TAGWAYE By Maman Maama Marubuciyar Maimoon A'isha Humairah Diyam Episode One: The Bad Dream Free episode Bismillahir Rahmanir Rahim Ina rokon ubangiji ya bani ikon gama littafin nan lafiya kamar yadda ya bani ikon fara shi lafiya. Ina kuma rokonsa ya bani ikon rubuta alkhairi, ya haneni ga rubuta sabo. Ga masu bin rubutu na tun a Maimoon, zaku fahimci cewa a cikin wannan labarin mun koma can baya ne mun dauko wani zaren labari da muka ajiye, yanzu zamu jawo shi mu hade da sauran labarurrukan mu. We are going far back in time. Please bana son jin "a zamani kaza babu kaza da kaza" saboda ni ban fadi a wanne zamanin labarin ya faru ba. Babu littafi na dana rubuta shekara. Just read and understand. We are going to look at life from the villain side of the story. Let's be villains. Lol ILYSM Tafiya yake yi, yana jin jikinsa cikin yanayin tafiya amma kuma baya jin alamar ƙafafuwan sa suna taka kasa, jinsa yake yi tamkar wanda yake shawagi a sama, wannan yasa yayi saurin bude idanunsa da da suka kasance a rufe, idanuwansa suka sauka a kan fuskar ta. Yaji wani abu da baisan menene ba ya taba zuciyarsa a dai dai gurin da ba'a taba taba masa ba. Ya kura mata idanu yana son ya haddace dukkan kamannin ta a lokaci daya amma ya kasa, gashi dai yana kallon ta amma baya ganinta, so yake ta kalle shi ko yaya ne ya samu ya kalli cikin idonta amma taki kallon nasa. Wannan yasa ya bude muryarsa da niyyar yi mata magana ko Allah zai saka ta kalle shi koda kallo daya ne, ko da na second daya ne, ko yaya ne. Amma ga mamakin sa, maimakon yaji murya ta fito daga bakinsa kamar ko da yaushe in yayi magana sai yaji kuka ya fito, kuka mai dauke da sauti irin na jarirai. Cikin mamaki ya sauke idonsa kan jikinsa, sai a lokacin ya fahimci dalilin da yasa yake jin kamar yawo yake yi a iska, yake jin yana tafiya amma baya taka kasa, ashe shi jariri ne, ashe a rungume yake a hannun wannan matar da ta taba can cikin zuciyar sa. Sai a lokacin ya fahimta, ashe mafarki yake yi. Mafarki yake yi da mahaifiyar sa, abinda bai taba yi ba tunda yake a duniya, wannan fuskar da yake kalla amma ya kasa gani fuskar mahaifiyar sa ce. Wannan ya saka shi ya sake rudewa tare da sake dagewa wajan tattaro dukkan karfinsa dan ya yi mata magana ya samu ta kalle shi amma sai kokarin nasa ya kare a canyarewa da kukan jariri. Ba tare data kalle shi ba ta saka hannu tana dan jijjiga shi kadan da niyyar rarrashi, fuskarta cike wani yanayi da yayi masa kama da tsoro, fargaba hadi da damuwa amma sam babu soyayya a fuskarta ko da ta digon alkalami. "Why?" Yayi kokarin tambayar ta a cikin muryar sa ta kukan jarirai. Wannan itace tambayar da yake da burin yi wa mahaifiyar sa a duk ranar da Allah ya hada su. "Me yasa ba kya so na me nayi miki?" Maimakon ta amsa masa sai yaga ta jawo bakin dankwalin ta da tayi amfani dashi gurin rikon sa ta rufe masa fuska dashi yadda ganin nata ma ya daina. Nan ya fara kusur kusur da harbe harbe irin na jarirai a ransa yana burin sake ganin fuskar ta. Har ya samu ya bude fuskarsa, sai ya kalli gurin da suke tafiya. Gefen titi ne, kuma daga dukkan alama cikin dare ne dan gurin yayi duhu sosai amma yana lura da bishiyoyin da suke wucewa alamar wajen gari ne. Sanyi yake ji yana ratsa jikinsa saboda kasancewar babu kaya a jikinsa sai dankwalin da ta rufe shi dashi. Ya hango fitilar mota ta taho, sai yayi murna a ransa yana tunanin wani ne yazo zai taimaka musu sai dai ga mamakin sa sai yaga ta yi sauri ta buya a bayan wata bishiya, sannan ta saka hannu ta toshe masa baki dan hana kukansa fitowa, numfashin sa yaji yana kokarin daukewa saboda cikin rashin sani ta hada ta rufe har hancinsa wannan ya saka shi harbe harbe da kokarin kwace kansa amma bata cika shi ba har sai da motar ta wuce. Data bude masa baki da hancin ko kallon fuskarsa bata yi ba........... Gajiya da wahala ya saka ya kwanta lamo yana maida numfashi yayin da ita kuma ta cigaba da tafiya. Suddenly yaji ta tsaya. Ya kalli inda suka tsaya din sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi. Ba zai taba manta gurin ba, dan shine inda ya fara kira da kalmar "home" a rayuwar sa. "Nigerian National Orphanage". Tsohon gate din gurin ne da kuma tsohon ginin. A hankali yaga tana bin jikin katangar dan kaucewa hasken fitilun da suke gurin, yayin da hannunta yake rufe a bakinsa. A dai dai kofar ta tsaya sannan without thinking twice ta durkusa ta ajiye shi a kasa. Tana ajiye shi ya dage da duk karfinsa yana kuka, yasan me take yi, amma ba wannan me damuwarsa ba, damuwarsa shine rabuwa da ita, rabuwa da dumin jikinta. Burinsa kawai a lokacin shine ta kalle shi, ko da sau daya ne, ko da second daya ne, ko yaya ne. Bata kalle shi ba bata taba shi tace "good bye" ba, asali ma hankalinta a tashe yake kar wani ya ganta, burinta shine tayi sauri ta bar gurin. Yana ji hannunta ya bar jikinsa and his heart went with it. Kuka yake sosai, kukan da bai taba sanin cewa ya taba yin irinsa ba sai yau. Sanyi yake ji, tsoro yake ji. Cikin kukan nasa ne yaji takun mutum, wannan yasa ya sassauta, a hankali fuskarta ta kuma bayyana a gare shi tana tsaye a kansa, wani irin dadi yaji a ransa wanda bai taba jin irin sa ba, ashe dai tana sonsa, ashe dai tace "good bye my son, ina sonka sosai zan rabu da kai ne kawai dan dole ba dan zuciya ta na so ba amma nayi maka alkawarin zan dawo gare ka" Wannan sune kalmomin da kullum yake gaya wa kansa a matsayin wanda mahaifiyarsa ta gaya masa sanda zata yar da shi. Amma maimakon haka, sai yaga ta durkusa ta zare dankwalin ta data lullube shi dashi, sannan ba tare data kalle shi ba, ba tare data ce komai ba, ta ruga da gudu ta shige cikin bishiyoyi.......... Wani azababben sanyi yake ji, wani irin kuna zuciyarsa take yi. Tsakuyoyi da kasar gurin suna sukar fatar jikinsa. Sai a lokacin ya lura da ko cibiya bata yanke masa ba daga shi har mahaifar sa ta yar. Kuka yake yi, kuka wanda zai ratsa zuciyar duk wanda zai ji shi a lokacin. Amma banda zuciyar wadda ta ajiye shi. Banda zuciyar wadda yake ganin tafi kowa kusanci dashi a lokacin. Wadda yake tunanin zata fi kowa son shi. Mahaifiyar sa. A firgice ya farka. Kukan jaririn ne ya farkar dashi, kukan sa. Ya tashi zaune gabaki daya jikinsa yana kakkarwa yana jin sanyi yana ratsa kasusuwansa tamkar yadda yaji a cikin mafarkin. Ya jawo gwuiwoyinsa zuwa kirjinsa sannan ya dora kansa akan gwiwarsa a hankali yana kiran sunan ubangiji har yaji nutsuwa ta fara zuwa masa sannan ya karanto addu'ar da annabi ya koyar cewa ayi idan anyi mummunan mafarki. Lallai wannan mummunan mafarki ne, bai taba yin irin wannan mafarkin ba, irin mafarkin da zaka yi kaji tamkar gaske ne amma kuma kasan mafarki ne. Bai taba mafarki da mahaifiyar sa ba. Bai taba ko da tunanin ta irin haka ba. A cikin mafarkin fuskartar babu ko da digon sonsa ne, babu tausayinsa ko kadan. Kullum in tunanin iyayensa yazo masa yana consoling kansa ne da cewa dole ce ta raba su, suna sonsa amma babu yadda zasu yi shi yasa suka yar da shi amma wannan mafarkin ya goge wancan tunanin. Ya mike yana taka lallausan kafet din dakinsa ya wuce zuwa toilet ya wanke fuskarsa da yake jin ta dauki zafi kamar mai zazzaɓi. Sai ya samu kansa da karewa kansa kallo a cikin mudubin gabansa. A hankali ya furta "Amir, mafarki kayi ba wai gaskiya ba ne ba" wani bari na zuciyarsa yace dashi "idan kuma ba mafarki bane ba memory ne fa?" Ya girgiza kan sa da sauri, it can't be a memory, ranar da aka haife shi ne, ta yaya zai samu memorin abinda ya faru ranar da aka haife shi? Ya shafa gashin fuskarsa da hannayensa biyu "this is crazy, it can't be" sannan ya lura cewa magana yake yi shi kadai. Ya goge ruwan fuskarsa dana hannunsa a jikin towel sannan ya dawo cikin Bedroom din ya kalli agogo, karfe daya dai dai, ya rage ac ya koma kan gado ya kwanta. Maybe gobe yaje asibiti gurin Moon ta duba kwakwalwar sa, maybe ya fara tabuwa. Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account GT Bank Account Name : Nafisa Usman Tafida Account Number : 0139433741 Sai su turo screenshot na transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin 08067081020 Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin 08067081020. Sai na jiku.... Episode Two: The Beginning Labarin ya samo tushen sa na farko ne daga wasu ma'aurata biyu, Alhaji Aminu da Hassana. Alhaji Aminu dan kasuwa ne kuma maaikacin gwamnati, yana kuma da dukiyarsa dai dai gwargwado. Asalinsa dan Gombe ne, zama da aiki ne ya kawo shi Kaduna inda anan ne tushen labarin yake. Matarsa Hassana ita ma ƴar Gombe ce, daga can ya auro ta ya taho da ita Kaduna, ganin cewa bata da kowa a Kaduna ya saka iyayenta suka hado ta tare da kanwarta Amina dan ta ke debe mata kewar gida kuma take tayata yan aiyuka. Amina a lokacin tana da shekaru goma sha biyar. Dan haka suna zuwa Kaduna aka saka ta a makaranta dan ta cigaba da karatunta, kuma yayarta da Alhaji Aminu suka rike ta sosai. Shekara biyu da auren Alhaji Aminu da Hassana sai Allah ya bata ciki, ciki mai cike da tarin laulayi tare da tarin girma. Inda tun a awon farko aka tabbatar wa Hassana da cewa tana dauke da tagwaye. Hakan ya saka su cikin matsanancin farin ciki duk kuwa da cewa dama suna saka ran hakan saboda kasancewar Hassana tana da abokiyar tagwaitaka ya saka chances dinta na haihuwar tagwaye ya zama yana da yawa. Ganin wahalar da cikin yake bata ya saka mahaifanta suka nemi su tafi da ita gida ta haihu a can amma son da Aminu yake yi mata ita da cikin yasa ya kasa barinsu su tafi ya nemi a bar masa matarsa shi zai ke kula da ita da kansa. Aka bar masa ita, ya kula da ita tamkar sabon kwai, har lokacin haihuwar ta yayi. Da farko sanda ta fara nakuda likitoci sun dauka zata iya haihuwa da kanta, sai data yi awanni babu wani progress sannan aka fara shawarar yi mata aiki dan gudun samun matsala. Sai da aka gama shirya ta tsaf sannan kuma sai jini ya balle mata, a haka akayi mata cs aka fitar da tagwayen maza, masu kama daya, sai dai daya ya dauko fatar babansa "baƙi" dayan kuma yayo fatar Hassana "fari". Bayan an dawo da ita dakin hutawa ne ta farfado aka saka mata jariran a hannayenta biyu, Hassan a hannun dama, Hussain a hannun hagu. Ta rungume su a jikinta, a haka Allah ya dauki ranta. Fadar bakin cikin Aminu tamkar bata lokaci ne, dan mutane har sun fara tunanin ko zai bita ne, amma sai soyayyar yayansa ta danne bakin cikin rashin matarsa. Da farko anyi niyyar karbar yaran daga hannunsa a tafi dasu Gombe gurin kakannin su amma Aminu yace sam babu mai raba shi da yaransa. Wannan yasa bayan dan gajeren zama tsakanin iyayensa dana Hassana aka yanke shawarar aura masa Amina. A gurin aka biya sadakin aka kuma daura auren. Bayan dan karamin biki a Gombe aka dawo da amarya kaduna gidan mijinta tare da tagwayen ƴaƴan ta. Da farko Amina ta dauki auren ta tamkar wasan yara dan ita babu komai tsakanin ta da Alhaji Aminu bayan mutunta juna, ganinsa take tamkar yayanta da suka fito ciki daya. Abinda yake gabanta kawai shine karatunta da kuma marayun da aka bar mata wadanda ta dauki son duniya ta dora akan su, dan har ba'a iya banbance wanda yafi son yayan a tsakanin ta da Alhaji Aminu wanda kullum a jikinsa suke bacci. An samo mata matar da zata ke tayata kula da yaran saboda lura da karancin shekarun ta da kuma makarantar da take zuwa, amma fa tana dawowa zata karbo yayanta. Ranar nan bayan ta dawo daga school ta samu mai renon tace "Baba Yaha Dan Allah ko kinsan maganin da za'a sha ruwan nono ya zo?" Baba Yaha ta kalle ta da mamaki tace "me zaki yi da ruwan nono Amina?" Tace "a makaranta an gaya mana irin amfanin nonon uwa agurin jarirai, yaran nan nake tausayi, su basu samu wannan alfanun ba tunda kinga madara suke sha. Shine nake so in samu magani insha sai inke basu nawa" baba Yaha ta jinjina irin soyayyar da Amina take yiwa yaran sannan tace "to wannan dai ba magana ta bace ba, kije ki samu mijinki kuyi shawara a tsakanin ku, in ya amince shikenan sai in samo miki, amma in bai yarda ba dole ki hakura. Dan haka sai ki lallaba shi". Da wannan Yaha ta kashe maganar, dan a lokacin babu yadda za'a yi Amina ta samu Alhaji Aminu da magana makamanciyar wannan saboda sam basa irin wannan da shi, ko wasa ma basa yi saboda shi ba mutum ne mai son wasa ba. Amma tsakanin mata da miji hausawa suka ce sai Allah. Tagwayen suna da shekara biyar a duniya sai ga Amina da ciki. Ai kuwa ranar da tagwayen suka fara lura da cikin a jikinta suka sakataa gaba da jerin tambayoyi har sai da ta gaya musu cewa baby ne a cikin, baby zata haifa musu watarana. Nan suka fara tsalle a saman gadonta suna adungure zuwa kasa. Alhassan yace "Please, Please aunty ki haifa mana namiji dan muke wasa tare" Alhussain yature shi yace "me za'ayi da namiji, anyi ta haihuwar mazan kenan? Mace zata haifa mana shikenan na samu budurwa" nan sai fada, harda kokawa, sai da kyar ta raba bayan sun gama doddoke ta. Sannan ta zauna tana dariyar sokonci irin na Hussain, ko ta yaya yar da zata haifa zata zama budurwar shi? Haka yake shi Hussain, akwai surutu, akwai fitina, akwai karambani kuma akwai kokari a makaranta. Shi kuma Hassan shine mai wayo, manyance, da zarar magana. In yayi wani abin zata ce yafi karfin shekarunsa, komai sai ya nuna kamar ma ya fika iyawa kuma ba wai iyawar yayi ba. Komai na shi careful yake yinsa, in dai taga anyi barna to tasan Hussain ne, shi ko abinci kika bashi daga kitchen ya kawo daki to sai ya zubar a hanya. Hussain ne yayi nasarar wannan musun nasu. Dan mace ta haifa wadda aka mayar mata da sunan Hassana kuma ake ce mata Hassana ɗin. Daga ita kuma sai ta haifi Safiyya, Khadijah, Nafisa, sannan Zulaihat. Duk kusan a jejjere tayi su. Daga nan kuma sai ta dakata tukuna tace sai sun girma zata sake wani set din. Amma Allah baya barin wani dan wani yaji dadi. A shekarar da tagwayen suka gama secondary school dinsu a shekarar ne Allah yayi wa Alhaji Aminu rasuwa bayan yar gajeriyar jinya. Ya mutu ya bar mata daya da yaya bakwai. Maza biyu mata biyar. Wannan mutuwa ta taba ba wai family dinsa ba har wadanda suka sanshi da sauran abokan aikinsa kowa sai da ya koka kuma ya tausayawa iyalinsa, kasancewar su kanana babu wanda za'a ce ya rike kansa ballantana ya rike yan uwansa, ita kanta uwar ba wasu shekarun kirki ne da ita ba. Bayan anyi arba'in sai yan'uwa suka nemi su koma Gombe su zauna a cikin dangi. Hussain ya shafawa fuskarsa toka ya ce babu inda zasu je "yanzu yaran nan sai a cire su daga makarantun su kenan? So kuke yi mu koma can a fara yi mana dauki dai dai? Wannan uncle din ya dauki uku wancan ya dauki biyu wannan auntyn ta dauki daya?" Aunty Amina ta share hawayenta, dama Hussain shi take tunani, tasan shi da rigima, tasan shi zai bata problem, tace "to Hussain ya kake so muyi? Eh? Ya kake so inyi da raina? In bamu koma Gombe ba ina zamu je? Wa zai rike mu? Ni dai kasan ba zan iya ba, kasan ba aiki nake yi ba ba sana'a nake yi ba, kasan kuma ba dogon karatu nayi ba ballantana in saka ran zan samu aikin da zan rike ku dashi. Ku kuma baku kawo karfi ba tukunna, kuma mai taimaka muku kuke bukata a yanzu, kuna bukatar wanda zai shige muku gaba ku cigaba da karatun ku. Yan uwanku yaya zakuyi dasu? Duk fa primary suke Hassana ce kawai take ajin farko a secondary. Hussain dole muna bukatar taimako, ba kuma zamu samu taimakon nan anan ba sai mun koma cikin yanuwanmu". Ya mike tsaye yana girgiza kai yace "duk wanda yake bukatar taimaka mana a cikin yanuwanmu ai zai iya taimaka mana muna zaune anan. Kuma ma ai bama bukatar taimakon kowa aunty. Mu, ni da Hassan zamu rike kan mu zamu rike ku" Hassan ya mike yana kallon sa yace "ta yaya? Ta yaya zamu rike kan mu Hussain? Gaya min me muke dashi? Ko da karambani zamu rike kan namu? Ana maganar reality ne fa anan, ana maganar future din mu ne data yaran nan kannen mu" Hussain yace "in ba zaka iya ba kawai kace ba zaka iya ba ba sai kayi min dogon sharhi ba" ya wuce shi ya dawo gaban Amina. "Aunty ki yarda dani dan Allah. Wallahi zan iya" tayi ajjiyar zuciya tace "zaka iya? Ta yaya?" Ya zauna a kan kafafuwansa yace "kasuwanci zan shiga, ba da akwai kudade a hannun mu ba? da akwai wasu a bank? Ga kuma motoci har guda uku a waje? Kuma ga filayen da Abba ya siya ya ajiye? Mu siyar dasu ku bani kudin in shiga business dasu.........." Hassan ya dawo kusa da Aunty da sauri yace "hauka ma kenan. Yanzu in business din zamuyi Hussain sai mu dauki dukiya mu baka? Kai din? In ka lalata ta kuma shikenan sai mu dawo mu zuba tagumi? Gaba ake dubawa Hussain. Komai a hankali a kuma nutse ake binsa, kullum sai na gaya maka wannan amma kai baka ji" Hussain yayi masa kallo daya ya dawo da dubansa kan Aunty yace "Please Aunty, ki bani wannan damar dan Allah. Wallahi zan iya, ki rabu da Hassan. Shi yana living ne in the future ni kuma ina living now, in dama tazo wa mutum kawai yayi amfani da ita ba sai ya jira wata damar tazo sanda yayi masa dai dai ba. Yanzu ne damar mu Aunty, ki bani wannan damar dan Allah. Aunty ta jima tana kallon sa, tasan halinsa sarai, tasan karambanin sa da daukan abinda yafi karfinsa ya dora wa kansa, tasan kuma kokarin sa dan duk sanda ya fadi baya zama a kasa yayi kuka mikewa yake yi ya cigaba da tafiya. Duk abinda yake bashi wahala kuma sai yayi ta maimaita wa har sai ya iya. Ta tuna farkon sanda aka siyo musu kekuna, ana kawowa Hussain ya dauka ya hau ai kuwa ya fado ya kukkurje, amma bai hakura ba, yayi ta hawa keken nan yana faduwa har sai da ta dauke saboda tausayin sa sai babansu yace ta bar masa ai a haka ake girma. Hassan kuwa sai yayi ta studying keken nan yana gwada yadda komai nasa yake aiki har sai da ya fahimce shi sannan ya hau, shima kuma a hankali yadda ko ya fadi ba zaiji ciwo ba, kuma bai fadin ba, sai yake tukawa a hankali yadda in yaga zai fadi sai yayi sauri ya sauka, ko kuma yake bin jikin bango yana dafawa. A karshe sai ya zamanto Hussain ya riga Hassan iya keke, amma kuma duk ya ci uban keken nasa ya babballashi. Sanda Hassan ya iya nasa keken, keken Hussain ya riga ya lalace. Amma kuma akwai wani abu a dangane da Hussain tun yana yaro, yana balain, tsananin son sana'a. Duk wani abu indai ance abinda zai kawo kudi ne to Hussain ya sanshi kuma yana sonshi. Hussain har fruits din bishiyar umbrella din gidansu yake cira ya siyar wa da yaran unguwa. Hussain in yaje da abu makaranta wani yaron yace yana so yakan iya siyar masa ya kara riba sannan ya fito waje ya sai wani. Amma fa kudin in ya samu rabarwa mutane yake yi. Ta tuna wata rana da ya dawo daga school da ulu da kwarashi, ta tambaye shi inda ya samu sai yace "Nanny din mu ta makaranta na gani tana saƙa, tace min ana samun kudi sosai in akayi saƙa, shine na bata kudi ta siyomin zan ringa yin saƙar hula ina bata tana siyar min" sai da baban su ya zane shi akan sakar nan sannan ya daina. Babansu ya taba tambayar su abinda zasu zama in sun girma. Hassan yayi shiru yana tunani sannan yace "ban sani ba Abba, sai nan gaba in nayi tunani" ana tambayar Hussain sai ya washe baki yace "Dangote". Ta dawo da tunaninta kansa da har yanzu yake durkushe a gabanta yana roko, ya kamata ta bashi dama, amma ya kamata tayi tunani, saboda kamar yadda Hassan ya fada wannan future dinsu ne basu kadai ba harda yan kananan yaranta mata. Dole zata yi tunani kafin tayi taking wannan risk din kuma dole zata yi shawara. Shawara da abokin shawarar ta sarkin tunani. Hassan. Tace "shikenan Hussain ka bani lokaci inyi tunani, duk abinda na yanke kuma shine final babu jayayya" Ba haka yaso ba, amma yadda take so dole hakan za'ayi. Bayan ya fita sai ta juyo ta kalli Hassan, a take ya girgiza mata kai. Ta sauke ajjiyar zuciya tace "bana son discouraging dinsa, ka bani shawara yaya zanyi?" Ya gyara zama yana kallon carpet yace "dukiyar marayu ce aunty, ina ji masa tsoro, kinsan halin Hussain in ya kafa kasuwancin ma raba wa mutane zai tayi" Ta gyada kai cikin fahimta, ya cigaba da cewa "a shawarce ina ganin a raba, a fitar masa da kasonsa a bashi ya kafa kasuwancin dashi yadda ko sun rushe ba zai rusa mu gabaki daya ba, mu dashi zamu samu abinda zamu dogara dashi. Idan kuma ya zama successful sai a kara masa wata" Aunty taji dadin wannan shawarar, amma kuma a ranta bata son rabon gadon nan saboda tana ganin kamar raba kan ƴaƴanta ne, taso a ce komai zasuyi tare zasuyi. Amma kuma shawarar abar dubawa ce. Haka akayi, aka raba gado aka bawa Hussain nasa, sauran kuma suka ajiye suna amfani dashi gurin harkokin rayuwarsu. Hassan yayi amfani da wani kaso a cikin nasa gurin nema wa kansa makaranta. A lokacin da shekara ta zagayo Hussain ya kira su yana nuna musu lissafin abubuwan da yayi da kudin da ya samu sai su ka ga cewa kudin da yake dashi a yanzu ya ninka wanda yake dasu a waccan shekarar sau huɗu har da doriya. Suka rike baki suna mamaki, shi kuma ya gyara zama yana murmushi yace "na gaya muku ai, Dangote zan zama" Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account GT Bank Account Name : Nafisa Usman Tafida Account Number : 0139433741 Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin 08067081020 Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin 08067081020. Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only Sai na jiku.... Episode three : The Beginning 2 Free Episode Labarin, ya samo tushensa na biyu ne daga gurin wasu ma'aurata. Yusufu da Sa'adatu. Sa'adatu wadda ake kira da Sa'ade, sai kuma yara suka sake rage sunan zuwa Ade, sunan Aden kuma sai ya bita har girmanta, asalinta mutuniyar zamfara ce a garin kauran namoda, kyakykyawa ce, irin kyawun da ake kwatance dashi a unguwarsu. Baka ce doguwa, kusan komai nata dogo ne sannan tana da sanyin hali da nutsuwa sosai. Kuma nutsuwar ta ta kara karfi ne saboda ta kasance mahaddaciyar Alqur'ani ce ita. Babanta malami ne, mai tarin almajirai da suka zo saga garuriwa daban daban kuma suke daukan karatu a karkashin sa. Ita ma a gurin sa tayi karatun ta, ta sauke tayi tilawa sannan tayi hadda. Tsakanin son da take yiwa Alqur'ani ya saka takan zauna tayi ta rubuta ayoyi a jikin allo, hakan yasa ta kware sosai gurin rubutu yadda ko shi mahaifinta malam shehu ya sara mata a gurin iya rubutu, dan haka kusan duk rubutun da aka aiko masa dashi ita yake bawa tayi masa. Bata yi karatun boko ba, sai dai tana yin rubutu sosai da ajami. Yusufa almajirin malam shehu ne, mutumin garin Zaria ne. Tun zuwansa gidan zuciyarsa take son Ade dan haka ya ringa siyan ta da magana mai dadi da yabo da kyautatawa har ya samu nasarar kafa soyayyar sa a zuciyarta. Suka fara soyayyar su mai tsafta a boye dan gudun bacin ran Malam Shehu. A haka har ya kammala karatun sa ya koma Zaria, daga nan kuma sai yake aiko mata da wasika a boye itama tana bashi amsa, wani lokacin kuma sai ya shirya ya tafi kauran Namoda yace yazo gaishe da Malam amma a badini ganin Sa'adatu yazo. Kwanci tashi har Sa'adatu ta isa aure, a lokacin ne Malam Shehu ya zabi wani babban malami anan garin faskarin jihar Katsina da niyyar ya hada su aure da Sa'adatu amma sai Sa'adatu ta nuna bata son shi, aka tambaye ta wanda take so sai tace Yusufa. Malam shehu yasan Yusufa yasan halayensa,ya kuma san iyayensa da danginsa, kuma a iyakacin saninsa shine basu da wani aibu da zai hana a basu aure sai dai yana jiye wa yarsa zaman talauci, dan matalauta ne danginsu sai dai Malam yasan cewa shi arziki na Allah ne dan haka ya kira Yusufa ya bashi auren Ade Yusufa ya dauke ta ya tafi da ita Zariya. Daga nan suka kara gaba zuwa Kaduna inda ya sama musu gida a unguwar hayin rigasa suka zauna shi kuma ya ke iyakacin kokarin sa gurin ciyar da ita da kyautata mata. Duk da cewa rayuwar tana yi musu wahala sosai, saboda Yusufa bashi da takamaiman aikin yi sai dai kullum in ya fita duk abinda ya samu na aikin karfi shi zaiyi yayo musu cefane ita kuma ta cancana ta sarrafa musu abinda zasu ci. Ita kuma Sa'adatu sai ta bude makarantar allo anan tsakar gidan ta inda take dorawa yaran unguwa karatun Alqur'ani, har mata ma sukan shigo ta koya musu, tana dan samun abin sadaka daga iyayen yara da kuma dan sauran abubuwan buƙata, kuma tana yin kitso shima a biya ta. Da haka take samun abin da take taimakawa maigidan ta gurin kula da iyalin su. Zama suke mai tsafta, basu da wadata amma cike suke da soyayyar juna a haka har Allah ya albarkaci Sa'adatu da samun ciki. Wata tara ta haifa musu tagwayen yammata masu tsananin kama da junansu, kyawawa kamar ita. Aka saka musu sunaye Ruqayya da Sumayya. Tun daga jarirantaka Sa'adatu ta fahimci banbancin halayya a gurin tagwayen nata, Sumayya tana da hakuri sosai, Ruqayya kuma tana da zafin zuciya. Bayan sun fara girma sai banbancin ya sake bayyana sosai, in dai iyayen suka ji suna fada, ko kuma suka ji an kawo kara daga waje, to ba sai sun tambaya ba sun san Ruqayyah ce. Wata irin bakar zuciya ce da ita da wani irin taurin rai, bata da tsoro ko kadan kuma bata shayin yin komai ko fadar komai. Zata iya yiwa babba rashin kunya komai kuma girmansa, komai furfurarsa, hatta Inna Ade (Sa'adatu) Rukayya tana iya ta murguda mata baki tayi mata kunkuni. Babanta kawai take dan daga wa kafa shima kuma ko zai yi dukan duniyar nan ko fadan duniyar nan ba zata daga kai ta kalle shi ba ballantana ya saka ran zata bashi hakuri. Kullum Sa'adatu addu'ar ta akan Ruqayyah ne, ta dauke ta a matsayin wata jarabawa da ubangiji yake musu ita da Yusufu dan yaga yadda zasuyi tarbiyyar ta kuma ta dage sosai wajen kokarin ganin sunci wannan jarabawar. Wannan yasa duk sanda Yusufu yake dukan ta sai tayi kokarin hana shi tace "Duka baya gyara Baban biyu, addu'a zamu yi ta mata da nasiha, mu kuma saka idanuwa sosai a kanta. Allah zai gyara mana ita insha Allahu" ya kan bata amsa da cewa "tsoro nake ji Maman biyu, tsoro nake ji kar mu kasa yi mata tarbiyya a karshe duniya tayi mata" Bayan tagwayen, Sa'adatu ta haifi Suleiman, sannan kuma ta haifi Usman mai sunan Malam Shehu, wanda suke kira da Zunnoor. Sai dai fa duk wannan halayyar ta Ruqayyah to kuwa tana son iyayenta, tana kuma son yanuwanta musamman Sumayya. Ita ce babbar kawarta ita ce kuma abokiyar shawarar ta sannan ita ce abokiyar sirrinta. Wannan ya saka Sumayya ce kawai tasan sirrin Ruqayyah, ita kadai tasan dogon burin Ruqayyah na zama mai kudi a nan gaba. Ita kadai tasan frustration din Ruqayyah. She hates kasancewarta ƴar talakawa. Bayan Shekaru Goma Low-cost, Unguwar Rimi Kaduna. A wani gida, wanda yake daya daga cikin manya manyan gidajen da suke layin, za kuma a iya kiran sa da daya daga cikin kayatattun gidajen da suke jahar ta kaduna, anan gidan ne labarin ya cigaba. A compound din gidan na hango wasu tagwayen samari, masu tsananin kamanni a fuska amma masu tsananin bambanci halayya. Alhassan da Alhussain. Marayu, wadanda suka rasa mahaifiyar su a gurin haihuwar su sannan suka rasa mahaifinsu a lokacin da suke da karancin shekaru. A harabar gidan na hango samarin su biyu sun fito daga cikin gidan, sun jera suna tafiya suna hira suna dariya. Kallo daya zaka yi musu ka fahimci cewa kaunar da suke yiwa junan su mai yawa ce, shakuwar su mai karfi ce, bond din da yake tsakanin su special ne wanda babu wanda zai fahimta sai wanda aka haife shi irin haihuwar su. Tagwaye. Daya baki ne, daya fari. Bakin ne ya kalli farin yana dakatawa daga dariyar joke din da farin yayi "Hussain yanzu wai da gaske kake? Kana nufin komawar zakayi gobe? Wai yaushe ka dawo Nigeria ne ma gabaki daya? Ayyuka fa sunyi min yawa anan Hussain nasan Aunty ma in taji zaka koma ba zata barka ba" farin, wanda aka kira da Hussain yayi dariya yana bayyanar da dimple din sa guda daya tare da kyawawan jerarrun hakoransa. His eyes twinkling. Daga gani zaka fahimci shi mutum ne mai yawan fara'a, mai yawan murmushi, irin mutanen nan da murmushi baya barin fuskarsu no matter how much they try. "Ta yaya Aunty zata san zan koma? Ni dai bazan gaya mata ba sai dai in naje can mayi waya, kai ma kuma ai nasan ba zaka gaya mata ba ko Hassan?" Ya karasa maganar cikin shigar lallashi, wanda aka kira da Hassan ya dauke kansa tare da ture hannun Hussain daga kafadarsa daya dafa yace "aikin ka kenan ai, in anyi maka Magana ka kalallame mutum da dadin baki" sai kuma ya juyo yana kallonsa tare da jingina bayansa da jikin motar da suka zo gabanta yace "ka dai bi a hankali Hussain ina gaya maka, you are too open, ga ka da seeking attention, kudin da kake samu suna da yawa and you are showing it to the world. Ni ina jiye maka halin mutane" Hussain ya jingina shima a kusa da Hassan yace "mutane rahama ne Hassan" "eh mutane rahama ne idan da ace nagari ne zasu biyo ka, yanzu mutane nagari wahala suke yi. Mutum ake kiwo yanzu a duniya ba wai dabba ba" Hussain ya daga kafada tare da juyawa yana kallon motar da suke jiki cikin kokarin chanja topic ya yamutsa fuska yace "phew! What a mess! Wannan motar wai dama haka ta tsufa? Ji duk tail lights dinta sunyi scratches? Amma a hakan kake cewa in tafi da ita Kano?" Hassan ya juyo yana kallon motar shima yace "wannan motar ce ta tsufa? Da yaushe ka siye ta?" Hussain ya dan sosa kanshi kadan yana kankance ido alamar tunani sannan yace "it doesn't matter. Ni ba zanje da wannan motar gurin gimbiya ta ba" ya fadi kalmar gimbiyar dramatically, har yana bowing kansa kamar mai gaisuwa, wannan ya saka Hassan dariya, yana girgiza kai yace "kar Allah yasa kaje da ita din, mai gimbiya, in kayi wasa sai inyi maka addu'a Allah yasa mai martaba ya fasa ba ka auren ta inga ta tsiya" Hussain ya zaro ido waje "what! Amma da kafi kowa ƙina a duniya" Hassan ya zagaya side din driver yayin da Hussain ya jefa masa key ya cafe yace "common, get in, muje in nuna maka warehouse din dan in ka tafi bansan ranar dawowar ka ba". Sai da Hussain ya gyara zaman hularsa sannan ya bude motar ya shiga kusa da danuwansa, mai gadi ya bude musu gate suka fita, Hussain ya juya yana kallon gate din bayan an rufe shi sannan yayi tsaki yace "gate din nan so nake a zo a cire shi a saka wani" Hassan ya bude baki yana kallonsa shi kuma ya dauke kai gefe yana murmushi, Hassan yace "saboda me? If I may ask your highness?" Yace" saboda baiyi kama da gate din gidan dangoten Kaduna ba" Gabadaya suka yi dariya. Hassan yace "oh sunan da ka rada wa kanka kenan? To Allah ya taimaka" Hussain ya daga kafada yace "to me yayi saura? Menene maraba ta da shi? Wannan fa companyn da zan bude wata mai kamawa will be my third. Kuma, it is just the beginning of *H & H group of companies* " Hassan ya saka hannu daya ya ture masa hular kansa yace "Allahu ka shirya min wannan kanin nawa". Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account GT Bank Account Name : Nafisa Usman Tafida Account Number : 0139433741 Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin 08067081020 Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin 08067081020. Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only Cigiya! Ina cigiyar wasu bayin Allah su biyu da suka turo kudinsu tun jiya har yanzu basu yi magana ba. Episode Four: Gimbiya Fatima Hayin Rigasa, Kaduna state Yammata biyu na gani suna shigowa cikin gidan su wanda katangar sa ta kasa ta zube dan haka aka zagaye shi da tsohon langa langa, sai dakuna guda biyu a tsakiyar gidan suma dakunan na kasa ne amma anyi musu plaster da siminti, a gefe akwai bandaki shima rabinsa na langa langa ne kuma babu rufi, tsakar gidan gabaki dayansa kasa ne da bishiya a gefe a kasanta akwai murhu da tukwane da sauran kayayyakin da suke nuna anan ake girki, sai kofar dakunan da akayi yar karamar baranda, wadda simintin ta duk ya mutu yayi ramuka. A gefen barandar akwai jerin alluna da gwangwanin tauwada. Jikin yammatan sanye yake da uniform. Kansu daya, kamannin su daya, yanayin su daya dan sai ka kalla sosai, ko kuma wanda ya riga ya sansu sannan ake iya gane banbancinsu. Dariya suke yi suma, karar dariyar su ta hade da karar kofar gidan da suka bude, wanda ko soro babu, hannayensu sarkafe dana juna suna tafiya ƙafafuwan su suna hardewa cikin na juna. "Ruqayyah baki da kirki wallahi, hahhaha, kinga yadda kika ruda shi kuwa ya kasa gane ina ne kofar fita daga ajin?" Wadda aka kira da Ruqayyah ta rike ciki tana dariya, sannan tace "kinga ai gobe ma ya kuma dan kaniyar sa....., Ko waye ya gaya masa ni sa'ar sa ce? Harda wani "wallahi Rukee da gaske nake sonki nake yi, ni ban taba kula ko wacce mace ba sai ke" ta karashe maganar cikin kwaikwayon muryar maza. Suka sake kwashewa da dariya, dayar tace "baki da tausayi wallahi, kika sani ko da gasken yake?" Ruqayyah tace "to ke Sumayya, wadda aka haifo da layar tausayi a wuyanta ba sai kije ki ce kina sonsa ba? Ai ba lallai ne ya gane bani bace ba. Ni wannan me zanyi dashi? Me na sama yaci ballantana ya bawa na kasa?" Sumayya ta tura baki tace "ai ba ce miki nayi ina sonsa ba, ni cika min hannu ke da ba'a fada miki gaskiya" Ruqayyah ta warce hannunta tare da hankada Sumayya gaba "in kina son Allah da annabin sa, daga yau kar ki kara gayamin gaskiya". A lokacin mamansu ta fito daga daki, doguwar macece kyakykyawa, baka, daga ganinta kasan anyi kyakykyawa a zamanin yarintarta. Amma a yanzu fatarta duk ta yamushe tamkar tafi shekarun ta, bakinta a bushe, hannayenta rudu rudu da jijiyoyi. Gefen rigarta a yage. Ta tsaya da labule a hannunta tana kallonsu tace "to sarakan rigima, ku dai kamar masu ganin hanjin juna ba kwa minti biyar tare sai kun yi fada. Me ya faru kuma?" Ruqayyah tazo ta wuce ta kusa da ita tana kunkuni ta shige dakin da yake kusa da inda maman nasu ta fito, Sumayya ta karaso gabanta tace "Inna Ade barka da gida. Mun dawo. Akwai abinci?" Inna Ade tayi ajjiyar zuciya, haka suke tunda ta haife su, sunfi shiri da junansu akan kowa kuma sunfi fada da junansu akan kowa, sannan ko wanene kai baka isa kaji sirrinsu ba. Ta amsa gaisuwar Sumayya Sannan ta nuna mata kwano a gefe wanda tun daga wajensa zaka ga ya farfashe, murfinsa daban. Sumayya ta dauka ta shiga dakin da Ruqayyah ta shiga. "Rukee ga abincin mu. Za muci yanzu ko sai munyi sallah?" Ruqayyah ta ajiye hijab din da take ninkewa a gefen yamusashshiyar katifar su, ta bude kwanon abincin sannan ta saki murfin ya fadi a kan sumuntin dakin tace "again! Yau ma shinkafa da mai da yaji? Yau ko waken babu?" Ta karashe maganar kamar zata yi kuka. Sumayya takaraso tana kallon abincin sannan ta tabe baki tace "ni yunwa nake ji, damuwata shine ba lallai abincin ya ishe mu ba" Ruqayyah ta cigaba da cire uniform dinta tace "ki haɗa da nawa ki cinye duka, ni ba zanci wannan abincin ba, ni na gaji da cin irin wadannan abincin. Ni na gaji da talauci, ni so nake muyi kudi, na gaji da gidan nan, na gaji da kayan da muke sakawa na gaji da inda muke kwanciya. Na gaji da rayuwa" ta saka kafa tana haurin katifar tasu, sannan ta zauna dabas a gefe ta hade kai da gwuiwa. Sumayya ta bita da kallo da sakakken baki, sannan ta zauna a gefenta ta jawo kwanon ta juya abincin ta fara ci sannan tace "kinga, kin san dai in baki ci abincin nan ba babu abinda zaki ci ko? Kinsan tabbas da daddare tuwo za'a yi kuma nasan shima cewa zaki yi ba zaki ci ba, ƙin cin fara da mai ba zai saka gasassun kaji suyi fiffike su zo gabanki ba ko?" Jin bata ce komai ba ya saka ta kara cewa "In baki ci abinci ba kuma kinsan ba zaki samu karfin zuwa makaranta kiyi exams gobe ba" Hakan yasa Ruqayyah ta miki hannu a hankali ta saka a cikin kwanon abincin, sannan ta debi loma ta saka a baki tana taunawa kamar mai cin kashi. Babu abinda bata so irin abinda zai kawo mata cikas a cikin ssce exams din da suke yi a yanzu, dan tana ganin zuwa makaranta shine kadai hanyarta na cikar burinta, burinta na zama mai kudi. ******************************** A bangaren samarin, bayan sunje warehouse din da suka tafi, sun gama duk abubuwan da zasu yi sun dauko hanyar dawowa sai suka biya ta gurin da ake ginin sabon companyn da za'a bude musamman saboda sarrafa rake a mayar dashi zuwa sukari. Wannan shine Company na uku da Hussain zai bude a cikin shekaru biyar da bude companyn sa na farko. Bayan sun gama sun shiga mota ne yace "bayan wannan kuma sai na fulawa ne zai biyo baya. Shine abinda zai kaini Beijing gobe saboda injinan da nake son siyowa na harkar noma da gyaran alkama har zuwa na sarrafa ta zuwa fulawa duk anyo su sabon design, munyi magana dasu sun turo min hotunan su na gani shine nake so in je ayi launching dinsu a gaba na, injinan suna zuwa *H & H Flour Mills* zai tashi. Kasan Sawun dangote nake takawa" ya karasa cikin sigar tsokana, Hassan ya dauke kansa gefe yana driving dinsa hankali a kwance, amma idanunsa sun nuna cewa tunani yake da yawa a zuciyar sa, ba tare da Hussain ya lura ba ya dauko wata magazine yana bubbudewa da sauri sauri har yazo inda yake so sannan ya nuno wa Hassan "there! Ya kaga wannan babyn?" Hassan yayi wa motar da take cikin page din magazine din kallo daya ya dauke kai gefe yace "ita ce sabuwar da za'a chanza?" Hussain ya ajiye magazine din yace "noooo, ni da akwai wadda nake jira, har yanzu basu sake ta ba, wannan Gimbiya ta nake so inyi wa kyautar ta ranar birthday dinta" Hassan yayi saurin jefa masa wani kallo yace "kyauta? Hussain me yake damunka ne? Anya kuwa ka duba kudin motar nan?" Hussain yayi dariya yace "na gani mana mr tsimilmila. Fatima fa zan bawa, wannan ba komai bane ba indai a kanta ne" Hassan ya girgiza kansa yace "Hussain. Naga alamar yarinyar nan ta kwace min gurina tun kafin ta shigo a zuciyar ka. Ina jin in akayi auren nan in ina son ganin ka sai na sayi form a gurin ta na cike" Hussain ya sake dariya yana kara kwanciya a kan kujerar sa, ya lumshe ido sannan yace "ba a haife ta ba ba kuma za'a haife ta ba. Yarinyar da zata raba ni da kai bata zo duniya ba ba kuma zata zo ba." Hassan yace "kana raina power ta mata Hussain. Shaidan da kansa ya ce yana tsoron kaidin mata ballantana mu da bamu san ma me duniyar take ciki ba. Mace tana iya raba tsakanin uwa da danta, ko tsakanin uba da yayansa, ballantana mu da muke brothers" Hussain yana taping hannunsa a kan cinyarsa yace "yanzu so kake in rabu da ita kenan?" Hassan yace "no, ba haka nake nufi ba, just be careful, be very careful akan mata" Hussain yayi murmushi yace "mr be careful. I am being careful ai, I have always been. Yarinyar nan fa shekarun mu uku, almost hudu tare da ita, duk wani abu nata daya kamata in sani na riga na sani, wanda ban sani ba kuma in an yi bikin mun shiga daga ciki zan sani" ya karashe maganar da dariya a muryar sa, Hassan ya bata rai yace "kasan problem dinka? Babban problem dinka a rayuwa shine komai a gurin ka abin wasa ne, komai a gurin ka is not serious, ita kuma rayiwa ba haka take ba" Hussain ya dago kai yana kallon sa yace "ka san wani abu Hassan? Ita rayuwa nan guda daya ce, shi ran nan nan guda daya ne. In ya kare babu refilling. So ko dai kayi enjoying rayuwarka kafin ta tafi ta barka ko kuma kayi spending your entire life being careful ba tare daka mori all the goodies of the life ba, sai kawai rana daya kaga time ya kare maka a lokacin da kake tsakiya da tsara abubuwan da zaka yi nan gaba. What we have is today, what we are sure of is now, ba ayi mana alkawarin gobe ba. Zata iya kasancewa ina bude kofar motar nan zan fita mota tazo tabi ta kaina in mutu and that will be the end of me, babu abinda zai rage nawa sai memories na abinda na aikata, abinda na aikata ba wai abinda na zauna ina ta tunani ina planning cewa zan aikata sati mai zuwa ko wata mai zuwa ko kuma shekara mai xuwa ba. Bani da tabbas din zan kai wannan lokacin. Kuma ba zan iya chanza komai na daga kaddarar rayuwata ba so why worry? In na tafi bayan aiyukana da zanje in tarar a can abinda zan bari a duniya bayan memory na a zuciyoyin masoyana sai kuma sunana. And that's what am working on. Ina so in kafa H &H irin kafuwar da zai jima kafin sunansa ya goge a garin nan, ina so kuma inyi aure, auren nan daga zuriya mai karfi irin zuriyar masarautar kano, in hada jini dasu in samu yaya yadda zan bar bayana. Wannan shine burina, wannan kawai shine burina" Hassan yayi packing motar a compound din gidan su sannan ya juyo yana kallon Hussain yace "nima duk ina da wadannan burikan Hussain, musamman burin aure da samun zuri'a kafin barin duniya, amma ni ban damu da familyn da zan hada zuri'a da su ba, ni dai fatana kawai shine in samu mace ta gari, mai kyawawan halayya, mai addini, wacce duniya sam bata gabanta balle abinda yake cikinta, reserved, wacce ba zata damu da abinda nake dashi ba balle abinda zan bata. Mai zurfin tunani, mai ilimin addini dana boko, Wacce......" Hussain ya daga hannunsa yace "in short, kafi son ka samu mace mai irin halayen ka.....boring.....to bara kaji, Gimbiya ta ma tana da duk wadannan characters din daka lissafa. But wait a second...." Ya matso da fuskar sa kusa da tashi yana kare masa kallo yace "wannan dogon lissafin da kake yi gaya min? Ta samu ne?" Hassan ya dungure masa goshi yace "tukunna dai, still searching..." Hussain yayi tagumi dramatically da hannu daya yace "still thinking about it... Planning... thinking and re planning.... Malam if you want to do something, do it now" Hassan ya fito daga motar yana cewa "sai kayi tayi yanzu din ai, gobe kuma kazo kana nadama" Hussain ya fito shima yana cewa "gwara inyi yanzun tunda bani da tabbas din zan kai gobe. In ma nayi nadamar a goben sai in sake yin wani". A palo suka tarar da Aunty da yammatan ta ana ta hira, mostly hirar jami'a da Zulaihat take shirye shiryen tafiya, Nafisa tana ta bata tsoro akan irin wahalar da ake sha ita kuma tana korafin bata son zuwa, nan suma suka shiga cikin hirar Hassan ya shiga team din tsokanar Zulaihat Hussain kuma ya jawo ta jikinsa yana lallashinta. "Kinga autar Aunty, kije kiyi semester daya, in kika ji bata yi miki ba kina dawowa ki gaya min shikenan kin daina ta, sai ki zabi duk makarantar da kike so koda kasar waje ne zan kaiki. Ita rayuwar nan mai sauki ce, babu wani takura a cikin ta". Washegari da sassafe Hussain ya tafi kano zance gurin Gimbiya. A jirgi ya tafi, dan haka cikin yan mintina ya isa kuma ya zarce direct zuwa fada ina Gimbiya Fatima ta aiko aka tarye shi aka kai shi masaukin da ake saukar baki irinsa sannan aka cika masa gabansa da kayayyakin abincin karin kumallo tunda tasan bai karya ba kuma tasan sauri yake yi dan tasan da tafiyar da zaiyi a yau. Kusan komai na Hussain Gimbiya Fatima ta sani. Sai dai a bangaren Hussain din shi ba wai abincin ne a gabansa ba duk kuwa da cewa kamshin abincin ya gama cika masa ciki ya kuma tayar masa da yunwar da take kwakular hanjinsa, amma shi abinda yake gabansa shine ganin fuskar gimbiyar tasa, dan haka ya dora idanuwansa a kofar da yasan tanan zata fito, a haka har sai da ta fito din, sai ya samu knsa da mikewa tsaye yana yarfar da hannayensa, fiskarsa dauke da madaukakin murmushi wanda ya samu tarya da makamancinsa daga fuskarta. Gimbiya Fatima diya ce a gurin maimartaba Sarkin Kano na wancan lokacin, kyakkyawa ce, mai kyakkyawan jiki wanda yaji komaida ake bukata a jikin mace. Hutu, gata, ilimi, mulki sun gama ratsa duk wata gaba ta jikinta. Kallo daya zaka yi mata zaka fahimci cewa yar sarauta ce ba wai sai an gaya maka ba kamar yadda magana day azata fada maka zaka fahimci cewa mai ilimi ce ita ba sai anyi maka bayani ba. Hanklain ta da nutsuwarta ya saka babanta yayi burin had ta aure da wani sarkin ko kuma wani dan sarkin dan ya karfafa karfin masarautar sa amma Fatima already idanuwanta suna kan Hussain. Dole mahaifinta ya bawa Hussain dama, tare kuma da fatan cewa ba zai bashi kunya ba. Sun hadu ne a airport, Hussain ya dawo daga daya daga cikin tafiye tafiyen sa ita kuma zata kaiwa yaruwarta da take aure a Egypt ziyara. Yana cikin waya da Hassan bai gani ba suka yi karo, wayarsa ta fadi ita kuma jakar hannunta ta fadi tarkace ciki suka zube kasancewar jakar ba'a rufe take ba. Da sauri ya sunkuya ya tattaro mata kayayyakin ta ya zuba mata a jakar shima ya dauki wayarsa,a ransa yana saka rn zata sunkuyo su debe tare tunda ba laifinsa bane shi kaɗai, amma bata yi haka ba. Sai da ya gama ya mike zai mika mata sannan ya kalli fuskarta kuma a lokaci daya yasan cewa she is the one. Kuma kallo daya yayi mata yasan cewa ba zata kula shi ba, ko sunan ta ba zata gaya mishi ba ballantana phone number dan haka sai yayi dabara ya dauke wayarta ita kuma ya saka mata tasaa cikin jakarta. Ya mika mata tare da cewa "am sorry" sai data jima kafin ta motsa bakinta tace "it's okay" sannan without a second look ta juya tayi tafiyar ta. Shi kam zuciyarsa fal murna ya fito daga airport din, sai daya fito sannan ya tuna cewa bai gaya wa abokin sa da yazo kano gurinsa cewa gashi nan yazo ba kuma gashi yayi musayar wayarsa, a dolensa ya nemi taxi. Tunda ya koma kaduna yake kiran layin wayarsa amma shiru, sai tunani yazo masa cewa maybe kasar ta bari dan haka babu network. Option daya da yake dashi shine ya jira a kira ta ko kuma ita tayi amfani da wani layin ta kira layinta, amma shima shiru. Gashi kuma wayar tata da pin ballantana ya bude shi yayi kira da number dinta. Kwana biyu kullum yana zaune da waya a hannunsa yana kallon hoton ta dake kan screen din yawar har sai daya haddace duk wani angle da wani hill da wani valley na fuskarta. Sai da yaga yana neman zautuwa sannan ya yi dabarar cire sim card dinta daga wayar ya saka a wata wayar ya nemo contacts dinta, a ciki ya ga "kid sis" sai ya kira, a nan ya samu bayanin cewa tana sauka a Egypt ta kira waya gida ta sanar cewa tayi loosing phone dinta dan haka kar wanda ya neme ta. A gurin sister din nata, da yake mai surutu ce ya samu duk bayanan da yake bukata kuma ita tayi guiding dinsa har zuwa sanda Fatima ta dawo kasar sannan ta hada su. Shi kuma yayi amfani da duk kanin carm dinsa da duk dadin kalaman sa da kuma good looks dinsa ya sayi zuciyar Fatima Zahra. Bai kuma taba gaya mata komai dangane da dukiyar da yake da ita ba har sai data riga ta karbi soyayyar sa, daya gaya mata kuma bata nuna cewa it matters ba, sai dai tana iyakacin kokarin ta gurin supporting dinsa da kara masa kwarin guiwa da bashi shawarwari akan business dinsa. Matsalar ta daya shine Hassan, tun ranar farko da Hussain yazo dashi gidan ta fahimci cewa Hassan baya son ta kuma bata san dalili ba, amma abinda ta sani shine she is never going to change herself saboda shi, zata yi kokarin kyautata masa, a hankali maybe zai so ta din. Sannan kuma bata taba yi wa Hussain complain ba akan hakan. Kuma a hankali din ta fara ganin Hassan yana saukowa, har in suna waya da Hussain ya kan karba su gaisa. Sai ta fahimci cewa ba wai sonta ne baya yi ba, shi mutum ne mai studying abu first kafin ya karbe shi. Shi mutum ne wanda yake very careful before making choices dinsa. A lokacin tana level one, a yanzu kuma ta kammala karatunta, dan haka bayan ta zabe shi a matsayin wanda zata aura sai aka bashi damar fitowa kuma ya fito din, sannan aka saka musu rana. Kafafunsa ya samu da takawa zuwa inda take a tsaye ta ci kwalliya da lace dinkin bubu, tayi daurin dankwalin ta da ya zauna das a saman cikakkiyar sumar kanta. Wuyanta, kunnen ta da hannayen ta sanye da gold da yake haskawa tamkar yadda murmushin kan fuskarta yake haskawa. Yammata biyu ne a bayanta wadanda suka rako ta, suka durkusa suna gaishe da Hussain, ya amsa musu da murmushi amma ba tare daya dauke idonsa daga kan gimbiyar sa ba. Sai da suka yi musu sallama suka tafi sannan cikin sassanyar muryarta tace "welcome, Mi Amour" bai amsa ba, tace "kayi kyau sosai" ya cire hularsa ya shafa gashin kansa sannan ya mayar da hular yace "kyau, in kina guri Fatima har ana iya ambatar wata kalma wai ita kyau?" Ta wuce shi tana bade shi da kamshinta ta zauna a edge din 3 sitter, ya zagayo shima ya zauna a dayan edge din sannan ta gaishe shi ya amsa ba tare da ya dauke idonsa daga kanta ba. Tace "to ka gama kallon nawa in tashi in zuba maka abinci?" Ya sake shafa kai yana murmushi, ba ya gajiya da kallonta, in dai tana guri to idonsa baya ganin komai sai fuskarta, duk sauran abubuwan da suke gurin suna yi masa duhu ne. Ta tashi ta jawo table gabansa sannan ta dauko dan madaidaicin bowl ta bude wani food warmer ta zubo masa farfesun naman ragon da tayi masa ta ajiye akan table din sannan tace "kaci wannan da duminsa zaka ji dadinsa" sai kuma ta bude wani ta zuba masa wainar shinkafa ta ajiye kusa da naman sannan ta jawo wani madaidaicin tray da akayi wrapping da foil paper ta bude wani lafiyayyen potato pritata da yaji naman kaji da vegetables ta ajiye masa shima tare da jera masa knife da fork sannan da dauko mug tace "tea ko coffee?" Ya saki baki yana kallonta yace "duk wannan wai a ciki na zan saka su?" Ta langwabe kai tace "eh mana, in dai ba so kake duk wahalar dana tashi nasha a kitchen tun assuba ta tashi a abanza ba" ya ce "wai Fatima kina nufin ke kika yi wannan girkin da kanki" tace "to wa zan bawa tayi wa mijina abinci? Tea ko coffee?" ya jawo bowl din naman ya debi romon yayi tasting sannan yace "coffee please" ta hada masa tazo ta durkusa ta mika masa sannan ta koma gurin ta ta zauna tana kallonsa yana cin naman kamar zai hada har da hannunsa, ya juyo suka hada ido sai suka yi dariya a tare, yace "lallai sai nayi wa Hassan takeaway din naman nan, kin san shi kure ne" tayi murmushi tace "kace masa ya sha kurumin sa, duk sanda na shigo gidan sai yaci nama har ya ture" ya ajiye bowl din yana kallonta a ransa yana jin tamkar ya jawo watanni hudun da suke gabansu yace "Fatima, wallahi kinyi a rayuwa" Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account GT Bank Account Name : Nafisa Usman Tafida Account Number : 0139433741 Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin 08067081020 Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin 08067081020. Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only Episode Five : Adam A bakin kofar makarantar jeka ka dawo ta gwamnati ta yammata, tagwayen ne a tsaye suna jiran abin hawa. "Kinga Sumayya, na gaya miki fa babu me napep din da zai dauke mu tun daga nan zuwa gida a naira hamsin, ai ba baban mu ne ya saya masa ba" Sumayya tace "kai Rukee, shekarar mu nawa muna tafiya gida daga nan a naira hamsin ɗin? Kullum ba goyo muke yi mu basu hamsin ɗin ba?" Ruqayyah ta fara tafiya tana barin bakin gate din tana cewa "a da kenan. Yanzu ƙatin ƙatin da mu zamu yi goyo? Ni wallahi na gaji ba zan iya da wannan abin kunyar ba, yanzu ni ina labor prefect kawai sai yara su ganni ina goyo a napep? Ke kina ganin hakan dai dai ne?" Sumayya tana bin ta a baya tace "to labor prefect, sai ki gaya mana yaya zamu yi? Hamsin din ce zata haifi wata hamsin ɗin ko kuma mune zamuyi aman wata hamsin ɗin" Ruqayyah ta ja hannuta suka yi sauri suka shige gaban wata taxi data tsaya a gaban makarantar da niyyar daukan dalibai. Wasu daliban duk suka shiga baya. Sai da mai motar ya tayar ya fara tafiya sannan sumayya ta rada wa Ruqayyah "kudin mu fa ba zai kai ba, gwara mu gaya masa tun kafin muyi nisa in yaso ya karo wasu mu zauna tare, ko a cinyoyin mu mu dora su" Ruqayyah ta ture ta tana gyara zamanta tace "sai dai a dora miki a cinyarki ba dai a tawa cinyar ba. Bari kiji in gaya miki, hamsin din ma ni bani da niyyar bayarwa ajiye wa zanyi gobe in an bamu kudin motar sai mu hada da shi dan ya ishe mu" Sumayya tace "to shi wannan ta yaya zamu sallame shi?" Ruqayyah ta kalli driver din ta gefen ido sannan ta tabe baki tace da Sumayya "look at him, ba bahaushe bane ba. Dan haka duk baya jin abinda muke cewa. Muna zuwa gida sai mu nuna masa kamar mun yar da kudin a hanya bamu ganshi ba, sai mu bashi hakuri" Sumayya ta leka ta bayan Ruqayyah ta kalli driver din. Saurayi ne daga ganin sa bai dade da gama secondary ba, that's in yayi secondary din, kana ganin sa kasan ba bahaushe bane ba amma Sumayya ba zata iya tantance wanne yaren bane ba. Kuma a fuskarsa babu alamar cewa yana jin abinda suke cewa. Fari ne tas kuma jikinsa fes yake babu alamar wahalar duniya a tattare dashi dan haka daga gani kasan asarar naira dari ba zata dame shi sosai ba amma kuma a ranta tasan naira darin nan still hakkin sa ce, ta tuna da jerin waazin da Inna Ade take yi musu kullum akan cin haram, cin zali, daukan alhakin mutane, ballantana wannan bayan cin haram din ma kuma akwai karya, gaskiya zunubin yayi mata yawa. Ta dawo da dubanta kan Ruqayyah tace "Rukee babu kyau fa, kinsan babu kyau" ta harare ta "to shehiya malama Sumayya. Sai ki zaba, ko dai ki karyata ni ki tona min asiri ni yaruwarki kuma har abada ba zan manta ba ko kuma ki yi shiru kici zalin inyamurin da ba kara ganin sa zaki yi ba a rayuwarki. Ai ina sane muka shigo motarsa, sai dana kalle shi sosai na zabe shi sannan muka shigo" Sumayya tace "to yanzu in ma mun gaya masa haka, what if yaki yarda yace sai mun biya shi kudinsa? Idan ya fara yi mana hayaniya fa a unguwa ya zamuyi dashi?" Ruqayyah tayi murmushi tace "da zarar naga ya fara kokarin daga murya zan zunduma ihu ince ya rike ni yana tattaba ni" ta kare maganar da murmushin mugunta a fuskarta. Sumayya ta sunkuyar da kanta kasa tana kallon hannayen su da suke cikin na juna ita da Ruqayyah. Tasan Ruqayyah kusan fiye da Inna Ade data haife su, tasan kuma zata iya aikata abinda tace ɗin, but it is not right, in ta biye mata ita ma ta zama irinta kenan kuma kamar ta kara encouraging dinta kenan. A hankali ta zare hannunta daga cikin na Ruqayyah ta juya tana kallon titi. Luckily sai da duk aka sauke sauran passengers din sannan aka zo bakin layin su Rukee. Suka nuna masa inda zai tsaya ya tsaya sannan ya juyo sosai yana kallonsu yace "your money please, 100 for the both of you" Ruqayyah tayi pretending as if tana nemo kudi a jikinta, sai kuma ta hau duba jakarta tana da bincike, in ka kalli fuskarta zaka iya rantsewa da Allah cewa da gaske neman kudin take yi, sannan ta dago kai tana kallonsa da budaddun idanunta da suke nuna alamar tsoro tace "I can't find it. I can't find the money." Ta sake shashshafa aljihunta sannan tace "I swear I put it inside my pocket. I must have lost it at school" ta langwabe kai "we are sorry sir. Please dash us the money". Sai ya dauke kansa gefe yace "check again. Maybe you hid it somewhere" sumayya ta juyo tana kallonta tace "Rukee ki bashi hamsin din, sai mu roke shi yayi hakuri in yaki yin hakurin sai inje gida in karbo masa a gurin Inna Ade" Ruqayyah ta harare ta tace "chafdi, wallahi ba za'a bashi din ba, so kike Inna Ade ta saka mu a gaba da nasiha" Sai ta juya gurin drivern da fuskar tausayi tana ta shashshafa pockets dinta "I can't find it. It must have been stolen at school" ya juyo yana kallonta sannan ya kawo hannu kamar zai taba ta yace "let me help you check. Da azama ta rike hannun daya miko, idanuwa a waje, sai ya kawo daya hannun, Sumayya tayi saurin rike shi shima. Abin duk ya faru ne in seconds. A take kuma Ruqayyah ta bude baki da niyyar zunduma ihu, sai Sumayya ta saka hannu ta rufe bakin tana girgiza mata kai sannan ta juya tana kallon driver din tace "please, please sir, we are sorry, let me go and get you the money" Sai ya zare hannayensa daga nasu yana kallon Ruqayyah yace "ki bata hamsin din jikin ki sai ta karbo wata hamsin din ta kara akai" sai tsoron fuskarsu ya juye zuwa mamaki. Ya daga kafada yace "I might not be hausa, but ina jin hausa kamar jakin kano, dan haka you picked the wrong target" ya bude musu kofar motar yace "get out of my car. Da nayi niyyar ganin karshen drama dinki, but naji tausayin twin sister dinki dan naga kamar ita ta gari ce" a salube Sumayya ta fito daga motar, Ruqayyah kuma ta fito tana kumbura baki sannan ta juya tana kallon sa ta rike kugu tace "aikin banza aikin wofi, dan kana jin hausa kuma sai me? Dan kaji abinda muka ce sai me? Naira darinka din banza, drivern taxi kawai" Sumayya ta sunkuyo ta window tace "dan girman Allah kayi hakuri. Ni ka tsaya ma dan Allah in karbo maka kudinka a cikin gida, ta boye hamsin din kuma nasan ba bani zata yi ba" ya juya hannun sa yace "ki barshi kawai. Na bar miki, ita ma na bar mata hamsin din tayi arziki da ita. Sannan ki fada a gida a kara muku kudin mota in ba haka ba wata rana zaku samu wanda zai daki kudinsa. Sannan ki saka ido akan twin sister dinki, bata da kirki" ta gyada kanta da sauri yayinda Ruqayyah take neman irin zagin da zata yi masa, da sauri sumayya tace "dan Allah kar ka kulata" ya kalli Ruqayyah yana tayar da motarsa yace "I will not, am not her mate" daga nan yayi tafiyar sa. Ruqayyah ce ta fara shiga gidan su a fusace kamar zata tashi sama. Inna Ade tana gaban murhu tana zubawa yan samarinta abinci wadanda suma dawowarsu kenan daga tasu makarantar. Duk da cewa daga Ade har Yusufa basuyi karatun boko ba hakan bai hana su saka nasu yayanba, amma sai sun tabbatar cewa sunyi sauka kuma sunyi hadda. Hatta karamin su zunnur yayi hadda, duk iskancin Ruqayyah babu ayar da zaka bude mata ba tare da ta karanta maka ba. Bayan Alqur'ani kuma sun san sauran littattafan addini. Bata ko kalli inda suke ba ta wuce su da sauri tayi hanyar dakinsu. Suleiman yace "kububuwa! yau kuma wanne mai tsautsayin ne yayi wasa da jelar damisa?" Zunnur ya kwashe da dariya. Inna Ade tace "Allah yasa ta jiyo ku, in ta kama ku tana jibga babu wanda zan ceta" Sumayya ta shigo da sallama, ta zarce kan baranda ta ajiye jakarta da robar abincin su sannan ta dawo inda suke ta gaishe da Inna Ade, Suleiman yace "wa ya taba Rukee ne yau" Sumayya tace "ina ruwanka? Bana son tsegumi" daga nan babu wanda ya kuma tambayarta dan sun san babu wanda zai samu amsa, sai dai ita kanta bata iya bin Ruqayyah zuwa daki ba sai tayi sallar ta anan sannan ta debi ruwa ta fara wanke musu uniform dinsu wanda zunnur ta aika ya dauko na Ruqayyah, sai data gama sannan ta daukar musu abincin su ta shigar musu dashi daki, tasan dai zuwa lokacin Ruqayyah ta sauko, dama ita saurin hawa ne da ita da kuma saurin sauka. Ta tarar da ita a kwance tana karanta littafinta na makaranta. Ta zauna ta bude shinkafa da miyar da akayi har da yankakken salak a sama. Rukayya ta mike zaune tare da karbar chokali a hannun sumayya suka fara ci babu wanda yayi magana, sai da suka kusa gamawa sannan Ruqayyah tace a hankali "duk laifin Baba ne" Sumayya ta dago kai cikin rashin fahimta tace "laifin baba kuma? Menene laifin nasa? Shinkafar ko miyar ko kuma salak din?" Ruqayyah tace "talauci. Talaucin da muke ciki. Shine ai yake da alhakin kula damu, shi yake da alhakin nema mana abinda duk muke bukata a rayuwa amma kuma ya gaza, ya gaza sauke abinda yake dole ballantana abinda yake ganin ba dole bane ba" sumayya tace "kina da hankali kuwa Ruqayyah? Kin manta Allah? Ina karatun ki ya tafi? Shin arziki da rashinsa ba duk na Allah bane ba" Ruqayyah ta ajiye spoon din hannunta tace "Allah ba zai taba taimakon wanda ba ya taimakon kansa ba. Allah ba zai taba baka abu in baka tashi ka nema ba" Sumayya tace "amma kuwa in zaki yiwa Baba adalci ke kanki kinsan yana neman ai. Kinga yadda hannun Baba yake kuwa? Kanta ce fa a hannunsa saboda tsabar leburancin da yake yi. Shine aikin labura shine gini, har dako fa baba yi yake yi, kuma duk dan mu yake yi dan muci abinci muyi suttura muje makaranta. Tunda muke bamu taba kwana da yunwa ba, shin ba zamu gode Allah ba? Shinkafa muke ci da rana, gidajen masu hali irin na Baba nawa ne suke samun shinkafa a sati? Jiya fa ina jin Inna ade taji kina complain kin gaji da cin mai da yaji shine fa ta karbo wankau tayi na tabbatar kudin da aka bata shine ta siyo kayan miya da salak din nan tayi mana. Kuma duk dan kar muga gazawar sune a matsayin su na iyayen mu. Kar ki zama butulu mana" Duk maganar da Sumayya tayi abinda Ruqayyah taji kawai shine kalmar butulu, "nice butulun ko? Ni zaki kira da butulu ko? To ki jira, in dai nice muna nan dake zaki ga nayi kudi. Gabaki daya gidan nan sai na saka an rushe shi anyi mana sabo, an zuba mana kayan alatu irin na gidajen masu kudi. Inna Ade sai ta manta da cewa ta taba yin wani abu wai shi wankau ballantana har a goranta min a saboda shi" Sumayya tace "oh oh, Inna Aden ce zata yi miki gori? Kenan biyanta kike nufin zakiyi na hidimar da tayi dake? Duk kudin da zakiyi Ruqayyah kin isa ki biya iyayenki wahalar da suka sha a kanki? Ballantana ma baki da tabbas din zaki yi kudin" Nan take rigima ta kuma kachamewa. Inna Ade ta shigo ta tsaya tana kallonsu. "Ya ilahi, yaran nan ko hanjin junan su suke gani ne ni ban sani ba? Ba yanzu kuka gama wani fadan ba har kun sake wani? Kuma in an tambaye ku me ya hada ku ba zaku fada ba ballantana a sulhunta ku?" Ruqayyah ta mike zata fita daga dakin tana kunkuni. Inna Ade ta jawo hannunta "ke Ruqayyah ban hanaki in ana miki magana ki fita ki bawa mutane guri ba? Wato bama zaki tsaya kiji abinda za'a gaya miki ba ballantana kiyi aiki dashi ko?" Sumayya tace "kiyi hakuri Inna" Inna tace "ke ce bakinta? Ita bata da bakin magana ne?" A hankali Ruqayyah tace "Allah ya baki hakuri" Inna Ade ta sake ta ta fita daga dakin zuciyarta babu dadi. Sai da suka yi sallar laasar suka yi wanka suka shirya sannan suka fito tsakar gida, yau thursday dan haka masu zuwa daukan karatu basu shigo ba sai Ruqayyah ta dauki tsintsiya ita kuma Sumayya ta harhada kayan wanke wanke suka fara gyaran gidan. Suna gamawa Sumayya ta hada wuta ta dora tuwon dare Ruqayyah kuma ta dauko dutsen guga ta hada wuta ta fara goge musu kayan gugar su daya taru. A lokacin Inna Ade ta rufe Alqur'anin da yake gabanta tana karantawa tunda tayi laasar, ta shimfida tabarma kusa da inda Ruqayyah take guga ta zauna. Kamar hadin baki sai ga Sulaiman ya shigo tare da Zunnur, suka zauna suka gaishe da Inna Ade suma bata labarin shagon da suke zuwa koyon dinki. A lokacin kuma Baba ya shigo, da sauri yan samarin suka mike suna karbar kayan hannunsa suna yi masa sannu da zuwa. Ya amsa yana zama akan tabarma kusa da Inna, Sumayya ta ajiye rariyar hannunta da take tankade da ita ta wanke hannun ta ta debo masa ruwa a randa. Ya karba yayi mata godiya, yasha ya ajiye kwanon sannan inna ta gaishe shi, yace "yauwa Sa'adatu. Ya gida?" Ta amsa da fara'arta, "ka dade yau baban biyu, har na fara tunanin in aika gidan maman Minal in aro wayarta a kira ka muji ko lafiya" Yace "wallahi na je gurin wannan neman aikin da na gaya miki ne, wannan sabon kamfanin da aka bude, *H & H* to naji sanarwa a gidan radiyo cewa sun fara daukan kanana da manyan ma'aikata shine naje ko Allah zai sa a dace su dauke ni ko aikin gadi ne inke yi musu, ko wani aikin dai daban, aikin dai da za'a ce mutum kullum in ya fita yana da aiki kuma duk wata zai samu albashinsa" Inna tace "insha Allahu muna da rabo a aikin nan. Mun gaya wa Allah kuma insha Allahu zai dube mu" yace "ameen" sannan ya jawo ledar daya shigo da ita yace "ga garin masara nan na auno mana uwar biyu, sai a lallaba ya kai mu wani satin" ta shafa ledar tana jin yawan garin tace "wannan baban biyu ai har wani satin zai kaimu in sha Allah. Mungode Allah ya kara budi, jazakallah bi khair" yace "ameen. Amma bance ake yin tuwo kadan ba dan kar gari ya kare, a yi isashshe wanda yara zasu ci su koshi da safe a dumama suci kafin su tafi Makaranta. Bana so suke zuwa makaranta da yunwa" Inna tana murmushi tace "lallai masu 'ya'ya" ya jawo wata karamar leda yace "wannan busasshen kifi ne na siyo dan ake saka wa a cikin miyar kaɗi, saboda yara suji dadin cin ta" Inna Ade tace "Lallai yara yan gatan baban su, komai dai ace dan yara, ni ba a yin komai dan ni" ta fada da sigar tsokana, Zunnur yace "ai sai dai kiyi hakuri Inna mum kwace miki power a gurin Baba" duk sukayi dariya banda Ruqayyah da take ta gugar ta kamar bata gurin. Inna ta tashi ta dauko masa abincinsa ta kawo masa, yana bude wa yace "lala, uwar biyu miya akayi mana haka harda salak? A ina kika samu kuɗi?" Ta dan bata rai tace "saboda nasan kana so shi yasa na danyi wani aiki na samu kuɗi nayi dan in faranta maka. Ni dan kai nayi ba dan yara ba" duk akayi dariya har da baban shima, sai kuma yace "to ai ke nasan baki da matsala, tunda ke kika zabe ni kika ce kinji kin gani, su kuwa yara basu suka zabi zama yayan mu ba, bana so suke sha'awar iyayen wasu suna cewa ina ma dai sune nasu" Sulaiman yace "haba dai Baba, ni da ace za'a sake haihuwa ta ace in zabi iyaye ai da ku zan zaba sau goma, kunyi mana komai sai fatan Allah ya saka muku da alkhairi ya bamu ikon yi muku biyayya da faranta muku". Sai a lokacin Baba ya juya yana kallon Ruqayyah da take ta gugar ta kanta a kasa yace "Hassana. Baki ga na shigo ba ko gaishe ni baki yi ba?" Ta dago da murmushin yake a fuskar ta tace "na gaishe ka Baba, baka ji ni bane" ya girgiza kansa kawai ya fara cin abincin sa. Sai da yayi nisa da cin abincin suna yar hirarsu da Inna sannan ya dago kai yana kallon Sumayya yace "Hussaina yaya jarabawar taku? Ana dai kokari sosai ko?" Ta rufe tukunyar data ke juyawa ta taho tana cewa "Baba alhamdulillah, ai mun kusa gama wa ma insha Allahu nan da sati biyu zamu kammala gabaki daya" Ruqayyah ta ajiye iron din hannunta wanda ta gama guga dashi tace "nan da sati biyu zamu gama Neco Baba, saura Waec" yayi shiru sannan yace "ita ce wadda ba'a biya muku bako?" Sumayya tayi saurin cewa "ai bata da wani muhimmanci Baba. Kaga Minal ita fa waccan shekarar ta gama amma har yanzu bata karbo waec dinta ba tunda taci duk abinda ake bukata a Neco" Ruqayyah ta zauna akan tabarmar tace "muhimmancin ta daya shine idan mutum bai ci Neco ba, ko kuma yaci rabi bai ci rabi ba, zai iya hada wa da waec sai ya samu duk abinda ake bukata a jami'a" Baba ya gyada kai kawai bai ce komai ba, amma fuskarsa ta nuna damuwa. Inna Ade tace "maganar jami'a fa naji kuna yi, ita minal din bata gaya muku uban kudin da mamanta take bani labarin an kashe kafin a saka ta a jami'a ba? Ita kadai ma ballantana ku biyu?" Baba yace "abin ai na Allah ne, insha Allahu, indai sunci wannan jarabawar kuma suna so zasu je. Ko ba zan iya turasu su biyu a lokaci daya ba sai in saka daya wata shekarar sai a saka dayar. Abin ai na Allah ne" Friday bayan sun tashi daga makaranta, suna tsaye a bakin titi suna jiran abin hawa sai ga wata taxi ta tsaya a gaban su. Ruqayyah ta sunkuyo da niyyar yi wa driver magana sai taga mutumin ranar nan ne, ta ja tsaki tare da komawa baya tana hade rai. Sumayya ta leka itama ta gashi zata matsa taji yace "ku shigo in kai ku" Ruqayyah ta leko tace "ko babu motocin haya a titin nan gwara mu tafi a kafa" ta kuma komawa baya ta tsaya. Yace da sumayya "ke shigo in kaiki" ta girgiza kanta "bazan iya tafiya ba tare da sister ta ba" yace "I understand" tace "mungode bawan Allah" yace "yes, ni bawa ne na Allah but sunana Adam" Ruqayyah ta leko "babu wanda ya tambaye ka sunanka saboda babu wanda ya damu daya sani" Sumayya ta kalle shi tana murmushi tace "Sunana Sumayya, yar uwa ta kuma sunanta Ruqayyah,". Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account GT Bank Account Name : Nafisa Usman Tafida Account Number : 0139433741 Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin 08067081020 Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin 08067081020. Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only Episode Six : Chloroform Hira tayi dadi tsakanin Hussain da gimbiyar sa, har lokaci ya tafi ba tare daya sani ba, tun suna kan kujera suna hira har suka sauko kan carpet suna ta magana cikin yiwa juna murmushi da dariya, kasancewar duk su biyun masu fara'a ne sosai. Suna cikin hirar ne alarm ya kada a wayar Fatima, ta dauka ta kashe tace masa "lokacin tafiyar ka yayi kar kayi missing Flight dinka" yana kallonta da mamaki yace "wai kina nufin har alarm kika saka min?" Ta juya idonta tace "nasan zamu iya mantawa, kuma tafiyar ka tana da muhimmanci, bana so inso kaina da yawa" Ya jinjina kansa yana jin soyayyar ta tana karuwa a zuciyarsa, sosai yake son yadda take gudanar da al'amuran ta, komai nata a tsare yake, komai nata a nutse take yinsa. Har airport ta kai shi sannan sukayi sallama a ransu suna jin kamar kar su rabu, Hussain yana ji a jikinsa cewa in sukayi aure duk tafiyar da zaiyi tare da ita zai ke yi tunda dai matarsa ce kuma babu abinda zata zauna tayi a gida. Cikin sauri yaje gida, ya tarar Hassan ya gama hada masa kayan tafiyar sa ya zuba masa a mota dan haka wanka kawai yayi ya chanza manyan kayan jikinsa zuwa ƙanana sannan ya shiga mota Hassan ya mayar dashi airport. A hanya babu wanda yayi magana har suka je, haka kawai Hussain yaji jikinsa yayi sanyi and for the first time tunda ya fara tafiye-tafiye yaji cewa baya son tafiya, yaji cewa baya son ya rabu da danuwansa. Sai da Hassan ya karkada masa key a fuska sannan ya juyo yana kallonsa yana kirkiro murmushi. Hassan yace "what's wrong? Tsoron jirgin kuma kake yi yau ko me?" Hussain ya duba agogon sa yana noticing mintinan daya rage kafin jirgin su ya tashi, wata zuciyar tana gaya masa ya juya ya koma gida amma sai yayi sauri ya girgiza kansa yace da Hassan "take care of yourself bro. Bazan jima ba dan bana jin zan wuce sati daya. Duk abinda ya kamata ayi to ayi kawai kar ace sai an jira ni. Ka bawa Aunty hakuri kace tafiyar ta zama dole ne bana so auction din nan ya wuce ni" Hassan ya rike dariyar da take taso ma sa yace "Badan na sanka ba da sai ince kamar tsoro nake gani a fuskarka kuma nake ji a muryarka, amma na sanka kuma nasan Hussaini baya jin tsoron komai, shi jarumin jamurai ne" Hussain yayi murmushin da ya tsaya a lips dinsa yace "bana jin dadi ne kawai. Amma nasan kafin mu sauka zan ware" ya sake kallon abogon hannunsa sannan yace "take care of yourself bro" Hassan yace "you already said that bro" sai hussain yayi murmushi yana bude hannu yace "okay take care of everyone at home" sannan ya bude kofa ya fita. Hassan ya bishi da kallo har ya shiga kofar departure hall, sai daya daina ganin sa sannan ya tayar da motar ya bar gurin yana jin part of him ya tafi tare da Hussain. Amma dama ya saba da wannan feeling din, kullum in basa tare da Hussain sai yaji kamar rabin sa ne a gurin rabi kuma yana inda Hussain din yake, tun suna yara haka yake ji, duk fadan su duk rigimar su amma duk duniya babu abinda yake so sama da Hussain, baya jin kuma akwai wani abu da zai raba shi da Hussain. Direct gida ya koma, yana ta lissafin abubuwan da suke gabansa abubuwan da ya kamata ya yi kafin dawowar Hussain daga Beijing. Dazu dai yayi wa kananan ma'aikatan da za'a dauka aiki a sabon kamfanin interview kuma har ya riga yayi grading dinsu, sai ya zauna zai yi final zabe sannan sai a kira wadanda aka zaba din a sanar musu. Shi komai yafi so yayi a hankali, ya tuna yadda suka yi da Hussain a lokacin da suke maganar daukan ma'aikatan. "Kaga Hassan, don't stress yourself akan maganar nan. Kananan ma'aikata ake magana fa ba manyan ma'aikata ba, ba takardu zaka duba ba ba komai ba, kawai just look at their physique ka tambaye su akan past experiences dinsu shikenan. Wanda kaga ya dace ka bashi aiki kawai a take wanda bai dace ba ka sallame shi kace masa babu aiki dan kar yaje gida yayi ta saka ran zai samu" Hassan yace "so kake mu dauki baragurbi kenan mu bar masu kyau? Ai shi lamari na daukan ma'aikata a nutse ake bi ayi interview idan da hali ma sau biyu dan aga mai juriya, ni har medical certificate nake so suje suyi saboda in tabbatar da lafiyar su, sannan sai na zauna a nutse sai in tace wanda naga sun cancanta" Hussain ya mike tsaye yana bude hannu yace "do whatever you want. Ni dai abinda na sani shine, duk wanda Allah ya tsara yana da rabon samun aiki a *H and H* ko ka bashi yau ko kuma kayi ta delaying sai nan da shekara daya still dai sai ya samu. To gwara ka bashi ka huta shima kuma ya huta". Hassan yayi murmushi yana kashe motar bayan yayi packing a compound din gidan su. Tun suna yara kusan kullum sai sunyi irin wannan musun kuma har yau babu wanda ya taba chanza ra'ayin danuwansa. Ya shiga gidan. A kan dining ya hango yar autar su Zulaihat da takardu a gabanta tana karatu, shirye shiryen ssce take yi dan yanzu haka sun kusa kammala neco sauran su waec. Dama ita kadai ta rage a secondary School sauran yammatan duk suna jami'a dan Hassana har ta kammala ta kuma yi service dinta, ta kuma samu mijin aure dan yanzu so ake yi ma a hada bikin nata dana Hussain. Zulaihat ta amsa sallamar sa tana binsa da kallo sannan ta kalli bayansa da sauri sai kuma ta sake kallonsa "ina yake?" Ta fada tana kara kallon kofa. Ya jawo kujera a can karshen dining table din ya zauna tare da jawo food warmer din daya gani a gurin, yasan duk gidan sunfi son Hussain a kansa, sunfi sabawa da Hussain saboda ya fi shi faran faran da wasa da dariya, ya fishi kuma kashe musu kudi da shagwaba su, shima kuma yana taya su son Hussain din. Ta sake tambaya "yaya H1 ina yaya H2 yake? Bai dawo daga kanon ba?" Ya fara zuba abinci sannan yace mata "ya tafi China" ta bude ido da baki tana kallonsa sannan ta ajiye littafin hannunta ta tashi a guje ta tafi saman Aunty. Yayi murmushi yana cigaba da zuba abincinsa. Sai daya fara ci sannan yaji saukowarsu kusan gabaki dayansu . Duk suka taho inda yake, Aunty ta zauna a kujera tana kallonsa "ina Hussaini?" Ya dago kai shima yana kallonta yace "ya tafi China, suna kan hanya ma yanzu". Ta fara fada "yanzu lamarin Hussain har ya kai haka Hassan? yanzu ni a gidan nan ban ma isa a gaya min in za'ayi tafiya ba ballantana in saka ran za'a nemi izini na kafin ayi? Yanzu har sai yayi tafiyar ma sannan zai aiko ka ka gaya min?" Bai ce komai ba har ta gama fadanta sannan ya ajiye spoon din hannnunsa yana kallonta yace "tsakanin ku ne Aunty, kun fi kusa. Nasan in ya sauka zai kira ki sai ki yi masa fadan. Nima sai dana gaya masa rashin dacewar hakan amma sai yayi min bayanin cewa in ya gaya miki hana shi tafiya zakiyi kuma in kika riga kika hana shi ba zai iya tsallake maganar ki ba, sannan kuma tafiyar mai muhimmanci ce sosai saboda injinan da za'a yi amfani dasu a sabon Companyn yin flour nan su zai siyo, in ya aika kuma za'a iya siyo masa fake shi yasa ya tafi da kansa. Kinsan halin Hussain, he settled for nothing less than the best" Tayi shiru tana tunani, yayin da yammatan suka fara mita, Safiyya tana korafin ai yayi mata alkawarin tare zasu tafi kuma shine ya tafi ya barta. Aunty tace "yanzu yaushe zai dawo kenan?" Hassan yace "sati daya yace zaiyi" tayi ajiyar zuciya tace "Allah ya kaimu, ya kuma dawo mana dashi lafiya. Ni wallahi na ƙagu azo ayi bikin nan nasa ko zai rage wannan yawon, tunda naga yana son Fatima sosai dole zai ke son zama anan tare da ita" Hassan yayi murmushi yace "in yana son yawon zai iya daukan matarsa su tafi tare, menene a ciki?" Aunty ta bata rai "don't put that idea into his head" yayi dariya yana bude hannu "nayi shiru. Amma ina tunanin already idea din tana cikin kan nasa sai mu jira ayi auren mu gani. Hussain ne fa, bana jin aure zai saka ya zauna guri daya" Suka yi shiru gabaki daya, Hassan yana cin abincin sa amma kuma yana jin idon Aunty a kansa, take ya fahimci tunanin me take yi, sai yaji tace "kai kuma fa?" Ya gane me take nufi amma sai yayi keeping blank expression yace "ni kuma me aunty? Ni ma yaushe zan tafi chinan?" Ta hade rai tace "kai ma yaushe zaka yi auren? shine abinda nake tambaya, kai ko budurwar nan ma ta zamani baka da ita, kaki kula duk yammatan da suke sonka" Nafisa tayi saurin cewa "ai kuwa Aunty akwai wata course mate dina, baki ga yadda take son shi ba, kullum sai ta tambaye ni ina yake" ya harare ta yace "hala bata ga Hussain ba? Am sure tana ganin sa zata ce shi take so bani ba" Aunty tace "Hussain ai ya riga ya samu matarsa, a very good girl from a very good family. Family dinta is one of the best a duk fadin kasarnan. Kai ma ya kamata ka kara kokari ka samo wa Fatima yaruwa" ya shafa kai yace "za'a samo wa Fatima yaruwa Aunty, amma sai a hankali, kuma ba irin Fatima za'a samo ba dan ni bana son abinda yake all covered in gold and praises. Saboda nasan most of the books with good cover basu da good contents. Ni am more interested in the content" Aunty tana girgiza kai tace "ai kuwa ana samu Hassan, ana samun wanda yake da goodness in both the cover and the content, ko ita fatiman ai haka muke fata" ya girgiza kansa yace "I am not going to take that risk gaskiya, nafi son in nayi aure ya zamana har abada, mace daya in na samu irin wadda nake so ta ishe ni har abada. Nafi son in auri mace from a lower background than ours, yadda ba xata ke looking down on us ba, yadda zata ke girma ma ku iyaye na kuma ba zata ke yiwa sisters dina magana anyhow ba kamar yadda take yiwa bayin gidansu. Nafi son wadda duk abinda na bata, no matter how small zata yi appreciating ba zata raina ba saboda ta saba da wanda yafi shi. Nafi son me low life style irin nawa not extravagant kamar Fatima" Aunty tace "to Allah ya kawo mana ita, Allah yayi muku zabin alkhairi baki daya" ya amsa da ameen. Sun jima suna hira, yana updating dinta akan shirye shiryen bude sabon company, sai gata ta dauko masa wani dogon list wai daga Gombe aka aiko dashi inji uncles da auntys dinsu na mutanen da suke so a dauka aiki. Ya karba kawai yayi murmushi amma shi a ransa yasan babu wanda zai bawa aiki sai wanda ya cancanta sai dai duk abinda za'a ce ace. Daga nan part dinsu ya nufa, ya shiga palo yana karewa luxurious kujerun da suka kawata falon kallo, amma last dawowar Hussain daga Japan yana shigowa palon cewa yayi "what? Wannan kujerun har yanzu ba'a cire suba? Wadannan ai sun zama old models yanzu sam ba'a yayinsu" Hassan yayi murmushi yana jin kewar danuwan nasa, Hussain sarkin rikici. Ya bude kofar dakinsa ya shiga, komai tsaf tsaf kamar yadda ya barshi. Yayi wanka ya chanja kayansa zuwa kanana sannan ya fito ya rufe dakinsa ya shiga na Hussain. Komai na dakin abin kallone, ko bakasan kudin kaya ba kana shiga dakin zaka san cewa tabbas an kashe kudi a gurin tsara dakin zuwa kayan da aka zuba a ciki. Sanda Hussain zaiyi renovating babu yadda baiyi da Hassan ba amma yaki yarda a gyara masa nasa dakin "ni dakina babu abinda yayi bana bukatar a gyara min shi, wannan ai almubazzaranci ne, Ni fa da ka ganni yanzu zan iya yin 10 years nan gaba ba tare dana chanza komai a dakina ba". Sai dai Kamar yadda Hassan yayi tsammani a hargitse dakin yake, kaya sun kai set goma duk a baje a kan gado kuma yasan duk a kokarin shirin zuwa gurin Gimbiya ne aka hargitsa kayan. Yayi tsaki kawai ya wuce wata drawer ya dauko takardar da yazo nema, sketch ne na sabon companyn da ake gina wa wanda kusan an gama komai yanzu, finishing touches kawai ake yi. Ya dauka ya fita, a compound din gidan ya kira wani amintaccen yaron su Salisu, salisu tun babansu yana da rai yake gidan shi da babansa, bayan rasuwar baban nasa sai Hassan da Hussain suka cigaba da zama dashi a matsayin amintaccen su wanda shi kadai yake da access da dakunan kwanan su da abincin su da komai nasu da yake personal, yace "kaje ka gyarawa Hussain dakinsa, ni zanje site sai magrib zan dawo" sannan ya ja motar ya tafi. Site din ginin ya tafi. So yake yaje yabi ko ina ya tabbatar yadda aka yi sketching din haka aka yi aikin. Dama sunyi waya da engineer dan haka already a can ya same shi sai dai ma'aikatan sun fara tafiya gida tunda magriba ta fara gabato wa. Haka suka yi ta zagayawa sako da lungu na gurin Hassan yana yi yana duba sketch din hannunsa a tsanake duk inda yaga kuma ba'ayi dai dai ba sai yayi magana sai engineer yayi masa bayani in bayanin ya gamshe shi shikenan in kuma baiyi ba yace a gyara. A haka har suka gama, engineer yayi masa sallama ya tafi shi kuma ya tsaya ya dan yi rubuce rubuce a takarda ya saka a cikin sketch din sannan ya fito. Sai daya fito sannan ya lura da yadda gari yayi duhu, masallatai ana ta sallah wasu ma har sun idar. Da sauri ya bude motarsa yana jin takaicin missing jam'i da yayi, ya ajiye takardar hannunsa a kujerar kusa da driver sannan ya zauna a kujerar driver yana zura key a jikin ignition. Wani abu mai sanyi yaji ya taba wuyansa, sanyi irin na karfe. Da sauri ya kalli side mirror sai idanunsa suka sauka a kan yar karamar bindiga da ake kira da pistol, bakin bindigar a rufe da silencer. Zai iya cewa bai taba ganinta a zahiri ba sai yau ballantana ya taba ta amma yana ji a finafinai cewa karfenta sanyi ne dashi sai gashi yau ya tabbatar, sai dai abinda basu fada a films din ba shine yadda sanyin yake wucewa har cikin zuciyar mutum. Ya runtse idonsa ya bude, yana tunanin Hussain, ko yaya zaiyi copping da labarin mutuwarsa? Murya yaji dai dai kunnen sa, cikin rada amma kuma da kakkausan amo "take your hand of the ignition and place it on your head" a hankali yabi umarnin da aka bashi, ta gefen idonsa yaga wani ya bude kofar gefen driver ya shigo, bai juya ya kalleshi ba amma daga yadda motar ta amsa zaman nasa yasan cewa katon gaske ne, yasan ba zai iya tarar sa da fada ba ballantana kuma gashi su biyu ne da wanda ya saka masa bindiga a wuya. Amma yasan da Hussain ne da zai gwada, zai gwada ko da kuwa chances dinsa na winning is 1% in yayi failing ma zai sake gwada wa, amma shi ba zai gwada ba, shi yana analysing situation dinsa ne kafin ya gwada sa'ar sa kuma wannan karon baya jin akwai Sa'a. Yaji alamar wani ma ya bude baya ya shiga, su uku kenan, yayi shiru yana jiran yaji instructions din da zasu bashi amma basu ce komai ba sai kawai ji yayi wani hannu rike da wani tsumma ya zagayo ta baya ya rufe masa hanci da bakinsa. A jikin tsumman ya shaki kamshin wani abu, kamshin da yayi bringing back memory din lokacin da suka je South Africa shi da Hussain, lokacin da suka je kallon namun daji a reserve dinsu, lokacin da wani tiger ya tsallake shingen da aka yi masa yana kisan sauran dabbobi sai aka watsa masa wani abu mai irin wannan kamshin. Ya tuno sanda ya tambayi mutumin game da abin sai yace masa dashi suke amfani dan suyi knocking down dangerous animals, sai ya gaya musu cewa "masu satar mutane ma dashi suke amfani su fitar da mutum daga hayyacin sa dan suji dadin satarsa" ya tuno sunan da mutumin ya gaya musu "sunan sa chloroform". Da sauri Hassan ya dauke numfashin sa yaki shakar abin ya kuma fara amfani da hannayen sa dan ganin ya cire tsumman daga fuskarsa amma sai mutumin ya kara danna masa shi wanda ya zauna a gaban kuma ya fara kokarin rike hannayen sa, tunanin Hassan daya a lokacin, tsoron sa daya a lokacin shine kar su sace shi suyi amfani dashi gurin cutar da Hussain. Shi farko ya dauka robbers ne sai yanzu ya fahimci kidnappers ne. Yaji sunyi magana a tsakanin su amma bai fahimci mai suka ce ba sai dai kuma yaji muryar wanda yake bayan tamkar muryar wanda ya sani, wanda ya sani sosai amma ya kasa placing. Sai yaga sun dauke hanky din daga fuskarsa sannan na bayan ya saka hannayen sa biyu yayi amfani da duk karfinsa ya shake wa Hassan wuya yana toshe masa hanyar wucewar iska zuwa huhunsa, Hassan yaji kamar zai mutu, kwakwalwar sa ta totse kirjinsa kamar ana hura wuta a ciki babu abinda yake so illa ya shaki iska amma sun hana masa, ya yi tunanin this is what suffocating feels like, this is the end of him. Regret dinsa daya a rayuwa shine baiyi aure ya bar yaya ba kamar yadda yake da buri, sai yaji cewa ashe Hussain is right akan kayi komai a lokacin da ka samu dama kar ka jira sai wani lokacin, sannan yayi wa kansa alkawarin indai har yayi surviving the first thing da zaiyi shine aure, duk yarinyar data fara kwanta masa a rai ita zai aura. A lokacin daya gama saddakar da tafiya lahira a lokacin ne kuma suka cika masa makogwaron sa sannan suka yi placing wannan jikakken hanky din a kofar hanci da bakinsa. Farkon abinda ya fara kokarin yi shine shakar iska zuwa huhunsa da yake ji on fire, wannan yasa ya shaka da karfi, ya kuma shaki abinda baya so din har cikin huhunsa. Ya jima yana shaka, a kokarin sa na dawo da numfashin sa dai dai, a lokacin da numfashin nasa ya fara dawowa dai dai a lokacin ne kuma hankalin sa ya fara gushewa, a lokacin ya fahimci cewa ya shaki chloroform din. Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account GT Bank Account Name : Nafisa Usman Tafida Account Number : 0139433741 Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin 08067081020 Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin 08067081020. Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only Episode Seven : Lost Free Episode Sai da suka tabbatar jikinsa ya gama saki, suka mammare shi a fuska suka tabbatar babu alamar motsi a tare dashi sannan suka cika shi, suka bude booth din motar suka jefa shi a ciki roughly sannan suka shiga motar suka bar gurin. Babu wanda ya gani, kasancewar babu kowa a cikin building din sai masu gadi guda biyu da sun tafi sallah basu dawo ba, dan haka basu samu matsala ba suka yi tafiyarsu. Bayan sun hau kan titi sosai ne katon wanda yake gaba yace cikin budaddiyar murya "ina dan uwan nasa yake?" Wanda yake zaune a baya yace "yayi tafiya, ina jin ma ƙasar ya bari" mai tuka motar yace "what? To a gurin uban wa zamu karbi kudin tunda baya nan? Tunda kasan bayanan ba sai ka gaya mana ba mu bari sai ya dawo sannan mu dauki wannan ɗin? Yanzu anything can happen kafin ya dawo din, kuma bamu da number din da zamu same shi a can ɗin" na bayan ya gyara zamansa yana murmushi yace "kun san kuwa yadda yake son dan uwan nan nasa? Da zai san mun dauki dan uwansa a yanzu, da zai iya biyan ko nawa ne dan jirgin da yake ciki ya juyo ya dawo dashi Nigeria" ya karasa maganar yana dariya, na gaban duk babu wanda ya taya shi dariyar har ya gama sannan katon yace "to yanzu ta yaya zamu gaya masa mun dauki wannan ɗin" na bayan yace "Hassan ba zai rasa wayar sa a jikinsa ba, Hussain yana sauka wanda zai fara kira ya gaya wa ya sauka shine Hassan, mu kuma sai mu dauki wayar.....ina tabbatar muku da cewa next jirgin da zai dawo Nigeria da Hussain a cikin sa" ya sake yin wata dariyar "nasan mutanen nan kamar yadda nasan tafin hannuna". Babu wanda ya kula shi a na gaban amma kuma duk sun yarda da abinda yace, a hankali suke tafiya da motar da normal speed dan gudun jan hankalin mutane zuwa gare su, har suka yi nisa sannan suka sauka daga titi suka fara shiga cikin unguwa, unguwar rimi, suka ringa wuce gida je har suka zo wani incomplete gida, suka shigar da motar cikin kofar da ba'a saka wa gate ba suka yi packing, na bayan motar ne ya fita ya tsaya yana yi musu gadi su kuma biyun suka bude booth suka fito da Hassan suka shiga dashi cikin gidan zuwa wani daki sannan suka bude kofar bandakin da suka riga suka yiwa aiki suka saka mata lock suka jefar dashi akan simintin toilet din, sannan suka dauko igiyar su da suka riga suka tanada suka daure masa hannayensa a bayansa suka kuma hada ƙafafuwan sa guri daya suma suka daure sannan suka dauko masking tape suka nannade masa bakin sa. Sai da suka gama sannan suka lalube jikinsa sula cire wayoyinsa da ID cards dinsa da duk abinda yake jikinsa, suka dauke shi hoto da wayarsa sannan suka fita suka rufe kofar dakin da key. Suna fita katon ya jefa wa wanda ya zauna a bayan motar key din motar yace masa "discard the car, kafin safiya nasan police zasu fara neman ta". ************************************ Washegari Saturday, babu school, dan haka kamar yadda yake alada a gidan Inna Ade tunda suka tashi sukayi sallar asuba sai suka zauna suna tilawar karatun Alqur'ani har gari ya waye, sannan suka fara ayyukan gida. Yammatan suna gyaran gidan wanda kusan kullum kalkal yake cikin tsafta, ita kuma inna Ade ta hada wuta ta dora musu dumamen tuwo ta kuma kunu. Tana saukewa kuma ta dora musu ruwan wanka. A lokacin ne Baba ya fito daga daki da radiyo a hannunsa, Sumayya ta shimfida masa tabarma ta saka masa pillow ya zauna, duk suka gaishe shi. A lokacin samarin suma suka shigo duk suka gaishe shi ya amsa. Inna Ade tace "Baban biyu yau ba zaka fita bane ba? Naga ka dauko radiyo" yace "zan fita, labarai dai nake so inji ko zanji sanarwar sunayen wadanda aka dauka aikin nan da muka je nema jiya" Sumayya tayi dariya tace "Baba jiya fa kuka yi interview din, daga jiya zuwa yau har a sanar da wadanda suka ci?" Yace "ahau, ba aikin kamfani bane ba, ai su basu da bata lokaci sha yanzu ne magani yanzu ba kamar aikin gwamnati ba da za'a yi ta fama kamar cin kwan makauniya. Su kuwa wadannan tunda sunyi mana intabiyu shikenan" yaran duk suka kwashe da dariyar yadda yayi pronouncing interview din, yayi musu dakuwa yace "ku ungo ku raba, ni kuke wa dariya" Ruqayyah tace "Baba interview ake cewa ba intabiyu ba" yace "ko ma inta uku ne ku kuka sani,ni dai abinda na sani shine a bani aiki kawai, kunga inna samu aikin gadin nan sai innar ku take yi min abin siyarwa ina tafiya dashi ina siyar mata a bakin gate" Zunnur yace "baba ni zan taya ka dauka" Baba yace "makarantar kuma fa?" Sumayya tace "Baba ni zan daukar maka tunda kaga mu mun kusa gamawa, kafin ka fara aikin mun gama sai in ke kai maka" yayi murmushi yace "Husaina in dai har ina da rai kuma ina da lafiya ai ba zaki yi talla ba. Har kar neman kudin da zaki yi idan ba sana'a a gidan mijinki ba to sai dai aikin office" Inna Ade tace "allahumma ameen Baban biyu, Allah ya nuna mana wannan rana ya Allah" yace "ameen. Kinga yaron da yayi mana intabiyu din nan, wallahi ya burge ni sosai yaron nan, sai naji ya kwanta min a rai ina kallon sa nace Allah ameen, Allah ka muna min Suleiman dina watarana kamar haka. Dan saurayi dashi fa wai amma shine mai gurin gabaki daya" Suleiman yace "Baba ba H & H ba? Ai yanzu su suke tashen kudi a garin nan, wannan kamfanin da za'a bude na goma kenan fa kuma ance ogan ko aure bai yi ba" Ruqayyah tace "kai Suleiman banda kari, yanzu har sunyi goma?" Sai kuma ta langwabe kai gefe tace "sunji dadin su, wasu mutanen da sa'ar su suke zuwa duniya" Baba yana kallonta yace "Hassana ni banji kin ce zaki tayani daukan kayan abinci mu siyar a bakin gate ba" ta sunkuyar da kanta tana zuba kunu a cup tace "Baba in nace ma cewa zakayi a'a shi yasa ban ce ba" ya dauke kansa yana maida hankalinsa kan tuwon da Inna Ade ta ajiye masa a gabansa yace "insha Allahu ina samun aikin nan zan fara tara kudin da zan biya muku kudin jami'a. Insha Allahu ba zan kasa biya muku ba kamar yadda na kasa biya muku kudin wannan jarabawar". Kasa kasa Ruqayyah tace "hmmm. Allah yasa. Necon ma dam gwamnati ce take biya da cewa za'a yi ita ma mu hakura babu kudi" Inna Ade tace "me kike cewa ne Ruqayyah?" Ta dago kai tace "cewa nayi Allah yasa, Allah yayi jagora" duk suka amsa da ameen. A bangaren su Aunty kuwa da safe, Aunty ta sauko daga samanta idanun ta akan dining table tana lura da cewa ba'a taba abincin gurin ba, tasan kuma Hassan kullum shine na farkon tashi a gidan dan kusan kullum akan dining take samunsa. Ta karaso tana bude warmers din taga babu alamar an taba abincin. Ta ja kujera tana kwalla wa Safiyyah kira amma maimakon taji ta amsa daga san su sai taji ta tana amsawa daga bakin kofa, da alama daga waje take, Aunty tabi fuskarta da kallo har tazo ta zauna a kusa da ita tace "wai har yanzu baki samu number din Hassan ba?" Safiyyah ta ce "ban samu ba Aunty. Da daddare wayar tana shiga amma yanzu da safe a kashe take" Aunty tace "je ki duba mim dakinsa, tashi da sauri" Safiyyah bata motsa ba fuskarta kamar zata yi kuka tace "daga can nake aunty. Yaya Hassan bai kwana a gidan nan ba, motar daya fita da ita ma bata nan. Tun daya fita kafin magriba mai gadi yace bai dawo ba". Aunty tayi shiru tana kallon gefe daya, sannan kuma sai tayi saurin dauko wayarta tana kiran Hassan, switch off taji, ta katse kiran ta ajiye wayar tana jin yunwar data sauko da ita tana guduwa tana barinta. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ta ringa fada tana maimaita wa "ina yaron nan ya tafi? A ina ya kwana?" Tunda take da Hassan bai taba kwana ba'a gida basao lokacin da yana makaranta kuma shima dan a hostel ya zauna. Ta juya tana kallon Safiyyah wadda idanunta suka cicciko da kwalla tace mata "maza ki kirawo min Jabir" Jabir shine babban abokin Hassan wanda kuma za'a iya cewa shine kadai abokin sa bayan Hussain, shine kuma saurayin Safiyyah. Ta dauko wayarta ta nemo number din Jabir da kyar saboda hawayen da ya lullube mata idanunta ya rage mata gani. Ta kira ta saka a handsfree, yana dauka tace "yaya Jabir ina kwana? Aunty ce take tambayar ko kuna tare da yaya Hassan, bai kwana gida ba" shirun da Jabir din yayi shi ya tabbatar musu da amsar sa, basa tare, Safiyyah ta fara kuka sosai, Aunty ta karbi wayar daga hannunta tace "Jabir ba kwa tare ko?" Ya danyi gyaran murya yana kokarin boye tashin hankalin sa yace "bama tare Aunty, tun jiya da safe dana raka shi yayi interviewing kananan ma'aikatan kamfanin su ban kuma ganin sa ba, na kira wayarsa dai da daddare bai dauka ba sai nayi tunanin ko har yayi bacci lokacin, da wacce motar ya fita?" Aunty ta gaya masa sai yace " bara in zo gidan, amma ku kwantar da hankalin ku, bara in kira Khalid, maybe gidan su ya kwana kuma maybe bashi da charge" ya fada cikin kokarin sa na ganin ya kwantar musu da hankali amma tabbas shi nashi hankalin ya kai kololuwar tashi. Aunty tace "Khalid? In kwana yayi a gidan su Khalid din kuma bashi da charge mai yasa ba zai karbi wayar Khalid din ya kira mu ya gaya mana ba? Wannan ba halin Hassan ba ne ba. Hassan zaiyi tunanin cewa ya kamata ya kira ya fada. In Hussain ne ba zan damu ba" ta danyi shiru sannan ta dora da tambayar "waye ma Khalid din?" Jabir yayi saurin kashe wayar,shima baisan wani Khalid ba kawai sunan ne ya fado masa kuma yana son kwantar mata da hankali ko da ta hanyar karya ne. Ya zauna a bakin gado yana dafe kai. Tabbas babu lafiya, Hassan ba zai taba tafiya wani gurin ya kwana ba sannan ya kwashe wayarsa. Ko wanka baiyi ba ya fita, duk inda yasan suna zuwa da Hassan ko wanda yasan suna harka da Hassan sai da ya nema amma babu wanda ya gan shi. A karshe dai ta tafi police station ya sanar wa yan sanda ya kuma basu description din Hassan da kuma motar da ya fita da ita. Anan ya bata lokaci da yawa, saboda police suna fahimtar waye Hassan din suka daukaki maganar kuma abinda suka fara kawowa shine kidnapping. Sai wajen azahar sannan yaje gidan Aunty ya same ta ita da yara sunyi kuka har gode Allah. Ya yi musu bayanin duk abinda yayi sannan yace "ku kwantar da hankalin ku dan Allah. Police sun riga sun shiga maganar nan kuma sun bazu gurin nemansa a lunguna da saƙunan jahar nan, an bada cigiya gidajen rediyo da talabijin duk an baza hotunan sa. An aika asibitoci suma da mortuary duk za'a duba" Zulaihat ta saka kuka tace "mortuary kuma Yaya Jabir?" Ya dafe kansa yace "baya can Zulaihat, dubawa kawai za'a yi amma baya can" tace "to in baya can me yasa za'a neme shi a can?" Yayi kokarin kawar da maganar ta hanyar tambayar "ina Hussain. Aunty ta dago kai daga kallon charbin hannunta tace "Hussain ya tafi China Jabir. Har yanzu kuma bai kira mu yace mana ya sauka lfy ba, shima bamu san halin da yake ciki ba" ta karasa tana goge hawayen idanunta. Da yamma a gidan Inna Ade. Inna Ade tana yiwa Ruqayyah kitso Sumayya kuma tana tsefe nata kan. Suleiman da Zunnur suna gefe suna dorawa wasu yara karatu sai ga Baba ya fito daga daki fuskarsa dauke da tashin hankali, hannunsa rike da radiyo. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Maman biyu kinji wai an sace shi. Yanzu shikenan ya bata sai kace ba mutum ba? Sai kace wata jaka?" Inna Ade ta saki kitson da take yi tana dafe kirji tace "wa aka sace baban biyu? Waye ya bata?" yace "yaron nan da na ce miki na jishi a raina kamar Suleiman, yaron da muka je neman aiki gurin sa, mai sabon kamfanin nan, yan zu ake sanarwa a gidan radiyo wai tun jiya ba'a ganshi ba ana tunanin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa dashi". Gabaki daya suka dauki salati. Inna Ade tace " wannan wacce irin rayuwa ce muke ciki a yanzu? Dan adam ba'a bakin komai yake ba, talaka bai tsira ba mai kudin ma bai tsira ba. Ubangiji Allah ka bayyanar dashi, Allah ka hana azzalumai yin zaluncin su a kansa, Allah ka kare shi ka kare mu baki daya. Allah sarki iyayensa, har naji tausayin su wallahi. Allah ka bayyanar musu dashi in kuma ya mutu Allah ka sa su ga gawarsa" gabaki daya suka ce ameen. Ruqayyah tace "at least dai ya dana jin dadin rayuwa ko yaya ne, bai zo a bati ya koma a alakoro ba" duk suka juya suna kallonta A ranar da daddare sai Inna Ade ta samu kanta da saka Hassan a cikin addu'ar ta duk kuwa da cewa bata san shi ba amma tayi masa adduoi sosai da fatan alkhairi duniya da lahira. A gidan Aunty ma daren ranar basu yi bacci ba, gabaki daya suka hadu a bedroom din aunty suna kai wa ubangiji kukansu. Daga mai sallah sai mai karatu sai mai zikiri a haka har assuba da cimmusu, suka yi sallar assuba sannan suka zauna Aunty tana jero Adduoi su kuma suna amsa mata da ameen har ta gama suka shafa. Suna shafawa ana turo kofar dakin da sauri, suka waiga kusan a tare suna kallonsa kamar yadda yake binsu shima da kallo daya bayan daya yana haki tamkar wanda ya taho a guje tun daga China. Aunty ta mike "Hussain?" Yace "Aunty kidnappers ne suka dauki Hassan, sun kira ni da wayarsa sun kuma turo min hotonsa a daddaure, kudi suke nema, 1billion naira suke nema". Episode eight : Kidnapped Hasken da ya shigo ta window ne ya sauka a dai dai fuskarsa. Ya kikkifta idon sannan yayi kokarin amfani da hannunsa gurin tare hasken amma sai yaji ya kasa motsa hannun nasa. Wani irin ciwo jikinsa yake yi masa tamkar wanda aka kwana ana duka da ƙulki. Ya bude idonsa da kyar, su kansu eyelids dinsa sunyi masa nauri kamar an dora wani abu akan su. Idonsa ya sauka akan window din da take kallonsa ta inda hasken ranar yake shigowa. Ya sake rufe idon da sauri saboda hasken daya kashe masa ido amma already yaga tagar kuma a ransa ya fahimci cewa bai san ta ba. A ina yake? Ya sake kokarin motsa hannunsa amma yaji ya kasa, wannan ya tabbatar masa da cewa hannayen sa a daddaure suke sannan ya fahimci ƙafafuwan sa ma haka. Bakinsa ma a like yake ta hancin sa kawai yake numfashi. Ya juya fuskarsa gefe sannan ya bude idonsa yana numfashi sama sama cikin tsoro, a hankali ya zagaye gurin da yake da idanunsa sannan ya fahimci cewa toilet ne, ya kuma fahimci shi kadai ne a gurin. Sai a lokacin tunanin abinda ya faru dashi ya dawo masa. Farkon abinda ya fara fahimta shine har ya kwana ya hantse kenan, tashin hankalin sa shine wanne hali yan'uwansa suke ciki? Wanne hali Hussain yake ciki? Shin kidnappers din sunyi contacting dinsu ko kuwa? Abu na biyu daya tuna kuma shine bai yi Sallah ba, bai yi magrib ba bai yi isha ba baiyi assuba ba. Ya ja ƙafafuwan sa ya lankwasa su yana jin tamkar zasu karye saboda sandarewa da suka yi ga kuma azabar ciwo da suke yi masa, ya yi kokari ya jingina bayansa da jikin bango sannan yabi bangon ya mike zaune yana jin jikinsa gabaki daya yana amsawa saboda ciwo, ciwon tafiyar da akayi dashi a booth din mota, daure shin da akayi for hours da kuma kwana da yayi akan tantagaryar sumunti. Ya sake karewa ban dakin kallo yaga bashi da wani girma sosai daga kofar da take a rufe sai yar karamar tagar da take can sama a rufe itama da glass. Kasa kasa yake jin muryoyin mutane yana shigowa ta kofar. Ya muskuta a hankali har yaje jikin kofar sannan ya jingina jikinsa da kofar ya kasa kunnen sa yana so yaji abinda suke cewa amma har kansa ya fara ciwo saboda stressing kunnensa da yayi bai samu ya fahimci komai a maganganun nasu ba saboda can kasa suke maganar. Ya fara buga kansa a jikin kofar, yana jin kan yana kara yi masa ciwo amma yana so yayi calling attention din wadanda suke waje in mutanen kirki ne su taimaka masa in kuma holders dinsa ne ya nemi su kunce shi yayi sallah. Sukayi shiru da maganganun su a lokaci daya sannan suka taho bakin kofar da sauri suna gyara abinda suka rufe fuskokinsu dashi. Katon ne ya bude kofar da sauri yana auna Hassan da bakin bindigar da take hannunsa "Will you stop banging that door?" Ya fada murya can kasa kamar me rada. Hassan ya fara kokarin magana amma sai ya kasa saboda bakinsa yana rufe. Mutumin ya saka hannu daya ya cire abin bakin Hassan, Hassan yaji tamkar ya cire ne tare da fatar bakin gabaki daya saboda zafin da yaji amma babu hannun shafawa dan haka kawai ya runtse idonsa har zafin ya lafa, sannan yace "ina son zanyi Sallah dan Allah" mutumin ya sunkuyo fuskanta kusa data Hassan yace "kaga nayi kama da mai yin Sallah? Reserve your sallah kayi ta addu'a twin dinka ya biya mu kudin da muka nema and you will be out of here kaje kayi ta sallolinka". Dayan ya matso yana turawa Hussain robar abinci data ruwa gasansa, ya kunce masa daurin hannunsa sannan yaja baya, mai bindigar yace cikin gurbatacciyar hausarsa "mu na nan a bakin kofa, if you dare try to make any sound I will fill your brain with bullets" and Hassan knows he means it. Sai da suka rufe kofar sannan ya dauke ganinsa daga kansu ya mayar kan hannunsa yana shashshafa shi, bringing back blood, sai da yaji hannun ya danyi masa dama dama sannan ya jawo kafarsa yana noticing yadda ta kumbura ya fara kokarin kunce ta, da kyar ya iya kuncewa saboda karfin daurin da suka yi masa da kuma kumburin da kafar tayi. Ya jawo ta yana shashshafa ta sannan yayi kokarin mikewa yayi alwala da ruwan da suka bashi, bai san inane gabas ba kuma ko ya tambaya ba zasu gaya masa ba dan haka sai ya zabi guri ɗaya yayi niyya ya tayar da sallah sa, saboda shi addini mai sauki ne, ubangiji masani ne kuma mai rahama ne. Bayan ya idar, yayi dogayen adduoi sannan ya zauna ya runtse idanunsa yana kokarin tuno yana yin da ya hango cikin dakin da mutanen suke. Dakin bashi da girma kuma da alama ba'a kammala shi ba dan jikin bangon babu penti kuma tagogin babu frames. Yayi assessing yadda yaga situation din, mutane biyu ya gani amma yasan su uku suka dauko shi, ina dayan? Ya tuno da muryar da yaji a mota, muryar da yaji kamar ya sani. Shin mai muryar ne baya nan? Ya tuna da yadda yaga suna magana cikin rada, da kuma yadda suka buga masa warning din kar yayi making sound, hakan yana nufin cewa a cikin gari suke, a cikin mutane suke. Ya kalli window din da take saman toilet din, glass ne, yana fasawa zasu ji kara kuma kafin ya gudu zasu harbe shi, dan babu imani sam sam a cikin idanun wannan katon. Yayi ajiyar zuciya ya jingina kansa da jikin bango yana shafa fuskarsa yana jiyo maganagun su kasa kasa a cikin dakin, his only option is to wait har Hussain ya basu abinda suke so su sake shi. Ba shi da ko digon kokwanto cewa Hussain zai biya kudin, ko da kuwa zasu nemi dukkan abinda ya mallaka zai basu, ko da zasu nemi ya bada kansa zai basu, ko da wani aka kama ba shi ba Hussain zai iya biyan kudin ransom ya ceto mutum. Shi mutum ne da dukiyarsa sam bata dame shi ba. Hassan ya yanke shawarar zai jira, yasan jiran ba zai yi masa dadi ba amma bashi da wani option than that. Zai jira har sai Hussain ya biya kudin sannan su sallame shi ya koma gida sannan kuma ya yanke shawarar yana komawa gida zai yi aure. Five days later............... Tunda Hussain ya dawo Nigeria yake jiran barayin Hassan su sake kiransa amma shiru, ba kira babu message babu komai, shima kuma in ya kira number din Hassan din bata tafiya. Hankalin sa in yayi dubu ya tashi kuma commissioner of police ya gaya masa abinda suke so kenan, so suke su gama tsorata shi yadda duk abinda suka ce yayi zaiyi. Hussain ya girgiza kansa yace "then they don't know me as they claimed they do. I will give up anything for Hassan. One billion naira suka ce masa suna so in dollar bills kuma gata nan na hada na zuba a irin jakar da suka ce in zuba su kawai naje jira su gayamin yadda zanyi da ita" ya karasa maganar yana mikewa yana zagaye dakin. Haka yake tun sanda ya dawo daga China, baya taba zama na minti biyar a guri daya zai mike kamar wanda ake mintsinin sa, fuskarsa tayi baki, idonsa yayi ja kuma ya fada ciki saboda rashin cin abinci, rashin bacci da kuma rashin kwanciyar hankali. A ranar da aka sace Hassan, Hussain Yana sauka a Beijing ya kira Hassan da niyyar ya gaya masa ya sauka, a lokacin kidnappers din suka dauka kuma direct suka gaya masa cewa yana hannunsu, suka bashi umarnin ya dawo Nigeria sannan suka gaya masa adadin kudin da suke bukata. Sai kuma suka turo masa hoto, hoton Hassan a daddaure a yashe a bandaki, hoton da har yau shine yake yawo a kwakwalwar Hussain, shine yake hana shi bacci. Ranar da ya dawo Nigeria gidan su ya cika da police da yanuwansu na Gombe da sauran abokan arziki da abokan aiki, kusan duk uncles dinsu da aunties da cousins dinsu sun zo. Yana shiga gidan zai gansu duk a zazzaune da charbi suna ja kamar gidan makoki, sai gidan yake nuna masa kamar Hassan ya mutu ne, sai yake tunawa da mutuwar Abban su. Wannan ya saka ya tattara kayansa ya bar gidan ya kama daki a hotel duk kuwa da nuna wa da Aunty tayi cewa bata yarda da hakan ba, tana jin tsoron kar wani abu shima ya same shi. A hotel din ne commissioner of police ya same shi kuma ya hada shi da SS dan suke tsaron lafiyar sa "bamu san menene nufin su na yin shiru haka ba, maybe tarko suka dana, maybe kai suke nema mistakingly suka kama Hassan". Bayan kwana biyar da kama Hassan ne kidnappers din suka sake contacting Hussain da wayar Hassan din. Message suka tura masa "Kana so ka sake ganin twin dinka? Ka cire police daga gidan ka sannan su daina zuwa hotel din da kake zaune, SS din da suke gadin ka ma ka sallame su idan ba haka ba zamu dawo maka da Hassan, but in PIECES" Ya ajiye wayar a gefe ya mike ya fara pacing dakin da yake ciki yana yarfar da hannayen da, sai kuma ya shiga toilet ya yo alwala ya dawo ya gaya wa Allah sannan ya dauki wayar sa yayi wa commissioner forwarding message din na su. Jima wa kadan kira ya shigo daga commissioner din ya dauka baice komai ba. Commissioner yace "barazana ce suke yi maka kar hankalin ka ya tashi ba zasu iya yi masa komai ba tunda suna bukatar kudin ka" Hussain ya lumshe idonsa ya bude, he is not going to take that risk, yace "ku janye mutanen ku. I will do this thing alone, zan iya" commissioner yayi ajiyar zuciya yace "I understand, zamu matsa, but Please keep us updated, daga an karbe shi kuma zamu yi moving in mu kama su mu dawo maka da kudin ka" Hussain yace "alright. Nagode" ya ajiye wayar tare da saka hannayen sa ya rufe fuskarsa. A lokacin wayar Gimbiya Fatima ta shigo, she had been very supportive dan sau biyu tana zuwa Kaduna gurin sa tare da brother dinta. Mai martaba ma ya aiko takanas anyi masa jaje kuma yayi alƙawarin saka Hassan a cikin adduoin sa da kuma umartar malamai suyi ta addu'a akan lamarin. Ya dauka wayar ya gaya mata duk halin da ake ciki. Cikin shigar lallashi tayi ta bashi baki tare da bashi shawarwari har sai da taji alamun ya dan daidaita sannan suka yi sallama. Dare yana yi yabi shawarar da Gimbiya ta bashi, ya kira Salisu ya taya shi hada kayansa sannan ya zame jikinsa ya bar hotel din ba tare da sanin kowa ba, ya koma wani hotel din ya saka Salisu yayi masa reserving daki secrectly ya shiga yayi zamansa. Washegari da safe wani message din ya shigo. "Ka dauki kudin, da karfe goma sha biyu na dare ka saka a back seat din motarka ka fita kai kadai, make sure police basu bi ka ba, kaje kofar companyn ka, inda muka dauki Hassan kayi packing motar daga gefen katanga ka bar key a jiki ka fita ka hau babur ka koma gida. Ko Aunty ka gaya wa zamu sani" Ya karanta sannan ya ajiye wayar, a ransa yana noticing yadda suka ambaci Aunty da sunan Aunty. Sai ya dauki wayar yayi musu reply "Then how do I get my brother?" Suka amsa "Zai dawo gida da ƙafafuwan sa, that's in kayi abinda mukace, if not, zaka tsince shi somewhere" Hussain bai kira commissioner ba kuma bai yi niyyar kira ba. Da magrib ya fita shi kadai a mota ya koma gidan su, an tafi masallaci dan haka mai gadi ne kadai yaga shigarsa shima kuma ya gaya masa kar ya gaya wa kowa yazo. A dakinsa bayan yayi sallah ya bude safe box dinsa ya dauko jakar da ya zuba kudin ya sake kirgasu ya tabbatar sun cika sannan ya ajiye ya kwanta akan gado ya rufe idonsa. Sai karfe goma ya tashi yayi wanka yayi sallar ishai sannan ya zauna yana kallon agogo yana ticking har ya sauka kan 12 sannan ya mike ya dauki jakar ya fita. Babu wanda ya ganshi sai salisu sai kuma mai gadi. Ya dauki hanya har zuwa inda suka gaya masa yayi packing ya tabbatar babu wanda yake ganinsa sannan ya fita ya danyi tafiya a kasa sannan ya tari babur ya hau ya koma gida, yana sauka sako yazo masa "very good boy, aikin ka yayi kyau. Ka zauna ka jira zuwan danuwanka". Ya mayar da wayar cikin aljihun sa ya shiga gida ya zarce Bedroom dinsa ya sake wanka ya zabi kaya masu kyau ya saka, ya saka hula, agogo, socks da takalmi ya fesa turare ya dawo palor ya zauna, idanunsa akan kofa, waiting...... Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account GT Bank Account Name : Nafisa Usman Tafida Account Number : 0139433741 Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin 08067081020 Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin 08067081020. Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only Episode Nine : Gun shots Kwanakin nan guda bakwai sune one of the worst kwanaki da Hassan ya taba gani a rayuwarsa. Sau daya suke bashi abinci ruwa ma sau daya, sunce in yaci ya koshi zai iya kokarin playing hero. Ruwan da suke bashi kuma shi yake cancanawa yayi alwala dashi saboda bashi da ruwan alwala, wanda ya rage kawai shine wanda yake sha sai gobe kuma. Wanka kuwa tunda yazo jikinsa bai ganshi ba, shi lanshi yasan jikinsa warin datti yake yi dana gumi, saboda toilet din da yake rufe a ciki babu hanyar iska sai ta cracks din kofa. Addu'a ita Hassan ya rike a ransa, Alqur'ani kuma shine abokin hirarsa, shi yake debe masa kewa tunda bashi da wanda yake magana dashi sai dai in sun shigo sau daya, in suka shigo ɗin kuma babu magana a tsakanin su sai tsoratarwa a kan in yayi trying wani abu, suna kuma lissafa masa abubuwan da zasuyi masa idan har dan uwansa bai basu kuɗin da suke nema a gunsa ba. Sannan ga kafar sa guda daya da take damunsa, har yanzu a kunbure take, yana tunanin wani kashin ya samu matsala wanda yake bukatar attention din likita, da yayi musu complain sai suka yi dariya suka ce "you won't be needing the leg in bamu samu kudin mu ba, so worry about our money not your leg". A ranar da ya cika kwana bakwai ne suka yi masa albishir da cewa "yau zamu karbi kudin twin dinka, yau zaka tafi gida one way or another, in yayi abinda muka ce zaka tafi gida da ƙafafuwan ka in kuma bai yi ba........." Suka kwashe da dariya. Tun lokacin hankalin sa yake tashe, yasan halin Hussain sarai yasan zai bayar da kudin amma kuma yana da kankanba, yana da taurin kai kuma bai fiya bin umarni ba koda kuwa umarnin daga Aunty ya fito balle daga wadansu garorin unguwa, but since his life is at stake maybe, just maybe, zai zama careful for once. Magrib tayi, yayi sallah, yaji ana kiran ishai itama ya tashi yayi sannan ya zauna ya mike kafar sa yana kallon guri daya, waiting.......... Wadannan sune awannin mafi ya tsaho da Hassan ya gani a rayuwarsa, gashi babu agogo balle ya duba yaga lokaci, a zaune kawai yake yana sakawa yana warwarewa. Mutum daya daga cikin kidnappers din yana lekowa gurinsa yayi reminding dinsa cewa yana nan fa, kar yaji shiru ya dauka babu kowa, sai Hassan ya fahimci cewa shi kadai ne maybe sauran sun tafi karbar kudin ne, sai yaji yana jin tsoron kar suyiwa Hussain wani abu. After the long hours yaji tsayuwar mota a gaban gidan, jikinsa ya bashi cewa this is it. Yaji maganganun su a dakin suna magana kasa kasa da dariya. Sai yaji yana son jin maganar da suke yi, Allah yasa ba wani abin suka yiwa Hussain ba, ya mike tsaye jikinsa babu isasshen karfi yaje bakin kofar ya jingina kunnen sa yana son jin abinda suke tattaunawa akai. And then something happened........... Jinginar da yayi a jikin kofar ya saka kofar ta bude da kanta, ashe wanda ya shigo dazu ya manta baiyi locking dinta ba, sai kawai ga Hassan ya fado cikin dakin kamar an jefo shi, ya fado tsakiyar kidnappers din, gaban jakar kudin da suke budewa fuskokin su cike da farin ciki da murnar cikar burinsu na shiga layin masu kudi. Farko tsorata sukayi duk suka mimmike kamar yadda shima ya tsorata, sai kuma tsoron fuskarsu ya rikide zuwa wani rikitaccen yanayi yayin da nashi tsoron ya koma mamakin abinda idanunsa suka gani a gurin. "Salisu?" Ya fada da wata irin murya, "me kake yi a gurin nan? Ko kai Hussain ya turo ka kawo musu kudin?" Salisu ya mike tsaye daga durkushen da yake a gaban jakar, fuskarsa dauke da yanayin tashin hankali da kuma tsantsar rashin gaskiya yace "am oga....ai wato oga.....oga me kake yi anan?" Ya fada cikin inda inda. Sai yanzu Hassan ya fahimci muryar da yake ji, sai yanzu yayi placing muryar, yaji zuciyarsa tayi sinking, yaji gwuiyoyinsa sunyi masa sanyi sun kasa daukan sa har sai daya durkushe a gurin yana jin zuciyarsa tana yi masa zafi. "Salisu? Me yasa? Me yasa zaka yi mana haka ni da danuwana? Wannan wanne irin cin amana ne? Menene bamu yi maka ba? Menene bamu yiwa iyayenka ba? In kudi kake so mai yasa ba zaka tambaye ni ba? Me yasa ba zaka tambayi Hussain ba? Duk abinda kake so zai yi maka" Salisu ya shafa kansa yana girgiza kansa yace "zaku bani kudi na sani amma ba irin wadannan kudin ba" ya fada yana zaro wrapper ta dollars ya jefa a gaban Hassan "irin wannan kudin na keso, irin kudin da zan ke chanja motar da naga dama a lokacin da naga dama kamar yadda oga Hussain yake yi" Hassan yana girgiza kansa shima yace "akan kuɗi? Akan kuɗi zaka ci amanar mu? Akan kudi zaka saka rayuwata acikin hatsari salisu? Menene kuɗi? Is the money really worth it? Is this money really worth haɗa rayuwarka data irin wadannan mutanen?" Ya fada yana nuna sauran mutanen guda biyu, maganar ta makale a bakinsa sanda ya hada ido dasu, duk su biyun shi suke kallo kuma idanuwansu babu ko da digon imani a ciki sannan bakin bindigarsu yana saitin sa, zuciyar Hassan ta sake bugawa yana kara fahimtar situation din daya ke ciki. Yanzu ya tabbatar ba zasu barshi da rai ba, ya gan su yaga fuskokin su, asirin Salisu kuma ya tonu yasan yana da hannu a ciki, babu yadda za'a yi su barshi da rai. Ya girgiza kansa da sauri yana daga hannayen sa sama "babu wanda zan gaya wa, ku dauki kudin ku kuyi tafiyar ku nima zanyi tafiya ta babu wanda zai ji komai daga bakina" Dayan yace "ai ba yau aka haife mu ba Malam, kana fita daga gurin nan zaka bawa duk wanda zai tsaya ya saurare ka labari a kanmu, zaka kwatantawa police kamannin mu da bayanin gidan nan. Niyyar mu mu sake drugging dinka mu mayar da kai har kusa da gidan ku inda za'a tsince ka a mayar da kai gidan ku, but you seems to be in a hurry, shine ka fito ka rusha pland din mu. Kai kayi asara, mu mun riga mun karbi kudin mu". Salisu ya kalli Hassan sannan ya kalli sauran mutanen biyu, sai ya tsallaka ya shiga tsakani "ba zaiyi magana ba, bamuyi haka daku ba, kuɗi muka ce zamu karba kuma gashi mun karba bamuyi daku cewa zaku kashe shi ba, na gaya muku brother dinsa zai bada kuɗin kuma gashi ya bayar. Let him go". Babban ya saka hannu ya ture shi yana cewa "bamuyi Yarjejeniyar cewa zai ga fuskar mu ba, yanzu yaga fuskokin mu kuma yaganka, the deal is off, dole ya mutu" Nan take musu ya kaure a tsakanin su, shi Salisu baya son a kashe Hassan, so yake a barshi ya tafi in yaso sai su gudu su bar kasar, su kuma basa son taking that risk. A lokacin ne Hassan ya ga dama ta same shi, ya lura da yadda mutumin ya rike bindigar a sassauce dan haka yayi yunkuri ya doke bindigar ta fadi kasa can karshen dakin, cikin second daya duk su ukun suka kaiwa bindigar wawaso, shi kuma a second din ya kama window ya haura, ba tare daya jira komai ba ya doshi kofar shigowa gidan a guje duk da ciwon da kafarsa take yi masa. Yana fita daga gidan yaji karar harbin bindiga, bai waiga ba kuma bai tsaya ba sai ma kara mai da yayi yayi hannun dama ba wai dan yasan hanya ba sai dan neman Sa'a. Kamar yadda yayi tsammani, gidan a cikin unguwa yake, duk da dai ya dan yi gefe kadan kuma kwangwaye ne a zagaye dashi kuma shi din ma kusan kwangon ne, inda ya hango gidaje sosai nan ya dosa duk kuwa da cewa duhun dare ya ratsa sosai dan ma dai akwai hasken farin wata wanda yake haska masa hanya, layikan babu kowa, duk gidajen mutane da shaguna a rurrufe, a lokacin yaji zafin wani abu kamar an saka karfe a wuta an goga masa a gefen wuyansa, zafin yazo tare da sake jin wata karar bindigar daga bayansa. Bashi dako tantama yasan cewa harbinsa akayi kuma bullet din ya wuce ta gefen wuyansa. Kwanar daya gani a gabansa ita ya sha a guje, yana shan kwanar yaga wani gida a zagaje da langa langa sai ya samu kansa da bude gefen langa langar ya shige cikin gidan, yaji tsinin wani abu ya shige cikin kafarsa dako takalmi babu, azaba ta saka shi ya fadi kasa yana rike kafar tasa da hannu biyu yana tunanin cewa koya tsira daga wannan halin zai iya rasa kafarsa. Ya saka hannu ya shafa kafar yaji kusa ce ya taka ta shige cikin kafar, ya kama ta ya zare daga jikin kafar yana rintse idonsa cikin azabar zafi sannan kuma ya saka hannu daya ya rike gefen yuwansa da yake zubar da jini, daya hannun kuma ya rike kafar tasa itama da take zubar da jini. A hankali ya zame ya kwanta a gurin yana mayar da numfashi. ******************************************** Tun farkon dare Ruqayyah da Sumayya suka dauko littattafan su suna karatu saboda yanayin jarabawar da suke ciki. Babu wanda yake magana a cikin su sai dai lokaci zuwa lokaci sukan dan tambayi junan su abinda basu fahimta ba kuma suyi wa junan su bayani har su samu su fahimta din. Lokaci zuwa lokaci kuma Ruqayyah takan yi tsaki "yar wayar nan ma ta zama ni bamu da ita, ballantana mu ringa shiga yanar gizo muna duba abubuwan da bamu sani ba kamar yadda sauran ɗalibai suke yi" Sumayya tace "Rukee ki gode Allah. Ke ta waya kike yi, wani ta abincin da zaici yake yi, wani haka ya kwanta yau bai ci komai ba, wani ma kuma bama ya zuwa makarantar gabaki daya" Ruqayyah tace "kaina na sani Sumayya, abinda yake damuna nake fada ba abinda yake damun sauran mutane ba. Idan ba kyason ji ki to she kunnuwanki" daga nan Sumayya bata kara tanka mata ba suka cigaba da karatunsu har dare ya raba sosai sannan suka yi adduoin su suka kwanta. Bayan sun kwanta ne suka ji wata kara mai kama da harbin bindiga. Sumayya ta mike zaune da sauri "Ruqayyah? Kinji abinda naji kuwa? Kamar karar bindiga nake ji" Ruqayyah ta gyara kwanciyar ta "ke kika sani, karar bindiga kuma Allah na tuba a zamanin nan ai ba bakon abu bane ba" Sumayya ta jawo jiki tazo ta makalkale a jikin Ruqayyah "ni wallahi tsoro nake ji, kar fa ace yan fashi ne suka shigo unguwar nan" Ruqayyah ta ture hannunta, "dan Allah malama ki bar ni inyi bacci na, in yan fashin ne ma nan gidan zasu shigo? Me zasu dauka a nan gidan? Alluna ko ƙasa?" A lokacin suka sake jin karar wani harbin na biyu, Sumayya ta takure a guri daya tana adduoi, Ruqayyah kuma tayi tsaki tana gyara kwanciyar ta. Sai kuma ta mike zaune kamar wadda aka mintsina tana cewa "ni fitsari nake ji ma, toilet zanje" Sumayya ta rike ta "harbi fa ake yi Hassana, ke wacce irin zuciya ce dake?" Ruqayyah tace "to ni tunda bani ake harbi ba ina ruwana, ko so kike yi inyi fitsarin a kan katifa? Ki kwantar da hankalin ki ba anan kusa bane ba can layin bayan mune maybe ma police ne suke training" Daga nan ta fita ko fitila bata dauka ba saboda dakakkiyar zuciyarta. Da addu'a a bakinta ta shiga toilet din, ta tsugunna bakin rariya tayi fitsarin ta tayi tsarki sannan ta tashi tana gyara rigarta, anan ne taga abu kamar jini, tayi shiru tana kallon abin sannan idonta ya sauka akan langa langar da take a bude kamar an dube ta da karfi, tabbas an shigo gidan nasu kuma wanda ya shigo din yaji ciwo. Ta mike da sauri tana buɗe baki da niyyar yin ihu sai taji an saka hannu an toshe mata baki ta baya an saka wani hannun an jata baya zuwa cikin inuwar da take jikin katanga, ta jita a jikin mutum, ya hada ta kirjinsa, shi kuma ya jingina da jikin katangar. Daga karfin hannun daya riketa ta fahimci namiji ne, daga warin da take ji yana tasowa daga jikinsa na datti tasan ba daga guri mai kyau yake ba, daga kuma bugun zuciyarsa da take ji tana bugawa da sauri sannan da kuma karfi a kirjinsa tana bugun bayanta tasan cewa a matukar tsorace yake. A lokacin ne taji motsin wasu sun shigo kwanar gidan su a guje, daya yana tambayar dayan cikin hausa marar kyau "ka tabbatar nan kaga ya shigo?" Dayan yace "nan ya shigo, am very sure" suka wuce da sauri. Mutumin daya rike ta ya sassauta rikon da yayi mata, sannan ya kawo fuskarsa dai dai kunnen ta a hankali yace "help me, please. Ki taimakamin, dan Allah" Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account GT Bank Account Name : Nafisa Usman Tafida Account Number : 0139433741 Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin 08067081020 Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin 08067081020. Episode Ten: Brave and Selfless Last free Episode "Please, help me. Dan Allah, ki taimaka min" Sai kuma ya cika ta a hankali ya bi jikin katangar ya fadi kasa. Sai data ja numfashi sosai ta dawo cikin hayyacin ta sannan ta juyo tana kallonsa daga tsayen da take a kansa, sai kuma ta sunkuyo sosai tana kare masa kallo, he looked dirty and terrible. Ta kuma lura da ciwon da uake fitar da jini a wuyansa. But there is something about him, something da yake ta fincikar zuciyarta zuwa gare shi ta kuma kasa fahimtar menene, ta durkusa tana karewa fuskarsa kallo ko zata fahimci ko ta sanshi somewhere amma taga cewa bata taba ganin wannan fuskar ba. But something a zuciyarta keeps screaming "money" ta kuma rasa a ina money din yake. Tayi analysing situation din. Ta tuno da sautukan da suka ji a daki masu kama dana harbin bindiga, ta kuma tuno da mutanen da taji sun wuce ta kusa da gidan su kuma da alama wani suke nema, ta kalli Hassan tana tabbatar wa da kanta cewa shi ne wanda suke nema, kuma sune suka ji masa ciwon jikinsa. Amma me yasa? Waye shi su kuma su waye? Zata iya yiwuwa shi mugu ne su kuma police, za kuma ta iya yiwuwa sune mugaye shi kuma victim dinsu. " A kidnapped victim" zuciyarta ta gaya mata. Ta kalli kayan jikinsa, duk da cukurkudewar su amma ta fahimci masu tsada ne, meaning shi din mai kudi ne. Ta girgiza kanta tana son ta saita tunanin ta. "Uwar biyu an sace yaron nan, yaron da yayi mana interview wai ana tunanin masu garkuwa da mutane ne suka dauke shi" ta tuno da maganar Baba tun last week, dazu da yamma ma sai da taji yayi maganar "yaron nan har yanzu ba'a ganshi ba uwar biyu, dogo ne baki mai matsakaiciyar kiba da kyakkyawar fuska. Har yanzu ina ganinsa a idona. Allah ya bayyana shi" Ta sake kallon Hassan, he fits the description. Akwai kyakkyawar fuska kam babu laifi. She might be wrong but she is going to help him, tasan in taci nasara zata samu reward mai kyau. Bata san ta yadda zata taimaka masa ita kadai ba kuma bata son taso mutanen gidan su saboda tana son ya san ita kadai ta taimaka masa saboda yafi ganin kokarin ta sosai dan tafi samun reward mai kyau. Abinda zata yi din yana da hatsari but she is going to do it. Ruqayyah ce fa, Ruqayyah kuma bata jin tsoro. Ta tattaba fuskarsa, ya dan bude ido yana kallon fuskarta ta cikin hasken farin wata kamar yadda itama take kallon tasa fuskar tace "zan taimaka maka. Bansan ko waye kai ba za kuma ka iya cuta ta na sani amma na fahimci kana bukatar taimako dan haka zan taimaka maka dan Allah ba dan komai ba". Ta cire dankwalin kanta ta yaga shi gida biyu ta ninke part daya ta dora a ciwon wuyansa sannan ta daure wuyan da dayan part din. Ta taba jikinsa taji ya dauki zafi alamar zazzaɓi ya fara saukar masa. Ta rafa lissafin abin yi. A lokacin taji maganganun mutanen sun kuma dawo wa farkon layin daya yana cewa "police might be on their way. Wani zai iya reporting harbin" dayan yace "not Nigerian police. Am not leaving unguwar nan sai na mayar dashi gawa. Gida gida zamu bi. Am sure na ganshi ya shigo layin nan na tabbatar he is hiding a cikin wani gidan. Ta nan farkon layin zamu fara" ya fada yana knocking kofar gidan da yake opposite nasu da karfi yace "open this door ko mu fasa ta". Hassan ya kamo Ruqayyah jikinsa, idonsa yana kokarin juyewa, jini yana dibansa ya sake cewa "help me please. Ki kai ni gurin Hussain" dusu dusu yake ganin ta. Ta cire hannun sa daga jikinta tana jin wani iri, ita tun da take namiji bai taba taba ta ba, ko brothers dinsu basa irin wannan wasan saboda sun samu tarbiyya mai kyau a gurin Inna ade da Baba. Ta rada masa. "Ka kwanta anan, kar kaje ko'ina. Kar kayi motsi. Ina zuwa" sai ta mike zuciyarta tana yi mata plan na abinda zata yi. Ba tare da tsoro ko shayi ko kokwanto ko kuma tunanin komai ba ta zagaya ta daya side din toilet din ta taka bucket ta kama katanga ta haura, Hassan ya bi katangar da kallo sannan ya mayar da idonsa ya rufe yana jin tunanin sa yana barin kwakwalwar sa. Ruqayyah ta dira a bayan gidan su, tana jin kafarta tana amsawa ta dan jima har taji kafar ta saki, tana jin maganganun mutanen a daya side din gidan daga dukkan alamu an bude musu kofar gidan sun shiga. Ta ja dogon numfashi sannan ta fita a guje tamkar yar tseren gudu, dogayen ƙafafuwan ta suna taimaka mata gurin covering distance mai yawa cikin lokaci kankani taje karshen layin bayansu sannan ta zagayo kan layin su gaban gidan dayake karshe, ta durkusa tana mayar da numfashi sannan ta mike tsaye tayi gyaran murya ta bude muryarta da dukkanin karfinta ta fara ihu "wayyo Allah jama'a ku taimaka min ga wani ya shigo min daki. Wayyo Allah gardi a dakina. Jama'a ku taimaka min jini ne a jikinsa"! Ta ringa fada tana maimaita wa, daga can ta hango mutanen sun fito da sauri daga gidan da suka shiga suna hasko inda take da fitila, sai kuma taga sun taho a guje zuwa wajenta. Daya da touchlight a hannun sa dayan kuma da bindiga. Ta yi saurin shigewa cikin wani kango yadda ba zasu ganta ba sai dai suji sautin muryarta. Tana jin sun kusa zuwa tayi shiru, taji sunzo gidan karshe suna buga kofar da karfi, mai bindigar ya ture dayan ya saka bindiga ya harbi lock din gidan, karar bindigar yana amsa amo a cikin shirun daren. Tun harbin farko inna ade ta bude idonta, ita dama bata fiya yin nauyin bacci ba. Ta jima kwance tana tunanin anya kuwa da gaske karar bindiga taji? A lokacin ta sake jin ta biyun. Ta mike zaune tana salati, abinda da uwa, yayan ta ne suka fara fado mata a rai, matan suna cikin gida kuma dakin da suke ciki na kasa ne, an ce kuma bullet baya iya wuce katangar kasa, samarin ne take jiwa tsoro, sune suke kwana a shagon gidan makotansu tate da samari da yawa kuma ginin siminti ne kar fa bullet ya same su. Daga nan ne kuma taji ana bubbuga kofar gidan daya ke kallon nasu. "Open this door ko mu fasa ta" taji an fada da murya mai karfi. Ta fara jijjiga Baban biyu tana salati "baban biyu ka tashi barayi sun shigo unguwar nan, gasu can suna buga gidan Maman Minal" ya mike zaune yana salati shima yana mitstsika idonsa. A lokacin ne suka ji karar dirar mutum daga katanga. Kuma kamar katangar toilet dinsu ta baya, ko dai an hauro katangar an shigo gidan ko kuma an haura an fita. Inna ade ta mike "yan biyu na!" Ta fada cikin tashin hankali "baban biyu an shigo mana gida kar a shiga dakin yaran nan ayi musu wani abu na shiga uku" ta fada tana laluben hanyar fita daga dakin. Dama fitilar su daya a gidan kuma yaran suke bawa su su kwanta a haka. Baban biyu ya rike ta "tsaya anan kar ki fita, bara ni inje gurinsu" ba tare daya jira abinda xata ce ba ya wuce ta ya bude kofar dakin ya fita. A bakin kofar dakin yaga Sumayya a tsaye, idanuwanta a waje, da touchlight a hannunta amma kuma a kashe. Cikin rawar murya da karkarwar jiki tace cikin rada "Baba naji an hauro gidan nan ta bandaki kuma Ruqayyah tana bandakin" bai jira karashen maganar tata ba ya karbi fitilar hannunta ya tafi bandakin cikin sauri. Inna ade itama da kunnuwanta suka jiyo mata kalaman Sumayya ta fito da sauri daga dakin tabi bayan mijinta zuciyarta kamar zata bar kirjinta. Sumayya, ganin an barta ita kadai yasa itama ta bisu da sassarfa. Yana shiga toilet din ya kunna fitilar hannunsa, haske ya karade bandakin tare da bayyanar masa da jinin da yake malale a gurin, yayi kokarin kare Inna ade kar ta gani, a lokacin ne kuma ya ga Hassan a kwance a kasan katanga yana numfashi da kyar. Wannan ya tabbatar masa da cewa jinin bana Ruqayyah bane ba na wannan mutumin ne. Amma ina Ruqayyah? A lokacin ne suka jiyo ihu "wayyo Allah jama'a ku taimaka min ga wani ya shigo min daki. Wayyo Allah gardi a dakina. Jama'a ku taimaka min jini ne a jikinsa"! Ko daga bacci aka tashe su sun san muryar Ruqayyah ce. Inna Ade tace "Ruqayyah! Baban biyu wannan ai muryar Ruqayyah ce. Daga ina take wannan ihu? Yaushe ta fita daga gidan nan?" Baban biyu ya shige ciki yana tallafo fuskar Hassan, kallo daya yayi masa ya gane shi, ya kuma gane dankwalin Ruqayyah da yake daure a wuyansa. A take ya fara guessing abinda yake faruwa. Amma kuma hankalin sa ya tashi saboda fahimtar hadarin da Ruqayyah take ciki. Hassan ya bude ido a hankali yana kallon baban biyu, cikin magagin ciwo yace "Hussain? Ku kaini gurin Hussain" shima kuma yaji muryar da take ihun daya cika gabaki dayan unguwar. Yaji kamar yasan muryar, kamar muryar wacce tace zata taimaka masa, wacce ta haura katanga saboda shi, saboda Allah tace zata taimaka masa ba dan komai ba. Ya fahimci mai take cewa a ihun nata kuma ya gane mai take yi, tana kiran mutanen da suke nemansa ne away from him and toward her, tana jawo danger away from him and unto herself. So selfless, so brave. A lokacin suka ji mutanen da suka shiga makota suna nemansa sun fito da gudu sun tafi inda take ihun. Hassan ya runtse idonsa, Inna Ade ta saka kuka "wayyo Allah na, wayyo 'yata". Sai suka ji ta daina ihun, sannan kuma suka ji karar harbin bindiga, karar data cika unguwar baki daya. Sumayya ta kwalla kara "Hassana!!!" Hassan ya maimaita a hankali "Hassana!" Yaji sunan ya zarce zuciyarsa ya zauna a gurin da wani abu bai taba zama ba. Sunan mahaifiyarsa ne, sannan kuma female version of his own name. Ya tuno fuskarta sanda ta durkusa tama daure masa ciwonsa. So Young, so beautiful, so brave, so selfless. Sai yaji a ransa cewa zai iya bayar da tasa rayuwar saboda ita, me yasa ya gudu har ya shigo gidan nan ya saka yarinyar nan in danger? Me yasa bai tsaya kawai mutanen can sun harbe shi kowa ya huta ba? Ya fara addu'a a hankali "ya Allah indai wani zai mutu Allah ka dauki raina ka bar yarinyar nan. Allah ya bani dama da kuma ikon kwatanta sakawa yarinyar nan da kwatankwacin abinda tayi gare ni. Allah ka .........." A lokacin suka ji jiniyar police ta cika unguwar, sai kuma harbe harben bindiga ya biyo baya. Sannan kuma shiru. Shiru except for kukan Sumayya da Inna. Sai kuma kamar daga sama suka ganta ta durgo daga katanga. Duk suka juya suna kallonta ita ma tana kallonsu. "Hassana?" Baban ya fada. "Hassana" Hassan ya maimaita yana mika mata hannunsa kamar mai kiranta zuwa gare shi. Ta taho straight ta durkusa a gabansa tace "it is okay, yan sanda sun kama su. It is over" ************************************************************************************************* Hassan ya sauke idonsa daga kallon agogon daya kafawa ido kusan mintina ashirin da suka wuce, ya gaji da kallon kofar ya koma kallon agogo kuma zuciyarsa tana bugawa tare da kowanne bugu na hannun agogon. It is already after 3am. Tun 1am yake zaune a guri daya yana jiran shigowar Hassan kamar yadda kidnappers din suka yi mishi alkawari "zai zo gida da ƙafafuwan sa" they said, but he was a fool to believe them. Ta ya akayi ma ya yarda da maganar barayi? Barayin ma na mutane. Ya cire hular sa ya ajiye a gefe, duk ta dame shi ciwo take sakawa kansa yana yi. Ya cire agogon hannun sa shima yayi jifa dashi, ji yake komai ya fita daga ransa dan uwansa yake so ya gani, gabansa faduwa yake yi, ji yake kamar ya dora hannu aka yayi ta rusa kuka amma kuma sai ya tuna da cewa shi fa Hussain ne. Jarumi ne shi. Sanyi yaji ya fara ratsa shi, irin sanyin da yake kadawa idan assuba ta gabato. Ya lumshe idonsa sai yaji wani ruwa ya zubo daga idon nasa zuwa kan kuncinsa. Yayi sauri ya goge. Ba zai iya tuna ranar da ya taba yin kuka ba. But he can't take it anymore. He just can't allow himself to think, baya son yayi imagining wani abu ya faru da danuwansa, yayi komai da suke bukata ya cire police ya kai musu kudi shi kadai yayi isolating kansa duk a banza? For the first time in his life da yayi abu with care kuma shine zaiyi failing? Wayarsa tayi kara a gefensa, ya juya slowly yana kallon screen din "commissioner of police" ya gani. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ya fada ya sake fada, sai da kiran ya katse wani ya sake shigowa sannan ya dauka. Bai iya yin magana ba. Commissioner yace "yalllabai albishir nazo dashi. Mun samo Hassan" ya fada muryar sa cike da farin ciki. Wani sanyi ne ya taso daga kafafuwan sa ya dire har kansa. Sannan kuma wani dumi mai dadi ya ratsa zuciyarsa da kwakwalwar sa ya fara saisaita masa tunanin sa. Ya mike tsaye "a ina? Yana ina? Lafiyar sa kalau? Is he okay?" Ya jera tambayoyin da suka saka commissioner din yin murmushi sannan yace cikin kwantacciyar murya "dan uwanka yana raye, kuma alhamdulillah mun samu nasarar kama barayinsa, sannan mun karbo maka kudinka daga hannun su" cikin zakuwa Hussain yace "bar maganar barayi da kudi, ina Hassan yake?" Commissioner yace "muna asibiti yanzu tare dashi. An shiga dashi theater room" Hussain yace "asibiti kuma, wani abin ya same shi ne?" Commissioner yace "a'a, kawai dai ya danji ciwo ne kadan, but it is not that serious. Na kira kane saboda nasan zaka so a fito dashi kana gurin, shima kuma nasan zai so yana fitowa ya ganka" Hussain yayi murmushi, rabon da yayi murmushi tun sayi daya daya wuce "na gane. Nagode. Gani nan zuwa". Ya ajiye wayar yayi kamar zai je dakinsa sai kuma ya fasa ya koma dakin Hassan ya dauko key din mota ya fito ya dauki hularsa ya fita da sauri, har yaje gaban mota kuma sai ya koma cikin gidan da sauri ya hau saman Aunty yana bin kofofin kannensa yana knocking cikin sigar kida, kudan duk a tare suka fito tunda ba wani dogon bacci suke samun yi ba. Fuskarsa kawai suka kalla suka rude da ihun murna, gabaki daya suka rungume shi shima ya bisu daya bayan daya yana rungume wa. Aunty ta fito tana kallonsu, sannan ta daga hannunta sama tace "alhamdulillah. Allah mun gode maka". Sanda aka fito da Hassan, duk family dinsa suna bakin kofa suna jira amma shi bacci yake saboda allurar baccin da akayi masa. Wuyansa a nade da bandage, kafarsa ma haka. Aunty ta fara sharar hawaye, Hussain yana kallon doctor yace "akace min minor ne ciwon, menene haka?" Doctor yayi murmushi yace "ba wani abu yallabai, bawai ciwon bane yasa kuka ganshi haka wahalarda yasa ne, daya kwana biyu zai warware, harbinsa akayi a wuya amma bullet din bai shiga ba gogar gurin kawai yayi. Kafarsa kuma targade ne sai kuma ciwo da yaji a kafar itama. Duk it has all been taken care of". Da kyar Hussain ya iya sakin hannun Hassan yaje yayi sallah, yana dawowa ya koma ya zauna ya cigaba da rikon hannun. Sauran yanuwan a zagaye dasu. A haka Hassan ya farka ya gansu. Daya bayan daya yake binsu da kallo, duk suma suna kallon sa da murmushi a fuskokin su har ya iso kan Hussain. Ya lira da yadda yayi baki ya rame, ya danyi masa murmushi yace "hello bro" Hussain yace "hi bro. Welcome back" Hassan yace "na dawo gida, amma kafin in dawo na samo matar aure a inda naje" duk suka bude ido suna kallonsa cikin mamaki. Hussain yace "matar aure kuma?" Safiyyah tace "tare aka kama ku?" Khadijah tace "a ina take?" Nafisa tace "ya kamannin ta suke" Zulaihat tace "yaya sunanta?" Yayi murmushi yana kokarin mike wa zaune yace "no ba tare aka kama mu ba, a can dai unguwar take, she is the most beautiful, brave, and selfless person I have ever met" ya juya yana kallon Hussain yace "sunanta Hassana and she saved my life". Anan muka kawo karshen free Episodes na littafin tagwaye. Anan ne kuma muka fara labarin. Wannan tafiyar ba irin sauran ba ce ba, wannan tafiyar da zafi muka debo ta. Ga dai Hassan da hassanar sa (Ruqayyah, Rukee) ga kuma Hussain da gimbiyar sa, sannan ga Sumayya a gefe. Shin yaya wannan tafiyar zata kasance? Shin cikin wadannan su wanene iyayen Amir? Shin menene ya faru har Amir ya samu kansa a yashe a kofar gidan marayu? Wacece matar data kira Amir zata bashi labarin iyayensa kuma menene alakar sa da ita? Yaya zata kare tsakanin su? Zaku samu amsar wadannan tambayoyin in kuka turo kudinku ₦300 ta account GT Bank Account Name : Nafisa Usman Tafida Account Number : 0139433741 Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin 08067081020 Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin 08067081020. Nagode, sai na jiku. Episode Eleven : The two sides of a coin Hussain ya kama Hassan yana mayar da shi kwance, yana cewa "wannan Hassana ba dan sunan ta ba da na fara kishi da ita tun yanzu" Hassan ya runtse idanunsa cikin nuna jin zafin ciwon wuyansa yace "ba zata kula ka ba, komai neman maganar ka ba zata kula ka ba. Ita kamilalliyar yarinya ce" Hassan ya nade hannayensa a kirjinsa yana bata rai yace "me kake nufi da kamilalliyar yarinya ce? To waye kuma ba kamilallen ba?" Aunty ta matso tana dariya tace "zaku fara ko? Hussain sai kace ba kai bane mai kuka kana neman Hassan ba shine daga dawowarsa zaku fara musu. Ni na dauka in ya dawo ba zaku kara rigima ba" duk suka yi murmushi Hussain yace "ban fa yi kuka ba Aunty, kar ki sa ya raina ni mana. Kawai dai ina mamakin yadda mutum zai shiga irin halin da ya shiga sannan the very first thing da zai fada bayan ya dawo hayyacin sa shine wai ya samu mata" ya karasa maganar yana rike baki "mata fa? Hassan din? Ni na dauka duk macen da Hassan zai kira da mata sai tayi passing through different stages na gwaji. Ko guda daya ta fadi kuwa to an cire ta a list amma wannan cikin dare daya har tayi passing? Ni nafi tunanin zafin ciwo ne ya saka shi wannan maganar" Hassan yana daga kwance ya harare shi yace "ko kakan zafin ciwo ba. Nasan abinda nake yi kuma nasan duk mutumin da zai saka rayuwarsa on the line to save someone da bai taba gani ba a rayuwarsa to kuwa tabbas dole a kira shi dukkanin suna na gari da yake available. Like I said, she saved me. Nasan Allah ne mai raya wa kuma na yarda Allah ne yasa ka zan ga yau, zan ganku, amma through Hassana taimakon Allah yazo min. Don't you think this means something?" Aunty tayi replacing kujerar da Hussain ya tashi daga kai tace "ban san yarinyar da kake magana akanta ba, amma na san ka Hassan, nasan kuma duk abinda ka zaba kuma har ka yaba dashi to kuwa abu ne mai kyau. Dan haka bani da kokwanto cewa duk sanda naga yarinyar nan nima zan yaba da ita" Hussain ya kalli agogon sa yace "don't stress yourself da tunani, rest, ka koma baccinka. Ni zan je gurin police suna ta jirana tun dazu suna so suyi briefing dina akan case din. In ma dawo kuma zan samu doctor muyi maganar fitar da kai waje dan kafi samun cikakkiyar kulawa" daga haka ya bar dakin. Zuciyarsa tana cike da farin cikin dawowar danuwansa amma kuma bai san dalilin da yasa yaji hankalin sa bai kwant da maganar da dan'uwan nasa ya dawo da ita ba. A gurin police ne ya kuma samu wani shock din, shock din ganin Salisu a zaune a kasa duk rigarsa jini, kafadarsa daya a nannade da bandage. Yana ganinsa yace "Salisu? Me kake yi anan? Ciwon menene kaji haka a hannunka? Salisu ya sunkuyar da kansa kasaya kasa dago kai su haɗa ido. Hussain ya kalli dan sandan da yake wajen yace "me yake yi anan gurin ga kuma ciwo nan a jikinsa? accident yayi? A kaishi asibiti mana" police din ya saka kafa ya daki Salisu a bayansa yace "juya ka bashi labarin a inda kaji ciwon jikinka?" Salisu ya sake dunkule wa guri daya sam ya kasa dago kansa. Hussain ya rike dan sandan da sauri "ya zaka dake shi, ga ciwo a jikinsa ga kuma duka? Wanne irin police ne kai?" A lokacin commissioner ya fito, suka zazzauna shi da Hussain suka gaisa ya kuma taya Hussain murnar warwarewar lamura sannan yace "ka san wancan yaron?" Ya fada yana nuna Salisu, Hussain ya hadiye abinda yaki tafiya a makwogwaron sa saboda fara fahimtar inda maganar ta dosada yayi. Yace "yaron mune, a gidan mu aka haife shi a gidan mu ya taso, a hannun mu yayi karatunsa, a yanzu haka mahaifiyar sa tana cikin gidan mu tana shirya mana abinda zamu bukata in muka koma gida" commissioner ya girgiza kansa yace "am sorry to inform you cewa shine mastermind na wannan kidnapping din" Hussain ya mike da sauri kamar wanda aka yi wa allura, Salisu ya fara kuka yana rarrafe ya rike kafar Hussain "oga Hussain dan Allah kayi min rai kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne oga Hussain, nayi nadama ba zan sake ba. Ba hali na bane ba ka sani sharrin shaidan ne" Hussain ya saka kafa ya doke shi tare da ja da baya kamar wanda yake gudun ya sake taba shi yace "sharrin shaidan? Salisu? Wannan shine sakayyar soyayyar da muke yi maka ni da danuwana? Wannan itace muguntar da zaka saka alkhairin mu da shi? Dama yanzu duniya har ta kai wannan lalacewar Salisu? Dama yanzu har dan Adam bai mayar da saka alkhairi da mugunta komai ba a duniya? Dama yanzu duniya ta zama babu wanda zaka yarda dashi komai kuwa kyautatawar ka gare shi? Shikenan komai dan adam ya aikata sai ya kira shi da sharrin shaidan. To auzubillahi minash shaidanir rajim. A yanzu mutane sune shaidanun kansu basa bukatar taimakon wani shaidan wajen aikata ta'asa" commissioner ya jashi ya zaunar dashi a kujera yana bashi hakuri. Hussain ya sake cewa "Hassan fa, rayuwar Hassan yayi wasada ita, har harbin Hassan fa akayi ba dan yana da sauran kwana ba da yanzu mun dawo daga sutturar sa" Salisu yace "wallahi oga Hussain bansan zasu cutar dashi ba. Alkawari suka yi min cewaba zasu cutar dashi ba. Nayi kokarin hana su cutar dashi shine suka harbe ni su suka yi min wannan harbin sannan suka bishi" commissioner yace "kadan ma kenan, dama ai karshen irinku kenan. Wadannan mutanen sun saba kashe mutane akan kudin da bai kai wannan yawa ba ma. Ko ba dan ka shiga tsakaninsu da Hassan ba dama kashe ka zasuyi su raba kuɗin a tsakanin su. Kai da tunani kake xasu baka? Kuma su barka da raj ayi tracing dinka ka tona musu asiri? Ai anyi irinka da yawa kuma basu kai labari ba" Hussain ya mike yana cewa "babu hannuna a cikin case dinka Salisu, ban sanka ba daga yau, danuwana ma bai san ka ba. Ko an sallame ka kar kabi koda hanyar gidan mu ce. Babu mu babu kai har abada" Salisu ya fara kuka wiwi yana bada hakuri, commissioner yace "ballantana ma ba za'a sake shi din ba, za'a hada shi da sauran a tura su court a yanke musu hukunci dai dai da laifin su". Da wannan Hussain ya bar Salisu. Bayan cike ciken takardu da yayi da kuma sauran abubuwa sai ga kudinsa an dawo masa dasu cif ko kwandala bata yi ciwo ba. A ciki ya fitar ya bawa police kaso mai tsokar da yasa duk sai da suka ji sun kasa rufe bakunansu saboda murna, sannan kuma yayi alƙawarin biyan hospital bill din police guda daya daya samu rauni. A hanyarsa ta komawa asibiti ya kira gimbiya ya gaya mata duk halin da ake ciki, tun daga muryarta ya fahimci cewa tana cikin farin ciki sosai. Shima sai yaji duk damuwar da take ransa tana wucewa tana tafiya tare da sautin dariyarta. Yayi dariyar shima. Tace "kasan wani abu? This is the first time da naji kayi dariya tun ranar da aka dauki Hassan. Lallai ba karamin so kake yiwa Hassan ba, Allah ya bani, ko ince ya bamu ni da matar da Hassan zai aura ikon cigaba da karfafa kaunar da take tsakanin ku" sai yace "kinsan kuwa daga farkawar sa har ya fara xancen aure? Wai ya hadu da wata yarinya ta taimaka masa kuma wai ita zai aura" Fatima tayi dariya tace "anya kuwa Hassan din mu ne ba'ayi mana chanji a can ba? This is something that you would do, not him" yayi dariya yace "nima abinda nace masa kenan. Mr Careful is now not being careful" tace "amma nasan ai ba wai direct kawai za'ayi auren ba. Nasan zasu samu time together su dan fahimci junan su kadan. Hey! Why not a haɗa da namu kawai ayi tare?" Ya danyi tsaki yace "ke ma kin fara biye masa kenan ko? Ni kuma na rasa dalili nine yau nake zama Careful din akan maganar" tace "what happened to the Hussain I know, the Hussain that just go with the beating of the drum, relax and chill" A asibiti ya tarar Hassan ya kuma tashi, har Aunty ta na bashi abinci a baki yana ci. Ya leka bowl din hannunta yaga fruit salad ne yace "kai da zaka ci abincin da zai saka ka ciko ka mayar da jikinka ina kai ina fruits?" Aunty tace "a yanzu ai lafiya yake nema ba wai kiba ba, yana bukatar alot of vitamin c" Hussain ya shafa kafadar Hassan da fatar duk ta fara yamushe wa yace "and alot of meat. Me suke baka ne a wajen?" Hassan ya doke hannunsa yana hararar sa yace "what I need is a deep bath, in na gaya maka rabona da wanka sai kayi dariya dan haka ba zan gaya maka ba" Hussain ya toshe hanci yace "shi yasa atmosphere din dakin take chocking mutane". Hussain da kansa ya hada wa Hassan ruwan wanka sannan kuma ya taimaka masa yayi wankan yadda ruwa ba zai taba sannan suka fito ya kuma taimaka masa gurin shiryawa a tsanake ya saka kayan da Safiyya taje gida ta dauko masa. Sannan suka kuma saka shi ya sake cin abinci duk da cewa da kyar yake hadiya saboda yuwansa yana yi masa ciwo sosai. Hassan yace "ina fita daga nan zan fara shirya mana tafiya waje, gwara muje can a duba ka sosai" Hassan yace "ni da zaka bi ta tawa da ka bar maganar tafiyar nan. Babu abinda doctors din mu nan nan ba zasu iya bafa, wadansu daga cikin su fa su suke aiki a can din" Hussain yayi murmushi cikin rada yace "ai ba dan asibiti nake so mu fita ba, dan ka samu ka huta ne sosai. Anan yan dubiya da yan jaje ba zasu barka ka huta ba" Aunty ta dago kai daga zubawa Khadijah abinci tace "me kake cewa?" Ya shafa kansa Yace "babu komai Aunty, cewa nayi abincin yayi dadi sosai". Daga baya ne Hassan ya basu labarin duk yadda lamarin ya kasance, briefly ya gaya musu irin zaman da yayi a hannun kidnappers din da kuma yadda suka yi jiya. Hankalin Aunty ya tashi jin Salisu ne a ciki, yammatan suka fara masifar sai sunci ubansa, Hussain yace "wanne uban nasa zaku ci bayan ubansa yana lahira? Shi kuma yana police station daga can za'a kai sji court sannan a wuce dashi prison, me zakuyi masa wanda Allah bai riga yayi masa ba? Daga nan Hassan ya basu labarin haduwarsu da Ruqayyah da yadda ta saka rayuwarta a cikin hatsari dan ta taimaka masa. Duk jikinsu yayi sanyi sosai, suka kuma jinjinawa kokarin ta. Aunty tace "tabbas alamu sun nuna cewa yarinyar ta kirki ce, tunda bata san ko kai waye ba, zata iya kasancewa kai mugu ne da zaka iya cutar da ita ko ahalin gidansu. Wannan shine taimako na gaskiya, ka taimaka wa wanda baka da tabbas din shi zai taimaka maka" Hassan ya gyada kai yace "tabbas, tunda ba sani na tayi ba ballantana muce tayi ne dan ta samu wani abu a gurin mu" duk sauran suka amince amma banda Hussain, har yanzu maganar bata kwanta masa na, yace "tunda naji kace talakawa ne sosai ina ganin abinda za'a yi in mun dawo sai a kira babanta a samu wani abu mai kyau a bashi, yadda zai samu jari, ko kuma ita a bata scholarship tayi karatu" Hassan ya girgiza kansa yace "ba haka za'a yi ba, aurenta zanyi, sometimes money is not always the solution, kudi in muka basu zasu iya karewa amma aure, hada jini, babu yadda za'a dawo dashi baya" Hussain yace "exactly my point, babu yadda za'a yi undoing aure, ko an rabu tambarin yana nan, shi yasa ya kamata ayi dogon tunani da dogon nazari kafin ayi shi. What if suna da wani aibu, wani ciwo ko wani tambari marar goguwa? What if da akwai wani hidding halinta ko na iyayenta wanda ba'a sani ba? What if a cikin rescue mission din nata akwai wata hidding agenda da bamu sani ba?" Hassan yace "shi yasa nace zan aureta, ni Hassan, bance Hussain ya aure ta na. Ko ma menene a tare da ita it will be my burden not yours" Suka tsaya suna kallon kallo Aunty tayi tagumi tace "zaku tsaya in yi magana ne ko kuma ba kwa bukatar jin ta bakina? Yanzu ku shirya ku tafi inda zaku je ku huta din kar a dame ku. Kafin ku dawo zan nemi gidan inje da kaina inyi musu godiya daga nan zan ga yarinyar zan kuma ga iyayenta, sannan zan san abinda za'a yi musu" ta juya tana kallon Hussain tace "su kuma wadanda baka son su zo su dami dan uwanka yanzu zanyi musu yawa su zo su ganshi, tunda ya bata suke garin nan kuma babu yadda za'a yi ace an ganshi kuma har ya bar kasar ba tare da sun ganshi ba. Daga nan ta dauki waya ta fara sanar wa da jama'a, kafin laasar Asibitin ya cika da yan dubiya da jaje. Washegari gimbiya tazo da safe, bayan ta duba Hassan ta kuma zuba masa lafiyayyen girkin data shiryo masa tun daga kano wanda duk masu ruwa ruwa ne yadda zai ji dadin hadiya, duk kamewar Hassan sai daya yaba mata da girkinta sannan yayi mata godiya. Daga nan sai suka fita ita da Hussain tana tayashi shirye-shiryen tafiyar su shida Hassan. Sai da suka gama komai sannan ya kaita airport shi kuma ya koma gida. Two Day's Later Ranar Monday, kwana daya da tafiyar Hassan da Hussain India inda Hassan zai ga likita kuma zai samu ya huta sosai. A ranar ne su kuma su Ruqayyah bayan sun taso daga makaranta as usual Ruqayyah ta fito daga taxin tana mita. "Allah kaɗai ne yasan irin gajiyar da nayi wallahi. Yunwar da nake ji kuwa ina jin zan iya cinye abincin da akayi a gidan mu gabaki daya" Sumayya ta fara kokarin fitowa tana kuma zaro Naira dari a aljihun rigarta. Ta juya tana mikawa drivern sai taji yace "ki bata, ta sayi awara ta kara akan abincin dan ya ishe ta" tayi dariya yayin da Ruqayyah ta juyo da niyyar juye wa mai maganar kwandon bala'i, suka yi ido huɗu da drivern ranar nan. Ta bude ido tare da cewa "kutumelesi! Dama motar ka muka shigo?" Ya daga kafada kawai yana murmushi, ta juya gurin Sumayya da take dariya tace "da haɗin bakin ki muka shigo motar sa ko? Ya akayi ban gani ba?" Sumayya tace "nima sai da muka shiga sannan naga shine, nayi kokarin nuna miki ke kuma kina can kina yiwa yarinyar data taka miki kafa bala'i dan haka na rabu dake kawai" Ruqayyah ta kalle shi taga har yanzu murmushi yake yi sai taji tamkar ta kama kyakkyawar fuskarsa ta goga ta akan kwalta. Ta juya ta bar gurin tana maganganu kanana kanana. Adam yace da Sumayya "sister dinki drama queen ce" ta gyada kai tace "sosai. But she is not as bad as she always acts" yace "Allah yasa, dan nasan ke kullum tare mata zaki ke yi, kullum kina side dinta ko?" Ta sake gyada kai tace "yes, bayan Inna da Baba bani da wanda ya kaita. Komai zafinta dole ita din tawa ce, she is a side of me that I can never get rid of. In babu ita to babu ni kuma ba zan........." Ya daga mata hannu "bla bla bla. Naji, amma nasan kinsan cewa bata da kirki, wannan side of her din kinsan dashi fiye da kowa" ta fito daga mitar tana kara mika masa kuɗin hannunta "ga kudin ka Adam. Mun gode" ya jefa mata murmushi "ki siya wa sister dinki awara, tunda ta riga ta gama debe wa abincin gidan ku albarka ko zata cinye ba zata ko shi ba" ta rufe masa kofar sannan ta jefa masa kuɗin ta window ta juya tabi bayan Ruqayyah ba tare data kuma cewa komai ba. Ta sani, tabbas tasan Ruqayyah bata da kirki amma kuma it hurts her in taji wani ya fada, kullum tana wa Ruqayyah addu'a, kuma bata taba barin tayi wani abu marar kyau ba tare data yi kokarin gyara mata ba. Kuma sosai tana ganin gyaran, gashi nan ta fara chanzawa, gashi nan ranar nan har ta kusa rasa rayuwarta saboda taimakon wani Allah. Ta tarar da Ruqayyah tana kokarin shan kwana, har yanzu mita take yi amma kuma daga dukkan alamu ba wai mitar mai taxi take yi ba kuma, mitar wani abun ne na daban. "Mutane yanzu basu san a kyautata musu ba, shi yasa taimako yake da wahala, in ka taimaka ma babu abinda zaka samu" Sumayya ta kalle ta tana girgiza kant cikin takaici tace "shi taimako in dai kayi shi dan Allah ai baka bukatar komai daga gurin wanda ka taimaka wa" Ruqayyah tace "ko godiya? At least dai ai yazo yace min thank you for saving my life ko?" Sumayya tace "Rukee kenan. Kina kallon dai yadda aka fitar dashi daga gidan mu cikin jini, na tabbatar asibiti za'a wuce dashi kuma na tabbatar har yanzu yana asibitin, bai kamata ace har kin fara mita ba, kuma ai yayi miki godiya tun kafin ya bar gidan mu" Ruqayyah tace "wacce godiya yayi min? Ni me yace min ma in banda kira kamar tsohon makaho, 'Hassana" ta fada cikin kwaikwayon muryar Hassan, Sumayya tayi dariya ita kuma tayi tsaki, "bai san yadda na tsani a ce min Hassana ba, Baba ne kawai yake fada shima kuma dan babu yadda zanyi dashi ne". A lokacin suka sha kwanar gidan nasu, abinda suka gani a kofar gidan ya saka su taka burki cikin mamaki, suka rike hannun juna, Sumayya ta rada wa Ruqayyah "ga mutumin naki nan yazo godiyar" Ruqayyah tace "ni Companyn sa nake so ya bani daya". Manyan motoci ne guda biyu a kofar gidan, irin motocin da ba a kan kowanne titi su Ruqayyah suke ganin irin su ba. Ga kuma wadansu bakaken mutane masu bakaken kaya da bakaken tabarau a tsaye a gaban motocin, twins din suka rakube suka wuce su suka shiga gidan suna masu hada baki gurin yin sallama. Babbar tabarma ce wadda Ruqayyah ta tabbatar aro wa aka yi daga gidan su Minal a shimfide a tsakar gidan, akan ta akwai wata mata wadda idan gaskiya za'a bi zata iya girmar Inna ade amma a kamanni zata iya cewa Inna ade ta haife ta. Kana ganinta kasan cewa naira ta zauna mata. A tare da ita akwai yammata, su biyar reras, wadansu farare wasu bakake. A gaban su da tray shima da aka aro a gidan su Minal aka siyo pure water mai sanyi guda goma aka zuba akai. Daga gefen su karamar tabarma ce wadda tasu ce ta gida, akanta Baba ne tare da Inna Ade fuskokin su dauke da faffadan murmushi. Gabaki daya jama'ar gurin suka amsa musu sallamar. Inna Ade tace "yauwa, gasu nan ma sun dawo" Aunty tana kallon yan biyun da suke karasa shigowa tsakar gidan tace "tubarkallah masha Allah, ashe suma yan biyu ne?" Inna Ade ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Hassana tace "Kai! Amma fa kyawawa ne, wacece takwarar tawa?" Inna Ade ta dago tana kallon ta tace "kuma yan biyu ne?" Hassana tace "a'a, ni suna kawai naci, yayyen mu maza ne dai yan biyun. Shi wanda kuka taimaka shine Hassan, akwai hussainin sa". Daga dan nesa su Ruqayyah suka durkusa suna gaishe da bakin. Duk suka amsa da fara'ar su. Aunty ta miko hannunta, ku zo kusa dani ku zauna kunji yayan albarka? Wacece hassanar a cikin ku?" Da sauri Sumayya ta nuna Ruqayyah itama Ruqayyah ta nuna Sumayya. Duk aka kwashe da dariya. Inna Ade tace "Ruqayyah ki amsa mana anayi miki magana" Ruqayyah ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da tsinke a kasa tace "na'am" Aunty ta taso da kanta tazo har gabanta ta ruko hannunta tace "zuwa nayi har gida inyi miki godiya Ruqayyah. Nagode Nagode Nagode, Allah ya biya ki da gidan aljanna" duk sukace ameen banda Ruqayyah da take murmushi kasa kasa tana boye fuskarta. Aunty tace "Allah yasa wannan abu daya faru ya zama silar zumunci a tsakanin mu daku zumunci na har abada. Dan mu kam abinda kukayi mana ba zamu iya biyan ku ba, bamu da kudin da zamu iya biyan ku fatan da zamuyi kawai shine mu hada jini daku idan kun amince. Shine kadai sakayya". Bayan baƙin sun tafi, Inna da Baba sun tafi rakasu mota su kuma su Ruqayyah sun shiga daki suna cire uniform dinsu sai Ruqayyah ta daga labule tana leken waje tace "ni banga ana shigo da kwalayen ba" Sumayya ta ce "wadanna kwalaye kuma?" Ruqayyah tace "kina nufin wai hannu rabbana suka zo mana gida? Sai pure water din mu da suka shanye?" Sumayya tace "ho! Rukee. Wai duk bayanin matar nan baki fahimta ba?" Ruqayyah ta saki labulen tana kallon ta tace "wanne bayani fa? Ni ban fiye gane dogon bayani ba nafi son in ga aiki a aikace" Sumayya tazo ta kama hannun ta tace "ni abinda na fahimta daga bayanin ta shine kamar tana neman aure ne a gidan nan. Kamar tana nema wa wannan mutumin da naji sun kira da Hassan auren ki". Ruqayyah ta saki hannunta tana kallonta dalala da baki cikin mamaki, she never thought it possible, ta dauka yana da aure sannan da jerin manyan yammatan da suke rushing a kansa, bata taba tunanin mutane irin su zasu nemi hada zuri'a da irinta ba shi yasa dam bata gane bayanin ba. Ita jira kawai take taga an miko. Sai ta kama rawa tana juyi a dan karamin dakin nasu, Sumayya tana dariya cikin taya yaruwarta farin ciki. Har sai da hajijiy ata kama Ruqayyah ta fada kan katifar su tana birgima. Sumayya tazo tana janye kayan shanyar su data debo tana cewa "ni daga mana kaya kar kiyi masu squeezing ki kara min wahalar guga" Ruqayyah ta jawo ta ta fado jikinta tana cewa "ke ta guga kike yi? Yar uwarki zata zama matar CEO na H and H amm kina damun kanki da guga?" Sumayya ta mike zaune tana dariya tace "zata zama kika ce, ba wai ta zama ba. In banyi gugar ba ai ba zaki samu kayan sakawa ba in CEO din yazo ganin ki" Ruqayyah ta mike tsaye tana kallon kanta, ta dauko mudubi ta kalli fuskarta sannan ta ajiye tana cewa "farko aiki zan saka shi ya fara bawa Baba, Babban aiki irin wanda hatta yan Zariya sai sun san yarsa tayi babban kamu. Sannan sai in saka ya rushe gidan nan ya gina mana wani, irin gidan Alhaji Kabiru sabon kudi wanda aka saka tiles har a jikin bango. Kuma ginin hawa uku nake so, kasa su Zunnur ne zasu zauna tare da abokansu da suke kwana tare a shagon Bala, hawana biyu kuma inna ade da Baba, hawa na uku ni da Sumayya, sai im saka ayi min personal balcony a can sama inda zan ke hawa ni kadai ina kallon kowa a kasa na, ina kallon duk unguwar nan a kasa na, ina kallon kaduna a kasa na. And that, will only be the beginning" Wannan littafin na siyarwa ne, wanda yake so ya nemi wannan number 08067081020 Twelve : A Kind Suggestion Sumayya da tun da Ruqayyah ta fara lissafin ta take tsaye a bayanta rike da kaya a hannu baki a bude cikin mamaki, tasan yaruwar tata tana da dogon biri amma bata taba sanin cewa burin nata ya kai tsahon haka ba sai yau. Gida mai hawa uku, balcony, kallon kowa a kasa, lallai Ruqayyah ta wuce duk inda Sumayya take tunani. Tace "Ruqayyah? Duk wannan lissafin kawai dan babarsa ta nuna tana so a haɗa ku? Tun shi bai ce yana son ki ba tun baku fahimci juna ba ballantana ayi zancen auren har kin fara lissafin abinda zaki samu daga gare shi? Tabbas zaki fara ginin auren ki akan tubalin toka dan kuwa shi aure ana gina shine saboda Allah ba wai saboda abin duniya da ake burin za'a samu ba" Ruqayyah ta juyo tana kallonta, ita lissafi take yi a zuciyarta ba ta san cewaa fili tayi maganar ba amma so what? Waye baya son kuɗi? Kowa fa aka bashi daɗin su zaiji amma mutane da munafurci sai suke nuna wa kamar basa so. Ta hade rai tace "shikenan kuma yanzu Sumayya mutum bashi da ikon ya fadi a binda yake zuciyarsa sai a sako shi gaba da wa'azi? Ni banga aibu dan mutum ya nemi duniya at the same time kuma ya nemi lahira ba. Shi yasa ake addu'a ana cewa rabbana atina fidduniya hassanatan wa fil akhirati hassanatan......." Sumayya tace "kyakkyawar rayuwar ake nema ba wai kudi ba Ruqayyah, kudi ba shine farinciki ba, kudi ba shine abu mafi muhimmanci a rayuwa ba Ruqayyah. Happiness. Ka zauna cikin farin ciki shine abinda ake nema, wannan kuwa baya samuwa sai da wadatar zuci ba wai wadatar aljihu ba, the more kina samun kudi da more kina kara jin cewa ya kamata ki samu wasu, amma in dama baki saba dasu ba You will be contented with the little you have. Ni wannan shine abinda na fahimta, wannan shine abinda nake so. Wadatar zuciya. Kuma su kudi a fahimtata sukan kawo rabuwar kawuna ne a cikin iyali. Idan family da basu da kuɗi kamar mu din nan zaki ga sunfi haɗin kai ana haduwaa rufawa juna asiri but the moment kudi ya shigo ciki sai kiga an samu rarrabuwar kawuna musamman idan wani bangare ne ya samu kudin wani kuma bai samu ba. Ni abinda nake gudar mana kenan. Ruqayyah bound din da yake tsakanin mu yafi min gida mai hawa ukun da kike buri" Ruqayyah ta jawo ta jikinta tace "my darling sister, ba kudi ba, babu abinda zai raba tsakanin mu, duk inda zanje a rayuwa duk matakin da zan taka a rayuwa you will always be by my side, family na will always be y top priority, shi yasa a lissafin nawa Baba na fara sakawa nasan yana wahala damu" Sumayya ta zame daga jikinta tace "how can I be always by your side idan kika auri CEO na H and H? Zaku tafi ne unguwar masu kudi ya gina muku gida mai hawa biyar. Ni ma kuma dole zanyi aure, yanzu misali in na auri....... Na auri..... Na auri Adam drivern taxi yaje ya kama mana hayar gidan kasa kinga ai mun rabu kenan, banbancin yayi yawa" Ruqayyah ta kuma jawota tace "sai in saka mijina ya gina muku gida a kusa da gidan mu ya baku kyauta dan mu zauna tare" ta hade rai tace "kuma ba zaki auri Adam ba, kar ki ma kuma saka shi a misali" ta fita ta tafi yin alwala tana mita "na tsani wannan gayen wallahi, he is so arrogant and rude, gashi shi ba kowan kowa ba amma in yana magana kamar yafi kowa" tayi tsaki "inyamuri kawai. Watakila ma ba musulmi bane ba". Ruqayyah tayi ta saka ran taji Baba ko Inna Ade sunyi mata maganar abinda bakuwarsu tace amma sai taji shiru, in ta taso da maganar sai Inna Ade tayi saurin chanja topic saboda bata son sauran yaran su san da maganar, Ruqayyah ta cika tayi ta kumburin ta sai duk suka shareta saboda dama ta saba fushin ta ita kadai. Sai da dare bayan duk yara sun watse sannan Inna Ade tace wa Baba "Baban biyu ka fahimci inda maganar bakuwar na ta dosa kuwa? Ka gane abinda naso na gane?" Yayi ajjiyar zuciya yace "na fahimce ta uwar biyu, kawai dai nayi shiru ne kuma kema ina son ki cigaba yin shiru akan maganar saboda bama bukatar wani yazo ya gaya mana cewa mutanen nan ba sa'annin auren yayan mu bane ba, bana fatan yiwa yayana aure a gidan da za'a wulakanta su duk da dai su wadannan naga kamar ba irin sauran masu kudi bane ba, ni nafi son suyi karatu su nemi nasu na kansu ba wai su jingina da wani ba. Sannan kuma ita matar nan zata iya yiwuwa kawai nata ra'ayin ta fada bawai ra'ayin shi yaron ba, in yaron yana so da kansa zai zo ya nema. Dan haka mu bar maganar, muyi ta addu'a,idan yazo ya nema din kuma an samu daidaito tsakanin sa da yarinyar sannan mun bincika mun tabbatar da nagartarsa to alhamdulillah sai mu bashi ita" Inna Ade tace "to Allah ya shi ge mana gaba, ni ba wai maganar auren ce ta bani tsoro ba halin Ruqayyah nake gudu,dama Sumayya suka ce da sauki" Baba ya kalle ta kawai ya dauke kai, amma maganar ta ta tsaya masa a rai. Tabbas gaskiya ta fada, duksu biyun yayansa ne amma suna da banbanci kwarai da gaske ta fuskar halayya. A ɓangaren su Aunty bayan kuwa bayan sun koma gida su Nafisa suke ta zancen gidan. Hassana tace "Amma Aunty mutanen nan daga ganinsu suna da hali na gari, kinga yadda suka tarye mu da kulawa da karramawa? Basu da kudi amma tabbas suna da kamala" Safiyyah tace "suna kuma da addini, yanayin shigarsu da nutsuwar ƴaƴan ta birgeni" Khadijah tace "da tsaftar gidan, har muka fito banga datti ko digo ba, kayan sawarsu sun tsufa amma babu datti a jikin su" Nafisa tace "gasu kyawawa, kai twins din nan akwai kyau. Wato in suka samu kulawa sai an jinjina irin kyawun da zasuyi" Zulaihat tace "a yanzun ma ni banga alamar yunwa a tattare dasu ba, basu da rama kuma basu da datti. Hoda kawai suke bukata da jambaki" duk suka kwashe da dariya. Aunty tace "nima nutsuwa da tarbiyyar yaran ta bani sha'awa. Allah dai yasa yarinyar nan rabon Hassan ce dan ni kam nayi masa sha'awar ta sosai. Gata yarinya karama yadda juya ta ya kuma tarbiyyan tar da ita yadda yake so" Wannan yasa washegari tana tashi ta kira Hassan, Hussain ni ya dauki wayar suka gaisa sannan ya bawa Hassan da yake kwance yana ta juyi. Ya karba ya gaishe ta sannan tayi masa bayanin zuwan da tayi gidan su Ruqayyah "Jabir ne ya karbo min address din a gurin police, gaskiya Hassan naji dadin ganin yaran nan da iyayensu. Alamu na zahiri sun nuna cewa mutanen kirki ne, badini kuma Allah ne ya barwa kansa sani" Hassan ya shafa sajen fuskarsa yana murmushi a ransa yana jin kamar an yaye masa wani nauyi yace "naji dadi sosai Aunty, naji dadi da kika yaba dasu" sai kuma ya danyi shiru cikin jin nauyin Aunty yace "kin ganta?" Sai da tayi dariya sannan tace "na gansu, su biyu ne ita da husainar ta. Kamar su daya komai nasu daga, daga dukkan alamu basu kammala secondary school dinsu ba dan ba gansu da uniform" ya gyada kai yana tuno fuskar Ruqayyah sanda take daure masa ciwon sa,ya lumshe ido ya bude yace "Nagode Aunty" suka yi sallama ya ajiye yana kallon Hussain take ta zabga masa harara, ya dga kafada yace "me nayi?" Hussain ya gyara zama yace "sai wani murmushi kake yi wai kai nan kayi budurwa. A dai bi a hankali" Hassan yayi dariya har sai da yaji wuyansa ya amsa sannan yace "oho dai" Hussain yace "wai yarinyar da ka hadu da ita cikin mintinan da basu wuce talatin ba, sannan kuma cikin tsakiyar dare ita ce kake ta kwarara wannan murmushi saboda ana yi maka maganar ta" ya danyi dan karamin tsaki. Hassan ya mike daga kwanciyar da yake yi ya hade rai yace "ai ba mintuna ko lokacin da muka hadu ɗin ne madu muhimmanci ba, abinda tayi a cikin mintinan shine abu mai muhimmanci, ni na kasa gane kan ka Hussain, yarinyar nan fa rayuwata ta ceta, I owe her my life. Amma maimakon ace ka kasance mai farin ciki da ita sai kake furuci masu daci a kanta. It hurts me wallahi, and it makes me question matsayi na a gurinka" Hussain ya ajiye magazine din hannunsa yace "haka ne, I should be grateful to her, but bansan me yasa ba nake jin something odd about her ba, kawai ji nake sam ban yarda da ita ba" Hassan yayi murmushi yace "kamar yadda nima farkon soyayyar ku da gimbiya nake jin ban yarda da ita ba, gashi yanzu na fara sabawa da ita har muna zama muyi hira, kamar yadda na yarda da gimbiyar ka kaima one-day zaka yarda da tawa gimbiyar". Sai da suka yi sati uku a can sannan suka dawo Nigeria, a lokacin Hassan ya warware sosai har ya maida kibar sa kuma yayi haske abinsa, Hussain wata daya yaso suyi amma Hassan yaki yarda dan shi Allah Allah yake yi su dawo yaje yaga Hassanar sa. "Kar tayi fushi, tace naki zuwa" Ai kuwa Ruqayyah tayi fushin, tun tana kirga kwanaki har ta koma lissafin sati, gashi iyayenta sunki kwata kwata suyi mata maganar, Sumayya ma ta share ta. She became very edgy daga an taba ta sai bala'i har yan gidan duk suka share ta suka daina shiga harkarta. A haka har suka kammala neco dinsu, shikenan suna daina zuwa makaranta tunda ba waec zasu yi ba. Wannan zaman gidan shi ya cigaba da frustrating Ruqayyah, har mafarkin Hassan take yi wai ya dawo daga kasar waje ya siyo mata sabuwar waya mai kyau ƴar yayi. A ranar kuwa ya dawo kasar, washegari ya taho ganin ta. Drivern da ya kawo su Aunty shi ya saka ya rako shi gidan tunda ba zai gane ba. Suna yin packing yabi katangar gidan da take rabi ta langa langa da kallo yana tuno memory din ranar nan sai ya jinjina hikimar ubangiji, ya tuna sanda ya shiga gidan ta tsakanin langa langa ya kwanta a toilet din gidan yana birgima saboda azabar ciwon da yake ji a kafarsa da jinin da yake zuba a wuyansa. Ya tuna sanda ta shigo toilet din tayi fitsari a gabansa ba tare da tasan yana gurin ba, yayi murmushi tare da alkawarin wata rana sai ya tsokane ta da abin, ya lumshe idonsa yana misalta yadda zata ji kunya ta kifa kanta a kirjinsa tana cewa "kaga bana so, ka daina tsokana ta, Allah zan rama nima" ya sake yin murmushi shi kadai yana girgiza kai, yasan da Hussain yana kusa dashi da sai ya dungure shi yace masa "idiot". Drivern ne ya fita ya nemo yaro sannan ya tambayi Hassan "oga Hassan wa za'a ce ana kira?" Ya sake murmushi kamar idiot sannan yace "Hassana. Kace Hassan ne yazo yana son ganin Hassana" yaron da drivern duk suka yi dariya sannan yaron ya shiga ciki. Wanke wanken kwanuka take yi tana mitar Zunnur da ya ki cin abinci dare da Sulaiman ya zuba nasa daban ya kara mata kayan wanke wanke. Sumayya tana dora wa yara karatu akan baranda Inna kuma tana ruɗa tuwo. Yaron ya gaishe da inna sannan yace "Inji wani mai babbar mota yace wai Hassana tazo inji Hassan" Karaf a kunnuwan Ruqayyah, ta saki kwanon hannunta tana juyo wada sauri idanuwa a waje, suka hada ido da Inna, sai ta mike da sauri tana wanke hannunta da ƙafafuwan ta. Inna ta ajiye muciyar hannunta sannan ta bita dakin, kafin ta shiga har Ruqayyah ta birkito dukkan kayan su na cikin bagko tana neman wadanda suka fi ko wanne kyau. Inna ta tsaya tana kallonta tace "gashi kuma baban ku baya nan ballantana a tambaye shi izinin ki fita gurinsa" Ruqayyah ta yar da rigar hannunta ta juyo idonta har ya ciko da kwalla "Inna yanzu kuma jira zai tayi a waje har sai Baba ya dawo? Baban da bamu san lokacin da zai dawo ba? Inna tunda ke kina nan ki bani izinin mana, in Baba baya nan ai ke ce wakiliyarsa" Inna Ade ta girgiza kanta tana tabbatar wa da kanta hasahen da tayi akan Ruqayyah dai dai ne, sai dai kuma abinda Ruqayyah ta fada gaskiya ne, bai kamata abar bakoa waje yana jira ba kuma ita bata da waya ballantana ta kira baban biyu ta gaya masa labarin zuwan bakon. Sai tace "bana son ku tsaya dashi a waje, bana son kuma ku zauna a cikin motarsa, gashi kuma bamu da soro ballantana ya zauna. Abinda za'a yi bara in sallami yaran nan sai ayi masa shimfida a tsakar gida ku zauna ku gaisa, dake da Sumayya zaku je. Ni kuma zan zauna a daki. Ki kiyaye ni Ruqayyah, in kika nuna masa halinki wallahi xan saka baban ku ya gaya masa kar ya sake zuwa gidan nan" Ruqayyah tayi saurin gyada kanta, ta yarda, ta yarda da ko wanne sharadi in dai za'a bata wannan chance din. Wannan chance ne one in a million ta samu kuma ba zata yi wasa da shi ba. Tana cikin shirya wa Sumayya ta shigo itama ta wanko fuskarta, duk basu yi kwalliya ba sai mai da suka shafa suka saka kaya da dogayen hijabs dinsu. Sannan Sumayya ta shimfida tabarmi guda biyu a kasan bishiya sannan ta shimfida sallaya a saman tabarma daya. Ruqayyah kuma ta dauko sabon kwanon shan ruwan Inna Ade ta debo ruwa ta ajiye sannan ta dora kofi akai. Sumayya ce ta fita kiransa. Yana motar dai a zaune suna hira shi da drivern, lokaci zuwa lokaci yana kallon kofar shiga gidan zuciyarsa tana son ganin fitowarta. Sai ga Sumayya ta fito, idonta ya sauka kan motar amma da yake tinted glass ne bata hango na ciki ba amma shi ya hango ta, yaji bugun zuciyarsa ya karu, ya dakata da hirar da yake yana samun damar kare mata kallo tare da tunowa da waccan fuskar da ya gani ranar nan. Abinda ya fara fahimta a tare da ita shine yadda take tafiya cikin nutsuwa. Ta tsaya a gaban motar cikin yanayin rasa abinyi. Sai kuma tayi sallama tare da knocking window din. Yaji dadin sallamar da yaji tayi. Ya sauke glass din window din a hankali sannan ya sauke idonsa cikin nata. Tayi murmushi mai fadi, ko ba'a gaya mata ba ta san shine wannan duk da cewa ranar nan bata wani ga fuskarsa sosai ba. Ta dan durkusa kadan tace "ina yini, sannu da zuwa" ya jefa mata best smile dinsa yace "lafiya lau....." Sai ta katse shi "ammmm an ce ka shigo ciki, Ruqayyah Hassana tana ciki" ya kankance idonsa yana kallonta cikin mamaki, sai ta danyi yar dariya tace "ni sunana Sumayya...." Yace "Hussaina?" Ta daga masa kai ya bude kofar motar ya fito ya na kallon ta yace "gwara in gane ki sosai kar aje ayi min chanje" ta sake dariya, ya fahimci tana da fara'a sosai tace "baza ayi maka bama, ka kwantar da hankalinka" suka jera yana cewa "amma kuna kama sosai fa" tace "haka ake cewa, amma if you get to know us zaka gane banbancin mu" ita ta fara shiga sannan shi, abinda ya fara lura dashi shine tsaftar gidan da kuma alluna alamar ana koyar da karatu a gidan. Sai kuma yaga shimfidar da akayi masa sannan yaji kamshin tuwon da yake kan wuta. Ya zauna akan shimfidar sannan Sumayya ta durkusa ta sake gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa sannan ta tambaye shi mutan gida. A lokacin Ruqayyah ta fito daga dakin su, kanta akasa, hannayenta a boye a cikin hijab dinta, fuskarta cike da wani yana yi mai wahalar fassara. Tun da tayi taku na farko taji idonsa ya saukaa kanta, sai taji wani irin yanayi ya lullube ta taji abin duk ba yadda tayi tsammani bane ba, taji ta kasa dago kai ta kalle shi, taji kuma tana son ta kalle shi din. Kan daya tabarmar taje kusa da Sumayya ta zauna tare da gaishe shi murya can kasa " ya jikin? Allah ya kara lafiya" ya dan kalli dakunan d aduke gefe, ya san akwai mutum a cikin dakin dan haka dole yayi ajjiyar kalamansa sai wani jikon kuma. Amma shi kam yasan zuciyarsata tafi ga wannan yar karamar yarinyar da take kokarin gaisheshi. "Ya naki jikin? Ina fatan ranar nan baki ji ciwo ba" ta girgiza kanta tace "babu ciwo, Nagode" ya sunkuyo yana kokarin kallon fuskarta sai ta kara jawo hijab dinta ta kara rufe fuskar, ya danyi murmushi mai sauti yace "kin gode da me?" Tace "da ka damu dani har ka tambayi lafiya ta" yace "lallai ke ɗin ta daban ce tunda har zaki yi min godiya bayan nine ya kamata inyi miki godiya. Ki sani Hassana, bana jin akwai abinda zanyi miki wanda zai nuna irin godiya ta gare ki, duk abinda zanyi kwatanta wa ne kawai amma ninba zan iya biyan ki ba, Allah ne kadai zai biya ki. Ina kuma fatan ya biya ki da aljannar firdausi" Sumayya tace "ameen, tare da mu baki daya" ya sake kallon dakin yana feeling uncomfortable, akwai maganganu daya ta tsarawa tun a India amma duk ba zai iya fadin su ba a wannan setting din, dole ya bar wannan ziyarar a matsayin ta godiya kadai in yaso in ya kuma xuwa ya fara kafa gwamnatin sa. Amma duk da haka zai gwada ko dan kadan ne, at least dan asan inda ya dosa. Ya kalli Sumayya yace "kinga har na gano banbancin ku da Hassana ta" Sumayya ta bude ido tace "menene banbancin?" Yace "Hassana ta ta fiki nutsuwa, ta fiki kunya tunda gashi nan ta kasa kallona har yanzu kuma ta kasa bari in kalli fuskarta. Ki roka min ita ta kalle ni ko da sau daya ne kar ta saka yau in manta hanyar gidan mu in dawo nan in kwana" Sumayya tayi dariya tace "in kai ka manta drivern ka aishi ba zai manta ba" ya dafe kai yace "haka ne fa. To amma ai na kasa bacci ko? In banyi bacci ba kuma kinga ba zan samu karfin da zan dawo gobe in tambayi Baba ya bani izinin fara zuwa zance gurinta ba" Sumayya ta sake dariya, Ruqayyah ma ta danyi dariya a cikin hijabin ta, tana kallon saitin fuskarta ta cikin hijab din yace "kuma na sake gano wani banbancin naku, ta fiki kyau, dan na hango dogon hancinta ta jikin hijab" Ruqayyah tayi sauri ta kuma jan hijab din gaba yadda fuskarta ba zata fito ba. Yayi gyaran murya yace "abinda duk nake nema zan iya cewa na same su gabaki daya a gurin ki Hassana. Addini, tarbiyya, kunya, nutsuwa, kyau duk kina dasu. Ni na riga na samu mata Ruqayyah in dai kin amince kina sona ni da gaske nake aurenki zanyi in dai har iyayenki zasu bani ke" ya sake rage murya yace "amma ai ba zaki amince ba in nayi miki, ba zaki gane nayi miki ba kuma sai kin kalle ni" Sumayya ta kuma yin dariya, sai yaga tana tuna masa da Hussain ta bangaren fara'a. Sai ya samu kansa da fara yi mata hirar Hussain. Ruqayyah ta dan bude fuskarta kadan ta mike ta zuba masa ruws a kofi tace "ga ruwa, ka sha" ya karba yana cewa "nagode sosai" sannan ya kalli Sumayya yace "kinga inda aka damu dani an fahimci ban sha ruwa ba, ke kuwa sai magana kuke saka ni" Sumayya tace "to bara in tashi in tafi in ya so sai kuyi hirar kurame tunda na fahimci ba magana zata yi maka ba" ya shanye ruwan ya ajiye cup din yace "kiyi zamanki, nine dai zan tafi. Ki mika min gaisuwata a gurin Mama sannan ki yi kokari gurin kafa min gwamnati na, ki fara da Foundation mai kyau dan ginin da nake so inyi na har abada ne" ya mike sannan yace "in Baba ya dawo ki gaishe min dashi sannan ki gaya masa in babu damuwa gobe da kamar wannan lokacin zan dawo ina son magana dashi" ta amsa masa da insha Allah, sai ya dauko daurin kudi ya ajiye akan shimfidar yace "gashi ki sayi sweet, dan naga alamar kina da kwadayi" Ranar Ruqayyah bata iya bacci ba. Tana ta sakawa da warwarewa. Washegari ya dawo kamar yadda yayi alkawari. Baba kuma already yana zaune yana zamn jiransa kuma ya yanke shawarar abinda zai gaya masa, danda aka aiko ya zo sai Baba ya saka Sulaiman ya shimfida musu tabarma a waje daga gefe inda mutane ba zasu dame su ba, sannan ya fita gurinsa. Ganin haka yasa Ruqayyah ta kira Zunnur ta tambaye shi a inda suke, ita kuma ta tafi dai inda suke daga cikin gida tayi shimfida ta zauna tana yanke farcenta. Kawai haka nan taji zuciyarta tana son taji maganar da zasu yi. A waje Hassan ne tare da Jabir, yaso Hussain yazo du taho tare amma sai ya kirkiri wani excuse ya kawo amma Hassan ya fahimci zuwa ne baya son yi kuma yaji babu dadi. Bayan sun gaisa cikin mutunci da girmama juna, sun kuma yo doguwar godiya a bisa taimakon da aka yiwa Hassan a gidan sai Jabir ya shigar da maganar kudirin Hassan na neman izinin fara neman auren Ruqayyah. Baba ya masu kudurin su cikin nuna jin dadin wannan karramawar amma kuma sai yace "amma wani hanzari ba gudu ba, ni ba zan boye maka ba tun ranar dana fara ganinka naji zuciya ta tana sonka, naji a raina ina ma dai kai dana ne, kuma yanzu zanji dadi sosai idan ka zamo dan nawa wato in ka auri yata, sai dai, in har ka amince ina son ka chanza daga Ruqayyah ka nemi Sumayya" Ruqayyah ta dago kai daga yankan farcen ta, ba tare da ta ce komai ba ta mike ta tafi daki tana jin zuciyarta ta zama tamkar dunkulallen garwashin wuta. Wannan littafin na kudi ne, duk mai son siya tayi wa wannan number din magana 08067081020 Episode thirteen: The Strategy Duk suka yi shiru suna kallon sa, Hassan cikin sanyin jiki yace "saboda me Baba?" Baba yace "Saboda kamar yadda na fada ina sonka, duk su biyun yaya na ne basu da banbanci a guri na kuma suma duk ina son su, dan haka nake fatan idan sunyi aure auren nasu zai zauna har mutuwa, bana fatan ka auri yata kuma ka rabu da ita saboda wani hali nata da zaka ga baiyi maka ba, wannan shi yasa nake ganin alakar ku zata fi tafiya daidai da Sumayya, saboda a yadda na fahimta kamar halin ku yafi zama daya akan ita Ruqayyah" Jabir yayi gyaran murya yace "Baba ita Ruqayyah tana da wani aibu ne? Wani hali da ya kamata a sani kafin a aure ta? Ko tana da wata cuta ce?" Baba ya girgiza kai, Ruqayyah yarsa ce kuma yana sonta, kuma son da yake mata ne ya saka shi wannan batu, aure ba abin wasa bane ba, ba kuma a gina shi a kan ƙarya da rufa rufa in dai har ana so ya dore. Yana son auren Ruqayyah da Hassan ya dore in dai ya kasance, shi yasa zai gaya masa in zai aure ta a haka shikenan in kuma ba zai iya ba sai ya karbi Sumayya in ita ma baya so shikenan. Yace "Ruqayyah tana da zafin zuciya sosai, taurin zuciya da kafiya, ko mu iyayenta muna fama da ita a kan hakan. Bata da son mutane sosai saboda tana da fada, bata da tsoro sam. Kai kuma na fahimci mutum ne mai jama'a dan haka nake ganin kamar tafiyar ku ba zata zo daya ba" Hassan ya shafa kansa yana sauke ajjiyar zuciya, shi baiga aibu a duk abinda Baba ya fada ba, dama ai ya riga yasan da rashin tsoron da taurin zuciyar tun sanda ta taimaka masa, rashin son mutane kuma shi zai iya cewa abin dadi yayi masa dan shi din ma ba mai son mutanen bane ba dan haka kullum yake fatan kar ya samu mace mai kwashe kwashen mutane yadda zasu ji dadin zamansu su kadai. Yayi murmushi yana kallon Jabir shima da yake murmushi, sun dai fahimci cewa Baba mutum ne mai karanci da yawa yadda har zai fada musu abinda yake ganin aibu ne akan yar da ya haifa a cikinsa saboda ya kyautata dangantakar sa da su. Hassan yace "Baba ni ina ganin wannan ai duk ba wani abu bane ba, wannan ba abinda zai hana ayi aure bane ba, kuma ni itan dai Baba in za'a bani ita nake so Sumayya kuma sai ta zama kanwata" Jabir yace "wannan haka ne, kuma kusan duk halin daka lissafa irin na Hassan ne" ya fada cikin tsokana, "haka muke ta fama dashi, baya daukan raini ga kafiya, ina jin abin nasu a sunan ne" suka yi dariya su biyu banda Baba, shi gani yake yi kamar basu fahimce shi bane ba, amma zama da Ruqayyah su kansu da suka haife ta dauke kai kawai suke yi a lokuta da dama, suna ta yi mata addu'a kuma suna saka ran idan ta kara girma zata rage, sai dai baiyi tsammanin za'a zo neman aurenta haka da wuri ba. Yayi wa Hassan tayin auren Sumayya ne saboda yana ganin Hassan da Ruqayyah ba wai saba wa suka yi da junansu ba. Yace "shikenan tunda kunji kuma kun amince, kunga nan gaba ba zaku zo min da korafi ba kuma. Zamuyi ta muku addu'a, Allah yayi mana jagora baki daya, Allah ya hada kanku. Na baka damar ka neme ta, idan kuma ka chanza shawarar a tsakiyar neman ka sani ba zan kullace ka ba sai dai ba kuma zan baka Sumayya ba a lokacin". Hassan yace "insha Allahu hakan ma ba zata faru ba. Kowa a duniya ai dole yana da wani aibu da wadansu daga cikin mutane ba zasu so ba, ko ba Ruqayyah ba nasan bazan samu mace da take da komai ba dole sai an samu aibu". Suka yi godiya, sannan Baba ya jero musu doguwar addu'a duk duka shafa suka tashi. Hassan yaso yaga Ruqayyah amma kuma yana jin nauyin Baba, haka ya shiga mota suka tafi yana kallon kofar gidan da fatan ko Allah zai saka yaga giftawar ta. Ruqayyah tana shiga daki sai ta kwanta akan katifa ta jawo zani ta lulluba duk da ba wai sanyi take ji ba, so take tayi kuka amma kukan yaki zuwa, haka taje ji lokuta da dama idan aka bata mata rai sai dai tayi ta jin zafi a ranta ba zata iya kuka ba har sai ta samu tayi masifa tukunna zata ji ta huce. Idonta ya kada yayi jawur kamar garwashin wuta. Anya kuwa Baba ne ya haife ta? Anya kuwa uban da ya haifi ya zai iya yi mata abinda Baba yake shirin yi mata? Har zai ce zai bawa Hassan Sumayya? Zai ce da Hassan kar ya aure ta? Ita kuwa wanne irin laifi tayi wa Baba da yayi mata irin wannan tsana haka? A lokacin Sumayya ta shigo dakin, farko bata lura da Ruqayyah ba sai daga baya ta ganta a takure a karshen katifa, ta taba jikinta da sauri "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Ruqayyah baki da lafiya? Menene ya same ki?" Sai a lokacin Ruqayyah ta samu hawaye suka zubo mata, ai kuma ta fara rera kuka marar sauti kamar zata fito da zuciyarta, Sumayya kawai ya rungume ta ta barta tayi ta kukanta sai data gama sannan tace "Sumayya Baba baya sona ya tsane ni" da sauri Sumayya ta rufe mata baki tace "subhanallah, me kike fada haka? Baba yana son mu mana, yana son mu sosai da sosai" Ruqayyah tana girgiza kai tace "yana sonki dai amma banda ni. Ni ya tsane ni kamar bashi ya haife ni ba" sai ta bata labarin abinda taji. Sumayya ta dora hannu aka fuskarta rubuce da tashin hankali sannan ta sauke tace "me ya kaiki Ruqayyah? Me ya kai ki zuwa kiji abinda zasu ce, ina ruwanki" Ruqayyah tace "magana ta fa zasu yi, zuciyata tana ta gaya min inje inji abinda zasu ce ashe akwai dalili, ashe zuciyata bata yarda da Baba bane ba" Sumayya tace "wato ke kuma shikenan duk abinda zuciyarki ta gaya miki shi zakiyi? Ba zaki yi tunani da kwakwalwar ki ba sai kiyi aiki da zuciyarki? Ban shiga ran Baba ba Ruqayyah, bansan menene dalilin sa na fadar abinda ya fada ba amma nasan ba wai dan baya sonki bane ba sai don yana tsoron halinki, yana tsoron kar kije gidan kiyi ta musu halayyar ki azo aji kunya, kuma ni banga laifinsa ba" Ruqayyah ta fara ture ta tana kokarin mikewa tsaye tana kunkuni, Sumayya tace "ko me zaki ce sai dai kiyi ta cewa amma ni dai ba zan daina gaya miki gaskiya ba, kuma ina so ki sani, ko maza sun kare a duniya bazan auri Hassan ba dan haka kar ma ki saka wani abu a ranki, tunda Hassan ya nuna yana sonki to kuwa tabbas ya haramta a gareni. Amma in baki chanja hali ba zaki yi loosing dinsa, ko Baba bai hana shi ke ba shi da kansa zai gudu yace ya fasa" Ruqayyah tayi hanyar kofa zata fita kuma sai ta tsaya, sai ta juyo tana kallon Sumayya tace "menene zai saka yace ya fasa?" Sumayya ta jawo ta ta dawo da ita zaune tace "halinki. Yadda na fahimce shi shi kamilar mace yake so mai kyawawan dabi'u, to in kina so ya aure ki sai kin zama mai wannan halin, abu mafi muhimmanci kuma sai kin cire son abinsa a zuciyarki, dan in dai ya fahimci kudinsa kike so bashi ba to kuwa zai gudu, ki nuna kudinsa bai dame ki ba, kinuna masa kina sonsa sosai, watakila ma kiga har kin fara son nasa da gaske" Ruqayyah tace "waye yace miki bana sonsa yanzu" Sumayya tayi murmushi tace "ina fata. In ma kina sonshi to kinfi son dukiyarsa a kansa, ba Hassan kike so ba CEO na H and H kike so, ko ba haka bane ba?" Ruqayyah tace "shi din dai shine duk biyun, to menene abin damuwa a ciki?". Sun jima suna hirar abin a tsakanin su, Sumayya tana ta bawa Ruqayyah shawarwari a ranta kuma tana fatan Hassan bai karbi tayin Baba ba saboda in ya karba dole zata yi wa Baba musu, dan ba zata iya auren Hassan din Ruqayyah ba. Ko da ace ita yace yana so zata iya barwa Ruqayyah shi dan a zauna lafiya. Ita farin cikin family dinta shine gaba da komai a gurinta. A bangaren Ruqayyah kuwa hankalin ta ya kwanta sosai ta jin ikirarin Sumayya na cewa ba zata auri Hassan ba, kuma tasan indai Sumayya tace haka to Baba ba zai matsa mata ba. Sai kuma ta fara duba shawarwarin da Sumayya ta bata, ta kuma yarda lallai Hassan mace ta gari yake nema kuma indai ta nuna masa iri dabiun ta zai iya cewa ya fasa sai dai duk su biyun suyi asarar sa, ita kuma bata fatan wannan irin babbar asara ta same su. Ba dai mace ta gari yake so ba? To kuwa tabbas zai samu mace ta gari. Ita Ruqayyah ta kama shi a cikin faratan ta kuma ba zata taba releasing dinsa ba har sai burin ta ya cika, burinta na zama matar CEO of H and H. Tagwayen sunyi ta jira suji Baba yayi musu magana akan abinda suka tattauna da Hassan amma bai ce musu komai ba, dan haka suka kasa tantancewa ko Hassan ya karbi tayin Baba ko kuma bai karba ba. Ruqayyah kuma tayi iyakacin kokarin ta na dannewa bata nuna wa Baba cewa taji tayin da yayi wa Hassan ba, sai dai a zuciyarta ta kuduri aniyar cewa zata tabbatar cewa watarana yayi nadama, wata rana sai yayi nadamar zaben Sumayya akan ta. A bangaren Hassan kuwa fushi yake yi sosai da Hussain saboda halin ko in kula da yake nunawa akan Ruqayyah, rigima a tsakanin su har gaban Aunty "Aunty yaron nan wai yaje yaga yarinyar nan yayi mata godiya akan abinda tayi min amma yaki, kiri kiri yake nuna min kiyayyar sa akanta" Hussain yace "ni nace maka bana sonta? Ni nace maka ina kinta? Kawai hankali na ne bai kwanta da ita ba" Hassan yace "ta yaya to hankalin naka zai kwanta da ita idan baka je ka ganta ba? Ta yaya zaka yarda da ita in baka fahimce ta ba?" Hussain ya mike yace "alright, send me the address, zanje gobe mu gaisa shikenan?" Hassan yace "ba shikenan ba, sai kaje sannan maganar zata wuce". Suka mike a tare suka fita suna cigaba da rigimar, aunty ta bisu da kallo sannan ta girgiza kanta, ita da aka zo gurinta da niyyar tayi Shari'a amma ba'a bar ta tace komai ba har aka gama shari'ar. Bayan sun fita daga gurin Aunty dai suka ajiye maganar Ruqayyah suka koma hirar Company, dama batan Hassan ne ya tsayar da maganar amma yanzu tunda komai ya lafa zasu cigaba da shirye shiryen su. Hassan yace "already dama na riga nayi sanarwar wadanda aka yiwa interview su dawo a sake musu, tunda na rasa duk bayanan su a cikin mota ta data bata" Hussain ya daga kafada yace "shikenan, duk abinda kace haka za'ayi. Ina dai son mu gama daukan ma'aikata as early as possible saboda in samu in mayar da hankali na kan ginin gidan can da kuma sauran al'amuran biki" Hassan ya juya ya kalli side din da twin houses dinsu suke. Gida ne Hussain ya siya ajikin gidansu, mai gidan ne Allah yayi masa rasuwa sai magada suka saka gidan a kasuwa shi kuma Hussain ya siya, katon gida ne na gaske, amma Hussain ya saka akazo akayi flat dashi, a lokacin sai da suka yi ta rigima da Hassan saboda shi yana ganin rashin dacewar hakan. "Wannan ai almubazzaranci ne" shi kuma Hussain yace "plan din mutum daya ne a gidan, ni kuma so nake muyi twin houses ni da kai yadda zamu zauna da iyalan mu seperately but together, sannan kuma ga Aunty a kusa damu". Sai dai kuma ganin cewa da akwai sauran lokaci ya sa har yanzu bai mayar da hankali wajen kammala ginin ba saboda so yake yayi shi a nutse, using the very best of komai, dan Hussain baya karbar komai in ba best ba. Hassan ya bude motar sa yana shiga, Hussain ya leko da kansa yace "zanje fa" Hassan ya haɗe rai yace "kar Allah yasa kaje ɗin". Washegari Hussain ya shirya yaje. A kofar gidan da aka kwatanta masa da Google map ya tsaya yana karewa gidan kallo sannan ya juya yana karewa unguwar kallo, yana lura da yadda mutane yara da manya suke ta kallon motarsa. Ya dan sauke glass ya kira wani yaro wanda ya taho da gudu yana leka cikin motar. Hussain yace "ka shiga gidan nan kace wai ana kiran Hassana tayi bako" yaron ya girgiza kansa yace "babu Hassana a gidan" Hussain ya hade rai yace "babu Hassana kuma? Sai wa?" Yaron yace "akwai Sumayya akwai Ruqayyah" Hussain ya tabe baki yana sake kallon gidan, tabbas nan ne gidan ta yadda aka fasalta masa shi. Yace "to kace ana kiran su duk su biyun" da sauri yaron ya shiga. Yana bude kofa kofar gidan suka kusa yin karo da Ruqayyah wadda taji alamar tsayuwar mota ta taho yin tsegumi, a ranta tana fatan Hassan ne ya dawo kuma gurinta yazo ba gurin Sumayya ba. Ta ja yaron gefe, "waye a waje?" ya wangale mata baki cikin murna yace "wani farin kyakkyawan saurayi ne yake kiran ku ke da Sumayya" ta bata fuska cikin mamaki "fari kuma? Baki dai ko? Ko baka gani sosai ba?" Yaron ya girgiza kansa yace "fari ne wallahi, tas ma kuwa" Ta juya tana kallon dakin da Inna Ade take ciki sannan ta leka ta tsakanin kofa, ba irin motar ranar nan bace wadda Hassan yazo da ita, wannan ta ci uban waccan, ita bata taba ganin irin wannan motar ba ma. Ta koma da baya tana dafe kirjinta. Waye wannan kuma? Ko Hassan ne yayo mata aike a daya daga cikin motocin sa? Ko motar ya aiko mata da ita kyauta? Muryar Inna Ade taji daga bayanta, "me kike yi a gurin nan Ruqayyah?" Ta dan tsorata kadan sai kuma ta saki fuskarta. "Wai wani ne yake kiran mu ni da Sumayya" Inna Ade tace "kuma shine kike leka shi" ta juya gurin yaron tace "kaje kace waye" yaron ya fita ya tambayi Hussain, ya danyi tsaki yana kallon agogon hannun sa yace "kace hussainin Hassan ne" yaron ya koma ya fada. Ruqayyah ta dan bata rai. Me yasa shi Hassan ɗin