalminshi yana fad'in "Kinga 'yar butan uban nan..." Da gudu ta shige d'aki tana fashewa da kukan shagwab'a, girgiza kai mamanta tayi tace "Allah ya kyauta." Shi kam tsaki yayi tare da k'arasawa wajen Yaseen dake kwance yace "Har yanzu jikin nashi da zafi?" A sanyaye ta sake tab'a goshin Yaseen tace "Da zafi malam, ko zamu kaishi asibiti ne? Ina tsoron zazzab'i wallahi musamman ma na dare." A tausashe shi ma yace "Rabi'a ta ina zamu fara to? Abinda muka ci ma waccen ja'irar ce kika ce ta bayar da kud'in data samu a hannun yaron da muke tsammanin zai zama mijinta, yanzu kud'in taxi ma da zata kaimu asibitin kawai bana da shi." Jinjina kai tayi kanta a k'asa, laluba aljihunsa yayi ya mik'o mata wasu canji yace "Kinga karb'i wannan, ba wa Mimi ta karb'o masa ko parac茅tamol ne ya sha zafin ya rage, bari naje gidan Iya Delu na ga idan malam na nan ba zai rasa wani taimakon da zai mana ba." Hannu biyu tasa ta karb'a ta bishi da kallo har ya fita, a sanyaye ta k'wala kiran Mimi dake d'aki, tana fitowa da k'aton hibajinta fari na makaranta da tayi sallah da shi, kud'in ta mik'a mata tace "Inji mahaifinki ki siyo parac茅tamol a bawa Yaseen." Karb'a tayi tare da komawa d'akin ta d'auko sabuwar wayarta da har yanzu bata bari kowa ya gani ba, ficewa tayi a gidan ba tare da ta kula kowa ba. *************** Tsaye tayi bakin titin tana jiran shawagin ababen hawan ya tsagaita ta samu ta tsallaka dan ta isa ga mai shagon dake siyar da maganin, ta jima a wurin kafin tayi nasarar tsallakawa ta siyo ta juyo. Watak'ila Allah ne ya k'addara had'uwarsu, shiyasa ma ya fito shi kad'ai har ya buk'aci ruwa dan mak'oshin shi a bushe yake, gefe ya paka motar ya tsallaka titin ya siyo swan water, zai tsallako ya dawo ne ita kuma ta k'etara ta siyo maganin. Tunda ya ganta ya gane wacece, tsaf ya shaida kamanninta da ita ya had'u da ita na farko, babban abun da ya masa dad'i bai wuce ganinta da yayi a suffar daya fara ganinta a wurin sabkar nan ba, dan tun daga k'asa ya kalli k'afafunta da ake gani da k'yar saboda girman hijabin, gashi da k'yar take kallon gefe da gefe ba irin idonta a tsaye yake a kan titin b芒, dan har rintse ido take ko ta kawar da kanta idan wani abun hawan ya hasketa sosao. Hakan yasa ya ji cewa lallai 'yar babban gida ce (yar masu tarbiya). Da kallo ya bita har ta wuce ta gefenshi ta siyo magani ta dawo bakin titi, yanzu haka tsakaninshi da ita bai fi tako biyar zuwa shida ba ya isar dashi gareta, amma tunanin rashin dacewar yi mata magana a kan titi, da kuma hangen ta yanda zata kalleshi yasa duk sai yaji gwiwarsa tayi sanyi. Amma dake zuciya da abinda take so kuma take muradi, sai yaji a ranshi ai kamar dama ce da zaka san asalin d'abi'ar dake lullub'e a cikin zumbulelen hijab d'in nan, hakan yasa shi takawa a nutse tare da d'an sakin jikinshi ya b'oye k'irarshi ta kakk'arfan dattijo har ya tsaya gefenta, shi ma kallon titin yayi cikin wata daddad'ar murya kuma sanyayya yace "Bayan nema miki amincin Allah, ko zaki iya kawo hannunki na k'etaraki?" A hankali ta juyo tana yatsina fuska alamar za tayi halin na ta, amma ganin Sheikh Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif ya saka ta waro idonta tare da bud'e bakinta, murmushi ya sakar mata sanda suka had'a ido tare da cewa "Sannu." Rufe bakinta tayi gam tare da yin k'asa da idonta, a hankali har ta sauke kanta k'asa tana d'an jujjuya kanta cikin siririyar murya tace "Assalama alaika, ina wuni?" Da mamaki ya kalleta, mamakin shin bata ganeshi bane? Yasan dai fuskarshi ta gama garin nan da kewayenshi baki d'aya, ko baku da telebijin zaka iya ganinshi a telebijin d'in wasu, idan ba a nan ba kuma ga waya data game ko ina, wa'zinzikanshi masu tsayi da gajeru suna cikin wayoyin mutane dayawa, idan ka tara mutum goma zaiyi wuya ka kasa samun karatunshi a wayar mutum biyar ko ma sama da haka. Kowa yana son ya ganshi, kowa ya ganshi haba-haba yake da son su gaisa har su tattauna ko na minti d'aya ne, dan hakan ya zama abun alfaharin wani ko abun nishad'i. Amma ita ta kalleshi da fari kamar zatayi mamaki amma kuma sai ta wani d'auke kai tace wai wani sannu a k'arshe. D'an d'auke kanshi yayi daga kanta ya kalli titi yace "Muje, karki yarda na barki a nan, hakan zai jawo miki kwana a bakin titin nan, ki saka k'afarki a inda na d'auke tawa." Da sauri ta kalleshi da tunanin shi ne kuwa? To me zatayi? Tayi yanda yace ko kuma shi ma ta d'an gurza mishi ne kamar sauran? Wata zuciyar ce tace da ita "Malam ne fa! Kiyi yanda yace." Sake kallonshi tayi ta kalli titin a hankali ta d'aga kan ta tana jinjina shi tace "... Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa. Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai. Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa. _Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._ _'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_ Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:51 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa. Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai. Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa. _Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._ _'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_ Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *8* Sake kallonshi tayi ta kalli titi a hankali ta d'aga kan ta tana jinjina shi tace "To." Tana kallo sheikh ya fara kutsa titi a wani gadarance, motocin dake kai kawone suka shiga rage gudu wasu dan ganin mutum na wuce kuma ko kallonsu baya yi gabansa kawai yake kallo, kamar wutsiya haka ta ji tana biyarshi har suka k'etara, wani numfashi ta sauke tana kallon k'eyarshi, tana ganin zai juyo tayi saurin yin k'asa da kanta tace "Nagode, sai anjima." Zata gifta ta wuce yayi saurin cewa "Dakata." Cak ta tsaya amma kan ta a k'asa, dan fatanta d'aya ne su rabu ba tare da yace ga abinda tayi da bai kamata ba har ya shiga jawo mata ayoyi da hadisai, ita kam sauri take bare ta tsaya ta saurareshi. Hakan yasa ke iya k'ok'arinta wajen ganin ta sauke idonta k'asa karsu had'a ido, sosai take k'ok'arin yin sanyi har tana ta wasa da maganin a cikin hijab d'inta, ta nutsu sosai ta kuma bashi hankalinta matuk'a, ta yanda duk wanda ya ganta a lokacin zaiyi zaton ba ita bace, zaka d'auka tsuntsu ne a kan ta kuma aka saitata da bakin bindiga idan ya tashi a bakin ranta. Ta b'angaren shi ma kallo yake sake k'are mata duk da dai yasan bai dace baa kan titi,saidai yana son sanin wata makama dazata isar dashi ga ahalinta, a lokacin da zai nemi aurenta garesu kuma shari'a ta bashi damar ya kalleta son ranshi dan ya tabbatar komai ya masa. A sanyaye cikin muryar nutsuwa yace "Ya sunanki?" Saida ta gilgid'a kanta kamar k'adangaruwa tana sake kwantar da murya tace "Maryam." D'an murmushi ya saki ya furta "Masha'Allah, *Ryam*, ina ne gidanku?" A hankali ta d'ago ta kalli fuskarshi, amma sai taji kamar fuskar babanta zata kalla daga tsaye, sai kawai ta sunkuyar da kai tana jin gabanta na wani dum dum dum. A d'an kallon nan ta fahimci wani irin kwarjini da haiba dake tattare a fuskar mutumin, ashe dai yayi arha ne sosai da har suke iya had'a kallon fuskarshi a majigin wayoyinsu ko kuma telebijin, wani babban abu data fahimta a game da dattijon shi ne ma'abocin iya kwalliya ne, ko a wa'azi ka ganshi tsaf tsaf cikin d'aukar ado, yau kam data ganshi a zahiri saita sake tabbatarwa, gashi dogo da kuma wata murdadd'ar sura a cikin manyan kayan nan, uwa uba k'amshin da yake zubawa na d'aukar ran bawa ya killace shi, wani irin k'amshi ne mai k'arfi da sanyi ga mai shak'arshi wanda hakan ya tabbatar mata turare ne irin na manya masu tsadar nan. Saida ta had'e yawu sosai kafin tace "Nan kwana." Kallon hannunta yayi da tayi nuni dashi daga cikin hijabi ya kuma kalli kwanar, bai gane komai a kwatancen ba dan haka yace "Ya sunan mahaifinki?" Da sauri ta d'ago kai sai kuma tayi k'asa da shi, cikin raunin murya da rawar murya kamar zatayi kuka tace "Dan Allah *Abdul* kayi hak'uri idan wani laifi nayi kar ka fad'awa Abbana, ka fad'a min ni zan gyara kuskure na wallahi, ba'a sani na bane nayi." Rigiji-gabji! Shi dai da kan shi shine yau aka kira a gabansa da Abdul? Hakan ma k'aramar yarinyar daya tabbatar ko ta girmi Eesha shekarun basu wuce d'aya zuwa biyu ba, tun yana shekara ashirin da biyar a duniya ya rasa duk mutanen da zasu iya kallon cikin idonshi, a wannan shekarun na shi akwai masu daka mishi tsawa har ma su kirashi da *Abdul Waheed*, hatta Hajia sarakuwarshi wacce yake kallo kamar uwa bai tab'a jin ta kirashi da sunan da ba sheikh ba, uwa uba kuma Hafsat ko Ashraf, kowa dai sheikh sheikh ko gafarta malam ko ustaz ko ranka shi dad'e, a ko ina kallon wanda zaiyi alfarma ake masa, girmama shi ake kamar za'a masa sujada. Shine yanzu aka kira da Abdul, lallai ko ba komai yarinyar ta ciri wata tuta da ba kowa ya cira ba, watak'ila a dalilinta zai iya gano wasu abubuwa da suka jima da shige masa duhu. Saida ya gama tsareta da ido ya kuma d'aureta da su kafin yace "Kin sanni ne?" A hankali ta jinjina kai tace "Waye bai san fuskar nan ba, ai sai dai makaho." A dak'ile yace "Kenan ke ma makauniya ce?" Da sauri ta girgiza kai alamar a'a, numfashi ya sauke ya gyara tsayuwarsa yace "Ina son magana da iyayenki mai mahimmanci, zaki lamunce min na je." Da sauri ta kalleshi tace "Abbana baya nan." Da sauri ta rintse ido tana danne harshenta daya sakata yin k'arya, sai kuma ta ji ai hakanne zai rabasu lafiya kar ya sake tunanin neman gidansu. Ba tare daya d'auke idonshi ba yace "Ina ya tafi?" Murya k'asa k'asa tace "Ya je k'auye." Jinjina kai yayi yace "Kenan zaki iya bani lambarki dan na samu labari idan ya dawo." Tsuru tayi tana kallon k'afafunshi masu kyawun fasali, hummm! A zuciyarta take jin idan fa ta ciro IPhone d'inta ya gani misali zai bayar da ita wajen wa'azi, sai kawai ta girgiza kai tace "Bana da waya ni, dama data mamana nake kiran k'awaye na, shi ma ba kullum take bari na ba." Wani sanyayyan murmushi yayi saboda jin dad'in abinda ta fad'a, dan gaskiya kai tsaye ya fad'i hakane saboda yaga kalar ta ta k'awar (wayar), cikin farin ciki yace "Ki bani lambar mamar, kafin ki isa gida zanyi kira dan kiga lambar, idan kinje ki saka suna." Da mamaki ta d'an kalli gefen fuskarshi sai ta jinjina kai alamar to, murmushi ya sak茅 yi yace "Idan Abba ya dawo saiki fad'a min idan na kiraki." Sake jinjina kai tayi alamar to, gyara tsayuwa yayi yace "Saida safe Ryam." A nutse tace "Saida safe." Takawa tayi d'aya biyu uku taji yace "Wane suna zaki saka a lambar?" Juyowa tayi taga ya hard'e hannayenshi a k'irji ya zuba mata ido, cike da kunya tace "Ku fad'i wanda kuke so to." Murmushi yayi da a lokacin ta kalli fuskarshi wanda ya birgeta sosai, saida ya lumshe ido yace "Ki saka *Abdul*." Da sauri ta bud'a baki irin zatayi mamakin nan sai kuma cak ta tsaya ta shkga tariyo kalamanta na d'azu, sunan Abdul na fitowa ta ji kunya ta kamata kawai ta juya da d'an sauri tana murmushi ta bar gurin. Shi ma murmushin ya shiga sakar mata har ya ga ta shiga kwanar hannun hagu, girgiza kai yayi ya bud'e motar ya shiga yana bud'e ruwan hannunshi, saida ya d'aga kai ya tsiyaya a mak'ogwaronshi yasha sosai kafin ya rufe ya aje, wani murmushi ya sake yi y'a shiga juyawa yana fad'in "Abdul, hmmm! K'uruciya kenan, ni ne Abdul ko Ryam?" Kamar jiran gusawarta yake daga gaban sheikh sai kuwa ya kirata, da rawar jiki ta shiga lalubo wayar a k'ugunta da tunanin guy nan ne, amma ganin sunan d'an wahala saiya sakata jan wani dogon tsaki, saida wayar tayi daf da tsinkewa kafin ta d'auka tana sake yin k'asa da tafiyarta a sannu sannu, shiru dukansu sukayi saida ya tabbatar ba zatayi magana ba sannan yace "Mimi, kina ji na?" A dak'ile ta amsa da "Um! Ina aji." Numfashi ya sauke mai sauti yace "Mimi me yasa kike son wulak'antani?" Yatsina baki tayi ta harari wayar tace "Me yasa ka ce haka?" Ba alamar fara'a yace "Saboda na ga take-takenki ne, Mimi ki fad'a min gaskiya idan kinsan ba kya so na, bana so duk abinda nake a kan ki ya zama wahalar banza ce." Cikin jin haushi da rashin bawa abun mahimmanci tace "Ba komai, ka daina tunanin haka." "Kin tabbata Mimi?" Ya tambaya kamar yana gabanta, ba tare da shakkun komai ba tace "Umm." Daga inda yake y'a jinjina kai yace "Mimi, ina da karamci ga wanda ya min karamci, ina da alkairi da kuma b芒 wa abubuwa baya, saidai Mimi bana son yaudara da k'arya, na so ki fad'a min ba kya so na dana barki na nemi wata, amma tunda kika ce babu komai shikenan, saidai fa Mimi kiji da kyau, wallahi duk randa na fuskanci akwai cin amana a tafiyar nan ta mu wallahi zaki sha mamaki na, indai har kina so na Mimi ni mai iya jure duk wani wulak'anci ne saboda ke, amma ki wulak'anta ni akan wani? Wannan abu ne da ba zan d'auka ba ko kad'an, akan kuma haka zan iya komai wallahi." Tunda ya fara magana ban da gwalo da marmad'a masa ido babu abinda take yi tana turo baki da jan tsaki, saida ya kai k'arshe tace "Me zaka iya yi to? Ba zaka hak'ura ba kenan? Amma ai kasan ance *matar mutum* k'abarinsa ko?" Cike da tabbaci yace "Haka aka ce, iya gaskiya na gad'a miki Mimi, wallahi saidai duk mu rasaki daga ni har masu son na ki." Da d'an k'arfi tace "Kamar ya duk ku rasani? Kasheni zakayi?" Tab'e baki yayi yace "Kusan haka." Wani murmushi kuma ya saki yace "Mimi ina da zuciya da bana so ki san kalarta, saida safe kawai ki kula min da kan ki." Datse kiran yayi ta bi wayar da kallo, sai kawai ta tab'e baki tace "Baka da wuta, baka da aljanna, ba a hannunka arzikina yake ba, dan haka baka da rayuwa ko mutuwa, banza jahili mummana kawai." Da haka ta k'arasa gida, da sallamarta mamanta ce ta fara kllonta tace "Sai yanzu daga siyan maganin?" Saida ta sunkuya ta mik'a mata tace "Mama da k'yar fa na tsallaka titi, kinsan dare baiyi ba sosai?" Shigewa tayi d'aki ta cire hijabi ta haye gadon k'arfen mai rumfa da knarfi hakan yasa ya shiga d'an yin k'asa da sama da ita tana lilawa, wayar ta ciro bayan ta rage haskenta duka ta shiga chat da k'awayenta, ta wani b'angare kuma tunanin sheikh take yi, sai kawai ta tab'e baki tace "Watak'ila ma ko taimako ne zaiyi wa Abbana." D'aga kafad'a tayi alamar ohon d'in nan, hakan yayi daidai da shigowar kira a wayarta na bak'uwar lamba, wani sharme ta saki ganin wata k'asaitacciyar lamba mai tsari da sauk'in hardacewa a kai, saida ta gyara kwancinta ta kashe murya sosai ta d'auka tayi shiru, daga wajenshi ne ya fara fad'in "Amincin Allah su tabbata a gareki *maah*." Wani sanyayyen murmushi ta saki tayi shiru kamar ba zata amsa ba, sai kuma ta lusmhe idonta tana tsinkayo amon muryarta tana fad'in "Kai ma haka, *bak'o*." Murmushi yayi har tana jin sautinshi kafin yace "Ba sunana bak'o ba, sunana *Ashraf Sabi'u Aliyu Sharif*, amma dai dayawa daga cikin mutane sun fi kirana da *Asas*." Jim tayi tana sauke numfashi tana jin yanda muryarshi ke ratsata, a sanyaye ta sake maimaita "Asas?" Da fara'a yace "Eh, amma fa ba sunan gaskiya bane, gaba d'aya sunana dana iyayena ne aka had'a akayi abr茅g茅 suka tayar da Asas, lokacin ina makaranta ne aka lak'aba min shi." D'an murmushi tayi tace "Asas." Murmushi yayi yace "Da alama sunan ya miki dad'i ko? To nawa zaki siya sai ki d'auka gaba d'aya na bar miki." Murmushi tayi tace "Ban siya ba, idan na siya ai b芒 zan samu alfarmar kiranka da shi ba." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Maah, ina *sonki*, ke ma kina so na? Zaki iya bani dama na zama abokin rayuwarki." Lumshe ido tayi ta sauke wani numfashi, haka kawai taji wata k'walla kamar yau aka fara fad'a mata kalmar nan, bud'a ido tayi ta sauke numfashi tace "Zanyi tunani a kai." Waro idonshi yayi yana sake kallon shukokin da iska ke d'an kad'asu, kai duk yanda aka yi yarinyar nan yar sarkin abzin ce, dan wannan shan k'amshin nata da ajin abun ba'a cewa komai. Wani numfashi ya sauke yace "Maah ki taimake ni, ina sonki da zuciya ta, ina son aure sosai a rayuwata, ki amince min na zo gidanku ta yanda ba zan sha wahala ba kafin dogaren gidanku su barni shiga." Da mamaki tace "Dogarai? Wane iri?" Da d'an sauri yace "Oh! To ina nufin jami'an gidanku?" Tashi tayi zaune ta gyara zamanta da kyau tana k'arewa d'akinsu kallo tace "Ni ba 'yar kowa bace, k'yalek'yale ne kawai na zamani ya haskani, mahaifina talaka ne da a kullum saiya fita yake samo mana abinda zamu ci, mahaifiyata ba 'yar kowa bace ita ma, duka iyaye na suna da wata baiwa da Allah ya hallicesu da ita, watak'ila kai ma idan ka gansu ka tuna cewa su suka haifeni zaka iya gano wannan baiwar, karatu na ba wani mai zurfi bane, a matakin bac kawai na tsaya, islamiyya ce har yanzu nake kai kuma ina ci gaba da nema har gobe, a tak'aice ni ce *Maryam Adam Shehu*." Wani basaraken murmushi ne ya kubce mishi ba dan komai ba saidan jin dad'in yanda ta fad'a masa gaskiyar wacece ita, kai lallai ta dabance wannan, saidai wace irin baiwa ce take magana a kai? Ajiyar zuciya kawai ya sauke yace "Maah, naji dad'i sosai yanda kika fad'a min wacece ke? Na yarda dake d'ari bisa d'ari, kuma ni dama nasan bakiyi kama da wacce zata iya cutar da kowa ba, Naana ki min alfarma d'aya dan Allah?" A hankali tace "Wace irin alfarma?" Cikin zumud'i yace "Ki min alfarma na zo gidanku, a gaban mahaifinki zan durk'usa na nemi ya taimaka ya bani aurenki, wallahi zan kula dake Mimi, zan tallafi rayuwarki data iyayenki da dama duka yan uwanki, dan Allah na rok'eki kinji." Shiru tayi tana sakin murmushi mai tsadar gaske, jin bata amsa ba yasa shi saurin cewa "Dan Allahhhh! Kada ki ce a'a mana mai sunan mamana, Hajiata tana da tausayi da kawaici, sannan ga ta da magana d'aya tak, dan Allah ki kasance mai irin halinta kema." Yanda yake mata magiyar yasa ta cewa "Shikenan na ji, a karon farko na ji kaine mutum na farko daya shiga zuciyata, na amince Asas." Da wata irin k'ara ya saki ihu a kunnenta yana fad'in "Yess! Yess! Ta amince, kai naji dad'i sosai, maah, insha'Allah gobe zan zo gidanku na ga Abbanki, idan ya amince ya bani ke saina turo mgabata na, amma fa maah ni maraya ne uwa kawai gareni, amma ina da wanda ya zame min kamar uba, sheikh." Murmushi tayi tace "Daga gobe zamu yanke kai maraya ne ko akasin haka, idan Abba na ya amince zaka zama kana da mahaifi kai ma." Murmushi yayi yace "Nagode da wannan karramawar Mimi, sai kin ji ni gobe." Jinjina kai tayi tace "Saida safe." Shi ma a nutse yace "Saida safe *beaut茅* (beauty)." Lumshe ido tayi har taji ya datse kiran, wani farin ciki ne ya mamayeta ta shiga murna sai kawai ta kashe wayar gaba d'aya ta gyara kwancinta jin mamanta na fad'in "Amir shi ga ka ga wai Mimi tana ciki kuwa?" Tan jin shi ya shigo ya fita yana fad'in "Mama bacci take." "Bacci?" Ta maimaita da mamaki. Bata sake fitowa a d'akin ba har baccin na gaskiya ya d'auketa, saida mamansu ta mik'e ta shiga d'akin ta daddab'ata, tana bud'a ido tace mata "Nan kike kwana ne?" Saukowa tayi daga kan gadon tana murza ido tace "Mama an gama shinfid'ar ne?" Dak'uwa ta mata tana fad'in "Ni ce zan miki shinfidar?" Hanyar fita ta nufa cikin sumalin bacci mamanta tace "Ke zo nan?" Dawowa tayi ta zube durk'ushe dan a tsaye take ita, da hannu ta mata alama tace "Mik'e tsaye." Mik'ewa tayi amma duk da haka saida ta d'an rank'wafa sabida nauyi take ji sosai ta tsaya a kansu kamar zata ci tuwo a kawunansu, matsawa maman tayi ta jawo rigarta tare da zura hannunta a k'asan rigarta, a tsiyace taja baya tana fad'in "Mama?" Wani kallo ta mata tace "Ba ki da gaskiya kenan?" Girgiza kai tayi tace "A'a mama, ba abinda nayi fa." Da d'an gajeran hannunta tace "To zo nan." Sunkuyawa tayi cikin dubara ta yaran zamani ta zage wayar dake k'ugunta tayi baya da ita ta b'oye, tana ji ta shiga zura hannunta a cikin rigarta saida ta kai kan mamanta, dama rigar t-shirt ce dan haka ta fizge bras d'inta da k'arfi tana fad'in "Wannan jarabar ba zaki dinga cirewa kina hutawa ba." Tsaki tayi tare da damk'ar nononta na dama da k'arfi, cije leb'e tayi ta rintse ido tace "Washhhhhh!" Zage hannunta tayi tana mata kallon tuhuma tace "Me yasa nonuwanki keta cika suna batsewa Mimi?" Girgiza kai tayi tana sunkuyewa tace "Ba komai Mama." Sama da k'asa ta kalleta tace "Kin tabbata?" Jinjina kai tayi, k'ofa ta nuna mata alamar ta wuce, saida ta b'oye hannayenta a cikin riga kafin ta fice a d'akin, ganin har su Yaseen ba'a musu shinfid'a ba yasa ta jan tsaki tace "Yanzu nan duk sai nayi shinfid'ar nan?" Cikin hushi ta shiga shinfid'a musu tabarmarsu da ta ta wacce suke kwana da mama, duk da wani lokacin ta kan farka a tsakiyar dare ta nemi maman ta rasa, amma kuma idan aka wayi asuba zata ganta a gefenta (馃槑 Yo mamana ina Abba yake? Caskalewa ake). *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:51 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa. Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai. Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa. _Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._ _'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_ Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *9* Washe gari ta tafi makaranta kuma kamar kullum ana shiga hutun minti talatin duk suka had'e wuri d'aya dan ayi hirar duniya, saida ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta kalli Jamila dake kallon IPhone d'inta tana fad'in "Wai Mimi da gaske jiya ya baki wayar nan? Kai ina ma ni ce wallahi ta birgeni sosai." Wani malalacin murmushi tayi tace "Kinga ban fad'a miki ba, jiya fa mutuminki na had'e dashi har mukayi magana baki da baki." Da sauri ta kalleta tace "Shapi'u?" Harara ta dalla mata tace "Mayyar Shapi'u, to uban Shapi'u." Dariya su Asma'u suka saka duk da dai basu gama shiryawa da ita ba, turo baki Jamila tayi tace "Mimi ban son cin zarafi, surukin nawa?" Tab'e baki tayi tace "Kinga ni sheikh na had'u dashi nake son fad'a miki." Da farin ciki tace "Lah! Sheikh Bala?" Cikin jin haushi tace "Ke sheikh Balan wa? Sheikh Abdul Waheed nake fad'a miki, haba." Ta k'arashe da d'auke kanta, duk zaro ido sukayi Jamila tace "Sheikh Abdul Waheed?" Asma'u kuma kallonta tayi tace "Mimi ban sonki da k'arya ba fa, a ina kika ganshi ke kuma?" Hararanta tayi tace "Tunda kinsan haka me yasa zanyi muku yanzu? Da wacce nake jin tsoro a nan?" Jamila ce tayi saurin cewa "To ina kika ganshi?" Gyara zama tayi tace "Jiya da dare ne na je siyowa Yaseen maganin zazzab'i, kawai na ganshi zai tsallaka titi har ya min magana..." Yanda ta fad'a musu duk abinda ya faru yasa Jamila cewa "Tabb'! Mimi sheikh Abdul waheed ne fa aka ce mai bawa gwamna shawara akan harkar ilimi, sannan an ce shi kad'ai mahaifinshi ya haifa, kuma mahaukatan bilyoyi ya gada fa, uwa uba ga ilimin addini da Allah ya bashi, a hakane zaki ce kin ganshi a kan titi har ya shiga mota ya tuk'a? Mutumin da a wa'azi ma mutum biyu ne a bayanshi." Cikin jin haushi ta kallesu su ukun tace "Yanzu mak'aryaci kuka d'aukeni ko me? Kun dai kunsan mutumin nan ba birgeni yake ba bare na yi k'aryar had'uwa da shi, tayiwu fa kawai sun san juna da Abbana ne." Duk wani shek'ek'e suka kalleta alamar sam zancenta bai samu karb'uwa a wajensu ba, dan haka cike da alfahari tace "Ban wayata ke na nuna miki sanfiri." Mik'o mata wayar Jamila tayi tana sake tab'e bakinta, karb'a tayi ta shiga jerin t茅l茅phone d'inta, lambar data gani mai jan rubutu data nuna an kira ba'a d'aga b芒 ta danna wacce ta mata kama sosai data Asas wacce ta sakawa sunan *d'an beauty*. Tana jin wayar ta fara k'ara tayi saurin sakawa a amsakuwa tana nuna musu su mayar da hankali kan wayar, duk zubawa wayar ido sukayi kamar zai fito daga ciki. Ana d'agawa ta sake nutsuwa ta shiga caracterta ta jiya a gaban ustazu tayi shiru, daga b'angarenshi ne ya rangad'a sallama a sanyaye sosai, saida ta kalli Jamila kafin tace "Wa'alaikumus salam, barka." Da sauri Asma'u ta k'yafaceta a kafad'a tana mata nuni da ido da hannu "Sheikh d'in zaki ce wa barka?" Yatsina fuska tayi da sauri ta kalli wayar tana sauraren yana fad'in "Ryam antashi lafiya?" A sanyaye ta amsa da "Lafiya lau sheikh." A hankali yace "Ba sheikh ba, Abdul, ki kirani da Abdul Ryam hakan zai sa na ji nima bawa kuma ba kowa ba." Da ido ta musu alamar ba kun ji ba? Ai na fad'a muku, jinjina kai sukayi suka sake kafe kunnuwansu, a nutse cikin murmushi tace "Wacece ni da zan sake maimaita wannan kuskuren, na jiya ma sub'utar baki ce." D'an murmushi yayi har tana jin sautinshi kafin yace "Na so hakan, kuma akwai lokacin da zai zo na tursasaki fad'ar Abdul." Da alamar tambaya duk suka kalli junansu, a nutse suka sake jin muryarshi yace "Ryam Abbanki ya dawo ne?" Cikin rarraba ido tace "A'a bai dawo ba." Rik'e hab'a Asma'u tayi alamar mamakin nan tana kallonta, cikin taushin murya yace "To me yasa kika kirani?" Cikin murmushi tace "Tun jiya da kuke kira ne sai naji bana jin dad'in ganin lambarku a jan rubutun nan, shiyasa na karb'i wayar a hannun mama na kira." Duk mamaki ne ya kusan kashe su Asma'u dake kallonta da saurarenta, ita kam ko a jikinta saima saurarenshi yana fad'in "Ba kina islamiyya ba?" Da "Eh ina yi." Ta amsa, kallon agogo yayi a lokacin yace "Amma naga 10:14, kuna hutu ne ko?" Jinjina kai tayi tace "Eh dake yau ban je islamiyya ba, saboda k'anina da baya da lafiya, jiya ma magani na siyo mishi muka had'u, shiyasa na zauna taya mamana aiyukan gida da kula dashi." Cikin jin dad'i yace " Masha'Allah, Alhamdulillah, na ji dad'i sosai da kika kirani, na kuma gode." A ladabce tace "Nima nagode, muna barar addu'a." Lumshe ido yayi daga inda yake, to wai me yasa kowa ke fad'an hakane? Shin bakinshi yafi na kowa tsarki ne? Ko kuma waliyi ne shi da aka bugawa hatimin waliyantaka? D'an sauke ajiyar zuciya yayi yace "Insha'Allah, nima ina barar addu'arki." Tana cikin k'yak'yabta ido yace "Zan sake kiranki anjima, ina wajen aiki ne." A sanyaye ta amsa mishi sukayi sallama ta kashe kiran, cike da kuri da k'apapa ta shiga kallonsu a sama tana fad'in "Me na fad'a muku? Mak'aryaciya kuka d'aukeni ba." K'wafa tayi ta mik'e tsaye cikin takon kuri da isa da k'asaita ta fita a ajin dan neman abinda za ta ci, kallon da Asma'u ta bita dashi ne yasa Jamila fad'in "Ke daina kallonta, Allah ne ya bata farin jinin nan sai hak'uri." Harara ta galla mata tace "Na ce miki ina haushin hakane, ai baiwarta a jikinta take." Sai lokacin kawai Aisha ta samu damar fad'in "Wallahi ni har birgeni take, farin jini ne da ita kamar k'asa mai tsarki, da babba da k'arami da tsoho da yaro mai kud'i da talaka kowa son ta yake." Jinjina kai Asma'u tayi tace "Shiyasa ai take murza kambunta yanda take so." Jamila ce tace "Kamar yanda idan ta shiga gidan sai labari ba." Asma'u ce tace "Gaskiya ne kam, dan tana aure komai zai zama tarihi." *Asas* Kafeshi tayi da ido har ya gama d'aure takalminshi k'afa ciki ya mik'e yana sake nad'e hannun rigarshi, girgiza kai tayi tace "Yanzu Ashraf idan ka fita a haka waye zai kalleka yace d'an musulmi ne kai? Me yasa ba ka jin magana a kan saka k'ananan kayan nan." Kallon kanshi yayi ya langab'e kai yace "Hajia basu min kyau bane?" Hararanshi tayi tace "Wane maganar kyau ina maka maganar kimarka? Kasan da ko sheikh ya sha yi maka magana a kan saka irin kayan nan amma ka k'i ji." Numfashi ya sauke ya had'e hannaye yace "Zan daina Hajiata." "Yaushe?" Ta fad'a cike da katsalandan, murmushi yayi yace "Da zaran nayi aure, dan bana so 'ya'yana su tashi su ganni a haka." Wata hararar ta masa tace "Oho! Kenan kai ma kasan ba abun kirki kake yi ba?" Girgiza kai tayi ta dora da fad'in "Allah ya sawak'e." Saida ya matsa kusanta ya sumbaci kuncinta kafin yace "Hajia zan tafi saina dawo." Cike da gargad'i tace "Ashraf, bana so ka jima a wajen nan kamar yanda kayi jiya, ka dawo da wuri kaji." Girgiza kai yayi yace "Hajia, me yasa kike damun kanki dani kamar wani k'aramin yaro? Na fad'a miki a茅roport kawai zan je saboda maganar tafiyarmu, daga nan kuma gida zan dawo." Cikin rashin yarda ta nuna shi da yatsa tace "Da gaske zaka dawo yanzu?" Rik'e yatsarta yayi yace "Da gaske hajiata, wai me ye duk na damuwar nan? Naji sauk'i fa sosai Hajia, kuma ba gashi jiya har na samo miki wacce zata zama sarakuwarki ba." Turo baki tayi irin shagwab'ar nan tace "Ba wani nan, har yanzu bata zama ba tunda sheikh yace sai ya gamsu da tarbiyarta." Mik'ewa yayi tsaye daga rank'wafawar da yayi yana fad'in "Zai ma gamsu Hajia, na yarda da yarinyar sosai." Jinjina kai tayi tace "Ashraf ina sake jadadda maka karka jima, idan ka wuce azahar zan fita nemanka da kaina." Zaro ido yayi yace "Hajia nema na kuma? Anya kuwa zan iya yin aure nayi nesa dake?" A marairaice kamar zatayi kuka tace "Nima abinda na fara tunani kenan, Ashraf larurar ciwon cikin nan naka ne yafi komai d'aga min hankali, shekara bakwai kenan ana fama babu likitar da bamu je ba, magani babu daga k'asar da ba'a aiko mana ba amma shiru, idan kayi aure kuma ba kowace mace ce zata iya jinyar ka ba, dan haka zan so ka zauna kusa dani, yanzu kaga fa wata biyu daya wuce daga waje abokanan ka suka kaika asibiti a some baka san inda kake ba." Tallabo kumatunta yayi duka biyu yana fad'in "Hajiata, ki kwantar da hankalinki dan Allah, ina ji a jikina auren da zanyi shine silar warakar duk wani ciwo nawa insha'Allah." Jinjina kai tayi tace "Da gaske haka kake ji?" Jinjina mata kai yayi alamar eh, ita ma jinjina kai tayi alamar shikenan tare da fad'in "Allah ya yarda." Lumshe ido yayi yace "Ameen, saina dawo ko?" D'aga kai tayi tana kallon fuskarshi, juyawa yayi zai fita ya d'aga mata hannu yace "Banda yawan kirana kuma karki fito nemana Hajiata." Dariya tayi ta gyara zamanta a kan kujerar tana girgiza kai. *Maryam* Kwana biyun da bata lek'a ba yasa Maimuna aiko yaro kiranta, mik'ewa tayi duk da magriba ta kawo kai ta shiga gidan, da alama ta gama duk aikin gidanta zaune take ita kad'ai, dama bata tab'a haihuwa ba in kaga yara na mak'wabta ne. Da sallama ta shigo hakan yasan Maimuna amsawa tana fad'in "Mimi ina aka shiga kwana biyu shiru ba'a lek'o ba?" Dariya tayi tana zama kusa da ita tace "Wallahi aunty Maimuna karatu ne, kuma kinsan ni bana zuwa haka kawai in ba wani film ake mai kyau ba." Ita ma dariyar tayi tace "Na sani, shiyasa ma da naga sun saka wannan nace su kiraki, nasan ke gwanar kallon film d'in india ce saboda soyayya." Murmushi tayi tana kallon tvn data nuna mata, tabbas tana son film d'in sosai saboda soyayyarshi da kuma nishad'i da yake sakata a ciki, amma fa ita bata cika son mai-mai ba, bata son ta kalli abu yau ta kalla gobe, dan haka tayi shiru kawai ba tace komai ba, Maimuna ce ta mik'e tana fad'in "Bari nayi alwala an kusa kiran sallah." Ita ma mik'ewa tayi tana fad'in "Aunty bari nima na tafi nayi sallah saina dawo anjima." Kallonta tayi a maraice tace "Haba Mimi ki zauna mana kiyi sallahn a nan, wallahi gidan shiru ban da abokin hira duk ba dad'i." Murmushin yak'e kawai ta mata ta jinjina kai, cire hijabinta tayi dan ita ba mutuniyar son zama da hijabi bace tana fad'in "Bari nayi alwala to." Da kallo Maimuna ta bita, kai ita dai wallahi hallitar yarinyar na birgeta, kukkukup da ita digir-digir, kawai abinda ta fahimta Mimi irin mutanen nan ne da ko dusar dabbobi suka ci sai sunyi b'ul-b'ul, kumarinsu ba daga cin abinci bane hallita ce kawai. Dan yanzu ma riga da zane ne simple d'inki a jikinta, amma zanen sai ya mata hegen kyau k'ugunta na kad'awa sosai, ga rigar kamar dai sauran rigunanta ne masu tsayawa a iya kumkumi kawai. Farfajiyar ta fita tayi alwala a bakin panpo ta dawo ta d'auki hijab d'inta a lokacin an fara kiran sallah, sallaya ta d'ora suka kabbara sallah a tare har aka idar, suna gamawa Maimuna tare "Mimi zaki ci abinci?" Girgiza kai tayi tace "A'a Alhamdulillah." Mik'ewa tayi tace "Ina zuwa to." D'akinta ta shiga ita dai tana kallonta, jim kad'an ta dawo ta zauna tana aje wasu kaya a gaban Mimi tace "Mimi zab'a min wanda suka fi kyau a ciki? Ku ne yan zamani fa." Dariya tayi tana k'arewa kayan baccin kallo, a hankali ta shiga dubawa saida ta cire guda uku ta mik'a mata tace "Aunty Maimuna kamar wannan sun fi ko? Kinga kalarsu ma ta dace da yanayin dare da kuma d'aukar hankali namiji, sannan sun fi sauk'i yakicewa a jiki." Da mamaki Maimuna ta kalleta tace "Haka abun yake Mimi?" Kunya ce ta kamata ta rufe ido tace "Haka dai nake tunani." Jinjina kai tayi tace "To zab'a min wanda zan saka yau, kinsan fa Alhaji baya nan yayi tafiya amma zai shigo anjima." Da tsantsar kunya ta nuna mata kalar fari tace "Ki saka wannan aunty, sannan ki shinfid'a zanin gadon da zai dace da kalar kayan, har labulenki ma idan zai yiwu komai ya zama kala d'aya." Da farin ciki tace "Da gaske?" Jinjina mata kai tayi, cikin rarrashi tace "To mimi ko zamu je ki tayani saina canza d'in, na gyara komai wannan ne daai banyi tunani ba." Murmushi ta mata tace "Ba komai aunty." Mik'ewa sukayi inda Mimi ta sake cire hijab d'inta ta aje suka shiga d'akin, komai a gyare yake a kimtse, dan Maimuna kam ba k'azama bace ko wata wawuya, farin zanin gado mai kyau ta mik'owa Mimi ta karb'a ta d'auke waccen ta d'ora farin, ita kuma ta taka kujera ta cire labulayenta ta saka farare dan dama guda biyu ne a d'akin, bakin k'ofa da kuma tagar dake jikin bayan gado, suna gamawa Maimuna tace "Shikenan?" Da d'an mamakinta ganin ko ba komai fa shekararsu shida da aure amma tana tambayarta ita da bata da auren, cikin rashin sakewa tace "Eh to ai har kun gama girki, zaku iya zuba abincinku a kwanukan da zasu dace da wannan kalar ma, sannan kuyi shigar da kuka san zata faranta mishi kuma yake so." Fita sukayi daga d'akin da haka a sannu sannu har saida suka sha aiki ba kad'an ba, dan har jus saida Mimi tasa suka had'a, ita fa ba k'warewa tayi ba, kawai a harkar kalle kalle ne da karance karance duk ta iya wani salon kinibibi, da kuma wannan take tak'ama ko yau aka kaita gidan mai mace uku zata iya zama kuma ta birge. Amir ne ya shigo da sallama suka amsa mishi, kafin yace komai Mimi tace "Kira na ake?" Girgiza kai yayi yace "Mama ce ta ce na zo na duba idan kina nan, sannan na ji wai aiki kika ma aunty Maimuna." Da fara'a Maimuna tace "Allah sarki, Amir ka fad'awa Mama aiki ne take kama min, amma har mun kusa kammalawa ma." Juyawa yayi yana fad'in "To." Da kallo Mimi ta bishi yanda yake tafiya da k'arfinshi k'undul k'undul, mayar da hankalinta tayi kan lomar da take tace mata dafaffiyar mazark'waila da karanfani. Mik'ewa Maimuna tayi tana fad'in "Bari na shiga ko wanka nayi kafin ki tace na fito sai ki tafi gida Mimi tunda an fara nemanki." Jinjina kai tayi alamar gamsuwa, shigewa tayi ita kuma ta ci gaba da tacewa, tana idawa ta d'auki madara peak d'in ta fasata ta juye mata a ciki haka ma maltina, d'auka tayi ta kai mata fridge ta aje, kankanar da suka yanyanka ta d'auki yanka d'aya ta juyo tana kai wa bakinta hannunta d'aya kuma tana gyara gashinta daya d'an sauko mata a kan goshi duk ya jik'e da gumin da take yi kasancewarta mai yawan gumi a kai musamman idan bata da kitso. Cak ta tsaya tana neman sark'ewa saboda ido hud'u da sukayi da Alhaji Saminu, kallon tashin hankali daya wuce k'a'ida ne yake mata kamar zai afka mata, ya kasa ko motsawa bare ya had'a ko da yawu. A gaskiya dole ya samu yarinyar nan dan in ya rasata zai shiga matsala a yanda ya jima da soyayyarta, indai kud'i na samawa mutum alfarma to ba shakka zai kashe ko nawa ne ya sameta, ta mishi a yanda yanzu yake son ganin mace, komai na ta birgeshi yake, uwa uba wasu wadatattun mazaunai da Allah ya bata. Da k'yar cikin k'osawa da tsaarguwa tace "Sannu da zuwa, ina wuni." Da sauri ta dawo dashi hayyacinshi yana washe baki da fad'in "Sannu Mimi, aiki ake ne? Sannu ko? Kina lafiya?" D'an murmushi kawai ta yak'o masa tace "Um." Takowa ta fara yi dan ta d'auki hijabinta ta bar gidan, amma saiya gyara tsayuwa ya shiga k'ure gabanta da kallo zuwa wuyanta dake wani mul-mul dashi. Saida ta zo daf dashi zata wuce duk da kuwa kayan data gani a hannunshi nik'i-nik'i kawai ta ji ya rik'e hannunta ram a ciki na shi yana binta da wani kallo. A tsorace kuma a gigice ta kalleshi tace "Subhanallah, kawu..." Bai bari ta k'arasa ba ya aje ledojin hannunshi ya damk'a mata wata ledar yana sake murza hannunta yace "... *Asma'u* *Aminatu* *Rabi'atu* (Bintu Yusuf) *Yagana ta* *Rahamah* (Mom) *Maryam* (Mom) *Pretty Aeeshartyy* _Sannunku da k'ok'ari, Allah ya saka muku da alkairi, comment d'inku yafi na kowa._ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:52 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *10* Bai bari ta k'arasa ba ya aje ledojin hannunshi ya damk'a maya wata ledar yana sake murza hannunta yace " Wannan na ki ne Mimi, ki rik'e kinji karki ce a'a." Da k'arfi ta ja hannunta ta raba da nashi tana binshi da wani fitanannen kallon mamaki, sake matsawa yayi daf da ita murya k'asa k'asa yace "Mimi lafiya? Kinga ki saurareni, indai zaki amince ki aureni wallahi zan miki komai a rayuwar nan, zan d'auki nauyin karatun k'annanki, zan canza muku gida na sabinta muku rayuwarku, Mimi amincewarki kawai nake buk'ata." Da sauri ta ja baya saboda hannunta da yayi k'ok'arin kamowa, a razane cikin al'ajabi tace "Aure na fa? Ni d'in? Aunty Maimuna fa?" Sake matsawa yayi ya samu kusanci da ita sosai yana fad'in "Mimi ai ba haramun bane, ina sonki wallahi kuma zan aureki, ki amince kin ji." A kid'ime ta girgiza mishi kai tace "Gaskiya ba zan iya ba, kayi hak'uri kawu." Da sauri ta k'arasa kan kujerar da hijabinta yake zata d'auka, tana juyowa suka had'e dan yana biye da ita ne, kamar jira yake dama a samu wannan tsautsayi sai kawai ya k'arasa rumgumeta jikinshi har rawa yake kar-kar-kar dan jaraba, dan shi fa irin mazan nan ne da kalami kawai zai iya tsumasu bare su ganki zahiri, ji yake kamar ya shige da ita d'akinshi ya samu sauk'i da sukuni, yana hawaltuwa sosai da azabtuwa akan yarinyar, siririyar ihu ta k'walla dan a rayuwarta haka bai tab'a faruwa ba sai yau, da sauri ya d'ora hannunshi ya rufe mata baki yana fad'in "Shiiiii! Haba mimi kamar ba wayayya ba." Iya k'arfinta ta saka ta tureshi tare da fita a guje rik'e da hijabinta tana kukan takaici, duk da nauyin jikinshi bai hanashi shiga tashin hankalin da shi ma ya bi bayanta ba yana kiran "Tsaya, tsaya na ce." Ganin bata saurarenshi yasa shi hangen mai gadi yace "Karka bari ta fita." A gigice ta tsaya ta juyo ta kalleshi saboda mai gadin daya shiga kakkarwa rufe k'aramar k'ofar, kar ta fita yake nufi? Me zai mata? Tana ganin ya kusa k'arasowa ta durk'usa tana kuka tace "Dan Allah ka k'yaleni na tafiyata gidanmu, ni ba zan koma zuwa nan ba." Yana zuwa sunkuyawa yayi ya kamo hannayenta ya mik'ar da ita tsaye, janye jikinta tayi daga na shi ta ja baya, cikin sigar rarrashi yace "Mimi ba zaki aureni bane? Ina sonki wallahi so na aure, ki fad'a min duk abinda kike so a duniyar nan zan miki shi da yardar Allah." Girgiza kai tayi hankali a tashe tace "Ba zan iya ba, ba zan iya aurenka kawu, bamu dace ba ko kad'an." Numfashi ya sauke yace "Kar ki ce haka mana Mimi, miye a cikin rashin dacewar m没 to? Ina sonki kuma ke ma zaki soni da mun yi aure, ina da kud'i zan iya baki komai kike so." Cikin b'arin jiki ta kalli fuskarshi tace "Kud'i basu dameni ba, dacewata da mutum ita tafi komai mahimmanci a gareni, ba zan iya auren wanda bamu dace ba." Juyawa yayi ya kalli k'ofar d'akin saboda tunanin kar Maimuna ta fito sannan ya kalleta yace "Yanzu dai ki tafi kinji, zamuyi magana dake a waya, bani lambarki?" Ya fad'a yana mik'a mata wayarshi, a tsorace ta kalleshi tace "Ni bana da waya ai." Wani sakaran murmushi yayi yace "Mimi ni ba kamar sauran mutanen bane da kike ninkesu ta baibai, nasan kina da waya wacce saurayinki ya baki, ki saka min lambar a nan kin ji." Rarraba ido tayi cikin rashin gaskiya ta karb'i wayar tana fad'in "Dan Allah to karka fad'awa Abbana, wallahi hushi zaiyi dani." Girgiza kai yayi yace "Karki damu, bana son abinda zai b'ata miki rai ai." Saka mishi lambar tayi ta mik'a mishi wayar, karb'a yayi yana fad'in "Zan kiraki kinji sai m没 had'u." Jinjina kai kawai tayi ta juya ta fita zuciyarta kamar zata fito tsabar b'acin rai da kuma shiga rud'u. Sai a k'ofar gida ta saka hijab d'inta ta k'arasa shiga cikin gidan, Abbanta ta samu yana cin abinci akan tabarma, saida ta durk'usa tace "Abba sannu da zuwa." Da sakin fuska ya amsa mata da "Yawwa sannu Mimi, har kin dawo ne?" Jinjina kai kawai tayi dan shashek'ar kuka ce a lokacin ta zo mata, mik'ewa tayi ta k'arasa shiga d'aki ta cire hijabinta ta fito ta d'auki buta tayi alwala ta koma d'akin, ko da tayi sallah isha'i daga nan kan dardumar ta kwanta tana jin kamar ta daka ihu ta d'urawa Saminu ashar, dan ya sakata yanayin da babu mahalukin daya tab'a mata irin haka. Da wannan tunanin bacci ya d'auketa duk da tasan za'a ta kiran wayarta, amma bata damu ba tunda saida ta kasheta kafin ta saka a akwati, dan samarin na ta ba lissafuwa suke ba tsabar yawansu, kowa shi dai yana son ta kowa son yake yayi hira da ita, wani lokacin bata san d'aga waya ne dan tana magana da wani kiran wani ke shigowa, haushin wannan k'arar d'in-d'in-d'in kuma bata son ta. *Laraba* Ranar yau ta kasance ta musamman a wurinsu saboda farin cikin abinda zai riskesu, musamman da sukayi waya da rana ya sak茅 tabbatar mata zai zo anjima, hakan yasa ta wuni cikin farin ciki da mantwaa da b'acin ran data kwana dashi, amma fa sam bata nuna mishi wannan haba-haban ba saboda ita ta tsani rawar kai ga namiji ma bare mace. Tunda suka taso daga makaranta ta shiga sharar gidan tas, inda ta tura Amir a k'ofar gida tace ya share, dake lokaci lokaci ta kan yi haka sai Mama ba tayi mamaki ba, tana gamawa ta d'auki bokiti ta d'ibi ruwa a randa, d'aki ta koma ta cire kayan jikinta ta d'auro zani ta fito, duk'awa tayi zata fito daga d'akin a rashin kulawa yasa ta buga k'afarta a d'an dakalin dake bakin k'ofar, wata razanannar ihu ta saki tana kiran "Wayyo k'afata, mamana k'afata ta cire, wayyo Allah n..." Tsawar da mama ta mata tana fad'in "Dallah yi wa mutane shiru uwar rakin tsiya." Cikin hushi ta nufota dungui-dungui dan duba k'afar ta ta, d'an durk'usawa tayi tana kallon k'afar, wani dogon tsaki taja tana fad'in "Shirmen banza, ko gurjewa babu amma kike wa mutane wannan kukan." Cikin kukan shagwab'a tace "Mama Allah da zafi, baki ji yanda na ji ba." Juyawa tayi tace "Ai ke haka kike, da abunda ya kai na kuka da wanda bai kai na kuka ba haka kike, kina mace amma sai rakin sababi, dalilin da yasa kika yafe kitso kenan a rayuwarki, na ga yanda zaki rayu a haka." Turo baki ta dinga yi tana mik'ewa ta nufi ban d'akin, dan gaskiya mama ta fad'a tana da jin zafi sosai fiye da kima, tana iya yin kwana tana kuka akan d'an abu da bai taka kara ya karya ba, uwa uba idan aka ce watanta yayi, har ta gama ba zaka daina ganin hawaye a idonta ba, shiyasa duk gidan basa fatan rashin lafiya daga gareta. *Sheikh* D'an murmushi ya saki dan lamarin na Asas kam ya fara bashi dariya, daga had'uwa da yarinya shekaran jiya duk ya damesu da zancenta, fatanshi d'aya a kan yarinyar nan ta zama ta k'warai, kamar yanda shi ma ya had'u da tashi a shekaran jiyar, a tare yasa a binciko masa komai a game da 'yan mata da sunansu ma ya zama d'aya, Allah yasa na gari ne da zasu zama abokan rayuwarsu, wannan shi ne burinshi. Asas kam Hafsat yake kallo yana zuba mata zance da shirin tafiyarshi gidansu Mimi da zaiyi yanzu, hakan ne yasa *Abbakar* dake bi ma Eesha cikin ladabi yace "Amma dai tonton zan raka muje ko? Dan ina so na ga auntynmu." A sanyaye sheikh ya kalleshi yana sakin murmushi, cikin fara'a Asas yace "Kana son ganinta kai ma? Ni kaina yaro a matse nake, amma kayi hak'uri idan na fara samun karb'uwa a wajen iyayenta yau, kaga jibi sai mu koma ka ganta." Kallonshi sheikh yayi bai ce komai ba sai Hafsat da tace "Babu abinda zai sa ma su ce baka musu ba, zasu amince insha'Allahu." Da zulud'i yace "Allah ya yarda aunty." Wayar sheikh ce tayi k'ara babbar hakan yasa shi d'aukawa yana dubawa, mik'ewa yayi yana fad'in "Ina zuwa." Fita yayi farfajiyar su kuma suka ci gaba da hirarsu cikin nishad'i, yana fita ya samu wani yaronshi da ake kira *Mudanseer*, hannu ya bashi sukayi musabiha kafin yace "Ya ake ciki? Ka kammala abin da na saka ka." Kamar zai durk'usa ya sunkuya yana fad'in "An gama komai ranka shi dad'e, hak'ik'a a unguwar an bayar da shaida mai kyau a kan duka yaran, dan kusan kamar anguwarsu d'aya, wanda ya ban bayani a kan su ya fad'a min Maryam uku ke cikin layin, biyu 'yan mata sai d'aya k'arama, kuma duk kusan anguwar suna wannan islamiyyar ne dan ita tafi kusa dasu, a gaskiya dai babu wani b'atanci a kan duka biyun." Lumshe ido yayi ya sauke ajiyar zuciya yace "Nagode." Jinjina kai yayi yace "Sai dai kuma ranka shi dad'e d'ayar an fi kiranta da sunan Mimi, dan da k'yar aka samu wanda yasan asalin sunanta ma, an tabbatar iyayenta mutanen kirki ne, dan mahaifinta ma an ce yana zaune lafiya da kowa, d'aya Maryam d'in ce kuma a hannun kakarta tak ke wacce ta haifi babanta." Wani murmushi ya kuma saki yana tunanin kenan wacce ke hannun kakarta ita ce Maryam d'in Asas, shi kuma ta shi ita ce ke gaban iyayenta, numfashi ya sauke ya sake bashi hannu yace "Nagode sosai." Hannun ya bashi sukayi sallama ya fita shi kuma ya dawo falon kamar zaiyi tsalle dan murnan jin haka, dan shi yafi ma damuwa da Asas d'in saboda yanda ya ga ya zurma da yawa akan ta. Shigowarshi shi kuma ya mik'e yana fad'in "Sheikh, ka bani wani wurdi nan na neman sa'a." Yar dariya yayi ya girgiza kai yace "Bana da shi, ni ma nemanshi nake saboda abinda na saka a gabana." Hannunshi Asas ya kama yana murmushi yace "Ya ustaz muje na ji to miye haka? Kar fa a zo kai ma yarinya ka samu zaka k'arawa yayata abokiyar zama kamar yanda kake fad'a." Wata suka da Hafsat taji daga zuciyarta zuwa d'an cikin dake jikinta yasa ta saurin kallonsu tana mai tsaresu da ido, aje cokalinta tayi ba tare data d'auke idonta daga garesu ba, su kam juyawa sukayi suka fita sheikh na fad'in "Asas lafiyarka ita tafi damuna akan komai." Suna fita farfajiyar ya kalleshi yana gyara tsayuwa yace "Sheikh nagode sosai da k'ok'arin da kake akan gaanin na samu lafiya, na tabbata Alhaji bai bar amanarmu a hannun da bai dace ba, Allah ya bamu ikon faranta maka kai ma." Murmushi yayi yace "To miye a ciki? Mahaifinka namahaifina nono d'aya suka sha, mahaifina ne ya saki mahaifinku ya kama, duk abinda zan muku yan uwana na jini na yi ma." Jinjina kai yayi yace "Hakane, Allah ya saka da alkairi." Murmushi kawai ya masa yace "Saika dawo." Jinjina kai yayi yace "Addu'arka fa sheikh." Lumshe ido kawai yayi alamar to yana kallo har ya fita daga gidan a tsaleliyar hondarshi. Duk da ba had'uwa zasu yi ba amma haka ta shirya cikin ratsatsen leshen da Mas'ud ya siya mata a lokacin sallah, wani irin kyau tayi duk da b芒 kwalliya b芒 ce tayi mai yawa, turare ma yau na musamman ta bud'e a kwalinshi, d'an k'arami ne mai masifar sanyayyen dad'i mai sunan *mukhalat* ta shafa, mayafinta ta d'auka ta ce wa mama zata shiga gidansu Asma'u, bata hanata ba dan tasan mahaifinta ma yana k'ofar gida a lokacin dan ko sallah isha'i ba a yi ba. Tana shiga a soron gidansu Asma'u suka ci karo da yayanta da suke uba d'aya zai fita, tare gabanta yayi yana kallonta yana murmushi da fad'in "Mimi gari zaki tafi ne?" Fuska a d'aure tamau tace "A'a, kauce min a hanya." Wani murmushi ya kuma yi tare da gyara mata ta wuce ta barshi nan, tana shiga da sallama a bakinta, dayawa daga cikin mutanen gidan ne suka amsa har da Asma'u, idon kowa a gidan a kan ta yake yayin da suke shak'ar k'amshin tufafinta dana jikinta daya gauraye illahirin gidan, kowa zuciyarshi na girgiza tana jijjiga akan lamarin yarinyar. Mimi kam ko a jikinta sai ma hannun Asma'u data kama suka shiga d'aki tana fad'in "Wai ke miye haka? Dubi fa yanda kika yi wani gamin gambiza riga daban siket daban, a hakane zaki samu saurayi?" Tsaki tayi sai Asma'u data fahimci yau kanta take neman juyewa kawai tace "Ina zaki je Mimi kikayi wannaan shirin haka?" Murmushi ta saki tare da cire mayafinta ta aje akan gadonsu dake shirge da kaya tace "Ko ina, bana fad'a miki Asas zai zo wajen Abba ba, shiyasa na baro gidan." Wani murmushi tayi ita ma tace "Allah dai ya nuna min Abba ya amince da Asas d'in nan ko hankalina ya kwanta." Kallonta tayi tace "Idan Abba ya amince saina baki kyautar jaka goma." Zaro ido tayi tace "Jaka goma fa? Ina ma laifin jaka guda." Yatsina fuska tayi tana gyara zamanta da wayarta a hannu, bud'e tsaron wayar tayi ta shiga d'an daddanawa, hira suka dinga yi da Asma'u har aka kira sallah isha'i ta saka hijabin Asma'u ta kabbara sallarta dan da alwalarta dama, tana gama akan sallayar wayarta ta shiga vibration, d'auka tayi tare da sakin murmushi, Asma'u kanta murmushin tayi tace "Tunda na ke dake ban tab'a ganin an kiraki a waya kinyi murmushi ba sai yau, Asas kai d'an baiwa ne." K'ala bata ce ba ta d'auki wayar ta d'ora a kunne, daga b'angarenshi yace "Maah, barka da dare." A sanyaye cikin b'oye farin cikinta ta k'irk'iro muryar gajiya da kasala ta saka tace "Barka, ya kake?" Da fara'a yace "Komai ba daidai ba daga yanzu har sanda zan k'araso gidanku mu tattauna da Abba." A hankali tace "Uhumm!" A shagwab'e cikin sangarta ta autanci yace "Maamah, dan Allah ki tayani addu'a Abba ya bani ke." Da mamaki tace "To wai me ye idan ka rasani, ka daina jin tsoron zai hana maka ni mana, ka sameshi kan ka tsaye kawai." Saida yayi kamar zaiyi kuka yace "Shikenan to, amma Mimi ni kad'ai nasan tashin hankalin da zan shiga idan na rasaki." D'an murmishi tayi tace "Ba zaka rasani ba insha'Allah." A tausashe yace "Allah ya amince." Shiru ne ya d'an biyo baya kafin sukayi sallama a lokacin ya kawo daidai da kwatancen data mishi tunda rana. Fitowa yayi daga motar yana gyara rigar shaddarshi gezna kalar ruwan k'asa mai duhu sosai wacce aka ma gajeren d'inki ya mishi kyau, saidai babu hula a kan shi sai gyaren kai irin na matasan zamani. Abba ne dasu Yaseen wanda yaji sauk'i suka jero sun dawo daga masallaci, ganin zasu shiga gidan yayi saurin matsawa yana musu sallama, Abba ne ya amsa tare da mik'a mishi hannu, lura d'脿 yayi irin hallitar Allahn nan ce ta gajerun mutane yasa Asas cikin ladabi yace "Dan Allah Baba gidan malam Adam nake tambaya?" D'an juyawa Abba yayi ya kalli Yaseen da Amir kafin ya k'arewa Asas kallo, duk da shigarshi ta yi kama data wayayyun yara ce kawai amma kuma ta fito mishi da haibarshi had'e da kamala ta cikakken bafulatani, dan haka ya d'an saki fuskarshi yace "Yaro ni ne malam Adam a dai layin nan, Allah yasa lafiya?" Tarrr ya sake zaro ido a kan shi, daga k'asa ya sake d'aukowa ya kalleshi, daga shi har su Yaseen d'in duk tsayinsu bai wuce zuwa cinyarshi dan babu wanda ya kawo k'ugunshi, har gwara ma Amir ya d'an fisu tsayi da kad'an. Wani irin nauyi ne yaji tare da kunya sun kamashi, sai kawai ya tuna kalaman Mimi na safiyar shekaran jiya da take fad'in akwai baiwar da Allah ya ma iyayenta, shi ma idan ya gansu zai tabbatar da suna da baiwarsu. A take yayi saurin durk'usawa yana shafa sumarshi da fad'in "Ina wuni Baba." Da murmushi Abba yace "Lafiya lau d'an saurayi, muna lafiya." Gaisawa sukayi har saida Abba yace "Gashi kuma ban shaidaka ba? Daga ina haka?" D'an d'ago kan shi yayi ya kalli su Yaseen, hakan yasa Abba cewa "Ku shiga ciki kunji." Saida suka ga shigarsu kafin suka sake maido hankalinsu ga juna, a sanyaye cike da kunya yace "Abba dama mun had'u da Mimi..." Tunda ya ji haka sai yace "Dakata samari, bari na kawo mana abun zama ko." Cikin fara'a yace "A'a Abba da kun barshi, haka ma yayi nagode." Gyara tsayuwa Abba yayi yana kallon sumar dake kan Asas yana fad'in "Dama mun had'u da ita ne, to na nemi na fara gabatar da kaina ne kafin na fara zuwa wajenta saboda a gaskiya aure ne ya kawoni ba wasa ba, shine na zo da kaina dan gabatar muku da kaina." Numfashi Abba ya sauke yace "Yaro ya sunanka? D'an wane gida ne kai? Waye mahaifinka? Sannan me ce ce sana'arka?" Ba tare da jin d'ar ba Asas yace "Sunana Ashraf Sabi'u, ni d'ana ga margayi Alhaji Sabi'u Aliyu Sharif Maina, ina zaune tare da mahaifiyata a unguwar Tchanga, sannan nayi karatu jarida ne amma ina kasuwa ne tare da d'an uwana sheikh wanda ya zama kamar uba gareni, dan gaba d'aya shi yake kula da harkar kasuwancinmu ni da 'yar uwata." Jinjina kai Abba yayi yace "Masha'Allah, masha'Allah, yayi kyau haka, amma na ji ka ambaci Aliyu Sharif maina, kana nufin kai d'an uwan sheikh Abdul Waheed ne kenan?" Da fara'a yace "Hakane Baba, mahaifinsa da mahaifina ciki d'aya suke fito." Da farin ciki ba yace "Masha Allah, abu yayi kyau gaskiya." D'an kallon Abba yayi yace "Saidai Baba akwai abu guda da ba zan b'oye muku ba." Gaban Abba ne ya fad'i ya tsira masa ido, d'orawa yayi da "Baba shekara bakwai kenan da Allah ya jarabceni da wani azababben ciwon ciki mai tsanani, a duk shekarun nan mahaifiyata magani take nema min, amma insha'Allah komai ya kusa zuwa k'arshe dan yanzu haka muna ta shirin tafiya k'asar waje ne dan sama min magani." Wata nauyayyen ajiyar zuciya Abba ya sauke tare da jinjinawa yaron sosai yace "Malam Ashraf wannan ai ba komai bane, ita larura tasan d'akin kowa kuma babu wanda Allah ya wuce ya jarabeshi da ita, Allah ya baka lafiya yasa a yi a sa'a." Da murmushi yace "Nagode Baba." Cikin murmushi da jin dad'i Abba yace "Masha'Allah, abu yayi kyau, Allah ya shi albarka." Gyara tsayuwa yayi yace "Insha'Allah idan na shiga ciki yanzu zan tuntub'i yarinyar a kan maganarka, idan ta amince to fak'at, insha'Allah zan nemeka sai na maka bayani, bana da tamtama akan zuri'ar su sheikh, ina ji kai ma mutumin kirki ne kamar shi, ba zanyi bak'in cikin damk'a amanar 'yata ga wannan ahali ba." Wuuuuu! Asas yaji kamar zaiyi kwasan karan mahaukaciya da Abba ya d'aukeshi ya goya, ko a haka aka tsaya yasan kam zai samu shiga da izinin Allah, dan haka bakinshi har kunne ya shiga godiya yana mishi addu'ar Allah k'ara girma da lafiya da d'aukaka da sauransu, Abba ma cikin farin cikin yau *uwar ta shi* bata yi masa jaye-jayen nan ba ya shiga shi mishi albarka, da haka suka rabu Asas ya d'auki hanyar gidan sheikh dan tsaigunta masa wannan labari mai armashi. Mimi ma da tun tsayawar motar ta lek'o tare da Asma'u tsaf ta k'are masa kallo ta kalli Asma'u tace "Gaskiya guyen nan ya had'u, kinga wani mahaukacin shiri kamar yau ne d'aurin aurenmu." Kallon Asma'u tayi ta kama hannunta suka koma ciki tana fad'in "Ai dole ma Abba ya amince, inba haka ba kuka zanyi." Dariya kawai Asma'u tayi har suka shige d'akin suna yar hirarsu. *Masha'Allah* Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa. Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai. Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa. _Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._ _'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_ Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:52 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *11* Ko da Abba ya shiga gida kam ya kalli mama yace "Ina Mimi ne?" Kallon Amir tayi sannan ta kalleshi tace "Tana gidansu Asma'u har yanzu." Shi ma kallon Amir yayi yace "Je kira min ita." Gyad'a kai yayi ya mik'e ya fita, 'yar kujerar robar da Amir ya tashi ya zauna yana fad'in "Bak'o na yi yanzun nan, kai uwata da kwashe-kwashe ake, ni ko a ina ta kwaso farin jinin nan? Yarinya kamar wata 'yar sarauta." Wani murmushi Mama tayi ta saci kallonshi tace "Farin jini ko shirme, hauka ke damunta yarinyar nan." Girgiza kai yayi yace "Harda farin jini ga uwata, ki duba ki ga ba dan bud'e mata ido da nayi ba da yanzu gidan nan bai zama dandalin tara kowane jahili da sakarai ba?" Yar dariya tayi tace "Allah dai ya shirya mana ita." Da fara'a ya amsa da "Ameen." D'orawa yayi da "Yanzu fa kam indai har ba zata saka shirmen nan da ta saka game da lamarin yaron nan Mas'ud ba, to Mimi kam ta dace da miji na gari mai hankali." Cike da tsantsar damuwa Mama tace "Ni wallahi a tsayar da ranar aurenta shi zai sama min kwanciyar hankali, dan lamarinzamanin nan da rayuwar da Mimi ta saka kanta tana kayar min da gaba." Jinjina kai yayi yace "Ai dai kin shirya aurar da ita ko?" Sunkuyar da kai tayi ba tace komai ba, murmushi yayi yace "Indai har komai zai zo mana da sauk'i, to insha'Allahu auren uwata ba zai wuce wata d'aya da rabi ba, dan ni kaina bana son ganinta a k'yal-k'yal d'in nan, tun muna sanin inda take samu wata rana zata rufemu ta bai-bai, duk da muna shaidar halayenta amma ai yaro ka haifesa ne baka haifi halinsa ba." Cike da tabbaci tace "Tabbas hakane, Allah ya mana jagora." "Ameen." Ya fad'a a dai-dai sallamar Mimi da Amir a tare, amsa musu sukayi har suka zuba mata ido tana sunkuyawa tun bata k'araso garesu ba ta durk'ushe, kusan a tare suka saki murmushin jin dad'in yanda Mimi take matuk'ar girmama su, tunda tayi wayo ta mallaki hankali ta daina tsayawa a sanda suke tsaye, dukansu hakan na musu dad'i fiye da kima kawai dai basu tab'a nunawa bane, saidai kullum suna mata addu'ar Allah ya bata yaran da zasu mata biyayya ita ma fiye da yanda ta musu. Cikin nutsuwa Abba dake kallonta yanda kanta ke k'asa yace "Mimi, kinsan wani yaro mai sunan *Ashfar*?" Da sauri ta d'ago kai sai kuma ta sunkuyar da kanta tana murmushi, Mama dasu Yaseen duk tintsirewa sukayi da dariya hakan yasa shi rarraba ido yana kallonsu, cikin had'e fuska yace "Wai lafiya dariyar ku kuma?" Cike da kunya mama tace "Malam ai sunan ka fad'a ba daidai ba, ina kyautata zaton Ashraf ne ba Ashfar ba." Sai lokacin shi ma ya ma kan shi dariya yace "To ni na sani ne, suna ne gashi nan dai idan uwaye suka saka ma yaransu." Kallon Mimi yayi yace "Kin san shi ne?" D'an sunkuyar da kai ta sake yi tace "E Abba." Tsareta da ido yayi yace "Ya zo yanzu gidan nan, kuma izinin neman zuwa wajenki yake, shin kin amince da haka?" Shiru tayi saida ya sake cewa "Kin amince?" A hankali ta jinjina kai alamar eh, shi ma jinjina kai yayi yace "Shikenan tashi kije, zan d'anyi bincike a kan yaro na k'ara sanin halayenshi duk da dai d'an babban gida ne, gashi d'an manyan mutane kuma jinin malamai, amma ki sani uwata wannan karan ba zaki min iskancin nan ba, wallahi kika sa na shiga maganar nan kika sake kunyata ni Mimi sadakarki zan bayar." A zabure ta d'ago tace "Sadaka Abba?" Yatsina fuska yayi yace "K'warai kuwa, kina shakkar hakane? Ki jaraba ki gani." Shiru tayi sai mama dake murmushi, tana so ta ce a bayar da sadakar ta ta ai zai fi, amma kunya da kuma girmama sunan sarakuwarta musamman da ya zamana a gabanshi take, Abba ne yace "Tashi ki shiga ciki." Mik'ewa tayi zata shiga ya bita da kallo yana fad'in "Uwata ba dai zaki daina saka wannan sangen ba ko?" Juyowa tayi ta durk'usa tace "Abba na daina fa, kawai idan zan shiga gidansu Asma'u ne ko aunty Maimuna nake sakawa fa." Jinjina kai yayi yana kallonta ta mik'e ta shige d'akin kamar ta shiga taka rawa tsabar farin ciki. *Yau* alhamis bbu karatu, hakan yasa tunda safe tayi shara da wanke wankenta ta kammala, tana idawa gaban mama ta durk'usa tace "Mama bani dala arba'in zan siyi k'osai da bredi nayi kari." Wani murmushi Mama tayi tace "Ina ce jiya kinga tuwo aka dafa? Sannan kinga miyar da aka yi a matsayin mahad'in tuwon? Shi ne kike neman dala arba'in a hannu na?" Girgiza kai tayi tace "Mimi idan ina da dala arba'in d'in da zan baki ai zan iya taimakawa mahaifinku ta hanyar yi mana cefanai me kyau muyi miya." Wani huci ta sauke da tunanin mafita, ita fa tana da kud'in matsalar tambayar da zata sha yasa take b'oyewa, d'an kallon maman tayi tana karkare akaihunta dake jikin gajerun yatsunta tace "Mama to bari na ga ba zan rasa ba kam a jakata." Mik'ewa tayi ta shiga ciro jakunkunanta masu kyau dake jikin hannun gado, zaune tayi ta shiga lalubarsu tana zazzagewa kamar gaske, Abba ne ya shigo da sallama d'akin suka amsa, shigowa yayi yana kallonta yana fad'in "Ke kuma lafiya? Me kike nema?" Cikin ladabi tace "Abba dala arba'in nake fatan samu a nan." "Me za kiyi da ita?" Ya tambaya kai tsaye, amsa ta bashi tana ci gaba da lalabawa da fad'in "Abba abun kari zan siyo." K'uri ya mata da ido, duk da yasan halin Mimi tana da saka kanta a uku a wasu lamura, amma maganar tuwo kam tunda yarintarta ne bata son cin shi, shiyasa basa matsa mata da sai ta ci d'in, saidai yana tsoron yanayin rayuwa, baisan ina rayuwa zata kai ta ba nan gaba, ya zatayi kenan? Idan fa su iyayenta sun d'auka wani ba zai d'auki haka ba, laluba aljihunshi yayi ya ciro talatin yana fad'in "Karb'i nan, je ki siyo abinda zaki ci." Kallonshi mama tayi tace "Bata kayi wai?" Shiru yayi yana kallon mimi data mik'e da sauri ya ta d'auki hijab ta saka ta fita, k'arasa shiga yayi ya zauna bakin gadon da kyau yana fad'in "To ya zamuyi in ba'a bata ba? Ta fita waje ta nemo muke so? Ai kinfi kowa sanin bata cin tuwo, hakan ba dan d'aukarwa kai bane ko kuma k'arya, hakane take tun fil'azal." Numfashi Mama t sauke tace "To yanzu daka bata su kana da kud'in ne?" Girgiza kai yayi yace "Allah zai dubemu ya bamu wasu insha'Allah." Jinjina kai tayi tace "Allah ya bud'a mana." "Ameen." Ya amsa dashi kafin ya mik'e yace "Zan fita yanzu, insha'Allah zuwa anjima zan dawo na kawo muku abinda ya samu." Nan ma jinjina kai tayi tace "Allah ya bada sa'a, Allah yasa a dace." Amsawa yayi da ameen ya fita a gidan, kwanar daya shiga anan ya samu Mimi tsaye bakin kaskon mai suyar k'osan, murmushi ya saki ganin ta wani d'aure fuska ta dafe k'ugu, yasan saboda su Maryam da su Na'ima na wurin ne dan basa shiri ko kad'an. Har saida ya kawo daf da ita zai wuce ya kalleta yace "Mamana da an baki ki wuce gida kinji." Sai lokacin ta farga dashi hakan yasa ta saurin sunkuyawa tace "To Abba." Wucewa yayi ita kuma ta mayar da kallonta ga mai k'osan, su Na'ima kam bushewa sukayi da dariya har da tab'awa inda Maryam ke fad'in "Wa ya ga d'an k'wak'ur, dunk'ul-dunk'ul kamar zai shige a k'asa, a haka kuma aka haifffffffff..." Saukar marin daya zauna a kumatunta ne yasa ta jan harafin na k'arshe, bata gama fahimtar me ya sauka a kan ta ba Mimi ta kuma kifa mata wani marin, tuni ta canza yanayinta daga nutsatsiyar nan zuwa mahaukaciyar k'arfi da yaji, dan kuwa bakin wuta ta jawo a cikin murhu ta shiga tik'awa Maryam tare da cakumar hijabinta. Cikin tashin hankalin samarin dake gefe zaune da kuma mai k'osan duk sukayi kansu, dan Na'ima na ganin haka ta daka da gudu ta shige wani gida tana fad'in ta kashe Maryam, da k'arfi Bello ya karb'i iccen hannunta daya rage babu wuta a jikinshi yana fad'in "Haba Mimi da hankalinki, me ye haka? Me ya had'aku?" Kafin ta bashi amsa muryar wani saurayin ta daki ku'nuwansu yana fad'in "Inna lillahi! Ta kashe yar mutane fa." Duk kallon Maryam sukayi da zafin duka da iccen wutar nan yasa ta fad'uwa a sheme, dan hijabinta ma duk yayi shaidar ya ci wuta, kafin ka ce kwabo wurin har an taru daddazon jama'a, yanda ake ta cacar maganar ana tuhumar Mimi yasa mai k'osan ne cewa "A'a fa! Domin Allah yaran nan basu da gaskiya, ba dan basu da tarbiya ba ai iyaye sun wuce gaban wasa, kuma hallitar iyayen Mimi ai Allah ne ya hallicesu haka, shi ne suka tsaya suna mishi dariya harda shak'iyanci saboda ya wuce ta nan, ni fa ban ga laifinta ba wallahi 'yar halak kenan." Ruwa aka shafawa Maryam ta farfad'o tana fashewa da kuka da zagin Mimi tana fad'in sai ta rama, Mimi kam uwar k'asaita da isa da fad'in rai, a lokacin da kakar Maryam ta iso lokacin ta matso kusan Maryam d'in tace "Wallahi ba dan anyi gaggawar k'watarki ba, da sai na miki wanka da ruwan man nan, na kasheki na kashe banza wallahi." Juyawa tayi ta shiga takawa da k'arfi har k'irjinta na wata nutsatsiyar kad'awa a cikin hijabinta, tsuguno tayi gaban farantin k'osan da aka kwashe ta jawo farar leda, a nutse ta shiga k'idayawa kanta k'osan har ta zuba daidai kud'inta, mik'ewa tayi ta kalli mai k'osan ta aje kud'in akan kujerar katakon ta tace "Ga kud'in nan, na talatin na zuba, ko d'aya ban k'ara a kai ba." Cikin takon izza kamar wacce ta ci kwalliya ta shiga takawa har ta k'arasa gida ta barsu nan ana cecekuce, tana shiga hannayenta ta wanke sosai ta d'auki ledar k'osanta ta shige d'aki, yanayinta sam bai nunawa mama wacce wani abu ya faru ba, dan haka bata tambayeta komai ba sai kallonta da take jefi jefi tana cin k'osan da d'a-d'aya, hayaniyar Zara ta ji da alama dai biyota sukayi a kawo shedarta gida, dan har kukan Maryam take ji wiwi, a sauk'ak'e tayi murmushi tace "Hummm!" Mama da taji abun a tsakiyar gidansu fitowa tayi dan ta d'auki murya, abun kamar wasa sai kuwa tsohuwar nan Zara ta d'aga musu hankali, dan ta dage sai an bi mata hakk'int dan an ga ita marainiya ce, in ba haka ba kuma zata yi k'arar Mimi wajen yan sanda. Mama baiwar Allah wacce da k'yar ma take kallon ciwon Maryam d'in dan doguwa ce ita ma ta shiga bata hak'uri da jajantawa ganin duk inda jikinta ya samu bakin wutar nan ya fara d'urar ruwa ya mata bororo, saida makwabta suka shigo suka tayata bata hak'uri amma fa ta ce zata jiran uban Mimi ya dawo saita nuna mishi abinda ta ma Maryam. Duk hargagin da ake tana d'aki zaune tana jin su, Mama kuma kawaici ne ya hanata shigowa ta mataa magana, saida aka ci aka sid'e mama ta shigo tana k'are mata kallo, bata yarda ta d'aga kai ta kalleta ba, sai ma mik'ewa da tayi ta fito ta jefar da ledar k'osan ta d'ibi ruwa ta shiga wanka. Saida ta gama ta shigo d'akin ta gama shafa mai ta jawo akwatin k'arfenta tana duba kayan da zata saka ta ji mama tace "Mimi kin kyauta yanzu?" Ba tare data juyo ba tace "Mama, karki shiga zancen nan dan Allah, ba Maryam ba wallahi ko waye a garin nan ya nemi raina min iyayena sai na illatashi, saidai a kasheni ni ma." Tsuru ta mata da ido tana kallonta ta mik'e tana k'ok'arin saka pant tana kare jikinta da zanin data d'aure k'irji, tsaf ta gama shirinta cikin doguwar rigar atamfa mai kyau, hoda kawai ta shafa da d'an man leb'e kafin ta kashe d'aurin d'an kwalinta, hijabinta ta d'auka bleue wanda ya dace da kalar atamfar ta saka takalmi masu kyau ta kalli Mama tace "Mama ni zan wuce, baki da sak'o wajen Iya?" Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi, bata hanata fita ba dan duk alhamis dama ta kan je gidan kakarta data haifi mamanta ta wuni a can, ranar juma'a kuma ta kan yi wanki ne sannan ta shiryawa kayanta zamansu a cikin akwati, hakan yasa take da tsari a kan komai. Girgiza kai tayi tace "Ki gaida Iya, nima zan shigo gidan watakila gobe insha'Allah." Jinjina kai tayi tare da d'aukar jakarta mai kud'i da kuma wayarta ta fita, unguwar kam tayi shiru a lokacin dan yara duk sun tafi makaranta, a nutse ta shiga takawa a k'afa dan ba nisa ne da gidan ba gaban islamiyarsu ne kad'an. Tana k'arasawa gidan da sallama ta shiga a k'ofar tana fad'in "Salam salam, ina tsofaffin gidan nan wai? Har yanzu suna nan da ransu?" Iya Delu dake k'ofar d'akinta zaune ne ta tarbeta da fad'in "Uwarki ma sai ta mutu ta barni ni da mijina." Dariya Mimi tayi tana k'arasawa gareta tace "Haba dai Iyeye, ina kika tab'a ganin haka? Ai mutuwa dole ce ko?" Takalminta silipas ta d'auka zata jefa mata daidai fitowar malam daga d'aki yace "A'a! A'a karki fara." Da shagwab'a Mimi ta k'arasa gareshi ta rik'e hannunshi kan ta a kafad'arshi tana fad'in "Ranka shi dad'e ka gani ko? Na fad'a maka matarka bata so na." Kallon Iya yayi yace "Ba sa茂 kin fad'a ba na gani da idona, ke dama haka kike mata?" Kallon Mimi yayi yace "Amaryas ya kike so nayi da ita?" Murmushi ta saki ta Iya tace "Kin gani ko? Ki bani hak'uri saina yafe miki, inba haka ba kuma zan sa mijina ya yanka miki ticket." Dak'uwa ta mata tace "Kin jima baki saka d'in ba, dama fa ina cike da haushinki yarinyar nan." Dariya tayi ta kalli malam tace "Malam wai dan ban mata wanki ba a ranar, kuma fa sai da taga nayi lalle kawai zata ce na mata wankin tsofaffin kayanta, amma ynzu ba gashi na zo ba sai nayi." Murmushi malam yayi yace "Ai idan ma ba zaki iya ba ki bari idan na dawo na fansheki." Girgiza kai Iya tayi tace "Kana iya wankin dama kake barina na wanke maka na ka kayan?" Dariya sukayi sai Mimi da tace "To ai saboda aikinki ne dama, kuma lada kike samu." "Fad'a mata dai amayata." Ya fad'a harda bata hannu suka tapa, lokacin kawai suka nutsu suka gaisa sosai tare da tambayar iyayenya, saida suka gamsu kafin malam ya musu sallama ya fita suka bishi da addu'a, saida ta ga b'acewarshi ta d'auke kanta tana tunanin duk yanda akayi shi ne ta yi, shiyasa ta zama doguwa a cikin iyalinta, dan ita dai shi ne dogo a cikin kakaninta, wacce ta haifi mamanta ma wadarce yar duk'ul, wanda suka fi mahaifinta ma dukansu gajeru ne. Dan kakanin na ta ma sun bata labari dalilin dagiya da kakanta yayi ya auri Delu (wacce ta ke bin maza uku ko sama da haka a haihuwa) yasa duk danginshi suka juya mishi baya, dan a lokacin ana canfa komai ne ana ganin aurensu ba alkairi bane, hakan kuma zai jawo musu gauraya zuri'a da masu gajeruwar hallitar nan, amma gashi suna zamansu lafiya har suka haifi yayar mamanta wacce uta ma haka take gajera mai sunan *Sahura* sai kuma *Shapi'atu* sannan mamanta ita ce k'ara. Cire hijabinta tayi tana zaman kan tabarmar da fad'in "Iya me kika aje na ci ne gidan?" Hararanta tayi tace "Komai, uwar kwad'ayi." Turo baki tayi amma ba tace komai ba dan a lokacin tana jin wayarta na vibrations wacce ta kunna a kan hanya, jin shiru yasa Iya cewa "Bari dai na d'auko miki d'umamen tuwo, tunda na ga yau alhamis zaki zo na tanadar miki shi." Dariya tayi tace "In dai tuwo ne Iya ki ci abun ki kam." Dariya kawai Iya tayi ba tace komai ba, jim kad'an ta fito daga d'akin ta mik'o mata langar (kwanon samira馃槶馃槬 a da fa sai yar g芒ta ake ma jere da su, ynzu kuma yar gatar ma k'walele suke mata saboda tsada馃槣), karb'a tayi tana bud'ewa, da sauri ta kalli Iya tace "Iyeee! Iya dad'i kuka ci ne jiya?" Zaune tayi tana murmushi tace "Gashi kuma ke ma zaki ci ba." Aje kwanon tayi gabanta tare da saka hannu ta d'auko tsokar naman ta jefa baki, duk da girkin tsofaffi ne amma dad'in ma na musamman ne, dan daga jin d'and'anon zaka san a nutse aka yi aikin, babu k'arni ko kad'an saboda yaji kayan k'amshi ga kuma uwar daddawar da aka saka hakan yasa shi zama kamar naman kai. Tsaf ta cinye naman tana jin kamar kar ya k'are kafin ta mik'e ta shiga d'akin, saida ta saka wayar a silent sannan ta shiga aikin gyarawa Iya d'akinta kamar yanda take yi a kowane sati, saida ta gama ta had'o kayan wankin ta fito dasu waje, sabulu Iya ta bata inda ta zauna kan kujera 'yar tsuguno ta fara wankin suna hira da Iya cike da armashi. Haka ta wuni a gidan kakanin nata cikin farin ciki ba tare data amsa wayar kowa ba a wannan wunin, har bayan sallah magriba tana tunanin shiga d'akin Iya ta d'auki wayar ta duba sai kuma Iya ta zaunar da ita, wasu k'ullikan magani ta bata tana fad'in "Wannan mai duhun ki dinga wanka dashi, d'ayan kuma hayak'i zakiyi, sai d'ayan kisha a hura ko kunu." Wani iska ta furzo tace "To fa Iya! Matsalata dake fa wallahi, da an had'u sai kin b芒 mutum wannan abubuwan." Hannu ta kai kamar zata bigeta tace "Ke ni bana son iskanci, ke a yanda kike d'in nan kina ganin da ban jik'aki da wannan abubuwan ba da yanzu bakin duniya ya barki ne? Ko farin jininki kin d'auka haka kawai kika sameshi? To ni ce nan na shiga na fita tun kina k'arama na miki turaren farin jini." Da mamaki tace "Yo Iye ina ga ma ke kika hallice ni haka ko?" Duka ta kai mata hakan yasa ta tserewa a guje ta shige d'aki tana fad'in "To kaji Iya da rigima, Allah ya yi ni da farin jinina ki ce wai ke kika shiga kika fita, ta ina kika shiga to bare ba ki fita?" Daga nan zaune Iya tace "Wallahi na sameki d'akin nan sai na ci uwaki Shapi'a, yar banza mai zubulin larabawan maroco, ba dan kina da d'an tsari a jikinki ba da yanzu ba kina nan a lalace ba." Mimi kam ba tace komai ba dan a lokacin tana duba jerin sunayen wanda suka kirata, kama daga d'an beauty, bak'uwar lambar da take kyautata zaton ta Saminu ce, d'an wahala da kuma sauran 'yan wahalan suna take masa baya, har da d'an ajinsu na islamiyya da sauran lambobi barkatai. Sai lambar Salma data turo mata hotunan ta wanda aka had'a da suke nuna an kawo lefennta, taji dad'i sosai kuma saida tad'ora a status a take. Murmushi kawai tayi ta sake kashe wayar dan kar Iya ma ta gani ba tare data tuntub'i lambar kowa ba. *Bayan kwana biyu* A kwana biyun nan babu kiran wayar data d'aga musamman ma bak'uwar lambar data fi kyautata zaton ta Saminu, dan ko kallon k'ofar gidan bata sake yi ba tun daga ranar, dan jiya Maimuna har shigowa tayi da kan ta dan dubata, amma tana jin sai ta nuna bacci take a d'aki kawai har ta ban gidan tana jin tana wa mama k'orafin ta tafi ranar bata sani ba. Duk wani abu da zai b'ata mata rai ne yanzu bata k'aunarshi tunda daren jiya Abba ya bata izinin sauraren Asas idan ya zo, ba wannan ne yafi komai faranta mata rai ba kamar yanda ya ce ya turo magabatanshi, duk da tana jin d'ar a kan hakan dan bata san wane iri ne su d'in ba. Da wuri suka gama shiryawa ita da Asma'u zasu je ganin kayan Salma da basu samu an kawo dasu ba, tun a kan hanya suke hirar Asas saidai ba wani sani ne da su ba sosai. Suna karya kwanar gidansu dan isa bakin titi suka had'e da motar Muttak'a, saida ta feso wani iska a bakinta tare da furta "Iska na wahalat da mai kayan kara." Tsayawa sukayi suna kallo har ya fito fuskarshi a had'e babu alamar wargi, yana tsayawa gabanta ya shiga kirta mata wani kallo irin na 'yan k'waya mai tsoratarwa, da yatsa ya nunata yace "... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:52 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *12* Yana tsayawa gabanta ya shiga kirta mata wani kallo irin na 'yan k'waya mai tsoratarwa, da yatsa ya nunata yace "Ke wannan wane irin rashin mutumci ne da ake kiranki baki d'aga? Akan me zaki tsaya kina min wasa da hankali ne wai? Dan kinga ana sonki ne zaki tsaya yi wa mutane iskanci? Mimi surarki da albarkatun da Allah ya hore miki a jiki ba zasu hana ni daddarza miki buru'uba fa, ki kiyayeni kinji na fad'a miki." Tunda ya fara magana suke kallonshi kowace gabanta na fad'uwa sun yi sak'e, dan gaba d'aya yanayinshi da alamu sun nuna wani abun yasha dan idonshi ma a jajir suke, duk ta daga ciki kam a mugun bala'in tsorace take, amma a zahirinta sai ta k'i nunawa a fuskarta bare kuma jikinta, dakewa tayi kawai tana binshi da kallo da matsakaitan idonta, sai kakkauran leb'enta na sama data turo gaba amma fuskarta a had'e sosai. Ganin yanda take kallonshi sai kuma ya sassauta murya yace "Mimi, dan Allah ki d'auki wayata kin ji, damuwa nake shiga sosai idan ina kiranki ba kya d'aga min, kin gani ko Mimi?" Ya fad'a yana nuna mata k'irjinshi yace "Wallahi a nan ne kawai nake jin zafi, bansan me yasa ba amma an jarabceni da sonki sosai, Mimi zaki aureni?" Da sauri ta yatsina baki a ranta tana fad'in "Kana d'an k'wayar? Allah ya tsareni." A zahiri kam ko alamar magana ma ba tayi ba sai binshi da ido, cikin wata irin murya yace "Mimi ki min magana mana, bana son shirun nan naki fa, ko dai yan jan ajin ne suka motsa?" Da sauri Asma'u ta kalleshi sosai tace "Eh wallahi su ne, ni ma tunda muka fito har yanzu bata min magana ba, sai fa kana hak'uri da ita." A rikice a kuma shagalce yayi ram da hannun Asma'u yana fad'in "K'awar matata, dan Allah ki fad'a min tana so na? Tana baki labari na wata rana?" Mutsu-mutsu Asma'u ta fara na son ya sake mata hannu, ganin bai saketa ba yasa Mimi d'ora hannunta akan na shi hannun dake rik'e dana Asma'u, kallon hannayen nasu duka sukayi, hannun Asma'u dake da sirkin fari mai masara, sai na Muttak'a dake bak'i wulik, sai kuma na Mimi dake da kauri da tuwon hannu ga shi kuma jajir akan na su. Washe baki yayi tare da sakin hannun Asma'u ya kalli Mimi yana fad'in "Mimi na kinji lallausan hannunki kuwa? Shi yasa kullum nake k'ara son ki." Wata uwar harara ta wurga masa tare da kama hannun Asma'u ta rik'e gam, cikin amon muryar gargad'i tace "Kar ka sake tab'a jikinta, bana so." Fizgar Asma'u tayi suka barshi nan tsaye, juyawa yayi ya bisu da kallo da d'umbin mamaki, amma kuma sai yayi murmushi yace "Ai ce wa tayi bata so, kishina ne take wallahi, da bata jin so na ai ba zatayi kishi na ba, daga yau na daina Mimi ba zan kuma kula kowace mace ba ma, amma fa idan kin min alk'awarin aurenmu nan kusa." Tunda suka barshi babu wacce tayi magana saida taxi ta d'aukesu sukayi nisa, da k'yar Asma'u ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in "Kin gani ko? Abinda nake fad'a miki kenan Mimi, wallahi mutumin nan d'an k'waya ne na gaske." Wani dogon tsaki taja tare da d'aga mata hannu alamar ya isa tace "Kinga dallah ba'a son yin magana akan waccen shashashan banzan." D'auke kanta tayi ta juya tana k'ara had'e fuskarta sosai alamar hushi, babu wacce ta k'ara magana har suka isa gidansu Salma ana shirye shiryen magriba. Saida suka fara gabatar da sallah kafin suka zauna kallon lefen, sosai kayan suka birge Mimi suna kallo kuma tana bata labarin Asas daga had'uwarsu har matsayar da ake kai yanzu. Wayarta dake cikin jaka ta samu ta cire ta a silent ne ta shiga ruri, saidai sautin kiran ya tabbatar mata da layinta na Moov ne ake kira wanda ba sosai ta cika aiki da shi ba, d'aukar jakar tayi ta ciro wayar ta duba lambar, gabanta ne ya tsinke ya fad'i sakamakon ganin lambar sheikh ta fito, yanda tsoro da fargaba suka ziyarce ta ne yasa Salma lek'o screen d'in wayar tana fad'in "Besty halan wani jakin ne kika samu." A rashin sanin me tayi da kuma jin zafin abinda Salma ta fad'a kawai ta kai mata bugu a baya tana fad'in "Ke ce jaka marar mutumci, wannan d'in?" Salma da taji zafin bugun sosai ta dafe bayanta tana fad'in "Wai-wai-wai! Ni kika daka haka besty?" Tsaki tayi tace "Dan Allah ni ku min shiru na amsa kiran ya sheikh, kinsan abun laifi ba kad'an yake a wurinsu ba, ni kuma ina so mu rabu lafiya da shi wallahi." Shiru kam sukayi suka daina k'wak'waran motsi, danna ok tayi tare da saka amsakuwa ta aje wayar akan wani akwati mai kaya. Sheikh da tashin hankali ne ya d'ugunzuma shi har ya saka shi kiranta bai shirya ba shi ma yayi shiru, a kwana biyun nan yake jin sabon abu a game da yarinyar, matuk'ar son had'uwa da iyayenta yake sosai, amma har yanzu bata kirashi ba ta ce Abbanta ya dawo, sai kawai ya kasa hak'ura ya d'an dannawa lambar kira, dan so yake idan komai ya tabbata ayi aurenshi tare da Asas wanda yau yake sanar dashi an ce ya tura magabatanshi, kuma yayi alk'awarin tafiya anjima tare da kawun Ashraf d'in. Kamar babu wanda zaiyi magana sai kuma ya rangad'a sallama a tausashe, d'an numfashi ta sauke ta amsa mishi kamar yanda ya mata, d'orawa tayi da fad'in "Barka da yammaci, anwuni lafiya?" Murmushi ya saki daga inda yake yana mamakin me yasa ita bata iya kambama abu ba? Asma'u dai kallonta take tana kuma mamakin yanda take gaisawa da babban mutumin nan, haka, a tausashe ya amsa da "Lafiya lau, ya kike?" Da fara'a da kuma ladabi tace "Lafiya lau, ya fama da mu?" Murmushi yayi wannan karan ma mai sauti yace "Fama da ku? Ke zan tambaya Ryam ya aka ji da hak'uri da mu?" Murmushi ita ma tayi tace "Alhamdulillah, amma ai mu ne iyayen k'iriniya." Yar dariya yayi yana jin wani nishad'i na ratsashi, a hankali yace "Ryam kar ki ga na kiraki ki d'auka na haukace fa, a gaskiya ina son sanin idan Abba ya dawo ne, a matse nake sosai da son tattaunawa dasu." A d'an ladabce da kuma sigar mamaki tace "Me yasa haka? Wani abu ya faru ne?" Saida ya girgiza kai kamar yana gabanta kafin yace "Ba komai, kawai dai zamuyi magana ne a kan ki." Tsam tayi ta kalli su Salma da Asma'u tana musu alama da ido a kan ta kuma? Saita nutsuwarta tayi tace "A kai na malam? Allah yasa dai ba laifi nayi ba." Murmushi yayi bai ce komai ba na tsayin dak'ik'u kafin yace "Ryam, shekaruna sun fara ja gaskiya, saidai a shekarun nan nawa na ji ina son yin aure sosai, shin zaki *iya aure na*?" Wani bahagon fad'uwa gabanta yayi har saida ta dafe k'irjinta da hannu ta waro ido tana kallon wayar, aurenta? Sheikh Abdul waheed? Da sauri ta zabura ta d'auki wayar ta cire amsakuwar ta d'ora a kunne, saidai bakinta ya gaza furta komai, d'an sautin murmushin shi ta ji yana fad'in "Na yi tunanin haka Ryam, nasan zaki ce na miki tsufa dama, ni kaina nasan wauta nayi dana bari zuciyata ta fara k'aunarki, ba komai zan hak'ura." Jikinta yayi mugun sanyi duk sai take jin ba dad'i, da k'yar ta d'aga labb'anta tace "Ni ban ce fa." Cikin fara'a yace "To me kike nufi da shirun kenan?" Sai kuma ta kasa bashi amsa ta k'yale, wani murmushi ya sake yi yace "Ina jin ki mana, zaki iya aurena a haka?" A zuciyarta tace "Ba zan iya ba gaskiya, ka min tsufa Abdul." A zahiri kuma sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsar k'afarta cikin fitar da kalmomi da d'ad'aya tace " *Zan iya mana*, ai ba shekarun ne abun dubawa ba, nagartar da kuma dacewa." Lumshe ido yayi daga inda yake tare da sakin murmushi, shiru kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "Da gaske Ryam?" Jinjina kai tayi tace "Eh, gafarta malam." Cikin jin dad'i yace "Kenan kin amince yanzu na zo gidanku neman aurenki?" Rarraba ido tayi tana tunanin abun yi, gaskiya har zuciyarta take jin bata son b'ata mishi rai, shiyasa ko kira yayi a na farko take d'agawa, amma shi kan shi Asas da take begen yin hira da shi bata damuwa dan ta share kiranshi, gashi tun had'uwarsu ta farko ta mishi k'arya da dama, bata so ya gano hakan zai zubar mata da kimarta, kawai ta fad'a mishi y'a zo ta tabbata idan ya zo za'a ce an bayar da ita, daga nan ita kuma saita cire layinta na Moov ta shiga sha'aninta, zai manta da ita ya kuma shiga rayuwarshi, idan kuma dole ne k'ara auren to zai nemi wata. Da wannan shawarar tayi ammana kawai ta sanyaya murya sosai tace "Eh, amma sai Abba ya dawo." Da sakin fuska yace "Naji dad'i Ryam, yaushe Abban zai dawo?" A hankali tace "Nan da kwana biyu ne inji Mama." Jinjina kai yayi yace "Shikenan Allah ya nuna mana, zan kashe waya dan bana son kaucewa shari'a, magana da nayi da ke ma babu izinin mahaifinki saina nemi afuwarsa akan haka, saida safe." Jinjina kai tayi ita ma tace "Saida safe." Aje wayar tayi ta sauke ajiyar zuciya, kallon Asma'u tayi ta mik'e tana fad'in "Tashi tashi malama mu koma, hankalina a tashe yake wallahi na yi wa malam k'arya." Mik'ewa Asma'u tayi tana fad'in "Ke kuwa me yasa kikayi haka to?" Saida ta saka hijab d'inta tace "Ba zaki gane ba Asma'u, muje kawai." Salma ma mik'ewa tayi suka fita tana fad'in "Besty zan kiraki fa ki bani labarin wannan sabon kamun." Dariya kawai tayi tace "In kika kira ban d'aga ba karkiyi hushi." Dariya ita ma tayi tace "Wane hushi kuma? Ai har na saba, shiyasa na matsu iyayenki su san kina rik'e waya wallahi." Da sauri ta shiga takawa tana fad'in "Bari kedai, zasu sani kinji." Da azama suka fita kamar wasu masu laifi suka samu taxi suka nufi gida, a taxin kam yaua saida sukayi baram baram dan Asma'u fad'a ta mata akan me zata mishi k'arya? Babban mutum ne fa ya zata mayar da shi wani shashasha haka? Ita kumaa ta ji zafi har sukayi fad'a, ana saukesu kowace ta shige gida babu mai yi ma wata magana. Tunda suka dawo take d'aki kwance tana waya da Asas d'inta, da ta ji motsi za'a shigo take saurin b'oye wayar har sai ta ji shiru, a haka har Amir ya shigo yana fad'in "Mimi Alhaji ne ya aiko yaro yana kiranki ki kama ma aunty Maimuna aiki." Zaune tayi cikin jin haushi tace "Kai je ka ce masa bana nan, jaraba kai." Juyowa yayi yana turo baki ya fito, saukowa tayi ta durk'usa k'asan gadon ta jawo akwatinta ta saka wayar, ta mik'e kenan Mama ta shigo tana fad'in "Wace buru'ubar ce yau kika tashi da ita da zaki k'i zuwa kiran Alhajin, Maimuna ce bata jin dad'i ya ce ki je ki kama mata aiki." Turo baki tayi ta rarumi hijabinta akan gado tace "To." Hanyar fita ta nufa Mama tace "Yanzu aikin da zaki masa ne kike wannan kumburar? Mimi anya kina tunawa da alkairi kuwa?" Sake kumburo fuskar tayi tare da k'arasa fita a d'akin ta saka takalminta, a k'ofar gidan ta samu Abbanta zaune har da Alhaji Saminu akan tabarma suna hira, yatsina fuska tayi ta harareshi ta wuce, shigewa tayi cikin gidan kan ta tsaye ta shiga falon da sallama, ba wani abu daya nuna mata mai d'akin nan na faman da jinya, dan haka suka gaisa a sama sama tace "Mama ta fad'a min kin shiga gidan ai ina bacci." Da fara'a tace "Eh wallahi, ranar na ga babu sallama sai fitowa na yi ban gan ki ba, sai Alhaji ne yace ya had'u dake a k'ofar gida kin fita ai." Yak'e tayi tace "Hakane wallahi." Jim ta d'an na wasu mintuna sa茂 kuma ta mik'e tace "Aunty Maimuna saida safe, dama dan mu gaisa ne." Da fara'a tace "To Mimi saida safe." Tana fitowa daga falon suka had'e ya shigo, had'e fuska tayi ta sunkuyar da kan ta tana jiran ya kauce, a yanda idonshi suka rufe sai yaji baya shakkar Maimuna tasan komai, kan shi tsaye kawai yace "Me yasa ina kiranki baki d'agawa?" A dak'ile cikin b'acin rai tace "Haka kawai, ka kauce min na wuce ko na maka ihu yanzu." Wani malalacin murmushi yayi ya d'an kauce mata yana fad'in "Malam ya ce mu tayashi karb'an bak'i, ina fata dai ba aurenki zasu zo nema ba?" Saida ta saka takalminta tace "Eh, su ne, aurena zai basu insha'Allah." Wata yar dariya yayi sanda take fita a k'ofar d'akin shi kuma cikin wayancewa saboda kallonshi da Maimuna tayi yace "Allah yasa alkairi Mimi, ai haka ake so." Banza tayi da shi har ta fita a gidan gaba d'aya, sai dai shi kam haushi kamar zai kasheshi, ba wai rashin girmama shin da ba tayi ba, ba kuma yanda bata d'aga wauarshi ba kamar da ta tabbatar masa masu neman aurenta ne zasu zo, to kenan shi jiran banza yayi mata kenan? Tana fita gida ta sake shiga mama na tambayar ta "Har kin mata aikin ne? Ko kuma had'e mata fuskar kikayi ta gane tace ki tahowarki?" Sakin fuska tayi tace "A'a mama, dama dan na juye mata abinci ne a kwanuka." K'ala mama ba tace ba har ta shige d'aki, tana zaunen ne d'aki ta ji tsayawar mota a k'alla guda biyu, tana jin Abbanta ya shigo ya d'auki ruwa masu sanyi ya fita, gabanta fad'uwa kawai yake sai wani sabon fargaba da take ji yana ziyartarta, a k'alla minti talatin kafin ta ji bak'in sun bar k'ofar gidan. Abinda bata yi tsammani bane kuma shi ma bai fad'a mata ba, sa茂 ga Abba da mahaifin Asma'u da suka tayashi karb'an bak'in sun shigo da akwatina har da goro da kuma kud'inta, akwati set biyu aka shigo da su masu kyau na zamani, goro d'auri biyu da kuma kud'in lefe million d'aya da rabi. A tsakar gidan kam tana jin hayanuyarsu har da kakanta ma suna tattaunawa su fa basu d'auka da kayan zasu zo ba, sai kakanta dake fad'in ai haka shine harkar girman, kawai a musu addu'ar fatan alkairi. *To fa* Da safe tsaf ta shirya ta tafiyarta makaranta, saidai tana zuwa abun mamaki labarin har ya riga ta isa, dan kuwa Asma'u ce ta sanar wa su Jamila su ka suka yayata, saidai abun d'aure kan shi ne yanda Mimi bata cika bakin nan ko shan k'amshi da jin dad'i, murmushi kawai take musu sai tace "Hummm!" A gida ma tana fita mama ta fara karb'an bak'i daga makwabta har zuwa dangi suna taya murna na abun arzik'i. Har Mimi suka taso ta riski yan uwan mahaifiyarta su biyu aunty Shapi'a da aunty Sahura suna ta hira, d'aki ta shiga bayan ta durk'usa ta gaishesu, kayanta ta cire ta fito ta shiga ban d'aki ta dawo, har zata koma d'aki Shapi'a tace "Mimi zo." Tahowa tayi tare da durk'ushewa dan suma kamar mamanta ne, cikin nutsuwa aunty Sahura tace "Mimi kin ji lokacin da mahaifinki ya tsayar da ranar aurenki?" Girgiza kai tayi tana kallonta alamar a'a, jinjina kai tayi ta nuna mata kud'in hannunta masu yawa tace "Kinga wannan yanzu mahaifinki ya bayar da su, ya ce muje a rakaki kiyi siyayyar duk abun buk'atarki, dan gaba d'aya wata d'aya suka saka na auren." Da sauri ta kalleta ta kalli mama tace "Wata d'aya mama? Bai yi kad'an ba kuwa?" Kawar da kai mama ta yi saboda kunya ba ta tanka mata ba, aunty Shapi'a ce tace "Bai yi kad'an ba Mimi, me za'a tsaya jira tunda dai kin kai minzalin auren nan, sannan ba wani karatu kike ko wani abun ba na daban da za'a ce zai ja lokaci." Sahura ce ta d'ora da "Ba komai kinji Mimi, kiyi addu'a Allah yasa haka shi yafi zama alkairi." Ajiyar zuciya ta sauke ba tace komai ba, Shapi'a ce tace "Ranar alhamis baku karatu saiki shirya da wuri ki zo gidan Sahura ki same su, sai mu wuce kasuwa daga nan ki siyo duk abinda ya danganci sutura." Jinjina kai tayi tace "To insha'Allah." Mik'ewa tayi zata koma d'aki Sahura tace "Sannan Mimi, dan Allah a cikin waccen akwatin da kike da na kaya har guda biyu, an fad'a min shak'are suke da kaya dan baki da aiki sai d'inki, kiyi k'ok'ari kafin alhamis ki zauna ki ware kayanki sabbi masu kyau, saiki ajiye su gefe ki je dasu d'akin mijinki, ko ba komai zasu anfaneki suma." Jinjina kai tayi sai Shapi'a da tace "Ki godewa Allah miji kika samu d'an babban gida mai karamci, ya ce ke ya gani yana so kuma ke kad'ai yake da buk'ata, tsinke baya so a kai miki." K'uri ta musu da ido tana kallo da tunanin anya kuwa! Hakan ba zai jawo mata abinda ta tsana ba? Wato *raini* a wurin danginshi, ta sani ne dole ta fuskanki k'alubale daga garesu, a yanda ta fahimta shi d'in d'an masu hannu da shuni ne, ita kuma yar talaka, sannan ita ce doguwa, amma dayawa ahalinta duk wadanni ne, ta sani ne ita kanta bata cire rai da haifar yara masu irin halintar iyayenta ba, saidai hakan sam ba zai zama abun k'yama a gareta ba, to amma dangin mijin da zata aura fa? Numfashi ta sauke mai nauyi tana tunanin idan mahaifinta ya zo zata mishi magana, gaskiya a mata kayan d'aki ko kad'an ne, dan ba zataa iya ji da wulak'anci da gori har biyu a lokaci d'aya ba, *yar talakawa*! *'yar wadanni*! Shigewa tayi d'aki tana lalubo wayarta a akwati ta kunna, duk da hankalinta na kan wayar amma tana jin yanda ake ta shiga da fice a gidan, daga yanda makwabta ke ta shigowa zaka san ana shigowa dan ganin gaske dai Mimi ce aka kawowa kaya jiya babu wanda aka fad'a ma? Sannan da aka ce million d'aya da rabi da gaske? *Masha'Allah* Assalamu Alaikum Masoyanmu da fatan kuna lafiya. Muna mik'o maku godia da fatan alkhairi masu matuk'ar yawa a yadda kuka nuna mana kara da kauna wajen siyan littafinmu na kud'i. Alal hak'ik'a munji dad'i kuma mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i. Muna kuma k'ara kira ga masoyana wadanda basu siya ba dasu garzayo su siya domin muhimman darussa rayuwa, ilmantarwa da nishadantarwa dake cikin littafin. Dukkan wanda yaji taken littafin na *AURE YAKIN MATA* yasan littafi ne mai cike da ilmantarwa da bude ido akan irin rayuwar zaman auren da muke a zamanin yanzu don haka babu dana sani a siyan littafin. Yadda kuke siyan littafin yana k'ara mana k'warin guiwa wajen yi maku typing din littafinmu na *KOMIN NISAN JIFA* da *Matar Mutum*, muna fatan zaku cigaba da siye don mu samu k'warin guiwar yi maku typing din littafin na kyauta akan kari ba tare da b'ata lokaci ba. Mun yarda daku mun aminta da irin k'aunar da kuke mana, nasan kuma zaku siya littafinmu mai take *AURE YAK'IN MATA.* *MUNA SONKU SOSAI MUNA ALFAHARI DA KASANCEWA A CIKIN DUNIYARKU.* Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa. _Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._ _'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_ Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke mana don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna muna kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafinmu馃グ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:52 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *13* Saida ta shiga gidansu Asma'u kawai ta samu damar amsa wayar Asas, sun jima suna hira wacce duk rabinta hange-hangensu ne na yanda zamansu zai kasance da kuma bikinsu, mafi yawa kam shi ne yake fad'in tsarinshi da yanda yake so ayi, ita kuma da ta ga yana fad'in duk wani abu da ita ma take da burinshi ne sai take amsa mishi da hakan ma yayi, saida ta ji sallah isha'i ta tabbatar Abba yanzu zai shiga gida sukayi sallama ta dawo gida. *Sheikh* A hankali ya d'aga idonshi ya sauke a kan ta yana murmushi, da kallo ya bita yanda take takawa a cikin doguwar rigarta ta bacci da cikinta daya fito sosai, saida ta zo daf da shi ta sunkuya ta aje farantin hannunta tana fad'in "sheikh na wa, ga shayinka." Ba tare daya d'auke murmushin ba yace "Nagode, Allah ya miki albarka." Saida ta nufi wajen wadrob d'in kayanshi tace "Ameen, nima nagode." D'aukar kofin yayi ya shiga had'awa kan shi lipton d'in a tsanake, ita kuma gyara zaman kayanshi ta ci gaba da yi cike da fara'a da son wahaltawa mijin na ta, tana cikin gyaran ya kalleta yace "Ki had'a mana kayanmu mana, mun kusa tafiya ai." Juyowa tayi tace "Angama sheikh, yanzu kuwa." Murmushi ya mata ya ci gaba da kurb'an shayin, juyowa ta sake yi tace "Wannan karan ma ba zamu tafi da ko da *Saifil islam* ba?" 'Yar harara ya cilla mata yace "Rashin samun isashen lokacinki fa yasa nake ware miki k'arshen watan nan, idan muka tafi dashi me zamuyi?" Da murmushi a fuskarta tace "Me za muyi to dama? Na d'auka hutu zamu tafi." Wani malalacin murmushi yayi yace "Za muyi yak'i ne." Girgiza kai tayi ta juya tana dariya tace "In an girma a san an girma, ka fa tuna miji kake nemawa Eesha, kuma ka ce ko yanzu ka samu wanda ya dace zaka aurar da ita ne." D'an zaro ido yayi yace "To auren Eesha zai hana nawa auren farin ciki ne? Haihuwar Eesha ba zai hanani sake yi miki wani cikin ba idan kika sauke wannan, saidai ku haihu tare da 'yarki." Zaro ido tayi tace "Lahhh! Har da surukin na mu sai yaga mun haihu?" Jinjina kai yayi yace "Ai da gani na yasan banyi tsufan da zan kasa abinda zai iya yi ba shi ma." Girgiza kai tayi sosai tana dariya tace "Gafarta malam, gyaran kimtsi." Kallonta yayi ba fara'a a fuskarshi yace "Gafarta malam, ina ma laifin ki ce Abdul." Da sauri ta juyo tana fad'in "Wace ni? Ka rufa min asiri malam, ai fad'in wannan suna yafi k'arfin bakina." Murmushi yayi yace "A haka kuma babu wanda ya kai ki sani na." Murmushi jin kunya tayi tace "Wannan kuma ai daban ne ko sheikh na wa." Girgiza kai yayi yana sakin murmushi kawai saboda tuna wacce kai tsaye tace masa Abdul, Abdul! Har yanzu sunan na mishi amsakuwa a kunnenshi, duk da a cikin rud'u da kid'imewa da tsoro ne ta fad'a saboda tsoron mahaifinta, amma dai sunan data kira yayi tasiri sosai ta yanda har yanzu idan ya tuna ya kan saki murmushi shi kad'ai. *Asas* K'atuwar sanda ce a hannun Hajia ta d'aga tana fad'in "Ashraf zan buga maka sandar nan a kai idan baka shanye magasin nan ba kaban kofin." Yatsina fuska ya sake yi ya kalli Hajia dake tsaye gabanshi ta zaunar dashi ta tisashi a gaba, a hankali ya kalli kofin data jik'a maganin na gargajiya a ciki, kamar zaiyi kuka yace "Hajia wai dole sai na sha ne? Ki aje min har a jima mana." Girgiza kai tayi tace "Ko kad'an, ai dole ka shanye ka bani yanzu yanzun nan, kasan daga ina nasa aka amso min maganin nan?" Sake had'e fuska yayi yace "Wallahi ni dai Allah yana gani na gaji da shan maganin nan." Buge mishi baki tayi tana fad'in "Uwa ka, mutumin banza kawai, god'e-god'e da kai amma baka san shan magani, kuma kafi kowa sanin larurarka, yanzu da ka sa aka nemo maka auren 'yar mutane haka zaka sakata titseyeka kasha maganin?" Turo baki yayi yace "Hajia ni Mimi ma nasan ba zata titseyeni da sanda ba ai, zata lallab'ani ne har na shanye saita bani sweet na sha." Yanda yayi maganar da kanne ido d'aya yasa ta dungure masa kai tace "Maza bani kofin na gaji da tsayuwar nan." Rufe ido yayi yasa yatsa biyu ya rufe hancinshi ya kifa kofin a baki, da k'yar ya shanye kamar zaiyi amai kafin ya mik'a mata kofin ya mik'e ya nufi fridge, zaune tayi tana aje sandar hannunta tace "Shan magani ya zama aiki, kamar ba namiji ba." Dariya yayi ya kurb'i ruwa ya fita waje yana kuskure bakinshi, dawowa yayi yana fad'in "Hajia magani fa ba dad'i ne dashi ba, ai ke k'ok'ari ne dake da har kike zuba guda biyar a bakinki lokaci d'aya." Girgiza kai tayi tana tab'e baki, kallonta yayi yace "Hajia zan fita, saina dawo." Kallonshi tayi ita ma tace "To ina aka nufa yanzu? Nasan dai ba'a zuwa zance da yamma haka." Dariya yayi yace "Zan je zance amma sai anjima, yanzu zan je gidansu " Sadeeq ne ya kirani yace babu mota a hannunshi." Jinjina kai tayi tace "Yayi kyau, amma ni yaushe zaka kawo min surukuwar ta wa ne na ganta? Ko sai randa ta shigo gidan zamu ga juna." Dariya yayi yace "Hajia karki damu, da zaran na je yau zan mata magana, idan iyayenta sun amince saina kawo miki ita ta wuni." Jinjina kai ta sake yi tace "A'a ba sai ta wuni ba, ni da bana da wasu yara yan mata a gidan, kaga ai indai mai kunya ce ko numfashi ba zata sauke ba har sai tabar gidan nan, tsawon wuni d'aya kuwa ai akwai takura." Jinjina kai yayi yana shafa sumar kanshi yace "Shikenan Hajiata, yanda mukayi da ita zan fad'a mki." Jinjina kai tayi ta bi shi da kallo har ya fita, daga nan b'angarenshi ya wuce ya shirya ya fita ya bar gidan bayan yasha gargad'i a wurin Hajiar ce wa kar ya jima a waje ya dawo. *Mim-Sas*馃槣 Ana idar da sallah isha'i ta hana kai da kawon su Yaseen ta k'unshesu a d'aki suna karatu, ta k'alk'ale gidan tsaf ta kawar da komai yanda ya samar da fili kuma a tsaftace, kujeru ta aje guda biyu na roba kafin ta bankawa d'akinsu turaren tsintsiya, wanka ta shiga a k'alla minti ashirin ya d'auketa ka rantse canza fatarta take yi a ciki, haka ma a gurin shafa mai da tsantsara sassauk'ar kwalliyar data fito mata da tsarin ainihin kakkauran fuskarta, wata galleliyar rigar shadda ta saka wacce bata jima da d'inka ta ba da kud'in data yafata hannun wani Alhaji Bukar, tunda ta karb'i kud'in ta yi bloqu茅n lambarshi ta rufe duk wata k'ofa da zasu had'u. Wani shara-sharan mayafi ta d'auka ta shafeshi da turarenta mukhalat, fitowa tayi farfajiya ta d'auki jug d'in data wanke sabuwa da sai azumi mama ke aiki da ita, zata shiga d'akin ta ji wani sassauk'an numfashin mota a k'ofar gidan, da sauri ta kalli k'ofar ta tabbatar a nan mota ta tsaya, shigowa tayi d'akin ta kalli Yaseen da suke binta da kallo tace "Fita waje ka gani idan shi ne sai ka masa iso ya shigo." Gyad'a kai yayi shi dai ya mik'e ya fita, mik'awa mama jug d'in tayi tare da d'auko d'an k'aramin bokitin data had'a jus a ciki a abarba ta saka k'ank'ara tace "Mama juye min shi a ciki." Karb'a tayi ita ma tana kallonta kawai ta shiga yin abinda tace, dan tunda rana take wannan kimtse kimtsen da shirin tarbanshi, abinci ma yau da kanta ta girka na musamman inda mama tayi ta mamakin inda ta iya sarrafa wannan abu data ga ta had'a, domin kuwa kud'i ta kashe sosai wanda ta amsa a hannun maman ita ma wanda Abba ya bata ne tayi abun buk'atar ta. Mayafin ta d'auka ta rataya a kafad'a tana k'ara kallon kan ta a madubin, d'aurin d'an kwalin ya zauna mata a kai yayi kyau dan irin mai hawa-hawan nan ne ta yi sai kuma ta ja shi baya sosai ta yanda ya bayyanar da cikon dandazon gashinta bak'i, kallonta mama tayi tace "Ki d'ora mayafin da kyau mana, haka zaki je masa?" Kallon mama tayi tace "Mama, ai haka shi ne daidai, kinga had'uwarmu ce ta biyu, waccen lokacin da hijab ya ganni, kuma kinga ai addini ya yarda ka fito yanda mai son aurenka zai kalleka ya tabbatar komai ya masa yanda yake buk'ata." Galala mama tayi da baki ta sake d'aga kan ta da kyau ta kalleta dan a tsaye take tana k'ara gyara fuskarta tace "Kenan idan ya shigo zaune zaiyi ke kuma a tsaye kina jujjuyawa yana k'are miki kallo?" Murmushi tayi tace "A'a mama ba haka ba kuma." Girgiza kai tayi tana fad'in "Allah ka shirya mana zuri'a." Da murmishi Mimi tace "Ameen mama." Daga farfajiyar suka ji murya a tausashe a nutse a hankalce ana sallama a sirrince, Yaseen dake gaba ne ya sake amsa mishi yana fad'in "Suna ciki, bari na musu magana." D'akin ya shigo da sallama shi ma yana fad'in "Mama gashi nan ya shigo." Zaro ido tayi tace "To ya zanyi? Ni zanje muyi zancen?" Dariya Mimi tayi murya k'asa k'asa tace "Mama ki shirya da kyau dan zaki fito ku gaisa." Girgiza kai ta shiga yi alamar a'a, d'an turo baki tayi tace "To nan zan shigo dashi ya gaisheki." Takalminta ta saka kalar ruwan hoda da suka dace da shaddar da kuma gyalenta, a hankali cikin tako kamar d'awisu ta shigo takowa tana fitowa harta yaye labulen ta fito bayan ta d'an sunkuya gaba d'ayanta, tarr! Idonsu suka sark'e dana juna domin kuwa akwai hasken fitila a k'ofar d'akin, a tare suka saki murmushi kowa na sake kafe d'an uwanshi da kallo. Shi kan shi saida ayar nan ta sake fad'o masa a rai da take magana akan buwayar Allah, mai fitar da matacce a jikin rayayye, ya kuma fitar da rayayye a jikin matacce, Allah mai yin yanda ya so, mai yin sakamako ba tare da hisabi ba. Yanda ta fito kamar wata yar sarkin Istanbul, ko waye kai ka had'u da ita a waje ba zaka ce ta tab'a shiga wani wai gidan k'asa ba, amma a ciki take rayuwarta, kuma bata kunyar a san da haka. Ita kan ta irin kyawun da yayi sai take tabbatarwa kan ta lallai ta ciro *fure a cikin k'aya*, dan kuwa irinsu Asas bibiyarsu ake kamar a yi farautarsu, da k'ok'on bara yan mata ke neman irin su, yanzu data samu sai take ji kamar tayi hannun riga da kwanciyar hankali kenan, dan tasan dole tasha fama wajen tsare da kula da mutumcinshi, musamman a yanda ita ma ta kula mazan wasu, dan ita tana da ma tsari da idan ka nace mata ne zata kula ka. A nutse ta k'araso gabanshi ta tsaya kamar yanda shi ma yake tsaye cikin wata dakakkiyar shadda bak'a k'irin sai k'yalli take tana d'aukar ido kamar zaka matsata mai ya fito, ya had'u sosai yayi kyau a cikin shaddar da ke d'auke da d'inkin zamani. Sunkuyar da kan ta tayi cikin jin kunya murya k'asa k'asa tace "Barka." Murmushi ya sakar mata yace "Barka madame Asas, gani na zo." D'an d'ago da idonta tayi ta kalleshi da fara'a tace "Barka da zuwa kurkukun mu." Lumshe ido yayi yan ci gaba da murmushi yace "Kurkukun dake d'auke da mace kamar Mimi ta a ko ina yake zan iya nemanshi na zauna a ciki." Murmushi tayi har yana bayyanar da hak'oranta tace "Ka zauna to." Cikin kafeta da ido yace "A ina kenan?" Nuna mishi kujerar tayi tace "A nan." Murmushi yayi yace "Tabarma nake so, domin na zo nan ne da niyyar na ci abinda kika girka min da hannayenki." Rarraba ido tayi tace "Tabarma kuma?" Jinjina kai yayi yace "E, tabarma." Murmushi tayi tace "To me kake so ka ci?" Rumgume hannaye yayi yana kallon fuskarta yace "Me kika dafa min na tarbena?" A sanyaye tace "Tuwon masara, miyan kuka." Wani sanyayyen murmushi yayi shi ma yace "Masha'Allah, abunda na wuni ina buk'ata kenan yau, kawo min tabarma da tuwo na ci Maah, yunwa nake ji." Da mamaki ta kalleshi da son gano wai gaskiya yake fad'a kuwa, cike da tabbaci yace "Ki kawo min mana." Rarraba ido ta shiga yi dan yau ba tuwon suka dafa ba, sai kawai tayi murmushi tace "A gaskiya ba ma da tuwo, yau ba shi aka girka ba saboda zuwanka." Da mamaki ya nuna kan shi yace "Ni kuma? Me yasa?" Sunkuyar da kai ta sake yi ba tace komai ba, girgizz kai yayi yace "Maah, ni fa ke nake so ba matsayinki ko abinda kuka mallaka ba, rayuwar da kuke yi ita ke bani sha'awa kuma ita nayi niyyar farawa tare da ke, dan haka duk wata wacce kika san gwana ce ita a harkar tuk'a tuwo to zai fi kyau ki nemi kusanci da ita, dan a kowane dare na rayuwarki gidana shi zaki tuk'a min nayi ta sulmar kayana." Kecewa tayi da wata siririyar dariya saboda maganarshi ta k'arshe, jinjina kai tayi tace "Ai ni ma na iya, na iya tuwon masara, tuwon hatsi, tuwon dawa dana shinkafa, sannan na iya na garin doya ma da kuma na semovita." Jinjina kai yayi yace "Yawwa *maah le* ta, haka nake son ji." Juyawa tayi tana fad'in "Bari na kira mama ku gaisa." Shiga d'aki, tabarmar dake jingine a farkon shiga ta d'auko mama ta kalleta da alamar tambaya, ita ma da ido ta amsa mata da "Shi ya ce na d'auko." Saida ta juyo zata fito tace "Mama muje ku gaisa." Sunkuyar da kai tayi ba tace k'ala ba, cikin shagwab'a tace "Mama muje, ko na ce ya shigo ne?" Da sauri ta kalleta da mamakin wai me yasa wasu lokuta bata gane cewa tana jin nauyinta a matsayinta na babbar 'yarta ne? Girgiza kai tayi ta mik'e ta d'auki d'an gajeran hijabinta ta saka har k'asa, gaba take mama na baya hakan yasa sam bai kula da mutum a bayanta ba, saida ta duk'a dan shinfid'a tabarmar ya ga mama, har ga Allah tunaninshi bai bashi mahaifiyarta ma haka take ba, gashi fuskar maman ba wani tsufa ko dattijantaka, tarrr! Ya kalli fuskar mama da murmushi ya d'an d'ago hannunshi irin yana jiran ta k'araso d'in nan a cabke hannu tunda ga k'anwar matar da zaka aura. Mik'ewar da Mimi tayi ne ta juyo ta nuna mishi Mama tace "Ga mama ku gaisa." Luuuuuu! Yayi ya sauke hannunshi tare da durk'ushewa yayi tsugunno irin na maza kan shi k'asa, gaba d'aya sai ya rasa bakin magana daya tuna yanda ya dinga kallon fuskarta, har fa yayi shigo dafa kan ta ya bata hannu su gaisa yace mata " *beby ya kike? Ya sunan k'anwar ta mu*?" Lallai ashe da ya tabka kuskuren da har abada ba zai daina jin kunya ba, ganin ya kasa fad'an komai sai mama ce tace "Ina wuni?" Da sauri cikin kunya yace "Ina wuninku?" Da fara'a tace "Lafiya lau, an zo lafiya?" "Lafiya lau, na sameku lafiya?" Ya fad'a kan shi a k'asa sosai, ita ma kan na ta a k'asa tace "Lafiya lau, ya mutan gida?" Da fara'a yace "Lafiya lau, sun ce na gaisheku." Da fara'a ita ma tace "Muna amsawa, a gaishe su sosai." "Insha'Allahu zasu ji." Juyawa tayi tana fad'in "Allah ya shi albarka, a gaida 'yan gidan." Saida y'a ji shigewarta ya sake d'ago kai, eh lallai Mimi baiwar Allah ce daya jarabeta ya cirota daga tsatson bayin Allahn nan. Alama ta mishi da hannu ya zauna, saida ya cire takalminshi a nutse ya zaune tare da jingina a bango, d'aki ta koma ta d'auko duk abinda ta tanada domin shi ta kawo ta aje mi shi, cire takalminta tayi ita ma ta zauna kan tabarmar ta fara tsiyaya masa jus d'in, mik'a masa tayi ya karb'a yana murmushi yace "Nagode gimbiyar mata." Murmushi tayi ita ma tana k'ara gyara zamanta irin na tsakiyar sallah (zaman tahiya), izinin shi ta nema ta zuba mishi abinci, jinjina kai yayi alamar eh, cikin nutsuwa ta fara zuba mishi farar macca da soyayyan nik'ak'en naman da aka nad'e cikin k'wai, sai soyayyen dankali da ta yi wa jus na mayonnaise da waken gwangwani. Tura mishi tayi gabanshi ya gyara zamanshi yana fad'in "Da nasan wannan shagalin zan tarar ai da na taho da tsohuwar katifa ta." Dariya tayi tace "Ka me da ita?" Cike da zolaya yace "Da na ci nayi kwance mana." Murmushi tayi ta girgiza kai tace "Gashi gidanmu baya d'aukar bak'on da baisan da zuwanshi ba." Dariya shi ma yayi yanaa fad'in "Da alama dai baki son bak'o saboda karki raba shinfid'arki da shi, amma karki damu a gidana gadona zan ara miki kina kwana a kai." Kunya ce ta rufe ta kawai ba tace komai ba, a nutse ya fara aika lomar abincin nan yana lumshe ido, da yatsa ya shiga nunata yana fad'in "Kar ki ce santi ne nake fa, dama ina so na tambayeki kalar kayan da zaki saka a ranar aurenmu?" Waro ido tayi tana doka murmushi tace "To me kake kenan?" Girgiza kai yayi yace "Na kare kaina tun kafin na yi magana fa." Murmushi kawai tayi tace "Ka zab'a mana kawai." Kallonta yayi yace "Kin yarda dani kenan?" Lumshe ido tayi tace "D'ari bisa d'ari." Jinjina kai yayi yace "Insha'Allah gobe zan turo d'an sak'o ya kawo miki wanda na zab'a." Zaro ido tayi tace "Da wuri haka?" Hararanta yayi yace "Ban gane da wuri ba? Wata d'aya ne fa, ni fa ranar kawai nake jira ta zo dan na gama komai, Maah kawai nake jira ta sameni gidana." Sunkuyar da kai tayi cike da kunya, da haka suka ci gaba da hirarsu cikin farin ciki har yayi shirin tafiya, duk mik'ewa sukayi inda ya ce ta kira masa k'annanshi sannan ta fad'awa mama ya wuce, yanda ya buk'ata haka tayi dukansu tare suka isa har k'ofar gidan, saida y'a fara sallama da ita ya nuna mata cikin gidan yace "Koma ciki, nagode da rakiya." Ba musu ba d'ard'ar tayi abinda ya ce, saida ta shigo kuma saita samu kan ta da tunanin wai ita ce yau namiji ba ubanta ba ya umarta haka, da yatsa fa ya mata wani fit fit koma ciki, murmushi kawai tayi tana fad'in "Allah kar ka kawo ranar da wani zai ramawa yan uwanshi maza abinda na musu, dan ba zan iya d'auka ba gaskiya." D'aki ta samu mama ta shiga cire kayanta, Mama kam kallonta take har ta cire rigar ta saka riga da wando na bacci, tana idawa su Yaseen suka shigo da sallama da murna, duk gaban mama suka zube suna nuna mata ledar hannunsu, da sauri Mimi ta zauna gabanta ita ma ta jawo ledar ta shiga duba kayan, kayan k'walam ne sai turaruka da kuma kud'in daya zuba a ledar, d'aukar kud'in tayi ta ware jaka bibbiyu har guda goma ta ninkesu tace "Wannan na Abba ne." Ragowar mama ta mik'awa tace "Mama ga na ki." Kallonta su Yaseen sukayi suka ce "M没 fa aka ba, shi ne komai ba zaki bamu ba." Harara ta dalla musu ta nuna Amir da yatsa tace "Daina kumburo min bakin nan kafin ka ji jini a ciki." Kud'in data d'ora kan cinyar mama ta koma ta d'auka ta zagi jaka bibbiyu ta mik'a musu tace "Ku yi abinda zakuyi." Farin ciki ne ya lullub'esu wanda ko dala biyar suka samu a hannu murna suke. Mama dai bata tanka musu ba sai al'ajabin lamarin Mimi, ta d'auka zata d'auki wani kaso a cikin kud'in ita ma, amma ba wannan ne gabanta ba mahaifinta ne yafi damunta, dama kuma ko bata cire mishi ba dole ita zata damk'a mishi, kawai ta bar ta tayi yanda take so ne, dan tsabar kawaici ko d'an abun tab'awa wata rana Allah ya hore Abba ya kawo indai Mimi na gidan ita ke rabawa. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:52 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *14* Washe gari tsaf ta shirya ta kama hanya zata fita Abba dake cin d'umame ya kalleta yace "Mimi." "Na'am." Ta fad'a tana juyowa, saida taje daf dashi ta tsuguna kafin yace "Yanzu ba zaki fara jaraba cin tuwo ba? Ki gwada mana ko dan halin rayuwa." D'an yatsina fuska tayi tace "Amma ba zan iya ci ba, idan na je makaranta na ci alala ko meat pae." Gyara zamanshi ya d'anyi yace "Mimi, zan amince ki je gaida mahaifiyar yaron nan, amma abisa wani sharad'i." Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar, d'orawa yayi da "Zan amince ne saboda sanin d'an wane gida ne shi, a sanina da iyalen Aliyu Sharif ba mutanen banza bane, mutane ne manya masu dattako, matsalarsu d'aya shine auren *k'warya* ta bi *k'warya* da suke yi, gaba d'aya ahalinsu sun dunk'ule sun zama d'aya saboda suna auren zumunci ne a tsakaninsu, idan har kika ga wani wanda ba daga cikin ahalinsu ba to tabbas akwai huld'a ta kasuwanci ko abinda yayi kama da haka, idan kika ga wanda ba ahalinsu ba kuma d'an talaka to rabo ne ya kai shi ahali, amma yana fuskantar tsangwama daga garesu da wariyar launin fata, a hakan ma dan akwai dattawan arzik'i da suke son dak'ile wanna' d'abi'a ta iyalin, saidai duk abinda aka ce maka mata sun rik'eshi da hannu biyu sai an sha wuya ake cin nasara." Shiru tayi har saida yace "Abu na farko ina so ku min alk'awarin yin hak'uri da duk kalar tarban da kika samu daga danginshi, na biyu kuma kiyi hak'uri da duk irin wulak'anci ko cin zarafin da zai biyo baya, na uku shi ne ban yarda ba bayan gidan mahaifiyarshi da kuma yayarshi ki yarda ki k'ara binshi wani wurin ba, ko da hakan na nufin ki b'ata masa rai ne, sharad'i na gaba kuma shi ne dole sai in kin yarda zaku tafi da Asma'u ko d'aya daga cikin k'annanki dan su rakaki." D'aga kai tayi ta kalleshi a ladabce tace "Abba, hakan na nufin tarayyata da Asas zata iya jawo cin mutumci kenan?" Girgiza kai yayi yace "Ban da tabbas Mimi, amma daga gidan da kika fito da tsatson da kika fito nasan dole wani abu makamancin haka zai iya biyowa baya." Girgiza kai tayi tana hawaye tace "Amma a dakatar tun yanzu, a dakatar kawai indai aurena da Asas zai sa a zagi hallitarku ko talaucinmu, bana son auren na fasa na hak'ura dashi." Duk da mamaki suka kalleta sai Abba daya zura hannunshi ya dafa kafad'arta yace "Uwata, me yasa zaki ce haka? Kiyi hak'uri kinji, komai zai wuce kamar ba'a yi ba ai, abinda nake so ki sani shine yaron nan bai k'yamace ki ba duk da sanin wacece ke, dan haka kiyi hak'uri da k'alubalen da zaki fuskanta daga danginshi." Ajiyar zuciya ta dinga saukewa tana shashek'a tana jinjina kai alamar to, d'auke hannunshi yayi daga kafad'arta yana fad'in "To yanzu fad'a min wa kika zab'a dan ya rakaki?" Cikin rawar murya tace "Zamu tafi da Asma'u." Jinjina kai yayi alamar gamsuwa yace "To ki fad'a mata saita nemi izinin iyayenta ita ma sai ku tafi." Tab'e baki Mama tayi ba tace komai ba, har zata mik'e yace "Gashi ke baki da waya, da gobe sa茂 ki je ku gaishe da mahaifiyar yaron nan." Satar kallonshi tayi tana tunanin abinda ya fad'a, sai taji kunyarshi ta kama ta sosai duba da yanda take munafurtarsu haka, cikin ladabi tace "Abba dayake ina da lambarshi daya bani yace ko da ina buk'atar wani abu saina kirashi." Zaro ido yayi yace "Amma dai ai baki kirashi ba ko?" Girgiza kai tayi alamar a'a, jinjina kai yayi yana sauke b'oyayyar ajiyar zuciya yace "Yayi kyau, kuma idan kina buk'atar wani abun ki tuntub'eni zan miki." Jinjina kai tayi alamar to, d'orawa yayi da "To ya za ayi ki fad'a masa?" Jinjina kai ta sake yi tace "Zan kirashi ko da wayar Asma'u ne." Da sauri ya girgiza kai yace "A'a karki kira, ki bari idan kika taso lokacin na dawo nima da rana saina baki wayar ki kirashi." Jinjina kai tayi tace "To Abba, nagode." Murmushi ya mata yace "Allah ya miki albarka, tashi kije." Mik'ewa tayi ta fita a gidan tana share 'Yar k'walla da hijabinta mama na binta da kallo har ta b'ace ma ganinta. *12:06* Kamar kullum tafe suke tare da Asma'u cikin nutsuwa suna hirarsu, saida suka kusa k'arasowa gidan suka hangi gungun su Maryam tare da k'awayenta, tab'e baki Mimi tayi irin ko a jikina d'in nan, Asma'u kuma data lura da yanayin fad'a ne suke yasa ta kallon Mimi tace "Mimi dan Allah da manzonsa ki wuce cikin gida karki kula gayyar tsiyar nan." A yatsine ta kalleta tace "Ke! Bana da lokacin wanda suka fi su aji ma bare kuma su karan kad'a miya." Murmushi Asma'u tayi tace "Yawwa Mimi, rabu dasu kawai, kinsan fa amarya da tsautsayi" Murmushi sukayi a tare, zasu wuce kawai suka zagayesu su shiga, wasu sun d'aure k'ugu wasu kuma da itace a hannu, Maryam fake shugabar ce ta tsaya gaban Mimi tace "D'aukar fansa na zo Mimi, dan wallahi dukan da kika min baki wa banza ba." Wani luuuu! Tayi da idonta tare da jefanta da wani kallo sannan ta yatsina bakinta tace "D'aukar fansa? Da wannan zugar?" Tsaki tayi tare da d'auke kai daga gareta, hannunta Asma'u ta kama tana fad'in "Muje ke." Sak茅 tare gabansu sukayi Maryam na fad'in "Babu inda zata je sai jikinta ya gaya mata, idan sauri kike ki tafi." Wani dattijo ne ya zo wucewa ya kalli yanayinsu yace "Kai! Me yake faruwa ne? Ba daga islamiyya kuke ba? Maza ku wuce gida kar kuyi mana fad'a a nan." Gyara tsayuwa Maryam tayi tace "Ba ruwanka Baba kai dai yi tafiyarka kawai." Asma'u ce tace "Wai ke Maryam me yasa baki da tarbiya ne? Yanzu wannan ba yayi sa'an babanki ba." Tsaki tayi tace "Ke rufe min bakinki, ba dake nake ba." Tab'e baki tayi ta sake kama hannun Mimi tace "Mu tafi Mimi, karki kulata dan Allah." Cire hijabinta tayi ta wani jijjiga da fad'in "Ke babu inda zata je fa sai na..." Muryar Alhaji Saminu sukaji a bayansu da fitowarshi kenan yana fad'in "Mimi lafiya?" Duk kallonshi sukayi sai Mimi data wurga masa harara, juya baki Maryam ta fara yi tana fad'in "To fa! Ga kwarton na ta nan ya fit..." Bata rufe baki ba Mimi ta kasheta da mari a hassale tana cin kwalar rigarta da fad'in "Kwarton wa? Wa kike had'awa da shi?" Kacamewa sukayi duk su biyar d'in suka taran ma Mimi, Asma'u ma na ganin haka shigar mata tayi dan haka da gudu Saminu da mai gadinshi suka taho, haka ma yayan Asma'u daya fito yanzu sai wata mata da zata wuce ita ma, da k'yar suka rabasu su Maryam na ta aika musu zagi, a nutse Saminu ya kalleta yace "Haba Mimi, wannan ai ba girmanki bane fad'a a titi, me yayi zafi haka?" Cike da fitsara Maryam tace "Ka fad'i haka mana saboda karuwarka ce, kun d'auka bamu san me ye tsakaninku ba? Ai ko kallon da take zuwa yi bana Allah da Annabi bane." Da b'acin rai ya kalleta yace "Wai wace yarinya ce wannan fitsararriya marar kunya?" Juya baki ta shiga yi kamar zata cira shi, yayan Asma'u ne yace "Jikanyar Kaka ce mana, tarbiyar da aka bata kenan zank'amar banza." Shi ma harara ta wurga masa tana sake d'auke kan ta da gunaguni, Mimi dake hararenta ne ta nunata tace "Wallahi Maryam kika koma shiga harkata saina b'allaki, saidai kakarki tayi jinyarki." A fusace tayi cikin gida tana sab'a kakarta a kafad'a, hakan yasa Maryam binta da shewa har da bubbuga bakinta tana fad'in "Yeeeeeehu! Ku duneta karuwa kawai, karuwar gida daga nan zaune, ita ke ciyar da iyayenta da kud'in iskanci, yeeeehu anji kunya dai, har wani felek'e ake mana wai ita zatayi aurean kawo kud'inta, shi ma baisan ragowar samarin unguwar nan zai kwasa ba." A harzuk'e ta sake juyowa ta dawo kan ta da Sauri Asma'u ta rik'eta saboda ganin Abban mimi ya karyo kwanar layin, cikin jin haushi yayan Asma'u yace "Wai ke wace irin dabba ce? Wannan shi ne matsalar rainon Kaka kenan, mtssss?" Abba na zuwa ya shiga bin mutanen wurin da kallon tuhuma musamman ma Mimi, da k'yar yace "Me yake faruwa ne?" Asma'u ce tace "Abba wallahi su Maryam ne kawai suka mana taran dangi ni da Mimi." Kallon Mimi yayi data sunkuya kan ta a k'asa yace "Shiga cikin gida." Wucewa tayi tana kumbura hakan yasa shi kallon Maryam d'in dake fad'in "Dole ki shige mana anji tsoro, wallahi da sai mun miki terere a unguwar nan, kuma naje an fad'a karuwa karuwa karuwar gida." Rintse ido Abba yayi yana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Sake bud'ewa yayi ya kalleta, Asma'u ce cikin jin haushi tace "Saidai in kece karuwar amma ba Mimi ba, banza jahila sai tsayin kawai babu lissafi." A zabure tace "Ke rufawa kanki asiri, ai ke dama yar abi yarima asha kid'a ce, tunda duk h么tel d'in da za taje ke kika rakiyarta, sannan tana sammiki wani kaso a cikin kud'in tazubar d'in, gaba kad'an ke ma zata fara had'aki da alhazan birninta." Wani mahaukacin mari Saminu ya kifa mata cikin b'acin rai yana fad'in "Ke ashe mahaukaciya?" A hassale ya juya y'a kalli yayan Asma'u yace "Kai ina ne gidan? Yau sai kun bar unguwar nan fitinanniya kawai." Wani kuka ta fashe dashi tana fad'in "Kaka, Kaka." Ai kamar jira take ta kira sunanta ta fito ko mayafi babu tana fad'in "Waya tab'a min yar amanata? Wani tsinanne ya daki marainiyar Allah?" Saminu ne ya nuna kanshi yace "Ni ne nan, wannan jikarki ce Iya?" Saida ta kutsa ta kama hannun Maryam tace "Jikata ce? Me tayi ka daketa?" Cikin bud'e baki da rashin wayo Maryam tace "Wai kawai dan na ce Mimi karuwar gida ce tana bin samarin unguwar nan, shi ne ya mareni a fuska yana zagina yana kirana mahaukaciya, kuma ai gaskiya na fad'a ko Kaka? Waye baisan tana iskanci ba ana bata kud'in kashewa, kuma ai har IPhone gareta ma." Duk kowa babu wanda yace wani abu saboda mamaki, sai Abba dake jin knashi na sara mishi da k'yar yace "Wace irin IPhone kuma?" D'aya daga cikin yan matan ne wata tace "IPhone dai daka sani, waya salula ba." Zurum ya fad'a cikin gidan hankali a tashe, anan kam wannan hayaniyar suka ci gaba da yi inda muryar Kaka ta karad'e unguwar tana cin zarafin Saminu, saidai ya shiga mota ya barsu amma fa yayi niyyar sai sun bar unguwar nan, dan ta tab'a masa Mimin sa ba kuma zai lamunta ba. Abba na fad'awa gidan a d'aki ya sameta ta cire hijabi tana share k'walla, kalmar karuwar nan ta mata zafi sosai, Mama kam kallonta tayi tace "Ke da wa kuma?" Majina ta ja amma ba tace komai ba, tana shirin zame rigarta dan ta watsa ruwa Abba ya shigo d'akin b芒 sallama, saida ta tsorota ganin yanda ya shigo d'akin, wani kallo ya tsareta dashi ya jefa mata tambayar "Da gaske kina da waya?" Zaro ido tayi tana sulalewa k'asa ta shiga rarraba ido, dafe cikinta tayi daya shiga murd'a mata tana addu'a a zuciyarta, a tsawace ya sake fad'in "Ba dake nake magana ba kina ji na kinyi shiru?" Da sauri tace "K'arya ce Abba, bana da waya ni." Da sauri yace "To IPhone d'in da ake magana a kai fa ta uban wacece?" Cikin alaamar rashin gaskiya tace "Abba...IPhone kuma? Ni wa ya bani IPhone ? Ban tab'a ganinta a zahiri ba wallahi." D'an gajeran yatsanshi ya nuna mata yace "Uwata, wallahi fa duk randa na kamaki da waya a hnanu zaki ci ubanki a gidan nan." Tare suka kalleshi ita da mama, mamaki suke yanda ya b'angaro wannan ashar haka shi da ba mutumin ashar ba, jinjina masa kai tayi alamar to hakan yasa shi ciro k'aramar tecno d'in shi ya mik'a mata yace "Ki kira ki fad'a masa, idan kin gama wayar sai kije ki tambayi iyayen Asma'u idan zasu barta ku tafi tare." Karb'a tayi da ladabi tana fad'in "To Abba." Saida ya fita kafin ta zauna bakin gado tana saka lambobin Asas, ta jima tana kururuwa kafin aka d'aga tare da sallama, murmushi ta saki tana amsawa taare da fad'in "Na d'auka ba zaka d'auki kiran bak'uwar lamba ba." Murmushi yayi shi ma yace "Wane ni? Ban cika d'auka ba kam, haka kawai na ji wannan kiran na musamman ne saboda yanda zuciyata ta shiga bugawa." Yar dariya tayi tana satar kallon mama tace "Da baka d'auka ba ai da na ce na fasa auren." Jin haka yasa mama mik'ewa ta bar mata d'akin cike da kunya, Asas kuma d'orawa yayi da cewa "Maah da kin kasheni ashe, kinsan burin da na ci akan auren nan namu kuwa?" Yar dariya tayi tace "Idan na kashe Asas ai Mimi ma mutuwa zatayi, ka d'auka zan rayu ne babu kai?" Wani k'asaitaccen murmushi yayi yace "Mimi kar kisa na kuma durk'usawa gaban Abba na ce ya jawo lokacin aurenmu nan da sati." Dariya kawai tayi mai d'an sauti b芒 tace komai ba, a hankali cikin sanyayyar murya yace "Naanah wannan lambar waye?" A hankali ita ma tace "Lambar Abba ne, ya bani ne na kiraka dan na sanar da kai ya amince na je na gaishe da mama, saidai yace bayan gidanku da gidan yayarka kar na k'ara gaba sai gida kawai." Wani murmushi ya sake yi yace "Na ji dad'i sosai maah, hakan kuma yayi kyau sosai, ba komai zamuyi yanda Abba yace, yaushe zaki shirya." A tausashe tace "Abba yace gobe." Murmushi yayi mai sauti yana fad'in "Kinsan da kuwa yanzu haka na dawo daga gidan aunty Hafsat, kuma ina zolayarta ina fad'a mata gobe zaki zo, har take tambaya ta wai me zata dafa miki? Ni kuma na ce mata ta yanka miki bijimin sa." 'Yar dariya tayi tace "Ni kam ina zan kai bijimin sa? Ai zaka sakani na tafi da babbar jaka dan na yi wa 'yan k'annaina guzurin abinda suka jima basu ci ba." Wani d'an siririn murmushi yayi cike da tausayin yarinyar a ran shi, a tausashe yace "Ina wayarki? Me yasa zaki cinyewa Abba katinshi?" Murmushi tayi tace "Abba ne ya bani ai saboda ta wa babu caji, amma idan na saka a caji zan kiraka." Jinjina kai yayi kamar yana gabanta yace "Shikenan ina jira, kuma fa karki manta dani." Girgiza kai tayi ita ma tace "Wace ni na manta da angona? Ai sai na ji sammacin kotu ban shirya ba." Yar dariya yayi yace "Mimi girmanki ai ya isa kiyi laifi kuma babu mai k'arfin halin hukuntaki." Murmushi tayi tace "Zaka fasa min kai na fa, yanzu dai sai na kiraka d'in." Da haka sukayi sallama ta kaiwa Abba wayarshi a tsakar gida yana kallon mama dake tsintar shinkafa, tana durk'usawa ta mik'a mishi ta mik'e ta koma d'aki, kayanta ta cire ta fito da d'aurin k'irji da hijabi saboda kunyar uban ta shiga dan watsa ruwa, jim kad'an ta fito ta shiga d'aki doguwar rigar kanti kawai ta saka ta fita a gidan zuwa gidansu Asma'u, duk da kallo suka bita sai dai mama ta k'asan ido take kallonta saboda kunya. Saida ta fice Abba ya sauke ajiyar zuciya y'a kalli mama yace "Ina zaune lafiya da kowa a unguwar nan, ina k'ok'arin kiyaye hakk'in mak'wabtaka, wallahi duk ranar da yarinyar can ta sake kira min 'ya da karuwa sai nayi shari'a da ita a kotun musulunci, ba zan lamunta ba wallahi dan na yarda da 'yata." Mama kam a sanyaye tace "Ayi hak'uri dai malam, Allah ya kyauta kawai." K'wafa Abba yayi yana jinjina kai bai ce komai ba, ita kam mama a ranta take jin zafin maganar kamar zatayi kuka, ko da da gaske ne abinda suka fad'a ai akwai cin zarafi da tozarci, ita kan ta bata jin zata iya yin shiru idan aka sake maimaita haka gaskiya, dan 'yarsu mutumcinsu ce, babbar darajarsu kuma Mimi ce. *Mim-Ma'u* Labarin fad'ansu da Maryam babu inda bai shiga ba, shiyasa ma tana shigowa gidansu Asma'u suka sakar mata ido aka yi shiru, ita kam dake ta saba da irin wannan kallon dama sai bata kula da tsiyar kowa ba, maman Asma'u kawai ta kalla tace "Mama Asma'u fa?" Nuna mata d'akin tayi tace "Yanzu ta shiga ciki." Wucewa kawai tayi ba tace da ta jira izinin shiga ba, samunta tayi tana saka kaya da alama wanka tayi ita ma, cire hijabi tayi ta jefa kan gadi ta zauna tana fad'in "Asma'u wurinki Abba ya aikoni." Kallonta tayi tace "Wuri na kuma? Me y'a faru?" Saida ta kalleta da kyau tace "Asas ne ya nemi izinin na je na ga Hajiarsu, shi ne Abba ya amince amma dole sai in tare zamu je da ke." Da mamaki Asma'u ta zauna kan kujera tana gyara rigarta da fad'in "Da gaske Abba ya amince? Yaushe ne tafiyar?" Yatsina baki tayi tace "Gobe." Da fara'a tace "Ba komai Mimi, zan fad'awa mamanmu insha'Allah sai mu tafi." Gyara zama tayi tace "Asma'u, bana so ki je gaskiya." Da mamaki ta tsareta da ido tace "Ban gane ba? Me yasa?" Cikin rad'a tace "Kin gane Asma'u, shi fa Asas ni kawai ya buk'ata sannan ni ce zai gabatar a gaban mamanshi, Abba dai nasan tsoron faruwar wani abu suke, insha'Allah zan kare kaina babu abinda zai faru." Da mad'aukakin mamaki tace "Yanzu Mimi tsarin na iyayenki ne bai miki ba? Ina laifin kariyar da suke son baki ma?" Yatsina fuska tayi tace "Ban ce bai min ba Asma'u, kawai dai ina so ne na tafi daga ni sai shi, bansan wace kalar tarba zan samu ba idan na je." Cikin tsareta da ido Asma'u tace "To kinsan da haka me yasa kika zo kika fad'a min?" Ita ma idonta cikin nata tace "Saboda tare zamu bar gidan nan." Da mamaki tace "Kamar ya?" Gyara zama tayi tana wani malalacin murmushi tace "... *Muna barar addu'arku yan uwa? Allah ka bawa Khadija lafiya. Kwate na ma Allah ka k'ara mata lafiya mai inganci* *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:52 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *15* "Zamu fita daga nan muje gidan Iya Delu, ke zaki zauna a nan ni kuma saina wuce." Girgiza kai tayi tace "Mimi kina ganin ba matsala? Ya zakiyi idan Abba ya ganeki? Gaskiya ni dai ina jin tsoro ba za'a yi haka dani ba." Cike da tabbaci da tsaurin ido tace "Babu abinda zai faru Asma'u, kwantar da hankalinki kawai." Da alamar jimami sosai a fuskarta tace "Zamu ci amanarsu kenan? Yaudarar Abba zamuyi fa Mimi." Girgiza kai tayi tace "Ba yaudara bace, Asma'u ki fahimceni mana, kinga yanzu idan..." D'aga mata hannu tayi tace "Matsalata dake taurin kai, indai kikayi niyyar abu babu mai hanaki." Mik'ewa tayi ta fara k'ok'arin d'aura zanenta bata sake tankata ba, ita ma mik'ewa tayi ta d'auki hijabinta a hannu ta fito dan tasan sunyi fad'a kenan ko zasu shirya sai sun had'e a islamiyyar yamma, takalminta ta saka a k'ofar d'akin ta wuce tana k'ok'arin saka hijab d'in, da kallo yayan Asma'u ya bi k'ugunta yana murmushi, lura da hakan yasa kishiyar maman Asma'u (mahaifiyarshi) cewa "Kai!" Wannan tsawar data daka mishi tasa har Mimi juyowa ta kalleta, kallonta shi ma yayi yana zazzare ido, cikin jin haushi tace "Dan ubanka me kake kallo baki sake?" Yatsina baki Mimi tayi ta juya ta saka hijab d'inta ta wuce ta barsu tana jin yana fad'in "To wai mama bani da ikon kallon abinda na ga dama ni da ido na?" Ita kuma cikin fad'a take fad'in "Dan ubanka duk zalamarka waccen tafi k'arfinka, na d'aya dai kaga taxi ce ita da kowa ma shigarta yake, na biyu ba kowa take kulawa ba sai wanda taga akwai mamora a jikinsa." Mimi kam ko fa a kwalar rigarta sai ma fita da tayi daga gidan, ita indai ita zaka tab'a kai tsaye to bata da matsala da kai, ka dai saka iyayenta ne ko da ta hanyar zaginta ne bata lamunta ko kad'an, dan taana da tabbacin ko mijin aurenta zata iya tsinke fuskarshi da mari idan ya nemi fad'a ma iyayenta magana. *Sheikh* Cikin nutsuwa ya sake tank'washe k'afafunshi yana had'e tafukan hannayenshi ya ci gaba da fad'in "A duk inda zaku shiga a fad'in duniya, a duk halin da zaku tsinci kanku a ciki yarana kada ku yarda kuyi wasa da addininku, addininku shi ne gatanku, addinin islama shi ne alk'iblarku, addinin nan shi ne madogararku, dan haka duk inda zaku samu kan ku kuyi alfahari da addininku, kada bambamcin yare ko k'abila yasa ku ji kunyar nuna kanku a matsayin musulmi, kada wani rud'i na duniya ko kuma muzgunawa tasa ku wofantar da addinin daya baku madafa a sanda baku da tudun dafawa, addinin musulunci rahama ne a garemu kuma alfarma." A hankali ya kalli Aisha yace "Aysha, ke ce babba a gidan nan, ina sake gargad'inki da ki kula sosai da yan uwanki ki tayasu rik'e sallarsu ta farilla, kada ki barsu suyi wasa da ita a kowane hali, nasan macece ke kuma a halin yanzu kowane lokaci zaki iya shiga d'akin mijinki, amma hakan ba zai hanani sake jadadda miki rik'o da zumuncinku ba, a duk inda aure ko ratuwarki ta gaba zasu kaiki, zaki iya tsayawa tsayin daka wajen ganin kun rik'e zumuncin nan, ko bayan babu ranmu zaku zama gatan junanku." Cikin tsareta da ido yace "Kin fahimta?" Jinjina kai tayi alamar eh cikin sanyayyar murya tace "Eh Abie, insha'Allah zamu rik'e zumuncinmu, wannan alk'awari na ne a gareku iyayena." Jinjina kai yayi yace "Masha'Allah, sai kuma kai *Heezam*." Ya fad'a yana kallon k'annan Aisha mai bi mata, a nutse yace "Bana da d'ar a kan ka dan na saka maka ido sosai ina lura da duk wani tako da motsinka, a tak'aice kuma a yanzu dai banga wani abu daya nuna shagala akan sallahrka ba, haka kuma ban ga alamar wasa a cikin karatunka ba, kamar yanda banga wani b'ataccen aboki da zai iya b'ata tarbiyarka ba, saidai hakan ba shi zai sa na zuba maka ido ina kallonka haka kawai ba, Heezam." Ya kira sunanshi cikin dakakkiyar murya, amsawa yayi a ladabce yace "Na'am Abie." D'orawa yayi da "Daga yanzu zamu fara fita tare da kai zaman majlisi, sannan ina so kai ma ka fara wani k'ok'ari akan matasa yan uwanka dan bayar da ta ka gudummuwar." Da ladabi ya jinjina kai yace "Insha'Allah Abie." Kallon *Aswane* yayi ya saki murmushi yace "Manya masu gari, macijin k'aik'ayi kenan sari ka nok'e, wato yarona Aswane duk gidan nan babu wanda ya kai ka karatu, haka kuma babu wanda ya kai ka iya shegantaka." Duk dariya aka d'auka a wajen har Hafsat dake shafar cikinta saboda juyawar da yaron cikin ke yi mata, cikin muryar laushi tace "Akwai son gayu fa kamar ya ga ubanshi Asas, amma kuma yafi kowa tsanar irin shigar da matasa keyi ta k'ananan kaya." Dariya sheikh yayi sosai yana fad'in "Wannan ikon Allah yana bani mamaki, wai kai ka saka riga da wando na zamani ka d'aure k'ugu da ceinture (belt), amma idan ka fita waje ka ga wani matashi zai wyce da shiga irin ta kai saika gyara tsayuwa ka tsayar ka dinga yanko mishi hadisai da ayoyi harda karatun d'ab'ia na d'an adam ma kana nuna mishi rashin dacewar haka." A sanyaye ya kalli Aswa'ne daya d'aure fuska tamau yace "Sheikh Aswane ya kake nufi ne to? Shin kana so ka koyar da hallacin shigarka ne ga matasa a aikace? Ko kuma dai kana son su k'yamaci abinda kai suka ga kana yi ne?" Saida ya sauke ajiyar zuciya ya shafa tarin sumar dake kan shi a gaban yace "Abie, ai ni ba irin waccen shigar nake yi ba da ake zazzago wando ana takawa, kuma nima ina so na daina saidai Allah ne ya saka min soyayyar kayan a raina, kuma sun fi yi min kyau idan na saka." Girgiza kai yayi yace "Kash! A gaskiya tunani da idonka sun fad'a maka k'arya yarona, taya kake tunanin suturar yahudawa zata fi yi maka kyawu fiye data ka suturar? Wa ya fad'a maka kawai kana son su ne saboda Allah ne ya saka maka soyayyarsu? Aswane magana ta gaskiya sutura ta hausa ita ce cikakkiya kuma kamilalliyar sutura, na yarda idan ka ce sun fi maka kyawu a jikinka, to amma kamala fa? Ita ma suna fito maka da ita ne?" Shiru yayi kan shi a k'asa hakan yasa shi girgiza kai ya gyara zama tamkar zaiyi magana da d'an shekara ashirin ba wanda shekarunsa duka goma sha biyu bane yace "Aswane, wannan suturar da kake sakawa ta hayudu ce, manufa ce dasu data sa suka k'irk'iri wannan suturar, kuma sun cimma burinsu tunda har suka yi nasarar ribatar ire-irenku, amma ka sani cikar kamala na cikin tufafin hausa, fito da asalin haiba da kwarjinin mutum sai tufafin bahaushe, da wannan nake kira gareka d'ana ka siyawa kanka mutumci ta hanyar yafa shigar mutumci a jikinka." Jinjina kai Aswane yayi yace "Insha'Allah Abie, zan kiyaye." Jinjina kai yayi ya kalli d'an k'aramin yace "Wannan shi ne autana kuma ba autana ba, *Munzeer* yaron kirki ne, ba ruwanka da rigima ko fad'a, karatu kawai ka saka a gaba ko yaron kirki?" Cike da jin dad'i yaron mai shekara biyar ya jinjina kai alamar eh, dafa kanshi yayi yana jinjina kai da murmishi yace "Allah muku albarka, Allah ya k'arawa karatun albarka, Allah ya k'ara had'a kanku, Allah ya wadataku da lafiya mai anfani." Gyara zama yayi yace "Ku tashi ku tafi." Mik'ewa sukayi bayan sun amsa a ladabce, duk da kallo suka bisu har suka b'ace ma ganinsu, saida suka shige ciki kafin ya mik'e shi ma, hannun Hafsat ya kama yana fad'in "Muje ki kwanta ki huta, dare yayi fa." Murmushi tayi tana ci gaba da shafa yaron cikinta daya dunk'ule wuri d'aya kamar baya motsi, suna shiga d'akin ta fahimci yau kenan zai kawo mata ziyara, dan baya zaune sai mace ta sameshi d'akinshi, da kanshi yake zuwa inda kike sannan ya lallab'aki ya amshi hakk'inshi, dan haka saita daure sosai ta saki jikinta bata yarda ta nuna bata jin dad'i ba, saida ya tayata yin wanka kafin suka k'arasa gadon girma, duk da tana jin d'an cikinta ya dunk'ule mata a mara haka ta jure bata nuna bata ra'ayi ba, har tambayarta yake ya isa haka saita sunkuyar da kai tace "Sai ka gamsu." Shi kuma a duniyar Allah yana matuk'ar son mace mai raki, rakin ma irin na tsiyar nan, wallahi a duniya yana son y'a ga mace dake mayar da masassara ciwon kai, wacce zata dinga billi tana kuka akan abinda bai kai bai kawo ba, yana so wata rana Hafsat ta gwada yin haka ko sau d'aya ne, da zai yi zaune ya aje hularsa da babban riga da hirami ya dinga mata hidima yana rarrashinta. Da k'yar ya samu gamsuwa ya taimaka mata ta tsarkake kanta ta dawo ta gyara shinfid'ar ta kwanta a matuk'ar wahale. *Washe gari* Tana tsaka da tsantsara kwalliyarta a fuska ta ji wayarta dake cikin k'aramar jakar da zata fita da ita tana vibrations, saida ta d'an d'aga labulen d'akin ta tabbatar suna waje suna harkar gabansu kafin ta ciro wayar, zaro ido tayi ganin lambar sheikh ce wacce tsabar mahimmancin data bata har ta iya hardaceta a kan ta, ita kan ta bata san ta bashi wannan mahimmancin ba. Sam bata son d'aukar wayar a lokacin, amma abun mamaki lambarshi kanta kwarjini take mata ta yanda ba zata iya share kiran ba, hannunta da zuciyarta na kakkarwa ta d'aga kiran tana jan sallama, a sanyaye sosai ya amsa da "Wa'alaiki salam." Shiru ne ya d'an ratsa na dak'ik'u kafin yace "Ki gafarce ni Ryam na sake kiranki, zuciyata azalzalata take a game da lamarinki, dan Allah ki fad'a min idan Abbanki ya dawo na zo na ganshi." Wani sanyayyan murmushi ta saki a ranta tana fad'in "Allah mai iko, ni Maryam ba kowa ba kuma ba 'yar kowa ba, yau ni ce har babban malami kamar wannan yake min magiya haka?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da tunanin ai Abba ya karb'i lefenta har da ma kud'in aurenta, dan haka tasan duk girmanshi Abba ba zai yarda yayi magana biyu ba, dan haka ta saki murmushin jin dad'i tare da bud'a bakinta tace "Abba ya dawo jiya, dama na rasa yanda zanyi na kira ne." Wani sanyayyan murmushi yayi shi ma har tana jin sautinsa yace "Na ji dad'i sosai Ryam, zan zo gidanku yau insha'Allah." Cikin rashin jin dad'i a zuciyarta ganin yanda zata sakashi zama wani wawa haka tace "Shikenan, Allah ya amince." Da fara'a yace "Ameen, nagode, sai anjima." A k'asan mak'oshi tace "Uhum." Tana aje wayar ta kalli agogon screen d'in, da sauri ta aje wayar ta shiga gaggawar k'arasa shirinta, ta mik'e kenan tana gyara zaman rantsetsiyar abayar data saka bak'a wulik wacce ta fito da hasken fatarta ta yana kallabin y'a mata kyau sosai, Asma'u ce ta shigo da sallama mama ta amsa, tana shigowa suka kalli juna suna murmushi, ko gyara kayan data barbaza batayi ba ta d'auki jakarta tace "Muje kinji." Fitowa sukayi Asma'u na fad'in "Wa zai d'auke waccen kayan kuma?" Kafin tayi magana mama da taji ta tace "Ta bari jakarta ta d'auke mata mana." Dukansu dariya sukayi kafin Mimi tace "Mama zamu wuce gidan Iya, kinga idan ya gaishesu ita da malam sai mu wuce." Jinjina kai tayi tace "Allah ya yarda, ku kula dan Allah kunji." "Insha'Allah." Ta fad'a tana kama hannun Asma'u suka fita daga gidan. Kamar dai kullum zaka rantse da Allah wata 'yar hamshak'in mai kud'i ce, hatta takonta d'aukar hankali yake yanda duk da duhu ne ana k'are mata kallo, ga k'amshin da take bari a duk inda ta gifta ta wuce, da haka suka isa gidansu Iya D'茅lu, da raha suka shiga zolayar juna ita da kakanin nata data samu malam na cin abinci, kamar yanda tun a kan hanya ta fad'awa Asas dan haka suna zuwa ba jimawa ya iso. Da kan ta ta fito ta mishi iso zuwa cikin gidan, sosai suka gaisa har malam na fad'in "Ai bansan zaka zo ba da ban yarda ka sameni ba." Cikin shagwab'a Mimi ta kalleshi tace "Angona." Dariya yayi tare da shafar kumatunta yana fad'in "To ai bana so ya gane kishina ne a kan ki, zan iya cakumarshi yanzun nan mu hau sama." Dariya sosai Asas yayi yana sunkuyar da kai cike da kunya, Iya Delu ce tace "Ni kuma farin ciki nayi dana ganeshi, dan a take naji na samu miji nima mai jini a jika." Kallon Mimi tayi tace "Ba kullum cika baki a kan ni na tsufa bane ke kuma sabon jini? To ni ma na k'wace miki miji." Dariya sosai ake yi har Asas yace "Gaskiya ne, ni ma yanzu dana ganki na ji bana buk'atar sabuwar jinin, dan kuwa da tsohuwar zuma ake magani." Da irin rahar nan suka musu sallama suka fita tare da Asma'u, saidai a k'ofar gidan ita suka rabu inda Mimi ta sake jadadda mata "Asma'u ki zauna gidansu Jamila, idan na zo zan kiraki a waya saiki fito waje mu k'arasa gida, kin gane?" Jinjina kai tayi tace "Na gane, sai kun dawo." Murmushi ta mata tace "To." A raunane tace "Dan Allah Mimi ki kula da kanki kinji." Jinjina kai tayi alamar to, gidansu Jamila ta nufa ita kuma ta bud'e motar ta shiga, kallonta yayi yace "Ba tare zamu tafi da ita ba?" Girgiza kai tayi tace "Dama akwai inda zata je, hanya ce kawai ta had'amu." Jinjina kai yayi tare da tayar da motar suka d'auki hanya. A k'alla sun d'auki minti talatin kafin suka isa gidan, a sanda ya shiga gaba yana mata jagora zuwa babba kuma k'ayataccen falon, tsoro, fargaba, al'ajabi da kuma kunya ne suka taru suka baibayeta, da haka suka shiga falon Asas na fad'in "Hajiata, fito ga sarakuwarki na kawo miki, zo kiga yar beautyna." K'asa ta sake yi da kanta tsabar kunya tana sake rik'e jakarta tamau a hannu, da fara'a da kuma al'ajabin ganin kyakyawar yarinyar mai kama da larabawa ta shiga takowa tana fad'in "A'a masha'Allah, yau kam autana ya cika alk'awari." Tana zuwa ta ja Mimi a jikinta ta rumgume wacce ke neman sulalewa k'asa, sosai tayi mamakin yanda mahaifiyarshi ta tarbeta, bata zame da ita ko ina ba sai kan teburin cin abinci, zaunar da ita tayi tana k'walla kiran "Salamatu! Salamatu." "Na'am Hajia." Aka amsa daga ciki ana fitowa, tana zuwa Hajia tace "Kinga bak'uwa na yi, ki kawo mana abinci." Saida ta kalli Mimi da kanta ke k'asa, d'an k'ara lek'a fuskar tayi da son gano a ina ta san fuskar, tunawa da tayi yasa ta jinjina kai ta kalli Asas, murmushi ta k'ak'aro tace "To Hajia." Juyawa tayi ta koma tana mamakin shi kuma yallab'ai Asas me ya had'ashi da yarinyar? Ita ce zai aura? Wacce ake kira da karuwa, karuwar ma ta samarin unguwa, bugu da k'ari kuma 'yar wada, dan kuwa duk fad'an nan da akayi na jiya a gabanta, ita ce ma suka zaburo suka rabasu sanda suka kacame da fad'a. Haka ta gama duk abinda ya dace ta kawo ta kuma kula da komai amma bata daina kallon Mimi ba, gashi taga daga Hajiar har Asas d'in sai hira suke jan ta da ita da raha alamar dai ta samu karb'uwa a wurinsu sosai. Saida ta gama ta koma ciki Hajia ta kalli Mimi tace "Takwarata, ci abinci kinji, nan gidan fa ba bak'onki bane." Murmushi ta sake yi ta sunkuyar da kanta k'asa, da zolaya Asas yace "Kunyar Hajia wai kike ji? Kinga yanzu fa ke ce autarta ko, ni na bar miki yanzu dan na girma, tunda nan gaba kad'an zaki haifa min yara." Satar kallonshi tayi da mamaki baki bud'e, sai kuma tayi shiru kawai kan ta k'asa tana jin Hajia na fad'in "Matsalata da kai kenan rashin kunya." Jawo kujerarta tayi ta koma kusa da Mimi ta d'ebo abincin zata kai bakinta, sinne kai ta sake yi cike da kunya tana murmushi, tallabo hab'arta tayi tace "Maryam, ni ma fa mahaifiyarki ce, kinga bana da 'ya'ya dayawa sai guda biyu, ki saki jikinki dani kinga zaki shigo ahalin nan ba da jimawa ba." Jinjina kai tayi alamar to, sake kai mata cokalin tayi a baki haka yasa ta karb'a cike da kunya, duk yanda ta so zillewa bata samu dama ba haka ta dinga ciyar da ita da hannunta, tana tsaka da cin abincin ne ta kalli Asas tace "Kaga takwarata sai tayi kama da *Fanna*, ko dai 'yar uwarta ce?" Girgiza kai yayi yace "Bana jin ma sun tab'a had'uwa." Kallon Mimi tayi tace "Takwarata, waye mahaifinki? Ina ne gidanku?" Da sauri Asas ya kallesu yana neman k'warewa, to shi dai bai wani zauna ya fad'a mata wacece Mimi ba, yasan danginshi kuma farin sani zasu iya kawo mishi tangard'a, gata ita kuma bata b'oye komai daya shafi asalinta yasan tsaf zata fad'a mata komai. Mimi ma satar kallonshi tayi kafin tayi k'asa da kanta tace "... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:54 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *16* "Mama ni ba 'yar kowa bace, mu talakawa ne da muke fafuta akan abinda zamu ci, sannan iyaye na..." "Mutanen kirki ne." Cewar Asas da sauri yana tsare Hajia da ido, duk kallonshi sukayi da mamaki sai Hajia data d'an basar ta kalli Mimi tace "Ke 'yar talakawa ce?" Jinjina kai tayi ba tare data kalleta ba, a hankali Hajiaa ta aje cokalin hannunta tare da yab'awa fuskarta yanayin rashin jin dad'i, kallon Asas tayi ta mik'e tace "Ka sameni a d'akina." Lumshe ido yayi irin na ohh shiit d'in nan tare da kallon Hajiar bai ce komai ba, da kallo suka bita har da Mimi dake al'ajabi da mamaki, kallonta yayi ya mik'e yace "Ina zuwa Maah, karki damu kin ji, ki ci abincin." Da kallo ta bishi kafin ta kalli farantin gabanta, hak'ik'a tana son cin wannan gara da aka wadata gabanta da ita, saidai zalamarta bata kai wannan matakin ba, da taga fuska ne ma zata iya d'iba ta kai wa 'yan k'annanta su goge hak'ora, amma daga yanda ta ga fuskar matar kam tasan sai ta Allah aurenta da Asas yayi wu. *Suna* shiga a zafafe ta juyo tana fad'in "Asas dama yarinyar nan 'yar talakawa ce?" Cikin rashin karsashi yace "Hajia miye dan 'yar talakawa ce? Shikenan mu dake da hali ba zamu iya auren 'ya'yan marasa k'arfi ba dan a tallafawa juna." A kausashe tace "Kaga Asas ba kasancewarta 'yar talakawa ba yasa nake maka maganar nan ba, babbar matsalar shi ne dama ba daga ahalinmu ta fito ba, dangi zasu ga laifina ne na barka ka auri yarinyar da ba nasabarku d'aya ba sannan yar talakawa, kafi kowa sanin yanda ake son had'aka da 'ya'yan dangi amma ka k'i, larurarka tasa na ce a rabu da kai zaka zab'a da kanka, shi ne yanzu zaka zo min da waccen yarinyar." Sanyaya murya ya sake yi sosai yace "Hajia ta, dan Allah karki hanani auren Mimi, ina sonta da zuciya d'aya ba zan iya rabuwa da ita ba." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Yanzu ka je kusa da ita ka zauna, idan ta kammala ka kaita gidan auntynka tunda an fad'a mata zaku je can." Marairaicewa yayi yace "Hajia ba zaki hanani aurenta ba?" Yatsina fuska tayi tace "Ka je kawai zanyi tunani." Sake shagwab'ewa yayi yace "Hajia haka zaki tarbi bak'uwarki?" D'an murmushi ta k'ak'aro tace "Muje to." Da fara'a ya biyo bayanta suka fito falon, yanda suka barta haka suka sameta, bata yarda ta had'a ido da ko d'aya daga cikinsu ba, zaune sukayi Asas na fad'in "Maah, mun barki ke kad'ai? Kiyi hak'uri." Murmushin yak'e tayi haka ma Hajia murmushin yak'en ta shiga yi, jim kad'an ya kalli Mimi da kanta ke k'asa bata cin abincin yace "Kina lafiya ko?" Jinjina kai tayi ta kalleshi tace "Abba yace kar na jima." Murmushi yayi ya kalli Hajia yace "Hajiata zamu wuce gidan Aunty Hafsat." D'an kallon Mimi tayi tace "To Allah ya tsare, ku gaishesu da kyau." Mik'ewa Mimi tayi hakan yasa shi ma ya mik'e haka ma Hajia, k'wala kiran Salamatu tayi tana zuwa ta sunkuya tace "Hajia gani." A gadarance tace "Ki d'auko min sak'on nan dana ware dan bak'uwata." D'an d'aga ido Mimi tayi ta kalli Hajia, a kuskure kuma idonsu suka had'u ita ma tana kallonta tana mamakin yanda tace yar talakawa ce ita amma fatarta wata irin fresh da ita, uwa uba ga abayar jikinta wacce ta shekarar bara ta siyowa Hafsat su dayawa da shegiyar tsada, to a ina ta samesu kenan? Bayan tace talaka ce ita. Tana wannan tunanin Salamatu ta kawo manyan ledojin kalar pink guda biyu, ajewa tayi k'asa tana fad'in "Gasu Hajia." Cike da wulak'anci tace "Ki bata, zasu mata anfani." D'agowa ta sakeyi ta kalli idon Hajia tsaf kallo na ki fahimceni naa fahimceki, Hajia kan ta saida ta ji wani shakkun yarinyar saboda yanda ta kalleta babu tsoro a ciki da kuma rashin d'aukar raini, mik'o mata ledojin Salamatu tayi tana fad'in "Gashi k'aramar Hajia." A yangance ta kalli Salamatu ta yatsina fuska dan hakan d'abi'arta ce kafin tace "Nagode, Abbana ya hanani karb'an kyauta irin wannan." Da mamaki Hajia ta kalleta, sai kuma ta tab'e baki ta kalli Asas tace "Ka d'aukar mata kayan, watak'ila kunya take ji." Girgiza kai tayi a hankali tace "Bana so Abbana ya min fad'a sakamakon aikata abinda ya haneni." A ladabce ta juya zata fita tana fad'in "Nagode da karramawa, sai anjimanku." Da kallo Hajiar ta bita haka ma Salamatu, Asas kam tuni ya juya zai bi bayanta Salamatu tace "Alhaji ka d'aukar mata kayan mana, ina ga fa kunya ce kamar yanda Hajia ta fad'a, ai b芒 kyau mayar da hannun kyauta baya." Murmushi ya mata tare da d'aukar ledojin nik'i-nik'i ya bi bayanta da su, cikin al'ajabin lamarin yarinyar Hajia ta juya zata zauna kan kujera tana fad'in "Amma yarinyar nan akwai yar rainin hankali, wacece ita? Me take tak'ama dashi?" Cikin ladabi kamar wata jakadiya Salamatu ta bi bayan Hajia tana fad'in "Ai ni banyi mamaki ba Hajia, bansan yarinyar ba ko kad'an, amma bansan me yasa jiya muka had'u da ita ba." Kallonta tayi tace "Kun had'u da ita ne? A ina?" Zaune tayi k'asan k'afafun Hajiar tace "Hajia zaki tuna jiya kin aikeni gidan Kubra karb'o turarukan da kika saka a ledojin bak'uwarki?" Jinjina kai tayi alamar eh, d'orawa tayi da "To ai unguwar take basu da nisa sosai, a titi na gansu suna fad'a ita da 'yan makarantarsu Hajia, dambe kamar maza wallahi haka na ganta, kuma kalaman da abokiyar fad'an take fad'a mata sune suka fi d'aga hankali, dan bata musa ba sai dai kuka da take." Gyara zama Hajia tayi tace "Uhum! Ina jinki." Tas Salamatu ta kwashe duk abinda ta ji kuma ta gani ta fad'a mata, hankali a matuk'ar tashe Hajia ta zaro ido tace "Wada fa kika ce? Kina nufin ubanta wada ne?" jinjina kai tayi tace "Wallahi wada ne Hajia, da idona naga sanda ya shiga da ita cikin gida." Mik'ewa Hajia tayi a hassale ta juya zuwa d'akinta tana fad'in "Ina! Ba zai yiwu ba wallahi, yar wada? Shin ina hankalinshi ya tafi ne da zai jawo min wannan iskancin, baisan cewa wannan larurar jini take bi ba, ko ita ba kalarsu bace kuma ta auri dogo zata iya haihuwar irin ubanta." K'wafa tayi ta shiga d'aki dan d'aukar waya ta kira k'anninta wanda su suka karb'o mishi aurenta, shi ma bai fad'a mata komai ba kawai yace dai mutanen kirki ne, bayan haka babu wanda yace mata komai uwa uba kuma sheikh da tasan dama babu abinda zai fad'a mata na aibun mutanen. *Mim-Sas* Sam sai taji aurenshi ya fita a ranta, kawai tasan ma aurensu ba zai yiwu ba daga yanda mahaifiyarshi ta nuna mata d'in nan. Saidai tasan zata rasa namiji da yayi daidai da muradinta, numfashi ta sauke a hankali tare da d'an k'amk'ame jikinta saboda sanyin ac, d'an tab'e baki tayi data tuna a gidan ma ac ce ga mota ac, shiyasa masu kud'in nan zaka ga jikinsu ma daban yake da saura, wani taushi da laushi zaka ga fatarsu na fitarwa na musamman kamar dai yanda a ido ne kawai take ganin fatar Asas d'in zatayi wannan taushin. Lura da yanayinta ya sakashi fad'in "Mimi, ni kam wace k'asa ke birgeki a duniyar nan?" Kallonshi tayi ba yabo ba fallasa tace "Me yasa ka tambaya?" Da fara'a yace "Ina so ne na sani dan na fara nema miki visa, dan a can zaki ci amarcinki." Wani farin ciki ne ya kamata tare da yin murmushi ta sunkuyar da kai, shi ma murmushin yayi yace "Ina jinki." Saida ta tsagaita tace "Umm! K'asar Madina, sannan k'asar Saudia." Jinjina kai yayi yace "Da kyau, kinga kenan zaki jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya, zaki sha amarcinki sannan zakiyi aikin hajj." Wani murmushin ta sake yi kawai ba tace komai ba, shi kam dan ya sa ta saki jikinta yasa shi cewa "Akan maganar bikinmu, abokanaina sun fara hura min wuta wai dole na musu wata walimar tare da 'yan mata, me kika ce a kai?" Numfashi ta sauke tace "Duk yanda kayi d'aya ne." "Da gaske?" Ya fad'a yana satar kallonta, jinjina kai tayi tace "Da gaske." Jinjina kai shi ma yayi yace "Shikenan, zanyi tunanin abinda ya dace, matsalar da zaran mun d'auko maganar party sheikh zai taka mana burki, bansan ya zanyi ba gaskiya." Kallonshi tayi da mamaki da son jin waye sheikh d'in nan? Na biyu kenan tana jin sunanshi a bakinshi, a hankali tace "Wane sheikh?" Da mamaki shi ma ya kalleta yace "Wane sheikh? Kina nufin baki sanshi ba? Shi ne fa wakilina a wajen d'aurin aurenmu, kuma shi ne yake auren yayata Hafsat, banda kamarsa a cikin abokai da ma yan uwa." Jinjina kai tayi tace "Da alama yana da mahimmanci a gareka?" Murmushi yayi yace "Fiye da tunaninki, zan iya yin komai saboda sheikh, ina sonshi fiye da yanda nake son kaina, shi ma kuma yana so na sosai." Murmushi kawai tayi ba tace komai ba, kallonta yayi yace "Wai da gaske baki tab'a jin sunan sheikh Abdul w..." K'arar da IPhone d'inshi ta d'auka yasa ka shi yin shiru yana d'aukar wayar da dubawa, murmushi ya mata yace "Kinga shi yake kirana ma." Ya fad'a yana nuna mata wayar, saman kawai ta gani sunan daya fito b'aro-b'aro wato *d'an uwa na*, yana d'auka ita dai tana jin yana fad'in "Allah sheikh gamu nan a hanya, kad'an ya rage ka ganmu gabanka." Bata ji me aka fad'a b芒 amma taga yayi dariya yace "OK sai mun zo." Aje wayar yayi yana girgiza kai yace "Ya min alk'awarin tarbanshi da kanki ne, shiyasa ya matsu mu iso dan akwai inda zai je." Jinjina kai tayi tana murmushi tace "Allah sarki." Da haka suka isa k'ofar tamk'amemen gidan, irin ginin nan ne na zamani mai d'aukar ido, gashi had'e da masallaci abun gwanin birgewa, ga hasken fitilu masu kyau wanda suke ship ship a cikin shukoki, ita dai baki ta saki tanaa kallon ikon Allah, wato can data bud'e ido tana kallon gidansu Asas ashe b芒 komai ta gani ba, yanzu ne zata yi kallo uya son ranta, mai gadi na bud'e musu suka shiga ciki, a gaban wata jibgegiyar reng rover bak'a ya tsayar da motar, a hankali ta shiga fitowa tana sake kallon girman gidan lai d'auke da tsaki da kyan gaske, wani irin iska ne ta gauraye gidan na shukoki mai sanyin gaske da saka bacci. Gaisawa Asas yayi da jami'an sheikh dake jiranshi ya fito, gaba ya shiga ita kuma tana take masa baya tana kuma satar kallon gidan, suna zuwa k'ofar falon ta kalli kanta ta madubin dake k'ofar, tura k'ofar yayi daga ciki ya shiga, ita ma a hankali ta cire takalminta ta taka k'afarta akan pause pied d'in dake bakin k'ofar mai taushi kamar bargo, a sanyaye ta lumshe ido ta furta "Masha'Allah." Falon akwai girma amma kuma an cikeshi da kujerun alfarma kujerun dake birgeta, wanda take da burin lallai in zatayi aure dole Abba ya siya mata royal, ga ni'imtaccen k'amshi da kuma sanyi dake fita, yaran da mahaifiyarsu duk zaune suke a nutse sai hira da suke k'asa k'asa. Da farin ciki da kuma karramawa duk suka mik'e suka nufi Mimi yaran na fad'in "Aunty sannu da zuwa." Hafsat kuma tana fad'in "Sannu da zuwa yar uwa." Turo baki Asas yayi yana fad'in "Yau kuma a gidan nan babu wanda zai min lale?" Murmushi Eesha tayi tace "Kayi hak'uri tonton, na yau dai ka barwa auntynmu wannan ranar." Mayar da kallonta tayi kan Mimi tana jin ta samu k'awa tace "Aunty Mimi barka da zuwa." Da murmushu tace "Anwuni lafiya." Kama hannunta Eesha tayi suka zauna kan kujera, kallonta Hafsat tayi tace "To fa sarauniyar gwandagi, wato kin ga k'awa ko? To ai zaki kawo mata ruwa ko." Mik'ewa tayi da murmushi ta nufi wata kusurwa, ita ma zaune tayi kusan Mimi tana fad'in "Mai sunan Mama ya gida?" Sunkuyar da kanta tayi tace "Ina wuni." Gaisawa sukayi sosai, su Aswane ma gaisheta sukayi ta amsa, a kadabce ta kama hannun Munzeer dake k'arami tana fad'in "Ya sunanka?" A hankali yace "Munzeer." Da fara'a tace "Masha'Allah, suna mai dad'i." Shafa kan shi tayi sai Aswane da yace "Aunty ni baki tambayi sunana ba? Yafi na shi dad'i fa." Dariya tayi tace "Ya sunanka?" "Aswane." ya fad'a yana murmushi, girgiza kai Hafsat tayi tace "Allah ya shirya." "Ameen." Mimi ta fad'a tana satar kallon matar mai matuk'ar dattako, gata cikin shirin doguwar riga ita ma abaya tayi tsaf duk da ba kwalliya ce a fuskarta ba, haka ma cikin jikinta ya mata kyau dan b芒 wani girma ne dashi ba. Muryar Asas ce ta dawo da ita daga kallon Hafsat yana fad'in "Wai ina shehi ne kuma ya shige? Nan fa yake ta zura min kira kamar zan sameshi a k'ofar gida yana jirana." Dariya Hafsat tayi tana kallon Eesha data aje faranti a gaban Mimi tace "Nan yake zaune ma, yanzu ya shiga ciki amsa waya, da alama wani wurin zai je mai mahimmanci, dan na ji yana k'orafin ba zai fita da masu tsaron ba yau." Murmushi Asas yayi yace "Ustaz kenan, shi fa idan tashi ne yayi ta tafiyarshi sakaka a gari." Ita ma murmushin tayi tace "Ni kaina na fi son haka, duk abinda Allah ya rubuta zai faru ai shi ne zai faru, babu abinda zasu iya tare masa wanda aka rubuta zai same shi." Jinjina kai duk sukayi sai Asas da yace "Duk da haka, kula da lafiyar yana da kyau." Kallon Munzeer tayi tace "Munzeer, shiga librairie (labrary) kaga Abienka ya gama wayar." Jinjina kai yayi tare da nufa kusurwar da zata sadashi da d'akin karatun sheikh d'in, zai bud'e k'ofar shi kuma ya bud'e ya fito bayan ya gama wayar, dama shi da Muddaseer ne da yake k'ara kwatanta mishi gidansu Ryam d'in shi, dan yanzu can zai nufa dan ganawa da iyayenta. Sanyayyan k'amshin turarenshi mai matuk'ar tsada ne tr茅sor ya fara musu maraba, bud'add'en alkyabarshi irin ta malamai fara k'ar wacce ya d'ora akan farar shaddarshi mai k'yalli, fararen takalmi k'afa ciki da kuma farin hirami daya d'aure hular dake kanshi, siririn farin glas ya saka duk da bai cika sakawa ba, amma dake yau ranar ta musamman ce saiya saka. Takowa yayi ba tare da ganin fuskarta ba dan ta bashi baya ne daga inda take, saidai yana kallonta yaji fad'uwar gaba tare da tsanantawa da gudun jinin jikinshi, fararen hannayenta masu kauri yake kallo da take shafar kan Munzeer. Saida ya zo daf ita kusa da Hafsat ya tsaya, kafin kowa yace wani abu Asas yace "To malam ga amaryata dai na kawo maka." Murmushi yayi tare da kallon fuskarta dake sunkuye, a lokacin Asas yace "Maah ga sheikh da nake baki labari." A hankali, a ladabce kuma a nutse ta d'ago da innocent fuskarta, *ido biyu* sukayi k'uru k'uru suna kallon juna, dukansu babu wanda bai firgita ba haka kuma kowanensu ya kad'u. Da sauri tayi k'asa da kanta ta rintse ido sosai tana ambatar "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Saida ta maimaita sau uku, a take wata irin kunya da matsananciyar nadama ta rufeta a gurin, bata tab'a tsammanin haka zai faru da ita ba, ko a mafarki bata tab'a jin cewa zata iya hakaito haka ba, me kenan yake shirin faruwa da ita? Me ta aikata haka data tsinci kanta a wannan halin? Duk sanyin wurin saita samu kanta da jin wani irin gumi na tsatsafo mata, gashi komai na jikinta ya daina aiki hatta da jinin jikinta ma, ta kasa motsawa bare ta fita a guje ta bar gidan. Sheikh kam da kanshi ke neman yin bindiga gaba d'aya saiya rasa me zaiyi tunani a kai, a dai lokacin kam babu ta yanda zai fara tunanin lamarin, sai kawai yayi k'arfin halin cewa "Sannu ko?" Shiru Mimi tayi dan bakinta ya mata nauyi ta kasa furta komai, muryar Asas ce ta samar mata d'an k'wari k'wari yana fad'in "Sheikh gashi zaka fita, mu ma kuma tafiya zamuyi yanzu." Da k'yar da sud'in goshi ya k'ak'aro murmushi yace "Hakane, amma ai zaku iya zama, da alama ma tafiyar ta fasu, dan dama zan je ganin wani muhimman bak'o, amma ganinku ya tuna min da wani abu." Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi, sai kuma ta sunkuyar da kanta tana d'an ciza kakkauran leb'enta, wasu hawaye masu zafi na takaicin halin data samu kanta ciki kawai taji sun zubo mata, a hankali tasa bakin kallabin abayarta ta share cikin dubara. Mik'ewa Asas yayi yana fad'in "Aunty Hassu, zamu wuce fa dan b芒 jimawa zamuyi ba dama." Mik'ewa tayi tana fad'in "Da wuri haka? Amma dai zaka sake kawo min ita ta wuni ko?" Murmushi yace "Gaki nan gata nan kuyi magana, idan ta amince ni mai sauk'i ne." Kallonta Hafsat tayi ta matso kusanta sosai tace "Mimi zaki sake dawowa ko?" Shiru tayi kanta a k'asa tana kuma jin yanda idanun sheikh ke yawo a kan ta, ta tabbata kallon mamaki yake mata da al'ajabi, ita kam ina zata saka kanta ne yanzu? Shikenan aurenta da Asas ya gama rugujewa, ta gama samun lasisin rabuwarsu kawai, kallonta Asas yayi yace "Maah." A hankali ta kalleshi shi kanshi wata kunyarshi take ji, a sanyaye yace "Muje ko?" Da ido ta amsa da "To." A hankali ta yunk'ura ta mik'e tsaye tare da Hafsat, Eesha ce tace "Gaskiya tonton ka sake kawo mana aunty, ko ruwa fa bata sha ba." Murmushi ya mata yace "Ki shirya duk randa kike so saina kaiki wurinta." Da farin ciki tace "Yawwa tonton nagode, zan tambayi Abie sai na je." Kallon Eesha Hafsat tayi da ido ta mata alama, amsawa tayi tare da juyawa ta shiga d'akin uwar, jim kad'an ta fito da tsaraba ita ma ta mik'awa Asas tace "Tonton inji Mamie ka bawa aunty Mimi." Karb'a yayi yana fad'in "Mutanen nan kirkinku kad'an ne fa, babu wanda ya tab'a bani wata leda sai yau da na zo da bak'uwa." Hararanshi Hafsat tayi tace "Idan ka ji haushi mana ka daina zuwa kai kad'ai." Hannu ya saka aljihu yana lalubar wayarshi dake k'ara yana fad'in "Dole ai, daga yanzu tare zamu dinga zuwa." D'ora wayar yayi a kunne, daga yanda ya amsa wayar zaka san wani abu ya faru na tashin hankali, hakan yasa yana kashe wayar hankali a tashe ya juyo ya kalli Mimi yace "Mimi akwai matsala, masu min gyara gida ne wallahi wani wai ya samu mummunan rauni, zan wuce asibitin ne yanzu na ganshi, zaki bini muje?" Sak'e tayi tare da tuna maganar Abbanta, a haankali ta girgiza kai da k'yar a karo na farko tun bayan fitowar sheikh tace "Gaskiya Abba ya hana, yace na koma gida kawai." "Hummmm!" Suka ji sheikh ya fad'a daga bayansu, kallonshi Asas yayi yace "Sheikh mi ye abun yi yanzu, suna buk'atar kud'i a asibitin wallahi da gaggawa, gashi ita kuma bata so tati dare." A hankali ya shiga takowa hakan ya haddasa fad'uwar gabanta sosai, jikinta har wata rawa ya d'auka saboda jin yana kusantota, saida ya tsaya inda yake hangen fuskarta kafin yace " *Zan mayar da ita gida* idan Abbanta zai amince, dama yanzu can unguwar zan tafi." Da farin ciki Asas ya rumgumeshi kafin ya kalli Mimi da take jin kamar tace "Mutuwa." Ita kuma ta amsa mata yace "Maah, na yarda dashi, kiyi hak'uri kuje tare kinji, insha'Allah komai dare na dawo zan sameki a gida na fad'awa su Abba abinda ya faru." Idonta taf da hawaye ta kalleshi tace "... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:54 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *17* Idonta taf hawaye ta kalleshi tace "Tsoro nake ji ni dai." Murmushi yayi yace "Tsoron me? Ba mugu bane ba fa." Ya fad'a yana satar kallon sheikh da a lokacin yake kallon fuskarta, shi wallahi maamaki ma yarinyar ke bashi, ta ya ya k'aramar yarinya kamar wannan tayi abinda tayi? Me yasa ta aikata mishi haka? Me ye burinta a duniya ko a rayuwa? Da takon k'arfi ya juya da hanzari ya fita daga falon dan har ga Allah zuciyarshi tafasa take, musamman idan ya tuna shi ne aka wa wannan shak'iyancin, da sauri Asas ya kalleta yace "Muje." Bin bayanshi yayi da sauri inda Mimi ta shiga takawa da k'yar tana sab'a rigarta a hannu da take jin ta mata nauyi, Hafsat da yaran kam daga baya suke binta suna mata addu'ar Allah ya tsare, duk da dai Hafsat tana jin wani abu a zuciyarta, da fari yanayin mai gidanta kawai ta kalla a lokacin da yake kallon Mimi ta fahimci akwai wani abu, uwa uba daya ce zai mayar da ita gida, saidai dake tasan waye mijinta kuma ta yarda dashi, sam bata kawo komai a ranta ba musamman mummunan zargi, daga bakin k'ofar suka tsaya ita ta wuce wajensu, tsaye suke sheikh na shirin shiga mota ta kalli Asas tana sako hawaye tace "Ka mayar dani gida da kanka, na fad'a maka tsoro nake ji." Tsayawa yayi dan sarai yaji me ta fad'a, kallonta yayi irin kallon naan na ban tsoro duk da idonshi a cikin glas suke, cikin muryar da bata saba ji ba ko a tv yace "Me kike ji ma tsoro? Kina da laifi ne da ba kya son tafiya tare da ni?" Kallonshi tayi tana girgiza kai hawaye na zubowa a idonta, a sanyaye Asas yace "Wuce ku je maah." Hannu tasa a idonta ta shiga murzawa sosai tana fashewa da kuka cikin siririyar muryarta harda bubbuga k'afafu tana fad'in "Ni wallahi bana so, kawai ka san yanda zakayi da ni." Baki bud'e Asas ya shiga kallonta da matsanancin mamakin shagwab'ar da take bugawa. Inda a wajen sheikh kuma yayi saurin d'auke kanshi yana furta "Hasbunallahu wani'imal wakil." Cije leb'enshi yayi na k'asa tare da lumshe ido, ya d'auki minti d'aya haka kafin ya juyo ya kalli Asas yace "Ba sauri kake ba?" Jinjina kai yayi yace "Wallahi ina so naje naga halin da bawan Allahn nan yake." Da ido ya fara masa alama kafin yace "Je kawai." Jinjina kai yayi tare da kallon mimi, k'yabta mata ido yayi ya wuce bai ce komai ba, saida ya saka ledar da Eesha ta bashi kafin ya ja motar ya bar gidan. Tunda ya ba Asas umarnin tafiya ta kama bakinta ta rab'e wuri d'aya. Juyowa yayi ya kalleta a mugun dak'ile ya mata alama da hannu ta shiga, jiki na rawa ta matso daf da shi ta rab'ashi ta d'aga k'afarta ta wuntsila cikin motar, rufe k'ofar yayi tare da kallon dreban ya tara hannu alamar ya bashi makulli, mik'a mishi yayi ya karb'a tare da fad'in "Zan dawo yanzu, ku jirani a nan." Bud'a mazaunin dreban yayi ya shiga, a tsanake kuma a hankalce ya tayar da motar ya shiga janta har suka fita a gidan, shiru motar ta d'auka babu ko sautin numfashi bare redio, a sanyaye yake tuk'i sai d'an sautin ac kawai da sanyayyen k'amshin dake fita. Daga bayan nan da take hangenshi kawai take tana k'are masa kallo, hak'ik'a yanayinsa kalar fuskarsa, saidai a zahiri da bad'ini yana da b'oyayyen k'wanji, ga kuma iya d'aukar ado da k'wallisa da kuma kyau. Had'e hannayenta take a tsakanin cinyoyinta saboda fitsari take ji sosai, kayan cikinta yamutsawa kawai suke yi ga kuma fad'uwar gaba. Daidai babban hanyar dake d'auke da titi biyu a hannun da suke ya ratse gefe yaja birki ya tsaya, dum dum dudum! Gabanta ya shiga dokawa da mugun k'arfi, sake k'amk'amewa tayi sosai tana rintse ido hawaye na silalowa, a ranta take fad'in "Tabbas da tare nake da Asma'u, da haka bai faru ba, wayyo Allaana k'awata." Da sauri ta bud'e ido jin k'arar bud'e motar, tana kallo ya fito a nutse ya rufe k'ofar ya bud'e inda take, ganin ya bud'e k'ofar da take zaune yasa ta ja baya da k'arfin bala'i tare da kama d'aya k'ofar zata bud'e, wani kallo ya watsa mata duk da akwai duhu yace "Kina fita a nan zan had'ani da karnuka." Dakatawa tayi tare da fashewa da wani sabon kuka irin na tab'ara saidai kuma da gaske take yin shi, hannayenta biyu ta d'ora a kai tana fadin "Na mutu na lalace ni Mimi? Dan Allah dan annabi ka yafe min sheikh, na tuba wallahi b芒 zan sake maka k'arya ba." Ba tare daya daina kallonta ba ya shiga ya zauna yaja murfin ya rufe, shi kanshi sai yaji abun wani iri saboda rashin sabo, idan ba Hafsat ba babu macen da ya tab'a zama da ita haka a mota, gyara zama yayi sosai yanzu suke fuskantar juna, muryar a dak'ile ya shiga wurga mata wani kallo yace "Me yasa kika min k'arya? Akan me kika maidani shashasha? Akwai gaba a tsakanina da wani naki ne?" Girgiza kai tayi cikin matsanancin kuka tace "Wallahi babu, ni ma ba'a son raina bane haka ta faru, wallahi a lokacin..." "Shiru." Ya fad'a a matuk'ar tsawace, a harzuk'e ya kalleta yace "Taya kuka had'u da Asas? Wane irin so kike masa?" Cikin kukan tausayin kanta baki na rawa sosai tace "Ni wallahi ina son shi da zuciya d'aya, amma idan ka ce na daina kulashi zan daina daga yau, kuma ni na manta inda muka had'u." "Kin manta?" Ya tambaya yana mata tuhumammen kallo, cikin in'ina tace "Eh to...ina ga..kamar dai a hanya..., ni wallahi na manta ina ne, a rikice nake Abdul..." Duk da ta kai k'arshe sa茂 kuma tasa hannaye biyu ta rufe bakinta tana k'walalo ido, ita kanta bata san me yasa take son kiranshi da sunan ba musamman idan suna tare. Duk da wani mugun dad'i ne ke kasheshi ganin rud'ewarta da duburburcewarta had'e da kukan nan, ga kuma sunan data kira daya kwana biyu yana mararin sak茅 ji daga bakinta, daurewa yayi sosai ya had'e fuska yace "To me yasa kika amince na je gidanku yau?" Cike da makirci ta dafe cikinta tana fad'in "Cikina ciwo yake, ka ajiye tambayoyin zan amsa maka su a gaba idan mun sake had'uwa, yanzu ka kaini gida nasha magani." Wani k'ayataccen murmushi ya saki yana mamakin Mimi da ya ga sam bata d'aukeshi da girman da kowa ya d'aukeshi ba, jinjina kai yayi ya sake kafeta da ido yace "Fad'a min gaskiya, zaki iya zama da Asas domin Allah?" Da sauri ta kalleshi tace "Wallahi zan..." Nunata yayi da yatsa yace "Kika sake min rantsuwa a wurin nan kafin magana saina tsinka miki mari Ryam, tabbacin k'arya zaki fad'a shiyasa kika min rantsuwa akan k'arya." Girgiza kai tayi tana dafe kumatunta da hannu biyu, wata harara ya kuma wurga mata yace "Yi magana ina jinki?" Gyad'a kai ta shiga yi kamar k'adangaruwa tace "Ina son shi, zan zauna da shi." Lumshe ido yayi tare da jingina bayanshi a kujerar yasa hannun dama ya cire glas d'in fuskarshi, "Hasbunallah wani'inal wakil, La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntun minna zalumin." Abinda ya dinga maimaitawa kenan kafin ya bud'e idonshi tar a kan titi, cikin d'aga sauti yace "Astagfirullah, Allah na tuba ka yafe min zunubaina, Allah ka gafarta min laifukana, nasan ni d'an adam ne kuma ajizi, bansan yaushe kuma a ina ba, amma ina neman gafararka ubangiji." A hankali ya girgiza kai ya juyo ya kalleta, kanta a k'asa tana share hawaye ga wani mugun tausayin mutumin da taji ya dirar mata, fuskarta sam ba tayi kama da wacce zata iya aikata abinda ta aikata ba, sam *kamaninta bata da suffar cutar da kowa*, saidai shi ta cutar da shi sosai, ta raunata zuciyarshi yanda har takai matakin babbakewa k'urmus. A hankali cikin amon murya mai d'auke da alhini da jimami yace "Ban tab'a tsammanin haka zai iya faruwa dani ba." A hankali ta d'ago ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kai, d'orawa yayi da "Ryam idan kinsan ban miki ba me yasa kika b'ata min lokaci? Ko kinsan cewa da zuciya d'aya na so samunki a matsayin matar aurena? Ni ba yaro ba ne tunda har ina da 'ya kamarki, ni ba zauna gari banza ba tunda ina da aiki, daidai gwargwado zance ni ba mutumin banza bane, ana girmamani ana ganin darajata a k'asashe da dama bare kuma k'asata." Da k'arfi ya sake juyowa kanta a hassale sosai cikin daka tsawa yace "To a kan me zaki maidani wawa da bai san me yake ba?" Wani matsanancin kuka ta fashe dashi ta sake yin k'asa da kanta tana fad'in "Kayi hak'uri ka gafarta min, har zuciyata ban yi haka da niyyar cutar da kai ba saidan ganin kai d'in babban mutum ne, har zuciyata nake jin rashin dad'i idan ina son fad'a maka gaskiya, dan Allah kayi hak'uri karka cutar dani." Wani iska ya shiga furzowa mai zafin gaske na tsananin b'acin rai, bai sake magana ba sai kallonta kawai da yake, d'an tsaki yaja k'arami ya fita daga motar ya rufo mata k'ofar da k'arfi ya zauna mazaunin dreba, da k'arfin tsiya ya figi motar har saida ta gwara kanta a k'ofar da take zaune, kuka take kamar zata mutu ba k'akk'autawa, sosai take jin zafi a zuciyarta na jefa babban mutumin nan cikin wani hali marar dad'i. Shi kuma ko juyowa bai sakeyi ba har saida ya ja pakin a k'ofar gidansu ya tsaya, tashin hankalin da take ciki ya mantar da ita Asma'u da sukayi mahad'a da ita, tashin hankalinta yasa ta manta wayarta a jakarta kuma a kunne take saidai a vibrations. Shiru tayi bata bud'e motar ba bare ta fita ta k'ura mishi ido ta baya tana kallo yanda ya had'e fuska kamar hadarin gabas, saida ta sake share k'walla tayi k'arfin hali ta bud'a baki cikin dakusashiyar muryar kuka tace "Dan Allah ka gafarceni, karka rik'eni a zuciyarka, wallahi bana jin dad'i a zuciyata." A sanyaye kuma a ladabce kamar ba shi yayi maganar ba yace "Shiru! Mak'aryaciya kawai." Da sauri tace "Wallahi gaskiya nake fad'a maka." Girgiza kai yayi ba tare daya juyo ba yace "Alamar k'arya kika fad'a kenan, wannan rantsuwar da kikayi.". Saida ta gyara zamanta sosai cikin magiya tace " Abdul gaskiya nake fad'a maka, maganar nan daga zuciyata take fitowa, bana jin..." Wani kallo ya watso mata ta madubi na mamaki, suna had'a ido ta sunkuyar da kanta saboda kwarjininshi, a hankali ta jinjina kai cikin sanyin murya tace "Ni ma haka kawai nake jin bakina yace Abdul, kayi hak'uri dan Allah." Yanda fuskarta tayi gwanin tausayi tasha kuka gashi ta sunkuyar da kai, hakan ya bashi damar sakin murmushin gefen labb'a tare da d'auke idonshi a kanta, a dak'ile sosai yace "Na yafe, amma ki kula ki daina k'arya, ba kyau Ryam." Jinjina kai tayi da sauri tace "Insha'Allah." Matsawa tayi jikin k'ofar ta bud'e murfin a hankali ta sauka tare da rufo mishi murfin, ta glas d'in motar ta k'ura mishi ido tana takawa zuwa cikin gidan, ta gabanshi ta wuce hakan yasa shi saurin rufe idonshi, abayar ta fito da k'irar jikinta sosai kuma da yake ita d'in yar duma duma ce hakan ya wanzar da wani tasiri a zuciyarshi, ga kallabin rigar dake shirin fad'uwa a kan ta wanda yake nuna mishi lallai zatayi gashi a kan ta ko ba sosai ba, saidai yana so yasan su d'in wace k'abila ce? Mahaifinta bak'i ne sosai kuma gajere dake manne da k'asa, saidai kakanta daya haifi mamanta dogo ne sosai, amma kuma ita bata d'auko mahaifinta ba ta ko ina. Yana cikin tunanin ya sake bud'e idonshi a k'ofar gidan, a lokacin tana daf da shigewa ciki ta sake juyowa, a hankali ta d'ago hannunta ta mishi bye bye tana sakar masa murmushi. Da sauri ya kuma lik'e idonshi yana dafe gaban goshinshi ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Yanda shed'an ke ta k'awata mishi ita a zuciya ne yake son yakicewa, so yake ya manta da komai ya rik'eta surukarshi matar k'annanshi, saidai shed'an sai hura mishi wuta yake a kan yarinyar komai tayi sai yaji zuciyarshi na fad'a mishi " *Komai na ta yanda kake so*." Cak a daidai bakin k'ofar ta tsaya sakamakon komai nata daya daina aiki, Abba zaune dangalgal akan k'asa ba takalmi a k'afafunshi, ga kuma Mama zaune a gefe kan kujera sai Asma'u ita ma durk'ushe gefen Abba tana share hawaye, tunda ta ga haka ta san yau wannan rana bak'a ce k'irin a gareta, yau ranar kam babu sa'a a gareta, me ya faru? Me kuma zai faru? *Tun* bayan tafiyarsu ba jimawa Abba ya dawo daga masallaci ya samu Muttak'a a k'ofar gidan, ba yabo ba fallasa suka gaisa inda Muttak'a ke fad'in "Abba dama na zo wajen Mimi ne, saboda ina ta kiranta bana samu shi ne na zo naji ko lafiya." Da matsanancin mamaki Abba ya d'aga kai sosai ya kalleshi dan shi ma a tsaye yake ba ko rusunawa yace "Kiranta kuma? Dame kake kiran nata?" Da mamakin tambayaar yace "Da wayarta mana, ina ta kirane shiru ba'a samu, ko ita wannan wayar ta samu matsala ne? Idan ta lalace sai na sake mata wata ai ba damuwa bane." Jim Abba yayi yana kallonshi yana jin mamakin kalamanshi, ba tare da yabi ta kanshi ba kawai ya juya a fusace ya shiga cikin gidan, Mama data idar da sallah ya tsaya bayanta akan tabarma yace "Ke kinsan *Maryama* tana da waya ne?" Da sauri ta juyo da mamakin jin yau sunan mahaifiyar ma tashi ya kama haka, tabbas yana kiranta Maryam wasu lokuta, amma dai jin sunan Maryama ba dai a bakinshi ba, cikin rashin sani tace "Waya kuma? Wace irin waya malam?" Wani dogon tsaki yaja tare da kutsawa d'aki ya shige, akwatinta guda biyu duka ya jawo a k'ark'ashin gado, bud'esu yayi ya shiga ciro kayanta d'aya bayan d'aya yana zazzagewa yana dubawa, har k'ananan kayanta daya ci karo dasu pant da bras da cotton saida yayi cilli dasu a tsakiyar d'akin, jikinshi har rawa yake kamar mazari. Ganin bai samu komai a nan ba yasa shi jawo jakunkunanta na hannu sama da guda goma duk k'anana na yan zamani, a tsanake ya shiga dubasu yana bud'a kowane gida a cikinsu, babu waya babu alamarta, saidai ya samu layiyyika (sim) a k'alla guda bakwai, ga poshet na waya wanda take cirewa ta sake wasu suma har guda biyar, ga kuma tsabar kud'i daya samu a wata k'aramar jakarta har jaka ashirin da uku, wata irin juwa ta d'ebeshi ta kayar akan kujerar robar dake d'akin, wannan k'arar ce tasa Mama tashi da gudu gudu ta shiga hankali a tashe, tana k'arasawa ta shiga kiran sunan "Malam, malam lafiya? Wai me yake faruwa ne?" Bud'a ido yayi a matuk'ar wahalce ya kalleta, zunbur ya tashi tsaye yana sake kallon hannayenshi, nuna mata yayi amma bai ce komai ba saboda nauyin da bakinshi yayi, rab'a Mama yayi ya fito da sauri ya saka takalminshi ya fita a gidan. Yanda yake saurin zaka rantse dungurawa zaiyi ya fad'i saboda yanayin hallitar, amma kuma haka yake tafiyar yana sauri dan isa gidan Iya Delu, yau kam yasan sai yayi abun kunya gidan surukai, amma fa babu mai hanashi karya Mimi idan sukayi ido takwas takwas. Suna barin k'ofar gidan Abba na kawowa hakan yasa ya had'e da Asma'u da zata tafi gidansu Jamila, a tsawace sosai yace "Ke tana ina?" Duburburcewa tayi ta shiga rarraba ido, matsowa yayi zai kamo hannunta ya durk'usar da ita sai tayi saurin ja baya tace "Abba sun tafi." "Ina?" Ya fad'a da jin haushi, cikin rashin gaskiya tace "Can, wallahi Abba ni babu laifina, saida na fad'a mata mu tafi tare tace wai..." Shiru tayi saboda tausayin k'awarta tasan yau kam saita Allah Mimi, nuna mata hanya yayi yace "Wuce muje, zataa zo gidan ta sameni, zaku fad'a min abinda kuke shiryawa da bamu sani ba." Da sauri ta wuce har tana had'awa da gudu Abba ma biyarta yake da saurin kamar zai had'a da gudu shi ma. Mimi dake tsaye ta rasa yanda zatayi, ta koma da baya ne ta nemo taimako a gidansu Iya? Ko kuma dai tayi k'undumbala ta shiga? A gaskiya bata son abinda zai tab'a mata lafiyar jikinta, bata son jin duk wani abu daya danganci rad'ad'i a jikinta, muciyar data gani gefen Abba kuma irin muciyar nan ce mai kama da ice irin na yan damagaram, ta tabbatar da ita yake shirin dukanta. Ajiyar zuciya ta sauke a b'oye tana ci gaba da rarraba ido, d'agowa yaayi ya kalleta idonshi jajir kamar wanda yayi kuka yace "Shigo." Marairaicewa tayi ta durk'usa a wurin tace "Abba kayi hak'uri dan Allah karka dakeni, ka tambayeni da baki zan fad'a maka komai." Wuntsi Abba ya wulk'ita ya tashi tsaye yana sake d'aukar muciyar a hannunshi ya nuna mata gabanshi yace "Maryama ki zo nan indai ni na haifeki, in kuma kina so ki nuna min ke babbar mace ce da kika isa da kan ki to ki bar gidan nan." Fashewa tayi da kuka tana girgiza kai ta kalli Mama da kanta ma ke k'asa, cikin rikicewa tace "Abba karka dakeni dan Allah, zan maka bayanin komai wallahi da dalilina na yin haka, Abba karka dakeni ka ji, zan zo yanzu amma ban da duka." Sheikh da har yanzu bai guda daga wurin ba ne ya fara jin kamar hayaniya, sai zuciyarshi ta raya mishi ko dai jimawar da tayi ne ya sa tayi laifi haka, a hankali ya bud'e motar da tunanin ko sallama ne yayi ya fad'i dalilin jimawar, a hankali cikin kamala da dattako ya shiga takawa izuwa k'ofar gidan, a nan ya tsaya ganin Mimi durk'ushe tana magiya. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:54 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *18* Abba saida ya k'ara tamke fuskarsa yace "Mimi idan baki k'araso inda nake ba na damk'e ki saina fasa maki baki da hannuna." D'an mudil mudil d'in hannun sheikh ya bi da kallo kafin yake d'an k'ara k'arasawa yana son yin magana amma yanayin da mahaifin nata ke ciki saiya d'an dakata yana sauraronsa. Abba ya rasa ina zai saka ransa, kwata kwata bai kula da cheikh ba hakan yasa yayi taku ya kai goma yana kai kawo a d'an wajen da ba girman kirki ne da shi ba ga mama kanta sadde jikinta har yanzu b'ari yake cike da alhinin wannan tashin hankali. Su dukansu basu shirya ba suka ga Abba ya hau dutsin dake kusa da Mimi wanda ta durk'usa kad'an kusa da shi bata kai tsayinta kaf ba amma ta rage tsayin nata sosai ya d'aga wannan hannu nasa dugul ya wanka mata marin da ya sakata zabura daga d'an durk'ushen da tayi ta falla ihu ta shiga dira tana rik'e gefen kuncin nata tana kururuwar a taimaketa Abba zai kasheta. Rai b'ace ya d'aga muciyar nan zai kuma doka mata ita da sauri sheikh ya rintse idonsa yana jin wani irin rad'ad'i a zuciyarsa tamkar shi aka doka ba ita ba. A hassale Abba yace "Yanzu Mimi kece da wannan rayuwar? A gidan wa kike samu wayar dake hannunki da kud'in dake nanik'e cikin jakarki? Wato kin banzatar da kanki ko? Biye biyen maza kike da suke baki wannan d'in ko me?" Gaba d'aya ya bud'e idonshi zuwa yanzu yana jin wata zufa na son karyo masa da girmansa da komai haka kawai kan rigimar budurwar yar da bai san haka cikinta yake ba. Mimi kam tana dire diren nan ta tsaya da sauri jikinta na rawa ta had'e hannayenta tace "Abba na rantse da sarkin dake busa numfashi bana haka, sam ban san wannan hanyar ba, Abba ban tab'a aikata zina ba tunda mama ta haifeni, wallahi wallahi wallahi ban iya ba." Abba ya kuma matsowa yanzun da take tsugune ya damk'i kunnenta na hagu yace "K'arya kike uwata, wannan zamani da ya zama na bala'i me kike tunanin kina iya fad'a min na yarda dake? Ba zai yiwu ba wuce mu tafi wajen Hajia Gambo, wuce!" Zuwa yanzu mamanta kanta hawaye take sharewa a tsugunen da take kuma ita sarai ta ga sheikh wanda gaba d'aya ya jinginar da bayansa jikin garu yana jin juwa na d'ibansa na wannan abu dake faruwa. Mama dake son dakatar da shi dan kar a yi wannan abin a gaban mutane idan har abinda yake zargin kenan su tonawa kansu asiri muryarta na rawa tace "Malam, ka ga sheikk ne a tsaye fa, na san sallama yake." Malam ya kai dubansa inda take nuna masa, sai a lokacin ya ganshi, shi da kansa sai da gabansa ya k'ara fad'uwa cike da tsoron shikenan ta tabbata ta gama janyowa kanta tashon hankali mai yiwuwa maganar fasa auren ta kawo shi nan shima ya lumshe idanuwansa cike da tashin hankali muryarsa zuwa yanzun ta k'ara yin sanyi yace "Nasan abinda ka ji kenan ka zo wajena ko sheikh? Sai dai ka ganta nan ban san rashin jin nata ya kai cen ba, Innalillahi wa'inna ilaihi raju'une ban san cewa tana rik'e da wayar salula a hannunta ba har ta tara kud'i irin wannan a jakarta ba, ka ganni nan talaka ne mai wadatar zuci haka mahaifiyarta, sannan irin yadda muke taka tsantsan a kan shige da fitarta bamu san ta waye haka ba, idan ka ce kun fasa ba zan k'ullaceku ba domin ni kaina yanzu ban yarda da mimi ba. Zan kaita gidan Hajia Gambo cen layin likita ce ita ke duba mana mararsa lafiyar anguwa ni baba take ce min muna mutunci sosai da ita domin mai d'akina ke mata tuyar wainar juma'a, zan kaita ta duba min ita idan ta rigaya ta gama lalacewa shikennan sai a fasa ta dawo ta zauna..." Irin yadda Abba ke maganar gaba d'aya hankalinsa a tashe ransa a b'ace, Mama kuwa kunya da tashin hankali ya sakata shigewa ciki da saurinta, Asma'u kuwa hawaye take wani na korar wani inda mimi gaba d'aya bakinta ya gama mutuwa tana tsugune ne gaba d'aya jikinta na mata rawa hankalinta ya gama tashi. Sheikh yayi iya yinsa ya aro dukkan jarumtar da ta rage masa da k'arfin addu'a sannan ya gyara tsayuwarsa da shigarsa ta kamala ga k'amshin da yake ta fitinar hancin kowa da shi mai dad'in gaske ya tausasa muryarsa yace "Ba za'a yi haka ba malam, a yi hak'uri, na zata ko dan ta yi dare ne na zo na fad'i cewar shi wanda aka saka masu ranar ne ya je asibiti shi yasa na kawota, aman ina ga mai zai hana a shiga ciki a tattauna a nutse ta yadda komai zai shiga cikin haske ba tare da rayuka sun b'aci ba." Cike da girmama shi Abba yace " Akaramakallah, ba zaka gane wacece mimi ba, idan bamu je ba ba zan tab'a samun nutsuwa ba , kuma idan kuka fasa aurenta ba zan tab'a jin haushinku ba domin tsatso mai kyau ake wawa ba sakarya ba!" Ya k'arashe yana harararta. Zuwa yanzu ta gama gane cewar ashe duniya banza ce? Yar gajeruwar k'afarsa ya saka ya hanb'areta yana fad'in "Tashi muje, mutuniyar banza kawai." Tana ji tana gani mahaifinta ne gaba da aminiyarta da mutumen da zata iya rantsewa cewar bata tab'a jin nauyi da kunya da darajar wani d'an adam mai saka wando da zariya bayan mahaifinta irin na wannan bawa ba, sai gashi a yau sanadiyar yan samari da take kulawa, da d'an karb'ar abin hannayensu ba tare da iyayenta sun sani ba ta b'allowa kanta ruwa, an tisota a gaba za'a kaita wajen likita a ware k'afafunta a dubata ita ba mai shirin haihuwa ba ita ba mai rashin lafiya ba. Gaba d'aya ta nemi wani kukan ta rasa, haka kuma baki d'aya ta zama wata sukuku tana ganin ikon Allah har suka ja suka tsaya a k'ofar gidan wanda sheikh ne ya nemi a sirrinta shi kam in ba dan wani irin girman dattijon mahaifin Maryam ba da ba zai yarda a aikata wannan lamari da shi ba. Suna fitowa suka ga motar Asas wanda ganin shigarsu mota yayi gaba d'ayansu ya saka shi fasa tsayar da tasa ya karkata ya bisu dan a yadda ya ga da k'yar Abbban sahibarsa ya cibcib'a ya wuntsila cikin motar da irin yadda da k'yar ya shiga baya ga sheikh da kansa ke tuk'in sai ya ga kamar ba lafiya ba. Daga motar ta fito wannan karon d'an kwalin abayarta a hannunta yalwatacen gashin kanta ya bayyana bak'i sid'ik da shi har wajen gaban goshinta. Gabanta ne ya buga a lokacin da suka yi ido hud'u da Asas a hankali ta lumshe lumsasun idonta wasu hawaye suka zubo mata. Cire dubanta ta yi tana ganin yaron daya fito yake shaidawa Abba cewar su shiga, kasancewarta likita tana samun bak'i maza da mata ta ko ina a kowane lokaci. Cike da tausayawa take kallon Mimi bayan Abba ya gama kora bayanin abinda yake buk'ata, uwa uba sheikh dake zaune kansa sadde k'asa tunda ya shigo ta rasa ina zata saka kanta dan murna domin har k'asa ta duk'a ta gaishe shi dan kuwa a duniyarta wa'azi idan ba nasa bane bata jin dad'insa, nutsuwarsa, kamalarsa ya saka take son wa'azinsa domin a sanyaye yake isar da sak'on Allah. Sai Ashraf da ya zabura jin bayanin Abba yana kallon Abban, da Mimi da du wanda yake wajen yana son k'arin bayani amma ba hali domin sheikh ya had'e fuskarsa. A nutse Hajia Gambo tace "Ayya Abban Mimi, ai kam Mimi akwai nutsuwa duk da baka shaidar d'an yanzu amma bana tunanin idan har zata zubar da mutuncinta haka ba, ka san ba duka 'yan matan namu suka zama d'aya ba duda abin yanzu ya zama na tir sai addu'a, amma dayawa kuwa sun iya taka rawarsu daidai da kid'an ta yanda komai dubararka ba zaka iya gane takonsu ba. " Abba ya kawar da kansa daga duban da Mimi ke masa yace "Ni kam ki duba min ita Hajia, kin ga bana son na mutu da hakk'in kowa gasu nan da yaron da magabatansa idan aka yi komai a gabansu shikenan!" Mik'ewa Hajiar tayi tana mai yiwa Mimi maganar cewa ta tashi su shiga ciki. Asma'u kam kuka take sosai gaba d'aya ta bi ta tsurewa wannan lamari, ta sani ba tare suke kwana da Mimi ba, amma tana iya k'ok'arin bugar k'irji da hallayen k'awar tata, a bar Mimi da caje aljihun gara amma sam wancen harka ba halinta bane. Jiki a sanyaye ta mik'e tana kallon Abba, cikin tsawa yace "Zaki wuce ko saina ragargaza miki fuska, yar banza mai kama da aljanu." Idonsa da sukayi ja ya d'ago a hankali haka kawai ya sauke a kanta a lokacin da ta bada baya tana tafiya dukkan wani lamari nata na motsawa daidai da takun tafiyarta. Da sauri ya kuma sadda kansa yana mai jan "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'ne." Cike da fad'uwar gaba ya shiga korar shed'an a hankali ya sauke dubansa a kan Asas daya sauko k'asa ya had'e hannayensa yana hawaye harda shashek'a yace "Ya sheikh dan Allah koma mecece koma me tayi ni ina son aba ta, ni ba wai wannan nake so ba ni ita nake so, wannan zamani kuwa ba ita ce ta farko ba kuma ba zata zama ta k'arshe ba a fannin cin kud'in maza, wasu da haka suka gina gidaje da motoci da komai, ni kam ina sonta a haka dan Allah." Muryar Abba ne cike da tausayawa yana kallonsa yace "Yaro, halayan fa? Idan yau aka shaida mana ta banzatar da kanta ya ya tarbiyar 'ya'yanka? Ban tab'a sanin uwata ta kai cen ba har ta iya b'oye min waya, ina bada misalai da tarbiyarta? Ina saka baki idan ana maganar 'ya'yan wasu da suke irin haka, ashe tawa na kwance tamkar macijin kumba." Cikin ladabi Asas ya kalleshi yace "Abba na tabbata ko da an sameta da laifi wallahi yanayin rayuwa ne, ni fa gaskiya zuciyata bata gamsu da abinda kuke tunanin ta aikata ba, ta yaya yarinyar da bata jin kunyar fad'an ko ita wacece a gaban kowa zata aikata haka? Mimi fa yarinya ce mai aji ba ballagaza ba." A hankali ya kuma sadda kanshi k'asa maganganun nan suna hawa masa kai sosai, shi sai yanzu ne ma yake sake tantance yanda zuciyarshi ta wani d'aukaka yarinyar a matakin da baiyi tsammani ba. Abba kam gyara tsayuwa yayi yana fad'in "Ban sani ba ko dan Allah yayi ta kyakyawa ne? Amma ta yaya na zama sakarai haka a gaban yarinyar Ddna haifa?" Da sauri sheikh ya kalleshi da mamaki, sai yaji shi kanshi fa sunanshi kenan inda a gaban Mimi ne, domin kuwa ta mayar dashi wani sha-tara har ya kasa ganota. *A ciki* kuwa suna shiga Hajia Gambo ta umarceta ta cire pant d'inta ta kwanta akan gadon, sarewar da tayi a lamarin yasa Mimi ba gardama tayi abinda ta ce, tana kallo ta saka shafa ta likitoci a hannunta ta matso kusanta, kaallon fuskar Mimi tayi tace "Mimi, garin yaya kika bari har irin wannan zargi ya shiga tsakaninki da mahaifinki?" Hawaye ne suka sak茅 sulalo mata ta rintse ido tace "Tsautsayi, k'addara, da kuma rashin jin maganata." Girgiza kai tayi tace "Kenan da gaske kin zama babbar mace tun a waje Mimi?" Wani sakaran murmushi tayi tace "Ke da zaki tabbatar yanzu, me yasa zaki tambayeni kuma?" Murmushi ta mata tare da d'an gyara k'afarta tace "Hakane." Yanda take jin hannunta na neman shiga gabanta yasa ta k'amk'ame jikinta tana sake lik'e ido gam, tana jin hannun na daf da shiga tayi saurin rik'e hannunta ta sauke k'afafunta ta kwantar dasu, bud'a idonta tayi suka kalli juna, Hajia Gambo ce tace "Mimi ki fad'a min gaskiya mana, idan kinsan baki san namiji ba kar ma a fara shigar da wani abun da zai kawowa budurcinta rauni." Kawar da kan ta tayi hakan yasa Hajia Gambo ci gaba da aikinta, yatsanta biyu kawai ta saka amma saida ta nemi shid'ewa, ganin kawai zata wahala a banza ya cakata cire hannayenta tana murmushi tace "Ki ci gaba da tsare mutumcin kanki Mimi, a wannan duniya budurci ya zama kamar shine macen ma, kindai gani me ya faru, iyayenki ma sun kasa yarda dake, bare kuma mijin da kika aura ko zaki aura." Saida ta cire safar ta saka a kwadon shara tace "Tashi ki saka pant d'inki." A hankali ta tashi ta d'auki pant d'in zata saka Gambo tace "Nasan dai za'a sha dangwarma Mimi a daren farkonki, dan wannan kafin ki bada kai bori ya hau sai an nemi ji miki ciwo." K'ala ba tace mata ba saida ta saka ta gyara rigarta, Gambo na juyawa zasu fita ta rik'o hannunta, tsayawa tayi tare da kallonta da mamaki, durk'usawa tayi cikin magiya da neman alfarma tace "Hajia dan Allah na rok'eki ki rufa min asiri, karki fad'awa mahaifina komai a gaban mutanen can, ina jin kunyarsu bana so na ci gaba da tozarta a gabansu." Tsam ta kalleta sai kuma ta jinjina kai tace "Shikenan ba komai, muje." A sanyaye suka fito hakan yasa dukansu suka saki ido suna kallonsu, saidai banda sheikh da hannayensa ke jimk'e yana ta karanta hasbunallah wa'ni'imal wakil! Da sauri Abba ya taresu yace "Ya ake ciki Hajia Gambo?" D'an bud'a baki tayi sannan ta kalli Mimi, a hankali ta d'auke dubanta daga kanshi tace "Abban Mimi kayi hak'uri dan Allah, zuwa safe zan zo gidan na maka bayanin komai insha'Allah." Abun ka ga marar tsayi d'an duk'ul, ba wanda ya lura sai zamanshi suka gani a k'asa b'ingil yana tapa hannaye yana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Oh Allah na Mimi kin kasheni, kin gama dani a duniyar nan." Da sauri kuma ya wulk'ita ya mik'e tsaye ba zato ba tsammani kawai ya ja k'afar Mimi ta dama, yanda abun ya zo mata yasa ta fad'uwa irin fad'uwar nan ta yan bori tippp! Ta daki k'asa, "Ahhhhhhhhh!" Wannan k'arar data saki ta saka sheikh da Asas zabura a tare suka mik'e tsaye sa茂 sheikh daya had'a da jimk'e hannunshi gam, da gudu Asas ya rik'e k'afar Abba dake shirin hawa jikin Mimi ya takata, cikin magiya ya kalleshi yace "Abba karka kasheta, wallahi zan aureta a haka na ji na gani Abba, karka ji mata ciwo dan Allah." Cike da k'una Abba ya sake yin zaune ya fashe da kuka yana fad'in "Mimi ni kika tozarta haka? Ashe duk ladabin da kike mana da girmamamu duk na banza ne wawaye kika d'aukemu? Yau kinsa na ji ni tauyayye ni a cikin hallita, yanda nake d'an tsirit a cikin k'asa haka k'wak'walwata ma da tunani na, ke kad'ai mace amma na kasa kula da tarbiyyarki, uwata me na miki da kika min haka? Talaucinmu ne ya jawo?" Da sauri Asma'u da jikinta ke rawa ta sunkuya ita ma tana kuka tace "Abba wallahi wallahi wallahi ni dai nasan Mimi bata bin maza, Abba karka yanke hukunci ka tsaya kayi bincik..." Tsawa ya mata yana fad'in "Binciken uwaki zanyi, ke da ita ai duk kanwar ja ce, tunda kullum tare kuke manne da juna." Nunawa Asas Asma'u yayi yace "Kaga yarinyar nan da zaku tafi gidanku cewa nayi su tafi tare, amma a k'arshe suka zagaye ita ta dawo ita kuma ta tafi ita kad'ai, to nasan niyyarta da tayi maka tallar kanta ne tunda taga kai aure ne a g..." Cikin wani matsanancin kuka Mimi tace "Abba...abba ka daina ci min mutumci haka, wallahi ban aikata abinda kake zargina ba, ni ba 'yar iska bace Abba." Cikin muryar data fara shak'ewa Abba yace "Wacece ba 'yar iskar ba? Ke fita..." A tausashe cikin son danne abinda ke ranshi kamar an mak'ureshi yace "Dan Allah ko zaki iya barin maganar nan har kuje gida?" Cike da girmamawa Abba yace "Me zai hana sheikh." Wani rank'washi ya kai wa Mimi yace "Wuce muje." Da k'yar ta yunk'ura ta mik'e ga zafin da take d'an jin a k'asanta sakamakon hannun da aka so turbud'a mata, yanzu ma d'an kwalinta a hannu yake dan duk a rikice take a gigice, suna fitar k'ofar gidan kusan shi ne a bayansu sai Mimi dake bayanshi. Kamar daga sama sukaji muryarshi yace "Daure ki rufe kanki, hakan ba kyau." Dukansu saida suka kalleshi har da ita data fara k'ok'arin gyara kallabin ta d'ora a kai, yanzu ma dai duk a motar sheikh suka koma gida sai Asas shi kad'ai a motarshi, amma zuciyarshi zallo take sosai yana jin sirikin na sa na neman b'ata mishi rai. *Idan na ga ruwan comment gobe zaku ga uku ma (peut 锚tre)*馃槑 *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:54 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *19* Duk zaune suke akan tabarma guda sai Asas da sheikh dake kan kujerun roba farare duk da ba sababbi bane, mama kanta na sadde a k'asa dan bata so zama a nan ba saboda kunya da takaici, Mimi daf da k'ofar shiga d'aki take zaune ta had'a kai da gwiwa tana ta shashek'ar kuka, Asma'u na gefenta ta rik'e hannunta gam tana ta murzawa alamar rarrashi, cikin nutsuwa da dattako sheikh ya kalli Abba a nutse yace "Yaran da muka haifa wata rana sukan koya mana darasin rayuwa da bamu tab'a karanta ba, hakazalika wani lokacin sukan sa muji kamar su suka haifemu ba m没 muka haifesu ba, idan har Allah ya bawa mutum haihuwa dole wata rana sai ya zama tamkar jami'in binciki na k'asa da k'asa, wata rana kuma saiya koma kamar lauyan dake gaban wanda ake tuhuma, wani zagayen kuma rigar malunta zaka ara ka yafa dan yi musu nasiha a tsanake sannan su fahimci karatu, akwai lokacin da dole uba sai ya zama mai zafi da kausasawa ga yaranshi, kafin wata rana ka zama mai taushi kamar audiga sannan mai sakin jiki dasu dan suma su shiga jikinka. Amma fa duk wannan matakan tsaron zasu biyo bayan addu'ar nema musu shiriya ne, duk yanda zaka kai ga saka ido ko tattare al'amarin yaranka idan Allah bai nufesu da shiriya ba to fa zasu baud'e maka ne, dan haka malam kayi hak'uri ka b芒 wa zuciyarka hak'uri, idan har ta b'acin rai zaka bi tabbas zaka iya ganin bayan yarka, idan haka ta faru kuma wace akayi kenan?" Numfasawa yayi yace "Kayi hak'uri, ga Asas nan yace har yanzu yana son ta da aure, ni nan zan tsaya masa har naga hakan ya tabbata, mu musu fatan alkairi da zaman lafiya mai d'orewa kawai." Jinjina kai malam yayi ya sauke numfashi yace "Gaskiya ka fad'a sheikh, ni shaidane akan k'wak'waran darasin da uwata ta koyar dani, kuma kamar yanda ka rok'a mata alfarma na yafe mata duniya da lahira, Allah ya tabbatar da alkairi,Allah ya shirya mana zuri'a baki d'aya." "Ameen ya Allah." Suka amsa malam da Asas, kallon Mimi yayi da niyyar ya mata nasiha mai ratsa zuciya ya ja mata ayoyi da haddisai, sannan ya umarceta ta nemi gafarar iyayenta da ta ubangiji, amma tuna abinda ya faru da abinda likitar nan ta fad'a, alamu ne kenan na eh ta zubar da mutumcinta, sai zuciyarshi ta sake maimaita mishi kalmar nan "Kamaninta bata da suffar cutar da kowa, yanayinta bai nuna hakan ba." Da sauri ya d'auke kanshi kawai ya mik'e yana fad'in "Saida safenku." Mik'ewa duk sukayi banda Asma'u da Mimi suka fita sai Mama data shiga d'aki, suna ganin haka Mimi ta d'ora kanta a kafad'ar Asma'u cikin shashek'ar kuka da raunin murya tace "Asma'u kin gani ko? Kinga rashin jin maganarki me ya ja min? Asma'u Abbana ne yake zargina fa." Dafa kanta tayi tana shafa mata gashinta ita ma tana shashek'ar kukan tace "Kiyi hak'uri kinji Mimi, komai zai wuce insha'Allah." Ajiyar zuciya duk suka shiga saukewa har Abba ya dawo cikin gidan, a k'ofar shigowarshi ya ci karo da jakarta data jefar a nan, da k'afa yayi cilli da ita hakan yasa yar jakar buguwa a bango ya bayar da k'ara mai d'an nauyi dake nuna bana jakar bane, da sauri ya taka tare d'aukar jakar ya bud'e, ciro wayar yayi yana kallonta yana jujjuyata, sake jifa yayi da wayar ya kalli su Mimi da duk suka sunkuyar da kawunansu, dogon tsaki yaja tare da sake fita y'a bar gidan. A hankali Asma'u ta zame kan Mimi daga kafad'arta ta mik'e tace "Mimi zan tafi gida nima, saida safe kinji, kiyi hak'uri kuma kar kiyi kuka zai iya haddasa miki ciwon kai." Jinjina kai tayi ta bita da kallo har ta fita, wata irin k'aunar k'awarta ta take ji a ranta, lallai ita yar halak ce kuma ta cancanci ta so ta, a hankali ta yunk'ura ta mik'e ta shiga d'akin, zaune ta samu mama zugum sai su Yaseen dake rik'e da littafin karatunsu amma da gani kasan suma suna cikin alhini, a hankali ta durk'usa gaban Mama ta d'an rik'o zaninta tana fad'in "Mama, dan Allah kar kiyi kuka a kai na ba kyau mama, kina so Allah yayi hushi dani ne? Mama kin gani wallahi ban tab'a issss..." Kasheta tayi da mari tare da fizge k'afarta, hak'ik'a duk da basu da tsayi mutanen amma Allah ya basu wata baiwa, wannan baiwar kam ita ce ta k'arfi, k'ashi d'aya garesu da idan suka rik'eka zaka sha mamaki, hakan yasa Mimi k'arasa zaucewa taji wani zuuuuuu! A cikin kanta, da k'yar ta dafe kuncinta tana jin muryar Mama a cikin matsanancin kuka tana fad'in "Mimi a dalilinki fa aka mana wannan terere! Yanzu ke ko kunya baki ji ba domin Allah, yarinya kamar ki Mimi, ina miki kallon k'aramar yarinya ashe ke ma babbar macece ke tunda har kin iya d'aukar namiji, Mimi har ke ce wai za'a baki kud'i da abu dan ayi anfani dake?" Wani kuka ta kuma fashewa dashi tana zama kan kujerar tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Allahuma ajirni fi musibati, waklufli khairan minha." A hankali Mimi ta muskuta ma su Yaseen da zasu fita daga d'aki saboda ganin har yanzu rigimar bata k'are ba, mik'ewa Mama ma tayi tare da yin k'wafa ta bar mata d'akin, hakan yasa Mimi fashewa da kuka marar sauti kamar zata shak'e kanta ta mutu. A ranar dai kam bata sake jin motsin Abba b芒 dan a masallacin unguwar ya kwana, Mama kuma ko shinfid'a bata fitar waje ba a kan gadonta ta haye saidai ita ma ba bacci tayi ba kamar Mimi dake k'asa kwance. *Sheikh* Cikin nutsuwa ya sake gyara zamanshi yana kallon Hajiar da alama kalamanshi sun fara ratsata ya ci gaba da fad'in "Hajiarmu, ai sun gama kyau da daraja tunda Allah ya hallicesu a 'yan adam, domin kuwa fad'ar Allah ne cewa *lallai an hallici mutum cikin mafi kyawun hallita*, ita kuma wannan hallitar Hajia ubangijin daya hallici ta wa hallitar shi yayi ta ki, haka kuma shi ne dai yayi tasu hallitar, hakan ba dan baya son su bane ko kuma sun mishi wani laifi, hakan ganin damarshi, haka ya so kuma babu wanda ya isa ya hana, dan ya fad'a mana a littafi mai tsarki a suratul buruj aya ta goma sha shiga cewa *yana yin abinda ya so ne*, Hajia karmu k'yamacesu dan hallutarsu, mu k'yamace dan munanan d'abi'unsu ko halayensu, kuma mun tabbatar babu su Hajia, hallitarsu hallita ce ta Allah wanda idan ya so yanzun nan zai iya mayar dani irinsu, ko kuma cikin dake jikin Hafsat ta haifo mai kama dasu, duk yin ubangiji ne wannan, Hajiarmu, *shin da wace ni'imace kuke k'aryatawa*? Ni dai ba'a da ja akan cewa Allah ba zai iya salwantar da hallitata ba, ban sani ba ko ke Hajiarmu?" Da sauri ta girgiza kai tace "A'a sheikh ni a wa? Ni ma bana da ja, dama tun farko raina ya b'aci ne saboda babu wanda ya sanar dani kalar jinsinsu, sai kuma yarinyar da naga zubinta yafi k'arfin yanayin iyayenta a yanda aka fad'a min, bugu da k'ari Salamatu ta fad'a min ta gansu suna fad'a har ana kiranta da karuwa." Girgiza kai yayi yana fad'in "Subhanallah, astagfurillah! Wannan shaci-fad'i ne na mutane, dama ai babu inda za'a fara maganar aure ba'a samu masu kushewa ba, Hajiarmu Asas yana son yarinyar nan tunda har kika ga ya sameni gida da sassafe haka ya ce na sameki, ki musu fatan alkairi a matsayinki na uwa hakan nada matuk'ar tasiri akan su fiye da yankan wuk'a." Jinjina kai tayi cike da gamsuwa tace "Shikenan na amince, Allah ya tabbatar da alkairi." Murmushi yayi yace "Ameen Hajia, nagode da wannan alfarmar da karamci, Allah k'ara girma da lafiya." "Ameen." Ta fad'a cike da son suruki kuma d'an d'an uwan mijin nata, mik'ewa yayi yana mata sallama ya fita a falon inda ya samu Asas a bakin motarshi da alama shi yake jira. Yana zuwa cike da zumud'i yace "Ya ake ciki sheikh? Dan Allah ka ce min ta amince?" D'an zuba masa ido yayi da fari sai kuma ya jinjina kai ya lumshe ido yace "Ta amince, ka je ka ci gaba da shirye shirye." Rumgumeshi yayi yana fad'in "Alhamdulillah, gaskiya na ji dad'i." Murmushin yak'e kawai ya masa amma har zuciyarshi wani suka yake ji kamar ana soka mishi allura, ga wani irin mataccen yanayi daya taru ya baibayeshi saboda abinda ya zo mishi wanda bai tab'a tsammani ba, da kuma rashin baccin da bai samu ba a daren jiya ko na minti d'aya, saida ya raba jikinshi da nashi kafin ya d'an bubbuga bayanshi yace "Ni zan wuce, sai munyi waya." Da kallo Asas ya bishi har ya rab'ashi zai shiga mota Asas yace "Sheikh." Tsayawa yayi tare da juyowa ya kalleshi, kafeshi yayi da ido saboda yana son fahimtar yanayin da zai shiga idan ya ambaci sunanta sannan yace "Me ye tsakaninka da Mimi?" Sake zaro idonshi yayi yana k'urawa Asas da mamakin tambayar, a hankali ya had'e fuskarshi yana binshi da kallon tuhumen tambayarshi, lura da haka yasa Asas fad'in "A'a cheikh! Ba wai ina zarginka bane da wani abu, kawai dai na fahimci kamar akwai sanayya a tsakaninku, shiyasa na tambaya." D'an d'auke idonshi yayi daga kan Asas ya bud'e murfin motar yace "Ba komai tsakaninmu, karka k'ara min tambayar nan." Wani murmushi Asas yayi ya kallonshi har ya shiga motar, zai ja murfin ya rik'e yayi saurin rik'eshi yace "To ya maganar Ryam d'inka?" Ba tare daya kalleshi ba yace "Tana lafiya, zamuyi magana a gaba." Yanda ya amsa mishi yasa Asas bai da wani zab'i daya wuce yar rufe mishi murfin dreba ya ja shi suka bar gidan, saida ya ga b'acewarsu kafin ya nufi b'angarenshi dan shiryawa, yana so idan ya fara zuwa asibiti daga nan saiya wuce ya ga yanda Mimi ta kwana. *Mim-Ma'u* Ita maganar duniya bata b'uya ko da k'ark'ashin k'asa aka yi ta, tashin hankalin daya faru a gidansu Mimi tsaf a kunnuwan mutan gidan su Asma'u, dan dama katangarsu d'aya ne, wannan ya jawo cece-kuce har abun ya so juyewa kan maman Asma'u, dan ita kanta Asma'u saida kishiyoyin uwar suka fara yada musu magana suna cewa abokin b'arawo ai b'arawo ne, hakan ya jawo fad'a sosai a gidan suma jiya, dalilin haka kuma mahaifin Asma'u ya fad'a da babbar murya cewa ya soke k'awance tsakanin Asma'u da Mimi har abada. Ita kanta Mimi yau data tashi sai ta samu kanta kamar bak'uwa a gidan, suna fara had'a ido da Mama kamar yanda ta saba ta duk'a har k'asa tace "Mama ina kwana." D'auke kai tayi kamar bata ji ba ta wuce aikin gabanta, mik'ewa tayi jiki a sanyaye ta d'ora hannu akan mad'aurin gidan sangensu Yaseen zata kwance, murya a dak'ile Mama tace "Barshi zan d'auke da kaina." Kallonta tayi zuciyarta na harbawa tace "Amma Mama..." Kujera ta data ta d'auka ta aza ta kuma tak'ark'are ta taka kujerar ta shiga kiciniyar kwance sangen, kasa katab'us tayi tana kallo har ta kwance duka, mik'awa Yaseen tayi tace "Kai d'aki." Karb'a yayi ya wuce Mama kuma ta fara tattare shinfad'ar, muk'ut tayi ta had'e kukanta tare da k'arasawa gaban murhun da mama ta fara k'ok'arin hura wuta, shi ma dai cikin fad'a tace "Bana so, ban sakaki ba Mimi, idan baki da abinda zakiyi ki nemi waje ki zauna, dan makaranta ma kin gama zuwanta." Da tsananin mamaki ta kalli Mama hawayen da take rik'ewa suka gangaro, cikin muryar kuka tace "Mama ku yafe min, nasan nayi laifi amma dan Allah karku hanani samun albarkarku." Wani tsaki Mama taja tare da k'uk'utawa ta d'auki bargon zata shiga dashi d'aki, har ga Allah bargon yafi k'arfinta amma tsabar hushi haka ta wuce dan kai shi d'aki, a daidai k'ofar shiga tsautsayi yasa mama gurd'ewa ta fad'i ita da bargon, da gudu Mimi ta tunkareta haka ma su Yaseen da suka tsaya bakin k'ofar, kamata tayi ta mik'e cikin jin haushi tace "Sakeni, karki taimaka min." Cikin matsanancin kuka Mimi tace "Mama me yasa ba zaki bari na taimaka miki ba? Wani ma bana jurar ya cutar daku bare kuma ku naga kuna k'ok'arin haka." Duk'awa tayi zata d'auki bargon Mama ta fizge da k'arfi ta k'arasa dashi ciki ta aje ta fito, fitowa tayi ta samu Amir na nad'e tabarmar, Mama kuma na hura wuta zata d'ora d'umame, tsaye take saita rasa me zatayi ma sai hawaye kawai. Bud'e gidan da suka ji yasa Mimi saurin juyawa, tana ganin Abba sukuku dashi idonshi jajir tayi saurin durk'usawa tana fad'in "Abba ina kwana? Abba ina ka tafi mun..." Nunata yayi da yatsa hakan yasa ta yin shiru, ta gabanta ya bi zai shiga d'akin mama ta kalleshi tace "Ina kwana?" A dak'ile ya amsa da "Lafiya lau." Su Yaseen ma gaisheshi sukayi ya amsa, nan ya barta tsugune saida ya shige sai kawai ta ja k'ugu ta jinjina a bango ta rakub'e tana hawaye, haka Abba ya fito zai shiga wanka mama ta d'auki bokiti ta zuba mishi ruwa, a yanda suka saba Mimi ke d'aukar bokitin, amma yau basu barta ba Abba ne ya lailayeshi ya kai ban d'akin, tana zaune har mama ta zubawa su Yaseen tuwon suka fara ci Abba kuma ya fito. Gaba d'aya ta rasa ya zatayi ina zata saka kanta ta ji dad'i, a halin yanzu kam kunyar fita waje take kuma tana kunyar had'a ido da Asas, saidai gashi iyayenta ma na neman zama mata dodo su saka ta fara fatan mutuwa. Mik'ewar su Amir suka wanke hayyane suka d'auki jakunkunan makarantarsu yasa Mimi cikin shashek'ar kuka tace "Amir, lek'a gidansu Asma'u ka kira min ita kafin ta tafi makaranta." Juyawa yayi zaai fita Mama tace "Kai." Juyowa yayi yace "Na'am." A d'aure tace "Wuce ku tafi inda zaku je." "To." Ya fad'a yana bin bayan Yaseen suka fita, tusa kanta tayi tsakanin gwiwoyinta ta sake fashewa da kuka, fitowa Abba yayi yana saka takalminshi ya kalleta yace "Kuka ko? Yanzu kika fara ai Mimi, ai duk wanda yasa iyayenshi kuka shi ma sai yayi marar iyaka." D'agowa tayi cikin matsancin shid'ewa tace "Abba dan Allah dan girman Allah karku min baki, Abba ban aikata abinda kuke zargina da aikatawa ba, wallahi ban tab'a ko da d'aura niyyar fara bin wannan hanyar ba." Tab'e baki yayi yace "Maganar banza, shi wanda ya baki wayar kenan d'an mahaukaciya da zai baki ita ba tare da shi ma ya moreki ba." Rintse ido tayi tace "Abba ka tambayeshi kaji idan kana so, wallahi ko hannuna bai tab'a rik'ewa ba." Zaune yayi akan kujerar katako ba tare da yace komai ba, ga abinci mama ta aje mishi amma saiya tsura mishi ido yana kallo, ganin kamar baya hayyacinshi yasa mama fad'in "Malam." D'agowa yayi ya kalleta hakan yasa tace "Lafiya, ka ci abinci mana karka bari hawan jini ya kamaka a banza." Girgiza kai yayi yace "Wallahi Allah ba dan girman sheikh da nake gani ba, da na mayarwa da yaron nan kayanshi ita kuma na bayar da sadakarta a masallaci." Yanda Mimi ta k'ura mishi ido tana kallo yasa yace "E! To yaushe zamu d'aukeki gwalagwaje mu kai a wannan babban gida, bayan kasantuwar fak'irai kuma wadanni mun zama iyayen karuwar gida..." Sake had'a kanta tayi da gwiwa ta fashe da kuka tace "Abba ka daina dan Allah, Abba ka daina babu kyau wallahi, Abba ni ba karuwa bace." Sallamar Gambo tasa su dakatawa suka amsa, wuri mama ta bata ta zauna suka shiga gaisuwa cike da alhini, kallon Mimi tayi da ko d'agowa ba tayi ba tace "Abban Mimi ba dai har yanzu maganar nan bata wuce ba?" Kallonta yayi yace "Wucewa? Haba dai yaushe?" Girgiza kai tayi ta gyara zama tace "Abban Mimi, a gaskiya abinda kayi jiya baka kyauta ba ko kad'an, tabbas laifin Mimi ya isa ya hanaku nutsuwar zuci, amma kuma ai komai yana son sirri, yanda ka tozarta kimar yarinya a idon k'awarta da babban malami da kuma mijin da zata aura abin sam baiyi dad'i ba, ka fa sani duk lalacewar da Mimi zatayi wallahi ba zaka iya cireta a 'ya'yan daka haifa ba. Gashi yanzu kuna ta zargin yarinyarku a banza yarinyar da ko yatsa bai iya wucewa ta gabanta ba, kun d'auki alhakinta sosai gaskiya, dan zaku iya yin komai a tsanake." Kallon Mimi tayi tace "Kamar yanda na fad'a miki jiya Mimi ki ci gaba da rik'e mutumcin kanki, wannan d'in shi ne darajarki a wannan k'arni, iyayenka ma suna wofantar da kai idan ka zubar dashi a waje." Kallon Abba tayi tace "Idan baku yarda ba ku kaita wata asbitin, amma ka sani duk tozarcin da zaka jawo mata kanka ka jawo ma, dan kafin a nunata sai an nunaka da yatsa tunda kai ne namiji mai fita." Mik'ewa tayi tare da fad'in "Sai anjimanku, ina sauri dama zan wuce asibiti nace bari na tsaya dan cika alk'awarina." Babu wanda yace mata k'ala harta fita a gidan, jiniyar kukan Mimi kawai suke ji amma babu mai sauke ko da numfashi da k'arfi. Da k'yar Abba ya sauke numfashi ya kalli Mama yace "... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:54 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *20* Da k'yar Abba ya sauke numfashi ya kalli mama yace "Kina ganin gaskiya ta fad'a?" Zuru ta masa da manyan idonta tana kallonshi ba tace komai ba, kallon Mimi yayi tare da fad'in "Tashi shiga ciki." Mik'ewa tayi tana kuka kamar ranta zai fita ta shiga d'aki, kallon Mama ya sakeyi yace "Ni fa sai naga kamar gaskiya ta fad'a." Saida mama ta d'aure fusja tace "Ko da gaskiya ne bai kamata mu sake sakar mata fuska ba, ai ta yaudaremu ta munafurcemu, shi kuma wannan laifin fa?" Jinjina kai yayi yace "Hakane, a gaskiya ban tab'a kawo faruwar haka a raina ba, uwata? Uwata ita ce ta aikata wannan babban kuskure." Ajiyar zuciya kawai mama ta sauke ba tace komai ba, abincin ya ci gaba da ci yana idawa ya wanke hannu ya fita a gidan. Yana fita kuma malam ya sallamo gidan, jiki na rawa mama ta shiga amsawa tana k'ok'arin d'auko mishi kujera, ta tabbata abinda ya faru ne ya kawoshi gidan, dan ko haihuwa tayi malam ba gidan yake zuwa ba, ai kuwa ciki ya shigo fuskarshi a had'e tsabar b'acin rai, dan har gida Gambo ta biya yanzu ta sanar dashi abinda ya faru jiya, ita tausayin Mimi da ganin yanda ta sameta a gidan yasa ta zuwa ta fad'a mishi. Kanta k'asa ta durk'usa tana fad'in "Malam ina kwana." Cikin fad'a yace "Kwanan lafiya? Ina Mimi?" D'aki ta kalla tace "Tana ciki." Abinda bai tab'a yi ba a rayuwarshi, sai gashi yayi yau dan kuwa wucewa kawai yayi d'akin yana cire takalmi ya sake yin sallama, da mamaki mama ta bishi da kallo dan ita dai tasan baya haka. Mimi na jin sallamarshi ta sauko daga kan gado ta sake fashewa da kuka, a hankali ta d'ora kanta a k'irjinshi tana sake sako wani kukan, cike da tausayinta ya dafa kanta yace "Amaryata yi shiru kinji, ki rabu da mutanen gidan nan, yau ba zaki kwana a gidansu ba sai nawa, dan na basu amanarki har na gama k'era miki gidanki, shi ne za'a ci min amana haka." K'wafa yayi a hankali Mimi ta fara jin sanyi a zuciyarta ta ji tana neman yin murmushi, d'aga kanta tayi saidai bata kalli fuskarshi ba saboda kunya tace "Angona ban aikata ba, ban aikata abinda suke zargina ba, kawai dai ina karb'an kud'i ne idan aka bani amma ban tab'a rok'a ba da kaina, ko waya ma dana rik'e bani nace a siya min ba, kawai anga rashin dacewar ace bana da waya ne yasa aka bani, ni kuma na sa hannu na karb'a, amma wallahi kakana ban tab'a zubar da mutumcina ba kafin a bani wani abu." Kama hannunta yayi suka zauna kan kujerun robar yana kallonta yace "Na sani Mimi, ni ban tab'a ji a raina ba damaa zaki iya aikata wannan mummunan aiki ba, laifinki kawai karb'an abun hannun kowane gara da wawa, ta hakane wata rana wani zai zo miki da buk'atarshi, dan wani in ya baki dan Allah wani kuma wani abu ya hango a tare dake da yake son mora, dan haka saiya fara siye zuciyarki da kyaututtuka marasa anfani." Numfashi ya sauke yace "Naji dad'i da yaron nan yace bai fasa aurenki ba, hakan ya tabbatar min shi namiji ne kuma d'an halak." Cikin share hawaye tace "Kakana kunyar Asas nake ji, da wane ido zan kalleshi bayan abinda ya faru? A gabanshi komai ya wakana kakana." Sake dafa kanta yayi da babu d'an kwalin sai tarin sumar mai yawan gaske da tsayi saidai bai wuce iya wuyanta ba yace "Karki damu kinji, idan ya zo shi ma ki nemi gafararsa, sannan ki fad'a mishi abinda kika fad'a min yanzu, zai k'ara fahimtarki har ma ya sake miki alk'awarin aure." Jinjina kai tayi alamar to, cikin rarrashi yace "Zan tashi na tafi kasuwa yanzu, me kike so na taho miki da shi?" Cike da kunya ta sunkuyar da kanta tana d'an murmushi, hancinta ya lak'ace yana fad'in "Kaga ja'ira ko? Yaushe aka fara tausayina haka har ake tsoron ragargaza min aljihuna?" Fashewa tayi da dariya mai sauti har hak'oranta suka fito, sosai yaji dad'in ganin wannan annuri na ta, dan haka yace "To fad'a min me zaki ci?" Girgiza kai tayi tace "Bana son komai, kuma ma ai wannan tsohuwar matar taka ta hanani cin kayan yaji yanzu." Kumatunta ya shafa yace "Kenan da abu mai yaji zan siyo? To ai naji dad'in haka." Mik'ewa yayi hakan yasa ita ma ta mik'e tsaye, kama hannunta yayi yace "Fad'a min yanzu zaki zauna anan? Ko kuma kina so idan na dawo daga kasuwa na biyo mu tafi tare dake? Dan naga a nan cutar min ke a ke yi." Shiru ta d'anyi tana tunanin abun yi, ji tayi ya shafa kumcinta data sha mari jiya yana fad'in "Ga shaidar sawun hannu a fuskarki, wannan jar fata ai bayan sabulu da ruwa ban yarda komai ya tab'ata ba." Dariya tayi tace "Kakana zan fara tambayar izinin Abbana, idan ya amince sai naje." Jiijina kai yayi yace "Shikenan to, sai anjima." Jinjina kai tayi ta bishi da kallo cike da k'aunar kakan nata har ya fita a d'akin, mama na ganinshi ta sake sunkuyawa tace "Allah ya tsare malam, a dawo lafiya." A dake ya amsa mata da "Allah yasa." Ya fice a gidan, haka kawai ta samu kanta da sakin murmushi, wato duk abinda Mimi tayi ba tayi laifi ba d'an hukuncin da suke son yi mata shine su har sun aikata laifi, mik'ewa tayi ta ci gaba da kai da kawonta. Da k'yar ya samu yaron daya turo ya shigo cikin gidan da sallama, mama ce ta amsa tana kallon yaron da alama almajiri ne, cikin girmamawa yace "Ina kwananku? Aka ce wai ana sallama a waje." Da mamakin maganar yaron tace "Waye?" A nutse yace "Yace wai Ashraf ne." Numfashi ta sauke mai nauyi kafin tace "Ka ce ya shigo ciki." Da sauri ya mik'e ya fita dan isar da sak'on, jim kad'an ya shiga doka sallama mama na amsawa har ya shigo ciki, har k'asa ya durk'usa suka gaisa kafin ya ajiye ledojin hannunshi yace "Mama dama wannan sak'on Mimi ne na jiya, Hajia da kuma aunty Hafsat ne suka bata, shi ne nace bari na kawo mata." Cike da kunya da kuma rashin farin cikin ganin sak'on tace "Harda wahala haka? Wallahi da ma ka barshi ai, a halin yanzu bana jin mahaifinta zai yarda ta karb'i kayan nan." Ba tare daya kalleta ba yace "A daure a karb'a mama, tun jiya kayan ke hannu na, idan na mayar musu yanzu ba zasu ji dad'i ma suma." Jim tayi alamar tunani sai kuma tace "Shikenan angode, Allah ya biya." "Ameen." Ya fad'a da fara'a, mik'ewa mama tayi ta nufi d'aki tana fad'in "Tana ciki ai." Tana shiga zaune ta samu Mimi tana jin komai dake waknaa a wajen, cikin d'aure fuska tace "Kije ku gaisa, amma karki yarda ki wuce minti biyu." Jiki a sab'ule ta mik'e tana d'aukar hijabinta na makaranta, yau kam Mimi bata bi ta kan duba madubi ko shafa turare ba haka ta fita, tunda ta fito kanta k'asa bata so su had'a ido, amma tana jin yanda idonshi ke yawo a jikinta, saida ta tsaya d'an nesa dashi a fargajiyar gidan kamar zata duk'a mishi tace "Ina kwana." Da murmushi a fuska yace "Lafiya lau maah, antashi lafiya?" Bakinta kawai ta iya motsawa ta amsa amma bata fito da sautin ba, wani murmushi ya saki ganin yanda take ta wasa da hannayenta a cikin hijabi, saidai ta bashi tausayi ssoai ganin yanda fuskarta ta wahala dan kuka da marin da ta sha, numfashi ya sauke yace "Maah ni zan wuce, dama kayanki na zo kawo miki." Sake sinne kanta tayi, duk da kuwa bata so amma ba zata iya d'aga kanta ta kalleshi ba bare ta fad'a mishi, a sanyaye ya sake furta "Sai anjima, nan da jibi zan dawo insha'Allah." Jin ya juya zai tafi yasa Mimi d'aga kanta ta bi bayanshi da kallo, kamar yasan ta d'ago kai sai kuma ya tsaya ya juyo hakan yasa idonsu sark'ewa a juna, hawayen dake mata ambaliya ne yasa shi saurin matsowa yana fad'in "Maah lafiya? Me ya faru kuma yanzu kike kuka?" Cikin fashewa da kuka tace "Kayi hak'uri Asas na cuceka, ka yafe min dan Allah kaji." D'an tsakin nan yayi irin haba ke ma tare da fad'in "Naanah, tun jiya na fad'a aurena da ke babu fashi insha'Allah, gaskiyarki tasa nake k'ara sonki, kuma wannan gaskiyar yanzu haka gata nan ina hangowa cikin idonki, dan haka ki kwantar da hankalinki kinji." Jinjina kai tayi tana share hawaye tace "Nagode, amma ina jin kunyarka da ahalinka da iyayena da kowa da kowa, Asas ya zanyi da abun kunyar nan?" D'an matsowa yayi kusanta kad'an yana murmushi yace "Maah le, na ce ki kwantar da hankalinki kinji, karki damu da komai dan Allah, kinji." Jinjina kai tayi alamar to, wani murmushi ya saki yace "Yawwa ko ke fa, dan Allah karki bari damuwa ta samu muhalli a zuciyarki har tayi tasiri a shagulgulan bikinmu, ina so na ganki cikin walwala." Nan ma sake jinjina kai tayi alamar to, jinjina kai yayi shi ma yace "Zan wuce, sai jibi insha'Allah." Jinjina kai tayi tace "Allah ya kaimu." "Ameen." Ya fad'a yana juyawa, ita ma juyawa tayi ba tare data d'auki kayan ba ta koma d'aki, dan ita da sake karb'an abu a hannun wani kam har abada indai ba aure tayi ba, tana shigowa d'akin mama ta mik'e tana binta da wani kallo, yanda take ta b'oye hannayenta a hijabin ya dasawa mama alamar tambaya a game da ita, dan haka ta fizgota da k'arfi taja hijabin ta cire mata ta jefar, kallon hannayenta tayi tace "Me kike b'oyewa yanzu kuma?" Saida ta durk'usa k'asa tace "Wallahi mama ba komai." K'in yarda tayi da tsiya sunkuya ta saka hannu a k'ugunta tsakiyar siket d'inta, lalabawa ta shiga yi Mimi kam d'an kakkarewa take tana kallon Mamar, buge hannunta tayi tana fad'in "In kina da gaskiya ki bari na duba mana." Da sauri ta d'auke hannayenta da tunanin mama ta gani ko ta samu rangwame, a tsawace ta kalleta tace "Mik'e tsaye, mai ladabin kunama kawai, kin iya sinne kai kina wani durk'usa mana kamar gaske." K'are mata kallo ta shiga yi kafin tace "Zazzaga min siket d'in nan." Cikin marairaicewa tace "Wallahi mama babu komai, mama me zai bani yanzu daga zuwanshi?" "Ni ina zan sani? Ai kin fini sanin komai Mimi, dan yanzu ni tsoro ma kike bani." Cewar Mama tana ta lalabeta har cikin riga, saida ta tabbatar babu komai kafin ta tab'e baki ta juya ta fita, kayan da suka bari a tsakar gida ta d'add'ako da k'yar ta kawo ta aje, nuna mimi tayi da yatsa tace "Kuma ban yarda ko kallon ledojin nan kiyi ba har sai mahaifinki ya dawo." Jinjina kai tayi alamar to tare da d'auke idonta daga kan ledojin, fita mama tayi a d'akin ita kuma ta gyara zama ta kifa kanta a cinyoyinta ta saka wani kuka mai ban tausayi, cajewar da Mama ta mata yanzu ta tsaya mata a rai sosai, daga shigowar Asas yanzu har tayi tunanin ya bata wani abu data b'oye? To me zai bata dan Allah? Shi fa ba haka yake ba, aure ne kawai a gabanshi ba shashanci ba, hasalima har yanzu babu wanda ya tab'a jaraba yi mata wannan ko da cikin wasa ne. Da wannan Mimi ta ci kuka ta gode Allah a wannaan wuni kam, ba aikin fari dan ko tsintsiya ta d'auka mama zata ce bata so ta aje, sallah kawai take mik'ewa tayi amma hatta da abinci mama bata ce mata gashi ba, sai yamma ne da taji yunwa zata kasheta ta d'iba da kanta cike da zulumin kar mama ta hanata shi ma. Gashi tun tana zuba ido ganin Asma'u har ta cire rai, kuma babu damar aiken Yaseen ko Amir su kira mata ita ko taji sanyi a ranta. *Sheikh* A d'aki ya sameta tana sallah isha'i da ta kubce mata har aka idar, zaune yayi bakin gado ya buga tagumi yana kallon enveloppe d'in hannunshi, abinda ya wuni yana damunshi ne ya sake fad'o masa a rai a daidai lokacin, idan ya tuna abun nan har ji yake kamar yayi ihu ko yaji zuciyarsa ta rage nauyin nan, saidai ina ba zai iya hakan ba, sai ma kama istigfari da yayi a zuciyarshi, har ta mik'e ta nad'e sallayar ta cire hijabi ta zauna kusa da shi bai lura ba, saida ta dafa kafad'arshi tana lek'a fuskarshi tace "Sheikh da tunani hakka?" Da sauri ya kalleta yana murmushi, numfashi ya sauke yace "Kin idar ashe?" "Na idar amma sheikh nawa ya tafi duniyar tunani." Ta fad'a cikin shagwab'a, d'an murmushi yayi yace "Ba tunani nake ba, akwai abinda nake yi ne." Da mamaki ta kalleshi tace "Karatu kake? Ko wani sabon zikiri ne aka samu mai falala ba'a fad'a mana ba." Dariya yayi tare da jawota ya rumgume yanda ba zai cutar da abinda ke cikinta ba yace "Sabo ma kuwa, yanzun nan na bincikoshi a wani littafi." Cikin dariya tace "To fad'a min a kunne naji, dan kar iska ta d'auka ta fitar a waje." Shi ma cikin dariyar tare da son kawar da abinda ke ranshi ya tallabo fuskarta da hannu d'aya yace "Wannan ai ko ido bana bari ta gani ba bare kuma kunne ta ji." Daidaita bakinta yayi akan na shi ya had'e labb'ensu, a sauk'ak'e ya shiga paputukar neman kamo harshenta, cikin samun nasara ya shiga tsutsar harshen yana sake k'amk'ameta a jikinshi yana son zura hannayenshi cikin rigarta, da k'yar ta jawo bakinta tana mayar da numfashi da k'yar kanta a k'asa, sake tallabo kanta yayi yana son had'a ido da ita yace "Ba kya ra'ayi na ne?" Da sauri ta kalleshi tace "Ni d'in? Haka ya tab'a faruwa ne?" Mik'ewa tayi tana gyara rigarta tace "Kai ma ai kasan duk sanda ka zo min ina maraba da kai, kawai dai baka tab'a kirana bane a wannan lokacin." Dariya yayi ya sake yin tagumi yana kallonta yace "To yau na kiraki, wannan ai shi ne hadisin da kike son sani, an fad'a min akwai samun nasara sosai a fad'an bayan sallah isha'i da magauta." Dariya tayi tana girgiza kai tace "Ba sai an min wani wayo ba, kawai mutum ya fito fili ya furta abinda ke zuciyarshi." Wani shu'umin kallo ya mata da k'ananan idonshi yace " *Sawwama*." Cike da karsashi tace "Na'am yah sheikh." Mik'ewa yayi yana aje enveloppe d'in yace "To na kiraki da k'arfi yanzu, za'a iya bani had'in kai?" Yanda ya jawota a hankali ya had'a jikinsu tare da zame mata hannun rigarta yasa ta yin murmushi tace "Dole na mana, idan na k'i amsa kira na kwana ina shan mita ana min wa'azi a gida." Dungure mata kai yayi yace "Iyeeh! Ni ne ma sarkin mitar kenan? Yanzu fad'an Allahn da nake fad'a ma ya zama laifi, shikenan zan daina daga yau." Hafsat dai dariya kawai take yi har ya rage musu hasken nan mai k'arfi, saida ya kwantar da ita a nutse ya mata runfa yace "Me zaki bani tukuncin ziyarar da zan kawo miki yanzu?" Lumshe ido tayi cike da k'aunar mijin nata tace "Me kake da buk'ata *shugaba na*?" Saida ya waina ido alamar tunani kafin yace "Ki amince zaki tafi dani hutu k'asar waje na sati d'aya." Murmushi ta saki tace "Na amince." Sumbatar bakinta yayi tare da jawo musu babban bargo suka rufe rabin jikonsu. 馃槑(Sheikh ka ci gaba da zazzaga tsiyarka a nan, Asas ma lokaci ya kusa) *Bayan kwana biyu* Ba wani abunda ya zanca mata har yanzu, zaman shiru da kad'aici kawai take, ga makaranta da aka hanata zuwa bare kuma k'ofar gida, babban bak'in cikinta shiq ne yanda har yanzu Asma'u bata shigo gidan b芒 ita ma, sosai take buk'atarta take so suyi hira ko zata d'ebe kewa, amma ita ma shiru babu motsinta. Tunda safe su aunty Sahura suka zo kamar yanda sukayi da ita, da k'yar Abba ya yarda su tafi tare dan cewa yayi saidai su tafi kawai, Shapi'a ce ta nuna masa basu son kalar da zasu d'auko mata ba, shiyasa yace su tafi tare amma fa karsu yarda ko daidai da shiga fitsari ban d'aki ta b'ace musu. Haka suka fito suna gaba tana baya dan kunya take ji ta jera dasu tunda ta fisu tsayi, su kuma akan tafiya suke bare ta durk'usa musu saboda girmamawa. Haka suka je babbar kasuwa sukayi siyayya ta zab'i abinda take da buk'ata kafin suka juyo zuwa gidan har rana ta take sosai, taxi na aje su k'ofar gida ta sunkuya ta rik'e hannun Sahura cikin magiya tace "Aunty Sahura, dan Allah ku rakani na ga halin da Asma'u take ciki, kwana uku kenan ban ji motsinta ba kar a zo bata da lafiya." Juyawa Sahura tayi ta kalli Shapi'a tace "Shiga da kayan ciki muna zuwa." Jinjina kai tayi rumgumi kayan da k'yar ta shiga dasu ciki, su ma gidansu Asma'u suka shiga daidai da fitowar mahaifinta daga d'akin amaryarshi zai fita, saida Mimi ta duk'a tace "Ina kwana Abba." Shiru yayi kamar bai ji ba sai ma gyara zaman hularsa da yake, mik'ewa tayi Sahura na gaba zasu k'arasa shiga ciki, cikin dakakkiyar murya yace "Dakata Mimi." Tsayawa sukayi a tare suna kallonshi, sabo yasa saida Mimi ta k'ara durk'usawa saboda girmamawa tana saurarenshi, saida ya gyara tsayuwarshi da kyau ya shiga nuna mata da hannu yana fad'in "... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:54 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *21* "Mimi dan Allah ki tafi gida kinji, karki fahimceni ba daidai ba, ni ubane dole na so ganin 'ya'yana cikin kykyawan tarbiyar da za'a yi misali dasu, idan da hali dan Allah ki fita a harkar Asma'u, bana son k'awancenki da ita ko kad'an, dan in na bari kuka ci gaba da k'awance to ita ma tarbiyarta zata iya samun matsala, kuyi hak'uri kinji." Yana gama fad'a ya sa kai ya bar gidan da sauri, Mimi data kasa tashi tana d'ora kalamanshi a mizani tana basu kyakyawan muhalli tana son ta tantance me yake nufi, bata samu sahihiyar amsar da take buk'ata ba Sahura ta fizgi hannunta da k'arfi suka fita a gidan tana fad'in "Aikin banza kawai, ka raba k'awancen mana sai me, da me take k'aruwarta dashi da yanzu hakan zai zamar mata illa? Mtssssss! Kawai mutane baku da lissafi kudai jiran tab'i kuke kuce dama kunyi zaton haka." Suna shiga gida Mimi da gudu ta fad'a d'aki tana fashewa da kuka, da kallo mama da Shapi'a suka bita sai Shapi'a ce tace "Lafiya? Me aka mata?" Tsaki ta kuma yi tana zama akan tabarmar ta fad'a musu abinda ya faru, da k'yar Mama ta had'e wani mak'ulloton abu a wiyanta na bak'in ciki tare da share zancen kamar bai dameta ba. Sun jima gida suna tattaunawa da hira ta yan uwa tsakaninsu, sai kusan la'asar suka bar gidan, suna tafiya Mama ta sameta d'aki bayan sunyi sallama, kofi ta mik'a mata tace "Shanye wannan." Karb'a tayi tare da kifa kanta ta shanye tas saboda zak'in da taji da kuma k'anshin karanfani, karb'an kofin mama tayi ta juya tana murmushi da mamakin yanda Mimi ta karb'i maganin nan ta shanye, duk da dai tasan akwai zak'in mazark'waila amma kuma ana jin d'and'aon sassak'en b'aure. Shi ma kuma yanzu Sahura ta bayar a dinga dafa maata tana sha zai mata maganin zafi da wanke mata dattin mara sosai kasancewarta mai son kayan da suka shafi yaji da maik'o. *Sheikh* Yau kam Allah ya nuna sun bar k'asarsu Niamey inda suka shiga air france wanda ya saukesu Paris cikin awa hud'u, taxi suka samu ta kaisu babban masauki dan huta gajiya, da kan shi ya kama musu lafiyayyen d'aki da rakiyar ma'aikacin hotel d'in suka isa d'akinsu, tare suka fad'a wanka tare da rama sallahr data kubce musu, suna idawa sukayi oder abincin da zasu iya ci, saida suka gama sun samu nutsuwa kafin sheikh ya kira Aisha da wayar daya bar mata, hira sosai suka sha da yaran har da Hajia ma wanda wurinta suke kafin suyi sallama, daga nan ganin babu lokacin sallah da zai riskesu sai suka shiga bacci a tsanake cikin kwanciyar hankali. *Mimi* Yanda ta k'urawa littafin idonta da suke taf da hawaye zaka san ba karatun take ba, tun yamma sheikh ya fad'o mata a rai, haka kawai ta samu kanta tana mai jin wata matsananciyar kunyar sake had'uwa dashi, daki-daki take tuna tun daga had'uwarsu har jiya, lallai tayi kuskuren yi mishi k'arya, me yasa tayi tunanin daga waya ne ba zasu sake had'uwa ba? Me yasa bata zama mai taka tsantsan ba? Yanzu gashi sun had'u a matsayin surukai, zata shiga cikinsu a yanda lokaci yake nunawa, shin wace irin rayuwa zatayi a cikinsu idan ta je? A hankali ta nisa tare da sauke numfashi a zuciyarta tace "Abdul Waheed ka zama mai hak'uri da manta baya kaji, dan Allah ka manta da komai ka yafe min." Motsin da taji yasa ta d'aga kanta ta kalli Abba da mama dake fitowaa daga d'aki, tsaye Abba yayi a kan ta tare da mik'a mata kud'i masu yawa yace "Ki tashi kije yanzu ki kai d'inkin kayanki." Hannu biyu tasa ta karb'a tana fad'in "Abba nagode." Cikin had'e fuska yace "Ke dakata ba godiya ba, minti talatin na baki ki je ki dawo, kuma ga k'aninki nan Yaseen kuje tare." Juyawa yayi ya kalli Yaseen yace "Kai kuma kaji da kyau, wallahi karka yarda ta baka tsoro ko ta zare maka ido tayi wani wajen, umarnina ne wannan dan haka kar ka bari ta firgita ka, ka tabbatar ka saka k'afarka a duk inda ta saka ta ta k'afar, ka ji da kyau?" Jinjina kai yayi yace "Eh Abba." Wani irin babbakewa taji zuciyarta na yi na rad'ad'i da zafin rasa yardar iyayenta, shikenan ta b'arar da kimarta a wajensu, sun daina yarda da ita kenan har abada? Mik'ewa tayi tana sakin murmushin da mai ido 'a gani zaka san kuka ne take dannewa, a kwana uku kawai idonta har sunyi fari fat, fuskarta kanta ta canza kamar ba Mimi sarauniyar adon nan ba. D'aki ta shiga ta d'auko wanda zata fara dasu ta fito, jiki a sanyaye suka kama hanya ita da Yaseen suka fita, Abba ma fita yayi zuwa masallaci dan lokacin sallah isha'i ya matso. Hawayen da take tafe tana sharewa ya saka Yaseen kallonta yace "Mimi ki daina kuka kinji, Abba zai yafe miki kawai yayi hushi ne." Saida ta sake share hawaye ta ja majina tace "Na sani Yaseen, amma dole nayi kuka saboda yanda nake ji a zuciyata, ka duba kaga yanda su Abba suka sauya min gaba d'aya." Matsawa yayi kusanta sosai ya d'aga kai yana kallonta yace "Kiyi hak'uri kinji, bana son ganin kina kuka, kuma jiya da yaya Asas ya zo yace na fad'a mishi idan baki daina kuka ba." Share hawaye ta sake yi tace "Shikenan na daina, karka fad'a masa kaji." Da haka suka isa bakin titi ta samu taxi, duk da ba nesa bane sosai amma lokacin da Abba ya bata ba zai isheta ta tafi a k'afa ta dawo ba tare data sab'a ba, suna zuwa ana ta sallah isha'i a masalatai, cikin sanayya sosai suka gaisa da mai d'inkin har yana fad'in "Mimi manyan duniya kwana biyu ina aka shige? Nasan dai ba kya wata d'aya baki yi sabon d'inki ba, amma wannan karan naga har an share wata d'aya na biyu ya ci rabi, sai na fara tunanin ko aure kikayi." D'an murmushin yak'e tayi cikin muryarta mai kama da wacce tayi mura tace "Banyi aure ba amma dai na kusa, dan yanzu ma kayan bikina na kawo maka." Dariya yayi yace "Haba ko da na ce, ni kam wannan wane babban yaro ne haka Mimi? Wai kinsan da ranarki ta k'arshe a shagon nan kina fita wani Alhaji ya shigo yana tambayar wacece ke." Cikin son kawar da zancen tace "Allah sarki, gasu nan kayan ina fatan dai zan samu a kan lokaci." Kallonta yayi da mamaki yace "Mimi lafiyarki kuwa? Ko an miki wanka da ruwan lalle ne? A sanina dake rik'e k'ugu kike yi ki nunani da yatsa ki ce idan ban gama kika dawo sai kin wareni na zama zakka a cikin zarma." Yar dariya tayi tana girgiza kai tace "Can ma ai k'uruciya ce." Girgiza kai yayi yace "Ban yarda ba." Yaseen ya kalla yace "K'ane na wanene mijin da zata aura?" Cikin murmushi Yaseen yace "Sunanshi Ashraf." Cikin zolaya yace "Amma dai ustaz ne ko?" Girgiza kai yayi yace "A'a, amma dai k'annin sheikh Abdul Waheed ne." Zaro ido yayi kamar zasu fad'i k'asa ya d'auki ledar data aje yana fad'in "Ahh! An gama, Mimi bar d'inkinki an wuce wurin kawai, yanzu zazzago min yan uwan nima na soka aljihu." Mimi dai banda murmushi babu abinda take yi, saida ya nuna mata sabbin d'inkuna a wayarshi ta zab'a kafin sukayi ciniki ta biyashi ta bar shagon da zuwan zata dawo nan da sati biyu kamar yanda ya mata alk'awari. Har ta tsaya dan tare taxi sai kuma Yaseen yace "Haba Mimi mu tafi k'asa dan Allah, ni bana son shiga taxi nan da can kawai." Kallonshi tayi tace "Ba zaka gaji ba?" Dariya yayi yace "Gajiyar me? Baki ga tare da Abba har sa茂 muje masallacin kaddafi sauraren wa'azin sheikh ba." Numfashi kawai ta sauke tare da rik'o hannunshi suka shiga duba titi dan su tsallaka, da k'yar suka tsallaka suka d'auki hanyar komawa gida, suna tafe suna hira dashi jefi jefi, yana so ya k'wace hannunshi dan shi dai ba yaro ba, duka shekara uku ce tsakaninsu dan kaf Mimi shekararta *goma sha bakwai* ne a duniya, hakan yasa wani abun idan tayi shi har da wauta a ciki da zallar haukar k'uruciya, sam k'in sakin hannunshi tayi har suka kusanto unguwarsu. Da gudun tsiya ya sha gabansu da motar ya ci birki, take gabanta ya shiga luguden daka dan in akwai wanda ta fi tsana ma a cikin tarikicenta to Muttak'a ne, tsaye tayi sunaa kallo ya fito yana washe mata baki, kallonta yayi ya kalli Yaseen, cike da rashin sanin darajar d'an adam da mahimmancinsu gareta yasa hannu ya shafi kan Yaseen yana fad'in "Kai me sunanka? Wannan kai haka?" Da k'arfi cikin jin zafi ta buge hannunshi ta nunashi da kakkauren yatsanta tace "Karka sake tab'ashi, wai ke me yake damunka ne?" "Sonki." Ya fad'a yana kallonta kafin yace "Ranar na zo gidanku ai muka had'e da babanki, bai fad'a miki sak'o na bane? Me yasa ina kiranki ba kya d'agawa." Wani wawan tsaki cikin takaicin rashin girmama mata iyaye tace "Ban yi mamaki ba, ni nasan dama wani jakin ne ya jaza min sababi a gidanmu." Tsaki tayi ta kama hannun Yaseen zata wuce ya sake tare gabanta yana fad'in "Ke ni ne jakin?" A harzuk'e tace "E kai d'in, an fad'a da abinda zakayi ne?" Wani sakaran murmushi yayi ya sha wani d'an iskan sajenshi yace "Ba komai yarinya, soyayya ta jawo haka, yanzu fad'a min me yasa wai ba kya d'aga wayata ne?" Kai tsaye tace "Saboda zanyi aure." A firgice ya waro idonshi a kan fuskarta yace "Me! Aure fa kika ce?" "Eh." Ta fad'a tana yatsina fuska tace "Ko da matsala ne?" Gyara tsayuwa yayi yace "Babba ma Mimi, kinga fad'a min gaskiya?" Gyara tsayuwa tayi ita ma tace "Wallahi gaskiya nake fad'a maka, yanzu haka ma daga kan d'inki nake na shigar biki na, aure zanyi da wanda ya dace dani." Girgiza kai yayi tare da sunkuyar da kanshi, ya d'an jima kafin ya d'ago ya kalleta ba alamar wasa yace "Mimi, na fad'a miki a baya cewa idan har ban sameki ba babu wani d'an iskan da zai sameki, wallahi wallahi Mimi idan na rasaki kowa ma saidai ya rasaki." Cikin rashin tsoro tace "Me zaka min? Kasheni? To bismillah kasheni Muttaka, idan ka min haka ni ka hutar dani dakon tunanin abinda ke neman lalata min rayuwata, amma ka sani hakk'i'a da alhakina zasu rataya a wuyanka ne." Sama da k'asa ta harareshi zata wuce ya rik'e hannunta gam, jujjuya hannun ta shiga yi tana son k'wacewa amma ya rik'e jim a hannunshi, had'e fuska ya sake yi sosai cikin dakakkiyar murya yace "Na rantse miki da Allah indai ina raye babu wanda zai sameki Mimi, ko dai ki aureni hankalinki ya kwanta, ko kuma ki ci gaba da shirye shiryen bikinki da wani amma fa tabbas ba za'a d'aura auren ba." Cikin tsiwa da haushin rik'e mata hannu tace "Insha'Allahu zaka ga d'aurin aurena da mutumin da bakayi zato ba, sunanshi kawai zaka ji ya jijjigaka dan ko kusa dashi ka tsaya sai kayi fitsari a wandonka, kallon fuskarshi kula yafi k'arfin idaniyar mashayi kamar ka, kusa dashi ma idan ka tsaya sai zuciyarka ta buga tsabar tsoro da kwarjinin *mijina*." Sakin hannunta yayi yace "Shikenan zaki gani kuwa, ba dai ni kika wa haka ba saboda nace ina sonki? Wallahi ko a haukace sai kin zauna dani, banza 'yar k'ananan mutane." Juyawa yayi a fusace Mimi kam takaicin an tab'o iyayenta yasa ta duk'awa ta kwashi tsakuwa ta watsa mishi cikin k'arajin murya tana fad'in "Kai ne banza d'an k'ananan mutane, mashayi da baisan ciwon kanshi ba, kai baka san miye soyayya ba ma bare har ka samu wacce zata so ka, banza alade kawai." Da matsiyacin mamaki ya juyo ya kalleta, takowa yayi a hassale yana zuwa ya d'aga sangamemen hannunshi ya kasheta da mari yana fad'in "Ni ne banza alade? Ni ne aladen? Bari na nuna miki abinda dabba irina take aikatawa." Yanda ta fad'i k'asa ne yasa shi yunk'urin fad'awa kan ta, cikin k'arfin hali Yaseen ya jawo rigar Muttak'a yayi baya dashi da k'arfin da Allah ya hore mishi, yana tangal tangal kamar zai fad'i ya kalli Yaseen, cikin zafin nama ya sake kawo mata hari, durk'usawa yayi duka gwiwoyinshi k'asa ya shiga kiciniyar rik'e hannayenta da take kai mishi duka dasu. Cike da jarumtar data samo asali a jinin yan uwantaka, cike da rashin tsoro da kuma yarda da cewa Allah ya bashi makaminshi Yaseen yayi kukan kura ya bugawa Muttak'a faffad'an kanshi. Yanda abun ya zo a bazata yasa Muttak'a jin wani gummmmmmm! Cikin kanshi, duk yanda ya so ya bud'e ido kasawa yayi saboda gaba d'aya kanshi kamar ba'a jikinshi yake ba, suna ganin ya fad'i kwance a wuri dafe da kai yana mirginawa Yaseen ya kama hannunta ta mik'e da sauri da gudu gudu suka barshi nan wurin, saida suka kai daf da gida ta kama hannunshi ta durk'usa tana sauke numfashi, kallon hannunta yayi dake ta rawa yace "Mimi ba zan fad'a musu ba, nasan abinda zaki rok'a kenan, amma kiyi k'ok'ari ki dakatar da rawar da jikin naki ke yi, zasu iya ganewa." Ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina kai, shafa kanshi tayi tace "Baka ji ciwo ba?" Girgiza kai yayi yace "Ai babu abinda na ji." Murmushi tayi tace "Lallai kaine magajin Abba, tunda gashi ka ceceni." Murmushi yayi shi ma yace "Kullum fa muka ji fad'anki a unguwar nan akan mu ne ko iyayenmu, ni ma zan tsaya miki babu abinda zai sameki." Murmushi tayi ta shafa fuskarshi tace "Nagode k'anena." Mik'ewa tayi suka shiga gidan da sallama, Abba na tsaye ya maida hannaye baya alamar su yake jira, ko sallamar babu wanda ya amsa Abba yace "Me ya tsaidaku har minti shida ya hau kai?" Kallon Yaseen tayi da yayi saurin cewa "Abba k'asa muka dawo, har zata tare mana taxi na ce mu taho k'asa." Harara ya dalla mishi hakan yasa Mimi durk'usawa tace "Wallahi Ab..." Hannu ya d'aga mata yace "Dakata, bana buk'atar rantsuwarki." Hanyar fita ya nufa yana fad'in "Gobe ku k'ara." Suna ganin fitarshi Mimi ta mik'e ta shiga d'aki ta cire hijabinta ta d'an kwanta a kan gado ta shiga dawo da had'uwarsu da Muttaka baya, tsoro ne fal taji ya cika mata zuciya da tunanin abinda zai iya yi mata, d'an k'waya kam tasan zaiyi abinda ya fad'a, saidai me zaiyi? Kasheta zaiyi ko fyad'e zai mata? Idan kisan ne ta wace hanya zai kasheta? Idan fyaden ne wani iri zai mata? Da wannan firgitaccen tunanin har bacci ya d'auketa a kan gadon. 馃グ *Comment masha'Allah, shiyasa kuka sameni dayawa.*馃グ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:55 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *22* Saida ta wayi gari ne ta lura da illar da marin Muttak'a ta haifar mata, dan fuskarta kumbura tayi ga kuma shatin yatsunsu kwance a kai, haka tayi ta fama da hijabi har ta shiga wanka ta fito ta shirya a sauk'ak'e, Mama kam dama tun jiya da tayi baccin ta fahimta shiru ne ta mata, Abba kuma da safen daya gani sai hankalinshi ya tashi sosai, amma bai nuna ba saida ya fita daga gidan sai kuma ya lek'o ya kira Yaseen, da ladabi ya amsa mishi yayi tsaye yana jiran yaji me zai ce, cikin magiya ya kama hannunshi yace "Yaseen, kaga dai jiya tare kuka fita da uwata ko? Kuma kaga ina tafiya da ku wurin karatun malam, kuna jin yana yawan fad'a k'arya ba kyau, sannan kaga k'aryar da uwata ta mana ne ya sa mukayi hushi da ita, indai baka so kai ma nayi hushi da kai to ka fad'a min abinda ya faru bayan fitarku jiya?" Tsatsareshi yayi da ido yana tunanin me zai fad'a, baya so dai wani wulak'ancin ya sake biyowa baya akan yar uwarshi, dan haka ya gyara tsayuwa yace "Abba, ai tare muka tafi ko? To wani ne muka had'u dashi bamu san shi ba, saiya tsaidata zai mata magana, amma kuma sai yake tab'a kaina yana min izgilanci, shine ta ji haushi ta buge hannunshi a kaina ta ce mishi jaki, shi kuma yace mata banza yar wadanni, shi ne ta sake ce mishi banza alade sai yaji haushi sosai ya mareta." Sakin hannunshi Abba yayi yana binshi da kallo yace "Ka tabbatar?" Jinjina kai yayi yace "Eh Abba." Jinjina kai yayi tare da shigowa cikin gidan Yaseen ya biyo bayanshi, Mimi zata shiga d'aki kenan taji yace "Ke uwata." Tsayawa tayi tare da durk'usawa tana kallonshi gabanta na fad'uwa, cikin fad'a yace "A garin nan da ma kewayenshi, duk uban da ya sake cin zarafinki a kan wulak'anta miki iyayenki to ni ki fad'a min, ba a iya k'asar nan ba wallahi zan iya tsayawa da mutum a kowace kotun shari'a." Juyawa yayi zai fita mama tace "Lafiya malam? Wani abu ne ya faru kuma?" A hassale ya juyo yace "Maganar banza, ya za'a mayar min da yarinya kamar wata mahaukaciya ko marar gata, ko wane tsinannen albarka da baisan darajar mutum ba sai ya dinga tsokanar hallitarmu a gabanta, idan tayi magana har a dinga tab'a min lafiyar yarinya, to na daina hak'ura daga yau, duk wanda yake son mu zauna lafiya a shirye nake, wanda ke buk'atar daru ma a shirye nake da shi." Juyawa yayi ya fita a gidan Mama na kallon Yaseen tace "Me akayi?" Maimaita mata abinda ya fad'awa Abba yayi, hakan ya sata satar kallon Mimi dake kallonshi da mamakin lauyar da yayi, saidai kuma tana farin ciki akan abonda Abba ya fad'a, ko ba komai ya nuna zai hak'ura nan gaba kad'an. *Asas* A gaggauce yake shiri yana kallon wayarshi dake kan gado, sosai hoton da aka had'a shi da ita ya birgeshi, dama an ce lamarin duniya baya b'uya, yayi mamakin ta inda hoton ya fito har aka had'ashi da ita da kayan lefenta, sosai yaga dacewarshi da ita sunyi machtin sosai, agogo ya d'auka zai d'aura sai kuma yaji cikinshi ya tsamuka mishi kamar yanda ya saba mishi, da sauri ya aje agogon tare da zaunawa bakin gadon ya rik'e ciki yana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Shiru yyi jin kamar da sauk'i, sai kuma ya sake murd'a mishi da tsananin azaba, a tare ya durk'ushe k'asa yana neman yin sujada yana wash wash cikinshi, da iya k'arfinshi yake k'wala kiran sunan Hajia amma tayi nisa, b'angarenshi zuwa nata da yar tazara kam, murk'ususu ya dinga yi a d'akin baccin nashi ga masifar gumin da yake idonshi har sunyi jajir. Hannu ya kai yana son ya d'auki wayarshi yayi kira amma ya kasa lalabota akan gadon, a hankali jikinshi ya fara yin sanyi ya fara lumshe ido yana cije leb'enshi, numfashinsji na yin sama da k'yar kamar zai suma ko ya mutu, a daidai lokacin Sadeeq ya sallamo d'akin na shi yana fad'in "Asas zan maka iskanci fa wallahi, kai kasan sauri nake muna da wurin zuwa, ya zaka..." Da sauri ya k'araso ya durk'ushe yana kiran "Asas, lafiya? Me ya sameka?" Da k'yar Asas ya d'an mirgina yayi kwance a k'asa yana sake matse cikinshi, da sauri ya tallabeshi suka mik'e yana fad'in "Muje asibiti, cikin ne ko?" Durk'ushewa ya sakeyi yana fad'in "B芒...ba zan." Bai iya magana ba sai komawa da yayi ya kwanta a k'asa, da sauri Sadeeq ya fita yana hango mai gadi ya k'wala masa kira, da sauri ya taho suka koma d'akin, tare suka tallaboshi suka fita dashi, saida ya suka sakashi mota ya kalli mai gadi yace "Ka kira Hajia sai mu tafi tare." Da gudu ya juya yayi b'angarenta yana ta sallalami, jim kad'an kam sai gashi tare da Hajia har ta fara kuka da Salamatu a bayanta tana bar mata sallahun ta kula da yaran idan sun dawo daga makaranta gyalenta a hannu, baya ta zauna inda Asas yake suka bar gidan zuwa asibiti. Da isarsu aka karb'eshi kuma kamar kullum taimakon da yake kwantar masa da ciwon aka fara basho kafin a k'ara masa ruwa ya samu nauyayyen bacci. Lokacin kad'ai Hajia ta samu damar kiran sheikh ta fad'a masa halin da ake ciki, a sanyaye ya shiga fad'in "Hajia insha'Allah Asas ya kuma samun sauk'i, yanzu haka ina neman k'wararran likita a nan da zai iya bamu randez vous na had'uwa dashi sai na zo da Asas ko da kuwa hakan na nufin a d'aga bikinshi ne." Cikin muryar kuka tace "Sheikh ko dai za'a dakatar da bikin nan ne? Gaskiya hankalina yafi karkata kan lafiyarshi, idan ba damuwa a barshi ya samu lafiya mana." A tsanake yace "A'a Hajia, a kullum Asas yana fad'in yana ji a jikinshi aurenshi shi ne silar warkewarshi, watak'ila Allah ya nuna mishi ne a ilhama, muyi k'ok'ari muga an gama bikin nan lafiya, ko da anyi auren ne zai iya tafiya ai." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Shikenan sheikh yanda ka ce, Allah ya bashi lafiya." "Ameen Hajiarmu." Ya fad'a a tausashe kafin ya d'ora da "Zan sake kira anjima." "To shikenan, sai anjima." Suka datse kiran a haka suna mai mishi fatan samun lafiya. *Washe gari* Ko da Abba ya shigo da yamma yake fad'a ma mama ya samu labarin Asas na kwance asibiti har lokacin, dan haka yayi alwala zai fita sallah magriba daga nan yaje ya ganshi, har yana fad'in "Ba dan uwata ta zama wata kala ba ai ita ma ya ci taje ta dubashi, amma ba komai zan wakilceta." Murmushi mama tayi tace "A gaidashi da jiki, Allah ya bashi lafiya." "Ameen." Ya fad'a yana fita daga gidan, Mimi na d'aki tana jin komai dake wakana, saida taji kamar ta nemi alfarmar taje ta ganshi, dan kwanan baya ya fara labarta mata ciwon nan dake sakashi suma idan ya taso, amma babu halin zuwa ganinshi da kanta dan haka ta bishi da addu'ar samun sauk'i. *Asibiti* Cikin dattako yayi sallama da muryarshi da bata da maraba data yara, duk zubawa k'ofar ido sukayi dan ganin me shigowa, da sauri k'anin Hajia wanda shi yasan kowanene dan tare suka nemo auren Mimi ya mik'e da fara'a yana fad'in "Kai malam Adam, kai ne tafe?" Cike da murnan yanda ya karb'eshi ya bashi hannu sukayi musabiha yana fad'in "Ni ne, anwuni lafiya." "Lafiya lau, bismillah zauna." Ya fad'a yana nuna masa kujerar daya mik'e, d'an zaunawa yayi yana kallon Asas dake bacci da k'arin ruwa, a hankali kuma ya kalli Hajia dake binshi da kallo yace "Ina wuni." Kafin tayi magana k'aninta yace "Maryama ai shine surukin Ashraf, mahaifin yarinyar nan takwararki." Da k'yar ta k'ak'aro mirmushi a fuskarta tace "Ayyah! Ina wuni? An zo lafiya?" Murmushi yayi shi ma yace "Lafiya lau, ya mai jikin?" "Jiki da sauk'i, angode ma Allah." Sake kallon Asas yayi yace "Allah k'ara afuwa." Sai lokacin Aisha dake zaune sun kawo abinci tare da dreba tace "Ina wuni Abba." Da fara'a ya kalleta yace "Lafiya lau yarinya, kina lafiya?" "Lafiya lau." Ta fad'a cike da alhinin halin da kawunta yake ciki, k'anin Hajia ne yayi murmushi yace "Jika ce ga ita Maryama, 'yar sheikh ce ta fari, sunanta Aisha." Fad'ad'a fara'arshi yayi yace "To to masha'Allah, ah abu yayi kyau." Kallon Aisha yayi yace "Allah ya shi albarka, malam d'in ma kwana biyu na ji shiru ko ba'a gari?" Da murmushi Hajia tace "Baya nan ai, sun tafi Paris amma sun kusa dawowa insha'Allah." "Allah sarki, Allah ya kawosu lafiya." Ya fad'a da fara'a, jim kad'an kuma saiya mik'e yana fad'in "Alhaji *Saleh* ni zan wuce, dama na samu labarin bai da lafiya ne na zo na gaisheshi, ita ma yarinyar da mahaifiyarta duk sun ce a gaisheshi da jiki." Cike da jin har ranta an kula da d'anta tayi murmushi tace "Har zaka koma? To angode Allah ya saka, a gaishesu da kyau." Saleh kuma hannu ya bashi suka sake musabaha yana fad'in "Idan ya farka za'a sanar mishi." Saida ya rakashi har k'ofar fita kafin ya dawo, hakan y'a ma Abba dad'i sosai da bai ga k'yama ko izgilanci a tare da Hajia ba, hakan ba k'aramin kwanciyar hankali ya haifar masa ba. Ita ma kanta Hajia wannan dubiya da kuma ganin shi ya tabbatar mata dattijo ne na arziki ba tsoho ba, dan haka sai taji wani shauk'in auren Asas da Mimi tare da fatan tabbatar lafiyar da yake ikrarin zai samu idan yayi aure. *A gurguje* Tuni jikinshi yayi sauk'i har ma sun ci gaba da shirye shirye, komai yana tafiya musu daidai dan komai a walale yake, sheikh ma sun gama hutunsu sun dawo, saidai a ranar da suka shigo a daren kuma ya d'auki hanyar Maradi sakammakon wa'azi na k'asa da k'asa da ake yi duk shekara, hakan yasa Hafsat mayar da hankalinta ita ma kan bikin. Mimi kam bata ji dad'i ko kad'an, ana sabgar bikinta amma babu k'awarta kuma aminiyarta Asma'u, daga Jamila sai su Salma kawai ke yawan shige da fice, hakan yasa ma yanzu haka daya rage sati d'aya Sahura ta zo gidan kawowa Mama sabuwar katifar data siya ta kalli Sahura kamar zatayi kuka tace "Aunty Dan Allah idan kika koma gida ki turo min Zeinaba, ina so ta zauna a nan har a gama bikin nan." Da mamaki Sahura ta kalleta tace "Zeinaba kuma? Ke kuwa Mimi me zata zo tayi a cikin 'yan mata kamarku?" Tsuke fuska tayi tace "Aunty ni dai dan Allah ki turo min ita, idan ba haka ba wallahi zan fasa auren ma." Zaro ido tayi tace "Fasa aure saboda ban turo ta ba Mimi?" Cikin shagwab'a tace "Eh mana, aunty ki duba fa ki gani dan Allah duk yan uwana babu wanda ya zo inda nake, bansan me yasa suke min haka ba, har gayyatarsu nayi amma da sun zo zasu dinga yin baya baya." Ajiyar zuciya Sahuta ta sauke tace "Maganar gaskiya Mimi abinda yasa kika ga suna ja baya saboda kinga ke da k'awayenki duk dogaye ne, yan uwanki kuma tsaranki duk kusan hallitarsu irin ta mu ce, sannan k'awayenki duk wayayyi ne yan boko, shiyasa suke ja baya a lamarin." Kamar zata fashe da kuka tace "Yanzu aunty saboda hallitarsu sai su k'i zuwa inda nake, ni fa tun farko ban b'oye ma Asas daga ina na fito ba, sannan danginshi ma sun san komai dan haka dole zasu ga mutane kala biyu, aunty Sahura, wallahi na rantse da Allah zan iya fasa auren nan idan aka ci min mutumcin yan uwa." Mik'ewa tayi zata shiga d'aki tace "Kuma a turo min yan uwana, ina so na gansu kewaye dani suna kai da kawo a sabgar bikina, dan ni abun kunya ne ma gareni ace ba'a ga gajera ba a cikin yan mata, ni yar halak ce kuma ba butulu ba." Da kallo kawai suka bita har ta shige d'akin, murmushi Sahura tayi tace "Mimi kenan, ita dai ba ruwanta da k'yamar mutane." Tab'e baki mama tayi ba tace komai ba, haka suka ci gaba da tattaunawarsu kafin Sahura ta bar gidan. Saida tayi sallah magriba ta shirya tare da Yaseen zasu tafi karb'an d'inki, a k'ofar fita suka had'e da Maimuna ta shigo gidan, gaisawa sukayi sosai kafin ta shiga ciki dan tunda aurenta ya matso take zuwa suna yan shawarwari da Mama, fita sukayi ita kuma a daidai k'ofar suka had'e da Asma'u, cak duk suka tsaya suna kallon juna, tunda abun nan ya faru ko sautin muryar juna basu ji ba bare ganin juna, cike da murna Mimi ta fashe da kuka ta ruga a guje ta fad'a jikin Asma'u, ita ma kukan ta saka tana k'ara rumgumeta. Cike da k'aunar juna Mimi ke fad'in "Asma'u me yasa zaki bari su rabamu? Kinsan yanda nayi kewarki kuwa? Babu masifa babu fad'anki bare nusar dani daidai da ba daidai ba." D'agowa tayi tana sake fad'in "Bikina sati d'aya ya rage, amma Asma'u ko ki lek'o ki ganni kin shareni kawai." Cikin kuka ta shiga girgiza kai tana fad'in "Ba shareki nayi ba Mimi, Abbana ne ya hanani shiga gidanku, ya ce ko bisa hanya bai yarda na kulaki ba." Jinjina kai tayi tace "Na sani Asma'u, dan nima na zo gidan ya hanani shiga na ganki." Hannunta ta kamo jim ta jimk'e tana fad'in "Dan Allah Asma'u ki zo ayi hidimar bikina dake, idan baki zo ba ko an d'aura auren ba zan yarda a kaini gidan ba." D'an murmushi tayi tace "Na miki alk'awari Mimi ko da satar hanya ne na zo gidanku." Da sauri tace "A'a! Banda satar hanyar Asma'u, ba zan so ki jefa kanki a halin dana jefa kaina ba, a dalilin abubuwan dana aikata har yanzu gidanmu bana sakewa, iyayena sun daina sakin jikinsu dani kamar bak'i muke, duk yanda na motsa sai mama ta kalli kalar motsin da nayi, idan na sauke numfashi saita kula da wane iri ne na sauke, uwa uba ace na fita waje, tsaf take cajeni taga miye a jikina." Wani murmushi mai kama da kuka tayi tace "Ranar ma tsaf tasa na kwab'e kayana ta dubani saboda kawai Asas ya zo da daddare munyi hira ya tafi." Fashewa tayi da kuka mai cin rai, share mata hawayen Asma'u ta shiga yi tana fad'in "Kiyi hak'uri ki daina kuka dan Allah, komai zai wuce kinji daina kuka, kinga ynzu..." Cak ta tsaya saboda jin Abbanta ya fito daga gida yana fad'in "Asma'u." Da sauri suka kalleshi suna rarraba ido, a tsawace ya kauce daga bakin k'ofar yana fad'in "Maza shiga ciki, ban hanaki tsayawa da ita ba." Da sauri Asma'u ta taka zata shiga Mimi ta rik'e hijabinta gam, takawa tayi saida taje gabanshi ta durk'usa, kamar zata rik'e k'afarshi tana kuka tace "Abba dan Allah na rok'eka ka taimaka ka bar Asma'u ta halarci bikina, Abba ban da wata k'awa sama da ita, ita ce aminiyata da ita nayi wasar k'asana, ita ce take da zarrar fad'a min gaskiya gaba da gaba ba tare da tsoro ko shakku ba, bani da wacce take so na sama da ita a duniyar nan a cikin mutanen da ba iyayena ba, dan Allah dan Annabi karka raba k'awance da ita dan ni ce mai k'aruwa da hakan, ita take d'orani a hanya take nuna min b芒 daidai ba. Wallahi ban tab'a k'ok'arin kama hannun Asma'u ba na kaita a hanyar da zata halaka ba, na maka alk'awari Abba Asma'u zata ci gaba da zama a kamilalliyarta har ka damk'ata a hannun mijin daya dace." Shiru tayi tana ci gaba da kuka ba tare data saki hijabin Asma'u ba, tabbas jikinsa yayi sanyi da abinda ta fad'a, hakan yasa ka shi jinjina kai yace "Shikenan tashi daina kukan?" Girgiza kai tayi tace "Ba zan tashi ba Abba har sai ka hak'ura." A hankali yace "Na hak'ura mana, tashi tsaye." Mik'ewa tayi tana kallonshi, d'orawa yayi da "Na amince ku ci gaba da shagulgulanku, amma ki cika min alkkawarin da kika d'auka, bana so wani abu marar kyau ya faru daku kinji." Jinjina kai tayi tace "Insha'Allah Abba, nagode sosai." Murmushi yayi yace "Ba komai, Allah ya muku albarka." Da Murmushi ita ma tace "Ameen Abba." Sakin Hijabin Asma'u tayi ta juya tana fad'in "Sai gobe, karb'o d'inki zamu je." Abban Asma'u ne yace "To ku tafi tare mana, ba ita ce babbar k'awa ba?" Wata dariyar data jima batayi bane ta kubce mata tace "Ita ce Abba, ita ce." Da zumud'i ta sake kama hannun Asma'u ita ma Asma'u tayi ram da hijabin Mimi suka shiga takawa da k'arfinsu kamar zasiyi gudu, a baya Yaseen ya bisu shi ma yana murmushin jin dad'in ganinsu tare. *Da safe* tana farkawa bakinta kawai ta wanke mama ta mik'a mata dahuwar tamtabarun data mata tun asuba, karb'a tayi ba musu dan duk wani abu da mama ke bata ko ci bata cewa, saidai ta mik'a mata kawai ita tasan yanda zatayi tasha ko ta ci, yanzun ma ba dan tana so ba take ci duk da dahuwar tayi, amma ba wasu isashin kaya aka saka ba, tana ci tana b'ata rai kamar za tayi amai. Tana ji su Zeinaba sukayi sallama, murmushi ta saki na jin yan uwanta sun zo inda take, tanna jin su suna gaisawa da Mama kafin tace "Ku wuce ciki ku aje kayanku." Da fara'a suka wuce suna sake sallama, amsawa tayi da farin ciki tana fad'in "Marasa mutumci kenan an taho?" Dariya duk sukayi suna aje kayan hannunsu, Zeinaba irin gajerun nan ne sun fi wada tsayi kuma basu da tsayi sosai (ba wada haushi), Rauda ma bata da laifi amma Zeinaba ta fita tsayi, gaisawa suka dinga yi sosai har Mimi na fadin "Yanzu da ban nemeku ba kenan ba zaku zo ba?" Dariya sukayi Zeinaba tace "Kin san me? Ni bana jin dad'in shiga cikin dogaye ne, sai na sak茅 zama 'yar duk'ul dani." Wani wawan tsaki taja tace "Dallah ni karku b'ata min rai, wai me yasa kuke hakane?" K'yaci tayi tare da ci gaba da abinda take, sama sama suka dinga hira har ta sake saukowa suka ci gaba da hira, suna haka Asma'u ma ta shigo, gaisawa sukayi kafin Asma'u tace "Kinga ba zama zanyi ba, siyan ankona zan tafi yanzu saina dawo." Kallon Zeinaba tayi dake sun san juna tace "Zeinaba muje ki rakani mana." Mik'ewa tayi tana fad'in "Nawa zaki biya to?" Dariya tayi tace "Karki damu, muje zan biya." Mimi ce ta kalli Asma'u tace "Asma'u dan Allah karb'i kud'i wajen Mama ki siyo min madara peak." Kallonta tayi tace "Me zakiyi da ita?" Kashe mata ido tayi tace "Ina ruwanki? Sirri ne." Dariya duk sukayi Asma'u tace "Wato kin raina gyaran Mama ko?" Murmushi tayi tace "Ni na fad'a miki haka? Kawai ina buk'atarta ne dan nasha." Girgiza kai Asma'u tayi tare da ficewa a d'akin ita da Zeinaba, tana jin sautin Asma'u sanda take tambayar Mama kud'in, da fari ta shiga zulumi na tunanin ba zata bayar b芒, amma da taji ta bata saita saki murmushi. *Masu comment nagode, wanda basa comment ma godiya nake*馃榿馃 *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:55 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *23* Sosai suke shan hirarsu ita da Rauda suna raharsu, Mama saidai ta shigo tayi wani abun ta fita tana jinsu, 09:05 Hafsat ta zo gidan tare da rakiyar Salamatu, yanda ta shigo da nutsuwa da sallama ya saka mama d'aga kai tana amsawa, masha'Allah ta fad'a a ranta saboda ganin Hafsat d'in, indai had'uwa, kyau, aji, kamala ake nema a gurin mace tabbas alamun Hafsat sun nuna mata hakan, gata jajir da ita gwanin sha'wa ta fito a bafulatanarta sak, ga bak'in hijab kuma dogon daya fito da doguwar fuskarta har k'asa. Mik'ewa Mama tayi tana fad'in "Lale maraba, sannunku da zuwa." Da fara'a da girmamawa tace "Yawwa sannu Mama." Da fara'a ita ma tace "Sannu, ina wuni?" "Ina wuni?" Ta fad'a a matuk'ar tausashe, saida mama ta d'auko kujera ta aje tace "Lafiya lau, anwuni lafiya?" A ladabce ta zauna tana sauke numfashi kafin tayi murmushi ta sake gaisheta da mutumtawa, ruwa ta kawo ta aje musu Hafsat kam saida tasha dan kar Mama ta ji ba dad'i duk da bata da k'ishin ruwa, shiru ne ya d'an biyo baya kafin Hafsat tace "Mama baki ganeni ba ko?" Da fara'a tace "Gaskiya kam ban shaidaku ba? Dan na fara tunanin ko b'atan kai kukayi." Dariya Hafsat tayi ta kalli Salamatu dake k'arewa gidan kallon tsaf har zuciyarta take jin haushin wannan zab'i na mai gjdan nata Asas, sam abun bai mata ba sai take ganin kamar wannan shi ne *kaska* rab'i mai jini, matsayinshi da dukiyarshi yafi k'arfin a ce yarinyar da zai aura kenan. D'an gyaran murya Hafsat tayi hakan yasa ta maido hankalinta gareta, da ido ta mata alama hakan yasa Salamatu aje ledojin hannunta gaban Mama tana fad'in "Wannan ai ita ce yayar Alhaji Asas, uwa d'aya uba d'aya suke." Da fad'ad'a fara'a sosai mama tace "Masha'Allah, ko ita ce Hafsat d'in da nake ji?" Da murmushi Hafsat tace "Ni ce mama." "Abu yayi kyau kam, ya su Hajiar suna lafiya?" Ta fad'a cike da kulawa, amsa mata sukayi kafin Hafsat tace "Mama dama sak'o na zo kawowa amarya, nasan kunsan babu wani shagali da za'ayi a bikin kamar yanda addini ya tsara, amma daga baya sai muka yi shawara duba da yanayin zamani da kuma ita kanta amaryar, shi ne ango yace za'ayi kamu kawai na amarya, amma fa shi ma ita da k'awayenta ban da shi da abokanshi, haka kuma kowa a dangi ma ga mai buk'ata zai iya halarta." Shiru mama tayi tana saurarenta tana jinjina kai, saida ta kammala kafin tace "Wannan ai ba wata matsala bace, duba da kwana nawa ya rage Mimi ta shiga a k'ark'ashin ikonku? Ko yanzu kaso mafi girma yana hannunku ai, dan haka ba wata matsala wallahi, saidai idan mahaifinta ya dawo shi ma zan sanar dashi dan yasan abinda ake ciki." Cike da gamsuwa da maganganun Mama Hafsat tace "Masha'Allah, mun gode sosai Mama, wannan ba matsala bane dama." Ledar da Salamatu ta aje gaban mama ta nuna mata tace "Wannan kayan da amarya zata saka ne ango ya turo m没 dasu, insha'Allah ranar alhamis za'ayi kamun washe gari kuma d'aurin aurensu a babban masallacin juma'a." Cike da jin dad'i mama ta jinjina kai tace "Hakane, Allah ya nuna mana ya kai mu lokacin da alkairi." Cikin dariya Hafsat tace "Ina amaryar ne wai mama? Ko bata nan?" Cike da kunya mama tace "Tana ciki kam, ai kusan wata d'aya ma kenan ta daina fita, shiga ciki tana nan." Mik'ewa Hafsat tayi tana fad'in "Lallai mama kina kula mana da amaryarmu, Allah ya biyaki da aljanna, wannan sai mun bayar da tukuici ai." Dariya mama tayi tana amsa addu'arta a zuciya tana kallo har ta shiga d'aki, Salamatu kuma na zaune tana ta yatsina fuska tana wa mama wani gani-gani, mama kam har ga Allah bata ma kula ba bare ta sa wani abu a ranta taji ba dad'i ko kuma tunani. Mimi kam da suka kasa kunne tunda taji wacece ta d'auko hijabi ta labta ta haye gado tayi shiru, tana shigowa da sallama suka amsa mata da fara'a Mimi kuma na sinne kai k'asa, zaune tayi kusanta tana fad'in "Amaryarmu sannu? Ya hidima?" Da d'an murmushin jin kunya tace "Alhamdulillah." "Masha'Allah, yanzu ma na kawo kayanki ne na kamu ranar alhamis insha'Allah." Ta fad'a tana kallonta, k'ala ba tace ba sai ma sunkuyar da kai k'asa, cikin kulawa Hafsat ta sake fad'in "Gashi dai har kin kusa shigowa hannunmu baki sake zuwa gidana ba, na so ya kaiki ki wuni amma Allah bai nufa ba, dan zuwanki na ranar naga kuna sauri." Murmushi ta sake yi tace "Zan je." Dariya Hafsat tayi tace "Yaushe kuma amayar? Kwana biyu ana uku fa zaki shiga lalle, ai k'anena ba zai yarda ki fita ko ina ba." Cike da kunya ta sake sinne kai tace "Zan je insha'Allah." Dariya ta sake yi tace "Na yarda zaki je, amma fa bayan aure." Murmushi tayi sosai tana rufe fuska da hijabi, cike da jin dad'in ganin Mimi ta mik'e tana bud'e jakarta, enveloppe ta fito da ita ta aje kusa da Mimi tace "Wannan angonki ne yace na baki saboda ranar kamu zasu miki anfani." Juyawa tayi bata jira me zata ce ba ta fita tana fad'in "Sai anjima amaryarmu, sai ranar kamu insha'Allah." Da kallo Mimi ta bita kafin tayi saurin kallon enveloppe d'in, zaro ido tayi ta kalli Rauda dake ta murmushi tana saurarensu tace "Rauda na shiga uku, ta bani abu ta juya ta fita, ya zanyi da mama?" Jin su Hafsat na fita a gidan suna ban kwana yasa ta d'aukar enveloppe d'in tana fad'in "Shi ma fa na fad'a masa bana buk'atar komai daga gareshi, me yasa zai min..." Bata kai k'arshe ba mama ta d'aga labule ta d'auko kayan da aka kawo mata, cikin rashin gaskiya da tsarguwa da kuma sabawa da sabon halin Mama na cajeta yasa ta saurin sakin enveloppe d'in ta durk'ushe tare da fad'in "Na rantse da Allah mama bansan menene a ciki ba, ita kawai ta d'auka ta bani ban tambaya ba, kuma ga Rauda ki tambayeta zata fad'a miki." Girgiza kai Mama tayi ta zuro k'afarta d'aya ta aje ledar tace "Miye anfanin rashin gaskiya yanzu? Gashi abinda bai kai ya kawo ba ya firgita miki nutsuwarki, me yasa mimi kika dinga yi mana k'arya? Da kina ganin yanzu haka ta faru?" Girgiza kai tayi ta juya tana fad'in "Ko me suka baki a yanzu indai ba rok'onsu kikayi ba su suka ji suka gani zasu iya." Tana ganin ficewar Mama ta share yar guntuwar k'wallarta ta d'auki enveloppe d'in ta zauna bakin gado ta bud'e, wani irin fad'uwa gabanta yayi sakamakon ganin kud'i ne sababi far dasu yan jaka jaka, mayarwa tayi ta aje ta kalli Rauda tana fad'in "Nufinshi nayi lik'i da kud'in nan?" Wani murmushi tayi kawai ta girgiza kanta ta gyara kwanciyarta akan gadon ta shiga neman bacci. *05:30* Su Salma na fita a gidan sakamakon k'aratowar magriba yasa ta d'aukar madararta a kofi data b'oye k'ark'ashin gado had'e da yar zuma a ciki da karanfani da dabino data saka Asma'u mata a gida ta kawo mata, da sauri ta kifa kai ta shanye abinta, dan a gaskiya ranar taji su Sahura na fad'in har yanzu fa maganin zahi da kuma na sanyi (infection) ne aka mata, sai shi dai na zafi yanzu haka idan tasha tana jin yana saukar mata da d'umi a jikinta har ya saka ta kama ruwa. Yanzu ma da su Zeinaba zasu fita maltina ta basu su siyo mata amma tace su b'oye kar Mama ta gani (ba'a daddara ba kenan uwata?馃槬). Asma'u na shigowa da sauri taa fad'a d'akin hankali tashe, cikin rad'a ta shiga fad'awa Mimi "Ke yanzu na ga Muttak'a a k'ofar gidan nan, ya ce wai na kiraki na fad'a masa an hanaki fita saboda aurenki ya matso, ke kinga tashin hankalin?" Gyara zama tayi tace "Wallahi rantsuwa ya mana wai ba zaki auri wani ba shi ba, tunda har kika wulak'antashi kika yaudareshi to zaki gani." "Zan ga alheri." Ta fad'a tana mik'ewa dan shiga wanka, cikin nuna damuwa Asma'u ta mik'e ita ma tace "Mimi bana son matsala fa, mutumin nan tunda ba hankaline dashi ba me zai hana ba zaki fad'awa Asas ba? Watak'ila ya mana maganinshi." Kallonta tayi tace "Na ce masa me? Saurayi na ne dana ci kud'insa kamar hauka shine ya ke min barazana kayi wani abu a kai?" Tab'e baki tayi ta d'auki hijabi zata saka ta fita Asma'u tace "To ya kike so a yai? A barshi har sai wani abu ya faru marar kyau? Sannan mu sake shiga damuwa da tashin hankali." Dafa kafad'arta tayi tace "Ba abinda zai faru Asma'u, kwantar da hankalinki." Ture hannunta tayi tace "Kwantar da hankalin banza, wai me yasa kika cika taurin kai ne Mimi? Haka a baya kike fad'a min kwantar da hankali babu abinda zai faru, da nayi shiru kamar yanda kike buk'ata miye bai faru ba?" Tsaki tayi tace "Kinga idan wani abu ya faru wallahi babu ruwana ni dai, na fad'a miki d'an giyane mutumin nan kuma yana mana rantse rantse da cin alhwashi." Gyara tsayuwa tayi tace "D'an giya miye baya fad'a? Rantsuwa ko ruwa zai sha sai yayi rantsuwa da alhwashin shan su alhalin gasu sa gabanshi, dan haka ba zan saka matsalarshi a kai na ba." Jinjina kai Asma'u tayi cike da jin haushi ta fita tana fad'in "Ke kika sani ai." Ganin yanda ta fita ya tabbatar mata sunyi fad'a kenan ba zasu shirya ba sai kuma gobe, girgiza kai tayi tana murmushi a ranta take ayyana irin k'aunar da Asma'u ke mata, indai zasuyi fad'a to akan wani abu da Mimi tayi ba daidai bane musamman mai barazanar cutar da ita game da lafiyarta ko kuma zai shafi mutumcinta. *Sheikh* Dake a jirgi suka shigo hakan yasa suka zo bayan magriba, tunda yasan yau asabar yasan a lokacin Hafsat tana cikin gidan a b'angaren karatu tare da matan da suke karatun dare, kai tsaye b'angarenshi ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya ya nufi masallaci, saida sukayi sallah isha'i sukayi karatunsu kafin duk da gajiya kam kafin suka tashi k'arfe tara. Yana shigowa gidan a falo ya sameta tare da Aisha da wata budurwa mai d'inkinsu, gaisheshi tayi da ladabi ya amsa haka ma Aisha kafin ya wuce ciki, mik'ewa tayi a sanyaye ta kalli Aisha tace "Ki duba kayan kiga idan sunyi sai ki bata kud'in, idan akwai wanda bai yi ba saiki bata ta koma dashi a gyara." Kallon budurwar tayi tace "Dan na sanki da shiririta wani lokacin." Dariya tayi tace "Insha'Allahu ma anti daidai wannan Mamar Aisha." "Allah yasa." Ta fad'a tana murmushi ta shige falon yallab'ai, a tausashe a sanyaye ta furta "Assalama alaika sheikh na wa." Tsura mata ido yayi har ta k'araso sannan yace "Wa'alaiki salam *Manga* ta wa." Murmushi tayi tare da zama kusanshi tace "Sannu da zuwa uban gidana, an zo lafiya?" Saida ya d'ora hannu a cikinta yana shafawa yace "Yawwa sannu abokiyata, na sameku lafiya?" Da fara'a ta amsa da "Lafiya lau muke, ya k'ok'ari?" Murmushi yayi yace "K'ok'ari muna ta fama da taimakawarku." Murmushi tayi tace "To yanzu me ye abunyi? Nasan dai mijina sarkin tsafta ne bare nayi tunanin baiyi wanka ba, yanzu abinci zaka ci ko kuma karatu zamu shiga?" Gyara zama yayi yana kallonta yace "Sanin matata sarauniyar tsafta ce yasa na fara wanka kafin ta sakani dole, abinci kawai za'a taimaka min dashi yanzu dan yunwa nake ji, amma kafin nan a amsa min tambayoyi na." D'an bud'a idonta tayi sosai tace "To fa! Wane tambayoyi kuma?" Hannunta ya kamo ya rik'e yace "Hafsy na, yanzu kina ji kina gani da had'in bakinki da yardarki da kuma tallafawarki su Asas zasuyi wani abu wai kamu? Miye ma kamun nan ne? Shin bidi'a ce ko sunna? Me ake yi a wurin? Maza da mata ake tarawa ayi rawa a ci a sha a fita tsirara? Mi ye ma anfanin yin shi kamun?" Wata ajiyar zuciya ta sauke tace "Da fari dai ba sunna bace zamu iya cewa bidi'a ce tunda al'ada ce aka rik'e gam, na biyu kuma ana tara maza da mata amma wannan iya zallar mata ne insha'Allah, abu na gaba kuma ba zamu saka kid'a ba bare har ta kai ga rawar ma, dan mu ba iyata mukayi ba." Ta k'arashe tana k'yalk'yalewa da dariya, shi ma yar dariyar yayi yace "Yanzu kenan a matsayinki na ustaza kin bada goyon baya d'ari bisa d'ari akan al'ada marar tushe?" Marairaicewa tayi tace "Dan Allah ayi hak'uri a barmu, kaga fa har na kai wa amarya kayanta da zata saka a ranar, insha'Allah babu abinda zamuyi da ya sab'a k'aida." Zura mata ido yayi sakamakon fad'uwar da gabanshi yayi sanda ta ambaci amarya, Ryam! Lallai yarinyar ta koya mishi darasi na rayuwa akan karatun mata, hakan ya cire mishi sha'awar k'ara aure gaba d'aya, ita ce ma dai yake ta koyon yanda zai yakiceta a zuciyarshi, ma wani ikon Allah sai ma k'ara samun muhalli take tana zama, babban tashin hankalin shi ne ko waje ya fita aka kirashi da sunan sheikh ko wani suna na ladabi da girmamawa saiya tuna wacce ta iya kallonshi ta ce Abdul, wasu lokuta sai ya ji kamar ya biya kud'i ayi zaune gabanshi ayi ta kiranshi da Abdul, saidai tasirin ba d'aya bane ko kad'an, gashi lokaci na sake kusantata da d'an uwanshi da zasu zama abokan rayuwa mata da miji, shi kuma zuciyarshi na sake daffaruwa da tunaninta. Jinjina kai kawai yayi bai ce mata komai ba, hakan ya sata mik'ewa tace "Godiya muke sheikh, bari na kawo maka abinci a nan." Yana kallo har ta fita a d'akin kafin ya gyara zamanshi yana sauke numfashi, cire babbar rigarshi yayi ya aje tare da hula ya shiga shafa kanshi yana lumshe ido yana tuna abinda ya faru a waccen ranar, abunda yafi tsaya mishi a rai shi ne da likitar tace zata je ta samu mahaifinta suyi magana, da sauri ya bud'a idonshi yaja wani dogon tsaki a zuciyarshi yake fad'in "Me yasa Ryam? Me yasa kika ballagazar da kanki haka? Baki san cewa mutumcinki shi ne darajarki ba? Me yasa kika zama mai arha haka? Kika wofantar da abu mafi daraja?" Wani tsakin ya kuma ja tare da sake muskutawa ya gyara zamanshi, yana haka Hafsat ta shigo da sallama da babban tire a hannunta d'auke da kwanuka masu kyau na alfarma sa茂 d'aukar ido suke. *Safiyar lahadi* Su hud'u suka gama shirinsu har da Asma'u da sukayi fad'a jiya amma an shirya da safe, suna zaune tsakar gidan k'aramar wayar Asma'u tayi kuka, d'auka tayi tana fad'in "Abokin ango barka." Daga b'angarenshi ya amsa da "Barka k'awar amarya, kun shirya ne?" "Mun shirya ai ku muke jira." Ta fad'a tana kallon Mimi, daga can ya amsa da "Da gaske? Ko kuma dai maganar yan matan amarya za'a mana." Cike da tabbaci tace "Da gaske mana, idan baka amince b芒 gwada cewa mu fito ka gani, sai mu tabbatar su waye yan matan amarya da abokan ango tsakaninmu." Dariya yayi yace "Da gaske? To ku fito mu gamu a k'ofar gida." Saida ta mik'e tsaye suma suka mik'e tace "Kuma ka yarda idan baku k'ofar gida ku zama yan amatan amarya?" Dariya yayi sosai yace "Anya Asma'u kina son gaskiya? Yanzu so kike ki rabu da abokin namu?" Ita ma murmushi tayi tace "Ina so ne dai na nuna muku mu ma jarumai ne zamu iya d'aukan duk wani caji da yan matan amarya zasu mana." Cikin d'aga sauti yace "Iyeeh! Lallai Naanah Asma'u kin iya azanci, amma dai kina da sha'awar siyasa ko? Ko kuma dai a gidanku akwai d'an siyasa." Dariya tayi sanda suka fito k'ofar gidan tace "Ko kad'an, wayo ne dana fara koya a wajenka." A lokacin shi ma ya karyo kwanar gidan yana fad'in "To gashi mun iso tare, yanzu kowa sai ya zauna a matsayinshi ko?" Shiru tayi ba tace komai ba har ya tsayar da motar, sauke glas yayi yana aje wayarshi yace "Sannunku." Duk amsa mishi sukayi banda Mimi dake lab'e bayan Asma'u tana sunkuyar da kai, murmushi yayi yace "Ina amaryar ta mu? Asma'u ya zaki b'oye mana ita haka?" Kama hannun Mimi tayi ta bud'e motar ta shiga haka ma su Rauda, har zata shiga Sadeeq yace "A'a ya haka? Ki dawo gaba mana, ko ba kya son hira dani ne?" Murmushi tayi tace "Ni dai ban fad'a ba." "Amma ai aikinki ya nuna haka." Ya fad'a yana kallonta tana zagayawa, bud'ewa tayi ta shiga ta zauna kafin ya tayar da motar, a hankali suke tafiya yana jansu da hira irinta yan matan amarya da abokin ango wacce duk rigima ce a cikinta su ja ya ja, da haka har suka isa salon d'in da Asas ya umarceshi ya kai su. Duk ajin Mimi da son k'aryarta saida ta ji ta raina kaita da suka shiga ciki, babban wuri ne katafare daya tsaru ya had'u, ga ma'aikata suna ta aikonsu ga manyan mata na shiga da fice. Mai saloon d'in ba musulma bace amma tana ganinsu dake tasan su Sadeeq da fara'a ta mik'e ta tarbesu, fita yayi ya barsu bayan ta tabbatar masa ya dawo bayan awa uku. Nan fa ta shiga yi wa Mimi aiki da kan ta su Asma'u kuma yaranta suka kama musu, gyaran kai aka fara musu da wankin k'afa da hannaye, Mimi kuma saida ta shafa mata wani had'i na gyaran fuska tare da rufe mata idonta da kokonbre, minti k'alilan suka rage Sadeeq ya dawo aka kammala musu, dan haka yana zuwa ya damk'a mata kud'i suka tafi suna godiya inda suka ji Sadeeq na fad'in sai jibi idan ya maido su kuma. Suna dawowa gida ta samu Iya Delu da mama suna hira ta 'ya da uwa, gaisheta duk sukayi sai Mimi da tace "Ni dai ba zan gaisheta ba dan ina daf da shiga gidanki a matsayin kishiyarki." Duka Iya ta kai mata tana fad'in "Ke kauce can ja'ira, naga inda zaki je d'in ai." Dariya sukayi suka shiga d'aki sai su Iya da suka ci gaba da hirarsu akan dangin malam da har yanzu babu wanda ya tako k'afarshi, malam da kan shi ya basu goro ya kuma fad'a musu, sannan jiya ma da kan shi ya sake komawa k'auye ya tunashesu lokacin, amma babu wata gamsassen amsa daga garesu kowa yayi gum da baki saboda su aurenshi da Iya ne basu so ba, abu kuma an ja shekaru gasu da 'ya'ya da jikoki amma a ce sun kasa fahimtar hakane Allah ya nufa. Dan haka jiya d'in yace ma Iya suyi hidimarsu kawai, tsirarun danginshi ba zasu hana yiwuwar wani abu ba, auren 'ya'yanshi ma aka yi shi ba dasu ba bare kuma jikanyarshi, dan haka za'ayi bikin Mimi kuma dama ba wata tsiya suke buk'ata daga garesu ba. *Yammacin litinin* Daga farfajiyar gidan take jin shewarsu suna shigowa, kallon Asma'u tayi tace "Su Salma ne fa da Ruky, nasan sun samo muku d'inkin." Da zumud'i Asma'u tace "Allah yasa." Suna shigo d'akin ya gauraye da hayaniyar yan matan suna murnar samun d'inkinsu na anko wanda zasu saka ranar kamu dana kan amarya, zaune Salma tayi kusan Mimi tana nuna mata hotunan wasu amare da fad'a mata sunan wanda suka musu kwalliya, a haka ta kawo wata amaryar da kwalliyarta tayi kyau sosai kamar inji (ingine) ya mata, da zumud'i Mimi tace "Wannan tayi kyau, wa ya mata?" Salma ce tace "Sara ce." Da sauri Zeinaba tace "Baa ita ce jiya Sadeeq ya kaimu salon d'inta ba?" Asma'u ce tace "Ita ce." Mimi ce tace "Gaskiya aikinta na kyau, dubi kiga hannayena data wanke min jiya sun k'ara wani d'an banzan laushi wallahi, kinji k'afafuna." Asma'u ma dariya tayi tace "Ai ni k'afata a hannuna ta kwana wallahi, dan sai nake jin kamar b'era zai iya gwaguye min k'afa." Dariya suka kwashe da ita inda Salma tace "To kinga tunda ma kun tab'a zuwa dan Allah ki ma Sadeeq magana ya sama mana rendez-vous a wurinta ranar alhamis ta mana kwalliya, akwai tsada fa amma nasan zata mana sauk'i ai." Asma'u ce tace "Yace fa sun san ta sosai tare sukayi karatu da ita a universit茅, kuma jiya daya kaimu yace Asas yace gobe ma a koma saboda gyaran amaryarshi." Dariya sukayi inda Salma ta bawa Ruky hannu suka kashe tana fad'in "Shegiya Mimi, ta fa d'auko mai zafi wallahi, gayenta ya had'u k'arshe, komai na kece raini ya ke mata." Yatsina fuska Mimi tayi tace "Ba kamar ke ba da zaki auri sa'an babanmu ba." Dariya akayi sa茂 Salma data had'e fuska tace "Mimi bana son wulak'anci wallahi, wai me yasa kike min hakane? Kinga fa sati uku ya rage aurena amma saboda kece na zo ina ta zirga zirgan aurenki." Murmushi tayi tace "To yi hak'uri na daina." Da haka yan matan suka ci gaba da shirye shiryen bikinsu inda kowace ta gwada doguwar rigarta da aka musu iri d'aya mai kyau da dogayen hannaye, saidai babu wacce rigarta ke da d'an kwali hakan na nufin dole su nemi wanda zasu d'aura. Sun jima a gidan suna hirarsu kala kala ta nishad'i da k'aruwarsu dan Mama ta fita tare da Sahura da Shapi'a, har bayan azahar kafin suka ci abinci da Rauda ta musu mai sauk'i kafin suka bar gidansu suka barta tare da yan uwanta suka ci gaba da farin cikinsu. *Indai da comment to da aiki tuk'uru insha'Allah.* *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:55 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *24* *Asubar talata* tana cikin bacci bata riga ta farka ba Mamar Asma'u data shigo gidan yanzu ta shafa mata lalle a kan ta da hannaye da tafin k'afa, zunbur ta tashi zaune tana kallonta tana mata dariya, ganin ta fita a d'akin sai kawai ta cire lallen na hannayenta ta shafawa fuskar Zeinaba dake baccinta, a firgice ta tashi tana fad'in "Waye? Mimi." Dariya ta kwashe da ita tare da mik'ewa ta fita a d'akin ta shiga ban d'aki da d'an kwalinta a kai. Safiya na yi Mama ta dinga aikinsu Yaseen suna raba alawa ta wankan amarya da yamma, Mimi kam banda fad'uwa da gabanta keyi duk jikinta ma yayi sanyi sosai, sai taji tana rasa karsashinta da zumud'inta da ma farin cikinta, misalin 08:00 Mimi dasu Rauda suka shirya suka shiga gidan Maimuna, anan k'awayenta suka dinga zuwa suna shan hirarsu da haka har aka samu wuni, dan kuwa saida la'asar tayi kad'ai aka kirasu suka shigo gidan, lokacin gidansu kuma ya cika da mutane yan uwa da yan unguwa an zo wankan amarya. Daga gurin angaye aka turo da motoci guda takwas dan kai su inda za'ayi wanka, kusan mutanen babu wanda bai je ba saboda wadatar motoci da aka samu, gidan yar uwar su mama dan waankan farko ana yin shi ne a dangin uwa. Gaba d'aya basu d'auki minti arba'in ba tafiyarsu da dawowarsu, Mimi kam ta jik'a tayi laushi sosai dan tasha wankan ruwan lalle masu d'auke da itatuwan da kakaninmu suka yarda cewa yin wanka dasu yana zubar da duk wata shiririta da shirme, yana k'ara maka hankali da nutsuwa, tun a mota take hawaye har suka zo gida bata daina ba, tunda ta shiga d'aki kuma k'awayenta duk suka watse zuwa nasu gidajen aka barta da su Zeinaba kad'ai. Alhamdulillah kam aure rahama ne kuma alkairi ne, a dalilin auren Mimi Abba da Mama sun samu gudumuwa sosai daga dangi da kuma abokan arziki, hatta da Alhaji Saminu ya aiko da gudummuwar buhun shinkafa da kuma kud'i har jaka hamsin, duk da dai baya bayar bane cikin dad'in rai, kawai yayi ne dan kar ace bai yi ba amma sosai ya ji zafin yanda Mimi ta banzatar da shi ko wayarshi bata tab'a d'agawa ba. Wasa wasa sai gashi lokaci na ta tahowa kamar almara. *Ranar kamu* Ko da k'arfe 08:00 ta buga suna salon ana ma su Asma'u kitso da k'unshi Mimi kuma saida aka fara mata gyaran jiki, ana idawa aka shiga zana mata k'unshi da jan lalle, mai salon d'in ce ta tsaya kan ta zata fara mata kitso k'anana, da sauri ta janye kanta tace "A'a, a'a bana so." Da mamaki tace "Ban gane ba kya so ba? Kina amarya?" Kamar zatayi kuka tace "Bana so ni dai, zafi ke akwai wallahi, bana son kitso." Kamar da wasa Mimi ta ko dage ba za'a mata kitso ba ita kuka zatayi, dole k'arshe ta k'yaleta amma suna ta mata nasiha ta gyara a matsayinta na mace, ita dai saurarensu take bata kula kowa ba. Da azahar su Salma suka zo suma sunyi lalle da kitson su tsaf, dan haka ko da 03:00 tayi na rana suka fara shiri dan dukansu da kayansu suka zo, mimi ma ana ida lallen aka mata siraci ta shiga wanka, tana fito a sauk'ak'e kuma a nutse aka fara mata gyaran kakkauran gashin girarta, kad'an aka rage mata shi hakan yasa yayi kyau sosai tuni fuskarta ta fito shar da ita dake gashin nata bak'i ne wulik, kayan da Hafsat ta kawo mata ranar ta fara sakawa. Doguwar riga ce abaya kalar ja mai duwatsu da kwalliya, tun ranar da aka kawo kayan Mimi bata duba su ba har Asma'u ta so bud'ewa ta hana, yanzu kam data saka sai suka saki baki suna kallonta, yanda rigarta ta zauna mata d'as a jiki ta mata kyau, ga tsarin rigar na ban mamaki wanda ya birgesu, wato idan sun fahimta komai a mutumce ne ya mata shi dan kar a sab'a k'aida, rigar zubin babbar riga aka mata na maza saidai a rufe take kirip har k'asa tana jan k'asa, gashi hula ce a bayanta irin na rigar sarauta alkyabba, sannan tana da kallabi ware daban wanda ake fara d'aurawa. Kwalliya aka mata mai kyau da sauk'i wacce zaka rantse abonda aka shafa mata a fuska dama a fuskar ta ta yake, ana gama salllah la'asar dukansu yan matan sun fito sun haska a cikin rigunansu kalar pink na kakkauran yadi mai taushi, inda dukansu aka d'aura musu d'an kwali kala d'aya wanda suka siya. Dogayen takalma k'afa ciki aka saka mata da jakarsu k'arama mai kyau da walk'iya, ga agogo data kama tsintsiyar hannunta dam ta zauna, kallabin abayar yanda aka d'aurashi daga ciki da kuma hular da aka d'ora mata sai ta fito sak gimbiyarta yar sarki jikar sarki. Yamma sosai motoci guda uku dukansu k'irar benz suka paka a k'ofar salon d'in, a hankalce kuma a tsare yan matan duka suka kewayeta suka shiga takawa har waje, suna fita Asas ya hangesu daga cikin motar, wani murmushi ya sub'uce masa tare da jin yana sha'awar ya tsokaneta kamar ita d'in *matar yayanshi ce*, a sanyaye ya bud'e motar ya fito tare da bud'e mazaunin da zata shiga ta zauna, duk tsaye sukayi a bayanta saida ta shiga ta zauna ya rufe ya kallesu yace "Nagode k'awaye da gyara min amaryata." Murmushi sukayi Salma tace "Mu ba k'awayenka bane, ga k'awarmu nan kana shirin rabamu da ita." Murmushi yayi yana tsaye yana kalli duk suka shiga motar, sai Asma'u data zagaya d'aya b'angaren da Mimi take ta shiga, a hankali suka bar wurin suka d'auki hanyar gidan saukar bak'i na sheikh Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif. Kecup! Suka ji k'arar waya tare da hasken daya d'auke idonsu, da sauri suka kalleshi sai kuma kunya ta kamata ta sunkuyar da kai, murmushi yayi yace "Maah kin ga yanda kika had'u? Har saida na ji gabana ya fad'i tsabar razana." A hankali ta d'ago matsakaitan idonta da suka sha eyeshadow a tausashe kamar mai rad'a tace "Me yasa gabanka ya fad'i?" Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Sadeeq yace "Saboda ganin kamar *matar manya* na d'auka, bana so na zama tururuwa uwar jaye-jaye." A sauk'ak'e ta kalleshi tace "Wannan maganar kamar dani kake, kar kasa na ji ba dad'i mana." Sunkuyar da kanta ta sake yi shi kuma ya kalli Sadeeq dake fad'in "Ba wannan ba ma abokina, na ga amaryar ta mu kamar jinin sarauta, dan Allah daga wace masauratar take?" Yar dariya tayi cikin sanyayyar murya tace "Ni ba yar masarauta bace, hasalima ko gidan sarauta ban tab'a shiga ba daidai da gaisuwa, idonku ne kawai suke yaudararku." Dariya sukayi sai Asma'u data rik'o hannunta tace "Mimi gaskiya ya fad'a, jininki da zubi na tsarin yanayinki kamar na wacce aka haifa a cikin masarauta ne." Murmushi Asas yayi yace "Kin gani, k'awarki ma haka take gani, amma ba komai karki damu, gaba kad'an zan mayar dake kamar sarauniya." Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta sosai, Asma'u ma dariya tayi tace "Allah yasa." "Ameen." Ya fad'a yana gyara zamanshi, Sadeeq ne ya saci kallonta ta madubi yace "Ke ma da zaki bada dama ai gaban kad'an sai a mayar dake sarauniyar." Dariya Mimi tayi tana sinne kanta wani dad'i na ratsata Asma'unta zata samu babban yaro, Asma'u kuma cike da zolaya tace "Wa zai mayar dani sarauniya bayan bana da suffar ko gimbiya?" Dariya yayi yace "Gani, Allah da gaske nake Asma'u." Kallon Asas yayi yace "Abokina fad'a mata mana." Hararanshi yayi yace "Rainin hankali, ban tabbatar dana rik'e tawa a hannu ba zan zauna tayaka jefa k'uri'a? Kowa ya ji da kansa." Da mamaki ya kalleshi yace "Au! Hakane kenan?" "Eh d'in." Ya fad'a yana d'auke kai, jinjina kai yayi yace "Ba komai zan rama." Sake kallon Asma'u yayi ta madubi yace "Asma'u kinji ko? Dan Allah ki bashi kunya mana ta hanyar amince min." Kunya ce tasa ta sadda kanta k'asa tana wasa da yar wayarta a hannu, jin shiru yasa shi sake marairaicewa yace "Dan Allah *Asma'ul Husna* ki amince min kar na zauce." D'aga kai tayi ta kalleshi da mamaki, ita ina zata kai babban yaro haka kamar Sadeeq? Bata tab'a saurayin daya taka ko da matakala ta farko na a b'angaren aji bare hawa na uku, ita kam ya zata ce mishu ne yanzu? Tabbas tunda suka san juna yake nuna mata kulawarshi da abubuwa masu wuyar fassara, ta d'auka mutumci ne kawai ashe abinda ke ransa kenan? Mimi ce ta d'an tsamiketa a cinya hakan yasa ta fad'in "Washhhh!" Da sauri ta kama bakinta tana kallonta, da ido Mimi ta mata alamar ki amince mana, ita kuma ta mata alamar ni a wa? D'an tsaki tayi tare da yin kamar zata daketa, hakan yasa Asma'u jinjina kai tace "To zanyi tunani ko?" Cikin murmushi Sadeeq yace "Ba matsala, zan jiraki har kiyi tunanin." Bud'e baki sukayi da mamakin ashe ya ji me ta ce, da hirar raha da nishad'i har suka isa katafaren gidan daya had'u sosai aka k'watashi saboda hidimar da za'ayi. Tabbas gidan ya cika mak'il da mata manya da yara ga kuma yan mata, saidai maganar gaskiya sun zo ne ganin zahiri da idonsu, tabbas su d'in ahali ne masu ilimi da sani sosai, amma fa suna da wani abu da saika rantse gidan jahilai ne, maganar talaucin gidansu Mimi a yanzu ba shine gabansu ba kamar da aka fad'a musu su waye iyayenta, sai suka zo tabbatarwa da tambayar kansu dame yarinyar tafi na su yaran da dayawa daga ciki aka so had'a Asas dasu amma ya k'i. Yan matan kansu suna so suga yarinyar ne dan su mata kallon hadarin kaji idan da hali ma har su yaga mata rigar mutumcinta. Ai kuwa yamma na k'ara yin sanyi sai ga motocin angaye sun aje dangin Mimi, yanda suka fara shigowa harabar d'aya bayan d'aya yasa duk akaa kafesu da ido, su Shapi'a ne a gaba suka fara shigowa, hakan yasa wani gungu na 'yan mata kecewa da dariya ganinsu dunk'ul dunk'ul kamar yara amma kuma da fuskar dattijai, ajiyar zuciya Sahura ta sauke tace "Allah gamu gareka, nagode Allah da Mimi bata wurin nan da anyi b'atacciya." Shapi'a ce tace "Ni kam fatana yanzu ta zo dan naga yanda zata ci uwar yarinya idan aka nemi wulak'anta mu." Ido Sahura ta zaro tace "Rufa mana aisri Shapi'a, kai tsaye fa zata ce ta fasa auren d'an uwan nasu." Cike da rashin dana sani Shapi'a tace "Idan tayi haka ma ai sai ta birgemu, wannan ai rashin sanin darajar d'an adam ne kamar ba gadon ilimi Sharif ya bar musu ba." Murmushi Sahura tayi tace "Ya bar musu gadon ilimi, amma yayanshi kuma sun bar musu gadon dukiya, hakan ya jawo dayawa daga ciki dukiyar ce tafi aiki a tunaninsu." Tab'e baki tayi tace "Allah ya kyauta musu." Dogaye da gajeru ne suma haka duk suka samu wuri suka zauna ana d'an gaggaisawa sama sama, hakan ya jawo kowa ware nashi ya koma gefe ana k'us-k'us-k'us, tubarkallah farfajiyar ta cika har kujeru na neman yin k'aranci duk yawansu, dan kuwa kafatanin ahalin Sharif duk sun hallara, kama daga iyalin Aliyu Sharif, Usman Sharif, Salmanu Sharif da sauran abokan arzik'i, sosai Hafsat ke k'ok'arin ganin an samu sanayya da kuma fahimtar juna tsakanin danginsu da dangin Mimi, hakan yasa take ta nunawa iyayensu su Shapi'a a matsayin iyayen Mimi, wasu suna sakin jiki su karb'esu a gaisa, wasu kuma gaba da gaba suke yatsina fuska suna musu yak'e, hakan bai ma Hafsat dad'i ba amma ya ta iya, sharesu tayi ita ma tana fama da cikinta da wunin yau ta ji bai motsa mata ba ga wata muguwar kasala, jefi-jefi kuma sai taji gabanta ya fad'i kawai ba dalili, saidai bata bar ambaton ubangiji ba a bakinta da haka take jin sanyi sanyi a ranta. Sanda motocinsu suka tsaya angayen ne suka fara fitowa suna shigowa filin, sai k'awayen Mimi da suka jera gwanin sha'awa suka sakata tsakiya tare da Asas dake ta doka murmushi, Mimi kan kanta na k'asa tana fama da rik'e jakar hannunta rigarta kuma na jan k'asa. Kowa sake waro idanu yayi dan tabbatarwa kanshi abinda yake gani, dangin Mimi da dama sun san kayansu ba daga nan ba indai wajen d'aukar wanka ne da iya gayu, saidai yanda ta zama tamkar wata balarabiya ya k'ara birgesu da kashesu a game da ita. Inda yan matan nan kuma suka shiga tamtama wai dama haka yarinyar take, sam babu wata makusa a tare da ita da zasu kushe, duk da kwalliya tana canza hallitar mace ta gyarata amma dai sun tabbatar zata yi kyau, na farko tana da dogon hanci ga ta jar fata, su kam idan aka barsu sai su ce wata baralabiya ce, duk sai suka kasa motsawa a wurin dan kwarjini ma suka ji tayi musu yarinyar, sai yan matan amaryar ne da angaye da suka dage suna ta d'aukarsu hotuna, da haka aka isar da Mimi kan kujerarta sai su Asas da suka bar wurin dan dama fa anyi ba dasu za'a yi hidimar ba. A cikin taron yan matan nan akwai guda d'aya wacce ita ba fa abinda ya kawo kowa ya kawota ba, na ta k'udirin babba ne daya girmi na kowa dan kuwa sak'on Muttak'a ta zo isarwa, tasan kasada zatayi amma kud'in daya bata tare da yi mata alk'awarin aure yasa ta ji zata iya yin koma menene, tun shigowarsu Mimi ta mik'e ta shige zak'ewa akan komai tana kamkamba kamar wata yar uwa. Dangin Mimi kallonta suke yanda rawar kanta yayi yawa suna tunanin wata yar uwace makusanciya ta Asas. Inda suma dangin Asas suke kallonta wata marar hankali daga b'angaren Mimi take, da wannan kallon da duka kusurwoyin ke mata aka kasa samun wanda zaiyi mata maganar shishigewa da take musamman ta b'aangaren abinci. Magriba na gabatowa Hafsat ta gabatar da masu ruwa da tsaki ayi kamun amaryar, ana idawa Hafsat tasa Aisha da su Fanna suka kawo cake dan ta yanka tunda ba wani abun ci aka ware mata ba ita, da taimakon Asma'u ta yanka Asma'u ta d'an saka mata a baki aka musu tapi ana dariya, *Feena* ita tayi babakere ta d'auki lemu ta tsiyaya a cup na glas, a hannunta dama akwai k'aramar k'waya babu wanda ya kula da tsiyarta bare ya lura har ta saka, mik'awa Asma'u tayi ita kuma ta mik'awa Mimi, amsa tayi ta d'an kurb'a zata aje Feena ta sake fad'in "Ki k'ara mana, ko ruwa baki sha ba fa." Dayawa kallonta sukayi sai Mimi da take kallonta a matsayin dangin wanda zata aura, wannan kunyar tasa ta d'an k'ara kurb'awa kafin ta aje, Feena kam murmushi tayi duk da bata ji dad'i ba da bata sha sosai ba, amma dai tunda Muttak'a ya bata tabbacin guba ce mai had'ari sauta share kawai, a hankali ba tare da lurar kowa ba tayi kamar tana amsa waya ta fita a wurin. Ana kwad'a kiran sallah magriba su Asas na dawowa d'aukar amarya, Hafsat ce ta rik'e hannunta sa茂 Asma'u a gefenta sauran yan mata a gaba wasu a baya suka nufi hanyar fita, Mimi dake jin matsanancin murd'awar ciki da jin kamar an rik'e mata numfashi ba tare da ankarewar kowa ba ta tafi baya luuuu! Ta fad'i a wurin, da sauri Hafsat ta kalleta tare da sakin hannunta tana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Mimi." Asma'u ma da sauri ta durk'ushe tana kiran "Mimi, Mimi lafiya." Take aka rufe wurin ana tambayar lafiya, cikin tashin hankali Hafsat ta d'ago kanta ta kalli Aisha tace "Eesha kira Asas a waje." Mayar da kallonta tayi kan Mimi, a hankali ta lura da jinin daya fara b'ullowa ta hancinta, cikin tsananin tashin hankalin da take jin bata tab'a riska ba ta daure ta d'ora hannu a kai tace "Na shiga uku, me ya sameta?" Da gudu Asas ya shigo tare da rakiyar zaratan mazan a bayanshi, suna zuwa suka bud'a musu hanya, da sauri ya durk'usa yana fad'in "Me ya sameta? Me aka mata?" Shapi'a ce tace "Ba abinda aka mata, ni fa ina ganin ko mayya ce ta kamata a wurin nan?" Dayawa daga cikin mutanen suka kalleta sai wata mace mai aji sosai da tace "Nan ciki akwai wanda ya miki kama da maye ne?" Hafsat ce tace "Bana tunanin haka, mu kaita asibiti jini ne yake fita a hancinta fa." Wata dattijuwa ce tace "To ko tana da iska ne?" A sukwane Asas ya mik'e tsaye tare da tattara k'arfinshi ya d'auki Mimi cak ya fita da ita da gudu, duk rufa masa baya akayi hankali tashe da tunanin miye zai faru, yana sakata mota yaja da gudun tsiya zuwa asibitin sheikh data fi kusa dasu har da ma gidanshi duk yana kusa da masaukin bak'in na shi, duk tarin tilin motocin dake wurin kad'an ne suka bi su zuwa asibiti dan su san halin da take ciki. *Gobe d'aurin aure fa*馃榿 *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:55 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *25* Sanda suka samu aka amsheta da gaggawa ganin iyalen sheikh, a lokacin wasu suka sake taso da maganar ana bibbikawa, inda Asas ya d'ora hannu d'aya a kai yana amsa kiran Hajia da labari ya risketa, cike da tsananin damuwa ya marairaice yace "Hajia ni ma ban sani ba, sun ce wai fad'uwa tayi suma basu sani ba." Hankali tashe Hajia tace "To ko dai tana da aljanu ne?" Saida ya d'an juyo yana kallon mutanen dake bayanshi yace "Hajia na tabbata ma bata da su, ban tab'a ganin alamunsu a gareta ba, kuma fa har sheikh sun had'u da shi amma babu abinda ya sameta, kuma kinfi kowa sanin baiwar da Allah ya masa." Cikin son kwantar masa da hankali tace "To kaga yanzu dai ka zauna kusa dasu, sannan kar muyi saurin barin labarin ya fita tunda babu tabbacin me ke damunta." A sanyaye yace "To Hajia, Hajiata." Yanda ya kirata yasata cewa "Na'am autana." Kamar zai fashe da kuka yace "Hajia ina tsoron ta mutu." Da sauri tace "A'a autana, insha'Allahu babu abinda zai sameta, zata tashi da yardar Allah." A hankali yace "Allah yasa Hajia." Da "Ameen." Ta amsa mishi ta yanke kiran. Asma'u ma kiran Abban Mimi ne take amsawa da yaga magriba ta wuce basu dawo gida ba, gashi yana tsananin son ta had'u da dangin malam wanda suka yi niyya sa茂 gasu kwatsam sun shigo da yamma, sunyi farin ciki sosai na ganinsu amma gashi amaryar bata dawo ba, hankali tashe cikin kuka Asma'u ke fad'in "Abba muna asibiti, Mimi ce kawai ta fad'i jini na fita a hancinta, Abba kar na rasa k'awata ni ma mutuwa zanyi Abba." Duk zuba mata ido mutanen sukayi cike da tausayinta da jin lallai ita d'in k'awa ce ta gari, Sadeeq kam ji yake kamar ya rumgumeta a jikinshi tsabar tausayi, cikin kid'ima Abba ya amsa da "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, hasbunallahu wani'imal wakil! Mimi kuma? Me ya sameta to? To gani nan tafe yanzu wace asibiti ce." Cikin kuka tace " *Annur*." Ta fad'a a k'asan mak'oshi, k'it Abba ya datse kiran yana waige waige ya ma rasa ta ina zai bi, Abban Asma'u dake tare dashi ne ya tambayasa lafiya? Yana fad'a masa ya tashi motonta yace su tafi, zasu tafi kuma malam na fito a gidan dan tunda yayi sallah magriba yake tare da yan uwanshi da yake jin kamar ya goyasu, malam ma cewa yayi zai tafi hakan yasa mutan ciki basu san me ke faruwa ba malam ma ya samu taxi ya bi bayansu suka d'unguma asibiti. Saminu ma tunda Maimuna ta fad'a mishi halin da ake ciki yace zai je idan komai da sauk'i saiya d'aukota su dawo gida. Hafsat ma haka hankali tashe tana sanyayyan kuka ta rud'e sosai take fad'awa sheikh "Wallahi sheikh bansan me ya faru da ita ba, kawai gird'ewa tayi ta fad'i shikenan fa sai jini a hancinta, ni na shiga uku sheikh ya zanyi idan wani abu ya sameta? Ni na je har gidansu na nemi izinin a barta fita a ranar nan, wayyo Allah na!" Ta k'arashe tana sake fashewa da kuka, daddab'a kafad'arta Aisha tayi tana kallon mahaifiyarta da tausayawa, daga b'angarenshi kam jim yayi kamar ba zaiyi magana ba sai ma istigfari daya fara ambata a bakinshi, can sai kuma ya bud'a baki da k'yar yace "Su wa suka je taron? Me ta ci? Wa ya bata wani abu ta ci a wurin?" Cikin kuka tace "Babu wani abu da ta ci sai d'an cake kawai da lemu, dukansu bata musu wani cin da zasu isa cikin cikinta ba." Lumshe ido yayi ya ja numfashi, a sanyaye ya yanke kiran yana kallon matasan dake gabanshi, cikin dattako ya rufe littafin gabanshi yace "Zaku gafarce ni kad'an abokaina, kira ne na gaggawa daga ahali, suna buk'ata ta a asibiti yanzu, zamu d'ora karatunmu a sati mai zuwa insha'Allah." Kallon wani matashin yayi dake gefen damanshi yace "Malam *Anas* ka kula mana da inda muka tsaya, zamu d'ora wani satin insha'Allah." Cike da girmamawa da mutumtawa da ladabi ya sunkuya daga zaunen da yake yace "Insha'Allah sheikh, Allah ya tsare Allah ya sauk'ak'a lamura." "Ameen ya Hayyu ya Qayyum." Ya fad'a yana mik'ewa tsaye, duk mik'ewa sukayi suma inda ya saka taklminshi k'afa ciki, rufa masa baya sukayi har ya fito inda masu tsaron lafiyarsa ma suka rufu a bayanshi, da sauri d'aya a cikinsu ya bud'e mishi inda zai zauna y'a shiga, da gudu suka ja motar suka bar harabar gidan gonar zuwa asibiti. *Masha'Allah* duk da Mimi ba wasu babban ahali bane da sukayi suna, sai gashi a kad'an mutane a k'alla ashirin ne tsaye bakin d'akin da take ana ta jiran sakamako, saidai tun zuwan sheikh sai kallo ya koma kan shi, kwarjini da wani irin dattijantaka da dattijon had'a ga wani kyau da yayi a cikin fararen kayan da kuma kalar shud'i, wanda ko takalmin k'afarshi farare sai yar kwalliyar shud'i, shigar nan ce dai irin ta kullum babbar rigar malamai mai zubin alkyabba. Ya goya hannayenshi bayanshi a hankali yake d'an tattakawa dama yana tsaye a k'ofar shigowar ne, yanda yake tafiyar a hankali daga bango zuwa bango yana motsa yatsunshi alamar tasbihi, hailala, istigfari, tahmidi yake yi, sautin takalminshi dake fita wani gum gum gum ga fitinannen turarenshi daya had'e wurin duk sai aka zuba mishi ido. Kallon Hafsat yake da take kuka tayi zaune da k'yar kan kujerar robar da Aisha ta samo mata, a hankali ya k'arasa gareta tare da yin tsuguno a gabanta ya rik'o hannunta, cikin taushi ba tare da duk wanda ke wurin yaji ba yace "Sawwama, kukan nan ya isa haka mana, ko kina so ki babbaka min zuciyata ne?" Saida ta ja majina ta d'an girgiza kai alamar a'a, lusmhe ido yayi yace "To ya isa haka, karki sake kinji." Jinjina kai tayi tare da had'e kukan tsaf kamar ba ita ba, sai yar shashek'ar da ba'a rasa ba. A hankali ya mik'e daga gabanta ya d'an karkato da niyyar juyowa, yanda ya samu ido a kan su ne ya dakatar dashi daga juyawar gaba d'aya, duka kallonsu suke da mamaki inda matan ke jin kamar su d'aukesu hotu su nunawa mazajensu dan ya zamar musu hujja, Alhaji Saminu kam kallon Aisha yake yana d'an lashe leb'enshi, dan gaba d'aya 'ya'yan sheikh irin jikin nan ne dasu na girma, hakan yasa duk zaka gansu kamar rainon turawa, kowane da jikinshi masha'Allah kurtib'a kirtib'a dasu. Aisha data jima da lura da kallon da yake mata haushi ne yasa ta d'an jan tsaki, a hankali sheikh ya kalleta tare da bin wurin data harara ta d'auke kan ta, ido hud'u sukayi da Saminu da a lokacin yake kan kallonta, da nutsatsun idonshi ya aika mishi da sak'on a sauk'ak'e, a take wani bazawarin kwarjinin sheikh ya rufeshi, duk da dama dai a girme zai bashi yan shekaru amma ba wasu sosai ba da zasu jawo har ya ji wanan matsayacin shakkar tashi. Bud'a k'ofar d'akin da akayi yasa duk kowa ya gyara tsayuwa yana zubawa k'ofar ido, ganin likitoci ne guda biyu sai kowa ya sake matsawa daf dasu dan jin me zasu fad'a, Asas na gaba kusa da likitan yana kallon bakinshi, inda sheikh ke tsaye a inda yake saidai ya kasa kunnuwanshi dan yaji me zai fad'a shi ma kuma tsaf yake lura da motsawar bakin likitan. A hankali likitan ya goge zufar fuskarshi yana k'are musu kallo yace "Kune danginta?" "Eh mune." Abba da Asas suka fad'a a tare, numfashi likitan ya sauke yace "Alhamdulillah munyi nasarar ceto rayuwarta, saidai da mamaki yanda kamar wannan tasha wannan guba mai kaste hanjin ciki a lokaci d'aya, sa'a d'aya shine ba wani dayawa tasha ba bare ta gaggauta illatata, da yanzu fa wata maganar ake ba wannan ba." Duk zaro ido sukayi tare da fad'in "Guba kuma?" Jinjina kai yayi yace "Tabbas guba." Sallalami aka shiga yi inda Asma'u tace "Amma garin yaya? Me ta ci a wurin?" Salma ce tace "Cake ne ai sai lemu." Asma'u ce tace "Amma ai mu ma mun ci, kuma gashi ba abinda ya same mu." Cikin muryar kuka Zeinaba tace "To ai bamu sha lemu ba, saidai in a lemun aka saka." Cike da tuhuma Asma'u tace "Ai yar uwarsu ce ta bata lemun." Fanna ce ta harareta tace "Wace yar uwarmu kuma? Wannan mai rawar kan tsiyar? Kinga tayi kama da ahalinmu?" Aisha ce cikin ladabi tace "Ai mun d'auka yar uwar aunty Mimi ce." Asma'u ce tace "Basu had'a komai da ita ba, m没 ma nan kallon yar uwarku muke mata." Asas ne yace "To kenan wacece?" Duk tab'e baki sukayi suka ce "Uhum!" K'wafa yayi kawai yace "Ba wanda ya santa kuma?" Salma ce tace "Bamu santa ba gaskiya, amma ai ba'a rasa hotonta tunda tana ta shigewa jikin Mimi." Da sauri yace "Na gani." Jiki na rawa ta shiga duba hotunan da suka d'auka inda sheikh ke hangen komai daga can yana jan tsakin ganin Salma, ita ma dai shigarta kamar ta sauran, amma dake ta fito da gashin dokin data saka ga kwalliyarta tafi ta kowace yawa, sannan ga wayar daya gani a hannunta sai yake ganin wannan ba k'awar k'warai bace, watak'ila ma ita ta lalalata mi shi Ryam "Mtssss!" Wani tsaki ya kuma ja yana kallon Asas daya ciro wayarshi ya d'auki hoton Feena sannan ya mik'awa Salma wayarta. Sallalami suka shiga rabkawa har likita ya rab'asu zai wuce tare da wata a bayanshi Asas yayi saurin cewa "Yanzu babu wata matsala likita?" Kallonshi yayi yace "Babu insha'Allah." Zai wuce Abba ya sake bin bayanshi yana fad'in "Likita." Tsayawa yayi tare da kallon k'asanshi sosai ganin Abba ne yasa shi sunkuyawa cikin ladabi, cikin rad'a Abba yace "Likita yarinyar nan dake kwance da safe k'arfe 08:30 za'a d'aura aurenta, kana ganin ba wata matsala sosai za'a iya sallamarta?" Cikin sakin fuska yace "Nayi tunanin haka dama dana ga d'an uwan sheikh tare daku, indai ba wani iko na ubangiji ba kuma a gaskiya munyi iya bakin k'ok'arinmu, kuma muna saka ran zata farka lafiya lau nan da asuba ma, allurar bacci muka mata dan ta huta, a shawarce Abba ku d'aura aurenta babu abinda zai faru." Jinjina kai Abba yayi cike da gamsuwa yace "Nagode sosai likita, Allah yayi albarka." Da murmushi likitan yace "Ameen Baba nagode." "Zamu iya shiga mu ganta?" Cewar Abba, jinjina masa kai yayi yace "Zaku iya, amma dai kar a takura mata dan tana bacci ne, ta wahala sosai kafin amayar da gubar da tasha." Cike da jimami ya jinjina kai alamar gamsuwa tare da nufa inda mutanen ke tsaye, malam ne yace "Ya kukayi da likitan? Ba komai dai ko?" Cikin jin kunya ta suruki yace "B芒 komai malam insha'Allah, yace ma zamu iya shiga mu ganta amma kar a takurata." Da sauri malam da Asma'u suka nufi d'akin har suna had'a kafad'a, tare suka shiga kafin Asas da Abba su bi bayansu, sai kuma Maimuna da Saminu suma suka shiga. Cike da tausayawa suke kallonta, kwalluyarta na nan a fuskarta sai jan bakinta ne kawai ya d'an fara b'aci, hannayenta dake cikin lalle ja ya k'ara fitowa akan fatarta, sai tayi wani masifar kyau kamar gawa, kowa bakinshi addu'ar tashin kafad'unta yake amma banda Saminu daya shiga k'are ma nonuwanta kallo da sukayi cirrr a cikin rigarta zuwa d'uwawunta da suka baje akan gadon tana kwance, tsabar jaraba bakinshi ne kawai yake bushewa yana lashewa, sai ya samu kanshi da jin wata mahaukaciyar sha'awar yarinyar da kuma jin mad'aukakiyar tsanar Asas da yake ganin shi ne zai mallaketa. Haka dai suka fita aka bar d'akin Asma'u na kuka tana fad'in "Abba zan kwana a nan wurinta, ku barni a nan ba zan iya barin Mimi ba." Cike da dattako Abba yace "A'a ba za'ayi haka ba yata, wuce muje gida Iya zata zo ta kwana tare da ita." Cikin kuka kamar an ce ta mutu ne tace "To Abba kafin Iya ta zo waye zai zauna anan?" Da sauri Saminu yace "Ba komai zan zauna, sai ku tafi tare da Maimuna gida a motata." Kallonshi duk sukayi da mamaki musamman Asas daya bishi da kallon ban gane ba? Dan haka ya gyara tsayuwarsa ya kalli Abba yace "Abba, ku je kawai kafin Iya ta zo zan zauna a nan." Wata harara Saminu ya wurga masa wacce tsaf Asma'u ta gani ta shiga mamaki, haka dai suka fita shi ma Asas ya fito tare dasu suna sallama, Hafsat na ganinsu ta mik'e da k'yar tana fad'in "Asas ya jikin nata?" Da fara'a ya amsa mata da "Jikinta da sauk'i aunty Hafsy, kije gida ke ma ki huta insha'Allah zata samu lafiya." D'an satar kallonshi sheikh yayi sai kuma ya d'auke kai, su Salma dake ta kallon sheikh jikinsu na b'ari na zumud'in ganinshi kamar su je daf dashi suke ji, haka duk suka fita a asibitin tare Asma'u dasu Salma duk a motar Saminu suka koma gida, Abba ma suna zuwa a nutse suka fad'a musu abinda ya faru, da sauri Iya ta tarkato ta taho dama tana nan gidansu Mimi, wata tsohuwa ma yayar malam ta so su je tare malam d'in ya hana yace tayi hak'uri. 12:30 sheikh ya dawo asibitin, saida ya tsaya k'ofar d'akin kuma saiya tsaya cak ya tambayi kansa "Me ya kawoka? Miye hujjarka na zuwa ganinta?" Juyawa yayi da sauri kawai ya bar asibiti ya shiga mota, jingina kanshi yayi a sitiyari yana furta "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntum-mina zalumin, hasbunallahu wani'imal wakil, Allahuma ajirni fi musibati waklufli khairan minha." Sai kuma ya shiga fad'in "Astagfirullah wa'atubu ilaikh, astagfurullah wa'atubu ilaikh." Dan gaskiya ji yake ko wani laifin ya ma Allah ya jarabceshi da abinda yake ji a yanzun, har zuciyarshi yake son mantawa da ita, amma tunaninta na yawan addabarshi, gashi kuma awanni da basu gaza takwas bane suka rage ta zama matar shak'ik'insa. Ya jima zaune a motar yana istigfari da tunanin had'uwarshi da ita, fuskar nan ta ta mai matuk'ar kamala da nutsuwa, saidai kash *mage* ce mai *kwanciyar d'aukar rai*, wani wawan tsaki ya ja a motar tare da d'an dukan sitiyari yana fad'in "A kan me Ryam? Me yasa kika zama mai arha ballagazar matasan titi? Shitttt!" Ji yayi kamar ya samu wani ya ciza dan haushi yake ji sosai na tuna abinda ya faru a ranar, da k'yar ya samu ya bar k'ofar asibitin zuwa gida, saidai dake Hafsat tana can gidansu Hajia suna ci gaba da aiki dan Abba ya tabbatar za'a d'aura auren, sai kawai ya shiga ta k'ofar baya ba tare daya ratsa ta falon ta ba. *Safiyar juma'a* Tubarkallah duk girman gidan nan nasu a tumbatse yake da jama'a ana ta shan biki tun kafin ma a d'aura auren, Hajia kam cikin kulawa tasa Salamatu tare da dreba da Aisha suka kai wa su Mimi abin kari a asibiti, sosai hakan ya birge Iya da jinjina dattakonsu, suma kuma zuwa k'arfe 09:00 aka sallameta a asibiti, ba abinda ke damunta saidai rashin k'arfin jiki kawai, Asas da kanshi ya aje su har k'ofar gida ya juya cike da begen amaryarshi. Suna shiga ciki dangi aka shiga murna da tambayarta ya jiki? Jiki a sanyaye take amsawa da "Da sauk'i." D'aki ta shigata cire kayanta Sahura ta mata jagora ta shiga ban d'aki tayi wanka ta fito ta canza kaya, ta samu Asma'u a d'akin har ta zo dubata, da farin cikin ganinta take tambayar "Ya jikinki?" Saida ta zauna kusanta a sanyaye tace "Jiki da sauk'i Asma'u." Da fara'a tace "Allah k'ara kiyayewa." A hankali ta amsa da "Ameen." Lumshe ido kawai tayi tana jin yanda zuciyarta ke wani tsinkewa tana gudu da sauri, a k'asan mak'oshinta ta furta "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntum-mina zalumin." Su Zeinaba duk suna tare da ita a d'akin Shapi'a ta kawo mata abinci girgiza kai tayi tace "Um um aunty ban ci." Kallonta tayi tace "Iya fa ta ce har abinci aka kai muku asibiti kuma baki ci ba." Madara ta mik'o mata a roba tace "Daure kisha ko wannan to, kar yunwa ta hanaki tab'uka komai." A hankali ta karb'a tare da bud'e robar, sanyi da dad'in madarar yasa ta d'an kurb'awa dan dama tana jin yunwa sosai, ba zata iya tuna rabonta da abinci ba har ta manta ita kam. Tana jin su Asma'u da Salma da suka zo suna sake tattauna maganar yarinyar data bata lemu, ita dai kallonsu take da ido kawai, ba ta da wanda zata zarga tace shi ne, hasalima ba ta tunanin gabarta da wani takai matakin da zai nemi rayuwarta haka, shiyasa kanta ya kulle ta kasa tuna komai. 02:08 Shapi'a ta shigo ta kalleta tace "Ke taso kiyi wanka." Kallonta sukayi sai Rauda da tace "Mama har an d'aura auren ne?" Cike da rashin tabbas tace "An d'aura mana, tunda ai k'arfe biyu ne yanzu kuma biyu ta gota." A hankali Mimi ta mik'e Shapi'a ta kama hannunta suka fita, gud'a mutanen tsakar gidan suka saka har ta wuce zuwa ban d'aki, yan uwan Abba ne su uku a ban d'akin suna jiranta, nan suka mata wankan fita kamar dai yanda aka mata na farko, ana idawa aka d'auko sabon d'inkin da aka mata riga da zane na atamfa d'inki simple, abun ka da mai k'iba sai kayan suka kamata sosai suka mata kyau musamman zanin daya fito da mazaunanta, kallabinsu aka d'aura mata kafin aka bata takalmi silipas ta saka a fararen k'afafunta da kuma darar amare kalar ja, ruf aka rufeta da darar har aka fito da ita daga ban d'aki. A daidai lokacin wayar Sahura na kuka, tana d'auka sai kuma a ladabce tace "Kai ashe Abban Mimi?" Jim tayi kafin tace "To ga Iyar." Ta fad'a tana mik'awa Iya wayar, karb'a tayi ta nutsu tana saurarenshi, duk tsura mata ido akayi suna kallon yanayinta, saida ta d'an jima kafin a sanyaye tace "Allah yasa haka shi yafi alkairi, Allah basu zaman lafiya, shi kuma Allah ya jik'anshi da rahama." Sahura da yayar malam ne suka kalleta da fad'in "Iya wa ya rasu kuma?" Kallonsu tayi sannan ta kalli Mimi dake tsakiyarsu zasu rakata d'aki, sauke numfashi tayi kawai ba tace komai ba, Shapi'a dake kusanta ne ta aje tasar furar hannunta da za'a kai ma bak'in da suka shigo yanzu daga k'auye tace "Iya wa ya rasu dan Allah?" Cikin danne kukan tausayin Mimi cikin jin haushi Iya tace "Yaron ne ya rasu, angon." *Waiwaye* 11:00 Asas ya shigo da leda da hannunshi, abokan wasa na tsokanarshi yana dariya yace "Ban da lokacinku yau, duk kuyi ku gama matata ce zata rama min duk abinda kuka min." Da haka ya shige b'angarenshi dan shiryawa, tsaf yayi wanka ya fito ya zauna ya linde jikinshi da mai ya fesa turare kamar ba gobe, inda kayanshi suke ya nufa ya d'auki wandon dakakkiyar shaddar ya saka ya aje towel d'in k'ugunshi, ya d'auki rigar zai saka kawai ciwon ciki yace salam Asas, da sauri ya saki rigar ya sunkuye k'asa yana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, wayyo Allahna ciki Hajia, Hajia ciki zan mutu, wayyo Allah." Yunk'urawa yayi da niyyar d'auko wayarshi saidai ina kawai ya fad'i a wurin jikinshi na saki gaba d'aya tare da d'aukar wani irin sanyi k'alau. Tun ana saka ran fitowarshi har dai aka ga ya jima, 12:28 Sadeeq ya shigo gidan tare da wani abokinsu cikin shirinsu sunyi tsaf, Hafsat suka gaida kafin Sadeeq yace "Auntynmu wai ina yaron nan yake ne? Shiriritarshi yawa ne da ita fa." Nuna musu b'angaren tayi tace "Tunda ya shiga ina jin bai fito ba, ko shirin yake har yanzu?" D'an tsaki Sadeeq yayi yace "Martala gareshi wallahi, yanzu nan fa sheikh sai kirana yake yana jadadda mana karmu b'atawa mutane lokaci, mu zo akan lokaci dan ayi komai a gabanmu." Nufa b'angaren na shi sukayi dukansu biyu d'in Hafsat na murmushi dan sheikh ne zai karb'ar ma Asas auren ma'ana zai wakilceshi. Suna zuwa k'wank'wasa k'ofar suka fara yi suna kiran "Kai zaka fito ko sai na bankad'e k'ofar? Kaji iskanci ko kai ma kwalliya kake irin ta amaryar." Shiru babu motsi ko alamar mutum, cikin jin haushi Sadeeq ya sa k'arfi ya tura k'ofar ashe ma bud'e take, abinda suka gani ne ya d'aga hankalinsu tare da sandarewa suna sake kallonshi, kamar an tsikaresu sai kuma suka tafi a guje suka durk'ushe suna kiran sunanshi, Sadeeq ne ya kalli d'ayan yace "Lamin dan Allah kira mutane a kai shi asibiti, ina jin ciwon cikinshi ne ya motsa." Hankali tashe Lamin ya mik'e da gudu ya fita Sadeeq na ci gaba da jijjigashi yana fad'in "Dan Allah ciwon ciki ba'a wannan lokacin ba, kar ka shiga tsakaninshi da burinshi mana." Rututu aka shigo d'akin har da Hafsat da tsohon cikin ta ta durk'usa tana kallon d'an uwanta, cikin rawar murya tace "Haka kuka sameshi?" "Eh." Cewar Sadeeq, a hankali ta kai hannu a wiyanshi ta tab'a wajen shed'a, jin shiru yasa ta d'aga hannun sai taji yayi nauyi ya sake fad'uwa, a hankali ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." "Lafiya?" Cewar Hajia a kid'ime, zaune tayi dangal dangal ta kasa cewa komai, Sadeeq kam kallon Lamin yayi yace "Kamashi mu kaishi asibiti." Girgiza kai tayi ta musu alama da hannu kar su tafi, a tsorace Sadeeq ya kalleta yace "Kamar ya?" A tausashe tace "Saboda wanda ya fi mu son shi ya karb'e abun sa." Gaba d'aya d'akin aka d'auki salallami sai Hajia data fad'a kan gadon tayi zaman yan bori ita ma tana na ta salallamin, duk shiru sukayi a d'akin ana ta kallon kallo ana jimami babu mai magana, gasu ga gawar Asas kwance baya motsi, yayi kyau masha'Allah ga askin nan daya sha irin na zamani sumarshi ta asalin bafulatani an tara mishi ita a gaban tsaf, kukan wayar Hajia ne yasa su zabura suka kalli inda take zaune, sai suka lura kamar bata ma san ana kiran ba, matar kawu Saleh ce ta kai hannu a jakar Hajia ta d'auki wayar, tana dubawa sheikh ne mik'awa Hafsat tayi ta karb'a. Cikin ruwan sanyi yace "Hajiayarmu, ina Asas?" Wani murmushi ta saki mai kama da kuka tace "Asas ya amsa kiran ubangijinshi." Sai kuma ta fashe da kuka, jim yayi yana jin abun kamar alamara ko tatsuniya, can kuma saiya nisa yace "Manga, Asas na ce yana ina, hud'uba zan fara yanzu gashi basu zo masallacin nan ba." Cikin kuka tace "Sheikh ga Asas dai kwance a gabanmu amma baya motsi, ba zai iya anfanar kan shi da komai ba a halin yanzu, hatta da wanka ma sai an mishi." A gigice sheikh yace "Ban gane ba Sawwama, me ya same shi wai?" Wani kuka mai cin rai ta fashe da shi tace "Bamu sani ba mu ma, gawarshi kawai muka samu." Wani bala'in sanyi ne gabb'anshi sukayi hakan ya sakashi sakin wayar daga hannunshi, da sauri d'an agaji tare da masu tsaronshi suka matso suna tambayar lafiya? B'alle d'amarar dake gaban rigarshi yayi ta alkyabba ya shiga firfita da hannunshi, lura kamar cikin tashin hankali yake yasa d'aya fad'in "Allah gafarta malam ko zamu koma gida ne?" Da sauri yake jan numfashinshi kamar mai hawan jini, kiran sallah da aka kwad'a yasa shi d'an zabura yace "Astagfirullah, astagfirullah, Asas? ashraf? Astagfirullah." A gigice ya juya ya tunkari masallacin ba maa tare da yasan me yake ba, saida ya shiga ya tabbatar ba abinda yayi niyya ya aikata ba, shi fa gida yake so yaje ya gasgata abinda suka fad'a, bud'a mishi hanya aka dinga yi yana ta wuce har ya kai gaba inda ya kamata ya hau mimbari, saidai kuma kawai gani sukayi yayi zaune a layin masu biyarshi, kallon kallo ake saidai ba wanda yace wani abu ana tunanin ko wata sabuwar sunnar ce. Kawu Saleh da sukayi waya da matarshi ta sake fad'a masa abinda ke faruwa ne ya matsa a jerin sahun farko inda wasu malamai da sarakuna da manya suke, sheikh Bala ya ma magana kan ya wakilci sheikh dan shi yana cikin halin d'imuwa ne, shi ma abun dai ya razana shi tare da k'ara mishi tsoron Allah, haka ya hau mimbari ya fara gabatar da hud'uba a harshen larabci na minti sha biyar kafin ya d'an zauna na minti d'aya ya mik'e ya ci gaba da fassarawa a hausa, saida aka gama akayi sallah sheikh shi ma dai biya kawai yake, ana idawa ne aka gabatar da aure takwas da za'a d'aura. Duk waliyai da wakilai sun matso dan ayi abunda ya kawo amarya d'akin mijinta, aure biyar aka d'aura kafin aka kawo ga na su Mimi, Saleh ne ya kalli sheikh da sam hankalinshi baya kansu yace "Sheikh ya zamuyi yanzu? Basu san me ake ciki ba fa?" A zabure ya kalleshi kamar marinshi yayi a fuska, sai kuma ya d'aga kai ya kalli su malam da Abban Mimi ga Abban Asma'u a kusa dashi, girgiza kai yayi ya sunkuyar da kan shi k'asa, shiru aka sake yi ana ta kallon kallo ba wanda yace wani abu. Gashi sheikh Bala dake d'aura aura yana ta magana, a hankali Saleh ya kalli Abban Mimi cikin rawar murya yace "Kuyi hak'uri, d'aurin auren nan ba zai yiwu ba." Da wani matsiyacin sauri suka kalleshi suna rarraba ido, cikin kid'ima Abban Asma'u yace "Me yasa? Wani abu ne ya faru?" Abba kam tuni yayi k'asa da kanshi da tunanin ko wani abun kuma aka ji Mimi tayi, cikin alhini Saleh yace "Ba komai, saidai Ashraf Allah yamasa rasuwa, d'azune aka kira daga gida aka sanar mana." Kusan duk wanda y'a ji saida ya fad'i kalmar nan ta daga Allah muke kuma gareshi zamu koma, sosai aka jijjiga aka shiga jajantawa ana tattaunawa k'asa k'asa. Wani iska sheikh ya feso a bakinshi mai zafi tare da tattara babbar rigarshi ya yunk'ura zai mik'e yana fad'in "Ku gafarceni, zan koma gida." Da kallo wasu suka bishi sai Saleh daya shiga lalubo wayarshi dake ziiii! Ziiiii alamar vibration, yana ciro ya d'auka ganin lambar Hajia ce, d'orawa yayi a kunne yana kallon Bala daya ci gaba da d'aurin auren. Cikin sauri da gaggawa Hajia tace "Saleh ya maganar d'aura aure?" Saida ya d'an kare bakinshi da tafin hannu yace "Hajia ba'a d'aura ba." Da saurin bala'i tace "Karku kuskura, a d'aura auren nan da sheikh, karku bar yarinyar mutane tayi alhini, dan Allah ya karb'i aurenta." Tsam yayi yana kallon k'eyar sheikh dake tafiya a hankali har ya kusa fita, da sauri ya mik'e tsaye yana fad'in "Kin tabbata Mari?" "Eh, a d'aura." Ta fad'a cike da k'warin gwiwa, hannu ya d'aga ma na gabanshi yana musu alamar su dakatar da sheikh, cikin ladabi kam wani matashin ya mishi magana, juyowa yayi yana kallonshi da ido da alamar tambaya, da hannu shi ma ya mishi alamar taho kawai, a hankali ya sake juyowa yana dawowa yana jin yana so ya cire babban rigar nan dan zafi yake ji sosai, ac da pankokin dake wurin kamar basa aiki yau kam. Saida ya koma ya zauna inda yake Saleh ya kalleshi sannan ya kalli k'anan babansu sheikh Alhaji Ibrahim yace "Hajia tace a d'aura auren nan da sheikh, ya kuka gani?" Wani kallo sheikh ya watsa mishi da sauri inda Abba ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi, shi kam me zai hanashi ya so had'a zuri'a da Abdul Waheed? Su Abban Asma'u da malam da shi kanshi Alhaji Ibrahim duk murmushi sukayi, hakan yasa Saleh ciro kud'i ya damk'awa Alhaji Ibrahim yace "Ka karb'a mishi auren ta." Kallonsu yake kamar ya d'ora hannu yace wayyo shi wayyo kan shi, girmanshi da darajarshi ta hanashi mik'ewa yace " *Wallahi bana so, bana son yarku ku rik'e abarku, ni uwa ta gari nake nemawa yarana*." Ganin da gaske suke har sun fara daddala mishi nauyinta a kai yasa shi sunkuyar da kai yana furta "Allahuma ajirni fi musibari, waklufli khairan minha." Ba komai yake tunawa ba sai wani wa'azinshi da yake fad'in "Duk wanda a rayuwarshi ya auri ballagazar mace wacce ta riga ta zubar da mutumcinta, to hak'ik'a ko a kyauta aka baka ita kayi asara, dan ba zaka samu tsatso mai kyau ba bare ka haifi yayan da zakayi alfahari da su, ba lallai ka fad'a mata ta ji ba saboda babu wani abu da ke d'ad'ata a k'asa a game da harkar namiji..." Yau shi ne aka d'orawa wannan nauyin na yarinyar da shi dai ya tabbatar hidimar da take wa kanta wasu ne k'ashin bayan hakan, son zuciya watak'ila da halin rayuwar da suke, yarinyar da mahaifinta ke neman abinda zai ci, amma ita tana rik'e da waya IPhone, yarinyar da mahaifinta ma ya kasa yarda da ita, munin halinta yasa likitar ma ta kasa fad'a a gabansu saida ta nemi da a sirrinta. Salati kawai ya shiga farawa yana jin gumin na tsatsafo masa. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:55 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *26* Ana gama d'aurin auren ya lumshe idonshi yana jimk'e hannunshi kamar zai naushi wani, kabbara aka d'auka a masallacin dan shi ne aure na k'arshe da aka d'aura tsakanin *Maryam Adam Shehu* da kuma *Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif*, duk mik'ewa mutane sukayi ana fita da magana a baki, wasu hakan ya musu daidai da son zuciyarsu, wasu kuma hakan bai musu ba ko kad'an, sheikh kam bai motsa a wurin ba haka aka dinga bashi hannu ana mishi addu'ar fatan alkairi, su Abba ma fita sukayi yana kiran gida ba'a samu, dan haka mijin Sahura da suke tare ya jaraba kiranta kuma aka samu, shi ne fa suka sanar musu dan karsu ji abun daga sama kafin su isa gida. Saida yaji masallacin yayi shiru alamar ba mutane kafin ya d'aga kan shi, ai kamar wanda aka kora da gudun tsiya sai kuwa yayi wuf ya mik'e yana sab'a babbar rigarshi ya fita shi ma su Alhaji Ibrahim da Saleh suka rufa mishi baya tare da jami'anshi. Duk motocinsu suka shiga inda sheikh ya kalli dreba yace "Dan Allah kayi sauri, gidan Hajia zamu je." "To sheikh." Ya fad'a yana sake murza sitiyarin da kyau, ji yake an k'i kawowa gidan, gaba d'aya gani yake ba'a sauri kamar ya fita yaje da gudu a k'afarshi, tambayar "Anya kuwa Hajia tasan wa ta bani?" Yake yi, numfashi kawai yake saukewa lokaci zuwa lokaci, da wannan tashin hankali suka isa gidan daya k'ara kaurewa da mutane maza da mata, a k'ofar gidan motar ta tsaya sheikh ya fita, duk da hankalinshi a tashe yake kuma sauri yake sosai, amma tafiyar a nutse yake yin ta cikin hankali, gaisheshi ake da girmamawa kamar wani sarki shi kuma yana amsawa da murmushin yak'e a fuskarshi, har suka shiga cikin gidan ya fara hango Hajia a b'angaren Asas zaune a k'ofar shiga falon, mutane duk anyi cirko cirko wasu zaune wasu kuma tsaye babu mai magana. Da sauri ya isa garesu saida ya kai daf dasu ya fahimci matar Alhaji Ibrahim ma tana tare dasu Kubra da matar Saleh sai Hafsat zaune kan ta a k'asa, kallonta yake yana karantar yanayinta, sosai ta bashi tausayi dan alamu sun nuna tasan abinda Hajia ta aikata musu. Kallon juna sukayi da Hajia cikin rikitacciyar murya yace "Hajia ya haka? Ina Asas?" Sake rumgume hannayenta tayi tace "Yana ciki likita na dubashi." Sake kallon Hafsat yayi, matsawa yayi kusanta ya durk'usawa ya kamo hannayenta cikin na shi, da k'yar ta d'aga idonta ta kalleshi tana mai danne abinda ke zuciyarta tare da dakatawa da karatun suratul nisa'i data shiga tunda abun ya faru dan ta tunawa kanta cewa hukuncin Allah ne fa, shi ne ya hukunta musu suyi, da k'yar ta k'ak'aro murmushi da shi yana gani yasan bai kai ciki ba tace "Barka, ina tayamu murnar k'ara girma, ina tayaka murnar k'ara samun wanda zaka ciyar fisabilillah, Allah tayaka rik'o sheikh." Yanda muryarta ke rawa yasa ta dakatawa dole dan bata so tayi kuka, girgiza kan shi yayi tare da d'ora hannunshi a cikinta shi ma kamar zaiyi kukan yace "Kin tabbatar kuna cikin k'oshin lafiya?" Saida ta d'ora hannunta akan na shi ta jinjina kai tace "Eh, ba komai." Girgiza kai ya sake yi yace "Da komai Hafsat, zamuyi magana a gaba kinji." Mik'ewa yayi tare da sakin hannunta ya kalli likitan daya fito, yanda suka zuba mishi ido yasa shi girgiza kai yace "Saidai kuyi hak'uri, Allah ya gafarta masa." Da sauri ya rab'ashi ya wuce d'akin haka Alhaju Ibrahim da Saleh ma da kuma Sadeeq da suka samu a nan, tabbas dai abinda kowa ke gani shi suma suka gani, a hankali ya zauna bakin gadon yana k'arewa fuskar Asas kallo, lallai duniya *budurwar wawa*, jiya suna tare da bawan nan har safe ma haka, kai har k'arfe 10:45 suna tare dashi yana mishi mitar ya bashi jaka d'ari biyu shi babu kud'i a hannunshi, kuma banki a lokacin yasan ba zai samu ba dan juma'a ce, shi ne yanzu kwance haka a gabanshi baya motsi. A sanyaye ya sauke wani numfashi kanshi k'asa yace "Zamuyi mishi sutura yanzu, bayan sallah la'asar insha'Allah saimu kaishi gidanshi na gaskiya." Jinjina kai Saleh yayi tare da kallon Sadeeq da idonshi zasu tabbatar maka kuka yayi yace "A samo mana abinda ya dace a mishi wanka." Jiki a sanyaye ya fita yana sako da wasu hawaye, a kullum Asas fad'i yake "Aure na shine silar warakata." Ashe wannan warakar yake nufi? Duk tunaninsu zai warke ne daga ciwon ashe warkewa ta har abada yake nufi, bayan wani lokaci ya dawo gidan a lokacin kowa yayi zugum anyi zaune kan tabarmi an shirya zaman makoki, yana kawo musu abubuwan buk'ata sheikh ya mik'e yana aje hularsa akan gadon, cire babbar rigar yayi tare cire machette na wuyan hannun rigar ya aje ya tattare hannayen, cire agogo yayi da takalminshi haka ma safar k'afarshi fara tas, sunkuyawa yayi ba tare da jin nauyin gawa ba ya tallabi Asas kamar yaro ya shiga dashi ban d'aki, akan tabarmar da Saleh ya shinfid'a ya aje shi a hankali kamar k'wai. Farin towel babban ya rufa mishi daga k'ugu zuwa gwiwanshi kafin yayi dubara ya cire mishi singlet d'in daya saka da wandon shaddar da kuma na ciki k'arami, fararen ruwan masu kyau da aka jik'a da ganyen magarya ya d'iba ya fara da bismillah zai mishi tsarki. *Kamar* jira ake dama a zuba mishi ruwan sai kuwa Asas yayi *zunbur* kamar dukanshi ne aka yi, abun ka ga namiji mai zuciya sam sheikh bai girgiza ba bare ya tsorata saidai idonshi kawai daya zaro yana kallon Asas daya mik'e haka kamar wanda aka maidowa rai da k'arfin tsiya. Kallon juna suke sosai Asas yana so yayi magana bakinshi ne yayi nauyi, hannu sheikh ya kai ya tab'a goshinshi yaji babu wani sanyi k'alau, a hankali ya kamashi ya mik'ar dashi tare da d'aura mishi towel d'in a k'ugu, d'aukar kayanshi yayi ya bashi yace "Saka wannan." Karb'a yayi hannayenshi sunyi mugun nauyi, lura da haka yasa sheikh kamo hannunsa hakanan suka fito zuwa falon, da k'arfi Saleh ya mik'e yana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Su ma mik'ewa sukayi har saida ya zaunar dashi bakin gado, kallon kallo suka shiga yi babu wanda yayi magna, sun jima haka kafin Asas ya d'aga kai ya kalli sheikh, kamar mai koyon magana yace "She..ikh...Au...rena,,,an d...aura?" Ruf sheikh ya rufe ido da kunyar kallon Asas yace ai kanshi aka maida auren, a hankali ya rab'a Asas ya zauna gefenshi tare da dafe gaban goshin shi, Alhaji Ibrahim ne ya kalli Sadeeq yace "Kira mahaifiyarsa." Da sauri ya fita inda Saleh kuma ya karb'i kayan dake jimk'e hannun Asas har yanzu ya saka mishi rigar, aje k'amarin wandon yayi ya durk'usa ya zura mishi dogon, yana cikin d'aure mishi zariya Hajia da Hafsat suka shigo tare, da farin ciki Hajia ta fad'a jikin Asas tana fad'in "Allah nagode maka, Allah ka yaye mishi wannan ciwo dake rabashi da rayuwa idan ya taso." Kamar baya fahimtar me ke faruwa haka ya kalli Hajia data d'ago yace "Hajia, Mimi...aure...an d.aura?" Tarrr! Hajia ta sauke ido a kan shi, saidai dake ita d'in ba masu kwalo kwalo bace sai tace "Ai tunda muka ganka kwance kamar gawa muka d'auka shikenan, har za'a fasa d'aura auren sai kuma na ce kar ayi haka ko dan ita yarinyar, shiyasa na ce a d'aura auren da d'an uwanka sheikh." Shi ma dai wani kallo ya bita dashi duk da ya gane hausar da tayi, amma sai yaji yana neman k'arin bayani a sauk'ak'e, ya jima haka kafin ya iya cewa "Hajia matata sheikh ya aura?" Girgiza kai tayi ta kamo hannunshi tace "A'a autana ba matarka ya aura ba, da matarka ce ai da bai aureta ba." A sanyaye murya na shak'ewa yace "Hajia matata ya aura, ni ne fa zan auri Mimi." Had'e fuska tayi tace "Ashraf Mimi dama *ba matarka* bace, baka ga gaba d'aya numfashinka saida ya bar gangar jikinka ba kafin ya auri *abar sa*? Ko kana so ka ce min baka yarda da hukuncin Allah bane? *Maryam matar sheikh* ce shiyasa ka lek'a lahira kafin ka dawo aka d'aura aurensu." Kamar zai fashe da kuka yace "Hajia hakan ba daidai bane, wannan hukuncin bai yi ba sam, ina son matata, ina son ta Hajia dan Allah a bani matata tunda dai ban mutu ba." Wata tsawa ta daka masa tana fad'in "Kai kanka d'aya kuwa? Ya auri matar ne zaka ce a mayar maka da matarka? Ita d'in yar tsanace ko wata abar wasa? Ko kumaa auren kake so kayi wasa dashi?" Alhaji Ibrahim ne yace "Maryama ba haka za'ayi ba." Kallon Asas yayi yace "Kai Ashraf zauna kaji." Cikin sako hawaye ya juya ya kalli sheikh da kanshi ke k'asa yana ta matse tafukan hannayenshi, shi kanshi fatanshi shine su amince ya sauke wannan nauyin dake kan shi, dan ba zai iya d'auka ba, ba zai yarda ya fara zaman aure da yarinyar da har ga Allah yake jin k'yamarta da kuma zarginta a ranshi ba. Zaune yayi k'asa kusan k'afafun sheikh yana kallon Alhaji Ibrahim daya gyara tsayuwarsa yace "Ashraf, kasan da cewa a duniya *wani* baya *auren* matar *wani*?" Cikin kuka yace "Eh Abba." Jinjina kai yayi yace "Sannan kaji ana cewa *matar mutum k'abarinsa*?" Jinjina kai ya sakeyi yace "Na ji Abba." Jinjina kai yayi yace "To ka yarda da wannan maganganun na hikima sannaan ka d'aura abinda ya faru akaan mizani sai ka bawa kanka amsa cewa *Mimi matar waye a cikinku*?" Alhaji Saleh ne yace "Gaskiya ne, haka Allah ya so shiyasa abinda ya faru har ya faru, duba da ita kanta yarinyar jiya guba tasha mai had'arin gaske, amma a k'arshe Allah ya tashi kafad'unta, sannan kai ma gashi ka d'auki awanni a doguwar suma, amma kuma aka sake ara maka numfashi Asas, wannan ya isa ya nuna maka dama can Mimi sheikh ne mijinta." Hafsat da Asas kallonshi suke kamar basa gane me yake fad'a, cikin magiya Asas yace "Yanzu kuna nufin na hak'ura kenan bayan ni ne zata aura? Shi fa ba son ta yake ba ita ma haka? Kenan auren dole kuka musu?" Hajia ce tace "Wane irin auren dole kuma? A duniya ina ga bayan matarshi akwai wani mahaluki da zai nuna maka sanin sheikh ne? Ai kasan b芒 zai k'untata rayuwarta ba." Cike da k'arfin hali da dakiya da kuma jarumta da son yin abinda Allah zai yarda da ita tayi k'ok'arin kawar da komai a tausashe tace "Gaskiya ake fad'a maka Asas, na tabbata da Mimi matarka ce da ka aureta ko da kuwa minti d'aya ne da d'aurawa kai kuma kabar duniyar, zaka fahimci ba matarka bace tunda har Allah yasa bata da rabon yi maka takaba, kuma da matarka ce da igiyar aure bata had'ata da *mijina* ba." Cike da tausayawa Hajia tace "To kaji yar albarka ma." Alhaji Ibrahim ne ya kalli sheikh yace "Sheikh ana ta magana ba ka ce komai ba." Wani wawan numfashi ya sauke ya d'aga kan shi ya kallesu, sake sunkuyar da kai yayi yace "Da zaku min lamuni a gaskiya dana sawak'e mata, bana son shiga hakk'in d'an uwana, bugu da k'ari ni ko ita babu maganar fahimtar juna a tsakaninmu." Hajia ce tace "Ka sawak'e mata? Ka mayar musu da yarinya bazawara kake nufi daga d'aura auren?" Da sauri ya kalleta yace "A'a Hajia, dana saketa sai a d'aura musu aure tunda babu iddata a kanta." Saleh ne yace "A gani na fa da Allah bai hukunta wani abu a tsakaninka da ita ba da haka bata faru ba." Alhaji Ibrahim ne yace "Ni ma abinda nake so suyi duba dashi kenan, amma suna rufe idonsu." Caraf Asas ya rik'e k'afar sheikh yana fad'in "Dan Allah sheikh ka saketa tunda kai ma baka son ta, sheikh na ci buri sosai wajen tsara rayuwata da Mimi, ka taimaka min dan Allah sheikh." K'ura masa ido yayi yana kallo yana sauraren magiyarshi tare da yanda shi ma zuciyarsa ke wani tsalle tana duka, da sauri ya mik'e tsaye tare kallon Asas yace "Ka shirya zamu tafi gidansu *yarinyar*." Jiki na b'ari Asas ya fara kakkarwa saka rigar kayanshi da Allah bai nufeshi da sakawa ba, sheikh ma takalminshi ya saka ya d'auki babbar rigar ya saka ya d'auki agogo ya zuba aljihu, hula ya d'auka ya d'ora a kai zasu fita Alhaji Ibrahim yace "Sheikh karka manta wani abu, kai babban mutum ne bai kamata kayi abinda zai tab'a kimarka ba." Saleh kam cewa yayi "Ba ma zasu tafi su kad'ai ba, muje tare dasu kawai Alhaji." Hajia ma cewa tayi "Ku jira muje na ga me zakuyi, wallahi ba zaka saki yarinyar nan ba." Zasu fita Hafsat ta rik'o hannunshi hakan yasa suka kalli juna ido cikin ido, marairaicewa tayi ta girgiza masa kai tace "Na yarda da kai, nasan ba zakayi abinda bai dace ba, kayi tunani mai kyau kafin ka yanke hukunci, sannan kayi tunanin makomar yarinya da iyayenta, sannan ka duba girman wanda ya umarceka da aurenta." Tana fad'a ta saki hannunshi tare da kaucewa a hanyar, jiki a sanyaye ta kashe mishi gabb'an jikinshi suka k'arasa fita, Asas dad'i yake ji za'a je a sakar masa matarshi ya aura, inda iyayen suke ciki zulumi da tunanin hukuncin da zai yanke. Saleh ne ya tuk'asu a mota d'aya suka tafi inda Hajia ke gaba sai su sheikh baya tare da Asas da Ibrahim. *Mu ci gaba* Da sauri Mimi ta d'ago ta sauke ido akan Iya Delu data fashe da kuka, sallalamin da gidan ya d'auka yasa Mimi ta shiga bin kowa da kallo, yanda ta bud'e baki tana lumshe ido alamar jiri na d'ibarta ne yasa Sahura saurin rik'eta ta shiga d'aki da ita, zauna da ita tayi akan gado tana yaye mata darar dake kanta, k'ura ma Sahura ido tayi tana kallonta, d'an girgiza kan ta Sahura tayi tana fad'in "Yi magana ina jinki." Kamar wata doluwa saikuwa tace "Aunty, Asas ya mutu? Da gaske ya rasu? Yau ne fa aurenmu, shi ne ya rasu ya barni." Fashewa tayi da wani kukan tare da k'amk'ame Sahura da suka kawo kai d'aya sanda take zaune ita kuma aa tsaye, daddab'ata ta shiga yi tana fad'in "Dangai dangai, dangai yar Abbanta, shiru karki masa kuka kinji." A sanyaye suka ji sallamar su Iya da yayar Malam sun shigo d'akin, amsawa su Asma'u sukayi hakan yasa Iya kallonsu tace "Yan mata, dan Allah ku d'an bamu wuri zamuyi magana da ita." Mik'ewa sukayi jiki a sanyaye cike da tausayi Asma'u har ta fara zubar da k'walla, Sahura ce ta rik'e hannun Asma'u ta mata alamar ta zauna kusa da Mimi, zaunawa tayi sai su Zeinaba da Salma da suka fita k'ofar gida, Sahura ma zaune tayi tana kallonsu Iya su ma suna kallon Mimi, cikin nutsuwa Iya tace "Mimi, *wani hanin ga Allah baiwa ne* ki yarda ubangijin daya halliceki shi yafi sanin abinda ya dace a game dake, Asas ba alkairi bane a gareki ko nace ba mijinki bane, shiyasa Allah ya d'aukeshi a sanda lokaci k'alilan ne ya rage ku zama d'aya a baki wanda ya fi shi cancantarki." Yayar malam ce tace "Gaskiya ne, kuma dama ai *matar mutum* k'abarinsa, ya mutu ne saboda babu rabon aure a tsakaninku." Dafe kan ta tayi da hannu tana sako hawaye tace "Kai na juyawa yake Iya, waye ya daceni? Waye ya fi Asas alkairi a gareni? Jiya ni na kusa mutuwa yau kuma shi ya mutu." A hankali Iya tace "D'an uwansa ne, sheikh." "Me!!!" Ta fad'a a razane tana mik'ewa tsaye kamar zata had'esu da ido, girgiza kai tayi cikin d'aga murya tace "Abdul? Ba zai yiwu ba bana son shi, ban shirya aurenshi, akan me za'a d'aura min aure dashi? Shi ne ya buk'ata saboda hukuntani akan k'aryar dana masa?" Kama hannunta Sahura tayi tace "Yi hak'uri Mimi ki zauna kinji, babban mutum ne fa mai ilimi, na tabbata ba zai wulak'antaki ba." Kallonta tayi tace "Kawai ni ma bana son shi ne aunty, bai min ba ko kad'an, *tsohon*?" Yayar malam ce tace "Ke kin ci uwaki! Waye tsohon? An fad'a miki namiji na kad'an ne ko yayi yawa?" Cire darar tayi ta jefa akan gado tace "To ni bai min ba, bana son shi ko kad'an, kawai a warware wannan auren." Zata fito Sahura ta rik'e hannunta tare da Asma'u, rarrashi suka shiga yi da nuna mata tayi hak'uri, Mama na waje tana saurarensu, saida ta ji abun ya bata haushi ne ta lek'o d'akin, kallonsu tayi tace "Iya dan Allah ku k'yaleta, idan mahaifin na ta ya dawo saita fad'a mishi a warware auren tunda haka take so." Sakin labulen tayi zata fito Abba da malam suka shigo tare da Abban Asma'u, gaisawa sukayi da mutanen dake nan suna taya juna murna da kuma jimami, d'akin suka wuce da sallama inda matan suka gyara musu suka zauna a kujerun da Asma'u ta d'auko ta aje musu. Kallon Mimi Abba yayi yace "Uwata, kin ga abinda ya faru ko?" Cikin kuka tace "Abba ni kawai a warware auren nan, Abba bana son shi wallahi." Da mamaki Abba yace "Subhanallah! Ba kya son shi? Me yasa?" A take tace "Saboda bai min ba, Abba sa'anka ne fa, ya zan auri sa'an Babana." Salallami suka d'auka a d'akin inda malam yayi dariya ya zura hannunshi yana fad'in "Zo nan amarsu." Mik'o mishi hannun tayi t taso ta zauna a k'asa kusa da k'afafunshi, cikin dattako yace "Amarsu wani ne ya fad'a miki tsoho ne shi? Dama ba'a auren tsoho ne? Miji irin wanda kika aura ba'a kiransa da tsoho saidai dattijo, dan dattijon arziki ne daga gidan dattijai, Mimina, ni dai banga abun a had'in nan ba ko kad'an, kiyi wa iyayenki biyayya ke ma sai Allah ya baki masu yi miki biyayya, kinji ko?" Fashewa tayi da kuka tace "Kakana baya so na, na tabbata ya karb'i aurena ne dan ya hukuntani." Abba ne yace "Hukuntaki kuma? Kar dai wata tsiyar kika tabkawa babban malamin nan." Turo baki tayi ba tace komai ba, Abban Asma'u ne yace "Mimi 'yata kiyi hak'uri kinji, tabbas can dama Allah ya tsara shi ne mijinki, karki damu kanki bare kiyi k'ok'arin cutar da kan ki, nasan kina da ilimi kuma kinsan cewa zab'in Allah shi ne daidai." Suna kan tattaunawar nan Rauda ta shigo da sallama d'akin, amsa mata sukayi inda tace "Abban Mimi kunyi bak'i a waje." "Su waye?" Ya fad'a yana kallonta, da kamar tsoro a fuskarta tace "To har da dai Asas, da kuma sheikh sai wasu guda b..." Bata gama fad'a ba Mimi tayi tsaye tace "Asas kika ce?" D'aga mata kai tayi ai da gudu tayi niyyar fita a d'akin tana fad'in "Asas kuma?" Rik'ota Abba yayi yana fad'in "Zubar mana da mutumci zakiyi? Maza zauna acan." Komawa tayi ta zauna kusa da Asma'u inda Abba ya kalli Rauda yace "Ki ce su shigo ciki." Sahura kuma darar Mimi ta d'auka ta shiga gyara mata ita a jikinta, an d'an d'auki minti biyu zuwa uku kafin suji sallama da gaisawarsu da mutane, har suna jin mama na tambayar Asas Hajia na fad'in "Haka Allah ya nufa, suma yayi saidai gaskiya bai tab'a mana irin haka ba." Muryar Mama suka ji tace "Ku wuce ciki suna nan." Da sallama a bukansu suka shigo inda Abba' Asma'u ya kalleta suka mik'e yana fad'in "Malam Adamu na ga magana ce ta cikin gida, zan jiraka a waje." Da girmamawa yace "Haba malam *Bashir* ni da kai ai mun zama d'aya, dan Allah ka zauna zaka iya wakilta ta ai." Komawa yayi ya zauna inda Hajia ma ta zauna bakin gado, mazan kuma duk kujera aka basu suka zauna, a hankali ta d'aga dararta dan so take ta kalli fuskar Asas d'inta, tana d'aga darar tare da idonta sai kuma idonsu suka had'e da nashi. Da sauri ta ja darar ta koma gabanta na fad'uwa tana turo baki tace "Bana son ka dai, ba zaka bar nan ba saika sakeni." Alhaji Ibrahim ne ya shiga fad'a musu duk abonda abinda ya faru daga farfad'owarshi har zuwanshi gidan, malam ne ya kalli sheikh yace "Yanzu kenan ya zo ya bata takardar saki a gabanmu ne?" Da sauri sheikh ya kalleshi sai kuma yayi k'asa da kai cike da kunya, murya a raunane Asas yace "Ku taimaka min dan Allah, ina da buri sosai akan matar da zan aura, ina ji a jikina samun lafiyata zai ta'allak'a ne da matata, ku taimaka min dan Allah iyayena." Ajiyar zuciya Saleh ya sauke yace "Idan hakane Asas kayi hak'uri da Mimi, a dangi akwai yara birjik sai ka zab'i wata a ciki." Saida ya share hawaye yace "Tarbiyar Mimi ta min a rayuwa, halayenta na fad'in gaskiya tana birgeni, Mimi tana da *wayewa* daidai gwargwado, saidai ba kowa ke fahimtar kalar wayewarta ba sai wanda ya zauna da ita." Kallonshi Asma'u tayi haka ma sheikh da yaji kamar ya gaura masa tapi a kunci, d'an satar kallonta ya sak茅 yi amma bai iya ganin komai ba a jikina sai jar darar kawai. Abba ne ya gyara zama yace "Indai wannan ne yasa kake so Mimi, ni nasan wacce tafi ta komai, me zai hana ka amince sai a d'aura muku aure?" Duk kallon Abba sukayi inda Asas yace "Wacece zata fi Mimi a wajena?" Kallon Asma'u yayi yace "Gata nan, k'awarta Asma'u." Da sauri ta yaye darar fuskarta idonta tas akan fuskar Abba, sai kuma ta kalli Asas sannan ta juya ta kalli Asma'u data mik'e tsaye dafe da k'irjinta, wani murmushi ta saki tare da sunkuyar da kan ta k'asa. Asas ma kallon Asma'u yake data mik'e tsaye, ba ta da wata makusa namiji zai iya cewa bata mi shi ba saidai in baka son kyakyawa kuma fara, d'an kallon sheikh yayi da shi ma yake kallonshi, a tausashe cikin ladabi yace "Sheikh kai ne babba, ka zab'a min abinda ya fi dacewa dani, idan ta maka na amince ka min wakilci." Yana fad'a ya done kanshi k'asa cike da Alhini, d'an murmushi sheikh yayi ya kalli Abba yace "Wannan karamci ne, mun gode sosai." Kallon Asma'u yayi yace "Kin amince a had'in nan? Ki fad'i abinda yake zuciyarki." Mimi da ta ji kamar da ita ake kai tsaye tace "Bai min ba, bana so." "Uwata." Yanda Abba ya kira sunan yasa ta saurin d'aga kai ta kalleshi, sai kuma ya fashe da kukan shagwab'a tace "Abba na fad'..." Mik'ewa yayi cikin fad'uwar gaba kar ta fad'i abinda take fad'a a bayan idonsu kamar zai mareta, cukuikuye Sahura tayi tana kwamtsa k'ara da fad'in "Abba zai kasheni." Hannunta ya kalla dake kan k'irjin Sahura wanda yayi masifar yi mishi kyau a cikin k'unshin nan gwanin birgewa, d'auke idonshi yayi yana d'an girgiza kai a hankali, Abban Asma'u ne ya kalleta yace "Asma'u." A sanyaye tace "Na'am Abba." Zubewa tayi k'asa gabanshi cire da taradaddin wannan abun, cikin nutsuwa yace "Me kika ce akan zab'in nan?" Satar kallon Mimi tayi ita ma a lokacin lek'en fuskar Asma'u take, sunkuyar da kanta tayi tace "Abba ku iyayena, kun fi ni sanin daidai da ba daidai ba, duk abinda kuka yanke a kai na daidai zanyi biyayya insha'Allah, amma..." Shirun da tayi yasa Abbanta yace "Amma me? Yi magana kinji." Kamar zatayi kuka tace "Ina so k'awata Mimi ta amince da zab'in nan, bana so ta kalli hakan a matsayin cin amana." Duk kallon Mimi akayi har da sheikh daya bita da kallon banza yana so yaji me zata ce, tabbas indai ta hanata aurenshi to zai sa yarinyar nan a bak'in jadawakinshi, dan shi kam Hafsat rainon gata ta masa bai saba da wahala ba, yakiceta zaiyi a jikinshi ba tare da shakkun komai ba. A hankali Mimi ta kamo hannun Asma'u ta zaunar da ita kusa da ita, kallon Asas tayi tace "Indai uwa ta gari ka ke nemawa yaranka to Asma'u ta kai ta zama uwar kowa, gareni ta zama aminiyar da babu kamarta, gareka miji nasan zata zamar maka b'aren jiki, bata da k'yashi a zuciyarta bare ta ji tana hassada da kai, tana so ne dan Allah kuma tana k'i ne dan Allah, duk wani mugun abu dana aikata a baya ita ce mai nusasheni, mun yi fad'a da ita bila-adadin akan na daina ba kyau, *Ashraf da ina da yaya namiji dana nema mishi auren Asma'u*, ko mahaifina bai mishi tayin aurenta bane saboda a gaskiya ba zan so ta auri *tsoho* ba." Dak'uwa Abba ya mata yace "Uwaki ce tsohuwar, mutuniyar banza." Dariya Iya da Sahura sukayi har da Hajia ma sai Asma'u data sinne kai, Mimi kam gimtse fuska tayi tace "Ko sanda nake cika baki ina nuna nafi k'arfin na auri tsoho, ita ce ke dakatar dani tana nuna min kamar fariya nake, ashe gaskiya take fad'a tunda gashi na auri *sa'an babana*." Da sauri sheikh ya kalleta yace "Allah ka yafe min akan ashar d'in nan da zanyi." Jinjina kai yayi yace "Jar uba! Wai dama haka rashin kunya da fitsarar yarinyar nan ta kai? Lallai ashe dai *kallon kitse* nayi ma rogo ban sani ba." Numfashi Hajia ta sauke ta kalli Mimi tace "Kiyi hak'uri kinji takwarata, shi ma ba tsoho bane zaki gane haka gaba kad'an." Cikin k'arfin hali Asas ya d'aga kai ya kalli sheikh yace "Hajia tsoho ne mana kar ki sa ya ji dad'i a ransa." Kallon Mimi yayi saidai ba da waccen idon ya kalleta ba, a yanzu yanzun nan da idon ke *matar yayana* ce ya kalleta yace "Matar yaya karki yarda kin ji, idan kuma ana da ja ba tsoho bane ya cire hularshi mana." Dariya suka saka a d'akin bai da Mimi da Asma'u da kuma sheikh, Ibrahim ne yace "To yanzu ya zamuyi kenan? Za'a sake saka wata ranar ne kafin a d'aura musu aure?" Da sauri Asas yace "A'a dan Allah Abba, ni dai kawai a d'aura mana aure yanzu idan sun amince, bana so a k'ara jan lokaci wani abu ya biyo baya." Jinjina kai Saleh yayi ya kalli Bashir yace "Abban Asma'u ya kace?" Nuna Abban Mimi yayi yace "Ga uban yarinyar ai, duk yanda yayi wallahi d'aya ne." Abba ne ya gyara zama yace "A gani na kamar yanda ya buk'ata, indai akwai shedu da sadaki kawai a d'aura." Alhaji Ibrahim ne yace "To ina ga ai kamar maganar maza ce, muje waje sai mu tattauna." Mik'ewar da sukayi yasa Mimi kallon sheikh da tambayar kanta "Wai ba zai sakeni ba yake nufi?" Da sauri tace "Abba shi f..." Kallon da Abba ya mata yasa tayi shiru, cikin fad'a yace "Wai ke kina lafiya kuwa? Me yake damunki ne Mimi?" Fashewa tayi da kuka ta fad'a jikin Iya tana fad'in "Abba na fad'a maka ni bana so wallahi, kawai a sawak'e min." Wani uban rank'washi ya zuba mata a kai daya sata d'agowa dafe da gurin tana lumshe ido da suke rufe mata k'arfi da yaji, hannu ya kai kamar zai mareta yana fad'in "Ke dan ubanki har kinyi tsaurin idon da a gabana zaki dinga fad'in a sakeki? Yaushe aka d'aura auren Mimi, ina wasa dake ne da z..." Malam ne yace "Dan Allah wuce m没 je zaka tsaya kana biye mata." Hajia ce tace "Wai kuna nufin yanda zaku mata kenan idan mun barta a hannunku? A halin da take ciki kuma har ta cancanci duka da fad'a irin haka? Gaskiya ba zai yiwu ba jama'a." Kallon Iya tayi tace "Mama dan Allah ki mana alfarma yau kam 'yata ta tare a gidana kafin mijinta ya sama mata gurin da zata zauna." Cike da dattako iya tace "Wannan ai ba matsala bane Hajia, tunda dama ai a yau d'in ake da shirin tarewarta." Da fara'a Hajia tace "To a shirya mana ita zamu d'auki abarmu, dan nan kam naga matsi zata sha." D'an dungure ma Mimi kai Iya tayi tace "Gwara ta tafi ai ko na huta da jarabar taurin kan ta, dan in nan zata zauna saina fasa mata jikinta da duka." Da raha Hajia tace "Ai na ga alama ne Iya." Malam ma cewa yayi "Hajia kin kyauta min da zaki d'aukemin amaryata daga gurin sak'agunan nan, abinda suka iya kenan su sakata gaba suyita narka." Duk wannan rahar da suke su sheikh na tsaye na saurarensu gaba d'aya jikinshi ya mutu jin hukuncin da Hajia ke ta yankewa a kan shi, haka suka fita Mimi kuma ta sake b'allewa da kuka, Asma'u ma duk da halin da take ciki saida ta taya su Iya rarrashinta, a k'arshe dai wajen kukan nan baccin wahala ya d'auketa dan wajen kukan har jan numfashi take sama sama. Ai kuwa suna fita a masallacin unguwar sukayi sallah la'asar, ana sallamewa mutanen dake nan aka tattarasu aka d'aura auren Asma'u Bashir da Ashraf Sabi'u Aliyu Sharif, tuni unguwa aka d'auka kowa ya shiga fadin abinda ya ji ya kuma k'ara da abinda ya fahimta a kai, haka dai gidansu Asma'u ma sai suka fara wani shirin daban suma, inda kishiyoyin mamanta suka shiga bak'in cikin wannan had'i musamman da aka ce sheikh ne yace zai mata lefe bayan ta shiga d'akinta, tunda shi ma Asas ne yayi wa matarshi馃榿, abun bai musu dad'i ba ko kad'an sai ma da aka ce yau ita ma zata tare tunda dai da lallenta da kitsonta, ango kuma ya gyara d'akinshi to babu abinda za'a fasa. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:55 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *27* Sosai dangi suka ci gaba da bikinsu saidai kusan duka angaye da amaren zuciyoyinsu babu dad'i, Sadeeq kan shi yayi wani iri a zuciyarshi da ya ji an d'aura auren Asas da wacce yake da burin aura, amma sai bai nuna ma kowa ba kawai suka ci gaba da shagalinsu, Asas ma sosai yake k'ok'arin nuna dauriya amma abun ya gagara, yayi kuka sosai na rashin Mimi, yana tunanin yanda zai fara rayuwa da wacce sam ba ita ce a tsarinshi ba, sannan ya rayu a kusa da sheikh da matar daya ci burin aura, a wuni d'ayan nan duk sai ya zabge ya fita hayyacinshi, kana kallonshi zaka san yana da damuwa. Haka ta b'angaren Mimi ma ta kafe ta k'i cin duk abinda aka bata ta k'i shan komai ta fad'a ta nanata ita fa asa sheikh ya saketa, tun ana bata maganar har akayi banza da ita aka ci gaba da sabga, labari kuma ya karad'e gari da kewayenshi, sheikh Abdul Waheed yayi aure amarya shakaf, wasu na fad'in dalilin auren wasu kuma a iya auren suke tsayawa. Amma a wajen k'awayen Mimi abun ba haka bane, sosai suke Alhini da kuma son ganin yanda Mimi zata rayu a gidan sheikh, wacce take wanda suka auri tsoho iskanci, ita me fad'in Allah ya rabata da auren sa'an babanta, yau gashi ta samu a b'agas ba fahimtar juna ba soyayya? Abun kam ya jijjigasu inda kowace jiki yayi sanyi tare da komawa gefe dan suga me zai faru. *D'aukar amarya* Ta wajen Asma'u kam motoci ne manya da k'anana guda goma sha hid'u suka d'auki dangi da abokan arziki aka nufi da ita gidanta cikin yada magana, kayan jikinta kawai aka d'aukar mata dan dama Asas yace baya buk'atar komai. A wajen uwata Mimi kam saida Abba ya nunata da bakin muciya kafin ta fito a gidan, mota uku Hajia ta turo a d'auketa a had'a da wanda zasu rakata gidanta kafin ranar tarewarta, a mota saida ta cika kunnen shi kan shi dreba dan kuwa kuka take sosai tana kiran "Mama, mama ke, mama, wayyo mama." Har suka isa gidan Hajia dangi suka tarbeta aka sauketa a d'akin da Hajia ta ware mata wanda aka saka mishi komai na buk'ata, k'arshe dai kowa ya tafi ya barsu ana addu'ar fatan zaman lafiya da zuri'a ta gari. Kusan ba kowa a gidan kafin Hafsat ta zo dan su tarben matar Asas suka tafi, sanda ta samu Mimi aa d'aki kuka take sosai kamar ranta zai bar gangar jikinta, cike da tausaya mata ta zauna gefenta da k'yar tana cije fuska dan sosai ta gaji ga cikinta da take jin bak'in abubuwa da bata saba ba, saida ta dafa kafad'arta cikin taushin murya tace "Mimi." D'an tsagaitawa tayi amma dai bata yi shiru ba, d'orawa tayi da "Mimi kuka kike dan an aura miki sheikh?" Shashek'a ta shiga saukewa da sauri sauri, jin batayi magana ba yasa ta sake fad'in "Mimi ki kwantar da hankalinki kin ji ko, nasan waye mijina ba zai tab'a cutar dake ba, ki bani had'in kai mu zauna lafiya dake kinji Mimi?" D'aga kanta tayi ta kalleta ido sun mata jajir sun kumbura tace "Dan Allah ki sa mijinki ya sakeni, ba zan iya zaman aure da shi ba, bana son shi kuma ba zan so shi ba." Wani murmushi tayi mai ciwo tace "Mimi zaki so shi, ni ma da fari haka na d'auka, Mimi ko kinsan ni da sheikh *auren je ka ga d'akin ka* aka mana, ban sani ba shi ma bai sani ba dan a lokacin ma yana madina wajen karatu, mahaifina ya kwanta rashin lafiya kawai aka kira sheikh ya dawo gida, yana zuwa suka taramu suka fad'a mana ai sun d'aura mana aure, gidanmu kawai suka turamu muka fara zama." Numfashi ta sauke tace "Mimi ke ma idan kika nutsu kika wa iyayenki biyayya zaki ga ribar hakan, ki daina wannan tashin hankalin hakan zai tab'a zuciyoyi da dama wanda ba zasu tab'a mantawa ba har abada, musamman iyayenki da suke ganin sun isa dake, amma a zahiri sai nunawa kike kamar kinfi k'arfinsu ko kuma dai basu isa su umarceki ba, ya kike so mutane su kalleki? A matsayin 'ya wace ta raina iyayenta bata jin maganarsu?" Jikinta kam yayi sanyi dan haka ta dakata da kukan ta sake kallonta tace "Ban raina iyayena ba, hasalima ina fad'a da duk wanda ya raina min su, indai har abinda nake yi a yanzu yana nuna rashin girmamawa ne ga iyayena, to na daina, zan musu biyayya iya iyawata da yardar Allah." Murmushi Hafsat tayi tace "Yawwa *yer uwa*, ko ke fa, ki share hawayenki kinji ko." Jinjina kai tayi tasa hannu tana share hawayen, yunk'urawa Hafsat tayi da k'yar ta tashi tsaye tana fad'in "Wallahi ga gajiya ta baibayeni ga kuma nauyin da cikin nan ya min." Da kallo kawai Mimi ta bita har tace "Saida safe Mimi, kiyi alk'awarin kin daina kuka." D'an murmushin yak'e tayi tace "Na daina." Da kallo ta bita har ta fita tana jin anya kuwa zata iya abinda matar nan tayi? Tab'e baki tayi a ranta tace "Indai kuka na alamu ne na raina iyayena ai na daina har abada, amma wallahi sai mijinki ya shiga *uku* dan zai ga tab'ara." Cikin shashek'ar kukanta ta d'aga kai ta shiga kallon d'akin, ajiyar zuciya ta sauke da tunanin yau ita ce zata kwana a nan? Wacce take shinfid'a bargo ta kwanta, ba panka sai iskan Allah dake kad'awa, yau gata a d'aki mai ac lak'e ga kuma panka, gyara dararta tayi ta kwanta ta dunk'ule sosai tana ci gaba da sauke ajiyar zuciya. *Asas*! Shi ne sunan daya diro mata a lokacin, da yanzu fa tana d'akinshi a matsayin matarshi, amma shi ne yanzu take zaman matar sheikh k'awarta kuma tana gidan Asas a matsayin mata, lallai inba hukuncin Allah ba me zai juya wannan al'amari haka, ai ko cewa akayi ka tsara dole zaka buk'aci dogon nazarin ta yanda abun zai kasance, amma gashi dake yin Allah komai ya canza kuma da wanda ya so da wanda bai so ba dole an hak'ura da yanda Allah ya tsara. *Asa-Ma'u* Tunda ya shigo gidan dare ya tsala sosai ya buga tagumi yana kallon Asma'u dake dunk'ule cikin k'aton hijabi ta had'a kai da gwiwa, baisan ta ina zai fara ba ko kad'an, a yanda ya tsara da Mimi shi ne zai mugun riritata. Ganin zaman shirun ba zai masa ba sai kawai ya sake k'ureta da ido yace "Asma'u." A hankali ta d'an d'ago kanta tana jan majina da share hawayenta, a sanyaye ya sake fad'in "Muje muyi sallah ko?" Jinjina kai tayi tare da k'ok'arin sauka a kan gadon, ita ta fara shiga tayi alwala ta fito shi ma ya shiga, sallah sukayi inda ya dafa kanta yayi addu'ar neman alkairin dake tare da ita da kuma neman tsarin dake tare da ita, mik'ewa yayi ya fita hakan yasa ta mik'ewa ita ma ta koma bakin gadon ta zauna tayi tagumi, "Allah sarki Mimi." Shi ne abinda ta fad'a, wa yayi tunanin canzawar abubuwa haka? Sosai take taisaya ma k'awarta musamman data tabbatar ba zatayi saurin duk'awa k'asa ta yarda da zab'in nan ba...Shigowar Asas ta sata saurin juyawa ta kalleshi, d'auke yake da tire da k'aramin faranti a sama, gefenta ya aje tare da fad'in "Bismillah." Girgiza kai tayi cikin dakusashiyar murya tace "Na k'oshi." Wani kallo ya mata cike da kawar da komai yace "Kina son d'ure ne?" Girgiza kai tayi alamar a'a, fuska a had'e yace "To ci." Jiki a sanyaye ta kai hannu ta d'an tsakuri naman ta kai bakinta tana rarraba ido saboda yanda ya tsaya yana kallonta, murmushi yayi tare da zaunawa kusanta ya saka hannu shi ma ya shiga d'auka yana ci yana saka mata a baki ita ma. Suna idawa ta koma ban d'akin ta wanke hannaye ta kurkure baki ta fito, ganin baya nan sai kawai ta kwanta a kan gadon da zunbulelen hijabinta, ya d'an jima bai shigo ba har bacci ya d'an fara d'aukarta, kamar daga sama ta ji an bud'e d'akin da sauri ta bud'a ido amma bata juya ba, shi kuma yana ganin haka saiya kwanta gefenta yana karanta addu'a bacci. *Shei-Haf* Hannu ya kai zai bud'e k'ofar d'akin amma saiya tsaya cak saboda muryar Aisha da ya ji tana fad'in "Amie wai me yasa Hajia tayi mana haka? Kuna zaman lafiyanku ke da Abie zata had'ashi da wata, me yasa bata hak'ura ba ta sake samun wani saurayin ta aura, Abien mu ba son ta yake ba ita ma haka, idan fa a dalilin auren nan matsololi suka fara faruwa? Ni gaskiya Amie ba zan juri wata yarinya ta raina min uwata ba, kawai ki fad'a ma Abie ya saketa can ta samu wani ta aura." Bud'e k'ofar yayi sanda Hafsat ke k'ok'arin yi mata tsawa, kallon daya jefi Aisha da shi yasa sunkuyar da kai tana fad'in "Sannu da zuwa Abie." Cikin yanayi mai rikita bil-adam yace "Sannu da zuwa Kike min Aisha? Ke!" Yanda ya fad'i ke d'in yasa ta d'aga kai sai kuma ta sake sunkuyar dashi tana d'an wasa da maganin cowon k'afafun data gama shafawa Hafsat, cikin b'acin rai yace "Eesha ke ce da fad'ar wad'annan maganganun a bakinki? Yaushe kikayi girman da har magana mai girma irin wannan zata fita a bakinki? Kina so ki ce min taya uwarki kishi kike kenan?" Da sauri Hafsat ta kalleshi da mamakin abinda ya fad'a, sai kuma tayi k'asa da kan ta ita ma ba tace komai ba, a tsawace yace "Tashi ki bani wuri, kuma na sake jin bakinki na magana kan abinda bai shafeki ba ki kuka da kanki." Mik'ewa tayi jiki na b'ari tayi hanyar waje, tana daf da fita yace "Ke!" Tsayawa tayi ta juyo tana d'an sunkuyawa, cikin murd'add'iyar murya yace "Zan d'aura aurenki da Anas ki fara shiri akan haka dan kowane lokaci zan iya d'aura muku aure." Da sauri ta kalleshi ido waje baki bud'e, cikin rud'ewa tace "Abie Anas kuma?" Sama da k'asa ya harereta tare da zaunawa bakin gadon kusa da k'afafun Hafsat da ita dai take jin su da kallonsu, ganin bai kulata ba sauta mik'e tana maimaita Anas a ranta, ta sani bai da wata makusa yaro ne mai k'ok'arin neman ilimi a duk inda yake, d'aya ne a cikin almajiran mahaifinta, yana da ladabi da biyayya sosai suna kallonshi kamar yaya saboda sheikh na d'an sakewa da shi, wasu lokuta ma har karatu yake d'ora mata, to amma ai babu wani tsari na soyayya a gabanta a yanzu, to me ma ya jawo maganar aurenta? Dan kawai ta yi wannan maganar? Ko dai mahaifinta na tsoron kar zamanta a gidan yasa a samu matsala idan amaryarshi ta zo gidan? Babban fargaban shi ne yanda bai saka lokacin ba kawai yace a kowane lokaci, hakan na nufin rana tsaka zata iya jin an d'aura mata aure kenan? Kallon Hafsat yayi bayan fitar Aisha ya kai hannu kan cikinta yace "Ya kuke?" D'an murmushin yak'e tayi tace "Lafiya lau, ya hidima?" Numfashi ya sauke ya gyara zamanshi sosai yace "Manga, kin ga me ya faru a yau ko? Hakan ya sake tabbatar mana ba mu ke da ikon juya rayuwarmu a yanda muke so ba, k'arin aure Allah ne ya halatta mana shi, sai dai a yanda na wa k'arin ya zo a birkice sai naji hankali ya kasa d'auka, tabbas Hajia uwa ce a gaareni data isa zartar da kowane irin hukunci a kaina, saidai a wannan karan qta yanke min hukunci mai tsaurin gaske." Numfashi ya sauke ya kalleta yana rik'o hannunta yace "Sawwama, na so a ce idan lokacin nan yayi na shawarce, na rarrasheki kamar kowace mace, sannan na miki bajinta kamar yanda ake yi a al'adance ta hanyar kyautatawa, amma duk da haka *Qawwama* ina mai baki hak'uri da yanda abun nan ya zo mana, nasan ke mai hak'uri ce da kawar da kai ga kuma juriya, kiyi hak'uri da hukuncin mahaifiyarmu mu yi mata biyayya, ni dama ke ce k'ashin bayana kuma martabata, dan Allah ki yafe min kinji." Wani sanyayyen murmushi tayi tace "Hak'uri wai akan me kake bani sheikh nawa? Ni babu abinda ka min wallahi, sheikh karka manta fa na tab'a maka k'orafin k'ara aure amma sai ka ce lokaci ne baiyi ba, to yanzu lokacin ya zo ni kam zai saka ka tsaya kana bani hak'uri?" Da k'yar ta gyara zama tana fad'in "Idan dai a yanda abun ya zo ne karka damu kan ka, ni Hafsat ina bayanka ba zan tab'a bari a rasa zaman lafiya a gidanka ba insha'Allah." Murmushi yayi yace "Nagode Hafsy, yanzu fad'a min me kike so?" Dariyar tsokana tayi tace "Dokin wuya." Dariya yayi tare da mik'ewa ya durk'usa gabanta yace "Hau muje kinji ta wa." Dariya tayi sosai tace "Na yafe, wace ni dan zan haye wuyan babban malami a daren nan?" Wani shu'umin kallo ya mata yace "Ke a mai d'akin shehi mana." Gyara zama tayi tana yatsina fuska tace "Hakane, amma ai mala'iku ma zasu iya yin hushi dani." Cike da kulawa ya dafa cikinta yace "Ba kya jin dad'i ne?" D'an k'aramin tsaki tayi tace "Gaba d'aya cikin nan ya daina min dad'i yanzu, bansan me yasa ba." Cike da alhini yace "To kinga ki shirya gobe sai muje asibiti ko?" Jinjina kai tayi dan dama ba musu take mishi ba, ko tana so ko bata so indai yace ayi to yi kawai zatayi. *Asabar* Tun asuba da Hajia ta tashi Mimi a bacci ta ji zazzab'in dake jikinta, saida tayi sallah ta kawo mata magani tasha, kallon Hajia tayi da tunanin anya kuwa? Ta ya zata fara shan magani a gabanta? Bata son magani a kai saboda d'aci, karb'a tayi tace "To." Fita Hajia tayi hakan yasa Mimi d'aukar maganin ta jefa ta windown dake jikin gadon, d'an kurb'a ruwan tayi tare da komawa ta kwanta tana dunk'ulewa, ta d'auka bacci zai d'auke ta saidai sam zafin jikinta da kakkarwar da take ga ciwon kai sai suka hanata samun baccin. *08:00* Hajia ta turo Salamatu data zo tace ta kira Mimi ta zo tayi kari, tana shigowa d'akin da yatsina fuska ta tunkareta, yanda ta ganta a kwance ta d'auka bacci take har take fad'in "Hmmm! Yar matsiyata kenan an samu wuri, ga lafiyayyen gado ga ac na hura miki iska mai tafe da sanyi, kinga har da wani baccin safe take alhalin iyayenta na can na fama da rana a tsakiyar kansu." Duk bala'in ciwon da take ji saida ta yaye hijab d'in ta tashi zaune, wani kallon tsana da k'yama ta shiga jefawa Salamatu, ba wai ita mai aiki ba ko Hajia ce ta fad'i haka wallahi saita narka mata magana kafin ta tattara ta bar gidan, kamar yanda ta ji ita ce tasa aka aureta to saidai ta sa a bita da takardarta gida. Gyara zama tayi sosai cikin muryar wahala da jigatuwa ta kalli idon Salamatu tace "... _Wannan page gaba d'aya sadaukarwa ce gareki *Bilkissu Kanar*, Allah ya saka miki da alkairi._ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *28* Gyara zama tayi sosai cikin muryar wahala da jigatuwa ta kalli idon Salamatu tace "Gaskiya ne, saidai na ga dasu iyayen nawa da ke ma d'in duk a kanku ranar ta fito ai, tunda babu wanda ya tara dukanku nema kuma, kuma gwara iyayena tunda neman nasu yana wadata zuciyarsu, ke kuma fa? Dubeki kamar ba'a gidan masu kud'i kike aiki ba tsabar bak'ar zuciya, amma dubeni..." Ta fad'a tana nuna mata fatar jikinta tace "Duk da a cikin talauci muka taso sannan babu kyakyawan rayuwa, amma hakan bai hana fitowar hutu a jikinmu ba saboda wadatar zuci, kinga Baaba bansan ki ba, amma ya zama na k'arshe da zaki dinga huce haushina akan iyayena, bana d'auka wallahi." Murgud'a mata baki tayi tare da gyara kwanciyarta ta sake rufewa a cikin hijabi, da mamaki Salamatu data nemi daskarewa ga wani shakkun yarinyar ta zabura tayi waje, saida ta kai falon kawai ta fashe da kuka ta d'ora hannaye saman kai, hankali tashe cikin fad'uwar gaba Hajia ta tarbeta tana fad'in "Salamatu lafiya? Me ya faru da Mimin? Me akayi?" Cikin kuka kamar zata tsaga gidan tace "Hajia tunda na ke ban tab'a ganin fitsararriya kuma marar kunyar yarinya irin wannan ba, da girma na da mutumcina a gidan nan, duk zaman mutumci da amanar da muke daku ace yarinyar can daga zuwanta gidan nan jiya zata tsaya tana zagina tana min iskanci." Cikin jin haushin dogon sharhin Hajia tace "Wai me ya faru ne? Me ta miki da kike mana wannan kukan?" Ba tare data tsagaita kukan ba tace "Hajia daga shiga na tasheta kawai ta kama fad'a min magana wai bansan darajar mutum ba, hada fad'a min ina aiki gidan masu kud'i amma talauci ya k'i barina saboda abun a zuciyata yake, ni? Ni? Salamatu shi ne har da nuna min jikinta take wai ita yar talakawa ma ta fini kalar hutu." Me Hajia zatayi banda kecewa da dariya, girgiza kai tayi tana dariya kawai ta wuce d'akin Mimi ta bar Salamatu tsaye, da kallo ta bita na mamaki tace "Me ye abun dariya kuma?" Saida ta ga shigewarta d'akin sai kuma ta zaro ido tace "Kar dai ta fad'a mata abinda na ce?" Da sauri ta nufi madafa hannu a kai tana fad'in "Na shiga uku na lalace." Hajia na shiga da sallama Mimi bata iya amsawa ba, da sauri ta k'arasa ganin sai kakkarwa take, tallabota tayi cikin tsananin tashin hankali tana fad'in "Subhanallah Mimi! Dama zazzab'in nan bai rabu da ke ba har yanzu?" Saida ta gyarata ta zauna kafin ta kalleta da tausayawa tace "Wallahi na d'auka tunda kika sha maganin bacci kike, ashe zazzab'i ne yayi k'amari." Jiki na rawa ita ma ta shiga lalubar poshet d'inta da take yawo da ita ko a cikin gida, waya ta ciro tana fad'in "Bari na kira sai muje asibiti ko?" Lambar sheikh ta dannawa kira wanda a lokacin yake d'akin karatunshi da na'urarshi a gaba yana kurb'a shayin da Hafsat ta kawo masa, d'aukar wayar yayi a sauk'ake ya furta "Salam." Da sauri Hajia tace "Wa'alaika, sheikh kana ina ne?" Jim ya d'anyi kafin yace "Hajiarmu lafiya dai ko? Ina gida ban fita ba." Da sauri tace "Yawwa dan Allah ka zo yanzu, kaga Mimi ce wallahi zazzab'i tun asuba kuma tasha magani amma bai sauka ba, shi ne na ce gwara aje asibiti." Shiru yayi kamar bai ji ba ko kuma ba da shi take ba, wani numfashi ya sauke dan yana tashi da asuba ya tuna kan shi fa nauyin mace biyu ne yanzu, a hankali kuma a gadarance yace "Gani nan zuwa." Jiki na rawa Hajia tace "To sai ka zo." Kashe wayar tayi ta kalli Mimi data koma ta kwanta, sunkuyawa tayi ta shafi kuncinta tace "Sannu kinji takwara, kiyi hak'uri yanzu *mijinki* zai zo sai muje asibiti." Da k'yar ta d'aga idonta ta kalleta har sun canza mata launi, cikin son dole sai tayi magana ta rik'e hannun Hajia tace "A'a, a'a Hajia, bana so, bana son zuwa asibiti, ki ce yayi zamansa dan Allah na rok'eki." Zaune tayi gefenta tace "To banda abun ki Mimi an tab'a zama da ciwo haka? Zazzab'i bala'i ne takwarata, tsaf yanzu zai rabaki da jininki sai an koma tarbata ana k'ara miki." Sake jimk'e hannun Hajia tayi tace "Ni dai idan kika zuba min ruwa a jikina ma zanji sauk'i, bana son zuwa asibiti wallahi, kana zuwa allura suke maka." Komai Hajia ba tace ba sai mamatsa hannun Mimi data dinga yi, a k'alla minti ashirin ya kawoshi gidan, kai tsaye d'akin ya shigo da sallama a bakinshi, da sauri Hajia ta amsa sai Mimi da tayi ram da k'ugun Hajia cikin muryar galabaita tana fad'in "Karki bari ya kaini asibiti kin ji uwata, bana so wallahi na tsani allura, idan kika bari ya tafi da ni ba zan zauna gidanki ba." Yanda take cumimiye k'ugun Hajia yake kallo ita kuma tana ta murmushi, kujerar gaban madubi yaja ya zauna yana kallon Hajia, ita ma kallonshi tayi tace "Ya zamuyi yanzu? Tace bata son zuwa asibiti." Wani kallo ya wurga mata duk da ba fuskarta yake gani ba yace "Dama ba dan tana so zamu kai ta ba." Kallon Hajia yayi yace "Ku shirya sai mu tafi." Dariya Hajia tayi tace "Ba dani zaku tafi ba, dan har yanzu akwai bak'in da basu tafi ba." Kallon Mimi tayi data dunk'ule tace "Tashi ki gyara hijabinki sai ku tafi." Girgiza kai tayi alamar a'a, wani kallo kawai ya shiga bin ta da shi, cikin muryar da babu wasa a ciki yace "Jiranki fa nake, ina da abun yi." Gabanta ne ya shiga fad'uwa da k'yar ta yunk'ura ta d'ago, a kan shi ta sauke idonta wanda shi ma a kan ta na shi idon suke, da sauri ta sinne kan ta saboda wata irin kunya data kamata, ko a tv bata tab'a ganinshi da kaya irin na yau ba, zallar d'inki ne kawai riga da wando tazarce sai hula a kan shi. Ganin kallon da yake mata yasa Hajia mik'ewa tace "Bari na sama mata ko madara da zata saka a cikinta." Fita tayi ba tare da ta ji me zai ce ba, rawar da jikinta ke yi ne ta k'aru sai ta rasa yanda zata yi ta sauka a kan gadon, murya a dak'ile yace "Jiranki nake malama." Hijabi tasa tana murza ido cikin kukan shagwab'a tace "Ni bana son zuwa asibiti, na warke fa babu abinda yake damuna." Mik'ewa yayi tsaye yace "Ke." Da sauri ta kalleshi dan indai y'a ce ke dole ka kalleshi, da sauri kuma tayi k'asa da kan ta sanda yake fad'in "Sauko a gadon nan kafin na tsula miki tsumagiya, kinsan haushinki ne dani ko?" Da sauri cikin rashin k'arfin jiki ta shiga saukowa a kan gadon, saida tayi tsaye k'afafunta na mata rawa sosai ta kalleshi tace "Abdu..." Gumtse bakinta tayi sai kuma tace "Yallab'ai, dan Allah idan munje karka bari su min allura." Wani firgitacen kallo ya mata daya razanata yace "Har a baki sai na ce a miki ko zaki daina yin k'arya." Da sauri ta shiga nuna mishi da hannayenta tace "Na daina ai tun ranar, wallah..." Sake zaro mata ido yayi shi yasa tayi shiru saai kuma tace "Tun waccen ranar na daina, ba zan sake ba Allah ko." Yatsina fuska yayi yace "Wuce muje." Silipas d'inta dake gaban gadon ta zura k'fafunta tayi gaba jikinta na rawa gab-gab-gab kamar ba zata iya tafiyar ba, saida ta kusa kaiwa k'ofar fita yace "Miye wannan kuma malama?" Juyowa tayi sai taga ashe yana tsaye inda yake, dudduba jikinta ta shiga yi ganin bata ga komai ba saita kalleshi da alamar tambaya, cikin murtuke fuska yace "Wannan hijabi ne a jikinki?" Duk'ar da kanta tayi tana kallon hijabin daya saukar mata har wuce gwiwoyinta, d'agowa tayi da mamaki tace "Hijabi ne mana." A take cike da gatsali yace "Bai min ba, canza shi." Galala tayi da baki ta kalleshi, ganin bata da niyyar yin abinda yace yasa shi cewa "Na ce ki canza shi ko?" Turo baki tayi cikin sangarta tace "Ai duk sauran ma haka suke, kuma ba duka kayana bane aka d'auko." Tab'e baki yayi yace "To nik'ab fa?" Baki bud'e ta kalleshi tace "Nik'ab kuma? Ni da ba lafiya gareni ba?" Cikin wurga mata harara yace "Dan baki lafiya sai aka ce jikinki abun talla ne?" Gumtse bakinta tayi ta sinne kan ta, sama da k'asa ya harareta yace "Shi waccen sharb'eb'en da kike sakawa sai kina son nuna ta Allah ce ke ko?" Takowa yayi da sauri yana fad'in "Muje, amma ki sani dole ki canza tsarin shigarki, dan wannan bata min ba." Kaucewa tayi da sauri ya bud'e k'ofar ya fita sannan ta bi bayanshi, tana fitowa haka tayi ta jan hijabinta tana rufe fuskarta saboda bak'in dake nan wasu na ta haramar komawa inda suka fito, gaishesu tayi a ladabce suka amsa tare da fatan sauk'i a gareta. Tana fitowa daga falon ya shiga hangenta daga zaune da yake a motar, kamar wai ba ita ce yake jira ba take wata tafiya kamar wahainiya, yo shi ko Hajia ma ta tab'a sashi jiranta kamar haka kuwa? D'auke kai yayi daga kallonta yanaa d'an jan guntun tsaki. Baya ta kama zata bud'e ya juyo ya kalleta, saki tayi ta koma gaba ta bud'e ta shiga, kakkauran hannunshi ta kama wanda agogon hannun ta cikashi dam, d'auke idonta tayi a ranta tace "Hummm!" Saidai yanda ta fad'i humm! D'in yasa shi kallonta dan ta fito, saida ya juyar da kan motar zasu fita ya kalleta yace "Miye?" Kallonshi tayi tace "Ba komai." B芒 tare daya kalleta ba yace "Ban son k'arya, ki tabbatar kinsan me zaki dinga fad'a min kinji ko." K'wafar da yayi yasa ta saurin cewa "To." A ranta kuma tana sake k'iyasta yanda ta wani shiga mota d'aya da mijin aurenta, mijin ma kuma tsoho sa'an babanta, yanzu nan a ganta da k'uruciyarta sai kawai ta ce shi ne mijinta, wasu k'walla ne ta ji sun taho mata tare da saka yatsarta ta share kawai tana kallon titi ba mai ma kowa magana. Yana paka mota kamar jira take tayi saurin fita ta tunkari asibitin, cikin dak'ilalliyar murya yace "Ke!" Lumshe ido tayi a ranta tace "Ohhh! Wai wani ke! Miye haka dan Allah." Juyowa tayi a hankali tana kallonshi a ladabce, da ido ya mata alamar "Tsaya a gefena." Take fuskarta ta nuna alamar rashin jin dad'i, juyawa tayi ta d'an shiga kallon mutanen dake kai kawo, tana cikin yatsina fuska kamar yasan me take tunani yace "Kunya kike ji a ga kin jera da *tsoho a matsayin mijinki*?" Kumbura fuska tayi da baki tare da jan hijabinta ta rufe daga bakinta har zuwa hanci, k'wafa yayi tare da wucewa gaba yana fad'in "Bansan rashin kunyarki ta kai haka ba Ryam." Ita dai biyarshi take yi a baya yana shiga lungu da sak'o na asibiti, ganinshi a asibitin yasa duk ma'aikatan da suka ganshi suke gaisheshi da girmamawa, wani matashin ma'aikaci ya tambaya Dr. Rakiya? Dan haka da kan shi ya musu iso zuwa ofishinta dan tana tsaka da duba mata da suka kama layi, sanda zai shiga ofishin ne ya kula bata bayanshi, juyawa yayi saiya hangeta nesa dashi sai wani rufe fuska take, jinjina kai yayi a zuciyarshi yana fad'in "Ba dai ni kike jin kunyar jerawa dani ba? Zaki gane baki da wayo." Shigewa yayi ofishin ya zauna yana karb'an gaisuwar Dr. Rakiya, saida suka gama gaisawa kafin Mimi ta shigo da sallama k'asan mak'oshi, Rakiya ce kawai ta amsa tana sakar mata murmushi, sosai take kallon yarinyar wacce jiya labari ya karad'e gari sheikh ya aura ko kuma an aura ma sheikh ita, dan har hotonta ta gani wanda aka had'a ita da Asas amma Allah bai nufa ba. Tsaye tayi tana kallon kujerar da zata zauna wacce ke fuskantar sheikh dake zaune, hannu ta kai zata ja kujerar baya taa zauna sheikh yace "To ke da zaki fad'a mata abinda ke damunki, ya kuma zakija baya *Mari*?" Kallonshi tayi kamar ta gaura masa mari domin ta fahimci so yake ya cizgata a gaban mutane, kaikaitawa tayi ta d'an tsoma mazaunanta tana kallon likitar, murmushi ta sakar mata tare da d'aukar katin marasa lafiya tace "Madame sunanki?" Saida ta ja hijabinta sosai kafin tace "Mimi...au! Maryam." K'ura mata ido yayi kamar mai burin rikitata yana sakin murmushin mugunta, Mimi kam data fahimta ko kallonshi ba tayi ba har likitar tace "Sunan mahaifi?" A sanyaye tace "Uban kowa." Da sauri ta d'aga kai ta kalleta haka ma sheikh daya sake kafeta da ido, sai kuma yayi murmushi ya d'an d'ago daga jinginar da yayi tare da kai hannunshi ya lalubo hannun Mimi a cikin hijabi ya rik'o, a razane ta kalleshi tare da k'ok'arin k'wacewa, sai kuma ya jimk'e hannun gam yana mata murmushi, ba tare daya daina wannan murmushin ba yace " *Innar Issa*, sunan Babanmu zaki fad'a mata kinji, ki daure ki fad'a mata." Kyab'e fuska Mimi tayi ta fashe da kuka dan ta lura kawai ci mata mutumci ne ma zaiyi, wai babansu? Sa'an Abba ne fa amma yake cewa babansu, d'auke kanshi yayi daga kallonta ya kalli likitar yace "Dr. Ki saka Maryam Adam Shehu, shekaru 18." Da sauri ta fizge hannunta tace "Abdul ban kai 18 ba fa, 17 ne wallahi." Da sauri sheikh ya cije leb'enshi na k'asa sakamakon dariyar data nemi kubce mishi, hannu ya kai akan hab'arshi yana d'an saita kanshi tare da rik'e dariyar. Rakiya kam zaro ido tayi a ranta tace "Tofa! *auren yarinya* kenan." Duk'ar da kanta tayi tana rubuta abinda ta tambaya, d'agowa tayi ta mik'owa Mimi abun d'aukar zafi, karb'a tayi tare da marairaicewa tace "Dan Allah ba zaki min allura ba ko?" Murmushi ta mata tace "Ba zan miki ba indai zazzab'inki bai kai matakin ba." Sheikh dai na kallonta sai k'ok'arin saka abun awon zafin take, saidai dake tun kayan jiya ne jikinta da suka matseta sai hannunta ya k'i shiga bare ta saka abun ya zauna mata a hammata. Lura da haka yasa Rakiya fad'in "Ko ki zage zip d'in rigar? Dan naga kamar ta kamaki sosai." A hankali ta aje abun d'aukar zafin ta zura hannayenta baya ta fara kiciniyar cirewa, sheikh kam takaici ne ya kamashi da tunanin haka take saka kayan kenan ita ma kamar dai 'yan zamani. Kamar da wasa sai ko yasa hannu biyu ya jawo gaba d'aya kujerar da take zaune wanda hakan ya haddasa bayar da k'ara akan tiles d'in 'kiiiiiiii! Zaro ido Mimi tayi ganin yanda ya jawota kamar wata beby duk da girmanta, bata gama sarewa da lamarinshi ba saida ya zura hannayenshi a cikin hijabinta ya kaisu a bayanta ya shiga lalubawa inda zai ji zip d'in. Tuni Mimi ta fara kakkaucewa tana babbank'arewa, zafin da yaji a jikinta yasa shi jin kamar ya cire mata rigar gaba d'aya ya rumgumeta a jikinshi ko ya samu damar d'auke mata zafin, saida ya ji ya rik'e zip d'in ya ja shi a hankali tare da sake matsawa daf da ita a kunne ya rad'a mata "Tsofaffi ba ruwansu tunda ba sha'awa garemu ba, miye na d'aga hankali daga cire zip na riga." D'aukar abun awan zafin yayi tare da d'aga hannunta ya soka mata ya had'e mata hannun sannan ya ciro hannayenshi daga hijabin, Mimi kam addu'a take kar Allah ya d'auki ranta da mamakin tsohon nan, wata tambaya ta jefawa kan ta "To wai me yake nufi ne?" Gemunshi kawai ta k'urawa ido mai d'auke da farin gashi d'ai-d'ai, saida taji tinnnn! D'in abun awon zafin ta d'an zabura ta kalli likitar data tara mata hannu, cirowa tayi ta mik'a mata ta duba, mik'ewa tayi tana fad'in "Bari mu gwada jininki mu gani." K'ura mata ido Mimi tayi ganin ta d'auki d'an shud'i abu k'arami ta cire a gidanshi sai kuwa tsinin allura ya bayyana, zabura tayi ta mik'e tsaye tana saka kukan shagwab'a da fad'in "Bana so ni dai na fad'a miki tun farko, Abbana, Abba ma ya san bana son allura wallahi." Ganin tana shirin zabgawa da gudu yasa shi mik'ewa ya tura kejarar baya, hijabinta ya rik'e yana kallon fuskarta duk ta rud'e yace "Innar Issa ya haka? D'an tsikara miki ne fa za'ayi ba zafi, haba mana *'yan matan tsohonta*, so kike a mana dariya ne." Dariya Rakiya keyi inda Mimi ta shiga tsatsare k'aramin bakinshi da ido wanda bak'in gashi ma yake hanashi fitowa da kyau,wasu hawaye masu zafi ne suka taho mata akan kumatu, ba tare data d'auke idonta a cikin nashi ba murya a raunane tace " *Bawan Allah*, amma dai ai saida na fad'a maka bana so ko?" Wani daban yake ji shi wallahi a lokacin a wani sake sakayau, ga isashen lokaci ga kuma wata k'uruciyarshi da yake jin ana neman dawo masa da ita baya, babu masu fad'in gafarta malam, babu ranka shi dad'e, babu sheikh ko malam, babu kurantawa da girmamawa mai cike da kambamawa, babu amsa umarninshi cikin d'aukakawa. Hasalima a nan shi ne ke k'ak'arin rarrashi, kai tsaye ake kallonshi ana fad'a masa abinda akayi niyyar fad'a, yau gashi har yake iya bada umarni sau biyu, bugu da k'ari ma har yayi magana kai tsaye aka ce a'a ba haka bane, wanda ko cikin wa'azi da dubannin mutane ke kallonshi da saurare aka samu akasi da ajizanci na d'an adam ya fad'i ba daidai ba kai tsaye ba'a katseshi, wani saidai bayan an tashi ya fad'a ko kuma a kirashi a waya ko kuma dai a rubuta mishi wasik'a. Wani k'ayataccen murmushi ya sakar mata tare da jawota gaba d'aya ta kusa fad'awa jikinshi, d'an kashe mata ido d'aya yayi yace "... _Sadaukarwa ga duk 'yan *duk nisan jifa* da kuma *matar mutum*_ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *29* Wani k'ayataccen murmushi ya sakar mata tare da jawota gaba d'aya ta kusa fad'awa jikinshi, d'an kashe mata ido d'aya yayi yace "Kin fad'a min 'yan matana, amma ai lafiyarki tafi komai a wajena." Kallon ka tausaya min ta bishi da shi sharrr hawaye na dararowa a idonta, Rakiya dake kallonsu ce tace "Malam ko dai a bata magani ne? Dan naga kamar ba zata bari mu d'auki jininta ba bare muga zazzab'i me take." A hankali ya kalli Rakiyar saidai bai ce komai ba dan abinda ya fahimta shi ma kenan, kuma shi dai ba zai iya dagewa ya matseta a jikinshi ba, ganin haka ya tabbatarwa Rakiya me yake so, dan haka ta koma ta zauna mazauninta ta shiga duba magunguna da dama ake ajewa wasu na zazzab'i ne na rigakafi, Mimi dai na kallonta a ranta fad'i take "Shi ma ba sha zanyi ba, dan kin bar abinki ma kin bawa wani." Sheikh ta mik'a tare da fad'a mishi yanda zata sha, godiya ya mata ya mik'e hakan yasa Mimi mik'ewa ita ma, shigewa yayi gaban yayi da Mimi ke fad'in "Sai anjima." Da fara'a Rakiya tace "Sai anjima madame, daure a sha magani fa." Murmushi kawai tayi ba tace komai ba har suka fice, yanzu ma dai nesa da shi ta tsaya har saida ya shiga mota kafin ta k'arasa da sauri ta shiga ita ma, a d'an hassale ya kalleta yace "Wai kunyar me kike ji na jerawa tare da ni? Ryam abun k'yama ne a jikina?" Da sauri ta zaro ido baki bud'e tace "Ni? Wallahi ba ha..." Hannu ya kai kamar zai bugi bakinta yana fad'in "Komai zaki fad'a sai kinyi rantsuwa, me yasa babu gaskiya a lamarinki ne wai?" Mar-mar-mar! Tayi da idonta tare da nok'e kanta kamar wata mage tace "Kayi hak'uri to na daina." K'wafa yayi ya aje mata ledar maganin a cinyarta yana yi wa motar key, kallonta ya sake yi sanda yake k'ok'arin hawa kan titi yana fad'in "Ni ne kika kalli idona a gaban kowa kika kira tsoho ko?" K'wafa yayi yana jinjina kai, cikin turo baki ta d'anyi gunguni hakan yasa shi hararanta yace "Me kika fad'a?" Girgiza kai tayi alamar a'a, wani mugun kallon ya mata yace "Na fad'a miki ki koyi fad'an gaskiya, bana son k'arya Ryam ina tsanar mai yin ta, dan alamomi a cikin alamar munafiki." A hankali ta jinjina kai alamar gamsuwa, saida ya d'auki hanya kamar an bar zancen sai kuma ya kalleta yace "To yanzu fad'a min me kika fad'a?" A d'an gigice ta kalleshi a ranta tana fad'in "Matsalar tsofafin nan fa kenan jinini." A zahiri kuma cewa tayi "Ina tsoron na fad'a kayi hushi." K'uri ya mata da ido yana kallo sai kuma ya d'auke kanshi yace "Ba zanyi ba, zan kwatanta halin annabi Muhammad (S.A.W), har ma na had'a miki da halin dattijon arzik'i sahibin fiyayyen halita Abubacar Siddiq, bayan banyi hushi ba har sai na yafe miki ma sannan na miki kyauta." Baki sake tace "Dukana zakayi?" Kallonta yayi yace "Bana duka, saidai akwai hanyoyin da nake ladabtar da marasa jin magana irinki." Kallon titi tayi tana d'an kumburo baki, kamar daga sama ya sake fad'in "Ina jinki fa." Kallonshi tayi tasa hannu da hijabinta ta rufe bakinta, cikin muryar rad'a tace "Dama kawai...cewa nayi..ai sa'an Abbana ne." Da sauri ya kalleta ita ma da saurin ta fashe da kukan shagwab'a tace "Ai ka ce min ba zaka dakeni ba, kuma kai ka ce na daina yin k'arya." K'ank'ance idonshi yayi tare da d'auke kai yana girgizawa, kawai ya tabbatarwa kan shi wannan bata cika shekara sha takwas ba, shi kam ya zaiyi da ita yanzu? Shiru sukayi suka ci gaba da tafiya har ta gaji da kukan sakarcin ta daina, saida yaji tayi d'ip ya d'an saci kallonta, yanda ta rakub'e tare da dunk'ule jikinta tana kallon titi zai tabbatar maka har yanzu bata jin dad'in jikinta, murya a d'an dak'ile yace "Zan baki kyautarki zuwa gobe insha'Allah." Jinjina kai tayi alamar to, da haka suka isa gidan, a farfajiyar ya sauketa ta tunkari shiga ciki, da kallo ya bita har ya hangi Hajia ta tarbeta tana ta tab'a jikinta, lumshe ido yayi ya bud'e ya feso iska yana fad'in "Ina ma baki lalata k'uruciyarki ba." Jingina yayi a kujerar motar ya sake lik'e idonshi, a hankali abinda ya faru a asibitin ya fara dawo mishi, a gaskiya ya tabbatar mace ce har da k'ari, dan kuwa a yanda yaji indai ba gizo ko rud'un zuciya bane, to yaji komai ya nuna kuma a tumbatse yake. Wani dogon tsaki yaja sakamakon tuna waccen ranar da aka mata tereren nan, hakan na matuk'ar tayar masa da hankali, yana jin zafi da kuma d'aci a zuciyarshi idan ya tuna k'aramar yarinya kamar waccen tasan ta bayar da kanta a bata kud'i tayi sutura mai kyau da tsada sannan ta rik'e k'atuwar wayar da mahaifinta zai iya jan jari har da d'aukar nauyin gkdan shi ma. Saida ya ga b'acewarsu ita da Hajia sun shige falon kafin ya ja motar ya bar gidan shi ma. A falo Hajia ta zaunar da ita duk da har a lokacin akwai sauran mutane, abinci tasa aka kawo mata dan ta ci tasha magani, saidai rashin k'warin jiki da d'and'ano a baki ga kuma kunya yasa ta kasa cin komai, sai madara ta d'an sha ita ma saida yan uwan Hajia suka sa baki. Magani Hajia ta b'alla ta mik'a mata, girgiza kai tayi kamar zatayi kuka tace "Um um." Harara ta cilla mata tace "Ban gane um um ba, takwara karb'i nan kisha kafin kiji a jikinki." Karb'a tayi amma ta rik'e a hannu ta kasa sha, cike da rarrashi Hajia tace "Yawwa yar albarka shanye kinji, saboda lafiyarki ne ai, ko kina so ciwo ya kwantar dake ayi ta d'irka miki allurai?" Girgiza kai tayi alamar a'a, wata tsohuwa dake zaune sun gama shirin tafiyarsu ce tace "Ki barta ai kar ta sha, idan zazzab'i ya kayar da ita ni ba abinda zai hanani yi mata siraci da ganyen darbejiya." Murmushi Hajia tayi tace "Haba Hajia ai ba za ayi haka ba, amarya guda ta kwanta rashin lafiya kuma bata arzik'i ba." Kallon Mimi tayi tace "Kinga yar albarka shanye kinji, dubi fa guda uku ne kawai." Cikin marairaicewa tace "Idan nasha amai zai sakani ne." Girgiza mata kai tayi tace "Ba zakiyi ba kinji, idan kika saka a ranki zakiyi ne shiyasa kike yi." Sake marairaicewa tayi ta d'an d'aga hannunta tana so tasha, sai kuma ta sauke tana rintse idonta, ganin haka yasa Hajia kallon wata yarinya a cikin yaran bak'in tace "Ke Khadija tashi madafa d'auko min muciyar nan ki gani, na ga ita ma kamar d'an gidana ne wajen rashin son magani." Dariya mutanen d'akin sukayi inda Mimi ta shiga rarraba ido tana kallon hanyar madafar da yarinyar ta nufa da kuma Hajia, tsohuwar nan ce tace "Shi ma fa haka yake bai son magani, kuma kai gashi Allah ya jarabeka da ciwo." Cike da jimami Hajia tace "Ki bari kawai Hajia, Ashraf idan zai sha magani saina titseyeshi da mabugi kafin yasha." Da mamaki wata ta kalleta tace "Mabugi fa? Da girman na shi?" Cike da tabbaci Hajia tace "Wallahi kuwa, har yau har gobe idan zai sha magani sai raina ya gama b'aci na rik'e abun duka." Kallon Mimi tayi tace "Da fari da yake fad'a min aurenshi zai zama silar warakarshi na d'auka ke d'in zaki jajirce ne wajen kula da maganinshi, ashe kema kamar shi d'in ne a rashin son magani." Dariya tsohuwar tayi tace "Ashe da an taru an lalace." Sunkuyar da kai Mimi tayi dan k'awarta ce kawai ta zo mata a rai, "Ko ya ta kwana a gidan?" Shi ne abinda ta tambaya, cike da k'arfin hali ta d'aga kan ta ta jefa k'wayar magani d'aya a baki ta kora da ruwa da sauri, tana had'ewa ta sake jefa sauran idonta duk a rufe kamar zatayi amai, tana had'ewa aje kofin tayi tare da mik'ewa dan nufa masaukinta, kallonta Hajia tayi cikin tausayi da tunanin maganar Asas da akayi ne ta jawo mata sabon yanayin, rik'e hannunta tayi tace "Kinyi waya da mamanki kuwa?" Girgiza kai tayi a hankali tana jin amai na taso mata, da d'an mamaki tace "Me yasa to? Ya kamata ki kirata ki gaisheta, kinsan uwa mace tana kwana cikin zulumi da fargaba a ranar da aka d'auki 'yarta zuwa gidan wani da sunan aure." A hankali ba tare da ta fahimci zancen Hajia ba tace "Bana da waya ne." Zaro ido tayi tace "Ba kya da waya? A'a ai wannan kafin kiyi aure kenan, yanzu wuce ki kwanta zan kira *mijinki* na fad'a masa." Da wani irin kallo Mimi ta bita kafin ta d'auke kanta tana jin kamar ta d'ora hannu a kai tace "Wayyo ni wayyo kaina." Wai mijinta, mutumin daya haifeta shi ne ake kira mijinta? Ohh wannan wace irin rayuwa ce? Da k'yar ta kai kanta d'aki ga aman dake taso mata ga kuma rashin k'warin jiki. Tana shiga da gudu ta shige ban d'aki ta sako aman nan, kaf maganin da tasha ta amaye kafin ta kuskure baki ta fito ta kwanta a galabaice. *Asa-Ma'u* Da safe daga gidan Hajia aka aika musu da abun kari, bayan sun karya kuma Asas ya fita ya bar gidan ba wata hira a tsakaninsu, da fitarshi ba jimawa yayarta Rayya ta zo gidan bisa umarnin mamansu, kayanta data zo mata dasu ta shiga gyara mata har da wasu kayan aiki na mata da mamanta ta tara mata da kwanukan cin abinci, saida ta gama gyara mata komai a lokacin k'anwar Mamansu ma da kuma yayarta suka zo. Sosai Asma'u ta ji dad'in zuwansu dan sun mata nasiha da nuna mata tayi hak'uri sannan ta shiga jikin mijinta amma fa ba da fitsara da bud'ewar ido ba, anan har suka d'an dafa mata tamtabaru ta ci aka bata zuma tasha, da taimakon Rayya sukayi girkin rana mai rai da lafiya dan kauan abinci babu abinda babu, haka suka ci suka k'oshi suna raharsu har saida sukayi sallah la'asar suka tafi, lokacin ita kuma ta shiga d'ora girkin dare a nutse ta fara da gyara namanta, duk da ba wani girki ta iya na zamani mai kyau ba, amma dake Mimi uwar jaye-jaye ce da shige shige, wannan ma data d'ora yanzu Mimin ta ga sun tab'a yi ita da Maimuna shiyasa ta fara, hakan yasa ma sai taji kewar k'awarta da tunanin ko me take yanzu? Ya take a sabon gidan data samu kanta? Daf da magriba ta kammala ta gyara komai ta tsaftace gidan kamar ba tayi ba, ganin magriba ta gabato sai tayi alwala ta fara yin sallah, tana idawa ta shiga wanka tana jin kamar kar ta fito a ban d'akin, har yanzu zuciyarta ta kasa yarda ita ce a wannan daular, ta kasa yarda ita ce ta auri mijin da k'awarta tayi muradin samu, ta kasa yarda ita ce dai Asma'u ta auri Asas namijin da har k'awayensu gulmarsa suke wajen had'uwarsu akan komai. Tana fitowa a sauk'ak'e ta shirya cikin shaddar da sukayi ita da Mimi da niyyar suyi shigar bikin Mimi da ita a musu hotuna kafin su canza na d'aukar amarya, saida ta gama shirinta a tsanake lokacin har an gama sallah isha'i ta fito falon tana baza k'amshinta. Cak ta tsaya gabanta ya buga da k'arfi sakamakon ganin Asas zaune yana kallo fuskarshi a had'e sosai, rarraba ido ta shiga yi da tunanin me za tayi? K'amshin turarenta ne ya kai mishi a hanci da sauri ya juyo inda yake jin k'amshin, yana ganinta yayi saurin lumshe ido tare da hango surar Mimi a idonshi, farar fuskarta mai d'auke da dogon hanci da kakkauran labb'a da matsakaitan ido, ajiyar zuciya ya sauke tare da bud'e idonshi a hankali ya sake kallonta, k'ak'aro mata murmushi yayi tare da mata alama da hannu "Zo." A hankali cikin ruwan sanyi ta k'arasa tana daddafe cikinta dake motsawa, tana zuwa gefenta ta tsaya kusa da k'afafunshi ta zauna k'asa, da sauri ya nuna mata kan kujera yace "Zauna a nan." Girgiza kai tayi alamar a'a, shiru yayi ya na d'an kallon fuskarta da tayi kwalliya mai sauk'i ko gira bata zana ba, shi kuma a yanda yake son matarshi ta kasance mai cab'a kwalliya da ado ne kamar ba gobe. Jin bai ce mata komai ba yasa ta bud'a bakinta daya mata nauyi tace "Ina wuni?" A dak'ile ya amsa da "Lafiya lau, ya gida." Kasa amsawa tayi dan duk a duburburce take, sam bata tab'a ganin irin wannan had'ewar a tare dashi ba, kullum tsakaninsu wasa ce da raha irin ta mijin da k'awata zata aura da kuma aminiyar amaryar da zan aura, mik'ewa tayi kamar an cijeta ta kalleshi tace "Na kawo maka abinci ne?" D'aga manyan idonshi yayi ya kalleta, sai kuma ya mayar da kallonshi kan tv yace "Um." Da sauri ta juya hakan yasa shi bin bayanta da kallo, wani murmushi ya saki mai kama da kuka saboda tuna yanda *lokaci* yayi k'uli-k'ulin Rakiya da shi ya canza masa komai, duk da bai tab'a mata kallon daya wuce k'a'ida ba kula bata tab'a tsayawa gabanshi cikin shigar rashin kamun kai ba, amma dai a yanda yake ganin sittin saba'in a cikin hijabin Mimi yasan ba k'aramin kaya ta mallaka ba, duk da kuwa ita ma Asma'u tana da su saidai kawai a *barwa rai abinda ya ke so.* Kan k'aramin table ta aje kwanukan ta shiga zuba mishi hannayenta sai rawa suke, tana idawa ta aje mishi gabanshi ta koma gefe a k'asa ta zauna, cikin jin haushi ya kalleta yace "Ya zaki dinga zama a k'asa? Koma sama." Da sauri ta mik'e ta zauna kan kujerar tana mayar da kanta k'asa, jawo plate d'in yayi ya fara cin abinci a wani yatsine kuma a yangance, ita dai da ta ji ta k'osa da zaman sai ta mik'e tace "Da wani abu da kake buk'ata na yi maka ne?" Wani irin kallo ya jefa mata yace "Kamar me?" Yanda ya mata tambayar yasa Asma'u saurin durk'usawa tace "Kayi hak'uri." Mik'ewa tayi har tana had'a hanya ta bar falon ta shige d'akinta, da kallo ya bita sai kuma ya d'an ja tsaki ya ci gaba da cin abincin dan ba laifi ya masa dad'i a baki. Yana idawa yasha ruwan data zuba mishi ya mik'e da kanshi ya d'auko lemu a fridge ya dawo ya zauna, kallo ya shiga yi tare da giccirawa yana kuma tunanin abinda ya faru ranar *juma'ar jiya* wacce ta gigita mishi komai na shi, bai gushe a nan ba saida 11:00 ta buga kafin ya mik'e ya kashe komai ya nufi d'akinshi, shiryawa yayi cikin kayan bacci kafin ya dawo d'akin Asma'u dan kawai ya zauna d'akin kar ya bar yarinyar mutane ita d'aya. Yana shiga tuni ta jima da baccinta a cikin doguwar rigar bacci, kitsonta ya fito ras dan d'an kwalin ya fad'i, kashe fitilar yayi ya kwanta gefenta ba tare daya rufa da zanin data rufa ba. *Mim-Sheikh* Bayan sallah azahar Shapi'a ta zo gidan ganin Mimi, yanda ta sameta babu lafiya sai taji kamar ta mata kuka, Hajia ma cikin zulumi da jimami take fad'in "Kin ganta wallahi da zazzab'in nan ta kwana, tasha magani na d'auka yayi sauk'i ashe a banza, kuma sun je asibiti ta ce ba'a mata allura ba, ta sake shan magani da k'yar amma har yanzu jikin." Kallon Mimi Shapi'a tayi tace "Mimi da bata son magani, anya kuwa tasha?" Cikin rashin sani Hajia tace "Na fari dai bata nayi na fita, amma bayan dawowarsu daga asibiti a gabana tasha." Cike da kallon tuhuma ta kalli Mimi tace "Kin tabbata baki amaye shi ba Mimi? Na fa sanki a kan magani." K'asa tayi da kanta tana layi tana so ta koma ta kwanta, Hajia ma dake kallonta cewa tayi "Kenan da gaske maidoshi kikayi?" Shapi'a ce tace "Tabbas indai Mimi, da wuya ai ta had'e magani ya zauna mata." Hab'a Hajia ta rik'e tace "Oh Allah! To kinga ko mijinta zan kira ya maidata asibiti a k'ara mata ruwa ko allura?" Jinjina kai Shapi'a tayi tace "Gaskiya kam, dan a hankali yanzu nan tsaf zata rasa jini a jikinta." Waya Hajia ta ciro zata kirashi Mimi tasa kuka tana fad'in "Dan Allah karku fad'a masa, aunty ai kinsan Mamana jibda take shafa min ko? Dan Allah ki ce karta kirashi a shafa min jibda zan daina." Dakatawa Hajia tayi ta kalleta tace "Kin tabbata?" Cike da tabbaci tace "Wallahi jibda Mamana ke shafa min duka jikina saina daina." Juyawa Hajia tayi zata fita tana fad'in "Abu mai sauk'i, dana sani ma tun tuni da ba an wuce wajen ba." Fita tayi sai Shapi'a data kalleta tace "Yanzu Mimi me ke anfanin haka? Kina bak'unta ma amma sai an gane halinki na taurin kai?" Turo baki tayi tace "Amma aunty ai kuma kunsan bana son magani ko." "Mun sani Mimi." Ta fad'a tana tsareta da ido tare da d'orawa da fad'in "Amma ko dan bak'uwar fuska ai sai ki sha." Sake turo baki tayi tace "Ai nasha maidoshi ne nayi." Jinjina kai tayi tace "Dama zuwa nayi naga ya kika kwana, mamanki da tace ma ba sai na zo ba tunda dai b芒 gidanki bane aka kawoki, ni dai nace sai na zo dan bai kamata ace babu wanda ya zo dubaki ba kamar wata marar dangi." Kyab'e fuska tayi tace "Aunty ita Mama sai yaushe zata zo?" Zaro ido tayi saidai kafin ta bata amsa Hajia ta shigo rik'e da kwalbar jibda babbar a hannunta, tana zuwa mik'awa Shapi'a tayi tace "Gashi to shafe mata jikinta." Karb'a tayi tana dariya da fad'in "Kina ji da ita ko? Wai yaushe mamanta zata zo?" Dariya Hajia tayi tace "Mamanki zata zo amma bayan tarewarki gidan mijinki." Hira sosai suka sha har kusan la'asar Shapi'a bata tafi ba kuma sosai jikin Mimi yayi sauk'i dan har wanka tayi ta canza kaya, Hajia na mamaki sosai yanda ita jibda ce maganin zazzab'inta duk da tasan dama tana magani da dama. 10:30 daidai ya kawo k'ofar gidan, mai gadi na bud'e mishi zai shiga kawai ya tuna da akwai fa wani nauyi a kan shi, tunda suka dawo daga asibiti bai sake sanin abinda ke faruwa ba, dan ko Hajia basuyi waya ba saboda hidimar dake gabansa, juya akalar motar yayi dan ba zai yarda hakk'in k'aramar yarinyar nan ya zamar masa babban nauyin da zai kasa saukewa ba. "Bawan Allah..." Wannan sunan data ambata ne ya dawo a kunnuwansa, wani k'asaitaccen murmushi ya saki tare da sake murz sitiyarin dan yau kam shi kad'ai ya wuni yawo a gari yana fad'in "Marar kunyar yarinya kawai, gata yar firit amma firita ce a jininta." Da wannan ya isa gidan su Hajia tare da tunkarar falon kan shi tsaye... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *30* A tausashe ya rabka sallamar da tasa Salammatu amsawa tana kimtsa zamanta daga kallon tv, kamar zata nutse k'asa dan girmamawa ta shiga, gaisheshi, da girmamawa shi ma ya shiga amsa mata dan ba yarinya bace, cike da kulawa yace "Hajia tana ciki ne?" Nuna mishi d'akin Mimi tayi tace "Ta shiga ciki zata dubata." Da ido ya amsa alamar to tare da nufa d'akin, da kallo ta bishi da mamakin yanzu nan fa aka barshi da yarinyar can fitsararriya sai ka ganta da ciki wata rana, tab'e baki tayi tana mayar da kallonta kan tv da fad'in "Maza ho." K'wank'wasa k'ofar ya fara yi daga ciki Hajia tace "Waye?" A sanyaye yace "Ana." Da fara'a tace "Shigo sheikh." A hankali ya bud'a k'ofar tare da d'ora idonshi akan Hajiar dake tsaye, bai yarda ya kalli inda ya tabbatar tana nan ba saida ya gama gaisawa da Hajia, cikin sakin fuska take fad'in "Da na ga dare yayi ai na d'auka ba zaka zo ba, kuma dana tuna kai ne fa sai na sa a raina zaka zo komai dare." Wani lallausan murmushi yayi tare da d'an shafa sajenshi yace "Hajiarmu kenan, sabgogi ne dayawa, har zan shiga gida kuma na taho." Da fara'a tace "Allah sarki, Allah ya bada ladar d'awainiya." "Ameen." Ya fad'a tare da d'an kaikata idonshi ya kalleta, da sauri ya ji zuciyarshi ta fara bugawa, doguwar riga ce a jikinta ta bacci mai laushi, kan ta kuma babu d'an kwali sai gashinta data d'aure, jibda ce take k'ara shafawa a jikinta gaba d'aya. Tunda ya shigo bata kalleshi ba, kuma sam bata da niyyar zata kalleshi sai murzawa hannayenta jibda take, d'an cije leb'enshi yayi na k'asa kafin yace "Ya jiki?" Sai lokacin ta d'aga kai ta kalleshi, a cikin ranta tayi k'wafa tuna abinda ya mata a asibiti da tunanin "Zan rama, sai na mayar da kai kamar *kakana*." Sakin fuskarta tayi tace "Da sauk'i *malam*." K'uri ya sake mata da ido da nanatawa a ranshi "Malam?" Hajia dake ta murmushi tana kallonsu ne ta d'an gyara murya tace "Bari na baku wuri ko." Da wani matsiyacin sauri Mimi ta kalleta tace "A'a Hajia, ba abinda zai min." A lokacin shi ma yayi saurin juyawa cike da kunya yana fad'in "A'a Hajia, saida safenku." Amma jin abinda Mimi ta fad'a sai yasa ya tsaya ya sake juyowa, sai kuma ya jinjina kai ya juya zai fita, bayanshi Hajia ta bi tana fad'in "Dama ina son magana da kai." Da kallo Mimi ta bisu da addu'ar "Allah yasa ta masa maganar wayata, ina so na samu waya." Suna fita a falon ta zauna a kan kujera, tunda ta ga ya zauna a k'asa ya tabbatar mata yau uwa ake da ita kenan, dan akwai ranar da zasu zauna kan kujera ita dashi, to ranar ana matsayin malami kenan, cikin dattako ta k'ara gyara zamanta tace "Sheikh, nasan nayi maka hawan k'awara a lamarinka a game da auren nan, saidai ka sani ba nayi bane dan na nuna na isa da kai, na tabbata auren nan zai zame maka alkairi insha'Allah, ina fatan baka k'ullaceni ba ko?" Da sauri ya girgiza kai yace "Subhanallah Hajia! K'ullata kuma? Ko d'aya wallahi, na d'auki hakan a matsayin abu ne da dama Allah ya rubuta zai sameni, tabbas da ita d'in ba *matata* bace da ban sameta ba ko da kuwa ina son haka." Jinjina kai tayi tace "Naji dad'in haka, yanzu maganar tariyarta nake so naji, yaushe ka tsara?" Sunkuyar da kai yayi yana mai jin kunyarta sosai, to shi ya zai ce? Ya fad'i ranar da za'a kawo masa tsarar Aisha? Shiru kawai yayi ya kasa magana har saida Hajia tace "To idan ya maka mu barshi a sati d'aya, lokacin na tabbata ka gama gyara mata na ta b'angaren." Numfashi ya sauke a sanyaye yace "Allah ya sa haka shi yafi zama alkairi." "Ameen." Ta fad'a ita ma, d'orawa tayi da "Sannan sheikh dan Allah kayi hak'uri da yarinyar nan, kaga fa shekarunta k'alilan ne, dole sai kana kawar da kai da hak'uri, inba haka ba zatayi abu a cikin k'uruciya kai ka ga kamar wauta ce ko kuma da gangan." Jinjina kai yayi yace "Insha'Allah za'a kiyaye Hajia." Murmushi ta masa tace "Naji dad'i, Allah ya maka albarka, sai kuma magana ta gaba." Jinjina kai yayi alamar saurare, d'orawa tayi da "Waya na ce me zai hana ka siya mata? Kaga zata dinga kiran iyayenta ai." Da wani irin k'arfi ya d'aga kai ya kalli Hajia yana kiran "Waya kuma?" Ita ma da mamakin yanda taga firgici a tare dashi ta amsa da "E, waya." Iska ya feso tare da duk'ar da kanshi yana ambatar "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Shi ya siya mata waya? Yarinyar da baisan irin girma da mahimmancin data bawa waya a rayuwarta ba, idan fa ya bata ta ci gaba da rayuwarta data saba, har shi fa sai Allah ya hukuntashi dan yana da kamasho. Cikin nutsuwa da salon bayar da umarni Hajia tace "Zan jira zuwa gobe da safe sai ka kawo mata." Lumshe ido yayi tare da d'an sinne kai ya jinjina shi alamar to, shiru babu wanda ya sake magana har saida ya d'an tank'ware k'afafunshi yace "Hajia." Da kulawa ta amsa da "Na'am." D'orawa yayi da "Ki fara shirin aurar da jikarki Eesha, insha'Allah na mata miji kuma bana tunanin za'a d'auki lokaci mai tsayi." Da fara'a sosai tace "A'a masha'Allah, wannan ai abun farin ciki ne, Allah ya sa alkairi ya nuna mana ranar." A sauk'ak'e ya amsa da "Ameen." Jim ya d'anyi kafin yace "Hajia ni zan wuce gida." Mik'ewa dan ta fahimci so yake ta mik'e kafin yayi tsaye a kan ta shi ma, a hankali ya mik'e sukayi sallama a mutumce tana fad'in "A gaishe min da mazajen kwabon nan." Murmushi yayi yana amsawa da zasu ji ya fice kamar yace "Wayyo Allah." Hajia ta umarceshi ya siyawa Ryam waya, me zatayi da ita? Su wa zatayi mu'amula dasu? Ko dai ma ita ta ziga Hajia kan a siya mata wayar? Da tunane tunanen nan ya isa gida. *Saminu* "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Abinda ta fad'a kenan sakamakon ganin Saminu zigidir babu kaya a jikinshi da wayarta a hannunshi yana kallon hoton Mimi wanda sukayi ta d'auka ranar kamu, yana kallonta yana ta lailaya dokinshi a dole yake son biyan buk'atarshi daga kallonta, juyawa tayi hankali a watse zata fita, da gudu ya biyota ba tare da jin nauyin jikinshi ba yana d'aura towel d'in shi yana kiran "Maimuna, Maimuna tsaya kiji." Juyowa tayi a hassale ta kalleshi tace "Me zan ji? Wannan wace irin rayuwa ce? Me kake aikatawa haka dan Allah?" Fashewa tayi da kuka hankali tashe cikin son rarrashi ya rik'o hannunta, da k'arfi ta fizge tana fad'in "Karka k'ara tab'ani." Da alamar rarrashi yace "Naji to shikenan, amma dan Allah ki saurareni, Maimuna ba abinda kike tunani bane, wallahi..." Sai kuma ya rasa me zai fad'a, sake juyawa tayi ya yi saurin shan gabanta yace "Ina zakije Maimuna? Dan Allah ki rufa min asiri, na yarda nayi laifi ki yafe min kinji." Cikin sako hawaye tana kallon fuskarshi tace "Dama kana sonta ne? Ko kuma dai gaske ne abinda nake ji a gari a game da kai na neman mata?" Da sauri ya girgiza kai yace "Ko d'aya Maimuna, wannan jita-jita ne na mutane karki yarda, Mimi kuma kamar 'ya ko k'anwa take a garemu ai, ban tab'a jin haka a kan ta ba." Cikin d'aga murya tace "To me yasa kake kallonta kana son dole sai kaji dad'i ta haka? Fuskarta ce ke birgeka ko kuma albarkatun jikin da Allah ya hore mata?" Sassauta murya yayi yace "Ba haka bane, Maimuna ina da buk'ata ne kuma ke naga kina saurin gajiya dani, bana so na zama mai takura miki shiyasa ban nemeki ba." Tsareshi tayi da ido tana kallon fuskarshi, ta jima haka kafin ta sauke numfashi tace "Alhaji zan daina maka k'orafin gajiya idan ka min alk'awarin ba zaka sake kula mata a waje ba." Da sauri jiki na rawa yace "Na daina, dama kuma bana yi wallahi, yanzu muje to." A sanyaye ta bi bayanshi suka koma d'akin, d'auke wayar yayi ya aje gefe tare da kwantar da ita akan gadon, saidai tsaf abinda bata sani ba yana saduwa da ita ne amma kuma a idonshi Mimi yake gani, zuciyarshi ta gama haska mishi ita tare da k'awata mishi ita, musamman idan ya tuna kwancin nan nata a asibiti, yanda nonuwanta sukayi carrr daga sama kuma yake iya hangen matashiyarsu jajir dashi, ga s'uwawunta da suka kwanta akan gadon su ma sosai. Da haka har ya samu biyan buk'atarshi saidai babu gamsuwa dan hankalinshi a wani irin yake. *Ahalin Mimi* Aje abincin tayi gabanshi tare da zama gefenshi tace "Malam gashi." D'an zabura yayi ya kalleta da alamar nisa yayi a tunani, Yaseen da Amir da suke gefensu ne suka kalleshi Amir na fad'in "Abba kaga yau ma mama shinkafa ta dafa mana har da nama." Kallonshi yayi yana dariya yace "Da gaske? To ka k'oshi dai ko?" Da dariya shi ma yace "E, Abba." Murmushi yayi tare da jawo kwanon gabanshi zai fara cin abincin, da sauri Mama ta mik'e ta koma gefe kusa da k'ofar shiga ban d'aki, durk'usawa tayi ta shiga kwaranya amai, mik'ewa yayi hankali ya tashe ya k'arasa gareta yana fad'in "Subhanallah, uwar uwata lafiya? Baki da lafiya ne dama?" Kakarin aman ta take yi bata kulashi ba, saida ta gama ya bata ruwa ta kurkure baki, mik'ewa tayi ta zauna kan tabarbar tana dafe kanta dake ciwo, gabanta ya zauna yana fad'in "Rabi'atu, baki lafiya dama? Me yake damunki?" A hankali cikin muryar galabaita tace "Ba komai, ba wani abu bane." Da kulawa yace "To ko gajiyar bikin nan ce?" Da sauri tace "E ita ce." Yanda ta bashi amsar ya sa mishi shakku, kallon tuhuma ya mata yace "Uwar uwata, ko dai Amir zaki wa k'ane?" Da sauri ta kalleshi tana rufe baki tace "Kai." Sai kuma ta kalli su Yaseen, su ma su suke kallo, cike da kunya ta mik'e ta shige d'aki, dariya yayi tare da bin bayanta ya sameta zaune, kusanta ya zauna yana fad'in "Masha'Allah Rabi'a, nagode miki kinji, hak'ik'a wannan abun alkairi ne da farin ciki, Allah ya rabaki da abinda ke cikinki lafiya." Sunkuyar da kai tayi tace "Malam kunya nake ji wallahi, mun aurar da 'ya kamata yayi ace mun aje wannan gefe yanzu." Da mamaki ya kalleta yace "Iyeeeh! Kaji min matar nan, me zamu aje gefe d'in? Haramun muka aikata?" Turo baki tayi ta sake yin k'asa da kanta, mik'ewa yayi yace "Uwar uwata fito ki ci abinci kinji, bayan wannan ma idan da wani rabon ni zan antayo dashi zuwa duniya." Baki wangale ta kalleshi tace "Inna lillahi! Rashin kunya." Juyowa yayi ya nunota da yatsa yace "Ke Rabi fita idona in rufe, na lura take-taken iya shegenki ne duk uwata ta d'auka, har take kallona ni da sheikh take fad'a mana tsofaffi." Dariya Mama tayi ta sunkuyar da kanta, fita yayi ya zauna ya fara ci abincin cike da farin ciki a zuciyarshi, Mama kuma bata sake fita ba a k'arshe ma Yaseen da kansu sukayi shinfid'a suka taka kujera suka d'aura gidan sauro. *Mim-Sheikh* Da yake ba mai son zama da hijabi bace yanzu ma haka ta fito daga ita sai riga da siket d'inta na leshe, simple d'inki ne mai rap-rap amma dake tana da jiki sai ya mata wani irin kyau ya zauna a jikinta, gashinta data d'aure tayi irin d'aurin daya fi birgeta wanda tsakiyar gashin ke fitowa ta zauna a gadon bayanka. Duk da ta hangeshi amma bai dameta ba, k'arasowa tayi a sanyaye tana furta "Assalama alaikum." Da fara'a Hajia ta amsa da "Wa'alaiki salam, takwarata kin tashi?" Da ladabi ta zauna k'asa kusan k'afarta tace "Na tashi, ina kwana?" "Lafiya lau, ya jikin naki? Da sauk'i ko?" Da fara'a ta amsa "Da sauk'i sosai." A hankali ta d'aga idonta ta kalleshi, karaf idonsu suka had'e dan kallonta yake a lokacin ganin wani wata arniyar shiga da tayi, da sauri ya janye na shi idon yana fad'in "Astagfirullah wa'atubu ilaikh." Sunkuyar da kan shi yayi har sanda siririyar muryarta ta dakeshi tana fad'in "Ina kwana malam?" Da sauri Hajia ta kalleta tana murmushi, saidai bata ga laifinta ba dan bata san abinda yake so ba da wanda baya so, kallon sheikh tayi da a lokacin ya d'ago matsakaitan idonshi ya zuba mata harara yace "Ban ganshi ba nima, kun had'u dashi ne?" Kallonshi tayi sai kawai tayi mar-mar-mar da ido tace "Allah huci zuciyar gafarta." Da sauri Hajia ta gumtse dariyaarta dan ta fahimci wata yar tsama ce ke numen kunno kai tsakanin d'a kuma sirikinta da sabuwar amaryar ta shi, kwalin wayar dake gefenshi ya d'auka ya jefo mata sai a cinyarta, da sauri ta kalleshi sai kuma ta d'auki kwalin tana dubawa, a zuciyarta ta furta "Samsung galaxy." Muryarshi ta ji a d'aure yana fad'in "Hajia tasa na siya miki waya, ki kula ki kuma san abinda zakiyi da ita, wallahi na kamaki da wayar nan kina abinda bai dace ba jikinki zai fad'a miki." Kallonshi tayi a raunane tace "Amma malam ai ka ce baka dukan mutum, ni fa banaa son duka wallahi." Bud'e baki yayi da jinjina rashin kunyar Ryam, gyara zama yayi ya nunata da yatsa yace "Ki jaraba yin abinda zan dokeki ki gani, ke sai na d'aureki kafin zan sa a zane min jikinki da tsumagiya." Galala tayi sai kuma ta kalli Hajia ta sunkuyar da kanta, cikin muryar son yin kuka tace "Ai Hajia ta ce ni amanarta ce, babu wanda zai dakeni ta k'yale mutum." A d'an hassale yace "Ke..." Sai kuma yayi saurin kallon Hajia, jinjina kai yayi irin zamu had'u d'in nan, Hajia dake ta son kecewa da dariya rufe baki tayi, yau kam tana ganin ikon Allah, ko abokan wasa fa yanzu sun ajiye wasar gefe guda basa yin ta da sheikh, amma kaga yarinya yana fad'a tana fad'a, shi kuma har da wani biye mata wai kamar ba wannan mai taka tsantsan d'in ba? A hankali Mimi ta yunk'ara zata tashi tace "Hajia ki masa godiya." Rintse ido yayi yana addu'ar Hajia ta matsa daga gurin nan ya cabki wuyan yarinyar can, kai kutmelesi inji yan duniya, shi wai ake wa wannan iskancin? Da kallo Hajia ta bita tana jin wata irin k'aunar yarinyar na sake ratsa zuciyarta, dan abunda tayi yanzu sai ya nuna ba yarinta bace tayi ba kuma k'uruciya bace ko raini, aji ne, ajinta ta ja da kyau, dan har yanzu ita dashi basu keb'e ba bare su zama d'aya ta yanda zata zama mai arha a gareshi. Maido kallonta tayi ga sheikh da niyyar mishi magana sai taga ya bi Mimi da harara, saidai wani abu data k'ara fahimta a cikin hararar akwai kallon birgewa duk da shi baisan yayi ba, amma dai tabbas yanayin fuskarshi yanayi ne na shagala da kuma kallon birgewa da d'aukar hankali, idonshi ne kawai ke hararen suma gaba kad'an akalar hararan zata canza ba tare da sanin mai su ba. Juyawa tayi ta sake kallon Mimi dake daf da shiga d'akinta tace "Mimi." Juyowa tayi tace "Na'am Hajia." Dawowa tayi a nutse a sanda sheikh ya d'auke idonshi daga kallonta yana fad'in "A'uzu billahi mina shaid'ani rajim." Tana zuwa kan tebur ta nuna mata tace "Je ki fara cin abinci ina zuwa yanzu." Jinjina kai tayi tare da nufa kan teburin, sosai ya sunkuyar da kanshi yana son dole yafi k'arfin zuciyarshi ba sai ya kalleta ba, kallonshi Hajia tayi tace "Da wani abu da kake buk'ata sheikh?" Girgiza kai yayi a hankali yana jin wani irin mutuwar jiki da kasala a lokaci d'aya, jinjina kai tayi ta mik'e tace "To muje ka ci abinci?" Girgiza kai ya sake yi da k'yar ya iya cewa "Na k'oshi." Jinjina kai tayi ta nufi teburin tana fad'in "Bari na ci abinci ni, kasan uclerta bata jurar yunwa." Jinjina kai yayi alamar gamsuwa, so yake ya mik'e amma kallon fitinanniyar yarinyar can ya canza mishi yanayinshi, bayan kasalar da yake ji na sauko mishi har da wani shauk'i yake ji, a hankali ya d'an gyara zamanshi cikin dubara ya saki 'yar mik'a a zuciyarshi yana fad'in "La'ilaha ilallah Muhammadu Rasulullahi sallalahu alaihi wa sallam." Mik'ewa yayi ya d'an k'arasa kusa da su, yanda take tsaye tana zubawa Hajia abinci sai yaji yana sha'awar k'are mata kallo, yanda ya ganta yar dagwai dagwai d'in nan ga kayan nan da suka mata kyau, a hankali ya kalli kwabar madubin dake geffen shi saidai Hajia ta bawa kwabar baya ne, tsaf ya hangota a ciki tana zuba abinci, take ya jefawa kanshi tambayar "Wai me yasa ta fitsare ne tun a waje?" Haushin wannan tambayar da jin wani mahaukacin kishi yasa shi kallon Hajia yace "Sai anjima." Da sauri ya shiga takawa ya bar falon, Hajia da kallo da mamaki ta bishi har ya fita a gidan ma. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *31* Zumud'i ne ya hanata zama ta ci ta k'oshi da kyau, mik'ewa tayi tana d'aukar kwalin wayar tace "Zan shiga ciki." Da murmushi ta kalleta tace "Har kin k'oshi?" D'aga kai tayi alamar eh, wucewa tayi dakinta tana shiga ta zauna kan gado, jiki na rawa ta ciro wayar tare da k'ok'arin kunnawa, samunta tayi a kunne da kuma sim a ciki lokacin da komai nata daidai alamar dai an saita mata ita, gidan sim d'in ta gani da lambar a rubuce, murmushi ta saki dan irin lambar nan ce manya gata kuma duk suna kamanceceniya da lambar sheikh da yake kiranta a da da kuma lambar Ashraf. Tunani ta shiga wanda zata fara kira, Abba dai yanzu tasan an fita buga-buga neman na kai, Mama dama ba waya ne da ita ba, lmabar Asma'u kawai take da a kan ta, dan haka ta saka lambar tare da danna mata kira, ta d'an jima tana k'ara kafin Asma'u dake zaune suna kari tare da Asas jiki na mata rawa ta d'auki kiran tana satar kallonshi, dan tsoronta d'aya kar a zo namiji ne ya kirata tunda ba kowa yasan tayi aure ba, a sanyaye sosai Asma'u tace "Hello." Daga b'angaren Mimi ma a tausashe tace "Hello, Asma'u ta Mimi." Wani basaraken murmushi ne ya sub'uce mata tare da aje cokalin hannunta tace "Mimi ta Asma'u, kina lafiya? Ya kike? Kin daina kuka?" Da sauri ya aje cokalin hannunshi shi ma sai kumaa ya basar tare da d'auke idonshi daga kan Asma'u, cikin murmushi da jin dad'in k'aunar da Asma'u ke mata tace "Na daina, amma idan kika ga Abbana ki fad'a masa na daina masa magana, dan shi ne ya aurar dani ga sa'anshi." Dariya Asma'u tayi ta mik'e tsaye tana jan kujerar baya dan bata so su siyar da halin a gaban Asas, cikin fara'a ta nufi d'akinta tana fad'in "Ba wani nan, ai ke da Abba bata b'acewa, shi kuma wanda kike kira tsoho zakiyi bayani ne da bakinki a gaba." Da sauri Mimi tace "Me kike nufi? Wai ni zan zauna wannan tsohon ya lalata min k'uruciya?" Da mamaki Asma'u tace "Kayya Mimi! Da alama dai har yanzu baki fahimci karatun da nake so ki fahimta ba, kina fariya da cika baki akan rayuwar da baki da ikon tsarawa kanki ko da yanda zakiyi atshawa, bare kuma rayuwarki ta 'yanci, abokin rayuwarki." Sauke numfashi tayi cikin shagwab'a tace "Asma'u ke ma fad'a zaki min? Me yasa ba zaku dubi abin ta wata fuska ba, 'yarshi fa Aisha na tabbata ko na girmeta shekara d'aya na bata, ni yanzu ne nake fara tawa rayuwar, shi kuma ya gama cinye tashi contract d'in, so kuke na zo nayi masa takaba ne? Shikenan ni ba k'uruciyata k'arshe na shiga layin zawarawa yanda farashi na zai zube k'asa warwas." Dafe gaban goshi Asma'u tayi tace "Mimiiiii!" Yanda ta kira sunanta yasa Mimi fad'in "Me ya faru? Ko mijinki naa gida ne?" Sai kuma taji kamar zatayi hawaye, tana jin Asas sosai a cikin zuciyarta, irin yanda ta tsara rayuwarta dashi da yanda ya dinga tayata k'awata burinta abin hamdala, amma gashi *tafiyar k'addara* ta sauya musu komai, cikin son danne abinda ke zuciyarta tace "Zan kashe waya, sai anjima, ki kula da kanki." Da sauri Asma'u tace "Mimi." Dakatawa tayi daga shirin kashe wayar, a hankali tace "Dan Allah ki nutsu kinji Mimi, na sanki farin sani fiye da kowa, kar ki sake yin abinda zai sa wani ko wata ya zargeki." Marairaicewa tayi alamar rarrashi tace "Dan Allah kinji." A sanyaye Mimi tace "Insha'Allah Asma'u, nagode." Murmushi tayi kamar tan agabanta tace "Sai mun had'u kinji, wata rana zan zo na ganki." Jinjina kai tayi tace "Shikenan, Allah ya yarda." Kashe kiran sukayi inda Asma'u ta aje wayar, fita tayi ta koma falon ta sameshi yana tsakurar abincin, saidai kallo d'aya ta masa ta fahimci hankalinshi a tashe yake kamar akwai abinda ya shiga tunani har ya b'ata masa rai, sai kuma ta tuna wayar data fara gabanshi, hakan yasa ta tunnin ita ce silar b'acin ran nashi, a sanyaye ta zauna tana satar kallonshi, ganin yanda yake cin abinci kuma fuskarshi kamar zata tab'ashi ya fashe da kuka yasa ta cewa "Lafiya ko?" Kallonta yayi lokaci d'aya kuma ya d'auke kanshi yace "Ba komai." Ture plat d'in yayi ya mik'e yace "Ni zan fita, saina dawo." Da sauri ta mik'e tsaye tana fad'in "Amma yau k'awaye na sun zo zasu zo min wuni." Dakatawa yayi yana kallonta yace "To, da wani abun da kike buk'ata ne?" Girgiza kai tayi tana sunkuyar da kai tace "A'a ba komai, dama na fad'a maka ne dan ka sani." Lumshe ido yayi alamar shikenan, juyawa ya sak茅 yi zai fita tace "A dawo lafiya, Allah ya tsare." "Ameen." Ya amsa yana ficewa a falon, saida ta ga fitarsa a gidan sanda mai gadi ke mayar da k'ofar yana rufewa kafin ta zauna ta k'arasa abincinta, tana idawa ta tattare kwanukan ta kai madafa ta dawo falon ta zauna dan ba shara bare goge goge da zatayi, kallo ta shiga yi a tsanake tana canja tashar da take so ga sanyin ac na ratsata ga kuma sanyayyan lemun data aje, lallai Allah kai ne Allah, wacce ta tashi a gidan mutane dayawa, dan a kad'an mutanen gidansu zasu kai ashirin da biyar idan lissafasu za'ayi, a haka fa dan akwai mata masu aure ga maza da ba zaman gidan suke ba. Yau gata a k'aton gida ita d'aya tana yanda take so, lallai tarayarta da Mimi alkairice a gareta dama danginta. 12:02 su Salma suka diro gidan, da murna ta fito daga madafa tana fad'in "Marasa mutumci, shi ne sai yau aka ga damar zuwa?" Dariya suka saka sai Jamila data k'are mata kallo tace "Kinji wata tsifa kuma, ba shekaran jiya ne muka kawoki gidan ba." Salma ce ta cire mayafinta tace "Rabu da ita, me take so muzo muyi a jiya? Mu zo cin kaza ko kuma gasa mata jiki?" Dariya suka sake shek'ewa da ita Asma'u kula tab'e baki tayi tace "Ku zauna dan Allah ni bana son iskanci." Juyawa tayi zata d'auko musu ruwa Ruky tace "Asma'u wai me mijin nan naki ya baki ne har kin fara sauyawa haka?" Dungureta Salma tayi tace "Dan uwarki duk wanda aka kawo a wannan aljannar zai k'i canzawa ne? Ai sai marar rabo duniya da lahira." Wata dariyar sukayi har da Asma'u data kawo musu lemu da ruwa, d'auka duk sukayi suka fara jik'a mak'oshinsu, zaune tayi tana kallonsu tace "Amma daga nan zaku je ku gano min k'awata ko?" Da sauri Salma tace "Wa? Wai Mimi kike nufi?" Cikin d'aga murya ta tapa hannaye ta shiga fad'in "Ai Mimi zuwa na musaamman zan mata, ba dai ni ta dinga wa dariya zan auri tsoho ba mai k'aton ciki, wallahi idan na je gidan sai nayi dariya kamar cikina zai k'ulle, ke k'arshe ma saina kwaso mata shoki wallahi." Tsaki Asma'u tayi tace "Ramawa zakiyi kenan? Amma dai kinsan mijinki yafi nata tsufa." Da k'arfi Salma tace "K'arya ce wallahi, shekarun sheikh sun fi na mijina." Ruky ce ta kai mata duka tace "Shegiya wai mijinta, yaushe aka d'aura muku auren?" Hararanta tayi tace "Ke kauce dallah." Jamila ce tace "Maganar gaskiya fa Salma karki fara, dan in gaskiya za a bi ko sheikh ya girmi Alhajinki amma sheikh ya fi shi kyawun jiki." Ruky ce ta tintsere da dariya tace "Ai ko a majigi kika ga sheikh kinsan tsohon duniya ne wallahi, ke karfa kiyi mamakin idan yana d'aga k'arfe, dan a kujerar nan idan ya zaune haka zaki ga kafad'unshi a bud'e." Jamila ma dake dariya cewa tayi "Ai shiyasa ni nace wallahi da ya so ni da gudu zan aureshi." "Sai kuma ya zamaa rabon Mimi ba." Cewar Asma'u tana hararenta, Salma ce tace "Ko ma dai menene mijinta ya fi nawa tsufa, kuma sai na rama duk tsiyar data min wallahi." Tab'e baki Asma'u tayi tace "Allah ya shiryaku to, ni na matsu ku shiga hannun wad'anan dattijan arzik'i ko sun bambamce muku zare da abawa." Cike da salon shak'iyanci na yan mata suka saka mata dariya Salma na fad'in "Su Asma'u manya, wato har an shiga daga ciki ko? Da alama dai jarumi Asas ya gama aiki." Girgiza kai tayi tace "Har yanzu babu wannan tunanin a tare damu, ba anan kusa ba b芒 kuma lokaci." Kallonta sukayi kafin Ruky tace "Uhum! Ke dai bari muga kun shanye wannan satin tukuna, namiji da kinibibi ke kuma mace san kowa k'in wanda ya rasa." Jamila ce tace "Ai tsaf zai manta da wata Mimi ya kwashi garar Asma'u." Dariya sukayi sai Asma'u data girgiza kai tace "Ku wallahi baku da kunya." Mik'ewa tayi tana fad'in "Bari na kawo muku abinci." Da kallo suka bita har ta shige, da sauri Jamila ta kallesu tace "Ke ki dubi daula ki gani, wa ya san Asma'u zata auri mai kud'i? Ita da ko saurayin kirki bata da." Ruky ce tace "Allah ya kareta daga sharrin tarikitan samarin ne saboda mijinta bai bayyana ba." Salma kam cewa tayi "Ni ba wannan ba, wai yanzu ya zasu rayu ne suna auren yan uwan juna ita da Mimi bayan kuma abinda ya faru ranar auren nan?" Cikin rad'a Jamila tace "Bari kedai, nima abinda na fi tunaani kenan, kuma fa har yanzu da alama k'awancensu na nan, kuna ganin hakan ba zai shafi alak'arsu ba?" Ruky ce tace "Da zai shafi alak'arsu daya tab'a tun ranar, mazan dai na fi jiye ma, kinsan maza sun fimu rik'o fa, kar a zo tafiya tayi tafiya Asas ya kasa cireta a zuciyarshi." Salma ce tace "Ai shi d'in ne, baiwar Allah kuma fa zata fuskanci matsi idan haka ta faru." "Gaskiya kam." Cewar Ruky, jin fitowar Asma'u yasa Jamila saurin fad'in "Daga nan dai muyi k'ok'ari muje wajen Mimi, ina so naga tab'ara da iya hege." Dariya sukayi har da Asma'u data fito tana fad'in "Ta daina ma na sani, babu abinda zaki gani Jamila." Salma ce tace "Wacece? Mimin? Ai kuwa dana tsine mata, yo a zaman da zatayi gidan nan idan bata kafawa sheikh tarihi ba ai bata cika Mimin dana sani ba." Ruky ce tace "Gaskiya kam, ko wajen iya d'aukar wanka ai Mimi zata rikita gafarta malam." Tintserewa sukayi da dariya sai Salma da tace "Sai ma ta gifta ta gabanshi tana sittin saba'in." Cikin dariyar mugunta Asma'u ma dake rik'e ciki tace "Wata rana kam zamu ga yayanmu babu hula a kai." Da ire-iren hirar nan suka shiga cin abinci ana tapawa ana shewa, sosai suke nishad'i inda Asma'u ma ta ji dad'in zuwan nasu sosai duk da tana bak'i lokaci lokaci daga danginta zuwa mak'wabta, sai daf da magriba suka bar gidan dan girki ma su suka tayata yin shi ta gyara gidanta tsaf kafin suka tafi bayan sun karb'i lambar Mimi wacce ta kirata d'azu da cewa zasu kira su saka ranar da zasu tafi gidanta duk da bata tare ba. *Mimi* Tunda ta samu wayar nan ta shige d'aki ta shiga latse-latse, a k'arshe dai da taga wayar an loda mata kud'i sai kawai ta shiga yanar gizo, a take ta bud'e WhastApp duk da bata da lambar kowa, haka ta shiga man-hajar videmate ta dinga d'auko wak'ok'i na hausa na kallo dana saurare, kiran sallah azahar kawai ya tasheta a wurin tayi sallah kafin ta fito falo, ta samu Hajia na d'aki sallah sai kawai tayi zaune ta k'urawa tvn ido wacce ita dai ta fahimci kamar tasha d'aya suke kallo kullum wato *sunna tv*. Da yamma da kanta ta shiga madafar duk da har yanzu bakinta bai sake had'uwa dana Salamatu ba, haka ta shiga had'a abinda ranta ke so kamar yanda Hajia ta bata wannan damar, Salamatu dai na kallon ikon Allah, gata k'aramar yarinya mai jikin yan hutu, amma yanda take takawa tana wani motsa k'ugunta kamar da gayya, sai taji kamar yarinyar zata shiga ranta sai kuma tayi saurin tunawa kanta abokiyar gaba ce fa. 馃ゴ a banza indai uwata ce. Daf da magriba suka kammala ta kai komai kan tebur ta shiga d'akinta dan yin sallah, saida ta idar da sallah kafin ta shiga wanka, tana fitowa ta zauna a gaban madubi, wani karsashi take ji tare da jin bari fa ta cire komai a ranta kar ta zama wata 'yar k'auye. A sauk'ak'e ta shiga linde fuskarta da hoda ta ruwa mai haske sosai kalar fatarta, kafin ta zana gira da kalar maroon data fito da fasalin fuskarta, saida ta fara shafa eyeshdow a saman idonta ta shafa mascara kafin ta shafa jan baki kalar maroon mai duhu sosai a sama sai k'asa data shafa lips sannan ta shiga fitar da tsarin labb'enta da wata hodar mai haske amma mai d'an k'yalli. Mik'ewa tayi ta kalli kanta a madubi ta kanne ido d'aya dan ta birge kanta sosai, k'arasawa tayi gaban drower kayanta, wata fitinanniyar rigar shadda ta d'auka wacce tana d'aya daga cikin kayan da Asas ya fara aikata mata, d'inkin ya bala'in haukata ta yayi kyau sosai, yanda kalar fatarta take sai kalar kore mai duhu, tsaye tayi gaban madubi kamar wasan yara ta laulaya d'an kwallin, a yanda tayi d'aurin zaka rantse kawai tayi ne dan babu yanda zatayi, amma ko da ta ja shi baya ya fito mata da goshinta tare da fito da gashinta a gaba, a baya ma ta fito da jelar gashinta sai yayi wani irin kyau kamar zama akayi na musamman aka d'aura. Wayarta ta d'auka ta fita ko wuk'a aka d'ora maka zaka iya rantsewa matar wani shugaban k'asa ce dan wani d'aukar ido tayi wal wal wal, Hajia ta samu a falo tana kallon tv da kuma wayarta a hannu saidai da alamar damuwa a tare da ita, ganin Mimi ne yasa ta sakin baki tana kallonta, ajiyar zuciya ta sauke tare da tuna yanda Asas ke fad'a mata yana son mace yar gayu da iya ado, murmushi ta mata tana fad'in "Takwarata kin fito?" Murmushi tayi ita ma tace "Barka da hutawa." "Barka." Ta fad'a tana sake kallon komai na jikinta, a gaskiya ba dan taga gidansu ba sai tace ba daga nan ta fito ba, cikin fara'a tace "Yau fa kinsha aiki, dan na ga abinci jere akan table." Murmushi kawai tayi tana sunkuyar da kan ta, cikin zolaya Hajia tace "Sai nayi tunanin ko cheif ce ke a wajen iya girki." Da sauri tace "A'a Hajia, karambani ne kawai da sa kai, a wayar k'awaye na nake gani dama ko kuma a YouTube." Da fara'a tace "Masha'Allah, ai karambanin mai kyau ne." Cikin ladabi Mimi tace "Zan d'an zagaya farfajiya ne." Da murmushi tace "Ba komai, ki kula." Jinjina kai tayi tare da fita a hankali, tana fita kai tsaye wajen ajiye motoci ta nufa, mota biyu ce a pake a wurin, tsayawa tayi ta fara d'aukar hotuna masu kyau. Bud'e k'ofar gidan da taji anyi yasa ta juyawa dan ganin mai shigowa, tana ganin motar sheikh da sauri ta lab'e bayan motocin tana fad'in "Old man an taho, wai me yake kawoshi gidan nan ne kullum?" Kusa da motocin aka paka motar, tana hange taga wani mai bak'ak'en kaya ya bud'e mazaunin baya, a sanyaye ya fito cikin k'asaita da nutsuwa, tab'e baki tayi tana kallo ya rufe motar, zai fara takawa sai kuma ya tsaya tare da juyawa bayanshi kamar zai kalli inda take, da sauri ta sake lafewa tana dafe k'irjinta, sake juyowa yayi ya kalli jami'in yace "Ku jirani a nan." Gyara tsayuwa yayi yana hard'ewa wuri d'aya da bak'in glas d'in shi, takawa ya shiga ta b'angaren da take hakan yasa Mimi hanjinta motsawa kamar zasu fito waje, rintse ido tayi sosai data tabbatar wajenta ya nufo, saidai tana mamakin yanda yasan tana nan, ai kam gabanta ya tsaya yana k'are mata kallo daga k'asa har sama. Cikin dakakkiyar muryar shan k'amshi da b'acin rai yace "Me kike yi a nan?" Bud'a ido tayi tar a kan fuskarshi sai kuma tayi k'asa da su, cikin rawar baki tace "Um..dama..na zo shan iska ne." A gajarce yace "Shan iska?" D'aga kai tayi alamar eh, takawa yayi d'aya biyu na uku ya kai daf da ita, ja baya tayi dan sai taji ta kamar gaban wani basamude, tsaf ya rufe da girman jikinshi da kuma manyan kayanshi, d'ora hannayenshi duka biyu yayi jikin motar data jingina, hakan ya haifar da k'wak'waran kusanci a tsakaninsu kamar zai rumgumeta, d'auke numfashi tayi tana kallon fuskarshi da yanayin tsoro da kuma sakarci, fuskarshi a had'e sosai yace " *Ke yanzu matata ce, ba kamar matar kowane gaja bace, suturtata jikinki da kama min kanki ya zama wajibi a gareki, wannan kwalliyar ni kawai ya dace ki wa, gashinki kuma kar na sake ganinshi a waje.*" D'auke hannayenshi yayi tare da k'urawa fuskarta ido yace "K'amshin nan haramun ne ki sa ki fito waje, ke Ryam ba zan yarda hakk'inki ya kaini wuta ba, wallahi ki kiyayeni kinji na fad'a miki." K'wafa yayi tare da ja baya yace "Kuma ki zauna a nan karki fito har sai na bar gidan nan." Zaro ido tayi dan sai lokacin kawai ta farfad'o daga halin daya jefata, maganganunshi sun shigeta ta sama musu muhalli tare da tunanin abinda yake nufi. Yanda ta zaro ido yasa shi fad'in "Kin ji me na fad'a?" Da sauri ta jinjina kai cikin tsoro tsoro da firgici tace "Na ji, amma kuma..." "Amma me?" Ya fad'a yana binta da harara, girgiza kai tayi alamar ba komai, jinjina kai yayi yace "Magana ta dake mai yawa ce, zan tarasu ne har ki sameni gidana." Kyab'e fuska tayi tana neman fashewa da kuka tace "Ni wallahi ba zan je ba, haka kawai a wani kai ni gidan..." Da sauri ya kalleta yace "Gidan me?" Girgiza kai tayi alamar ba komai, zaro lata ido yayi yace "Me na fad'a miki akan k'arya?" Da sauri ta fashe da kuka tare da fad'in "Ai dama cewa ne zanyi gidan old man." K'ank'ance idonshi yayi yana kallonta da mamaki, bakinta data turo tana zuba shagwab'arta yasa yatsu biyu ya cabkoshi, gam ya rik'e hakan ya haddasa mata sakin k'arar data shiga dodon kunnen wanda ke gidan a lokacin, hankali tashe ba tare da tunanin zata iya yin haka ba ya had'ata da motar tare da yin wuf da bakinta ya had'a da... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *32* Hankali tashe ba tare da tunanin zata iya yin haka ba ya had'ata da motar tare da yin yuf da bakinta ya had'a da tafin hannunshi ya taushe, zazzaro ido tayi haka shi ma dake kallonta da mamaki, da gudu jami'an suka tunkaro wurin dan su lafiyar sheikh ce nauyinsu, kuma basu san shi da waye a wurin ba, daga d'aki ma Hajia fitowa tayi tana kallon Salamatu data rigata tace "Kamar ihun Mimi ko?" Jiki na mata rawa tace "Ni ma haka na ji Hajia." "Me ya sameta to?" Ta fad'a tana nufa farfajiyar gidan, yanda jami'an suka fad'o bayan motar d'aya har ya ciro bindigar da gwamnati ta basu tare da izinin harbi idan suka ga had'ari, juyowa yayi ya kallesu tare da sakin bakinta, babbaketa yayi yana kareta wai shi a dole kar su ganta, fuska a had'e sosai yace "Me ye?" Cikin girmamawa d'ayan yace "Yallab'ai mun d'auka da had'ari ne." "Ba komai, ku tafi." Ya fad'a yana sake wani ciccijewa, juyawa sukayi zasu tafi sai kuma ga Hajia da Salamatu apujajen, sake matsawa yayi nesa da ita yana k'wala mata harara, cikin tashin hankali Hajia ta shiga kallonshi tana fad'in "Sheikh lafiya? Naji ihun Mimi." Matse bakinshi kawai yayi da sauri Mimi ta tafi da sauri ta isa kusa da Hajia, da kallo ya bi bayanta yanda take tafiyar da sauri, zuciyarshi ce ta tambayi "Anya yarinyar nan ke da k'ugun nan?" Numfashi ya sauke a hankali yana kallon Hajia na share mata hawaye tana fad'in "Me ya sameki? Wani abu kika gani?" Girgiza kai tayi cikin kuka tace "Shi ne ya tsoratani." Kasa d'auke idonshi yayi a kan ta duk da kallon da Hajia ke masa tana fad'in "Sheikh wani abu ka mata?" Sai kuma ta kalli Mimi tace "Ko dai wasa ne yake miki?" Cikin shagwab'a ta kalleta ta turo baki tace "Hajia kina nufin wasar kaka da jika?" Da sauri Hajia tayi saurin rufe bakinta a bayyane tace "Kai." Salamatu ma ta zazzaro idonta waje tayi, shi kuma sheikh daga tsayen da yake duk irin yanda ya kai da b'acin ran masu tsaron nan nasa sun wani zo masa a wajen da bai dace su zo ba sai ya tsinci kansa da sakin k'ayataccen murmushi, lallai ma Ryam abun na ta yanzun ya fara d'agowa kamar so take ta hassala shi, so take kawai ta ringa juyi da shi kamar biri da abokin wasansa. Murmushi ya kuma yi ya juya ya nufi ciki ta d'ayan b'angaren ba tare daya ce komai ba, daga Hajia har Salamatu sun jinjina lamarin Mimi, Hajia na janye da hannunta har suka koma cikin d'akin sannan ta saketa ta nufi d'aki abin ta. Tana shiga ta kwanta tana lumshe idonta, k'amshin turaran Dadyn nan na mata dad'i a hancinta bata san dalili ba, ga wani tattausan hannunshi daya rufe mata baki dashi, yanda ya matsa a jikinta sosai sai abun ya nemi tsaya mata a kai da zuciya. Idonta ta sake lumshewa ta kuma bud'ewa tana tab'e bakinta ta shiga kiran lamber Abbanta. Tana fara ringin ya d'aga, amma daga nesa nesa take jin maganarsa yana fad'in "Kina gani kuwa wata lamba ce ban santa ba, kin san masu shan jinin nan fa an ce da gaske ne?" Yar dariyar mamanta ta ji tana fad'in "To kayi sallama mana malam ka ga fa kud'in mutumen na tafiya." Dariya tayi a bayyane ta furta "Abba ni ce fa." Dai-dai ya matso wayar ya ji muryarta a sanyaye tana kuma dariya tana kiran sunansa hakan ya saka shi fad'in "Uwata ce?" Wata yar dariyar tayi tace "Ni ce nan Abba." Shi ma dariyar yayi sai kuma da sauri ya gimtse yana fad'in "Ke wa ya baki waya?" Bakinta ta turo a sanyaye tace "Shi mana." Mamanta dake sauraro tace "shi wa?" Bakin ta kuma turowa tace "Shi akaramakalahun mana." Mama bata san lokacin da murmushi ya k'wace mata ba tana girgiza kai tana jin Abban na amsa gaisuwarta ta mik'e ta shiga kakkauda kayayyakin dake ajiye hankali kwance. Cikin sangarta tace "Abba yaushe zaku zo? Dan Allah idan ma ba zaku zo ba ku turo min su Yaseen mana." Abba yayi murmushi yana girmama rashin hankalin mamansa, su su zo? Ko a turo mata Yaseen? Sanin da yayi ita d'in ba 'yar a kwatantawa a laluma bace sai kawai ya datse kiran yana d'an murmushi, ko ba komai muryarta ta saka shi farin ciki, a bayyane yake yi mata addu'ar samun nutsuwa. Hajia na zaune saman kujera, sheikh na zaune saman kafet ya tank'washe k'afafunsa bayan sun k'ara gaisawa da kyau har an kawo masa ruwa ya d'an sha, da yanayin da take ciki ta dube shi a sanyaye tace "Sheikh, na rasa ina autana ya shiga, ka ga tunda aka yi abun nan ban ganshi ba ba shi ba labarin iyalinsa, idan na kira baya d'agawa, tun abun baya damuna har ya fara damuna, ka ga magungunansa duka a nan bayan nan ka sanshi da wasa da cikinsa, shin laifi nayi mai girman da ya saka yayi fushi har haka dani?" Sheikh da yake saurarenta ya kawar da kansa gefe guda yana d'an nazari kafin ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye yace "Ki yafe masa, sannan gobe insha'Allah zai zo ya gaishe ki, kar ki saka damuwa a ranki na tabbata da yana cikin matsala daya nemi uwa, kiyi masa addu'a sannan ki masa nasiha, idan ya zo ki saurareshi ki rarasheshi." Hajia na gyad'a kanta tana jin girma da soyayyar Sheikh kamar na wanda ta haifa a cikinta, a gaskiya shekarunsa basu kai irin girman da duniya ke bashi ba, amma da yake tun bai kai haka ba yake da halayya na dattako, girma da darajar Alk'ur'ani dake kansa ya k'ara masa kima da darajar da ko mutum ya tsofe shi sai ka ga yana neman zubewa ya gaishe shi sai idan shi yayi gaggawar tarewa domin kuwa arzikinsa da baiwar da Allah ya bashi bai saka shi barin kansa ganin manya na gaishe shi a tsugune ba. Da haka yayi masu sallama ya fita domin yana da wajen zuwa har uku, ga kuma na hud'u ya k'aru dan kuwa zai je ya same shi a wajen daya tabbata baya wuce nan. Saida ya je yayi yawace yawacensa, duka wajen da yake da na zuwa ya je ya gabatar da ayyukansa a tsanake kafin ya nufi wajen da ya tabbata Asharf na cen. Kusa da masallacin kadafi ne wajen da yake zama tare da abokansa, motocin sheikh na tsayawa samarin uku dake zaune suka mik'e duk suka yo wajen motar ciki har da Ashraf da sai da gabansa ya fad'i amma haka ya dake yana murmushi a lokacin da d'aya daga cikin mai kare lafiyar sheikh ya bud'e samarin duk suka duk'a suna mik'a hannayensu suna mik'a gaisuwarsu. Cike da kamala da daraja d'an adam yake amsa masu d'aya bayan d'aya har suka gama gaisawa kafin ya juya cikin halin kyauta irin nasa ya d'auko enveloppe ya mik'a masu kamar yanda ya saba indai zai tsaya sai ya basu duk da duk cikinsu ba zauna gari banza, amma a matsayinsa na yayansu kuma uba a wajensu sannan mai kyauta yakan yi hakan wanda hakan ke saka su nishad'i da farin ciki, su kansu suna koyan halayya irin nasa domin suma suna yiwa gajiyayyu da k'annensu bare kuma iyayensu. Ashraf na masu sallama ya shiga motar ya zauna aka rufe suka d'auki hanya, shiru ba wanda yayi magana har suka iso k'ofar gidan Ashraf, kuma ba waya suke daddanawa ba hasalima cikin motar ba hayaniyar komai sai shirun da yayi yawa. Muryarsa na rawa rawa yace "Dan Allah kayi hak'uri." Dan yau sheikh d'in tsoro ya bashi tare da jin shakkarshi da kwarjininshi ta yanda yake jin ba zai iya masa wasa ba yau. Sheikh kam d'an juyar da kansa gefe yayi ya kuma juyowa a hankali ya dube shi har ya d'an fad'a kad'an, a hankali ya cire dubansa yana jin zuciyarsa na tsintsinkewa, abinda yake son fad'a shi ne "Kai Ashraf shin dan na auri Ryam ne kake irin haka? Shin matata na zuciyarka ne ko me? Shin baka cire min iyali a ranka ba ko me? Kai marar kunya halan baka d'auki k'addarar aurenka ba? Shin ka isa ka auri matar wani ne?" Sannan ya d'an wanwanka masa marin da zai farkar da shi, sai dai kasantuwarsa da wanda yake a wajensa ya saka shi kawar da kansa a sanyaye yace "Gobe da safe wajen 11:00 ka zo gidan Hajia da iyalinka, insha'Allah zanyi jiranka a cen." Daga haka ya d'auke kansa a duban Ashraf wanda ya gyad'a kansa yana k'ara sadda kan nasa ya bud'e ya fita yana mai yi masa saida safe. Daga nan gidansa ya k'arasa, sai dai bai shiga ba sai da ya gabatar da wasu karatuttuna a masallaci sannan ya nufi cikin gidansa. K'arfe 10:30 ce, hakan ya sa ya samu yaransa duk sun yi bacci, Hafsat kuwa na saman kujera ta mik'e k'afafunta a sama tana jan carbi idaonta lumshe. Sanyi yaji a zuciyarsa a lokacin da yayi arba da fuskarta, sanyin idaniyarsa ce ita, sanyin zuciyarsa ita d'in, kwanciyar hankalinsa ce ita wacce ta amsa sunan *mar'atus-saliha*. Duk'awar da yayi a gabanta ya sakata bud'a idonta masu cike da bcaci tana kallonsa, murmushi ta sakar masa hakan ya saka shi lumshe idonsa a hankali ya d'ora hannunsa saman cikinta yana kallon fuskarta yace "Shin ajiyar *Abdallah* na ci gaba da wahalar da Nurul ayni ne?" Murmushi tayi masa a hankali tana d'an girgiza kanta, domin yanzun da sauki bata jin curewar nan saidai mugun baccin da take yawan yi ta kamo hannunsa tana dubansa tace "Ai komai nauyin kayan jagorana zan iya rik'ewa da hannu bibbiyu abu na." Murmushi yayi yana mik'ewa a hankali ya kamata ya mik'ar da ita ya nufi d'akinsa da ita domin ya san cewa ta gama da yaren ta gama da b'angarensu shi kuwa tuni ya rufe daya shigo. Saman lallausan gadon ya shinfid'eta ya d'an rank'wafa a hankali ya kama leb'enta na k'asa ya bata kyakyawan sumba mai sanyi, a hankali ya shiga tofa mata addu'a yana shafa gashinta kafin yace "Allah yayi maki albarka, Allah ya tashe ki lafiya cikin hayyacinki, Allah ya yafe maki kurarenki wad'anda kika sani da wad'anda baki sani ba, Ina son ki Manga na." A gaskiya ba zata iya kwatanta irin farin cikin da mijinta ke sakata ba, gata dai aure ne na had'i amma tunda ya fuskanceta suke zama irin na fuskantar juna, kowa na yin kaffa-kaffa da lamarin d'an uwansa, har zuwa yanzu da auren wata ya kuma hawa kansa bai saka rud'u da rawar kai irin na yawancin mazan da zasu d'auko yarinya ke shiga ya ringa nuna mata wasu abubuwan ba, yana bata lokacinta da kuma isashen darajarta, tana jin kanta tamkar ita d'aya ce tak a duniyarsa kuma tana jin dad'in hakan, ita kam ta yaba kuma tana k'ara yaba auren YA SHEIKH. Tun yana nan bacci ya kwasheta, a hankali ya nufi bayi dan yin wanka da alwala domin yana son kwantawa da wurin shi ma yau dan tashin tsakiyar dare yin nafilfili cikin nutsuwa. *Washe gari* A yau shigar sheikh ta gama tafiya da nutsuwarta, tsaye take gabansa ta d'an taka pillow d'in daya ajiye mata tana rik'e da hiraminsa ta k'ara d'an yin d'add'age ta d'ora masa a saman kansa shi kuwa yana tallabe da bayanta sanan ta tsaya tana kallon fuskarsa, zata iya rantsewa wannan dan tsili tsilin farin gashin dake gemunsa k'ara masa kyau yayi ko na mutum da masoyi ne? A hankali ta d'ora hannunta saman faffad'en k'irjinsa da kuma shafafen cikinsa , idonnta ta lumshe muryarta cen ciki tace "Kishin mijina nake, shin idan ya fita a haka ya ya yan mata zasu yi da begensa? Kayi kyau har ka gaji ya habibi." Murmushi yayi cikin nutsuwa yana k'ara tareta a jikinsa yace "Ke kike ganin haka ya Mar'atusaliha, kyau kuma ai an barshi tun k'ananun shekaru, ki kular min da kanki kafin na dawo, ban yarda ki yi aikin da zai wahalar min dake ba." Murmushi ta masa tana manna masa sumba a kumatunsa shi kuwa bai saketa ba sai da ya sauketa daga saman pillown sannan ya d'aga mata hannu ya juya ya nufi waje cikin sasaukar shiga irin ta larabawa domin doguwar riga ce ta jalabiya da dogon wandonta sai hiramin da ya d'ora, kayan sababi ne sannan manyan kaya ne masu tsadar gaske da daraja gashi sun amshi jikinsa sosai. A lokacin daya zo dan shiga falon Hajia ya samu takalma a k'ofa na mata hakan ya saka shi juyawa cikin nutsuwa ya koma cen wajen motocin gidan ya ajiye kujera ya zauna yana rik'e da wayarsa Android da d'an tissu ya shiga danna wayar dan yana son kiran Hajiar ya ji idan bak'in na gida ne ya shiga domin yanzun goma ce har da rabi duk inda Ashraf yake ya tabbata yana hanya. Yar hayaniyar da ya jiyo ce ta saka shi d'an duba gefen da yake zaune. Su Salma ne su uku sai Mimi ta hud'unsu sun fito sun nufo hanyar tsakiyar gidan wace take d'an kusa da motocin gidan suka ja suka tsaya. Idonsa ya so cirewa yana dan tab'e bakinsa saidai me? Da sauri ya maida kanta sakamakon ganin ba ko hula a saman kanta bare d'an kwali ko hijabi. Dariyar da Mimi tayi ne ya saka shi zuba mata ido ta dafa gefen kafad'ar k'awarta tace " Na dai ji, kina ta maganar na isheku tsoho tsoho gani daram a matsayin matar tsohon na ji, aman ai ko ya ya dai Old man ya fi mijinki wallahi tunda shi ban ga tumbi a tare da shi ba!" Salma ce ta zaro ido tace "Shegiya! kar dai ki ce min har kin gano girman oga? Wayo duniya wayo aure mai daraja yanzun Mimi ke din na da nake gani a b'agas har kin je cen da Haj man ya sheik?" Mimi ta yatsina bakinta tace "Kunga ni fa irin wannan zancen naku ke had'ani daku, shikenan ba damar a had'u da ku sai ana kauce layi? To bama wannan ba ke yanzu wannan kayan nawa ai kin san mai iya jansu sai d'anye sabon jini ...." Ta fad'a tana mai d'an juyawa a gabansu ta d'an juya mazaunanta A hankali ya lumshe idonsa yana furta " A'uzubillahi mina-shaid'anin rajim! subhanallah, subhanallah, subhanallah, hasbunallahu wa'imal wakil, Innalilahi wa'inna ilaihi raju'ne!" A hankali ya ringa jin ransa na biya tayin neman rigimar yarinyar cen, wai yanzun shine old man kuma bata jin kunyar fad'a a gaban kowa? Uwa uba yanzun su yaren nan ina iyayensu da suka fito da sassafe suke son fitar da matar mutane har suke maganganu na rashin d'a'a haka? Shin wai yaya aka yi tarbiyar 'ya'yanmu ta lalace? Wai Ryam ita ce da cewa shi ba zai iya juya wannan abin dake jikinta ba? Wani d'an murmushi mai ciwo yayi yana datse leb'ensa na k'asa, idonsa da suka yi ja suka kad'a ya kuma d'orawa a kan k'ugunta, lallai sai ya nunawa yarinyar cen meye namiji, meye mai sunan namiji, sai ya banbance mata k'arfin namiji ba a shekarunsa yake ba, sai ya danna mata abinda zata ji har mak'ogwaronta, sai ya jijiga rayuwarta da hajijiya ya timata a k'asa ta yanda ko an ce ga namiji gabanta zai fad'i! Da haushi haushi ya kalli yanayinsa yana mai jan tsaki a bayyane yayi gagawar d'ora k'afa d'aya kan d'aya ya matse k'afafunsa sannan ya dafe gaban goshinsa da hannunsa mai d'auke da agogon azurfa. Ruky ce tace "Kun ga ku wuce mu tafi dan Allah, shiyasa ban so muka biyo ba yau wallahi, zama na musamman nake so muyi dake ai." Salma ce tace "To wai yaya ke ma zaki koma makarantar?" Cike da tabbaci tace "Me zai hanani kuwa, ku zuba ido ku gani." A haka suka ringa yar hirarsu ta k'awaye suna shan dariyarsu kafin suyi gaba tana nan tsaye da rigar dake jikinta doguwa kalar bleu, rigar sosai take rawa a jikinta koda bata da abin kad'awa bare tana da su. Mik'ewar mai gadi ya nuna alamun zai bud'e k'ofa ya saka sheikh saurin mik'ewa tsaye daga zaunen da yake. Da sauri ya kuma kallonta ganin tsaye take ta zubawa motar dake danno hancinta cikin gidan ya saka shi d'aga k'afarsa da saurin da bai tab'a tunanin yana da shi ba sakamakon irin yadda zuciyarsa ke bugawa ya ware yan yatsunsa da kyau ta yadda zata shiga juwa idan ya isar mata da sak'on da yake son isar mata wanda ya tabbata duk dukan da Abanta zai mata da muciya bai tab'a shigarta haka ba ya nufeta gadan gadan idonsa har rufewa suke da tsabar kishi da tsoron kar Ashraf ya tarda ita da wannan shigar. Bata ankara ba, bata lura ba kamar yanda bata san dashi ba, hannunta kawai taji an figa da wani irinu k'arfi dake nuna wanda ya mata rik'on a hassale yake, da sauri ya shiga janta zuwa falon ita kam kamar zata kifa a k'asa, Hajia da fitowarta kenan tun da Mimi tayi bak'i ta shiga d'aki ta gansu tare, saidai yanda fuskar sheikh ke d'auke da mafificin b'acin rai sai kawai ta shiga furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Fatanta d'aya kar sheikh yayi abinda za'a bugashi a jarida, mutum ne da ba zaka ce ga abokin fad'ansa ba, amma dai bai iya hushi ba ko kad'an. D'akinta ya wuce da ita tare da wurgata ta fad'i k'asa, k'ara ta saki da k'arfinta ta furta "Ahhhhhh...." Tsaf ta had'iyeta sakamkon fizgo damtsenta da yayi ya mik'ar da ita da k'arfi, bata gama gane ko da fuskarsa ba kawai ya damk'i damatsanta ya shiga jijjigata kamar b'era a cikin kwano cikin wata irin muryar ban tsoro yake fad'in "Ke wai har yaushe kikayi girman da maganganu irin wannan zasu riga fita a bakinki? Ni ne kike wa duk abinda kika ga dama Ryam? To ki sani na karb'i wannan tayin rashin mutumcin na ki, wallahi ba dan tsoron Allah ba da inna kirta miki wata buru'ubar ke sai kin d'auka ko ni kad'ai ne d'an iska a duk fad'in niger, amma a haka ma zan miki daidai da kalar naki rashin mutumcin, ni zaki dinga kallo kina kirana da sunayen da kika ga dama har a gaban k'awayenki, ke duk duniya babu wanda ya tab'a kwatanta yi min abinda kike min a yanzu, wallahi idan kika ci gaba ba zakiyi sati a gidan nan ba gabana zan mayar dake dan na kula k'arancin sani ke damunki." Tureta yayi hakan yasa tayi tangal tangal zata fad'i dan sosai ya wujijjigata, hanayyenshi ya zagaya ta k'ugunta ya jawota da k'arfi, take ta fad'a kanshi tana zaro idonta tana kallonshi a matuk'ar tsorace dashi, bai tsaya jiran komai ba y'a damk'i d'uwawunta da hannayenshi yana matsawa yana fad'in "Wai har wannan kike juyawa kina fad'in ni ba zan iya jansu ba, na tabbata dan Allah ya tsara kowace halitta da mazaunai shiyasa ke ma kika mallakesu, amma ba dan haka ba ke ina abinda zai isheni a nan bare har ya d'aga min hankali na." Ba tare da tunanin komai ba ya kama hannayen rigarta yayi k'asa da su hakan hakan yasa nonowanta dake hulu-hulu farare tas dasu suka bayyana dan ita fa zuwan su Salma ne suka tasheta daga bacci, ba tayi wanka ba barre ta saka bras. Sheikh da yana zage rigar yace "Har wannan b'erayen..." Cak ya dakata dan ganin abinda ke neman fin k'arfinshi, bai tab'a hasashen zata kai haka ba sabida yanayin shekarunta da fuskarta, tabbas ko hannu zaisa ya damk'a zasu cika girman tafin hannunshi, hakaan ya haddasa mishi wani mugun jiri ya nemi kayar da shi, da sauri ya tureta a jikinshi ya juya baya yana rufe ido tare da furta "Ya Hayyu ya Qayyum." Mimi kam a gigice ta juya da gudu ta shige ban d'aki ta rufe k'ofar ta jingina, sulalewa tayi ta sako da wasu hawaye masu zafin gaske, a rayuwarta bayan mamanta ba wanda ya tab'a kwatanta tab'a inda mutumin nan yau ya tab'a, a hankali ta saki wani kuka mai tsuma zuciya tare da gyara rigarta, wani irin bugu zuciyarta ke yi kamar zata fito daga k'irjinta. K'wank'wasa k'ofar da Hajia tayi ya dawo dashi hayyacinshi, a hankali kuma a nauyaye ya shiga taka k'afafunshi da k'yar ya k'arasa fita, tsaye take bakin k'ofar duk a tsure take da tunanin abinda zai faru, cikin girmamawa tace "Ashraf ne suka k'araso." A hankali ya lumshe ido alamar to, takawa ya fara yi zuwa falon saidai kash wani babban tashin hankali da abun kunya ne ya bayyano a jikinshi, sai yaji kamar ya cire hiraminsa yayi walki da shi ko zai rufe mishi sirrinshi, da k'yar yayi dubarar dan jan rigar har ya k'arasa ya zauna akan kujera. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *33* Da girmamawa Asma'u ta sunkuyar da kanta ta rusuna sosai tace "Ina kwana." Da sauri Ashraf ya rik'e hannunta wanda yin hakan ya haifar mata da wani fad'uwar gaba da kuma tashin tsigar jiki, kallonta yayi cike da gargad'i cikin rad'a yace "Baya amsa gaisuwar ina kwana ko ina wuni, sallama kawai." Wasu yawu ta had'e sannan ta kalleshi, sai taga kamar ma bai san da zamansu ba kan shi a k'asa kamar yana wani tunani, zaman Hajia akan kujera ne yasa shi saurin d'aga kanshi ya kalli inda suke zaune, shiru yayi bai ce komai ba har saida ya tabbatar sun gaisa. D'aga kan shi ya sake yi ya kalli Asas cikin wata tsumamiyar murya yace "Ashraf, zan iya sanin dalilin da yasa tunda aka d'aura aurenka baka zo ka ga Hajia ba sannan baka d'aga kiranta?" Rarraba ido Asas ya fara yi yana kallon Hajia da sigar "Ki rarrashe shi dan Allah, ba zan iya da masifarsa ba a halin da nake ciki." D'auke kai Hajia tayi kamar bata fahimci me kallonshi yake nufi ba, sunkuyar da kai yayi sosai yace "Kuyi hak'uri dan Allah, ina cikin damuwa ne shiyasa." A tsawace kuma a hassale yace "Damuwa? Asas wace irin banzar damuwa ce ta gidan duniya da zata sa ka manta da mahaifiyarka? Har ita ta nemeka a waya amma ka k'i d'aga kiranta, kasan girman laifinka kuwa?" Wani wawan tsaki ya ja ya juyar da kan shi gefe sannan ya ci gaba da fad'in "Shin k'addarar aurenka ce ka kasa d'auka a matsayinka na musulmi? Ko kuma dai *Ryam* dana aura ce har yanzu baka cire a zuciyarka ba? Idan hakane ka fad'a min, yanzun nan a gabanka zan saketa sai ka aura inhar hakan zai sakaka farin ciki." Da sauri duk suka kalleshi har da Asma'u dake ganin kwarjininshi, da sauri Asas hankali tashe ya girgiza kai yace "A'a sheikh, wallahi na hak'ura har abada, na rumgumi k'addarata da hannu biyu, kuma insha'Allah zan ci gaba da rik'ewa." Wani nauyayyan numfashi ya sauke a sanyaye yace "Daga mu mazan har matan ya kamata mu d'auki wannan auren a matsayin k'addararmu, dukanmu babu wanda yayi hasashen hakan zai faru, babu wani mahaluki daya zauna ya tsara hakan, yin ubangiji ne, haka ya so ya kasance, shin da wace ni'ima ce muke k'aryatawa? Ikonshi ya fi gaban wasan bawa, komai yahudancin mutum idan mu'ujizarshi ta faru dole ya kan karya zuciya, saidai kawai mutum ya k'i gaskiya amma fa ya tgidanmu akan k'arya yake. Mu musulmi ne Ashraf da muka yarda a jerin rukunan imani guda shida akwai yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau, tunda muka amsa sunan musulmi mu yarda da duk jarabawar da zata samemu, ko kana so ko baka so dole ta zo, ta maka dad'i ko bata maka dad'i ba dole a jarabceka, saidai fa mu sani duk jarabawar da za'a wa mumini matuk'ar yayi imani kuma yayi hak'uri, to yana da sakamako mai tsoka. Yanzu wane gata ne ya fi wannan? Wane addini ne ya zo da irin wannan alkairan ga mabiyansa? Zazzab'i zakayi mai mugun zafi da zai saka ka fita hayyacinka, amma daga sanda ka kwanta har ka tashi lada ce mala'uku ke rubuta maka na sannan ana kankare zunubanka, da wannan zan rok'eka kayi hak'uri da jarabawarka sannan ka rik'e 'yar mutane da amana, ban da cin zarafi da halayen mata wato gori, watak'ila yarinyar nan ita ce warakarka da kake yawan fad'a mana." Sosai jikinshi yayi sanyi har yana share k'wallar dake taruwar masa, dan gaskiya da ya so yayi sati kafin ya zo gidan nan, sannan Asma'u ya so ya zauna da ita dumkum d'in nan har sanda zata gaji tace sallameni, amma yanzu sai yaji wata sha'awar son zama da ita na shigarshi da kuma kyautata mata. A tausashe sheikh ya sake fad'in "Mahaifiyarka da shaid'an ya zigaka har kake ganin ta maka ba daidai ba har da tagomashin hukuntata ta hanyar nesanta kanka da ita, ka bata hak'uri yanzun nan ka kuma nemi yafiyarta, sannan karka sake maimaita min irin wannan kuskuren dan ba zan d'auka ba, uwa daraja ce da ita, kima ce da ita da babu wani abu mai daraja da zamu iya had'awa da ita, munyi sa'a Allah ya bar mana ita, ita muke zuwa mu fad'a ma kukanmu da farin cikinmu, Ashraf kayi sa'a kai ta ka mahaifiyar ma tana raye, ni ina tawa take a yanzu? Nayi imani da zata dawo yanzu a duniyar nan na minti d'aya kawai ta umarceni da na auro biyu akan biyun da nake da a yanzu, wallahi tallahi zanyi dan farin cikinta, ita ta tsaya min na taka matakin da nake kai yanzu, ita ce k'ashin bayana da har na iya zama da d'uwawuna, addu'arta ce har yau take tasiri a gareni, kullum fata da burinta shi ne na zama babban malami kuma babban mutum." Wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi ya sa bakin hiraminsa ya share k'wallar data tarar masa a gefe, ya d'an jila yana shashek'ar kuka kafin yace "Sanda na fara hawa matakin da take da burin ganin na hau, sai Allah ya karb'i rayuwarta gaba d'aya ta bar duniyar, na d'auki hakan a matsayin jarabawata mafi girma, har yanzu ina kukan rashin mahaifiyata, ina kewarta, ina neman sa war albarka daga bakinta." Sake duk'ar da kai yayi dan sosai kukan nan ya ci k'arfinsa, mik'ewa yayi da sauri ya nufi hanyar fita, da kallo suka bishi jikinsu duk a tsume Hajia har da kuka ita ma, da sauri Asas ya taso ya zo kusanta ya zauna k'asa ya rik'e k'afarta yana magiyar "Dan Allah Hajiata, dan girman Allah ki yafe min, Hajia kar na mutu a yau kina hushi da ni, Allah k'onani zaiyi Hajia ki yafe min." Rik'e hannunshi tayi tana share k'walla tace "Ba komai Ashraf na yafe maka, ai tun jiya ma sheikh yasa na yafe maka." D'ora kanshi yayi a cinyarta yana sauke numfashi yace "Nagode Hajiata, Allah k'ara miki lafiya da nisan kwana." "Ameen." Ta fad'a tana kallon Asma'u da tayi shiru jikinta yayi sanyi ganin sheikh na kuka, da hannu Hajia ta mata alamar ta zo, mik'ewa tayi tana gyara hijabinta ta zauna k'asa ita ma, dafa kanta tayi tace "Allah ya miki albarka Asma'u, kuyi hak'urin zama da junanku kunji." A tare suka jinjina kai kafin ta rik'o hannayensu ta had'a wuri d'aya, a take suka kalli junansu sabida yanda ta had'a hannayen nasu, cikin fara'a tace "Zaman lafiyarku shi ne farin ciki na, ku girmama junanku ba tare da tuna ta yanda aurenku ya kasance ba, na tabbata akwai abinda Allah yake nufi da auren na ku, komai k'ank'antar alama a cikin tarayyarku zamu d'auketa mu rik'e a matsayin abinda Allah ya hukunta, dan haka kuyi hak'uri ku tallafi junanku wajen samar da kyakyawan sakamakon da zamuyi nuni da shi." Jinjina kai sukayi sosai kafin ta saki hannayensu, kallon Asma'u tayi tace "Ki shiga ciki k'awarki na nan." Da murmushi ta mik'e ta nufi inda Hajiar ta nuna mata, da sallama ta shiga d'akin tana tura k'ofar. Mimi da har lokacin take zaune a k'ofar ban d'akin da sauri ta mik'e jin saallamar Asma'u, bud'ewa tayi ta fito suka hada ido, wani kukan ta fashe da shi tare da tahowa a guje ta rumgume Asma'u tana fad'in "Asma'u mugu ne, ki tafi dani dan Allah ki kaini gidanmu, cire min kayana yayi." Cikin tashin hankali da rashin sanin inda zancen ya nufa Asma'u ta d'ago tana fad'in "Ya cire miki kaya? Wanene?" Cikin turo baki tace "Waccen malamin mana." Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke, kama hannun Mimi tayi suka zauna kan gado, a tsanake ta kalleta tace "Mimi me ya faru? Nasan dai haka kawai sheikh ba zai miki rashin kirkin da har zaki kirasa da mugu ba idan ba ke kika tsokano shi ba." Share hawayenta tayi dan zuwan Asma'un yasa duk ta ji babu wannan tsoron da k'uncin, cikin rashin damuwa tace "Ke ni bansan me na masa ba, kawai dai ya hau ni da masifa da tijara." D'an guntun tsaki tayi tace "Kinji fa yana malami amma yake fad'in idan iskanci zaiyi a niger zan d'auka shi kad'ai ne ya iya iskanci, hmmm." Ta fad'a tana mik'ewa tsaye, da kallo Asma'u ta bita tace "Ai gaskiya ya fad'a miki, mahaddacin Alk'ur'ani masanin sirrin yahudu da nasara kina ganin akwai wani abun ne da zai shige masa duhu?" Tab'e baki tayi ta d'auki dogon towel d'inta ta d'aura a k'irji sannan ta k'arasa cire rigar gaba d'aya, matsowa tayi kusan Asma'u cikin rad'a tace "Ke har da tab'a min d'uwawu yayi, wallahi ki fad'a masa yayi na k'arshe." Dariya Asma'u tayi tace "Ai sadakinsa ya biya, kad'an ma kika gani yarinya kafin ki tare." Sake tab'e baki tayi ta shige ban d'akin Asma'u na fad'in "Ke tare da shi fa muke zaki wani shanya ni a nan?" Tsayawa tayi ta juyo tare da kallonta tace "Tare kuke? Wani gurin zaku je?" Girgiza kai tayi tace "Ke bakiyi mamakin gani na ba a yanzu? Jiya ne dama yace sheikh ya ce mu zo nan." D'aga mata gira tayi tace "Wani abu ya muku?" Girgiza kai tayi tana fara'a tace "Nasiha ya mana mai shiga zuciya." Yatsina fuska tayi tace "Ki gaishe shi to." Ta fad'a tana shigewa ban d'aki dan yin wanka, girgiza kai Asma'u tayi ta mik'e tana murmushi ta fita a falon, jiranta ta samu Asas na yi tana zuwa yace "Muje." Yanda ya mata magana d sakin fuska sai ya bata mamaki, sallama tayi da Hajia suka fice a gidan, tun a mota ya so kasheta da mamaki sakamakon hannunta daaya rik'o yana matsawa yana sakar mata murmushi, yanda take sunkuyar da kai yasa shi kallonta yace "Wai kunya kike ji? Lallai ma *Naanah* gwara ki daina, dan babu abinda zai hanani yau dai na sa ki amsa sunanki a matsayin *Asma'ul-Husna* matar Ashraf." Gabanta ya shiga wani irin lugude yana fad'uwa, sake duk'ar da kai tayi ba tace komai ba sai rawa maa da bakinta ya d'auka, da haka suka k'arasa gida saidai bai sake fita ko ina ba, tare suka wuni kuma sosai suka samu wata irin fahimta da shak'uwa, dan yanda ya fahimceta shi ne ita d'in bata d'auki duniya da zafi ba, duk abinda aka mata ko ta samu zata karb'a da hannu biyu tayi godiya ga sarkin daya nufeta da samun wannan d'in, hakan yasa shi fara jin ta daban a zuciyarshi tare da mata wani kallo na matar aurenshi wacce zai iya yak'i a yanzun dan kare martabarta. *Yammacin litinin* Fitar Hajia yasa Mimi shigewa d'akinta ta kunna wak'a a wayarta, duk da ita d'in ba gwanar rawa bace amma sai gashi ta zage tana tik'ar abarta a d'akin tana kuma gyaran d'akin, dan in kid'a ya kai mata har tsayawa take a gaban madubi ta cashi abarta kafin ta ci gaba da aikin. Sheikh ma na shigowa gidan da niyyar daya bata sak'onta ya wuce gida, dan litilin d'in yau ta zama mai sauk'i aiki a gareshi a ofishi, dan haka yayi saurin baro ofishin ya fara biyowa ta gidan, Salamatu na gad'a mishi Hajia ta fita sai kawai ya wuce d'akin kai tsaye, duk da kuwa zuciyarshi na kwab'arshi k'walwarshi kuma na tuna mishi had'uwarsu ta safe, d'aure fuska yayi ya bud'a k'ofar da tunanin sai fa ya gyara mata zama dole yarinyar nan. Ai kam turus yaja ya tsaya sakamakon jin kid'a da kuma ganin k'anwar *shakira*馃ぃ, da d'an k'arfi ya furta "Hak'ik'a daga Allah muke kuma gareshi zamu koma." Waro ido yayi da kyau dan shi ko cikin yaranshi a k'iriniya ta yara bai tab'a ganin haka ba. Jin sautinshi ya fargar da ita da sauri ta tsaya tana kallonshi, pik'i-pik'i ta tsaya yi da ido tana neman hanyar dakawa a guje, takowar daya fara yi ce ta sa ta ja baya tana fad'in "Dan Allah malam dan soyayyarka da Allah karka dakeni, kaga dai Hajia amanata ta bari ko?" Yanda ta k'arashe maganar da nunashi da yatsa irin a dole tambayarshi ne take cikin yanayin yi mishi hannun ya mai sanda sai ta so bashi dariya. Tara mata hannun dama yayi yace "Bani wayar nan?" Galala tayi tace "Iyee?" Fito da idonshi yayi yace "Na ce ki bani wayarki?" Da sauri ta d'auka ta mik'o mishi tana sake fad'in "Malam ai ku an ce ba kwa hushi saboda magada annabawa ne ku, dan Allah kar ka rabani da wayar zan daina daga yau." Sama da k'asa ya kalleta ya mik'a mata k'atuwar ledar hannunshi, hannu biyu tasa ta karb'a shi kuma ya d'ora da fad'in "Wannan ita ce zata zama suturarki idan zaki fita." Juyawa yayi kawai ya fita yana sake hangota tana ta kiciniyar rawa a shigowarshi, girgiza kai kawai yayi ya fita a falon, saida ya shiga mota dreba na jan shi ya shiga duba wayar, irin tarikitan hauka daya gani saida yaji kanshi ya fara ciwo, vid茅os na wak'ok'i da girki da kwalliya da shirme da shiririta na dariya, hotuna na d'inki da matan da bai ma san dan d'inki ne aka aje hoton ba ko kuma dan kwalliyarsu, tsaf ya tattara komai ya goge ban da girki da yake ganin zasu anfani mace, sai kuma hotunan ta daya samu barkatai wanda ya tabbatar zuwan k'awayen nan nata zata samesu, kallon hotunan ya shiga yi yana murmushi, idan ya ga wani style d'in sai kawau ya tintsire da dariya shi kad'ai, lallai kawai ya gama yarda yarinyar yar zamani ce, da wannan ya isa gida inda suka zauna a duka babban falon shi da ahalinsa suka shiga hira da raha ana tsokanar juna, a sauk'ak'e kuma iyayen ke fahimtar wani kuskure na kalma a tare sa yaran sai su d'orasu a hanya. Bayan fitarshi kuma Mimi ta bud'e kayan nan, hijabbai ne zumbula zumbula har k'asa ko hannaye basu da, sai nikab da safar k'afa. Kecewa tayi da dariya tana fad'in "Wayyo Allah na akaramakallah, yo wannan ka d'auka ni d'in wata aljana ce? Tabb' lallai ma!" Tattaresu tayi ta zuba akan gado ta shiga harkar gabanta da tunanin ta yanda zai dawo mata da wayarta ma, dan ita tafi damunta kam. *Asa-Ma'u* A wajen amaren kula yau fa daren na musamman ne dan sosai Asas ya zage damtse wajen kwasar amarcin shi da matarshi, kamar yanda yake hari matarshi ce zata zama silar warakarshi hakane ta kasance. Sosai Asas ya rik'e wuta akan baiwar Allah Asma'u, tun tana jin kunyar nuna gajiyawarta har ta fara mishi kukan tab'ara tana magiyar ta gaji haka, mamaki yake yanda ya kasa sararawa 'yar mutane, jikinshi k'ara rik'ewa yake yana d'aurewa, hakan yasa suka galabaita daga shi har ita. Wata masifaffiyar zufa ce ta shiga tsatsafo masa sanda ya sauke wani curarren abun daya tarar mishi a mara, take kuma sai jikinshi ya kwashi b'ari sosai, cikin tashin hankali Asma'u ta yunk'ura ta shiga tureshi a jikinta saboda ganin yana wani shure shure kamar zai mutu, fashewa tayi da kuka tana jan zanin jikinta da k'yar tana fad'in "Assss...a..." Gaba d'aya sai ma ta manta sunan da zata kirashi da shi. Tsaf ta ga ya daina numfashi bare motsi, a firgice baiwar Allah duk da azabar da take ji a jikinta sai ta manta, da gudu ta shiga ban d'aki da zanin rufa a jikinta ta rufe jiki ta d'ebo ruwa ta shafa mishi, shiru ba alamar Asas zai dawo, ai da sauri ta bud'a kayanta ta d'auko doguwar rigar atamfa ta saka ta fito wajen gidan, cikin tashin hankali take k'wala kiran "Mai gadi, mai gadi." Kamar daga sama yaji kiran sunan shi ma a kid'ime ya fito yayo kanta, da gudu ta juya ta koma tana fad'in "Muje ka taimaka min, bashi da lafiya." Da gudu ya bi bayanta suka shiga d'akin, ganinshi kwance babu kaya a jikinshi sai zanin gadon data ja ta rufa mishi, juyawa yayi yana fad'in "Hajia saka mishi ko duguwar riga, bari ni saina kira lambar Hajiarshi." Fita yayi a d'akin da sauri tana matsar k'walla da cije leb'enta dan sosai take jin ciwo a jikinta, kawai dai tashin hankali ne wani yafi wani, da k'yar ta saka mishi dogon wandonshi na bacci da doguwar farar rigar, zaune tayi ta sakashi gaba tana kallo tare da rik'e hannunshi, babban abinda ke ranta a lokacin bai wuce "Kar a zo *sanadin takaba* ne yasa aure na da Asas ya tabbata, Allah ka tashi kafad'unshi kasa kar ya mutu ya barni, duk da ba son shi ne a zuciyata ba amma zan so ya zama mutumin da zai ci gaba da abonda ya fara." Mintuna ashirin da biyar suka kawo Hajia gidan tare da drebanta, tana shigowa d'akin Asma'u ta mik'e tana sake fashewa da kuka, cike da dagiya Hajia ta dafata tace "Me ya sameshi Asma'u." Cikin kuka tace "Hajia ban sani ba nima, kawai...kawai fad'uwa yayi haka." Sake kallonshi tayi ta kalli gadon, da sauri ta d'auke idonshi daga birbid'in jinin data gani a kan zanin gadon dake jikinshi, saidai tana mayar da idonta k'asa sai kuma akan pant d'in Asma'u, cikin dattako da hangen nesa ta fahimci me ya faru, kallon k'ofar shigowa tayi tace "Kabiru." Daga falo drebanta ya amsa da "Na'am Hajia." "Ku shigo ku kama mana shi." Da sauri suka shigo tare da mai gadin, wani ikon Allah yau Hajia sam bata jin wannan rud'ewar da furgicin da take shiga idan ciwonshi ya tashi, sauta samu kanta da fad'awa zuciyarta "Idan har wannan ita ce warakar Allah ya yafe kurakurenshi, idan yana da sauren shan ruwa a gaba, Allah ya tashi kafad'unshi." Kallon Asma'u tayi sanda zata fita tace "Yata ki nutsu kinji, ki zauna ki kula da kanki kafin jikinki yayi tsami, ina tare dashi insha'Allah zan kula dashi." Cikin kuka Asma'u tace "A'a Hajia zan biku nima, a tsorace nake gaskiya ina so nasan halin da yake ciki." Girgiza mata kai tayi tace "A'a Asma'u, ki zauna ki samu euwan zafi kiyi wanka kinji, ki kula da kanki nima zan kula dashi." Cikin marairaicewa tace "Hajia ina so na je na ga halin da... *mijina* yake ciki." Murmushi tayi ta shafa kumatunta cike da tausayinta tace "Yanzu ki fara gyara jikinki, idan gari ya waye zan turo k'awarki sai ku tafi tare." Da sauri ta kalleta tace "Mimi?" Da fara'a ta d'aga mata kai alamar eh, jinjina kai tayi ta bita da kallo harta fita, jiki a sanyaye ta fito falon ta shiga madafa dan d'ora ruwan zafin kamar yanda Hajia ta fad'a. *Washe gari* Tunda asuba sheikh ya zo asibitin ganin halin da yake ciki, cikin nutsuwa Hajia ta shiga fad'a mishi abinda Dr. D'in ya fad'a "Ya ce dai wannan karan ciwon ba kaman waccen ba, dan haka ruwa suka k'ara mishi ba tare da alluran da suka saba yi mishi ba." Numfashi ya sauke yana sake gyara tsayuwarsa yace "Insha'Allah Hajiarmu komai ya kusa zuwa k'arshe, jiya da dare nima na sak'o a email d'ina daga wani abokin karatu na dake Tunisie, kuma ya fad'a min ya sama mana lokacin had'uwa da wani babban likita daya k'ware a wannan fannin, insha'Allah yau zan gama shirya mana tafiyata da shi, gobe ko jibi zamu bar k'asar nan da izinin Allah." Da farin cikin jin haka tace "Masha'Allah, Allah nuna mana, Allah yasa ayi a sa'a." "Ameen." Ya fad'a a sanyaye yana kallon Asas, d'an sake kallon Hajia yayi yace "Ina iyalinsa?" Kallonshi tayi tace "Tana gida, amma na tura Kabiru ya d'auki Mimi a gida saiya kai ta can wajenta, dan na lura hankalinta ya tashi sosai kuma kamar bata da lafiya, amma na ce Salamatu ta fad'awa Mimi idan ta ga jikinta da sauk'i su zo nan tare ta ga jikinshi." K'uri! Yake kallon Hajia duk sanda tace Mimi yana jin wani b'all! A zuciyarshi, kallon fuskar Hajia kawai yake yi yana tunanin "Anya kuwa Hajia tasan wacece yarinyar nan?" D'an d'auke kan shi yayi a hankali yana sauke numfashi, jim kad'an ya sake kallon Hajia yace "Hajiarmu zan wuce gida, dama daga masallaci nake, amma idan na shirya kafin na wuce aiki zan sake biyowa na ganshi." Da sakin fuska tace "To sheikh ba damuwa, sai ka dawo." *Mim-Ma'u* *Assalama alaikum* _Kwanakin da suka wuce zaku ga na zage ina ta baku page bibbiyu a wuni d'aya wata rana ma har uku, ba komai ya kawo haka ba sai ganin kuna comment masha'Allah. Watak'ila lura da kukayi ina yi akai akai ne yasa wasu tunanin ko zaman banza ya min yawa, dan haka zakuyi tunanin barin comment da tunanin ai zan ci gaba da sako muku, magana ta gaskiya abinda yasa a can ma kuke ganinshi a kai a kai comment d'inku ne ya ban k'arfin gwiwa, yanzu kuma da kuka rage sai gaba d'aya na mayar da hankalina kan harkokina da kuma rayuwata, *jiya* da k'yar da taimakon *Kwate ta* (Sajida) na samu na saki page d'in jiya, to da irin haka wata rana ma kasa rubutun zanyi._ _Dan *Allah* mu daure mu k'arasa yan tsirarun page d'in da suka rage mana, dan *MATAR MUTUM* ba labari ne ba da zan ja shi da tsayi ba, kuma ina fata matar mutum ya zama labarina na k'arshe a harkar rubutu, idan Allah bai nufeni da hakan ba kuma ina fatan nayi hutu mai dogon zangon da har za'a fara mantawa da sunana kafin na ci gaba, dan Allah ku karfafa min gwiwa ta hanyar sambad'a comment ko na samu na kai k'arshen labarin nan, a grp d'ina a k'alla sama da mutum 50 suna karanta labarin nan a sanda na turashi, amma mafi aksarinku saidai ku turo stekers da sunan kun yi naku comment d'in shikenan, ba zan sake ganin motsinku ba sai na jinkirta yin posting. To a gaskiya idan haka ta ci gaba da faruwa zan dakatar da posting zan kammala rubutu ne saina had'a document na ajiye kayana, dan ni bana tsayar da rubutu idan na fara, kunga kenan shi ma zai shiga sahun litattafaina dana mallaka._ *MOM LATEEF* *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *34* Duk da duhun safiya ce amma haka Mimi ta shirya tsaf abinta a cikin atamfarta riga da siket d'amammu ta saka hijab d'inta mai hannaye iya gwiwa tsayinshi, gashi kuma hijab ne irin na zamani mai wuya biyu ga kwalliya, dreba na ajeta gidan Asma'u ta shiga kallon gidan daga waje har ciki, saida ta kai daf da shiga falon ta sauke wata ajiyar zuciya tana jinjina kan ta, sosai tsarin gidan ya birgeta dan kamar yanda Asas yake fad'a mata haka ta samu gidan. Saida ta bud'a k'ofar ta shiga a tausashe ta furta "Salam." Asma'u da dama zaune take tana jiranta da sauri ta fito daga uwar d'akin tana amsawa da "Wa'alaiki salam." Murmushi Mimi ta sakar mata inda Asma'u ta mata murmushin yak'e, cikin ciccije lab'e ta k'araso gareta tana fad'in "Muje." Hararanta tayi tace "Wai ke duk kin damu ko? Ke ga mai miji." A raunane tace "Ba zaki gane ba Mimi, halin da nake ciki Allah ne kad'ai ya sani kuma zai sama min mafita." Cikin gimtse fuska tace "Wani abu yana faruwa ne?" Kama hannunta tayi tace "Muje, zamuyi magana." Yanda ta ga Asma'un na tafiya ita ma sai ta shiga bin ta a haka har ta rufe gidan suka fita, dukansu zaune suke a bayan motar sunyi shiru suna kallon titi. Numfashi Mimi ta sauke tace "Hajia tace min ba kya jin dad'i na zo na taimaka miki, ke kuma hankalinki yana gun mijinki." D'an murmushi tayi tace "Hummm! Na ji sauk'i ai." "Kin tabbata?" Ta fad'a taana binta da kallon tuhuma, dan duk da bata da sani akan wannan harkar amma dai a karance karance da kutse kutse tana iya gane kad'an daga ciki, shiru kawai tayi bata sake cewa komai ba har suka isa asibitin clinique de gazobi. A wajen ajiyar motocin ya paka suka bud'e cikin nutsuwa suka fita. Tsaf daga shigowarsu har fitarsu daga motar duk a kan idon Sheikh da shi ma shigowarshi kenan zai shiga d'akin da Asas yake, tsayawa yayi yana k'are mata kallo kamar ya d'ora hannu a kai yace "Wayyo shi wayyo Allah ya shiga uku!" Akan me zata fito babu hijab d'in daya bata? Babu nikab a fuska bare safar ta k'afa, kenan ba zata tayashi kare martabarta ba? Wani huci ya sauke mai d'auke da siracin bala'i da gudummuwar kishi ta haifar, a sauk'ak'e ya shiga takowa cikin shigarshi ta kamala da mutumci. Zasu wuce kenan suka ji drebansu Hajia na gaisheshi cikin girmamawa da ladabi, dakatawa sukayi inda Mimi cikinta ya fara juyawa ga fad'uwa da gabanta ya fara yi, Asma'u ma juyawa tayi tabbatarwa da tayi shine yasa ta sunkuyawa tace "Assalama alaikum." Da sakin fuska ya amsa mata da "Wa'alaiki salam, ya jikin na ki?" Tsili tsili tayi da ido da tunanin wai haka Hajia ta mata terere? Da murmushi ta amsa da "Na ji sauk'i ma." Da fara'a yace "Masha'Allah, a ci gaba da hak'uri kinji, insha'Allahu zai samu lafiya, dan muna shirin fitar da shi waje." Jinjina kai tayi cikin girmamawa tace "Allah ya aminta." "Ameen." Ya fad'a yana d'an satar kallon mutuniyar da tayi tsaye k'erere tana ta sinne kai alamar rashin jin dad'in had'uwa da shi duk ta bayyana a tare da ita, d'auke idonshi yayi ya mayar kan Asma'u da ita ma kan ta ke k'asa yace "K'arasa ciki." Gyad'a kai tayi da ladabi zata wuce Mimi ma kamar wutsiya ta bi bayanta, cikin dakakkiyar murya yace "Inna Issa." Kyab'e fuska tayi ta juyo ta kalleshi, wani kallon gargad'i ya mata yace "Zo mana." Turo bakinta tayi ta kalli Asma'u data shiga tafiya, a hankali ta shiga takowa tana ta turo baki gaba, ba tare daya kula da mutanen dake kai kawo ba ya rik'o hannunta dake waje dan ta saka hannayen hijabin, shi kuma abinda ya b'ata masa rai kenan yanda jan lallenta ya fito sosai kowa na kallo, cikin nutsuwa ya shiga nufa da ita wurin da motocinshi ke pake, jami'an na ganin haka su ma suka bud'e mishi mazauninshi, da hannu ya mata alamar ta fara wucewa. Kallonshi tayi ta fashe da kuka ta girgiza kai alamar a'a, wurga mata ido ya sake yi alamar fa ta shiga, d'aga kanta tayi tare da d'add'age yanda zata hangi Kabiru dan yanda yake tsaye gabanta masha'Allah ya gaje wurin da girman jikinshi da kuma manyan kayan. Tana hangen Kabiru sai kuwa ta d'aga murya iya k'arfinta cikin kuka tace "Kabiru, ka fad'a ma Hajia an d'aukeni...." Hararar daya wurga mata yasa ta saurin shiga motar tana sake fashewa da kuka tana ja baya har ta dangane a d'aya murfin k'ofar tana fad'in "Ustaz kayi hak'uri, kaga dai ni wallahi ban yi komai ba, ai ka karb'e wayata tun jiya ko? Kuma na hak'ura ban ce komai ba, dan Allah yanzu kuma me na yi? Kuma kuka hana cin zalin na k'asa, ni dai yanzu kayi..." Jin an tayar da motocin sanda ya shiga yana kallon zasu bar asibitin yasa ta jujjuyawa, duka motocin guda uku kuma suka bar asibitin, shiru tayi da bakinta ta sinne kan ta da k'ura mata ido ne yayi yana kallo kamar zai cinyeta d'anye. Tunani ne kala kala ke ta bijiro masa na yanda zai tsawatar mata ta fara gane idan ya ce tayi to kawai tayi ko bata so, zuciyarshi na ta hasaso mishi abubuwa da dama saidai ba d'aya wanda yayi ammana da su. Amma fa k'wala kiran sunan Kabiru da tayi ya masa zafi, a bainin nasi zata fitar da muryarta haka, to wai ko bata da ilimin addini ne? Amma kuma ai tana zuwa islamiyya. Numfashi ya sauke a ranshi yana fad'in "Watak'ila asarar lokaci ne bata fahimtar komai." Da sauri ta kalleshi dan abinda ya fad'a ya fito fili, yanda ta kalleshi yasa shi farga da abinda ya aikata, fuska kawai yayi yace "E, ko kina ganewa ne?" Had'e fuska tayi ta kumburo baki alamar fa ranta ya b'ace, waro idonshi yayi yace "Idan da kina ganewa ai da kin zama mai suturta kanki a cikin gida ma bare idan zaki fita, kinsan kuwa me Allah ya fad'a akan ku mata yanda zaku saka jalbab d'inku?" Girgiza kai yayi yana sake tausasa murya yace "Ba zaki sani ba, shiyasa nake so na mayar dake islamiyya." Kawar da kanta tayi tana gunguni tare da fatan ya kaita inda zata sauka ta fad'i abinda ke ranta. K'ofar gidansu Hajia taga motocin sun paka sun tsaya, a hankali cikin nutsuwa ya bud'e b'angarenshi ya fita, mamaki da rashin sanin me ya dawo da ita nan yasa tana kallo har y'a zagayo b'aren da take, bud'e mata k'ofar yayi ya mik'a mata tafin hannunshi yana sakar mata murmushi da fad'in "Yan matan tsohonta muje." Marairaicewa tayi ka rantse da Allah marainiya ce, k'in mik'a masa hannun tayi ta fita a motar ta rufe da kan ta, gaba ta shiga zata wuce cikin sanyin murya mai kama da rad'a yace "Jirani." Cak ta tsaya amma bata juyo ba, saida ya tsaya kusa da ita kafin suka k'arasa shiga ciki, bai bi ta kan kowa ba sai wucewa da yayi har d'akin daya zama na ta a yanzun, tana kallo ya d'auki makullin d'an wani fau da fleurs alamar dai yasan inda ake ajewa ko kuma aljanunshi ne suka fad'a mishi, bud'e d'akin yayi tare da mata alama ta shiga, jiki a mace ta shiga kafin shi ma ya shiga maida k'ofar ya rufe. K'yak'yabta mishi ido ta fara yi wanda suka kawo ruwa dan gani take irin na jiya zai sake mata, jan majina ta faraa yi a dole ita kuka take, cike da rarrashi ta kalleshi sanda yake zama bakin gadon ta shiga fad'in "Bawan Allah, ai dai yau ban maka komai ba? Amma idan akwai laifin dana maka wanda ban sani ba dan Allah ka yafe min, kaga kai babba ne mai halin girma, biye ma yarinya mashiririciya iri na b'ata lokacin ka ne zakayi." Cike da izza da gadara ya d'ora gwiwar hannayenshi akan cinyoyinshi yana kallonta, a dak'ile cike da d'aure fuska yace "Ina kayan dana kawo miki jiya?" Da sauri ta nuna wurin kayanta tace "Suna can." "D'auko." Ya fad'a ba alamar wasa, jiki na rawa ta nufi kayan ta shiga kakkarwar d'aukowa, tana zuwa ta zube gabanshi tare da durk'usawa tace "Gasu." D'an d'aga hannayenshi yayi daga tangalewar daya musu ya kalleta da kyau yace "Ryam." Tarr! Ita ma ta sauke nata idon cikin nashi, a ladabce ta amsa da "Na'am." A sanyaye ya shiga fad'in "Mutum ne ni dake da tsari a rayuwa, ina so idan na ce wa mutum yayi to yayi abun nan ba tare da nayi maimaici ba, kamar yanda kika fad'a ni babba ne ke kuma yarinya mashiririciya, Ryam na fahimci kanki yana rawa sosai, hankalinki ba wuri d'aya yake ba, sannan nutsuwarki bata tare da ke. Abu d'aya nake so ki sani shi ne idan na baki uamrni kawai ki bi, kin fahimta?" Samun kanta tayi da kallon cikin idonshi tare da furta "Ko da umarnin ya sab'awa ubangiji?" Yanda ya kalleta yasa ta sunkuyar da kai, cikin muryar shan k'amshi yace "Bana fatan na umarci wanda ke k'asa dani da sab'awa mahaliccina." Numfashi ya sauke yace "Yanzu d'auki hijab d'in nan ki saka, dan wannan na jikinki ba hijabi bane shirme ne da hauka." Da sauri ta kalleshi ta bud'e baki irin mamakin nan, sai kuma ta jinjina kai ta mik'e, d'aukar d'aya daga cikin hijaban tayi ta cire wannan ta saka, yanda ya sauka k'asa ya rufe mata k'afafu ne yasa ta kallonshi tace "Abdul amma wannan hijabin na mamansu Aisha ne ka d'auko min ko? Dubeshi fa sharb'eb'e ya zanyi tafiy..." Shiru tayi dan ashe kallonta yake tana maganar nan, mik'ewa yayi tsaye tare da figota da k'arfi ta fad'a kan shi, lab'e fuska tayi alamar zatayi kuka tayi k'asa da kanta, cikin tsatsareta da ido yace "Maimaita na ji." Rarraba ido tayi tana d'an jan majina a hancinta sakamakon yanda k'amshin turarenshi ke shiga hancin na ta, cikin rawar murya tace "Mmm..ee?" Ba tare daya d'auke idonshi a kan ta ba ya saka yatsanshi manuniya ya shiga zagaya labb'enta yana fad'in "Abdul mana, maimaita na ji." Wasu yawu ta had'e masu nauyi tana kakkauce fuskarta tace "Kus...kure.. ne." Tallabo hab'arta yayi yana son tilastata ta kalleshi, duk da fuskarta suna kallon juna ne amma idonta k'irjinshi suke kallo sai kuma hawaye masu d'umin gaske da suka shiga kwaranyo mata, cikin tattausan murya yace "Ni kuma kuskuren na ki nake so, sake fad'a naji." Idonta rufe ta girgiza kai alamar a'a, ba tare da shi kan shi yasan yayi ba y'a marairaice yace "Dan Allah Ryam, sake fad'an Abdul na ji." Rintse idonta ta sake yi gaba d'aya take ji kamar an zare mata rai dan ta kasa motsi, labb'enta ne suka shiga hard'ewa tana fad'in "Aaaaabbbbdulll." Murmushin gefen labb'a yayi tare da jan dogon hancinta yace "Mai tsiwar tsiya." Sakinta yayi yana fad'in "D'aura nikab d'in." Sharb'ar majina tayi irin shmmmmm! D'in nan kafin ya d'auki nikab d'in, d'orawa tayi zata d'aura sai kuma wata zuciyar tace "Kenan ma yin abinda yace kiyi zakiyi ?" Sai kawai ta d'aura ta ba daidai ba ta fito da ido da hanci duk waje, wani k'ayataccen murmushi ya saki yana girgiza kai, matsawa yayi daf da ita yana kallon k'wayar idonta yace "Wato dai ni za'a ma wayo ko? Kin manta sanda aka haifeki ina daf da haifo kamarki ni ma." Cike da sangarta da sub'utar baki tace "Ai mamanmu ma ka girmeta." Sake bud'e idonshi yayi fes a kan ta yace "Inji wa?" K'asa tayi da idonta tana turo baki, hannu ya kai tare da kunce d'aurin da tayi, a tsanake kamar yanda yasha ganin Hafsat na yi ya d'aura mata, cas kuwa ya fito mata da idonta biyu tare da kallonta ya saki murmushi yace "Daga yau haka nale son ganinki, ya kamata kisan cewa ke yanzu matata ce, akwai buk'atar shigarki ta nuna kamala, nutsuwa, tarbiyya da kuma ilimi, kin fahimta?" K'ala ba tace ba hakan yasa shi zaro mata ido yace "Ryam..." "To." Ta fad'a tana kawar da kan ta, hannu yasa ya d'aga nikab d'in yasa yatsu biyu ya cabki leb'enta na k'asa kamar yanda ya mata shekaran jiya, wata k'walla ta matso cike da azaba tana rintse idonta sosai, ba alamar wasa a tare da shi yace "Muryarki, fuskarki, surarki, mutuncinki, duk mallakina ne a yanzu, kuma ina matuk'ar kishin wani ya hangi inuwar gonata, kada ki sake min d'anyan kan da kika min d'azu wajen kiran sunan Kabir, idan kika sake kuma wallahi kinji na rantse saina taune bakinki." Cikin wahala taa jinjina kai alamar to, sakin leb'en nata yayi tare da shigewa gaba yace "Saki nikab d'inki ki biyo bayana." Hannu d'aya ta d'ora a kai ta fashe da kukan da babu sauti tace "Wayyo Allah na ni Maryam, wannan ita ce jarabar da nake gudu ta auren tsoho, sam bai san miye soyayya ba bare ya nuna min, sai wasu dokoki da sharud'ai kawai yake gindaya min, yanzu ni gidan uban wa zan kai wannan hijab?" K'wank'wasa k'ofar da yayi yasa ta zabura ta juya, tsaye yake yana jiranta da sauri ta fita a d'akin ya rufe kafin suka fita, da kanshi ya bud'e mata mota ta shiga ya rufe kafin ya shiga shi ma suka sake d'aukar hanyar asibiti. Shirun daya ratsa motar yasa Mimi sauke numfashi a hankali, d'an kallonshi tayi da idonta dake waje cikin sanyin murya tace "Ni fa ba jahila bace, kuma Abbana ba a banza yake biya min kud'in laraba ba, ina da ilimin addini daidai gwargwado, karambani ne kawai da bud'ewar ido na 'ya'yan yau da aka haifemu ba'a haifi halinmu ba, iyayena a tsaye suke kan tarbiyata, ni ce kawai nake ja musu zagi da zund'e, amma na tabbata duk wanda ya zageni iyayensa ya zaga, dan ni ban yi wa iyayena rainin da har zanyi cacar bakin da zata kaini ga zaginsu ba." Duk da maganarshi ta so tsaya mishi sai yayi gaggawar kawar da ita a rai ya d'an tab'e baki yace "Kin tabbata ba asara ake yi ba?" Kallonshi tayi rai b'ace tana sako hawaye tace "E, na tabbata." Wani shak'iyin murmushi yayi yace "A Alk'ur'ani mai girma Allah yana fad'awa manzonsa cewa " Qumi-llaila illa k'alila, (suratul muzammil, aya ta 2) me ye fassarar hakan?" Kallonshi tayi tana malalacin murmushi tace "Ka tsaya a kowane dare sai kad'an kawai." D'orawa yayi da "A wata ayar yana cewa, Yah ayyuha-llazina amanu qu anfusakum wa'ahalikum nara'waquduha-nasu walhijara,alaiha mala'ikatun gilazun, shidadun-laya-asunallaha ma'amarahum wayaf-aluna ma'yu'umarun (suratul tahrim, aya ta 5)." Ba tare data daina kallonshi ba dan mamakinshi take a yanzu kam tace "Yah ku wad'anda sukayi imani, ku kare kawunanku da iyalenku daga shiga wuta-wacce mutane da duwatsu ce makamashinta'a cikinta kuma mala'iku ne masu tsananin k'arfi da basa sab'a umarnin Allah kuma suna yin abinda aka umarcesu." Ba tare daya kalli sashen da take ba yace "A wata ayar cewa ake, Wa'iza sa'alaka ibadi anni'fainni qarib-ujibu da'awati-da'i iza'da'an, falyastajibuli-walyu'uminubi-la'alahum yarshudun (suratul baqara aya ta 185)." A kaikaice ita ma ta amsa da "Idan bayina suka tambayeka a game dani ka fad'a musu ina kusa da su, ina amsa rok'on mai rok'o a a sanda ya rok'eni, ku rok'eni kuyi imani dani i..." Kallon daya mata da sauri yasa tayi shiru tana d'auke kallonta daga kanshi gaba d'aya, sake d'auke idonshi yayi yana jin zuciyarshi na wani daka da k'arfi k'arfi, cikin k'arfin hali da son rikitata ya fita a b'angaren Alqur'ani ya koma hadisi ta hanyar fad'in "Fawallahu lazi-la'ilaha gairuhu, ina ahadakum-laya'amaluahalin-janna hatta'mayakunu bainahu-wabainaha illa'zira'un, fayasbik'u'alaihul kitab faya'amalu ahalin'nar fayadakulaha..." Kallonshi Mimi tayi a ranta tana fad'in "Wato ita zai wa wannan jirgen?" Cije leb'en k'asa tayi kafin tace "Hadisi na 4 mai taken ahwalul insan, Abi Abdul-Rahaman Abdullahi bin Mas'ud ne Allah ya yarda dashi ne yake fad'a, fassarar kuma ita ce na rantse da Allahn da babu wani bayan shi, lallai d'ayanku yana aikata aiki irin na yan aljanna harsai ya kasance tsakaninshi da ita saura zira'i d'aya, sai a rufe littafinshi sai ya dinga aikata aiki irin na yan wuta, kuma sai ya shigeta...Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi." Kallonta yayi cike da gatse yace "Wane hadisi ne a gaban wannan?" Murmushi tayi tace "A wane littafin hadisin???" Yanda ta gama harbo jirginshi yasa shi saurin kallonta da ido cirrr kamar zai had'eta, d'auke idonta tayi daga kanshi tace "Idan a matin-l'1arba'una nawwiya fi ahadisin-lsahiha nabbawiy, hadisi na 6 shi ne hani akan bidi'a,, wanda uwar muminai uwar Abdullah A'ishata Allah ya k'ara yarda a gareta tace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa yace "Duk wanda ya zo mana da wani abu cikin lamarinmu ba'a cikinmu ba to mun mayar mishi" Bukhari da Muslim ne suka ruwaitoshi, a cikin wata rawaya ta muslim kuma yace "Wanda ya aikata wani aiki ba'a cikin lamarinmu ba to mun mayar mishi." Wani nauyayyen numfashi ya sauke a sirrince yana jin abun wani iri kamar mafarki, to dama tana da sani haka take sanin ne tayi take tsula tsiyarta? Kafin ya samu gamsashiyar amsa dreban ya kutsa hancin motar cikin asibiti, a inda motocin suke da farko yanzu ma aka paka, yana shirin bud'ewa tayi saurin cewa "Abinda nake yi ai baiyi kama dana jahilai ba, kuma bai aikata abunda ya sab'awa shari'a ba bare har kayi tunanin rashin ilimi ne ya jawo hakan." Saida ta bud'e motar zata fita ta sake kallonshi tace "Yana daga cikin kyautata musuluncin mutum ya bar shiga abinda bai shafeshi ba, hadisi ne ingantaccen, idan ka manta ka tuna hakan." Ficewa tayi ta shiga takawa da sauri tare da d'age nikab d'in ta kwanceta gaba d'aya har ta shige duk da bata san d'akin da zata shiga ba, tana shiga ta corridor suka had'e da Alhaji Saleh ya fito zai tafi, gaisheshi tayi har k'asa ya amsa da fara'a ya nuna mata d'akin, wucewa tayi da sallama aka amsa da bata izinin shiga, a hankali ta bud'a k'ofar tana mai sauke idonta akan Hajia, k'arasa shiga tayi daga Asma'u sai Hajia sai kuma wata matashiya da bata san ta ba tare da Aisha da kayan makaranta a jikinta. Da fara'a Hajia tace "Mimi sai yanzu? Nayi taa jiran shigowarki ai." Murmushi tayi tana sunne kan ta, Asma'u ma murmushi tayi tace "Da alama gida ta koma ta canza hijabi." D'aga kai Mimi tayi ta kalleta tare da satar kallon Asas dake kwance yana bacci, d'auke kallonta tayi daga kan shi ta kalli Aisha dake fad'in "Aunty Mimi ina kwana?" Da sakin fuska cike da jin kunya tace "Aisha sannu." "Yawwa." Ta fad'a da fara'a, d'ayar ce tace "Ina kwana aunty." A sanyaye tace "Muna lafiya?" "Lafiya lau." Ta fad'a da sakin fuska ita ma, Hajia ce tace "Mai aikin gidanku ce ai, Hafsat take kama ma aiki." Sunkuyar da kai tayi a ranta tana fad'in "Gidan mu dai, ni ba zan zauna da tsohon nan ba, d'an rainin wayo ne." Yanda tayi maganar a zuciyarta yasa har bakinta saida ya motsa, mik'ewa su Aisha sukayi tana fad'in "Hajia ni zan wuce makaranta dreba na jirana a waje." Tab'e baki Hajia tayi tace "To Umma ta gaida Aisha mana." Kallonta Aisha tayi tace "Kuma dan kin samu ma na miki magana?" "Kar ki min mana." Ta fad'a tana d'auke kai, murmushi tayi tace "Nasan me ye matsalarki, idan na dawo zamu zauna dake Hajia." Zasu fita shi kuma ya bud'o k'ofar da waya a hannunshi, juyawar da tayi yasa suka fara had'a idonsu, da sauri ta janye nata gabanta na fad'uwa da sauri sauri, takawa tayi ta koma bayan Hajia ta lab'e tare da yaye hijabin ta baya ta d'orashi akan kafad'unta, hakan yasa bayanta ya bayyana a waje. A sanyaye ta ji yace wa Aisha "Har yanzu baki tafi ba?" Da ladabi kanta a k'asa tace "Abie Amie ce ta aikoni tare da Assia muka kawowa su Hajia abinci." Lumshe ido yayi tare da kaucewa a k'ofar suka fita, k'arasa shigowa yayi yana kallon yanda ta yaye hijabin, wato har tayi halin? Girgiza kai yayi ya kalli Hajia dake fad'in "Hajiarmu, mun gama shirin tafiya komai da komai, insha'Allah yau da k'arfe 08:00 na dare jirginmu zai tashi." Kallonshi tayi da mamaki tace "Yau kuma? Da wuri haka?" Lumshe ido kawai yayi alamar eh, jinjina kai tayi daan ta fahimci ya gama kenan, a sanyaye tace "To da wa zaku tafi?" A dak'ile yace "Ni, da kuma shi." Nan ma jinjina kai tayi ba tace komai ba, juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya, kallon Mimi yayi da ita ma ta kalleshi ganin ya tsaya, nunota yayi da yatsa yace "... _Nasan kunsan da gani posting da wuri ya nuna komai ya tafi zan-zan, hak'ik'a comment k'arfin gwiwa ne da kuzari馃榿 dan gashi allurarku ta sokeni da kyau, a ci gaba da gashi._ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *35* Nunota yayi da yatsa yace " *Maamah* wallahi idan baki gyara hijabin nan ba saina ajeta hulata gefe na miki abinda baki tsammani." Wani bazawarin murmushi ta saki tare da yin durk'ushe bayan kujerar Hajia tana fad'in "Hajia ai kinsan tun ina yarinya bana son zafi, shiyasa Mamana ma a waje take min shinfid'a ina kwana, wannan hijabin zai iya kasheni saboda girmansa yayi yawa." Hajia daketa rik'e dariyarta rufe baki tayi da tafin hannu, Asma'u kam kallonta tayi tace "Yaushe haka ta fara faruwa?" K'wafa sheikh yayi ya juya zai fita Mimi dake hararan Asma'u ta sake fad'in "Sheikh baka bani wayata da ka ce ba." Da sauri ya juyo jin ta kimkima wata k'aryar, kallonta ya shiga yi irin mai nuna "Ke Mimi dan Allah zo ki kasheni ki huta." Jinjina kai yayi yasa hannu aljihu ya ciro wayar dan dama tana tare dashi, mik'a mata yayi yace "Gashi." Karb'a tayi tana washe baki har kunne, juyawa yayi ya fita da sauri ta zagaya kusan Asma'u ta zauna tana bud'e wayar, abubuwan data fi damuwa da su ta fara dubawa, saidai mummunan gani tayi dan komai ya shafe hotunanta da girki kawai ta gani, sannan an yi d茅sinstaller WhastApp d'inta alamar ba'a son ta dashi, gumtse baki tayi ta kalli Asma'u kamar zata kifa mata mari tsabar takaici. Zuwa k'arfe 10:20 aka sallamesu a asibitin, har gida suka rakasu saidai daga cikin mota Hajia ta musu sallama ban da Mimi dake kunyar had'a ido da Asas, dan shima kunyarta yake ji fiye da yanda ita take jin kunyar shi ma, suna shiga gidansu su kuma dreba ya wuce dasu gida. *07:00* Cike da son danne kewarta ko na ce buk'atuwar mace ya sake matseta a jikinshi yana sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske, tun ranar da ifiritiyar yarinyar can ta tashi boma-bomanshi sun kasa kwantawa, dan ya fahimci Hafsat bata jin dad'i sosai, dan haka bai ma nuna mata buk'atar hakan ba, lumshe ido yayi yana sake jin komai na dad'a mik'e mishi tsaye cikin muryar dake nunawa duk mai hankali halin da mamallakin muryar yake ciki ya shiga rad'a mata "Zzzanyi...kewarki manga na, ki kula min da kanki." Sake d'an rumgumeshi tayi ita ma tana yatsina fuska saboda rik'ewar da bayanta keyi tace "Insha'Allah, ka kula min da kanka kai ma, Allah ya tsare mana ku ya kareku." Kasa amsa mata yayi sai wuyanta daya shiga shinshinawa yana goga mata gemunshi a kafad'a, cije leb'e tayi tana rintse ido dan sosai take da buk'atar zama, hannu tasa ta dafe cikinta da sauri ya d'ago ya kalleta yace "Lafiya?" Murmushi ta sakar masa tace "Ba komai." Da alamar tuhuma yace "Kin tabbata?" Jinjina kai tayi, ajiyar zuciya ya sauke yana rik'e da hannayenta yace "Ki tayamu da addu'a muje a sa'a da fatan dacewa, idan kika ji jikin nan ya matsa miki dan Allah kiyi k'ok'ari ki kai min kanki asibiti, Hafsa ba'a son zaman nan naki a wannan halin." Jinjina kai tayi tace "Insha'Allahu zan je." Jinjina kai yayi shi ma yace "A d'aki na aje miki katin banki na gida, sannan akwai makulin mota guda biyu na bar miki wanda zaki iya buk'ata." Murmushi tayi tace "Allah ya saka da alkairi, zanyi kewarka." Sake rumgumeta yayi tare da manna mata sumba yace "Nima haka." Sakin juna sukayi a hankali yana rik'e da hannunta suka fito falon, yaran suka samu suna tilawar karatu, duk mik'ewa sukayi suna binshi da addu'a, shafa kawunansu yayi dukansu ya sumbaci goshinsu har Aisha kafin ya musu addu'a ya fita zuciyarshi cike da kewar iyalinshi musamman ma matarshi da yake matuk'ar tausaya mata. *Asa-Ma'u* Fashewa tayi da kuka duk da bai fad'a mata kalmar so ba, amma dai yanda ya nuna mata jin dad'inshi da godiya akan martaba da kimarta data kawo masa, had'e da jinjina mata akan irin bajintar da tayi a darensu, madadin ace yana kula da ita sai ya zama ita ce ta kula dashi har ta kasa bacci a wannan daren saboda halin da yake ciki. Ganin yayi rarrashin amma ta k'i yin shiru yasa shi aje jakarshi k'asa yace "Shikenan to tunda ba kya son tafiyar, bari na kira sheikh saina fad'a masa kawai na fasa tafiyar saboda ba kya so, kinga sai na zauna a gidan tare dake, amma fa kiyi hak'uri dan kullum zan dinga suma miki a guda." Da sauri ta rik'e wayar da yake k'ok'arin cirowa aljihu tana fad'in "A'a baan ce ba." Kallonta yayi ya sauke numfashi yace "To me kika ce yanzu?" Sunkuyar da kai tayi tana share hawaye tace "Ka tafi Allah ya bada sa'a, Allah ya baka lafiya kamar kowa." Tallabo hab'arta yayi tare da fad'in "Sannan na dawo miki gida mu d'ora shagalinmu daga inda muka tsaya." Duk'ar da kai tayi cike da kunya tana Murmushi da sauri ya tallabota ta fad'a jikinshi, rumgumeta yayi sosai yana furta "Na fad'a miki wata magana." A k'asan mak'oshi tace "Um." Sake matseta yayi yace "Zaki yarda dani idan na fad'a miki?" "Um." Ta sake fad'a a sanyaye, cike da k'warin gwiwa yace "Ina sonki a zuciyata *Husna*." Da sauri ta d'ago kanta daga k'irjinshi tana kallon fuskarshi, kamar wanda aka ce mishi zata hango burbushin sauran son Mimi da har yaanzu ke zuciyarshi sai kawai ya sunkuyar da idonshi k'asa, sautin murmushinta ne yasa shi kuma kallonta, cikin raha tace "Kamar ba gaske ba." Da alamar tuhuma yace "Kenan baki yarda ba?" Girgiza kai tayi tace "Na yarda mana, kawai dai ina ji ne kamar a mafarki." Murmushi yayi yace "To ba mafarki bane, zahiri ne wannan." Murmushi tayi mai k'ayatarwa tare da gyara zaman hijab d'inta, rik'e hannunta yayi yace "Muje dreba na jiranmu a waje." Jinjina kai tayi tare da bin shi a baya duk da yana rik'e da hannunta d'aya hannun kuma jakarshi yake ja, tare suka nufi airport dan suna so suga tafiyarsu kafin su juyo su dawo. *Mimi* Kwance take akan gado tana ta karatun muktasur-lakhdari da ta samu a wayar, ba kuma shi kad'ai bane ta samu ire-iren litattafan nan dayawa a wayar wanda ta tabbatar shi ya saka mata su. Da sauri Hajia ta shigo d'akin hakan yasa ta tashi zaune tana kallonta, hijab ne hannunta tana ta k'ok'arin sakawa tana fad'in "Mimi tashi mu tafi ki rakani, na tabbata yanzu suna filin jirgin nan." Da mamaki tare da wani fad'uwar gaba da taji a sirrince tace "Hajia tare zamu tafi?" Saida ta gyara hijab d'in a fuskarta tace "E mana, ina so ne na samu abokin tafiya, ko ba zaki je ba?" Sauke numfashi tayi a fili ta furta "Shikenan zan je." Saukowa tayi a kan gadon tare da nufa wurin kayanta, har ta d'auki hijab sai kuma ta yatsina baki ta mayar dashi tace "Dare ne fa, wa zai kula dani ma." Wani arnen mayafi ta d'auko shara-shara kalar fari kamar yanda fari yafi yawa a atamfar jikinta, riga da siket ne dai kamar mafi yawan lokuta d'inkin zamani, gidan nonuwan nan ya fito cas da shi haka siket d'in ya bi jikinta ya fito da mazaunai da wajen gwiwa ma ya ciresu daban, takalmi ta d'auka masu tudu hakan yasa ta shiga bada sautin d'as-d'as-d'as. Gaban madubi ta tsaya ta d'an gyara d'aurin kallabin irin kawai zahra Buhari tare da shafe jikinta da turarenta mukhallat, masha'Allah yanda wuyanta ya fito sai kuma ta d'ora mayafin a kafad'u ta rik'e wayarta ta fito. A mota ta samu Hajia tana amsa waya da alama kuma da Hafsat suke waya, dan haka Hajia bata kula da shigarta ba ta dai ji k'amshin turarenta kawai, saida ta kammala ne ta juyo ta kalleta tana fad'in "Daga nan zamu wuce gidanku na ga jikin Hafsat, da alama bata jin dad'i..." Dakatawa tayi sakamakon ganin Mimi kamar wacce zata je bikin walima, zaro ido tayi tace "Takwarata da mayafin naan kika fito?" Tsareta tayi da ido tace "E." Ajiyar zuciya ta sauke ta furta "Ya Hayyu ya Qayyum." Jinjina kai tayi ta kasa cewa komai ba, dan badan sauri da take ba da sai ta canza mayafin nan, kar sheikh ya d'auka ita ke d'aure mata gindi ma take wani abun. Basu jima ba suka isa dan sun fi dukansu kusa da filin jirgin, ko da motarsu ta paka wajen ta hangi na shi motocin da kuma ta Asas saidai babu kowa a wurin, fita sukayi saidai a yau Mimi jin ta take a sake kamar sanda tana budurwa, dan ta kwana biyu rabonta da mayafi ma, gaba Hajia ta wuce Mimi na bayanta suna tunkarar shiga cikin filin da mutane dayawa ke ciki sun rako ahalinsu a iya inda kujerun zama na farko suke, wasu kuma kai tsaye suke wucewa wajen kejuru na biyo wanda aka tanada domin masu tafiya. Hajia na shiga suka kallo wajen kamar wacce ta k'wala musu kira, saidai kuma a take kallo ya koma sama wau shaho ya d'au giwa, " *Mimi*?" Shi ne kawai abinda ya furta tare da damk'ar hannun Asas d'aya hannun kuma gam a k'irjinshi, lumshe ido yayi yana son ambatan sunan ubangiji amma yau sai ya samu kan shi da kasa furta komai. Kallonshi Asas yayi da son gano yanayinshi murya k'asan makoshi yace "Sheikh kana lafiya?" Ba tare daya bud'a idonshi ba murya na rawa a rashin sanin yanda yayi magana yace "Banda lafiya Asas, jikina ya min nauyi, zuciyata bugawa take da sauri, ban da lafiya gaskiya." Da sauri Asma'u ta kalleshi cike da tausayi dan tasan yanda ya ga Mimi ne, tsaf suka k'araso sai Asas daya shiga binta da kallo yana jin kamar ya tsawatar mata, sheikh dai har ya kasa kawaici ya iyaa furta haka? Lallai abinda yake ji a game da ita babba ne. Da sauri Asma'u ta fizgi hannunta suka koma gefe Hajia kuma na kallonshi da mamaki ganin idonshi a rufe. Cikin b'acin rai tace "Me ye haka Mimi? Ya zaki fito babu hijab kuma kinsan zaki had'u da sheikh?" Yatsina fuska tayi tace "To sai me? Tsirara na fito." A hassale tace "Ba tsirara kika fito ba a wajen mutane, amma a wajenshi tsirara ne, haba Mimi wai me yake damunki ne? Ya kike abu kamar mahaukaciya wani lokacin?" Da d'umbum mamaki Mimi ta kalleta tace "Mahaukaciya? Asma'u akan sheikh d'in ne kike kirana da mahaukaciya, saboda kina so ki nuna min kin fini zama d'aya daga cikinsu kenan?" Juyawa tayi zata bar wurin Asma'u ta rik'o hannunta cikin jin haushi tace "Ni ba mahaukaciya na kiraki ba, amma Mimi ke ma kinsan baki kyauta ba, a ganina ko dangata ta jini ce ta had'aki da shi ya zama dole gareki suturta jikinki, yanzu ya kike so mutane su kaalleshi idan aka san ke ce matarsa?" Fige hannunta tayi da k'arfi tace "To sai me? Ya sakeni mana idan ba zai iya ba, ni na ce dama ya aureni ne? Kinga ba zan iya rayuwar takuran nan ba, tunda yanzu ke ma ahalin Sharif ce ki fad'a ma masu fad'a masa yaji ya sawak'e min." Juyawa tayi a hassale ta nufi hanyar fita mayafin na sauka a kafad'unta, gyarashi tayi cikin hushi ta sab'a a kafad'a d'aya ta shiga takawa da sauri na b'acin rai wanda ya haddasa k'adawar mazaunanta da kyau tare da tsallen zuciyar sheikh kamar zai suma a wurin yana binta da ido. Numfashi ya shiga saukewa da sauri sauri da kuma k'arfi k'arfi, Hajia na d'an gefe tare da Asas dan tunda suka kula baya hayyacinshi suka matsa suna tattaunawa na tsakanin d'a da uwa, matsowa Asama'u tayi ta rumgume hannaye cike da jimami, idonshi kawai ya iya wulk'itawa ya kalli Asma'u cikin k'arfin hali kuma har yanzu hannunshi na kan k'irjinshi yace " *Wacece ita*? Wacece Mimi da take son na sakata a cikin jarabawar da Allah ya min, yanayin nan sabo ne a gareni da ba lallai na iya sabawa da shi ba, ina tsoron kar a fara fahimta har na fara zama mahaukaci a idon jama'a, me yasa k'awarki ba zata bini a baya ba yanda zamu jima muna tafiyarmu? Wanene dalili ne yasa dole take so sai na mutu a kan ta? Me yasa? Me yasa Asma'u." Gaba d'aya jikinta sanyi yayi kanta a k'asa tana sauke numfashi, tunaninta shine ta yanda zata fara bashi amsar tambayoyin nan bayan gaisuwa ma har yanzu a kunyace take mishi, amma tunda akan abinda ya shafi k'awarta ne sai ta aro jarumta tayi k'arfin halin gyara muryarta tace "... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:57 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *36* Aro jarumta tayi k'arfin halin gyara muryarta tace "Mimi da kake gani a zahiri haka bad'ininta yake, ba kowa bace ita amma tana da suffa mai ban tsoro, sani na halayya babu wanda ya santa sama dani, dan ko iyayenta suna zarginta, saidai Mimi tana da sauk'i sha'ani idan kuka fahimci junanku, tana da ladabi da biyayya idan har tana girmama abu, matsalarta d'aya taurin kai, wanda shi ma nake fatan ka zama wanda zai canza mata wannan d'abi'ar." Gyara tsayuwa tayi ba tare data kalleshi ba tace "Idan halinku ya zo d'aya da Mimi zaku jima kuna tafiyarku, ni k'awarta saidai akwai wasu halaye na ta da muke samun sab'ani akan su, saidai hushin Mimi kamar d'igon ruwa ne, taurin kan ta ma haka na tabbata zaka iya ji da haka." D'an takawa tayi ta matso kusanshi ta kalli fuskarshi da har yanzu yake kallon hanyar da Mimi ta bi tace "Tana da suffar kura ne a jikinta, ga *tsoro* ga ban *tsoro*, ga wanda bai santa ba har ya had'a da tagomashin *zarginta*, amma nasan gaba kad'an kai ne zaka bamu masaniya akan wacece Mimi." K'arasawa tayi kusa dasu Hajia, a lokacin lokaci ya cika har an fara kiran sunayen matafiya, kamar wanda aka tsikara da tsinin allura sai kawai ya d'an zabura yana fad'in "Hasbunallahu wani'imal wakil." Da wani irin sauri ya shiga takawa yana nufa hanyar fita, kallonshi suka shiga yi inda Asas yace "Ina kuma zai tafi?" Cike da dagiya Hajua ta d'auke kanta tace "Barshi zai dawo." Yana fita bakin k'ofar ya hangeta tsaye jikin motar ta rumgume hannaye sai cika take tana batsewa, tana ganin ya nufi inda take ta had'e fuska ta gyara tsayuwarta, ai akan shi ne Asma'u ta kirata mahaukaciya ko? To ta daina yi masa wasa daga yanzu (Kaji k'arfin hali ga uwata). Yana zuwa bud'e motar yayi tare da kama hannunta ya wurgata ciki da k'arfi, shiga yayi yana rufe motar Kabiru ya fita a mazauninshi na dreba ya koma gefe. Sam sai ta k'i ta nuna tsoron yanayinshi, had'e fuska tayi sosai ta k'ura masa ido tana kallo, yanda take kallonshi sai ta dubutburtashi ya rasa me zai mata. Hannayenshi ya d'aga da niyyar sake cakumota ya mata irin jijjigar ranar, sai kawai ya sauke a hankali ya kamo hannayenta ya rik'e a cikin na shi, sunkuyar da kan shi yayi k'asa baki na rawa rawa yace "Ryam *ya kike so dani ne? Dan Allah ki taimaka ki killace min kan ki, kinga wallahi zan iya fasa tafiyar nan idan kika ci gaba da yi min irin haka, Ryam kuka na ke so nayi saidai bansan ko zaki iya rarrashi na ba, Ryam hankalina tashi yake idan kina fad'in ba kya son tsoho, hankali na bari jikina yake idan kina fad'in na sakeki, gaba d'aya rasa nutsuwata nake idan kina min irin rigingimun nan, shin so kike na ajiye babbar rigata ne na dinga saka k'ananan kaya? Ryam so kike na ajiye sanina a gefe na dinga yawo dake a gari muna tafe muna shan ice cream?* Ryam ina ake rage shekaru? Zan je a rage min indai zaki zauna dani, Ryam ina jin ki a zuciyata sosai kuma ina kishinki, sannan ina jin haushin wanda suka fara kalle min surarki, da zan iya hukuntasu to hukuncinsu shi ne k'wak'ule idonshi ne kawai abinda zan iya yi mai sauk'i, dan Allah Ryam ki taiamaka ki daina saka zuciyata na bugawa sosai a kan ki, kinga fa zan iya haukacewa dan rigimarki yawa gareta." Sakin hannayenta yayi ya tallabo fuskarta, yanda gaba d'aya tayi wani sororo tana kallonshi zai nuna maka kalamanshi sun sakata a wani yanayi na mamaki da d'imuwa, bakinta ya kalla da babu komai a kan shi sai kalarshi ta asali wato pink da bak'i, a hankali ya shiga matsawa da fuskarshi kusa da ta ta har saida ya d'ora labb'anshi a na ta labb'an. Wani irin salo ya shiga mata mai tsayawa a zuciya, yanda yake zura harshenshi a bakinta yana zagayawa da shi ko ina, yanda yake d'an tattauna leb'enta a hankali, ga hannunshi d'aya daya jima da shiga rigarta, cabkar nononta yayi hakan yasa ta waro ido sai kuma ta lumshe saboda idonshi a kan na ta suke, a hankali a nutse ya shiga mulmula kan k'irjinta yana lailayawa yana shafasu, Mimi da gaba d'aya jikinta ya mutu yayi wani irin sanyi lak'was, ji take kamar ana mata tafiyar tsutsa, yam-yam d'in da take ji da kuma k'yak'yayi a gabanta sai kawai ta shiga sako hawaye masu zafi, hannu tasa cike da k'arfin hali ta fara tureshi, da k'yar ya cire bakinshi a nata tare da sake damk'ar fuskarta ya d'aga yana kallo, hawayen dake zubo mata ne ya shiga saka harshenshi yana lashewa, saidai abun ya fi k'arfin d'aukar hankalin Mimi, sai labb'anta suka shiga rawa tana son yin magana hawaye kuma suka ci gaba da sintiri, cike da k'warewa ya tsayar da bakinshi kusa da kurmin idonta yana tsotse hawayen da zaran sun zubo. Kasancewarsu a kusa yasa ana kiran sunanshi tayi gaggawar bud'a idonta wasu hawaye na fitowa, tar ta sauke cikin na shi idon tana son tace masa "Ana kiran sunanka." Saidai ba wannan kuzarin. Murmushi ya sakar mata cikin muryar da shi ma yasan ya sake tak'alowa kanshi fitina yace "Ryam...indai..baki daina zubo...da haway..nan ba..., to babu inda zan tafi." Rufe idonta tayi tana jin yanda yake ci gaba da murza nononta, sunanshi da aka sake kira yasa ta k'arfin halin ture hannunshi taja baya ta dangane a jikin motar, sake matsawa yayi daf da ita ya mata rumfa ya had'a goshinshi da nata, sumbatar bakinta ya sake yi yana murmushin mugunta, harshenshi yasa a kunne yana zagayawa dashi, tuni ta fara k'amewa tare da sarewa da lamarin old man d'in, dan wani irin abu take jin yana taso mata da shi da bata tab'a ji a rayuwarta ba, wani marayan kuka ta saki daya fallasa sirrin muryarta na halin data shiga ita kan ta na son a sosa mata wajen dake k'yaik'yayi, d'agowa yayi ya kalleta ba tare daya daina murmushin nan ba, k'wank'wasa glas d'in motar akayi, juyowa yayi ba tare daya d'aga daga rumfar daya mata ba, d'aya daga cikin jami'anshi ne sai kuma Hajia a can gefe, wani numfashi ya sauke wanda iskar bakin ya sauka a fuskar Mimi, sake rintse ido tayi inda shi kuma ya zauna daga rank'wafawar. Hannunshi yasa aljihu ya ciro katinshi na banki na aikinshi na gwamnati, kamo hannunta yayi ya damk'a mata yana kallon fuskarta yace "Dan Allah Ryma ki kula da kanki, daga million d'aya har abinda yayi sama ki d'iba a asusun nan, amma ki sani *ba zan tab'a yafe miki ba idan kika nemi kud'i a hannun wani gara*." Sakin hannunta yayi tare da tallabo kumatunta ya manna mata sumba a goshi, fuskarta ya sake kallo yace "Ki shiryawa tarewarki kafin na dawo." Bud'e motar yayi ya fice tare da rufowa, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sake jingina a kujerar, numfashi ta shiga saukewa d'ai d'ai hawaye sun kasa tsayawa a idonta, d'ora hannunta na dama tayi a k'irjinta ta dafe tare da katin daya bata, cak tunaninta ya tsaya ta rasa me zatayi inba hawaye ba da kallon titi. Yana fita shima had'e fuska yayi sosai bai ko kalli jami'in ba ya nufi inda Hajia take tsaye, dake manyan kaya ne a jikinshi sai bai ji wani d'ar ba dan ya tabbatar asirinshi a rufe yake, sallama sukayi da Hajia a kunya ce kafin ya wuce ciki da hanzari ya samu Asas har yayi gaba ya barshi. A tare Hajia da Kabiru suka shiga motar, tana jinsu amma sai ta kasa motsawa bare ta kalli b'angaren da suke, har suka fara tafiya Asma'u ma dreba ya d'auki hanyar mayar da ita gida, saidai Hajia ta ce ta dawo ta zauna tare da ita tunda bak'uwa a gidan har yanzu. Tunda Hajia ta fahimci yanayin Mimi tasan an d'an matseta ne sai batayi magana ba kawai har suka isa gidan sheikh, kallonta Hajia tayi tace "Mimi zan shiga na duba saina fito mu wuce." D'an k'yabta ido kawai tayi alamar to dan jikinta a mace yake sosai, shiga tayi ta sameta a falo ita kad'ai zaune yaran suna d'akin karatun mahaifinsu, yanda ta ganta ne yasa tana zama tace "Hafsat haka kike zaune gida ba zaki tafi asibiti ba?" Murmushi tayi kawai tace "Hajia wallahi ni duk tsoron zuwa asibitin nake, bana so na je su fad'a min abinda zai d'aga min hankali ne." Cikin fad'a Hajia tace "Saboda haka kuma sai kiyi ta zama a gida har ciwo ya cimmiki? Ni sai naga kamar ma nak'uda kike." Zaro ido tayi tana dariya tace "Hajia nak'uda kuma? Wata shida ne fa da sati biyu." Tab'e baki tayi tace "To miye a ciki? Ba'a haihuwa a wata bakwai ne?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "Ana yi Hajia, amma bana fatan nayi." "To yanda Allah ya tsara ai shine daidai." Cewar Hajia tana gyara zaman jakarta, jinjina kai tayi tace "Hakane." Kallonta tayi tace "Kinga tafiya zanyi, daga filin jirgin muke dama na ce bari na biyo naga jikin na ki." "Har sun tafi Hajia?" Ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa da k'yar sanda Hajia ta mik'e, tana gyara hijabinta tace "Sun tafi, sai fatan sauka lafiya da kuma dacewa." A sanyaye tace "Allah yasa a dace." "Ameen." Hajia taa fad'a, saida suka kai daf da k'ofa Hajia tace "Tare da Mimi fa na ke." Wani fad'uwar gaba ta ji ya ziyarceta har saida ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." A tsanake Hajia ta kalleta tace "Lafiya?" Girgiza kai tayi tace "Ba komai, bayana ne." Wani murmushi tayi tace "Kiyi hak'uri kinji Hafsat, insha'Allahu Allah yana tare dake, nasan kina mamakin wace irin uwace ni? Ni kaina Hafsat sai bayan na yanke hukunci na fahimci me na aikata, hakan ya tabbatar min da k'arfin dake a cikin *tafiyar k'addara*, na tabbata auren Mimi da sheikh shine rubuce a *laulil mahfuz*, Asas kawai sanadi ne na tabbatar da auren, ba kuma za'a rasa samun rabo ba." Jiki a sanyaye ta danne kukan dake son taho mata tace "Hajia baki mana komai ba, nima na gane aurenta da shi ne abu mai yiwuwa shiyasa ya yiwu." Jinjina kai tayi tace "Ni zan wuce, saida safe." "A gaida gida Hajia." Ta fad'a tana kallonta, tana hangenta har ta shiga mota suka fita a gidan sai kawai ta sako wasu hawaye zuciyarta tana fad'in "Allah ka bani juriyar cinye wannan jarabawa, hak'ik'a ba dan mahaifiyata bace da sai na nunata a matsayin wacce ta fi kowa tsanata a duniya, had'a min sheikh da wata mace ba k'aramin rud'u bane a tare da ni." Juyawa tayi tana share hawayen fuskarta ta koma ta zauna tana shafar cikinta tana tasbihi da hailala dan samun sassauci a zuciya. Suna k'arasawa gida da k'yar ta kai kanta d'aki ta kwanta ruf da ciki tana rufe fuskarta da mayafinta, zumbur ta mik'e tana yakice mayafin a fuskarta, shinshinawa ta sake ta tabbatar dai k'amshin turaren shi ne, shinshina jikinta ta shiga yi sai ta ji kamar ita ta shafa shi, fad'awa ta sake yi rairan tana kallon sama a hankali ta furta "Ya Allah." Wasu hawaye ne suka taho mata masu zafi ta had'e wayu masu nauyi, yanayin da take ji wallahi kaamar ta k'wala masa kira ya dawo. (馃槼 Ya dawo yayi me uwata?) *Sheikh* Sararin samaniya suke jirgi na tafiya ba da gudu sosai ba, jingine yake a kujerar idonshi ruf kan shi na ta dawo mishi da abinda ya faru, wata masifaffiyar sha'awar yarinyar ke ciciyarshi, yanda yake lailaya kan mamanta saida ya ji sha'awar kai shi a bakinshi, lokaci ne kawai bai bashi damar haka ba, sosai yake ciki da bege da shauk'in kasancewa da ita. Asas na gefe shi dai kallonshi yake yana murmushi, yasan abubuwa dayawa a ge da Mimi haka kuma baisan abubuwa dayawa a game da ita ba, babban abinda ya tabbatar yana birgeshi da ita kuma shi ma sheikh tunda namiji ne zai birgeshi shi ne k'amshi, akwai yawan anfani da tunani ga kuma iya d'aukar ado, riga t-shirt da zani zata d'aura sai kaga yarinyar ta bada kala sosai. Sheikh kuma har maganganun Asma'u saida ya d'orasu a mizani, dan a wajenshi ta sake tabbatar mishi da Mimi fa tana bin maza a rayuwarta ta baya, lokacin data fad'i "Mimi da kake gani a zahiri haka bad'ininta yake..." Haka kuma maganarta ta cewa "Ni k'awarta ce saidai akwai wasu halaye da na ta da muke samun sab'ani..." Tabbas ya yarda Mimi ce jarabawarshi a rayuwa, kuma a yau ya yarda d'ari bisa d'ari zai karb'i jarabawar da Allah ya mishi ya rumgume da hannaye bibbiyu, ba k'aramin abu bane musamman daya kasance babban mutum, yasan daga lokacin da za'a fahimta al'umma zasuyi mishi tofin Allah tsine, sannan za'a iya kafa mishi hujja da maganganunshi na wa'azi da yake fad'in "Mace 'yar duniya ko a kyauta aka b芒 wa namiji ita an cuceshi, an cuci zuri'arshi." Kusan kowa a wurin ya rintsa idonshi da sunan bacci amma ban da sheikh dake tunanin Ryam da abubuwan da suka faru daga d'aura aurensu zuwa yau. Bayan awannin da suka kwashe sai gasu tsaye akan k'afafunsu Allah ya saukesu lafiya, su ma kamar sauran matafiyan abokin sheikh da kan shi ne ya zo ya d'aukesu zuwa gidanshi, duk da a wajensu ba dare bane a lokacin amma saida suka ci abinci sukayi wanka suka kwanta dan huta gajiya. *Niger* Sam a daren kasa bacci tayi, gaba d'aya tunanin sheikh da abubuwan daya mata ne ya tsaya mata a rai, ga masifaffen k'amshin turarenshi daya tsaya mata a jiki, har saida tayi wanka ta goge jikinta da kyau amma a banza, ga wani sabon yanayi daya bayyana a tare da ita, wani irin shauk'i ke d'ibarta kamar tayi kuka. Dap da asuba ta mik'e tayi alwala ta d'auro alwala ta shiga nafilfili duk ita d'in ba mai k'ok'arin yin nafilar bace, saida akayi sallah asuba ta gama duk azkar kafin ta kwanta rama baccin da bata yi ba. *06:10* Kiran wayarta ya tasheta, da k'yar ta bud'a idonta da sukayi mata nauyi sosai dan baccinta baiyi nisa sosai ba, ba tare data duba lamba ba kawai ta d'ora a kunne a magagin bacci da tunanin cikin k'awayenta ne tace "Hello, dallah miye haka zaki katse min bacci na? Wannan ai shiga hakk'i ne." Sautin k'ayataccen murmushi ta ji a cikin wata tausashiyar muryar data sakata bud'a ido sosai yace "Ki gafarce ni yan matana, na d'auka a daidai lokacin nan kina azkar ne, amma baccin na ki ma samun nutsuwata, a huta lafiya zan sake kira anjima." Cikin muryar rad'a yace " *Ina k'aunarki*." K'it! Ya datse kiran ita kuma sororo ta bi wayar da kallo, wata ajiyar zuciya ta sauke tana tashi zaune ta gyara zama, murmushi tayi tana girgiza kai tace "Wai yana k'aunata, ko kunya baya ji ya haifeni yake fad'an wannan maganganun." Tab'e baki tayi ta yatsina fuska tace "Tsoho kawai." Kaikatawa tayi da niyyar komawa ta kwanta sai kuma aka k'wank'wasa k'ofar d'akin, mik'ewa tayi tana d'aukar kallabi ta d'ora a kan ta, tana bud'ewa taga Hajia da shiri da alama fita zatayi, da girmamawa tace "Inaa kwana Haji." Da kulawa ta amsa da "Lafiya lau Mimi, antashi lafiya?" Ita ma da kulawa tace "Lafiya lau, Hajia fita zakiyi ne yanzu?" Cike da jimami tace "Fita zanyi Mimi, Hafsat ce jikin nan sai a hankali, zan je dai yanzu dole zan tisata gaba muje asibiti, dama dan na fad'a miki idan kin tashi ki d'ora abinda zaki ci ne dan tare da Salamatu zamu tafi." Da yanayin alhini tace "Ayya Allah bata lafiya, insha'Allah zan d'ora." Da fara'a tace "Yawwa to, kuma zan kiraki idan ma zamu iya jimawa a can dan kiji halin da ake ciki." Jinjina kai tayi tace "Zan ji dad'i idan ya zama babu wata matsala." "Allah ya tabbatar." Ta fad'a tana d'orawa da fad'in "Anjima kkawarki zata zo Asma'u, dan naga ba zata ji dad'in zama a can ba shiyasa na ce ta dawo nan." Da fara'a tace "To shikenan, Allah kawota." "Ameen." Ta fad'a tana wucewa, bin bayanta tayi saida ta rakata har farfajiya, ido biyu kawai sukayi da Salamatu a k'asan mak'oshi tace "Na kwana." A zuciyarta ta k'arasa da cewa "Lafiya." 馃ぃ _Ku fahimta fa, ba gaisheta tayi ba fad'a mata tayi ta kwana lafiya._ Salamatu dai da kallo ta bita dan ita yarinyar tafi mata kama da masu shafar aljanu, saida ta ga fitarsu a gidan kafin ta koma ciki a falo ta zauna ta kunna tv. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:57 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *37* Daga kallon nan bacci ne ya d'auketa dan saida ta bincike receiver nan amma tashoshin nan dai ne tsiraru, 09:45 daddab'ata Asma'u tayi da shigowarta kenan, bud'a ido tayi a nauyaye tana kallonta, da k'yar ta yunk'ura ta tashi zaune tana sake kallonta, tunawa fa jiya ta cizgata dayawa sai kawai ta d'auke kan ta, zaune Asma'u tayi a inda ta d'auke k'afafunta tana fad'in "Bacci kike sha a bin ki?" Kallonta tayi kallon dake nuna ina jin haushinki, murmushi Asmaa'u tayi tace "Haba Mimin Asma'u, kiyi hak'uri mana komai ya wuce ai." Turo baki tayi gaba tace "Kin tabbata ba zaki sake ba?" Dariya tayi tace "Wannan shagwab'a haka kamar ana gaban sheikh, to na tabbata ba zan kuma ba." Harara ta galla mata tace "A gaban carbi nake iyakar sheikh." Mik'ewa tayi zata shiga d'akinta dan yin wanka Asma'u tace "Dan Allah me kika dafa da zan iya ci ne? Yunwa fa nake ji." Juyowa tayi tace "Baki ci komai a gidanki ba?" Girgiza kai tayi tace "Ban ci ba." Tab'e baki tayi tace "Ni ma kuma ban dafa ba, in zaki shiga madafar da kanki to." Girgiza kai Asma'u tayi tace "Naki salon karb'an bak'in kenan?" Juyowa tayi tace "Ke ce bak'uwar? Ai nan gidan sirikarki ne, ko kin manta ne?" Murmushi kawai tayi tace "Hummm!" Dan bata so su tado maganar data shafi ranar d'aurin aurensu ko kuma baya, d'aki ta shiga tayi wanka har Asma'u ta kai kayan data zo dasu d'akin da Mimi take, fitowa tayi ta shirya cikin doguwar rigar kanti mai kyau da d'an kwalin daya dace da ita. Tana fitowa ta samu Asma'u zaune tace "Me kika dafa mana?" Zaro ido tayi tace "Me na dafa? Me kuwa zan dafa daga zuwana?" Tsaki tayi tace "Karki dafa d'in, shiga zanyi yanzu na had'a sauce na k'wai da doya, ko kallona kikayi ina ci Allah ya isa zan miki." Mik'ewa tayi ta bi bayanta tana fad'in "Tare zamu je ai ki dafa a gabana na gani, kinsan babu abinda nake da buk'atar k'warewa a kan shi yanzu kamar girki." Ba tace komai ba har suka shige madafar dan in zata iya tunawa tasan waye Asas a wannan fannin, yanda yake so matarshi ta zama yar kwalliya haka yake so ta zama gwanar girki, shiyasa ta dage a lokacin ta dinga koyon sababin kala na yan zamani, saidai kash ta auri old man da ta tabbatar tuwo ne cimar sa.馃槑 Mimi na fasa k'wai Asma'u na yanka albasa suka shiga hirarsu ta rayuwa, saidai dukansu babu wacce ta tab'o hirar bikinsu ko kuma mazansu kamar dai kowa da abinda yake b'oyewa a zuciyarshi, Mimi na cikin soya sauce d'in ta wayarta ta shiga kururuwa, jim tayi dan a take tayi tunanin shi ne, juyawa tayi ta koma falo inda ta bar wayar, tana dubawa sai ta ga lambar Hajia ce data saka mata lambar sanda suka dawo daga asibiti, d'auka tayi da ladabi tace "Assalama alaikum." Daga wajen Hajia ta amsa da "Wa'alaiki salam, Mimi." "Na'am." Ta fad'a a sanyaye, d'orawa tayi da "Dama dan na fad'a miki ne gamu a asibiti har yanzu..." Da sauri tace "Hajia lafiya? Jikin nata ne?" Amsa mata tayi da "Lafiya lau Mimi, Hafsat dai gata ma har ta haihu." Da d'an k'arfi tace "Haihuwa kuma? Cikinta ya isa haihuwa dama?" Da murmushi kamar tana gabanta tace "Bai isa haihuwa ba tunda ko wata bakwai bai shiga ba." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Allah sarki, me aka samu?" A raunane tace "D'iya ce gata can a kwalba an sakata dan bata kai haihuwa ba." Cike da tausayawa tace "Ayya! Allah ya rayata akan sunna, Hajia to kuna buk'atar abinci ne?" Cike da jin dad'in karamcinta tace "Kinga kam kamar kinsan ina tunaanin yanda zamuyi." Da 'yar fara'a tace "Shikenan Hajia dama nima yanzu kad'ai na shiga madafar, bari na k'arasa sai mu je mu kai muku." Da fara'a tace "Asma'u ta zo kenan?" "E Hajia ta zo." Taa fad'a kai tsaye, Hajia ce tace "To shikenan dreba yana nan idan kun kammala sai ku ce ya kawo nan asibitin sheikh." Jim ta d'anyi da tunanin dama yana da asibiti ne? Sai kuma ta tab'e baki tace "To Hajia." Da haka suka yanke kiran ta shiga da sauri madafar suka k'arasa aikinsu tare Asma'u, hibajinta zumbulele na wajen sheikh ta saka saidai duk da Asma'u tace "Ki d'aura nik'ab mana." Sai kuwa ta d'aga kafad'a tace "Na k'i d'in, idan ya dawo ki fad'a masa." Dariya tayi tace "Wahalar fad'a masa ma zanyi? Ai zai ji a jikinsa kuma zai matsi mutum wallahi a hannu." Sak'e tayi tana kallonta da alamar rashin yarda da kai tace "Me kike nufi? Ko dai shi ne ya fad'a miki?" Dariya Asma'u tayi tace "Kin tsargu kenan? Ke ma ai kinsan ko gaisuwa da k'yar mukeyi bare magana irin wannan." Tab'e baki tayi suka fita a gidan indz Kabiru ya d'aukesu zuwa asibitin. *Tunisie* Zaune yake k'afa d'aya kan d'aya yana danna wayarshi jefi jefi kuma ya d'an kalli Asas dake kwance gadon duba marasa lafiya da likitan ke dubashi duk da a rufe wurin yake da labule, yana kuma jin tambayoyin da yake masa har da tambayar yana da aure? Yaushe yayi auren? Mayar da duban yayi kan waya yana son kiran Hafsat saidai kuma baya son shiga hakk'in likitan, aje wayar yayi tare da zubawa wani hoto dake bayan kujerar likita mai d'auke da sassan kayan cikin mutum, motsin daya ji yasa shi saurin kallon wurin, likitan ne ya zauna akan kujerarshi yana kallon Asas dake saka rigarshi, saida ya zo ya zauna kafin ya kalli sheikh. Likitan ba wani babba bane dan sheikh ma zai iya yin k'ane dashi, cikin wani kwarjini da sheikh d'in ke masa ya sassauta muryarshi a harshen turanci yace " Matsalar ta shi na ga ba kamar yanda nayi tunani ba, da nasan haka ciwon na shi yake da ban bari kuyi wahalar zuwa ba, a magani kawai zan d'orashi daga can ma." Gyara zama sheikh yayi cikin k'wamewa sosai yace "Ba wata matsala bace? Suma fa yake idan ciwon ya tashi, ya jima yana wahala." Murmushi yayi yace "A gaskiya abinda bincike na ya nuna min kenan, gashi har jininshi da aka d'iba da kuma scanin da aka masa duk ban ga wata matsala ba." A hankali sheikh ya kalli Asas shi ma kuma ya kalleshi, numfashi suka sauke a tare kafin likitan yace "Zan d'orashi a magani na kwana bakwai, na tabbata zai warke daga ciwon nan har abada, idan kuma bai samu lafiya ba to gaskiya saidai ku hak'ura da larurar nan." Kallonshi sheikh yayi yana jinjina al'amarin bayahude, wato ba zai ce a kaishi wurin wani ba yana ganin shi ne k'arshen k'warewa? Wata ma'aikaciyar lafiya ya kira wacce ita ta musu jagora zuwa d'akin da za'a kwantar da shi, kaya ta bashi ya canza na jinya kalar shud'i kafin ta fita, jim kad'an ta dawo tare da likitan da d'an haranti a hannunta d'auke da magani, suna kallo Asas dake zaune likitan ya b'alli magani yasa a k'aramin kofi mai kama da tangaran, maganin dake gari ne dandanan ya jik'a, sirynge yasa na allura ya daidaita daga bakin 5 cl ya zuk'a, mik'awa ma'aikaciyar yayi ta d'ora a faranti sannan ya mik'awa Asas na cikin kofin ya shanye, fita sukayi yana sake jadaddawa ma'aikaciyar da k'arfe 05:00 na yamma ta bashi sauran maganin, kuma ta kula haka zata dinga mishi zai dinga dubashi lokaci lokaci. Suna fita kira ya shigo wayar sheikh, yana dubawa yaga Hajia sai bai d'auka ba dan yasan za'a ja kud'i sosai, saida ta tsinke sannan ya maida kira, a gaggauce ta d'auka a lokacin dan zasu tafi da Hafsat asibiti ne, yanda ya ji muryarta yasa shi saisaita nutsuwarshi yace "Hajiarmu, nutsu ku fad'a min abinda ke faruwa?" Daidaita nutsuwarta ta tayi tace "Sheikh Hafsat ce ba lafiya, ina so na kaita asibiti ne." Lumshe ido yayi yana jin zuciyarshi ta canza bugawa, wani sanyi yaji jikinshi yayi lak'was kafin a raunane yace "Hajiarmu na damu akan cikin nan nata, ina yawan fad'a mata ta je asibiti sai ta ce to kawai, dan Allah Hajia a kaita asibiti a dubata." "To, to yanzu dama can zamu." Ta fad'a alamar a gigice take, yana aje wayar Asas dake kallonshi yace "Lafiya? Me yake faruwa da Hafsy?" Kamar zai fashe da kuka yace "Bata da lafiya, zasu kaita asibiti ne." Cike da tausayawa yace "Ayya! Allah bata lafiya." "Ameen." Ya fad'a a hankali, mik'ewa yayi daga kujerar da yake zaune yace "Ni zan fita, kaga sun ce ba sai na zauna tare da kai ba, zasu kula da komai." Yar dariya Asas yayi yace "Salo ne ai na cin kud'in mutane." Hararenshi yayi yace "Kuma kaga salon ya min, tunda zai bani damar fita na je yawona." Waro ido yayi yace "Au! Dama wahala kake tunanin zakayi? Lallai ma zan fad'a ma Hajia." Tab'e baki yayi ya nufi hanyar fita, cike da zolaya Asas yace "Ashe dama da shirin shak'atawa ka zo shiyasa na ganka yau cikin k'ananan kaya." Girgiza kai yayi yana murmushi bai ce komai ba ya fice, yana rufo k'ofar wata tsohuwa na rik'e rigarshi ta fashe da kuka cikin harshen french take fad'in "Dr. Yarinyata zata mutu, muje ka duba ta." Galala yayi yana kallonta sannan ya kalli jikinshi daga k'asa har sama, bleue rigar daya saka shemise ya tank'wasa hannayen zuwa gwiwar hannu da bak'in wandon daya saka na lallausan yadi sai kuma bak'ak'en takalmi k'afa ciki su ne suka sakata kiranshi likita? Tab'e baki yayi tare da bin bayanta dan tuni taja rigarshi alamar dai a rud'e take, suna shiga d'akin na kusa da su takawa yayi har daf da gadon da matashiyar ke kwance kamar gawa, wani madanni ya danna hakan yasa ya d'anyi k'ara kad'an girrr! Ko minti d'aya ba'ayi ba sai ga ma'aikaciyar jinya ta shigo d'akin da farantin magani, yana ganin ta fara duba yarinyar kawai ya fice a d'akin yana fatan samun waraka ga kowa. Bayan minti talatin yana zaune a wani k'aramin shagon shan coffee ya sake kiran Hajia, labarin haihuwar Hafsat kawai ta fad'a masa, da mamaki yace "Hajia ta haihu fa? Amma ai cikinta ko wata bakwai baiyi ba." Da fara'a tace "Ai kam dai ta haihu, saidai abinda aka haifa yana cikin kwalba." Lumshe ido yayi a sanyaye yace "Ya Manga take?" Murmushi tayi tace "Lafiya k'alau take babu wata matsala, bacci dai take." A tausashe ya furta "Alhamdulillah ala kulli hal." *Niger* Suna zuwa asibiti sun samu d'akin da take kusan a cike da mutane, haka kawai Mimi ta samu kanta da jin kunya da kuma jin dad'i data zo da wannan hijabin, ajiye kwanukan sukayi suka samu wuri suka zauna a kan tabarma inda su Aisha suke, tunda suka shigo ta kasa kallon Hafsat ta furta ko da kalmar a, kanta na sadde k'asa taji Hafsat tace "Mimi sannu da k'ok'ari, hada wahala haka?" Da sauri ta kalleta, tun ranar kamu rabonta da ita, ta d'auka idan suka had'u zata shak'i wuyanta ne ta mata d'an banzan duka ai, sake sunkuyar da kanta tayi tana mirmushi mai d'auke da kunya tace "Ba komai aunty Hafsat, ya jikin?" Da murmushi sosai a fuska tace "Jiki da sauk'i sosai." Daga haka basu sakewa juna magana ba, haka dangi suke ta kai da kawowa ana ta hira, Asma'u da Mimi kuma dake bak'i ne a cikinsu su dai suna saurarensu kawai, wani abun suyi dariya wani su murmusa, Mimi kuma kunya da takaici ke rufeta idan aka nunawa wasu ita aka ce ga matar sheikh, musamman da wata abokiyar wasa ta kalleta tace "Kai kai kai! Wannan ce sheikh ya kwasa, gaskiya yan mata karki yarda, ya za'a had'aki da tsohon gwangwani wanda ya kusa ritaya a duniya ma ba'a aiki ba, ke kika yarda? Lallai da ni ce ke saina nunashi da bakin wuk'a nace ya sakeni." Dariya wasu sukayi sai Hafsat da tace "Ke dai kina jin haushin rasa mijinmu da kikayi." Kallon Mimi tayi tace "Kinga Mimi kafin tayi aure ba irin asirin da batayi ba dan mijinmu ya aureta, da k'yar ta shafa masa lafiya har kotu aka shiga tsakaninsu." Dariya aka yi sai Hajia da tace "Yanzu *Karima* d'an nawa ne ma gwangwani? Kinsan fa da a gabansa kike ba zaki iya furta a ba." Cikin d'aga murya Karima tace "Hajia ai gaskiya na fad'a, shi ma tunda ya zama malamin duba ne ya asircemu indai muna gabansa bama iya d'aga kawunanmu mu kalleshi saboda cuta." Kallon Mimi tayi tace "Ke k'anwata bari in fad'a miki, yana dawo ki ce ya maida ke gidanku kinji, daga shi har Asas d'in banga wanda ya dace dake b芒 tubarkallah dake, idan kuma kikayi wasa yana dawowa nan da wata tara bikin sunan d'anki ko d'iyarki zamu zo, kinga kenan dai kin tabbata a *matar tsoho*." Sunkuyar da kai ta sake yi inda Hafsat tayi murmushin yak'e sakamakon tunawa yanzu fa duk yanda suke da sheikh ko dan sauke hakk'in yarinyar nan sai yaje mata, sanyayyan numfashi kawai ta sauke aka ci gaba da hira ta raha da nishad'i har su Aisha suka zo ganin k'anwarsu bayan dawowarsu daga makaranta. Bayan sallah la'asar Rakiya data kula da Hafsat ta shigo tana fad'in "Hajia zaku iya tafiya gida, ba wani abun yanzu insha'Allah." Take idon Hafsat suka kawo ruwa da tunanin tafiya da zatayi ta bar yarta anan, kallonta likitar tayi tace "Ayya madame! Kiyi hak'uri karki damu, ko ba yarinyarki bace ai zamu kula da ita saboda abinda sheikh ya d'aukemu muyi kenan, bare kuma 'yar sheikh guda?" Murya a raunane tace "Dan Allah yaushe zan iya zuwa ganinta to?" Shiru ta d'anyi dan gaskiya ba dan tana ita ba a tsari da dokar asibitin nan da wata biyu da yarinyar zatayi ba zai wuce ta zo ta ganta sau uku ko kad'an da haka ba, amma dake ita ce sai tace "Madame zamu iya yi miki alfarmar zuwa ganinta sau uku a kowane wata." Da sauri Hafsat ta kalli su Hajia ta kalli Rakiya tace "Sau uku kawai? Amma kuma taya zan rayu nesa da 'yata." Murmushi tayi tace "Karki damu madame, zata kasance cikin kulawarmu." Kamar zata fashe da kuka tace "To amma Rakiya ina so 'yata tasha nono ko kad'an ne." Da fara'a tace "Wannan ba matsala bane madame, duk sanda kika zo ma idan kina so za'a iya tatsa mata nonon na ki sai a bata." D'an murmushi tayi ta jinjina kai alamar to, da haka ta mik'a musu katin maganin da za'a siya kafin ta fita, haka suma suka mik'e suna shirin tafiya, Hajia ce ta fara kallon Mimi tace "Mimi ku zaku wuce gida ke da Asma'u, idan kunje saiku d'ora abinda zaku ci ko? Zuwa dare zan dawo nima." Jinjina kai sukayi a tare kafin suka fita dukansu kowa yayi hanyar da zata sadashi da inda ya nufa. Suna zuwa gida madafa suka shiga suka d'ora lafiyayyen girki da miyar hanta, Asma'u ma na taimaka mata saidai tana koya daga haka, suna kammalawa daf da magriba suka nufi d'akinsu dan yin alwala, wayarta ce tayi k'ara ta duba dan ganin mai kira, lambar sheikh ce ta bayyana hakan yasa gabanta fad'uwa, gyara tsayuwa tayi ta dafe k'ugu tace "Wai me tsohon nan yake nufi dani ne?" D'auka tayi ta kara a kunne tace "Hello." Sautin muryarshi ta ji yana murmushi kafin yace "Assalama alaiki yan matan tsohonta?" Numfashi ta sauke ta dafe k'ugu tace " Ustaz, wai me yasa kake kirana yan matanka ne? Hakan fa da kake ba kyau ko kad'an, kaga dai ni yarinya ce har yanzu, idan kana min irin haka kunya nake ji wallahi." Yar dariya yayi ya gyara zamanshi sosai yana lumshe ido yana sauraren tab'ara yace "Allah ne ya wankeki ya bani duk da tsufana, kinga dole na kiraki yan matan tsoho, batun kunya kuma da kike fad'a wannan ki aje gefe, dan ina dawowa da kaina zai d'aukeki zuwa gidanki." Bud'e baki tayi tace "Lahhhh! To ni ai na fad'a maka bana son zama da kai ko, ya kake so na zauna da kai ne a takure?" Numfashi ya sauke yace "Ba a takure zaki zauna ba, na miki alk'awarin zaki ji dad'in zama dani har ma ki so ni a zuciyarki." Kyab'e fuska tayi baki tab'e tace "Tabd'ijam, a hamsin ba biyu d'in?" Shafa sumar kan shi yayi yana lumshe ido sosai yace "Ba hamsin ba biyu bane, nan da d'an lokaci da mun zama d'aya ni dake zai zama 48+17 kinga zasu zama 65, ni dake zamu zama yan shekaru d'aya." Shiru tayi dan kanta ya kulle da wannan lissafin daya mata, d'an sosa k'eya ta shiga yi na tunanin ya ne abun yake? Muryarshi ta ji yace "Yan matan tsoho, zan turo miki da lambar bud'ewa na asusun nan, na rok'eki Ryma ki ciri duk abinda kika da buk'ata amma karki rok'i wani kinji, kinga fa yanzu ke matata ce ko?" K'yabta idonta tayi kafin tace "Me yasa kake tunanin zan rok'i wani to idan ka yarda ni matarka ce?" Ajiyar zuciya ya sauke yayi shiru, kamar ba zai amsa ba sai kuma ya bud'i baki da k'yar yace " *A tsorace nake Ryam, tsoro nake ji*." Da rashin bawa abun mahimmanci tace "Tsoron me?" Murya k'asan mak'oshi yace "Tsoron kar wani ya sake shiga *gonata, hurumi na*." Gyara tsayuwarta tayi cike da k'uruciya da rashin hankali ta bud'e baki ta fashe da kuka tace "... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:57 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *38* Gyara tsayuwa tayi cike da k'uruciya da rashin hankali ta bud'e baki ta fashe da kuka tace "Ni d'in dama taxi ko wata katifa ka mayar dani, Allah zan fad'awa Abba na ce kawai kallon taxi kake min." A rikice kuma a rud'e ya mik'e tsaye daga zaunen da yake yana fad'in "Ba fa haka nace ba Ryam, nufi na ta wa gonar, ni kad'ai." Dakatawa tayi dan dama kukan ba hawaye ne da shi ta shiga sharewa tana turo baki tana fad'in "To naji, kuma ai kai ma nasan ba zaka maidani gonarka ba ko? Tunda ai kaga ni kamar y'arka ce bani da wayo." Wani murmushi ya saki mai sauti yana girgiza kai ya koma ya zauna a k'asan mak'oshi yace "Um." Cikin shagwab'a tace "To zanyi sallah." A ladabce yace "Ki min addu'a kinji yan matana." Kamar wata sakarya sai kuwa tace "Me zan rok'a maka?" Cike da jin dad'i yace "Na dawo lafiya na sameku cikin k'oshin lafiya, sannan ki rok'a min Allah ya bani nasara a kan ki." Bud'e baki tayi tace "Kai! So kake ka cuceni?" Murmushi yayi yana jin a ran shi "Oh Allah." Kafin a zahiri yace "Ba zan cutar dake ba." "To me zaka min." Ta fad'a tana turo baki, cikin raha yace "Kawai ina so ne idan kin tare gidana na mayar dake yar lelena, autar gidana, shagwab'ab'iyata, rigimammiyata, rikicina kuma sarauniyar kukana." Kyab'e fuska tayi tana d'an zama bakin gadon tace "Duk ni ce ma mai wannan halin? Shikenan Allah dai yana gani." Cikin rarrashi yace "Oh ba haka nake nufi ba, ina so ne na mayar dake kamar wata sarauniya, na dinga miki wanka ina baki abinci sannan kiyi bacci idan kin gama kukan jin dad'i." Rufe fuska tayi saboda jin kunya tace "Da gaske?" Cikin gasgata yarintarta tace "Da gaske." Jinjina kai tayi tace "To amma ai ba'a wanka sai an cire kaya, kana nufin saina tsaya a gabanka babu kaya?" Me sheikh zai yi sai ya tintsire da dariya yana dafe goshi, jin yana dariya sai kawai ta murgud'a baki ta daste kiran ta aje wayar ta mik'e, jin ta kashe yasa shi kallon wayar da mamakin wai kashe mishi waya tayi? Girgiza kai yayi yana sakin wani murmushin. Har suka ci abinci wajen k'arfe 09:00 na dare sannan Hajia ta dawo, sannu suka mata kafin Mimi tace "Hajia a kawo miki abinci ne?" Cike da gajiya tace "A'a Mimi barshi, mun ci abinci a can, wanka zanyi yanzu na samu kwanta." D'an murmushi tayi kafin ta mik'e tana d'aukar jakarta da hijab zata shiga d'aki tace "Idan kunyi waya daa sheikh ki nemi izininshi gobe sai kuje can ku wuni ko?" Cike da kunya ta jinjina kan ta alamar to, suna kallo ta shige kafin Mimi ta gyara zama daga d'an durk'usawar da tayi tana kallon Salamatu, yanda ita ma take kallonta yasa Mimi had'e fuska tace "Na zubo miki tuwon ne?" Tab'e baki tayi ta wuce na ta d'akin ita ma dan a nan take kwana, tsaki Mimi tayi tana binta da harara, dariya Asma'u tayi tace "Ke kuma me ya had'aki da tsohuwar mutane?" Tab'e baki tayi tace "Hum! Bata da kirki da kike ganinta." Nan ta kwashe komai ta fad'a mata daya faru wanda ya jawo silar rashin shirinsu, Asma'u dai dariya take sosai. *00:10* Mimi na bacci ta ji wayarta na vibration, daddab'ata Asma'u tayi ta farka tana d'aukar wayar, kallon Asma'u tayi da ita ma wayarta mak'ale a kunne da alama da na ta mijin take waya, sake kallon wayar tayi tana danna ok tana fad'in "A wannan lokacin kike wani waya da miji ke jarababbiya, mtsss!" Tsakin da tayi yasa shi lumshe ido can k'asan mak'oshi yace "Shiyasa nake son ki yan matana, ke ba jarababbiya bace, ko?" Yanda ya tambayeta yasa saurin cewa "E mana." Ta k'arashe tana hararen Asma'u, kamar wata mai iskokai sai cewa tayi "Yawwa sheikh, Hajia tace gobe zamu je gidanka wajen aunty Hafsat." Jim yayi yana d'orawa da tantancewa hak'ik'anin me yake ji a kan yarinyar, shirme dai take tabka mishi na gaske, amma sai ya ji ranshi bai b'ace ba, idan kuma ya b'ace na wucen gadi ne komai zai wuce. Asma'u ma kallonta tayi dan wallahi ita tasan da gangan Mimi ta maida kanta kamar wata sakara idan tana gaban sheikh, ai ba haka take ba a da, yarinyar mai ajin tsiya wani zubin ma har da d'aukar kai, amma yanzu ta zama wata mai ido a tsakar ka. A saanyaye sheikh yace "To fitar d'azu da kukayi da izinin wa aka yi?" Kan ta tsaye tace "Ai Hajia ce tace muje." A hankali yace "Kenan Hajia tana bada izini ne?" A sangarce tace "To kayi hak'uri dai yanzu amma ka barmu mu tafi gobe." Cike da baccin dake idonshi yace "Shikenan, Allah ya kiyaye hanya." Kamar wacce aka kad'awa da hanji sai kawai tace "To saida safe." Da sauri yace "Baki ji ba." Dakatawa tayi tace "Uhum." Kamar zaiyi bacci yace "Bacci nake ji, dan Allah ki min addu'a." Da mamaki murya a sanyaye tace "Addu'a kuma? Kamar ya?" Saida ya sauke numfashi yace "Na saba idan ina cikin iyalina na kanyi musu addu'a idan sunyi bacci, yau kuma da bana tare dasu sai naji ina sha'awar nima a yi min, Hafsana ta jima da yin bacci bare tayi min." Maganarshi ta k'arshe ce tasa ta jin wani irin duka da k'arfin gaske a zuciyarta, shirun da dukansu sukayi yasa ta jin idonta taf da hawaye, lumshe ido tayi murya na rawa tace "Abdul zuciyata rawa take, bana jin dad'i kaji, ban da lafiya yanzu bacci zanyi." Shiru yayi yana saurare da karantar yanayin muryarta, a sauk'ak'e yace "Shikenan rik'e waya zan tofa miki addu'a." Wayar na kunnenta ta ji yana karanta mata addu'ar bacci, yana kammalawa cikin muryar rad'a yace "Saida safe yan matan tsohonta, kiyi bacci lafiya, ina k'aunarki." K'it! Ya kashe kiran yana k'urawa wayar ido, maganarshi ta k'arshe da maganarta ta k'arshe ya shiga d'orawa a mizani yana san yasan me ya jawo mata rashin lafiyar data fad'a a nan take? Da wannan har ya yi addu'ar bacci ya gyara kwanciyar kafin ya tashi anjima ya gana da mahaliccinsa. *03:00* daidai goshinsa na k'asa yayi sujada ga ubangiji yana fad'a masa buk'atunsa idonshi na zubar da ruwa, cikin k'ank'anr da kai da kadnaita Allah da mayar da kai ba kowa ba yake kuka yana fad'in "Ya Allah ka gafarta min zunubaina, ni mai laifi ne a gareka Allah ina tuba a duka kurakuraina dana sani da wanda ban sani ba, Allah ka yafe min zunubaina, Allah nagode abisa ni'imominka gareni, Allah nagode da ni'imarka gareni, buwayarka mafi d'aukaka, izzar mulkinka mafi guda, tsarkakar mulkinka wanzanjiya, kyautarka mafi anfanuwa, Allah ina k'ara gode maka. Allah ka shirya min yarana shiri irin na addinin musulunci, Allah ka shirya min kan iyalina su zama mafiya kyawan alak'ar zumunci, Allah ka raya min *Khadija* ka inganta lafiyarta, Allah ka bawa mahaifiyarta lafiyar shayar da ita, Allah ka bata juriya da ikon tarbiyar yaran. Ryam! Allah ka fini sanin sirrin dake cikin tarayyata da ita, bansan komai ba Allah face ilimin daka yarje min na sani a bayyane, ina k'ara neman zab'inka akan lamarina da ita, idan har alkairi ce a gareni Allah ya ka dawwamar da alak'armu tare da saka mana fahimtar junanmu, idan kuma akasin hakane Allah ka gaggauta yin nesa da ita dani da kuma ahalina, Allah na rok'eka da zuciya d'aya inhar Ryam ba alkairina bace duk son da nake mata Allah ka cire min ita a zuciya sannan ka nesanta ta dani da iyalina na har abada. Idan kuma aurena da ita yana nufin koya min darasi akan kalamaina da suke nuna k'yamar mace mai biyar maza ne, Allah gani a gabanka kaina k'asa, ka fini sanin abinda ke cikin zuciyata, idan har tubana na gaskiya ne Allah ka shirya min yarinyar nan ka d'auke idonta da hankalinta daga kowane namiji bayan ni mijinta, Allah na rok'eka inhar tubana na gaskiya Allah ka saka farin ciki a rayuwata data iyalina, astagfirullah, astagfirullah, astagfirullah-alzeem, astagfirullah wa'atubu ilaikh." D'agowa yayi hawaye na ci gaba da zarya a fuskarshi, sunkuyar da kai yayi tsabar k'ask'antar da kai yana tahiya kafin ya yi add'u'oin bayan tahiya ya sallame, jim ya d'anyi kafin ya d'aga kanshi ya kalli gabanshi, wata k'akk'arfar ajiyar zuciya ya sauke, cikin muryar data sha kuka a shak'e yace "Nayi alk'awari tsakani na da ubangijina, Allah kaine shaidata kan alk'awarin nan da zan d'auka a yanzu, *Ryam ta riga da ta zama matata, nayi alk'awarin tsare mutumcinta da k'arfina, sannan nayi alk'awarin rik'eta abisa gaskiya da amana, nayi alk'awari ba zan tab'a k'yamarta ba saboda laifin data aikata a baya, nayi alk'awarin ba zan gujeta ba haka kuma ba zan tab'a fallasa sirrinta*, Allah na rok'eka idan har wannan nayi shi ne saboda kai ina fatan zan samu sakamako na a wajenka kamar yanda kayi alk'awarin kyakyawan biya ga ma'abota kyauta da kyautatawa." Wata ajiyar zuciyar ya sake sauke yana jin wata nutsuwa na ratsashi a sanyaye, gyara zama yayi ya tokare k'afarshi d'aya ya fara zikhri da hannayenshi, bai gushe a wurin ba saida wayarshi ta alamta mishi k'arfe 05:00 kafin ya mik'e ya kabbara sallah subh dan a nan ba masallaci zai ji ba. *Niger* Masha'Allah kam Mimi dake akwai wayewa da kuma kunya, tuni ta sake a cikin gidan dan kuwa ita da Asma'u da Fanna cousine d'in su Hafsat sukayi girki na rana dana dare, sosai ta saki jikinta saidai bai hanata kama jikinta ba, dan ko abun dariya akayi zata murmusa, aiki dai nai zata mik'e ta taimaka ko ba'a nemeta ba, yamma nayi ita da Asma'u suka gyara falon tsaf sukayi turaren wuta dana tsintsiya dan sun fahimci a fannin tsafta dai kam Hafsat bata da tsara, dan in maganar gaskiya za'ayi to Mimi zata iya cewa gabanta ya girgiza sanda ta shiga d'akinta ta samu ko ina k'al-k'al kamar ba mutum ke rayuwa a nan ba, amma dake ita d'in yar sa kai uku ce sai ta yatsina fuska ta nuna inhar zasu zauna a matsayin kishiyoyi to zata zauna da ita kuma zata iya ita ma. Sun idar da sallah magriba tana zaune a falon tare da Munzeer da Aswan kasancewar akwai d'akin da aka ware ana shiga ayi sallah, Hafsat ne gefe zaune akan katifa tana waya k'asa k'asa tana murmushi da alama da sheikh suke magana, Mimi kam da bata damu ba ma remonte ne a hannunta tana ta canza tasha (馃ぃBaiwar Allah mbc take nema), kallon Munzeer tayi dake kan k'afarta tana murmushi tace "D'an tanti, wai ku baku da wasu tasha ne bayan wannan?" Cikin maganarshi ta yara yace "E aunty, duka wannan ne kawai." Aswan dake jinsu ne yace "Auntynmu ai idan nishad'i kike so saidai in kin fita mak'wabta." Harara Hafsat ta cilla mishi daga nesa hakan shi mik'ewa ya fita waje, Mimi kam aje remonte d'in tana ji a ranta ai ba nishad'i babu mbc, fitowar Asma'u yasa ta fad'in "Asma'u mu wuce gida ko?" Hafsat dake jinsu d'an d'auke wayar tayi a kunne tace "Ku tafi kamar ya? Tun yanzu?" Cikin jin kunya tace "E aunty, naga dare ya fara ai." Girgiza kai tayi tace "Ba yanzu ba gaskiya, to ke Mimi me zai hana kiyi zamanki ma kawai tunda gidanki ne?" Da sauri ta kalleta sai kuma ta sunkuyar da kanta, murmushi Hafsat tayi ta d'ora wayar a kunne, duk da ya ji me take fad'a kuma yaji kamar yace "E hakane Manga, ki matsa mata ta zauna dana dawo ba sai na wahala d'aukota ba." Amma kuma sai ya nuna kamar ma bai ji ba suka d'ora a inda suka tsaya, fitowar Hajia ne tasa su shiryawa suka d'auki hanyar gida tare da Kabiru dreba. Suna hanyarsu ta komawa gida Mimi ke fad'in "Wai ita matar nan bata kishina ne? Sai tayi ta abu kamar ba mace ba." Murmushi Asma'u tayi tace "Hankalin data nuna ne baiyi kama da d'abi'ar mace ba? Ko kuma dai iliminta da take anfani dashi ne ya zama illa?" Tab'e baki tayi tace "Ke maganar gaskiya idan ni ce ita ko yaya sai nayi kishin mijina, haba ai ko d'an tayar masa da hankali sai nayi ko da nayi masa kuka ne na kwana bakwai." Dariya Asma'u tayi tace "Ke sarauniyar kuka ba?" Kallonta tayi dan a take ta tuna mata da shi, rabonta da shi dai tunda safe da zasu zo gidan sukayi waya, a sanyaye ta furta "Ko me yake?" Sai kula tayi saurin yin k'yaci tace "Ina ruwana ma." Kamar kuwa yasan me take yi yana kuma son k'aryata ta sai kuwa kiran wayarshi ya shigo, tana ganin lambar kuma sai tayi d'an murmushi, dama tun fil'azal kiransa bata gagara d'aukarshi, dan haka yanzu ma da sauri ta d'auka, shiru tayi har saida ya furta "Ina fatan kina cikin aminci?" D'an satar kallon Asma'u tayi kafin ta matse bakinta tace "Lafiya lau." Murmushi yayi jin tayi shiru yace "Har kun tafi kenan?" "Um." Ta fad'a shi ma a tak'aice, ba tare daya gaji ba yace "Me yasa kika k'i zama a gidanki? Kinga fa da ina nan da tun jiya kika tare." Tsam tayi sai kuma tace "Kamar wata yar beby? Kuma ma ai ni ba yanzu zan tare ba." A take yace "Sai yaushe kenan?" Cike da lalata tace "Sai na k'ara girma." Wani malalacin murmushi yayi yace "A gidan Hajia zaki zauna kuma?" A hankali tace "Me yasa ka tambaya?" A zuciyarshi cewa yayi "Saboda na ji a inda zaki min rainon cikina mana." A zahiri kuma sai yace "Saboda nasan inda zan dinga aika miki madara." Yatsina baki tayi tace "Ni bana shan kowace irin madara sai lacstar." Da wani shak'iyin murmushi a fuskarshi yace "Ni ma ita nake nufi." A wani d'arare yace "Ryam." A sanyaye tace "Na'am." Cikin muryar saukar da kasala yace "Zan sa Hajia ta fara miki shirin tariyarki, ina so ranar da zan dawo garin nan ki tare a d'akinki." Baki sake tace "Yaushe kenan?" Cikin muryar rad'a yace "Insha'Allah ina sa ran zamu dawo ranar laraba, dan maganin da aka d'ora Asas talata zai k'are, laraba mu kuma zamu juyo." Waro ido tayi tace "Ana gobe bikin aunty Hafsat fa kenan?" Yar dariya yayi yace "Yan matan tsohonta kenan, ban da abinki yarinyar dake cikin kwalba a asibiti ne za'a wa biki? Kuma ni ai a tsarina ba'a min wannan bidi'ar, ana zanawa yaro suna ne ranar da yayi bakwai sai yan uwa da akan gayyata a ci abinci dan godiya ga Allah, sannan a lissafinki ya nuna a al'adance kike lissafi shiyasa kike tunanin ranar alhamis ne sunan." A girmame ta furta "Tabbd'!" Baya biki fa? To yanzu da yake son ta zauna da shi idan ta haihu shikenan ba zatayi biki ba? Cikin rashin fahimta tace "Yanzu nan shikenan ba za'ayi biki ba ayi shagali? To yaushe ne sunan ya kama?" Cikin sakin murmushi yace "Ranar laraba, idan kika k'idaya kwanakin zaki ga a ranar ne bakwai." Shiru tayi ta ma rasa me zata fad'a, jin haka sai kawai yace "Katin dana bar miki na ga har yanzu bakiyi aiki dashi ba, ai ya kamata ke ma ki bawa Khadija wata kyauta ko?" A sanyaye jiki a mace tace "Zan yi, sai gobe insha'Allah." Cike da rarrashi yace "Ryam, dan Allah idan zaki tafi karki manta da hijabanki manya da kuma nik'abi kinji, sannan karki jima ki dawo gida ki huta." "To." Ta fad'a a hankali, da haka sukayi sallama ta aje wayar kan cinya tana kallon Asma'u tare da labarta mata abinda ya faru, dariya Asma'u tayi haka ma Kabiru dake tuk'i murmushi yayi yana jinjina lamarin wannan sabuwar sirika ta gidan yar gayu kuma da alama ma yar casu ne. Washe gari tsaf suka shirya ita da Asma'u zasu je banki, Hajia dai da addu'a ta rakasu dan tasan da mijinta bai bud'e mata bakin aljihu ba me zai kawo maganar zuwa banki, Kabiru ne ya kaisu kuma basu jima ba dan tana nuna katin wa wani ma'aikaci aka shiga girmamata alamar sani, saida ta d'ibo kud'in sai kuma ta kalli Asma'u ta fashe da dariya tace "To wai me zanyi da kud'in nan ma?" Tab'e baki Asma'u tayi tace "Kud'i ana rasa abunyi ne dasu dama?" Rik'e hannunta tayi suka nufi mota tana fad'in "Muje zanyi tunanin abun yi." Bin ta tayi tana fad'in "Allah yasa dai ba a leshe da atamfa zasu k'are ba." Dariya tayi tace "A'a zan san me zanyi kedai, ba mijinki zai dawo ba?" Mota suka shiga Asma'u na fad'in "Me ya shafi kud'inki da shi kuma?" "Zaki gani kedai." Ta fad'a suna barin wurin, daga nan gidan Hafsat ya ajesu dan yau ma nan zasu wuni, suna zuwa sun samu Hafsat dake zaune tana magana da Salamatu tana fad'in "Baaba Salamatu ki fara d'ora min su na fi so na yi anfani dasu anjima." Juyawa tayi zata shiga madafa tace "To bari na wanke su sai a d'ora silalarsu." Da ladabi Mimi tace "Aunty Hafsat me za'a d'ora ne?" Da fara'a tace "Hanji ne na ke son romonsu, ita kuma da tana so ta fara da girkin rana." Mik'ewa tayi tana cire zumbulelen hijab d'in tace "Bari na d'ora miki to." Asma'u ma mik'ewa tayi tana fad'in "Bari ni saina kama ma Salamatu girkin to." Da jin dad'i tace "Ba kwa gajiya da aiki, to sannunku." Wucewa sukayi madafar suka shiga aiki gadan gadan. Sanda ta gama silala ganin ta juye ruwan silalar zata zubar yasa Salamatu saurin fad'in "Ke ke! Baki da hankali ne zaki zubar? Ko dai baki san miye silala ba?" Numfashi ta sauke ko kallonta ba tayi ba ta juye ruwan ta zubar, Asma'u ma kallonta take saidai tasan akwai dalilin da yasa tayi haka, saida ta tsane hanjin kafin a tsanake ta shiga soya miyarta da kayan miya masu yawa, sanda ta gama girkinta tsaf ta zubawa Hafsat a kula mai kyau ta kai mata falo, dawowa tayi ta zuba a k'aramin plate ta b芒 wa Salamatu tace "Iya ne sunanki ko Baaba? Ki d'and'ana ki ji kiga kalar dahuwarki ce, a ido kawai zaki tabbatar da banbanci." Tana fad'a ta fito daga madafar, cikin sakin fuska ta kalli Hafsat tace "Aunty ko na zuba miki ne?" Da fara'a tace "Da kin barshi ma ai." Mik'ewa tayi ta d'an zauna bakin katifar ta shiga zuba mata, mik'a mata tayi kafin ta koma kan kujerar, Hafsat na kai lomar hanta bakinta ta kalli Mimi ba tare da bak'in ciki ba tace "Mimi dahuwar nan ta min dad'i, kinga kuwa miyar batayi irin kaurin nan ba wani har kaga yana tayar ma da zuciya." Murmushi kawai tayi ba tace komai ba, sosai Hafsat ta ci naman nan kamar zata tsinka harshenta, saida ta kammala tasha ruwa tace "Wannan a ranar da sheikh zai dawo zaki girki masa wannan, dan mutum ne shi mai son miyar hanji sosai." Dariya ita dai kawai tayi ba tayi magana ba sai a zuciyarta da take fad'in "Sheikh d'inki dai, zaki dafa masa ne yarinya in kuma ba haka ba to yunwa zata kamashi." Ko da k'arfe 01:00 tayi su Asma'u ma suka gama girkinsu suka cire ma kowa na shi, lokacin Mimi ta shiga sallah a d'akin da aka ware bak'i na sallah Mamanta ta zo gidan yin barka tare da Shapi'a da Sahura. Asma'u ce ta karb'esu inda Hafsat ma ta shiga girmamasu ta nuna musu murnarta a fili, Mimi na fitowa ta gama sallah ganinsu yasa ta k'arasowa da farin ciki tana fad'in "Mama, aunty." Tana zuwa bata zauna akan kujera ba k'asan carpet ta zauna tana rik'e hijabin Mama tana fad'in "Mama yanzu kuka shigo? Me yasa baku fad'a min zaku zo ba? Mama ina su Yaseen? Ina Abba na Mama?" Mama sunkuyar da kai tayi cike da kunya dan ita Mimi ma kunya ta bata sosai, ganin ba zata amsa ta ba yasa ta kallon su Shapi'a tace "Aunty Ina wuninku?" Da fara'a suka amsa mata suka gaisa sosai, Hafsat ce tace "Mimi ki kawo musu abinci ko?" Mik'ewa tayi zata tafi su Sahura tace "A'a Mimi barshi, saida mukayi abinci a gidan kafin muka taho." Duk yanda Mimi ta so matsa musu su ci abincin k'iyawa sukayi saboda dattako, basu fi minti ashirin ba suka mik'e zasu tafi, cikin kukaan shagwab'a ta bi bayansu dan rakiya Mama na fad'in sa ta ci uwata idan tana mata shiriritar nan, saida suka kai farfajiyar Shapi'a ta mik'a mata wani dogon bidon da zuma a ciki tace "Yar albarka karb'i tsaraba kinji ki sha abarki." Karb'a tayi tana kallon robar Mama tace "To dan hauka ki shiga da shi a haka sai kin nunawa kowa sirrinki." Dariya tayi murya k'asa k'asa tana fad'in "Wai nan su fa tsuma ni suke saboda tsohon nan, ko me ya fad'a musu zai iya?" Sahura ce tace "Magana kike?" Da sauri tace "A'a ban ce komai ba." Rakasu tayi suka fita tana jin kewarsu kamar ta bi su." Tana dawowa kuma Hafsat da kallon birgewa ta bi ta dan yanda suka mik'e suna tafiya daga yanda take bin bayan iyayenta tana risinawa zai nuna maka tana girmamasu ne bata son ta fi su tsayi. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:57 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *39* Da dare suna komawa gida saida sukayi shirin kwanciya ta samu zumar nan saboda kwad'ayi tayi ta sha duk da ana jin d'and'anon magani, saida ta ji cikinta ya fara k'ullewa kamar zai mata ciwo ta mik'awa Asma'u tace "Sha ke ma." Murmushi tayi ta karb'a tana fad'in "Sai yanzu kika da damar bani saboda kina so ki nuna min ke babban Alaji gareki." Duka ta kai mata tana dariya tace "Shegiya Asma'u, ke ni me zaanyi da wannan d'an uwan naku, wanda ya haifi kamata?" Murmushi ta sake yi tace "Ke dai kika sani." Har suka kwanta cikinta na k'ulle mata daga baya sai taji har mararta ma wani ciwo ciwo take mata,da haka dai bacci ya d'auketa dan abun ba wani mai tsanani bane. Kullum hakane ke faruwa Mimi da Asma'u sukan wuni gidan Hafsat ne suna kama aiki, kuma duk da ba taron biki ake ba amma lokacin na matsowa sai aka shiga yin lalle da kitso wasu ma har da d'inki kamar Hafsat da Aisha da sauran yaran. A gefe guda kuma an gama shirin tariyar Mimi lokaci kawai ake jira, ranar da su aunty Shapi'a suka zo kamar yanda Hajia ta buk'ata dan ganin b'angaren da sheikh ya ware mata da kuma kayan da aka zuba mata bata zo gidan ba sai Asma'u kawai, masha'Allah abun ya birgesu tare da neman zautar dasu, tunaninsu bai wuce yanda yake babban malami ba amma ya daki dukiya haka kamar zatayi kuka, kaya ya mata na kece raini aka cika mata falonta da kuma d'aki biyu. *Ranar talata* Cikin tsantsar farin ciki da murmushi d'auke a fuska sheikh ya mik'awa likitan hannu bayan sun gama biyan duk cajin da aka musu yana fad'in "Alhamdulillah, naji dad'i sosai likita, Allah ya saka maka da alkairi, munyi farin ciki sosai." Shi ma da fara'a yace "Ba komai, wannan aiki na ne dama, d'an uwanka ya samu lafiya kenan." Kallon Asas sukayi dake ta murmushi shi ma cikin zolaya likitan yace "Idan ka ga yayi ciwon cikin nan mai tsanani, ina tabbatar maka fad'a yayi da madame ta daina kulasa a shinfid'a." Dariya sukayi shi kuma ya sunkuyar da kai yana murmushi, mik'ewa sukayi suna musabaha kafin sukayi sallama suka fito a ofishin, suna fitowa daga asibitin sheikh ya tari taxi ya kalli Asas yace "Kai kaje masauki ni zan je na ciro mana ticket na komawa gobe insha'Allah." Zaro ido Asas yayi yace "Da wuri haka? Na warken ma ba zaka barni na d'anyi yawon bud'a ido ba." Tab'e baki yayi yace "Kana da damar da zaka tsaya bud'a ido amma fa ba tare dani ba." Murmushin shak'iyanci Asas yayi yace "Sheikh dai na ganoka so kake ka koma wajen matanka ba." Hararenshi yayi yace "To kaga laifina ne? Mace biyu kamar d'aya ce aka fad'a ma? Sannan karka manta har amarya gareni fa." Tsuke baki yayi yana shiga taxin yace "Dad'inta dai nima amaryar gareni." Murmushi kawai yayi shi ya samu wata taxin zuwa filin jirgi dan kam yayi niyya gobe saiya bar k'asar nan dan bayan iyalinshi da yake son had'uwa dasu akwai abubuwa da dama yake so yaje ya d'ora a inda ya tsaya. *Ranar laraba* A masallacin aka zanawa Khadija sunanta, sai jibgegiyar sa da aka yanka yan uwa aka shiga sarrafata, duk da ana cewa ba'a biki amma fa dangi an ci kwalliya har mai jego kan ta, sannan mmak'wabta da yan uwa sun cika falo da farfajiya. Mimi kam tare da Asma'u da su Aisha da Fanna suka je salon aka musu kwalliya, yau kam Fanna duk wayewarta da k'aryar kud'in saita shafawa Mimi lafiya, ba wai kyan da tayi ko tsarin shigarta ba, yanda take kashe tsayuwa ta d'auki hoto su kansu har tana nuna musu yanda zasuyi sai ta jinjina mata. Saida suka gama shirmen hotunansu kafin suka kama aikin da mutane keyi. *06:00* daidai suka sake gyara shirinsu bayan sunyi wanka Mimi ta sake cab'a kwalliyarta, suna tsaka da shirin Hajia ta shigo d'akin Aisha tana fad'in "Aisho zo mana na aikeki." Yatsina fuska tayi tace "Kaji tsohuwar nan kuma, ina zaki aikeni." Dak'uwa ta mata tace "Uwaki, sauri ake mana ki zo, gidan Hajia Kubra zan aikeki ga Kabiru nan na jiranki." Cikin shagwab'a tace "Hajia Kubra kuma? Ba yaanzu ta tafi daga nan ba." Dak'uwa ta sake mata tace "Uwaki Aisha, dan Allah ta so mantuwa tayi kuma abu mai mahimmanci." Mik'ewa tayi tana turo baki tace "Ni faa ko gidan data koma ban sani ba." Jim ta d'anyi kafin ta kalli Mimi tace "Mimi ai kinsan gidan Hajia Kubra ko?" D'aga kai tayi a hankali tace "E, amma ban tab'a zuwa ba." Cikin rarrashi tace "Yawwa yar albarka to tashi rakata dan Allah." Jinjina kai tayi sai Fanna da ita ma tace "To muje tare ko?" Kallonta Hajia tayi tace "Ba komai kuje, amma kuyi sauri kafin magriba ku dawo." Mik'ewa sukayi duk suna gyara mayafensu har Aisha da ba sabonta bane, dan mayafin ma na Fanna ne ta bata ta saka, suna zuwa suka shiga Kabiru ya d'auki hanya da su, hirarsu suke sha sosai har suka isa unguwarsu Mimi a gidan Hajia Kubra, Aisha ce kawai ta fita da ledar a hannunta ta shiga, tana fitowa ba jimawa suka juyo, yanda aka bi ta k'ofar gidansu Mimi yasa Mimi kallon Kabiru tace "Dan Allah Kabiru ka tsaya na shiga na ga gidanmu, wallahi kuka zanyi idan ka wuce." Tsayawa yayi inda suka shiga mata dariya, dukansu suka fita sai Asma'u da ita ma ta nufi gidansu tana fad'in "Nima bari na ga namu gidan to." Shigewa duk sukayi saidai Aisha ta bi Asma'u ne Fanna kuma Mimi. Yanda Mama ke kallonta da mamaki da kuma Abba dake alwala yas ta saurin duk'awa k'asa tace "Abba, mama ina wuninku. Abba ne yace " Ke uwata daga gidan uban wa kike ana shirin magriba?" Mama ce tace "Ina ce ma yau ne bikin gidanku? Halan sato hanya kika yi ba wanda ya sani?" Zunbur Abba ya mik'e yana d'aukar takalminshi da fad'in "Ai kuwa zan ci ubanta a gidan nan, sheikh d'in zaki wa satar hanya?" Bata motsa daga inda take ba tasa kukan shagwab'a tana rik'o hannun Fanna da ita ma take durk'ushe tana ta kallonsu tace "Wallahi Abba ba satar hanya nayi ba, Hajia ce ta aiko mu gidan Hajia Kubra." A zabure yace "Wacece hakanan kuma?" Nuna mishi k'ofa tayi tace "Abba Hajiar data dawo nan gaban gidansu Bello." Mama ce tace "To kuma sai tace ki zo nan? Yaushe ma aka yi aurenki da zaki zo gidan?" Cikin tsawa Abba yace "Ke tashi ki koma gidanki." Sai lokacin Fanna tace "Ina wuninku?" A tare Abba da Mama suka amsa cikin fara'a, Yaseen ne ya fito daga ban d'aki yana ganinta ya k'araso da murna yana kiran "Mimi ke ce? Lahhh!" Rik'e hannunshi tayi tace "Yaseen kana lafiya? Shi ne baka j茅 ka ganni ba ko?" Dariya yayi yace "Mama ce ta hana, amma zamu je tare da Amir." Abba ne ya nunota yace "Uwata ki tashi fa ki koma inda kika fito?" Marairaicewa tayi tace "Abba dan Allah ka barmu muyi sallah magriba to, kaga fa ba kyau fita ana magriba." Jinjina kai yayi jin an fara kiran sallah yasa shi cewa "To kuyi sauri amma." Da farin ciki ta mik'e tsaye ta d'auki buta ta mik'awa Fanna, Abba na gama alwala suka fita tare da Yaseen Mimi na fad'in "Yaseen ina Amir?" "Yana gidan Iya." Ya fad'a yana wucewa, cikin d'aga murya tace "Ka fad'awa Kabiru ya je yayi sallah zamuyi sallah m没 ma." Mama dai kallonta kawai take tana karantar duk yanayinta, ba tace mata k'ala ba har sukayi alwala suka laulaya mayafensu suka kabbara sallah akan tabarmar da Mama ta shinfid'a. Kamar jira take su gama Mama tace "Tunda kun idar tashi ku tafi." Turo baki tayi tana kallon Mama, had'e fuska tayi tace "Wato sai mun siyar da hali kike so?" Girgiza kai tayi ta mik'e tana kallon Fanna tace "Muje." Mik'ewa Fanna tayi tana jin iyayen sun birgeta akan wannan kulawar ta su, kamar zatayi kuka tace "Mama idan su Yaseen sun zo dan Allah ki tura min su gobe, sannan ki ce Abba ma ya je na ganshi." Sororo Mama ta kalleta sai kuma tace "To." Tana kallo suka fita kafin ta bita da addu'ar shiriya da farin ciki, suna fitowa gidansu Asma'u suka fad'a dan su basu fito ba, da sallama suka shiga saidai babu wanda Mimi ta kula kamar yanda ta saba, d'akinsu Asma'u ta wuce kai tsaye Fanna na binta a baya, suna shiga zaune suka samu Asma'u akan sallaya Mamanta daf da ita suna magana k'asa k'asa, Aisha na gefensu duk ta matsu ko su koma, dan ita inba hali na larura ba sai silamiyya ce ke fitar da ita a irin wannan lokacin a gida. Tsaye sukayi Mimi tace "Malama ki tashi mu tafi ko? Ko nan zaki kwana?" Mik'ewa Asma'u tayi tare da Aisha suna gyara mayafansu tace "A'a muje." Kallon Maman Asma'u tayi suka gaisa sosai kafin su fito, suna shiga mota wayar Mimi tayi k'ara, tana dubawa ta ga Hafsat ce ta d'aga da sauri tana fad'in "Assakama alaiki." Daga b'angarenta ta amsa da "Wa'alaiki salam, Mimi Aisha na kusanki ne?" "E, gata." Ta fad'a tana mik'awa Aisha wayar, saida Kabiru ya fara tafiya kafin Hafsat cikin k'arfin hali na abinda bata tab'a yi mata ba tace "Aisha dan uwarki me ya tsaidaku?" Gabanta ne ya fara fadkuwa kafin jiki na rawa tace "Amie gamu nan a hanya." A dak'ile tace "Ba tambayarki nayi kina ina ba? Me ya tsaidaku shi na tambaya, Aisha fitarku kenan mahaifinki ya dawo gidan nan, duk mutanen dake wurin ke ya fara tambayata kina ina? Na lallab'a shi na fad'a masa Hajia ta aikeku amma ba zaku jima ba, shi ne har ki zauna acan an gama sallah, yanzu haka yana shigowa daga masallaci ke ya sake tambaya?" Tuni bakinta ya fara rawa idonta ya kawo hawaye tana ji aurenta ya tabbata tace "Amie gamu nan tafe, dan Allah ki ba Abie hak'uri kar ya min fad'a." K'it! Ta kashe wayar inda Aisha ta mik'awa Mimi ta ta jiki a sanyaye, tagumi ta buga tana tunanin hukuncin da zai mata, Mimi kuma fad'uwa taji gabanta naa yi tana tambayar kan ta "Yaushe kuma ya dawo?" Duk jugum sukayi a motar har suka isa gida babu wani nishad'i, tare suka rankaya zuwa falon saidai kamar ba'a yi wata hidima a ciki ba, babu kowa saai Hafsat da yaranta zaune an share ko ina anyi turare, Fanna ce ta nufi d'akin Aisha tana fad'in "Bari nayi shirin gida nima." Asma'u maa bin bayanta tayi tace "Bari nima na had'a mana kayanmu Mimi." Hafsat ce tace "Ki had'a kayanki mijnki zai zo nan ya d'aukeki." Da sauri ta kalleta tace "Ya zo ne?" Da murmushi tace "Sun zo, dama suna so su shammace mu ne." Juyawa tayi jiki a sab'ule duk ta rasa me ke mata dad'i, kallon Mimi tayi data zauna tana cire mayafin tace "Ya akayi kuka jima haka?" Cikin ladabi tace "Wallahi dan naga kusa da gida ne shiyasa na ce mu tsaya na ga gida daga nan mukayi sallah." Jinjina kai tayi tace "Hajia ta gaji da jiranku tayi tafiyarta tun kafin ayi sallah ai." Murmushi tayi tace "Allah sarki, zamu je gida na bata hak'uri ai." Munzeer ne ya fito daga wata k'ofar da Mimi dai a iya saninta bata san ina k'ofar zata kai mutum ba ya kalli Aisha dake tsaye daf da Hafsat yace "Abie ya ce ki je." Da sauri ta gyara tsayuwarta ta kalli Hafsat tace "Amie..." Nuna mata k'ofar tayi tace "Wuce kije." Juyawa tayi jiki a mace tana share k'walla, shigewa tayi d'akin hakan yasa Mimi kyab'e baki a ranta tana fad'in "Old man shi ma ya iya tsanani haka?" Jim kad'an Asma'u ta fito da ledar kayansu tana d'auka da k'yar, saida ta zo gaban Mimi tace "To tashi mu tafi Kabiru na jiranmu." Mik'ewa tayi a kasalance tana rik'e gyalenta a hannun, saida safe suka ma Hafsat ta amsa musu kafin suka nufi hanyar fita, suna daf da k'ofa muryar Aisha suka ji tace "Aunty Mimi inji Abie wai kije." Cak ta tsaya ta juyo da sauri dan da gaske jikinta ya d'auki rawa, sai kuma ta kasa tambayar Aisha sai kawai ta shiga takawa ganin Aisha ta juya ta koma d'akin, gyalenta a hannu ta kasa sab'ashi a kafad'a haka ta shiga inda taji k'afarta ta taka wani basaraken carpet mai laushin gaske. Waro idonta tayi tana kallon d'akin tana lumshe ido, a hankali ta furta "Old man *d'an duniya*, ashe mbc ce a d'akinshi shiyasa baya buk'atar tashar dan kallo." D'asss! Wani fad'uwar gaba mai lasisi ya sake ziyartarta sakamakon ganinshi zaune akan kujera ya hakimce fuskarshi a had'e cikin doguwar riga fara tas, yanda ta ga Aisha ta durk'usa ita ma saita durk'usa tana kallon k'afarshi daya d'ora kan d'ayar jawur da ita gwanin kyau. Kallon Aisha yayi dake ta share hawaye saboda fad'an daya mata ya mata nuni da yatsa ta fita, mik'ewa tayi tana fad'in "Nagode Abie." Mimi na ganin fitarta ta juyo ta kalleshi fuska a tamke, wani sakaran murmushi ta saki tana washe baki tace " *Tsohon yan matanshi*, ashe ka dawo, sannu da zuwa, ban fad'a maka ba ai Hajia ce ta aikemu, daga nan sai muka d'an lek'a gida mukayi sallah, sheikh kasan wani abu? Wata marar kunyar k'awata take ce min wai matar tsoho, ni kuma nace e tabbas mijina tsoho ne amma adali ne kuma mai hak'uri da yafiya, saida na rufe ido ma na ce mata ni ta bar ni da abuna ina sonka a haka, kuma fa ita ma...hum bari dai na fara kawo maka ruwa kasha akwai labarai fa bayan tafiyarka duk suka faru." Mik'ewa tayi tsaye tana aje gyalenya akan kujerar da yake zaune ya zuba mata ido yana kallo, gyara rigarta ta shiga yi tana fad'in "Da aunty Hafsat ta fad'a min kana son miyar hanji, ni kuma gwana ce a wajen iya girkasu, bari na kawo maka ruwa mai sanyi saina d'ora maka." Juyawa tayi zata fita ya mik'e tsaye ya rik'o hannunta gam, a hankali ya shiga takawa da ita zuwa uwar d'akinta dan a b'angarenta uwata Sosai jikinta ya d'auki kakkarwa ta shiga rarraba ido, bakinta ya mutu dan bata san me zai mata ba, d'akin da suka shiga sak irin na Hafsat har kayan ma iri d'aya ne da tsarinsu, amma dake a rikice take sai bata kula ba ta shiga tsatsareshi da ido sanda yake rufe d'akin da makulli. *Sheikh uwata* 馃槶 *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:57 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *40* Wajen drower kaya ya nufa ya bud'e ya d'auko wata doguwar rigar bacci da hijab, ajewa yayi kan gadon ya juyo ya kalleta fuskar nan har yanzu a tamke, ba alamar wasa a tare da shi ya nuna mata ban d'aki yace "Je kiyi wanka ki fito." Da sauri jikinta na b'ari tace "Nayi wanka d'azu fa kaf..." Yanda ya sake k'ura mata ido sai kawai ta nufi hanyar ban d'akin da sauri, zaune yayi bakin gadon yana kallon k'ofar data shiga, tunda ta shiga ita ma take k'arewa ban d'akin kallo, jiki a sab'ule ta cire kayanta ta shiga yin wankan saidai sam bata da k'arfi a jikinta, tana gamawa kayanta ta mayar ta fito a d'arare. Yana ganinta ya d'aga kai ya kalleta yace "Kinyi alwala ne?" Girgiza kai tayi sai kallonshi take a tsorace dan ya canza mata kamar ba mai kiranta a wayan nan ba yana mata hira, fuska a d'aure yace "Je kiyi alwala." Juyawa tayi tana fad'in "To." Ta koma ban d'akin, jim kad'an ta fito ta sameshi ya shinfid'a sallaya guda biyu, nuna mata kayan nan yayi yace "Ki canza waccen kayan ki zo muyi sallah." Had'e yawu tayi tace "Sheikh gida zani." Juyowa yayi ya sauke idonshi a kan ta yace "Daga yanzu har zuwa safiya karki sake min gardama akan abinda na sakaki." Zaro ido tayi ta kyab'e fuska zatayi kuka tace "Safiya? Sheikh Hajia fa..." Nunata yayi da yatsa sai tayi shiru kawai, d'aukar kayan tayi saida ta zunbula hijab d'in kafin ta cire kayan jikinta ta saka rigar, yanda ya umarceta haka tayi ta tsaya bayanshi daga gefe suka kabbara sallah, raka'a biyu sukayi kafin su sallame ya juyo ya kalleta, d'ora hannunshi yayi a kan ta yana karanta addu'ar "Allahuma ina as'aluka khairuha wa khairu ma jabaltaha alaihi, wa'a'uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi." D'auke hannunshi yayi ya mik'e tsaye tana kallo ya bud'e d'akin ya fita, gyara zamanta tayi ta had'a kai da gwiwa tana jiran tsammani, amma fa har ga Allah a can k'asar zuciyarta dukan tara tara take mata. *Yana* fita falon Hafsat ya sake komawa, abun mamaki sai bai samu kowa a wurin ba, d'akinta ya nufa da sallama a bakinshi, kallonshi tayi ba tare data daina ninke kayanta ba ta amsa da "Wa'alaika." Zaune yayi gefenta yana kallon fuskarta yace "Bacci zakiyi ne?" Da k'yar ta k'ak'aro murmushi tayi tace "Bacci zanyi sheikh, gajiya fa ke tare da mu." Kamo hannunta yayi ya zaunar da ita akan cinyarshi, hannunta d'aya ya rik'e yana wasa da yatsunta cikin sigar tuhuma yace "Hafsy me yake damunki?" Kallonshi tayi da mamaki tace "Ban gane ba sheikh?" D'auke idonshi yayi a kan ta yace "E, me yake damunki?" Girgiza kai tayi tace "Ba abinda ke damuna." Girgiza shi ma yayi yace "Ba gaskiya bane, kuma ina so yanzu abinda zaki fad'a min ya zama gaskiya." Kallon fuskarta yayi yace "Me yake damunki?" Shiru tayi tana kallon hannayensu dake had'e yana ta wasa da su, kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta d'ora kanta a k'irjinshi ta fashe da sanyayyan kuka tana fad'in "Zuciyata ce, laifin zuciyata ce, zafi nake ji wani lokacin da b'acin rai, dan Allah ka min addu'a na daina jin haka sheikh, kaga bana so na d'aga maka hankali, ina so na d'auki Mimi a matsayin yar uwa ba kishiya ba." Hannunshi dake rik'e da na ta ta d'ago ta d'ora a k'asan mamanta daidai zuciyarta tana fad'in "Ka min addu'a Dan Allah sheikh." Wani numfashi ya sauke tare da d'ora hannunshi a kan ta yana shafa gashinta dake reras da kitso k'anana, murya a sanyaye cikin son kwantar da hankali yace "Hafsat ta wa, nasan me kike ji a zuciyarki kuma nasan ba dad'i, kiyi hak'uri kinji kiyi ta ambaton ubangijinki, Sawwama, aure na da Mimi kima da daraja da kuma soyayyarki ya k'ara min, wallahi Hafsat ina sonki har zuciyata, a duniyar nan bana tunanin akwai wani abu da nake girmama lamarinshi sama da naki, dan haka ki kwantar da hankalinki Mangana, auren nan ba zan tab'a yarda ya zama sila na tashin hankalinki ba, 'ya ko 'yar wacece a garin nan ba zata tayar miki da hankali ba kuma ta ci gaba da zama a gidan nan." Yanda yayi maganar da sigar bala'i da masifa yasa ta sakin murmushi dan har ranta ta ji dad'i tare da jin kanta ya girmama tace "Me zaka mata to?" Kumatunta ya shafa yace "Gidansu zan turata mana." Murmushi tayi tace "A'a ni dai bana so." D'ago hab'arta yayi suka kalli juna yace "Har zuciyata nake fad'a miki maganar nan Hafsyna, wallahi kin ji na rantse duk wacce ta b'ata ranki dole ta samu hukunci mai tsanani a gareni, ke ko ni na b'ata miki saina hukunta kaina bare kuma wani." Sumbatar kuncinshi tayi cikin jin dad'i tace "Nagode mijina, ina alfahari da kai." Shi ma sumbatarta yayi yace "Ni ma ina alfahari dake, matar da babu kamarta a duk duniya, matar da zata shiga aljanna ba tare da hisabi ba, matar data zama silar tsayuwar sheikh Abdul Waheed, matar data haifawa Abdul Waheed farin cikinshi, Hafsat ke fa kin riga da kin gama zama komai a rayuwata, fatana kawai Allah ya barmu tare har tsufanmu." Gyara zamanta tayi a jikinshi ta rumgume shi k'am tana jin wani sanyi na ratsata na kukan da ta samu da kuma maganganun adalin mijinta, shafa jikinta ya dinga yi yana rera mata baitin wak'ar hausa mai dad'in gaske da saka zuciya tsuma wak'ar da tayi shura wak'ar jaruma, tun tana sakin murmushi na jin dad'i tana ji kamar shi ya rerata dominta har bacci ya fara d'ibarta a nan, saida ya tabbatar bacci ya kwasheta ya gyara mata kwanciyarta ya ja mata bargo, ac ya kunna mata ya tofa mata addu'a sannan ya kashe wutar d'akin ya fita cike da tausayi da k'aunar Hafsat d'in. Yana shiga a zaunen nan take har yanzu kan ta a gwiwa, tana jin an bud'e k'ofar ta mik'e tana kallonshi a marairaice tace "Yawwa yallab'ai, dan Allah ka taimaka ka mayar dani gida, kaga fa Asma'u na jirana mu tafi gida." A dak'ile ya ce mata "Ta tafi gida." Binshi tayi da kallo sanda ya fad'a ban d'aki, k'ofar ta nufa da niyyar satar hanya ta fita sai gani tayi babu makulli a jikin k'ofar, wanu iska ta furzo da tunanin yaushe ya zage shi bata sani ba, tsaye tayi bakin k'ofar ta rik'e k'ugu tana jijjiga jiranshi kawai take ya fito tayi burususuwa a k'asa tayi birgima dan ya bud'e mata k'ofar. Ya jima a ciki sosai kafin ya bud'o k'ofar, tar ta sauke idonta tana kallon k'ofar a tsaurare dan kar ma ya ga damarta, saidai yanda ya fito daga ban d'akin ya haddasa mata bugawar k'irji a sanda bata tsammani ba, babu kaya a jikin sheikh sai d'aurin k'ugu kawai na towel kalar yelow mai haske. Da saurin da bata san tayi ba ta durk'ushe k'asa tana bubbuga yatsunta akan cinyarta, bata ji takon tafiyarshi ba sai k'afafunshi ta gani masu kama dana yara kusa da ita, hannu ya zura ta bayanta ya kashe hasken d'akin kafin yasa hannayenshi ya tallabota. Cire mata hijabin ya fara shirin yi da iya k'arfinta ta bud'e baki zatayi kuka yasa hannunshi ya rufe bakin, cikin kid'ima da rud'ewa duk da ya rufe mata baki tace "Sheikh tsoro nake ji, kaga kai babba ne ko? Dan Allah ka bud'e min k'ofa na fita." Cire mata hijabin yayi yana kallon idonta dake zubar da hawaye, cikin dakusashiyar murya k'asan mak'oshi yace "Ryam na kula ba kya jin magana, ba kya gane yarena a sauk'ak'e, kin raina ni kin raina girmana, watak'ila sanin da kika ma wasu yasa kike ganin duk d'aya muke, amma yanzu zan tabbatar miki ba haka bane abun, ba wai a shekaru abun yake ba, zan sa ki yarda dani kamar yanda ni ma na yarda da kai na." Takawa yayi da ita zuwa gadon yana neman kwantar da ita ta bank'are tana girgiza kai, yanda yayi wani bake-bake a gabanta ita tasan ba dan Allah yasa ya zama malami ba to da d'an boxing ne shi, dan wani murdadd'en jiki ne dashi b'oye a bayan manyan kayan nan, da k'arfi ya zaunar da ita ya tsaya gabanta k'ik'am yace "Ryam *wacece ke* da zaki dinga ja na a k'asa ba ko takalmi a k'afarki? Me yasa kike yin duk abubuwan nan? Saboda ki hassalani ne?" Da sauri ta girgiza kai ta janye hannunshi a bakinta cikin kuka tace "Zan fad'a maka, kaga dai ai ranar nan a gabanka komai ya faru ko? To shiyasa nake yin haka a gabanka saboda ina nasan dole kai ma zaka zargeni." Rik'e hannunshi tayi jim tace "Ka yafe min kaji, ba zan k'ara ba wallahi zan dinga jin maganarka, ka barni na tafi yanzu kaga dai kafin zuciyata ta fashe." Mik'ar da ita yayi tsaye, sunkuyawa yayi cak ya d'auketa gaba d'ayanta, wutsil wutsil ta shiga yi da k'afafu tana zazzaro ido tana fad'in "Baban Aisha ka saukeni, Baban Aisha kaga dai baban k'awata ne ko? Saukeni dan Allah." Saida ya zagaya da ita ta d'aya b'angaren ya kalli fuskarta yana murmushi yace "Wannan haukan na ki yana birgeni." Kwantar da ita yayi tare da mata rumfa ya lalubo bakinta yasa a na shi ya fara tsutsa. Kaucewa take tana zillewa amma sheikh yayi ram da bakinta ya k'i saki, haurawa yayi kan gadon ya fara shirin cire mata riga, k'arfi tasa tana son mik'ewa dan abun ya fara fitar da ita a hayyacinta, ba tare daya cire bakinshi a nata ba yace "Shiiiiiii." Girgiza kai tayi tana so tayi magana amma ba dama, tsaf ya rabata da rigar ta zama daga ita sai pant d'inta dan bras na tare da atamfarta data cire, jin yana sab'ule mata pant yasa tayi kukan kura ta tureshi amma jim ya lik'e a jikinta. Shafa k'irjinta ya fara yi a hankali yana lailayasu cikin salo...wasa sosai yayi da ita har ya gama kashe mata jiki lak'was, banda hawaye da motsa bakinta babu abinda take iya wa, tsohon data raina take ganin ba zai iya da ita ba, sai gashi ya kahe馃榿 mata jiki da mahaukatan salo, ba ma dai k'irjinta daya fi sha musu kai da linda da tsutsa, k'ura mishi ido kawai tayi tana kallo tana addu'a a zuciyarta kar ya zubar mata da mutumci. Bud'a k'afarta yayi yana rik'e da sojanshi da hannu yana saitawa a hanya sannan yana kallon fuskarta yana furta "Allahuma jannibna shaid'an wa jannibin shaid'ani ma razak'tana." Rintse ido tayi tana girgiza kai cikin rarrabe kalamai da tsananin firgici ta fara fad'in "Sheikh kar...kayi...ban...tab'a..." Yanda ya danna kanshi cike da son ya banbanta mata tsakaninta da kuma wasu mazan yasa Mimi fito da muryarta iya k'arfinta tace "Ahhhh..." Rufe ya rufe mata baki da tafin hannunshi tare da zaro idonshi yana gigicewa, shiru yayi, jim yayi yana rarraba ido tsakanin fuskarta, shiru yayi a dole yana so ya tantance abinda ya ji gaskiya ne, saiya kasa motsawa saboda jin shi a wani k'aramin wurin da zai iya rantsewa da Allah wurin ya ma hallitarshi kad'an. Tsurawa fuskarta ido yayi yana sake k'walalo idonshi saboda tuna waccen ranar, yanda take magiya take rantsuwa wa mahaifinta kan cewa bata aikata ba, da kuma tuna ranar da k'awarta tace gaba kad'an shi ne zai fad'a musu wacece Mimi, da kuma tuna kalamanta na yanzun da take fad'in "Sheikh...kar...kayi...ban...tab'a..." Da wani irin firgici ya shiga d'an mammarin kumatunta yana fad'in "Ke Mimi! Mimi fad'i ina jin ki, me ye baki tab'a yi ba? Fad'a min kinji." Cije leb'enta tayi tana luuuuu? Da idonta dake son rufewa dan azabar da take ji, kallon fuskarshi tayi da kallo irin na jin haushi da tsana, bata tab'a jin haushinshi kamar na yau ba, bata tab'a jin tsoronshi kamar yanzu ba. Cikin shashek'ar kuka tana kallon k'wayar idonshi tace "Na ce...maka... Ban tab'a yi ba... *na tsaneka* Abdul." Lumshe ido yayi da sauri yana dantse harshenshi, wani masifaffen tausayin yarinyar ne ya ratsa duka ilahirin jikinshi, saiya samu kanshi da kasa aiwatar da komai, gashi dai a cikin jikinta amma sai yake so ya fito dan kar ya ji mata ciwo, amma kuma tsoron fitowar yake dan gani yake kamar tsagata zaiyi yanda ya tabbata ya k'ara 'yar mutane wajen shigar nan, to ya zaiyi kenan? _Fan's ku bawa sheikh shawara, ya fito ko ya ci gaba ne?_ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:57 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *41* Numfashi ya sauke yana ci gaba da kallon fuskarta, hannu yasa ya fara shafa gaban goshinta zuwa gashinta yana hura mata iskan bakinshi, kallonshi take kam ba ko k'yabtawa cike da jin haushi, tana ji ina ma zata iya magana da k'arfi tace ya daina bari gemunshin nan yana tab'a mata fuska, muryarshi ce ta katse mata hassalarta cikin rad'a yace "Ryam kiyi hak'uri kinji ki yafe min, ni mai zunubi ne kuma babban mai laifi a gareki, ki yafe min kinji, duk yanda na kai ga son rashin tab'a lafiyarki ya zama dole na d'aukeki na kaiki mataki babba, ina so na kaiki muk'amin da kowace mace ke alfahari tana rik'e da kambunshi a gidanta, kiyi hak'uri kinji yan matana, ki juri wannan rad'ad'in iya na yau ne kawai." Yana fad'a ya had'a goshinsu wuri d'aya ya sake lalubo bakinta, kakkaucewa take dan bata so amma saida ya had'a bakinsu, yana fara hak'arta ta sake zabura ta fashe da kuka tana babbuga damtsenshi, k'in cire bakinshi yayi sai ma ya shiga neman harshenta ido rufe dan yasan in ya barta tsaf zata tashi har yaranshi daga bacci barre kuma Hafsat. Kuka na hawaye da majina babu wanda ba tayi ba, ta yageshi ta cijeshi ta mintsene shi duk da ya k'yaleta, duk yanda yake tausaya mata ba laifi dai sha'aninshi yasha sosai, shi kan shi ya tabbata data matsu, saida ya zo gab da zai kawo ya wani damk'eta ya shiga jijjigata, yana saki ya fad'a kanta inda ita kuma ta shiga sauke numfashi kamar tayi gudu had'e da shashek'ar kuka. Kallonta yake sai gumin kanshi zuwa fuskarshi dake d'iga a jikinta na wahalar da yasha sanda ya shiga yanayin kawo da curarren ruwan dake mararshi, yatsanshi yasa yana zagaya labb'anta a hankali kuma yana cire jikinshi daga na ta jikin, rintse ido take kamar za'a d'auki ranta tana k'amk'ameshi gam, yana cirewa gaba d'aya a tare suka saki wani irin numfashi, ita na wani sabon rad'ad'in da ta ji ya ratsata kamar wacce aka watsawa barkono, shi kuma jin wani iska daya bugeshi sakamakon fitowa daga duniyar d'umi. Yunk'urawa tayi zata tashi zaune ya mayar da ita, d'aukar towel d'inshi yayi ya d'aura kafin ya tsuguna gabanta, hannunta ya rik'o yana kallon fuskarta, kawar da kanta tayi tana shashek'ar kuka, cikin muryar rarrashi yace "Haba yan matan tsohonta, ki kalleni mana." Da k'arfi ta juyo dan ta d'an jujjuya masa baki, sai kuma ta kasa kawai ta shiga sauke numfashi kamar mai cutar asma, cikin rarrashi yace "Shikenan kinji, ya isa haka yi hak'uri." Fashewa tayi da kuka da sauri ya rufe mata baki hankali tashe yana "Shiiiiii! Ryam kar kiyi kuka mana, girma ne fa Allah ya baki da ba kowace mace yake ba wa ba, kada kiyi wa Allah butulci mana ta hanyar zubar da hawayenki, kamata yayi kiyi godiya da Allah ya nuna miki ranar nan, Ryam karki manta fa mata dayawa basa samun gatan da zasu ga ranar nan da idonsu, wasu kuma ba mazajensu dake halilinsu bane suke karb'ar wannan abun mai daraja, kinga ke kuma..." Bai k'arasa fad'a ba ta kalleshi da wani yanayi daya sa gabanshi fad'uwa yaji yarinyar ta bashi tsoro. Dafe gaban goshinshi yayi yana d'an murmushi cikin k'arfin hali yace "Ki yarda dani Ryam gaskiya nake fad'a miki." Cikin shashek'ar kuka ta sake d'auke kanta daga kallonshi tana yatqina fuskarta. Mik'ewa yayi yana tallabarta yace "Muje na taimaka miki to kinji." Kumburo baki tayi amma ba tace k'ala ba har suka shiga ban d'akin, komai dama ya tanada dan haka yana zuwa hannunshi ya d'an fara sakawa a ruwan dake cikin baho, jin zafin ba zai cutar da ita ba yasa shi sakata a nutse, zunbur tayi tana rik'o hannunshi zata tashi a matuk'ar gigice, da sauri ya rik'e ya mayar da ita ta zauna mutsu mutsu ta shiga yi tana girgiza kai alamar rad'ad'i amma ta kasa magana. Durk'usawa yayi yace "Kinga yi hak'uri, idan ba haka ba fa jikinki zaiyi ta ciwo ne." Rintse ido tayi wasu k'walla suka d'aso mata tana cije baki sosai, sake rik'e hannunshi tayi gam ta k'i saki, kallonta yake yana jin k'aunarta na sake shiga zuciyarshi, wani basaraken murmushi ya saki a ranshi yace " *Hak'ik'a tawakallin da nayi ne Allah ya musanya min da alkairi akan abinda nake zargi, tabbas wannan shi ne sakamakon da ubangiji yai min*." Sakin murmushi ya sake yi yana kallonta ido rufe cikin sanyayyar murya yace " *Ina sonki Maryam*." Bud'a ido tayi a hankali ta sauke a kan shi, saida ta ja majina ta d'auke idonta a tsaurare tana kawar da kai, cike da rashin jin dad'in yanayin da yake kallonta ya raunana murya yace "Dan Allah mana ki min magana Ryam." Kallonshi tayi a zuciyarta tace "Kai ne mutum na farko da nake shakkar cizgawa, amma yanzu kai ma lokaci yayi da zaka d'and'ani *sarautar Mimi* ka ji idan da dad'i." Kamar zaiyi kuka ya sake fad'in " *Mahmi*, kada ki yanke min wannan hukuncin yanzu, ki gafarceni kinji." Sunkuyar da kai tayi tana cije baki dan sosai take jin zafi a k'asanta, kallonta yayi ya kalli ruwan da take zaune ciki, zunbur ya mik'e yana fad'in "Oh subhanallah!" Bud'a idonta tayi ta kalli kanta a cikin bahon sai taga yanda zuwan suka canza, a rud'e ta kalleshi ta fashe da kuka amma ta k'i magana, sunkuyawa yayi ya rufe mata baki da yatsarshi yace "Shiru." Tsaf ta had'iye kukanta sai kallonshi da take tana shashek'a, tana kallo ya bud'e wurin magudanar ruwan suka tafi kafin ya zuba mata wasu masu zafi amma ba sosai ba, kyab'e fuska tayi tana kallonshi da ta je tayi kuka saiyaharareta, ganin su ma ruwan sun canza kala ya sak茅 gasgata lallai fa tayi k'ari, amma sai bai fad'a mata ba kawai ya taimaka mata ta fito ya aje mata buta yace tayi wanka, har zai fita a ban d'akin sai kuma ya tsaya ya kalli kan ta. Cike da tuhuma yace "Ban tab'a ganinki da kitso ba, yanzu da kan haka zakiyi wankan tsarki? Taya ruwa zai samu kowane silin gashinki?" Wani irin turo baki tayi gaba ta rufe ido irin fa ba ruwankan nan, cike da gargad'i yace "Dani kike?" Bud'e idon tayi ta girgiza kai alamar a'a, k'wafa yayi ya juya ya fita ita kuma ta fara wankan tana mitar "Ba dai ni ka ma haka ba? Gobe kaf a gidajen jarida sai na buga labarinka, malam ba tausayi bare imani." Tana gama wankan ta fito tana tafiya kamar wacce ta haihu, kayanta ta d'auka ta mayar ta nufi k'ofar fita dan bata ganshi a d'akin ba, had'ewa sukayi a bakin kofar ya kamo hannunta ya dawo da ita, zai zaunar da ita bakin gado tayi tsaye k'erere ta nuna mishi k'ofa da idonta alamar fa fita take so tayi. Ba tare daya kalli fuskarta ba yace "Kin dawo gidanki kenan." Da sauri ta juya ta kalleshi yana tattare zanin gadon, kawar da kai tayi ganin yanda zanin ya b'aci tana cije leb'e. Har ya gama abinda ya ke ya shiga ban d'aki, kuka ta shiga rerawa kmaar wata marainiya tana jin abun duniya duk ya dameta, yana fitowa tsaye ya sameta kamar ta had'iyi tab'arya, yanda take ta share hawaye yasa shi kallonta da kyau yace "Wai ke ba kya gajiya da kuka ne?" Ko kallonshi ba tayi ba bare ta kulashi, ban d'aki ya sake shiga da kayan baccin daya cire mata ita kuma ta zauna bakin gadon dan k'arfin halin ne take, dafe k'ugu tayi tana girgiza kai ta rintse ido, da sauri ta mik'e sakamakon tunawa da yanda abun ya ratsata da farkon nan, gaba d'aya tsigar jikinta ta ji tana tashi saboda tuna wannan abun al'ajabi, Anya kuwa sheikh ne mai shekarun nan? Ita ai ta d'auka zuwa yanzu irin sojan tayi la'asar d'in nan kad'an take iya zungura. Zafin daya k'ara tsikararta yasa ta kuma cije fuska tana matsa k'ugunta, yana fitowa tayi saurin sakin fuskarta kamar babu abinda ke damunta. Daga nan zaune take jin jikinta na wani gab-gab-gab yana rawa, d'an tab'a wuyanta tayi taji masifaffen zafi zazzab'i ya sauko mata, d'ora kanta tayi a cinyarta tayi lak'was abinta, gaba d'aya yanayin jikinta bata jin dad'inshi, abubuwa take ji kawai sabi da bata saba da su ba, fitowarshi daga ban d'akin yasa ta d'ago kanta a hankali amma bata kalleshi ba, gabanta ya durk'usa yana rik'o hannayenta yana kallon fuskarta, cikin rarrashi da tausayi yace "Ryam, ki yi magana kinji, ki ce wani abu dan Allah." Wani huk-huk-huk ta fara yi tana tuk'ak'o amai, da sauri ta mik'e zata nufi hanyar ban d'aki kawai rawar da jikinta keyi da rashin kuzari suka zubar da ita a k'asa warwas tare da dannowar amai, da sauri ya mik'e ya matsa kanta yana furta "Subhanallah! Ryam sannu kinji." A galabaice ta kalleshi duk da bata son yi mishi magana da k'yar ta iya bud'a baki tace "Ka cire min abinda ka saka min a ciki." Da mamaki ya kalleta sai kuma ya saki murmushi yana durk'usawa yace "Ba abinda na saka miki Ryam, watak'ila dan ina tsoho ne shiyasa na k'arar da k'arfi na a yau d'in nan." Kamata yayi zasu shiga ban d'aki amma ya kula k'afafunta sai hard'ewa suke, d'aukarta yayi suka shiga ta kurkure bakinta suka fito, tana kallo ya tsaftace wurin data b'ata kafin ya d'auki wayarshi, saida ya fita a d'akin kafin ya amsa. Kafin Rakiya ta zo gidan mintunan da aka d'auka sai Mimi ta k'arasa gigicewa ta fita hayyacinta, abu ga farar fata lokaci d'aya ta zube tayi fiyat da ita, zazzab'i sosai take ji yana taunar k'asusuwan jikinta ga kuma rad'ad'in da k'asanta keyi har yanzu, ko da Rakiya ta zo Mimi bata san tana kan ta ba tsabar raki da kuma wahala, banda muryar sheikh dake kayar mata da gaba ba abinda kunnuwanta ke ji. Mimi dai da ba allura take so ba, tunda aka kira Rakiya daga asibiti shi da Rakiya dake gaggawa ko ta tafi gidanta ita ma haka sukayi ta rarrashi amma ina, kuma ta k'i magana saidai ta girgiza kai kawai tana share hawaye dan tayi niyya daga yau har gobe sheikh ba zaiji muryarta ba, k'arshe dai Rakiya ce ta kalli sheikh cikin rad'a tace "Sheikh kawai ka rik'e mana ita a mata allurar bacci, dan ba zata tsaya a mata d'inkin nan ba." Saida ya je inda take zaune akan gadon ya zauna shi ma, jawota yayi a jikinshi ya rumgume, tana ganin Rakiya tana gyara tsinin allura ta nemi zillewa a jikinshi, tsam ya matseta a jikinshi hakan ya hanata damar motsawa sai yan k'afafunta kawai sa茂 kuma gunjin kuka, bata d'ago daga jikinshi ba bacci yayi awan gaba da ita, gyara mata kwanciya yayi kafin ya fita ya d'akin ya zauna falo kan kujera, kan shi sadde k'asa yana tunanin yanda yar mitsitsiyar yarinyar nan ta shayar da shi ruwan mamaki, murmushi kawai yake saki tare da cin burika na kyautata mata da kuma fanshe mata ranar ta. Fitowar Rakiya daga d'akin ta sashi mik'ewa ya tarbeta, da kulawa ya tambayeta "Ya take?" Fara'a ta masa tace "Da sauk'i, na mata d'inki sannan na k'ara mata ruwa." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Nagode Rakiya, kiyi hak'uri na saki latin zuwa ga iyalinki kema." Murmushi tayi tace "Ba komai sheikh aikinmu Kenan." Kallon d'akin yayi yace "Ba komai dai yanzu ko?" A ladabce tace "E sheikh, zuwa safe zan sake zuwa da kaina na dubata." Tana tafiya shi ma fita yayi ya siyo kaji ya dawo, alwala ya d'auro ya shinfid'a sallaya ya kabbara sallah, raka'a hud'u yayi masu tsayin gaske a jowace sujada yana godiya ga Allah daya masa wannan kyauta tare da neman gafara akan zargin yarinya da yayi, abun ne shi ma yafi k'arfinshi, so ne ya rufe mishi ido sai kishi yayi tasiri a zuciyarshi, abinda ya faru a ranar dole ya firgita nutsuwarshi ya jefa zuciyarshi a hali na wasi-wasi, bai san gaibu ba bare yasan gaskiya, dan haka kishi ya dinga d'awainiya da shi ya dinga jin kamar wani ya rigashi. *04:00* k'arar agogo tasa ta motsawa dan baccin ya saki idonta, da k'yar ta bud'a idonta da suka mata nauyi ta kalli rufin d'akin, dake harda allurar kashe jiki ta mata sai lokacin ta ji wani azababben ciwo ya taso mata na zafin d'inki da kuma musababbin d'inkin, yunk'urawa tayi ta tashi zaune tana sakin hawayen da ita kanta bata so suka taho mata ba, sauke idonta tayi akan sheikh dake gefenta zaune akan sallaya. Da sauri ya taso ya durk'usa yana fad'in "Ryam kin farka? Sannu kinji." K'asa tayi da idonta ta kasa kallonshi kuma ba tace komai ba, rik'o hannunta yayi tare da kai d'aya hannun a wiyanta, jikinta da zafi har yanzu sosai tab'a goshinta yayi shi ma dai da zafi alamar ciwon kai, wani huci yayi na rashin jin dad'in halin daya sa yar mutane a ciki, sai ya tuna sanda ta shigo d'in nan tana bashi labarin daya tabbatar k'irk'irarshi tayi. Mik'ewa yayi yana fad'in "Bari na taimaka miki ki shiga ban d'aki kiyi alwala, lokacin sallah subah tayi." Hannayenshi ya kai zai kamo na ta ta mak'ale kafad'a alamar um um, turo baki tayi gaba kan ta sadde, cikin rarrashi yace "Haba mana Ryam, muje ko?" Sake mak'ale kafad'a tayi alamar dai um um, tsaye yayi yana kallonta yana sauke numfashi, nufa hanyar fita yayi yace "Bari to na kawo miki abu ki ci sa茂 ki sha magani." Tana kallo har ya fita a d'akin, jim kad'an ya dawo d'auke da faranti k'arami, ajewa yayi kusanta ya zauna yana d'an yago naman kazar yace "Yawwa to bud'a bakin." Sake mak'ale kafad'a tayi har da fad'in "Um um." Waro ido yayi yace "Shi ma ba zaki ci ba?" Zuba mishi ido tayi tana kallo, cikin rarrashi yace "Kinga Ryam kiyi sauri ki ci, idan kika gama akwai abinda zan baki kinji." Kallon da take masa sai ya fara jin ya tsargu dan kamar macijiyar daka kashewa miji ce a gaban idonta, sunkuyar da kan shi yayi yace "Fad'a min me kike so? Ya kike so nayi Ryam? Har yanzu ban ji muryarki ba, kina tunanin hakan abu mai sauk'i ne a gareni?" Shiru ta masa hakan yasa shi d'ago kai ya kalleta, da sauri ta sauke na ta idon k'asa tana kallon farantin kazar (uwata ba'a wulakanta kazi fa馃槦) kofin madar daya zubo ya d'auka zai kai bakinta shi ma ta kawar da kai, kamar zai fashe da kuka ya kalleta yace "A'a, wai ya kike so dani ne? Ryam kin k'i ci kin k'i sha kuma kin k'i magana." Bud'e baki tayi da iya k'arfinta ta fashe da kuka, hankali tashe ya aje kofin hannunshi ya tallabo fuskarta yana fad'in "... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:57 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *42* Bud'e bakinta tayi da iya k'arfinta ta fashe da kuka, hankali tashe ya aje kofin hannunshi ya tallabo fuskarta yana fad'in "" A'a Mimi, me na miki kuma daga magana? Kinga idan ba zaki sha ba to shikenan, amma daina kukan kinji." Hannaye duka biyu ta rattab'a a fuska tana murzar ido tana ci gaba da kukanta, zaune yayi da kyau kusanta ya jawota ya d'ora kanta a k'irjinshi yana shafa kanta yana fad'in "Shikenan to, haba yan matan tsohonta, so kike ace raguwa ce ke a miki dariya?" Wata irin shashek'a ta shiga yi da gangan kamar zata had'e zuciya, sake tallabo fuskarta yayi ya marairaice yace "Haba Ryam, so kike sai kin nunawa duniya yau sheikh Abdul Waheed ya zo gareki? Ki daina mana kinji, ya isa haka kar kanki yayi ciwo fa." A tak'aice dai yanda sheikh yaga wannan dare haka ya wayi gari, rarrashin duniya ba wanda bai mata ba amma ina ta k'i ji, kuma gashu ba lokacin jawo aya ko hadisi bane bare ya tab'osu ko ta saurara, a daddafe yayi sallah ya dawo kan ta ya zauna yana kallonta, idonta sun kumbura sunyi ja har fuskarta ta canza. Wani dogon numfashi ya sauke yana jin tausayinta na k'ara tsumashi, kukan da take sam bai d'aukeshi na tab'ara ba saina hak'ik'anin gaskiya, kukan shagwab'ar ya mishi yanda yake buk'ata, ya so a ce iya su kad'ai ne a gidan nan da sai ya nuna mata k'arshen zalamarta, zai biye mata ya riritata ya goyata a bayanshi ya mata dokin wuya yanda dole tayi shiru, da zai aje komai na shi ne ya shiga faranta mata rai har sai yaga hak'orinta sun bayyana da sunan dariya. Tsaf take k'are masa kallo daga rufe fuskarta daa tayi da hannaye tana murzawa wai ita me kuka, sai yanzu ne ta kula ashe fa ustazun nan d'an gaye ne, askin fa kad'an ne ya banbantashi da irin na yan zamani, kawai dai shi ya aske duguzar ne sosai yanda ba'a barta a doron kan ba, amma har wani gyaran fuska yanda gemun ya masa sai ta ga ya birgeta yau kam, ga jallabiyar data fito da surarshi sosai. Hannayen na ta daya kamo yasa ta rintse ido tana shashek'a, cikin sanyin murya yace "Ryam, zaki sha chocolat?" Girgiza kai tayi alamar a'a, d'an jim yayi yana kallon gefe alamar tunani sai kuma yace "Zaki sha madara?" Sake girgiza kai tayi alamar a'a, da sauri yace "Zaki sha ice cream?" Girgiza kai ta sake yi alamar a'a, d'orawa yayi da "To fad'a min me kike so?" K'ura masa ido tayi da k'yar ta bud'i bakinta murya can k'asa tace "Gidanmu nake so." Tsura mata ido shi ma yayi, a take a shiga tunanin ta ya zai kaita gidansu a halin da take cikin nan? Kowa yasan ya zo wa wannan yar yarinyar? A gaskiya yana jin kunya kula ba zai iya ba, shi fa Hafsat ma baya so ta samesu a halin nan, gashi kuma ba zai iya kaita wajen Hajia ba dan kamar akwai cin fuska ma, duk da uwa take gareshi amma ai 'yarta yake aure, haihuwa kuma ba wasa bace, tun suna kawaici suna kawar da kai wata rana shaid'an da zai fara zugasu da saka musu tunani marar kyau. Rik'o hannayenta yayi da kyau yana kallon fuskarta yace "Ryam, ba zamu je gidanku ba gaskiya, amma idan kina so zamu je wani wuri, na tabbata zai k'ayatar dake, kina so?" Zuba mishi ido tayi kamar bata gane yarenshi, lumshe ido yayi alamar rok'o yace "Dan Allah Ryam." Rufe idonta tayi alamar ba ma zata kula shi ba kenan, mik'ewa yayi tsaye ya daddage ya daka mata tsawar data saka ta zabura ta bud'a ido sanda yake fad'in "Dake nake magana malama kina min shiru." Kyab'e baki tayi zata fashe da kuka ya nunota da yatsa ya sunkuyo daf da ita yace "Kika min kukan nan saina kuma zazzabga miki bulalar da zata fahimtar dake me nake nufi." Tsaf ta had'e kuka tayi k'asa da kanta, nuna mata k'ofar ban d'aki yayi yace "Maza je kiyi wanka kiyi alwala kiyi sallah." Jiki na kakkarwa ta shiga saukowa daga kan gadon, saidai allurar da har yanzu bata gama sakin jikinta yasa k'afafunta kasa d'aukarta, shirin fad'uwar da tayi yasa shi azamar tallabota jikinshi, cak ya d'auketa ya nufi ban d'akin da ita yana kallon fuskarta fuskarshi a had'e yace "Yarinya sai taurin kai, bakya gane magana cikin sauk'i." Tsayar da ita yayi ya shiga cire mata kayan jikinta, nok'ewa ta shiga yi ita ma hakan yasa shi d'aga kai ya kalleta yace "Miye na kunyar kuma? Ba mun zama d'aya ba?" D'auke kanta tayi tana kumburo baki, murmushi yayi yace "Shikenan bari ki gani, aidai zakiyi k'orafin na kalleki babu kayana ne ko? To bari muyi wankan a tare." Kar-kar-kar! Jikinta ya fara ta shiga taka k'afafunta zata fita a ban d'akin, rik'ota yayi ya had'ata da k'irjinshi yana kallon fuskarta yace "To miye a ciki? Ni ba naki bane?" Ko kallonshi ba tayi ba ta shiga sinne kan ta k'asa, b'alle botir d'in rigar yayi tare da tattarota daga k'asa yayi sama da ita, yanda ta ganta kwance a k'irjinshi da babu riga sai kwantaccen bak'in gashin daya kusa mamaye knirjin mai sulb'in gaske kamar na kan shi yasa ta saurin juya baya, hakan ya bashi damar k'arasa cire...馃槑 ya jawota ya had'a da jikinshi, yanda yaji jikinta ya fara d'aukar zafi da gaske ga rawar da yake mata yasa shi sakin murmushi ya d'ora hab'arshi a kafad'arta cikin kunne ya rad'a mata "Ryam ga ki da tsoro amma kuma ke ma kina bada tsoro." Kakkaucewa ta shiga yi saboda kayan jikinta daya fara shirin cire mata, bai bata damar matsawa nesa da shi ba saida ya rabata da kayanta, yanda jikinsu ke gugar na juna tana jin duk wata hallita ta bawan Allahn nan a fatar jikinta sai ta nemi numfashi ta rasa, gaba d'aya ta sarewa lamarin mutumin ko ta ce lamarin maza. Duk girmanshi, duk shekarunshi, duk matsayinshi yanzu nan ya aje su gefe har ya tsaya gabanta babu kaya zasuyi wanka? Tunda taja numfashinta sama bata maido shi ba ita dai ta k'ame wuri d'aya ta rintse idonta dan b芒 zata iya kallonshi ba. Sheikh ko a jikinshi, wanka yake musu sosai cikin nutsuwa tare da wasa da ita, Mimi dai abun jin shi take wani iri, ita dake burin d'an k'aramin mijinta suyi wanka tare sai gashi yau old man ne ke mata wanka kamar baby. Tana jin sanda ya kashe panpon ruwan suka tsaya, jim kad'an taji yana saka mata rigar wanka, kamo hannunta yayi suka fara takawa tana jin k'asanta na d'an mata zuzar zaren d'inkin nan hakan kuma na k'ara mata rad'ad'i. Kan kujera ya zzunar da ita gaban madubi, mai ya d'auka ya durk'usa ya fara shafa mata man, kallonshi take yanda har yanzu towel ne a k'ugunshi, sam sai yake mata kamar ba tsoho ba, yanda yake d'aukarta da yanda yake sarrafa jikinshi ba alamar manyanta irin ta tsofaffin da zaka ga suna fama da ciwon baya k'afafu da sauransu. Yanda take kallonshi idonta bud'e yasa shi sakin murmushi yace "Inna Issa har yanzu ba zaki min magana ba." K'in d'auke idonta tayi a kan shi, d'an murmushi kawai ya sake saki ya ci gaba da murza mata mai, yana gamawa doguwar riga abaya ya d'auko a cikin kayan daya k'ara zuba mata na ban mamaki, pant ya d'auko da bras ya sake durk'usawa ya zura mata k'afafun, kamata yayi ta mik'e zai k'arasa saka mata sai kuma ya kalleta, d'an sosa kai yayi da irin alamar jin kunya yace "Yan matan tsohonta, anya kuwa wannan zai isheki? Ni fa kallon baby nake miki." D'auke idonta tayi daga kan shi ta k'arasa saka wandon, tam ya mata alamun dai ya matseta sosai, d'aukar bras d'in tayi ta saka ita ma haka ta mata kip, d'aukar rigar tayi ta saka da sauri ya zaunar da ita kan kujerar, macaji ya d'auka ya fara caje mata gashinta, tsaf ya d'aure mata shi da mad'auri sannan ya d'auki kallabin rigar ya fara yane mata kan cike da k'warewa, yana gama mata ya tallabo fuskarta ya sumbaci goshinta sannan ya nuna mata sallaya yace "Kiyi sallah, zan je na saka kaya nima." Takawa tayi ta k'arasa gaban sallayar, tana ganin fitarshi a d'akin tayi saurin cire pant d'in nan dan yana tab'ata a jikinta sosai tana jin zafi saboda d'inkin da aka mata, sallah ta kabbara shi kuma ya shiga d'akinshi dake nan b'angarenta dan shiryawa. *Asa-Ma'u* Tunda Asma'u ta zauna jiran Mimi ta ga ba alamarta sai kawai ta ma Hafsat sallama suka taf tare da Kabiru, ita ma suna zuwa gidan suka had'e da Asas, ita kanta sai ta ji kunya da suka had'u da shi ba'a gida ba, a d'arare ta bishi suka nufi na su gidan suma. A daren kam tasha abubuwa da dama, kunya, fad'uwar gaba, farin ciki da kuma bak'ar wahala, dan kuwa Asas ya nuna mata ya samu lafiya, sun sha amarci sosai da kuma soyayya har garin Allah ya waye, daga wajen Hajia kawai yasa aka kawo musu abinci suna ci ya dunk'ule matarshi a bargo suka shiga ramuwar bacci. Sake matseta yayi a jikinshi yace "Husna." A hankali ta amsa da "Na'am." Cikin taushin murya yace "Kina so na?" Sinne kanta tayi a k'irjinshi tana d'an shafa cikinshi da hannunta ke kai tana murmushi, cikin shafa bayanta yace "Ina jinki mana, ko ba kya so na?" Girgiza kai tayi a hankali tace "Ni ban ce ba." "To me kika ce kenan?" Ya fad'a kai tsaye, cike da jin kunya tana b'oye fuskarta a jikinshi tace "Taya zan ce bana son mijina wanda a yanzu ya zama sirrina, a yanzu fa babu wani abu daya mana shamaki ni da kai, ko na so ka ko na k'i ka ka riga daka zama wani b'angare na jikina." Matseta yayi sosai ya sumbaci kanta cikin dadad'an murya yace "Ina sonki *Asmy* na, ina sonki sosai, Allah barmu tare." Cike da jin ya k'arawa kanta girma da farin ciki ta matseshi ita ma cike da jin kunya murya k'asa k'asa tace "Ni ma haka." D'an tsakulkuli ya mata yana dariya yace "Ke ma me? Sai kin fad'a fa malama ko nima na dawo da kayata na rik'e." Cikin bille bille ta shiga k'yalk'yala dariya tana fad'in "Nima haka, na fad'a to na fad'a." Dakatawa yayi yace "Me kika fad'a to? Fad'i ko kuma na sake juyewa a kan ki yanzun nan, dama ba isata kikayi ba dan naji kin k'ara wani irin dad'i." Dukanshi tayi a k'irji cike da kunya tace "Kai wallahi, haba dai." Cikin dariya yace "Gaskiya na fad'a ai, na tabbata shirya min kanki kikayi kafin dawowata." Girgiza kai tayi tace "Ni ba abinda nayi." "Kin tabbata?" Ya tambaya yana lek'an fuskarta, jinjina kai tayi alamar eh, murmushi yayi yace "To yanzu fad'a min na ji, ke ma kina so na?" Turo baki tayi tace "To wai me yasa ka damu da sai na fad'a maka nima? Ka yarda da abinda na fad'a maka mana." Mak'ale kafad'a yayi yace "Um um! Kawai ki fad'a min Husna ko nayi kuka." Waro ido tayi ta kalleshi da mamaki yanda kam duk ya kyab'e fuska shi shagwab'abb'e, kunya tasa ta rufe fuska tace "To ni ma ina sonka." Sake k'amk'ameta yayi yana murmushi yace "Ko ke fa, har na ji dad'i." Cikin farin ciki suka samu baccinsu a nutse suna k'amk'ame da juna kamar dama can asali masoya ne. *Mim-Sheikh* Cikin wata dakakkiyar shadda ya shigo d'akin wacce ta sa shi bayyana sak a angonshi, fara ce shaddar ga rigar daya d'ora irin ta malamai ga hula da takalmi k'afa ciki, shagala tayi da kallonshi dan gaskiya da zata iya bud'a baki a wannan lokacin tayi magana to zata ce "Kayi kyau." Ne, amma data ga yana mata murmushi saita d'aure fuska har saida ya tsaya gabanta yace "Zamu iya tafiya?" Mik'ewa kawai tayi ta nufi hanyar fita, rik'e hannunta yayi suka kalli juna, ba alamar sakin fuska yace "Bana son jin shirun nan idan muka fita, zan d'auki wannan shirun ne kawai saboda ni na ja, amma iyalina ki girmama min su ta hanyar bud'a baki kiyi magana idan sun miki, Hafsat a gaba take da ke, karki jira sai ta gaisheki kafin ki gaisheta." Shafa kumatunta yayi yace "Kin gane?" Sunkuyar da idonta tayi saboda k'wallar da taji sun cika mata ido, tallabo fuskarta ya sake yi cikin sanyin murya yace "Kiyi hak'uri kinji, nayi alk'awari na yau kawai zan baki lokaci na gaba d'aya, zan sa ki fara tunanin tsohonki a zuciyarki, sannan nayi alk'awarin saka murmushi a fuskarki yau d'in nan." Kama hannunta yayi suka shiga takawa a nutse, ta k'ofar waje suka fita kafin ya zagaya ta k'ofar shiga falon Hafsat, saida ya d'an k'wank'wasa sau uku kafin ya shiga da sallama a bakinshi yana sakin hannun Mimi, yaran dake zaune dukansu falo suna karatu ne suka juya suna kallonshi da amsa sallamarshi, da k'yar da lahaula ta cira labb'anta ta furta "Assalama alaikum." Ido suka fara zuba mata da d'an mamakin nan ta kwana ko me? Sai kuma suka amsa mata sallamar suna gaishe da mahaifinsu a ladabce, cikin k'arfin hali Mimi ta kallesu da fara'a tace "Karatu ake." Kallonta suka sake yi dukansu sai Munzeer dake k'arami daya washe mata baki yace "E aunty." Sheikh ne ya kalleshi yace "Ina mamanku?" Nuna d'akinta yayi yace "Tana ciki." Hanyar nufa d'akin Hafsat yayi sai kuma ya kula da wani kallo da Aisha da Heezam suka rakashi kallo ne mai tattare da "Abienmu me kake nufi? Yarinyar nan anan ta kwana? D'aki guda kai da ita?" Sai kawai ya ji ya tsargi kansa, saidai baiji kunya ba dan ita ma matarsa ce, halalinsa ce ba kuma haramun ya aikata da ita ba. Tsaye yayi dan sai yake ganin kamar zasu iya dakuwa da ita idan ya matsa, Mimi kuma da tsayuwar ta gundureta zaune tayi a kan kujera tana kallonsu ita ma. Zai sake nufa d'akin Hafsat sai gata ta fito da hijab d'inta a jikinta, duk zuba mata ido sukayi har ta k'araso da sakin fuska tana kawar da komai daga ranta tana fad'in "Mimi da safe haka aka taso ki? Amma dai sheikh ka shiga lokacinta." Duk murmushi sukayi sai Mimi data sunkuyar da kai tace "Ina kwana aunty." Da fara'a tace "Lafiya lau Mimi, antashi lafiya?" Da kunya ta amsa da "Lafiya lau." D'orawa tayi da "Ya kwanan bak'unta kuma?" D'an murmushin yak'e kawai tayi sai muryar Munzeer da suka ji yace "Amie gidanmu aunty ta kwana?" Da fara'a Hafsat ta kalkeshi tace "E." Aswan kam kamar da gangan kamar sub'utar baki sai cewa yayi "A b'angaren Abie ta kwana?" Kallonshi duk sukayi sai Mimi da taji kamar ta k'urma ihu, a tsawace Hafsat ta kalleshi tace "Aswan wace maganar banza ce wannan? Ina ruwanka to?" A tsorace ya kalli Hafsat yace "Amie kiyi hak'uri dan Allah, ba zan sake ba." D'auke kanta tayi ta kalli sheikh daya tsurawa Aswan ido yana tunanin dole yayi wani abu gaskiya, Aisha dake mace zai matsar da ita dan za'a fi samun matsala da ita saboda mace ce, mazan kuma dama dai lokacin karatunsu yafi yawa akan lokacinsu na zama gida, dan haka zaiyi k'ok'ari yaga raini bai shiga tsakaninsu da matarshi ba. Kallonta sheikh yayi yana k'ak'aro murmushi yace "Manga kin tashi lafiya?" Da fara'a tace "Lafiya lau, antashi lafiya?" Da fara'a shi ma ya amsa da "Lafiya lau." A ladabce tace "Ya gajiya kuma?" Kashe mata ido yayi yana murmushi amma bai ce komai ba, girgiza kai tayi tana murmushi ita ma ta d'auke idonta daga kanshi, d'orawa yayi da fad'in "Manga zamu fita da yarinyar nan mu dawo, ba wara matsala?" Murmushi ta fad'ad'a tace "Ba matsalar komai sheikh, Allah ya tsare hanya, sai kun dawo." Mik'ewa Mimi tayi tana d'an cije baki, kallonta Hafsat tayi tana sakin murmishi tace "A dawo lafiya?" Da murmushi ita ma ta amsa da "Allah yasa, mun gode." Gaba Mimi tayi sheikh ya ma yaran addu'a kamar yanda ya saba kafin ya bi bayanta yana duba agogon hannunshi ta azurfa data nuna k'arfe *06:20* na safe, da kanshi ya bud'e mata gaban motar ta zauna ya rufe kafin ya zagaya ya shiga suka bar gidan. *Sorry mutane na, wlh gaba d'aya ne aka d'auke mana network.* *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:57 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *43* Wani k'ayataccen gida ya sauketa da gaba d'ayanshi bai wuce zaman mace d'aya, tun wajen gidan take kallo kamar wata bak'auya, komai na gidan sai taji ya birgeta daga tsarin gidan zuwa kayan cikinshi, a matsakaicin falonta zaunatana kallo ya shiga ciki, ta d'an jima zaune kafin ta ji bud'e k'ofa alamar zai fito. Sunkuyar da kanta tayi saida ta ji shi tsaye a kan ta yana fad'in "Ryam me zaki ci na dafa miki?" Da sauri ta d'aga kanta ta kalleshi jin wai yace ya dafa mata, k'walalo ido tayi da matsanancin mamakin ganin shi da k'ananan kaya, riga da wando masu kamar na sport kamar kuma na bacci, amma irin kayan da yan zamani har fita suke dasu idan suka saka, wani irin kyau daya mata da kayan yasa ta saurin had'e mamakinta ta mayar da kanta k'asa a ranta tana fad'in "Oh Allah, wai me ye haka? Shi ma dai d'an duniya ne ashe." Gaban tv ya k'arasa ya kunna mata wani caset naa wa'azin Hafsat wanda tayi shi ne lokacin auren wata daga cikin d'alibanta, dake magana ce tsantsa akan zamantakewar aure shiyasa ya kunna mata shi, dawowa yayi gabanta ya sunkuya ya rik'o hannayenta yace "Ryam, ni ne ba zaki ma magana ba?" Lumshe ido tayi alamar eh, marairaicewa yayi yace "Saboda me? Dan na kaiki mataki babba?" Jinjina kai tayi alamar e, numfashi ya sauke yana murmushi yace "To na ji kiyi hak'uri, yanzu fad'a min me zaki ci na kawo miki, idan kin gama kinga ke ma saiki rama ko? Haka ya miki?" Girgiza kai tayi tana kawar da kan ta, wata ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mik'e zai shiga k'aramar madafar, hannunshi da har yanzu bai k'arasa sakin na ta ba tayi saurin rik'ewa gam, juyowa yayi yana kallonta, cikin had'e fuska ta kawar da kai tace "Ni gida nake so ka kaini." Sake sunkuyawa yayi yana kallon fuskarta yace "Me zakiyi a gida idan na kaiki Ryam? Ba kya jin kunyar Mama ne ke?" Turo baki tayi gaba cikin shagwab'a tace "To ai ba zan fad'a mata komai ba." Murmushi yayi ya girgiza kai yace "Ryam, ko ni dake namiji idan na kalli mace ina iya fahimtar halin da take ciki, bare kuma uwa mace, dole mama na kallonki zata fahimci me ya faru da ke? Ko kina so ki ce min Mama bata tab'a saka miki ido bane?" Jim tayi kamar mai tunani hakan yasa shi fad'in "Idan kina so zan kira miki Abbanki sai na baki shi ku gaisa." Had'e yawu tayi sai kuma ta jinjina kai alamar to, murmushi yayi na jin dad'i ya shafi kuncinta yana fad'in "Yarinyar kirki kenan." Mik'ewa yayi yana zame hannunshi a nata yace "Ina zuwa." D'akin daya shiga ya koma jim kad'an ya dawo da waya a hannu, yana zuwa ya mik'a mata yace "Gashi sai ki kira." Karb'a tayi shi kuma har ya juya sai kuma ya tsaya yace "Fad'a mine zaki ci to?" Sake turo baki tayi gaba ta nok'e kai tace "Ni bana cin girkin maza, mazan ma wanda basu da k'warewa." Fad'owa yayi kan kujerar ya mata rumfa kamar zai tausheta yana mata wani shu'umin kallo, had'ewa tayi a jikin kujerar tana sinne kan ta, cikin wani irin salo yace "Ni ne ban da k'warewar? Fad'i abinda kike so na girka miki idan ba tsoro ba." Cikin sissine kai tace "Indomie." Wani murmishin gefen labb'a yayi yace "Taliyar yara zaki ce, to kazarki kuma fa?" D'an d'aga idonta tayi ta kalleshi da alamar tambaya, d'aga mata gira yayi yace "E, kazar amarcinki fa? Na kawo miki ne ki ci?" Shiru tayi sai turo baki da take yi gaba, caraf ya damk'i leb'enta na k'asa yasa a bakinshi ya tsotsa kamar wata alawa, saida ya ja leb'en kamar zai cirashi ya sakar mata baki yana fad'in "Bani minti biyar yan matan tsohonta." Yana fad'a ya shige madafar, da kallo ta rakashi tana jin kanta na neman fashewa saboda abubuwan da tsohon ke zuwa mata da su, a gaskiya sai ta ga ya koma mata wani sharaf da shi a cikin k'ananan kayan, sai ta rantse kamar bai tab'a kyau irin na yanzu ba, ko kuma dai bata saba ganinshi da irin kayan bane? Wayar dake hannunta ta shiga saka lambar Abba, tsaf lambar ta fito da sunan *vieux* (tsoho), bata san lokacin data mik'e tsaye ba ta dafe k'ugu tace "Lallai ma!" Ai da sauri tsabar jaraba ta nufi madafar, tana isa k'ofar a bud'e take yana tsaye yanaa aiki kam tuk'uru, cike da yarinta ta nuna wayar tace "Yanzu Abban na wa ne tsoho?" Juyowa yayi yana kallonta da mamaki sai kuma ya d'aga kafad'a yace "Gare ni na ji." Cikin turo baki tace "Kamar ya gareni? Ni fa Abba nake cewa." Juyowa yayi da kyau yace "Ranar aurenmu na ji kince tsoho ne, shiyasa ni ma na rik'e a kai na." Shiru tayi alamar tunani, sai yanzu ne ta tuna sanda tace ta so nemawa Abbanta auren Asma'u saboda nagartarta, tab'e baki tayi ta murgud'ashi tace "Ai dai Allah bai ce hakanan ba, ina laifin ma ka saka mishi abokina tunda dai ai na ga ka girmeshi." Yanda take maganar ita fa iya gaskiyarta take fad'a, takowa ya fara yi tare da aje ledar indomie hannunshi, jawo k'ugunta yayi ya had'a da na shi yana kallon fuskarta yace "Ya kike so ayi yanzu *sarauniyata*?" Cike da sangarta tace "Kawai ka saka mishi aboki." Karb'ar wayar yayi yana fad'in "Angama yan matan tsohonta." Tana kallo ya shiga daddana wayar na yan dak'ik'u kafin ya nuna mata yace "Haka yayi?" Dubawa tayi ta ga ya saka aboki, murmushi tayi ba tare da saninta ba tace "Ko kai fa." Mik'a mata wayar yayi ta juya zata fita yana binta da kallo, wato indai ka auri yarinya dole ka zama yaro wani lokaacin kuma ka zama mai raino. Tana daf da fita kuma ta tsaya ta juyo irin da mamakin nan tace "Amma kuma ai sirikinka ne, ya zaka sakawa lambarshi sunan aboki?" Numfashi ya ja yace "Bai yi ba shi ma?" Marairaicewa tayi tace "Haka nake tunani." Murmushi yayi yace "Yanzu ki fara kiranshi ku gaisa, kafin ki gama wayar zan tayaki tunanin sunan da zamu saka, hakan yayi?" Jinjina kai tayi alamar e, fita tayi shi ma ya juya ya ci gaba da aikinshi yana tunanin sunan da zai saka ma lambar nan ya huta, dan alamu na nuna zai sha matsi akan sunan lamba kawai. Zaune tayi akan kujera ta d'ora kafafunta sama ta cire kallabin rigar abaya ta aje gefe, tana jin tana ringin da sauri aka d'aga Abba na fad'in "Assalama alaikum akaramakallah." Dariya tayi cikin ladabi tace "Wa'alaikum salam, Abba ni ce fa, Mimi." Kamar a d'an tsorace yace "Mimi? Ke me kike da wayar sheikh yanzu da sassafen nan?" Turo baki tayi tace "Abba ina kwana?" A dak'ile yace "Lafiya lau." Jin bai k'ara da komai ba yasa tace "Abba ina Mama? Ku bani ita." Muryarshi ta ji yana fad'in "Rabi'a karb'i nan, uwata ce yanzu ta kira da lambar sheikh?" Jim kad'an ta ji Mama a dak'ile ita ma tace "Ina jin ki?" Numfashi ta sauke tace "Mama ina kwana?" "Lafiya lau." Ta fad'a a tak'aice, cikin sanyin murya tace "Mama ina so na je gida wajenki, dan Allah Mama ki ce na zo kinji, bana da lafiya Mama ina son ganinki." Shiru Mama tayi tana nazarin duka maganganunta, can daga bisani ta nisa tace "Mimi, yanzu ke fa ba yarinya bace, ina so na ga kin aje wannan shirmen kin rungumi sabuwar rayuwarki, ba k'aramin mutum kike aure ba fa, Mimi a yanzu idon jama'a dayawa zai sake hawa kan ki ne da son ganin kalar damun da zaki wa ta ki rayuwar ta yanzu, ki nutsu ki kwantar da hankalinki, ajin nan dana sanki dashi da kuma tsafta, iya kwalliya da iya girki, Mimi na sanki da iya zama da mutane, na tabbata indai a b'angaren ladabi ne da girmama babba ba zaki samu ta biyu ba, ya kamata kiyi anfani da damarki kinji, sannan da kike maganar baki da lafiya, ya kamata kisan wacece ke, baki da k'anwa ko aunty da zasu iya taimaka miki a wasu abubuwan, tun yanzu ki fara koyon yanda zaki taimakawa kanki idan buk'atar hakan ta tashi, dan akwai gurin da ko giyar wake na sha ba zan iya tunkara ba da sunan taimaka miki, kin fahimta?" Mimi da jikinta ya gama sanyi wata ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi kafin tace "Na fahimta Mama, nagode." A takaice tace "Ba komai, ki kula da kanki." Saida ta had'e wasu hawaye da suka taho mata kafin tace "To Mama." A hankali ta kashe wayar tana sako da hawayen na jin zafin rashin mataimaki a rayuwarta, lallai zatayi kamar yanda Mama ta fad'a, zata koyi kula da kanta sannan ta fara koyon yaanda zata shanye damuwarta ita kad'ai, bugu da k'ari zata koyi yanda zata iya farantawa mijinta rai ita ma. Dan maganganun Mama ba iya wannan k'arfin gwiwar kawai suka k'ara mata ba, har da na d'amarar zama da sheikh ma, zata zauna da shi ta masa biyayya ta masa ladabi, saidai b芒 hakan na nufi ta zama sakara bane a gidan miji, kasancewarshi tsohon daya haifeta ba shi zai sa ta kwanta ya jata a k'asa ba, haka ma matarshi kasancesarta wacce ta haifi kamarta ba zata d'auki wani abun daga gareta ba, saidai ta yarda zata mata ladabi ta kuma bita sau da k'afa, kuma ta yarda ko a wayo ne zata iya wanketa ta shanye, dan haka tasan ba zata kara da ita ba ta kowane fanni, amma ita ma zatayi iya bakin k'ok'arinta. Aje wayar tayi gefe ta gyara zamanta sosai tana kallon tvn, ta jima zaunen kafin ya fito hannunshi d'auke da wani k'aramin tangaren mai kama da kwano, akan table d'in tsakiyar ya aje tare da d'auko table d'in gaba d'aya ya dire a gabanta yana fad'in "Oya Hajia, ga indomienki." Kallonshi tayi da girmamawa tace "Sannu da aiki." Gefenta ya zauna yana murmushi, cokali mai yatsu ya d'auka ya saka a ciki ya tallabe kwanon a tafin hannunshi, d'ibowa yayi ya nufi bakinta yana fad'in "Bismillah." Cike da kunya ta bud'a bakinta ta karb'a, jim tayi tana d'an taunawa a hankali tana son tantance abinda take ji, k'ura mata ido yayi yana murmushi yace "To ya kika ji?" D'aga gira tayi ta kashe masa ido d'aya tace "Ba laifi, dama ka iya girki ne haka?" Dariya yayi yace "Hakan na nufin na birgeki ta wannan fannin?" Sunkuyar da kai tayi alamar kunya, sake d'ibowa yayi ya ci gaba da bata a nutse tana karb'a, tas ta cinye dan yunwa take ji dama kuma shi ma bai barta ba saida ta cinye, kakkaurar madara ya bata ta sha sannan ya b'allo maganin da Rakiya ta bayar yace "Yawwa yan matan tsohonta, yanzu wannan zaki sha sai ki samu bacci ko?" Marairaicewa tayi tace "Abdul bana son magani wallahi, kaga dai wannan abubuwan biyu bana son su ko kad'an." Kallon tuhuma ya mata yace "Menene su?" Cikin turo baki tace "Allura da magani." Wata yar harara ya mata yace "Da duka kuma? Kin manta kin ce ba kya son duka." Da sauri tace "E hakane, da duka." Girgiza kai yayi yace "To yanzu fad'a min, idan na jik'a miki maganin zaki sha?" Kyab'e fuska tayi irin kamar zatayi amai tace "Tirrrrr! Amai zanyi." Matsawa yayi daf da ita yace "To kinga bari kiga dubarar da zamuyi." Gyara maganin yayi a yatsunshi biyu yace "Bud'e bakinki ki d'aga kan ki saiki rufe idonki sosai." Had'e yawu tayi sannan ta rintse ido ta bud'e bakin kamar yanda yace, bata ankara ba taji maganin can k'asan mak'oshinta, kafin tayi wani yunk'uri kuma ya kora mata ruwa tare da saka yatsu biyu ya rufe k'ofofin hancinta, hakan ya tilasta mata had'e maganin da ruwan tana sauko da kanta k'asa, kallonshi tayi tana zazzaro ido shi kuma yana murmushi yace "Gashi har kin shanye." Waro ido ta sake yi tace "Da gaske?" Jinjina mata kai yayi, cike da mamaki tace "Duka biyun?" Sake jinjina mata kai yayi alamar e, dafe k'irji tayi tana dariya tace "Yau ni na sha magani haka, kai Allah nagode maka." Dariya yayi ya jawota jikinshi ya kwantar yana shafata yace "Kinga yanzu haka zamu dinga shan maganin kenan." Sunkuyar da kanta tayi k'asa ba tace komai ba, gyara zamanshi yayi ya kwanta akan kujerar tana jikinshi ita ma, cikin sanyin murya yace "Ryam, kin yarda ina sonki?" Shiru tayi kamar ba zata amsa ba sai kuma ta numfasa tace "Ban yarda ba." Da sauri ya d'agota a jikinshi yana kallon fuskarta da mamaki da kuma tsoro yace "Baki yarda ba Ryam? Kina ganin zan miki k'arya ne." Tab'e baki tayi ta d'auke kanta daga kan shi, cikin tashin hankali da jin zuciyarshi na bugawa ba daidai ba ya cabko wuyanta ya juyo da kallonta kan shi yana fad'in "Dake nake magana kin wani shareni, fad'a min na ji mana, k'arya na fad'a miki kenan?" Fizge kanta tayi ta mik'e tsaye tana fad'in "Kawai ni na ce ban yarda ba." Shi ma tsaaye ya mik'e ya jawota gaba d'aya jikinshi yana kallon fuskarta yace "Me yasa Ryam? Dan kin tabbatar ina son ki ne kike min haka?" Mutsu mutsu ta fara na son k'wacewa tana fad'in "Ba so na kake tsakani da Allah ba, jikina kake so Abdul." Da wani matsiyacin mamaki ya kalleta yana sakinta gaba d'aya ya girgiza kai, yanda bakinshi yayi nauyi yasa shi d'agawa da k'yar yace "Ryam...soyayyar tawa...ce abar wannan..wulak'antawar? Me yasa Ryam?" Kawar da kanshi yayi kamar mai son b'oye hawayen idonshi, girgiza kai tayi ita ma cikin sanyin jiki tace "Ni ba k'aryatawa nayi ba, amma dai nasan jikina kafi so, sheikh na tabbata kana d'aya daga cikin mutanen da suke zargina da aikata zina, yanda kake min wani kallo, da yanda kake fad'in wasu maganganu akai na, da yanda ka zo min jiya, ni yarinya ce mai k'ananan shekaru, amma ba mahaukaciya ba." Gyara tsayuwarta tayi tana kallonshi tace "Ka d'auka ni ballagaza ce shiyasa ka zo min a yanda babu wata budurwa da aka tab'awa haka, kawai ni yanzu so nake ka kaini gidanmu dan ina so nima a rakoni kamar yanda ake rako kowace mace." Juyawa tayi zata fita a falon da niyyar ta zauna bakin k'ofar ya rik'o hannunta, hankalinshi tashe zuciyarshi ta makance ya jawota sosai, marairaicewa yayi cikin rawar murya yace "A'a Ryam, ba haka bane kinji, karki zargeni akan haka dan Allah, kuma maganar tariyarki na fad'awa Hajia kuma ta fad'awa Abbanki kin tare d'akinki, karki damu da wannan kinji." Da mamaki ta kalleshi tace "Ban gane na tare ba? A hakan?" Kamar zaiyi kuka yace "To miye a ciki? Dama ai ni ko mahaifinki ne ya kalata mu rakaki d'akinki, duk wannan shirmen da ake yi bidi'a ce Ryam, dan Allah ki kwantar da hankalinki kinji." Kallonshi tayi tana had'e hawayenta, tuna maganar Mama da kuma tabbatarwa bata da wata madafa, sai kawai ta fizge jikinta gareshi ta koma kan kujerar ta zauna, zaunawa yayi shi ma yana kallonta ya buga tagumi, cikin raunin murya yace "Ryam ke ce jarabawata, dan Allah ki taimaka min ko na samu cinye jarabawar nan a sauk'ak'e." Jan majina tayi saboda bata son yin kuka, ganin bata kulashi ba yasa shi jingina a kujerar ya jawota a hankali ya kwantar a jikinshi, hakan ne yasa ta fashewa da kuka tana cukuikuiye rigarshi tana fad'in "Abdul bana jin dad'i, jikina da zuciyata ciwo suke min, gashi kai kuma bansan me yasa ba bana iya maka tsayayya, dolena ne na girmama wanda iyayena ma suke girmamawa." Shafata ya ci gaba da yi yana sumbatar kanta yana fad'in "Shiiiii! Ya isa haka Ryam, kiyi hak'uri kinji, bari na miki addu'a to." Kwantar da ita yayi kan kujerar ya zura hannunshi ta saman rigar, a hankali cike da kissa da k'warewa ya shiga shafa nonowanta da suka k'ara kumbura, shiru tayi da mamakin wace irin addu'a ce haka? Tana ji tana saurarenshi yake ta shafawa yana lailayawa har saida ta ji sak'on ya fara isar mata, gaba d'aya ta ji tana wani bank'arewa tana neman shigewa jikinshi, jin abun zai fi k'arfinta sai kawai ta fashe da kuka ta matseshi tsam. A hankali ya laluba ya kamo bakin kuka ya had'a da na shi ya shiga tsutsa hakan ne ya tirsasa mata yin shiru tana saurarenshi. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *44* Hannun da taji yana zurawa ta k'asan rigarta alamun akwai gab'ar da yake son kaiwa yasa ta saurin hautsinawa ta mik'e tsaye, kallon juna suka shiga yi kamar masu tuhuma ko zargin juna, sai kuma ta dafe gaban goshinta tana yatsina fuska tace "Aouch!" Da sauri ya mik'e yana rik'o hannunta yace "Menene? Kina lafiya?" Cikin yatsina fuska tace "Bana jin dad'in jikina ne, bacci nake so nayi." Murmushi yayi ya jawota suka shiga takawa a hankali, d'akin daya shiga da ita yasa ta d'ago kanta tana k'arewa d'akin kallo, kwantar da ita yayi kan lafiyayyen gadon tare da shafa kanta yace "To kiyi bacci." Lumshe ido tayi alamar to, mik'ewa yayi daga sunkuyawar zai fita sai kuma ya tsaya, a nutse ya haura kan gadon ya d'aga kanta ya d'ora kan k'irjinshi, shafata ya ci gaba da yi yana fad'in "Bacci...bacci...bacci...bacci." Samun kanta tayi da d'oa hannunta na dama akan k'irjinshi ta rufe ido, sannu sannu sai kuwa bacci yayi gaba dasu dukansu. Awa d'aya ya samu a baccin nan ya tashi saboda rashin sabo, falo ya dawo ya zauna yana gudanar da wasu harkokinshi, a k'alla awa biyu ya d'auka anan zaune kafin ya shiga madafar nan, kazar daya sa mai gadi ya kawo masa ya saka a cikin na'urar d'umama abu, kafin tayi zafi kuma kokombre ya saka a blender tare da na'a na'a da citta d'anya ya markad'a, da k'aramar rariyar roba ya tace ya saka zuma ya kai fridge, yana kammalawa ya ciro kazar tare da sakata a plate ya yankata yanda zatayi daidai da cin mutum a sauk'ak'e kafin ya d'ora plate d'in a babbar faranti, lemun nan ya d'auko ya d'ora akan farantin sannan ya d'auko fresh milk ya d'ora ya nufi d'akin baccin. Baccinta ya samu take yi har yanzu, aje farantin yayi ya nufi ban d'aki ya had'a mata ruwan wanka masu d'umi, fitowa yayi ya zauna gefenta ya rik'o hannunta yana kallon fuskarta, a nutse ya shafa kumatunta tare da furta "Innar Issa." A hankali ta shiga bud'a idonta tana mitsikasu, saida ta bud'e duka ta saukesu fes a kan shi, tashi tayi zaune tana murza idon ta juya dan neman agogo ta ga awa nawa ta d'auka, murmushi ya mata yace "Awa hud'u babu minti goma kika d'auka kina baccin nan." D'an matse bakinta tayi tana k'ok'arin sauko da k'afafunta k'asa, taimaka mata yayi har ta mik'e tsaye tana jin bata jin k'warin jikinta, saidai ciwon jikinta ya ragu sosai, saida suka isa bakin k'ofar d'akin ya tsaya yace "Ki shiga kiyi wanka na gama had'a miki ruwa, kiyi alwala daga nan dan 12:30 tayi." Jinjina kai tayi ta shige ban d'akin ya rufo mata k'ofar, falo ya koma shi ma ya shiga ban d'akin dake nan yayi alwala, dawowa yayi d'akin ya zauna bakin gado jiranta, ta d'an d'auki lokaci kafin ta fito d'aure da towel babba a jikinta, kanshi na k'asa a lokacin yana ganinta ya d'aga gaba d'aya, santala santalan cinyoyinta masu kauri da haske ya fara kallo, da k'yar ya had'i wasu yawu tare da kawar da kanshi saboda alwalar dake jikinshi. Cikin shak'akk'iyar murya yace "Ryam gaggauta muyi sallah kafin k'arfe 01:00." Jinjina kai tayi da sauri ta nufi rigarta zata d'auka yace "Ki duba cikin drower nan akwai kaya." Da sauri ta nufi drower ta bud'a, duka abaya ne sai kuma kaya masu taushi na bacci da hijabai, d'auka tayi ta saka wata abayar ta d'auki hijab ta saka, gabanshi ta tsaya tace "Na gama." Mik'ewa yayi yana tsaya sosai akan sallaya yana fad'in "Na manta rabon da nayi sallah jam'i a gida, yau dalilinki zanyi hakan." Zaro ido tayi tace "Saboda ni? To ka je masallaci mana ni sai nayi a gida." Murmushi yayi yace "Ai anan kusa ne babu masallaci, kuma na miki alk'awarin zama tare dake na tsawon wunin nan." Kallonshi tayi ba tace komai ba ita dai har suka kabbara sallah tana daga gefenshi, a minti ashirin da d'aya suka gama sallah har Mimi ta fara tunanin ko k'iyamu-lail zai sa su yi, suna idawa ta mik'e ta cire hijabin ta aje kan gado, mik'ewa yayi shi ma yace "Zauna ga abinci." Zaune tayi kamar yanda yace ya aje mata farantin gabanta, hannunshi ya sa ya fara bata a bakinta shi ma kuma yana ci. Har suka gama ya bata madarar tasha shi kuma ya d'auki lemun nan ya shanye. *Wuni* ne na ban mamaki a wurin Mimi, wuni ne da zata iya cewa ya shiga tarihin rayuwarta, yanda ya mu'amulance ta ya tafi da ita sai abun ya tsaya mata cak a zuciya da tunani, yanda ya kula da ita ya riritata ya k'ara shagwab'ata, ko kare bai yarda ta d'auka daga nan zuwa can ba, komai shi ya yake mata saidai ta ci ta zauna suyita hira, duk da mamakinshi ya sa ko sakin jikin ta kasa yi da shi, amma dai ba laifi wunin nan yasa ya tsaya mata a rai har ta fara jin tsohon a k'asan zuciyarta. Saidai abu d'aya da bata sani ba shi ne dama ba tun yau take jin shi ba, can ma rashin bawa abun mahimmanci ne da shiririta yasa bata iya fahimta ba. 20:30 tana zaune kan cinyoyinshi biyu ya d'ora hab'arshi kan k'irjinta yana danna wayarshi ita kuma tana kallon tv, lumshe ido tayi ta sauke numfashi a hankali tace "Ab..yallab'ai." Kallon fuskarta yayi yace "Um um! Ki kirani da Abdul." Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um! Ni tsoro nake ji." Girgiza kai yayi yace "Tsoron me kuma? Allah Ryam kin d'aukeni kamar kakanki." Murmushi tayi tace "Ba haka bane, kaga idan na saba da fad'in Abdul idan a gaban mutane ne fa? Kaga su suna giramamaka idan na kira sunanka za'a kalleni marar tarbiya ne." Murmushi yayi yace "Hakane kam, to ki canza min wani sunan mana mai dad'i." Jim tayi ta d'aga kanta sama alamar tunani, sai kuma tayi saurin kallonshi tace "To idan na ce bawan Allah fa." Wani sanyayyan murmushi yayi yace "Haka ma yayi, babu abinda zai sani k'ara k'ank'ar da ka茂na kamar na tuna ni d'in bawan Allah ne ba wata tsiya ba." Murmushi tayi ita ma sannan tace "Abdul nan zan kwana?" Kallonta yayi yace "Kina son hakane?" D'aga kai tayi alamar e, sake matsata yayi jikinshi yana shinshina jikinta yace "Um um! Gida zamu koma, ba zan iya barinki a nan ba." Turo baki tayi gaba tace "Ni dai kawai ka barni nayi bacci na a nan." Girgiza kai ya sake yi alamar a'a, kyab'e fuska tayi ta turo baki ba tace komai ba, kallon fuskarta yayi ganin yanda ta kyab'e a dole tayi hushi yasa shi aje wayar hannunshi ya mata cakulkuli yana dariya da fad'in "Haba dai gimbiya, kinga fuskarki kuwa yanda tayi? Sai kika zama kamar wata mage na jin bacci." K'yalk'yalewa tayi da dariya bata sani ba tana bille-bille har ta fad'i kan carpet d'in tana zillewa, bin ta yayi ya mata rumfa yana fad'in "To yi min dariya sannan." Cikin k'yalk'yalawa take fad'in "Na yi to, nayi ya isa haka, Abdul cikina zan mutu." Dakatawa yayi yana dariya shi ma da kallon fuskarta, ba taee daya d'aga daga jikinta ba y'a kalli fuskarta yace "Ryam ina sonki sosai, ki yarda da haka kinji." Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um! Ban yarda ba." Kallon mamaki ya mata yace "Ya kike so nayi dan na tabbatar miki?" Cikin murmushi tace "Da kaina zan tabbatar da haka." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ta ya ya?" Kashe masa ido tayi ta d'an k'yata bakinta, sumbatar bakinta yayi sosai kafin ya d'agata yace "Tashi ki shirya mu tafi gida kafin dare yayi." Kamata yayi ta mik'e tsaye ta suka shiga d'akin, a tsanake suka shirya suna raharsu har suka gama suka fito bayan ya rufe kowace k'ofa suka d'auki hanyar komawa gida. Suna shiga cikin gari ta kalleshi a marairaice tace "Abdallah ice cream." Ta gefen ido ya kalleta yace "Me ice cream yayi?" Turo baki tayi tace "Zan sha." Girgiza kai yayi yana murmushi yace "Hummm! Amma dai kinsan ba zan lamunci shan kayan sanyin nan ba ko?" Dafa hannunshi tayi da yake tuk'i tace "Dan Allah fa, daga wannan ba zan k'ara ba." Jinjina kai yayi yace "Shikenan, watak'ila fa yarona ko yarinyata ce a cikinki." Da k'arfi tace "Me? Da wuri haka? Tabb'!" Kallonta yayi yace "Kina mamaki ne da yin ubangiji?" Girgiza kai tayi tace "A'a, amma dai ai yayi wuri." Murmushin gefen labb'a yayi mata har suka tsaya daidai shiga wani alimentation, fita yayi zai rufo k'ofar ta d'aga masa hannun tace "A dawo lafiya." Murmushi yayi yace "Wato ba zaki zo muje ba saboda ba kya son ki jera da tsoho." Dariya tayi tace "Ba haka bane, ai na d'auka ba zaka so na shiga gurin nan ba." Girgiza kai yayi ya rufe k'ofar ya juya ya shiga wurin, a hankali ta bud'e motar ta fito da k'afafunta kafin ta fita gaba d'aya, rufe k'ofar tayi ta tunkari shiga ita ma tana murmushin mugunta. Ta b'angaren kayan mak'ulashe ta nufa tana hangenshi tana b'oyewa, kwando ta d'auka ta dinga loda kayan k'walam biscuit chacolat da saurensu, saida ta cika basket d'in ta nufo inda yake tsaye yana laluban aljihu, tana zuwa ta aje basket d'in tana murmushi ganin ya tsaya sororo yana kallonta da mamaki. Murmushi ta masa ta kalleshi tace "Ga wanda na d'auko ta can." Galala ya kalli matashin sai kuma ya kalleta ya matsa kusanta yace "Ryam lafiyarki k'alau? Wa ya ce ki fito?" Murmushi ta saki tana takowa ta tsaya daf da shi tace "Kayan dad'i na siyo." Iska ya furzo da tunanin ya zaiyi da ita, yana kallo ta shiga ciro kayan tana d'orawa kan kantar da za'a dubasu a musu kud'insu, yana kallon ikon Allah shi dai aka fad'a mishi kud'in ya biya aka saka musu a leda, zai d'auka tayi saurin d'auka tana fad'in "Lahhhh! Haba Abdallah ya zan bari ka d'auka?" D'auka tayi suka fita yana kallonta shi dai, saida suka shiga mota ya fara tafiya ya kalleta yace "Ryam kinsan ina da kishi?" Ba alamar damuwa a tare da ita tace "Na sani." "Kuma kinsan zan iya yin komai a kanki?" Kai tsaye ta sake fad'in "Na sani." Kallonta yayi yace "To me yasa kikayi abinda kikayi?" Marairaicewa tayi tace "Sorry." Murmushi yayi tare da lak'ato hancinta yace "Nayi sorry yan matana, amma kar a sake daga yau." Jinjina kai tayi tace "Insha'Allah." Da hirarsu ta farin ciki suka isa gidan, ta falon Hafsat suka sake shiga kuma sunyi sa'ar samunta zaune tare da Aisha suna karatu, abun haushi shi ne kallon da Aisha ke musu shi da Mimi, gashi bai ji ta gaishe da ita ba sai ma Mimi ce tayi k'ok'arin fad'in "Aisha karatu ake?" Amma sai ya ga ta mik'e ranta a b'ace tana fad'in "Amie saida safe." Da kallo ya bi Aishar har ta shige, Mimi ma d'akinta ta nufa tana fad'in "Saida safenku." Shigewa tayi ta barshi tare da Hafsat, shi ma yau babu fara'ar nan ya kalleta yace "Zan shiga ciki nayi wanka, kafin na fito ina buk'atar ganin duka yaran nan a falona." Da fara'a ta amsa mishi da "Angama sheikh nawa." Shigewa yayi ta bishi da kallo sai kuma tayi saurin mik'ewa ta je had'o mishi kan yaran da tunanin ko lafiya? Bai d'auki lokaci ba ya fito daga wanka ya shirya cikin jallabiya fara tas da ita, yana fitowa falon kam ya samesu dukansu har da Munzeer, mutmushi yayi na jin dad'in girmama maganarshi da Hafsat tayi, duk da abinda zai fad'a yanzun bai shafi Munzeer ba, amma da yace yaran duka saita tasoshi daga bacci shi ma, dan gashi nan kanshi a cinyarta tana daddab'ashi ya tashi saboda ganin sheikh ya fito. Zaune yayi akan sofar yana kallonsu dukansu, had'e fuska yayi sosai cikin fad'a da muryar tashin hankali yace "Auren da nayi ne yasa nake gani raini k'arara a idonku ko kuma dama can akwai rainin tsakaninmu yanzu ne ya fito? Shin haramun ne na aikata da girmansa ya gawurta har zai iya janyo min rainin 'ya'yan cikina dana haifa? Me na yi? Akan me?" Ya k'arashe yana kallonsu musamman ma Aisha da Heezam, duk sanda kawunansu sukayi hakan yasa shi d'orawa da fad'in "Auren da nayi? Ko kuma yarinyar ce bata muku ba? Bana son tashin hankali kun sani, amma daga auren yarinya har zaku fara min kallon hadarin kaji har wasunku ma zasu iya bud'a baki su min tambayar da duk ta zo bakinsu bayan na tabbata kuna da hankalin tauna magana kafin ku furtata, to akan me?" Jinjina kai yayi tare da k'wafa yace "Da ba'a aure ai da ban haifeku ta hanyar aure ba, k'addarata ce ta kawo Mimi a Wanda k'arfina ya fara k'arewa, idan zamuyi adalci yarinyar ce abar dubawa anan, amma ku mahaifiyarku kawai kuka sani, ita kuke taya wa kishi kenan? Shin ita kunga tayi makamancin abinda kuka min ne a yau d'in nan? Haka kawai na tsaya gabanku kuna k'are min kallo cike da raini da son tantance me na aikata da matata a d'akinta." Kallon Hafsat yayi a sanyaye yace "Qawwama bana da matsala da ke, na tabbata kina iya k'ok'arinki akan tarbiyar yaran nan, amma ki sani zanyi wani abu da ban san ko zai miki dad'i ba, kasancewata uba namiji dole na d'auki matakin gyara kan iyali tun yanzu, dan a yanda na fahimta idan lamarin nan ya gawurta wata rana zan iya shigowa gidan nan na samu d'aya a cikin yaran nan suna dakuwa da Mimi, musamman ma da suke ganin shekarunsu d'aya kumaa tsayinsu d'aya da ita." Kallon Aisha yayi yace "Ki shirya ma aurenki ranar juma'a mai zuwa insha'Allah." Kallon Heezam yayi yace "Zan gama kammala maka shirin tafiyarka Madina a satin nan, da zaran kaga d'aurin auren yar uwarka zaka bar k'asar nan." Kallon Aswan yayi yace "Daga sallah magriba zuwa isha'i zaka fara darasi tare damu a majalisin su Anas, daga isha'i zuwa lokacin da zaka kwanta bacci zaka kasance a d'akin karatu na kana bitar karatunka." Duka yaran kallonshi suke kowa kamar zaiyi kuka musamman Aisha data fara hawaye, amma sai suka sadda kawunansu k'asa Heezam na fad'in "Ka gafarcemu Abie, mun tuba ba zamu k'ara ba insha'Allah." Aisha ma da sauri tace "E Abie, ka yafe mana dan Allah, ba zamu sake ba wallahi, zamu d'auki aunty Mimi kamar mahaifiyarmu." Da mamaki ya kallesu yace "A ganinku saboda ita ne na yanke hukuncin nan? Kar ku min gurguwar fahimta mana, hak'ik'a Aisha sai bayan aurena ne da naji wasu kalaman a bakinki na yanke hukuncin aurenki, amma sauran ai dama na jima da fad'a muku ina da wannan tsarin, yanzu ne lokacin zartarwa yayi." Cikin shahsek'ar kuka Aisha tace "Abie ka yafe min ba zan k'ara ba, ina so na kammala karatu Abie ba yanzu na ke son aure ba." Harara ya dalla mata yace "A lokacin da kike buk'atarshi kuma saiki kirashi ya zo?" Kallon Hafsat yayi da ita dai tayi shiru take kallon yaran, amma fa a zuciyarta kamar zata kama da wuta haka take ji, a gaskiya hukuncin yanzu bai mata ba, dan ita ma kawai ta ta'allak'a haka da aurenshi da Mimi ne, akan me zai yanke ma yaranta wannan hukuncin? Saboda sun kalleshi kawai? Ajiyar zuciya ta sauke sanda yace "Hafsat me kika ce akan haka?" Girgiza kai tayi a sanyaye tace "Ba komai sheikh, Allah yasa haka shi yafi zama alkairi, Allah ya mana jagora a lamuranmu." Wani tattausan murmushi ya saki yana kallonta, a gaskiya da zai bud'a zuciyarshi ya nuna mata irin girma da k'aunar da yake mata musamman halayen nan nata na karamci, tabbas da sai ta ji babu mace mai sa'a a duk duniya kamar ta, da zatayi rawa tayi tsalle ta buga k'irjinta a gaban dubbanin mata kan cewa babu kamarta. Kallon yaran yayi yace "Ku tashi ku je ku kwanta." Mik'ewa sukayi jiki duk a sanyaye sai Munzeer daya shiga baccinshi a k'afar Hafsat, saida suka fita dukansu ya taso ya d'auki Munzeer d'in sannan ya kama hannunta ta mik'e, a hankali suka fita har suka k'arasa d'aki ya shinfid'eshi ya tofa mishi addu'a, d'aki ya rakata ita ma ta kwanta kafin ya mata saida safe ya fito. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *45* Yana shiga d'akin ya samu Mimi bacci ya d'auketa, saidai da alama baiyi nisa ba dan hannunta har yanzu rik'e da robar ice cream d'inta, karb'a yayi ya aje gefe ya tattare kayan ya aje sannan ya gyara mata rufarta dan tayi wanka ta saka kayan bacci. *07:30* A sanyaye take amsa wayar Hajia tana fad'a mata auren Aisha kamar yanda sheikh ya fad'a, cikin son kwantar mata da hankali na iya abinda zata iya kawai Hajia tace "Hafsat karki damu kinji, dama ai sheikh ya sha fad'a idan har ya tashi aurar da ita babu abinda zaiyi na bidi'a, kar ki bari shed'an ya raya miki cewa ya yanke hukuncin nan ne saboda auren da yayi, ki mata addu'a matsayinki na Uwa Allah yasa haka shi yafi alkairi kinji." A hankali tace "Shikenan Hajia insha'Allah, yanzu ya maganar shirye shirye ko wani gyara?" Murmushi Hajia tayi tace "Hafsat ai ke ce uwarta kuma kinfi sanin me ya dace da ita, kawai kiyi tunani sai ki tuntub'i Karima kuyi magana, na tabbata dai sheikh ba zai mata kayan d'aki ba dan shi baya cikin wannan tsarin." A sanyaye tace "Haka yake fad'a Hajia, ba zaiyi kayan d'aki ba kuma ya baka 'ya sannan ya baka abincin da zaka ci, saidai yace a matsayin Anas naa d'alibin da yake ji da shi zai iya mishi kyauta tsakaninshi ne da shi wannan." Hajia ce tace "To kin gani, kawai ki mata addu'a tunda yaran ke kanki kin tabbatar da yaron kirki ne." A ladabce tace "Gaskiya ne Hajia, Allah ya tabbatar mana da alkairi." "Ameen." Hajia ta fad'a kafin suyi sallama ta aje wayar ta fito dan shiga madafa ta taimakawa mai aikin da ke tayata aiki idan ta haihu. Tun asuba daya tasheta ya tafi masallaci bata sake ganinshi ba, tana idar da sallah ta shiga gyaran d'akinta a nutse, duk da ba wani datti ko wani abun gyaran ke akwai ba, amma saida ta kimtsa komai tayi turaren ruwa dana wuta da kaskon na'ura, tana gamawa ta shiga wanka dan Alhamdulillah yanzu jikinta da sauk'i sosai, tana fitowa a wanka ta zauna ta d'auki ado kamar zata je gasar sarauniyar kyau, cikin wani leshi ta shige ta kashe d'aurin d'an kwali mai hawa-hawa. Yanda tayi wani masifaffen kyau yasa ta kallon kanta a madubi har ta d'auki selfie, saida ta gama ta aje wayar ta tunkari k'ofar fita, yanda falonta ke ta tashin k'amshin turaren wutar data saka yasa ta fita a falon ta rufo k'ofar. Falon Hafsat ta shiga da sallama a bakinta, Munzeer da Aswan ne suka amsa a tare suna kallonta, murmushi ta sakar musu tana k'arasawa da fad'in "Sannanku?" Da ladabi da girmamawa Aswan yace "Ina kwana aunty." Da fara'a tace "Lafiya lau Aswan, har an shirya tafiya makaranta?" Da ladabi yace "E aunty." Munzeer ta tarawa hannu tace "D'an Abbansa yaya? An shirya ne?" Tasowa yayi da dariyarshi ya mik'a mata hannun, sunkuyawa tayi tana shafa kanshi tana murmushi tace "Ina mamanka?" Madafa ya nuna mata yace "Tana ciki." Murmushi tayi tace "Kunyi karin kumallo ne?" Girgiza kai yayi yace "Shi muke jira." Mik'ewa tayi daga sunkuyawar tace "Bari na shiga ciki to na kawo maka naka na musamman ko?" Jinjina kai yayi yana dariya yace "To aunty." Hanyar madafar ta nufa sai kuma Aisha ta fito tana gyara jakar makarantarta a bayanta da alama sauri take, ba tare da tunanin komai ba Mimi ta sauko da kanta tana fara'a tace "Ina kwana Humaira." Kallonta tayi tana gimtse fuska, wani wawan tsaki taja ta ci gaba da takawa, ta gabanta ta wuce ta shiga madafar tana fad'in "Amie mun kusa makara fa, har yanzu baku gama ba?" Girgiza kai Mimi tayi ta shiga madafar ita ma tana tab'e baki a ranta tana fad'in "Kinyi da yar halak yarinya, akan tsohon ubanki zaki min tsaki?" Tana shigowa suka had'a ido da Hafsat dake aiki tuburan, dukansu murmushi suka ma juna inda Mimi tayi saurin fad'in "Ina kwana aunty?" Da fara'a sosai ta amsa da "Lafiya lau Mimi, antashi lafiya?" Jinjina kai tayi tace "Lafiya lau, aiki ake?" Cikin sakin fuska tace "Wallahi, kinga yau kamar an d'auremu na rasa me ya tsayar damu." Murmushi tayi tace "Allah sarki, yau da gobe kenan, bari na taimaka muku." Kamar daga sama Aisha tace "Amie indai wannan matar zata saka hannu a abincin da zamu ci yanzu wallahi saidai na hak'ura da shi." Da sauri Hafsat ta kalleta hankali tashe tace "Aisha kina lafiya? Me yake damunii ne? Wannan wane irin iskanci ne?" Turo baki tayi haar da bubbuga k'afafu tace "Lafiya ta k'alau Amie, akan ta ne fa Abie ya daina son m没 har zai min auren wuri." Zaburowa Hafsat tayi zata kwad'a mata mari sai kuwa tayi hanyar fita, Mimi dake k'ofar tsaye tana kallon Aisha da mamaki bata ankara ba ta bangajeta tana fad'in "Dallah malama matsa min ni." Yanda ta had'a kanta da bango yasa Mimi sakin siriryar k'ara tana dafe k'eyarta dan ta ji zafi sosai, da sauri Hafsat tayi kan Mimi tana tambayar "Subahanallah! Mimi kinji ciwo ne?" Daurewa tayi ta mayar da hawayenta ta k'ak'aro murmushi ta girgiza kai tace "Ba komai aunty, ki k'yaleta dan Allah." A tsawace tace "Na k'yaleta fa kika ce? Aisha yarinya ce da har zata min d'anyan kai a gidan nan?" Fita tayi a madafar a hassale, a sanyaye Mimi ta k'arasa kusa da mai aikin da take gaisheta ta amsa sannan suka ci gaba da aikin. Hafsat na fitowa a fusace Aisha na daf da k'ofar fita tana ta kumburo baki, nunata tayi da yatsa tana fad'in "Abinda zaki min kenan Aisha? Wannan ita ce koyarwar dana miki? So kike ki nunawa duniya ni malalaciya ce kenan? Kina so ki fad'a da babban murya cewa ban isa dake ba?" Cikin turo baki tace "Kiyi hak'uri Amie, amma faa ke ma kinsan gaskiya na fad'a, duk saboda ita ne komai yake faruwa." A zafafe tayi kanta sai kuma Heezam ya fito daga d'akinshi shi ma a shirye, da sauri Hafsat ta kalleshi tace "Heezam kamo min hannun yarinyar can?" Aisha na jin haka ta fita a guje hakan yasa Heezam kallonta sai kuma ya kalli Hafsat yace "Amie lafiya? Me ta miki yanzu da safe? Ban tab'a ganin b'acin ranki irin haka ba?" Kamar zatayi kuka tace "Dole ne Heezam, yanzu duk abinda mahaifinku ya fad'a muku jiya ace bai shiga kan Aiaha ba, har ta tsaya tana wa Mimi rashin kunya kuma a gabana." Girgiza kai yayi cike da rashin jin dad'i yace "Kiyi hak'uri, ina ga fa dalilin da yasa Abie yace zai mata aure kenan, kinsan matsalar Aisha kafuwa." D'aga kafad'a yayi yana feso iska yace "Ni dama a shirye nake da tafiyata Madina, dan gari ne da nake mafarkinshi kullum tun ranar da Abie ya labarta min zai turani can karatu, dan haka ban d'auki hukuncin nan da zafi ba, ya min dad'i ni kam." Wata yar k'wallar tausayinshi Hafsat ta matso tace "Allah ya maka albarka, Allah ya taimakeka ya haskaka maka neman iliminka." Murmushi yayi yace "Nagode Amie." Takawa ya shiga yi yana kallonsu Aswan yace "Ku tashi mu wuce kunsan Abie baya so mu tsayar da dreba yayi ta jiranmu ko." Mik'ewa sukayi inda Hafsat ke fad'in "To abun karin fa?" Kallonta yayi yace "Amie lokaci ya k'ure, kawai idan munje zamu samu abinda zamu sa a cikinmu." Jinjina kai tayi tace "To shikenan, Allah ya tsare." Shafa kan Munzeer tayi tana masa murmushi tace "A dawo lafiya ko yarona." Bye bye ya mata suna daf da fita Mimi ta fito da sauri tana fad'in "Ku tsaya ku tsaya." Tsayawa duk sukayi suna kallonta, bred ne ta saka musu soyayyen dankalin turawa a ciki da k'wai da tomate fresh, ninkeshi duka tayi a tissus tana mik'awa kowannensu tana fad'in "Ai ba zaku tafi da yunwa ba, taya za'a fahimci karatu?" A kunya ce Heezam ya kalleta dan gaskiya kwalliyar data cab'a sai ya gan ta wani wal-wal-wal, d'auke kanshi yayi yana fad'in "Ina kwana aunty." "Lafiya lau." Ta fad'a sanda take mik'a mishi ta d'ora da "Antashi lafiya?" "Lafiya lau." Ya fad'a yana karb'a da fad'in "Nagode." Dukansu godiya suka mata kafin ta mik'awa Aswan tace "Ka mik'awa Aisha wannan." Hafsat dake murmushi tana kallonsu ne tace "Ai da kin barta ja'ira ta je da yunwar." Murmushi tayi tace "A'a aunty ayi hak'uri." Ganin sun fita suna fad'in "Sai mun dawo Amie, sai mun dawo Aunty." Yasa su dukansu suka bisu da "A dawo lafiya, Allah ya tsare." Suna ficewa Hafsat ta kalli Mimi tace "To me kika girkawa mai gidan? Iya fa yaran kawai muka d'orawa su da zasu tafi." Murmushi tayi cike da kunya tace "Aunty ai duk abinda kika fad'a shi za ayi." Girgiza kai tayi tace "A'a fa uwata, karki manta girkinki ne yau da gobe da jibi ke har nan da kwana biyar, dan haka wannan alhakin yana wuyanki, muje dai na taimaka miki da wani abun." Cike da kunya ta sinne kai ta bi bayan Hafsat d'in, suna shiga ta tsare da tambayar me zata dafa mishi, dan haka kawai tace bari tayi sauce na k'wai da doya. *Duk* abinda ya faru daga sanda Hafsat ke fad'awa Heezam abonda ya faru har k'arshe duk a idon sheikh daya shigo falon ta k'ofar dake fitowa daga falonshi, jin abinda ya faru yasa shi jin ba dad'i sosai, sai kawai ya share ya koma falonshi ya zauna. Saida ta kamalla aikin nan tsaf Hafsat ta kalleta tace "Ki je b'angarensa ki ga ko ya dawo daga masallaci, ya kan jima dama bai shigo ba wani lokacin." Jinjina kai tayi da ladabi ta nufi hanyar, a tsoro tsoro ta k'arasa ta k'wank'wasa tare da bud'ewa a hankali ta tura tana kuma fad'in "Salam." Dake babu hasken fitila sai ta shiga waige waige, yana zaune kan kujera mai zaman mutum d'aya yana kallonta, saida ta sak茅 furta "Salam." Mik'ewa yayi a hankali yalallab'a yayi ramda k'ugunta, hakan ya haddasa mata sakin k'ara a tsorace, da sauri ya rufe mata baki da hannunshi yana fad'in "Shiiii! Ni ne." Ajiyar zuciya ta saukea hankali ta kalleshi, had'a goshinsu yayi wuri d'aya ba tare daya d'auke hannunshi a bakinta ba yace "Banda abun *Marya* a duk duniyar nan waye yake da lasisin tab'a jikinki bayan ni?" Lumshe ido tayi a hankali ta bud'e ta kalleshi, hannunta tasa ta d'auke hannunshi a bakinta tace "Ni ma kuma waye yake da hurumin tsoratani a garin nan idan b芒 tsohona ba." Dariya yayi ya shiga neman bakinta saida ya kamoshi ya had'a da nashi ya shiga tsutsa, shiru tayi tana saurarenshi ita dai saida tana yana neman zage mata zip d'in riga tayi saurin ja baya tana fad'in "Abdallah abinci na zo yi maka tayi fa." Rik'o hannunta yayi yana sumbatar kuncinta yace "To ai sai na yi wanka ko?" Jinjina kai tayi tace "To kayi wanka saika fito." K'ugunta ya sake rik'ewa yace "To muje a tayani wankan ko?" Zaro ido tayi baki bud'e tace "Lahhh! Ni d'in? Gaskiya kunya nake ji." Murmushi yayi y'a lak'aci hancinta yana fad'in "Kunyar me? Shin ni ba naki bane? Ko kin manta mun zama d'aya ne." Mak'ale kafad'a tayi tace "Gaskiya ni dai kunya nake ji." Cak ya d'auketa ya nufi uwar d'akin da ita yana fad'in "Ba wani nan, idan baki taimaka min ba to zan fasa wankan ma." Wutsil wutsil ta shiga yi da k'afafu tana fad'in "Abdul ka saukeni k'asa dan Allah kar na fad'o fa." Murmushi ya saki yana fad'in "Ryam zan iya zagaye garin nan dake a haka babu abinda zai sameki." Kallon fuskarshi tayi ta sagala hannayenta a wuyanshi tace "Da gaske?" Girgiza kai yayi yana murmushi, dan sosai take bashi mamaki idan yayi magana tace wai da gaske? Sai yaji wani daban a zuciyarshi yana jin wani nishad'i, tunda har shi ma zai iya yin magana ayi tamtama gaskiya ya fad'a ko akasin haka. Jinjina mata kai yayi alamar eh, ita ma jinjina kai tayi tace "Shikenan, ni kuma yau sai ka goyani ma nayi bacci a bayanka." Suna shiga d'akin ya sauketa yana fad'in "Ko zamu jaraba ne ki gani." Tattare siket d'inta tayi ta taka gadon sannan tace "To juyo bayanka." Da dariya ya tsaya kusanta ita kuma ta haye bayanshi, takawa ya fara yi da ita a tsakar d'akin yana fad'in "Kinga a haka sai na zaagaye k'asa d'ari ba d'aya dake." Dariya tayi ta d'ora hab'arta a kafad'arshi tace "Kenan gari na d'ari d'in ba zaka iya ba?" Dariya yayi ya duk'a da ita kamar zata fad'a ta gaba yana fad'in "Ke ko? To me zai gagareni indai a kan ki ne?" D'an bubbuga bayanshi tayi tace "Wai baka jin ciwo a bayanka?" D'an d'ago kanshi yayi ya kalleta yace "Me yasa kika tambaya?" Sunkuyar da kai tayi tace "To ai naga irinku..." Dariya tayi ta kwanta a bayanshi sosai kamar zatayi bacci tace "Shikenan dai." Girgiza kai yayi yana dariya yace "Tsofaffi iri na kike nufi ko? Ryam ban tsufa ba yanda kike tunani, amma sannu kad'an zan tabbatar miki da haka." Duk'o kanta tayi ta kafad'arshi tace "Ta ya ya akaramakallah?" Kamar daga sama ta ji ya juyo da ita gabanshi da k'arfi kuma ya rik'eta gam tare da yin k'asa da ita kamar zata fad'i k'asa, rintse ido tayi ta k'amk'ameshi sosaai, cikin kunne ya rad'a "Kin amince na nuna miki?" Girgiza kai tayi ta bud'e ido tace "Na yafe, na tuba Abdul." D'agata yayi ya direta k'asa ya jata zuwa ban d'akin yace "To muje a min wanka Innar Issa." Binshi tayi suka shiga ban d'akin, yanda ya tilasta mata yasa ta b'alle mishi botiran jallabiyarsa shi kuma ya cire, rintse ido tayi sosai tace "Abdallah fita zanyi waje kafin na suma a nan." Rik'eta yayi yace "Babu inda zaki je, ki suma a nan na gani." Da k'yar ta samu ta kubto ta baro ban d'akin, a haka ma cewa yayi ta fito mishi da kayanshi da zai saka, wurin kayan ta bud'a saai ta rikice ta rasa wanda zata d'aukar masa, da k'yar ta ciro wata shadda bleu ta d'auko hula da hiramin da takalma duk sa suka dace da kayan ta aje, feshesu tayi da turare ta zauna bakin gadon jiranshi. *Watak'ila mun shiga hutun sallah insha'Allah* *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *46* Fitowarshi tasa ta yin zunbur ta mik'e tsaye tana kawar da kanta daga kallonshi dan d'aure yake da towel, kallonta yayi ya kalli kayan data fito mishi da su yana goge ruwan jikinshi yace "Inna Issa ya akayi kika san kayan da zan saka?" Kallon kayan tayi tana murmushi amma ba tace komai ba, matsowa yayi kusanta yace "Na gane, wato ke ma kina so na ko? Hakan na nufin zuciya da tunaninmu d'aya ne." Da sauri ta girgiza kai tace "A'a ba haka bane." Wani kallo ya bita da shi yace "To ya ya ne?" Sunkuyar da kai tayi a sanyaye tace "Ba komai." Daf da ita ya tsaya kamar zai had'eta yace "Baki so na Ryam?" Cikin turo baki da rashin bawa abun mahimmanci tace "To ai ni ban ma san ya so d'in yake ba." Kallon tuhuma ya mata yace "Amma kuma a baya kika fad'a min kina son Asas?" Da saurita kalleshi saikuma ta sunkuyar da kai, jawo k'ugunta yayi ya had'a da nashi yace "Hakan na nufin k'arya kika min? Da sauri ta girgiza kai cikin sanyin murya tace " Ba k'arya bace sheikh, kayi hak'uri kaji, muje ka ci abinci." K'arasawa yayi gaban kujera ya zauna ya d'auki mai ya fara murzawa a nutse, tana kallonshi har ya gama ya d'auki kayan ya saka, duk da turaren data fesa musu tana kallo ya d'auki wata k'aramar kwalba ya kuma shafawa a bayan kunnenshi sannan ya d'an murza a tafukan hannayenshi ya murza sosai sannan ya d'auki hula ya mik'a mata yace "Oya Hajia d'ora min." Karb'a tayi tana dariya tace "Ai naga yanda Abba yake d'orawa na yi." Murmushi yayi tare da sunkuyowa sosai tsayinsu ya daidaita sannan ta d'ora mishi hular, kallonshi tayi ta saki murmushi tace "Umm! Kayi kyau." D'aga mata gira yayi yace "Da gaske?" Jinjina kai tayi alamar eh, nuna mata k'ofa yayi yace "Muje to." Wucewa tayi gaba ya bi bayanta yana fad'in "Ryam wannan kwalliyar wa ya miki?" Dariya tayi ta juyo ta kalleshi tace "Ni na yi." Rik'e hannunta yayi yace "In kuwa hakane zan bayar da kud'in siyan wasu kayan kwalliyar dan a ci gaba da canccara min ita ina kallo." Dariya tayi cike da jin kunya har suka fita falon, Hafsat na zaune tare da mai aikin, gaisheshi sukayi a ladabce ya amsa a mutumce shi ma, k'arasa yayi wajen cin abincin ya zauna, Hafsat da Mimi ma k'arasawa sukayi sai mai aikin data koma madafa ta zauna, Mimi ce ta zuba musu abincin ta aje ma kowa sannan ta zauna ita ma da na ta a gabanta. Cikin raha da farin ciki suka gama cin abincin, Mimi na kallonsu suna buga mata soyayyar manya, duk da Hafsat d'in na nuna kunya amma sheikh k'arara yake fad'a mata maganar soyayya ko ya rik'e hannunta, kallonsu ita dai take tana mamakin sheikh d'in. Ya rigasu gamawa ya mik'e, saida ya tsaya gaban kowace ya sumbaci goshinsu ya d'ora da fad'in "Allah ya muku albarka, Allah k'ara mana fahimtar junanmu da zama lafiya." Gyara rigarshi yayi yace "Zan fita." Kallon Hafsat yayi yace "Nasan kinsan yau juma'a bana dawowa gida da rana." Jinjina kai tayi tana murmushi tace "Hakane, Allah ya tsare." Lumshe ido yayi yace "Ameen." Mimi ma a d'arare tace "A dawo lafiya." "Allah yasa." Ya fad'a yana kallonta, mik'ewa Hafsat ma tayi ta juya ta nufi d'akinta tana fad'in "Bari na barku kuyi sallama." A kunyace Mimi ta mik'e tana fad'in "A'a...amma..." Shiru tayi ganin har ta bud'e k'ofar d'akinta ta shige, kallonta yayi yana murmushi yace "Duk abinda kika ga *yar aljanna* tayi to da dalili, tafi kowa sanin bana yarda mace ta rakani bakin k'ofa fita saboda mazan dake gidan nan,iya falon nan ne kawai zamuyi sallama dake, kuma tasan waye mijinta shiyasa." Jiki a sanyaye ta d'aga kai alamar gamsuwa, kamo hannunta yayi yana kallon fuskarta yace "Kinyi kyau Ryam, kamar na zauna tare dake ina kallonki." K'asa tayi da kanta alamar kunya, tallabo hab'arta yayi yace "Fad'a min ciwonki ya warke ne?" Cike da kunya ta sake sunkuyar da kai ta jinjina alamar eh, sumbatar goshinta ya k'ara yi yace "Jiya ai ina shiga na sameki kinyi bacci, sam ban ji dad'i ba da baccin nan ya hanani jin dad'ina." D'ora hannunta tayi a k'irjinshi ta d'ora goshinta ta rufe fuskarta tsabar kunya tana murmushi, shi ma murmushin ya shiga yi yana rad'a mata a kunne "Da gaske nake fad'a miki, kin kuwa san irin duniyar da kika kaini daren can Ryam?" Tallabo kanta yayi ya kalli fuskarta yace "Wani irin dad'i ne daya fi zuma gigita tunani, d'and'ano ne marar misaltuwa Innar Issa, yau d'in nan zan..." Duka ta kai mishi a k'irji tana sake nutsa kanta cikin rigarshi tana fad'in "Dan Allah ka daina fad'a, baka jin kunya ne wai?" Shi ma dariya yayi yana sake rumgumeta a jikinshi, cikin muryar nishad'i yace "Kyautar da zan iya baki ita ce ki ci gaba da rik'e katina na banki kina aiki dashi duk sanda kike so, kyauta ta biyu kuma da zan iya yi miki ita ce..." Nuna kanshi yayi yace "Ni ma yanzu na zama na ki, na zama mallakinki Ryam, dan Allah ke ma ki bani kanki da zuciyarki, kinji?" Sinne kai ta sake yi tace "Ni dai kayi sauri ka tafi dan Allah, wallahi kunya kake bani." Dariya yayi yana sakinta ya gyara kayanshi da kyau yace "Shikenan tunda korata kike, zan tafi kuma sai dare zan dawo, dan yau ina da abubuwa da dama a gabana." Da mamaki ta kalleshi tace "To a ina zaka ci abinci?" D'aga kafad'a yayi yace "Duk inda na yada zago." Girgiza kai tayi tace "A'a gaskiya ban yarda ba, a duk inda ka yada zago ka sanar dani zan tura a kai maka." Wani k'ayataccen murmushi ya saki yace "Da kamar wuya Ryam, Hafsat ma ta jaraba yin hakan amma ban amince saboda abun dayawa." Bubbuga k'afafu ta fara yi tana kukan shagwab'a da fad'in "Ni dai wallahi idan baka amince ba nima ba zan ci abinci yau ba sai ka dawo gidan nan." Tallaba kumatunta yayi da hannu biyu yace "To wai ni da aka ce ba'a so na me, me ye kuma na damuwa dani haka?" Kallonshi tayi da fuskar yarinta tace "Lahhh! Ni fa ban fad'a ba." Lak'ace hancinta yayi yace "Zaki fad'a nan kusa *mai tsada*, ki shirya ma hakan." Kallonshi tayi sanda ya nufi hanyar fita yana fad'in "Saina dawo." Bye bye ta masa tace "A dawo lafiya." "Allah yasa." Ya fad'a yana fita, saida ta matsa daf da k'ofar tana kallon yanda jami'an da mai gadi da mai bawa shukoki ruwa suke ta gaisheshi yana amsawa da fara'a, zagayeshi sukayi yana magana yana ta nunawa da hannu, saidai yanda yake maganar a nutse da kuma sakin fuska su kuma suna jinjina kai suna fara'a zai tabbatar maka da nasiha ko kuma dai gajeran wa'azi yake musu, bud'e mishi motar akayi ya shiga suka rufe kafin jerin gwanon motocin ukun suka fita a gidan. Wata nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana juyawa tace "Allah ya tsare mana kai." Rarraba ido ta shiga yi kamar wacce ta tuna wani abu, sai kuma ta d'aga kafad'a tace "Ai hakan ba yana nufin so bane." D'akinta ta nufa ita ma tana fad'in "Nayi yaya ma na so shi ni kam?" *10:20* ta fito kai tsaye madafa ta nufa inda ta samu mai aikin nan, da taimakonta suka shiga had'a girkin rana, sunyi nisa sosai Hafsat ta samesu madafar, da mamaki ta k'arasa shiga tana fad'in "Kai! Mimi wai ba dai aiki ne kuke ba?" Dariya tayi cike da ladabi tace "E aunty, har mun kusa kammalawa ma." Murmushi tayi tace "Kai amma sannunki da k'ok'ari." Murmushi tayi ta amsa da "Yawwa aunty." Ci gaba sukayi da aikinsu, hakan yasa 12:00 na bugawa suka kammala komai suka jere a table, d'akinta ta shiga dan yin wanka ta shirya, tana shiga wayarta na kururuwa da sauri ta d'auka ta d'ora a kunne ganin sheikh ne. Daga b'angarenshi ya fara fad'in _"Amincin Allah ya tabbata a gareki Innar Issa."_ Murmushi ta saki tana jin wani farin ciki na daban ta amsa da _"Allah yasa muyi tarayya a cikin amincin daka rok'a min *old man*."_ Dariya yayi yace _"Ni ko Ryam? Ni ne old man?"_ Turo baki tayi tana zafe zip d'in rigarta tace _"To yi hak'uri."_ Numfashi ya sauke yace _"Na yi to tunda ai mun zama d'aya ni dake dama."_ Murmushi tayi tace _"Ya aiki?"_ Saida ya sauke numfashin da har ta ji sautinshi sannan yace _"Ba dad'i Ryam, so nake na zo gida cikin iyalina na zauna amma ba hali. "_ D'an murmushi tayi kawai mai sauti dan gaskiya har zuciyarta ita kanta zata so ya zauna kusa da ita, dan zaman gidan idan da shi a kusa zata fi jin dad'i, a sanyaye ya d'ora da _" Ryam kina lafiya?"_ Jinjina kai tayi kamar yana gabanta sannan tace _"Lafiya k'alau."_ D'orawa yayi da _"Babu abinda ke miki ciwo yanzu?"_ A sanyaye ta furta _"Babu Abdul, dan Allah ka daina tambaya ka ji, kunya nake ji."_ Murmushi ya mata mai sauti yace _"Dole na tambayeki Ryam, ina tsananin buk'atarki ne kuma bana so na sake ji miki ciwo."_ Cikin jin kunya ta sunkuyar da kai tana murmushi tace _"Ni dai bana so ka k'ara."_ Dariya yayi yace _"Ke ma kinsan ai baki isa ba, tunda kika barni na fara lasa zumar nan dole na ci gaba da lasawa ko na mutu."_ Hira suka sha sosai har saida shi da kan shi yace _"Ryam hutuna ya k'are, zan kashe waya, watak'ila sai dare idan na dawo gida."_ Marairaicewa tayi tace _"Kenan baka so na aika maka abinci?"_ Ajiyar zuciya ya sauke yace _"Na yau na yafe miki, amma daga gobe zaki fara insha'Allah."_ Jinjina kai tayi tace _"Shikenan Allah kaimu."_ _"Ameen."_ Ya fad'a yana d'orawa da _"Ki kula da kanki kinji, ina sonki sosai."_ A sanyaye tace _"Insha'Allah."_ Da haka sukayi sallama ta shiga ban d'aki tayi wanka tare da d'auro alwala ta fito ta canza kaya tayi sallah. Saida ta gama komai a tsanake ta sake fita ta samu Hafsat, tare da duka yaran suka ci abinci saidai babu wani armashi dan ba hira suke ba. Suna gamawa kamar a kan k'aya take ta koma d'akinta ta kwanta abin ta. Tasha baccinta saida kiran sallah la'asar ya tasheta, a gaggauce tayi alwala tayi sallah ta fito dan d'ora girki. Falo ta samu Hafsat zaune da littafi a hannu tana karatu, zaune tayi kan kujera tace "Aunty barka da hutawa." Da fara'a ta amsa da "Barka Mimi, an fito?" Da fara'a ita ma tace "E aunty, zan shiga madafa ne dama d'ora girki, me za'a dafa ne?" Kallonta tayi cike da k'auna da jin dad'in tambayar da ta mata tace "Mimi ni kike tambaya? Kije ki d'ora abinda ranki yake so ko kuma mijinki." Yar dariya tayi tace "A'a aunty ku dai ku fad'a min." Jim tayi tana murmushi alamar tunani, can ta numfasa tace "To kinga ki d'ora nama, dan sheikh yana son romo sosai, sai kisan dubarar da zaki masa." Mik'ewa tayi tana murmushi tace "Shikenan aunty." Tana shiga madafar ta samu mai aiki tayi shara tana guga, a nutse ta d'auki nama a fridge ta fara aikinta, mai aikin na gama guga ta kama mata da yankan albasa da tumatir da b'are tafarnuwa da saurensu, suna aikin suna yar hira sama sama har Mimi taji hayaniyar yaran sun dawo daga makaranta, saida ta daidaita komai ta fito a madafar bayan ta kalli mai aikin tace "Ki duba min dan Allah zan je na d'anyi shara a d'akina kafin magriba." Jinjina kai tayi tace "To aunty." Fitowa tayi ta samesu suna ta labartawa Hafsat labarin abinda ya faru a islamiya, da gudu Munzeer ya tarbeta yana fad'in "Aunty." Rumgumeshi tayi tana dariya tace "Munzeer an dawo?" "E." Ya fad'a yana kallonta, kama hannunshi tayi tana kallon su Aswan da suke fad'in "Aunty sannu da gida." Da fara'a tace "Sannu Aswan, Heezam, har an sauko?" A tare suka fad'i "E." Satar kallon Aisha tayi da ita ma take kallonta, wucewa tayi tare da Munzeer d'akinta yana mata hirarshi ta yara, zaunar da shi tayi falo ta shiga ciki ta d'auko chocolat d'in da jiya suka siyo ta kawo mishi, da fara'a ya karb'a da hannu biyu yace "Nagode Aunty, Allah ya biya." Da fara'a tace "Ameen yaron Abbanshi." Mik'ewa yayi yace "Na tafi na cire kayan makaranta na." Jinjina kai tayi tana kallonshi har ya fita a falon, aikinta ta shiga yi ta d'anyi goge goge ta saka turaren wuta dana tsintsiya, tana gamawa ana kiran sallah magrib da sauri ta shiga madafa ta duba tukunyarta, ganin komai ya daidaita ta kashe wutar suka zuba a kwanuka suka kai table kafin ta koma d'aki tayi alwala. Kwalliya ta d'auka ta ban mamaki cikin doguwar rigar shadda ta kashe d'aurin d'an kwallin da d'azun nan ta kalleshi a YouTube, tana fitowa ita kanta sai ta ji kamar tana tsarguwa dan yanda suke kallonta jefi-jefi sai yasa ta ji d'ar a jikinta, haka ta samu wuri ta zauna suna kallon kallo ita da Aisha, sai Hafsat dake ta danna wayarta tana d'an hira da Munzeer. Odar da akayi da kuma k'arar bud'e k'ofa ya tabbatar musu da sheikh na shigowa, suna zaune har saida ya shigo da sallama a bakinshi da alamun gajiya a tattare da shi, kusan a tare suka amsa mishi sai Hafsat da sabo yasa ta mik'ewa tana d'orawa da fad'in "Sannu da zuwa sheikh." Da fara'a ya amsa mata da "Sannu Manga, ya gida?" Da fara'a tace "Alhamdulillah, ya aiki ya fama da jama'a? Yau juma'a nasan ansha fama." Murmushi yayi ya kalli Mimi da ita ma ta mik'e tace "Sannu da dawowa." A tausashe ya amsa da "Sannu da gida." Kallon Hafsat yayi yace "Gaskiya kam ansha fama, shiyasa ma na kubto da wuri dan na dawo gareku na samu nutsuwa." Dariya tayi tace "Allah sarki, Allah ya k'ara maka lafiya jigonmu, wannan d'awainiya da kake Allah ya baka wanda zasu tallafeka sanda kake neman taimako." Wani k'ayataccen murmushi ya saki tsabar farin ciki yasa shi jawo hannunta ya dafa kanta yace "Ameen ya Allah, Nagode sosai Hafsa, Allah ya miki albarka, ke ma kuma Allah yasa yaranki su zama masu jin k'anki." Mimi dake kallonsu bata san sanda ta saki murmushi ba dan gaskiya sun birgeta, kuma yana daga cikin abinda yasa ta kasa samun k'ofar rainin a wajen Hafsat d'in shi ne, yanda ta ga shi kanshi wanda take zaune dominshi yana girmama matarshi, sannan ita kan ta matar ta rik'e girmanta kam, ko irin d'an kishinta ta k'i nunawa, shiyasa ita kanta sai taji Hafsat na mata wani kwarjini. D'auke hannunshi yayi akan Hafsat d'in yana fad'in "Yaran nan basu dawo bane?" "E, amma na tabbata suna kan hanya yanzu." Cewar Hafsat, jinjina kai yayi ya sunkuya ya d'auki Munzeer ya nufi d'akinshi yana fad'in "Bari nayi wanka na fito, ina fatan kun kammala abinci?" Dariya Hafsat tayi tace "Amaryarka ta kammala maka komai, yau idan ka ci abincin nan sa茂 ka manta hanyar shiga d'akinka." Dariya sukayi banda Aisha dake kumbura baki sai sheikh da yace "Idan hakane kuwa ya dace a had'ani da d'an jagora ai." Zaune Hafsat tayi tana fad'in "Idan zaka biya ai ba matsala." Juyowa yayi ya kalleta yace "Yanzu Manga a gidan nan ba za'a min alfarma ba?" Girgiza kai tayi ta kalli Mimi ma data zauna tace "Ko kad'an, ban sani ba dai ko amarya zata iya." Shigewa yayi yana fad'in "Sawwama Allah ya shiryaki." Da k'yalk'yala dariya tace "Ameen malam." Yana shigewa ta kalli Mimi cikin rad'a tace "Mijinki fa yana son kulawa sosai, ki sameshi hakan zai faranta mishi rai." Sunkuyar da kai tayi cike da kunya dan ita har yanzu jin abun take babba idan aka had'ata da shi matsayin miji da mata, d'an dukanta Hafsat tayi a cinya tace "Haba Mimi, tashi mana, wallahi zai ji ba dad'i, ki yarda da maganata, ina fad'a miki hakane saboda na sanshi sosai." Jinjina kai tayi ta mik'e ta nufi d'akin na shi, hararanta Aisha tayi ta d'auke kanta, kallonta Hafsat tayi banka mata harara tayi tare da k'wafa ta jinjina kai alamar zaki sani, turo baki Aishar tayi tace "Kiyi hak'uri Amie." A dak'ile tace "Hak'urin me Aish? Tunda kin gama rainamu ai shikenan sai kiyi, nasan dai burinki bai wuce ki ji ana fad'a a gari cewa Aisha yar malam ce ta k'i halin malam, na tabbata abinda kunnuwanki suke so su ji shi ne ke kamar ba 'yar sheikh Abdul Waheed ba saboda halayyanki." Da sauri tace "A'a Amie, dan Allah ki daina fad'in haka, na tuba Amie ki yafe min." Jinjina kai tayi tana d'aukar wayarta tace "In gaskiya ne abinda kika fad'a idan Mimi ta fito ki bata hak'uri, hakan zai sa na yarda gaskiya kike fad'a." Kumburo baki tayi ta d'an jinjina kai alamar to, d'auke idonta Hafsat tayi daga kallonta, dan tana so dole ta ga canji a tare da Aisha, idan tace zata fito da kishinta ne yanda Aisha ke buk'ata gidan nan ba zai d'aukesu ba, idan ta ce zatayi kishi da Mimi ne to zata cinyeta ta had'eta. Amma duba da wasu abubuwq yasa ta d'auke kai da kawar da kanta, duk abinda zata gani yanzu tasan na d'an lokaci ne, a shekaru kamar na sheikh arba'in da bakwai zuwa da takwas ya samu yarinya kamar Mimi yar sha bakwai da zata shiga takwas, me zata tsammani dama? Idan ma baiyi rawar k'afa ba ai sai tace mijinta ba namiji bane, dan haka zata had'e komai har sanda ita ma zatayi cikar d'aki su zama d'aya, tabbata hakan zai sa ta tashi da riba biyu, ta farko shi ne daraja da mutumcinta basu zube ba a wurin mijinsu, sannan ita kanta Mimi ba zata samu k'ofar rainata ba, dan kuwa tayi 'ya da ita, miji da suka had'a ba zai sa ta rainata ba. *Barkanmu da sallah yan Uwa.* *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *47* Tana shiga ta sameshi yana cire kaya Munzeer kuma na gaban madubinshi da wayarshi a hannu, k'ura mata ido yayi har ta k'araso habanshi ta tsaya kanta sadde, shafa kuncinta yayi yana murmushi yace "Ryam kin ganki kuwa, a gaskiya kinyi kyau ba kad'an ba." Cike da kunya da ladabi ta amsa da "Nagode." Saida ya aje rigarshi babba daya cire ya sa hannu aljihu, kud'i ya d'ebo da shi kanshi baisan adadinsu ba ya kamo hannunta ya damk'a mata yace "Wannan tukuicin wannan kwalliyar nan, kuma a shirye nake na dinga biya kullum indai ba ayi wacce zata fi k'arfin aljihuna ba." Murmushi tayi tana son zame hannunta tace "Nagode, amma ba sai ka biya ba, yabawa ma da kayi ya wadatar dan shi ne k'arfin gwiwar, zan iya siyan kayan da gumina ma indai zaka yaba." Girgiza kai yayi yana dariya yace "A'a Ryam, ni fa ina d'aya daga cikin masu fad'a a waje a dinga yi wa mata kyauta musamman idan sunyi abinda ya birge, sai kuma ni na zama mai hannun jarirai a gidana? A'a wallahi baki isa ba." Ya fad'a yana damk'a mata kud'in, karb'a tayi da hannun biyu tace "Nagode, Allah ya biya." Da fara'a yace "Ameen." D'an kallon Munzeer tayi dake ta tak'ular waya tace "Zan fita na barku ka shirya." Shi kanshi dake akwai hirar da yake son yi da yaron sai bai hanata ba, da kallo ya bita ganin yar car da ita a fuska amma mazaunanta sai wani kad'awa suke, lumshe ido yayi ya girgiza kai yana d'an lashe leb'e. Mayar da kallonshi yayi kan Munzeer da hankalinshi ke kan waya yace "Yau an fad'a min kun makara a zuwa makaranta da yamma? Me yasa?" Zaro ido yayi ya kalleshi ya girgiza kai cikin muryar yarinta yace "Abie inji wa? Mun isa akan lokaci fa, a can mukayi sallah la'asar." Murmushi ya masa jin ya amsa tambayar daidai ya d'ora da fad'in "To amma ai da kuka tashi an ce kun tsaya a hanya ko?" Nan ma da sauri ya girgiza kai yace "A'a Abie, bamu tsaya ba, ka tambayi dreba kaji." Jinjina kai yayi yace "To amma me yasa Aswan bai bayar da sallah ba yau a masallaci?" A tsorace yace "Abie ya bayar fa, ka tambayi su Anas kaji." Kallon tuhuma ya masa yace "Amma ba a gaban Heezam ya tsaya kula yaran unguwar nan dana hanashi ba?" Turo baki yayi yace "Abie ba kulasu yayi ba, sun mishi magana sai shi ma ya musu saboda yace ka fad'a mana ba kyau wulak'anta mutum." D'auke kanshi yayi yace "Me suka tattauna?" Jim yayi alamar tunani sai kuma yace "Gaisawa ne sukayi sai kuma ya fad'a musu zai shiga majalisi, shi ne sai wani yace shi ma yana so ya fara karatu tare da shi." Murmushin jin dad'i yayi yace "To me yasa yau a gidan akayi ta fad'a? Baka tsawatar musu bane?" Galala ya kalleshi sai kuma yace "Abie yaushe?" Kallonshi yayi yace "Kana nufin baka san lokacin ba?" Girgiza kai yayi yace "Abie babu wanda yayi fad'a." Kallonshi yaayi da zolaya yace "Halan yawo ka tafi?" Girgiza kai yayi yana dariyar jin kunya yace "A'a Abie, ban fita ko ina ba." Dariya yayi cikin farin ciki da jin dad'in babu abinda ya faru marar kyau bayan fitarshi, ban d'aki ya shige ya barshi da wayar a hannu yana ta latsawa yana buga game wanda dama saboda shi yake a wayar, shi ma kuma dan abune na wasa da ta wani fannin yana anfanar tunani da k'walwar yaro yasa ya barshi har yake bugawa lokaci lokaci. Ya d'auki lokaci sosai kafin ya fito rik'e da hannun Munzeer, dukansu zaune ya samesu har su Heezam da basu jima da shigowa ba, gaisheshi sukayi su ma ya amsa da fara'a har da tambayarsu darasinsu sanda suke zama kan table, Hafsat da Mimi ne suka tsaya zasu zuba abinci Mimi ta kalleta tace "Aunty ki barshi ma zan zuba." Murmushi tayi ta zauna tana aje plate d'in data d'auka, a nutse ta shiga zuba abincin ta fara ajewa gaban sheikh, kafin ta zubawa Hafsat da a lokacin ta kalli sheikh take fad'in "Sheikh gaskiya satin nan ina so na je na ga 'yata, wallahi kewarta hanani bacci take." Dariya yayi yana kallonta yace "Kewarta na hanaki bacci ne jiya na sameki kina ta juyi akan gado?" Dariya tayi tana rufe fuska da tafin hannu, jinjina kai yayi ya kalli Heezam yace "Ki shirya sai kuje tare da shi ya rakaki, idan kuma zaki je gobe to ki shirya mu tafi tare." Farin ciki ne ya bayyana a fuskarta tace "Kai amma naji dad'i, zan shirya goben sai mu tafi." Jinjina kai yayi yana kallon plate d'in gabanshi, shinkafa ce mai curry da jar miyar kaji, saidai yanda yaga naman a ido ya tabbatar masa da ya samu aiki mai kyau kuma zaiyi dad'i, ga k'amshin dake ta shiga hancinshi tunda ta aje gabanshi, kallonta yayi sanda take zuba wani a plate yace "Ryam." A ladabce ta gaggauta kallonshi tace "Na'am yallab'ai." Kallon plate d'inshi yayi yace "Da alama abincin nan ba zai isheni ba, a k'aro min gaskiya." Dariya sukayi dukansu ban da Aisha da Munzeer dake cakalar waya, ganin Mimi bata ce komai bayasa Hafsat fad'in "Allah gafarta ka jira ka cinye na gabanka mana." Kallonta yayi a marairaice yace "Na sani ne ba zai isheni ba, amma tunda kince haka shikenan." Kallon Mimi yayi yace "Ki rage min saura kinji." Jinjina kai tayi tace "Angama yallab'ai." Aje plate d'in tayi gaban Aisha dan girma ne take bi wajen zuba abincin, d'an ture plate d'in Aisha tayi ta yatsina fuska tace "Na k'oshi ni." Kallonta duk sukayi sai Mimi da tace "Kin k'oshi? Kin ci wani abu ne?" Kumburo baki tayi amma ba tace komai ba saboda sheikh dake wurin, Heezam daya gama lura da kallon da sheikh ke ma Aisha ne yayi saurin cewa "Aisha ki ci abinci mana." Kallonshi tayi tace "Na k'oshi na ce." Hafsat ce tace "Ku barta mana, cikin waye? Dan kanta." Kallonta Mimi ta sake yi tana k'ak'aro murmushi da tunawa da maganar Mama ta turawa Aisha plate d'in tace "Aisha ki ci abinci kinji, idan ni ce ba kya son girki na saina daina." Cikin b'acin rai Hafsat tace "Ki daina kamar ya? Nan ba gidan mijinki bane? Ke da ita waye yake da iko a gidan nan? Ita fa kwana kad'an ya rage mata a gidan, ke kuma gidan mijinki ne da muke muku fata har mutuwa, shikenan saiki daina girki saboda ita, wacece ita? Kar Allah yasa ta ci mana taga idan wani zai daina rayuwa akan haka." Sharrrr! Wasu hawaye masu zafi suka taho ma Mimi, dan wani iri take ji a zuciyarta kamar ta koma gidansu tayi rayuwarta cikin yancin, aje cokalin da take zuba miya tayi ta juya da sauri ta nufi hanyar da zata sadata da b'angarenta, tana shigewa ta fashe da kuka ta fad'a kan kujera. Suma suna ganin shigewarta sheikh daya rasa me ke masa dad'i ganin abinda ke neman kunno masa kai ya kalli Aisha, a tsanake ya shiga kallon duka yaran sai kuma ya jawo plate d'inshi da kyau ya d'auki cokali yana shirin d'ibar lomar farko yana fad'in "Mu ci abinci." Kallonshi sukayi duk sai suka tsargu, duk da basu san shi da duka ba amma sun san shi da fad'a, Heezam ne ya mik'e ya fara zubawa kanshi abinci hakan yasa Aswan jawo na gaban Aisha da tace ba ta ci. Kallonshi Hafsat tayi tace "Sheikh kuka fa take? Ka bata hak'uri dan Allah, karta damu da haukan yarinyar nan." Yi yayi kamar bai ji ta ba ya lumshe ido yana fad'in "Gaskiya abincin nan yayi dad'i." Cike da damuwa da kulawa Hafsat tace "Sheikh." "Um." Ya fad'a yana kai wata lomar bakinshi dan ji yake kamar ya tsinke harshenshi, a sanyaye tace "Dan Allah kayi wani abu a kai." Sake shareta yayi hakan yasa ta mik'ewa a hassale tace "Shikenan nagode." D'akin Mimi ta nufa dan b芒 ta hak'uri akan wautar Aishar. Ko kallonta baiyi ba har ta shige, cike da rashin jin dad'i Heezam ya kalleshi a ladabce yace "Abie." A k'asan mak'oshi yace "Ina ji." Cike da tsoro yace "Dan Allah kayi hak'uri." Kallonshi yayi da idonshi da suka fara canzawa alamar b'acin rai, aje cokalin yayi ya tallabe hab'arshi da bayan hannu yace "Hak'uri akan me? Wani laifi kukayi ne?" Kallonshi Aisha tayi kamar zatayi kuka tace "Abie dan Allah." Wani kallo ya wurga mata kamar zai had'eta, da nuna rashin damuwa yace "Me ye a ciki? Kuka ne take, ku barta tayi mai isarta ta k'oshi zatayi shiru dan kanta, idan kuma ta ji ba zata iya zama a haka ba ta tafi gidansu, iyakarta dai idan taje ta ce Abdul Waheed azallumi ne wanda bai san darajar aure ba, sai iyayenta kuma su ce ni d'in ashe dama tsohon banza ne da bai san mutumcin mace ba, sai mutanen gari kuma idan suka ji su ce ashe ni d'in babban mak'aryaci ne kuma mutumin banza wanda ya kasa tarbiya a gida, wanda yaranshi basu da tarbiya da sanin girman mutum, su d'ora da fad'in *dama ba'a aikin da abinda malamai ke yi, kawai kayi aiki da abinda suka fad'a maka*, shikenan idan aka fad'i haka? Kunji dad'i kenan?" Cokalinshi ya d'auka zai ci gaba da cin abinci yace "Matata ce ita ma, ko bana sonta ba zan wulak'anta ta ba, ku kuma 'ya'yana ne da babu yanda zanyi na rabu da ku, tunda ba kwa so na da aurenta shikenan, ku fad'a min da bakinku yanzun nan sai na korata gidansu na ci gaba da zama da uwarku kamar yanda kuke buk'ata." Heezam ne yayi saurin fad'in "A'a Abie dan Allah, ka yafe mana mun tuba." Kallonshi yayi sai kuma ya mik'e ya bar wurin duk da kuwa yana son cin abincin sosai saboda yana jin yunwa kuma ya masa dad'i. Heezam ne ya kalleta rai b'ace yace "Aisha kin gani ko? Kin ga kina so ki ja mana hushin iyayenmu ko? To wallahi ba zai yiyu ba." Mik'ewa yayi shi ma ya bar wurin, Aswan ma harara ya galla mata ya mik'e yana fad'in "Ai gwara ma da zai aurar dake? Haka kawai zaki b'ata mana sunan gida." Da kallo ta bisu baki sake sai kuma ta mik'e ita ma da sauri ta nufi d'akinta tana fashewa da kuka. Hafsat na shiga ta samu Mimi a falon tana kuka, da sauri ta k'arasa tana fad'in "Subhanallah! Mimi kuka?" Da sauri ta d'aga kanta tana share hawayen ta k'ak'aro murmushi, saida ta zauna kusanta suna kallon juna tace "Mimi kuka kike? Kiyi hak'uri dan Allah, wallahi ban san a ina Aisha ta d'auko wann..." Da sauri Mimi ta rik'e hannunta data dafa kafad'arta tace "A'a aunty, dan Allah karki bani hak'uri, ba ina kuka bane saboda abinda Aisha ta yi, kiyi hak'uri idan na d'aga miki hankali." A marairaice ta ci gaba da kallonta da tausayi tace "Mimi bana so mu shiga hakk'inki, ni kaina dake uwarta bansan a ina ta samo sabbin halayen nan ba, hakan yasa har na fara matsuwa a d'aura aurenta dan kar ta ja min wata maganar." Da mamaki ta kalleta tace "Aunty Aisha dama aure zatayi?" Jinjina kai tayi tace "E, ranar juma'a za'a d'aura aurenta." Sak'e tayi tana saurare sai kuma tace "Allah yasa alkairi." "Ameen." Ta fad'a a sanyaye, kallonta ta sake yi da kyau tace "Kin daina kukan yanzu?" Jinjina kai tayi tana k'ara share hawaye tace "Na daina aunty, karki damu." Murmushi ta mata ta mik'e tana fad'in "Saida safe, zan shiga na kwana." Da fara'a ta amsa da "Saida safe aunty." Da kallo ta bita har ta fita a d'akin, ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana jin lallai Allah ya had'ata da yer uwar data rasa, tana jin k'aunar Hafsat d'in har ranta kuma zata ci gaba da girmamata iya iyawarta. Hafsat na ganin falon ba kowa kawai ta girgiza kai ta k'ara gaban table d'in ta tattara kwanukan sannan ta zauna ta k'arasa cinye na ta, saida ta ji ta k'oshi tasha ruwa ta mik'e da plate din ta kai madafa sannan ta wuce d'akinta. Ta jima zaune a falon tana tunanin shin zata kama ma Aisha ne su zama abokan fad'an juna? Ko kuma dai ta nuna mata na gaba yayi gaba, ta nuna mata lallai fa ita d'in matar ubanta ce? Da wannan shawarar ta mik'e ta fita a falon, shiru babu alamar kowa kamar ba kowa a gidan, table ta wuce kai tsaye ta d'ibi abincin da zata iya ci ta koma falonta ta zauna, yaghourt ta d'auko da ruwa ta zauna ta dinga cin abincinta cikin nutsuwa, dan tun shekaran jiya da suka wuni gidan can sunyi waya da Rakiya ta fad'a mata ta dinga ci tana k'oshi hakan zai sa d'inkinta ya warke da wuri, tas ta cinye abinta ta sha yaghourt din nan kafin ta sha ruwa, d'auke kayan tayi ta mayar sannan ta dawo kai tsaye ta wuce d'akin baccinta, cire kayanta tayi ta shiga wanka. Saida ta fara zama a ruwan d'umi har ta laluba ta ji d'inkinta yana warkewa kafin tayi wankanta ta fito, bata shafa mai ba dan tana da jin zafi, humra ta shafe jikinta da ita sannan ta d'ora da shafa turarenta na kullum mukhallat, riga mai dogayen hannaye da wando dogo ta saka na bacci masu taushi ta haye gado bayan ta kashe wuta taja bargo ta tofe jikinta da addu'a. *11:00* daidai ya gama da karatun da sukeyi tare da su Anas ya shigo gidan bayan sunyi waya da mahaifin Anas d'in kan maganar aurensu da Aisha, yana shigowa ma ya rufe kowace k'ofa dan yasan kowa ya kwanta yanzun, k'ofar shiga d'akin Hafsat ya fara bud'ewa, yanda ya sameta tana bacci a wannan lokacin ya d'an bashi mamaki, sai kuma ya share kawai ya k'arasa a hankali, kusanta ya sunkuya ya sumbaci kuncinta tare da shafa kanta, k'ara gyara mata rufar yayi sannan ya kalli Munzeer dake gefenta shi ma yayi bacci, murmushi yayi ya shafa kan yaron sannan ya juya ya fita. Duka d'akunan yaran ya duba saidai dukansu babu wanda yake bacci, Aisha na karatun Alqur'ani sai Heezam dake ta cakular na'ura kasancewarshi mai son zama mahaddacin hadisai, sai Aswan kuma da littafinshi na islamiya, babu wanda ya ma magana a cikinsu saidai ya rufe k'ofar kawai ya yi gaba. D'akin Ryam ya wuce yana sakin murmushi saboda yarda da yayi lallai yarinta na damunta, a zuciyarshi kawai yake fad'in "Ban da abun Ryam ta ya zaki daina girki a gidan mijinki?" Yana bud'a k'ofar ya ga shiru falon ya rufe ya nufi d'akin baccin, yanda yake takawa cikin sand'a kamar marar gaskiya, yana bud'e k'ofar ya hangeta da alama tayi nisa a bacci, ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe ido, k'arasawa yayi ya zauna bakin gadon yana kallon fuskarta, yanda ta kumburo baki fuskarta tayi fes babu d'igon kwalli sai ta masa kyau, shafa lallausan gashin kan ta yayi mai sulb'in gaske, d'an rank'wafawa yayi ya sumbaci goshinta sannan ya rad'a mata a kunne "Ina sonki Ryam." Motsawa tayi kamar zata farka sai kuma ta sake lumshe ido, jim kad'an baccin ya sake figarta yayi gaba da ita, ganin yanda tayi kamar wata jaririya yasa shi sakin murmushi yana mik'ewa tsaye, doguwar rigarshi kalar ruwan k'asa ya cire tare da sibglet d'in shi, haurawa yayi kan gadon daga shi sai dogon wando yaja bargon ya shige ciki, jawota yayi jikinshi ya rumgumeta tsam. Kamar zaiyi bacci sai kuma ya zura hannunshi a rigarta ya fara shafa k'irjinta, lumshe ido yayi saboda abunda ke tsarga masa har kwanyar kanshi, a hankali ya fara fita hayyacinshi yana sauke wani marayan numfashi mai fitar da sautin gurnani, sosai ya fara rikitata a cikin baccinta, neman rabata da rigar ya neme yi hakan yasa ta farkawa a tsorace tana rarraba ido, suna had'a ido ta sake jawo bargon ta zuba mishi ido, jawoya ya sake yi jijinshi yana son sumbatarta a baki, zillewa tayi ta kawar da kanta a ladabce tace "Abdul." A k'asan mak'oshi ya amsa da "Ummm!" Saida ya kwantar da ita ya d'ora harshenshi a kan mamanta yana zagayawa da shi ya kalli fuskarta yace "Uhum." Marairaicewa tayi tace "Ka daina." Da shanyayyun idonshi ya kalleta yace "Saboda me? Ina so na raya dare na Ryam." Cikin shagwab'a ta b'oye fuskarta cikin bargon tace "Ban warke ba fa har yanzu." Tsam ya kalleta yace "Da gaske?" D'aga kai tayi alamar eh, yatsina fuska yayi yace "Amma ke kika fad'a min kinji sauk'i." Turo baki tayi kamar zatayi kuka tace "Gaskiya ban warke ba." Shafa cikinta yayi daya d'an taso saboda k'oshin da tayi har yayi sama da hannun zuwa nonuwanta, shafawa ya dinga yi tare da saka d'aya a bakinshi yana tsutsa a sanyaye, shiru ta masa tana saurarenshi jikinta har kakkarwa yake na tsoron abinda yake mata, dan ba zata tab'a mantawa da daren ranar laraba ba, dare na daya shiga tarihin rayuwarta, dare ne da sheikh Abdul Waheed ya kafa mata tarihi da ba zai gogu ba, ya bata wahalar da ita kanta tasan tayi juriya sosai data sauk'ak'a masa hukunci, dan haka a yanzu dai da wuri ba zata bari ya sak茅 saka mata wannan al'amari ba da a ranar ya kwana a cikinta ba, dan abu ne da kad'an ya rage ta ji shi a cikin bakinta, abu ne da idan ya zungurota har amai ke neman b'allowa ya taho mata. Wasa tayi nisa sosai sheikh yana neman gangarawa dan ya rabata da komai na jikinta haka shi ma, yana neman hanya madaidaiciya tare da d'orawa da addu'ar neman kariya kawai Mimi ta fashe da kuka ka rantse da Allah cizonta yayi, dakatawa yayi yana kallonta da jajayen idonshi ya fizgo kalamai kamar haka "La..fiy...ya?" Girgiza kai tayi tace "Kayi hak'uri sheikh kar kayi, wallahi akwai ciwo." Rintse idonshi yayi jim leb'enshi na k'asa a cije gam, ya d'an jima kafin ya bud'e ya kalleta ya had'a goshinsu har numfashinsu na gauraya yace "Ryam...ina cikin wani hali, dan Allah ki barni nayi...kinji, na kai matakin da ba zan..." Sai kuma ya had'a bakinshi da na ta da sauri yana tsutsa tare da ci gaba da saita hanyarshi, hannayenta tasa duka biyu ta rufe gabanta duk da k'azantar da take ji sharkaf a gaban na ta, a rikice ta nemi tashi zaune tana wani kukan na shagwab'a tana fad'in "Abdul wallahi ciwo zan ji, ban warke ba har yanzu." Kwantar da ita yayi da k'arfi ya kai hannunshi k'asanta yana fad'in "Bari na ji to." K'asa yayi da kan shi ya janye hannayenta ya d'an bud'e k'afafunta...