ba zai zo ba sai ya bawa Hussain motarsa ta taho? Ko dai ya karbi shawarar Baba, ko kuma har yanzu yana tunani ne akan shawarar. Inna tace "ku saka hijaban ku ku je, zuwa yayi ku gaisa" sai ta dauki kudi a cikin kuɗin da Hassan ya ajiye musu shekaran jiya ta bawa yaron tace yaje ya siyo lemo guda daya da ruwan roba guda daya. A tare suka fita, ya bi su da kallo yana studying dinsu har suka zo gaban motar suka tsaya sannan ya sauke glass din. Sumayya tayi masa murmushi, sai ya mayar mata kuma yaji bai kamata suna tsaye a waje shi kuma ya zauna a mota ba. Ya bude motar ya fito. Wani irin lugude zuciyar Ruqayyah take yi. What? Wannan ai yafi Hassan dinta haduwa, ya akayi dan uwansa ya fishi haduwa? Ta sauke idonta kasa tana tuno karin maganar hausawa da suke cewa ba haka aka so ba kanin miji yafi miji kyau. Sumayya ce ta fara gaishe shi sannan Ruqayyah ita ma ta gaishe shi. Ya amsa yana rarraba ido a tsakanin su. Yace "wacce ce yayar tawa a ciki?" Sumayya tace "ka chanka" ya kalle ta ya kalli Ruqayyah da idonta yake kasa yace "hmmm. Hassan yace min hassanar sa tafi yaruwarta komai, hankali, nutsuwa, kyau, bla bla bla. Jiya haka ya kwana yana min sambatu duk ya hana ni bacci shi yasa nace yau dai sai nazo naga wannan Hassana na huta, kuma from all indications..." Ya nuna Ruqayyah "ke ce Hassanar" Ruqayyah taji sanyi a ranta, wato Hassan bai chanja ra'ayin sa ba, Baba bai yi convincing dinsa ba. Sumayya tayi dariya tace "son kai yake yi fa da yace ta fini komai" Hussain yace "na yarda dake, ta dai fiki sunkuyar da kai. Kin fita fara'a kuma daga alama zaki fita son mutane" ya fada cikin sigar tsokana, Ruqayyah ta danyi murmushi tana wasa da bakin jihab dinta sannan tace "na gane niyyar ku, so kuke ku hade min kai dan kunga baya nan ballantana ya tare min" Hussain yace "ohhh ashe kina magana. Ni na dauka ai mu biyu zamuyi hirar mu ban da ke" Yace "to Malama Hassana, nazo ne......." Ruqayyah ta katse shi "Ruqayyah" yace "what?" Tace "Ruqayyah shine sunan" yace "ohh, ni kuma Hassana ake ta gaya min a kunnuwa na" tace "wannan shi kadai yake fada ai. Special" yayi dariya sosai yana bayyana dimple dinsa, Sumayya ma ta taya shi dariyar tana cewa "Ruqayyah yaushe kika kile har haka?" Hussain yace "wallahi Hassan ya taro match. Kuma kamar kin fada a kunnuwan sa" ta dan rufe fuska alamun kunya "kar ka gaya masa dan Allah". Yace "kinsan me? Naga alamar kamar zaku daidaita da Gimbiya ta, Fatima sunanta, ita ce wadda zan aura. Tunda taji labarin ki take addu'ar ku daidaita da Hassan sai a hada bikin mu nan da wata biyar" ya zaro wayarsa yana bude lock din yace "ki saka min number dinki sai in bata ta kira ki ku gaisa" ta karbi wayar tana kallon hoton da yake kan screen din. Hoton sa ne tare da wata kyakkyawar yarinya wadda kallo daya tayi mata ta san ta fita komai, taji wani abu ya tsaya mata a wuyanta yana so ya kawo hawaye cikin idonta Ta yi sauri ta mika masa wayarsa tace "bani da waya ai ni" Sumayya tace "kasan yanzu ne muka gama secondary school, Baba kuma dama yace sai mun gama zai siya mana waya" ya dan bata rai yana tunani yace "ku ka gama ko zaku gama? ai ba'a gama exams ba an dai yi neco saura waec. Ba zakuyi waec din ba?" Suka yi shiru duk su biyun, sai ya fahimci bashi da amsa dan haka yayi saurin chanja topic din da cewa "amma dai zaku cigaba da karatu ko?" A tare suka ce "eh" yace "good, Allah ya taimaka". A lokacin ne yaro yazo ya kawo masa lemo da ruwa a jere akan karamin faranti tare da kofi akai. Sumayya ta karba sai ta bude motar ta ajiye masa sannan ta rufe. Yace "Nagode sosai. Dama kishirwa nake ji. Bara inzo in tafi kar in gajiyar daku da magana, ni bana gajiya da magana. Sai dai kuma gashi ban kawo muku komai ba" da sauri Ruqayyah tace "lah, babu komai, ai zuwan shine mafi muhimmanci akan wani abu" Sumayya ta kalle ta da mamaki sai kuma tayi saurin gyara fuskarta tace "haka ne" yace "a'a ba haka bane ba, ita kyauta ai abu ne mai kyau saboda tana kara soyayya a zukatan mutane, ko mai kankantar abu in aka baka shi kyauta sai kaji wanda ya bakan ya kara samun daraja a gurinka. Nima kunga yanzu ruwan da kuka bani ai naji dadi har cikin raina. Koda mutum ya fika komai na duniya in kuka hadu samu wani abu ka bashi, zaka kara daraja a gurinsa" Ya cigaba "wannan yasa duk wanda na hadu dashi ina kokari inga na bashi wani abu da zai ke tunawa dani kuma yaji yana son mu sake haduwa. Ku ma kuma ba zaku zama exceptional ba. Ban taho da leda ba amma na san a jikina ba za'a rasa wani abu ba, ko cash ne" sai ya fara laluben jikin sa, yayi tsaki "these days sai mutum ya duba jikinsa yaji wai bashi da kudi". Ruqayyah ta sake cewa "ba wani abu fa, ka barshi kawai". Sai ya bude motar ya bude aljihun mota, sai gashi ya dauko rafar farare bugun Abuja, ya fito ya miko wa Sumayya, ga wannan kwa sayi jambaki" Ruqayyah tayi saurin rike hannun Sumayya duk kuwa da cewa sumayyan ba wai miko hannun tayi ba tace "uhm uhm, ba zamu karba ba gaskiya." Da mamaki yace "saboda me?" Ta sunkuyar da kai still hannunta rike dana Sumayya Tace "kawai dai. Babu abinda zamuyi dashi. Mungode" Yace "ban taba jin yammata sunce babu abinda zasuyi da kudi ba sai yau. Ni sisters dina kullum complain suke kudi yayi musu kadan, kullum suna cikin siyan kayan kwalliya, jaka takalmi, da sauransu" Ruqayyah tace "mu duk wannan basu dame mu ba" Yayi ajjiyar zuciya sannan ya jefa kudin cikin mota, Ruqayyah taji tamkar zuciyarta ya ciro ya jefa a mota amma ta maze, yace "ban taba yin kyauta an dawo min da ita ba sai yau. Amma babu komai, nasan ta inda zan bullo muku" duk suka yi murmushi. Yayi musu sallama ya shiga mota suka matsa ya tafi. Sumayya ta juyo gurin Ruqayyah "what? Kece kika mayar da wannan kuɗin da kanki?" Tayi ajjiyar zuciya "kar ki kara min bakin ciki akan wanda nake ji already. Ke fa kika yi min wa'azin in chanja hali, to halin nake chanja wa" ta wuce ciki a ranta tana mitar yadda Hussain zai dauki wannan uban kudin a motar Hassan yayi kyauta dashi, Allah kadai yasan irin barnar kudin da yake yi masa. Hussain yana kallonsu ta mirror har suka shiga gida sannan ya mayar da hankalinsa fully kan tukinsa, ya girgiza kansa, shi har yanzu bai ji tayi masa ba duk kuwa da cewa bashi da wani dalili na feeling like that. He test them with money kuma sunci jarabawar amma still....... Ya dauki wayarsa ya kira Hassana (kanwarsu) "zan turo miki kudi yanzu kije ki fitar ki danyo min siyayya irin taku ta mata, kaya masu kyau, komai guda biyu iri daya. Zan kuma yi miki aike sai ki hada da kayan ki bawa drivern da yasan gidan su Hassana akai musu ita da yaruwata". Bayan sun gama wayar ya kira wani dealer na waya da yake kawo masa wayoyi yace "ina son wayoyi guda biyu, latest. Ka aika min dasu gida". Da daddare suna zaune a tsakar gida suna cin tuwon shinkafa miyar taushe har da nama, duk a cikin kudin da Hassan ya ajiye ranar nan ne. Gaba dayansu su hudu a tray daya Inna kuma da Baba suma suna ci tare, ga maganin sauro an kunna a gefe ga iska tana kada su. Baba yana basu labari "wato gobe akwai drama, an sake aiko mana fa mu koma wannan inta uku din nan. Gashi yaron nan Hassan naga alamar bai san dani a ciki ba sai dai kawai ya ganni" a lokacin suka ji tsayuwar mota sannan aka yi sallama. Sulaiman ne ya fita, an jima kadan sai gashi da bagco guda biyu da kuma karamar leda yana ta washe baki. "Wato yammatan nan sai kun bani tukuici, wai wannan kayan sako ne inji Hussain yace ace muku "asha yammatanci lafiya". Wannan littafin na siyarwa ne, in baki sani ba kika karanta a rashin sani to yanzu kin sani. In kina son cigaba ki nemi wannan number 08067081020. Episode Fourteen : The Gate man Da sauri Ruqayyah ta mike, zuciyarta fara kal kamar takarda, it is about time daya kamata suma su fara shigowa gari. Wannan talauci haka har ina! Ta tari Sulaiman a hanya tana karbar karamar ledar cikin zumudi tace "inji Hussain ko inji Hassan?" Ya dan dakata yana tunani sai kuma yace "kamar dai Hussain yace min, oga Hussain, haka yace. Amma bara in koma in sake tambayar sa" ya ajiye kayan zai juya Inna Ade tace "kai! Dawo nan. In Hassan in ma Hussain menene abin tambaya? Duk daya ne in daya ya bayar tamkar dayan ya bayar ne " Ruqayyah ta bude ledar hannunta, jikinta har rawa yake yi, tayi arba sa kwalayen waya guda biyu "wayyo Allah na" ta fada tana rungume kwalin wayar a kirjinta "Sumayya wayoyi ne, handsets ne ta so ki gani!" Sumayya ta ajiye cokalin hannunta ta mike da sauri tana karbar guda daya a hannun Ruqayyah sannan suka saka ihun murna suna rungume juna. Samarin kuma suka bude jakankunan suka fara fito da kayan ciki. Kayan sawa ne da sauran kayan bukatu na mata. Zunnur yace "wannan duk sanda ya sake dawowa sai naje na gaishe shi nima na samu rabona". Baba ya daga murya yace "lafiyar ku kuwa? Menene haka kuke yi? Menene wannan din?" Inna Ade ta karbe wayoyin hannunsu Ruqayyah sannan ta ja jakar zuwa gaban Baba, Ruqayyah ta biyo ta tamkar magnet, Inna tace "kaya ne baban biyu, Hussain ne dazu da bakanan ya zo yaga yaran nan shine yanzu ya aiko musu da kaya. Ta fada tana kokarin firfito masa da kayan, ya hade rai yace "kayan lefe ne?" Ta yi dariya "kayan lefe kuma Baban biyu? Kayan lefen ne za'a aiko driver ya kawo?" Yace "to kayan menene?" Tace "kyauta ce kawai yayi musu" ya kuma hade rai "gaya masa sukayi suka ce basu da suttura? Ko kuma sutturar jikinsu ya raina" Inna ade tayi shiru, ya juya kan yammatan, "rokonsa kuka yi kuka ce ya siya muku?" Da sauri Ruqayyah, cikin rawar murya tace "wallahi Baba ba rokonsa muka yi ba, daya bamu kudi ma cewa muka yi bama so, shine kawai ya aiko mana" ya juya kan Inna Ade "to ba da ni za'a yi wannan abin ba. Yanzu me kike tunanin zai faru idan Hassan din yace ya fasa aurenta? Ya zamuyi mu biya su kayan su? Gidan nan zan saka a kasuwa?" A hankali Ruqayyah tace "ba zai ce ya fasa ba" ya juyo yana kallonta yace "to fitsararriya, ina magana kina mayar min ko? Ta yaya kika san ba zai ce ya fasa ba? Kin san abinda gobe zata zo dashi ne?" Inna Ade tace "amma Baban biyu bana jin irin mutanen da zasu yi mana haka ne, in sun fasa ma bana jin zasu ce a biya su kayan su, kuma ma ai ba rokonsa suka yi ba" yace "to kaddara ma ba zasu ce a biya su ba. Yanzun in kika bawa wannan yarinyar" ya fada yana nuna Ruqayyah data rungume kwalin waya a kirjinta idonta ya kada yayi jawur "wannan wayar, kika kuma bata sannan leshin ta saka, idan ba'a yi auren ba ta yaya zata cigaba da girmama wannan" ya nuna wayar hannunsa "da kuma wannan" ya nuna kodaddiyar atamfar jikin Inna. Ruqayyah ta maimaita "ba zai ce ya fasa ba" yayo kanta "in kika kara Magana sai na kakkarya ki a gurin nan na zubar da kasusuwanki" Inna Ade ta shiga tsakani tana bashi hakuri "dan Allah kar ka taba ta Baban biyu, dan girman Allah kar ka dake ta" ya juyo kanta "ki tattara kayan nan ki nemi gidan wata kawarki ki kai a ajiye, duk ranar da akayi auren sai a dauko su a basu" Ruqayyah ta durkusa "Baba dan girman Allah kar ka karbe kayan nan, dan Allah ka bar mana abin mu, na tuba Baba wallahi na daina duk abinda baka so, dan Allah ka bar min kayana Baba" Inna Ade ta taya ta roko "ko ba zaka bar musu wayar ba ka bar musu kayan suma su samu suyi kwalliya, ba rokon su suka yi ba kyauta ce suka basu kuma shima Hassan din ai zai so ya ganta fes fes, gashi yan'uwansa suna zuwa, dan Allah Baban biyu kayi hakuri ka bar musu" yace "wato da saka hannunki kenan ko? Shikenan, su rike kaya amma babu ruwana" Ya juya ya saka takalmi ya fita, Inna Ade tasan fushi yayi amma kuma bata son abinda zai kara hargitsa tsakanin sa da Ruqayyah, kuma ita tana ganin babu laifi in an karbi kayan. Bayan ya tafi suka zauna suna dudduba kayan duk da dai duk jikinsu a sanyaye yake da fadan da Baba yayi, banda Ruqayyah da take ta lissafin wanne tailor ne yafi kowa iya dinki a kaduna? Gurinsa zata kai dinki. Ta dora wata doguwar riga kenan a cinyarta sai wata envelope ta fado daga cikinta, ta duba ta lura babu wanda ya gani sai ta zare ta ta saka a rigar ta. Tasan kudi ne a ciki, maybe kudin dinki, Bata so Inna Ade ta gani dan in ta gani karba zata yi kuma ba zata bata wani abin kirki ba kamar yadda wancan dubu ashirin din da Hassan ya ajiye musu duk Baba aka bawa ya siyo musu kayan abinci. Bayan sun gama suka tattara kayan suka mayar ,inna tace sai da safe sai su dauki wanda zasuyi amfani dashi su kai gurin dinki "sai dai kuma sai an nemo kudin dinkin" inji Inna. A daki bayan sun kwanta ita da Sumayya ne tace "Sumayya, kina ganin Hassan zai iya cewa ya fasa aure na?" Sumayya ta juyo tana kallonta tace "me yasa kike tambaya?" Tace "kawai dai. Baba baya son auren nan. Bansan me zai faru ba, ina jin tsoro" Sumayya tace "ki ji tsoron Allah. Kiyi ta addu'a" suka yi shiru kowa yana tunanin sa, har bacci ya fara daukan Sumayya sai Ruqayyah ta kuma cewa "Sumayya? Ya kika ga Hussain dazu? Sumayya tace "ya kuwa na ganshi? He is okay" Ruqayyah tace "ba haka nake nufi ba, ina nufin yafi Hassan haduwa ko?" Sumayya ta mike zaune tana kallon ta tace "no......bai fishi haduwa ba, kar ma ki sake wannan tunanin dan Allah" Ruqayyah ta mike itama zaunen tace "ba wani abun nace ba ai, kawai dai kamar ya fishi....." Sumayya tace "gayu? Ko kuma bagu da mota da kaya masu kyau da sababbin kudi" Ruqayyah ta fadi abinda yake ranta "ya fishi kyau" Sumayya ta runtse idonta tana jin zafin abinda yar uwarta take neman yiwa Hassan tace "bai fishi kyau ba. Ya dai fishi fari" Ruqayyah tace "ya fishi fari ko kuma dai kice shi fari ne shi kuma baƙi?" Sumayya tace "fari da baƙi duk halittar Allah ce, amma ni personally ma nafi son bakin mutum akan farin. Sannan ni bayan kalar fata banga wani banbancin halitta a tsakanin su ba dan kamannin su har abin mamaki ne dashi, hanci, baki, ido, shape din fuska, tsaho kirar jikinsu duk iri daya. Kuma Hassan yafi kama da matured kamilallen mutum shi kuma Hussain yafi kama da ladies man, ni in nice da zabi zan zabi Hassan sau goma kafin in zabi Hussain sau daya" ta koma ta kwanta tare da juya wa Ruqayyah baya cikin jin zafin maganar ta. Tana jin Ruqayyah tayi addu'a sannan ta kwanta, sai kuma tace "har dimple ne dashi" Sumayya ta kuma juyowa cikin fushi tace "gaya min gaskiya Ruqayyah, zaki juyawa Hassan baya ne ki ce hussainin sa kike so kuma? Kina ganin hakan mai yiyuwa ne?" Ruqayyah tace "Ni haka kika ji nace miki? Dan Hussain ya fishi kyau ai ba wai ya fishi komai ba ne ba, Hassan shine babba, sannan shine mai kudin," Sumayya tace "wrong. Wannan ba shine dalilin da ya kamata ki fada ba na zaben Hassan, ya kamata ki zabi Hassan ne saboda Hassan shi yake sonki ba Hussain ba, Hassan shi ya kamata ki so ba Hussain ba" Ruqayyah tace "shi nake so ɗin ai. Amma dai ai ba haka aka so ba kanin miji yafi miji kyau". Sumayya ta runtse idonta tana hana zuciyarta rinjayar ta gurin juyowa ta rufe Ruqayyah da duka. Sai taji cewa ta fahimci menene problem din Ruqayyah, ba wai bakar zuciya ko fada, ko son abin duniya ne da ita ba. A'a rashin godiyar Allah ne da ita. In taga abu zata kwallafa ranta akan tana sonsa amma da zarar ta samu to kuwa ya zama banza abinda ya fishi kuma take hari. And now she have her eyes on Hussain, and Sumayya knows that abinda yasa kawai ba zata rabu da Hassan ta makale wa Hussain ba shine saboda kuɗi, saboda tana son kudin Hassan din. Sai Sumayya taji tana tausayin Hassan. Tana kuma tausayin Ruqayyah saboda karin maganar hausawa da suke cewa "duk wanda bai gode Allah ba to kuwa tabbas zai gode wa azabar Allah". Washegari da sassafe Baba ya fita yace musu ya tafi gurin interview, suka yi masa fatan alkhairi ya tafi. A bangaren su Hassan kuwa suma da sassafe suka fita. Hassan ya kai Hussain airport ya tafi China zai siyo injinan da wancan karon bai samu damar siyowa ba, dama kudin su ne ya hada da kudin da yake account dinsa ya bayar kudin ransom din Hassan, yanzu kuwa tunda alhamdulillah kuɗin sun dawo shine zai koma ya siyo duk da cewa yasan ba zai same su a wadancan price din ba. Daga airport shi kuma Hassan gurin interview ya zarce, dan yasan cewa yanzu mutane suna nan sun taru suna jiransa shi kuma baya son ya bar mutane suna jiran sa. Baba yana zaune akan layi tare da sauran mutane, wani ya fara mita "haka kawai bayan mun riga munzo munyi interview din nan, sai da akayi wata guda kuma sannan sai a dawo a sake cewa muzo mu kuma yin wata? Shikenan yanzu a duniya masu kudi basa tausayin talakawa? Wannan ai zalunci ne, gashi kuma mum zo din sannan an shanya mu a waje kamar wasu kayan wanki". Baba yace "haba bawan Allah, ba ka san abinda ya samu mutumin nan bane ba? Masu garkuwa da mutane ne fa suka sace shi da kyar ya tsira da ransa" wasu a gurin suka fara jajanta abin wasu kuma suka ce "ina ruwan mu to mu, mu muka sace shi ko kuma mu aka bawa kudin diyyar? Ai irin wannan abin da masu kudi suke yi wa talakawa yana daya daga cikin abinda yake jawo musu irin wancan balain" Sai Baba yayi shiru kawai ya barsu, dan wadansu mutanen ko yaya ka kai da bayani ba zasu bude kwakwalwar su ba ballantana su fahimce ka. A lokacin ne Hassan ya shigo gurin da saurinsa, Baba ya lura da yadda yake amsa gaisuwar mutane cike da kulawa sannan ya dan bada hakurin jiransa da akayi sai kuma ya shige ciki. Sai Baba yaji dadi a ransa, yaji yana alfahari da shi yana kuma kara saka ran ya zamo surikin sa dan ya yarda dashi, sai dai ita yar tasa ce bai yarda da ita ba. Akayi ta kira ana shiga ana fitowa har aka zo kan Baba. Ya shiga da sallamar sa. Hassan ya amsa tare da dago kai, suna hada ido da Baba sai ya mike. "A'a, Baba, sannu da zuwa." Ya fada yana shafa kai, Baba ya zauna sannan shima ya zauna yana gaisheshi sannan yace "Baba ai da an kira ni ni sai inzo gida ba sai anzo nan ba" Baba yace "a'a, ai ba wani abin bane ba, maganar aikin nan ce ta kawo ni an kira mu ance mu sake dawowa za'a sake gwada mu" Hassan ya danyi shiru yana tunani sannan yace "wai wannan aikin dama kaima kazo wancan watan?" Baba yayi murmushi yace "nazo mana, ai ba zaka gane ba tunda mutanen da yawa" Hassan yayi shiru yana tunani, shi dai ba zai iya hana Baba aikin nan ba ba kuma zai iya bashi ba. Aiyukan na labourers, messengers da kuma na masu gadi ne, ba zai iya saka Baba aiki ba, ba zai iya aikensa ba ba kuma zai iya kullum yana bude masa kofa in zai shigo ba. A matsayin sa na surukinsa hakan bai dace ba. Ya gyara zama yace "Baba, yanzu misali in aka samu wani kasuwanci haka aka baka, zaka iya hakura da aikin nan?" Baba yace "to Hassan, ni dai ban taba yin kasuwanci ba, ni abinda na sani shine aikin karfi shi nake yi nake ciyar da iyali na har yanzu. Dan haka ba lallai ne in na fara kasuwancin ya dore ba tunda ban san kan abun ba, aikin dai shine, nasan abinda kake tunani kuma ina so ka cire komai daga zuciyarka ka gwada ni idan naci ka bani, wannan shine taimako mafi girman da zaka yi min". Hassan yayi ajjiyar zuciya yace "Baba ba zan so in ke ganin ka kana wahala ba, nafi so inke ganin ka kana hutawarka" Baba yace "amma zaka ji dadi in ka ganni ina neman halak dina ko? Hutu kuma ai da saura na tunda da karfi na ba wai shekaru na ne suka ja ba, in lokacin hutawar yayi zan huta ne". Haka suka yi ta ja in ja, a karshe dai a dole Hassan ya buga offer ya bawa Baba ya sallame shi saboda wadanda suke kan layi suna jira. Amma a ransa ya kudurce abinda ya kamata yayi akan lamarin. Baba yana zuwa gida da murnar sa ya fara bawa iyalinsa labari "alhamdulillah, aiki ya samu, aikin gadin nan dai da nake ta buri gashi nan Allah ya kawo shi" ya bude takardar yana nuna musu ita upside down. Inna ta karba tana dubawa duk da ba gane wa take yi ba fuskarta lullube da farin ciki. "Masha Allah baban biyu, Allahu ya sa albarka a ciki, Allah yasa ka fara a Sa'a. Amma na dauka ba yanzu za'a baku ba sai an gama tantancewa" ya zauna yana cewa "haka ya kamata, amma yaron nan Hassan kinsan shine mai abin, a take ya buga min takarda a matsayin mai gadi ya bani". Ruqayyah data fito daga toilet da buta a hannunta ta saki butar "mai gadi?" Ta fada, fuskarta tana nuna bacin ranta "wanne irin maigadi kuma? Yanzu Hassan din ne da kansa ya baka aikin maigadi a kamfanin sa? Wannan ai cin fuska ne" Inna Ade tace "haba Ruqayyah, in ba'a gode masa ba ai kuwa ba za'a zage shi ba. Aikin gadin bashi baban naku yake nema ba? Ba dan shi ba kuma aikin gadin ma zai iya rasawa ya koma ya cigaba da leburanci da dako" cikin bacin rai Ruqayyah tace "amma wannan lokacin ai ya wuce, wannan sabuwar rayuwa ce, a matsayin sa na wanda zai zama surikinsa ba kamata yayi ya bashi babban office a kamfaninsa ba?" Baba ya fara fada "bana son diban albarka Hassana, da wanne takardun zai bani aikin office din? Me zanyi a office din? Shi cewa yayi ma in hakura da aikin ya bani jari inyi sana'a nace a'a, saboda ni bana son dogara da wani. In ba zaki yi murna da abinda Allah ya bamu ba ki wuce ki bani guri". Bata kuma cewa komai ba ta wuce daki tana kunan zuci. Tabbas sai ta takawa Hassan burki, in dai yana sonta sai ya chanja wannan aikin, wannan ai ita zai zubarwa da kima a idon yan'uwansa da sauran jama'ar sa, shikenan kuma sai ace babanta shine mai gadin kamfanin mijinta? Ina! Ai sam ba zata sabu ba. Da daddare dan halak din yazo zance. Yaune zuwansa zance officially na farko. Yayi mata kwalliya sosai ya kuma gama shiryo kalaman da zai yi mata. Yayi packing sannan ya aika kiranta. Ita ma kuma a nata bangaren ta saka ran zai zo kuma ta shirya nata kalaman. Dan haka ana cewa ana sallama da ita ta saka hijab ta fesa daya daga cikin turaren da suke cikin kayan Hussain. A bakin kofar gidan ta tsaya ta gyara expression din fuskarta zuwa irin wanda tasan yana so, na yarinya mai kunya da nutsuwa A jikin mota ta ganshi a tsaye ya rungume hannunsa. Farin yadi ne a jikinsa mai taushi wanda ya karbi kafar jikinsa sosai ya kuma fito da kyawun gyararriyar sumar kansa wadda ta sha gyara kuma take a bude. Bakin takalmi, bakin agogo da bakin tabarau, sai kuma kyakkyawan murmushi a fuskarsa. Zuciyarsa kuma cike da soyayyar hassanar sa. Tayi masa murmushi itama. Sannan ta tako sannu a hankali tazo inda yake ta dan durkusa kadan ta gaishe shi. Ya amsa yana kara fadada murmushin sa. "Barka da fitowa uwar yayan Hassan" ta rufe fuska da hannunta. Yayi dariya yana karewa siraran dogayen yatsun hannunta kallo ya gyara tsayuwarsa yace "kinyi kyau sosai. Sai dai matsalar daya ce" ta bude fuskarta amma idanuwanta a kasa tace "wacce matsala kenan fa?" yace "wannan kunyar nake rokon alfarmar a rage ta ko yaya ne a bani dama inga cikin idanuwanki. Kullum su nake gani cikin baccina amma kuma a zahiri an hana mini ganin su" ta fara kokarin sake rufe fuskar ya hade hannayensa a guri daya yace "dan Allah, a tausayawa marayan Allah". Tace "maraya?" Ya cire glass din idonsa Yace "eh. Baki sani bako?" Tace "Allah yaji kansa" yace "Allah yaji kansu zaki ce. Duk su biyun babu" tace "ohhh, ya Salam, na dauka ai....." Yace "Aunty? Ba ita ta haife mu ba, amma uwa ce a gare mu, haihuwar mu ne kawai baya yi ba". Ko cikin abokan sa ba kowa ne yasan cewa ba Aunty ce ta haife su ba amma wannan ai Hassana ce, wannan aurenta zaiyi kuma aure akan gaskiya ake gina shi. Tayi masa gaisuwa sai ya bata brief labarin asalinsu da kuma cikakkiyar dangantakar su da Aunty, ya kuma lissafa mata sunayen kannensa mata sannan ya gaya mata irin soyayyar da yake wa yan'uwansa. Itama kuma sai ga bashi labarin nata asalin da sunayen nata family members din da stage din karatun kowanne. A lokacin ne ta ga time din shigar da maganar Baba yayi. Tace "ammm akan maganar Baba" sai ta dago kai kamar yadda tayi plan cewa zata saka idonta cikin nasa ta gaya masa ya chanja wa baban ta aiki. Amma the moment da suka hada ido sai komai nata ya ruguje, wannan mutumin ba wannan mutumin bane daya same ta a toilet yace mata "help me Please" wannan wani mutumin ne daban. Wannan is so strong and so sure of himself. Wannan mutumin will not be controlled, not by her, not by anyone. Ta sauke idonta kasa tana jin komai yana rushe mata, plan dinta duk ya ruguje, yace "uhum, ina jinki, me zaki ce min a game da Baba?"cikin sanyin murya tace "cewa zanyi dama an gode madallah da aikin da ka bashi" yace "noo. Babu godiya ai a tsakanin mu. Baba ai babanane, tunda nawa baban ya mutu kinga ai yanzu na samu Baba ko?" Ta kuma cewa "an kawo mana sako kuma, mungode" ya dan bata fuska yace "sako kuma? Tace "eh" a ranta tana tunanin bashi din bane ba kenan, sai ta kara da cewa "Hussain yazo jiya, da dare kuma sai ya aiko mana da wayoyi ni da Sumayya da kuma kaya" Hassan yayi dariya yana bayyana farin cikin sa yace "ya kyauta sosai. Ko gaya min bai yi ba. Hussain yana da kirki sosai yana kuma da kyauta sosai. Kinga ya rigani, ina ta lissafin siyan wayar amma bana so inyi laifi a gurin Baba tunda ban sani ba ko ba ya son kuyi waya yanzu" Ta harare shi ta gefe yadda ba zai gani ba sannan tace "ai kuwa yayi fadan, sai da kyar ya bari" yace "to Alhamdulillah tunda ya bari ɗin, yanzu an kunna ta kenan a bani number in samu ta rage dare? Kinsan abinka da gwauro" tace "bamu bude bama, sai mun siyo sim card" yace "gobe zan aiko, da sassafe ma kuwa" Sun dan jima suna hira, ita kanta Ruqayyah tasan taji dadin hirar Hassan yadda yake komai a nitse, sai kuma yace "naga alamar akwai sauro, gwara in barki ki koma gida kar ya cizar min ke ko?" Da haka suka yi sallama ya raka ta bakin kofa ta shiga sannan ya juyo. A lokacin ne wata taxi ta shigo layin, mai taxin ya dan wuce motar Hassan kadan sannan yayi packing. Ya fito a dai dai lokacin da Hassan yake kokarin bude kofar motar sa. Ya mika masa hannu, sai da Hassan ya kare masa kallo ya ganshi dan karamin saurayi da ba zai wuce ashirin zuwa ashirin da biyar ba, ya mika masa nasa hannun suka gaisasai ya nuna gidan su Ruqayyah yace "dan Allah nan ne gidan su wasu twins masu kama daya?" Hassan ya gyara tsayuwarsa yana studying saurayin yace "eh nan ne ya akayi?" Saurayin yace "Okay dama gidan nake nema shikenan na gode" Hassan ya kuma cewa "me yasa kake neman gidan su?" Saurayin yace "ohhh, dama muna haduwa ne dasu yawanci a school dinsu, to kwana biyu ban gansu ba shine nazo in duba su kuma mu gaisa" Hassan yace "really? Da wa zaka gaisa a cikin su?" Saurayin yace "Ruqayyah nasan ba zata kula ni bama, so.....da Sumayya zamu gaisa" Hassan yayi murmushi ya nuna masa kofar gidan yace "bismillah" sannan ya shiga motarsa ya bar unguwar zuciyarsa fara kal. Hassanar sa mai kamun kai ce ita, Hassanar sa mutuniyar kirki ce. Wannan littafi na siyarwa ne, in kina son siya ki nemi wannan number din 08067081020 Episode Fifteen : The New Driver Adam ya bi motar da kallo har ta kule, shi dai bai ga alamar wannan mutumin daga wannan gidan ya fito ba dan bai ma yi kama da unguwar ba ballantana gidan. Waye shi? Kwalliyar da yayi da kamshin da yake yafi kama dana wanda yazo zance, amma zance gurin wa? Ya kalli nashi kayan jikin, basu mutu ba amma kuma ba zasu tsaya a jere dana wanda ya bar gurin ba. Ya dan tsafa kansa yana kallon gidan, shi bai taba zuwa zance ba, sai kuma ya tambayi kansa in da gaske zancen yazo. Shi dai yasan yaran sun tsaya masa a rai, kamannin halittar su da bambancin halayyar su yana bashi mamaki kuma yana kara sawa yaji tsoron Allah a zuciyarsa. Wannan ya sa ya kasa cire su a ransa, sai ya mayar da makarantar su gurin zuwan sa kullum idan lokacin daukan dalibai yayi, a haka watarana ya gansu wata rana kuma sai dai yayi ta rarraba ido ba tare daya gansu ba, haka zai hakura ya koma gida. To yanzu kuma kusan sati uku kenan kullum in yaje school din baya ganinsu, sai kawai yaji zuciyarsa babu dadi, haka kawai yaji shi lallai yana so ya gansu duk da cewa bashi da wani dalilin ganin nasu. Wannan yasa yanzu yana tashi daga aiki ya taho unguwar su yazo dai dai inda yake sauke su ya fara tambayar ko akwai wanda ya san su. Bai sha wahala ba "ohh Sumayya da Ruqayyah kake nufi? A can layin suke amma bansan gidan su ba, sai dai in kaje can din ka tambaya" yana shiga layin ya tambaya sai aka nuno masa gidan, sai kuma yaga wannan hadadden saurayin yana kokarin barin gurin. Yayi ajjiyar zuciya yana tattaro duk courage dinsa. Bai san me zai ce musu ba, bai san kuma yadda zasu karbe shi ba. In sun tambaye shi dalilin zuwansa bai san me zai ce musu ba. But he is going to try, ko Ruqayyah zata wulakanta shi yasan Sumayya ba zata wulakanta shi ba, kuma shi bai damu da wulakanci ba, in da sabo ya saba, babu abinda bai gani ba. Ya ci dubu sai ceto. Ya kira yaro ya tura shi, "kaje kace wai Sumayya tazo inji Adam" sai yaji abin odd, sai yayi murmushi sannan ya jingina da jikin motar taxi dinsa. Yaron yana shiga ya bude muryarsa ya kwada sallama sannan ya fadi sakonsa "kutumelesi! Wannan dan rainin hankalin me ya kawo shi gidan mu? Uban waye ya nuna masa gidan mu" Inna Ade tace "ke Ruqayyah! Menene haka? Ban hana ki irin wannan maganganun ba?" Ta juya kan Sumayya "waye kuma Adam? A ina kika samo shi shi kuma?" Sumayya ita ma data cika da mamakin jin adam din a gidan su tace "Inna ban san yadda akayi yasan gidan mu ba, mai taxi ne kawai da wani lokaci yakan kawo mu gida daga makaranta" Inna tace "dan taxi? Dan taxi fa kika ce min Sumayya, menene hadin ki da dan taxi?" Sumayya tayi kamar zata sa kuka tace "wallahi inna babu komai a tsakanin mu, kawai......" "Babu komai a tsakanin ku yasan sunan ki?" Yaron da yake tsaye a gefe yace "me zance masa?" Sumayya ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannunta, Inna tace "ki fita, ki tambaye shi me ya kawo shi, in bai gaya miki dalili mai kyau ba ki ce kar ya kara zuwa gurinki, bana son jaye jayen mutane kina ji ko?" Sumayya ta mike da sauri ta shiga daki, Ruqayyah ta mike ta bita "ki bar ni inje in korar miki shi, irin wadannan mutanen in ba korar kare aka yi musu ba ba hakura suke yi ba" Sumayya ta saka hijab dinta tace "thank you, but I don't need your help. Zan iya yi masa Magana da kaina". A jikin taxi dinsa ta same shi kansa a kasa yana daddanna wayar sa, fuskarsa da murmushi. Sai da tayi sallama sannan ya dago yana kallon ta yana kara fadin murmushin sa yace "ameen wa alaikumus salam Sumayya. Nice to see you a cikin kayan da ba uniform ba" sai ta samu kanta da yin murmushi "it is nice to see you too" sai kuma ta tuna da abinda tazo gaya masa "ya akayi kazo gidan mu Adam? Me kuma ya kawo ka gidan mu?" Ya mayar da wayarsa aljihu yace "laifi ne kenan dan na nemo gidan ku? In laifi nayi kiyi hakuri. Nazo ne kawai dan in ganki, ko shima laifi ne?" Ta girgiza kanta "wannan ba dalili bane ba, babata da kyar ta barni na fito kuma cewa tayi inzo in sallame ka, idan kuma Baba yazo ya ganni anan tare da kai inajin sai ya targada ni, dan haka dan Allah Adam ka tafi kafin yazo ya ganmu" Yayi ajjiyar zuciya, fuskarsa tana nuna rashin jin dadi yace "lucky you. Yar gidan inna da Baba. Inna zata ce miki bari Baba kuma zai yi fada, kinji dadinki. Shikenan bara in tafi. Dama kwana biyu bana ganin ku a school ne shine nace bara inzo in duba ku ko lafiya?" Sai taji kuma babu dadi, taji something a tone din da yayi magana dashi ya taba ta tace "lafiya lau Adam. Mun gode sosai. Mun gama exams ne dama neco kadai zamuyi. Mun gode sosai da kulawa" ya gyada kai yana cewa "I understand. Allah ya bada Sa'a. Allah kuma yasa kuyi amfani da result din ku. Ni ga nawa nan a ajjiye suna ta kura" ya dan huri iska ta bakinsa, trying to hide his emotions ya sake cewa "bara in tafi nasan zaku je islamiyya ko?" Ta girgiza kanta "mu bama zuwa islamiyya ai. Inna Ade ce islamiyya mu, a gurinta muka koyi komai na ilimin addini da kuma duk wata tarbiyya ta musulunci" yayi murmushi "yan gata, kunji dadi. Lemme go kafin Baba yazo yayi fadan ganin ki tare da ni" sai taji tana son jin dalili chanjawar fuskarsa, amma kuma tana tsoron jan maganar kar tayi kaifi a gurin Inna Ade ko Kuma kar Baba yazo ya same su. Ta tsaya tana kallon sa har ya bude motar ya shiga sannan tazo kusa da motar ta sunkuyo tace "thank you Adam for the visit. I relly appreciate it" yayi murmushi yace "thank you for seeing me" ya ja motarss yana daga mata hannu ya tafi. Ta bi motar da kallo har ta kule, sai taji a ranta tana son ta ji abinda yake zuciyarsa, tana son taji menene labarin sa, kuma taji tana son su sake haduwa watarana. Da safe kafin Hassan ya tafi office ya biyo ya kawo wa Ruqayyah sim card dinta. Tana fitowa ta gashi a mota ta gaishe shi tace "na dauka aikowa zaka yi ashe da kanka zaka zo? Ko Hussain ai da sai ka aiko?" Yayi dariya sosai yace "Hussain? Hussain baya min ladabi ai, yace da minti biyar kawai na girme shi, baya ma kasar nan ya tafi China jiya. Akwai yara dai da zan iya aikowa amma I didn't want to miss the chance to see you, ina so inga wannan early morning look din naki" tayi murmushi tana dan juya masa baya tace "bayan ko wanka banyi ba" yace "and yet, you look like a model". Ta dauko kwalin wayar da har yanzu bata ko farke ta ba, amma bai kar ba ba sai ya sa hannu ya bude mata daya side din motar yayi mata alama da hannu cewa ta zagaya ta shiga. Ta zagaya ta danyi jim tana kallon motar kafin ta shiga, ita bata taba shiga cikin private car ba sai yau, kuma tasan wannan motar ko a cikin motoci sunanta mota. Ta zauna tana zagaye idonta a cikin motar sai suka hada ido da Hassan yana mata murmushi, sai ta nuna alamar jin kunya, cikin kwantar da murya yace "you like it?" Ta gyada kanta tace "tayi kyau, sosai" yace "thank you. Sai anyi bikin mu zan koya miki mota, kinga in zaki je unguwa sai ki dauki mota a gida kawai ki fita abinki ba sai kin nemi driver ba" tayi murmushi, fuskarta cike da annashuwa sai kuma ta girgiza kanta tace "ni me zanyi da mota. Ni babu inda ma zan ke zuwa" yace "dan dai baki saba yawo babe ba, ba dan kar Baba yayi fada ba da sai in kaiki yawo yanzu kiga gari" ta mika masa wayar hannunta tace "ni dai hada min wannan wayar, ni babu yawon da zanje, ni ba inda nake zuwa". Ya karba ya bude ya fito da ita yana nuna mata, yana jin dadin excitement din fuskarta kuma ya fahimci a matsayin ta na wadda bata taba yin waya ko raka ni kashi ba dole ta zana excited idan tayi irin wannan wayar. Ya kunna ya saka mata komai yayi mata duk setting din daya kamata. Yana yi yana mata bayani dalla dalla na yadda zata yi operating komai. Sai da ya tabbatar ta gane sannan yayi kamar zai mika mata sai kuma ya juya wayar ya dauke ta a hoto. Ya jima yana kallon hoton sannan ya miko mata, itama ta kurawa hoton ido, camera din ta fito da fuskarsa sosai tayi kyau, ga background na mota mai kyau, ga kuma kyakkyawan murmushi a fuskarta, sai taga kamar ba ita ce ba, sai taga kamar irin yayan masu kudi din nan wadanda basu da matsalar komai a rayuwa. Yes, that's who she wants to be, yes, that's who she is now. Da yamman ranar ta shiga makotansu gidan su Minal, a tsakar gida ta same ta taba kwance tana daddanna wayarta. Ruqayyah ta zauna tana cewa "albishirinki Minal" sai ta mika mata sabuwar wayarta. Minal ta karba sannan ta mike zaune baki da ido a bude. "Na shiga uku! Ruqayyah a ina kina samu wannan wayar" Ruqayyah tayi dariya tana jinta tana yawo a saman gajimare. Sai dai tayi plan din ba zata gayawa friends dinta ba tukunna, so take tayi surprising dinsu, so take kawai sai dai su ga iv. Tace "a inda nasamu bashi da muhimmanci, abu mai muhimmanci shine na samu din" Minal ta kuma juya wayar a hannun ta sannan tace "Ruqayyah wannan fa babbar wayar mijin Aunty Hafsa ne. Irin wannan din yaso siya ya kasa shine ya sayi karamarta " (yayarta, wadda da kudin mijinta suke ji a gidan su' Ruqayyah ya kara kumbura tace "kuma gashi ni nayi ta ba. Kinga, ni zuwa nayi ki bude min irin su facebook din nan da sauran su. Ni na kasa gane yadda zan bude" Nan take Minal ta bude mata facebook account, tayi mata komai sannan tace "saura hoton da za'a saka miki" Ruqayyah tayi sauri tace "akwai wani hoto, zaki ganni a cikin wata mota shi zaki saka min" Minal ta budo hoton sannan tace "wannan motar kuma fa, motar waye?" Ruqayyah ta juya idonta tace "ina ruwanki, in ba zaki saka min ba ki barshi" sai Minal tace "daga tambaya? Ke fadan ki bw matsalar ki. Kinga, a shawarce kar ki saka hotonki, saboda shi facebook guri ne na maza da mata gabaki daya, kinga babu dadi ki saka hotonki maza suna ta kallonki, gwara ki saka wani abu haka" Ruqayyah ta gyada kai tana daukan shawarar ta, yasan Hassan ba zai kasa yin facebook ba, kar yaje ya ga hoton ta kuma a samu matsala, amma kuma taso yin fafa da wannan hoton, sai dai dole ta hakura. Tana komawa gida ta tarar da Sumayya a zaune a daki ita kadai, daga ganin fuskarta tasan akwai problem, tace "ke kuma fa? Lafiya?" Sumayya ta dauko farar envelope ta miko mata tace "wannan kudin na gani a cikin rigar ki, kudin menene" Ruqayyah ta bata rai tana miko hannu tace "kudi nane, bani abina? Sumayya tace "a ina kika same su? Yaushe aka baki su" Ruqayyah tace "a cikin kayan nan aka sako su, inna tana gani nasan Baba zata bawa ninkuma ina bukatar su shi yasa na boye" Sumayya taji ranta ya kuma baci tace "tun yanzu? Tun yanzu Ruqayyah har zaki fara boye abin duniya dan kar family dinki su mora, nan gaba me zai faru kenan?" Ruqayyah ta warce kudin tace "ai na bayar da wancan, wannan kuma ina bukatar sa kuma bazan bayar ba" Sumayya tace "kin duba kinga yawan kudin nan kuwa? Na tabbatar kudin sun isa ayi katangar gidan nan dasu, kinga ai kema in Hassan yazo ba zaki ji kunya gidan ku babu katangar arziki ba" Ruqayyah ta daga kafada tace "a haka ya ganni, a haka kuma yace yana sona. In baya son gani gidan nan ya gina mana wani". A ranar bayan Baba ya dawo gida Sumayya ta dauki wayarta ta kai masa "Baba ga wannan, ni babu abinda zanyi da ita kuma naga kamar zata yi tsada sosai, a siyar da ita mu gani ko kudin zai isa ayi katangar gidan nan" Baba ya karbi wayar yana jujjuya ta sannan yace "Nagode sosai Hussaina. Allah yayi miki albarka". Kwana biyu bayan nan Hassan ya zo gurin Ruqayyah zance, sai yayi mata bayanin cewa a karshen satin nan suke saka ran zuwa Gombe gabaki dayansu shi da yan'uwansa, idan kuma sunje zai shigar da maganar auren su dan azo a nema masa. Ruqayyah murna kamar tayi rawa amma ta maze tace "da wuri haka? Da ka bari ai an dan kara kwana biyu mun kara fahimtar juna ko?" Yace "menene baki fahimta nawa ba in fahimtar dake yanzu? Ni dai a bangare na babu wani abu da nake ganin ya kamata in kara sani, abinda na sani ya gamsar dani sosai" Kamar ranar nan, suna yin sallama tana shiga gida sai ga Adam a tashi motar yayi packing a kusa da Hassan. Hassan ya gane motar, Adam kuma ya gane Ruqayyah duk da bai ga fuskarta ba, a ransa yace "ta tabbata zance yake zuwa" ya fito kamar ranar nan suka gaisa da Hassan sai yace "ashe zance kake zuwa gidan nan? Gurin Ruqayyah" Hassan ya rungume hannunsa a kirjinsa yana studying yaron gabansa yace "kai kuma zance kake zuwa gurin Sumayya" Adam yayi dariya "noo, ba zance nake zuwa, na shigo ta nan layin ne kawai dan maybe in samu in ganta, but in na aika ba lallai ma a barta ta fito ba dan ranar nan ma da kyar aka barta ta fito" Hassan yace "and you want to see her?" Adam yace "yes, I do. I really do. But I guess babu bahaushe Musulmin da zai bar yarsa take kulani ko". Hassan yace "no, no, no. Kar kace haka. Babansu yana da kirki sosai. In baka shawara? Kayi kokari ka ganshi ka gaya masa abinda yake ranka, bana jin zai ki amincewa. Ina iyayenka?" Yace "basa nan" sai ya dauke kansa gefe, Hassan yace "a ina kake da zama" yace "daki nake renting, ni da friend dina" Hassan yace "school fa?" Adam yace "na gama secondary, zan cigaba in na tara kudin". Hassan ya dauko wayarsa ya kira layin Ruqayyah. "Sorry na danyi mantuwa. Turo min Sumayya Please" sai ya kashe ya mayar da ita aljihu yace "gata nan fitowa, you can see her" Adam yayi murmushi, Hassan yana lura da yadda yaji dadi sosai. Ruqayyah ta ajiye wayar tana cewa "yes! Sumayya kije waje Hassan yana kiranki, sako zaki karbo min" Sumayya bata ce komai ba ta dauki hijab dinta ta fito, har yanzu haushin yaruwarta take ji na hana babansu kudi duk da tasan yana bukatar su. Tana fitowa taga Adam a tsaye tare da Hassan, take taji bakin cikin ta ya yaye farin ciki ya maye gurbin sa, ta rufe baki tana dariya, shima dariyar yake yi yana tahowa inda take. Sai Hassan yaga sun bashi sha'awa sosai, Sumayya tace "Adam? You are here" yace "yes am here, na shigo layin, hoping to see you sai wannan bawan Allah ya taimake ni ya kira min ke. Da fatan ranar nan ba'a yi miki fada ba" tace "no, ai cewa tayi kar in dade kuma ban dade ba" Ta juya tana kallon Hassan tace "ina yini" yace "hmmm. Sai yanzu kika ganni? Ai ni har nayi fushi" ta karaso tana cewa "ayi hakuri babban yaya, ya zanyi in kasa ganinka bayan gaka a gabana?" Yace "na sani ko wani ya rufe miki ganin ki?" Ta danji kunya kadan tace "haba dai". Ya danyi murmushi sai ya dauko complimentary card dinsa ya mika wa Adam yace "come to my office duk sanda ka samu dama, I might get something for you" ya karbi katin yana kallon sunan sai yayi dariya yana rike baki, ya juya kamar wanda zai rungume Sumayya sai kuma ya rungume hannunsa, yace "thank you sir, thank you so much. Amma bani da credentials din da zaka bani aiki dasu" Hassan yace "I am already getting an idea na aikin da zan baka, ba ka iya driving ba?" Adam ya kalli motarsa yace "sosai ma kuwa" Hassan yace "hmmmm, then maybe it is about time da ya kamata Hussain ya samu personal driver. Yana dawowa daga wannan tafiyar zan zuga shi ince bai kamata dangoten Kaduna yake driving kansa a mota ba, he will like you, tunda naga kana da tsafta da gayu, a matsayin drivern Hussain zaka sami daki a gidan mu, zaka ke samun abinci kaga baka da wannan matsalar, Hussain ba mazauni bane ba, dan haka you will have alot of hutu im baya nan, in yana nan ma am sure sometimes mantawa zai ke yi da kai. Motar ka sai ka vayar ana yi maka haya ana kawo ma ka balance, that, plus albashinka and all the goodies da za kake samu daga gurin Hussain zai ishe ka kayi sponsoring karatun ka" Adam daya kasa rufe baki ya juya ya kalli Sumayya ita ma da take ta murmushi yace "sai in biya mana makaranta ni da Sumayya mu tafi tare" Hassan ya gyada kai yace "I like you, I really like you". Wannan littafin na siyarwa ne. In kina so kiyi min magana ta wannan number 08067081020. WhatsApp only, banda calls please. Sixteen : The Houses Bayan Hassan ya tafi Sumayya tace wa Adam "ka je fa ka same shi din, yana da kirki sosai" yace "zan je, gobe weekend amma ranar Monday first thing in the morning zanje in same shi" ya sake jujjuya card din a hannunsa yace "H & H fa" tace "yes, tashi ce" yace "to who is Hussain?" Tace "dan gayun brother dinsa" suka yi dariya gaba ki daya. Yace "yanzu in zan iya biya mana school tare, Baba zai barki ki je?" Tace "it is so nice of you to say that Adam. But bana jin Baba zai yarda ka ce zaka boya min. Shima yana da burin ya biya mana muyi karatu sannan kuma Baba mutum ne da bai fiya son ayi masa abu ba, yafi son komai yayi da kansa in dai zai iya" yace "Ruqayyah fa? Ita ma zata yi karatun? Naga....." Ya nuna inda Hassan ya tsaya, ta dan bata rai tace "tare muke da niyyar zuwa, but yanzu all of a sudden Hassan yazo da maganar aure kuma nasan ba zai jira ta gama makaranta ba, to gaskiya ban sani ba ko zai barta bayan aure ta cigaba da karatu" Adam yace "yanzu misali, just for example, idan..... Idan na aure ki nima, kinga ai ni zan biya miki karatu ko?" Tayi dariya, "Adam kenan, aure fa kace" ya dan hade rai "aure fa, ko ba zaki auri Igbo ba" ta dago kai tana kallonsa, ita dai tun ganinsa na farko ta san ba Bahaushe bane ba amma bata iya tayi placing yarensa ba. Kuma bata tantance ko musulmi ne ko akasin haka ba. To yanzu gashi ya fada mata, Igbo. Akwai kabilar da suka fi Igbo samun sabani da hausawa kuwa? Ta sunkuyar da kanta ai taji shima yayi shiru bai kuma cewa komai ba, ta dago kai sai taga bacin rai a fuskarsa, ya juya yana cewa "it is okay, bara in tafi before I put you in trouble" yayi taku biyu tace "Adam" sai ya dakata amma bai juyo ba, ta karasa inda yake ta zagaya ta gabansa tana noticing kirar jikinsa, tace "Igbo, hausa, fulani, yaroba, Igala, kanuri duk ba shine mai muhimmanci ba, babu wanda yafi wani muhimmin a gurin ubangiji sai wanda yafi tsoronsa" ya gyada kai yace "na sani, but a gurin ubangiji kika ce ai, ni kuma a gurinki nake tambaya, can you.......marry an Igbo guy". Ta kuma sunkuyar da kanta kasa, maganar aure ba karamar magana bace ba, sai ta juya maganar tace "ba la san hausawa yanzu cewa suke auren wani yaren yafi dadi ba? Yace "hausawa ne suka fada ko ke ce kika fada? Ni view dinki nake son ji ai bana haudawa ba" da daga kai tana kallonsa a cikin hasken farin wata, ita dai tasan he is the most handsome man data taba gani a rayuwarta, fuskarsa irin fuskarnan ce da in ka kalla ba ka iya cire ta daga ranka. Tace "my view, tribe doesn't matter, what matters is the person himself. In dai kasan mutumin da zaka aura kuma dabiun sa sunyi maka kuma shima haka, tribe dinku doesn't matter" yayi murmushin daya kara wa fuskarsa kyau yana kallon cikin idonta yace "then, nayi miki?" Tayi kokarin cire idonta daga cikin nasa amma sai taji ta kasa, sai taji bata so, she want to live there forever. Kasa kasa tace "I can't say, I don't know you" shima kasa kasa yace mata "I know you and I like you" taji maganar sa ta shige ta har cikin ƙafafuwan ta sai tayi saurin cire ionta daga nasa ta zagaye shi tana tafiya zuwa gida tace "good night Adam" bai juyo ba yace "good night Sumayya". Taji sautin dariya a cikin muryarsa itama sai tayi murmushi. A tsakar gida still da murmushi a fuskarta suka kusan cin karo da Ruqayyah. Yace "na jiki shiru, nace bara inbi sawu inji ko lafiya" Sumayya ta wuce ta tana cewa "ya tafi ai yariman naki, tun dazu" Ruqayyah ta bita a baya "and? Ina sakon?" Sumayya tace ba tare data kalle ta ba "bai bani ba komai ba, gaisawa kawai muka yi, sai dai ki kira shi ki sake tambayarsa ko ya kuma mantawa ne". Ruqayyah tayi tsaki tana kananan maganganu ta wuce Sumayya ta shige daki. Sumayya bata gaya mata zancen zuwan Adam ba kuma bata da niyyar gaya mata din saboda tasan zata iya gayawa Inna, ita kuma tafi son in Inna zata ji ma ya kasance daga bakinta zata ji bana wani ba. A dakin su ta kwanta still da murmushi a fuskarta, idonta a lumshe tana tuno murmushin Adam, Ruqayyah ta kalle ta tayi tsaki tace "this one that you are smiling kamar wadda aka yiwa kyautar mota" Sumayya ta sake murmushi tace "abinda aka bani yafi mota muhimmanci a gurina. But I guess ke ba zaki fahimta ba". Saturday family din Aunty baki dayansu banda Hussain da baya kasar suka tafi Gombe, a can suka yi weekend, a cikin weekend din ne kuma suka shigar da maganar neman auren da Hassan yake yi suka nemi alfarmar azo a nema masa officially. In kuma anje naman an bayar din suna so a saka rana ta zama daya data Hussain da kuma Hassana. Ranar Monday suka dawo da safe, Hassan ne ya sama suka yi fitowar sassafe saboda yana so yaje office akwai abubuwa da yawa a gabansa. A office din ne bayan ya gama abubuwan da yake yi sai yaga kiran wani agent da ya saka ya samo masa gida. Ya daga a ransa yana tunanin an samu kenan. Dan yasan in baa samu ba mutumin ba zai kira shi ba tunda specifically ya yi masa bayaniy irin gidan da yake so, hatta girman gidan, yawan dakunan da tsarin dakunan sai daya lissafa masa. Shi komai nasa a tsari yake yin sa and he sticks to wannan tsarin nasa. Ba dan emergency yake neman gidan ba ma da gina wa zaiyi yadda zai yi exactly irin yadda yake so. Tun sanda Allah ya hada shi da Ruqayyah da family dinta yake tunanin mai ya kamata yayi musu, farko yayi tunanin kudi, sai kuma ya fahimci Baba ba mutum ne mai son ake bashi kuɗi haka nan ba, ya san in zai karba ma sai sun kai ruwa rana kamar yadda suka yi ta yi akan aiki, kuma shi yana ganin girman sa sosai baya son yayi tayi masa musu. Wannan yasa ya yanke shawarar siya masa gida saboda ganin yanayin yadda gidan nasu yake ciki. Dama yana da kuɗin sa da yake tarawa, kudin albashin sa a matsayin sa na chief of staff na H &H group of companies. Tun sanda Hussain ya bude kanfanin sa na farko ya bashi wannan matsayin kuma shi yake running kusan komai, ma'aikata da yawa basu san Hussain ba Hassan suka sani. Da yawa daga cikin su kuma suna yi masa kallon kamar shine mai gurin shi kuma bai taba tsayawa yayi wa wani bayani ba saboda yana ganin babu bukatar yin bayanin. Albashin sa account dinsa yake shiga kawai, baya taba using dinsa sai dai in zai siya wa kansa wani personal abu kamar kayan sawa ko kuma in zaiyi wa wani kyauta, amma duk kudin da ake kashewa a gidan su, duk bukatun Aunty da yammatan ta, duk motar da take cikin gidan na Hussain ne, shi yake komai amma ta hannun Hassan, check book ya samu duk yayi signing ya ajiye a dakin sa yace da Hassan "duk abinda ake bukata kawai ka cike ka fitar ba sai an neme ni ba, ni bani da lokaci kar inje inke manta important things". Amma Hassan bai taba cirar ko da kwandala yayi buƙatar kansa ba..... Da lissafin sa shine zai yi amfani da kudinsa gurin siyawa kansa gidan da zasu zauna shida iyalinsa in yayi aure, amma kuma sai ga Hussain ya sai gida ya fara gina musu tare. Abinda ya saka baiyi rejecting ba shine idea din tayi masa kyau na zamansu tare, iyalinsu tare sannan kuma a kusa da su Aunty. Yana ganin wannan zai karfafa zumunci a tsakanin yayansu da matansu. Amma duk da haka sai ya kuduri aniyar gina gida da kudinsa ya ajiye shi a matsayin nasa in yaso ko haya ya bayar. Tunda dai gidan da zasu zauna din na Hussain ne dan bai furta yace ya bar masa kyauta ba, kuma baisan abinda gaba zata haifar ba. Sai dai kuma yanzu ga Hassana ga iyayenta da kannenta, wanda Hassan yake jin yanzu kamar sun zama responsibilities dinsa. Dan haka yayi niyyar daukan kaso mai tsoka a cikin ajjiyarsa ya siya musu gida. Shi nashi ginin can wait. Ya daga wayar yana cewa "an samu kenan" mutumin yace "an samu oga Hassan, naga kamar yayi dai dai da bukatar ka sai dai in ka samu lokaci sai inzo muje in kai ka ka gani kafin ayi finalising" Hassan ya yarda da hakan, gwara yaje ya gani da idonsa kar ya sayi abinda bashi yake so ba. Washegari da sassafe kafin yaje office agent din yazo ya dauke shi suka je ganin gidan. Madaidaici ne kamar yadda ya bukata. Cikin gidan akwai dakunan bacci guda uku da kuma madaidaicin falo kowanne daki kuma da bandaki a ciki. Sai tsakar gidan da aka rufe kasan sa da interlocks, sai kitchen da bandaki a tsakar gidan. Akwai kuma dan siririn soro, a cikin soron akwai daki wanda yake da kofa guda biyu daya ta soro daya ta tsakar. Ya gyada kai cikin gamsuwa, komai yayi yadda yake so kawai dai yaso a samu shago a kofar gida inda yayi niyyar zubawa sulaiman kayan provisions ya ringa siyarwa inya dawo daga school. With that and salary din daya yi doubling ya bawa Baba, da kuma shi a matsayin sirikin gidan, yana ganin they are set for life. A take ya saka hannu a takardar siyan gidan sannan kuma ya tura kudin, duk da cewa yayi tunanin cewa gidan yayi tsada da yawa but for Hassana it is worth it. Yayi tunanin irin farin cikin da gidan zai saka ta, ya tuno irin farin cikin da ya gani a idobta ranar daya ke kunna mata wayar da Hussain ya siya mata. Briefly ya sa akayi furnishing gidan, light furnitures irin wanda yasan ko shi zai iya amfani dasu sannan wadanda yasan su din zasu yi murna dasu sosai. Daga nan kuwa sai ya sake ware wasu kudin masu kauri ya kaiwa Aunty "Aunty maganar lefe, nace kina ganin wannan kudin zai isa?" Ta duba kudin tace "zai isa mana, in dai ba irin na Hussain kake son kayi ba" ta karasa tana dariya, shima yayi dariya yace "Allah ya kiyaye, wadannan barsu kawai, Hussain shi kudi kamar mintsinin sa suke yi" sai kuma ya kara da cewa "kuma shi saboda irin gidan da ya debo wa kansa aure ya saka banyi masa maganar ya rage kayan ba, abu ne na manya da manya" ya fada sarcastically. Aunty ta girgiza kanta tace "kasan halin Hussain ko ba gimbiya Fatima bace bama irin abinda zai yi kenan. Ballantana kamar yadda ka fada ai shi tuwon girma miyarsa nama ce" Hassan ya mike yana cewa "ai shikenan. Sai yaje yayi ta cin naman" Aunty ta sake daukan kudin ta juya tace "amma fa in bai isa ba zamu ce maka ka karo" yana dariya yace "manage it aunty, bafa gimbiya Fatima ba ce ba". An sanar da Baba maganar zuwa neman aure amma sai ya umarce su dasu hadu a Zaria gidan yayansa Malam Isyaku. Haka akayi kuwa suka hadu acan suka tambayar wa Hassan auren Hassana , a take aka ce an bashi, sai suka nemi a saka musu ranar da zata hadu da ta yan uwansa nan da wata uku da yan kwanaki. Malam Isyaku yace "anya kuwa? Wata uku ai yayi mana kadan ace mun shirya aurar da ya a cikin su. Kuyi dai wancan din wannan kuma sai a shirya a tsanake sannan ayi shi daga baya. Baba Mustapha, ganin baban su Hassan yace "haba malam, wacce shiryawa zakuyi kuma? Mu ai ƴa kawai muka zo nema gurin ku bama bukatar komai daga gare ku. A yadda Hassan ya a bani labarin yarinyar nan ai nasan idan ma bashi zata aura ba shi zai yi mata kayan daki ballantana shi zata aura. Babu wani abu. Ita kawai zaku bamu. Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya da zuriya mai albarka". Anan jayayya ta kare, date fixed. Bayan dawowar Baba daga Zariya ne yan uwa suka yi ta tururuwar zuwa gar gida suna yi musu murna shi da Inna Ade. Fatsar su tayi babban kamu. Ruqayyah kuwa kullum bata iya rufe bakinta dan murna, lissafi take tayi na irin shagalin bikin da za'a sha, irin wanda aka jima ba ayi irinsa a Kaduna ba. "I can't wait to see the reaction on my friends faces. Ruqayyah a ina kika hadu da mai H & H? Ko yanuwanku ne dama?" Ita kuma will be like "gani na kawai yayi a hanya ya like min. Yaga irin zubin matar manya" ta lissafa adadin parties din da za'a yi, dinner, luncheon, Arabian night, mother's day, sisters eve. Irin kayan da zata ke sakawa zuwa kowanne event da kuma irin kawayen da zata je dasu "ba kowa za'a gayyata ba, kar suje su ba ni kunya a cikin dangin miji". Bayan Hussain ya dawo ne ya aiko wa da Ruqayyah tsaraba. Wani set din mayukan gyaran gashi ne, ya kira ta yace "gimbiya ta ce ta bani sako in siyo mata, shine kema na siyo miki ban sani ba ko zaki so shi. Kayan ku ne na mata, ni ban san kyansu ba" Ruqayyah ta bude dan akawatin kayan tana dubawa, ita duk bata san ma ya akeyin amfani dasu ba. Tayi tsaki ta mayar ta rufe. "Wannan Fatimah daga dukkan alamu ta fiya iyayi". Hussain yana dawowa ya tarar an gama saka rana, dan haka shi kuma sai ya mayar da hankalinsa kan ginin gidajensu. Shi Hussain a nasa tsarin so yayi yayi mudu ginin iri daya, komai daya, amma Hassan yana ganin plan din ya girgiza kai yace "wadanna dakunan duk me za'a yi dasu? Ni gaskiya bana son wannan plan din sai kace ba za'a bar duniya ba" Hussain yayi kamar zaiyi kuka yace "dan girman Allah kar ka bata mana tsarin nan, mun riga mun gama shirya komai na gama magana da engineers din nan sun gama fitar da plan dinsu....." Hassan yace " sai ayi maka naka plan din daban ayi min nawa daban. Ni I won't be feeling comfortable a irin wadannan gidajen" haka Hussain a dolensa ya hakura saboda babu yadda zaiyi amma shi a son ransa yaso ace iri daya suka yi, komai iri daya. A karshe sai da Hussain ya hada baki da engineers din sannan suka shawo kan Hassan ya bari aka dora masa bene, amma shi da cewa yayi shi baya son bene "ni bana jin zan iya rayuwa a sama kamar wani tsuntsu" sai engineer yace "amma oga Hassan tunda an riga an dora wa Hussain in ba'ayi a naka ba gidajen ba zasuyi kyau, zasu zama dogo da gajere kenan. Sannan kuma ginin oga Hussain zai toshe maka iska a naka gidan". Da wannan aka samu Hassan ya yarda, amma shi ya tsara kayansa. "Two bedrooms a sama three bedrooms a ƙasa. Shikenan sun ishe mu. Ni plan dina na rayuwa da mace daya ne ni Hassana ta ishe ni har abada. Tunda muna kusa da gida nasan ba wasu baƙin kwana zamu ke samu ba sai dai daga nata bangaren, suma in sunzo dakunan kasa guda uku sun ishe su" Hussain yayi ajjiyar zuciya yace "wannan Hassana, ina tausaya muku kai da ita". Haka aka yi ginin part din Hassan aka gama, kullum yana gurin yan tabbatar wa cewa anyi masa yadda ya tsara abinsa. Ssi da aka gam ak koma kan na Hussain anan aka kure adakar gayu. Part dinsa daban na gimbiya daban na bakinta daban na bakinsa daban. Faluka iri-iri, ga gym ga swimming pool, irin kofofi da fitulun da aka saka a gidan ma kadai abin kallo ne. Amma Hassan ko a jikinsa bai ji cewa gidan Hussain ya burge shi ba. Shi tsarin nasa yafi yi masa kyau sosai dan har yana tunanin in ya fara gini irin wannan tsarin zaiyi sai dai maybe ya dan fi wannan girma saboda lokacin an fara tara iyali. He just can't wait yayi rayuwa da hassanar sa a wannan gidan. Ana tsakiyar shirye shiryen ne ya dauki Hussain ya kai shi gidan daya siyawa Baba ya gani, yayi masa bayanin aikin daya dauke shi da irin albashin daya bashi. Hussain ya gyada kai yace "ka kyauta sosai, yayi kyau sosai. Ni kuma a tawa gudun mawar zan siya masa napep yake zuwa dashi gurin aiki, ranar kuma da bashi ne da duty ba sai ya zagaya ya samu karin kudin cefane" Hassan yayi masa godiya suka bar gidan. A hanya Hussain yake cewa Hassan "amma sai yaushe zaka bashi?" Hassan ya yi murmushi yana shafa kansa yace "sai satin bikin mu, sai su tare a sabon gida suyi bikinsu acan" Hussain yace "why? Hassan the planner. Da nine a ranar da na siya, maybe ma kafin inga gidan shi zan dauka muje mu gani tare. To me zan jira kuma? Yanxu in kai ka mutu kafin biki ko kuma shi ya mutu kaga ai siyan gidan bai yi serving amfaninsa ba". Seventeen: Ungrateful Hassan ya dauke kai tana bata fuska "kai dai baka da zance sai na mutuwa, kullum sai ka ambaci mutuwa kake jin dadi, at the same time kuma kana gina rayuwa kamar ba zaka mutu din ba. Sometimes I find you confusing wallahi" Hussain yayi dariya "to mutuwa ai dole ce, kullum saka rai nake cewa ba zan kai gobe ba shi yasa bana taba barin abinda zan iya yi yau ince sai gobe, at the same time kuma ina living rayuwata the fullest tunda nasan in na mutun bani da second chance, ina kashewa kaina da mutanen da suke tare dani kuɗi saboda ina ganin basu da wani amfani banda a kashe su din, to inna ajiye me zasu yi min? In na mutu sai dai dangi suyi fada akan su to ba gwara in basu ba sanda nake raye? Ni fa kullum ina addu'ar ka da Allah ya bani kudin da ba zan iya kashewa ba". Hassan ya jinjina maganar Hussain a ransa, to ko dai ya bawa Baba gidan nan ne yanzu? Yana tunanin rikicin da zasu yi akan gidan kafin ya karba amma kuma sai ya yanke wata shawara. A iya kacin saninsa da Baba yasan babu abinda yake so sama da iyalinsa, dan haka dasu zaiyi amfani. Ya gama shirinsa tsaf sannan ya yiwa Ruqayyah waya "hello sweetie. Ya gida" ta gyara kwanciyarta tace "lafiya kalau. Ya office?" Yace "na dawo ai tun dazu. Baba yana gida kuwa?" Tace "eh, ya dawo" yace "Okay, ko zaku tambayeshi dake da Sumayya da su Zunnur ku shirya zan zo in dauke ku mu tafi unguwa" ta mike zaune daga kwanciyar da take tace "ina zamu je?" Yayi murmushi "it is going to be a surprise" tace "ina ne dan Allah" yace "to in na gaya miki kuma ai bai zama surprise din ba kenan" Tayi rolling idonta cikin takaici, ita bata taba ganin mai zurfin ciki irin Hassan ba, baya taba gaya mata komai, shi hirar sa kawai ta kalaman soyayya ce wanda dasu da kuma kwarjinin sa yake amfani gurin kashe mata baki ta kasa challenging dinsa, amma sam bata jin dadin yadda alakar su take tafiya, sam bata jin dadin abubuwan da take fahimta a tare dashi sai dai ba zata yi magana, ko da zata iya challenging din nasa ma ba zata yi ba saboda kar ya fahimci true color dinta yace ya fasa. Target dinta daya shine a daura auren dai, in ta riga ta shiga gidan sa a matsayin matarsa kuma ai shikenan tana da control over duk wani abu da yake nasa. Ta tashi ta fita tsakar gida in da sauran yan gidan suke, Baba ya a magana "Zunnur in na dauki albashin wannan watan keke zan siya maka. Saboda ka rage wahalar zuwa makaranta" Zunnur ya tashi da murna yan uwansa suna taya shi, Ruqayyah ta tabe baki, su keke manya. Ta durkusa a gaban Baba "Baba dama Hassan ne yayo waya yace mu shirya ni da sauran yara zai zo ya dauke mu zamu je unguwa" Baba ya bata fuska "unguwa kuma? Wacce unguwa?" Ta tabe Baki "nima bai gaya min ba fa, ya dai ce wai wani mamaki zai bamu. Ba zai wuce shopping ne zai kai mu ba" a ranta ta karasa da cewa "it is about time daya kamata ya bude wannan matsatstsen aljihun nasa" Baba yayi shiru bai ce komai ba, Inna Ade tace "tunda da sauran yara zasu je ai ina ganin babu komai ko Baban biyu? Kaga bikin ya fara matsowa sosai yanzu haka wani abu ne daya shafi bikin nasu" Sumayya cikin doki tace "baba mu shirya, yanzu haka gidan da zasu zauna zai kai mu mu gani" Inna Ade tace "haka ne kuwa, shi din nema yanzu haka" Baba yace "sai ku tashi ku shirya ai, ku bi a hankali, banda rawar kai banda kwadayi". Ai kuwa cikin murna suka mike da sauri suka shirya, su Ruqayyah suka yi dressing daga cikin sababbin kayan su suka yi wa juna kwalliy mai kyau, sunyi kuma matukar kyau da yanayin su mai daukan hankali. Sun gama shiryawa kenan Hassan yayo waya cewa gashi nan ya kara so, suka yi wa Inna sallama suka fita tana yi musu fatan alkhairi. Suna fita ya bude musu mota suka shiga. Ruqayyah ta zauna a gaba kusa dashi su kuma duk suka shiga baya suna hada baƙi gurin gaishe shi. Ya amsa musu individually kowa yana tambayarshi makaranta, sai da suka nutsu suna kus kus a tsakanin su suna santin motar sannan ya juya side din Ruqayyah yace "ranki ya dade" tayi murmushi tana sunkuyar da kanta tace "tare da naka" daga nan bata kuma cewa komai ba, hankalin ta yana kan titinan da suke bi tana lissafin wanne mall zasu je, wanne nema wanda yake tashe yanzu? Sama sama Hassan yaje hira da kannen Ruqayyah, lokaci zuwa lokaci kuma yana juyo wa ya kalle ta yayi mata murmushi itama ta mayar masa, shi shirun ta da nutsuwarta suna burge shi sosai, wannan yana nuna cewa bata da hayaniya kamar yadda yake so sannan kuma bata da mita. A kofar gidan ya tsaya, duk suka juya suna kallon gidan with different thought a zuciyoyin su. Ruqayyah "wait! What? Ba dai nanne gidan da zamu zauna din ba" Sumayya "kai!!!, Ji wani gida mai kyau" Sulaiman "duk sanda na tashi yin gidana irin wannan kofar zan saka" Zunnur "me muke yi anan?" Hassan ya bude motar yana cewa "okay, we are here, kowa ya fito" suka fara fitowa daya bayan daya duk idon su akan gidan, Ruqayyah trying so hard not to scream. Ya dauko key ya bude gidan fuskarsa cike da farin ciki yace "ku shigo, kowa ya zagaya ya gaya min view dinsa akan gidan nan". Ruqayyah a tsakar gida ta tsaya tana jin kamar kafafuwanta ba zasu iya kaita double door din da taga sun shiga ba, sai da Sumayya ta dawo da sauri ta ja hannun ta. "Zo ki gani, Ruqayyah, har furnitures an saka" Ruqayyah bata ce komai ba ta dai bita a baya kirjinta yana bugawa. Ɗakunan guda uku duk an saka musu set din gado masu kyau da labulaye, falon ma an saka set din kujeru irin wadanda ita kanta Ruqayyah ta san cewa bata taba hawa irin wannan kujerar ba amma duk da haka ji tayi sam basu yi mata ba, sam basu dace da ceo na H and H ba. Ga set din kayan kallo, plasma tv ce amma Ruqayyah a idonta sai taga it is not big enough, ita katuwa ta ke so. Hassan sai murmushi yake yi yadda yaga yaran suna zagaya gidan cikin murna, ko bai tambaya ba yasan cewa gidan yayi musu. Yaga Ruqayyah a tsaye a falo tana daddanna wayarta sai ya saka hannu ya karbe wayar yana cewa "I am here, ba sai kin kalli hotuna na ba" ta dan yi murmushi tace "to ai baka tsaya na kalle ka ba, kana ta zagaye" yace "ke ma ba sai ki zo muyi zagayen ba?" Tace "bana jin dadi ne, kafafuwana suke ciwo" taga yanayinsa ya chanja, ya durkusa a gabanta yana kallon kafafuwanta da suke sanye da takalmi tace "subhanallah. Wacce ce daga ciki take yin ciwon?" ta kara jan skirt dinta kasa tana kuma rufe kafafuwanta tace "ba nan bane ai yake ciwon" ya dago kai yana kallon ta yace "ina ne yake ciwon?" Ta juya masa baya tana jin zuciyarta tana zafi, kamar zata yi kuka take ji. A lokacin ne su Sumayya suka fito daga dakin da suka shiga na karshe, suka dawo palo, Zunnur yace "kai! Wannan tv da girma take, zata yi dadin kallon ball" Hassan yayi dariya yace "you like it?" Duk suka amsa da yes banda Ruqayyah data juya musu baya tana kokarin rike hawayen ta. Sumayya tace masa "nan ne gidan ka? Anan zaku zauna da Rukee?" Yace "yaya Ruqayyah, yaya Ruqayyah zaki ke ce mata ba Rukee ba, and no, ba gida na bane ba kuma ba anan zamu zauna ba" Ruqayyah ta juyo tana jin kamar an yaye mata wani abu a kirjinta. Yace " wannan sabon gidan ku ne dana siya muku , nan nake so ku dawo tare da Baba da Inna ku cigaba da rayuwar ku anan". Yaran suka dauki sowa gaba ki daya, Ruqayyah ma ta rufe bakinta tana dariya, wannan ce dariya ta farko data yi tunda suka shigo gidan, Hassan yace da samarin "ga naku dakin can a soro, akwai tvn ku a ciki da zaku yi ta kallon ku a ciki. Ku zo muje in nuna muku" suka bishi a baya da sauri suna hada hanya. Sai a lokacin Sumayya ta zagaya da Ruqayyah ta ga gidan, sai a lokacin taga kayan sunyi mata kyau amma da duk dusu dusu ta gan su. Sai a lokacin ta lura da cewa toilets din modern ne. Suka fito suka yi joining sauran a dakin soro inda aka yi masa tsarin samari da toilet dinsu. Sai da suka gama sannan suka fito, ya rufe gidan suka shiga mota suka juya suna barin gurin. Ruqayyah ta juya tana kallon gidan, sai taga baiyi mata kama da gidan su matar mamallakin H and H ba. A hanya ne yake ce musu. "Ya kuka ga gidan? Yayi muku? Suka yi dariya, Sumayya tace "yayi mana, sosai ma kuwa. Mungode mungode Allah ya saka muka da alkhairi Allah ya biya ka da aljanna" yace "ameen na gode nima da addu'a. Yanzu abu daya nake nema daga gurinku shine ku taimaka ku lallaba min Baba ya yarda ya karbi gidan nan. Ku hada kanku ku nuna masa kuna so ya karba. Kunji" Duk suka amince, ya juya yana kallon Ruqayyah da take ta zabga murmushi yace a hankali "do you like it" tace "sooo much. Yayi kyau sosai. Mungode Allah ya saka da alkhairi" yace "bana hana ki yi min godiya ba? Duk abinda nake dashi naki ne, to menene in mutum yayi amfani da abinsa?" Taji wani irin dadi a ranta, duk abinsa nata ne, tabbas bata da sauran wata damuwa a duniya. Bayan ya ajiye su ne yace musu, "bayan gida kuma, akwai Napep da Hussain ya bashi shima saboda transport da kuma ko zai kezagayawa dashi, na san Baba baya son zaman banza" ya karasa maganar yana fadada murmushin sa. Sumayya ta taya shi murmushin "lallai kasan Baba. Ai kuwa Hussain ya kyauta sosai ayiwa Baba Godiya" Sama sama Ruqayyah take jinsu. Tunda kalmar Napep ta shiga kunnuwan ta taji kunnen ya toshe. what? Baban nata ne zaike yin hayar Napep bayan ya taso daga aikin gadi? Ta juya ba tare da tace da kowa komai ba ta shige gida. Hassan yana sallama da yaran vai lura da shigar ta ba sai daya waigo yaga bata nan. Ya ji babu dadi, ya so su dan taba hira kadan amma kuma sai ya bata uzuri da maybe ta gaji ne, gashi kuma dama tace kafarta tana ciwo. . Ruqayyah tana shiga gida ta fara masifa "Napep fa yace, wannan wanne irin cin mutunci ne da cin fuska. Me nayi wa Hassan da zai ke wulakanta ni irin haka? Wannan ce sakayyar da zai yi wa taimakon da nayi masa?" Sumayya data biyo bayan ta tace " ke baiwar Allah! Yanzu menene laifin Napep din? Menene laifin wanda yaso mahaifin ki da arziki?" Tace "arziki? Ina arzikin yake? Napep din ne arziki? Mutumin da na tseratar da rayuwar sa shine zai jefi ubana da keke Napep? Ji nake a sanadiya ta ne ya samu ransa, kuma ya samu dukiyar sa daga hannun wadanda suka sace shi. Ji nake naira billion daya aka xe an karba daga hannun barayin kuma an bashi kayarsa? Me ya bani a ciki? Me ya taba bani? Sim card din?" Sumayya tace "wannan ra'ayin sa ne ya baki ko ya hana ki, ganin damarsa ce. Amma ya kamata ace abinda kika samu daga gare shi ki gode Allah. Yaushe rabon da kinkwana da yunwa? Yaushe rabon da kici mai da yaji? Ji nake duk a dalilin haduwarki dashi ne? Yanzu kayan da suke jikinki ta dalilin wa kika samu. Ina laifi? Ina laifin wanda ya bawa mahaifinki aiki ya daina leburanci da turin baro? Ina laifin wanda ya bawa mahaifinki Napep yace yayi sana'a dashi? Gidan daya siya mana kuma fa? Mai tilesda ac da ban dakin water system? Shima duk bai kyauta ba?" Ruqayyah tace "wannan kuturun gidan kike magana akai? Ai wannan gidan is nothing in aka duba irin dukiyar sa, wannan gidan ai bai kai gidan da a za'a nuna ace ga gidan surukan mutumin daya mallaki kamfanoni ba. Ban taba lissafin cewa zan auri mai kudi ba sai da na hadu dashi, ban kuma san cewa marowacin mai kudi zan aura ba sai yau. Wallahi yayi da yar halak, ba dai za'a yi bikin ba? Ba dai zan shiga gidan sa a matsayin matarsa ba, wallahi sai na chanza masa takunsa tunda dai ace duk motocin da yake ta shiga yana fita dasu ya rasa wadda zai bawa mahaifina sai ya bashi Napep. Wallahi har wannan gidan sai ya chanza in dai yana son zaman lafiya" Ta wuce Sumayya kamar kububuwa. Duk maganganun su Inna Ade tana tsaye akan baranda tana jinsu. Sai da Ruqayyah ta zo zata wuce ta sannan tace "zo nan Hassana" ta dakata da tafiyar da take yi amma bata juyo ba ballantana Inna Ade ta saka ran amsawa. Inna Ade tace "yanzu rashin godiyar Allahn naki har ya kai haka Ruqayyah?" Ruqayyah tayi magana kasa kasa sannan ta juya zata shige daki. Inna ta saka hannun ta na hagu ta finciko ta baya sannan ta saka na dama ta wanke ta da mari tace "watakila wannan ya dawo dake cikin hayyacin ki". Hussain yana ta shirye shiryen sa. Gida ya kammala, an gama finishing touches da komai. Takanas aka yo masa yawa daga masarautar kano akan cewa kar ya saka wa Fatima komai a dakunan ta. Bai so haka ba, amma sai ya bar musu ya fara zuba kaya a nasa dakunan, the best of the latest of komai yake sakawa. Hassan ya fada tuntuni cewa shi zai yiwa da Ruqayyah kayan daki. Amma kuma Hussain ya ga shiru, kullum in yayi masa magana ko kuma yayi masa tayin wani design na kaya sai yace ai zaiyi ne "tunda nace maka zanyi ka bar ni mana, ina ta planning irin wadanda zan saka da wanda zan saka mata, ba lallai ta so irin naka ba kasan taste dinta ba irin na gimbiya bane ba" Hussain yace "ka tambaye ta ne kaji wanne taste ne da ita? Ko kuma dan sunan ta Hassana sai ya zamanto tana da ra'ayi irin na Hassan?" Daga nan bai kuma bi ta kan Hassan yakira kamfanin daya bawa kwangilar nasa aikin yace su shiga gidan Hassan su saka komai "kaya masu kyau zaku saka a ko'ina, karku gaya masa, in kuma yazo ya same ku kuna aikin kuce masa ni na saka ku" ai kuwa kamfani suka zage dantse suka fara kure adakar su a gidan Hassan. Gashi dai gidan ba za'a kira shi da katon gida ba amma kuma sanda suka gama aikinsu sai ya zamanto kyan da gidan yayi ba karami bane ba. Babu abinda zaka kalla ba tare da ka kuma kallo ba. Sanda Hassan ya samu Hussain da fadan me yasa ya taba masa gidan sa sai yace "ba kai na sakawa ba, Ruqayyah na saka wa. It is my wedding gift to her, it is just my little way of saying thank you for saving my brother". Kuyi hakuri in kunga typos...... Wannan littafin na siyarwa ne, duk mai so tayi min magana ta wannan number din 08067081020. No calls please, WhatsApp only. Eighteen : His Religion Ranar da Hassan ya bawa Adam complimentary card dinsa, a hanyar sa ta komawa gida yana ta bitar hirar su da Sumayya yana murmushi, yana mamakim kansa yadda har ya iya ce mata he likes her. He saw the look in her eyes kuma ya fahimci abinda take tunani, alaka tsakanin su zata yi wahala gaskiya, bazai ce impossible ba saboda yasan babu wani abu da yake impossible agurin ubangiji, idan Allah yayi zasu kasance tare to ko sama da kasa zasu hadu tabbas sai sun kasance din. Rayuwar sa kadai ta isa misali a gurinsa na cewa nothing is impossible indai aka saka Allah a ciki. Bai taba tunanin zai yi wannan rayuwar ba, sanda ya fara ta kuma bai taba tunanin zai yi surviving ba amma gashi nan yanzu har ya saba. Da dadi ba dadi he still prefers wannan rayuwar akan wacce ya baro a baya. Yanzu gashi cikin ikon Allah da kudirarsa sai gashi ya fada hannun ogan h and h, gashi har yace yaje ya same shi a office zai bashi aiki, wai aiki a matsayin driver. Still yana feeling excitement in ya tuno da yadda aka tsara masa aikin, irin benefits din gaskiya abin ya burge shi sosai. Dan haka monday da sassafe yana tunanin shi kansa Hassan din sai dai yaje office ya same shi yana jiran sa. Fatan sa kawai kar ya ganshi cikin hasken rana ya fahimci ko wanene shi yace ya fasa bashi aikin. Kamar yadda yake tsoron ranar da baban Sumayya zai kama shi yace kar ya sake dawo masa gidan sa. Haka ya karar da weekend din nan cikin saka da warwara, sai dai ko sau daya tunanin sa bai bashi cewa ya fasa zuwa ba dan shi mutum ne da yakan doshi abu ko da kuwa yasan da illarsa ballantana wannan da bai tabbatar ba, dan haka monday nayi ya shirya ya tafi, sai ya zamanto har ma ya riga shi kanshi Hassan din zuwa office din. Ya zauna ya jira har aka ce masa yazo, sannan aka sanar da Hassan zuwan Adam sai yace ya jira shi. Daga nan Adam ya zauna jira, shiru shiru shi dai yana zaune yana jira yana kuma lissafa yadda rayuwarsa zata kasance a matsayin drivern gidan masu kudi, yayi murmushi yana girgiza kansa yana tuna drivers din da suke gidansu yana kuma zaben wanne daga ciki zaiyi koyi da, but sai dai duk cikin su babu yaro karami kamarsa, babu mai background irin nasa dan haka babu wanda rayuwarsu zata zo daya. Ba zaiyi koyi da kowa ba he is going to live as himself. A haka aka leko aka kira shi. Ya shiga yana kallon fuskar mutumin da suka gaisa ranar nan amma da yake ranar da daddare ne sai yanzu ya samu ya ga cikar halittar sa da kwarjinin sa. A ina Ruqayyah ta samu wannan? Me yasa ya zabi Ruqayyah a matsayin matar aure? When? Where? How? Why Ruqayyah bayan duk yammatan da suke gari babu wadda zai ce yana so tace a'a? Sai kuma yayi saurin kawar da tunanin sa daga kan maganar, zuciyarsa tana kwabarsa da cewa "ina ruwanka? Kai da kazo neman aiki ina kai ina bin diddigin insa ogan ka ya samo budurwar sa? Ya zauna akan kujerar da Hassan ya nuna masa sannan ya gaishe shi, ya amsa yana rubutu a takardar da take gabansa, sai Adam yaga kamar he is not as nice as he was ranar nan. Sai da ya gama rubutun sa ya dago kai sannan yace "barka da zuwa. Sorry I kept you waiting. Ban dauka zaka zo yau ba ban kuma dauka zaka zo da wuri ba, already akwai masu appointment so I have to see them first. Ina fatan ka gane" Adam ya gyada kai da sauri. Sannan Hassan ya tambaye shi full name dinsa. "Adam......." Hassan "Adam who? Adam ya dauke kansa gefe yace "Adam Clement Young" ya fada yana studying Hassan yana so yaga yadda zaiyi reacting to the name amma sai yaga ya rubuta ba tare da yanayin fuskarsa ya chanja ba. Daga nan ya cigaba da jero masa tambayoyi, "age" "23" "tribe" "igbo" "state of origin" "imo" "religion" "islam" haka suka yi tayi yana jero masa tambayoyi akansa shi kuma yana amsawa, ya tambaye shi contact address dinsa sai ya bashi adireshin dakin da yake haya sai kuma ya tambayeshi permanent home address sai ya kuma bayar da same address. Hassan ya dago yana kallonsa sai shi kuma ya sunkuyar da kai, Hassan ya ajiye biron hannunsa yace "for this, you have to give me address din inda mahaifanka suke, gidan ku nake son sanin a ina yake" Adam yace "Kano" Hassan yace "kano wacce unguwa, wanne layi wanne number din gida?" Adam ya dago kai yace "that's a very private question" Hassan ya bude baki cikin mamaki yace "you think so? I am about to give you a very private job na entrusting rayuwar only brother dina a hannunka, and you are telling me address din gidan ku is a private thing? I have to know as many things as possible akan ka kafin in iya baka wannan aikin". Adam ya gyada kai, ya yarda da abinda yake cewa but it is just that bai fiya magana akan parents dinsa ba sai in ta kure, kamar yadda ta kure yanzu dan gaskiya yana son wannan aikin sosai saboda chance din da ya gani a cikin aikin na komawa makaranta. Yana son karatu sosai. Dan haka ya fada "house number 14, badawa layout, Nassarawa local government, kano state" Daga nan tambayoyin suka ci-gaba kamar ba zasu kare ba, "wannan mutumin da bin kwakwkwafi yake" Adam ya fada a zuciyarsa. Sai kuma ya yi kokari wajen ganin cewa ya fadi gaskiya to the best of his knowledge. Sai da suka gama sannan Hassan ya rufe file din gabansa and for the first time tunda ya shigo yayi masa murmushi yace "that will be all. Kayi kokari sosai, but I will have to run a background check on all what you said, ba zai dauki lokaci ba zan gama within this week next week insha Allah zan kira ka in gaya maka yadda ake ciki" Adam yaji gabansa ya fadi, ya dago da budaddun idanuwa yana kallon Hassan, Hassan ya daga kafada yace "yes now, ta haka ne zan tabbatar da gaskiya, ko akwai wani abu da kake boyewa ne?" Adam ya sunkuyar da kansa yana girgiza kansa, wani bari na zuciyarsa yana gaya masa cewa yace ya fasa neman aikin amma kuma ita magana ai kamar zarar bunu ce inta fita bata komawa. There is no going back. Fatan sa kawai in Hassan ya samu abinda yake fatan kar ya samu to kar ya gayawa Sumayya. Idan zai gaya mata to shi zai gaya mata da kansa. Adam yana fita Hassan ya dauko wayarsa yayi kira "Hello. Kanawan dabo. Kana lafiya? Ya iyalin? Dan Allah dan wani taimako nake nema, zan turo maka info din wani yaro ina son kadan bincika min shi. Eh nan kano yace min unguwar badawa. Okay, just find out if there is anything that I should know about. Thank you." Ya kashe wayar yana murmushi, rami ya gina wa Adam kuma ya fada ciki. Tun sanda ya ganshi yana zagaya gidan Baba kuma ya fahimci gurin Sumayya yake zuwa kuma ya fahimci cewa ita ma Sumayyan kamar tana da interest akansa sai ya kudurce a ransa yana so yayi bincike akansa amma ya san ba zai bashi hadin kai ba shine ya yaudare shi da aiki dan yaga alamar yana bukatar aikin, yanzu sai yayi binciken sa sosai akansa, in ya samu alkhairi zai bashi aikin kuma yayi masa jagora zuwa ga Sumayya in kuma ya samu sharri sai yayi warning Sumayya kuma aikin ma ya bi ruwa. Bayan ya tashi daga aiki ne ya koma gida ya tarar Aunty tana palo tana jiransa "kudin nan fa sai ka karo su Hassan. Kaya gasu an fara siya basu fi rabi ba amma kudi sun kusa karewa, ko boxes din ba'a siya ba. Ga sauran kayan al'ada da ake yi duk ba'a siya ba" ya shafa kai, "aunty, kayan nan wai me zata yi ne dasu? Ji nake dai sakawa zata yi a jikinta in tazo gidana ko? To ba gani ba muna tare? In tazo din duk abinda take so ai za'a siya mata" Aunty ta girgiza kai tace "ba shi kadai ne amfanin lefe ba, ai ana rabawa dangi, kusan rabin kayan ma rabarwa ake yi ballantana su da ba masu kudi ba ai kaga duk zasu so su rarrabawa dangi suma su samu albarkacin ta ko? Shi yasa nake siyan kayan kashi biyu akwai masu tsada sosai akwati daban za'a saka su a matsayin nata, masu dan saukin kudi kuma sai a siya da yawa a basu a ce a raba wa yan'uwa" yayi ajjiyar zuciya "mata dai da al'ada. Shikenan nawa za'a karo yanzu?" Ta gaya masa, ya bude baki yana mamaki tace "to boxes din ma set uku zan siya, biyu nata daya na rabo" ya rufe bakin yace "set daya ya ishe ta, set daya na rabon. Yarinyar nan ba sabawa tayi da irin wannan spending kudin ba, nafi so kuma ta cigaba a haka. In an siya da yawan ma sai dai tayi ta ajiiyar su sai a hankali zata saba da amfani da wasu abubuwan ma. Dan haka gwara a bari in tazo din ta fara sabawa a hankalin sai ake introducing dinta to sauran abubuwa" Aunty tace "in an siya mata a kayan lefen nata ai dole zata koya, in bata dasu ta yaya zata koya? Kuɗi fa sai ka fito dasu komai wayon ka" yayi dariya yace "shikenan Aunty, zan kawo gobe" tace "yauwa, kuma ina son inji yadda kuka yi da ita akan sauran hidimomin biki, nawa zaka bata?" Ya sake bude baki "bikin ai da saura ko" tace "sauran wata daya ba? Yanzu lokacin yadda yake gudu kafin ka gama lissafin ka wata dayan ya kare. Kaje ku zauna da ita ta fada maka shirye-shiryen ta sai ka lissafa ka bata abinda zai ishe ta" ya mike tsaye yana cewa "an gama Aunty" tayi dariya tace "zaka gudu ko? To ai ban gama da kai ba" yace "in na cigaba da zama sai kaina ya kunce saboda lissafin kudin da za ki cigaba da yi min". A bangaren Ruqayyah ranar da ta sha mari a gurin Inna kusan kwana tayi ta kasa bacci, ba wai marin ne yayi mata zafi ba a'a yadda akayi mata marin a gaban kannenta sannan inna ta wanke ta tas da soso da sabulu shi yafi kona mata rai. Yanzu ai sai su raina ta su cigaba da kallon ta da sunan da Inna ta kira ta dashi "butulu". Ita kuma Inna hankalinta gaba daya a tashe yake da jin kalaman Ruqayyah, ita da kanta wai take ikirarin saita wa mijin da zata aura zama idan anyi auren su. Wannan kadai ya nuna cewa ita ba ta rike alkhairi a ranta ba akan auren nata, Inna taji tana jin tsoro, tana jin tsoron abinda Ruqayyah zata aikata a gidan mijinta. Sai taji a ranta cewa kamar ta bawa Baban biyu shawarar cewa ya dakatar da auren baki daya, amma kuma tana jin tsoron abinda Ruqayyah zata aikata in akace an fasa wannan auren, zata iya yin komai koda kuwa abinda zai lalata mata rayuwa ne, tsoron wannan yasa Inna Ade ta kasa yiwa Baba maganar. Ita dai tuntuni ta san cewa Ruqayyah jarabawa ce a gare su ita da Baba, iyakacin iyawarta tayi tarbiyyar, ta bada ilimin, ta kuma yi addu'ar. Ba dan Allah ya saka sauran ya'yan sunyi turning out good ba da sai taga kamar laifin sune su iyayen amma yanzu su sun sani, Allah ya sani, sannan duk wanda ya san su ya sani cewa sunyi kuma suna yin iyakacin kokarin su. Allah shi ya barwa kansa sanin yadda zaiyi da Ruqayyah. Da safe yaran suka zagaye uban. "Baba ba ka ga gidan ba, bandakin fa irin wanda ake korawa da ruwa ne" "kaga kujerun Baba? Wannan in inna ta zauna ba zata iya tashi ba" Sumayya ta fada tana tsokanar Inna, Inna ta harare ta tace "ai dai kinsan ba daga ruga aka dauko ni ba ko? Sai dai ki fada wa zazzagawa sune basu saba hawa manyan kujeru ba" Baba yayi shiru bai kula ta ba duk da ya fahimci tsokanar sa take yi, shi wannan lamari da yaran nan suka kawo masa yana da girma sosai, gida kuma? Har da dakuna kowa da nasa? Da bandakuna na zamani da palo mai kujeru da talabijin? Anya kuwa abinda yaron nan yake yi bai yi yawa ba? Anya kuwa ya dace ya karbi wannan kyautar? In ma zai karba ai kamata yayi ace sai bayan biki tukunna sai ya iya karba a matsayin surikin sa amma yanzu gani yake yi anytime yaron zai iya zuwa yace ya fasa auren. Inna tace "Baban biyu, nima gaskiya ina tsoron karɓar gidan nan, daga yadda suke kwatanta shi kasan ba karamin gida bane ba. Ya bar mu anan din mu tunda gashi nan har kana kokarin yin katangar nan" yace "har plaster nake so ayi wa dakunan nan ayi musu penti kafin bikin" yaran duk suka fara bata rai "dan Allah Baba, dan Allah Inna yace fa da sunan ka ya sayi gidan nan, kyauta ya baka shi, bana jin ko ba'a yi auren ba zai dawo da kalaman sa baya" Sumayya tace tana karya wuya. Sulaiman da Zunnur suka durkusa kusa da ita suna hade hannayensu "dan Allah Baba ka karba, dan Allah Baba ka karba". Baba yayi shiru yana kallon su yana tunani sannan yace "shikenan ki ce wa Hassana ta kira min shi tace in ya samu dama yau da magariba yazo ina son magana dashi.. Sakon yana zuwa kunnuwan Hassan ya gane cewa akan maganar gida ne, ya shirya ya taho yana addu'ar Allah yasa ba rejecting gidan Baba zai yi ba. A tsakar gida aka shimfida musu tabarma suka zauna daga can bakin kofar shigowa. Hassan ya gaishe shi cikin ladabi da jin kunya, Baba ya amsa sannan yace "jiya yara suka zo min da wani lamari mai girma, shine na kira ka inji daga bakin ka" Hassan yace "gaskiya ne abinda suka fada baba, ina kuma fatan ba za'a ki karba ba kamar yadda aka ki karbar kuduri na na bada jarin sana'a, yadda na hakura na bayar da aiki ina fatan wannan karan nima za'a dube ni a karbi wannan din. In ba'a karba ba gaskiya zanji babu dadi, zanga kamar......" Baba yace "kamar an raina?" Hassan yace "a'a kamar ba'a sona tunda ba'a son abin hannuna" Baba yace "ba haka bane ba, son naka da nake shi yasa nake maka haka. Bana son in cutar da kai" Hassan yace "ta yaya zaka cutar dani Baba? Karbar wannan kyautar ai faranta min zaiyi ba bakanta min ba" Baba yace "haka ne, amma ina matukar jin kunyarka" Hassan yace "Allah yasa hakan yana nufin za'a karba" Baba yayi ajjiyar zuciya yace "na karba Hassan. Allahu yayi maka albarka ya baka masu yi maka kaima a lokacin da kake bukata" Hassan ya sunkuyar da kansa, fuskarsa tana nuna irin jin dadin da yayi yace "Nagode sosai Baba, na gode da karamcin ka da soyayyar ka" Baba ya dago kai yana kallon sa, yaron kirki ne, sam bai dace da Ruqayyah ba, sai yaji kamar baiyi masa adalci ba. Hassan da kansa ya turo da driver ya debe su zuwa sabon gidan su. Kafin su tafi duk suka shiga gidajen unguwa suka yi musu sallama tare da basu kwatancen sabon gidan su. Kayan sakawarsu kawai suka dauka da dan abinda suka san zasu bukata a sabon gidan sannan suka rufe dakunan su suka rufe gidan suka tafi, zuciyoyin su fal da mabanbantan feelings. Yaran suna jin feeling na murna sosai, suna ganin sun taka wani babban matsayi a rayuwa kuma suna ganin wannan wani chanji ne mai kyau a rayuwarsu yayin da iyayen suke jin rashin dadi na barin gidan da suka yi shekara da shekaru suna zaune a ciki, suna kuma alhinin shiga wata sabuwar rayuwa wadda basu san menene a boye a cikin ta ba. Ruqayyah kuwa a nata bangaren, ji take yi cewa wannan chanjin kamar misalin wanda zaije sama ne sai ya taka dutse, wannan ba komai bane a gurin ta, wani step ne da ta taka zuwa gaba. Wannan kenan........... A bangaren Gimbiya Fatima kuwa shirye shirye sun kankama sosai, a da lokacin da aka saka bikinta wata takwas ji tayi kamar ta dora hannu aka tayi kuka saboda ganin tsayin lokacin da kuma zakuwar da tayi na ganin ta kasance da hasken idanunta, Hussain. Sai gashi yanzu har watan bikin ya kama. Tana ta shirye shiryen ta iyayenta suma suna yin nasu. Duk tsarin gidan Hussain babu abinda bata sani ba dan tare suka tsara kayan su, sun kuma shirya duk events din da zasu yi. Ita a bangaren ta zata yi bridal shower a gidan babban yayan su a nan cikin garin kano, sai kuma kamu da yini da za'a yi rana daya anan cikin palace ranar Friday, ranar Saturday kuma za'a yi grand dinner da maimartaba ne da kansa ya shirya musu kuma har da ango da abokan sa da yanuwansa duk za'ayi. Ana saka ran zasu zo su wuni ranar Saturday din da daddare ayi dinner sannan su kwana sai da safe a daura aure su tafi da amaryar su zuwa Kaduna. Duk wasu ashobis sun fitar uta da kawayenta wadanda yawancin su tare suka yi jami'a a Europe, sai wadanda suka yi secondary school tare a Abuja, sai kuma family friends dinta. Sun gama tsara komai kuma Hussain ya sakar musu kudi wanda wani lokacin har sai ta daga masa hannu dan bata son kawayen natakuma su mayar dashi saniyar tatsa dan shi duk abinda suka ce ya basu basu kawai yake yi. An aika an gano gida kuma kusan komai an gama siya jira kawai akeyi bikin ya kara matsowa sai aje ayi jere. Sakamakon binciken da Hassan ya tura ayi masa a kano a kan Adam ya fito, kuma kusan komai yayi tallying da abinda ya fada banda abu daya. Hassan ya dago da kansa daga karatun report din yana shafa sajensa, fuskarsa da alamar damuwa. Ya dauko form din daya cike biography din Adam yana kuma dubawa dan yayi confirming maganar, sai kuma ya dauko wayarsa ya saka number din da Adam din ya bashi ya kira. Adam ya ciko mota passengers yana tukin sa a nutse kamar kullum, yaji vibration din yawarsa da take ajjiye akan dash board, ya kalle ta, sunan daya gani ne ya saka shi daga kafarsa yana kara rage gudun motar sannan ya sauka gefen titi yayi packing yana cewa "excuse me Please, I have to answer this" sannan ya daga wayar da sallama. Hassan yayi mamakin sallamar da yaji amma sai ya maze yace "kazo gobe, around noon ina son ganinka" Adam yace "yes sir. Insha Allah" Hassan ya katse wayar still yana noticing insha Allah din da Adam yace. A ranar da daddare Hassan yaje zance gurin Ruqayyah, suna zaune a dakin su Sulaiman kamar yadda suke zama kullum. Tana ta so ta shigar masa da maganar shirin biki amma ta rasa ta yadda zata fara ba tare data bata pentin da tayi wa kanta a gurin sa ba. Sumayya ta shigo da sallama ta zauna a hannun kujerar da Ruqayyah take zaune, ta gaishe da Hassan ya amsa yana tsokanar ta. "Ance min kina ta kuka wai ba kya son rabuwa da friends dinki" tayi ajjiyar zuciya, ita duk ba wannan ne problem dinta ba, ba shine abinda yake hana ta bacci tunda suka dawo ba. Tace "yaya Hassan, dama tambayarka zanyi......." Ya gyara zama yace "ina jinki" tace "yaje kuwa? Yaje office din naka kuwa?" Ruqayyah ta juyo tana kallon ta tace "wa? Waye zaije gurinsa?" Sumayya ta dauke kanta daga kallon ta ta sake mayarwa kansa tana jiran amsa, ya danyi murmushi duk da ya fahimci wa da take nufi amma sai yace "wa kenan fa?" Ta dan vata fuska tace "mutumin ranar nan" ko da wasa bata son Ruqayyah ta san maganar Adam. Ruqayyah ta sake cewa "wai waye kike magana akan sa? Bashi da suna ne?" Sumayya tace "shi yasan maganar wanda nake yi ai" Hassan yayi yar dariya, ya fahimci Sumayya tana boyewa Ruqayyah wannan Igbon. Ya gyara zama da dariya a Muryar sa yace "yes, na gane wanda kike nufi, and yes, yaje munyi magan dashi" cikin zakuwa Sumayya tace "and?" Yace "and, sai gobe zai dawo mu karasa maganar" Sumayya tayi ajjiyar zuciya tace "okay, thank you. At least nasan yaje din, ina ta tunani ne kuma bani da hanyar sani shi yasa na tambaya" yace "kar ki damu. I have his phone number if you want" Sumayya tayi saurin miko wayarta da Baba ya dawo mata da ita bayan sun dawo sabon gidan tace "yauwa saka min Please" yana dariya yace "ko kunya babu" ya karba yana saka mata Ruqayyah tayi mata alamar tambaya da hannunta ita kuma sai ta dauke kai kamar bata gane me take nufi ba, ta san dai yau sai sunyi rigima a daki". Yana gama sakawa ya miko mata, tayi saving sannan tayi masa godiya ta fita, Ruqayyah ta jiyo tana kallon sa da alamar tambaya sai yace mata "wani aboki na ne". Daga nan bata iya ce masa komai ba duk da bata yadda da amsar daya bata ba. Sumayya direct dakin da yake matsayin nasu ita da Ruqayyah ta zarce, ta rufe kofa sannan ta zauna a bakin dago ta kira number din da aka saka mata. Ring biyu ya dauka da sallama kuma a take ta gane muryarsa. Yace "who is on the line please" sai data dan jima sannan tace "someone, da ka manta" ko a cikin mafarki ne zai gane muryarta. Ya matsa daga gurin da abokan su suke hira yana cewa "Sumayya? Ke ce da gaske? A ina kika samu number ta?" Bata bashi amsa ba sai kuma yake "ohhh I get it. Yazo zance....." Ya fada da dariya a muryarsa. Ta dan bata fuska tace "ni da na damu da inji yadda kake ai na ajiye kunya ta a gefe na nemi number dinka" yace "oh dear , you have no idea sau nawa nake zuwa unguwarku a rana. Sumayya kullum sai naje, kawai dai na kasa samun courage din da zan aika a kira ki tunda ranar nan kince min za'a yi miki fada, bana so ayi miki fada, bana so in jawo miki trouble. In naje kawai hoping nake ko zan ganki an aike ki ko kin fito unguwa" Ta lumshe idonta tace "ni ba'a aike na, ni babu inda nake zuwa, sai in kwana biyu ban fita daga gida ba, dama zuwa school ne kuma yanzu bama zuwa, islamiyya ma a gida muke yi anan muke daukan karatu kuma mu dora wa yaran unguwa karatu" yace "wow, har karatu kuke koyarwa?" Tace "gidan mu ai makaranta ce, makarantar addini ce" sai taji yayi shiru har sai da tace "hello?" A hankali yace "zan iya shiga nima? Makarantar gidan ku zan iya shiga?" Tace "ban gane ba, ba ka yi sauka ba ko akwai littattafan da kake son sani?" Sai da ya danyi shiru sannan yace "banyi karatu ba ni. Bani da ilimin addini ni" Overlook the typos please. Wannan littafin na siyarwa ne, in kina so kiyi min magana ta wannan layin. 08067081020 Nineteen: The Real Princess An kusa zuwa dai dai gurin. Lol Jin tayi shiru bata ce komai ba ya saka yayi saurin chanza topic din. "Ina son ganinki sosai Sumayya, amma ban san yadda za'a yi in ganki ba. Ko kina da shawara?" Ta girgiza kanta tana kokarin kawar da shock din waccan maganar tace "bama gidan da ka sani yanzu mun tashi" ya ce "what? Kina nufin duk zaryar dana ringa yi da karawa wuyana tsaho ko zan hango ki a banza nayi ta kenan?" Tayi dariya shima yayi sannan tace "mun tashi daga unguwar" yace "to ina kuka koma?" Tace "naji Hassan yace gobe zaku hadu dashi, ka tambaye shi sai ya baka full address din, ni am not familiar with unguwar har yanzu dan haka ba zan iya yi maka kwatance ba" yace "wannan mutumin? A gurinku ne fa ku yammata yake sakin fuska har da dariya. Da naje office dinsa har na fito banga hakorinsa ba" Sumayya ta sake dariya tace "haba dai, yana da kirki fa sosai. Shi ya siya mana sabon gidan nan da muka dawo" Adam ya taya ta murna sannan ya bata labarin yadda suka yi da Hassan a office dinsa ranar nan, sannan ya kara da cewa "yace gobe inje in same shi. Maybe ya gama binciken nasa ne zan je inji result. Pray for me please" Tayi masa alkawarin addu'a da kuma fatan alkhairi, a ransa yana so ya tambaye ta game da hadin Ruqayyah da Hassan da har zai siya musu gida amma sai yaji kamar yin haka zai zama stepping on the boundary tunda dai ba abinda ya shafe shi bane ba. Sun jima suna hira, yana ta bata labarin yadda yake zuwa unguwar su nemanta baya ganinta. Tana ta yi masa dariya yace "ni ko? Zan rama ne. Dadinta ma kema gashi kin kasa hakuri kin nemi number ta kin kira ni. But Wait, wai layin kine wannan?" Tace "oho maka. Tunda gori zakayi min" yace "to ko ba layin ki bane ba kiyi wa mai layin albishir cewa baccin sa is now limited, dan zanyi ta kira ne ba kakkautawa" sun jima suna hirar su freely like old friends, har sai da ta ji alamar shigowar Ruqayyah palo sannan tayi masa sallama ta kashe wayar, amma ta kasa cire murmushi daga fuskarta. Ruqayyah ta shigo tana binta da kallo, sannan ta kalli wayar tace "sai yanzu kika gama wayar? Tun dazu wayar kike yi" Sumayya tace "a tambayo" tace "wa za'a tambaya? Ke nake tambaya ai" Sumayya tace "shi bai gaya miki number din waye ya bani ba?" Ruqayyah ta zauna tana cewa "ina zai gaya min? Shi bayan maqon kudi ma har maqon magana yake yi. Kwaji dashi daga ke har shi, shi ce min yayi wai wani abokin sa ne ni kuwa nasan ya za'a yi ni bansan kowa a abokan sa ba amma ke ki sani har kuke exchanging numbers" Sumayya bata kula ta ba ta fara chanja kayan ta zuwa na bacci, sai data gama sannan ta zauna a bakin gado tace da Sumayya "Sumayya so nake in ya sake dawowa jibi ki je gurin sa dan Allah kuyi maganar bikin nan, ni bansan me yake shirya wa ba kuma kinga lokaci yana ta kurewa. So nake ya bayar da kudin da za'a siyawa kawayen mu anko kowa a kai mata ba wai ace mutum ya siya ba, nima kuma ya bani kudin kayan fitar biki. Sannan kuyi maganar events din da za'ayi, da event centers din da za'a kama tunda kinga gidan nan ba zai isa ba. Ku dai yi maganar sosai Sumayya ni na kasa yi masa". Sumayya ta tashi zaune tana cewa "to baki sani ba ai koya gama shirya komai. Amma dai zanyi masa maganar ai. Ke ma tun tuni nake miki maganar kawayen nan a samu a gaya musu, a fitar da anko kin ƙi" Ruqayyah ta tabe baki tace "ni so nake yi in na samu aka sai musu ankon sai a kai musu har gida, ai yafi a mutunce. Zan baki list din wadanda za'a siyawa sai ki fada masa number din, in aka yi musu kala biyu ai ya ishe su ko? dasu za'a yi duk events din". Washegari da wuri Adam ya shirya ya tafi office din Hassan, tun kafin 12 din tayi dan kar yayi late ya kara laifi akan wanda yasan already ya riga yayi, dan yasan Hassan ya samu labarin da baya so ya samu din. Yau bai jima yana jira ba, 12 din tana yi aka aiko kiransa. Ya shiga da sallama sannan ya zaune, still fuskar Hassan ba yabo ba fallasa ya mika masa hannu suka gaisa sannan yace "kamar yadda nace maka zan sa a yi min background check to anyi din kuma zance kusan komai yayi dai dai da abinda ka gaya min except your name, ance ba sunan ka Adam ba, traditional name dinka Gbenga, Christian name dinka Joseph. To bansan inda ka samu Adam din ba" Adam yace "it is my Islamic name" Hassan ya daga kafada yace "but baya reading a duk takardun ka" Adam yace "zan gyara ai, so nake in na samu shiga makaranta zan gaya sai in cigaba da using" Hassan yace "it is okay, kawai dai so nake inyi confirming cewa kai din ne ba using info din wani kai ba, duk da dai description din duk irin naka ne sai dai wancan is a Christian kai kuma musulmi. Or aren't you?" Adam ya bata fuska, ransa ya fara baci yace "I am" Hassan yace "an samu misinformation kenan. Sai na dauka cewa ko ba dai dai naji ba sanda kace min you are a muslim, saboda wancan is a Christian daga shi har parents dinsa". Ran Adam ya kara baci yace "to amma shi mai baka info din bai gaya maka cewa Joseph yayi converting to Islam ya chanja sunan sa zuwa Adam sannan ya bar gida two years ago ba? Maybe you should dig dipper" Hassan ya danyi murmushi kadan sannan yace "nasan wannan, just want to confirm, kuma an gaya min Joseph yana da bad temper" Adam ya mike tsaye yace "so does Adam" sannan ya juya ya fice daga office din tare da bugo kofar. Ransa a bace yake har yaje gida, bai san neman aikin zai zamar masa terere ba da bai fara ba tuntuni. Yasan dole zai digging that part of him tun sanda ya gaya masa zaiyi bincike a kansa but bai san zai zauna yayi ta jifansa da kananan maganganu ba, tunda har ya binciko Christian name dinsa kuma ya gaya masa Adam is his Islamic name ai ba kuma sai ya bashi labarin cewa he is a convert ba. Wannan tambarin shi yasa ya bar kano, ya bar iyaye sa da siblings dinsa da friends dinsa gabaki daya saboda ya kasa belonging, to the christians suna kallonsa a matsayin wanda yayi wa addininsa ya kuma yi musu butulci dan haka har farautar rayuwarsa suke yi, to the Muslims kuma suna kallonsa a matsayin wanda yake da wani bakin penti da komai yawan sallarsa da ibadar sa ba zai iya goge shi ba. Wannan yasa ya bar kano ya dawo Kaduna, to burry his past. Asalin iyayen Adam mutanen jahar imo ne, neman kudi ne ya kawo babansa kano, anan aka haife shi a matsayin first born sannan aka haifi brother dinsa Samuel sai kuma sisters guda biyu Gloria da Martha. Lokacin da aka haifi Adam mahaifinsa bashi da kudi sosai, sai daga baya dukiyar sa tayi ta habaka kamar an sakawa flour yeast, dan haka Adam ya tashi ne tare da sauran yaran unguwa, wadanda yawancin su hausawa ne kuma musulmai. Duk gidan da Adam yake shiga wasa gidajen musulmai ne, makarantar da yake zuwa malaman da daliban yawancin su musulmai ne, a na kuma koya musu islamic studies har shi da ba musulmi ba. Kuma wasu lokutan idan abokansa zasu je islamiyya yana binsu ya zauna a aji tare dasu yaji karatun da ake yi musu, Tun daga nan yake son musulunci. Alokacin takaicinsa shine sunday tayi mamansa da babansa su tafi dashi church suje ayi ta waka da kida da rawa, shi a zuciyarsa sai yake ganin a dira goshi a kasa kamar yadda musulmai suke yi a sallah yafi kama da ibada akan ayi rawa ayi waka. Shi kalaman da yake ji ana karantowa a cikin Alqur'ani sunfi yi masa kama da kalaman ubangiji akan abinda pastors dinsu suke fada musu a church. Behavoirs din da yake gani a gurin musulmai tafi yi masa kama data mutanen kirki akan wadda yake gani a gurin iyayensa da sauran Christians. Tun daga nan ya saka musulunci a ransa, har ya girma ya shiga secondary school, a nan ne ya fara fitowa da abinda yake zuciyarsa yana nunawa a fili. Kullum ya samu musulmi sai yayi tayi masa tambayoyi akan addini, in ya shiga cikin abokan da basu san shi Christian bane ba sai yayi basaja ya bisu suje masjid suyi sallah. Anan ya iya sallah complete dinta, ya iya karatun wasu daga cikin surorin Alqur'ani kuma yake karantawa a cikin sallar kamar yadda yaga anayi. And he finds peace duk sanda yayi sallar. He finds peace in the masjid. Tun daga nan ya sani har zuciyarsa cewa musulunci shine addinin gaskiya ba Christianity ba, yasan cewa kuma one day he is going to walk in cikin wani masallaci ya samu imam din yace a musuluntar dashi. Already yasan abinda ake reciting in za'a musulunta din ma kuma ya iya. Already har ya zabi sunan Adam a matsayin sunan da zai zaba. Ya daina zuwa church. Tun daga nan trouble dinsa ya fara, tun daga nan iyayensa suka gane halin da yake ciki. Farkon abinda suka fara yi masa shine cire shi daga school sannan suka dauke shi gabaki daya suka mayar dashi gidan pastor, akayi ta masa wa'azi irin nasu ana yi masa adduoi irin nasu aka rarrataya masa cross iri iri a jikinsa but duk abinda suke yi shiga yake yi ta kunnen hagu yana fita ta dama. The more suka yi masa magana akan Jesus Christ da Bible da Christianity the more yake kara fahimtar cewa it is wrong. Yana kara jin cewa he never belong there, haifarsa kawai akayi a can. Bayan ya dawo gida iyayensa suka fahimci babu chanji sai suka sake daukarsa suka mayar dashi imo gurin kakanninsa suna ganin cewa zama cikin musulmi ne ya jawo musa halin da yake ciki. A can imon kakanninsa suka dora daga inda iyayen suka tsaya, suka kara da binne binne da tsaface tsaface da preaching, pampering, promises amma a banza, a lokacin ne babansa yayi masa kyautar motar da yake ja yanzu saboda yaga yadda yake son mota da kuma alkawarin in dai ya cire musulunci daga ransa zai kai shi kasar waje yayi karatu acan saboda yasan yadda yake son karatun. Anan ne Adam ya nuna musu ya sauko, ya fara binsu zuwa church ana ayyukan ibada tare dashi, ganin haka yasa iyayensa suka dauko shi suka dawo dashi kano tare da su. A lokacin mahaifinsa yayi arziki sosai da sosai Abinda Adam ya fara yi a ranar da suka dawo shine ya shiga cikin masallacin unguwarsu ya durkusa a gaban limamin masallacin yace "ina so a musuluntar dani" and that was it. Babansa a ranar cewa yayi sai ya yanka shi. Limamin unguwar sune ya dauke shi ya boye shi sai ga uban da police wai an sace masa da. Inda ya samu sassauci kawai shine he was 19 years then dan haka he can stand up for himself legally, dan haka ya zamanto his words against his father's words. Ya fada cewa shi baya son komawa gidansu saboda babansa yace zai kashe shi tunda ya musulunta kuma yasan zai iya aikatawa. Wannan yasa dole aka barshi a gidan Imam din but still his father started to hunt him, har makaranta ya aika yan daba su kamo masa shi Allah ya taimaka masa ya gudu, sai liman din ya dauke shi daga unguwar ya mayar dashi hotoro gurin kaninsa. Ananne ya samu ya fara karatun addini ya kuma kammala secondary school dinsa, but anan ne ya fara fuskantar kyama daga gurin musulmai da kuma christians, hatta gidan da ake rikon nasa kyamatarsa suke yi basa barin yayansu su zama close to him. Akwai wata budurwa a gidan da mamanta ta taba zanewa saboda ta shiga dakin da yake ta kai masa abinci. Kuma wani abinda yafi damunsa a lokacin shine in mutane suna kyamar sa sai ya tuno da family dinsa, ya tuno da irin soyayyar da suke yi masa musamman iyayensa shine favorite dinsu Saboda kwazonsa a makaranta da kuma kyawun halittar sa, haka siblings dinsa, ya shaku dasu sosai and he misses them everyday. Sai yayi taji a ransa cewa yana so ya gansu, yana so ya koma gidan su. Sai dai ya kasa chanza ra'ayin sa akan addini, fata kawai yake yi cewa suma su gane gaskiya suyi joining dinsa. Shekarar sa daya a wannan gidan ya fahimci cewa zaman ba zai yi masa haka ba, and that's when his mother found him ashe nemansa take yi tsahon shekarar nan bata huta ba, tunda ta gane inda yake kuma bata huta ba ta cigaba da zarya tana rokonsa ya dawo gida, har siblings dinsa take kawo masa har cikin gidan da yake akan dan su ja ra'ayinsa ya dawo din amma bata saka ubansa a ciki ba saboda shi yayi fushi sosai. Ganinsa da ake yi da mahaifiyar sa sai aka kara kyamatarsa a unguwa ana ganin kamar komawa zaiyi zuwa Christianity, wadansu ma cewa suke yi ya koma, wannan ya saka mai rikon sa ya kirawo shi ya buga masa warning cewa in uwarsa ta kara zuwa gurinsa zai kore shi daga gidansa. And that's when he decided to leave Kano for good. Ya hada kayansa ya je har gidansu lokacin da yasan duk suna church ya sato motarsa ya saka kayan a ciki ya kama hanyar Kaduna. A hanya ne ya dauki waɗansu mutane zuwa Zaria suka biya shi kudin mota, sai kawai yayi deciding cewa he is going to be a taxi driver a haka har ya tara kudi ya kai kanshi makaranta. But kudin sunki taruwa. Sannan yasan karatun ma kuma ba zai zo masa da sauki ba. That's why he needed aikin gurin Hassan saboda yaji possibility na komawa school, but yanzu yana jin cewa he doesn't need it anymore. A ranar da Ruqayyah da Sumayya suka shirya zasu hada kai su tunkari Hassan da Maganar shirye shiryen biki, a ranar da rana sai ga kannensa mata sunzo gidan gabaki dayansu su biyar. A tare dasu akwai akwati guda biyu masu dan girma. Suka shigo da fara'ar su da kuma sallamar su, abinda Ruqayyah ta fara aiyanawa a ranta da taga akwatinan shine; "ba dai wannan ne lefen nawa ba". Daga nan sai ta tashi ta shige daki tun kafin su shigo palon. Inna Ade da Sumayya suka tarye su sosai suma da fara'a, suka gaggaisa Inna tana tambayar su Aunty suka ce tana lafiya lau kuma tana gaisheta. Sai suka fara neman Ruqayyah "ina amaryar tamu take? Sumayya ta waiga tace "tana jin shogowar ku ta gudu daki" Nafisa tayi dariya "ba dai kunyar mu take ji ba? In kuwa har kunyar mu take ji to kuwa na tausaya mata dan kuwa ni ana gama bikin a cikin bedroom dinta zan tare" Hassana ta harare ta tace "kar ku ce zaku takurawa takwara ta dan kungan ta shiru shiru bata da magana, gashi kuma bana nan ballantana in tare mata" Sumayya tace "wacece shiru shirun? Lallai ba ki san Ruqayyah ba alkunya takw yi muku amma in ta saba daku sai kunyi mamaki, watarana sai kunji kamar ku dauki ta ku dawo mana da abarmu" suka yi dariya Safiyya tace "abarku ku abarmu? Ai daga an daura ta zama tamu ku da ita sai tarihi" Inna Ade da take jinsu tana ta murmushi tace da Hassana "ke ce daya amaryar ko?" Hassana ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi, Inna Ade tace Allah ya sanya alkhairi kinji? Allah ya baku zaman lafiya bakiɗaya". Daga nan sai Inna Ade da Sumayya suka fara hidimar bakin su, suka kawo musu duk wani abin sha da abinci da yake available a gidan, su kuma bakin suka diba kadan suka ci banda Khadijah da tace ta koshi. Bayan sun gama ne Hassana tace "dama Aunty ce ta aiko mu, tace mu kawo muku wadannan kayan inji ta, akwati daga kayan amarya ne na fitar biki akwati daya kuma naku ne kuma ku saka da biki. Tata gudummawar kenan" Inna Ade ta rike baki tace "me yasa ta wahalar da kanta har haka? Da ta barshi ma Baban biyu duk zaiyi mana" Hassana tace "ita dai gashinan to ta riga shi samun ladan". Inna da Sumayya suka yi musu godiya sosai sannan kuma Hassana ta kara da cewa "kuma tace mu tambaye ku menene tsarin ku na hidimar biki? Kuma in akwai wata al'ada da kuke yi bayan lefe ku fada kar azo ba'a yi ba tunda bamu sani ba" Inna Ade tace "aa babu wata al'ada wallahi, mu lefen ma da dan tamu ne ai zamu iya cewa Hassan ya barshi" Nafisa tace "ai kuwa lefe kan an riga an gama hada shi, jira kawai ake yi lokaci yayi azo a kawo" Inna Ade tace "maganar biki kuma ki gaya mata mu nan kamu kawai zamuyi sai yini, shikenan sai ku zo ku dauki amaryar ku" Hassana tace "ita amaryar ba zata yi komai ba?" Sumayya tace "jiya muka yi Magana da ita, ita wai kunyar angon ta ke ji ta kasa tambayarsa ko akwai abinda yake shirya musu" Hassana tayi dariya tace "lallai an gaishe ta, to ki gaya mata wallahi sai ta shafawa idonta toka ta cire kunyar nan, dan in dai yaya H1 ne na tabbatar babu abinda yake shiryawa. Gwara ita ta shirya sai ta gaya masa" Sumayya tace "to insha Allahu zan gaya mata" Hassana ta kuma cewa "Inna, kuma Aunty tace in rokar mata ku, dan Allah tana son za'a dauki amarya ranar juma'a da daddare, saboda assabar ne yinin da za'ayi a kano na amaryar yaya Hussain, to Aunty tana so a tafi harda ita Ruqayyah din mu kwana acan lahadi sai a dauko waccen amaryar a dawo" Inna tayi saurin cewa "babu komai ai insha Allah, in babansu ya dawo zan gaya masa kuma shima nasan ba zai ki ba. Sai a daura auren juma'a da safe in yaso da daddare sai a dauke ta". Daga nan suka cigaba da tsare tsaren bikin, maganar kawo lefe da sauran su. Nafisa ta mike, "ni ina ne dakin da yayar tawa take ne inje in ganta, dan ita nazo kuma ba zan tafi ba sai na ganta" Sumayya ta nuna mata kofar dakin da Ruqayyah take ciki sannan ta juya suka cigaba da maganganun su. Sai da suka gama sannan Sumayya ta mike ta shiga zata kirawo Nafisa. Tana shiga dakin ta gansu dare dare akan gado suna hura har da dariya, da alama tasu ta zo daya. Nafisa tana cewa "wallahi ina baki labari, shi yasa wannan karon da Aunty zata tafi dubai karaso siyayyar kayan lefen ki naki binta sai ta tafi da Zulaihat. Kinsan ita Aunty bata son tafiya ita kadai tafi son ta dauki wata a cikin mu ta yafi da ita, shi yasa muke shifting in ya tafi da wannan yanzu wata tafiyar kuma sai ta dauki wata. Kinga in akayi bikin ku kema sai ki shiga layi ake yin shifting din da ke" Ruqayyah baki har kunne, already har ta fara hango kanta a Dubai tace "eh wallahi, sai mu shiga layi dani da wannan yarinyar da Hussain zai aura, Fatima sunan ta ko wa?" Nafisa ta bata rai tace "yarinya? Gimbiya Fatima ba yarinya bace ba dan tare suka gama service da yaya Hassana. A England tayi karatun ta ma ita." Murmushin fuskar Ruqayyah ya dauke, tace "Gimbiya Fatima? Ke ma bakin Hussain kike bi kike ce mata gimbiya?" Nafisa tace "to ai gimbiyar ce, ya ce fa a gurin maimartaba sarkin kano kuma naji ance ita ce favorite dinsa. Kinsan kuma yadda suke da kudi, shi yasa yaya H2 ya zage dantse sosai gurin hada kayan lefenta dan kar azo aji kunya. Jiya ma naga sunzo sun bude gidan sun shiga, wata kila a cikin satin nan zasu fara kaso kayan dakinta. I can't wait to see irin kayan da zasu yi mata" idanuwan Ruqayyah suka chanja kala "you mean she is a real princess?" Nafisa tace "ta gasken gaske ma kuwa" Nineteen: Shattered Dreams Yadda Ruqayyah ta bude bakinta a haka ta barshi, magana ta kasa fitowa. Sumayya tayi saurin cewa "Nafisa ki zo suna jiranki zaku tafi" Nafisa ta sauko daga kan gadon tana gyara skirt dinta sannan ta dauki mayafin ta. "To yayata. Na ganki naji dadin hira dake kuma. Zamu koma sai mun dawo daukan ki" ta fada da yanayin tsokana, but Ruqayyah is in no mood for wasa, Sumayya tayi dariya tana distracting Nafisa tace "haba dai, yanzu kina nufin ba zaku zo komai ba sai daukan amarya? Nafisa tace "ai kinsan can din ma wasu events din ne, kin san biki uku ne zamuyi amma dai nasan ko bamu zo duk ka ba zamu zo wasu abubuwan" Khadijah ta budo kofa tana cewa "to suda me bakin magana, ki taho mu tafi" sai ta kalli Ruqayyah tayi mata murmushin da yafi kama da yake itama Ruqayyah ta mayar mata da irin sa, tana jin murmushin yana kokarin bude fanfon emotions din da take ta kokarin rufewa. Nafisa da Khadijah suka fita a tare, Sumayya tayi wa Ruqayyah alamar ta taso suje su raka su amma sai ta makale kafada ta kwanta ta ja bargo, Sumayya ta fita da sauri tana yi musu Allah ya kiyaye hanya tare da kara yi musu godiya. Ruqayyah ranta kuna yake yi, kalmar Princess ce take ta yawo a cikin kanta, wai yar sarkin kano, sarkin kano fa? Sarkin kanon da take ganin pictures dinsa yanzu a social media, sarkin kanon da tasan kudin takalmin sa daya zai iya siyan duk sutturar da Baba yake da ita har da ciko, yarinyar da akace tayi karatu a kasar waje bayan ita a Nigeria tayi nigerian ma a makarantar gwamnati kuma iyakacin secondary school sannan secondary din ma ko waec bata yi ba saboda talaucin ubanta? Gaskiya akwai aiki a gabanta. Ta tuno maganar Nafisa na she can't wait to see kayan dakin Fatima, ita kuwa babu wanda yake zancen nata tunda kyauta ma za'a yi mata kayan dakin, kuma ta tabbatar watarana sai an goranta mata. Dadin abinma kudin na mijinta ne, shi kansa Hussain din da ake zancen ya hada kayan kefe na gani na fada saboda zai kai gidan sarki ai da dukiyar mijinta yayi, dan zai auri yar sarki hakan bai chanja komai ba, dole ne ta shafawa idanunta toka kafin ta shiga gidan nan kuma dole ta kwatarwa kanta yanci a gurin Hassan dan in babu hadin kansa ba inda zata je za'a mayar da ita ne kamar takalmi kowa ma yake takata da wanda ya isa da wanda bai isa ba. A haka Sumayya ta dawo ta same ta a kwance idanunta a rufe, ta zauna akan bedside tana kallon ta a ranta tasan tunanin da take yi sai tace "it doesn't mean anything. Dan tana yar sarki ke kina yar malam Yusuf mai gadi ba komai bane ba, dan tana gimbiya Fatima ke kina plain Ruqayyah doesn't mean anything, rayuwarki daban rayuwarta daban, Allah ya halicce mu different for a reason, we are all unique for a reason, Allah yana amfani da uniqueness din mu dan yayi testing din mu, dashi yake jarabtar mu dan yaga yadda zamuyi. Idan mukayi kokarin copying others, ko muka yi kokarin comparing kan mu da others to kuwa zamu fadi jarabawar mu saboda mu da su ba daya bane ba. You are Ruqayyah, yar malam Yusuf da yake aiki kullum ba weekend babu annual leave yake ciyar da ke da duk sauran bukatun ki, ita kuma Fatima yar sarkin kanon da shima a sarautar aka haife shi ba wahala yasha ya samu ba, let her be gimbiyar ta matar Hussain while you be Ruqayyah matar Hassan cos that's your role, that's what............" Ruqayyah ta yaye rufar ta ta mike ta shiga toilet tana wanke fuskarta maganganun Sumayya ciwo suke kara wa kanta. Tana fitowa daga toilet din bata kalli inda Sumayya take ba ta wuce palo. Sumayya taji zuciyarta tayi babu dadi, ta jima a zaune a gurin hannayenta tallafe da kuncinta sannan tayi ajjiyar zuciya ta mike ta tafi palon itama. Abin mamaki sai ta samu Ruqayyah kace kace cikin kaya tana ta bubbudewa ita da Suleiman da ya shigo yanzu. Inna tana gefe tana kallon su. Tan fitowa Ruqayyah ta kira ta. "Zo ki taya ni zaben wanda zan saka ranar kamu, kina ganin wannan lace din yayi?" Sumayya ta zauna tana karbar lace din tace "too heavy, kamu ai atamfa ya kamata ki saka. Wannan kuma kya saka ranar yini. Yauwa ga wani yadi can sai ki hada dashi. Kai! Kinga wani takalmi? Amma ya shiga da lace din nan" Ruqayyah sai murmushi take yi tana lissafa irin kyan da zata yi. Gimbiya Fatima is in for a surprise. Da daddare Hassan yazo zance, kamar yadda suka shirya tare suka fita gurinsa. Suna gaisawa da Sumayya yace "mutumin ki fa yayi zuciya, ya tafi kuma bana jin zai sake dawowa" Sumayya ta bude ido tace "me ya faru? Lafiya?" Ya daga kafada yace "maybe na fadi abinda baiji dadi ba I don't know, maybe I was unintentionally rude to him amma ki kirashi ki ba shi hakuri on my behalf please, ina da interest akansa sosai and I like him a lot. I found out something about him da baya son a sani and it pissed him off, ni kuma abinda na samu din shine ya kara min karfin guiwa a kansa. Tell him that dan Allah and make him come back to my office" Sumayya ta dan bata rai tana kokarin hasashen abinda ya hada su amma Sai kawai ta bar maganar saboda bata son Ruqayyah ta shiga ciki amma sai da ta shiga. "Wait, you two, wai maganar me kuke yi ne? Maganar wa kuke yi wanda ku biyu kuka sanshi amma ni bn san shi ba?" Hassan yana kallonta yace "saurayin Sumayya ne,tace kuma kar in gaya miki ban kuma san dalilin ta ba amma zan rike mata amanar ta, it is her call, ita ya kamata ta gaya miki" ya juya yana kallon Sumayya yace "amma zan rike amanar ne daga nan zuwa bikin mu, in akayi biki to I can't promise cewa zan iya boye wa matata wani abu kuma" ya kare maganar yana murmushi, Ruqayyah ta sunkuyar da kanta tana murmushi a ranta tana cewa "you better not". Sumayya ce ta shigar masa da maganar biki, ta tambayeshi plans dinsa, sannan tayi masa bayanin kayan da Aunty ta aiko musu dashi takuma yi godiya. Ya gyada kai yace "yeah, Aunty ta gaya min dazu da naje gida. Ina ganin ku shirya duk abinda kuke son yi ni amma personally babu abinda nake shiryawa gaskiya, akwai dai dinner da zamuyi gabaki dayan mu ranar Sunday bayan an dauko Fatima, dinner ce for dukkan couples din uku da friends din kowa da kuma family din kowa. To ita kadai zanyi attending gaskiya, sai daurin aurarrakin duk ukun. So, in kuka tashi sai ku shirya abinku da friends din ku kawai". Ruqayyah taji tamkar ya kwada mata mari, taki gaya wa friends dinta maganar auren su saboda tana son tayi showing dinsa up a bikin su, amma yana ce mata ba zaiyi attending komai ba, ita kadai zata je ba miji, kamar wadda akayi wa auren dole?" Sumayya tace "it is okay" Ruqayyah tayi saurin juyowa tana kallon ta tana jin kamar ta makure ta, it is definitely not okay. Ita da ta kirawo ta saboda ta taya ta fighting shine zata yi saurin giving up? Yace "duk abinda kuke so fa ku fada kar ku boye min. Zan aiko muku da kudin da zasu ishe ku komai, in na baku kuma ko bai ishe ku ba ku gaya min sai in kara muku, ai nasan ba zakuyi abinda bashi da muhimmanci ba ko Hassana?" ta gyada kanta da sauri tana kirkirar murmushi, ba haka taso ba amma sai zuciyarta, har dark heart ta hana ta yin magana, a take kuma ta kitsa mata abinda zata yi. Washegari kuwa sai ga sakon kudi ya aiko musu dashi, kudade ne masu yawa a idon Sumayya da Inna Ade da sauran mutanen gida, but as usual a gurin Ruqayyah taga kankantarsa duk kuwa da cewa bata taba rike kudi masu wannan yawan ba, ita kawai position dinsa take hangowa tana ganin yafi karfin wannan kudin. Sai ta saci jiki ta shiga daki ta dauki wayar Sumayya ta rubuta masa sako kamar haka. Assalam. Yaya Hassan ina yini? Munga min gode sosai Allah ya kara arziki. Sai dai muna so ko za'a karo mana wasu dan ina ganin kamar wadannan din ba zasu ishe mu ba, kawayen mu suna da yawa, zamu yi arabian night da bridal shower kuma zamu basu soveniers gashi muna so muyi musu anko kala bibbiyu. Ruqayyah tace a barshi kawai amma sai nace bara ni inyi maka magana tunda kace in basu isa ba a gaya maka. Nagode Sumayya Ta tura masa sannan ta goge message din ta juya tayi kwanciyar ta. Ba'a jima ba ya kira wayarta, ta dauka ta gaishe shi sannan tace "munga sako dazu, mun gode sosai. Nace amma wadannan kudaden ai kamar sunyi yawa ko? Me zamuyi da kudi har haka, da rabin su ma ka bayar ai da sun isa" sai taji ya yi dariya, muryar sa cike da farin cikin da zuciyarsa take ciki, yace "dariya na baka ko?" Yace "nooo ba ke kika bani dariya ba, zuciyata ce cike da murna da farin cikin samunki a matsayin matata, a yanzu haka bani da buri illa inga ranar da za'a daura auren mu in ganki a gida na a matsayin matata, gaskiya daga ranar banajin ina da sauran wani buri a rayuwa dan nasan with you by my side my life will be completed" murya can kasa tace "so will mine". Yace "yanzu na samu sako daga Sumayya, tana zancen wai kudin ba zasu ishe ku ba" Ruqayyah tace "what? Amma lallai wannan Sumayyan...." Yace "it is okay. Kowa dama ai da halinsa da kuma kalar tunanin sa. Sumayya kanwa tace dan haka ba zan watsa mata kasa a ido ba saboda nasan duk danke take yi sannan kuma yarinta ma tana damunta wai harda cews za'a yi wa kawayen ku anko kala bibbiyu" ya sake yin dariya, "babu wani abu, zan sake aiko da wasu kudin but kiyi monitoring dinta kar tayi almubazzaranci da yawa" Ruqayyah ta karya murya "ni wallahi da ka barshi ma. Wannan ai ni ta bawa kunya wallahi" yace "kunya, mijin naki kike jin kunya?" Tayi dariya, yace "kar kiyi mata maganar,kar ma ki nuna mata nace bata yi dai dai ba, dan mu take yi kinji? For you, I will do anything" tace "nagode. Allah ya bar mu tare har abada" yace "ameen, ni har gaban abada ma nake so muje tare. In naje office gobe zan aiko da sakon". Washegari sai ta zama alert, tasan zai aiko da sakon kuma bata son wano ya rigata karba, dan haka a hannunta dan aiken ya danka envelope din. Ta wuce daki ta kirga taga dai dai yawan wadancan ne, sai ta bude cikin kayanta ta dauko wadancan kudin da take ta ajiiyar su na wajen Hussain ta hada da wadannan a ranta tana cewa, "in kasan wata ai baka san wata ba. Dole in tara kudi ko dan in kankarowa kaina mutumci a gurin yan uwanka da sauran mutane". Sau ta debi kadan ta bawa Sumayya tace "inji Hassan, wai ko zaki yi wani abu" Sumayya tace "ni me zanyi? Duk abinda zanyi ai tare dake zamuyi. Shi dai kawai ya fiya kirki". Next zuwan da Hassan yayi suka hadu da Sumayya yace "sako na yazo miki ko?" Ta yi murmushi tace "yazo fa, na gode sosai" yace "asha biki lafiya". Tun ranar da Hassan ya gaya wa Sumayya yadda suka yi da Adam take neman layinsa amma yaki dauka, sai bayan kwana biyu sai ta tura masa text "In na sake kiran ka baka dauka ba ba zan sake kiran ka ba" Mintuna kadan bayan nan sai gashi ya kira ta, tana dauka yace "why? Me yasa ba zaki sake kirana ba? Saboda abin da ya gaya miki a kaina ko?" Tace "me ya gaya min a kanka? Ni babu abinda ya gaya min a kanka kawai dai yace kayi fushi in kira ka in baka hakuri on his behalf, yace kaje ka karbi aikin" taji yayi ajjiyar zuciya sannan yace "naki daukan wayarki ne saboda bana son inji kalmomin daga bakin ki, na dauka ya gaya miki, na dauka kin kira ni ne kiyi robbing abin a fuskarta" tace "wanne abin kenan? Menene abinda baka so in sani?" Ya danyi shiru sannan carefully yace "ba wai bana so ki sani bane ba, ina tsoron yadda zaki yo reacting ne idan kin sani ɗin" tace "idan nasan me? Ba zaka gane ya zanyi reacting ba har sai ka gaya min tukunna" murya can kasa yace "reacting to the fact that I am a religious convert. I was a christian before..." Ya rintse idonta tare da kwanciya akan gado. She suspected as much, amma tafi son ya furta mata da bakinsa. Tace "you said it yourself, you said the word "before' before yana magana akan past, past is in the past, you are a muslim now, and that's all that matters. Kaje ka karbi aikinka, yace it doesn't matter" yace "I don't care about the job, I care more about you, zaki iya cigaba da kula....zaki ke kula....." Ya kasa fadan kalmar sai tace "kula musulmi? Idan ban kula musulmi ba wa kake son in kula Adam?" Ya lumshe idonsa ya bude "but my parents are still......" Tace "your parents are not you. Kai daban su daban, ba'a taba judging wani a bisa laifin wani. It doesn't matter who you were, what matters is who you are. And you are a muslim, you are Adam. And I like you" ya sauke ajjiyar zuciya mai karfi yana dora goshinsa akan stirring motarsa. Tun ranar nan, ranar daya saka kafafuwansa cikin masallacin nan ya karbi kalmar shahada bai taba jin wani ya gaya masa wadannan kalmomin da sune abinda yafi so yaji fiye da komai ba, cewa his past doesn't matter, kowa nuna masa yake yi kamar past dinsa wani rubutu ne a goshinsa da ba zai taba gogewa ba. Shi kuma tun kafin ya karbi addinin a dan ilimin da yake dashi akan Islam yasan cewa duk wanda ya musulunta tamkar sabon jariri yake, duk abinda ya aikata ya wuce kamar bai taba yi ba, an bude masa sabon littafi. But nobody made him feel like that, sai yau, sai Sumayya. Yace "thank you" yadda yace thank you din kawai yasa ta fahimci daga can wani lungu na zuciyarsa ya fade ta. Taji itama maganar ta taba tata zuciyar. Tace "kaje ka karbin aikin Adam, you need it" sai ta danyi dariya tace "kuma kasan me? In ka karbi aikin we will be closer tunda Ruqayyah zata yi aure a gidan" yayi dariya shima yace "you mean zan ke ganin ki ba tare dana yi dogon wuya ba" suka yi dariya a tare. Adam yaje gurin Hassan, ya kuma karbi aikin personal driver na Hussain. Kallo daya Hussain yayi masa yace "he is strong, young and handsome. I like him" daga nan ya shiga daki ya kwaso masa kayan sawa jaka guda da takalma da huluna yace "a cigaba da gayu daga inda aka tsaya" Lokaci ya tura, satin biki ya kama. Tun farkon satin yan'uwa da abokan arzikin Inna Ade da Baba suka cika gidan, da yawa sunzo ne dan su kashe kwarkwatar idonsu akan zancen da suka ji na wanda Ruqayyah zata aura. Ita kuma Ruqayyah sai da ta tabbatar duk wanda yazo gidan nasu, ko a kawayen data gayyato ko kuma a yan'uwa ya san wa zata aura."CEO ne na H & H group of companies" daga nan sai ta bi sakakkun bakunan su da kallo tana jin cewa she have made it in life. Ruqayyah duk tayi abubuwan da take son yi da First kudin da Hassan ya bata, ta zabi friends na fita kunya, most of them ma ba kawayen ta bane ba kawayen Minal ne. Suka shirya bridal shower dinsu a gidan Aunty Hafsa yayar Minal aka ci aka sha aka yanka cake akayi hotuna, shigar da Ruqayyah tayi kowa sai ya tabbatar da abinda take fada akan mijin da zata aura, kowa ya tabbatar shi din ne dai. Akayi yini anan gidan su ranar Alhamis, a ranar ne kuma aka kawo lefen Ruqayyah. Hatta ita kanta Ruqayyah duk abinta sai data yadda cewa tabbas anyi mata lefe, dan bata taba ji ko ganin lefe irin nata ba. A hankali a hankali take jin burikanta na rayuwa suna cika. Ranar juma'a da safe aka daura auren Hassan Aminu Abdullahi da Ruqayyah Yusuf Mu'awiyah. Farin ciki a gurin ango da amarya ba zai misaltu ba, kowa da abinda yake zuciyarsa, kowa da sirrin da yake zuciyarsa. Sai dai muyi mudu fatan zaman lafiya da zuriya mai albarka. Gobe zamu kai amarya dakinta insha Allah, daga nan kuma sai muje kano mu dauko daya amaryar. Wannan littafin na siyarwa ne, duk wanda yake so ya neme ni through WhatsApp ta wannan number din 08067081020 Twenty : Shattered Dreams 2 Yinin ranar nan murmushi ya kasa daukewa daga fuskar Ruqayyah, kowa in ya ganta sai yaga ta burge shi ga kyau, ga kwalliyar da ta ci ta gani ta fada, ga gyaran jiki da taje ta kashe kudi aka yi mata sannan ga farin ciki lullube da zuciyarta da kuma fuskarta. Yau ce ranar da burikanta suka fara cika, yau ce ranar data taka wani matsayi wanda zai zamo mata jagora zuwa ga matsayi na gaba a rayuwarta. Sumayya kuma tunda aka gama daura auren taji jikinta yayi sanyi matuka, ita kawai lissafin rabuwa da yar uwarta rabin jikinta take yi, bata jin tun da aka haliccesu sun taba rabuwa ta cikakken kwana daya amma wai yau Ruqayyah zata tattara ta koma wani gidan da zama kachokan. Tsakanin su sai dai ziyara, ziyarar ma tasan Baba ba barinta zai ke yi tana yi akai akai ba kamar yadda bata ga alamar Hassan zai zamo mai barin mata tana yawo koda yaushe ba. Sai data shiga toilet tayi kukan rabuwa da yar uwarta, amma ita yar uwar tata ko a jikinta, hirarta kawai take yi a cikin kawayen aronta suna ta dauke dauken hotuna tare da shirin dinner din da za'a yi ranar Lahadi da daddare. Already dama Hassan ya kawo mata cards na mutum hamsin, wanda sai da suka yi rigima da Sumayya dan boyewa tayi ta hana yan uwansu da suka zo biki "zuwa zasuyi wallahi su tsinka ni a cikin mutane, wasu fa ko cin abinci da chokali basu iya ba, gwara mu aro mutanen da zasu je a matsayin yanuwana shikenan mun huta. Mu dan dauki kudi mu basu sannan mu basu kudin liki" amma Sumayya taki yarda, dan me bayan ga yan uwanka sannan zaka tafi kaje kayi hayar yan uwa? Ita bata ga logic a cikin maganar ba. Ta gayawa Inna Ade ita kuma ta kira Ruqayyah tace mata "bani katinan" dole ta dauko ta miko mata tana kunkuni. Inna Ade ta bata guda ashirin na kawayenta sannan sauran ta rabawa duk wanda take ganin in ya dace yaje yaci arziki ya bar arziki a mazauninsa. Juma'a din tunda yamma aka fara shirye shiryen kai amarya, Ruqayyah ta hada kayanta kaf a guri daya, ita bata yi wani alkunya ma ba na kin hada kaya ta bar Sumayya ta hada mata a'a tare suka hada ɗin, tana tunawa Sumayya akan duk abinda ta manta. Ita bata ga wani abinda zai saka ta bata ranta ko tayi wani kuka ba a ranar da ya kamata tayi farin ciki fiye da wanda take yi a kowacce rana, a ranar data yage rigar talauci ta lulluba ta arziki? Tun da yamma Inna Ade ta aika aka kirawo Hassana zuwa dakin Baba, suka tafi tare da Sumayya, tun kafin suje Ruqayyah ta riga tasan dalilin kiran, tasan fada ne za'a yi mata a kan zaman aure ita kuma tana ganin kamar bata lokacin su zasu yi su kuma bata bakin su, su fa irin zaman auren talakawa suka sani dan haka akan irinsa zasuyi ma ta fada, wannan kuwa aure na na masu abin hannunsu wadanda basu dawata sauran damuwa a duniya sai dai suci mai kyau su sha mai kyau su kuma kwanta a mai kyau. Ita tuntuni ta gama yiwa kanta fada akan yadda zata yi wannan zaman auren, ta riga ta kama bakin zaren Hassan ta fahimci cewa ba zata iya yi masa musu ba saboda yayi mata kwarjini dayawa amma zata iya cigaba da lullube kanta da hijabin daga riga ya santa dashi sannan tana jan zaren sa a hankali ta karkashin kasa kamar yadda tayi masa a lokacin karbar kudin hidimar biki. Let someone else take the fall, someone else, in dai har ba ita bace ba. Anyone. Suna shiga dakin sai taji Baba ya fara tsokanar ta, abinda ta jima bata ji yayi ba, da alama shima yana alhinin rabuwa da yar tasa ne. Sai da ya saka su duk yi dariya gabaki dayan su sannan ya fara magana. "To Hassana, alhamdulillah, gashi kamar yau Allah ya bamu ku keda yaruwarki amma gashi cikin kudirarsa yau zaki bar gidan nan zuwa gidan mijin ki. Babu abinda zamu cewa Allah sai dai godiya tunda munsan kudirarsa ce kawai ta hada ku keda Hassan sannan ta saka soyayyar ki a zuciyar Hassan din. Dan girman Allah Ruqayyah kar ki bamu kunya, ina tsananin ganin girman yaron nan wallahi kuma in da zaki bi ta ta shi na tabbatar ba karamin zaman lafiya zaku yi ba tunda yana son ki sosai. Da farko shi aure bautar ubangiji ne, ita kuma bauta ita ce abinda ake yi dan a samu shiga aljanna, ita ce kuma abinda idan an ƙi yi sai a halaka a fada wuta Allah ya kiyaye, wannan kadai ya nuna miki darajar abinda kika yi, aure. Aure sunna ne, amma abinda ake yi a cikinsa farilla ne, dole ne ki bi mijinki Ruqayyah indai kina son lahirar ki tayi kyau, dole ki sauke wannan bakar zuciyar taki da wannan saurin fushin naki kiyi masa biyayya Hassana idan ba haka ba ina tausaya miki, ina tausayawa duniyar ki da lahirar ki baki daya" Baba ya jima yana ta yiwa Ruqayyah fada, fadan daya saka Sumayya kuka amma ba Ruqayyah ba. Bayan ya gama yayi mata adduoi na fatan zaman lafiya a gidan mijinta sannan yayi musu sallama ya fita. Bayan ya fita ne Inna da yanuwanta da suka zo daga zamfara suka dora da nasu, suka yi mata doguwar nasiha akan zaman aure da kuma hanyoyin da za'a kyautatawa miji ta hanyar magana mai dadi, godiya, ladabi da biyayya, nuna soyayya da kulawa "ki mayar da duk abinda ya shafe shi ya zama top priority dinki, yan uwansa su zama naki, shimfidar ki ta zama abinda kullum yake muradin komawa ga, abincin ki ya zamanto shi kadai yake iya ci yaji dadi, wadannan sune manyan abinda namiji yake bukata. In dai har kin rike wadannan to kuwa ba kya bukatar boka ko Malam akan mijinki. Zaki juya kayan ki yadda kika ga dama musamman idan yana sonki" Daga nan kuma sai suka dauko nata tsarabar da suka taho mata da ita suka fara bata, dake dake ne da kulle kulle iri iri, wasu a leda wasu a robobi da kwalabe ko wanne an rubuta yadda za'a yi amfani dashi. Gwoggo Habibah tace "bamu baki su bane ba saboda bamu san kalar halittar ki ba kema kuma baki san ta mijin ki ba, dan haka sai kinje gidan kin kwana biyu kin fara gane yadda abin yake sannan zan kira ki in kara miki bayanin abinda kike bukata da kuma yadda zaki yi amfani da shi sosai. Ko wacce mace da irin halittar ta haka suma mazan, in akaje akayi ta bawa yarinya abubuwan da suka fi karfinta sai azo a zamu matsala kuma. " Bayan sun gama nasu sannan sauran yanuwa kowa yazo ya dora da nasa, hakuri, biyayya, girmama wa, soyayya, su akayi ta maimaita wa Ruqayyah har sai data ji ta haddace kalaman tsaf a kwakwalwar ta. Abinda Ya rage mata shine yin amfani na kalmomin. Bayan magrib akazo daukan amarya. Aunty ce da kanta tare da hajiyan Kano, kanwar baban su Hassan su suka jagoranci sauran mata zuwa dauko Ruqayyah, Ruqayyah har tayi wankan ta ta shirya cikin wata green atamfa mai adon pink wadda tayi matukar karbar ta, dinkin yayi kyau sosai a jikin ta, sai a lokacin taga Sumayya tana kuka sannan nata jikin ya fara sanyi, sannan ta fara tunanin zata yi missing Sumayya da sauran yan gidansu, sai kuma tayi saurin kawar da maganar ta hanyar gayawa kanta cewa ai zata ke yawan zuwa tana ganinsu, suma kuma haka musamman in suka je gidan nata suka ga daular da taje ciki. Kuma zata saka Hassan yazo ya roki Baba ya bar Sumayya ta koma can da zama. Sai a lokacin taga ana fito kayan gararta, ita bata san ma cewa anyi mata garar ba kuma bata da idea a inda Baba ya samo kudin yin garar. Ta daiji Aunty tana cewa "haba malama Sa'adatu, dan me zaku takura kanku kuce lallai sai kunyi gara? Ai da kun barta kawai" Inna Ade tace "aa auntyn yara, ai babu wani takura kai wallahi, kayan dakin ma dan dai an saka lokacin ne gajere Amma da babansu duk zaiyi dai dai iyawarsa". Bayan anyi duk abubuwan da akeyi na al'ada cikin barkwanci da wasa da dariya tsakanin bangarorin biyu sai aka bayar da Ruqayyah Aunty ta rungumo ta ta fito da ita ta saka ta a motar da tazo a cikinta ita da hajiyan kano da gwoggo Habibah sauran motocin da suka zo daukan yan uwan amarya suka mara musu baya. Sumayya ta tambayi inna ta hada yan kayanta a karamar jaka, tana so zata raka Ruqayyah kano, so take sai an gama bikin gaba-daya sannan zata dawo gida. Tun da ta fito kofar gidan ta samu gefe daya ta tsaya hannunta rike da jakarta tana ta sharar hawayen ta tana bin mutanen da suke ta turereniyar shiga motoci da kallo, sai kuma taji tana jin haushin kanta na damuwar da tayi, ita me auren ma ko a jikinta dan ko digon kwalla bata gani a idanuwan ta ba amma ita har nata idanuwan sun kumbura saboda kuka. Tana tsaye taji mutum a kusa da ita, ta gefen idonta ta gane namiji ne dan haka ta yi saurin juyowa side dinsa a tsorace, ya jefe ta da best smile dinsa, ta ji half of damuwarta ta tafi amma sai ta kara bata rai "har da kai aka zo za'a dauke min yar uwa ta ko Adam?" Yayi dariya "mu menene laifin mu? Gidan miji fa zamu kaita, at least ai yanzu zata daina runton kudin mota" Sumayya ta harare shi "be careful, matar ogan ka ce dai yanzu, or else you get fired" ya saka hannu ya kama bakinsa ya ce nayi shiru, ba zan kara cewa komai ba" Sumayya ta nuna shi tace "you better, kasan Hassan baya wasa da yara" yace "yeah, ba sai kin tuna min ba na sani, Hussain ne mai wasa da dariya, dadinta kuma shi na ke yiwa aiki ba Hassan ba" tace "amma Hassan din ne ya dauke ka aikin kuma he can fire you" yace "to mai mijin sister, naji, can we go now" yayi kasa kasa da murya yace "daga ni sai ke, na boye motar da nazo da ita" ya kashe mata ido. Yayi gaba, da kamar ba zata bishi ba sai kuma ta juya tana waige waige sai data tabbatar babu wanda hankalin sa yake kanta sannan ta bishi inda taga yayi, tana zuwa ya zagayo ya bude mata kofar front seat ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga gurin driver ya tayar da motar. Sai kuma ta juyo tana kallonsa da budaddun idanunta tace "gidan amaryar zaka kaini ai ko?" Bai kalle ta ba yace "yeah, sure" ta kuma cewa "ba wani gurin zaka kaini ba ko?" Ya juyo yana kallonta da guntun murmushi a bakinsa yace "babu inda zan kaiki, daga nan straight zuwa gidan oga Hassan" tace "ka rantse" yace "I cross my heart and hope to die" ta bata rai tace "da Allah ai nace ka rantse" seriously yace "na rantse da Allah ba sace ki zanyi ba. Can we go now?" Dogon convoy aka hada ana ta sharara gudu akan titinan garin Kaduna, manyan mata suna ta rangada guda yayinda samari da yammata kuma suke kara volume din kida suna rausaya a cikin motoci, amarya kuwa motarta na tsakiya tana jinta kamar a cikin gajimare take tafiya ba wai a cikin mota ba. Ta lullube fuskarta da mayafinta amma da yake ba mai duhu bane ba tana hango gabanta, a haka har suka isa low cost, har suka shiga jerin gidajen da a cikin films da kuma social media ne kawai take ganin irin su. Ta bude ido sosai zuciyarta tana bugawa da karfi tana son ganin wanne ne nata a ciki, a haka taga anzo kofar gidan tun daga wajensa zata iya cewa kaf jerin gidajen babu wanda ya kaishi kyau da tsari. Aka bude gate, mutane da yawa a ciki mata suna ta guda, wannan ya tabbatar mata da cewa wannan shine gidan nata, sai da motar taje gaban gidan sannan ta lura gidajen guda biyu ne a jere amma ko kusa basu yi kama da junan su ba, na farkon yayi ukun na biyun, tayi murmushi a ranta, maybe na biyun na Hussain ne, ko daga nan wannan so call gimbiyar zata gane tayi mata zarra. Amma sai me, sai taga an wuce katon an tafi ga an karamin, sai a lokacin ta lura cewa kofofin katon a rufe suke fitulun sa a kashe karamin kum komai a bude yake tana iya hango mutane a ciki ma. Ta juya side din Aunty, zuciyarta tan agaya mata t tunawa Aunty cewa anyi mistake ba nan ne gidan Hassan ba nan gidan Hussain ne. Amma sai taji aunty tana cewa "alhamdulillah Ruqayyah Allah y kawo ki gidan ki lafiya, sai kiyi masa godiya sannan ki fito da kafar dama tare da bismillah" sai wata zuciyar ta gaya mata to ko nan part din Aunty da yara ne aka kawo ta ayi mata fada sannan a kaita part dinta? Yes, that must be it. Ta fito da bismillah kamar yadda Aunty tace, sannan Hajiyan Kano ta kama hannayenta tana tafiya da ita yan uwanta ta suka rako ta suna take musu baya. A palo ne taga hoton su ita da Hassan wanda suka dauka last week yace enlargement za'a yi musu a kafe musu a palon su. Kafafuwanta taji sun kasa daukan ta, jikinta yayi sanyi kwakwalwar ta tana neman toshewa. Ta tafi kamar zata fadi, Aunty tayi saurin riketa "subhanallah. Ruqayyah lafiya? Sai ta taba wuyanta, wuyan da lokaci daya da dauki mugun zafi ta ce "ya salam, jikinta zafi, dama bata jin dadi?" Goggo Habibah yayar Inna Ade tace "anya kuwa, kamar lafiyar ta kalau" Ruqayyah ta fara kuka a hankali irin wanda sheshsheka ce kawai take fitowa, tana jin tamkar duniya ce gabaki daya take ruguzo mata aka, tana jin kamar duk mafarkanta suna tarwatsewa a gaban idonta. Zuciyarta tana rada mata wata magana, wata mummunar magana. Hussain shine CEO na H and H ba Hassan ba. And that explains alot of things. Tayi saurin tana girgiza kanta kamar mai fada fa zuciyar tata. No, no, no. Ta ringa maimaitawa She felt her dreams shattering. Ta sake girgiza kanta trying to comport herself, wani barin na zuciyarta yana gaya mata "ba haka bane ba, kinsan Hassan da makale aljihu, shine zai zabi gina karamin gida ba wai dan ba shine mai Company ba" sai daya barin yace "kuma sai yabar kaninsa ya gina babban gidan da ya fi nashi?" Nan take sautin kukanta ya karu Kuka take yi kamar ranta zai fita, Hassan ya yaudareta yaci amanar ta, yayi mata karya dan ya aureta. Zuciyarta zafi take mata, zuciyarta ciwo take yi mata, anya kuwa ba ciwon zuciya ne zai kama ta ba? Tana jin maganganun mutane a kusa da ita, yawancin su hakuri suke bata, sama sama kuma tana jin dariyar wasu. Sai ta fahimci sun dauka kukan barin gida take yi. "Kaji yarinyar nan, har muna yabonta muna cewa yarinya karama amma bata yi kuka ba ashe kukan zuci take yi sai yanzu zata yi na fili" "kiyi hakuri Ruqayyah, muma duk da haka muka sossoma wai kuturu yaga mai kyasbi" suka kwashe da dariya wasu daga ciki suka yi guda, "ni sanda za'a kaini gidan nawa mijin ma guduwa nayi, sai da akayi ta nema na aka rasa har aka hakura sannan na dawo, ina dawowa kuwa aka kama ni aka kaini" aka sake wata dariyar. Ruqayyah taji tamkar ta samu bindiga Ak47 duk ta bi su da bullet goma goma. Dan dai tasan sun fi ta karfi ne da babu Abinda zai hana ta tashi ta rufe duk mutanen gurin da duka. But bata son ta bata rawar ta da tsalle, zargi ne ai kawai take yi, bata tabbatar ba lokacin taji muryar Nafisa a kusa da ita, "kiyi hakuri kiyi shiru kinji yayata kar kanki yazo yana yi miki ciwo, kinga duk su Aunty tsokanar ki suke yi" sai itama tayi dariyar sannan kuma ta juya tana waigen neman Sumayya tace "ina Sumayya? Wata kila ita zata iya rarrashinta" "Kaga Adam kazo ka mayar dani inda ka dauko ni ko kuma ka kaini inda zaka kaini, ka daina yawo dani a titi" yace "sai kinyi dariya tukunna. Haka kawai dan Ruqayyah tayi aure sai ki zauna kiyi ta kuka har idonki yayi wannan kumburin? Kinga fuskarki kuwa?" ta kuma hade rai "ni bana cikin mood din dariya, dan Allah ka rabu dani" yace "in rabu dake fa kika ce? Kamar fa kina nufin in rabu da wani sashe na jikina in daina amfani dashi kenan fa? Kina ganin haka zai yiwu?" Ta kara hade rai "kaga fa za'a neme ni a can, in aka fahimci yawo na tafi kuma za'a yi min fada. Dan Allah ka kaini, ni jikina bani yake yi kamar Ruqayyah tana nema na" yace "Ruqayyah da aka kai dakin miji, maybe ma suna can suna zuba soyayya ita da mijin ta ke kina nan kin hana ni ganin hakorinki" tace " koma dai me take yi ni ka kaini in ganta, dan Allah" yace "sai kin yi dariya" ta sake hade rai yace "Please, pretty please!" Ta dauke kanta gefe daya sai ya saki stirring ya hade hannayensa alamar roko "Please Please Please" da sauri tace "Adam zaka yar da mu fa?" Yace "kiyi dariya to" ba shiri ta yangare baki daga gani kasan dariyar karya ce, ya kama stirring yana dariya yace "bara dai in kaiki, ba dan halinki ba" sannan ya juya kan motar zuwa gidan su Hussain. Suna shiga idanunta suka sauka a kan gidan Hussain, ta saki baki tana kallo sai taga kuma gidan Hassan, sannan sai taga sunyi packing a kofar Hassan, ta juya tana kallon gidan Hussain sai kuma ta sake dawowa ta kalli gidan Hassan, tagan shi a bude mutane suna ta hada hada, daga ciki ta jiyo an rangada guda. Gabanta ya fadi, ta juyo da budaddun idanuwa tana kallon Adam fuskarta da alamun tambaya. Yace "can gidan oga Hussain ne, he Calls himself "dangoten Kaduna" . Nan shine gidan Ruqayyah, gidan oga Hassan kenan. Nan zaki shiga". Sumayya bata jira sauran wani karin bayani ba ta bude kofar mota ta fita da sauri, ko rufewa bata tsaya tayi ba, yace "hey, babu thank you balle goodnight? Kin bar jakarki a ciki" bata ko kalle shi ba ta shige gidan da sauri. Tun a bakin kofa ta jiyo gunjin kulan Ruqayyah, gabanta ya fadi. Innalillahi, wannan wanne irin rashin ta ido Ruqayyah take nuna wa? Ba tare da tunanin komai ba ta ratsa mutanen da suke palon har zuwa gaban Ruqayyah da har yanzu take durkushe a kasa tana ta risgar kuka da iyakacin karfin ta. Nafisa tace "alhamdulillah, ga Sumayyan nan ma, zo ki yi mata magana ko zata yi shiru" Sumayya ta durkusa a gaban Ruqayyah sannan ta tallafi fuskarta a hannayenta tana jin yadda fatarta tayi zafi, ba tare data ce mata komai ba sai ta kama ta ta mikar da ita tsaye ta rungume ta a jikinta ta fara tafiya tace "ina za'a kaita?" Nan take aka yi mata jagora zuwa Bedroom din Ruqayyah da yake sama. Ta zaunar da ita a bakin gado kamar yadda ake zaunar da ko wacce amarya sannan ta goge mata hawayen fuskarta ta ja mayafi ta rufe mata fuskarta ta kuma zauna a kusa da ita ta rike hannun ta a cikin nata, a hankali Ruqayyah tace "Sumayya, Hassan ya yaudare ni" Sumayya tayi shiru bata bata amsa ba saboda mutane da suka fara shigowa, suna ta tsokanar Ruqayyah da sunan amarya mai kuka, yan uwansu da suka kawo ta suka yi mata sallama abokan wasa suna tsokanar ta, kusan kuma duk wanda yazo yi mata sallama sai ya yabi gidanta "Ruqayyah ki godewa Allah, kinga kyawun gidan ki kuwa? Masha Allah. Wannan miji naki ba karamin sonki yake ba, ki rike kayan ki hannu bibbiyu Allah kuma ya baku zaman lafiya" Sumayya ce mai amsawa da ameen. Sai da aka ragu saura kawayensu da suke palon kasa suna ta dauke dauken hotuna dan a samu na burga sannan Sumayya ta rufe kofar dakin ta dawo kusa da Ruqayyah ta zauna tace "Ruqayyah me nene hakan kika so ki aikata? Wannan wanne irin abin kunya kika so ki jawo wa kanki ki jawo mana?" Ruqayyah ta bude fuskarta data kumbura cikin dasashshiyar murya tace "abin kunya? Abin kunya kike magana akai? Shin baki kalli gidan can ba? Kin tambayi kanki gidan waye kuwa?" Sumayya tace "ba kaina na tambaya ba, mai motar daya kawo ni na tambaya kuma ya gaya min cewa gidan Hussain ne and so what? Me yasa za ki juya ki kalli gidan Hussain bayan ga gidan Hassan kina cikin sa? Me yasa ba zaki kalli abinda yake hannun kin a matsayin mallakin ki ba sai kike juyawa kina kallon abin hannun wani? Ba ki ji abinda yanuwan mu suke fada ba? Cewa badu taba ganin gidan da yake da kyawun naki ba? Ni ma kuma haka, ban taba shiga gida mai kyan wannan ba, ban taba zama a kan gadon mai kyan wannan ba. Which of the favors of your God do you deny?" Ruqayyah tace "amma ba kya ganin kasancewar gidan Hussain yafi na Hassan yana nufin ba Hassan ne mai Company ba?" Sumayya tace "and so what? Hassan kika aura ko kuma Company kika aura? Ni I don't get you Ruqayyah. Na kasa gane kanki. Me kike so ne? Hassan mutum ne mai nagarta da kamala da sanin ya kamata, mai addini mai asali mai kyawun sura, mai lafiya mai aikin yi da rufin asiri, no ba rufin asiri ba, mai arziki. What more do you want" Ruqayyah ta mike kamar an mintsine ta tace cikin daga murya "but he made me believe cewa Companyn sa ne. He made a fool of me" Sumayya tayi saurin yi mata alama da tayi shiru, ta na leqa window sannan tace "yaushe? Ban sani ba ko kunyi maganar sanda bana tare daku amma ni ban taba jin ya jingina kansa da H and H ba, ni ban ma taba jin ya ambaci sunan kamfanin ba" Ruqayyah ta dafe kanta tan zama a bakin gado tare da cigaba da kuka tana jin kanta kamar zai tsage, Sumayya ta dawo ta zauna kusa da ita tace "kin taba zama kinyi tunanin ma'anar H and H?" Ruqayyah ta juyo tana kallonta amma bata ce komai ba, ita bata taba tunanin me yake nufi ba. Sumayya tace "ni ma ban sani ba, but ina tunanin Hassan da Hussain yake nufi" Ruqayyah tayi saurin cewa "meaning nasu ne su biyu right?" Sumayya tace "maybe, maybe not, but you will soon find out tunda kin auri daya daga cikin su. Am sure zai gaya miki koma na waye a cikin su. But Please Ruqayyah ki kwantar da hankalin ki, dan Allah kar ki nuna masa cewa hakan wani abu ne" Ruqayyah ta rike hannunta tana hawaye "dan Allah Sumayya ki kwana anan. Ni goben nan tsoron zuwa Kanon nan nake ji, ban san me zan gani ba acan. Dan Allah ki zo muje tare" Sumayya ta goge mata hawayenta tace "tare zamu tafi, na taho da kayana ma jakata can a mota, tare zamu tafi ba zan tafi in barki ba. We are going to get through this together" ta samu ta lallabata ta kwanta sannan ta fita neman Adam ta karbi jakarta. Sai kuma ta sanarwa da kawayensu na kasa cewa Ruqayyah bata jin dadi ta kwanta bacci. Amma sai suka bita da tambayar "nan ne gidan Ruqayyah? Can kuma gidan waye? Ko gidan dan'uwan mijinta ne da ake bikin su tare? Waye mai Companyn ne wai a cikin su? Ruqayyah tace mana mijinta ne CEO haka ne?" Da sauri Sumayya tayi excusing kanta tace bako ne da ita a waje ta fita, a ranta tana tunanin tabbas baki shine yake yanka wuya, Ruqayyah ta saka igiya ta daure wuyanta ta mika wa mutane bakin igiyar. Bayan saukar Sumayya ne wayar Ruqayyah tayi kara, ta daga kai da kyar tana kallon sunan Hassan a jikin screen din "mijina" kamar yadda tayi saving. Tayi tsaki tana jin wutar data kwanta a kirjinta tana dada ruruwa. "Munafiki" ta fada a fili sannan ta kife wayar ta juya bayanta. Can kuma sai ta juyi ta daga wayar ta saka a kunnen ta "hello" ta fada da murya mai sanyi. "Hassana" ya fada da murya mai cike da conceri. "Yanzu Aunty ta kira ni tace kina ta kuka wai ko zan zo in rarrashe ki. Me ya faru? Waye ya taba min ke inzo in nuna masa matsayin sa?" Ruqayyah tayi shiru, a ranta tace "kamar gaske" yace "Please kiyi min magana mana inji dadi, in baki magana ba yanzu zan ajiye duk abinda nake yi in taho" a hankali tace "kana ina?" Yayi murmushi yace "gidan yafi karfin mu, baki sunyi yawa shine muka kama hotel mu da friends din mu. Kin gansu ma duk suna ta tsokana ta wai na kasa rufe baki saboda an kawo min amarya ta" bata ce komai ba saboda bata jin zata iya gaya masa magana mai dadi, dan haka shirun yafi. Yace "ba zaki gaya min abinda ya saka ki kuka ba? Ko sai nazo na gani da idona? Inji kuma da kunne na?" Ta gyara kwanciyar ta tan jin cewa bata son ganinsa kwata kwata, at least not today, tace "na dauka a can zakuyi zamanku? Tunda nan din akwai mutane da zasu kwana saboda tafiyar da za'ayi kano gobe ko?" Ta shafa kansa yana runtse idonsa yace "yeah, right. Haka ne. But what about siyan baki and other traditional stuff?" Tace "it can wait ai......jibi in akayi dinner din kowa kaga zai watse ai, sai ku zo kuyi ta siyan bakin ku" yace "hakane......but ni kuma fa? Shikenan ba zanga matata ba? Ni fa yanzu ba gwauro bane ba fa" tace "ko? You will see me tomorrow ai in ka shigo da wuri kafin mu tafi" yace "ni ba wannan ganin nake nufi ba ai....." Tayi shiru, yace "ko abinda kike wa kuka kenan dazu?" Tace "good night" yayi ajjiyar zuciya yace "to ya zanyi da raina, ba haka dai aka so ba" tace "kanin miji ya fi miji kyau ba". Wannan littafin na siyarwa ne, duk wanda yake so ya neme ni through WhatsApp ta wannan number din 08067081020 Episode Twenty Two: Envious Thank you so much for the birthday wishes. I had a great day, and you guys contributed a lot to that. Nayi mistake din numbering, na shekaran jiya twenty ne na jiya twenty one na yau kuma twenty two. Muna ta Allah wadai da halayen Ruqayyah, ina fatan muna tsintar pieces of halayyar mu a cikin nata. Idan kina jin haushi a yayin da wani ya samu daukaka kina jin ina ma ke ce ba shi bane ba. Idan kina kallon saurayin kawarki kina jin ina ma dai naki ne ba nata ba. Idan kina jin bacin rai idan kika ga business din wata ya bunkasa ba naki ba, ko wata ta chanja kayan dakinta ke bami chanja ba, ko wata ta sayi kaya ke kuma baki da kudin siya. Idan kina jin dadi a ranki idan wani ya samu wata matsala. Wadannan duk kadan ne daga cikin siffofin hassada. Hassada daban kishin kai daban, kishin kai shine ki nemi na kanki a lokaci guda kuma kina yiwa sauran masu neman kansu wadanda suke sama da ke da wadanda suke kasa dake fatan alkhairi. Yar uwa, a duk lokacin da kike kallon na sama dake a samun abin duniya to zai toshe miki idanuwanki ki daina ganin kyawun abinda yake gabanki, abinda kike dashi, wannan kuma shi zai sa ki zamanto marar godiyar ubangiji. Yar uwa ki kalli na kasa dake, ki duba dubunnan mutanen da suke fatan su samu daukaka irin taki, wannan zai saka ki samu wadatar zuci. Irin wadannan halayen baka sanin kana dasu har sai kayi nisa a cikin su. A lokacin kuma sun riga sun bi jini da tsokar jikin ka. Yes, akwai mutane irin Ruqayyah and they walk amongst us ******************* Da kyar Sumayya ta samu ta lallaba kawayen da mostly Ruqayyah hayar su tayo, ta gaya musu babu siyan baki yau sai ranar lahadi, farko suka ki tafiya suka ce ai dare yayi sai dai su kwana da safe sa tafi, ita kuma tasan indai suka kwana din to kuwa cewa zasuyi sai anje dasu kano kuma Allah kadai yasan abinda zasu aikata acan din. Ba zata dauki wannan chance din ba, dan haka ta koma sama ta samu kudi a gurin Ruqayyah ta kuma lallabasu dashi, sannan ta fita waje ta samu Adam "Adam da Allah a cikin drivers din gidan nan ka samu wani ya mayar da mutanen Ruqayyah gida" yace "ohhh okay, gani ai, kim manta nima drivern gidan ne?" Ta nuna shi tace "banda kai, someone else" yana murmushi yace "why? Ba kya so insha wahala?" ta juya kamar zata bar gurin sannan ta juyo tace "saboda yammata ne" ta shige da sauri tana jin sa yana mata dariya. Washegari da sassafe aka aiko su bayar da kayansu, wai kayan duk a mota za'a hada su tare da motar da zata dauki kayan lefe, su kuma in sun shirya sai su bi jirgi. Ruqayyah ko hada kayan bata yi ba, sai a lokacin Sumayya ta taimaka mata suka debi wadanda ta saka da bikinta tunda bata dinka lefe ba kuma kayanta na gida duk ta barsu a gida saboda bata bukatar su. Suka hada akan kayan Sumayya a yar karamar jakarta suka bayar. Sai a lokacin sannan Sumayya ta jawo Ruqayyah da kyar suka fito zasu zagaya gida. Tun daga kan Bedroom din da suka kwana a ciki, daya Bedroom din wanda suke tunanin na Hassan ne amma daga alama shima bai tare ba tunda babu kayansa komai a ciki sai dai set din furniture shigen nata sai banbancin design da color. Suka zagaya katon palon da yake sama mai hade da dining room, su kansu set din dining din abin kallo ne, sannan suka sauko kasa suka duba three bedrooms din da suke kasan kowanne in suka shiga sai Sumayya taga kamar yafi ba baya kyau, Ruqayyah kawai binta take yi fuskarta babu yabo babu fallasa, suka dawo falon farko komai Sumayya ta gani sai tayi ta kambamawa dan ta jawo hankalin Ruqayyah har ta samu ta dan fara yabawa da kalmomi irin " eh, yayi kyau" duk kuwa da cewa bata bata ganin makamancin shi ba ballantana wanda ya fishi. Suka shiga kitchen Sumayya tana ta santin kitchen din da duk kayan da suke ciki, sannan suka fita waje ta kofar baya Sumayya tana yaba shuke shuken da akayi a surrounding area din, flowers masu kyau da kamshi aka zagaye backyard din gidan dasu, gidan Hassan mai kyau ne, mai matukar kyau ne, sai dai ace masa karami, kankantar ma za'a fada ne in akayi comparing da gidan Hussain. Amma sai Ruqayyah ta daga kanta kana kallon gidan Hussain, ita so take ta shiga ciki taga menene a cikin wannan katoton gidan, tasan anyi wa gimbiya jere so take taga dame dame aka saka mata, so take taga sun kai nata kyau ko kuma sunfi nata? Sumayya ta kama hannun ta suka koma, tanata yi mata hirar yadda mutane suka yi ta santin gidan har suka koma dakin ta sannan Sumayya ta cire kayanta ta shiga bandaki zata yi wanka. Kayan bandakin ma sai data yi ta gwadawa kafin ta iya gane yadda zata yi amfani dasu. Bayan ta shiga toilet din ne sai Ruqayyah taga kofa a tsakanin windows, ta saka hannu ta bude ta shiga. Nan take taji farin ciki ya kamata "a balcony!" Madaidaicin balcony ne mai kyau da tsari, railers din sa kawai abin kallo ne ga set din kujerun hutawa da dan karamin teburin su. Ta zauna akan kujera daya tana murmushi, sai ta juya da niyyar ganin gari, da niyyar ganin Kaduna a kasan ta amma sai taga gidan Hussain yayi bakevake ya tare mata hanya. Ta daga kanta tana hango karshen gidan sai taga balcony a can karshe, meaning idan matar Hussain ta fito ita ma ta fito to matar Hussain zata ke hango ta a kasanta. Taji zuciyarta ta buga, ranta ya baci, hankalin ta ya tashi. Ita gidan Hussain take so, wancan balcony na sama shi take so ba wannan ba. Ta mike da sauri ta shige ciki ta rufe kofar ta murda key sannan tazo ta wuce Sumayya da take ta santin closet din data bude duk da babu kaya a cikin ta, ta shiga toilet, ta jefa key din a toilet tayi flushing dinsa. Suna gama wanka Aunty ta sake aikowa tace su tafi can main house din suyi breakfast, suka shirya sama sama sannan suka fita tare da yar aiken data ce musu ita cousin din su Hassan ce. "Mamana ita ce Hussainar Maman su yaya H1" ta fada proudly, kawai sai Ruqayyah taji yarinyar bata yi mata ba duk kuwa da cewa bata yi mata komai ba. Sumayya tace "hmmm. Lallai kice akwai twins da yawa a wannan family din" ai kuwa kamar ta tsokano Magana sai ta fara lissafa mata su, gidan Aunty wance gidan gwoggo wance gidan auncle wane, Sumayya tace "haka kuke da yawa ashe? Lallai Ruqayyah kina da aiki a gaban ki. Duk sai kinyi kokari kin gane su saboda gaba" yarinyar tace "au wai ba ke ce yayar tamu ba? Ni fa ba gane ku nake yi ba" Ruqayyah tace "in dai kika yi magana kika ji an cika miki kunne da surutu to ba ni bace ba" Sumayya tace "in dai kika yi magana kika ji an baki amsa gida daya an dauke kai to ita ce yayar taki" duk sukayi dariya. Suka wuce ta gaban gidan Hussain sannan suka shiga wani dan karamin gate da akayi a tsakanin gidajen guda niyu yadda ba sai an zagaya ta babban gate ba, suka shiga main gidan su Hassan, inda Aunty take. Suna shiga suka tarar gidan a cike da yan uwa, ana ta hayaniya. Nan da nan aka fara drama din banbance Ruqayyah da Sumayya, a karshe har sai da aka kira Hassan a waya aka ce ya fadi bambanci guda biyar. Nan ya fara jero musu "nutsuwa, kunya......" Suka katse shi, physical banbanci muke so kafada mana ba abstract ba" yayi dariya yace "let me close my eyes and think. Kunga na farko fuskar Ruqayyah tafi ta Sumayya tsaho, idanuwan Ruqayyah kwantattu ne na Sumayya kuma zagayayyu ne, lips dinsu ma ba iri daya bane, na Ruqayyah sunfi siranta na Sumayya sunfi kauri. Sannan Sumayya ta danfi Ruqayyah kiba kadanita kuma Ruqayyah tadan fi ta tsaho kadan. Hassana ta bata da yawan magana sosai, tana dai da yawan murmushi, Sumayya kuma tana dariya as much as she talks". Duk mutanen gurin suka kwashe da dariya. "Wallahi to kowa ya jika a gurin nan har su Aunty" ya kashe wayar yana dariya. Kowa a gurin jan su yake a jiki, ana ta nan nan dasu, aunty tayi wa Sumayya godiya data zauna a tare da Ruqayyah. "In kina nan zata fi sakin jikin ta, tunda ita ba mai magana ba ce ba sosai" Suka yi breakfast tare da family ga baki daya, sannan aka fara shirye shiryen tafiya, aka kai su Ruqayyah dakin yaya Hassana akace su shirya a can. Suna ta tunanin wadanna kayan zasu saka, su a niyyar si na jikinsu da shi zasu tafi dan a cikin sababbin kayansu suka dauko, amma sai sukaji ance suje su canja kaya su shirya. Ma'ana na jikin nasu basu yi ba. Suna cikin tunani sai ga kaya an kawo wa Ruqayyah, iri daya Aunty tayi musu ita da Hassana tunda sune amare, Ruqayyah ta saka doguwar rigar jan lace din mai kwalli tana kallon kanta a mudubi, tana noticing yadda shape din jikinta mai kyau ya fito sosai a jikin rigar, ashe duk tailors din da suke yi mata dinki bata mata kaya suke yi? Ita kanta tasan tayi kyau sosai duk da bata yi kwalliya ba, amma kuma sai taji a ranta tana tunanin ko gimbiya fatima zata fita kyau? Ta dai ga tana da kyan fuska a hoto, ko tana da kyan jiki irin nata? Sai kuma taji tana fatan ya kasance bata da shi din da at least ya kasance ta fita da wani abu. "Ai babu wanda yake perfect" ta gaya wa kanta. Bayan ta gama shiryawa ne sai akace tazo ayi mata kwalliya, mai kwalliya ce aka dauko ta Musamman zata yiwa amare sannan da wata wadda zata yi wa sauran mutane duk mai so. Aka yiwa Hassana sannan aka yiwa Ruqayyah aka daura mata head, Ruqayyah ita kanta data kalli kanta a madubi bata gane kanta ba. "Dama haka take da kyau amma tsumma ya boye mata shi?" Tayi murmushi, tabbas tasan tafi gimbiya Fatima kyau. Sumayya ma taje aka gyara mata tata fuskar akayi mata simple makeup, tayi kyawunta ita ma sosai da sosai. Ana ta hidimar shiryawa sai ga angwaye sun shigo tare da abokan su, suka je gurin su Aunty suka gaishe su aka yi ta saka musu albarka sannan akayi hotuna, Aunty ta aika aka kirawo su Ruqayyah, Ruqayyah ta taho idonta a kasa hannunta rike da jakarta, tana takawa a hankali yadda duk hankalin mutanen gurin ya dawo kanta. Hassan ya juyo ya kalle tavsai ya dauke kai, sai kuma ya sake juyowa da sauri yana kallon ta, wai Hassanar sa ce wannan, jinyake kamar ya rashi yaje gurinta ya gaya mata irin kyawun da tayi a idonsa amma yana jin nauyin iyayensa da suke gurin, sai ya bo ta da idanu kawai, a ransa yana jin dadin mayafin data saka ta rage bayyanar surarta. Nan akayi ta jera su ana daukan hotuna dasu, iyaye kowa ya shigo ayi dashi haka kanne ma da sauran yan'uwa. Anan Ruqayyah taga Hussain. Kaya iri daya suka saka shi da Hassan amma sai taga kamar tasa shaddar tafi haske ta Hassan tayi duhu, ko dan hasken fatarsa ne? Ko kuma a idonta ne taga hakan. Fuskarsa cike da annuri, idanunsa suna haske, dimple dinsa yaki komawa saboda murmushin da yaki daukewa daga fuskarsa. Kowa a gurin in ya gaishe shi sai ya ambaci sunansa kuma ya tambaye shi a game da wani abu daya shafe shi, ma'ana yasan kowa kenan, yasan affairs din kowa, kuma sai taga kamar yan uwan sunfi tafiya inda Hussain yake akan inda Hassan yake, ko ita ce take ganin haka? Sai da aka shigo aka tuna musu da cewa lokaci fa yana tafiya sannan suka bar hotunan haka. Sai a lokacin Hassan ya samu magana da Ruqayyah. Yana kallon fuskarta yace "kinyi kyau sosai matata" tayi murmushi tace "kaima kayi kyau mijina" ya danyi gajeriyar dariya yace "maimaita in kara ji" ta saka hannu ta rufe fuskarta tare da dan juya bayanta kadan. Yayi dariya "zanji ne ai, one way or another. Kinsan wani abu?" Ta bude fuskar tana girgiza kai, yace "ji nake kamar in fasa zama in biku kanon nan" ta ji ranta ya fara baci "zaka bi mu kuma? Kai fa kace hutawa zaka yi" yace "yadda naga kwalliyar nan anya zan iya zama in sake kwana ina rungumar pillow" ta sake juya masa baya "kai dan Allah!" Sai kuma ta juyo tace "In ka bimu ma fa ba tare zamu zauna ba, ku kuma waje ko kuma kuna hotel mu muna cikin gida. Ni nafi si kayi zamanka anan kar kabi Hussain da abokansa su zo suyi ta wahalar da kai" yana murmushin gefen baki yace "really?" Tace "eh mana. Kaga gobe daurin aure biyu ne daku ga dinner da dare. You rest today" ya daga murya yana kiran Hussain "ka ga inda aka damu dani ake so in huta, kai kana mitar nace ba zan je ba ita tana cewa inyi zamana in huta" Hussain ya juyi yana kallon su sannan yace "soyayyar da muke yi maka ce daban daban, ni nafi sonka by my side through thick and thin, ita kuma ta fi son ta sha wahala ita kadai kai kuma ka huta" ya dauke kansa, Hassan yayi dariya yana ce mata "fushi yake yi wai nace ba zan je ba. I think zan je ɗin kawai, kar ransa ya kara baci" tayi shiru tana hararar bayan Hussain a fakaice, shine zai zamanto obstacle dinta kamar yadda gidan sa ta toshe mata ganin ta. Ya kuma tsaya mata a zuciyarta. Har an fara fita ana shiga motocin da zasu tafi dasu airport sai Aunty ta kira Hassan dakinta suka tsaya tace "nace ka sallami Ruqayyah kuwa?" Yace "sallama kamar yaya?" Aunty tace "eh mana, zaka bata kudi sanoda liƙi da sauran abubuwa" ya zauna akan kujera yana dafe kanta "Aunty ita tace miki tana bukatar tayi liki? Shin wai ma menene amfanin yin likin? Yana daga cikin sharudan biki?" Aunty ta hade rai "to mu dai ko kayi mana wa'azi dai sai munyi, ya zamu je gidan biki gidan fitar kunya kuma na tabbatar za'a yi kida sannan kace ba zamu fita muyi wa amarya da ango liki ba? Ita kuma ya kake so tayi? So kake ta zauna ta zuba tagumi tana kallon mu muna yi?" Yace "Aunty, ke kinfi kowa sanin dalilin da yasa tuntuni naki auren yayan masu kudi saboda bana son macen data saba da barnar kudi da saka kaya masu tsada da sauran su, saboda a hala zata tarbiyyan tar da yaya na, a haka family na zasu tashi. Kuma babu wanda yasan abinda gobe zata zo mana dashi. Ni daban Hussain daban, kudi na daban na Hussain daban. Ranar da bani dashi kuma yaya zanyi dasu aunty? Shi yasa nayi murna da Allah ya hada ni da Hassana saboda background dinta da kuma halayyar ta sannan da yarintar ta yadda zanji dadin tarbiyyan tar da ita akan tsarin rayuwa ta ita kuma ta tarbiyyan tar da yaya na. To yanzu idan kuma na fara nuna mata zubar da kudi a kasa a gurin biki dole ne me akayi kenan? Ai anyi ba'a yi ba ko?" Aunty tace "to mister smart, komai sai ka nuna wa mutane kai kamar ka fimu iyawa. Wannan dai biki ne, kuma har yanzu bikin ku ne ba'a gama ba, ka dauko kudin liki ka bata tun muna shaida juna ni da kai" yayi ajjiyar zuciya yana shafa aljihun sa sannan yace "i don't have cash on me, in na fita zan samu sai in bata" ta nuna masa kofa, "jeka daki ka dauko ka kawo mata ina nan ina jiran ka" yayi murmushi yana karya wuya, tace "ai na fika wayo, ni na haife ka fa ba kai ka haife ni ba". Dole ya tashi yana murmushi ya tafi tsohon dakin sa, ya bude drawer ya dauko kudi yana jujjuya, ya gama plan din abinda zaiyi da kudin nan, yayi tsaki sannan ya mike ya fita. Yau dai sai ga Ruqayyah da Sumayya a jirgi. Ruqayyah ta maze wai dan kar tayi kauyanci ayi mata dariya amma lokacin da jirgi zai tashi ji tayi kamar dodon kunnen ta ne ya fashe a cikin kunnen, amma taki tabawa dan kar wani ya gani yace tayi kauyenci, ta kankame rigarta cike da tsoro amma fuskarta babu ko alamar tsoro a ciki. Ta shanye kayanta. Suna sauka suka tarar an aiko da motocin da zasu tafi dasu gidan sarautar kano, suka shiga aka kaisu sannan akayi musu jagora har masaukin su, daga nan aka shiga hidimar kawo musu abinciccika na alfarma irin na sarauta, wani kalar abincin ma Ruqayyah bata taba ganin sa ba. Nan take bayi da hadiman gida suka fara saving dinsu, daga kinyi motsi za'a ce "me kike so? Me za'a karo miki? Ko kafafuwan ki sun gaji a tausa miki su?" A haka har sai da aka tabbatar kowa is fully satisfied sannan aka yi musu jagora zuwa wani katon palo da yafi kama da hall din taro amma yasha shimfidu da kujeru na alfarma. Anan Ruqayyah take tambayar kanta ko wannan ce fadar? Amma kuma bata ga karagar sarki ba, sai taga an nuna musu kujerun suka zazzauna sannan sai ga matan gidan suna isowa daya bayan daya ana gaisawa dasu cikin mutunta juna da karramawa. Duk inda Aunty zata je hannunta yana rike dana Ruqayyah, duk Wadda suka gaisa kuma zata nuna mata Ruqayyah tace "ga daya ƴar tawa, matar Hassan ce, jiya aka kawo ta" nan da nan sai taga an jata an rungume "ga yar uwar Fatima" "Allah ya baku zaman lafiya" "Masha Allah, kyakykyawa daita kuwa, ya sunan ki?" A haka a haka har laasar tayi, Ruqayyah tana cewa "wato ita ogar ba zata fito ba ko?" Bakin cikinta kawai kar kwalliyar ta ta karasa lalacewa ba tare da Fatima ta fito ta ganta ba, kar ta raina ta, tunda taji ance first impression matters alot. Ba'a fito da Fatima ba sai da suka je suka yi sallar laasar, dole Ruqayyah ta wanke kwalliyar ta tunda zata yi alwala amma duk da haka sai Nafisa ta dan gyara mata fuskar dai dai gwargwado kuma ta mayar mata da head dinta. Sannan suka koma suka zazzauna side daya dangin ango daya side din kuma dangin amarya, akayi ta rabon snacks da drinks daga can gefe kuma ga masu kidan kwarya nan suna yi . Sannan sai ga amarya nan an fito da ita lullube da alkyabba fara tas mai adon golden, ko tafin kafarta ba'a gani, aka zaunar da ita akan kujerar da aka tanada musamman domin ta sannan kawayenta suka zagaye ta duk sun sha ankon lace kalar zaren da akayi dinkin alkyabbar ta dashi. Kasanta kuma bayinta ne a jere duk sunyi ankon riga da zani na atamfa mai hoto da sunan ta a jiki. Hannayensu rike da shantu suna kida da cinyoyinsu sannan suna rera waka, a cikin wakar taji an ambaci sunan gimbiya Fatima, sannan ne ta fahimci wakar ma musamman saboda ita aka shirya ta. Nan take guri ya tashi da sowa da tafi, wasu kananan yammata suka fito suma a jere hannayensu rike da mahutai wadanda side dinsu daya tambarin masarautar daya side din kuma hoton gimbiya fatima, suka jeru suna rawa gwanin ban sha'awa. Mutum biyu ne aka nema daga dangin ango suka je suka bude fuskar gimbiya sannan suka feshe ta da turare, duk da haka sai ya zamanto rabin fuskar ne kawai a bude idanuwan ta da goshinta still suna rufe, amma duk da haka zaka iya hango tsantsar kyawunta ta bakinta da yake dauke da murmushi da kuma dogon hancinta da yake tsaye chas. Ruqayyah tayi tsaki a ranta. "Ashe ma na fita hasken fata" ta fada a hankali tana hararar iska. Sai dai ita kanta tasan koda tafi Fatima haske to kuwa kulawar da fatar fatiman ta samu ba zai bar hasken Ruqayyah ya haska ba. Daga nan sai taga an fara shigowa da kaya ana jere wa a tsakiyar gurin wai kayan gara ne, amma abin mamakin shine ba wai kayan abinci bane ba kamar yadda tasan ana yin gara aa wannan kayan suttura ne kawai, akwati akwati, jaka jaka. A al'adar gidan sarauta duk wadda aka yiwa aure a gidan sarauta idan wani gidan sarautar aka kaita to kuwa hatta bayin gidan sai an yi musu suttura kuma an basu kudi albarkacin ta, idan kuma ba gidan sarauta bane ba to kuwa za'a binciko duk dangin angon na nesa dana kusa sai kowa ya samu rabonsa albarkacin gimbiya, yan uwansa shakikai kuwa da iyayensa da gwoggonninsa nasu na musamman ne, sai an yi musu kamar wani karamin lefe. Haka akayi ta kiran sunan tun daga iyayen Hussain dangin uwa da dangin uba har zuwa kan dangin dangarere, wasu ma basa gurin, wasu ma ko kadunan basu je ba ballantana kano amma an kira sunan su kuma an basu rabon su, kowa aka bashi kaya kuma sai an hada da kudi, maza da mata. A cikin rabon sai taga na Hassan, sunanshi na biyu daga Aunty sai shi, akwatin sa guda mai cike da dangin shaddoji masu tsada, da yar karamar jaka ita kuma takalma ne a ciki da huluna da turaruka na maza. Tunda babu maza a ciki dan haka ita aka ce taje ta karbo masa, ta taka kaje har gaban gimbiya, ita bakin cikinta kenan wai sai anje gaban gimbiya, ta tsaya a gefen gimbiya akayi musu hoto sai mai hoton ya yi mata magana da cewasai ta sunkuya saboda ita gimbiyar a zaune take, ita kuma Ruqayyah a ganin ta in da sunkuya kamar gimbiyar ta sunkuyawa amma ganin mutane suna kallo dole ta sunkuya din tana kirkirar murmushin karya aka sake daukan wani. A lokacin da zata bar gurin ne taji gimbiyar ta riko hannunta tayi mata alamar data sunkuyo, bakin ciki ya toshewa Ruqayyah makogwaro, amma dole ta sunkuya sannan ne suka hada ido, da murmushi a fuskar gimbiya fatima, ga wani fitinannen kamshi yana tashi daga jikinta tace "ban san dake aka zo ba ai, da tun dazu na aika an kawo min ke gurina, ke bakuwa tace ai bata mutan gida ba" Ruqayyah tayi yake "yeah right" sannan ta zare hannun ta ta bar gurin, ko ta kan kayan bata bi ba. Ita sunkuyawar da tayi wa gimbiya shi yafi komai kona mata rai. Tana dawowa ta fara sansana kanta dan taji ko tana irin kamshin da gimbiya fatima take yi? Abin takaici sai gashi tana zama an sake kiran sunanta again, wannan karon kuma nata kayan taje aka bata, exactly zubin da akayi wa Hassan irin sa akayi mata kawai dai nasa na maza nata na mata. Wannan karon da akace taje suyi hoto cewa tayi ai tayi, tayi tafiyar ta. Sai da aka kwashe kayan gara sannan su kuma dangin ango suka shigo da lefe, tun Ruqayyah tana lissafa akwatunan har taji kanta ya fara ciwo ta kwanta a jikin kujera ta rufe idonta, bata son ma ganin kayan ciki tunda ance kazantar da baka gani ba tsafta ce. Sumayya ta kama hannayenta, ta juyo ta kalle ta sai tayi mata murmushin kwarin guiwa, sai taji har Sumayyan ma haushi take bata. Gabaki daya mutanen gurin haushi suke bata, ranta zafi yake yi, zuciyarta ciwo take yi. Ta mike da sauri tana daukan jakarta. Aunty ta riko hannun ta "ina zakije Ruqayyah?" Ruqayyah ta langwabe kai "Aunty kaina yake ciwo wallahi, zuwa zanyi in dan kwanta kafin a gama" Aunty tayi murmushi "Akwai ciwon kai kam, nima kaina ciwon yakeyi, amma zaki iya gane hanya kuwa" Ruqayyah tayi shiru, ita wadannan sorayen da suka wuce ina zata iya gane su? Aunty ta waiga ta kira wata a cikin wadanda ta lura bayin gidan ne tace "dan Allah raka su inda aka sauke mu". Suna zuwa can Ruqayyah ko ta kan Sumayya bata bi ba tayi kwanciyar ta, taji karar wayarta ta dauko ta taga ten missed calls daga Hassan, hayaniya ce ta hana ta ji. Tayi tsaki ta mayar da wayar cikin jakarta sayi kwanciyar ta. Sumayya ta bita da kallo sannan ta tabe baki tace "kin dorawa kanki aiki. Babban aiki ma kuwa" a kara gyara fuskarta Sannan ta juya ta koma gurin taron. Ita ba zata iya zama tayi tagumi ba bayan ga shagali can ana yi. Wannan littafin na siyarwa ne, idan kina so kiyi min magana ta WhatsApp ta wannan number 08067081020 Sai magrib aka tashi daga taron, daga nan duk aka dawo masauki aka yi Sallah masu son yin wanka suka yi sannan aka fara shirin tafiya dinner, sai a lokacin Ruqayyah ta tashi tayi sallah sannan itama ta shiga tayi wanka, suka zo suka fara shiryawa, kayan ta data zubo a jakar Sumayya ta dauko, daya daga cikin kayan da aunty ta siya mata ne na fitar biki, tayi kwalliyar ta tsaf ta shirya duk da cewa bata cika make up da yawa ba amma tayi kyau sosai. Sumayya ma tayi wanka ta chanja kaya, suka yi sallar isha i sannan suka fita suka tafi inda sauran mutane suke, ana ta yin make up da daurin dankwali, Aunty ta tambayi Ruqayyah ko tanaso ayi mata amma tace a'a, sai daurin dankwalin ta kawai aka gyara mata. Zuwa karfe takwas aka ce su fito za'a tafi. Sai a lokacin ta dauko wayarta ta kira Hassan, har ya gaji da kira ya hakura. Ring daya ya dauka. "Har na dauka ko an sace min amaryata" ta danyi dariya, "sace wa kuma sai kace kai" yace "ohh abin harda tsokana? To zan rama ne nima zan zo in sace ki kinga munyi one one" tace "ai ni bani na sace ka ba" yace "yeah, ke kika dawo dani gida, and I am never going to forget that" tace "me too". Yace "nayi ta kiranki ne dazu dan in gaya miki mun karaso muma, an kaimu masauki tare dasu Hussain and I was lonely nace bari in kira matata tayi min hira" tace "muna gurin taron can, and the place was so noisy shi yasa banji ka ba, sai yanzu dana dauko wayar sannan na gani. Sorry" yace "it is okay dear. Gamu nan muna shirya wa yanzu zamu tafi dinner" tace "muma haka" yace "okay, I will see you there angel" Tayi murmushi tana kashe wayar. Sai yanzu taji dadin zuwansa garin, ita sam bata son zuwa gurin dinner din nan dan bata ga abinda zata je ta gani a can ba. Sai yanzu kuma take kara gode wa Allah da Sumayya tayi dabarar sallamar kawayenta da sun biyo ta kano ai da ansha abin kunya. A cikin palace din za'a yi dinner amma sai da aka dauke su a motoci aka kaisu gurin saboda girman palace din, kamar wata duniya suka je. Suna shiga suka tarar da gurin already da mutane, taji ana zancen harda governor da matarsa ne zasu je gurin. Yanayin tsarin gurin kadai ya isa yasa mutum kamar Ruqayyah ciwon kai. Sumayya sai kalle kalle take tana daukan hotunan yadda akayi arranging tables din gurin da kuma kujerun amarya da ango, ta dauki hoton high table, wannan lallai sai ta nuna wa Inna Ade dasu Sulaiman, wannan lallai sai ta nuna wa Adam. Ruqayyah ta ja Sumayya zuwa can extreme end din hall din suka zauna, Sumayya tace "nan ai ba gani zamu ke yi ba, Please ki tashi mu koma gaba" Ruqayyah tace "ke da kika zo gani kenan, ni kuma zuwa nayi a ganni and I really don't want to be looked at, dan haka nan zanyi zamana. Ke ma kuma sai ki zaba, gurina kika zo ko gurin bikin gimbiya? The choice is yours" Sumayya tayi ajjiyar zuciya ta zauna tana ta daga kai, sai daga baya ta lura a gefen su ma akwai katon screen da kake iya hango can gaba kamar a gabanka akeyi, just like kana kallon TV. Shikenan Sumayya ta gyara zaman ta da niyyar shan kallo tana yi tana recording as much as she can. Basu jima da zama ba guri ya cika, sai ga Hassan yana kiran Ruqayyah, "kuna ina ne? Ga guri an tanadar mana" ta yamutsa fuska "mun samu guri mun zauna ma, kuyi zamanku kawai" yace "noo, ni ba zan iya zama ni kadai babu ke ba, common ki na ina inzo in taho dake inda nake" ta kwantar da murya "ni ba zan iya zama a can ba, dan Allah ka bar ni inyi zamana anan" yayi ajjiyar zuciya, he thought as much, yaso a rabu da yarinyar nan tayi zamanta a gida aunty tace lallai sai an taho da ita, ita bata saba da irin wadannan abubuwan ba dan haka dole zata jita a takure. Yace "kina ina? Ni sai inzo inda kike" ta gaya masa. Mintuna kadan sai gashi nan yazo, yaci kwalliya kamar babu gobe dan ita kanta tasan yayi kyau. Tayi masa murmushi shima ya mayar mata yana jan kujerar kusa da ita ya zauna. Sumayya ta gaishe shi yace "su Sumayya an samu abinda ake so ko? Biki dai ayi ta hidima dai" tayi dariya tace "eh mana, biki ai lokaci daya ake yinsa daga an gama shikenan" yace "Allah ya kaimu baki bikin to, mu sha shagali har mu gode Allah" ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Yace da Ruqayyah "muna shigowa ai Hussain ya kira ni wai gimbiyar sa tana ta nemanki, tana so wai ko zaki shiga cikin friends dinta and I said no, baki san su ba ba zaki ita zama a cikin su ba" Ruqayyah bata ce komai ba sai kira ya shigo wayarsa ya dauka yayi magana sannan ya mike "excuse me ladies, zan je zamu shigo da Hussain. Reserve my seat please dan anan zan zauna" Bayan fitarsa da kadan sai akayi sanarwar amarya da ango zasu shigo, kowa ya mike tsaye kamar wani president ne zai shigo, suka shigo suna taku dai dai abokan ango da kawayen amarya suna take musu baya, camera tana daukan su ta kowanne angle ana turo hotunan a manyan screens din da suke a gurin saboda wadanda ba zasu iya gano wa ba. Mai video yana dauka tun daga kan takalman gimbiya har zuwa kan sarka da dan kunnen ta, haka shima Hussain aka dauko shi, ba kuma wai shigarsu ko kuma kyawun surar sune abin burgewa ba, a'a, soyayyar junan su da take kwance akan fuskokin su. Kowa ya gansu ya san a cikin farin ciki suke. Ruqayyah ta kifa kanta a jikin table din gabanta tana rufe idonta kamar mai bacci, wannan abin shine abinda tayi ta mafarki zata samu a bikinta tun lokacin data hadu da Hassan. Mutane irin wadannan, governor, ita da mijinta su shigo kowa yana kallon su cike da sha'awa, amma ita nata mijin ma cewa yayi ba zai je kowanne event dinta ba, in dai bai je ba kuwa mutanen sa ba zasu je ba, shi yasa bata yi komai ba saboda baya ga amfanin yin ba tunda so take yayi introducing dinta ga mutanensa a matsayin matarsa ita kuma tayi a matsayin mijinta kuma ceo of h and h group of companies. Now she is just a guess a bikin ceo na H and H group of companies. Jama'ar amarya da ango suna wucewa ta mike ba tare da tace komai ba ta bar cikin hall din ta fita waje, a can gefe taga wata doguwar veranda da kujeru a ciki sai ta tafi can ta ja kujera daya ta zauna sannan ta zubawa bishiyoyin gurin ido tana kallon su tana lissafo rayuwar da take gabanta. Bakin ciki dai kam tasan zata sha shi har sai ta godewa Allah. Abu daya ne zai saka ba zata fasa auren Hassan ba shine saboda tasan in ta rabu dashi ko a mafarki ba zata samu mijin da ya kai ko da rabin sa bane ba, ceo or not ceo tasan cewa Hassan ba sa'an aurenta bane ba kaddara ce kawai ta hada ta da shi har kuma ta kulla aure a tsakanin su, ta kuma san cewa yana son ta da gasken gaske, dan haka zata yi amfani son da yake yi mata gurin samun cikar burinta. Burinta na auren ceo, bata san yadda hakan zai faru ba bata san ta inda zata fara ba amma tasan abinda take so kenan, abinda ta hango wa kanta kenan. Wannan gidan, wannan valcony din na can sama shi take so. Title din matar ceo na H and H shi take so. Su Hassan suna kai su Hussain gurin zamansu sai ya juyo ya dawo inda ya bar Ruqayyah, amma sai ya tarar bata nan sai Sumayya da bata ma san Ruqayyah ta tashi ba, ya zauna ya kira yawarta ta dauka ta gaya masa inda take, so take ya taso ya bar gurin bikin ya taho gurinta. Ai kuwa ko minti goma ba'a yi ba sai gashi a gabanta yana mata murmushi. "Shine kika gudu ko?" Tace "kida yayi kara da yawa, kaina kuma ciwo yake yi min" ya zauna a kusa da ita yana murmushi yace "wannan ciwon kai, ki gaya min yaya zanyi dashi ne" ta dafa kan tace "gajiya ce kawai, da ace ba'a taho dani ba kaga da yanzu ina can ina hutawa ta" ya gyada kai yana dada jin rashin dacewar tahowa da ita da Aunty ta dage sai anyi, sannan yace "kawo kan inyi miki addu'a" ta makale kafada yayi dariya "adduar ce ba kya so? Kin san dai adduar miji ga matarsa tana da saurin karbuwa inayi miki zaki ga kin warke" ita dai taki yadda, ta san wayon ya tabata ne babu wata addu'a da zai yi mata, wai ita zaiyi wa wayo bayan itama tana da wayon ta. Shi kuma yayi ta mata dariya, yasan abinda take gudu kuma abin yana kara masa sonta a zuciyarsa, yana kara nuna masa cewa she is pure, baya jin ta taba rike hannu da wani balagaggen namiji, dan haka tashi ce shi kadai babu wanda ya gutsira ya rage masa. Ya saka hannu a aljihu ya zaro kudi, sababbin 200 notes bandir biyu ya ajiye a tsakiyar su, sannan yayi folding hannunsa yana kallonta yace "ga kudi nan, ban sani ba ko kina so ki shiga cikin gurin biki kiyi liƙi" ta kalli kudin sannan ya kalle shi, tana lura da yadda idanuwansa suke studying dinta tace "liƙi kuma? Dole ne sai anyi likin?" Ya girgiza kansa yace "ba dole bane ba, ra'ayi ne, ban sani ba ko kina da ra'ayin yi?" Ta dan yi murmushi tace "kai me yasa ba zaka je kayi musu likin ba" yace "ni bana yi" tace "saboda me?" Yace "saboda banga abinda hakan zai amfane ni dashi ba, a duniya da kuma a lahira. Banga amfanin in dauki kudin da zan iya yin wani abu dasu mai muhimmanci a duniya, ko kuma inyi sadakar su in samu ladan a lahira, sannan in ringa watsi dasu mutane suna rawa akai ba. I don't see the logic in that" ta harde hannayenta itama irin yadda yayi tace "kuma ni shine kake bani inje inyi?" Yayi murmushi bai ce komai ba, ta dauki kudin ta jujjuya su a hannun ta mentally tana calculating adadinsu, ba laifi, shima fa yana da kudin, ta mayar dasu ta ajiye tace "har na lissafo irin amfanin da za'a yi da wadannan kudin, ba zan zubar dasu a kasa ba" ya jima yana kallon ta, fuskarsa da sassanyan murmushi sannan yace "take it" tace "bazan yi likin ba fa" yace "na sani, ki saka su a jakarki ko zaku fita shopping dasu Nafisa, nasan babu abinda suke kauna irin shopping, maybe zaki ga abinda kike bukata kema" ta girgiza kai sai ya saka hannu ya dauki jakarta ya bude ya zuba mata kudin a ciki sannan ya rufe ya mika mata. Ta karba a hankali tace "Nagode" zuciyarta fal farin ciki, tabbas ta samo bakin zaren sa. Hirar su suka kama yi, mostly labarin drama din da ake yi a gurin abokan su yake bata, yadda aka sako su a gaba ana ta tsokanar su shida Hussain akan aure, har zaunar dasu masu auren ciki sukayi wai suna koya musu yadda zasu yi wa matan su. Tun Ruqayyah tana dan basarwa har ta fara murmushi, daga baya sai gata tana kyalkyala dariya duk wani ciwon kanta ta bacin ranta ya tafi. Anan suka yi tasu dinner din, yayi waya aka aiko musu da abinci nan aka jera musu suka ci suka sha, yaji dadin zamansu a gurin sosai duk da yasan Hussain yana can ya kumbura in ya lura baya cikin gurin. Suna komawa masaukin su Aunty ta kama hannun Ruqayyah "Ruqayyah ina kika je? Ina ta nemanki ni da nake so in ganki a kusa dani?" Ruqayyah ta danyi murmushi tace "uhmm dama........" Sumayya tace "tare da yaya Hassan suka fita, nima bansan inda suka je ba" Aunty ta saki hannun Ruqayyah tana cewa " wannan yaro, zai zo ya same ni ne, wato shine shi bai zauna ba ita ma kuma ya hana ta zama? Menene amfanin tahowa da ita da nayi kenan?" Tayi ta fadan ta ita kadai su dai su Ruqayyah suka fara shirin kwanciya bacci. Karfe goma na safe aka daura auren auren Hussain Aminu Abdullahi da Gimbiya Fatima. Daurin auren daya samu halarta manya manyan kusoshin kasarnan dan Hussain duk wanda yake fada aji sai daya gayyace shi daurin aurensa, kuma yawancin su sunzo wadanda basu samu zuwa ba kuma sun turo representatives dinsu. An dauta auren ne a masallacin juma'a na kofar kudu, duk girman masallacin sai da mutane suka cika shi taf wadansu ma a haraba suka tsatstsaya, daga nan aka tafi reception, cikin gida kuma aka fara shirye shiryen daukan amarya zuwa kaduna inda acan kuma za'a daura auren Hassana da karfe biyu na rana. Dan haka ba tare da bata lokaci ba duk aka gama shiri, sannan aka dunguma gabaki daya har gaban mai martaba sarkin Kano, yau sai ga Sumayya da Ruqayyah a gaban sarki. Inda yayi wa Fatima doguwar nasiha akan aure, sannan kuma ya danka amanar ta a hannun yan uwan mijinta ya kuma yi musu addu'ar samun zaman lafiya da kuma zuriya mai albarka, daga nan sai aka bi aka rarrabawa duk matan da suke gurin littafin da maimartaba da kansa ya rubutawa Fatima na nasihohi akan zaman aure wanda yayi wa tittle da "Nasiha gareki yata Fatima" saboda ta ringa karantawa a duk lokacin da taji ta shiga duhu a game da zaman aurenta. Aka bawa duk matan gurin suma su ringa karantawa albarkacin Fatima. Sai da aka daga Fatima za'a fita da ita sai ta saka kuka ta ruga gurin mahaifinta ta rungume shi, aka je da niyyar a dauko ta amma sai ya dakatar da mutanen ya mike da kansa ya kamata ya fita da ita ya saka ta a motar da zata kaita airport sannan ya shiga shima tare da kishiyar mamanta suka raka ta har gaban jirgi. Anan kowa ya kuma tabbatar da son da mai martaba sarki yake yiwa yarsa Fatima. Ana sauka a Kaduna a ka cigaba da hidima, ana ƙoƙarin shiga da Fatima gidan ta kuma ana shirye shiryen daurin auren Hassana. Ruqayyah duk jinta take out of place, duk kuwa da cewa duk juyi sai Aunty ta kira sunan ta, sai ta lallaba ta ja Sumayya suka koma part dinta, Hassan ma ko duriyarsa bata ji ba bata sani ba mako ya dawo daga Kanon ko yana can, ta shiga daki kawai ta cire kwalliyar ta tayi wanka tayi kwanciyar ta, sama sama take jin guda da hayaniya daga gidan Hussain, ta san yanuwan amarya ne suke ta bidirin su a ciki, ta tashi ta jawo window ta rufe ta rufe curtain sannan ta kwanta, sai dai zafi take ji gashi dakin babu fanka ita kuma bata iya kunna ac ba, a haka tayi kwanciyar ta tana hada gumi. Cikin ikon Allah sai ga yan gidan su nan sun zo, har da su Sulaiman da Zunnur da yan uwan inna Ade dana Baba, duk wadanda Inna ta bawa card din dinner sannan kuma ta turo su suje suyi wa Aunty Allah ya sanya alkhairi na daurin auren Hussain da Hassana. Yan uwan Hassan din da basu shigo ganin dakin amarya ba ranar da aka kawo ta suma duk suka shigo, wasu daga cikin yan uwan gimbiya suma suka leko, sai ya zamanto kamar wani bikin ake sakewa amma babu amarya, amaryar tana can ta kulle kanta a daki tana baccin wahala. Sai laasar ta tashi, shima gwoggo Habibah ce ta aiko Sumayya akan lallai ta tashe ta tayi wanka ta shirya ta fito. Dole ta tashi ta shirya din sannan ta nemi doguwar riga a cikin kayan lefenta ta saka tunda dinkunan nata sun kare sai wanda ta ware saboda dinner din yau. Ta kalli kanta a mudubi taga cewa tayi kyau sai dai idanunta da suka fada ciki suka yi baki. Ta danyi tsaki tana kara shafa hoda akan idon sannan ta fita. Yadda taga gidan ya bata mamaki, ga abinciccika nan an kawo kala kala kowa yana serving kansa, ga kuma yan aiki nan an ajiye yadda daga an bata guri zasu gyara dan haka duk da yawan mutanen gidan fes fes yake yana kamshi. Ta gaggaishe da wadanda ya kamata ta gaisar su kuma wadanda ya kamata su gaishe ta suka gaishe ta. Ana cikin haka sai ga jama'a nan suna ta shigowa, wai an kawo gimbiya gurinta za'a bata amanar ta a matsayin ta na yayar miji. A ranta tace "iyayi iya reto, wai matar da ta kusan haifa ta ita za'a bani amanar ta" aka zaunar da gimbiya a kasa, itama Ruqayyah aka zaunar da ita a kusa da gimbiyar sannan Aunty da sauran manyan iyaye suka zauna akan kujeru. Akayi ta jero musu nasiha akan su rike junansu amana. Aunty tace "to Ruqayyah da Fatima, ga amanar Hassan da Hussaini na na baku. Na san cewa kun sani marayu ne basu da uwa basu da uba dan haka basu da wanda yafi junan su kusanci da kansu. Dan Allah ku zamo sanadiyyar sake karfafa musu zumuncin su kar ku zamo sanadiyyar rushewar sa. Na san cewa Hassan da Hussain basa minti talatin a zaune tare ba tare da sunyi rigima ba amma hakan baya nufin cewa basa kaunar junan su dan ni ban taba ganin yan uwan da suke kaunar junan su ba kamar su. Dan Allah ku zamanto sanadiyyar karfafa wannan kauna a tsakanin su kar ku zama sanadiyyar haddasa gaba kiyayyar junan su a zukatan su". Daga nan sauran iyaye kowa ya kara da tasa. Duk sai da jikin kowa yayi sanyi a gurin harda Ruqayyah Da zasu fita Aunty tace da Ruqayyah "in anyi magrib mai kwalliya zata zo tayi miki, sai ki fito da duk kayan da zaki bukata ki ajiye su a kusa sannan ki yi Sallah da wuri kar ta zo tana jira tunda ita zata yiwa Hassana ma. Fatima ta taho da nata" Ruqayyah ta gyada kai amma sai taji zuciyarta ta tabu, dan me aunty zata ce mata Fatima ta taho da nata? Ko tana tuna mata ne cewa ita bata taho da tata ba? Bata yi wanka ba tunda tayi dazu, dakunan kasa aka budewa yan uwanta suka yi ta shirin su a ciki, bata tuna da kawayenta ba sai data ji hayaniyar su sun shigo sannan suka hau sama gurinta. Suna ta hayaniyar su kuma mostly zancen basu akan waye mai gidan kusa dana Ruqayyah ne, ita Ruqayyah sai taji suna kara mata pressure ne , tayi nadamar ina ma bata yi hayar su ba? Kadan daga cikin su ta sani suma kuma Minal ce kawai wadda ta sani sosai, duk sauran hada ta akayi dasu. Anan suka shirya, tare da hargitsa wa Ruqayyah kayan kwalliyar ta, wasu suka debi rabon su a ciki. A karshe ma sai da Sumayya ta faki idonsu ta kwashe kayan ta saka a closet ta rufe sannan aka samu lafiya. Shima suka yi ta mata mita. Ruqayyah kuwa sai shiga toilet tayi ta rufe kanta saboda hayaniyar su tayi mata yawa. Sai da aka ce ga mai makeup din tazo sannan ta wanke jikinta tayi alwala ta fito. Sai data yi sallah sannan ta zauna suka fara kwalliyar, yarinyar ta kware sosai a aikinta dan haka nan da nan ta mayar da Ruqayyah zuwa irin matan da take ganin hotunan su a Instagram. Ta taimak mata ta sak kayanta, making some adjustments here and there, yadda rigar ta zauna sosai, sannan ta saka mata duk accessories din da suka dace, wanda taga baiyi ba kuma tace a chanja wani, har ta gama shirya ta tsaf yadda Ruqayyah tasan ko a Instagram din ne ma sai an duba kafin a samu amaryar da tayi kyawun ta. Sumayya ta fito da ita palon sama ta zaunar da ita sannan itama ta tafi ta fara nata shiryawar. Itama irin ankon kawayen Ruqayyah ne ta saka sai dai nata dark pink nasu light pink. Ita kuma amarya peach. Sai a lokacin Ruqayyah ta kira Hassan. "Ka manta dani" ta fada da muryar shagwaba, yace "kin taba ganin inda mutum ya mance da rabin jikinsa a wani waje? Tace "gashi kuwa, tun safe fa baka ko bi ta kaina ba" yace "sake dubawa dai, ki lissfa missed calls nawa na ajiye miki a wayar ki" tace "ni ban gani ba" yace "kun shirya? Cos Gamu nan fitowa yanzu" tace "mun gama ai, ku kadai muke jira" Abun ya matukar kayatar yadda angwaye Hassan da Hussain suka shigo su kadai a mota daya, Hussain da kansa ne yake driving Hassan yana gaba, suka fara zuwa kofar gidan Hassan Ruqayyah ta fito a bisa rakiyar kawayenta ta shiga sannan suka karasa kofar gidan Hussain Fatima ta fito itama ta shiga ita kadai, suka rufe mota suka ja suka yi tafiyar su. Sai bayan sun fita sannan aka fara rububin shiga motoci ana bin su a baya. Suna zuwa gurin taron suka yi packing a bakin kofar shiga gurin sannan suka yi zaman su a mota. Tun da Fatima ta shigo take ta yabon kyawun da Ruqayyah tayi, wannan yasa Ruqayyah ta kara kumbura tana ta faman fasa kai duk kuwa da cewa tun da Fatima ta shigo motar taji ta raina kanta, hatta kamshin da take yi na daban ne yanayin kwalliyar ta ma haka. Fatima irin cikakkun matan nan ne masu cikar kirji da hips, wannan yasa kayan jikinta suka yi mata matukar kyau suka fitar da kyakykyawan fasalinta duk da cewa ba kama mata jiki suka yi ba, ga kuma dogon trail din da aka dinka a jikin rigar kamar yanayin dinkin alkyabba daya taso tun daga kafadar ta ya rufe mata kurjinta sannan ya sauka har kasa yana jan kasa yana binta a baya, sai ya zamanto kamar yayi serving a matsayin mayafi kenan. Angwayen kuma anko suka yi, komai nasu iri daya ne hatta agogon hannayensu, sai a lokacin Ruqayyah ta kara tabbatar da kamannin su. Hira suke tayi, Hussain yana ta tsokanar kowa har Fatima bai bari ba ita ma kuma sai ta rama, yace wai kowa a cikin su ya kure adaka dan ace sunyi kyau shi kuma yasan duk ya fi su kyau, har da posing yake yi wai matso kyan sa yake yi, wai sai lallai sunce duk yafi su yin kyau. Ita Ruqayyah yadda taga Fatima tana magana da dariya sai abin ya bata mamaki, sai taga kamar ba wannan gimbiyar da bayi suke kwanciya a gabanta bace ba. Ita ta dauka ai da kyar take magana saboda mulki. Sunyi ta hotunan su a cikin motar, itama Ruqayyah ta dan ware tayi magana da taji Hussain ya saka ta a gaba wai in bata magana zata haifi kurma. Suna ganin mutane suna ta shiga hall din, sai da aka tabbatar kowa ya gama shiga sannan aka zo kiran su, a lokacin itama Hassana da angonta Saeed sun karaso. Sannan sai suka jera suka shiga. Kawayen sune suka fara shiga a layi, kawayen Ruqayyah a farko, sai na Fatima sannan na Hassana, kowanne sunyi anko. Daga sai masu gayya masu aiki, Hassan rike da hannun Ruqayyah a gaba, Hussain da Fatima a tsakiya, Hassana da Saeed a baya. Sai kuma abokan angwaye suka take musu baya. Abin gwanin burgewa. Komai ya tafi bisa tsari, anci an sha an bar abinci, anyi programs masu kayatarwa yawancin su na barkwanci, sannan Aunty ta gabatar da jawabin godiya ga duk wanda ya samu halartar bikin. Daga nan kuma sai akayi ta daukan group pictures. Anyi kida nayi rawa, amma sai amaren duk kamar sun hada baki suka ƙi yin rawar. Angwaye kan sun cashe abinsu, abin mamaki sai ga Hassan ya biye wa Hussain suna ta rawa, ai kuwa nan take guri ya dauki ihu da tafi aka fito akayi ta musu ruwan kudi, kudi dai kam kamar ba'a talauci a Nigeria. Daga nan sai suka yanka cake akayi addu'a aka tashi. Daga gurin taro aka wuce da Hassana gidan mijinta, wannan yasa duk yan gidan basu dawo gida ba can suka wuce, amaren ne kawai da kawayensu suka dawo. Kamar yadda aka dauke su haka aka dawo dasu, aka fara sauke Ruqayyah sannan aka karasa da Fatima. A gajiye Ruqayyah ta shiga gida. Gidan ba kowa tunda su suka fara fita amma tas tas dashi yan aikin da aka kawo mata sun gyara mata shi kamar ba'a yi taro ba. Ta wuce sama ta cire tarkacen kayan jikinta dama duk sun bi sun ishe ta sannan ta kwanta akan gado yana mayar da ajjiyar zuciya. Ta lumshe idonta tana tunanin event din, gaskiya ya kayatar da ita, tayi ta kokarin ta gano fault a ciki amma ta kasa, sai dai kawai tasan kawayen Fatima sunfi nata haduwa, ta kuma san mutanen gurin sunfi bada karfin su ga Hussain da Fatima akan ita da Hassan. Tana nan kwance ta jiyo hayaniyar kawayenta suna shigowa. Kamar yadda suka sabarwa kansu direct bedroom dinta suka zarce suna ta hayaniya. "Ni ban gane ba Ruqayyah, naji a gurin kamar ana cewa kanin mijinki ne mai kamfanin ba mijin ki ba, menene gaskiya wai?" Wata tace "ni kuma ji nayi ance nasu ne su biyu wai Hassan and Hussain shine h and h din" Sumayya data fara rage kayan jikinta itama tace "to ku menene naku a ciki? Me zaku karu dashi in kun san waye?" Minal da take kwance rashe rashe akan gado tace "dan musan yadda zamu yi pricing kudin siyan baki mana? Ai iya kudin ka iya shagalin ka ne abin" ita dai Ruqayyah baya ce musu komai ba, sai kuma suka koma hirar wai waye yafi haduwa a tsakanin angwayen, kowa tana fadar gwaninta tana kuma fadar dalilin ta. Can suka ji tsayuwar mota sai suka garzaya taga suna leken motocin da suka tsaya a gaban gidan Hussain. Wata tace "wai Allah! Wannan gida! Gaskiya Ruqayyah da sake, in dai har kamfanin nan nasu ne su biyu to ki tubure ki ce sai dai ku zauna tare a can gidan, ai zai ishe ku" wata kuma tace "ni ta mijin nake bata gidan ba, gayen ya hadu karshen haduwa gashi ya iya daukan wanka" Ruqayyah ta mike ta shiga toilet ta rufe kanta kamar dazu, bata so su kara mata bakin ciki, ta samu zuciyarta ta dan kwanta su kuma suna so su kara taso mata da ita. Sumayya ta cire kayan ta ta saka simple ones sannan ta hada duk kayan da tazo dasu a jakarta, ana gam siyan baki itama zata tafi gida, sun riga sunyi magana da Adam yana jiranta a waje zai je ya kaita. Suna nan zaune har Hassan yazo, suna jiran suga ya zo da motoci kanar yadda Hussain yazo dashi sai gashi daga shi sai Jabir. A palon sama suka zauna sannan Hassan ya kira wayar Sumayya yace mata gasu sunzo. A dole suka fito da Ruqayyah daga toilet suka kara gyara ta sannan suka lullube ta da mayafi suka fita da ita, sai taji a ranta cewa bata son mayafin ta irin alkyabbar gimbiya take so. Suka zaunar da ita a gefe sannan suka zagaye ta suna gaisawa dasu Hassan. Minal tace "ina sauran abokan?" Jabir yace "gani!" Tace "gaskiya kayi mana kadan kai kadai, ai munfi son da yawa yadda zamuyi ciniki sosai" yayi dariya yace "ciniki kuma sai kace wani kayan gabas?" Tace "ina jin dai ba ka kalli amaryar nan sosai ba, ai ta wuce kayan gabas ma ita" yace "wannan kuma sai dai a tambayi ango, ni ina ni ina kallon matar mutane?" Hassan ya dan leka kasan mayafin Ruqayyah yace "kinyi gaskiya, ta wuce kayan gabas, ta wuce kaya baki dayansu. Ni a gurina ta wuce komai fa. She is soo PRECIOUS to me" duk suka kwashe da shewa daya ta miko wa Hassan hannu tace "to kawo, tunda dai ka yaba sai ka biya" ya koma ya kwanta a jikin kujera yace "wanne biya zanyi kuma? Bayan na riga na biya sadaki ai na gama komai" tace "sadaki wannan nata ne, wannan kuma mu zaka sallama" Jabir ya zaro kudi daga aljihun sa wanda dama ta riga ya tanada saboda su ya ajiye a kan cinyar ta kusa dashi yace "duk tsadar ku dai wannan ya ishe ku" Minal ta dauka tana kimasta adadin kudin tace "wannan din, haba dai, kar ku bada mu mana, a matsayin sa na the whole CEO of H and H ai mota muka saka ran zai sallame mu da ita". Hassan ya danyi dariya yace "CEO na H and H? A ina kika samu wannan tatsuniyar?" Duk kawayen suka yi shiru suna kallonsa kamar yadda shima yake kallon su daya bayan daya, sannan suka juya suka kalli Ruqayyah, shima ya juya ya kalleta duk da fuskarta tana rufe da mayafi. A hankali Ruqayyah ta saka hannu ta kamo hannun Sumayya ta rike a cikin nata, kamar me neman karin courage daga gareta. Minal ta sake cewa "wai kana nufin ba kaine CEO ba?" Hassan yace "ke waye ya gaya miki nine?" Jabir ya dafa kafadar Hassan yana kallon Minal yace "to ke menene naki a ciki? In shine in ma bashi bane ba ina ruwanki? Ku dai ba kudin siyan baki kuke so ba kuma gashi an baku?" Wata a kawayen tace "to ai matar tasa ce ta gaya mana shine CEO, wannan yasa muka fitar da kudi masu yawa muka yi kwalliya da sauran abubuwa dan kar azo aji kunya, kuma dan muna saka ran zamu fanshe kudin mu a jikin ku, yanzu kuma gashinan daga dukkan alamu ashe yaudarar mu tayi bashi bane ba ko kuma shine yake boye mana dan kar ya bamu abinda muke nema. Mu kuma ba za mu bar gidan nan ba sai an bamu mota" Hassan yayi kokarin mikewa, ransa yana baci zuciyarsa tana baƙi, bai taba tsammanin yadda yake jin farin ciki a ransa lokaci daya zai iya komawa baƙin ciki ba. So yake ya kira security din gidan su zo su fitar musu da wadannan marasa kunyar yaran masu niyyar haddasa musu fitina a daren farkon auren su. Jabir ya sake rike shi fuskarsa da murmushi yace "to ke yanzu baiwar Allah da kike ta wannan jawabin akan lallai sai an baku mota in aka baku din me zakuyi da ita? Ku kusan goma sharing zaku ke yi?" Tana juya idonta tace "siyarwa zamuyi mana, mu raba kudin ko ma samu na kashewa zuwa wani lokaci" Jabir yace "shikenan, yanzu wata a cikin ku ta turo min account details dinta sai in tura muku kudin motar ku" Hassan yayi sauri zaiyi magana Jabir ya sake yi masa alamun yayi shiru da hannunsa. A take suka bashi kuma a take ya tura musu kudin. Yana shigar musu suka duba "ahhh wannan ai sai dai karamar mota zamu siya" yayi dariya yace "ku da ya kamata ku gode min na taimaka muku ba sai kunyi wahalar neman mai siyan mota ba? Kuma in kuka tashi siyarwa tayin wulakanci za'a yi muku ba lallai ne ma ku samu irin wannan kudin ba. Yanzu kuwa babu ruwanku da jira, kafin kuje gida ma zaku iya raba abin ku" da haka ya shawo kansu suka yadda, sannan suka dan saya fuskar Ruqayyah kadan yadda za'a gani. Jabir ya dan leka fuskar yace "to amarya, Allah ya sanya alkhairi, sai nazo cin ta tsotse" ya mike yana mikawa Hassan hannu "ango, Allah ya bamu alkhairi, na yi maka wannan yakin saura kai kuma kayi naka" ya fada da dariya a muryarsa amma Hassan bai mayar masa da dariyar ba kuma bashi da niyyar rama wasan da yayi masa. Minal tayi wa Jabir fari da ido tace "kuma tafiya zaka yi, ko dan ragin hanya babu?" Yace "rufa min asiri kar matata tayi min duka, sai dai ku fito a samo muku driver ya kai ku har gidajen ku, amma ni yanzu ma kira na take tayi nayi dare" ya fada yana duba wayarsa duk da babu wani missed call a kai. Suka kwashi tarkacen su ba tare da wata kyakkyawar sallama ga Ruqayyah ba ballantana ga mijinta daya tasa ta a gaba yana kallon ta , fuska babu walwala. Suna fita gidan yayi tsit kamar an kawo sakon mutuwa. Sumayya ta cire hannun ta daga na Ruqayyah tana jinta totally out of place ta mike. "Tooo da haka haka, nima bara in kara gaba" Ruqayyah ta sake rike mata hannu "ba sai gobe zaki tafi ba? Dare fa yayi sosai" ta sake zare hannunta daga nata tace "ai ina da me kai ni, tun dazu ma yana waje yana jirana" ta fada tana kallon fuskar Hassan tana jiran ya bata amsa tunda yasan wanda take nufi amma sai taga ko kallonta bai yi ba. Ta shiga daki da sauri ta dauko jakarta ta fito sannan tace musu sai da safe ta sauka da sauri tun kafin bomb din ya tashi da ita, tana fita taga Adam a tsaye a jikin mota yana danna wayarsa, ya dago kai yana kallon ta yace "I thought you are never coming out" tace "kai dai tunda na fito shikenan" bata jira ya buɗe mata kofa ba ta bude baya ta saka jakarta sannan ta bude gaba ta zauna. Ya shiga ya kunna motar suka bar gurin, ta juya tana kallon gidan Hassan a ranta tana jin kamar wani ticking bomb ne a gidan wanda zai iya exploding any time. Ta san dama shi ramin karya kurarre ne amma bata san zai kure tun a ranar farko ba. But something yana gaya mata Ruqayyah will find a way out of this. Sun jima a zaune, ita kanta a kasa, hannayenta a kan cinyarta, shi kuma yana facing dinta ya jingina bayan sa da jikin kujera. Studying dinta yake yi, amma sai ya kasa karantar fuskarta, so yake ya hango guilt ko kuma tsoro ko kunya amma bai ga komai ba sai dan guntun murmushi a fuskarta. Ta danyi gyaran murya yace "CEO? Really?" Ta dan dago fuskarta ta kalle shi sai ta mayar da kanta kasa tace "ceo? Menene ceo?" Ya bata fuska yana jin confusion yace "kawayen ki suka ce kince nine CEO na H and H" ta daga kafada tace "ba fa kawayena bane ba, ni kasan ba kawaye ne dani ba, da za'a yi bikin ne Sumayya da Minal suka gayyato su dan su tsaya a matsayin kawayena tunda bani da kawaye" yace "wacece Minal?" Tace "yar makotan muce a wancan gidan, wadda ta zauna anan" ta fada tana nuna inda Minal ta zauna. Ya sake cewa "amma suka ce kince musu nine CEO?" ta danyi dariya tace "ni fa na ce maka bansan abinda hakan yake nufi ba" yadda ta fadi maganar so innocently ya sa ya fara yarda da ita, to ita ina zata san wadannan business terms din? Yanzu fa ta gama secondary school kuma ga yanayin gidan su. A ina zata san me duniya take ciki? Yace "amma da suka fada me yasa baki karyata su ba a gabansu, duk da baki san term din ba sai ki musa ki ce ke baki fada ba, dan nan gaba kar su sake yi miki karya" ta dan sunkuyar da kanta tana dan rufe fuskarta kamar mai jin kunya tace "siyan baki na fa akeyi, in ana siyan baki fa ba'a magana" ya dafe kansa da hannu biyu yana jin kansa yana neman fara ciwo. Zuciyarsa da kwakwalwar sa suna yaki a tsakanin su, but son Ruqayyah yana rinjayar sense dinsa. Ya cire hannun sa daga kansa sannan ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna. Ya kamo hannun ta ya rike a nasa, ta sunkuyar da kai cikin jin kunya tana kokarin karbe hannunta amma yaki cikawa sai ta bar masa. Yace "amma kunyi magana dasu akan aikina?" Ta daga kai tace "sun tambayeni aikin ka nace ban sani ba, amma sai na basu labarin daukan Baba aiki da kayi a H and H. Ina jin daga nan suka samu kalmar CEA din" yayi dariya yana girgiza kansa yace "CEO ake cewa. It means Chief Executive Officer, wanda shine matsayin da yafi Kowane matsayi girma a Company, shi yake da final say a duk decision making, wani ceo din kuma shine mamallakin Company, shine founder, shine kuma sole share holder" ta dago idanu tana kallonsa tace "and are you?" Ya girgiza kansa yace "noo, am not" taji dan sauran hope din da take dashi yana bin iska. Ta sunkuyar da kanta kasa, Ya sa hannu ya kuma dago da fuskar tata suna kallon juna yace "Hussain shine CEO kuma owner na H and H bani ba. Ni ko share ma bani da ita a cikin Companyn. Duk group of companies din nasa ne shi kadai. Ni maaikaci ne a karkashin sa nake aiki. Matsayina shine chief of staff, duk wani maaikaci na kamfanin a karkashi na yake, ni nake daukan su kuma Ni nake kula dasu. Nima Hussain albashi yake bani kamar yadda yake biyan sauran ma'aikata albashi. Gidajen nan guda biyu duk nasa ne, shi ya gina su, duk motar da kika gani a gidan nan da kuma gidan Aunty to Hussain ne ya siye ta, yana da passion for mota shi yasa yake chanjata kamar yadda yake chanja sutura. Duk abinda kika gani a gidan nan tun daga kan gadon da kika kwana akai zuwa chokalin da zamu ci abinci dashi Hussain ne ya siya" ta sunkuyar da kanta kasa tana fighting kukan da yake taho mata. Dama abinda ta aura kenan? Solobiyon miji wanda zai zauna kaninsa yayi masa komai? Shi me yake yi a lokacin da Hussain yake neman kudin? Ta rabu da Baba ta dawo hannun Hassan. Ita dai bata da Sa'a a rayuwa. Ya sake dago kanta da hannunsa yana cewa "do you have a problem with that?" Ta girgiza kanta da sauri tace "babu matsala, kayansa ai kamar kayan ka ne. Kuma wata rana Allah zai hore mana namu mu tasar masa daga gida" yace "yes, da banyi niyyar zama anan ba, gida nayi niyyar in gina mana da kudin da nake ta tarawa. But ganin Baba ya fi mu bukatar gidan shi yasa na siya masa sauran kudin kuma nayi amfani dasu a biki, yanzu zan sake tara wasu kafin nan kafin mu tara zuri'a sai muyi ginin mu, shi yasa ban bari Hussain yayi mana gini irin nasa ba, saboda ba lallai bane mu gina irin nasa, kuma bana so in mun zo tashi muga kamar munci baya ne gwara muji cewa munci gaba. Kin fahimta?" Ta juya tana kallon side din gidan Hussain, ta nuna da hannu tace " you mean....... Irin wancan zai gina mana......sai ka hana shi kasa ya gina irin wannan........?" Yayi murmushi ganin irin tarin mamakin da yake kwance a fuskarta yace "eh mana. Har fushi yayi ya kaini kara gurin aunty" wasu hawayen takaici masu zafi suka zubo mata, wannan wanne irin rashin rabo ne da Hassan? Ya saka dan yatsa ya gogi hawayen yace "kuka? Kukan me kike yi kuma?" Sauran kukan ya kwace mata gaba daya, tace "kukan godiya nake yi ga Allah, wanda ya bani miji mai gudun duniya da hangen nesa kamar ka" ya zauna sosai yana kwanto da ita jikinsa yace "it is okay. Ki bar kuka, you have cried a lot a cikin kwanakin nan. Murna zamuyi muyi godiya ga Allah kinji" ta gyada kai tana tashi daga jikinsa. Ya mike yana mikar da ita itama. "Ki tashi muje to muyi sallah mu gode masa, in mun gode masa sai ya karo mana. Haka yace da kansa" ta mike tana goge idonta da bayan hannunta. Sai da ya kai ta har dakin ta sannan ya fita, har yanzu bai debo kayansa daga tsohon dakin sa ba, yan kayan da zai bukata kawai ya dauko ya dawo gidan. Ya kai kayan dakinsa sannan ya koma dakinta ya tarar tana toilet har yanzu. Ya koma dakin sa ya shiga wanka shima. Sai da ta yi kuka mai isarta a toilet sannan tayi wanka tayi alwala ta fito ta saka doguwar riga tayi sallar ishai da bata yi ba. Tana tashi yana shigowa da basket a hannunsa ya ajiye akan side table yace "kar dai har kinyi sallah kin barni" tace "sallar ishai nayi ai" yace "ohhh okay" sannan yazo ya shiga gabanta suka gabatar d sallar sunna da annabi ya umarci ma'aurata suyi. Bayan sun idar Hassan ya yi musu adduoin neman albarka a auren su, neman samun dacewa a duniya da kuma a lahira. Suka shafa ya juyo yana kallonta ya dan hade rai yace "idonki, kamar ya kumbura, duk kukan ne?" Ta sunkuyar da kai tace "da rashin bacci ma, kasan in mutum yazo bakon guri baya iya yin bacci" yana murmushi yace "kar ki damu, yau zakiyi bacci har da munshari" ta mike tana jin wani iri a jikinta, sai yanzu take tunanin yama akayi ta yadda tayi aure yanzu ne? Ita yar karamar ta ina zata kai wannan mutumin? So take tayi tunanin ta yadda zata zille masa amma kwakwalwar ta ta toshe ta kasa aikin tunanin yadda zata yi dashi dan ita sam yau bakar rana take gani kar yazo ya kara wa ranar ta duhu dan bakikkirin take ganin sa. Ta mike tana kokarin shiga closet taji hannunsa ya rufe kofar sannan ya murda key, ta juyo da sauri sai gata a kirjinsa, ya saka hannunsa a dayan side din ta yadda ta kasance a tsakiyar hannayensa. Ta fara yayyarfe hannu sauran kukan da bata karasa dazu ba yana dawowa. Yayi dariya yace "cry cry baby, tunda kin zama baby let me treat you as a baby" ba tare daya jira amsarta ba ya daga ta chalak kamar baby, ya zauna akan gado yana dora ta a cinyarsa, ya lura da yadda jikinta yake rawa kadan kadan, ta boye fuskarta a jikinsa. Yace "bafa wani abu zanyi miki ba, look at me, look at me precious" ta dan dago kai tana kallon serious face dinsa yace "nace ba wani abu zanyi miki ba, I just want to feed you that's all. Na ga dazu baki ci abinci a gurin dinner ba, am sure da rana ma ba ci kika yi ba" tace "to ka sauke ni, zan ci da kaina" yace "to zan sauke ki, amma sai kin gaya min a fruits me kika fi so?" Tace "ni banason komai, ni bana shan fruits ma" ya dauko ayaba yana barewa yace "in dai kika cinye wannan to zan sauke ki kuma ba zan yi miki komai ba" ya fada yana kaiwa bakin ta, ta girgiza kai sai ya mayar nasa bakin yace "to shikenan, bara in cinye abata amma kuma duk abinda ya biyo baya ke kika siya da kudin ki" tayi saurin dawo da hannunsa baya tana saka ayabar a bakinta tana ci a hankali idonta a cikin nasa har ta gama cinyewa sannan tace "na cinye to" ya dauko cinyar kaza yace "saura wannan" tayi kamar zata yi kuka "ni ayaba kawai kace min ai" yace "ai ba rantsewa nayi ba". A haka sai data ci kazar, shima kuma yaci. Tace "to na koshi, ka sake ni to" yana murmushi yace "ai ba rantse wa nayi ba" sannan ya juyo da fuskarta zuwa gare shi, ta rufe idonta, ya dora bakin sa akan nata. A part din Hussain, a cikin Bedroom dinsa. Fatima tsaye a gaban mirror tana cire ear rings dinta. Hussain yana zaune a kujera yana amsa waya yana ta dariya, tana kallonsa ta mirror fuskarsa tana reflecting farin cikin da yake zuciyarsa. Tayi murmushi itama tana jin zuciyarta wasai. Bata da wani tension bata da pressure din komai sai farin ciki da annashuwar cikar burinta na zama matar Hussain. Rabin ranta. Ya ajiye wayar yana cewa "Time to switch off the phone, duk wanda bai kira ba yayi missing, duk kuma wanda bai zo ba shina yayi missing" ya karaso bayan Fatima ya tsaya yana tayata cire sarkar wuyanta yace "duk wanda bai ga kyalliyar Fatima ta yau ba yayi missing" tayi murmushi tana juyowa suna facing juna sannan ta mika masa hannunta yana cire mata awarwarayen ta tace "wanne mai missing din ne ya kira ka? Nasan duk wanda ya bar gidan nan yanzu ba zai kira ka ba" ya kamo yatsunta yana cire zobuna guda biyu da suke yatsun yana ajiye su a gefe yace "Sadiq ne, dan banza, bayan yaki zuwa bikin kuma shine zai kira ni yana min dadin baki" tayi murmushi tace "the prince of Abuja kenan. Shalelen Sarki Abdallah. Ina zai iya tahowa daga america ya bar his Arabian girlfriend?" Hussain yayi dariya yace "sai na gaya masa kina tsokanar sa" ta durkusa tana cire masa socks din kafarsa, sai ya kamota ya dago da ita yana kallon fuskarta yace "kinsan me yace min" ta girgiza kanta idonta a kasa, ya jawo ta zuwa jikin sa sannan ya kai bakinsa dai dai kunnen ta yace "yace wai insha strawberries before I kiss you, so that I will taste like a strawberry to you" ta danyi dariya tana sunne fuskarta a kirjinsa. Yace "kinsan amsar dana bashi?" Ta girgiza kanta ba tare data kalle shi ba, ya saka hannu ya dago fuskarta amma sai ta rufe idonta sai dai ta kasa daina murmushin da take yi, yace "nace masa ba zan sha din ba, cos when I kiss you, I want you to taste me, to taste Hussain not strawberry". Nasan ba yawa, ayi hakuri Tun da ta shiga motar bata ce masa komai ba, hankalin ta yafi karkata ga halin data baro yaruwarta dan taga babu alamar Hassan zai bata kofar da zata kubuce masa. Ta lumshe idinta a ranta tana fatan Allah ya huci zuciyar Hassan ya rangwantawa Ruqayyah, duk da dai tasan ko da Ruqayyah ta samu kafar zamewa to kuwa tabbas Hassan zai diga mata alamar tambaya, wannan zai kawo doubt a rayuwar aurensu, zargi kuma zaizo ya shiga ciki, daga nan komai zai rushe. Dan zargi yana lalata aure komai karfin soyayyar da aka gina auren a kai. Adam ya kalleta sannan yayi ajjiyar zuciya yace "ni bani na kar zomon ba, ratayar ma kuma ba'a bani ba amma an daura min laifi" ta juyo tana kallon sa tace "wato bayan magana da yaren hausa har karin magana ka iya ko?" Yace "ina cin A+ a hausa language sanda ina school" ta danyi murmushi ta sake yin shiru. Yace "what's wrong? Ko har kin fara missing sister dinki ne?" Ta girgiza kanta da sauri, sai kuma taji hawaye ya taho mata. Tayi saurin gogewa kar ya gani amma da yake hankalinsa yana kanta ya gani din, yace "subhanallah. Kuka Sumayya?" Sai ya sauka gefen titi yayi packing duk kuwa da cewa babu motoci sosai akan titin. Ta sake goge idonta tana kokarin kirkiro murmushi tace "babu komai fa, mu tafi kawai, maybe kamar yadda ka fada ɗin ne, maybe missing Ruqayyah na fara tun yanzu" yace "is that right? Ni kuma a fuskarki banga haka ba, fuskar ki tafi kama da wadda take jin tsoron something will happen, ko kuma ma ya faru din" tana girgiza kanta tace "am just scared for Ruqayyah, ina tausaya mata rayuwar da zata yi a gidan Hassan" Adam yace "tausayi kuma? Ruqayyah fa oga Hassan ta aura, kin san kuwa kudin da mutanen nan suke dashi? She will never lack anything a rayuwarta" Sumayya tace "and that's the problem Adam. Kudi sune problem din. Babu wanda ya san halin Ruqayyah Kamar ni a duniya kuma ni din babu wanda nake zama muyi hirar Ruqayyah dashi dan ita din tamkar wani barin jiki na ce da bazan iya butulcewa ba. Ruqayyah bata taba zama satisfied a rayuwarta, Ruqayyah bata taba murna da abinda ta samu, abinda bata samu ba shi take so. Na san kaddara ce ta hada Hassan da Ruqayyah amma aurensa da tayi, tayi ne saboda kudinsa, saboda tana tunanin kamfanin sa ne, yanzu da akayi auren ta fahimci na dan uwansa ne ina tsoro abinda zata aikata akan hakan" sai ta bashi labarin haduwar Hassan da Ruqayyah, dan brief soyayyar su, furtawar da Ruqayyah tayi da bakinta cewa Hussain yafi Hassan kyau, nuna wa da tayi tafi son gidan Hussain akan na Hassan, kin zama ta kalli kayan lefen gimbiya, da kuma abinda ya faru a gurin siyan baki. Bata san me yasa ta iya sakin bakinta tayi masa wannan zancen ba maybe dan abin yayi mata yawa a ranta ne, maybe kuma dan dadin ac da comfort din motar ne, maybe kuma it is something else. Bai yi mamakin maganganun Sumayya ba saboda shi dama yasan Ruqayyah bata da kirki, but bai san how deep rashin kirkin nata ya kai ba sai yau. Ya fahimci yaudarar Hassan take yi, ya fahimci kuma she is a danger to that nice lovely family. Amma kuma babu abinda zai iya yi akai, shi dai ba zai tafi gurin Hassan yace masa "matarka yaudarar ka take yi ba" in yayi haka yasan bayan aikinsa da zai rasa maybe har a cell sai ya kwana. Sannan babu wani problem din da hakan zaiyi solving dan Hassan din ba yarda zaiyi ba. Ya juyo yana kallonta yace "now, what do you propose we do?" Tace "ban sani ba nima. Ni dai nasan sanda Ruqayyah tana gida ina yin iyakacin kokari na wajen ganin duk sanda zata yi ba dai dai ba na hanata. Ko da kuwa zata yi fushi dani. Amma yanzu bama tare babu kuma wanda zai ke bata shawara acan inda take, duk abinda yazo mata zuciyarta shi zata yi, wannan shine tsorona" yace "still you can do something" ya juyo sosai yana kallonta yace "na fahimci cewa ta yarda dake tana gaya miki dukkan sirrinta, to kiyi kokari ki yi keeping that relationship a tsakanin ku, ki ringa bibiyar ta kina jin abinda take ciki ta yadda zaki san plans dinta, ke kuma sai kiyi kokarin ganin kin dakatar da ita ko kuma in abin yafi karfinki ki gayawa wanda zai iya dakatar da ita. Kin fahimce ni?" Ta gyada kai. Yayi murmushi yace "and you stop worrying about her, yes ku twins ne kina son sister dinki and all that but still you have to put yourself first, rayiwarku daban daban kar ki zama so caught up a ta ta rayuwar ki manta da taki rayuwar, musamman yanzu da ba kwa tare, find something to enjoy, someone to love, someone like me" ya karashe maganar ta sigar wasa yana nuna kansa, tayi murmushi tana hararar sa, yace "ha! Finally tayi murmushi, you have no idea yadda murmushi yake yi miki kyau. Please don't ever let something stop you from smiling" ya mayar da motar kan titi suka cigaba da tafiya a hankali, har yanzu da murmushi a fuskarta tace "enough about Rukee, tell me about you. Who is Adam?" Yayi ajjiyar zuciya, yes ya gaya mata secrect dinsa amma har yanzu baya son yin maganar fast dinsa, not now, sai yayi kokarin chanja maganar yace "Adam is going back to school this session" ta bude baki cikin mamaki tace "really?" Proudly Yace "yes ma" tayi dariya "amma naji dadi wallahi na taya ka da murna kuma. But wait...wai har ka tara kudin" ya girgiza kai yace "nooo. Oga Hussain ya tambaye ni abinda yasa ban koma school ba sai nayi mishi bayanin plans dina and he said da zarar am fara siyar da form inje in siyo zai biya komai" Sumayya tace "Masha Allah. Allah ya biya shi da alkhairi" yace "ameen. Yana da kirki sosai, ni dai zan iya cewa ban taba haduwa da mutum mai kirkin sa ba, kowa kuma a gidan haka yake fada, daga haduwa ta dashi zuwa yanzu ba zan iya lissafa alkhairan da yayi min ba, kuma ba wai kyautar ce mafi muhimmanci ba, a'a yadda yake treating mutane shine abin so" Sumayya tayi murmushi tana tuno fuskar Hussain, bata tunanin ta taba ganin sa babu murmushi a fuskar sa. Adam yace "yanzu sai inje in siyo mana tare ko?" Ta bude ido "noo. Kar ma ka fara" yace "why not?" Tace "baba ba zai yarda ba, in dai har ina karkashin sa ba zai bari wani ya dauki nauyi na ba" Adam yace "okay, sai mu dauke ki daga karkashin nasa ai, ki dawo karkashina" ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da fingers dinta, a hankali kamar mai magana da kansa yace "ban ma san ta yadda hakan zai kasance ba but ina son ya kasance din, ya ilahi see me through" ta dago kai tana kallonsa yace "I want to marry you amma ban san ta inda zan fara ba" suka hada ido briefly, tayi saurin sunkuyar da nata idon kasa dan bata da amsar da zata bashi. Sai da yayi packing sannan ta dago kai tana kallon kofar gidan nasu, tayi ajjiyar zuciya tace "nagode sosai Adam. Sai da safe" yace "kar kiyi saurin yi min sallama, go and knock ina nan ina jiran ki. Know that in Baba ya dake ki I will feel it here" ya nuna kirjinsa, ta kalli kofar gidan sannan ta kalli agogon motar, 12:32. Ta ja numfashin tsoro tana bude ido sannan ta fita da sauri taje ta fara knocking kirjinta yana bugawa. Ba'a jima ba aka bude mata. Allah ya taimake ta yan uwan su da suka je dinner duk suna nan dan haka ba'a yi bacci ba ana ta hira ana mayar da magana. Ta juyo tana kallon cikin motar da Adam yake zaune suka hada ido sai yayi kissing hannun sa yayi mata blowing, ta dauke kanta tana blushing, hoping wanda ya bude mata kofa bai gani ba. Sai da ta shiga ta rufe kofa sannan ya juya motar ya bar layin, sai a lokacin ya lura cewa bata dauki jakar kayan sawar ta ba. Sumayya ta samu ta shige cikin mutane, amma bata buyar wa Inna Ade ba dan sai data yi mata magana "Sumayya ke kuwa me yasa kika taho da daren nan haka? Ba suna da dakuna a gidan ba ba sai kiyi kwanciyarki ba in yaso da safe sai ki taho?" Sumayya tace "Inna kawai ji nayi ina son in taho gida, shine suka saka driver dinsu ya kawo ni har gida" Inna tace "nan gaba kar ki sake tahowa da irin wannan daren, gwara ki kira wayar baban ku ki gaya masa dare yayi zaki kwana, karkarinta yayi miki fadan me yasa kika bari dare yayi miki amma ba zaice ki taho da daren ba" Sumayya tace "insha Allah Inna" sai kuma ta fara tambayarta yadda ta baro Ruqayyah "bata kukan ko? Ranar nan ance min kuka tayi tayi" Sumayya taji wani abu ya taba ranta, Allah sarki uwa, ita bata san Ruqayyah duk ba wannan ne a gabanta ba, tace "ta daina kukan Inna". Ruqayyah kam ta gaya wa yan garinsu a hannun Hassan, dan sam bai daga mata kafa ba duk kukan da take masa, a take ta yanke a ranta cewa shi din azzalumi ne bayan kasancewar sa solobiyo, ba wai nadamar aure kadai tayi ba, sai data yi nadamar taimakon sa dan bata san wannan shine sakamakon ta ba. Shi kuwa oga Hassan bakinsa har kunne dan exactly abinda yake so shi ya samu a gurin Ruqayyah wannan ya saka yaji duk sauran gurbin da bata gama cikewa a zuciyarsa ba yanzu ta cika shi taf. Sai yazo kuma ya fara aikin rarrashi, shine rarrashi shine gyaran gado shine jinya. Yawan kukan da tayi ya saka mata ciwon kai da zazzabi, da kyar ya samu ya lallabata ta sha paracetamol sannan ta kwanta ya lullube ta. Amma kuma sai ta saka masa rigimar cewa ba zai kwanta a kan gadon ba dan kar ya kuma tabata haka yana ji yana ganin lafiyayyen gado da lafiyayyar shimfida ga kuma matarsa a kai amma dolensa ya saka pillow a kasa a gaban gadon ya kwanta ya rufe idonsa saboda ya lura idonta yana kansa, sai daya tabbatar tayi bacci sannan ya hau kan gadon ya jawo ta jikinsa ya lullube su yana ajiyar zuciya. Me yafi aure dadi? Da murmushi a fuskarsa bacci ya dauke shi. Da safe ma bata chanja zani ba, zaman jinyar ya cigaba dayi. Anan akan gado taci abincin safe da na rana, sallah kawai take tashi tayi itama sai ya fita tukunna wai dan kar yaga yadda take tafiya yayi mata ɗariya. "Ba zanyi dariya ba fa" ya fada yana kokarin gimtse dariyar, ta saka kuka "wallahi gashi nan dariyar zaka yi, gashi nan na gani bakinka yana abin dariya" dariyar ta kubuce masa yayi, tace "ba ga shi nan kana dariyar ba" ya rufe bakin yace "na daina, bara in fita in baki guri" ya fita yana cigaba da dariyar yarintarta. Yana fita yaji mutane suna shigowa da sallama, ya sauka yana amsawa. Yan uwansu ne kaf dinsu da suka zo daga Gombe suka shigo, daga alama sallama zasuyi musu. Ya kara fadin murmushin sa yana karasa saukowa sannan ya gaida manyan ciki yaran kuma suka gaishe shi. Suka zazzauna shima ya zauna dattijan ciki suna tsokanar sa wai yana kyallin goshi. Ya shafa goshin nasa kamar mai son gogewa yana dariya, ya kasa daina dariya. Wata a ciki tace "ina amaryar to? A kira mana ita mana muyi sallama" ya shafa kai yace "tana sallah amma ban sani ba ko ta idar yanzu" Zulaihat data rako su ta mike tace "bara in dubo" ya bita da kallo kehar ta hau saman, a ransa yana tunanin irin dramar da za'ayi da Ruqayyah a gurin saukowa daga bene. Daga nan suka cigaba da hirar su shida yan uwansa, kawai sai jin muryar Ruqayyah yayi a bayansa, tana gaishe da mutanen gurin, suka amsa da amarya bata laifi ko ta kashe dan masu gida. Sai da ya waiga sannan ya lura cewa a tsaye tayi gaisuwar, yaji babu dadi a ransa amma sai ya bata uzuri da ciwon da jikinta yake yi, ai tayi ma kokari data iya saukowa daga stairs din. Yace "Zulaihat tashi ki kawo musu ruwa" nan take suka ce "a'a alhamdulillah, yi zamanki Zulaihat ba zamu iya sha ba" "ni cikina kamar zai fashe saboda koshi" "kayan gara muka samu a gidan Hussain, Fatima tayi ta loda mana wai sai munci, sai da kyar ta rabu damu kagan su can ma tray guda ta aika mana dashi gurin Amina wai ma ci a hanya in munji yunwa" Hassan yace "ta kyauta, kamar ta san ummah (kanwar kakarsu) dama da cikin zani, bata koshi" tace "ko ma cikin menene dani ci zanyi, dama zubi na daban tayi min kuma tace kar in bawa kowa in ajiye a firji in na koma gida" Ruqayyah tace "can kuka fara shiga kenan?' Yadda tayi maganar yasa duk suka juyo suna kallonta tana tsaye a bayan kujerar da Hassan yake kai, Ummah tace "eh, can muka fara zuwa, shine a farko ai" kadan ya rage Ruqayyah bata bata amsa da cewa ai Hassan ne babba ba, sai kawai ta rabu da ita saboda Hassan yana gurin amma a zuciyarta tana tunanin ba suyi dai dai ba, ai Hassan ne babba dan haka gidan sa ya kamata su fara zuwa ba wai suje gidan Hussain sannan su zo suna basu labarin abinda suka ci a gidan ba, wannan gaskiya a ganinta rashin adalci ne da nuna bambanci. Shirun da gurin yayi ne ya saka suka fara mikewa daya bayan daya "to mu zamu tafi, Allah ya sanya alkhairi, sai mun dawo suna kuma" suka fada cikin tsokana, Hassan yayi murmushi sannan ya bisu a baya zaiyi musu rakiya, Ruqayyah kuwa ko ci kanku bata ce musu ba ta juya ta komawarta sama. Kwanaki suka wuce suka samar da sati biyu A cikin sati biyun nan kowane amarya da ango sun ci amarcin su son ransu. Hussain da gimbiya suna ta zuba lafiyayyiyar tsadaddiyar soyayyar su irin ta wayayyun ma'aurata. Duk yawon Hussain a wannan satin babu inda yaje in banda gidan Aunty. Amma fa shi nasa gidan kullum a cike yake da mutanen sa da mutanen gimbiya wadanda suke zuwa ganin gida da kuma cin arziki, duk kuma wanda yazo ɗin to sai yaci arzikin ya kuma bar arzikin a inda yake. Dan ita ma Fatima budadden hannu ne da ita babu yadda zaka shiga gidanta ka fito ba tare data baka wani abu ba, in ka hadu da Hussain shima ya kara maka. Kullum daga gidan aunty ake yin girkin safe rana da dare a kai gidan Hassan da kuma gidan Hussain, bayan yan aikin da Aunty ta basu kowa bibbiyu duk da cewa Fatimah ta taho da nata daga gida amma an kara mata, yammatan aunty kuwa tun da akayi auren gidan Fatima suke wuni su shiga duk inda suke so a gidan suyi duk abinda ransu yake so. In kika tarar dasu tare zaki dauka kannen ta ne. A bangaren Ruqayyah ma bakin suna dan leka mata, amma basa wani jimawa suke tafiya su koma gidan Hussain, abinda yake kara kona ran Ruqayyah kenan, ita gani take yi saboda kudin Hussain da tittle din Fatima ne yasa mutane suka fi zama a gurin su. Tun da akayi auren bata taka kafarta part din Hussain ba, ba kuma ta jin zata shiga anytime soon dan bata jin tana da zuciyar da zata dauki abinda idonta zai gani, dan duk wanda ya shigo gidan ta indai ya shiga gidan Hussain sai ya bata labarin wani abin burgewa da ya gani a gidan. Bata kulasu sai dai kawai tayi musu fuskar shanu, wannan ne yake sawa su tashi su tafi dan kansu. And those comments are killing her inside. Ga nacin Hassan, shi ya kasa fahimtar ita ba wai son wannan abin take yi ba, tana dai bashi ne dan taga yadda yake tsananin son abin ita kuma top priority dinta shine ta kanannade komai nashi, yadda duk abinda take so zaiyi mata abinda bata so kuma ba zaiyi ba. Ya na sakata ta shiga ta gaida Aunty kullum da yamma, a can suke haduwa da Fatima wasu lokutan. Ranar nan ma a kitchen ta tarar da ita da aunty da sauran yaran gidan wai tana koya musu wani tuwo da ake yi a gidan sarauta da ake kira da tuwon dalayi. A ranta tace "ji munafurci, sai kace ba bayi ne suke musu abincin a can ba" a lokacin ne Fatima take cewa da Aunty "aunty ni dai da zaki bi ta tawa da kin daina mana girkin nan haka, kiyi zamanki kiyi hutawarki" aunty tace "yanzun ma ai ina hutawa Fatima, babu fa abinda nake yi a gidan nan, ni ba aiki ba ni ba kasuwanci ba sai dai in saka TV a gaba inyi ta kallo" Fatima tace "duk da haka dai Aunty ki barshi, na gidan nan ma ku daina, in yaso su Nafisa suke zuwa can muna yi tare sai ake kawo muku kawai. Lokacin hutawarki ne yanzu. In kin gaji da zama guri daya sai a fitar dake ki zaga gari, in kin gaji da garin ma sai a kaiki wata kasar ki cigaba da hutawa. Ko Ruqayyah?" Ta juyo tana yiwa Ruqayyah wadda tun da ta shigo bata kulata ba murmushi, Ruqayyah tayi murmushi kawai, amma a ranta tana jin kamar ta rufe Fatima da duka, yanzu ita in aka daina kai mata abincin daga gidan nan ta ina zata fara dora abinci a gidan ta? Ita da bata iya irin wadannan girke girken ba. Sai da suka gama tuwon suka jera a dining, wai yau duk a nan za'a hadu aci tuwon Fatima. Suka zauna a palo suna ta hira, anan taga Fatima ta kira Hassana suna magana a waya tana tsokanar ta wai tayi missing gashi nan za'a ci abinci gabadayan su banda ita, har tana cewa zata tura mata hotunan su. Yadda suke maganar ya nuna cewa sun saba sosai, sai Ruqayyah tayi realizing ita ko number din Hassana bata da ita kuma in banda rannan da suka gaisa a wayar Hassan basu taba waya ba tunda akayi bikin su. Wato dan ita yar talakawa ce kuma mijinta bashi da kudi shine suke wareta ko? Suna nan zaune har Hassan da Hussain suka shigo, suma suka zauna aka cigaba da hira, Hassan yana ta kokarin ya saka Ruqayyah a cikin hirar amma sai dai tayi murmushi kawai ta sunkuyar da kanta, ita ba zata iya irin wannan rashin kunyar irin na Fatima ba. Loma daya tayi wa tuwon taji ba zata iya ci ba, zuciyarta har ta fara tashi kamar zata yi amai, wani iri taji shi a bakinta. Amma sai taga su ci suke tayi suna santi, har da Hassan dinta dan abin kunya, wannan ai kunyata ta yakeyi. Sai da suka gama sannan Hussain yake cewa "aunty dama ina so in gaya miki monday muke so zamu tashi zuwa honeymoon" Hassan ya rankwashe shi sannan"yanzu auntyn kake gayawa zaka je honeymoon saboda baka da kunya?" Hussain yace "ouch, Fatima kina ganin sa zai nakasa miki miji ko? So yake ya hargitsa min ƙwaƙwalwa ta in kasa lissafi" Ruqayyah ta dauke kanta tana dan karamin tsaki, shi komai sai y nuna shi mai kudi ne, ko me y kawo zancen lissafi? Fatima Ta daga kafada tana masa alamar kunfi kusa, Aunty tace "Masha Allah, Allah ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya. Ruqayyah kin shirya dai ko?" Zulaihat tace "ni na shirya Aunty, dani zaku tafi" Khadijah ta harare ta "ke kin fiya sakarci wallahi" Ruqayyah ta juya tana kallon Hassan, shima ita yake kallo, Hussain yace "ask him ooo Aunty, Mr Tsimilmila cewa yayi wai ba zasu je ba" Hassan yace "cewa nayi ba zamuje kasa biyar ba, me za'a je ayi a kasashe har biyar? Guda daya ko biyu in muka je sun ishe mu" Hussain ya kalli Aunty yace "kinji ba" Sannan ya juya gun Ruqayyah yace "convince your husband akan kuzo mu tafi tare, idan kika biye masa you are going to miss a lot." Ruqayyah tana jin tunda akayi auren yau ne Hussain yayi addressing dinta directly. Ta tura kujerar ta baya tana mikewa, abinda yasa Hassan shima mikewar yana tambayarta lafiya? Aunty ma tace "lafiya Ruqayyah? Ko abincin kirki baki ci ba" Tace "bana jin dadi ne sosai, wannan tuwon kamar bai karbi cikina ba. Zan dan koma gida, Aunty sai da safe" Aunty tace "ki je ki kwanta to, Allah ya baki lafiya, zan aiko miki da wani abu ki ci ko tuwon ne ba kya so". Hassan bai zauna ba ya bita da sauri a baya, amma saboda saurin da take yi da kyar ya kamota har ta kai kofar karamin gate din da ke tsakanin part din su dana aunty. Ya ruko hannunta "Hassana" ta juyo, tun daga idanuwan ta yasan ranta a bace yake yace "lafiya wai? Menene yake damun ki?" Ta juyo gaba daya tana rike kugu, tace "me akayi min? Okay yanzu na gane inda problem din yake" ta karbe hannunta tana kara sauri. Baya son ya ja hankalin ma'aikatan gidan zuwa kansu, dan haka sai ya rabu da ita ya koma cikin gida ya karasa cin abincin sa duk da hankalin sa yana kanta. Yana gamawa ya tashi ya tafi gida. A daki ya tarar da ita tana kwance da waya a hannunta. Ya zauna a kusa da kafafuwanta yana mammatsa mata su yace "ya jikin naki? Hope kinji dadi yanzu" ta ajiye wayar tana tashi zaune tace "naji dadi, dama tuwon ne naji ya tsaya min a kirji ya ki karasa wa" yace "akan maganar tafiya honeymoon ne? In kina so sai muje, bana son mu biyewa Hussain ne " Ta girgiza kai tace "I don't care about honeymoon, in baka so muje ba zamu je ba, duk abinda kake so shi zamuyi. What i care about is you mijina. Raina ya baci ne saboda naga ana neman a gaya maka magana a cikin mutane" ya dan bata rai yace "magana kuma? Wacce irin magana kike magana akai Precious?" Ta bude ido Tace "wai baka ji abinda Hussain ya gaya maka bane ba? Mr Tsimilmila fa yace maka, it is insulting ni a ganina" sai taga yayi murmushi sannan yayi dariya yace "my dear precious wife. Ba magana Hussain ya gaya min ba kinji? Wasa yake min, tun muna yara, tun primary school yake gaya min haka, mr Tsimilmila ko mr Careful duk haka yake ce min in yana so ya zolaye ni" ta daga kafada "okay, maybe dan ni macece shi yasa naji raina ya baci akan hakan, kasan mu mata muna da daukan karamin abu mu mayar dashi Babba. Dan haka ko da ace yana gaya maka haka a tsakanin ku bai kamata ya gaya maka a gaban mu ba, musamman a gaban matarsa, wannan ai sai ta zo ta raina ka tana yi maka wani kallo da daban, ni kuma ba zan iya tolerating wannan ba in tayi min na kyaleta bazan kyaleta ba in ta taba min mijina" Hassan yace "hold it! Fatima tana yi miki wani abu ne?" Ruqayyah ta koma ta kwanta sannan tace "bana son in fiya complain ne shi yasa ban taba gaya maka ba. But dama ya kake tunanin yar sarki zata yi treating yar mai gadin kamfani? Kamfanin ma kuma na mijinta. But ni ban damu ba ......." Ya kamo ta ya tayar da ita zaune, idanunsa suna nuna bacin ransa yace " yar sarki da yar mai gadi, dukkan ku matsayin ku daya a gidan nan, duk kan ku zaman aure kuke yi a gidan nan. Daga yanzu duk ranar da ta kara miki ko da kallon banza ne ki gaya min ni kuma zan nuna mata cewa she is no longer in her father's palace" Wannan littafi na siyarwa ne, in kina so ki yi min magana ta WhatsApp through this number 08067081020 Da fatan munsha ruwa lafiya, Allah ya karbi ibadun mu ameen. Not edited Ruqayyah tace "uhm uhm, ni bance kayi mata magana ba, kar taga kamar na hada ta da kai, ka barni da ita kawai ni ce dai dai yin ta va kai ba" sai kuma tayi murmushi tana ratayo hannunta a wuyansa "sorry mijina, na bata maka mood dinka" ya danyi mata murmushi yana shafa gefen fuskarta, kullum kyau take kara yi masa yace "kar ki kula ta kema kinji, ki fita daga harkarta kawai bana son wani abu ya hada ku saboda Hussain. Kinji? Promise me ba zaki kulata ba, one day zaiyi realizing abinda ya auro cos na gaya masa tun dadewa. I warn him about her" tayi ajjiyar zuciya tace "shikenan, duk abinda kace shi zanyi". Ya mike ya fita sai gashi da system dinsa ya dawo, ya zauna akan kujera tare da kiranta "Precious zo ki gani, kinga guraren da Hussain yake son muje. In kina so sai mu bi su mu tafi tare" ta taso ta zauna a gefen sa tana kwanto da kanta jikinsa, ta karanta sunayen guraren, ita ko sunan ma vata taba ji ba kuma bata san wadanne kasashe bane ba. But koma ina ne tunda har jirgi za'a shiga a bar kasar nan ai kuwa va za'a barta a baya ba. Amma sai ta boye excitement dinta tace "ba naji kace ba zamu je ba?" Yace "in kina so sai muje" tace "ina ganin muje din kawai, kar Hussain yaji babu dadi, kaga har ya kai kararka gurin Aunty" yace "ai ya riga yasan saboda menene. Ni bani da lifestyle irin nasa" sai kuma yayi murmushi yana kallon dan karamin bakinta yace "but since we are talking about a honeymoon tare da ke, I think I can make an exception" lips dinta suka bude tana murmushi, yayi murmushin shima yana kallon fuskarta, duk wata damuwarsa tana wucewa tare da murmushin ta. "I am going to enjoy this" ya fada yana jan fuskarta zuwa gare shi. A gurin Aunty Fatima tayi hirar darenta, Hussain yai ta zungurin ta akan su tashi su tafi tana share shi. Sai ya mike yana kirkirar hamma "na gaji sosai yau din nan. Aunty sai da safe zan tafi in kwanta" Aunty tace "Allah ya bamu alkhairi" ya kalli Fatima yace "sai da safe" ta dauke kanta tana kokarin rike dariya. Yana fita Aunty tace mata "tashi ki bi mijin ki, dan ba ta ido ce dashi ba zai iya sake dawowa ya sake yi mana wata sallamar" Dole Fatima ta mike Khadijah da Nafisa suka raka ta har kofar part dinta. Tana shiga ta amsa gaisuwar bayinta su biyar da suke da dakuna a karamin palonta na kasa, inda anan din ne dai kuma yan aiki da Aunty ta bata suke. Sai data dan yi hira dasu kadan sannan ta wuce kitchen. Yarinyar ta da taje da hakkin kula da kitchen ta bita a baya da sauri, suna shiga ta tambaye su abincin da suka dafa, ta gaya mata sai ta yamutsa fuska tana girgiza kai sannan ta bude freezer ta saka yarinyar ta dauko kaza, tace "ina irin pepper soup din nan da muke yi a gida mai dankali?" Yarinyar ymta gyada kai da sauri tace "shi za'a yi miki? Yanzu kuwa zanyi miki" Fatima tace "shi zakiyi, amma bani zaki yi wa ba in kin gama ki zuba a mazubi mai kyau ki je ki kaiwa Ruqayyah kice gashi in ji ni" da sauri ta amsa da "to ranki ya dade, an gama" daga nan Fatima batakuma tsayawa ba sai turakar mijinta. A dakinsa ta same shi daga shi sai towel yana ta zagaye da waya a hannu. Ya juyo yana kallomta sai ya yar da wayar ya rike kugu, ta jingina da jikin kofar tana murmushi yace "da baki taho ba ko, da zuwa zanyi in dauko ki aka tun daga gaban Aunty har nan" ya fada yana nuna kan gadon sa. Ta bata rai tana kallonsa tace "na yi fushi, shine kayi wankan ka ka rabu dani ko?" Ya tako zuwa gabanta yace "waya gaya miki nayi wanka? Ni na isa? Ta yaya zan wanke baya na?" Ta dan taba gashin kansa tana dubawa ko da ruwa a jiki, yayi dariya yace "banyi ba fa na gaya miki" tace "da kayi wanka ka barni ko, da yau ba zanyi wanka ba haka zan kwanta" ta fada cikin shagwaba. Ya jawo ta zuwa jikinsa, hannunsa a bayanta yana zuge zif din rigarta yace "na gaya miki ai, ba zan sake wanka ni kadai ba" ta fara dariya kuma sai ta dauke wuta saboda hannun sa da taji a cikin rigarta. Bayan Hassan ya gama nunawa Ruqayyah guraren da zasu je sai ta sake komawa dakinsa zai mayar da system dinsa, a lokacin ne ta jiyo maganar mutane daga waje, ta daga labuke ta leka window ta hango Fatima dasu Nafisa a kofar gidan Hussain, sai taga su Nafisa sun juya sun koma Fatima kuma ta shiga. Ta tabe baki, wayo gimbiyar ba ma zata iya tahowa ita kadai ba sai an take mata baya, amma ita sanda zata taho ai babu wanda ya rako ta duk kuwa da cewa ta nuna bata jin dadin jikinta. Ta fara kokarin cire kayanta da niyyar yin wanka, so take yau tayi amfani da rashin lafiyar da take ji ta gudu daga gadon Hassan. Tana fitowa daga wankan Hassan ya dawo dakin, shima har yayi wankan sa ya saka na bacci, ya bibta da kallo tana shafa mai a jikinta. Ya karaso yana karbar robar man. "Menene aiki na a gidan nan idan har na barki kina shafa mai da kanki" ta dan bata fuska "shafa mai ai ba aiki bane ba, zan iya da kaina" yace "akwai guraren da hannun ki ba zai kai ba. Ki kawo in shafa miki ko ina da ina, in tabbatar ko ina ya samu" ta lura da irin kallon da yake yi mata sai ta dan rike cikin ta kadan tana yamutsa fuska. Yace "ya dai? Ko cikin ne?" Tace "dazu ma sai da nayi amai, kuma yanzu yunwa nake ji. Ni tunda aiki kake nema ma da abinda zanci ka samo min" ya dan shafa kansa kadan yana kallon kirjinta "kuma shafa man fa?" Ta tura baki, ni ina jin yunwa ina zan damu da wani shafa mai" yayi ajjiyar zuciya "shikenan, let me go and get you something". Ta bishi da ido har ya fita, sannan tayi dan karamin tsaki. "Duk an bi an lugwuigwuicewa mutum jiki an bar ni da ciwon jiki". Key din mota Hassan ya dauka ya fita, bai ma san inda zai samu abinci ba, shi ba mutum ne da ya saba da cin abinci a waje ba dan haka bai san guraren cin abinci ba. Yana fita yarinyar Fatima tana kaiwa Ruqayyah abincin da ta aika mata dashi. Tata yarinyar ta karba sannan ta hau dashi sama saboda ta ga fitar Hassan, ta shiga dan madaidaicin dining area dinsu ta ajiye sannan taje tayi knocking a kofar Ruqayyah, sai data ji tayi magana sannan tace "sako ne gimbiya Fatima ta aiko miki dashi". Sai da Ruqayyah ta gama shafe shafen ta sannan ta saka doguwar rigar bacci wadda ta tsaya a gwuiwar ta mai siririn hannu ta fito tana daure kanta da ribbon, a ranta tana mitar tunda tazo gidan kullum sai ta wanke kanta gashi har gashinta ya fara lalacewa. Ta bude warmer din abincin a take taji yawunta ya tsinke, ta saka spoon ta dandana sai ta ja kujera ta zauna ta fara ci, sai data kusa koshi sannan ta tuna ta tura Hassan neman abinci. Ta dauko wayarta ta kira shi "kina ta jira na ko? Yanzu na kira Jabir yayi min kwatancen wani guri" tace "ka bar shima, har na dan dafa wani abu ma naci" yace "ayyah. Sorry Precious. Jikin yayi sauki kenan" tace "babu laifi" Sauran data rage yazo shima yaci "amma yayi dadi sosai, sharp sharp haka har kin gama? Kai amma yayi dadi sosai" tayi murmushi kawai. Ita bata taba ganin irin wannan abincin ba ma ballantana har ta iya. Sai kuma ya ajiye chokalin hannunsa yana kallonta, ta gane kallon dan haka ta mike zata gudu, ya jawo ta ta fado cinyarsa. Wannan dai wankan da bata son yi sai data yi shi. Washegari yace mata ta shirya zasu je ayi mata passport. Ta roke shi kuma zata je ta yiwa yan gidan su sallama. Ta shirya sosai tayi kyanta, shima haka, sannan suka fito tare suna hirar su yana yi mata alkawarin zai koya mata mota in sun dawo. "Duk san da zaki fita ko ina office ne sai kiyi tafiyar ki kawai" a kofar gidan ne taga abin mamakin da ya saka ta tsaya ta kasa motsi. Adam ne a tsaye a jikin mota yaa goge ta, ya dan rissina ya gaishe da Hassan sannan ya mika masa key din motar. Sai kuma ya juyo yana kallon Ruqayyah yace "Madam barka da fitowa" ta nuna shi da hannu "kai! Me kake yi anan?" Hassan ya juyo yana kallon ta yace "kin san shi ne?" Bata amsa ba ta sake cewa "me yake yi a gidan nan?" Yace "Sumayya bata gaya miki ba? Let's go, zan gaya miki a hanya" ta sake juyawa tana kallon Adam sai ya daga mata kafada sannan ya juya yayi tafiyar sa hannayensa a cikin aljihun wandon sa. Ta bude motar ta shiga shima ya zagaya ya shiga. Yana zama tun kafin ya tayar da motar tace "me Adam yake yi a gidan nan?" Yace "wai dama kin san shi ne? Da naga Sumayya tana biye miki shi na dauka baki san shi ba bata son ki sani" ta kara bata fuska tace "Sumayya? Wai kana nufin kasan shi tare da Sumayya?" Yace "a tare ma na gansu. Daga baya ba dauke shi aiki, yanzu driver ne shi a gidan nan. Yadda na fahimta kamar saurayin ta ne" ta sake cewa "Sumayyan? Lallai wannan yarinyar ta wuce duk inda nake tunani wallahi. Wato ashe Adam ne suke waya dashi, shine wanda ta karbi number dinsa a hannun ka kuka ce min wai abokin ka ne" yayi dariya, "I noticed bata son ki sani, I tot zata gaya miki kafin bikin mu shi yasa ban gaya miki ba" tace "ba zata gaya min ba ai. Ta san bata da gaskiya" ya dan bata rai yace "menene problem din? Ni a ganina kamar bashi da problem except that he was a christian sai ya musulunta, iyayensa har yanzu Christians ne. But character wise bana jin yana da aibu" Ruqayyah ta rike baki, tubabbe? Yanzu Sumayya a kan tubabbe zata kare? Amma ganin Hassan yana nuna hakan ba komai bane ba sai bata yi comment akan hakan ba. Amma sai tace "no you are wrong, yana pretending ne amma bana gari bane ba. A inda na sanshi, a inda muka fara haduwa dashi a motar sa ne taxi ya dauko mu daga school ni da Sumayya, and ge tried to touch me, a gaban Sumayyan. Shi yasa nayi mamaki da har zata kula shi har suke soyayya" Hassan yayi shiru maganar tana taba zuciyarsa, wato abinda ya dauko ya kawo musu gidan su kenan? Yace "tabbas biri yayi kama da mutum. Ranar dana fara ganin shi a kofar gidan ku ya faya min gaisawa yake so kuyi, amma sai yace da Sumayya zasu gaisa dan yasan in ya miki magana maba zaki kula shi ba. Wato wannan shine dalili" tace "tabbas. Yasan ni ba zan kuka mai dabi'a irin tasa ba". Kafin su je gidan Baba Hassan ya yanke hukuncin korar Adam. "Muna da yammata a gidan, he is a risk to them". Sai da suka je aka yiwa Ruqayyah passport aka gama sannan suka biya ta bakery suka yiwa su Inna siyayyar kayan kwalama, suka kuma siya musu fruits da drinks da yawa sannan ya kaita gida, bai shiga ba yace zaije unguwa shima sai ya dawo zai shiga, ta turo Zunnur ya kwashi kayan ya shigar musu dashi. Ita kanta sai data gansu sannan ta san tayi missing dinsu. Suma suna ta murnar ganinta kamar wadanda suka yi shekara basu ganta ba. Ta basu labarin tafiyar da zasuyi da Hassan da Hussain da Fatima, nan take su Zunnur suka fara jera mata list na kayan da zata siyo musu tsaraba. Anan suka ci abincin rana tare a palo, sai taji ta kasa cin abincin sosai duk kuwa da cewa babu laifi da kyansa duk da babu kaji amma akwai kifi da ganye a ciki. Amma kifin ne ma taji yana tayar mata da zuciya. Sai da suka shiga daki da Sumayya zasuyi sallah sannan ta tayar mata da zancen Adam "yanzu dama Sumayya ashe Adam ne kuke wayar nan dashi? Duk wannan murmushin da kike yi ashe Adam kike yiwa? Yanzu ki rasa wanda zaki yi soyayya dashi Sumayya duk mazan garin nan sai inyamuri? Ina samarin hausawa? Ina fulani? Ina bare bari ina shuwa ina duk sauran kabila masu mutunci amma duk basu yi miki ba sai inyamuri? Kema kanki kinsan Inna Ade da Baba ba zasu taba karbar wannan maganar ba" Sumayya da take tsaye da hijab a hannun ta tace "kin gama? To bara in tuna miki, ni ce nake sonsa ba ke ba, in auren nema ni zan aure shi ba ke ba, ina ruwanki?" Tace "da ruwana mana, ke fa yaruwa tace, shi kuma drivern miji na ne, ba kya ganin alakar tsakanin ku kamar disgrace ne a guri na. Dama can ana min kallon wulakanci ballantana kin kara zubar min da mutunci" Sumayya tace "okay shine problem dinki? To ni babu ruwa na da kasancewar sa drivern mijin ki wannan problem dinki ne" Ruqayyah tace "amma dai ai na tabbatar kina da problem da kasancewarsa tubabbe ko?" Sumayya ta juyo tana yi mata wani irin kallo, Ruqayyah tayi dariya "ohhh kar dai kice min duk murmushin da kuke yiwa juna bai gaya miki ko shi waye ba" Sumayya ta ajiye hijab din hannunta tace "don't ever call him that again" Ruqayyah tace "in na sake kuma fa? Me zaki yi min?" Sumayya tace "zan tabbatar baki sake yiwa wani rashin kunya ba" Inna ta bude dakin ta tsaya tana kallon su "ohh ni Sa'adatu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yanzu yaran nan kwanan ku nawa baku hadu ba, amma daga haduwarku har zaku yi fadan naku da kuka saba? Yanzu kuma me ya hada ku?" A tare suka ce "babu komai Inna". Not edited yau ma, sai an kara hakuri dani. Lol Inna Ade ta bisu da kallo daya bayan daya, tana lura da tension din dake tsakanin su, da kuma bacin ran dake fuskar Sumayya, tasan cewa koma menene to tabbas babban abu ne tunda har ya bata wa Sumayya rai dan ko mai fadan da zasuyi Ruqayyah ce mai fushi amma Sumayya takan mayar da maganar kamar wasa. Amma bata so ta matsa musu akan lallai sai taji, ta fi son ta barsu suyi sulhu a tsakanin su kamar yadda suka saba. Tace "to ku fito ga baban ku nan ya shigo ku gaishe shi" tana fita Sumayya ta saka hijab din ta ba tare data kula Ruqayyah ba ta fita, ita ma Ruqayyah tayi kwafa ta bita a baya. Tana zuwa ta tarar da baban a zaune da Sumayya a gaban sa tana bude ledar daya shigo da ita. "Baba naman kai ne wannan, ka ce gobe mu ci dadi kenan" yayi murmushi yace "sai ki dafa mana shi tun dare, da safe sai mu karya kumallo dashi. A zuba kayan kamshi da daddawa suji sosai" ta dauka ta fita dashi zuwa kitchen sannan Ruqayyah ta karaso ta durkusa ta gaishe da Baba. Da fara'a ya amsa mata. "Ya mutanen gidan naku? Kowa lafiya dai ko?" Tace "lafiya lau Baba. Kuma kuna lafiya ko?" Yace "alhamdulillah Hassana. Lafiya lau muke hankalin mu a kwance yake, banajin muna da wata matsala yanzu. Kinga abin hawan nan da kanin mijinki ya bani? Sulaiman ne yake jansa yanzu tunda suna hutu kuma kusan dashi muke cin abinci a gidan nan. Dan abinda zamu kara akai kadan ne, tunda mu ba yawa ne damu ba, kuma dama ba saba wa mukayi da kashe kudi masu yawa ba" Inna da take ajiye masa abinci tace "ni dai Baban biyu matsala ta daya ce a gidan nan" ya harde hannaye yace "matsalar me fa?" Sumayya ta shigo tana ajiye masa zobo mai sanyi a jug ta zuba masa a kofi. Inna Ade tace "duk jina nake yi babu dadi saboda rashin dalibai na da nake koyawa karatu. Na saba shekara da shekaru tun ina yarinya ta babu ranar da wani ba zai dauki karatu a gurina ba. Yanzu sai inji kamar ina asarar wani abu kullum" Baba yace "ai kuwa nima kadan ne banyi magana ba, musamman in yamma tayi sai inji gidan shiru babu dadi na saba da inji yara suna ta karatu" Ruqayyah tace "to ko a aika makota haka a gaya musu suke zuwa suna daukan karatun? Musamman in aka ce kyauta za'a ke yi musu zasu zo" Sumayya tace "anya kuwa? Bana jin zasu zo dan nan unguwar ba irin waccan bace ba, yaran su already suna da islamiyyar da suke zuwa, kunsan yanzu iyayen zamani sam sun daina kai yaran su makarantun allo sunfi gane wa da islamiyya" Inna tace "haka ne, acan na unguwar da muka taso ai duk daliban sun ragu, kuma abinda iyaye basa gane wa shine ba kowacce islamiyya ce ake iya baƙi sosai kamar yadda ake iya wa a makarantar allo ba, yaro zai iya baki, zai iya rubutu ta yadda karatunsa zai inganta sosai." .Sumayya tace "amma Inna vda Baba, idan zaku yadda akwai wani dalibi da nake so in kawo muku ya koyi karatu a gidan nan. In kun amince" iyayen suka kalli juna sannan suka kalle ta, Ruqayyah ma ita take kallo, Baba yace "wanene dalibin? A unguwar nan yake? Yaro ne?" tana wasa da carpet tace "wani ne Baba, ba yaro bane ba kuma ba a unguwar nan yake ba. Amma duk inda yaje zai zo ya dauki ilimi a gurinku in dai gar kun amince zaku koyar dashi" Inna tace "mai zai hana mu koyar dashi? In dai yana so kice masa yazo ya karbi ilimi, mu kullum muna maraba da mai neman ilimi a gidan nan" Baba da yake ta studying Sumayya yace "a ina yake? Waye shi? Kuma shi yace miki yana neman ilimi?" Sumayya ta dago tana kallon Ruqayyah tace "a gidan su Ruqayyah yake, drivern mijinta ne" Ruqayyah ta bude baki tace "unbelievable! This is soooo not going to happen. Ina kokarin yakice shi daga can gidan ke kuma kina kokarin lika shi a gidan iyaye na? Ba zai yiwu ba, kar ma ki saka a ranki" iyayen suka juya suna kallon ta, Sumayya tace "iyayenki ko iyayen mu? Yadda kike ji dasu nima haka, yadda ba zaki kawo abinda zai cutar dasu ba nima haka ......" Baba ya daga mata hannu "ya isa! Ya ishe ku! Menene wai? Waye kuke magana akansa?" Ruqayyah tayi saurin cewa "Baba wani inyamurin drivern taxi ne fa, wai dan abin kunya wai shi Sumayya take so, bayi kokarin hanata shine ta kakabawa Hassan shi ta matsa masa lallai sai daya dauke shi aiki kuma yanzu shine take so ta kawo shi gidan nan" Inna Ade ta bude ido tana salati "Sumayya? Me ya hada ki da inyamuri ni Sa'adatu?" Sumayya taji hawaye ya taru a idonta bata dauka inna zata yi reacting haka ba, Baba yace "dakata Sa'adatu. Hussaina gaya min menene hadin ki dashi" Ruqayyah tace "Baba saurayin ta ne, Hassan ma ya sani" ya daga mata hannu, "bake na tambaya ba Hassana. Ki barta ta gaya min ai tana da bakin ta itama" Sumayya tace "Baba Musulmi ne shi, iyayensa ba musulmai bane ba shine ya musulunta ya baro gidan su da kowa nasa a kano ya taho kaduna saboda kyamatarsa da ake yi da kuma iyayensa da suke so ya koma gurin su. Bai gayamin cikakken labarin ba amma na fahimci haka ne abinda ya faru. Bashi da ilimin addini sai wanda yake tsinta a titi, yana so ya koya amma yana gudun tsangwama da kyama daga mu musulmai, mu wadanda ya zabi addinin mu akan na iyayen sa. Ina so ne in taimaka masa ya samu a gurin mu. Muma kuma mu samu ladan ilmantar dashi. Kuma bani na hada shi da Hassan ba, a tare na gansu, Hassan kuma shi yayi niyyar daukansa aiki bani nace masa ya dauke shi ba" Ruqayyah tace "amma dai saurayin ki ne ko?" Sumayya tace "wannan kuma ba abinda ya shafe ki bane ba" Ruqayyah tace "abinda ya shafe ni ne mana, saboda ke yar uwa ta ce ba zan so abinda zai cutar dake ba. Adam kuma ba alkhairi bane ba a tare dake" Sumayya tace "ta ya akayi kika sani? Ji nake Allah shine kadai masanin gaibu ba Ruqayyah ba. Ko kuma kin fara duba ne ban sani ba?" Ruqayyah tace "ai ba sai nayi duba ba, ko makaho da baya gani in ya shafa ki ya shafa Adamu yasan baku dace ba. Driver ne fa" Inna tace "ya isa haka, maganar ta ishe ku haka" Baba yace "ai na dauka zasu tashi ne su rufe mu da duka, tunda mu bamu isa dan muna guri su kama kansu ba, bamu kai wannan matsayin ba. Ke Ruqayyah da kike cewa basu dace ba saboda shi driver ne ji nake ke naki uban dako yake yi sanda uwarki ta aure shi? Kuma gamu nan har yanzu muna zaune lafiya bamu taba fada ba bata taba yaji ba. Ko kin dauka kudi shine komai a rayuwa? Ko kin dauka dan kin auri Hassan mai kudi shikenan kin gama tsallake siradin rayuwa? Ko kin dauka in ta auri talaka shikenan rayuwarta ta tabe ta lalace? Bani da komai aka dauki uwarku aka bani auren ta dan haka nima ba zan taba hana wani auren yata ba saboda dalilin cewa shi talaka ne. In dai har yana da addini yana da asali yana da lafiya yana da kuma hanyar da zai ciyar da ita kuma yana sonta itama tana sonshi to kuwa zan ba shi auren ta" Ya juya kan Sumayya "ke kuma ki kiyaye ni ki fita daga idona, kin fara jaye-jayen mutane kuma ko? Wato shine wanda ranar nan ya dawo dake gidan nan da daddare ko? To zan hana ki zuwa gidan Hassan din sai inga inda zaku ke haduwa dashi. Kuma ki turo min shi kice yazo ya same ni a tambayi izini na indai har yana so ya nemi auren yata. Idan kuwa ba haka ba duk sanda na sake ganin ku tare ko kuma na ganki ko naji labarin kin shiga motarsa sai ranki ya baci" ya mike yana tsallake abincin sa. Sumayya tace "Baba maganar karatun fa? Yake zuwa gurinka kana koya masa?" Yayi shiru amma bai juyo ba, sai kuma yace "a cikin ilimi aka haife mu a cikin sa kuma muka tashi, babu abinda yake saka mu farin ciki kamar bayar da ilimi ga wanda bashi dashi. Ki ce masa yazo, zan bashi ilimi da yardar Allah". A ranar haka Ruqayyah ta bar gidan su zuciyarta babu dadi, duk da dai taga alamar hankalin Inna Ade bai kwanta da cewa Adam inyamuri ne kuma iyayensa ba musulmai bane ba amma kuma bata jin hakan zai kawo wani babban nakasu a cikin lamarin, dan tasan yadda suke da soft heat for addini da zarar sun ga yana da rikon adfini kuma sun fahimci yana son Sumayya sosai to babu abinda zai hana su aura masa ita. Ita kuma bakin cikinta shine auren Sumayya da Adam zai kara rage mata kima a gidan mijinta, "ai kanwar Ruqayyah ce matar Adamu drivern. Ta runtse idonta already har ta fara jin ciwon abin a ranta, Hassan da yake ta bata labarin shirye shiryen da suke yi na tafiya shida Hussain yace "lafiya? Ko dai jikin ne? Naga kamar ranki babu dadi ko yauma kukan barin gidan zakiyi?" Ta tura baki "ka daina tsokana ta da kukan nan wallahi, nima zan nemi wani abun in ke tsokanar ka dashi" yayi dariya "haba yarinya, ai na gaba yayi gaba na baya sai labari, babu wani abu da zaki samu wanda har zaki ke tsokana ta dashi" tace "zan tambayi Aunty, na san sanda kana yaro ba zaka rasa wani abu da kayi ba wanda baka so a gaya maka" daga nan kuma sai hira, ya fara bata labarin yarintar su da irin yadda suke da Hussain, irin rigingimun Hussain shi kuma yana kare masa. Har ya bata labarin farkon fara kasuwancin Hussain da kason sa na gadon babansu. Tace "yanzu da ka yadda kun bashi kudin gabaki daya da maybe companies din sunfi na yanzu yawa, kuma da naku ne gabaki daya ba nasa bane shi kadai" Hassan yace "maybe. Maybe kuma da kudin sun lalace gabaki daya da yanzu mun koma Gombe gurin dangi da yanzu daya daga cikin mu ya fara shaye shaye, mayb. Haka rayuwa take komai bashi da tabbas" ya juya kansa yace "kullum abinda Hussain yake fada kenan. And now, I am beginning to believe him. Yanzu misali Adam bai yi min kama da zaiyi abinda yayi ba, tunda muka rabu dazu nake tunanin sa a raina. I so much wanted to help him especially saboda his religious issue, bana so ya koma ruwa duk dabanga alamar hakan ba amma an ce iyayensa har yanzu basu yi giving up ba. But tunda har zai kasance danger to my family dole I will have to let him go, amma zanyi kokarin ganin na taimaka masa ya samu kyakkyawar rayuwa outside my family" Ruqayyah tace "kana da kirki sosai mijina, in kayi haka ka kyauta sosai sai dai ince Allah ya vada lada. Kuma ina rokon wata alfarma, tunda kana maganar family ne dan Allah ka hada da Sumayya a ciki. Kayi wa Baba magana yayi mata iyaka dashi. Sumayya tana da rawar kai, ina tsoron kar ya jata zuwa wani abu wanda ba dai dai ba" ya gyada kai yace "insha Allah. Sumayya ai kanwa tace nima, zanyi wa Baba magana zan kuma yi masa bayani yadda zai fahimta" taji dadi a rata dan tasan yadda Baba yake girmama Hassan. Ta dora hannunta akan nasa tace "thank you mijina. Allah ya bar mu tare" yace "ameen my precious wife" suka yi wa juna murmushi. Kwana biyu bayan nan Hassan ya gama yanke hukuncin abunda zaiyi akan maganar Adam. Sai ya dauko check yayi signing kudi masu kauri wadanda yasan zasu ishi adam ya kuma samun wani dakin na haya sannan kuma in ya chanchana su ishe shi ya kafa wani harkar samun kudin. Amma still baya jin dadi a ransa, sai dai wani barin na zuciyarsa yana gaya masa wannan shune dai dai, musamman in zuciyarsa ta hango masa Adam da Ruqayyah a mota yana kokarin tabata sai ya kara karfafa guiwarsa wajen ganin ya kori Adam din. Ya dauko wata ya kira shi. "Kazo ina neman ka" sai ya ajiye. Tunda Adam yaga kiran yaji gabansa ya fadi, kawai Ruqayyah ce ta fado masa a rai dan yaga irin kallon da tayi masa ranar ban uma yasan dole ba zata so zamansa a gidan ba matsayinsa na wanda yasan the bad side of her. Ya runtse idonsa yana karanta hasbiyallahu wa nieemal wakeel, yana neman Allah ya kawo masa dauki. Tabbas yana son wannan aikin nasa kuma yana jin dadin zama a wannan gidan yana kuma son mutanen gidan including Hassan, baya son rabuwa dashi, baya son abinda zai saka shi ya sake sabon zibi a rayuwa. To ina zai dosa ne ma? A haka ya tashi jiki ba kwari ya tafi part din Hassan, yayi sallama a bakin kofa yaji muryarsa a palo ya amsa masa yace "come in" ya shigo, half expecting to see Ruqayyah amma sai yaga Hassan din shi kadai a zaune, ya he gabansa ya zauna tare da gaishe shi, Hassan ya sake jinjina korar yaron a ransa amma dai sai ya daure ya mika masa takardar daya rubuta ta sallamar sa tare da check din kudin daya rubuta masa yace "am sorry Adam, na dauka cewa binciken da nayi a kanka ya bayyana min komai a game da kai amma ban sani ba ashe akwai wani hidden part da ban sani ba. Kayi hakuri Adam amma ba zamu iya cigaba da zama da kai a gidan nan ba" Adam ya dago kai yana kallonsa, maganar tana taba masa zuciya more than yadda yayi tunanin zata taba shi din" ya kalli takardar hannun Hassan sannan ya sake kallon Hassan din, mutumin kirki, shi kuwa menene wannan da Ruqayyah ta gaya masa da har zai kore shi irin haka? Bai karbi takardar ba yace "Ruqayyah ce ko? Me tace maka? Wanne sharri tayi min haka?" Hassan yace "matata ce fa, ka iya bakinka. Na tabbatar ai kasan abinda ya hada ku" Adam yace "nasan abinda ya hadamu amma a gurina abinda ya kamata ayi min kyauta ne ba wai a kore ni daga aiki a kansa ba" Hassan ya ajiye takardun a hannun kujerar da yake zaune yace "did you or didn't you try to touch her ranar nan a motar ka?" Adam ya runtse idonsa yana kokarin control zuciyarsa, wato sharrin da Ruqayyah tayi masa kenan ko? Sai da Hassan ya maimaita tambayar sannan Adam yace "yes, I acted kamar zan taba ta amma ban taba ta dinba. Nayi haka ne kuma saboda in koya mata darasi dan kada watarana ta hadu da wanda zaiyi abinda yafi taba ta" Hassan ya dan bata rai yace "ban gane ba, wani abin tayi da har zaka koya mata darasi ta wannan hanyar?" Adam ya mike tsaye yace "like you said, she is your wife and it is your job to find out who she really is" Hassan yaji zuciya ta taso masa amma sai ya danne ta tana gaya wa kansa cewa bacin ran korar da akayi masa ne ya saka Adam fadar haka, ya mika masa takardar yace "karbi" Adam ya girgiza i "I don't need it" Hassan ya mika masa check din "ga wannan ka fitar ka rage wani abu" ya sake girgiza kansa "I don't need it. Gwara ka ajiye abinka dan duk ranar da Ruqayyah ta gama da kai you are going to need it more than me" ya juya ya fita. Hassan ya mike kamar zai bishi sai ga Ruqayyah, bai ma san tana jin su ba tace "ka rabu dashi, ba girman ka bane ba, ba sa'an rigimar ka bane ba" yayi ajjiyar zuciya ya koma ya zauna itama ta zauna a hannunkujerar da yake kai tace "you did the right thing" ya lumshe idonsa ya bude yace "did I?" Sai ya mike ya hau sama. And for the first time in his life sai yaji insecurities, yaji he is no longer in control. Daga part din Hassan Adam dakin sa ya zarce, ta jawo akwatin sa ya fara jawo kayansa babu ko ninki yana zubawa a ciki. This is one of the times da wani voice a ransa yake gaya masa cewa ya koma gida, inda babu wanda zai kuma wulakanta shi ballantana yayi masa sharri, bai san takamaiman abinda Ruqayyah ta gayawa Hassan ba amma yasan sharri tayi masa, bakin cikinsa kuma shine Ruqayyah yaruwar Sumayya ce, wannan shine dalilin da yasa bai gaya wa Hassan actual a binda ya faru ba saboda kar ya bata wa Sumayya inya lalata auren yar uwarta, zata ga kuma kamar yaci amanar maganganun data gaya masa akan Ruqayyah. Zai tafi, yasan Allah yana tare dashi a duk inda zaije. Yayi ta zuba kaya har akwatin ya cika sannan ya jawo jaka yana tuna ranar da Hussain ya bashi jakar a cike da kayn sawa masu kyau, sai ya kara jin ransa ya baci, yaji mafarkinsa ya komawa karatu yana rushewa a gaban idonsa. Ruqayyah bata san me ta aikata ba amma yasan tabbas wata rana sai tayi dana sani, sai tayi nadama a ranar da nadama ba zata amfane ta da komai ba. Ya gama hada kayan sa kaf ya ajiye a gefe, baya jin zai sake kwana a gidan nan. Sai dai kuma yana gama shiryawa ana kiran sallar magrib, sai kawai ya shiga toilet ya yi alwala sannan ya fita zuwa masallacin gidan akayi sallah dashi. Yana fitowa yaga oga Hussain shima tare akayi sallar dashi, ya kura shi."Adam ka shirya gobe da sassafe zamu fita, akwai gurin da zamu je mai muhimmanci" Adam ya dan shafa kansa kadan yana jin rashin kyautawar sa ta niyyar tafiya ba tare daya gaywa Hussain ba, sai dai kuma baya son ya zamanto kamar ya hada tsakanin yan uwan ne yafi son sai ya tafi sannan Hussain ya sani. Ya dan shafa kansa bai ce komai ba sai Hussain ya kankance ido yana kallonsa "akwai problem ne?" Adam tayi saurin girgiza kai yace "babu komai oga Hussain. Allah ya kaimu goben" Hussain ya bishi da kallo har ya wuce sannan shima ya tafi, amma sai ya samu kansa da kasa shiga part dinsa sai ya sa aka kawo masa kujera ya zauna a waje. Bai jima da zama ba yaga shigowar taxi gidan, ya dauka baki sukayi sai yaga Adam ya fito daga bq da akwati a hannun sa ya kai motar ya koma ya dawo da jaka, sai ya mike ya bishi a baya zuwa wajen motar yace "are we going somewhere?" Adam yabdan tsorata dan bai san yana ganin sa ba, sai kuma ya shafa kansa yana kokarin ƙirƙirar murmushi amma yaƙi zuwa, Hussain ya sake cewa "ina zaka je da kaya haka Adam?" Adam ya fahimci an kama shi sannan yace "I got fired" mamaki ya bayyana a fuskar Hussain yace "what? Fired? By who? The last time I checked I am your boss, waye kuma ya kore ka bani ba?" Adam yace "it doesn't matter oga, just let me go, bana son ku yi jayayya a sanadiya ta. Kuma kona cigaba da zama ba zamu daidaita da ita ba" Hussain yace "Ita? Wacece ita? Fatima ko wa?" Adam yace "noo, Ruqayyah" Hussain yayi murmushin takaici yana bubbuga hannunsa a jikin motar, "Ruqayyah, Ruqayyah ce ta kore ka? Menene dalilin ta? Huh? Me kayi mata?" Adam yace "it doesn't matter oga" Hussain yace "no it does matter, kai ne na farko kuma bani da tabbas din kai zaka zamo na karshe, ba zan barta tana korar min ma'aikata ba anyhow. Zaka zauna har sai naji dalilin ta idan yayi min sannan zan barka ka tafi idan kuma bai yi min ba you are going no where. Kana ji na?" Adam yace "yes sir" Hussain yace "ka mayar da kayan ka zanje in ganta". Daga nan bai shiga part dinsa ba duk da yasan Fatima tana jiransa su ci abinci sai ya wuce part din Hassan. Ya zauna a palo ya kira shi a waya sai gasu sun sauko tare shida Ruqayyah. Ta gaishe shi ya amsa sannan ta zauna kusa da mijinta. Yace "Ruqayyah driver na Adam yace min kin kore shi. Menene dalilin ki?" Ta dafe kirji ta fito da ido "ni? Ni ina nagan shi ma ballantana in kore shi?" Hassan yace "nine na kore shi ba ita ba" Hussain ya gyara zamansa akan kujera yace "can I know why please?" Hassan yace da Ruqayyah tashi ki shiga ciki. Sannan ya juyo yayi wa Hussain bayanin abinda Ruqayyah ta gaya masa akan Adam, da kuma yadda suka yi da Adam din, ya kara da cewa "bai yi denying ba, ya dai yi wa maganar data fada kwaskwarima" Hussain yayi dariya yace "wannan shine dalilin? Saboda yayi kokarin taba matarka a tun kafin ka hadu da ita?" Hassan yace "ba da wannan nayi judging dinsa ba, wannan abinda ya faru tsakanin su ya nuna mana wata character dinsa wadda nayi judging dinsa da ita. Muna da kanne mata a gidan nan, zai iya daukan su zuwa unguwa wata rana. What if he tries them? Yana da kyau wanda zai iya amfani dashi a kansu" Hussain ya daga kafada yace "Ruqayyah bata barshi ya taba ta ba saboda tana da tarbiyya, haka kannen mu suma suna da tarbiyya. Besides, personal driver na ne, bashi da hadi da kanne na ballantana matarka" Hassan ya girgiza kai yana jin ramsa yana baci yace "na riga na kore shi, and that's final" Hussain ya mike yace "ni kuma na sake renewing contact dina dashi, he works for me and that's final" daga nan ya juya ya fita. Hassan yaji ransa ya baci sosai. Hussain ya jima bai bata masa rai irin na yau ba. Ruqayyah ta kuma saukowa ta zauna a kusa dashi tace "shikenan ai yanzu kaga ya zubar maka da girman ka a gurin Adamun, ya zubar maka da girman ka a gurin duk sauran ma'aikatan gidan nan dan nasan duk sai Adamu ya gaya musu abinda ya faru" Hassan ya mike yana jin haushin Hussain yana karuwa a ransa, sai kuma yaji haushin Ruqayyah data saka yaji haushin dan uwansa har haka. Ba tare daya ce mata komai ba ya hau sama ya shiga dakinsa ya rufe kofa. Da sassafe Hussain ya fito ya tarar Adam har ya fito da mota, ya bude masa baya ya shiga shi kuma ya shiga seat din driver ya kunna ta suka fita. Suna fita Hussain yace "tell me about Ruqayyah, me ya hada ka da ita? Da gaske kayi kokarin taba ta a motar ka" Adam yace "yes sir, amma nayi haka ne saboda in ja mata kunne akan abinda tayi" Hussain yace "menene abinda tayi din?" Adam ya girgiza kansa yace "matar yayanka ce oga, kuma yayar Sumayya" Hussain yayi murmushi yace "Sumayya ce tauraruwar ka kenan" Adam yayi murmushi shima bai ce komai ba. Hussain yace "this means kasan abubuwa da yawa akanta ko?" Adam yace "yes sir" Hussain yace "yanzu dai ba zaka gaya min ba kenan" Adam ya sake murmushi kawai. Hussain ya kwanta a corner din motar yana taping hannunsa a kan cinyarsa, fuskarta tana nuna zurfin tunani yace "tell me one thing, should I be worried about Ruqayyah?" Adam yayi jim sannan yace "you should be very worried sir" Wannan littafin na siyarwa ne, in kina so kiyi min magana through WhatsApp 08067081020 Har suka gama abinda zasu yi suka dawo gida Hussain hankalin sa yana kan maganar Adam. Yaron yaki ya gaya masa gaskiyar abindaya faru maybe daya gaya masa da yasan abinda ya kamata yayi. Shi tun farko hankalin sa bai kwanta da Ruqayyah ba, sai dai kuma a yanzu matar dan uwansa ce dan haka bibiyarta da kuma saka ido a kanta ba zai yiwa dan uwan nasa dadi ba. Dole sai yabi a hankali, dole sai ya nemi dabara yadda zai bullowa lamarin ta lumana ba tare daya taba zuciyar dan uwan sa ba. Suna dawowa gida ya wuce part din Aunty ya gaishe ta, a can ya tarar da Hassan shima ya shiga gaisheta, Hassan ya dauke kansa yayi kamar bai ga shigowar Hussain ba shi kuma sai ya kama tsokanar sa wai yaga alamar har wani tumbi ya fara ajiyewa saboda jin dadin amarci. "Me Ruqayyah take baka ne? Zan ke aiko da kwano na nima ana sammin ko na kara kumari da kwarjini" Hassan ya kalle shi kawai ya dauke kai, Aunty tace "an kuma kenan, me ya hada ku?" Hussain yace "aunty driver na ya kora, ni kuma nace na mayar dashi bakin aikinsa shine yake fushi" Aunty tace "akan driver kuma? Hassan me yayi maka da zafi haka da har zaka yi fushi da dan uwanka?" Hassan ya mike yana daukan wayarsa yace "ya wuce aunty, laifi na ne dama, drivern sa ne shi yake biyan sa albashi, motar sa ce gidan sa ne, I should have know my place, yanzu kuma na sani dan haka zanyi minding business dina" aunty ta rike baki tana salati yayin da Hassan din ya juya ya bar gidan. Tabbas yan biyun nata suna fada, amma mostly fadan nasu yafi yi mata kama da wasa dan akan silly silly things suke yin fadan,but na yau is different. Na yau ba wasa bane ba. Ta juya tana kallon Hussain tace "ka sallami drivern Hussain" ya girgiza kansa "Aunty ba zan iya ba. Kuma akwai dalilin da yasa ba zan iya din ba" ya dago yana murmushi yana kallonta. "Ki rabu dashi, yadda ya hau shi kadai haka zai sauko shi kadai" Daga gidan aunty hassan gidan sa ya zarce, a palo ya tarar da Ruqayyah a kwance a kujera da packet din chewing gum a gaban ta tana kuma cin wani, tayi masa murmushi amma sai ya wuce ta ba tare daya mayar mata ba, ta bi bayansa da harara sannan ta cigaba da wayarta. "Wallahi ina gaya muki Rukee sai kin waye, in ba haka ba kina ji kina gani za'a mayar dake tsumman goge kashi" tace "to Minal me zanyi? Kin ga fa su Fatima ce tasu, sam basa ma shigo bangare na sai gurinta, saboda zata dauko abin duniya ta basu ni kuma bani dashi" Minal tace "nema zakiyi kema ai, in baki dashi ai mijinki yan dashi shine zai baki ai. Ki san me yafi so ki ringa yi masa, ki kwantar da kanki sosai kar ki sake ki nuna masa wannan zafin ran naki, ba dai shine babba ba? In dai kin kama babban yayansu ai kin kama su gabaki dayan su babu wanda zai isa yayi miki musu. Kuma suma ki shiga cikin su, ki nuna musu soyayya kamar ruwa, ai da haka ake jan ra'ayin mutane, ke yanzu ko yar kissar nan ma ashe baki iya ba? Ai nuna musu zaki yi duniya babu yasu. Ki kafa gwamnatin ki sosai sannan ki fara diban rabonki. Dakin samu kin tara ki sayi gida, in kin kuma tarawa ki kuma siyan wani. A haka in rabuwa ma tazo Allah ya kiyaye kin ga kin samu madafa, tunda dai ba wani sonsa kike yi ba nasan auren ba wani guri zaije ba" Ruqayyah ta bata rai tace "wannan ai mugun fata ne, kuma ni yaushe nace miki bana sonsa?" Minal tace "ko kima sonsa ma na tabbatar kinfi son kudinsa a kansa, ko ba haka bane ba?" Ruqayyah ta jiya ido tace "to waye bayan san kudi? Annabi ma da kansa yace mu nemi tsari da talauci dan talauci musiba ne. Duk wanda yace baya son kudi to munafiki ne" suka yi dariya tare. Minal tace "yanzu yana ina?" Ruqayyah tace "yana dakinsa ina jin. Yanzu muna wayar nan ya shigo ya haye sama, kin san fushi yake yi akan maganar drivern nan" Minal tace "amma lallai Ruqayyah sai na kai ki ina jin gurin Aunty Hafsa ta wanke min ke, yanzu mijin naki yana fushi shine kika barshi ya tafi daki shi kadai? Mijin ma kuma mai kudi irin wannan? Ai ko da baki yi laifi ba zuwa zakiyi ki ba shi hakuri. Ki lallaba kayanki in ma yaga laifin ki ya dawo yana ganin laifin wanda ya fadi laifin ki". Da haka suka yi sallama Ruqayyah ta tashi ta hau saman itama, sai data fara shiga dakinta ta shafa turare saboda jin ta take yi kamar tana dan tashi kadan duk kuwa da cewa tayi wanka ta kuma saka turaruka iri iri, amma ta na jin kamar kalar turaren da ta saka ne bata so. Ta shiga dakinsa ta tarar ya fito daga wanka yana shafa mai, ta bi kirar jikinsa da kallo sannan ta danyi masa murmushi "yanzu ni shikenan sai mijina yazo ya wuce ni ko kula ni ba zaiyi ba, kawai sai yake fushi dani duk da bansan laifin da nayi masa ba?" Bai ce komai ba ya fara shafa man sa, ta zo gabansa ta tsaya tana shagwabe fuska kamar zata yi kuka. Ya zauna a bakin gado sai ta bishi ta zauna akan cinyarsa tana leka fuskarsa. "To ni ka kalle ni mana? Ni ka gaya min laifin da nayi maka" ta fada tana kakalo kuka. Ya dakata da abinda yake yi yana kallon ta sai ya fara tunanin laifin menene tayi masa wai? Menene laifinta a cikin maganar? Ai kamar ma ita akayi wa laifi ko? Sai ya kara hade fuska yace "shine kuma bayan kinga nayi fushi kika rabu dani ko?" Ta matso hawayenta "to ni ai bansan me zanyi maka ba, ka taho daga dakina ka dawo nan bayan tunda nazo a dakina muke kwana, ka saka ni na kasa bacci ina ta jin tsoro cikin dare" ta kara matse kwalla "kuma dazu ma da nayi maka murmushi baka rama min ba" ta turo baki. Ya bi bakin da kallo yana jin murmushi yana forming a fuskarsa, yarinya ce Ruqayyah in ma laifin tayi kamata yayi ya gaya mata abinda tayi din ballantana shi yanzu ya fahimci babu laifin da tayi in banda fadar laifin Hussain. Wannan ne laifinta. Kamata yayi ya gaya mata cewa baya so a fadi laifin Hussain ba wai yayi fushi da ita ba. Ya zagaye hannayensa a kugunta yana dora goshinsa akan nata, idonsa cikin idonta da yake cike da kwalla "am sorry Precious ki daina kuka kinji. Nine ko?" Ya kama kunnensa daya da hannu daya ya ja yace "wannan Hassan din baya jin magana tunda ya sa matarsa kuka" ta dan yi dariya kadan sai ya goge mata hawayenta yace "baki yi min laifin komai ba kinji? Raina ne kawai ya baci. Kema kiyi hakuri akan maganar drivern nan kinji? A hankali zanyi wa Hussain baya ni yadda zan gamsu da dalili na na korar sa" ta kwantar da kanta a wuyansa tana jin dadin kamshin shower gel din da yayi amfani da shi tace "ni na bar maganar ma ai, ina fata ne kawai kar Hussain ya gane when it is too late. Damuwa ta kawai ita ce kai mijina, ina tsoron kar drivern nan ya raina ka" Hassan ya danyi dariya yace "it is never going to happen kinji. Kar ki damu akan hakan" ya dagi fuskarta yana kallo yace "mutane suna tsokana ta wai ina kyallin angonci, they should come and see yadda fuskarki take haske kamar wata zahra" ta kwace fuskarta tana sake mayar da kanta cikin wuyansa, yace "daga ni to Madam in tashi in shirya" ta makale kafada "naki din. Kamshin ka dadi" ya kyalkyale da dariya yana komawa da baya yana kwanciya akan gadon, ta bi jikin sa ta kwanta itama, ya rufe ta da hannayensa yana sauke ajjiyar zuciya. Hussain daga gurin Aunty shima nasa part din ya tafi. Part din gimbiya ya zarce ya shiga har cikin Bedroom dinta amma bata nan, sai ya dauki waya ya kira ta, ta masa tace masa tana gym, ya fita ya tafi can. A can ya same ta ta kunna slow music kan treadmill tana tafiya da dan sauri kadan, bata ji shigowar saba, shi kuma yayi amfani da damar gurin tsayawa yana kare mata kallo a cikin gym wears dinta yana lura da jikinta yake motsawa tare da kowanne motsin ta, gashin ta data tubke guri daya yana kwance akan kafadarta guda daya, bakin ta yana motsawa a hankali tana bin wakar da take tashi a gurin. Ya danyi gyaran murya kadan sai ta juyo da sauri tana kallonsa, sai kuma tayi masa murmushi tayi amsa alamar ya taho da hannunta. Ya zo ya tsaya a gefenta yana kara bin jikinta da kallo, fuskarta ta nuna alamun jin kunyarsa, yace "what are you doing?" Tace "getting in shape for the honeymoon" yayi dariya, "wa ya gaya miki ana fafe gora ranar tafiya?" Ta bata rai "to ni bana son in munje kaga turawan da suka fini shape mai kyau" ya dora hannunsa akan plat cikin ta yace "ni ban taba ganin baturiyar da take da shape daya kai naki ba Fatima, in kuwa akwai to babu wadda nata ya wuce naki" ta harare shi tace "in akwai kuma fa" yayi dariya yace "bazan kalla ba, kona kalla ma ba zan gani ba" tayi masa murmushi tana slowing down har ta tsaya sannan ta kashe machine din, ya jawo towel a gefe yana goge mata jiki yace "daga gurin Aunty nake, Hassan fushi yake yi dani" ta juyo tana kallon sa tace "akan me?" Sai ya bata labarin abinda ya sani a game da Adam. Sai kawai yaga tayi dariya, ya bata rai "au dariya kike yi min ma ko?" Tace "ba kai kadai nake wa dariya ba, ku biyun nake yiwa dariya da har kuka biye wa Ruqayya. Ruqayyah fa? Ruqayyah ai yarinya ce, sa'ar Zulaihat ce fa aka ce. Yarinta ce take damunta bawani abu ba kuma shima kansa Adam din da kuke magana a kansa yaron ne shina. Ni kasan abinda bake tunanin ya hada su? Irin abin yaran nan ne ko shi yace yana sonta tayi turning dinsa down sai ya koma kan kanwarta ko kuma ita tace tana sonsa shi kuma yace kanwar yake so. Shine suke holding grudges. Amma hakan bai kai ta saka a kore shi ba. Abinda Ruqayyah take bukata yanzu shine guidance, tana bukatar wanda zai koya mata abubuwan da suka danganci zama da miji zama da mutane da sauransu. Wannan zai taimaka mata wajen girma. Shi yasa na sage akan muyi tafiyar nan tare saboda mu samu damar bonding ni da ita, I have so many things to teach her" ya bata rai yace "wato da ita za kiyi bonding ba dani ba ko?" Ta zagaye hannayenta a wuyansa tace "kai ai kaine ginshikin komai, kowa kaga na kula albarkacin ka yake ci" yayi murmushi yana kallon cikin idonta yace "you know I love you right?" Tayi murmushi "and I love you too". Tun ranar da Baba ya bawa Sumayya damar ta gaya wa Adam yake zuwa gidan daukan karatu ta kira shi a waya da niyyar sanar masa, sai dai abinda ya gaya mata akan ganinsa da Ruqayyah tayi da kuma abinda yake tunanin zata aikata ya saka taji jikinta yayi sanyi ta kasa gane a wanne bari na zuciyarta zata saka maganar, tasan kuma tsaf Ruqayyah zata iya sakawa a kori Adam daga aiki vabu abinda yayi mata zafi da future dinsa da hakan zaiyi destroying ko kuma tunanin inda zaije, in dai har birinta zai cika ita bata tunanin kowa. Washegari kuwa sai gashi ya kira ta yana gaya mata cewa an kore shi din, amma kuma an sake daukan sa wani aikin. Ya bata labarin yadda suka yi da Hassan da kuma yadda sukayi da Hussain, sai ta taya shi murna sosai musamman daya gaya mata Hussain ya sake bashi sabuwar offer of employment wadda albashin daya rubuta masa ya fi na wanda Hassan ya rubuta masa. Sai dai kuma a wani bangare na zuciyarta tana jin rashin dadin sabanin ra'ayin da aka samu a tsakanin tagwayen. Tasan irin shakuwar dake tsakanin tagwaye tunda ita ma sune, sai tayi addu'ar Allah ya tsayar haka. Daga nan kuma sai ta shigar masa da maganar Baba "albishirinka" yace "goro, Baba yace ya bani ke?" Tayi dariya "haka nan kawai sai Baba ya baka ni ba tare da ka tambaya ba? Sai kace wata riga?" yayi ajjiyar zuciya yace "haka ne, to meye albishir din?" Tace " nayi wa Baba maganar karatunka, ya amince kake zuwa gidan nan shi da kansa zai koya maka karatun Alkur'ani da duk littattafan addini" yace "WOW my Sweet Sumayya lallai wannan babban albishir ne kika yi min. Nagode Nagode" tace "nima na gode da ka amince cewa zaka ke zuwa ɗin" yace "kinga duk abinda ban gane ba sai in kira ki kizo ki kara min bayani ko?" Tace "no. Babu ruwana. Baba yayi fadan cewa nayi saurayi ban sanar a gida ba. Ruqayyah ce ta gaya masa abinda yake tsakanin mu" yace "to menene a tsakanin mu ɗin" tayi shiru, yace "ki fada min mana inji. So nake ki fada da bakin ki" tace "nima bansan sunan abin ba" yace "in gaya miki?" Tace "ina jin ka" yace "it is called Love. Ni dai abinda nake feeling a raina kenan, ina ji a zuciya ta cewa ke na ke so, da ke nake so inyi tafiya cikin rayuwar duniya har zuwa karshenta. Dake kuma nake so in tashi a can muyi rayuwa wadda bata da karshe a aljanna" tace "ameen, Allah ya amsa" yace "to ke kuma fa? Fada min menene a zuciyarki" ta danyi murmushi tana nuna jin kunya duk da ba tare suke ba tace "nima haka" yace "ke ma me?" Tace "duk abinda kace, nima irinsa" yayi dariya yana jin yana kara sonta a ransa yace "ki fito ki bude baki kiyi magana, in ba haka ba ba zan fahimta ba" tace "to zan gaya maka wata rana" yace "wacce rana kenan?" Tace "nima ban sani ba" yace "to shikenan, zanzo gobe sai ki gaya min a kunnuwa na inji" tace "hold it. Baba yace in ya kara gani na tare da kai sai ya zane ni" ya bude ido zuciyarsa tana bugawa yace "what? Saboda me?" Ta danyi dariya tace "yace sai ka nemi izninsa tukunna. Sai ya yarda ka ke ganina sannan zaka cigaba da gani na" ya yi ajjiyar zuciya yace "yau zan tashi da dare inyi sallah in nemi Allah ya dora ni akan sa. Kar ki damu, in na samu yadda nake so a gurinsa I will show you love the Igbo way". Kamar yadda Adam ya fada, ranar sai da yayi sallar dare saboda samun courage da kuma neman nasarar fuskantar Baba. Ya nemi iznin Hussain, wanda yake ta shirye shiryen washegari zasu tashi zuwa honeymoon dinsu sannan ya tafi. Ya fada wa Sumayya ta sanar wa Baba da zuwansa da haka shima Baban bai fita ba ya zauna ya jira shi. Da yaje ya aika aka fadi cewa yazo, Zunnur ya fito yace ya shigo, yana ganin sa ya fahimci kanin su Sumayya ne, dakin su ya kai shi sannan ya gaishe shi ya amsa yana tambayarsa sunansa. Sannan Zunnur ya koma cikin gida ya gaya wa Baba zuwan sa. Baba ya fito ya same shi a dakin. Adam ya mike tsaye saboda jin shigowar Baba, kansa a kasa, sai da Baban ya zauna sannan shima ya zauna a kasa, Baba ya miko mada hannu amma sai ya ki bashi nasa hannun sannan ya durkusa ya gaishe shi. Duk wannan yayi practicing tun safe, zamansa da hausawa ya saka ya koyi dabiun su da abinda yake dai dai da abinda yake akasin haka a gurin su. Baba yace "Husaina tace min kana so kayi karatu tare damu hakane?" Adam yace "haka ne Baba. Ina son yin karatu saboda ni... Saboda ni...." Baba yace "ta gaya min ko kai waye. Shi yasa nace kazo kayi karatun, zamu baka baka ilimi dai dai iyakacin abinda Allah ya bamu. Naji tace kana aiki, nima ina yi, dan haka zamu tsayar da lokaci wanda zamuke yin karatun" Adam yace "Nagode Baba, nagode sosai" Baba ya cigaba da kallon shi, yana nazarin sa yayin da shi kuma Adam din yake ta lissafin ta yadda zai shigo da maganar Sumayya. Yana kuma jin idon Baba akan sa kamar Baba yana jiran ya fadi wata magana. Sai yace "kuma Baba, dama Sumayya tace in gaya maka....." Baba yace " Sumayya ce tace ka gaya min ko kuma kai ne kake so ka gaya min?" Adam yayi saurin gyara wa. "Nine, ba Sumayya bace nine nake so in tambayeka dama in ka amince..... In ka yarda..... Ina so....dama Sumayya......" Baba yace "kana so zaka nemi auren Sumayya" Adam yace "eh Baba. Haka nake so in ce" Baba yace "me yasa kake neman auren Sumayya?" Adam bai yi in ina anan ba, yasan amsar direct ya fada "saboda ina son ta Baba" Baba yace "saboda me yasa kake sonta" anan sai Adam yayi murmushi, yasan wannan amsar itama. "Saboda kyawun halayyar ta Baba" ya tuno ranar daya fara haduwa da yan biyun a mota, yadda Ruqayyah tayi niyyar damfarar sa Naira hamsin har kuma tana yiwa Sumayyan warning akan kar ta tona mata asiri, tana so su had kansu suyi masa karya idan kuma yaki yarda suyi masa ihu su yi masa sharri, duk akan naira hamsin, amma Sumayya ta zabe shi, inyamurin direban taxi akan twin sister dinta. Ya sake maimaita wa "saboda kyawun halinta Baba" Baba yayi murmushi yace "kayi gaskiya, Sumayya tana da hali mai kyau, kuma ina son ya cigaba da zama a haka. Bana son ka zama dalilin chnazawar ta dai dai da kwayar zarra ne. Allah yayi muku albarka" Washegari da sassafe jirgi ya tashi da tagwayen maza tare da amaren su zuwa yawon cin amarcin su inda zasu fara ta Amalfi Coast, Italy. Kannen su gaba daya sunzo rakiyar su har Hassana da bata gidan, suna gab da tashi sai ga Adam ya kawo Sumayya, Sulaiman da Zunnur, suma sun zo yiwa yar uwarsu sallama. Kallo daya Ruqayyah tayi masa ta dauke kanta ta je gurin yan uwanta. Sai da jirginsu ya tashi sannan ya rakiyar tasu kowa ya kama gabansa. Wannan littafin na siyarwa ne, duk wadda take so tayi mini magana through WhatsApp 08067081020 A cikin wata guda da suka yi a honeymoon dinsu, abubuwa da dama sun faru, na farko dai a wannan lokacin ne idanun Ruqayyah suka bude, a wannan tafiyar ne tasan kiyasin how much Hussain is really worth. Kudin data kiyasta kuma ba kadan bane ba, ta lura da duk inda suka je da mutanen da suka hadu dasu da kuma irin girman da mutanen suke bashi. Sunansa yaje inda ita bata taba zato ba. Irin hotels din da suke zama kadai ko a cikin mutanen kasashen ba kowa ne yake zama a irin wadannan gurin ba. Irin guraren da zata iya kira da aljannar duniya dan ita in tana lissafin aljanna a ranta irin haka take hasko wa. Duk kuma kalar dakin da Hussain ya kama musu shida Fatima to irinsa yake kamawa Hassan da Ruqayyah, daga nan kuma kowa zai shiga harkokin sa babu wanda zai takurawa wani sai dare sannan zasu hadu suyi dinner tare suyi maganganun su shikenan kuma kowa sai ya kama gabansa. Amma duk da haka Fatima sai da tayi kokarin ganin ta cika alkawarin ta, kullum takan ware wasu lokuta a cikin lokutan mijinta ta zauna da Ruqayyah. Kullum da akwai darasin da suke yi, tun daga kan kwalliya, dresssing, passion trend, tafiya, zama, magana da kuma harkar kula da miji musamman a gado. Da farko Ruqayyah taki bata hadin kai, tana ganin kamar wata hanya ce ta dauko dan ta kaskantar da ita amma daga baya bayan tayi waya da Minal sai ta fahimci wannan hanya ce da zata shiga gari itama. Tasan Fatima karshe ce a abubuwa da dama, dan haka in ta kiya daga gare ta kuma ta yi koyi da ita to kuwa tabbas in vata zama kamarta ba to kuwa zata zama a kusa da ita. Dan haka ta zage dantse ta bude kunnuwanta da kwakwalwar ta take koyon duk abinda Fatima take koya mata sannan tana lura da ita ta a kwaikwayon yadda take duk wani abinta. Amma ko sau daya bata taba gayawa Hassan abinda suke yi tare da Fatima in suka kebe ba. Daya tambayeta sai tace "hira ce kawai muke yi. Kullum labarin gidan sarauta da sarakuna kamar bansan xewa daga can take ba, ni na gaji wallahi. Bana so dai in daina zuwa kar taga kamar wani abu ne" shima kuma Hassan bai hana ta ba, saboda a lokacin ne yake samun personal time dinsa ya dan gudanar da wasu ayyukan office din ko kuma suyi maganar aiki shi da Hussain, musamman maganar da ta shafi bikin bude kamfanin da za'a yi da zarar sun koma Nigeria. Amma duk wannan abin Ruqayyah tana lura kuma tana sane da Hussain, ta lura baya kula ta amma idanuwansa yana kan ta, kamar wanda yake studying dinta, kamar wanda yake so ya kama ta da wani laifi. Sai dai ko da wasa bata taba barinshi ya kama ta da laifin ba, in tana gabansa tana jin kamar dalibi marar gaskiyar da yake gaban principal. Wannan yasa bata enjoying dinner din da suke yi tare duk kuwa da cewa abinci ne irin wadanda bata taba tunanin akwai abinci irin su a duniya ba. Bayan sunyi sati daya a Amalfi coast, Italy, sai suka tafi.........daga nan sai Maldives sannan......... Anan ne Fatima tayi suggesting ahe a duba lafiyar Ruqayyah, dama tun zuwansu take lura da ita musamman wayan kwadayin da taga tana dashi, da farko ta dauka saboda bata saba wadannan ciye ciyen ba amma sai daga baya ta lura da cewa yafi karfin haka. Bata taba zama bata cin wani abu, jikinta ya murje sosai tayi kiba da fari, sannan kirjinta sun kara girma kamar ana hura musu aska. Girman kirjin ya saka Fatima tace akai ta asibiti. "Ruqayyah ki shirya gobe muje asibiti a duba ki" Ruqayyah ta bude ido kwakwalwar ta tana zama alert, wannan matar me take nufi? Tace "asibiti kuma? Dama an taba kai mai lafiya asibiti? Ni na dauka marar lafiya ne yake zuwa asibiti?" Fatima tayi murmushi tace " Mr Careful Hussain ya bi Hassan da Ruqayyah da kallo fuskarsa dauke da mixed emotions na shock da kuma tambayoyi kala-kala, har suka wuce shi suka fita suka bar kofa a bude, ya juya ya rufe kofar sannan ta juyo yana kallon fatima da take tsaye tana sheshshekar kuka. Tunda yake da ita tunda ya santa sama da shekaru hudu bai taba gani ko jinta tana kuka ba, bai san gaskiyar me ya faru a gurin ba amma sai yaji zuciyarsa tafi karkata gurin Fatima, yaji kukan ta har cikin ransa. Da sassarfa ya karasa inda take ta jawo ta jikinsa ya zagaye ta da hannayensa yana jin kukan ta yana karuwa. Bai lalllashe ta ba sai ya barta tayi kukan ta sosai ta gama. Tunda take a zata iya tuna ranar da aka yi mata tsawa ba, in ma an taba yi mata gaskiya bata sami ba ballantana hara akai ga daga mata hannu kuma akan laifin da bata san ta aikata ba. Ita da soyayya aka raine ta, im ma tayi laifi ana yi mata fada ne ta sigar lallashi da kuma nasiha, wani lokacin ma ba zata fahimci fada ake yi mata ba sai anyi mentioning laifin da tayi. Duka kuwa is totally out of the question, amma ita yau Hassan yake daga wa hannu, ta dauka marin ta zaiyi duk da cewa bata san me tayi ba, ya kuma kirawo ta da munafuka amma bata sam munafuncin me tayi masa ba, and above all yayi violating privacy dinta ya ganta a yana yin da in ba mijinta ba babu namijin da ya taba ganin ta haka a duniya, ko babanta, ko brothers din ta babu wanda yake shiga Bedroom dinta ballantana yaga tsiraicinta. Idan a waje ne kuwa ko gashin kanta babu wanda zai ce ya taba gani saboda yadda take adanawa da tattalin jikinta. Amma yau Hassan, yayan mijinta....... Ta sani cewa tun kafin ta auri Hussain ta san cewa Hassan baya sonta, but ta dauka ya fara saukowa tunda taga suna Magana yanzu sosai har suyi wasa da dariya, menene ya chanja lokaci daya? Ta tuna abinda yace mata "stay away from my wife" to me tayi wa wife din tasa? Ita dai tasan babu abinda tayi wa Ruqayyah sai alkhairi, babu wani abinda yaje zuciyarta a game da Ruqayyah sai alkhairi. Me yayi zafi haka shi ba wuta ba? Hussain ya fara jijjigata kamar baby yana cewa "shshsh, ya isa haka. Kar kiyi ciwon kai kuma Princess. Ya Isa haka" ta dago jajayen idanunta tana kallon sa tace "babu abinda nayi masa, wallahi babu abinda nayi masa" yayi kissing idanuwanta da goshinta yace "I know, I know. Zan same shi kinji? Zai gaya min dalilin da yasa yayi abinda yayi idan kuma bashi da dalili zan dauki mataki akansa. Ki daina kuka dan Allah" ta dan ture shi daga jikinta tana cewa "ka ga fa a yadda ya shigo ya ganni, in gurin matarsa yazo ba zai tsaya a pao ya aiko a kira ta ba? Ko kuma yayi mata waya ta fita? Ko kuma daya shigo ya ganni a haka ai sai ya koma ko? Sannan kuma ya ce min munafuka, munafuncin me nayi masa? Me nayi masa?" Ta sake saka kuka. Ya ji ransa ya kara baci, bai san me zai ce mata ya lallashe ta ba, bai san wanne kalami zaiyi amfani dasu wajen nuna mata bacin da ransa yayi akan abinda twin brother din nasa yayi ba. Sai kawai ya jawo ta ya hade bakin su guri daya, wannan ya tsayar da kukan da take yi sannan a hankali tayi relaxing jikinta ya saki. Ya sauke ta yabi ta siraran stairs din da zasu kai ka har kofar bedroom dinsa, ya kaita ya kwantar da ita a kan gado ya lullube ta sannan ya sauka da sauri, zuciyarsa tana kuna cike da kishin matarsa. Part din Hassan ya dosa da sauri, ya bude kofa kuma sai ya tsaya yana kallon hoton Hassan din da yake rataye a gurin, his twin brother, ya kuma tuna da maganar Annabi Muhammad SAW da yayi hani da yanke hukunci a yayin da mutum yake cikin fushi. Sai kawai ya saki kofar ya koma da baya. Dama fita zaiyi ya shiga da niyyar ya sanar da Fatima cewa zai fita, bai ma san suna tare da Ruqayyah ba balle ya saka ran ganin Hassan. Dan haka motarsa ya dosa ya tarar Adam har ya tayar da ita ya shiga suka fita. Hassan yana dauka Ruqayyah mota ya kaita, tana ta dan kuka kadan kadan hannunta akan marar ta ya zagaya ya kunna motar suka fita daga gidan "Allah sarki baby na, wallahi ina sonka kar ka tafi dan Allah" ya dan kara gudun motar yana jin ransa yana kara baci, in wani abi ya samu babyn sa ba yar sarkin kano ba ko yar sarkin macca ce Fatima sai jikinta ya gaya mata. Ta samu yarinya yar karama tana neman ta cuceta saboda bakin hali irin nata. Saboda tana mata bakin cikin ita ta samu ciki ita bata samu ba. Dama tun farko sai data gaya wa Hussain ya kuma ja masa kunne akan auren yarinyar nan saboda ta riga ta saba da samun duk abinda take nema and now she can't stand ganin Ruqayyah da ciki ita babu. Tun kafin auren yayi nisa har ta fara nuna hali. Suna zuwa asibiti aka karbi Ruqayyah aka shiga da ita, Hassan yana rike da hannun ta doctor ya gama duba ta yayi mata tambayoyi akan abinda take ji sai tace marar ta ce take mata ciwo, ya tambaye ta wanne irin ciwo sai tace "bazan iya yi maka bayani ba, ciwo dai sosai kamar zan mutu" doctor yayi murmushi yace "kar ki zama raguwa mana, in lokacin haihuwar yazo kuma ya za'a yi kenan? Kuma ba zaki mutu ba kinji?" Ya saka ta kwanta yayi mata scanning yana duba lafiyar cikin yace da Hassan "Babu wani problem da na gani gaskiya, duk babies din lafiya kalau suke mahaifar ma haka" Hassan yace "babies?" Doctor yace "eh fa, double gestation na gani. But zaku iya dawo wa after two weeks ku sake confirming, but am sure" Hassan ya bude baki cikin murna, yana jin duk fushin sa yana tafiya. Blessing often blessing. Allah ya na sonshi sosai babu abinda zaiyi masa sai godiya dan shi kam duk burikan sa na duniya suna ta cika. Doctor din ya tambayi abinda yasa Ruqayyah ciwon marar sai Hassan yayi masa bayani kamar yadda Ruqayyah ta gaya masa, likitan duk ya gama dube dubensa bai ga problem ba amma sai yace su koma gida on bed rest, ta daina yin zirga zirga sosai ko daukan abi mai nauyi ko makamancin haka, amma zata iya yin normal tafiya just dai kar ta gajiyar da jikin ta sosai. Daga nan ya rubuta mata pain reliever da prenatal vitamins ya sallame su. Har suka dawo gida still tana kwance tana dan complain dama sama, har dakinta Hassan ya kaita ya kirawo Sumayya da sai a lokacin ta tashi daga bacci ya gaya mata abinda ya faru sannan ya fita da kansa ya siyo mata drugs din. Hussain suna mota tare da Adam, abinda ya faru a gida yana ta yi masa yawo akai and even without bincike kawai zuciyarsa Ruqayyah take pointing at. Ita ce a tsakiya, duk abinda ya faru ta sani dan tana tare da Hassan kuma tana tare da Fatima. Ya tuno maganar da yaji Hassan ya fada wa Fatima "stay away from my wife" ya juya kansa, tabbas koma menene Ruqayyah is at the bottom of it. Yasan Hassan baya son Fatima amma bai kai har hakan ba, dan shi ya dauka ma wannan maganar ta wuce, to ko dai Ruqayyah tace da Hassan Fatima tayi mata wani abu ne? Gabansa ya fadi tunawa da yayi da cikin jikin Ruqayyah. Yes, that must be it. Cikin nan shi ya saka Hassan reacting the way he did. But me tace an yi mata? Dan shi har cikin zuciyarsa yasan Fatima ba zata yi harming pregnant woman intentionally ba, sai dai in a rashin sani. To ko sharri tayi mata? Ya kalli Adam yana tunanin sake gwada sa'ar sa ko zai samu wani bayani a gurin Adam din. Yace "Adam, kana tunanin Ruqayyah is capable of sharri?" Sai yaji Adam ya danyi dariya yace "ohh dariya ma na baka?" Adam ya yi shiru yana kallon reflection din Hussain ta center mirror, yana yinsa yana nuna cewa he is serious. Adam yayi gyaran murya yace "sorry sir" Hussain ya kuma cewa "amana zan karbi maganar ka, nayi maka alkawarin ko Hassan bazan gaya wa ba balle wani. Ina so inji ne kawai for the mental health of my family" Adam ya saje yin shiru yana jujjuya maganar a ransa, sannan yace "ranar da na fara haduwa da Ruqayyah da Sumayya sharri Ruqayyah tayi niyyar yi min. Ta dauka bana jin hausa sai take shiryawa yar uwarta plan din yadda zasu damfare ni naira hamsin. Yar uwarta taki yarda kuma ta nuna mata rashin dacewar hakan. Bata ci nasara ba, wannan yasa har yau take jin haushina duk da cewa banyi mata laifin komai ba. Dan haka your answer is yes, Ruqayyah is capable of hada sharri" Hussain yayi shiru yana tunani sannan yace "kana ganin zata iya hada sharrin da zai raba aure? Ko ya raba yan uwa?" Adam ya girgiza kansa yace "ban sani ba sir, but ni sharrin data yi niyyar hada min irin wanda defending on my destiny zai iya sawa mutanen unguwarsu suyi min duka, ko kuma su kona min mota, ko kuma su hada dani da motar su kona, kowanne daga cikin wadannan zaibiya jawo rikicin tsakanin kabila wanda zai iya jawo asarar rayuka da dukiyoyin daruruwan mutane. So ina ganin haddasa husuma a tsakanin mutum biyu ba wani abu bane a gurin ta". Hussain ya koma ya zauna sosai yana kokarin digesting yadda zai bullowa maganar amma sai yaji ya kasa, Hassan yayi masa shield, sannan ga cikin da yake jikin Ruqayyah. Sai yamma ya dawo gida, shima kuma ba wai dan ya gama abinda suke gabansa ba sai dan yana son yazo yaga halin da Fatima take ciki duk kuwa da cewa bayan kowacce awa yana kiranta, kuma daga muryar ta ya fahimci cewa ta daina kukan sai dai still akwai miki a ranta, mikin da dan uwansa ya dasa mata. A dining room din su ya sameta, ta cika masa shi da kayan abinci kamar yadda itama taci kwalliya kamar babu abinda ya faru. Ta tare shi tana zura hannunta cikin nasa. "Welcome Mi Amour. I made your favorite dises for you" kyawun fuskarta kadai ya saka shi yaji rabin damuwarsa ta tafi. Yayi murmushi yana kokarin kissing dinta, ta juya kanta gefe tana dariya "zaka bata min kyalliya ta tun kafin ka gama gani" ya juyo fuskar yana kare mata kallo sannan yace "na gama gani, can I kiss you now please?" Tayi dariya sannan ita tayi kissing dinsa da kanta, sai kuma ya hana ta janyewa sai da ya sake ta dan kansa sannan yace yana kallon ta idonsa cike da kaunarta "me yafi wannan dadi?" Tace "kiss din?" Yace "that included but ina nufin mutum ya dawo daga aiki ya tarar da kyakykyawar matar sa tayi masa kwalliya ta tare shi fuskarta da murmushi ga abinci ta jera masa, this is perfect, komai yayi dai dai my life is finally complete" ya bata fuska tace "complete? Tun yanzu? Tun kafin suzo?" Ya bude ido "ohhh kinga wannan kwalliyar taki ta saka ni na manta da babies dina ko? Wannan ko sunzo din in dai zaki cigaba da irin wannan kwalliyar to mantawa zan ke yi dasu" tace "hmmm really? Kai din kuwa? Duk ran da muka haihu a gidan nan ina jin ni kaina kaiyade min lokacin daukan jaririn zakayi" yace "kamar kin sani, dashi zan ke fita a mota, in bashi madara a office" suka yi dariya. Tace "to Baban baby, wanka ko abinci?" Yace "wanka ya kamata, but this food is so tempting har na kasa controlling appetite dina" ta sunkuyar ta dauko masa samosa guda daya a cikin wadanda ta jera da tayi arranging dinsu a shape din heart, a tsakiya kuma ta zuba tomato sauce din da tayi garnishing da vegetable. Ta saka masa a baki tace "kayi taste sai muje ayi wanka" ya cinye yace sai ta kara masa ta kara masa daya sannan ta jashi zuwa toilet yayi wanka, wanda rabi ita tayi masa dan cewa yake wai hannunsa baya kaiwa, anan aka karasa bata kwalliyar sannan suka fito suka shirya suka dawo gurin cin abinci, a nan kuma yayi ta hadama, komai sai yaci, ita dai tana tayi masa dariya tace idan tayi tumbi babu ruwanta. Sai da suka gama cin abincin su, wanda akan cinyarsa taci nata, sannan yayi mata magana "Princess kiyi hakuri kinji? Akan maganar Hassan kiyi hakuri. Ba halin sa bane ba treating mutane that way ballantana ke da kike matata. Naso inyi masa magana dazu amma kuma raina ya baci sosai bana son in dora akan barnar ya shi ya riga yayi, na fi son in zanyi masa magana ya kasance maslaha ce zamuyi" ta gyada kai kanta a kasa tace "kar ka damu, dama na riga nasan baya sona tun kafin auren mu, amma bansan kiyayyar sa gare ni ta kai haka ba. Ka rabu dashi kawai, yace in rabu da matarsa ni kuma na barta har abada. Ba zance babu ni babu ita ba saboda matar dan uwanka ce ita sai dai bazan kuma nemanta ba sai dai in ita ce ta neme ni, bazan shiga gurin su ba but she is welcome to come here anytime. Shi kuma ka gaya masa kar ya kuma trying daga min hannu dan wata rana hannun sa zai iya gocewa ya same ni. Duk kanin mu kuma bama fatan haka ta kasance" Hussain ya girgiza kansa "I promise you Princess, hakan ba zata taba kasancewa ba kinji?" Ta danyi murmushi. Yace "zan je in ganshi in an jima. We will talk things out kinji?" Ta kuma gyada kai. Hussain baya son ya shiga gidan Hassan suyi magana a can saboda bai son Ruqayyah ta shiga maganar su, ba kuma yaso taji mai zaice. Yasan kuma ko ya kira shi nashi part din ba zai zo ba dan haka ya tafi palon Aunty ya zauna, yasan duk dare yana shiga ya gaishe ta su danyi shawarwarin su. Dan haka ya kwanta akan kujera ya rufe idonsa yana jiransa. Ganin haka yasa aunty ta kora yammatan ta sama ita kuma ta zauna suna hirar dinner din da yake shiryawa ta family and friends na taya shi murnar bude sabon kamfanin sa, a lokacin yake gaya mata motocin da ya siya wa Fatima tare da Ruqayyah. Tayi murna kuma tayi masa godiya. Sunanan a zaune Hassan ya shigo, ya kalli Hussain ya dauke kai ya gaishe da Aunty suka dan yi magana kadan sai ta tashi ta basu guri dan ta fahimci akwai dan tension a tsakanin su. Tunda basu saka ta a ciki ba kuma bata son ta saka kanta gwara ta barsu su warware kayan su. Tana tafiya Hussain yace "me Fatima tayi maka?" Hassan yace "wrong question, abinda ys kamata ka tambaya shine 'me Fatima tayi wa Ruqayyah?" Hussain "as far as I know babu abinda tayi mata face kokarin taimaka mata" Hassan yace "okay haka ta gaya maka? Taimakon nata ne ya kai Ruqayyah asibiti? Ko baka san cewa she is now under bed rest ba? A saboda Fatima?" Hussain ya bata rai yace "ban gane ba, dukanta tace tayi ko me?" Hassan ya bashi labarin duk abinda Ruqayyah ta gaya masa, har da shawarar da tace Fatima ta bata na cewa ta zubar da ciki bata isa haihuwa ba. Hussain ya bude baki yana mamaki. Ko a mafarki bai taba tsammanin Ruqayyah zata iya wannan mugun sharrin ba kamar yadda bai taba tsammanin Hassan zai yarda da wannan maganar ba. Tabbas da gaskiyar Adam da yace "he should be very worried" . Yace "and you believe that bro?" Hassan ya daga kafada yace "what's there not to believe? Kar ka manta Ruqayyah yarinya ce karama, only 18 years, bata san komai akan abinda duniya take ciki, I doubt it in tasan ma ana shan pills dan a zubar da ciki kamar yadda I so much don't believe zata iya hada magana irin wannan ta fada" Hussain ya dafe kansa yace "and you believe Fatima zata iya yin abinda Ruqayyah tace tayi mata?" Hassan yace "sosai. Ta fita shekaru ta fita wayewa ta fita wayo da sanin duniya" Hussain ya gara zamansa yace "I dated Fatima for full four years kafin in aure ta, nasan 90 percent na halayen ta kuma nasan duk abinda ka fada na cewa tana da shekaru, wayewa, ilimi, wayo, dabara duk yes tana da su amma kuma hakan bai sa ta zama mai munanan halayya ba. Fatima tana da kirki fiye da yadda kake tunani, yes, tana da flows dinta kamar kowa amma ba zata taba cutar da mace mai ciki ba, ko a mafarki ba zata aikata haka ba. Duk da nasan ka sani, maybe wani abu ne yaje rufe maka idonka baka gani amma nasan kasan cewa age is just a number, halayyar mutum bata da alaka da shekarun sa ko background dinsa ko ilimin sa ko yanayin tarbiyyar da aka bashi, wadannan duk suna shaping halayyar mutum ne amma ainahin halayyar da ita ake haifar kowa. Shi yasa tagwaye suke tashi da mabanbantan halayya duk kuwa da cewa sun samu komai iri daya. Bance Ruqayyah bata da hali mai kyau ba amma ina tuna maka da cewa baka san ko da kashi daya cikin uku na halayyar ta ba saboda wata uku da sanin ta ka aure ta kuma ba.... " Hassan ya daga masa hannu, "nasan cewa baka son Ruqayya, tunda ka fada min haka tun farko amma kar kayi kokarin tura laifi kanta saboda kana son ka kare matarka. Idan baka manta ba in tuna maka, Ruqayyah saved my life. Ta saka rayuwarta a danger saboda tana son ta kubutar da rayuwar wanda bata taba gani ba a lokacin daga danger. She could have lost her life a ranar nan saboda ni. Wannan kadai shi ya nuna min kyawun halayyar ta. Babu wanda zai aikata abinda ta aikata sai mutumin da bashi da son kansa, mutum wanda duniya bata gabansa, mutum mai kyakykyawar zuciya wanda ba zai iya harming wani ba, mutum.... " Hussain ya daga masa hannu yace "kasan wani abu bro? Tun ranar da Allah ya dawo min da kai gida ranar daka bani labarin taimakon da Ruqayyah tayi maka da kuma hanyar da tabi gurin taimaka maka din, tun a lokacin naji bata kwanta min arai ba amma ban taba sanin dalilin da yasa hakan ba sai yanzu da kake wannan maganar. Yes she helped you and I am very grateful for that. Amma inda matsalar take shine hanyar da tabi wajen taimaka maka din. In reality, idan yarinya karama kamarta wadda bata san komai na duniya ba mai bla bla bla ta shiga toilet taga mutum cikin jini yana neman taimako abinda ya kamata tayi shine taje ta taso mahaifanta ta nuna musu shi su taimaka masa, but Ruqayyah sai ta kama katanga ta haura ta fita. Taje ta yaudari manyan matured top criminals har ta dalilin ta police suka kama su. Ta haka musu rami suka rufta ciki. If her brain can work out that plan a cikin mintuna kadan Allah ne kadai yasan abinda brain dinta take shirya mata a yanzu. In dai zata iya yaudarar criminals kamar wadannan in minutes ka gaya min dalilin da zai sa ba zata iya yaudarar ka ba. Ka gaya min idan har sun fada ramin data gina a cikin mintuna kai me yasa ba zaka iya fadawa ramin da take kwana take wuni tana gina maka ba?" Hassan ya mike "ya ishe ka, ya ishe ka. My God, matata fa kake magana akai. Uwar yaya na" Hussain ya mike yace "wannan shine abinda yake rufe maka ido, ina fatan kuma ba zai makantar da kai nan gaba ba" Hassan yayi hanyar fita da sauri, Hussain yace "hey bro" ya juyo yana kallon sa bai ce komai ba, Hussain yace "Please in ka hadu da Mr Careful ka gaya masa ina bukatar taimakon sa. Cos you are no longer him". *My Better Half* A palo Hassan ya tarar da Ruqayyah da Sumayya suna ta hira suna dariya, suka yi masa sannu da zuwa ya amsa musu sama sama ya wuce dakinsa, Ruqayyah tabi bayansa da kallo sannan ta tabe baki tace "mutum yayi ta kumbura shi kadai kamar ana saka masa yeast? Ni wannan ban san wanne irin mutum Allah ya hada ni dashi ba" Sumayya tace "ko ma dai menene dai mijinki ne shi, kuma mijinki ya dawo gida kamata yayi ki tashi ki bishi in yaso ko ma menene yake damunsa sai kiji daga can" Ruqayyah tace "ke ni fa ba zan iya da wannan fushin nasa ba, sai inje inyi ta faman lallashinsa kamar wani jariri bayan ni ba dani yayi fadan sa ba?" Ta koma ta kwanta tace "shi da dan uwansa ne, babu ruwana ni ai ance babu kyau shiga tsakanin yan uwa. Suje su kare kalau" Sumayya ta zauna tana nazarinta tace "ya akayi kika san shida dan uwansa ne? Anya kuwa kina da gaskiya Rukayya? An ya bake kika hada su ba?" Ruqayyah ta ajiye wayar hannun ta tace "ke fa kullum kamar ba nice yar uwarki ba ba kya kyautata min zato wallahi. Ni bani na hada su ba, ni ba dashi naso in hada su ba Allah ne kawai ya kawo Hussain din ya shiga maganar". Sumayya tayi shiru tana nazarin ta sannan tace "gaya min gaskiya Ruqayyah, menene gaskiyar abinda ya faru dazu?" Ruqayyah ta kalle ta, tunda suke bata taba boye mata kaifi idan tayi duk kuwa da tasan cewa zata yi mata fada amma yanzu anya zata gaya mata plans dinta, na farko tasan ba zata goyi bayanta ba kamar kullum, na biyu kuma yanzu bata yarda da amanar ta ba musamman saboda wannan inyamurin drivern da take ta faman yashe wa baki a waya. She can't risk her telling him. Ta girgiza kanta "in na gaya miki gaskiya ma babu abinda zaki yi akai" Sumayya tace "dazu babu abinda ya same ki kika saka Hassan ya kai ki asibiti ko?" Ruqayyah ta juya idonta tace "idan na yi miki bayani ma ba zaki gane ba, Please just let me be okay? Ni da wadannan tambayoyin naki ma gwara inje in rarrashi jariri na" ta mike da sauri ta tafi dakin Hassan. Sumayya tace "ki bi a hankali fa, ko kin manta doctor yace ki ke bi a hankali?" Ruqayyah ta juyo ta harare ta ta shige, Sumayya ta sauke ajjiyar zuciya a hankali tace "what are you up to sister?" Hassan yana shiga dakinsa kofar valcony ya bude ya shiga, ya ja kujera ya zauna ya harde hannayensa a kirjinsa yana ta lissafin maganganun Hussain a ransa, amma kuma ya kasa fitar da ma'anar maganar, ya kasa tsayawa a guri daya yayi tunanin. Idan kwakwalwar sa ta jashi nan sai kuma zuciyarsa ta jashi can. A haka yaji shigowar Ruqayyah dakinsa. Ta tsaya tana kallon kofar valcony din tasan yana can amma ita har ga Allah bata son zuwa can din saboda bata son ganin gidan Hussain. Ita in tana cikin gidan mantawa take yi da gidan Hussain saboda babu ta inda take hango shi sai ta valcony din nan kuma in taga gidan ji take yi ya tsaya mata a ranta har hana ta numfashi mai kyau yake yi dan haka bata son ma ganin sa, at least not now, sai ranar da ganin gidan zai faranta mata ba wai bakanta mata ba. Sai ranar da zata kira gidan da nata. Ta shiga tana lura da yadda bai dago kai ya kalle ta ba. Sai ta jawo kujerar da take facing dinsa wadda kuma ta juya wa gidan Hussain baya ta zauna tana kallon fuskarsa tana lura da irin tension din da take hangowa a can. Tace "Allah dai yasa lafiya kake mijina. Naga kamar baka jin dadi" ya dan kalle ta kadan yana tuno maganganun Hussain a kanta yace "lafiya ta kalau Precious, ki je kuyi hirar ku, in kina jin bacci kije kiyi kwanciyar ki ni anan zan kwana yau" ta marairaice fuska "haba dan Allah, bayan kasan bani da lafiya, bayan kasan bazan iya kwanciya babu kai ba shine zaka ce anan zaka kwana?" Ya dora hannunsa akan nata yace "kiyi hakuri Precious. Ina so zan danyi tunani ne shi yasa bana son yawan magana kinji" ta bishi da kallo a ranta tana dariyar yadda yake mata magana kamar wata karamar yarinya, sai ta gyara zamanta "ni ba zan tafi ba, nayi alkawarin ba zan ke yi maka magana ba amma nafi son in zauna a kusa da kai, kaji? Please? Nafi son kayi ta kallona kana tunanin" yaso yayi mata murmushi amma sai ya kasa, ransa yayi baccin da ba zai iya murmushi ba, ya gyara kujerar sa yadda zai ke kallon gefe sannan yayi shiru, yana ta so ya hada kyakykyawar innocent fuskar Ruqayyah da maganganun Hussain amma ya kasa, sam ba suyi kama da juna ba musamman in aka yi la'akari da gidan da Ruqayyah ta fito. Gidan malamai ne gidan tarbiyya ne. Da safe Sumayya ce ta hada musu breakfast din soyayyen dankali da wainar kwai sai tea. Amma sai taki zama a dining din ta debi nata ta tafi daki tana ci a can. Hassan da Ruqayyah kuma suka zauna suna cin nasu anan. Suna cikin ci ya dago kai unexpected yace mata "Fatima ta musa duk abinda kika ce tayi miki, tace da Hussain sharri kika yi mata" ya tsaya yana nazarin expression din fuskarta, ga mamakin sa sai ya ga babu wani shock ko wani tsoro mai nuna rashin gaskiya kawai blank ne. Yace "me zaki ce akan hakan?" Sai yaga tayi murmushi sannan tace "wai kana expecting zata karbi laifinta ne? Dama ai cewa zata yi bata yi ba, duk hanyar da zata bi ta tsara mijinta ya yarda da ita ta kuma nuna masa nice marar gaskiya dole sai ta bita. Amma ni ina ruwana in ma mijinta bai yarda da ni ba? Ni dai tunda nawa mijin ya yarda dani ai shikenan ko?" Ta karasa tana kamo hannunsa ta rike tare da langwabe kai, yayi mata murmushi, exactly, tabbas duk abinda Hussain ya fada Fatima ce ta tsara masa, zata iya tsara masa komai dan ta kare kanta. To ma banda abin Hussain ribar me Ruqayyah zata samu idan ta yi wa Fatima sharri? It is not as if miji daya suke aure ballantana ace kishiyoyin juna ne. Sai kuma wani bari na zuciyarsa ya tambaye shi "to menene ribar da Fatima zata samu idan ta zubar da cikin Ruqayyah?" Yana gama wa ya shirya ya fita sai Ruqayyah ta shirya itama tace Sumayya tazo ta raka ta gidan Hussain. Sumayya ta shirya ta bita dama tana ta so ta shiga gidan ta kashe kwarkwatar idonta. Ai kuwa tun daga bakin kofa ta fara kashe wa "wow. Ruqayyah haka gidan nan ya hadu dama?" Ruqayyah tayi tsaki, komai akayi da jaki sai yaci kara dama. Bata jira yan aikin gidan sunyi mata iso ba kawai ta kama hawan bene zuwa sama. Sai data je karshen benen kuma sannan ta rasa inda zata yi taga wadansu benayen daya yayi hagu daya yayi dama ga kuma kofofi nan ta ko ina. Dole ta nemo yarinya daya ta tambayeta inda matar gidan take, sai yarinyar ta bude mata wani guri tace su shiga bara ta kirawo ta. Suna shiga suka ga daki ne kawai da akayi masa ado da tsarin sarauta, in kana ciki zaka ke jinka kamar a gidan wani sarkin kake, anyi masa irin zanen jikin bangon nan na sarakuna sannan babu kujeru a ciki sai tintin da aka jejjera a ko ina ga lallausan carpet ga kuma lallausan kamshi. Suka zauna suna bin dakin da kallo Ruqayyah tana aiyanawa a ranta cewa ko gidan ya zama nata ba zata chanza tsarin wannan dakin ba. Sun jima a zaune, sannan fatima ta shigo amma bata kofar da suka shigo ba, su bama su lura da kofa a gurin data shigo ba sai kawai ganin ta suka yi ta shigo din. Fuskarta babu yabo babu fallasa ta zauna a saman tintin daya ta harde kafafuwan wa irin na sarakuna sannan tace "sannun ku da zuwa, kuyi min uzuri na barku kuna jira, ina wasu aiyuka ne a lokacin da kuka shigo" Ruqayyah ta tabe baki, wai aiyuka, ko ita tunda tazo gidan hatta Bedroom dinta share mata ake yi, na Hassan kuwa bata san sanda ake gyara shi ba kuma bata san waye yake gyara shi ba kawai dai tana ganinsa a gyare. Sai ta kirkiro murmushi tace "babu komai wallahi, dama zuwa nayi in baki hakuri akan abinda ya faru jiya, dan nima kaina ba zan iya cewa mai ya faru ba wallahi. Dama tun da akayi bikin mu yana ta cewa baya son in ke shiga harkar ki waye da waye, to amma ban dauka zai dauki zafi irin haka ba. Na san baki ji dadin abinda yayi miki ba amma dan Allah ina bada hakuri on his behalf" Fatima ta bita da kallo tana studying dinta, ta saba da zama da mutane iri iri a gidan su tana kuma kyautatawa kowa zato har sai ya bata rawar sa da tsalle sannan sai tayi placing dinsa a inda ya dace, and right now ta yi placing Ruqayyah a dai dai inda ya dace da ita. Sai kuma tayi murmushi tace "it is okay, ya wuce. Zaman Hussain nake yi bana Hassan ba, duk wani abinda Hassan zaiyi tunani a kaina duk kuma wani abinda Hassan zai yarda dashi a kaina bazan damu ba saboda nasan Hussain ya sanni ya kuma san halina, yasan abinda zanyi da kuma abinda ba zanyi ba. Wannan shine abinda na damu dashi kuma na riga na samu, saura Hassan. Ba zance ba damu da abinda Hassan yake tunani a kaina ba saboda shi Hassan wani sashi ne mai girma na jikin Hussain kamar yadda Hussain yake sashe mai girma na jikina. Ba'a taba raba hanta da jini. Da sannu shima Hassan zai fahimci wacece ni kuma lamura zasu dai-dai ta a tsakanin mu. Kamar yadda na gaya wa Hussain, you are always welcome zaki iya shigowa gidan nan a duk sanda kika ga dama kuma kiyi abinda kike so ki ci arziki ki bar arziki a inda yake. Nima kuma duk sanda kike bukatar wani abu a gurina Please don't hesitate to ask, tun daga kudi zuwa shawara zuwa a listening ear duk zan baki". Ta mike tsaye tana duba kyakykyawan agogon hannun ta tace "lokacin shiga kitchen yayi, kuyi min afuwa" har ta kai bakin kofar data shigo sai ta juyo tace "Sumayya in kin je gida ki gaishe min da Inna da sauran yan uwa" Sumayya tayi mata murmushi tace "zasu ji. Insha Allah". Kafin Sumayya ta sauko daga dogon benen har Ruqayyah ta kai gida, bata taba jin ranta ya baci irin na yau ba. A palon ta Sumayya ta same ta tana ta safa da marwa, Sumayya tace "kiyi hankali fa, kin manta likita ya baki bedrest?" Ta jefa mata harara tare da tsaki a hade, tana jin kamar ta hada da ita da likitan da kuma Fatima ta babbaka musu wuta. Ta fara masifa "kutumar...ni matar nan zata zauna ta gaya wa maganganu har haka? Lallai ba ta san wacece Rukee ba tana kuma gab da sani wallahi. Wallahi sai tayi nadamar hada hanya dani" Sumayya ta saki baki "magana? Wacce magana ta gaya miki? Ni dai banji ba, kinje kin bata hakuri kuma tace ta yafe miki shine maganar? Ko kuma cewa da tayi mijin rabin jikinta ne shine maganar" Ruqayyah ta juyo kanta "baki ki ta ba? Baki ji ba wai har da wani cewa inje inci arziki in bar arziki a inda yake?" Sumayya tayi dariya tace "salon magana ne fa kawai. To in kika je gidan aka baki wani abu ba arziki aka baki ba? Kuma dole dai in kika fito kin bar sauran arziki a gidan. Ni banga abin tada jijiyoyin wuya a nan ba" Ruqayyah ta rike kugu tace "dama ai ke ba zaki gani ba, tunda ke din ba sosai idanuwan ki da kunnuwan ki suke miki amfani ba. Ki kuwa naji kuma na gani kuma sai na rama. Tana so ta nuna min wato ban isa in hada ta da mijin ta ba ko? To mu zuba mu gani. Ita ce a tsaye a gurin da nake bukatar tsayawa dan haka dole ko tana so ko bata so dole ta matsa ta bani guri" Sumayya tace "guri? Wanne gurin kike magana akai Ruqayyah? Ji nake ke da ita kowa mijinsa daban, dan haka gurin tsayuwar ku daban daban menene zaki yi a gurinta bayan kema ganaki gurin nan?" Ruqayyah ta bata rai, bata so tayi subutar baki ba a gaban Sumayya dan tasan ko bata tona mata asiri ba zata bita da nasiha ne, ta juya tana cewa "wannan kuma ba abinda ya shafe ki bane ba" ta wuce sama ta shige dakinta. Sumayya ta zauna akan kujera tana tattauna maganganun Ruqayyah a zuciyarta. "Ya Salam! Me yarinyar nan take so ta zama ne mai kuma take shirin aikatawa? Ko ma menene akan Fatima ne, that nice Fatima. Ai gwara ka zalunci wanda ya ke azzalumi ne akan ka zalunci wanda ya ke kyautata maka. Ta tashi ita ma ta tafi saman gurin Ruqayyah ta tarar da ita zaune a bakin gado har yanzu tana huci, ta zauna tace "ko ma menene kike shirin yi ina tuna miki da cewa ba dai dai bane ba, matar nan bata yi miki komai ba. In fact tare ma kika gansu ke ce outsider a cikin su. In baki gode taimakon su a gare ki ba kuwa ai bai kamata ki zamar musu kadangaren bakin tulu ba" Ruqayyah tace "taimako? Kina nufin taimako na suka yi da Hassan ya aure ni? Ni dana taimake shi na tseratar dashi daga mutuwa kuma fa?" Sumayya tayi murmushi tace "in kin manta Ruqayya bara in tuna miki, shi rai Allah ne yake hurawa mutum shi kuma shi yake cire shi a lokacin da ya ga dama. Da ace Allah yayi Hassan zai mutu a ranar da babu ta hanyar da zaki bi ki cece shi. Shin bakya tunanin cewa Allah ya hada ku a ranar ne a matsayin jarabawar ki? Dan yaga yadda zaki yi da haduwar taku? Think about this please" ta mike ta sauka kasa ta fara hada yan kayanta da tazo dasu. Ba zata iya cigaba da zama a gidan nan ba kar bakin cikin yar uwarta yayi mata illa amma kuma tana tsoron tafiya ta bar ta ita kadai tare da wannan muguwar zuciyar tata mai kissima mata abubuwa iri-iri. Sai ta ajiye jakar tata a kasa ta zauna a bakin ttare da yin tagumi tace "oh Allah. What should I do?" Kamar amsar tambayar ta sai gashi Hassan ya dawo yana ce mata ya hadu da Baba a office ya kuma roke shi a kan ya bar ta ta dan yi musu kwana biyu saboda Ruqayyah bata jin dadi "duk da cewa da akwai masu aiki a gidan, amma nata ke bukatar wani a kusa da ita sosai yadda ko wani abun zai faru za'a yu saurin taimaka mata" sai Sumayya taji tausayin sa, shi duk ya damu Ruqayyah bata da lafiya bayan kuma karya take yi lafiyar ta kalau, shi duk ya damu da Ruqayyah bayan Ruqayyah bata damu dashi ba ko kadan, ita wani abin take hange na daban. A hankali sati ya zagayo, babu wanda ya kuma neman wani a tsakanin Ruqayyah da Fatima, Hassan da Hussain kuma babu wanda ya kuma tayar da maganar sun maida hankalin su kan bikin bude kamfanin da yake gaban su, har ranar tazo kuma aka gabatar da bikin successfully komai ya tafi yadda aka shirya, sannan da daddare suka gabatar da dinner ga friends and families dinsu. Da farko Hussain yayi niyyar samun gurin da za'a yi a can, amma sai Fatima ta bashi shawarar tunda dai dinner din ta mutum dari ce very close friends da kuma immediate family members why not a mayar da ita informal kawai ayi a gida? Akwai filin da swimming pool dinsu yake, katon guri ne zai dauki duk mutanen. Shawarar tayi masa dan haka aka kira masu decoration suka zo suka gyara gurin aka saka kujeru da tables aka shirya komai tun two days to day din. Abinci kuma tace tunda informal dinner za'a yi home cooked meals zai fi dacewa akan ayo order. Amma duk da haka sai da tayo hayar wasu chefs gida biyu sannan suka hadu har ita da kuma kannen ta biyu da suka zo ga kuma su Khadijah duk da suka shigo ga kuma yan aiki nata dana Aunty duk aka hadu a katon kitchen dinta ana tayi. A soya wancan a dafa wannan a yanka wancan. Nafisa ce ta fita zuwa part din Hassan ta gaya wa Ruqayyah cewa ana aikin abinci fa a gidan Hussain ko zata leka ayi da ita? Tana dariya tace "duk da dai nasan yadda kike ta laulayin nan ba wani taya mu aikin da zaki yi amma dai ai ayi hira a dan wataya ko?" Ruqayyah ta tabe baki tace "kin san bana son warin kitchen, kar in je in tayi muku amai in haramta muku abincin ku gwara inyi zamana kawai" sai Sumayya taji babu dadi dan haka ta dauko mayafin ta tabi Nafisa suka tafi. Suna zuwa Khadijah tace "bata taho ba ko? Dama ai nasan ba zuwa zata yi ba kawai dan kar in sagar muku da gwuiwa ne yasa banyi magana ba amma gashi nan kun tabbatar ai yanzu" ashe da rabon tata guiwar ce zata sace dan tana rufe baki sai ga Ruqayyah ta shigo. Nafisa tace "a'a, aman fa?" Tace "yaya zanyi? Abinda ya zama dole ai dole ne ayi shi. Wannan abu ai namu ne maganin a kwabe mu bare ma suka zo ballantana mu?" Sai duk suka yi shiru suna kallon kallo ban basu san waye bare a gurin ba. A lokacin Sumayya ta koyi abubuwa da yawa ta fannin girki, musamman a gurin Fatima da kuma chefs din da aka gayyato sai ta fahimci cewa Ruqayyah sam bata da wayo kuma bata san ma me take so ba, da ta kwantar da kai da ta samu abubuwa da yawa daga gurin Fatima. Amma zafin ran ta da girman kanta ba zai barta ba. Idan wani ya shigo gurin yaga yadda Ruqayyah ta kame tana bada order sai ka dauka itace matar gidan, sai ka lura sosai sannan zaka fahimci cewa kare ne da fatar kura dan kayan girkin da ake amfani dasu ma kansu ba sanin su tayi ba ballantana abinda za'a yi dasu. Sai wajen karfe biyar na yamma suka kammala komai, suka jera komai a gurin da za'a yi taron sannan kowa ya tafi da niyyar shiryawa kafin baki su fara zuwa. Ruqayyah tana komawa gida tayi wanka sai ta saka rigar zaman gida tayi sallah tayi kwanciyar ta tana chatting dinta a waya da sababbin kawayenta. Har Sumayya ta shirya ta fito ita kuwa tana kwance, tayi mata magana sai tace ta tafi kawai zasu taho tare da Hassan. Wannan yasa tayi tafiyar ta ta rabu da ita. A kofar shiga gurin ta ga Adam, and he took her breath away, all suit up kamar shine oga Hussain, ya tsaya yana kallon yadda tayi kyau itama cikin doguwar rigar lace dinkin bubu da akayi wa landing da red aka kuma yi mata ado da red flowers a gaban rigar, ta daura dankalin lace din sannan ta yafa red mayafi, fuskarta babu kwalliya sosai amma kyawun da tayi ba kadan bane ba. Ya mika mata hannu, smiling from ear to ear, ta makale kafada yayi dariya yace "a kwana a tashi dai" tace "Allah ya kaimu lokacin, but not now" sai ya dauka wayarsa yace "wannan kwalliyar sai nayi mata hoto dan in ajiye a gefen pillow na" tayi murmushi tana rufe fuskar ta da hannunta shi kuma yana yi mata hoto, sai daya gama tace "ban dauka zan ganka anan ba, tunda naji ance taron is for specific people" ya juya suka jera yana cewa "oga Hussain ne ya banj wadannan kayan yace in shirya in shigo tare dashi saboda in kula da manyan bakin sa, in tabbatar sun zama fully satisfied" tace "ohh kace taron ma yana hannunka gaba ki daya, to plate dina yana gurinka" yace "ke xe ta farko da zaki samu komai da kike bukata, ko oga Hussain ne sai dai ya jira ki gama tukunna" suka yi dariya a tare. Ruqayyah tana kwance har Hassan ya shigo a gaggauce, ya kalle ta yace "what? Wai baki shirya ba? Ki yi sauri Please ki shirya zan shiga in shirya nima, saboda ina so duk wanda zai zo ya tarar dani a gurin" kafin ta bashi amsa har ya shige dakinsa. Ta koma tayi kwanciyar ta har ya gama shiryawa ya fito yana daura agogon hannu, sai kawai ya tsaya yana kallon ta, fuskar sa tana nuna bacin ransa. "Hassana wai baki tashi ba har yanzu?" Ta tashi zaune tana yamutsa fuska tace "ni fa ba zan je ba mijina, kayi tafiyar ka kawai" sai yana yin fuskarsa ya chanja daga bacin rai zuwa concern yace "ba kya jin dadine precious? Ko jikin ne?" Ya zauna a kusa da ita sai ta fara kakaro kuka, hawaye yana zuba tace "ni ba zanje a wulakanta ni a cikin mutane ba. Ranar nan na shiga gidan da niyyar mu dai-dai ta tsakanin mu tunda naga ka damu da abinda ya faru, naga yadda kake son dan uwanka shine naje dan muyi sulhu, amma matar nan sai ta rufe idonta ta ci min mutunci wai naje cin arziki" ta kara sautin kukanta "babu irin zagin da bata yi min ba wai kar ta sake ganin kafata a gidan ta, harda cewa wai a gidan su banfi darajar bayin su ba, ita tafi ƙarfin tayi harka dani....." Ya daga mata hannu idanunsa sun kada sunyi ja. "Kinga dakata Hassana. Please not now. Kinga baki ne damu suna waje suna jiran mu ki tashi muje ki shirya mu fita" ta bishi da kallo tana sheshshekar kuka, bata ji dadin yadda yayi reacting ba, tace "yanzu kafi son inje a wulakanta ni a gaban jama'a? Kafi son a gaban kowa da kowa ta nuna wa duniya cewa ba mijina ne mai kudin ba mijinta ne?" Ya mike tsaye yace "she wouldn't dare. Kuma ita bata isa ta hanaki shiga gidan Hussain ba saboda ba gidanta bane ba. Babu yadda zata yi ta rabaki da ni kamar yadda babu yadda zata yi ta raba ni da Hussain. Ki tashi muje in gani in zata yi wani abu akai. I want to see her try something in yaso ni kuma sai in koya mata hankali" a dolen ta ta tashi ta shirya, amma ita ba haka taso ba, so tayi ace ya hau sosai ya tafi gurin taron ya ciwa Fatima mutunci ita kuma ta rama, sai taga Hussain wa zai zaba a cikin su. Ta riga ta san amsar, wannan shi yasa take son ta hada rigima a tsakanin su. Haka suka shiga cikin gurin taron hand in hand, suka tsaya a bakin kofar shiga gurin tare da Hussain da Fatima, duk wanda yazo zasu tarye shi su gaisa yayi musu murna sannan ya shiga ciki, a haka har bakin suka gama zuwa sannan ya kuma kama hannunta suka shiga ciki suka sake zagaya bakin sannan suka he suka zauna aka fara gabatar da taro. A lokacin ne yan gidan su Ruqayyah suka shigo gurin, ita kanta bata san Hassan ya gayyace su ba kuma bata nemi ya gaiyace sun ba saboda tana ganin kamar zasu ata mata show ne, kamar zata wulakanta a idon mutane irin wadannan in aka ga Baba da Inna Ade a matsayin iyayenta. Tana ganin su ta fara sunne sunne wai kar su ganta ai kuwa Hassan ya kama hannunta har gaban su ya hada su sannan ya koma gurin sauran bakin sa. Yana ta zuba ido yaga Fatima ko wani wanda ya danganci Fatima yazo yayi wa Ruqayyah ko wanda ya danganci Ruqayyah wulakanci amma bai gani ba, sai ma yaga Fatima ta nuna wa Hussain su Baba sannan sun tafi takanas sunje sun gaishe su. Taron ya kayatar sosai dan ko dinner din bikin su bata yi wannan haduwar ba musanman saboda wannan din babu mutane sosai kamar wancan. Sumayya tana ganin du Inna ta bar gefen Adam da da suke tare ta taho gurinsu tana nuna jin dadin ta, a ganin ta honouring dinsu Hassan yayi daya gayyace su zuwa inda sai wane da wane ne a gurin. Ita ta kai su gurin Aunty suka gaisa sannan ta samar musu gurin zama yayin da Adam ya tabbatar sun sami komai da suke bukata. Yayin da Ruqayyah tayi excusing kanta ta koma side din Hassan, ta gaya masa cewa bata son ta barshi shi kadai shi yasa ta dawo "naga kowa yaci kwalliya, har da yammata, bana son idon mijina yayi yawo nafi son ya tsaya a kaina ni kadai" yayi mata murmushi "ke ma kin sani ai ba sai na gaya miki ba, idanun Hassan will always be on Hassana". Komai ya faru a gurin sai Ruqayyah tayi wa Hassan complain cewa anyi wani abu ba dai dai ba. Ko tace mutane sunfi kula Hussain a kansa, ko tace wata tayi mata kallon banza dan ba Fatima bace ba ko kuma tace wani ya tafi bai yi masa sallama ba amma yayi wa Hussain. Hassan Allah Allah yake yi a tashi saboda zuciyarsa gaba ki daya ta dawo makwogwaron sa. Ana fara tafiya bayan ya tabbatar personal abokan sa sun tafi kuma su Baba sun tafi sai ya jata suka koma gida. Suna shiga gidan tayi tsaki tace "ni duk raina a bace yake wallahi, ni ban ga dalilin ma da yasa za'a yi taron nan a gidan Hussain ba bayan kuma kaine babba, ko da yake dole ayi acan dan a nuna wa mutane babban gida" ya kama hannun ta bai ce mata komai ba suka hau sama. Suka wuce dakinsa tana cewa "dakina zan je in dan huta kadan naji wannan zirga-zirga ta sa mara ta ta fara ciwo" yayi murmushi yace "wani abu nake so in nuna miki a dakina" suna shiga ya wuce da ita valcony dinsa ya tsayar da ita ya tsaya a bayan ta yana nuna mata Hussain a tsaye a kofar gidan sa suna sallama da wasu baki daya rako yace "kin ga wancan mutumin?" Ta dauke kanta tace "wai Hussain kake nuna min? Na gane shi mana, ko dan show up dinsa da san a sani ai dole in gane shi ko a ina na hango shi" ya runtse ido ya bude ya sake juya mata fuskarta side din Hussain yace "ki kalle shi sosai" tayi kokarin dauke kanta amma ya rike fuskar a guri daya ya hana ta juyawa yace "ina so ki kalle shi sosai ki gane shi sosai. Sunansa Hussain Aminu Abdullahi, and he is my better half, kaf duniyar nan babu wani mutum ko wani abu da nake so sama dashi. In nace kowa ina nufin kowa, har wannan" ya fada yana dora hannun sa akan marar ta. "Har wadannan zan iya giving dinsu up for him. For a smile on his face. So I want you to listen to me carefully. Daga yau, bana son ki sake fada min wata magana marar dadi a kansa. Bana so, bana son ji. Am I clear?" *New Chapter* Ji tayi jikinta gabaki daya ya zama kamar na statue, ko hannunta ta kasa motsala, ko idonta ta kasa kiftawa, zata iya rantsewa cewa hatta zuciyarta ta tsaya da aikin buga jini zuwa sassan jikinta. Ya kawo bakinsa dai dai kunnenta ya sake cewa cikin rada but harshly "is that clear?" Automatically kanta ya motsa da alamar eh, ya saki fuskarta sannan ya dan buga kafadar ta yace "good girl" sai kuma yayi kissing side din fuskarta ya juya ya bar gurin. Ta lushe idonta tana jin zuciyarta data zama kankara tana narkewa ruwan yana taruwa a idanunta, ko a cikin mafarkinta bata taba tsammanin Hassan zai iya furta mata wadannan kalaman ba, yes, ta san he is strong tun sanda yana zuwa zance gurin ta amma bayan bikinsu, irin son da taga yana yi mata ta dauka ta kama shi a hannun ta, musamman a matsayin da take rike dashi na wadda tayi saving life dinsa ga kuma darajar abinda yake cikin ta. Ta dauka zai zabe ta akan kowa a duniya, amma shine ya furta mata to her face cewa yafi son Hussain akan komai, harda jaddada mata in yace komai yana nufin komai, harda misaltawa da abinda yake cikinta, wato ita bama ta cikin layin da Hussain din yake ciki. Taji duk wani shiri nata yana kuncewa yana bin iska. Taji duk wani abu da yake kanta yana sauka kasa yana farfashewa. Taji duniya tayi mata zafi. Tasa hannu da niyyar goge hawayen da ya taru a idonta amma sai taji babu. Ita dama haka take in ranta ya baci irin wannan to sai hawaye yaki zubar mata sai dai tayi na zuci. Sai dai in kukan karya ne to da gudu hawayen yake zuwa. Ta mayar da hankalinta zuwa inda Hassan yayi forcing dinta ta kalla taga Hussain har yanzu yana tsaye hannunsa rike dana Fatima suna dariya tare da wasu mutanen su da suka rako waje. Ta dauke kanta gefe tare da rufe idonta, mafarkin ta yana karasa tarwatsewa a gaban idanun ta. Ta saki karfen, sannan ta juya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta shiga dakin Hassan, ta jiyo motsin sa a toilet daga dukkan alama wanka yake yi sai ta fita daga dakin a ranta tana cewa "yau sai dai kaje ka rungume Hussain ba dai ni ba" Dakin ta ta tafi ta yar da jakar hannunta a kasa sannan ta haye kan gado tana kara jin zafin maganganun Hassan a ranta. Tabbas sai ya san ita ya gaya wa haka, sai yayi nadama. Ta jima a kwance taji motsin shigowar Sumayya, sai ta jita ta murda dakin ta shigo da sallama. Bata motsa ba har tazo gaban gadon ta dan taba ta tana cewa "Ruqayyah ki tashi ki cire kayan ki mana, a haka zaki yi bacci? Kiyi wanka mana ki tafi dakin mijin ki" ta karasa maganar cikin nishadi, da alama tana cikin farin ciki, to mai zai hana ta farin ciki ita kuwa tunda bata da wani problem a rayuwa? Komai yana tafiyar mata yadda take so ga Adam kullum yana kara cika ta da kaunarsa? Jin Ruqayyah bata ce komai ba yasa ta kuma taba ta, ta dauka bacci take yi. Sai taga ta bude idonta tana kallonta a take gabanta ya fadi, tasan irin wannan jan idon tasan irin wannan kallon, tace "Ruqayyah? Me ya faru?" Ruqayyah tayi juyi tana kara hayewa can saman gadon, tana jin kamar zuciyarta zata fito waje ida bata gayawa Sumayya ne yake damunta ba. Sumayya ta zauna a kan side drawer tace "me ya faru Ruqayyah? Wani ne ya bata miki rai a gurin taron?" Ruqayyah ta dauke kai gefe tace "mijina ne, baya sona kuma yanzu, yace yafi son Hussain a kaina. Kamar yadda Baba yace yafi son ki a kaina" sai kuma hawayen suka fara zuba. Sumayya ta hau kan gadon ta jawo ta jikinta tana cewa "Ruqayyah, ba wai ke ce ba'a so ba kuma kema kin sani, duk muna son ki sosai da sosai kawai wasu daga cikin halayen ki ne ba'a so. Na tabbatar shima wani abu kika yi masa har ya fadi haka, amma son ki daban a ransa son Hussain kuma daban, ai ku din ba abu daya bane ba kowa da gurbin da yake zaune a kai" Ruqayyah ta fara kokarin kwace jikin ta daga Sumayya tana cewa "cewa fa yayi har abin da yake cikina zai iya hakura dashi saboda Hussain yayi murmushi, wanne irin so ne wannan? Wacce irin magana ce wannan?" Sumayya tayi murmushi tace "Ruqayyah! Hassan duk duniya bashi da kamar Hussain kuma har a nade ta ba zai samu kamar Hussain ba. Abinda yake cikin ki kuwa zaku kuma samun wadansu har goma ko fiye da haka, kinga kuwa ai ba za'a taba hada soyayyar su a guri daya ba. Amma ke me kika yi masa haka da zafi har ya gaya miki wannan? Na tabbatar kin kure hakurin sa ne" Ruqayyah tace "dama ai ba hakurin ne da shi ba, fada ne dashi da saurin fushi. Shine har da yi min warning wai kar in kara gaya masa laifin Hussain baya son ji" Sumayya tace "ai tun farko dama sai dana gaya miki, nasan duk boye boyen halinki da kike yi dole sai ya sani tunda shi hali ai baya boyuwa indai har za'a zauna tare ballantana zama irin na aure. Kin nuna masa ke mai hakuri ce da kawar da kai bayan kuma ba haka bane ba yanzu zafin zuciyar taki da mita kika nuna masa ko? Ni bansan halin maza ba amma nasan ko a matan ma ba kowa ne yake son zama da mutum mai mita ba. Ballantana har ki kai ga fadin aibun dannuwansa a gaban idonsa. Gaskiya baki kyauta ba, kuma duk abinda ya gaya miki ke kika jawo wa kanki. Amma nasan hakan daya fada ba wai dan baya sonki bane ba sai don yana so ya nuna miki cewa abinda kike yi din ba dai dai bane ba. Nima kuma na gaya miki ba dai dai bane ba, dan nasan yadda nake sonki nasan kuma ko menene zaki yi na rashin kyautawa ba zan so inji wani ya fada ba ballantana kuma in naji anyi miki sharri" Ruqayyah ta dago kai da sauri "sharri? Au sharri nake yi masa? Bashi da son a sani ne da nuna wa mutane basu isa ba? Shi fa jinsa yake yi tamkar sama yake da kowa, jin kowa yake yi a kasan sa dan nayi kokarin ankarar da danuwansa shine nayi laifi? Dan shi fa nake yi ba dan wani ba, dan in kwato masa yancinsa nake yi badan komai ba" sai tayi shiru tana kallon hannunta, Sumayya ta gyara zamanta tace "gaya min, menene plan dinki? Me kike so kiyi archiving? What are you up to?" Ruqayyah ta danyi tsaki fuskarta tana nuna bacin ranta ta share hawayen da ya rage a idonta tace "ke kinfi kowa sanin ban taba tunanin zan auri mutum kamar Hassan ba sai da na ganshi. Na kuma dora raina akan cewa kudin nan nasa ne, na riga na gama saka zuciya ta akan hakan. Bayan naga Hussain naso ace shine Hassan, naso ace shi zan aura, naso ace shine wanda na tarar ranar nan a toilet amma kuma na hakura na karbi Hassan din tunda a lokacin ina tunanin shi yake da kudin, yanzu kuma na fahimci suma kudin ba nasa bane ba" ya danyi tsaki tana girgiza kanta tace "na tsani wannan Fatiman ta fiya iyayi da gulma da munafurci da nuna isa, na kuma fahimci Hussain yana matukar sonta, sannan yana son Hassan sosai" ta sake yin shiru kamar mai tunani sannan tace "I just want to be her. I want her husband, her house and her power" Sumayya ta zaro ido "Ruqayyah baki da hankali? Ta yaya zaki so mijinta bayan ga naki? Ta yaya zaki so gidan ta bayan ga naki? Ta yaya hakan zata yi wu?" Ruqayyah tace "hakan ba zai yiwu ba na sani, na fahimci Hussain tun da nazo gidan nan na gane baya kaunata ko kadan, ko kallo ban ishe shi ba, bana jin ko babu Hassan a duniya Hussain zai kalli inda nake sai dai ko da niyyar taimako amma ba da niyyar aure ba. Wannan yasa na hakura dashi. Sannan nake so in mayar da Hassan shi ya koma Hussain din. So nake in mayar dashi CEO" Sumayya tace "how?" Ruqayyah tace "niyya ta in hada rigima tsakanin Hassan da Fatima, ta hanyar amfani da abinda yake cikina saboda na fahimci irin son da Hassan da shi kansa Hussain suke yi wa cikina. So nake su yarda bata son abinda yake cikina yadda duk abinda ya samu cikin ita za'a yi zargi. So nayi in rura wuta tsakanin su ta yadda Hussain will be forced to choose between them kuma nasan cewa Hassan zai zaba duk kuwa da cewa rabuwa da Fatima zata yi destroying dinsa. And that destruction shi nake after. Idan ya zama ba zai iya cigaba da rikon kamfani ba dole Hassan will take over. Idan kuma something bad ya faru dashi komai ya zamana Hassan din" Sumayya da mamaki ya ishe ta ta katseta ta hanyar cewa "something bad as in?" Ta daga kafada tace "babu wanda ya san gawar fari dan haka dan Adam babu abinda zai yi fata illar Allah ya bashi rayuwa mai tsaho" Sumayya ta dafe kanta tace "Ruqayyah wai kina nufin kima fatan Hussain ya mutu saboda Hassan ya samu gado" tayi shiru kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace "kowa ma wata rana zai mutu ai" Ruqayyah tace "exactly, hakan yana nufin kema zaki iya kwanciya yanzu gobe kuma ba zaki tashi ba. Shi kuma Hussain zai iya ya kara shekaru saba'in ko fite da haka a rayuwa. Dan Allah Ruqayyah ki gaya min cewa ba wai kina tunanin harming Hussain bane ba saboda dukiyarsa. Dan Allah Ruqayyah ki gaya min babu wannan tunanin a ranki" Ruqayyah ta bata rai tace "ni na isa in yi masa abinda Allah bai yi masa ba? Buri na ne dai kawai. Dan Adam kuwa ai ba'a raba shi da buri in dai akwai rai a jikinsa. Kuma wannan burin nawa ba zai cika ba indai har Fatima tana zaune a gidan sa saboy a kowanne lokaci zata iya samun ciki ta haifa masa da, samun da a gurinsa kuwa yana nufin ni da shiga gidan can sai dai da ziyara" ta mike zaune tana kokarin sauka daga kan gadon tace "besides, duk wannan burin nawa yabi iska tunda Hassan ya debi kasa ya watsa min a idona. Hussain zai cigaba da zama da fatiman sa ta haifa musu yaya and they will live happily ever after. Ni kuma da nawa yayan Hassan yayi conderming din mu to life of bakin ciki a karkashin dan uwan sa" sai da takai bakin kofa sannan ta juyo tace "kar ki damu yaruwa ta, the plan is off, shi yasa har nake gaya miki". Daga nan ta shige toilet. Sumayya ta jima a zaune tana kallon kofar toilet din, zuciyarta tana gaya mata "anya lokaci bai yi ba da ya kamata ta shigo da Inna Ade da Baba cikin maganar Ruqayyah? Amma bata da mental related issues kuwa?" Ruqayyah ta jima a toilet tana wanka, tana jin kamar tana wanke bakin cikin da Hassan ya cusa mata sannan tana bin maganganun sa a hankali tana digesting tana so ta fitar da ma'anar su. Abinda ta fahimta shine, babu wani abu daya gane a kanta, frustration dinsa kawai shine maganganun data fada akan Hussain, amma da sannu in ta cigaba a kan wannan hanyar data dauko to sai komai nata ya bayyana gare shi dan haka dole ta rufe wannan babin ta bude sabon babi, this will be the end of her first chapter yanzu zata bude second. Sanda ta fito daga wankan bata tarar da Sumayya ba, dama ba'a dakin take kwana ba a kasa take kwana saboda bata son ta takurawa Hassan. Ta zauna akan dressing chair tana goge jikinta sai kuma ta dauko wayarta ta nemo number din Minal ta kira sai taji waya take yi, ta ajiye tana saka kayan baccin ta sannan tai Minal din tayi mata flashing, ta dauka tana cewa "ke yanzu da girman ki kike flashing?" Minal tace "ke babu wani girma anan, ke yanzu ai hajiya ce dan haka gwara ke ki kirani dan ni lallaba katin waya ta nake yi. Ya akayi? Ina mijin naki har yanzu baki kwanta ba?" Tace "ni ba wannan ba da Allah can, so nake ki damu lokaci ki zo akwai maganar da nake so muyi" Minal tace "dama gobe nake cewa zan shigo in karbi tsaraba ta, naga baki da niyyar zuwa ki kawo min har gida" Ruqayyah ta kalli cikin closet dinta, ita in ba shiga tayi ba har mantawa take yi ta lodin kayan da Hassan ya siyo mata a matsayin tsaraba, tace "akwai tsaraba kam, in kin zo kya karba" tace "to sai nazo din. Akwai wata magana nima da zamu yi" daga nan suka yi sallama ta kashe wayar ta ajiye sannan tayi shirin bacci ta kwanta tana jin wani freedom a ranta. Yau dai zata kwanta tayi ta juyin ta babu wanda zai dame ta. Washegari da safe Sumayya ta shirya tace gida zata tafi. "Naga kin warke ai, kuma kina da yan aikin ki gwara in koma gida in cigaba da taya inna ayyukan gida" Ruqayyah ta bata rai "ba dai akan maganar jiya zaki tafi ba ko?" Sumayya tace "maganar jiya ai mun gama ta tunda kince kin rufe wannan babin, ni dai zan yi ta miki addu'a kullum, sauran kuma tsakanin ki da mijin ki ne". A lokacin Hassan ya fito daga dakinsa, daga dukkan alama yanzu ya tashi dan fuskarsa da alamun bacci. Sumayya ta gaishe shi Ruqayyah ma haka, ya amsa yana kallon Ruqayyah ita kuma ta dauke fuska gefe tana kara bata rai yace "Sumayya ya na ganki da jaka haka da sassafe ko karyawa baki yi ba?" Tace "na karya ai duk kuna bacci. Akwai abinda nake so inyi a gidan ne da safen" yace "ohh. To bara in dauko key sai in kaiki ko?" Tace "lah, kayi zamanka, ina fit zan samu abin hawa" yayi murmushi yace "I insist" daga nan ya koma daki ya fito yana cewa "Precious bara in kaita in dawo ko" can kasa tace masa "a dawo lafiya" sai yayi murmushi, yasan fushi take yi. A hanya suna tafiya yace da Sumayya "ina saurayin ki? I half expected to see him a waje yana jiranki, na dauka shi kuka yi dashi zai kai ki gida" ta danyi dariya tana wada da bakin hijab dinta tace "yana gidan mu ai yanzu. In kaje zaka ganshi a can in dai har ba zasu fita da sassafe da Hussain ba" ya dan bata fuska yace "gidan ku kuma? Me zaiyi acan da sassafe bayan kuma ke kina nan gidan?" Tace "karatu, karatu yake zuwa dauka acan kullum da assuba sannan kuma da daddare in ya gama da Hussain" ya maimaita "karatu?" Tace "yes, kasan ai...." Yace "I know, but kawai nayi mamakin boldness dinsa da zai je gidan surukai koyon karatu" ta dan ji kunyar kalmar surukan da yace. Suka cigaba da tafiya shiru, sannan yace "a gida Ruqayyah tana da fada ko? Baba ya taba ce min tana da fada" ta dan kalle shi tana hango damuwa a fuskarsa sai taji tausayinsa har ranta, tace "haka ne, kasan kowa da halinsa, amma I believe zata daina" ya gyada kai yace "eh zata daina, nima haka nace da baban a lokacin. Sai me take dashi bayan fadan?" Tayi shiru, a ranta tana tunanin wadannan tambayoyin Hassan kamata yayi ace yayi su tun kafin ya auri Ruqayyah ba wai yanzu da take dauke da cikin sa ba. Ta dan yi murmushi a lokacin da yake packing tace "a hankali duk zaka fahimci yar uwata. Kai dai yanzu kayi ta addu'a kana hakuri kuma kana saka ido, komai zai wuce" ta bude kofa ta fita. Bayan Hassan yayi breakfast, wanda shi kadai yayi kayansa dan kafin ya koma Ruqayyah har ta gama nata ta shiga daki, sai ya shirya ya leka ya ganta a kwance ya gaya mata ya fita. Yana so ya zauna suyi magana amma kuma akwai abinda zasuyi a office yau dashi da Hussain dan haka dole ya fita da wuri. Da rana Minal tazo, Ruqayyah ta tare ta sannan ta jata zuwa dakinta. Minal tace mata "ke wani gara ne fa na samu nake wanka, shine ya kawo ni gidan nan ma yanzu. Har ya fara yi min maganar aure" Ruqayyah tayi dariya "kuma shine kike ce masa gara?" Minal tace "ke babba ne fa, a haife zai haife ni wallahi, zan baki labarin sa amma gaya min abinda yasa kika kirawo ni". Sai Ruqayyah ta bata labarin rigimar da suka yi da Hassan jiya. Tace "to ni yanzu duk komai ya kunce min wallahi. Shawara nake so ki bani ta inda zan dora" Minal tayi tsaki tana hararar ta tace "ke matsalar ki shine har yanzu baki ware ba wallahi, gidadan ci ne yake damun ki ba kadan ba. Ba tun yau ba na baki shawarar yadda zaki yi amma kin kasa fahimta. Kuma wallahi in kika cigaba a haka to ina yi miki albishir da komawa gidan Baba a matsayin bazawara" Ruqayyah taji wata irin faduwar gaba tace "Allah ya tsari bakin ki, kije ki kuskure bakin ki dan Allah. Kin ga ni fa aurena da Hassan mutuwa ce kawai zata rabamu" Minal tace "ai kuwa kina gab da tafiya in gaya miki. Mutanen nan fa wayayyu ne kuma ilimi ya ratsa su ta ko'ina, ba zaki taba iya hada su ba wallahi saboda kafin ki gansu ke sun ganki. Kinga wannan gimbiyar, to wallahi idan ke baki kore ta ba tabbas ita zata kore ki with just a blink of her eyes. Dole sai kin ajiye wannan zafin kan naki da wannan gidadan cin naki. Kinsan abinda yake zaune da ke a gidan nan? Son da mijin ki yake yi miki ne ba wani abu ba. In kuka cigaba a haka kuwa son zai dusa she then zaki zama baki da sauran wani madogara kuma" Ruqayyah tace "ni duk ba wannan ba, ki gaya min abinda zanyi nace ba wai kike min bitar abinda na riga nayi ba" Minal tace "na gaya miki ai, kissa xaki bisu da ita, ki kama mijin ki ki kama surukarki ki kama yan uwan mijinki. Kinga wannan fatiman? To itace gidan nan ki kama ta hannu bibbiyu ina gaya miki. Zan je gidan Aunty Hafsa yanzu xan gaya mata halin da kike ciki zata saka ki a group dinsu na matan aure zasu koya miki duk yadda zaki bi da su. Sannan kuma sai kin hada da addu'a, ke kina yi kuma kina sakawa ana yi miki, kina musu kissa kuma kina toshe bakin su da addu'a yadda ko sun ga wani abu ba zasu iya magana ba. Akwai wani malami da Hajiya Binta kawar Aunty Hafsa ta hada ni dashi yayi min addu'a akan wannan garan da nake gaya miki. Kinga shi matarsa ce bata haihuwa shekara da shekaru ga uban kudi kamar ya kashe shi, shi kuma son matar yake kamar me, ya kasa yi mata kishiya, da kyar Alhaji Kabiru ya hada ni da shi yana ta yanga amma dana samu naje aka tottofe min shi shikenan. Yanzu bina yake kamar jela" Ruqayyah tana girgiza kai tace "bana son harka da bokaye, bana son in rasa sallolina na kwana arba'in" Minal tace "ke dalla can ba boka bane ba, malami ne, da ayoyin Alkur'ani da sunayen Allah zai rufe miki bakunan su gam" *The Fortune Teller* Ruqayyah tayi shiru tana kallon Minal, abubuwa da yawa suna yawo a cikin kwakwalwar ta zuciyarta tana rabuwa kashi kashi, ta girgiza kanta. "Minal tsoro nake ji, irin wadannan malaman da su da bokaye duk tafiyarsu daya. Baki san wanda yasan Alqur'ani yasan irin sirri kan da ke cikin sa kuma in zuciyarsa bata da kyau to there is no limit to what he can do ba? Kuma wadannan laifin su yafi na boka muni ba? Kinga kakan mu, Malam Shehu? Babu abinda ba zai iya yi da ayoyin Alqur'ani ba amma baya yi din, ya zabi yayi aikin alkhairi dasu saboda ya zabi lahirar sa akan duniyar sa, inna Ade ma haka, ko kin san Inna Ade tafi baban su ilimin Alqur'ani? Amma ta zabi ta koyar da shi ga mutane saboda shine abinda take so. Nima nasan iya kacin abinda na sani, banbanci na dasu shine ni ina so in samu duniya sannan itama lahirar in samu yayinda su kuma suka ajiye duniyar a gefe suke neman lahirar. Duk iskanci na Minal bana wasa da ibada ta, ba zance bana zunubi ba dan ina yin karya da sauran kananan zunubai amma ban taba aikata wani a cikin manyan zunubai ba kuma ba zan fara ba. Kinga zuwa gurin boka ko malamin tsubbu to shirka ce, ita kuma shirka ita ce oga kwata kwata saboda in kayi ta tamkar ka bar addini ne, wanda kuwa duk ya bar addini kuma ya mutu ba tare daya dawo hanyar dai dai ba to ya mutu a kafiri. Ni kuwa Minal ba zanso in mutu a kafira ba bayan ita kanta duniyar ba samunta nayi ba, two zero kenan". Minal tayi tsaki tace "ke kam ana baki kina kin karba. Na gaya miki ba boka bane ba kuma malamin tsubbu bane ba. To gaya min, shi Malam shehun da kike yin magana akan sa mutane basa zuwa gurinsa ya taya su da addu'a akan wani abu daya shige musu duhu ko wani abu daya taso musu?" Ruqayyah tace "suna zuwa mana" Minal tace "exactly, shima wannan haka yake. Na gaya miki sunayen Allah kawai zai kira sai kuyi addu'a ku shafa shikenan. Kinsan ita addu'a baki baki ne, wani yana yi kamar yankan wuka haka take wani kuma sai yayi tayi bai samu nasara ba. Ke kina yi shima can yana yi miki shikenan" Ruqayyah dai tayi shiru tana tunani sannan tace "baya duba kasa?" Minal tayi dariya tace "babu kasa ma a gidan sa. Charbi kawai zaki gani da Alqur'ani a gaban sa". Ruqayyah tace "shikenan, zan zo muje din amma in naga wani abu da bai kwanta min ba zan gudu, ehe, dan ba zan zo duniya a banza in koma a banza ba sannan in tarar da can din ma wayam" Sai suka shirya plan akan cewa Ruqayyah zata je gidan su ta kai musu tsarabar tafiyar da tayi, daga nan zata ce zataje gidan su Minal din ta kai mata tata tsarabar daga nan zata wuce gida. In yaso sai suje gidan malamin tare. Bayan tafiyar Minal ne Ruqayyah ta shiga kitchen dinta. Yau ne rana ta farko data shiga kitchen din da niyyar girki, ta bude freezer taga akwai naman da bata ma san lokacin da aka zuba shiba, sai data tambayi yan aikin ta suka gaya mata ranar da zasu dawo Aunty ta aiko aka zuba musu duk kayan amfani a kitchen dinsu. Ta bude store taga akwai kayan garar ta suna nan suma jingim dan babu wanda aka raba wa duk zuba musu kayan su akayi a store. Har da drinks a jere a gefe wanda shima aka ce aunty ce ta aiko da shi. Tayi shiru tana tunanin me ya kamata ta dafa ne, in dai har zata bi maganganun Minal to dole ta koyi abubuwa da yawa a ciki kuwa har da girki dan ta rike Hassan a hannunta. Ta tuna Fatima tayi mata alkawarin zata koya mata girki in sun dawo Nigeria amma yanzu kuwa anya in taje zata kulata? Maybe ma ta bita da bakar magana. Ta danyi tsaki, gaskiya lamarin nan sai ta dage sosai sannan zata cimma burinta, ita zuciyarta a kusa take, ita bata iya munafurci ba shi yasa har suka fara harbo jirgin ta. Amma dole ta koya koda kuwa a gurin Hassan ne dan dama shi tun tana gida take rufe shi a bai bai kuma yake rufuwa yanzu ne dai kawai frustration dinta akan Fatima ya saka ta fara bude masa kanta shi kuma a take ya buga mata warning. Ta kalli yan aikin tana realizing ita ko sunayen su ma bata tsaya ta wani rike ba, tace "wace ta iya girki a cikin ku?" Duk su biyun suka ce sun iya. Tace "to ayi mana girki, tuwon shinkafa miyar agushi a saka nama sosai" suka ce shikenan ? Ta daga kafada tace "eh shikenan" sai bayan ta tafi sai ta tuna ai yan gayu abinci ba kala daya suke yi ba ko? Kamar har da snacks ake hadawa da kuma dan farfesu haka. Sai ta koma ta gaya musu suyi farfesun kaji sai su saka naman kasuwa a cikin miyar. Suka gaya mata babu fresh kayan miya sai markadaddu, babu kuma kayan kamshi, ta koma sama ta dauko kudi ta basu tace su bayar a waje wani ya siyo. Tayi kamar zata zauna suyi aikin tare, maybe ta koyi wani abu, amma sai ta kasa zaman kar su fahimci bata iya ba su raina ta. Ta debi drinks ta tafi dasu sama ta zuba a fridge din daya ke can ta kunna sannan ta koma dakinta ta gyara inda suka bata ita da Minal ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atampa wanda daya ne daga cikin dinkunan da ta bayar kala ashirin kafin su tafi honeymoon. Tayi kwalliya irin wadda taga Fatima tana yi, daurin dankwalin ma shigen nata tayi. Sannan ta saka awarwarayen gold kamar yadda taga tana yi sai tayi sallar azahar sannan ta koma kitchen din ta tarar sun kusa gama abincin. Sai ta dawo sama ta kunna tv tayi kwanciyar ta akan kujera tana danna wayarta. A lokacin ne taga an saka ta a sababbin groups, ta kuma fahimci aikin Minal ne, taga wata ta aiko a bata shawara akan uwarmijinta da ta sako ta a gaba, mutane kowa yana fadar albarkacin bakinsa wasu suna bata shawarar da hatta ita Ruqayyah ta fahimci ba dai dai bane ba wasu kuma suna bata shawarar dai dai, masu cewa tayi addu'a kuma suna ta fada. Tayi shiru tana ta lissafi, tabbas social media guri na na samun abubuwa da yawa, alkhairi da sharri dukka, ya danganta da menene a zuciyar mutum. Tana nan a zaune yan aikin suka hawo da abincin suka shiga dashi dining room sannan suka tambayeta in akwai wani abu kuma, da hannu tayi musu alamar suje kawai, har laasar tayi sannan ta tashi ta koma daki tayi sallah tana jin anya kuwa zata iya cigaba da jiran Hassan dan ita yunwa take ji already, sai ta tunawa kanta da cikin da yake jikinta dan haka tana fitowa ta tafi gurin abinci ta bude zata zuba. Kallo daya ta yiwa tuwon tasan bai tuku ba, tana saka shi a plate kuwa ya fara tarwatsewa. Tayi tsaki tana jin ranta yana baci, ta tuno da tuwon da taci ranar nan a part din aunty wanda ko kwayar shinkafar baka gani a ciki. A bude miyar taga babu laifi a ido, ta dan zuba tana ci taji gishiri yayi yawa. Ranta bai kara baci ba sai data bude farfesun. Gaba ki daya kazar ta narke romon kuma yayi ruwa tsululu. Ta zauna ta zuba tagumi, yanzu ya zata yi kenan? Ita da taso in abincin yayi dadi ta nuna masa kamar ita ce tayi? Wannan ai ita suka bawa kunya. Kamar daga sama taji sallamar Hassan, tayi kokarin kirkirar murmushi dan ta tare shi amma sai ta tuna cewa fada fa suka yi kuma har yanzu basu shirya ba, dan haka ta bata rai ta koma ta zauna tana cika tana batsewa. Taji motsinsa ya shiga dakinta sannan ya dawo palon sannan ya taho dining din, ya tsara yana kallonta ita kuma ta maze tan cigaba da jujjuya abincin gabanta. Ya jawo kujerar kusa da ita ya zauna yana kokarin leka fuskarta sai ta dauke kai gefe, ya danyi murmushi mai sauti "haba my Precious wife, wai fushin ne har yanzu vaki gama ba?" Ya kama hannunta tayi kokarin kwacewa yace "look. Nasan abinda na fada jiya ya bata miki rai, but dole ce ta saka na fada. Kinga munyi aure ne ba tare da mun fahimci halayen junan mu ba, dama nasan dole watannin farkon auren mu a going to be rough on us, tunda a lokacin ne zamu fahimci kanmu, ina son duk abinda nayi miki, ko menene wanda kika ga ba kya so dan Allah ki fada min dan in san cewa ba kya so kinji? Ni ma kuma in kika yi min abinda bana so zan gaya miki kinji? Kamar jiya, na gaya miki bana son jin magana marar dadi akan Hussain saboda bana so din, idan kuma ban gaya miki ba ai ba zaki sani ba ko? I know I was harsh a magana ta but kiyi hakuri raina ne ya baci saboda abinda kike fada kina kara maimaita wa. Na sani Hussain dan Adam ne kamar mu, kowa kuma yana da bangaren sa mai kyau da marar kyau dan haka duk wasu halaye na Hussain na sani bana bukatar ki gaya min su. Kinji?" Ya saka hannu ya juyo da fuskarta da take zubar da hawaye yana kallo sannan ya girgiza mata kai yace "ya isa haka, ko nima so kike inyi kukan?" Ta turo baki "ba kai ne kace baka sona ba wai kafi son Hussain a kaina" yayi dariya "ohh kukan kishi ne ashe kike yi. To bara in gaya miki Hussain side dinsa daban a zuciya ta kema haka. Kin san wani abu? Sai da na aure ki ne fa na zama complete mutum, Hussain yana tare da ni tun a ciki amma ba zai iya completing dina ba sai ke ce kika iya. Kin gane banbancin?" Ya kamo ta yana dawo da ita cinyarsa, ya dora kansa ya wuyanta yace "ga kuma babies zaki bamu, abinda Hussain ba zai taba iyawa ba. Kuma bara kiji, kamar yadda nayi defending Hussain a gabanki haka zanyi defending dinki a gaban Hussain idan ya taba ki because you are my precious wife". Tayi kokarin tashi ya dake riketa, "Please ki ce min kin hakura komai ya wuce kinji? In ba haka ba tuwon nan ba zai iya wucewa cikina ba" Ta bata rai tana kara kwanciya a jikinsa tace "tuwon ma babu dadi ai" ya jawo plate din yace "me ya same shi?" Tace "har na shiga kitchen din zan fara girkin kuma amai ya hanani, bana son mixed kamshin abubuwan girki, shine na barwa yaran nan suyi kuma gashi bai yi dadi ba" ya ture plate din yana cewa "it is okay, bara in samo mana wani abun ko a gurin aunty ne" tace "aunty kuma? Kar ka takura mata mana" ya mikar da ita tsaye shima yana mikewa yace "no, babu wani takura ai tasan baki da lafiya, daga nan ma sai ce ta samo mana cook mai tsafta sosai tunda dai babies sun hana maman su girki" ya karasa yana tsokanar ta sannan ya fita, ta zauna tana jin kalmar maman babies tana bata mata rai, sai kace ita ce Inna Ade da ake cewa uwar biyu. Sumayya bayan ta shiga gida su Inna suka yi ta mamakin ganin ta haka da sassafe, sai tace musu kawai tayi kewar gida ne shi yasa ta dawo, amma Inna Ade ta lura da damuwa a fuskarta. Sai data bari ta shiga daki tana gyara kayanta sannan ta bita ta zauna tace "ya kika baro su Ruqayyah? Jiya da dare da muka ganta naga tayi girma sosai, kamar hankalin ta a kwance yake ko? Bata da damuwa ko?" Sumayya ta ajiye kayan hannunta ta dawo kusa da Inna Ade ta zauna tace "bana jin Ruqayyah tana da damuwa Inna, ki kwantar da hankalin ki, mijinta da surukan ta suna da kirki sosai kuma suna son ta sosai" sai kuma ta dan yi shiru idanunta a kasa, Inna Ade tace "sai dai kuma me? Akwai magana a bakin ki ki gaya min mana wani abun ya faru ne?" Sumayya tace "kawai dai ina tsoro ne Inna, kin san halin Ruqayyah tun tana gidan nan, yanzu kuma tayi aure ga kuma irin gidan da tayi auren a ciki, cikin yan kwanakin nan da auren nata har idanunta sun kara budewa sosai, ta kara chanjawa sosai, ina tsoron nan gaba kar ta kauce hanyar da kika dora mu akai Inna, so nake kiyi tayi mata addu'a Inna" Inna Ade tayi ajjiyar zuciya tace "ko sau daya ban taba cire wannan tunanin daga zuciyata ba Sumayya, kullum ina yi muku addu'a gabaki dayan ku kullum dare sai na tashi nayi muku addu'a neman tsari daga shaidan, mutum da kuma aljan. Kuma na tabbatar ubangiji ba zai jiyar da addu'a ta ab saboda yayi alƙawarin amsar addu'ar uwa akan ƴaƴanta. In sha Allah yar uwarki ba zata tabe ba. Xan kara wata addu'ar akan wacce already nake yi kullum. Sumayya taji dadi kuma taji hankalin ta ya dan kwanta, tasan babu abinda addu'a ta bari dan karfin addu'a yakan iya chanza kaddarar mutum gabaki daya. Cikin kwana biyu Ruqayyah ta kuma dawo da mijinta gare ta, ta kuma fara shiga cikin yan uwansa kamar yadda Minal ta bata shawara. Idan ya fita itama sai ta shirya ta tafi part din aunty tayi zamanta acan, ba zata dawo ba sai yayi mata waya yace gashi nan zuwa sannan zata debar musu abinci ta tafi can ta kuma shirya tayi masa kwalliya kafin ya dawo. Wannan yasa shima ya wanke zuciyarsa gaba ki daya akan waccan maganar yake enjoying matarsa. Motocin su da Hussain ya siya musu ita da Fatima sun iso kuma Ruqayyah tayi murna sosai dan bata dauka haka motar ta hadu ba sai da tagan ta kiri kiri sannan ta kuma fahimtarta. Hassan ne yayi suggesting ya kamata ta shirya taje gida ta nuna musu motar dan tun da suka dawo bata je gidan ba. Dan haka ta dauki kayan tsarabarsu sannan shima kuma ya dauki kudi masu kauri ya bata yace ta kai musu, sai ya hada ta da driver yace ya kaita tunda bata fara koyon motar ba tukuna. Dan haka hankalin ta kwance ta tafi a zuciyarta tana plan din daga can zata biya ta gidan su Minal suje gurin malamin nan mai addu'a. Tana shiga soron gidan taga Adam yana fitowa daga dakin su Sulaiman. Yana shafa kai yace "welcome Madam" ta watsa masa harara tare da jan dogon tsaki ta wuce cikin gidan sai yayi murmushi kawai ya fita. Tana shiga Zunnur yana ta murnar ganinta amma ita da fada tafara "me wancan kedarin yake yi a gidan nan? Duk ya cika masa gida da warin karti" Sumayya da take daki suna waya da Adam yana gaya mata ya gama zai tafi ta fito tana kashe wayar ta nuna ta "kar ki kuma, wallahi Ruqayyah ki fita daga idona na gaya miki" Ruqayyah tace "in na kuma nace sai me? Me zakiyi min? Wallahi sai ya daina zuwa gidan nan ai badan irin su Hassan ya sai gidan ba" Sumayya tace "to maza, yi mana gorin cewa mijinki ne ya siya mana gida, dan ma dai ba rokar sa mukayi ba kuma daya siya din ba ke ya siya wa ba Baba ya siya wa dan haka baki da iko da gidan" Ruqayyah tace "amma dai saboda wa ya siya? Saboda ni ya siya baby girl amma ina da say akan waye zai ke shiga gidan nan yana fita kuma wancan katon kedarin baya daga cikin su" Inna data rike baki tana kallon su tace "to kuyi dammara ku daku a gaban kannen ku kunji. Akan saurayi zaki yi fada da yar uwarki Sumayya? Ke kuma akan wata akida taki ta daban zaki yiwa yar uwarki damu iyayenki gori cews mijin ki ya siya mana gida? Ruqayyah? Har kin kai haka? Har kin yi girman da zaki yi mana gorin gida Ruqayyah?" Ruqayyah ta zauna taa magana kasa kasa "ni ba gori nake muku ba inna, ni kawai mutumin nan ne bana son yake zuwa gidan nan wallahi. Na tsane shi bana son ganin sa" Sumayya ta bude baki zata yi magana sai kuma ta kalli Inna ta juya ta koma daki tana rufo kofa. Tana ragawa Ruqayyah akan komai amma ta rasa me yasa bata iya raga mata akan Adam. Ko da wasa bata son Adam yaji irin maganganun da Ruqayyah take fada akan sa, babwai dan tana son sa a matsayin saurayi ba sai don tana sonsa a matsayin sa na wanda yayi loosing everything for islam. Inna ta jima tana yiwa Ruqayyah fadan abinda tayi sannan kuma ta koma yi mata nasiha, daga nan kuma sai suka shiga hira. Su Sulaiman da suka tafi dauko kaya daga mota suka suka dawo suna baje kayan anan tsakiyar palo kowa yana diban nasa. Ruqayyah ta dauko na Baba ta bawa Inna ta ajiye masa sannan ta bata nata itama. Ta ware na Sumayya gefe tace "ita kuma wannan inntaga dama ta fito ta dauka to in kuma tayi fushi in kinyi bakuwa inna ki bayar" Sulaiman yayi dariya yace "babu wanda zai shiga tsakanin ku dan duk wanda ya shiga to kuwa zai ji kunya" duk suka yi dariya amma ita Ruqayyah bata ga abin dariya a cikin fadan su da Sumayya ba, ita bata san me yasa suke daukan lamarin Adam for granted ba. This is very serious issue amma su suna dariya akai. Sai daga baya Inna da kanta ta aika aka kirawo mata Sumayya ta fito suka cigaba da hirar si tare, Ruqayyah tana ta nuna musu hotunan guraren da suka je da kuma abubuwan da suka yi, sannan tace "ohh ni na manta ma, ga mota can Hussain ya bani kyauta. Tana waje" sai murna da ihu. Suka fita waje gabaki daya har da Inna, suna ta gani suna saka albarka, Ruqayyah ta saka drivern ya dauke su ya dan zaga dasu unguwa sannan ya dawo dasu. Anan Ruqayyah ta kusan yini har laasar, sai da Baba ya dawo ta gaishe shi sannan ta fara shirin tafiya. Inna tace "da wuri haka zaki tafi?" Tace "yace kar in kai dare ne, yace in koma gida kafin ya dawo kuma karfe biyar yake dawowa" Inna Ade ta gyada kai tana jin dadin yadda Ruqayyah take wa mijinta biyayya. Ta dauko kudin da Hassan ya bayar ta ajiye musu sannan tayi musu sallama suka raka ta har bakin mota, Baba yana sakawa motar albarka. Suna fita daga layin ta saka driver ya dauke kan motar zuwa gidan su Minal, ta dauko waya ta kira ta ta gaya mata gasu nan zuwa dan haka suna zuwa ta fito ta shiga motar suka tafi. Basuyi wata tafiya mai nisa ba suka zo gidan malamin, sai Ruqayyah tayi mamakin ganin hadadden gida ba irin gidan malam Shehu ba dan tasa ran ganin dan karamin gida mai dakin almajirai a soro da kuma malami a zaune akan buzu a kofar gidan amma sai taga an bude musu gate sun shiga hadadden gida drive in, suka fito daga motar kamar zasu shiga cikin gidan sai Minal ta kira wani a gurin tace a gaya wa Malam sunzo. Sannan ta juya gurin Ruqayyah tace "dama tun ranar da muka yi magana dake na gaya masa ta WhatsApp cewa zamu zo" Ruqayyah tayi dariya "wai kina nufin malamin ne yace WhatsApp?" Minal tace "to me za'a fasa, na gaya miki fa ba irin wadanda kike jin labarin su bane ba. Mu shiga ciki zaki kara tabbatar da abinda na gaya miki" suka shiga cikin wani palo suka zauna, Ruqayyah tana ta mamaki "yanzu dama ana samun irin wannan kudin a harkar malinta shine malam Shehu yake zaune a gidan kasa? Duk ilimin sa?" Minal tace "shi ya zaba. Kinga shi fa wannan yan siyasa suna zuwa gurinsa yayi musu addu'ar nasarar zabe, a haka ya gina wannan gidan ya kuma sayi motoci har biyu, ko da yake dayar ance min kyautar ta aka bashi" Suna nan zaune malamin ya fito, middle age mutum ne mai kamala da komai, ya saka manyan kayan sa da babbar riga hannunsa rike da charbi yana ja ya zauna suka gaishe shi yace "Ruqayyah ko? Amina ta gaya min zaki zo. To madallah Allah yayi albarka. Yanzu mu fara yiwa Annabi salati kafa goma tukunna" suka yi salatin nabiy a tare kafa goma sannan yace su karanto sunayen Allah 99 a tare, suka karanta sai ya jefar da charbin sa a gaban Ruqayyah yace ta miko masa, ta dauko ta miko masa sai ya rike gefe da gefen inda ta taba ya kirga adadin beats din da suke gurin sannan ya kalle ta yayi murmushi yace "Amina ta gaya min bukatar ki, dukiya ce ta kanin mijinki ke kuma a ranki kina so ta zama ta mijin ki. Shine kike so ayi miki addu'a Allah yayi miki jagora akan wannan kudiri naki" Ruqayyah ta gyada kai tace "haka ne" Yace "to ai malama Ruqayyah ni dai abinda na gani a tattare dake shine arziki, naga dukiya fiye da wadda kike saka ran samu, na ga budi, indai kudi ne wadanda ake kira da kudi na gansu. Amma kuma naga kadaici. Zabi ya rage naki Ruqayyah, nan gaba kadan wata damazata same ki wadda zata barki da zabi guda biyu, ke da kanki zaki zabi rayuwa cikin dauka marar iyaka ko kuma rayuwa a karkashin masu daula marar iyaka. Zabi ya rage naki. Idan kin je gurin zaki fahimci abinda na gaya miki kuma sai a lokacin zaki biya ni kudin aikina da kanki ba tare da wani ya tuna miki ba" Ruqayyah ta mike da sauri tana jin uneasiness, wannan ai duba yake yi, malamin duba ne Minal ta kawo ta gurinsa. Ba tare da tace komai ba ta yi hanyar waje, tana zuwa bakin kofa yace "Allah ya sauke ki lafiya Ruqayyah. Ki gaishe min da Hassan da Hussainin da zaki haifa". Babu shiri ta karasa fita tana hada hanya, tana shiga mota bata jira Minal ba tace da drivern su tafi, gabanta yana ta faduwa amma maganganun malamin suna ranta kamar yayi zane akan dutse. *The Twins* Sai da ta kusan zuwa gida sannan kiran Minal ya shigo mata, tana dagawa ta fara yi mata bala'i "shine dan kuturun wulakanci zaki tafi ki barni ko? Wato ke ga mai mota ko? Laifi nane ni da na dauko ki na kawo ki inda za'a taimaka miki. Kuma kinyi da yar halak in dai ni Amina kika yiwa haka wallahi zaki gane kim wulakanta ni a gaban mutane" Ruqayyah tayi ajjiyar zuciya tace "kiyi hakuri Minal, wallahi ba zan iya bane ba tsoro nake ji, kema ki daina zuwa gurin sa duba yake yi. Ko waye ya gaya mishi ina da ciki har zai gaya min abinda zan haifa? Ki bashi hakuri kawai ki ce ba zan iya ba" ga mamakin ta sai taji Minal tayi dariya tace "bai ji haushi ba ai. Yace in gaya miki kiyi kokari ki aiko masa da date of birth na Hassan da Hussain da kuma na Fatima, rana da wata da shekara, da su za'a yi amfani gurin yi miki adduar" Ruqayyah ta girgiza kai tace "ni fa babu abinda zan bashi, ban sani ba kuma ko na sani ba zan gaya masa ba. Ke da jin wannan kinsan malamin tsibbu ne irin su kuma sunfi boka hadari" Minal tace "if you say so bazan yi miki musu ba, ni dai nasan bai bani komai na binne ba kuma bai bani komai na barbada ba. Dan haka ni banga tsibbu a cikin abinda yake yi ba, besides, burika na suna ta cika tunda yanzu gashi yayi min albishir cewa Alhaji Ahmed ya kusa aikoda kudin aurena, daga na shiga gidan na haifa masa yaya shikenan gidan ya dawo hannu na matar sa sai dai ta bini da kallo kawai" suka yi dariya tare, Ruqayyah tace "Allah ya bada saa, amma nikan ba dani ba" suka yi sallama Ruqayyah ta karasa gida. A compound din ta hango Hassan da Hussain suna tsaye suna ta magana suna dariya, daga gani suna cikin murna ne. Tana zuwa Hussain yace "yauwa gata nan ta karaso, shawara nake bashi cewa ya ke turo ki kullum kina zuwa kina gaishe ni ko Allah zai taiamake ku ku haifi yaya masu kama da ni, kin dan ni din fa kyakykyawa ne" ta tabe baki tace "Allah ko? Ni dai ban gani ba" yace "ohh baki gani ba? Zo muje in nuna miki" ya wuce gaba zuwa part dinsa Hassan yana binsa a baya yana cewa "kar kasa matata a cikin maganar nan walllahi ranka zai baci. In ka sake kayi forcing dinta tace ka fini kyau ko? Ni kadai nasan me zanyi maka" suka shiga palon Hussain, Ruqayyah ta tsaya daga bakin kofa dan bata taba shiga gurin ba sai yau. Ya juyo yana kallonta yace "common in, ki fadi kuma tsakanin ki da Allah waye ya cinye hoton nan" ta shigo tana kallon hoton da yake nuna wa. Su biyu ne a hoton, kamar kuma a wannan palon akayi saboda taga kujerar irin ta palon ce, Hussain yana zaune akan kujera ya harde kafafunsa fuskarsa da murmushin da yake bayyana dimple dinsa, Hassan a tsaye a bayan sa, ya dora guiwar hannunsa akan kafadar Hussain looking as serious as ever. Ta danyi murmushi tana rarraba ido tsakanin fuskokin su, ita sai yanzu take kara tabbatar da kamannin da suke yi sai dai banbancin fatarsu tana boye kamannin nasu. Ta jiya tana kallon Hassan ya bata rai yace "don't say it" tayi dariya tana kama hannunsa "me zance? Ai ko makaho ya shafa yasan mijina yafi na kowa kyau" Hussain yace "kin dai so kanki kawai" ta dauke idonta daga kan hoton tana kallonsa yace "ka manta da maganar hausawa da suka ce so duka so ne amma son kai yafi?" Hassan ya zagayo tabayanta ya tsaya suka jeru shima yana kallon hoton yace "gobe za'a kawo mana namu, this is just a sample. Hussain ne ya saka aka yi mana wai za'a kafe a duk kamfanonin sa dan kowaya shiga gurin yasan su waye masu gurin" ya karasa maganar yana dora habarsa a kafadarta. "Kin san halin kanin naki". Ta dan yi murmushi a ranta tace "kai zaka fada amma ni ban isa in fada ba sai aji haushi a gaya min magana". Bayan sun koma part dinsu ne Aunty ta aiko musu da abincin dare da kuma sakon cewa cook dinsu zata fara zuwa gobe. Suka zauna suka ci abinci yana tambayar ta ya mutanen gidan su suke, tana yi masa bayani amma hankalin ta yana kan maganganun wannan mai duban, yace dama zata same ta wadda zata iya zabar abu daya cikin biyu, ko dai ta zabi yin kudi fiye da kudin da take saka rai ko kuma ta zabi xama a karkashin masu kudi, bata bukatar amsa tasan idan lokacin yazo wanne choice din zata dauka, tabbas tasan kudi zata dauka dan shine babban burinta a duniya amma kuma abinda bata sani ba shine yadda zabin zai zo mata, yace zata yi rayuwar kadaici, wanne irin kadaici yake nufi? Indai kuwa har zata yi kudi to kuwa ai babu zancen kadaici saboda tasan mutane kamar magnet suke da kudi, duk wanda yake da kudi shine yake da mutane, misali Hussain da Fatima kullum gidan su a cike yake da mutane saboda suna da kudi, ita ma in ta samu irin wannan haka nata gidan zai ke cika irin nasu. To kuwa in dai abinda ya fada gaskiya ne then bata bukatar bata lokacin ta gurin korar Fatima ko raba Hassan da Hussain ko duk wani abu da yake on agenda din ta. But ita kanta tasan ba komai da yan duba suka fada ne yake zama gaskiya ba, kuma tasan yadda da abinda suka fada shirka ne saboda babu wanda yasan abinda gobe take tafe da shi sai Allah. Washegari weekend, haka kawai Hassan ya tashi da aikin gyaran gida, sai yau ya gama kwashe kayansa daga tsohon dakinsa ya kuma shirya komai tsaf a dakinsa na yanzu. Ita dai tana ta binsa a baya tana yi masa hira har ya gama sannan suka yi wanka suka zauna breakfast. Bayan sum gama ne ya dauko littafi karami da biro ya zaunar da ita ya rubuta wasu adadin kudi a jiki yace mata "jiya anyi mana salary, wannan shine salary na" ta kalli numbers din mentally tana calculating abinda zata yi dasu ranar da tayi kudin da take saka rai, sannan ta kirkiro murmushi tace "masha Allah, Allah ya sa musu albarka" yayi murmushi yana jin dadi yace "ameen Precious. Yanzu kinga lissafi na shine, 50% zan ajiye, su zanke tara mana na ginin gidan mu" sai kuma ya shafa kai yana kallonta da murmushi a fuskarsa yace "though, ga babies kuma a hanya, but we can manage kudin su isa har hidimar babies din" ya cigaba da rubutu yace "20% zamu siya daily needs din mu, komai na bukatar gida da kuma personal needs din mu for a month, 10% zamu kaiwa Baba, 10% percent kuma ina so in bude miki account sai kike ajiye wa kema duk sanda kike bukatar wani abu sai dai kawai ki dauka ba sai kin tambaye ni ba. Ko zaki yiwa wani kyauta ko dai wani abu mai muhimmanci haka, kamar harkar makarantar su Zunnur zaki yi musu out of your pocket. Ragowar 10% din kuma sai mu ajiye a gida in case of emergency. Ya kika gani? Lissafin yayi?" Ta cire tagumin da tayi tun da ya fara lissafin sannan tayi murmushi tace "gaskiya baiyi ba, kusan komai a kaina zai kare? Kai kuma fa? Ni banji ka ware wasu kudade kace naka ba ne ba" ya dago kai yana kallon ta fuskarsa cike da yana yin da yake nuna yaji dadin maganar ta har cikin zuciyarsa yace "don't worry about me, kin manta all that 50% yana gurina? Sannan kuma already ina da kudade a account dina zan iya dauka inyi duk bukatu na. Ke dai kawai kiyi managing wanda zan baki. Kar kike siyan unnecessary things. Kin san yadda nake siyayya ta?" Ta girgiza kai yace "duk abinda na dauka zan siya sai in tambayi kaina "do I really need this? Can I live comfortably without this? Ko kuma da akwai wani abu da nake bukata more than this? Idan har na tabbatar bana buƙatar abin sai in ajiye shi inyi gaba. That is how I avoid unnecessary spendings" tayi dariya tace "nima na koya to, haka zan ke yi" ya shafa fuskarta yace "good girl" sai ya mike tsaye yana cewa "monday sai muje a bude miki account din ko? Bara in shirya in an jima zan kai su Hussain airport" tace "airport? Ina zasu je?" Ya juyo yana kallonta yace "Thailand zasu je, zai ji signing wani contract ne da wani kamfanin shinkafa a can" ya juya ya shiga ya barta da sakakken baki "kuturin kare! Wato mijin wata yana can yana daukan matarsa tana rakashi business kasar waje ni nawa yana lissafa min albashin sa a takarda?" Sai taji duk ranta ya baci, taji ta raina albashin nasa gaba ki daya ko da kuwa gabadayan sa zai bata. Tana nan zaune har ya fito, yana daura agogo yana cewa "so nake in shiga gidan Aunty muyi rigima da ita, dama na gaya mata aure ba zai zaunar da Hussain a gida ba, in yayi auren ma daukan matar zai ke yi suna tafiya tare" sai kuma ya lura da chanjawar yanayin ta, yace "what's wrong?" Ta dago kai tana kallonsa, tace "babu komai, kawai dai zanyi missing din su ne" yayi mata murmushi sannan ya durkusa yayi kissing goshinta yace "kar ki damu, I will be here to keep you occupied" ya kashe mata ido, tadan dungure masa kai kadan ta juya baya tare da kwanciya akan kujera. Ya tashi yana dariya yace "sai na dawo. Please ki rubuta list din duk abinda muke bukata a gida kafin na dawo. Make sure you include everything. Ni kuma in na dawo zan biya in kaiwa Baba nashi kudin". Yana fita taja tsaki. "Ni bansan wanne iyayin ne ma yasa Hussain ba zai dauki driver ya kaisu airport din ba sai yasa Hassan ya kai su sai kace wani yaron su" ta sake tsaki tana jin bacin ranta yana karuwa, sai kuma ta mike ta shiga daki ta dauko hijab ta saka ta fita. A part din Aunty ta same su suna ta magana suna dariya har da Fatima, ta gaishe da Aunty da take rike da hannun Fatima sannan ta gaishe da Hussain tare da yi masa fatan alkhairi. Tace da Fatima "yanzu kuma shine zaku tafi ko sallama babu?" Fatima tayi murmushi tace "ban san baki san da tafiyar ba ai, tun jiya nake ta zuba idon ganin kin shiga munyi sallama" Ruqayyah ta juya ido, wato ita ba zata shiga tayi mata sallama ba saboda ita yar sarki ce..... Lokaci ya cigaba da tafiya, Ruqayyah ta lullube kanta da barguna na mutum mai kirki ta yadda a gurin Hassan ta zama the best wife he could have ever asked for, sometimes tana dan kwace mata ta dan saki baki haka ko tadan nuna halin ta kadan amma sai tayi saurin basarwa, shi kuma in hakan ta faru yana dangana hakan ne da maganar da Baba ya gaya masa na cewa Ruqayyah tana da zuciya tana kuma da saurin fada. Dai ya dage wajen ganin duk abinda tayi ba dai dai ba sai ya nuna mata ya kuma gyara mata ya gaya mata wanda zata yi dai dai din. Tsakanin ta da mutanen gidan kuma dai mutunta juna, duk da ita ta sani suma kuma sun san cewa ta sani sunfi son Fatima akanta saboda Fatima ta fita sakin jiki da su kuma ta fita kyauta. A tsakanin lokacin ne kuma Sumayya da Adam suka samu admission a tare suka fara zuwa makaranta, Hussain ne ya dauki nauyin komai na Adam, Baba kuma yabiya na Sumayya duk da cewa Adam ya so ya biya mata amma pride din Baba ya hana ya barshi ya biya din. Shigar su makaranta tare ta kara shakuwa a tsakanin su ta yadda har sai da Inna tayi wa Sumayya magana kan cewa ya kamata ta rage alakar ta da Adam saboda shaidan ya kan iya shiga even the most purest of hearts, wannan ya dan taka musu birki kadan, amma kuma bai rage musu kaunar junan su ba ko da da kwayar zarra. Sai dai har yanzu bai fito officially neman aurenta ba saboda bai san ta inda zai fara ba, bai kuma san ko za'a bashi ita da considering ko shi waye, duk da dai bai taba ganin kyama ko kiyayya a idon Baba ba. Bangaren Hussain da Fatima soyayya sai abinda ta karu, amma kuma even after months da bikin su babu ciki, abin yana ransu duk da cewa a tsakanin su babu wanda ya taba furtawa dan uwansa damuwarsa akan hakan, sai dai kullum suka zauna sai sunyi zancen haihuwa, har list ne dasu na sunayen da zasu saka wa ƴaƴan su, in an samu wani sunan kuma sai a kara sannan a rage wani. Da wahala su zauna tsahon wata daya a Nigeria, kullum Hussain yana tafe harkar neman kudin sa kuma duk inda zai je Fatima tana gefensa. Ruqayyah ciki ya girma. Tun kafin ya tsufa kusan duk wanda ya santa ya san tagwaye ne a cikin ta kuma babu wanda yayi mamakin hakan saboda daga ita har mijinta duk hakan ne, sai dai duk yadda Hassan yaso ta yarda a duba musu gender din babies din kin yarda tayi tace babu kyau, amma a cikin zuciyarta tana tsoron abinda zata gani ne, idan maza ne to maganar wannan mutumin mai duban nan zata tabbata kenan idan kuma mata ne to sauran maganar sa ma zata kasance karya ce kenan kuma hakan yana nufin dole ta sake sabon shiri dan ba zata iya cigaba da wannan zaman ba kullum cikin bakin cikin yadda Hussain da Fatima suke bushasha da kudi ita kuwa tana faman lissafi. Hassan yana ta fama da tarin kudin siyan kayan babies yana lissafin nawa ne zasu isa nawa ne ba zasu isa ba sai gashi rana daya Hussain da Fatima sunyi wata tafiya suka dawo musu da komai da ake bukata na haihuwa. Komai da komai, tun daga kan crib har kan diaper kuma komai na twins. And knowing the Hussain we know, komai na zamani ya siya kuma komai mai tsada. Rashin sanin gender ya saka suka siyo gender neutral, suna dawowa aka shiryawa babies din nursery dinsu a kasa using grey color da theme na forest. Duk rashin godiyar Ruqayyah sai da tasan cewa sun kyautata musu dan dakin babies dinta ko a films ita dai bata ga irin sa ba, hatta nata kaya bukatun na haihuwa an siyo mata, sannan Hussain yace Fatima ta tambayeta in akwai wani abu kuma daban da take bukata ta fada ayi mata. Sai kuma yayi suggesting in watan haihuwarta yayi a fita da ita waje ta gaihu a can dan tafi samun medical care mai kyau. Tashin farko Hassan yace a'a "idan masu kudi suna fitar da matan su waje in zasu haihu ka gaya min ta yadda za'a gyara asibitocin kasar nan" Hussain yace "ohhh. Takan matarka za'a fara misali kenan? Sai ka bari idan matar president ta haihu a Nigeria sai kaima taka ta haihu a nan, at least sai in san footsteps din shugabanni kake bi" Hassan yace "ni ban damu da shugabanni ba fa, ni kaina na sani and I know that I can make a difference. Idan da kowa a Nigeria zai saka a ransa cewa zaiyi making a difference, zaiyi setting good example, dana tabbatar abubuwa zasu yi mana sauki a kasar nan" Hussain yace "to Allah ya bada saa good samaritan, ni dai duk ranar da matata zata haihu to sai na samu asibitin da yake one of the best a duniya sannan zan kaita ta haihu" Hassan yace "a dawo lafiya, mu muna nan kuma in dai an haihu lafiya din ai shine abinda ake nema" Duk da cewa a tare take da Aunty, ga kuma yaran da suke gidan ta amma da watan haihuwar yazo sai da Hassan ya roki Baba akan cewa Sumayya ta dawo gidan su da zama saboda ba'a san sanda haihuwar zata zo ba. Allah yasa su Sumayya suna hutun semester dan haka ta taho din dan itama tana son ayi komai a gabanta da inda hali ita mai iya karbar wa yar uwarta wani part na ciwon haihuwar ne. Tare suke wuni da rana, da dare kuma Ruqayyah ta tafi gurin mijinta su kwana tare, wanda duk juyi sai ya tambaye ta ko akwai abinda take buƙata. Da ranar ma kuma haka Sumayya take lallabata tana koya mata irin abubuwan da take koyo a makaranta da kuma abubuwan da suke haduwa suyi browsing tare da al'amuran da suka shafi ciki, haihuwa da kuma prenatal. Suka yi installing wani application mai suna Baby Center wanda yake taimakawa masu juna biyu sosai gurin tracking cikin su sunan kowanne stage da kuma abinda ya kamata suyi expecting a stage din, akwai tips na abubuwan da zasu kara wa mai ciki lafiya da kuma abinda ya kamata ta guda wadanda zasu iya harming dinta ko abinda yake cikin ta. Sannan kuma akwai signs and symptoms na labour, yadda mace zata banbance true labor da false labor, yadda zata ke timing contractions dinta dan tasan how far along in labor take da kuma yadda zata ke counting baby kicks dan ta tabbatar da lafiyar abinda yake cikinta. (Try using it in kina da ciki, am sure zaki ji dadin app din) Sanda Sumayya take yi mata wannan bayanin sai Ruqayyah ta tabe baki tace "they are always kicking, bana jin ina bukatar wannan". Wannan ilimin data samu ya saka laborn yana zuwa ta fahimci shine, anan ne kuma hankalin ta ya fara tashi tana jin tsoron wahalar haihuwar amma kuma bata jin tsoron mutuwa "in na mutu a haihuwa nayi mutuwar shahada kenan" Tun safe ta fara, ita da Sumayya suna ta timing contractions din suna son sai ciwon ya fara zuwa kurkusa sannan zasu fada wa Aunty, dan haka wajen azahar Sumayya ta kira Aunty ta gaya mata, ai kuwa sai gata da kanta tazo, tana ganin yadda Hassana already ta fara shan wahala sai ta kamata da kanta ta saka ta a mota, Sumayya ta debo kayan da suka hada a jaka na zuwa asibiti suka tafi, dama Hussain da Fatima basa kasar a lokacin. Duk sun dauka ba zasu dade a can din ba Ruqayyah zata haihu amma sai gasu har magrib, dole suka kira Hassan suka gaya masa dan kar yaje gida ya tarar basa nan, amma duk da haka aunty tace kar a gaya wa Inna saboda kar hankalin ta ya tashi gwara a bari sai ta haihu tukunna a kira ayi musu albishir. Karfe goma sha biyu na dare Ruqayyah ta haifi santalelen jaririnta namiji, bayan ta leka lahira ta dawo, karfe daya na dare kuma ta haifi na biyu, shima namiji, dukkanin su masu kama da baban su da yake tsaye a bakin kofa cikin dimuwa yana jira. Sorry for the typos Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki ki neme ni through WhatsApp ta wannan number din 08067081020 *Unveiled* Bakin Aunty har kunnen ta saboda murna, aka miko mata na biyun ma ta hada