馃槑 (gyara kimtsi). Sosai take kuka da hawayenta har da majina, salon da yake mata ya girmi shekarunta bare kuma tunaninta, a nutse ya dinga kashe mata da bakinshi, ko ina ya kai hannunshi kuma ya kai bakinshi, tun jikinta na yin lak'was dan sanyin har ta fara zabura tana jin kamar zata mayar mishi da raddin abinda yake mata, hakan yasa ta yin kuka dan ba zata iya sakin jikinta ta dinga mishi abinda yake mata ba. Wannan kukan data fara ne kad'ai yasa shi sarara mata ya barta haka bayan shi kanshi ya d'an samu nutsuwa, shafa bayanta ya fara yi yana fad'in "Shiiiiiii!" A hankali gumin da yayi ya fara tsanewa saboda acn dake kunne, sai kuma bacci daya fara neman d'aukarshi, da sauri ya jayeta daga jikinshi ya sauka a kan gadon, bakin k'ofar ban d'aki ya k'arasa ya d'auki towel ya d'auka a k'ugu sannan ya dawo ya d'auketa cak yayi ban d'akin da ita. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *48* Tunda tayi sallah asuba ta shiga madafa ta fara da dafa dankalin turawa, kafin su dahu ta fara yankan albasa da tamatir ta jajjaga tarugu ta aje gefe, k'wai ta buga adadin da zai isheta ta ajiye gefe shi ma, dankalinta na gama silala ta juyeshi ya rage zafi kafin ta fara b'are bayan, tana gama b'arewa ta yankashi k'anana ta aje gefe guda, k'wanta data buga ta gyarashi ta d'auki abun suyarta (frying pan, casserole) ta d'ora a wuta, tana d'aukar zafi ta zuba mai kad'an ko da yayi zafi ta d'auki k'wanta ta zuba, yana fara soyuwa daga k'asa ta d'auki dankalin nan ta zuba tasa cokalin katako ta juyeshi da kyau suka had'e tare da k'wan, saida ya soyu ta juyeshi a kwano mai rik'e zafi sannan ta ci gaba da soyawa, cikin d'an lokaci ta gama ta bud'a fridge ta d'auki zobon da Hafsat ke ajiyewa dafaffe kuma tattacce, zubawa kawai tayi a roba ta d'auki markadadden citta da na'a na'a da flavour ta saka, kokonbre ta d'auko ta wanke ta yankashi ta saka a blender ta markad'a ta tace a ciki kafin ta d'auki zuma ta saka kamar yanda Hafsat ta fad'a mata zuma suka fi aiki da ita, tana gamawa tasa a fridgr ta rufe sannan ta d'auki kular abincin ta kai akan table, madafar ta koma ta gyara komai kamar ba tayi aiki ba sannan ta wuce d'akinta dan har lokacin bata jin motsin kowa a gidan. *08:05* fitowarta daidai da fitowar Hafsat falon, suna had'a ido suka sakarwa juna murmushi inda Mimin tace "Aunty ina kwana?" Da fara'a sosai ta amsa da "Lafiya lau Mimi, antashi lafiya?" "Lafiya lau, ya k'arfin jiki?" Ta fad'a suna k'arasawa falon gaba d'aya, da sakin fuska ta amsa da "Alhamdulillah, ina d'aki ai ina jin motsi nayi tunanin ke ce, ban lek'o bane saboda ina d'aukin zan je asibiti ganin Khadija." Da yar dariyarta tace "Hakane aunty, dama abun kari na had'a." Saida ta aje jakarta kan kujera tace "Sannunki da k'ok'ari Mimi." Kallon k'ofar d'akunan yaran tayi tace "Ina su Munzeer ne? Ko basu tashi ba." Kallonta Hafsat tayi tace "Suna shirin islamiya ne, yanzu zaki gansu nan." K'ofar falon sheikh Hafsat ta kalla tace "Bari na duba yallab'ai na fad'a mishi na shirya." Jinjina kai tayi alamar to ta bita da kallo har ta shige, zaune tayi tana murmushi da mamakin yanda Hafsat d'in ke kula da jikinta kamar bata haifi Aswan ba ma bare kuma Aisha, dan masha'Allah yanda yaran sukayi jikin girma Heezam kan shi sai ya d'auki uwar ta shi idan aka shiga halin rintsi. Kuma ba komai bane ya kawo haka sai hutu da jin dad'i, sannan da gado, dan yanda ta ga Hafsat doguwa shi kanshi sheikh dogo haka Asas da ita kan ta Hajiarsu, da ma dayawa a cikin danginsu ya nuna dama can mutanen tsayi ne su d'in. Da sallama ta shiga falonshi tana sauke idonta akan kujerar da ta san ya fi zama a kai a wannan lokacin, a sanyaye ya amsa sallamarta tare da rufe littafi mai tsarkin dake hannunshi, saida ta k'arasa kujerar kusa da shi ta zauna tana sunkuyar da kanta tace "Barka da safiya yallab'ai." Da fara'a yana kallon fuskarta yace "Barka matar sheikh, kin tashi lafiya?" Da murmushi tace "Lafiya lau, ya himma?" Saida ya muskuta zai mik'e tsaye yace "Angode Allah, har kin shirya?" "Um." Ta fad'a a tak'aice tana kallonshi, mik'ewa yayi yana yar gajeruwar mik'a yace "Bari na gaggauta na shirya sai mu tafi, kinsan yau asabar babu aiki." Mik'ewa tayi ita ma tace "Idan muka dawo kenan ba zaka fita ba?" Saida ya nufi shiga d'akin na shi yace "E to gani dai, sai yanda kuka zab'a mana." Jin haka yasa ta yin jim kamar mai tunani, sai kawai tace "In kuwa hakane zaman gida ya kamace ka gaskiya." Murmushi yayi yace "Yanda kike so haka za'ayi yar aljanna." Shigewa yayi ita ma ta fita a falon dan bashi damar shiryawa a tsanake, tana zuwa ta samu Mimi zaune ta saki murmushi, haka kawai har zuciyarta ta ji ta bata tausayi, ba dan komai ba sai dan yanda ta ga yarinyar bata wani damu da kulawa da mijin na ta ba, kawai babu ruwanta da shi bare al'amuranshi, k'arasowa tayi ta zauna kusanta dan tana zzune ne kan kujera zaman mutum biyu, murmushi suka sakarwa juna inda Hafsat d'in tace "Sheikh na magana." Da sauri ta kalleta sai kuma ta mik'e tana fad'ad'a murmushinta tace "To." Nufa d'akin tayi da saurinta ita tsakani da Allah shi ne ke kiranta, da kallo Hafsat ta bita sai kuma ta ji wata suka a zuciyarta, d'auke idonta kawai tayi a kan ta tana fad'in "Allah kasa na fi k'arfin zuciyata." Fitowar yaran a d'akinsu yasa ta juyawa tanz kallonsu, kowanensu cikin kayan makaranta sun shirya tsaf, da yake sun gaisheta tun safe sai kawai tace "Ku hanzarta ku ci abinci ku wuce lokaci ya kusa." Gurin table d'in suka nufa suna aje kayan karatunsu, mik'ewa tayi ta fara zuba musu da kan ta dan yau asabar mai aiki bata zuwa, ita kanta ta yaba ta kuma fara amanna cewa Mimi k'arshe ce a fanin girki da kwalliya. Yaran kansu suna fara cin abincin saida suka yaba musamman ma Aswan, ita ma zaunawa tayi ta fara cin nata kafin sheikh ya fito su wuce. *Mimi* kam na shiga ban d'aki ta ji motsinshi yana wanka, d'an k'wank'wasa k'ofar tayi tare da fad'in "Kana magana ne?" Shiru yayi yana rarraba ido sai kuma yayi gyaran murya, turo baki tayi ta bubbuga k'afafu ta sake fad'in "To ni kayi magana ko na ji me kake so." Kashe panpon yayi tare da takowa ya zo ya bud'e k'ofar, jin motsin yasa ta zubawa k'ofar ido tana kallo, yana bud'ewa yaja k'ugunta zuwa ban d'akin da k'arfinshi, k'ara tayi lokaci d'aya kuma tayi shiru tana zazzaro ido, tabbatarwa dai babu komai a jikinshi yasa gabanta wani mummunan fad'uwa ta rintse idonta gam, had'a jikinshi yayi da na ta hakan yasa shaddar jikinta d'aukar damshin ruwan jikinshi, kallon fuskarta yayi yana kashe mata ido yace "Ya dai? Me kike nema?" Ba tare data bud'a ido ba cikin gigicewa tace "Ni fa wallahi, ni fa cewa akayi kana kirana, ban san wanka kake ba ai da ban shigo ba, yanzu dai kayi hak'uri ka sallameni to." Sake matseta yayi a jikinshi yace "Tunda har aka ce ina kiranki to hakane, aljanin daya fad'a miki haka bai miki k'arya ba, ina son wanda zai min wanka ne dama sai kuma ga ki." Da sauri ta bud'a ido tana ware bakinta tace "Dama akwai aljanu a gidan nan?" Lumshe ido yayi ya d'an jinjina kai kad'an yace "Sosai, kin tab'a ganin gidan malamin da babu aljanu?" Da k'arfin bala'i cike da gasgatawa tayi ram da k'ugunshi da hannayenta biyu ta d'ora kanta a k'irjinshi tana kukan shagwab'a tace "Wayyo Allah, Mama kin gani ko, saida na fad'a muku a'a amma baku saurareni ba." D'aga kai tayi ta kalleshi duk da alamunshi ya nuna yana gumtse dariyarshi ne tace "Abdul, ka rantse da Allah akwai aljanu a gidan nan?" Bushewa yayi da dariyar daya rantse da Allah ya shekara baiyi irinta ba, shi wai ya rantse da Allah? K'yalk'yala dariya yake sosai har da sakinta yayi yana ja baya, kamar sakara ta bi shi da kallo da mamakin me yake ma dariyar? Saida yayi mai isarshi ya tsagaita yana kallonta yana girgiza kai, da k'yar ya iya fad'in "Da gaske Ryam, kina so na kira miki autansu yanzu ya zo ya gaisheki?" Matsawa tayi daf da shi ta shiga d'an jujjuyawa tana kallon ban d'akin. Rumgumeta yayi a jikinshi yace "Ryam ba yanzu ba fa, saida dare suke shawaginsu." Kallonshi tayi tace "Abdul tsoro nake ji, ina tsoron marin aljani fa." Shafa bayanta yayi da sigar rarrashi yace "Haba wa ma ya isa? Wane marar kunyar aljani ne zai mari amaryar Abdul a gidan?" Sake lafewa tayi a k'irjinshi tace "To ka daina tsorata ni ka ji." Jinjina kai yayi alamar to, d'agata yayi daga jikinshi yana kallon fuskarta yace "To za'a min wankan yanzu?" Da sauri ta kalleshi ta zaro ido tace "Wa? Ni d'in?" Da gudun tsiya ta juya ta bar ban d'akin tana rufowa tace "Ban iya ba Abdul." Da dariya ya bita yana kallonta yana jin kamar shi ma ya shek'a da gudu, hakan yasa shi jin ina ma su kad'ai ne a gidan ai da sai yayi koyi da fiyayyen hallita da matarsa Nana Aisha, amma duk da haka ba komai zai jira ya samu wata damar zai d'abbaka wannan sunnar ita ma. Yana fitowa a gaggauce ya shirya yace Mimi ta kawo masa abun karinsa, falon ta samesu su ma suna ta hanzarin gama na su karin, a nutse ta d'auki plate ta fara zuba soyayyen k'wan da dankalin, yanda ta zuba shi a plate d'in yayi kyau a ido ma, kafin ta d'auki robar yaji ta d'an zuba kad'an ta d'auki mayonnaise shi ma ta zuba a gefe, sai Hafsat ta samu kanta da kallonta dan ita data zuba ma yaran duk bata zuba wannan abubuwan ba, saboda bata d'auka haka ake zubawar ba ma, wani plate ta ga ta d'auka ta rufe da shi sannan ta d'auki juge d'in lemun ta d'ora a babban faranti sannan ta nufi d'akin na shi, suna ganin shigewarta suka mik'e suka ma mahaifiyarsu sallama suka bar gidan. Da sallama a bakinta ta shigo yana tsaye yana gyara mab'ullan hannun rigarshi, aje farantin tayi ta k'arasa kusa da shi ta kama hannun na shi ta shiga gyara mishi, murmushi ya mata yace "Nagode." Ita ma murmushin tayi tace "Sheikh." Zuba mata ido yayi cikin sangarta yace "Ryam." Kallonshi tayi saboda shagwab'ar da ta ji yayi sai ya bata kunya, d'orawa yayi da fad'in "Na fad'a miki'a fi so naji sunan Abdul daga bakinki, fad'in sheikh baya miki kyay ko kad'an." Cikin rangaji da rausaya tace "To Ab-dul." Murmushi yayi saboda yanda ta ja sunan yace "Ina jinki." Cikin shagwaba da turo baki tace "Ina so na ga Mama na da Abba na da su Yaseen, zaka kaini?" Girgiza mata kai yayi yace "Um um! Amarya bata fita sai ta kwana biyu." Da sauri tace "To amma ai ni na kwana uku a gidanka." Dariya yayi yana girgiza kai yace "Ba irin wannan kwana biyun ba, ina nufin sai kin jima." Bubbuga k'afafu ta fara yi a k'asa tana kuka tana fad'in "Ni dai wallahi sai na je." Da mamaki ya kalleta yace "Sa茂 kin je? Ta ya ya?" Kallonshi tayi tana kumburo baki tace "Kana fita ni ma zan tafi, tunda ai na fad'a maka kai ne baka barni ba." Kyalkyalewa yayi da dariya ya nufi wajen farantin data aje yace "To ki je ga hanyar nan, ina dawowa aljanuna zasu fad'a min kin fita ba da izini na ba." Matsawa tayi kusanshi a marairaice tace "Yanzu Kenan ba zaka barni na tafi ba? Gidanmu ne fa? A can ka d'aukoni ko ka manta ne?" Girgiza kai yayi yana jefa lomar farko bakinshi, lumshe ido yayi yace "Uhummm! Ryam wai a ina kika koyi girki ne?" D'an hararanshi tayi irin ranta ya b'acen nan tace "Ban sani ba nima." Hanyar fita ta nufa yayi saurin cewa "Ina zaki je?" Juyowa tayi tace "To miye na ka a ciki? Ba ka hanani ganin iyayena ba." Ficewa tayi a d'akin ya bita da kallo yana cin abincin shi, murmushi kawai yake saki a zuciyarshi yana fad'in "Da alama sai na koma makaranta dan na k'ara fahimtar yanda ake zama da yara irinki." A gaggauce ya gama cin abincin ya mik'e ya fita ya samu Hafsat na jiranshi, basu b'ata lokaci ba suka fita a gidan, a hanya ita ma Hafsat ke fad'in "Sheikh na wa dan Allah me zai hana idan kayi niyya ka aje ni wajen Hajia, ina so zamuyi magana dasu akan auren Aisha ne." Wani kallo ya watso mata yace "Idan banyi niyya ba fa?" Murmushi tayi tace "Dan Allah kayi niyya to." Dariya yayi ya dangware mata kai yace "Ja'ira." Murmushi ta sake yi tace "Sheikh na wa." Shi ma murmushin yayi yace "Hafsat ta wa." Da haka suka isa asibitin suka shiga ciki, saida aka fara killacesu aka basu kayan kariya suka saka har da takalmi da hula duka suka rufe jikinsu kafin aka shiga dasu d'akunan da yaran suke, ba'a barsu sun shiga ciki ba daga k'ofa kawai ta madubin k'ofar suka iya hangen yarinyar dake nad'e a cikin farin bandeji da oxyg猫ne a hancinta a cikin kwalba. Wata ajiyar zuciya Hafsat ta sauke mai k'arfi tare da lumshe ido, hakan yasa hawaye sauko mata a kumatu cike da tausayin yar ta ta, jawota sheikh yayi ya rumguma a jikinshi yana fad'in "Kiyi hak'uri kinji, yar ki zata warke har ma ki ganta tana gudu a gabanki." Cikin shsheka tace "Allah ya yarda sheikh." "Ameen." Ya fad'a yana kallon yarinyar shi ma yana jin wani imani da tsoron Allah na k'ara shigarshi, wannan kad'ai idan ka gani zai k'ara maka tsoron Allah a zuciya. Suna barin asibitin gidansu Hajia ya sauketa ya wuce sabgar gabanshi, saidai Ryam na zuciyarshi da tunanin rabuwarsu ta safiyar yau, hakan yasa shi saka dreban Hajia Kabiru ya je gidansu ya d'auko su Yaseen ya kaisu gidan, yasan hakan ne kawai zai faranta mata rai. Tana falonta ta dinga jin muryar Yaseen da Amir suna ta sallama, ai da gudu ta taso ta bud'e k'ofar ta fito, tana ganinsu da farin ciki ta k'araso tana fad'in "Yaseen, Amir, Ku ne dama?" Rumgume Amir tayi ta zauna k'asa tana kallonsu suna ta washe mata baki suna k'ara daga kai suna kallon gidan, gaisawa sukayi sosai kafin su fad'a mata wanda ya kawosu da wanda yasa a kawosu, murmushi kawai tayi tace "Abdul kenan, ni ce ba zai bari na fita ba." Da mamaki Yaseen ya kalleta yace "Abdul fa kika ce? Mimi sheikh d'in?" D'an kyaci tayi alamar kai share dallah tare da mik'ewa tace "Me kuke so na dafa muku?" Da sauri Amir yace "Miyar nama da shinkafa." Tintsirewa tayi da dariya ta dunguri kan shi tace "Amir kwadayi ko?" Dariya suma sukayi suna kallo ta wuce madafar, aiki ta shiga gadan gadan na gaba daya gidan, cikin nutsuwa da hankali ta kammala girkinta mai rai da lafiya, saida ta kwashe kamar yanda take yi kwana biyun nan sannan ta zubawa su Yaseen ta kawo musu, tare da ita suka ci a kwano daya a lokacin 12:00 tayi, mik'ewa tayi ta gyara falon sannan tace su wuce falonta, su Aisha na dawowa daga makaranta basu samu Hafsat ba, saida sukayi wanka sukayi sallah sannan suka ci abinci, ban da Munzeer babu wanda ya je inda take, ita ma tana falonta tare da kannanta suna ta kwasar hirarsu. 04:07 Kabiru ya dawo d'aukarsu dan dama Mama ta ce su dawo dan su tafi islamiyya, tare suka fito tana rik'e da ledar kayan makulashen data siyo ranar zata basu, suna fita farfajiyar su Aisha na tsaye jiran drebansu su ma zasu tafi islamiyya, da wani kallon raini ta shiga bin su Yaseen Wanda tsaf a idon Mimi hakan kuma ya mata ciwo. Da mutumtawa su Heezam da Aswan suka gaisa dasu Yaseen har Aswan na d'an tsokanar Yaseen ma dan suna had'uwa da shi a babban masallacin Kaddafi wajen karatun sheikh. Wucewa sukayi ta bude musu k'ofar motar zasu shiga, taimakawa Yaseen tayi ya shiga ya zauna dan tsayinshi bai kai ma, zata d'auki Amir ta saka kawai Aisha tayi yar dariya tare da fad'in "Sunan wata waina wai ita 'yar k'unbu." Sake fashewa tayi da dariya, da k'arfin bala'i Mimi tayi kan ta bata ankara ba ta kasheta da mari tare da shak'ar wuyan hijabinta ta had'ata da bango. A kid'ime kuma a tsorace duk suka kalleta suna zaro ido, kallonsu suka tsaya yi cirko cirko kowa cikinshi ya d'uri ruwa, cikin b'acin rai da fitar hayyaci tace "... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *49* Cikin b'acin rai da fitar hayyaci tace "Ke Aisha wacece ke da zaki raina min yan uwa? Akan wane dalili ne zaki shammaci halittarsu? Saboda ina auren ubanki ne?" Turata tayi da k'arfi har saida kanta ya bugi bango ta d'ora da fad'in "Zaki takani yanda kike so a gidan nan na k'yaleki, amma idan kika ce zaki tab'a iyayena ko yan uwana wallahi kutumar ubanki zan ci a gidan nan saidai uban ki ya sakeni." Juyawa tayi har zata nufi wajensu Yaseen sai kuma ta juyo ta kalleta tace "Ba kiyi kama da yar Abdul ba, sam halayenki basu dace dana wacce ta fito a tsatson Abdul da Hafsat ba, kaiconki wallahi, kuma fa duk wannan abun da kike yi kina yi ne saboda na auri Abdul ko?" Yatsina fuska tayi tace "Mun riga da mun zama d'aya Aisha, zan fad'a miki wani abu kuma wanda na tabbatar cikin biyu za'ayi d'aya tunda ke ma aure zakiyi, ko dai mu haihu tare da ke, ko kuma na rigaki haihuwa dan tsohonki ya jima da tura sak'onshi kuma na karb'e da hannu bibbiyu, mu zuba ni da ke a gidan nan tunda kin kasa fahimtar a yanzu ni ma d'in uwarki ce tunda na gauraya da ubanki ." Sama da k'asa ta bi ta da harara ta wuce zuwa wajen su Yaseen da sukayi tsuru suna kallonta, saida suka fita a gidan ta juya ta koma ciki ko kallonsu ba tayi ba, Aisha kam ta cika kamar zata fashe ta kawo wuya, Heezam kam girgiza kai yayi yace "Kin ga irinta ai, gobe ma ki k'ara." Aswan ma murmushi yayi yace "Gaskiya ta fad'a miki, sam bakiyi kama da yar gidan nan ba." Odar da sukaji tasa su fita da sauri amma ban da Aisha da take tafiya kamar wacce k'wai ya fashe ma a ciki, kalaman Mimi sun tsaya mata sosai a zuciya, musamman yanda take kiran sunan mahaifinta ba girmamawa Abdul gatsau, saida suka shiga mota sai kawai ta fashe da kuka kamar wacce aka k'wak'ulewa ido. Har suka isa islamiya tana kuka bata daina ba, a aji ma ba abinda take sai shashek'a, shiyasa ma ana tashi daga islamiyar ko da dreba ya d'aukesu bai tsaya ko ina ba gida ya diresu. *Tun* fitarsu dama sunyi waya ita da sheikh suka sha hirarsu ta soyayya, Hafsat ma a can ta wuni sai yamma lik'is ta dawo daf da lokacin tashinsu, tunda sheikh ya dawo da ita kuma bai fita ba yana gida, hakan yasa suna shigowa falon da sallama sun samesu dukansu a falon. Sheikh na tsaye zai shuge b'angarenshi ya dakata saboda jin shigowarsu, Mimi ta fito daga madafa rik'e da kofi a hannunta ta kawowa Hafsat shayin da tayi na goruba, Hafsat d'in kuma na zaune kan kujera. Kusan a tare suka amsa sallamar yaran duk suna kallonsu, da sauri Hafsat ta mik'e gabanta na fad'uwa saboda ganin fuskar Aisha, idonta sun k'ank'ance sun kumbura abu ga jar fata, fuskarta ma duk tayi wata kala tsabar kuka sai shatin yatsun daya zauna a kuncinta, dan marin da Mimi ta mata a bazata ne ya zo kuma da mugun k'arfi, da hanzari ta tarbeta tana fad'in "Aisha lafiya? Me ya sameki?" Sake sinne kai tayi tana ci gaba da shashek'ar kuka, hankali tashe ta kalli su Heezam tace "Kai me ya sameta? Fad'a tayi ne? Ko wani laifin tayi da aka daketa a makaranta?" Aswan ne ya turo baki ya girgiza kai alamar a'a, sai Heezam daya d'aga kafad'a shi ma alamar uhum! Muryar sheikh ce ta dakesu a bayansu yace "Munzeer yaro na." Cikin d'aga sauti Munzeer yace "Na'am Abie." Ya fad'a yana nufa inda yake tsaye, kusanshi ya tsaya ya shafa kanshi yace "Shi ne bayan bana nan tayi fad'a ko?" Da sauri Munzeer yace "A'a Abie, aunty Aisha ce ta yi wa aunty Mimi rashin kunya, shi ne ta mareta a fuska kuma ta zageta." Tsuru tsuru duk suka zubawa Mimi ido da ita ma ta kafe Munzeer da ido, amma data ga kallon da suke mata sai kawai ta d'auke kan ta tare da aje kofin shayin hannunta akan k'aramin table d'in ta dafe k'ugu alamar tana jiran a yi duk wacce za'ayi. Hafsat ma d'auke kanta tayi daga Mimi ta kama hannun Aisha da k'arfi suka nufi d'akinta cikin hushi, ganin haka sai sheikh ma ya bi bayanta dan gaskiya baya son b'acin ran Hafsat musamman ma da ita d'in macece da bata cika saurin nuna b'acin ranta ba, Mimi na kallo suka shige d'akin tana tsaye zuciyarta na tafasa tana jin kamar bak'uwa ce ita a gidan nan, kamar bata da wani galihu ko mutumci. Had'e hawayenta tayi tare da wani abu daya tsaya mata a wuya ita ma t shige d'akinta, saidai zaune tayi a kujerar falo zama irin na jiranka kawai na ke ka zo a yi ta ta k'are, ka zo ayi duk wacce za'ayi amma ba zan d'auka ba. *A* d'aki kuma yana shiga Aisha na zaune bakin gado Hafsat na tsaye a kan ta tana d'an tab'a fuskar ta ta, da sauri ta juya ta kalleshi cikin hushi da b'acin rai tace "Akan me zata marar min yarinya? Ni ko kai akwai wanda ya tab'a dukansu ne bare kuma mari a fuska mai daraja, fuskar da ubangijinmu kad'ai muke turmusata a k'asa dan bauta masa, me ta mata da zata mareta haka har hannunta ya kwanta a fuskar yarinya?" D'auke idonshi yayi a fuskar Hafsat d'in ya kalli Aisha yace "Me kika mata?" A tsorace ta kalleshi cikin shakakkiyar murya tace "Abie ban mata komai ba, kawai daga zata raki k'annanta da suka zo, daga sun wuce nayi murmushi shi ne kawai ta mareni, har zagina ta dinga yi tana ambatar sunanka da sunan Amie tana fad'in wai ita ma matarka ce kuma zata..." A tsawace yace "Shiru!" Shiru tayi tana kallonshi tana sauke ajiyar zuciya, da mamaki Hafsat ta kalleshi tace "Tsawa ma kake mata? To wallahi ba zan d'auki wannan wulak'ancin ba, nayi hak'uri akan abubuwa da dama sannan na shanye b'acin rai bila-adadin, amma ba zan tab'a d'aukar cin zarafin 'ya'yana ba." Kusa da shi ta matsa tana kallon idonshi tace "Ka fad'awa matarka karta sake sauke gigin haukarta akan yarana, inba haka ba wallahi da kaina zan d'auki mataki." Tana fad'a ita ma ta shige ban d'akinta dan samo ruwan d'umin da zata gasa mata fuskarta data kumbura. Kallon Aisha yayi ya girgiza kai yace "Allah ya kyauta." Fita yayi a d'akin shi ma ya nufi d'akin Mimi, tana ganin ta mik'e dan cike take da bala'i ita ma, saida ya tsaya gabanta cikin halin ko in kula yace "Me ya had'aki da Aisha? Shin baki san 'yarki bace ita da zaki zauna d'aukarwa kanki raini a wurinta." A gadarance ta yatsina fuska tace "Sanin haka yasa ni gaggauwar d'aukar matakin dakatar da rainin da take son d'ora min saboda na tuna mata ni ma uwarta ce." K'ank'ance idonshi yayi yana kallonta da mamaki yace "Shiyasa kika d'aga hannu kika mareta?" Rumgume hannaye tayi a k'irji tace "E, saboda ta raina min yan uwa, ni kuma ba kowane raini nake d'auka ba." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Na ji to kiyi hak'uri, Aisha ba zata sake miki rashin kunya ba na miki wannan alk'awarin." Shiru tayi tana wani kumbura baki ba tace komai ba, matsawa yayi kusanta ya rumgumota jikinshi yace "To saki fuskar mana, ko sai na had'aki da aljanuna?" Da sauri ta saki hannayenta daga rumgumesu da tayi a k'irjinta tana dariya tace "A'a Abdul karka kirasu." Dariya yayi shi ma ya rad'a mata a kunne "Ko ke fa, bana so irin wannan hatsaniyar na d'aga min hankali a gidan nan, kamata yayi ki nuna musu ke ma fa gyatumarsu ce." Dariya ta k'yalk'yale da ita ta d'aga k'afafunta sosai ta rad'a masa a kunne cewa "Shiyasa nake so na kama girmana, dan ni d'in ba matar yaro bace." Dariya yayi ya bata hannu alamar su bige yana fad'in "Gaskiya ne matar old man." Farin cikonsu suka ci gaba da yi kamar babu abinda ya so faruwa yanzun. Saidai a daren bayan fitar sheikh da su Heezam zuwa masallaci, Hafsat da Aisha basu fito cin abinci ba, Mimi kuma bata damu ba hasalima ita ma tana b'angarenta, sai kusan 10:54 na dare suka dawo gidan, da kan ta ta zubawa su Aswan abinci suka ci sannan ta d'iba ta kai wa sheikh falonta shi ma ya ci. Saida kowa yayi bacci a gidan baka jin komai sai k'arar panka da ac, a lokacin sheikh ya mik'e ya nufi d'akin Aisha, cikin nutsuwa ba tare da tunanin komai ba ya bud'a k'ofar d'akin, ganinta kwance akan gadon tana bacci a nutse ba k'aramar salama ya sama mishi a zuciya ba, dan sosai yake tsoron zamanin nan da mutanen cikinshi, k'arasawa yayi gaban gadonta ya tsaya ya daddab'ata, cikin magagi ta bud'a ido ganinshi yasa ta yin zunbur ta tashi zaune tace Abie?" Yanda ya tsaya gabanta k'ik'am yasa ta sauka daga kan gadon tana lalubar hijabinta kan gadon, sakawa tayi ta b'oye rigar baccinta tana zaunawa k'asa. Zaune yayi bakin gadon ya had'e hannayenshi yana kallonta, saida ya gama mata kallon tas kafin ya d'aga hannunshi ya kwad'a mata mari, a gigice a rikice ta dafe kunci tana sakin k'ara. Kallonshi tayi tana sako hawaye inda shi kuma ya nunata da yatsa cikin taushin murya yace "Wannan marin dana miki tun ranar da kika ma Mimi rashin kunya da safe ya dace na miki shi, ya kamata ki sani ita ma uwarki tunda ni ke aurenta, darajar aure ya siya mata darajar da zaki kalleta kamar uwa, addininmu ya koya mana yanda zamu mutumta d'an adam ko baka san shi ba bare wanda kake da alak'a dashi." Kama kunnenta yayi a cikin hijabin cikin sigar fad'a yace "Aisha har na zauna na nuna ga yanda za'ayi saboda gudun matsala amma ke ki nuna ba haka, da kika ma yan uwanta fitsara me kike so ki nuna musu kenan? Ke *tantiriyar gidana ce*? Haka kawai zaki tarwatsa min farin ciki da zaman lafiyar gida, tunda kike kik tab'a ganin b'acin ran mahaifiyarki a zahiri? Ko kin tab'a ganin ta kalli idona ta fad'a min abinda ke ranta kai tsaye? Sai yau kuma duk a dalilinki." Jinjina kai yayi sanda take neman tashi daga zaunen tana rik'e kunnenta tana fad'in "Abie zafi zafi, kayi hak'uri na tuba wallahi." Mik'ewa yayi ya sake nunata da yatsa yace "D'aurin aurenki ba fashi Aisha ranar juma'a, ko ki shirya ma hakan ko karki shirya duk d'aya, amma ki sani kin fara sani tunanin ko dai kin san me aure yake nufi shiyasa kike kishi da wata wacce kike ganin ita ma ta rab'i jikin ubanki, to koma a ya ya dai kika d'auka ki sani hakan ne." Yana fad'a ya wuce ya barta nan tana wani kukan tare da gyara zamanta a k'asan ta had'a kai da gwiwa. Daren yau ma sheikh ya so ratsa gonar Mimi amma ta buga kai k'asa tace bata warke ba, dole ya hak'ura ya d'anyi wasa da ita kamar dai jiya sannan yayi wanka ya shiga karatun Qur'ani. *Da* safe ma haka yara suka shirya suka fito, saidai Aisha kai tsaye ta wuce farfajiya sai su Aswan ne suka tsaya suka karya kumallo, suna gamawa suka fita Mimi na musu a dawo lafiya, saida suka fita ta nufi d'akin Hafsat da sallama a bakinta, zaune ta sameta bakin gado da wayarta a hannu, k'asan mak'oshi ta amsa sallamarta, bata damu ba haka ta k'araso tsakiyar d'akin tace "Aunty Hafsat abincinki na ce ko na kawo miki nan? Na ga baki fito ba yau." Yatsina fuska Hafsat tayi tace "A'a ki barshi ma na k'oshi." D'an satar kallonta tayi sai kawai ta jinjina kai tana murmushi tace "Shikenan, na barki lafiya." Fita tayi a d'akin tana jinjina kai a ranta tana fad'in "Ku kaini bango kuka aiki da cikawa." Fita tayi ta kai wa sheikh na shi abinci yana gama ci sukayi sallama ya fita. Haka har rana ta dora girki ta gama bata ga Hafsat ba sai zuwan yaran daga makranta ta dinga jin hayaniyarsu a d'akinta, tana gama aikinta ita dai ta shige d'akinta uta ma da abincin dan tayi niyya bama zata fito ba sai yamma in zata d'ora girki. *Dare* ma haka suka kasance kasancewar sheikh bai shigo da wuri ba Mimi ta nemi su ci abinci, kowa ya zo amma ban da Aisha da Hafsat, saida ta gama zubawa su Heezam ta kallesu tace "Ina zuwa, bari na kira aunty." Jinjina mata kai sukayi alamar to, tana zuwa ta fara k'wznk'wasa k'ofar tana sallama, jin ta amsa yasa ta turawa a hankali ta shiga, da ladabi tace "Aunty Hafsat ina kwana?" "Lafiya lau." Ta amsa ba yabo ba fallasa, sharewa Mimi tayi tace "Abinci na ce ko zaki ci?" Yatsina fuska tayi tace "Um um! A ci lafiya." Ita ma yatsina fuskar tayi ta juya dan fita, k'wafa Hafsat d'in tayi ta jin haushin takurawar Mimin, juyowa Mimi tayi cike da shak'iyanci tace "Magana kike?" A gatsala ita ma tace "Kika ji nayi?" D'aga gira tayi tace "Ok, Allah ya kyauta." Juyawa tayi amma dake Hafsat dama can fin k'arfin zuciyarta ne takeyi sai kawai tace "Ke! Rashin kunya zaki min?" Juyowa Mimi tayi cike da rashin tsoro tace "Rashin kunya kuma? Kika ga alama zan miki?" Sai kuma ta gyata tsayuwarta tace "Wai tsaya, ko dai haushina kike ji saboda na daki 'yata? To ai ke ma na ga kamar uwa kike gareni kina iya rama mata." Mik'ewa tayi tsaye ta nunata da yatsa tace "K'arya kike wallahi, Aisha ba 'yar ki bace, da 'yarki ce ai da baki mareta a fuska ba, saboda baki san darajar haihuwa ba." Bushewa tayi da dariya tace "Haihuwa? To ai ban tab'a yinta bane shiyasa, amma kwana nawa ne ya rage ni ma na haifo nawa." Ta fad'a tana shafa mararta, girgiza kai Hafsat tayi tace "Dama da ganin idonki zakiyi fitsara, to ki ji da kyau karki k'ara dukar min yarinya dan b芒 jakarki bace, da fari na so baki girma da darajar da zasu dinga kiranki da Amie, amma tunda baki da mutumci na fasa." Gaba d'aya jikin Mimi ne yayi wani irin sanyi har tsakiyar ranta ta ringa jin wani iri, yau gata ta daki yarinyar data mata rashin kunya a kan gaskiyarta amma mahaifiyarta da take jin k'aunarta a zuciyarta tamkar 'yar uwarta har tana jin ta samu 'yar uwa ta kalleta ta wulak'antata a kan hakan, anya kuwa idan jininta ce koma ta ce idan 'yar uwarta ce ko zane mata 'ya ta yi zata kula? Zata d'aga kai ta kalleta? Duk da zamani ya cenza amma akwai na kirki har yanzu, akwai zumunci har yanzu. Shin Hafsat bata ganin irin abinda 'yarta ke yi ta katseta tunda wuri ko hakan na mata dadi? Shin Hafsat so take su fara zaman kishi da juna ko menene? A matsayinta na babba, babbar ma wace ta san ba haka kawai ta d'auko kanta ta kawo gidan mijinta ba a ganinta ya dace ta mata adalci. Muryarta a sanyaye ta d'ago tana kallon Hafsat cikin ido tace "Allahn da ya baki aunty nima bai manta da ni ba, kuma ina rok'onsa idan ya tashi bani ya bani masu tarbiyar da ko da Abdul na da damar k'ara wani auren nan gaba su kirata da Amie, bare kuma ke, ke ina so yarana su kiraki da Mama, haka kawai na ga kin isa ki zama uwarsu dan a d'an zaman da na yi da mijinki sai nake ji da kuma ganin girma da darajar wani ma wanda ya rab'e shi bare matar daya hayayyafa da ita." Suna tsaka da muhawarar nan sheikh ya shigo, rashin sa'a kuma shi ne daidai Mimi ta kuma sakin wani murmushi tana girgiza kanta ta bud'i bakinta zata yiwa Hafsat wata maganar wacce Hafsat d'in kuwa gaba d'aya yanayi na b'acin rai ya saka har wata k'walla da b'acin rai sun nuna a tare da ita, uwa uba a yau idonnta ko kwali babu tsabar ta sakawa kanta damuwa bayan ba haka Hafsat take ba, hakan ya saka hankalinsa tashe ya kuma nazartarsu kafin muryarsa kamar a d'an kausashe yace "Ryam, rashin kunya kika zo har d'aki kike yi wa matata ko me? Shin rashin kunya kike yi wa Hafsat? Kin kuwa san zan iya take komai na had'iye komai na danne komai amma banda cin zarafin uwar gidana? Kar na ji, kar na gani kar na ji kar na gani ko da wasa kar ki saki ki kuskura na kama ki da y iwa matata fitsara domin zaki yi mamakina Nana." Da mamaki take kallonsa, yanayi na yarinta da d'anyen kai da b'acin rai ne ya sakata kuma kallonsa idanunta a bayyane tace "Wato ni ga matar kutse ko Abdul? Ni matar haye? Allah ya sa nima ce min aka yi jeki ga mijinki ba hauka nake a kanka ba bare daga kai har matarka ku wulak'antani!" Ta karashe tana mai danne muryarta dake rawa sakamakon b'acin rai da kukan dake son k'wace mata. Ransa ne ya b'aci saboda jin ya ya zata ringa maida masa magana ta wani siga wai kenan shi ga sakarai shi da bata so ko? Ransa b'ace ya nufota yace "Me kike nufi da maganarki? Kenan kina so ki nuna ni d'in banza wofi ne a wurinki? Ya zaki nemi raina min matata na miki magana kuma ki nemi yi min fitsara." Cikin d'aga murya da kwaratsi Mimi ta ja baya tace "Ya isa! Ya isa haka." Kallonshi tayi tana sako hawayen da take rik'ewa tace "Kowa sai ya dinga kirana da fitsararriya ko marar mutumci, to na gaji kunji na fad'a muku, idan zaman gidan nan ba zai yiwu ba ka sallameni na tafiya ta mana, a'ah, wai ana dole ne?" Da wani irin sauri ya kai hannu zai shak'o wuyanta ya gaura mata mari, sai kuma ya tsaya tare da dunk'ule hannunshi yana kallon fuskarta, girgiza kai yayi ya feso iska dan maganar sakin nan na tab'a mishi zuciya wallahi, kai dole ma ya zauna zama na musamman da ita ya nuna mata babu kyau abinda take fad'a, wani numfashi ya kuma saukewa yana ci gaba da kallonta yace "Ryam ban tab'a dukan mace ba, ba zan fara yau ba, amma ki sani ita mace da kika gani kamar abun tuk'i ce, idan har kika zamar min mummunan abun tuk'i har tuk'inki ya k'wace min zan zama sakarai kuma malalaci, a gaskiya ba zan bari haka ta faru ba." Ja baya yayi sosai ta yanda yake hangensu tsaye dukansu kuma yana kallon kowace yace "Na yardaina sonki ne daga lokacin da muka fara zama a matsayin ma'aurata, soyayyata ta farko gareni na farata, k'aunarki na gaba d'aya zuciyata saboda ke d'in nan ke ce b'angare na jikina, zubar hawayenki ba k'aramin d'aga min hankali yake ba, karki so kiji yanda zuciyata ke bugawa musamman dana shigo d'akin nan na fahimci ba kya cikin farin ciki, ina son ki, na fad'a miki haka bila-adadin, ki yarda, ki yarda da ina sonki kinji." Kamar shed'an nan da aka tofawa a'uziya haka duk suka zuba mishi ido sukayi tsuru, kowace tana d'aukar kalamai tana d'orasu a muhalli, saidai kuma wani b'angare na zuk'atansu na sa musu wasi-wasin da wa yake a ciki? Musamman Mimi da tafi raja'a ce wa da Hafsat yake, a wajen k'arshen ne kawai zata ce da ita yake dan yana yawan fad'in yana son ta kuma ta yarda. hafsat kam ta yarda tabbas da ita yake, tafi kokonton me yasa bai tsayar da kallonshi kan ta kawai ba. Mimi kam juya baki tayi tace "Ni da ba'a so sai naje na nemi mai sona ai." Tsai yayi yana kallonta, "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Ya fad'a a zuciyarshi, wallahi wani irin gudu zuciyarshi tayi sanda ta anbaci ya sallameta, anya kuwa ba mutuwa zaiyi ba ko kuma dai yarinyar nan ce hawan jinin shi ba? Kasa maganar da yayi yasa ta kallonshi tace "Ba ma kada lokaci na ko? Shikenan ka tura min takardata a gidanmu." Juyawa tayi zata fita ya rik'o hannunta a mugun firgice, kallon juna sukayi tana kallon yanda yake sauke numfashi. Sautin kukan Hafsat daya ji ya dawo dashi daga shirin fad'in "Ryam kiyi hak'uri, karki tafi dan Allah." Kallon Hafsat yayi cikin fizgo kalamai yace "Me ya had'u Manga? Ban san ki da rikici ba." Da sauri ta nuna Mimi tace "Ka tambayi dak'ikk'iyar yarinyar nan mana." Kallonta Mimi tayi da mamaki tace "Dak'ikk'iya kuma?" Kallon sheikh tayi tana jiran ta ga me zaiyi amma sai wani kakkawar da kai yayi kamar mai kokarin b'oye kukanshi, fizge hannunta tayi ta kallesu da kyau tace "A tare na sameku dama, zan tafi na barku yanda na ganku, ni ma Allah zai had'ani da wanda zai iya kare kima da darajata, amma wannan ba gidan zama bane." Tana fad'a ta juya da sauri ta fita a d'akin wanda kowane tako ke sauka kan k'irjin sheikh, iya yanda mazaunanta ke juyawa cikin tafiyar b'acin rai yasa jinin jikinshi rage saurin gudu. Juyawa yayi ya kalli Hafsat dake ta sharar hawaye, wani iska ya feso dan gaskiya zuciyarshi na son ya bi *yarinyarshi*, amma kuma ga Sawwama na kukan b'acin rai wanda bai tab'a ganin hakan daga gareta ba, duk da bai san asalin me ya kawota d'akin ba yasan dai zaiyi wuya a ce bata da gaskiya. Zaunar da Hafsat d'in yayi ya zauna gefenta yana shafa bayanta ya kasa ceewa komai dan hankalinshi da nutsuwarshi na wani wurin gaskiya. Mimi kam na fita ai kuwa da gaske take dan akwatin da aka mata na lefe ta d'auko guda a ciki ta shiga zuba mata kaya saida ta mata nak da kaya ta d'auki hijab ta saka ta fito, su Heezam na zaune suka ga fitarta babu wanda ya mata magana saidai suna fatan ba matsalar Aisha ce ta jawo wannan babbar matsala ba. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *50* Jin yanda zuciyarshi ke ta buga mishi da sauri har sai ya bud'e baki yake sauke numfashi yasa shi d'an janye Hafsat daga jikinshi ya mik'e, zai fita ta rik'o hannunshi ya juyo suka kalli juna, cikin dakusashiyar murya tace "Kayi hak'uri idan na b'ata maka rai." Kasak'ai yayi yana kallonta kamar baya hayyacinta sai kuma ya kawar da kan shi yace "Ya zanyi idan ba hak'urin ba, tunda kun sani mun taru mun wa yarinya rashin adalci, mun nuna mata mu jahilai ne marasa tunani..." Sab'ule hannunshi yayi daga rik'on data mishi ya juya ya bar mata d'akin, da kallo ta bishi tare da jin wata matsananciyar kunya ta rufeta, sai ta samu kan ta da jin nauyin kan ta da kuma mijinta da Mimi, tabbas tasan abinda ta aikata har da rashin fitar da abinda ke ranta da tayi na wani lokaci, shiyasa yanzu ta fake da abinda ya faru ta d'an furzar da abinda ke ranta, gashi sun tafi sun barta da tunani kamar kan ta zai fashe. Alamu sun nuna sheikh yayi hushi da ita, ga kuma mamakin yarinyar da take kallon fuskar mijinta tana kiranshi da Abdul. Wani lallausan murmushi ta saki ta furta "Har yanzu bana iya kiransa da sunan Abdul Waheed ko da bayan idonsa ne, amma ita kai tsaye a gabanshi take kiran Abdul Abdul." Yana fita a rud'e ya nufi d'akin Mimi, ganin bata nan sai kaya dake kan gado a barbaje yasa shi durk'ushewa ya kifa kanshi a gadon yana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Ya maimaita haka sau uku kafin ya mik'e yana lalubar wayarshi tare da fita a d'akin ya nufi waje, d'aya daga cikin jami'anshi na ganinshi ya taso a sukwane, da sauri ya tara masa hannu yace "Makulin mota?" Da girmamawa yace "Sheikh mu je sai na sauk..." Bai gama fad'a ba a tsawace yace "Ka bani makulli bana so." Da sauri ya mik'a mishi yana ja baya da d'umbin mamaki, tunda suke haka bai tab'a faruwa ba sai yanzu, bak'ar Mercedes ya shiga yana d'ora waya a kunne yana kiran lambarta, data fara k'ara sai ta kashe kiran hakan ya k'ara d'imauta tunaninshi, yana fita dama ya nufa da fatan had'uwa da ita, saidai sam bai ga alamarta ba har saida ya iya kwanar unguwarsu. K'ofar gidan ya k'urawa ido yana kallo dan yasan dai nan zata zo, amma shiru bai ga alamarta ba saida ya d'auki waya ya sake danna kira, k'it ta datse kiran da sauri ya shiga rubuta mata sak'o kamar haka _"Ryam ki rufa min asiri, karki d'ora min hawan jini da tsufana, dan Allah na rok'eki."_ *Mimi* kam ta jima da shiga gida dan haka ma bai ganta ba, tunda ta shiga taxi take kuka kamar an mata mutuwa, tana fita ta mik'awa mai taxi jaka guda ta shige gida da jakarta, Abba dake shirin fita kicib'us sukayi a k'ofar shiga, kaucewa yayi a hanye ta wuce yana d'aga kai sosai yana kallonta da fad'in "Ke daga ina? Uwata anya kuwa baki da aljanu? Me ya fito dake yanzu daga gidanki?" Durk'ushewa tayi ta fashe da wani kukan ba tayi magana ba, sake gusawa yayi a bakin k'ofar yace "Ina zaki da k'atuwar jaka haka?" Had'a kanta tayi da gwiwa cikin kuka tace "Abba ni gidanmu na dawo, Abba na ba zan iya zama a gidan Abdul ba, wallahi bak'in cikin 'ya'ya..." Da k'arfi ya kai mata bugu a baki yana fad'in "Astagfirullah! Uwata sheikh d'in ne Abdul kai tsaye? Ban gane ba zaki iya zama ba ?" Juyawa yayi ya kalli k'ofar d'akinsu ya k'walla kiran sunan Mama da "Rabi, Rabi'a kina ina? Zo nan zo kiga haukan 'yarki." Da sauri Mama ta fito k'undul k'undul kamar zata fad'uwa tana fad'in "Malam lafiya?" Nuna mata Mimi yayi data rufe bakinta daya buga yace "Ga ta nan ta fad'a miki kiji." Kallon Mimi tayi hankali tashe tana jin wani suka a zuciyarta bakinta na hard'ewa tace "Mimi lafiya? Me ya faru?" Abba ne yayi tsal yace "Ba wani lafiya, wai fad'i take ba zata iya zaman gidan sheikh ba, ke dan Allah a nan gidan ba hak'uri kike dani ba ?" Sunkuyar da kai Mama tayi tana jin kamar tace mishi ya fita ya barsu ita da 'yarta ta ji me ye matsalarta, amma yanda ta ji ya fara fad'in "Ke Maryama bana son shashancin banza da wofi, ni zaki mayar k'aramin mutum da bai san me yake ba, duka yaushe kika tare a gidan na ki da zaki fara min yaji, kenan kinfi k'arfin a b'ata miki rai ke 'yar gwal? Yanzu haka ma ba da izinin gafarta malam kika taho ba, to ni ba za'ayi haka dani ba, maza tashi ki koma gidanki kamar yanda kika kawo kan ki, ba zan zauna na baki mafaka a gidana ba kwana kad'an ki fara min laulayi kamar yanda uwarki ke fama da na ta laulayin." Da sauri Mimi ta d'aga kai ta kalleshi sai kuma ta kalli Mamanta, a ranta tace "Mama ciki ne da ita?" Sai kuma ta yatsina fuska tace "Allah sawak'e ma na d'auki cikin mutumin nan, tsoho kawai da wata akwalar matarshi da 'ya'yanshi marasa kunya." Had'e fuska ta sakeyi ta kalli Abba ta marairaice tace "Abba dan Allah karka koreni a gidan nan, Abba ka ga fa da shi da matarshi da 'yarsu suka min taron dangi, ni wallahi Abba..." Takalminshi ya cire yana fad'in "Ke in ban kakkarta miki..." Ganin Mama ta juya tana rufe bakinta dan dama ya gama kasheta da kunya tunda yayi maganar cikin nan yasa shi binta da kallo, Mimi da tuni ta mik'e da gudu ta fita waje ta fashewa da kuka, akwatin ya kama da nufin cilla mata ita saidai ta fi k'arfinshi dan a tsayi ma kusan kansu d'aya da akwatin, turata ya dinga yi saida ya fito mata da ita ya nunata da yatsa tana tsaye nesa da shi yace "Wallahi kika bani na d'aga murya a kan ki ba zakiji dad'i ba uwata, har gidan na ki zan sameki na zazzabga miki dukan mutuwa." Cikin sand'a ta jawo akwatin na ta tana kallonshi ya koma cikin gidan yana fad'a, had'e hawayenta ta kalli unguwar ta su da kyau, duk da ba dare bane sosai amma babu mutane sai masu wucewa, numfashi ta sauke cikin disassashiyar murya tace "Kayi hak'uri Abba na ka yafe min, amma ba zan iya komawa gidan Abdul yanzu ba, idan na koma kamar ban da zuciya ne da kuma gata, ku a wajenku haka da kukayi shine daidai, amma ni tunda ni ke zaune dashi dole na bi kowaxe hanya dan samawa kai na mutumci a gurinshi, Mama na ta fad'a min na koyi yanda zan kula da kai na, kuma na yi alk'awarin zan k'watarwa kai na 'yancina ba tare da taimakon kowa ba." A hankali ta ja akwatin na ta ta d'auki hanyar zuwa gidansu Iya Delu, haka ta dinga kakkare fuskarta dan bata so yan unguwar su ganeta musamman da take d'auke da akwati shak'e da kaya. Tana zuwa gidan malam na cin tuwo Iya na gefenshi suna hirarsu a nutse, ko sallama ba tyi ba ta k'arasa cikin shagwab'a tana saki akwatin ta fad'i ta cire hijabi ta zauna tsakiyarsu, mamakinta na neman kashesu da k'yar Iya ta kalleta galala tace "Ke kuma fa daga ina?" D'ora kan ta tayi a gwiwar Iya ta shiga rera kuka a sanyaye tana fad'in "Kakani na bani da g芒ta a duniyar nan, kasheni zasuyi da bak'in cikinsu da bautarsu, dan Allah ku zame min gata kunji." Cire hannu malam yayi a tuwo ya kalleta ya dafa kafad'arta yace "Ta gaban goshina, waye ya tab'a min ke?" D'agowa tayi ta kalleshi cikin Luka tace "Malam na gaji da zaman gidan sheikh, dan Allah ku barni na zauna anan na huta, na je can Abba bai ma saurareni ba ya koroni da takalmi." D'ora kanta tayi shi ma a kafad'arshi tare da rik'e damtsenshi gam, cikin tausayawa da nutsuwa yace "Me ya faru amaryata?" Ba tare data d'aga kan ta ba ta shiga labarta masa komai daya faru tun daga farkon abinda Aisha ta fara mata har zuwa yau d'in, saida ta gama abinda bata tab'a tsammani ba daga Iya ta ji tace "Maganar banza, yo an fad'a musu ke d'in a bishiya muka tsinkoki? Ya zasu taru gard'ama gard'ama dasu su nuna miki fin k'arfi." Gyara zama tayi ta jawo Mimi ta shiga daddab'ata tana fad'in "Ke rabu dasu kinji, nan zaki zauna na ga wanda ya isa ya maidaki k'arfi da yaji, kaga iskanci." Dariya malam yayi yana girgiza kai bai ce komai ba, dan gaskiya yanda yake son Mimi shi ma sai yaji bai ji dad'i ba musamman da ita kan ta uwar yarinyar ta fad'a mata maganganu sannan shi bai tsaya ya bincika ba kuma ya d'ora mata da fad'in matarshi matarshi, yana gama cin abincin shi ya wanke hannayenshi ya d'auki k'aramar r茅dion shi zai fita ya kalli Mimi yace "Ki shiga da kayan ciki ki kwanta zuwa safe zan san abun yi." Mik'ewa tayi da sauri tana fad'in "Ni da safen ma makaranta zan tafi, kawai ka k'yaleshi yana tsohonshi dan ma ya samu na kulashi." Da kallo suka bita malam na dariya ya fita a gidan. *Ya jima* nan amma bai ga wulgitawarta ba sai kawai ya sake kiran wayarta, a lokacin tana d'akin Iya tayi kwance a gadon k'arfe tana d'an lilawa kad'an kad'an, d'aga wayar tayi ta d'ora a kunne cike da gatsali tace "Ina ji?" Shiru yayi idonshi lumshe murya k'asan mak'oshi yace "Ryammm." Tsam tayi tare da dakatawa da lilawar da take a gadon, wani tsammm ta ji gaba d'aya jikinta saida ya amsa, d'an basarwa tayi tace "Ina jinka." Cikin sanyi da taushin murya yace "Kina ina Ryam? Dan Allah ki dawo." Cikin shagwab'ar da bata san tayi magana ba tace "Um um! Ni ba zan koma ba tunda ba so na kake ba, Abdul baka so na kuma baka son zamana a gidanka, sannan 'yarka da mahaifiyarta basa so na sun tsaneni, kawai ka zauna da iyalinka na yafe musu kai har abada, kaga ai dama ni ma kawai had'ani ne aka yi da kai ba dan ina so ba." Da sauri kamar wanda zai fashe da kuka yace "Ba haka bane Ryam, nasan an miki ba daidai ba amma ki yafe mana kinji, Ryam in kin san yanda nake ji wallahi da baki tafi kika barni ba." Tashi tayi zaune tace "Ba wani nan, kawai wayo kake so ka min dan ina yarinya, to ni ma da hak'orana ashirin da bakwai." Dariya ce ta kubce mishi har tana jin sautinta a kunne kafin yace "Ryam, kenan bakiyi hak'oran hankali ba." Turo baki tayi irin bata ji dad'i ba kafin tace "Ni dai saida safe, kaga yanzu ba gidanka na ke ba." Zata kashe wayar yayi saurin fad'in "Inna Issa ina kika je?" Cike da yarinta tace "Ina wani wuri." D'if ta kashe wayar ta aje gefe ta kwanta, wayar ya bi da kallo sai kuma ya aje ta ya wa motar ky, ba zai iya tafiya gidansu ba a yanzu dan haka zai bari har da safe, duk da yana jin wata irin kunyar had'uwa da iyayen na ta, dan gaskiya abin nan ya dakeshi sosai, kuma yasan yana da laifi ta wani b'angaren, da wannan tunani ya isa gida kai tsaye b'angarenshi ya wuce. Hafsat ma ta jima zaune kafin ta mik'e dan duba yaran ko sun kwanta, saida ta shafawa dukansu addu'a kafin ta nufi d'akin Aisha, zaune ta sameta tsakiyar gadonta tana karatu da Qur'ani, k'arasawa tayi ta tsaya gabanta tana kallonta, ita ma d'aga kai tayi ta kalleta tace "Amie baki kwanta ba?" Ba sakin fuska a tare da ita tace "Ta ya zan kwanta bayan bansan halin da kike ciki ba." Murmushi tayi na jin dad'i tace "Amie lafiya ta lau, kiji ki kwanta ke ma." Wani malalacin murmushi tayi tace "Yayi kyau, haka yayi kyau tunda gashi har ina ganin murmushinki saboda yau kina farin ciki mahaifiyarki tayi fad'a a kan ki." Wani kallo ta mata baki sake irin tana jiran k'arin bayani, ruugume hannaye tayi tace "Kin fahimta mana, ya kamata kiyi farin ciki a zuciyarki tunda dai Mimi ta tafi gidansu." Zabura tayi tana aje Qur'anin tace "Me? Ta tafi Amie?" Wani dogon tsaki ta ja ta juya zata bar d'akin Aisha ta sauko tana rik'e hannunta tace "Amie da gaske ta tafi? Amie ku yafe mi..." Tureta tayi ta fizge hannunta tace "Shiru dallah! Hak'urinki na banza da wofi kike ba mutune, kullum ki ce kin tuba kuma ba zai hana anjima ki sake aikata abinda kika aikata ba, Aisha me yake damunki? Me aka miki da zafi haka da kike neman tarwatsa mana zaman lafiyar gida? Tunda kike kin tab'a ganin sab'ani tsakanina da mahaifinku? Kawai saboda an yi min kishiya k'waya d'aya, ba dan mahaifinki ya kasance mutum da bai san matsala da a yanzu Mimi ta hud'u ce ita." Nunata yayi tana k'yasta hannunta tace "Ki ji da kyau zan daidaita gidana da kai na, wallahi wallahi wallahi kinji uku ko? Na rantse miki da Allah Aisha kika sake wani abun da bai min ba a gidan nan sai na miki d'an banzan duka sannan na wankeki a haka na kaiki d'akin miji." Harara ta watsa mata sannan ta wuce ta barta nan tsaye, wani iri take ji gaba d'aya ta ma rasa inda zata saka kan ta ta huta, haka ta koma kan gadon ta zauna ta buga tagumi tana tunanin abun yi. *Washe gari* Tunda sassafe malam ko da yayi sallah ya samu Abba a masallacin unguwarsu ya fad'a musu abinda ya faru, rai b'ace duk da kunyar sirikina shi saida ya kalleshi yace "Yanzu malam can ta tafi kenan? Dama bata ji magana ta ba?" Saka takalminshi yayi yace "Malam muje gidan nan dan Allah ka yarje min na daki hancin yarinyar nan." Dakatar da shi malam yayi yace "A kan me? Kaga ni bana fad'a maka bane dama dan ka je ka d'aga min hankalinta ba, na fad'a maka ne dan ka sani kuma ko da mijin na ta ya nemeka ka sanar da shi inda ta ke." Jinjina kai yayi alamar gamsuwa yace "Shikenan malam, insha'Allahu da kai na ma zan kirashi." Jinjina kai malam yayi yace "Hakan ma daidai." Da wannan suka rabu kowa yayi gida, Abba na zuwa da fad'a ya shica fad'awa Mama tare da d'aukar wayarshi ya fara kiran lambar sheikh, yana ganin kiran amma bai d'aga ba saida ta tsinke sannan ya d'aga, a mutumce kuma a kunyace suka gaisa kafin Abba ya d'an sosa kai yace "Gafarta malam dama shiriritacciyar yarinyar nan ce jiya da dare ta zo mana da wani hauka, to ko da ta zo ma na maidata ashe bata tafi can ba." Shiru sheikh yayi kamar bai ji, har ga Allah lamarin yi masa yake kamar a mafarki, da k'yar ya cira bakinsa yace "Ayi hak'uri malam, insha'Allah idan na dawo daga aiki zan zo da kaina gidan muyi magana, ina mai bada hak'uri dan Allah, insha'Allah haka ba zata k'ara faruwa ba. " Cike da girmamawa Abba yace "Shikenan sheikh ba komai, ban da ma abin yara ina abun hushi a nan? Allah dai ya shirya mana su." "Ameen." Ya fad'a a hankali, sallama sukayi kafin Abba ya kalli Mama dake kad'a miyar d'umame yace "Ban san me uwata take son zama ba, ki ji yanzu babban mutum kamar wannan yanda yake kwantar min da murya yana bani hak'uri." K'wafa yayi ya mik'e zai nufi d'aki yana fad'in "Yarinyar nan in batayi sannu dani ba saina b'ata mata rai wallahi." Mama dai da kallo ta bishi dan ita ban da ganin 'yarta babu abinda take son yi, dan wannan kamar a dakeka ne a hanaka kuka, yarinya kamar Mimi a kai wa dattijo kamar sheikh, shin in bai bita a sannu ba ya za'ayi? *Mimi* Tana zaune ta tank'washe k'afafu tana cin tuwo tare da malam hannunta hannunshi suna ta ma Iya tsiya wai ba zasu ci da ita ba wayarta tayi k'ara, juyawa tayi ta d'auka tana dubawa ta ga Asma'u, wani murmushi ta saki ta danna ok ta d'ora a kunne, cikin nutsuwa tace "Hum! Ashe kina iya tunawa da mutane?" Dariya Asma'u tayi daga wajenta tace "Dan kar na fara miki k'orafin shi ne kika rigani?" Tab'e baki tayi tace "Ba wani nan, kin manta da mutane saboda kina shan amarcinki." Asma'u dai na dariyarta tace "Kedai tafi can, yanzu har sammakon da na yi na kiraki ban tsira ba kenan?" Gwalo ido tayi tace "Oho! Kenan kin kirani da safe ne dan na yafe miki?" Cikin marairaicewa Asma'u tace "Kiyi hak'uri to, amma ke me ya hanaki kirana? Ke ma amarcin kike sha da yayanmu ko?" Yatsina fuska tayi tana kallon malam tace "Ba wani nan dan Allah, ni da ma na bar muku yayan na ku ku dafa ku cinye tunda baku san mutumci ba." Dariya Asma'u tayi tace "Kamar ya? Su waye marasa mutumcin?" Kai tsaye tace "Ke da yar uwarki mijinki mana." Da sauri Asma'u tace "Wani abu ya faru tsakaninku? Me Hafsat d'in ta miki kuma?" Tab'e baki tayi tace "Rabu dasu can su k'arata tunda ni dai na baro musu gidan." Hankali tashe a kid'ime Asma'u tace "Kamar ya Mimi? Ban gane kin baro musu gidan ba? Kina ina yanzu ke?" Kallon kwanon tuwon tayi tace "Ina gida wajen Iya gani ma ina cin tuwo da angona." Wata nauyayyar ajiyar zuciya Asma'u ta sauke tace "Me ya had'aku Mimi? Me yayi zafi haka?" Mik'ewa tayi ta cire hannunta a d'umamen burabuskon da Iya tayi ta fito waje ta shiga d'akin Iya t zauna ta shiga labarta mata abinda ya faru, Asma'u kam kamar tana gabanta girgiza kai ta shiga yi kafin ta saita nutsuwarta ita ma ta bar d'akin da Asas yake kafin tace "... *Hohoho, gaskiya fa an sha muhawara, sannunku sannunku, sunana har ya kare馃榿.* *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *51* Asma'u kam kamar tana gabanta girgiza kai ta shiga yi kafin ta saita nutsuwarta ita ma ta d'akin da Asas yake kafin tace "Assha kuwa? Mimi ke da kan ki kikayi kuka a gaban kishiya? Ke ce kika rasa sanin hanyar shawo kan matsalarki har kika bari aka fara sakaki yaji ko kwana bakwai bakiyi ba, ya akayi haka ta faru? Ni da nake tunanin ke ce malamata ta wannan fannin, sabida kin tab'a fad'a cewa ko a cikin mata uku aka kaiki zaki iya zama dasu kuma ki k'waci kanki a hannunsu." Numfasawa tayi tace "Kinga Mimi duk yanda nake k'aunar yar uwar mijina bai kai k'aunar da nake miki ba dan ke tare muka tashi, ban ce ina so ta zama mowa a gidan nan ba, amma kuma ina so ki zama bora a gidanki ke ma, dan haka kiyi wani abu Mimi, a sanina dake kina da shiga mutane da kutsa kan ki inda yafi k'arfinki, kina karance karance da saurare da kallo sannan ga babbar waya a hannunki, dan Allah ki daure ki samu shawarwarin da zasu taimaka miki zama da mijinki da abokiyar zamanki da ma 'ya'yanku." Mimi da tayi shiru tana saurarenta saida ta ji ta dasa aya ta numfasa sannan tace "Nagode k'awata, kin k'arfafa min gwiwa kuma zanyi aiki da abinda kika fad'a min." Da fara'a Asma'u tace "Yawwa Mimi ko ke fa." D'orawa tayi da fad'in "Ni fa na kiraki ne dan muyi wata magana." Da zumud'i Mimi tace "Wace magana fa?" Cikin jin kunya Asma'u tace "Dama wani abu nake so ki d'an fad'a min da zanyi na k'arin..." Shiru tayi hakan yasa Mimi fad'in "Ina jinki?" Cikin dariya tace "Kedai kawai zan miki magana ta WhastAp." Kyab'e baki tayi tace "Kin samu babbar waya kenan?" A sanyaye tace "Na yi, idan mun had'u zaki gani." A take Mimi tace "Yaushe ma zamu had'un?" Cike da tsokana Asma'u tace "Ga bikin 'yarki da za'ayi juma'a." D'an gajeran tsaki tayi tace "Hummm! 'Yar masu ita dai." Suna sallama Mimi ta fito da sauri ta wanke hannayenta ta koma d'akin, wayarta ta shiga dannawa tana duba abubuwan k'aruwa musamman a WhastAp, duk abinda ta ga an turo a grp ta kan tsaya ta dubashi a tsanake, ita da Asma'u ma hira suka sha inda Asma'un ta fad'a mata tana son abun k'arin ni'ima ne, wanda ta sani ta fad'a mata sannan tayi alk'awarin binciko musu wasu.Tana tsaka da aikin gabanta kiran sheikh ya shigo wayarta, tana ganin kiran kawai ta datse shi tare da ci gaba da aikin gabanta, haka yayi ta kira dan su gaisa amma ta k'i d'agawa, sai sak'o ya tura mata da _"Amincin Allah ya tabbata a gareki, da fatan kin wayi gari cikin k'oshin lafiya?"_ Shiru yayi ta jiran amsa amma bata maida ba dole ya sake tura mata _"Da alama ba zaki yafe min cikin sauk'i ba, Ryam ki yi hak'uri kinji."_ Nan ma shiru bata maida ba sai kawai ya aje wayar ya buga tagumi yana kallon na'urar gabanshi dake jiran ya loda mata wasu bayanai dake gabanshi a takarda amma ya kasa. Saida tayi sallah azahar ta d'auki wayarta ta rubuta duk abunda take da buk'ata sannan ta shirya ta fito Iya na tsakar gidan tana gyara wake, tsaye tayi gabanta inda Iya ta shiga kallonta da mamaki tace "Ke kuma ina zaki je kika wani shirya haka?" Turo baki tayi tace "Iya kasuwa zan je akwai wasu abubuwan buk'ata da zan siyo." Cike da raini ta kalleta tace "Ke fita ido nq in rufe? Wato ga marainiyarki ko? Daga tahowarki jiya zaki ce zaki fita a gidan nan? To da izinin wa?" Bubbuga k'afafu tayi tace "To Iya dan Allah ba gidanmu ne nake ba kuma na fad'a miki." Cikin fad'a tace "A'a, dan kin fad'a min a banza tunda ba ni ke aurenki ba, ke Mimi in kikayi wasa wallahi saina hau bishiya na tsinko tsumagiya na ci ubanki a gidan nan, ni zaki mayar tsohuwar banza?" Galala ta kalleta tace "Ka ji min tsohuwar nan da wata magana, to ki hau bishiyar mana dan Allah, ni na fad'a miki ki daina zagar min uba fa." A harzuk'e tace "An zaga d'in, kiyi abinda zakiyi na gani." Murmushi tayi ta durk'usa gabanta ta dafa hannunta tace "Iya ta, kinga fa idan na je kasuwar nan zan siyo miki goro da tantak'washi da kifi d'anye, sannan yanzun nan Asma'u ta fad'a min wani abu da ake sha ana zama mowa a wurin miji, shine fa zan je na siyo." Hararanta ta dinga yi amma ba tayi magana ba, sun jima suna kallon juna kafin Iya ta sassauta murya tace "Shikenan na yarda ki je, amma Mimi kar kiyi abinda zaki sa a zageni dan Allah." Shafa kuncinta Mimi tayi tana mik'ewa tace "Yawwa Kakata, shiyasa nake son ki." Girgiza kai tayi tace "Kiyi sauri dan Allah kinji, ni ma zan je wajen malam Hadi na sa ya maki rubutu na bakali a wurin miji." Wata lalatacciyar dariya Mimi tayi ta jinjina kai dan tuni ta hango yanda zatayi ta tsokano sheikh kafin ta fice a gidan. Ta d'aya hanyar ta bi ta kusa da makarantarsu anan ta samu taxi ta wuce, tana ciki Salma ma ta kirata bayan sun gaisa take sanar mata jibi fa zata shiga lalle, da rawar kai da zumud'i Mimi take ta fad'in Allah kai su ranar su sha biki. Gurin masu siyar da litattafan hausa ta fara zuwa ta siyo na girki da kuma wasu na ki gyara da kan ki da saurarensu, daga nan gurin masu kayan marmari ta nufa ta shiga had'owa kala kala, ta gama siya ta juya zata nufi Inda zata samu dabino da cukui suka had'e da yayar Asma'u Rayya, gaisawa sukayi saidai jikinta har rawa yake tsabar ta kwab'ar da zance tace "Mimi ke ce kasuwa a lokacin nan? Dama malamai na barin matansu fita haka?" D'an murmushi tayi dake tana kallonta kamar yar uwa sai tace "Ni ma na je gidan Iya ne shine na biyo siyan wannan." Murmushi tayi ita ma tace "Lallai fa su Mimi an shiga sahun manyan mata, kin ga yanda kikayi wani fresh dake wallahi kamar na saki a jakata." Dariya Mimi tayi ba tace komai ba, kama hannunta tayi tace "Zo muje ki gani, ni ma nan ga ne zan je neman d'anyen madarar rak'umi." Mimi dai bin ta kawai tayi suna tafe take fad'in "Kina ji ko k'anwata, wani sirri ne zan baki ni ma wata malamata ta bani shi, amma fa karki fad'a ma kowa kinji?" Jinjina kai tayi suka ci gaba da tafiya tana fad'a mata abubuwan buk'ata, hakan yasa Mimi kallonta galala dan duk kayan data fad'a ita ma sune a ledarta, hatta da nonon rak'umin a wata alimentation ta sameshi nan bakin kasuwar, amma sai ta bita da to kawai har saida ta rakata ta siyo na ta kayan ita ma. Duk da haka ta k'aru da zamansu a d'an lokacin sanda take fad'a mata "Kinga kishiya gareki, karki yarda abokiyar zamanki ta dinga fahimtar halin da kuke ciki ke da mijinki, idan ya b'ata miki karki bari ta sani, idan duka ya miki a d'aki ki fito kina dariya, karki bari ta san k'uncinki ko kukanki bare damuwarki, dinga sakin fuskarki kina nuna farin ciki kawai. Haka kuma dan kina yarinya ba mahaukaciya bace ke, ke ma ki ja d'amara sosai ki k'waci wani kaso a zuciyar mijinki." Kallonta tayi ta rik'o hannunta sanda suka tsaya bakin titi zasu tafi tace "Mimi ki kula sosai, kishiyarki ta girmeki nesa ba kusa ba tunda ta haifi kamarki a yanda na ji, kinga kenan ta fiki sanin wanene mijinku, kuma kinsan an ce wanda ya rigaka kwana to fa tabbas zai rigaka tashi, zata iya biyo mikita wata sigar da ba lallai ki fahimta ba, zata iya nuna miki ta fiki wayo dan haka ta dinga miki siyasa tana mikina babba da yaro, to fa idan ba nutsuwa kikayi ba a wannan lokacin zata iya rubtawa da ke." Galala Mimi ta kalleta tace "Kamar ya kenan Aunty Rayya?" Murmushi tayi ta dafa kafad'arta tace "Misali ko a wajen kula da mijinku, zata iya nuna miki yafi son abu kaza alhalin ba gaskiya ba ne, ko kuma ta nuna miki baya son abu kaza alhalin yana son wannan abu, ke ko a wurin girki idan kika samu makira zata iya saka ki zuba awon da ba zai ishi fad'in gidanku ba, k'arshe da an tambayi ba'asi zamewa zatayi ta barki a ciki." Shiru Mimi tayi saidai inzata fad'i gaskiya tasan Hafsat tsakani da Allah take fad'a mata wasu abubuwan, tunda wani abu bai tab'a faruwa ba dalilin taimaka mata da tayi, to amma ai ba'a k'in ta mutane tunda shawara ce ta bata. Daidai lokacin da Rayya ta tsayar da taxi a lokacin Mimi tace "To ya zanyi kenan aunty?" Kallonta tayi a gaggauce tace "Nutsuwa zakiyi da kyau kisan me mijinki yafi so me ye baya so, sannan ki kwantar da kanki ki girmama duk wanda kika ga yana girmamawa, hakan ba fad'uwa bane ke siyawa girma da soyayyarsa." Murmushi tayi sosai tace "Nagode aunty Rayya." Ita ma murmushi tayi tace "Ba komai, kamar Asma'u na d'aukeki." Mik'o mata wayarta tayi tace "Aunty saka min lambarki mana." Karb'a tayi tana saka mata tana fad'awa taxin inda zai kaita, mik'o mata tayi kafin ta shiga suna sake sallama, ita ma taxin ta samu ta d'auki hanyar komawa gida abin ta zuciyarta fes bata jin wani k'unci. *Sheikh* Lallai idan har bak'on yanayin da baka saba dashi ba ya riskeka dole ko da a yanayi na gangar jikinka ne zai nuna, yau sheikh Abdul Waheed bai iya jira gari ya waye mishi ba a masallaci ya taho gida, kai tsaye kula bayan gidan ya nufa ya tsaya ya zubawa tsintsayen dake shawagi ido, shi ba salatin Annabi ba, shi ba hailala ko istigfari ba, haka kawai yake tunanin yanda 'yarcikin ke neman zama silar tarwatsewar gidanshi da kuma jefashi damuwar da bai san ya zaiyi ya fito da kan shi ba, yarinyar daya rena da hannunshi ya tarbiyanceta, yarinyar da har a cikin gidan nan idan mahaifiyarta bata samu dama ba ita ke karantar da matan auren unguwar nan, amma ita ce yau take neman canzawa gaba d'aya har take iya shiga hurumin da sam b芒 na ta bane. Babban abun damuwar shi ne yanda daga jiya zuwa yanzu da gari ke wayewa yake sake jin wata kewa da muguwar k'aunar Mimi na sake baibayeshi ta yanda har yake jin idan yaje gidansu ko k'asa ne zai durk'usa ya ce tayi hak'uri ta dawo gareshi, uwa uba matsananciyar kunyar had'uwa da iyayenta da yake ji, baisan ya zai ce musu ba, ya fad'a musu 'yar shi ta fi k'arfinshi ne ko kuma dai yace yaro ne na yanzu ka haifa baka haifi halinshi ba? Wata ajiyar zuciya ya sauke ya na ci gaba da kallon yanda tamtabaru ke tsatsagar k'asa suna d'aukar abincin da ake watsa musu, yana wannan yanayin ne kiran Abban Mimi ya shigo wayarshi, wani mummunan fad'uwar gaba ya ji kamar wanda aka daka da k'atuwar gudumar bak'in k'arfe, har tsigar jikinshi ne ya ji ta tashi saboda rud'anin daya shiga, da k'yar ya d'aga kira ya d'ora a kunne jikinshi har wata makyarkyata yake, a daddafe suka gaisa har ya fad'a mishi zai zo anjima, suna sallama ya sake maida wayar aljihunshi yana tunanin dole ya kira Alhaji Ibrahim tunda uba ne gareshi ya rakashi wajen iyayen Mimi. Rintse idon shi yayi sosai dan har ga Allah wani kuka kuka yake jin yana taho mishi sakamakon abinda yake ji a zuciyarshi, shi da Hafsat ko da wasa basu tab'a musayar yawu ba ta fad'a ya fad'a bare ta kai ta ga yaji, amma yau ga shi wai zai je bikon macen daya tabbata idan bai je ba rayuwarshi ma zata shiga garari. Wasa wasa sai gashi lokaci ya wuce mishi a wurin nan bai tsinana komai ba. Hafsat ma da taga shiru kuma ta duba d'akinshi baya nan ta tambayi su Heezam sun ce ya jima da dawo gidan sai ta d'auki waya ta kirashi, lalubo wayar yayi ya k'urawa lambarta ido, saida kiran yayi kamar zai tsinke ya d'aga amma kuma sai yayi shiru alamar yana saurare. Hafsat kuma sai ta d'auka ko har yanzu hushi yake da ita, a sanyaye tace "Ranka shi dad'e, barka da safiya." A yanayin da zaka san mutum baya cikin walwala ya amsa da "Barka, antashi lafiya?" "Lafiya lau." Ta fad'a a ladabce kafin ta d'ora da "Dama na ga shiru baka dawo ba tun asuba, ko ka wuce wurin aiki ne?" Wata zabura yayi yana waro idonshi akan tsintsayen, dafe gaban goshinshi yayi yace "Subhanallah! Na manta wallahi, ina zuwa." Da sauri ya kashe wayar ya nufo hanyar sashen shi, Hafsat kam da mamaki ta bi wayar da kallo tana fad'in "Mantawa kuma? Aikin da babu abinda ka d'auka da mahimmanci bayanshi sama da mu?" Tana nan tsaye a falon na ta ta ji k'arar k'ofar b'angarenshi alamar ta k'ofar baya ya shiga, takawa tayi ta shiga falon na shi, a gaggauce ta sameshi yana cire kaya zai shiga ban d'aki, d'an murmushi tayi tace "Yallab'ai garin ya ya ka manta da aikin jama'a haka?" Kallonta yayi yace "Kuyi hak'uri dan Allah, wallahi na..." Sai kuma yayi shiru ya sauke numfashi, ban d'akin ya shige da sauri inda ta rakashi da ido, d'an murmushi tayi dan ita dai wani abu ta hango a tare da shi, juyawa tayi da sauri ta je ta had'o masa abun kari a babban faranti ta dawo, tan a shigowa shi ma ya fito alamar bai yarda ya d'auki lokaci ba, cikin sauri yake goge ruwan jikinshi yana fad'in "Manga kiyi hak'uri ba zan tsaya cin abincin nan ba na sake b'ata lokaci, idan na je can na ci idan na shiga hutu." Kallonshi tayi jikinta a mace tace "Amma ko ya ya ka ci mana, jiya ma fa baka ci abinci ba." Girgiza kai yayi yace "Ba zan k'ara b'ata lokaci ba Manga, aikin nan na jama'a ne ba nawa ba, hakk'in mutane dayawa ne a kai na, bana so Allah ya tambayeni ko da da lattin minti d'aya ne." A ladabce tace "To ko na juye maka shi sai ka tafi da shi?" Da sauri ya kalleta tarrr a fuska dan Mimi ta tuna masa sanda take magiyar ta dinga aika masa abinci, k'arasa d'aure zariyar wandonshi yayi ya girgiza mata kai, bata k'ara magana ba har ya gama saka kayan ya d'auki jakar na'urarshi ya nufota, sumbatar goshinta yayi yace "Sai na dawo." A sanyaye ta bishi da kallo dan har ya nufi fita tace "A dawo lafiya." Saida ya bud'e k'ofa zai fita yace "Allah yasa." Yana fita bai ga ko d'aya daga cikin yaran ba alamar duk sun taafi makaranta su ma, da sauri ya shiga motar da jami'in ya bud'e mishi k'ofa suka tayar da jiniya suka d'auki hanya. *08:30 na dare* Tun yamma da malam ya dawo yace mata mijinta zai zo anjima ta shirya dan tare zasu koma ta fara fad'awa Iya "Ni wallahi kai na ma ke ciwo." Iya kam da bata san manufarta ba sai ta d'auki jibda ta bata tace ta shafa dan ta santa ba magani take so ba, ana magriba ta sake kallon Iya tace "Iya kai na fa bai daina ba, kuma ma amai nake ji yana taso min." Kallonta Iya tayi ta rufe baki sai kuma ta kawar da kai, murmushi ta saki tana girgiza kai tace "To Allah ya sawake ya raba lafiya, bari a yi sallah sai na baki garin hatsin nan kisha aman zai kwanta." Zuwa 08:30 ta rikita Iya da tsarabe tsaraben kaza ke mata ciwo kaza ta jin na mata ciwo, Abba ne suka shigo tare da malam dake kallon Iya yana fad'in "Mik'o mana tabarma ga mai gidan na ta nan su zo." Mik'ewa Iya tayi tana fad'in "Sannunku da zuwa, bari na d'auko." Tabarma ta d'auko ta shinfid'a musu a kusa da d'akin malam d'in tana kallon malam tace "Amaryar ta ka ma fa bata da lafiya." A tare suka kalleta da Abba suka ce "Bata da lafiya kuma?" Kallonsu tayi ita ma tace "E wallahi, tunda yamma daka fita tace kanta na ciwo, yanzu haka dai amai ne tace ya fi damunta da tashin zuciya." _馃ぃ Uwata sha'ani_ A rikice malam ya nufi d'akin yana fad'in "Subahanllah! Amma kuma baki aika a fad'a min ba, ina bakin masallaci ai da ba an kaita asibiti ba." Wani galala Abba ya kallesu dan shi yanzu lamarin Mimi ya daina bashi al'ajabi ma, tab'e baki yayi yace "Malam karku wahalar da kanku, iskanci ne wallahi yarinyar nan zata mana." Shigewa malam yayi bai ce komai ba sai Abba daya fita dan shigo da su sheikh, jim kad'an suka shigo suna ta gaisawa da Iya a mutumce shi da Alhaji Ibrahim, zaune sukayi inda Iya ke sake fad'a musu "Ai ja'irar ma tana ciki duk ta rikice ba lafiya." Da wani sauri ya kalli Iya yana d'an jimk'e hannunshi akan gwiwarshi sai kuma ya kalli k'asa ya huro iska bai ce komai ba dan baya so yayi magana ya kwafsa a fahimci rauninshi akan yarinyar, Alhaji Ibrahim ne yace "Assha kuwa, an tafi asibiti kuwa?" Fitowar malam yasa Iya bata bashi amsa ba dan yana fad'in "Jikin na ta dai babu zafi, aman ne kawai tace yake damunta da ciwon kai, sai k'afafunta da tace suna tauna mata." Wani kallo Abba ya masa sai yaga ai fa yarinyar nan ma ta rainasu wallahi, to me take nufi? Sheikh kuma sake sunkuyar da kai yayi bakinshi na son furta "Ku min izini na shiga na ganta dan Allah." Amma kunya da kawaici yasa shi had'ewa ya shanye, Alhaji Ibrahim ne ya kalli sheikh d'in yace "To me zai hana ka kaita asibiti?" Iya ce tayi saurin cewa "Wacece? Mimin? Tabb'!" Malam ne yace "Ai bata san zuwa asibiti saboda magani da allura." Abba ne ya gyara zamanshi kan tabarmar yace "Allah gafarta malam bari na fito maka da ita ku wuce gida, ba wani ciwo dake damunta iskanci ne." Mik'ewa yayi zai shiga d'akin malam yace "A'a fa Adamu, kiyaye ni wallahi akan amaryata." Sunkuyar da kai Abba yayi yace "Kuyi hak'uri malam dan Allah ku barni da yarinyar nan." A tausashe kuma a sanyaye sheikh yace "Ku barta." Shiru sukayi suka zuba masa ido shi kuma yana kallon k'asa, d'orawa yayi da "Ina me baku hak'uri dan Allah da gaba d'aya zuciyata, abinda ya faru sabo ne a gari hakan yasa na rasa hanyar da zan dakatar da abun, amma insha'Allah na tsawatar ta yanda bana tunanin hakan zai sake faruwa nan gaba, kuyi hak'uri dan Allah ita ma ku bata hak'uri, nasan an shiga hakk'inta dayawa amma muna neman afuwarta ni da iyalina." Cike da girmamawa da ganin dattakonshi Malam ya zauna yace "Ba komai sheikh, komai ya wuce ai insha'Allah, Allah ya yafe mana baki d'aya ya kuma baku zaman lafiya." Da "Ameen." Duk suka amsa kafin Iya tace "To ya za'ayi da ita yanzu? Zaku tafi tare ne?" Sheikh ne yace "Tunda bata jin dad'i kawai ku barta, amma dai ya dace a tafi asibiti." Da murmushi Iya tace "Insha'Allahu zamu k'ok'arta mu gani, indai bata yarda ba ka sani ni zaneta zanyi sannan ta bar min gida." Murmushi yayi ba tare da sanin bakinshi ya furta ba yace "Kiyi hak'uri Iya karki tab'a ma..." Sai kuma yayi shiru sanda sukayi ido hud'u da Abba, mik'ewa malam yayi da Abba tare da Alhaji Ibrahim, a sanyaye sheikh ya mik'e sai malam daya kalli Iya yace "Ki mata magana ta fito ko gaisawa suyi." Iya ce ta mik'e tace "Ko kuma dai ya wuce ba, ciwo ne fa ya zo ga uwayen mita da raki, ko ruwa bata tashi zaune tasha." Dariya sukayi inda Iya ta gyaraw sheikh tace "Wuce ciki." Jim yayi a tsaye yana sussunkuyar da kai sai kuma ya shiga takawa babu takalmi a k'afarshi ya nufi d'akin, yana d'aga labulen da sallama Mimi ta sauko daga kan gadon da sauri ta shige k'ark'ashin gadon da babu komai a k'asa sai buhuna. Baki ya saki yana kallon sarautar Allah matarshi a k'ark'ashin gado, takawa ya shiga yi a sanyaye saida ya tsaya kusa da gadon yayi tsugono irin na maza yana lek'awa k'asa yace "... _Masha'Allah, hak'ik'a aka ce yaba kyauta tukuici, bamu rok'a ba, bamu shawarci wani ba, haka kawai kuka ga cancanta ta isa ta sa kuyi mana kyautar kud'inku, lallai kun cika mutanen kirki masu daraja a garemu da karamci, kayi a yaba ma kad'ai babban arzik'i ne, sai gashi a wasu grps d'in har da ware mu mu biyu kawai ni da kuma k'awata aminiyata *Sajida* kuka ce zaku mana kyauta saboda k'ok'arin da muke, tabbas zan iya kiran labarin *matar mutum* da gawurtaccen labarina kuma bakandamiyata, dan Allah ya k'ara d'aukaka ni ta dalilinshi, Allah nagode maka ina k'ara godiya a gareka, ba dubarata bace ba kuma wayona bace._ Yan *Nigeria* da kuka kawo wannan shawara ta yi mana kyauta, da kuma yan *Niger* da kuka goya musu baya Allah ubangiji ya saka muku da alkairi, duk da mun dakatar daku mun ce ku bari muyi littafi na kud'i ku siya, amma gaba da gaba kuka nuna mana kunyi niyya kuma ba zaku fasa ba, Allah ya saka muku da alkairinsa, Allah ya biyaku da aljanna ya yafe mana kurakurenmu. *Sajida* & *Samira* _(Kwate da Kwate)_馃榿 *Allamdulillah* 06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *52* Takawa ya shiga yi a sanyaye saida ya tsaya kusa da gadon yayi tsuguno irin na maza yana lek'awa k'asa yace "Ryam." Yanda ya kira sunan na ta a tausashe yasa ta yin shiru ta sake lafewa, tayi niyya ba fa zata bishi ba saidai in da k'arfi zai d'auketa ya kai gidanshi, a hankali ya sake fad'in "Ryaaaam." Yanda yaja a d'in yasa ta saurin fad'in "Na'am." Cikin barkwanci yace "Ki fito kinji, ke ba mage ba, ke ba b'era ko kaza ba, ya zaki shige k'asan gado ki taushe min cikina, ko kina so ki ja min b'ari ne?" Zazzaro ido tayi baki bud'e tana rarraba ido, muryarshi ce ta katse mata tunanin data tafi yi tana fatan Allah yasa dai kar Iya ta d'auka ma ciki ne da ita, kai ita yaushe ma ta d'auki cikin na shi? Haba haba ai abun kunyar sai yayi yawa, ita wallahi ba zata yarda tsohon nan ya mata ciki ba, shikenan sai a kalleta a kalli sheikh Abdul Waheed a ce ya kusanceta har ma ta samu ciki? Haka kawai ta ji tausayin kan ta ya kamata sai ta fashe da kuka tana murza ido tare da gyara kwanciyarta, cikin sangarta da sakarci tace "Ni kawai ka tafi bana son ganinki kuma ba zan bika d'in ba." Sanyayyen numfashi ya sauke yana sakin murmushi ya zura mata hannunshi na dama yace "Na yarda ba zan tafi da ke ba, amma ki fito na ganki kinji, zan miki addu'a ne ki samu sauk'i." Shiru tayi tare da tuna ranar da suka wuni gidan shi nan yace zai mata addu'a, salon tashi addu'ar ba irin ta kowa ba ce, da sauri ta girgizz kai alamar a'a dan ba zata yarda ta had'a jiki da shi ba a gidan Iya, ai zata sha tsiya a wurin Iya har ranar da zata daina numfashi, saita d'auka ita ma jarababbarshi ce, mak'ale kafad'a tayi tace "Um um! Ni lafiya ta k'alau." D'an k'ankkance ido yayi yace "Kamar ya? Amma kuma aka ce baki da lafiya." Shiru tayi tana mutsu mutsu da bakinta, cike da gargad'i yace "Ryaaaam! K'arya ko? Bana hana ba?" Shiru tayi tana kumburo baki ba tace komai ba, mik'ewa yayi yana fad'in "Shikenan bari na fad'awa Abba k'arya kike, sannan na bashi carbita ya zane min ke da kan shi." Wani marayan kuka ta saki a hankali tare da fad'in "To ai ba zan k'ara ba ko, kayi hak'uri." Kallon gadon yayi yana jin ina ma ba gidan da yake jin matsananciyar kunya bane, da cak zai d'aga gadon ya fito da ita su kalli juna, amma saiya d'aure fuska yace "Haka kike fad'a kullum amma ba kya dainawa, Innar Issa duk randa kika kaini bango a game da k'aryar nan wallahi zaki gane shayi ruwa ne." K'wafa taji yayi ya laluba aljihunshi ya aje mata d'aurin kud'i akan gadon tare da fita a d'akin, da sauri ta fito tana murnar bai tafi da ita ba, kwance ta sake yi akan gadon dan kar Abba ya dawo ya ganta ya wulak'anceta, jin alamun ta zauna abu yasa ta lalubawa ta jawo kud'in, d'auka tayi tana dariya ta jawo k'aramar jakarta ta sokasu a ciki. D'akin Iya ta shiga tace mata "Ya kike jin jikin yanzu? In kinsan baki jin dad'i ki tashi muje asibiti." Mik'ewa tayi zaune tana yatsina fuska tace "Iya aman ma ai ya kwanta, ki bari na gani zuwa safe." Jinjina kai tayi tace "To shikenan, ni dama bana son k'aramin ciki a saba mishi da likitar nan, sai ya zama komai kaji sai ka je asibiti." A zabure ta kalleta tace "Iya waya fad'a miki ciki ne dani? Haba dan Allah bana son haka fa." Turo baki tayi ta juya kan ta, dak'uwa ta mata tace "Ubanki ne ya fad'a min, in b芒 ciki ne da ke ba uban waye dake saka ki jin amai." Cike da tsiwa tace "To wai ke Iya dole komai sai dai ki zagi ubana ne, me yasa baki tab'a zagin Mama ba? Dan baki haifeshi bane, kuma ni ba abinda nake da." Juyawa Iya tayi zata fita tana fad'in "Ina zan tsaya fad'a dake ki ja min jafa'i, ina tab'aki a ce ni ce silar komai, can ki k'arata da jarabarki." Kallonta tayi har ta fita saidai ran ta a b'ace dan sosai ta ji haushin maganar wai tana da ciki, cikin sheikh? Tsoho wanda ya girme ma Abbanta? A tsiwace ta murgud'a baki tace "Allah ya rabani." *Washe gari* Saida ta gama shirinta tsaf kawai ta zauna bakin gado ta d'auki wayarta ta danna masa kira. Suna tafe a nutse cikin mota zai fara biyawa wajen Hajia ya gaisheta su wuce ya d'aga kiran cike da farin cikin yau ita ta fara kiranshi, cike da karsashi yace _"Assalama alaiki."_ Cikin yarinta ta amsa da _"Wa'alaika salam, ina kwana?"_ Kyab'e baki yayi yace _"Ban gan shi ba."_ Kallon wayar tayi sai kuma tace _"Ya aiki, ya gajiya, ya gari, ya hak'uri, ya fama damu?"_ Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi yace _"Allah nake rok'a ya k'ara min hak'uri da juriyar iya tafiya dake, dan na lura Ryam d'ina tana son gayyato min ciwon da har yanzu ko Hajiarmu bata da."_ Wata shak'iyiyar dariya tayi ta yan duniya tace _"Ni Maryama a wa? Da zan d'ora maka wannan ciwon?"_ Samun kanshi yayi da kalar dariyar da tayi kafin yace _"Ke mai mulki a zuciyar Abdul mana."_ Waina idonta tayi tace _"Daina zolayata malam, ni dama na kiraka ne na fad'a maka ina so zan fara tafiya makaranta."_ Wani dam! Ya ji gabanshi ya buga, makaranta ta me kuma? A nan zaman lafiya zata wani tsokano masa fitina, d'an girgiza kan shi yayi yace _"Wace irin makaranta kuma?"_ Turo baki tayi alamar bata so tambayar ba tace _"Amma fa kana da yara, kuma kasan tun jiya an koma makaranta."_ A hankali ya fara sauke numfashi yana sauraren na ta bugun numfashin a kunnenshi, a sanyaye sosai kamar mai rad'a yace _"A'a Ryam, karki d'auko min abinda zai fi k'arfina dan Allah, ni ban yi maganar karatunki da iyayenki ba, bana so gaskiya, ki hak'ura kinji."_ Mik'ewa tayi tsaye tana dafe k'ugu irin fa da gasken nan take tace _"Me? Baka so fa ka ce? Kasan matakin karatu na ne da za'a datse min shi ban shirya ba? Ina so na zana jarabawar bac shekara mai zuwa, dan Allah Abdul ka barni na tafi ka ji." Saurarenta yake tas yayi shiru abun shi, yanda ta fara maganar da zafi da farko sai ya bashi mamaki, amma a k'arshen nan da ta kashe murya tayi a sigar rarrashi ta kirashi da sunan da saka mi shi jin k'uruciya sai ya murmusa akan labb'enshi, tunani ya shiga yi ya barta ne ko kuma dai ta hak'ura, sanda aka yi aurensu da Hafsat ma tana tsaka da karatu kamar yanda shi ma yana tsaka da na shi karatun a Madina, yana tafiyarshi k'arasa karatunshi ita ma ta ci gaba da na ta a gidan Hajia, saidai inda matsalar take Hafsat da Mimi ba d'aya bane a halaye da yanayin zubin halitta kai har ma yanda yake jin su a zuciya, yana da yak'ini d'ari bisa d'ari Hafsat bata karya dokoki da sharud'an daya gindaya mata ba, amma Mimi? Wani iska ya feso yace "Ba zai yiwu ba gaskiya." Da sauri Mimi tace _"Yanzu duk magiyar da na maka ba zaka barni ba? Haba sheikh na Allah, haba ustaz haba Abban Humaira da Munzeer, haba an tsohon yan matanshi."_ K'yalk'yalewa yayi da dariya yana fad'in _"Ryam, na ji to na ji."_ Da zumud'i tace _"Yawwa ka amince?"_ A take yace _"A'a, yanzu ki fara fad'a min me ye burinki idan kin kammala karatun?"_ A sanyaye ta feso iska ta koma ta zauna tace _"Abdul."_ A tausashe kamar zai k'urma ihu saboda yanda ta kirashi yace _"Na'am."_ Cikin shagwab'a tace _"Kud'i na zasu k'are, ka kirani da wayarka."_ K'it ta kashe kiran tana murmushi, shi ma dariya yayi yana maida mata kira da fad'in "Allah shirya min baiwar nan ta ka ta min sauk'in juyawa." Tana ganin kiran ta d'aga shi kuma yace _"To ina jinki."_ A ladabce tace _"Ka ga dai idan na gama karatu ina so na samu babban aikin da zan siyawa Abbana gida, na siya mishi mota na siyawa Mama mota na had'ata da dreba, sannan na d'auki nauyin karatun su Yaseen a makarantar kud'i mai kyau ba kamar ni da nayi ta gwamnati ba, sannan na cika musu d'aki da kayan abinci da masu aiki a kewaye dasu, sannan duk shekara ina kaisu aikin hajd, shikenan."_ Cikin farin cikin jin burinta ba wani mai tsanani bane yace _"To ke kuma baki da abunda kike son yi ma rayuwarki ne?"_ Sauke ajiyar zuciya tayi tace _"Ni kam ba wani babban abu na ke so ba, dama dai burina bai wuce na samu d'an yaro ba na aura, wanda zai dinga kai ni shan ice cream sannan duk shekara ya kai ni k'asar waje nayi yawon bud'a ido, sai kuma na dinga haihuwa duk bayan shekara bakwai bakwai."_ Dariya ya shiga shek'awa kamar yaron daya samu kallon kartoon d'in Tom and Jerry hannunshi rik'e da sweet, sakin baki tayi tana mamakin me ya bashi dariya haka? A marairaice ta sake fad'in _"Abdul in tafi ne? Lokaci na tafiya."_ D'an tsagaitawa yayi da dariyar yace _"A'a Ryam, zamuyi magana a kan karatunki idan kin dawo gidana."_ Kyab'e fuska tayi irin zatayi kuka tace _"Yanzu duk yanda na gamaka da Allah baka ji ba, ku fa malamaina magada Annabawa, ko bakuyi niyyar abu ba aka had'aku da Allah kuna yi, ka tuna da cewa Imam Malik har mata ya aura saboda kawai ta had'ashi da Allah, kuma ya zauna da ita da kyautatawa duk da baya sonta a zuciyarshi, amma kai...shikenan sheikh ba komai, ka nuna min ban da mahimmanci a wurinka da zaka iya yi min wannan alfarmar."_ Sheikh ban da saurarenta da girmama lamarinta babu abinda yake yi, rik'e hab'a yayi a ranshi yace "Oh Allah! Wai ka haifi mutum a shekaru amma ya ce da tsiya zai maka wayo." Cikin sakin murmushi yace _"Ya kike so na yi Ryam? Bana so ki je gaskiyar magana, amma tunda kika had'ani da Allah zan miki wani lamuni."_ Gyara zama tayi da zumud'i tace _"Yawwa ina ji."_ Sanyaya murya yayi yace _"Ki girka min abinda zan ci anjima."_ Yatsina fuska tayi tace _"Girki kuma?"_ A hankali yace _"Um! Ko ba zakiyi ba dan ki samu lada?"_ Da sauri tace _"Ni d'in me da zan ce ba zan yi ba? Zan yi mana."_ Murmushi yayi yana hangen falon Hajia dan tun d'azu suka shigo kafin yace _"Da kyau yar albarka, Allah ya faranta miki yanda kika faranta min."_ Wata dariya tayi tana nunashi da hannu kamar yana gabanta tace _"Abdul wannan addu'ar wallahi ta wayo dan kayi galaba a kai na, ba komai ka ci gaba da yi min yawo, wata rana zan rama ni ma."_ Dariya yayi yana fitowa a motar yana me jin kamar ya zauna yayi ta hira da ita yace _"Ai kin rama tun jiya, ko kin manta na je bikonki kika min wayon baki da lafiya, haka na dawo ni da k'atuwar rigata."_ Tintserewa tayi da dariya _"To wai idan na dawo yanzu me zan maka? Ga matarka nan da kake so da kuma 'yarka da kuka shigar ma fad'a kuka min taron dangin, dan kunga bana da wanda zai shigar min ne ai."_ Cikin murmushi yace _"Ryam ba na bayar da hak'uri ba? A yafe mana dan girman Allah mana."_ D sauri tace _"Na yafe, wallahi na yafe tunda ka ce girman Allah."_ Da jin dad'i yace _"Yawwa ko ke fa, ina sonki Ryam, na sumbaceki a bakinki."_ Da baki sake tace _"Ta ya ya? Bayan ban ji sumbatar ba."_ Dariya ya bushe da ita cikin tsokana yace _"Ke wata Mairama, ashe ma kina so na sumbaceki."_ Rufe fuska tayi da kunya tace _"Ni bana so, kawai tambaya ce na yi."_ K'it ta datse kiran tana dariyar jin kunya, shi ma soka wayar yayi aljihu yana girgiza kai da murmushi a fuskarshi yana shafa k'eyarshi, jami'an su dai da kallo suka bishi har ya shige falon suna mamakin wannan sabon shehi na su, su dai kam tun daga ranar da aka d'aura aurensu suke ganin bak'in abubuwa a tare da shi, kuma basu ga laifinshi ba tunda yarinya ya aura wacce ko su dake da k'uruciyar da baya da suka auri sa'arta zasuyi fiye da haka ma bare kuma shi. A nutse yake zaune k'asa gaban Hajia yana d'an jujjuya kofin tangaren d'in data aje masa da zazzafen shayin na'a na'a a ciki, bayan sun gaisa ne Hajia ta numfasa cikin d'an fad'a fad'a da dattijuwar uwa kuma wacce take gaba dashi ta kalleshi a zafafe tace "A ce duk abubuwan nan na faruwa amma ni babu wanda zai iya fad'a min, ba ma wannan ba sheikh akan menene zaka zauna k'aramar yarinya 'yar cikinka har tayi sanadiyar barin matarka d'akinta? A kan me?" Kuma sunkuyar da kai yayi bai yi magana ba yana son bata damar fad'an abinda take son fad'a, d'orawa tayi da "Yanzu fa kwana biyu kenan, tunda Hafsat ta fad'a min tun shekaran jiya ta tafi, ni abunda ya ke k'ona min rai shi ne yanda ku ma dana ha茂fa kuka min biyayya kuka karb'i Mimi da hannu biyu, bare kuma 'yar da kuka haifa a ce ita ce zata bamu matsala." Cikin ladabi da nutsuwa da girmamawa ya kuma sadda kan shi yace "Ayi hak'uri Hajia, insha'Allahu zamu gyara kurenmu." Kawar da kai tayi tace "Shikenan Allah yasa, amma ku sani ban ji dad'i ba, kuma nayi niyyar tafiya gidan na ci uwar Aishan a gabanku, in ya so na ga zaku rama mata ne kamar yanda kuka taru akan baiwar Allahr yarinya, wannan ma ai shirme ne sai kusa na ji kamar tusa muku ita ne nayi a dole kuke zaune da ita." Girgiza kai yayi ya d'an d'aga kai ya kalleta yace "A'a Hajiarmu, sam ba haka bane, mu kanmu iyayenta kun isa damu bare kuma ita." Sake d'auke kai tayi tana sauke numfashi da k'arfi, dan har ga Allah jarumta ce tayi wajen yi mishi fad'an nan, abu ne da bai tab'a faruwa ba a tare dasu, shiyasa ko da Hafsat ta fad'a mata a waya abinda ya faru tare da cewa ta rok'a mata gafararshi yasa ta yanke shawarar dole ta nuna masa ita ma kamar uwa ce a gareshi. Cikin sanyin murya kuma ta d'ora da fad'in "Sannan Hafsat ta ce tana mai baka hak'uri akan abinda tayi, ta fad'a min ita ce da laifi ba Mimi, ita ta fad'a mata magana mai zafi, sannan ta ce na fad'a maka a d'an zaman da sukayi babu wani abu mai sunan raini daya shiga tsakaninsu, Mimi yarinyar kirki ce kawai wannan ma shed'an ne ya shiga tsakaninsu, kayi hak'uri ka ji." Shi ma wani sanyayyen numfashi ya sauke yana lumshe ido lokaci d'aya kuma ya bud'e, kallon kofin hannunshi yayi yace "Ba komai Hajia na yafe mata, dama kuma ni babu abinda ta min, abinda na gani ne a ido ya min kama da za'a ci mutumcinta, ni kuma ba zan bari haka ta faru ba indai ba na daina numfashi bane, shiyasa na yi haka." Jinjina kai tayi cike da k'aunarshi tace "Mun gode Allah ya biya, kuma ni ma insha'Allah zan je na samu iyayen na ta na sake basu hak'uri, dan kuwa ni ce nan na karb'a maka aurenta, dole wasu abubuwan su rataya a wuyana, kamar yanda idan kuka cuta mata to ni kuka ci amana." K'anshi sadde kasa yace "Insha'Allahu ma haka ba zata sake faruwa ba Hajiarmu, amma kuma..." Da kulawa ta kalleshi tace "Amma me?" Cikin jin kunya yace "Bata gidansu tana wajen kakaninta, ina ga kamar bata san komawa ne ita ma shiyasa da muka tafi jiya tace bata da lafiya." Dariya Hajia tayi tace "Allah sarki Mimi, ina k'aunar yarinyar wallahi, ai ko ni ce ita zanyi abinda ta yi, dole ta tsorata daku ta ga baku da adalci a rayuwarku." Rufe ido yayi sai kuma yayi saurin d'aga kan shi yace "Hajia ki je ki bata hak..." Shiru yayi dan ya tuna zai yi kwafsi fa a gaban suruka kuma uwar ta shi, murmushi Hajia tayi tana girgiza kai tace "Ba damuwa zan je na bata hak'uri, sannan na fad'a mata ba haka kake ba akasi ne aka samu yanzu ma, amma kai ma abinda nake so da kai shi ne ka bita a hankali kana lallab'ata har ta koma, kaga fa haka kawai sai kirana kayi a waya ka ce min ta tare a gidanta, na tabbata bata ji dad'in haka ba, to bana so yanzu ma tayi yaji a tilasta mata dawowa." Yar dariya yayi yana jin wata kunya na rufeshi tare da tuna washe garin ranar daya angwnce ya kira yace ai ta tare gidanta, k'eyarshi ya shafa yana mai d'an turo hularshi a gaba yana sissine kai. Murmushi t sake yi tace "Shikenan Allah yayi albarka, Allah ya baku zaman lafiya da hak'urin zama da juna, ka tashi ka tafi lokaci na wucewa." Da ladabi yace "Ameen Hajiarmu, nagode Allah k'ara lafiya." Mik'ewa yayi suka sake sallama ya fita yana mai godiya ga Allah da yasa yau akwai wanda zai iya zaunawa gabanshi kanshi k'asa ya masa fad'a, lallai wannan ma babbar ni'ima ce a gareshi ace akwai mai fad'a maka ka ji. Yana daf da shiga mota motar Asas ta danno hancinta cikin gidan, shiga yayi suka saita na su motocin zuwa k'ofar fita, tsayawa sukayi inda Asas ya tszya a daidai da motar sheikh, sauke glas duk sukayi suka kalli juna, dukansu mamakin yanda zumuncinsu ke neman ja baya sukeyi saboda mata, tunda akayi aurensu ta waya dai babu wanda ya nemi wani, Asas bai sake zuwa gidan shi ba har yau, hakan duk saboda abinda ya faru ne? Murmushi Asas yayi cike da kunya yace "Sheikh barka." Lumshe ido yayi alamar amsawa, cike da zolaya yace "Gashi kuma ganinka na zo kai zaka fita, tunda na ga yanzu amarci yasa ka manta da d'an uwanka." Harara ya watsa mishi yace "Tunda kasan inda nake ka sameni a can." D'aga gilashinshi yayi ya ma dreban umarni da su tafi, dariya Asas yayi yace "Zan zo har gidan na sameka." K'arasawa yayi shi ma su kuma suka fice a gidan zuwa wurin aiki. *10:46* *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:59 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *53* Sak'o ta tura masa gahere kamar haka _"Me za'a dafa?"_ Sanda sak'on ya riskeshi dubawa yayi da kyau dan baya tunanin ta tambayeshi, a gajarce shi ma ya maida mata da _"Idan zan samu had'in salade ma ya wadatar."_ A gajarce ta sake maidawa da _"An gama."_ Shi ma a gajarce ya maido da _"Nagode."_ Fitowa tayi ta samu Iya zaune a cikin rumfar da take girki, zaune tayi Iya ta kalleta sama da k'asa ta girgiza kai tace "Mimi Allah ya shiryaki, kuma tun jiya ciwon bai sake dawowa ba." Dariya tayi irin ta 'yan zamani tace "Haba Iya share zancen nan, kin san wani abu ma?" Tab'e baki tayi tace "Sa茂 kin fad'a." Cikin nutsuwa tace "Kinga sheikh ne yace na had'a masa salade, kinga kuma yanzu ba yara ke akwai ba da zan aika, shi ne na ce na aikeki mana." Dak'uwa Iya ta mata tace "Uwarki! Wato ni da aurena ba aure bane ko?" Dariya Mimi tayi tace "Ba haka bane Iya, to idan kinyi niyya ki barni na je da kaina mana na siyo." Wata dak'uwar ta kuma yi mata tace "Uwaki, an k'i a barkin." Turo baki tayi ta tura k'afafunta kamar zata hamb'are Iya tace "To ni wanga tsohuwar na rasa gane miki, yanzu kuma so kike na sab'a umarnin mijin na wa ko me? Na ce ki je kin ce a'a, na ce zan tafi kin ce a'a." Cikin fad'a Iya tace "Tashi d'auko kud'in ni zan je na siyo miki, amma ba zan bari ki fita ba kinji na fad'a miki." Galala ta kalleta tace "Taya zan baki siyayyar nan mai yawa haka? Wallahi na san ba zaki iya fad'in sunan kokombre ba bare kuma su karas da mayonnaise." Jim Iya tayi tana kallonta sai kuma tace "Ai shegun abubuwan nan naku ne na yan zamani da wuyar fad'a." Dariya tayi tace "Yawwa to na je ko?" A hankali ta kalleta tace "Gaskiya Mimi ina tsoron fitarki, ba wai dan ban yarda dake ba saidai kinga yanzu kamar amana ce ke a wurina, in wani abu ya faru ni za'a ce da sanina." Marairaicewa tayi tace "Iya na miki alk'awarin babu abinda zai faru, kuma ba zan jima ba zan dawo tunda kinga ba k'asa zan tafi ba." Sallama suka ji a farfajiyar gidan suka amsa yaron ya shigo, cikin girmamawa ya kalli Iya yace "Ina kwana Iya?" Da kulawa ta amsa da "Lafiya lau Sadam." Mik'o mata k'ullin goro yayi yace "Gashi wai in ji mamanmu ta ce goron Nuseiba ne aka raba." Da fara'a ta karb'a tace "A'a masha'Allah, har an raba kenan?" "E." Ya fad'a yana juyawa zai fita, da sauri tace "Sadam zo nan d'an albarka." Dawowa yayi yana kallonta ita ma ta kalli Mimi tace "D'auko kud'in ki bashi ya siyo miki." Cikin kumburo baki ta mik'e ta nufi d'akin ta d'auko kud'in, kawo tayi ta zauna ta lissafa mishi komai sannan ta ce ya shiga taxi zuwa kasuwa, cike da dattako yaron yace "A'a ki bar kud'in taxin, akan moton yaya Bello na ke." Da jin dad'in dattakon daya mata tace "To nagode sosai Sadam, ka kula da titi kaji." Fita yayi ita kuma ta d'auki wayarta ta kira Jamila dake kusa da gidan Iya, tana d'agawa daga b'angarenta ta fara fad'in "Shegiya Mimi amarya, sai yau kika tuna damu?" Tsaki Mimi tayi cike da jin sarauta akan ta ta yatsina baki tace "Ke bana son iskanci, wai ku baku san inda mutum yake bane?" Cikin dariyar mugunta Jamila tace "Ke tafi can marar mutumci, waye zai je gidanki kina kwasar amarci ke da sugar Dady d'inki." Wani irin b'acin rai ne ta ji ya taso mata da bata tab'a jin shi ba, haka kawai ta ji ta bata masifaffen haushi, da k'unar zuci ta katseta da fad'in "E d'in, sai me? Na ci amarcin da shi da matsala ne?" Tsagaitawa tayi da dariyarta tace "Ke ni ba masifa nake ji ba yau, fad'a min me ke labari? Zaki zo ranar k'umshina ne?" Cikin dak'ilewa tace "K'umshin me?" Da mamaki tace "Baki san ni zanyi k'umshin Salma ba na farko?" Ba tare da wani kulawa ba tace "Ko? Ya akayi ta baki k'umshinta kamar ta rasa dangi?" Cikin jin haushi Jamila tace "Ban gane ba Mimi? Wannan ai wulak'anci ne ma, yau a makaranta mun d'auka zaki zo ai shiru." Cike da iskanci tace "Ke ni fa ba lafiya ma gareni ba, laulayi nake, ciki ne da ni." Cike da zumud'i Jamila tace "Da gaske? Kai amma na ji dad'i, ashe dai shehinmu da saurenshi, da wuri haka?" Wani lalataccen murmushi Mimi tayi a ranta tace "Can da yawonki, wai ciki, mtsss?" A fili kuma d'orawa tayi da "Ke farantai nake so manya masu, idan akwai ki aiko a kawo min ina nan gidan Iya." Da sauri tace "Da gaske? Yaushe kika zo?" Tsaki tayi tace "Ban sani ba, idan zaki aiko min to, in kuma babu ki fad'a min." Dariya Jamila tayi tace "Zan kawo miki da kaina ma, zan zo gidan yanzu dawowata kenan daga makaranta." Tab'e baki tayi tace "Wato kuna zuwa kuyi shik'a ou dawo ko? Ai kunsan yanzu ba'a fara komai ba." Dariya Jamila tayi tace "Ai ki bari kawai, in fad'a miki PC (Physique Chimie) ma wallahi saida ya tambayeki, Lariya ma tana ganinmu ke ta fara tambaya, ga su Sadiq da su Omar, ke kowa fa bakinshi a Mimi." Wata shak'iyiyar dariya tayi kafin tace "Allah sarki Mimi mai masoya dayawa." Cike da izgili Jamila tace "Kamar aljanna ba." D'auke wayar tayi a kunne tace "Sai kin zo." K'it ta kashe kiran tana dariyar saboda tuna rayuwarta ta makaranta, a gaskiya zata sake lallab'ashi dan ta koma makaranta, tana son rayuwar nan sosai saboda rayuwa ce mai cike da 'yanci da nishad'i. *Bayan kwana biyu* Dke yammacin alhamis ne aiki take tuburan wajen had'awa sheikh abun bud'a bakin da ita ta saka kan ta ba tare da saninshi ba, 04:30 ta gama da komai ta saka a basket d'in da Jamila ta kawo mata ta ajiye jug d'in lemu gefe ta shiga wanka, wanka ta tsala ta fito ta shirya cikin doguwar rigar leshe wacce ta mata masifar kyau, kwalliya tayi sassauk'an mai ban mammaki ta kashe d'aurin d'an kwali, turare ta shafe jikinta da shi kafin ta d'auki mayafinta mai d'an girma ta rufe duka jikinta da shi ta saka saka da takalmi ta fito. Kallo Iya ta k'are mata cike da jimami tace "Mimi kina ganin shirin nan baiyi yawa ba kuwa?" Kallon kanta tayi tace "Iya wane yawa kuma? So kike na je a hargitse ne to ina wari." Jinjina kai tayi tace "Ba haka nake nufi ba, Allah ya kiyaye hanya." Dariya tayi tace "Yawwa Iya ta, sai na dawo." Cikin zolaya tace "Kuma ki tabbatar kin karb'o min na wa abun bud'a bakin a wurinshi." "To." Ta fad'a tana kallon Jamila dake shirin d'aukar basket d'in kwanukan da sauri tace "To uban wa zai d'aukar miki jug d'in?" Hararanta Jamila tayi tace "Ban sani ba, ke uban me zaki d'auka bayan jakarki?" Juyawa tayi ta kalli Iya tace "Iya dan Allah ba gabanki likita aka ce na daina d'aukar abu mai nauyi ba?" Da mamaki Iya tace "Yaushe? Akan wane dalili kuma?" Dariya Jamila tayi tace "Iya rabu da ita raina min hankali ne zaatayi." Matsowa tayi daf da ita tace "Nima dai na kusa auren nan na samu ciki." Hararanta tayi tace "Kafin kiyi dai ai har cikina yayi k'wari." Iya dai na jinsu har suka fita suna wannan cacar bakin bayan Mimi ta karb'i basket d'in ta b芒 wa Jamila jug d'in lemu, suna fita kam basu sha wahalar samun taxi ba suka d'auki hanya, wayarta ta ciro a jakarta ta dannawa lambarshi kira. Yana tsakiyar masallacin dake ma'aikatarsu duk yan ma'aikatar sun zagayeshi suna d'aukar darasin daya zamar musu saurare dole, ba komai kullum yake fad'a musu ba sai rik'o da amana da kuma yin aikin domin Allah, sannan nuna musu mahimmancin aikinsu da tuna musu al'umma suke ma. Wayarshi na fara vibration ya laluba aljihu ya cirota dan ya kashe kiran, sai dai? Wacce take kira tafi k'arfin ya katse kiranta, hasalima mamakin ganin kiran na ta ya shiga yi sanda sunan daya saka mata a lambar ya bayyana da *yan matana*. Kamar wani marar gaskiya ya saci kallon mutanen dake gabanshi sannan ya d'aga wayar ya d'ora a kunne, cikin rad'a yace "Salam, ina darasi ne, zan sake kiranki." Da sauri jin zai kashe wayar tace "Abdul." Sam ba da son ranshi ba ya dakata saboda sunan Abdul data kira, cikin shagwab'abb'iya kuma siririyar muryarta tace "Gani nan fa tafe wajenka, zamu had'u a gidan nan ne ko kuma na zo ma'aikatar?" Zabura yayi yana nufin tashi tsaye sai kuma ya kalli mutanen gabanshi ya dakata, ture hularshi yayi ta gaba ta koma baya yana tsatsare mutanen da ido da suma dayawa shi suke kallo, gyara zamanshi ya sake yi da kyau ya rufe bakinshi da tafin hannu cikin rad'a yace "Ryam ban gane gaki nan tafe ba? Munyi dake zaki fita ne?" Cike da shagwab'a tace "To ba kai ne ka fad'a min kana azumi ba, shiyasa na maka abun bud'a baki, ni kawai ka fad'a min inda zan zo na sameka kaga fa ina cikin taxi ne." A hankali ya lumshe ido ya furta "Hasbunallahu wani'imal wakil." Bud'ewa yayi fes a kan mutanen dake gabanshi yana jin kamar ya fashe da kuka, ba wai fitowar babu izininshi bane matsalar, tunanin yanda ta fito daga gidan shi ne yake masa yawo a kai, shin ta rufe jikinta da hijab ne? Ta saka nik'ab da safar k'afa? Ko kuma dai yanda ya santa a haka ta fito kowa da komai ya gama kalle masa halalinsa? Zunbur ya mik'e tsaye yana fad'in "Ku gafarceni, kira ne na gaggawa." Da sauri ya juya inda jami'anshi suka rufa masa baya da sauri su ma, suna shiga mota yace "Gaggauta dan Allah, Tallague zamu je." Yana maganar ne yana kiranta a waya, tana d'auka hankali tashe kamar wanda aka shaidawa iyalinsa na d'akin nak'uda yace "Ryam kina ina yanzu?" Cike da rashin damuwa a tare da ita tace "Yanzu muka baro gida." Da sauri yace "Hakan na nufin bakuyi nisa da gida ba?" "E." Ta fad'a kan ta tsaye, wata ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi yace "Ryam ku dakata, ku dakata dan Allah gani nan tafe sai mu tafi tare." Kallon Jamila tayi dake gefenta tace "Amma fa ba ni kad'ai bace, tare da k'awata muke." A sanyaye yace "E, har da ita d'in." D'aga kafad'a tayi alamar shikenan sannan tace "Ok." Yanke kiran yayi ya mayar da wayar aljihu, maida kan shi yayi ga kallon gabanshi sai sukayi ido hud'u da dreba dake tuk'i fuskarshi d'auke da mamaki, matse bakinshi yayi ya feso wani sanyayyen iska yana tsare dreban da ido yace "Yarinya ce, wahala take bani, amma dai nasan na d'an lokaci da ta k'ara girma zata bari." Murmushi dreban yayi yace "Hakane." Ci gaba yayi da aikinshi sai sheikh daya sake fad'in "Kana ga na ci gaba da lallab'ata a haka? Wani lokacin kamar mahaukaci nake zama wallahi, ban san ya zanyi ba." Satar kallonshi dreban ya sake yi a ran shi yana fad'in "Allah ya sauk'ak'a maka sheikh, abun ya ta'azzara kam." *Bakin* titi aka aje su suka gyara tsayuwarsu dan jiran tsammani, duk da suna cikin unguwar ne amma sun d'an yi nisa, suna tsaye sun aje kayan hannunsu a k'asa motar ta tsaya a gabansu. Mugun bugawar da k'irjinta yayi yasa ta dafe k'irjin dan tsaf ta san motar waye, bata gama tsurewa ba saida Muttak'a ya fito a gadarance har ya tsaya gabanta k'ik'am yana k'are mata kallo daga sama har k'asa. Bata tab'a jin haka ba sai gashi tana kallonshi a mugun tsorace bakinta bud'e tana had'a yawu da sauri sauri, hannu ta d'ora a kan cinyarta tana ta cumimiye rigarta, wani sakaran murmushi ya saki yace "Mimi kenan, ashe kina nan?" Ba tare data d'auke idonta a kan shi ba ko ta rusuna su ta ci gaba da kallonshi, wani mayen kallo ya mata yace "Mimi na fad'a miki idan ban sameki ba babu wanda zai sameki, na yarda wannan karan an fi k'arfina, Sheikh ko aljanun kaina suna kunyarshi bare kuma ni kaina." Daf da ita ya sake matsowa yana kallon fuskarta yace "Kinyi kyau fa, amma ki sani baki dace da zama matar tsoho ba, babu abinda zai iya yi miki." Baya ya ja ya bud'e murfin motarshi yace "Ki kula da kanki, hakan ba yana nufin na hak'ura bane." Shigewa yayi ya tashi motar yayi baya baya sai kuma ya tsaya, Mimi da har wata zufa ta keto mata sauke numfashi tayi da k'yar ta kalli Jamila dake kallon Muttak'a da bai gusa a wurin ba, dafata tayi cikin b'arin murya tace "Mu tafi kinji, mu matsa gaba dan Allah." Sunkuyawa Jamila tayi tana d'aukar kayan tace "Waye shi kuma waccen mahaukacin?" Yatsina baki tayi tace "Rabu dashi kawai, d'an k'waya ne." Sun fara takawa kenan ta hangi motar sheikh tsaye ga dukkan alama kuma tsaye suke a nan watak'ila sun jima, takawa ta shiga yi a hankali sai Jamila data tsaya tana kallonta dan ta tabbatar su d'in ne, Muttak'a na ganin haka shi sam bai ga motar su sheikh ba sai ya sake murd'awa motar giya ya taka da k'arfi ya nufi Mimi gadan gadan wanda hakan yasa Jamila kaucewa da sauri har tana sakin jug d'in hannunta. Sheikh da ke hangen komai a cikin mota zufa ta jik'eshi sharkaf sakamakon ganin Muttak'a na wani shigewa jikin matarshi kamar zai tab'ata, ga mugun wankan da ya ga ta d'auka, yanzu kuma da yake ganin motar da wani matsiyacin gudu tana nufi kan Mimi yasa shi bud'e motar da sababin sauri ya fito takalminshi d'aya irin babush d'in nan k'irar Rusia mai sunan MisTsar ya baroshi a motar sai d'aya a k'afarshi ya tako da mugun sauri har da gudu gudu ya fizgi hannunta hakan yasa shi ya tsaya ta inda motar ke tahowa ita kuma ta koma baya. Kallon juna sukayi saidai kafin wani cikinsu yayi wani yunk'uri Muttak'a ya taka birki da iya k'arfinshi saboda gaba d'aya ya razana saboda ganin sheikh, duk da haka saida motar ta daki gwiwan sheikh daya bada baya yana kallon fuskar Mimi. Sanda motar ta dakeshi lumshe ido yayi amma sam bai motsa ba, da sauri yayi baya-baya ya ja motar ya d'auki titi da gudu ya bar wurin a tunaninshi sheikh bai ganshi ba. Numfashi ta shiga saukewa gaba d'aya fuskarta ta nuna yanayin tsoro, ba tare daya saki hannunta ba ya juyar da ita ya shiga takawa da ita da k'arfi suka nufi mota, saida ya fara takawa yana jin lallausan k'afarshi na taka tsakuwa ya fahimci babu takalme a k'afarshi, turata yayi cikin mota ta shiga sannan shi ma ya shiga ya zauna, tayar da motar sukayi suka bar Jamila nan tsaye ta rasa me zatayi? Ina zata nufa? Ya zatayi da d'an sauran abinda ya rage musu? Tunda jug d'in ya fashe kasancewarshi na kwalba sanda ta sakeshi abun ciki ya zube. Gidan daya kaita ranar suka je kai tsaye ya bud'e da makulli suka shiga, a falon ya zauna kan shi a k'asa hannayenshi a jimk'e, ita ma jiki a sanyaye ta zauna kan kujera tana kallonshi, shiru d'akin babu wanda yace wani abu a k'alla minti talatin, gajiya tayi da zaman shirun kawai ta muskuta tana ci gaba da kallonshi tace "Abd..." Jajayen idonshi da jar fuskarshi da k'arara ta nuna b'acin rai ya d'ago ya kalleta kafin ta k'arasa, da sauri ya mik'e kamar an mintseneshi ya cire hularshi ya aje kan kujerar, tattara babbar rigarshi yayi ta malamai ya aje gefe ya nufo kan ta, yana tsayawa gabanta ya rik'o hannunta tayi tsaye ba tare data shirya ba, hab'arta ya tallabo ya zuba idonshi cikin na ta cikin muryar b'acin rai yace "Waye shi?" Muryarta na rawa tace "Tsohon...saurayi..." Bata gama fad'a ba ya saki hab'arta yace "Shi ne kuka had'u dan ku gaisa?" Da mamaki ta kalleshi tace "Kamar ya? Kasan me kake fad'a kuwa? Kai fa ka tsayar damu a hanya ka ce kana zuwa." A mugun tsawace yace "Amma na ce ki kula wani d'an iska ne? Ba ma wannan ba ni na fad'a miki ina buk'atar abun bud'a baki ne? Da izini na kika fito daga gida? Me kika d'aukeni ne Ryam? Nema kike ki mayar dani wani sakarai mahaukaci, akan wane dalili?" Yanda ya rufe ido yake mata masifa a cewarta yasa ta yin zaune kan kujerar tana had'e hannayenta, da mamaki ya kalleta sai kuma ya d'auke kallabin kan ta hakan ya bayyanar da yalwataccen gashinta yana fad'in "Wannan shirin fa? Wai ke baki da hankali ne?" Da sauri ta kalleshi idonta taf da hawaye ta mik'e tsaye, cikin zubo da hawayen idonta tace "Ni ce ma marar hankalin? Saboda ina ganin nayi abinda zan birgeka." Juyawa tayi kan kujerar ta d'auki jakarta da kallabinta ta juya a fusace zata fita ita a la dole ita ce yanzu aka b'atawa rai, rik'e k'ugu yayi shi ma yana kallonta har ta fita yana jin shi ma fa shi aka b'atawa dole ma a bashi hak'uri. Tana fita taxi ta shiga aka nufi gida da ita shi kuma zaune yayi a falon ran shi a b'ace kamar zai ciji wani, banda tsaki da dukan iska babu abinda yake yi yana ta tunanin lamarin yrinyar nan, ya yarda akwai k'uruciya saidai a lamarin Mimi har da wauta da hauka ma. _(Dan Allah ku fahimce ni, ba labari ne da nake rubutawa dan daidai da son ran kowa ba, abunda nake da tabbacin zai iya faruwa ga duk wanda hakan ya faru dashi nake rubutawa, ma'ana zahirinmu ba wai abinda ba zai yiwu ba, idan mukayi duba da shekarun Mimi da bud'ewar idonta, da kuma shekarun Sheikh dole hakan ya b'ata masa rai, sannan ita ma dole ta ji kamar tsuntsuwa ce da ake neman cirewa pika-pikinta dan hanata tashi sama.)_ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:59 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *54* *Kwana biyu* kenan da faruwar abun nan amma babu wanda ya kula wani ko a waya, Sheikh ya zuba ido ne ya ga tana da wayon da zata tuntub'eshi har tayi k'ok'arin bashi hak'uri, amma shiru kake ji kamar malam ya ci shirwa yasha ruwa, hakan ya d'ugunzuma hankalinshi wajen tashi sosai, dan shi fa ba haka Hafsat ta koya mishi ba, ba haka ta raineshi ba, shiyasa rainon na Mimi yanzu yake neman dagula masa lissafi gaba d'aya. Gashi a daren ranar kuma shi da uku daga cikin wasu malamai suka tafi k'asar Abuja dan gabatar da wani babban taro na malaman k'ungiyar ahlul-sunna wal-jama'a, duk da yana wurin amma kuma hankalinshi yana kan wayarshi yana saka ran ganin ko da flashing d'inta ne, gashi muguwar kewarta na damunshi, har yau idan ya tuna darensu na farko da sauren dareren da yake wasa da ita sai ya ji yana buk'atarta a kusa da shi, wasu lokutan yana d'aukar wayar dan ya kirata amma kuma saiya dakata da niyyar ya d'an hukuntata ta gane ta mishi ba daidai ba. *Mimi* Sabo aka ce tirken wawa, rashin ganin kiranshi a wayarta, rashin jin muryarta uwa uba a kwana biyun nan da ta zama mai masifar son jin k'amshin turarenshi had'e da son taji tattausan hannayenshi a na ta hannayen, sai suka taru suka mata yawa kamar zatayi hauka, tsabar d'orawa kai damuwa daren jiya mafarki tayi da ita dai ba zata kirashi da mummuna ba tunda da mijinta ne ta ga suna wata kalar azababbiyar soyayyar data saka ta tashi a wani mugun kasalance jikinta yayi mugun nauyi ga kuma fitowar ruwan da suka sa dole wanka ya kamata. *Kwana* na uku kenan yau ta tashi da wannan muguwar kasalar, haka ta zauna tana kallon Iya na kad'a miya zatayi d'umame, yar yaloluwar rigar jikinta mai k'ananan hannuwa duk sai ta ji ta mata nauyi, tagumi ta buga tana ci gaba da kallon Iya tana jujjuya wayarta. Kallonta Iya tayi tace "Tunda kin tashi me zaki ci na samu yaro ya siyo miki? Nasan dai b芒 mtuwo kike ci ba ai." Ba tare data d'auke tagumin ba a kasalance tace "Ki barshi kawai Iya, idan na tashi ci zan nema." Da kulawa ta sake kallonta tace "Kunyi waya da mijinki kuwa? Tun shekaran jiya da Hajiar ta zo nan ta ce yayi tafiya." Cikin turo baki tace "Ina kira ba'a samu, amma zan sake kira." Daga haka Iya bata sake cewa komai ba ta ci gaba da aikinta, Mimi kuma wayarta take kallo tana d'an kai hannunta kamar zata danna lambarshi kuma sai ta dakata, ajiyar zuciya kawai take saukewa lokaci lokaci tana d'an tuna shawarwarin Rayya wanda ko jiya sun jima suna hira a waya, tunawa da wata shawarar ta saka ta mik'ewa da sauri ta shiga d'aki, kwance ribom d'inta tayi take gashinta ya zuba a kafad'unta, gyara zamanta tayi sosai ta d'an duk'o yanda gwiwan hannayenta ke kan cinyoyinta, hakan kuma yasa rigar matsewa sosai nonuwanta suka d'an turo gaba. Saita wayarta tayi ta d'auki kan ta selfie tare da shiga lambar sheikh, turawa tayi bayan ta tabbatar ta kyab'e fuskarta irin zatayi kuka sannan ta rubuta daga k'asa _"Na fad'a maka baka so na, dubi yanda na rame saboda kewarka?"_ *Abuja*, a babban d'akin taro suke kowanensu da babbar riga da ruwa da lemu a gaban teburen suna ta ci gaba da tattaunawa musamman a game da harkar sabon tsarin kula da marayu, wayar dake kan teburi ne tayi zuuuuu! Alamar shigowar sak'o kasancewar idan yayi nesa da gida yana barin connexion a bud'e, ganin sunan wacce ya kwana uku yana marari da d'okin son ganin sunanta ya fito ne yasa shi d'an jan 茅cran d'in sama ya bud'e tsaron wayar, ko da ya shiga lambar da sauri ya d'aga kai dan ya tabbatar babu mai kallonshi. Gyara zama yayi a kujerar ya tallabe hab'a yana k'arewa k'irjinta kallo da ya ga ya mishi wani kyau yayi mulmul da shi, wani k'asaitaccen murmushi ya saki yana girgiza kai ya furta "Ryam." D'aga kan shi yayi ya mik'e daga kujerar yana kallon shugaban ahlul-sunna ya d'an mishi alama da kai da hannu, da ido shi ma ya amsa mishi dan ya fahimci zai yi waya ne mai mahimmanci. Yana fita ya kirata hoto mai motsi (vid茅o call, appel vid茅o). Tunawa da maganar Rayya cewa _"Ke macece kuma kin riga da kin shiga gidanshi, wani sauran aji ya rage miki da zaki ja a gidan miji? Akwai lokacin da kina jan shi ma tsinkewa zai yi dan an riga da an gama da ke, ladabi da biyayya da kuma hak'uri sune zasu zama miki jigo a rayuwar zaman aurenki, akwai lokacin da zaki ja ajinki amma kuma akwai lokacin da dole ki sauke girman kai dan ke ce a k'asa da ke, musamman ma ke Mimi da kike auren shahararren mutum wanda a iya majigi kawai 'yan mata da zawarawa ke kallon fuskarshi suna jin ina ma zai zama na su, ki iya takunki Ryam ta yanda zaki san lokacin da zaki gasawa mijinki aya a hannu da kuma lokacin da zaki fi k'ank'ara sanyi a gareshi. Kamar yanda kike da abokiyar zama zai fi kyau duk tsanani sirrinki tsakaninki da mijinki ya dinga tsayawa iya falonki ko na sa, karki bari ko da wasa ta san bakwa shiri bare har ta kaiki ga daka yajin barkono, na haneki da haka Mimi ba dan na isa ba saidan jin dad'in zaman aurenki."_ Tuna wannan kalamai yasa Mimi d'aga kiran tana sake narkewa tana wani karairaiyewa, fahimtar yau bebyn rigima take ji kuma ta gama faranta masa rai da tayi abinda bai d'auka zatayi ba sai kawai ya shagwab'e shi ma kamar yaro yace _"Ni fushi nake yi ma, shi ne sai yanzu za'a tuna da ni?"_ Kamar wata jaririya haka tayi da fuskarta cikin murya mai d'auke da shauk'i da son yin kuka tace _"Ni ce ma na manta da kai? Abdul kai ne fa baka so na, me yasa kayi hushi dani?"_ Gyara tsayuwarshi yayi ya girgiza mata kai yace _"Ryam ina sonki, na fad'a miki haka har na kusa gajiya, ki yarda ina sonki mana."_ K'wallan da take rik'ewa ne suka taho tace _"Yaushe zaka dawo? Ina so na gan ka Abdul."_ Lumshe ido yayi ya k'urawa k'irjinta ido yace _"Ry..ammm!"_ A hankali ta amsa da _"Na'am."_ Bud'e idonshi yayi fes cikin na ta yace _"Ki rufe abubuwan nan...indai ba so kike...na miki."_ Zuba mishi ido tayi tace _"Me zaka min?"_ Cikin murmushi yace _"Na miki ciki mana."_ Rufe fuska tayi da tafin hannu cike da kunya, cikin murmushi yace _"Bud'e fuskar mana, ai babu kunya a tsakaninmu, ko kin manta ke d'in matata ce sirrina."_ D'an bud'e fuskar tayi amma ba duka ba ta kalleshi tace _"Ni dai ka fad'a min yaushe zaka dawo?"_ Sauke numfashi yayi yace _"Ryam yanzu haka muna zaman k'arshe, insha'Allah yau komai dare zan koma gida, dan na bar aikin al'umma a can hutu ne na nema."_ Da saurinta tace _"Tom, sai ka zo."_ Kashe kiran tayi irin kunya take ji fa, wata dariya ya saki yana girgiza kai yace "Watak'ila fa shirin tarbata zatayi." Juyawa yayi zai koma d'akin taron yana fad'in "Ashe dai tana d'an hankali wani zubin." K'arasa shiga yayi yana ta dariyarshi shi bai ma san yanayi ba, haka ya zauna da wannan yanayin har suka gama taron nan misalin 12:30 na rana, daga nan ma tare da sakataran (secr茅taire) k'ungiyar suka halarci wani wa'azi, haka dai suka kasance har sanda dare yayi suka rakashi filin jirgi suka d'aga. *Tuni* Mimi bacci ya jima da d'aukarta a gadon Iya dan ba wani abun take yi ba, Iya ma dai har ta kwanta bacci ya fara d'aukarta taju gadon na zuuuu! Bud'e ido tayi ta daddab'a Mimi tana fad'in "Ke tashi, hala shegiyar wayar nan ce ta ki mai kukan raguna." Da k'yar ta bud'a ido ta lalubo wayar tana fad'in "Wai ke Iya a dare ma masifa kike?" K'ulli ta shirga mata a baya tana fad'in "Zan ci uabnki yanzu." Mimi kam ganin lambar sheikh ce nutsuwa tayi ba tare da sanin tayi ba ma ta d'ora a kunne, shiru kamar babu wanda zai yi magana sai kuma yace _"Fatan kina cikin aminci?"_ Numfashi ta sauke sannan tace _"Um! Ba kayi bacci ba?"_ Murmushi yayi mai sauti kafin yace _"Um! Gani a k'ofar gidansu Iya na zo d'aukarki."_ Da k'arfi ta zabura tace _"Me?"_ A dak'ile ya sake fad'in _"E, ina jiranki yanzu."_ Da mamaki tace _"Amm..."_ Bai bari ta fad'a yace _"Ryam ina jiranki yanzu ki shirya ki fito, ba buk'atar sai wani ya rakaki, ni da ke ma mun isa."_ K'it! Ya datse kiran alamar ya gama magana kenan, da sauri ta sauka a gadon tana fad'in "Iya tashi, tashi tashi Iya." Mik'ewa tayi zaune tana fad'in "Lafiya wai? Ke wannan akwai jaraba." Tsaye tayi ta kalleta tace "Wai shi ne a k'ofar gida ya zo mu koma." Da sauri ta sauko tana fad'in "Alhamdulillah, ka ga malamai magada Annabawa, haka ai shi ne daidai dama wallahi, maza maza to a tafi a bar min gidana." Tale baki tayi tace "Eyeee! Wallahi Iyar nan ma dai, ba komai." Zage doguwar rigarta tayi gaban Iyar ta shiga neman abaya a cikin kayanta, kawar da kai Iya tayi tana fad'in "Kai Allah ya shiryaki, bawan Allahn nan haka yake shan tab'arar nan iri iri a wurinki." Ba tare data juyo ba tace "To me na yi kuma?" Tab'e baki Iya tayi tace "Bakiyi komai ba." Murya k'asa k'asa kuma tace "Allah yasa ki je gabansa kina cire kayan ya tsala miki bulala a baya." Kad'awa Iya d'uwawu tayi tace "Ba bakin ki ba Iyale." Tsaki Iya tayi tace "Yar banza kinga yanda kika k'ara zama dumemiya kuwa?" Saka doguwar rigar tayi ta saka kallabinta ta yane kan ta, turare ta d'auka ta shafe jikinta sannan ta tusa duk kayanta data barbaza ta rufe jakar, d'aukar k'aramar jakarta tayi da wayarta ta kalli Iya tace "To su Iya, a yafi juna kuma dan Allah, ni na koma inda na fito, idan Abba ya zo ki fad'a masa na koma." Girgiza kai Iya tayi tace "Allah raka taki gona." Waro ido tayi tace "Yanzu Iya ina ce wa na zo gidanki shan kunu amma kike min irin haka, shikenan zan je gidan Aunty Shafi'a kawai." K'yaci Iya ta mata tace "Allah ya sawak'e min wahalar zan d'orawa kai na, ai can kuje ku k'arata." Jan jakar tayi tana fad'in "Iya har da madara fa zan dinga sha a madadin kunu, baki so mu sha tare?" Hararanta tayi sai kuma tayi murmushi ta girgiza kai irin ba magana kawai, dariya tayi tana k'arasa fita a d'akin tana fad'in "Iya dai baki yasan dad'i, to ki kula min da mai gidana idan ya dawo." Da kallo ta bita har ta fita sannan tace "Allah ya tsare, Allah ya baku zaman lafiya, Allah k'ara miki farin ciki a rayuwarki." Tana fitowa ta tsaya turus saboda ganinshi jingijine a jikin motar, cikin tak'on k'asaita ya shiga takowa gabanta, jakarta ya karb'a a hannunta ya jata zuwa bayan motar ya bud'e ya saka, juyowa yayi ya kalleta tana tsaye har yanzu. Tunani take daga tsayen tare da hango yanda zata kwanta a k'irjinshi, wallahi har ranta take son taji ta shiga jikinshi tayi luf shi kuma ya sake rufeta da hannayenshi dake d'auke da babbar rigarshi, tan so ta lumshe ido ta ja numfashi sosai ta sake k'amk'ameshi. Amma wani abu d'aya shi ne daga ganinshi yanzu da yanda turarenshi ya daki hancinta sai taji tsigar jikinta ta tashi, wata kasala ta ji a take har saida ta lumshe ido saboda sanyayyen fad'uwar gaban da ta ji, haka kawai ta ji har wani abu yana tsikara mata a gabanta tare da jin wani mutsu mutsu kamar ruwa na zubo mata. Gyara tsayuwarta ta sake yi ta matse k'afafunta wuri d'aya sai kuma ta ji tattausan hannunshi data kwana biyu tana mararin ya tab'a na ta hannun, janta yayi a hankali ya bud'e mata k'ofar ta shiga ta zauna, shiga yayi shi ma ya zauna sai lokacin ta tatbbatar tare suke da dreba ashe. Har suka d'auki titi babu wanda ya ce wani abu, saidai hannunshi dake cikin na ta har yanzu yana ta murzawa yasa gaba d'aya ya kashe mata jikinta, banda zubar abu a k'asanta babu abinda take ji, k'aik'ayi take ji jikinta na d'uka musamman ma k'asan dz kuma nonuwanta, lumshe ido take tana lashe leb'enta da take jin yana bushewa. Sheikh da a hankali yake satar kallonta shi ma lumshe idon yake yana jin dad'in yanda yake tattausa hannun na ta mai tuwon gaske, saida suka yi nisa a hanya kafin ya d'an sunkuya kusan kunnenta yace "Kinyi kewata ne?" K'ara rintse ido tayi sai taji kamar zata ce "Wayyo Allah na." Sunkuyar da kai tayi dan ita kam wannan abu da take ji kuka ma yake neman sakata, murmushi ya saki na jin dad'i tare da kuma rusunawa yace "Ina kewarki." Rawa bakinta ya d'auka hakan yasa ta d'agowa ta kalleshi da idonta da suka canza kala dan jaraba bakinta na hard'ewa tace "... _Karku saka ran ganin rubutu gobe dan ina da abubuwa dayawa gaskiya._馃グ *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:59 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *55* Rawa bakinta ya d'auka hakan yasa ta d'agowa ta kalleshi da idonta da suka canza kala dan jaraba bakinta na hard'ewa tace "Ab..du...l." Murmushi ya saki yana kallonta bai ce komai ba har suka isa gida, da kanshi ya bud'e mata k'ofar ta fito ya zagaya ya d'auki jakarta, tunkarar shiga falon sukayi yana fad'in "Da fatan ba zaki sake yi min yaji ba ko?" Cike da kunya ta sunkuyar da kai sai kuma ta kalleshi tace "Indai Aisha ba zata daina min rashin kunya ba gaskiya..." Kallonta yayi yace "Da matsala kenan? To indai Aisha ce kwantar da hankalinki, tana d'akin mijinta ita ma." Da sauri ta kalleshi tana zaro ido tace "Aishar? Har..." Sai kuma tayi shiru, jinjina kai yayi yana tura k'ofar falon a sanyaye yace "E, kwananta biyu d'akin mijinta." Cak ta tsaya tana kallonshi da yanayin rashin jin dad'i tace "Amma kuma baka fad'a min ba, ban sani ba wallahi da na..." Ajiyar zuciya ta sauke da rashin jin dad'i, murmushi yayi yana kallonta yace "Ba biki akayi ba, nasan kuma fushinki ba zai wuce ki ce baki zo biki ba, aure kawai aka d'aura a masallaci, ni ma bana nan akayi d'aurin auren." Sallama yayi a falon a tausashe yana shiga gaba d'ayanshi, gaba d'aya k'ofar suka zubawa ido suna amsa sallamar da fara'a a fuskarsu, duk mik'ewa sukayi da sauri sukayi kan shi, Munzeer ya fara d'auka kafin Aswan ya rumgume shi haka ma Heezam, Hafsat ma a hankali ta k'araso tana kallon Mimi dake bayanshi tana amsa gaisuwar su Heezam da fara'a. Tafukan hannayenta ta saka ta rufe fuskarta cike da raha tace "Har na ji kunya k'anwata, na ji kunyar ganinki ba tare da ni na je na taho dake ba." Sai kuma ta bud'e fuskarta ta matsa kusan Mimi suna kallon juna tace "Amma kiyi hak'uri dan Allah, wallahi sabgar auren Aisha ne ta d'auke min hankali na." Cike da dauriya da jin kunya ita ma ta d'an turo baki tace "Ni ai hushi nake daku aunty." D'an waro ido tayi tace "Lahhhh! Me mukayi kuma? Ko da yake nasan muna da laifi, amma ki gafarcemu." Takwaf takwaf tayi da fuskarta tace "Aunty auren Aisha fa akayi ban sani ba." Sai kuma ta sunkuyar da kanta tace "Ko da yake laifi na ne, inda ina nan da anyi komai da ni ai." Da farin ciki Hafsat ta rumgumeta a jikinta tana fad'in "Kiyi hak'uri Mimi, ranar ma sharrin shaid'an ne abinda ya faru, insha'Allah ba zai sake faruwa ba." Cikin d'ari d'ari ita ma ta d'an shafa bayanta tace "Ni ma ki yafe min aunty wallahi nayi nadama." "Ba komai." Ta fad'a tana d'agowa daga jikinta, Sheikh dake kallonsu cike da jin dad'i ne yace "Wato ni an wareni ko? Ko ganina ma ba'a yi." Wani farrrr Hafsat ta masa da ido tace "To ina ta yar uwata ina zan dubeka sheikh." Jinjina kai yayi yace "Uhum! Ni kuma da ba d'an uwanki ba ko?" Murmushi tayi tace "Ranka shi dad'e barka da zuwa, an zo lafiya?" Da murmushi shi ma yace "Lafiya lau Sawwama, ya gida da yara? Na bar miki ragamar komai a hannunki ko? Allah ya miki albarka ya ci gaba da baki ikon kula da gidan nan ko bayan raina." Wani dammm! Mimi ta ji tayi saurin kallonshi, murmushi Hafsat tayi tace "Ameen ya Allah." Murmushi ya mata ya kalli Mimi yace "Ki wuce ciki." Jinjina kai tayi ta ja jakarta ta nufi na ta falon, d'an kallonta Hafsat tayi sai kuma ta dawo da kallonta kan Sheikh dake fad'in "Hajia muje a had'a min ruwan wanka ko." Kallon yaran yayi yace "Zan shiga na fito sai m没 zauna da ku muyi hira." Da ladabi Heezam yace "A fito lafiya Abie." Saida suka nufi hanyar d'akinta cikin rad'a Hafsat tace "Yallab'ai, ina ga me zai hana ka je wajen k'anwata, kaga yau ta dawo ya dace ka zauna da ita." Da mamaki ya kalleta yace "Ban gane ba? Kin manta kwananki ne? Ai ita tayi yaji ta bar gidan, hakan ba zai sa dan ta dawo ba na d'auki kwananki na kai mata ba." Murmushi tayi tace "Ba haka nake nufi ba nima, nufi na na bar mata kwanan na wa, duba da yajin ma ai ni da 'yata ne silarshi." Girgiza kai yayi yana wucewa da alamar bai fa gamsu ba, rik'o hannunshi tayi a marairaice tace "Dan Allah sheikh, wallahi na bar mata ne har cikin zuciyata." Harara ya galla mata yace "To na fad'a miki ina da buk'atar wani abu ne a gurin wata? Bacci zanyi na huta gajiya malama, idan kwa'a dani ne ba zaki iya ba sai ki je d'akina." Wucewa yayi ya barta hakan yasa ta binshi da kallo, girgiza kai tayi ita ma kafin ta bi bayanshi gabanta na fad'uwa tana tunanin ta yanda zata fara fad'a mishi bata sallah yanzu, a k'aida dama tana ganin jini take fad'a masa ko da baya gidan, wannan kuma an yi katarin baya gari kuma yau data kira dan ta fad'a masa sai layin ya k'i shiga har sai yanzu da ya zo, da a ce bata riga ta masa tayin kwana d'akin Mimin ba, yanzu idan ta fad'a masa sai ya ce dan tana so a dole y'a kwana a can ne. Cikin kissa da salo take tayashi cire kayan tana ta langab'ewa tana son fara d'aukar hankalinshi zuwa kan ta kafin ta fad'a masa, tsura mata ido yayi yana kallo sai kuma ya saki murmushi yace "Menene?" Cikin shagwab'a kamar wata yarinya tace "To ni ai..ai jiya ne..." Sai kuma ta turo baki ta k'i cewa komai, ba tare daya daina kallonta ba yace "Ke ai me? Ina jinki." K'asa tayi da kanta sannan tace "Ai bak'ona ne ya zo jiya, kuma ina ta k'ok'arin fad'a maka amma..." Tallabo hab'arta yayi yana kallon cikin idonta yace "Manga? Ya kike neman zo min da wata sabuwar tsirfa kuma? Ni d'in ne baki buk'ata yau a shinfid'arki?" Da sauri ta kalleshi ita ma tace "A'a a'a! Ba haka bane wallahi, da gaske nake fad'a maka." Da zolaya ya bita da wani kallo yace "In gani to." Zaro ido tayi sai kuma ta ja baya tana dariya tace "Haba dai." Hararanta yayi yace "Baki da gaskiya kenan?" Sake marairaicewa tayi tace "Na rantse gaskiya na fad'a maka." Jawota yayi ta fad'a jikinshi da k'arfi cikin rad'a yace "Ko gaskiya ne ai kin fi kowa sanin hanyar da kike bi kina saukeni idan na hau." Cikin jin kunya ta sunkuyar da kai tace "Da zaka daure ka je wajen yar uwata da na ji dad'i sheikh, wallahi tausayi take bani yarinyar bata da matsala." K'arasa cire kayan yayi kawai ya shige ban d'aki ya barta nan, girgiza kai tayi ba tace komai ba sai ma fita dan ta shirya masa wajen cin abinci, bata jima ba ta dawo haka shi ma bai jima ba ya fito, zaune yayi ya ci abincin sosai ya k'oshi kafin ya kalli agogon dake d'akin inda ya nuna masa k'arfe 10:58 na dare, nauyayyen numfashi ya sauke tare da fad'in "Bari na duba k'anwarki na ga ko tayi bacci." Da sauri ta mik'e tana murmushi tace "To, saida safe." Da mamaki sosai a fuskarshi yace "Wai da gaske kike?" Jinjina kai tayi ta matse d'an k'aramin bakinta alamar e, a sanyaye ya jawota jikinshi ya rumgume yana lumshe ido, sumbatar wuyanta yayi tare da saka harshenshi ya d'an lashi wuyan na ta, tsam! Ta sake rik'e bayanshi tana mai sake lumshe idon ta, cikin kasalalliyar murya yace "Allah ya miki albarka Qawwama, zanyi kewarki." Kamar zatayi kuka tace "Ni ma haka." A hankali ya d'agota daga jikinshi yana kallon fuskarta yace "Allah ya baki ladar abinda kikayi na alkairi." "Ameen." Ta fad'a tana sauke numfashi, kuncinta ya sake sumbata sannan ya fita a d'akin, saida ya samu su Heezam suka d'an tattauna a tsatsaye kafin suyi sallama kowa ya nufi d'akin baccinshi shi ma ya wuce d'akin Mimi. Da sallama ya shiga amma shiru babu amsa, saida ya k'arasa shiga cikin d'akin bacci ya fahimci har ta kwanta, saidai bai da tabbacin bacci take ko kuma idonta biyu, dawowa yayi ya kashe wutacen ya koma d'akin, cire doguwar rogarshi yayi ya aje sannan ya haura gadon ya kwanta daf da ita, zanin data dunk'ule cikinshi ya ja ya shiga shi ma yana lek'a fuskarta yace "Ryam." Cikin magagin baccin daya fara d'ibarta ta amsa da "Uummm!" A sanyaye yace "Bacci wai?" D'an muskutawa tayi ta gyara kwanciyarta hakan ya bashi damar jawota gam a jikinshi, shiru tayi ba tace komai ba tana tunanin me ya tsaida shi bai shigo ba har tayi wanka ta shafa mai da turare ta saka rigar bacci ta kwanta, jin hannunshi cikin rigarta yana shafa mararta yasa ta saurin zabura ta kalleshi, shi ma kallonta yayi saboda yanda ta zabura yace "Ya dai? Yunwa kike ji ne?" Da sauri ta girgiza kai alamar a'a, ci gaba yayi da shafa marar har ya fara haurawa zuwa sama yana shafa k'irjinta cikin lumshe ido yace "Waye shi Ryam? Me yake fad'a miki a ranar?" Shiru tayi tana jin gaba d'aya hankalinta na neman gushewa ya barta saboda al'amarin da take ji yana ratsata, kasa magana tayi dan har ga Allah idan tana jin yanayin nan sai taji kuka ke son taho mata, cikin kunne ya sake rad'a mata "Uhum! Ina jin ki?" Zubo da hawayen tayi cikin shashek'a tace "Abdul jaki ne wannan mutumin, ban tab'a jin ko da sha'awar kallon fusskarshi ba na minti d'aya bare har na ji k'aunarshi, na tsaneshi, na tsaneshi saboda baya da hankali." D'ago hab'arta yayi ya kalli fuskarta a hankali ya had'a bakinshi da na ta ya shiga tsutsa, duk k'ok'arinta na son rik'e kan ta saida ta samu kan ta da matse k'afafunta tana bank'arewa tana kuma shafa kan shi da hannayenta biyu, alamar dai abun na mata dad'i kuma a shirye take data karb'eshi. Inda a wajen Sheikh kuma ya ke sake gasgata lallai fa yarinyar na da wadatar lafiya, hakan ya saka mishi tsoron kar fa a zo ita d'in irin hallitar nan ce mai maysananciyar sha'awa, idan hakane kam dole yayi gaggawar canza sabon tsarin tafiyar da gidanshi, dan kam ba zai yarda yayi sanadiyar shiga yarinya halaka ba, haka kuma zai dage wajen k'ra inganta lafiyarshi dan ganin bai cutar da ita ba. Cikin nutsuwa ya sab'ule mata rigarta ya shiga lailaya k'irjinta, a hankali ya kai hannunshi k'asanta ya soka a cikin pant d'inta, da sauri ya d'ago kan shi ya kalleta a d'an tsorace yace "Ryam, me kika sha? Wani abu kika sha ne?" Mimi da idonta ke rufe ta cije leb'enta girgiza masa kai kawai tayi, da sauri ya hau ruwan cikinta ya k'arasa yin k'asa da pant d'in ya d'an wara k'afafunta, shi ma sab'ule...馃槑 ya kalli fuskarta yana mai saita kan shi izuwa duniyarta yana rad'a mata "Inna...kin, kin shirya? In shiga? Kin tabbata ba za..." Shiru yayi yana sauke tagwayen numfashi tare da fara danna kan shi izuwa matancinta, rintse ido yayi ya cije leb'e yana addu'ar saduwa tare da addu'ar Allah sauk'ak'a mishi shi dai ya shiga hanyar nan ba tare da an ji kan su ba, cikin ikon Allah kam dake wurin a jik'e yake kuma ya tafi a hankali a hankali har ya samu hanya ya wuce. Yana shiga ta waro idonta tana sakin k'ara da fad'in "Wayyo Allah!!! Washhhhhhh! Abdul zafi." Lumshe ido tayi hawaye suka gangaro mata a gefen idonta, shi kan shi sauke wani numfashi yayi ya kwantar da kan shi a tsakiyar mamanta, sannu sannu ya ci gaba da gyarawa kansa zama a jikinta saida ya ji komai daidai, a hankali ya fara aikatar da ita cikin nutsuwa da fitar hayyaci da zaucewa, tun yana daurewa yana rufe bakinshi yana fito da sautin gurnaninshi har saida al'amarin yar babyn yafi k'arfin tunaninshi ya fara bud'a muryarshi yana fad'in "Wayyo Allah! Wayyo Ryam, Ryam, wayyo Allah...." Dad'in da yake jin yana ratsashi ga ambaliyar ruwan da ke sauka mai damk'o da kauri yasa shi dagewa iya iyawarshi yayi ta caccakar yarinyarshi yana yi yana sambatu mai d'auke da muryar kuka da dariya. Mimi kuma na jin azabar ta fara mata yawa ta fara rera kuka tsakaninta da Allah tana fad'in ita fa wallahi ta gaji zai kasheta, wani k'arfi yaji kukan na ta na k'ara masa tare da ji a ran shi ashe shi ma ya cika namijin da ke wahalarwa akan gado, hakan yasa shi sake nuk'urk'usarta yana fad'a mata sannu ya kusa zuwa. Saida tayi laushin da hannu kawai take iya d'aga tana daddab'a damtsenshi tana fad'in "Ya isa, ya isa Abdul na gaji, ka daina hakanan ka ji." Saida ya kammala k'ark'af kafin ya cire jikinshi a nata a hankali, wata rumguma ya mata kamar za'a rabashi da ita yana manna mata sumbata a baki da hanci da kumatu da goshi yana fad'in Allah ya mata albarka Allah ya faranta mata kamar yanda ta faranta masa. Sai gashi yau sheikh ko da sukayi wanka tare ya canza musu zanin gado rumgumeta yayi tsam suka shiga bacci hankali kwance a nutse ba tare da jin yau zai tashi cikin dare ba, ita ma k'am tayi a jikinshi ta lafe tana sauke ajiyar zuciya tana fad'awa kan ta "Ashe haka yake? Dama haka tsofaffin suke? Wai ya akayi ne take neman kwafsawa ta kayar da kan ta? Garin ya ya lamarin tsohon nan ke neman gagararta ne? Gaba d'aya al'amarin shi neman fin k'arfin tunaninta yake, gashi a gado ma tun tana jin dad'in abun da farko har ta fara jin rad'ad'i tana kuka da hawaye tana nuna tayi saranda, gashi wani abu da da take ji daban a game dashi abun ya fi k'arfin wasa, abu ne da zata iya kwatantashi da har ranta zata iya fansar raina dana sheikh." Da wannan tunanin bacci ya fara yin gaba da ita kafin ya fahimci haka ya tofeta da addu'a shi ma ya rufe ido yana neman bacci ido rufe. *Asuba ta gari* Soyayya mai tsafta da mutumta juna ke guda a gidan na sheikh Abdul Waheed, matanshi na zaune lafiya suna girmama junansu kowace tana ba wa yar uwarta da darajarta, gashi yanzu gidan na su ya sake yin shiru babu yara, Heezam Allah yayi tafiyarsa Madina, Aswan kuma wasu lokutan sai daf da magriba yake dawowa gidan ya sake shiryawa ya tafi masallaci wani sa'in sai shiga kwana yake dawowa, daga su sai Munzeer kawai dan Khadija ma har yau tana asibiti saidai su je su ganta su dawo. Hakan yasa lokuta da dama sheikh ke titseyesu yana fad'in dan Allah su haifo masa yara mana da zasu dinga masa oyoyo, Mimi dai murmushi take yi bata magana, dan ita fa indai a gaban Hafsat ne nunawa take ita d'in wata manja-gara ce da bata san me ye aure ba, amma fa idan suka shiga daga ciki sheikh har yi yake kamar zai suma dan lamarin Mimi kam abun sai addu'a. Duk da wata nutsuwa ta fara zuwa mata tare da wani irin sanyi kamar ba ita ba, amma kuma ranar da take jin k'arfin jikinta yana shan mamaki, dan kad'an ne a aikinta ta tsaya gabanshi ta dinga kwasar shoki tana jefa masa ita a fuska ko tana masa rawar mazaunai, tun abun na masa wani banbarak'wai har ta d'an fara bashi kunya, yanzu kuma kawai sai take birgeshi tunda dai ai shi ne ake ma ba komai bane. Tabbas akwai k'uruciya a tare da ita mai d'auke da wautar kasancewarta 'yar fari kamar yanda aka canfa, saidai a haka yake tafiya da abarsa kuma babban abun farin cikin a yanzu shi ne yanda take d'aukar kowane na shi tana sawa a kan ta, hatta makaranta daya umarceta ta dinga fita tare da Hafsat bata masa musu ba, watak'ila abubuwan da ake koyarwa suna tasiri a gareta shiyasa yanzu take sake girmama shi da kambamashi har take tutiya da ita ma matarsa ce, dan idan kwananta ya k'are a kwana biyun Hafsat babu abinda take yi ban da kula da kan ta, idan kuma kwana biyun ta ya cika haka zatayi ta masa billi tana botsarewa tana kukan shagwab'a a dole zai tafi ya barta har kwana biyu. *Bayan wata uku* Da sauri ya shigo d'akin dan duba me ya tsaida ita Hafsat har ta shiga islamiyya ban da ita, zaune ya sameta bakin gado ta buga tagumi, shigowarshi yasa ta d'aga kanta ta bishi da kallo, d'auke tagumin tayi ta mik'e a kasalance ta nufeshi ita ma. Sheikh daya bi gaba d'aya jikinta da kallo ganin kayan dake jikinta alamar ko shiryawa ba tayi ba, gashi kayan nan masifan birgeshi suke idan ta saka, duk wata tsohuwa da sabuwar sha'awarshi tayar masa suke yi, kasancewarta fara sai kayan kalar bak'ak'e suke karb'an fatarta, rigar hannayenta kamar na singlet suke ta kamata sosai, sai wandon da tsayinshi iya cinyarta ne kawai sai rubutun Gucci da aka zagayesu da shi, suna mata kyau sosai, suna had'ewa kawai ta fad'a jikinta ta kwanta luf cikin shagwab'a tana fad'in "Abdul bana jin dad'in jikina, dan Allah ka min addu'a ka ji." Tallabo kan ta yayi suka kalli juna cike da kulawa yace "Me yake damunki yan matana? Shiyasa baki yi shirin islamiyya ba kenan?" Cikin turo baki tace "Um." Da kulawa yace "To fad'a min me kike ji?" D'an d'aga girarta tayi sama tace "Kai! Abun fa dayawa ne." Shi ma d'aga Girard yayi yace "Allah? To zo zauna ki fad'a min na ji." Jan ta yayi suka zauna bakin gado yana kallonta yace "To ina jinki." Cike da shirme da sakarci ta shiga nuna masa da hannu tana fad'in "Ka ga nan marata sai ta dinga ciwo idan na tab'a, sannan ina jin ana motsi wani lokacin kamar ana harbina." Ta fad'a duk tana d'ora hannunshi a marar ta ta, tas ya zuba idonshi kan marar ta ta yana fad'ad'a murmushi a ran shi yana godewa Allah dan shi kam har ya harbo jirgin, d'orawa tayi da "Kuma ka ga sai kaina ya dinga min ciwo dan danan, sannan ga ciwo a tafukan k'afafuna kamar ana kunna min wuta, sannan bayana sai ya dinga min ciwo..." D'ora kan ta tayi a cinyarshi tace "Ni wallahi ma kamar na mutu nake ji..." Duk da ta kai k'arshen kalmar amma saida ta dakata ba tare da shiri ba, fizgota yayi da k'arfi suka kalli juna a wani yanayi na daban, yanayin rauni ne ya bayyana a tattare da shi tare da sassauta muryarshi yace "A'a Ryam! Ba yanzu ba kinji? Mutuwa dole ce ga mai rai, amma ba yanzu ba Ryam, ina sonki, ina son ki ci gaba da rayuwa har ki ga jikokinki." Murmushi tayi ta rumgumeshi tsamtsam tana sako da hawayen da take jin su daga zuciyarta ne tana fad'in "Abdul wani abu nake ji a kan ka, a can cikin zuciyata nake jin wani muhimmin abun da bayan iyayena babu wanda nake jin kwatankwacin haka a kan shi sai kai." D'agota yayi a jikinshi ya kalli fuskarta yace "To ki fad'a mana ki huta Ryam, ki fad'a min ki ce Abdul ina sonka." Mak'ale kafad'a tayi tace "Ni ai ba so bane, kawai dai dan mun shak'u ne." Dungure mata kai yayi yace "To tashi canza kaya muje asibiti a duba min ke, kafin mu dawo na wa su Hajia albishir kina da ciki." Da k'arfi ta kalleshi ta dafe k'irjinta da taji ya buga tana zazzaro ido tace "Me? Ciki?" Sai kuma ta mik'e a tsoraxe tana shafa mararta ta kalleshi tace "Tsohon yan matanshi ka daina min irin wannan wasan, kaga dai babu kyau tsorata musulmi ko? Ka daina dan Allah bana so." Juyawa tayi zata nufi falo tana fad'in "Haba dan Allah, na samu ciki na kalli mutane da wane ido kuma? Shikenan sai na yi tsaye na kallesu su kalleni su kalleka su ce ni da kai dama lalatattu ne?" Mik'ewa yayi da sauri ya rik'o yana fad'in "Mu ne lalatattun? Ko kuma dai ni da nayi cikin?" Da sauri ta rufe ido tace "To ai haka mutane zasu fad'a, haba dan Allah ni fa yar yarinya ce, kai kuma ka ga babba ne ko?" Da zolaya yace "Sa'an Abba ko?" Dariya tayi ta fad'a jikinshi tana sauke numfashi tace "Abdul tsoro nake ji, bana so na samu ciki yanzu dan Allah kayi wani abu a kai." K'am k'am ya matseta a jikinshi yace "Tsoron me kuma bayan ina tare da ke?" Sake lafewa tayi jikinshi tana jin wata k'aunarshi na ratsata, dan gaskiya soyayyar da yake nuna mata bata tunanin da Asas ta aura zata samu kwatankwacinta, kai ita ta ga aya k'arara, tsohon nan ya bud'e mata kwanyarta ta d'auki darasin rayuwa, ita kam da za'a maida rayuwarta baya da zata sake fatan auren *babban mutum* mai addini kamar sheikh d'in ta. Duk yanda ya so su je asibiti nunawa tayi ai babu abinda ke mata ciwo kawai ba zata je ba, k'yaleta yayi bai takura ba saidai yasan dole zata buk'aci ganin likita. *Aish-Nas* Duk da ba wata soyayya bace a tsakaninsu, amma dai akwai girmama juna da mutumtawa, yau ma shiryawa sukayi zuwa gidansu Anas d'in dan gaishe da mahaifiyarshi da bata da lafiya, a tartsetsiyar motar da sheikh ya bashi a matsayin kyauta ta kyautatawa tsakanin d'alibi da malami suka isa k'ofar gidan, suna zuwa tare suka fita yana rik'e da kwanukan abincin, suna kaiwa daf da k'ofar ya mik'a mata yace "Shiga zan jiraki a nan." Da mamaki ta kalleshi duba da sau uku haka na faruwa, idan ya kawota gidan saiya tsaya ita kad'ai ke shiga, ba tare data daina mamakin ta sunkuyar da kan ta cike da ladabin da uwarta ta d'orata a kai tace "Ka gafarceni idan ka ji haushin tambayata, amma dan Allah me yasa kai baka shiga kullum sai dai ka tsaya a nan?" Murmushi yayi ya d'an kalli gefenshi kafin ya kalleta yace "Aisha ba zan shiga gidan nan ba a yanzu, amma zan shiga wata rana." Sake d'agowa tayi da mamaki tace "Me yasa to?" Numfashi ya sauke ya gyara tsayuwa da kyau yace "Kin gane? Abbanmu ne ya mana iyaka da shiga gidansa, ba ni kad'ai ba duka 'ya'yanshi maza masu hankali, ke har da ma mata masu aure ya gindaya mana tsinuwa idan muka shigar masa gida ba tare da izininshi ba." A firgice ta kalleshi tace "Subhanallah! Yaya Anas me kuka masa da zafi haka? Babu kyau irin wannan fa ko kad'an, ka fad'a min dan Allah sai na tayaku bashi hak'uri ya yafe muku." Ba tare daya daina murmushin fuskarshi ba yace "Humaira, ba wani babban laifi bane muka aikata, k'anina dake bi min ne wata rana ya samu mahaifiyarmu da matar Abbanmu amaryar da yayi suna fad'a, shi ne ya siye fad'an har yayi gangancin dukanta, akan wannan ne ya had'amu gaba d'aya ya nesantamu da shi." Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta yace "Tunda yayi auren nan komai ya canza, mahaifiyarmu ma bata da lafiya ne saboda shi, amma bamu da bakin magana, kullum cikin fatattakarmu yake da hantararmu, akan amaryar nan nunawa yake babu mai mahimmanci sama da ita." Murmushi ya mata ya nuna mata k'ofar yace "Shiga ciki zan jiraki a nan." Jiki a mace Aisha ke kallonshi tana jin wani abu a zuciyarta, sai take tuna sanda na su uban yayi aure da kalar iskancin da tayi amma sau d'aya kawai mahaifinta ya iya marinta, kai a dalilinta ma har yaji matar uban na ta tayi kuma a haka bai d'auki tsatsauran mataki a kan ta ba, hasalima har gaisheshi take ya amsa saidai sake mata fuska kamar baya ne ya daina. Kuma har yau idan ta je gidan bata wani sakin fuska da jikinta ga Mimin, hasalima daga gaisuwa bata k'ara ce mata komai ba, amma yanzu da ta ji abinda Anas ya fad'a mata sai kawai ta ji wata kunya ma ta kamata, sai taji tana buk'atar b芒 wa Mimi hak'uri sannan su koma kamar yanda suke a baya kafin ta tare gidan uabnsu. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:59 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *56* Rayuwa kenan, yau Mimi da kan ta ce tasa a tuk'a mata tuwo dan ta ci, tunda ta kira Aunty Shapi'a ta fad'a mata haka sheikh ya tsura mata ido yana kallo da mamaki, tunda ta fahimci kallon me yake mata ta d'auke kai tana basarwa, murmushi yayi ya mik'e tsaye yana fad'in "Allah ya raba lafiya." Kallonshi tayi cikin turo baki tace "Ni fa babu abinda nake da, a fa daina alak'antani da ciki." Bai juyo ba sai ma wucewa da ya ci gaba da yi zai fita yana fad'in "Yo mutum idan masifa yake ji ya fita waje yayi mana, ni a wani tsatsareni nan dan an ga ba ruwana bana duka." Fashewa tayi da kukan shagwab'a tace "Sheikh ni ko? Ni kake fad'a ma magana? Ba komai ka ci gaba da yi cizgani, kuma ai ko dan cikin jikinka ga dinga lallab'ani kana lelena." Juyowa yayi yana gimtse dariyarshi yace "Toh! Dama ciki ne da ke?" Da sauri ta girgiza kai hakan yasa shi sakin mirmushi ya juya ya fita a d'akin yana fad'in "Na tafi tafsir sai na dawo." D'aga masa hannu tayi alamar bye bye tace "A dawo lafiya tsohon yan matanshi." Shi ma hannun ya d'ago mata sanda yake fita a d'akin zuwa falonta kafin yake ficewa, saida ta tabbatar ya isa falon ta mik'e da gudu tana hangen bayanshi tayi tsalle ta hayeshi wanda hakan ya zo mishi a bazata saida yayi gaba da k'arfi yana tangal tangal sai kuma ya tsaya da k'afafunshi yana juyo da kan shi yana son kallonta yace "Oh Allah! Oh Allah ka ga baiwar nan taka ka shirya min ita." Dariya ta kyalkyale da ita tare da saukowa a bayanshi tana fad'in "Ni ma na rama abinda ka min a ranar." Da fara'a ya kalleta yace "Amma Ryam ke ai yanzu ba ke kad'ai bace, ciki ne da ke fa, ko kina ki zubar mana da shi ne? Kinsan dai ina son ku aje min yara ko?" Bubbuga k'afafun ta shiga yi a k'asa tana fad'in "Um um fa! Idan fa kana kirana mai ciki zai daina yi maka shokin ma, kasan dai kai ka ce tana birgeka idan ina yi ko?" Cikin fad'ad'a dariya yace "Idan kika daina sai ki koya min ni na dinga yi miki." Da sauri ta zaro ido tace "Lahhh! Astagfirullah, Allah ya tsareni da koyawa shehi na rawa, ai sai mala'iku su tsine min." K'yalk'yalewa yayi da dariya yana fad'in "Wato dai so ake na makara a tafsir ne ko?" Matsowa tayi daf da shi ta shiga gyara masa zaman hularsa da rigarsa tana fad'in "Kaga dai yau babban tafsir zakayi kuma haskawa kai tsaye ne, ka kula sannan ka nutsu ka aje hankalinka wuri d'aya ko Allah ya sa ka dace da fad'arsa." Sumbatar kuncinta yayi yace "Nagode Ryam, ina k'aunarki sosai, ina alfahari dake." Murmushi tayi tace "Baka buk'atar komai?" Girgiza kai yayi alamar a'a yace "Babu, sai abu biyu kawai, bansan ko zan samu ba?" Da kulawa ta kalleshi tace "Me fa? Yallab'ai ka d'auka ma angama." Suna kallon cikin idon juna yace "Na farko ina so ki bani damar sumbatar k'aramin Abdul Waheed d'in dake kwance cikin mararki, hakan zai k'aramin karkashi. Na biyu kuma ina so na ji kin fad'a min kina so na." Murmushi ta saki tare da d'aga rigarta tace "Na baka izini tsohona, idan ma kana buk'ata zan iya ara maka shi ku tafi tare ai." Tintserewa yayi da dariya yace "Taya zan tsinana wata tsiya a tafsir ina da k'aramin cikin nan, ai zan zauna nayi ta shafarshi ne." Dariya ita ma ta dinga yi har saida yace "To na biyun fa." Wulwula idonta tayi sai kuma ta d'aga k'afafunta ta cimma tsayinta ta manna masa sumbata a kuncinshi da ke zagaye da yalwataccen gemu, da gudu ta nufi shiga d'aki inda ya bita da kallo yana dariya, girgiza kai yayi ya sa kai ya fita zuciyarshi wasai yana jin wani nishad'i. Babban masallacin Gaddafi suka sauka inda yake d'auke da manyan mutane, masallacin cike yake da dubbanin jama'a sun kasa kunne suna sauraren nutsatsen wa'azin, inda yake nusar dasu da raha yanda zasu fahimta tare da kafa musu misalai, gabanshi cike yake da wayoyi ga kuma kamarori dake d'auka da babban gidan telebejin t茅l茅 sahel dake d'auka su ma suna haskawa kai tsaye. K'aramar wayarshi daya bari kunne ne mai d'auke da lambobi masu mahimmanci tayi haske alamar sak'o ya shigo, sanin ko ma waye yasan yana tsaka da mahimmin abu yasa sheikh d'aukar wayar dake gabanshi, duk da haka kuma bai daina fad'an abinda yake fad'a ba a bakinshi, saidai yana sauke idonshi a kan gajeren sak'on da Mimi ta turo masa mai d'auke da tsirarun kalmomi kamar haka _"Ina sonka."_ Sai ya samu kanshi da yin shiru na 'yan tsirarun sakanni, aje wayar yayi a ranshi ya fad'i "Nagode Ryam." A zahiri kuma d'an saita nutsuwarshi yayi ya kalli gabanshi yana d'an gyaran muryar da zummar ci gaba sai kawai suka had'a ido da Abba dake zaune sahun gaba kuma a kullum ya ga sheikh d'in shi dai fatanshi bai wuce "Allah ka tsayar da hankalin yarinyar nan wuri d'aya, Allah ka cire mata duk wasu tsutsotsi dake kan ta kar ta tarwatsawa bawan Allah nutsuwarshi." Ba yasa yanzu ma tar yake kallonshi, dan shi a kowane lokaci gani yake za'a ce ga abinda Mimi tayi marar kyau. *Washe gari* Ana addu'ar kaffaratul majalis aka fara mik'ewa, da sauri ita ma ta mik'e tana kallon Hafsat d'in data kasance malamarta a aji ta nufi wurin, tana zuwa sunkuyawa tayi tana d'an mamatse k'afafu tace "Aunty Hafsat ba zan jiraki mu tafi tare ba yau, da gudu zan tafi wallahi saboda..." Sai kuma tayi shiru suna kallon juna, da fara'a Hafsat tace "Saboda me?" Matse k'afafu tayi gam har tana d'ora hannunta a mararta tace "Aunty fitsari, fitsari nake ji sosai..." Da sauri ta juya ta nufi k'ofar fita inda Hafsat ta bushe da dariya tana fad'in "Kar dai ki b'ata mana aji malama." Ko juyowa ba tayi ba ta d'auki takalminta a hannu da gudu tayi b'angarensu, sauren yan ajin da suke d'aukar hadda da basu fita bane suka dinga dariyar Mimin da kuma k'iyasta yanda zamansu da Hafsat ke birgesu, kawai rayuwa ce suke irin ta yaya da k'anwarta, ko da suna kishin juna to saidai sun b'oye a zuk'atansu, amma a zahirinsu kam babu wannan alamar. Tana shiga falon da gudu d'akinta tayi hari dan tunda ta tare bata tab'a shiga ban d'akin Hafsat ba dake falon, tana cikin gudunta zata shiga d'akinta ta ji muryar Aisha tace "Aunty Mimi." Cak ta tsaya tare da juyawa ta b'angaren k'ofar d'akin Hafsat d'in da mamaki, ganin tabbas Aisha ce yasa ta sake fad'ad'a mamakinta dan tun kafin ta tare gidan nan rabon da taji ta kirata da aunty, a zahiri kuma sai ta d'an d'aure fuska dan kar ta kawo mata wargi tace "Umm." Da fara'a a fuskarta ba kamar da ba tace "Auntyna gudun me kike haka?" Ba yabo ba fallasa tace "Zan shiga ciki ne." K'arasowa Aisha tayi wacce ta d'an jima da zuwa bata samesu ba hannunta rik'e da plate da biscuits a ciki tana ci, gaban Mimi ta tsaya tace "Auntyna kuma shi ne sai ki dinga gudu cikin gida, idan fa kika wahalar mana da k'ane." Bud'e baki Mimi tayi ta zaro ido bata san sanda tace "Ke kuma wa ya fad'a miki?" Murmushi Aisha tayi tana sunkuyar da kai tace "Ai kwanan baya da mukayi waya da Hajia ta fad'a min baki ji dad'i ba, sai kuma akayi sa'a ciwo iri d'aya mukayi da ke, shiyasa na gane." Sunkuyar da kai Mimi tayi ta bushe da dariya haka ita ma Aisha, suna cikin k'yalk'yala dariyarsu Aisha tace "Aunty Mimi wajenki na zo dama." Da kulawa ta kalleta tace "To, ina jinki, lafiya dai ko?" Jinjina kai tayi tana wasa da biscuit d'in cikin plate d'in tana fad'in "Lafiya lau Aunty, dama hak'uri na zo baki akan abubuwan da suka faru a baya, dan Allah ki yafe min insha'Allahu ba zan k'ara ba." Da murmushi a fuskarta tace "Aisha na yafe miki da jimawa, taya kike tunanin na rik'e a zuciyata har haka, wallahi ba komai na yafe miki, nima ki yafe min kinji?" Da sauri Aisha ta fad'a jikinta ta rumgumeta tana fad'in "Nagode auntyna, Allah ya saka da alkairi." D'an shafa bayanta tayi tace "Ba komai Aisha, ya wuce har abada." Da wata fara'ar tace "Nagode." D'an sake shafa bayanta tayi tace "Aisha." A sanyaye ta amsa da "Na'am." A hankali ita ma tace "Fitsari nake ji, kar ya fara b'ata min jikina." Da sauri ta janye daga jikinta tana dariya tace "Haba Aunty, ashe shiyasa kika shigo a guje." Ai bata tsaya cewa komai ba ta kwasa da gudu tayi falonta, a ban d'akin nan ta shiga tayi fitsari har wani rufe ido take saboda yanda yake fita tana jin mararta na yin wani sakai, tana fitowa Aisha ta samu ta zauna kan kujerar dake kusa da fridge ta bud'a alamar zata d'auki wani abu, cire k'aton hijabinta tayi ta aje tana fad'in "Wai kin jima a nan ne?" Kallonta tayi tace "E aunty ba sosai ba, dama nasan kuna aji shiyasa na zauna jiranku." Ita ma fridge d'inta nufa ta d'auki ruwa ta bud'e zata sha ta zauna kan kujera, ganin Aisha ta d'auko bud'on had'in dabinonta da madara mao had'e da kankana yasa ta saurin fad'in "Karki sha wannan, magani ne." Kallonta Aisha tayi ta kuma kalli bidon, ita dai tana ganin alamun madara a ciki, cikin yatsina fuska tace "Aunty maganin me?" Ita ma yatsina fuskar tayi tace "Mama ta aiko min da shi jiya, na kasa sha ne ma da naji babu dad'i." Da sauri Aisha tace "Halan na ciki ne? Haka ni ma Hajia ta ce zata kai min magani na dinga sha wai yana wanke dattin yaro, amma ba yanzu ba sai cikin ya girma." Cike da dagiya da son b'atar da ita Mimi tace "E su ne, amma wannan d'in Mama ta ce na sha ne." Mayarwa Aisha tayi ta d'auki maltina ta bud'e tana sha tana korawa da biscuit d'inta, Mimi ma tana shan ruwan ta cire safar k'afarta ta mik'e da kayan da jakarta mai d'auke da kayan makaranta ta nufi ciki, tana shiga siket d'in yadin na uniforme ta cire ta cire riga ta d'aura towel ta shiga wanka. Sanda Hafsat ta dawo gidan ta samesu ta ji dad'in ganinsu a tare, ko ba komai alamu ya nuna sun manta da komai kenan zasu rumgumi junansu, hakan yasa ita kan ta a nan falon Mimin suka dinga hirarsu ta rayuwa tunda akwai 'yarsu ba zasu yarda su saki layi ba, sai sallah azahar ce ta tashesu Mimi tayi a nan d'akinta Hafsat da Aisha suka fita, a can ne kad'ai suka samu damar tattaunawa na 'ya da uwa tare da k'ara mata da shawarwari na zaman aure. Mimi na idar da sallah Aisha ta shigo tace "Aunty Mimi inji Amie ki zo mu ci abinci." Mik'ewa tayi akan sallayar tace "To." Cire hijab tayi ta nad'e sallayar ta wuce tana fad'in "Muje." Da kallo Aisha ta bi bayanta, a gaskiya ita ma dake mace kuma tsararta wannan sura da halitta ta Mimi abar kallo ce, musamman yanzu ma da kwanciyar hankali da jin dad'i suka tilasta mata k'ara zama rusheshiya tubarkallah, tayi k'iba ta cika mulmul ko ina mazaunanta sun sake fitowa, kuma sa'ar ta d'aya tana da tsayi amma fa a haka ma ta fara gajarcewa, saidai duk k'ibarta bata da wawan tumbin nan, gashi dai tana da ciki amma kuma dake k'arami zaka rantse bata da shi har yanzu mararta ce kawai ta taso. *Zaune* suke yana tsakiyarsu yana kallon kowace duk sun zubawa takardun gabansu ido suna kallo, Mimi a ranta addu'a take "Allah kasa Hafsat ce zata ci zab'en nan, ba zan iya tafiya na bar k'asata a wannan halin ba." Inda ita ma Hafsat addu'arta ita ce "Allah kasa Mimi ce zata d'auka, ni na tafi so ba adadi ya kamata ita ma na bata 'yar damarta, Allah ka sani nayi iya k'ok'arina wajen ganin ba sai ya bi ta hanyar nan ba, amma ya nuna min hakan ne adalcin da zai iya yi." Sheikh dake ta kallonsu ganin kowace sai mi-mi take da bakinta yasa shi fad'in "Ku fa nake jira, kowace ta d'auki d'aya." Kallonshi Hafsat tayi ta marairaice tace "Sheikh na fad'..." Bai bari ta fad'a ba ya d'aga mata hannu alamar tayi shiru, shiru tayi cikin sand'a ta kai hannunta ta d'auki d'aya a cikin takardun, Mimi ma a hankali ta kai hannu ta d'auka, jikinsu duk a mace suka shiga warwarewa, Hafsat na ganin babu komai a ta ta takardar ta daka tsalle kamar yarinya tana fashewa da dariya da fad'in "Woooo! Mimi tafiyarki ce, dan haka a tashi a shirye, ni dai a taho min da tsaraba." Juyawa tayi ta nufi d'akinta tana fad'in "Allah ya kiyaye hanya oga, a dawo lafiya." Da kallo suka bita saida suka ga shigewarta Mimi ta kalleshi tana matsar k'walla tace "Sheikh bana son tafiyar nan, a tsorace nake sosai wallahi, ji nake kamar ajalina ne ke kirana." D'ora yatsarshi yayi a labb'anta yace "Shiiiii! Babu abinda zai faru dake Mimi, ki had'a kayanki kinji, muna tare insha'Allah." Marairaicewa tayi tace "Amma kuma fa ciki ne da ni." Jinjina mata kai yayi yace "Ba wani abu bane wannan, na gama da matsalar nan tun tuni." Shiru tayi tana kallonshi sai kuma ta saki murmushi tace "Wow! Yau ni ce burina zai cika ta hanyar keta hazo." Rik'o hannunshi tayi tace "Kuma ka ga fa zan samu damar rainon cikina ba tare da kowa ya ganni ba, dan ni dama kunya nake ji wallahi." Dungure mata kai yayi yace "Kina jin kunyar a kalleki a ce cikin tsoho ne jikinki ko?" Dariya tayi ta kwanta a k'irjinshi tana fad'in "Tsoho, humm! Ni kad'ai nasan waye wannan tsohon, tsohona jarumi ne, ingarman doki ne ko kuma na ce matashin doki ne." K'amk'ameta yayi yana dariya yace "Ki ce dai na ciri tuta?" Ita ma cikin dariya tace "Tun a waccen ranar." D'ago hab'arta yayi yace "Wace rana?" Kallon idonshi tayi tace "Waccen ranar mana, ranar daka kusa sumar dani." Tintserewa sukayi da dariya ya mik'e da ita a jikinshi yana fad'in "Mu shiga daga ciki sai ki rama to." D'an shak'o wuyan rigarshi tayi tace "Da gaske? Zaka bani dama na rama?" "Um." Ya fad'a yana d'aga mata kai, jinjina kai tayi tace "Kuma karka rama, ka barni ni kad'ai nayi komai na." Cak ya d'auketa suka nufi d'akin yana fad'in "Na yarda yan matana, zan baki dama ki more ke ma." Cike da kunya ta rufe idonta har suka shiga ciki ya direta, cike da farin ciki da k'aunar juna suka shiga farantawa junansu rai musamman Mimi ma data zage damtse ta nemi susuta shi da yammacin da har saida jam'in sallah la'asar ya sub'uce musu dukansu. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:59 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *57* Sun jima wajen Hajia suna ta hira tunda suka zo mata ban kwana, Mimi na gefensu tana saurarensu tana sinne kai tana ta b'oye cikinta a cikin hijabi duk da ba fitowa yayi ba sosai, saida suka tashi zasu tafi duk suka mik'e tare Hajia na sake jaddada "Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare, ku kula dan Allah." Da fara'a suka amsa da "Ameen." Dafa kafaf'ar Mimi tayi tace "Ki kula da kanki kinji ko, duk abinda kika ji a jikinki kar kiyi k'auron baki ki fad'a masa." Sunkuyar da kai ta sake yi tana jinjina kai alamar to, takawa sukayi zata rakasu saidai daf da fita k'ofar Asas ya turo k'ofar da dama a bud'e take yana fad'in "Assalama alaikum." A tare suka amsa da "Wa'alaika salam." Ban da Mimi da ta amsa k'asa k'asa tana kakkawar da kan ta, dan ita fa yanzu kunyar Asas take ji, shiyasa duk lokacin nan da aka d'auka sau biyu kawai taje gidan Asma'u. Da fara'a kamar yanda suka saba sukayi musabaha Asas na fad'in "Hajia bak'i kikayi ashe?" Dak'uwa ta masa tace "Su waye bak'in a gidan nan?" Sheikh ne ya tab'e baki yace "Watak'ila shi Hajiarmu, ya manta mu 'yan gidan nan ne." Dariya Hajjia tayi tace "Da alama kam." Kallon sheikh yayi yana turo baki gaba yace "Ni fa ba bak'o bane, ni da gidan Hajiata d'in." Harara sheikh ya dalla masa yace "Kai bana da lokacinka, tafiya zanyi sai na dawo." Murmushi yayi ya d'an saci kallon Mimi dake bayan Hajia kad'an yace "Matar yaya ina wuni?" Rintse ido tayi tana d'an yatsina fuska ta amsa k'asan mak'oshi da "Barka." Da murmushin shi a fuska ya d'ora da "Ya su Hafsy? Kwana biyu baki lek'a k'awarki ba?" Bud'e ido tayi a hankali ba tare data kalleshi ba tace "Lafiya lau." Mayar da kallonshi yayi kan sheikh dan ya fahimci bata cika son kulashi ba yace "Sheikh sai ina? Ko shak'atawa aka fito?" "Um." Ya fad'a yana wucewa inda Mimi ta bi bayanshi yana fad'in "Zan sameka gida ne?" Juyawa Asas yayi ya kalleshi yace "Yaushe?" "Yanzu." Ya fad'a kai tsaye, da mamaki yace "Da gaske wai? To indai hakane saidai na tafi yanzu dan ku sameni." Juyowa yayi ya kalleshi yace "Ba abun ujila bane, daga nan gidansu zan kaita, daga nan ne zan wuce da ita can." Da kallo ya bisu suka k'arasa fita kafin ya maayar da hankalinshi kan Hajia. *Tsaye* suke k'ofar gidan cirko cirko kamar masu jiran fitowar wani, a karo na ba adadi kenan da sheikh ya kalleta yace "Ryam, yanzu a nan zamu tabbata a tsaye kamar wasu masu zance?" Sake marairaicewa tayi tana d'an kukan shagwab'a tace "Ustaz ba haka bane, ni wallahi kunyar Mama nake ji, data ganni fa zata shiga k'are min kallo har sai ta gane ina da wannan." Ta fad'a tana dafa cikinta, girgiza kai yayi yace "Ryam abun farin ciki ne fa, Mama zatayi murna da haka fiye da tunaninki, ita a wajenta hakan ya tabbatar mata lallai 'yarta ta girma, hakan yana mata nuni da cewa 'yarta ta zama babba, hakan na alamta mata ashe 'yarta tauraruwa ce ita ma a gidanta, hakan na nuna mata ke ma mijinki na kulaki, ba wai kara zube kike a gidan shi ba, Ryam Mama zatayi farin ciki zata samu jika daga gareki, ke 'yarta ta farko, duk soyayyar da take miki da wannan alkunyar kasancewarki 'yar data fara haifa, yanzu zata koma kan d'an dake cikinki ne, a da idan Mama bata kulawa da ke, a yanzu sanadin cikin nan zata zamo tana kulawa da ke fiye da yanda kike jaririya, dan Allah Ryam ki shiga mu gaishesu sannan ki nemi afuwarsu abisa komai kafin mu bar k'asar nan." Jikinta a mace ta jinjina kai tana kallonshi tace "To muje." Gaba tayi yana d'an binta a baya yana fad'in "Ki fara shiga sai ki fad'a musu tare muke." "To." Ta fad'a tana saka k'afarta d'aya a cikin gidan, kamar an tsayar da ita kuma sai ta tsaya ta juyo tasa yatsarta babba a baki tana d'an cizawa tana kallonshi tace "Sheikh kasan wani abu? Kuma fa Mama ma..." Sai ta nuna mishi ciki ta nuna cikin gidan alamar Mama ma ciki ne da ita, sai kuma tayi kamar zata fashe da kuka tace "Ni wallahi kunya nake ji." Da k'arfi sheikh ya rik'e dariyarshi a zuciyarshi yana fad'in "Oh Allah." A zahiri kuma saiya gimtse ya kalleta yace "Ryam zan shiga masallacin nan na shelantawa mutane kina d'auke da ciki, kinsan dai zan iya ko?" Zaro ido tayi da sauri ta shige cikin gidan tana fad'in "Sheikh." Da sallama ta shiga Abba dake wanke hannaye ya gama cin tuwo ya amsa yana zuba mata ido, bai bari ta k'araso ba yace "To uwata shirmatu, yau kuma da wace aka zo mana?" Murmushi tayi ta k'arasa kusa da shi ta durk'usa da ladabi tace "Abba na daina komai fa, ina wuni?" Girgiza kai yayi yace "Za dai ki daina uwata, ni tunda na ga ruwan lalle basu sa kinyi hankali ba ai na sare da lamarinki." Mama data fito daga d'aki ne ta kalleta tace "Ke kuma fa daga ina warhaka?" Da girmamawa tace "Ina wuni Mama?" Zaune mama tayi tana d'an shanye cikinta daya fito sosai a k'alla wata shida tace "Lafiya lau." Mik'ewa Mimi tayi ta k'arasa kan tabarmar kusa da Mama ta zauna tana satar kallonta, kunya take ji sosai tana rufeta ita da ciki mamanta ma haka, sai kawai ta sunkuyar da kan ta tana d'an cije leb'e, Abba ne yace "Wai ke da wa kika zo a daren nan?" Turo baki tayi ta kalleshi tace "Abba tare da shi ne fa." Kallon Mama tayi tace "Mama wai ina su Yaseen?" A dak'ile Mama tace "Sun tafi gidan Iya na aikesu." Mik'ewa Abba yayi yace "Kinga irinta ko? Kin gani, yanzu shigowa tayi ta baro waje ko a jikinta." Ficewa yayi yana gyara zaman hularsa, jim kad'an ya dawo da sauri yana d'auko kujerar roba ya aje ya cewa Mama "Shigowa zaiyi ya gaisheki, kinji wai yana mahaukaciyar zai d'auka su tafi k'asar waje." Kyab'e fuska Mimi tayi ta kalli Mama da ita ma ta kalleta, mik'ewa mama tayi ta d'auko d'an k'aramin hijabinta ta saka ta zauna tana takura kanta yanda ba za'a gane cikin jikinta ba, cikin nutsuwa da dattako ya shigo d'ai bayan d'ai cikin shigarshi ta kamala, a nutse ya zauna kan kujerar bayan yayi sallama Mama ta amsa, kanshi sadde k'asa yana kallon hannayenshi suka shiga gaisawa da Mama sosai, kafin daga bisani ita ma ya fad'a mata zasuyi tafiya ne su ka zo yi musu ban kwana. Cike da dattijantaka Mama tace "Allah ya kiyaye hanya, a je lafiya a dawo lafiya." Kallon Mimi tayi tace "Sai a kula kuma, ban da shiririta dan Allah." Murmushi yayi a ranshi a furta "Akwai ta kam." Mimi kuma turo baki tayi tana mamakin yanda duka iyayen na ta har yanzu suke ganinta da shirme bayan ita tasan ta daina yanzu. Sun jima zaune kafin ya mik'e yace "Zamu wuce, sai anjimanku." Mik'ewa Abba ma yayi yana fad'in "To shikenan, sai anjima, Allah kiyaye hanya Allah tsare." "Ameen Ameen." Ya fad'a yana d'an satar kallon Mimi duk da ba hasken wuta ke akwai ba, Mama ce ta d'an zunguri Mimi hakan yasa ta mik'ewa a kasalance ta saka takalminta cikin shagwab'a tana fad'in "Abba, Mama ni dai ku yafe min duk abinda na muku, kunga dai jirgi zan hau ko? Ban son ko na sauko a raye ba." Bata jiran amsarsu ba ta yi gaba sai sheikh ne ma ya bita a baya,a k'ofar gidan suka ci karo da su Yaseen sun dawo, tsayawa tayi da k'annanta suka gaisa tana fad'a musu zasuyi tafiya, ai da sauri Amir yace "Mimi ni dai ki kawo min irin moton nan na wasa." Yaseen kam cewa yayi "Ni dai duk abinda kika kawo min ina so." Dariya tayi tace "To shikenan zan kawo muku, amma ku kawo kud'i?" Zazzaro mata ido sukayi suna kallo sai kuma suka saki murmushi Yaseen na fad'in "Idan kika siyo zamu biyaki." Sheikh dake saurarensu ne ya kamo hannun Amir yana sunkuyawa sosai yace "Rabu da ita kaji, idan ma bata siyo ba ni zan siyo." Hannunshi yasa aljihun babban rigarshi ya ciro sababbin kud'i a mik'e zar ya damk'a mishi yace "Wannan na kashewa ne idan zaka tafi makaranta." Godiya yayi cike da jin kunya yana rik'e kud'in da hannu biyu, shigewa sukayi ciki su ma suka shiga mota suka nufi gidansu Iya, nan ma sun d'auki lokaci suna ta raha da tsokanar juna malam na fad'in ya yarda ya ara mishi amaryarshi su je su dawo, hakan yasa sheikh farin ciki sosai da jin wani sabon nishad'i, nan ma d zasu tafi kud'i a aje musu suka fito zasu tafi. Iya ce ta rik'o hannunta cikin rad'a tace "Ke! Wai yanzu wata na nawa koke ciki ne? Bana son sai kinje can zaki fara awon farko." Da mamaki Mimi ta kalleta tace "Iya watan me? Wane irin awo kuma? Na masu tamowa?" Dak'uwa Iya ta mata tace "Na masu shan Inna dai, ina maganar k'warai zaki saka min shirme." Turo baki tayi tace "To Iya ban gane me kike nufi ba ko?" D'auke kai Iya tayi daga gareta tace "To na ji, cikinki na ce watanshi na nawa ne yanzu?" Bud'e baki tayi tace "Lahhh! Iya kuma haka kika koma? To ni gaskiya ban sani ba." Dungure mata kai tayi tace "Ke wai ba zaki cire shirme a rayuwarki ba, to karki sani bari na tambayi wanda ya sani." Zaro ido tayi tace "Wa wai?" Nuna mata sheikh tayi dake tsaye bakin mota shi da malam suna d'an hira, ganin ta nufesu yasa ta rik'o hannun Iya tana fad'in "Kinga Iya ki daina bana so, a kan me zaki tambayeshi wai cikina, na fad'a miki ina da shi ne to?" D'an gajeran hannunta ta kwad'a mata a kan ta tana fad'in "Sakeni ja'ira kawai, kin rainani dan kinga tsawona bai wuce k'ugunki ba ko?" Ai kuwa fitowa Iya tayi ta tsaya daga bakin soron tana kallonsu da kunya tace "Yarinyar can wai nake tambaya watanta nawa ne yanzu? Ina so ta fara awo a nan gaskiya ba k'asar masu jajayen kunnuwan nan ba." Kallonta sheikh yayi sai kuma ya kalli makullayen hannayenshi yana fad'in "E to, ina jin dai watanta na hud'u ne wannan." Murmushi Iya tayi tace "Yawwa to ina ga tunda tafiyar ta ku jibi ne me zai hana gobe na rakata ta je awon fari, kenan idan kun dawo ta ci gaba da zuwa." Da fara'a sheikh yace "Hakan ma yayi Iya, Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya." "Ameen." Ta fad'a ta juya zata koma ciki Mimi kuma ta k'arasa fitowa, hararan juna sukayi ita da Iya tana murgud'a baki tace "Gaskiya ni a daina min haka, ina ce dai yanzu na bar miki tsohon mijinki tunda ni ma na samu nawa, to me ye na son cizgani a cikin mutane kuma?" Kallon malam tayi dake ta k'yalk'yala dariya yace "Malam na tab'a fad'a maka wani abu ne tunda muke?" Girgiza kai yayi yana ci gaba da dariyarshi, Iya kuma shigewa tayi tana fad'in "Idan jin ta kike dani ki bari gobe da safe na sameki gidan naki sai muyi." Juyowa tayi tana kallonta tace "Iya kika je gidana da sassafe da angulu zan had'aki." Dak'uwa ta mata tana dariya tace "Ta jima bata kasheni ba angulun, yar banza b'ulelliyar wofi." Gwalo ta mata tace "Yo Iya kuma yaushe aka fara hassada da k'ibata? Yar mulmujewar dana fara yi har an fara saka mata ido." Zagayawa tayi ta mota zata shiga ganin yanda malam da sheikh kamar zararri suke ta k'yak'yata dariya, Iya ma dariyar tayi a yanzu tace "Wannan k'ibar ce 'yar mulmujewa? Ai ina ga da kin haihu sai an ganki a d'auka ma ke ce uwar gida, dan jikinki bud'ewa kawai yake." Saida ta bud'e murfin motar zata shiga tace "Na ji dai, ki ci kanki Iya." Shiga tayi ta zauna tana ci gaba da kallonshi yana ta dariya, haka ya tayar da motar suka d'auki hanyar komawa, ba tare daya tsagaita da dariyar ba yace "Wasar Kaka da jika akwai dad'i, ina ma na wa kakan ko kakata suna raye, dana kwatanta irin haka da su nima." Murmushi tayi tace "Hakan ya birgeka ne?" Jinjina kai yayi yace "Sosai, kun birgeni matuk'a, kamar na zauna nayi ta kallonku." Cikin zuba mishi ido tace "Idan zaka dinga biyanmu ai sai ka dinga kawoni kullum muna dramar a gabanka kana dariya." Wata dariyar ya sake bushewa da ita yace "Ke mai wayo ko?" Turo baki tayi tace "To miye a ciki, ai kowa yan...tsaya tsaya tsaya sheikh, dan Allah." Ta k'arashe tana kallonshi, da sauri ya taka birki bai shirya ba dan yanda tana tsaka da magana ta shiga fad'in ya tsaya ta sa gabanshi fad'uwa, kallonta yayi yana sake dudduba jikinta yace "Lafiya? Me ya faru Ryam?" Nuna mishi mai baron da suka baro baya kad'an tayi tace "Bredi nake so, gashi nan baya." Wata k'akk'arfar ajiyar zuciya ya sauke ya had'a kanshi da sitiyari yace "Hasbunallahu wani'imal wakil." D'an dafa kafad'arshi tayi a sanyaye tace "Akaramako, kan ka ne ke maka ciwo?" D'agowa yayi ya zuba idonshi cikin na ta da mamakin jin wai akaramako, girgizz kai kawai yayi ya juya ya kalli mai bredin dake tafiyarshi ya soma musu nisa, bud'e murfin motar yayi ya fita zai rufo sai kuma ya kalleta ya nunota da yatsa cikin muryar gargad'i yace "Ki jirani na dawo, idan kika fito a motar nan ranki zai b'ace." Jinjina kai tayi alamar to, da kallo ta bi shi har ya siyo bredin aka saka mishi a leda ya dawo motar, mik'a mata yayi tana karb'a ta fara sincewa, tayar da motar yayi yace "Da fatan dai ba ciye-ciye zaki min a mota ba?" Kallonshi tayi tana kwance ledar tace "Yawuna har tsinkewa suke, idan ka hanani wallahi hukumar kula da hakk'in yara zan kai k'ararka." Murmusawa yayi yace "Ki ce na tauye hakk'in abinda yake cikinki?" Nuna kanta tayi tana fizgar bredin mai laushin gaske ta kai bakinta tana taunawa tace "Ni dai, ni nake nufi." Zaro ido yayi yace "Oh! Wai ke ce yarinyar dama?" D'aga kai tayi alamar e, shi ma jinjina kai yayi yace "Lallai, Ryam zanyi addu'ar Allah yasa mace zaki haifa." Da sauri ta kalleshi tace "Me yasa? Ni ma ai ita nake so na haifa." Kallonta yayi yace "Me yasa kike son haifar mace?" Cike da rashin damuwa tace "Na dinga mata kitso na saka mata ribom na mata kwalliya na saka mata riga da siket na kanti ko kula riga da wando sannan na tafi biki da ita." Galala kawai yayi yana kallonta yana jin ba dan tuk'i yake ba da sai yayi tagumi ya k'are mata kallo, sai kawai ya girgizz kai a zuciyarshi yace "Allah ya miki albarka Sawwama, duk da shekarun k'uruciya aka had'amu, amma ban ga irin haka daga gareki ba." Sake kallon Mimi yayi yace "Ni kuma saboda ta zama silar zamarki uwa ta gari nake son ki fara da mace." Kallonshi tayi irin kallon na na fahimta na basira, sai ta d'auke kan ta a hankali tace "Zan zama, zan zama insha'Allah, da kuma taimakonka." Murmushi yayi yace "Da taimako na, amma kuma da taimakon Qawwama, dan ta fini kula da yara yanda Allah da manzon sa suka fad'a." Da fara'a ta kalleshi ita ma tace "Na ji dad'in kasancewata a cikinku." Murmushi kawai ya sake mata da haka har suka isa gidansu Asas kamar yanda dama suka shirya zasu je suyi ban kwana da su, Asma'u ta ji dad'in ganin Mimi haka ta sako hijab bayan Asas ya shigo da sheikh ta cika gabansu da kayan ci, saidai babu abinda suka tab'a sai ruwa musamman ma Mimi data ci bredi ta k'oshi a mota, basu jima ba suka mik'e dan 10:00 na dare har ta wuce sosai, sallama suka musu tare da addu'ar Allah ya kiyaye hanya. Daga nan kuma gida suka wuce, dake dama kwana Hafsat ne kai tsaye d'akinta ya wuce yayi shirin bacci. Tana kwance kan k'irjinshi hannayensu a had'e suna wasa da su, d'aya hannunta kuma k'irjinshi take shafawa tana fad'in "Sheikh nawa, ka ga dai zanyi kewarka na wata d'aya ko? Dan Allah kamar yanda ka min alk'awari ka dawo nan da wata d'aya, ina buk'atarka a kusa dani." Sumbatar yalwataccen gashinta yayi dake ta tashin k'amshi yace "Na miki alk'awarin nan Mangata, insha'Allah zan dawo a kan lokaci." Hannunshi dake sakale cikin na ta ta sumbata tace "Nagode mijina, duniyata, aljannata." Da fara'a yana d'an lumshe ido yace "Madalla da mata ta gari." Ita ma a sanyaye tace "Madalla da miji na gari." A tare suka fad'i "A bisa koyarwar addinin islama." Tallabo hab'arta yayi suka kalli juna yace "Ina sonki sosai Hafsat, ina sonki uwar ya'yana, Allah ya sani ke ce ni kamar yanda ni ma ni ne ke, ke ce farin cikin gidana kuma salama a cikin rayuwata, wani lokacin har tuna irin gararin da zan shiga nake yi idan aka ce yau babu ke a tare da ni, sai na tambayi kai na an ya kuwa zan iya ci gaba da rayuwa? Sai na tambayi kai na anya zan sake murmushi a fuskarta? Anya kuwa idan na rasaki daga ni har 'ya'yana ba zamu tagayyara ba?" Da sauri ta d'ora yatsanta a labb'anshi tace "Shiiiii! Haka ba zata faru ba mijina, Allah yana tare da ku, insha'Allah muna tare ka ji." Ta fad'a tana k'amk'ameshi k'am a jikinta, numfashi a dinga saukewa a kan ta mai fito da zafi ya sake fad'in "Ina k'aunarki sosai." A sanyaye ta furta "Ni ma haka." A hankali ya rad'a lata a kunne "Muje na miki wanka, kar ki yi bacci da najasa a jikinki." Dariya tayi tace "To a d'aukeni mana." Yunk'urawa yayi ya sauka a gadon ya d'auki towel ya d'aura ya kimkimeta tsaf suka nufi ban d'akin. *Washe gari* Sosai Iya ta ji dad'in yanda tunda safe ya tura mota sukutum aka je d'aukarta, saidai ga ta zaune falo tana jiran ja'irar ta bakinta ta fito bata gama shiryawa ba. Sheikh ma dake kwance kan gadon tun shigowar Iya ya shigo tashinta, kallonta yake tana shiryawa a tsanake, da yaga dai shirin ba mai k'arewa bane yasa shi fad'in "Ryam Iya fa jiranki take, a k'alla ta d'auki minti ashirin zaune a falon nan ita kad'ai." Yatsina baki tayi tace "Ai na fad'a mata tun jiya kar ta min sammako a gida, kuma ma awon sai ta wani rakani, salon muje tayi ta tona min asiri." Dariya yayi yace "Ke da zaki jira layi a b'angaren masu ciki, ai kallon kallo zaku yi wa juna ke da su, da dukanku abu d'aya ya takaru, ta inda kika bi kika sameshi haka suma." Juyowa tayi ta dakata daga shirin shafa jan bakin da take tace "Da gaske? Tabb'! Lallai zan sha kallo, wallahi sai na k'arewa kowace kallo, kuma idan kika min kallon da ban so b芒 na ce ni da ke duk kanwar ja ce." Ban da k'yalknyala dariya babu abinda yake kafin yace "Amma dai kiyi a hankali kar ki ja fad'an da zaki daku fa a asibitin nan." Murmushi ta masa tace "Karka damu ba zan yi ba." Da son gasgatawa yace "Kin tabbata?" "Na tabbata." Ta fad'a tana juyawa zata shafa jan bakin, mik'ewa yayi da sauri ya rik'e hannunta ya karb'e jan bakin yan fad'in "Kina da sani akan mutanen da Allah ya yarje ma ganin kwalliyarki kawai, amma me yasa kike son take saninki ne Innar Issa?" Shagwab'e fuska tayi tace "Kayi hak'uri to, ka yafe min?" D'aga kai yayi alamar ya yafe, mak'ale mishi tayi a wuya tana sumbatarshi, warware hannayenta yayi yana fad'in "Maza dan Allah, hanzarta Iya na jiranki." Turo baki tayi tace "Ni fa na ga Iyar nan sai wani ji da ita kake, zan fara zargin ko son ta kake fa?" Da mamaki ya kalleta yace "Yanzu ne ma zaki fara zargin? Ke a ganinki dan bana son ta ne na auroku? Ai da tsohuwar zuma ake magani." Da sauri ta kalleshi tace "Lahhh! To sabuwar fa?" Kyab'e fuska yayi yace "Tafi haukatamutum." Tintserewa tayi da dariya ta d'auki jakarta ta rataya kafin suka fito a tare, Iya na had'a ido da ita ta wurga mata harara tana d'auke kai, Mimi ma d'auke kai tayi tace "A zo gidana kuma a harareni." Kallon sheikh tayi tace "Yallab'ai ina angulayen nan suke wai?" B'oye dariyarshi yayi yana kallon Iya yace "Iya kiyi hak'uri ta tsaidake." Kallon Mimi yayi yace "Ku je dreba na jiranku." Mik'ewa Iya tayi tana fad'in "Nagode Allah daya zamana ana allura a awon fari." Zaro ido Mimi tayi tana kallonta sai kuma ta kalli sheikh, girgiza masa kai tayi tace "Um um! Wai da gaske ana allura?" Lura da Iya zata b'allo musu aiki yasa d'an saisaita murya yace "Ina jin fa wasa take miki." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Haba, tunda ai ka ga bana jin ciwon komai ko?" D'aga kai yayi alamar e, juyowa Iya tayi ta kalleta da kyau sai kuma ta gyara tsayuwa tace "Ke! Doguwar riga ce kika saka?" "E." Ta fad'a tana kallon kan ta, cikin fad'a Iya tace "Ke bana son k'ananan iskanci, awon cikin ne zakiyi mje da doguwar riga, to ya zakiyi idan za'a miki awon kwance? So kike ni ma d'in a ce mahaukaciya ce kamar ke?" Cikin jin haushi Mimi tace "Kamar 'ya? To me rigata tayi kuma? Haihuwar ce zan je yi?" Matsowa tayi irin a zafaffen nan tayo kanta tana fad'in "Ke ki kiyayeni wallahi." Baya ta ja sai sheikh daya kalleta da alamar gargad'i yace "Je canza kayan ki fito." Juyawa tayi ta shige d'aki inda suka bita da kallo, a sanyaye Iya ta kalli sheikh dan sai taji ma ya fara bata tausayi, a ladabce tace "A yi ta hak'uri dan Allah, yarinyar ce kamar mai shafar aljanu wani zubin, ka d'an dinga tofa mata ayatul kursiy wasu lokuta." Murmushi sheikh yayi yace "Insha'Allah." Suna nan tsaye ta fito sanye da riga da zane mai kamar siket ya fito mata da tsarin zubin k'ugunta sosai, tuni sheikh ya bita da kallo "Lahaula walaquwatta illa billahil-aliyul azim!" Sai kuma ya had'e yawu ya ci gaba da kallonta tana saka hijabinta da d'aura nik'ab, kallon Iya tayi tace "Sai mu tafi ko?" Harara Iya ta banka mata tayi k'wafa, ita ma hararen gefenta tayi tace "Wannan awon ni sai na ce ma na fasa." Cikin sub'atar baki Iya dake daf da fita tace "Yo fasa mana, ni na ce kiyi cikin ko a jikina yake?" Da sauri Mimi ta juya ta kalli sheikh daya d'an zaro ido sai kuma ya kalleta ya saki murmushi, cikin fashewa da kukan sangarta ta nuna Iya data fita tace masa "Ka ji ko? Wai ita ce tace nayi cikin?" Matsawa yayi kusanta yana share mata hawayen da ko alamarsu babu yana fad'in "Yi shiru haba rabu da Iya, kinga fa so take ta tsufar min dake, shiyasa take yawan sakaki jin haushi da surutu, daina kukan kinji ko tawajena." Turo baki tayi tace "To na yi, amma ka min alk'awarin kafin na dawo zaka siya min tsire.?" Jinjina kai yayi yace "Zan siya, kuje Allah ya tsare." Juyawa tayi ta nufi hanyar fita tana fad'in "Kuma ka kira Rakiya ka fad'a mata wallahi ban da allura." "To." Ya fad'a yana kallonta har ta fita, yana hangensu daga nan ma yana kallon bakunansu na ta motsawa alamar dai sun d'ora a inda suka tsaya, girgiza kai yayi ya k'arasa ya rufe mata d'akin ya kulle kafin ya nufi d'akin Hafsat, dan nutsuwa yake son samu yayi bacci cikin sallama tunda an bashi hutu a wurin aikin. A gidan nan kuma indai nutsuwa mai sunan nutsuwa yake so da hutu to fa dole sai wajen uwar 'ya'yansa, mahutarsa kuma annashuwar gidansa wato Hafsat. Amma Ryam! Ryam! Ryam! Zuciya ce kawai da abunda take so, b芒 dan haka ba irin gwaramar da yarinyar ke had'a masa da babu soyayya to tabbas tuni ya yanka mata ticket, idan ba zuwan Ryam ba wa ya tab'a gigin taka rawa a gidanshi, sai gashi a gaban idonsa ake yi tun yana kakkawar da kai har ya fara kallo wani lokacin ma yaji ta birgesa har ya juye da ita a cikin kogi su shiga iyo. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:59 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *58* *A gurguje* Yau Mimi ce ta bud'e idonta k'afarta akan babbar birnin k'asar Duba茂 wato Abu Dhabi, lokaci lokaci sa茂 mta kalli sheikh ta tintsire da dariya, shi kuma sai dai ya girgiza kai yana kallonta kawai, da haka suka isa babban masaukinsu suka shiga wanka kafin su zauna cin abinci, buga kai tayi a k'asa wallahi ba zata ci wannan kalan abinci ba, da k'yar ya lallab'ata ta ci gasassar kazar da ita ma tace babu d'and'ano ba yaji ita kawai ba dad'i. Da fari dukansu sun d'auka ko rashin sabo ne da tafiya ya jawo mata zazzab'i da kuma ciwon k'afafun, amma data kwana uku babu sauki sai ya nemi su tafi asibiti, data nuna a'a k'yaleta kawai yayi dan ba zai manta da suka tafi awo da Iya ba, iya d'ibar jinin da ake na kan yatsa ma bata yarda an mata ba, haka aka zo allura bata tsaya ba kafatanin asibitin saida aka san Mimi ta halarta, mutane dayawa sun sa baki kan ta tsaya a mata dan lafiyarta da ta abonda ke cikinta, amma bata saurari kowa ba ta ce gida zata koma, haka wasu suka dinga fad'in ai tayi raguwar dubara tunda ta yarda ta d'auki cikin, zasu su suka ga yanda zata haihu d'in. _(Ina nak'udar Khalid na ga mai cikin da bata son allura,馃ぃ haka na manta da nak'uda nake na shiga kallonta ana neman tausheta a mata allura, wallahi a k'arshe sai likitocin ransu ya b'ace suka ce mijinta ya d'auki tsiyarshi馃ぃ su basu wuri)_ Haka sheikh ma sukayi saida rana da suka dawo gida aka kira Hajia tare da Rakiya ta mata abinda ya dace shi ma saida sheikh ya had'e fuska ya nuna sam bai san ta zai ma kikkifa mata mari kad'ai ta tsaya. Magani dai yake mata dubara a sauk'ak'e tana sha, saida ta d'auki sati a haka kafin jikinta ya warware da kyau, daga ranar fa ta ce k'afa mai na ci ban baki ba? Sa茂 ta bud'e shafin yawo ita da sheikh, soyayya suke bugawa mai rai da lafiya mai cike da yarinta da wauta a ciki, tunda suka zo sheikh zanzarewa yake da k'ananan kaya irin wanda suka dace da shi dattijon arzik'i. Yanzu kam ya fara zarmewa shi ma, dan ranar farko da suka fara fita Mimi b'oye fuskarta take wai kar a ganta a d'auka ko kakanta ne? Da fari maganar cakarsa tayi sosai a zuciya, amma daya d'auki hak'uri ya d'ora bai san sanda ya sureta ba ya labta a bayanshi, wutsil wutsil ta fara yi sai ya sauketa shi kuma ya k'i saida suka yi nisa, har saida ta kai ta gyara kwanciyarta a bayanshi tayi shiru dan ta fahimci babu ma wanda ya kula da su, tun daga ranar ne ya zama ko fita sukayi bata shakkar tab'a shi a wani sassa na jikinshi shi ma baya jin d'ar d'in tab'ata ko sumbatar goshinta ko kunci. Wasa wasa sai ga Mimi ta sake wata k'iba masha'Allah wacce ita kan ta ta fara jin ta fara mata nauyi yanda take ganin idan ta k'ara fiye da haka zata takura mata, shi kan shi sheikh da wasa wasu lokutan yake fad'a mata "Ryam ki dakata da k'ibar nan haka dan Allah, bana so ki kai matakin da ba zan iya d'aukarki ba, kinga dai tsufa nake k'arawa ke kuma kina k'ara k'iba." Marairaicewa kawai take tace "To ya zanyi? K'ibar ce lokacinta ya zo ni kuma ban tara ko sisi ba, zan zubawa sarautar Allah ido kawai." A haka suka kwashe wata d'aya cir a k'asar Abu Dhabi wanda a wannan lokacin har Paris saida suka lek'a kwanansu hud'u, zuwa lokacin kuma shirye shirye ya kam-kama sosai saboda gabatowar watan azumi, hakan yasa suka juyo zuwa dawowa k'asarsu dan duk yanda abubuwa zasu taso ma sheikh da zasu iya sa shi barin k'asa ban da wannan watan, ko ma menene ya kan hak'ura d shi dan ya samu damar azumtar watanshi a cikin iyalenshi da kuma jama'arshi. *Ramadan* Kaf ya gama da duk wata buk'ata ta gidanshi, kama daga kayan sallahnsu zuwa kayan abinci da yasan ya kan tanada na bud'a baki da suhur. Dan haka suka zauna duka a falonshi bayan ya kalli kowace yace "Muna saka ran tashi da azumi gobe, mu d'ora niyyar azumtarshi, idan Allah yasa mun riskeshi mu tsawwala aiyukanmu na alkairi, kada mu raina aikin lada komai k'ank'antarshi, mun fahimta?" Jinjina kai duka sukayi inda ya kalli Hafsat yace "Kinsan komaai Hafsat a game da watan nan, Mimi ce bak'uwata a yanzu." Ya fad'a yana kallon Mimi dake ta jijjiga k'afafunta dake mata masifar ciwo, d'orawa yayi da "Sai kinyi hak'uri Mimi da yanda zaki sameni a yanzu, duk watan azumi abubuwan sukan taru su sak茅 min yawa, hakan na jawowa iyalina rasa kaso mai yawa a cikin lokacina, amma idan kikayi hak'uri kamar yanda 'yar uwarki tayi, zaki zo ki saba ke ma har ma wata rana ki k'arfafa min gwiwata." Saida ta cije leb'enta na k'asa sosai kafin ta sauke numfashi, nauyi sosai take ji a jikinta wallahi gaba d'aya bata jin dad'in jikinta, a sanyaye tace "Ba komai Abban Humaira, Allah ya mana jagora, Allah ya taimakeka a dukan lamuranka ya bada sa'a." "Ameen." Ya fad'a da farin ciki tare da kallon Hafsat yace "Ba wani abu dana manta ban yi ba? Ko kuma kuke da buk'atarsa?" Girgiza kai tayi da fara'a tace "Ba komai yallab'ai, ban sani ba dai ko uwar yan hud'u." Tare suka kalli Mimi da ita ma ta kalli Hafsat d'in suna mata dariya, turo baki tayi cikin shagwab'a tace "Ka gani ko? Wai saita dinga kirana uwar hud'u?" Dariya ya sake fashewa da ita yace "Haka ta gani ai." Sake turo baki tayi ba tace komai ba ta kawar da kai, cikin dariya yace "To Hajia ba abinda kike buk'ata?" Girgiza kai tayi tace "Babu, idan ma akwai ba zai wuce yakuwa da nake son ci ba, kuma zan sa su Yaseen su kawo min." Murmushi yayi yana girgiza kai yace "Nagode Allah da ba'a ce na je na tsinko da kai na ba." Hafsat ce ta kalleta ta k'yabta mata ido tace "Tab'! Da ni ce kam sai ya cirota da kan shi." Wani kallo Mimi ta mata ta murmusa tace "Bar shi auntyna, akwai abinda zai min ne na musamman shi." Zaro ido yayi yace "Ba dai ni zan kwad'a miki ba ko?" Fari ta masa da ido tace "Wannan ai mai sauk'i ne." A hankali ya kanne mata ido ya d'auke kan shi tare da mik'ewa tsaye, har zai fita ta marairaice tace "Dan Allah taimaka min na koma d'aki na kwanta yallab'ai." Cike da kulawa da tausayi Hafsat tace "Har yanzu k'afafun basu daina ba?" Cike d jimami tace "Aunty idan na sha maganin ma kamar k'arawa yake." Mik'ewa tayi ita ma tsaye tace "Allah ya sauk'ak'a miki, ya baki ladar." "Ameen." Suka fad'a tare da sheikh daya kama hannayenta ta mik'e tsaye, a hankali suka shiga takawa tana jin kamar tana takawa akan garwashin wuta, haka suka k'arasa d'akinta zai zaunar da ita tayi tsaye tace "Um um!" Kallon tuhuma ya mata yace "Me?" Cikin shagwab'a tace "Ni d'akina nake so nayi bacci." Kama hannunta yayi yace "Muje to." Mak'ale kafad'a tayi tace "Sai dai ka d'auke ni." Girgiza kai yayi yace "Nawa zaki biya?" Kashe masa ido tayi tace "Ka yarda na shayar da kai?" Da sauri ya matso da ita kusa da shi yana mata wani mayen kallo yace "Zan fi son haka fiye da komai, d'an bani naji." Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um, sai mun shiga d'aki ko." A hankali yasa hannunshi cikin rigarta daga sama ya fito da nononta, sannu sannu ya kai harshenshi kan nononta yana zagayawa da harshenshi daga haka har... *Bayan wata hud'u* Wahala iya wahala Mama ta yi ta a wannan ciki har kawo yau da take nak'uda, dama ita ke haihuwa da kan ta yanzu ma haka likitocin suka tabbatar zata haihu, saidai yau kwana biyu kenan tana ta nak'uda a asibiti shiru, Abba hankalinsa ya tashi ya fita hayyacinsa, dan kamar dai yanda tayi nak'udar cikinta na farko ne na Mimi. Suna zaune dukansu a tabarmar da suka shinfid'a wayar Abba tayi k'ara, yana dubawa ya ga lambar sheikh ce, da sauri ya kalli malam dake gefenshi yace "Kunga malam sheikh ne ke kira, bana so yarinyar nan ta ji halin da mahaifiyarta ke ciki, shiyasa tun shekaran jiya ina ganin kiranta bana d'agawa." Malam yace "Gaskiya ne, ga Mimi da saka abu a rai ga kuma ita ma halin da take ciki." Iya ce tace "To ka d'auka mana tunda ba ita bace." Da sauri ya danna ok ya d'ora a kunne yana rangad'a sallama, fashewa tayi da kuka cikin tashin hankali tace "Abba me nai maka baka d'aga kirana? Abba kwana na uku ban da lafiya shi ne nake ta kiranka dan na nemi gafararku, amma baka d'aga kirana." K'urawa su Iya ido yayi sai kuma ya sunkuyar da kai a sanyaye yace "Uwata me yake damunki?" Cikin shashek'ar kuka tana sunkuyar da kan ta ita ma tace "Abba jikina ne gaba d'aya babu dad'i, k'afafu na sun kumbura sosai, jiya da muka je asibiti sun ce ban da jini ne." Sai kuma ta sake fashewa da kukan da yasa sheikh sake rumgumata a jikinshi yana jin kamar zaiyi kukan shi ma, dan sosai yake tausaya mata halin da take ciki. Da k'yar Abba ya b'oye damuwarshi yace "Kiyi hak'uri uwata, zan zo na dubaki da kaina to." A raunane tace "To Abba, yaushe zaka zo?" A hankali yace "Gobe." Sai kuma yace "Ina sheikh?" Mik'awa sheikh wayar tayi tana fad'in "Gashi." Karb'a yayi cikin nutsuwa yayi sallama, sama sama suka gaisa dan kowa da abinda ke damunsu na larurar matan na su, daga b'angaren Abba ne yace "Kwanan biyu yau a asibiti mahaifiyarta na kan gwiwa ne, bana so ta ji dan bansan wane hali zata shiga ba, gashi ita ma tace bata da lafiya." A hankali sheikh ya zameta a jikinshi ya mik'e tsaye ya shiga uwar d'akinshi yana fad'in "Subhanallah, Allah ya bata lafiya, Ubangiji Allah ya sauketa lafiya, amma ai da ko ni an sanarma, amma ba komai insha'Allah zan zo asibitin yanzu." Godiya Abba ya masa kafin sukayi sallama ya fito, kusanta ya zauna ya d'auki madarar daya kad'a mata yace "To karb'i ki shanye, kin min alk'awarin zaki sha idan na kira miki Abba da ma." Yatsina fuska tayi tana sako da hawaye ta rik'o hannunshi gam gam tana kallon fuskarshi tace "Sheikh tsoro nake ji, tsoro ya kamani sosai akan cikin nan, ji nake kamar ba zan rayu ba wallahi, sheikh ka yafe min ka ji, na san nayi maka abubuwa da dama..." Da k'arfi ya fizgo kan ta ya d'ora a k'irjinshi ya k'amk'ameta, numfashi mai zafi ya shiga saukewa a saman kan ta daya dunk'ule sosai ya cukurkud'e saboda rashin gyara dan halin da take ciki ya fi k'arfin wasa, yanda zuciyarshi ke suka tana k'onewa, tausayinta na ratsa duk wata gab'a ta jikinshi sai ya ji idonshi sun cika taf da k'walla, a hankali ya lumshe idonshi sai kuwa hawayen suka sauko a kumatunshi, hakan yasa shi k'ara rintse ido ya furta "Ya isa haka Ryam, baki min komai ba kinji, na yafe, na yafe miki, ni ma ki yafe min dan Allah, duk ni ne silar shigarki wannan halin, ki yafe min dan Allah." D'ago kan ta tayi suka kalli juna tana zaro ido tayi saurin saka hannunta ta share mishi hawayen tana fad'in "Lahhhhh! Sheikh? Kuka kuma? Haba dai, sai ka karya min zuciyata ai." Sake kwantawa tayi a k'irjinshi tayi luf tana fad'in "Ni ma baka min komai ba, kawai ka tayani da addu'a na sauka lafiya." Yana k'ara k'amk'ameta shi ma yace "Ina ta miki addu'a Ryam d'ina, tunda kika samu cikin nan nake miki addu'ar sauka lafiya, insha'Allah zaki haihu lafiya." Shiru sukayi babu wanda ya sake magana saida ya ji tana sauke numfashi a hankali a hankali alamar bacci, cikin nutsuwa ya zameta daga jikinshi ya gyara mata kwanciyarta, d'aukar k'afafunta yayi da suka zama sumtuma sumtuma ya d'ora a kujerar, tsaye yayi yana k'are mata kallo yanda ta sauya kamar ba ita ba, tayi fuyau da ita alamar babu jini a jikinta, babbar damuwarshi da tashin hankalinshi da suka jawo masa rage walwala da cin abinci bai wuce yanda Rakiya ta fad'a masa wai jinin Mimi ya hau a awon ta na satin daya wuce, jinin Mimi ya hau kamar ya? Me ya kawo mata hawan jini? Ga matsalar rashin jini ga ta rashin cin abinci ga kuma kumbura da kullum k'afafunta ke k'arawa, ga nauyi da take jajen jikinta na dad'a yi mata kullum, hatta da alwala fa yanzu indai yana gidan sai ya taimaka mata, akwai ranar da taimama ya ce tayi dan shi baya gida kuma ta kasa ta shi a inda take ga lokacin sallah n wuce kawai yace tayi taimama a waya. Madarar ya d'auke ya kai fridge kafin ya rufo mata k'ofar da makulli saboda ko Munzeer ba zai so ya tasheta ba, dan baccin kan shi ba samu take yi da dare ba, sauk'inta d'aya da Hafsat ta d'auke mata aikin gidan. *09:20* Sai wannan lokacin kad'ai Allah ya sauke mama lafiya ta samu 'yarta mace, sanda sheikh ya samu labari saida yaje asibitin, kuma bayan ya je gida ya fad'a ma su Hafsat suka ce zasu tafi, haka ya kaisu duk da dare yayi kuma har da Mimi dake fama da ciwon k'afafu. Da suka je Iya na ganinta ta shiga bin ta da addu'ar sauka lafiya, dan tana ganinta tasan ita ma lokaci ya kusa, sun jima asibitin suna ta hira ana dariya kafin suka bar asibitin. Kwana biyu da haihuwar Mama sheikh ya bawa Mimi kud'i yace ta yi wa iyayenta bajintar da zata birgesu, saida ta shawarci Hafsat ta bata shawara kafin ta raba kud'in uku kamar yanda ta ce, kaso d'aya a cikin uku ta ba wa aunty Sahura tace su yi siyayyar kayan cefanai na ranar suna, kaso biyu kuma ta bawa Abba tace yayi hidimar gabanshi, sai ga Abba na neman yin kuka da hawaye dan a lokacin ba wai sheikh ba daya masa kyauta data zautar d shi, Asas kan shi saida ya d'auke masa nauyin ragon suna da wasu abubuwan dayawa, gashi kuma 'yar Mimin sa ita ma ta kai lokacin da zata iya tallafawa rayuwarsa, sai kawai ya nemi fshewa da kuka, da k'yar Mimi ta dakatar da shi daga barin hakan. *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 11:59 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *59* A nauyaye ta tashi zaune tana furta "Hasbunallahu wani'mal wakil, hasbunallahu wani'imal wakil." Gefenta ta zura hannu ta kunna siririn haske ta shiga rarumar wayarta dan kiran sheikh dake d'akin Hafsat yau, saidai wata zungura da aka mata a ciki tasa ta dafe mararta ta rintse ido tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Sheikh, Abdul, aouch!" Zuro k'afafunta tayi da k'yar ta sauko a gadon tana sake kai hannu zata d'auki wayarta, wani irin ciwo ne marar misaltuwa bayanta ke yi da ba zata iya kwatantashi da komai ba, tana mik'ewa tsaye tayi saurin durk'ushewa tana sakin k'ara da fad'in "Wayyo bayanaaaaa! Wayyo Allahna." Durk'ushewa tayi sosai k'asan gadon ta shiga cakumar darar dake kan gadon tana girgiza kan ta, wata zufa ce ta shiga tsatsafo mata tana ta sauke numfashi tana cika bakinta da iska. Tun k'ararta ta farko ta sauka kan Hafsat dake zaune kan gado tana karatun Qura'ani, da sauri ta zabura tana kallonshi ta sauko daga kan gadon tana waiwaya wa inda zata ga hijabinta, tana d'aukar hijabin zata fita sheikh ma dake tsaye yana sallah ya kalleta yace "Ina zaki je?" A rikice tace "Mimi, ihun Mimi ne, ina ga fa nak'uda take." Juyawa tayi shi ma da sauri har doguwar rigarshi na nad'e mishi k'afa kamar zai kifa ya fad'i, saidai bud'a k'ofar da Hafsat tayi ya farkar da Khadija da yanzun ta saba kwana da ita kuma bata rabuwa da mahaifiyarta, fashewa tayi da kuka hakan yasa Sheikh saurin dawowa gareta ya d'auketa cak ya fita da ita hankali tashe. Suna shiga suka sameta durk'ushe kan gadon ta fita hayyacinta ta canza kala, a rikice Hafsat tace mi shi "Nak'uda take, muyi gaggawar kai ta asibiti gaskiya." Aje Khadija yayi kan gadon Mimi yace "Taimaka mata ta canza kayan jikinta to." Da sauri Hafsar ta nufi inda kayan Mimi suke ta bud'a ta shiga duba mata riga da zane simple, sheikh daya durk'usa kusanta gashinta ya shiga gyara mata cike da tausayi yana fad'in "Sannun kinji Ryam, zamu tafi asibiti yanzu, komai zaiyi...haaaa" Wani yunk'uri yayi ba tare daya ankara ba sanda ta shak'o wuyan rigarshi ta had'a goshinsu wuri d'aya, huci ta shiga saukewa tana fad'in "Zan mutu, zan mutu, sheikh mutuwa zan yi, Abdul bayana, bayana ciwo yake..." Cikin dubara ya zura hannunshi ya b'amb'are na ta hannun a wuyanshi yace "Ba zaki mutu ba, insha'Allah zai bari kinji ko, kiyi ta addu'a." Da sauri Hafsat ta dawo kusansu ta shiga k'ok'arin kamata ta mik'e tsaye, sheikh ma kamata yayi suka mik'ar da ita tsaye, kayan Hafsat ta mik'a mi shi tace "Ka taimaka mata ta canza wnnan, bari na dubo kayanta da aka siyo." Karb'a yayi yana jinjina kai, juyawa Hafsat tayi ta fita a d'akin zuwan d'akin da aka ware na zuba mata kayan haihuwa har abinda yaro zai buk'ata, zare mata rigar baccin yayi ya saka mata wanda Hafsat d'in ta bashi, a hankali ya shiga jan ta zuwa fita a d'akin yana fad'in "Muje to." Shigowa Hafsat tayi ta kalleshi da mamaki tace "A'a, hijabinta fa." Sakin hannun Mimi yayi ya juya dan d'auko mata hijabin Mimi ta matse hannunshi gam gam ta durk'ushe tana fashewa da kuka da fad'in "La'ilaha illalahu Muhammad rasulillahi sallalahu alaihi wasallam! Wayyo Allah na bayana, bayana wallahi zai tsage." Da sauri ya tallabota ya kalli Hafsat yace "D'auko mata hijabin dan Allah." Da sauri ta nufi kayan na ta ta d'auko mata suka saka mata kafin suka fita, sai gashi yau sheikh da indai yana tare da matanshi bai cika barin ana tuk'ashi ba amma yau duka matan dole ya bari dreba ya jasu, dan kuwa Mimi ta rik'e rigarshi gam ta k'i saki, a haka har suka isa asibitin yana godiya ga Allah da yasa ba shadda ce jikinshi ba da tayi biji-biji a jikinshi, dan ba laifi fa yasha matsa daga gida zuwa asibitin nan, dan har akaifu take luma mi shi a cinyoyinshi ko kuma ta dinga bubbuga cinyarshi tana sallalami da salati. A gaggauce aka shiga da ita d'akin haihuwa inda Rakiya ce ta jagoranci tsayuwa a kan ta, saidai tabbatarwa da tayi Mimi ba zata iya ba yasa ta fitowa ta shiga ofishinta ta cike takardar daya kamata sannan ta fito wurin sheikh dan b芒 shi ya saka hannu, suna zaune shi da Hafsat dake goye da Khadija sun buga tagumi, dan Hafsat d'in ce tace kar suyi gaggawar sanar ma gida tukuna su ji me ake ciki, zunbur ya mik'e yana kallonta yace "Ya ake ciki Rakiya? Ta haihu ne?" A sanyaye ta sauke numfashi ta girgiza kai tace "A gaskiya sheikh Mimi ba zata iya haihuwa da kan ta ba, kwal d'inta k'arami sosai kuma gaskiya abinda ke cikinta ba k'arami bane, yana da girmama sosai shiyasa ba zata iya ba." Wani iska ya furzo ya sunkuyar da kai yana tasbihi, ya d'an jima kafin ya d'ago jin Hafsat na fad'in "Yanzu miye abun yi Rakiya?" Kallonta tayi tace "Zamu mata aiki ne a cire shi indai ana son ceto rayuwarta dana abinda ke cikinta." Da sauri sheikh ya kalleta yace "A yi mata, a mata Rakiya indai zata rayu, dan Allah ki k'ok'arta ki ceci rayuwarta." Da mamaki Hafsat ta kalleshi tace "Rakiya tayi iya k'ok'ari, muyi fatan Allah ya bata damar ceto rayuwarta." Baya baya ya ja ya zauna inda Rakiya ta mik'a masa takardar hannunta da alk'alami, karb'a yayi ya saka hannu tare da mik'a mata, da sauri ta nufi d'akin nak'udar suka shiga kimtsa duk abun buk'ata ita kuma Rakiya ta kira babban docteur d'in dake wannan aikin. Lokacin da aka fito da ita zasu shiga d'akin tiyata lokacin sheikh na waya da Abban Mimi suna sanar musu halin da ake ciki, Abba sai da yayi hawaye tare da koro musu addu'a, da kallo ya bita sanda suke wucewa tayi lak'was kamar bata motsi, saida ta b'ace ma ganinshi kad'ai ya lumshe idonshi, sannu ya shiga taro 'yar gajeruwar rayuwarshi da ita, k'iriniyarta da rashin jin ta, kwalliyarta da shan k'amshinta, a hankali ya d'an murmusa yace "Allah ka bata lafiya." "Ameen." Hafsat ta fad'a tana kallonshi, da sauri ya bud'e ido ya kalleta dan ya d'auka a zuciyarshi ne yayi addu'ar. *02:00* aka fito musu da santaleliyar yarinyar aka mik'awa Hafsat data rigashi tara hannunta, k'urawa yarinyar ido tayi mai d'auke da gashi luf luf a gaban goshinta kamar zai rufe mata ido, ba tayi mamakin ganinta mai gashin nan ba dan Mimi ba laifi tana da yalwarshi uwa uba kuma sheikh dake bafulace. Saidai wani abun mamaki a tare da yarinyar shi ne irin girmanta, tubarkalla gata jaririyar amma wata b'ulleliya ga kuma kan ta masha'Allah mai fad'i, haka kuma daga yanda halittar hannayenta da k'fafunta suke zaka san tabbas yarinyar nan irin hallitar iyayen Mimi ce da ita indai ba wani nufi na Allah ba kuma. D'agowa yarinyar tayi sosai ta sumbaci goshin yarinyar tare da sakin murmushi tana kallon sheikh ta mik'a masa ita, karb'a yayi hannayenshi na rawa shi ma ya k'ura mata ido, murmushi ya saki ya kalli Hafsat yace "Kinga kamar uwarta, ja'ira Allah yasa kada tayi k'iriniya irinta uwarta, dan ta wahalar dani ba kad'an ba." Hafsat da Rakiya a tare suka k'yalk'yale da dariya sai kuma ya kallesu yana had'e fuska yace "Ya mahaifiyarta take? Tana lafiya?" Murmushi Rakiya tayi tace "Tana lafiya, insha'Allah za'a fito da ita nan da awa biyu a kai ta d'akin hutu." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhamdulillah." Kallon yarinyar ya sake yi yana jin k'aunarta ita ma kamar sauran yaranshi a sanda ya d'ora idonshi a kan su, duk da wannan d'in yafi wahaltuwa wajen rainon cikinta, amma ganinta na yanzu ya zama sanyin idaniyarshi tare da jin ya manta kowace azaba har da ta murzar daya sha yau sanda uwarta ke fama. Iya ce ta zo tare da Abba saidai shi ya koma ya barta nan ta kwana tare da Mimi. Kwanansu hud'u aka sallamesu bayan an tabbatar da ingancin lafiyarta data abinda ta haifa wacce ta ci sunan *Halimatu-Sadiya*, sunan mahaifiyar sheikh kenan wanda sanda ya rad'a sunan Mimi ta kalleshi tace "To yanzu ya zan kirata kenan? Mimi ko Maama?" Murmushi yayi yace "Ya rage na ki." Iya ma tab'e baki tayi tace "Gaskiya kam, idan tana so ma ta ce Uwani." Turo baki tayi tace "To Iya na k'i na ce Uwanin, ba zan ce ba." Hafsat dake ta musu dariya ne tace "Gaskiya Iya sunan gayu zamu dinga kiranta da shi." Kallon Mimi tayi tace "Kinga k'anwata mu dinga kiranta da *Amatullah*." Dariya Mimi tayi tace "Shiyasa nake son aunty na, ba kamar yan cikin bak'in ba." Dariya sukyi dan sun fahimci da Iya take. Sun isa gida kuma Mimi ta fara gurza kalar na ta jegon mai cike da wuyar sha'ani, a zahiri ita ake ganin wautarta na k'in wasu abubuwan da take yi, bata shan kunu saita gaurayashi da madara yayi fari fat tasha sugar sannan ta kifa kai ta shanye, shan maganinta kam wannan k'a'ida ne sai sheikh ya zo yake bata shi ta sha, inba shi b芒 kam kowa aikin banza ne, duk wani abu da za'a ce tasha dan ruwan nono su zo ko 'yar ta mulmuje ta k'i, kuma a bad'ini sheikh ne ke zugata yana nuna mata ba addini bane, ta ci ta k'oshi kawai indai abun mai anfani ne a jiki zata samu ruwan nono ba sai tasha komai ba. _馃ぃDole fa mu k'are yan uwa, komai yayi farko da ma yana da k'arshe ai, wasu ma馃榿 a account d'in aure yak'in mata suke ta tura kud'i wai na matar mutum, ai da kun fad'a min tun farko dana siyar da littafin tunda na ga ya kawo wuta馃槑馃槣 amma zan muku *Mim-Sheikh* returns._ *Bayan wata biyu* Da k'arfi ta fizge zata yi waje tana fad'in "Wallahi ban yarda." Sake rik'ota yayi ya had'a da jikinshi yana kallon cikin idonta yace "Da gaske Ryam, ba an miki allura ba ranar da kika kai Amatullah wajen tsaga ba? To ai a ranar kema na sa aka miki, ba zaki d'auki ciki yanzu ba." Marairaicewa tayi muryar na b'arin tsoro tace "Abdul kaga dai cikin Ama ai na kusa mutuwa ko? To dama baka so na ne shiyasa yanzu ma ka lallab'o kake son sake min wani cikin?" Sinne kan shi yayi yana ta k'ok'arin lalabo bakinta, d'ago da kan shi tayi tace "Fad'a min gaskiya sheikh na sani." Kallonta yayi da idonshi da sukayi jajir suka rine yace "Ryam ina sonki mana, ke yanzu fad'a lin zaki ji dad'i idan na shareki bana kulaki?" Da sauri tace "E, ni babu abinda zan ji, kawai ka tafi wajen Aunty Hafsat ta maka abinda kake so." Had'e fuskarshi yayi yana kallonta yace "Korata kike ne?" K'wacewa tayi daga rik'on daya mata ta ja baya tace "Ni ba korarka nake yi ba, amma dai ka je wajenta na yafe mata har zuciyata." Da irin kallon nan mai nuna ran shi ya b'ace kuma zai iya yin komai ya kalleta yace "Kin tabbata na je?" Ba abinda ya dameta tace "E, ka je." Jinjina kai yayi ya juya inda Amatullah ke kwance cikin d'an gadonta, sumbatarta yayi a goshi d'aga hannayenshi ya tofa addu'a ya shafa mata sannan ya juya ya fice a d'akin bai kulata ba. Tun daga ranar Sheikh yayi wuri ya aje ta, dan yana so ya nuna mata akwai abinda dole ko yana cikin ran ta ta b'oyeshi indai akan shi ne, dan shi ba banza bane mijinta ne? Ko d'akinta ya shiga Ama ce ke kai shi ya d'auketa ya fito yasha wasarshi da ita sannan ya mayar d ita ya aje, yanzu dake tana zuwa d'akinshi gaishe shi ko taje gaisuwart yake amsawa ya shiga sabgar gabanshi. Wasa wasa sai hakan ya fara damunta, musamman kayan marmarin data dinga had'awa tana ta kambama tana sha sai abun ya fara zam matsala, dan kuwa dan sha'awa ke neman haukatata inda k'amshin turarenshi kawai take ji ta dinga jin tsigar jikinta na amsawa. Gashi kuma ya k'i kulata bare ta bada kai bori ya hau, sai hakan yasa ta zama kullum a b'acin rai take, dan danan ta hau ta tunzura, gudun kar a samu matsala tsakaninta d Hafsat sai t zab'i zaman d'akinta kawai indai t gama abinda take. *Yau* ma kamar kullum da sassafe ta shiga d'akin na shi sanye d hijab d'inta tayi sallama, amsawa yayi tare da aje Qur'anin hannunshi ya mik'e, dan ba komai yasa shi kakkauce mata ba sa茂 gudun kwafsawa, dan shi ma turarenta na rikitashi ga uwar k'ibar da tayi jikinta yayi wani irin luwai luwai, fatarta ka rantse zallar madara yanda ta kwanta da kyau abu ga fara dama, shiyasa baya son dogon zance ko mu'amula a tsakaninsu. Zai shige ban d'aki tayi saurin fad'in "Ina kwana." Ba tare daya juyo ko ya tsaya yace "Ban ganshi ba." Ba tayi mamaki ba dan tasan baya amsawa dama, saidai ganin ya shige ya barta tsaye yas ta sakin baki tana kallon k'ofar, sai kuma wata zuciyar ta izata kawai ta sa kai a ban d'akin. Yana tsaka da cire rigarshi t shigo amma bai kulata ba, k'arasa cire rigar yayi dan dai ta fita ta bashi wuri yayi shirin zame wandonshi, ganin bata kula da haka ba sai ma gyara tsayuwa da tayi ta fara zazzga masifa tana fad'in "... *Alhamdulillah* 06/08/2021 脿 22:49 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *MATAR MUTUM* _(K'abarinsa)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA* _GA DUKA_ *'YAN AMANA TA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *K'arshe* *60* Ganin bata kula da haka ba sai ma gyara tsayuwa da tayi ta fara zazzaga masifa tana fad'in "Wai ni kam Abdul me na maka ne kake wulak'antani a gidan nan? Dama da ake cewa da ka fara haihuwa sai namiji ya canza maka gaskiya ne? Duka haihuwa d'aya sai ka wani fara d'auke min kai? Me na maka dan Allah? Idan ka fara gajiya da ni ne ka fad'a min mana dan nasan inda dare zai min." Dakatawa yayi daga shirin cire wandon ya k'ura mata ido, tsakaninta da Allah take maganar kuma babu alamar wasa, saidai abu d'aya daya fahimta duk da cikin fad'a take maganar, amma kuma muryarta a sanyaye sosai kamar wacce ke neman wani abu. D'auke kai yayi yana sake had'e fuska ya kalleta da kyau yace "Kina buk'atar wani abu ne?" K'yabta masa ido tayi idonta na cika tap da hawaye sai kuma tace "A'a." Nuna mata k'ofa yayi yace "Fita to ki bani wuri, wanka zanyi kuma dai kinsan ba zan yi tsirara a gabanki ba ko?" Galala tayi tana kallonshi sai kuma ta ji gabanta ma na fad'uwa dan yanda ya mata maganar ba da wasa bane, a hankali ta juya zata fita jiki a mace sai kuma ta juyo da sauri ta kuma kallonshi, marairaicewa tayi sosai ta sake kashe muryarta tace "Abdul kana hushi dani ne akan abinda ya faru ranar? Kayi hak'uri to kaji na tuba, wallahi ba zan sake ba, Abdul idan kana min irin wannan hushin a gidan nan ya kake so nayi to? Gidan nan dai ai saboda kai nake zaune, kai ne abokin hirata kuma farin cikina, idan ka yi hushi dani ya zanyi kenan?" Kafeta yayi da ido yana kallon fuskar tausayinta kamar ya jawota ya rumgume, saidai a yanda yasan Mimi kai shi yasan da walakin goro a miya, tabbas akwai abinda take da buk'ata, amma sau nawa suke samun sab'ani saidai shi ya d'auki da dangana da girma ya nemi sulhu, amma ita ta dinga botsarewa kenan tana fusata tana hawa da sauka. Ita ma kallonshi take ganin yana ta kallonta sai kawai ta fad'a jikinshi ta fashe da kukan shagwab'a tana fad'in "Kayi hak'uri yallab'ai ka yafe min ka ji." Wani munafikin murmushi ya saki a ran shi yace "Na-san a rina dama, mata da kurb'e kurb'e musamman idan sun haihu." Dariyar mugunta ya dinga saki ya shiga shafa jikinta yana zura hannayenshi cikin rigarta, tsam tsigar jikinta ta fara tashi tana rage sautin kukanta sai kuma ta d'ora hannunta na dama kan nonon shi tana shafawa tana rufe ido. Biye mata yayi shi ma sosai saida yaji suna buk'atar kwanciya kawai ya janyeta a jikinshi ya sake nuna mata k'ofa da idonshi da shi ma ya kamu da jarabar yace "Fi...ta a nan." Da mamaki ta kalleshi sai kuma ta sake langab'ewa ta matso zata rik'e hannunshi ya sake nuna mata k'ofar alamar ta fita, duk k'ok'arinta saida hawaye suka fito mata dan sosai take jin yanayi marar dad'i a jikinta, juyawa tayi a fusace ta bar d'akin zuwa d'akinta ta cire hijabinta ta kwanta gefen 'yarta dake baccinta ta k'ura mata ido. Tun tana d'an lumshe ido tana matse k'afafunta har bacci ya d'auketa ita ma marar dad'i. A hankali ya shigo d'akin ya zuba mata ido, murmushi ya saki yana godewa Allah daya nuna mishi lagon yarinyar nan, kamar kowa'e d'an adam yana da rauninshi, haka shi ma yanzun ya hango na ta raunin, ba zai cutar da ita ta haka ba dan cituwar zata iya shafarshi, saidai shi ya d'an samu sauk'in wani abun daga gareta, abu d'aya da zaiyi shi ne ya sake dagewa wajen inganta lafiyarshi dan samun sauke mata hakk'inta, ya sani har ga Allah wasu lokutan idan ya zurfafa tunani ya kan ji kamar ya tauyeta, dan a lokacin da tsufa zai riskeshi ya kai k'adamin da baya buk'atar mace, ita kuma a lokacin ne zata kai ganiyar shekarunta da dole wutar sha'awa ke ruruwa a jikinta, tambayar anan ita ce shin ya zaiyi idan lokacin nan ya zo? Shin zai saketa dan kar ta fad'a halaka? Ko kuma idan ya rik'eta zata fad'a wata mummunar hanya ce? Nauyayyen numfashi ya sauke yace "Hasbunallahu wani'imal wakil." A hankali ya k'arasa kusanta tare da sunkuyawa yasa hannayenshi cak ya d'agata gaba d'aya, bud'a ido tayi da sauri tace "Waye?" Sai kuma suka had'a ido, rufe idonta tayi jin yace "Waye kuwa ban da na ki." Turo baki tayi tana wuntsila k'afafu tace "Sauke ni k'asa malam, bayan yanzu ka koroni a d'akinka." Dariya yayi yace "Na gane ban kyauta ba ai, shiyasa na zo bada hak'uri." "Ni kawai ka saukeni ba zan hak'ura ba." Ta fad'a tana kumbura, cikin fara'a yace "Muje kan gado tukuna na bada hak'urin, sannan ne zan tantance an hak'ura ko ba'a hak'uran ba." D'akinshi ya shiga da ita ya rufe ya kaita kan gadon ya sauke, rumfa ya mata ya nemi had'a bakinsu sai kuma tayi zurum ta had'a bakinshi da na ta, waro idon da yayi ya kalleta yasa ta jin kunya ta cire bakinta a na shi ta sunkuyar da kai, tallabo hab'arta yayi yana kallonta da tausayi yace "Ryam, ni ne ko? Ni ake da buk'ata a wannan lokacin ko?" A hankali ta jinjina kan ta sai kuma ta sunkuyar da kai cikin muryar kuka tace "Abdul k'aik'ayi nake ji a jikina, sai na dinga ji kai kawai nake so na ji kana tab'ani, ko k'amshin turarenka kad'ai na ji saina ji wani irin abu da bana gane ko miye, Abdul tsoro hakan yake bani, wasu lokuta ma idan kana d'akin Aunty Hafsat haka nake jin zuciyata na bugawa da sauri, sai na dinga jin haushin komai sai nayi ta kuka ni kad'ai a d'akina, amma ban tab'a fad'a maka ba dan bana so ka d'auka zan raina Aunty Hafsat ne." Wuf yayi da bakinta a na shi ya shiga tsutsa dan kad'an ya rage ta saka shi kuka wallahi, ta bashi tausayi sosai yarinyar, hakan na nufin tana jin kishin shi kenan, amma bata nunawa ko kad'an ko da daga ita sa茂 shi ne saboda kar tayi laifi. *Asa-Ma'u* Sagala yaron yayi a gabanshi irin goyon nan na zamani hannunshi rik'e da bulunbotin yaron yana d'an jijjiga madarar da ake bashi wasu lokutan. Da sauri ta fito a d'akin tana fad'in "Yasha ne?" Kallonta yayi yace "Yanzu dai zan bashi, kin shirya ne?" K'arasowa tayi tana gyara hijab d'inta tace "Na shirya Baby, to wai me ya tsayar da kai da har yanzu bai sha ba?" Turo baki yayi yace "To ni na iya ne, dan Allah ki bashi da kan ki." Dariya tayi tace "Nima ban iya ba, yanzu dai muje Baby, kaga fa an kusa sallah la'asar yanzu." Nufa hanyar fita yayi tayi saurin fad'in "Kawo shi to, so kake ka fita a haka a ce kai ke goyonshi?" A hankali ya shiga since yaron daga jikinshi, saida ya kalli fuskarshi yana ta baccin shi ya mik'a mata ta karb'eshi, fita sukayi a gidan yana rufe k'ofar take fad'in "Yau nasan sai na ci d'an banzan duka a wurin Salma, bikin sunanta a ce sai yanzu nake fita a gida." Juyowa yayi ya kalleta yace "A'a fa Hajia ba dole, idan ana ganin kinyi rana a warhaka ma wallahi sai mu koma ciki, ai kinsan duka kwananki uku yau da yin arba'in, babban jarumta fa na yi ta barinki fitar nan." Dariya tayi tana kallonshi tace "Nagode to jarumi na, amma idan ka hanani ai kuka zanyi." D'ora yatsarshi yayi a baki yace "Dan haka to a min shiru, kuma a je a dawo mu d'ora inda muka tsaya." Bud'e mata k'ofar mota yayi zata shiga ta kalleshi ta ja kunnenshi tace "Wai kai abun nan baya isarka ne?" Girgizz kai yayi ya rintse ido cikin shagwab'a yace "Wayyo Hajia zata cire miki kunnen yaro." Sakinshi tayi tana dariya ta shiga ta zauna, saida ya shiga shi ma yayi oda mai gadi ya bud'e musu k'ofar sannan ya kalleta yace "Ko kad'an ba kya isata Ma'u na, ni kaina ina mamakin yanda bana gajiya dake kamar wani maye." Dariy ta fashe da ita tace "Mayen Ma'u kenan?" Jinjina kai yayi yana dariya ya bata hannu suka buge yana fad'in "Ashe kin gane, mayen Ma'u ne ni." Isowar motarsu tayi daidai da isowar jibgegiyar motar sheikh, Asma'u na ganin motar tayi dariya tace "Shegiyar k'awa kenan, na d'auka ni kad'ai nayi maraice, ashe harda kayan gidan sheikh." Dariya Asas yayi shi dai bai ce komai ba dan kan abinda ya shafi Mimi bai cika zak'ewa ba yanzu, karbar *Mujaheed* yayi ta fita sannan ta zagayo ta karb'eshi, k'aramar sumba ya aika mata tare da fad'in "Ki kula da kan ki Ma'u na, sannan ki kula min da zakina, ina sonku." Murmushi tayi tace "Kai ma ka kula da kan ka, sai ka dawo." Shiga gidan Salma ta nufa inda Mimi ma ta fito d'auke da Ama ta mata wani irin shiri na ban mamaki ga hijab d'un da aka saka mata yarinyar mai d'aukar hankali ta ci uwar kwalliya a fuskarta, murmushi Asma'u tayi ta nufesu a ran ta tana fad'in "Da alama shirin Ama kad'ai zai d'auketa awa uku." Tana k'arasowa da ladabi ta d'an lek'a ta gaishe da sheikh Mimi na k'ok'arin karb'ar Mujaheed tana masa wasa, ita ma Asma'u karb'ar Ama tayi sukayi musaye. A mutumce sheikh ya amsa mata tare da mik'awa Mimi hannayenshi ta bashi yaron, sumbatarshi yayi kafin ya mik'o musu shi, zasu wuce ya sake kallonta yace "Ryam." "Na'am." Ta fad'a tana juyowa, cike da gargad'i yace "Kin dai san aikina na baro na zo dan na kawoki nan, ki koma gida a kan lokaci kinji?" "To tsohon yan matanshi." Ta fad'a tana wucewa ta bi bayan Asma'u data wuce da Ama, cike da zolaya Asma'u ke fad'in "Mimi irin wannan shiga haka kamar wata 'yar mafiya, wallahi babu mai ganeki sa茂 wanda ya sanki." Banza ta mata har suka shige ciki suna ta ratsa taron matan suna shiga inda d'akin Salma yake, suna shiga da sallama Asma'u dai da ba nik'ab gareta ba an ganeta, amma dayawa basu gane Mimi ba, dan ruf take k'afafunta da safar k'afa d'auke da takalmi mai tsini, hijabinta dogo har k'asa ga kuma nik'ab, saida ta d'aga nik'ab d'in suka gane wacece, ai tuni suka kwashe da shewa ba ma kamar Jamila da ita ma ba'a jima da aurenta ba tace "Iyee! Ashe kayan gidan sheikh ne." Salma kuma dak'uwa ta ma Mimi tace "Shegiyar matar malam, Mimi ke ce." A hankali ta mik'awa Jamila Mujaheed ita kuma ta cire nik'ab d'in tasa a jakarta ta tattaro hijabin shi ma ta jefawa Jamila data fashe da ihu tana fad'in "Wai wai wai! Ke Mimi me kika ci haka a gidan sheikh wai? Kin ganki kuwa?" A sanyaye kamar ba Mimi ba ta haura kan gadon ta samu wuri ta zauna tana gaisawa da sauren k'awayensu wanda ta sani da ma wanda bata sani ba, suna had'a ido da Asma'u dake kallonta da mamakin yanda ta ga bata kula da tsiyar da su Jamila ke mata ba, a sanin data ma k'awarta ta d'auka zata juya musu manyan d'uwawun nan na ta ne data k'ara masha'Allah sannan tayi fari da ido ta kwankwatsa musu magana, amma sai bata ga hakan ba ta ma fita a harkarsu. Mimi ma murmushi ta sakar mata tace "Asma'u nayi hankali fa yanzu, ta y'a zan tsaya ina shiririta a gaban 'yata." Dariya su Jamila suka fashe da ita inda Mimi ta kalleta taja tsaki, hararanta Jamila tayi tace "Mimi an matan tsohonta, wai dan Allah me kike sha ne." Cikin jin haushi tace "Ke madarar mijina nake sha, ina dalilin wannan jaraba haka, na ji tsohon ne amma ai dan ubanki ke gaki nan har yanzu baki da ciki, ni kuma zuwa d'aya tak ya min na d'aukeshi." Sauke numfashi tayi ta nunata da yatsa tace "Kinga ki rabu dani ko na ji da abinda ke damuna." Salma dake ta k'yalk'yala dariya ce tace "To fa! Me ke damunki ne?" Jamila ce tace "Watak'ila wani cikin ya mata." "To sai me?" Cewar Asma'u, a raunane Mimi ta kalli Salma tace "Wallahi jiya kusan kwana mukayi a asibiti Mamar malam ba lafiya." Da sauri Asma'u tace "Mamar malam kuma? Wane malam d'in?" Nuna Ama tayi tace "Ama nake nufi dan Allah." Cike da tausayawa Salma tace "Me ya sameta?" Cike da jimami tace "Wallahi asma (athim)." "Take da?" Cewar Jamila a tausashe, jinjina mata kai tayi tace "E, kamar da wasa fa yanzu gashi abun sai girma yake." Addu'a sukayi ta jera mata kafin su ci gaba da hirarsu irin ta k'awayen zamani. Sanda aka fara shigo da abinci ne Mimi ta hangi Aisha na shigowa d'auke da *Ahmad* yaronta ita ma, da sauri ta kalli Salma tace "Ke dan ubanki ba dai k'awance kike da d'iyata ba?" Kallonta Salma tayi ta kalli inda ta nuna sai kuma tace "To miye a ciki? Ke 'yarki ce ni kuma k'awata." Duka ta kai mata tana fad'in "Ke tsir!" Dariya Salma tayi tace "Ke wallahi ba wani k'awance bane muke, kawai irin gaisawar nan ce ta yanar gizo." Shigowar Aisha yasa Mimi d'auke wuta ta kama jikinta irin ba wasan nan, da farin ciki Aisha ta k'arasa kusanta tana mik'a mata Ahmad ita kuma ta d'auki Ama tana mata dariya da fad'in "Aman Abie, kina lafiya?" Mimi ma wasa take ma Ahmad dan ko gida Aisha ta tafi da shi Hafsat ce ke mishi tsiya, amma ita Mimi tace tana son abun ta, hakan yasa wata rana ma sheikh yace ta daina kawo masa shi gida tun kafin ya hanashi kwanciyar hankali a gida. *10:30* Fitowarshi kenan daga d'akin Hafsat ya mata saida safe ya shigo d'akin, ganin wuta kashe yasa shi lalubawa ya kunna, dau! Idanshi suka sauka a kan ta tana tsaya bakin gado ta dafe k'ugu da hannayenta duka biyu, daga k'asa ya fara kallon irin guma guman takalmin data saka, takalmi ne fa irin na 'yan matan zamani k'afa ciki wanda har maza na sakawa, wando dogo na mata wanda ya matse daga k'asa sama kuma a bud'e a wajen gwiwan da cinyoyi duk a yage irin dai na 'yan gayu, sai rigar mai botira a gaba amma duk ta b'allesu saita d'aure daga k'asa sosai, sai bras d'inta fara tas data d'an bayyana kad'an ita ma. Hula ta d'ora da ake kira hana sallah ga wani uban gilashi tartsetse a fuskarta da ta ci uwar kwalliya, sai bakinta dake d'auke da lolipop tana tsutsa. D'an k'asa tayi da gilashin ta kalleshi da idonta da suka sha eyeshadow ta kashe mishi ido d'aya, a saukake ya had'a yawu murya can k'asan mak'oshi yace "A'uzu billahi mina shaid'anin rajim." A hankali ta shiga takowa cikin takon birgewa har ta tsaya gabanshi hannunta dafe da k'ugu, sauke gilashin ta sake yi ta d'ora hannunta a kafad'arshi tace "Sheikh ni ce shaid'aniyar kuma?" D'an zabura yayi dan wallahi sai yaji kamar mafarki ne yake, tar ya sauke idonshi a kan ta yana mata wani kallo kamar wacce ta gaura masa mari yace "Ryam yau kuma wane fitsararren ne a jikinki haka? Na ga kayan bacci kala kala a jikinki har da wad'anda kamar babu, amma wannan fa? Baturen wace k'asar ce?" Bushewa tayi da dariya kamar zararra sai kuma ta had'e rai tana kallonshi tace "Abdul, ni ce mai iskokai a kai? Haka kake nufi ko? Nagode." Sake d'ora hannunta tayi a kafad'arshi cikin rad'a tace "Abdul ka manta ne, yau muka shekara cif da aure, shiyasa na maka wannan shigar, kuma kai na ji ka fad'a a wa'azinka cewa babu laifi mace ta wa mijinta gayu na d'aukar bakin duniya indai daga ita sa茂 shi ne, to shi ne nawa sai ya zama abun fad'a har an tofe ni da a'uziyya." Kallon k'wayar idonta yayi shi ma yace "Da gaske? Yau ne aka d'aura aurenmu." D'aukarta yayi cak ya shiga lalubar k'irjinta yana fad'in "Lallai yau zan baki mamaki, wannan gayu ai sai na biya ma zuwa safiyar gobe, amma kafin goben mu fara ban ruwa wa gonarmu ko yan matan tsohonta." Cire hular kan ta tayi ta jefar haka ma alewar bakinta tana fad'in "Hakane tsohon yan matanshi." Fad'awa sukayi kan gadon inda suka shiga tallafawa junansu cike da so da k'auna da kuma...馃ぃ _Allah nagode maka daka nuna min ranar nan, yau gani a k'arshen *matar mutum*, Allah ka bani ladar fad'akarwa kasa a anfana da hakan, kuskuren da nayi Allah ka yafe min tare da makaranta na._ *Kamar yanda na fad'a muku ina son yin dogon hutu insha'Allah a k'alla na tsawon watanni, a wannan lokacin zan samu damar nazari da bincike akan labarin da nake son tab'owa insha'Allah wanda ni ce zan k'irk'iri k'asata da kuma sunayen mutane na dan kaucewa cin zarafin kowa, watak'ila kafin nan mu had'u daku a labaren dake riskata na gaskiya, akwai yiyuwar hakan akwai kuma yiyuwar barin hakan, fatana dai Allah ya sake sadamu da alkirinsa.* *Alhamdulillah*