dana farkon ta rungume a jikinta tana jin hawayen dadi yana taruwa a idonta, ganin jariran sai ya tuna mata da ranar da aka haifi Hassan da Hussain, sai ta tuno da yar uwarta, take taji son yaran ya shiga ranta kamar yadda taji tana son Hassan da Hussain lokacin da aka haife su. Ta juya tana kallon Ruqayyah wadda take ta mazar kwalla ana yi mata dinki, tabbas ta jinjina wa kokarin yarinyar yadda ta haifi yan biyu da kanta duk da karancin shekarun ta. Sai dai fa tabbas ita kanta auntyn ta san ta sha wahala ba kadan ba. Duk da azabar da take sha amma bai hana ta tambayar Aunty ba "aunty me na haifa?" Aunty ta shafa kanta tana murmushi tace "duk maza ne Ruqayyah" Ruqayyah ta sauke ajjiyar zuciya, deep down tana jin dadi saboda hakan yana nufin sauran maganar mai duban nan itama gaskiya ce, zata yi kudi fiye da wanda take saka rai. And she just can't wait. Ko ma menene option din tasan zata yi decision mai kyau wanda zai amfane ta ya amfani ahlinta baki daya, ya amfani twins dinta. Ta fita da yaran a hannunta zuwa waiting room inda Hassan yake ta faman safa da marwa dan kunyar Aunty ce kawai ta hana shi shiga ayi labor din tare dashi. Yana ganin ta da yaran ya tafi gurin ta da sauri yana mika hannu sai kuma ya janye hannun yana murmushi, tayi dariya "karbi abinka, ai kayi kokari, da wancan marar kunyar ne da har ciki zai bini yace in fito in basu guri" yayi murmushi yana mika hannayensa duk biyun ita kuma ta saka masa yaran a kowanne side, ba zai iya misalta farin cikin da zuciyarsa take ciki a lokacin ba, ba zai iya misalta soyayyar yaran da yaji a cikin zuciyarsa ba tun daya dora idanuwan sa akan su. Sumayya ta leko da kanta ta gefensa tana kallon babies din tana murmushi, hannunta yana yi mata kaikayi tana so ta dauke su, ta miko hannu amma sai ya maze yayi kamar bai ganta ba. Dole ta hakura ta cigaba da leken su ta gefensa. Ya dago kai yana kallonta yace "suna da kyau ko?" Ta gyada kai da sauri tace "suna da kyau sosai ma. Kama suke yi da kai" ya girgiza kansa yace "no, da Hussain suke kama" tayi dariya, "da Hussain da kai ai duk kamar ku daya" shima sai yayi dariya yace "da yana nan da kunyi fada yanzu, zai ce ya fini kyau ai" ita ma tayi dariya tana shafa hannun daya daga cikin babies din, sai kuma ya bata daya ya zauna da dayan a hannunsa yana yi masa kiran sallah a kunnuwan sa. Ya gama ya miko mata shi ya karbi na hannun nata shima yayi masa. A lokacin ne aka turo Ruqayyah daga labor room zuwa dakin hutu, idanunta a rufe aka wuce da ita, sai kuma duk hankulan su ya koma kanta suka bita a baya sai Aunty ta dakatar dasu tace "anyi mata allurar bacci ne saboda ta huta sosai, kar ku shiga kuma ku dame ta" Hassan ya dan shafa kansa yana kara leka inda aka shiga da ita sai aunty ta karbi babyn hannunsa tace "shiga ka ganta, kar ka tashe ta amma ka barta ta hutawar ta Please, yarinyar nan ta sha wahala wallahi" ba musu ya mika mata shi da sauri ya shiga ya rufo kofa su kuma suka zauna a kujerun gurin Sumayya tana shafawa babies din dabinon data tauna suna ta lashewa tana dariya, sai kuma ta dan basu zam zam kadan, Aunty kuma ta dauko waya ta fara kiran yin albishir, Inna Ade ta fara kira ta gayawa, daga inda Sumayya take zaune tana jiyo muryar Inna tana hamdala sai tayi murmushi, Allah sarki uwa. Ko dazu da rana sai data kirawo su ta tambayi lafiyar Ruqayyah. Daga nan kuma sai Aunty ta kira Hussain, bata sami wayarsa ba sai ta kira ta Fatima ta gaya mata tace ta gaya masa. Ita ma tayi ta murna kamar ita aka ce ta haihu, sauran kuma Aunty tace sai gari ya waye tukunna tunda yanzu dare ne. Sumayya kuwa bata bari sai gari ya waye ba tuni ta dauki hoton babies din ta saka a social media. A lokacin nurses suka zo suka karbe su aka tafi dasu aka yi musu duk gwaje gwajen da za'a yi musu sannan aka yi musu wanka aka shirya su cikin kayan da aka taho dasu daga gida. Hassan yana shiga dakin ya ja kujera kusa da Ruqayyah ta zauna ya zuba mata ido, da ace zai iya hadiye ta dan kauna to kuwa da tabbas ya hadiye tan, ya rike hannunta a cikin nasa, yayi kissing hannun, still yaji hakan bai yi masa ba sai ya sunkuya yayi kissing goshinta, ta dan bude ido kadan tana kallonsa dusu dusu sai yayi mata murmushi yace "sannu Hassana. Allah ya baki lafiya kinji" cikin magagin bacci tace "bana so" yace "menene ba kya so? Gaya min menene ba kya so?" Tace "suna Hassana, bana so" sai ta koma baccin ta. Yayi shiru yana kallonta ammaya kasa judging komai a cikin maganar ta, maybe abinda yake ranta kenan, maybe kuma magagin allura ne. Bata tashi ba sai da gari ya waye, har Inna da Baba dasu Sulaiman sunzo, yammatan Aunty ma kaf dinsu sun zo kowa yana ta daukan babies ana yabawa. Hassan kuwa baki har kunne ya kasa boye farin cikin sa. Ganin ta farka yasa hankalinsu ya dawo kanta suka yi ta mata sannu tana amsawa sai dai ko yaya ta motsa sai taji gurin dinkin da aka yi mata yana damunta, ganin bata da wani problem ya saka Aunty ta nemo musu sallama kuma a take aka sallame ta suka dawo gida. Part din aunty suka sauka, anan Aunty ta hada ruwa mai dumi da isasshen detol ta saka ta shiga ciki, "ba za'a saka miki ruwa mai zafi sosai ba saboda dinkin zai iya budewa, zafin ruwan yana iya lalata zaren da akayi dinkin dashi" sannan kuma ta gasa mata jikinta sosai da towel tana fitowa kuma aka kawo mata tuwon kanwa miyar kukar da Inna Ade ta tashi tun asuba ta tuka mata shi ta taho mata dashi, sannan kuma aka kawo mata dahuwar nama mai romon da Aunty tayi mata, sai ta zauna ta ci naman tuwon kuma taki ci. Tana cikin ci Sumayya ta shigo da babies din ta kwantar dasu akan gado tana cewa "ni fa Ruqayyah banga kin dauki yaran nan ba, ya kamata ki dauke su suji dumin jikin ki suji dadi suma" Ruqayyah ta harari inda babies din suke tace "bayan sun gama bani wahalar? Ai dole duk dan da bai bi uwarsa ba ya hadu da bala'i" Sumayya tace "am glad kin fara fahimtar haka" Ruqayyah ta daga kafada tace "me kuma nayi?" Sumayya ta nuna mata tuwon Inna Ade tace "baki ci tuwo ba, dan ke ta zauna ta tuka shi sannan tayo dakonsa tun daga gida har asibiti har nan gidan amma still baki ci ba" Ruqayyah ta tura baki "ni baki na babu taste ai, ya za'a yi mutum ya haihu a kawo masa wannan bakin tuwon fisabilillahi" Sumayya ta jawo robar yajin daddawan da Inna ta taho dashi tace "saboda tasan bakin ki babu taste shi yasa ta hado miki da yaji dan ki zuba kiji taste din, ga kuma man shanu ta kullo a leda duk dan saboda tasan halinki kar ki ƙi ci. Ki tuna, irin wannan wahalar da kika sha irinta itama ta sha lokacin da zata kawo mu duniya" Ruqayyah ta sake hararar yaran da suka fara mutsu mutsu tace "irin wancan harbe harben fa suke min a cikina, duk sunbi sun duba min fatar ciki na" Sumayya tayi dariya tana zuba mata tuwon tace "kin san fa naji ance tuwon kanwa yana taimakawa wajen samar da ruwan nono ga mai jego, ki samu ki ci ko suma sa samu abinda zasu saka a cikin su" Ruqayyah tace "chafdi, ai kuwa dai babansu dole ya bude bakin aljihu ya siyo madara dan bazan iya shayar da su duk su biyun ba wallahi. Sai an siyo madara an hada musu da ita" Sumayya tace "wannan kuma tsakanin ku ne, ni dai abinda nake so shine ki ci tuwon nan sai ki dauki yaran nan ki basu nono su sha. Kim san kuwa cewa wannan ruwan nonon na farko yellow marar kauri yafi komai amfani a gurin jariri? A cikin sa anti bodies suke, suna sha shi zai zama kariya gare su daga dukkan wani abu da zasu saka a bakinsu nan gaba. Dan haka ko ma ba zaki basu nonon ba kwata kwata ki daure ki basu na farkon su sha" Da kyar da lallabawa Ruqayyah ta dan ci tuwon Inna kadan, sannan Sumayya ta dauko mata Hassan dinta tace "wannan shine babba, a fara bashi tunda ya riga dayan zuwa duniya" Ruqayyah takarbe shi tana kallon sa fuskarta da murmushi "da babansa yake kama" ta fada tana lakuce masa hanci" saura kuma kayo halin babanka" Sumayya ta zauna kusa da ita hannunta rike da dayan tana kallon yadda Hassan din yake ta kokarin kama abincin sa, tace "mene halin baban nasa? Kirki?" Ruqayyah ta harare ta "so kike yi inyi magana ki fara yi min wa'azi, kin san halin nasa ai" Sumayya tace "hmmm Ruqayyah kenan. Ruqayyah ki gode wa ubangijin ki. Babu abinda bai yi miki ba a rayuwa. Kin san kuwa akwai matan da babu abinda ba zasu yi ba dan su samu miji irin Hassan? Amma ke kina korafi? Ubangiji bayan ya yi ki mutum mai daraja a cikin halittun sa sai yayi ki musulma wadda aka haifa a gidan ilimi, sai kuma ya baki lafiya, hankali, ya baki iyaye da mu yan uwa masu tsananin sonki, sai kuma ya dauki miji one in a million ya baki, miji kuma mai tsananin sonki sannan yanzu kuma ya baki haihuwa, da kika tashi haifa bai baki daya ba sai ya baki biyu, biyun ma sai ya baki su duk maza, zaman da shi da kansa yace sune zugabanni akan mata. Ko gaya min, which among the favors of your God do you deny?" Ruqayyah ta saki baki tace "ni yanzu da kike min wannan lissafin me kika ji nace ne?" Sumayya tace "baki ce komai ba, na fada ne dai tun kafin ki ce din" ta mike tana ajiye haririn hannunta sannan ta tattara kayan abincin ta fita dasu. Da kyar Inna Ade ta lallaba Aunty ta bar ta ta tafi da Ruqayyah gida wankan jego, sai dai ita Ruqayyan ce gaba ki daya ba haka taso ba ita so tayi a barta tayi zamanta a gidanta, ta fara mita "to yanzu in na tafi can Inna kuma wadanda zasu zo min barka kamar sababbin kawayena da matan abokan sa ya zasu yi kenan?" Inna Ade tace "shi ai yasan gidan, sai yayi musu kwatance su je, ke ma kuma sai kiyi wa kawayen naki. Ba kuna waya ba?" Ta kara bata rai "Ni yanzu can din ne Inna ban san inda zanke ajiye baki ba, kuma dakin Sumayya yayi mana kadan ni da yaran da ita, kuma....." Inna tace "Sumayya sai ta dawo dakina ke kuma ki zauna a nata, in yaso in yaran sun tashi kukan dare ke sai kiyi ta rarrashin su ke kadai. Ke da ba a miki abin arziki har zaki nuna ke ba kya son zuwa gida wanka. To kuma da a wancan daya gidan muke kuma fa? Da ya zaki yi? Dolen ki dai can din shine tushen ki shine tutiyarki, nan gidan mijin ki ne ba gidan ki bane ba* Ruqayyah tayi shiru a ranta tana jero istigfari dan bama zata iya imagining komawa wancan gidan ba. A ina zata kwanta? Ita kuwa inna a ranta taji zafin abinda Ruqayyah tayi, godiyar ta ga Allah da babu kowa a gurin sai su kadai dan da ta basu kunya a cikin dangin mijin ta. Wannan kuma shi yasa Baba ya dage sai ta taho da ita "in dai har mijinta ya bari ki taho da ita gida tayi wankan ta anan, ayi taron suna anan, dan a tuna mata cewa nan ne gidan su ba can ba". Sosai Ruqayyah take samun kulawa, ko juyi tayi Sumayya ko Inna zasu tambayeta abind take so. Ita kuma sai iko take zubawa da iyayi son ranta. Duk baya kwana biyu kuwa sai Aunty tazo ta ganta sannan kullum sai tayi abinci ta turo wata a cikin yayanta takawo mata. Hassan sau biyu yake zuwa, safe da yamma, kuma bashi da shamaki da har dakin yake shiga gurin matarsa da yayansa. Kullum kuma yazo sai tayi masa mita, "jiya sauro ya ciji Hassan" "yau Hussain ya kasa bacci da safe sabida hayaniyar mutane" ita dai kawai so take yace tazo su koma gida shi kuma ya toshe kunnuwan sa yayi mata kamar bai san me take yi ba saboda duk da cewa shima yana son su zauna tare amma ba zai iya taka maganar Baba ba.. Ranar suna ta zagayo aka sakawa yaran sunan mahaifin su Hassan "Aminullah" da kuma sunan Baba "Yusuf" ko wanne kuma aka bar masa sunan sa ba'a boye musu ba. Ruqayyah an sha hidima, a shiga wadannan kayan a fita wadannan, kawayenta suna kara zuga ta na kara kumbura kai duk dama dai ba haka taso ba, taso ayi a gidan ta ne ko gidan aunty tunda sunfi girma da kaya masu tsada. A ranar sunan ne kuma Hussain da Fatima suka zo, ba a ranar ya shirya zasu dawo ba sai dai yadda Fatima ta matsa tana son ganin babies din ya saka a dole yayi squeezing ya gama abinda yake da wuri suka taho, duk kuwa da cewa taga babies din a waya. Suna sauka direct gidan sunan suka taho, suna zuwa gaba ki daya idanuwa suka koma kansu, yan tsegumi suka fara, Hussain har cikin palo ya shiga duk da mutanen da suke ciki ya dauki babies din aka yi musu hotuna sannan yayi wa mutanen gurin ruwan kudi ya tafi, tafima kuma ya barta a gidan. A take maganganu suka fara wayo "wannan waye haka?" "Ai shine mai kamfanin nan na H and H" "au ba mijin Ruqayyah bane ba dama mai H and H din ba?" "Aa, wannan ne, mijin Ruqayyah dan uwansa ne" "kun ga matarsa kuwa?" "Ai Yar yar sarkin kano ce" maganganu dai iri iri, a take marokan da Ruqayyah ta saka aka dauko mata hayar su dan suzo su koda ta a gaya wa mutane wanne irin suna akeyi sai suka juya kan Fatima suna yi mata kirari, ita kuma ta bude bakin jaka tayi ta musu barin kudi. Wannan ya saka Ruqayyah ta zare jikinta ta koma daki ta cire gwagwgwaron ta yi kwanciyar ta, sai ga Fatima ta shigo dakin ta tsaya tana kallonta tace "lafiya Ruqayyah kika kwanta ana tsakiyar taron sunan ki?" Ruqayyah ta juyo tana kallon ta tana yamutsa fuska tace "wallahi stitches din nan ne suke min ciwo, sun takura min. Kin san azabar zafi ne dasu. Ko da yake ashe fa ke baki sani ba ko?" Ta juya ta cigaba da kwanciyar ta. Bayan Fatima ta koma gida tun da ta shiga babu labarin da take yi irin na taron sunan Ruqayyah. "Ruqayyah tayi kyau, twins din nan sunyi kyau sosai, sooo cute. Kamar in sako su a jaka ta in taho dasu in kawo mana su gida" Hussain yayi dariya "kar ki damu, in duka dawo gida zamu ke dauko su suna yi mana wuni anan" ya sunkuyar da kansa yace "kafin mu samu namu muma" sai tayi shiru tana breaking knuckles dinta, ya tsaya yana kallonta dan yasan wata magana take son fada, sai tace "Mi Amour, nace ko zamu fara zuwa asibiti ne?" Ya girgiza kansa da sauri yana rike hannunta yace "ko wata goma fa ba'a yi ba da bikin mu, let's not be inpatient please, mu jira ikon ubangiji kinji Princess. Our time will surely come kinji?" Ta gyada kai a hankali, ya jawo ta jikinta yace "nima ina so Fatima, ina son naga jinina a duniya ko ba biyu ba ko daya, ko mace ko namiji, ina so nima. But nasan cewa what ever will be will be". Ta kwantar da kanta a kirjinsa tana sauraron bugun zuciyarsa, sun jima a haka sai wayar sa ta fara ruri ya dauko ta ya daga kiran ya saka a kunne. "Manya manya maganin kanana kanana. Ya akayi? Ya garin? Nayi fushi ai in dai har ka kuma barin kasar nan ba ka zo kaga gidana ba to nasan matsayi na" ya danyi shiru sannan yace "ai na gaya maka tun ranar nan da muka yi Magana, in har baka gwada ba babu ta yadda zaka yi ka tabbatar cewa zasu baka auren yarinyar nan ko kuma ba zasu baka ba? Fargaba fa asarar namiji ce" yayi dariya "ka sami takawan kawai ka gaya masa halin da ake ciki, shi zai tura a nemar maka auren ta" "oh haka yace? To shawara ta rage naka kuma, amma ni dai personally bana giving up without trying, ka shirya kaje Riyad din da kanka ka nemi auren yarinyar nan in an baka you come and thank me in ba'a baka ba kuma to kar kace ni na baka shawara" yayi dariya, "gata nan a kirjina. Kai dai tsaya wasa sai da kaga munayi" ya cire wayar daga kunnensa yana dariya, ya juya yana kallon Fatima "mutumin ki dai ya kusa zuwa karshen katanga. Babansa ya ki zuwa nema masa auren balarabiyar nan" ta gyara kwanciyar ta a kirjinsa tace "shine kai kuma kake zuga shi ya tafi shi kadai ko? Ba zasu bashi ita ba ko me zaiyi. Am sure" yayi ajjiyar zuciya yace "I know. But there is no harm in trying, right?" A daddafe Ruqayyah tayi sati uku a gidan su, sai kawai ta shirya plan ta gaya wa Inna Ade cewa Hassan yace ta shirya zai zo ya dauke ta su koma gida, sai kuma ta gaya wa Hassan tace Baba yace yazo ya dauke ta su tafi. Shi bai san me ta shirya ba yayi ta murna ya gaya wa Aunty, ita kuma ta saka aka gyarawa Ruqayyah part dinta duk dan ta faranta mata. Ita kuma Ruqayyah ta dawo da niyyar in Fatima ta taba mata ya'ya ta gurza mata amma sai ta tarar Fatiman ma bata kasar gaba ki daya. Wannan ya kona mata rai, ita gani take yi wannan tafiye tafiyen kamar dan a kona mata rai ake yin su. Farkon dawowarta tare da Sumayya suka dawo, Sumayyan ce kuma tayi mata register da online catering classes da yawa inda take koyon girke girke da sauran kitchen tips kuma suna gwadawa tare a kitchen dinta, sannan suka koyi yadda ake amfani da kitchen appliances din da suke kitchen din nata. Anan ne Sumayya ta gwada tambayar ta ko tana da niyyar komawa karatu? Tayi dariya Tace "karatu kuma? Ni dama tun farko ai kin san ina karatu ne saboda in yi kudi, yanzu already ina da kudin da ko aikin nake yi ba lallai in samu albashin da zai bani wannan rayuwar ba so why should I bother myself?" Sumayya tace "shi karatu fa ai ba dan ayi aiki ko dan ayi kudi ake yinsa ba ko? Nima da nake karatun ba lallai ne inyi aiki ba musamman in na samu mijin da baya son matarsa tayi aiki ai kinga dole in hakura ko ? Tunda dai ai auren yafi aikin" Ruqayyah tace "say what you may, ni dai ba wata school da zan koma". A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, bakar zuciyar Ruqayyah tana nan a kirjinta amma har yanzu dafinta bai bayyana ga Hassan ba. A haka akayi bikin Minal da alhajin ta lokacin su Yusuf suna da watanni uku a duniya. Ruqayyah tana tsananin son yayanta a zuciyarta amma being the Ruqayyah that she is, bata iya nuna soyayya ba dan haka sai ya zamanto yaran sunfi sabawa da Abban su, sai uncle dinsu wanda in dai yana gari to kullum suna tare har ya iya hada musu madara yayi feeding dinsu. Daga nan sai Aunty wadda dama daga sun dami Ruqayyah zata hada su da mai renon su su tafi gidan aunty, ita kuma ta dauki wayarta ta cigaba da daukan darasin mallakar miji. A lokacin bikin Minal ne kuma Minal din da kawayenta suka zo gidan Ruqayyah da niyyar zasuyi bridal shower dinsu anan. Sai dai suk ayi rashin Sa'a suka tarar Hassan yana gida kuma Ruqayyah bata gaya masa za'a yi event din ba. Ya shigo yana kallon su, yana lura da yanayin shigarsu da kuma yadda babu wadda ta gaishe shi a cikin su. Sai ya sunkuya ya dauki yaransa y ahau sama da su, Ruqayyah ta bishi a baya. Tana shiga dakin sa taga ya ajiye yaran akan gado yana musu wasa suna bangala masa dariya, ta tsaya a bakin kofa tana murmushi, bai kulata ba tace "dama bikin Minal dana gaya maka an fara, shine kawayen mu suka zo zasu dan yanka cake su kuma yi hotunan" ya juyo yana kallonta yace "kawayen ku? I thought you said kawayen Sumayya ne da na Minal? Ina ita Sumayyan take? Ko bata zo ba sai kawayenta?" Ruqayyah ta dauke kai gefe tana juya ido yadda ba zai ganta ba sannan ta karasa shiga dakin, ta dora kanta a bayansa tace "to yanzu menene dan nace musu kawayena? Ina laifin wanda ya kula ka? Ka manta su suka tsaya min da bikin mu?" Ya juyo yana kallonta yace "ina fa zan manta? Har duk rashin kunyar da suka yi min ina sane da kowacce kalma. I thought daga ranar ba zaki kara kula su ba saboda marar tarbiyya ne kadai zai riki wadannan a matsayin kawaye, baki san masu magana sunce 'nuna min abokin ka Ni kuma in gaya maka halayen ka ba?" Ta daga shi tana jin ranta yana fara baci tace "ni banga abin daga hankali a wannan maganar ba, ko ma menene sukayi ko suka ce ai ya wuce ko? Idan da kai wani ne yanzu da ba sai dai inji kace ka dauki nauyin duk abinda za'a yi a gidan ba, ko kuma inga ka fita ka siyo mana duk abubuwan da muke bukata ba? At least haka akeyi a gidajen arziki, at least da Hussain ne da hakan zai yi ba wai ya zauna yana mitar abinda akayi shekara guda data wuce ba" Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kuna son ki sayi halaliyar ki ki neme ni ta wannan number din through WhatsApp 07067081020 *Unveiled 2* Farko daskarewa yayi a zaunen da yake, sai kuma yayi blinking idonsa dan ya tabbatar cewa ba wai mafarki yake yi ba, sai kuma ya saka hannu yana bubbuga kunnuwansa ko sune suke yi masa karya sannan ya juyo yana kallonta, bakinsa da idonsa a bude amma kalma daya ta kasa fita daga bakin nasa, so yake ya tabbatar ita ta fadi wadannan maganganun, har da waigawa yayi dan ya tabbatar su kadai ne a dakin ba wata ce ta shigo ta fada ba, sai dai yana yin daya gani a fuskarta kadai ya isa ya tabbatar masa da cewa ita ta fada din. Rashin gaskiya kiri kiri a rubuce a fuskarta. Ta tosa kanta da sauri tana nin gabaki daya jikinta ya dauki kaikayi, sai kuma ta juya da sauri zata bar dakin. Tana son ta kasance ita kadai tayi bitar abinda tace din ta kuma shirya abinda zata ce ta rufe maganar tata. Charaf ya rike hannunta,bata juyo ba sai idonta data rufe, ya mike daga kan gadon ya zagayo gabanta sannan ya saka cika hannun nata ya rike fuskar ta da hannayensa biyu. "Hassana?" Ta kwace fuskarta ta na kokarin juya masa baya ya sake rike ta, jikinsa har rawa yake yi "Hassana me kika ce min? Me kike cewa? Wacce magana kike gayamin Hassana? Are You okay?" A ransa ya fara tunanin anya ba aljanu suka taba Precious wife dinsa ba? Bata ce komai ba still, yace "gidan arziki Ruqayyah gaya min me kike nufi da gidan arziki? Hussain? Da ace ni Hussain ne? Me kike nufi da haka?" Tsabar zafin da maganar tayi masa ya hana ya nuna bacin ransa sai ma karyewa da zuciyarsa tayi. So yake tayi magana, so yake ta gaya masa bata fada masa wadannan maganganun ba kawai imagination dinsa ne. Ta bude idonta ta sauke su a kansa "kayi hakuri mijina ban fada da niyyar in bata maka rai ba, kawai dai ji nayi nawa ran ya baci kuma ban san na fada maka haka ba" ya sake ta, ta fada din kenan, bawai kunnensa ne bai ji masa dai dai ba wai imagination dinsa bane ba Hassana ce tace gidansa ba gidan arziki bane ba, da Hussain ne zaiyi abinda shi ba zaiyi ba. Tana jin ya sake ta ta juya da sauri ta fita tare da rufe kofar, da ace da key a hannunta ma da rufe shi zata yi ta waje dan ita kan ta tsorata da fuskarsa da kuma rikon da yayi mata. Amma wannan bai hana ta shiga dakin ta ta dauko kudi ta fito gurin kawayenta suka cigaba da hidimar su ba. Sai da suka gama sannan ta fito da kudin ta basu tace inji Hassan yace suyi kudin mota. Minal tace "shi wannan mijin naki wallahi da kayan haushi yake, maimakon ma yace ga driver nan a waje a kai kowa gidansu sai ya wani bamu kudi?" Daya a cikin kawayen ta karbe kudin tana lissafawa tace "mu dai muna so, ke dan kin samu zaki shiga daga ciki shine har zaki yi yanga in an baki kudi?" Suka raba kayansu kowa ta saka a jakarta. Ruqayyah tabi jakankunan su da kallo tana hadiye daci a ranta, ta jima tana tara kudin nan tana son siyan wata sarka. Da zasu tafi Minal ta jata kefe "to sai kin shigo dinner gobe" Ruqayyah tayi ajjiyar zuciya "dinner nan Minal ba lallai bane in shigo ta" Minal ta bude ido "amma kuwa da kin cika babbar marar m...dinner din bikin nawa zaki ki zuwa" Ruqayyah tace "ba cewa nayi ba zan zo ba, cewa nayi ba lallai bane inzo din, kin san ai komai sai Allah yayi ko? Ku tafi kawai, zamu yi waya zan baki labarin abinda yasa nace haka" Minal ta bata rai "ko ma menene ni ba uzuri bane ba a gurina, kuma in baki zo dinner ba wallahi nasan matsayina a gurin ki kuma na san kema a gurin da zan a jiye ki a zuciyata" Ruqayyah dai ta lallabata ta raka ta waje suka shiga motar da alhajin ta ya aiko ta dauke su. Ta gefen idonta ta hango Adam yana fitowa daga part din Hussain yana tafiya hanyar shiga part din Aunty, a can yaje tare da sauran yaran Hussain a tsofaffin dakunan su Hassan. Ya saka hannunsa a aljihu yana taku dai dai jikinsa sanye da kaya masu kyau, in ka ganshi zaka iya tunanin kanin mai gidan ne dan yarintar sa ce kawai zata sa ba zaka ce shine mai gidan ba. Tayi tsaki, ta tsane shi har cikin zuciyarta, ya tsani guts dinsa, yadda yake tafiya da yadda yake magana da komai nasa. More importantly ta tsani alakar sa da only sister dinta. God knows tana son Sumayya har cikin ranta kuma zata yi iyakacin kokarin ta ta ga cewa alakar Sumayya da wannan tubabben bata cigaba ba, bata je inda su suke son taje dinba. She can't imagine having nephews and nieces masu Christian blood a jikin su, masu kama da kedarai. Ta kara tsaki tana juyawa cikin gidan ta, dole zata nemi hanyar raba wannan alakar duk da tasan ba zata samu goyon baya daga Sumayyan ba ko Baba ko Inna but duk da haka she will find a way, zata yi shawara da zuciyarta kuma tadan zata samu mafita kamar yadda kullum zuciyar tata take bata mafita a duk problems dinta. Yanzu ma already ta bata mafita akan problem dinta da Hassan. A palo ta fara tsayawa tana bawa yaran ta directives na yadda zasu gyara gidan, sannan tayi musu sallama ta hau sama. Dakin ta ta shiga ta fara yin wanka ta shirya cikin kayan bacci masu daukan hankali ta dauko ajjiyoyin kayan matan ta ta sha na sha ta shafa na shafawa. Tunda suka yi aure bai taba resisting dinta ba kuma bata jin zai fara daga yau. Tunda Ruqayyah ta juya ta fita Hassan ya zame ya zauna a bakin gado ya dafe kansa da hannayensa biyu. "What just happened? What happened to his perfect precious wife? Did she just said what she said ko kuma zuciyarsa ce take playing tricks on him? Ta tabbas there must be an explanation to her behavior ko dai yayi mata wani laifi ne mai girma da out of anger ta fada masa haka? Amma shi duk a tunaninsa bai tuno wani abu da yayi mata marar dadi ba. Ya tuna a yanayin da ta gaya masa maganar, babu wani emotions irin kamar normal mutum yana magana ne directly from her heart, daga dukkan alamu itama bata san ta fada ba sai bayan data fada din. Zuciyarsa tana ta kokarin kawo masa wani excuse da zai kare ta amma kwakwalwar sa taki karbar excuse din, sai ma wadansu maganganu da suke fado masa a rai. Farko maganar Baba "zan so ka janye auren Hassana ka auri Hussaina a madadin ta" Hussain "in har zata iya yaudarar top criminals ta haka mudu rami su fada ciki why not you?" Sumayya "kayi ta hakuri, kana addu'a kuma kana saka ido". Ya mike yana jiyo karar kidan da suka kunna a kasa, Yusuf ya fara kuka, ya dauke shi yana rarrashinsa, Aminu ya saka kuka shima yana miko masa hannu, ya durkusa shima ya dauke shi yana zagaya wa dasu a hannunsa yana raba idonsa a tsakanin fuskokin su. Sai ya samu kansa da tambayar kansa "Did he make the worse choice for the most important thing?" "Did he chose a bad wife for himself and a bad mother for his children?" Where was his carefulness? Ya shiga da yaran toilet dinsa ya saka su a wash hand basin ya wanke musu jikin su da ruwan dimi, suna ta wasa suma jika shi, ya fito da su ya kashe acn dakin ya goge musu jiki sannan yaje dakinta ya samo musu kaya yazo ya saka musu, ya koma ya dauki madara ya hada musu ya basu, a take suka yi bacci ya kwantar dasu yana kallon su sannan shima ya kwanta a tsakiyar su tare da rufe idonsa, amma bacci shine abu na karshe a zuciyarsa. "At least haka akeyi a gidan arziki, da Hussain ne da haka zaiyi va wai ya zauna yana complain akan abinda akayi shekara guda data wuce ba" Ya girgiza kansa yana son ya cire maganar ta daga cikin kansa amma ya kasa. A haka yaji ta bude kofar dakin ta shigo ta tsaya tana kallon su Ta dan jima a tsaye tana assessing din sa shi da yayansa, yaran bacci suke yi amma shi tana kallonsa ta san idonsa biyu rufe idon kawai yayi. Ta karasa tare da dauke Yusuf ta mayar dashi kusa da dan uwansa sannan ta zauna a inda ta dauke shin tana dora hannunta akan goshin Hassan. Ya bude ido yana kallon ta, tayi masa murmushi "dama nasan ba kayi bacci ba shine ka wani rufe ido ko?" Bai ce mata komai ba amma ta hango wani bakon al'amari a cikin idon nasa, tace "wai fushi kake yi dani mijina? Kayi hakuri mana dan Allah ai kasan dai babu wani wanda yake baya kuskure a rayuwa ko? Nayi kuskure, raina ne naji ya baci a lokacin ka yafe min kaji mijina?" Sai taga yayi dan murmushi, a take taji hankalin ta ya kwanta, dama ta san babu inda fushin nasa zai je in dai har ta bayar da hakuri musamman kuma ace da wannan shigar a jikinta tana kuma wannan kamshin ai magana ta riga ta wuce. Sai taji yace "ranki ne ya baci ko? Kinsan wani abu. A lokacin da ran mutum ya baci a lokacin ne yake fadar duk abinda yake cikin zuciyarsa, so chances are very high cewa abinda yake zuciyarki shi kika fada min" ya fada idanuwan sa cikin nata. Ta fara jujjuya hannunta tana kokarin controlling anger dinta tace "don't be like that mana, haba mijina, ya kamata kayi min uzuri mana. Nima fa ina da zuciya a kirjina, kuma zuciyata tana son irin rayuwar su Hussain da matarsa yadda suke wadaka da dukiya suna zuwa duk ƙasar da suka ga dama a lokacin da suka yi niyya. What do you expect your wife to do? How do you expect me to feel bayan ka kawo ni ina zaune da kanin ka da yake da everything while you have nothing?" Ya mike zaune yana kankance idonsa a kanta, "do you just said "nothing"? Do you mean I have nothing?" Ta juya idonta, yau me yake faruwa ne da ita? Me yasa bata da sa'ar magana ne? Daga dukkan alamu yau da hannun hagu ta tashi daga bacci. Tace "ah ah. Me kake so ne ince mijina? Ina nufin kamfani nasa ne, gidan nan da muke ciki nasa ne, motar da kake hawa tasa ce, motar da nakr hawa shi ya siya. Komai da muke takama dashi a rayuwa nasa ne" ya ture hannunta daga jikin da ya mike tsaye, idanunsa sunyi ja jijiyoyin kansa sun fito, ya bude bakinsa zaiyi magana amma voice din ya kasa fitowa saboda ciwon da zuciyarsa take masa, da kyar yace "I understand. I now understand everything. Ni da ke Hassana yanayin yadda muke kallon rayuwa ba iri daya bane ba. Rayuwa ni a gurina ba wai tana revolving around yawan kudin da kake dashi bane ba, tana revolving ne around things that are much more important than money, like love, honor, friendship. But you have no idea me wadannan suke nufi do you? Yes, Hussain yana da kudi, but that doesn't mean ni bani da komai. Yes, gidan sa ne wannan shi ya gina da kudin sa but that doesn't mean ni bazan iya gina nawa ba. Na karba na zauna a ciki ne dan in faranta masa tunda burinsa shine mu zauna tare mu da iyalin mu, saboda yana so na, nima kuma na karba saboda ina son sa. Na fasa gina mana namu gidan ne saboda in siya wa Baba gida, saboda naga yafi mu bukata, saboda ina ganin sa kamar family na ne shima" "Ruqayyah bayan rai da lafiya da imani da Allah ya bani sai ya bani family, Aunty da siblings dina, masu sona sosai yadda na tabbatar ko da bani da komai zasu kula dani, ko d abana duniya zasu kula da bayana. Sannan ina da aikin yi ba zaman banza nake yi ba, wahalar da nake yi a aikin nan shi kansa Hussain yasan cewa ko shi baya yiwa kamfanin nan wahalar da nake yi masa. Ke kinfi kowa sanin cewa albashi na can more than sustain me, you and ko yaya nawa zamu haifa. And I have these...." Ya fada yana nuna babies din da suke bacci abin su "I have abinda babu wanda ya isa ya samar wa kansa sai Allah ya bashi. Do you know that last week Fatima ta matsawa Hussain sun fara zuwa ganin fertility doctor? Suna nema but mu Allah ya bamu gida biyu" ya tsaya yana kallon ta da jajayen idanuwan sa yace "I tot I also have a pious wife. Ashe I was wrong" ya bude toilet ya shige ya rufo kofa. He just can't stand the sight of her. Ta mike tsaye tana kallon kofar toilet din, tunda taaure shi tasan baya son nonsense shi yasa kullum in suna magana take jinta kamar mai tafiya akan tight rope kamar slight mistake in tayi zata fada ramin da ba zata iya fitowa daga ciki ba. And yau ta tabbatar da haka. Ta mike itama ta fice daga dakin ta koma nata dakin, tasan dama dole watarana sai haka ta faru a tsakanin su amma bata dauka hakan zata faru da wuri ba, plan dinta shine ta haifa masa as many yaya as possible yadda babu yadda zai yi da ita. Ta tsaya tana kallon sticker din data lika a jikin mirror dinta "Have you taken your pills today?" Sai ta saka hannu ta cire ta ta yar. Ta jawo drawer din da birth control pills dinta suke ta kwashe su gabaki daya taje ta zuba a waste bin. In yasan wata ai bai san wata ba. Ta kashe fitilar dakin ta kwanta, tana jin haushin sa a ranta, har da gori ma yayi mata wai ya siya wa baban ta gida. Tana jinsa ya shigo dakin, ya jera mata yayan ta a kan gado, yayi musu addu'a ya shafa musu sannan ya tashi ya fita. Ta juyo tana kallon yaran, sai kuma tayi murmushi, dolen sa yayan ta ne yaya kuma dole sai uwarsu. And yes. Hussain da Fatima sunje sunga fertility doctor a Washington DC. Doctor din yana kallonsu yana murmushi yace "one year you said?" Hussain ya daga kafada yana kallon Fatima da take twisting hannunta yace "she insisted sai munzo" doctor din ya juya yana kallon ta yace "am sure babu wani abu madam, but zamuyi running some tests dan mu tabbatar babu komai din. Pregnancy takes longer to get in some couples than in others ba tare da wani dalili ba". Daga nan aka fara yi musu tests, a dauki jini a dauki fitsari, vaginal swab, sperm samples da sauransu. Kwanan su biyu ana ta faman abu daya, Hussain dai yana zuwa ne saboda ya farantawa Fatima amma shi a ransa yasan babu mai bashi haihuwa sai Allah. A week after aka kira su karbar result, suka zauna kamar yadda suka zauna last week, Fatima looking very nervous while Hussain is relaxed yana ta tsokanar ta. Doctor din shima ya dan tsokane ta kadan sannan yace "results dinku gasu nan sun fito gabaki daya, amma babu wani problem da muka gani, gabaki dayan ku lafiya lau kuke kuma zaku iya samun haihuwa a kowanne lokaci. Abinda zamu iya yi muku na taimako kawai shine zamu baku magunguna da zasu yi boosting fertility dinku sannan zamu baku shawarwarin da zasu taimaka muku sosai da kuma diet din da shima zai taimaka wajen boosting fertility din. Most importantly kuma ke Madam dole kiyi relaxing ki kwantar da hankalin ki saboda anxiety, rashin kwanciyar hankali, yawan tunani da damuwa duk suna affecting fertility din mace" Hussain ya juya yana kallon Fatima tare da kama kunnensa daya yace "kina dai ji ko? To babu ruwa na" tayi murmushi. Aka gama yi musu bayanin duk da za'a yi musu, aka basu drugs dinsu aka sallame su. A hanya Hussain ya tasa Fatima da tsokana. "Sai kin shirya fa, tunda dai kinji sunce yawan yin abin nan yana kara chances, to double za'a ke yi yanzu" ta harare shi "to ayi double din ma mana, kasan dai ai bana jin tsoro ko?" Yace "kar ki cika baki fa? Sai kuma anzo gurin kuma ki fara neman a tausaya miki. To babu tausayi yanzu yarinya in....." Ta rufe ido "ka daina dan Allah kunyar ka nake ji fa" yayi dariya "to zamu karasa maganar a turaka". Washegari da safe karar wayarsa ce ta tashe shi, ya daga cikin muryar bacci yana cewa "Hello. Who is on the line please?" Daga can aka yi masa bayanin cewa doctor din daya gansu ne yake son ya dawo shi kadai, akwai maganar da za'a yi masa. Ya ajiye wayar yana danyin tsaki, ya koma ya kwanta yana kara jawo Fatima jikinsa sai kuma ya mike, ya sake tsaki sannan ya shiga toilet. Mintuna kadan har ya fito, motsinsa ya tashe ta ta dago kai tana kallonsa "ina zaka je?" Yana daura agogo yace "zan dan fita, ki koma baccin ki yanzu zan dawo. Zan yi musu magana su kawo miki breakfast" ta tura baki "bayan ka hana ni bacci da dare ba dole in rama ba yanzu? Ba sai sun kawo ba dan ni banga ranar tashi na daga wannan baccin ba. In ka dawo ka taho mana da shi" yayi murmushi, "better eat something Madam, kar in dawo kuma kice ke ga zance ga magana. Cos da nayi niyyar mu koma Nigeria gobe but yesterday night ta saka na chanja shawara, sai next week zamu koma. Anan za'a yi making baby din" ta dauki pillow ta jefa masa, sannan ta rufe fuskarta da wani pillown. Direct gurin doctor din ya koma, zuciyarsa tana ta yi masa sake sake iri iri. Doctor ya kalle shi da murmushi yace "kar ka damu da wannan kiran, I hope bamu tayar maka da hankali ba" Hussain yace "it is okay. What's up?" Doctor yace "result din da aka baku still stands, babu wani chanji. But a cikin gwaje gwajen da muka yi muku munga something da muke tunanin ya kamata ka sani kuma kayi taking action akai. It is just a suspicion Sir, we are not sure. Sai dai in ka yarda zamu tura ka gurin doctor din da zai sake maka wasu tests din for confirmation" Hussain ya gyara zaman sa yace "menene wai doctor, just say it" doctor ya gyara zama yace "we suspect that you have a column cancer" Yana shiga hotel room din ya bude labulen da sauri, haske ya shigo ya haske dakin. Fatima ta daga kanta tana kifta ido tana adjusting to light din sannan tace cikin muryar bacci "har ka dawo? Ka taho da abincin?" Yace "tashi ki shirya, we are taking the next flight back to Nigeria" ta mike zaune tace "What? Why?" Yace "I said we are taking the next flight back to Nigeria" yanayin muryarsa ya sa ta san da gaske yake, ta san kuma something has happened. Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani guri na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki ki yi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020 *The Brothers* Cikin mintuna kadan suka gama hada kayansu, ita dai duk bata yarda da yanayin sa ba tace "wai me ya faru a Nigeria ne? Ko wani ne ya mutu aka gaya maka?" Ya kalle ta yana kokarin kirkirar murmushi yace "babu wanda ya mutu fa, kawai ji nayi ina missing Hassan" ta kalle shi kawai amma a ranta bata yarda da uzurinsa ba tace "Hassan din da kuna haduwa zaku fara rigima? A waya ma ina jin ku kuna yi" yace "mun daina daga yau, daga yau ba zan sake fada da Hassan ba ko ya neme ni da fadan ma cewa zanyi ni bana fada" tayi dariya, shima yayi, at least ta dan ji dadin ganin yayi dariya hakan yana nuna mata ba mutuwar akayi ba, but something is definitely up. Sai da suka fito sannan suka samu abinci suka ci, har lokacin tana ta yi masa nacin sanin inda yaje da safe kuma me aka ce masa dan tasan abin yana da alaka da wannan tafiyar ta gaggawa amma sai yace mata abokin kasuwancin sa ne kawai ya gani, kuma kawai ji yayi yana son su koma gida. A hanyar airport ya kira Hassan ya gaya masa gasu nan zasu taho yanzu. A airport yaga wani bookshop, kawai sai ya shiga, a cikin jerin book yaga wani diary mai kyau mai girma kuma daga ganin sa zai yi kwari sai ya dauka tare da pen ya biya ya fita. Suna zama a cikin jirgi ya dauka dairy din ya bude front page ta fara rubutu. Dear Baby....... Fatima ta leko tana cewa "me kake rubuta wa ne haka?" Ya rufe littafin yana zare mata ido "ke, sirri ne" tayi murmushi "fada min, love letter kake rubuta min?" Yace "in kalaman soyayya zan gaya miki Fatima ba zan rubuta su a takarda ba, zan kalli cikin idonki ne in gaya miki, ko kuma in rada miki a kunnuwan ki" ta bata fuska "to wa kake rubuta wa?" Ya bude littafin ya nuna mata inda ya fara rubutu yace "our baby" tayi dariya tana shafa rubutun tana jin son babyn da ko cikinsa babu. Sai ta gyara zaman ta ta kwantar da kanta a kafadar sa tace "me zaka rubuta masa?" Yace "a letter. Daga yau kullum zan dinga rubuta masa letter har sai ranar da aka haife shi. In ya girma ya iya karatu sai in bashi ya karanta" tace "kullum? Me zaka ke rubuta masa kullum?" Yace "duk abinda nayi a ranar zan bashi labari, maybe a ciki zai dauki wani darasi na rayuwa". Ta lumshe idonta a lokacin da jirgin yake dagawa dasu zuwa sararin samaniya, ya bita da kallo har sai daya tabbatar bacci ya dauke ta sannan ya jawo diary din ya cigaba da rubutu. Dear Baby. Idan kana tare da littafin nan hakan yana nufin baka tare dani, dan in har ina raye ba zan baka littafi ba zan zauna ne in saka ka a gaba in yi ta baka labarin irin son da nake yi maka. Idan har bana tare da kai, Idan har ban samu naga fuskar ka a duniya ba, ina fatan ka zama yaro na gari kayi aiyukan alkhairi dan in samu damar ganin ka a lahira. A aljanna.............. Kiran wayar Hussain ce ta tashi Hassan daga bacci, yayi juyi yana kifta idonsa yana jin kansa yana yi masa ciwo saboda baccin da bai samu ya ishe shi ba. Ya dauki wayar "ya akayi?" Hussain yace "wai bacci kake yi? Karfe nawa ne a nan? Nan da 30 minutes zamu taso" Hassan yace "zaku taso kuma? I tot jiya kace min sai next week, what's up?" Hussain yace "nothing kawai na chanza shawara ne, kawai nayi missing dinka ne" Hassan yayi tsaki "neman magana dai kake yi. Ni ka katse min bacci ka sa kai na zai fara ciwo. Okay sai kun karaso" ya kashe wayar tun kafin Hussain ya bashi amsa, ya koma ya kwanta tare da dora pillow a kansa yana so ya koma bacci amma shi kansa yasan wasa yake yi. Dama jiya da kyar bacci ya dauke shi saboda abubuwan da suka yi masa yawa akai. Ruqayyah. Ta bashi mamaki ba kadan ba kuma maganganun ta sun taba zuciyarsa ba kadan ba, gidan arziki, you have nothing, wadannan sunfi duk sauran kona masa zuciya. Bai taba tsammani ba in wani ne ma ya gaya masa cewa ida zata fada masa haka to kuwa tabbas ba zai yarda ba. Abu daya daya gano a gurinta shine ta bawa kudi wani babban matsayi a zuciyarta. Wannan wani abu ne da tayi matuƙar kokari gurin boye masa tun haduwar su sai jiya ya fahimta, bayan wannan kuma bai san what other things ta boye masa ba, bai san how many lies ta gaya masa ba. Ya mike ya shiga toilet ya hada wa kansa ruwa mai zafi yayi wanka wai ko zaiji ya watstsake, ya fito ya kalli dining yaga babu alamar an bude shima, ya kalli dakin Ruqayyah bai ji motsin kowa ba sai ya fito ya tafi gidan Aunty. A palo ya tarar dasu suna ta hayaniya suna ta cin abinci, ya gaishe da Aunty sannan ya ce Khadijah ta zuba masa abinci, Aunty tace "ina Ruqayyah kuma?" Yace "bata jin dadi, ta kwanta kuma bana so in tashe ta" Aunty tayi murmushi tace "ai ko wadannan guntayen yaran aka barta dasu sai sun saka mata ciwo" Safiyya tace "kai Aunty, salihan yara irin wadannan da ko kuka basa yi?" Aunty tace "basa kuka fa, amma duk wanda ya dauke su shine zai yi kuka dan sai sunyi masa duka" Nafisa tace "lafiyar kenan Aunty, duk yaran da kika ga ya zauna shiru to kuwa tabbas bashi da isashshiyar lafiya" Aunty tace "sai kuyi tayi ai, ku da ba'a taba muku yaya" Hassan dai yana jinsu bai tanka ba yana ta murmushi, duk wata magana data shafi gudan ransa yana sonta. Ya jima a gurin Aunty suna shawarwari akan shirye shiryen bikin Safiyya da Jabir daya gaba to, ga kuma Hassana da tsohon ciki, sannan ga graduation din Khadijah tace sai an shirya mata party. Shi so yayi manemin Khadijah ya fito a hada bikin dana Safiyya a huta amma hakan ba zai samu ba saboda ya tafi karo karatu sai ya dawo za'ayi, kafin nan ta gama service dinta. Sosai yake jim dadin yadda rayuwar kannen nasa take tafiya duk da maraicin uba amma abinda suke samu ko da ace suna da uban ba lallai ne su samu kamar haka ba. Sai da ya gama zai fita sannan ya fada wa Aunty zancen dawowar su Hussain yau. "daga nan zan dan leka gurin Jabir sannan sai in wuce dauko su" sai yaga jikin Aunty yayi sanyi tace "Allah dai yasa lafiya, Hussain bai taba cancelling trip dinsa ba sai dai in da babban dalili" Hassan ya mike yana cewa "rabu da shi Aunty, kin san halin Hussain, he can be dramatic sometimes, wai missing gida yake yi sai kace wani jariri" Aunty tace "to Allah ya kawo su lafiya. Ai gwara hankalin nasa yake dawowa gida, gwara ya zauna a gida muma mu samu mu ganshi sosai". Sai daya biya gurin Jabir suka gama tsare tsaren su na shirin da suke yi zuwa Gombe gaisuwar iyaye, sannan yayi masa sallama ya tafi airport dan ya lokacin isowar su Hussain ya gabato. Bai jima da zuwa ba suka zo. Tun daga kallon farko da yayi wa fuskar Hussain ya fahimci akwai damuwa a tare da shi, kuma yaji gabansa ya fadi damuwar da take zuciyar Hussain ta wuce har zuwa tashi zuciyar ta kuma samar masa da damuwa. Ko menene yake damun Hussain to babba ne dan Hussain bashi da damuwar, da wahala kaji abinda zai bata masa rai balle har ya nuna a fuskarsa. Kuma duk da haka ma a yanzun in ba Hassan din ba da wahala wani yace akwai damuwa a fuskarsa, sai dai ko Aunty. To ko an samu problem ne a fertility test din nasu? Sai dai kallon fuskar Fatima ya saka ya fahimci ko ma menene problem din Hussain bai shafi Fatima ba kuma bata da masaniya akan sa. Hannunsu sarkafe dana juna suka karaso gaban Hussain "hello bro" sai kuma ya jawo Hassan ya rungume shi a jikinsa, d Hassan felt the tighness of his grief. Fatima tayi dariya, "Lallai Hassan da gaske anyi missing dinka" yayi murmushi yana cire Hussain daga jikinsa yace "iyayi, in yayi niyya kuma gobe ma ya ce wata tafiyar zai sake yi". Har suka je gida Hassan yana lura da ya yanayin Hussain, yana kuma kara tabbatar wa da kansa da cewa akwai abinda yake damun Hussain din. Suna zuwa yayi packing, Hussain ya fito yana mika yace "home sweet home" sannan yabi kannensa da suka taho tarensa har Hassana ita kowa yayi hugging dinta sannan ya wuce har cikin gidan yayi hugging aunty itama. Duk suna tayi masa dariya, shima dariyar yake yi yace "baku san yadda nake son ku bane ba, you are all here, my life is all here" sai kuma ya tuno da twins yace "ina yaya na? Aje a dauko min yayana". Ranar nan suka karasa wuni tare, sukayi lunch tare dinner ma haka sannan mijin Hassana yazo ya dauke ta, Fatima da Hussain ma suka tafi saboda sun dauki gajiya gashi basu huta ba. Hassan ma yayi wa Aunty sallama bayan ta bawa yaran ta su Yusuf sun mayar dasu gurin Ruqayyah, sai ta tsayar da hassan tace "menene yake damun Hussain?" Ya daga kafada yace "ban sani ba Aunty, tun da suka sauka na lura akwai abinda yake damunsa amma gobe zan tambaye shi" ta gyada kai tace "ka tambaye shi kaji, naga damuwa a fuskarsa. Sai da safe, ka duba Ruqayyah da jiki" ya gyada kai tare da ajjiyar zuciya, ambatar sunan Ruqayyah da tayi ya tayar masa da mikin da ke cikin zuciyarsa a kan Ruqayyan. Har baya son ya koma gida ma, amma babu yadda zaiyi dole ya koma. A palo ya tarar da ita da plate din abinci a gabanta tana waya tana dariya, da alama hirar tayi mata dadi. Ta dan dauke wayar daga kunnenta tayi masa sannu da zuwa, ya amsa babu ya bo ba fallasa. Yaran suna kwance akan kujera Aminu yana bacci Yusuf kuma yana kokarin rigima. Ya saka hannu ya dauke shi yana mishi wasa ya wuce dashi dakin sa. Ta bi bayansa da kallo sannan ta koma kan wayarta. "Na gaya miki Minal ba lallai bane ya barni inzo, ynazu ma kin ganshi ya shigo gidan ko kallo ban ishe shi ba duk uwar kwalliyar da naci" Minal tace "k kika so ai, na gaya miki ki zo mu koma gurin mutumin nan kin ki, bawan Allah jiya ma sai da ya tambaye ni ke yana cewa ya kike ciki. Ki je kawai a rufe miki bakin Hassan yadda ko Aunty kika zaga sai dai ya kalle ki ya dauke kai" Ruqayyah tace "hmmm. Ke dai bar ni kawai in tashi in je kar in kara wani laifin akan wani" ta katse wayar tana tauna shawarar minal a zuciyarta. Ta tarar da shi a kwance da Yusuf akan cikin sa yana yi nasa wasa yaron yana bangala masa dariya, ta zauna a gefen gadon tace "ashe Hussain ya dawo, no sai ji nayi ance a kawo twins inji Hussain" " eh ya dawo" yace mata. Tace "amma ko ka gaya min? Ai da na shoga nayi masa sannu da zuwa ko?" Ya juyo yana kallon ta yace "da aka aiko ki vada Twins din ai kinsan ya zo din kenan, idan da kinyi niyya da zaki iya fita a lokacin kice masa sannu da zuwa" tace "to ai ban tambayeka ba ko? Ya zanyi in fita ba tare dana tambaye ka ba" yace "okay, sorry. Nayi tunanin kina da number waya ta ashe baki da ita" ta ji daci a ranta, tayi shiru tana kallon yadda ya cigaba da wasa da yaron sa ko ta kanta bai bi ba. "Kayi hakuri" tace tana kakaro hawaye, "dan Allah kayi hakuri ni bana son wannan fushin naka wallahi ni sai inji gidan gabaki daya yayi min zafi, mi duniyar ma gaba daya zafi take min in kana fushi dani. Tun jiya nake ba ka hakuri fa, sai maganganu kake gaya min dan nayi kuskure sau daya" ya ajiye Yusuf yace "kin kwantar da Aminu? Kar ki bar min yaro akan kujera ya fado yaji ciwo" daga haka ya mike ya shiga toilet. Har washegari basu dai daita ba, wannan yada bata samu damar tambayarsa zuwa gurin dinner din ba sai text din ban hakuri ta tura wa Minal sannan ta kashe wayarta dan tasan ba zata barta ta huta ba da masifa. Shi kuma Hassan, washegarin neman yadda zasu zauna da Hussain yake yi saboda ya samu ya tambaye shi abinda yake damunsa. Basu samu zaman ba har yamma, yana shigowa gidan ya gansu sun shigo shi da driver dinsa Adam. Adam ya fito ya gaishe shi, ya amsa ba yabo ba fallasa kamar kullum, amma yau sai ya kara da "yaya karatu?" Adam ya shafa kansa yace "alhamdulillah oga" Hussain ya fito yana cewa "can you believe yaron nan First class yaje ja a school? Gashi wai yanzu har suna level two kamar fa yau suka shiga" Hassan ya kirkiro murmushi yana "good for him" sai ya juya kan Hussain "yalllabai ina son magana da kai fa, tun dazu nake neman ka kana can kana gantali" Hussain yace "ba gantali na tafi ba, napeps din nan ne aka kawo su naje gani, dama ina so mu zauna ayi shortlisting wadanda za'a bawa" Hassan ya gyada kai. Haka Hussain yake fitar da zakkar sa duk shekara, baya rabon kudi ko kayan abinci, wadannan sai dai idan normal kyauta ne amma zakka yafi son ya bayar da abinda mutum zai yi sana'a dashi. Ganin yadda Baba yake morar Napep dinsa ya sa ya yanke hukuncin zakkar bana ta Napep zaiyi ga matasa. Tare suka jera zuwa cikin gidan Hussain sannan suka hau har samansa suka zauna a palon sa. Ya dauko takardar da aka kawo masa ta list din eligible mutane kowa da description dinsa yace "a cikin wadannan za'a zabi wadanda za'a bawa" Hassan ya karbi takardar yana noticing yawan mutanen sai ya ajiye ta a gefe yace "forget about them. Tell me about you. Me yake damunka?" Hussain ya saki baki yana kallon sa yace "ni? Me ka gani a tare da ni? Ni babu abinda yake damuna ni lafiya ta kalau" Hassan ya gyara zama yace "hmmm really? Wannan maganar da kayi ita ta tabbatar min akwai abinda yake damun naka kuma ta nuna min cewa abin is related to your health. Tunda ni dai ban yi maganar ciwo ba amma har kace lafiyar ka kalau" Hussain ya saka hannunsa a cikin gashinsa sannan ya cire yace "to mr smarty-pants, ni babu abinda yake damuna health wise ko other wise". Hassan ya kwantar da kansa a jikin kujera yana kallon Hussain din da yake ta rarraba ido a dakin kamar yau ya fara ganin dakin. Sannan yace "is it about the fertility?" Hussain ya bata fuska yace "no. In baka yarda ba ma bara in dauko maka result din ka gani, sun ce komai lafiya lau sun kuma bamu drugs da kyma shawarwari. Ni ka tuna min ma, ya kamata in tafi gurin matata yanzu....." Hassan yace "to idan ba akan fertility bane ba akan menene?" Hussain ya mike yace "na gaya maka babu komai, babu komai fa. Please ka bar maganar ta wuce haka nan" Hassan ya mike shima yace "bani kadai ba, hatta Aunty sai da ta lura akwai damuwa a tattare da kai. Tell me damuwarka, that's all I asked" Hussain yace "damuwata a yanzu itace yadda ka damu da abinda babu. Ni babu abinda yake damuna" Hassan ya daga kafada yace "shikenan, fine, kar Allah yasa kayi min magana din" ya juya ya bar gurin amma a ransa yana mamakin girman abinda har Hussain yake boye masa shi, mostly shine mai boye magana ba Hussain ba, Hussain zai fadi abinda yake ransa ne kawai ko a mutu ko ayi rai. A gida ya tarar Ruqayyah ta shirya masa abinci, taci kwalliya da shigar kananan kayan da tasan yana so. Yana hawowa sama ta mike da twins are both arms dinta tace "sannu da zuwa mijina. Muna nan muna ta jiran ka ni da boys" ya karaso yana pinching cheeks din yaran da suke ta kokarin miko masa hannu. Yace "yauwa sannunki, ya gida?" Ba tare da ya jira amsar ta ba ya zagaye ta zai wuce, cikin muryar kuka tace "wai kai ba zaka hakura bane ba, na baka hakuri na baka hakuri, nayi kuka nayi kuka, kuskuren da nayi guda daya amma ba zaka yafe min shi ba" Ya juyo yana kallon ta, yana kallon hawayen da take matsowa daga idanunwanta, sai yaga kukan nata yayi masa kama da kukan karya, hawayenta yayi kama da crocodile tears, sai ya samu kansa da tambayar kansa in wannan shine irin kukan da take yi masa all the times kuma me yasa bai taba lura da cewa ba kukan gaskiya bane ba sai yau? Ya dawo ya karbi Aminu daga hannunta yace "ni bance miki ba zan yafe miki ba ban kuma ce miki ban hakura ba kawai dai ina bukatar tume alone to process things, am surw zamu dawo kamar yadda muke ada ko? Besides, love concurs all" Ta dan yi murmushi tana goge hawayenta tace "yes, love. Shine abinda na sani, abinda na sani shine ina son mijina sosai bana kuma son bacin ransa. Kaga fa yau ake yin dinner din Minal amma saboda bana so in tambayeka ranka ya baci shi yasa ban ma tambaya ba ballantana inje" ya karasa share mata hawayen yace "good girl. In ba kyason bacin raina ba dinner din Minal ce kadai ba zaki je ba, harka da Minal din gabaki daya nake so ki daina. Yes, nasan childhood friend dinki ce saboda makotan ku ne and all, but ni kuma yanzu mijinki ne kuma nace bana son harkar ki da ita" ta sunkuyar da kanta sannan ta gyada kai da sauri, yace "good" ya juya zai tafi daki tace "ga abinci fa, abincin da kafi so shina dafa maka" ba tare daya juyo ba yace "zan ci, sai nayi wanka na huta tukunna". Har sati ya zagayo Ruqayyah bata gane inda Hassan ya dosa ba, tayi amfani da hawayen, tayi amfani da kalaman, tayi girkin, har sanitation din dakinsa tayi masa amma sai ya gyada kai yace mata "Nagode" yayi tafiyar sa. Shi kuma Hassan ba wai case din Ruqayyah bane ba kadai a ransa, da akwai case din Hussain, tunda ya dawo ya kasa gae kansa yanzu ma gani yayi kamar yana avoiding dinsa baya son su zauna su biyu a guri daya sai dai in da third party Saboda yasan suna kadaicewa zai dame shi da tambayar menene problem dinsa. Shi kuma akan sa Hussain ya ki barin zuciyarsa tayi processing abinda doctor din ya gaya masa, ya san cewa akwai chances na cewa doctor din is wrong but tunda maganar ta daki kunnensa yaji a jikin sa cewa gaskiya ne maganar. Tun da yayi hankali, kullum zuciyars tana kan mutuwa, kullum gani yake ba zai kai gobe ba zai mutu kuma bai taba jin cewa hakan ya dame shi ba, but he always thought about sudden death, accident da sauran su. Sannan kuma abinda yasa maganar ta taba shi sosai shine rashin Da, yaci burin ya haihu kafin ya mutu, yadda sunan sa ba zai taba ba, blood line dinsa zai cigaba da tafiya a duniya. Amma kuma sai da yake tsaka da neman haihuwar sannan wannan labarin zai riske shi. Wannan shi yasa ya gudo daga America, saboda baya son ayiasa test din ballantana a tabbatar masa da abinda likitan ya fada, ya fi son ya cigaba da rayuwarsa without having to go through all that cancer treatment processess sai dai in mutuwar tazo kawai ya tafi. Ya san babu mai kara masa ko da numfashi guda daya ne akan wanda aka riga aka rubuta masa. But.......ten days after. Ya tashi da safe ya gama using toilet sai yaga jini, and his heart sank. A kasan toilet din ya zauna ya dafe kansa da hannayensa biyu yana lissafo rayuwarsa tun daga wayonsa zuwa yanzu da yake jin tana crashing down on him. So yake yaga mistakes dinsa ko zai iya gyarawa, so yake yaga abubuwan da yake so yayi kuma bai yi ba dan yayi kokari yayi su yanzu. Ba mutuwar ce damuwar sa ba sam, rabuwa da loved ones dinsa ne damuwarsa. A wanne hali zasu kasance bayan babu shi? Wacce irin damuwa zasu shiga ta rashin sa a tare da su? Ya tuna Hassan, he is going to be broken to pieces but with time zai yi surviving saboda yana ga kakkarfar zuciya duk kuwa da yasan ba zai taba komawa dai dai ba, saboda su biyun kowannen su tamkar sashi ne na ruhin danuwansa dan haka rayuwar Hassan will take a sharp change without him, sai dai yayi masa addu'ar Allah ya bashi strength din da chanjin zai zama for the better. But halin da Hassan zai shiga bai yi breaking heart dinsa ba kamar halin da Fatima zata shiga. His poor innocent princess. Sai yaji kamar bai yi mata adalci ba daya aure ta, ya cika ta da soyayyar sa ya mayar da ita karamar bazarawa without even a child to look at and remember him. Auren Fatima is the best thing that happened to him and rayuwar da yayi da ita so far are the best days of his life. Looking at his life sai yaga his only regret is not having a child of his own, someone to carry on his name tunda dai duk yadda yake da Hassan babu ta yadda za'a yi yayan Hassan suyi bearing sunansa. Ya fara lissafin abinda ya kamata yayi yanzu, shin ya tara family dinsa ne gabaki dayan su ya gaya musu halin da yake ciki su taya shi da addu'a ko kuma ya barsu sai mutuwar ta zo sa sani? Ya tashi ya shiga shower ya kunna wa kansa ruwa, kafin ya fito ya yanke shawarar abinda zaiyi. Bai samu Fatima a dakin ba, ya san tana kitchen tana shirya masa abinda zai ci. Poor sweet thing. Da sauri ya shirya ya fita ta hanyar da yasan ba zasu hadu da Fatima ba dan baya son ta ganshi a wannan yanayin dan zata iya karanto wani abu a fuskarsa. Yana so yaje ya samo wa kansa strength dan haka inda zai samu ya tafi. A palon kasa ya tarr da Ruqayyah daga dukkan alamu aiki take yia kitchen, ta saki baki tana kallonsa da mamaki sai kuma ta gaishe shi, ya amsa yana tanbayarta Hassan tace yana daki, "bara ayi masa magana" ya dakatar da ita "no, yi aikin ki kawai, bara inje" daga nan ya wuce ta ya hau saman. Ta bishi da kallo, tana jin motsinsa har taji ya bude kofar Bedroom din Hassan ya shiga, ta tabe baki, "yau kuma wani kuturin wulakanci ne ya tashi za'a shigar min har dakin miji?" Hussain ya shiga dakin yana karewa tsarin dakin kallo, it has Hassan written all over it, tas tas komai a arrange kamar yadda yake a kowanne dakin sadaya sani. Babu ko digon datti a kasa. Ya zauna a bakin gado yana jin kewae Hassan already tana ra tsa zuciyarsa. Sai ya jawo pillow ya kwanta ya kifa fuskar sa a kai. Hassan ya fito daga toilet da robe a jikin sa hannunsa kuma rike da towel yana gige ruwan kansa. Ya tsaya yana kallon Hussain da sakakken baki, yace "kai! Me kake yi min a kan gadon aure na?" Hussain ya dago kansa yana kallon sa da lumsassun idanuwa yace "kar ka yi min gori Malam, nima ina da gadon auren a gidana, klin kana son ka rama kaje ka kwanta kaima akai" Hassan yace "ni ai ina da hankali, ba zan kwanta a gadon matarka ba. Kuma wannan pillown na Ruqayyah ne ba nawa bane ba" Hussain yayi jifa da pillown ya jawo dayan, Hassan yayi dariya yana cigaba da goge kansa. Hussain yace "ka tuna sanda nake baro dakina in taho naka in kwanta in ce acn dakina bata da sanyi?" Hassan yace "kuma in kazo ka takura min kace sai akan pillow na zaka dora kanka wai yafi laushi" Hussain yayi dariya yace "har zuwa kake ka siyo min pillow dan in bar maka naka, ka saka aka zo aka gyara min ac amma duk ban dai na zuwa ba" Hassan yace "ai dama babu abinda ya samu acn, kawai dai kana so ka takura min ne ka hana ni jin dadin bacci" Hussain ya danyi shiru yana kallon wani hoton su a cikin karamin frame a gefen gado, da uniform din secondary school a jikin su duk kanin su suna murmushi, ya tuno ranar da aka dauki hoton ranar da suka yi wani match ne kuma suka yi winning, a lokacin Hussain cewa yayi footballer zai zama tunda yaga suna saurin yin kudi, ya juyo yana kallon Hassan yace "ba wai dan in takura maka bane nake zuwa dakin ka ba, ina zuwa ne dan ina son ka, bana son rabuwa da kai" Hassan ya tsaya da towel din a hannunsa yana kallon Hussain amma ya kasa cewa komai, Hussain yace "promise me idan na mutu kullum zaka ke zuwa kabarina kana yi min addu'a" Hassan ya saki towel din hannunsa yace "stop it" amma bai ga alamar wasa ko murmushi a fuskar Hussain ba, sai ma yaga murmushin da yake masking damuwarsa da shi ya gushe sai damuwar ta bayyana gabaki dayan ta. Ya bude baki a hankali yace "I am dying bro" Hassan yace "No!" Da kakkaurar muryar da sai da dakin ya amsa. Sannan ya tako zuwa gaban Hussain fuskar sa babu ko digon annuri ya nuna shi yace "don't ever say that again". Hussain ya juya fuskar sa gefe yace "ko da hakan ne gaskiya? Baka son in fada maka gaskiya? Ni da nazo da niyyar in samu kwarin guiwa daga gareka sai kuma ka satar min da guiwa ta? Zuwa nayi fa dan ka bani courage, dan bani da inda zan je inda yafi nan gurin ka" Hassan ya zauna a kusa dashi yana juyo da fuskarsa yana so ya karanto alamar wasa a idonsa amma ya kasa karantowa yace "yau ba 1st of April bane ba, ka tuna ranar da kayi min April pool kace min dakina ya kama da wuta? You are fine brother, you look good, very good even." Hussain ya dan yi murmushi yace "Cancer ce Hassan, colon cancer" Hassan yana girgiza kansa da sauri ya sake cewa "no! Karya suke, duk likitan daya gaya maka karya yake yi, he is a crook doctor da yake using fake machines" Sai Hussain ya bashi labarin yadda suka yi da likitan daya duba su shida Fatima a america, sai Hassan yayi murmushi yana jin sanyi a ransa yace "you see? Kana tayar da hankalin ka a banza kana kuma tayar min da hankali Hussain. Ta ya fertility doctor zai diagnosing Cancer? Karya yake yi, he is wrong, he is very wrong" Hussain ya girgiza kansa yace "he is not wrong bro" sai ya bashi labarin jinin da ya gani yayi a toilet. Murmushi Hassan yabace sai kuma ya sake yin wani yace "that doesn't mean anything, zata iya yiyuwa basir ne ko rana ko wani abu na daban. Wannan zaman da kake yi a jirgi ma ba dole basir ya kamaka ba?" Hussain ya girgiza kansa cikin raunanniyar murya yace "Hassan Please, don't give me false hope mana" Hassan bai bashi amsa ba sai ya mike ya dauko wayar sa da take jikin chargi ya kira family doctor dinsu yace "ina so dan Allah ka bincika mana best oncologist ko a wacce kasa yake kayi mana booking din ganinsa" ya ajiye wayar yana kallon Hussain daya koma da baya ya kwanta a kan gadon yace "zamu je ayi wannan test din daka gudo baka tsaya anyi maka ba. Anan zan tabbatar maka cewa likitan is wrong" Hussain yace "what if he is right?" Hassan yace "then zamu ne mi magani, babu wata cuta da bata da magani Hussain. You will have the best care in the world" Hussain yayi murmushi yace "you are beginning to sound like me. But you are forgetting something, even the best doctor in the world ba zai kara min second daya a cikin lokacin da Allah ya kayyade min ba a duniya. Ni ba mutuwa ce problem dina ba, dan haka ba zan yi going through wannan procedure din ta doctors ba, that chemotherapy treatment and those surgeries da ba zasu kare ni da komai ba. Ko so kake in koma kamar aljani kafin in mutu? So kake doctors su ringa gutsirar hanji na piece by piece har sai ya kare sannan su barni in tafi? In zan mutu Hassan na fi son in mutu in one piece. At least nafi son in mutu looking my best ba wai kwarangal da kai babu gashi ba" ya karasa maganar yana murmushi. Hassan yace "wannan ba abin wasa bane Hussain. Look, dan Allah yace ka yarda da kaddara ba ya na nufin in ciwo ya kamaka kayi folding hannunka ka jira mutuwa ba. Promise me zaka bini mu tafi" Hussain yace "zan bika muje dan ayi maka confirming abinda ni na riga na sani. But I will not go through those cancer treatment processess". Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son karanta halaliyar ki ki yi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020 *The Surgery* Tun Ruqayyah tana zuba idon ganin saukowar Hussain har ta hakura ta hau saman, ta ga kofar dakin a rufe tasan kuma suna ciki, tayi tsaki ta shiga nata dakin, sai data yiwa twins dinta wanka ta shiryasu sannan ta fito dasu falo, still tana tunanin menene suke ta magana haka a cikin daki. Ta kira mai renon twins ta bata su tace su tafi gidan Aunty duk da tasan cewa basu gaisa da baban su ba ballantana uncle din su daya shigo, sai dai kuma ita bacci take so ta koma. Suna tafiya Hassan ta bude kofa suka fito shida Hussain, fuskar Hassan kadai ta saka taji gaban ta ya fadi. Ya dan kalle ta yace "zamu fita, sai mun dawo" ta dan bata fuska "abinci fa? Ba ka karya ba fa" ya wuce ta yana cewa "ki ajiye min, inna dawo zan ci" shi a ransa ya ma manta da wani abu wai shi abinci. Hussain yace "sorry Madam. Na dauke miki miji ko? Aro na dauka zan dawo miki dashi in one piece". Ta bi si da kallo har suka fita a ranta tana tunanin something is up, kuma koma menene it is not good. A ranar suka gama binciken oncologist din daya kamata Hussain ya gani, a India yake, a ranar kuma suka fara kokarin booking yadda zasu ganshi. Ruqayyah tana zaune a palo suka kuma shigowa tare shida Hussain, gaisuwar ta kawai Hassan ya amsa ya wuce daki, Hussain ne ya dan tsaya yayi wa twins wasa sannan yabi bayan Hassan din suka shige dakin sa. Ruqayyah ta saki baki tana kallon wani sabon salo wai kiran sallah da usur sai kuma taga Hussain ya fito shi kadai yayi mata sallama ya fita. Bata bi ta kan Hassan ba sai data gama duk abinda zata yi ta kwantar da babies dinta tayi wanka tana shirin kwanciya sannan dai tace bara ta leka shi. A kwance ta tarar da shi ya lullube har kansa kuma ya kashe acn dakin. Ta zauna a bakin gado tana dan bude shi kadan sai dai tiririn da taji yana taso wa daga jikin sa kadai ya sa ta fahimci cewa bashi da lafiya "subhanallah. Ai zazzabi ne a jikin ka mijina" ya bude ido sa yana kallon ta, tayi kokarin daga shi "ka tashi ka sha magani, ko in kira Hussain ya kaika asibiti?" Sai ya kama hannun ta ya rike "Hussain? Bana son komai ya samu Hussain" daga yadda yayi maganar ta san magagin zazzaɓi yake yi, tace "babu abinda zai samu Hussain kuma kai ma babu abinda zai same ka, zazzaɓi ne kawai kake yi" tayi kokarin tashi sai ya jawo ta jikinsa yana cewa "babu abinda zai same shi? Thank you, ohhh thank you" ya fada yana shigar da ita cikin bargon sa tare da lullube su tare. Washegari Ruqayyah ta tashi da murnar Hassan ya fara saukowa, a ranar ne kuma doctor din da suka yi contacting jiya ya aiko musu da email na cewa zasu iya ganin sa next week, dan haka tun a ranar suka fara shirye-shiryen tafiya. A dakin Fatima tana zaune tana kallon Hussain da yake shirya mata maganar zuwan da zasuyi India shida Hassan saboda Hassan din da yake son ganin likita a can. Tayi kamar zata yi kuka, "kuma yanzu tafiya zakayi ka barni? Ni baka taba yin tafiya ka barni ba fa dan Allah. Ni bana son ka tafi ka barni, zan biku kaji?" Yayi murmushi yana zama kusa da ita. "Haba Princess, in nace zan tafi dake Hassan ba zai ji dadi ba tunda shi yace ba zai tafi da Ruqayyah ba, kinga babu dadi ko? Itama Ruqayyah ba zata ji dadi ba. Ki bari akwai tafiyar da zan shirya mana muna dawowa daga indiyan nan, daga ni sai ke kuma duk kasar da kike so ita zaki zaba" ta fara biga kafarta kamar me shagwaba "ni dai bana so ka tafi ka barni. To ka lallaba Hassan din mana ya tafi da Ruqayyah kaga sai mu tafi gabaki daya" Yace "Ruqayyah tana shayarwa kin manta? Tafiyar ba zata yi mata dadi ba da babies har biyu ko?" Fatima tace "zan ke tayata rainon ai, sai in karbi daya in bar mata daya" ya hade hannayensa "Please Princess kiyi hakuri, nima bana so in tafi in barki babu yadda zanyi ne" sai yaji maganar tasa tana bada wata ma'ana ta daban wadda tasa yaji jikinsa yayi sanyi. Ita kuma sanyin da taga jikin nasa yayi ne ya sa ta sauko. "Shikenan, Allah ya kiyaye hanya. Amma dan Allah kar ku dade. Kuma kullum sai munyi video call sau biyu" yayi murmushi yace "sau uku ma zamu ke yi, safe da rana da daddare". Ruqayyah kuma da Hassan ya gaya mata zancen tafiyar tasu cewa tayi "yanzu daga zazzaɓi sai tafiya India? Bana baka magani ba tun a ranar kuma har ka warke" ta fada cikin zolaya, sai dai baiyi dariya ba kuma bata ga alamar zaiyi dariyar ba. Yace "bamu san tsahon lokacin da tafiyar zata dauke mu ba amma muna saka ran insha Allah ba zamu dade ba" Ta fara kokarin kawo masa korafin cewa ya kamata su tafi tare amma a take ya nuna mata hakan ba zai yiwu ba, daga shi sai Hussain zasuyi tafiyar. Dole ta ja bakin ta tayi shiru, a ranta tana mita "ni sanda ina da ciki har na haihu cewa yayi ba za'a fita dani ba, amma da yake shine daga yin zazzaɓi har anyi booking ganin likita a India" Babu bata lokaci suka tafi, su ka bar yan'uwa da iyalin su da tunani amma kowa ya dauka Hassan ne marar lafiyar musamman yadda a cikin kwana biyu yayi rama sosai sannan annurin fuskarsa gabaki daya ya disashe. Suna isa Mumbai suka zarce asibitin da Dr din yake suka shigar da information dinsu da komai sannan suka tafi suka kama hotel. Ranar kwana suka yi suna hirar childhood memories, irin rashin jin Hussain da kuma kaffa kaffan Hassan, farkon kafa H and H da kuma yadda tafiyar ta kasance zuwa yanzu. Sai kuma suka yi hirar future dinsu yadda suke son ta kasance, yadda suke da burin yayansu su taso tare and maybe wata rana idan har an samu wadanda suka daidaita a tsakanin su a hada su aure. Sai bayan da suka yi sallar asuba sannan suka kwanta suka yi bacci tunda appointment din Hussain sai 12. Bayan sun tashi suka yi wanka suka shirya suka fita waje suka ci abinci sannan suka tafi asibitin, duk cikin su babu wanda yake maganar ciwon Hussain amm kuma abin duk yana ransu suna kuma tsoron sakamakon da binciken zai bayar. A office din bayan sun gaisa da doctor din sai ya saka Hussain ya kwanta a kan wani gado ya mike kafafuwansa sosai sai doctor din ya tsaya a kusa dashi yana yi masa tambayoyi yana amsawa, sai ya dora hannunsa a kasan cikin Hussain ya dan danna da dan karfi, Hussain ya mike zaune da sauri yana damkar hannun doctor din ido a waje yace "ouch, zafi sosai fa" sai doctor din ya bishi da kallo kawai, Hassan ya mike da sauri yana rike hannun Hussain wanda lokaci data gumi ya rufe masa fuska, jikinsa har rawa yake yi. Sai doctor din ya koma ya zauna yayi rubutu a takarda. Hassan ya koma gaban doctor din ido a bude yana tambayar, "yani zafi, me hakan yake nufi doctor?" Doctor ya dago yana kallon Hassan, ya kasa kallon Hussain yace "ba zan iya ce maka komai ba a yanzu. Zan tura ku dakin gwaje gwaje za'a yi hotuna kuma za'a dauki samples ayi gwaje gwaje. Sai result ya fito sannan zan iya cewa komai" Hassan ya karbi takardar da sanyin jiki sannan ya taimaka wa Hussain ya mike suka fita Hussain yana rike da marar sa. Wata maaikaciyar lafiya tayi musu jagora zuwa katon lab dinsu, inda aka fara gudanar da bincike sosai akan Hussain amma sai daya ja musu kunne kar wanda ya kuma danna masa marar sa, nurses din suka yi dariya suka ce ba zasu yi ba. Har dare suna can, sai da suka yi exhausting energy din Hussain gaba ki daya sannan suka rabu dashi yana ta yi musu mita. Suka ce washegari ya dawo za'a yi mishi abinda suka kira da colonoscopy. Hassan dai ya lallaba shi suka tafi, a daren Hussain yayi ta bincike akan menene colonoscopy din sai ya fahimci zasu zura mishi micro cameras ne cikin hanjinsa ta yadda zadu ga ko menene a cikin hanjin a screen, anan zasu fi fahimtar in akwai ko babu kuma zasu san exact location din da ciwon yake da kuma stage din da yake ciki. Shi dai a ransa baya so, zuciyarsa tana ta gaya masa cewa ya hada kayansa cikin daren ya gudu ya dawo Nigeria amma yasan in ya gwada yin haka sai sunyi rigima da Hassan, kuma shi yayi alƙawarin ya daina fada da Hassan amma kuma yasan gobe za'a tabbatar masa da cewa yana da wannan ciwon, shi kuma baya son a tabbatar masa din saboda yana son ya cigaba da rayuwarsa freely har zuwa mutuwarsa, wadda yasan zata iya riskar sa gobe ko kuma nan da shekaru masu yawa, Allah ne kadai masani, akwai hikima a cikin tsarin ubangiji da ya hane mu da neman sanin gaibu dan ba zai yi maka dadi ba, ta yaya zaka iya rayuwa in aka gaya mata nan da wata biyu ko uku zaka mutu? Bai gudun ba ya zauna, ranar da sassafe suka je suka zuwa akayi preparing Hussain aka yi masa allurar bacci, sai Hassan yaji zuciyarsa ta karye dan haka doctor din ya amince masa cewa zai iya shigowa ayi a gabansa. "It is not a surgery, we are just going to view the tumor on a screen and classify it. Then take a sample, that's all". Hassan yana zaune rike da hannun Hussain aka gama procedure din, doctor din yana nuna masa abinda yake gani yana kuma yi masa bayani, ya nuna masa ciwon da idonsa ya gani ya kuma gaya masa tun jiya da yayi wa Hussain manual exam ya fahimci cewa akwai ciwon da gaske, ganin hankalin Hassan ya tashi sosai sai ya kwantar masa da hankali ta hanyar gaya masa cewa ba wani problem bane ba tunda an yi detecting da wuri kuma akwai means na neman magani babu wani problem, ya gaya masa kuma yayi iyakacin kokarin sa na ganin ya kwantar wa da Hussain hankali dan lokuta da dama tashin hankali shi yake kashe patient ba wai ainahin ciwon ba. Ya kuma jaddada masa muhimmancin jin surgery da wuri "ita cancer tana spreading ne, tana kara yaduwa, in aka barta zata ci gaba kuma ba zata tsaya a hanjin kadai ba zata taba wadyu vital organs din da suke cikinsa. Dan haka I suggest ayi surgery as soon as possible. Daga anyi surgery an cire tumor din sai kuma a kashe surrounding area din da radiotherapy yadda in akwai saura ma zata mutu" Hassan ya gyada kansa yana assuring doctor din cewa kafin su bar kasar za'a yi surgery din. Ba zai bar kasar ba sai da healthy Hussain. Sanda Hussain ya farka, Hassan ya gani a gefensa rike da hannun sa ya kwantar da kansa a jikin gadon da Hussain yake kwance idonsa a rufe. Hussain ya dago hannunsa ya dan taba fuskarsa yace "hey bro" Hassan yayi saurin bude kumburarrun jajayen idanuwan sa ya dora akan Hussain, sai yaga Hussain din yayi masa dariya yace "have you been crying?" Ya sake dariya "sai na gaya wa Ruqayyah mijinta rago ne" Hassan ya harare shi ya tashi ya shiga toilet ya wanke fuskarsa ya fito sai ya tarar dashi yana kokarin tashi zaune sannan ya zare drip din da aka saka masa. Ya kamashi yana kokarin kwantar dashi amma yaki kwanciya ya tashi yana cewa "ni yunwa nake ji wallahi, kamar anyi min sata a hanji na" sai kuma ya bude ido yana kallon Hassan yace "gaya min gaskiya, ko har sun yanke hanjin ne?" Sai kawai yayi dariya ya kama hanyar fita. Hassan ya bishi amma yaki dawowa, sai da ya tuna masa da cewa rigar asibitin ce a jikin sa sannan ya dawo briefly ya mayar da kayansa ya kuma fita. A dole Hassan ya dauko takardun su da kuma wayoyin su ya biyo shi a baya. Sai da suka je gurin cin abinci suka zauna suna ci sannan Hussain yace "na san abinda doctor yace, you don't have to tell me, na riga na gaya maka dama kai ne baka yarda ba. Yanzu tunda ka yarda can we please go home? I have to get back to making that baby you know?" Hassan ya dauke kansa gefe yace "babu wani home da zaka tafi, you are going to have a surgery next week. Na riga nayi filling takardu har na biya kudi" Hussain ya bude ido cikin mamaki yace "no, na riga na gaya maka am not going to go through that" ya ajiye spoon din hannunsa ya mike ya fice daga gurin. Hassan ya biya bill da sauri ya bishi a baya. Ya tarar dashi a hanya suka jera yana cewa "Hussain Please, doctor din nan fa yayi min bayani, ya nuna min komai a screen na gani ba wai wani guri ne mai yawa ba, yace da zarar sunyi surgery sun cire shikenan sai......." Hussain yace "sai ayi radiology a kashe gurin sannan chemotherapy dan a tabbbar komai ya mutu, after three months kuma sai in dawo a sake wani colonoscopy din a gani idan bata yi regrowing ba, idan kuma tayi sai a sake going through that same precess, a haka har sai hanjin ya kare yadda babu abinda za'a kuma yankewa, ko kuma in ta taba wani vital organ din, sai kuma abar mutum ya karasa mutuwa, yes I know about all the process and no am not going through that. Na gaya maka tun acan". Haka suka yi ta fama har suka je hotel din da suka sauka, suna ziwa Hussain ya fara hada kaya yana zubawa a jaka Hassan kuma yana kashewa yana mayar wa gurin ajjiyar kaya, "waye ya gaya maka zata sake regrowing? Dan ta wasu tayi that doesn't mean taka ma zata yi. Doctor din fa yace tana stage 2, he is 90% sure cewa zai iya cire ta completely" Hussain yace "I am sorry but I don't believe him. Tunda za'a bashi kudin sa ya karbe ai zai fadi haka dama. Ni ba zan bari likitoci su mayar dani lab animal dinsu ba". Hassan ya koma ya zauna yana kallon Hussain, he have been stubborn and strong headed tun suna yara, anty ma da kanta ta sha ba da labarin irin taurin kansa da yadda yake bata wahala kafin ta juya shi, in yasa kansa abu to kuwa sai da dabara kafin a iya hana shi. Sai ya dauko wayarsa yace "shikenan tunda kaki jin magana ta, bara in kira Fatima in gaya mata halin da ake ciki watakila in ita tayi maka magana zaka ji" sai Hussain ya tsaya daga hadan kayan da yake yi yana kallon Hassan yace "you won't do that, ai amana na baka maganar nan, kana nufin zaka karya alkawarin da kayi min na cewa ba zaka gaya wa kowa ba?" Hassan ya daga kafada yace "yes of course, idan har hakan yana nufin saving life dinka ne zanyi. Kuma try me ka gani idan ba da gaske nake ba" Hussain ya tsaya yana kallonsa, baiga alamar wasa a fuskarsa ba sai ya ajiye kayan hannunsa ya hau kan gado ya kwanta, sai kuma ya tashi ta shiga toilet yayo alwala ya fito ya tayar da sallah. Hassan ya mike ya mammayar da kayan da Hussain ya baza, sannan shima yaje yayo alwalar ya fito ya tayar da tasa sallar. Hussain ya hakura ya yarda za'a yi masa aiki amma sam babu walwala a fuskarsa, sai Hassan ya fahimci kamar aikin yafi damunsa a kan ciwon ma gabaki dayansa. A haka har aka gama preparation ya zama saura kwana daya ayi aikin sai suka tafi asibitin zasu kwana acan, a lokacin ne zuciyar Hassan ta karye yace da Hussain "ina ganin a fasa aikin nan Hussain, ni bana jin dadin yadda kake reacting to it ka ƙi kwantar da hankalin ka bayan kuma kai ba mai yawan tayar da hankali akan abu bane ba, ni duk sanyaya min jiki kake yi wallahi, na kasa fahimtar if am doing the right thing or not. Please bro, ka gaya min cewa ba wai takura maka zanyi ayi maka aikin nan ba, dan Allah ka gaya min" sai Hussain yayi masa murmushi yace "ba wai ka takura min bane Hassan, ba kuma na yarda bane saboda kayi threatening cewa zaka gaya wa Fatima ba, na yarda ne saboda kai, saboda ina so in faranta maka, saboda ina so kaji cewa you did your best kar kayi feeling cewa ka gaza gurin kula dani. But ina so kai ma kayi mini wani alkawari Hassan. Ina so kayi min alkawarin cewa wannan shine surgery na farko kuma na karshe da zaka saka ayi min akan wannan cutar" Hassan ya sunkuyar da kansa kasa, Hussain ya dago fuskarsa yana kallon idonsa yace "say it. Kace kayi min alkawari" Hassan ya karbe fuskarsa sannan yace "nayi alkawari. Kuma nasan ma wannan aikin akwai nasara a cikin sa, mun gaya wa Allah kuma ya dubi kokarin mu. Zamu samu nasara am sure" sai Hussain yayi murmushi yace "good" . Sai ya koma ya kwanta ya rufe idonsa har aka zo aka tafi dashi. The surgery took 3 hours. A cikin 3 hours din nan Hassan sai da yayi nadamar da basu gaya wa kowa ba, at least da an taya su addu'a, dan ji yake yi kamar bakin sa shi kadai yayi kadan a addu'ar. A cikin awa ukun nan har wata irin rama yayi. Yana tsaye aka fito da Hussain, aka tura shi recovery room, inda kuma anan ne zai cigaba da karbar treatment dinsa. *The Email* Washegarin da akayi aikin aka fara yiwa Hussain chemotherapy treatment tare kuma da radiation therapy, at the same time kuma ana monitoring warkewar gurin da aka yi masa aiki internal da external. It has not been easy on him duk da cewa Hassan yana tare dashi kuma likitocin suna kulawa dashi sosai, magana mai dadi, karfafa guiwa, da tabbatar da cewa he is comfortable. Shi kansa yasan ya rame, tun kafin ayi aikin kuma ya rane din dan Fatima tasha yi masa mita a waya cewa ya rame, tun yana kakkaucewa har dai ya daina kiran ta video call itama kuma inta kira baya dauka sai yace mata phone dinsa ta samu matsala. A haka har ya fara jin dadin jikinsa, su kansu doctors din suna yabawa da yadda jikin nasa yayi kyau, ya rage yin amai sosai wanda yana daga cikin side effect na chemotherapy kuma shi yake saka rama, saboda jikinsa ya fara sabawa da magungunan da ake bashi. Sai kuma ya dage da cin abinci, ya kuma cire damuwa a ransa nan da nan ya kara murmure wa. An gama radiation therapy din, magunguna ne kawai yake sha dan haka ya fara maganar yana son ya tafi gida. Da farko doctor din yaki yarda, ya fi son ya kara kwanaki ciwonsa ya kara warkewa duk da cewa ba zasu tabbatar da cewa surgery din is a success ba sai bayan wata uku sannan zasu sake dubawa su gani idan cancer din bata dawo ba, still daga nan ma ba za'a saki kiji ba za'a cigaba da dubawa bayan wata uku uku har sai an tabbatar ta tafi. Sai daya tabbatar jikinsa yayi kyau sannan ya kira Fatima video call, suka yi hirar su ya tabbatar mata nan da kwana biyu zasu dawo, dan shi kam ya gaji ko ba'a sallame shi ba guduwa zaiyi. *Nigeria* Tun bayan tafiyar su Hassan sai Ruqayyah ta samu sake, a lokacin ne ta samu damar zuwa ta ga dakin Minal. Gidan ta mai kyau kuma mai girma part dinta daban na uwargidan ta daban, shi kuma mijin ya raba kayan sa a tsakanin su tunda akwai dakin sa a kowanne part. Minal ta baje sosai abinta ta na zuba wa uwargida rashin kunya son ranta yayin da shi kuma mijin ya ja bakinsa yayi shiru, yan uwan miji ma sun fara dawowa gurin Minal musamman uwar mijin da shekarun ta suka riga suka ja kuma bata da buri irin taga jikokin ta daga ɓangaren Alhaji Kabiru kuma a yanzu dukkan hopes dinsu yana kan Minal tunda suna ganin cewa rashin haihuwar daga matar ne ba daga mijin ba. Wannan yasa uwargidan mai suna Hajiya Baraka ta ja kofar part dinta ta rufe, bata gani ba ballantana ranta ya baci, babu mai shigar mata sai nata bakin idan sunzo, sai kuma mijinta idan ranar kwanan ta ce. Ranar wuni suka yi suna hira, farko Minal ta nuna fushin ta akan kin zuwa bikinta da Ruqayyah tayi, daga baya kuma sai ta sauko ta nuna dama ai tasan wannan matsolon mijin na Ruqayyah ne zai hana ta zuwa dan kar ya kashe kudi. "Ni dai Ruqayyah da Allah ya bani miji irin naki gwara in yi ta xama a gida, ya za'a yi ina kallon dukiya kuma ace ba zanyi abinda nake so da ita ba? Kema walllahi da laifin ki, ai wallahi idan ni ce ba ka isa ba, a matsayin na na matar ka sai nasan yadda nayi na lankwasa ka kabi ra'ayi na wallahi" Ruqayyah ta tabe baki tace "kema dai kya fada Minal, ke ni fa duk kwanan nan abubuwa sun cushe min wallahi, ji nake yi ma kamar ba ya sona yanzu. Irin soyayyar da nake gani a idonsa yanzu duk sai inga kamar babu" Minal tace "haba dai! Kuna nufin ki ce min babban makamin naki ya ragu? Soyayyar da yake miki ce fa take rike dake a gidan, wallahi kar ki bari ta tafi, chafdi, ki zo mu koma gurin Malam a juyo miki da hankalin sa kachokan ya dawo kanki. Ke ba ki ga yadda mai gidan nan da yan uwansa suke rawar kafa a kaina ba? Ai ba haka na barsu ba fa". Ruqayyah ta dauke kai gefe tace "ke raba ni da wannan malamin duban, ki barni kawai zan samar wa kaina mafita dan ni tsoron malaman nan nake yi wallahi, na tabajin ance aikin su gaba yake ci sannan ya dawo ya ci baya, ku barni in lallaba kawai" Minal tace "sai kiyi ta lallabawar ai. Ni kam babu wata lallabawa da zanyi a rayuwa" sai kuma tace "ni bamu yi maganar wannan maganar da Malam yayi a kanki ranar nan ba, na cewa zakiyi kudi. Kinga fa maganar sa ta fara tabbata tunda gashi kin haifi yara biyu kamar yadda yayi alƙawari" Ruqayyah tayi murmushi tace "maganar da nake miki kenan ta lallaba war ai, na sani duk wani kudi da zan saka ran yi to ta hanyar Hassan zai taho, dan haka nake lallaba abuna har zuwa lokacin da zamu ga abinda rayuwa zata zo mana dashi kuma" Minal tayi dariya tana dan dukan Ruqayyah tace "munafuka, ashe dai kim yarda da Malam din tunda kin yarda da maganar sa. Ina tabbatar miki da cewa abinda ya fada zai faru din. Ni dai fatana daya shine Ruqayyah kar ki samu duniya kuma ki manta dani, ko me kika samu ina so na zama a hannun daman ki" Ruqayyah tace "a'a ban yi miki wannan alkawarin ba Minal, za dai ki zauna a hanun hagu na amma Sumayya ita ce a hannun dama na" Minal ta bata rai, "shikenan tunda wariya za'a nuna min, hannun hagun ma ban raina ba". Sai dare Ruqayyan ta koma gida, bata shiga gurin Aunty ba dan kar tayi mata fadan ina taje ymtayi dare haka sai ta wuce part dinta ta hau sama direct tunda ta riga taci abincin ta a can gidan. Tayi wa yaranta wanka tana ta yi musu wasa suna dariya gabaki daya, tana jin son si sosai a zuciyarta irin son da bata taba yi wa kowa irinsa a duniya ba. Sai dai kuma a ranta tasan bata son su taso a karkashin masu kudi, tafi son su taso a matsayin masu kudi kuma tasan she is going to make the right decision at the right time. Ta dauki wayarta ta kira layin Hassan na india. Kullum kamar lokacin suke yin waya duk da shi a gurinsa cikin dare ne amma ta fahimci kamar baya bacci sosai, ko kuma da rana yake baccin ne oho. Ring daya ya dauka yace "yanzu nake tunanin kiran ku inji yadda yarana suka wuni" ta bata rai kamar yana kallonta tace "yaranka kadai? Ni ba zaka ji yadda na wuni ba? Allah sarki ni babu mai sona" ya danyi murmushi yace "ni na isa ince haka? Kin san yadda kike hana min bacci kuwa?" Tace "kamar gaske, baya ka fin ku tafin ma wani shashshare ni kake yi" yace "na tuba ai, kwana biyu da babu ke ai jiki na ya gayamin" tace "kai da baka da lafiya? Ko dama ciwon na yan gayu ne" ya danyi dariya, sai taji wani iri, yaushe rabon da taji yayi dariya ko a wayar ne tana iya jiyo rashin nutsuwa a muryarsa, tace "masha Allah, jiki yayi sauki kenan" ya juya ya kalli Hussain da yake ta danne danne a wayarsa, yace "sosai ma, alhamdulillah is all we can say" tace "alhamdulillah. Sai shirin dawowa kenan ko? Kaga ni ina son mijina ya dawo fa" ta fada da shagwaba, ya sake dariya "ki sha kurumin ki yarinya, in nazo har sai kin gaji dani". Suka jima suna hirar su, ko da wasa bata gaya masa taje unguwa ba, ta kara wa yaran wayar duk da basu san me take yi ba amma shi ya jiyo motsinsu kuma yaji dadi a ransa. Tabbas yaya rahama ne dan komai bacin ra sa ko zancen su yaji anyi sai yaji ransa yayi dadi. He can't imagine zuciyar Hussain, bayan wannan ciwon kuma ga babu haihuwa yet. Washegari ta tashi da gyaran dakinsa tunda taji yace sun kusa dawowa. Duk da dai ba wani datti dakin yayi ba dan fes ya tafi ya barshi kuma tunda ya tafi bata bude dakin ba. Ta dan karkade kura ta gyara abinda yake bukatar gyara sai ta bari da niyyar sai ana gobe zasu dawo sai ta kuma gyarawa ta wanke toilet. Anan taga system dinsa a kan study table dibsa tare da takardu, ita ta dauka da ita ya tafi dan haka bata lura ma da ita a gurin ba, sai kawai ta dauka ta hau kan gado ta bude ta fara dudduba abubuwan ciki, babu komai dan shi ko irin videos din nan ma ba ajjiyewa yake yi ba duk yawancin tarkacen kayan office ne, har tayi kamar zata rufe sai kuma zuciyarta ta raya mata cewa ta duba e-mail dinsa, maybe ta samu something interesting. Ta bude ta fara bin mails din briefly, suma duk tarkacen office ne dan ba ma gane me ake cewa take yi ba. Sai kuma idonta ya sauka akan wani "re_suspected Cancer patient" ta bude ta karanta, ta kuma karantawa tana so ta fahimta, ta dauko wayarta tana duba ma'anar wasu daga cikin kalmomin da akyi amfani dasu, sai da tayi wa e-mail din filla filla sannan ta fahimci cewa wani doctor ne a india ya rubuto yana gayyatar "Hussain Aminu Abdullahi" yaje za'a yi masa gajin cancer. Ta duba date din taga kwanaki kadan kafin tafiyar su, sai kuma taga wani email ne na Hassan wanda ya turawa doctor din akan yana son ganinsa amma kuma info din na Hussain ne. Ta cigaba da bincike amma takasa samun wani abu da zai kara fahimtar da ita cikakken ma'anar abinda ta karanta din, Cancer, Hussain, India. Haka ta wuni da abin a ranta kuma can kasan zuciyarta tana jin wani excitement yana taso mata. Tana jin maanar abin tana kwanta mata a zuciyarta, Hussain yana fama da cutar cancer, wannan shine dalilin zuwansu India ba wai zazzabin da Hassan yayi ba. Yes, ta samu wannan information din amma me ya kamata tayi dashi? Ta yaya zata yi amfani dashi to her own advantage? Sai dare sannan ta yanke shawara. Dakin Hassan ta koma ta samu wata newspaper ta zauna tana duba front page din a hankali har taga hotline dinsu, ta dauka a wayarta sannan ta sauka kasa ta aika a ka siyo mata sabon sim card, ta dawo dakinta ta zauna ta saka a wayarta sannan ta nemo waccan number din data yi saving ta tura message. "Hussain Aminu Abdullahi, the CEO of H and H is suffering from cancer and currently receiving treatment in india" sai ta rubuta address din asibitin data gane tare da email din ta tura. Sai data tabbatar ya tafi sannan ta zare sim card din ta balla shi ya jefar. Tayi murmushi yana jujjuya wayar a hannunta. "Let's see how Fatima will react to this". **********. **********. ********* Tun tafiyar su Hussain Fatima bata jin dadi, ji take gabaki daya kamar duniyar tayi mata zafi duk kuwa da cewa kullum suna makale a waya amma empty take jin duniyar ta. Wannan yasa ta roke shi akan zata je kano ta dan zauna kafin ya dawo, bai yi tunanin komai ba ya bar ta ta tafi saboda tunda akayi auren su bata taba zuwa ta zauna a gida ba, on few occasions ne yake barin ta tayi weekend kuma yasan tana missing gidan sosai duk da bata taba yi masa complain ba. Babu bata lokaci ta shirya ta tafi, sai ta dauki Khadijah suka tafi tare dan babu abinda take yi a gida a lokacin. Satin ta daya a gida, kullum sai sunyi video call da Hussain sau uku kamar yadda yayi mata alkawari kuma hakan yana debe mata kewa sosai. Sai dai problem dinta daya shine yadda taga kamar yana ramewa, tayi complain sai yace mata ai kewarta ce take damun sa. "To ku dawo mana" ta fada kamar zata yi kuka "bana jin dadi da baka nan, kullum zuciya ta sai in ringa ji kamar wani abin yana faruwa wallahi, ga faduwar gaba, kuma duk dan baka nan ne" yace "ya zanyi in taho in bar Hassan baya bashi da lafiya? Kimga ai ban kyau ta ba ko? Gashi ciwon nasa kamar karuwa yake yi ni duk hankali na a tashe yake, an bamu wasu test da za'a yi da hotuna da za'a tabbatar da me yake damunsa" sai kuma taji babu dadi, kamar ba ta kyauta ba da take cewa Hussain ya bar dan uwansa ya dawo gurinta. Tace "to maybe ma damuwar hakan ce ta saka nake ganin kamar ka rame, ka daina damuwa sosai kaji Mi Amour? Zai samu sauki kaji?" Yace "insha Allah. Amma duk da haka a zamu dade ba nan gaba, in anyi test din zamu taho in results ya fito ma dawo" tace "noo, ku tsaya kawai a bashi kulawa sosai. In abun zai dauki lokaci sai in dauko Ruqayyah muntaho tare kawai, na tabbatar shima zai bukaci matarsa a kusa dashi" Hussain yace "yeah right. Nima kuma ina bukatar matata a kusa dani." A hankali take lura da yadda nayayin sa yake cigaba da kalacewa, kullum kuma sai tayi masa complain, hakan yasa ana gobe za'a yi masa aikin yace mata wayarsa ta lalace ba zata yi video call ba sai dai suyi voice. Wannan yasa ta sake tabbatarwa da cewa something is definitely wrong, tasan cewa karya yake yi mata amma sai ta kasa karyata shi din. Babu yadda za'ayi Hussain ya zauna da lalatacciyar waya, wayar da bata yi komai bama Hussain yana chanjata zuwa sabuwar yayi ballantana ace wayar da tayi lalacewar da zata hana shi ganin ta? He is definitely hiding something. Wannan yasa ta tattara ta dauki Khadijah suka koma Kaduna, ta samu Aunty ta zayyana mata abinda suka yi da Hussain ita ma kuma auntyn ta tabbatar da maganar Fatima sai dai sun kasa gane dalilinsa na yin hakan, sai Aunty kawai ta bawa Fatima shawarar su yi ta addua, dan Hussain ba mutum ne mai boye boye ba tunda har ya boye to abu ne mai muhimmanci a gurinsa, ta tabbatar duk abinda yake boyewa in ya dawo a hankali zasu sani. Sai dai hakan bai sa baccin Fatima ya dawo gare ta ba, sai dai ta dauki shawarar Aunty bata nuna masa ta fahimci yana boye wani abu ba kuma ta dage dayi masa addu'a da fatan alkhairi aduk abinda yake gabansa...... Sai dai sati daya bayan dawowar ta, sai gashi ya kuma kiranta video call, kuma sai taga yana looking much better than ganinsa da tayi na karshe sai dai shadow din da yake kwance a kasan idonsa. Tace "you look so handsome" yai murmushi yana saka hannu tare da kara gyara gashin kansa yana kashe mata ido yace "Hussain ne fa, Hussain will always look handsome" tayi dariya "kai ka fiya son kanka da yawa" sun jima suna hira, yana tabbatar mata da cewa Hassan ya samu sauki sosai kuma nan da kwana biyu zasu dawo gida. A ranar tayi bacci mai dadi sosai. Sai dai.......... Washegari a morning news ana fadar major headlines na jaridun kasar nan taga katon hoton mijinta ya cika screen din tvn ta, da rubutu a kasa..... "Hussain Aminu Abdullahi, H and H boss, is suffering from colon cancer and currently receiving treatment in India" Ta saki kofin tea din hannunta idon ta a cikin na Hussain din da yake murmushin sa da baya rabuwa dashi. Sai news din ya cigaba yana nuno hotunan Hassan dana Hussain, kunnuwan ta basa jin abinda ake cewa, amma daga hotunan ta fahimci a asibiti ne sannan basu sani ba ake daukan su, kuma yanayin hotunan yana nuna Hussain din ne marar lafiyar. Screen din ya tsaya akan hoton Hussain a kwance akan dago, ga naurori a zagaye dashi, ga kuma doctors a tsaye a kansa. Kwakwalwar ta tayi blacking out, sannan ita ma ta zame ta bi kofin shayin ta zuwa kasa. Yarinyar ta da abin ya faru a gabanta ce ta saka ihu, sauran jama'ar gidan suka zo tare da Khadijah wadda tun tafiyar Hussain a gurin ta take, ganin halin da take ciki ya saka Khadijah ta kira aunty ta gaya mata sannan tace a samu driver a tafi da ita asibiti, ita Khadijah sam bata ga labaran ba saboda kafin ta futo daga daki an dauke gurin an tafi wani labarin daban. Adam aka kira cewa ya kawo mota za'a je asibiti, sai dai yanayin da aka tarar dashi shima a rikice yake, dan shima akan idonsa akayi labarin. "Dama oga Hussain bashi da lafiya? Dama tafiyar da suka yi asibiti ya tafi?" A hakan dai ya dauko motar aka saka Fatima, Aunty da Khadijah suka shiga Aunty tana kiran doctor dinsu tana gaya masa gasu nan akan hanya. Sannan dauko robar ruwan data fito dashi a hannunta tana bismillah tana shafawa fatima a fuskarta, tana kuma zuba mata har cikin rigarta. Ta sauke ajjiyar zuciya a hankali tana dan bude idonta ta dora su akan Aunty. Aunty ta fara jera mata sannu, ta juya ta kalli Khadijah tace "ya dawo? Kun kira shi a waya ya taho?" Khadijah tace "waye?" Fatima ta juya tana kallon Aunty tace "Hussain Aunty ashe abinda yake boye mana kenan?" Sai ta rushe da kuka tana tuno fuskarsa a zagaye da doctors. "Na shiga uku ni Fatima Allah ka tashe ni daga wannan mummunan mafarkin. Dan Allah Aunty ki ce min mafarki nake yi Hussain lafiyar sa kalau" Aunty ta rungume ta "Hussain lafiyar sa kalau mafarki kika yi, ban san me kika gani a cikin mafarkin ba amma mafarki kika yi dan Hussain dina lafiyar sa kalau babu abinda ya same shi dan dazu ma munyi waya dasu" ta rike fuskar Aunty "ba mafarki nayi ba aunty a tv na gani. A labarai na gani sunce Hussain bashi da lafiya wai cancer ce take damunsa yana asibiti, har da hotuna suka nuna Aunty, Aunty Hussain dina....." Sai ta rufe fuskarta tana kuka mai ratsa zuciya. Aunty ta fara girgiza kanta "uhm uhm, karya suke yi, makiyane kawai suke yi masa mugun fata, Hussain lafiyar sa kalau, Hassan ma ya warke sun kusa dawowa, karya ne ki daina bata hawayen ki akan karya Fatima. Bara in kira miki shi ya tabbatar miki da cewa karya suke yi. Ko kuma mafarki kika yi Fatima" a haka suka asibitin, sai da suka yi packing sannan Adam ya kira Khadijah gefe ya gaya mata shima yaga labaran da haka ba wai mafarki Fatima tayi ba, nan take Khadijah itama ta rude dan da duk tunanin ta mafarki Fatima tayi dannita tana bacci ne ma taji hayaniya ta tashi. Nan da nan ta bi Aunty a baya cikin asibitin, ta tarar har karbi Fatima daga hannun Aunty, ta ja ta gefe ido a waje ta gaya mata abinda Adam ya gaya mata. Aunty tana girgiza kanta da sauri ta dauko wayarta ta danna number din Hassan ta India Yau Hussain tunda yayi sallar asuba ya kuma fita yayi exercise din da likitoci suke saka shi yayi dan taimakawa ciwon sa yayi healing da wuri, sai ya dauko diary dinsa kamar kullum ya fara rubutu. Dear baby "Na samu sauki sosai, gobe nake shirin guduwa daga asibitin nan saboda naga basu da niyyar sallama ta ni kuma gida nake son komawa gurin mommyn ka, naga ta fara zama frustrated, bana so tayi fushi da yawa kar tayi min bulala. Kaima kabi ta a hankali dan in mayi mata laifi zata ke zane ka but ba wai dan bata sonka ba sai don tana so ka zama yaron kirki, zata so ka sosai na sani amma kuma nasan ba zata yi maka irin son da take yi min ba. Wait, kar kayi kishi, matsayi na daban naka daban" Hassan ya shigo yana kallon sa yace "an fara rubutun?" Hussain ya rufe diary din yace "hmmm. Duk abinka dai ba zaka gani ba" Hassan yace "ban yi niyyar in gani din ba dai, san da kake sheka uban baccin ka in nayi niyya ai zan dauka in karanta ne" Hussain yace "sata kenan ai" Hassan yace "ni dai ba zanyi fada da kai ba, ni na daina fada da kai" Hussain yayi murmushi yace "makaho ne aka ce masa ga ido yace baya so, saboda yasan ba zai samu ba. So kake muyi fadan kuma ni ba zan kula ka ba" ya rufe littafin yana saka shi a cikin yar karamar jakar da ya siya musamman saboda littafin. Ya sauko daga kan gadon ya zauna a kujera da ke kusa da table din da aka jera musu breakfast, shi dai duk ba dadin wannan abincin yake ji ba, shi babu abincin da yake jin dadinsa kamar na gimbiyar sa. Bayan sun gama cin abincin ne aka zo aka bawa Hussain magungunan sa yasha, yana ta mita yana cewa ya kusa daina shan magungunan nan dai ya huta, "ko ku sallame ni ko kar ku sallame ni guduwa zanyi" su dai basu ji abinda yake cewa ba, Hassan yana hararar sa sai ya daga kafada yace "ai nayi kokari" a lokacin ne wayar Hassan tayi kara, ya dauka yaga number din Aunty sai yaji hankalin sa bai kwanta ba dan dazu da ya fita waje ita ya kira kuma duk sun gama maganar da zasuyi, tabbas wani abin ne sabo ya taso. Ya dauki wayar ya fita waje yana magana "Aunty" "Hassan duk abinda kuke yi ku bari ku taho gida, makiyan ku suna nan suna yawo a gidajen radiyo suna yada karyar cewa wai Hussain bashi da lafiya, sun ce wai cancar hanji yake fama da ita, sunce wai abinda ya kaiku India kenan" ta karashe maganar cikin muryar kuka. Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani gurin na sata ne. In kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number 08067081020 *Dear Baby* Not edited Kafin Hassan ya dawo dakin har nurses din sun gama da Hussain sun fita, yana shigowa Hussain yabi fuskar sa da kallo sannan ya bude hannun sa yace "now what?" Hassan ya jawo kujera ya zauna yana kallon sa yace "zamu tafi Nigeria gobe da safe insha Allahu" maimakon Hussain yayi murnar cewa Hassan ya goyi bayan tafiyarsu sai fuskarsata nuna madaukakiyar damuwa, yace "me ya faru? Dawa kukayi waya yanzu?" Hassan ya gyara zama yana kallonsa yace "Aunty ce, ta kira tace duk abinda muke yi mu koma gida yanzu" ya dan sosa kansa "wani gidan tv dazu yayi broadcasting cewa baka da lafiya, sun fadi ciwon da yake damunka da kuma asibitin da kake kwance" Hussain ya mike "what?" Hassan yayi shiru bai ce komai ba. Sai Hussain ya mike, ransa a tsananin bace ya doshi kofar fita yana huci, Hassan ya mike shima da sauri ya rike hannunsa yana cewa "me zaka yi? Ina zaka je?" Hussain yace "zanga management na asibitin nan ne, zanji dalilin da yasa suka yi releasing information dina to the press bayan sunyi min alkawarin secrecy" Hassan yace "how do you know cewa sune? Anything can happen. Yanzu mutane sun koma kiwon mutum bana dabba ba. It ca be anyone har wadanda ba zamu taba zarga ba" Hussain ya juyo yana huci yace "waye to? Hatta iyalan mu basu san abinda yake faruwa ba mu kadai muka sani sai asibitin nan, dan haka dole sune suka fitar da bayanin nan. Wallahi sai na yi sueing dinsu, wannan ai keta privacy ne. Allah kadai yasan dawa dawa ye suka ji labarin nan a yanzu" sai kuma ya dawo ya zauna akan kujera yana dafe kansa yace "Fatima! Oh my God" ya mike da sauri ya fara neman wayarsa. Hassan ya riga shi gani sai ya dauke ya saka a aljihun sa yace "don't worry about Fatima, she is fine, yanzu ka shirya zanje in karbar mana takardar sallama gobe mu tafi" Hussain yace "ba zan kai gobe a kasar nan ba. Bani waya ta. Bana so inyi fada da kai Hassan ka bani wayata in kira Fatima" Hassan bai ce masa komai ba sai ya kuma yi. Hanyar fita yana cewa "yau ko ni ko mai asibitin nan sai ya gaya min uban da ya bashi damar fitar da information dina" Hassan ya kuma rike shi "Hussain, take this easy, zata iya yiwuwa basu bane ba, akwai patients a asibitin nan kuma nasan a cikin su ba za'a rasa wanda suka zo daga Nigeria ba, ba za'a rasa wanda ya san fuskarka ko tawaba especially yadda kake watsa hotunan mu a media, wani zai iya gayawa wani, shima wanin ya gaya wa wani har maganar taje gurin yan jarida su kuma duk abinda zai dauki attention din mutane shi suke so su buga. Creating scene a asibitin nan ba zai gyara komai ba sai dai ma ya bata. Maybe yan jaridar suna waje suna kallon mu, maybe suna daukan hoton duk wani motsin mu, creating scene zai kara musu labarin da zasu buga ne, abu kadan yanzu suke nema su kara gishiri da magi su sake bugawa" Hussain ya juyo ya dawo dakin yana zura hannunsa a cikin gashin kansa, ransa a matukar bace. Ya juya bayansa ya dora goshinsa a jikin bangon dakin. Ko wanene wannan in ya kamashi Allah kadai zai raba su, it pains him that someone will make use of ciwon da yake yi ya in this way. Ko waye yayi wannan abin ko me yake tunanin zaiyi gaining??? Hassan ya kama shi ya zaunar dashi a bakin gado yace "na kira airport, babu jirgi zuwa Nigeria a yau, tomorrow da sassafe zamu tafi" Hussain ya dago kai yana kallon sa, sai Hassan ya mika masa wayarsa yace "call her" Hussain ya karbi wayar yana jujjuya ta, shi bai ma san me zaice mata ba idan ya kirata din. Ya san dole dama zata sani tunda zata ga tabon surgery din a jikinsa but so yayi ace shi zai gaya mata da kansa at his own convenient time, har ya gama shirya kalaman da zai yi mata yadda ba zata tayar da hankalin ta sosai ba, amma yanzu bai ma san ta inda zai fara ba. Ya runtse idonsa sannan ya ajiye wayar a gefensa. Hassan ya mike yana dan bubbuga kafadar Hussain da niyyar bashi courage, sannan ya nemi huka ya saka ya dan rufe fuskarsa kadan sannan ya fita daga dakin. Hussain ya jima a zaune a inda Hassan ya barshi, zuciyarsa tana yi masa zafin abinda aka yi masa, sai kuma ya dauki wayarsa ya lalubo number din Fatima ya tura masa text "am sorry" Hassan ya je ya shigar da complain din abinda ya faru ga management din asibitocin, sannan kuma ya nemi a basu sallama. Farko doctor din da yake kula da Hussain ya ki amincewa da hakan amma kuma da yaga Hassan din ya dake har yana threatening kai karar asibitin sai ya hakura sai dai amma sai da ya hada su da wani doctor a Nigeria wanda zai cigaba da monitoring lafiyar Hussain din tare kuma da yarjejeniyar cewa bayan wata uku Hussain xai dawo a sake gwada shi, kuma kafin nan in dai ya ji wani chanji a tare dashi zai dawo. Hassan duk ya amince, suka gama komai aka bashi takardar sallama. A dakin ya dawo ya tarar da Hussain a kwance akan gadon ya rufe idon sa, ya zauna a kusa dashi, sai ya bude ido yana kallon sa yace "ko da wani ya ganninko kai a asibitin nan ba lallai ne yasan takamaiman me yake damu na ba, zai dai san cewa bani da lafiya, sai dai in asibitin su zadu fadi me yake damuna" Hassan yace "Hussain......it doesn't matter. Let it go please...." Hussain ya tashi zaune yana kallon Hassan yace "babu wanda kuka yi maganar dashi?" Hassan ya girgiza kansa yace "babu" Hussain yace "ko Ruqayyah?" Hassan ya bata rai yace "what? Kana zargin Ruqayyah? Shikenan kuma dan baka son ta jinin ku bai hadu ba sai ya kasance duk wani bad abu zata iya aikatawa? Hassana ba zata taba aikata wannan aikin ba, ballantana ma ban gaya mata ba. Nasan abinda nake yi ai" Hussain ya koma ya kwanta ya mayar da idonsa ya rufe, yayi alƙawarin ya daina fada da Hassan, but zuciyarsa tana kan Ruqayyah. Hassan ya cigaba da magana. "ko da ace na gaya wa Ruqayyah ba zata taba aikata hakan ba, kar ka mata secondary school kadai ta gama, bata da wata exposure a rayuwa, bana jin ma tasan ta yadda zata fitar da maganar" Hussain yana kwance still idonsa a rufe yace "kace baka gaya mata ba, case Closed". A ranar suka bar asibitin, washegari da sassafe suka dauko hanyar Nigeria bayan sun kira Aunty sun gaya mata cewa gasu nan tahowa. Sai a lokacin suka samu labarin cewa Hassana ta haihu, ashe itama taga labarin kuma tashin hankalin ne ya tayar mata da nakuda ta haifi danta namiji, lafiya lau take sai dai jinin ta da ya hau sosai dan haka tana asibiti har lokacin. Kowa yaje taryen su a airport amma banda Fatima, duk kuwa da cewa an sallame ta daga asibiti amma har lokacin kuka take yi musamman da ta ga message din Hussain da yake bata hakuri, hakan yana nuna mata cewa abinda aka fada gaskiya ne kenan, shi yasa tayi zamanta a gida dan bata jin kafafuwanta zasu kaita airport din. A airport din ne kuma suka tabbatar da cewa maganar ta watsu sosai, dan sun ga yan jarida suna ta daukan su hotuna amma sai suka share suka nuna kamar basu lura dasu ba. Hussain ya bi dukkan yan uwansa ya rungume su daga bayan daya, yazo kan Ruqayyah sai ya karbi twins a hannunta yace "welldone babbar yaya" tayi murmushi tace "barka da dawowa gida" ya juyi yana kallon Hassan yace "ga mijin ki nan na dawo miki dashi in one piece kamar yadda nayi alkawari" tayi faffadan murmushi, sai yake ji a ransa kamar murmushin nata yafi karfin na ganin mijinta, kamar a can cikin idonta akwai wanda boyayyen abu. Daga airport din asibiti suka wuce gurin Hassana, suka duba ta suka kuma ga sabon dansu. "Hussain ya rike hannunta yace "kin ganni lafiya kalau ko? Kar ki kuma tayar da hankalin ki akaina girlfriend" haka yake ce mata tun suna yara, ta goge kwallar idonta, "amma ai gashi nan naga duk ka ka rame boyfriend" yayi dariya yace "ke kuma kinyi kiba ba, wa ya sani ma ko ke ce kike tsotse ni?" Ya fada cikin tsokana dan yasan bata son ki ba kwata kwata, ta bata rai "bata kiba nayi ba yaya H2, kumbura nayi kuma zan sace ne kafin suna". Ya zauna a kusa da ita tmya dauki babyn yana yi masa addu'a, sai yaji a ransa yana fatan inama inama. Basu dade ba suka tafi gida saboda ita ma yanzu ake shirin sallamar ta tunda bp din ya fara normalizing, kuma shi hankalin sa duk yana kan Fatima musamman saboda ganin yadda tunda suka zo Ruqayyah take makale da Hassan. Shima sai yaji yana son yaji tashi matar a jiki sa. Sai dai yasan akwai drama a tsakanin su. Shi kadai ya shiga part dinsa, duk yan rakiyar sun tafi gurin Aunty, Hassan kuma da matarsa sun tafi nasu gidan. Bata kasa, ya hau sama zuwa part dinta ya zarce har Bedroom dinta inda ya same ta a kwance akan gado ta lullube har kanta. Yayi sallama amma sai ya tsaya a bakin kofa ya kasa karasowa, ta yaye rufar da sauri tana kallonsa da kumburarrun jajayen idanuwan ta, sai yaji a jikinsa cewa tun juya take dakin a kwance kuma tun jiyan kuka take yi, sai zuciyarsa ta raya masa ko ya zata yi ranar da yayi tafiyar da babu dawowa, nan take zuciyarsa ta karye yaji kamar zai taya ta kukan amma sai ya hadiye dan baya son ya kara mata damuwa, ya kama kunnuwan sa da hannayensa biyu ya fara yin sama da kasa kamar mai frog jump, ta sauko daga kan gadon da sauri taa kallon sa ta cikin hawayen ta sai taga ya cije baki alamar ciwo, da sauri ta karaso ta rungume shi tana saka kuka, sai suka zube a kasa gabaki daya, ta saka hannu ta daga rigarsa tana kallon ɗinkin da akayi a kasan cibiyarsa, ga shi nan raw ko warke wa bai gama yi ba. Ta kara karfin kukan ta "na shiga uku ni Fatima, Allah kar ka dora min kaddarar da ba zan iya dauka ba" ya kamo fuskarta yana kallon idanuwan ta da suka fada ciki yace "Allah, Fatima Allah baya taba dora wa bawansa abinda yasan ba zai iya dauka ba, duk abinda kika ga ya samu bawa jarrabawa ce dan a gwada karfin imanin sa, wannan ciwon jarabawa ta ce, idan wani abun ya faru dani ta sanadiyyar ciwon to jarabawar ki ce ke kuma" ta fara girgiza kanta tana neman shide masa "wayyo Allah na, babu abinda zai faru da kai Hussain babu abinda zai same ka" ya gyada mata kai yana kokarin ya dawo da ita cikin nutsuwar ta yace "eh Fatima, babu abinda zai same ni. Look at me, na warke kin gani an yi mini aiki kuma na warke kinji, babu abinda zai same ni" sai ta kara makalkale kamar mai shirin tsaga kirjinsa ta shige ciki. Ya zagaye ta da hannayensa yana jin zuciyarsa tana yin nauyi a kirjinsa. Ya runtse idonsa a ransa yana addu'a "Allah in har ka kaddara zaka dauke ni, Allah give Fatima the strength to bear it". Sai data nutsu sannan yayi mata bayanin yadda ciwon yake da aikin da akayi masa, ya kuma gaya mata irin confidence din da doctor din yake dashi a aikin, da kuma assurance din daya basu na cewa aikin will be a success. Ya fahimci hankalin ta ya fara kwanciya, tana ta jera ajjiyar zuciya, sai ya cigaba da bata positive vibes har sai daya ga tayi murmushi, sannan ya sake assuring dinta "I am fine princess, babu abinda zai same ni kinji?" Ta gyada kai, yana kallon kayan jikinta yace "anya kuwa kinyi wanka yau?" Sai ta boye fuskarta a kirjinsa tana jin kunya, yace "tashi muje inyi miki wanka" A ranar da daddare ya tara yanuwansa gaba ki daya ya gaya musu gaskiyar abinda yake damunsa, yayi musu bayani kamar yadda yayi wa Fatima sannan ya kwantar musu da hankali kuma sosai hankalin nasu ya kwanta musamman sabod yadda suke ganin murmushi a kwance a fuskarsa babu wata alamar damuwa a tare dashi. A lokacin ne kuma ya fada musu kudirin sa, tafiya yake so suyi gabaki dayansu zuwa Umrah tunda ga azumi ya gabato sai suyi amfani da damar gurin roka masa lafiya a gurin ubangiji tunda shi kadai ne zai bashi lafiya. Zasu zauna a can har zuwa lokacin aikin hajji suyi sannan su dawo. Gaba ki daya za'a yi tafiyar har su Ruqayyah da twins dinta, Hassana mai jego kadai za'a bari sai jikinta yayi karfi sannan zata bisu a baya. Washegari yan dubiya suka fara zuwa, labari ya bazu kowa ya sani, Hussain ya sauko babban palon gidansa ya zauna tare da Fatima a kusa dashi suna karbar duk wanda yazo duba shi hannu bibbiyu, duk kuma wanda yazo sai ya fahimci cewa ciwon ba yadda suke dauka bane ba. A cikin yan dubiyar har da Sumayya, wadda ta taho daga makaranta bayan Ruqayyah ta kira ta ta sanar da ita. Part din Hussain ta fara shiga ta duba shi kuma suka gaisa da Fatima, Hussain yana ta tsokanar ta wai ita tana karatu amma maimakon take ramewa kamar yadda Zulaihat take yi sai take yin kiba. "ko dai Adam ne yake miki karatun bamu sani ba?" Ta sunkuyar da kai tana jin kunya, Fatima ta tambaye shi "Adam din gidan nan? Kai amma wannan abu yayi min dadi" Hussain yace "sun dace ko?" Sai Sumayya ta tashi da sauri tana yi musu sallama, suka yi ta mata dariyar kunyar ta. A part din Ruqayyah, tana shiga ta dauki Yusuf "ubana na kaina, ubana yafi na kowa" Ruqayyah tayi dariya tace "zama dai ki cigaba da fada har masu gidan su jiki kina cewa baban ki yafi nasu" Sumayya ta daga kai tana kallon sama tace "ai ba haka nake nufi ba, salon magana ne kawai amma shima uban masu gidan ai ina son shi" ta karasa tana daukan Aminu, Ruqayyah tace "zaki sha kwana ko?" Sumayya ta zauna tana kiran A'isha ta kawo muta ruwa. "Daga school nake, kishi na yunwa kamar zan tafi barzaq" Ruqayyah tayi dariya "ai kuwa dai baya nuna wa a jikin ki, sai wani kyau kike yi yarinyar nan kamar kece a cikin daular da nake ciki. Ninkuma gashi kullum karewa nake yi kamar kudin guzuri" Sumayya tace "ai abin ba'a daula yake ba Ruqayyah, ni babu abinda zai hana ni kiba tunda babu abinda na nema na rasa, hankali na a kwance yake, karatu kuma ina ganewa sosai kuma zuciyata fes take, lafiya lau nake bacci na" Ruqayyah ta harare ta "to me kike nufi? Waye tasa zuciyar ba fes ba?" Sumayya tace "ni fa ba wani abu nace ba, salon Magana ne kawai". A'isha ta kawo mata ruwa da lemo, ta daga robar ta kusan shanye wa sannan ta ajiye. A lokacin Hassan yake saukowa daga sama "manya manyan yan jami'a, tun da naji gidan nan ya cika da hayaniya nasan ke ce kika zo, kin ga matata ita ba mai surutu ba ce ba" Sumayya ta ajiye robar ruwan tace "shi yasa gidan naku ai kullum yake yanayi da gidan makoki, sai nazo nake mayar dashi lively" ya karasa saukowa yana cewa "lallai wannan makarantar kullum kara kilar da ke take yi, ko kuma Adam ne yake yawar da ke?" Tayi murmushi tana dan saukowa daga kujera yayin da take gaishe shi, ya zauna yana amsawa "yasu babana da inna ta" tace "lafiya lau suke, nasan maybe da yamma zadu zo su duba oga Hussain" yace "ohh kema kin fara bin bakin Adam ko? Oga Hussain oga Hassan" ta danyi dariya, Ruqayyah tayi tsaki. Sumayya tace "ohh har zan manta ma, Baba yace a gaya muku yana gayyatar ku walima" Ruqayyah tace "walima? Walimar menene" Sumayya tace "walimar saukar Adam" Hassan ya bude ido "sauka? Yaushe Adam din ya fara karatu ballantana har ya sauke? Allah yasa dai ba saukar zuƙu yayi ba" Sumayya tace "haba dai, Baba ne fa malamin sa, idan baka yarda ba ma zaka iya kiransa kayi masa exam da kanka" ya gyada kai yace "na yarda, tunda kika ce Baba ai na yarda kuma. Allah yasa na tsoron Allah yayi" Sumayya tace "ameen" Ruqayyah tace "kuma shine Baba zaiyi masa walima?" Sumayya tace "eh fa, Baba da kansa ya shirya masa walimar. Kunsan cewa yake yi shine babban dan Baba" Hassan yace "a'a, ki ja masa kunne ya daina shiga hurumin da ba nasa ba, wannan position din nawa ne sai dai ko ya zama shine na biyu" ya mike tsaye yana cewa "zamu zo insha Allah, kiyi masa murna inji ni, in mun hadu ma zanyi masa da kaina" Sai daya fita sannan Ruqayyah ta sauke tsakin da take ta rikewa "lallai Baba da barnar kudi, har wata walima za'a shirya wa wani kedari can? A dauri kashi ko a bata igiya?" Sumayya ta bata rai "kinga fa abinda yasa bana son zuwa gidan ki kenan kwanan nan. In dai har kinsan ba zaki fadi alkhairi a kan Adam ba dan Allah kar ki sake maganar sa. Kuma baban kike cewa zaiyi barnar kudi? Kudin ki ne?" Ruqayyah tace "ko ba kudi na bane ba ai kudin mijina ne. Ko kim dauka van san cewa duk wata yana kai wa Baba kudi ba?" Sumayya tace "still ba naki bane ba, in ya kai masa ma ai ba rokar sa yayi ba kuma ko babu kudinsa yana da aikin yi yana daukan albashi zai iya komai da kudinsa. Wai ni in tambaye ki Ruqayyah, menene matsalar ki da Adam ne? Menene laifinsa? Me yasa ba kya sonsa?" Ruqayyah tace "ba son shine bana yi ba, bana son shi tare da ke dan sam baku dace ba wallahi" Sumayya ta mike tana yin hanyar kitchen tana cewa "matsalar ki ce wannan kuma. Ni ina sonsa shi yana sona iyayena suna sonsa dan ke ba kya son sa bani da problem" Ruqayyah ta sake tsaki, dole ta sake shiri na musamman, babu yadda za'a yi ta bari Sumayya ta auri inyamurin drivern kanin mijinta. An gabatar da walima lafiya, Adam ya gayyaci friends dinsa na gida dana school dinsu, Hussain da Hassan duk sunje sannan Hussain yayi masa kyautar zuwa aikin hajjin bana, murna a gurin Adam kamar bakinsa zai yage, su Baba suna ta taya shi godiya. Ruqayyah bata samu zuwa walimar ba saboda rashin lafiyar da take fama dashi, a jikinta ta fara tunanin ciki ne da ita dan haka tayi home pregnancy test kuma ya tabbatar mata da zargin ta, hakan yasa ta fahimci tun kafin tafiyar su Hassan India cikin ya shiga, amma sai ta boye abinta a ranta saboda tana tsoron kar ta fada ace ba za'a yi tafiyar nan da ita ba, tafi son in anje can a gane, sai ta nuna cewa itama bata san dashi ba. Ko babu komai ta samu abin nunawa Fatima. Aka kammala duk shirye shirye, ranar tafiya tayi suka tashi gabaki dayan su Aunty, Hassan da Hussain, Ruqayyah da Fatima, Safiyyah, Khadijah, Nafisa, Zulaihat. Tunda suka je suka dukufa gurin gaya wa Allah bukatun su, babbar bukatar su ita ce ta neman lafiya ga Hussain, babban fatan su shine in Hussain ya koma asibiti a tabbatar masa da cewa ya rabu da wannan cancer din. Ruqayyah kam nata bukatun take roka babu ruwanta da wani Hussain, bata rokar masa rashin lafiya ba kuma bata rokar masa sauki ba. Fatima ce ta fara lura da chanjin yanayin Ruqayyah kuma direct ta gaya mata cewa tana zargin tan da ciki, ta kuma raka ta asibiti kamar lokacin cikin Twins sannan kuma aka tabbatar mata da zargin ta. Kowa yayi murna da kasancewar hakan, amma kuma kirikiri suka ringa nuna wa ina ma dai Fatima ce mai cikin amma sai Hussain ya ringa basarwa duk kuwa da cewa duk sujjadar da zaiyi sai ya roki Allah ya bashi magaji kafin ya karbi ransa. A haka suka gama azumin su, lokaci ya kuma tafiya har lokacin aikin hajji yayi, a lokacin ne Adam da Sumayya wadda Hassan ya biyawa suka taho tare da Hassana, suka hadu da sauran family din suka gabatar da aikin hajjin su sannan kuma suka juyo zuwa Nigeria. Sai dai Hassan da Hussain su ba Nigeria din suka taho ba India suka tafi inda za'a sake duba Hussain dan a tabbatar da warkewar sa ko akasin hakan. Suna zuwa aka sake yin wani colonoscopy din aka dauki sample daga hanjin Hussain sannan aka tura shi lab dan gwadawa. Fir Hussain yaki zama ya jira result din yace sai dai a aiko masa ta email dan haka kwanan su biyu a India suka bi iyalinsa zuwa Nigeria. Yana zuwa Nigeria ya tarar Fatima babu lafiya, wai tun a jirgi ta fara amai kuma har yanzu yaki tsayawa. Da kansa ya dauke ta zuwa asibiti "wato da banzo ba zama zakiyi tayi ba zaki je asibiti ba ko Princess?" Tace "ni bana son allura" amma a ranta tsoron ta daya, tana ta saka ran cewa ciki ne da ita tana jin tsoron kar a gwada ta ace babu, wannan heart break din take tsoro, shi yasa duk yadda Aunty tayi da ita akan zuwa asibitin taki yarda. Tashin farko PT aka rubuta mata, aka yi mata kuma aka bata result sai dai ta kasa budewa, idonta har hawaye ne ya taru a ciki, ta mikawa Hussain tace ya bude, shima tsoron budewar yake yi sai ya mika mata yace ta bude. Doctor din yayi dariya yace "to ni ku bani in bude tunda naga kamar tsoron takardar kuke yi" suka mika masa sannan suka zauna suka zubawa juna ido, doctor din ya karanta yana murmushi sannan yace "to a bani goron albishir da kuma ladan karantawa. You are going to be parents in the next seven months" Basu san sanda suma tashi suka rungume juna a gaban doctor din ba, Fatima sai kuka, Hussain yana dariya, doctor yace "kar a manta da goron albishir dina" Hussain ya juyo yana kallon sa yace "just name it, ko me kake so in dai ina dashi ya zama naka". A ranar kaf gidan babu wanda bai san da labarin cikin nan ba, hatta masu gadi sai da suka sani dan aljihunsu sai da yayi nauyi, rabon kudi har mutanen waje sai da suka samu nasu. A ranar ne kuma e-mail ya shigo wa Hussain daga doctor. "Dear Hussain Aminu Abdullahi, we regret to inform you that the operation performed on you was not successful in eliminating the cancerous tumor, it has regrown. We suggest performing another surgery as soon as possible" Ya rufe e-mail din sannan ya rufe system din tare da kwanciya ya rufe idonsa, mintuna kadan sannan ya bude su ya mike ya dauko diary dinsa da biro ya fara rubutu. Dear baby . A yaune aka tabbatar min da cewa kana nan kan hanyar ka ta zuwa duniya, a yaune kuma aka tabbatar min da cewa ni kuma ina kan hanyata ta barin duniya. Tunani na daya shine "ko zan ga fuskar ka kafin in tafi?" Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020 *The News* Ya rufe diary din da sauri dan ji yayi kamar zuciyarsa ba zata iya cigaba da rubutun ba, sai ya koma ya kwanta yana mai dora diary din akan kirjinsa tare da rufe idonsa yana tunani, Fatima ce ta fara fado masa a rai, tunda doctor ya karanto musu result din PT dinta har yazu ta kasa rufe bakinta dan murna sai yaji baya son ya katse mata murnar ta da wannan mummunan labarin, baya son ya katse mata murnar ta har abada. Zai so ace murmushin da yake kan fuskarta zai dore ne har karshen rayuwarta. Sai ya dauki wayarsa ya fita valcony tare da rufe kofa, ya kira number din doctor din daya duba shi a Indiya, doctor din was so sympathetic yana kuma jaddada masa muhimmancin komawa a sake yin wani aikin. Bai musa ba ya nuna masa zai dawo as soon as possible amma kuma sai ya roke shi wata alfarma guda daya, alfarmar ita ce yana so ya sake turo masa wani email din stating cewa ya warke completely daga ciwon da yake damunsa "my wife is pregnant, and I don't want to break her heart" da farko doctor din kin yarda yayi saida Hussain yayi ta nace masa ya kuma tabbatar masa da zai dawo sannan ya amince, washegari da safe kuwa sai ga wani e-mail din da sa hannun doctor din da logo din asibitin da komai amma a ciki an yi bayanin cewa Hussain ya warke completely babu sauran trace na Cancer a tare dashi. Hussain yana samun wannan sai ya koma baya ya goge wancan da aka fara turo masa dashi. Sannan sai ya dauki system din ya tafi dakin Fatima da murmushi a fuskarsa. A palonta ya same ta tana saka turaren wuta, tun daga nesa ya hango annurin fuskarta ya kuma san tun na jiya ne, tun na albishir din doctor ne. Yace "hey princess" ta juyo tana kallonsa tare da kara fadada murmushin ta, sai ta ajiye incent burner din hannunta ta taho gurin sa da sauri. Kafin ta karaso yace "albishirinki" sai ta dakata zuciyarta tana ayyana mata albishir din da zaiyi mata dan ita yanzu bayan sakon doctor na jiya to wani sakon doctor din ne kadai zai faranta mata maybe ma fiye da wancan, dan lafiyar Hussain ta fiye mata komai yawan yayan da zasu haifa. Ta fara kokarin studying fuskarsa dan ta tabbatar da abinda yake mata albishir din akai, sai ya gyada mata kai kamar mai kokarin tabbatar mata da zargin ta sannan ya juyo mata da screen din system din da take hannunsa "read this". Da sauri tayi yawo da idanunta akan screen din, tana taking information din at ones sannan tayi tsalle tana rufe baki, idonta kamar zai fado daga fuskarta, haka ma zuciyarta. "Ka warke! Hussain ka warke. Oh my love, ohh Allah na na gode maka, Alhamdulillah" ya ajiye system din yana kokarin rike ta amma taki rukuwa, farin cikin da take ciki yafi karfin tsayawa a guri daya sai ta fara zagaye a palon tana tsalle yana binta har ya samu ya kama ta ya daga ta sama yana zare mata ido "ke! Garin murnar mijinki ya warke kuma shine zaki je ki sabauta shi?" Bata kula fadan da yake mata ba sai ta kama fuskarsa da hannayenta sannan ta fara kissing duk inda ta samu a fuskar, sai shima ya fara dariya a ransa yana hoping ina ma inama? Ina ma farin cikin su mai dorewa ne. Haka yayi ta juyi da ita a palon sai da suka gaji sannan ya zauna da ita a kan cinyarsa yana nishi "yarinyar nan fa nauyi ne dake wasa wasa" tayi dariya tana juya idonta "kasan dai bani kadai bace ba yanzu ko? Dan haka nauyin ba nawa bane ni kadai" ya dora hannunsa a marar ta "ayyah, bawan Allah za'a yi masa sharri dan anga bashi da baki ko?" Sai ya kai fuskarsa kusa da cikinta yace "hello angel, this is your father speaking, maman ka tana yi maka sharri tace kai dan lukuti ne kamar ta" ta dago kansa tana hararar sa "wace lukutar?" yace "wai da" sai ta dauki pillow ta fara dukansa dashi, ya tashi yayi daki da gudu ta bishi. A ranar labari ya kai wa duk wanda ake tunanin ya kamata a gayawa cewa result din Hussain ya fito kuma ya warke tas babu sauran abinda yake damunsa. Aunty da kanta ta shirya musu dinner gaba ki dayansu to celebrate the news. Ta ai kawa kowa sakon azo part dinta a ci abincin dare, har Hassana da mijinta da kuma Jabir wanda sati uku ya rage bikin su da Safiyya. Da kuma Ruqayyah da Hassan. Lokacin da Hassan ya shiga gida baki har kunne yana nunawa Ruqayyah email din da Hussain yayi masa forwarding zuwa wayarsa, a daki ya same ta a kwance dan wannan cikin kasala yake saka ta ba kadan ba, ya jawo ta ya rungume ta "Hassana Hussain ya warke, ya warke ya warke, Hassana ki taya ni murna Hussaini na ya warke" farko bata ma gane me yake cewa ba, ta dan bata rai tana ture shi saboda bata son kamshin turarensa tace "me kake cewa? Me ya samu Hussain din?" Ya sake ta yana murmushi, idonsa yana kyalli "babu abinda ya same shi babu abinda zai same shi likitoci sunce ya warke" ta danyi shiru tana digesting maganar "wait, what? Ya warke fa kace, dama ana warkewa daga cancer ji nake yi bata da magani" ya danyi dariya "babu ciwon da bashi da magani Ruqayyah, ita cancer maganin ta shine ayi aiki a yanke bangaren da yake da ciwon sai kuma a kashe gurin yadda ciwon ba zai dawo ba balle ya yadu, in dai akayi nasara a wannan to shikenan mutum ya rabu da ita, akwai mutane da yawa da suka warke daga cutar cancer kuma Hussain yanzu is one of them. I am so happy, I was so scared cewa wani abun zai iya samunsa" tayi sauri ta mike ta shiga toilet pretending as if amai ne ya taso mata. Ta rufe kofa sannan ta jingina da jikinta. Daga inda take tana iya hango katangar gidan Hussain ta tagar toilet dinta. Ta runtse idonta tana tuno mugun labarin da jiya ya cika gidan na cewa Fatimah tana dauke da ciki, kuma a yadda Nafisa take gaya mata wai cikin har yayi wata biyu ma'ana banbancin wata biyu ne tsakanin nata da na Fatima. Wannan wacce irin bakar rana ce? Dukkanin mafarkanta sun tarwatse a cikin kwana daya. Fatima ta samu ciki sannan Hussain ya warke. Ta tari ruwa a hannunta tana wanke fuskarta, a zuciyarta tana jin haushin kanta data daina shan pills dinta har ta kai ga samun ciki a hope dinta na rike gidan ta hanyar amfani da ƴaƴan ta, gashi yanzu gimbiya zata haifi nata, guda dayan da zai doke dukkan nata guda ukun tunda ubansa shine mai kudin gidan. Ta tuna da irin celebrating din da akayi tayi a gidan tun jiya bayan ita sanda ta samu nata cikin farin babu wanda ya ko da daga murya ne da sunan murna. Wannan ciki kuwa ko maganar sa ma ba'a yi, wani abin haushin shi kansa uban yayan sanda ya fahimci tana da cikin sai da yayi mata magana, a lokacin suna Saudiyya . "Ina pills din da doctor ya baki" tace "suna Nigeria, ban taho dasu ba" ya bata rai "ai dama ba nan nake nufi ba, ai ba anan aka samu cikin ba, a Nigeria din nake nufi ba kya sha dama" ta bata rai "ina sha mana, wasu kwayar magani sun isa su hana mutum haihuwar abinda Allah ya riga ya rubuta sai an haifa. In baka so ka gaya min kawai ba sai kana boye boye ba" ta fara hawaye, ya kamo hannunta, ya zanyi ince bana so Hassana? Ko ya'ya nawa zan haifa ai duk Allah ne ya bani kuma duk ina so kawai dai jariran can nake tausayawa wallahi, kin ga basu yi wani kwari ba yanzu suke kokarin fara rarrafe" tace "ai dama suna shan madara, sai su cigaba da shan madarar su kawai ni kuma su barni in ji da kaina" daga nan kusan babu wanda ya kuma yin maganar cikin nata a zaman nasu na Saudiyya, su duk sunfi mayar da hankalin su akan addu'ar samun sauki gun Hussain. Gashi yanzu addu'ar tasu ta karbu ita kuma sun barta a tasha. Ta tuna da alkawarin da wannan malamin duban yayi mata "zaki yi kudi fiye da kudin da kike saka ran zaki yi" tayi tsaki "banza makaryaci" ta fada a fili. "Allah yaso ban bashi ko kwandala ta ba" ta dawo daki ta tarar Hassan ya fita ta koma tayi kwanciyar ta ta na jin duniya duk tayi mata kunci, me yasa ne duk plan din data shirya sai ya wargaje ne wai? Ita har yanzu fa ko quater din abinda take so bata samu ba. Wata zucuyar ta gaya mata ko dai tayi giving up ne ta koma school irin na Sumayya tayi karatu ko zata samu aiki ta dan kara wani abu? Tayi tsaki, kuma shikenan yadda ake ganin ta kuma sai aga ta koma makaranta? Wanda ma bai san cewa bata yi jami'a ba shikenan sai ya sani. A haka har magrib tayi, dama yanzu tun dawowar su ta dawo da cook din su ta da ta cigaba dayi musu abinci saboda tana laulayin ciki, twins kuma shekaran jiya taje ta kaiwa su inna tsarabar su ta barsu a can zasu dan kwana biyu. Dan haka a daki take wuni sai dai ta fita taci abinci ta dawo, wani lokacin kuma abincin ma a daki ake kawo mata taci abinta takwanta. Balle yau da bata so taga fuskar kowa dan tana jin duk wanda ya kula ta zata iya rufe shi da masifa ko da kuwa babu laifin da yayi mata. Starting from Hassan dan da yasan haushin sa da take ji yau din nan da ko inda take ba zai dosa ba. Tana zaune a kan sallaya ya shigo ya tsaya yana kallonta a ransa yana jin ba dadi akan irin yadda tayi reacting to labarin samun saukin Hussain. Baya son ya yadda da abinda kwakwalwar sa take gaya masa akanta. Yace "ki shirya in an jima zamu je gurin Aunty, ta shirya mana cin abinci na musamman dan murnar abinda ya samu Hussain" ta mike daga kan sallayar tana kallon sa "cin abinci na musamman? Saboda me? Saboda matar mai kudi ta samu ciki ko kuma saboda yar sarki ta samu ciki? Ni sanda na samu nawa cikin ko shan ruwa na musamman ba'a shirya min ba balle cin abinci, kai ni ko magana ta musamman ba'a gaya min ba" ya karaso tsakiyar dakin yana kallonta yace "da ni da Hussain duk daya muke a gurin Aunty, da ke da Fatima duk daya kuke a gurin Aunty, Aunty kuma uwa ce a gareni dan haka ina so ki san maganar da zaki fada a kanta. Ba kudin Hussain ko matsayin Fatima ne yasa zamu taya shi murna ba, ba kuma cikin jikin Fatima zamu yi celebrating ba, samun lafiyar Hussain zamuyi celebrating saboda ba wai abu ne common ace mutum yayi Cancer briefly ya warke ba, warkewar sa shine abinda zamuyi celebrating" ta cire hijab dinta tana ninkewa tana huci "eh dama ai kai kowa yana da muhimmanci a gurinka banda ni, ban isa in fadi magana akan kowa ba sai kace kar in kuma amma ni duk abinda za'a yi min mai baka gani, duk irin wariyar da ake nuna min kai baka gani" yaji bacin ransa yana karuwa, yace "dan Allah Ruqayyah kar ki bata min rai bayan ina cikin farin ciki, can't you at least pretend to be happy ko dan in shiga cikin yan uwana cikin jin dadi? Menene problem dinki ne wai? Yanzu rashin son da kuke yiwa Hussain har ya kai baki damu da samun lafiyar sa ba" ta ajiye hijab din ta hau kan gado ta kwanta tace "tunda bata maka rai nake yi it will be better idan banje gurin ba, kar in cigaba da bata maka ran acan ma. And ina taya Hussain farin ciki da samun lafiyar sa, kawai dai am not in the mood for celebration ne" ta ja bargo ta rufe har fuskarta. Haka ya juyo ya fito daga dakin ya shiga nasa ya shirya ya fito, ko kallon dakinta baiyi ba ya fita ransa duk babu dadi, shi duk ba haka yayi tsammanin auren sa zai kasance ba, shi ba haka yayi tunanin matar da ya zaba a cikin matan duniya zata ke treating dinsa ba, shi ya saka ran total submission daga gurin matarsa yadda zata faranta masa shima kuma ya faranta mata. Bai taba tsammanin yarinya karamar daya dauko daga cikin talauci ya kawo ta cikin daula zata raina abinda yake dashi take kuma mayar masa da magana aduk lokacin daya fadi wani abu ba, bai dauka young and innocent hassanar sa zata iya fadar bakar magana akan Hussain ba ballantana Aunty. Godiyar Allahn da yayi shine duk sun san tana fama da laulayin ciki, duk da dai sai da da yawa daga ciki suka yi korafin ya kamata axe ta daure ta dan leko ko na yan mintuna ne ta koma. Dole ba da son ransa ba yayi musu karya yace ai jikin ne ya matsa mata sosai. Sai yayi ta sha'awar Hussain yadda Fatima take makale dashi tana jinyar sa shima yana jinyar ta, a tare suke rige rigen serving junan su abinci , sai yayi tunanin shi yaushe rabon da Ruqayyah ta zauna ta zuba masa abinci? A table yake zuwa ya tarar mai girki ta ajiye ya zuba ya ci ya tashi ya tafi. Ko sanda tana girkin ma bata iya jiransa sai ya dawo daga office cin kayanta take yi in ya dawo yaci shi kadai. A cikin kwanakin da suka biyo bayan nan abubuwa duk sun kara tabarbarewa Hassan, Ruqayyah gabaki daya ta kara rikice masa ya kasa gane kanta gabaki daya, har sai da wata zuciyar ta raya masa cewa ya je ya kai karar ta gurin Baba amma sai ya fasa ya saka ta a gaba da nasiha duk da dai cewa shi bai san laifin da yayi ba. A cikin wannan yanayin ne akayi bikin Safiyya da Jabir, a matsayin Hassan na babban yayan amarya sannan babban abokin ango amma haka yayi bikin duk babu dadi saboda cikin gidan sa babu dadi, saboda bai yi dace da mace ta gari ba. Bayan hakan ne Minal tazo mata ziyara. Suka shige cikin dakinta suka zauna Minal tana cewa "kai Ruqayyah wannan dakin naki ai yayi datti da yawa, kwanan ki nawa rabon da ki share shi?" Ruqayyah tace "wannan kuma matsala ta ne. Ke dai ki zauna a nan dan yallaban gidan nan ya xe baya son mu'amala ta dake kuma dama kwana biyun nan ba dadi muke yi dashi ba" Minal tace "mijin naki ne ba kwa dadi da shi? Lallai sannun ki da aiki, in dai ta nine ya kwantar da hankalin sa in baya son inzo gidan sa ba zan kuma zuwa ba dan nima ina da gidan mijina ba wai a titi nake ba" Ruqayyah tace "ke ba akan ki bane ba, ni din ce dai kawai duk zuciyata babu dadi kwana biyun nan. Kinsan matar gidan nan kuwa ciki ne da ita?" Minal tace "wacce matar gidan? Aunty?" Ruqayyah tayi dariya tace "ke yar iska ce Allah. Auntyn ce zata yi ciki dan baki da kunya. Gimbiyar gidan nake yi miki magana matar dan goten kaduna" Minal ta bude ido "to fa babbar magana. Ni da nake ta saka ran ta hanyar rashin haihuwar ta ne maganar Malam zata tabbata" Ruqayyah tace "ke dai bari, abin nan ba karamin daga min hankali yake yi ba wallahi, musamman ace ta haifi namiji shikenan fa mu da dukiyar su daga hange sai leke sai harara daga nesa, duk yayan da zan tara zasu yi ta bin yayanta ne a baya kamar yadda mijina yake bin mijinta a baya" Minal tace "ki zo mu koma Ruqayyah, kina bukatar taimako, rayuwarki tana cikin matsala sai an hada miki da addu'a. Kinga fa ni yanzu albishir din da na zo inyi miki shine ciki ne dani, idan kinga yadda Alhaji, mahaifiyarsa da yan uwansa suke nan nan dani sai kinyi mamaki, ita fa uwargidan nasa da suke cewa matar so yanzu babu son duk ya dawo gurina da abinda yake cikina. Tana nan kamar zata mutu kullum kofarta a rufe" Ruqayyah tace "Allah Minal? Yanzu ciki ne da ke? Kai amma na taya ki murna wallahi Allah ya raba ku lafiya" daga nan sai ta bata labarin nata cikin itama suka taya juna murna suka cigaba da plans din su na yakar mutanen da suke gani a matsayin makiyan su. Rayuwa ta cigaba da tafiya ba tare da kowa yasan cewa Hussain ba wai warkewa yayi da gaske ba, hatta Hassan bai san cewa ciwo yana cin Hussain kadan kadan ba, itama kuma Fatima saboda tana fama da nata laulayin cikin sai ta gaza gurin fahimtar changes din da yake samu. Ciwon ciki ne yafi damunsa mostly idan yaci abinci amma sai ya boye yaki yarda fatima ta gani. Duk sanda kuma baya jin ciwon hakan keeping wide smile a fuskarsa wanda yake boye damuwar da take cikin idanuwansa, amma duk da haka damuwar bata boyu ga Hassan ba, tambaye shi "wai kai me yake damunka ne?" Sai yace "ni babu abinda yake damuna, maybe idonka ne yake nuna maka hakan" "babu wani ido na, gashi nan har ramewa naga kayi? Are you sick or something?" Hussain ya daga kafada yace "babu wani abu, gajiya ce kawai, aiki yayi min yawa ina bukatar hutawa. Ga kuma marar lafiya ina da ita a gida" ya fada yana murmushin dan ya kawar da maganar amma Hassan bai yarda ba, sam zuciyarsa bata yi masa dadi da yanayin na Hussain. Baya son abinda zuciyarsa take fada masa akan yanayin na Hussain amma kuma dole ya kamata ya bincika wannan angle din ko dan ya samu nutsuwar zuciya. Wannan ya sa ya tura sako zuwa ga doctor din Hussain, ya roki sanin health status din Hussain duk da cewa yana tunanin ba zasu bashi ba amma kuma ganin cewa ya tura sakon ne da same email da ya fara registering Hussain sai ya saka ran samu. Sai da aka kwana biyu sannan sai ga phone call daga doctor din. Yana office ne a lokacin, yaga number da code din India sai jikinsa ya bashi doctor din ne tunda bashi da business da wani a India kuma yana saka ran ji daga doctor din. Sai dai kuma sai yaji yana tsoron dauka dan bai san abinda zaiji ba, da kyar dai ya hakura ya dauka ya kara a kunnensa yare da cewa "Hello" doctor din yace "are you Hussain aminu's brother?" Hassan yace "yes, I am" sai ya fara fada "then why are you not bringing him back to hospital? He should be in the hospital right now taking treatment" Hassan ya runtse idonsa yana jin tamkar wukake doctor din yake soka masa a kirjinsa yace "but he said the operation was a success" doctor yace "no it wasn't, and we told him that. You should bring him in again, he is .... ....." Hassan bai karasa jin maganar doctor din ba ya saki wayar hannu sa ta fadi kasa. *Kuyi hakuri babu yawa, bana so in barku jira babu dadi shi yasa na baku a haka, tomorrow's episode will insha Allah be longer and more action packed*. Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani guri na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020 *The Accident* Ko bi ta kan wayar ta sa da ya yar bai yi ba, bai kuma kula da mutanen da suke tambayar da ko lafiya suka gandhi a rikice ba, kokarin sa kawai shine ya ganshi a gida ya ganshi a gaban Hussain kuma ya yi convincing dinsa su tafi asibiti. Ko parking bai kammala ba ya fito ya rufe kofa ya doshi part din Hussain dan yaga Adam ma'ana Hussain yana gida kenan. Yana shig ya samu daya daga cikin yaran Fatima "ina Fatima take? Me gidan yana ciki?" Ganin Yadda hankalinsa yake a tashe ya sa ta rude "gimbiya bata nan, sun fita dazu ita da Aunty Khadija, amma yallaban yana ciki banga saukowarsa ba....." bai jira ta karasa bayanin ta ba ya wuce ta ya haura sama da sauri ya nufi wing din Hussain. A palo ya same shi a kwance akan doguwar kujera da diary dinsa a gabansa, idonsa a rufe, hannun daya akan cikinsa dayan kuma akan diary din. Motsin shigowar Hassan ne ya saka shi bude idonsa da sauri. Sai kuma yayi kokarin mikewa zaune yana dan cije lips dinsa amma kuma fuskarsa da murmushi "hey, gidan mijin aure ne fa kake shigo min kai tsaye, ko baka san ni mijin aure bane ba?" Hassan ya share shi ya nufi diary din kamar zai dauka sai Hussain ya riga shi, a tura shi bayan sa yace "sirri ne na gaya maka" Hassan yana kallon sa yana lura da yadda yake iyakacin kokarin sa na ganin yayi keeping straight face sannan yace "why? Me yasa zaka yi mana karya Hussain? Ko zaka yi wa kowa karya ni mai yasa zaka yi min Hussain? Why do you choose to suffer alone bayan ba kai kadai aka haife ka ba tare dani aka haife ka? Me yasa zaka ware ni when you need me the most?" Hussain ya dauke kansa gefe, ya fahimci cewa ya sani, sai ya girgiza kansa yace "what does it matter in na gaya maka din, babu abinda zaka iya yi min, babu abinda kowa zai iya yi min, wanda zai yi min komai na gaya masa na kuma roke shi ya bani lafiya, na saka kun taya ni rokonsa ya bani lafiya, tunda ka ga bai bani ba to lafiyar bat da alkhairi a gurina, shi kadai yasan me yake nufi da ni". Zuciyar Hassan ta karye ya durkusa a gaban Hussain tare da dafa gwuiwar sa yace "Hussain dan Allah kazo mu koma asibiti, dan girman....." Hussain yayi sauri ya rufe masa baki "mun gama maganar nan Hassan, na roke ka kuma ka amince, kayi min min alkawarin ba zaka sake mayar dani asibiti ba. Hassan likitoci ba zasu hana mala'ikan daukan rai ya dauke ni ba, kudina dukka ko zan karar dasu ba zasu kara min adadin kwanakin da aka kayyade min ba. Dan Allah Hassan kar ka tilasta min komawa asibitin nan, bana so in mutu a zagaye da likitoci da injina,bana son in karasa sauran kwanaki na a asibiti looking at faces din mutanen da basu da muhimmanci a rayuwata. Na fi son in zauna a gida tare da ku, tare da Fatima, nafi son inyi making use of my last days doing abinda zai amfani lahira ta ba wai neman lafiyar da babu wanda zai bani ita ba. Wancan aikin da akayi min na gaya maka na amince ne dan in faranta maka ba wai dan raina yana so ba" Hassan ya sake girgiza kansa "ba dan ni ba, yanzu kayi dan Fatima, dan abinda yake cikin Fatima" Hussain ya dauko diary dinsa yana budewa yana murmushi yace "Allah baya taba barin wani dan wani yaji dadi, ko babu ni nasan abinda yake cikin Fatima yana da uba, nasan ba zai yi kuka maraici ba, zai samu gatan uba a gurinka kuma a bangaren mahaifiyarsa ma ba zaiyi rashin komai ba". Hassan ya zauna sosai yana kallon Hussain guiwoyin sa sunyi sanyi da suka kasa cigaba da daukan sa, ya runtse idonsa yana fatan hawaye yazo masa ko zaiji sanyi a zuciyarsa. A ransa yana addu'a "Allah in zaka dauki wani a cikin mu Allah ka dauke ni ka bar Hussain, Allah ka dawo da ciwon Hussain kaina shi ka bashi lafiya ya Allah. Allah kar kasa Hussain ya tafi ya barni Allah" ya bude idonsa sai suka hada ido da Hussain yana yi masa murmushi yace "don't cry bro, kar kabada maza mana, everything is going to be okay". Babu yadda Hassan bai yi ba amma Hussain ya tubure yace shi babu asibitin da zai koma, babu aikin da za'a sake yi masa, kuma ya roke shi Allah da Annabi kar yabari kowa yaji cewa ciwonsa ya dawo. "Bana so inga hawayen su, ga halin da Fatima take ciki bana so in tayar mata da hankali" sai dai Hassan bai hakura ba sai da ya kuma kiran wancan doctor din yayi masa bayanin irin taurin kan Hussain da dagewar da yayi akan ba zai koma ba, sai doctor din yayi referring dinsu to wani oncologist din a nan Nigeria ya kuma bawa Hassan shawarar ya lallaba Hussain ya kaishi can "ko ba za'a yi masa aiki ba sai a bashi drugs din da zasu rage masa radadin ciwo, cos he is in pain right now, ina mamakin ma yadda har kace yan iya harkokin sa har yana boye ciwonsa, he really is strong". Hassan ya gyada kai yace "the strongest man I have ever known". Likitan da aka hada shi da shi a Abuja yake da private hospital dinsa kuma ya kware sosai a aikinsa. Hassan ne ya shirya yaje asibitin, ya tarar already an aiko da record din Hussain da komai daga can asibitin dan hak kawai takardu ya ciccike sannan ya koma Kaduna ya fara yakin lallaba Hussain akan ya taho yaga wannan likitan. Da kyar ya yarda suka zo, da alkawarin cewa ba kwantar dashi za'a yi ba. Da daddare suka zo secretly saboda gudun sa idon yan media, Doctor din ya duba shi sosai, yayi masa hotuna sannan yayi masa prescribing drugs din da zasu taimaka masa wajen dulling pain din da yake ji. Amma Hassan bai ji yayi promising komai ba. Haka suka karasa kwana a hotel tunda Hussain yaki kwana a asibitin. Da safe ne da zasu taho yake cewa "da akwai wani abokina Sadiq, dan sarkin Abuja ne ina jin baka san shi ba dan a wani zuwa da nayi London muka hadu dashi kuma bai taba kawo min ziyara ba nima ones na taba zuwa gidan su tunda shi ba mazauni bane ba. Amma we are very close a waya munsan affairs din juna" Hassan yace "to ko zamu shiga ku gaisa?" A ransa yana fatan hakan zai farantawa Hussain rai, Hussain yayi murmushi yace "baya nan, ya bata" Hassan ya danyi dariya, "ya bata fa kace? Ya bata kamar yaya?" Hussain yace "wata yarinya yake so balarabiya, babansa sarkin Abuja yaki zuwa ya nema masa aurenta shine na bashi shawarar yaje ya nema da kansa, he went there kuma suka hana shi. Tun daga nan ba'a kuma jin labarin sa ba yayi cutting off ties da gida gaba ki daya har mu abokan sa babu wanda yasan inda yake. Rumors have it that ya sace yarinyar ne yaje ya aure ta, but babu wanda yasan a wacce kasar suke yanzu" Hassan ya bude baki yana mamakin wannan irin karfin hali na wannan bawan Allah, amma ya sani dole duk inda suka tafi ma watarana da kafafuwan su zasu dawo gida kuma yana guje musu abinda zasu tarar a gidan musamman saboda kasancewar su yan sarauta. Hussain yaji dadin magungunan sa sosai, dan da suka kare shi da kansa ya kira Doctor din ya sake bashi wasu. Sun rage masa ciwon da yake ji a cikinsa sosai kuma yanzu yakan ita zama yaci abinci ya koshi, yaji dadin hakan dan hakan ya kara taimaka masa wajen kara boyewa Fatima halin da yake ciki. Cikin Fatima yana ta girma abinsa, cikin lafiya ita kuma cikin kwanciyar hankali dan babu abinda yake damunta, ga Hussain yanzu da yake kara makale mata kamar cingam dan office din ma yanzu ba fita yake yi ba in ma ya fita da wuri yake dawowa, yawon kasashen duniyar ma duk ya daina kullum yana tare da ita yana yi wa babyn cikinta hira, haka zai ta bawa cikin labarai yana dariya shi kadai ita kuma tana yi masa dariyar wautar sa "ba fa ta jinka" yace "injiwa? Haka ya gaya miki?" Tace "wai kai wa yace maka namiji ne? Na gaya maka mace ce" yace "ke wa yagaya miki macece? Ni na gaya miki namiji ne" tace "ai a cikina take ko? Muna communicating through placenta" yayi dariya "gori zaki yi min ko? Nima ai muna communicating through you, kuma ya gaya min shi namiji ne" tace "to aje a duba mana, sai a kure musu" yace "anki wayon. Ni bana so a kure ni". Sai dai ba wai rashin son a kure shine ya hana shi zuwa a duba gender din abinda yake cikin Fatima ba, damuwarsa shine yadda rabon gadonsa zai kasance idan ya mutu, dan haka ya yanke wani hukunci kuma ya gama tsara duk plans dinsa gabadaya sannan yaje ya samu Hassan a office dinsa ya ajiye masa takardu a gabansa yace "I need to sign these" Hassan ya dauki takardar yana jujjuya ta yana karantawa briefly, ya dago kai yana kankance idonsa yace "what is this? Me kake yi haka?" Hussain ya daga kafada yace "I am giving you half of h and h and all it's assets. Dama sunan sa H and H ma'ana Hassan da Hussain, it is yours as much as it mine, ka sani kuma" Hassan ya girgiza kansa yana dawo masa da takardun gabansa yace "bazan karba ba kuma kaima ka sani, ba tun yau ba ka nuna kana son bani nace bana so saboda ni nafi son inyi working in kuma yi earning kudi na da kaina. Wannan naka ne, H and H naka ne ba namu bane ba kuma kai ma kasan wannan" Hussain yace "shikenan, in baka karba ba ya zama na lawyers dina dan already na riga na fitar dashi kuma sun saka hannu, yanzu saka hannun ka kawai ya rage" suka yi shiru suna kallon juna. Hussain yace "look Hassan, ba wai na baka bane dan baka dashi ko dan in taimaka maka ba a'a na baka ne as security for our family, ban san abinda Fatima zata haifa ba, in ta haifi namiji yayi muku katanga da duk wani abu dana mallaka ni kuma ba zan so haka ba, zanso ace kun gaje ni kai da kannen mu saboda dama dan in kula damu na fara business din nan. Gidan mu da wannan kamfanonin aka dogara gabaki daya, idan Fatima da danta suka karbe komai kai da Aunty da sauran yan'uwa zaku koma a karkashin ta kenan, you will be working under my son and wife abinda ni kuma ba zai min dadi ba duk da nasan Fatima kuma ina saka ran abinda zata haifa zai samu tarbiyya mai kyau daga gurinta da kuma gurinka. But zan so ace kun zama partners ne. Yadda ko ma me ta haifa you still have your share, wadda nasan zaka yi amfani da ita ne gurin kula da kanka da Aunty da yan uwan mu da yayan mu, all of them". Hassan yace "stop talking as if mutuwa zaka yi Please, idan da kasan yadda maganganunka suke taba zuciyata da ka daina yin irin su Hussain. You are getting well, ba ka ganin yadda jikin ka yayi kyau?" Hussain ya mike yanakara tura masa takardun gabansa yace "sign this please, and try to get some sleep dan ka rame da yawa". Daga nan ya fice ya barshi a zaune, ya jawo takardun yana duba signature din Hussain baro baro a jiki cewa ya bashi rabin duk abinda ya mallaka a duniya. Sai ya jawo drawer ya saka takardun sannan ya mayar ya rufe. Ya koma ya kife kansa akan table din gabansa yana jin kansa yana sarawa sosai. Shi kansa yasan ya rame ya kara baki ya bushe, mutane da yawa suna tambayarsa "lafiyar ka kalau kuwa?" Yakan amsa da eh amma shi kansa ya san bashi da lafiya, ciwon nan na Hussain yana damunsa sosai kullum hankalinsa ba a kwance yake ba, ko magana yaji anyi da karfi ko kuma yaji hayaniya sai gabansa ya fadi, sai ya dauka za'a ce masa wani abu ya samu Hussain din sa. Ga kuma problem din Ruqayyah. Duk da wani bangare na zuciyarsa wanda yake cike da sonta kullum yana yi mata uzuri amma kaso mafi yawa na tunanin sa yafi karkatuwa ga karbar gaskiyar magana. Gaskiyar magana kuma shine bai yi dace da mace ta gari ba. Lokuta da dama yakan samu kansa da tambayar kansa shin ina wannan Hassanar daya aura take? Anya ba'a chanja masa da wata ba kuwa? Ina wannan karamar yarinyar nan data dora rayuwarsa a saman tata ta ceto shi daga bakin bindiga take, ina yarinyar nan yar gidan malamai mai cike da tarbiyya, kunya da ilimin addini? Ina yarinyar da bata saba da kyale kyalen duniya ba? Dan yasan ba ita bace wannan wadda last week ta hana masa sakat a gidan sa da mitar Hussain ya sake wa Fatima mota ita banda ita ba, dan waccan yarinyar babanta ko keke bashi dashi. Yanzu gidan sa ya koma abin gudu a gurinsa, wannan yasa kullum yana office, har weekend zuwa yake yi yayi ta aiki shi kadai musamman tunda yanzu Hussain ya tattara harkar kamfanin yayi watsi da ita. Shi kuma sai ya dauki aikin yake tayi da iya kacin karfinsa dan yana so ya rage wa kansa tunani kuma ya nesanta kansa da fada da kuma mitar Ruqayyah. Yau ma kafin ya fito sai data saka shi a gaba da zancen tana son ya bata kudi ta tafi Dubai siyayyar haihuwa. Hussain yana komawa gida yayi wa Fatima alkawarin ta lissafa masa dream countries din da take son zuwa a rayuwarta shi kuma zai kaita. Ta bude baki cikin murna "lah! Na dauka yanzu baka son fita" yace "yanzu ina so, so nake mu fita mu samu good quality time daga ni sai ke sai baby" ai kuwa nan take ta fara lissafa masa duk inda take son zuwa, shi kuma ya ware wasu kudade masu kyau daga cikin personal kudinsa ya fara shirya musu tafiyar. Kafin wani lokaci komai ya kammala, suka shirya suka tafi and they spent the best days of their lives together. A lokacin ne ciwon Hussain yafi karfin drugs din da ya ke sha har Fatima ta fara fahimtar bashi da lafiya, amma sai ya gaya mata cewa ulcer ce take damunsa, ta nemi suje asibiti sai ya shiga drug store kawai ya siyi magani ba tare da ya bari an wani do ba shi sosai ba. A lokacin ne labarin haihuwar Ruqayyah ya same su, ta haifi danta namiji kuma kowa ya kira sai ya gaya musu irin tsananin kamar da yaron yake yi da Hussain. Kuma Hassan ya rada masa suna Hussain duk da cewa bashi da abokin tagwaitaka. Wannan yasa hankalinsu kuma yayo gida dan itama Fatima nata cikin ya kai wata bakwai kenan, tace "naga alama dai gidan nan sai maza ake ta haifa, ni kam nafi son mace dan ta zama kawata amma ko namijin nema ina sonsa shima". Hussain shima ba wai ya damu da lallai sai namiji ba, kawai dai yana ganin kamar namijin zai fi jan nasabarsa sosai akan mace, tunda ita mace in tayi aure ta haihu yayanta da gidan baban su zasu yi tutiya ba da shi ba, amma a yanzu yadda yake jin ya matsu yaga abinda zai haifa ko macen cema yana so sosai. Sai suka shirya dawowa Nigeria dan ayi sunan takwaran Hussain dasu, kafin su taho sai Hussain ya dauke ta zuwa asibiti inda ya nemi ayi musu 4d scan na babyn cikinta. Tayi ta mamakin dalilinsa nayin hakan bayan da yace ko gender baya son sani, ta tambayeshi dalili sai yace "I changed my mind, ina tsananin son ganin abinda yake cikin ki ko da a hoto ne" ita bata taba sanin cewa 4d pregnancy scan is possible ba sai yau, lallai technology babu abinda ya bari rai ne kawai Allah bai bawa turawa ikon hurawa jiki ba, babyn da yake kwance a cikinta sai gashi suna ganinsa clearly a jikin screen a kwance a cikin amniotic fluid yana ta tsotsar hannunsa, idanuwan sa tar a bude. Ba sai Doctor ya gaya musu ba su da kansu suka gani cewa namiji ne, ta juyo da sauri ta kalli Hussain sai taga hankalinsa yana kan screen din yana kallon babyn, and she saw a tear in his eyes but sai yayi sauri ya mayar da ita a hankali yace "bai yi miki kara ba, kamar mu daya" ta turo baki "ai dama hada baki kuke yi kullum in kana yi masa hira, a lokacin kukayi meeting kuka ware ni" ya danyi dariya, tace "amma ai kalar fata ta ce dashi, bai kai ka haske ba" yace "waya gaya miki? ai hoton black and white ne kuma yayi duhu ba zaki gane kalar fata ba". Sun jima suma kallon babyn su for 30 minutes wanda shine medically advisable sannan aka kashe, Hussain yaji kamar an kashe wani part na zuciyarsa ya daina amfani, sai dai kawai jin dadin sa shine an musu record na scan din a CD aka basu. At least ya samu abin gani kafin babyn yazo, that's in babyn zai zo ya tarar da shi. Kwana biyu bayan nan suka dauki hanyar Nigeria. Suna sauka suka je suka ga jaririn Ruqayyah, Fatima tana jin kamar ta sace shi saboda kamannin da taga yana yi da Hussain. Bayan an kammala suna ne Hussain ya koma Abuja gurin Doctor din da yake dubashi yayi requesting ya bashi wasu magungunan da suka fi wadancan karfi, amma sai Doctor din ya nuna masa cewa babu sama da wadannan, from kallon da Doctor din yake yi masa yasan cewa lokacin da ya rage masa bashi da yawa, amma sai yaji har cikin zuciyarsa baya jin tsoro kawai dai yana bakin cikin rabuwa da masoyansa ne. A ranar bayan ya koma gida ya dauko diary dinsa wanda har ya kusa cika shi da rubutu ya rubuta.. Dear baby Duk rubutun da zan yi maka daga yanzu zai iya zama abu na karshe da zan gaya maka. Rayuwa ta kadai ta isa nasiha a gare ka akan cewa babu wani abu da yake da tabbas, lokaci ne kawai yake da tabbas sai dai mu bamu da tabbas din kaiwa zuwa lokacin, an rigaan kayyade wa kowa iya kacin adadin seconds da zai yi a duniya kuma duk yawan kudin daka tara, duk kyawun fuskarka, duk yawan masoyanka da makiyanka, duk martabar ka, duk yawan ibadarka da rokon Allahn da zana yi akan ya kara maka kwanaki a duniya ba zaka wuce wadannan seconds din ba. Kowanne dan Adam yana tafiya ne akan nasa lokacin, dan wani yayi kudi da wuri ya sayi katon gida da manyan motoci ya auri kyakykyawar mace yar nasaba ba lallai ne shine successful man a duniya ba, maybe shi kwanaki kadan aka kayyade masa da kuma arziki da yawa, wannan shi yasa yayi arziki da wuri dan ya cinye arzikin sa kafin lokacin sa ya cika. Wani kuma sai yayi ta neman kudin da karfin sa da kwakwalwar sa amma sai ya dauki dogon lokaci bai samu ba kuma zata iya yiwuwa shi mai tsahon rai ne, dan haka yake cin arzikin sa kadan kadan. Wani kuma a wahala zai fara kuma a wahala zai kare saboda tasa kaddarar kenan. Babu wanda yake sauri babu kuma wanda yake lakaki, kowa yana tafiya ne akan lokacin sa. Shi arziki ba komai bane ba illa wata hanya da ubangiji yake jarabtar bayinsa, sai ya baka kudi yaga abinda zaka yi dashi ko kuma ya hana ka yaga abinda zaka yi. Ida har ka nemi kudi ka samu to Allah ne ya baka, idan kuma baka samu ba to shine ya hanaka. Idan ka samu dama ka nemi kudi ta hanyar halak, idan zaka kashe su ka kashe su ta halak. Idan kana dashi ka taimaka wa wanda bashi dashi, idan baka dashi ka nemi na kanka ta hanyar halak kar ka zama mai matacciyar zuciya ko mai roko a gurin mutane. A duk lokacin da dama ta same ka tayin wani abu to kayi shi a lokacin kar ka jira sai wani lokaci, dan ba kai kake da lokacin ba. Duk abinda kaji kana son yi to kayi abinka, as long as bai sabawa ubangijin ka ba kuma ba zai zamanto cutarwa ga wani abin halitta ba ba to kayi abinka kar ka damu da abinda mutane zasu ce dan su mutane ba'a taba iya musu, in kabi ta tasu ba zaka yi achieving komai ba. Ka zauna da clean heart, kar ka nufi kowa da sharri kar kuma ka rike kowa a ranka, always think positive dan shi negativity yana huda zuciya ne ya kuma hana ka ganin alkhairi ko da yana gabanka Bana tunanin halin da zan barka saboda nasan na barka da best mother in the world da kuma best father in the world. Na san ko ban bar maka ko kwandala ba Hassan zai iya yin dako ya ciyar da kai. Dan haka indai a kan wannan ne bani da damuwa" Shigowar Fatima tasa yayi saurin rufe wa, ta tsaya tana kallon sa "wannan diary, ina jin kwanan nan a karkashin pillown ka zaka ke sakawa saboda tsabar baka so a karanta" yace "kar ki damu, shi wanda nake rubutawa da kansa xai karanta miki wata rana. Have patience" ta zauna da kyar tana cewa "Allah y kaimu, a gabanka zai karanta min ai, sai inji in ka rubuta abinda ya shafe ni a ciki" ya taso yana rungume ta ta gefe yace "a duk page da akwai sunan ki Fatima. Idan babu ke babu ni Princess" ta shafa fuskarsa tana murmushi tace "kaima in babu kai babu Fatima " sai ya dora kansa a kafadar ta ya lumshe idonsa. Hajiya Ruqayyah an haihu, da namiji na uku kenan data haifawa Hassan kuma tana tutiya a ranta cewa ko a haka ta barshi ta riga ta zamar masa karfen kafa, ta zamar masa kadangaren bakin tulu duk kuwa da cewa a yanzu ta fara fitar da ranta daga dukiyar Hussain musamman bayan ganin tulelen cikin Fatima da tayi duk da bata san me nene a ciki ba amma tana ganin haihuwar Fatima zata kara nesanta ta da H and H. Duk da cewa Hassan yayi signing takardun da Hussain ya bashi amma bai gaya wa kowa ba hatta Aunty, and definitely not Ruqayyah dan yasan in ta sani to kuwa ba zata haihu a Nigeria ba cewa zata yi ya fita da ita waje ta haihu a can. Amma duk da haka sai data matsa masa ya bata uban kudi kawai tayi ta siyan kaya wai na fitar suna, kayan babu kuwa haka tayi su daki guda duk dacewa akwai kayan twins wadansu ko amfani dasu basu yi ba, wadansu kuma kudin data karba kawai a account ta zuba su ta ajiye. Sai dai duk wannan abin da take dasu bai saka saka farin ciki a zuciyarta ba, kullum ranta babu dadi zuciyarta bakikkirin musamman inta lissafa taga plans dinta duk babu su, Adam din ma da take ta kokarin ganin ta raba shi da yar uwarta har yanzu abin ya gagara sai kara samun karbuwa yake yi a gurin iyayensu da kuma a gurin Hussain, hatta Hassan din data juya wa ra'ayi akan Adam yanzu ya fara chanjawa dan kwana biyun nan har hira taga suna zama suyi su kuma yi dariya. Ta saka ta warware ta kuma saka wa ta kuma warwarewa amma har yanzu ta kasa samun mafita. Then one day, bayan Hussain din ta yayi wata daya a duniya sai taga Hassan yana aiyukan files din staff din da suke dasu a gidan, kowa da file dinsa tun daga kan masu gadi har zuwa masu ban ruwan fulawa. Ta zauna tana taya shi sorting, yana ware wasu wadanda yake so zai yiwa karin albashi a ciki har da Adam, ta miko masa file din ya bude yana going through, anan ne idonta ya sauka akan sunan Adam na gaskiya da kuma address din gidan iyayen sa mahaifa. Anan wani plan ya fara forming kansa a zuciyarta. Bata ce komai ba har suka gama aikin sannan ta tafi dakin ta. Ta kira Minal a waya "Minal ya kike ya nauyi? Dan Allah taimako nake so" Minal tace "taimako? Taimakon me?" Ruqayyah tace "ina neman wanda zan aika kano, a sirri, wanda zan aika din bana son ya san ni zan aike" Minal tayi dariyar "me kika kulla wa?" Ruqayyah tace "ke dai bari, ina ganin na samo hanyar da zan kori wannan yaron daga gidan nan, kuma in raba shi da Sumayya" Minal tace "wanne yaron fa?" Ruqayyah tace "Adam. So nake ki samu wani ki aika shi kano on my behalf, yaje unguwar badawa layout gida mai number 49 ya gaya wa masu gida cewa dansu da suke nema yana kaduna, ya basu address din gidan nan ya gaya musu cewa yana nan ynaa aikin driver". Minal tace "ke Ruqayyah! Ji nake kin ce min iyayensa christians ne. In kuma suka tafi dashi suka mayar dashi Christian fa?" Ruqayyah tace "in haka ta faru to na tabbatar dama musuluncin nasa bana gaskiya bane ba, ai in dai da gaske yake to ba zai koma ba. Ni dai ina son in daina ganinsa anan gidan ne kawai, yadda ya gudu daga can ya taho nan haka in suka zo nemansa nan ma zai gudu ya kara gaba" Minal tayi shiru tana tunani, Ruqayyah tace "ni in ba zaki yi min ba ki gaya min in samu wanda zai yi min" Minal tace "babu komai, akwai wani yaron Alhaji Kabiru da nake dan saka wa aiyuka, zan tura shi Kanon" Ruqayyah tayi murmushi "shi yasa nake son ki Aminiya" Minal tace "babu wani Aminiya, yaudhe rabon ki da gida na? Ni kuma kullum ina kan hanyar zuwa gidan ki. Ina son ma zanzo ki raka ni in karasa siyayyar haihuwar nan" daga nan suka cigaba da hirarrakin su. And so it happened.... Sanda cikin Fatima ya shiga watan haihuwa, a lokacin ne kuma sako ya samu Hussain na dawowar abokin sa Sadiq zuwa garin Abuja tare da balarabiyar matarsa da kuma dan su da suka haifa. Sai Hussain ya shirya da niyyar tafiya yaje ya gano abokinsa da kuma sabon family dinsa, sannan kuma yana son ya ga likitansa daga nan. Tunda yayi maganar tafiyar Fatima take kuka, ita bata so ya tafi, ita so take ta bishi amma kuma cikinta yayi nauyi sosai. "kiyi hakuri Fatima, Abuja ne fa ba wani guri ba, a yau zanje in dawo" amma ta tubure dole ya hakura da tafiyar sai gobe, goben ma ya kuma daga wa sai wata goben a haka har sati, dan haka ya yakice ya tafi da kyar ba wai dan ya damu da ganin abokinsa ba sai dai dan ya damu da zuwa gurin likita, ciwo ya dame shi sosai, ga kuma jini da yake fitarws sosai. Sau da takai shi har bakin mota yayi kissing dinta sannan ya sunkuya yayi kissing cikin sannan ya shiga mota shida Hassan Adam yana tukawa suka tafi. A hanya suka yi hira sosai da Hassan, hira mai dadi duk da cewa baya jin dadin jikinsa, Adam ma kuma suna sako shi a cikin hirar yana jin labaran irin yarintarsu da kuma abubuwan da suka faru lokacin tasowarsu. A haka har suka iso garin Abuja suka shiga har cikin palace, sai dai kuma fitowa daga mota ya gagari Hussain. Nan take hankalin Hassan ya tashi ainun ya kuma umarci Adam daya juya motar zuwa asibiti, kafin su karasa asibitin jikin Hussain ya rikice gabaki daya dan sai tura shi akayi zuwa dakin likita kuma take aka saka masa oxygen dan numfashin sa sama sama yake fita. In hankalin Hassan yayi dubu to ya tashi gaba ki daya, amma a dole aka cire hannunsa daga na Hussain aka shiga da Hussain ciki shi kuma aka barshi a waje yana jira. Bayan tsahon lokacin da Hassan ba zai iya tunawa ba sai doctors din suka fito sannan suka bashi damar ya shiga ciki gurin dan uwansa. Yana shiga Hussain ya dago hannunsa yana masa alamar yazo, ya tako a hankali ya zo ya jawo kujera ya zauna tare da kamo hannun Hussain ya rike a cikin nasa. Hassan yace "Hussain " Hussain yace "don't talk. Just hold me. Let me talk" Hassan yace "a'a kayi shiru ka rufe idonka ka huta kaji? Ka samu kayi bacci in ka tashi zaka ji ka warke" Hussain yayi murmushi, sai Hassan ya jinjina masa cewa duk da halin da yake ciki amma still yana iya yin murmushi. Ya bude baki a hankali yace "take care of our kids bro. All of them" Hassan ya maimaita "all of them" Hussain ya sake cewa "take care of everyone at home" sai kawai Hassan yaji yana so ya karanta masa kalmar shahada, sai ya karanta masa sau uku sannan ya maimaita sau daya. And then he is gone. A hankali Hassan yaji hannunsa yana zamewa daga cikin nasa, sai ya kara rike hannun hopping yaji ya rike amma bai rike ba sai kara saki da yayi, sai Hassan yaji tamkar wani bangare na ruhinsa ya fita ya barshi, tamkar ya zama rabi ne shi ba cikakken mutum ba. Tamkar ruhin Hussain ya fita ne tare da wani sashe na daga nasa ruhin. *********. ************. ********** Tunda su Hussain suka fita Fatima bata koma cikin gida ba, sai ma ta samu kujera ta kafa a bakin kofar ta zauna tana jiran dawowar sa, kowa ya yi mata magana amma taki shiga ciki, gani take yi bata da wani sauran abinyi a cikin gidan, gani take yi kamar rayuwar ta ta kare a cikin gidan. Bayan awa biyu da tafiyar su ta dauki wayarta ta kira Hussain, tana so taji ko sun sauka lafiya amma wayar shiru ba'a dauka ba, ta kuma kira still shiru, sai ta kira ta Hassan shima bai dauka ba. Ta mike tana dosar part din aunty, a lokacin ne Ruqayyah ta shigo a mita tare da Minal sun dawo daga soyayyar zasu dauki wasu kayan sannan ta kai Minal gida. Suka tsaya a gefen Fatima, Ruqayyah tace "Fatima ya dai nag kamar hankalin ki a tashe? Wani abu ya faru ne" Fatima tace "yauwa Ruqayyah ki gwada kira Hassan da Allah muji ko sun sauka lafiya" Ruqayyah tace "sun je wani guri ne? Ni tun safe bana gida" Fatima tace "sun tafi Abuja, shi da Hussain, na kira Hussain bai dauka ba, ina so ne kawai in san ko sun sauka lafiya. Ruqayyah da Minal suka kalli juna suna tabe baki. Sannan Ruqayyah ta dauko wayarta ta kira Hassan amma bai dauka ba tace "bai dauka ba" Fatima ta fra yarfe hannu, "na shiga uku, ni gaba na faduwa yake yi. Ji nake yi kamar babu lafiya, kamar wani abu ya sami mijina" Ruqayyah ta tabe baki tace "kin san dai halin su in suna tare, na tabbatar da cewa hira ce ta saka basu ga kiran ki ba" Fatima ta sake girgiza kanta, sannan ta hango wani driver lawan ta kira shi "lawan dan Allah dauko mota ka kaini Abuja yanzu" Ruqayyah ta saki baki "for real? Wai bin sa zakiyi dan bai dauki wayarki ba? Fatima tace "ba rashin daukan waya bane ba, it is something else" sai ta juya ta nufi inda lawan yake fito da motar. Minal ta kalli Ruqayyah tace "wai ke ma ba da mijin ki akayi tafiyar nan ba? Ke ba kya jin wani iri a jikin ki?" Ruqayyah ta tabe baki tace "ni lafiya nake jin jikina" Minal tace "dalla tashi ki bita, kema ki nuna kin damu da naki mijin" Ruqayyah tace "Abuja? Na bar fa dan jariri na tun safe a gurin Aunty" Minal tace "ba zai mutu ba ai, ki tashi ki bita ki ce kema naki jikin babu dadi mijinki kike so ki gani" Ruqayyah ta karasa packing sannan ta fito, Minal ma ta fito sai kuma lokaci daya tayi tunanin to in taje gida ma me zata yi? Ai gwara kawai ta bisu ta ga yadda dramar zata kare, sai kawai ta tafi itama ta bude gaban mota ta shiga ba tare da tayi tunanin bata tambayi mijinta ba ko kuma tunanin abinda zai je ya zo, Fatima kuma tare da Ruqayyah suka shiga baya sannan lawan driver ya ja suka dauki hanyar Abuja. Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani wajen na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020. *The Accident 2* Kafin mu dora. Sanda zamu fara banyi wa kowa alkawarin smiles and laughter a lokacin karatun tagwaye ba, besides, ni ban taba yin rubutu da niyyar in saka readers nishadi ba, a koda yaushe dalilin rubutu na shine dan in yi sharing abinda ni na fahimta akan bangarorin rayuwa tare da sauran mutane, fahimta ta ce, bance lallai ita ce dai dai ba, kawai dai ina fatan wani zai iya ya dauki wani abu da zai amfane shi a ciki. And yes, Duk wadda take son refund na kudinta tayi existing paid group sannan tayi min magana ta private. But the story will continue as it is.............. Hassan ya sake kamo hannun Hussain ya kankame a kirjinsa yana jin hucin da zuciyarsa take yi yana huda kirjinsa yana dukan hannayensu, kuka yake so yayi amma ya kasa, tabbas wani tashin hankalin yafi gaban kuka. Ya jawo hannun zuwa bakinsa yayi kissing, baya bukatar likitoci suzo suyi masa bayani ya riga ya sani cewa Hussain baya tare da shi ya tafi gurin mahaliccin mu baki daya, ya tafi inda Maman su ta tafi, babansu ma ya tafi, yanzu shima ya tafi, sai Hassan yaji a ransa bai san me yake zaune yake yi a duniyar ba, zai iya bayar da komai da yake dashi dan ya bi bayan dan uwansa. Ya kalli fuskarsa fes da ita kamar yana bacci, dai yaga yayi masa wani irin kyawun da bai taba ganin yayi irin sa ba. Fuskarsa da hancinsa sun kara yin tsaho tamkar ba nasa ba. Sai yaji a lokacin babu abinda yake so kamar shima ya zama tamkar Hussain, shima ya zama gawa ko ruhinsa zai tafi gurin mutane mafiya soyuwa a gurinsa. Yaji wani irin kadaici ya rufe shi tamkar shi kadai ne dan Adam din daya rage a duniya. Sai rufe idonsa ya kwantar da kansa a kirjin Hussain yana lura da yadda baya jin motsin bugun zuciya a kirjin. Ina ma dai shima tasa zata daina bugawar? Ina ma dai zata daina yi masa zafi da radadin da take yi masa yanzu. Sun jima a haka sannan yaji an bude kofar dakin an shigo, bai motsa ba dan baya son motsawar, so yake ya cigaba da kwanciya a haka har tasa zuciyar ta daina bugawa shima ya tafi inda Hussain ya tafi. Inda mahaifan su suka tafi. Hannu yaji an dora akan kafadar sa, ya dan bude ido kadan yana kallon likitan a cikin Scrubs dinsa, Doctor din yace "I am very sorry Hassan. Allah yayi wa Hussain cikawa. Allah yaji kansa da rahama" sai Hassan ya mayar da idonsa ya rufe, yana so yace Ameen amma bakinsa ya kasa motsawa, zuciyarsa ma ta kasa amsawa. He just can't accept cewa gaisuwar Hussain ake yi masa. Sai doctor din ya cire wa Hussain duk machines din da suka jojjona masa, ya kuma cire masa abin oxygen din da suka saka masa dan baya bukatar oxygen a yanzu, sannan sai ya jiya ya fita dan ya lura Hassan yana bukatar karin lokaci tare da Hussain. Bayan fitarsa ce wata nurse ta shigo ta dauki takardu ta fita, sannan wani ya shigo shima ya dauki wani abu da Hassan bai san menene ba, ya kuma rufe idonsa yaji shigowar wani, shi bai dauki komai ba ma ya fita. Sai Hassan ya fahimci wani abu, ya dago kansa yana kallon bakin kofa yana tunanin abinda ya faru a lokacin da akayi wa Hussain aiki a India ballantana yanzu da suke Nigeria, yadda Hussain yake public icon kowa zai so ace shi ya fara sanar da labarin mutuwarsa. Ya mike yaje ya rufe kofar dakin ya dawo ya ja abin rufa ya lullube Hussain har fuskarsa. Har yanzu kwakwalwar sa bata aiki sosai dan haka ya kasa tunanin mai zai yi. Ya jingina bayan sa da jikin kofar ya rufe idonsa yana sauraron bugun da zuciyarsa take yi, sai kuma yayi sauri ya bude idonsa ya fara laluben aljihunsa yana neman wayarsa, sai yaji bata jikinsa, ya barta a mota. Hankalin sa a tashe ya bude kofar ya fita tare da yin amfani da key din daya gani a jikin kofar ya rufe ta ta waje, babban abinda ba zai so ba shine yaga hotunan gawar Hussain tana yawo a social media. Yes, people are that cruel, wasu tamkar jira suke yi abu ya same ka su fara yadawa babu ruwansu d halin da kake ciki ko abinda yadawar tasu zai iya janyowa. Ya tabbatar da yawa daga staff din asibitin by now sun san cewa Hussain Aminu Abdullahi ya mutu a cikin asibitin su, wani ya gaya wa wani wanin shima ya gaya wa wani, ya tabbatar kafin nan kafin minti biyu wani zaiyi posting a social media sannan wasu suyi sharing suma kuma ayi sharing nasu post din. Yasan kannensa gabaki daya suna social media haka ma Fatima, tashin hankalin sa kadai shine Fatima taji wannan labarin a media kamar yadda taji na rashin lafiyar Hussain. Musamman duba da halin da take ciki. Shi kuma a yanzu ba ya jin akwai wani abu da yake so fiye da abinda yake cikin Fatima, hatta yayan da ya haifa a cikinsa kuwa. Adam yana ganin ya fito ya taso da sauri ya taho gurinsa, kallo daya zakayi masa kasan cewa hankalin sa a matukar tace yake dan yanzu a duniyar sa bayan Sumayya da iyayenta da suka karbe shi irin karbar da akeyi wa family member baya jin yana da kamar Hussain a duniya, shine gatan sa, shine tutiyarsa, a makaranta har kallon dan masu kudi ake yi masa saboda irin suturar da yake sakawa kuma duk na Hussain ne, babu wanda zai gansu tare yace drivern sa ne shi sai dai a dauka ko kaninsa ne. Yace "oga Hassan ya jikin oga Hussain? Sun hanani shiga ciki tun dazu" Hassan ya bude motar yana duba wayarsa a inda ya zauna bai ganta ba amma sai yaga ta Hussain. Ya dauka ya fito yana kallon Adam da fuskarsa take nuna cewa yana gab da fashewa da kuka, ya dafa kafadar sa yace masa "Adam, Allah ya karbi oga Hussain" sai Adam yaji kamar bai ji sosai ba, sai yaji kamar bai iya hausa ba kuma, yace "what? Ban gane ba oga Hassan" Hassan ya tsaya kawai yana kallon sa ya kasa furta kalmar mutuwa tare da sunan Hussain a tare. Sai daya hadiye wani abu sannan yace "Adam Hussain ya mutu, Hussain ya tafi ya barni" sai ya dora kansa a kafadar Adam ya fara wani irin kuka wanda babu maiji sai Adam din da yake yi a jikinsa. Adam ya sandare a tsaye, oga Hussain, oga Hussain din da suka taho yanzu tare suna hira suna dariya suna nishadi shine za'a ce ya mutu? Me ya same shi? Sai ya dora hannunsa a kafadar Hassan, yana jin yadda jikinsa yake motsawa da kukan sa, yanajin yadda hawayensa yake jika rigarsa da kuma yadda zafin jikinsa yake ratso har nasa jikin yace "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ka ringa maimaita innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allah zai saka maka nutsuwa kuma zaka ji sanyi a zuciyarka. Kayi kukan kuma yana da kyau ga lafiyar ka, amma kar kayi mai kara dan yana kara azaba ga mamaci" Hassan ya cikashi ya koma ya zauna a cikin motar kafafuwansa a waje. Ya jingina kansa da head rest yana sauraron rarraunar muryar Hassan yana maimaita masa fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Shima sai ya fara fada har ya samu nutsuwa sannan ya bude wayar Hussain da take hannunsa. Missed calls din fatima ya gani har 30+, gabansa ya fadi, kar dai har taji? Amma in taji baya jin zata samu karfin zuciyar kiran Hussain. Amma baya so ya kirata dan vai san me zai ce mata ba, sai dai bai san wanda zai fara kira ba, Aunty? Ko kuma wani a cikin yaran gidan maza? Ko Gombe zai kira? Amma kafin suzo Kaduna fa? A karshe ya yanke shawarar kiran Aunty yayi mata dabarar da zata kai Fatima part dinta sannan ta karbe wayarta. Sai dai bai san me zaice da auntyn ba. Amma kuma kafin ya kira sai ga kiran auntyn ya shigo wayar Hussain din. Ya runtse ido tare da gyaran murya ya dauka, kafin yayi magana ta fara magana ita "Hussain kuna ina? Kasan Fatima ta biyo ka Abuja kuwa? Yanxu na shiga gidan mai gadi yace min ai Lawan driver yace masa Fatima tace zai kawo ta Abuja. Me zata yi a nan din" Hassan ya rikice "Abuja? Fatiman?" Tace "Hassan? Ina Hussain din? Neme su a waya dan ance tare da Ruqayyah suka fito sun biyo bayan ku" Hassan yaji hankalin sa ya sake tashi, bai iya cewa da ita komai ba sai ya kashe wayar tare da dafe kansa yana digesting maganar, Fatima da Ruqayyah suna kan hanyar tahowa Abuja a mota saboda me? Kuma wai harda Ruqayyah, Ruqayyan da tun safe ta fita daga ce masa gata nan yanzu zata dawo amma har suka fito bata dawo ba kuma bata dauki duk kiran da yake mata da niyyar gaya mata zaiyi tafiyar ba. Yanzu kuma wai tabiyo Fatima sun taho Abuja. Shi bai ma san ta inda zai fara ba, da abinda yake ji a zuciyarsa zai fara ko kuma da gawar Hussain da take kwance a daki tana jiran a shiryata ga magrib tana dosowa ko kuma da tracing Fatima da Ruqayyah a garin Abuja, ko kuma da rarrashin sisters dinsu da yasan labarin mutuwar Hussain yana gab da zuwa gurin su. Ya sake daukan wayar ta nemo number din Ruqayyah ya kira. Bugu daya ta dauka tana cewa da Fatima "ga mijin naki nan yana kiran wayata" Fatima tayi zumbur ta mike daga kwanciyar da tayi bayan ta gaji da kiran number din Hussain. Ruqayyah ta ce "Hello, yallabai" sai taji muryar Hassan yace "Hassana kuna ina yanzu?" Ta dan kalli Fatima tana girgiza mata kai sai tace "yanzu muke shigowa garin Abuja ni da Fatima, muna ta missing dinku a gida shine muka biyo ku dan ba ..........." Yace "listen to me please. Ki gaya wa Lawan ki ce inji ni nace ya juya mota ku koma Kaduna yanzu, muma mun gama duk abinda muke yi yanzu muke shiga mota zamu taho" tace "to mu karaso mana sai mu dawo tare?" Yace "Ruqayyah, just do what I said please. Ina Fatima?" Ta kalli Fatima da take zaune a edge of her seat tace "gata nan muna tare" yace "ki kula da ita please Ruqayyah, kuna zuwa gida u tafi part din Aunty ku jira mu karaso please. Dan Allah Ruqayyah kiyi haka kinji?" Tace "me ya samu muryarka ne?" Yace "mura nake yi" ta dan tabe baki tana jin haushin yadda yake jaddada mata ta kula da Fatima kamar wata yar gold, tace "shikenan, za'a yi duk abinda kace" yace "good" ya katse wayar. A lokacin ne wani Doctor ya fito yana yi masa maganar yazo ya bude dakin da Hussain yake za'a yi preparing dinsa for release. Sai yaki basu key din instead sai ya mike da kansa ya tafi zai bude musu, dai dai nan yaji gabansa ya fadi, ya juyo da sauri yana kallon bakin gate yana jin zuciyarsa tana ingiza shi kamar ya fita da gudu ya tafi kaduna a kafa,ya juya kuma ya kalli cikin asibitin yana tuno gawar Hussain a daki. Sai ya dawo da baya ya samu Adam yace "Adam dan Allah tafi kabi su Fatima, in ka gansu a hanya ka kula dasu and make sure sunje gida lafiya, ni zan tsaya mu taho da Hussain a ambulance. Please. Adam ka kula da Fatima kaji?" Adam ya gyada kai yana ganin ba sai an roke shi ba, abinda Hussain yayi masa ya wuce haka a gurinsa dan haka zai iya ajiye rayuwarsa for Fatima. Ya shiga motar da suka zo da ita ya tayar ya bar compound din asibitin. A wata mota a gefen asibitin, wanda yake gaban stirring yace "oga, gashi nan ya fito, kuma kamar shi kadai ne a motar" wanda aka kira da oga yace "then what are you waiting for? Follow him. Maybe mu samu chance din kama shi shi kadai" **********. **********. *********** Fatima ta kalle ta "ba Hussain bane ba? Me yasa bai kira wayata ba bayan yaga ina ta kiran sa?" Ruqayyah tace "ba Hussain bane ba, Hassan ne yace mu juya mu koma gida suma gasu nan har sun gama zasu taho" Fatima ta fara girgiza kanta tana bubbuga hannunta a jikin kujera "ba dai Hussain ba, Hussain ba zai taba haduwa da Sadiq abokinsa bayan tsahon lokaci sannan su gaisa briefly ba, wani abun ne ya faru, wani abun ne ya faru da Hussain dina" Sai Ruqayyah taji jikinta yayi sanyi dan itama taji abin odd, mai yasa Hassan zai kira ta da wayar Hussain bayan kuma Hussain din ai biyo lodin kiran da Fatima take masa ba? Bayan kowa yasan irin tsananin son da yake yi mata. Amma sai bata ce komai ba ta gaya wa Lawan sakon Hassan. Bai musa ba ya rage gudun motar lokacin duna gab da shiga cikin gari sannan ya fara kokarin juya motar ya koma hannun dawowa. A lokacin ne sukaji Minal da tun dazu ta dukufa akan wayarta tana ta danne danne ta rafka salati, "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" Fatima ta yunkuro kamar zata mike tsaye, babyn cikin ta ya harba da karfi. Minal ta juyo tana kallonsu idonta kamar zai fado kasa tace "Ruqayyah? Hussain din ku ba shine Hussain Aminu Abdullahi ba" Fatima bata ce komai ba, saboda ba zata iya magana ba, Ruqayyah tace "shine? Me kika gani? Me ya faru?" Ta juyo musu da screen din wayar ta tace "Ya mutu? Gashi nan ana fada a twitter ya mutu a wani asibiti a Abuja" Idon Fatima ya juye ta zube akan kujerar ta, Ruqayyah ta dora hannu aka tare da rafka salati, and then, Lawan driver ya juyo yanason yaga sakon da Minal take nunawa, wannan abinda yayi hadi da karar kwana, ya saka ya saki stirring kuma maimakon ya taka burki sai ya taka accelerator. Motar tayi gaba kamar fitar kibiya, ta daki edge din titi sannan tayi adungure da sauri, kasanewar gurin slope ne mai tattare da duwatsu ya saka ta cigaba da gangarawa da sauri tana yin cikin daji. Babu mota a kusa dasu dan haka babu wanda yaga faruwar abin. Ruqayyah tana salati, tana jiyo salatin drivern tare da Minal banda Fatima da already ta riga ta suma tun kafin abin ya faru, a haka har kanta yayi buguwar da ta daina ganin komai ta kuma daina jin komai. Ta suma. Lokacin data farfaɗo jin kanta tayi yayi mata nauyi sosai. Ta saka hannu tana dafe kan tare da kokarin yin salati, amma sai taji ba wai kan bane kadai yayi nauyi gabaki daya jikin tane yayi nauyi, ta jima a kwance a inda take sannan ta fara samun karfin bude idonta, abinda ta fara lura dashi shine duhun da gari ya fara yi. Ta dafe kanta ta mike zaune tana numfashi da sauri da sauri har ta samu ta dawo hayyacin ta. Abu na farko da taji a jikinta shine azabar zafin da yake tahowa daga kafarta zuwa sauran sassan jikinta. Gabanta ya fadi tana kai duba izuwa kafafuwan ta. Wani karfe ta gani ya huda naman cinyarta ya wuce. Ta kama shi da hannu daya sannan ta dafe kafar da hannu daya ta zare shi daga jikin ta tana jin azaba tamkar ranta zai bar jikin ta. Sai ta samu kanta da godewa Allah da bata taho da Hussain karami ba. Ta yanki gefen dankwalin ta ta nannade ciwon tana tsayar da zubar jinin da yake yi. Sai a lokacin tasamu damar karewa gurin da take kallo, motarsu tana can gefe ta daki wata bishiya ta tsaya a kife, tayoyinta a sama, daga inda take tana iya jiyo kauri kamar wani abu yana konewa. Ta mike a hankali tana dai-dai ta tsayuwar ta sannan ta fara jan kafa zuwa inda motar take ta leka ciki, sai ta dawo baya da sauri tana rufe bakinta idanuwan ta kamar zasu fado kasa, kallo daya tayi wa drivern ta san ya mutu saboda yadda wuyansa ya karkace gefe, ta hadiye kukan daya taso mata tana zagayawa barin da Minal take. Idanuwan ta a bude suna kallon Ruqayyah amma ita bata kallon ta, jini yana fita ta kunnen ta da hancin ta. Ta girgiza ta. "Minal, Minal, Minal" amma ita kanta tasan babu Minal ta tafi inda ba'a dawowa. "Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun" ta fada tana kallon katon cikin Minal din wanda ake saka ran haihuwarsa ko yau ko gobe. Ta zame gefe daya ta zauna hannun ta akan ta tana rusa kukan rashin kawarta aminiyarta tare da abinda yake cikinta. Ta sake tashi tana leka bayan motar tana neman Fatima, babu ita babu alamun ta. "Fatimah! Fatimah" ta fara kwalla kiran Fatima da duk iyakacin karfinta amma shiru. A lokacin ne ta lura da abinda yake kauri, motar ce take kamawa da wuta daga kasa, nan take tsoro ya kama ta fara kokarin jawo gawar Minal daga gurin da take dunkule a tsakanin karafunan inji amma ta kasa, duk da ita ba likita bace ba daga yanayin kwanciyar Minal din ta tabbatar tayi rugu rugu. Ta zagaya side din driver tayi kokarin fito dashi shima amma injin motar da kuma kujerar sa sun matse shi a guri ɗaya. Ta ja baya tana mayar da numfashi tana kallon yadda wutar take kara ruruwa har ta fara cin seat din baya, hasken ta yana haska gurin, a lokacin ta lura da alamar sawun mutum ya bar gurin motar ya shiga cikin bishiyoyi. Fara bin sawun tana kiran sunan Fatima, tana dauke ganin ta daga wutar da take cin gawawwakin a cikin mota. A hanya taga wayar Fatima, ta dauka tana lura da cewa bata mutu ba duk da cewa screen din ya fashe amma tana ganin hoton Hussain a jikin screen din yanayi mata murmushi, ta tuna da labarin da Minal ta basu a mota wai Hussain ya mutu. Ta cigaba da kiran Fatima tana kara kutsa kai cikin bishiyoyi, suddenly ta ganta a gabanta kamar an jeho ta tana kallon ta da budaddun idanuwa tana cewa "help me please, ki taimaka mini dan Allah" gaban Ruqayyah ya fadi saboda fahimta da tayi cewa wadannan suna exact words din da Hassan ya gaya mata ranar da ta fara ganinsa a toilet din su, and it seemed like a long time ago amma shekaru biyu ne kawai. Ta rike ta "Fatima lafiya kike? Babu abinda ya same ki? Minal ta mutu ita da driver" Fatima tace "mafarki nake yi, ki tashe ni dan Allah. Mafarki nake yi wai Hussain ya mutu, wai munyi hatsari a hanyar Abuja, wai ina labor zan haihu a daji" sai a lokacin Ruqayyah ta lura da jinin da yake bin kafafuwan Fatima. "Innalillahi, na shiga uku, Fatima haihuwa zaki yi" Fatima tace "ki tashe ni daga bacci dan Allah, ki kira min Hussain dan Allah" surutai kawai take yi wanda Ruqayyah tabbatar ba a cikin hankalin ta take ba, ta jata gefe ta kwantar da ita, a haka ta haihu a hannun Ruqayyah, danta namiji katoto dashi lafiyayye. Ruqayyah ta daga dan bayan mabiya ta fito , ita bata san yadda zata yi ta yanke masa cibiya ba dan batada wani abun da zata iya yanke cibiya dashi. Ta daga shi tana nuna wa Fatima, "gashi kin haihu, kin samu da namiji" Fatima ta karbe shi ta rungume shi a kirjinta duk da ba'a hayyacin ta take ba amma taji matsananciyar soyayyar abinda ta haifa. Hawaye ya zubo mata, Sai kuma ta mikawa Ruqayyah tace "ki kaiwa Hussain shi shima ya ganshi, burinsa kenan yaga abinda zan haifa. Bana so in ganshi ni kadai ba tare da shi ba" Ruqayyah ta karba tana kallon babyn, kamar an tsaka kara shida Hassan, hakan yana nufin kamannin Hussain ne dashi kuma da fatar Hassan tunda yafi Fatima ma duhun fata. Ta mayar da dubanta ga Fatima sai ta ji ta shiru, ta girgiza ta da hannu daya "Fatima Fatima" amma shiru. Ta mike tsaye tana kallon Fatima sannan kuma ta kalli babyn da yake hannunta yana ta tsanyara kuka da dukkan karfin sa. Shikenan yanzu bashi da uba bashi da uwa kenan? Shikenan yanzu shine....... Sai kuma wani tunani ya fado mata. Yanzu wannan jaririn na hannunta shine sole heir na H and H and all its assets. Dogon gidan Hussain, tarin motocin sa, kamfanonin sa na shinkafa, fulawa, sukari, siminti duk yanzu na wannan yaron ne na hannun ta. Wannan yaron na hannunta shine kadai yanzu abinda yake tsakanin ta da H and H, tsakanin ta da zama matar CEO. Wannan yaron da bai fi ta taka shi ta wuce ba. Tayi saurin katse wannan tunanin daga ranta tana realizing cewa wannan moment din da take ciki, right here right now shine maganar da malamin duban nan yayi mata. A yanzu tana da options guda biyu, ko dai ta tafi da yaron nan gida ta kaishi gurin Hassan da dauran yan uwa su raine shi ya girma su cigaba da rayuwar su a karkashin sa, maybe ma in ya girma ya wulakanta su tunda basu duka haife shi ba ko kuma ta bayar dashi right here and right now and her husband will have majority share ta H and H. Already ta haifa masa maza guda uku, already gidan sa nata ne. Ta girgiza kanta da sauri, no no no, no matter how much take son dukiya, no matter how much take son ta zama mai kudi she can never kill for it, ko babba ba zata iya kashewa ba ballantana wannan dan jaririn. Ta tuna da maganar malamin "zabi ya rage naki" ta sake girgiza kai kamar yana kallonta, ta kalli Fatima, tana tunawa da Matsayin ta da martabar ta, sai ta tsallake ta ta wuce, ta fara tafiya a hankali har yanzu vata yanke shawarar abinda zata yi ba. Ta cire dankwalin kanta ta nannade jaririn tare da mahaifarsa a ciki sannan ta cigaba da tafiya, a haka ta fito bakin titi tana kallon motoci suna wucewa amma saboda bata yanke hukuncin abinda zata yi da jaririn hannunta ba sai ta kasa tsayar da mota ta nemi taimakon su, ta cigaba da tafiya a kafa ta cikin bishiyoyin bakin titi, tana cikin tafiyar ne taga wata mota kamar ta Hussain tazo wucewa, sai tayi sauri ta buya, jaririn hannunta ya fara kokarin kuka sai ta toshe masa baki, sai taga kamar motar tayi slowing down kamar zata tsaya sai ta kara shigewa cikin bishiyoyi da sauri. Kamar daga sama taga wani katon gini a gabanta, a jikin gate dinsa an rubuta baro baro "Nationa Orphanage of Nigeria" ta tsaya tana kallon rubutun sannan ta kalli yaron da yake hannunta "orphane" bashi da uba bashi da uwa dan haka orphane ne kuma babu inda ya dace dashi irin Orphanage. Ba tare da tunanin komai ba tabi inuwar jikin ginin zuwa bakin gate din sannan ta sunkuya ta ajiye shi tana kawar da ganinta daga kansa dan kada tausayin sa ya hana ta aikata abinda ta riga ta yanke shawara. Ta juya da sauri tana barin gurin, sai kuma ta tuna da dankalin ta da yake jikin yaron, evidence ne, za'a iya amfani dashi a binciko wadda ta ajiye shi dan haka ta koma da sauri ta zare dankwalin nata daga jikinsa ta koma cikin bishiyoyi da sauri, tana jin gurin gabaki daya yana amsa kuwwa da karar kukansa. Ta saka hannayenta ta toshe kunnuwan ta tana kara sauri, zuciyarta tana gaya mata yanzu za'a dauke shi dan ta tabbatar kukan ya shiga har cikin gidan. Sauri take yi sosai tana retracing steps dinta har ta dawo gurin accident din, wutar har tayi kasa sosai ta kusa karasa mutuwa, a gefe taga jakar Minal tare da karafunan motar da suka fita, ta dauka ta jefa ta cikin wutar tana kallon ta ta kama tana konewa, tana jin wani abu a zuciyarta wanda ta kasa fasaltawa. Babu wanda yasan sun taho da Minal, maybe mai gadi ya ganta shima kuma in ya fada zata iya cewa a hanya suka ajiyeta ta tafi gida, babu mai musa mata. In akazo gurin motar abinda za'a gani shine gawar driver da mace mai ciki a gaba, babu wanda zai ce ba Fatima bace ta mutu tare da abinda yake cikin ta. Problem solved. Ta juya tana kallon hanyar inda Fatima ta haihu, ta kunna fitilar wayar Fatima da take hannunta ta tafi gurin tana tunanin yadda zata yi ta kawar da gawar . Amma......... Babu gawar Fatima babu alamar ta....... Ta cigaba da haske haske a gurin amma babu ko trace na Fatima sai jini a inda akayi haihuwar. Hankalin Ruqayyah ya tashi. Taji kafarta da taji ciwo ta rike, ta kama ta amma sai taji ta sandare, sai ta fara janta tana barin gurin, tsoro kuma yana zuwa mata zuciyarta. Kamar daga sama taji wayar Fatima da take hannunta tayi kara, network ya dawo kuma, "Mi Amour" taga an rubuta, ta dauka da sauri "hello" taji muryar Hassan da alamar tashin hankali a tare dashi "Hassana ina kuke? ina Fatima? Ya akayi baku karasa gida ba har yanzu" a rikece ta amsa masa "Hassan mun shiga uku, kuzo ku taimaka min, accident muka yi, duk sun mutu, duk sun mutu Hassan na shiga uku" shiru taji a wayar, sai hayaniyar mutane a background amma babu muryar Hassan. **********. ************ ********* Adam yana ta kwarara gudu a hanya, hankalin sa a tashe, lokaci zuwa lokaci yana share kwallar idonsa da take kokarin kare masa ganin titin da yake gabansa, yana kuma dudduba motocin da yake wucewa ko zai ga motar da su Fatima suka taho da ita. Mutuwar Hussain ta daga masa hankali ba kadan ba, yaji duniya gabaki daya ta fita daga kansa yaji duk wasu birikan sa ashe duk shiririta ne. Duniya gabaki dayan ta zancen banza ne. Yana barin gari ne ya hango wata mata tana tafiya a gefen bishiyoyin bakin titi, hannunta kamar da jariri kanta babu dankalin, ta mirror ya ga kamar tayi masa kama da Ruqayyah. Sai ya dan daga motar yana so ya gani sosai amma sai ya neme ta ya rasa, ya girgiza kansa, maybe idonsa ne yake yi masa gizo. Yana yin gaba kadan kuma sai yaga wani abun daya daga masa hankali ya saka ya taka burki da sauri. Fatima, a tsaye a bakin titi, jikin ta futi futu kamar tayi wanka da kasa. Ya yi packing ya fito da sauri yana kallon ta dan ya tabbatar ita din ce, kallon sa kawai take yi kamar bata gane shi ba sai kuma ta miko masa hannu tace "help me" Ya lurada ciwo a kafadar ta yana jini, sannan ya lura da kasan rigar duk jini da kasa, sai kuma ya fahimci babu ciki a jikinta. "Madam? Me ya faru daku? Accident kuka yi, ina sauran suke" tace "Hussain. Ka kaini gun Hussain dan Allah" ya ji zuciyarsata karye, hankalin sa kuma ya tashi, daga gani a rude take bata san ma me take cewa ba, ya fara kalle kalle dan ya tabbatar a kusa da gurin ne suka yi accident din tunda ya ganta a gurin kuma a kafa. Ya kama ta ya zaunar da ita sannan ya dauko wayar sa ya fara neman number din Hassan amma bai san ma me zai ce masa ba, yana tsananin tausayawa halin da Hassan din yake ciki, ga mamakin sa sai yaji wayar tana kara a cikin mota, sai ya katse ya fara neman ta Hussain, sai dai kafin ta shiga yaji tsayawar mota a bayansu, ya juya da sauri, abinda ya gani shi ya saka shi sakin wayar ya juya kamar zai fita a guje sai kuma ya tuna da Fatima sai ya dawo ya tsaya a gabanta yana kare ta daga wandanda suke tahowa. Babansa ne mahaifi, tare da wasu maza karfafa su biyu. Ya dauke kansa yana kallon gefe a ransa yana tsananin mamakin yadda aka yi suka iya biyo shi har nan. Uban yace "Joseph? Wannan shine taryen da zaka yiwa babanka? Ka gama guje gujen?" Adam ya girgiza kansa yace "sunana ba Joseph ba, sunana Adam, Joseph din da kuka sani ba shine wannan ba" uban yace "say whatever you want to say, call your self whoever you want to call your self amma ni nasan you are my son, my responsibility, and I am taking you home" Adam ya girgiza kansa, "ni ba danka bane ba, kuka babu inda zanje" sai ya juya ya kalli wadanda ya taho dasu yace "ku dauko min shi" Adam ya sake yin kamar zai gudu amma kumaba zai iya barin Fatima ba wadda duk abinda suke yi take binsu da ido. Ya kalle ta sai ya daga hannunsa yace "zan bika, ka barni in taimaka mata please, in ka barni na taimake ta bazan kuma guduwa ba" mutumin ya kalli Fatima yace "wacece ita? Your girlfriend?" Adam ya gyada kansa yace "yes. She is injured, let me help her please" Uban yayi murmushi, a ransa yana ganin ya samu weakness din dan, ya dauki wayar adam da ta fadi a hannunsa ya yi jifa da ita cikin ciyayi sannan yace ya dauko Fatima ya shigo da ita cikin mota su tafi, sai da suka shiga motar sannan yace "say bye bye to the north. You are never coming back here". *This is the Intermission of the Story* Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020 *Broken* Tunda Hassan ya tura Adam yabi bayan su Fatima hankalin sa bai kwanta ba, magana likitan yake yi masa amma shi hankalin sa ya kan kofa, yana ta kallon hanya yana jin kamar ya bi bayan Adam din dan ya tabbatar ta samu su Fatima ya mayar da su gida lafiya lau. Amma kuma baya sin ya tafi ya bar gawar Hussain tare da mutanen da bai yarda dasu ba duk kuwa da cewa yanzu police sun zo asibitin kuma su zadu raka gawar Hussain har Kaduna. Sama sama yake jin abinda suke cewa, aka miko masa takarda yayi signing duk da bai san signing din me yayi ba but yasan ba zai wuce ta sallamar su ba. Sannan aka dora Hussain akan gado mai taya aka turo shi zuwa waje, inda by now mutane sun fara tsatstsayawa a waje suna kallo, wasu da wayoyi a hannunsu suna daukan hoto, Hassan ya kara tabbatar da cewa duk jikin Hussain a rufe yake babu abinda ake gani sannan ya sa aka kawo bakin ambulance din dai dai kofa yadda suna fitowa kawai shiga ciki sukayi shi da police guda biyu da kuma maaikacin lafiya guda daya, sannan aka rufe kofa. Daya police din kuma ya zauna a gaba tare da driver suka dauki hanyar kaduna. Hassan yana zaune kawai hannunsa daya a dafe da gawar Hussain ya zubawa farin matafin da aka rufe shi dashi ido amma ba zai ce ga abinda yake tunani ba, tabbas kukan da yayi dazu a jikin Adam yaji dadin yinsa dan yaji nauyin da yake ji a kirjinsa ya ragu sosai amma duk da haka tunanin sa bai dawo dai dai ba. Suna kokarin barin gari ne wayar Hussain da take hannunsa tayi kara, ya duba yaga sunan Adam. Gaban sa ya fadi sai ya dauka da sauri "Hello, hello" amma baya jin magana clearly sai dai yan maganganu a can nesa, a cikin maganganun akwai muryar adam din amma baya fahimtar me suke cewa amma kamar shi da wani namiji suke magana. Ya katse kiran sannan ya sake kira amma har ta gama ringing ba'a daga ba, ya sake kira shima shiru. Sai ya kuma jin hankalin sa ya kara tashi. Ya dan daga labulen da aka rufe tagar motar yana lekawa yana jin a ransa yana so yake kallon hanya. Amma kuma babu abinda yake gani din. Ya sake gwada number din Adam amma ba'a dauka ba still, ya kira wayar Ruqayyah bata shiga sai ya nemo number din Fatima ya kira itama not reachable, ya sake gwadawa sai taji ta shiga kuma lokaci daya aka daga "Hello" yaji muryar Ruqayyah, da alamar tashin hankali a tare da ita, yace "Hassana ina kuke ne ya akayi har yanzu baku je gida ba?" Cikin dimauta yaji tana magana da sauri "Hassan mun shiga uku, kuzo ku taimaka min, accident muka yi, duk sun mutu, duk sun mutu Hassan na shiga uku". Ya girgiza kansa da sauri sannan ya kalli wayar hannun sa yana so ya tabbatar daga ita ne maganar take fitowa, ganin seconds suna reading ya tabbatar masa da tabbas daga ciki ne kuma abinda ya ji gaskiya ne dan ta muryar Ruqayyah kadai yasan babu maganar masa a cikin bayanin ta. Sunyi accident, duk sun mutu saura ita kadai, su waye duk din? Fatimah? Abinda yake cikin Fatima? Dan Hussain? Is only link to Hussain? Ji yayi wayar ta zame daga hannunsa ta fadi a kasan motar. Kwakwalwar sa ta tsaya chak sannan kuma a hankali jikinsa ya zame daga kan kejerar ya fadi kasa. Mutanen cikin motar ne suka fara salati, ma'aikatan lafiyar yayi sauri ya kai hannun sa wuyan Hassan yana feeling heart beat dinsa kuma ya tabbatar da akwai sannan ya fara bashi taimakon gaggawa yayinda daya daga cikin police din ya dauki wayar wadda suka tabbatar ta cikin ta aka gaya masa abind ya sumar dashi ya kara a kunnensa "hello" Ruqayyah tace "hello waye? ina Hassan?" Yace "wacece? Hassan gashi muna tare dashi, wacece ke?" Duk da Ruqayyah taji wani iri kuma taji a jikinta wani abu ya faru da Hassan amma itama a yanzu taimakon take bukata ido rufe, tace "sunana Ruqayyah, ni ce matar Hassan Aminu Abdullahi. Ina cikin daji munyi accident tare da gimbiya Fatima matar Hussain Aminu Abdullahi da kuma drivern mu, motar mu ta kama da wuta, Allah yayi musu rasuwa, ni kadai na rage yanzu. Ina neman taimako dan bansan a inda nake ba" san sandan ya juya yana kallon yanuwan sa, sai kuma ya kalli gawar Hussain yana jinjina hikima ta ubangiji daya dauki ran mata da miji a lokaci daya ba tare d kowannen su yasan da mutuwar dan uwansa ba. Tabbas wannan labari ne da zai iya saka Hassan yayi abinda yafi suma ma ba suma ba, briefly ya fada wa sauran abinda matar tace, sai wani a cikin su ya karbi wayar yayi setting dinta ta yadda zasu ke tracking wayar hannun Ruqayyah suka ga inda take sannan suka sanar mata da cewa gasu nan zuwa, sai kuma suka yi waya station aka turo musu da wata motar suka hadu a hanya suka rabu biyu wadansu suka tafi gurin Ruqayyah wadansu kuma suka wuce da gawar Hussain da kuma unconscious Hassan. Ruqayyah kam tsoro take ji, ta bar gurin motar tayi hanyar da zata mayar da ita kan titi dan ji take kamar gawawwakin da suke cikin mota suna miko hannu zasu jata zuwa cikin sauran wutar da bata karasa mutuwa ba. Sannan kuma tana jin tamkar Fatima tana binta a baya, tamkar nemanta da tayi ra rasa ta zama fatalwa ne zata galaka ta saboda yar mata da yaron ta da tayi. A idonta take ganin kamar wulkawar Fatima ta gefenta, in kuma ta rufe idon ko da da niyyar kifta shi ne sai taga idanun Minal suna kallonta kamar yadda ta ganta a cikin mota a mace. Ga kafa ta rike, sam taki lankwasuwa sai janta takeyi ta sandare kamar wani ita ce. Duk kuma wannan da sauki akan abinda take ji a zuciyarta, wani irin feeling wanda ba zata iya misalta shi ba. Ta fara tuno masoyan ta, ƴaƴan ta guda uku, Sumayya, inna Ade da Baba, suleiman da Zunnur dan duk abinda take yi, duk wannan fadi tashin da take yi da wannan dakakkiyar zuciyar tata amma ita kanta ta san tana son su sosai sai dai kawai ita bata iya nuna soyayya ba, ga kuma Hassan , da kin ta da sonta he have come to be part of her, ba zata ce tana masa so na soyayya ba amma ta damu dashi. Ta runtse idonta tana matse hawayen daya taru a idonta yake disashe mata ganin ta amma kuma hoton fuskar Minal data gani shi ya saka ta yi saurin bude idon tana kokarin kara sauri ama kafa taki bada hadin kai. Gani take kamar gawawwakin ne suka rike mata kafar. A kunnuwan ta har ji taje yi kamar ana maganganu kasa kasa. Sai kuma taji kukan jaririn data ajiye yana amsa kuwwa a kunnuwan ta. Kuka take yi sosai, tana kokarin yin sauri iyakacin iyawarta amma in ta waiga sai taga babu inda taje, still bata wani yi nisa da motar ba. Sai data kwashe lokacin da a gurinta kamar ya kai tsahon shekara guda sannan taji gunjin mota tana shigowa gurin, sai kuma taji hayaniyar mutane sannan taga an haske ta da fitila. Hasken da ta ji shi har cikin zuciyarta, ta sauke ajjiyar zuciya tana tunanin karshen wahalar ta yazo. But that is just the beginning. Tana ji suka karaso inda take suka kamata suka sakata a motar da suka zo da ita sannan wasu suka tafi gurin accident din suna kokarin karasa kashe sauran wutar da take ci, tana jin su suna ta yawa suna fadar abinda ta gani, sun dan fara yi mata tambaya amma ganin yadda take a rikice yasa wani wanda take tunanin shine babban su yace su rabu da ita kawai, a lokacin wata motar ta karaso kamar ta fite service da kuma wata karamar mota again, taji suna ta maganar abin taji kuma sun ambaci mutuwar Hussain, sun kuma fahimci abinda take so su fahimta na cewa Fatima matar Hussain ce a cikin motar, sun kuma fahimci wacece Fatima dan take taji wani yana waya Kano cewa a sanar da gidan sarautar kano sunyi rashin yarsu, gimbiya Fatima. Ta lumshe idonta tana jingina da jikin kujerar motar, the dead is now complete, ta haka ta binne sirrinta babu gudu babu ja da baya, amma kuma ina Fatima take? In kuma bata mutu ba fa? In kuma tashi tayi ta tafi fa? In kuma yanzu already tana hanyar Kaduna kuma fa? In ta fada tace ta haihu ta bawa Ruqayyah dan ya zata yi kenan? Me zata ce? Ta girgiza kanta da sauri tana cewa "uhm uhm" a fili kamar wata zararriya. It is going to be her words against fatima's. Zata musa ne da duk iyakacin iyawarta tace ita bata karbi da ba, tace Fatima sharri take yi mata. To amma kuma in aka tambayeta game da gawar da take cikin mota wadda ta riga ta furta cewa ta Fatima ce fa? Me zata ce akan hakan? Tabbas bata haƙa ta binne sirrinta ba, tabbas yana nan a bude kuma yana tare da Fatima a duk inda take. But What if ta mutu da gaske wani ne ya dauke gawarta, ko matsafa, ko naman daji? There is still hope for her amma bata da tabbas, kuma tasan wannan rashin tabbas din tabbas zai ke hana ta bacci. A koda yaushe, Fatima zata iya bayyana kuma bayyanar ta yana nufin bankaduwar sirrinta. Wannan kuma yana nufin rasa komai nata......... Including iyayenta, dan tasan direct Baba zai tsine mata inna Ade kuma tace babu ita babu ita har abada But for now, shin gawar Minal tayi konewar da ba za'a Iya gane ta ba? Ta tambayi kanta tana lekawa ta taga, kamar amsar tanbayarta taji wani a gurin yana cewa. "Ayi wa yanuwansu waya, sai dai a binne su anan dan ba zasu dauku ba, sun zama gawayi" ta lumshe idonta da niyyar yin ajjiyar zuciya amma fuskar Minal data gani ya saka ta bude idon da sauri. Motar da take ciki aka bawa umarnin ta tafi, a kaita Kaduna gidan mijinta, wannan yasa taji hankalin ta ya kwanta, sai dai suna barin gurin ta juya tana kallon gurin. A nan ne rayuwarta ta kare, anan ne kuma rayuwarta ta fara. Su Kusan rai shida suka bar Kaduna a mota, amma a cikin su ita kadai zata koma garin Kaduna. ***************. **********. ********** Da taimakon maaikacin lafiyar da yake cikin ambulance din Hassan ya fara dawowa hayyacin sa, amma sai dai shi har cikin zuciyarsa bai so dawowar tasa ba, so yake ya tafi shima, so yake yabi Hussain, baya so ya cigaba da rayuwa. Wannan wacce irin jarabawa ce uban giji yake yi masa? Ya kamo hannun Hussain ya rike "Hussain! Ka tafi dani nima mana! Hussain Fatima ta bika ka roka min ubangiji nima ya dauke ni in biku! Hussain Fatima ta tafi , ta taho tare da abinda yake cikin ta. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" duk rarrashin duniya babu wanda ba'a yi masa ba amma ya kasa yin shiru. So yake wai maybe in ya ishe su da magana su gaya masa cewa ba gaskiya bane ba, su gaya masa Fatima da abinda yake cikinta suna raye, su gaya masa Ruqayyah ba gaskiya ta fada ba ko kuma anje an tarar basu mutu ba but instead of su ce haka sai yaji suna waya da yanuwansu na can akan a gaya masa gawar Fatima ba zata dauku ba sai dai a binne ta a can. Girgiza kansa kawai yake yi, so yake yayi kukan amma ya kasa sai magana kawai yake yi da gawar Hussain kamar wani tababbe. Tabbas mutuwar Hussain ta taba shi amma bata yi masa dukan da wannan ta Fatima tayi masa ba. Saboda dama yasan Hussain bashi da lafiya, kuma a hannun sa ya mutu. Amma Fatima fa? Hussain yana mutuwa ba abinda yake so sama da abinda yake cikin Fatima amma ashe ko ganin sa ba zai yi ba, ashe ko numfashi ba zai shaka ba. Wannan wacce irin jarabawa ce? Anya zai iya ci kuwa? Ace a rana daya babu Hussain babu family dinsa? Babu komai sai memory dinsa? Memory mai dadi....... Memory mai zafi....... Memory mai tsayawa a zuciya...... Yana jin wayar Hussain tanata ringing amma ya kasa kallon ta ma ballantana yayi tunanin dauka. Ba zai wuce mutanen gidan su ba, ba zai wuce aunty ko yan uwansu ba, sun kira shi suji da gaske ne? Da gaske Hussain dinsu ya tafi ya barsu? Da gaske Fatima tare da babyn su sun bi shi inda ba'a dawowa? Ba zai iya amsa musu ba..... Ba zai iya kallon wayar ba..... Ba zai iya kallon hoton Fatima hannayenta a dafe akan cikin ta tayi shape din heart da yatsunta a kan cikin ba, wanda shine hoton da yake kan wayar. Sai ya saka hannu ya kife wayar, baya jin zai iya magana da kowa. Ya tuno da nasihar da Adam yayi masa dazu "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya fara fada yana maimaita wa hannunsa biyu rike dana Hussain "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" sauran mutanen motar suka cigaba da taya shi har suka iso Kaduna suka je gida. ********. *********** ***** Tun tafiyar su Hussain Aunty take zarya a falo, in ta hau sama sai ta sauko sai ta kuma komawa sama ta kwanta sai ta tashi ta dawo kasa ta zauna. Ta rasa me yake yi mata dadi. Su Zulaihat suna kallo a palo ta kora su daki ta kashe kallon, ji tayi bata son karar tvn, bata son karar komai. Ta jima a nan sai kuma ta koma sama ta saka hijab dinta ta fita da niyyar shiga part din Hussain ta duba gimbiya Fatima, dama tunda cikinta ya girma kullum sai taje ta dubata. Sai dai a compound din gidan ta hadu da maigadi wanda yayi mata bayanin cewa ai Fatima bata nan yaji Lawan driver yace tace zai kaita Abuja "tare suka tafi da Aunty Ruqayyah" Wannan yasa a take ta dauko wayarta ta kira Hussain dan taji dalilin da zaisa ya bar Fatima ta bi bayansa da tsohon ciki. Sai dai Hussain din bai dauka ba sai Hassan, ta gaya masa abinda ake ciki sannan ta koma gida ta cigaba da zaman jiran dawowarsu. Har magrib tayi, sai ta kuma dauko waya ta kira Hassan amma bai dauka ba, ta kira Fatima not reachable Ruqayyah switched off. Ta kira Hussain shima ba'a dauka ba. Hankalin ta yayi dubu ya tashi, ta shiga dakin Khadijah ta tarar da ita a kwance wai zazzaɓi takeyi, ta dafa jikin ta taji zafi sosai, sai ta koma dakinta ta dauko mata magani ta taho da niyyar zata bata sai taga kira daga Bauchi. Babban yayan su Alhaji Lukman, tayi gyaran murya ta dauka tana gaishe shi, sai taji yayi shiru kafin ya amsa sannan yace mata "duk kuna gida tare da yara?" Tace "eh" tana mamakin tambayarsa, sai yace "shikenan ku zauna a gidan gamu nan tahowa komai dare insha Allah" sai ya kashe wayar ya barta da sakakken baki. Me zai zo yayi komai dare? Koma menene a barwa gobe mana? Ta samu gefen gado ta zauna kusa da kafafuwan Khadijah tana cigaba da kiran number din Hassan da Hussain amma duk babu wanda ya dauka. Ta gaji ta tashi ta daga window tana hangen titi ko zata hango tahowar su amma babu alamar su. A lokacin ne taji an rusa ihun kuka da muryar Nafisa, taji wani abu ya tsirga mata tun daga kanta har tafin kafarta. Taji wani irin daci a makwogwaron ta. Sai taji sautin kukan Nafisa yayi mata kama da sautin kukanta a lokacin mutuwar Alhaji Aminu uban ƴaƴan ta. Khadijah da take kwance ta mike da sauri ta tafi dakin Nafisa tana hardewa, a hanya suka hadu da Zulaihat itama tana dosar dakin Nafisa. A dai dai lokacin Aunty taga tsayawar ambulance a kofar gidan. Ta sandare a gurin tana kallo aka bude gate aka shigo da ambulance din sannan akayi packing aka bude baya, taga police sun fito, sannan taga Hassan ya fito amma bata ga Hussain ba sai taga an turo gado da wani abu da yayi kama da gawa akai. Ta saki labulen sannan a hankali ta zame ta zube a gaban tagar. Hassan yabi gawar Hussain da kallo ya tabbatar an shiga da ita ciki sannan ya juya gurin limamin unguwar su da ya biyo bayan motar rasu. Ashe har sun samu labari sun zauna jira. Hussain mutumin kirki. Liman yace "dare yayi yanzu, sai dai yayi kwanan keso sai da safe ayi masa sallah" Hassan ya gyada kai kawai. Liman din yace "da assuba zan tura aje makabarta a haka kabari, yanzu kuma zan sika a siyo likkafani, sai asa lokaci saboda yan uwanku su sami sallah" sai Hassan ya girgiza kansa yana kallon garden din gidan, inda tun suna raya suke yin shuke shuke shida Hussain har suyi rigima in wani ya tabata wani yace "anan za'a binne shi, a cikin garden din mu. Nayi masa alkawarin zanke zuwa kabarinsa kullum ina masa addu'a. Anan za'a binne shi a kusa dani" Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta WhatsApp through wannan number 08067081020 Sorry about the typos please Mai sharing littafi, bana ganin ki Amma *Allah* yana kallon ki kuma na barki da shi. *Hidden Strength* Sumayya yau bata tashi daga school ba sai da akayi kusa kiran sallar magrib. Ta gaji likis saboda yau sun safe suke lectures babu kakkautawa, dan yau sau daya taga Adam shima briefly yazo wai zasuyi sallama zai je Abuja tare da oga Hussain. Tana murmushi tave masa "kwana nawa zakuyi?" Yace "yau zamu dawo" tace "yau zaku dawo din shine harda sallama?" Ya langwabe kai "kika sani ko kawai so nake yi in ganki shine na fake da sallama" ta dan rufe fuska da mayafi, ya kama mayafin yana leka fuskar. Ta rufe idonta "ka bari fa" yace "ni ba zan bari ba, kallon fuskarki ma yanzu na fara" ta kwace mayafinta tana kara rufe fuskar dashi, yayi murmushi yace "kinsan wani abu?" Ta girgiza kai, yace "so nake in mun gama semester din nan inyi wa oga Hussain maganar mu, so nake a fara maganar auren mu tun yanzu ba wai sai mun gam school ba tunda kinga ai ina da aikina kuma ina samun kudi ba laifi, tunda na fara aikin kuma nake tarawa ba wani abin nke yi dashi ba. In nayi masa Magana nasan zai yi min jagora a maganar auren insha Allah" Sai taji ranta yayi mata dadi, zuciyarta tayi fari tas, yace "kin amince da hakan?" Ta gyada kai tana murmushi, still fuskarta a boye, ita da ace amimcewarta kadai ake bukata da zata iya auren Adam ko da bashi da wannan aikin, koda sadaki kadai zai bayar babu lefe babu komai, thats how much take son shi. Da zasu rabu ya jaddada mata "you know I love you right?" Ta danyi murmushi tana kallon cikin idonsa ta gyada kai, sannan kuma kamar ba zata yi magana ba sai tace "and I love you too". Har yanzu, har bayan ta wuni sir a makaranta ta dawo gida a gajiye da yunwa da ƙishirwa amma bata daina jin kaifin kallon da yayi mata a jikinta ba. Tana cin abinci tana zuba murmushi ita kadai, tayi sallah tayi wanka ta fito tama shiryawa Inna Ade ta shigo tana kallon ta. "Ke kuma fa kike ta farin ciki kamar anyi miki albishir da kujerar makka? Au ashe ba kinje, dan haka ba lallai ne ma kiyi farin cikin da kike yi yanzu ba" samayya tayi dariya, "haba Inna, farin ciki ma kuwa ai har marar misaltuwa zanyi in za'a mayar dani in sake ganin Ka'aba. Amma dai duk son da nake yiwa komawar in dai aka bani a yanzu sai dai in baki ko Baba tunda ni na sauke farali" Inna ta zauna a gefen gado tace "to gaya min abind yake saka ki wannan farin ciki haka"Sumayya ta zauna a kusa da inna tana kare mata kallo. Cikin yan shekarun nan da suka dawo gidan nan baba kuma ya samu aiki duk Inna ta chanja, jikinta ya murmure sosai babu wannan muguwar ramar fatarta tayi kyau tayi haske, kyawunta ya sake fitowa sosai. Sai Sumayya tace "kawai dai ina duba rayuwa shine naji raina yayi dadi sosai. Ina duba halin da mutanen da nake tsananin so suke ciki misali ku Iyaye na, Ruqayyah, kannena da sauran su duk kowa yana cikin rayuwa mai kyau sai naji zuciya ta tayi dadi sosai" Inna tace "banji kin lissafa da Adam ba" Sumayya ta sunkuyar da kai, Inna tace "ko shine da sauransu din?" Sai Sumayya ta rufe fuskarta, a dai dai lokacin wayarta tayi kara, ta bude idon ta tana kallon bakuwar number din da bata sani ba sannan ta dauka a hankali tare da sallama "Assalamu alaikum" daga daya barin taji muryar Ruqayyah "Sumayya nice, yar uwarki Ruqayyah ce. Accident muka yi ni da m.......... nida Fatima, Allah ya musu rasuwa ita da driver. An tafi dani asibiti ni kuma" Sumayya ta zaro ido cikin tashin hankali "accident? Mutuwa? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ya kike Ruqayyah me ya same ki ke? Wanne asibitin?" Ta jera mata tambayoyin cikin tashin hankali. Ruqayyah tace "da sauki. Asibitin da nake haihuwa. Ki gaya wa su Inna" sai ta kashe. Inna Ade da dama tun da taji Maganar accident ta mike tsaye tana kallon Sumayya tace "me ya samu Ruqayyah? Hatsari suka yi?" Sumayya ta gyada mata kai already hawaye yana zuba a idonta tace "hatsari sukayi wai Fatima ta mutu. Allah sarki Fatima. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ta fada tana neman hijab dinta. Sannan suka fito palo tare da Inna ita kuma tana nemna waya ta kira Baba ta gaya masa zasu tafi asibiti gurin Ruqayyah, a lokacin ne shi kuma baban suka shigo sun dawo daga masallaci tare da Suleiman. Sulaiman yana goge hawaye, Sumayya tace "kunji labarin kuma ko? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allah yaji kan Fatima" Baba yace "wacce Fatima ce kuma ta rasu? Mu yanzu ake gaya mana mutuwar yaron nan dan uwan Hassan. Hussain. Yanzu aka kawo gawarsa daga Abuja" Sumayya ta dora hannu aka Baba ya daga mata hannu, "kar kiyi, ba da haka zaki nuna wa Ubangiji godiyar ki daya baki rai shima ya bashi rai sannan ya ƙaddara saduwar ku a duniya ba" Sumayya ta sauke hannnun tana sheshshekar kuka, Inna Ade tana tayata. Sannan Inna ta gaya musu kiran da Ruqayyah tayi musu da sakon data sanar dasu. Nan take suka shirya gabaki dayan su suka hau Napep din Sulaiman suka tafi asibitin. Asibitin da aka kai Ruqayyah dana shine asibitin da suke zuwa, dan hka suna zuwa ba tare da wani matsala ba aka karbe ta aka bata taimakon gaggawa kafin karasowar likita. Kafin likitan yazo su Baba sunzo, sun kuma ji dadin yadda suka ganta complete ba tare da ta rasa wani abu na jikinta ba a hatsarin da ita kadai ta fita da rai. Wannan babban abin godiya ga Allah ne. Bayan likitan yazo yayi mata complete check up sai ya fahimci ko karaya bata dashi sai tarkade a hannun ta na hagu wanda ita Ruqayyan ma bata san dashi ba sai kuma ciwon da taji a cinyarta, wanda karfe ne ya soke ta a gurin. Amma problem din shine complain da take yi cewa kafar ta makale, ta kuma fadi cewa farkon data tashi tana iya motsa ta amma yanzu ta kasa. Sai doctor din ya rubuta mata hoto da za'a yi mata a kafar da safe yadda za'a fi ganin komai. Daga nan ya barta aga yanuwanta. A gurin su ne ta kuma tabbatar da labarin mutuwar Hussain. Ita kuma tana kuka tana basu labarin mutuwar Fatima "tunda na tashi dama na fahimci cewa ta mutu, nayi nayi kokarin in fito da gawarsu daga cikin motar ita da driver amma na kasa, ga wuta kuma ta kama" sai ta rufe fuskarta tana rusa kuka Sumayya tana taya ta. Tace "wuta ta kone su kurmus. Ance ma ba za'a iya dauko gawawwakin su ba sai dai a binne su a can" Sumayya ta share hawayen ta tana tuno kyakykyawar fuskar Fatima, sai kuma ta kara karfin kukanta data tuno da tsohon cikin da Fatima take dauke dashi. Dai kuma Hussain, ta tuno ganinta dashi na karshe sanda taje gidan ta hadu dashi. Cikin barkwanci irin nasa yace "Sumayya kin kuwa san gimbiya ta tsohon ciki ne da ita?" Tayi dariya Tace "na sani mana, na shiga ai mun gaisa" yace "to ki je gida ki fasa bankin ki ki tattara kudaden ki ki sayi lace dan yayi ki kai wa tailor yayi miki dinkin zamani dan suna ne za'a yi shi irin wanda ba'a taba yin irinsa a garin kaduna" sukayi dariya gaba daya. Yanzu gashi babu shi babu matar babu dan. Duniya labari, duniya zancen banza, duk wanda ya dauke ta gurin zama tabbas yana tare da babbar nadama. Baba ne yace da Inna Ade tazo su tafi gidan mutuwar, Sumayya kuma da Sulaiman su zauna a gurin yar uwarsu a asibiti gobe sa je suyi musu gaisuwa. A gidan mutuwar ne suka tarar da abin mamaki, layin gabadaya a cike yake da mutane maza da mata daga lunguna da sakuna na garin kaduna, wasu a zazzaune wasu a tsatstsaye kowa yana addu'ar samun rahama ga Hussain da iyalinsa saboda Hussain yana da wata al'ada ta kyautata wa duk wanda ya hadu dashi dan yana cewa "ita haduwa kaddara ce, rabuwa dole ce. Duk mutumin da ka hadu dashi a rayuwa to kayi amfani da wannan damar wajen kyautata masa dan babu tabbas din zaku kuma haduwa, ko baka bashi komai ba kayi masa magana mai dadi, ko baka yi masa magana mai dadi ba kayi masa murmushi dan shima sadaka ne" Cikin gidan kuwa da Inna ta shiga dakunan duk a bude suke kuma duk da mutane a ciki duk kuwa da cewa yan Gombe basu karaso ba, kowa kuka, musamman ma'aikatan gidan da suke ganin ba zasu kuma samun wani uban gidan kamar Hussain Aminu Abdullahi ba. Labarin Mutuwar Fatima ya dira tamkar kibiya a zuciyoyin iyayenta, yanuwanta da masoyansa ta. Nan take masarautar kano ta hargitse kowa kukan rashin Fatima musamman da suka ji irin mutiwar da ake tunanin tayi. Wai ko gawar ta ba zasu gani ba, wai ko sun gani din ma ba zasu gane taba saboda ta zama gawayi. Fatimah dai ta su, Fatima da suke ji da Ita tamkar kwai ita ce ta mutu kuma wuta ta kone ta. Wannan wanne irin tashin hankali ne? Mai martaba sarki duk da cewa ya dimauce ya gigice da alhinin mutuwar yar tasa amma duk da haka sai ya hada kan ya'yansa maza gabaki daya suka hau jirgi a daren suka tafi Abuja. Da assuba suka yiwa gawar da suke tunanin ta yar uwar su ce sutura tare da ta driver aka yi musu sallah sannan aka binne su a gurin da suka mutu. Daga nan kuma sai ya juyo ya koma kano dan fara karbar taaziyya daga mutanensa, yayan sa kuma ya tura su Kaduna dan su halarci jana'izar Hussain wadda aka daka karfe goma sha daya na safiyar asabar. Abinda yake bawa kowa mamaki a gidan gaisuwar shine Hassan. Da kansa yayi wa gawar Hussain wanka ya kuma suturta ta tare da taimakon limamin gidan tun cikin dare. Kallonsa kadai idan kayi ya isa abin tausayi amma zuciyarsa tana tsaye. Yana zaune a gaban gawar yana yi masa addu'a kamar yadda cikin gidan da wajen gidan yake cike da mutane da suke masa addu'a har gari ya waye. A lokacin yan Gombe suka karaso, dangin maman su da dangin babansu. Da gari ya waye ne Hassan ya kira Aunty, wadda duk ta gama fita daga hayyacinta, tare da dukkan yan uwansu mata su biyar yace su zo suyi sallama da Hussain. Kuka suke suna karawa, haka yahada su ya rungume duk a jikinsa in ya share hawayen wannan sai ya share na wannan yana cewa "ku daina masa kuka kuyi masa addu'a, ku ringa cewa innalillahi wa inna ilaihir rajiun zaku ji sanyi a zuciyoyin ku" sai daya kaisu sannan ya dawo ya kama Aunty da kyar ya daga ta ya tafi daita itama. Suka zagaye gawar Hussain suna ta karanta masa suratul ikhlas suna maimaita wa, yadda suke kallon Hussain a kwance a cikin likkafanin sa duk sai sukaji duniyar gaba ki daya ta fita a kansu, suna tuno da sutturu irin na Hussain wanda baya saka kaya idan ba na zamani ba, komai nasa latest ne, in kuwa akayi wani design din to ya daina saka wancan design din. Amma yanzu gashi da brand din kaya irin wanda ake sakawa tun dubunnan shekaru da suka wuce, babu safa ballantana takalmi, babu agogo da sauran kayan adon maza, sai dai in suka kalli fuskarsa sai suji dadi a ransu, yayi kyau irin wanda bai taba yi ba koda kuwa yayi ado da kwalliyar. A hankali suka daina kuka suka cigaba dayi masa addu'a tare da sallamar bankwana, ban kwana na har abada, ban kwana na sai a lahira kuma ba dai a duniya ba dan haduwarsu a duniya ta kare. Sai dai ko bayan sun daina kukan ma in suka tuna da Fatima sai su sake wani, a lokacin babu abinda ba zasu bayar babko da kuwa kawunan sune, babu abinda ba zasu iya yi ba idan za'a dawo musu da Fatima da abinda yake cikinta. Musamman Khadijah wadda tun zuwan Fatima gidan ita ce suka fi shakuwa akan duk sauran, kullum suna tare, tasan irin son da Fatima da Hussain suke yiwa cikin Fatima ta kuma san irin shirin da suke yi na taryar sa, ashe ba mai rayuwa bane ba, ashe ko numfashi bashi da rabon shaka a duniya. Auncle din su ma da aunties dinsu duk sun shigo sunyi sallama da Hussain, yaron da yayi achieving abinda mutum goma in aka hada ba zasu iya achieving ba. Shi mutum daya ne tamkar dubu. Mutum ne da su kansu sunsan za'a jima a dangi ba'a samu irinsa ba a arziki, alkhairi, kyautata wa da kuma yawan jama'a. Mutuwar Fatima itama ta daga musu hankali ba kadan ba, dan da tana nan da suna saka ran zata haifar musu abinda zasu ke gani suna tunawa da Hussain. Abokan Hussain, abokan business dinsa da sauran abokan muamalar sa duk sunzo jana'izar sa, a ciki har da Sadiq wanda mutuwa ta riski Hussain a hanyar sada zumunci tsakanin su. Ya koka sosai da mutuwar abokin nasa kuma ya jinjinawa karfin hali irin na Hassan. "Ban san bashi da lafiya ba, bai taba gayamin bashi da lafiya ba. And his family, ohhh dear God. Fatima and His baby! Kullum sai sai ya bani labarin Fatima ta kusa haihuwa. Wannan mutuwar mutuwa ce da ba zamu taba mantawa da ita ba". Karfe goma da rabi aka fito da gawar Hussain daga cikin gida, abinda ya saka yanuwansa suka kara rikicewa, Khadijah da Hassana suka zube a kasa. Sha daya dai dai aka yi masa sallah a cikin compound din gidan Aunty, amma mutane sun rufe gabaki daya titin unguwar har da bayan layin da cikin gidajen mutane, kowa yana so ya halarci zanazar Hussain saboda ya taba rayuwarsa in positive way. Dama shi alkhairi haka yake, in ka shuka shi to kuwa zai bika ne tun a duniya kafin ka je lahira, shima kuma sharri haka yake, babu yadda za'a yi ka shuka dawa ka kuma girbi shinkafa. Hassan da hannunsa tare da taimakon Jabir mijin Safiyya, Saeed mijin Hassana, uncle Mustapha kanin Alhaji Aminu da Baba Amadu yayan su aunty suka saka Hussain a cikin kabarinsa akan barin sa na dama sannan fuskarsa tana kallon gabas, sai kuma aka jejjera itatuwa a saman gawar tasa aka kuma bi da kwababbiyar kasa aka lullube itatuwan tare da like duk gurin da yake da kofa. Sannan aka mayar da kasar da aka fito da ita daga gurin sai kuma aka yayyafa ruwa a saman kasar. Sai aka durkusa kuma aka yi doguwar addu'a ga ruhin Hussain, masu kuka a hankali nayi nasu dauriyar zuciya nayi har aka shafa sai kowa ya fara kama gabansa. Hassan yana tsugune, tunda ya saka Hussain a cikin ramin ya koma gefe ya tsuguna yake kallonsa har aka rufe shi da itace ta daina ganin sa amma bai dauke idonsa daga inda yake ba, yana kallo aka gama komai aka kuma yi addu'a, ya daga hannunsa, duk da cewa kunnuwan sa basa fahimtar me ake cewa amma yasan addu'a ce akeyi ga Hussain. Yana kallo aka shafa shima ya shafa. Sai kuma yaga mutane sun fara tashi suna tafiya, na kusa dashi kowa in zai tafi sai yazo ya dan dafa shi alamar bada hakuri sannan ya wuce, a haka , a hankali a hankali har kowa ya watse, har aka barshi shi kadai tare da kabarin Hussain. A hankali yace "Hussain. Amanar da ka bar min ta danka ban sami damar rike ta ba saboda shima ya biyo ka, shi da Fatima, ina fatan zai zamo mai ceto a gare ku damu baki daya" sai ya mike tare da daga kansa ya kalli dogon gidan Hussain wanda tun daga nesa ake hango shi saboda girmansa da kuma kyawunsa, sannan ya sunkuyar da kansa ya kalli kabarin Hussain. Lallai wannan ma wani darasi ne da mutum mai hankali ne kadai zai iya ganewa. Yana komawa cikin gidan ya karbi gaisuwa daga mutanen da suka taru suna jiran sa, sama sama yake ganesu, sai ya sanar musu da cewa babu zaman makoki kowa ya tafi gida yayi wa Hussain addu'a daga can. Ranar sadakar uku sai azo ayi addu'a a kuma watsewa ranar bakwai ma haka dan baya so yadda mutane suke da yawadin nan a zauna ayi ta zaman hira zaman gulmar mutane, wasu ma har mamacin gulmarsa suke yi a gurin zaman makokin sa. Dan haka sai yaga zaman bashi da wata ma'ana tunda ubangiji yana ko'ina kuma yana amsa addu'a duk daga inda aka yi ta. A haka ya lallaba ya shiga cikin gida, inda ya tarar fa labarin wai an tafi da Aunty asibiti saboda jininta ya hau sosai. Shi bai san Aunty tana da hawan jini ba sai dai in yanzu ta samu. Ya tuna Ruqayyah, tun da akayi accident din ma bai ganta ba yaji dai ance tana asibiti amma ko waya bai samu yayi mata ba. Ba zai iya zama ba dan yana son ganin jikin Aunty dana Ruqayyah sai dai kuma mutane ta ko'ina tahowa ake yi zuwa yi musu gaisuwa musamman wadanda basu samu janaza ba, kuma kowa yazo shi yake nema tunda duk auncles din su da cousins dinsu ba'a san su ba sai few wadanda suke aiki a kamfanin su. Dan haka dole ya dan zauna sama sama yana amsa adduar mutane har lokacin sallar azahar yayi suka tashi sukayi jam'i aka sake doguwar addu'a ga Hussain da iyalinsa sannan aka gaya masa cewa an dawo da Aunty daga asibiti, sai yace a kaita part dinsa inda babu hayaniya dan ta samu ta huta sosai. Shima kuma ya samu ya zare jiki ya tafi, yana tafiya kamar iska zata kayar da shi. Yana shiga twins dinsa suka taho da gudu suka rungume shi. Ya durkusa a gabansu yana jawo su jikinsa tana jin wani iri a ransa, kamar yayi neglecting dinsu gashi uwarsu tana asibiti an barsu a gurin yan aiki. Shima kansa Hussain junior yana gurin mai reno tun jiya. Suna ta tsallen murnar ganinshi, sai kuma suka fara leka bayansa suna "ancol, ancol" ya runtse idonsa dan ya gane auncle din su suke nema. Sai ya rungume su yana maimaita "auncle is no longer with us, he is gone and he is never coming back" yayi ta fada yana maimaita wa a hankali duk da yasan ba fahimtar sa suke yi ba amma kamar kansa yake tunawa, kansa yake consoling. A lokacin Sumayya ta shigo, ta taho daga asibiti zata daukar wa Ruqayyah abubuwan bukata. Ta tsaya tana kallon su tana jin abinda yake cewa, sai taji matuƙar tausayin Hassan ya kama shi, Allah ne kadai yasan abinda yake ji a zuciyarsa a yanzu, kuma ta jinjinawa jarimtarsa sosai da sosai dan duk da bata san me yake ji ba bata tunanin zata iya surviving irin situation dinsa, ita tana da uwa tana da uba tana da twin sister dinta, tasan kuma duk yadda take ji dasu a zuciyarta so she can't imagine ace duk bata dasu, her life will have no meaning. But menene meaning din rayuwar ma? Dama ai Allah ya halicce mune with the sole purpose of worshipping Him dan haka duk wani abu da muke yi secondary purpose ne, worshipping din shine primary purpose din mu amma munyi neglecting munfi mayar da hankali akan abinda ba zai amfane mu ba. Ta karasa shiga ta zauna akan kujera tana kallonsa, idonsa yana rufe, hawaye yana bin kumatunsa, bakinsa yana motsi a hankali yana ta maimaita maganganu daya. Ta hadiye abinda yake tsaye a makogwaronta, itama jiya yadda taga rana haka taga dare saboda abubuwa da yawa, na farko alhinin abubuwan da suka faru, na biyu irin yadda Ruqayyah ta ringa zabura tana sambatu, tunda take da Ruqayyah bata taba ganin tsoro a fuskarta ba sai jiya, kuma bata yi mamaki ba dan tabbas wanda yaga irin abinda Ruqayyah ta gani zai iya zaucewa ma ba sambatu ba, har sai da aka yi mata allurar bacci sannan ta samu ta rintsa, shima kuma tana yi tana firgita dan haka ita Sumayya ta zauna tayi da yi mata adduoi tana tofa mata. Abu na biyu kuma shine Adam, tunda labarin mutuwar Hussain da Fatima ta same ta take kiran number dinsa wai dan ta samu tayi consoling dinsa dan tasan matsayin Hussain a gurinsa amma ta kasa samun sa, farko wayar tana ta ringing ba'a dauka daga baya ma kuma bama ta shiga, sai ta dauka rudewa ce ta saka yayi misplacing wayar tasa. Amma har gari ya waye shiru, har akayi janaza shiru, ba su Baba suka je asibitin ma sai data cire kunyar idonta ta tambayesu ko sunga Adam amma suka ce basu ganshi ba, sai dai babu wanda ya dauki abin da wani abu saboda irin yadda mutane suka cika a gurin dan baka ga wani ba ba zaka ce baya gurin ba. Yanzu ma da tazo gidan baza ido tayi tayi tana son ganinsa amma babu ko takalmin sa. Mai gadin gidan su Ruqayyah ta tambaya amma sai ya amsa mata da cewa "anya kuwa Adam ya kwana a gidan nan? Tun jira da suka fita tare da marigayi ban kuma ganinsa ba, motar daya tafi da ita ma bata dawo gidan nan ba" ya fada yana kara duba inda tarin motocin Hussain suke. Wannan ya kara daga hankalin ta, me ya faru da Adam? Yana ina? Lafiya kalau yake? Tana shigowa cikin gidan kuma sai ta tarar da wannan tashin hankalin. Dan halin da taga Hassan a ciki ya taba zuciyarta sosai. A hankali ta kira sunan sa "Yaya Hassan" ya dago kansa yana kallon ta da jajayen idanuwan sa. Tace "Allah yana nan. Yana kallon halin da kake ciki kuma yasan zaka iya daukan wannan kaddarar shi yasa ya dora maka ita. Allah baya taba dora wa bawansa abinda ba zai iya ba. Nasan kayi babban rashi wanda ni ba ma zan iya kwatanta yadda kake ji a zuciyarka ba. Amma ina so in tuna maka wani abu, kalli nan..." Ta fada tana numa masa yaran da suke gabansa. Ya kalle su sannan ya kuma kallonta, tayi masa murmushi tace "su wadannan yaran misali ne na irin Blessings din ubangiji gare ka. A duk lokacin da ka rasa wani abu da kake so kar ka kalli irin girman rashin da kayi but ka kalli irin abubuwan da kake dasu. Always count your blessings not your losses, a lokacin zaka san how blessed you are. You have a hidden Strength wanda kai kanka baka san kana dashi ba sai yanzu da wannan abin ya same mu sannan zakayi finding dinsa, kai kanka sai kayi mamakin what you can do alone in kayi concentrating on your blessings. Ka kuma godewa Allah da niimar sa. A lokacin shi kuma zai cigaba da tallafa maka". Ya dauke kansa daga kanta ya kuma kallon yaran da suke ta jan rigarsa suna masa gwaranci sai ya samu kansa da yin murmushi, yana goge hawayen idonsa yace "Nagode Sumayya, nagode da kulawarki gare ne. Nagode da kika bude min idona naga haske" sai ya mike yana daukan yaransa ya tafi dakin da ya ke tunanin an kai Aunty can. Ya samu tana bacci sai Khadijah a tare da ita tana karatun Alkur'ani. Ya karbi bayanin da likita ya rubuta ya karanta sannan ya kuma daukan yaran ya fita dasu kar su dame ta. Yana fitowa Sumayya tana saukowa daga sama da karamar jaka a hannun ta, ta karbi Yusuf tace "kawo su in tafi dasu can, sai Inna ta tai dasu gida su zauna acan. Dama dazu na aiko Zunnur ya karbi Hussain ya tafi dashi dan tun jiya bai sha nono ba" ya dafe kansa yana tunanin kamar ya gaza, tunda har ya manta cewa Hussain yana bukatar uwarsa. Sai yace mata ta jira shi ya dauko key din mota su tafi tare ya gano Ruqayyan. Ta jira shi ya hau sama ya sauko sannan suka fita tare, ita da Yusuf a hannunta shi kuma da Aminu suka je gurin mota suka saka yaran a baya sannan suka shiga gaba suka fita. Sai da suka dauki hanya sannan yace mata "ya jikin nata? Akwai wani major ciwo ne?" Ta girgiza kanta tace "Babu. Kafa ce kawai ta rike ta kasa motsa ta har yanzu, anyi hoto ance jijiya ce ta tabu, in an jima zasu sake wani hoton dan suga exactly inda ta tabun" tayi shiru tana kallon gabanta sannan tace "sai kuma tsorata" ya gyada kansa cikin fahimta, a ransa yana jin dadin yadda bata samu babbar matsala ba, yace "dole akwai tsorata dama, dan ma dai Ruqayyah ce" ta gyada kanta itama tace "dan ma itace. Da ni ce da sai na samu mental problem or worst" ya kalleta yace "yanzu kike min magana akan inner strength, da ke ce you will find out that you are stronger than you think". Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani gurin na sata ne, idan kina son ki karanta halaliyar ki ki yi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020 *A Lost Soul* A zaune suka tarar da Ruqayyah akan gado tana shan tea, Inna Ade tana zaune akan kujerar gaban gadon da Hussain a hannunta tana fada "in baki samu kin sha tea din ba yaron nan ba zai samu abincin sa ba fa shima. Ki daure ko rabi ne ki sha, ai yayi kokari ma" sallamar su ta saka Inna dago kai tana kallon su, Ruqayyah ma haka. Kallo daya ta yiwa Hassan ta sunkuyar da kanta kasa, ji tayi ta kasa hada ido da shi, wani irin nauyi take ji a zuciyarta in ta kalle shi. Musamman da taga irin yadda ya koma a cikin kwana daya. Shima a nasa bangaren kallon baki da ramar da tayi a cikin kwana daya yake yi, tayi zuru zuru idanunta duk firfito waje. Ya dan durkusa yana gaishe da Inna ta amsa masa cikin muryar tausayi tana kara yi masa gaisuwa "ya karin hakuri? Ohh Allah. Insha Allah Hussain da Fatima suna aljanna, kowa yana yi musu kyakykyawan zato kaji? Allah kai kuma ya kara maka hakuri tare damu baki ɗaya dan rashin na kowa da kowa ne" kansa a kasa yace "ameen Inna. Nagode." Yana jin wave din zafin mutuwar Hussain tana kara dukansa, haka yake ji duk sanda wani yayi masa gaisuwa, kuma yasan haka zai cigaba da ji har ranar da shima zai daina numfashi. Ta mike ta fita daga dakin, Sumayya ma ta ajiye kayan hannunta ta kuma ajiye yan biyun da suke ta zillo sunga uwarsu. Sannan ta fita itama. Ya jawo kujerar da Inna ta tashi daga kai ya zaune yana kallon yadda kirjin Ruqayyah yake hawa da sauka kamar wadda tayi gudu ko kuma take cikin jin tsoro. Sai ya kamo hannunta guda daya a cikin nasa biyu ya rike yana cewa "it is okay Hassana. You are safe kinji? Kina tare da mu yanzu, babu abinda zai same ki kuma. It is over" ta gyada kai hawaye yana zuba daga idon ta, sai ya hau kan gadon sosai ya jawo ta jikinsa ya rungume ta yana dan jijjiga ta kadan. Ta zagaye shi da hannayenta tana cigaba da kukan ta. "sun mutu Hassan sun mutu, gaba dayan su sun mutu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya kara rungume ta a jikinsa yana jin tsananin tausayin ta, what she went through, what she witnessed, yana jin rayuwarta ba zata taba komawa dai dai ba kamar yadda yasan ta sa rayuwar ba zata koma dai dai ba. Ta dago kai tana kallon sa, "na dauka mutuwa zanyi mijina, na dauka ba zan kara ganin ka ba mijina" ya saka hannu yana goge mata hawayenta "am here, ina nan tare da ke babu abinda zai same ki insha Allah" sai ta juya tana kallon kafar tace "kafata ce take ciwo mijina, na kasa motsa ta, tsoro nake ji kar in zama gurguwa" ya girgiza kansa "uhm uhm ki daina fada, babu abinda zai samu kafar ki kinji? Me Doctor din yace?" Ta nuna masa takardar da likitan ya kawo ta hoton da yayi wa kafar dazu da safe tace "yayi hoto, yayi bayani no ban gane me yace ba. Ni tsoro nake ji kar in rasa kafata. Bana so in zama gurguwa Hassan" ya dauki takardar yana dubawa sannan yace "yace zasu yi wani hoton ai ko? Ki daina kuka please mu bari su sake yin wani hoton mu gani kinji? Sun san abinda suke yi duk abinda ya kamata suyi akan kafar zasuyi" ta rike hannunsa tana girgiza kai "ni dai kawai ka fitar dani waje, ai kuna da doctors masu kyau a waje wadanda zasu kyara min kafata a lokaci daya. Ka fitar dani kawai waje tun kafin lokaci ya kure suce an makara" yayi ajjiyar zuciya yana jin kansa yana fara ciwo, ya kamo fuskarta a cikin hannunsa yace "Hassana. Hussain ne ya mutu, shi da Fatima da babyn su gaba ki daya. Jiya suka mutu, yau aka binne su. Hassana ba zan iya daukan ki mu fita kasar waje yanzu yanzu ba, gidan ma yanzu dan ina son in ganki ne kawai yasa na yi karfin zuciya na fito na taho nan, amma ba zan iya barin garin nan ba ballantana kasar nan. Kiyi hakuri. Wannan likitan is the best a garin nan, in mun fita wajen ma irin sa zamu gani ko kuma ma wanda bai kai shi kwarewa ba, matsalar kayan aiki ne, idan yaga cewa kina bukatar kayan aikin da basu dashi a nan shi da kansa zai fada kuma yayi referring dinki zuwa kasa da kuma asibitin da yasan suna da kayan aikin da kike bukata" a karasa yana jin babu dadi dan ba zai iya yi mata abinda take so ba, amma wani barin na zuciyarsa yana ganin bai dace ba tambayar tasa ma da tayi bayan tasan halin da yake ciki, amma considering halin da ita din take ciki sai ayi sauri ya kawar da batun daga zuriyar sa. Yayi ta rarrashin ta har ta daina kukan sannan yayi kokarin kara mata kwarin guiwa, ya kuma yi mata bayanin abinda yasa ba zai zauna tare da ita a asibiti ba tunda ya bar mutane masu zuwa gaisuwaa waje. Da kyar ta cika shi, ita tana ganin bai kyauta mata ba da ba zai fita da ita waje ya nema mata magani ba ko kuma ya zauna yayi jinyarta ba, bayan kuma a ganinta a yanzu babu wanda ya kaita muhimmanci a gurinsa tunda dai Hussain din da yake ta ambato to yanzu babu shi. Ta kara jin dadin hukuncin da ta yanke akan dan Hussain dan tasan da yana nan da bata jin ko kallo ita da ƴaƴan ta zasu ke samu daga gurin Hassan da yanzu yana can yaa rainon sa. Dan haka sanda zai tafi ma fushi ta nuna tana yi, wannan ya kara masa rashin jin dadi a zuciyarsa amma kuma a hakan dole yayi mata sallama ya kuma yi sallama da ya'yan sa ya fito. Sumayya ta biyo shi a baya, taa ta so ta tambayeshi Adam amma kuma tana ganin kamar hakan ba dai dai bane ba considering halin da yake ciki. Har sai da yaje bakin mota zai tayar sannan ta daure tace "Adam acan Abuja kuka bar shi ne?" Sai da yayi blinking idonsa sannan ya juyo yana kallon ta, tabbas bai ga Adam ba, tunda ya dawo bai ga Adam ba kuma bai tuna da neme shi ba. Ya dafe kansa da hannu daya yace "noo, ba acan muka baro shi ba. In fact, ya riga ni tahowa ma, shi yayo gaba neman motar su Ruqayyah ni kuma na tsaya na taho da Hussain. Kin neme shi a waya?" Idonta ya kawo kwalla, tace "nayi ta kiransa tun jiya wayar tana shiga baya dauka, daga baya kuma bata shiga sam, yanzu ma kafin ka fito sai dana kira amma switch off" yace "kar ki damu, am sure mutane ne da kuma alhinin wannan abin ya hana shi dauka. Amma in naje gida I will get him to call you" ta goge hawayen ta tace "baya gidan, bai koma gida ba, bai dawo daga Abuja ba" yayi shiru yana kallonta bai ce komai ba, tace "dazu da naje gidan na tambaya duk babu wanda ya ganshi. Mai gadi ma yace bai shigo gidan ba, yace motar da kuka fita da ita ma bata dawo gidan ba". Sai Hassan ya rasa me zaice mata, yaji hankalin sa yana tashi amma sai yayi karfin hali yace mata "am sure yana wani gurin ne, ko school ya tafi ya kwana acan kinsan tunda gidan da mutane ba zai ji dadin zama ba" ta girgiza kanta again tace "na kira abokin sa na makaranta baya can, sunce suma nemansa suke yi they were supposed to meet yau da safe suyi karatu" yanzu hankalin sa ya kuma tashi, but baya so ya nuna mata yace "still, think positive Sumayya, yana da abokai a cikin gari wata kila yana tare dasu ne. Shima nasan wannan mutuwar ta taba shi, maybe he just needed space ne ya danyi cooling down" ta gyada kai da sauri trying to believe him, hoping abinda ya fada shine abinda ya faru din. Sannan taja baya shi kuma ya tayarda motar ya tafi. Amma shi zuciyarsa duk ta tsinke, me ya faru da Adam? Babu wanda ya ganshi, shi kuma yasan babu yadda za'a yi Adam yayi missing jana'izar Hussain in dai har yana da rai yana kuma da lafiya, sannan kuma zai kira Sumayya yagaya mata lafiya kalau yake, dan haka shi kansa bai yadda da abinda ya gaya wa Sumayya na cewa yana wani guri ba. Yana zuwa gida mai gadi ya sake tambaya, ya kuma maimaita masa abinda ya gaya wa Sumayya, sai ya duba gurin motoci da kansa ya tabbatar babu motar da suka tafi da ita Abuja, daga nan ya tafi part din da Adam yake kwana tare da sauran yaran gidan ya tambaye su duk duka ce basu ganshi ba. "Kuma wayarsa bata shiga" wani daga cikin su ya kara jaddada masa. Sanda ya bar part din kansa har juyawa yake yi yana jin jiri, abubuwa sunyi masa yawa, ga mutane duk inda yayi kowa yanaso yayi masa gaisuwa kowa yana so yayi masa magana. Haka ya samu ya dan zauna kadan a cikin mutanen da suke jiransa sannan ya tashi ya shiga gidan sa yana jin kansa yana tsananin sarawa. Menene yake faruwa a rayuwarsa? Hussain, Fatima and now Adam? Me ya samu Adam? Ko shima yayi accident ne a mota kuma babu wanda ya ganshi? Dan suma su Ruqayyah dan ita ta rayu ne ta nemi taimako ba dan haka ba da zasu iya kwana daya ko biyu ma ba tare da an san inda gawawwakin su suke ba. Ya dauko wayar Hussain wadda da ita yake amfani yanzu ya kira number din Jabir. "Please ka sa a binciko motar da muka tafi da ita Abuja jiya, I will send you the plate number din yanzu" Jabir yace "lafiya? Ta bata ne?" Hassan yace "ba ta motar nake ba, ta yaron da yake cikin motar nake". Har dare babu labari, har gari ya waye babu labarin Adam. A lokacin hankalin Sumayya ya kai makura gurin tashi, ta gaya wa inna halin da ake ciki ita kuma ta gayawa Baba wadanda a take suka fara addu'ar Allah ya bayyana shi. Suna cikin jajantawa da kuma tunanin zuwa suyi reporting gurin police Hassan ya shigo dakin asibitin. Ya gaishe su yana kallon Ruqayyah da take bacci dan jiya ma sam bata samu baccin kirki ba. Baba yace "Hassan da kokari da kayi zamanka ai" ya danyi murmushi kadan, sai ya kalli Sumayya yace "bai kira ba?" Ta gyada kanta kawai tana kallon wayar hannunta dan number dinsa cewa akai tana dialing, kamar jan charbi ta mayar da kiran number dinsa daga jiya zuwa yau. Baba yayi musu sallama ya fita sai Inna tabi bayansa. Ya zauna akan kujera yana kallon Sumayya yace "za'a ganshi insha Allah kinji?" Ta gyada kai tana kokarin mayar da hawayen idonta. Allah kadai yasan yadda take ji a zuciyarta, sai yanzu ta san zafin batan mutum da ake cewa gwara kaga gawarsa a gabankaakan ace ya bata baka san halin da yake ciki ba. Tun jiya babu abinda take yi sai sake sake na irin halayen da yake ciki, maybe yayi accident ya mutu babu wanda ya ganshi, maybe masu garkuwa da mutane ne suka kama shi yana hannunsu, maybe yana can yana neman taimako kuma babu wanda zai taimaka masa. Ta fara hawaye, Hassan ya jingina da jikin kujera yana kallon ta. "Ki daina kuka fa, zai dawo gurinki indai yana raye I promise you this kinji?" Ta gyada kai amma hawayenta yaki tsayawa, she just can't get it through her head cewa Adam ya bata, ya za'a yi ya bata kamar wani thing ba mutum ba? A lokacin Ruqayyah ta bude ido, ashe tun shigowar Hassan idonta biyu ta rufe idon ne tana jin abinda suke cewa, ta yi kokarin mikewa zaune, Hassan yayi saurin taimaka mata yana yi mata sannu ta zauna tana kallonsa tace "Adam din Finally ya tafi kenan" yace "me kike nufi Finally ya tafi?" Ta danyi murmushi tace "wai da kun dauka zama zaiyi? Me naji kna cewa? A gabasa fa Hussain ya mutu kuma ka bashi mota kace ya taho Abuja, yanzu wannan motar idan ya siyar da ita ba yayi arziki ba, ai kawai ku fitar da ran ganinsa kawai na san ya debi rabon sa ne ya kara gaba" ran Sumayya ya baci, ta taso kan Ruqayyah da sauri "kar ki kara! Kar ki kuma alakan ta shi da sata ko cin amana, ba halinsa bane ba, motar banza motar wofi, ana tunanin ima mutum yake kuma wanne hali yake ciki ke kina zancen mota? Wacce irin zuciya ce a kirjinki Ruqayyah?" Hassan ya dafe kansa yana jin kamar zai tsage, sai Sumayya ta ja da baya tana jin babu dadi tayi masa hayaniya aka Sannan ta juya ta bar dakin da sauri tana hawaye, a ranta kuma tana Allah wadai da halin Ruqayyah da har after all what happened zata iya fadar abinda ita kanta tasan karya ne akan wani, wanin ma kuma wanda ake tsammanin yana cikin matsala. Bayan tafita Ruqayyah ta bi ta da kallo sannan ta dawo da dubanta kan Hassan tace "kayi hakuri da halin Sumayya, tana da problem musamman in akaxmce akan wannan stupid yaron ne, ga gaskiya kiri kiri amma ba zata ganta ba, yaron nan ya saci mota ya gudu, period" Hassan ya girgiza kai yace "you are wrong Hassana, bana jin gudu wa yayi, you need to see yadda hankalin sa ya tashi a lokacin da Hussain ya rasu, he gave me support and a shoulder to cry on. Da yana son ya saci mota da tun da yake gidan zai sata, keys din Hussain duk suna hannunsa ko ni lokuta da dama a gurinsa nake karbar key din wasu motocin, in yana son ya dauki mota ya gudu da tuni ya dauka ya gudun" Ruqayyah tace "to ai lokacin yasan mai motocin yana da rai, yanzu kuwa yana ganin sun zama kayan gado shi yasa zai kwashi rabonsa" yayi shiru yana kallonta kawai yana lura da yadda ta ambaci gadon. It never occurred to him cewa kayan Hussain sun zama na gado ba, shi komai na Hussain ne a gurinsa duk kuwa da xewa tun kafin Hussain ya bar duniya ya mallaka masa rabin duk abinda ya Mallaka. Sai kawai ya girgiza kansa a ransa yan aiyana rigimar da zasuyi da Ruqayyah duk sanda ya gaya mata kudurin da ya yanke a zuciyarsa na abinda zaiyi da duk abinda Hussain ya bari. But he has already made up his mind tun kafin Hussain din ya bar duniya. Yau ma sai da ta sake yi masa maganar fita waje, ya kira Doctor din yazo a gabanta suka yi magana yayi masa bayanin problem din da yake tunanin ya samu kafar da kuma solution din daya yanke. "jijiyar ce ta rike ba wani abu ba. We can treat her here, duk abinda za'a mata a waje zamu yi mata anan ma in dai har ta bamu dama" Hassan yace "babu problem, just do your best but in kunga akwai problem sai ku fada da wuri dan musan abin yi. Kana ganin zat warke ai ko?" Doctor din yayi murmushi yace "ras kuwa. In no time zata cigaba da amfani da ƙafafuwan ta. Garin accident din ne kashi ya bude a hips dinta sai jijiya ta shiga ciki, wannan yasa ta zata ita motsa kafar voluntarily ba sai dai in ta saka hannu ta motsa ta. Manually zamu fito da jijiyar daga cikin kashin sai mu daura mata belt a gurin mu barta tayi healing shikenan" Hassan y gyada kai cikin gamsuwa yace "shikenan Doctor" Ruqayyah kuma sai tace "amma Doctor ba tunda akayi accident din bane ba ta rike, nayi amfani da ita sai daga baya ta rike" Hassan yace "kinyi amfani da ita? Ina kika je?" Ta dauke kanta tana kallon gefe tace "na.... Ammmm naje nayi......na dan zagaya ina neman network zan kira ka" ya kalli Doctor din yace "to kaji, she used the leg after the accident" doctor yace "I can't say me ya faru gaskiya, it maybe sanda take tafiya ne, ko kuma wannan ciwon da taji, but hoton mu bai nuna mana komai a keg din ba shi yasa mukayi tunanin daga hip bone be, but zamu sake dubawa". Doctor din yana fita ta fara mita "kaji ko? Basu ma sani ba, basu ma san aikin su ba. Wannan mutanen babu abinda zasu iya yi min, idan kai ba zaka iya hakura da abinda kake yi ba ka taho mu tafi ba ni ka barni in tafi ni kadai" ya mike yana kallon ta, baya son ta kara masa wani tension din akan wanda yake ciki already yace "in zuwa karshen satin nan basu tsayar da matsaya ba zan nemi Doctor din da zai duba ki a waje sai ku tafi tare da Sumayya" tayi murmushi tana bayyana jin dadin ta tace "yauwa. Ko kaifa. Allah ya kaimu" ya juya ya fita yana lura da yadda bata ce masa a dawo lafiya ba, sai kuma ya tuna cewa har yanzu bata yi masa gaisuwar Hussain ba ballantana ta Fatima. Ranar sadakar uku gidan gaisuwar ya cika har ma yafi ranar da akayi jana'iza cika. Dan yan uwan Fatima ma duk anan suka zo aka hada akayi musu addu'a tare, sannan aka fito da dukiya akayi ta bayarwa sadaka da niyyar Allah ya kai ladan kabarin Hussain da iyalinsa. A ranar saida Hassan ya karar da kudin da yaje cikin account din Hussain kaf, amma yayi noticing amount din dan yasan ba shi kadai ne yake da gadon Hussain ba. Kuma sadakar da yayi irin wadda yasan Hussain yana yi ce da Hussain ya kan ce "Da ka tara mutane da yawa ka basu abu kadan wanda wani ma a kudin motar komawa gida zai karar da abinda ka bashi gwara ka tara mutane kadan ka basu abinda in suka lallaba shi kum Allah ya sa ka musu albarka zasu rabu da talauci" Hussain baya taba kyautar abu kadan. Shim Hassan haka yayi. Bayan an watse ne wajen laasar sannan ya samu ya tafi asibiti gurin Ruqayyah. Yauma Sumayya ce a wajenta, suka gaisa ya zauna yana lura da irin ramar da Ruqayyah tayi yace "kin rame da yawa. Hope ba wai har yau ba kya iya cin abincin ba?" Ta girgiza kai tace bacci ne bana iyawa. Tsorata nake yi duk dare." Haka ne, tun da Ruqayyah tazo asibitin bata iya bacci, in fact she is even scared of closing her eyes dan in banda gawawwaki babu abinda take gani. Gawar Minal, ta driver. In kuma tayi bacci mafarkin Hussain take yi, a very angry Hussain, abinda bata taba gani ba sanda yana raye amma yanzu a mafarkin ta tana ganin tsananin fushi a fuskarsa kuma yana binta kamar zai hallaka ta. Bata fada wa Sumayya ba, ta dai gaya mata tana mafarkin gawawwakin Fatima da ta driver a irin yana yin data gansu lokacin mutuwar su kuma Sumayya tagawa wa Inna Ade ita kuma ta bata adduoi kuma tayo mata rubutun da zai bata kariya daga tsorata. Dan sun san cew tsorata ce tayi. Sai dai kuma a mafarkin nata sai taga kafarta tana motsewa har sai ta koma irin ta jarirai sannan sai ta fadi tana kukan jarirai a haka har abinda ya biyo ta zai cimmata. Tayi kokarin yin addu'a akan hakan, tana so ta roki Allah ya yaye mata abinda yake damunta amma sai taji t kasa, me zata ce wa Allah a cikin addu'ar tata? Menene uzurin ta na aikata abinda t aikata? Duk wani link da take feeling a tsakanin ta da ubangiji idan tana addu'a a da yanzu jinsa take yi ya yi cutting, kamar ubangiji baya dubanta, bata son kuma tayi tunanin abinda hakan yake nufi dan amsar tunanin nata ba zaiyi mata dadi ba. Bayan wannan kuma a duk lokacin da taji shiru babu maganganun mutane, sai taji kunnuwan ta sun cika da kukan jariri, kukan jaririn data ajiye a kofar orphanage. A dole kullum ake yi mata allurar bacci, amma even with allurar baccin haka zata yi ta yi tana tsorata tana komawa tana dada farkawa har gari ya waye. Amma ba zata gaya wa Hassan wannan ba. "Bana iya bacci ne mijina" ta maimaita tana kallonsa. Ya gyada kai "ki yi kokari ki cire abinda yake ranki kinji? Na san ba zaki manta ba, babu yadda za'a yi ki iya mantawa amma ki rage tunanin abin kinji? With time baccin ki zai dawo kamar yadda yake da" ta gyada kai kawai a lokacin da aka bide kafar aka shigo,suka juya ga aki daya. Maman Minal ce ta shigo tare da sallama, fuskarta jeme jeme kamar wadda ta kwana tana kuka. Ruqayyah ta kware da abincin da ta saka abakinta, Hassan ya tashi da sauri ya bata ruwa tasha yayinda Sumayya take yiwa maman Minal barka da zuwa tare da nuna mata kujera. Ta zauna duk suka gaishe ta, Ruqayyah ma ta gaishe ta ba tare da ta hada ido da ita ba. Sai matar tace "ya hakurin mu yaran nan? Allah yaji kansu yayi musu rahama. Ni naji labarin rasuwar amma ban dauka hatsari ne aka yi ba, ashe har da ke Ruqayyah a cikin accident din, Allah ya bami Lafiya" suka ce ameen, sannan tace "daga gidan ai nake, naje inyi muku gaisuwa kuma in tambaye ki labarin kawarki" Ruqayyah tace "ammmm....... ban ganta ba, ban san inda take ba. Ina nufin ba ta zo ta duba ni ba" Maman Minal tace "baku yi waya da ita b kuma?" Ruqayyah tace "babu waya a hannuna ai, ta kone tare da.......tare da mota" Maman Minal ta share hawaye tace "kawarki yau kwanan ta uku rabont da gida. Ta tambayi mijinta zata je kasuwa ta karasa siyayyar kayan haihuwar ta, tunda ta fita shikenan. Anyi neman, duk inda muka san tana zuwa munje amma babu ita babu alamun ta." Sumayya ta yi salati "mun shiga uku, abinda ya same mu kenan kuma? Allah in laifi muka yi maka Allah mun tuba ka yafe mana" Ruqayyah ta dauke kai gefe "ban ganta ba Mama. Na kwana biyu ban ganta ba" Maman ta bita da kallo sannan tace "amma mijinta yace tace masa gidan ki zata zo tare zaku tafi kasuwar. Har tace masa a can zai je ya dauke ta da daddare, kafin yaje daukanta ne akayi wannan rasuwar kuma da yaje ya tarar gidan a cike da mutane. Ya kura wayarta kuma a kashe" Ruqayyah ta kuma girgiza kanta tace "batazo ba gaskiya, ni ta jima ma rabon da tazo gidana" ta karasa tana kallon Hassan wanda ya tsare ta da ido yana lura da rashin gaskiyar da yake rubuce a fuskarta. Maman Minal tace "na shiga uku ni Hauwa. Yarinyar nan ita ta shiga da tsohon ciki? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" Hassan yace "Allah ya bayyana ta. An kai cigiya gidan radiyo?" Maman Minal tace "mijinta ya kai, har hoton ta duk yakai a gidajen talabijin" Sumayya tace "Allah sarki Minal. Kai duniya. Allah ka bayyana mana inda wadannan bayi naka suka shiga" Maman Minal ta mike tana cewa "dan Allah, idan kunji wani abu ko kunga wani abu ku gaya mana. Duk wanda yake da saka hannu a cikin batan yarinyar nan insha Allahu ba zai gama da duniya lafiya ba. Ni na san saka hannun makiyane dam anga zata haihu" sai kuma ta saka kuka "wayyo yata, Allah kar ka basu ikon cutar min da yata". Duk sai da zuciyoyin su suka karye, Sumayya tana tayata kuka. Tana fita wayar Hassan tayi kara. Ya daga yana sauraro sannan yace "shikenan, gani nan zuwa" ya mike yana kallon Sumayya yace "anga motar da Adam ya taho da ita" ta mike itama tana dafe kirji. "Shi kuma fa? An ganshi?" Yace "an kusa dai" ya jura zai fita ta tari gabansa tace "me suka ce, dan Allah ka fada min" yace "a hannun wasu mutane aka kama motar, sunce wai tsintar ta suka yi a gefen hanya babu kowa a cikinta kuma da key a jikin ignition, da kuma waya ta a ciki, they may be lying, zanje gurin yanzu za'a kara tambayar su dan a tabbatar" ta rufe fuskarta da hannunta shi kuma ya wuce ta ya tafi. Gurin police ya fara zuwa, yaga wadanda aka ga motar a hannunsu amma su sun dage basu ga Adam ba. Ya barsu a hannun police din ya koma gida yace a cigaba da bincikar du sai sun fito da shi. Yana zuwa gida ya shiga part dinsa ya hau saman sa ya dauko spare key din motar Ruqayyah ya sauko, tun sanda suke magana da maman Minal yasan da akwai wani abu da take boyewa kuma jikinsa ya bashi abin yana cikin motar ta. Dan a ranar tace masa zata je kasuwa, kuma ance Minal tace zasu je kasuwa tare. Ya bude kofar motar ya shiga ciki yana ta dube dube bai ga komai ba, sai ya bude booth, idonsa ya sauka akan manyan ledojin kaya, ya saka hannu ya bude a hankali sai idonsa ya sauka akan kayan babies da tarkacen kayan haihuwa. Ya koma da baya yana dafe kansa yana tunawa da maganar Maman Minal "siyayyar kayan haihuwa zata karasa". Tabbas Ruqayyah tayi masa karya. *First Wave* Ya mayar da booth din ya rufe yana jin ciwon kansa yana karuwa. Tun sanda tana magana yasan karya take yi, amma baya so ta karya ta ta sai ya tabbatar da cewa karya take yi din, wannan shi yasa ya bincika motar ta dan yasan cewa in dai sun fita tare da Minal to kuwa zai iya ganin shaida a cikin motar tata. Ya juya yana kallon gate zuciyarsa tana gaya masa ya koma asibiti ya tuhume ta akan karyar da tayi masa amma sai ya fasa, ya rufe motar ya koma cikin gida dan magrib ta gabato. Sai da yayi wanka sannan ya tafi masallaci aka yi Sallah yare da gabatar da Adduoi ga Hussain da iyalinsa sannan shi kuma ya shiga cikin gida gurin Aunty wadda har yau take kwance babu lafiya, jiya ma sai da aka mayarda ita asibiti saboda jinin ta daya kuma hawa, wannan ya sa ya kuma jaddada cewa babu zaman makoki dan ta samu ta huta, da yayi yayi da ita akan a mayar da ita asibiti tayi zamanta acan inda zata ke samun kulawar likitoci kuma ba za a dame ta ba amma taki, tana so ta zauna take karbar gaisuwar Hussain kamar yadda ta karbi ta yaya Hassana da Alhaji Aminu. A lokacin ne ta zaunar dashi briefly ta saka aka zuba masa abinci ta matsa masa sai da ya dan ci kadan, dan shi mantawa yake yi ma ana cin abinci in yana ci din kuma baya jin taste kwata kwata sai yaji kamar magani yake ci, bakin sa har daci yake yi, amma haka ta matsa masa ya cusa kadan ya sha kunun gyada. Ya kuma dudduba kannensa sannan ya fita ya koma gidan sa. Direct dakinsa ya wuce ya rufe kofa ya kwanta a kan gado rigingine yana kallon ceiling, hannayensa biyu a harde akan kirjinsa yana sauraren yadda zuciyarsa take bugawa. Ya rufe idonsa hawaye yana gangarowa ta gefen idon zuwa wajen kunnensa. Kwana ukun nan da yayi a duniya alhalin Hussain baya cikinta ji yake sune mafiya kuncin kwanakin da yayi a duniya so far, bai san abinda rayuwa zata zo masa da shi ba nan gaba amma ya san ba zai kuma jin zuciyarsa ta dawo dai dai ba, saboda Hussain ya cire wani part na sa ya tafi dashi kuma baya jin zai kuma jinsa complete sai dai ko a lahira amma ba'a nan duniyar ba. Sosai yake bukatar wanda zai lallashe shi ya gaya masa maganganu masu dadi amma waye kenan zai masa haka, wa zai runguma yayi kuka a jikinsa yaji sanyi a zuciyarsa? Wa zai gaya wa damuwarsa ko da kuwa ba zai masa magani ba? Yan uwansa duk mata ne suma karfin halin da suka ga yana nunawa shine a binda yake kara karfafa su to in sunga yayi rauni kuma suyi yaya da kansu? Ga Aunty tana fama da hawan jini kuma yasan daga strenth dinsa ita ma take samun nata Strength din na facing rayuwa a yadda ta zo musu. Ruqayyah? Ruqayyah tunda akayi rasuwar bai ji ta ambaci sunan Hussain ba ballantana tace Allah yaji kansa, abin ya tsaya masa a ransa amma koda yaushe sai zuciyarsa take bata uzurin itama halin da take ciki, a tsorace take sosai dan idonta zaka kalla kawai kasan a tsorace take. Maybe rudewa ce ta hana ta yi masa gaisuwar. Maybe. Sai kuma ya tuno da kalaman Sumayya da tayi masa ranar nan, yaji dadin maganganun ta sosai kuma irin su yake so ake yi masa, a ranar ya fara sanin tana da hankali dan shi kullum kallon marar nutsuwa yake yi mata. Amma sai yaji tayi masa magana mai dadi mai ma'ana, sai yaji yana fatan idan Ruqayyah ta warke, idan ta dawo cikin hayyacin ta itama take gaya masa irin wadannan maganganun. Sai kuma yayi bitar abinda ya faru yau, karyar da Ruqayyah tayi masa akan Minal, yana trying to make sense out of it, me yasa zata yi kokarin boye fitar da sukayi da Minal? Me ya faru da Minal? Me Ruqayyah ta sani a ciki me kuma take boyewa? Yasan Minal kawarta ce sosai duk da cewa shi ba son kawancen nasu yake yi ba amma yasan Ruqayyah ba zata hada baki da wanda zai zalinci kawarta ba. Ya mike zaune yana girgiza kai, in bai bi a hankali ba shima sai nasa jinin ya hau soon irin yadda na Aunty ya hau koma zuciyarsa ta buga yabi Hussain, sai yaji wani bari na zuciyarsa yana son hakan ta kasance amma kuma kamar yadda Sumayya ta tuna masa sai ya tuno da ƴaƴan sa da kannensa, idan ya fadi ya mutu ina rayuwarsu ta dosa? Ya tashi ya shimfida carpet dinsa na sallah sannan ya zauna akai ya jawo Alqur'ani ya fara tilawa, tabbas bashi da wanda zaije ya rungume yayi kuka a jikinsa amma yana da Allah, shi zai rarrashe shi ya karfafa masa zuciyarsa ya cigaba da facing rayuwarsa komai dacin ta. A kan sallayar ya kwana yau ma kamar jiya da shekaran jiya, ya fita masallaci yayi sallar asuba sannan ya kuma komawa dakinsa ya kwanta yayi bacci mai cike da mafarkan Hussain, sweet memories din rayuwarsu tare, sai daya farka ya fahimci ashe mafarki yake yi kuma sai yaji yana so ya koma ya kwanta ya cigaba da wannan mafarkin har abada. Amma dole ya tashi, dole yayi facing rayuwarsa. Ya shiga yayi wanka ya shirya sannan ya fito daga dakinsa ya shiga dakin Ruqayyah ya sake daukar mata wasu kayan tare da na little Hussain duk da cewa bata bukata ba, ya sauka kasa dakin twins ya dibar musu nasu kayan jaka guda, so yake su cigaba da zama a gurin Inna for now, sai in anyi bakwai yan Gombe sun fara komawa sannan sai ya karbo su ya dawo dasu gurin Aunty kafin Allah ya bawa Ruqayyah lafiya, in kuma ta samu lafiyar kafin lokacin shikenan. Ya fito yana kallon gidan Hussain, standing so tall and mighty but empty. Dan tun washegarin da akayi rasuwar duk ma'aikatan gidan suka fito aka rufe kofar gidan aka kai wa Aunty keys din. Ya dauke kansa ya wuce zuwa mota ya zuba kayan hannunsa yana kallon motar Ruqayyah yana tunawa da kayan da suke cikin booth, ya wuce ya shiga part din Aunty ya gaishe ta, ya lura da mutanen gidan sun fara raguwa, duk kannne sa suka gaishe shi yana lura da yadda duk suka rame annurin fuskokin su duk ya dusashe. Yanzu ma sai da Aunty ta matsa masa ya ci abincin, ya gaya mata zai je asibiti gurin Ruqayyah, duk suka tambayeshi ya jikin nata duk da Inna tayi musu bayanin ciwon na Ruqayyah, shi ma kuma ya kara jaddada musu cewa babu wani major problem. "Babu karaya babu tsagewar kashi, ko daddaujewar kirki babu, kafar ce kawai ta rike kuma likita ya gaya min insha Allah babu matsala zata warke" duk suka ji dadi kuma suka tabbatar masa zuwa yamma zasu je su dubata. Yau Inna ya tarar a dakin Ruqayyah tana ta karanto addu'a tana tofawa Ruqayyah. Ya gaishe ta yana karanto yanayin damuwa a fuskarta, ta amsa tace "yarinyar nan har yanzu ta kasa samun bacci mai nauyi, dama Sumayya ta gaya min zabura take ta yi cikin dare tana firgita sai jiya nima da na kwana na gani da idona. Nayi mata rubutu ta sha dai, sai an hada da addu'a gaskiya" ya mike yana kallon yadda Ruqayyah take ta jujjuya kanta a cikin bacci yace "haka ne Inna, sai an hada da addu'a, kuma nasan kina iyakar kokarin ki. Allah ya saka da alkhairi" maganar da yake yi ta farkar da Ruqayyah ta mike da sauri tana cewa "Fatimah ta dawo? Tana ina?" Yi take kamar zata mike daga kan dagon amma babu kafar tashi, Inna ta rike ta tana karanto mata adduoi har ta sami nutsuwa sannan ta lura da Hassan a tsaye, ya ja kujera ya zauna yace "Ruqayyah, Fatima ta rasu, wanda ya mutu kuma baya taba dawowa kinji? Ki rage, ko yaya ne ki rage saka damuwa a ranki kinji? Kiyi kokari kike tunanin wani abin daban ba abinda kika gani ba, sannan ki ringa addu'a sosai ki na karanta Alqur'ani zai saka miki nutsuwa" sai ta fara kuka, tana kokarin yin addu'ar amma sam bata jin alamar addu'ar ta tana karɓuwa, daga ta daga hannunta da niyyar addu'a sai taji munanan aiyukan ta sun dawo ranta, sai taji ta kasa samun kalmomin da zata yi amfani dasu gurin rokon ubangiji bukatar ta. Amma kuma babu wanda zata iya gaya wa wannan. Ta gyada kai kawai, sai ya karbi Hussain daga bayan Inna ta fita ta basu guri, shi kuma sai ya zauna a bakin gadon, ya kwantar da Hussain a gefenta ya jawo ta jikinsa yana tsananin son jin dumin jikinta, ta kwanta a jikinsa tana shaƙar kamshin sa tana jin ta dan yi missing dinsa ba laifi, yace "it is all going to be alright kinji? Ki daina damuwa kiyi ta addu'a" ta gyada kai tana jin hawaye yana sake taruwa a idonta, tace "promise me zaka kashe ku nawa ne, zaka yi duk anything possible dan ka samar min lafiya" yayi ajjiyar zuciya sannan ya dago kanta da hannunsa yana kallon cikin idonta yace "zanyi duk iyakacin iyawa ta dan in nemar miki lafiya Hassana, amma bani zan samar miki lafiya ba suma doctors din basu zasu samar miki lafiya ba sai idan Allah ya baki lafiya. Idan har Allah ya riga ya rubuta rashin kafa a cikin kaddarar ki, idan har amfani da zakiyi da wannan kafar taki ta kare to babu yadda zanyi babu kuma yadda likitoci zasu yi dole mu hakura" ta fara ture shi tana kuka ya sake kamota yace "look at me Hassana, ki tuna da rayuwar Hussain, ki tuna da irin dukiyar sa da yadda jama'a suke sonsa amma duk hakan bai sama masa lafiya ba. Kudin sa basu samar masa lafiya saboda Allah ya riga ya rubuta ciwon nan shine sanadin sa" ta fara girgiza kanta "bana so in rasa kafata Hassan bana so in zama gurguwa ka taimaka min mijina" yace "Ruqayyah, kwana hudu da suka wuce Hussain yana da rai, haka ma Fatima tare da abinda yake cikin ta, amma yanzu sun rasa rayukansu gabaki daya, ki duba Adam da kawarki Minal, babu wanda yasan inda suke babu ma tabbacin in suna raye, sai mu gode wa Allah da ya saka mu muke da ranmu kuma tare da yan uwan mu Ruqayyah, menene kafa? Allah ba shi ya baki kafar ba? Da yaso tun daga ciki zai yi halittar ki babu kafa kuma me zakiyi akai? Me zaki ce masa? An yi accident din nan kin fita lafiya, kafar nan tana nan ba wai guntulewa tayi ba kuma akwai tsammanin cewa zata warke. Menene abin damuwa a ciki? Mu gode wa Allah Ruqayyah". Sai tayi shiru ta kwantar da kanta a kirjinsa tana mayar da ajjiyar zuciya. Sai da yaji numfashin ta ya dai dai ta sannan yayi mata tambayar da take cinsa a rai tun jiya. "Me yasa jiya kika yi min karya Ruqayyah?" Ta dago kai tana kallonsa, irin kallon da taga yayi mata ne ya saka ta yi saurin mayar da kanta ta sunkuyar sannan ta tashi daga kirjinsa ta zauna sosai tana wasa da yatsun hannunta, ta san wacce karya yake magana akai kuma ta gama shirya amsar da zata bashi. Yace "jiya kika ce da babar kawarki ba kwa tare ranar Friday, kika ce ba tare kuka je kasuwa ba kuma bayan tare kuka je, naga kayan da ta siya a booth din motar ki" ta dago kai tana kallonsa, bata san binciken nasa zai je har cikin motar ta ba tace "kayi hakuri mijina. Na fadi haka ne dan kada ranka ya baci tunda nasan ba ka son mu'amala ta da Minal, ta kira ni tace min zata zo muje in raka ta tayi siyayyar haihuwa ni kuma bansan me zance mata ba, babu dadi wanda yake kula ka kai kuma ka dinga wulakanta shi bana so tayi tunanin ko dan miji na yafi nata ne ko kuma wani abi daban, sji yasa mace tazo muje din, bayan mun gama kuma naso in sauke ta a gida sai tace min wai gidana zata taho muyi hira kafin dare sai mijinta yaje ya dauke ta, ninkuma bana son ka dawo ka tarar da ita a gidan ka ga kamar bana jin maganar ka shi yasa muna shiga na ga Fatima zata tafi Abuja sai nace zan bita ba wai dan ina son zuwa ba sai dan ina so Minal din ta hakura da shiga gidana tunda ta ga nima fita zanyi, shine ta bar kayan ta a mota ta tace zata aiko driver ya dauka, sai ta bi mu muka fita da ita bakin hanya muka sauke ta zata hau taxi ta tafi gida. Wannan shine karshen gani na da ita" ta karasa tana rintse idonta a ranta tana bitar ƙawancen su da Minal tun yarinta, is the money really worth it? Amma ta riga ta shiga iya wuya kuma babu damar fita ba tare data tarwatsa komai nata ba. Hassan ya mike ya tafi bakin tagar dakin ya tsaya yana kallon bishiyoyin da suke wajen, koma na labarin Ruqayyah ya tafi dai dai babu tangarda sai abu daya, abu dayan nan shine labarin is so perfect yafi kama da labarin da aka zauna aka jima ana tsara shi ana kuma bitar sa har sai da aka tabbatar babu giɓi a tare dashi. Bai yi kama da true life story ba. Ya juyo yana kallonta, itama shi take kallo tace "kayi hakuri dan Allah, na fadi haka ne jiya dan kar in bata maka rai" cikin fada yace "amma kin fahimci cewa ran kawarki ne kika yi wasa dashi saboda kar ki bata min rai? Kin fahimci cewa rayuwarta tana cikin hadari amma ke kina karya dan kar inyi miki fada? Wacce irin kawa ce ke? Bata fa aka ce tayi? Kwana hudu yau ba'a san inda take ba amma kina tunanin kar raina ya baci in kin fadi gaskiya. Ba kiyi tunanin cewa ke ce mutum ta karshe da ta ganta kafin batanta ba? Ba kiyi tunanin cewa yanuwanta da mijinta ya kamata su san gaskiyar magana ba? Baki yi tunanin abinda zaki fada zai taimakawa police gurin binciken inda take ba?" Tayi sauri ta dago kai tana kallonsa jin ya ambaci police, ita sam bata dauka zai dauki zafi haka ba dan tasan ba wai ya damu da Minal din bane ba, a sali ma ba ya son muamalar ta da ita, ta dauka zasuyi maganar su a tsakanin su su gama ta bashi hakuri shikenan maganar ta wuce, amma gashi taji yana ambaton yan sanda. Ta sake cewa "kayi hakuri dan Allah" ya dawo ya tsaya a gabanta, so tall and so strong, hannun sa a aljihun sa yace "kar ki sake yi min karya irin wannan. Banaso" ta gyada kai da sauri, yace "idan kin fadi gaskiya zanyi miki fada, amma fadan nawa na yan mintuna ne shikenan ya wuce, amma idan kika yi karya zaki kara yin wata karyar ne dan ki kare waccan daga nan kuma ki sake yin wata dan ki kare wannan a karshe sai ki ga kin zama makaryaciya. Kina da ilimi kinsan menene karya, fadin Annabi ne yace karya tana daga alamomin munafiki, kin kuma san hukuncin munafiki Allah da kansa yace ba zai shiga aljanna ba. Ballantana karya irin wannan da zata saka ran kawarki a hadari" tayi shiru kanta a kasa, ita dai so take ya gama fadansa amma kar ya kuma ambaton police din nan. Sai ya zauna a kujera yana kallon ta yace "kin ga motar da ta shiga" tayi sauri ta gyada kanta tace "taxi ce" yace "zakiniya tuna plate number dinta?" Tace "a'a, ban ma kalla ba. Sabuwa ce dai motar" ya dafe kansa yana daidai ta numfashin sa saboda yadda yaji kan ya dauki zafi, yana tsoron kar jininsa ya hau, har yanzu yana ganin alamun karya a fuskarta. Yace "sai menene ya kamata in sani?" Ta girgiza kanta tana daukar Hussain data fara mutsu mutsu zai tashi daga bacci tace "shikenan, shikenan nima abinda na sani" Ya jima a zaune yana kallon ta tana feeding Hussain sai kuma ya mike yace mata "zan dawo da daddare, if you need anything call me" har ya kai bakin kofa kuma sai ya juyo yace "bani wayar Fatima da take hannun ki" tace "to ai da ita nake amfani" yace "bani, zan kawo miki wata da daddare in na dawo" still bata bayar ba tace "to da wacce zan kira ka in ina bukatar wani abun?" Ya dafe kansa yace "Ruqayyah ki bani wayar mutane, fa Inna nan ga Sumayya duk suna da number ta, wannan wayar ba tawa ba ce ba ba taki bace ba ba kuma ta gadon Hussain bace ba" ta mika masa watar ganin ya dauki zafi kamar zai rufe ta da duka. Ta bishi da kallo har ya bar dakin sannan ta mayar da idonta kan kafarta marar lafiyan, a idonta sai taga kamar kafar ta fara kankancewa kamar yadda take gani a mafarkin ta. Yana kokarin fita Sumayya tana shigowa, kallo daya yayi mata taji tausayin ta ya kama shi gaba daya tayi zuru zuru kamar wadda ta tashi daga jinya. Ta gaishe shi sai ta tsaya bata ce masa komai ba amma yasan tana son jin yadda aka kwana a neman Adam, sai yace "munyi magana dasu, suna yin iyakacin kokarin su. Kiyi hakuri kinji? Za'a ganshi insha Allah" ta gyada kai kawai, har zai wuce ta sai ya kuma ya dawo yace "kiyi murmushi mana. Nafi son inga kin ware kina harkokin ki yadda inya dawo zaiji dadin ganin ki ba wai ya tarar da ke kin zama kashi ba" still bata yi murmushin ba, shi bai taba ganin ta a wannan yanayin ba shi Sumayyan da ya sani kullum cikin dariya take har gani yake kamar ta fita sakarci. Sai ya kasa wucewa yace "kin manta Adam din naki ne? He is strong, yayi going through abubuwa da dama Allah ya jarabce shi ta hanyoyi da dama am sure wannan ma wata jarabawar ce yaje yi kuma he is going to come out stronger and better" ta gyada kai tace "insha Allah. Nagode" ya kuma yin kamar zai tafi sai ya kuma dawowa yace "dan Allah, ina son ki binciko min number din mijin Minal kawarku, ina son yin magana dashi akan case dinta" tace "Okay insha Allah" yace "in kin samu sai ki ajiye min a gurinki, zan dawo da dare sai in karba" ta amsa masa sannan ta wuce ciki shi kuma ya fita waje. Yana ji a ransa cewa dole ya shiga cikin neman Minal tunda matarsa ita ce last person da ta ga Minal din, zai kuma yi iyakacin kokarin sa wajen ganin case din to the end. Bai tafi gida ba duk da wayarsa ta yaji tana ta kara kuma yasan daga gidan ne ake nemansa, yasan wasu ne suka zo masa gaisuwa amma idan ya koma gidan ba lallai bane ya kuma samun damar fitowa ba sai kuma dare, kafin nan police sun tashi. Station din jiya ta sake komawa, har yanzu yaran da aka kama da motar suna tsare, sai dpo din ya shigar dashi office dinsa suka zauna yace "yaran nan ina ganin iyakacin gaskiyar su suka fada, bana jin sun san inda yaran nan yake. Barayi ne, irin kananan barayin nan na unguwa masu sane da satar waya, suna yafiya kawai suka ga motar a bakin hanya ita kadai, sun dauka ko mai motar ya fita ne zai kama ruwa shine suka tsaya da niyyar su tsorata shi su karbi wayar sa da yan kudaden hannunsa. To sai suka ga babu kowa a cikin motar, ga kuma key a jikin ignition shine kawai suka dauko motar suka shigo da ita Kaduna da niyyar su siyar da ita, to amma kasancewar motar babba ce dan irin ta guda uku ce a Kaduna sai ya sa suka kasa batar da ita, ta ki siyuwa har aka kama su da ita. Sun ga wayarka a cikin motar, sun cefanar da ita" Hassan yayi ajjiyar zuciya yace "wayar yaron fa?" Yace "basu ganta ba, mun duba motar kuma ba mu ganta ba muma". Hassan ya mike yace "ku yanke musu hukuncin duk daya dace, ni bani da case dasu, ni case dina shine na yaron nan" dpo ya mike shima yace "muna iyakacin kokarin mu, amma yaron tamkar wanda ya bace ne a cikin iska". Da dare Hassan ya koma gurin Ruqayyah, tare da Aunty da dukkan kannensa da aunties dinsa guda uku. Suka duba ta ita kuma tayi musu gaisuwa. Sannan suka yi mata sallama suka koma gida, Hassan ya karbi number din Alhaji Kabiru a hannun Sumayya, sannan shima ya tafi. Da safe ya kira shi suka hadu yayi masa bayanin da Ruqayyah tayi masa na inda suka rabu da Minal da kuma yadda suka yi. Ya kuma roke shi alfarmar cewa duk abinda ake ciki ake sanar dashi, duk kuma wani taumako da ake bukata na kudi ko na wani abu azo gurinsa zai taimaka. Da haka suka rabu. Sai yaji a zuciyarsa yana tausayin Alhaji Kabiru, batan mata matar ma kuma mai tsohon ciki lallai akwai tashin hankali a ciki... Kwanaki suka wuce har akayi sati daya da rasuwar Hussain. A cikin satin nan ba karamar wuta Ruqayyah ta hura wa Hassan ba akan lallai sai ya fita da ita waje taga likita dan har yau wannan likitan da yake ganinta bai gama tabbatar da abinda yake damunta ba. Ita gaba ki daya a tunanin ta fita waje shine babban solution din problem dinta. Dole Hassan ya nema musu bisa ita da Sumayya zuwa Germany, inda aka hada shi da wani doctor da akace ya kware a bangaren jijiyoyi, a hakan ma sai data nuna rashin jin dadin ta dan ita tafi son su tafi tare tana ganin zata fo samun kulawa in tana tare da shi, shi kuma yaki binta saboda he is not mentally ready, ji yake yi kamar yau ne Hussain ya mutu. Ya riga ya gama shirya musu komai, daga asibiti za'a turo mota har airport ta dauke su,a asibitin kuma suna da duk abinda zasu bukata na yau da kullum, a kwai kuma mota idan suna son shiga cikin gari su nemi wani abu da babu a asibitin, duk bill kuma za'a turo wa Hassan. A haka suka rabu, ya kai su airport suka tashi sannan ya juyo da niyyar dawowa gida. Amma sai me? Tun kafin ya karasa gida sai ga kira da number din Sumayya. Yayi packing gefe yana jin hankalin sa yana tashi ya dauka "Sumayya lafiya? Naga fa tashin ku da ido na, me ya faru" muryarta yaji cikin karkarwar baki tana magana "yaya Hassan, gamu a Abuja" yace "Abuja kuma? Me ya faru Sumayya kiyi magana mana" tace "jirgin yana tashi Ruqayyah ta fara complain da kunnenta wai kamar zai yi bursting, na dauka raki ne sai naga ta rude har da faduwa kasa tana kuka tana cewa azo a taimaka mata. Muna dubawa sai muka ga jini yana fitowa daga kunnuwan ta. Dole jirgin yayi emergency landing a Abuja aka ajiye mu, kafin mu sauka har ta suma". Hassan ya dafe kansa yana maimaita innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Sai da yaji nutsuwa sannan yace "kuna ina yanzu?" Tace "muna hanya za'a kaimu asibiti. Ma'aikatan airport din ne suka dauke mu zasu kaimu" daga cikin wayar yana iya jiyo kukan Hussain Junior, Sumayya kuma duk a rude take kamar ma kuka take yi. Sai yace ta bawa driver wayar, ya tambaye su asibitin da zasu kai su suka gaya mishi sai ya kashe wayar sannan ya kifa kansa a jikin stirring yana mayar da numfashi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Me yake faruwa da su ne? Daga nan bai karasa gida ba sai ya juya zuwa airport, bai kuma kira Aunty ya gaya mata ba saboda tana gudun duk wani abu da zai tayar mata da hankali. Sai daya je airport din sannan ya kira Jabir ya gaya masa in case ko za'a neme shi. Daga nan ya samu jirgi sai Abuja. Kafin ya sauka har anyi admitting Ruqayyah kuma likitan kunne ya hau kanta yana bincikar abinda ya kawo mata ear bleeding. Sai bayan ya fito sannan Hassan ya karaso dan haka direct office dinsa ya wuce sai doctor yayi masa bayani kamar haka. "I am sorry sir, but matarka ta hadu da ear problem a sanadiyyar shiga jirgi da tayi with an ear infection wanda kuma it is not advisable. Ear drum dinta yayi bursting, sai munyi mata surgery a kunnuwan ta duk biyu sannan maybe jin ta zai dawo, but bani da tabbas din zai dawo dai dai. Sannan kuma abinda nake da tabbas akai shine, ko anyi nasarar aikin ko ba'a yi nasara ba, kar a kuma barinta ta hau jirgin sama ever again, in ta kuma hawa kuwa, zata yi loosing hearing dinta completely ko ma ta rasa ranta baki daya" Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, idan kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020. *The Second Wave* Hassan ya saki baki yana kallon doctor din, ya girgiza kansa yana dan dukan goshinsa wai dan ya farka idan bacci yake yi amma sai ya ganshi still a gaban doctor din da yake kallonsa. Ya bude bakinsa amma ya kasa magana. Ya kasa tabbatar da cewa dai dai kunnuwan sa suka jiyo masa, kamar fa ji yayi likitan yana cewa Ruqayyah ta kurumce. Matar sa Hassana. Precious wife dinsa. Yace "doctor? What are you trying to say? Ni duk ban gane bayanin ka ba kayi min gwari gwari Please. Kana nufin Hassana ta kurmance ko me kake so ka gaya min" doctor din ya gyada kansa yace "haka nake nufi, ina nufin dodon kunnenta na dukka kunnuwa biyun ya samu matsala. A yanzu haka bata ji, in kayi mata magana ba zata ji ka ba but in ka saka hannu anyi mata aiki da gaggawa zata iya dawowa tana ji kadan kadan ba kamar da ba. Sai dai kuma kamar yadda na fada ina bada shawarar kar ta kuma attempting shiga jirgi ko da kuwa nan da Kaduna ne" Hassan ya kuma dafe kansa yana ambaton innalillahi wa inna ilaihir rajiun, daga neman kafa kuma yanzu shikenan sai a rasa kunne kuma? Kunne fa, shi fa a gurinsa yana ganin kunne duk yafi muhimmanci a cikin sense organs na jikin mutum, saboda shine yake responsible for balance in baka da kunne kana rasa balance ne yadda ko tafiya ma wahala take zamar maka, wani rashin kunnen ma ya kan taba har da kwakwalwar mutum sai mutum ya zama kamar mai mental problem, shi yana ganin anya ma kuwa kunne bai fi ido muhimmanci a jiki ba? Ya dago kansa yana kallon likitan da yake kallonsa seriously, sai ya mika masa hannu yace "kawo takardar inyi signing" ya mika masa ya saka hannu yace "yaushe za'a yi mata aikin?" Doctor yace "as soon as possible, kamar tomorrow morning insha Allah" Hassan yace "tomorrow morning? Ba za'a iya yi mata yau ba? I mean ba za'a iya yi mata yanzu kafin ta farka ba?" Doctor ya girgiza kai yace "noo, ba za'a iya ba. Muna bukatar preparation ita ma kuma muna bukatar preparing dinta. Dan ma kune, kuna da kudi, idan babu kudi wani ya kan dauki weeks ba'a yi masa aiki ba wani ma months, wani ma har abada ba za'a yi masa ba haka yana ji yana gani zai zama kurma" Hassan ya gyada kai a ransa yan godiya ga Allah, there is always something to be grateful for. Sai kuma yaji ya samu idea akan wani abu daya kamata yayi da kudin Hussain. Sai dai kuma he is not looking forward to seeing Ruqayyah, dan bai san me zai ce mata ba kuma ko ya fada din ma ba jinsa zata yi ba. Yaji hawaye ya taru a idonsa, yana matukar tausayin ta a ransa, wannan shine ana kukan targade ga karaya ta samu. Ya fita ya tafi dakin da aka kwantar da ita, ya tarar tana bacci, fuskarta duk jirwayen hawaye, tana ta zabura alamar tsorata take yi a cikin baccon nata, Sumayya tana zaune a gefenta tana rera kuka a hankali, ga Hussain a hannunta. Yana shiga Sumayya ta mike tana kallonsa, tana jin kamar wani babban solution yazo da zaiyi maganin problem dinsu, sai dai abinda ta karanto a fuskarsa yasa ta koma ta zauna tana sake wani sabon lalen a kuka. Ya zauna a bakin gadon yana dora hannayensa akan goshin Ruqayyah, ya fara shafa gashinta a hankali sai yaji ta sauke ajjiyar zuciya. A ransa yace ina ma dai zata cigaba da baccin nan har zuwa sanda za'a yi mata aikin? Baya son tayi experiencing total deafness yafi son in akayi aikin ko yaya ne tana ji hankalin ta ba zai tashi kamar yadda zai tashi in taji dif ba. A bangaren Ruqayyah kuma mafarki take yi, mafarki take yi wai gata a cikin daki tana karbar haihuwar Fatima sai Fatima ta miko mata babyn "in go shi ki kaishi gurin Hussain. Ki kaiwa Hussain shima ya ganshi" sai ta barta a gurin ta juya ta kama hanya tana tafiya da sauri tana waige, sai kawai taga orphanage a gabanta, ba tare da tunanin komai ba ta ajiye babyn a kofar orphanage din yana ta kuka ta juya da sauri amma bata fi taku biyar ba sai kafarta ta makale, tayi tayi ta kasa tafiya ga kukan babyn ya cika mata kunnuwan ta tana kokarin ya fasa mata dodon kunne, sai kuma kafafuwan ta suka fara motsewa a hankali suna komawa kanana, a hankali har suka komawa irin na jarirai, har ta fadi kasa tana birgima tana kuka irin na jarirai, sai kuma taga jaririn data ajiye shi kuma yana girma yana girma har ya zama katoton namiji mai cikar kamala da kwarjini, sai ya taso ya taho inda take ya tsaya a kanta yana kare mata kallo, kamannin sa sak irin na Hassan sai kuma ya rikide ya koma Hussain sannan ya daga kafarsa wadda take sanye ta wani kafcecen takalmi ya sai ta tada niyyar talitse ta. Ta farka a firgice tare kwalla kara "Hussain" amma kuma sai taji bata ji muryar tata ba, bata ji komai ba sai wani irin duumm marar dadi mai shiga har cikin kwakwalwar mutum. Ta bude idanuwan ta tana numfashi sama sama, sai ta ga Sumayya a zaune kamar kuka take yi tunda ga hawaye nan a idonta amma kuma bata jin karar kukan nata, ta ji an taba ta sai ta zabura ta waiga taga Hassan, me Hassan yake yi a nan? Ita dai a saninta sun bar shi a kaduna su sun tafi Germany inda zata ga likitan kafa. Ina ne kuma nan? Mai suke yi anan tare da Hassan? Tayi kokarin tambaya "me muke yi anan? Ina ne nan?" Amma sai taji bata jin maganar tata. Sai ta tuna da abinda ya faru da ita a jirgi, the pain, the blood, sai ta saka hannayenta biyu tana dukan kunnuwan ta dasu "menene ya samu kunne na? Wayyo Allah na na shiga uku, menene a kunne na? Hassan, mijina ka taimaka min wani abu ya shigar min kunne na" Hassan ya fara kokarin kamata, yana yi mata magana, tana ganin bakinsa yana motsawa amma sam bata jin abinda yake fada, tana ganin Sumayya tana kuka tana magana amma ita ma bata jin abinda take fada. Ta kara rikicewa, ta mirgino ta fado daga kan gadon, ta fara kokarin tashi amma kafa taki cooperating. Hassan yayi sauri ya daga ta yana kokarin rungume ta ya lallashe ta amma taki barin shi, kuka take yi tana magana da karfi tamkar zata tsaga masa nasa dodon kunnen, babu shiri Sumayya ta kwantar da Hussain shima da hayaniyar uwar ta sa ta tashe shi ya fara kuka ta fita waje da sauri ta samo nurse, haka suka hadu da kyar suka rirrike Ruqayyah sannan suka sake yi mata wata allurar baccin ta koma. Kafin dare labari ya iske gida, Aunty ta hada Nafisa da Zulaihat sannan suka biya suka dauko Inna da sassafe suka taho Abuja, lokacin da suka isa har an shiga da Ruqayyah dakin da za'a yi mata aiki dan haka sai suka hadu da Sumayya suka zauna zaman jira kawai da addu'a a bakin ta na samun nasarar yin aikin. Nafisa tace "ni ban taba ji ba, ko a labarai ban taba jin wanda ya samu irin wannan problem din ba kawai dan ya hau jirgi. Kuma jirgin nan ba yau ta fara hawansa ba da duk bai sa mata ciwon ba sai yau?" Sumayya tace "doctor din yace ana samu but it is very very rear. Amma yana saka ran success a surgery din sai dai kuma babu sake shiga jirgi a gun Ruqayyah" Zulaihat tace "to wa yake ta shiga jirgi kuma? Ana maganar lafiya? Fatan mu dai kawai ta samu lafiya dan itace tafi komai muhimmanci yanzu a gare ta" Sumayya ta gyada kai, amma a ranta tasan maganar shiga jirgin nan ba karamin taba zuciyar Ruqayyah zata yi ba. She is not going to like the news. Alhamdulillah anyi aiki lafiya an kuma gama lafiya, aka turo Ruqayyah aka fito da ita yan uwanta suna ta bin ta da addu'a kowa yana cikin alhini da tausayin ta. Inna kuma ta na tayi mata addu'ar Allah ya bata karfin zuciyar da zata karbi kaddarar ta da hannu bibbiyu. A haka har ta farka, ta gansu a zagaye da ita suna kallon ta, Sumayya ido ya kumbura saboda kuka, still tana jin wannan feeling din marar dadi a kunnenta. Ta saka hannu da niyyar bubbuga kunnen wai ko zai bude amma sai ta ji su a nannade da bandage, sai a lokacin tunani yazo mata, tunanin irin azabar da taji a kunnenta lokacin da jirgin su ya tashi da kuma yaddata taba taji jini yana fitowa daga kunnen. Bata bukatar tambaya tasan ta samu matsala a kunnenta, bata bukatar tambaya tasan tafiyarta zuwa Germany ganin likitan kafa bata yi ba, sai ta fara kuka a hankali ba irin na jiya ba, tana kallon yadda bakunan su suke motsawa tasan sannu suke yi mata da kuma kokarin bata hakuri amma sai ta mayar da idonta ta rufe tana cigaba da kukan ta dan ba jin abinda suke cewa take yi ba. Wannan wacce irin mummunar kaddara ce? Ita Ruqayyan ita ce ta kurumce bayan kuma kafar ta da har yanzu aka kasa gane menene matsalar ta? Babu wanda bai tausayawa halin da Ruqayyah take ciki ba musanman Hassan wanda bayan ta tashi ya fahimci bata jin abinda suke cewa sai ya koma gurin doctor da complain, amma sai doctor din yace masa ai ba yanzu ne zata ji din ba sai aikin yayi healing an kunce bandage din. Sai nan da sati biyu masu zuwa tukunna sannan za'a tabbatar da success din surgery din ko akasin haka. A cikin sati biyun nan Hassan da Sumayya sun kasance tare da Ruqayyah, supporting her, encouraging her tayi accepting duk abinda result din ya nuna amma ita ta tubure so take yi su bar asibitin, su bar Nigeria gabaki daya su tafi kasar waje tunda ita a ganinta acan ne zata samu lafiya, gani take nan kawai karasa lalata mata kunnen zasu yi ga kuma kafarta da take getting worst everyday. Sai dai har yanzu Hassan ya kasa samun courage din gaya mata abinda likita yace, tausayinta yake ji, ya kasa samun right time da zai ganta cikin mood mai kyau yayi mata bayani, kullum cikin kuka take, kullum cikin mita take. Ga magana da karfi in ya nuna mata ta rage Muryar ta sai ta fara kuka tana ganin kamar yana mocking dinta ne. In zasuyi mata magana a takarda suke rubuta mata, in zata basu amsa kuma sai ta fada, da karfi kamar zata tsaga dakin. Ta zama very edgy, abu kadan sai fada sai kuka shi har tsoron shiga dakin yake yi gurinta shi yasa yake jinjinawa kokarin Sumayya dan tunda suka zo tana tare da Ruqayyah ko nan da can bata zuwa tana ta hidima da Hussain ga kuma nata ciwon da yake cin zuciyarta na rashin sanin inda Adam yake. Amma bai taba jin tayi complain ba ko sau daya. Wannan yasa ya karbi Hussain daga hannunta ya mayar dashi Kaduna gurin Inna aka cigaba da bashi madara dan ga uwar tasa nan amma ba samun shan nonon yake yi ba madarar ake bashi. Ranar da sati biyun suka cika a ranar ne aka budewa Ruqayyah bandage din kunnen ta, doctor din ya kunce tare da wanke kunnen a gaban Hassan da Sumayya sannan ya gwada yiwa Ruqayyah magana "Hajiya Ruqayyah, can you hear me?" Ta juyo tana kallon sa, tana ganin bakin sa yana motsawa sannan tana jiyo Maganar sa can nesa kamar irin ana hira a makota din nan. Bata fahimtar abinda yake cewa sai data tattara dukkan hankalin ta a guri daya sannan ta fahimce shi, ta rufe idonta hawaye yana zuba, tace "ina jin ka, amma bana fahimtar ka, maganar bata clear" sai doctor din yayi murmushi cikin jin dadi yace "alhamdulillah. An samu nasara kenan" duk suka kalle shi cikin mamaki, Hassan yace "an samu nasara fa kace, bayan kana jin tace bata fahimta? Menene amfanin ji idan ba'a fahimta?" Doctor din yace "jin shine babbar nasarar da muka samu, ear drum din ya gyaru kenan ya fara receiving sound. Clearing sound din kuma sai anyi mata taimako da hearing aid. Zai kara enhancing ya kuma kara clearing din sounds yadda weak ear drums dinta zasu karbe shi sosai" Ruqayyah dai tana kallonsu suna ta magana, bata jin mai suke cewa tana dai jin mixed voices dinsu kamar masu rada da juna tace "me kuke cewa ne wai? Ai kin bai yi ba ko? Na gaya maka ai mijina, aikin nan ba kyau zaiyi ba kazo mu tafi Germany din, a warkar min da kafata shima kunnen ayi min aikinsa acan, anan babu abinda za'a samu sai wahala. Dan Allah Hassan kar ka bari na kurmance" ta karasa tana kuka. Doctor din ya kalle shi yace "baka gaya mata ba?" Ga mamakin ta sai taji taji wannan tas, ta juyo tace "menene za'a gaya min" yace "cewa ba zaki kuma hawa jirgin sama ba ballantana har kije wata kasar. Likitocin dai da suke Nigeria damu zaki yi hakuri ki lallaba har zuwa karshen rayuwarki" ta zaro ido tana kallonsa sannan ta kalli Hassan tace "he is lying" likitan ya dauki takardun sa yace "in baki yarda ba akwai hanyar tabbatar wa, ki tafi airport yanzu ki hau jirgi ki gani. Ina tabbatar miki dan guntun jin da kika fara samu zaki rasa shi gabaki daya". Daga haka ya fice ya bar su da rigima. Yasan bai kyauta ba yadda yayi breaking news din amma kuma shima haushinta dama yake ji yadda take ta nuna wa cewa basu iya aiki ba da sauransu, wai ita matar mai kudi. Yanzu sai yaga amfanin da kudin nata zaiyi mata. Washegari suka bar asibitin dan Ruqayyah cewa tayi ba zata iya cigaba da zama ba. Hassan yayo mata order hearing aid din da zata ke amfani dashi, yaso kuma ace gida zasu koma amma taki komawa tace ita sai dai a chanja mata wani asibitin inda wani likitan zai sake duba kafarta tunda tana tsoron daring likitan kunne da yayi warning kar ta kuma shiga jirgi. Wani private asibitin kashi ta tafi anan Kaduna, doctor din yayi mata alkawarin zai warkar mata da kafarta tana zuwa yayi admitting dinta ya fara karbar kudade yana sakawa a aljihunsa, tana asibitin aka kawo mata hearing aid dinta ta fara amfani dashi kuma alhamdulillah jinta ya dawo tana ji tas amma sai da shi, in ta cire sai dai taji kadan kadan kuma shima sai tayi stressing kunnenta tukunna. Daga baya ta fahimci cewa likitan bashi da clue akan abinda yake damunta dan haka ta nemi sallama kuma ya bata sai ta hada kaya sai Kano, AKTH, tana zuwa nan ma suka hau kanta da gwaje gwaje da hotuna da magunguna amma bayan shafe wata guda cur a cikin asibitin sai suka tabbatar mata da cewa su basu da idea me yake damun kafarta. A guri daya kuma kafar sai kara motsewa take yi kamar ta mai ciwon shan Inna, yanzu har kankancewar tata ya zama ana gani ake ganewa dan kana gani zaka gane daya kafar tafi dayar girma. A karshe sai likitoci suka yi mata cast, tun daga hips dinta har zuwa tafin kafarta dan ya taimaka mata wajen motsa kafar, daga nan suka ce babu abinda zasu kuma iya yi mata. Ta zama mai kafa daya kamar yadda ta zama kurma. *Ina mai bawa wadanda suka sayi littafin nan hakuri na rashin jina da basuyi ba jiya, nayi tafiya ne kuma gurin da naje suna matsalar nepa, naso in muku typing da yawa dan in wanke muku zuciya amma shima ba zai samu ba. Ayi min afuwa. Biki ne muke yi na dana, zaku jini shiru yau da gobe amma insha Allah jibi za'a samu mai tsaho kuma mai dadi. Zamu ji third wave din da zata yi hitting Ruqayyah.* Ayi hakuri Please Wannan littafin na siyarwa ne, in kin ganshi a wani gurin na sata ne. In kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020 *The Third Wave* Kusan watanni biyu kenan da rasuwar Hussain. Kusan watanni biyu kenan da rushewar farin cikin rayuwar Hassan. A cikin wata biyun nan ba zai iya tunawa da ranar da yayi murmushi ba ko da kuwa na yake ne, ba zai iya tunawa da ranar da yaji farin ciki a cikin zuciyarsa ba komai kankantarsa kuwa kuma baya jin zai kuma jin farin ciki a kusa, bao san abinda ubangiji ya tanadar masa in the future ba amma ya san da wahala ya samu waniabu da zai maye masa gurbin abinda ya rasa, babu abinda zai maye masa gurbin Hussain da family dinsa including his own family. Amma kuma duk da haka yasan abinda ya rasa, bayan rashin Hussain ya rasa wanda zai rarrashe shi ne kuma wannan rarrashin da kalamai masu dadi da kantar da hankali su yake bukata, soyayya da kulawa yake bukata, babu kuma abinda ba zai iya bayarwa ba dan yaga ya samu abinda yake so amma shima kanta yasan abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Dan inda zai samu wannan, wadda take da hakkin bashi wannan ita yanzu sam hankalin ta baya kansa ma kwata kwata yana kan nemawa kanta lafiya. Yes, yasan abinda ya faru da ita is quite unfortunate yasan dole ita din abar tausayi ce amma abinda yaso tayi shine ta fawwalawa Allah komai ta gode masa akan niimomin da already ya riga yayi mata bawai ta tayar da hankalin ta kamar yadda ta tayar a yanzu ba. Ba zai iya tuna ranar da yaje dubata ya tarar bata kuka ba, ko kuma ranar da suka yi waya yaji muryarta babu alamar kuka ba. Yanzu gashi doctor din da yake dubata yanzu yace jinin ta ya hau, on top of everything kuma tana kokarin ta dora wakanta hawan jini. Tunda aka yi mata aikin kunne aka samu nasara kuma aka saka mata hearing aid jin ta ya dawo yaso ace ta dauki kaddara ta dawo gidan ta ta zauna a hankali har asan yadda za'a yi da matsalar kafarta, tunda dai kafar ba wai ciwo take yi mata ba amma sai taki yarda ta tubure masa ta fara bin asibitoci desperately tana neman miracle, kuma kowanne likita in taje gunsa abinda zai gaya mata daban da wanda wani likitan ya fada. Yayi yayi taki hakura, su Baba ma sunyi taki jin maganar su, har ta fara tunanin wai dan nakasa ta same ta shine ba zasu taimaka mata ta samu lafiya ba, shi kuma tace masa dama ba sonta yake yi ba so yake ta zama nakasashshiya dan ya ajiye ta a gefe ya sake sabon aure, shi yasa yace ba zata nemi lafiya ba. Jin haka yasa ya rabu da ita, kuma duk bill din da akayi masa na magani yana bayarwa amma baya zama tare da ita yana gida yana jinyar tasa zuciyar, dan shi yanzu sam baya son barin gida, baya son abinda zai saka yayi nisa da kabarin Hussain inda kusan kullum nan ne gurin zamansa. Indai ana nemansa a gida nan ake zuwaa same shi ya tasa kabarin a gaba ya zuba tagumi yana tunani, nan ne spot dim tunaninsa tunda dama Hussain ne abokin shawarar sa to yanzu tunda babu Hussain din shine ya mayar da garden din da aka binne Hussain gurin zam yayi tunani, a cikin tunanin ne kuma ya yanke shawarar da tun sanda Hussain ya raba dukiyar sa biyu ya bashi yabi ya fara yinta. Kuma babu gudu babu ja da baya abinda zai yi kenan. Ya nemi lauyoyin H and H group of companies sun zauna meeting, ya gaya musu kudirin sa kuma kamar yadda ya riga yayi tsammani sun nuna masa rashin amincewarsu. "Ba haka ake business ba Sir" ya mike yace "am not a business man, dan haka ba business ne a gaba na ba. Hussain ne business man kuma yanzu baya duniyar, cigaba da business daga inda ya tsaya ko kuma akasin haka ba zai kare shi ko ya rage shi da komai ba. An riga an rufe littafin sa, abinda zai amfane shi kawai shine sadakatul jariya da yayi sanda yana da rai ko kuma akayi da sunan sa. Ko kuma sadakar da akayi da sunan sa bayan bashi da rai, ko kuma yayan da ya bari a duniya, to shi bai bar Da a duniya ba dan haka abinda ya rage wanda zai amfane shi a yanzu shine sadakar da akayi da sunan sa" ya jawo takardar da already ya riga yayi drafting har ya saka hannu ya mika musu yace "I am going to sell H and H group of companies and all its assets. Zan kuma rabar da dukkan kudin, nawa share din da nasa, ga mabukata da niyyar Allah ya kai ladan kabarin Hussain" Sai yaga dukkan jikinsu yayi sanyi. Yaji shima zuciyarsa ta karye, yana tunawa da duk irin fadi tashin da Hussain yayi gurin kafa Kamfanin, but keeping kamfanin ba zai amfani Hussain da komai ba a yanzu, bai kuma bar dan da zai gaji sunansa ba ya kuma cigaba da running kamfanin, shi kuma da ya ke da share mafi yawaya gadonsa bashi da wani interest a yin kudi ko kuma living lifestyle irin na Hussain, bashi da interest din zama Hussain dan yasan shi ba Hussain din bane ba, shi a yanzu ma bashi da wani interest na rayuwa kawai dai yana yin ta ne. Abinda zai amfani Hussain kawai yake nema dan da ace idan yayi sallah za'a kaiwa Hussain ladan da kullum in yayi tashi sai yayi masa shima. Dan haka ya yanke wannan shawarar..... Bayan ya koma gida ya dauko wayarsa da take ta faman ruri tun dazu amma baya cikin mood din amsa waya dan haka yaki dauka, sai da yayi packing sannan ya daga yaga sunna Ruqayyah, sai da gaban sa ya Fadi dan yasan complain din wani abu zata yi masa ko kuma kuka zata yi masa. Ya dauka, kukan kuwa yaji tana yi "tun dazu nake kiran ka mijina kaki ka dauki wayar" yace "am sorry Hassana. Ina meeting ne da lauyoyin H and H shi yasa ban dauka ba" ta danji sanyi a ranta, at least dai dukiyar ta na nan, at least dai komai nakasarta still ita matar mai kudi ne, still ita matar CEO din H and H ce dan haka zata shana kuma zata huta ko da kuwa a Nigeria din ne kadai. In ma kuma kasar take son bari ai ana iya tafiye tafiye a mota ko a jirgin ruwa, yes, zata iya yin tafiya a jirgin ruwa tunda dai mijinta yana da kudin da zai kaita duk inda take so. But before that, tana bukatar kafarta. Tace "doctor ne dama ya rubuta mana sallama" Hassan yace "to alhamdulillah. Masha Allah" ta fara kuka "haka ma zaka ce? Ba zaka kira shi ka gaya masa cewa ban warke ba? Ta yaya zai sallame ni bayan ban warke ba?" Ta kwantar da kansa yana dora hannun sa a goshinsa yace "Hassana alhamdulillah fa nace, idan bam godewa Allah ba me kike so ince masa? Ko a bakin kura nake dole ne na godewa Allah tunda har ya halicce ni kuma yasa na rayu cikin imani har lokacin da yayi niyyar daukan raina" tace "kullum haka kake cewa, sai kake acting kana making dina ina feeling guilty ina jin kamar bana godewa Allah bayan da bana gode masa da yanzu zuciya ta ta buga na fadi na mutu" yace "ni ya akayi tawa zuciyar bata buga na mutu ba? Bani da uwa bai da uba dan uwana kuma ya tafi, ina ma zamu iya exchange din guri ni da ke? A dawo min da iyayena da Hussain a karbi kafata daya da kunnuwa na, ke ni ko da idon aka ce za'a hada zan bayar dan nasan Hussain zai kula da ni kamar yadda Sumayya take kula da ke. But you never appreciate her. Ban taba jin kin gode mata ba ko kuma kinyi mata magana mai dadi ba duk da kokarin da take despite halin da ita ma tata zuciyar take na rashin masoyinta" ai kuwa kamar ya tsokano wata rigimar "ni ina mamakin ku kai da Sumayya, yanzu duk halin da nake ciki amma wai baku manta da maganar inyamurin drivern nan ba, baku san irin takaicin da kuke saka min a zuciya ta in kunyi maganar sa ba....." Sai ya cire wayar daga kunnensa ya ajiye ta a gefe ya lumshe idonsa, baya bukatar wani bacin ran in ba so yake shima nasa jinin ya hau ba, sai da ya bar wayar ta huta a gefe sannan ya dauka ya mayar kunnensa yace "hello" tace "shine kayi shiru ko?" Yace "to ai babu abinda zan ce miki ne. Gobe zan taho kanon da wuri insha Allah, ku shirya kafin inzo, ina zuwa sai mu karbi takardar mu taho gida" daga nan ya katse kiran sannan ya kashe motar ya fita, ya daga kai yana kallon gidan Hussain wanda har yanzu yake a rufe, har yanzu ya kasa samun courage din shiga ballantana ya samu damar duba personal kayayyakin Hussain. Gidan Aunty ya shiga, ya tarar tana cin abinci shima ya zauna ta zuba masa da kanta ya fara chachchakula kamar mai cin magani, tunda akayi rasuwar nan haka yake cin abincin sa dan shi kansa ba xai iya tuna ranar da yayi enjoying abinci ba. Ta zuba masa lemo tana cewa "Fulani Hadiza, kishiyar Maman Fatima tayo min waya jiya" ya tsaya da taunar abincin ya dago kai yana kallonta yace "me tace?" Tace "cewa tayi gobe idan Allah ya kaimu zasu aiko a debi kayayyakin Fatima" ya ajiye chokalin yana jin abincin ya tsaya masa a kirjinsa, a idonsa yana tunawa da ranar da aka zo akayi jeren kayan Fatima ana ta kide kide da fara'a da wasa da ɗariya, babu wanda zaiyi tunanin shekara biyu ne kadai ya rage mata daga ita har mijinta a duniya, yatuna da irin lodin kayan da aka zuba mata har sai da aka juya da wadansu duk kuwa da yawa da kuma girman dakunan ta. Can cikin makwogwaron sa yace "Allah ya kaimu goben. Akwai keys a nan ko?" Tace "eh akwai" sai ya gyada kai kawai yana ture abincin. Zuciyarsa tana yi masa zafi, tragic deaths of family din dan uwansa yana dawo masa sabo. Aunty ta lura da chanjin yana yin sa sai ta fara kokarin cheering dinsa ta hanyar bashi labarin twins dinsa da da irin rigimar da suka yi tayi mata da taje gurin Inna ganinsu suna cewa sai sun biyo ta,ta san babu abinda yake faranta masa kamar labarin ƴaƴan sa amma sai taga ko murmushi bai yi ba ballantana dariya, yi yayi ma kamar baya jin abinda take cewa har sai da yaji tayi shiru sannan ya mike yayi mata sallama ya fita. A ranar da daddare ya bude gidan Hussain ya shiga. A palon farko ya tsaya ya kunna fitila, idonsa ya sauka a kan katon hotonsu shi da Hussain, ya taka a hankali ya je gaban hoton ya tsaya ya a kallon fuskar Hussain, a kansa yana bitar maganganun da suka yi lokacin da akayi hoton da yadda Hussain ya ringa gyara zama wai shi lallai sai yayi zaman da yafi kyau. "Ka tabbatar na fishi kyau fa!" Ya gaya wa camera man din. Hassan ya saka hannu ya shafa fuskar sa, a hankali yace "ranar da ka bar duniya kafi kyau akan kowacce rana". Sai ya juya ya doshi stairs din da sauri kafafuwan sa har suna hardewa cikin junansu. Bangaren Hussain ya shiga ya kunna fitila yana kallon gurin kamar yau ya fara shiga, taste din Hussain yana da karfi sosai dan haka sai yake ganin kamar komai na gurin kama yake yi masa da Hussain. Sannan ya wuce cikin Bedroom dinsa, ya tarar da komai a gyare tas kamar jiran mai dakin ake yi yazo, sai dai yar kura da dakin yayi. A kan bedside ya ga hoton su replica na wanda yake dakinsa, ya dauka yana kallon yace "mai gasa kawai. Dan na saka a dakina shine kasa a dakin ka ko?" Sai yaji a ransa kamar Hussain yace masa "ni ba zanyi fada da kai ba" shima sai yace "nima ba zanyi fada da kai ba" sai ya ajiye hoton ya zauna akan gado, har yanzu ya kasa yanke hukuncin abinda zaiyi da gidan, shima da yayi niyyar zai siyar da shine kamar yadda zai siyar da duk sauran gidajen Hussain amma yanzu da ya shigo gidan, da yaga gidan, sai yaji kamar ba zai iya siyarwa din ba, akwai memories na mutanen gidan sosai a cikin gidan, sweet sweet memories da ba zai so ya rabu dasu ba. Da ya shigo dakin sai yaji ya rage jin loneliness, kamar Hussain din yana tare da shi. Ya ja pillow ya dora kansa yana tuna ranar da Hussain yaje kan gadonsa ya kwanta har ya tsokane shi yace pillow din Ruqayyah ya kwanta akai, shima sai ya ture pillow din kamar yadda Hussain ya ture a lokacin, a nan ne idonsa ya sauka akan diary din, diary din da Hussain kullum yake ta faman rubutu a ciki kuma ya hana kowa karanta wa. Ranar nan babu yadda baiyi ba ko page daya ya bashi ya karanta amma ya hana shi. Ya saka hannu ya dauka a ransa yana tambayar kansa if it's right ya karanta a yanzu. Shin Hussain zai so ya karanta a yanzu da bashi da rai ko kuma zai so yayi destroying ba tare da ya karanta ba? Ya jima yana lissafin abin sannan a karshe ya yanke shawarar zai fara karantawa amma in yaji abin da bai kamata ya karanta bane ba zai fasa karantawa sai ya kona shi. A zauna akan study table da yake can gefe ya kunna lamp din gurin sannan ya fara karantawa. Dear baby .... A hankali yake bin handwritten rubutun Hussain yana karantawa har ya gama page din farko ya bude na biyu, a lokacin ne ya fahimci wasiyya ce Hussain ya rubuta zuwa ga abinda Fatima zata haifa. Sai ya rufe diary din yana jin hawaye yana sauka a gaban rigarsa ba tare da yasan lokacin da suka fito daga idanun sa ba. "Yah Allah, kai ka barwa kanka dalilin da yasa wannan abin ya faru, ya Allah ka bani zuciyar dauka". Bai kuma bude diary din ba saboda baya jin zuciyarsa zata iya daukan abinda yake ciki, musamman idan ya tuna da cewa shi wanda ya rubuta din bai san cewa wanda ya rubutawa ba zai zo duniyar ba ballantana har ya girma har ya karanta. A dakin ya kwana ranar, amma sai ya kasa daukar komai kamar yadda yayi niyyar daukan very personal abubuwan Hussain. Da safe ya tashi yayi sallah a dakin sannan ya dauki diary din ya je karshen sa ya rubuta date din da Hussain ya rasu sannan ya bude safe box din Hussain, wadda su biyu kadai suka san code din ya saka a ciki ya rufe. For some unknown reason sai yaji yana so ya ajiye diary din, duk da cewa a zuciyarsa yana jin komai dadewar mutuwar Hussain ba zai iya karanta wa ba. Bayan ya koma part dinsa ya shirya sai ya dauki hanyar kano shi kadai. A kan hanya ne ya yanke hukuncin zai saa sake bincika masa kwararren likita guda daya wanda Ruqayyah zata ke gani amma kuma zai gaya mata da kakkausar murya cewa shi kadai zata ke gani babu chanji, sai su jira kuma suga abinda hali zaiyi. Yana zuwa gurin likitan dayake dubata ya fara zuwa, dama sunyi waya tun kafin ya karaso, sai likitan yayi masa bayanin cewa sunyi iyakacin kokarin su wajen ganin cewa sun fahimci inda ciwon Ruqayyah ya dosa amma basu fahimta ba, in sunbi ta nan sai kuma suga wani abu daban. "Sai dai in zaku gwada wani asibitin kuma ko kuma ku fitar da ita waje" Hassan ya gyada kai yace "haka ne, mungode sosai. Allah ya saka da alkhairi" daga nan bai kara komai ba. Yana zuwa gurin su Ruqayyah ya tarar sun shirya, sai dai wai tun da assuba Ruqayyah taki saka hearing aid dinta taki yiwa Sumayya magana duk da ita Sumayyan bat san laifin da tayi mata ba. Shima ya yi kokarin yi mata magana amma ta dauke kanta gefe taki kula shi duk da tasan magana yake yi mata. Tunda yaga haka sai ya rabu da ita suka gaisa da Sumayya wadda already har ta saka hijab dinta tana ganinsa ta dauki jaka, dama duk zaman asibitin ya ishe ta. Sai ya daukar mata daya jakar ya juya kallon Ruqayyah yace "mun tafi" yasan ta fahimci abinda yace, kamar ba zata tashi ba kuma sai ta yunkura ta tashi tana kokarin gyara karfen da aka saka mata a kafa, sai ya ajiye jakar hannunsa ya durkusa yana gyara mata sai ta ture hannun sa, a idonta yaga hawaye ya taru sai yaji babu dadi a zuciyarsa, tabbas ita din abar tausayi ce. Ya dago kai yana kallon ta cikin ido yace "am sorry" ta fahimci abinda yace daga motsin bakinsa, sai ta dauke kai ta mike tsaye ta fara tafiya tana jan kafa har ta bar dakin. Ya juyo yana kallon Sumayya wadda itama shi take kallo fuskarta da alamun tausayi, tace "kayi hakuri, haka take very edgy. Yau kuma tafi kullum zama worst" ya gyada kai yace "ke zan bawa hakuri ai, zama da Ruqayyah a irin wannan yanayin nata sai ke din. I was selfish dana tafi na barki da ita. Ya kamata ace na zauna tare da ku" tace "babu komai, ai kana kokari ma tunda ba wai baka zuwa bane ba kullum kana kan hanya, sannan kana da abubuwa da yawa a gabanka" yaji dadin fahimtar sa da tayi sai ya dauki jakar itama ta dauki tata suka fita tare, suna hango Ruqayyah har ta danyi nisa, Hassan ya kara sauri dan ya kamota, tare suka isa gurin motarsaya bude mata ya sake kokarin taimaka mata wajen shiga amma taki karbar taimakon nasa ta shiga ita kadai ta zauna tare da rufe idonta. Sumayya ta shiga baya shi kuma ya tayar da motar, sai Sumayya taga ya kamata tayi masa maganar da tunda tazo kanotake zuciyarta kawai dai bata son ta takura masa ne saboda ganin yadda abubuwa suka cunkushe masa, amma ganin dama tana so ta barta sai tace "yaya Hassan, dama tunda muka zo nake wani tunani" bai kalle ta ba yana kallon gabansa yace "wanne tunanin fa?" Tace "Adam. Nan ne garin su, ban sani ba ko kana da address din gidansu?" Ya dan kalle ta ta mirror yace "gidan su? Wai kina tunanin ya tafi gida ne? After what he went through kina tunanin zai juya ya koma gidan su kawai saboda Hussain ya mutu? Abandoning karatun sa? Abandoning you?" Ya danyi shiru sannan ya dora da "abandoning his religion?" Ta girgiza kanta "no, Adam ba zai taba yin haka intentionally ba. But what if he was forced to go? Maybe iyayensa somehow sun samu labarin inda yake kuma suka zo suka dauke shi forcefully, ina nufin what if he was Kidnapped by his own family?" Hassan yayi shiru, tabbas maganar ta abin dubawa ce, jin yayi shiru sai tayi ajjiyar zuciya tace "nasan hakan is not possible, sorry for bothering you, kawai dai hausawa sunce idan rakumin ka ya bata har cikin kuratandu kake nemansa" bai ce mata komai ba sai taga yayi setting wani address a Google map sannan sai yayi u turn kamar yadda map din ya nuna masa, da sauri tace "ina zamuje?" Yace "let's check out gidan nasu mu gani" taji wani irin dadi a ranta dan tana ji a jikinta cewa ko da ba'a samu Adam a gidan ba za'a samu wani hint na inda yake. Ruqayyah tana jin su suna maganganu sama sama amma bata fahimtar su sosai, amma kuma tana so ta san me suke magana akai sai dai kuma duk su biyun fushi take yi dasu, gani take yi kamar basu damu da samun lafiyar ta ba dan har wani murna taga suna yi cewa an sallame ta daga asibiti duk da cewa ko kama hanyar warkewa bata yi ba. Sai ta dauko handbag dinta ta dauko hearing aid dinta ta saka dan taji abinda suke cewa sosai. Sai kuma taji sun daina maganar sai dai taga chanji a yanayin Sumayya kamar tana murna da wani abu, sai kuma ta lura da cewa motar ce take guiding Hassan zuwa inda zasu je. A haka har suka je kofar wani gida suka tsaya, yayi horn sai ga mai gadi ya fito ya tsaya yana kallon motar da alamar rashin sani a fuskarsa, sai Hassan ya fita ya tafi gurin sa, Sumayya tana hango su suna maganganu amma bata jin mai suke cewa sai ta tashi ta fita itama dan zuciyarta ba zata bari ta zauna a mota tana jira ba bayan zata iya samun labarin daya shafi Adam idan ta fita. Tana zuwa taji Hassan yana yiwa mai gadin kwatancen Adam yana cewa shi suke nema, friends dinsa ne. Sai taji mai gadin yace "Joseph?" Da sauri tace "eh shi" sai ya girgiza kansa yace "about five years kenan rabo na da in ga Joseph. Tun daya musulunta ya gudu ya bar gida ban kuma ganin sa ba" Hassan yace "kuma baka da ko labarin inda yake? Ba ka ji masu gidan suna fadar wani abu daya shafe shi ba?" Yace "banji suna fada ba. Amma kusan wata hudu da suka wuce a guy came here yana gaya min wai yasan inda Joseph yake a Kaduna, nace zan shigar dashi gurin mai gida amma sai ya ce shi ba zai shiga ba, yace wata ta turo shi ya fada anonymously, kamar tana son helping parents din ne su same shi" Hassan ya kalli Sumayya wadda itama shi take kallo sai yace "ko zaka iya gaya mana address din daya gaya maka please? Maybe ko zamu same shi acan din? Neman da muke yi masa mai muhimmanci ne sosai" sai mai gadin ya tsaya yana kallon su da alamar rashin yarda, sai Hassan ya zaro kudi masu yawa ya bashi yace yayi cefane, kamar ba zai fada ba kuma sai ya fada, address din gidan su Hassan. "mutumin yace wai aikin driver yake yi a gidan" Hassan yaji kansa ya dau zafi, yana iyakacin kokarin ganin bai nuna tashin hankalin sa a fili ba yace "kuma ka gayawa parents dinsa?" Mai gadin ya gyada kai "sosai. Sun jima suna nemansa, suna sonsa sosai" Hassan yace "yanzu masu gidan suna ina?" Mai gadin yace "mai gidan watansa biyu rabonsa da nan, Madam kuma da yara three weeks ago suma suka bishi, sun tafi state din su, imo". Ikon Allah ne kawai ya dawo da Sumayya cikin mota, bata iya zama ba sai ta zauna ta fara kuka a hankali. Hassan ma da ya shigo bai yi wa kowa magana ba sai ya tayar da motar yayi reverse suka bar gurin. Sai a lokacin Ruqayyah tayi magana "ina kuka je wai? Kun fita kun barni a mita ni kadai, ne kuka yi? Ta juyo tana kallon Sumayya tace "ita kuma wannan mai aka yi mata?" Babu wanda ya amsa mata a cikin su, sai Hassan ne ya kalli Sumayya yace "ki daina kuka Sumayya, farin ciki ya kamata kiyi, ko babu komai munsan cewa yana da rai yana kuma da lafiya, kar ki manta maganar mai gadin da yace suna sonsa sosai? They will never harm him" Ruqayyah ta sake cewa "wai waye kuke maganar sa?" Hassan yace mata " Adam" tayi sauri ta kalle shi idanuwa a bude, yace "yes, gidan iyayen sa ne nan, kuma muna suspecting wata ce daga gida ta aiko gidan su ta fadi inda yake, dan haka muna tsammanin iyayensa ne suka dauke shi" Ruqayyah ta dauke kai gefe tana kallon titi, trying so hard ta boye tashin hankalin ta, ta jima tana juya maganar sannan tace "at least yanzu zaku ragewa kanku damuwa saboda, he is in the safest of places for him. Yana tare da iyayensa". Har suka je Kaduna babu wata maganar kirkin da suke yi a tsakanin su, gidan sa ya zarce dasu direct kuma suka tarar already Aunty ta aiko an yi duk gyare gyare-gyaren da ya kamata a yi a cikin gidan, har abinci an kawo musu an ajiye a dining. Suka ci abinci suka yi wanka sannan sai ga su Aunty sun shigo sun duba Ruqayyah. Daga baya kuma sai ga Inna Ade da Baba dasu Sulaiman, Baba ya barsu a gidan bai dawo daukarsu ba sai dare, a lokacin ne kuma inna Ade ta saka Ruqayyah a gaba da nasiha saboda ta fahimci ta sauki maganar ciwon nan da zafi sosai. Sumayya kuwa jin su kawai take yi tana tunanin maganganun mai gadin nan, kalmar wata mata ta tsaya mata a zuciya, wacce matar? Kuma wai a gidan take. Wacece ita? Tunani da yawa yana crossing mind dinta amma sai ta kawar dashi, no, it can't be, her sister can't be that cruel da har zata raba ta da happiness dinta saboda selfish reason dinta. It can't be. Idan haka ta kasance zuciyarta ba zata iya dauka ba, idan haka ta kasance babu ita babu Ruqayyah, har abada. But she is going to find out, zata yi bincike da kanta saboda bata son tayi zargin yaruwarta........ Sai dare Baba ya dawo ya dauke su gaba ki dayan su har Sumayya suka tafi gida. Bayan sun tafi ya rage Ruqayyah da Hassan da kuma yara su guda uku. Shi yayi wa yaran wanka yana jin missing dinsu a ransa ya fito dasu ita kuma ta fara shirya su da kayan baccin su suna tayi mata gwaranci da alama sunyi missing dinta sosai. Sai ya jawo kujera ya zauna yana kallon su yana jin dadi, ta daga kai tana kallon sa tace "mijina. Nace wai yanzu tunda ba zan iya shiga jirgi zuwa kasar waje ba, why not kayi min kokarin yadda za'a yi shi doctor din yazo nan ya duba ni?" Ya nade hannunsa a kirjinsa yana kallonta yana mamakin ta, yace "yazo nan ya duba ki? Da wadanne kayan aikin? Da wannan kudin kuma zan iya hayar likita kamar wannan yazo har Nigeria ya duba matata?" Ta tsaya da abinda take yi tana kallonsa Tace "ban gane ba? Kai fa kace min zaka yi duk iyakacin kokarin ka kaga na samu lafiya, I am just trying to hold you to your promise" yace "haka na fada kuma haka zanyi, amma abinda kike fada is not possible" tace "not possible? A gurin ka? Kar ka manta fa yanzu fiye da rabin abinda Hussain yake dashi sanda yana da rai ya zama naka" sai ya mike tsaye yana kallon ta yace "tunda kince haka let me tell you plans dina duk da ban gaya wa kowa ba yet. Nayi putting up H and H gabaki dayan ta for sell, already har ance dangote ya fara tayawa, zan siyar da komai, in nace komai ina nufin komai including gidan nan da muke ciki da motocin da Hussain ya bari duk zan siyar, za'a fitarwa da Fatima gadonta a kaiwa iyayen ta, za'a fitar dana sisters din mu a basu abinsu sannan sauran zanyi sadaka dashi, gaba dayansa, da fatan Allah ya kai ladan kabarin Hussain". Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020 *The Fourth Wave* Yana kallo rigar Yusuf da take hannunta ta zame ta fadi, yanayin fuskarta ya fara chanzawa from fair to bad then to worst. Har saida yanayin ta ya juya zuwa yadda bai taba gani ba, sai yaga gabadaya ta chanja daga Hassanar da ya sani ya kuma aura zuwa wata halitta ta daban wadda bai taba sani ba. Tabbas yasan tana son kudi, yasan ta boye masa cewa tana son kudi tun ranar da tayi subutar baki a gabansa ta gaya masa cewa shi bashi da komai dan uwansa yana da komai, amma bai taba zaton son da take yiwa kudi ya kai wanda yanayin ta zai iya wannan chanzawar a lokaci daya ba dan yace zaiyi wa dan'uwan sa sadaka da kudin da dan'uwan nasa ne ya tara da kansa ba wani ne ya tara masa ba. Yana kallonta ta mike tsaye, har tana bude Yusuf da yake kusa da ita yana jiran ta saka masa riga, amma bata kalli yaron ba kamar ma bata san ta bige shi din ba tace "what? Me naji kace?" Ya rungume hannunsa yana kara studying dinta yace "abinda kika ji shi na fada, zanyi sadakar duk abinda Hussain ya bari da kuma share din daya bani kafin rasuwar sa ga mabukata, da fatan Allah ya kai rahama kabarin sa, thats how much nake son sa" Idonta yaga ya kawo ruwa sannan hawaye ya fara zuba daga idon, ta bude baki ta mayar ta rufe, amma bai fita ba kuma bai daina kallon ta ba yana so ya karanta wani abu a idonta, yana so ya hango ko da burbushin yarinyar nan data taimaka masa ranar nan a idonta amma babu, she is totally gone. Ta hadiye abinda ya hana ta magana sannan tace "love? Love kake cewa? That's how much kake son Hussain, Hussain da baya duniya bayan mu kuma gamu a duniya, what about us? Mu baka son mu? Ni da yayanka. In kai baka bukatar dukiyar mu ai muna bukata, ni da yayanka, ta yaya zaka kula damu? Ko dan na zama nakasashshiya shine kake saka ran zan fita inyi bara in samo abin bukata? Wannan shine abinda kake nufi?" Fada take yi tana magana da duk kan karfinta, daga inda yake yana kallon yadda jikinta yake rawa, yana kallon yadda rage yake burning a cikin idonta. Bai taba dauka zata dauki zafi irin haka ba akan kudin da ba nata ba. Sai ya tako xuwa kusa da ita yace "yayana da ke da kannena da aunty duk responsibility dina ne, zan kula daku koda dako zanyi a kasuwa, kudin Hussain shi ya tara bani ba and am sending it back to him, nima zan tara nawa zan kuma kula da ku da iyakacin arzikin da aka rubuta min, na yanke wannan hukuncin tun ranar da Hussain ya raba dukiyar sa biyu ya bani saboda in kula da kaina in kuma kula da aunty da yan uwanmu saboda yana gudun kar Fatima ta haifi namiji in kasa gadarsa, yes, that's how much he loved me. And....." Ta kwace hannunta daga nasa tana masa wani irin kallo, tace "rabin dukiyarsa? Ya baka? Amma baka taba gaya min ba a matsayi na na matarka?" Yace "yes, saboda banyi niyyar amfani da ita ba tun a wancan lokacin, dan haka nayi tunanin gaya miki bashi da amfani" ta dafe kanta da hannu biyu tana fitar da numfashi sama sama, Wato tayi spending time a matsayin matar ceo without her knowing, kuma da tasan da wannan maybe da bata yi abinda tayi har yake hanata bacci ba. Ta bude idonta tana kallonsa tace "da kasan abinda kayi da bakayi ba, da zan gaya maka abinda kayi da kayi nadama babba" ya bude ido yace "me nayi? Dan ban gaya miki kanina yayi min kyauta ba shine zanyi nadama? I don't think so" sai kawai yaga tayi wani irin murmushi ta kawar da kanta gefe sannan tace "lallai rashin sani kukumi ne" ya saka hannu ya juyo da fuskar tata yace "me kike nufi, what don't I know?" sai ta rufe idonta saboda bata son ganin cikin idonsa, ko wuka zai saka mata a wuya ba zata fada masa abinda tayi dan ta samu dukiyar da yake kokarin rabarwa ga mutanen da ko sanda basu taba dagawa dan ganin samuwar dukiyar ba, bayan ita sai data....sai data...., Ko a cikin zuciyarta bata fadar abinda tayi ballantana a fili, ballantana a kunnen Hassan. Amma wannan hanyar daya dauko ba mai bullewa bace ba, she deserves that money, ba zata yi biyu babu ba, ba zata taba barinsa yayi mata wannan tozarcin ba, za kuma tayi komai dan ganin baiyi abinda ta gani a idonsa cewa ya gama daukan niyyar yi ba. In tace komai tana nufin komai. Ya saki fuskarta jin bata ce komai ba. Ya yi taku biyu baya yana kallonta yace "akwai abinda kike boye min. Me kika sani wanda ni ban sani ba? Me kika aikata?kina son kudi na sani, ba kya son in bayar da kudin nan na sani, amma ina so ki san cewa kamar nayi na gama ne, ke matata ce, responsibility dina ce kuma zanyi iya kacin kokari na na ganin cewa na kula da ke na sauke duk wasu nauye nauyen ki da yake kaina. Amma dukiyar Hussain, no" Ruqayyah tace "ni kuma zanga ta yadda zaka rabar da ita din, tsakanin ni da kai dan halak ka fasa, wallahi in dai ina numfashi ba zaka bayar da ko da kobo a cikin kudin nan ba, saboda kudin nan is as much mine as it is yours saboda ni matarka ce uwar yayan ka ce" bai ce mata komai ba sai ya juya yana kokarin barin dakin, shi duk inda tashin hankali yake yanzu baya baya yake yi dashi ba wai dan yana gudun mutuwa ba sai dan yana gudun wahala, yana gudun ya zama responsibility a gurin wadanda suke responsibilities dinsa saboda shi kansa yasan ciwo yana daf da kama shi indai rayuwa ta cigaba da tafiyar masa a haka. Ta bi bayansa da kallo tana daga kafarta da kokarin zuwa ta tari gabansa, ta manta ma da problem din kafarta, jin kafar taki responding ya tuna mata da cewa kafar ta daina aiki wannan kuma ya kara tunxura ta tace "wallahi baka isa ba Hassan, wallahi baka isa ba kayi kadan wallahi. Wallahi sai dai ka zaba ko Hussain din da baya duniya ko kuma ni da yayana da muke da rai kuma muke da hakki akan ka. Wallahi ba zan taba barin ka ka aikata abinda kake da niyyar aikatawa ba, wallahi....." Karar rufe kofarsa ya ankarar da ita cewa ya fita ya bata guri. Ta zauna tana rusa kuka kamar wadda aka aiko mata da labarin mutuwar Baba da Inna a lokaci daya. Dan yadda take ji a ranta bata jin ko daya daga cikinsu ne ya tafi zata ji wannan bakin cikin. Yaran ta da suka gaji da jiran ta saka musu riga suka fara wasan su a kasa ta kalla, duk mafarkan ta tana hango yaran a ciki, tana hango cewa sun girma cikin dukiya da wadata ba irin yadda ita ta girma cikin talauci da kunci ba. Duk dan su take yi, shi kansa Hassan din da yake ta wannan firirita dan shi take yi dan shine zai zauna akan kujerar da take fighting for ba wai ita ce zata zauna ba. Shi wanne irin mutum ne mai zuciya kamar dutse? Da wani irin rikakken ra'ayi kamar dangin firauna. Sai taji a ranta tana missing Minal, da tana nan da yanzu ta dauki waya ta kirata ta gaya mata problem dinta amma Minal bata da rai a yanzu kuma babu wanda ya sani sai ita kadai. Ta goge hawayenta tana tuno da yadda gawar Minal tayi a cikin mota da yadda kaurin konewar gawawwakin ya cika dajin, sai taji a hancin ta kamar tana shakar kaurin a yanzu. Tayi sauri ta girgiza kanta dan it has been very hard for her to keep that secret to herself sannan kuma Hassan yace duk wannan a banza? Gaskiya ba zata yiwu ba. So yake tayi biyu babu? Bayan ta tafka kuskuren da ita kamta tasan zai taba lahirar ta dan ta sami duniya shine zai ce duniyar ma ba zata samu ba? Wato babu duniya babu lahira kenan! Hassan yana fita daga dakin ya dafe kujera saboda yadda yake jin bugawar zuciyarsa yana kara gudu sosai kamar zata fito daga kirjinsa, yana jin kalaman da Ruqayyah ta bi bayansa dasu amma kuma baya son ya koma su cigaba da rigima akan dukiyar Hussain. Dukiyar da babu abinda zata kara musu gabaki dayan su. Shin wannan ita ce matar da ya zabawa kansa? Ita ce kuma uwar daya zabawa yayan sa? Duk su biyun babu wanda ya rintsa da niyyar bacci, haka ma Sumayya, a ranar itama bata samu tayi bacci ba tana ta bitar abubuwan da suka faru a ranar musamman maganganun mai gadin gidan su Adam, abubuwan daya fada sun nuna cewa akwai chance mai karfi na cewa Adam yana hannun iyayensa, wata kila sun jima suna bibiyarsa suna gudun kar ya fahimta ya sake gudu kamar yadda ya gudo daga Kano, suna binsa a baya da niyyar kidnapping dinsa idan sun ganshi shi kadai a haka har Allah yasa suka samu nasara ranar da Hussain ya mutu suka kama shi a hanyar Abuja, mai gadin yace matar da ta aiko musu da sakon inda Adam yake a gidan da Adam din yake aiki take, kuma duk gidan ita tana ganin babu wanda ya damu da wanzuwar Adam a gidan kamar Ruqayyah tunda har furta hakan tayi da kanta. Sai dai kuma ita kanta Sumayya tana fatan kar hakan ta kasance domin kuwa abinda zai biyo baya ba zasu taba jin dadin sa ba daga ita har Ruqayyah. Tana so tayi bincike dan ta san gaskiyar abinda ya faru amma tana ganin abune mai wahala ta samu amsar ta ta hanyar bincike dan bata san ta inda zata fara ba sai kawai ta samu kanta da addu'ar idan Ruqayyah ke da hannu Allah yasa tayi Confessing da bakinta dan wannan shine kadai solution, kuma kamar kullum tayi wa adam addu'ar samun guidance daga Allah. Washegari Hassan bai bari ma sun hadu da Ruqayyah ba ya fita daga gidan da wuri saboda yau ne zasu yi pricing duk komai da komai na Hussain including motocin sa, da kuma gidan sa, sai dai kuma a ransa yaji yana son ya cire gidan nasa ya fasa siyar dashi. So yake sai ya gama pricing komai sannan zai gaya wa Aunty kafin ya siyar duk da yasan abin bazaiyi mata dadi ba amma yana saka ran in taji dalilinsa zata yi masa kyakykyawar fahimta kuma zata kara masa kwarin guiwa. Shi dai kam yayi damara baya jin akwai abinda zai saka ya fasa kudurin sa. Ruqayyah tana hango fitarsa itama ta jawo kafarta ta fito palo tana amsa gaisuwar da masu aikinta suke jera mata, sai kuma ta kira daya daga ciki ta aika ta gurin aunty tace taje tace in ji ta ta bata key din gidan Hussain, tun jiya ta yanke hukuncin abinda zata yi. Ta gurgunce ta kuma kurumce sabida babu yadda zata yi tunda wadannan Allah ne ya aiko mata dasu, kaddara ce, amma ba zata talauce ba kawai dan wani son zuciya irin na Hassan. Aunty tayi mamakin aiken dan tasan Hassan yana da spare key din gidan Hussain a hannunsa kuma Ruqayyah tana son budewa a gurimsa zata karba ba a gurinta ba. Taso ta aika a tambayi Ruqayyah abinda zata yi da key din amma sai ta fasa saboda ita macece mai jan girmanta sosai bata son shiga abinda zai zubar mata da kima a idon na kasa da ita, ta kuma san yaran zamani da rashin kunya. Sai kawai ta dauko key din ta bawa yar aikin. Ana kaiwa Ruqayyah, tea kawai ta sha ta tattara yaran ta bawa nanny dinsu sannan ta debi sauran sai gidan Hussain, ita da kanta ta bude gidan ta shiga, ta tsaya tana kallon palon tare da sauke ajjiyar zuciya a ranta tana jin ta shiga kenan wallahi, ba Hassan ba ko Hussain ya dawo daga lahira bata jin zata fita ta bar masa gidan. Nan take ta saka yaranta suka fara aikin gwaran gida, ta gaya musu cewa sun dawo nan da zama kachokan, suka yi ta murna abinsu, sai kuma ta aika gidan Aunty tana kiran yan aikin Fatima da da suke gidan bayan mutuwar Hussain kuma suka koma gurin Aunty suke zaune a can tace su zo suma ayi aikin dasu tunda sune suka san duk wani lungu da sako na gidan. A haka ta ja kafarta da kyar ta hau har saman, sai dai ta tarar wing din Hussain a rufe yake na Fatima ne a bude tunda jiya anzo an debi kayanta, amma kuma sai taga kamar ba'a diba ba dan furnitures din duk suna nan sai few abubuwa aka dauka. Ta kira wata a yaran gidan ta tambayeta "ba'a kwashe kayan Fatima ba dama?" Tace "sunzo sun diba, amma sunce sunbar furnitures din duk wanda zai zauna a gidan yayi amfani dashi" Ruqayyah ta gyada kai, lallai ma mutanen nan wato su kudi ba komai bane ba a gurinsu, ita dai gaba ta kai ta gobarar titi a Jos, dan haka kawai ta bude dakin Fatima aka fara gyara, sai da suka gyara komai tsaf can wajan azahar sannan ta koma part dinta ta fara hado kayata tana bawa yaranta suna shigar mata dashi gidan Hussain, sai a lokacin ta dauki wayata kira Sumayya. "Hello Sumayya? Nace ko zaki taho ki taya ni aiki? Yau muna tare wa a sabon gidan mu" Sumayya tace "sabon gida? Wanne irin sabon gida kuma? Yaushe kuka yi sabon gida" Ruqayyah tace "bayi mukayi ba, gidan Hussain ne can zamu koma" sai Sumayya taji wani iri, anya kuwa bai yi wuri ba su koma gidan Hussain su zauna? Tasan ya zama gidan su amma dai ai ta dauka zasu bari mutuwar ta lafa sosai tukunna kafin su tare. Sai tace "Allah ya sanya alkhairi, amma ba zan samu damar zuwa ba saboda nima ina gyara dakina yau tunda na kwana biyu bananan". Sai Ruqayyah ta tabe baki kawai tace "shikenan, kwazo daga baya kuga sabon dakina" amma a ranta taji babu dadi, tana son duk sanda ta bukaci Sumayya tazo gurinta dan a lokacin ne take jinta fully satisfied. Hassan bai dauko hanyar gida ba sai da biyar na yamma ta wuce, saboda yasan masifar Ruqayyah zai je ya tarar a gidan. Sun gama komai yau da lawyers dinsa da kuma sell agents, anyi pricing komai kuma dama tun jiya daya sanar da muradin sa na siyar da kamfanonin already har labarin ya iske manyan yan kasuwar kasarnan kuma sun fara nuna interest din su akai. Shi dama ya fi son ya siyar wa da yan kasuwa yadda zasu cigaba da running business din ta yadda babu wanda zai rasa aikin sa a cikin ma'aikatan kamfanonin, in suna bukatar service dinsa shima zai cigaba da yi musu aiki yana karbar albashin sa kamar yadda ya saba, idan ma kuma basa bukatar sa zai nemi wani aikin kuma yasan insha Allah ba zai sha wahala ba kafin ya samu in akayi la'akari da experience dinsa da kuma links din da yake dashi a cikin masu hannu da shuni na kasar nan. Sannan kuma a account dinsa yana da kudin da yake tunanin zasu rike shi daga yanzu zuwa lokacin da zai samu aikin. Gurin Aunty ya fara shiga kamar yadda ya saba, ya gaishe ta sai yaga fuskarta da damuwa, bata bashi abinci ba kamar kullum saboda ta san matarsa ta dawo, sai shi ya kira Zulaihat yace ta kawo masa, ya fara ci sai Aunty tace "Hassan ya akayi baka gaya min yau zaku tare a gidan Hussain ba? Ai da sai in tura wadannan yaran su taya ku shirya kayan ku ko? Ko ba haka ba ma fadar ai tana da dadi akan ace sai dai inji a gurin yan aiki" ya ji abincin bakinsa yana kokarin shake shi, da kyar ya hadiye shi ido a waje yace "tarewa kuma? Gidan Hussain kuma?" A take Aunty tabbatar da abinda take zargi, Hassan bai san abinda Ruqayyah tayi ba kuma dama tayi tunanin haka dan babu yadda za'a yi Hassan ya aikata haka ba tare da ta sani ba dan shi Hassan baya taba yin komai sai ya tuntube ta first. Chokalin hannunsa ya ajiye sannan ba tare da yace komai ba ya mike da sauri ya fita daga gidan. Sai kuma Aunty taji babu dadi a ranta ta ji kamar ta hada shi da Ruqayyah ne. Yana shiga gidan ya hango kofar part din Hussain a bude ga mutane suna ta kai komo, da sauri ya shiga ciki ransa a matukar bace, yaran da ya tarar a palon kasa suka fara matsawa suna bashi guri saboda ganin yana yin sa, yace "ina take?" Suka nuna masa sama da sauri, ya hau da sauri yana hada stairs guda bibbiyu a lokaci daya sannan ya doshi wing din Fatimah dan yasan na Hussain a rufe yake. Bai taba shiga ba saboda duk haduwar da suke yi da Fatima a part din Hussain ne ko kuma a palon kasa sai ranar daya ganta a gym, yayi sauri ya kawar da tunanin daga ransa dan bama ya son tuno abinda ya faru a ranar. A can kuryar Bedroom din Fatimah ya tarar da Ruqayyah tana zaune akan gadon da ba nata ba hannunta rike da wata yar karamar box din da ba tata ba tana jera wasu kaya a ciki, gefenta Hussain karami ne yana kwance so innocently yana tsotsar hannunsa. Yana kokarin saita numfashin sa yace mata "me kike tunanin kina yi?" Ta juyo tana kallon sa sannan ta mike tsaye tace "sannu da zuwa mijina" yace "me kike tunanin kina yi? Wa ya baki izinin shigowa nan har da kwaso kaya? Ki zo ki fita daga gidan nan" tace "na shigo ne saboda gidan mijina ne, kuma fita ta ba yanzu ba, am here to stay. Idan kai baka so mu muna so ni da yayanka, zaka iya cigaba da zama a can gidan duk sanda kake bukatar ganin mu sai kazo ka ganmu anan. Amma mu anan zamu zauna" yace "ni nine mai gidan, kuma ni nace ki fita, ba'a nan nayi niyyar ki zauna ba kuma ba'a nan zaki zauna ba, ki fita ko kuma in saka a fitar dake. Na gama magana" ya fada dead serious, ya juya zai fita daga dakin sai tace "ni kuma ban gama magana ba, in fact, ban ma fara magana ba tukuna, in har kana ganin zaka iya sakawa a zo a fitar da matarka da yayanka daga cikin gidan ka bismillah. Amma ni ba zan fita ba kuma ba zan barka ka bayar da ko kwandala daga cikin kudin nan ba" ya juyo yana kallonta yace "and how are you going to stop me? Taya zaki hana ni yin abinda na yi niyya?" Itama ta juyo tana kallon sa tace "da ace kasan abinda nayi kafin in samu kudin nan da baka tambaye ni yadda zanyi in hana ka rabar da su ba" ya kara matsowa cikin mamaki yace "kika samu? Yaushe kika samu? Me kuma kika yi? What have you done?" Ta danyi murmushi tace "komai, from the beginning to the end" sai ya dakata a tafiyar da yake yi, a lokaci daya yana realising truth, tun farko ba shi ta aura ba dukiyar da tayi tunanin tasa ce ta aura, daga baya kuma da ta san ba tasa bace ba ta zauna dashi ne saboda tana tunanin zai samu, tana burin ya samu. Zuciyarsa tayi sinking a cikin kirjinsa, ji yayi kamar ta koma cikinsa ta bar kirjinsa. Cikin muryar da yaji kamar ba tashi bace ba Yace "me yasa kika taimaka min ranar nan? Me yasa kika yi saving rayuwata?" Sai ta sake wani murmushin, she hates breaking his heart amma yau ranar gaskiya ce, dole ta fada masa dan ya san dalilin da yasa zata aikata abinda ta riga tayi niyyar yi. Tace "Baba yaje neman aiki gurinka, sanda aka sace ka sai ya bamu labari, shi ya dauka kaine mai kamfanin dan haka ce mana yayi kai ne mai H and H. Muna ta following labarin batanka saboda Baba ya damu da kai sosai, and then sai gaka a toilet din mu, daga yanayin ka da kayan jikinka nayi tunanin kai ne shi yasa na saka rayuwata a hadari na taimaka maka dan inaso ka rike taimakon da nayi maka a ranka kar ka manta, dan ina so ka biya ni. Na dauka wasu kudi zaka bani wanda zai fitardani daga talauci sai kai kuma ka yi Maganar aure na and I thought auren mais even better dan maybe abinda zaka bani din zai iya karewa amma in na aureka komai naka ya zama nawa. That's why I married you" Ya dafe kirjinsa yana jingina da jikin bango dan ji yake yi kafafuwan sa kamar ba zasu iya daukarsa ba. Yana girgiza kansa yace "kina nufin ba kya sona Hassana? Kudina Kika aura bani ba Hassana?" Ta bata rai tace "I can't say gaskiya, ban sani ba ko zaman da muka yi da kai na fara sonka amma ban sani ba but abinda na sani shine bana son wannan sunan da kake gaya min, I hate it, kullum kuma ka gaya min raina baci yake yi" ya bude baki zaiyi magana amma sai ya kasa, his heart breaking into pieces, bleeding, kunnuwan sa har kara suke yi masa dan suna so su daina jin maganganun Ruqayyah amma sai ta cigaba da cewa "nasan heart dinka zata yi breaking kaima kamar yadda tawa tayi breaking lokacin da aka kawo ni gidan nan na fahimci cewa ba kai ne mai kudin ba, na fahimci cewa you are just your brother's puppet. But I thought zan iya juya ra'ayin ka tunda naga kana sona, I thought zan iya hada ka da brother din naka yadda zaka kwasar mana wani abu daga cikin dukiyar sa da muma mu kafa kanmu amma kaki bani hadin kai, saying wai kafi son sa akan kowa". Hassan ya tuna da maganganun da Ruqayyah tayi ta gaya masa akan Hussain, akan Fatima, wato duk karya ce kenan, duk da ta hada su ne, wato duk dan taci dukiyar Hussain ne. Ya tuno maganar Baba, ya tuno maganar Hussain kamar yanzu yake gaya masa "me yasa bata je ta kira iyayenta sun taimaka maka ba sai ta zabi ta kama katanga ta haura?" Sai yau Hassan ya samu amsar sa.. yace "bayan wannan kuma sai me kika yi?" Tayi shiru tana kallonsa, yace "kina da hannu a gurin batan Adam?" Ta juya hannu "what does it matter? Sai me? Ni ba zan bari yaruwata ta auri wannan inyamurin drivern ba" yace "ke kika aikawa iyayensa suka zo suka tafi dashi" ta juya idonta, me za'a yi mata in an sani? Karkarinta Sumayya tayi fushi na wani lokaci da zarar kudi sun zauna kamar yadda take saka rai shikenan komai zai dawo normal tsakanin su tace "eh ni na aika musu, me za'a yi min?" Yace "you are not human being Ruqayyah ke shaidaniya ce. A devil in human form". Sai kuma wani tunani yazo masa, tunanin da ya sa ya mike straight yana mantawa da ciwon da yake ji a zuciyarsa ya karasa gabanta tare da rike hannunta yace "what else did you do saboda kudin Hussain? Me kika yi? Did you cause the accident? Did you kill Fatima and her baby saboda kici gadon su?" Tayi kokarin kwace hannunta amma karfin rikon da yayi mata yasa ta kasa kwacewa, cikin wata irin budaddiyar murya yace "answer me!" Saboda karfin muryar da yayi mata magana da ita sai da taji dakin ya motsa, ta kalle shi taga yana yi mata wani irin kallo mai nuni da cewa zai iya yi mata komai, ta kalli cikin idonsa tace "wallahi, tallahi, billahillazi la ilaha illa huwa ban kashe Fatima ba ballantana abinda yake cikinta, kuma bani nayi sanadiyyar accident din mu ba" a idonta yaga cewa gaskiya take fada masa sai ya saketa, ta matsa baya tana murza hannunta inda ya rike din, ya juya hannunsa dafe da kirjinsa zai bar dakin sai tace "ina sake tuna maka, kar ka bayar dako kwandala a kudin nan" ya juyo yana kallonta da juyayyun idanuwa yace "are you threatening me?" Direct Tace "yes" ya juyo a kufule yace "me zaki yi? Idan na rabarda dukiyar mezaki iya yi akai? And after duk abinda kika gaya min kina tunanin zanyi abinda kike so?" Tace "ba zaka yi ba amma ni zan saka ka kayi. Ba dai Hussain ba? Ba dai dan kana son Hussain ne kace zaka rabar da dukiyar sa ba? To albishirinka, in dai kayi haka ni kuma sai na tabbatar nayi destroying duk wani kykykyawan fenti da Hussain ya shafa wa kansa sanda yana da rai, I will make sure mutanen da suke sonsa suke kuma yi masa addu'a sun dawo suna kinsa suna kuma tsine masa" yaji tamkar ta saka mashi ta chaki zuciyarsa, yace "and ta yaya zaki yi hakan?" Sai ta koma bakin gado ta dauki Hussain da yake kwance tace "zan je gidajen rediyo in fadi cewa wannan yaron dansa ne ba naka bane ba, in ce raping dina yayi har na haife shi. Nasan wasu ba zasu yarda ba amma da yawa zasu yarda saboda mutane sunfi yarda da labarin karya aka na gaskiya. Zan ce kudinsa na cult ne, ta yaya Mutun mai kananan shekaru kamar sa zai tara kudade irin wadannan? Zan fada cewa baban ku ya fara bayarwa, shine silar yin kudinsa, zan kuma ce sanadiyyar mutuwar sa shine matarsa aka ce ya bayar tare da abinda yake cikinta, shi kuma yaki bayarwa shine suka sanye jininsa a gabanka tare da drivern ku shi yasa drivern ya bata har yau ba'a ganshi ba, sannan kuma suka yi causing accident dinda matar da mutu da tsohon ciki dan su dauki fansar kin bin maganar su da yayi. Am sure wasu ba zasu yarda ba amma wasu zasu yarda. Kuma am sure su kansu wadanda basu yarda ba dinzan saka musu doubt a kan sa. Zan kuma ce wannan dalilin ne yasa ka rabar da dukiyarsa saboda kace ba zaka iya cin dukiyar haram ba........." Wata shakada yayi mata tare da bugata da bango ce tasa sauran maganar ta tsaya a makogwaronta, idanuwan ta a waje, ta saka hannunta duk biyun tana kokarin raba hannunsa da wuyanta amma ta kasa, a take ta fara jin kamshin mutuwa, ta fara fitar da rai da rayuwa, lallai tayi playing too bad dan wannan rikon da yayi mata bata jin zai sake ta har sai numfashin ta ya bar jikinta. Ya fara magana da karfi kamar zai tsaga dakin "why??! Why?! A kan kudi? Akan kudin da baki san ta yadda yayi ya tara su ba? Akan sa zaki yi ikirarin yi masa wannan mugun sharrin? Saboda duniya? Saboda kina so ki samu duniya, Allah wadaran ki Ruqayyah. Allah wadaran haduwata dake Ruqayyah. Kaico na, ina ma dai na mutu a ranar dana hadu dake da ban kawo wa family na jaraba ba. Allah wadaran aure na dake Hassana" Kafafunsa yaji an kama ana jan wandonsa, ya sunkuyar da idonsa da yake cike da hawaye zuwa kasa yana kallon yan biyun sa da suka rike kafafuwan sa suna kuka, bai ji shigowar su ba bai kuma ji kukan su ba kawai taba shin da suka yi ne ya dawo da hankalin sa kansu. "daddy don hut mommy" yusuf ya fada yana matso hawaye, Aminu yaje ya kama rigar Ruqayyah data kusan suma saboda azaba yace "mommy mommy". Hassan ya cikata da sauri yana ja da baya yana girgiza kai, ta durkushe a gurin tana jan numfashi da kyar hawayen azaba yana zubowa daga idonta. Yaran suka tafi da gudu suka fada jikinta suna kuka ita kuma ta rungume su tana kallon Hassan. A hankali yace "Baba da Inna sunyi asarar haihuwa" Sai ya juya ba tare da ya sake cewa komai ba yabar gidan, ya shiga mota ya dauki hanyar gidan su Ruqayyah a hanya yana iya kacin kokarin sa dan ganin bai concentrating akan maganganun ta ba har yaje kofa gidan yayi packing, yana fitowa Baba yana tsayawa a cikin Napep dinsa, amma ganin yanayin Hassan kadai ya saka hankalin sa ya tashi ya kira Sulaiman da sauri suka kama Hassan din da kyar yake iya taka kafarsa suka shigar dashi cikin gida suka ajiye shi a palo suna ta tambayar shi "lafiya Hassan? Wani abu ne ya faru? Wani ne ya kuma mutuwa? Ko Ruqayyah ce?" Hassan ya dago kai yana kallon Baba yace "Ruqayyah ce Baba, amma ba mutuwa tayi ba, mashi ta dauko ta soke zuciyata da shi" Baba ya dafe kansa, tabbas ranar da yake gudu kuma har ya fara tunanin ba zata zo ba tabbas tazo yau. Ruqayyah tayi aika aika, kuma daga yanayin Hassan yasan abinda tayi yafi abinda yake tunanin zata yi din. Ya wuce duk lissafin sa. Ya dago kai yana kallon Hassan, yana kara ganin rashin dacewar Hassan da Ruqayyah sai yace "Hassan zan roke ka wata alfarma duk kuwa da bansan abinda Ruqayyah tayi maka ba" Hassan ya fara girgiza kai tun kafin yaji alfarmar dan ba zai iya yafewa Ruqayyah na, amma sai yaji baba yace "Sulaiman dauko min takarda da biro" Sulaiman yaje ya kawo sai Baba ya mika wa Hassan yace "dan Allah Hassan, dan Annabi, ina rokon ka ka saki Ruqayyah" Hassan ya kalli Baba sai yaga cewa har cikin zuciyarsa hakan yake nufi, ya dauki biron ya dora akan takardar, lallai yasan Baba ya gaya masa haka ne dan ya cire masa nauyin sa kar yaga mutumcin su ya kasa sakin Ruqayyah shi yasa ya zamanto shine ma ya roke shi, sai yayi rubutu kamar haka... *The Fifth Wave* "Ni Hassan Aminu Abdullahi na saki matata Ruqayyah Yusuf saki uku" Ya ajiye biron, amma sai ya kasa mikawa Baba takardar duk da yasan baban ba iya karatu yayi ba balle ya karanta abinda ya rubuta, sai dai a ransa da ace ana iya yin saki goma da kuwa tabbas shi zaiyi wa Ruqayyah. Dan babu abinda yake nadama a yanzu irin aurenta, babu abinda yake dana sanin yi irin hada zuri'a da ita, babu kuma abinda yake tausayi irin yayan da suke a tsakanin su. Tunda ya fito daga gidan Hussain yake tambayar kansa dalilin da yasa haka ta faru dashi, ina carefulness dinsa ya tafi lokacin da ya zabi Ruqayyah a matsayin matar aure, ina smartness dinsa da dabarar sa da hangen nesan sa suka tafi, me yasa yayi failing akan abinda yafi komai muhimmanci a rayuwarsa? Ya ninke takardar a hankali ya ajiye a tsakiyar su shida Baba, ya kasa mikawa baban, sai Baba ya saka hannu ya dauka ya warware yana kallonta duk da cewa ba gane rubutun yake yi ba, dai kuma ya mikawa Sulaiman yace "karanta muji" sai Sulaiman ya karanta a fili, Hassan ya sunkuyar da kansa yana jin nauyin Baba amma ko kadan baya jin wani abu mai kama da regret na saki ukun da ya yiwa Ruqayyah. Inna Ade ta fara kuka, Baba ya dago kai yace "ina rokon ka ka gaya min abinda tayi maka, saboda ina son insan muma iyayenta abinda ya kamata muyi mata" Hassan yana girgiza kansa yace "zuciyar ku ba zata iya dauka ba Baba, nima tawa zuciyar yanzu kuka take yi, Ruqayyah ta riga tayi mata mikin da ba zai taba goguwa ba" Baba yace "tunda har kana numfashi hakan yana nufin zuciyarka ta dauka, kai da ba dolen ta ba ballantana mu da muka haife ta, mu da ba zamu taba iya chanjata ba, ka gaya mana dan Allah dan musam ta yadda zamu taimaka mata". Sai Hassan ya basu labari, labarin duk abinda Ruqayyah ta gaya msa da bakinta cewa tayi he told them everything har labarin abinda tayi wa Adam da kuma zargin da yake na cewa abinda tayi shine sanadiyyar batan Adam din. But duk wannan ba shine dalilin da ya saka ya sake ta ba, dalilin da ya saka ya sake ta shine abinda tace zata yi, sharrin da tayi ikirarin zata yi wa brother dinsa duk kuwa da cewa yana cikin kabarinsa a kwance, zata bata masa suna ta kuma bata nasabar dan ta data haifa da kanta duk dan saboda kudi. Yana tsoron cewa babu abinda ba zata iya yi ba saboda kudi. Inna ta kasa juye labarin sai ta tashi ta shiga daki tana kuka, Sumayya da take tsaye a kofar dakinta tun shigowar su tana jin abinda suke cewa ta juya ta koma daki ta turo kofa, sai ta zauna akan gado blindly tana kallon bango sannan sai ta dauko wayarta ta nemo number din Ruqayyah ta saka ta a blacklist sannan ta goge ta daga cikin wayar ta, sai kuma ta ajiye wayar ta kwanta tana tunanin hanyarda zata bi ta tafi imo... A palo Baba da Sulaiman suna zaune har Hassan ya gama basu labarin duk abinda Ruqayyah tayi. Da kyar yake magana amma bai yi shiru ba sai da ya kai aya sannan yace "kayi hakuri Baba, zaman da nayi ma da Ruqayyah a baya da ace zan iya dawo da hannun agogo baya da banyi shi ba har na hada zuri'a da ita ba, da ace zan mayar da rayuwata baya da nabi zabi irin na Hussain, na zabi mace kamar Fatima ba kamar Hassana ba, na zabi wayayyiya mai zurfin ilimin boko yar gidan masu kudi mai budadden ido irin Fatima ba irin Ruqayyah ba, wata kila da nayi haka da yanzu ban samu kaina a halin da nake ciki yanzu ba" Baba ya girgiza kansa yace "tabbas kayi kuskure a gurin zaben matar aure, amma ba wannan ne kuskuren ka ba. Arzikin mutum, zurfin ilimin bokon sa, yanayin al'ummar daya taso a cikin ta, shekarunsa ko kuma wayewar sa basu suke nuna halayyar sa ba. Ita halayyar mutum da ita ake haifar sa, su duk wadannan abubuwan dana lissafa suna taimakawa ne gurin kara wa ko rage karfin halayyar mutum. Ana samun nagari a cikin kowanne kaso na al'umma kamar yadda ake samun bata gari a cikin kowanne kaso da al'umma. Ana samun shaidanin mutum a cikin malamai kamar yadda ake iya samun salihin mutum a cikin shaidanu. Dan mun kasance malamai hakan baya nufin cewa yayan da zamu haifa lallai zasu kasance na gari ba, mu dai iyakacin mu mu bada ilimi mu bada tarbiyya amma ita shiriya ta Allah ce, Allah ne kadai zai iya shiryar da bawansa a lokacin da yaso. Kamar kuma yadda na gaya maka cewa yana yin guri da yanayin al'ummar da mutum ya samu kansa a ciki yana karawa ko rage halayyar mutum, wannan shine abinda ya faru da Hassana. Tun farko Hassana halinta ba mai kyau bane ba, ni da mahaifiyar ta mun sani kuma kamar yadda mahaifiyar ta take yawan fada ita Hassana kamar harabawa ce ubangiji yayi mana dn yaga yadda zamu yi da ita, kuma munyi iyakacin kokarin mu, a inda muka yi kuskure shine da muka biye mata muka hada auren ku kai da ita, komawar ta cikin ku da shiga irin rayuwar ku da bude idon da t kara yi da duniya shi ya kara lalata mata halayyar ta, shi yasa har ta zama abinda ta zama. Wata kila da mun barta a gabanmu, ko kuma mun samu wani mijin wanda ba irin ka ba, mai rufin asiri dai dai gwargwado mun aura masa ita da ba zata ga dukiya irin taku ba har ta saka a ranta sai ta mallake ta. Wannan shine abinda naso in nunawa mahaifiyar ta a lokacin da kake neman aurenta, amm ita kuma sai tayi tunanin idan bamu bawa Ruqayyah abinda take so ba shine zata kara lalacewa. Wannan shine kuskuren mu, wannan shine inda muka fadi jarabawar mu. Amma hakan ba wai yana nufin shikenan mun hakura ba, zamu cigaba da kokarin ganin mun gyara kuskuren mu, abinda zamuyi kuma a yanzu shine zamu barta da duniya, zamu barta ota da kanta ta gane cewa abinda take yi ba dai dai bane ba muyi fatan kuma komai ba jima komai ba daɗe zata yi nadama za kuma ta nemi yafiyar wadanda ta zalunta. Ta haka ne kadai zata samu rahamar ubangiji. Ni ba zance kayi wa Hassana komai ko ince kar kayi mata komai ba, in ka ga dama zaka iya hada ta yan sanda kace ga ikirarin da tayi na cewa zata yiwa dan uwanka kazafi akan dukiyar sa, in kafa dama zaka iya duba ya'yan da suke tsakanin ku ka barta da duniya kamar yadda muma zamu barta din. Duk zabin ka ne." "Ina so ka sani, a yanzu ima tsananin jin kunyarka saboda abinda yata ta cikina tayi maka duk kuwa da irin kyautatawar ka a garemu. Sannan kuma ina so in tabbatar maka da cewa Ruqayyah ta aikata abinda ta aikata ne kawai saboda halin ta ne haka. Bawai saboda ta fito daga gidan talakawa ba. Ina rokon ka idan ka amince ina son ka auri SUMAYYA a madadin Ruqayyah. A lokacin ne zaka gane abinda na fada maka ranar nan, a lokacin ne kuma zaka gane abinda nake gaya maka yau" Hassan ya bude ido yana kallon Baba da mamaki yace "Sumayya kuma Baba? Sumayya ai ƴar uwar Ruqayyah ce ciki daya ta yaya zan iya aurenta bayan ita Ruqayyan tana da rai?" Baba yayi murmushi yace "ni dai iya kacin sani na babu wata aya ko wani hadisi daya haramta aure a tsakanin ku a irin wannan yanayin. Abinda aka haramta shine hada yan uwa a aure su a lokaci daya, sai dai alkunya tana sakawa sau da yawa a ki yin irin wannan auren dan shi musulunci addinin zaman lafiya ne, amma mu a yanzu babu wata alkunya wadda zamuyi wa Hassana. Na baka auren husaina" Hassan ya cigaba da girgiza kansa, abubuwan sunyi masa yawa, zuciyarsa ba zata iya dauka ba, kansa ya toshe a yanzu ba zai iya yin tunanin komai ba. Sai Baba yace "na sani, na san yanzu ba zaka iya bani amsa ba kuma nima bana son ka bani amsar a yanzun, kaje kayi tunani, ka nemi zabin Allah kayi addu'a, na baka daga nan har zuwa shekarar da Sumayya zata gama karatun ta na jami'a, idan har zuwa lokacin ba kaji zaka iya auren ta ba shikenan, idan kuma kaji zaka iya to alkawarin da nayi maka yana nan na baka ita ko bayan raina". Still Hassan bai ce komai ba. Sai Baba ya aika Sulaiman ya kira Inna, ta zauna a kusa dashi idanuwan ta da alamar kuka sai yace "ki zama shaida, ko bayan raina in Hassan yazo neman auren husaina na bashi ita." Ta gyada kai tace "Allah yasa haka shi yafi musu alkhairi" sai kuma ya mika mata takardar sakin Ruqayyah yace "ga wannan ku tafi tare da Sulaiman gurin Hassana ki kai mata, sannan ki gaya mata in ji ni ni ubanta Malam Yusuf mai gadi nace ta baro gidan nan a yanzu ta taho gidana, kuma ban amince ta dauko koda tsinke na daga abinda yake gidan ba tunda sanda ta shiga bata shiga da ko tsinke ba. Wannan shine umarni na, idan kuma taki bi ki gaya mata nace babu ni babu ita har abada, ke ma babu ke babu ita har abada, babu ita babu duk kan abinda muka haifa a duniya, har sai ranar da tayi abinda nace sannan kuma ta nemi dukkan wanda ta batawa ta nemi gafarar su suka yafe mata to a lokacin nima zan yafe mata" Inna ta fara kuka tana son ta rokar wa Ruqayyah gafara a gurin mahaifinta amma sai ya daga mata hannu yace "wannan umarni ne na baki a matsayi na na mijinki, sai ki zaba ko ki bi umarni na kiyi abinda nace ko kuma ki biye wason da kike yiwa yarki ki bita gidan da take son kwata daga hannun masu shi ku zauna tare" wannan yasa inna ta mike dan tasan aljannar ta tana tattare da bin umarnin mijinta kuma tasan wannan wata sabuwar hanya ce daya biyo da ita dan ganin Ruqayyah ta dawo kan hanyar dai dai. Amma a ranta tana tunanin abinda Ruqayyah zata zaba, tsakanin su iyayenta da yanuwanta da kuma dukiya. Kafin Inna ta kai bakin kofa Sumayya ta fito daga dakinta ta riga ta fita, duk tana jin maganganun da Baba yayi har maganar bada ita ga Hassan da yayi taji amma ba wannan ne a gaban ta ba yanzu, abinda yake gabanta shine tana so taga Ruqayyah, tana so ta gaya mata abinda yake zuciyarta face to face. A cikin Napep din Baba suka tafi, babu wanda yayi wa wani Magana a cikin su har suka je gidan, direct part din Hussain suka dosa dan sun san tana can kamar yadda Hassan ya fada. Ai kuwa a can din suka same ta rashe rashe a palon Fatima tana ta wasada yaranta kamar bata aikata komai ba. Sai dai ganin su da yanayin fuskokin su ya saka taji zuciyarta ta tsinke, wato Hassan karar ta ya kai gida ko? Zai zo ya same ta ne. Tayi kokarin mikewa, "Inna sannu da zuwa. Ban san zaku zo ba ai. Ga guri zauna" Inna tace "a ina zan zauna Ruqayyah? Akan kujerar da ba taki ba? A cikin dakin da ba naki ba a kuma gidan da ba naki ba? Me kika mayar da rayuwar ki ne Ruqayyah? Yaushe lalacewar ki har ta zama haka ban sani ba?" Ruqayyah ta bude baki zata yi magana sai kuma ta rufe, bata jin ko ma menene zata gayawa Inna zata fahimta tunda ita duk bata san komai ba a game da jin dadin rayuwa ba. Sai Inna Ade ta mika mata takardar da Hassan ya rubuta mata tace "gashi inji mijinki" ta karba amma bata bude ba, a zuciyarta taji ta san menene a ciki, sakinta Hassan yayi, wayo threats din ta baiyi ba kenan tunda har ya sake ta, wato taje ta fadi duk abinda zata fada kenan yake nufi ko? Lallai kuwa zaiyi nadama mai girma. A can kasan zuciyarta taji sunan bazawara ya karu akan sunan kurma kuma gurguwa. Duk sunayenta ne ita kadai. Sai kuma taji wata magana da tafi sauran zafi a gurinta. "Baban ku yace ki taso ki biyomu mu tafi gida tare, tunda can shine gidan uban ki ba nan ba. Yace kuma kar ki sake ki dauki ko chokali a cikin gidan nan tunda ba ubanki ne ya siya ba" Ruqayyah ta zaro ido waje tana girgiza kai, zuciyarta tana kaduwa, ba zata iya ba, after all what she went through ba zata iya yin asarar duk wannan dukiyar data samu bayan ta aikata abubuwa da yawa kafin ta same ta ba, biyu bau kenan, noo ba zata iya ba. She can't imagine ta koma gidan su da zama, gurguwa, kurma, bazawara kuma talaka? Impossible. Inna Ade ta maimaita "ki tashi ki dauko mayafin ki mu tafi Ruqayyah. Ki duba ki karanta ki gani saki uku mijinki yayi miki" Ruqayyah bata motsa ba, Inna tace "Baban ku yace in baki taso kin biyo mu gida a yanzu ba, babu shi babu ke har abada, babu ni babu ke har abada, babu ke babu yanuwanki har abada ko kuma har sai kinyi nadamar abinda kika yi kuma kin nemi yafiyar duk wadanda kika batawa sannan muma zamu yafe miki". Hawaye suka fara bin fuskar Ruqayyah, ta kama hannun Inna "Inna dan Allah ki fahimce ni kije ki fahimtar da Baba, ni ba zan iya komawa waccan rayuwar ba saboda yanzu ba zan iya yin irinta ba, na saba da wannan rayuwar, ga kuma nakasa da ta same ni, inna da wanne zanji? Da nakasa ko da saki ko kuma da juya min baya da kuke kokarin yi? Dan Allah ki fahimce ni Inna, kudin nan da nake fafutukar samu ai ba wai dan ni kadai bane ba, dan kune gabaki daya, yadda muka sha wahala a baya nake so muji dadi a gaba, zuwa aikin hajji duk shekara, su Zunnur su tafi kasar waje suyi karatun su a can su zama likitoci, Sumayya sai mijin data zaba zata aura, mazan ma ai kudi suke bi kamar yadda matan suke bin kudi" Inna ta kwace hannunta tana kukan takaici tace "ban taba tunanin abinda na haifa a cikina zai yi wannan tunanin ba, kina son Sumayya ta samu miji kuma kika korar mata yaron da yake sonta? Kika yi sanadiyar da yanzu yana can a hannun ahlul kitabi suna kokarin mayar dashi addinin su? A hakan kike sonta, wannan ce taki soyayyar?" Ruqayyah tayi sauri ta kalli Sumayya,bita ta manta ma ta gaya wa Hassan wannan maganar, dan bata yi niyyar gaya masa ba saboda baya son abinda zai bata tsakanin ta da Sumayya dan tana ganin ko duk duniya zasu guje ta Sumayya ba zata taba guje mata ba. Amma yanayin data gani a fuskar Sumayya ya saka taji zuciyarta ta tsaya da bugun da take yi. Inna tace "na tafi Ruqayyah kamar yadda babanki ya fada zabi ya rage naki. Ko ki biyo ni ko kuma ki cigaba da zama ki cigaba da rayuwa amma ba tare da mu ba. Kuma babanki ya bawa tsohon mijinki damar yayi miki duk abinda yayi niyyar yi miki babu ruwansa, ko da kuwa abinda zaiyi mikin yana nufin ya hada ki da police ne" ta juya zata tafi sai Ruqayyah ta kuma kamo hannunta tace "dan Allah inna kiyi hakuri, ki rokar min Baba ya bani lokaci muyi magana da Hassan komai zai dai dai ta. Dan Allah Inna baku san wahalar da nasha ba kafin in samu kudin nan baku san irin abinda nayi ba kafin in samu kudin nan bazan iya hakura dasu ba tare da nayi iyakar kokari na ba" Inna ta kuma kwace hannunta tana goge hawayen ta tace "abinda kika yi ai duk tsohon mijinki ya gaya mana, lokaci kuma mun baki lokaci daga yanzu zuwa sanda zamu bar gidan nan ki dauko mayafin ki mu tafi tare, in baki yi haka ba kuwa to na gaya miki abinda zai biyo baya kuma da gaske muke" ganin Ruqayyah bata da niyyar tahowa ya saka Inna ta kama hannunta tana janta zata fitar da ita da karfi amma Ruqayyah taki fita, ganin Inna tana kokarin jin ciwo ya saka Sulaiman ya kama hannunsu ya raba su sannan ya ja Inna ya fita da ita tana ta kuka, aka bar Ruqayyah itama da take kukan tana kiran Inna da kuma Sumayya da tun da suka shigo take tsaye tana kallon su. Sai bayan fitar su sannan Sumayya ta matso gaban Ruqayyah, Ruqayyah tayi sauri ta rike hannunta tace "Sumayya kibi bayan Inna kije kiyi musu bayani yadda zasu fahimta, kudin nan fa har dasu za'a ji dadinsa, su bani lokaci in samu in yi Magana da Hassan ni na san abinda zan gaya masa komai zai dawo dai dai" Sumayya tace "kin tuna da ranar nan? Ranar da na yi miki warning cewa ki fita daga harkar Adam?" Ruqayyah tace "zamuyi wannan maganar daga baya, yanzu maganar Inna da Baba sunyi fushi dani akeyi akan maganar da Hassan ya gaya musu ba tare ma da sun tsaya sunji nawa side din ba. Kije ki basu hakuri kice zanzo gidan zamuyi magana sosai" Sumayya tace "kin tuna warning din da nayi miki ko baki tuna ba?" Ruqayyah ta ce " ta tuna kince kar in kara, na daina yanzu ba shikenan ba?" Sumayya tace "da nace kar ki kara dai kika ce in kin kara mai zanyi miki? To yanzu zan baki amsa" Ruqayyah tana tsaye tan kallon t da mamaki tace "me zaki yi min?" Sumayya tace "babu ni babu ke har abada. Shine abinda zanyi miki" daga nan ba tare da ta kara cewa komai ba ta juya ta bar palon. Ruqayyah bata iya motsawa ba, bata kuma iya cewa komai ba har taji sun tayar da Napep dinsu sannan yaji motsin bude gate din gidan alamun sun fita. Sai bayan da su Inna suka bar gidan Baba sannan Hassan ya fito shima bayan Baba yayi masa doguwar nasiha akan yarda da kaddara da kuma mika lamura ga Ubangiji da neman zabinsa dan samun dacewa. Daga gidan Baba bai koma gida ba dan baya jin zai uya shiga gidan, sai ya tafi ya kama hotel ya zauna, ya kira Aunty ya gaya mata yana nan lafiya amma zai dan zauna a hotel kwana biyu, ita kuma Aunty sai ta dauka rigimar da suka yi da Ruqayyah akan tarewar da tayi a gidan Hussain ne ya saka shi yayi mata yaji, sai ta fara yi musu addu'ar samun fahimtar juna. Sai da Hassan yayi sati guda a hotel din shi kadai. A cikin satin nan yayi abubuwa da yawa, na farko ya kara dawo da alakar sa da ubangiji, yayi Adduoi da dama akan rayuwarsa, ya nemi ubangiji yayi masa jagora ya bashi ikon cin dukkan jarabawowinsa, ya nemi zabin Allah a dukkan hukunce hukuncen da zaiyi a yanzu wadanda yasan zasu taba gaba ki dayan zuri'arsa kar karshen rayuwar su. A cikin satin yana daga hotel din ya yi abubuwa da yawa. Na farko ya siyar da share dinsa ta H and H kamar yadda yayi niyyar yi, sadakar nan da yayi niyyar yiwa Hussain sai ya yi ta babu fashi, abin mamaki sai Umar yayan Fatima wanda a lokacin shine yake tashen kudi a gidan sarkin kano ya siya. Sauran rabin kuma wanda shine na Hussain sai yasa aka kaiwa masana rabon gado suka raba, na Fatima Umar din ya sake siya, ya bawa iyayenta kudin. Wanda ya kasance nashi rabon kuma sai yace a barshi a cikin kamfanin a matsayin share. Satin nayi daya fito sai yaji kamar duk wasu nauye nauye da yake jin su akan kafadar sa duk babu su kamar an dauke masa su. Yaji confidence a ransa, yaji a zuciyarsa kuma dukkan al'amuran suna warware masa da kansu. Bai je gida ba sai daya je office ya aiwatar da duk abinda ya riga ya yanke hukuncin zai aiwata, sannan ya tafi gida. Direct part din Hussain ya tafi inda yasan acan ne zai samu Ruqayyah. A can kuwa ya same ta, tana dakin nan mai zanen sarauta tana feeding Hussain. Yana shiga ta dago kai tana kallonsa, idon ta kamar zai fado kasa, ta ajiye feeder a gefe cikin rawar murya tace "da gaske nake wallahi, duk abinda nace zan fada sai na fada wallahi. Har kafata, zan ce su suka shanye min kafata a gurin accident din suka mayar dani gurguwa" ga mamakin ta sai taga yayi murmushi ya samu guri ya zauna yana facing dinta yace "say whatever you want to say, do what ever you want to do. Hussain yana kabarin sa kuma duk maganganun ki ba zasu taba hurting dinsa ba dan he is out of your reach. Ko mutane sun tsine masa tsinuwar su ba zata taba yi masa komai ba saboda shi Ubangiji yasan gaskiya and that's all that matters. In ma da akwai wanda abinda zaki fada zai yi hurting to nine, ni kuma zuciyata yanzu ta zama ta karfe babu abinda zai iya hudata balle ya dame ni" ta sake jawo little Hussain jikinta tace "ba zan fita ba, wallahi ba inda zanje, ai na haihu da kai dan haka I deserve something" sai ya gyada kai yace "haka ne, kin haifa min yara har gida uku sune kuma dalilin da yasa ba zan kira police yanzu su fitar da ke daga gidan nan ba, kuma sume dalilin da yasa nazo gurinki yanzu zamuyi magana" sai ya tura mata takardu gabanta yace "wannan takarda ce, na riga na saka hannu nayi komai akan cewa na baki dukkan abinda na gada na daga dukiyar Hussain. Share ce mai tsoka a kamfanin H and H. Ba'a siyar da kamfanin ba yana nan kuma a yanzu kece kike da share mafi girma a ciki, na kuma nema miki manager da zai runga gudanar miki da komai yana saka miki kudadenki a cikin account dinki" ta bude baki tana kallon sa sai kuma ta kalli takardar, ya mika mata ta karba da sauri, sai shi kuma ya saka hannu ya dauki little Hussain, ta kalle shi tace "me kake so to? Tunda kace baka damu da in yi shiru ko inyi magana akan abinda nace zan fada dangane da Hussain ba" sai yace "yayana nake so. Babu ke babu su, shine deal din" ta zaro ido "yayan nawa? Ni fa na haife su ta yaya zaka ce babu ni babu su?" Sai ya daga kafadar sa yace "zabi ya rage ya naki kuma, ko ya'ya ko dukiya, in baki yarda ba zan karbi takardata kuma zan saka a fitar min dake daga gidan nan ki tafi duk inda zaki je sannan kuma zan karbi yayana ta karfi, kinsan ina da karfi najiki dana aljihu, kuma a iyakacin sanin da nayi Baba da inna sunce babu su babu ke, zabi ya rage naki" ta fara kuka tana kallon Hussain tace "Hassan baka da imani" yayi murmushi yace "bana jin akwai wanda ya kai ki rashin imani Hassana. Wannan shi yasa zan raba ki da yayana saboda ke din macijiya ce mai dafi, bana son ki shafa wa yayana mugun dafin ki" tace "yayana ne nima ai, kuma ko ka raba ni dasu dole wata rana da kansu zasu neme ni" yace "tabbas haka ne, but before then sun mallaki hankalin kansu sun samu tarbiyya mai kyau" A lokacin twins suka shigo dakin da gudu sunji labarin daddy ya zo, suka rungume shi sai yace "ku je maza Nanny ta hada muku kayan ku, ku gaya mata zamu je unguwa daku" suka fita da sauri suna murna. Ruqayyah ta dafa bango ta mike tsaye tana kallon sa, ya tako zuwa gabanta, ta mika hannu zata karbi Hussain sai ya matsar dashi gefe yace "for the sake of our children, for the sake of your parents, ina fatan watarana zaki dawo kan hanyar dai dai ki gyara kurakuren ki" ta kara sautin kukan ta. "Yanzu Hassan abinda zaka yi min kenan? Dan nakasa ta same ni? Wato na gama yi maka amfani kenan ko? Kaci moriyar ganga ko?" Ya gane abinda take kokarin yi, so take ta saka yayi feeling guilty kamar shine mai laifin ba ita ba. Bayan shi gani yake yi ba karamin adalci yayi mata ba. Ya yanke hukuncin bata kudin ne saboda yana son ta fahimci wani abu a rayuwa, ta fahimci cewa kudi is nothing compared to love, ta fahimci cewa akwai abubuwa da dama wa'danda kudi basu isa su siya mata ba, idan ba haka yayi mata ba bazata taba fahimta ba, kuma no matter how he tried ba zai taba cire ta daga rayuwar sa ba ko da kuwa saki dubu yayi mata. Bai kula ta ba sai ya fita yayi locking duk dakunan Hussain ya cire keys din ya saka a aljihunsa, ba dai babban gida take so da dogon bene da katon valcony ba? Gashi nan ta samu, ba dai H and H take so ba? Gata nan ya bata. Ya kuma barta da duniya. Yana fitowa twins suna dawowa Nanny tana jan akwatin kayansu, yana kallon Ruqayyah ta jawo kafa zuwa bakin kofar dakin da take tana kallon su tana sheshshekar kuka. Har yaran zasu tafi gurinta sai ya rike su ya yaudare su da zancen ice cream suka sauka kasa da sauri, har sunje bakim kofa ya sake juyowa ya kalli Ruqayyah ya kama rails tana kallonsu, ta bude baki zata yi masa magana sai yayi sauri ya fita ya turo kofa. Washegari da safe tana kwance duk da ba bacci take yi ba taji kara kamar ana gini, ta tashi da sauri ta ja kafa zuwa taga ta leka sai ta hango katanga ake ginawa ana raba tsakanin gidan Hassan da gidan Hussain, sannan kuma ana toshe karamin gate din daya hada gidajen gida biyu dana Aunty. *Life Afresh* Bayan Hassan ya rufe kofar gidan sai ya jingina da jikin kofar yana mayar da numfashi, tabbas shi kansa yasan zuciyarsa tana son Ruqayyah amma dole ya barta saboda shi dai bai taba haduwa da shaidanin mutum irinta ba, ba zai cigaba da zama da ita ba kuma ba zai bar yayansa a hannunta ba for his sake and for the sake of his children. Har cikin ransa yasan wannan hukuncin da ya yanke shine dai dai duk da wani bari na zuciyarsa yana nuna masa kamar bai yi wa yayansa adalci ba daya raba su da mahaifiyar su, sai kuma ya gaya wa kansa "ita ta zabi haka, ita ta zabar musu haka". Gidan Aunty ya shiga dasu, wani yaro ya daukar masa akwatin da aka zubo musu kayansu. Aunty tana zaune palo tana kallon wa'azi taji sallamar sa, ta daga kai da sauri tana kallonsa rabe rabe da yara, cikin kwanakin da bata ganshi ba sai taga fuskarsa ta fada ciki, manyan idanuwan sa sun kara fitowa waje sannan fatarsa ta kara duhu. Tabbas bayan rashin Hussain akwai wani bakon al'amari da yake damunsa. "Allah ga dan marayan nan Allah ka tausaya masa" ta fada a ranta lokacin da yake zama a gabanta yana mika mata Hussain, Yusuf da Aminu kuma suka fara rige rigen hawa jikinta. Hassan ya gaishe ta ta amsa tana shafa kan tagwayen da tun da aka haife su take jin soyayyar su a zuciyarta tamkar irin son da tayi wasu Hassan sanda suna kanana. Ta kalli akwatin kayan da aka ajiye a can gefe tace "gidan Sa'adatu zaka kai su ne? Ba kwanan nan suka dawo ba?" Yace "ba can zan kai su ba, nan na kawo su, anan zasu cigaba da zama" sai tayi shiru bata ce komai ba amma tana ji a jikinta cewa wani abin ya faru da ma'auratan. Sai tasa baki ta kira Zulaihat tace "dauki yaran nan ki tafi dasu sama zamu yi magana da yayan ku" Zulaihat ta amsa mata sannan ta gaishe da Hassan, itama tana lura da lalacewar daya sake yi. Sai da suka tafi sannan Aunty tace masa "ina jin ka, wanne dalili ne ya saka zaka raba uwa da yayanta ka kawo min su har da jariri?" Ya gyara zamansa yace "Aunty abubuwa da yawa sun faru wadanda baki san su ba, akwai abubuwa da yawa wadanda ban fada miki ba, kuma nayi haka ne saboda ina gudun bacin ranki musamman a yanzu da lafiya bata ishe ki sosai ba, kuma a yanxun ma ina so ki yi hakuri kar ki tashi hankalin ki akan duk wani abi da xan gaya miki, ki sani, tashin hankalin ki ba zai chanza komai ba tunda hannun agogo baya taba dawowa baya, da yana dawowa dana dawo dashi na chanja abubuwa da dama, da na chanja wasu choices da nayi a rayuwata. Amma kwantar da hankalin ki zai taimaka sosai wajen kwantar min da nawa hankalin, zai taimaka mana wajen hada kai mu samar da matsaya a lamarin mu" "Abu na farko da bamu gaya miki ba shine tun lokacin da Hussain ya a da rai, tun lokacin da aka sanar dashi surgery din sa was not successful sai ya raba H and H biyu ya bani rabi, tunanin sa a lokacin shine kar in ya mutu Fatima ta haifi namiji ya kasance bamu da komai a cikin dukiyar sa, ban fada miki ba tun a lokacin saboda bana son ki san cewa Hussain bai warke ba" "Abu na biyu da ban fada miki ba shine na siyar da rabin H and H, share din da Hussain ya bani tun yana da rai" Aunty ta bude ido "ka siyar? Saboda me? Wa ka siyar wa? Me zaka yi da kudin?" Bai ce komai ba har tayi shiru tana mayar da numfashi sai ya kuma cewa "Aunty dan Allah kar ki tayar da hankalin ki, zan miki bayanin komai" sai data jera ajjiyar zuciya sannan tace "ina jinka" ya cigaba.. "Umar ne ya siya, yayan Fatima. Dalilin dabyasa na siyar kuma saboda tun a lokacin da Hussain ya bani nayi alkawarin in har ya kasance bai rayu ba to ni kuma ba zanci wannan kudin ba, zanyi masa sadaka dasu ne" "Abu na uku da nayi ban gaya miki ba shine an raba gadon Hussain. Bana so in gaya miki dalilin da yasa na sa ayi rabon da gaggawa saboda bana so ki tashi hankalin ki har sai nayi solving problem din. Problem din kuma shine Ruqayyah" ta bude ido "Ruqayyah kuma? Menene hadin Ruqayyah da rabon gadon Hussain?" Sai kuma ta tuno da tarewar da Ruqayyah tayi a gidan Hussain, sai tayi shiru, sai ya dauko mata labari a nutse cikin hankali ya gaya mata duk abinda Ruqayyah tayi da wanda tace zata yi, da kuma shi abinda yayi. Aunty tayi mamaki kwarai da gaske, maganar kuma ta taba ta sosai musamman iƙrarin da Ruqayyah tayi na tarwatsa sunan Hussain, Hussain din da baiyi mata komai ba a rayuwarta dai alkhairi, amma yadda Hassan ya bi da maganar da matakin daya dauka ya saka tashin hankalin nata bai tsananta ba. Tace "tabbas Ruqayyah tayi asara Babba, tabbas rabata da yaran nan shine abinda yafi dacewa dan kamar yadda kace ita din guba ce, ita kuma halayya naso take yi sai wanda Allah ya tsare" Hassan yace "haka ne, wannan yasa na datse igiyoyin aure na da ita, duk ukun" Aunty ta dafe kai tana salati, yace "kiyi hakuri Aunty, bana jin zan bar duk wata alaka tsakani na da wadda zata iya yiwa Hussain wannan sharrin. Yaya Allah ya riga ya bani tare da ita, amma zanyi iya kacin kokari na wajen nesanta su da ita duk da cewa ba zan iya chanja musu uwa ba" Aunty ta jimanta abin, ita iyayen Ruqayyah take ji, mutanen kirki sai dai sunyi asarar haihuwar Ruqayyah. Amma kuma ta fahimci dalilin da yasa Hassan ya bar mata kudin daya gada daga Hussain tare da gidan Hussain din da take haƙo, wannan kadai zai koya mata darasin rayuwa, ko da badan ita ba ko dan ƴaƴanta dole zasuyi fatan Allah ya shiryeta. Sai kuma Hassan ya mika mata wasu takardu daya fito dasu daga aljihunsa yace "ga wannan, kason su Hassana ne na daga gadon Hussain, ban siyar ba yana nan a matsayin share a kamfanin H and H wanda a yanzu yake a ƙarƙashin Umar da Ruqayyah. Zabin sune suyi duk abinda suke so suyi dashi" ta daga tana kallon rubuce rubucen jikin takardar, maganganu irin na lauyoyi da tasan ko ta karanta ba gane wa zata yi ba sai ta ajiye tana kallon Hassan tace "kai kuma fa? What are you going to do?" Ya rufe idonsa ya bude, wannan tambayar ta Aunty is a one million dollar question, me zaiyi shi kuma? Ina ya dosa a rayuwa? Ya girgiza kansa, "ban sani ba Aunty, a yanzu haka ban san menene matsayi na ba, ban san me zanyi next ba. Ki bani shawara dan Allah" sai tayi shiru tana tunani sannan tace "you need to start afresh, ka tattara duk tabbunan baya ka tura su bayanka ka manta dasu ka kuma rungumi gaban ka. Ba zaka iya mantawa da baya ba na sani amma ina so ka saka ta a wani bangare na zuciyarka wanda ba ko da yaushe kake bude gurin ba. You need to be strong for your children sake, for our sake gabaki dayan mu" sai ta mika masa takardar ta ya bata tace "ka karbi wannan ka kafa naka business din, forget about H and H, ka siyar da share din su Hassana suma, mun rasa Hussain da iyalinsa baki daya mun hakura babu abinda zai same mu dan mun rasa H and H" yace "Aunty wannan kudin yaran nan ne, in kuma suna da bukata fa? Besides, kuma kuma bukatar abubuwan amfani da yau da gobe, gidan nan yana bukatar maintenance, yara suna bukatar kudin makaranta, wannan kudin shine future din kowa, in na dauka na fara business dasu suka lalace yaya zamuyi kenan?" Sai tayi murmushi, wannan maganar daya fada exactly irin wadda ya fada ce shekaru goma sha uku da suka wuce lokacin da Hussain yake rokonta ta bashi gadon su ya shiga kasuwanci dashi, tace "Hassan kenan. Always the smart one. Muka bawa Hussain kudi ya kafa kasuwanci ma ballantana kai? Hussain din da yake kashe kudi tamkar wanda yake saka musu wuta ballantana kai da nake da tabbacin zaka adana su? Maganar yanuwanka kuma ina tuna maka cewa suma yanuwan Hussain ne kuma suna sonsa kamar yadda kake sonsa dan haka in suka ji abinda kayi da kudin daya bar maka murna zasuyi suji dadi, in kuma suka ji abinda ni kuma nayi da nasu kudin sai su kara jin dadi saboda kai ma dan'uwan su ne kuma suna son ka sosai" Kar ka manta, tabbas Hussain ne yake biya musu kudin makaranta amma kai kaine kake tsaye a kansu a matsayin babansu, tun daga sec sch dinsu har jami'ar su kai kace fafutukar samar musu kuma duk wani abu da ake bukata na uba kai kake yi musu, wadanda suka yi aurea cikin su kai ka tsaya musu a matsayin uba Hussain kudin kawai yake fitarwa. Kar kuma ka manta cewa Hassana da Safiyya yanzu duk aiki suke yi, aiyukan kuma da kai ne kayi fafutukar samar musu, nan zuwa karshen shekarar nan muke saka ran Khadijah zata karbi certificate dinta a matsayin cikakkiyar likita, Nafisa tana shekarar ta ta karshe, Zulaihat tana shekara ta biyun karshe, to menene kuma ya rage wanda suke bukata? Allah yayi mana komai Hassan, mun gode masa kuma mun gode maka kai da danuwanka, ko Hassana kadai a yanzu zata iya kula damu kafin business dinka ya kafu, tunda mijin da kai ka zabar mata bai rage ta da komai ba kuma salaryn ta mai kyau ne. Maganar house maintenance kuma bana jin muna bukata, motocin nan da Hussain ya tara mana duk ka hada kansu ka siyar ka kara jari, ka bar mana guda daya ta ishe mu kaga an rage kudin maintenance da kudin mai, an kuma rage drivers, driver guda daya ya ishe mu mai gadi guda daya. Ina da kudade a account dina da kuke bani kai da danuwanka a matsayin kudin kashewa, babu abinda nake yi dasu sai ajjiya, suma zasu yi mana wani amfanin, yaran nan gaba ki daya babu wadda bata da personal kudi a account dinta, mai muke bukata kuma? Wacce daga cikin niimar ubangijin mu muka raina?" Sai ta mike ta hau sama, Hassan ya bita da kallo sai gata ta kuma saukowa dawani karamin box a hannunta ta ajiye a gabansa tace "gwala gwala-gwalai nane da Hussain yake siya min duk sanda yayi tafiya, yasan yadda nake son gold shi yasa yake siya min a matsayin toshiyar baki dan kar inyi masa fada. Ka bawa Jabir naga yana harkar gold ya siyar maka ka kara dasu" ya girgiza kansa yace "Aunty ai kina son kayanki ko?" Tace "eh ina son su mana, shi yasa na baka ai saboda nafi son ka akansu. Kuma nasan in kayi kafuwar da nake so kayi zaka siya min abinda yafi gold ma ba gold ba. A yanzu so nake kayi kafuwar da Ruqayyah in ta kalle ka sai ta sake kallonka. Allah ya sa maka albarka a cikin duk abinda zaka yi, na yarda dakai Hassan, na tabbatar nan da shekara mai zuwa sai ka kai gurin da kai kanka sai kayi mamaki ba mu ba". Yayi shiru yana mamakin Aunty da irin tarin kyautatawar ta gare su shi da Hussain, ko uwar data durkusa ta haife su iyakacin soyayyar da zata nuna musu kenan. Ya dauki takardun da box din ya mike zai tafi sai tace "Hassan, abinda Ruqayyah bata fahimta ba shine da family da kuɗi akwai banbanci mai girma a tsakanin su, in kana tare da family dinka babu irin matsayin da ba zasu tallafa maka taje ba, shi kuma kudi baya taba siyawa mutum family, amma nan gaba kadan zata gane" ya gyada kai yace "insha Allah Aunty. Nagode sosai. Thank you for your understanding, thank you for believing in me". A ranar yayi waya ya bayar da kwangilar yin katanga tsakanin gidansa da gidan Hussain inda Ruqayyah take ciki. Washegari da sassafe suka fara aikin, shi kuma ya fita ya kaiwa Jabir akwatin gold din Aunty yace ya siyar masa, daga nan kuma sai ya tattara hankalin sa kachokan ya mayar kan harkar sadakar da yayi niyyar yi. Ba wai mutane ya tara ya rarrabawa kudin ba a'a sakawa yayi aka bincika masa ƙauyuka da unguwannin da suke fama da matsala ko ta rashin ruwa ko masallaci ko makarantar islamiyya ko harkar lafiya, wannan yayi tayi, abinda yasan zai zaman to sadakatul jariya ga Hussain. Boreholes an haka babu adadi, masallatai an gina an saka alquranai a ciki, an kuma gina islamiyyoyi da yawa an zuba duk littattafan addini an kuma dauki malamai, sai kuma ya koma asibitoci yana neman marasa lafiyan da ba zasu iya biyan kudin aiki ko siyan magani ba, duk da sunan Hussain, da fatan Allah ya kai rahama kabarin Hussain. Wannan abin da yake yi shi ya taimaka masa sosai wajan mantawa da Ruqayyah and all what she did, dan baya ma tunawa da ita sai yazo kwanciya bacci tukunna zaiyi ta juyi a gadonsa zuciyarsa tana kuna da kalaman ta wadanda har yau yake jin su tamkar mashi ne a kafe a cikin kirjinsa, tabbas ta riga tayi masa illar da ba zai taba warkewa ba. Yayi mata so iyakacin so ita kuma ta zalince shi iyakar zalinta. Sai da abubuwa suka lafa sannan ya waiwayi Jabir da maganar gold, nan take ya dauko kudi da takardar lissafi tsaf na yadda ya siyar da kowanne, Hassan bai karbi lissafin ba kudin kawai ya karba yana jinjina yawan su, tabbas gwalagwalan masu matukar tsada ne, tabbas Hussain ne ya siye su. Wannan kudin su ya hada da kudin gadon kannensa da suka bar masa, ya kuma hada da kudin da ya dade yana tarawa a banki inda yake ajiye rabin albashinsa na kowanne wata, jimillar abinda ya samu sai data bashi mamaki, amma sai dai har yanzu bai yanke shawarar abinda zai yi ba, shi ba Hussain bane ba, shi bai iya shiga abu sama ta ka ba, shi yafi gane ya zauna yayi tunani akan abu yayi bincike sannan yayi. Dan haka wannan karon ma haka yayi, yayi tunani yayi bincike yayi shawara sannan yayi addu'a. A karshe ya yanke shawara. Real Estate management. Ya yanke wannan shawarar ne saboda fahimta da yayi cewar risk na asarar kudi a real estate market is very low, ko mutum bai ci riba ba to ba zaiyi asara ba in dai ba disaster ya hadu da ita ba kamar gobara, flooding da ire-iren su, ya gaya wa Aunty shawarar sa kuma ta amince da hakan ta saka masa albarka sai yaje ya sayi land babba, ya zagaye shi sannan ya fara gini, blocks guda shiga kowanne kuma sama da kasa, kowanne gida kuma three bedrooms da palo, tsarin gidajen kuma irin na zamani masu kyau da akayi da kayayyakin aiki masu nagarta, a cikin watanni shida ya gama komai, ya zuba duk abinda ake bukata a gidajen. Wannan itace estate dinsa ta farko wadda ya sakawa "Hussain Aminu Abdullahi Memorial Estate". Ginin estate din nan sai daya lamushe duk tarin kudin da yake ganin ya tara dan har sai daya fara tunanin ya daga gidan sa ya siyar amma Aunty da sauran yanuwansa suka hana shi, suka sake tallafa masa sosai, daga mai siyar da sarkar ta sai mai siyar da motar ta a haka gini ya kammala. Suka shirya walima ta taya shi murna wadda aka hada tare da addu'ar shekara ta rasuwar Hussain, aka gayyaci yanuwa da abokan arziki aka hadu anan cikin Estate din aka gabatar da adduoi aka kuma ci aka sha aka gode Allah sannan aka zazzaga aka ga gidajen, a take aka fara kama hayar su, abin mamaki sati bai rufa ba duk an kame gidajen guda goma sha biyu. A ranar ne bayan an tashi Aunty ta saka shi ya mayar da Sumayya gida. Babban kuma abinda ya jawo hankalin mutane kan gidajen bayan kyawun shine sunan da aka saka wa Estate din, kowa yasan Hussain Aminu kuma yasan taste dinsa bana banza bane ba. Kudin da aka hada wa Hassan a matsayin kudin hayar gidajen sai yaga sun ishe shi siyan wani land din har da kafa foundation din wasu gidajen suma irin wadancan, dan ma dai abin ya hadu da bikin Khadijah wadda shi yayi mata komai da ya kamata uba yayi wa yarsa, sai kadan daga kayan kitchen wadanda ta siya da kanta tunda ta fara daukan albashi sannan kuma yanuwanta ma suka siya mata wasu. A cikin shekara gudar nan Hassan went through a lot a zuciyarsa, yayi fighting sosai da soyayyar Ruqayyah, yayi fighting da impulse din da yake gaya masa ya shiga gidan da take ya duba jikinta, ya dai taba ganinta a bakin gate kamar tana so ta shiga gidan, tana jan kafa tana bin katanga, a take ya kira maigadi yace kar ya barta ta shiga, sai dai ganin nata ya taba zuciyarsa kuma ya gaya wa Aunty, tun daga nan dai yasan Aunty ta kan aika mata da yaran lokaci zuwa lokaci su ganta, bai taba tambayarsu ya take ba, bai kuma taba shiga shi ya ganta din ba. Wannan kenan...... Sumayya, in ka ganta a cikin shekarar nan zaka kasa tantance wanene yafi shiga damuwa tsakanin ta da Hassan. Ta rame ta lalace ta fita daga hayyacinta, rashin Adam, tunanin halin da yake ciki shine yake hanata bacci, yake hanata karatu, yake hanata cin abinci, yake kuma hanata fara'a. Kowa ya santa ya san ta chanja. Tun a watannin farkon bayyanar gaskiya ta samu Inna Ade, wadda itama a lokacin duk ba'a cikin nutsuwar ta take ba saboda tunanin Ruqayyah. Ta zauna a kusa da ita tace "Inna magana nazo da ita dan Allah, ki daure ki dan saurare ni ko kadan ne" Inna ta juyo tana kallonta, bata jin dadin yadda yar tata take rauzayewa a guri daya tace "Sumayya wani abun kike so?" Sumayya tace "dama Inna akan maganar Adam ne, nace ko zaki dan yiwa Baba magana muji ko da akwai yadda zamu iya zuwa nemansa" Inna ta bude ido tace "nemansa Sumayya? A ina zamu neme shi? Kina ji dai Hassan yace yana tare da mahaifansa a can garin inyamurai, ta yaya zamu iya zuwa can mu neme shi?" Sumayya ta fara sharar hawaye, "ni zan iya zuwa Inna in kun barni, ko ku hada ni da Sulaiman, Inna dan Allah" Inna tana girgiza kai tace "Sumayya! Sumayya munsan kin damu da Adam kuma muma mun damu dashi, mun damu da musan halin da yake ciki, amma ba zamu barki ki tafi nemansa ba Sumayya, ko da a kusa yake damu ba zamu barki ki fita nemansa ba ballantana yayi nisa sosai, yana cikin mutanen da ba irin mu ba wadanda shiga cikin su zaiyi mana wahala" sai Sumayya ta kara sautin kukan ta, inna ta jawo ta jikinta tana lallashin ta "ba zan iya yiwa babanku maganar nan ba, ransa a bace yake har yanzu akan maganar yaruwarki, ga kuma alkawarin da yayi wa Hassan a kanki...." Sumayyan ta kwace jikinta, bata so ko zancen hadin su da Hassan ayi mata dan kullum so take ta gaya wa kanta cewa hakan ba gaskiya bane ba, in aka fada kuma sai taji yana so ya zama gaskiya. Tace "Inna Adam fa? Shikenan mun bar shi? Shikenan ba zamu taimaka masa ba?" Inna tace "Sumayya Adam jarumi ne, kuma islam ya zauna a zuciyarsa, bani da shakku a kansa, kuma indai har da gaske yana son ki yana kuma son auren ki zai samu hanyar da zai dawo zuwa gare ki. Shi yasan inda kike, ke kuma baki san inda yake ba dan haka shine ya kamata yazo gare ki ba ke zaki je gare shi ba". Wannan maganar bata saka Sumayya ta hakura ba, ta cigaba da yiwa Inna Ade maganar Adam lokaci zuwa lokaci amma kuma ga mamakin Inna Ade ko sau daya Sumayya bata taba ambatar sunan Ruqayyah ba duk kuwa da yawan zancenta da Inna Aden take yi kullum. Ko ranar da Ruqayyah tazo gidan Baba yayi mata korar kare ma Sumayya bata fito daga daki ba balle taga ramammiyar fuskar Ruqayyah. A hankali Sumayya ta cigaba da zuwa makaranta, ta cigaba da karatu duk da dai ba kamar da ba. Sukan hadu da Zulaihat lokaci zuwa lokaci kuma a hankali sai suka fara kawance, basu taba haduwa sunyi zancen Ruqayyah ba, sai dai sukan yi hirar Aminu da Yusuf da kuma little Hussain. Wani lokacin kuma Sumayyan ta kan je har gida taga yaran wani lokacin har ma ta tafi dasu gida su kwana biyu tare da ita kafin ta dawo dasu. Wannan ya saka basu manta da ita ba, suka saba da ita sosai. A haka shekara ta zagayo, Sumayya da Zulaihat suka shiga shekarar su ta karshe a jami'a. A lokacin ne akayi addu'ar shekarar Hussain da mutuwa, a lokacin ne kuma aka gabatar da walimar bude estate din farko da Hassan yayi, a lokacin ne kuma Zulaihat ta gayyaci Sumayya. Tare suka tafi da Inna da Baba da Zunnur, saboda Hassan yazo har gida ya gayyace su suma. Anyi addu'a, anci ansha kuma an zagaya anga gida. Ita da Sumayya taga Inna tare da Aunty suna hira, sai ta basu guri ta tafi gurin su Zulaihat suna admiring flowers din gidan. Bata ankara ba sai waiga wa tayi ta nemi su Inna ta rasa, data nemi ba'asi sai aka ce mata ai sun tafi. Hankalin ta ya tashi dan bata da ko kwandala a jakarta, me yasa su inna zasu tafi su barta? Tana cikin tunanin Aunty ta kira ta, sai ta tarar dasu tare da Hassan suna magana sai taji tace masa "Hassan in ka gama sai ka sauke Sumayya a gida, su Sa'adatu sun tafi sun barta". *The Fortune Teller* Ya juyo yana kallonta, suna hada ido tayi sauri ta sauke kanta kasa tana kokarin barin gurin sai Aunty tace "Sumayya ki jira shi ya karasa dai ya kaiki gida" ta gyada kai, amma sai aunty tace "kinji?" A dole tace "eh naji aunty, zan jira shi" Aunty tace "good" sannan ta juya tana harhada kan yayanta da jikokinta. Sumayya tana kallon su suka shiga motocin su suka fara fita daga gurin, tana son tace su rage mata hanya amma babu dama dan haka ta ja bakinta tayi shiru ta bisu da kallo har suka fita sannan ta samu kujera can gefe ta zauna da waya a hannunta tana kallon tsofaffin pictures dinsu da Adam, in ta kai karshe sai ta dawo farko ta kuma maimaitawa sannan ta koma kan chats dinsu tana bi tana karantawa tana murmushi, ta karanta message dinsa na karshe "you know I love you, right?" sai taji hawaye yana diga akan wayar, tayi sauri ta dauke su a hankali tace "and I love you too" sai ta kife screen din wayar tana jin zuciyarta tana zafi. Me yasa ba zai zo ba? In dai har yana tare da iyayensa kuma yana cikin koshin lafiya ai ya kamata ya nemeta ko dan ya gaya mata cewa yana lafiya tunda yasan zata shiga damuwa saboda jin shiru daga gare shi. Sai taji tana jin haushin sa, To ko dai wani abun ya same shi ne? Ta daga kai tana kallon mutanen da suke ta hada hada a gurin, kusan duk yan uwa sun tafi sai abokan Hassan suma da yake ta sallama dasu suna shiga motocin su suna fita, tasan da Adam yana nan maybe shima da yana gurin nan, da dashi za'a yi wannan hidimar, duk da babu Hussain tasan da Hassan zai cigaba da rikon sa in ma ba zai rike shi ba tasan Baba zai iya rike shi a gidan su. Da yanzu yana nan yana karatunsa, da yanzu sun shiga level four tare. Kamar dag asama taji ance "in kina yawan zurfafa tunani.....kina zama ke kadai kiyi kuka.....zaki tsufa da wuri" ya fada da sigar tsokana. Ta dago kai tana kallon Hassan, fuskar sa babu yabo babu fallasa. Ta fahimci tsokanar ta yake yi but she is in no mood for wasa dan haka ta mike tana gyara hijab din jikinta tace "kun gama?" Yace "mun kusa dai, kar mosquitoes su cinye ki naga kin zauna kusa da flowers shi yasa nayi miki magana ko zaki koma daga can" ya fada yana nuna inda aka saka kujeru "saura few mutane mu gama" taji babu dadi, tana so tace masa zata yi tafiyar ta kawai in yaso in taje gida ta karbi kudi ta biya, amma kuma bata so yaga hakan a matsayin rashin kyautata wa. Sai ta tafi inda yace mata ta zauna tana cigaba da daddanna phone dinta har taga ya kuma tahowa shida wasu maza su biyu, suna ta hirar su sai ya dago mata hannu yace "let's go" ta mike tabi bayansu, amma ta bar dan space a tsakanin ta dasu. Suka je gurin mota sai taga ya zagaya ya bude mata kofar gefen driver, yayi mata alamar ta shiga da hannunsa. Zata shiga kenan taji wani a gurin yace "Madam babu magana? Ya gida ya yaran?" Ta juyo tana kallon sa, daga yadda yayi maganar ta fahimci ya dauka Ruqayyah ce, sau ta kalli Hassan sai taga ya bude baki ya rufe ya kasa yin magana, sai tayi sauri tace "lafiya lau. Yara sun bi Aunty" sai dayan yace "ohh anyi musu wayo an kora su dan asha soyayya a hanya ko? To ayi a hankali dai kar a soye" suka yi dariya su biyun. Da sauri Sumayya ta shiga ta rufe kofar, tana kallon suka yi sallama da Hassan sannan suka fara tafiya kafin shima yazo ya shiga kusa da ita ya zauna ya tayar da motar, sai taji a ranta ina ma a baya ta zauna ba'a gaba ba? Duk kuwa da cewa ba wai yau ne karo na farko da suka zauna kamar haka ba ita da Hassan amma da yana a matsayin mijin twin sister dinta ne amma yanzu babu wancan link din, sai taga kamar zaman nasu bai dace ba. Bai ce mata komai ba har yayi magana da mai gadin gurin sannan suka fita. Sai da suka dauki hanya sannan yace "sorry about that. Da yawa daga friends dina basu san mun rabu da Ruqayyah ba, and you guys look alike, sun dauka ita ce" ta gyada kai tace "babu komai,na fahimta ai" suka sake yin shiru sannan ya kuma yin gyaran murya yace "to ya kikaga gurin? Yayi? Huh?" Tace "yayi kyau sosai, Allah ya sanya alkhairi" yace "ameen, yayi kyau fa, ko Hussain in da zai gani sai yace yayi kyau. Kinsan shi ba komai ne yake burge shi ba" ya danyi dariya, "but it took a lot out of me, sai da aikin nan yayi min tas, in nace tas ina nufin tas, account dina sai da yayi reading 0.00" yadda ya jera zeros din yasa ta danyi murmushi, tace "tunda an gama ai shikenan" yace "shikenan fa, sai da family suka saka min hannu sannan na samu na kammala, gashi already yanzu har an karbi wasu daga ciki" tace "Masha Allah. Allah yasa musu albarka baki daya". Ji take yi a ranta kamar ta tura motar dan suyi sauri amma shi ta fahimci wani taking time dinsa yake yi. Ta dan kunna wayar ta tana kallon time, ya kalle ta yace "expecting a call?" Ta girgiza kai, ira waye zai kirata a wannan lokacin in ba Inna ba? Inna ce kawai zata iya kiranta tace ya akayi bata dawo gida ba har yanzu, ita ma kuma bata kira ba dan tana tunanin she is in safe hands. Suka sake yin shiru sannan yace "ya labarin friend dinku kuwa? Any development? Da muna waya da mijinta kuma daga baya da abubuwa suka dan sha kaina sai na manta da maganar" tace "Minal? Har yanzu babu labari fa, har an fitar da rai kuma. Iyayenta sunyi kuka sun gama, yan uwanta ma haka. Ni har bana so in je gidan su wallahi saboda Maman su tausayi take bani sosai" yace "dole ta baki tausayi, batan mutum akwai tashin hankali ai ballantana a yanayin da take ciki" ta gyada kai da sauri hawaye yana cika idonta, ya lura da sanda ta goge hawayen sai yace "yana gidan su, kin sani" ta girgiza kanta "bamu tabbatar ba. We don't know for sure" yace "Ruqayyah ta aikawa iyayensa labarin inda yake, dama sun dade suna nemanshi, babansa yayi tafiya a dai dai lokacin da shi kuma ya bata, ko motar da yake ciki ba'a dauka ba, ko waya ta da take cikin motar ba'a dauka ba. It adds up to me. Yana tare da iyayensa" ta juyo tana kallon sa ta cikin hawayen ta tace "da zai kira ni ai, a zaiyi making effort na ganin ya dawo gare ni ai. Ba zai manta dani gaka lokaci daya ba, except...." Yace "except what?" Tace "ta gyara zamanta tace "except ko iyayen sunyi masa asiri ko something" ya danyi murmushi yace "mu kuma sai muyi masa addu'a. Duk a inda yake zata same shi am sure watarana zai zo gare ki da kansa" Tace "ina so ya dawo gare ni tabbas, but ba wannan ne babban abinda nake bukata ba, I just want to know cewa he is fine. In na samu wannan assurance din hankali na zai kwanta sosai" ya gyada kai yace "na fahimce ki. Me kike so ayi?" Ta girgiza kai tace "abinda nake son yi ba zai yiwu ba, ba za'a barni ba" yace "menene kike so?" Tace "inje nemansa" ya danyi dariya yace "imo? Zaki tafi neman Adam? To in kinje ta ina zaki fara? Ta wanne local government din ta wanne unguwa?" Tayi shiru tana wasa da hannunta, itama bata sani ba, basu taba wannan maganar da Adam ba. Sai yace "Baba ba zai barki ba, nima ba zan barki ba" ta dago kai tana kallonsa tan mamakin yadda ya dauki responsibility din barinta ya dora a kansa. Sai yace "abu daya zan iya barin ki kiyi, ko kuma ince zanyi miki, zamu saka rana mu koma Kano tare, mu sake gwada bribing mai gadin nan mu gani ko zai kara bamu wani info din. Daga nan zamu gani idan family din sun dawo gida sai mu gani ko suma zamu iya samun wani abu daga gare su" ta gyada kai da sauri. "Yaushe zamu tafi?" Yayi dariya yana jinjina soyayyar da Sumayya take yiwa adam yace "zan saka rana, sai in gaya miki. Sai dai ni yanzu kamar ma bani da phone number din ki" ya fada yana mika mata wayarsa, da sauri ta saka masa number din tayi saving ta mika masa. Ya karba yana packing a kofar gidan su, tayi masa godiya sannan ta fita, ya bita da kallo har ta bude kofar gidan su ta shiga sannan ya ja motar, a ransa yana tunawa da ranar daya fara zuwa zance gurin Ruqayyah, lokacin da Sumayya ta fara fitowa yayi tunanin Ruqayyah ce. Da safe Hassan ya shiga gaishe da Aunty kamar yadda ya saba yi kullum kafin ya fita, ya tarar da ita a dakin ta bata fito ba, ya zauna a kasa yana gaisheta tayi hamma tace "har zaka fita Hassan? Ni kaga gajiya ta hana ni saukowa daga kan gado har yanzu" yayi murmushi, "nima akwai ciwon jikin fa, akwai wasu tenants ne da aka hada ni dasu jiya, to munyi dasu zamu hadu a can yu da karfe goma na safe zasu ga gidan. Bana so suje ni banje ba" Aunty ta gyada kai tace "hakan dai dai ne, Allah ya bada Sa'a. Ka sauka kasa kaci abinci amma kafin ka fita, kar kaje ka fadi a hanya" ya mike yana cewa "faduwa kuma Aunty sai kace wani tsoho? Da saura na fa" tace "to waye tsohon? Kasan dai in muka yi tsere dai sai na wuce ka" baice komai ba sai yayi kamar zai fita sai tace "yauwa Hassan? Jiya ya kukayi da Sumayya kuwa?" Ya dawo yana kallon agogon sa yace "ya muka yi kuwa Aunty? Kince in kaita gida kuma n kaita, and that is all" ta mike zaune tana kallonsa tace "jiya Sa'adatu take gaya min maganar da kuka yi da Yusuf a kan Sumayya, me yasa ni baka gaya min kunyi haka dashi ba?" Ya zauna akan side table yana kallon ta, ya marairaice murya "Aunty, magana ce yayi min wadda take close to impossible, to menene kuma amfanin ayi ta jan maganar" tace "gwara da kace "close to impossible" ba impossible ba. Kag hakan yana nufin it is possible kenan. Ni da ta gaya min maganar dadi naji wallahi, sai naji hankali na ya karkata a wannan bangaren. Ko ba dan komai ba ko dan yaran nan guda uku da Allah ya bamu" ya girgiza kai yace "Aunty don't get like that please, yara ko a hannun wa suke zasu rayu, kuma yanzu they got you and they are doing just fine. Kar azo ayi abu for the wrong reason kuma azo ana dana sani daga baya" tace "eh yara yanzu suna dani, amma daga ni har kai bamu san kwana nawa yarage min a duniya ba" ya sake mikewa kamar an mintsine shi yana cewa "mu bar maganar nan haka please, babu wanda yasan gawar fari sai Allah, maybe ma ita Sumayyan ta riga ki tafiya Allah ne kadai ya sani" bata bar maganar ba tace "haushin Ruqayyah suke so su huce maka da Sumayya, baka ganin kin karbar kamar watsa musu kasa ne a ido? Ina laifin wanda ya nuna ya damu da damuwarka?" Ya dafe kansa yace "Aunty, yarinyar nan bata sona, akwai wanda take so daban, kuma tasan nasan alakar ta da wancan din kusan nine ma na hada su, idan na karbi tayin Baba b akya ganin kamar na zubar da girmana a gurin su ita da saurayin nata?" Tace "bansan wannan ba, abinda nasani kawai shine matar mutum kamar kabarinsa take, in matarsa ce ba zaka taba auren ta ba" Yusuf ya bude kofar dakin ya shigo, sai ya dane kafafuwan babansa yana murna sannan ya je ya kama hannun Aunty yana janta, "Aunty ki tashi daga baccin nan ki zo muje muci abinci" Hassan ya hade rai yace "kai! Fita ka bamu guri" yaron yayi kamar zaiyi kuka amma sai ya juya zai fita, Aunty ta kira shi ta dauko wayarta ta nemo wani hoto da Sumayya suka dauka tare da Zulaihat da Nafisa ta nuna masa tace "Yusufa wacece wannan?" Ya karba ya gani sannan cikin murna yace "mommy!" Sai ya fita da gudu gurin yan'uwansa. Aunty ta kalli Hassan ta daga kafada tace "a gurin su mommy ce, ba step mom ba, duk matar da zaka aura will be their step mom not their mom. Kamar yadda nake a matsayin uwa a gare ku not a matsayin kushiyar uwa Sai kayi lissafin abinda zai iya faruwa da ku idan da ace iyayen mu basu yi tunanin hada aure na dana mahaifin ku ba. Maybe da bamu samu kan mu a matsayin da muke kai a yanzu ba. Wannan kadai ya ishe ka misali" ya sake cewa "aunty, this is a different case, na gaya miki yarinyar nan bata sona, in anyi abin nan zai zamanto kamar an tilasta mata ne" Aunty tace "nima sanda aka aura min babanku bana yi masa soyayyar aure, amma a yanzu da za'a dawo min da rayuwata baya ace in sake zabar miji da shi zan sake zaba over and over again" Sai ya kama kofa ya bude zai fita ba tare da yace mata komai ba, tace "Hassan" ya juyo yanab kallon ta amma bai amsa ba sai tace "misali idan Sumayya ta yarda zata aure ka, zaka amince?" Yace "bata so na Aunty, ba zata yarda ta aure ni ba" ta sake cewa "misali nace ai, in ta yarda, zaka yarda kaima?" A rufe idonsa ya bude, sai kuma ya gyada kai yace "yes, zan yarda, but only in ta yarda, in ba tilasta mata akayi ba". Wannan kenan......... Bara mu leka muga yadda rayuwa ta kasancewa Ruqayyah a cikin wannan shekarar........... A ranar data farka ta tarar ana katange gidan da take ciki, a ranar ne kuma yan aikin gidan kaf dinsu, wadanda suka yi aiki a karkashin fatima suka hada kayan su kaf suka zo yi mata sallama "zamu tafi, Allah ya sada mu da alkharinsa" Ruqayyah ta bude baki "ba gane zasu tafi ba, ni na sallame ku ne? Ni da iya kacin saninaba sallami kowa a cikin ku ba, ko akwai wata matsala ne wadda ban san daita ba?" Babbar cikinsu tace "babu wata matsala, kawai da bazamu iya cigaba da aiki a gidan nan ba alhalin masu gidan basa cikinsa" Ruqayyah tafara kufula, "ban gane masu gida basa ciki ba, ni nice mai gidan, wadanne masu gidan kumakuke magana akai?" Tace "gimbiya Fatima itace uwargidan mu, mutuniyar kirki da sanin ya kamata, tunda akayi auren ku ita muke yiwa aiki da haka yanzu lokaci daya ba zamu iya cigaba da aiki a cikin gidan nan sannan kuma ba a karkashin taba. Gwara mu tafi mu nemi wani aikin a wani gurin daban" Ruqayyah mamaki ya kamata, me suke nufi? Zasu iya yiwa Fatima aiki ammaita ba zasu iya yi mata ba? Dame Fatima ta fita? Ta fara lallashin su da nuna musu cewa duk abinda Fatima take musu itama zata dora akai amma suka tubure suka ki zama. Har sun mike tace "zanyi muku doubling salaries dinku in kuka zauna" ita tana ganin wannan wani abu ne da ba zasu taba iya turning down ba amma sai taji daga daga cikin su tace "it is not about the money, it is about loyalty" daga nan suka fita suka barta a zaune. Takaicin duniya ya ishe ta, ita bata san inda ake samo yan aiki ba dan tunda akayi bikin su Aunty ce take samo mata yan aiki har da mai girki duk ita take samo mata ita da Fatima, gashi yanzu na Fatima sun gudu saura nata kuma aikin yayi wa nata yawa dan gidan ba irin nata bane ba, duk kuwa da cewa bangaren Hussain a rufe yake. Sai taji gida yayi mata shiru sosai, taji wani irin kadaici kamar ita kadai ta rage a duniya, wannan yasa ta kira zuwaira a waya, kawarta ce da Minal ta hada su kuma tana cikin kawayen ta da suka tsaya mata a wajen bikin su ta gaya mata problem dinta "ban sani ba ko kin san yadda zanyi in samo yan aiki? Kamar gida biyu haka masu hankali" babu bata lokaci zuwaira tace zata samo mata sannan kuma suka jajanta labarin batan Minal, zuwaira tace "ance man ke ce mutum ta karshe da kika ganta ko?" Ruqayyah tace "inji wanne munafikin? Inji wanne makaryacin?" Zuwaira tace "a'a, ni da mijinta ne yake gayamin kuma yace mijinki ne yagaya masa, ba san waye munafikin ba a cikin su ba kuma san wate makaryacin ba" Ruqayyah tayi kokarin chanja maganar "okay ban san sunyi maganar ba ai. Ki gayyato duk kawaye ku zo kuga sabon gidana" sai ta bata labarin tarewar da tayi a gida Hussain. Tun a wayar taji excitement a muryar ta, kafin a jima kuwa wajan mutum biyar a kawayen su sun kira ta aka maganar, shi kenan aka bar maganar batan Minal aka cigaba da lissafa yadda za'a ci duniya. Wannan yasa Ruqayyah taji kadaicin taya dan ragu, sai dai tayi ta kiran wayar Sumayya amma bata shiga, taso ko ma menene zata yi Sumayya takasance a hannun damanta kamar yadda suka shirya tun suna yara amma abin ya gagara, daga dukkan alamu Sumayya tayi fushidaita amma tasan zata sauko tunda ita ba iya fushi tayi ba, dawani ma ballantana da ita yaruwarta Ruqayyah. Sai ta bata lokaci da niyyar ta huce, kafin nan suma su Inna da Baba sun huce sai taje har gida tayi musu bayanin cewa Hassan da kansa ya dauki kudin nan ya bata ba takura masa tayi ba, wata kila ma daga nan su yarda su biyo tasu dawo gidan da zama gabaki daya. Wata kila idan sunzo ta samu nutsuwar zuciya har ta iya bacci, dan yanzu sam bata bacci sai ta sha maganin bacci shima idan ta sha a wahale take yin baccin. Wannan kukan jaririn ne yake damunta a kunnuwan ta, ko ta cire hearing aid dinta bata daina jin sa dan kamar a cikin kanta yake ba wai ta kunnen ta kukan yake shiga ba. Da zarar ta rufe idonta kuma gawar Minal take gani, bata yo mata magana sai idanuwa da take tsare ta dasu, idanuwa masu ban tsoro, in kuma ta samu tayi baccin to kuwa sai Hussain ya ziyarce ta a cikin baccin ta, kullum mafarkin kusan guda daya ne cewa jaririn data ajiye a kofar orphanage ya girma ya rikide ya zama Hussain ita kuma ta koma jaririn, so defenseless so vulnerable and so scared, shi kuma sai yazo yasa kafa ya tatsile ta, kullum mafarkin iri daya ne amma kuma kullum sai ya bata tsoro tamkar ranar ta fara yinsa. A haka har tayi sati daya agidan ita kadai kamar mayya, wanda zata yi magana dashi ma babu sai yan aikin da ba wata sabawa sukayi ba balle suyi hira, a lokacin ne kuma kawayenta suka kawo mata ziyara ta zagaya dasu duk suka ga gida suna ta yabawa. A ranar ne kuma alert ya shigo wayarta na ribar data samu a kamfani a cikin wannan satin. Ta rike baki tana mamaki hade da murna, da gaske Hassan yake kenan, da gaske wannan kudin duk nata ne. Lokaci yayi da zata je gida ta yiwa su baba bayani ta kuma lallabasu su dawo gidan ta da zama ko ta danji dadi a ranta, dan ita har yanzu data ga alert din kuɗin bata ji dadin da take tunanin zata ji ba. Zuciyarta a kuntace take, maybe in suka zo zata ji dama dama. Ta shirya ta ja kafa ta sauka kasa ta aika aka kira mata drivern data bari a matsayin nata ya jata zuwa gida, ta ja kafa cikin murna ta shiga gida amma tun a soro Baba ya dakatar da ita "me kika zo yi gidan nan?" Tace "Baba ina wuni? Nazo muyi magana ne" yace "maganar me? Innar ki bata gaya miki sharadin dana kafa ba? Amma na ganki da mota? Cewa nayi ki ajiye duk abinda kika san a gidan Hassan kika same shi ki taho ke kadai kamar yadda aka kai ki ke kadai, idan ba haka kika yi ba kar ki shigo min gida na" ta fara girgiza kanta "Baba shi ya bani da kansa matsa masa nayi ba, kaso ya bani a cikin kamfanin su, da kuma gidan daya gada na danuwansa, yanzu duk nawa ne, zuwa nayi ku binimu tafi can zai fi nan dadin zama sai......" Ya daga mata hannu "duk ya gaya min abinda kika yi wanda yasa har ya baki wadannan kudade, bama son ko kwandala a cikin su, ke kadai muke so, in kina son mu ki jiye masa kudinsa ki dawo gare mu, in kuma kinfi son kudi ki koma ga kudi mu ki barmu" Ruqayyah ta zabi kuɗi.....ko cikin gidan Baba bai barta ta shiga ba....ko Sumayya bata samu ta gani ba..... Tun a mota ta fara kuka, kuncin zuciyarta yana karuwa. Tana som family dinta tabbas kuma zata iya zabensu akan kudi idan da ace bata samu nakasa ba, amm yanzu she can't even imagine herself a matsayin kurma, gurguwa, bazawara kuma talaka. In tana cikin wannan nakasar kuma tana cikin kudi ai da sauki ko? Sai ta samu kanta da questioning choices dinta, shin me yasa ma tayi abinda tayi ne? Me yasa kuma ta tona asirin ta ga Hassan har ta kai shi ga sakinta har kuma ta kai iyayenta suka sallama ta? Yes, tana son kudi, kuma koda yaushe tana yin dogon tunani akan hanyar da zata sami kudin amma yanzu me yasaya zamana kamar kanta ya toshe ne? A haka ta koma gida ta cigaba da rayuwa, ta tashi ta jawo jiki zuwa palo tayi kallo taci abinci ta koma daki ta kwanta ta kasa bacci ta kuma dawowa palo ta zauna. Sai in ta gaji ta kira kawayenta suzo suyi ta mata hir ta dauki kudi ta basu du tafi. Shikenan. Hatta wayarta takan wuni batayi kara ba. A cikin wata daya sai da loneliness din ya zamanto kamar zai kasheta da ranta. Ta rame tayi duhu kuma ita kanta tasan rashin bacci ne. Tsoro da fargaba dan ko kofa aka taba sai taji kamar zuwa za'a yi ace mata ga Fatima nan ta dawo. Ta koma gidan su har sau biyu amma ko tsakar gida bata taka ba, kamar Baba yanzu ya daina gadin kamfani ya koma gadin kofar gidan sa. Sai a lokacin ta tuno da malamin duban Minal, sai a lokacin ta samo amsar tambayar da take yiwa kanta na dalilin da yasa ta aikata abinda ta aikata din, abinda malamin duban nan ya gaya mata shine dalili, wannan kudin daya kwadaita mata shine tabi ta kuma dauki zabin da take ganin shi zai kaita ga kudin, kuma ya kaita din. Amm kumaa cikin duban nasa bai gaya mata cewa zata zama musaka ba, ko bai ga wannan ba? Ko kuma ya gani bai fada mata ba? Sai ta ya ke shawarar komawa gurinsa. Bata manta gidan ba, ta kwatantawa drivern kuma ya kaita har kofar gidan sannan t fita tana jan kafa ta shiga ta aika aka gaya masa yayi bakuwa kamar yadda taga Minal tayi ranar nan. Akayi mata iso ta shiga har palon da suka zauna ranar nan, kamar babu abinda ya chanja amma komai ya chanja, babu Minal, babu kunnuwan ta babu kafarta guda daya. Tana zaune ya fito fuskarsa da murmushi ya zauna yana kallon ta "Hajiya Ruqayyah barka da zuwa. Har na fara tunanin ko kin manta da alkawarin mu ne" ta bata fuska tace "alkawari kuma? Wanne alkawari muka yi da kai?" Yace "alkawarin idan aikina ya tabbata zaki zo ki biya ni kudin aikina" tace "ni babu aikin dana saka ka ballantana in biya ka. Ni sanda nazo gidan nan bansan kai malamin duba bane ba da ba zanzo ba ma. Sanda ka yar da charbin ka bansan duba zakayi min ba shi yasa na dauka, da na sani da......" Yace "and yet, you believed what I said" ta tsaya ta saki baki tana kallon sa, ya daga kafada yace "eh, mana. Idan har Abinda kika fada har cikin zuciyarki ne me yasa da na gaya miki maganar kika yarda da ita har kuma kika yi amfani da ita? " Tayi shiru ta kasa magana, a lokacin ta fahimci cewa wannan shine kuskuren ta a wannan bangaren, yarda da abinda malamin duba ya gaya mata, da bata yarda ba da ba lallai ta kawo idea din yarda jaririn a ranta ba, da bata yarda ba da ba zata yi tunanin wasu options guda biyu ba har ta zabi daya, da bata yarda yaron ba kuma da ba zata hadu da wadannan masifu da suke ta samun ta a jere ba, da bata hadu da masifun ba kuma da ba zata zama frustrated da har zata gaya wa Hassan maganganun da zasu saka ya sake ta iyayenta kuma su sallamawa duniya ita ba. It all starts here.........duk da dai ya tarar da hali. Ta mike tana jan kafa zata bar gurin yace "baki sallame ni ba har yanzu" ta juyo a fusace "me zan baka ne wai ni? Ka barni da masifun da nake ciki mana kar ka kara min da naka masifar kuma. Wallahi kwandala ba zan baka ba kuma babu abinda zance maka sai Allah ya isa tsakani na da kai" ta sake juyawa sai yace "ina kawarki Amina? Har yanzu ba'a tono gawarta ba ko?" Ta juyo da sauri ta zube idanuwan ta akansa, yayi murmushi yace "yar uwarta tazo nan gurina akan in duba musu ko zanga inda Amina take, na duba kuma na gani, naga mutuwarta, na kuma ga inda aka binne ta" Ruqayyah ta dauke numfashin ta tana jiran mai zai ce sai kuma yace "amma ban gaya musu ba, ina jiran sai kinzo tukunna" tace "abinda ka gani karya ne, in da gaskiya kana ganin badini me yasa baka gayawa Minal cewa ga abinda zai faru da ita ba? Me yasa baka gaya min cewa ga masifun da zasu same ni idan nabi kudi ba?" Yace "ba komai nake gani ba sai abinda Allah Ya banj ikon gani, in kuma na gani din ba komai nake fada ba, ina fadar abinda zai saka mutum ya sake dawowa gurina ne ba wai abinda zai saka mutum ya daina zuwa ba. Idan da ace na gaya miki zaki zama kurma kuma gurguwa ai da ba lallai ki bi hanyar da nake so kibi ba, kinga kuma da ba zaki dawo yanzu ba" ta dafe kanta tana jin hawaye yana cika idonta, sai yace "wannan da jaririn yana nan lafiya kalau, mahaifiyar sa ma kuma tana da rai" ta bude idon tana kallon sa, bakin ta ya kasa budewa balle har tayi masa magana, sai ya dauko wata takarda ya ajiye a gabanta yace "account number dina ce, da kuma adadin kudin da nake so kike turo min duk wata a cikin account din, in ba haka ba zan gayawa yan uwan Amina exactly a inda gawarta take zan kuma gayawa Hassan a inda dan danuwansa yake in kuma bashi labarin yadda akayi yaje gurin. Wannan karon in ya shake ki sai ya kai ki lahira. Sannan Inna da Baba su biki da tsinuwa har cikin kabarin ki. Zabi ya rage naki". *Her New Life* Ta fara girgiza kanta hawaye yana zuba tana cewa "karya kake walllahi, kai baka isa kayi blackmailing dina ba karya kake wallahi, babu abinda ka sani, kawai kame kame kake yi dan ka mayar dani saniyar tatsar ka amma karya kake babu abinda zaka iya yi min" yace "da gaske? To ki gwada ki gani mana. Nan zuwa karshen wata kar inji alert a waya ta kin ga a lokacin zaki tabbatar da gaske nake ko karya nake yi, zaki tabbatar na sani din ko kuma kame kame nake yi" ta zauna a hannun kujera saboda yadda taji tana neman faduwa tace "azzalumi, mugu, in Allah ya yarda ba zaka gama da duniya lafiya ba" yace "ni wanne zalunci nayi? Ni ban dauki jariri daga jikin uwarsa na jefar dashi ba, kuma ban boye mutuwar aminina ba, dan haka tsakanin ni da ke za'a warware waye azzalumi. Ni sana'a nake yi, wannan aikin duban shine sana'a ta dashi nake samun kudi kuma dashi zan cigaba da samun kudi ta wajen ki, ban jawo kafarki na kawo ki gurina ba da kanki kika zo, da kanki kuma kika aikata abinda kika aikata ni ko shawara ban baki ba, sannan kuma da kanki zaki ke biya na kudi duk wata" bata ce komai ba har ya mike, yana kallonta yace "kar ki manta da takardar in zaki fita" sannan ya koma ta kofar daya shigo. Ta jima a zaune a gurin tanajin hawayen ta yana zuba akan rigarta, sannan ta saka hannu ta dauki takardar tana karanta amount din kudin daya rubuta sannan ta girgiza kanta da sauri, inaa, ba zai yiwu ba, wato kura da shan bugu gardi da kwace kudi? In dai har zata ke bashi wannan kudin duk wata sannan zata ke biyan maaikatan data dauka a gida albashi plus kayan abinci da sauran house maintenance to babu abinda zata tsira dashi ita din. Tunda ta fara ganin alert daga H and H lissafin ta shine ta tara kudi ta nemi hanyar da zata bi ta dauko likita daga waje yazo ya duba mata kunnen ta yadda zata iya hawa jirgi ta tafi neman lafiyar kafar. Yanzu kuma gashi wannan yallaban yace shi zata ke bawa kudin, wato ita kuma ta cigaba da zamanta a matsayin musaka har karshen hargitstsiyar rayuwarta? Gaskiya da sake wai an bawa mai kaza kai. Ta dauki takardar ta saka a jakarta ta koma mota suka fita daga gidan, a zuciyarta tana tambayar kanta dalilin daya dawo da ita zuwa gurin dan duban, duk dadai tasan in yaso blackmailing din nata zai iya binta har gida ya gindaya mata sharadin sa. Amma wannan sharadin sam ba zata iya binsa ba ba zata iya zama baiwar sa ba. Ita da zunubin, ita da rashin iyaye, ita da nakasa, ita da rashin miji sannan kuma shi da samun kudi? Wannan sam ba zata yiwu ba. Tana zuwa gida ta wuce cikin bedroom ta jawo akwati ta fara zuba kayan sakawarta, gida zata koma ta zauna, gwara ta mayar wa da Hassan dukiyar sa kamar yadda Baba ya bukata, gwara ta bi sharadin Baba wanda ya haife ta ya kula da ita har girmanta akan ta bi sharadin wani kazamin mutum da yake kiran kansa da Malami. Ai dai tasan Baba ba zai hana ta daukan kayan sakawarta ba tunda dai ya'ya uku maza ta haifawa Hassan ai kuwa ta ci lefenta. Gwara taje ta zauna a matsayin musaka, bazawara, talaka amma kuma tare da iyayenta akan ta zauna anan a dukkan wadancan matsayin amma kuma babu iyayen. Sai data cika akwayi biyu da kayan sannan ta fita da niyyar kiran nai aikinta ta fitar mata da kayan bakin gate sai kuma wani tunani yazo mata, yanzu in ta mayar wa da Hassan dukiyar sa ba zata ke biyan mai duba ba, in kuma ba ta biya shi ba zai iya aikata abinda yace zai aikata. Ta tuno da Fatima da matsayin ta da matsayin mahaifinta da irin tarin son da yake yi mata, me zaiyi idan yaji labarin cewa gawar daya binne ba ta Fatima bace ba, in yaji cewa Fatimah tana raye amma ba'a san a inda take ba, sannan kuma danta, jikansa an jefar dashi cikin kaskanci a gidan marasa gata? Tasan in ya fara daure ta har sai igiya tayi saura kuma babu wanda zai taimaka mata tunda ita a yanzu bata da kowa. Ta tuno irin zuciyar Hassan kuma da irin son da yake wa Hussain, idan yaji abinda ta aikata ga da daya tilo na Hussain in ya shake ta tabbas sai ta dangana da lahira. Idan haka ta faru sunayenta zasu karu daga kurma gurguwa bazawara talaka zuwa yar prison, ko kuma worst, matacciya. Ita kuwa bata shirya tafiya lahira yanzu ba dan tasan bata aikata abinda can din zata yi mata kyau ba. Ta zauna akan kujera tana dafe kanta, ita kanta tasan cewa rayuwar ta ta kare tun kafin ma ta soma. Ita da kanta ta dauko biro da takarda tayi signing contract da shaidan shi kuma ya zuga ta ta haka rami da kanta ta shiga sannan malamin duba ya binne ta da ranta. Menene kuma yayi mata saura? Babu abinda ba zata iya bayarwa ba a yanzu dan ta dawo da hannun agogo baya. Dan ta dawo da rayuwarta ta baya, dan ta dawo da alakar ta da Hassan. Ta tuno da irin son da Hassan yake yi mata da yadda yake tsayuwa akan dukkan al'amuran ta, da ace suna tare ne da wannan mai duban bai isa yayi blackmailing dinta ba Hassan sai ya kwato mata yancin ta. Ta tuno Sumayya, da irin yadda suke open to each other, babu abinda ba zata bayar ba a yanzu dan ta samu Sumayya ta gaya mata halin da take ciki ko zata bata shawarar yadda zasu bullowa lamarin. Ta dauki wayar ta for the nth time ta kira number din Sumayya amma ko ringing ba tayi ba ta katse kamar yadda take yi kullum alamar an yi blocking layinta kenan. Wai Sumayya ce tayi blocking dinta, kuma tasan akan Adam ne. Ita a ganinta taimakon Sumayya tayi data rabata da Adam bata sam cewa zata dauki zafi haka ba. Shikenan kowa ya guje ta, kowa banda mutum uku, mutum ukun da take ganin har abada ba zasu taba gudun ta ba, ƴaƴan ta, suma kuma Hassan ya raba ta da su. Sai ta mike ta saka hijab dinta ta sauka kasa sannan ta fita, ta fita gate ta tsaya tana kallon gidan Aunty, ta san can ya kai su, tasan bashi da inda zai kai su idan ba can din ba. A fara bin katanga a hankali tana jan kafarta har taje bakin gate din gidan Aunty a dai dai lokacin ne kuma taga motar Hassan tazo gurin, ta dauke kanta gefe dan bata son su hada ido, not now. Tana kallon sa ya sauke glass daga alama kare mata kallo yake yi, tai expecting ya rufe ta da bala'i amma sai taga an bude masa gate ya cusa motar sa ciki, ta lura da yadda ya tsaya yayi magana da mai gadi tare da nuna ta sannan ya shiga gidan, duk da vata ji su ba amma tasan cewa maganar ta suka yi kuma tasan Hassan cewa yayi kar a barta ta shiga gidan, kar a barta taga ƴaƴan ta. How cruel! Duk da haka bata hakura ba dan tana ganin ai itama ƴaƴan ta ne, amma kafin ta shiga sai maigadi ya tare ta yace "kiyi hakuri hajiya, yallabai yace kar in barki ki shiga, kiyi hakuri dan Allah kar ki matsa, bana son inyi miki abinda ba zamuyi dadi ba gabaki daya" ta tsaya tana kallon katon mai gadin, to in ma bata hakura mai zata yi masa? Ita dai ba zata kama shi da kokawa ba kuma ba zata iya kama katangar ta haura ta shiga gidan ba. Time din da take haura katanga ya riga ya wuce, those good old days! Ta juya a hankali kamar wadda kwai ya fashe wa a ciki ta sake bin katangata koma cikin tangamemen gate din tafkeken empty gidan da yake matsayin nata, gidan da tunda ta dora idonta a kansa take son ta mallake shi amma yanzu data mallake shin take jinsa kamar wani prison. A ranar tayi kukan da rabon da tayi irinsa ita kanta ba zata iya tunawa ba. A daren ranar kuma bata yi bacci ba duk da maganin baccin da tayi ta bunkawa kanta, ba wai kukan jariri da idon Minal ne kadai suka hana ta bacci ba a'a abubuwan da suka cunkushe mata a ranta ba zasu kirgu ba. Zuwa safiya ta yanke shawara. Tana idar da sallah ta dauko takardar da mai duban ya bata ta saka number din wayarsa data gani a ciki ta kira, ya dauka tare da sallama, bata amsa masa ba dan tana ganin bai cancanta ba tace "na amince zanke baka kudi kamar yadda ka bukata, amma ba amount din da ka nema ba, zanke baka rabi" yace "baki so a daidaita ba kenan. In rabi ne ki rike kayan ki ni kuma in fara tunanin inda zan fara aikawa da sako na, gidan su Minal? Kano? Ko kuma ofishin tsohon mijinki?" Ta lumshe ido ta bude tace "in nace zan baka duk abinda ka nema, ni zan tashi bani da komai kenan, in haka ya kasance ko zan gwammace in mayar wa da Hassan kudinsa in koma gidan mu, kaga dani da kai munyi two zero kenan. Ka karbi rabin dana baka ko kuma ni da kai duk mu rasa" ya danyi shiru sannan yace "na rage miki, ki bada kashi uku cikin hudu" ta girgiza kai kamar yana ganinta tace "rabi ko nothing. Karkari ta kashe zaka tona min asiri, ni kuwa a yanzu na kuna bana jin tsoron wuta, to waye ya rage min wanda zai guje ni in an san abinda nayi?" Yace "in ma bau wanda zai guje ki ai zaki tafi gidan yari ko? Kinsan....." Ta dakatar dashi tace "zan tafi prison ko kuma zamu tafi prison? Inajin a duban naka baka duba sosai ka ga wacece Ruqayyah ba, if I am going down I will surely take you down with me, zan ce tare da kai muka shirya komai kuma za'a yarda saboda in ba haka ba ya akayi kasani? Wannan takardar da ka bani da sunanka da account details dinka da kuma adadin kudin dazan baka ita ce shaidata, zan bayar daita a matsayin shaidar payment din da nayi maka na taimaka min da kayi gurin duk abinda nayi. Dan haka kayi tunani kafin ka yanke shawara" yayi shiru, tabbas sai yau ya tabbatar cewa yarinyar nan shaidaniya ce. Yayi gyaran murya yace "shikenan, ki ringa turo rabin" bata ce komai ba ta kashe wayar ta ajiye. Ta kama shi a inda ba zai iya kwacewa bakuma wannan kamun na farko ne, nan gaba sai yayi nadamar hada hanya da ita. A yanzu plan dinta shine zata ke biyan mai duba rabin kudin da ya nema a cikin kudin da za'a ke kawo mata na ribar share din da Hassan ya bata a H and H, sauran kudin kuma bayan ta fitar da abin bukatun ta na yau da gobe zata ke tarawa a hankali sannan sai ta fara neman maganin ciwon ta, zata gwada na hausa dana islamic chemist har in Allah ya taimake ta ta samu kafin nan kuma ta san yadda tayi tayi maganin malamin duba sannan sai ta koma gida, at least dai taji da talaucin ba tare da nakasar ba. A ranar sai ga mai aikin Aunty ta shigo mata da su Aminu wai inji Aunty tace suzo su gaisheta, murna a gurin Ruqayyah harda hawayenta, ta jawo su jikin ta ta rungume tana kallon yadda suke fes fes dasu babu alamun wata matsala a tattare dasu, at least tana da kwanciyar hankali ta wannan bangaren, tasan ƴaƴan ta suna hannun tiko na gari duk da tasan albarkacin Hassan suke ci . Haka rayuwa ta tafiyar wa Ruqayya tsahon wannan shekarar, kudi suna shigo mata daga kamdani ita kuma tana bawa malamin dubanta sannan tana tarawa, bayan ya taru kuma ta fara neman magani dashi, duk inda taji mai magani daya danganci kafa ko kunne sai taje amma shiru babu sauki sai a wurin Allah, kafa kullum kara motsewa take yi har ta kai cast din ma yayi mata girma ta koma amfani da crutches, kuma har yanzu bata iya ji da kunnenta sai ta saka hearing aid, har yanzu kuma bata iya bacci sai ta sha sleeping pill, har yanzu kuma bata samu hanyar da zata bi ta rabu da wancan karfen kafar ba. Rayuwar Ruqayyah kenan...... Sorry guys.... bacci....ina typing ina bacci......ayi hakuri da wannan duk da kankantarsa. Tomorrow zamu dan fara rushing things up yadda zamuyi covering shekarun da wuri. *Destiny* Tun ranar da Aunty tayi wa Hassan maganar Sumayya bai kuma yi mata maganar ba ita ma kuma haka, amma ya dukufa da addu'a, duk sallah sai ya gaya wa Allah ya kuma roki yayi masa zabin mace ta gari wadda kuma zata zama uwa ta gari a gurin yayansa, waɗanda yake dasu da kuma wadanda zai samu nan gaba. Sai kuma ya mayar da hankalinsa kan business dinsa. Sai dai lokaci zuwa lokaci maganar tana fado masa amma sai ya kawar da ita dan shi bai san da wacce fuskar zaije yayi sallama da Sumayya yace mata yana sonta, shi kansa sai da yadafe kansa daya aiyana abin, wannan ai abin kunya ne kuma zubar da girman sa ne a gurin yarinyar da yake gani kamar kanwarsa. In ma za'a yi to yana ganin sai dai manya su shiga maganar in yaso in anyi auren sai yasan yadda zaiyi. Even at that ma bai san ta yadda zaiyi din ba. To shi ma kenan da yake namiji kna gaita da take mace? Ta yaya zata so shi irin soyayyar aure? Ta ya kuma zata iya muamalar aure da shi? Musamman in yayi la'akari da yadda take girmama shi sosai. Amma ta ko'ina im ya duba sai yaga ita din ce dai a sama a cikin zabin sa. Dan yayansa, dan farin cikin iyayensu, dan nutsuwar zuciyarsa, dan abubuwa da yawa. Tunanin abin ya sa ya kara kaimi gurin addu'ar sa, yana kuma rokon Allah ya bashi kwarin guiwar tunkarar ta da maganar indai har ita ce alkhairi a gare shi. Daga nan sai maganar ta fara damun shi sosai har ta kan hanashi bacci sometimes, ya saka ya warware, har mafarki yake yaje ya gaya mata yana son auren ta ita kuma tayi mishi masifa tace masa maci amana, a wani mafarkin kuma sai ta karbi tayinsa ta ce Allah yasa hakan shima nafi alkhairi, ya san dole a cikin biyun nan daya ne zai faru amma bai san wanne ne ba, ba zai kuma sani ba har sai ya gwada, Sumayya kamar wani unopened page ce a littafin rayuwarsa, ba zai san menene a ciki ba har sai ya bude, courage din budewa ne kuma ya rasa. Sai ranar nan dai da sukayi magana da Zulaihat ta gaya masa cewa suna exam din first semester ta final year dinsu, ma'ana semester daya ta rage musu a karatun su na jami'a, sai ya fahimci cewa time yana kure masa, lokacin da Baba ya bashi ya kusa karewa tunda cewa yayi alƙawarin yana nan daga lokacin zuwa sanda zata gama jami'a, yasan kuma Baba jira yake kawai ta gama jami'a ya aurar da ita ko gare shi ko ga wani, wanin kuma yasan ba Adam bane ba tunda dai Adam har yanzu babu labarin sa, dan shi kansa yasan Baba yayi kokarin barin ta har ta gama jami'a ba tare da miji ko kuma wani tsayayyen mane mi ba dan iyaye irin Baba musamman wadanda ba yan boko ba da wahala suke barin haka ta kasance ga ƴaƴan su, maybe ma Baban ya barta har yanzu ne saboda shi, saboda ko zai zo yace ya karbi tayinsa. Dan haka a ranar sai ya shirya da yamma ya tafi gidan nasu a fili da niyyar gaishe da Baba amma a ransa so yake ya ga ko zai samu wata kafa da zai fake da ita. Sai dai cikin rashin Sa'a sai ya tarar Baban bayanan, duk gidan ma babu kowa duk suna makaranta dan Sulaiman shima ya shiga jami'a last year Zunnur ne dai yake kokarin kammala secondary school dinsa, sai Inna kadai ya tarar a gidan, ya shiga ya gaishe da ita tana ta tambayarsa mazajenta tana korafin cewaya kwana biyu bai kawo mata suba "ko da yake ba laifin ka bane ba laifin Sumayya ne, dama ita ceai zuwa ta dauko su kuma yanzu ta daina wai dan taji muna maganar ku kai da ita ranar nan da Amina a waya. Shine ta daina zuwa gidan dan kar Amina tayi mata maganar" sai ya sunkuyar da kansa kasa shima yana jin kunya, wato har maganar suke yia tsakanin su tun kafin su wadanda za'a yiwa auren su amince. Kuma daga yanayin da Inna tayi maganar itama sai ya fahimci tana son hadin, Aunty ma tana so, Baba shi yayi initiating, saura su kadai ya rage. Ya tashi yayi mata sallama tare da alkawarin kawo mata maxan ta ranar Friday idan anyi hutu tunda sun fara zuwa school yanzu. Sai dai kuma yana fita kofar gida suka kusa yin karo da Sumayya tana kokarin shigowa gidan a gajiye, kallo daya yayi mata sai ya rike baki yana boye dariyarsa. Ga jaka ga lecture notes a hannunta, ga uban hijabi har kasa wanda daga dukkan alama zafi take sha a cikinsa, fuskarta kadai zaka kalla kasan tsabar gajiyar da tayi da kuma irin yunwar da take kwakwular cikinta. Ta bata rai "dariya kake min ko?" Yayi saurin girgiza kai dan yasan yana bude baki dariyar zata fito, tayi kwafa, "dan ma dai kaima kayi karatun kasan wahalar da ake sha" sai ya bude bakin yayi dariyar sannan yace "ni sanda ina zuwa makaranta da ace kin sanni a lokacin da ba zaki damu dan na yi miki dariya ba, dan kin fini kyan gani, ni kamar skeleton nake komawa baƙi na kuwa ko bayan tukunya nan ya ganni ya bari" tace "ni ma ai kamar skeleton din nake yanzu, hijabi ne ya biye ramar" Yace "an kusa gamawa ai, wahalar ta kusa karewa" ta langwabe kai tace "ameen. Bismillah ko har ka shiga ka fito?" Ya girgiza kai pretending as if bai shiga ba yace "ashe Baban baya nan" ta dan duba wayarta tace "ya kusa dawowa ai, bara in bude maka dakin soro sai ka zauna ka jira shi" ta shiga gidan da sauri bata jima ba ta dawo da key ta bude masa dakin ya shiga ya zauna yana kallon dakin kamar yay ya fara gani, sai yake jin memories na da suma dawo masa, memories din sanda yake zuwa gurin Ruqayyah suke zama a dakin. Yayi sauri ya ture tunanin a gefe dan baya son ya bata mood dinsa, yaji dadin yadda Sumayya ta tarye shi bata bata rai tayi mishi kallon wanda yake forcing kansa a gurinta ba. Bai jima ba ta shigo da sobo mai sanyi da ruwa ta ajiye masa tace "yanzu zai dawo" sai kuma ta zauna a gefe tana wasa da hannunta, ya zuba sobon data kawo masa ya daga yana sha yana kallon hannun da take wasa da shi, sai daya ajiye cup din sannan yace "fadi, ina jin ki" ta dan kalle shi kadan suka hada ido tamayar da kanta kasa tace "dama ina ta son in tuna maka maganar nan damukayi ranar nan, kuma bana so kaga kamar na dameka shi yasa na kasa yi maka maganar" ya gane maganar da take nufi amma sai ya nuna kamar bai gane ba yace "wacce maganar kenan?" Tace "maganar zuwa Kano, kace zamu je tare kuma har yau bamu je din ba, kuma ni ba za'a barni naje ni kadai ba. Na san Baba yana jin maganar ka dan Allah ka tambaye shi ko kai ba zaka samu damar zuwa ba ni sai inje" ya rungume hannunsa yana kallonta, a ransa yana jinjina soyayyar ta ga Adam, ina ma dai zai samu irin wannan soyayyar ta gaskiya, soyayyar da za'a yiwa mutum ko da a bayan idonsa ne. Sai kuma wata magana da Hussain ya taba gaya masa akan mata ta fado masa "the way to a woman's heart is through kyautata wa, tausayawa, nuna soyayya da kuma kyauta. In kayi mata haka you don't need to say I love you, zata gane, itama kuma zata so ka". Yace "shine abinda kike so? In munje kano gidan su Adam mun nemi labarin sa zaki ji dadi?" Yadda yayi maganar ya sa ta dago kanta suka hada ido, amma hakan bai hanata gyada kai ba, yace "good, in dai haka kike so to haka za'a yi, zanyi wa Baba magana, in ya amince kuna gama exams sai muje" tace "yaya Hassan muje da weekend din nan mana" sai kuma ta sunkuyar da kanta tace "that's if you are not busy" ya gyara zamansa yace "am not, amma kinga exams kuke yi, abinda zamuyi finding out a kano zai iya ya taba ki emotionally hakan kuma zai iya taba exams dinki, ni kuma ba zanso hakan ba. Shi yasa nace after kun gama exams sai muje. Kinji?" har cikin ranta taji maganar sa, sai ta gyada kai lokacin da taji tsayuwar sabuwar Napep din da Baba ya siyar da waccan ya cika ya siya kwanan nan, sai ta yashi da sauri ta shige gida, a ranta bata son Baba ya ganta tare da Hassan kar yayi tunanin wani abu. A ranar Hassan yayi wa Baba maganar yana son zasu je kano da Sumayya su bincika labarin Adam, amma sai Baba ya nuna kin amincewar sa yace "ina so a ji labarin Adamu, amma me yasa lallai sai Sumayya taje? In zuwan za'a yi ai gwara kai din kaje tare da ni ko tare da Sulaiman, amma ita menene nata na zuwa?" Hassan yayi kokarin kare Sumayya, "Baba kasan dangantakar Sumayya da yaron nan, kasan kuma ita zuciya tafi yarda da abinda taji ko abinda ta gani ba wai abinda wani yaji ko ya gani ba, in ba ji tayi da kunnenta ko ta gani da idontaba ba lallai ta yarda ta cire yaron daga xuciyarta ba" Baba ya tsaya yana kallon Hassan yace "ita ce tayi maka maganar sa ko?" Hassan ya girgiza kai da sauri "kawai dai naga kamar hankalin ta har yanzu yana kansa, ina so ne ta samu nutsuwar zuciya" Baba ya fahimci boye laifin Sumayya Hassan yake son yi, kuma yaji dadin hakan dan wannan shine alaka ta gaskiya ba wai kayi ta kokarin kawo karar mutum kana nuna shine mai laifi a komai ba. Sai ya nuna ya amince, ba dan Sumayya ba sai dan Hassan. Ranar Friday aka yi wa yara hutu sai Hassan ya dawo tare da ƴaƴan sa duk su ukun, ya kira Sumayya a waya yace tazo ta shiga dasu suna ta murna an kawo su gurin mommy, ya fahimci cewa basa banbance Sumayya da Ruqayyah kuma yaji dadin hakan dan baya so su gane Ruqayyah ce ta haife su, at least not now. Bayan ta gaishe shi tana ta murnar ganin yaran suma suna ta makalkale ta sai ya dauko wata yar karamar jaka irin ta computer ya mika mata "laptop, nasan zaki bukace ta saboda project" ta karba da murna, fuskarta tana nuna irin farin cikin da zuciyarta take ciki tace "you are are real life savior Yaya. Kamar kasan yadda nake ta fama da hada project a waya ina ta rigima da yan café. Thank you thank you" yayi dariya, "you are welcome, sai a dage aci jarabawa sosai" Daga lokacin sai ya samu excuse din kiran wayar Sumayya sai ya nuna mata kamar yaran ya kira su gaisa, wani lokacin kuma sai ya fake da tambayar ta yaya exams, a haka har suka gama exams din, ranar da suka gama a ranar Sumayya ta kira shi da kanta ta gaya masa sun gama sannan ta tuna masa maganar tafiya Kano, sai yace ta fada a gida gobe zai zo ya dauke ta su je, gwara dai suje Kanon nan ko ya samu ta sakar masa mara yayi fitsari. Data sanarda Baba sai yace "a dawo lafiya. Amma ki sani, ko kun samu Adamu ba zan bashi aurenki ba sai dai in Hassan ne da kansa yace ya janye ya bar masa" Da sassafe Hassan yazo suka dauki hanyar kano, yana ta kokarin yi mata hira a hanya amma ita hankalin ta yana kan abinda zasu tarar a kanon, wannan shine last chance dinta na samun labarin Adam dan tasan Baba ba zai kara barin ta ta dawo ba kamar yadda ta san ba zai cigaba da kallon ta a gida ba dole zai yi mata aure ko da Hassan ko ma da waye amma dole zaiyi mata aure, ita kuma a yanzu batada wani saurayi dan babu wanda take kula wa duk kuwa da cewa babu ranar da wani a school ko a unguwa ba zai yi mata magana ba amma ita sam bata da interest, bata jin zata iya soyayya da wani idan ba Adam ba. Ta fahimci duk wannan kame kamen da Hassan yake yi a kanta, tana kuma sane da alkawarin da Baba yayi wa Hassan din kuma tasan babu yadda za'a yi ta ketare maganar Baba musamman im tayi la'akari da abinda ya faru da Ruqayyah, bata so tayi breaking heart din iyayenta ta fama musu ciwon da Ruqayyah ta riga taji musu a zuciyoyin su, dan haka chnace dinta na gujewa auren Hassan guda daya ne shine samun Adam, idan suka sami Adam tana da tabbacin Hassan zai hakura ya bar masa ita wannan kuma zai saka Baba ya hakura da maganar. Amma idan ba Adam ba,bata jin Hassan zai barwa wani. Hassan bai manta da address din gidan su Adam ba, tiryan tiryan suka tafi har bakin gate din gidan sukayi packing, zuciyarsa cike da abubuwa da dama itama tata zuciyar haka. Kamar yadda yayi tsammani gidan looks deserted kamar babu mutane a ciki, ya dudduba ko zai ga mai gadin da suka gani ranar nan amma bai gashi ba sai ya fita zai he yayi knocking ko yana ciki, a lokacin aka bude gata din gidan sannan wata mota ta fito. Macece a cikin motar, tayi packing kusa da su Hassan sannan ta fito ta koma tana locking gidan. Daga Sumayya har Hassan sai da suka yi mamakin ganin yarinyar, kamar an tsaga kara ita da Adam, ko ba'a fada ba kana gani kasan ciki daya suka fito. Sumayya ta bude kofar motar da sauri ta fito, a lokacin da yarinyar take kokarin komawa cikin motar ta, Sumayya tace "Assalamu........ excuse me" yarinyar ta tsaya, hannunta daya rike da handle din mota tana kallon Sumayya sama da kasa tace "hi" Sumayya tace "dan Allah muna tambaya ne, Adam.....amm Joseph muke nema" tana kallon yadda expression din fuskarta ya chanja tace "and who are you if I may ask" Sumayya tace "am his friend, munyi secondary school tare, naji labarin ya bar gida kuma sai naji kamar ance ya dawo shine nake son in ji ko gaskiya ne" yarinyar ta kalli Hassan sannan ta kalli plate number din motar tace "Kaduna. Ba a Kaduna yayi secondary school dinsa ba ai" Sumayya ta rasa me zata ce sai tace "dan Allah......please, just tell me idan yana nan. Is he okay?" Yarinyar tace "he is fine alright, amma ba zaki ganshi ba. Cos baya North and he is never coming back to North, haka Daddy yace, duk family sun koma can nima dan ina karasa school ne shi yasa nake nan" Sumayya ta hadiye wani abu da bata san yaa makogwaronta ba sai yanzu tace "can you at least give me number wayar da zan same shi? Am worried about him" yarinyar ta girgiza kai tace "kune fa, irin kune kuka makala masa addinin ku kuka asirce shi ya bar mu, gashi nan har yau ana ta fama dashi har yanzu bai dawo dai dai ba, how can I just get you together again? If you are truly worried about him ai na gaya miki he is Okay, har an karba masa transfer dinsa ma ya koma school, they are both okay shi da girlfriend dinsa daya tafi da ita" Sumayya ta daskare "girlfriend?" Tace "yes, that beautiful lady daya tafi da ita" sai kuma ta lura da yanayin Sumayya sannan tace "ohhh, ko kema wata girlfriend din tasa ce?" Ta danyi dariya tana girgiza kai tace "he was double dating kenan, amma daga dukkan alama yafi son waccan tunda ya tafi da ita ke ya barki without even a phone number to call him with" daga nan ta bude motarta ta shige ta ci taya tayi tafiyarta. Sumayya ta jima a gurin a tsaye har sai da Hassan yazo yace mata "lets go" sannan ta dago fuskar tadata jike da hawaye tana kallonsa, bata ce komai ba ta bude mota ta shiga shina ya zagaya ya shiga suka juya. Tun da suka shiga mota ta rufe fuskar ta da hijab ta cigaba da kukanta, bai kulata ba shi kuma ya cigaba da driving dinsa. A hanya ya samu bakery ya siya musu snacks da lemo da ruwa ya ajiye mata a kusa da ita ya cigaba da tukin motarsa. Taci kukan ta ta koshi sannan bacci ya dauke ta. A haka har suka kusa shiga Kaduna sannan ta farka ta rarrashi kanta ta goge hawayenta sannan yace "he is fine, alhamdulillah, he is still a muslim, alhamdulillah" ta gyada kai tace "yes, alhamdulillah" sai yace "zancen girlfriend din nan zata iya kirkira ta gaya miki dan kiji haushi" ta sake gyada kai tace "karya take yi, na sani, bashi da wata budurwa karya take yi. But still it hurts me that yana nan lafiya kalau har ya koma school amma be neme ni ya gaya min cewa yana lafiya ba, ni ban damu da wai wani abu da yake tsakanin mu ba, abinda nafi damuwa dashi shine lafiyar sa at least dan hankali na ya kwanta kuma....." Yace "yanzu kin sani ai, hankalin ki ya fara kwanciya?" Sai tayi shiru bata bashi amsa ba. Yace "Sumayya shi aure rubutacciyar kaddara ce, matar mutum kaddarar sa ce, idan Adam mijin ki ne dole sai ya zo daga duk inda ya tafi ya aure ki, idan kuma babu aure a tsakanin ku duk kukan da zakiyi duk neman da zakiyi masa ba ba zai aure ki ba ko da kuwa kun hadu din. Idan kuma shine kaddarar ki sai kin aure shi kamar yadda na auri twin sister dinki. Allah ya riga ya rubuta sai munyi aure kuma sai mun haifi yaya har uku da ita. Haka zalika idan da rabon ke ma sai na aure ki, maybe har da zuri'a a tsakanin mu, to babu yadda zamuyi sai hakan ta kasance tunda wani baya auren matar wani kamar yadda wani baya haihuwar yayan wani" Jin yayi shiru yasa tace "Baba ne yake son wannan hadin" yace "Baba, da Inna da Aunty" ya kalle ta yace "da ni" tayi sauri ta dago jajayen idonta tana kallonsa sai ya daga kafada yace "yes, nima ina so, ke kadai kika rage yanzu, amsar ki kadai muke jira" tana girgiza kanta tace "nayi wa Ruqayyah alkawarin ba zan taba auren ka ba" da mamaki yace "Ruqayyah kuma? Yaushe kuka yi wannan maganar da ita?" Tace "ba yanzu bane ba, tun lokacin kana neman auren ta ta ji Baba yana baka shawarar ka aure ni ka rabu da ita, ranta ya baci a lokacin, and I promised her ba zan aure ka ba saboda in kwantar mata da hankali" Hassan yayi mamakin halin Ruqayyah, wato har labewa tayi taji maganar su da Baba, wato wannan shine dalilin rufa rufar hali da tayi tayi masa tana nuna masa ita ta kirki ce, ya tuno da lokutan da tayi kokarin bata Sumayya a gurinsa, yace "I don't think a yanzu dai akwai wani alkawari da yake kanki tsakanin ki da Ruqayyah. Mai yasa ba zaki bamu chance ba? Idan ninba mijinki bane ba babu yadda zanyi in aure ki ko da kuwa duk duniya suna son hakan. Just give us a chance muga inda Allah zai kaimu akan wannan maganar. Tayi shiru tana tunani. Me yasa ne mutanen da tayi trusting the most sune sukayi hurting dinta the most, Ruqayyah, yanzu kuma ga Adam. Few months ya rage mata ta kammala karatun ta, ta san kuma tana gamawa Baba zaiyi mata aure ko da Hassan ko kuma da wani daban maybe ma wanda bata sani ba, kuma ance the devil you know is better than the angle you don't know, ballantana kuma Hassan is not a devil dan tun lokacin da yana neman Ruqayyah har zuwa auren su da zaman auren nasu ita dai a iyakacin abinda ta sani bata san yana da wani babban aibu ba, duk da dai ance kowanne mutum tara yake bai cika goma ba. Besides, tana son ta farantawa iyayenta rai. Yayi packing a kofar gidan su ya juyo yana kallonta yace "me kika ce? Zaki bamu dama ko kuma in hakura" ta sunkuyar da kanta tana jin wani iri a zuciyarta, wannan wani decision ne da zaiyi affecting rest of her life, amma kuma kamar yadda yace in ita ba matar sa bace ba bazai taba auren taba. Tace "na amince, zan bamu dama muga inda Allah zai kaimu". And so it happened.... Ba wai soyayya ce Hassan sukayi da Sumayya ba amma akwai kulawa da mutum ta juna da aminci sosai a tsakanin su, duk wani abu daya shafe ta yana tsaye akai haka ita ma take yi a nasa affairs din. A hankali suka fara zama abokan shawarar juna musamman a harkar business dinsa wanda yanzu yake kokarin kammala ginin estate dinsa na biyu yayinda ita kuma take final exams dinta. A lokacin ne ya nemi permission dinta na turowa neman aurenta kuma ta amince masa. A take yayi wa Aunty magana wadda ba zaka iya tantance wanda yafi murna tsakanin ta da inna ba, ita ma nan take ta aika Gombe magabatansa suka zo suka tafi Zariya neman auren Sumayya, sai dai a nan ne aka fara samun matsala inda yan uwa da abokan arziki suke ganin rashin dacewar auren nasu musamman wadanda basu san abindaya raba Hassan da Ruqayyah ba. "Ta yaya zai auri Hassana ya sake ta bayan ta haifa masa yaya ta samu nakasa sannan kuma ya auri hussainar ta? Wannan wanne irin cin amana ne?" Yan gari kuma sai suka dauka da gulma "dan ta samu nakasa shine yayi mata saki uku ya bata gida da kudi a matsayin cin hanci, sannan kuma ya koma zai auri yar uwarta sunkuma iyayen saboda kwadayin kudi suka bashi ita" Yes, haka rumour din mutane yake, abinda kaji most of the times ba shine abinda yake gaskiya ba. There is more to it than you know. But wannan bai hana komai faruwa ba saboda su immediate family dinsu sunsan ainahin abind ya faru kuma su suka fi kowa son wannan hadin musamman iyayen su da suke ta saka musu albarka tate da fatan alkhairi duniya da lahira. Ba'a saka wani dogon lokaci ba kamar yadda Hassan ya buƙata, watanni uku aka saka bayan kammala jarabawar su Sumayya, wannan ma kuma dan Hassan yana bukatar lokacin gyare gyare-gyaren gida ne. Yana son yayi renovating gidansa completely dan ya cire duk wani traces na memory din Ruqayyah. Duk abinda yake gidan sai da aka fitar dashi sannan aka chanjawa gidan fasali yadda komai sanin da kayiwa gidan ba lallai ne ka gane shi ba yanzu idan ka ganshi. Dakunan kasa duk an rushe su sai aka mayar da palukan guda biyu, da nasa da nata, kowa kuma sai aka yi masa stairs din sa a palonsa zuwa samansa, a saman kuma sai aka hade palon sannan aka yi dakin yara a saman. Ta yadda in yayi baki babu ruwanta dasu ita ma inta yi baki ba zasu hadu bama. Wannan karon Baba ya dage shi zaiyi kayan daki, wannan yasa Hassan ya bude hannu sosai a wajen kudin aure da kudin sadaki dan ya taimakawa Baban ba tare da ya nuna hakan a bayyane ba. Aunty ce ta siyo lefe kamar yadda tayi lokacin auren Ruqayyah, dai dai gwargwado kamar yadda akayi na Ruqayyah. With that, komai ya gama kammaluwa ranar daurin auren kawai ake jira. *Neighbors* Hassan ya fitar da kudi masu dan kauri ya bawa Sumayya wai ko zata yi wasu events haka, amma sai taki karba tace ita babu abinda zata yi, sai yaji bai ji dadin haka ba tunda shi yasan ita din mai son kashe kudi a biki ce, sai yayi tunanin ko dan bata son sa ne ya saka ba zata yi ba? Sai ya bawa Zulaihat ta kawo mata kuma ta roke ta on his behalf ta karba, ita kuma sai ta karba din dan bata son ayi ta jayayya musamman tunda ya saka Zulaihat a ciki. Sai bayan Zulaihat ta tafi sannan ta kira shi tayi masa godiya yace "ko kefa, har na fara tunanin ko laifi na ne ya shafi bikina" tace "wanne laifi kayi kuma? Kawai dai babu abinda zanyi dasu ne shi yasa" yace "duk son ki da biki kuma sai a naki zaki ce ba kya so" tace "haka ne ina son biki, ina son ayi ta hidima haka da mutane ayi ta abubuwa amma ba hakan yana nufin ni ina da ra'ayin shiryawa da kaina ba. Kuma ni bani ma da kawayen da zanyi wa wata hidima" yace "ina kawayen ku? Wadanda kika gayyato da wancan bikin?" Baya son ambatar sunan Ruqayyah a duk lokacin da suke tare da Sumayya saboda baya son ya tuna mata tsohon matsayin sa a gurin ta. Tace "wai da bikin Ruqayyah? Ni ban san su ba fa, ita ta nemo abin ta, duk kawayen mu ma na school kin gayyatar su tayi tace basu kai matsayi ba" yayi shiru yana cihe baki, he thought as much, but so yake ya tabbatar, ya sake cewa "ohh na dauka naki ne ai, tunda naga ke ce kirjin biki a lokacin, harda yi min text din in kara muku kudin biki" ya danyi dariya "shi yasa nayi mamaki yanzu da kika ce ba kya so" ta bata rai kamar yana ganin ta tace "wanne text? Wanne kudi?" Tun kafin ya bata amsa yasan inda maganar ta dosa, ya fahimci Ruqayyah ce tayi masa text da number din Sumayya dan ta cigaba da yaudarar sa da kyawawan halaye, what more ne Ruqayyah tayi wanda bai sani ba? Sai yaji yana jin tsoron sanin wannan amsar. Yayi saurin cewa "forget about it, ki bar maganar kawai, and saboda ina son in faranta miki duk abinda kika shirya zanzo" tace "a'a fa, kayi zamanka kawai, babu abinda zanyi sai walima tare da few friends dina shikenan, sai abinda zasu yi a gida kawai" A dole ya hakura ya rabi da ita duk da dai yaso ace ta saki jiki tayi bikinta sosai, amma ita kuma a nata bangaren ta ki yin komai a bikin ne dan bata son maganganun da mutane suke yi akan auren, ta san duk kawayensu na unguwa da na primary da secondary school duk sun san mijin Ruqayyah zata aura dan haka duk ba zata gayyace su ba dan kar suzo su kara mata wani takaicin akan wani, kawayenta na jami'a kadai zata gayyata suyi walimar su a nutse inda Inna Ade da kanta zata yi hosting walimar ta kuma yi musu wa'azi akan zaman aure a musulunci. Yan uwa da abokan arziki ma dukka are invited dan walimar ita zata yi serving a matsayin yini, bayan ita kuma sai ayi kamu da daurin aure shikenan da dare akai amarya. Ita albarkar auren take nema, tana kuma neman Allah ya bata ikon cin jarabawar ta dan wannan auren ta san shine jarabawarta. Ta kuma daura damarar karbar sa hannu bibbiyu da fatan samum dacewa albarkar biyayyar da zata yiwa iyayenta. Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya inji Hausawa, ranar da aka saka tazo kuma aka daura auren Hassan Aminu Abdullahi da Sumayya Yusuf. Sumayya ta sha kuka kamar ranta zai fita duk dauriyar da ta ringa yi akan maganar amma labarin daurin aure ta yana zuwa kunnenta ta fara kuka, dan wannan labarin shi yake tabbatar mata da cewa tayi bye bye da Adam, ita dashi sai dai wata kaddarar da ita kanta bata yiwa kanta fatan ta dan zata so ace zaman auren su da Hassan ya dore har tsufansu, sai ta samu kanta da tambayar kanta ko yaya Adam zai kalli auren nata in labari ya je masa? Musamman in ya san wanda ta aura din? Shin zai fahimci maganar ko kuma zai saka ta a matsayin cin amana? Kamar yadda tunda aka fara maganar take tunanin Ruqayyah a zuciyarta, shin tasan da maganar ko bata sani ba? Ya zata dauki maganar? Ita ta fi kowa sanin cewa Ruqayyah bata son Hassan, tun sanda suna gida kafin ayi aurenta ta san bata son Hassan kudinsa take so kuma yanzu ta samu kudin, shin zata damu idan taji cewa twin sister dinta ta auri tsohon mijinta uban ƴaƴan ta. How will she reacts? Ai kuwa dai Ruqayyah bata da labari sam dan ita gidanta kamar kango yake, ga shi dai hadadde kayatacce amma kuma babu kowa sai yan aiki, su kadai suke bidirin su a gidan dan ita sai ta kwana biyu ma bata sauko kasa ba dan yanzu saukowar tana yi mata wahala sosai, sai dai da safe a shiga a gyara mata dakunan ta sannan akai mata breakfast, in an gama na rana ma akai mata, duk abinda babu kuma a gaya mata ta bayar da kudi a siyo. Sometimes sai take wondering wai kudin nan ma kamar yan aikin ne suke cinye su dan ko ba komai abincin da take siya duk wata ba ita take cin kashi daya cikin goman shi ba, bata so kuma ta matsa musu kar su tarwatse su barta, ga kuma albashi da take basu duk wata. Wannan yasa kudin da take son tarawa dan ta nemi magani suka gaza taruwa tunda duk wata sai ta fitar da kudin wancan cima zaunen ta tura masa. A ranar da aka daura auren ne bayan tayi sallar magrib tana ta shige da fice a social media, dan yanzu nan ne gurin hirarta a nan ne kawai take ɗebe kewarta sai taga Khadijah ta saka hoton Hassan da Sumayya, a kasan hoton ta saka "Allah ya sanya alkhairi yaya H1, Allah yasa abokiyar tsufaka ce" ta tashi tana murza idonta dan ta tabbatar da abinda idon nata yake nuna mata, ko dak shima idon ya fara samun matsala ne kamar yadda kafarta da kunnenta suka samu? Still dai hoton Sumayyan ta sake gani taci kwalliya irin ta amare tana murmushi duk da dai fuskarta ta dan kumbura kamar tayi kuka sosai, Hassan kuma a gefenta bakinsa har kunne. Ta mike da sauri, tama manta cewa yanzu bata iya mikewa tsaye sai da croches, wannan yasa ta fadi flat akan fuskarta akan tiles din falon, a take bakinta da hancinta suka kama zubar da jini amma ba shine abinda yafi daga mata hankali ba, wayar ta ta sake laluba tana kuma kallon hoton Hassan mijinta uban ƴaƴan ta da kuma Sumayya kanwarta twin sister dinta. Da sauri ta shiga comments taga mutane suna ta addu'ar fatan alkhairi, ta fita ta fara laluben accounts din sauran kannen Hassan, duk sai taga suna ta celebrating abin ba wai Khadijah ce kadai ba. Ta lalubi crutches dinta ta mike da sauri ta bude kofar da zata sadata da valcony din dake hade da palon da take zaune a ciki, ta fita tana leken gidan Aunty sai ta ganshi a cike da motoci, mutane suka ta hada hadarsu, can da nisa ta jiyo wata ta rangada guda. Ta girgiza kanta tare da marin kanta kadan dan ko zata farka daga mafarkin da take yi "no!" Ta fada da dan karfi, it can never be, ta yaya mijinta zai auri twin sister dinta alhalin gata da ranta tana numfashi? Ta yaya haka zata kasance? Ta juya da sauri ta dauki hanyar fita, ba zata iya kirga yawan faduwar da tayi ba kafin ta sauka palon kasa sannan ta tsare yan aikinta da suke zaune rashe rashe a kan kujeru a palo suna kallo tace "bikin wa ake yi a gidan Aunty?" Tayi maganar da karfi tana goge jinin da ya fito daga bakin ta. Duk suka kalli juna sannan suka kalle ta, wai dama bata sani ba? "Ba tambayarku nake yi ba? Bikin wa ake yi?" Saya daga cikin su tace "daddyn su Yusuf naji ance an daurawa aure dazu da safe, amma ban san wa ya aura ba" tayi kokarin damko wadda tayi maganar amma saboda cika crutch din da tayi sai ta tafi zata fadi, suka rike ta "karya kike yi kice baki san wadda ya aura ba, kuna sane baku gaya min ba, kuna sane kuka bari mijina ya auri kanwata" Su dai yan aiki basu ce komai ba dan basu da abin cewa, wannan magana ba tasu bace ba, amma sun san wadda aka aura din dan tun satin da ya wuce ake ta tsegumin abin a tsakanin yan aikin gidajen da drivers da masu gadi, kowa yana fadar albarkacin bakinsa wasu suna ganin kamar hakan ma ba musulunci ba ne ba. Amma ganin ita din wadda aka yi wa rashin kyautawar bata ce komai ba yasa suma basu ce mata komai ba, ashe bata sani ba. Har ga Allah su tausayin ta suke ji dan aganin su karshen rashin adalci anyi mata, saboda ta zama musaka sai mijinta ua sake ta ya raba ta da yayanta sannan ya auri kanwarta? Wannan wanbe irin rashin adalci ne? Jin sunyi shiru yasa Ruqayyah ta tabbatar da maganar, ta tabbatar kuma sun sani, sau ta kwace daga hannun su ta zauna a kasa ta dira hannu aka ta fara rusa kuka da duk iyakacin karfin ta, tasan waye ya kulla wannan abin, tasan Baba ne,dama ai ba tun yanzu yake ikirarin aurawa Hassan Sumayya ba saboda ita baya sonta ya tsaneta, saboda ya fi son Sumayya akan ta, wannan kawai shine dalilin sa ba wai wani abu ba. Ba zasu kyale ta da bakin cikin shakulatin bangaro da suka yi da rayuwar ta ba a matsayin su na iyayenta duk da cewa sun san tana bukatar kulawar su a halin da take ciki amma shine zasu yi mata bi ta da kulli da wannan mummunan lamarin? Ita kuma Sumayya, munafuka, bayan alkawarin da tayi mata shine ta karya ta aure mata mijinta? Wanny shine dalilin da yasa tayi blocking dinta a waya saboda tana busy yaudarar Hassan da nuna masa cewa ita ta Allah ce kamar yadda ta saba yi tun suna yara. Shi kuma Hassan, munafiki, dama can watakila yana som Sumayyan shine ma dililin da yasa yayi sauri sakin ta kuma har saki uku a lokaci daya dan yaje ya hada baki da Baba ya auri kanwarta. Wallahi basu isa ba, sai ta yi maganin su gaba ki daya, sai ta hana su zaman lafiya, wannan auren ba zasu zauna ba. Ta sake jiyo wata gudar, kamar kuma a gidan Hassan, wato gyaran data lura ana tayi a gidan kenan? Ita da taga ana aikin ta dauka siyar da gidan zaiyi shima ya sake yin wata sadakar ashe munafikin aure zaiyi, auren ma kuma twin sister dinta. Tana son ta fita taje ta tara musu mutane akan su kowa ya fahimci irin cin amanar da akayi mata amma kuma bata son fita a yanayin da take ciki, tunda ta sami nakasa ta rasa self confidence dinta, bata son shiga mutane dukda cewa dama can ita ba mai son mutanen bace ba, yanzu kuwa sai take ganin kamar duk wanda suka hadu dashi kallon yamusashshiyar kafarta yake yi. A gidan Hassan kuwa gida ya cika makil da mutane, kowa sai fadan albarkacin bakinsa yake yi a game da irin chanjin da gidan ya samu, ba zata taba cewa wancan gidan bane ba dan komai an chanja masa tsari. Yanuwan Hassan sunje sun dauko Sumayya wadda tasha nasihohi da adduoi da kuma tarin albarka daga gurin iyayenta da duk yanuwan da suka san gaskiyar abinda ya faru. Zuciyarta wata iri take jinta tayi mata wani irin nauyi saboda kukan da tasha, tun safe take kuka har dare, sai dai bata tare da bakin ciki, ita kanta tasan biyayyar da tayi insha Allah ubangiji ba zai barta ta tabe ba, tasan Allah zai sanyaya mata zuciyarta ya cire mata son Adam ya saka mata son mijinta wanda ita kanta tasan shi din already ya fara sonta saboda yadda ta lura yana lallaba ta. Kamar yadda Aunty da hajiyan kano suka kamo Ruqayyah haka suka kamo Sumayya wannan karon ma, karkashin rakiyar gwoggo Habibah da matar kawu Sama'ila har zuwa gidan mijinta, suna shigowa duk da chanjin da akayi wa gidan sai da Sumayya ta tuna da ranar da aka kawo Ruqayyah, ta tuna da kukan da tayi a ranar da yawon da Adam ya tafi da ita har sai da ya ga tayi murmushi sannan ya dawo da ita gidan, ta tuno da yadda ta shigo ta tarra Ruqayyah tana ta gursheken kukan bakin cikin gidan Hussain yafi na Hassan kyau. Sai ta daga kanta tana kallon gidan Hussain, tana jin a ranta cewa yanzu twin sister dinta kuma tsohuwar matar mijinta tana cikin wannan gidan, zasu yi kuma zaman makotaka, a matsayin su na wadanda suka hada miji a mabanbanta lokuta kuma a matsayin su na tagwaye. Aka shigar da ita da kafar dama da bismillah zuwa gidan ta, da fatan sai mutuwa ce zata fitar da ita daga gidan. A palo aka zaunar da ita akan kujera, Yusuf a hannun ta na dama Aminu a hannun ta na hagu ga kuma Hussain akan cinyarta, fuskarta da jikinta gaba ki daya katon farin mayafin ta. Yan uwa ana ta daukan hotuna da ita, masu nasiha nayi masu saka albarka nayi. A lokacin ne suka ji kururuwar Ruqayyah ta shigo, muryarta har ta dashe saboda kuka, "wallahi baku isa ba, karya kuke yi munafukai, azzalumai, maciya amana, almurai, wallahi kunyi kadan ku yi min wannan cin mutuncin" a bakin gate take amma har cikin gidan ana jiyo ta. Nan take jama'a suka dunguma suka fita kwallon ta, masu kokarin bata hakuri suna yi masu tsegumi suna yi. Kokari take lallai sai ta shigo ana riketa, yan uwan Baba dana Inna Ade ne masu kokarin riketa su hana ta shiga ciki yayinda yan uwan Hassan suka zama yan kallo, ita kuma ga babu kafa, ga masifa tana cinta, so take ta shiga ciki ta kalli idon Sumayya, ta kalli idon munafuka. Sumayya tana jin ta amma bata ko motsa daga inda take zaune ba kuma bata bar yaran sun motsa ba suma, amma duk abinda Ruqayyah take fada tana ji, kuma munanan kalaman ta suna taba har cikin zuciyarta. A lokacin ne ta jiyo murya kamar ta Hassan, ita bata san ma yana gidan ba ko kuma kirawo shi akayi ya taho oho. "Ki kama hanya ki fitar min daga gida Hassana, kar ki sake ambaton matata da wata kalma marar dadi idan kuma kika sake wallahi sai na yi miki marin da zaki rasa idanuwan ki bayan rashin kunne da kafa. Waye yaci amanar ki? Ke kika ci amanar kanki, ke kika zabi kudi a madadin ni mijin ki da yayan ki da iyayenki da yan uwanki. Bakin cikin abinda kika yi ya saka babanki ya bani kanwarki ita kuma ta karba saboda ta faranta zuciyoyin iyayen ku da kika riga kika bata. Kin zabi kudi, na baki kudi, me kuma ya rage a tsakanin mu? Menene kuma abinda ya rage wanda zaki zo ki karba a hannuna?" Hassan ya kula ta yabata amsa ne saboda yana son ya wanke Sumayya dashi kansa a idon mutane, yana so ya gaya wa mutane ita ta zabi kudi a kansa ba wai dan ta nakasa bane yarabu da ita ba. Ta yi kokarin kamo hannunsa "mijina, kar kayi min haka, ni na hakura da kudin da Allah kar ka auri kanwata, dan Allah Hassan, wallahi ina sonka, na hakura da kudin ka mayar da ni dakina dan Allah, na gaji da wannan rayuwar Hassan ka tausaya min dan Allah. Yanzu bana son kudin, bama ni nake cin kudin ba dan Allah ka saurare ni mijina. Wai ina son da kake yi min ne? Ta fada cikin matsanancin kuka Yace "so? Wanne irin so kike magana akan shi? Ni wadda naso kuma nake so ba ke bace ba, I fell in love with halayen da nayi tunanin naki ne ashe ba naki bane ba, ashe na yar uwarki ne kika ara kika yafa wa kanki, sai yanzu na fahimci dama can ashe Sumayya nake so bake ba, rabo ne yahada ni da ke kuma rabo ya kare tsakanin mu". Sumayya duk tana jin su, hawaye yana zubowa daga idanunwanta yana sauka akan rigar Hussain da yake kan cinyarta. Bata taba jin Hassan yana fada ba sai yau, ashe dama fada ne dashi haka? Tana ji har hayaniyar ta lafa daga alama an fitar da Ruqayyah daga gidan amma ita tasan this is not the end but the beginning, tafi kowa sanin hali da kuma masifar Ruqayyah tasan tabbas zata dawo ko ba yau ba ko gobe ne. Gwoggo Habibah ta kira Baba ta gaya masa abinda ya faru ta roke shi ida ya yarda su taho da Ruqayyah gida sai yace "itace tace zata taho? Ta amince da duk sharudda na? Idan ba haka ba ko kofar gida na ban amince ta zo ba" Ruqayyah taji Abinda Baba yace, sai ta saki hannun gwoggo Habibah ta shige gidan da take kira da matsayin nata a ra ta tana mamakin karfin hali irin na Baba da har bayan wannan abinda yayi mata sannan yace wai ta koma gidan shi, ba san cewa ita a yanzu hanyar da ake bi aje gidansa ma ba zata bi ba. Lissafin da take yi na komawa gida in ta samu lafiya ma yanzu babu shi, sun gama nuna mata karshen kiyayya dan haka su rike soyayyar su ita kuma xata rike rayuwarta. Duk wani ragowar string da take ji yanarike da dangantakar da take tsakanin su yanzu ya tsinke. Da ta shiga gidan ma bata iya ta hau sama basai tayi zamanta a kasa, kukan ma ta daina yi sai kunan zuciya, bata taba tunanin tana son Hassan ba sai yau, sai data ga shi a matsayin mijin wata, watan ma kuma twin sister dinta. She just can't imagine, zuciyarta ba zata iya daukan tunanin Hassan da Sumayya a matsayin ma'aurata suna yin duk irin abubuwan da ita da Hassan din suka yi a da ba, the bedroom things, yanzu kuma sai yayi da Sumayya? Da tace ba zata iya kisa ba, now she is not sure ......... Sumayya tana zaune har mutane suka yi ta mata sallama suna tafiya, yanzu duk wanda bai san dalilin rabuwar Hassan da Ruqayyah ba ya sani ko ma ba'a san complete dalilin ba amma an san ita ta zabi ya bata kudi ya sake ta. Hussain already yayi bacci a cinyar ta, sai ta dauke shi a kafadar ta ta tafi dashi sama ita da Zulaihat, sauran kawayensu duk sunyi musu sallama sun tafi musamman saboda ganin dan hargitsin da aka yi sji yasa basu tsaya siyan baki ba. Sumayya ta saka Zulaihat ta nuna mata dakin yara a saman, ta nuna mata sannan ta nuna mata nata. Ta shiga tana kallon tsarin dakin, sam baiyi kama da na Ruqayyah ba, kayan Ruqayyah sunfi tsada amma ita a idonta sai taga nata kayan sunfi kyau kuma sun dace da ita sosai. Ta kwantar da Hussain akan gado ta sannan ta koma da niyyar tahowa da Aminu da Yusuf sai Zulaihat tace mata "a ina kike tunanin zasu kwana? Wannan din ma ba lallai Aunty ta bar miki shi ba. Sai kin gama cin amarci tukunna za'a kawo miki shi" ta fada da sigar tsokana. Sumayya ta marairaice "dan Allah kinga yayi bacci, kar a tashe shi kansa yayi ciwo ki tafi dasu Aminu kawai, a barshi shi yayi baccin sa anan" Zulaihat tace "ni dai babu ruwana, zan tafi dasu amma in aunty ta lura baya can na san zata aiko a dauke shi" Sumayya tace "ba zata lura ba ma" a haka sukayi sallama Zulaihat ta kama hannun twins suna ta bacin rai su a gurin mommy zasu kwana, suka tafi. Ta koma sama dakinta ta shiga ta zauna a kan gado ta saka Hussain a gaba tana kallon sa, amma ba wai shi take kalla ba zuciyar ta tana saka mata urin rayuwar da zata yi a gidan nan tare da Ruqayyah a matsayin makociyarta, da kuma rayuwar da zasu yi da Hassan a matsayin miji da mata. Bata an kara ba taji an bude kodar dakin an shigo, ta dago kai tana kallon Hassan shima daya tsata yana kallon ta, ta sunkuyar da kanta kasa tana shafa kan Hussain daya sauke ajjiyar zuciya ya cigaba da baccin sa, Hassan yace "ina kawayen naki?" Tace "sun tafi. Kai ina abokan ka?" Yace "sun tafi" sai ya karaso ya zauna akan side drawer yana kallon ta, ita kuma bata kalle shi ba sai kirjinta da yake dukan tara tara. Ya kalli Hussain yace "shi wannan me yake yi anan?" Ta kara jawo Hussain jikinta tace "yayi bacci ne, shine nace a bar min shi ya kwana anan" ya girgiza kai, "ki ce in koma in bude kofar gida kenan, dan na tabbatar Aunty sai ta aiko an dauke shi" Sumayya tace "ba zata lura ba, dan Allah ka barshi ya kwana anan dan Allah" ya bita da kallo, a tsorace take sosai, sai kara kankame Hussain take a jikinta kamar zata tsaga kirjinta ta saka shi a ciki. Sai ya mike tsaye yana kallonta yace "shikenan, in kwanan nasa anan zai faranta miki" ya danyi faking hamma yace "sai da safe" *The Sixth Wave* Kanta yana kasa tace "Allah ya bamu alkhairi" tana jin sa har ya fita ya rufo mata kofa sannan ta dago kai tare da sauke ajjiyar zuciyar da take ta rikewa. Ta tashi tayi locking kofar sannan ta dawo ta dauki Hussain ta kaishi toilet sannan ta dawo dashi ta kwantar dashi itama tayi shirin kwanciya duk da tasan ba bacci zata iya yi ba, kukan Ruqayyah dazu ya taba ta, ta tina rabon da ta ganta tun ranar da Hassan ya sake ta and she ca only imagine abinda Ruqayyah take ji a zuciyarta yanzu. Duk da tasan ba son Hassan Ruqayyah taje yi da gaske ba amma still dole auren su da Hassan sai ta taba zuciyarta sosai. Ta kwanta tana tuna Adam, sai kuma ta daina tausayin Ruqayyah dan ita ta jawo komai, idan da Adam yana nan da babu yadda za'a yi Baba ya hana shi ita ya bawa Hassan dan tasan Baba yana son Adam kamar yadda yake son Hassan. Ruqayyah ce tayi sanadiyar rabuwarsu dan haka this will be her price to pay. Ta dauko wayarta tana going through hotunan su kamar yadda take yi kullum, sai data gama gani sai kuma ta koma farko tayi marking all sannan ta danne delete tana jin zafin abin a ranta amma tasan hakan shine dai dai hakan shine zai kara taimaka mata gurin cire shi daga zuciyarta. Bayan ta gama gode hotunan sai ta koma kan messages dinsa da take ta ajjiyar su suma ta goge su sannan ta shiga contact ta goge number dinsa, tasan ko zai dawo ma he won't be using that same number again. Sai data gama sannan ta tashi tahe ta dauro alwala tazo ta tayar da sallah, tana gayawa ubangijin ta bukatar ta, and for the first time tun bayan rabuwar su da Ruqayyah sai ta samu kanta da yi mata addu'a tana neman Allah ya shiga lamarin ta ya huce zuciyarta ya daidaita tsakanin su. Sai da taji bacci yayi mata nauyi har bata iya bude idonta sannan ta kwanta, saboda bata son ta kwanta tayi ta tunani, tana kwanciya kuwa tayi bacci abinta. Da assuba ta tashi tayi sallah sannan tayi wanka sai ta koma ta cigaba da baccin ta dan sai yanzu gajiyar bikin ta ke sauko mata, duk da dai ba wani dogon biki tayi ba. Motsin Hussain ne ya tashe ta, ta farka ta ganshi ya kafe ta da ido yana ta murna wai yau sun kwana tare, daga nan sai ya saka ta a gaba da zance a dole ta mike duk da baccin ba isarta yayi ba ta ja shi xuwa toilet tayi masa wanka yana tayi mata hira "mommy wai yanzu kim dawo gidan daddyn mu ne? Anan zaki ringa kwana ko? Kin daina kwana a gidan Inna?" Tace "eh" yayi tsalle yana bata toilet din da kumfa "nima na daina kwana a gidan Aunty ko? Tare zamu ke kwana anan da su Aminu ko? To ina suke? Ko a dakin mu suka kwana? Daddy ya kawo mu jibi ya nuna mana dakin mu ya saka mana gado a ciki kowa da nasa yace banda fada. Kinga Daddy shi fada yake yi mana idan munyi fitina, Aunty kuma sai ta bamu sweet tace mu fita backyard muyi ball. Ni ban iya ball ba faduwa nake yi......" Haka yayi ta zuba kamar fanfon daya lalace ita dai tana tayi masa dariya har ta gama masa wankan tayi masa brush da alwala ya fito ita kuma ta tsaya ta gyara toilet din sannan ta biyo bayansa ta tarar ya jawo drawers din dakin wai yana neman kayansa. Ta goge masa jikinsa sannan ta mayar masa da kayan da ta cire masa saboda bashi da wasu sannan ta saka shi yayi sallah, ya duddungura abarsa duk rabi wasa, ita kuma ta shirya cikin riga da skirt na atamfa da suka karbi jikinta sosai, ta gyara fuskarta dai dai gwargwado sannan ta gyara dakin shima ta dauki Hussain suka fito yana ta yi mata complain din yunwa yake ji "a gidan Aunty ina tashi aunty take bani tea nake sha ba ta yi min wanka sai nasha tea" suka fito tana lakuce masa hanci "ninkuma a gidana sai mutum yayi sallah yayi wanka sannan zai sha tea, in luma mutum bainyi abinda nace ba to zan mayar dashi gidan Aunty" ya kankame ta yana kwabe fuska "ni nafi son gidan nan, nafi son mommy na da Daddy na" ta rike fuskarsa a hannunta tana murmushi tace "nima ina sonka sosai sweetie pie" Sai taji gyaran muryar Hassan a bayanta, suka juya da sauri, Hussain ya zame daga jikinta ya ruga gurinsa "daddy yau akan gadon mommy na kwana kuma banyi mata fitsarin kwance ba kuma tace a nan gidan zata ke kwana kuma bata bani tea nasha ba sai tayi min wanka" Hassan yayi dariya yana shafa kansa yace "kai, da kai da parrot ban san wanda yafibwani surutu ba. To gaya min gadon mommy da dadi?" Hussain yace "da dadi mana, wankan ta ma da dadi, dama tana yi min wanka in naje gidan Inna shi kuma Baba ya siyo min Mango" Sumayya tace "Hussain baka gaishe da Daddy ba fa kake masa zance haka" Hussain yace "lah na manta, daddy good morning. Zaka bani tea insha?" Hassan ya dauke shi yace "zan baka, amma sai kayi shiru ka barni mun gaisa da mommyn ka tukunna" Ya juya yana kallon Sumayya sai taji babu dadi, sai taji Kamar bata kyauta ba data fito babu hijab dan bata jin ta taba tsayawa a gabansa babu hijab. Ta dan rage tsaho ta gaishe shi ya amsa yana studying fuskarta "anya kuwa kinyi bacci sosai? Ko bakunta ce?" Ta danyi murmushi tace "nayi bacci fa" yace "amma ba sosai ba ko?" Tayi shiru, yace "kar ki damu, babu dodo a gidan nan" Hussain daya kwantar da kansa a kafadar Hassan yace "Daddy akwai dodo a gidan aunty, yana nan acikin closet aunty Zulaihat tace duk wanda ya kuma shiga ciki ya buya sai dodon ya kama shi kuma tace yana da manyan hakora da zai cinye mutum dasu kamar haka" ya fada yana kokarin demonstrating a wuyan Hassan, Hassan ya sauke shi yana cewa "a'a kar a fara cinyewa ta kaina a cuci amarya ta" Sumayya ta danyi dariya tace "ban san lokacin da bakin yaron nan ya bude haka ba, maganar sa tafi shekarun sa yawa, biyu da rabi yake yanzu fa" Hassan yace "sai next month ma zai yi two and a half years. Yawo be dashi da surutu da kirinki irin na mai sunan shi. Dama kamar su daya" Sumayya tabi Hussain daua fara tsalle tsallen sa a corridor din da suke tsaye tana tuno late Hussain tace "Allah yasa yayi halinsa" Hassan yace "banda iyayin" tayi dariya, sai ya bi ta da kallo yana jingina da jikin bango, ta hadiye sauran dariyarta tana kokarin kamo hannun Hussain yace "kinyi kyau sosai" Hussain ya juyo yace "yes mommy kinyi kyau, amma na jiki kyau" ta juyo tana kallon Hassan sai ya girgiza kansa yace "too late, har iyayin ya dauko". Tana kokarin hada wa Hussain tea sai ga breakfast an kawo musu daga gidan Aunty, a tare da breakfast din akwai Aminu da Yusuf hannayensu ruke da kayan su wai sun taho ana gidan zasuyi wanka. "Mommy ce zata yi mana wanka yau, bama son wankan Aunty Zulaihat" Zulaihat ta dungure musu kai, "kar Allah yasa ku so din, kafin dai ayi daran akayi kwande" Sumayya tayi murmushi "tuba suke yi auntyn yara" sai ta jasu suma zuwa dakinta tayi musu wanka ta shirya su sannan suka dawo suka tarar Hussain ya saka Hassan a gaba da surutu shi kuma sai loda masa abinci yake yi yana ci yana kara wani zancen. Suka hadu sukayi breakfast tare as a family, sai Hassan yaji bai taba jinsa complete ba irin na yau dan tun da yaran suka fara tashi basu taba samun sun zauna sunci abinci da iyayen su ba. Ko kafin su rabu da Ruqayyah ma mostly kafin ya tashi ta tura su gidan aunty. Suma kuma yaga abin yayi musu dadi sosai musamman yadda Sumayya take tarairayar su kowa yana zuba shagwabarshi son ranshi. Tare suka gyara gurin da suka ci abincin, har da Hassan shima a dauke plate Sumayya tana tayi masa dariya sannan ya bisu kitchen yana kallon ta tana wanke kayan da suka bata yaran kuma suna tayata kifewa, har layi suke hawa in aka bawa wannan yayi drying plate ya kai cikin drawer sai a bawa wannan cup shima yayi drying ya kai, a haka har suka gama ita bata san Hassan video yake tayi musu ba sai data lura sannan ta rufe fuska tana dariya, sai ya dawo bayan ta ya tsaya sannan ya jera yaran a gabansu yayi musu selfie, Hussain yana ta gyara riga yana dago kai wai dan yayi kyau kuma kar a yanke shi. Wannan hoton shi ya dora a dpn sa kuma shine abinda Ruqayyah ta tashi dashi a yau. Dama jiya a palo bacci ya dauke ta akan carpet, shima kuma dan ance bacci barawo ne amma da babu yadda za'a yi ta iya yin bacci a yadda take jin zuciyarta. Bata taba shiga bacin rai irin na wannan karon ba, bata jin ko rashin kafarta ya yi affecting dinta kamar yadda auren Hassan to her twin sister yayi affecting dinta. Taji duniyar gabaki daya ta fitar mata a kai, taji tana son mutuwa ko zata huta da ganin wannan bakin cikin amma kuma bata san abinda zata tarar in taje can din ba, a lokacin ta fahimci frustration na matan da suke kashe mazajen su idan sunyi musu kishiya, kishiyar ma da babu dangin iya balle na Baba ballantana ita d mijinta ya auri twin sister dinta, anya kuwa an taba yi wa wata irin cin mutuncin da akayi mata? Kuma iyayenta? Wadanda suka haife ta? Ta tabbatar cewa Baba ne ya hada wannan kwamachalar saboda dalilin shi baya son aurenta da Hassan dama tun farko, Inna kuma ta zabi tabi bayansa akan ta goyi bayanta ita yarta, ita kuma munafukar Sumayya ta amince, tasan kuma dalilin da yasa Sumayyan ta amince va dan komai bane ba sai dan ta rama rabatan da tayi da Adam. Sai taji nadamar abinda tayi wa Adam yazo mata, da ta sani ta barshi yayi ta auren Sumayya tunda ita Sumayya bata fahimci gata tayi mata ba, ita tana so ta hana ta auren wanda nan gaba zata zo tayi nadama shine ita kuma ta huce by auren mijinta? Uban yayanta? Tabbas da ace zata iya kama Sumayya a yanzu da sai tayi mata abinda duk su biyun sai sunji a jikinsu. Tabbas sai tace ina ma ta zabi ta bata ran Baba taki auren Hassan akan auren Hassan da ta zabi yi a yanzu. Sai taji tsanar family dinta a ranta, tsana mai tsanani kamar irin tsanar da take tunanin suna yi mata, tunda zasu iya hada auren Hassan da Sumayya. Yan aikinta babu wanda ya zauna ya tattashe ta, sannan dama ita babu wanda yake zuwa gurinta ballantana ya rarrrashe ta. Tabbas a ranar tunanin lahirar ta ne kawai ya hanata kashe iamta cikin dare. Sai da assuba sannan ta ja jiki ta hau sama tayi sallah ta kuma kwamta akan sallayar bacci ya dauke ta. Tana farkawa kuma ta farka da wannan mugun hoton da Hassan ya saka a dp dinsa. Yayanta data haifa da cikinta, mijinta, data sha wahala kafin ta samu, wai duk sun zama na twin sister dinta bayan gata nan da ranta a duniya. Wannan hoto yafi saran maciji dafi a zuciyar Ruqayyah, yafi kuma kibiya tsini saboda sukar da yayi mata. Kamar yadda ta kwanta da kuka haka ta tashi da kuka tana neman Allah ya dauki ranta ta huta, to me zata yi musu ne ita yanzu? In ma tace zata yi musu wani abu dan ta rama abinda suka yi mata ta yaya zata yi musu bayan ita yanzu sauka kasa ma daga dakin da tayi wa kanta a sama ba karamin tashin hankali bane ba. Sharrin data saba yi wa mutane kuma yanzu ta yaya zata yi musu bayan babu wanda yake sonta hatta iyayen da suka haife ta. Sai ta tashi ta ja kofar dakin ta rufe, locking herself in, dan bata son ganin kowa bata son kuma jin maganar kowa yau, duk da cewa ma tasan babu wanda zai zo gurinta sai yna aikinta, sai kuwa kawayen ta da sukan dan leko su gnta musamman in rashin kudi ya motsa musu. Sai dai kuma tana kwanciya taji kukan jaririn nan ya cika gidan gabaki daya, har amsa kuwwa gidan yake yi da kukan nasa. Ta saka hannayenta ta toshe kunnuwan nata tare da rufe idonta"dan Allah kayi hakuri ka rabu dani, kayi hakuri dan girman Allah" amma rufe idon yasa ga ganin gawar Minal a idon nata, kamar kullum ta zuba mat ido tana kallon ta. Tayi saurin bude idon nata taba numfashi sama sama, har wani duhu duhu take gani da wani jiri da yake fibanta duk da cewa a kwance take, ta mika hannu ta bude side drawers ta jawo sleeping pills dinta da kuma robar ruwan da tane ajiyewa permanently a nan saboda bata iya bacci in bata sha ba. Ta mike zaune tare da bude robar maganin ta debo a hannunta, sai dai maimakon ta debo biyu kamar yadda take sha kullum sai ta devi guda biyar sannan ta watsa su a bakinta ta bisu da ruwa. Ranar through out Hassan yana gida bai fita ko bakin gate ba, kawai duniyar ce take yi masa dadi duk da cewa ba wai angwancewa yayi da Sumayya ba amma shi gani yake ko haka ta barshi ta biya shi. Yana jin dadin yadda suke yi da yaran, da shima yadda take yi masa, duk da yasan bata sonsa amma ko a fuskarta ba zaka ga alama ba. Yan uwansu na Gombe suka zo yi musu sallama zasu tafi, ta durkusa har kasa ta gaishe su tare da rufe fuskarta tana jin kunyar tsokanar ta da suke yi, sai ya tuna da aurensa da Ruqayyah rana irin ta yau yadda ta tari yanuwansa, sai yayi mamakin kansa ta yadda bai lura da komai ba a lokacin sai ynazu. Da zasu tafi Sumayya ta hau samt ta bude lefenta ta debowa yammatan kayan kwalliya masu yawa a leda, manyan kuma ta basu turaruka, suka yi mata godiya kowa yana saka mata albarka sannan ta kama hannun twins dinta suka raka su har bakin gate. Suna ta tsokanar yaran da cewa sunga gidan amarya sun guji Aunty saboda ita tsohuwa ce, Hussain yana ta zuba musu surutu da iyayi har suka tafi. A daren ranar Sumayya duk yara ukun ta jere akan gadonta tace duk anan zadu kwana, Aunty ta aiko a tafi dasu suka hada kai suka yi ta zunduma kuka su bazasu koma gidan aunty ba, Hussain har da bada sakon a gaya wa aunty ta aiko masa da kayan sakawarsa da kuma kayan wasan sa. Haka Hassan ya saka su a gaba ya zuba tagumi yana kallon yadda suka kankame Sumayya suka bacci, exhausted, saboda kiriniyar da suka yi tayi. Ya gaji da tsaiwa ya kuma gaji da hamma, yana lura da Sumayya ba bacci take yi ba idonta biyu amma ta rufe ido sai yace "zan tafi in kwanta" ta dan bude ido kadan tace "sai da safe" ya tsaya yana kallon ta sai tayi sauri ta mayar da idonta ta rufe. Ya juya a hankali ya kashe musu fitila ya fita, ba zai taba takura mata ba, yasan tana bukatar lokaci kuma zai bata as much time as possible dan yafi son duk abinda zai faru a tsakanin su ya faru da son ranta ba wai bisa tursasawa ba. Washegari ma suka tashi kamar jiya, sai dai yau yara suna da school dan haka da wuri Sumayya ta tashe su tayi mudu wanka tana tunanin yadda zata taso Hassan ya karbo musu uniform dinsu a gidan Aunty sai gashi Aunty ta aiko musu har da abinci a lunch boxes dinsu. Dan haka Sumayya ta saka musu kayan ta hada musu tea duk suka sha sannan sai ga Hassan ya sauko dakansa yace zai kaisu duk kuwa da cewa drivern su yazo already, but yafi so ya kai su da kansa dan yanzu fatherhood din yake ji sosai. Sun tafiya ta koma saman da sauri ta shiga dakinsa, ta yaba da tsaftar dakin sosai dan ba zaka taba cewa dakin namiji bane ba ta gyara masa gadon ta share ta wanke toilet ta fitar da kayan wanki sannan ta koma bata dakin shima ta gyara. Kafin ya dawo har ta kusa gama gyaran gidan, sai ya dage wai lallai sai ya taya ta aikin ta hana shi yakinyarda sai ta bashi duster ya fara goge goge, tana tayi masa dariya, ita sai taga abin mamaki namiji da aiki, hannun sa kamar yayi wa duster din girma, sai shi kuma ya fara bata labarin yadda yake aikin gidansu sanda yana saurayi "Hussain baya komai sai bata guri, ninake yin kusan komai a gidan lokacin su Hassana basu girma ba aunty kuma bata da yan aiki. Har wanke wanke nayi wa aunty. A haka na saba, ni ina enjoying gyaran gida ma sosai sai inji kamar wani responsibility ne daya kamata inyi" Tare suka gama komai har kitchen ta gyara ta hada wa Aunty kayan abincin da ta aiko musu dashi jiya, kamar hadin baki tana fitiwa dashi ana aiko musu da wani sai ta bayar da na jiya aka tafi dashi sannan ta dauko musu plates suka zauna a kasa akan carpet ta zuba masa zata zuba nata yace sai dai su ci tare, sai taji wani iri dan jiya ma da daddare haka ya dage ta hada musu abinci gabaki daya har yara a tray suka ci gabaki daya, but wancan da yara, wannan kuwa su biyu ne kawai. Amma bata son yi masa musu, tayi wa kanta alkawarin ba zata ke yi masa musu ba dan haka ta saka chokali a nasa suke ci tare, ya lura a takure take sai ya fara yi mata hira, a lokacin ta lura da wani abu a tare dashi, da wahala yayi dogon sentence ba tare daya ambaci sunan Hussain ba, sai ta tuna da tata twin din, ko a wanne hali take ciki? Ta dauka zata dawo da safe amma shiru har gari ya sake wayewa. Bayan sun gama ne ya hau sama ita kuma ta gyara gurin da suka bata. Bai jima ba ya sauko yace mata zaije gidan Aunty "zanje gurin Hussain". She was confused sai daga baya ta tuna a gidan aka binne Hussain, kabarin sa zaije kenan. Sai takara jin tausayin sa sosai, lallai shi din ya hadu da jarabawowi da yawa a rayuwa, lallai shi din abin a tausaya masa ne, lallai yana bukatar mai faranta masa rai a yanzu. Bayan ya tafi ta koma dakinta tayi wanka ta shirya tsaf da ita ta bade kanta da turare, sannan ta hada kayan wankinsa data dauko da nata dana yara da suka cire da towels din da suka yi amfani dasu duk ta je toilet din yara inda taga washing machine sabo a ciki, ta dauki manual dinsa taga yadda ake amfani dashi sannan ta dauko detergent din da ta gani a toilet dinsa ta wanke kayan tsaf ta matse su, ta zagaya baya ta backdoor inda tasan akwai igiyar shanya tun Ruqayyah tana gidan ta shaya kayan ta dawo palo tadauki wayarta tana duba messages din da kawayenta da kuma yan uwan da basu samu damar zuwa bikin ba suka turo mata. A lokacin ne aisha ta shigo, tsohuwar yar aikin Ruqayyah ce tun tana tare da Hassan, Sumayya ta tashi zaune tana kallon ta ganin tashin hankali a rubuce a fuskarta. "Aisha lafiya? Aisha ta fara hawaye "Aunty Sumayya dan Allah ki zo, Aunty Ruqayyah tunda ta kwanta jiya da safe har yanzu bata tashi ba. Kofar dakin arufe munyi ta bugawa bata bude ba" Wani abu ya dunkule a kirjin Sumayya, ya tokare mata hanyar da numfashi yake shiga hunhun ta. Ta mike tsaye tana kallon Aisha "tun jiya? Tun jiya da safe fa kika ce? Kuma ku baku yi tunanin ya kamata ku fada ba?" Tace "dama ita kadai taje zama, mun dauka idonta biyu ko dan bata son a dame tane ya sa ta rufe kofa, sai da muka ga duk abincin da muke kai mata bata tabawa sannan muka fara buga kofar kuma bata bude ba" ta share hawaye, "muna tsoron tayi mana fada ne shi yasa muke gudun damunta" Cikin karkarwar hannu Sumayya ta dauki wayarta ta fara neman number din Hassan, shine a kusa shine namiji shi ya kamata ta fara kira, kuma shine zai bata izinin fita taga halin da yaruwarta take ciki. Sai dai tasan yana gurin kabarin Hussain ko zai iya daukan waya? Bugu daya ya dauka "hello Noorie" bata kula da sunan daya kirata dashi ba tace "dan Allah kazo ka taimaka min" yadda yaji tashin hankali a muryar ta haka shima nashi hankalin ya tashi. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Me ya faru?" Cikin rawar murya ta fada masa abinda Aisha ta gaya mata, bai jira komai ba yace ta fita ta shiga gidan, ta kira mai gadi ko duk wani namijin da yake gidan tace inji shi yace su balla kofar dakin, shima gashi nan tahowa. Kusan a tare suka je gidan, sai dai da yake shi namiji ne yafi ta doguwar kafa sai ya wuce ta zuwa saman, sanda taje already yana kokarin balla kofar amma being kofar da Hussain ya saka sai taki balluwa. Da sauri ya fita, a lokacin Sumayya ta gama rikicewa kuka kawai take yi tana buga kofar amma babu ko alamun Ruqayyah a ciki, a hargitse ya shiga dakinsa ya binciko key din part din Hussain da ya ajiye sannan ya dawo ya shiga part din Hussain ya nemo spare keys din gidan gabakidaya sannan kuma suka fara neman key din dakin da Ruqayyah take ciki. A ransa yana cewa gidan da Ruqayyah take so fiye da shi shine zai zama ajalinta in tayi wasa, da kyar suka samu wanda ya bude kofar dakin sannan suka shiga. Tana kwance a kan gado, idanunta a rufe, a gefenta da robar ruwa da sleeping pills. Da sauri Sumayya ta tafi kanta tana jijjiga ta, sai taga kamar ba Ruqayyan ta ba, kamar wata ramammiya mai kama da Ruqayyah. Hassan ya karaso yana janye Sumayya daga jikin Ruqayyah sannan a hankali ya dora hannunsa a gefen wuyanta yana so yaji heartbeat. Can ya jiyo shi da nisa, she is alive but barely. *Unstable* Sorry for the typos Ya mike tsaye tare da ja da baya, sannan ya dauko wayarsa yayi dialing number din doctor dinsu, ya fita yana waya dashi, wannan ya sa Sumayya ta koma da sauri gaban Ruqayyah ta saka hannun ta a inda Hassan ya dauke nasa tare da kara dan yatsanta na daya hannun a kofar hancin Ruqayyah, ta jiyo heart beat din sannan taji hucin numfashin ta a hannunta amma bayan wannan babu alamar rai a tare da ita. "Ruqayyah! Ruqayyah ki tashi dan Allah, ki tashi muyi magana dan Allah" tana jim Hassan ya dawo dakin yace "doctor yana zuwa yanxu" bata ce komai ba sai ya karaso ya dauki robar maganin yana karanta wa yace "maganin bacci ne, overdose tayi maybe" Sumayya ta gyada kai tana share hawaye tace "na gane shi, tun sanda ina jinyar ta a asibiti shi take sha kafin tayi bacci, bata iya bacci tsorata take yi duk dare" sai kuma ta fashe da kuka, tausayin halin da Ruqayyah take ciki take yi sosai, wannan wacce irin rayiwa ce yar uwarta ta dora wa kanta. Tana tuno yarintar su da irin burikan Ruqayyah amma bata taba tsammanin cewa zata kai ta ga haka ba, bata taba tsammanin kaddarar su zata zama haka ba. Ta fara kallon fuskarta tana shafa kanta a hankali tana kiran sunan ta, ga dai kaya masu kyau a jikinta amma shi jikin bashi da kyau, ta rame fiye da tunanin Sumayya, dama kuma ita Ruqayyah bata da jiki sosai. Ta mayar da idonta kan kafarta marar lafiya taga yadda kafar ta kara motse wa ta yamushe kamar ma jini baya zuwa kafar. Sai kawai ta fara karanto mata adduoi tana tofa mata a haka har doctor din ya karaso suka shigo tare da Hassan, suna shigowa Hassan ya dauki robar maganin ya mika wa doctor din suka yi maganganu sannan Hassan yazo ya kama hannun Sumayya ya daga ta tsaye sannan ya jata suka fito waje. Sai da suka fito palo sannan ya saki hannun, tayi sauri ta saka hannun a cikin hijab tana mummurza shi tana sunkuyar da kanta kasa, ya jingina da jikin bango yana kallon ta yace "wai dan na rike hannunki shine kike wannan abin?" Ta girgiza kai da sauri, amma a ranta tasan haka ne, ita wani namiji bai taba kama hannun ta ba kuma bata taba zaton cewa Hassan mijin twin sister dinta shine zai zama na farko ba. Da tago kai suka hada ido taga har yanzu ita yake kallo yana murmushi, sai taja hijab dinta ta rufe fuskarta, ita bata san ya akayi yake tsokanar ta har yake murmushi ba bayan ga halin da Ruqayyah take ciki, yana nufin wai shi yanzu bashi da wani concern akan Ruqayyah? Ko babu komai ai sister dinta ce kuma uwar yayan sa. Tace "me Doctor din yace?" Ya dan daga kafada yace "yace zata warke, zai dai duba ta yanzu amma yana tunanin sai an kai ta asibiti sunyi flushing system dinta, in akwai sauran maganin duk zasu fitar mata sannan su saka naya drip sabida ta samu nourishment tunda ta kwana ta wuni bata ci abinci ba sannan kuma a jira sanda zata farka" Sumayya ta gyada kai hawaye yana tarar mata a idonta tace "me yasa zata yi overdose?" Ya daga kafada yace "Allah masani, maybe ta gaji da duniyar ne" Sumayya ta girgiza kanta da sauri tace "no! She will never do that. Ni nasan Ruqayyah fiye da kowa" yace "really? I don't think so" ya mika mata hannu "ki zo mu tafi gida" sai ta girgiza kai "ina so in zauna a gurinta, in za'a kaita asibitin ma ina son in bisu can din" ganin kallon da yake mata ya saka ta sunkuyar da kanta tace "in ka amince". Yayi ajjiyar zuciya, tabbas yasan akwai soyayya da shakuwa sosai a tsakanin Sumayya da Ruqayyah, amma shi yanzu Ruqayyah tsoro take bashi, yana gudun kar ta cutar masa da matarsa akan kishin da take iƙrarin tana yi duk da yasan cewa na karya ne, ita da bakinta ta gaya masa bata sonsa, ta aure shine saboda tana tunanin mai kudi ne shi. But, ba zai raba hanta da jini ba sai ya tafi ya zauna akan kujera yace "we will wait together then. Bazan taba barin ku tare daga ke sai ita ba" ta biyo shi itama ta zauna tana kallon sa tace "wai kana tunanin Ruqayyah zata iya cutar dani? She is my twin sister, she will never hurt me" yace "she already did hurt you, not once not twice, wanda na sani ma kenan, Allah ne kadai yasan sau nawa ta cutar da ke, bana fatan ta sake wani. I won't wait har sai ta sake kafin in raba ku" Tace "nasan akan Adam kake wannan maganar, ita a nata juyayyen tunanin tana ganin kamar taumako na tayi data raba ni da Adam" ya daga mata hannu yace "mu bar maganar Adam please" tayi mamakin yadda ya hade rai, wato kishi yake yi kenan ko mene ne? Amma sai tayi shiru ta bar maganar kamar yadda ya bukata. Suna zaune sai ta dauko wayarta zata kira Inna ta sanar da ita sai ya hana ta "menene amfanin gaya mata? Hankalin ta ne zai tashi kuma Baba ba zai barta tazo ta ganta ba, ki bari kawai in kin tabbatar ta warke sai ki gaya mata daga baya yadda hankalin ta ba zai tashi ba" ta gyada kai cikin fahimta, tabbas Hassan ya san halin baba kuma yasan cewa in dai har Ruqayyah bata yi abinda yace ba to ba zata shiga gidan sa ba kuma Inna ma ba zata shiga nata gidan ba ballantana shi. Suna nan zaune doctor din ya fito ya sauka kasa sai gashi ya dawo da kujerar marasa lafiya, Sumayya ta tashi tataimak masa suka dora Ruqayyah akai sannan suka kama shida Hassan suka sauka da ita kasa, doctor din yana cewa "akwai problem gaskiya, I tot zan iya farkar da ita tun anan amma abin ya gagara, dole zamu tafi da ita za'a yi mata some tests. Nan take hankalin Sumayya ya kuma tashi, a dole Hassan ya dauke ta a mota suka bi baya ambulance din da doctor din yasa Ruqayyah a ciki suka tafi asibiti suna bayar da sakon cewa idan yara sun dawo su tafi gidan Aunty. A asibitin anyi duk abinda za'a yi dan ganin an tashi Ruqayyah daga bacci amma abin ya gagara, suna can suna ta abu daya har yamma har aka yi sallar magrib sannan ta farka tana jinsu suna ta maganganu can nesa, babu hearing aid dinta dan haka bata fahimtar abinda suke cewa, sai ta bude idonta a hankali ta sauke shi akan Sumayya da take tsaye suna magana da wata nurse akan tests din da doctor din ya rubuto wa Ruqayyah, yawancin su akan lafiyar kwakwalwar ta. Ruqayyah ta mayar da idonta ta rufe sannan da dan karfi tace "me kike yi anan?" Sumayya ta juyo da sauri tana tahowa inda take sai Ruqayyah ta daga mata hannu tana yi mata alamar ta dakata daga inda take "babu ni babu ke. Maci amana. Kamar yadda kika ce babu ke babu ni saboda adam to nima babu ni babu ke saboda Hassan" Sumayya ta tsaya daga inda take ta kasa karaso wa ballantana tayi kokarin kare kanta. Duk da tasan ko tayi maganar ma Ruqayyah ba jinta zata yi ba tunda babu hearing aid a kunnenta. Ruqayyah ta dafa gado ta mike zaune, tana jin jikinta wani iri sannan kuma kanta yana wani mugun sarawa kamar zai tsage biyu, ga cikinta kamar an yashe duk abinda yake ciki. Idonta da yake cike da tsana akan Sumayya, bata taba tunanin akwai ranar da zata zo wadda a cikin ta zata tsani Sumayya ba amma sai gashi yau ranar tazo. Ta dauke kanta ta daina kallon ta cikin tsawa ta kuma cewa "ki fita daga nan nace. Bana son ganin ki ba tsane ki na tsani kowa na tsani komai, bana bukatar ku babu ni babu ku kar ku sake nema na kar ku sake zuwa inda nake kar ku saje tunanin ma akwai wata alaka a tsakani na da ku" Sumayya ta karasa da sauri ta kama hannunta sai ta ture ta da karfi, dai dai lokacin da Hassan ya shigo, kallo daya Ruqayyah tayi masa ta juyar da kanta gefe hawaye masu zafi suna zubowa daga idon ta. Gani tayi yayi mata kyau, irin kyan da bata taba tunanin yana dashi ba, irin kyan dabata taba gani a gurin sa ba sanda yana nata sai yanzu da ya zama ba nata ba tukuna. Sanda yana nata bata kallon sa, wadansu take kalla shi yasa bata taba zama ta yabi surar sa ba, kamar yadda gidan Hussain kafin ya zama nata take ganin sa kamar shine aljannar duniya yanzu kuma daya zama nata sai ya koma mata kamar makabarta, sanda bata da kudi kuma sai ta ke kallon masu kudi a matsayin wadanda basu da wani problem a duniya, yanzu kuma da tayi kudin sai taga a yanzun ne ma problems suka fara mata. Kaicho.... Hassan yazo da sauri ya rike Sumayya yana janye ta daga kusa da Ruqayyah, ya saka hanu ya goge mata hawayenta a kunnenta ya rada mata "let's go home". Har sun kai bakin kofa Sumayya ta sake juyowa ta kalli Ruqayyah, sai suka hada ido and she can see the heart break da yaje idon Ruqayyah and her heart went out to her. Har suka je gida basu yi magana da, suna tsayawa sai Sumayya ta roki Hassan ta shiga gidan Ruqayyah ta saka aisha ta hada kayan da ta san Ruqayyah zata bukata a asibiti ta hada da hearing aid dinta sannan ta saka driver ya tafi da ita asibiti ita kuma Ruqayyah ta dawo gida. Dakinta ta wuce direct tayi alwala tayi sallah sai ta samu kanta da kuka a sujjadar ta tana rokawa Ruqayyah dai-dai to a rayuwarta. Sai data idar sannan ta shiga toilet tayi wanka. Tana fitowa suka hada ido da Hassan a zaune a bakin gadonta, a guje ta juya ta koma bandakin tare da rufo kofa, dariya ta kama Hassan, dama yana sane ya zauna dan yaji motsinta a toilet din yasan kuma zata fito babu kaya. Sai yaja pillow ya kwanta kafafuwan sa a kasa hannayensa a rungume a kirjinsa idonsa akan toilet din. Ya san dole zata fito shi kuma yana nan yana jira. Ta jima a tsaye tana mayar da numfashi, Inna lillahi, yau ya zata yi? Ta yi ta dube dube babu wani abu da zata rufe jikinta dashi, towel din nan na jikinta shikenan sa dan ko kaya dama bata shigo dasu ba da towel din ta shigo. Ta jingina a jikin kofar tana tunanin abinda zata yi, ta jima a haka sannan ta leka ta ramin key ta hango shi yana nan a kwance akan gado. Ta dafe kanta tana jin ana kiraye kirayen sallar ishai, ga sanyin toilet din ya fara ratsa ta tasan kuma in tayi wasa yanzu zata kama zazzaɓi. Ta danyi knocking kofar toilet din sannan ta dan bude kadan. "Dan Allah yaya Hassan ka miko min zani da hijab" ya gyara kwanciyar sa yace "saboda me?" Tace "saboda Allah. Wallahi sanyi nake ji, zanyi mura da zazzaɓi" yace "to ki fito mana ki shirya, ni ina ruwa na dake" taji kamar zata yi kuka tace "ba zan iya shiryawa a gaban ka ba, dan Allah ka tafi dakin ka" yace "nan ma dakina ne, dan dakin matata ne" tace "ai Allah nace maka. Kaga ana kiran sallah zaka rasa jam'i" yace "shikenan sai muyi tare, in mukayi tare ma zamu samu ladan jam'i ni dake" Ta dora goshinta akan kofar idonta a rufe tana jin sanyi yana ratsa ta tace "dan Allah dan Annabi daddyn Hussain ka fita, wallahi sanyi nake ji" ya mike zaune yana kallon toilet din yace "to ke me yasa ba zaki fito ba sai na fita, ni ba mijinki bane ba?" Tace "kunyarka nake ji Allah, ba zan iya fitowa babu kaya a gaban ka ba" yadda tayi maganar kamar zata yi kuka yasa ya ji tausayin ta, ya mike yai kamar zai shiga toilet din, yaga ta rufo kofar da sauri har da murda key sai yayi dariya yace "na fita to. A shirya lafiya, amma zan dawo". Sai data leko ta tabbatar ya fita sannan ta fito da sauri taje ta murda key din dakin. Ta jingina da jikin kofar tana ajjiyar zuciya, a ranta tana rokon courage daga gurin ubangiji. Ta shirya cikin plain doguwar riga budaddiya sosai mai adon stones a wuyanta kuma hannayenta. Mai kawai ta shafa sai turaruka a jikinta amma ko hoda bata shafa ba ta saka hijab tatayar da sallah, tana idarwa ta ji ya murda kofar amma ya jita a rufe sai ya wuce. Ta tashi ta nade sallayar sannan ta dan kara turare a jikin ta sannan ta bude kofar sau suka hadu dashi yana hawowa da basket din abinci a hannunsa, daga dukkan alamu daga gidan Aunty aiko musu. Ta karba daga hannunsa da sauri, ya juya yana cewa ki kai mana dakina" sai ya juyo kuma yace mata "yau dinner in bed zamuyi" daga haka ya koma kasa da sauri. Tayi kamar zatayi kuka amma sai ta wuce ta tafi dakin nasa ta ajiye basket din tare da budewa tana ganin abincin da yake ciki amma sai taga gasashshiyar kaza ce da aka yayyankata aka kuma bade ta da yaji, tana budewa kamshinta ya cika dakin gaba kidaya. Ta bude dayan food flask din shi kuma ta tarar da farfesun kifi mai kyau, daga dukkan alamu yanzu aka sauke shi dan turiri yake yi sosai kamshinsa yana chakudewa tare da na kazar. Taji an bude kofar dakin an shigo, sai tayi sauri ta rufe ta mike tsaye tana rarraba ido, ya bita da kallo sannan ya kalli basket din yace "kwadayi ko? Daga baki sako sai kizo kina budewa?" Taji kunya ta kamata sai ta wayance da cewa "ina yarana? Ka aika a dauko su please" ya zauna yana ajjiye drinks din hannunsa a kan table yace "kina da number din Aunty ai, ki kirata kice ta dawo miki da ƴaƴan ki" sai ta tura baki, wato magana ya gaya mata kenan. Ta zauna akan kujera, rnata yana son kifin nan data gani, kuma tana son tayi masa maganar Ruqayyah ta gaya masa abinda nurse ta gaya mata akan case din Ruqayyah, tana so ta gaya masa abinda nurse ta tsegunta mata na cewa doctor yana tunanin Ruqayyah ta hadu da mental related disorder. Amma kuma ta lura tun da aka fara zancen aurensu har akayi har yau kuma bai taba yi mata maganar Ruqayyah ba, bai ma taba ambaton sunan Ruqayyah ba. Shin ita tayi masa ko ta barshi kawai tunda baya so........? Amma mental health din Ruqayyah ai abu ne muhimmanci ko? Amma sai ta kasa samun courage din yi masa maganar. Ta mike zata fita yace "ina zaki? Ki zauna inyi wanka in fito sai in sammiki nama ki ci, dan naga kina ta hadiyar yawu" ta dan bata rai "ni na koshi, ni bana cin nama dama, baka sani bane ba" ya fara cire kayansa, ta rufe idonta, yace "amma ai kina cin kifi ko?" Ta girgiza kai "shima bana ci" ya zo gabanta ya tsaya "to me kike so ki ci?" Idonta yana rufe tace "bana son cin komai, bacci kawai nake so inyi" Numfashin sa taji a fuskarta, tayi saurin jan fuskarta baya sai taji yayi dariya, sautinsa dai dai fuskarta amma ta kasa bude idonta sai da taji takunsa ya matsa sannan ta dan bude idon kadan sannan taga ashe babu komai a jikinsa sai dan karamim towel na kugu, tayi sauri ta mayar da idon ta rufe kirjinta yana lugude, bata taba ganin namiji a haka ba, ko a hoto ko a zahiri. Wasu abs data gani a kafadun sa su suka saka yayan hanjinta suka kada, yana shiga toilet ta mike da sauri tana jin kifin duk ya fita daga kanta ta fice ta a hardewa kamar zata fadi. Dakinta ta shiga ta rufe kofa ta kashe fitila sannan ta zauna a kasa ta saka kanta a tsakanin cinyoyinta, nasihohin da akayi ta yi mata na hakkokin miji akan matarsa da kuma hakkokin mata akan mijinta. Bata san tsahon lokacin da ta dauka a gurin ba, ga cikin ta yana kugin yinwa dan abincin rana bata samu ta ci ba tana asibiti gurin Ruqayyah. Kamar daga sama taji an bude kofar dakin sannan aka kunna fitila, ta sake rufe idonta, bata son ta kuma ganinsa babu kaya kamar dazu, sai taji kamshin turarensa sannan ta ji motsin sa ya zo gabanta sannan ta kuma jin hucin numfashin sa a fuskarta, ta sake rintse ido tana cije lebe, sai taji sautin murmushin sa. "Shine kika gudu ko? Ba zaki ci abincin ba?" Ta gyada kai da sauri yace "to ki zo muyi sallah, ai dai ita sallah ba'a koshi da ita ko?" Bata ce komai ba sai ya hura mata iska a fiskarta, ta kara runtse idon, ya mike tsaye yace "ki bude idon ki, na saka kaya ai" ta bude a hankali sai taga ya saka jallabiya, ta danyi ajjiyar zuciya sannan ta tashi ta bishi suka koma dakinsa suka gabatar da sallar sunna ta ma'aurata, suka gabatar da adduoin samun dacewa a cikin zamantakewar su tare da neman zuri'a mai albarka sannan suka shafa. Da kyar ya matsa mata ta ci abincin kadan ta sha lemo, duk da cewa shi kansa yasan bata koshi ba amma tsoro da fargaba sun hana ta ci, daga kwashe kayan abincin kuwa ta makale taki dawowa sai da ya bita ya kuma dawo da ita dakin yayi ta fama da ita akan ko hijab din jikinta ta cire amma taki, sai ta saka masa kuka. Ya sake ta ya hau kan gado ya kwanta tare da cewa "good night" Da sauri ta fita daga dakin ta kuma shiga nata dakin tare da rufe kofa ta jingina da jikin kofar hawate suna bin idonta tana girgiza kanta. Wani bari na zuciyarta yana jaddada mata cewa ba zata iya ba wani barin kuma yana tuna mata da hukuncin laifin da take aikatawa. Tasan ba a son ransa ya kyale taba, kuma da yanayin da yayi maganar kamar wanda yayi fushi, sai ta tuna da abinda ta riga ta sani "duk matar da mijintaya kwana yana fushi da ita akan kin bashi hakkinsa da tayi to Mala'iku zasu kwana suna tsine mata" idan ta mutu a cikin daren nan kuma fa? Menene makomarta? Sai ta juya ta fita, ta koma dakin nasa ta bude kofar ta tsaya a bakin kofa tana kallonsa hasken security light din daya shigo ta taga. Yana kwance ya lullube har kansa da abin rufa, amma tasan ba bacci yake yi ba kuma tasan yaji shigowar ta, sai ta tsaya a gurin bata ce komai ba, sai taga ya bude fuskar sa yana kallonta sai kuma ya bude abin rufar tasa sosai sannan ya miko mata hannu, ta tafi a hankali ta saka hannun ta a cikin nasa sai ya jawo ta kan gadon da hannu daya sannan ya cire hijab din jikinta da daya hannun, sai kuma ya saka hannayensa duk biyun ya rike fuskarta yana kallon cikin idonta a hankali yace "may I?" Ta rufe idonta tare da gyada kanta a hankali, and she felt his lips on hers together with some kind of feeling da bata taba jin irinsa ba a rayuwarta. **********. ************. ************** Washegari da Hussain yazo neman mommyn sa Hassan cewa yayi mommy tayi tafiya sai next week zata dawo, haka ya zauna yaci amarcin sa son ransa su rayan duk sun dauka da gaske tafiyar tayi, sai da sati yayi sannan yaje ya dauko su yace mommy ta dawo, har da tsaraba ya raba musu yace inji ta, su kuwa sai murna. A ranar aunty ta hado musu kayansu gabaki daya suka dawo gidan iyayensu. A ranar ne kuma aka sallamo Ruqayyah daga asibiti ta dawo gidanta bayan gwaje gwaje da akayi mata a karshe likita yayi concluding "mentally unstable". Ya rubuta mata magunguna kuma ya bata shawarwari sannan ya hada ta da therapist din da zata ke gani duk sati. Abubuwan da suke damunta sune rashin bacci, halucination, rashin abokin magana, damuwa da kuma shan sleeping pills din da take yi. Yayi suggesting therapist din ne saboda yana tunanin at least zata samu wanda zata ke yiwa magana tana fitar da abinda yake ranta tana rage damuwarta. Ya bata shawarwarin ta koma gida cikin yanuwanta sai tace masa ita bata da yanuwa duk sun mutu. Sai kuma ya bata shawarar ta nemi abinyi, something to keep her busy yadda kullum in ta tashi she will be looking forward to doing something kuma kafin dare zsta gaji yadda zata fi saurin yin bacci. And she already decided on abinda zata yi, she is going to make money. In mutane ba zasu so ta ba dan Allah to zata siye su da kudi. Tana zuwa gida abinda ta fara yi shine neman number din Umar, yayan Fatima wanda suke partny a H and H sai ta gaya masa tana son shiga business din sosai, tana son ta zama involved a duk al'amuran kamfanin kuma tana son ribar da take samu da share dinta a daina turo mata gabaki daya, ake bata rabi rabin kuma ana sake re investing. Bayan sun gama wayar ta bude kofar valcony tashiga tana kallon duk saura gidajen unguwar a kasanta dan duk unguwar babu gidan da ya kai na Hussain tsaho. Ta danyi murmushi tana lumshe idonta, hayaniyar da taji a barin gidan Hassan ya saka ta juya tana kallon side din, Hassan ta gani hannunsa rike dana Sumayya suna dariya, sannan ga yayanta suna zagaye su da ball a hannun Aminu, bata jin abinda suke cewa amma duk a cikin farin ciki suke. Sai taga Hassan ya cire rigarsa ya bawa Sumayya riko sannan sun fita a guje shida yaran suna ball, Sumayya kuma tana kallon su tana cheering dinsu, duk wanda ya buga yaci zai je Sumayya tayi masa kiss, yaran sai rige rigen ci suke yi amma uban yafi zakewa har sai da yaci ya tafi da gudu gaban Sumayya ya durkusa yana dariya ita kuma tayi kissing dinsa a both cheeks. Ta juya tana barin gurin, ta koma palo sannan ta saka key ta rufe kofar valcony din ta tafi toilet ta jefa key din a cikin toilet tayi flushing. *Home Coming* *Amira ta gode da adduoin ku, ni kuma na gode da fahimtar ku. Allah ya bar kauna ya kuma bar zumunci. Nagode sosai* Washegari Ruqayyah ta fara ganin therapist din da aka hada ta dashi. Dr Mahmud. Shi yazo har gidan ta suka zauna a kasa, he talked to her, trying to get her to talk amma babu abinda tace masa mai amfani har awa dayan da yayi scheduling for her ta kare sai yayi mata sallama ya tafi. Daga lokacin kuma ya cigaba da zuwa duk sati suna zama suna hirata awa daya,a lokacin ya fahimci abubuwa da yawa a tare da ita, na farko akwai abinda da take boyewa a ranta, abinda ba zata bata iya fadawa kowa ba kuma yana tunanin wannan abin shine sanadiyyar shigar ta halin da take ciki, na biyu tana halucination, ma'ana tana gani tana kuma jin abubuwan da basa guri a lokacin, sai dai bai sam yaushe ne ta fara gani da kuma jin haka ba. Ya kuma fahimci tana da high spirit, a never giving up spirit wanda baya jin zata yi giving up akan abinda ta saka a gaban ta kuma a yanzu abinda ta saka a gabanta shine business, sai ya bata shawarwaro tare da kara mata karfin guiwa akan hakan, dan yana ganin hakan sai kara mata mental health dinta wanda a gurinsa shine top priority dan aikinsa kenan. Ita kuma sai ta kara kaimi, ta sake neman Umar akan maganar da suka yi kuma ya nemi su hadu a cikin kamfanin sak ta shirya taje, with crutches and all, for the first time taji bata damu da kallon da mutane zasu yi mata ba cos tana da missing, ta san abinda take so and she is going to get it. So take ta saka duk wadanda suka guje ta su fahimci irin mistake din da suka yi sannan su dawo gareta. Umar ya amince mata a game da harkar H and H, ya bata office dimda zata ke zuwa kullum ko kuma duk sanda tasamu dama, sannan kuma za'a ke briefing dinta na duk abinda yake faruwa a kamfanin. She accepted that, sannan ta karbi copy din duk takardun da suka shafi harkokin H and H ta tafi dasu gida, daga nan ta mayar da hankali sosai wajen karantawa da fahimtar duk yadda al'amurran kamfanin suke tafiya, and then she got enrolled in online business classes, giving it her all, and within a year sai gata ta san komai da yake shiga kuma yae fita daga H and H. A shekara ta biyu sai ya kasance Sau dayawa ma Umar yana bar mata ragamar kafanin tacigaba da juyawa saboda shi yafi mayar da hankali akan sarauta da ita yake so, business kawai yana yi ne dan ya cika aljihun sa but not because yana da interest akai. Ita kuma ta cigaba da investing, sai ga kudi suna ta multiplying kamar an saka musu yeast. A yanzu har bata damuwa da kudin da take biyan mai duba dashi dan bashi da wani yawa a cikin kudin da take samu. Yes, wannan ua taimaka mata sosai gurin rage mata damuwa da yawan tunani, amma har yanzu yaki ya yalwata mata zuciyarta, ga kudi dai har kudi tana samu, ga yalwataccen gida ga kuma yalwataccen account amma zuciyarta kullum a kuntace take jinta. Sai tayi tunanin kadai ci ne, dan haka ta gayyato all her friends, duk wanda take buƙatar gurin zama ta taho ta zauna, wasu ma daga gidan iyayensu suka fandare suka dawo gidan Ruqayyah da zama ita ce cinsu ita ce shansu ita ce komai nasu wai dan kawai tana so su cike wani rami da take ji a zuciyarta amma sai taji ramin yaki cika. Sai kuma ta yi tunanin ko dan nakasar da take da ita ne, sai ta dukufa gurin ganin ta nemo likitan da zai taho daga kasar waje yazo har gidaya duba ta amma ta rasa, ta samu guda biyu sunzo baya ta kashe musu uba kudi amma sai da suka zo suka ganta sannan suka gaya mata ba zasu iya duba ta ba sai da kayan aiki, kayan aiki kuma suna can kasar waje ba zasu iya dauko su su taho dasu ba. Sai dai kawai suyi mata prescribing magani wanda har yau babu abinda yake kara mata. Ita kuma har yau ta kasa taking risk din sake shiga jirgi balle tabi su can. And she misses fita kasashen duniya musamman ida kadaici yayi mata yawa kuma ta gakudi account dinta sai taji babu abinda take so irin ta keta hazo zuwa wata kasar kamar yadda Hussain yake yi a duk lokacin da yayi niyya. A duk tsahon wannan shekaru ukun da auren Hassan, shekaru biyar da mutuwar Hussain, babu moment guda daya da Ruqayyah ta daina jin kikan jariri a kunnen ta, babu kuma lokacin data rufe idonta ba tare da taga fuskar Minal ba, duk kuwa da magungunan da take sha wadanda likitan ta yake ganin zasu taimaka mata but it is getting worst everyday. Sai ya zamanto zuciyarta ta kara bushewa ma yanzu bata jin tsoron abubuwan da take gani da ji. Kullum tana sak ran Fatima zata dawo, tunda akwai chances na cewa she is alive duk da dai rashin ji daga gareta na tsahon shekaru biyar ya saka ta fara kwantar da hankalin ta da tunanin maybe ta mutu da gaske. Ita bacewar Fatima is a mystery agurin ta, dan ita har ga Allah sanda Fatima ta bata baby bayan ta haihu data ta bata bata ji alamar rai a tare da ita ba, wannan shi ya kara mata karfin guiwar yar da jaririn. Amma duk da haka ta yanke wani hukunci a ranta. Duk ranar da Fatima ta dawo, that's in zata dawo din, zata tubure tace ita Fatima bata bata jariri ba, it will be her word against hers tunda babu shaida, babu wanda akayi a gabansa dan haka da wahala alkali yayi convicting dinta. Zargi ne kawai, mutane zasu zarge ta yan uwa zasu kara nisanta kansu da ita amma sai dai suyi tayi, ba zata yi asara goma da ashirin ba, ba zata taba furta abinda tayi ba ballantana ta rasa dukiya da kuma freedom dinta. Yes, wannan shine abinda zata yi. Kanenta maza ne kawai suke kai mata ziyara sometimes, duk da cewa ta fahimci Inna Ade ne take turo su su duba lafiyar ta ba da sanin Baba ba. Tana jin dadin zuwansu sosai duk da bata nunawa amma tana jin dadin yadda taje jin labarin gida a gurinsu, ta fahimci kowa yana lafiya, sannan a gurin su ta ji labarin haihuwar Sumayya, amma duk da yadda suka so su jata ta shiga gidan taga baby sai taki zuwa. Bata jin akwai tsautsayin da zai kaita gidan Sumayya ballantana har taga abinda zai saka zuciyarta ta buga. Wanda ta riga ta gani ma is enough. ***************. ***************. **************** Shekaru uku sun wuce bayan auren Hassan da Sumayya, rayuwa mai kyau suke shimfidawa abinsu tamkar basu da sauran wani problem a duniya. Sumayya ta gama karantar Hassan kuma ta taya yar uwarta bakin cikin rasa miji irin Hassan ta kuma yiwa kanta murnar samun miji irin Hassan. Hassan irin namijin nanne da in suka samu abinda suke so a gurin mace su kan iya zama tamkar bayi a gun matansu. Ta fahimci abinda yake so din kuma, na farko yana son respect, baya son raini ko kadan duk kuwa da cewa yana da wasa da dariya amma yana so a girmama shi, yana son other room sosai da sosai dan baya taba bari ya wuce shi indai ba da wani kwakwkwaran dalili ba, ita ma kuma sai ta fahimci ashe tana so din, dan haka sai suka kara makalewa da manne wa juna ta wannan bangaren. Sai kuma ta fahimci baya son rainuwa kuma ya tsani mita, and she wondered yadda har suka iya rayuwar aure ta tsahon shekara biyu shida Ruqayyah dan ita a rayuwarta bata taba ganin mutum mai mita mai kuma rashin godiya ba irin Ruqayyah. Lallai Hassan ba karamin hakuri ne dashi ba, kuma tabbas ba karamin so yayi wa Ruqayyah ba. Basu jima da aure ba aka yi posting din ta a service, aka tura ta bayelsa, amma haka Hassan ya shige mata gaba har sai da aka dawo da ita nan Kaduna musamman saboda a lokacin tana fama da laulayin ciki. Sai ta fahimci cewa shi din tsayayyen mutum ne irin wanda zaka iya gayawa problem dinka ya tsaya maka har sai kun samu solution. And she wondered yadda akayi Ruqayyah take kiran sa da matsolo. A gurin Sumayya sam Hassan bashi da maƙon kudi kawai dai baya son almubazzaranci, baya son unnecessary spendings, irin mutum ya sayi abu ba tare da yana bukatar saba, ko ka sayi abu kawai dan kaga wani ya siya kai ma sai ka siya dan ace kana da shi, amma kuma duk abinda yake da amfani Hassan zai siya in abundance, dan kayan abinci drinks fruits kala kalan nama har sai tace sunyi yawa kar su lalace. Musamman duk abinda ya fahimci cewa tana so ko kuma yaran suna so to ya ringa siyowa kenan. Kuma ta lura haka yake yiwa su Aunty ma, kafin su nemi abu ya kai musu shi indai yasan suna bukatar sa. Baya sai ya Aunty gwala-gwalai, baya chanja wa kannensa waya duk wata irin yadda Hussain yayi musu but yana kula da dukkanin bukatun su yana tsayawa a duk kanin al'amuran su kamar yadda ya tsaya a auren Nafisa bayan ya tabbatar yayi mata securing aikin da zata mori ilimin ta dashi, babu wanda zai ce marainiya ce dan Hassan ya cike gurbin uba a gurin ta kuma a yanzu yana kan cike wa a wajen Zulaihat dan ya matsa mata number akan ta fito da miji haka nan tunda har sun gama service dinsu. A bangaren Hassan kuma bayan abinda ya faru tsakanin sa da Ruqayyah bai taba tsammanin zai samu farin ciki a rayuwar aure ba amma sai gashi ya samu more than abinda yayi tunani ma. Sumayya ta kawo haske sosai cikin rayuwarsa shi yasa ya makala mata suna "Noorie". A yanzu ne kuma ya gaskata maganar Baba, a yanxu ne kuma ya fahimci mistake dinsa na danganta wani category na mutane da munanan halayya. Tabbas auren sa da Ruqayyah tamkar lesson ne ubangiji ya koya masa kuma ya dauki darasi sosai, sannan kuma aurensa da Sumayya shi kuma sakayya ce Allah yayi masa saboda yadda ya bude hannayensa duk biyun ya karbi kaddarorin rayuwarsa tare da gode Allah a bisa niimomin sa. Gasu dai Sumayya da Ruqayyah tagwaye ne, uwa daya uba daya, ciki daya mahaifa daya, sun kuma sha nono daya a lokaci daya, sun rayu a guri daya, an yi musu tarbiyya iri daya sun kuma samu ilimi iri daya, hatta cup da plate din da suka ci abinci sanda suna tasowa iri daya ne gashi kuma kamannin su daya amma banbancin halayyar tamkar banbancin dake tsakanin annabi da kafiri ne. Kamar ace positive and negative sides of a battery ne. Shine zai bada wannan shaidar sama da kowa tunda shine wanda yasan in and out of them, shi yayi zaman aure da duk su biyun a mabanbanta lokuta. Shekarar farko ta bayan aurensu Allah ya azurta su da haihuwar da namiji wanda suka saka wa Abdullahi. Tabbas, a farkon auren su har zuwa yanzu ma da suke shekara uku da yin aure sukan fuskanci financial problems, saboda Hassan yanzu ba ya aikin da zai ke samun albashi duk wata, sannan auren da yayi da kuma auren da yayi wa kanensa har biyu Khadijah da Nafisa ya dakatar da harkar gine ginen sa, estate din nan ta farko dai har yanzu ita ce, har yanzu bai samu ya kammala ta biyun ba, kuma gidajen yearly suke biyan sa rent ba monthly ba dan haka dan ma dai shi mai kulawa ne da lissafi a komai shi yasa har suke samun condition din da suke ciki a yanzu. Akwai lokacin da har sai da ya siyar da motar sa yake hawa ta haya saboda rashin kuɗi, amma fa iyalinsa basu taba zamada yunwa ba. Sai Sumayya ta bashi shawarar kafin ya kammala wannan ginin ya yi shaguna a gaban estate din sai ya saka musu monthly rents yadda duk wata zai ke karbar wani abu, sannan itama kuma ta nemi ya amince mata ya nema mata aiki amma sai yaki yadda da maganar aikin duk da cewa ya ji dadin waccan shawarar data bashi ta shaguna, dan haka sai yace mata ya bata aiki a karkashin sa a matsayin personal adviser dinsa, zai ke bata salary duk wata, ita kuma taki yarda tunda already yana bata kudin da suke isarta yin duk bukatun ta. Shi kuma sai yaji babu dadi, dan yasan yadda Baba yasha wahala akan karatun ta ya kamata ace iyayenta sun mori ilimin ta amma sai dai shi baya son ace matarsa kullum sai ta fita gurin aiki, baya son abar tarbiyyar yayansa a hannun yan aikin gidadan haka sai ya mayar mata da matsayin ta zuwa secretary dinsa sannan yayi mata office dinta anan cikin gidan su inda anan ne suke ajjiyar duk wasu takardu da duk wasu bayanai da suka shafi business dinsa, ta ce mai kula da komai. Sai ta karba saboda tana ganin aikin zata yi ai ba wai bada shawara kadai ba, kuma tasan idan ma bata karba ba dole zai dauki wani ko wata a wannan matsayin. Kiri kiri Hassan ya hana ake kai su Aminu gidan Ruqayyah, yace "I don't want them getting confused su kasa gane wacece mommy din a cikin ku. In sun girma sun fahimta da kansu zasu je but not now" a dole Sumayya ta amince da hakan ba dan zuciyarta tana so ba sai dan bata taba yi masa musu, ko abu taga yayi va dai dai ba bata musa masa directly sai dai indirectly ta kawo masa shawarar da zata rushe waccan maganar ba tare da ya fahimci abinda tayi ba. Wannan kenan............... Bara mu leka Kano. Shekaru biyar bayan mai martaba Sarkin Kano tare da yayansa sunje sun binne konanniyar gawar mace da ciki, wadda suka yi tunanin ta yarsu kuma yaruwarsu gimbiya Fatima ce. Experience din da har yanzu yake fresh a zuciyoyin al'ummar gidan musamman mahaifanta. Ana tsakiya da hidimomin yau da kullum kamar yadda aka saba, sai ga baki sunzo a airport taxi, tun daga bakin gate aka tsayar dasu ana tuhumar su da su fadi daga inda suke kuma wa suke nema. Hakan ya faru ne saboda lura da akayi da cewa ba hausawa bane ba, duk da cewa ba za'a iya fadin direct wanne addini suke bi ba. Na mijin da yake gaba tare da driver ne yayi Magana "Sunana Adam, ina son ganin maimartaba sarki" Kallon da dogarin ya watsa masa ne yasa yayi saurin chanja maganar sa "ko kuma wani a cikin manyan gidan wanda yake kusa" Dogarin ya kuma bata rai, gashi dai hausa yake yi amma yafi kama da inyamuri. "Me zaka yi musu in ka gansu?" Adam ya dauke kai, dama yasan haka zata kasance, shi yasa ya nemi da su fara aiko da sakon zuwansu kafin suzo dan shi baya ciki da wulakanci, zai iya fita yanzu ya wanke dogarin nan da mari. Ya hadiye bacin ransa, wai me yasa kananan ma'aikata suke da wulakanta mutane ne bayan su kuma manyan nasu ba haka suke ba. Cikin bacin ra yace "kwadon su zanyi in cinye. Ina ruwanka da abinda zanyi musu, ji nake kai aikinka shine isar da sako kuma na baka sako ka tsaya kana bata min lokaci da tambayoyi marasa amfani" shima dogarin ya kufula "an bata maka lokacin, aikina ba isar da sako bane ba tunda ni ba masinja bane ba, aikina shine kula da lafiya da dukiyar mai martaba tare da iyalinsa, kai kuma kayi kama da marasa gaskiya shi yasa na tsare ka na hana ka shiga, kuma ko duk garin nan zasu taru wallahi ba zan barka ka shiga gidan nan ba" Adam ya dube kofa ya fita "amma lallai zaka shirya yin azumi uku kenan na rantsuwar da kayi dan shiga gidan nan kamar nayi ne na gama ko kana so ko ba ka so, ko zaka bude kofa ko ba zaka bude ba ni dai sai na shiga, and I will be talking to the emir while you will be fasting saboda rantsuwar da kayi" dogari ya daga kafada yace "kai ka san me kace a karshe. In ma zagi na kayi to kai ma haka. Ni dai kofa ce ba zan bude ba sai dai ka fadi abinda zaka fada anan, in naji mai ma'ana ne in aika a fada a ciki, in marar ma'ana ne kuma in koma ciki in barka anan kayi ta maganganun ka kai kadai" Adam yace "Ni ai da masu gidan nazo inyi magana, ma'ana mamallaka gidan ba masu saka ja da koren kaya suna tsayawa a kofar gida ba" dogari yace "in ma baki da fari ne mun saka din, gida ne dai ba zaka shiga ba" A hankali aka sauke glass din tagar baya na motar, sannan kyakykyawar fuskar Fatima ta bayyana. Tana nan babu abinda ya ragu daga kyawunta sai ma fari data yi saboda chanjin weather, sai kuma rama da tayi sosai, ga wanda ya santa zai iya cewa ta kankance ta koma kamar sanda take secondary school, yanayin takuma yayi kama da yanayin marar lafiya. A tare da ita akwai wata mata wadda kana ganin ta kasan ita ta haifi Adam. Ta kare wa dogarin da suke cacar baki da Adam kallo, ta gane shi tsaf dan rayuwarta a gidan su bata daga cikin abubuwan data manta. For years, shine dogarin da yake gadin gate din farko na gidan, sannan tace "Auwal dogari" ya juyo da sauri jin an ambaci sunansa, suka hada ido sai ya makale a yadda yake, baki a bude yana kokarin mayar wa da Adam magana, tace "dan Allah ka bude mana kofa mu shiga" ya rufe bakin sannan ya mitstsika idonsa da sauri sannan ya sake kallonta, anya tsufa bai fara kama shi ba kuwa? Wannan kamar gimbiya Fatima fa. Gimbiya Fatima data mutu shekaru biyar da suka wuce. Cikin rawar murya yace "gimbiya Asma'u?" Kanwar Fatima ce wadda suke yanayi. Fatima taji zuciyarta ta amsa da jin sunan kanwar ta, taji ta kosa da taga iyayenta da yanuwanta, ta kosa taga dan jaririn ta. Tace "ba Asma'u bace Auwal, Fatima ce" sai ya saki bulalar dogarai da take hannunsa, ya sake matsowa yana kuma lekawa cikin motar sannan kuma sai ya zabura kamar wanda akayi wa allurar karfi ya fita a guje, bai bude kofar gate din ba sai ya wuce cikin gidan a guje, ba zai bari wani ya riga shi kai wannan maganar cikin gida ba. Sai dai yana shiga gate din gida ya fara kururuwa "jama'a ku zo ku taya ni gani, gimbiya Fatima ce gata can a cikin mota tare da inyamurai. Jama'a kuzo ku tayani dubawa ko ido na ne yake yi min gizo" nan take mutane sukafara cincirindon zuwa inda yake wasu kuma suna wucewa bakin gate, sai dai daga zarar sun ga abinda ya gani sai su koma da baya suna neman suma wadanda zasu gayawa. Ganin haka yasa Adam ya tafi da kansa ya bude gate din gidan sannan drivern ya shigo da motar suka zarce zuwa gurin da aka tanada dan packing din motocin baki. Suka bude suka fito su uku sannan Adam ya biya drivern, yana tuna lokacin da shima yake a matsayin drivern taxi. Fitowar Fatima ya saka sauran mutane suka karasa hargitse wa, wannan hayaniyar ce Adam baya so shi yasa yayi plan din neman audiance da mai martaba sarki ko wani mai fada aji direct yadda za'a yi maganar a tsanaki. Baya son hayaniyar tayi affecting Fatimah, not now, not when ta fara samun lafiya. Suka fara tafiya, Fatima tana yi musu jagora dan babu abinda ta manta a tsarin gidan nasu, Maman Adam tana rike da ita, supporting her, irin rikon da akeyi wa marasa lafiya. A haka suka doshi cikin gidan, duk inda suka wuce sai mutane su dare su basu hanya, wasu kuma su fita a guje. Har suka isainda Adam ba zai iya wucewa ba sai ya dakata yana jin kamar ya bisu amma babu dama dan haka yace "Mama" maman sa ta juyo tana kallon sa sai yace "take care of her please" sai tayi murmushi ta gyada masa kai ba tare da tace komai ba. A cikin gida, a dan karamin shamakin da yake tsakanin bangaren Hajiya Fulani mahaifiyar Fatima da kuma Hajiya umma abokiyar zamanta, kamar kullum da yamma, yau ma suna zaune tare a karkashin bishiyar da take gurin suna shan fresh air tare da jin labaruka daga barorin su. Hajiya Fulani kawai jinsu take yi amma bata fahimtar hirar da suke yi, ita yau bata jin dadi sosai gabanta sai faduwa yake yi, dama kuma ita ba lafiya xe ta ishe ta ba dan tun lokacin da labarin rasuwar yarta Fatima ya iske ta, ballantana kuma jin irin mummunar mutuwar da tayi, tun daga ranar har yau bata kuma kasancewa cikin farin ciki ba, bata kuma jin wani labari dazai saka ta farin ciki ba, bata kuma jin dadin rayuwa ba, tana yin rayuwa ne kawai dan da akwai rai a jikinta. Sai da yawa ta kan ce "ni kullum sai inke jin kamar Fatima zata shigo gidan nan, har jin taku nake yi kamar nata" sau da yawa idan tayi wannan maganar sai mai martaba ko kuma duk wanda tayi wa maganar ya amsa mata da cewa "ai dama dole zaki ke jin haka, tunda baki ga gawar ta ba, kullum gani zaki ke yi kamar bata mutu ba zata dawo". In mai martaba ne sai ya kara da cewa "ni ma kaina dana binneta da hannu na ji nake yi kamar ba ita na binne ba, tunda babu sauran wasu kamannin ta a tare da ita". Yau ma wannan feeling din take ji, kamar Fatima zata zo ta zauna a tsakiyar su kamar yadda ta saba yi in dai tana gidan. Takan ce "tsakiyar ku yafi dadin zama, in juya duk ta side din da nake so in kwanta akan cinya". Hayaniyar da gidan ya dauka shi ya katse labarin da wata baiwa take basu, sannan kuma sai ga wasu bayi su biyu sun shigo gurin a guje kamar an koro su, jakadiya ta mike "kai! Lafiyar ku kuwa? Wanne irin rashin hankali ne haka?" Suka zube a kasa suna tuba sannan daya tace "wata mata muka gani yanzu mai kama da gimbiya Fatima" Hajiya Fulani ta mike tsaye, Hajiya umma ta mike itama tana tambayar "a ina? Ko yar uwa ce?" Sai suka ce "gasu nan zasu shigo nan gurin ita da wata mata, kowa gudu yake yi in ya gansu, kamar an tsaga kara ita da marigayiya". Hajiya Fulani ta fara tafiya da sauri zuwa hanyar shigowa gurin daga waje, zuciyarta tana gaya mata Fatima ce ba mai kama da Fatima ba, kafin ta karasa su ka shigo, Fatima a rike a hannun Maman Adam. Kallo daya tayi mata tasan cewa yarta ce Fatima, tasan cewa gawar dasu Mai martaba suka binne bata Fatima bace ba. A hankali Fatima ta saki hannun Maman Adam sannan ta mika wa Hajiya Fulani hannu tace "Hajiya ta, umma na na dawo gida" Jin muryar ta ya tabbatar wa da Hajiya Fulani cewa Fatima ce, mai makon ta amsa mata ko kuma ta kama hannun data mika mata sai ta zame ta yanke jiki ta fadi. *Back From The Dead* Appreciate this please...... Cikin mintuna da basu kai talatin ba gaba ki daya gidan sarautar kano ya hargitse, masi gudu nayi cike da tsoro da fargabar sunga fatalwa, wasu kuma suna tahowa da gudu dan gani ya kori ji, suna so si tabbatar wa da idanuwan su cewa gimbiya Fatimah data mutu shekaru biyar itace yanzu ta shigo cikin gidan da kafafuwanta. Fatima ta karasa cikin sassarfa ta durkusa a gaban hajiya Fulani tana girgiza ta kadan "Hajiya? Hajiya ta?" Umma da tun shigowar Fatima ta daskare a gurin ta matsa inda Hajiya Fulani ta fadi ganin cewa jakadiya da sauran barorin da suke gurin duk sun tsorata sun ki zuwa gurin. Ta jijjigata sannan ta dauko robar ruwa ta yayyafa mata tana kiran sunanta har suka ji ta sauke ajjiyar zuciya sannan a hankali ta bude idanunwanta, ta sauke su akan Fatima datake rungume da ita tana hawaye "Fatima? Fatima zahra ke ce wannan a duniya ko dai mutuwa nayi nima nake ganin ki a can?" Fatima tace "hajiya nice mana, baki gane ni ba ko? Na rame ko? Rashin lafiya nayi sosai. Nasan kuna ta nemana duk shekarun nan" sai ta kara kukan ta tace "nima ina ta neman ku Hajiya, ina ta so in taho gurin ku amma babu dama". Umma da take jin su ta kamo hannun Fatima tace "mu bama neman ki Fatima, mu bamu taba neman ki ba ko sau daya saboda mu ce mana akayi kin mutu, mu a gurin mu kin mutu dan har anyiwa gawarki suttura an binne ki" Fatima ta bude ido cikin mamaki, sai kuma ta waiga tana kallon yadda kowa a gurin yake kallon ta,wasu tana hango tsoro a idonsu. A lokacin Asma'u kanwarta ta shigo gurin, ita ma labari ya iske ta a dakinta cewa Fatima tayo fatalwa tana yawo a gidan, tana shigowa kuwa taga Fatima a durkushe kusa da iyayen su, ai kuwa sai ta zunduma ihu ta juya a guje, Fatima ta mike "Asma'u? Asma'u Fatima ce fa, Asma'u nice Fatima wallahi ba mutuwa nayi ba, karya ake yi min wallahi ban mutu ba" kuka yaci karfinta, tana jin zafi a zuciyarta cewa yan uwant data gama cin burin zuwa ta gansu ta rungume su taji dadi sune suke gudunta sun dauka fatalwa ce, wai ashe duk tunanin da take cewa babanta yana nan yana zazzage Nigeria yana nemanta ashe ba haka bane ba shi ya dauka bata duniya, for five full years, hakan yana nufin har sun fara mantawa da ita kenan. Hakan yana nufin badan Mama ta taimaka mata ba, da sai dai ta karashe rayuwarta a rufe babu mai zuwa cetonta kamar yadda da take tsammanin babanta zai yi bincike ya gano inda take sannan ya taimaka mata. Sai ta juyo ta rungume Maman Adam, "Mama dan Allah ki gaya musu, ki ce musu wallahi ba mutuwa nayi ba ina tare daku, ki gaya musu su bar guduna ni ba fatalwa ba ce ba" kafin Maman tayi magana Hajiya ta tashi ta rungume ta, "ba sai kin rantse ba Fatima, ba sai kin nemo ma yi miki shaida bani nasan kece, tunda aka ce min kin mutu jikina yake bani kina raye kuma zaki dawo wata rana,ni na san bagawarki suka binne ba". A lokacin suka jiyo maganar shamaki, "takawa sannu, zaki ɗaukawa sannu, sunkuye alher" Hakan yana nufin mai martaba sarki ne da kansa ya taho gurin, abinda baya taba yi, baya taba shigowa bangaren matansa sai dai in watace a cikin su bata da lafiya ko wata a cikin yayansa. Jin haka yasa ka Fatima ta saki Hajiya ta kuma fita a guje zuwa inda yake tahowa, ita dama can tun tana karama yar babanta ce, ma'ana tafi shakuwa da babanta akan kowa, yaga tahowar ta, yakuma gane ta, ba ko girgiza ba ballantana yaji tsoro sai ma farin ciki da ya cika zuciyar sa cewa labarin da aka kai masa gaskiya ne, Fatima bata mutu ba kuma ta dawo gida. Tana zuwa ya shige jikin sa tana kuka, "wallahi ban mutu ba Takawa, ina imo, ina can an rufe ni an hana ni tahowa, ina can bani da lafiya Baba". Bai amsa mata ba sai ya rungume ta yana shafa kanta, a ransa yana tasbihi ga ubangiji daya dawo masa da Fatima duk da cewa bai taba addu'a akan hakan ba, bai taba yi ba saboda bai san cewa hakan zai iya kasance wa ba, bai san cewa tana da rai ba. Sai kuma ta cika shi da sauri ta dago kai tana kallonsa sa, zuciyarta a karye, yana yin fuskarta kadai ya isa ya saka mai karyayyiyar zuciya yayi kuka, tace "Baba ina Hussain? Ina Hussain dina? Baba dan Allah ka gaya min ba gaskiya ba ne ba abinda naji, dan Allah ka gaya min bai neme ni ba saboda shima ya dauka na mutu, ka gaya min cewa yana nan yana kukan rashina ba wai ni ce zanyi kukan rashin sa ba". Dauke kansa yayi gefe ya lasa hada ido da ita, hakan yana kara tabbatar mata da maganar da Adam ya gaya mata amma kullum take gayawa zuciyar ta cewaba haka bane ba, kullum take saka ran cewain ta dawo goda zata tarar cewa ba haka bane ba, amma expression din fuskar maimartaba sarki kadai ya saka ta fahimtar cewa yaudarar kanta take yi, Hussain ya mutu, shekaru biyar da suka wuce, ita da Hussain sai a Darussalam. Sai ta sake shi sannan ta zame zuwa kan kafafuwan sa, idanuwan ta a kasa amma hawaye ya tsaya a cikin su, Kamar yadda duk tunani ya tsaya a zuciyarta fuskar Hussain kawai take gani. Ta tuno da maganar sa "wannan ciwon da yake damuna jarabawa ta ce, abinda zai same ni kuma jarabawar ki ne" Ta girgiza kanta kamar ta girgiza lokacin daya gaya mata maganar "no, no, no, Hussain, babu abinda zai same ka, please babu abinda zai same ka, ba zan iya ba Hussain, ba zan iya rayuwa babu kai ba" Hajiya ta zo gurinta tana kuka ita ma, tana cewa "zaki iya Fatima, Allah ya san zaki iya shi yasa ya dora miki, sai ki karba kuma ki gode masa bisa ga sauran ni'imomin da yayi miki" ta dago tana kallon ta, her mind racing, sauran ni'imomin da Allah yayi mata? Hajiya tana nufin dan ta kenan? Danta da suka haifa ita da Hussain? Mai kama da Hussain? Ta mike da sauri ta fara waige waige tana neman sa, tana neman yaro dan shekara biyar mai kama da Hussain ko da Hassan, yaron da tasan zata yi dedicating duk kan sauran rayuwarta a gun tabbatar da cewa ya samu kyakykyawar rayuwa ba tare da yayi kukan maraici ba, yaron da tasan zai goge mata dukkanin kewa da kadaicin Hussain. "Ina yake?" Tace tana bin mutanen gurin da kallo, "Allah sarki, ya dauka bashi da uwa bashi da uba ko?" Ta share hawayen ta "it must have been so hard on him, it must have been so hard on all of you" amma sai ta ga duk suna binta da kallon rashin fahimta, wa take nema? Wa take nufin ya tashi ba uwa ba uba? Ganin kallon da suke yi mata ya sake tsinka zuciyarta, God please no, not her son please. Bata son tayi musu tambayar dan bata shirya jin amsar da zasu bata ba, zuciyarta ba zata iya dauka ba. Sai ta tambayi kanta "me ya saka ta dawo gida, me nene yayi mata saura a gida? Ina ma dai da gaske ne abinda suke tunani, ina ma dai ta mutu a ranar nan kamar yadda suka yi zargi. Duk da haka tana so taji me ya faru da dan nata, ta kama hannun umma "ina Da na?" Ta tambaya da wata irin murya data huda zuciyoyin duk wadanda suke gurin "ko yana gurin Hassan ne? Ku kawo min mota in tafi Kaduna in ganshi, ku gaya min inda yake don Allah". Ummah tace "Fatima ke zamu tambaya ai inda yake, mu gawar da aka bamu muka binne da ciki a jikinta dan haka bamu nemi inda abinda yake cikin ki yake ba, mu duk mun dauka tare muka binne ku. Kin haihu ne dama kafin kuyi accident din? A ina kika haihu? A ina kika bar babyn?" Fatima ta dafe kanta da hannayenta biyu tana jin yadda kan ta yake juyawa, "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ta ringa fada cikin muryar ban tausayi. Duk iyayenta suka yi kanta kowa yana kokarin rarrashin ta Maman Adam ce tazo itama tace "ku barta dan Allah ta huta, kar ku gaya mata abinda zai bata ranta Please" duk suka juyo suna kallonta, suna lissafin inda zasuyi placing dinta. An enamy or a friend? Amma sai aka dauki shawarar ta aka shigar da Fatima cikin gida, nan da nan kuma aka guda da shewa da murnar dawowar Fatima gida, labari ya bazu ko'ina cewa gawar da aka binne ba ta Fatima bace ba. Sai dai kowa aka gayawa labarin sai ya tambaya "how comes?" Lallai akwai zare cikin nadi. Duk wannan murnar da ake yi Fatima bata tare da murna, bata kuka kuma bata dariya, tana dai zaune kawai tana kuma yin duk abinda aka umarce ta tayi batare da musu ko doki ba. Kafin wani lokaci maganar ta zagaye ko ina, duk yan uwan Fatima sun samu labari kuma da yawadaga cikin su wadanda basa gida sun kamo hanyar gida, hatta wadanda basa kasar sun nemi next flight to Nigeria sun yi booking, Asma'u kuma da take gida already ta dauki hotunan Fatima ta tura wa yan uwadan su tabbatar da gaskiyar magana. An sauki Adam a gurin saukar baki maza a waje, an kuma sauki Mama a kebantaccen guri a cikin gida har sai anji labari daga bakin Fatima tukunna kafin ayi tunanin matsayin ta a cikin maganar, sai dai ba Fatima ba kadai duk wanda aka gaya wa dawowar Fatima sai ya tambaya "har babyn suka dawo tare?" Amsar, ita take saka su cikin jimami da kuma tunanin ya akayi aka kwana a ragaya? Bayan anyi sallar magrib ne maimaita sarki ya kira iyalinsa gabaki daya, immediate family dinsa, wadanda da yawa daga cikin su sun iso gidan kuma duk suna son suji inda maganar ta kwana. Bayan sun zauna ne, fuskokin su dauke da mixed feelings na farin ciki da kuma jimami, Fatima a kusa da baban ta, fuskarta unreadable, sai aka gabatar da addu'a tare da godiya ga ubangiji akan wannan abin farin cikin daya same su tare da kuma neman jagorar sa akan duk hukuncin da zasu yanke. Tambayar da tafi damun kowa a gurin ita Takawa ya fara yiwa Fatima. "Fatima Zahra, ina kike tsahon shekarun nan kuma mai ya hanaki dawowa gida? Ko kuma neman munki sanar mana a inda kike mu muje mu taho dake?" Ta dago kanta tana kallon sa, sannan cikin karamar murya tace "ina imo, bani da lafiya, kuma an rufe ni ba'a barina na fito ko da kofar gida, ban san yadda zanyi in neme ku ba" suka fara kallon juna cikin mamaki sannan Hajiya Ummah tace "imo? Ya akayi kika je imo?" Duk suka dawo da hankalin su kanta suna jiran amsa, amma ga mamakin su sai suka ga ta juya hannayenta, alamun bata sani ba. Umar ya gyara zamansa yace "Fatima abinda ke cikin ki a lokacin fa? Kin san yadda akayi kika rabu dashi?" Idonta ya ciko da kwalla, ta dora hannunta akan cikinta sannan tace "ban sani ba Yaya, ni bansan komai ba, ni dai na ganni acan baninda lafiya, Adam ya gaya min accident mukayi ni bansan ma munyi accident din ba, ya gaya min tsinta ta yayi a daji sai kuma babansa ya hada mu gaba daya ya tafi damu can, ya gaya min shima bai ganni da ciki ba, yace sanda ya ganni babu ciki a jikina amma da alamar na haihu ne a lokacin, ni na dauka a inda muka yi hatsarin na haihu, na dauka an kawo muku babyn kuma kuna ta nemana, na dauka...." Muryarta ta makale saboda kukan da ya ci karfin ta, Hajiya, Ummah tare da yan uwan Fatima mata suna taya ta kukan. Mazan kuma suna ta kokarin amfani da kwakwalwar su wajen ganin sun fahimci menene ya faru. Abubakar yace "tunda ga Fatima anan a gaban mu, wacece kenan muka binne da tsohon ciki? Menene dalilin da yasa aka faya mana cewa Fatimah ce bayan ba ita bace ba?" Umar ya juya gurin Fatima yana tausayin yadda take kuka na rashin sanin inda danta yake ga kuma mikin mutuwar mijinta, yace "Fatima Zahra, ki daure, ki tuna, ranar da kuka yi accident din menene ya faru? Dake da waye a cikin motar? Shin kunyi accident din ma ko ba kuyi ba? Ko wani cover up aka shirya dan a salwantar da ke da kuma abinda yake cikin ki? Ki tuna Fatima, ki bamu labarin menene ya faru, wannan ne zai taimaka mana gurin gano inda yaron yake". Ta goge hawayen idanunta, duk da cewa tana goge su wadansu suka yi replacing dinsu. Tun sanda ta dawo hayyacin ta, tun sanda ta fara tuna ko wacece ita tare da taimakon Adam, babban abinda take kokarin tunawa shine yadda akayi ta haihu, saboda tana so ta tuno koda fuskar danta ne, ta tuna feeling din nakuda da fitowarsa daga jikinta, ta tuna muryar sa sanda yayi kukan sa na farko amma ta kasa tunawa. Abu na biyu da take kokarin tunawa shine accident din da Adam yace sunyi, menene ya faru, amma abinda kawai take tunawa shine Hussain ya mutu, bata san ya akayi ta sani ba amma ta san ta san Hussain ya mutu kuna shine last abinda ta sani. "Kiyi kokari ki tuna Fatima" Asma'u ta fada tana shafa kafadar ta, ki tuna a ranar tunda safe me kikayi har zuwa tafiyar ku Abuja, ke da waye a cikin motar? Me ya faru a cikin motar" tayi shiru tana kallon Asma'u, daga alama tunani take yi, sai ta runtse idanunwanta ta yare da dafe kanta da hannunta, ta jima a haka sannan tace "Hussain........ Hussain ya tafi Abuja shi da Hassan da Adam a mota, ni kuma bana son ya tafi, hankali na ya tashi da tafiyar sa. Bayan na lissafa lokacin daya kamata su sauka sai na kira wayarsa amma baya dauka, nayi ta kira amma baya dauka dai hankali na ya tashi, na kira driver nace yazo ya kaini Abuja gurin Hussain, sai muka tafi tare da ........tare da ........matar Hassan, Ruqayyah, tace ita ma tana son taje taga Hassan. Sai muka tafi, mun kusa shiga Abuja sai Hassan ya kira ta yace mata mu koma gasu nan sun gama abinda suke yi zasu taho, muna juya mota sai aka ce min Hussain ya mutu ......" Sai ta rufe fuskarta tana kuka "shikenan abinda na sani" Umar yace "waye ya gaya miki Hussain ya mutu?" Ta bude idonta da suka juye saboda kuka tace "ban sani ba Yaya Umar, ba zan iya tunawa ba" ya matso kusa da ita "okay, just close your eyes ki tuna sanda kuke zaune a motar, a ina kika zauna?" Ta rufe idonta a tana tunani sannan tace "a baya nake, a side din driver" Suka kalli juna suna tunawa cewa gawar da aka samu a gaban mota take, yace "good. Ruqayyah fa? A ina take?" Ta kara tunani Tace "a baya itama, tare muke da ita a baya" yace "waye a gaba, akwai mutum a gaba" tayi shiru, her eyes squeezing, tana jinta kamar a cikin motar take, tana jin tension din son taji halin da Hussain yake ciki, tana tuno maganganun su da Ruqayyah da kuma maganar da Ruqayyah suka yi da Hassan a waya da kuma umarnin da Hassan ya bayar, she remembered the driver, da yadda yake kokarin juya motar, and then.....then she remembered her face sanda ta juyo daga seat din gaba tana kallon su da budaddun idanu, she remembered her voice, kamar yanzu take mata maganar tace "Ruqayyah? Ba Hussain dinku ne Hussain Aminu Abdullahi ba? Ya mutu! Yanzu ake fada a twitter wai ya mutu a wani asibiti a abuja!" Fatima ta tuna yadda dan cikinta ya harba da karfi a lokacin. Ta dafe cikin ta tana tsananin missing dinsa. Ta bude idonta tana kallon Umar, ta gyada kai da sauri tace "na tuna ta, na tuna kamannin ta da komai, kawar Ruqayyah ce tare suka shigo gida sanda zan fita, ita ce a gaba, ita ce ta gaya min Hussain ya mutu" Abubakar yace "zaki iya tunawa ko da akwai ciki a jikin ta?" Ta gyada kanta ba tare da tayi wani tunani ba tace "tsoho ma kuwa". *************. ************** ***** A yau, bayan shekara hudu da bude estate dinsa na farko, Hassan ya samu nasarar bude na biyu wanda kamar na farkon ya saka masa suna "Hussain Aminu Abdullahi memorial estate phase 2". Kamar na farkon, shima wannan block shida ne sai dai wannan hawa uku ne ba biyu ba, dan haka wannan gidaje goma sha takwas ne a ciki ba sha biyu ba. Kamar wancan karon, yan uwa da abokan arziki sun taru sosai dan taya shi murnar wannan abin farin cikin. Aunty da family dinta, yaya da jikoki, dan yanzu Hassana da na uku take goyo, Safiyya daya, Khadijah tsohon ciki, Nafisa karami, Sumayya da one year old Abdullahin ta sai Zulaihat da take ta cin yammatancin ta har yanzu. Hassana ta kira Zulaihat "zo ki dauki Ilham ki tafi da ita gurin samarin, in sun baki kin kasa karba ita sai ta karbo ta kawo min mu raba" ta fada tana miƙa mata ikram da take ta tsalala kuka. Zulaihat ta bata rai "kai yaya Hassana! Ni ya zanyi da ita?" Sumayya ta miko mata abdullahi "hada da Abdul, sai ya taya ki renon ta" Abdul ya mika wa Zulaihat hannu yana murna za'a dauke shi. Zulaihat ta bata rai tana dungure masa kai sannan tace "Aunty kin gan su ko?" Aunty tace "ina ruwan Amina? In da kinyi aure ai da ba zasu ke hada ki da rainon yayan su ba. Ki dauki yaran, maybe in samarin ki suka ganki dasu suka fahimci cewa kin iya raino zasu fahimci cewa kin isa aure". Duk suka kwashe da dariya banda Zulaihat, ita ta gaji da wannan sa idon da suke mata suna cewa taki aure, ga Aunty tana tare mata amma tun da taga Sumayya ta haihu sai ta fara matsanta mata itama akan ta fitar da miji ayi mata aure. Ta tura baki, "babu dan da zan dauka, ai duk kuna da yan aiki ku basu yaran mana su rike muku" ta tashi tana kokarin barin gurin wayar Aunty tayi kara. Ta fito da ita daga jaka tana duba sunan sai ta dafe kanta "innalillahi" Khadijah tace "waye?" Aunty tace "Hajiya Umma ce, wallahi shaf na manta ban aika musu maganar taron nan ba, yanzu haka labari suka ji zata kira tace min ban kyauta ba" Hassana tace "kash, walllahi an manta kuwa, amma kinga wancan ai an aika musu har suka zo ma" Aunty ta dauki wayar da kiran har ya riga ya katse tace "bara in kira in basu hakuri, ban kyauta ba wallahi" Kafin ta kira sai wani kiran ya sake shigowa, ta tashi tsaye ta dauka yana matsawa inda babu hayaniya ta fara wayarta, bata jima da tashi ba sai sai Hassan yazo, yan samarin sa guda uku suna binsa kamar jela, ya saka hannu ya dauki Abdullahi da tun daya hango shi ya fara tsalle a cinyar maman sa, ya daga shi yana kissing forehead dinsa sannan yace "shine kika zo kika yi zamanki kika barni da mutane ko?" Ta mike tana murmushi tare da pretending hamma, ya harare ta, tayi murmushi "ba laifi na bane Habibi, laifin wannan katon yaron na hannunka ne" sai shima ya ja kujera ya zauna "nima zama zanyi, duk wanda yazo yanzu ke zaki zagaya dashi" ya zauna Sumayya ta fara zuba masa drink sannan ta zubawa boys din suma. Suna ta hada baki gurin bata labarin abubuwan da suka faru a gurin. Sun jima a haka sannan Aunty ta dawo daga wayar da taje yi. Yanayin fuskarta ya saka kusan gaba ki dayansu suka mike tsaye, Nafisa tace "Aunty mutuwa akayi? Waye ya mutu kuma?" Aunty ta bisu da kallo daya bayan daya sannan tace "ba mutuwa akayi ba, the most strangest thing has happened, Fatima ta dawo gida, bata mutu ba" *The Story* Shirun daya biyo bayan maganar ta hatta kurma zai iya jinsa. Hassan ne ya fara cewa "what? Aunty menene kika ce yanzu? Fatima fa kika ce bata mutu ba" kallon sa take yi itama da alama shock din maganar bata gama hitting dinta ba har yanzu, cikin rawar murya tace "abinda Hajiya Ummah tace min kenan yanzu, wai ga Fatima a gida, wai bata mutu ba duk tsahon shekarun nan tana jihar imo tare da Adam, wannan drivern Hussain din". Sumayya ta koma ta zauna, saboda kafafuwan ta da taji ba zasu dauki jikinta ba in bata zauna ba zata iya faduwa "Adam?" Ta fada a hankali, Hassan ya jiya ya kalle ta sannan ya kalli Aunty shima yace "Adam?". Khadijah ta bude ido tace "in bata mutu ba kenan ta haihu, babyn yaya H2! Ina babyn yake? Suna tare a kanon?" Hassan ya kuma juyawa sharply yana kallon Khadija, zuciyar sa tana bugawada karfi kwakwalwar sa tana analysing maganar Khadija, tabbas in Fatima bata mutu da ciki ba to kuwa ta haife shi, shekaru biyar da suka wuce, meaning abinda ta haifa har yayi yawo ma kenan, meaning an haifa wa Hussain da a duniya. Sai kuma yaji amsar Aunty ta daki kunnensa kamar yadda tambayar Khadijah ta daka "babu baby, ita kadai ta dawo, ba'a san inda babyn yake ba" ya dawo da idanuwan sa kan Aunty, this is too much to take a cikin mintuna kadan "what?" Ya sake cewa, "ban gane ba Aunty ban fahimta ba" tana kallonsa tace "nima ban gane ba Hassan, kai na ya toshe ban san ma wanne tunani zanyi ba, bana ma gane komai, abinda ta fada min kenan" Hassana tace "a dauko mota mu tafi kanon, a xan ne zamu fahimci maganar nan dan ba maganar da za'a yi a waya bace ba, wannan fa ba karamar magana bace ba, ya za'a yi Fatima da tayi accident ta kone kurmus ita da abinda yake cikinta kuma aka binne su sannan bayan shekara biyar su dawo? Wannan ko a film, ko a Indian film bana jin zai iya faruwa" Safiyya tace "to ai yar su ce, ba zasu yi karya suce ta dawo ba indai ba dawowar tayi ba. Kuma ma in sunyi karya me zasu yi gaining?" Khadijah tace "amma ku dakata, in da gaske Fatima bata mutu ba, in ba gawar Fatima aka binne da ciki a cikin daji ba, wacece kenan? Wa aka binne?" Duk suka kalli juna banda Sumayya data ke zaune ta dafe kanta da hannayenta biyu tana sauraron yadda zuciyarta take bugawa. Hassan ya kalli Khadijah yana lissafin amsar tambayar da tayi, tabbas bai ga gawar da aka binne dinba amma ance ba za'a gane kamannin ta ba except that macece mai tsohon ciki, in dai har iyayen Fatima da kansu sun tabbatar wadda ta koma gida Fatima ce then su basu da ja cewa ita din ce, in dai har Fatima tana da rai to wa aka binne? Ko wacece har yanzu ana neman ta kenan ba'a same ta ba, His mind raced, putting two and two together. Tsohon ciki, kayan baby, Ruqayyah. Ya ajiye Abdullahi dake hannunsa sannan ya dafe kansa da hannayensa biyu "oh my God. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" aunty da sauran yan'uwa duk suka juyo suna kallonsa, Sumayya ta mike da sauri tana kokarin rike shi dan gani tayi kamar zai fadi, ya bude idonsa yana kallon ta. Aunty tace "Hassan lafiya? Mai ka tuna?" Bai kalle ta ba sai Sumayya yake kallo, yana tunawa da yadda Ruqayyah taki kallon idon mahaifiyar Minal a asibiti sanda taje dubata tare da tambayarta ko ta san inda Minal take, ya tuna da karyar da tayi masa, ya tuna da yadda ta chanja magana tace sun hadu da Minal amma sun ajiye ta a hanya ta hau taxi zuwa gida. Gidan da har yau bata je ba kenan. Yana kallon cikin idon Sumayya yace "bayan driver da Fatima da Ruqayyah a cikin motar ranar da suka yi accident akwai wata, akwai Minal kawar ku, ita ce a gaba, ita ce ta mutu ranar nan, ita ce aka binne ba Fatima ba". Labarin dawowar Fatima ba karamin tayar da mikin mutuwar Hussain yayi a zuciyoyin yan uwansa ba, musamman Hassan, ga kuma wannan sabon al'amari wanda bai gane kansa ba na cewa ba'a san inda yaron Hussain yake ba. Ta yaya? Sannan kuma ga dawowar Adam tare da Fatima, me ya hada Adam da Fatima da har zai dauke ta su tafi garin su tsahon shekaru biyar? Me ya faru dasu. A dole ya tafi ya sallami mutanen da suke gurin taron da excuse din cewa something emergency ya taso masa tare da bada hakuri, amma baya bukatar ya badu hakuri dan duk wanda ya ganshi zai lura ba'a cikin nutsuwar sa yake ba. Wani bari na zuciyarsa gaya masa yake yi kawai duk ya bar wannan bata lokacin ya shiga mota ya tafi gidan Hussain ya shake Ruqayyah yayi ta dukanta sai ta warware masa zare da abawa na duk wannan rikicin, gani yake itace answer to everything. For starters, ta yi karya, muguwar karya, akan mutuwar kawarta, what kind of himan being is Ruqayyah? Shin idan Ruqayyah zata iya yiwa friend dinta haka me nene abinda zata yi wa makiyin ta? Ya tuno Fatima, Ruqayyah ta rike Fatima a matsayin makiyiyar ta, dan haka tabbas, yana da 90% assurance cewa Ruqayyah tana da hannu a cikin abinda ya faru da Fatima. Amma babyn Fatima fa? Ita Fatima ai ita zata san duk abinda ya faru da babyn ta. Sai yaji ba zai iya jira zuwa goben da aunty tace su bari tayi sannan su tafi Kano ba. Yana so yaga Fatima a yau, yana son ya ji inda ɗan Hussain yake a yau. Sai dai baya son ya ki bin maganar Aunty, tace dare yayi yau su bari gobe da assuba sai su dauki hanyar kano kafin gari ya gama wayewa sunje. Sai daya gama sallamar mutanen roughly sannan ya dawo inda Sumayya take zaune har lokacin tana kuka, babu abinda take tunowa sai fuskar Minal da irin yarintar su tare a matsayin makota, in dai sun fita wasa gidan su Minal zasuje Kamar yadda itama take yawan zuwa gurin su wasa duk kuwa da cewa su Minal din sun fi su abin hannu, wannan ya sa basuyi makaranta tare ba amma duk da haka suna kawance a unguwa, bayan haduwar Hassan da Ruqayyah ne kuma kawancen Minal din ya kara karfi da Ruqayyah saboda ra'ayin su na karya da son kudi yazo kusan daya. Ta tuna yadda ta kan yi wa Ruqayyah nasiha akan kula Minal saboda tana gudun kar ta jata ga halaka, bata san cewa bakar zuciyar Ruqayyah tafi ta Minal baki ba. Bata san cewa da ace Minal zata san yadda karshenta zai kasance da ko hanyar da Ruqayyah ta ke bi ba zata bi ba. Ta goge hawayen ta da bayan hannunta tana kallon yaran da suka zauna a layi suna kallon ta, Hussain shima yana ta sheshshekar kuka duk da bai san abinda Sumayya take yiwa kukan ba. Kaicho, dan Adam baya zaben iyayen da zasu haife shi, tabbas wadannan yaran basu yi sa'ar uwa ba. Tabbas inna da Baba badu yi sa'ar Ruqayyah a matsayin ya ba. Ita bata san ma ta yadda zata yi musu breaking wannan mummunan labarin ba, musamman Inna da har yau kullum sai tayi addu'ar Allah ya bayyana Minal dan har yau suna mutunci sosai da iyayen Minal din. Baba kuwa dashi aka yi ta yawo gidajen rediyo yana raka Baban Minal ana bada cigiyar ta, har hoton ta ya lika a gurin aikin gadinsa da cikin Napep dinsa wai ko Allah zai saka wani da ya ganta ya gani yayi magana. Ga maganar Adam, menene role dinsa in all of this? Hassan yazo yana daukan Abdullahi daga cinyar ta sannan ya juya yana kallon yaran da suka jeru suna kallon ta suna hawaye yace "ku tafi ku shiga motar Aunty ku tafi gida, gamu nan zamu taho muma" suka mike ba tare da musu ba sai dai har suka yi nisa suna waigen mommyn su suna son sanin menene ya saka ta kuka, sun san dai akan wata Fatima ne da wata Ruqayyah ne, sai dai basu san me Fatima da Ruqayyah suka yiwa mommyn su ba. Ta mike tana kallonsa tana goge hawayenta tana jinjinawa jarimtarsa, tana mamakin inda yake samun kwarin gwiwar facing abubuwa in suka same shi. Ita bata taba ganin mutumin da yake karbar kaddararsa hannu bibbiyu irin Hassan ba. Hannun ta ya kama ba tare da yace komai ba sannan yafara tafiya da ita zuwa motarsa, sai data shiga ya dora mata Abdullahi a cinyar ta ya zagaya ya zauna shima sannan yace "let's go home" yaayin muryar sa kamar zai saka ta kuka. Menene rayuwa bata jefo wa Hassan ba? Matarsa matar daya zaba ya so kamar rai duk da banbanci mai girma da yake tsakanin su ya kuma taimaka mata in ways that ita kanta ba zata iya lissafawa ba ita ce tayi sanadiyar destroying family dinsa, ta yadda matar kaninsa tayi shekaru biyar ba tare da an san ma tana raye ba, ta yadda da daya tilo da kanin nasa ya mallaka yake kuma so fiye da ransa ba'a ma san inda yake ba a halin yanzu, ba'a san ma ko yana da rai ko bashi da rai ba. She can't even imagine the heartbreak...... Duk da cews basu san menene ya faru da Fatima da babyn ta ba amma duk su biyun sun san cewa akwai hannun Ruqayyah a ciki. Me yasa tayi karya akan mutuwar Minal? Sai da suka yi nisa a tafiyar su sannan yace "bansan ta yadda zan gaya wa Alhaji Kabiru wannan maganar ba" ta dora hannunta akan nasada yake kan gear tace "you don't have to, ba alhakin ka bane ba, kar ka dorawa kanka wannan nauyin bayan already wanda yake kanka, ka bari in munje kano munji details din maganar sai a sanar wa da police din da aka gayawa zancen baran ta, su sai su kira shi su gaya masa" ya girgiza kansa "dile in gaya masa Sumayya, dole in gaya masa da kaina, tunda abin nan ya faru nake keeping in contact da shi Saboda haka kawai nake jin kamar I am responsible for something da bansan menene ba, ko last week sai daya kira ni ya gaya min matarsa, uwar gidan sa ta haihu bayan kusan shekara goma sha biyar tana neman haihuwa. First child dinsa kenan wannan. I have to tell him da kaina dan in rage feeling guilty" Sumayya tace "quilt? Habibi you are not guilty of anything. Babu laifin ka ko kadan a cikin wannan maganar" ya girgiza kansa, "akwai laifi na Sumayya, laifi na kuma shine auren yaruwarki. Da ban aure ta ba da duk wannan bata faru ba" Suka shiga layin gidan su, suka zo dai dai kofar gidan Hussain sai Hassan ya tsaya da mota yana kallon gidan , Sumayya ta kamo hannayensa duk biyun tana cewa "no, no, please. Violence baya taba solving problem sai dai yayi adding. Kar ka shiga dan Allah. Kar ka bata abinda zata fake dashi. Kan taba ta yanzu sharia ta hau kanka. Kar ka taba ta dan Allah" ya sauko da idonsa kanta sannan ya kuma kallon gidan, babu abinda yake so, babu abinda zai sanyaya masa ransa a yanzu irin ya kama Ruqayyah yayi ta duka kamar Allah ya aiko shi. Sai kuma ya taka motar suka karasa nasu gidan. Sumayya ta sauke ajjiyar zuciya tana hoping ya hakura kenan ba ajiye ta zai yi ya koma ba. Sai da yayi packing sannan ya juyo yana kallonta yace "you are right, in na taba ta na bata abinda zata fake dashi, ninkuma bana son ta samu abinda zai zamar mata madafa, ba zan shiga gidan ba sai da yan sanda, sanda zan fito kuma zan fito ne da ita a cikin sarka. Amma kafin nan ina son ganin Fatima, ina son jin gaskiyar magana ina kuma son inji abinda ya faru da ɗan Hussain" daga yadda ya fadi maganar tasan zuciyarsa kuna take yi. Tana son ta bashi hakuri ta rarrashe shi amma bata san ta yadda zata fara ba. A haka suka shiga gida, kamar yadda tayi tunani haka yayi ta pacing, yayi ta safa da marwa ya kasa zama ma ballantana kwanciya, a karshe sai taga ya cire kayan jikin sa yayi wanka ya saka jallabiya ya fita, sai dai bata tambayeshi inda zashi ba dan jikinta ya riga ya bata amsar, kabarin Hussain zaije. Daren ranar haka ta ringa bacci tana tsorata, tana ta tunowa da Minal, tana kuma lissafin yadda zata gayawa iyayensu, yan uwansu da kuma kawayensu abinda Ruqayyah ta aikata. Jin dadin ta daya shine yaran duk suna gidan aunty ba dan haka ba da tasan zasu saka ta a gaba ne da tambayoyi su kuma karamata tension tare da tuna mata cews Ruqayyah ce mahaifiyarsu ba ita ba, no matter how much she pretend, b aita ta haife su ba. Assubar fari suka dauki hanya, gabaki dayansu banda yara, dan sai da suka je Zaria sannan suka yi sallar asuba suka cigaba da tafiya. Mota biyu sukayi, da motar Hassan wadda Jabir yake tukawa Hassan yana gaba, Aunty da Sumayya da Zulaihat suna baya, sai motar Aunty wadda drivern ta yake tukawa Hassana tana gaba, Safiyya, Khadijah da Nafisa suna baya. Karfe bakwai da yan mintuna suna kofar fadar Kano. Dama tun dare Aunty ta gayawa Hajiya Ummah yadda tafiyar tasu zata kasance dan haka already an san da zuwansu. Suna shiga aka tafi dasu Hassan masaukin baki maza, anan ne suka hadu da Adam. Suka tsaya suna kallon juna Hassan yana kokarin kawar da batun Adam da Sumayya daga zuciyarsa, for years ya jima yana fatan ganin adam amma bai taba tsammanin haduwar tasu zata kasance a irin wannan yanayin ba. Sai dai hakan bai hana shi nunawa Adam din farin cikin ganin sa ba kamar yadda shima Adam din yake fatin cikin ganin Hassan. "Oga Hassan!" Ya fada da murmushi mai kyau a fuskarsa. Hassan ya kirkiri murmushi shima "Adam! Oh my God. Har mun fitar da ran zamu sake ganin ka" ya bawa Adam din hannu amma sai adam ya rungume shi yana dariya "you have no idea how happy I am that you are alright" Hassan yace "it is good to see you too" sannan ya raba shi da jikinsa yana lura da yadda Adam din ya kara girma ga wani gyaran fuska na musamman da yayi wanda yayi matukar yi masa kyau. Sai yaji abinda tun kafin su taho yasan zaiji idan yaga Adam din. Kishi. Sai yaji a ransa ina ma dai bai taho da Sumayya ba? Baya so taga Adam especially when he is looking this good. Sai kuma ya kama hannun Adam din suka tafi suka zauna a kujerun alfarmar da suke gidan bakin yace "come, tell me everything. A ina kuka hadu da Fatima kuma ina kuke tsahon wannan lokacin? Me ya hana ku dawowa?" Suka zauna, Adam yana kallon Hassan yana lura da yadda ya bashi dukkan attention dinsa sai yace "bayan na rabu da kai a asibiti, kace in taho in duba su Fatima a hanya. Na bar Abuja kenan banyi nisa sosai ba sai na ganta, tana tafiya a gefen titi kayanta a yage jikinta da jini kanta babu dankwali. Sai na tsaya nayi mata magana, na fahimci accident suka yi, na kuma fahimci ba'a cikin hayyacin ta take ba dan ka.ar ma bata san inda tame ba tnaa ta ce min wai in kaita gurin Hussain. Kuma na lura babu ciki a jikinta, na lura kamar ta haihu ne..........." Hassan ya daga masa hannu "wait wait wait.....wai kana nufin a inda suka yi accident din anan ta haihu?" Adam yace "possibly, but am not sure ko a exact gurin ne ko kuma a wani gurin ne daban amma ta haihu kafin in ganta" Hassan ya mike yana dafe kansa, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, shi duk hope dinsa shine Fatima a hannun Adam ta haihu,cewa yaron ya a gidan su Adam ne ko something. Ya dawo ya zaunaz idonsa yai ja yace "kuma bata gaya maka inda ta haihu ba? I mean ta san inda ta haihu right?" Adam ya girgiza kansa, zuciyarsa cike da tausayin Hassan dan yasan how much dan Fatimah means to him yace "Fatima bata sani ba. Fatima bata san komai ba. Ko sunan ta bata ba sai watanni kadan da suka wuce" Hassan ya bude ido cikin mamaki, Adam ya gyada kai yace masa "yes, she is suffered from memory lost, har yanzu akwai abubuwan da bata tuna ba. Har yanzu bata tuna sanda suka yi accident ba da kuma abinda ya faru bayan accident din da kuma sanda na dauke ta". Hassan yaji kamar an kwada masa mari a duk sides din fuskarsa, sai kuma ya daure ya juyo yana kallon Adam yace "okay, tunda gaka ai, tell me yadda ka dauke ta da kuma dalilin da yasa ka tafi da ita shekara biyar ba tare daka neme mu ka gaya mana tana hannunka ba" Adam yaji threat din da yake cikin maganar Hassan amma ya riga yayi expecting hakan dama, dan haka ya cigaba da bayani. "A lokacin na dauko wayata na kira ka, kiran ya shiga kenan sai ga motar Daddy na nan tazo gurin. Ban san yadda akayi yasan inda nake ba a lokacin bansan kuma yadda akayi har ya kama ni irin haka ba,ka riga kasan issues dina da gidan mu. Shi ya kwace wayar ya hanani kiranka sannan ya jefar da ita, nayi kokarin guduwa, kuma zan iya guduwa a lokacin amma ba zan iya guduwa in bar Fatima ba. Dole na hakura na tsaya saboda ita, na kuma hakura ya kama ni saboda ita, sannan nayi masa karyar cewa budurwa ta ce tare muke saboda ya dauke ta in ya dauke ni, tare da yi masa alkawarin bazan kuma guduwa daga gurin sa ba in har ya bari na taimaka mata" "Nayi hakan ne saboda in tserar da ita dan baxan iya tafiya an barta a cikin dajin nan ita kadai ba ga ciwuwwuka duk a jikinta gashi bata cikin hayyacin ta, ban san hannun su wa zata fada ba dan zata iya rasa ranta a gurin. A lokacin nayi lissafin daga mun je gida zan dauke ta in kaita gidan iyayen ta, saboda na dauka kano zamu tafi a lokacin, sai da muka shiga mota sannan na fahimci ba Kano zamu dawo ba, na fahimci imo yake da niyyar ya kai mu" "Babu irin magiyar da banyi masa ba a lokacin da muka shiga Abuja akan mu samu asibiti mu ajiye ta sai mu kira ku mu gaya muku inda take sai muyi tafiyar mu amma yaki yarda, sai a lokacin na fahimci dalilin da yasa ya yarda ya dauko ta, saboda ya fahimci na damu da ita ne shi kuma yana neman abinda zaiyi amfai dashi gurin rike ni. Tun a lokacin na kasa tantance cewa daukan Fatima da nayi shine dai dai ko kuma kuskure ne?" "Sai da muka je lokoja sannan na roke shi da kyar ya yarda muka kaita asibiti, shima dan yana ganin in bai kai ta asibitin ba zata zamar masa gawa a cikin mota dan sosai take zubar da jini yadda daga ni har ita duk jinin ne a jikin mu. Idonta ya juye gabaki daya sai sumbatun kiran Hussain take yi. Asibitin ma kin karbar ta sukayi suka ce sai an dauko police, sai Allah ya taimake mu ya dan basu cin hanci sannan suka karbe ta suka tsayar da jinin suka kuma bata first aid treatment sannan suka kara mata jini leda daya, haka muka kuma daukan hanya duk da cewa jinin bai ishe ta ba amma dai ta dan samu kanta kadan". "Daga nan bamu kara tsayawa ba sai a imo, ko sallah basu tsaya nayi ba duk da magiyar da nayi ta yi musu, tun a lokacin na fara dana sanin daukan Fatima, dana sani na nuna masa ban san ta ba maybe Allah zai hada ta da na gari su taimaka mata amma na fara tunanin wannan tafiyar tamu a kwai matsala babba a cikin ta. Na farko matsayin Fatima a kasar hausa, yar sarki, kuma matar prominent person kamar Hussain Aminu ba kowa ne zai fahimci gaskiyar magana ba. Musamman in aka yi la'akari da banbancin yare da addini da yake tsakanin yankin da take da yankin da aka kaita" "Muna zuwa ya saka a ka rufe ta a daki, I had to sign some papers na agreement a tsakanin mu kafin ya bari likita yazo ya dubata sosai yayi treating dinta sannan kuma ya fahimci cewa haihuwa tayi, shi duk a tunaninsa sai ya dauka ni ta haifa wa Da, shi ya dauka da gaske budurwa tace kuma ina sonta sosai tunda har na aikata abinda ya samar da Da a tsakanin mu, ni kuma ban gaya masa gaskiya ba saboda bana son ya fahimci matsayin ta, dan wannan zai chanja motive dinsa na riketa. Bayan ya rufe ta sai ya zauna ya shirya min warnings akan ko da wasa in na nemi barinsa ko kuma kubutar da budurwa ta daga hannunsa to zai kashe ta ya binne ta a gidan yadda babu wanda zai kuma jin labarin ta. Ni na san shi, na san halinsa, na kuma san abinda zai aikata da kuma abinda ba zai aikata ba, dan haka nasan zai iya yin abinda yace ba tare daya ji komai a jikinsa ba" Ba wai hakan yana nufin babana yana da mummunan hali ba ko kuma ya taba kashe wani ba, a'a, amma yaki jinin hausawa kuma ya tsani musulmai, yana kallon su a matsayin terrorist dan kullum yana iƙrarin in rigima zata tashi tsakanin kabilu zai yo iyakacin kokarin sa gurin ganin ya kashe as much Muslims as he can, "dan a rage iri". Sannan kuma abinda ya faru dani na juya wa addinin su baya da nayi ya kara wannan tsanar, kuma nasan yana sona sosai, babu abinda ba zaiyi ba saboda yaga ya zaunar dani a tare dashi" "Yayi deleting all my social media accounts, yakuma hadani da bodyguards yadda duk inda na saka kafata nan suke mayarwa duk dan kar inyi trying guduwa ko contacting wani daga North. Amma ni ko sau daya ma ban gwada guduwar ba saboda nasan zama na ne kadai yake keeping Fatimah alive a hannunsa, kuma ko sau daya ban gwada contacting dinku ba, duk da cewa bani da numbers dinku gabaki daya, amma ban gwada nema ba, saboda ina tsoron abinda hakan zai haifar" "Ban sani ba ko zaka fahimta, ko sauran mutane zasu fahimta, amma ni nayi gudun kar in neme ku ya fahimci na neme ku yayi mata wani abu kuma kuje ku tarar da yayi mata wani abu and that can lead to religious and tribal crisis musamman in akayi la'akari da matsayin fatima. Fatana shine ta samu lafiya sai in dauko ta mu gudu tare in kawo ta har gidan su" "Dakin da take ciki babu wanda yake shiga sai ni, sai Mama, ita ma kuma da farko babu ruwanta da ita sai da na roke ta taimaka mata, ita ma na nuna mata cewa budurwa tace na nuna mata kamar haihuwa tayi babyn ya mutu shine an taho kaita asibiti akayi accident har kuma Daddy ya same mu a hanya. Wannan yasa ta kulata ta yi jinyar ta da duk irin abinda ya kamata ayi wa matar data haihu har ya kasance ta warke sosai. Ina nufin external injuries dinta" "Babban tashin hankali na shine yadda na lura da halin da Fatima take ciki, farko ko sunan ta bata sani ba, sunan Hussain kawai ta sani, shima kuma dana nemo hotonsa na nuna mata sai naga bata gane shi ba sai cewa tayi "kaga wani saurayi kyakykyawa kamar kai" bata san kowa ba bata san komai ba sai ni, dole sai dai in zauna tare da ita in kuwa har na fita to zata yi ta kuka ne har in dawo. Ni kuma bansan much ba akanta except cewa yar sarkin kano ce kuma matar Hussain. Sai nayi ta nemo pictures din sarkin kano dana yayan sarkin wasu hotunan ma harda ita a ciki sai in nuna mata wai ko zata tuna amma ba abinda take tunawa sai dai ta nuna hoton ta tace "ga me kama da ni". Adam ya girgiza kansa yace "it was hectic. I couldn't get her to remember anything. In kuma bata tuna ba ba zan iya smuggling dinta out ba dan zata tona mana asiri ne, kuma I needed her to remember saboda ta bada shaida a kaina idan munzo nan din in ba haka ba ni zan fada ciki. Ba kowa ne zai fahimta ba. I almost lost my mind ni din ma akan hakan. Zaman guri daya, rashin waya, rashin wanda zan gaya wa damuwa ta ya fahimta sai dai in saka ta a gaba muyi ta hira, inyi ta bata labarai na few of abinda na sani na rayuwar ta da kuma ni tawa rayuwar, inyi ta bata labarin ku, da labarin Sumayya" ya danyi murmushi yana shafa fuskarsa yace "how is she? Tayi aure ko?" Hassan ya dauke kai gefe yace "she is fine. Ya akayi kuma kuka fito?" Adam yace "rana daya, a farkon wannan shekarar, na shiga da magazine ina nuna mata hotunan celebrities wai ko zata gane wata ko wani a ciki, sai kawai taga hoton wata da ciki, and that was the switch, sai ta fara neman cikinta wai ina cikin ta yake? Ina babyn cikin ta? Daga nan kuma sai aka fara samun improvement ta fara tuna abubuwa kadan kadan, little at a time, amma kuma tumawar sai ya saka ta koma very emotional, kullum cikin kuka, kullum cikin tunani, ta fahimci ita wacece ta kuma fahimci cews bata gida yanxu. A ranar data tuna da labarin mutuwar Hussain naga tashin hankali, sai da na nemo allurar bacci nayi mata duk da ban iya ba sannan ta samu nutsuwa." "Daga nan ta tuna abubuwa da yawa, yarintarta tashinta da komai amma banda accident din su banda kuma haihuwarta. Wannan shi ya tayar mana da hankali, muka hada kai ni da ita muka nemi solution. Solution din kuma da muka tsayar shine mu nemi taimakon Mama na, kasan tsakanin Da da uwa sai Allah, na nuna mata in bata taimaka mana ba zamu gudu da kan mu kuma komai zai iya samun mu. To ita ma dan zaman da tayi da Fatima ta shaku da ita, she forged an ID card for us yadda zamu iya tahowa ta jirgi, and jiya she used kissar su ta mata ta kawar da hankalin Daddy da guards dinsa daga kan mu sannan muka taho tare" Maybe ba zaka yarda ba, and maybe wasu mutanen ba zasu yarda ba amma wannan labarin dana baka to the best of my knowledge, shine gaskiya. In akwai wani abu da na manta ban gaya maka ba in na tuna zan gaya maka. Ina fata kuma ina saka ran ko kowa bai yarda dani ba kai zaka yarda dani" Forgive the typos please *She Smiles* Hassan ya dago kai yana kallon sa, yana lura da yadda damuwa take bayyane a kyakykyawar fuskar sa, ya fahimci damuwarsa da ba kowa ne zai dauki uzurinsa a matsayin uzuri ba, sai mai zurfin tunani musamman akan yadda alaka take a tsakanin kabilun guda biyu. Idan sanarwa ta fita cewa an samu gawar gimbiyar kanawa wadda aka rasa ta shekara da shekaru a gidan inyamuri a garin owerri, wannan ba karamar magana ba ce ba, wadda zata iya jawo asarar rayuka masu yawa a cikin kabilun. A lokacin kuma babu wani bayani da Adam zaiyi wanda za'a fahimce shi, laifin zai zamo kidnapping, enslaving, maybe a hada da sexual assualt da kuma murder. Ya fahimci cewa kokarin Adam shine ya dawo da Fatima gida alive and in one piece, kuma alhamdulillah ya dawo da ita din a hakan. Wannan kadai ya isa a jinjinawa rikon amanar sa, idan wani ni ko blinking eye ba zaiyi akan ta ba musamman idan ya fahimci ta yi loosing memory dinta. Ko kuma ma ya taimaka wa baban nasa gurin assaulting din ta, kuma yanzu he risked his life, and his mother's life dan ya dawo da Fatima gidan su. But still..... "Na fahimce ka Adam, really na fahimce ka, but you could have done something, you could have contacted me ta hanyar wayar either mamanka ko one of your sisters. You could have at least warn me cewa you two are alive amma ga halin da ake ciki in yaso sai mu hada kan mu muyi finding solution ba tare da wani ya sani ba. You should have contacted Sumayya, ta damu sosai da rashin ji daga gare ka, sau biyu muna zuwa kano gidan ku dan neman labarin ka" Adam ya bude ido "but how? Ya akayi kukayi tunanin nemana a gida? Na dauka zaku dauka na mutu ne, grieve and just move on?" Hassan yace "Ruqayyah. She admitted cewa ita ce ta sanar da mahaifinka cewa ga inda kake, I guess shi kuma ya ringa binka har ya same ka kai kadai ya kamaka" Adam ya dafe kansa yace "Ruqayyah! I thought as much duk da cewa shi kansa ya nuna min bai san wacece ba but ita nayi zargi dama. Ban san me na tsare wa Ruqayya a duniya ba" Hassan yace "babu abinda ka tsare mata, bata sonka ne kawai, and that's what she did to mutanen da take iƙrarin tana so ma ballantana kai data ambata cewa bata son ka. You should be grateful to Allah daya kasance a haka kawai ta barka bata illata ka ba" yadda ya fadi maganar da daci ya saka Adam ya kalle shi, yana tuna irin son da yake yiwa Ruqayyah da kuma yadda yake tsayawa a bayanta akan komai. Ko ya fahimce ta ne yanzu? But bai tambaya ba sai Hassan ya kuma cewa "zuwan mu na farko mun samu mai gadi, shi ya tabbatar mana da cewa kana tare da iyayenka, amma ko kadan bai gaya mana wani abu daya danganci Fatima ba, zuwa na biyu kuma muka samu kanwarka, she told us kana lafiya tare da girlfriend dinka and that ka koma school." Adam ya dago kai yana kallon sa a hankali yace "and Sumayya heard that?" Hassan ya dauke kai yace "taji mana. And wannan ne ya saka har yanzu nake ganin saka cin ka. You should have told us cewa kana raye ko da kuwa baka gaya mana zancen Fatima ba" Adam yace "in Sumayya ta san ina raye she won't move on, zata dage cewa in dawo gare ta abinda ni kuma ba zan iya ba, in taga ban dawo ba kuma zata yi tunanin bana son ta ne ko dama yaudarar ta nayi. Nafi son in bar good image of me a ranta. Nafi son tayi aurenta ta haifi yayan ta, I sacrificed my love for Sumayya saboda Fatima" Hassan ya gyada kai yana kara fahimtar sa yace "not just for Fatimah, for something much more than Fatimah. Na yarda da kai Adam, na fahimce ka da manufar ka, kuma zanyi iya kacin karfina in ga cewa iyaye da yan uwan Fatima suma sun fahimce ka insha Allah kuma zasu yi saboda mutane ne masu ilimi ba gidadawa ba ne ba". Sai ya mike a lokacin da Adam yake cewa "how is she?" Hassan ya juyo yana kallon sa, ya gane wace "she" din da yake magana akai amma sai yayi shiru har sai da Adam ya sake cewa "tayi aure ko?" A cikin muryar sa yana jin hope, hope din cewa maybe har yanzu bata yi aure ba. Sai ya gyada masa kai ba tare daya kalle shi ba yace "tayi aure, ta haihu ma last year" Adam yayi shiru yana jin haushin kansa da ya saka ran cewa Baba zai barta a gida har tsahon shekara biyar ba tare da yayi mata aure ba. Ya danyi murmushi, irin murmushin nan mai ciwo yace "Allah ya sanya alkhairi, Allah kuma ya raya abinda aka samu. Ni kuma Allah ya hada ni da wadda zata zame min alkhairi fiye da Sumayya" sai dai shi kansa daya fadi maganar yana tunanin anya kuwa zai samu wadda tafi Sumayya? Shi gani yake Sumayya ta hada komai da yake bukata a gurin mace. Sai dai tunda Allah yace, yasan tabbas Allah babu abinda ba zai iya ba. Tabbas soyayya Sumayya is the biggest sacrifice da yayi for Fatimah. A lokacin ne aka shigo akayi musu iso zuwa inda aka gabatar musu da breakfast daga nan kuma aka shigar dasu inda zasu hadu suyi magana. A cikin gida kuma tun sanda su Aunty suka shiga komai ya rikice, sunga Fatima sun kuma tabbatar ita din ce ba wata ba, sai dai ganin Fatima ya tayar musu da mikin mutuwar Hussain, dan babu wanda bai yi kuka ba a cikin su musamman ita ma Fatima din da sai da suka gama nasu kukan suka koma rarrashin ta. Ita tana tambayarsu ina baby su suna tambayar ta labarin baby. Lamarin daya daga dukkan hankulan su baki daya, dan daya kamata ace ya kasance mafi soyuwa a gurin su baki daya shine kuma dan da basu san inda yake ba, hasali ma basu ma san ko yana da rai ko bashi da rai ba. Da kyar aka samu suka dan ci abinci kadan, sannan ne kuma aka raka Fatima gidan baki dan su gaisa da Hassan, sai dai kuma zuwan nata sai ya kasance sai da akayi nadamar yinsa, dan ganin Hassan ya saka gabaki daya ta nemi ta fiya daga hayyacinta a dole aka dawo da ita zuwa gida babu shiri, shi kansa Hassan duk da jaruntar sa da dauriyar sa da kuma karfin zuciyarsa amma ganin Fatima sai da saka yaji tamkar yau ne ya binne Hussain. Sai da komai ya nutsa sannan aka samu aka zauna gabaki daya, tun daga kan yanuwan Fatima da ita kanta Fatimah zuwa Hassan da Aunty da yanuwansa da Sumayya, sai Adam wanda yau aka shigar dashi cikin maganar sannan kuma da Maman sa wadda tun jiya Fatima da kanta ta saka aka dauko ta daga inda akayi mata masauki aka dawo da ita bangaren Hajiya fulani inda ita fatiman take. Mai martaba sarki ne kawai da matansa basa gurin, amma suma suna dakin da yake jikin nan kuma suna ji suna ganin duk abinda ake yi ta hanyar Camera. Farko an fara gabatar da addu'a sannan kuma aka yi bitar abubuwan da already kowa ya sani, sai kuma ka koma kan abubuwan da ba'a sani ba. Adam aka fara tuntuba akan ya fadi nasa side din, sai ya bayar da labari kamar yadda ya bawa Hassan dazu. Sai dai bayan ya gama, kamar yadda yayi tsammani sai ya fahimci fiye da rabin mutanen gurin suna binsa da kallon rashin yarda kuma idanunsu cike da tambayoyi, ai kuwa tambayoyin suka yi ta jera masa yana amsa musu dai dai da sanin sa, sai dai wani abu da ya burge Hassan shine ko kadan babu alamar tsoro ko rashin gaskiya a fuskar Adam sai dai takaicin cewa an kasa fahimtar sa. A karshe Umar yace "ni har yanzu na kasa gane cikakken dalilin da zai sa ka dauki shekaru biyar ba tare da ka sanar mana da cewa yar uwar mu tana hannunka ba". Maganar da Fatima tayi ne ya saka duk suka dawo da hankalin su kanta, tace "ba zaka fahimta ba yaya Umar, ba zaka taba fahimta ba babu kuma wanda zai fahimta sai wanda ya ke a matsayi irin wanda Adam yake ciki. Sai wanda ya kasance a tsakanin kabilu guda biyu masu kiyayya ga junan su, sai wanda ya kasance tsakanin addinai guda biyu masu rigima da junan su, sai wanda ya kasance dukkan bangarorin biyu sunyi rejecting dinsa sannan kuma kuskure daya idan yayi zai iya tayar da rigimar da Allah kadai zai iya kwantar da ita, wannan shine kadai zai gane cewa Adam yayi iyakacin kokarin sa" "Adam ya gaya muku duk abinda ya kamata ya gaya muku, abinda kawai ya cire daga cikin maganar bai gaya muku ba shine ba wai memory na kawai nayi loosing ba, nayi loosing har da sanity dina. I was crazy. Kuma nasan yaki fadar haka ne kawai saboda kada ya bata image dina, saboda yana so ya kyautata min dan shi din ya kasance mai kyautatawa ne sosai a gare ni" "Adam yayi min abinda ba kowa ne a cikin ku zai iya yi min ba, ba kowa ne zai iya kula da marar lafiya irin rashin lafiyar da nayi ba har na tsahon shekaru biyar ba tare da ya gaza ko ya nuna gazawa ba. Farko ya taimaka min, ya dauke ni daga dajin nan wanda da ya ga dama zai iya bin babansa su tafi su barni anan, ko da ban hadu da mugaye sun azabtar ko kuma kashe ni ba to da yanzu watakila ina can ina yawon hauka a kauyuka. Daga nan kuma yayi sacrificing dukkan rayuwarsa for me, his freedom, his choices, his love" ta fada tana kallon Sumayya, wadda ta sunkuyar da kai hawaye yana zuba a fuskarta. "A duk tsahon shekarun nan Adam shine uwata, shine ubana, shine brothers and sisters dina, shine friend dina, shine doctor na, shine maid dina. Kuma he did duk wadannan roles din perfectly. Adam har allura ya koya kuma yake yi min a duk lokacin da bani da lafiya. He cried and laughed with me. Duk abinda ya fada, wadanda na tuna haka suke babu gyara, wadanda ban tuna ba kuma na yarda da abinda yace hundred percent saboda banajin a rayuwata na taba haduwa da honest man irin Adam" Sai ta taso daga inda take zaune tazo gaban Adam ta durkusa tace "bayan na dawo hayyacina, bana jin na samu damar gode maka, hankali na gabaki daya ya tafi ga cewa in dawo gida in tabbatar da labarin rasuwar Hussain sannan kuma inji labarin dana, that was so selfish of me, kayi hakuri. Nagode Adam. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi dan ni nasan ba zan iya saka maka akan abinda kayi min ba. Allah ya biya ka da gidan aljanna Adam" Sai yayi murmushi yana kallon cikin idonta yace "Allah, ya bamu aljanna gabaki daya. And thank you too for standing up for me". Daga nan babu wanda ya kuma bude bakinsa yayi questioning Adam. Sai kuma Hassan ya fara nasa bayanin, bai rufe komai ba akan tsohuwar matarsa Ruqayyah da kuma karyar da tayi akan wadda ta mutu da kuma zarginta da yakeyi a yanzu da yaji komai na cewa tana da masaniya akan jaririn Fatima. "Sanda Adam ya ganta ta haihu, meaning a gurin da suka yi hatsarin ko kuma a kusa da gurin ta haihu, babu wanda yake witness sai Ruqayyah tunda ita kadai ta tsira sauran sun mutu, sannan kuma boye maganar mutuwar kawarta makes her guilty, idan bata da hannu a batan yaron mai yasa zata ce Fatima ta mutu? Me yasa zata yi karya? Sannan dagewarta akan dukiyar Hussain harda threatening bata masa suna duk dan saboda kudi makes her guiltier, saboda ya nuna irin tsabar son kudin datake dashi ya nuna cewa zata iya yin komai saboda kudi" Sai kuma ya bada labarin irin yadda Ruqayyah ta yaudare shi har ya aure ta saboda kuɗin sa, da yadda tayi ta kokarin hada shi da Hussain da kuma Fatima duk dan saboda kudi, daga nan sai ya bawa Fatima hakuri akan sabanin da suka yi ta samu a lokacin zaman su tare, ta gyada kai kawai tana share hawaye, har a cikin bargon ta tana ji cewa Ruqayyah tasan inda dan ta yake. Abubakar yace "then what are we waiting for? Aje a kama ta mana ayi ta dukanta har sai ta fadi gaskiya" Umar yace "that crazy crippled witch. Tabbas zata aikawa dan aikin da nake yi a yanzu a tare da ita na san irin masifar son kudinta, amma ba wai a kamata ayi ta dukan ta bane ba solution, mu masu hankali ne masu ilimi ne dan haka zamuyi aiki irin na masu hankali kuma masu ilimi, zamu shigar da karar ta court, a tsaya ayi Shari'a, hakkin Shari'a ne ta tuhume ta a matsanta mata har ta fadi gaskiya sannan a yanke mata hukunci dai dai da laifin ta. Wannan shine abinda za'a yi" A haka aka tashi. Kowa ya yarda da shawarar da Umar din ya bayar, sannan mai martaba sarki ma bayan Umar din ya shiga gurin sa sai ya nuna masa amincewarsa akan hakan. A take kuma suka sake sabon zama tsakanin umar da Hassan suka nemi lauyoyin su suka yi hadin gwiwa gurin shigar da karar Ruqayyah a federal high court, Abuja. A bangaren Sumayya, tunda suka zo gidan take jin babu dadi, take jin inama bata zo ba da ta sani tayi zamanta a gida amma kuma tana so tayi supporting mijinta, tana son duk sanda mijinta ya shiga wani hali ya kasance cewa tana kusa dashi yadda da ya juya zai ganta ya fahimci cewa he is not alone. Sai dai kuma jin ta take yi tamkar outsider a cikin su, musamman bayan an shiga taron an fito, bayan an gama maganganu akan abinda ake zargin Ruqayyah tayi, kuma duk kusan kowa a gurin yasan cewa Ruqayyah twin sister dinta ce, sai take jin tamkar Ruqayyah ta dauki wani mummunan tambari ta biga a goshinta. Taji stress din gayawa iyayensu ya kuma dawo mata, musamman yanzu data fahimci mugun abinda Ruqayyah ta aikata ba wai boye mutuwar Minal bane kadai, har ma da batan dan jaririn Fatima. Bata san ta yadda zata iya gaya musu ba, tana tsoron kar zuciyar wani daga cikin su ta buga su rasa shi. Sannan ga Adam. Tunda suka shiga gurin taron ta ganshi, standing out a cikin duk mutanen gurin, tun daga kallon farko ta sunkuyar da kanta tana hana zuciyarta sake kallon inda yake, tana kara tunawa kanta cewa ita da Adam har abada, tana da mijin ta yanzu Hassan kuma yana sonta sosai itama kuma tana sonsa, yana kuma kyautata mata iyakacin kyautatawa. Bata kuma kallon sa ba, bata sani ba ko shi ya kalleta, bata sani ba ko yasan da zancen auren Hassan da yake kanta a yanzu? Dan haka suna komawa cikin gida sai ta ware kanta daga cikin mutane ta zauna ita da zuciyarta tana lissafin yadda rayuwa take tafiyar mata. Taji hukuncin da aka yanke akan Ruqayyah and her heart break for her sister. Me Ruqayyah ta mayar da rayuwar ta da tasu gabaki daya? Ba zata taba iya musa laifuffukan da ake tuhumar Ruqayyah akan su ba kamar yadda ba zata iya musa cewa Ruqayyah twin sister dinta ce ba, ko ma menene tayi, ko ma menene za'a yi mata she is still her sister. Ta goge hawayen fuskarta a lokacin da kira ya shigo wayarta daga Hassan. Ta daga tana kokarin gyara muryar ta tare da yi masa sallama sai yace "are you crying?" Ta girgiza kanta kamar yana ganin ta amma kuma sai kukan ya kwace mata gabaki daya. Yayi shiru yana sauraron ta, sai data gama kukan ta sannan yace "ki zo ki same ni yanzu" sai yayi mata kwatancen inda yake. A wani kebantaccen guri ta same shi shi kadai akan kujera. Ta zauna a gefensa tana kara goge idonta. Sai ya rike hannun da hannun sa daya ya kuma dago fuskar ta da daya hannun yana kallon cikin idonta yace "she doesn't deserve a single drop of your tears" ta gyada kanta amma sai wasu hawayen suka sake zubowa. Ya sake ta yana kallon ta "kinsan dai dole ne a kaita court ko?" Ta gyada kai "na sani, I just can't believe zata iya aikawa duk wadannan laifuffukan. The baby, the innocent baby, I can't believe Ruqayyah zata iya hurting baby". Ya dafe kansa da hannunsa, tunda ake yin maganar yakasa barin kansa yayi tunanin possible abubuwan da Ruqayyah tayi da babyn. Ba zai iya tunanin abin ba, in yayi tunanin kuwa tabbas zai iya rasa hankalin sa baki daya. Tace "ni yanzu ta yaya zan gaya wa su Baba, ni kaina yaya nake jin maganar nan ballantana su? Ina tsoron abinda zai iya samun su ta dalilin Ruqayyah" yace "babu abinda zai same su, ki barni ni zan san yadda zanyi in gaya musu, kamar yadda zan san yadda zanyi in gaya wa Alhaji Kabiru ta hanyar da za'a samu maslaha da fahimtar juna. Amma Ruqayyah kiyi hakuri, dole hukunci sai ya hau kanta, dole ta fadi abinda tayi da yaron nan kuma dole a hukunta ta da duk laifin da aka kamata da shi" Sumayya ta gyada kai, tana so ta saka zuciyarta akan abinda yake cewa amma ta kasa. Sun dan jima a haka sannan yace "Adam yana tambayarki. He wants to know if you are okay" ta dan dago kai tana kallonsa tace "ka gaya masa ai, kace masa am okay ko?" Ya gyada kai yace "na gaya masa, ina so inji ne ko kina son ganinsa, kina so kuyi magana dashi dan ku......" Tace "duk abinda zanji daga gare shi na riga naji dazu, ya fadi dukkan excuse din sa kuma na gamsu dashi. Na ganshi lafiya lau yake. Babu sauran Magana tsakanin mu kuma" yayi shiru yana studying dinta, ita kuma tana jin idinsa a kanta amma taki dago kanta, kuma har cikin ranta tana jin cewa babu wata magana da zasuyi da Adam kuma. Sai yace "shikenan. Na gaya masa dama cewa kinyi aure, though ban gaya masa wanda kika aura din ba yet, sai dai nan gaba" ta gyada kai kawai, shi kuma a cigaba dayi mata bayanin yadda suka fara shirya shigar da karar Ruqayyah. Already har sunyi waya da police za'a kamata a yau kafin su koma Kaduna. "Bama son ta samu damar guduwa ko planning something" *************. **************. ************* Jaririn ne a hannun ta yana ta tsalala kukan da take jinsa a cikin kwakwalwar ta ba a kunnuwan ta ba, kamar daga sama taga gate din gidan marayun a gabanta, cikin sauri taje ta ajiye shi a kofar gate din sannan ta juya da sauri zata bar gurin sai dai kafarta ta rike ta kasa tafiya, sai kuma kafafuwan duka fara kankancewa suna motsewa har suka koma kamar na jarirai sannan sai ya fadi a gurin da take, shi kuma jaririn data ajiye din sai yayi ta girma har ya koma katon cikakken mutum, ya taso zuwa inda take kwance sai taga kammannin sa sun zama irin na Hussain, sai ya daga kafa dai dai saitin fuskarta tamkar zai talitse ta. Ta farka a firgice tana hada gumi, zuciyarta tana bugawa kamar zata fito daga kirjinta. Wannan ba shine karo na farko data yi irin wannan mafarkin ba amma kullum in tayi shi tana jin wani irin matsanancin tsoro da yake ratsa duk sassan jikinta, irin tsoron da bata taba jin irinsa ba a rayuwar ta. Ta share gurin fuskarta da bayan hannunta tana jin ana kiraye kirayen farko na sallar asuba. Ta yaye abin da ta rufa dashi tana kallon motsatstsiyar kafarta, her heart breaking. Babu irin maganin da bata yi ba a cikin shekarun nan, na asibiti dana gargajiya dana islamic amma babu cigaba sai dai irin cigaban mai hakon rijiya. A halin yanzu ta fara tunanin duk son da take yiwa bene dole ta hakura ta koma dakunan kasa dan hawa benen ya fara gagarar ta. Ta kuma yi kokarin a saka mata lift a gidan amma likitan ta yayi advising dinta against it "the same pressure change da ake samu a jirgin sama irinta ake samu a lift" wannan yasa dole ta hakura dan bata shirya tafiya lahira ba. Yanzu haka tayi order din wheel chair zata karaso next week... Ta mike tana dogara sandan ta taje bakin taga sannan ta jingina da jikin bango ta daga labule tana kallon duhun garin, zuciyarta blank ita kanta bata san tunanin me take yi ba. A lokacin taga motsin mota ta fito daga gidan Hassan, tabi motar da kallo amma sai taga ta tsaya a kofar gate din aunty amma ba'a fito daga cikin motar ba. Jimawa kadan taga wata motar ta fito daga gidan Aunty, sai taga Hassan ya fito daga motarsa wani a shiga shi kuma ya koma seat din gaba, sannan taga Aunty da wata da bata gane sosai ba saboda duhu sun shiga motar Hassan sannan kuma ta lura akwai wasu a daya motar, sai taga sun tafi a tare. Ta saki labulen kwakwalwar ta tana fara daukan chaji. Ina zasu je haka? Har tayi sallah gari ya fara wayewa bata ji hankalin ta ya kwanta daga wannan tafiyar tasu ba. Ta lallaba da kyar ta sauka kasa inda tayi breakfast sannan ta zauna tana observing yaran ta suna ta kai kawon gyaran gida da sauran aiyuka. Sai ta kira lubabatu, daya daga cikin sababbin kuma amintattun yaranta. "Luba kije gidan Aunty, ki dan yi dabara ki tambayi mai gadi ko yasan inda suka tafi. Ki dan bugi cikinsa kadan in kinga ya fara tunanin wani abu sai ki rabi dashi ki tambayi na gidan Hassan". Ta koma ta kwanta akan kujera tana jiran Luba ta dawo, tasan duk sanda mutum zai fita ya kan gayawa mai gadin gidan sa inda zashi. Maybe gurin da zasu je bashi da wani muhimmanci amma tana so ta sani, tana son ta san komai a harkokin su kar su shirya mata wata gadar zaren da bata san da ita ba. Luba bata dade ba ta dawo dan direct mai gadi ya gaya mata kano suka tafi, kuma ya tabbatar mata gabaki dayan su ne suka yi tafiyar yara kadai suka bari a gidan. Labarin daya rikita zuciyar Ruqayyah, Kano? Me zai saka su tafi kano irin wannan tafiyar? Gabaki dayan su? Har yamma tana ta sakawa da warwarewa. Tayi tunanin tayi amfani da wannan damar ta shiga gidan taga ƴaƴan ta, dan kullum suna ranta amma bata da damar ganin su sai ta taga, kuma tana zargin Sumayya ce ta hana ake kawo mata su dan da kafin a aure ta ai ana kawo mata su. Amma kuma mood din ta ba zata iya fita ba, zata jira har sai ta yanke hukuncin me Hassan da family dinsa suka tafi yi Kano irin wannan tafiyar. Amsa daya kanta yake bata, Fatima ta dawo, ta jima tana jiran dawowar Fatima gida dan yana daya daga cikin abubuwan da suke hanata bacci, idan kuwa hakane to sun tafi kano ne dan suyi deciding fate dinta. Na farko tasan by now sun fahimci gawar wa suka binne, meaning yan uwan Minal will soon be after her too. Tayi bitar yadda komai ya kasance, bata san daga ina Fatima take ba kuma bata san me tayi a lokacin da bata gida ba but tasan soon zata sani dan tasan soon police zasu shigo cikin gidan su kama ta. Ta yanke hukuncin abinda ya kamata tayi a yanzu, sauran hukunci kuma sai taji sauran bayani. Ta dauko wayarta ta ta kunna kamar yadda ta saba yi kullum ta shiga twitter neman labari. And there, ta tabbatar da zargin ta. "Yar maimartaba Sarkin Kano da ake zargin ta mutu a hadarin mota shekaru biyar da suka wuce ta dawo gida". Ta rufe shafin ta nemo number din secretary dinta. "Hello Lukman. Ina so ka bincika min the best lawyer available a kasar nan, as soon as possible. And I also want you to hire bodyguards for me" ta katse wayar sannan ta kira Luba ta aika ta sama ta dauko mata kaya masu kyau complete set, sai kuma ta saka ta ta hada mata ruwan wanka anan kasa ta shiga tayi ta shirya shaf da ita kamar zata je gida biki sannan ta dawo ta zauna ta zubawa kofar shigowa palon ido Bata jima ba kuwa aka turo kofa aka shigo, police, as she expected. "Madam you are under arrest" sai ta dago musu hannu ta miko musu. Suka saka mata handcuffs sannan wata macen police ta taimaka mata suka fita da ita suka saka a motar su, a lokacin da suke fita daga gidan a lokacin ne kuma motar su Hassan take kokarin shiga gidan sa. Ta side din idonta ta kalle su, suka hada ido da Sumayya, sai kuma da Hassan, and she smiles. A very wide smile. *Shari'a, Saɓanin Hankali* A ranar Ruqayyah a cell ta kwana bayan police sun karanto mata abinda ake tuhumar ta dashi, direct kuma tayi denying all accusations against her, sai dai police din sun gaza gurin amfani da karfi dan tuhumar ta saboda kasancewar ta nakasashshiya kuma mace. Sai dai basu tausaya mata gurin garkama ta a cell tare da barin ta ta kwana akan dandaryar siminti cikin sauro da zafi. Haka ta kwanta a kasa a kudundune a cikin hijab dinta. Zuciyarta blank. Sai dai kamar yadda ta rigata sani, sam bata yi bacci ba dan ta raba ga ta gama zama addicted to sleeping pills dinta, in dai bata sha ba to kuwa tabbas ba zata ko rintse idonta ba kuma tana sane taki tahowa dasu daga gida kuma taki fadar cewa tana shan magani, kukan jaririn bai barta ba haka kuma hoton gawar Minal bata daina kallon taba kamar duk sauran darare, amma haka ta daure sai cikin dare sannan ta tashi daga kwanciyar ta ta fara kurma ihu tana cewa gasu nan sun biyo ta zasu kamata. Police din gurin suka yi kanta cikin tsawa da hargagi amma bata kula su ba ta cigaba da ihun ta har sai da suka bude cell din suka fito da ita sannan ta kankame wata police tana kuka wai copses ne suke binta zasu kama ta. Sannan ta gaya musu cewa kullum haka suke zuwa mata tayi ta ganin su, tayi ta ganin abubuwa wanda mutane basa gani, ta gaya musu cewa a yanzu haka tana kan medication a gurin likitan ƙwaƙwalwa kuma tana ganin mental therapist duk sati. Wannan yasa da sassafe yan sanda suka tafi da ita gurin doctor din da tace ya dora ta on medication, likitan data gani tun lokacin da tayi overdose na sleeping pills, kuma ya tabbatar musu da cewa tana da file a gurinsa sannan ya tabbatar musu da cewa tabbas tana abinda ta fada na gane gane da jiye jiyen abubuwan da sauran mutane basa gani ko ji hakane. Wannan yasa police din suka bar ta a gurin sa dan ya cigaba da bincike akan lafiyar kwakwalwar ta, a bisa tsaron dan sanda guda daya. Wannan abin yayi mata dadi, at least komai ya tafi a yadda take so kuma bata damu da cigaba da zama a asibitin ba dan dama ita da asibiti kawayen juna ne. Abu guda daya da ta sani dai shine, ko sama da kasa zasu hadu ba zata taba karbar laifin da ake tuhumar ta dashi ba, saboda da zarar ta karbi laifinta to ta tashi daga aiki, she is definitely going to prison and zata rasa duk abinda ta mallaka saboda kudin da Hassan ya bar mata na gadon Hussain ne, in kuwa har dan Hussain yana da rai to Hassan bashi da gado ballantana har ya bar mata. Ko da ace an bar wa duk sauran da suka ci gadon Hussain saboda basu sani ba ita dole a karbi kudin hannunta saboda ta sani. She will never, never plead guilty. Duk wata sharia da za'a yi lalube ne a cikin duhu dan basu da wata shaidar cewa tabbas ta aikata abinda uke zargi, zargi ne kawai, kuma babu alkalin da zai yanke mata hukunci based on zargi. Karkarinta ayi ta jan shari'ar har a gaji a kore ta batare da an yanke hukunci ba. Matsalar ta kawai shine case din Minal, anan ne kuma take buƙatar lawyer din da zai tsaya mata yadda maganar zata tafi kamar yadda already ta riga ta tsara. Daga Hassan har Sumayya sunga murmushin fuskar Ruqayyah, and that made Hassan very frustrated. Wato murmushi ma take yi ko? Ta salwantar da rayuwar dan Hussain and she is smiling, tana ganin taci banza kenan ko me take nufi? Sai a lokacin yayi nadamar da ya yarda suka shigar da police ciki. "Ruqayyah shaidaniya ce, shaidan ma kansa ya sara mata wajen shaidan ci. She is planning something, I can feel it" Sumayya ce tayi ta rarrashin sa, da kyar ya nutsu sannan suka shirya da daddare suka tafi gidan Baba tare, Hassan kamar yadda yayi wa Sumayya alkawari shi ya zauna ya gaya wa Baba, Inna Ade, Sulaiman da Zunnur labarin halin da ake ciki, da duk kanin zargin da ake yiwa Ruqayyah. Sannan a karshe ya gaya musu cewa tana hannun police. Ranar Sumayya taga tashin hankali. Bata taba ganin kukan Inna Ade irin na ranar nan ba, kuma bata taba ganin kukan Baba ta sai a wannan ranar,tsinuwa ce kawai bai yi wa Ruqayyah ba har sai da Hassan yayi ta basu hakuri dan hada kai suka yi gaba daya su biyar din suna kuka kamar rayukan su zasu fita. Baya jin da ace labarin mutuwar Ruqayyah aka kawo musu zasu yi irin wannan kukan kuma su shiga irin wannan tashin hankalin ba, sai yaji cewa ba su yake tausayawa ba, Ruqayyah yake tausaya wa, in dai har iyayen ta zasu iya yin irin wannan kukan su zubar da irin wannan hawayen a kanta baya jin tana bukatar wasu sauran alhakin dan rusa rayuwar ta. Hakkin iyayen ta ma kadai ya ishe ta. A gidan ya bar Sumayya yace ta kwana tare da iyayenta ta kwantar musu da hankali, daga nan gida Alhaji Kabiru ya je, ya yi packing a kofar gidan sannan ya kira wayar sa ya gaya masa yazo. Ba'a jima ba sai ga shi ya fito da kansa yana murmushi tare da yi masa iso kan cewa ya shiga cikin gidan, shi kuma sai yaki shiga. Yanayin fuskarsa ya katsewa Alhaji Kabiru murmushin sa, dan ko makaho ya shafa fuskar Hassan yasan hankalin sa a tashe yake, yace "lafiya kuwa Hassan? Da fatan dai duk iyalin lafiya lau suke?" Hassan ya shafa fuskarsa yana jin ina ma dai bai zo ba? Ina ma dai ya bi maganar Sumayya ya bar police sun zo sun gaya masa amma sai yaje jin in yayi haka kamar bai kyauta ba, kamar honouring din Alhaji Kabiru zaiyi by telling him by himself. Yace "iyali duk suna nan lafiya Alhaji. Nazo ne in sanar maka da cewa an samu labari, akan Amina" Alhaji Kabiru yayi shiru yana kallon sa, ya kasa cewa komai dan yanayin Hassan ya tabbatar masa da abinda yake gayawa kansa kullum cewa Minal bata raye, kawai dai rashin ganin gawarta ko kuma wani abu da zai tabbatar masa da haka ne yasa har yanzu yake dan saka rai kadan. Jin yayi shiru yasa Hassan ya kara da cewa "sai hakuri Alhaji, Allah yayi mata rasuwa tun a ranar data bar gida". Alhaji Kabiru ya rufe ido yana jin information din yana sinking sai kuma ya bude yana kallon Hassan da yaji kamar zaiyi kuka yace "bismillah Hassan, mu shiga ciki sai kayi min bayanin yadda ka riga ni samun wannan labarin" Hassan ya gyada kai, da yaso suyi magana briefly amma ganin yanayin alhajin ya saka yaji ya kamata yayi masa bayanin komai dan duk da cewa Minal ba mace ta gari ba ce ba amma still matarsa ce kuma dansa ne ta tafi lahira dashi a cikin ta. Kwana biyu bayan nan Hassan bisa jagorancin police suka raka Alhaji Kabiru, baban Minal da kuma yayyen ta guda biyu zuwa inda kabarin ta yake. Shirye shiryen zuwa court ake tayi daga dukkan bangarorin uku, bangaren Hassan, Fatima, da kuma Ruqayyah da har yau take tsare a asibitin ƙwaƙwalwa a bisa kulawar yan sanda. Sai dai sun samo mata maganin baccin ta kullum tana sha tana yi bacci kadan kamar yadda dama a gida kadan din take iya yi. An samo mata lawyers har gida uku amma duk babu wanda yayi mata, sai a karshe bayan ta kwana biyar a hannun police sannan aka samo mata wanda yayi mata. Barrister Lukman. Tana kallonsa taji cewa yayi mata, so smart looking, sannan ga record dinsa na cewa baya loosing case no matter how bad it is sai yabi ya warware shi, bai damu da ko client dinsa yana da gaskiya ko kuma bashi da gaskiya ba, abinda ya damu dashi shine yayi winning ya kuma keeping reputation dinsa na cewa baya loosing case. Kudinsa yana da tsada sosai, amma tasan idan tayi nasara to yaci kudinsa dan kudin are nothing compared to going to jail and loosing everything. Dan haka ta zauna ta tsara masa duk yadda take so al'amurra su kasance, making sure cewa shi kansa da yake lawyer dinta bata fada masa gaskiyar magana ba amma shi ya gane cewa she is guilty ita ma kuma tasan ya san bata da gaskiya. Amma sai ya gyada kai yace "this is a piece of cake. Consider it done". A bangaren su Hassan sun hada kai sun shigar da single kara da sunan Fatima, sunyi staring dukkan charges din da suke accusing Ruqayyah with, sannan sun shirya dukkan shaidun su suna ji a ransu cewa Ruqayyah bata da hanyar kubucewa wannan shirin nasu. Ba'a saka da nisa ba shari'ar saboda ta manya ce, aka saka rana, rana tazo sannan aka zauna zaman court, kowa ya hallara har da miji da kuma yan uwan Minal wadanda suka zo da ganin an yi serving justice for Minal. Alkali ya shigo aka tashi sannan ya zauna kowa ma ya zauna a gurin sa. Lawyers din Fatimah gida biyu na Ruqayyah guda daya, aka gabatar da kara sannan alkali ya bayar da da umarnin aka shigo da Ruqayyah, jikinta sanye da kayan marasa lafiya, hannunta da ankwa. Aka karanta wa Ruqayyah charges dinta guda biyu. Na farko zambo cikin aminci, inda ta boye mutuwar kawarta tayi replacing dinta da mutuwar matar kanin mijinta dan mijinta ya samu gado ita kuma ta samu daga gare shi. Na biyu salwantar da rayuwar jaririn dan Fatimah. "How do you plead?" "Not guilty" ta fada direct. Daga nan sai Lawyer din mai kara guda daya ya tashi ya fara bayani, ya dauko labari tun daga kan rasuwar Hussain, tafiyar su Fatima a mota da Ruqayyah da Minal da kuma accident din da suka yi a hanya. Zuwa kiran da Ruqayyah tayi wa Hassan da wayar Fatima ta gaya masa cewa sunyi accident kuma Fatima da driver sun mutu, zuwa karyar da Hassan ya kamata tayi akan bata san inda Minal take ba sannan kuma da karyar data sake yi dan rufe waccan karyar. Ya kira wo shaidar sa ta farko Hassan yazo yayi bayani dalla dalla na yadda suka yi da Ruqayyah a waya har zuwa yadda yaga kayan baby a motarta da abinda tace masa, sannan kuma ya dora da mugayen furucin da tayi akan Hussain wanda har ta dalilin haka ya datse igiyoyin aure tsakanin su. Shaida ta biyu mijin Minal yazo ya fadi abinda Minal tace masa sanda zata bar gida sannan kuma Maman Minal ta bayar da shaida akan abinda Ruqayyah ta fada sanda taje tambayarta game da Minal, tana bayani tana kuka. Sai kuma aka kirawo Sumayya tabbatar da cewa a gabanta ne akayi maganar. Daga nan sai mai gabatar da kara ya cigaba da bayanin yadda shekaru suka tura ba tare da kowa yasan cewa Fatima tana raye ba sai yanxu da ta dawo gida da kanta sannan aka san cewa va ita aka binne ba, Minal ce. Ya kira Fatima a matsayin shaida ta gabatar da kanta sannan tayi bayani yadda tafiyar tasu ta kasance da kuma yadda Minal ta gaya musu labarin mutuwar Hussain a hanya. "Wannan shine kawai abinda zan iya tunawa. Daga wannan maganar ban kuma sanin inda kai na yake ba sai dana farka na ganni a imo State" sai ta dora da labarin abinda ta sani na daga zamanta a gidan su Adam da irin taimakon da Adam yayi mata har ta dawo cikin hankalinta zuwa dawowar su gida. Shaida ta gaba shine Adam, shi kuma yayi bayanin rabuwar su da Hassan a Abuja zuwa tsintar Fatima da yayi a hanya ya kuma tabbatar da cewa babu ciki a jikinta sanda ya tsince ta da kuma kama shi da baban sa yayi ya tafi dasu ba tare da ya varshi ya sanar wa da yanuwan Fatima cewa tana gurin sa ba. Yayi bayanin uzurin sa na daukan wannan lokaci batare da yayi contacting yan uwan Fatima ba. "Mu duk mun dauka cewa ana nan ana nemanta, bamu san cewa an dauka ta mutu bane ba". Daga nan sai daya lawyer din ya tashi yayi concluding da cewa "da wadannan shaidun namu muke fatan mai girma mai Shari'a zai duba ya tabbatar da cewa duk laifukan da ake zargin wannan baiwar Allah dasu ta aikata su, dan idan har bata salwantar da jaririn ba menene nata na boye mutuwar kawarta? Me yasa zata ce Fatima ta mutu bayan bata mutu ba? Mai yasa zata yi ta karya akan maganar? "Mutum hudu ne suka yi tafiyar mai girma mai Shari'a, biyu daga cikin su suna dauke da juna biyu. Ga dai gawawwaki can an binne ta driver da mace mai ciki wadda a yanzu aka tabbatar gawar Amina ce, ga kuma Fatima ta dawo babu ciki babu da kuma bata da masaniyar abinda ya faru da cikin nata. Wanda ya rage mana kadai ita ce Ruqayyah, wadda ita kadai ce ta fito fes daga cikin hatsarin dan haka ita muke sauraro tayi mana bayanin inda abinda yake cikin Fatima ya shiga, da kuma dalilin da yasatace Fatima ta mutu bayan ga Fatima a gaban mu kuma da rai a jikin ta" Alkali ya gama rubuce rubucen sa sannan ya dago kai yana kallon barrister Lukman yace "lawyern wadda ake kara, kana da abin cewa?" Barrister Lukman ya mike yayi gaisuwa sannan yace "duk abubuwan da masu kara suka gabatar na yarda dasu, ban musa ba kuma ko kadan bani da ja a game dasu. Amma abin da zanyi bayani akai shine; menene dalilin da yasa Ruqayyah ta fadi wannan maganar, menene dalilin da yasa tace Fatima ce ta mutu ba Amina ba? Amsar itace, saboda abinda idanuwan ta suka gane mata kenan." Kamar yadda wannan hatsarin yayi sanadiyar rayukan lawan driver da Amina da kuma abinda ke cikin Amina, ya kuma yi sanadiyyar daukewar tunani tare da mantuwa ga Fatima, haka yayi sanadiyar samun jirkicewar ƙwaƙwalwa ga Ruqayyah. Ruqayyah tana iya ganin abin da ba haka bane ba tace haka ne, kuma ita a idanun ta haka ta gani. Ruqayyah ta samu wannan matsala ne a gurin da hatsarin ya faru sakamakon buguwa da tayi da kuma irin horror din da tayi witnessing na kawarta aminiyarta tana ci da wuta tare da driver a cikin dajin da babu gida gaba babu gida baya. Wannan kadai is enough ya haukata mutane da yawa daga cikin mu. Wannan abin data yi witnessing ne ya saka kwakwalwar ta ta nuna mata cewa ba kawarta Amina bace ba, Fatima ce, sai kuma a cikin kanta ta shafe tunanin cewa sun taho tare da Amina a wannan tafiyar gabaki daya" Gabaki daya yan court din sai suka koma kallon juna suna mamakin wannan rainin hankalin da wannan lawyern yake so yayi musu. Hassan zai mike Jabir ya rike shi ya hana shi tashi. Alkali yace "kana da hujjojin da zasu tabbatar mana da abinda kake cewa?" Lukman yace "of course" sai ya fara gabatar da shaidun sa, shaida ta farko shine likitan da a yanzu Ruqayyah take asibitin sa, wanda ya taho da file din Ruqayyah ya kuma yi bayani akan diagnosis din da yayi mata shekaru uku da suka wuce, "tabbas tana fama da extreme hallucinations wanda har ya kaita ga tayi overdose na sleeping pills danta samu tayi bacci, tun a lokacin na dora ta akan magunguna kuma har yanzu tana kan shan magungunan bata warke ba" Lukman yace "zaka iya fadar lokacin da kake tunanin ta hadu da wannan lalura ta gane gane?" Doctor yace "gaskiya ba zan iya fadar exact lokaci ba, amma dai nasan ba dashi aka haife ta ba samu tayi daga baya ta dalilin wani abu daya faru da ita" Lukman yace "kana ganin hatsarin mota tare da ganin wani abu na tashin hankali zai iya jawowa ta samu wannan matsalar?" Likitan ya tabbatar da cewa eh accident ko tashin hankali mai tsanani zai iya samar wa da mutum wannan cutar. Sai kuma ya sake yi masa wata tambayar, "shin accident zai iya sakawa wani memory na mutum ya goge daga kansa yaji tamkar abinda ya faru bai faru ba? Likitan ya sake amsawa da "ofcause, memory lost yana daya daga cikin mental problems din da ake yawan samu as a result of car accident" Sai Lukman ya karbi file din ya mika wa alkali tare da cewa "wannan ya nuna cewa Ruqayyah, a matsayin ta na mutum kamar komai tana iya samun wadannan cutuka dana lissafa a baya" alkali ya bude file yana dubawa, duk maganganu ne irin na likitoci, a kasa kuma an rubuta "mentally unstable". Sai shaida na biyu shine therapist dinta, shima yayi bayanin yadda take yawan yi masa complain akan cewa tana tsorata tana kuma ganin abubuwa wadanda ita da kanta tasan sauran mutane basa gani. Ya kuma kara bayani akan kadaicin da take ciki da kuma yadda mijinta ya sake ta ya auri kanwarta, da kuma yadda iyayenta suka juya mata bata. "Wannan dalilin zai iya sakawa ta zamanto har yanzu bata warke ba, saboda kadaici kadai yanaiya saka cuta ballantana dama ya tarar da cutar". Shaida ta uku ita ce Luba yar aikin ta, tayi bayanin yadda suke jin tana ihu sometimes cikin dare, da yadda take kasancewa kullum cikin kadaici. Sai police suka bayar da shaidar yadda sanda suka je kamata ta bisu salin alin ba tare da jayayya ba, abinda Lukman ya kira da "innocent submission" hakan yana nuna cewa tasan tana da gaskiya shi yasa bata gudu ko ta yi tirjiya ba. Ga mamakin su sai ya kira Sumayya ita ma a matsayin shaidar sa, ya tambaye ta ko a zaman sa tayi na jinyar Ruqayyah ta lura da irin wadannan alamomin a gurin ta? Sumayya ta amsa da "eh, tana tsorata cikin bacci kuma tana kasa yin bacci, sometimes sai anyi mata allura ko ta sha maganin bacci" Lukman yace "amma me yasa baku dauki abin da muhimmanci ba?" Sumayya tace "mu a gurin mu firgita ce saboda abinda ya faru da ita, mu a gurin mu abu ne da zai zo ya wuce" yace "amma ya wuce?" Tace "ban sani ba, bayan mun bar asibiti muka daina kwana tare, dan haka ban sani ba ko ta daina" yace "amma kinsan tayi kokarin kashe kanta ta hanyar overdose ko? Tunda an ce ke ce tare da mijinta, oh sorry mijin ki, kuka kaita asibiti" tace "eh mun kaita asibiti, amma daga nan ta nuna mana bata bukatar taimakon mu dan haka muka rabu da ita" Sai ya kira Hassan shima, kusan irin tambayoyin Sumayya ya maimaita masa inda Hassan din yace shi sam bai san wani mental issue a tare da Ruqayyah ba. "duk abinda ta fada, karya take yi. Saboda ita din tafi shaidani iya shaidanci, ta sani, tana sane duk abinda tayi kuma wallahi she will never go free, sai ta fadi inda ta kai jaririn nan dan babu wani tabin hankali da take dashi" Lukman yace "kai likita ne da zaka ce bata da tabin hankali bayan ga likita nan ya fadi cewa tana dashi?" Hassan yace "ni tsohon mijinta ne kuma uban ƴaƴan ta, na san duk irin abinda zata iya aikatawa...." Lukman yace "Tsohon mijinta kuma mijin kanwarta a yanzu, wannan shine dalilin da yasa ba ka fahimci cewa bata da lafiyar kwakwalwa ba saboda kana can kana bibiyar kanwarta a lokacin da ita kuma take struggling da lafiyar ta. Bayan ta rasa kafarta ta rasa kunnuwan ta ga kuma matsalar ƙwaƙwalwa da take damunta kai kuma sai kazo ka hada ta da saki uku ka raba ta da ƴaƴan ta sannan kaje ka auri kanwarta". Lawyer din Hassan ya mike yace "objection my Lord, lawyen wadda ake tuhuma yana magana akan abinda bashi da dangantaka da abinda ya hada mu anan" alkali yayi wa Lukman warning sai yace Hassan yaje ya zauna, amma kuma a ransa ya samu abinda yake so, ya nunawa alkali irin rashin adalcin da Hassan yayi wa Ruqayyah. Bayan Hassan ya zauna sai Lukman ya rufe jawabin sa da cewa "client dina ta rufe maganar mutuwar Amina tace Fatima ce ta mutu saboda haka idanuwan ta suma gane mata, sakamakon matsala ta tabin hankalidata samu a sanadiyar wannan hatsarin da suka yi. Sannan client dina bata da masaniya kwata kwata akan inda cikin Fatima ya tafi, dan ita sanda ta farka bayan anyi matsayi gawar Fatima ta gani tana ci da wuta. Ita ma, kamar kowa tayi tunanin Fatima ta mutu ne a ranar" ya yi gaisuwa ya koma ya zauna. Kotu tayi shiru ana jiran alkali yayi magana sai Adam ya daga hannu yace yana da magana idan alkali ya yarda, alkali ya bashi dama ya sake fitowa ya tsaya yace "akwai abinda ban fada ba a cikin labarin dana bayar, ban fada bane ba kuma saboda ban tabbatar ba kuma bana so in bada shaida akan abinda ban tabbatar ba, bana so in tsaya a gaban Ubangiji saboda nayi shaidar zur" alkali yace "menene abinda baka fada ba?" Yace "lokacin dana taho daga Abuja a mota ina duban hanya ko zanga su Fatima, I saw something ta mirror, someone that looked like Ruqayyah was carrying something that looked like a baby. Dana juya kuma sai naga ban gansu ba sun bace a cikin bishiyoyi" A take court din ta rude da hayaniya, alkali ya ajiye biron hannunsa yana kallon Adam yace "amma me yasa dazu baka fada ba?" Adam yace "saboda ban tabbatar ba, ta mirror kawai na gani dana juya kuma ban gani ba, bayan nayi gaba kadan kuma sai na ga Fatima" Alkali ya yi rubuce rubucen sa sannan yace ya daga shari'ar zuwa sati mai zuwa inda zai yanke hukunci. Sannan kuma ya bayar da bail din Ruqayyah kamar yadda lawyer dinta ya nema. A matukar fusace Hassan ya dawo gida, a ranar duk yadda Sumayya ta kai da iya kalamai da iya lallabawa amma ta kasa kwantar masa da hankali, "ta kashe dan Hussain, and she is going free" Sumayya tace "Habibi, bana jin Ruqayyah ta kashe jaririn nan fa, bana jin Ruqayyah zata iya kisa ballantana kisan jariri. Ya kamata mu duba possibility na kasancewar abinda lawyer din nan yake fada gaskiya ne, tunda akayi accident din nan Ruqayyah has not been herself, what if he is right?" Ya ture hannun ta daga jikinsa yana mikewa a fusace "don't tell me kin yarda da wancan rubbish din, don't tell me you love your sister so much that ba zaki iya ganin laifin ta ba ko da kuwa an ajiye miki shine a gaban ki" ta mike tana kallon sa tace "ba wai rashin ganin laifi bane ba, Ruqayyah tana da laifuffuka da dama amma wannan bayanin na likita, likitan da ni da kai ne muka kai ta gurinsa ballantana muce hada baki suka yi. Ya kamata mu sauko mu fahimci abin sosai. Sannan kuma ga shaidar da Adam ya bayar, mu jira please mu ga abinda Shari'a zata yanke sai ya wuce ta ya dauki key din mota ya fice daga gidan. This is the first time da yayi nata fushi irin haka. A palon gidan Ruqayyah, tana zaune a wheel chair dinta daaka kawo mata bata nan, Lukman yana zaune a daya daga cikin kujerun palon yana ta kokarin kwantar mata da hankali "wannan shaidar ba zata yi amfani ba, shi da kansa yace he is not sure a gaban alkali da sauran jama'a, he is a fool to even come out and say something sannan yace he is not sure" Ruqayyah tayi shiru tamkar bata jinsa, hankalin ta yana can wani guri daban daga alama ta shiga zurfin tunani, sai ta juyo tana kallon sa tace "yaro ya bata, and definitely someone is responsible for batan sa, a yanzu kuma ni kadai ce suspect, and I don't like that, ina son kayi creating another suspect din in an koma court" ya jima yana kallonta, tabbas maganar ta gaskiya ne amma tayaya zai creating another suspect kuma? Yace "ban gane ba" ta fara bubbuga yatsunta akan hannun kujera fuskar ta kamar an aiko mata da sakon mutuwa tace "that stupid Igbo guy, wanda yake ikirarin ya ganni da baby, make him take the fall" yace "how?" Tace "anyi accident, Minal da driver sun mutu, ni na fita daga cikin hayyacina Fatima kuma ta kama hanya ta bar gurin. Adam shine mutum na farko daya fara ganin ta, ita kuma ba zata iya tuna lokacin da suka hadu din ba ballantana ta tuna in da ciki a jikinta lokacin ko kuma babu. Make the judge believe cewa da ciki a jikinta Adam ya dauke ta." As always, forgive the typos.......... *The Lone Cat* Yayi shiru yana kallonta, yana mamakin shaidanci irin na Ruqayyah, wato shi shine lawyer amma ita itace mai lauya magana zuwa yadda zata yi serving interest din ta. Tabbas, abinda ta fada zai kara wa shari'ar su light amma kuma bashi da wata shaida da zaiyi proving maganar kamar yadda suka wadancan lawyers din basu da yadda zasuyi suyi proving cewa Ruqayyah is guilty, duk lalube cikin duhu suke yi, kuma yasan ko yayi abinda Ruqayyah tace ko bai yi ba Ruqayyah will go free, na farko saboda babu wani takamaiman shaidar cewa ta aikata abinda ake zarginta da shi, na biyu kuma ga statement din doctors na cewa she is mental unstable, sannan shi kansa Adam da yayi ikirarin ya ganta ko da ace ya tabbatar da cewa ita din ce wannan statement din na doctor ya hau kan shaidar sa, ko da ta dauki babyn za'a yi ruling out as ta aikata laifin a cikin hauka. But then, that will make the judge mark her as dangerous, dole kuma zai saka ayi isolating dinta ko a gidan mahaukata saboda a kare sauran al'umma daga gareta. Dan haka Maganar ta akan Adam zata taimaka musu sosai, in suka nuna wa judge cewa zai iya kasance wa shi ua aikata laifin shi yasa yayi wannan maganar against Ruqayyah dan ya kara rufe nasa laifin, wannan zai sa alkali ya rushe shaidarsa ko da kuwa basu yi proving cewa shi yayi din ba. Already har kansa ya fara aikin samun hanyoyin da zai bi ya haka ramin da zai rufta da Adam. Yace "that was excellent! Me yasa baki karanci harkar law ba? You would have make a good lawyer" ta kalleshi kawai, she is in no mood for jokes dan ranta a bace yake sosai. Komai ya tafi dai dai a court, wannan stupid Adam din ne yaso ya cika wa kabar ta ruwa. Tace "ka tafi kaje tayi aikin ka. I want to see that guy behind bars,I want to see yadda Sumayya zatayi reacting idan taga an kama shi, I want to see yadda Hassan zaiyi reacting to yadda Sumayya tayi reacting. I want to see idan da gaske ne suna son junan su ko kuma pretending kawai suke yi. A haka suka rabu, ya tashi ya tafi ita kuma ta aika aka tabbatar mata da cewa bodyguards din da tayi hiring suna nan a gurin, tasan Hassan might try something on her shi yasa ta tanadi guards din, kuma there is a possibility that suna yan uwan Minal in basu yarda da jawabin Lukman ba, za kuma su iya zuwa suce zasu taba lafiyar ta dan tasan ba mutunci ne ya ishe su ba. Ita kuma ba lafa ba ballantana ta gudu idan sun zo, gwara ta nemi kariya. Washegari aka sake sabon zama tsakanin Hassan, brothers din Fatimah da lawyers dinsu. A nan suka duba abubuwan da suka faru a court suka kuma fara planning next thing daya kamata su yi. Lawyen farko ya fara bayani. "I want to be frank with you, tun farko dama munsan ba zamu iya nailing dinta akan batan jariri ba, saboda bamu da shaida" Hassan yace "wacce irin babu shaida, kowa yasan ita ta dauke shi, idan ba ita ba to waye?" Lawyer yace "abinda aka sani da abinda za'a iya proving a court daban ne, babu eye witness, dan haka idan ba ita ce tayi confessing da kanta tace ta dauke shi ba, ko kuma ita Fatima ta tuna abinda ya faru ta fadi cewa ita ta dauke shi ba, to babu yadda za'a yi muyi proving ita ta dauka" Dayan yace "dama laifin da muke saka ran za'a iya kamata dashi shine na chanja labarin mutuwa da tayi, saboda muna da isassun shaidu akan hakan, yanzu kuma wannan medical report din, wannan statement din na likita na cewa tana da matsalar ƙwaƙwalwa ya rushe duk shaidar da kuka bayar" Umar yace "yanzu kana nufin ba zamu iya yi mata komai ba kena?" Yace "yanzun wannan shaidar da Adam ya bayar ita kawai muke counting on, even with it, the worst she can get is a kaita gidan mahaukata, daga tayi shekara daya zuwa biyu zata ce ta warke shikenan ta dawo gida ta cigaba da rayuwar ta" Hassan ya mike ya fara zagaye, "it is all my fault, it is all my fault" Abubakar yace "amma yanzu shikenan babu abinda za'a sake gwadawa?" Lawyer yace "zamu iya samun wasu shaidun da zasu bada shaida akan rashin kyawun halayyar ta da son kudin ta, yadda alkali zai san cewa zata iya aikawa haka saboda kudi, za kuma mu gwada yi mata tambayoyi muma a gaban alkali with hope na cewa zata yi subutar baki ta fadi wani abu da zai tona asirin ta. Wannan shine kadai hope din mu. Kuma zamu yi requesting a bamu dama mu kaita gurin doctor of our choice ya sake duba kwakwalwar ta ya rubuta nashi findings din" Da wannan hankalin Hassan yadan kwanta kadan, sai ya zauna suka fara rubuta all possible mutanen da yasan zasu iya fadar halin Ruqayyah, shine na daya, sai Sumayya, zasu kuma nemo wasu daga cikin kawayen su na unguwa da kawayen da tayi haya da bikin su, sai kuma Adam. And they also need one more person, sai dai Hassan bashi da tabbas din zai yi magana. Baba. But sai baban ya bashi mamaki, yanayi masa bayani yace zaiyi, sai kuma Hassan yaji babu dadi, kamar cin fuska ne ga Baba amma kuma dole ce ta kama. Daga nan suka ci-gaba da shirye shiryen su musamman a bangaren tambayoyin da zasu yiwa Ruqayyah, da yadda zasu tsara tambayoyin yadda zasu rikita ta. Shima kuma Lukman a nasa bangaren yana ta nasa shirin tare da taimakon Ruqayyah wadda shi kansa mamakin yadda take tsara masa abubuwa yake yi, abubuwa irin wanda shi tunanin sa baya zuwa gurin. A haka har ranar komawa court tazo, kowa ya hallara, duk witnesses din dasu Hassan suka gayyata duk babu wanda ya basu kunya dan kawayen Ruqayyah ma sunzo musamman da Hassan ya basu kudi. Farko bayan alkali ya zauna an gabatar da kara sai aka shigo da Ruqayyah akan wheel chair dinta, aka saka ta a akwatin wanda ake zargi, tadaga kai tana kallon mutanen da suke gurin, ta fahimci cewa kusan kowa data yi mu'amala dashi at one point in her life, sai ta fahimci cewa tabbas akwai problem, duk wadannan mutanen, mutanen da suke important a rayuwarta, yau sun taru ne sun hada kai against her, ita kanta bata san sanda tayi reaching this stage ba. Ta lura da Baba, Baban ta mahaifi yana daga layin farko a zaman court din, kallo daya yayi mata ya dauke kansa gefe, rabon sata ganshi tun ranar daya yi mata korar jare daga gidan sa kuma yace babu shi babu ita, a gurin aiki ma transfer ya nema daga kamfanin flour inda office dinta yake ya koma kamfanin sukari. Ta zauna tana binsu da kallo daya bayan daya, ta lura da yadda Sumayya taki yarda su hada ido, da yadda Hassan yake binta da mugun kallo mai cike da nuna tsana da kyamata. Shin dama soyayya tana zama kiyayya? Wai ba taji ance bakin daya furta so vaya taba furta ki ba? Ko nata case din daban yake ne? Bayan an karanta abinda aka tattauna akai a zaman daya gabata sai alkali ya tambayi lauyoyin masu kara ko suna da wani abu da zasu kuma gabatar wa? A take suka mike suka gabatar da kansu sannan daya ya zauna daya kuma ya fito ya fara jawabi kamar haka "shaidun da lawyer mai bada kariya ya gabatar a wancan zaman da akayi suna kokarin nunawa ne cewa Hajiya Ruqayyah Yusuf tana da matsalar ƙwaƙwalwa, dan haka mu kuma a yanzu zamu nuna wa mai girma mai Shari'a cewa wancan claim din nata na karya ne. Abu na farko shine muna neman alfarma a bamu dama idan an tashi daga court zamu kai Hajiya Ruqayyah zuwa gurin wani likitan daban dan ya bamu second opinion akan lafiyar kwakwalwar" Alkali ya ce ya amince, sai kuma lawyer ya sake neman alfarmar yiwa Ruqayyah tambayoyi. Aka bashi dama ya tafi gurin ta ya fara mata. "Farko zanso ki gabatar mana da kanki, suna da shekaru da kuma stage din karatu" sai tayi shiru tana kallonsa kamar bata ji abinda yace ba, kowa yayi shiru yana kallonta sai tace "magana kayi ne? Kasan ni kurma ce, bana ji sosai sai ka daga muryarka sosai". Yayi murmushi sannan ya daga muryar ya sake maimaita mata tambayar, ta amsa masa a takaice, sai yace "ranar goma ga watan december, shekaru biyar da suka wuce, kunyi hatsarin mota, ko zaki bami labarin yadda abin ya kasance?" Ta gyara zama tare da tattara hankalin ta guri daya kamar mai tunani sannan tace "abin duk a cukurkude nake ganin sa, na san dai a ranar munje kasuwa tare da Minal, sannan muka dawo gida, muna dawowa muka ga Fatima tana shiri zata tafi Abuja sai nace zan bita, muka shiga motar ta da driver muka tafi, mun kusa shiga Abuja sai Hassan ya kira ni yace mu koma gasu nan zasu taho suma, mun juya zamu dawo sai muka yi hatsari, ni bansan ya akayi ba, dana farka sai naga wuta ta kama motar mu ninkuma ina gefe a kasa, na leka cikin motar sai naga Fatima da driver sun mutu suna ci da wuta" Sai ta rufe fuskarta tana kuka. Lawyer yace "ita kuma kawarki fa? Da kuka dawo daga kasuwa tare, tana ina?" Tace "ni ban ganta ba, ban san inda take ba, sai dana dawo sai naji ana neman ta wai ta bata ba'a ganta ba" yace "amma mijinki yace farko kin gaya cewa baki san inda take ba, kince kun dade rabon da ku hadu, daga baya kuma sai kika ce masa kun ajiye ta a hanya ta shiga taxi ta tafi gida" tace "eh haka na gaya masa, saboda bana so yayi min fada, shi fada ne dashi da yawan fushi da tsawa, kuma baya son Minal, baya son muna mu'amala da ita shi yasa ba boye masa dan banaso yayi min fada, amma ni ba zan iya tuna komai a game da Minal ba, ni dai nasan munje kasuwa mun dawo, shikenan abinda zan iya tunawa akan ta" ya gyada kai yace "to yanzu mu koma gurin accident din. Bayan kin tashi sai kika ga me?" Tace "naga Fatima ta mutu tare da driver, naga gawawwakin su suna cin wuta" ta sake saka kuka, yace "kinga waccan?" Ya fada yana nuna Fatima, Ruqayyah ta bita da kallo yace "wacece?" Tace "Fatima ce" yace "kuma ki ka ce kin ganta ta mutu, an bata mutuwa dama an dawo?" Ta dafe kanta, "ni ban sani ba, ni ban san ya akayi ba, ne dai abinda na gani kenan a lokacin ban san ya akayi bayan ta mutu kuma ta dawo ba". Yace "Malama Ruqayyah, bayani ya nuna cewa kunyi hatsarin nan ne da misalin karfe biyar da rabi, ke kuma kin kira wayar Hassan ne da misalin karfe shida da rabi. Menene kika yi a cikin awa dayan da take tsakani?" Ta dago kai tana kallonsa, yace "baki ji ba ko? Bara in maimaita" sai ya kuma maimaita tambayarsa sannan ta amsa tace "uhm, ina ta yawo ne ina neman network din da zan kira shi, gurin bau network" yace "kina ta yawo, har na tsahon awa daya. Amma kuma a lissafi distance din da yake tsakanin inda motar ku ta fadi da titi bai fi tafiyar minti goma ba ko da kuwa ga marar lafiya ne, a cikin awa dayan nan duk baki zo titi ba? Tunda banji Labarin kin nemi taimakon a gurin motocin da suke wucewa ba, ko kuma kinzo titin ne kika sake komawa ciki? Tunda a ciki police suka dauke ki?" Tayi shiri tana kallonsa, kwakwalwar ta tana aiki, ta gane me yake yi, so yake tace tazo titi ta koma, ma'ana yana so yayi proving maganar Adam na cewa ya ganta. Ta girgiza kai, "banzo titi ba. Ban iya tafiya mai nisaba saboda kafata taki takuwa sai janta nake yi" yace "kafarki ta rike shi yasa baki yi tafiya mai nisa har kin je titi ba?" Tace "eh" doubtfully, dan ta lura akwai magana a bakinsa, sai ya nuna bay yace "amma likitan daua fara duba ki bayan kunyi hatsarin ya tabbatar mana da cewa kin gaya masa cewa kinyi amfani da kafarki bayan kunyi accident, daga baya ne ta makale" ta kalli inda ya nuna sai ga doctor a zaune, ta dauke kai, lallai wadannan mutanen, ya maimaita "awa dayan da kika yi kafin ki kira Hassan me kika yi a cikin ta" ta dauke kai tace "ba zan iya tunawa ba" Ya juya ya na kallon alkali yace "ya mai girma mai sharia, magana uku kenan akan tambaya daya, tace tayi ta yawo tana neman network, ta ce kafarta ta makale ta kasa tafiya, sannan kuma tace ba zata iya tunawa ba". Sai ya sake juyo wa kan Ruqayyah yace "tambaya ta gaba Malama Ruqayyah, kinyi furuci ga Hassan lokacin da kike a matsayin matarsa cewa da yasan abinda kika aikata dan ya samu gadon Hussain, da ba zai boye miki cewa Hussain ya bashi rabin dukiyarsa ba. Mai zaki iya cewa dangane da wannan maganar? Me hakan yake nufi?" Ta daga kai tana kallon Hassan wanda shima ita yake kallo a lokacin, sannan ta dawo da hankalin ta kan lawyer din tace "karya yake min, ni ban fadi haka ba, yana dai neman abinda zai kare kansa dashi ne saboda abinda yayi min". Lawyer yace "menene yayi miki?" Tace "ya sake ni saki uku saboda na hadu da nakasa, sannan ya raba ni da yaya na kuma ya auri kanwata, twin sister dina" lawyer yayi murmushi yace "saboda kin samu nakasa, ko saboda halin ki? Saboda iƙrarin da kika yi na yin kazafi ga danuwansa daya rasu in bar baki dukiya ba. Idan ba haka ba zaki iya yi wa court bayanin dalilin da yasa ya baki kusan dukkan abinda ya mallaka bayan ya sake ki?" Tayi sauri tace "ya bani ne a matsayin toshiyar baki?" Yace "toshiyar baki na me?" Ta sunkuyar da kanta tace "na kar in ce ya sake ni saboda na nakasa". Ya girgiza kai yace "wannan ai ba abu ne boyayye ba, kowa ai yasan ya sake ki tunda har ya auri kanwarki. Da haka ba zai baki wannan uban kudin dan ki boye abinda yake a bayyane ba. Ya baki ne saboda iƙrarin da kika yi na tarwatsa good name din Marigayin dan uwansa, wannan shine dalilin rabuwar auren ku ba wai dan kin nakasa ba, wannan kuma shine dalilin da yasa iyayen ki da suka haife ki da kansu suka sallama ki suka ce babu su babu ke har abada. Bana jin akwai wata nakasa da Da zaiyi wanda zai saka iyayensa su guje shi" Lukman ya mike "objection my Lord. Lawyen mai kara yana kokarin yayi concluding akan abinda bai sani ba" lawyen Fatima yace "ayi min afuwa my lord, amma ba wai ni zanyi concluding ba, zan kira mahaifin Hajiya Ruqayyah, Malam Yusuf, shi zaiyi concluding da kansa. Daga nan aka kira Baba, wanda ya zauna opposite Ruqayyah wadda ta rufe idonta hawaye yana zuba yana jika fuskarta sannan yana zuba a kan hijab dinta. Baba ya yi rantsuwa akan zai fadi gaskiya and nothing but the truth. Sai ya fara magana akan halayyar Ruqayyah tun dag tashin ta har zuwa girman ta da aurenta da Hassan, ya dora da bayanin abinda yayi sanadiyar rabuwar auren su "ni na roke shi da kaina na hada shi da Allah da Annabi ya sake ta, na kuma roke shi ya auri kanwarta dan ina yi masa fatan samun farin ciki tare da ita" ya cigaba da bayanin yadda ya aika har gida a gayamata ta dawowa da Hassan dukiyar sa ta dawo gida amma taki. "Mu bamu guje ta ba, ita ta guje mu ta zabi dukiya akan mu. Ina fadar haka ne yanzu a gaban duniya ba wai dan bana son Ruqayyah ba sai don ina sonta sosai da sosai, ina fatan court zata kama ta da laifin da ake tuhumar ta, ina fatan za'a hukunta ta, kuma ina fatan hakan zai zamanto sanadiyyar shiryuwar ta". Tabbas maganganun Baba sun taba kowa a court din, harda shi kansa alkalin, daga nan sai aka kira Sumayya ta dora da bayanin halayyar Ruqayyah, Hassan ne next, ya fadi duk abinda ta ringa yi na nuna son kudi, yadda ta ringa comparing dinsa da kaninsa saboda dukiya. A karshe yace "duk uwar da tayi ikirarin tarwatsa nasabar danta data haifa da kanta saboda kudi, bana jin akwai abinda ba zata iya aikatawa ba saboda kudi". Haka akayi ta kiran mutane kowa yana fadar aibun Ruqayyah, shi halin mutum tamkar inuwarsa ne, duk inda ya shiga sai ya bishi kuma indai aka haska shi da fitila sai an gani. Hatta kawayenta sai da suka bayar da labarin yadda ta dauki hayar su a bikinta da Hassan da yadda ta nuna musu shine CEO na H and H, sai daga baya suka gane ba shi bane ba. A karshe aka kirawo Adam, shi kuma yayi magana akan ranar da suka fara haduwa a motar sa da abinda ya faru a tsakanin su. Ya gama zai koma kenan ya zauna sai Lukman ya mike yace yana da tambayar da zaiyi masa. Ya mike ya tsaya a gaban sa yace "ka tafi da Fatima garin ku, baka dawo da ita ba kuma baka sanar da kowa kana tare da ita ba sai bayan shekara biyar, menene dalili?" Adam yace "nayi hakan ne saboda in kare ta, ina gudun abinda mahaifina zai iya yi mata idan na ki bin sharudan daya kafa min" yace "menene yace zaiyi mata idan ka fadi tana tare da kai?" Direct Adam yace "yace zai kashe ta, amma bai yi mata komai ba tunda ban karya duk dokar daya kafa min ba" Lukman yace "kuma kai ka yarda in ka karya dokar tasa zai kashe ta din?" Adam yace "nasan zai iya" Lukman yace "na yarda da kai, 100%, akan cewa zai iya din, dan a dan binciken da nayi na fahimci cewa mahaifinka mutum ne mai tsananin ra'ayin rikau akan kiyayyar hausawa kuma musulmai, musamman saboda yana ganin sune sanadiyyar raba ka da shi, tabbas zai iya kisa akan hakan, musamman kisan dan jaririn da zai iya zama masa tonon silili da kawo masa cikas akan manufarsa" Adam ya bude baki ya kasa rufewa, yace "kamar ya? Ban gane mai kake cewa ba?" Lukman yace "tambayar da zanyi maka ta gaba ita ce, me ya sa tun farko baka fada cewa kaga wata mai kama da Ruqayyah dauke da wani abu mai kama da jariri a kusa da inda aka yi accident din ba?" Adam yace "saboda kamar yadda na fada tun ranar nan ban tabbatar ba, bana so in fadi abinda ban tabbatar ba" Lukman yace "daga baya kuma, bayan kowa ya gama kawo shaidar sa sai ka yi volunteer ka fada, a lokacin ka tabbatar din kenan?" Adam yace "no, naga mai laifi tana neman ta tsallake shi yasa na fada ko hakan zai taimaka wa Shari'a" Lukman yace "zai taimaka wa Shari'a ko kuma zai taimaka maka wajen rufe naka laifin? Idan Ruqayyah ta dauki laifi shikenan babu wanda zai kuma bibiyar maganar jariri kuma" Adam cikin mamaki yace "me kake nufi ne wai?" Lukman yace "ina nufin bayan anyi accident, kai ne mutum na farko da ya ga Fatima, ita kanta Fatima ba zata iya tunawa da lokacin da ka ganta din ba, dan haka babu wanda yake da tabbas din cewa da ciki ka ganta ko babu ciki" Adam yace cikin bacin rai "babu ciki, na fada ai tun wancan karon, sanda na ganta babu ciki a jikinta kuma da alamar a lokacin ta haihu" Lukman yace "haka ka fada, amma kai kadai ne kasan da haka mu duk bamu sani ba, zaka iya samar mana da shaidar cewa babu ciki a jikinta sanda ka ganta?" Yace "eh. Ina ganin ta babana yazo tare da yaran sa su biyu, a aika azo dasu zasu bayar da shaida" Lukman yace "nasan zaka ce haka, shi yasa tun kafin muzo nan na bibiya har garin naku har gidan naku amma sai na tarar da labarin cewa tun da ka dauko Fatima ka gudo da ita shi ma ya hada kayansa ya kara mai, ba'a san inda yake ba. Baka ganin yayi haka ne saboda yasan za'a tono wannan laifin?" Adam ya dafe kansa, tabbas tun da suka zo Kano sun nemi numbers din daddyn sa sun rasa, sai sister dinsa ce take gaya musu cewa ya bar gida shima. Sun dauka fushi ne yayi dasu amma zai huce amma yanzu ga wannan batu. Yace "ba saboda wannan ne ya bar gida ba. Kuma bashi kadai ne shaida ba, akwai yaransa guda biyu da yazo dasu gurin zasu tabbatar da abinda nake fada" Lukman yace "in kace yaransa kana nufin masu yi masa dirty work, kana nufin zasu bayar da shaida akan abinda idan ma an aikata shi sune aka saka suka aikata" Ran Adam ya gama baci, yace "na gaya maka ban dauki Fatima da ciki ba, babu ciki a jikin ta sanda na ganta, babana ko ni bamu da hannu a batan babyn Fatima" Lukman yace "baban naka da a yanzu kake furucin cewa zai iya kisa? Yanzu kuma kake cewa bai yi ba?" Adam ya buga hannun sa akan bench din gabansa yace "zai iya da yayi are two different things. Bai yi ba, kuma ba zan taba xewa yayi ba no matter how much I don't like him. If you like kayi min komai and I assure you I will be the last person da zakayi wa sharri, I will be the last person da ke" ya fada yana nuna Ruqayyah da hannu yace "zaki yiwa sharri" Lukman yace "wannan ya nuna irin zafin zuciyar da kake dashi. Mai zafin zuciya kuwa ya kan iya aikata komai a lokacin da ransa ya baci" Adam yace "you can't prove anything" Lukman yace "tabbas, duk shaci fadi ne kawai nake yi, kamar yadda duk shaidun da ake gabatarwa akan Ruqayyah suke shaci fadi" sai yayi gaisuwa ya koma ya zauna Alkali ya gama rubuce rubucen sa sannan yace "kotu ta dage karar zuwa mako mai zuwa, kafin na za'a sake mayar da Ruqayyah a kuma duba kwakwalwar ta kamar yadda masu kara suka bukata, sannan court ta bayar da order a rike Adam Clement a hannun yan sanda har zuwa sanda za'a gudanar da bincike a kansa" Sumayya ta mike da sauri "karya suke yi masa wallahi" ta juya gurin Ruqayyah, "ta hanyar da kika ɓullo kenan? Ta inda kike tunanin zaki rama kenan? Dan na auri Hassan shine zaki yi sanadin da za'a rufe Adam?" Adam ya koma ya jingina da jikin kujerar da yake zaune akai ya rufe idonsa. Yana ji ana ta hayaniya a court din yayin da security suke kokarin saka order. Yana ji har aka zo aka kama shi aka saka masa handcuffs za'a fita dashi daga gurin. Aka bi dashi ta gaban Fatima, sai ya tsaya ya dafa table din gabanta yana kallonta cikin ido yace "i didn't do it". Bata ce masa komai ba aka wuce dashi. Anje an sake gwada kwakwalwar Ruqayyah. Again, the result shows mental instability. A ranar Fatima ta zauna da lawyers dinta. "Koda alkali ya yarda ta aikata laifin, hukuncin dazai iya yanke mata kawai shine a kaita gidan mahaukata tayi receiving treatment. Idan kuma ba gamsu tayi ba zai iya sakin ta free" Fatima da take zaune emotionless tace "sannan zai iya sentencing Adam idan bai yi presenting shaidun da zasu gamsar dashi cewa bashi da laifi ba" babu wanda ya bata amsa sai ta mike tace "none of which will bring back my son" daga nan ta dauki jakarta ta fita. Washegari, ranar daya kamata ayi zaman court sai ta riga kowa zuwa, tana zuwa tace "nazo zanyi withdrawing case din gabaki daya. Na janye kara". * The Wishes* Ba'a barta tayi signing ba sai da lawyers dinta suka zo, su kuma at first suka nuna mata rashin jin dadin su akan hakan "munyi winning fa, am sure with all the behavioral witnesses da muka gabatar shi kansa alkalin is convinced cewa ita tayi, yana holding Adam ne kawai for precautions amma ba zaiyi sentencing dinsa ba" tace "ita kuma me zata samu, two or three years a gidan mahaukata sai ace ta warke a sallamo ta? While only God knows where my son is? And in na bar case din Adam zai cigaba da zama a hannun police har sai ya gabatar da shaidar da zai nuna cewa ba shi ya dauki babyn ba. I won't let him suffer akan laifin da ni na san bai yi ba. I won't add this to his list of sufferings". Dole suka hakura suka barta tayi signing komai, kafin su Ruqayyah da Lukman su zo gurin. Sannan suka karbi release letter daga gurin alkali suka tafi zasu fito da Adam tun kafin a taho dashi court. A bangaren Adam, tun ranar da aka kama shi aka rufe yake cikin kunchi da damuwa, abubuwa ne suka taru suka yi masa yawa ta ko wanne bangare na rayuwarsa. Shi ba wai kama shi din ne ya dame shi sosai ba, zafin sharrin da akayi masa a gaban mutane ne, a gaban Fatima, a gaban Sumayya da duk wani wanda yake ganin mutuncinsa. Duk da yasan da yawa ba zasu yarda cewa yayi abinda aka ce yayi din ba amma dole ko yaya ne sai zargin sa ya shiga zuciyar wasu daga cikin su. Fatan sa dai shine zarginsa ko mai kankantar sa ya shiga zuciyar Fatima. Shi yafi kowa sanin yadda Fatima take son dan nan nata, dan dashi ta dawo cikin hayyacin ta, son ganin sa ne ya taimaka mata gurin tuna ko wacece ita, sannan shi ya jawo ta zuwa dawowa cikin yan uwanta. Shin ya zata ji a ranta idan zargin shine ya rabata da danta ya shiga zuciyarta? Abu na biyu da yake damunsa shine maganar da maman sa tazo tayi masa tun a ranar da aka kama shi kuma daga nan vata sake dawowa ba "ka gani ko? Ka ga abinda muke fada maka kullum ko Joseph? Wadannan mutanen ba mutanen kirki bane ba, basu damu da kai ba, basu damu da rayuwar ka ko mutuwar ka ba, kaga sakayyar da suka yi maka ko? Bayan kin jin maganar mu da kayi ka zabe su a kan mu sannan bayan duk wahalar da kasha akan yarinyar nan har sai da ta kaini nima nayi disobeying Baban ka dan ka taimaka musu ka dawo musu da yarsu amma kalle ka a yanzu? Ina fatan wannan zai zama darasi a gare ka, ina fatan idan ka fito zaka fahimci damu da su waye a side dinka, waye yake son ka da gaskiya. Ni zan tafi inje in nemo babanka duk da bansan inda zan same shi ba, amma zan nemo shi, zan kuma bashi labarin irin sakayyar da your muslim friends suka yi maka" Tun da ta tafi yake juya maganar a ransa, a shekaru biyar din daya kasance tare da family dinsa, tare da Fatima, babu abinda yake yi besides kula da Fatima sai kokarin janyo hankalin mahaifansa da yanuwansa zuwa ga addinin Musulunci, kuma ya fahimci ya fara nasara a hankali musamman a bangaren Maman sa da sisters dinsa, complain dinsu shine basa son yadda Musulmin da suka sani suke behaving. "Suna da karya, yawancin su makaryata ne, ga cin amana, yaudara, munafurci, da sauran munanan halaye" ya kan yi dariya yace "wannan individual choices ne, it is not religious, teachings din addinin musulunci babu komai a cikinsa sai dabi'u masu kyau, duk wanda kuka ga yayi akasin haka to shi ya zabawa kansa kuma yana yi ne against addinin sa. Kunga kamar a Christian, shiga marar kyau, shaye shaye, zinace zinace, duk dabi'u ne munana a cikin addini amma kuma sune manyan dabiun da wasu Christians din suka rika a matsayin halayya. Dan haka ni da na zabi musulunci na zabane saboda addinin ba wai saboda masu addinin ba". A lokacin sun gamsu da bayanan da yayi, dan har yana tunanin idan yayi Sa'a kafin babansa ya gama fushi ya dawo maybe maman sa ta musulunta dan ya lura ta rage zuwa church sosai, haka sisters dinsa, amma wannan abin da akayi masa tabbas ya dawo da lissafin sa baya dan ta kufula sosai, shi kuma ko kadan hakan bai sa soyayyar da yake wa musulunci ta ragu daga zuciyarsa ba. Tabbas akwai mutanen kirki a mudulmai kamar yadda akwai mutanen kirki a Christian. Abu na uku shine maganar Sumayya, bai dauka haka maganar aurenta zata daga masa hankali ba, tunda tun yana can kullum yana kokarin gaya wa kansa cewa Sumayya ba zata jira shi ba zata yi auren ta, ya dauka yai bracing kansa for the news, kuma sanda news din yayi hitting dinsa sai yaji bai ji zafin sa sosai ba amma sai.....sai aranar da aka yi zama court na farko, a ranar da yaji wannan lawyer din na Ruqayyah ya ambaci Sumayya a matsayin matar Hassan, a ranar ne yaji labarin ya dake shi sosai, amma sai ya cigaba da karyata wa a zuciyarsa yana ganin kazafi ne irin na lawyers, Sumayya ba zata bata auren Hassan ba ko da mazan duniya sun kare. Wannan ya sa yayi calming kansa down har aka tashi daga court din inda sam Sumayya taki yarda su hada ido dashi kamar yadda taki yarda su hada ido a gidan su Fatima, inda ya fara ganinta bayan dawowarsa. Kuma ko a can din ma dama yayi mamakin abinda ya kaita tunda yaji maganar cewa Hassan ya saki Ruqayyah. Bayan an tashi daga court din kuma sai yaga Hassan ya buɗe mata mota sun shiga tare sun tafi. Farko yaji daci sosai a zuciyarsa, dacin da har ya saka shi ya fasa zuwa Kaduna ya gaishe dasu Baba kamar yadda da yayi niyya, yaji a zuciyarsa auren Sumayya da Hassan tamkar cin amana ne a gare shi. Yaji wani irin kishi, kishin da bai taba tunanin yana da irin sa ba, shin wai waye ma ya bada shawarar ayi wannan hadin gambizar auren ne? Ya san Baba ne, dan haka yayi fushi yaki zuwa ya gaishe shi ya koma kano ya cigaba da jinyar zuciyarsa kuma yana fatan cewa lift ne Hassan ya bawa Sumayya zai ajiye ta a gidan ta shima ta tafi nasa gidan. Amma ranar zaman court na biyu, ranar da aka kama shi, sai yaji Baba da bakinsa ya fadi maganar auren kuma yace shi ya hada shi, sannan yaji Hassan a nasa bayanin ya fada sannan Ruqayyah ita ma ta fada. Wannan ya tabbatar masa, beyond doubt, cewa Hassan shine mijin Sumayya. Kuma wannan shine abinda ya fara hana shi bacci a kwanakin sa na farko a cell. Sai dai a hankali sai ya fara fahimtar cewa it is for the best, at least yasan Sumayya is in good hands dan Hassan mutumin kirki ne, a little strict but mutumin kirki ne. Kama shi da akayi ko kuma tunanin hukuncin da za'a yanke masa duk basu daga masa hankali ba, yasan yana da gaskiya, yasan masu kokarin yi masa sharri basu da wata shaida mai karfi, dan haka yasan dole a karshe za'a sake shi ne. A haka har ranar zuwa Court ta zagayo yana lissafe, amma maimakon ya ga anzo an tafi dashi kamar yadda ya saka rai sai ya ga anzo an bude masa kofa ance "you are free to go". A waje daya fito ya ganta, a tsaye a jikin mota tana magana da wasu maza su biyu wadanda ya gane a matsayin lawyers din ta, sai kuma yaga sun yi sallama kowa a cikin su yaje ya shiga motarsa ya tafi. Ta juyo tan kallon sa, sai yaji kunyar chukurkudewar kayan jikinsa, tace masa "let's go" yace "ba court zamu je ba? Na ga ba police" tace "will you like to drive ko ni in tuka?" Ya karbi key din a hannunta yace "I am your driver kar ki manta" ta zagaya ta zauna a gaba shi kuma ya zauna a seat din driver sannan tace "you are not my driver, kai drivern Hussain ne" yace "duk daya, abin Allah ai na annabi ne" ya tayar da motar yace "court?" Ta girgiza kai tace "an gama zaman court ai, na janye kara" ya bude ido "what? Why?" Bata amsa masa ba sai ta gyara zamata ta daura seat belt sannan tace "Kaduna zamu je. Gidan da Ruqayyah take. I want to talk to her". ********************** Satin nan gaba ki daya Hassan ya zama very edgy. Shi kansa ya sani dan haka yake raba kansa da mutane, kusan koda yaushe idan baya tare da lawyers ko kuma tare da umar to yana garden din Aunty gurin kabarin Hussain. Baya shigowa gida sai ya gaji sosai yadda yana zuwa wanka kawai zaiyi ya kwanta. Sumayya ta fahimci hakan, kuma ta jingina hakan ga cewa fushi yake yi da ita saboda tayi magana akan kama Adam da akayi. Sai dai bata yi masa maganar ba kamar yadda shima bai yi mata maganar ba. Asali tamkar ya cire ta daga dukkan plans na shari'ar. Sai dai hakan bai hana ta lissafin ranar komawa court din ba, ranar kuma tana tashi bayan ta shirya yara sun tafi school ta kuma hada wa Hassan ruwan wanka tare da fito masa da kayan da zai zaka ta kuma hada tare da ajiye masa duk abinda tasan zai bukata a kusa da kayan, ta fesa turare a jikin kayan kamar yadda ta saba yi masa kullum sai ta kom dakin ta ta shirya ita ma tare da Abdullahi sannan ta fito, a lokacin shima ya ke fitowa daga nasa dakin yana gyara zaman hularsa, tana dan murmushi tace "Allah yasa dai bamu makara ba, naga har karfe tara tayi" yana kallonta yace "ban dake zamu je ai. Kiyi zaman ki a gida" ta bude ido cikin mamaki "ban da ni kuma? What if aka neme ni ko bukatar inyi wata maganar ta taso? Yace "babu wanda zai neme ki, an gama bayar da shaida ai, hukunci kawai za'a yanke" Taji ranta ya baci, wato hukuntata yake so yayi ko? Ko tunanin sa zata je taga Adam ne ko wani abu? Ta bishi da kallo yana sauka daga stairs ta dan daga murya tace "this is not fair, you are doing exactly what she wants" sai ya juyo da sauri ya dawo yayo kanta gadan gadan, bata motsa ba har yazo daf da ita ya tsaya sannan yace "at least ni ba a gabanta nayi abinda take so din ba, ke kuwa a gabanta, a gaban kowa da kowa kika nunawa duniya cewa kin damu dashi" Tace "of course na damu dashi a matsayin sa na musulmi dan uwana, yes, na damu dashi a matsayin sa na mai gaskiya da ake neman a makala wa laifin da bai aikata ba kuma...." Yace "duk kanin mu mun damu dashi, duk munsan cewa makirci ne kawai Ruqayyah ta shirya akan sa amma babu wani acikin mu da yayi feeling the need to raise his voice sai ke, a matsayin ki na matar aure" tayi shiru tana kallon sa sannan tace "are you jelouse? Yace "of course I am, what where you thinking?" Ta sauke idonta kasa tace "kayi hakuri". Yayi ajjiyar zuciya, da wannan take cinsa da yaki, ko tayi masa laifi, wanda hardly ne ma tayi masa laifin, to da ya hau zata bashi hakuri wani lokacin ma sai daga baya sai ya fahimci ashe shine bashi da gaskiya ba ita ba, amma ita already har ta bashi hakuri. Ya dan rage tsaho kadan yayi kissing dinta yace "sai na dawo" still baya jin zai barta taga Adam yau. Yana sauka kasa akayi masa waya, ya daga suka yi magana da wanda ya kira shi sai kawai ya juyo ya dawo palo ya zauna akan kujera ya cire hularsa ya dora ta akan fuskar sa, Sumayya ta ajiye Abdullahi ta zauna kusa dashi tare da dafa kafadarsa "lafiya naga ka dawo? Wani abun ne kuma ya faru" bai bude fuskar sa ba yace "Fatima ta janye karar gabaki daya" Suka yi shiru gaba dayansu, tama rasa me zata ce masa dan bai bari taga fuskarsa ba ballantana ta karanci halin da yake ciki. Babu motsin kowa a gurin sai na Abdullahi da yake ta bin kujeru yana waƙoƙin sa. Sunfi minti goma a haka sannan ya mike da sauri zai fita, ta mike itama tace "ina zaka je?" Ya juyo yana kallonta, sai taga fuskarsa tayi so calm ba kamar yadda ta saka ran gani ba, yace "zanje gurin Ruqayyah. Ina son magana da ita". ************************* Ruqayyah kamar kowa itama yau ta tashi da niyyar zuwa court, sai dai zuciyarta jin ta take yi kamar bakar tukunya, kuma haka take jin ta tun last zama da akayi a court dan bata jin cewa ranta ya taba baci irin na ranar nan, wai ita Ruqayya ita ce a zaune tana sauraron duk wani wanda take jinsa a zuciyarta yana keta mutuncin ta a cikin jama'a, ciki kuwa harda babanta mahaifi, twin sister dinta, da kuma mutumin da a yanzu rake jinsa a ranta sama da kowanne namiji. Kawayen ta ma ba'a barsu a baya ba, munafukan kawayen da a yanxu ita take yi musu komai na rayuwar duniya, tana nan tana jiran ta ga ranar da zadu dawo neman wani abu a hannunta. Duk da dai bata san ya hukuncin zai kasance ba amma ita kawai tana ganin it won't be on her favor, duk da cewa Lukman yayi ta gaya mata cewa wannan result din na likita ya shafe duk wata shaida da aka gabatar a court din amma hankalin ta bai kwanta ba, musamman da taji yace "highest da za'a yi miki shine a kaiki gidan mahaukata" wannan shi ya kara daga mata hankali, yama za'a yi a kaita gidan mahaukata? Ita ina zata iya zama a gidan mahaukata? Tan gam shiryawa Lukman yazo, ita haushi yake bata, asarar kudi kawai, ashe ma reputation din nasa na banza ne. Yazo yana yake mata baki "kar ki wani damu. Tunda medical report din ya sake nunawa kamar wancan, muna zuwa alkali zai yanke hukuncin kuma na tabbata bamu da matsala" tace "bamu da matsala? Tafiya gidan mahaukatan shine ba matsala? " Yace "ba lallai bane ba wannan, tunda na rusa shaidar Adam basu da wata hujjar da zata saka ace....." Tace "ka rusa shaidar Adam ko kuma na rusa shaidar Adam? Wai kai me kayi ma a cikin maganar nan? You just sat there like a zombie a lokacin da ake keta mutunci na a cikin mutane, a gaban media, you sat there and did nothing" Yaji zafin maganar ta amma yayi shiru, shi dai so yake ya lallaba ya karbi sauran kudin sa ya kara mai. A haka ya lallaba ta suka fita, a ranta tana jin maybe ta fita kenan daga gidan nan, tayi sallama da guards dinta tace zata kira su inta dawo dan bata so ta tafi dasu court saboda yan social media, tafi son take zuwa court a matsayin abar tausayi. Sai dai basu yi nisa da tafiyar su ba sai ga waya cewa Fatima taje ta janye kara. Maganar ta basu mamaki gaba ki dayansu, dan basu taba tsammanin haka ba, sai Ruqayyah taji a ranta kamar there is something behind wannan janye karar. Bata jin Fatima zata yi giving up this easily, ta san zata so ko da gidan mahaukatan ne a kaita. Dan haka sai taji bata ji wani dadi sosai a labarin ba. Suka juya suka koma gida, amma Lukman yana ajiye ta shi kuma ya huya zai tafi Abuja dan akwai takardun da zaije yayi signing kuma ya karbo. In ya dawo kuma sai yazo Ruqayyah ta sallame shi. Bayan tafiyar sa bai fi da minti uku ba sai ga Hassan ya shigo, kamar daga sama ta ganshi a gabanta, sai a lokacin ta tuna cewa ta sallami guards dinta. Gabanta ya fadi, wato plan din da suka shirya kenan? Ita Fatima ta janye kara shi kuma yazo yayi ta jibgar ta harsai ta fadi gaskiya sannan sai su sake shigar da fresh kara. Lallai kuwa zasu sha mamaki dan babu a binda zata fada. Ta fara ja da baya a kan wheel chair dinta, tana saka ran zai biyo ta amma sai taga ya jingina da bango ya rungume hannunsa yana kallonta, sai data kai jikin bango sannan ta tsaya tare da dauke numfashin ta tana kallonsa tana jiran taga abinda zaiyi sai taji yace "ki dana guduwa, I won't lay a single finger on you Ruqayyah, kin san saboda me?" Ta girgiza kai da sauri, yace "saboda idan na kama ki ba zan barki ba har sai na tabbatar kinyi numfashi na karshe a duniya. Ni kuma ba zanso haka ba, saboda in nayi haka tamkar na taimaka miki ne na kwashe miki tarin alhakin da yake kanki. Kuma na san ko mai zan yi miki ba zaki fadi gaskiya ba dan haka ba zan bata lokaci na ba. Na barki da Allah." "Ni nasan kin aikata laifin da ake tuhumar ki dashi Ruqayyah, you killed a baby, Hussain's baby, Hussain's only child, a ranar da Hussain ya bar duniya. Kuma nasan kinyi haka ne saboda ki ci dukiyar Hussain, shi yasa na baki ita, gata nan, na baki ita ne a lokacin da bansan cewa an haifi dan Hussain ba, amma yanzu na sani, dan haka ina tuna miki cewa bani da gadon Hussain indai har namiji Fatima ta haifa. A yanzu kuma babu wanda ya san me ta haifa sai ke, ke kuma ba zaki fada ba, dan haka babu mai karɓar dukiya a hannun ki kije ki rike dukiyar gado, ki ci ki sha kiyi suttura ki more rayuwar ki da dukiyar maraya, marayan kuma da kika halaka da hannun ki. Wannan shine punishment dina a gare ki. Wannan shine hukuncin da ni Hassan na yanke miki because you know what? Wannan dukiyar" ya fada yana nuna gidan "is going to be the end of you" "Ga dukiyar maraya nan a hannun ki, kiyi ta bauta mata, irin bautar da ko Ubangijin daya halicce ki baki yiwa ba, kiyi ta ninkata tana karuwa amma kuma duk ba taki bace ba, ita kuma zata yi ta cinki, slowly, piece by piece har sai ya zamanto kina addu'ar ki mutu ki huta saboda babu abinda zaiyi saura naki sai your pathetic soul, wannan kuma sai ya koma gurin ubangiji sannan ne zaki fahimci cewa ashe mutuwa ba hutun bace ba a gare ki, ashe mutuwa mukulli ce ta bude lodi lodin azabar da ubangiji ya tanadar miki a can, azaba ta musamman saboda kasancewar ki mai ilimi" "Ni Hassan, a madadin Hussain, da dukkan ya uwanmu da kuma yayan da Allah ya bamu a tsakanin ni da ke, Allah ya isa. Da ina yi miki fatan shiriya kuma shine dalilin da yasa nake ta fafutuka a kan ki, ko dan yayan mu, amma a yanzu, a kan maganar jaririn Hussain ba zamu taba yafe miki ba". Daga nan ya juya, and without another word, ya fice ya bar gidan. Sai taji kamar maganganun sa suna amsa kuwwa a cikin kunnuwan ta, sai taji kamar gidan gabaki daya yana nanata kalmar Allah ya isan da yayi mata. Tasa hannayenta biyu ta toshe kunnuwan ta amma sai taji Allah ya isan a cikin kanta take ba wai daga kunne take shiga kan ba. Ta rufe idonta tana kokarin digesting maganganun sa, cursing dinta yayi fa, lallai ma Hassan din nan. Amma kuma tasan maganganun sa zasu zauna a cikin zuciyarta har ranar da zata koma ga mahaliccin ta. A jikin ta taji kamar ana kallon ta, sai ta bude idonta da sauri tana tunanin ko shine ya dawo ko ya chanja shawara akan dukan ta. Amma abinda tagani ne yasa taji kamar zata kifo daga kan kujerar guragun ta. Fatima ce a tsaye tana kallon ta, as smartly dressed as ever, ita sai taga kamar ma kyau fatiman ta kara a cikin shekarun nan. Ta tako a hankali tazo kujerar da take facing Ruqayyah ta zauna, sannan ta daga kai tana kallon gidan a ranta tana kokarin cire memories din rayuwar ta a gidan daga ranta dan kar ya hana ta yin maganar da tazo zatayi. Ruqayyah tace cikin rawar murya "me kike yi anan?" Fatima tace "zuwa nayi in tambaye ki, ina dana?" Ruqayyah ta dauke kanta gefe kirjinta yana dukan tara tara, ko da wasa datasan abinda zai faru da rayuwarta kenan da bazata taba yaron nan ba. Amma shi hannun agogo idan ya wuce ba'a iya dawo dashi baya. Fatima ta sake tambaya "what have you done with my child?" Ruqayyah tace "ni bansan me kike magana akai ba" Fatima tace "kudi kike so? Nawa kike so? Gidan nan, kudin da already yake hannun ki, babu abinda zan karba daga gareki in dai zaki dawo min da dana, ni dana kawai nake bukata in kari kike so ma na kudi zan kara miki" Ruqayyah ta sake cewa "ni bansan me kike magana a kai ba, ni bansan wanne dan kike magana akan sa ba" a ranta tana tunanin tarko ne Fatima take dana mata dan tayi confessing, wannan shine kadai abinda suke bukata dan su rufe ta kuma su kwace komai. Faima ta mike tsaye tana goge hawayen daya taru a idonta tace "shikenan, dama last chance nabaki a matsayin ki na mutum kuma musulma, amma tunda kinyi watsi da damar ki shikenan. Ki sani, na janye karar daga court ne ba dan komai ba sai dan naji ance sentence din da zaki samu ba zai wuce yan shekaru a gidan mahaukata ba, and my son is worth much more than that, shi yasa ni nazo zanyi miki nawa hukuncin. Idan da naso zan iya daukaka kara zuwa court din da za'a yi ta jan shari'ar har ki rasa kudin daukan lawyer, ko kuma in biya doctors suyi faking wannan result din kwakwalwar ki kuma in je in ce na tuna abinda ya faru, in kirkiri labarin da zai nuna cewa ke kika dauki dana, yadda Shari'a zata kamaki ta matsanta miki kiyi confessing abinda kika yi wa dana a karshe a yanke miki hukuncin rataya. Amma duk ba wannan nake so ba. Yin wannan tamkar taimako ne a gare ki" "Dani da ke dukka munsan cewa ke kika salwantar min da rayuwar dana. Dani da ke dukka munsan cewa in ma kina da mental problem to kin same shine bayan kin aikata abinda kika aika ta, maybe ma sanadiyar abinda kika aikata ne yasa conscious dinki yake playing tricks with you. Maybe mental problem din yana daya daga cikin azabobin ubangiji da suka fara sauka akanki sanadiyyar abinda kika yi" ta fada tana kallon Ruqayyah. Sai tayi murmushi tace "shi yasa na fasa Shari'a dake na barki dashi, domin abinda zaiyi miki ko rabi rabinsa ni bazan iya yi miki ba. A matsayi na na wadda na haifi yaron nan sannan kika raba ni dashi ba tare da kin barni ko fuskarsa na gani ba, ba tare da ko kukan sa naji ba, ba tare da ko dumin jikin sa naji ba, Allah ya isa. Daga yau na dauki alkawarin a duk sallar da nayi zanyi miki Allah ya isa har zuwa ranar da zan daina numfashi" "Ina ji a jikina cewa dana is in a good place, ko yana duniya ko baya duniya nasan he is safe, but you are not. Azabobin ubangiji suna da yawa Ruqayyah, ki fara lissafi daga kan kunnuwan ki, kafafuwan ki, kwakwalwar ki da sauran abubuwan dani kaina ban sani ba. This is just the beginning. Ina miki fatan tsahon rai, tsahon rayuwar da har duk wadanda kika zalinta zasu mutu su barki a yayinda ke kuma zaki yi nadama amma wadanda kika zalunta sun mutu ballantana ki neme su gafara. A lokacin ne zaki fahimci abinda yasa mutane suke addu'ar samun kyakkyawan karshe. Ke kuma bazaki samu ba. These are my wishes for you" Sai ta juya ta bar gurin, har ta kai bakin kofa sai ta juyo tana kallon Ruqayyah, hawaye yana zuba daga idonta tace "you are not going to tell me where my son is, are you?" Still Ruqayyah tayi shiru, amma daga inda Fatima take tsaye tana iya hango hawayen da yake bin fuskarta. Sai ta dauko sun glasses ta saka a idonta dan ta boye hawayen ta sannan ta juya ta fice. *Jungle Justice* Adam da tun da ta shiga ciki yake tsaye yana kallon kofar shiga gidan, ji yake yi kamar ya bita ciki ya tsaya a gefenta har ta gama maganar da tace zata yi da Ruqayyah ta fito, shi bai yarda da Ruqayyah ba, duk da gurguwa ce amma ai maciji ma gurgu ne kuma a haka yake cutarda mutane nasu kafafuwa. Yana nan a tsaye, zuciyarsa tana ta tsinkewa har ya fara tunanin ya shiga sai gata ta fito, tana gyara glasses din idonta wanda sanda ta shiga babu shi a fuskarta. Kallo daya yayi mata ya san ranta a matuƙar bace yake sai ya bude mata kofar mota ta shiga shi kuma ya zagaya side din driver ya shiga suka dauki hanya. Bata nemi Hassan ko Aunty ba kuma Adam ma bai yi mata maganar su ba har suka bar gidan, sai ta kwantar da kujerar ta kwanta tana kuka. Bai tambayeta inda zai kaita ba dan bai san daga ina ta taho ba amma kawai sai ya dauki hanyar kano dan yasan tana bukatar iyayenta, sai ban maganar da suka yi da Ruqayyah ba, bai san zafin da take ji a zuciyarta ba amma ko ma menene yasan soyayyar iyayenta zata yi mata magani. Ya kunna radio ya saka mata karatun Alkur'ani sannan ya dauke kan mota da niyar barin gari. Suka wuce hanyar gidan Baba, ya kalli layin yana ji a ransa cewa yana so yaje ya gaishe shi amma yasan ba zai iya kai Fatima gidan su Ruqayyah ba, ko da kuwa bata cikin halin da take ciki a yanzu. Dole zuwa gidan Baba ya jira zuwa nan gaba, amma very soon zai dawo Kaduna musamman saboda wannan niyyar. Har suka iso Kano bata ce masa komai ba kuma shima bai tambaye ta komai ba, suna zuwa kofar fada aka bude musu gate suka shige direct ya kai ta har bakin kofar da zata shiga cikin gida. Ta dago kai tana kallonsa, tace "Nagode sosai, ka tafi da motar gida ka dawo da ita later" yace "nine da godiya Madam. Duk da dai baki fada min dalilin ki na janye kara ba, but am very great full that you did, you have no idea how much it means to me. Sannan kuma duk da daki gaya min maganar da kuka yi da Ruqayyah ba, shima ia fatan a samu maslaha a cikin lamarin" ta girgiza kanta tana jin hawayen daya tsaya yana dawowa tace "babu maslaha a cikin lamarin Adam. Nayi kokarin im hada ta da Allah ko kuma in tsorata ta wai ko zata gaya min gaskiya amma taki magana. Bayan duk abubuwan dana gaya mata bana jin zata taba fadar gaskiyar maganar nan, bana jin zansan abinda ya faru da baby na Adam" yaji kukan ta yana taba shi yace "listen Fatimah, baki da bukatar Ruqayyah dan sanin abinda ya faru da baby, wata rana, you are going to remember, kinji? You will remember" ta share hawayen ta tace "ni tsoro nake ji, bana son in tuna ma Adam, what if abinda zan tuna din yafi karfin ƙwaƙwalwa ta? What if i remembered my baby's death? What if akan ido na ta kashe min dana" ya dafe kansa "stop thinking like that, kinsan dai baki da lafiya ko? Let me tell you something, ninina da hope, gani nake yi kamar wata rana zai bayyana, out of no where zaki gan shi. Maybe ya zama dan saurayi ma, sai ki ganshi kamar Hussain tunda kin ce min da Hussain yake kama" sai ta samu kan ta da yin dan gajeren murmushi, tana tuno da fuskar baby a scan din da suka gani, ta sake wani murmushin sannan sai ta bude kofar motar ta fita, ya bita da kallo yana jin dadin yadda ta murmusa, ko a imo da sunan Hussain yake samun kanta, ko mai bacin ranta in ka tuna mata da Hussain sai ta sauko. Ta leko ta window tana kallon sa tace "get your self a phone please, in zan kira ka bansan ta yadda zan same ka ba" ta dan daga kafada yace "ni mantawa ma nake yi cewa ana rike waya, sabo da yi" ta bude jakarta ta fito da kudi ta ajiye akan kujera tare da card mai dauke da number dinta tace "get your self a phone and call me" yace "an gama Madam. Thank you" sannan yayi reverse ya tafi. A ranar da dare Fatima ta gana da mahaifinta, ta gaya masa dalilin ta na janye kara sannan ta gaya masa yadda sukayi da Ruqayyah. Ya gyada kai yana fahimtar ta sannan kuma yana tausayin sa, at her young age tayi going through abubuwa da yawa kuma yaji dadin yadda take daukan kaddarar ta. Yaji dadin hukuncin data yanke, da yadda ta bar Ruqayyah da Allah duk da cewa tana da karfin kwatar justice amma ta bar hukunci a hannun the most just. Sai kuma yayi maganar sake kiran wani meeting din da yanuwan Hussain, ya kuma sa aka kira Hassan aka gaya masa cewa su zo da weekend zasu yi magana da mai martaba sarki. Kafin weekend din kuma sai ya sake zama da Fatima tare da mahaifiyarta Hajiya Fulani akan menene zasu yi mata dan su faranta mata. "Ni yanzu I just want a break Takawa, ina so in da matsa daga gurin mutanen da suka sanni suka san abubuwan da suka same ni, ina ganin wannt zai taimaka min wajen mantawa, duk da nasan ba zan manta ba amma zai rage min tunani akan maganar" Hajiya tace "to ko Dubai zaki tafi gurin Asma'u?" (Babbar yayar su) mai martaba yace "kin ga dama can suna da kwararrun likitoci, sai su cigaba da duba lafiyar ki, watakila a dace ki samu ki tuna da abinda kika manta" Hajiya tace "in kina sha'awa ma sai ki koma makaranta kiyi degree dinki nabiyu, in ma PhD kike so sai ki dora" Takawa yace "kuma hamid, mijin Asma'u yaro ne mai kirki, ba zai damu da zamanki a tare dasu ba" Fatima tayi murmushi tana jin dadin yadda suke ta kokarin faranta mata, tasan zasu so zama da ita amma kuma suna da so su faranta mata shi yasa suke ta wannan maganar. Tace "bana so in kuma barin ku, nayi missing dinku sosai sannan bana tare da ku" Takawa ya dafa kanta yace "duk sanda kika ji kuma son ganin mu sai ki taho ki gan mu, ko kuma mu mu tafi mu ganki. Kuma kullum zamu ke kasancewa tare a waya, mu dai farin cikin ki kawai muke bukata" Ta lumshe idonta, anya tana tare da sauran farin ciki kuwa? Anya? Ita yanzu fatan ta bai wuce kwanakin ta suyi sauri su kare ta mutu ta tafi gurin Amour ba. Sakon sarki ya samu Hassan kuma sun shirya sun taho dan honouring gayyatar sarki, sai dai wannan karon daga shi sai aunty ne suka taho. Suna zuwa bayan dukan gaggaisa an kuma gabatar musu da kayan refreshment sai aka yi musu iso. A hanyar tafiya suka hadu da Adam. Shima har dashi aka kira duk da baisan dalilin kiran ba tunda family issue ne. Suka gaisa awkwardly, sai Adam yace "ya Sumayya da baby? In an koma a gaishe su please" Hassan yadan shafa kansa yace "zasu ji" suka jera suna tafiya sai Hassan yace "thank you Adam, for understanding" Adam ya gyada kai yana dan murmushi yace "nine da godiya". Daga nan suka shiga gaban sarki tare da yan uwan Fatima da kuma ita kanta Fatiman. Bayan sunyi gaisuwa daya bayan daya kuma sarki ya amsa sai ya fara godiya ga Allah sannan ya gode musu a bisa hadin kan da suka nuna akan wannan case din, "Allah ya saka muku da alkhairi ya kara hada kan ku ya kuma bar zumunci" sai kuma yayi jinjina tare da yabawa ga Fatima da kuma abinda ta aikata. "Hakan da tayi shine dai dai. Tabbas gaba ki dayan mu zuciyoyin mu sun tafi a kan cewa ita waccan yarinya ta aikata laifin da ake tuhumar ta dashi, amma gabaki dayan mu bamu da hujjar da zata tabbatar da haka, dan haka duk da cewa muna da ƙarfin ikon da zamu hukunta ta amma ba zamuyi din ba har sai mun tabbatar da tayi din. In kuma tayi din ma bamu da tabbas din hauka ne ya saka ta tayi ko kuma da sanin ta tayi. A yanzu haka Allah ne kadai yasan gaskiyar lamarin nan dan haka abar masa lamarin shine dai dai. Shi zaiyi hukun ci, idan ta aikata tabbas hakki zai fita, idan bai fita a duniya ba zai fita a lahira" "Maganar gadon Hussain da aka riga aka raba a kan cewa Fatima ta mutu da ciki, a yanzu ma a sharian ce za'a bar shi ne a haka. Abinda za'a gyara kawai shine kason Fatima da za'a damka mata kayanta. Amma sauran za'a barsu saboda bamu da tabbas din cewa da rai Fatima ta haifi abinda yake cikinta ko babu rai, bamu da tabbas din mace ta haifa ko namiji" "Shi kuma ko ita kuma abinda aka haifa din, zamu cigaba da addu'a in dai yana raye ko tana raye Allah ya bayyana mana shi ko ita, Allah yasa watarana ya tako da kafafuwan sa ya shigo cikin gidan nan ya kawo kansa gare mu, ko kuma mu Allah ya bamu ikon fahimtar inda yake ko take, mune mu taho dashi. In kuma baya duniya, Allah ya hada fuskokin mu a lahira, inda za'a hadu kuma ba za'a sake rabuwa ba har abada" "Magana ta gaba shine jinjina da godiya gare ki Amina akan irin rikon da kika yiwa yaran nan, da kuma rikon da kika yiwa Fatima sanda tana hannunku, tabbas ke din abar yabawa ce dan macece ke mai kamar maza, ina takaicin zumuncin da muka kulla a tsakanin mu kuma mutuwa ta katse mana shi. Bana so muyi asarar wannan zumuncin shi yasa nake neman alfarma a gurin ki idan kin amince. An sanar dani cewa Allah ya albarka ce ki da yaya mata, idan akwai wadda bata yi aure ba a cikin su ina son zamu tura Abubakar yaje ya ganta su daidaita in Allah ya amince sai ayi musu aure" Aunty sai murna, baki yaki rufuwa, lallai ba karamar karramawa sarki yayi mata ba. Lallai jinkirin Zulaihat alkhairi ne a gare su gabaki daya. Abubakar kuma ya sunkuyar da kansa yana murmushi, duk d abai san yarinyar da ake magana akan ta ba amma yasan ba zai taba bijirewa maganar da mahaifinsa ya fada a gaban mutane ba. In dai har yarinyar ta karbe shi to anyi an gama. Daga nan sai ya juyo kan Adam, yace "Adam. Fatima ta bani dukkanin labarin ka, kuma na fahimci cewa kai din na musamman ne ko a gurin ubangiji ma, dan irin ƙarfin imanin ka kafin a samu irinsa a cikin al'ummar mu sai an bincika sosai. Kayi sacrificing abubuwa da dama saboda musulunci kum kayi sacrificing abubuwa da dama saboda yar mu Fatima, saboda kuma gujewa rikici da samun zaman lafiya tsakanin kabilar mu da taku. Babu abinda zamu ce maka sai godiya da fatan alkhairi a duniyar ka da kuma a lahirar ka. Ba zamu iya biyan ka ba tabbas amma zamu gwada faranta maka iyakacin kokarin mu tare da kokarin replacing maka abubuwan daka rasa da wadansu. Misali itaye, daga yau ka dauke ni a matsayin mahaifin ka, ni ma daga yau ka zama dana kuma dukkanin wani guri da dan dana haifa a cikina zai taka kaima na baka uzinin takawa, duk wata alfarma da za'a yi wa dan dana haifa a cikina kai ma daga yau za'a yi maka ita. Zaka tattaro kayan ka ka dawo gidan nan dan gidan nan ya zama gidan ku yanzu" Adam sai murna, yama rasa mai zaice, shi bai san yadda ake nuna godiya ga sarki ba, sai yaga yayan gidan suna yiwa sarki godiya a madadin sa kamar yadda suke yi aduk lokacin da akayi wa wani daga cikin su wata kyauta ko wata alfarma. Shima sai yayi yadda suka yi. Yaga Umar da Abubakar wadanda sune maza suna jansa jikinsu suna taya shi murnar shigowa family. Sai kuma yaji sarkin yace "yanzu ina so ka fada min menene burin ka a rayuwa? Menene abinda kake so kayi? Aure? Karatu? Kasuwanci? Me kake so?" Sai Adam yayi shiru yana shafa kai, sai kuma ya juya yana kallon Fatima wadda ita ma shi take kallo fuskarta tana nuna jin dadin ta akan karramawar da mahaifinta yayi wa Adam, ta fahimci kamar shawara yake nema sai tayi mishi alamar yayi magana, ya fadi abinda yake so, ya juya yana kallon Takawa yace "karatu ran sarki ya dade. Ina son in cigaba da karatu" Sai Sarki yayi murmushi yace "to alhamdulillah. Dama abinda nayi maka sha'awa kenan, amma a koda yaushe abinda ake so iyaye suke yi shine su vawa yayan su dama su fadi abinda suke so su kuma sai suyi amfani da wannan su basu shawara ba wai su yanke hukunci ba tare da sunji abinda yayan su suke da ra'ayin yi ba. Ga dan uwanka nan Umar, ka same shi ku zauna ku bincika duk makarantar da kake so ya nema maka ka tafi kayi karatun ka, Allah ya baka sa'a, Allah yayi maka albarka". Daga nan aka gabatar da adduoi aka tashi. Bayan an fito, Adam yana ta murna ya tafi gidan su na Kano inda babu kowa a ciki yanxu sai shi, ya kwaso kayansa ya dawo, Abubakar da kansa ya taimaka masa suka saka aka kai masa part dinsa aka gyara masa daki daya a ciki aka saka masa, suttura kadai ya debo, dan babu abinda yake bukata bayan su dan ya samu komai har ma abinda bai saka ran samu ba, ya samu family, Royal family. A daren ranar Fatima ta kira shi a waya suka hadu a gurin saukar baki tace "maganar school nake so muyi, kun fara maganar da yaya Umar?" Yace "a'a, bamu yi ba tukuna" tace "tayi dama zanyi maka na inda zanje, let's go together, in na samu abokin karatu maybe zan iya yi, dan a yanzu ji nake yi bazan iya ba" yayi sauri yace "zaki iya mana, in dai ba so kike kiyi ta samun carryovers ba har in gama in barki" tayi murmushi "maybe, maybe zanyi ko dan kar ka gama ka barni". Sai ya dauko sabuwar wayarsa ya saka number din Maman sa from memory, ya kira ta dauka yace "Mama" da sauri tace "Joseph. My son is that you?" Yace "it is me mother. It is Adam" tace "thank you Jesus. I was so worried about you. Ko bacci bana iya wa" ta fadi maganar so emotional, ya danyi mata shagwaba "bayan Kin gudu kin barni. Baki damu dani ba" tace "how can you say that. Wa na damu dashi duk duniya sama da kai? Na barka ne saboda kayi learning lesson ka gane mutanen nan ba kaunarka suke yi ba, they will always used and dump you. Haka halin su yake..." Yana kallon Fatima yace "not all of them mother. Fatimah ce ta fito dani, ta hakura da damar da might lead her to find out about her baby saboda ta fitar dani. Because she believe in me. And her father took me in, yanzu ina gidansu. Har sun fara maganar fitar dani waje inyi karatu. They are good people Mama, excellent people". *********************** A Kaduna, Ruqayyah tana kwance a dakinta na kasa inda ta dawo da zama yanzu, saboda hawa bene ya kare mata. Tun da Hassan da Fatima suka shigo suka fita take kwance a dakin tana kuka, kukan da ita kanta bata san na menene ba, dan Lukman ma daya dawo da niyyar ta sallame shi bata kula shi ba a haka ya hakura ya tafi yace zai dawo. Tafiyar su Hassan kano babu jimawa, ita kuma Sumayya ta hada kan yara suka tafi gidan Baba zasu wuni a can. A lokacin ne kuma Ruqayyah ta fara jin kara kamar ana ruwan sama da kankara, ta na jiyo karar kamar ta fashewa glasses, Sannan kuma da hayaniya kamar a waje. Ta danna kararrawar da ta saka saboda kiran yaranta, sai ga Luba a guje, idonta kamar zai fado, tace "Aunty, mutane ne a waje suke jifan gidan nan, sun balla gate sun shigo, masu gadi duk sun gudu, Aunty mun shiga uku kashe mu zasu yi" Ruqayyah ta bude baki "mutane kuma? Me suke so?" Luba tace "ban sani ba, kamar dai ke suke so su kama" cikin Ruqayyah ya kada, taji kamar zata yi kashi a wandon ta, me tayi musu? Me tayi musu? Da gaske babu abinda tayi musu, not directly, amma Hussain, Hussain ya kyautata musu iyakacin kyautatawa dan da yawa daga cikin su suna a matsayin da suke a yanzu ne saboda Hussain. Wasu kuma saboda sadakar da Hassan yayi da sunan Hussain. Kuma duk abinda ya faru, duk shari'ar da akayi, mutane sun gani kuma sunji labari a media, sun kuma fahimci tabbas ita ce ta salwantar da da daya tilo da Hussain ya mutu ya bari kuma ta zaune akan dukiyar da ya bari, Shari'a bata kama ta ba saboda babu shaida, shine su suka zo zasu kamata suyi mata hukunci irin nasu. Suyi mata justice din da law ba zata yi mata ba, suyi mata jungle justice. *One One* Ina neman afuwar masu karatu saboda maimaicin suna da aka samu na yaya da kuma kanwar Fatima, Asma'u. To zamu bar sunan a matsayin na kanwar Fatima, yayar kuma sai mu chanja mata wani, let's say Maryam. Wani dutse aka jeho wanda ya fasa glass din window ya zo har gaban Ruqayyah, ta kalli dutsen idanuwan ta a waje tana lura da girman sa, da ace a goshinta ya sauka da tsaf zai fasa goshin in ma da karar kwana ya aika da ita lahira, lahirar da bata shirya zuwa ba yanzu. A guje Luba ta kwasa tayi hanyar kitchen, daga nan kuma Ruqayyah tasan waje zata fita ta kofar baya, ta juya tana kallon kofar shigowa palon sai taji an fara jijjigata ana dukan ta da abin da yayi kama da sanda, dan ma mai kwari ce yasa basu iyaballa ta ba yet, taji ance "ki bude kofa, shegiya mayya, in baki bude ba sai mun saka miki wuta mun kone ki da ranki, munafuka, macuciya, mayaudariya, azzaluma". Ta rikice, kalmar konewa tana ratsa kunnuwan ta tana shiga har zuciyarta tare da saka matsanancin tsoro a ranta, jikinta ya dauki karkarwa har ta kasa driving kujerar ta ballantana ta gudu, to in ta gudun ma ina zata je, babu abinda take tunawa sai yadda wuta ta kama gawar Minal da ta driver tana cin su, da irin kaurin konewar naman su da ya cika dajin, su da suka kone bayan sun mutu kenan, ita kuma fa? Da ake barazanar kone ta da ranta? Ta tuna da zafin da take ji idan ta taba tukunya mai zafi ko kuma wuta unintentionally, ta tuna da irin azabar da take ji idan mai ko ruwan zafi sun taba ta, ta tuna da abinda tataba karantawa cewa the most painful thing in the world is to be burned alive. Allah da kansa ya haramta azaba da wuta komai kuwa laifin mutum. Bata san sanda ta mike daga kan kujerar ba, sai ganin ta tayi ta fadi, a dai dai lokacin da wani dutsen ya kuma faso glass din taga ya sauka akan dagon bayan ta, taji zafin saukar sa ta kuma ji zafin faduwar da tayi amma tsoron azabar wuta ya saka ta shanye zafin ta fara jan kafa da sauri ta tafi hanyar da dakin da take zaune a yanzu yake. Girman falon ya saka ta sha wahala kafin taje dakin, tana zuwa kofar dakin suna balla kofar falon, tana jin wani yana cewa "gata can, gata can. Gurguwar banza" ta shiga dakin da sauri sannan ta rufe kofa ta murda lock, ta jingina da kofar jikinta yana karkarwa kamar mazari "wayyo Baba, wayyo Inna ku taimaka min zasu kashe ni. wayyo Allah na" ta matsa daga jikin kofar da sauri sanda taji an taba kofar. "Ba zaki bude ba? Sai munyi gunduwa gunduwa da namanki in muka kamaki". Ta ja da baya da sauri, jikinta gabaki daya yana karkarwar yadda ta ma kasa motsawa daga inda take kamar yadda kwakwalwar ta ta toshe ta kasa lissafa mata abinda ya kamata tayi. Tunanin daya fara zuwa mata ranta shine Inna da Baba, ina suke? Me yasa ba zasu zo su ceceta ba? Sai ta tuno da last ganinta da Inna ranar nan data leka ta taga ta ganta a compound din gidan Hassan tare da Sumayya, last ganinta da Baba kuma a court ne inda ya fede biri har wutsiya a kan halayyar ta, amma duk da wannan tasan su biyun nan sune kadai zasu iya zuwa ceton ta a yanzu, bata jin akwai sauran mai kaunarta yanzu a duniya bayan su da suka kawo ta duniyar. Ta kare wa dakin kallo tana neman wani gurin buyan dan taji har sun fara saran kofar dakin da Adda, duk karfin kofar kuwa tasan zasu balla ta dan da gaske suke ba wasa ba. Idonta ya sauka akan kofar toilet din da yake cikin dakin, ta ja jiki da sauri tana rarrafe ta shiga toilet din sannan ta tura kofar ta saka lock dinta ita ma, amma ita kanta tasan bata tsira ba dan in suka balla kofar dakin babu abinda zai hana su balla kofar ban dakin. A jikinta taji cewa this is the end of her. Ta kama bango ta mike da kyar, karkarwar jikinta shi ya kara wa mikewar tata wahala, ta dafa tagar toilet din tana girgiza bars din da suke jiki, babu abinda zai iya wucewa ta ciki in ba hannayenta ba, ko da ace zata iya wucewar ma ta yaya zata iya hawa tagar da wannan kafar tata mai suffar lagwani, in ta haura ma kuma ina zata je? Kofar shigowa gidan guda daya ce kuma ta can suka shigo, da wacce kafar zata gudu ta tsere musu? Waye zai taimaka mata? Sumayya? Ta bar wayarta a falo, ko da wayar ma har yau number din Sumayya bata shiga in ta kirata. Har yanzu fushi take yi akan ta maganar gatawa iyayen Adam inda yaje da tayi, sai ta tuna cewa ashe yanzu abin ya wuce nan, ashe tayi sanadiyar da aka rufe Adam din ma gabaki daya, duk dadai tasan by now an fitar da shi. Amma yanzu ita tamkar wanda ya fada ruwa take, taimako take nema ta kowacce hanya, ko bakin tako bi ata miko mata karba zatayi. "Sumayya!" Ta dage tun karfin ta tana kwalla mata kira, koma menene ta zama, koma wacece ita a yanzu ta tabbatar Sumayya zata taimaka mata a irin wannan yanayin "Sumayya, Sumayya ki zo ki taimaka min dan Allah zasu kashe ni. Sumayya! Sumayya dan Allah ki zo. Sumayya!" Amma Sumayya bata jiyo ta ba, saboda Sumayya bata gidan bata ma unguwar ta tafi gidan su tare da yara gabaki daya, sai ita kuma ba yar aiki ne da ita ba dan haka babu wanda yaji yo Ruqayyah. Aunty ma bata nan sun tafi kano ita da Hassan, Zulaihat ma taje gidan friend dinta, sai mai aikin su wadda cikin ikon Allah taji ihun Ruqayyah bayan taji hayaniyar mutane kuma mai gadi ya gaya mata abinda yake faruwa, sabuwa ce ita dan haka bata san takamaiman gaskiyar abinda yake faruwa ba, dan haka ta dauko wayarta hannu yana rawa ta kira Sumayya ta gaya mata abinda yake faruwa. Ruqayyah ta saki karfen tagar tare da zamewa kasa saboda jikin ta ba zai iya cigaba da dauka ta ba saboda karkarwar da yake yi, ta saki kuka mai karfi, "wayyo Allah Sumayya ki zo ki cece ni" sai kuma ta mike zaune da karfi tace "Hassan!" Ita kanta bata san sanda ta ambaci sunan ba kuma batasan dalilin da yasa ta fadi sunan ba, bayan Fatima, Hassan shine mutum na karshe da zai taimaka mata. Jin an fara bugun kofar toilet din yasa ta zabura ta koma can karshen toilet din, a coner ta rakube tare da jan guiwar ta ta hade da kirjinta, hakoranta na sama na dukan na kasa, a zuciyarta tana rokon Allah ya dauki ranta kafin su cimma ta, dan ita zancen wutar nan shi yafi komai dagamata hankali. Tayi bitar rayuwarta tun daga sanda ta bude idonta zuwa yanzu sai taga cewa idan da zabi za'a bata ace wanne stage din ne tafi so, wanne ne tafi kasancewa cikin farin ciki da zata dauki lokacin da take gidan su, lokacin da suke zuba wake da shinkafa a tray su ci tare ita da siblings dinta wani lokacin ma har tare da Inna suke ci. Those were the happiest days of her life............Those where the good old days Rayuwar ta da Hassan would have been good too, but duk a zamanta da Hassan hankalin ta baya kanshi kuma baya kan auren, hankalin ta yana wani gurin daban. Ta tuna da ƴaƴan ta, ƴaƴan da sai ta taga take leken su lokacin tana sama, yanzu kuwa sai dai wani lokacin in gari yayi shiru sosai sai taji muryoyin su suna wasa da dariya. Tasan in ta mutu ma ba zasu damu ba, tasan yadda mutuwar tata zata kasance ma ba zata dame su ba, tasan ko nan gaba ba zasu yi missing dinta ba musanman in suka girma suka fahimci abinda tayi, in suka fahimci ta zabi kudi maimakon su, ko addu'a ma tasan ba zasu ke yi mata ba duk kuwa da cewa zata bukaci addu'ar sosai. Amma anya akwai sauran wanda ya rage wanda zai yi mata addu'a kuwa? Daga cikin dakin taji ance "idan kofar ba zata ballu ba ku saka mata wuta, idan mu ba zamu iya shiga mu tarar da ita ba ai wuta zata iya shiga" *************************** Hassan ne a cikin mota tare da Aunty, tun daga kano suka taho suna ta nishadi suna hira da dariya, Aunty har ta fara lissafin yadda bikin Zulaihat zai kasance da irin taron da zata shirya "irin wanda ba'a taba yi a gidan ba" ta fada dramatically. Hassan yayi dariya, "wato bikin auta ko aunty? Gashi kuma autar aunty zata auri dan sarki" Aunty tace "tabbas, Zulaihat mai yayye da yawa, yar gatan dangi" yace "amma fa ina tausaya miki aunty, in Zulaihat ta tafi zaki ji babu dadi. I mean saura ke kadai fa kawai duk girman gidan nan" tace "Hajiya yaya zanje in dauko a Gombe, sai kuma in nema a dangi a bani rikon yammata ko biyu ne haka" yace "ohh na dauka wai ko zaki.......ina nufin kema zaki.......kinga ai yanzu babu nauyin kowa a kanki zaki iyayin auren ki ba tare da damuwa ba" Ta dauki jakar hannunta ta dake shi da ita a kafada, ya sosa gurin da hannu daya "ouch Aunty, driving fa nake yi" tace "mara kunya fitsararre" yace "Allah ya baki hakuri tunda ba kya so. Wai dama tayi ne nayi miki" ta harare shi tace "bana so din" sai kuma suka yi shiru hankalin sa yana kan traffic din dasuka tarar, can daga baya sai yace "da Hussain yana nan zai ji dadin wannan hadin auren na Zulaihat" sai tayi murmushi, a ranta tana hasko yadda fuskar Hussain take in yana farin ciki tace "sosai, zaiyi murna sosai. Allah baiyi zai gani ba, Allah ya kai rahama kabarin sa" Hassan yace "ameen" sai kuma yace "Aunty, akan maganar nan gabaki dayan ta, me kike tunani aunty? Me kike gani? Kina ganin dan Hussain yana da rai ko kuma Ruqayyah ta kashe shi da gaske? Sumayya tana ce min ita bata yarda Ruqayyah zata iya kashe baby ba" aunty ta girgiza kanta tace "ban sani ba Hassan. Babu abinda zan iya cewa akai. Babu wanda ya gani, babu wanda yaji, babu wanda ya tabbatar. Shi kuma zato zunubi ne ko da ya zamo gaskiya. Kamar yadda mai martaba sarki ya fada, zata iya yiyuwa Fatima ta haifi dan babu rai tunda accident suka yi. Zata iya yiwuwa Ruqayyah bata ma san sanda Fatima ta haihu ba. Za kuma ta iya yiyuwa ta kashe dan da gaske. It can be anything. Babu yadda zamu yi mu tabbatar idan har ba Ruqayyah ce da kanta ta furta da bakinta ba. Dama ina so inyi maka magana akan maganar nan Hassan, ya kamata ka sakawa zuciyarka ruwan sanyi kamar yadda Fatima ta janye maganar nan kai ma ka janye ta, ko ba da komai ba ko dan Sumayya. Sumayya tana dauriya fa sosai. Ka tuna yadda suke ita da yaruwarta da, kafin ka auri Ruqayyah, ya kamata kake sanyaya zuciyar ka ko dan kayi mata alkunya dan duk munin halin Ruqayyah dole Sumayya zata ji wani abu a ranta in aka muzanta ta" Can kasan makoshin sa yace "insha Allah Aunty, an daina" tace "yauwa. Kamar yadda sarki ya fada, in muna da rabon ganinsa zamu ganshi, in bamu ganshi anan ba zamu ganshi a can. Kowa da kaddarar rayuwarsa, babu wanda zaiyi wa mutum wani abu sai in Allah dama ya nufa cewa hakan zai faru. Idan har yana raye to kaddarar sa bata tare damu, tana wani gurin daban. Idan lokacin da kaddarar mu zata hadu yayi, zaka ganshi da kafafuwan sa yazo har gaban mu".. A lokacin suka shawo kwanar gidan, taron mutanen da ya gani a kofar gidan Hussain suna ta hayaniya shi yasa ya daga kafar sa yana salati "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, kar dai rigima ake a garin nan bamu sani ba" aunty tana kallon taron mutanen ita ma tace "amma tun a hanya ai bamu ga alamar komai ba, gidan Hussain suka shiga, subhanallah, Hassan fita ka gani me yake faruwa" ya girgiza kansa yana lura da sandunan da suke hannun wasu daga cikin mutanen. "Bara in shiga dake gida first aunty, in kin shiga ki rufe kofa kar ki budewa kowa" Sai daya shigar da ita cikin gidan ta sannan ya bar motar a ciki ya fito da sauri, ita kuma sai taji hankalin ta bai kwanta sosai da fitar tasa ba, kar fa wani abun ya same shi shima. Da sauri ya shiga gate din gidan, mutane ne suna ta zage zage ta fashe fashen tagogi a falon, hankalin sa ua tashi ya fara ratsa su yana tambayar su abinda yake faruwa, wadansu daga cikin su suka gane shi "yallabai abinda kuka kasa muka zo zamuyi mu. Wannan munafukar matar har ta isa ta halaka jaririn Alhaji Hussain ta kuma zauna akan dukiyar sa sannan mu kyale ta? Gata can an banka wa shegiya wuta, taje lahira tayi bayani a can" Hassan ya bude ido cikin tashin hankali, no matter how much he hate Ruqayyah bazai so a kashe ta for hussain's sake ba, ba zai so karshen ta ya zama haka ba ko dan saboda Sumayya da iyayensu da kuma yayansa. Ya ture mai gaya masa maganar ya wuce ciki da sauri yana tafiya yana kiran number din police, ya lura wasu daga cikin mutanen ba wai fansa suka zo daukar wa Hussain ba sata suka zo yi dan kowa ya dauki rabonsa a cikin kayan da suke gidan. A palon kasa ya hango dakin da aka balla kofar sa still da mutane a ciki, kafin ya karasa ya ga hayaki ya fara tashi yana cika dakin yana fitowa waje, yayi sauri ya ture su ya shiga dakin. Kofar toilet din dakin yaga tana ci da wuta. Hankalin sa ya kara tashi "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me kuke yi haka? Menene haka" wanda yake leading mutanen, Hassan ya gane shi tsohon dan daba ne wanda tasu tazo daya da Hussain har ya mayar dashi makaranta, yace "yallabai barka da zuwa. Wannan gurgun magen zamu aika lahira ta tarar da oga Hussain acan sai tayi masa bayanin abinda tayi wa dansa" Hassan yace "oga Hussain? Kuna tunanin Hussain zaijidadi idan kuka kashe ta saboda shi? Waye wanda ya baku Shari'a a hannunku?" Yace "yallabai tunda tafi ƙarfin Shari'a ai mu bata fi karfin mu ba, gama mata aiki kawai zamu yi kuma wallahi ruwa ta sha" Hassan yace "waye yace muku tafi ƙarfin sharia? Mu da kan mu fa muka yanje karar saboda muna ganin barin ta da Allah yayi mata hisabi yafi duk wani hisabin da wani alkali zaiyi mata. Littafin ku daban nata daban, in kun kashe ta alhakin ta yana cikin littafin ku, shin kuna son ranar lahira a debo tarin alhakin ta a jibga akan ku?" Ya bude ido Yace "ina! Wannan muguwar, ai zunubin ta yafi karfin kafaduna" Hassan ya lura wutar ta fara cin karfin kofar ga hayaki yana kokarin hana su numfashi sai ya fita da sauri zuwa kitchen din gidan, yasan Hussain ya saka fire extinguisher a different parts na gidan including kitchens, ya dauko ta da sauri ya dawo ya fara fesawa kofar, yana ji suna ta bala'i wadansu suna nuna basu so hakan ba, wadansu kuma suna so ya gama kashe wutar su shiga toilet din du dauko ta tunda sunsan yanzu kofar ta zama weak. Wutar tana mutuwa sai yayi sauri ya riga su shiga, a can karshen toilet din ya hango Ruqayyah a durkushe a corner, hannunta rike da hand spray, daga dukkan alama niyyar ta tayi amfani dashi kurin kashe wutar in tazo gurin ta sai dai shi yasan da wutar tazo babu yadda zata yi da ita, a matuƙar tsorace take, daga inda yake yana iya hango yadda jikinta yake rawa, ta jike sharkaf da gumi. Ya karasa gurinta sai yaga ta yar da abin hannun ta ta kamo rigarsa ta kankame shi. Ya juya yana kallon mutanen gurin yace "ba zan barku ku taba taba, not in my brothers name, na kira police zasu zo yanzu, kuyi sauri ku gudu kafin su karaso" Wadansu suka fara kokarin fita wadansu kuma suka fara mita "yawa ne da Allah, kabarmu mu cika mata aiki kawai" yace "if you want her, you will have to come through me". Siren din police ne ya saka suka fara fita daga gidan a guje, a waje police suka jejjefa musu tear gas sannan suka samu suka shigo amma still wasu sunanan, wadanda suka matsa ma gefe suka je suka tsaya suna jifa da duwatsu. "Wallahi indai ba'a dau mataki akan ta ba sai mun kashe ta. Police din nan duk basu san aikin su ba wallahi. Ku bari a nuna muku yadda ake adalci. An nafsi bin nafsi" A cikin gidan a cikin toilet, Hassan ya cire hannun Ruqayyah da yake jikin sa ya juyo da ita yana kallon fuskarta, she looks so different, shi sai yaga ma kamar tayi tsufa akan shekarun ta. Yace "I just saved your life. Kamar yadda ranar nan kika yi saving mine. You now owe me nothing. Munyi one one. Sai dai banbancin shine ni nayi saving dinki ne saboda Allah ba dan wani abu da nake saka ran zan samu daga gare ki ba. Saboda abinda ya kamata musulmi yayi kenan a duk lokacin da yaga ɗan uwan sa musulmi cikin bala'i sai yayi kokari ya taimaka masa dan Allah. Na gama nawa, yanzu tsakanin ki da police ne su zasu baki kariya" sai ya tura ta baya, ya manta ma gurguwa ce sai daya ga ta fadi kasa a dai dai lokacin da police suka shigo toilet din. Bai koma ta kanta ba ya juya yana magana da police din, biyu daga cikin su da aka taho dasu mata suka je suka daga Ruqayyah, bai ga me zasuyi mata ba ya yi tafiyar sa. Yana fitowa daga gidan motar sa da Sumayya ta tafi da ita gida tana isowa kofar gidan dauke da Sumayya, Baba da Inna da Sulaiman. Sulaiman ne yake tukawa dan Sumayya ba zata iya ba dan gaba ki daya a hargitse take tunda aka gaya mata abinda yaje faruwa. Inna taci kuka ta gode Allah kafin su kara so. Tun kafin motar ta gama tsayawa Sumayya ta bude kofa ta fito kamar zata fadi ta taho da gudu gurin Hassan, ya kamata "she is okay, she is okay. Allah yasa nazo da wuri da abin ba zaiyi kyau ba, amma she is okay yanzu tana hannun police" Sumayya ta rungume shi ba tare da tunanin inda suke ba tana kuka tace "mun gode, Allah ya saka maka da alkhairi" a dai dai lokacin police suka fito da Ruqayyah daga gidan, nan take mob din da suke jira suka bisu da ruwan duwatsu, sai da suka saka shield suka kare amma duk da haka sai da wani ya samu Ruqayyah a tsakiyar kanta, nan take jini ya wanke mata fuska, amma duk da hakan bata kasa ganin Sumayya rungume a jikin Hassan ba. Da kyar police din suka saka ta a mota suka tafi, suna tafiya mob din suka bisu a baya, sai Hassan shima suka shiga mota tare da Baba da Sulaiman suka bisu a baya, amma an bar Sumayya da Inna a gida tare da Aunty. Asibiti ya kamata a kai Ruqayyah saboda jinin da take zubarwa a kan ta amma hakan ba zai yiwu ba dole aka tafi da ita police station saboda tsaro, acan aka samu akayi dressing din ciwon, wanda sai da aka aske tsakiyar kanta sannan akayi mata dinki. A kofar station din kuma saboda yawan mutanen da suke gurin sai da commissioner yazo da kansa, ya kuma hana mutanen sa suyi wa mutanen komai, instead sai ya fito ya tsaya yayi magana dasu "me kuke so?" Wani yace "justice" yace "akan me?" Wani yace "matar data salwantar da rayuwar dan Hussain Aminu Abdullahi, ita muke so a yanke mata hukunci dai dai da laifin ta" commissioner yace "yanke hukunci ai aikin alkali ne bana police ba, mu aikin mu shine mu kama mai laifi kuma mu bamu kama matar nan da laifi ba, bamu ne muka kai karar ta ba, wadanda suka kai karar tata ma kuma da kansu suka janye karar. An riga an rufe file din shari'ar" wani yace "mu duk bamu gane wannan jawabin naka ba, mu kawai muna so a yanke mata hukunci" commissioner yace "to abinda zakuyi a shawarce shine kuje court ku shigar da sabuwar karar akan ta, sai ku gabatar da hujjojin ku in sun gamsar da alkali sai ya yanke mata hukunci. Amma ku sani. Matar nan takarda daga asibiti ta nuna cewa tana da matsala a kwakwalwar ta, dan haka ko kunje Court akwai yiyuwar ba zaku iya shari'a da ita ba saboda ba'a shari'a da mahaukaci" wani yace "in na mahaukaciya ce shikenan sai a barta a gari tana kashe mana yaya, ba akwai imda aka tanada saboda ajiye masu tabin hankali ba? Akaita can mana in dai da gaske bata da hankalin" commissioner yace "yauwa, yanzu kuka yi magana, in har haka kuke so ni zanyi muku jagora zuwa ga hukumar da abin ya shafa dan a tabbatar an killace ta a gida mahaukata kamar yadda kuka bukata" da haka aka samu suka yarda, amma suka ce in dai aka sake suka kuma ganin Ruqayyah a gari to duk abinda ya same ta babu ruwan su, kuma suma ba zasu bar shaidar da za'a kamasu da ita ba. Sai washegari aka samu aka kai Ruqayyah asibiti aka duba ta properly, sai kuma a washegarin ne Sumayya da Inna suka samu damar ganinta duk da cewa har lokacin tana cikin matsanancin shock, Sumayya tayi kuka kamar babu gobe daga nan kuma sai ciwo, tayi mamakin Hassan da yake barinta tana zuwa duba Ruqayyah duk da shi baya shigowa, Baba ma kuma sai gashi ya sauko ya bar Inna ita take jinyar Ruqayyah. Anan ne ta kara fahimtar halin da yar tata take ciki, wannan firgicin yana nan har yanzu, ga wata uwar rama da tayi, hannunta kamar skeleton. Lukman yaji labarin abinda ya faru, kuma ba bata lokaci ya garzaya asibiti gurin Ruqayyah, a zahiri ya nuna kamar ya damu be da halin da Ruqayyah take ciki, a badini kuma ta cikon kudin sa yake yi. Sunyi magana da police kuma sun tabbatar masa da cewa kai Ruqayyah mental institution shine kadai hanyar tseratar da rayuwar ta. Lukman ya danyi tunani akan hakan sai yaga shima wata kafar samun wasu kudin ne ta bude masa. Idan Ruqayyah ta tafi mental institution dole tana da bukatar mai kula mata da dukiyar ta, a matsayin sa na lawyer zai iya wannan aikin, zai ci rabon sa ya bar mata saura, in ta kwashi shekaru acan sai yayi kokari ya fito da ita, daga nan kuma zata biya shi kudin aikin sa, in yayi Sa'a ma kuma zata iya......... Amma sanda ya samu Ruqayyah da maganar sai yaga kamar ba Ruqayyan daya sani bace ba. "Ina so zanje inyi confessing. Ina so ka shige min gaba inyi confessing" ya bude baki a ransa yana cewa "ji wannan sakartar yarinyar, in tayi confessing kuma da wanne kudin zata biya ni?" A zahiri kuma yace "no.... don't even try that... Kin san kuwa me hakan yake nufi? In kika yi confessing you will loose everything" ta juyo tana kallon sa, "I don't care" sai hawaye suka zubo mata. "I already lost everything long time ago". Ya gyara zama yana jera kalmomin da zaiyi mata amfani dasu yace "okay, tunda haka kike so haka za'a yi. Let's go over abubuwan da zasu faru if you confess" tace "na riga na sani, za'a kai ni gidan mahaukata kuma za'a karbe dukiyar da take hannu na a bawa masu ita" yace "no, that was before, lokacin da ba'a tabbatar ke kika yi laifin ba, amma in kika yi confessing shikenan an tabbatar beyond doubt, za'a hada miki dukkan laifuffukan ki kuma a kara miki da laifin wasa da hankalin Shari'a, you will be hanged. Amma wannan ba komai bane ba tunda naga kamar kin shirya tafiya lahirar, abinda nafi ji miki shine family dinki, kin ga duk wannan abin da ake yi har yanzu basu tabbatar da kinyi abinda ake zargin ki dashi ba, amma kina confessing shikenan sun tabbatar, and they will be so heart broken. Basu bama, ni nafi jin yayanki, those innocent cute babies, the fact that anyi hanging uwarsu zai bi su ne har karshen rayuwar su. Wannan shine abinda kike so musu? If that is your wish I will help you to get it granted". ********************* A sanda ake ta wannan rikicin a Kaduna, a kano kuma shirye shiryen tafiyar su Fatima ake tayi, ya yarda zai biya Dubai kamar yadda ita da kanta ta bukaci hakan. Yayi settling down sosai a gidan Sarki, da yake he is social nan da nan yayi mingling. Ranar nan Umar ya kira shi a wayarsa ya gaya masa ya same shi a cikin gida a falon Hajiya Ummah kuma ya tafi da takardun sa, yana so zai fara processing neman admission dinsu shi da Fatima. Farko ya dan ji tsoron shiga cikin gidan amma sai yaga daya tafi ba'a hana shi ba, ya kira Fatima a wata ita tayi directing dinsa a waya har part din Hajiya Ummah kuma ya shiga har falon ta, anan ya tarar da Fatima already ta riga shi zuwa suna tare da Umar, ya dan rissina ya gaishe da Umar din shi kuma ya tsokane shi saboda yaji shi a waya yana gayawa Fatima tsoron shigowa yake kar dogarai su kama shi. Ya zauna yana mika wa Umar folder din hannunsa, ya karba ya hada data Fatima data bashi already, sai kuma yayi musu bayanin duk procedure din da za'a bi da kuma requirements din da makarantar suke bukata. Sai ya fara going through takardun nasu dan ya tabbatar suna wa komai. A haka suka baje takardun suna ta dubawa Adam yana ta tattara nasa a guri daya wai baya son Fatima ta gani, tace "meye kake boyewa, ko baka yi kokari bane a makarantar ka" ya bata rai " kina magana da head boy ne fa" tace "in ma waye, if you have nothing to hide then why are you hiding?" Umar ya dauko birth certificate din Adam ya mika mata yace "kinga abinda yake boyewa" Adam a dafe kai sai kuma yayi dariya yace "ba boyewa nake ba fa, kawai dai bana son a raina ni ne" tayi dariya "boyewar kake yi kenan, let me see shekara nawa na baka dan in san Aunty zaka ke ce min ko yaya" Ta bude takardar tana dubawa sai ta bude baki "wai kana nufin ka girme ni?" Adam ya gyara zama yana murmushi, "an gaya miki ni din na yau ne" ya dauki tata folder din yana neman tata birth certificate din, ya dauko yana dubawa yana murmushi yace "yaya Adam daga yau" tace "only in your dreams. Wata takwas kadai ka bani" yace "oho dai, am sure na fara tafiya sanda aka haife ki" tayi dariya, "sai dai rarrafe" yace "ko rarrafen ne dai na riga ki yi". Umar yayi gyaran murya yace "zaku cigaba da musun shekaru ne ko kuma zaku zo muyi abinda yake gaban mu?" Sai suka matso either sides of him suna sauraron sa har ya gama, amma a ransa yana mamakin yadda yaga Fatima tana dariya, this is the first time da yaga dariyar ta tunda ta dawo gida. Bayan sun gama sai ya basu labarin abinda yake faruwa a kaduna akan case din Ruqayyah, Fatima bata ce komai ba dan ita bama ta son jin maganar dan dai in ta tashi zata zama rude to her brother. Bayan ya gama yi musu bayani ne Adam yace "to! Allah yasa haka shi yafi alkhairi. Ni iyayenta nake tausayawa, mutanen kirki ne sosai, they help me alot a lokacin da nafi bukatar taimakon. Dama gobe nake saka ran zan je Kaduna in gaishe su in kuma yi musu bayanin tafiyar nan inyi musu sallama" Fatima ta dago kanta tace "in zaka je zan bika. Zan tambaya in an bar ni sai mu tafi, ina son inyi wa Aunty sallama nima" Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020 *The Seventh Wave* Washegari kamar yadda Adam ya fada sai ya shirya da niyyar zuwa gaishe da Baba da Inna Ade, ya gaya wa Takawa kuma ya barshi sannan ya saka Umar ya bashi kudi masu dan kauri a envelope yace ya kai wa Baba ya kuma gaishe shi saboda yaji dadin labarin da Adam ya bashi na yadda Baba da iyalinsa suka karbe shi ba tare da kyamatar inda ya fito ba, duk da kasancewar su iyayen Ruqayyah bai sa maimartaba ya ga aibun Baba da family dinsa ba saboda yasan Allah yana iya fitar da mummuna a cikin kyakykyawa kuma ya fitar da kyakykyawa a cikin mummuna. Fatima ma ta tambaya an kuma barta, amma sai aka hada ta da Asma'u dan tafi jin dadin tafiyar, har sun shirya kuma sai aka kira Abubakar aka ce ya bisu su tafi tare, ba'a fada masa dalili ba amma shima yasan dalilin, bai kuma musa ba sannan bai bata lokaci ba ya shirya suka tafi. Adam ne yake jan motar Abubakar yana gaba, Fatima da Asma'u suna baya. Fatima seems moody tun da ta tashi da safe, sun fara kokarin cheering din ta amma basu yi nasara ba sai duka rabu da ita suka cigaba da hirar su a tsakanin du suna dan saka ta kadan a ciki duk da dai bata amsa musu. Kasancewar sun fita da wuri ya saka suka isa Kaduna da wuri, direct gidan Aunty suka tafi, Aunty wadda Hajiya Ummah ta gaya mata zuwansu ta tare su baki har kunne, amma ganin mood din Fatimah ya saka ita ma nata jikin yayi sanyi, Zulaihat ta fara hidimar saukar baki mata da suka shiga ciki, Asma'u tana ta tsokanar ta tana cewa ta zama in-law dinta, wai sai yanzu ta lura duk gidan ta fisu kyau. Hassan kuma a waje ya dauki Abubakar da Adam. Dan refreshing kadai suka yi suka fita zuwa gidan Baba, sunyi Sa'a sun tarar dashi a gida, yayi murna sosai da ganin su. Gaisawa kawai suka yi sai Hassan da Abubakar suka koma gidan aunty suka bar Adam anan tare da Baba. Baba ya shigar dashi har cikin gida ya gaishe da Inna Ade tana ta murna "oh Adam, muna ta jajen ka sai Sumayya take bamu labarin abinda ya faru, munyi murna sosai. Allah yasa hakan shi yafi muku alkhairi" Adam yayi murmushi yace "ameen Inna, yasu Zunnur? Nayi kewar su sosai" Inna tace "suna lafiya lau, Zunnur fa har ya shiga jami'a, Sulaiman kuma ya gama sai cigaba da yake shirin tafiya, Hassan ne ya dauki nauyin sa" Adam ya bude baki yace "wow Inna, Masha Allah. Gaskiya nayi murna da jin wannan labarin. Alhamdulillah Allah abin godiya, zan so in gansu kafin in tafi" tace "au tafiya zaka yi? Na dauka zaka yi mana kwana biyu ne anan ai". Adam ya dan sunkuyar da kai yana jin nauyin rashin kyautawar da yayi musu na kin zuwa da wuri duk da cewa sun damu dashi sosai, sai yayi saurin chanza shawara "ina nufin kafin in tafi gidan Aunty in dauko kayana dana bari a mota, kwana uku zanyi ai anan" Inna tayi murna, "yauwa, kaga sai inyi maka irin abincin da kake so". Sai ta dauko wayar ta tana kiran numbobin su Zunnur cikin doki tana gaya musu labarin zuwa Adam, sannan ne shi kuma Adam din suka kebe da Baba ya bashi labarin halin da yake ciki na komawar da yayi gidan sarki da zama da kuma maganar tafiya karatun sa. Baba ya taya shi murna sosai "ikon Allah, Lallai Adam kai din akwai tarin baiwa sosai a tare da kai, wannan abinda ka fara gani kenan, Allah ne kadai yasan abinda ya boye maka wanda zaka samu nan gaba." Adam ya gyada kai, dan shi kansa yana mamakin irin yadda rayuwa take juya masa, sai kuma Baba yace "ni ai na dauka ko kayi fushi ne shi yasa baka zo ba, na dauka kayi fushi akan maganar Sumayya" Adam yace "haba haba Baba, ba haka bane ba ai, Sumayya ba rabo na bace ba shi yasa ban aure ta ba, kuma ni na zabi hakura da ita dan nasan idan da ace na dawo da wuri da ba za'a hana ni ita ba. Na kuma yi murna da zabin da akayi mata na miji dan Hassan mutumin kirki ne. Allah ya basu zaman lafiya da zuriya mai albarka" Baba yaji dadi yace "ameen summa ameen Adam" Sai kuma suka dora da labarin abubuwan da suke faruwa, Adam yana ta kwantar masa da hankali akan maganar Ruqayyah "kayi iyakacin kokarin ka Baba, mu mun sani, duniya duk ta sani" Baba yana juya kai yace "amma duk da haka nayi asarar yata" Adam yace "amma kuma ka samu Da, ni dan ka ne, a koda yaushe zaka kira ni da Da kuma karbi rile din dan a gurin ka insha Allah" Baba yayi murmushi yace "bayan an kwace min kai, mai martaba sarki yayi min fin karfi" Adam yace "duk ku biyun nawa ne Baba, duk iyaye na ne ku, nayi rashin uba sai gashi na samu iyaye har biyu" Baba yace "tabbas Adam kai aya ne ta ubangiji, cewa yana fitar da kyakykyawa daga cikin mummuna, kamar yadda Ruqayyah take aya kan cewa ubangiji yana fitar da mummuna daga cikin kyakykyawa". A gidan Aunty, Fatimah ta rikice musu da kuka, musamman bayan taga hotunan Hussain da har yanzu suke rataye a falon Aunty. Gaba daya rayuwar ta a gidan ce take dawo mata, duk inda ta kalla akwai wani memory na Hussain a wajen, sai taji kamar har muryarsa take ji yana dariya tare dasu kamar yadda suke zama anan falon ayi ta wasa da dariya, duk inda ta kalla sai taga kamar zata ganshi a gurin yana yi mata murmushi. Aunty ta zauna lallashi sai itama ta fara kukan, Allah yaso Zulaihat ta fita gurin baki wajen Abubakar da itama da ita za'a yi kukan. Hassan sai ya zama ya saka su a gaba ya rasa wadda zai bawa hakuri a cikin su, a karshe sai ya tashi ya fita ya koma gidansa sa inda dana ya gaya wa Sumayya ta shirya yara zai kawo du su gaishe da Fatima, tunda baya jin Fatima zata shiga gidan sa, Sumayya ta gama shirya su ta kuma faya musu auntyn su ce tazo zasu he su gaishe ta dan duk cikin su babu wanda zai iya tunawa da ita. Yana shiga ya tarar suna jiran sa, yana kallon Sumayya yace "are you sure ba zaki je ku gaisa ba?" Sumayya ta girgiza kai, "bana son fuskata ta kara mata more emotions dan what she already is in" sai ya kama hannun yaran suka fita tare Abdullahi kuma ya dauke shi. A hanya suna ta tambayar sa alakar su da wadda tazo, sai da suka shiga cikin falon sannan ya durkusa a gaban su yace "kun tuna uncle Hussain?" Hussain ya bude ido cikin murna "uncle Hussain da nake kama da shi ko? Wanda in na girma zanyi irin halinsa" Hassan yace "that's right sweety, to wannan matar sa ce lokacin da yana da rai, sunan ta Aunty Fatimah" Sai ya jasu gaban Fatima, ta dago kanta daga kan kafadar Aunty inda take kukan ta, ta zuba wa yaran ido, lokaci daya ta gane Aminu da Yusuf, sai kuma ta sauke idonta akan little Hussain. Nan take ta bude ido tare da rufe bakin ta da hannayenta guda biyu, Hassan ya jawo shi zuwa gabanta yace "Fatima, this is Hussain, Hussain Hassan Aminu" Fatima ta zame ta durkusa akan guiwowinta, fuskar little Hussain irin ta Hussain dinta sak har dimples din. Ta rike fuskarsa a hannun ta cikin karyayyiyar murya tace "Hussain!" Sai yace "na'am" ta jawo shi ta rungume shi a jikinta tana sake wani sabon kukan. Abu biyu ne suka saka ta kuka akan little Hussain, na farko shine kamannin sa da Amour dinta, na biyu kuma dan ta tuna cewa wata daya da yan kwanaki ne tsakanin sa da nata dan, da yana nan da yanzu shima ya kai haka a girma, da yanzu shima ya fara zuwa makaranta ta, da yanzu shima ya fara kiranta da mommy, da yanzu ta rungume shi kamar yadda ta rungume Hussain. Tabbas kuwa da duk duniya bata jin zata samu wani abu as valuable as him. Ta dago daga jikin Hussain tana kallon fuskar sa sai yasa hannunsa yana goge mata hawayenta yace "ki daina kuka kar kiyi ciwon kai, mommy tace in mutum yayi kuka dayawa kansa zaiyi ciwo" ta gyada kai tace "na daina, na daina Hussain" Hassan ya zauna a kujerar kusa da ita yace "kina son sa in bar miki shi?" Tayi sauri ta juyo tana kallon sa, sai kuma ta sake juyawa ta kalli Hussain, Hassan yace "in dai kina sonsa, na baki shi ki tafi dashi" ta girgiza kai tace "I can't take him Hassan, kaima kana bukatar sa dan yake debe maka kewar dan uwanka" yace "haka ne, amma ke kewar mutum biyu zai debe miki. Ni ina da abubuwa da yawa da zasu debe min kewar Hussain" Sai ya mike tsaye yace "let me show you something" ta mike itama duk da bata san me zai nuna mata ba, ta bishi a baya tana tafiya tana waiwayen little Hussain. Baya taga ya zagaya, tasan dai babu komai a bayan sai garden din da Aunty take shuke shuken ta, ta tambaye shi "menene a gurin?" Sai ya dakata da tafiyar da yake yi ya juyo yana kallonta yace "kabarin Hussain" sai ta dafe kirjinta ta fara tafiya da baya baya tana girgiza kai, hawayen daya tsaya yana dawo wa. Cikin in ina tace "you, you....burrrrry him here?" Ya gyada mata kai. "zaki iya zuwa kiyi masa addu'a? Ko kuma mu koma?" Ta kalli inda taga ya dosa da sauri, tana jin tamkar wani abu yana janta zuwa gurin, irin abinda yake jan ta ga Hussain a duk lokacin da yake kusa da ita. Da sassarfa ta wuce Hassan ta doshi gurin, sai kuma da kabarin ya bayyana a gabanta sai ta durkushe akan guiwowinta ta rufe fuskarta da hannun ta tana kuka. Hassan ya tsugunna a kusa da ita tare da diban kasar kabarin a hannunsa yace "kar kiyi, kar kiyi masa kuka dan Allah. Kiyi masa addu'a ki nema masa rahamar ubangiji dan shine abinda yake bukata daga gare ki a yanzu, shine kuma abinda ya saka na kawo ki gurin sa" sai ta same ta zauna kan dandaryar kasar gurin tana kallon kabarin, a idonta tana tuno irin rayuwar da suka yi da Hussain sanda suna dating da kuma shekara biyun da suka yi a matsayin mata da miji, the love, the care, the life.........babu abinda Hussain bai bata ba. Those two years da tayi a tare dashi bata jin zata kuma yin masu dadin su anan gaba. "Hussain" ta fada cikin rawar murya "my love". Sai Hassan ya mike ya juya zai bar gurin, ta juyo tana kallon sa tace "Hassan" ya dakata amma bai juyo ba, tace "naji labarin abinda kayi wa Hussain da dukiyar da ya bar maka da nufin daji dadi in baya duniya, sai kai kuma ka zabi ka yi masa sadaka danshi yaji dadi yanzu da baya duniya. Ban taba ganin dan'uwan da ya yiwa dan'uwan sa haka ba, ban taba ganin dan'uwan da yake son dan'uwan sa kamar yadda kake son Hussain ba. Ina son ka sani shima yana son ka sosai. An gode, Allah kai ma ya baka wanda zaiyi maka haka" Ya gyada kai kawai sannan yace "ameen" muryarshi can kasan makogwaronsa. Bai juyo ba saboda baya son taga hawayen da yake fita daga idonsa. Abubakar yana can yana soyewar sa, sai daya gama sannan ya fara tattaro kan su suzo su tafi, Fatima amma taki dawowa cikin gida ko abinci bata zo taci ba, sai da Aunty ta zagaya da kar sannan ta taho da ita shima kuma sai da ta nuna mata cewa lokacin sallah yana wucewa sannan ta taho, sai dai suna kiran Adam sai ya gay musu ya fasa komawa yau sai yayi kwana uku tukunna. Wannan yasa basu jira shi ba suka tafi. Fatima bata dauki kyautar da Hassan yayi mata ba, sai dai ya gaya mata duk lokacin da ta chanja shawara tazo ta dauka ya bata shi. Bayan sun tafi ne Hassan ya hada kan boys din sa suka koma gida. Suna shiga suka hau sama da gudu suna rige rigen neman mommy, har da Abdullahi daya fara tattakawa kadan. Hassan ya bisu da kallo, amma shi jikin sa yana bashi cewa bata saman, sai ya tafi dining section dinsu, yana shiga kuwa yaganta tana ta aikin setting table, yatsaya tae da jingina bayansa da jikin bango yana studying din yadda take komai nata cikin nutsuwa kuma a tsare, kowanne plate dagurin ajiye shi kowanne spoon ma da gurin sa. Yana bin surarta da kallo yadda jikinta musamman hips dinta suke motsawa with every move da tayi making. Tabbas Sumayya da Ruqayyah suna kama sosai ta fuska, amma jikin su sam ba iri daya bane ba, Sumayya a cike take ta ko'ina musamman hips din ta da bayan ta suna daukan hankalin sa sosai. Hatta fuskar Sumayya tafi ta Ruqayyah cika, musamman lips dinta, very beautiful. Ya danyi gyaran murya sai ta juyo da sauri, ta bata rai, "ka tsorata ni fa wallahi. Baka yi sallama ba" yace "sorry, but I enjoy watching you in kina abubuwan ku unaware of me" ta harare shi "so kake ka kare min kallo har ka hango munina ko?" Yayi dariya tare da jan kujera ya zauna, "muni kuma? A ina? Kin san kuwa yadda kike da kyau Sumayya?" Ta zagayo ta zauna akan cinyarsa tana zagaya hannayenta a wuyansa, yace "ya babyna?" Tayi fari da idonta "lafiya lau. Me zaka siyo masa yau?" Ya dora hannunsa akan lips dinta yace "shshsh. Mata, macece ba namiji ba, I have got a lot of boys to last me a lifetime" tayi dariya "to shikenan baban baby, me zaka siyo mata" ya fara sansana jikinta yana lumshe ido, "me take so yau? goruba ko agwaluma" ta dago kansa daga jikinta tana kallonsa tace "you! Kai nake so" ya danyi gajeren murmushi yace "kamar dagaske, in baby taji sai ta dauka da gaske ana son babanta" ta mike ta zagaya daga vayansa ta saka kanta a wuyansa tace "waye ya gaya maka maman baby bata son baban baby" yace "to ta fada mana inji" tace "actions speaks louder than words" sai ya mike, tana kallon yadda yake kallon ta ta fara ja da baya, yace "show me. Ya kike guduwa kuma? Kar dai ki gaya min a bakine kawai abin" Sai data kai karshen dakin ta hada bayanta da bango sannan shi kuma ya karaso ya bi jikin ta da nasa, ya saka fuskarsa a wuyanta kenan suka jiyo hayaniya an doso inda suke. Ya danja da baya yana bata rai, tayi dariya, ya nuna ta da hannu "tonight, I will get the words out tonight" yaran suna shigowa gurin ya hargitse, kowa yana kokarin bata labarin abinda ya faru a gidan aunty yau, sai da ta samu suka yi settling ta zuba musu abinci ta zubawa Hassan shima sannan suka nutsu suna ci dan sun san babu kyau surutu in ana cin abinci. Sun fara ci kenan Hassan yace mata "Fatima tare suka zo da Adam" ya fada yana studying dinta, tayi murmushi "kai amma ya kyauta daya rako ta" yace "ba rako ta yayi ba, yazo ne dan ya gaishe da su Baba, yana can ma yanzu zai danyi musu kwanaki a can" ta bude ido "kai madallah, ya kyauta sosai, kullum Inna tana yi min maganar sa, suna so suji halin da yake ciki. I told them he is okay" yace "nima Baba yana tambayata shi. Ya kyauta sosai da yaje gurin su. Sun damu dashi sosai" sai kuma ya bata labarin tafiyar dasu adam din zasu yi, sannan ya gaya mata kyautar da yayi wa Fatima duk da cewa bata karba ba. Da dare Adam ya fita taje boutique ya siyo kaya sakawa, sai ya nuna kamar a gidan aunty yaje ya karbo. Kwanan sa uku kamar yadda yayi alkawari sannan ya yiwa su Baba sallama dan next week suke saka ran tafiya, duk da dai yayi musu alkawarin in ya sauka a can zai nemi numbers din su su cigaba da gaisawa. Da zai tafi ya dauko sakon da mai martaba ya aiko wa Baba dashi ya bashi. Baba harda kwallar sa, ba wai kudin ne damuwar sa ba dan yanzu kam alhamdulillah kudi sai dai ya bawa wani, Hassan da Sumayya sun tsaya masa a komai. Sai dai the fact that sarki guda yasan da zamansa kuma har ya aiko masa da sako shine ya taba zuciyarsa. ****************************** Lukman yaci galaba akan Ruqayyah, da maganganu na tsoratar wa, duk da cewa ta nuna masa cewa ko tayi Confessing she won't be hanged, wannan ya nuna masa cewa indirectly tana nuna masa bata kashe yaron ba, sai kuma ya koma tsoratar da ita da irin horrors din da zata fuskanta a prison, musamman a matsayin ta na nakasashshiya. Sai kin gwammace ma kashe kin a kayi da rayuwar da zaki fuskanta a can. Ki bari a kaiki mental institution din, ni kuma I will do my best a waje inga cewa an fito dake da wuri, sai a nuna kin warke ayi faking result, sai ki cigaba da rayuwar ki normal ba wata matsala" She fell for that, tana ganin zuwa mental institution din zai iya taimaka mata wajen samun waraka daga nightmares da kuma demons din da suke hunting dinta. In ta dawo kuma tana ganin kafin nan zuciyar wadanda ta bakanta wa tayi sanyi yadda zata ji dadin neman gafarar su. A ranar da aka tafi da Ruqayyah asibitin mahaukata bayan ta danka komai a hannun Lukman tunda tayi tayi da Sumayya taki karba, a ranar ne kuma jirgi ya tashi da Fatima da Adam zuwa kasar da zasu bude sabon babi na rayuwar su. *Five Years Later* A shekara ta farko bayan an kai Ruqayyah mental institution, Sumayya ta haifi danta namiji, sanda ta haihu tayi tunanin Hassan ba zai ji dadi ba tunda ya gaya mata da bakinsa cewa yafi son mace yanzu, amma sai taga murnar sa har bata kwatantuwa, a take yayi wa yaro huduba ya saka masa suna Abdulrahman, sai kuma taga hidimar da yayi mata ita da baby da sauran boys dinsu har bata iya lissafawa. Tace "anya kuwa Habibi ba ka fi son yaran akan duk sauran yaran mu ba?" Yayi dariya, "kar kiyi min sharri Noorie, duk ina son su gabaki daya" tace "naga wannan hidima haka, kamar dan fari" yace "kowa ai rabonsa yake ci, kema kanki kinsan samu na na yanzu da na da ba daya bane ba, abinda zan iya yanzu da ba zan iya ba" Ta gyada kai cikin fahimta, tabbas Hassan yanzu ba karamin kudi yayi ba kuma yake kanyi, sosai sana'ar sa take kawo masa kudi duk da dai har yanzu bai kuma gina wata estate din ba saboda kudi yake tara wa tukunna, yace mata "sai na hada kudin da zasu ishe ni complete sannan zan fara, within short time zaki ga anyi an gama kuma cost of labour din ma zai fi sauki, dan yin aiki kadan kadan yafi jan kudi da yawa, su kansu kayan aikin ma in aka siya in bulk sunfi sauki". Ya sayi dai fili ya ajiye, kuma in the mean time yana siyan gida yayi renovating zuwa tsari irin na zamani sai ya siyar. Mutane kuma duk sun san shi akan sana'ar sa dan haka duk mai son siyar da gida sai a hada shi da shi, mai siya ma sai a hada shi da shi. A cikin shekarar ne kuma akayi bikin Zulaihat da Abubakar. Bikin da Sumayya tayi uwa tayi makarbiya a ciki, tana da role din babbar kawa kuma yayar amarya. Bikin shine lokaci na farko da Fatima ta dawo Nigeria, amma Adam bai samu zuwa ba dan yana tsakiyar exams a lokacin, a lokacin ne kuma Fatima tazo har gidan Hassan ta karbi kyautar daya bata ta little Hussain sannan ta kuma kai ziyara kabarin Hussain. Sumayya tayi mamakin yadda Fatima din ta shigo har cikin gidan ta kuma ta sakar mata fuska sannan tayi wasa da yaranta. Little Hussain yana ta murna musamman da yaji ance kasar za'a bari dashi. Amma Sumayya sai taji babu dadi da zai tafi, duk da ta fahimci dalilin da yasa Hassan ya bawa Fatima shi kuma gashi tana da yara da yawa a gabanta amma hausawa sunce sabo tirken wawa, sai dai bata yarda ta nuna ba dan kar Fatima taji babu dadi dan taga dokin daukan yaron take yi sosai shima kuma yaron haka, already akwai soyayya a tsakanin su. Bayan sun tafi ne Sumayya ta jinjina maganar, Ruqayyah ta salwantar da dan Fatima, and now dan Ruqayyah ya zama da Fatima. A bangaren Ruqayyah, tun sanda za'a kaita mental institution din tayi signing takardar data ke nuna cewa ta barwa Lukman rikon dukiyar ta, sai kuma tayi masa bayanin fortune teller dinta da kudin da take bashi duk wata, "nayi niyyar zan daina bashi dama wannan watan, sai dai bansan how much ya sani ba, ba san kuma ko da gaske yake ko kuma empty threats yake yi ba" yayi murmushi tare da karbar number da kuma address din mutumin yace "don't worry, I will take care of him for you" sai kuma yayi mata alkawari "the most da zaki yi a can shine shekara daya, kawai ina so hankalin mutane ya dauke daga kanki ne for the mean time, daga na fahimci sun bar maganar sun koma harkokin su zan fito dake. And it will be as if nothing has happened". Amma ita kanta Ruqayyah ta san ba haka bane ba, ta tabbatar she is never going to be normal or have a normal life again. Ga kudin dai tana da shi amma tasan she will never know peace but she is scared, she is scared of menene zai zamanto sakamakon ta idan har tayi admitting abinda tayi da bakin ta, will they really forgive her kamar yadda Fatima ta fada? Ta dauke mata da ta yar dashi tsirara anya zata yafe mata? And Hassan, bata jin ko zata yi kukan jini Hassan zai juyo ya kalleta ballantana yace ya yafe mata. Will they let her go to prison kamar yadda Lukman ya fada? And Lukman, ko kadan bata yarda dashi ba amma bata da choice dan tasan harkar kamfani komai a lussafe yake dan haka in dai yaci wani abu kafin ta fito to kuwa tabbas in ta fito zata sani. And he will definitely vomit it out, dan kare ba zai sha bugu ba sannan kuma gardi ya kwashe kaya ba. Amma abinda bata sani ba shine sanda ta saka kafarta ta a cikin institution din, Lukman bashi da niyyar fito da ita har abada, a lokacin da ake cike ciken ciken yi mata registration, shi kuma a lokacin ya hada baki da wani staff a gurin da niyyar ake bata treatment din da yafi karfin ta, wanda zai rikita kwakwalwar ta ta yadda ba za'a taba barin ta ta koma gida ba, yadda zata zama mahaukaciya tuburan. Yes, kudin Ruqayyah yayi mata amfani gurin dauko mata lawyer din daya kare ta a court, without her knowing that wannan lawyer din shine daya daga cikin mugayen kaddarorin ta. A cikin shekarar ta ta daya a gidan, maimakon ta fara warkewa daga mugayen mafarkai da kuma gane ganen da take yi sai ya kasance sai ma karuwa da suke yi, she stays up most of the nights saboda sun hana ta shan sleeping pills dinta. And that drove her crazy, rashin bacci, kadaici tinani da bakin ciki made her extremely depressed. Lukman yana zuwa ganin ta duk wata kamar yadda suka yi alkawari , yana zuwa yayi mata bayanin duk shige da ficen kudin data samu a watan, ya kuma kawo mata takardun d zata saka hannu akai, amma a zahiri abind yake kawo shi kenan dan yana bukatar saka hannunta kafin ya fitar ko kuma ya shigar da kudi. Tun a watan farko ya gaya mata cewa yayi mata settling problem dinta da malamin duba, bata san how ba amma she was grateful ta yarda kwallon mangwaro ta huta da kuda. Sumayya, Baba da Inna da kannen su suna zuwa lokaci zuwa lokaci su ganta, amma basa jin dadin yadda suke zuwa su tarar da ita, sai suke ganin kamar kullum kara kamanni take yi da mahaukaciya. Ta rame ta koma kamar skeleton ta kuma yi baki fatar ta duk ta lalace. And sometimes in suna magana sai tayi ta repeating magana daya, irin dai yadda zararru suke yi, kamar in akayi mata addu'a sai tayi ta repeating "Ameen ameen ameen" har sai ka gaji da ji, ko kuma in ta tambayeka abu in ka bata amsa sai anjima kuma sai ta kuma repeating the same tambaya. Sai Sumayya ta fahimci wani abu...... That smart and sharp brain of Ruqayyah is deteriorating. She is gradually loosing her sanity. Kuma bata yi kasa a guiwa ba tayi complain ga hospital management din amma sai suka nuna mata cewa suna yin iyakacin kokarin su akan ta. Babu yadda Sumayya zata yi a dole ta hakura, amma halin da take ganin Ruqayyah sai ya kara mata tunanin cewa Ruqayyah may be innocent akan abinda ake zargin ta da shi. Watakila ma duk bata san me take yi ba. Amma wani side ba zuciyarta yana tuna mata who Ruqayyah truly is. A bangaren Lukman kuwa tun a satin da aka kai Ruqayyah mental institution ya shirya kamar yadda yayi wa Ruqayyah alkawari yaje gidan malamin dubanta, direct ya dauko masa ID card dinsa na aiki a matsayin cikakken lawyer mai zaman kansa ya nuna masa kuma ya gaya masa yasan abinda yake tsakanin su da Ruqayyah "kasan hukuncin blackmail kuwa a court? Kasan hukuncin da za'a yanke maka? Yarinyar nan bincike ya tabbatar da tana da tabin hankali dan haka in ma kaje ka tona mata asiri kamar yadda ka fada to kaine a ruwa ba ita ba, ita yanzu an gama ta tata, saura ta ka kai kuma a matsayinka na mai yaudarar kananan yara marasa wayo irin ta kuma tura su ga halaka sannan kuma kuna amfani dasu gurin samun kuɗi". Nan take hankalin sa ya tashi musamman saboda ganin ID card din Lukman, dama kuma duk yana following yana jin abinda yake faruwa da ita, a ransa kuma ya riga ya saka ran cewa cin batin sa ya kare kenan. Amma bai saka ran za'a biyo shi har gida ayi maganar rufe shi ba. Sai ya rikice ya fara bada hakuri, sai da Lukman ya tabbatar ya gama tsorata sannan ya nemi ya gama masa gabaki daya abinda ya sani a game da Ruqayyah, shi kuma ya gaya masa iyakacin abinda ya sani " tabbas naga sunyi hatsari, kuma naga mutuwa na kuma ga haihuwa a wajen da akayi hatsarin, amma ban tabbatar waye ya mutu waye kuma ya haihu ba, batan Amina da kuma kasancewar Ruqayyah ita ce mutum na karshe da ya ganta shi yasa na tabbatar da abinda na gani farkon zuwanta shine ya tabbata. Ta zabi kasancewa mai kudi maimakon zama a karkashin masu kudi, abinda ni kaina tun sanda na gani din ban san me hakan yake nufi ba." Lukman yace "amma kuma ka bata tsoro da cewa zaka tona mata asiri? Kace zaka fadi inda ta ajiye yaron?" Mai duba yace "tsoro ne kawai na bata amma nima ban sani ba, ba komai nake gani ba sai abinda Allah ya nufe ni da gani" Lukman yace "yanzu dai baka san inda yaro yake ba" mai duba yace "ban sani ba, nasan dai yana raye tunda a mutuwar da na gani banga tasa ba" Lukman yayi shiru yana tunani sannan yace "shikenan, ba zan rufe ka ba kamar yadda na fada a baya, kuma zan cigaba da baka rabin wanda Ruqayyah take ba ka, amma ina son wani abu daga gare ka" malamin duba yaji dadi, yace "menene? Me kake so?" Yace "ina so kayi min aiki akan ta, wannan taurin kan nata ka sauko min dashi. Kasa take amincewa da duk abinda na gaya mata ba tare da musu ko jayayya ba ko bin kwakwkwafi ba". Wannan, hadi da magungunan da ake bunkawa Ruqayyah a asibiti kullum shi yasa ko wacce takarda Lukman ya kai mata take saka hannu akai ba tare da lissafi ko tunanin komai ba duk kuwa da cewa ita a zuciyarta bata yarda dashi ba. Shi kuma sai yayi rashe rashe akan dukiyar da take hannun Ruqayyah, dukiyar da ita kanta ba tata bace ballantana shi. Yayi ta bunkawa cikin sa haram yana tunanin yaci bati, ya manta cewa wasu Allah ya kan basu dama ne su tuba tun a duniya wasu kuma ya kan dauke ransu lokaci daya sanda kuma suke tsaka da cin duniyar su da tsinke. A lokacin da Ruqayyah tayi shekara biyu a rufe ne Adam da Fatima suka kammala karatun su na masters, a lokacin ne kuma mai martaba sarki ya bukaci Adam daya dawo gida a nema masa aiki kuma yayi settling down amma jin Fatimah bata da niyya dawowa Nigeria sai yace shima bai gama karatun da zai dora da PhD ne. Itama sai ta biye masa dan itama deep cikin ranta bata son ya dawo Nigeria din. Kasancewar gidan dayake zaune a ciki a can din gidan mai martaba sarki ne ba wai a gidan Aunty Maryam yake ba, ya saka ya cigaba da zamansa hankali kwance ba tare da yana tunanin ya takura wa wani ba, kyawun takardun sa ya saka ya nemi aiki yake yi tun kafin ya samu sabon admission na PhD din, wannan ya fara supplying dinsa da kudi, duk da cewa dama duk wata ana aika masa da pocket money amma yaga lokaci yayi da zai fara standing up for himself tunda yanzu har ya bawa talatin baya. Duk wanda yake tare da Adam, ko Fatima, ko kuma yake tare da Adam da Fatima to kuwa ko makaho ne in dai har zai saurara yaji yadda suke magana a tsakanin su yasan akwai soyayya a ciki, amma babu wanda ya taba furtawa a cikin su kuma babu wani wanda yayi musu magana akan hakan. In dai har kanason kaga dariyar Fatima to ka kira wo Adam gurin, amma in baya nan to little Hussain ne kawai yake ganin hakoranta. In Adam yana guri ta kanji ta manta da duk bakin cikin ta da stress dinta suna tafiya ne taji kamar babu su, ko mai yayi, ko me yace, tana jinsa ne har cikin ranta, komai nasa is valuable a gurinta. Wannan yasa ta ke supporting dinsa akan kokarin sa na ganin ya jawo hankalin real iyayensa zuwa addinin musulunci. She befriended kannensa mata, tana supporting dinsu tana badu shawarwari tana kuma nuna musu good behavoirs na islamic teachings. Sanda tazo Nigeria ma unexpectedly taje gidansu ta gaishe da Maman sa, tunda yanzu sunyi breaking up da uban ta dawo kano kuma yayan sun biyo ta. Daga Fatima har Adam sun sani cewa kadan ya rage su karbi shahada, kawai dai basa so suyi forcing dinsu ne sai dai su idan sunyi ra'ayi da kansu. Babu takura wa a addini. A shekara ta uku ne Sumayya ta kuma haihuwar Abdulrahim, wanda aka hada taron sunan sa da bikin bude estate ta uku wadda ita ce his biggest so far. A yanzu, in ana maganar masu kudi a garin kaduna, tabbas za'a saka da sunan Hassan Aminu Abdullahi. Sumayya kuma ta mori ladan biyayya dan a yanzu idan da za'a dawo mata da baya ace ta kuma zaben miji da Hassan zata kuma zaba ko da kuwa sau goma ne. Bata da wani problem wanda ya wuce lafiyar yaruwarta da har yanzu take cigaba da lalacewa dan last zuwanta ma Ruqayyah nuna wa tayi kamar bata santa ba, sai daga baya kuma sai ta fara yiata kuka tana tambayarta ina yayan ta. Babu irin rokon da bata yiwa Hassan akan ya barta ta tafi da yaran Ruqayyah ta gansu amma ya shafa wa idonsa toka yace bai san wannan maganar ba, "in sun ganta kuma sai kice musu wacece? Ta yaya zaki musu bayanin dalilin da yasa kuke kama?" Tace "sai ince yaruwa tace, saboda yar uwa tace, kuma banajin ma zasu ga kamannin da muke yi, dan yanzu babu wata sauran kama a tsakanin mu" ta fada tana share hawayen fuskarta. Tasan yanada soft spot for her, balle yaga tana kuka, sai ya dawo ya zauna a kusa da ita ya rike hannunta "Sumayya! Yaran nan are not ready for Ruqayyah and her drama. What if kuka je ta gaya musu ita ta haife su? Ta yaya zaki fara yi musu bayani? Kinsan yaran nan fa sunyi wayo yanzu sosai, suna lura da komai. Nasan dole zasu santa watarana amma not now please, dan Allah kar ki tayar min da hankalin ki akan wannan maganar" ta share hawayenta, tana kallon sa, yayi kokarin yi mata murmushi da fatan ko zai samu ta mayar masa amma sai ta kasa mayarwa, fuskar Ruqayyah kawai take gani a ganin da tayi mata. Tace "dan Allah, ka samu lokaci kaje ka ganta, na tabbatar in kaga halin da take ciki zaka shiga cikin maganar". Haka tayi ta lallaba shi amma yaki yarda. Ta koma tayi ta bin su Baba amma suma duk babu abinda zasu iya yi akai tunda suna ganin case din Ruqayyah a hannun police yake ballantana suje suce zadu dauke ta ko su chanja mata asibitin, Hassan din ne dai tunda yana da masu gidan rana zai iya jan wasu zarurruka ya fitar da ita, shi kuma Baba ya kasa yi masa maganar tunda ya san cewa in yayi masa magana ba zaiyi masa musu ba amma zai zama kamar ya takura masa ne. Sulaiman ne yayi kokarin neman Lukman akan maganar, ya tuntube shi kan batun fito da Ruqayyah kamar yadda yayi alƙawarin zaiyi tun farko amma kuma sai Lukman din ya nuna masa cewa yana yin iyakacin kokarin sa akan hakan abin ne yafi karfin sa, ya dauko masa takardun bogi ya nuna masa yana masa bayanin irin kokarin da yake yi akan maganar Ruqayyah. Amma sai Sulaiman ya nemi cewa zai ke shiga cikin duk fafutukar da Lukman din yace yana yi, ma'ana zasu ke yi tare da ya tabbatar da cewa anayi din. Farko Lukman ya tsorata da cika ido da hargagin Sulaiman, amma ganin bai yi masa maganar kudin Ruqayyah dake hannunsa ba sai ya sauke ajjiyar zuciya, amma shi Sulaiman babu abinda ya dame shi da kudin Ruqayyah, shi Ruqayyah din yake so. Amma maganar kudin Ruqayyah dake hannun Lukman, duk da bushashar da Lukman yake yi dasu amma kullum karuwa suke yi suna kuma ninkuwa, H and H group of companies kullum cigaba yake samu da kuma karin samun karɓuwa a gurin mutane a ciki har ma da wajen kasarnan. Shekara ta hudu tazo ta wuce, a cikin tane kuma akayi bikin Sulaiman wanda Hassan ya bashi gida a cikin phase 1, ya kuma tare da matarsa Ummulkhairi, bayan bikin ne kuma Sumayya ta same shi da magana akan Ruqayyah inda ta nemi su hada kudi a tsakanin su, tunda yanzu shima yana aiki yana daukan albashi, Zunnur kuma tunda ya gama jami'a ya kama business, ya bude boutique yake siyar da kayayyakin maza dana mata na zamani. Shawarar da suka yanke shine zasu hada kudi, shi Sulaiman zaije gurin police yayi following case din Ruqayyah yaji menene options dinsu akan ta, suka kuma yanke shawarar kar su saka Lukman a ciki dan sun fara fahimtar inda ya dosa akan maganar. Daga nan suka fara fafutuka, daga waccan station din zuwa wannan, daga waccan court din zuwa wannan, police suna ta cin rabon su daga hannayensu, alkalai suma suna cin nasu, amma shiru babu Ruqayyah babu labarin ta. A shekara ta biyar bayan an rufe Ruqayyah ne Sumayya ta kuma haihuwa, ta haifi mace this time around, a cikin murna ne Hassan yace ta fadi duk abinda take so ya bata shi kuma zai bata, ko kuma in akwai abinda take so yayi mata ta fada ko menene shi zaiyi mata. Ita kuma anan ta yi amfani da damar ta ta shigar masa da maganar Ruqayyah, ta fara kuka "dan Allah Habibi ka shiga maganar nan, munyi iya kokarin mu mun kasa, she is dying slowly, dan Allah" ta dauko wayar ta tana kokarin nuna masa hoton Ruqayyah amma sai ya daga mata hannu "bana son ganinta. Kina so in fito da ita?" Ta gyada kai da sauri, yace "to zan fito da ita, saboda ke, saboda bana son ganin wannan a idon ki" ya fada yana goge mata hawayenta. And, anan kudi da power suka yi aiki. Within a week akayi komai aka gama. Ranar sunan babyn Sumayya wadda aka saka wa Amatullah, a ranar ne kuma aka sallamo Ruqayyah daga gidan mahaukata, Sulaiman ne yaje dauko ta amma da yake sunan Lukman ne a matsayin care taker din ta dan haka dole asibitin suka kira shi shima yazo, sai dai daga nan Sulaiman bai taho da ita gida ba sai ya zarce da ita private hospital sannan ya kira gida ya gaya musu inda suke da halin da suke ciki. Dubai, United Arab Emirates Ranar da aka fito da Ruqayyah ta zamo dai dai da ranar zagayowar haihuwar little Hussain, shekara goma, meaning wata daya da kwanaki ne kadai suka rage Hussain yayi shekara goma a kasa. Fatima ta shirya masa Birthday party, ta kuma yiwa su Hassan video call sun gani suma kuma sun nuna musu kwalliyar su ta suna sun kuma nuna musu baby, little Hussain yana ta murna yayi kanwa mace atlast. Adam ya cika little Hussain da gifts, dan shima ba kadan yake son yaron ba, kuma son nasa yana da nasaba da kamar dayake yi da oga Hussain da kuma son da Fatima take yi masa. Bayan sun gama ne Fatima ta tafi raka shi mota zai koma gidan sa, tana ta yi masa hira amma shi yau sam ba hirar yake ji ba. A mota ne ya bude baya ya dauka wani dan karamin akwati kamar na sarka ya mika mata yace "a beautiful gift to the most beautiful woman in the world" sai ta harare shi, "yau kuma wani abu ya hau kan ka haka?" Ya dan shafa kai yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa yace "open it mana" Ta dauki box din tana kallo, tayi mata kyau sosai amma kuma zuciyar ta tana bigawa sosai akan abinda zata gani a ciki. Tana kallon Adam wanda shima ita yake kallo yace "open it" ta hadiye wani abu da yake neman kawo kwalla idonta ta bude, sai a lokacin ta lura da cewa music box ce, irin dan box din da kana bude shi zai yi kida, "There are three words, that I have been dying to say to you" "it burns in my heart, like a fire that ain't going out" "there are three words and I want you to know they are true" I need to let you know, I wanna say I Love You, and I wanna hold you tight, I want your arms around me and I want your lips on mine I wanna say I Love You, but beb am terrified, my hands are shaking my heart is racing, but it is something that I can't hide, something I can't deny. So here I go......... Darling I love you Sannan sai box din ya karasa budewa and a ring appears. A very beautiful ring. *Rejection* Tayi sauri ta rufe box din sannan ta rufe idonta, jin take yi a ranta tamkar ta rufe kunnuwan ta suma ko zata daina jin yadda kalmomin suke amsa kuwwa a cikin kanta. Siraran hawaye ne suka fito daga idanunwanta suka biyo ta kan kyakkyawan kuncinta sannan suka sauka akan kirjinta. Adam ya bi hawayen da kallo har suka iske destination dinsu yana jin tamkar digar dalma ne a cikin tashi zuciyar. Ya dafe goshinsa da hannu daya yana jin haushin kansa, how foolish of him to say these words to her, yana jin haushin zuciyarsa data zuga shi tana masa creating scene iri iri na yadda Fatima zata yi accepting proposal din sa and they will live happily ever after. "Stupid" ya fada wa kansa, "idiot" ya kara. Ta bude idonta sannan ta juyo tana kallon sa, yana jin kukan ta yana soya zuciyarsa "Adam" ta fada a hankali, sai kuma ta kasa ci gaba da magana, ya hadiye abin da yake barazanar hanashi numfashi sannan ya gyada kai "am sorry Zahra. It was foolish of me" sai ta kara karfin kukan ta tana matse box din a tsakanin hannayenta. "Ba kai ne mai laifi ba Adam, ba kayi min laifin komai ba. Ni ce mai laifi to, zuciyata ce mai laifi Adam, ita ce take yi min zafi" ya gyada kai yana jin tamkar ya kamata ya share mata hawayen ta, yace "am sorry da na zama silar da yasa zuciyarki take yi miki zafi" Ta juyo tana facing dinsa, dan box din still a hannunta, sai ta girgiza kanta tace "am sorry Adam, I can't do this" sannan sai ta kama hannun sa ta bude ta saka masa box dinsa a ciki sannan ta rufe tayi taku biyu baya sannan ta kuma cewa "am sorry". Sai kuma ta juya da sauri cikin gidan, duk da baya kallon fuskarta amma yasan cewa kukan take yi har yanzu, ya bude hannun sa yana kallon box din, yana jin ina ma dai bai kawo mata ba? Ima ma dai bai biye wa zuciyarsa ya fadi mata abinda yake dakon sa for over five years ba, but komai da limit dinsa, a hakan ma yana jinjinawa kokarin da yayi. Sai dai kuma turning dinsa down da tayi yafi komai bata masa rai, da bai fada mata ba ba zata yi turning dinsa down ba, da ya cigaba da samun damar ganin ta kamar kullum suyi hira suyi dariya together, amma yanzu yasan wannan abin ya shiga tsakaninsu kenan, dole ba zasu koma kamar yadda suke before yayi fooling kansa ba. Sai yanzu yake ganin foolishness dinsa, waye shi? Shi a suwa da har zai gaya mata wannan three words din da yayi ta practicing yadda zai gaya mata su for a very long time. She is a princess, a widow of his former employer, how dare he even said that to her! Yayi kicking tayar motarsa sai kuma ya rike kafar yana jin zafi, amma zafin da yake ji a zuciyarsa yafi yawa. Shi ba kowa bane ba face dan riko a gidan su, duk abinda yake takama dashi a yanzu, hatta wannan motar da yake shiga yake kira da tasa duk ya samu ne albarkacin babanta, duk mahaifin ta ne yayi masa komai, ilimin sa kuma dayake ji dashi a yanzu Marigayin mijinta ya taka muhimmiyar rawa wajen samar masa da shi. Amma ita zuciya ai bata san wannan ba, not when dealing with a lady like Fatimah. Perfect in every way. Shekaru goma kenan da rasuwar mijinta, a cikin shekaru goman nan kullum sai ya ganta, sanda suna imo kullum suna tare for five years, su abinci tare suyi hira tare suyi sallah tare, kullum jam'i suke yi tunda bashi da masallacin da zai je yayi sallah a cikin mutane, ya tuno da yadda take saka masa rigima kullum sai ya bata labari zata yi bacci, she always calls him handsome. Shin ina laifin zuciyarsa dan ta fada cikin soyayyar ta? Bayan sun dawo kuma bata taba nuna masa fifiko ko wani dagawa saboda title din ta ba, ta cigaba da treating dinsa kamar suna can dan sau da yawa yana jin comment daga gurin brothers ko sisters dinta cewa "in kana son ganin dariyar Fatima to ka kira mata Adam" duk sanda ta shiga cikin one of her moods shi suke kira, shi kadai yake iya soothing dinta ta saki ranta har kuma ya saka ta dariya. Ko bai kira ta ba ita sai ta kira shi a waya kullum, a can Nigeria da kuma nan Dubai, in suna makaranta suna tare in ya dawo da ita gida sai ta hana shi tafiya tace ya zauna tare da ita, sai ya bambare kansa da kyar yake guduwa, da daren ma kuma ko yana gidan sa sai sunyi waya,ta kan yi girki na musamman ta kai masa har gida a duk ranar da yaki zuwa gidan Aunty Maryam yaci abinci. Shin menene laifin zuciyarsa dan ta fada cikin soyayyar ta? Ya bude motar ya shiga yana jin wani irin zafi a zuciyarsa, dama haka mutum yake ji in aka ce ba'a son sa? Dama wannan shi ake kira da real heartbreak? Kaji duniya tayi maka zafi, hatta yawun bakin ka yayi maka daci, kaji kana jin haushin kanka kuma kana jin haushin kowa da yake kusa da kai hatta wadanda basu yi maka laifin komai ba, amma no matter how much he tried ya kasa jin haushin ita wadda tayi rejecting din nasa. Sai dai yayi ta dorawa kansa laifi. Karar wayarsa yaji a aljihun sa da ringtone din da yayi setting just For her, ringtone din da a rana ya kan yi kara kamar sau goma ko ma fiye da haka. Bai kula wayar ba ballantana ya dauka, ya cigaba da tukin sa a hankali dan yasan in yayi gudu to kuwa sai dai ya kuma ganin fuskar Fatima a lahira dan tabbas sai yayi accident. Bai tsaya ba sai a kofar gidan da yake a matsayin nasa, zuwa lokacin wayar tayi kara yakai sau biyar ko fiye da haka, ya kashe motar sannan ya dauki ring dinsa yana kallo, it is such a beautiful ring da ya jima yana zaba yana saka wa ana kara trimming dinsa, har sai da ya saci zobenta ranar nan ya kai aka gwada size din wai dan ya tabbatar yayi mata dai dai bai yi mata kadan ko yawa ba. In ya kalli yatsunta har imagining yadda ring din zaiyi mata kyau yake yi. Ya adana shi a cikin motar sannan ya fita ya rufe ta ya shiga gida a lokacin da wayarsa take sake wani kidan. "You make me wanna call you in the middle of the night, you make me wanna hold you till the morning light, you make me wanna love, you make me wanna fall, you make me wanna surrender my soul. I know this is a feeling that I just can't fight, you are the first and last thing on my mind, you make me wanna.............." Ya dauko wayar ya katse kiran tare da tafiya gurin setting dan ya chanja mata ringtone, zuciyarsa ba zata iya dauka ba. Kafin ya chanja wani kiran ya kuma shigowa, da yake yana cikin danna wayar ne sai yayi rashin sa'a ya dauki kiran. Muryar Aunty Maryam "Adam kana ina? Me ya samu Fatima take ta kuka haka?" Ya shafa fuskar sa, wannan kukan yasan kwana zata yi tana yin sa yace "kuka take yi? Me akayi mata?" Tace "to ni dai ban sani ba, gashi ta saka shima Hussain ya zo ya saka ta a gaba suna tayi. In baka ita ko zata gaya maka?" Yaji zuciyarsata so su, kullum indai akan Fatima ne a gurin mutane to shine solution, ammaita a gurin ta ashe ba shine ba. Bai bayar da amsa ba amma sai ta dora wa Fatimah wayar a kunnenta. Yana jiyo sheshshekar kukan ta. Ya zauna akan kujera yana dafe kansa "ba na baki hakuri bane wai Zahra, menene kuma? Na janye magana ta yinda ba kya sona, please kiyi imagining cewa it never happened. Idan da nasan it will hurt you this much da ko maganar zata zama ajalina ba zan furta ta ba" Yayi shiru yana ci gaba da sauraren yadda take rera kukan ta. Wata zuciyar tana gaya masa cewa ya dauki key din mota ya koma gidan yaje ya lallashe ta, the same zuciya da ta saka shi ya furta mata kalaman inda first place, amma yasan zuwan nasa ba zaiyi wani amfani ba tunda shine sanadin kukan nata, duk kukan kiyayyar sa ne wannan take yi da takaicin kamar sa yace yana son kamar ta. Yaji zuciyarsa ta yi nauyi a kirjinsa yace "nasan ban isa ba, it was an insult to you, I am sorry Fatimah me zan ce ne kuma ki daina kukan nan haka?" Cikin karyayyiyar murya tace "stop talking like that. You are hurting my heart". Yaji wani sabon arrow wanda aka fara narka shi da wuta ya sauka a zuciyarsa. Yace "shikenan. In dai Adam ne ya daina yi miki magana balle ya bata miki rai. Kiyi hakuri". Sai ya kashe kira sannan ya saka wayar a flight mode ya ajiye ta sannan ya kwanta rigingine akan kujera, shi kansa bai san tunanin da yake yi ba. Amma yasan cewa tunanin Fatima tana can tana kuka shine a saman zuciyar sa. Sai kuma ya mike ya shiga daki ya jawo akwatin sa ya fara zuba kayan sa a ciki, he is going to take a break, dole zai dauki hutu a makaranta ma dan ko yaje ba gane mai akeyi zai ke yi ba. Sai daya gama sannan ya dawo ya dauki wayar sa yayi booking next flight to Nigeria. Kamar yadda yayi tunani Fatima kusan kwana tayi tana kuka da kunan zuciya. Har sai da Aunty Maryam bayan ta yi ta kiran wayar Adam har ta hakura bata shiga sai da tayi tunanin kiran likitan da Fatima take gani a garin, sai ya bata shawarar cewa ta rabu da itata barta tayi kukanta amma kar ta barta ita kadai a daki, ta saka su kwana tare da wani. Wannan yasa ta turo mata Firdausi, budurwar yarta tace su kwana tare, sannan ga little Hussain Wanda dama tare suke kwana. Sai da tayi kukanta ta gama sannan ta tashi ta wanke fuskarta, a lokacin har Hussain ya gama nasa kukan yayi bacci a jikinta, ta gyara masa kwanciya sannan ta jawo akwati ta fara zuba kayan ta a ciki, she is going to take a break, Nigeria zata ta fi ta dan sha iska kadan. Amma a zuciyarta tana lissafin can she really spend some days ba tare da ganin Adam ba? Ba tare da ji daga gare shi ba? Dan tasan yayi fushi, daga jin yadda yayi mata magana yayi fushi ba lallai ne ya kuma yi mata magana ba ma in ta duba yadda ta rufe ido tayi turning down proposal dinsa, kuma ta fahimci irin fahimtar da yayi wa answer din tata, gani yake yi dan bai isa bane ba, ita kuma ta san ya isa in every way kawai dai she can't. Tun ranar da ta tabbatar da mutuwar Hussain da kuma bata jaririnta ta riga ta tsayar da zuciyarta akan cewa ba zata cigaba da rayuwa ne kawai dan dai bata da ikon katse rayuwar ta, zata jira har lokacin da kwanakin ta na duniya zasu kare ta tafi gurin mijin ta da ɗan ta. Dan haka ita ko a zuciyarta bata taba kawowa zancen soyayya ba ballantana aure, bata taba tunanin cewa wai ko tana son Adam ba ko kuma wai shima yana son ta. Sai yanzu, sai daya fada mata three words din, sannan ne tayi realising abinda yake faruwa. And her heart hurts, ji take yi kamar zata tarwatse. Taji ta tsani kanta akan abinda tayi wa Adam amma kuma wani bari na zuciyarta yana gaya mata cewa it is for the best. But can she? Ita ba zata iya moving on ba dan rayuwarta ta kare a ranar da aka saka Hussain a kabari amma dole tasan shi Adam zaiyi moving on komai daren dadewa, amma kuma wani part na zuciyarta baya so yayi din. And she hates herself for being so selfish. A duk tsahon shekaru goman nan da Hussain yayi a kabari babu wanda ya taba yi mata zancen aure har iyayenta, dan haka ita gabaki daya a ranta ta gama saddakarwa cewa kowa ya fahimci manufarta. And then Adam came with his three words. "Darling, I love you" he said. Ta zauna tanadafe zuciyarta, the words remind her so much of Hussain, sai taji kamar shi yake fada mata. Wannan kuma shi ya dawo mata da mutuwar sa sabuwa a zuciyarta. Dole ta tafi kano, maybe ganin iyayen ta ya danyi cooking dinta down, kuma ta fara practicing rayuwa without Adam. But his ring is soooo beautiful, his words soooo touching. Poor Adam.. Sai data gama hada kayan ta jaka daya na little Hussain a wata jakar sannan ta dauko wayarta tayi booking next flight to Nigeria. Da sassafe ta tashi, tayi wanka ta tashi little Hussain tayi masa wanka tana cikin taimaka masa gurin shiryawa Aunty Maryam ta shigo dan ganin yadda ta kwana. "A'a Fatima? Unguwa zaku je ne haka?" Fatima ta zauna tana kallon ta da kumburarrun idanuwan ta tace "zamu je Nigeria ne Aunty" Maryam ta zauna tana kallon ta "lafiya? Tafiya lokaci daya? Me za kuyi a gidan? Wani abin ne ya faru Fatima?" Sai Fatima ta zauna a bakin gado, hawayen ta na jiya suna sake dawowa, Maryam tace "ikon Allah, Fatima lafiyar ki kuwa" ta fada tana tura Hussain waje dan su samu suyi magana "Gaya min, me ya hada ki da Adam jiya, lafiya lau kika fita raka shi kuma kika dawo kina kuka?" Fatima ta share hawayen ta, a hankali tace "cewa yayi yana sona wai, wai zai aure ni yace" Maryam ta zauna a kusa da ita tana dafa kafadar ta, "shine dalilin wannan kukan Fatima? Har kika saka yaron nan ya zauna shima yayi ta rusa kuka kamar ance babansa ya mutu? To ai ni na dauka already kun gama wannan maganar da Adam din ai" Fatima tace "wacce maganar?" Maryam tace "maganar auren mana, ni ai na dauka karatu yake jira ya gama ko dai wani abu daban" Fatima ta rike fuskar ta tace "aure fa Aunty? Aunty aure fa kike cewa kin dauka zanyi? Ni ya zanyi inyi aure kuma?" Maryam ta bude baki cikin mamaki "to ke me kike nufi da? Kina nufin haka zaki yi ta zama ba zaki yi aure ba? To shi Adam din da duk bata masa lokaci kike yi ko me?" Fatima tace "Aunty babu komai fa a tsakanin mu wallahi" Maryam tace "babu komai a tsakanin ku kuma kika ce yace zai aure ki? Sannan kuma kika zo kika zauna kike kuka saboda yace yana sonki? Fatima, you are just confused. You don't know what you want. Bazan ce na fahimce ki ba saboda ban taba shiga irin halin da kike ciki ba a yanzu, amma abinda na sani shine abinda kike cewa bazai taba jiyuwa ba, wai ki zauna ba tare da kin kara aure ba, kin san wannan ba zai yiwu ba Fatima, ba za'a taba barin ki a gida ba. Yanzu ma da kika ga anyi shiru an saka miki ido to duk saboda ana saka ran cewa zaku daidaita da Adam ne, mu jira kawai muke yi kuce mana kun shirya mu saka rana" Fatima ta mike ta fara zagaya dakin "ba zan iya auren Adam ba Aunty, ki taimaka min kiyi musu bayani a gida, ba zan iya auren Adam ba dan Allah" Maryam ta mike itama tana kallon ta da mamaki "saboda me? Me yayi miki da zafi haka? Mu muna ganin cewa babu wanda ya dace da auren ki sama dashi" Fatima ta tsaya a tafiyar da take ta juyo tana kallon Maryam "Aunty, babu abinda yayi min Adam, he is just too good for me, I don't want to hurt him. Duk wanda na aura will end up heartbroken, I don't want it to be Adam". Sai Aunty tayi murmushi tace "shi yasa nace, you are just confused" sai ta mike, "ba zan hana ki tafiya gida ba, amma Hussain ba zai biki ba, yana school, in kin dawo kafin suyi hutu to, in kuma baki dawo ba in anyi hutu sai a turo miki shi". Ta juya ta fita. Fatima ta tsaya tana bubbuga hannayenta together, wai da gaske maganar maganar Aunty na cewa duk family sun dauka aure zasuyi da Adam gaskiya ne? Ta sake girgiza kanta. She can't, she can't marry Adam. Yadda tayi breaking heart dinsa ma jiya kadai ya isa ba sai ta cigaba ba, he doesn't deserve that. He doesn't deserve her. Saboda ita zuciyarta a cike take taf kuma a rufe take da padlock.. Bata fasa tafiyar ba duk da Aunty tace ba zata tafi da Hussain ba, amma kuma tana tunanin yadda zata iya zama a Nigeria babu Adam babu Hussain. Ta dan je airport late, saboda rikicin da Hussain ya saka cewa ba zata tafi ta barshi ba. Tana zuwa ta karbi boarding pass dinta taga seat number 25b, ta tafi da sauri ta shiga tunda already passengers din sun kusa gama shiga, ta duba seat dinta blindly va tare da ta lura da waye a seat din kusa da ita ba ta zauna tae da sauke ajjiyar zuciya tana rufe idonta. Adam ya dago kansa daga karanta jaridar da take hannun sa saboda kamshin turare da yaji irin na Fatima a kusa dashi. Ya kalli side din da yaji alamun an zauna, and there she is, ya ajiye jaridar "Fatima?" Ya fada cikin mamaki, ta juyo da sauri saboda jin muryar sa da tayi tana kallon sa "Adam? Me kake yi anan?" Yace "me nake yi anan ko ke me kike yi anan?" Tace "gida zan tafi in dan huta, kai fa?" Yace "nima gida zani in huta" suka yi shiru, sai yace "so... saboda ba kya ma son ganin fuskata shine zaki bar gari ko? Da kinyi zamanki ma, ni zan bar miki garin. Abinda na fada jiya shine abinda yake cikin zuciyata tabbas babu kuskure a ciki. Kuskuren shine furta miki da nayi, kamata yayi in shigaba da rikon abina a raina har zuwa kabarina. Once again am sorry. Zaki iya sauka kafin su rufe kofa" Tana girgiza kanta tace "ni zan baka hakuri Adam, laifi nane ba naka ba. Ni ce mai matsala ba kai ba. Ina kuma ba ka hakuri akan yadda matsala ta ta shafe ka. Kayi hakuri Adam, Please kayi hakuri" ta fada a lokacin da jirgin yake tashi dasu, bai ce mata komai ba har sai da jirgin ya daidaita a sama sannan sai ya mike, ba tare da yace mata komai ba ya bar gurin. Ita a tunanin ta rest room ya tafi dan haka sai ta mike ta dauki jakarta da ta bar seat din da niyyar in ya dawo ya tarar bata nan. Shi kuma Adam niyyar chanja seat dama yayi, sai ya hango wani seat da babu kowa na kusa dashi ma babu kowa, sai ya tafi can dan baya son ya zauna a kusa da wani yayi masa magana, so yake yaji da ciwon da zuciyarsa take yi masa, musamman saboda ganin ta da ya sake yi. Ya zauna tare da reclining seat din sannan ya cire hular kansa ya rufe fuskarsa da ita tare da rufe idonsa. Bai fi minti daya ba ya kuma jin kamshin taa kusa dashi, ya cire hular yana kallon gefen sa da sauri, ita ce a zaune tana waigen seats din da suka baro. Yayi murmushin takaici "are you following me?" Ta dan zabura kadan tare da kallon sa, sai kuma ta fara hawaye, haka take kamar baby, magana daya kuka musamman duk sanda take emotional. "Wallahi ba binka nake yi ba, can seat din na bar maka na dauka zaka koma can ne" a lokacin wata attendant tazo, tana kallon Fatima da take share hawaye tace "are you okay Madam?" Adam yayi saurin cewa "she is fine. Thank you" matar ta gyada kai sannan tace "what will you like, tea or coffee" yace "tea for her and coffee for me". Sai data tafi sannan yace "kiyi hakuri ki daina kukan nan haka. Zan bar miki nan din ma. Kiyi zamanki anan kinji?" Ta goge hawayen ta. "Kar ka tashi, ka zauna Please. Ina so muyi magana dan Allah. Ina so mu fahimci juna Adam bana son yadda na fahimci tunanin ka ya karkata akan maganar nan, you are making it harder than it should be" ya karbi drinks din da aka kawo musu ya kurbi coffee dinsa yace "menene nake tunanin ke kuma me kike nufi" tace "bansan cewa abinda ka dauki alakar mu ba kenan Adam, da na sani da tuni na gaya maka cewa ni ba haka na dauke ta ba. You mean so much to me Adam. But I can't marry you" Yace "saboda me?" Duk da a ransa yaji baya son jin amsar, duk kuwada cewa daga jiya zuwa yau ya lissafa dalilai kusan cikin charbi na abinda ya sa Fatima ta ki shi. Amma sai yaji ta tsallake duk wadancan dalilan nasa tace "saboda bana jin zan iya samar maka da farin cikin da ka yi deserving a rayuwa. I am not the one for you. I can't replace Hussain with you, it is not fair for both of you" yace "and I don't want you to replace Hussain with me. I can't replace him no matter how much I try, saboda ni ba Hussain bane ba and I can never be, ni Adam ne. Kowa a cikin mu daban yake. Bance ki cire shi a ranki ki saka ni ba, ban kuma ce ki dora ni a space dinsa ba, abinda kawai nake so, nake roka a gurin ki shine ki bani nawa space din a zuciyar ki komai kankantarsa, in dan samu in rakube ko ba zai ishe ni zama ba zan iya tsugunnawa in dai har a cikin zuciyarki ne" ta girgiza kanta "but it is not fair, you don't deserve that. Kana bukatar fresh zuciyar da babu kowa a cikinta inda zaka kafa kingdom dinka ka sake kayi abinda kake so kai kadai. Ita kake bukata ba tawa ba" Sai yayi murmushi yace "kin manta da cewa da Adam kike magana ne? Adam din daya ajiye iyayensa da dukiya da motoci da karatu for something da zuciyarsa take so? Ya tafi yake squarting a dakin abokai yana driving taxi saboda ya samu abinda yake so. Ke nake so, and that's all that matters to me" ta sake girgiza kai "ba zaka fahimta ba Adam, yanzu kake tunanin haka amma ba haka bane ba, ba zaka fahimta ba, sai nan gaba zaka fahimci cewa you deserve someone better than me. Please Adam don't make this harder than it already is, please accept my decision" A haka suka iso Nigeria. Ta riga tayi waya gida an san da zuwan ta, dan haka tana sauka ta tarar da mota tana jiranta, ta shiga suka tafi amma Adam sai yaki shiga ya dauki taxi, a ransa yana jin cewa ba zai zauna ma a fadar ba, daga yaje ya gaishe su zai tafi Kaduna gidan Baba yayi zamansa a can. Dan ya daina ganinta yayi wannan tafiyar amma kuma gata yadda ta kasance, ba zai ke tubka tana yi masa warwara ba dan in dai har yana ganinta to cire ta daga zuciyarsa zaiyi masa matukar wahala. Amma sai dai ana sauke ta shima yana shigowa, dan haka ganin natan dai da baya son yi sai da yayi din. Sai yayi zamansa a mota yaki fitowa amma duk da haka bai dauke idonsa daga kanta ba har sai data shiga ciki sannan ya fito shima ya bayar aka shigar masa da kayan sa ciki. Fatima tana shiga gurin Hajiya Fulani da murnar ta ta gaishe ta sai tambayeta "ina Adam din? Ki kira shi yazo yaci abinci ko waje za'a fitar masa dashi?" Sai tayi shiru a ranta tana mamakin yadda automatically Hajiya tayi tunanin tare suke da Adam, ba zata iya tahowa ita kadai ba sai tare da shi? Taso ace ba taren suke ba dan ta ga reaction din hajiyan, amma kuma yanzu sai Tace "yana waje, maybe yana gurin da yake sauka in yazo. Sai dai a aika masa" daganan taga Hajiya ta saka an fara hidimar shirya masa abinci, ita ko abincin ma baay bata ba. Takaicin wannan ya saka ta mike ta tafi part din Hajiya Ummah ta gaishe ta. A can ta samu ta zuba abinci taci ta koshi, amma still sai taji Hajiya Ummah ita ma tace "ina Adam? Ya karatun nasa? Na ga dai alama sai yaga karshen biro da takarda tukunna za'a yi auren nan" Let's rest here for today.... Team Adam and Fatimah together ina gaisuwa Team Adam and Fatimah seperated I salute you *Re-Married* Ta bude baki "aure kuma Ummah? Auren wa kike fada?" Hajiya umma ta juyo tana kallonta tace "in ina maganar Adam auren wa nake nufi kenan? Sai na fito nace auren Fatima sannan zaki gane?" Ta ajiye chokalin hannunta. "Ummah! Ni bansan waye yace aure zamuyi da Adam ba, ni ban san waye yace aure zanyi ba" Hajiya umma ta bita da kallo "ba aure zaki yi ba me zaki yi kenan? Zancen banza kenan kike yi ai. Dan kinga Takawa ya daga miki kafa to wallahi alkunya yake yi miki sosai da sosai saboda yana ganin irin abubuwan da kika yi going through amma shekara goma Fatima ba kwana goma bace ba, duk cikin mu babu wanda ma yayi tsammanin za'a barki ki shekara goma ba tare da kin sake aure ba" Fatima ta ajiye spoon din hannunta. Daga jiya zuwa yau gabadaya rayuwarta tana kokarin ta koma upside down, to wai wanne tsautsayin ne ma ya kawo ta Nigeria yanzu. She thought she was running away from something bata san cewa she was running toward it ba. Tace "umma ta, dan Allah kiyi masa magana, please make him understand, am not ready" Hajiya Ummah tace "sai yaushe zaki zama ready? Sai kin shiga menopause tukunna? Ko ba kya son ki haihu kema ki ga ƴaƴan ki a duniya? Bara in gaya miki wani abu Fatima, duk da nasan ba zaki ji dadin sa ba. Kinga marigayi Hussain? Mutumin kirki ne duk mun yaba da halayyar sa kuma muna fatan Allah yaji kansa da gafara, amma da ace kece kika mutu shi yana raye bana jin zai shekara biyar ma ba tare da ya sake wani auren ya haifi wasu ƴaƴan ba ballantana shekara goma. Ko da ace kuna raye kuma tare da ke da shi a matsayin mata da miji to baki da guarantee din cewa Ku biyu zaku yi rayuwar ku ba zaiyi miki kishiya ba. Fatima, ten years is enough. Gaki nan ras dake, tas abinki, you deserve a chance at happiness, ba wai dan mijinki ya mutu shikenan hakan yana nufin kamar kin tashi daga matsayin mace ba, na tabbatar kina da bukata kema kamar kowa, kina kuma son ki samu lada ki samu aljanna ta hanyar aure. Dan menene ba zaki yi ba? Shi fa wanda ya mutu ya riga ya mutu Fatima, Hussain ya mutu, ko kinyi aure ko baki aure ba babu abinda ya dame shi a yanxu, wadanda suka mutu damuwar su daban take da mu wadanda muke raye. In fact, idan da za'a taso shi yanzu da zai so ya ganki cikin farin ciki ba wai kina kunshe a daki kina kuka ba". "Sannan kuma wannan yaron da kike riko, no matter how much you love him ba dan ki bane ba, ba dan mijinki bane ba, ba dan yan uwanki bane ba, babu wata alaka ta jini a tsakanin ki ke da shi sai dai shakuwa, shin ba kya so ki haifi naki? Ki haifi dan da zaki kira da naki?" Fatima ta dora hannun ta akan marar ta tana missing feelings din being pregnant. Hajiya umma tace "kuma ki sani, ba ko wanne miji ne da zaki aura zai yarda ki tafi da yaron ba, dan wan tsohon mijinki wanda kike ruko saboda yana kama da tsohon mijinki" Fatima ta girgiza kai, "Adam ba zai ki daukan sa ba" Hajiya umma ta harare ta "Adam din da kika ce ba zaki aura ba? Ji nake abinda kika ce kenan" Fatima tace "Adam saurayi ne umma, budurwa yake bukata wadda bau kowa a zuciyarta sai shi kadai. Ya dauki lokaci mai tsaho a rayuwarsa yana sacrificing abubuwa da dama saboda ni, bana son yayi sacrificing rayuwar aurensa saboda ni" Hajiya umma ta zauna kusa da ita tace "shi saurayi ne tabbas, ke kuma gimbiya ce darajar ki ta dara ta duk wata budurwa da za'a bashi. Kuma ina ganin ai shi yafi kowa sanin cewa ke ba budurwa bace ba tunda shine yayi jinyar ki sanda kika haihu, shi yafi kowa sanin kin haihu, amma kuma ya furta yace ke yake so" Fatima ta dago kai tana kallon ta, sai Hajiya umma ta gyada kanta tace "munyi waya da Maryam dazu, ta gaya min dalilin tahowarki gida. Kin taho ne saboda Adam yace yanason aurenki. Shin kina da wani dalili na kin aurensa bayan fadin da kika yi cewa shi saurayi ne ke bazawara?" Fatima tayi shiru kanta yana kasa amma bata ce komai ba, shin tana da dalili? Hajiya umma tace "babu wanda zai matsa miki ki aure shi, ko ba shi ba ko wani ne, amma duk kan nin mu zamu so kiyi aure, ko baki auri Adam ba dole ki auri wani. In yaso shi kum Adam din sai ya samu wata yayi aurensa" Fatima ta bude ido da sauri tana fasalto maza da yawa a zuciyarta, da yan lukutaye da sirara da tsofaffi da masu mata biyu ko uku tana jin kamar zata amayo abincin da dama bai gama sauka a cikin ta ba. Sai yanzu take kara realising din issue din da yake gabanta, ko Adam ko wani. Shima kuma Adam ko ita ko wata. Zabi ya rage nata tunda dai shi ya fadi nasa zabin. Ta sake girgiza kanta da sauri, "uhm uhm. I can't" Hajiya umma tace "you can, and you will. Sai dai in baki bawa kanki dama ba, sai dai in baki bawa wanda zaki aura dama ba. Nawa akayi kuma? Mata nawa ne mazajensu suka mutu kuma suka same aure? Wata ma bata shekara take kara wani auren. Amma ke kinyi goma, goma is very much okay, dan ma biyar din farko ba'a gida kika yi su ba da babu yadda za'a yi a barki kiyi goman" Sai ta kara zuba mata wani abincin ta mika mata "ki ci kiyi wanka ki huta, zuwa anjima sai kije ki fuskanci Takawa, ki kuma shirya wa yadda zakuyi da shi". Fatima bata kara ko loma daya abincin ba, abinda take ta lissafawa a ranta shine; ko Adam ko wani, shima kuma Adam ko ita ko wata. Allah ya taimake ta Takawa bai nemi ganin ta ba sai dare, a tsahon lokacin ta gama lissafe lissafenta. Idan ta tata ne, idan ta son zuciyarta ne, zata zabi Adam a cikin ko maza dari ne aka jera mata. Dan tasan in ta barshi ba lallai ta samu mai nagartarsa ba. Bata taba ganin mutum mai gaskiya irin sa ba, bata taba shakuwa da wani, ko da kuwa a cikin siblings dinta bane irin yaddata shaku da Adam ba, babu wanda ya santa ciki da bai kamar yadda Adam ya sanya. Ta tuno rayuwara su a imo, babu irin abinda baiyi mata ba, har abinda mace ce ya kamata tayi mata amma Adam yayi mata kuma ita dai a cikin abubuwan da zata iya tunowa bata taba tuno ranar daya taba gwada taking advantage of her ba, ko da gwaji bai taba ba, wanda kuma hakan abu ne mau matukar girma a gurinta musamman a matsayin sa na balagaggen namiji mai jini a jika. Sannan ga kyau, Adam kyakykyawa ne, irin kyan da duk kushen mai kushe sai dai yayi shiru amma ba zai iya aibatawa ba. Ga gayu, a lokuta da dama gayunsa yana tuna mata da Hussain, they have almost the same taste na yadda suke dressing da kuma yadda suke tafiya da zamani. Matsayin iyayen sa, da kuma kabilar sa, basu taba damunta ba a zamanta da shi. Amma kuma in ta cire selfish interest din ta sai kuma taga cewa gwara ta zabi wani akan Adam, saboda tana ganin bai dace da ita ba. Tana ganin ba zata bashi kulawa da kuma soyayyar da yayi deserving a rayuwar aure ba. Sai take ganin kamar in taki zaben nasa shi ta taimakawa, sai dai amma wa zai aura kuma? Sai taji bata son sanin wadda zai aura din. Da dare tana falon Hajiya Fulani taji sallamar sa zai shigo, sai taji kamar zata tashi ta bar gurin, ta lura da yadda shima ganin ta ya saka yayi kamar zai koma da baya amma dai sai ya shigo din ya durkusa ya gaishe da Hajiya Fulani yayi godiyar irin saukar da akayi masa sannan yayi mata sallama. "Zan dan je Kaduna ne in kwana biyu" tace "kwana biyu na bahaushe ko kuma kwana biyu na lissafi" ya dan shafa kai "na bahaushen dai Hajiya, ban san dai kwana nawa zanyi ba gaskiya. Sai an ganni dai kawai, suna ta korafin bana zuwa ne" Hajiya tace "Allah sarki, ka kyauta sosai kuwa, gidan su yarinyar nan ne ko? Wama sunan ta" "Sumayya" ya fada "sunan ta Sumayya" ta gyada kai "haka ne. To Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya. Ka gaishe da su sosai. Allah yasa dai ba zaka yo laifi a gurin aikin ka ba, ga kuma makaranta kana fama ita ma" yace "na dau leave a office, school kuma dama thesis nake yi, babu wani problem insha Allah" tace "Allah ya yarda. Allah kuma ya kiyaye hanya" yace "ameen, Nagode sosai. A huta lafiya" Ya mike ya dauki hanya fita daga gurin without a single glance at side din da Fatima take zaune, duk kuwa da cewa zuciyarsa tana ta tunxura shi akan ya kalleta ko da sau daya ne, sai da ya kai tsakiyar falon sannan Fatima da tun da suke magana da Hajiya kanta yake kasa, amma tunda ya tashi kuma ta bi shi da ido, tana jin babu dadi yadda yayi ignoring dinta. Tace "adawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya" ya dakata sannan ya waigo yana kallon ta, sannan yace "ameen Nagode" then ya juya ya karasa fita. Fatima ta bishi da kallo kamar yadda Hajiya ita kuma take kallon ta. Bai jima da fita ba jakadiya ta shigo tana yiwa Fatima iso cewa mai martaba sarki yana nemanta yanzu. Ta tashi ta nemi babban mayafi ta dora akan doguwar rigar jikinta sannan ta tafi. A bakin kofa jakadiya ta sannan Fatima ta shiga ita kadai, yana zaune a an kujera Hajiya Ummah tana zaune a kasa saga gefenta, Fatimah tana ganin Hajiya Ummah sai gabanta ya fadi, tana ganin cewa bata rike mata alkawari ba. Ta durkusa ta gaishe shi cikin biyayya, shi kuma ya amsa mata cike da kauna da kulawa. Sannan ya tambaye ta "ya kika baro yaruwar taki da iyalinta?" Tace "suna nan lfy lau Allah . Sunce ayi musu gaisuwa sosai" yace "madallah. Allah yayi muku albarka baki daya" Hajiya Ummah tace "ameen". Sai Fatimah taji tana son tashi, duk da dai bata gama ganin mahaifin nata ba amma sai taji tana son tashi tun kafin yayi mata maganar da bata so, maganar kuma da take ji a jikinta cewa zaiyi mata. And it is rude ka tashi daga gaban manya ba tare da sun sallame ka ba. Sai yace "Adam yayi min sallama dazu wai zaije Kaduna ya kwana biyu a can, kunyi maganar da shi?" Ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da hannunta tace "eh munyi maganar ran sarki ya dade" yace "da safe zai tafi, na dauka ko zaki so zuwa ki gaishe da Hajiya Amina" ta girgiza kanta da sauri, "zan je, amma nafi son in dan kwana biyu a gurin ku in gama ganin ku tukunna" Yayi murmushin "mun ganki ai, munji dadin ganin ki kuma, mun fahimci lafiya ta same ki sosai yanzu alhamdulillah. Amma mu ba haka muke so ba, ba so muke muyi ta ganin ki haka ba kin taho daga gidan yayarki kin kwana biyu anan kin kuma komawa gidan yayarki. So muke mu ganki a gidan mijinki kema, idan har Allah ya bamu yawan rai ma muna so muga yayanki kamar yadda muke ganin na yanuwanki. Ba zamu matsa miki ba saboda munsan irin abubuwan da suka faru dake a baya, amma kuma ba zamu barki haka ba ba kuma zamu zabar miki miji ba, ke zaki zaba da kanki namu shine mu baki shawara mu kuma tabbatar da nagartar duk wanda kika zaba din" "Amma abinda zan tuna miki shine, mu lokacin mu ya tafi, mun gama zamanin mu mutuwa kawai muke jira" ta rufe baki cikin rudani "Takawa!" Yace "ai mun gode ubangiji, yayi mana komai alhamdulillah, rayuwa kuma ai mun mora, fatan mu dai kafin mu tafi mu tabbatar cewa dukkan ku mun barku cikin rayuwa mai kyau. Mun aurar da ku mazan ku da matan ku idan da rabo ma munga yayan ku. Ke da yaruwar ki Asma'u ne kadai kuke a gida, ita ma kuma an saka ranar ta wata biyu suka rage mata a gida, ke kuma yau shekara goma da Allah ya karbi ran mijinki dan haka muna umartarki ki fitar da wani mu sake aurar dake. Kije kiyi tunani kuma kiyi addu'a, sannan sai ki sanar damu zabinki mu kuma sai mu karasa sauke nauyin da Allah ya dora mana" Fatimah ta dago kai tana kallon Hajiya Ummah wadda ita ma ita take kallo sannan tace "tashi kije kiyi abinda aka umarce ki dashi. Allah yayi miki albarka yayi miki jagora" tace "ameen. Na gode. Allah ya ja min da ranku" sannan ta mike ta koma cikin gida tana harhada hanya, ta tuna da lokacin da aka kira ta aka vata irin wannan umarnin na cewa ta fitar da miji. A lokacin zuciyarta fara kal ta fito daga gaban mahaifinta tana zuwa daki kuma ta kira Hussain tayi masa albishir. A lokacin bata yi tunanin za'a kuma bata irin wannan umarnin. Lallai mutuwa mai yankan kauna, mutuwa mai tonon asiri. Bata tsaya ko'ina ba sai dakin ta, wanda yake part guda ne a gidan wanda mai martaba sarki da kansa ya saka aka shirya mata shi tun dawowarta gida, duk da dai ba sosai take amfani da gurin ba dan ba zaman kasar take yi ba, in tazo kuma tafi son zama tare da hajiyan ta ko kuma tare da Ummah. Amma yau sai ta tafi can, an riga an gyara mata shi da niyyar ko zata yi amfani da shi, dan haka ta wuce cikin bedroom ta kwanta akan gado rigingine tana kallon ceiling. Maganar data fi tsaya mata a rai a cikin maganganun Takawa shine na mutuwa da yace zaiyi, ya kuma gaya mata cewa burin sa a yanzu shine ya aurar da ita kuma yaga yayanta kafin mutuwa ta riske shi. Sannan a karshe ya bata umarnin ta fito da miji. Duk da bai gaya mata limit din lokacin daya bata din ba. "Oh Hussain, oh Mi Amour, what should I do?" Sai ta rufe fuskarta da hannunta ta fara kuka. Sai kuma taji tana son yin magana da Adam, shine kullum a kusa da ita in tana bukatar a shoulder to cry on. Bata jin a cikin shekaru goman nan akwai wata magana da aka taba fada mata ba tare da ta gaya masa ba, ballantana wannan maganar mai girma haka. Amma wannan dole zai zamanto na farko a tsakanin su. Washegari da wuri ya fita, kasancewar yana son fita da wuri ne ya saka tun jiya yayi sallama da kowa, sannan ba tare da ko breakfast yayi ba ya dauki hanyar Kaduna. Bai samu Baba a gida ba sai Inna da Zunnur, wadanda suka yi masa sauka ta musamman kamar yadda suka saba yi masa a duk sanda ya samu damar zuwa gidan. Sai kuma Inna Ade ta fara yi masa zancen da yasan dama dole zata yi masa "Adam har yanzu babu aure ko? Ko mangofak kake so ka zama?" Yayi dariya, "a'a fa Inna, lokaci ne dai kawai bai zo ba amma babu ruwan karatu" tace "to Allah ya nuna mana lokacin, ya kamata dai ayi kokari ayi, shi aure ai shine cikar mutum, duk shekarun mutum duk hankalin sa idan bashi da aure to tamkar rabin mutum yake" ta cigaba da nasiha akan aure, a inda ta tsaya anan Baba ya dora da yazo gidan bayan Zunnur ya kira shi ya gaya masa zuwan Adam. "Ni na dauka ma maganar aure ce ta kawo ka?" Yace "Baba zuwa nayi fa in gaishe ku in kuma ganku ku ganni" Baba yace "mungode munji dadin ganinka amma munfi so ace ba kai kadai kazo ba, ace tare kazo da matar ka da yayan ka sai kuyi mana sati a nan" Adam yayi murmushi yace "watarana Baba, insha Allah" Baba yace "Allah yasa. Amma dan Allah ka kara himma kaji? Ni bani da sauran yaya mata da na baka, da ace ina da yar budurwar ya a gaba na da tabbas bata da miji idan ba kai ba dan kuwa duk wata nagarta da ake nema a gurin miji ina ganin kana da su malam Adamu" Adam yace ya gode, yana kokarin chanja maganar dan baya son ta kunan zuciya take kara saka shi. Amma Baba bai bar maganar ba sai yace "amma ida ka amince, idan kuma babu wata a ranka a yanzu, ni zan samo maka mata a cikin yayan yan'uwa na" sai Adam yace ya amince din, na farko saboda ya faranta ran Baba, na biyu kuma dan abar maganar, amma shi yasan zai bi duk hanyar da zaibi dan ganin ya kubce daga wannan tarkon. Daga nan kuma sai suka kama hirar abinda ya shafe su, Baba ya bashi labarin halin da Ruqayyah take ciki a yanzu shi kuma yayi alƙawarin zuwa duba ta kafin ya bar garin, sai kuma suka yi hirar Hassan da irin daukakar da yake samu yanzu, Baba yana bawa Adam labarin yadda yake kula dashi sosai. "Ya dage sai na bar gadin nan, ni kuma bana son inzo gida inyi ta zama a daki kamar mace shi yasa na ke son aikin, amma dole yanzu na hakura dan in faranta masa, tare da Sulaiman, shima lallai so yake in daina" Adam yace "nima kuma na kara roko akan nasu, lokaci yayi da za'a huta Baba, tunda Allah ya raya zuria kuma yayi musu albarka ina ganin a zauna a gidan a huta shi yafi" Baba yace "kash, zaman gida ai kashe jiki yake" Adam yace "to me ake so ayi yanzu in an var wancan aikin da bama so?" Baba yace "makarantar islamiyya nake sha'awar budewa in ringa koyar da yara da kuma manya karatun Alqur'ani, wannan shine burinsa. Dai Adam yaji yana fatan Allah ya bashi iko ya cikawa Baba wannan burin nasa. Amma yanzu addu'a yake so ayi masa akan abinda yake damunsa. Yinin ranar gabaki daya haka yayi ta babu dadi, ya kasa tuna lokacin da ya shiga cikin kuncin zuciya irin na wannan lokacin. Bama ya son yaga wayarsa dan zuciyarsagaya masa takeyi ya dauka ya kira ta, yana son ganin ta , yana kuma son jin muryar ta amma yasan kiran a waya ba zai taba haifar masa da Da mai ido ba, shida ya tahoda niyyar ya rarrashi zuciyarsa ta manta da ita, tabbas in ya kira ta zai bata shirin sa. A Kano kuma a ranar tun safe Gimbiya Asma'u take tare da Gimbiya Fatima a sashen ta tana debe mata kewa tare da kokarin ganin ta saka ta nishadi, which ya zama a banza dan da kyar take samun amsa daga Fatima. Ta lura da yadda ta ke ta kallon wayarta from time to time kamar mai jiran wani abu. Amma abin bai zo ba. Sai Asma'u tace "ki kira shi mana, in bai kira ki ba ai ke sai ki kira shi. It doesn't matter waye ya kira wani first" Fatima ta bata rai "waye kike magana a akansa ne wai? Waye yace miki ina son wani ya kira ni ko ina jiran kiran wani?" Asma'u tace "Allah ya baki hakuri. Wai kawai naga kina ta kallon wayarki ne shine nayi tunanin haka" But a zuciyar Asma'u ta san abinda Fatima take missing, in normal circumstances yanzu dan zaman da sukayi din nan da Fatima ta kira Adam ko kuma shi ya kira ta, ko kuma da yanzu ta ambaci sunan Adam sai ba adadi. Anan ta fahimci menene matsalar Fatima, ba wai umarnin da aka bata bane yake damunta, rashin Adam ne yake damunta, but she is struggling to keep it aside, for a reason best known to her. Asma'u bata tabbatar da zargin ta ba sai da Adam ya kwana uku a Kaduna babu waya, at least not to Fatimah but ya kan kira Asma'u yace ya kira ne su gaisa, duk da ita a ranta ta san Fatima yake nema shima. Bata san me ya faru tsakanin su ba amma tasan suna yaudarar kansu ne kuma sun dauki hanyar da ba zata bulle dasu ba. Tayi kokarin communicating da Fatima amma taki bata fuska, tana ganin ita kanwarta ce ba zata yi magana irin wannan da ita ba. A lokacin da Adam yayi sati a Kaduna, a ranar ya kira Asma'u ya tambaye ta idan Fatima ta koma Dubai ko kuma tana Nigeria, sai ta gaya masa tana nan, ya tambaye ta idan ta san sanda zata koma, sai ta ce masa babu rana. Wannan yasa shi ya yanke shawarar zai koma can din, tunda aim dinsa shine yayi nesa da ita tunda ita ba zata koma ba shi zai koma. Bai san zata taho ba dama shi yasa ya taho. Sai Asma'u ta fadawa Fatima abinda Adam din yace mata. A ranar ne kuma Fatima ta gama yanke shawarar ta bayan gabatar da istikhara da tayi, bata son bata lokaci tunda tasan cewa ko da shekara zata bata babu abinda zai chanja a cikin zuciyarta. Dan haka taje ta samu Hajiya Ummah da amsar ta. "Umma a sanar da Takawa cewa ni bani da zabi na mijin da zan aura, bana jin kuma zan iya zaba din kamar yadda ya umarce ni. A gaya masa na bar masa zabi, a zaba min duk wanda yake ganin ya dace, ni kuma nayi alkawarin yi muku biyayya" Daga baya Takawa ya kirata ya nuna mata jin dadinsa tare da sa mata albarka da tabbatar mata da cewa ba zata yi dana sani ba, ta dawo daki ta kwanta, sai ta dauko wayar ta ta nemo number din Adam ta tura masa message. "Am sorry" an jima kadan yayo mata reply "am sorry too". Tana nan a kwance Asma'u ta shigo ta zauna tana kallon ta tace "yanzu naji ummah tana gayawa hajiya abinda kika ce a gaya wa Takawa" Fatima ta mike zaune tana jingina bayan ta da jikin gado tace "eh", Asma'u ta bata rai "kin san kuwa abinda kika yi? Ba dan kar inyi miki baki ba da sai ince Allah yasa ya aura miki daya daga cikin dagatan sa sai inga ta taurin kai" Fatima tace "ke, baki da kunya? In ma wa zai aurawa ni ina ruwanki? Uba na ne shi fa kuma ya san abinda ya dace dani, ya ma fini sanin abinda ya dace dani. Bani da zaɓi, to menene laifi na dan na bashi zaɓi?" Asma'u tace "kina da zaɓi mana, kina son Adam, no matter what you said babu wanda zai yarda cewa ba kya son sa, ke kadai ce baki sani ba, maybe kuma kin sani kawai kina dannewa ne saboda wani dalili da ki ka barwa kanki. Amma zan gaya miki cewa kin yi rashin miji dan bana jin zaki samu irinsa ko mai kuwa zaben da za'a yi miki, dan babu wanda ya sanki kamar shi, babu wanda zai dauki nauyin ki kamar shi, babu wanda zai saka ki farin ciki kamar shi. Babu......" Fatimah tana juya kanta tace "ba zaki gane ba Asma'u ba zaki gane ba" Asma'u ta rike hannunta tace "ba zan gane ba tabbas saboda ban saka irin takalmin da kike tafiya dashi a yanzu ba, amma na san cewa akwai matan da suka rasa mazajensu kamar irin yadda kika yi, wasu ma sun fi ku dadewa tare, wasu ma akwai ya'ya a tsakanin su da mazajen da suka rasa amma kuma they eventually moved on. Mutuwar miji ba yana nufin karshen rayuwar ki bane ba, va yana nufin kiyi ta denying kanki happiness duk da cewa kina zagaye da happiness din ba. Ba yana nufin cewa zuciyar ki ba zata kuma karbar wani a matsayin miji ba. Adam yana sonki duk mun sani kuma kema kina sonsa duk mun sani, me yasa ba zaki bawa junan ku dama ba? Fatima tace "Asma'u, bawai dan kaina naki zaben Adam ba, dan farin cikin sa ne, na gaya masa, na gaya wa Ummah, ban san me yasa duk kuka kasa fahimta ta ba" Asma'u tace "duk mun fahimce ki, amma hujjar bata gamshe mu ba, kin san abinda nake tunani? Kina so ne kiyi wa Hussain biyayya bayan rai, ki hana kanki farinciki saboda ke a ranki kina tunanin in kika yi auren soyayya zai zamanto kamar cin amana ga Hussain. Kin san kina son Adam shi yasa kike kokarin hana wa kanki shi. Kin san zaki samu farin ciki da Adam shi yasa kike gudun sa. Amma kinsan wani abu? Hussain da zai dawo zai yi farin ciki idan ya ganki cikin farin ciki ba zai kuma damu da wanda ya saka ki farin cikin ba. Bara kuma in tuna miki wani abu, yadda kika yi moaning mutuwar Hussain haka zakiyi moaning rabuwa da Adam, koma fiye da haka, saboda sho Hussain ba kya ganin sa shi kuma Adam zaki cigaba da ganin sa tunda yanzu kamar dan gida yake a gidan nan". Fatima tayi shiru a ranta ta san gaskiya Asma'u ta fada mata, tana kuma tunanin halin da already take ciki na rashin Adam a cikin kwanakin nan, menene zai faru da ita nan gaba? Sai kuma ta sake neman wani excuse din "Asma'u, Adam yayi min karami" Asma'u cikin tsokana tace "Adam din? Are we talking about the same Adam? Ni wanda na sani giant ne" Fatimah ta kwace hannunta tana kai mata duka tace "ba wannan nake nufi ba" Asma'u tayi dariya, tana jin dadin yadda taga kamar Fatima ta fara saukowa tace "to me kike nufi?" Tace "tsakanin mu babu tazara sosai ta shekaru, ni farko ma na dauka na girme shi sai daga baya na fahimci cewa wata takwas ne kawai ya bani, kuma......." Asma'u tace "kin manta Sani na gidan wambai da akayi bikinsa kwanaki? Wata biyu ya bawa matarsa, and they are so in love with each other. Age is just a number my sister. Age baya determining halayya ko maturity. Ita halayyar mutum da ita ake haifarsa sai dai abubuwan da mutum yayi facing a rayuwa su zasu kara ko su rage yanayin halayyar sa, maturity kuma yana da dangantaka da ilimin mutum da kuma exposure dinsa, ilimi ina nufin na cikin kai ba wai na takarda ba. Ni kuma banga wanda Adam ya rasa ba a cikin wadannan. Ko kuma maybe dan yana Igbo ne?" Fatimah tayi mata dakuwa, sai kuma suka yi dariya tare, ita mantawa ma take yi da tribe din Adam dan bama ya yin yaren nasa in dai ba haduwa yayi da wani Igbo din ba yana kuma son ya nuna masa shi Igbo ne ba. Ko da yan gidansu va sosai suke yi ba sunfi yin English, ko suyi hausa. Asma'u ta mike "inje in fada ince kin chanja shawara?" Fatima ta zaro ido "nooo, kar ma ki gwada. Na gama magana ai. Ba kuma zan chanja magana ba not to Takawa. Bakin alkalami ya riga ya bushe" sai ta koma ta kwanta Babu wanda a gidan yaji dadin hukuncin Fatima amma kuma babu wanda zai iya tunkarar Takawa da magana biyu, ta riga ta bashi amsa, zabi kuma yana gare shi a yanzu. Adam ya gama zamansa na sati guda a gida a cikin daki a kwance, ko duba Ruqayyah da kuma gaida Hassan da yace zaije yayi baiyi ba daga kwanciya sai tashi. Har sai da Baba yace ko za'a kai shi asibiti ne da ya fahimci bashi da lafiya kawai boyewa yake yi. Amma sai yaki, ya nuna cewa shi tafiya ma zaiyi, zai koma Dubai ne saboda ana bukatar sa a inda yake aiki. Har ya shirya da nufin washegari zai taho kano yayi sallama kuma ya wuce Dubai, sai Baba yace ya dakata zasu taho tare, yana so yazo yayi gaisuwa a gurin mai martaba, dama bai taba zuwa ba. A dole ya jira shi ba dan yaso ba sai da ya kara kwana biyu sannan suka shirya suka taho tare da Baba da Sulaiman da Zunnur. Sanda suka zo ana zaman fada ne, kuma fadar ta cika sosai, suka shiga sukayi gaisuwa, sai Adam ya fahimci kamar dama jiransu akeyi. Sai kawai ya ji an fara gabatar da daurin aure, a cikin sigar yaji an ambaci sunansa, baba ne kuma waliyyin sa, sai kuma yaji an ambaci sunan Fatima a matsayin matarsa, sai kuma ya ga Baba ya dauko kudi dubu hamsin ya mika a matsayin sadaki, aka karba aka kuma shafa fatiha. Bayan an gama ne mai martaba sarki ya fara jawabi "ya ta Fatima ta bani damar in zaba mata miji, ni kuma na zaba mata wanda nake ganin yafi kowa cancanta daya aure ta. Wannan hukunci na ne da na yanke ina kuma fatan wannan aure zai zamanto kamar mabudin cigaba da ire iren wadannan aurarrakin a tsakanin al'ummar mu. Ina fatan al'umma zasu yi kwaikwayo da abinda nayi su jawo mutane irin Adam jikin su su kuma aura musu ƴaƴan su idan bukatar hakan ta zo. Wannan wani abu ne da zai kawo mana cigaba sosai a cikin addinin mu da kuma zaman lafiyar kasar mu. Ina fatan wannan zai kara wa kwarin gwiwa ga duk wadanda ba musulmi ba wadanda suke da niyyar shiga musulunci, ina kuma fatan sauran kabilun da ba hausawa ba wannan auren zai saka su fahimci cewa dan muna yin magana da mabanbanta harshe ba yana nufin muna da banbanci ba. Dukkan nin mu mutane ne, dukkanin mu kuma yan Nigeria ne, dukkanin mu daya ne" *The New Couple* Adam yana jin dukkan abinda ake cewa amma zuciyarsa tana ta gaya masa cewa ba shi Adam din ake nufi ba, wani ne daban. Wani Adam din ne mai irin labarin sa aja daura masa aure da Fatima, amma ne ya shigar da Baba cikin maganar? Ta yaya akayi Baba ya tsaya a matsayin waliy har da bada sadaki? Sai kuma yaga mutane suna ta miko masa hannu suna yi masa Allah ya sanya alkhairi, wasu su dan buga kafadar sa cikin alamun taya murna fuskarsu. Baba ma sai murna yake shi ma kuma ana taya shi murnar, haka su Sulaiman ma. Wannan yasa ya fara tunanin to ko shi Adam din ake nufi ne? Amma kuma sai yaji tunanin hakan bai saka ya as excited as he thought he would be a duk ranar da Fatima ta zama ta sa ba. Tunanin sa daya shine, Fatima bata son shi, ta gaya masa da kanta tace ba zata iya aurensa ba, kuma yanxu dakunnen sa yaji Mai martaba sarki yana fada cewa shi ta bawa zabi, shine ya zabi Adam din ba wai ita bace ba, as far as he knows ma maybe bata ma san da zancen daurin auren ba kamar yadda shima bau san da shi ba. Wannan ya saka ya janye jikinsa daga cikin mutane, yanalura da yadda ake ta buga tambura da busar kakaki da sarewa, kowa cikin murna amma banda ango. Dakin da yake a matsayin nasa ya tafi ya shiga ya rufe kofa, daga nan ma yana cigaba da jin kide kiden da yake tashi a cikin gidan, daga cikin gida kuma ya ji an rangada guda, ya san ko bata sani ba ma yanzu ta sani and she will hate him, zata ga kamar shiya matsa aka aura mata shi duk da ta gaya masa bata son sa. Shi kuma gwara ya haura da aurenta akan ya aure ta bada son ranta ba, dan farin cikin ta shine burinsa, ko da kuwa nata farin cikin yana nufin rushewar nasa ne. Ya dauko wayarsa yana jujjuya wa yana lissafin ko ya kira ta ya gaya mata bashi ya nemi aurenta ba? If she knows him as well as he thought then tasan baya karya, musamman akan abu mai muhimmanci irin wannan. Ya danna kira layin wayarta for the first time in ten days, ya saka a kunne yana zagaya dakin yana jin yadda wayar take kara amma ba'a daga ba, ya sake kira haka har sai da yayi kira sau biyar. A lokacin ne kuma aka zo ana knocking kofar da ya rufe. Ya bude suka hada ido da Abubakar da yake ta washe masa baki, ga kuma Sulaiman a bayan sa. Sai kuma wani dogari dauke da karamar jaka a hannunsa, Abubakar yace "ango kasha kamshi. Menene kuma na zuwa da rufe kofa haka? Common ka fito mu je za'a yi reception tare da bakin Takawa. Gaskiya muna binka bashi duk bamu san da maganar ba bamu shirya komai ba" Adam bai ce komai ba sai ya matsa ya basu guri suka shigo, dogarin ya ajiye jakar hannun sa ya mika gaisuwa ta musamman ga Adam sannan ya fita. Sulaiman yana kare wa palon kallo yace "wow" sai ya zauna akan kujera yace "amma fa mu mun sani" Adam ya juyo yana kallon sa yace "What?" Sai yayi dariya "wallahi kuwa. Daga nan aka kira Baba shekaran jiya aka gaya masa yau za'a yi, shi yasa ya hana ka tahowa yace sai yau, shi ya nema yace zaiyi maka walicci, mu kuma ya kira mu muka taho tare" Adam ya dafe kansa "amma baku gaya min ba? Alkawari yace haka ne?" Abubakar yayi dariya "ai gwara da ba'a gaya maka din ba da tuni ka bata wa mutane show, itama amaryar taka bata sani ba sai da aka daura, tana can tana halin nata, sai ka shirya shirin yin rarrashi" Adam yace "ya Salam" Abubakar yace "yanzu tashi ga kaya na taho maka dasu ka dauka ka saka ka fito a angon ka sak, mu kuma sai mu bude bakin aljihu muyi ta yi maka liki" Sulaiman yace "ni ko kamun ango ba'a yi ba, wai shin ma menene al'adun ku na aure a Igbo land!" Adam ya mike yana cewa "ba'a sani ba, nima ba sani ba, sai dai ku kama wani ba ni ba. Now park all your wahalas and all your likis and go, am not in the mood" Abubakar yace "to va sako na bane ba ai, nima bani kayan akayi akace in kawo maka ka saka kuma ka fita gurin mutane, in kuma ka ki in je in gaya wa mai aiken cewa kace ba zakayi ba you are not in the mood" Sulaiman yayi dariya, Adam ya bata rai sannan ya dauki jakar kayan da yaron ya shigo da ita bai kara ce musu komai ba ya shiga cikin bedroom. Bayan shigar sa Umar ya shigo shima tare da wasu cousins dinsu da kuma Zunnur, nan suka baje suna ta hira, Sanda ya fito gaba ki daya sai da suka tashi, complete set na jabba ne a jikinsa milk colour wanda ya dace sosai da hasken fatarsa kuma ya shiga da hular daya dora a kansa, agogon hannunsa da ya shiga da takalmin kafarsa wanda yake irin na sarauta (shambatse), fuskarsa kuma dauke da murmushi, sai dai zuciyarsa tana rawa dangane da wannan babban abinda ya same shi. Suna fita guri ya kara rudewa da shagali, a cikin taron Hassan ya iso yana ta bada hakurin cewa yayi missing daurin auren "Baba ya gaya min ai tun jiya, da tare zamu taho kuma wani abu ya taso min da dole nace kuyo gaba, Allah ya sanya alkhairi Adam. Ina taya ka murna sosai" Adam da yaji nauyinsa duk ya kama shi yace "au kai ma ka sani kenan?" Hassan yayi dariya, "naso in fasa kwan ai, Baba ne ya hanani yana ganin cewa tun da aka boye maka anan din to akwai dalilin yin hakan. Tabbas nasan mai martaba ya zabe ka ne ya kuma baka auren Fatima saboda abinda ya hango a tare da kai. You really are a lucky man Adam. Am sure Fatimah will make you happy. She will be the best thing that happen to you" Adam ya gyada kai "yes, am really lucky haka ne, but Fatima is not the best thing that happened to me, the best thing is Islam. It will always come first" Hassan ya gyada kai yana murmushi, tunda ya taho a hanya yake lissafin lamarin Adam da irin sa'ar da yake da ita a rayuwa, sai yanzu ya kuma fahimtar source of luck dinsa. Adam a ransa yai dadin daya kasance Hassan ya fahimci sarki ne ya hada aurensa da Fatima ba shi ya nema ba, duk da dai hakan is not completely true, amma tunda Hassan bai sani ba ai there is no need to tell him ko? A hankali tashin hankalin da yake zuciyar Adam ya fara rauzayewa yana komawa murna, it is going to be tough but he will eventually get that space da yake nema a zuciyar Fatima. A cikin gida ma shagalin ake tayi kamar yadda ake yi a waje, masu kidan kwarya nayi nasu kidan shantu nayi, masu sauran wasanni suna yi suma. Kasancewar daurin auren ba'a shirya masa ba ya saka sai yanxu yan'uwa suke shigowa gidan, kowa kuma yana fadar albarkacin bakinsa akan auren da kuma angon. Kamar yadda Hajiya Fulani da Hajiya Ummah suka riga suka sani, wadan su daga cikin yan'uwa musamman mata suna nuna kamar auren bai dace ba, "yar sarauta mai daraja kamar Fatima za'a dauka a bawa tubabben inyamuri?" Amsar da suke bayarwa mostly itace "shi wanda ya bayar da ita din ai yafi kowa sonta, mu menene namu a ciki" da wata kanwar takawa ta dage sai Hajiya Ummah tace "to ko ayi miki iso ne a gurinsa sai kiyi masa bayanin rashin dacewar abinda yayi?" Kamar yadda abin yazo wa Adam a shekara shock haka ma yazo wa Fatima ita ma. Bata san dalili da kuma amma bayan labarin yayi sinking a zuciyarta sai taji kamar an dauke mata wani nauyi daga kafadunta. Tayi addu'a ta nemi zabin Allah sannan ta bawa mahaifinta zabi dan haka tasan Allah shi yayi guiding Takawa gurin zaba mata Adam, dan haka tana saka ran cewa shine mafi alkhairi a gurin ta insha Allah. It is going to be tough at first tabbas, amma tasan insha Allah with time babu abinda baya chanjawa. Ko menene kake ji a zuciyarka, give it time it will go away eventually. Tasan kallon da da yawa a family suke yi kuma zasu yi wa auren nata, amma bata damu ba saboda immediate family dinta suna tare da ita dan sun san ko waye Adam kuma sun san ya cancanta ya aure ta. Ta ga duk Calls din Adam har guda biyar amma taki dauka dan bata shirya yin magana dashi yanzu ba, bata san me zata ce masa yanzu ba. Sisters dinta sunzo kuma sunyi iyakacin kokarin su gurin cheering dinta up, sun debe mata kewa sosai kuma sun gaya mata maganganu masu dadi sosai dasuka kara kwantar mata da hankali suka kuma tsayar mata da hankalin ta akan abinda ya tunkaro ta. Tana ta aikin gofe hawaye Asma'u tana kallon ta tace "da ace ba Adam din bane bana jin akwai wanda zai dauki wannan arhar hawayen naki" Fatima ta harare ta amma hawayen basu daina zuba ba. Wannan shine abinda ya rage na daga trauma din mutuwar Hussain, komai kankantar abu sai tayi kuka, tasan kuma kukan mutuwar Hussain ne take tayi har yanzu kuma she will continue har sai ta bar duniya. Sai dare ya turo mata text bayan ya sake kira bata dauka ba. "Am sorry. Nima ban san za'a yi ba. Bani na zaba ba" sai ta mishi reply "I know. Allah ne ya zabe ka" A daren ranar bayan kowa ya watse sai Adam ya kira Maman sa ya gaya mata abinda ya faru, and she cried, bata taba sanin cewa alkhairin da yake bin dan nata ba kenan bayan su yanzu suna cikin matsaloli ta ko'ina. Mijinta yana cikin rigima yana hannun police, Samuel babu ruwansa dan ita rabon data ganshi ta manta, Martha tayi ciki saurayin ya gudu ya barta kuma cikin yaki fita, Gloria ce kadai mai dama dama, ita ce kuma take kara jan ra'ayin ta akan su dawo Kano su zauna, su kuma nemi Adam yayi guiding dinsu zuwa hanyar da yake ganin zata bulle dasu, irin hanyar da shi ya bi kuma har yakai ga ci. "Princess" ta fada, "they let you marry a princess Adam?" Yace "yes Mom" yana realising cewa yaune rana ta farko data kira shi da sunan Adam. Babu wani biki da Fatima tayi a nata bangaren, Adam ma bai shirya komai ba dan yaga alamar bata so, shi kuma yanzu lallabawa yake yi dan har yanzu taki yarda suyi magana ko a waya ne ballantana su ga juna, har yau taki yi masa magana. Shi kuma sai ya mayar da hankalinsa ka family dinsa da suka tattaro suka dawo Kano suka bar Samuel a can, Daddy kuma basu ma san inda yake ba ya kuma cika wandon sa da iska. Abinda ya fara yi shine tabbatar wa da sun karbi shahada kamar yadda suka nuna masa suna so, bayan sun karba kuma ya tabbatar ya ajiye musu duk abinda yasan zadu bukata na amfanin gida anan gidan su na Kano ya kuma samar musu malamar da zata ke koya musu addini sai ya koma Dubai dan ya cigaba da shirye-shiryen sa a can. Gidan da yake zaune a ciki Takawa yace yabar masa saboda yace a matsayin sa na dan sa hakkin sa ne ya bashi muhalli. Shi kuma Adam sai yayi gyare-gyaren da yake ganin gidan yana bukata, acan aka yiwa Fatima jerenta ta hannun Aunty Maryam, Aunty Maryam din ce kuma ta taimakawa Adam gurin hada lefen Fatima wanda ya cinye kusan duk ajjiyar sa, Aunty Maryam din kuma ya roka ta taho Nigeria ta kawo, sai kuma ya kira mamansa itama taje tare da sisters dinsa akayi dasu. Sannan aka saka ranar tariyar. Tariyar ma Fatima cewa tayi ba zata yi taro ba, kai amaryar ma tace babu wanda zai raka ta ita da kanta zata tafi, duk suyi zamansu duk wanda ya samu lokaci ya je daga baya yaga dakin ta, amma sai a gida aka ga rashin dacewar hakan, aka hada kan yanuwanta da surukan gidan suka tafi can gidan Aunty Maryam suka shiryawa Fatimah walima sannan da dare suka kaita gidan mijinta. Sai a ranar Adam ya samu ganin matarsa, ya kuma samu damar yi mata magana. "Abinda na roka ranar nan shi zan kara roka ya ma. Just a space a zuciyar Zahra, ko bazai ishe ni zama ba zanyi hakuri in tsugunna ko dana tsahon shekaru nawa ne" ta dago kai tana kallonsa, this is the first time data ganshi tunda aka daura auren sai a hotunan da aka nuna mata na daurin aure, tace "ka tabbatar ba zaka fadi ba? Shekara da shekaru a tsugunne?" Ya gyara zama tare da zabga tagumi yana kallonta yace "to ya zanyi? Abinda na samu ba da shi zanyi amfani ba? Amma in za'a taimaka min sai a dan kara min space dan in samu in zauna" Tace "ya danganta da irin yanayin yadda ka kula da space din da aka baka daga farko, in ka kula dashi sai a kara maka wani" yayi murmushi "Nagode sosai" tace "bar saurin godiya. Akwai sharadi" ya bude ido "sharadi kuma?wanne irin sharadi?" Tace "sharadin shine zaka kara aure nan gaba" sai abin ma ya bashi dariya, yayi dariya ita kuma ta bata rai "dariya na baka ma?" Yace "shine sharadin naki? To na amince" ta bude ido "ka amince fa kace?" Yace "yes, abinda duk kike so shi za'a yi. Na amince. Amma a bisa nawa sharadin" tace "na me fa?" Yace "idan har nayi failing gurin chanja ra'ayin ki akan wannan maganar to zanyi abinda kika ce din" tace "I will never change my mind" yace "really" sai ya gyara zama yace "kin san me? I assure you, ki bani shekara daya, ke da kanki zaki ce "Darling dan Allah kar ka yi min kishiya" tayi dariya, rabon da tayi dariya tun ranar Birthday din little Hussain, tace "I will never say that" yace "kar ki cika baki, dan zaki sha mamaki. Kin amince da sharadi na?" Ta gyada kai tana kallonsa fuskar ta still da murmushi. Shima yana murmushin, yana jin dadin ganin murmushin ta at last, yana kuma lura da yadda ta kara yin kyau sosai daga dukkan alamu ta sha gyaran amare yace "I really did miss you Zahra" bata amsa masa ba sai ta mika masa hannun ta tace "where is my ring?" Ya bude ido sai kuma ya mike da sauri ya fita wajen mota neman zoben da ya ajiye, ya dauko shi ya dawo da sauri ya durkusa a gabanta, ya kama hannunta ya saka mata yana lura da yadda yayi mata kyau kamar yadda yayi hasashen zaiyi. A hankali ya dago hannun ya kai bakinsa yayi kissing. Tayi saurin karbe hannunta tana wayencewa da kallon zoben tace "yayi kyau sosai" sai ya dawo kusa da ita ya zauna yana bata details labarin yadda akayi zoben. Shekara guda bayan nan ta haifa masa yarsu ta farko Islam, bayan shekaru uku akayi Iman, Sai Huda, sannan auta Muhammad. Sai kuma little Hussain da yake tamkar shine babban dansu. And their life continue. A Dubai suka yi basing rayuwarsu, saboda Adam ya samu aiki mai kyau a can kuma yana samun budi sosai da sosai. Ya kuma gina musu katon gidan su anan Kano inda suke sauka idan sunzo Nigeria. Fatima kuma bata aiki amma a yanzu ita take owning half share na kamfanin H and H wanda zuwa lokacin ya baza branches dinsa har garin Kano, Umar kusan ya rasa duk shares dinsa saboda baya investing, yanzu Fatima da Ruqayyah ne owners din su biyu. Former matar Hassan da former matar Hussain. That's the irony of life. Shekaru biyar bayan auren Adam da Fatima lokacin an haifi Islam da Iman Allah yayi wa maimartaba sarki rasuwa, Umar ne ya gaji sarautar sa......... Bara mu bar Fatimah da Adam anan su huta. Tomorrow zamu koma bangaren su Ruqayyah suma muyi concluding sannan mu koma ga Amir. Sorry for the late posts. It has not been easy lately. *Re-married 2* Ranar da aka daura auren Fatima da Adam, bayan an gama reception da sauran hidimomin da akayi a waje gurin maxa sai Baba da ƴaƴan sa, with Hassan a matsayin babban Da, suka je suka sake yiwa Adam godiya gurin mai martaba sarki sannan suka yi sallama suka tafi. Dama a motar Adam suka taho, yanzu kuma ba tare da Adam zasu koma ba, niyyar Adam shine in sun gama ai samu driver ya mayar dasu Kaduna amma yanzu tunda ga Hassan sai suka koma tare. Haka suka tafi a hanya suna ta hirar abin, da kuma hirar rayuwa in general, sannan suna godewa Allah da abubuwa suke kasance suna tafiyar musu cikin sauki. Baba kuma yana ta cigaba da yi musu nasiha akan lamarin rayuwa. Sai da Hassan ya ajiye su gida sannan ya tafi nashi gidan. Ya san Noorien sa tana can tana jiran dawowar sa tare da daddadan abincin ta. Yayi murmushi, tabbas sunan da yake kiranta dashi yayi tsananin dacewa da ita, she really is the light of his life dan tun auren ta dashi bau abinda yake samu sai alkhairai ta ko'ina, kullum zuciyarsa cikin haske take har mantawa yake yi da cewa da ya kasance cikin tashe tashen hankula da jarabawowi. His family is now settled, sisters dinsa kowa tana gidan mijinta lafiya lau ga yayansa guda bakwai chif da Allah ya bashi shida maza daya mace, to menene kuma sauran abinda yake bukata? Abu daya yake fata, bai sani ba kuma ko zai tabbata ko kuma bashi da rabo amma zuciyarsa kullum tana yi masa wannan kwadayin, ko Allah zai saka maybe wata rana idinsa ya gane masa dan ko yar Hussain. Duk da kaso tamanin cikin dari na hope dinsa yana gaya masa cewa abinda aka haifa din baya duniya, amma kaso ashirin dinnan yana kuma tuna masa da cewa anything is possible. Kamar yadda kullum Sumayya take gaya masa, "ni ban yadda Ruqayyah zata kashe yaron nan ba, ko da ba'a cikin hayyacin ta take ba ban yadda zata iya kisa ba" a lokuta da dama yakan share ta yayi kamar baiji me take cewa ba. Baya son musu da ita akan Ruqayyah saboda baya son bata mata rai amma shi a nasa ganin gani yake yi babu abinda Ruqayyah ba zata iya aikata wa ba in da akan kudi ne.. Sanda yaje gida kuwa kamar yadda yayi tsammani haka ya same ta a falo ta chanchada ado kamar amaryar da aka kawo yau, da two years old Amatullah a gefenta ita ma anyi mata kwalliya har da sabon kitso. Yana shiga uwa da yar suka fara rige rigen zuwa rungume shi, sai ya fara tarar uwar yana manna mata kiss a lips dinta, Amatullah ta saka kuka tana bubbuga kafa a kasa, suka yi dariya duk su biyun sai ya durkusa ya dauke ta ya daga ta sama yana yi mata chakulkulin daya saka ta dariya. Yace "duk wannan ƙwalliyar Amaty tawa ce" tace "eh, mommy yi min kyau" ya shafa kitson ta yace "kai amma Allah yayi wa mommy albarka, wannan kitson yayi kyau sosai" Sumayya ta fara shagwaba "nima fa nayi kitson ko baka gani bane ba?" Ta fada tana fari da idonta, ya ajiye Amatullah ya kunche daurin dankwalin yana kallon kananan kitson da aka jera mata, yace "matar nan shagwaba ni kike yi da yawa, daga zuwa kano daurin aure shine akayi min wannan taryen?" Tace "kano ai tana da girma, nasan yammata nawa ka gani a a can? Ko kaga wata ta fito da kitson ta ya burge ka? Kasan sai anayi ana updating fa kar ina zaune inji na zama outdated" Yayi dariya sosai yace "idanun Hassan a guri daya suke a tsaye ko rawa basa yi, saboda Sumayyan sa kuma hasken zuciyarsa kullum kara zama amarya take yi" tace "wacce amarya kuma ka jika da zolaya. Haihuwa hudu wasa ce" ya jawo ta jikin sa yana dora hannun sa a marar ta yace "saura ta biya" ta zaro ido shi kuma ya kashe mata nasa idon yace "please" yana hade hannayensa guri daya, ta rike hannun "da wahala fa Habibi,hudun ma ai nayi kokari" yace "kinga Amaty bata da yaruwa, ya kamata a sama mata sister" tace "in kuma na sake haihuwar namiji kuma fa? Sai in sake wani cikin again?" A lankwasa kai kamar abin tausayi sai ta ja hannun sa tana jansa ciki, ya kalli yadda bayanta yake motsawa in tana tafiya yace "I will convince you one way or another". Sai da ya fara cin abinci yace "tun a hanya nake addu'ar Allah yada yaran nan badi daeo daga school ba, in dan samu in mori matata kafin su zo su kwace min" tayi murmushin da yake kara mata kyau a idon sa, tace "kasan islamiyyar su sai sunyi sallar magrib sannan ake sallamar su" yace "good, da suna nan da yanzu hidima tayi miki yawa" tace "lah! Yaran nan fa basu da fitina fa, ina jin ana fadar fitinar boys amma ni nawa kam alhamdulillah suna da nutsuwa tunda basu taba burning down gidan nan ba" ta karasa sarcastically, yace "gado suka yi ai, babar su ce mai nutsuwar shi yasa ta koya musu duma suke yi" tace "da kuma babansu mai kula ba? Ai hannu daya baya daukar jinka, tare muke shukawa......." Yace "tare kuma zamu girbe insha Allah" suka yi dariya tare. Sai daya gama cin abincin sannan ya fara bata labarin daurin auren da abubuwan da suka faru, sai yaga tayi tagumi tana kallon sa tana ta zabga murmushi, yace "what's funny?" Tace "life. Gaba ki daya rayuwar ce lamarin ta ya saka ni nishadi. Fifteen years ago babu daya daga cikin mu da yake saka ran sai samu kansa a inda yake a yanzu. I remember sanda kake zuwa zance gurin Ruqayyah and the way da kake nuna mata soyayya ko? Mhen! And I was so in love with Adam then. Ka tuna sanda kake kiransa a waya ka bani muyi hira ta wayarka?" Yayi dariya, tace "I never thought cewa one day kaine zaka zamo jini da tsokar jikina ba" yace "and I never thought Adam zai zama mijin gimbiyar Hussain ba" tayi dariya, "duk wanda aka fadawa a cikin mu a lokacin zai ce wannan tatsuniya ce marar ma'ana" yace "tabbas. Dukkan mu a lokacin muna da plans for our lives, but Allah ya riga yayi mana nasa plan din kuma in muka duba yanxu in muka waiga baya sai muga abubuwan da muka samu sunfi wadanda muka rasa. Saboda shi ubangiji shine ya fi mu sanin menene dai dai damu" ta gyada kai. Yes. Kowa a cikin su abinda ya samu yafi abinda yayi tunanin samu. In dai har kabar wa Allah zabi kabi komai a sannu, tabbas va zaka taba kokawa ba, in kuwa ka nuna iyawarka ce iyawa to kuwa zaka yi kuka da idonka, zaka yi nadama mai tsanani. Hassan is a living example of that. Yace "and Hussain. Hussain lived his life to the fullest. Ban taba ganin carefree mutum irinsa ba yayi tapping duk wami goodness na duniyar nan kuma ba tare da ya tsallake limit na ubangiji ba, hakan yana nufin mutum zai iya samun both duniya da lahira masu kyau kenan, hakan yana nufin kudi if used a kan hanyar dai dai zasu iya samar maka duniya su kuma samar maka lahira. Kudi yana iya jawo maka mutane, yes, but depending on abinda kayi da kudin har ya jawo maka mutanen shi zai yi determining wadanne irin mutane ne zaka jawo din. Ko wanne second a raruwar mutun is an opportunity for him, Hussain has been saying this to my ears amma ban taba dauka ba, but I think it is about time da zan dan dauki page daya daga pages din rayuwarsa". Ta tsaya tana kallon sa cikin rashin fahimta sai yayi murmushi yace "am planning a trip for us idan yara sunyi hutu, any country of your choices, kowa ya zabi daya" Sumayya sai murna, ta kama hannun Amatullah suna rawa duk da ita Amatullah bata san murnar me ake yi ba, sai ya mike yana kallon su yana jin dadi a ransa yace "amma in muka je da kanwar Amaty zaki dawo a cikin ki". ******************************** Ruqayyah tana private psychiatric hospital inda ake kula da lafiyar kwakwalwar ta. Sumayya, Sulaiman su suke ta hidima da aljihun su akanta, musamman ma Sumayya tunda shi Sulaiman yanzu yana da iyali, Inna Ade kuma da Zunnur su suke yi da jikin su kullum suna zirga zirga, Baba bai hana su ba kuma shima yana dan lekawa ya ganta ya kuma yi mata addu'a, amma a zuciyarsa har yanzu yana kan bakan sa na babu ruwansa da Ruqayyah har sai ta bi abinda ya ce tayi. Lukman ma yana zuwa ya dubata, duk da bai taba cire ko kwandala a cikin kudinta yace a siya mata magani ba su kuma basu taba cewa ya bayar ba. Zuwa duba tan ma yana yi ne da yake samun updates akan yanayin jikin nata. Da yake matsalar Ruqayyah tana da dangantaka da maganin da Lukman ya saka ake bata a wancan asibitin da take na farko, wannan ya sa yanzu da aka daina bata irin su kuma aka koma treating matsalar da akayi diagnosing dinta dashi, sai gashi cikin watanni ta fara dawowa hayyacin ta har tana gane yan uwanta in sunzo dubata. Ta kan gane Sumayya har tayi mata murmushi, tana gane Inna kuma musamman in taga tana kuka sai tayi mata alamar tayi shiru da hannunta. Wannan ta sa suka cigaba da kokari da kuma kara wa doctors din courage na cewa they can get there. Sanda su Sumayya zasuyi tafiya da yara ma Sumayya tazo tayi mata sallama tana ta yi mata hira tana bata labarin irin kasashen da yaran suka zaba da rigimar da suka yi tayi a tsakanin su akan hakan. Sai dai Ruqayyah ba komai takw fahimta a labarin ba amma ganin Sumayya tanata zabga murmushi ya saka Ruqayyah ira ma tayi tayin irinsa. Da suka je suka dawo ma sai da Sumayya tazo ta nuna wa Ruqayyah irin hotunan da sukayi ta dauka a kasashen da suka je. Ga mamakin Sumayya sai taga kamar Ruqayyah ta gane twins dinta, ta dago tana kallonta sai taji tace "ina Hussain?" Wannan shine Magana ta farko da Ruqayyah tayi a kusan tsahon shekara daya. Farin ciki a gurin Sumayya har baya iya misaltuwa, taje ta samu doctors da bayani cewa an kuma samun wani cigaban. Wannan ya tabbatar musu da cewa rashin samun kulawa a wancan asibitin shine ya saka Ruqayyah bata warke ba sai ma kara rikicewa da tayi. Sai kuma Sumayya ta fara bibiyar Hassan akan dan Allah ya bar yaran su zo Ruqayyah ta gansu. "Duk da shekarun da suka wuce, duk da girman da suka yi amma ta gane su kuma har ta lura cewa babu Hussain a tare da su" amsar daya bata kawai ita ce "no" daganan bai kara ko kalma daya ba. Dole ta hakura ta bar maganar dan tasan ba zai kara wata kalma akai ba, in kuma ta cigaba da matsawa to itama zai iya ya hana ta zuwa ganin Ruqayyah. Sosai Ruqayyah take samun lafiya, cikin shekara daya ta gama gane kowa ta kuma tuna da duk labarin rayuwar ta wanda da aka saka drugs sukayi blanketing, sai kuma ta lura da yadda family dinta suke ta zarya akanta da suna kuma iyakacin kokarin su da aljihun su dan ganin ta samu lafiya da kuma kyakykyawar kulawa. And it touched her stoned cold heart, tana ganin duk abinda tayi musu, duk irin bujirewar da tayi musu da zaben kudi da tayi a maimakon su amma gashi su basu guje ta ba sun kula da ita a lokacin da take buƙatar kulawar. Kudin nata kuma bai yi mata amfanin komai ba dan tana sane da cewa babu ko kwandalar ta a cikin nemar mata magani. Sai dai abinda ya bata mamaki ya saka kanta a duhu shine yadda ta kasa yiwa Lukman magana akan hakan, ta kasa yi masa magana akan komai, dan ko breakdown na yadda abubuwa suka kasance a shekarun nan bata tambayeshi ba duk da kuwa cewa yana zuwa dubata. A cikin ziyarar da yake kawo mata ne kuma ranar nan ta samu courage din yi masa magana "ya kamata bilks din kudin maganin nan su Sumayya su daina biya haka, hidimar tayi musu yawa" yayi murmushi duk da maganar tata tabashi mamaki yace "da ma ina so inyi miki magana akan hakan, suna kokari sosai gaskiya, suna sonki sosai musamman da kika yi wannan rashin lafiyar suka tabbatar da cewa ba ko aikata laifin da ake tuhumar ki dashi ba, it will break their hearts in suka fahimci ba haka bane ba. Tace "ina Fatima? Ina Hassan?" Yace "suna nan lafiya, suna nan sunyi kudi sosai, enough money to send you to prison for life. Duk kudin da Sumayya taje ta wannan hidimar da shi na Hassan ne, Fatima tayi aure tana Dubai kuma a yanzu she owns as much as you do na H and H. Kin san wa ta aura?" Tayi shiru bata amsa masa ba, tana dai kallonsa, yace "wannan yaron da kika yi kokarin framing shi ta aura, suna can dubai tare, tare kuma da danki Hussain" Ruqayyah ta zaro ido cikin tashin hankali "Hussain dina?" Yace "eh, babanshi ya bayar dashi ga Fatima tun a shekarar ki ta farko a asibiti" sai ta saka hannun ta ta cire sabon hearing aid dinta da Sumayya ta siya mata daga kunnen ta, bata son ta cigaba da jin wannan labaran. Hawaye ya a bin fuskarta, ta rasa wanne be zata roka a gurin ubangiji mutuwa ko rayuwa? Ita dai tasan rayuwarta bata da amfani a yanzu, ta kuma san mutuwar ta ita ce mabudin wahalar ta. Ko ta roki Allah ba zai yafe mata ba saboda ba shi tayi wa laifi ba, Fatima kuma ta tabbatar ba zata yafe mata ba ko mene zata yi balle Hassan, wanda tafi jin tsoron zuciyarsa akan ta Fatima. A ranta tana so taga ƴaƴan ta, tana so ta kula dasu ta basu tarbiyya ko zasu zamo sanyin idaniyar ta wata rana amma tasan ko tana mutuwa tana dawowa duniya Hassan ba zai bata su ba. A dan fahimtar da tayi na short stories din da taji ta fahimci cewa kowa ya samu rayuwa mai kyau amma banda ita. Shin menene mafita a gareta? Shekarar ta biyu ta warke sosai. Duk sababbin abubuwan da suke damunta sun tafi, Minal ma finally ta daina binta da kallo amma wannan jaririn, wannan jaririn mai shegen kuka yana nan yana cigaba da kukan sa a cikin kanta, amma ta saba dashi dan haka bata gayawa doctors ba dan bata so su kara jan zaman nata a tare dasu. Kuma a ranta tasan cewa ba zai daina yi mata kuka aka ba gar sai ranar da taje inda ta ajiye shi ta dauko shi ko kuma ranar da ta mutu ta bar duniya. Sai dai tsoron abinda dauko shi din zai haifar gare ta shi yasa ta cigaba da barin shi a can din. Da za'a sallamota Lukman ya fitar da kudi a cikin kudinta sa saka akayi mata gyare gyare-gyaren gida, ya kuma daukar mata wasu sababbin yan aikin dan wadancan duk sun watse ya sallame su ya rufe gidan tun tafiyar ta. Ya gama shirya duk plans dinsa, fatansa shine aikin Malam ya cigaba da ci akanta ta cigaba da yi masa biyayya tare da cigaba da boye maganar yaron nan. Tun farkon sanda ya lura ta fara warkewa ya yanke shawarar sa. Idan ma yayi kokarin kashe ta ko wani abu to zai rasa dukiyar ne dan bashi da gadon ta, yasan iyayen ta ma ba zasu karba ba, maybe a karshe kudin ya kare da tafiya baitil mali, dan haka shawarar sa itace ya aure ta. In yayi haka zai samu damar cigaba da huya dukiyar ta hankali kwance, kuma inya kasance mai saa ma, in ta haifa masa Da, zai kuma samun dama akan dukiyar da yasan wadancan yayan nata ba zasu karba ba. Kuma samun wani dan a gurin ta zai kara dakusar da yunkurin ta na bayyana gaskiya. A ranar da aka sallame ta Baba da Inna basu zo ba dan har yanzu Baba yana kan bakansa, musamman yanzu da ya ga ta samu lafiya sosai. Sumayya ma bata zo ba dan Hassan bai barta ba. Sulaiman da Zunnur ne suka zo sai kuma Lukman da ya riga ya gama shirin sa, ya kuma cika wa Malam aljihu da kudin Ruqayyah akan yayi masa addu'a akan kudurin sa, har da sabuwar wheel chair yazo mata da ita mai remote control sannan kuma a gaban su Sulaiman ya gaya mata cewa yana so idan ta amince zai aure ta. Aure shine abu na karshe a zuciyar Ruqayyah a lokacin, dan ita bayan rabuwar ta da Hassan bata taba tunanin zata yi aure ba kuma tunda ita ba wai sin abin take yi a rabta ba amma sai ta samu kanta da kasa yi masa musu, a gaban su Sulaiman ta amsa masa tace zata aure shi, amma sai tace yaje gurin Baba tukunna suyi Magana. Ba Baba ba hatta sauran yanuwa sai ta suka yi mamaki da wannan batun, a take Baba yace babu ruwansa shi ba zai daura mata aure ba. Sai Lukman bisa jagorar Sulaiman ya tafi har Zaria ya nemi auren Ruqayyah ahannun dangin Baba kuma suka bashi. Ya kuma bayar da sadaki a ka daura musu aure. Yes, kamar yadda dukiya ta jawo wa Hussain mutane ta jawo wa Ruqayyah ma, banbancin shine kalar mutanen da ta jawo mata din. *The Final Wave* Aure ya tabbata tsakanin Ruqayyah da Lukman, da farkon auren a can kasan zuciyar Ruqayyah ta san karya yake yi da yace yana sonta, tasan cewa ba ita ya aura ba kudin ta ya aura, kuma ta saka masa ido sosai tana so ta ga iyakacin gudun ruwansa amma kuma sam ta kasa yi masa magana ko kuma yin wani yunkuri na karbe wani abu daga hannunsa. Sai kuma daga baya zuciyarta ta fara karkata akan tunanin to ko yana sonta din ne da gaske? Tana lura da irin wadda yake nuna kulawa a gareta, ya tattare gaba ki daya a wajenta ya ajiye matarsa ta farko da yara biyu da suke dasu a gefe, kullum yana tare da Ruqayyah yana kula da ita tare da kula da dukiyar ta. Yana paying attention to duk wasu bukatun ta musamman a gadon aurensu, abinda tunda ta nakasa take tunanin ta rasa kenan har abada amma sai yazo yana bata ba tare da kyama ba amma fa sai dai maganar kudinta ne babu su babu lissafinsu dan ko zancen baya yi mata ita ma kuma ta kasa samun courage din yi masa maganar, wannan shine kadai matsalar ta dashi a farkon auren su, yadda take kasa musa masa akan duk abinda yace mata ko da kuwa a ranta tasan ba haka bane ba gabaki daya ita ta manta da zancen malamin tsubbun da ita ta hada shi da shi kamar yadda Minal ta hada ta da shi. A hankalin take jin hankalin ta yana kwanciya da shi, tana jin cewa kamar shi din wani solution ne na dukkan problems dinta tunda ya cigaba da taimaka mata wajen boyewa iyaye da yanuwanta ainahin gaskiyar lamarin ta, a ganinta boyewar ne ya saka suka sauko yanxu suke kula ta ba kamar da ba, duk da yanzun ma ba kamar da can ba, tana ganin shi a matsayin wani shield ga dukiyar da ta samar wa kanta, dan tasan zamanta a matsayin mace mai kudi babu miji zai iya zamanto wa hatsari gare ta da kuma dukiyar ta, amma shi ya bata protection kenan. A hankali sai ta fara farin ciki, thinking that she deserves happiness ita ma a rayuwar ta kamar yadda Fatima da Sumayya suka samu. Tana ganin Fatima da take bazawara ta samu auren zankadeden saurayi kamar Adam, kuma kasancewar yadda Matsayin ta yake ta san Adam yana can yana riritata kamar kwai, giving her all the happiness, to in Fatimah zata samu wannan why not her? Dan haka sai tayi kokarin ganin ta yi accepting Lukman a zuciyarta dan tayi making kanta happy. And then she yearns for children, tana ganin sune zasu zaman to kamar wani murfi na farin cikin ta, su zasu taimaka mata gurin kara binne laifuffukan ta a zuciyarta, su zasu cika mata dadadden burin ta na haifa tare da raising yaya a cikin dukiya saɓanin irin tashin da ita da yanuwanta sukayi cikin talauci. Akansu take burin gyara yarintar ta. Shima kuma Lukman a tasa zuciyar abinda yake so kenan dan haka suka hadu suka yi ta nema and three years after aurensu God granted their wish, Ruqayyah ta samu ciki, cikin da akayi ta rikita wa, Ruqayyah feeling like ita ce Fatima take samun kulawa daga Hussain, sai dai ita tata kulawar iya kacin cikin gida ne sai sometimes ya dan fita da ita taga gari ya kuma dawo da ita gida amma ko hanyar airport bata zuwa ballantana ta hau jirgi, ita da wata kasar kuma sai dai a mafarki. Ita da jirgin sama sai dai ta taga kai ta kalle shi idan zai wuce ta saman gidan ta. A haka har ciki ya girma ya isa haihuwa akayi mata cs aka fito mata da kyawawan yayanta guda biyu namiji da mace. Wannan ranar a lokacin Ruqayyah zata iya kiran ta da happiest day of her life, yayanta manya masha Allah, gasu kyawawa masu kama da ita, ga kuma tarya mai kyau da ubansu yayi musu, duk da dai tasan da kudin ta ta ne akayi, but she is just happy cewa anyi din, komai daga waje aka shigo mata dashi irin yadda take so, kuma duk da cewa Lukman yana da wasu yayan amma yadda yake yi akan wadannan yaran zaka dauka bai taba haihuwa bane ba, shi ganin su yake yi a matsayin source of arzikin sa, a matsayin security dinsa, duk da Ruqayyah ta nuna masa ba zata yi suna ba amma sai yace sai anyi, shi a gurinsa yana so ya samu as many witnesses as possible na cewa Ruqayyah ta haifa masa yaya, ita kuma a nata bangaren tasan ba lallai bane yanuwanta su je gurin sosai, ta san in tayi taron bakin ciki zata kwasa kawai shi yasa ta ji bata so, amma kasancewar bata iya ce masa a'a dole aka yi taron suna. Sumayya bata samu Hassan ya barta ta leka wa Ruqayyah suna ba, duk da dai ya barta taje gurinta a asibiti amma da yaga tana shirin suna sai yace ma kasar zasu bari gabaki daya, "I want my children as far away from her children as possible". Haka ya tattara ta da yaran gabadaya duk da yaran ba hutu suka yi ba suka tafi San Francisco sukayi sati daya sannan suka biya ta Dubai suka dauko Hussain zaiyi musu hutu suka dawo gida. Bayan sun dawo ne Sumayya ta sami Hassan da maganar yaran "Habibi, yaran nan fa girma suke kara yi kullum. Aminu da Yusuf fa yanzu fifteen years suke Hussain yana Fourteen, ba ka ganin lokaci yayi daya kamata su san maganar Ruqayyah?" Ya bata rai yace "akan maganar matar nan fa na raba ki da kasar gabaki daya, shine kuma yanzu daga dawowar mu zaki dora a inda kika tsaya? Kinsan Allah? Saboda bana so muyi nisa da Aunty shi yasa kika ga har yanzu muke unguwar nan amma da tuni mun tashi mun tafi as far away from her and her sting as possible" Ta sauko daga kan kujera ta dawo gabansa ta durkusa tace "ba maganar Ruqayyah nake yi maka ba Habibi, maganar yayan mu ne. Ina jin tsoro ne wallahi. Kasan yanzu a duniya mutum ake kiyo ba dabba ba, maganar nan a fili aka yi ta ba'a sirri ba dan duk wanda yake unguwar nan yasan da maganar nan, social media duk ta san da maganar nan, ina tsoron kar wani ya tari yaran nan a hanya ya gaya musu maganar nan. Ko zuji a cikin friends dinsu ana maganar, ina jin tsoron kar aje a kara musu gishiri da maggi a cikin maganar su zo suyi mata fahimtar bai bai. Yaran nan suna da hankali, ina ganin in muka zaunar dasu muka yi musu bayani da kanmu zasu fi fahimta akan ace a wani gurin suka ji" "Ba sai lallai sai sunje sun ganta ba in baka so, ba sai lallai mun gaya musu komai in details ba in baka so, but at least let them know from us not from an outsider. Please Habibi. Maganar zata yi affecting dinsu sosai idan suka ji a wani gurin" Cikin sa'a sai ya yarda, a daren ranar suka tara yaran manyan sukayi musu bayani iyakacin wanda suke ganin kwakwalwar su zata dauka. Ai kuwa dai sunga rikici dan sai da Sumayya tayi nadamar matsawa akan maganar shi kuma Hassan sai yanzu ya fahimci Sumayya ta fishi gaskiya dan da a wani gurin sukaji da sai tashin hankalin yafi haka, a ranar babu wanda yayi bacci a gidan dan hatta kananan yaran sai da suka fahimci something is wrong duk da basu san menene ya faru ba. Kwana biyu bayan nan Hassan ya amince Sumayya ta shirya yaran gabaki dayansu suka shiga gidan Ruqayyah. Katon gidan da kullum suke daga kai suna hangowa amma basu taba shigar sa da wayon su ba, duk da dai twins din suna da memories na kamar da suna shiga amma ba zasu iya tuna me suke yi a gidan ba. Suna shiga falon suka tsaya suna kallon katoton hoton da yake rataye a sama yana kallon su, hoton Hassan da Hussain wanda duk cikin shekarun nan Allah bai bawa Ruqayyah ko Lukman ikon sauke hoton ba. Ruqayyah da take zaune akan kujera tare da wasu matan abokan aikin Lukman da suka zo musu barka tayi kokarin mikewa kuma babu kafa. Da sauri ta fara sallamar bakin nata zuciyarta tana bugawa da karfi. Tana jin excitement din ganin yayanta Musamman Hussain da ba zata iya tuna rabon data ganshi ba, a gefe kuma tana jin tsoron irin yanayin da taga fuskokin su a ciki. Bakin suka fara mikewa suna ajjiye jariran hannun su suna kallon yan samarin yayan da suka jeru a gaban hoto suna kallo, sai dai kallo daya zakayi musu kasan cewa daya daga cikin na cikin hoton ne suka haife su. Sai da suka fita sannan Ruqayyah ta mayar da hankalinta kan bakin nata, "Hussain" ta fada tana dafa kujera da rawar murya, Hussain ya juyo yana kallon ta da irin kallon da yasa ta sandare a inda take a tsaye "I hate the sight of you" ya fada da karfi "kar ki kara tunanin kin haifi ɗa mai kama dani. Hanyar da duk nabi kar ki yarda ki bita ballantana ki hadu dani har kiyi kokarin kirana da sunan danki. You are not my mother" sai ya juya da sauri ya fita. Abdullahi, Abdulrahman da Abdulrahim suka bi shi a baya suna kiransa dan su basu fahimci abinda yace ba, basu fahimci menene yake faruwa ba. Ruqayyah taji kafar ta guda daya ta kasa daukar ta duk da kujerar data rike, sai ta zame ta zauna akan carpet numfashin ta yana fita sama sama. She always dreamed of ranar da yayanta zasu shigo da kafafuwan su har cikin gidan nan su rungume ta su kira ta da mommy kamar yadda tayi bragging to Hassan sanda ya dauke su daga gabanta, she always thought tunda ta haife su ai ta gama musu komai, ta dauka a son will always stand for his mother no matter how bad she is, ta dauka wannan karin maganar ta uwa mafi uba ko da uban sarkine tayi applying to her, ta dauka...... Takun da taji ya saka ta dago kanta da sauri, twins dinta ne a tsaye a gabanta, and she wonders yaushe suka girma haka? Aminu ya durkusa kusa da ita, idonsa cike da hawaye yace "dazu da mommy tace mu shirya zamu shigo mu ganki mu gaishe ki, cewa muka yi ba zamu zo ba, kinsan saboda me?" Bata amsa masa ba, zuciyarta tana tuna mata da cewa ba ita suke referring to as Mommy ba, sai girgiza masa kai take yi, at least Hussain ta fahimci frustration dinsa dan tasan Adam da Fatima sun gama hure masa kunne a kanta, dama tasan dole ta samu problem dashi, amma not her gentle twins.. Sai Yusuf ya durkusa shima a kusa da dan'uwan sa yace "saboda bamu ga amfanin zuwa mu ganki ba, bama jin ko mun ki gaishe ki Allah zai kama mu da laifi" Aminu yace "da ana zabar uwa da ba zamu taba zaben ki ba" Yusuf yace "da ana chanja uwa da mun chanja ki" Yusuf yace "da ana goge memory da mun goge dukkan memoryn ganin ki da muka yi yau" Aminu yace "da ana un hearing magana da munyi unhearing labarin ki da muka ji" Yusuf yace "forget about us, kamar yadda kika riga kika yi dama tuntuni" Aminu yace "mu ma zamu manta dake ba zamu sake yin maganar ki ba ko da a tsakanin mu ne" Tun da suke maganar take rarraba ido a tsakanin su inta kalli wannan sai ta koma ta kalli wancan, tana jin maganganun su tamkar saukar mashi a cikin zuciyarta, tana girgiza kanta tana cewa "no, no, no wallahi ba haka bane ba. Karya suka shirya dan su raba ni da ku, duk abinda aka fada muku karya ne ba gaskiya bane ba" ta saka hannu biyu ta rike kafafuwansu guda dai dai "babanku ne yayi min fin karfi ya raba ni daku, wallahi ina sonku, ni na haife ku fa, har nan ya shigo ya dauke ku yace ba zan kara ganin ku ba, shine kuma yanzu suka shirya magana dan suna ganin kunyi hankali zaku nemi ku dawo gurina. Ni na haife ku fa!" Ta fada da karfi a lokacin da suka mike sannan kuma a tare suka saka hannu suka cire hannayenta daga jikin kafafuwan su. Kuma ba tare da sunce komai ba suka juya zasu fita daga gidan. Ta sake kwallawa da karfi tana jan jiki akan carpet da manta ma da surgery wound dinta, "I am your mother" sai suka juyo a tare, Aminu yace "a gurin mu you are not, mun chanja ki da mafi alkhairi" Yusuf yace "mun chanja ki kamar yadda kika chanja mu da kudi" sai suka juya suka fice. Ta kifa kanta a carpet ta saka kuka mai karfi, dama haka iyaye suke ji idan dan da suka haifa ya gaya musu magana? Dama haka Inna Ade da Baba suka ringa ji a lokacin da take mayar musu da magana? Sai wata zuciyar take tuna mata da cewa abinda suka ji yafi wannan tunda su suka raine ta suka yi mata komai da yake hakkin yaya akan iyayen su, ita kuma haihuwar Aminu da Yusuf kadai tayi. Sai kuma ta dago kanta ta sauke jajayen idanuwan ta a kan Sumayya wadda tunda suka shigo take tsaye a guri daya hannayenta rike da na Amatullah da duk abinda akayi a gabanta ne. Cikin dacin murya tace "Nagode Sumayya, kin karbe mijina kin karbe gidana kin kuma karbe yaya na. Tabbas Lukman yayi gaskiya da yace abu kadan kike jira ki ga bayana. I thought we are twin sisters, ina alkawarin mu na cewa we will always be there for each other? Ina alkawarin da kika yi na cewa you will always be by my side, ina ........" Sumayya tace "kin zubar. Duk abubuwan da kike tambaya ta ke kika zubar dasu da kanki. Mental problem ko not mental problem duk hali yake tarar wa, mijinki ke kika rabu dashi, yayanki ke kika zabi kudi a kansu, gidan ki ke kika fita daga ciki fa kafafuwan ki" sai ta ja hannun Amatullah zasu fita sannan tace "am still your sister shi yasa ma kika ganni a cikin gidan nan" daga nan ta fita da Amatullah wadda already har ta fara jero mata tambayoyin "ina ne nan! Wacece take kuka? Me akayi mata take kuka?" Bayan sun fita Ruqayyah ta koma ta kwanta akan carpet tana cigaba da kukan ta, childhood memories din ta ne suke ta dawo mata tana tuno da irin shakuwar su da Sumayya ta irin alƙawarin da suka yiwa junan su. What happened? What has changed so much?. Kukan jariranta ya saka ta bude ido, saitin inda ta kwanta duk ya jike da hawaye. Tana jin nannies dinsu guda biyu da aka dauka na musamman dan kula dasu suka zo suka dauke su a inda bakin da suka zo barka suka ajjiye su. Sai kuma taji anzo an kama ta an mikar da ita an mayar da ita kan kujera, bata san waye ya mikar da ita din ba amma tasan dan tana biyan sa kudi ne ya taimaka mata ba dan Allah ba, ta san tayi loosing wadanda zasu taimaka mata dan Allah dan ita ma sanda tayi taimako ba dan Allah tayi ba. Twice. *16 years Later* Shekaru talatin kenan da mutuwar Hussain....... Shekaru talatin da batan jaririn dansa Rayuwa ta cigaba da tafiya, lokaci yana ta gudu kamar yadda kowa yasan cewa baya jiran kowa. Ko kana aikata alkhairi ko kuma kana aikata sharri shi lokaci babu ruwansa tafiya zai cigaba da yi kuma yana tafiya tare da adadin kwanakin da aka lissafa maka a duniya. Ko wanne wayewar gari kuma tamkar dama ce da take gaya wa mutum yayi aikin alkhairi, kamar tunatarwa ce ta cewa kwanakin ka suna tafiya, damammakin ka suna karewa, change! repent! Amma kash, mai hankali ne kadai yake ganewa, mai hankali kadai yake chanja munanan halayensa da kyawawa a lokacin da ya gane, mai hankali ne kawai yake nadama a lokacin daya fahimci ya aikata zunubi kuma ya tuba ga ubangiji, mai hankali ne kawai yake neman yafiya ga wadanda ya zalunta a take a lokacin daya fahimci ya zalunce su din. Ba zai jira sai nan gaba ba....... Ba zai jira sai ya samu another chance ba........... Saboda bashi da tabbas din zai samu wani chance din Saboda tomorrow is never promised. Komai zaka yi kayi shi a yanzu, dan today is what you have. Abinda kake dashi kuma dashi kake amfani Yara sun zama manya, manya kuma sun zama magidanta, magidanta kuma sun zama dattijai. Baba da Inna shekaru sun tura, Adam ya yi surprising din su da gina musu sabuwar makarantar islamiyya anan karshen layin da gidan su yake, aka dauki malamai da yawa da Baba a matsayin oga kwata kwata, Inna ma kuma sai ta roka aka bata ajujuwa a ciki da take koyawa matan aure karatu, wannan abin ya faranta musu rai matuka dan duk a rayuwar su babu abinda yake basu joy irin du koyar da ilimin addini. Lafiya lau suke zamansu sai dan abinda ba za'a rasa ba saboda shekaru. Sai kuma Ruqayyah da har yau suke ganinta a matsayin jarabawar su da suka fadi, sai dai a matsayin ta na yarsu har yau basu fidda ran zata bude bakinta ta fadi laifinta ta kuma nemi yafiya. Aunty ma tana nan duk da shekaru sunja mata amma tsabar jin dadin da take ciki ya saka hankalin ta a kwance yake tana rayuwa cikin tarin jikokin ta, ta kuma samu sabuwar dabi'a ta dauko yara yammata na cikin dangi su zauna a gurinta na dan lokaci kuma ta aurar dasu cikin bajinta da karamci. Bata yi aure ba duk da nacin da Hassan yayi ta yi mata har ya hakura ya barta. Fatima da Adam har yanzu suna Dubai. A yanzu ma sun zama tamkar yan kasa a can Adam yayi kuɗi na gasken gaske saboda kwazon sa da kokarin sa a gurin aikinsa, da kuma zurfin da yayi a ilimin abinda yake aiki a kai. Babban jin dadin su kuma shine yadda suke tarairayar junansu cikin tsantsar soyayya, shakuwa, abota da kuma wayewa. Fatima har yanzu gap din da yake cikin memory dinta bai cike ba duk kuwa da irin doctors din da tayi ta gani har ta gaji ta barwa Allah ikonsa. Soyayyar Adam da kuma soyayyar yayansu guda hudu ya taimaka wajen rufe ramin da yake zuciyarta duk da dai ciki hollow ne, bata sani ba ko zai cike a duniya ko kuma sai a lahira? Kannen Adam duk sunyi aure, mamansa ma tayi, babansa ya mutu a imo da bakin cikin rashin family dinsa, brother dinsa is no where to be found. Sumayya da Hassan komai zam zam, kamar yadda yaran sukayi alkawarin sun bar Ruqayyah haka suka yi, basu kuma waiwayenta ba duk da cewa katanga daya ce a tsakanin su dan suna ganin sun samu komai a gurin Sumayya a matsayin uwa. The boys are now men, Aminu da Yusuf sun gama duk karatun suke da burin yi a rayuwa, Aminu ya samu aiki a Abuja a NESREA, Yusuf kuma yana nan ya kamawa Baban sa harkar Real Estate da har yanzu Hassan yake kanta, yanzu kusan shi yake jagorantar komai sai dan abinda ba'a rasa ba da Hassan yake yi da kansa. Duk su biyun sunyi aure harda karuwar ya'ya ɗai ɗai. Hussain yana gurin second parents dinsa har yanzu kuma kamar yadda yace zai gaji mai sunan sa haka yayi, kasuwanci sosai ya kafa kuma yake cigaba da kafawa a bangaren suttura, kasancewar garin da yake dama na kasuwanci ne sai ya samu budi sosai ta wannan bangaren. A yanzu haka yayi nisa gurin neman auren takwarar Fatima da sarki Umar yayi mata. The three Abduls duk sunyi nisa a nasu bangarorin na rayuwa, Amatullah tana jami'a kuma bakin Sumayya ya karbu dan ba'a yi mata kani ko kanwa ba. Kowa yana having good life, an excellent life, banda Ruqayyah....... Komai na rayuwar Ruqayyah bai tafi mata dai dai ba a wadannan shekarun, yan biyun ta sun girma cikin dukiya da gata kamar kamar yadda take mafarki, tayi kokarin ta yi replacing din lost children dinta da su amma abin ya gagara, problem na farko shine gaba-daya tarbiyya yaran taki tafiya mata dai dai, musamman Sa'ad, tun yana yaro tantiri ne na karshe dan Ruqayyah tana jin duk abinda take tunanin tayi tun daga yarintarta har zuwa girman ta to Sa'ad yayi doubling. Baya jin maganar ta ko kadan, ya raina ta karshen raini, zai iya gaggaya mata magana a duk lokacin da yayi niyya ba tare da ko kadan ya ji cewa bai yi dai dai ba, kuma a fahimtar Ruqayyah sai ta fahimci cewa Lukman ne mai daure masa gindi yayi duk abinda yake so. Sa'adatu ce mai dama dama, dama daman ta kuma shine tana son Ruqayyah tana kulawa da ita sosai da sosai dan duk wasu hidimomi nata a yanzu Sa'adatu ce take yi indai har tana gida. Abu daya da Ruqayyah take jin dadin sa shine yadda yaran suke tsananin kaunar junansu, ba'a taba daya daya ya kyale koda kuwa ita ce, ko fada tayi wa Sa'ad sai Sa'adatu ta nuna bacin ranta. Babban abinda yake bata mamaki a halayyar Sa'ad shine shegen son kudin sa, duk kuwa da cewa an wada ta shi da komai in abundance amma hakan bai hana shi ya saka hannu ya dauki duk abinda ta ajiye ko ubansa ya ajiye ba. An saka su a makarantar kuɗi irin wadda Ruqayyah take ta mafarkin saka ƴaƴanta, amma kuma sai dai kan babu komai, duk uban kudin da ake zubawa a cikin makarantar amma babu abinda yaran suke fitowa da shi sai lalacewar tarbiyya musamman ta bangaren Sa'ad. Sa'ad ya fara shaye shaye tun yana js class, sanda ya shiga senior class kuwa ya gama gwanancewa akan duk wasu munanan dabi'u da dukkan wata lalatacciyar tarbiyya. Hawan jini, ciwon zuciya babu wanda Ruqayyah bata dashi a yanzu, ba wai matsalar yaya bane kadai har data miji, yanzu ta kuma tabbatar wa cewa Lukman ba sonta yake ko kankani ba ya aure ta ne dan ya cigaba da juya dukiyar ta, sannan ya haihu da ita for security, dan zuwa yanzu ko magana mai dadi babu a tsakanin su kamar yadda babu komai tsakanin ta da dukiyar ta in banda ta saka masa hannu a takarda, abinda a ranta take tunanin shine kadai zaren da yake rike da su a tare. And then one day...... Ranar da Sa'ad da Sa'adatu suka yi graduation na secondary school, a ranar ne Sa'ad din yazo kamar yadda ya saba ya jefi Ruqayyah da hoton wata sport car, a bayan hoton ya rubuta wani amount na kudi, tace "na menene wannan din?" Yace "ji nake yi kina gani, ko idon ya tafi ne shima ban sani ba? Kudi ne zaki bani" tace "me zakayi da wannan kuɗin Sa'ad? Wannan uban kudin me zakayi dasu?" Ya rike kugu, daga dukkan alamu a buge yake yace "kaji wata tambayar rainin hankali, yama zakiyi ki tambaye ni abinda zanyi da kuɗi? Kudi fa? To mota zan siya, sabuwar sport car din da ake yayi yanzu irin wadda yayan masu kudi suke yayi ita nake so inyi order a matsayin gift dina na kammala ssce" tace "kammala ssce? Ssce din dana tabbatar da cewa babu abinda zaka ci a ciki shine har zanyi maka wannan gift din? Da ace kayi abin kirki ne ma da sai in baka something amma ba wannan kudin ba". Ya harzuka "wallahi baki isa ba, chafdi, bayan na riga na gama gayawa abokai na duk cewa za'a siya min wannan motar? Har fa hoton ta na nuna musu, wallahi sai an bani kudin nan ko sama da kasa zasu hadu" tayi shiru tana kallon sa, tsananin kamar da yake yi da ita yasa take ganin fuskarta sanda ta gama secondary dinta a cikin tasa, maybe da iyayenta sun tsaya strong a kanta sun hana ta auren Hassan, maybe da bata samu kanta a inda take a yanzu ba, she is going to be strong for her children, tace "to nace ba zan bayar ba, in kuma zaka kwata ta karfi ne to bismillah" Sai yayi murmushi "baki san irin abinda zan iya yi saboda kudin nan ba wallahi da baki ce haka ba" Sunfi sati a haka, yayi mata iya rashin kunya ta ki bashi tana ganin hakan a matsayin hanyar taimaka masa, uban ma yayi magana ya nuna ta bashi kudin still taki, the first time da tayi masa musu, wannan yasa ya sha jikinsa cewa malam mai tsubbu ya tafi lahira da asirinsa, dole ne kuma ya dauki wani matakin. Wannan dalilin ne yasa yaga lokaci yayi daya kamata ya debi rabonsa a cikin dukiyar, ya debi kudin pension dinsa sannan ya nemi inda dare zaiyi masa. Ya shirya komai ya rubuta check kamar yadda ya saba bata tana signing a matsayin na house maintenance, ya bata ta duba amount taga dai dai sai tayi signing ta bashi, sai daya fita ya shiga mota sannan ya dauko biro ya kara zeros guda shida a amount din ya fita. Jaka guda ya ciko da kudi, amma basu ishe shi ba dan haka ya taho dasu gida da niyyar zai hada da duk golds da duk abubuwa masu amfani na gidan ya tafi dasu. Yana shigowa Sa'ad yana kokarin fita, sai ya kama masa jakar suka shiga da ita ciki suka hau sama da ita, shi duk Lukman bai yi tunanin Sa'ad ya san menene a cikin jakar ba, shi ya kai sama ne dan yasan Ruqayyah bata iya hawa. Dakin sa ya shiga ya kuma bude safe box din cikin dakin ya saka jakar sannan ya saka pin ya rufe safe box din. A take zuciyar Sa'ad ta yanke masa abinda zai yi ......... A daren ranar yan fashi suka shigo musu gida, abinda ba'a taba yi musu ba, kuma abin mamaki shine yadda alamu suka nuna ta cikin gidan aka bude musu gate din. Ruqayyah tana dakinta tana bacci, a cikin baccin ta fara mafarkin da yafi mata kama da memory, mafarkin ranar da ta fara haduwa da Hassan, ranar da ta zamo farko kuma karshen rayuwarta. Ta gansu suna karatu tare da Sumayya a daki, sai kuma ta ji harbin bindiga, sannan ta kuma jin wani harbin. Sai ta dauki buta ta tafi toilet, Sumayya tana ta gaya mata kar taje. A toilet din taga Hassan, wuyansa da kafarsa suna zubar jini. Ya rike ta. "Help me please, ki taimaka min dan Allah" Kuma sai taga toilet din ya rikide ya koma dajin da suka yi accident a ciki, Fatima tana tsaye a gaban ta hannunta rike da cikin ta, jini yana zuba daga sholder dinta, tace "Help me please, ki taimaka min dan Allah" Sai taji karar harbin bindiga na uku. Wanda shine ya tashe ta a tsorace tana salati jikinta yana karkarwa. Babu Lukman a kusa da ita, dama ita kanta ba zata iya tuna rabon da su kwana tare ba. Ta zauna a saman gadon tana addu'a tare da goge gumin daya jika mata fuska, a ranta tana rarrashin kanta tana tunawa kanta cewa memory ne kawai. But ita bata gane last karar bindigar da taji ba, dan babu shi a memory din nata. A lokacin taji an bude kofar dakinta an shigo kamar daga sama, bata fahimci ne yake faruwa ba taji an daga ta an dora akan wheel chair dinta sannan roughly aka tura ta zuwa palo, sai a lokacin ta fahimci me yake faruwa, sai a lokacin ta lura da maza kusan su goman da suke zagaye da ita fuskokin su rufe da bandana hannunsu dauke da mugayen bindigogi. Tana gurin aka shigo da Sa'adatu wacce take a tsananin rude, tana zuwa ta tafi ta rungume Ruqayyah tana kuka, amma babu Sa'ad babu labarin sa a gurin, suka sakawa Lukman bindiga aka suka tafi dashi dakin sa suka tirsasa masa ya bude safe box din ya dauko musu jakar, daga nan kuma suka zagaya duk ɗakunan gidan da suke a bude suna dauko duk wani abu da suka san yana da tsada. Ruqayyah ta jima bata ga tashin hankali irin na lokacin ba, ta rasa da mamakin wannan uban kudin da aka fito dashi daga dakin Lukman zata ji ko kuma da bindigogin da ake ta waving a fuskarta, ko kuma da Sa'adatu data kankame ta tunda suka shigo tana cewa ta ceceta zasu kashe ta. Ko kuma da rashin ganin Sa'ad ko sanin halin da yake ciki? Ta kara jawo Sa'adatu jikinta tana rarrashin ta "kiyi shiru ƴata I am here, babu abinda zai same ki kinji" for the first time tana jin zata iya bayar da komai da take dashi dan ta tseratar da ƴaƴan ta. Sai dai kuma wannan wani alkawari ne ta dauka wanda bata san cewa ba zata iya cika shi ba. Ba zata iya protecting yarta data girma ta shaku da ita ba daga hannun yan fashin, kamar yadda Fatima bata iya protecting danta daga nata hannun ba. Bata fahimci haka ba sai da taga shugaban yan fashin yayi signing cewa a dauki Sa'adatu a shigar masa da ita daki. Wannan shi ya zamanto tonon asiri ga Sa'ad, wanda shine ya gayyato kuma yayi leading yan fashin har cikin gidan su, sai yanzu kuma yace ba yarda ayi raping sister dinsa ba. Ba Ruqayyah kadai ba, hatta Lukman da Sa'adatu sai da suka rude da ganin Sa'ad a cikin yan fashin "Ba haka muka yi daku ba, ni kudi kawai nace kuzo ku dauko mana mu raba 50/50 ni daku" sai Ruqayyah taji maganar tayi mata kama da yadda Hassan ya bata labarin abinda ya faru da kidnappers dinsa, mafarkin ta ya dawo mata a ranta. Rokon Sa'ad bai samu karbuwa ba, duk suka fara yi masa dariya, ogan yace "and you think ana alkawari damu? Ka ka dauka in mun dauki kudin da gaske zamu baka? Da gaske kuma zamu barka da rai ka tona mana asiri?" Sai Ruqayyah ta tuna da abunda ya faru ranar da ta hadu da Hassan, ta tuna cewa harbi uku akayi a ranar and she silently pray cewa yau ba za'a yi ko daya ba, cewa ba zata rasa dan ta ba. Haka suma yayan a zuciyoyin su duk addu'ar suke yi Amma addu'ar su bata karbu dan bata daga cikin adduoin da ubangiji yake karba tun da tun daga abincin da akaci aka samu maniyin da akayi cikin su dashi har zuwa sutturar da take jikinsu duk na haram ne, kowacce gaba ta jikin su an gina ta ne daga haram, to ta yaya za'a amsa musu addu'ar su? A gaban idon Ruqayyah babban yan fashin ya daga bindigar sa ya auna Sa'ad da ita, ta kwalla kara da karfi, sai dai fitar karar tata tayi dai dai da yunkurawar da Sa'adatu tayi daga jikin ta ta shiga gaban Sa'ad, kuma hakan yazo dai dai da tashin bindigar. A tsakiyar goshin Sa'adatu. Wadda ta mutu ba tare da ko shurawa tayi ba, sai gangar jikinta ya zame ya fado jikin Ruqayyah da take zaune akan wheel chair dinta. Ta saka hannu ta riko kanta tana kallon fuskarta da jini ya wanke, tana kallon dan karamin ramin da bullet din yayi a tsakiyar goshinta, sannan tana kallon idanuwan ta da suke kallon ta itama, irin kallon da Minal tayi mata bayan ta mutu a accident. "Sa'adatu" Sa'ad ya fada cikin kara, sannan ya kwace daga hannun wanda ya rike shi ya taho da gudu zai rike yaruwarsa sai dai kafin ya karaso Ruqayyah taji wani karar harbin, jininsa ya watsu a fuskar Ruqayyah, sannan gawarsa ta fado a kan cinyarta, a saman gawar yaruwarsa. Ta dago kai tana kallon yan fashin, kunnuwan ta suna amsa kuwwa da kalmar Allah ya isan da Fatima tayi mata, sannan bakinta yana motsi a hankali tana addu'ar Allah yasa bullet na uku ya kasance a cikin kanta. Amma sai taga sun dauki jakar kudin da sauran kayan da sauri suna fita ba tare da ko second look at her ba. Sai da suka gama fita sannan ta mayar da dubanta ga gawawwakin ƴaƴanta, ta rintse idonta tana so hawaye ya zubo mata amma babu shi babu alamun sa. Ta rasa me yasa take tuno wa da kidnappers din Hassan, kuma take ji a jikinta kamar harbi uku za'a yi a yau? me yasa take jin sai an kara yin harbi daya sannan mugun daren zai kare? Lukman ne ya dawo da ita hayyacin ta ta hanyar jijjiga yaran da suke kan cinyarta yana kiran sunayensu amma ko ba'a gaya mata ba tasan ba zasu kuma amsawa ba har abada. Lukman ya mike tashin hankali rubuce a fuskarsa ya hau sama da sauri. Shi a gurinsa ba yaya kadai ya rasa ba, ya rasa everything, dan duk wani abu mai daraja wanda zai dauku yan fashin sun dauke, kudin daya debo sun kwashe sai share din kamfani, sai kuma sauran kudin da ya rage a cikin account din Ruqayyah. Yadda yake ganinta din nan kuwa baya jin zata wuce ranar nan musamman saboda ciwon zuciya da hawan jini da take fama dashi, with his children dead, in ta mutu abinda zai samu bashi da yawa considering sauran yayanta. Check book ya dauko da biro a dakinsa, a gefen gado yaga bindiga, daga dukkan alamu a wadanda suka shigo ne suka manta ta, ya dauka ya saka a aljihunsa ya fita, blindly ya kuma saukowa kasa inda har yanzu take zaune a kujerar guragu da gawawwakin ƴaƴanta a kan cinyarta ta cire hearing aid dinta ta jefar. Ya mika mata check book din sannan ya auna ta da bindigar hannunsa yana nuna gurin signing yace "sign here" ta bishi da kallo, her heart breaking into thousand pieces. Automatically tayi signing a inda ya nuna mata tana tunawa da threats din data yiwa Hassan dan ya bata kudi, tana tuna wa da maganar Hassan da yace "this money is going to be the death of you" ta mika masa tana cewa "this money is going to be the death of you". Ya karba da sauri ya saka a aljihunsa, niyyar sa sai ya fita zai duba sauran abinda ya rage a account din ya kwashe. Sai kuma taga ya daga bindigar and while looking into her eyes ba tare da ko digon soyayyar ta ba a cikin zuciyarsa ya sakar mata third bullet din da take jira, a wuyanta. Sannan ya juya da gudu ya fita. Baya son yayi taking risk din cewa zata rayu ta tona masa asiri. Komai daren dadewa, whatever goes up most come down...... Bar ganin lokaci yana tafiya, bar ganin kamar kowa ya manta, hakkin wani will eventually destroy you........ Your karma will eventually catch up with you........ Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020 *Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800* *bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa* *Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin Allah* *The Orphanage* Forgive the typos please *Have you seen my collection of abayas or are you yet to?........ Ki garzayo into my DM ki gani ki zaba ki biya a kai miki har garin da kike a Nigeria. Prices ranges from 10k _25k. Kar ki bari ayi babu ke!"* Sumayya tana kwance tana tsakiyar baccin ta mai dadi, a kan gadon ta a kusa da mijinta a lullube da bargo. Karar bindigar da taji ne ya ratsa baccin nata ya kuma farkar da ita. Ta mike zaune a tsorace tana tunanin kamar tasan irin wannan karar, ta fara karanta addu'ar tsorata sai taji wata karar, a lokacin ta tabbatar da karar menene kuma kunnuwan ta suka tabbatar mata daga inda karar take fitowa. Tayi sauri ta kankame Hassan idanuwan ta a waje cikin tsoro. Ya bude ido cikin bacci yana kallonta, tsoron da ya gani a nata idanun ya saka ya watstsake. "Lafiyar ki kuwa Sumayya? Menene yake damunki? Mafarki kika yi?" Cikin rawar murya tace "harbi akeyi, karar bindiga naji, yan fashi ne suka shigo" ya mike tsaye da sauri, automatically hankalin sa yana komawa kan ƴaƴan sa, musamman Amatullah da take budurwa. "Amaty" ya fada yana kokarin saka jallabiyyar sa, Sumayya ta sauko daga kan gadon tana kokarin daga labule ta leka sai ya rike hannunta, "don't" ya fada a hankali sannan ya jata zuwa bayansa shi kuma ya daga labulen kadan ya leka zuwa compound din gidan sa. Bai ga kowa ba baiga komai ba duk da security light din data cika gurin da haske, gate a rufe amma kuma sai ya ga bai ga maigadi a gurin ba, sai da idonsa ya saba da yanayin gurin sannan ya ga mai gadin tare da securities dinsu guda biyu a lafe a jikin katanga hannayensu rike da makamai. Ya rufe labulen da sauri, "ba gidan nan suka shigo ba, maybe makota ne* Sumayya ta rike hannunsa "eh ba a anan gidan dama naji ba ai, a makota naji, a gidan Ruqayyah naji" ya juyo yana kallon ta da budaddun ido sai kuma rike fuskarta yace "baki tabbatar ba, kina cikin bacci ne, you maybe be wrong, bara in je in bincika in gani" sai kuma ta sake riƙe hannunsa "kar ka fita fa, kar suyi maka wani abu fa, dan Allah kar ka fita" sai ya koma amma ba zama yayi ba wata drawer ya jawo ya dauko ajiyayyar bindigar sa daya dade da siya kuma ya sama mata license amma har yau bai taba amfani da ita ba, yayi checking ya tabbatar it is still loaded sai ya saka ta a aljihunsa sannan ya fita da sauri tare da rufe kofar dakin. Dakin Amatullah ya fara zuwa ba tare da bude kofar ba ya saka key yayi locking dinta ta waje sannan ya mayar da key din aljihunsa ya sauka kasa inda dakunan mazan yake, yana sauka yaji karar third harbin, a lokacin da Abdulrahman ya fito daga dakin sa da sauri shima, suka hada ido da uban sai yayi masa alama daya koma ciki amma yaki yana nuna masa shi ya koma sama. Yasan ba zai koma din ba sai yayi hanyar waje shima ya bishi a baya, Hassan yana godiya ga Allah da Hussain baya gidan da tuni ya wuce securities din ya bude gate din ya fita yana neman a inda ake harbin dan ya taimaki wanda aka harba. A bakin gate yayi confirming abinda Sumayya ta fada, a gidan Ruqayyah ake harbin, amma kuma sai security din suka gaya masa sunji fitar motoci tun mintuna biyar da suka wuce. A take ya tambayi kansa "third harbin fa waye yayi shi?" Karar tashin motar daya ji daga gidan ne ya saka ya bude spy window din jikin gate din ya leka, idonsa ya sauka akan fuskar Lukman a lokacin da yake wuce gidan a cikin motarsa, fuskarsa cike da tashin hankali. "To ko police ya tafi kirawo wa?" Ya tambayi kansa lokacin da Abdulrahman ya karaso gurin yana janye shi daga jikin gate din. "Daddy ka koma ciki dan Allah, mu zamu fita mu gani". Amma kafin ya bayar da amsa suka ga Sumayya a gaban su tana danna security pin din bude gate din. Kafin su rike ta har ta bude ta kuma tura ƙaramar kofar jikin gate din ta fita ba tare da tace musu komai ba, a second daya duk mazan uku suka fita suma ita kuma a second daya tayi hanyar gate din Ruqayyah, sai a lokacin ta lura ko hijab babu a jikinta, gate din a hangame yake babu kowa a gurin, daga inda take tana hango compound din gidan shima bata hango kowa a ciki ba, zata shiga kenan Hassan ya rike ta samarin kuma suka shiga gabanta, Hassan yana magana a hankali yace "menene hakan? Kika san ko suna ciki?" Ita kuma tace "basa nan sun fita, naga fitar su a mota, naga fitar Lukman a mota, my sister is injured dan Allah ka sake ni inje gurinta" yaki cikata sai ta fara kalla kira "Ruqayyah! Ruqayyah!" Hassan ya rufe mata baki yana tsorata da yanayin ta, yace "shshsh, zamu shiga yanzu amma kiyi shiru" Ya damka ta a hannun Abdulrahman yace "rike ta, ku tsaya a waje gabaki dayan ku zan shiga in gani" amma ko rabin compound din bai kai ba yaga mazan sun biyo shi da sauri, ba zasu bar babansu ya shiga cikin danger ba, zasu tare masa kamar yadda shi kuma zai iya tare wa Sumayya yayinda ita kuma take jin zata iya tarewa kowa daga cikin su. That's what family means. Jin sun biyo shi ya saka ya kara sauri ta yadda ya kasance shine na farko daya fara shiga cikin falon, hannunsa rike da bindigar sa, a lokacin ne idon sa ya sauka akan tashin hankalin da yake jin bai taba ganin irinsa ba idan ba'a media ba. Uwa, gurguwa kuma kurma, a zaune akan kujerar guragu kafarta daya mai lafiyan a kasa dayar kuma shanyayyiya a makale a gefen kujerar, yayanta twin teenager a kwance a jikinta daya akan daya, jini a zagaye dasu, babu alamar rai a jikin duk su ukun.. Farko sandarewa yayi a tsaye, yanajin shekarun sa suna sauka akan kafafunsa, sai kuma yaji karfi yazo masa, ya juya baya da sauri lokacin da Sumayya take kokarin ture yayanta ta shigo, sai ya saka hannunsa biyu ya tura su baya gabaki daya ya rufe kofar tare da murda key din daya gani a jiki. Sai kuma ya same ya zauna a jikin kofar yana jin yadda Sumayya take kuka tana buga kofar. In no way zai barta taga Ruqayyah a haka because he can't imagine seeing Hussain like that, yasan da yanzu yana lahira ko gidan mahaukata. Yana mayar da numfashi ya daga murya yace "take your mother home and lock her up. Call the police" Yana jinsu suna rigima da Sumayya, daga baya sai yaji shiru da alama daukan ta sukayi suka fita da ita. Ya mayar da dubansa kan Ruqayyah, daga inda yake zaune yana hango yadda jini yake fita daga wuyanta yana jika gaban rigarta tare da sauka akan yayanta. Sai ya mike ya ciro labule dakin da sauri ya tafi da niyyar lullube su, a ransa yana tuno da ranar da ya fara ganinta da kuma rayuwar da suka yi tare musamman a farkon auren su. Sai dai yana zuwa inda take ya lura da yadda kirjinta yake dagawa alamar jan numfashi, numfashin ne kuma yaje kara bulbulo da jinin daga wuyanta. Da sauri ya yar da labulen hanunsa, a lokacin da yaji an bude wata kofa a cikin falon, ya kalli gurin ya ga ma'aikatan gidan ne suke lekowa daya bayan daya. "go back inside" yayi musu tsawa da budaddiyar muryar sa, sai kuma yaga wani saurayi a cikin su yace "you, come here, get me a towel" yaron ya tafi da sauri sauran kuma suka koma ciki, wasu daga cikin su suna kuka. Ya kama gawar Sa'ad ya sauke shi kasa ya kwantar dashi akan carpet yana jin wani zazzaɓi yana rufe shi, a lokacin ya kalli gawar Saudatu, her eyes looking at her mother, sai yaji ya kasa taba ta ya zauna a kasa hawate yana zuba da gudu daga idanuwan sa. Abdullahi ya gani a kusa dashi, bai ma san ta inda yaron ya shigo ba amma bai yi mamaki ba saboda kasancewar sa SS officer, sai ganin sa yayi yana dauke Sa'adatu ya kwantar da ita a kusa da dan'uwan ta sannan yaga ya cire t-shirt din jikinsa ya yaga ta biyu yana kokarin daure wuyan Ruqayyah da ita. Ya daga masa hanu "akwai bullet a ciki, kar ka danna da karfi" sai ya karbi karamin towel din da yaron daya aikaya kawo ya dora akan wuyan Ruqayyah sannan ya karbi rigar Abdullahi ya daure wuyan da ita. A ransa yana tunawa da ranar data daure masa wuyansa da dankwalin ta. Bai san hannun sa ya sauka a cinyar ta ba sai ji yayi ta rike hannun da dukkan karfinta, tamkar rayuwar ta a hannun take, yayi sauri ya kalle ta yaga idonta a rufe yake but she is still concious, "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya fada yana jin wani irin imani yana kara shigar sa, wato duk wannan abin Ruqayyah tana feeling komai. Lallai duk wandabai gide wa Allah ba tabbas zai godewa azabarsa. Sai ya kai bakinsa dai dai kunnenta yadda yasan zata ji ko da babu hearing aid dinta yace "na yafe miki Hassana, na yafe miki duniya da lahira ba dan halayenki ba sai dan Allah. Ina fatan nima Allah ya yafe min kurakurai na ni da iyalina" Sai yaji ta saki hannun Ya juyo a dai dai lokacin da Abdulrahman da Abdulrahim suke shigowa palon da sauri, fuskokin su cike da tashin hankalin abinda idanuwan su suke gani, ya kalli Abdulrahman yace "she is alive, do something" nan take Abdulrahman da yake a matsayin likita ta tafi gurin Ruqayyah, sannan ya dauko wayarsa yana kiran ambulance din asibitin da yake aiki. Abdulrahim da yake shine mai karyayyiyar zuciya a cikin su sai ya tsaya a gaban gawawwakin yaran hankalin sa a matukar tashe, hawaye yana zuba daga idonsa, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, so innocent. Basu saba sosai da yaran ba saboda basa shigowa nan babansu ya hana su suma kuma yaran basa shiga nasu gidan saboda mamansu ta hana su, amma suna haduwa a waje kuma suna haduwa a gidan Baba, ya tuna Sa'adatu duk inda ta ganshi sai ta gaishe shi, har wani abokin sa ya taba tsokanar sa cewa budurwar sa ce shi kuma yace ba zai iya budurwa da mai kama da mommyn sa ba. Ya tuna Sa'ad kullum suka hadu sai ya roke shi kudi ko kuma ya nuna masa wani abu yace ya siya masa. They were his cousins, they were his s family. Sai yaji a ransa kamar abinda ya faru dasu fault dinsu ne gaba ki daya. Yace yana rufe wa Sa'adatu idonta "wanne marar imani ne ya aikata wannan abin? Wanne mara imani ne zai kashe uwa da ƴaƴan ta ba tare da sunyi masa komai ba? Kawai saboda abin duniya? Abin duniyar da ba zasu iya hanaka dauka ba dan basu da karfin hanawar. Allah wadaran dan fashi" sai wannan yaron gidan da ya kawo towel yace "a'a yallabai, basu suka harbe ta ba" gaba-daya suka juyo suna kallonsa da alamar tambaya, sai ya nuna kofar da take shiga part din ma'aikatan gidan yace "da yawa daga cikin mu witnesses ne, su suka harbi yaran, ita kuma mai gidan ne ya harbe ta bayan ya saka ta saka masa hannu a wata takarda" Hassan ya kalli Abdullahi da sauri, kafin yayi magana har ya dauko wayarsa ya fara waya yana describing Lukman da motar daya fita a ciki da address din daya gidan nasa. Yana gamawa police suna zuwa kusan a tare da ambulance, police din ne suka ga maigadi a dakinsa an buga masa wani abu aka ya suma, aka dauko shi shima aka hada da Ruqayyah, Abdulrahman ya bisu a baya, Abdullahi kuma ya shiga cikin police suka fara karbar report, Hassan kuma ya koma gidan sa yana tunanin ta inda zai fara bawa Sumayya da sauran yara wannan labarin. Kafin gari ya waye labari yaje duk inda ya kamata yaje. Sumayya a asibiti gari ya karasa waye mata hannun ta rike dana Ruqayyah har aka gama shirya ta aka shiga da ita dakin aiki aka yi kuma nasarar fitar da bullet din ya samu gurin zama a makogwaronta. Sai dai tun kafin a shiga daita aikin doctors din sun warning Sumayya cewa ba lallai ne a samu sakamako mai kyau ba "the most da zamu shine ranta, bayan haka bamu yi alkawarin komai ba" A gida kuma Inna Ade da Baba su suka wanke kuma suka suturta jikokin su, sannan akayi musu sallah aka kuma kai su gidan su na gaskiya. Dama can Allah bai rubuta cewa masu tsahon kwana bane ba, ya kuma karbe su tun kafin su loda wa kawunan su zunuban da zasu halakar dasu, rayuwar su gabaki daya da kuma mutuwar su ta kasance aya ce akan Ruqayyah. Daga nan kuma sai suka tafi asibiti dan duba lafiyar Ruqayyah, wadda da kyar likitocin da suka yi mata aiki suka cire bullet din da Lukman ya saka a makogwaronta. Sai dai ana gama aikin ta fara convulsing, sannan kuma ta shiga coma. Coma din da har sai da yan uwa suka fara fitar da ran zata tashi sannan ta tashi, bayan watanni. A cikin watan farko police suka tsinci gawar lukman a cikin motarsa, gefensa da jaka cike da kudin da yayi withdrawing using check din da ya saka Ruqayyah tayi masa signing. Ya gama shirinsa kaf har da passport dinsa ya cikin aljihun sa yana niyyar barin gari. Bayan dogon zama da Ruqayyah tayi a asibiti, wanda a cikin sa ne yayanta manya suka dawo cikin rayuwarta da dukkan karfinsu, suna fatan wannan kulawar da zasu yi mata zai zamanto sanadiyyar kankare zunuban da suka dauka ada na watsar da rayuwar ta da suka yi. A lokacin ne kuma akayi bikin Hussain da gimbiya Fatiman sa. Problem din Ruqayyah shine, ta zamanto tamkar mutum mutumi, dama already doctors sunce tayi loosing her ability to talk, amma sai ya zamanto ta koma emotionless, tamkar jikinta ne kawai a duniya amma ruhinta is somewhere else, bata motsi, ko yatsunta sai dai a motsa mata su. Ko kayi mata magana ba zata yi responding ba ko da kuwa an saka mata hearing aid dinta. Sau da yawa sai dai kawai kaga hawaye yana zuba daga idonta, wannan ne kadai alamar da suke gani wanda yake nuna musu cewa she is there, amma Allah ya dauke komai daya bata. Ganin babu wani sauran abinda asibiti zasu iya yi mata ya saka aka tafi da ita gida, Baba da kansa yace a kaita gidansa duk da dai bata shiga da kafafuwan ta ta roki gafarar su ba kamar yadda yayi mata kwadayi, sai dai duk da hakan ma shi da Inna gabaki daya sunce sun yafe mata duk hawayen da ta saka su zubarwa, fatan su shine Allah ma ya yafe mata. Anan gidan Baba ta zauna, Hussain ya dauko mata kwararriyar maaikaciyar jinyar da aikin takawai shine kula da Ruqayyah, dan Inna Ade ba zata iya ba saboda jikin tsufa. Babu irin addu'a da ayoyin Alqur'ani da Inna bata rubuta ta bawa Ruqayyah ba, amma laifin Ruqayyah ba tsakanin ta da ubangiji bane ba, dan haka shi ba zai taba yafe mata ba. Bayan lokaci mai tsaho Ruqayyah tana a wannan hali sai Allah ya dauki ran Baba, a kwance akan gadon sa bayan yar karamar jinya, rasuwar Baba ce ta kawo Adam gari, sai a lokacin ya ga Ruqayyah kuma kallo daya yayi mata yace shi kam ya yafe mata duniya da lahira, ya kuma yi alkawarin zai yiwa Fatima magana akanta, but shi kansa bai san ta inda zai fara yiwa Fatima din magana ba, yana fara kame kamen sa akan maganar ta daga masa hannu tace "har abada ba zan taba yafewa Ruqayyah ba" daga ranar bai sake yi mata maganar ba amma sai yaji yana jin kunyar Hussain sosai, uwa ai uwa ce, ko yaya take kuwa. Rasuwar Baba da yan watanni Inna Ade ta bishi. Wannan ya tashi hankalin gabaki daya yayansu musamman Sumayya, sun zama kamar Hassan, babu uwa babu uba, gwara shima yana da aunty, karin tashin hankalin Sumayya kuma shine yadda taga Ruqayyah tamkar bata san anyi mutuwar ba, duk kuwa da cewa likita ya tabbatar musu da cewa tana sane da duk abinda yake faruwa, bata da ikon nunawa ne, bata da ikon yin komai. Mutuwar Inna ta saka yaran suka hadu da niyyar zasu mayar da Ruqayyah gidan Aminu a Abuja, amma sai Sumayya taki yarda tace ba zasu raba ta da yar uwarta ba, bisa amincewar Hussain sai aka dawo da ita gidan da take da, aka cigaba da biyan masu kula da ita sannan Sumayya tana shiga ta dan zauna da ita in Hassan baya nan, in kuma yana nan Amatullah tana shiga ta zauna da ita. A lokacin Sumayya ta fara farautar duk wanda tasan Ruqayyah ta zalunta tana rokar mata yafiya a gurin su. Wannan sun hada da iyaye da tsohon mijin Minal, duk da Sumayya bata tabbatar da abinda ya faru a lokacin ba, cikin ikon Allah Maman Minal tana nan da ranta sai dai babanta ya mutu, mijin ma yana nan sai tsufa daya saukar masa tunda ko a lokacin ma ba karami bane ba, kuma albarkacin Sumayya da kuma ƴaƴan Ruqayyah sai duka zo har gida suka ga halin da Ruqayyah take ciki kuma suka ce sun yafe mata. Bayan sun tafi ne Sumayya ta zauna tana rike da hannun Ruqayyah a cikin nata kamar yadda take yi a duk sanda suke tare, sai ta tuna itama tana daga cikin wadanda Ruqayyah ta zalunta one way or another, sai tace "Ruqayyah, bansan dalilin da yasa ubangiji yake hukunta ki haka ba, ban kuma san ko hukunci ne yake yi miki ko kuma jarabawar ki ce haka ba. Amma nasan bazan bar ki ba har sai mutuwa ta raba mu, ko ke kin tafi ko ni na tafi. I will always be by your side kamar yadda nayi miki alkawari. Ni dai a bangarena na yafe miki duk abinda kika yi min da wanda na sani da wanda ban sani ba. Kuma zan cigaba da bincikawa duk wanda nasan kunyi alaka dashi zan nemar miki yafiyar sa. Na fatan Allah yaji kanki ya dauki ranki haka nan ko kuma ya baki lafiya" Ga mamakin ta sai taga Ruqayyah ta motsa hannunta, hawaye yana fita daga idonta ta yi rubutu da yatsanta akan bedsheet kamar haka "Alive" Sumayya ta gane mai ta rubuta, cikin zakuwa tace "yes, Ruqayyah you are alive, gaki nan da ranki, yanzu ma alwala zanyi miki kiyi sallah" sai ta kuma rubuta wa "He is alive".. Gaban Sumayya ya fadi, waye He din? Wa Ruqayyah take nufi da he is alive? Mutum daya ne ya fado mata a rai, dan Hussain. A mike da sauri taa dafe kirjinta, dama tun a lokacin har kuma zuwa wannan lokacin bata taba jin cewa Ruqayyah zata iya kashe jaririn ba kamar yadda Hassan da Fatima suka dauka, amma ita kanta ta girgiza da cewa wai yaron yana raye kuma Ruqayyah ta sani tayi shiru duk wannan shekarun. Lallai ba karamin so ubangiji yaje yiwa Ruqayyah ba. Da sauri ta fita tana tunanin abinda zata yi da wannan bayanin, Hassan ta kira a waya ta roke shi yazo suyi magana a gidan su. Amma da yazo sai kunnuwan sa suka kasa gaskata masa abinda yaji Sumayya ta fada "You are not sure" ya fada dan baya son getting hopes dinsa up, "maybe tana nufin someone else, maybe bata san ma abinda ta rubuta din ba" Sumayya tace "maybe, maybe not, Allah ne kadai ya sani, ba zamu sani ba kuma sai mun bincika maganar" yace "bincikawa? Bayan duk binciken da mukayi a da da binciken da court tayi wanne kuma zamuyi?" Tace "I don't know. Amma mu munyi namu ne, mu bar wa yaran nan ragama yanzu suma suyi nasu". A daren suka tara taron yayansu kaf har Amatullah, aka kira Hussain a Skype sannan Sumayya tayi musu bayanin abinda Ruqayyah ta rubuta da kuma ita abinda take tunanin hakan yana nufi. Tace "I may be wrong. Amma ina son ku hada kawunan ku a guri daya ku bincika maganar dan mu tabbatar da gaskiyar ta ones and for all" Hassan yace "Please, if he truly is alive, find him and bring him home" sai kawai ya kwanta a jikin kujera hawaye yana bin fuskarsa, abinda yayan basu taba gani ba. Washegari Hussain yayi shiri ya taho Nigeria, sannan suka kuma haduwa sukayi bitar maganar kowa yana kawo shawarar sa ta yadda yake tunanin za'a yi, yayin da Sumayya kuma ta sake komawa gurin Ruqayyah da fatan ko zata kuma yi mata wani sign din amma babu, abinda Allah ya bata ikon yi kenan for now. Sauran aikin kuma nasu ne. Abdullahi ne ya karbo musu police record na accident din, Aminu kuma a matsayin sa na maaikacin environment sai ya binciko musu dai dai spot din da akayi accident din, suka shirya gaba ki dayan su suka tafi gurin, da kyar suka samu an kaburburan duk sun shafe saboda shekaru, sai gwangwanin motar da suka gani a gurin wanda sun san da a cikin gari ne da tuni yan gwangwan sun dauke shi. Suka dauki gps din gurin sannan suka koma gida. Daga nan kuma sai suka satellite image na location din, suka saka gps din ya nuna musu exact spot din da suka je, sannan suka tuna cewa according to record din court, Ruqayyah tayi awa daya bayan anyi accident din kafin ta kira Hassan. A jikin satellite image din nasu suka yi mapping area din da za'a iya zuwa a kafa a dawo a cikin awa daya. A wannan area din ne Ruqayyah zata iya ajiye yaron ta kuma dawo gurin accident din kafin ta kira Hassan. Bayan sun dauki circumference din gurin, sai suka fara bin features din da suka fada cikin cycle din nasu one after the other suna tattauna possibility din kasancewar a can aka ajiye shi. Mostly gurin daji ne sai duwatsu, sai wani kauye can da nisa wanda suka dauke shi a matsayin suspected point dinsu, har zasu rufe system din kuma sai suka lura da wani gini da yake can karshen circle dinsu, Hussain ya saka hannunsa yayi zooming hoton building din, sannan Yusuf ya karanta sunan da yake saman gate din. "National Orphanage......" Bai karasa ba ya dago yana kallon yan uwansa, orphanage, of course orphanage is a perfect spot da za'a batar da jariri, babu wanda zaiyi cigiyar sa tunda kowa ya ganshi a kofar gurin abinda zaiyi tunani kawai shine uwarsa ce tayi cikin shege ta haife shi ta kawo shi nan ta ajiye. Basa son su tayar da hankalin babansu dan haka basu gaya masa ba suka bar maganar a tsakanin su da niyyar gobe zasu tafi Abuja suje orphanage din gabadayan su zasu binciki maganar, duk da dai sun san in ma can ne aka ajiye shi to tabbas yanzu baya can din, koma a ina yake indai yana raye to yanzu ya zama cikakken mutum, maybe ma yayi aure, maybe ma ya haihu...... A ranar babu wanda yayi bacci a cikin su....... Kamar yadda a ranar Amir ya kwana bai yi bacci ba saboda mafarkin da yayi........ *The Email* Yayi juyi yana shafa empty space din kusa dashi sannan yayi tsaki. Sai yanzu ya tuno dalilin da yasa yayi wannan mafarkin, dalilin da yasa yayi mafarkin mahaifiyar sa. Da dare kafin ya kwanta sunyi rigima da matarsa, rigimar da ta saka har suka raba gurin kwana, abinda basu taba yi ba tunda suka yi aure kullum tare suke kwana in dai har suna gida daya. Ya lumshe idonsa tare da sake karanto addu'ar bacci. Amma baccin da bai koma ba kenan. "What if it is not a dream but a memory?" Memory na ranar da mahaifiyar sa ta yar da shi. Memory na ranar da aka haife shi. Yayi ta kokarin ganin ta tuno da fuskar matar daya gani a mafarkin sa amma ya kasa. A haka har assuba ta riske shi Yayi juyi, tare da jan dogon tsaki. Ba zai iya tuna ranar da ya kwana tun daren Allah har safiyar Allah ba tare da ya ko da rintse idonsa da sunan bacci ba sai yau. Haushin A'isha yake ji dan yana ganin duk itace silar mafarkin sa. Me yasa? Me yasa zata yi masa haka? Me yasa zuciya take baci sosai idan wanda ta rike abin so ya kasance wanda yake bata mata? Jin kiran Sallah ya saka shi ya mike ya zauna a bakin gado tare da dafe kansa da hannu bibbiyu, sara masa kan yake yi goshinsa yana barazanar tsagewa kwakwalwar sa ta fito. Jikinsa gabaki daya ciwo yake yi saboda kwana da yayi yana juyi, Why? Ya tambayi kansa a karo na babu adadi kuma duk da yasan cewa shi dai bashi da amsar tambayar tasa, bashi da amsa kuma bai san wanda zai amsa masa ba bai kuma saka ran cewa zai sami wanda zai amsa masa din ba. Tunda ya bude idonsa a duniya ya fahimci shi din yana da bambanci da sauran yara amma bai fahimci menene bambancin ba. A lokacin da hankali ya fara shigar sa a lokacin ya fahimci banbancin ya samo asali ne daga bambancin asalinsa dana sauran yara amma kuma bai san asalin nasa ba ballantana ya gane a inda banbancin yake. Sai daga baya sannan kalmomin suka fara sinking a cikin kansa, gidan marayu, Maraya, dan tsintuwa, yasashshe, shege, marar asali, tsintacce. Wadansu kalmomin ma karamar kwakwalwar sa alokacin kasa dauka tayi sai daya hada da tambayar wadanda suka girme shi suka yi masa bayani inda a karshe suke hada wa da "kamar dai kai kenan" "Amir in akace marar asali a na nufin wanda ba asan iyayensa ba ko kuma wanda ba'a san daga inda iyayensa suke ba, kamar kai kenan" "Kalmar yasashshe tana nufin wanda iyayensa suka yar dashi saboda basa sonsa, misali jaririn da aka haifa sai uwarsa ta yar dashi ta gudu, kamar kai kenan" "In aka ce shege Amir ana nufin wanda aka haifa ba tare da iyayensa sunyi aure ba, irin wadannan yaran ba'a san su dan sau da yawa akan jefar dasu dan gudun abin kunya, kamar dai yadda aka jefar da kai" A lokacin abinda kansa yake dauka kawai shine duk wadannan kalmomin suna da dangantaka dashi. Sai da ya kara girma sannan takanas yaje office din shugaban orphanage din wanda yayi masa bayani sosai har ya fahimci cewa shi din uwarsa ta yar dashi ne a ranar data haife shi ba tare data ko tsaya ta yanke masa cibiya ba, ta hada dashi da mahaifarsa ta yar a kofar gidan marayu tsirara ko zani bata saka ta lullube shi ba. Wannan ya saka dole yake amsa wadancan sunayen da ake kiransa dasu. Dole, tunda iyayen sa sun riga sun zabar masa Wadannan sunayen duk da cewa basu samu damar zabar masa sunan yanka ba. Tun daga ranar daya fahimci wannan sai ya saka a ransa cewa yana son sanin dalili, ya saka a ransa yana son sanin iyayen sa dan ya kalli cikin idanunsu ya tambaye su "why?" Me yayi musu sukayi mishi kallo daya sukayi deciding basa sonsa? Suka yanke wa zuciyarsa hukuncin daurin talala na har abada? Amma sai Allah almusawwiru ya juya lamarin sa ya aiko masa da yaron da har yau da suke magidanta bayan tsahon shekaru ya kasa yanke hukuncin menene matsayinsa a gurinsa. Abubakar Sadiq sunansa, Sultan ake ce masa, jika ne shi a gurin sarkin garin Abuja a wancan lokacin. Sun hadu ne a lokacin da kakansa wanda shine ya yi wa Amir huduba da sunan sa "Abdullah" sannan kuma yayi masa inkiya da Amir, yazo ziyara gidan marayu kuma ya taho dashi.... "Hi, can we play together? My name is Sultan. Will you like to be my friend?" Da wannan friendship din ya fara, daga nan sai amintaka mai karfi sai kuma yanuwantaka wadda Amir baya jin ko da ace jini daya ne yake gudana a jikin su su biyun zaiyi masa irin son da yake yi masa tun daga lokacin har yanzu. Wannan soyayyar ce ta saka shi sarki Abdullahi wanda yake kakan Sultan yayi adopting Amir ya mayar da shi gidansa a matsayin dansa, ya hada su da jikan nasa ya rike su tare. Ta sanadiyyar Sultan Amir ya samu ilimi, na muhammadiyya dana boko, ya kuma sami family, duk kuwa da cewa kaf family din babu wanda bai san asalin shi ba kuma lokaci zuwa lokaci ana tuna masa a cikin bakar magana musamman idan aka ga yana kokarin shiga cikin abinda ake ganin bai shafe shi ba. Wannan ya saka ko dai dai da rana daya bai taba manta asalinsa ko kuma muce rashin asalinsa ba. Kuma bai taba boyewa ba, sai ya mayar dashi tamkar identity dinsa yadda duk wanda ya san shi sai ya tabbatar cewa yasan ko shi waye saboda kar nan gaba kayi kokarin robbing abin a fuskarsa, bai taba boyewa ba kamar yadda bai taba goge murmushi daga fuskarsa ba duk kuwa da irin tarin wahalwalun rayuwa da suka gani tare shi da Sultan, har gidan kangararru sai da suka je suka zauna bytsahon shekara guda, sai da suka rasa kowa suka rasa komai amma basu rasa junan su ba har zuwa ranar da Allah ya gyara rayuwar Sultan ta hanyar hada shi da bafulatanar yarinya *Maimoon*, gyaran Sultan sai ya kawo gyara shima a tasa rayuwar, ya nutsu ya ajiye shaye shayen da da suke yi tare da Sultan sannan ya karbi aiki a sabon office din Sultan "Moon Construction Company" sannan kuma yayi aure, ya kuma samu karuwar yaya biyu, na farko mai sunan amininsa Abubakar, wanda suke kira da Sultan kamar yadda ake kiran wancan, sai kuma jaririyar da aka haifa yanzu, Auren da aka sha gwagwarmaya kafin samuwarsa saboda wannan tambarin nasa na rashin asali, sai da Sarkin lokacin, Sarki Sadiq, mahaifin Sultan, ya shiga maganar sannan kuma itama yarinyar "Aysha" ta dage tace "ni ina sonsa a haka, duk da bashi da asali ni ban damu ba" and so it came to be. Wannan ne kuma abinda yake soya zuciyarsa a yanzu idan ya tuno kalamanta na jiya "ka manta halaccin da nayi maka? Ka manta yadda na rufe ido na na aure ka duk da kasancewarka marar asali amma sakayyar da zaka yi min kenan? Ka rasa abinda zaka saka min dashi sai kishiya Amir" Wannan maganar tata, a ganinsa ita ce dalilin mafarkin sa..... Ta fada masa hakan ne kawai dan ya nuna mata yana tunanin maybe zai kara aure, bai tabbatar ba tunda har yanzu yarinyar da yake nema *Aisha Humairah* bata bashi wata cikakkiyar amsa ba amma a ganinsa gwara ya gaya wa iyalinsa su san da maganar kar suji a wani gurin kuma azo a samu sabani, he thought he was doing the right thing, amma yadda tayi reacting shine sanadin da ya saka shi a halin da yake ciki a yanzu. Ya tashi ya koma toilet ya kunna wa kansa shower, yana so yasamu ya watstsake maybe ko mafarkin zai fita daga ransa, sannan sai ya dauro alwala ya zo ya saka rigarsa zai tafi masallaci, har ya wuce kofar dakinta sai kuma ya dawo da baya yayi knocking sannan yace "ki tashi kiyi sallah" sai kuma ya wuce. Bayan an ida da sallar bai bar masallacin ba sai yaja Alqur'ani ya fara karantawa a can edge inda masu shige da fice ba zasu dame shi ba. Sai daya dago kai yaga garo yayo haske sosai sannan ya yi adduoin sa ya tashi. Baya son ganinta, gani yake inya ganta ranshi baci zaiyi, sai yaji ina ma zai iya tafiya office da kayan jikinsa da kawai mota zai kunna yayi tafiyar sa, amma ba zai iya ba, dole ya shiga gidan nasa, yana jin motsinta a kitchen daga dukkan alama breakfast take hada wa, on normal days, kitchen din zai bita su kammala hada abincin tare ko kuma yaje ya shirya little Sultan, first born dinsu, amma yau sai ya wuce war sa dakin sa ya fara shiryawa. Yana jin ta ta bude kofar dakin ta shigo ta tsaya daga bakin kofa amma bata karaso ba, ya juya yayi mata kallo daya ya dauke kansa. Ta zagayo ta gabansa ta zauna a bakin gado tana kallon yadda yake ta fama da links din hannun rigarsa. Tace "ina kwana?" Bai kalle ta ba yace "lafiya" sai ta tashi ta kama hannun tana saka masa "kayi hakuri dan Allah Abban Sultan. Nasan na fada maka maganar da bai kamata ace na gaya maka ba, ba nufi na in bata maka ba raina ne ya baci kawai, ban ma san me nake fada ba. Dan Allah kayi hakuri" Ya bar inda take ya dauko turare yana sakawa kansa yace "abinda yake ranki kika fada, there is nothing more to it" tace "ba abinda yake raina ba kenan, wallahi ba abinda yake raina ba kenan, tunda muke tare da kai ka taba jin na fadi magana makamanciyar wannan? Dan Allah kayi min uzuri mana ina kishin kane shi yasa. Babu matar da take son mijinta kuma yace zai yi mata kishiya sannan ace ranta ba zai baci ba" ya juyo yana kallonta yace "in rai ya baci kuma sai hankali ya gushe? It is okay, at least na san irin kallon da kike yi min yanzu" sai ta zauna a bakin gado ta fara kuka, "haba Amir, ka yiwa zuciyata adalci mana, ni fa aka bata wa, ni fa kake kokarin yiwa kishiya kuma sannan kaine mai fishi ni ce mai bayar da hakuri? Ka bar ni inji da abu daya mana?" Ya fahimci abinda take so tayi, tasan sanyin zuciyarsa musamman in yaga mutum yana kuka, mutum din ma ace matarsa uwar yayansa, so take ta karya masa zuciyarsa ya sauko daga fushin da yake yi. Ya dauke kai ya fita ba tare da ya lallashe ta ba ko kuma yayi mata wata magana. Yana fita yaga Sultan da cup a hannunsa yana shan tea, ganin ya fito ya saka yaron ya ajiye cup din hannunsa ya taho da gudu ya rungume shi "Abhi, yau ni na saka kayana da kaina" Amir yayi murmushi tare da sunkuya wa dai dai tsahon yaron yana gyara masa neck tie dinsa yace "kayi kyau kuma sosai, just like the handsome gentleman that you are. Kayi breakfast?" Yace "eh na sha tea" Amir yace "to ina baby?" Sultan yayi dariya "tana bacci a daki, Ammi tace in na tashe ta sai ta zane ni" Amir ya mike yana rike hannunsa yace "zo muje mu tashe ta muce mata good morning kafin mu fita" Dakin Aysha ya tafi gurin jaririyar yarsu da a wannan satin ne suka dawo daga wankan jegon haihuwarta da Aysha ta je. Ya tsaya yana kallon babyn tana ta baccin ta a cikin crib dinta, ya saka hannu ya shafa gashin kanta yana kara mamakin hasken fatarta kasancewar daga shi har Aysha ba farare bane ba, ko a ina babyn ta samo fari har haka? Shin hakan yana nufin wani daga cikin iyayen sa fari ne? Ya tuno matar da ya gani a cikin baccin sa jiya, wadda ya saka a ransa cewa itace mahaifiyar sa, fatarta bata kai ta baby Afnan haske ba. Ya dauki yarinyar ya daga ta tayi mika sannan ta bude idon ta tana kallon sa, yace "good morning angel, how is the most beautiful girl in Abuja" ta dan tabe baki irin na jarirai, sai kuma kamar an saka mata battery ta fara tsandara kuka. Sultan ya ja baya yana rufe baki. "Babu ruwana Abhi, Ammi zata zaneka babu ruwana" ya juyo ya ganta a tsaye a bakin kofa, in normal days ta tuni ta shigo ta fara korafin ya tashi baby Afnan amma yau sai yaga tayi shiru, ya lura da yadda idon ta yayi alamar kuka, sai ya ajiye jaririyar ya kama hannun Sultan yace "let's go" kafin su fita tace "abinci fa?" Bai juyo ba yace "na koshi" Sai da ya ajiye Sultan a makaranta sannan ya wuce office, cikinsa yana ta karar yunwa, Aysha yake punishing amma nasa jikin ne yake gaya masa. Shi baiga dalilin da zai sa ta wani rikice har tana gaya masa maganganu ba. Shin dan shi bai kasance mai asali ba sai ya zama ba cikakken namiji ba kenan? Sai ya zamanto shi bashi da wannan damar da Allah ya bawa maza na auren mata daya zuwa hudu? Ya tuna da Aisha, yarinyar kirki, shi kansa bai tabbatar idan soyayya ce yake yi mata ko kuma tausayi ne, tun ranar da ta bashi labarin ta, tun lokacin da tasa matar ta tafi gida wankan jego, sai yaji kamar akwai wani link a tsakanin su duk da bai san wanne irin link bane ba, maybe ya na da nasaba da yadda mutane suke treating dinsu saboda abinda ba su suka dora wa kansu ba. Ya tarar da aiki a office kamar kullum, dan kusan babu ranar da ba'a kawo musu sabuwar kwangila ta gina gida ko masana'anta ko kuma wani abu daban, hakan kuma yana da dangantaka da irin aikin da suke yi mai kyau da inganci. Wannan aikin daya riƙe shi shi ya fara mantar dashi da damuwarsa, a haka har Aisha ta kira shi ta sanar dashi cewa ta gama da school, ya riga ya sabar mata da cewa duk sanda ta tashi daga school shi zai mayar da ita gida kuma baya son ya saba wannan alkawarin dan haka ya dakatar da sauran abubuwan da suke gabansa ya dauki mota ya fita daukan ta, daga nan kuma yana son yaje ya bawa Dr Maimoon labarin mafarkinsa yaji nata view din akai, shin tana ganin mafarki ne ko kuma memory ne? Sai dai a cikin saurin da yake yi ya manta wayarsa a office din nasa, wayar da dama babu isasshen charge a cikin ta. A daidai lokacin ne kuma mota dauke da Yusuf, Hussain, da Abdulrahman ta sauka daga kan titi zuwa karamar hanyar da ta tafi zuwa gidan marayu na kasa. Fuskokin su cike da tsoro tare da fargabar abinda zasu tarar. Sanda zasu taho sai da sukayi drama da Hassan, yace lallai sai sun gaya masa inda zasu je su kuma basa son su gaya masa matsayar maganar su dan kar su tarar da abinda ba zai faranta masa rai ba, gwara daga baya in sun samu good news sai su gaya masa. Jin ba zasu gaya masa abinda suke shiryawa ba ya saka ya ce ba zasu taho gabaki daya ba, dole wasu daga cikin su suka hakura. Zuciyoyin su cike da zulumin abinda zasu tarar suka yi packing suka fito suna karewa gida marayun kallo, tare da lodin yaran da suke zazzaune guri guri, ƙanana da manya, mata da maza, suna mamaki cewa akwai possiblity na cewa da ɗaya tilo na Hussain Aminu Abdullahi anan gidan cikin wadannan yaran ya tashi, hakan yana nufin da yawa daga cikin yaran nan suma kowa da akwai nasa story din. Sai suka ji a ransu suna fatan ba'a nan din bane ya tashi, suna fatan they are wrong, amma kuma wata zuciyar tana tuna musu da cewa kasancewar yayi rayuwa anan shine zai taimaka musu wajen gano inda yake anan a yanzu. Tambaya suka yi aka nuna musu office din shugabar gurin, an elderly lady, wadda ta tarye su cikin murmushi da karramawa tana fatan zuwa suka yi suyi adopting one of the kids, ko kuma zuwa suka yi su kawo musu donations dan taga alamar da maikomaiko a jikin su. Ta basu kujeru suka zauna sannan itama ta zauna tana kara yi musu sannu da zuwa, a ranta tana lura da wani yanayi a tare da su wanda ta kasa placing a zuciyarta. Suka sake gaisheta, sannan Yusuf yace "tambaya muke dan Allah. Shekaru talatin da biyar da suka wuce, ranar goma ga watan January, ko kun tsinci jariri ko kuma an kawo muku jariri gidan nan?" Matar ta saki baki tana kallon sa, sannan ta bi sauran samarin da kallo tace "shekarun da yawa ai" Hussain yace "shekarun da yawa Hajiya. Adadin shekaru na kenan a duniya" Abdulrahman yace "ba kwa keeping records? Na dauka duk yaron da aka kawo muku zaku bude masa file inda zaku ke saka bayanan sa na tsahon zaman da yayi a tare da ku da kuma inda ya tafi bayan ya barku" ta gyada kai tana kallon wasu tsofaffin drawers din da suke ajiye a gefe, takardu suna lekowa daga ciki saboda tsabar cika da drawers din suka yi. Sai tace "za'a iya samu a cikin takardun can, amma aikin da yawa" Hussain ya mike yana nannade hannun rigarsa yace "ta ina zamu fara? Idan bamu gama yau ba sai mu dawo gobe, ba zamu bar garin nan ba sai mun sami tabbacin in ya zauna anan ko kuma bai zauna ba. Daga nan zasu san daga inda zamu dora" Haka akayi, mazan uku plus ma'aikatan gurin suka yi dai dai da takardun gurin, amma har suka zo karshe basu tarar da na shekarar da suke nema ba, "shekarun da yawa" matar ta maimaita. Yusuf ya mike yana goge gumin fuskar sa da hanky dinsa yace "babu wasu takardun?" Ta girgiza kai. "Shekarun da kuke magana akai tun kafin in fara aiki anan ne, nima wadannan takardun su kadai na tarar, ina tunanin lokacin da akayi sababbin gine gine ne aka rasa takardun" Hussain ya zauna yana buga hannun sa a hankali a kan table, sannan yace "a cikin ma'aikatan ku, babu wanda kike ganin zai kai shekarun nan yana aiki a gurin nan?" Ta dan dafe goshinta tana tunani sannan ta dago kanta da murmushi tace "akwai Baba asabe, tafi kowa dadewa a gurin nan ta kuma fi kowa sanin yaran da aka raine su a gurin nan" Sai ta aika aka kirawo dattijuwar da aka kira da Baba Asabe, ta shigo tana gyara gilashin idonta tare da kikkifta ido tana kallon bakin, sannan tace "Sarki, kaima shafe shafen nan na zamani ka fara ne? Dan dai ince na dawo da auren to bana yi nima" duk sai suka tsaya suna kallon ta, Madam marry tace "Baba Asabe ba Amir bane ba fa? Ko dai idon ya karasa mutuwa ne?" Baba Asabe ta murza idonta tace "ke ashe ba shi din bane ba, har zance ina tarin gashin ya tafi? Na dauka yaji fada na yaje ya aske" Yusuf yace "Sarki? Baba waye sarki? Jikan ki ne?" Sai Madam marry ta mike tsaye, sai yanzu ta fahimci abinda ta gani a tare dasu wanda ta kasa fahimta, gabadayan su suna kama da juna kuma suna kama da Amir, daya daga cikin wadanda ta hannun su ne orphanage din yake cigaba da running har zuwa yanzu. "Amir" ta fada, "Amir kuke nema" ta maimaita. Duk duka mike suma suna kallonta. "Waye Amir din kuma yaushe aka kawo shi gidan nan? Yana ina yanzu? Ya akayi kika san shi muke nema" suka jero mata tambayoyin a tare, ta kalle su daya bayan daya tana jin hawaye yana sauka daga idon ta, tace "ban san ranar da aka kawo shi ba dan ban ma same shi a gidan nan ba. Na dai san cewa duk daga inda kuke ku yanuwansa ne, na kuma san cewa yana daga cikin yaran da aka yaye daga gidan nan wadanda har yau basu fitar da ran samun iyayen su ba". Abdulrahman ya zauna yana dafe kansa, yana jin kamar hawaye zai zubo masa. Yusuf a hankali yace "where is he?" Madam Merry tace "he was here last week, akan wannan kujerar da kake zaune a zauna, he was asking me ko anzo neman sa kamar yadda yake yi duk sanda yazo gidan nan" Hussain yace "ranar goma ga watan January aka kawo shi?" Baba asabe da take tsaye tana bin su da kallo kuma tana jin abinda suke cewa tace "ban san kwanan matan ranar da aka kawo shi ba, na dai san cewa ranar juma'a ne" Hussain yace "yes! Juma'a ne. A ina aka same shi?" Tace "da magariba, muna kokarin raba wa raya abincin dare muka ji kukan sa a waje, muna lekawa muka ganshi a kasa, cikin kasa da duwatsu, babu ko riga a cikin sa" ta goge guntun hawayen daya fito mata tace "ko cibiya ba'a yanke masa ba, ko zani ba'a saka an rufe shi ba duk kuwa da sanyin da akeyi a lokacin". Hussain ya zauna shima, how can their mother be this cruel? Anya ma kuwa akwai zuciya a cikin kirjinta? "Where is he?" Ya sake maimaita wa, yana tuna wa kansa cewa tunda tace he was here last week, hakan yana nufin he is alive kenan. Baba Asabe ta zauna akan daya daga cikin kujerun robar da suke gurin, tana kallon sa tace "yayanka ne?" Ya girgiza kai yace "kani na ne" tace "babarku bata da imani, ko kadan bata da imani" Hussain ya gyada kai cikin gamsuwa yace "haka ne Baba, bata da shi" ta cigaba "kuma tayi babbar asara na jefar da yaron nan da tayi. Yaron kirki ne, jarumi ne, bana jin gabaki dayanku wadanda bata yar din ba bana jin a cikin ku akwai wanda ya kai shi, bana jin akwai irinsa a cikin ku " Hussain ya girgiza kansa yace "babu, shi din na daban ne, special ne" ya kuma goge hawayen ta "ya jima yana neman ku, me yasa baku neme shi ba sai yanzu?" Yusuf yace "rashin sani Baba, bamu san yana raye ba da ko gida gida zamu bi a abuja sai munbi mun nemo shi" Baba Asabe ta kuma cewa "bata gaya muku ta yar dashi ba kenan, wannan wacce irin muguwar uwa ce haka? Amma dai ku baku yi kama da mugaye ba, amma dai ba ita ta raine ku ba ko?" Hussain yace "ba ita bace ba, ba kuma ita ta haife shi ba, sace shi tayi daga hannun wadda ta haife shi ta kawo shi nan ta yar". Sai gurin yayi shiru, gaba daya jinjina girman laifin Ruqayyah suke yi, "ina yake yanzu" Abdulrahman ya sake tambaya yana kallon Madam Merry, ta jawo wani file gabanta tace "akwai address dinsa anan da phone number dinsa da komai, duk sanda ya kawo donation muna rubutawa" Hussain ya mika hannunsa da sauri amma sai ta janye file din tace "amma ba zan baku ba" gaba-daya suka hada baki "why?" Tace "saboda haka dokar mu take, for security purposes, ba wai bamu yarda da ku ba dan kamannin ku kadai sun tabbatar mana cewa ku yanuwansa ne, amma still we gave to be careful" Yusuf yace "to amma in baku gaya mana inda yake ba ta yaya zamu same shi?" Tace "a ka'ida sai mun nemi izinin sa kafin mu gaya muku komai a kansa, shi zai yanke shawarar in yana so ya ganku ko kuma in baya so ya ganku" Hussain yace "amma kince last week ma yazo nan yana tambayar ko anzo neman sa, meaning yana son ganin mu kenan" Tace "still dole mubi protocol" sai ta dauko wayarta tana dialing number, duk zuciyoyin suna bugawa da karfi sanin cewa number dinsa take dialing, suna jin karar ringing din daga inda suke har suka ji karar wayar ta katse bai dauka ba, ta sake kira still bai dauka ba. Hussain ya gyara zamansa "zamu jira, in yaga kiranki ai zai kira back ko?" Tace "eh zai kira" Abdulrahman yace "then we will wait" Sai Yusuf ya juya yana kallon Baba Asabe yace "ki bamu labarin sa mana, ya yake? Ya Rayuwar sa take tafiya? Ta danyi murmushi tace "fitinanne ne, baya jin magana" sai suka yi murmushi gabaki daya, Madam Merry tace "he had had a rough life, a good life kuma" Baba Asabe tace "har zaman gidan kangararru yayi. Amma kuma america yayi karatun sa tun daga secondary har masters" Hussain yace "america?" Tace "eh. Ai shekaru hudu kawai yayi a tare damu anan, sarkin Abuja ne ya dauke shi daga hannun mu, ya gada shi tare da jikansa ya rike su tare" Yusuf yace "sarki Sadiq?" Tace "aa babansa, babansa, shi yayi masa yanka ai kuma ya saka masa sunansa" Hussain yace "Abdullah" he just can't wait ya bawa Fatimah duk wadannan labaran. Bai ma san ta inda zai fara bata labarin ba, ko kuma ya bari sai shi wanda aka kira da Amir din yaje har gabata sai ya bata labarin da kansa? Yes, haka shine ya dace. Abdulrahman yace "amma yanzu how is he?" Madam Merry tace "very good. Yayi aure, yana running a private company" sai duk sukayi murmushi hankalin su yana kara kwanciya, at least sun san cewa bai tagayyara ba, at least yana yin rayuwa mai kyau duk da dai sun san cewa abinda Ruqayyah ta dauke a cikin rayuwar sa ba zata taba iya dawo masa da shi ba. Ta sake daukan wayarta ta kuma kira, still babu ansa, sai kuma data kuma kira taji a kashe. "Dan Allah" Hussain ya roketa, ki gaya mana inda zamu same shi" ta yi shiru tana binsu da kallo daya bayan daya tana deciding ko da karya doka a kansu. Fuskokin su cike da dokin ganin dan'uwan su, sai ta jawo wata takarda a gefe tayi rubutu a ciki ta mika musu. Yusuf ya karba yana dubawa, e-mail address ne a jiki, tace "e-mail dinsa ne, kuyi contacting dinsa, shi zai yanke shawarar in yana son ganin ku or not" Hussain ya fara kokarin nuna kin amincewa da hakan, shi gani yake tunda gasu a Abuja kuma shima ance yana abujan nan me zai saka su tafi gida basu ganshi ba? Amma sai Yusuf yayi musu bayanin da cewa hakan is the best, sun san yana nan kuma yana lafiya, sun kuma samu e-mail address din sa, that's more than abinda suka saka ran samu. In suka je gida suka hadu da iyayensu da sauran yan'uwa sai suyi maganar best way da zasu yi contacting din sa. Bayan sun bar orphanage din suka je gidan Aminu, wanda shi yana Kaduna a lokacin amma iyalin sa suna nan suka ci abinci suka yi sallar sannan suka kira waya Kaduna suka bada labarin information din da suka samu. Sai dai sunyi shawarar kar a gaya wa Hassan "zai iya dauko mota yanzu ya taho Abuja har fadar sarki ko ya fara bi yana knocking gidajen mutane yana neman mai suna Amir" Hussain yace "that's not a bad idea though, muje fadar, a can zamu samu duk bayanan sa da muke bukata, ko kuma ma mu ga shi a can din, yanzu haka ma maybe yana can as muna wannan discussion din" Yusuf yace "I know, but kamar yadda matar nan ta fada, mu fara contacting dinsa first mu kuma nemi iznin ganinsa daga gurinsa tukunna, mu bi komai a sannu insha Allahu zamu samu maslaha" haka suka dauki hanya suka koma Kaduna. Suna isa Kaduna suka sake wani zaman, yanzu harda Sumayya da Hassan suka kuma fayyace musu duk abinda suka yi finding a Abuja. "Maybe ba shi bane ba. Tunda basu rike date din ba kuma babu file" Hassan ya fada, wata zuciyar tana gaya masa ya tafi a Abuja a daren nan yaje ya makure wannan Madam din har sai ta kai shi inda dan Hussain yake. Hussain yace "Daddy shine, yadda matar nan tayi reacting kadai ya tabbatar mana da cewa shine" Hassan ya juya kan Sumayya yace "har yanzu bata kuma rubuta komai ba?" Tace "bata rubuta ba" suka mika masa e-mail din. "Yanzu abinda ya kamata muyi shine mu aika masa da sako mu nemi yazo nan ko kuma ya bamu izinin zuwa can mu same shi, anan zamu tabbatar da cewa shine ko kuma ba shi bane ba" Hassan ya kalli Hussain yace "kar ka gaya wa Fatima komai" ya gyada kai cikin fahimta. Sannan Hassan ya mike da takardar a hannun sa ya hau sama. Ranar ko saukowa kasa cin abincin dare bai yi ba. Sumayya ita ma ta samu ta ja jikinta ta bi mijinta dan taga alamar su yaran ba yanzu zasu tashi daga zaman ba, da plans kawai suke tayi na irin taryar da zasu yi masa idan yazo da yadda zasu yi ta yawo dashi suna nunawa mutane. A zaune ta tarara da Hassan ya saka computer a gaba amma hankalin sa baya kanta, sai da tayi waving hannunta a kusa da fuskar sa sannan ya juyo yana kallon ta, ta zauna a kusa dashi tana matsa masa hannun sa tace "shi yasa su ka ƙi gaya maka maganar nan tun jiya, sun san tayar da hankalin ka zakayi akan maganar" yace "dole in tayar da hankali na Sumayya, kin fi kowa sanin matsayin yaron nan a gurina. Gidan marayu fa akace ya tashi fa Sumayya, dan Hussain, his only son, the sole heir to H and H" ta girgiza kanta tace "amma kuma sai suka ce ya tashi a gidan sarautar Abuja, yayi karatu a america, yanzu kuma yana running private company" yace "not his father's company" yace "haka ne, amma ba'a titi yake yana bara ba, ko a bola yana shaye shaye. Bana son kana saka damuwa a ranka, in kana cikin damuwa gabaki dayan mu ni da yara ba zamu kasance cikin farin ciki ba" ya kirkiri murmushi yayi mata yace "na sani, kuma na gode Allah da duk ni'imomin sa gare mu da kuma gare shi shima. Ina tsoron kawai kar ya zamanto bashi bane ba, bana jin zuciya ta zata iya dauka" tayi murmushi tace "Habibi, zuciyarka is stronger than you think, ta dauki abubuwa da dama a lokacin da kake tunanin ba zata iya dauka ba. Amma insha Allah, wannan ba zai zama daya daga cikin su ba" sai ya bude takardar yace "me zance mishi?" Ta karba tana dubawa tace "ka bar min, ni zan tura masa da sakon, zan san abinda zan gaya masa" ya gyada kai yace "shikenan, na gode Sumayya, Allah yayi miki albarka". Da kyar ya samu yayi bacci a ranar, amma ita kuma bata yi baccin ba tana ta tunani akan maganar, akan wannan yaron da aka kira da Amir da kuma irin girman laifin da Ruqayyah ta aikata masa. Bata jin hakkin sa zai bar Ruqayyah tayi kwanciyar kabari lafiya ballantana kuma in an tsaya hisabi a tsakanin su, tana so ta taimakawa yar uwarta in any way that she can indai har taimakon nata ba zai kaucewa iyakar ubangiji ba. Menene ya kamata tayi? Tabbas dawowar Amir gida wani abu ne da zai rage nauyi daga cikin nauye nauyen da suke kan Ruqayyah, amma babu guarantee din in ya dawo din zai yafewa Ruqayyah, but she is going to try, duk da bata san halinsa ba bata san irin zuciyarsa ba amma tasan Hassan yana da zuciya amma ganin irin yadda Allah ya matar da Ruqayyah kawai ya saka yace ya yafe mata da bakinsa ba tare da kowa ya matsa masa ba. Maybe, just maybe shima wannan yaron ya kasance haka. Maybe in ta samu hanyar da zata fara hada shi da Ruqayyah first, ya fara jin labarin Ruqayyah da laifin data aikata gare shi da kuma irin sakayyar da Allah ya fara yi masa tun few minutes bayan ta aikata masa laifin da duk irin masifun da ta ringa gamuwa dasu through out all these years, maybe hakan ya sanyaya zuciyarsa a kanta. In yaji labarin ta kuma sai ya ganta a zahiri, yaga yadda Allah ya mayar da ita saboda hakkinsa......................,waya sani ma ko ya taimaka gurin bawa Fatima hakuri? Amma ita kanta tasan she is asking for too much. Amma tausayin yaruwarta take yi, tun ranar data rubuta he is alive da hannunta take kwana ta wuni taba hawaye, yau ma wuni tayi tana hawaye, sautin kukan ma babu, hannun da zata share hawayen nata dashi ma babu, tayi ta tambayarta inda ta ajiye babyn tana kuma lura da yadda take stressing kanta gurin kokarin fada, gurin kokarin rubuta wa da hannun ta amma ta kasa. Bata da sauran hanyar da zata bi gurin neman gafara, sai dai mutum in ya ganta shi da kansa imani ya saka yaji ya yafe mata kamar yadda Hassan yayi, dan haka ita Sumayya zata zama bakinta, ita zata nema mata gafarar ko da kuwa zata kaita ga durkusa wa ne ko kuma birgima a kasa. Ta tashi ta koma kan study table din Hassan ta kunna reading lamp, sannan ta jawo drawers din da suke gefe ta binciko wani littafi sabo babu rubutun komai a kansa, ta dauko biro tana jujjuya shi a hannunta sannan ta fara rubutu. "Sunana Ruqayyah, wannan shine labari na"......... Tun daya yarintarsu ta fara bayani, da kuma abinda ta sani na daga yarintar su Hassan da Hussain. Labarin haduwar su da Hassan da kuma labarin aurensu. Komai har zuwa mutuwar Hussain da kuma accident din da sukayi, haihuwar da Fatima tayi a gurin accident din da kuma yar da babyn da Ruqayyah tayi. Sannan ta dora da labarin abubuwan da suka faru bayan nan. Har saida aka fara kiran sallar asuba sannan ta tashi, ta rufe littafin ta boye, bayan Hassan ya fita masallaci sai ta tashi tayi sallah itama sannan ta dauko wayarta ta shiga e-mails ta saka address din Amir sannan ta aika masa da sako kamar haka "Assalamu alaikum wa rahmatullah. I may be wrong but I think you are the person am looking for. Ina da labarin da zan baka, a story concerning your parents" Sai ta saka address din gidan da Ruqayyah take sannan ta tura masa. *The Book* Amir ya je ya dauko Aisha kamar yadda ya fita da niyyar yi, sai dai yau din ya lura da chanje chanje a tare da ita, na farko yau malamin ta da tace ba saurayin ta bane ba, wanda ya saba rako ta kullum zuwa mota yau bai zo ba. Na biyu kuma ya lura gabaki daya kamar yanayin ta bashi da dadi, shima kuma nasa yanayin babu dadi dan haka tafiyar tasu ta zama shiru, sai daga baya yayi breaking silence din ta hanyar tambayarta abinda yake damunta sai kawai ta kama yi mishi kuka, ta tsaya a gefen hanya ya barta ta gama kukan ta sannan ta fara yi masa bayanin irin problem din da take ciki na rashin matsaya akan wanda ya kamata ta tsayar a matsayin miji. Ta bashi labarin dukkan maneman ta da rawar da kowanne ya taka a cikin rayuwar ta. Sai yaji tausayin ta, yaji cewa kamar neman aurenta da yake yi suima wani karin nauyi ne a gurinta tunda yasan tana ganin mutuncin sa sosai, maybe shi yasa har yau ta kasa bashi amsar tayin soyayyar da yayi mata. Sai yaji a ransa kamar tana gaya masa haka ne dan ya fahimci cewa ba zata iya karbar tayinsa ba, and for some unknown reason sai yaji hankalin sa ya kwanta da decision dinta. Amma daya tambaye ta game da malamin ta da yake rakota mota sai ta ce masa kawai friend dinta ne tun na shekara da shekaru, da haka ya kaita gida, cikin palace, gidan abokinsa Sultan inda anan ne take zaune a lokacin. Suka yi sallama ta shiga ciki shi kuma ya koma da niyyar zuwa asibiti gurin Dr Maimoon matar Sultan kamar yadda yayi niyya, sai daya je kofar asibitin sannan ya fara neman wayarsa zai kira ta sannan ya fahimci cewa wayar bata tare da shi, maybe a office dinsa ya barta. "Damn it" ya fada yana dan dukan stirring kadan, ya fita ya shiga asibitin sai aka tabbatar masa da cewa ta koma gida tun dazu, dole ya sake kunna mota ya koma office dinsa, a nan ya tarar wayar har ta mutu, maybe anyi ta kiransa ne shi yasa battery din yayi running down. Daga nan sai ya saka phone din a charge sannan ya sake fita ya nemi abinci yaci, har lokacin lunch ya wuce amma shi ko breakfast bai yi ba, abincin ma babu dadi, ko dan zuciyarsa babu dadi ne? Sai daya gama sannan ya dan karasa aikin da yake gabansa a office din, akwai fita field daya kamata yayi amma sai yaji ba zai iya ba maybe sai gobe, dan haka ya tattara abubuwan sa ya dauki wayarsa ya fita, yana tunanin abinda zai tarar a gida, wata zuciyar tana gaya masa ya tafi palace kawai gidan Sultan yayi zamansa a can sai dare ya koma gida, ya samu ma Dr Maimoon ta duba shi a can, amma kuma sai yaga hakan ba dai dai bane ba tunda Aysha ta sauko ta bashi hakuri kuma ya kamata shima yayi meeting dinta halfway sai du bawa juna hakuri, amma sai ya tabbatar cewa ba zata kuma gaya masa magana irin wannan ba ko ba da shi ba ko dan ƴaƴan su, kar ta fada watarana a gaban ƴaƴan su. Yana packing ta fito bakin kofa ta tsaya, hannunta na dama dauke da Afnan hannun hagu kuma rike da Sultan. Duk sunyi kyalliya sunyi kyau abinsu kuma sun taba zuciyarsa sosai amma sai ya maze yana muzurai irin shi mai gidan nan, Sultan ya taho da gudu ya tare shi yana masa sannu da zuwa sannan yace "Abhi munyi maka cake ni da Ammi, mun rubuta maka we are sorry a jikin cake din" yace "kun kyauta, yayi kyau" sai kuma yaron ya tambaya "laifin me muka yi maka ne wai Abhi da muke baka hakuri?" Sai ya samu kansa da yin murmushi tare da rije kugu yace "kai baka san kayi laifi ba amma kake bada hakuri?" Aysha ta karaso inda suke tsaye tace "ni ce nayi laifin, ni nake bada hakurin, shi kawai taya ni yake yi ban sani ba ko zanci albarkacin sa?" Ta karasa tana langwabe kai, ya kankance ido yana kallon ta ita kuma ta sunkuyar da kai, sai ya mika mata jakar hannun sa, ta karba da sauri shi kuma ya karbi Afnan yana manna mata kiss a lips dinta, suka jera zuwa cikin gidan tana cewa "ka hakura?" Yace "tukunna dai". Haka suka matsanta masa sai da ya yanka cake duk da ba birthday dinsa bane ba kuma anniversary din auren su bane ba, kuma dole sai da suka saka shi yayi dariya, shi dama mutum ne da ba wai iya hade rai yayi ba. Sai da yayi wanka ya kwanta ya dan huta sannan suka fita masallaci suka yi sallar magrib shida Sultan sannan ya dawo ya tarar tana setting table, ya zauna kenan Afnan ta fara rigima, ya tashi ya dauko ta yana rocking dinta a hannayensa, sultan yana kallon su sai ya kwashe da dariya, Aysha ta juyo tana taya shi dariyar, Amir ya tsaya yana kallon su "wa kuke yiwa dariya?" Ta rufe baki "ni babu ruwana fa, Sultan ne" ya juya kan Sultan "wa kake yiwa dariya?" Ya sake dariya "yar fara na gani da ɗan baƙi" Amir ya dan bata ransa yace "kai! Waye baƙin? Kasan dai nafi Ammin ka fari ko?" Tana aikinta tace "a hakan dai aka gani akace ana so" Sai yayi murmushi, ita kuma taji dadin murmushin da yayi. Ta gama shirya komai sannan tazo ta karbi babyn daga hannunsa ta zauna tana feeding dinta shi kuma ya fara cin abinci shi da Sultan suna ta hirar su kamar abokai. Sai daya gama sannan ya zauna ya dauko phone dinsa, sai yanzu ya tuna da ita dan he is not a phone person, tsakanin sa da ita ya dauka yayi waya kawai, wannan yasa mostly in yana gida kasheta yake yi in ba haka ba clients zasu yi ta damunsa ne da zancen aiki, shi kuma in yana gida yafi son yayi dedicating time din to his family, aiki kuma sai yayi shi a work hours. Yana kwance a kan kujera da Afnan akan kirjinsa ya kunna wayar sannan ya ajiye ta a gefe yana sauraron hirar da Aysha take masa, duk a kokarin ta na ganin ya hakura da laifin da tayi masa, an jima kadan ya dauki wayar yana duba sakonnin da suka shigo masa, a lokacin ne yaga missed call din Madam Merry, shugabar gidan marayu na kasa, ya shafa fuskarsa yana tunanin dalilin da zai saka ta kira shi a wannan lokacin, last week yaje ya kai musu abinda ya ke kai musu duk wata a tallafin kula da marayun, to ko wani urgent issue ne ya taso kuma? Ko dai....... Yayi sauri ya kawar da maganar daga ransa tare da ajiye wayar a gefe amma sai ya kasa ture maganar gefen, ya kalli Sultan daya kwanta akan carpet yana bacci sannan ya mayar da dubansa kan Aysha yace "wannan yarinyar, Afny, farin nan nata kina ganin maybe ko ta same shi ne daga family dina? Ina nufin biological family dina" Aysha ta dora hannunta akan nasa, ba zata iya tunawa da ranar da yayi mata magana irin wannan ba, sai tayi murmushi tana rike hannunsa a cikin nata tace "haka ne fa, kasan nima nayi wannan tunanin kawai gaya maka ne ban yi ba" ya gyada kai kawai yana jin ina ma bai furta maganar ba, maganar iyayensa ta na saka masa wani irin longing for them. Sai ya chanja topic din hirar yana bata labarin Aisha, da kuma decision din daya yanke na yanke alakar sa da ita. Yaga alamar hankalin ta ya kwanta sosai akan maganar, musamman data fahimci cewa ba wata soyayya mai zurfi ce a tsakanin su ba. Bai kira Madam Merry ba saboda dare yayi, amma sai yayi wa kansa alkawarin zai kira ga first thing in the morning dan yaji kiran da tayi masa, "ba zai wuce wani emergency taimako ne suke nema ba". Da safen ma bai kira ta ba sai da yaje office ya gama da abubuwan da suke buƙatar immediate attention din sa sannan ya dauko waya ya kira ta. Haka kawai yaji zuciyarsa tana bugawa da karfi, ko dan mafarkin da yayi ne? Bugu daya ta dauka, yana kokarin gaishe ta tace "nayi ta kiran ka jiya, you didn't pick up and you didn't return my call" ya dan bata rai, shi ya tsani ace za'a yi masa fada, yace "ban gani da wuri ba, hope everything is okay" tace "basu neme ka ba? I thought they should have contacted you by now" yawun bakinsa ya kafe yace "su wa ye" "your siblings" ta fada excitedly. Ya cire wayar daga kunnensa ya kalla dan ya tabbatar da gaske waya yake yi ba daydreaming ba, ya ga sunan ta baro baro a screen din sannan kuma ga seconds suna tafiya, ya mayar da wayar kunnen sa yace "am sorry, banji me kika ce last ba, network yana cutting" tace "your siblings were here yesterday, three of them, suna neman ka" ya girgiza kansa da sauri yace "nooo, you are wrong, ni bani da siblings kuma kin san da haka" tace "not anymore Amir, yanuwanka sun zo suna neman ka" yace "maybe yan uwan wani sunzo suna nemansa, ba lallai ni suke nema ba, how can you be sure cewa ni suke nema? Akwai wata shaida da suka kawo? As far as I know babu wata shaida da aka barni da ita sanda aka yar dani" ya fada maganar tana kuna a ransa, Tace, muryar ta tana karyewa kamar zata yi kuka "basu kawo shaidar komai ba Amir, sun dai fadi date da time da kuma ranar da aka yar da kai. Ni ban san date din ba amma baba Asabe tayi confirming time din, kuma ....." Yace "10th of January. Shine birth date dina" sai yaji ta fara kuka "haka suka ce, haka suka ce Amir, yan uwan ka ne. Basu bamu shaidar komai ba sai ta kamannin fuskokin su, gabaki dayan su suna kama da kai, musamman ma farin, kamar ku daya banbancin hasken fata ne kadai dan Baba Asabe ta dauka kaine sanda ta ganshi" zuciyarsa ta tafi kan yarr jaririyar da ya baro a gida Siblings? Shi wai shi yana da siblings kenan? Kuma har wai sunzo nemansa? Kenan sun san dashi sun kuma san inda yake, that's in the gaske yan uwan nasa ne ba tsufa ne ya kama Baba Asabe ba. Abinda ya fara fado masa masa a rai shine mahaifiyar sa, itace ta yar da shi kuma ita ce yanzu ta gaya musu inda ta yar da shi din. He threw him away and kept his siblings. Why? A cikin wayar yaji har yanzu Madam Merry magana take yi, "...........shine na basu e-mail address dinka, na ce su neme ka su tambayi iznin ganin ka daga gurin ka. Check your email yanzu haka sunyi maka magana dan they were so eager to meet you" Ya cire wayar daga kunnensa sannan ya koma da baya ya zauna akan kujerar da take bayansa, maganganun suna harhaduwa da junansu a cikin kansa, Siblings, mother, eager to see him, suna kama dashi, e-mail. Sai ya ajiye wayar ba tare da yayi checking ko ya katse kiran ba ya jawo system dinsa ya kunna, sannan ya shiga e-mails dinsa roughly yana checking recent mails dinsa and then he saw it, daga wani address din da bai sani ba, yayi clicking ya bude zuciyarsa tana bugawa da sauri. "Assalamu alaikum wa rahmatullah. I may be wrong but I think you are the person am looking for. Ina da labarin da zan baka, a story concerning your parents" Sai address a kasa, "a story" ya maimaita a ransa, story za'a bashi? Shi answers yake so, so yake yaji dalilin da yasa aka yar dashi tsirara a kofar gidan marayu. Maimakon yaji dadin cewa zai ga family dinsa sai yaji wani irin bacin rai da kunan zuci a kasancewar mahaifiyarsa data yar dashi tana sane dashi all these years bata neme shi ba sai yanzu, maybe ma siblings din ne suka matsa mata ba wai dan ita ta damu da shi ba. Ya fahimci cewa ita ce ta aiko masa da sakon bayan yayanta sun koma gida ba tare da shi ba, me take tunani? Cewa zai fita a guje ya tafi gurin ta? Cewa yana bukatar ta a cikin rayuwarsa baya ita ta wofantar dashi a lokacin da yake tsananin buƙatar tata? Ranar bai koma gida ba bayan ya tashi daga office, a zaman office din ma bai iya aikata komai ba, ya ga kiran Sultan abokinsa yana ta shigowa amma yakasa dagawa dan baya son ya fahimci komai a tare dashi, baya son ya gaya wa kowa komai, not even his wife. Da farko shawara ya fara yi da zuciyarsa akan yaje kiran da akayi masa ko kar yaje? Amma mostly amsar da zuciyar ta sa take bashi shine yaje din, dan in bai je ba ba zai famu answers din sa ba, answers din kuma suna zasuyi determining next action din da zaiyi taking. A ranar bayan ya koma gida Aysha ta fahimci cewa hankalin sa baya tare dashi amma kuma duk iyakacin kokarin ta sai yaki gaya mata, ita kuma sai tayi fushi thinking dannyayi breaking up da budurwar sa ne ya saka yake cikin wannan yanayin, da safe ma daya fita bai je office ba zuwa yayi park ya zauna yana cooking kwakwalwar sa, yana getting ready for abinda zai tarar idan yaje Kaduna din, babu abinda zuciyarsa bata yi masa imagining. Yana gurin Aisha ta kira shi, yayi tunanin maganar dauko ta daga school ne amma sai ta gaya masa cewa wannan malamin nata, Nura, yayi accident tana asibiti gurin sa, sai kawai ya tashi ya tafi gurinta dan dama yana neman abinda zaiyi distracting dinsa daga tunanin da yake ciki, ba ya kuma son yin magana da wanda zai takura masa sai ya gaya masa abinda yake damunsa kamar Sultan ko Aysha matarsa. A can asibitin ya same ta, ya duba nuran sannan ya dauko ta suka tafi zai kaita gida. A hanya ta gaya masa cewa komai ya warware mata na maneman ta. Finally ta yi deciding cewa Nuran dai shine ta tsayar. Bayan yayi packing ne ya gaya mata "something came up, something related to my parents" ta juyo tana kallonsa ido a bude, ya dan kirkiri murmushi, "ba wani abu bane ba, It maybe nothing and it may be something, babu wanda na fada wa, not even Sultan" ta gyada kai tana jinjina irin yardar da yayi da ita, tana kuma jin farin cikin maganar daya gaya mata, yace "I want to go and investigate first, zan danyi tafiya zanje Kaduna, in na dawo duk abinda ake ciki I will let you know" ta guada kai da sauri idonta yana kawo kwallar da bata san ta menene ba. Yace "adious *A'isha Humairah*" ta fita ta rufo masa kofa tace "adious my friend". Washegari da sassafe ya dauki hanyar Kaduna, bayan ya gaya wa Aysha cewa wani harkar gini ce zata kai shi can, bata damu ba saboda tasan babu inda baya zuwa akan aikinsa. Sultan ma abinda ya gaya masa kenan kuma tunda yanzu ba sosai yake kula harkar kamfanin ba dan haka bai fahimci babu wani aiki a Kaduna ba. Yana shiga Kaduna hotel ya tafi ya kama, daga nan ba tare da ko da jakarsa ya sauke daga mota ba sai ya dauki hanyar address din da aka bashi a email din. Zuciyarsa kamar zata fado daga kirjinsa. A kofar gidan ya tsaya yana karewa layin da kuma gidan kallo, katon gida ne wanda za'a iya cewa duk layin babu gidan da ya kai shi girma amma alamu suna nuna kamar yana lacking maintenance, kamar mutanen gidan basa cikin gidan, amma wani abu mai karfi yana jan sa zuwa cikin gidan. Ya daga kai yana kallon manyan balconies din da suke ta two sides of the house, amma sai a idon sa yaga kamar an dade ba'a yi amfani da su ba. Bai san me yasa kallon gidan yake kokarin kawo hawaye cikin idonsa ba. Ya girgiza kansa yana so ya dawo cikin hayyacin sa. Ba irin wannan gidan ya saka ran zai gani ba, ba irin wannan gidan zuciyarsa take kwatanta masa a matsayin inda mahaifiyar sa take ba, gidan kamar yafi karfin wacce ta haihu ta yarda dan ta zauna a ciki. Yayi horn mai gadi ya leko yayi masa tambayoyi sannan ya koma, jimawa kadan, already har Amir ya fara kawowa wuya sai gashi ya dawo ya bude masa kofar. Ya shiga yana karewa compound din gidan kallo, it definitely lack maintenance kamar yadda ya fada, amma kuma a matsayin sa na engineer yasan cewa duk wanda ya gina gidan nan tabbas yana da taste, dan duk da shekarun gidan amma ko a zamanin nan ba ko ina ne za'a yi wannan aikin ba. Mai gidan, ba karamin mai kudi bane ba. Sai yaji kalmar mai gidan ta tsaya masa a ransa... Sama sama yaji mai gadin yana yi masa magana, yana nuna masa ta inda zai shiga cikin gidan. Ya bishi zuwa bakin kofar, amma sai yaji ya kasa shiga, har sai da ya sake masa magana sannan ya taka kafarsa ya shiga, yana jin zuciyarsa tamkar ta koma cikin hanjinsa. Ya zagaya palon da idonsa, babu kowa a ciki, ya daga ido yana kallon tafkeken benen da yayi sama sannan kuma ya rabu gida biyu ya sake yin sama. Ya dawo da idonsa kan kujerun gurin yana kokarin nema wa kansa gurin zama, a lokacin ne idonsa ya sauka akan hoton. A nutse yake taka ƙafafuwan sa yana nufar katon hoton da yake rataye a bangon parlon amma a cikin jikinsa ji yake tamkar wata maganadisu ce take jansa zuwa ga abinda idanuwansa suka gane masa. Wani iri yake ji a kirjinsa, ya kasa tantance wa cewa zuciyarsa ce ta tsaya daga aikinta na buga jini zuwa sassan jikinsa ko kuma huhunsa ne ya daina nasa aikin na zukar oxygen, amma ko ma menene dai yasan wani abu, abinda bai taba tabuwa a jikinsa ba yau ya tabu. Ya karasa gaban hoton, sannan ya daga hannayensa da suke karkarwa tamkar na wanda yake cikin matsanancin zazzaɓi ya dora akan hoton yana karewa halittun cikin hoton kallo. Daga ganin hoton zaka gane cewa ya kwana biyu a duniya, daga ganin camerar da akayi hoton kasan bata yanzu bace ba. Sai dai shekarun hoton basu saka yayi komai ba dan mutanen ciki tamkar zaka kirasu su amsa. Su biyu ne, daya a zaune akan kujerar alfarma daya kuma a tsaye a bayansa ya dora gwuiwar hannunsa akan kafadar na zaunen. Kallo daya zakayi musu kasan cewa yan'uwa ne, kallo daya zakayi musu kasan cewa ciki daga suka fito, sannan inka kalli fuskar su zaka tabbatar cewa ba wai jini da iyaye kawai sukayi sharing ba har da mahaifa. Tare suka rayu a ciki, tare kuma aka haife su. *Tagwaye* ne. Komai nasu iri daya ne, tsahon su, yanayin jikinsu, shape din fuskarsu, abubuwan da suke cikin fuskar, abinda ya bambanta su guda daya shine kalar fatar su. Na zaunen fari ne tas, na tsayen kuma baki ne irin fatar Amir da yake kallonsu. Ko digon alkalami na doubt babu a zuciyarsa, yasan cewa ta jikin daya daga cikin wadannan bayin Allan ya fito yazo duniya. Abinda bai taba tsammanin gani ba, ya saka ran ganin mahaifiyar sa a yau amma bai yi tunanin samun wani abu daya danganci mahaifin sa ba. Amma wanne daga ciki? Farin ko bakin? Na zaunen ko na tsayen? Ya dora tafin hannunsa na dama akan fuskar wanda yake zaune, farin, sannan ya saka idonsa cikin nasa yana jin wani abu mai girma yana ratsa zuciyarsa yana kawo kwalla cikin idonsa. Murmushi ne a kwance akan kyakkyawar fuskarsa, murmushi exactly irin wanda kullum yake kwance akan tasa fuskar. Ya hadiye wani abu da yaki tafiya a makogwaron sa. Sannan ya mayar da idanunsa kan na tsayen, Baƙin, and he felt as if yana kallon kansa a madubi ne. Ya tabbatar da cewa, da ace a yanzu zai shiga shagon aski a aske masa gashin da yake fuskarsa da tabbas za'a iya cewa shine a cikin hoton. Dan daga dukkan alama an dauki hoton ne a lokacin da shekarun su suke kusan nasa na yanzu. Motsi yaji a bayansa, hakan ya saka shi saurin waigawa a dan tsorace saboda baisan da shigowar mutum parlon ba. Idanunsa ya sauke a kanta. Baka ce kamar shi, bata da tsaho sosai kamar shi, kuma tana da manyan idanuwa irin nasa. Shekarunta zasu yi anywhere between 20-25. Ya girgiza kansa da sauri tare da dafe shi da hannu daya. Ba ita ya saka ran gani ba, a lokacin da yaga hoton mahaifinsa for the first time a rayuwar shi mahaifiyarsa yake saka ran gani tare da hoton. Ko ba dan komai ba dan ya samu yayi mata tambayar da ta jima tana cin zuciyarsa. Tambayar daya taho takanas dan yayi mata. "Why?" Tun yana yaro babu abinda yake son yaji irin dalilin da yasa mahaifiyar sa ta jefar dashi a kofar gidan marayu ba tare da ko cibiya ta tsaya ta yanke masa ba. "Excuse me" matashiyar matar ta fada tana kallon sa cike da zargi da rashin fahimta. Ya dafe goshinsa yana kokarin tattaro hankalin sa guri daya dan ya samu muryarsa ta fito amma sai yaga yanayin fuskarta ya chanja daga kallon rashin yarda da take masa zuwa kallon mamaki hade da excitement. Ta dauke idonta daga fuskarsa ta mayar kan hoton da yake bayansa sannan ta kuma dawo wa da shi fuskar tasa. Sai kuma ta saki keys din motar da suke hannunta ta rufe bakinta da hannayenta duk biyun amma ta kasa cewa komai. Cikin tuhuma yace mata "sunana Amir. Ke kika aika min da email cewa kina nemana?" Ta girgiza kanta cikin sauri, sannan tace "mahaifiya ta ce". Then there is hope, then she is here within these walls. Dan ya tabbatar ba tare da doubt ba cewa wannan yarinyar ta gabansa kanwar sa ce, then mahaifiyarta mahaifiyarsa ce kenan. "Where is she" ya fada cikin budaddiyar muryar da tayi amsa kuwwa a cikin gidan. Muryar da Amatullah taji tamkar ta daddyn ta idan yana fada, ta ja baya, yanayin Amir yana tsorata ta, Amir ya tabbatar ta jiyo shi indai tana cikin gidan. Cikin gaggawa Amatullah ta juya tana cewa "bara in gaya mata kazo" sannan ta bude wata kofa a can karshen parlon ta shige. Yabi kofar da kallo, jikinsa yana bashi cewa tana ciki, mahaifiyarsa tana cikin dakin da yake hade da parlon da yake tsaye a gaban hoton mahaifinsa. "Wannan wanne irin mafarki ne" ya fada yana dukan goshinsa da tafin hannunsa na hagu. Mintina suka yi ta wucewa, wannan ya saka shi ya fara sintiri a parlon yana kaiwa yana komowa ba tare daya dauke idonsa daga kan kofar da yarinyar ta shiga ba. "What is taking her so long?" Finally kofar ta bude, ya tsaya chak a tsakiyar taku yana son ganin fuskar ta amma sai yaga fuskar yarinyar data shiga ta dawo ita kadai. Me ya faru? Ko ta fasa ganin na shi ne? Ta tsaya a gabansa sannan ta mika masa wani littafi wanda sai a lokacin ya lura cewa ta fito dashi a hannun ta. "Gashi tace a baka" ta fada cikin muryar da tayi kama da na wadda tayi kuka. Yabi littafin da kallo sannan ya kalle ta, wani barin na zuciyarsa yana gaya masa cewa ya makure ta har sai ta daina numfashi. "Littafi? What the fuck am I supposed to do with a book?" Ya fada cikin kara ji. Ta goge hawayen daya fito a gefen idonta tace "tace kaje ka karanta, in ka gama sai ka dawo kuyi magana" ya juya yana kallon kofar data fito yace "Ki koma ki gaya mata cewa ni ba yaronta ba ne ba, she is not the boss of me da har zata ke bani directives, na zo ne kawai dan inyi mata tambaya daya kuma tana bani amsar tambaya ta zan koma inda na fito ba zata kara gani na ba. Tell her to come out and face me, tell her to come out and answer me. Menene dalilin da yasa ta yar da ni" ya fada da muryar daya tabbatar cewa ta cikin dakin ta jiyo shi Hawayen fuskar tane ya karu, yana biyo kuncin ta yana sauka akan bangon littafin da yake rike a hannun ta. Tace "she can't" ya juyo da kallonsa kanta amma bai ce komai ba, fuskarta da hawayenta sun taba zuciyarsa. Shi mutum ne mai rauni abu kadan yakan ta ba shi. Ta sake cewa "she can't come out and face you saboda bata iya tafiya. She can't answer you saboda bata iya magana". Yaji zuciyarsa ta dunkule a guri daya, ya mayar da idonsa kan kofar dakin wata zuciyar tana gaya masa yaje ya bude ya shiga amma wata tana hana shi. Sai kuma ya saka hannu ya karbi littafin da ake miko masa. Shi a hankali yayi niyyar karba amma sai ya kasance tamkar warta yayi, wannan yasa Amatullah ta tafi kamar zata fadi sai ta dafe kujera. Then without a second glance ya juya da sauri ya bar parlon. Blindly ya fita, har ya shiga motarsa ya jefa littafin a kan seat din kusa da driver sannan yayi wa motar key, sannan ya ja motar, faster than he intended ya bar harabar gidan. Yana ji a jikinsa cewa a yau din nan zai kuma dawowa. Hotel ɗin daya sauka ya zarce, yayi packing ya fito da littafin a hannunsa ya shiga ba tare daya amsa gaisuwar da ma'aikatan hotel ɗin suke yi masa ba. Yana shiga dakin ya jefar da littafin akan gado sannan ya wuce toilet ya wanke fuskarsa, ya jima yana kallon fuskar a madubi yana tuno hoton tagwayen daya gani, sai kuma ya koma cikin dakin da sauri ya tsaya yana kallon littafin. Wato a cikin wannan littafin ne duk amsoshin tambayoyinsa suke, maybe a ciki zai samu amsar dalilinta na jefar da shi. "She can't. She can't come out and face you saboda bata iya tafiya, she can't come out and answer you saboda bata iya magana" Ya tuna maganganun yarinyar. Ya girgiza kansa da sauri. Shi yasan bayan duk wannan abin ya wuce sai yaje asibiti gurin Moon ta duba lafiyar kwakwalwar sa. Ya zauna a bakin gado tare da ɗaukan littafin yana jujjuya shi. Babu wani rubuta a bangon sa. A hankali ya bude page din farko shima babu rubutun komai sai ya cigaba da flipping through pages din sannan ya ga ashe littafin a cike yake da handwritten rubutu, chapter by chapter. Ya danyi karamin tsaki. Shi bashi da wannan lokacin, bashi da lokacin karatun littafi shi amsa kawai yake so dan haka sai yayi deciding zai dudduba littafin ne kawai har ya nemo inda amsar sa take ya karanta shikenan ya gama dashi. Da sauri ya ringa bubbuda pages din, noticing only the keywords. Yayi noticing Hassan sannan da Hussain, ya kuma ga Ruqayyah da Sumayya, daga nan yaga kalmar kidnapping amma bai karanta yaga wa akayi kidnapping din ba amma dai yaga an biya ransom. Sai yaga wedding, amma bai san auren waye ba, sai kuma yaga Fatima. Ya jima yana kallon sunan fatiman amma bai karanta labarin daya zagaye sunan nata ba sai ya wuce. A can gaba da nisa yaga kalmar accident, a kusa da ita akwai baby. Wannan ya ja hankalin sa ya karance wannan chapter din tsaf dan jikinsa ya bashi anan amsar sa take. Ai kuwa ya ga amsar. Amsar da ta saka shi yayi jifa da littafin ya mike tsaye idanunsa suna ganin duhu kansa yana juyawa. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" yayi kokarin ambata amma sai wata zuciyar ta hana shi. Tabbas in ya kira Allah zai ji sassauci a abinda yake ji a zuciyarsa kuma hakan zai iya hana shi daukan hukuncin da tun kafin ya gama karantawa ya riga ya yanke a zuciyarsa. He is going to Kill her. A yanzu ba wai yar da shi da akayi ne yafi masa ciwo ba, abinda yafi masa ciwo shine blaming mahaifiyar sa da ya shafe tsahon rayuwarsa yana yi. Ashe ba ita ta yar da shi ba, ashe dauke shi akayi daga jikinta batare da an barsu sunji dumin juna ba. Wannan a gurinsa shine babban laifin da tayi masa wanda a gurinsa yake sama da jefar dashi da tayi.. Da lalube ya dauki key din motarsa, sannan ya fita cikin sauri mai hade da gudu. Bai kula da ma'aikatan da suke masa magana ba ya tayar da mota ya fita cikin sauri fiye da na sanda ya shigo. Blindly yake tukin, zuciyarsa tana yi masa bitar abinda ya karanta. Duk da bai karanta farkon labarin ko karshen sa ba, amma gani yake kisan da zaiyi mata shine hukuncin daya dace da ita. Da hannunsa zai shake ta sai ta daina numfashi, a yau ba sai gobe ba. A haka ya karasa bakin gate din gidan, ya tsaya yana jiran mai gadi ya bude masa kofa yayin da shi kuma ya sake komawa cikin gidan yana sanar da zuwansa. Tabbas da da bindiga a hannunsa da zai iya harbe mai gadin baki daya saboda lokacin da yake bata masa, ya akayi ya daina yawo da bindiga ne? He missed his gang bang days. At last aka bude masa ya shiga, sai dai kallon da mai gadin ya bishi dashi ya saka shima ya kalli hannayensa da suke rike da stiring, karkarwa hannayen suke yi kamar mazari, sai a lokacin ya lura cewa jikinsa gabaki daya karkarwa yake yi. Sai a lokacin ya lura ashe kuka yake yi. *The fire and the ice* *Two days ago.......* Tun ranar da Sumayya ta tura wa Amir e-mail din take jin rashin dadi a zuciyarta, tunanin ta shine Hassan zai dauki hukuncin nata, amma kuma sai take ganin ko yayi fadan zai fahimce ta tunda shima yana da Hussain, ya san kuma yadda yake jin sa a ransa, ya san abinda zai iya yi dan ya samar wa Hussain sassauci idan da ace zai kasance cikin kunci, ya san cewa babu abinda ba zaiyi ba indai yana da iko dan lahirar Hussain tayi kyau. Ita kanta shaida ce cewa yayi kuma yana kan yin komai saboda Hussain. Ita me yasa ba zata yi saboda Ruqayyah ba? Bata yi karya ba a duk abinda ta rubuta wa Amir a littafin ta, duk abinda ta rubuta gaskiya ne based on her knowledge, ita kuma bata yi niyya kuma ko a ranta bata da burin tursasa Amir ta kowace hanya ce dan ganin ya yafewa Ruqayyah ba, burin ta shine ya samu labarin gaskiyar abinda Ruqayyah tayi masa sannan kuma ya samu labarin sakayyar da ubangiji ya riga yayi masa a kanta, sannan ya ganta da idonsa one on one, ya tabbatar da abinda ya karanta din kuma ya fahimci babu wani ai da yayi saura da zai iya dauka a gurinta wanda Allah bai riga ya dauka ba, babu wani abu daya rage mata sai numfashin ta, then maybe, zai iya jin tausayin ta, maybe imanin sa zai iya sakawa yaji a ransa cewa ya yafe mata. Tasan cewa indai ya shiga hannun Hassan, ko Fatima, the last thing da zasuyi masa magana a kai shine ya yafewa Ruqayyah, hatta yayan Ruqayyah bata jin zasu roki Amir ya yafe wa Ruqayyah nan kusa, in ma zasu roke shi din to sai an dauki lokaci, lokaci kuma shine abinda a yanzu Ruqayyah bata dashi. Ita kanta Sumayya tasan a yanzu Ruqayyah numfarfashin ta na karshe take ja a duniya dan kullum ta barta sai taji kamar ba zata dawo ta tarar da ita da rai ba. And it breaks her heart kullum in ta ganta. No matter how bad she was, no matter what she has done, twin sister dinta ce, that bond will never break no matter what. Tana fatan Hassan zai fahimci haka......... Tun da gari ya waye ta gaya wa Hassan cewa ta aika wa da Amir e-mail ta sanar dashi cewa yazo gurin su akwai labarin daya danganci iyayensa, ta gaya masa cewa ta aika masa da address amma bata gaya masa wanne address din ta bawa Amir ba, sai ta kwantar masa da hankali da cewa in dai ya gani tana da tabbacin zai zo, dan babu wanda zai tashi cikin rashin sanin su waye iyayensa sannan kuma ace masa ga labarin iyayensa amma yaki zuwa. Ya yarda da haka, dan haka ya saka aka yi masa shimfida a harabar gidansa ya zauna yana facing gate tare da yayansa, anan suka yi breakfast anan suka yi lunch anan sukayi dinner. Daga an taba gate zasu juya gabaki dayansu, daga sunji horn zasu dakata daga maganganun da suke yi suna kasa kunne suji me ake cewa. Amma shiru babu Amir. Yaran gaba-daya anan suka wuni suna taya babansu hira da dauke masa hankali daga tunani, shima kuma sai yayi kokari sosai gurin tsayar da hankalin sa akan su yana basu labarin Hussain da irin yadda suke samun saɓanin ra'ayi akan abubuwa da yawa su kuma zauna suyi ta musu kowa yana ganin nasa shine dai dai. "Sai bayan daya fara rashin lafiya ne muka daina faɗa, in ma na neme shi da fada sai yace "ni ba zanyi fada da kai ba" ya fada yana murmushi, yana jin kamar yanzun be Hussain din yake gaya masa. Sai daya tabbatar dare yayi Amir bai zo ba sannan ya fara damuwa. "Ko dai bai ga sakon ba? Ko kuma fushi yake yi damu? Dole yayi fushi, zai ga kamar muna sane muka rabu dashi a gidan marayu, muka barshi ya taso ya girma a matsayin marar asali marar gata, bayan shi din mai asali ne mai cikakken gata ne" Sumayya tace "ka kwantar da hankalin ka, dole yana bukatar lokacin da zaiyi tunani akan zuwan nasa, kasan ba abu ne mai sauki ba mutum ya tashi bai san iyayensa ba sannan rana daya ace masa yazo ga iyayensa, ka bar masa yau zuwa gobe insha Allah zaka ganshi a cikin gidan nan" Sai ya hakura, ya kuma yi kokarin kwantar da hankalin satare da tursasawa kansa yin bacci duk da cewa baccin a tsitstsinke ya dunga yi, sai yake jin kamar ana knocking gate cikin barcin. Ita kuma Sumayya sai ta kwana bitar littafin ta tana tabbatar da ta rubuta duk abinda ya kamata ta rubuta, ta kuma yi duk bayanan da ya kamata tayi da irin yanayin da zai saka tausayi a zuciyar mutum. Washegari da sassafe Hassan ya kuma sakawa aka sake masa shimfida irin ta jiya suka kuma zama tare da yayansa irin na jiya. Sumayya kuma ta tabbatar ta tana dar musu duk abinda zasu bukata sannan ta nemi izinin Hassan ta tafi gurin Ruqayyah, ya san yadda jikin Ruqayyah yake dan haka ya barta ta je din, saboda katanga daya ce tsakanin su in wani abu ya taso zasu neme ta ko kuma ita ta neme su. Tana zuwa ta tarar mai kula da Ruqayyah ta gama shirya ta tana kokarin bata abinci. Sai ta karba ta na bata da kanta, sannan tana bata labari. "Yaran mu sun samo inda yaron Hussain yake, sunansa Amir, yana Abuja yanzu tare da iyalinsa" sai taga Ruqayyah ta juyo da idonta tana kallon ta, tayi kokarin yi mata murmushi "he is still alive Ruqayyah, watakila ma maganar nan da nake miki yana hanyar tahowa gidan nan dan an samu e-mail address din sa kuma na tura masa email" sai taga hawaye ya fara bin fuskar Ruqayyah, ta kama hannun ta a cikin nata tace "nayi wa Hassan laifi a kanki Ruqayyah, na ba wa Amir address din gidan nan ba gidan Hassan ba, ina so ya fara zuwa nan kafin yahe gurin Hassan" ta dauko littafin data rubuta tace "na rubuta masa duk labarin da nake ganin ya kamata ya sani anan, ina so in yazo nan din in bashi kuma in roke shi yaje ta karanta first kafin yaga kowa, ina fatan idan ya karanta kuma ya ganki zai yafe miki Ruqayyah, wannan shine fatana a yanzu, bana so ki mutu da hakkin yaron nan a kan ki Ruqayyah" ta fada tana taya Ruqayyah kuka Kuka Ruqayyah take yi, da alama wani abu take so ta fada amma babu dama, so take ta gaya wa yaruwarta kar tayi haka, kar ta bata ran mijinta saboda ita dan ita din bata yi deserving wannan ba, bata yi deserving duk abinda suke yi mata ba, bayan duk abinda ta aikata musu bata yi tunanin zasu daga ido su kalleta ba ma ballantana har su kula da ita har kuma Sumayya take kokarin bata wa mijinta saboda ita. Saboda tana so ta nema mata yafiya a gurin wanda tasan ba zai taba yafe mata ba, idan kowa zai yafe mata a duniya tasan banda Fatima banda kuma wannan yaron, wannan mutumin da aka kira da suna Amir. Amma kuma taji dadin labarin cewa an ganshi, ko bai yafe mata ba to dawowarsa gurin iyayensa shima wani rage nauyi ne a gare ta. Sai Sumayya ta dauko littafin tana karanta mata, tana jin ta kuma tana ta tuna yadda abubuwan da Sumayyan ta rubuta suka faru, amma kuma tana da gyararraki da yawa da zata iya yiwa Sumayya a littafin nata idan da tana da dama. Sai dai kash, damammakin ta sun kare a wannan duniyar, a lahira kuwa, bata jin za'a bata wata dama ko da kuwa guda daya ce. Haka suka wuni a ranar shima kamar yadda su Hassan sukayi irin wunin da suka yi jiya. Amatullah tana dan shigowa gurinsu ta dan zauna taji labaran da Sumayya take bawa Ruqayyah sai kuma ta fita ta koma can gidan yaji labaran Hussain da Hassan yake bawa yanuwanta. Sai ta jinjina karfin bond din tagwaye, ta jinjina irin soyayyar da suke yiwa junansu. And then on the third day, Hassan yana tashi shiryawa ya fara yi "fita zaka yi kuma yau Habibi? Na dauka yauma zamu zauna ne ko Allah zai sa yazo, kar yazo kuma bama nan" ya juyo yana kallonta yace "binsa zanyi, idan shi ba zai zo gare ni bani zan tafi gare shi. Ba dai gidan sarki ba? Zanje in yi ta tambaya har in samu wanda ya sanshi sai ya bani address din gidan sa, ba zan cigaba da zama ina jiransa ba alhali nasan yana raye kuma nasan inda zan same shi. Tafiya zanyi in nemo shi da kaina, a yau ba sai gobe ba, dan bani da tabbas din zan kai gobe" tayi murmushin kwara masa kwarin gwiwa, amma kuma tana jin hakan ya rusa duk plans dinta amma ba zata yi delaying dinsa ba in dai har hakan yake so da gaske. Tare suka fito suka tarar har Amatullah ta fara hada breakfast, ta samu ta lallaba shi ya dan ci kadan sannan ta aika Amatullah ta taso Hussain, wanda a gidan ya sauka duk da ya gina gidan sa da yake sauka in yazo da iyalinsa, sai kuma ta kira Abdulrahim shima ta gaya musu ga hukuncin da babansu ya yanke, suma basu musa masa ba sai suka yi gaggawa gurin shiryawa dan suyi masa rakiya. Ta jirgi suka tafi, Abdullahi ne ya kaisu airport daga nan shima ya wuce gurin aikinsa, Abdulrahman ma haka. Suna tafiya Sumayya da Amatullah suka gama duk abinda zasu yi suka tafi gurin Ruqayyah, Sumayya tana ji a ranta cewa yau za'a gama komai, ko dai Amir yazo gida ya same ta ita da Ruqayyah ko kuma su Hassan suje su same shi a gida. A ranar kuma duk jikin Ruqayyah ya kara rikicewa dan ko dan kunun da ake dura mata ta yau dawowa yake yi, kamar ta fara loosing her ability to swallow, wanda doctor ya gaya musu shine last stage da zata je. Sumayya ta saka ta a gaba tana hawaye, sai Amatullah ta dauko musu Alqur'ani suka hadu su biyu suna karanta mata. Can daga baya Amatullah suka yi waya da Abdulrahim ya gaya mata sun sauka a Abuja har sun dauki hanyar palace din ma, a lokacin ne kuma Lami, mai aikin gidan ta lokacin tazo tana sallama, ta bude kofar dakin ta fita sai Lami ta sanar musu da cewa mai gadi ya shigo yace anyi bako a waje. Amatullah ta katse wayar sannan ta amsa mata da cewa tace ya shigo, sai kuma ta fara tunanin waye wannan? Dan gidan kam ba baki ake yi ba, babu mai zuwa sai sulaiman da Zunnur wani lokacin, su kuma duk lami da mai gadi sun san su dan haka ba zasu tsaya tambaye tambaye ba. Ta juya tana kallon Sumayya "mommy? Wai bako akayi a waje ko waye kuma? Na dai ce ace ya shigo" Sumayya ta mike da sauri tana ajjiye Alqur'anin da yake hannun ta ganin haka yasa Amatullah tayi sauri tace "ko ince kar ya shigo?" Sumayya ta girgiza kanta da sauri amma bakin ta ya kasa magana, idanuwan ta a waje, suka tsaya suna kallon kallo ita da Amatullah har suka ji motsin kofa alamar an shigo palo, Sumayya ta hadiye wani abu sannan a hankali tace "leƙa kiga waye", Amatullah ta bude kofa ta fita, Sumayya kuma ta cigaba da tsayuwa idanunta akan kofa kunnuwan ta kuma a bude tana so taji ko da muryar sa ne, ba jimawa kuwa taji muryar "where is she?!" Taji gidan yayi amsa kuwwar muryar sa, idan ba dan tasan Hassan baya gari ba zata ce shine yayi maganar, murya mai amo murya mai sa tsoro a zuciyar wanda aka yiwa magana da ita. Ta juya da sauri ta kalli Ruqayyah, sai taga ta bude idonta da sauri bayan tun da ta shigo gidan idonta a rufe yake. Tana kallon yadda kirjinta yake dagawa da sauri alamar numfashi take yi cikin tsoro. Amatullah ta bude kofar ta shigo, fuskarta dauke da tsoro, murna, excitement da kuma jerin tambayoyi. "Mommy shine, Amir ne, mommy kamar su daya da Daddy, har muryar, idonsu amma ba iri daya ba, Daddy ya fishi tsaho kuma, mommy fada yake yi amma bansan me yasa yake fada ba wai ke yake nema. Ke kika tura masa e-mail dinnan ai ko?" Sai Sumayya ta zauna tare da kama hannun Ruqayyah ta rike a cikin nata, hawaye suka zubo a nata idanun kamar yadda suke zuba daga idanun Ruqayyah. Amatullah taji jikinta yayi sanyi, ta durkusa a gaban mommyn ta, "mommy lafiya? Me yasa yake fada? Me yasa kike kuka? Ji nake murna zai yi ya same mu kema kuma murna zakiyi cewa ya dawo gida" Sumayya ta juyo tana kallon ta tace "Amaty, na aika masa da sakon ne a matsayin nice Ruqayyah, ya dauka wacce ta yar da shi ce ta aika masa da sako shi yasa yake fada" Amatullah ta bude baki, ta kalli Sumayya sannan ta kalli Ruqayyah tana girgiza kai tace "mommy don't, kar ki dauki laifinta ki dora wa kanki, a zuciye yake, in yayi miki wani abun kuma fa? Ki bari in kira daddy yanzu su dawo, ki bari in jashi zuwa gida in kira su yaya A1 tunda yana gari kafin su Daddy su karaso, ko kuma in kaishi gidan Aunty" Sumayya ta saje girgiza kai tace "Amatullah Ruqayyah is dying, laifin da tayi wa yaron nan yana da girma, ba wai ina so in dauki laifinta in dorawa kaina bane ba tunda ba zan iya haka ba, bansan ta inda zan fara ba amma ina fatan zai yafe mata ne kafin ta bar duniya" Amatullah ta fara girgiza kanta, hawaye yana zuba daga idonta, Sumayya tace "Amatullah hakkin Amir ba zsi bar Ruqayyah ta kwanta a kabarin ta lafiya ba. Ki taimaka min.. " ta mika mata littafin da yake kusa da ita, "ki ce masa gashi wannan in ji ta tace yaje ya karanta sai ya dawo suyi magana. Kar ki kira babanki, ki barshi ya karanta yazo kuma ya ganta kafin su dawo" Amatullah ta karbi littafin tana goge hawayenta, idonta akan Ruqayyah da taga lokaci daya ta koma kamar yarinya yar shekara goma saboda kankancewar da tayi. Ta tuno da Sa'adatu da kuma Sa'ad, ta tuno da Inna Ade da Baba. Sai ta juya ta fita da littafin a hannun ta idonta yana zubar da hawaye. Sumayya tana jin duk abinda ya guda na a tsakanin su, kum ta tabbatar Ruqayyah ma taji, sannan kuma taji fitarsa daga gidan ta fahimci yana da zafin zuciya amma kasancewar ta zauna da masu zafin zuciya har biyu, Ruqayyah da Hassan, ta san suna da saurin saukowa, daga sun gama hayagagar fadansu shikenan zasu huce, amma kuwa anya Amir zai huce kuwa? Anya abinda akayi masa duk saurin saukowar mutum zai sauko da wuri kuwa? Bayan tafiyar sa Amatullah ta dawo dakin, ta jingina da jikin bango tana kallon twin sisters din, one dying and the other one looking after her dying sister. Sai ta dauko wayarta tana ta jujjuya wa a hannun ta tana tunawa da cewa babanta yana can yana bulayi a Abuja yana neman mutumin da ita kuma yanzu ta rabu da shi. Anya kuwa in tayi haka tayi dai dai kenan? Amma kuma in ta kira shi bata kyautawa mahaifiyarta ba kuma kamar ta hada su rigima kenan. Neman wanda zata gaya wa maganar tace yi, irin abun farin ciki ya same ka kana neman wanda zaku yi murna tare amma kuma tana gudun batawa mahaifiyar ta. Dan haka ta cigaba da zama wayar ta a hannun ta tana shige da fice a kafofin sadarwa amma bata da damar isar da sakon da zai faranta ran mahaifinta. Sai dai, cikin lokacin da bai wuce awa daya da rabi ba Lami ta dawo ta kuma yin sallama tare da sanarwar cewa bakon daya fita dazu ya dawo. Akayi kallon kallo tsakanin Amatullah da Sumayya. Har ya gama karanta littafin kenan? Amatullah tace "mommy har ya dawo wai, kince yaje ya karanta ya dawo kuyi magana kuma gashinan har ya dawo" Sumayya tace "ah ah, bai karanta ba, isa ace har ya karanta ba, amma me ya dawo dashi?" Amatullah tace "mommy na gaya miki a fusace yake wallahi, ina jin tsoro fa, ki bari in kira wani in hada shi da shi yadda zasu fi fahimtar juna" Lami ta sake knocking kofar tace "ace masa ya shigo?" Sumayya ta rintse idonta ta bude, gidan ubansa ne or rather gidan sa ne, babu yadda zata yi ta barshi a waje yana jira tace "ya shigo, a shigo da shi" sai Amatullah tayi sauri ta bude kofar ta fita, ita duk bata yarda da wannan dawowar ta Amir ba. Kafin ta fita Lami ta fita, sai ta jira ta tana dawowa tace "Lami taimaka min kije gidan Aunty, ki ce mata ina neman taimakon ta, ki ce mata ina nan gidan nan" Lami tace "akan bakon nan da yazo ne ko? Nima duk ban yarda da yanayin sa ba" Amatullah tace "bana son tsegumi Lami kije kawai kiyi abinda na saka ki" Lami ta fita da sauri, a dai dai lokacin da Amir yake shigowa da mota cikin gidan, mai gadi ya tambaye ta "wannan bakon an san shine a cikin gidan kuwa? Ni ban yarda da yanayin sa ba. Ina aka aike ki kuma?" Lami tace "ina ruwanka? Ni bana son tsegumi" ta wuce zuwa gidan Aunty da sauri. Sai da Amir yayi kokarin tsayar da karkarwar jikinsa sannan ya bude kofar motar ya fita tamkar an harba shi da kibiya yayi hanyar da yabi zuwa cikin gidan dazu. Bai rufe kofar motar ba kamar yadda bai rufe kofar palon ba bai kuma kula yarinyar dazu ba data fara yi masa magana tunda ya shigo palon dan bai ma san me take cewa ba. "Where is she?" Ya sake cika gidan da hargowa, sai kuma ya doshi dakin da yaga Amatullah ta shiga dazu ba tare daya jira komai ba ya murda komar ya kuma tura. Sumayya ta saki hannun Ruqayyah ta mike tsaye tana facing dinsa, shima ita yake kallo dan bai ma dauka da akwai mutum akan gadon ba. Cikin mamaki yace "you?! Aka ce ba kya tafiya kuma ba kya magana? Karya dama akeyi min kenan?" Ya juya yana kallon Amatullah da ta ke tsaye a bayansa. Sannan ya sake kallon Sumayya wadda ta kasa dauke idonta daga kansa tana tasbihi ga ubangijin halitta, gashi dai kana kallon sa direct xaka ce yana kama da Hassan amma yanzu da yake tsaye a gabanta yake magana sai take ganin kmaar Hussain ne yake yi. Tayi murmushin da ita kanta tasan duk da cewa tana cikin rudani a yanzu amma har cikin zuciyarta yake, tace "welcome home son" Sai yace mata "ke ce Ruqayyah? Wacece Ruqayyah?" Sumayya ta kalli Ruqayyah da take kwance tana kallon sa, idanunta kamar zasu fado waje dan tsoron da suke bayyana wa tace "baka karanta littafin dana baka ba, daka karanta da ba zaka tambayi wacece Ruqayyah ba" ya takonzuwa tsakiyar dakin yana jin kamar ya faffalla mata mari yace "na karanta iya kacin inda na karanta" ya kalli inda take kallo sannan ya lura da mutum a wajen sai ya kuma kallon Sumayya lokaci daya yana lura da kamannin su duk kuwa da irin lalacewar da Ruqayyah tayi, yace "a cikin ku wacece Ruqayyah? Wacece Ruqayyah nace! Wacece ta dauke ni a ranar da aka haife ni ta raba ni da iyaye na har na tsahon shekaru talatin da biyar?!" Ya karasa cikin tsawa, Amatullah tazo ta sha gabansa tace "yaya Amir, daka karanta labarin da mommy ta baka da baka bukaci sanin ko wacece Ruqayyah ba, da ka fahimci cewa babu wani fushi daya rage maka wanda zaka huce akanta, babu wani abu da ya rage wanda zaka yi mata wanda Allah bai riga yayi mata ba. Da ka fahimci irin fushin da ubangiji yayi da ita saboda taba ka da tayi. Daka fahimci cewa duk wannan abin da kake yi is not necessary kamar kana nuna rashin godiyar ka ne ga ubangiji, kamar........" Daga ta yayi chak daga gabansa ya ajiye ta a gefe sannan yace "shut your mouth" ya taka har gaban Sumayya yana kallon fuskarta, a cikin fuskar tata ya hango alamun gaskiya da kuma kamala, daga alama tana cikin rayuwa mai kyau, shi kuma yayi imani da cewa babu wanda zai yi masa abinda akayi masa sannan ya samu rayuwa mai kyau a duniya ko kuma a lahira sai ya mayar da idonsa kan Ruqayyah, a take ya hango abubuwa iri-iri a fuskarta, duk da cewa jikinta a rufe yake da bargo amma tsoron daya gani a fuskar ta kadai ta nuna masa cewa ita ce ta aikata masa duk wadannan laifuffuka, ita ce matar da tayi snatching 35years out of his life, ta hana shi samun duk wani abu da yaya suke samu a gurin iyayensu, ta shafa masa bakin fentin da duk wankan da yayi tayi ya kasa goge wa, ita ce ta dasa masa kiyayyar matar daya kamata ace ta zamanto mafi soyuwa a gare shi a zuciyar sa, ita ce Ruqayyah, his nemesis. Ba tare da tunanin komai ba ya daga kafarsa wadda take sanye cikin wani kafcecen takalmi da niyyar talitse mata fuskar da take kallon sa da ita. Sumayya ta rufe bakin ta da hannu bibbiyu tana hana ihun da yake kokarin fitowa karasa fitowa, Amatullah tazo ta rike shi ta baya tana kokarin janyeshi duk da cewa ko irinta guda hudu aka hada ba lallai su iya ture shi ba. Magana suka ji daga bayansu, maganar data dakatar dashi half way from doing abinda yayi niyyar yi, ya juyo da sauri yana jin kamar ya san sautin muryar duk da kuwa a zahiri bai sani din ba. Aunty ce a tsaye a bakin kofa, hannunta rike da sandan da take dogara wa saboda taji saukin tafiya. "Hassan" ta fada tana kallon sa, amma kuma wannan ai ba Hassan bane ba, ta kara sa shigowa dakin idon ta a kansa, yayinda shi kuma ya sauke kafarsa kasa tare da juyo wa yana facing dinta sosai, yana jin abinda yake jansa zuwa gare ta yafi wanda ya ja shi zuwa ga Ruqayyah karfi. "Hussain!" Ta kuma fada cikin mamaki tana kare masa kallo, sai ta yarda sandan hannunta, hannun yana karkarwa ta dora a fuskarsa ta sake cewa "Hussain dina" sai kuma kuka ya kwace mata. Ta jawo shi jikinta tana kuka, "Hussain" ta sake fada. Sumayya tazo ta kamata, "Aunty Amir sunansa, yaron Hussain da Fatima ne Allah ya dawo mana dashi gida" ya juyo yana kallon Sumayya da sauri, sai yanzu ne ya tabbatar da sunayen mahaifan sa Hussain da Fatima. Shi farko da tsohuwar ta shigo ya dauka ita ce Fatima din , ya dauka ita ce ta haife shi. Sai Aunty ta sake shi sannan ta kama fuskarsa a hannun ta tana kallon sa kamar yadda shima yake kallon ta amma a ransa yana lissafin wacece wannan, ko kakarsa ce? To babar Hussain din ce ko kuma babar Fatimah? Ko ma dai wacece shi yaji har cikin ransa yana kaunarta kamar yadda ya gani a idonta cewa tana tsananin kaunarsa. Sai yaga ta cika shi sannan ta koma gefe daya ta kalli gabas sannan durkusa duk da tsufanta ta dora goshinta a kasa tana sujjada, sujjadar godiya take yi ga ubangiji daya ja da ranta har zuwa yanzu sannan kuma ya cika mata burinta na ganin tilon dan Hussain. Kuma ganin nasa ma irin wannan ganin, a nutse a kammale ba wai a wulakance a kuma tarwatse ba. Sai yaji abin ya taba zuciyarsa sosai, dama ana sonshi har haka? Har za'ayi sujjadar godiya saboda ganin shi, wacece wannan. Amatullah ta matso kusa dashi ta tsaya tana kallon Aunty itama tace "Aunty kenan. Ita ce kakarmu" ya juya yana kallon ta yace "wacece ke?" Shi dai yaga suna kama amma kuma a iyakacin labarin daya karanta ya fahimci an yar dashi ne a ranar da mahaifinsa ya rasu. Kenan bashi da kanwa da suke same father same mother. Sai tayi murmushi tana share hawayen ta tace "ni kanwarka ce yaya Amir" shi bai taba jin an ce masa yaya Amir ba, sai yaji wani iri. "Mahaifina da mahaifin ka twins ne" ta kalli Aunty tace "Aunty kanwar mamansu ce, amman ita ce kamar mahaifiya a gare su dan mu da muke yayansu ne kadai muka san ba ita ta haife su ba." Ya kalli aunty sannan ya dawo da kallon sa ga Amatullah dan ya fahimci tana da amsoshi a bakin ta yace "ina Fatima? Ina mahaifiya ta?" Ta lura da tension din cikin tambayar, amsar ta ita zata nuna masa ko mahaifiyarsa tanada rai ko kuma a'a, and she was so happy to answer him. Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020 *Beloved Son* Tun daga yadda yaga murmushi a fuskarta da haske a idonta yaji abinda ya hana shi jin cikakken farin ciki har yanzu yana narkewa yana bawa farin ciki wajen zama a zuciyarsa, "tana nan da ranta yaya Amir, tana Dubai a yanzu tare da family dinta. Ba zan iya kwatanta irin farin cikin da zata yi ba idan wannan labarin ya same ta dan har yau bana jin akwai abinda take so sama da kai. Duk da ta haifi wasu yayan amma kai din na daban ne a gurin ta" ya lumshe ido sa ya bude, yana so ya kwatan to kamannin ta a zuciyarsa amma kuma ya kasa, bakin cikin sa kawai daya kasance ba yau zai ganta ba. Yana so ya cigaba da yiwa Amatullah tambayoyi amma ganin Aunty ta dago daga doguwar sujjadar ta sai ya tafi gurinta, yaga matar nan ita ma mai lafiyan ta taho gurin auntyn tana kamata ta mikar da ita tsaye. Sai ta sake kama shi ta rike kamar mai tsoron kar ya gudu tace wa Sumayya "ina Hassan? Tun safe ya shiga ya gaishe ni yace wai zai je Abuja" Sumayya tayi murmushi tace "gurin sa ya tafi ai abujan, nemansa ya tafi da kan shi" Aunty tace "au dama an samu labari shine ni ba'a sanar da ni ba?" Sumayya tayi dariya "baya so ya tayar miki da hankali ne aunty, bamu tabbatar shi din ne ba yafi so sai ya tabbatar sai ya kai miki shi har gida" Aunty tace "to alhaki nane to ya saka yayi gajen hakuri ya tafi, gashi nan ni na riga shi ganinsa" Amatullah tayi dariya, Amir shima yayi murmushi, murmushin sa na farko a ranar, sai dai shi gabaki daya a rude yake, su waye wadancan twins din? Amatullah tace masa mahaifiyarta ce ta tura masa sako, meaning daya daga cikin su ita ce matar auncle dinsa Hassan kuma ita ce babar su Amatullah amma kuma mai lafiyan yaji Amatullah ta kira da mommy bayan kuma jikinsa ya bashi marar lafiyan ce ta jefar dashi. How is that so? Ya juya yana kallon Ruqayyah da duk abinda suke yi tana jin su kuma tana ganin su, sai Aunty ta kamo shi, "kar ka kula ta, kar ma ka kalli inda take dan ita waccan guba ce, macijiya ce duk wanda ya rabe ta sai ta zuba masa dafinta, sai ta gurbata masa rayuwarsa, ita din albasa ce wacce bata yi halin ruwa ba. Kar ka kulata, ka barta a yadda Allah ya nannade ta ya ajiye ta a gurin ta cigaba da rayuwa a haka har sai ranar da wanda ya bata rai ya karbe kayansa" sai ta ja hannunsa suka fita daga dakin Amatullah tana binsu a baya, Sumayya ma haka, Ruqayyah ta mayar da idanunta ta rufe tana rokon Allah akan kar yabata ikon sake bude su. A nan palon suka zauna, Aunty ba zata iya tuna rabon ta da cikin gidan Hussain ba, dan tun da Hassan ya barwa Ruqayyah shi bata kuma taka kafarta zuwa cikinsa ba. Ta zauna akan kujera tare da aika Lami gidan ta ta dauko mata wayarta, hanyanza hawaye ne yake fita daga idonta, kuma har yanzu hannun ta yana rike rike dana Amir ta kasa sakinsa, Sumayya ta zauna a gefenta tana dauko tata wayar, a ranta tana lissafin wanda zata fara kira ta sanarwa da zuwan Amir. Duk da dai plans dinta bai tafi accordingly ba amma tayi achieving something, at least Amir yaga Ruqayyah da idonsa kuma tasan image dinta zai tsaya masa a rai, kuma yadda tayi masa kallon mai imani tana saka ran akwai tausayi a ransa, maybe wata rana ko ba yau ba zai iya yafe mata. Wayar Hussain ta kira tana tunanin ko a ina suke yanzu? Ko suna jirgi a hanyarsu ta dawowa gida in sun samu Amir din baya nan. Sai taji ya dauka da sauri yana cewa "mommy yana ina? Ya karaso?" Tayi murmushi tace "gashi nan a hannun matarsa ta rike shi kam kam, ina jin ma sai yayi ciwon hannu yau" Hussain yayi dariya yace "Hajiya Aunty ko?" Tana jin sa yana magana da daddyn sa sai kuma yace "gamu nan, yanzu muka sauka a Kaduna, munje har gidansa aka ce mana ya taho kaduna, mun san nan ya taho shine muka juyo" ya fada muryar sa cike da excitement, tace "gashi nan fa, idan baku yi sauri ba Aunty sai ta lashe shi tas ta bar muku saura" Ta ajiye wayar tana kallon Amir tana dariya, ta kasa karantar emotions dinsa dan shi kansa bai san menene emotion dinsa a lokacin ba, he was so furious sanda ya shigo gidan amma wannan dattijuwar, irin soyayyar da ya gani a idonta melted that anger and that hatred da ta cika zuciyarsa, matar kuma da aka gaya masa ba mahaifiyarsa bace ba ba kuma kakarsa ba ce ba kanwar kakarsa ce, wannan ya saka shi tunanin me zaiji idan yaga mahaifiyar ta sa? Ko kuma auncle Hassan din da yaji ana ta magana? Wanne irin so suke yi masa wanda har zaifi wanda ya gani a idon wannan dattijuwar da ta kasa sakin sa sai shashshafa shi take yi. Wayar ta da aka kawo mata ce ta saka ta cika shi at last ta fara waya tana kuka tana kuma dariya a lokaci daya, bai san da suwa take wayar ba amma dai labarin zuwansa take bayarwa. More relatives? How many if them are there? Ya kalli Sumayya yaga itama wayar take yi itama kuma da hawaye a idonta da kuma dariya a fuskar ta, ita ma wasu take gaya wa yazo, ya kalli Amatullah ita ma the same thing. Sai ya kalli dakin da suka fito daga ciki, idan yayi ra'ayi zai iya zamewa ya shiga dakin ya huce haushin sa akan wannan mokadaddiyar matar ta kwance amma kawai sai yaji a ransa baya son yi mata komai kuma, not anymore. But har yanzu yana bukatar answers, sai ya mike ya koma gaban hoton dazu ya zubawa twins din ido yana kallon su, daya daga cikin su shine mahaifin sa, shine kuma baya duniya. Ya mutu ranar da aka haife shi kamar yadda ya karanta a labarin accident din daya karanta a littafin. Sai ya juya ya kalli Amatullah da take ta yawa tana bayar da labari, yayi mata alamar tazo, ta katse kiran ta taho gurinsa da sauri itama tana kallon hoton, ta tsaya a kusa da shi sai yace "waye Hassan waye Hussain?" Ta gane abinda yake son sani, mahaifin sa yake son banbancewa, tace "Hussain, kamar yadda Daddy kullum yake bamu labarin sa yace shine the most handsome man in Kaduna a zamanin sa, the youngest richest man a lokacin sa, the most carefree and generous man, the proud dangoten kaduna" ta karasa tana dora hannunta akan fuskar Hussain. Sai kawai Amir ya samu kansa da yin murmushi, murmushin da ya zubo da kwalla daga idonsa, shima ya dora hannun sa a kusa da nata, a hankali tace "he lived the most beautiful life inji Daddy. Nothing but the best for Hussain. And he married a princess" Amir ya juyo da sauri yana kallon ta yace "Princess?" Ta gyada masa kai "yes, princess of Kano" yace "yar sarki Umar?" Tace "kanwarsa, zamanin babansu ne sarki" sai ya rufe idonsa tare da dora goshinsa akan hoton. Kullum abinda yake hangowa a matsayin mahaifiyarsa shine karuwa, ko wata marar daraja marar tarbiyyar da har zata iya cin ciki illegitimately ta haihu ta yar dashi, har yakan yi tunanin cewa itama kanta mahaifiyar tasa ba lallai ne ace tasan mahaifinsa ba, ace duk ba haka bane ba. Ashe shi din mai gata ne, gatan ma kuma mai girma sosai, ashe mahaifiyar sa mai cikakkiyar daraja ce fiye ma duk yadda tunanin sa zai iya bashi. Ya daga kansa yaa kallon cikin idon Hussain, he looked so happy and contented. The smily face exactly irin tasa, sai shima ya samu kansa da mayar masa da murmushi kamar wanda yake ganinsa, sannan a hankali yace "am home, father". A lokacin aka bude kofar palon da sauri sannan suka fara shigowa kuma duk suka doso inda yake tsaye kusan a tare, kowa yana so ya zama na farko daya fara rungume shi. Hussain da Abdulrahim da suka iso yanzu daga airport tare da daddyn su, Yusuf, Aminu, Abdullahi da Abdulrahman da suka taho urgently yanzu daga guraren aiyukan su, mazan su shida chif suka zagaye shi wannan ya runguma ya bawa wancan shima ya runguma, suna ta magana excitedly gabadayan su a lokaci daya babu wanda yake sauraren wani a cikin su kamar yadda shima Amir duk ba wai fahimtar abinda suke cewa yake yi ba, kawai abinda ya lura da shi shine duk yan'uwa ne kuma duk yanuwansa ne duk da bai san dangantakar ba, sai ya juya ya kalli Amatullah data matsa gefe ta basu guri da alamar tambaya a fuskarsa sai tace "cousins dinka ne duk, duk brothers dina ne" Sai da Sumayya ta taso ta fara janye su tana cewa "ku barshi haka, ku barshi ya ga Baban sa kuma" sannan suka tuna cewa daddyn su yana tsaye a bakin kofa yana kallon su tunda suka shigo, sai kuma Hussain ya kamo hannun sa ya juyo dashi yana facing Hassan. Hassan ya ganshi tun sanda suka shigo shida yaransa, ganin nasa ne kuma ya daskarar dashi a tsaye, baya bukatar tambaye tambaye ko wani dna test ko wani bincike, kallo daya yayi masa yasan cewa tabbas wannan daga jikin Hussain dinsa ya fito, ba kuma wai kamanni ba dan bakar fatar sa ta boye kamarsa da babansa, sai ya zamanto kamar dashi yake kama, sai dai wani soyayya da yaji ta yaron ta shiga ransa a lokaci daya, irin feeling din da rabon da ya ji irinsa tun sanda Hussain ya ja numfashin sa na karshe a duniya. Sanda kuma Hussain karami ya juyo dashi suka fuskanci juna sai yaga kamar Hussain dinsa ne yake tsaye a gurin, sanda suka jero tare suka taho gurinsa kuma sai yaga kamar shida Hussain ne lokacin suna matasa, ya taka da kafarsa da take barazanar gaza daukansa ya hadu dasu a tsakiyar palon, sai Amir daya kada dauke idonsa daga kansa yana jin alhinin labarin rasuwar mahaifinsa da bai ma san da shi ba tana tafiya daga zuciyarsa dan yasan wannan mutumin, wannan strong babban mutum na gabansa is more than he would have ever asked for a father. Sai ya sunkuyar da kansa tare da kokarin durkusa wa dan niyyar gaishe shi amma sai yayi sauri ya dago shi sannan ya rungume shi a kirjinsa tare da runtse idonsa. Sai a lokacin yaji wannan sashen na ruhinsa daya fita tare dana Hussain ya dawo cikin jikinsa, sai a lokacin yaji shi ya koma complete. Sai ya tuno da maganar Hussain da yake cewa "look after our children bro, all of them" a hankali Hassan yace "am sorry bro, I failed you" sai Amir ya kara rungume shi tare da cewa "no you didn't. Ban san me yasa baku neme ni ba amma soyayyar dana gani a idonku kawai tasa nasan you did all what you could" Hassan ya dago shi yana kallon idonsa yace "forgive me. Nayi failing. Duk laifina ne, duk abinda ya faru laifina ne. Dan ban aure ta ba, da ban nace lallai sai ita zan aura ba, da na nemi zabin Allah kafin inyi aure da baka tashi a gidan marayu ba ɗana" Aunty ta taho inda suke hannunta dafe da Amatullah ta ce "haba Hassan, sai yaushe zaka daina dorawa kanka laifin wannan abin daya faru ne? Idan da baka aure ta ba ta ina wadannan yaran zasu fito? Rayuka ba daya ba ba biyu ba duk ta ina zasu fito bayan kuma Allah ya riga ya kadarta musu rayuwa a duniya?" Ya juya yana kallon ta yace "amma Aunty ko bayan da na aure ta da na zama careful, dana ji maganar Hussain da duk haka bai faru ba. Hussain tun farko baya sonta ba kuma ya gaya min ba sau daya ba amma ban taba daukan maganar sa ba, ya kamata ace na lura cewa da wahala Hussain yace baya son mutum, shi mai son mutane ne, ace kamar yasan ita ce zata zama silar rusa mana farin cikin mu" ya kalli Amir yace "ashe babanka yasan ita ce zata tarwatsa rayuwar ka, his only child" Amir ya girgiza kansa yace "rayuwata bata tarwatse ba Daddy, banyi rayuwa da ku ba amma nayi rayuwa mai kyau nima. Nasan da a gurinku na girma zan samu soyayya mai yawa, zan samu kulawa mai yawa zan kuma rayu cikin farin ciki amma yanzu komai ya wuce, soyayyar da na gani a iyakacin yau ma kadai ta ishe ni wacce nayi asara ta duk shekarun nan" Sumayya ta dan daga murya tace "a'a bata ishe ka ba, ka ga wadannan?" Ta nuna cousins dinsa na gurin tace "one over six ne na cousins dinka na bangaren babanka kawai, sauran suna nan zuwa dan da yawa daga cikin su suna kan hanya already. Dan haka ina tunanin yau sai ka sha paracetamol kafin ka kwanta dan zaka sha runguma har sai ka gode Allah" duk a kayi dariya, sai Hussain yace "wannan kuma kafin ka hadu dana bangaren mamanka ne, sun fi mu yawa ma su nesa ba kusa ba, I know because am married to one of them" ya fada yana kallon Aunty dan yasan sai tayi magana, ta dake shi a a hankali da walk stick din ta tace "marar kunya fitsararre, to ni wai ko rashin kunyar a sunan take ne?" Hassan yayi dariya yace "haka suke Aunty sai hakuri" tace "ni yanzu ban ma san ta inda zamu fara bawa Fatima wannan labarin ba, Allah sarki Fatima ina jin sai tayi suman dadi in taga dan jaririn ta ya dawo" sai amir yaji kunyar ance masa jariri, Hassan yace "abinda za'a yi shine, ina jin lokaci yayi da ya kamata mu kaiwa Fatima da Adam surprise visit in Dubai. Who is in?" Gaba ki daya suka ce "yes!" Daga nan sai Hassan ya hada kan mazan gavaki dayansu suka fita zuwa Masallaci dan gabatar da sallah la'asar da ake ta kiran ta a lokacin, masallacin gidan suka bude wanda an jima ba'a yi sallar jam'i a cikin sa ba sai dai mai gadi ko wani a yaran gidan, Hassan ya jasu suka yi jam'i a tare, Amir kafada da kafada da yan'uwansa, a cikin masallacin da mahaifin sa ya gina a cikin gidan sa. A cikin gidan kuma sallar suma suka fara yi sannan suka shiga kitchen, sun rasa dalilin da yasa kawai suka ji yau a gidan zasu zauna basa bukatar komawa gidan su, kamar attraction din da gidan yake dashi na mutane da a da ake ganin yayi loosing to yau ya dawo tare da asalin mai gidan. Sumayya da Amatullah suka duba kitchen suka ga abinda babu suka aika mai aiki ta karbo musu a gidan sannan suka saka aka bude katon dining room din gidan wanda rabon da ayi amfani dashi har an manta, masu aiki suka hau aikin sa suka share suka wanke ko'ina. Suna cikin aikin Jabir ya kawo Nafisa da ta taho a rikice na jin labarin bayyanar babyn yaya H2, tun daga nan Amir ta ya cigaba da karbar runguma, kafin ta gama Hassana ta karaso da yar autar ta Ummulkhairi, dan duk sauran yayan nata sun yi aure. Kafin magrib gidan ya cika taf har dakunan da suke a rufe duk an bude su sai girke girke ake yi ana saukewa ana ɗorawa. Amir kuwa tun yana gane bayanin mutanen da ake yi masa har ya daina ganewa, abinda yake fahimta kawai shine manyan sune iyayensa kananan kuma sune cousins dinsa kuma duk yayan Aunty ne. Bayan an uwa kuma sai ga yan unguwa nan sun fara shigowa suma suna ganin Amir musamman wadanda suka san babanshi. Kusan Duk wanda ya ganshi kuwa sai yayi kukan tunawa da Hussain, musamman in suka ga yadda ake bude gidan ana ta hada hada kamar yadda ake yi sanda Hussain yake da rai, wadanda suka san shi sai suke ganin kamar shine ya dawo. Har Zulaihat da take a kano a ranar ta taho tare da yayanta maza su uku, Halifa, Hafiz da dan autan ta Haidar. Ranar duk sai akayi wa gidan aunty da gidan Hassan kaura, masu kwana ma duk cewa suka yi anan gidan zasu kwana suka ringa bude dakunan gidan suna bajewa son ransu. Sai da dare yayi duk wadanda ba yan uwa ba sun gama tafiya sannan suka hadu gabaki daya a babban palon gidan, manya suna zaune a kan kujeru yara kuma gabaki dayan su suna zazzaune a kasa, Amaty tana kusa da Amir dan ita ce mai yi masa bayanin kowa, duk wanda yayi masa magana sai ya tambaye ta waye shi. Bayan sun gama zama sai Aminu wanda shine babban jika ya gabatar da addu'a suka shafa sannan sai Aunty tayi musu introducing Amir, duk da cewa duk sun ganshi kuma sun fahimci ko wanene shi, amma sai ta sake yi musu bayani, ta kuma hada da tsokana cewa duk mazan ta da suke gurin ta daina auren su yanzu tayi sabon miji dan taga alamar sai ya fisu iya rike iyali. Bayan sun gama dariyar joke din Aunty sai Hassan ya fara yiwa Amir bayani, labari ya dauko masa na tarihin babansa, maraicin su da irin struggle din da yasha gurin kafa Kamfanin sa na H and H, anan Amir yasha mamaki "H and H Daddy?" Hassan yace "tabbas, kamfanin mahaifinka ne, shi yayi founding dinsa kuma har zuwa gab da rasuwar sa shine sole owner of H and H. Wannan kamfanin kuma da wannan gidan da muke ciki, zan iya cewa saboda sune aka batar da kai, dan kar ka mallake su". Sai ya bashi labarin yadda aurarrakin su suka kasance, da brief labarin Fatima da irin soyayyar da suka yi da Hussain da kuma irin yadda yanayin zamansu a gidan ya kasance, samun ciki sa da dara rashin lafiyar Hussain, da yadda suka dauki son duniya suka dora wa cikin da kuma yadda Hussain ya boyewa kowa rashin lafiyar sa yayi faking cewa ya warke dan kar ya tayar wa da yan'uwansa hankali, yadda yayi finding out da kuma kyautar da yayi masa ta rabin kamfanin sa, har zuwa ranar da ya rasu. Sai Hassan ya kasa cigaba da maganar, har yanzu mutuwar Hussain jinta yake yi kamar jiya akayi ta, har yanzu yana missing danuwansa fiye da tunanin mai tunani. Ganin yayi shiru sai Sumayya ta taya shi da bayanin accident din da su Fatima suka yi da kuma yadda suke tunanin haihuwar sa ta kasance a wajen accident din. Batan Fatima da kuma yadda Ruqayyah tayi replacing Fatimah da kawarta Minal wacce itama take dauke da tsohon ciki a lokacin. Tayi masa bayanin irin tashin hankalin da suka shiga na tunanin Fatima ce ta mutu da shi a cikin ta sannan kuma ta bashi labarin yadda greed din Ruqayyah ya jawo rabuwarta da Hassan bayan ta rasa jin ta da tafiyar ta, da kuma auren ta uta Sumayya da shi Hassan. Sai a lokacin Amir ya fahimta, dan shi tun dazu tambaya be ya kasa yi amma ya kasa fahimtar uta Sumayya menene role din ta a cikin gidan, ya dauka gaba daya yaran yayan Ruqayyah ne. Sai yanzu ya banbance kuma yaji dadin hakan, dai kuma yanzu ya fahimci cewa ita ce ta tura masa da sako kuma ita ta rubuta masa littafi kuma ya fahimci dalilin ta na yin hakan. Bayan ta dakata ne Hassan ya dora da labarin dawowar Fatima da kuma rigingimun da suka biyo baya, shari'ar da akayi da kuma zaman Ruqayyah a gidan mahaukata har na tsahon shekaru. Fitowar ta, aurenta, haihuwarta da kuma mutuwar twins dinta da kuma komawarta yadda take a yanzu. Sumayya ta fadi yadda Ruqayyah tayi mata nuni da cewa yana da rai just few days ago, da kuma yadda ta gaya wa Hassan aka kuma fara neman sa, sai Hussain yayi bayanin binciken da suka yi using satellite images da kuma zuwansu Abuja abinda ya gudawa tsakanin su da orphanage home din, sai kuma Sumayya ta fadi email din data tura masa da kuma littafin data rubuta masa ta kuma fadi dalilin ta na yin haka. "Ba lallai ne kowa ya fahimci abinda nake ji a raina ba, amma ina saka ran daddyn Amatullah zai fahimce ni tunda yana da abokin tagwaitaka kuma yasan irin soyayyar da take tsakanin yan biyu, ita Ruqayyah wani bari ce na jiki na da ba zan iya cire wa a koda kuwa ta mutu ne ta bar duniya, dan na tabbatar har yanzu kana jin Hussain a cikin ranka, to ina so ka fahimci nima haka nake jin Ruqayyah. Ka saka kanka a matsayi na ka kuma saka Hussain a matsayin Ruqayyah ka ga cewa zaka iya taimaka masa dan ya samu ra rage nauyin da yake kansa ko ya samu dacewa a lahira? Tunda duniyar ta kare va tare data samu komai a cikin ta ba sai wahalhalu da masifun da ita ta jawo wa kanta" Ga mamakin ta maimakon Hassan yayi mata fada sai taga ya riko hannun ta yace "Sumayya! Na fahimce ki and Believe me kusan kowa a gurin nan ya fahimce ki a yanzu, but ki gane wannan, you can't force a heart to forgive musamman a lokacin da mutum yake cikin fushin abinda ake rokon sa gafara akansa. Ki barshi ya huce da kansa, idan yayi niyya shi da kansa zai ce ya yafe mata idan kuma baiyi niyya ba ko ya fada bashi da amfani dan Allah da niyya yake aiki ba da maganar fatar baki ba". Amir bai ce komai ba kuma bai dago kansa ba dan nauyin Sumayya yake ji da kuma su Hussain, amma baya jin zai iya yafewa Ruqayyah, ba zaiyi mata komai ba da sunan ramawa dan Allah ya riga ya gama rama masa amma kuma ba zai iya yafe mata ba, at least not now..... Sai aunty Khadijah ta tambaye shi nasa labarin "an ce ka taso a gidan sarkin Abuja, ance a america ma kayi duk karance karancen ka. Bamu labari" Sai a lokacin Amir ya dago kai yana murmushi, yana jin zuciyarsa tarwai kamar wata dan daren goma sha biyar, wai kuma wannan duk kafin yaga mahaifiyar sa ne. Sai ya basu labarin yadda tasa rayuwar ta kasance, dan abinda zai iya tunawa na daga zamansa a orphanage da kuma zamansa a gidan sarautar Abuja, wahalhalun da suka sha da kuma rayuwarsu a america, hiding the bad side tunda ya daina kuma babu amfanin fadar hakan ga wadanda basu riga sun san cewa yayi ba. Sai ya gaya musu labarin aurensa da kuma albarkar da aka samu a cikin auren. "A aika a dauko min su" Aunty tace "gobe goben nan a aika a dauko min jikokin Hussain in gansu" Hassan yace "insha Allah Aunty" ya kalli Amir yace "ka kira su yau kace gobe da safe su biyo jirgin safe zuwa Kaduna. Suzo mu gansu kafin daga baya mu shirya gaba-daya muje abujan mu yi godiya a gurin sarki Sadiq. Amma kasan Sadiq abokin Hussain ne?" Amir ya girgiza kai cikin mamaki, sai Hassan yace "a can wani guri suka hadu kuma sukayi abota amma mostly through social media, a ranar da Allah ya dauki ran Hussain mun tafi ne dan su sada zumunci ga juna kuma muga dan da akace balarabiyar matar Sadiq din ta haifa masa" Amir ya bude baki yace "Sultan ne, shine abokina da nake gaya muku yanzu" Hassan yace "tun kana labarin na fahimta, ina nuna mana hikimar ubangiji ne na yadda yake gudanar da dukkan al'amuran sa yadda yaso". Daga nan suka cigaba da hira, wacce mostly take akan marigayi Hussain da irin tarin soyayyar da suke yi masa, kowa yana bada nasa version din, babu wanda ya ko kalli dakinda Ruqayyah take kwance tana jan numfashi da kyar, for a moment, ita kanta Sumayya hankalin ta ya dauke daga kan yaruwar tata. A haka har dare ya ja sosai sai manyan ciki suka tafi suka kwanta su kuma yaran suka bude sabuwar hira, har ma da kawo tea, coffee da snacks suka jibge a gefe suka yi daira suna taking turns gurin bawa Amir nasu stories din... Wannan ranar ita ce best day of Amir's life...... So far *Episode Finale* Till down suka yi a ranar, Amir kam ya san ko da ya je ya kwanta ma ba zai iya yin bacci ba dan babu alamar bacci a idonsa ko kadan, sannan kuma wani part na zuciyar sa yana gaya masa kamar idan yaje ya kwanta zai farka ya ga cewa mafarki yake yi ashe. Sai da sukayi sallar asubar su a jam'i a cikin masallacin gidan sannan kowa ya fara tafiya neman gurin kwanciya bacci, ma'aikatan cikin su kam yau sun san zasu yi fashi a office. Amir yana fitowa daga masjid yaga Hassan shima ya fito ta daya kofar, ana ta zuwa ana gaishe shi sai shima ya je ya gaishe shi din, sai a lokacin Hassan yake tsokanar sa "Fatima ce ta shafa maka rashin tsaho, ni dai dan uwana dogo ne nima kuma haka" Amir ya danyi dariya sai kuma ya tambaya "ba ta da tsaho ne?" Ya ji a ransa yana son sanin as much about his mother as possible, sai hassan yayi murmushi yace "ba wai bata da tsaho ba, for a lady tana da tsaho dai dai misali, ina nufin dai kawai baka yi tsaho irin namu ba" sai Amir ya dan bata fuska yana cewa "ni ban yi komai irin nasa ba, naso ace komai irin nasa nayi" sai Hassan ya dan jashi suka fara tafiya suna fita daga gidan yace "kayi kama dashi mana, sosai ma, dan ba kayo fatarsa ba ko tsahon sa ba ba yana nufin baka yo shi ba. In na kalli idon ka sai inga kamar dashi nake magana. Amma kuma duk wannan ba shine abu mai muhimmanci ba, abu mai muhimmanci shine kayo halayensa, shine kuma abinda nake so inyi maka magana akai, ka cigaba daga inda ya tsaya, ka zamanto masa cikakken magajin da yayi ta fatan samu kafin ya bar duniya yadda sakon nin aiyukan alkhairan ka zasu riske shi har cikin kabarinsa. Yadda shima zai san cewa ya haihu yabar magaji a duniya. Ban san adadin lokacin da Allah ya rubuta min zan yi tare da kai ba nima kafin in bi danuwana amma ina so inyi amfani da wannan lokacin gurin dora ka akan turbar da mahaifinka yafi, gurin baka labarai na irin rayuwar da mahaifinka a yayi" suka bude gate din gidan auntu suka shiga, Hassan ya cigaba da cewa "nan shine gidan mu, anan aka haife mu anan muka tashi anan muka yi komai kuma har yau anan Aunty take da zama, sannan anan na binne mahaifinka" Amir ya tsaya ya kasa cigaba da tafiya sai Hassan ya ja hannunsa yace "come, lets go and meet him" yana binshi a baya har suka shiga garden din gidan wanda har yanzu take cike ya yayan itatuwa irin su mango, ayaba, guiva, lemon zaki dana tsami, da sauransu. A can tsakiyar sane kuma Amir ya hango kabarin. Ya tsaya ya kasa cigaba da tafiya kuma ya kasa dauke idonsa daga kan kabarin sai Hassan ma ya tsaya a kusa dashi yace "kafin ya rasu ya sa ka nayi masa alkawarin cewa zanke kai masa ziyara kullum" ya danyi murmushi yace "mako ne dashi baya son rabuwa dani, wannan ne ya saka na binne shi anan kuma nake iyakacin kokari na na ganin cewa na cika alkawarin dana dauka masa duk da dai ba kullum din nake zuwa ba. Amma kuma babu sallar da zanyi in tashi ba tare da nayi masa addu'a ba, ina fatan duk ranar da nima na tafi zaka dora daga inda na tsaya" Amir da har yanzu idonsa yake kan kabarin babansa ya gyada kai da sauri ba tare da yace komai ba dan yana ganin kamar in ya bude baki kuka ne zai fito. Sai Hassan ya dan dafa kafadar sa yace "go and talk to him, kayi masa addu'a. In ka fito ka same ni a cikin gidan Aunty" sai ya juya ya ta fi ya bar shi. Amir ya jima a tsaye sannan ya taka a hankali ya karasa gaban kabarin ya durkusa, sai da yaga hawayen sa yana diga akan kabarin sannan ya fahimci kuka yake yi, bai goge hawayen ba yace "Assalamu alaika father. Am here. Finally" Sai da rana ta fito sosai sannan Amir ya baro kabarin Hussain, shima kuma saboda ya tuna bai yi waya da Aysha ba, bai gaya mata duk abinda ake ciki ba ballantana yayi mata maganar tahowa kamar yadda Hassan ya umarce shi. A cikin garden din ya samu kujera ya zauna sannan ya dauko wayarsa da tun jiya bai duba ta ba ya kunna da niyyar kiran Aysha amma kafin ma ta gama budewa har kiran ta ya shigo, sai yaji bai ji dadi ba a ransa dan yasan kwana tayi tana tunanin halin da yake ciki tunda bai taba tafiya ya wuni ya kwana basu yi waya ba. Ya dauka yana kokarin gyaran murya amma muryar tasa ta daskare sosai, cikin saurin magana take cewa "Amir, honey are you okay? Ka kashe phone tun jiya bamu ji ya kake ba" muryar ta kamar zata yi kuka, sai ya kara gyaran murya yace "am sorry sweetheart, nayi laifi kiyi hakuri" sai tace "lafiya kuwa? Naji muryar ka wani iri" yayi shiru yana tunanin ta inda zai fara yi mata bayani sai yace "daga ziyara nake Aysha, daga ziyarar kabarin mahaifina nake" ta danyi shiru kamar bata fahimci me yace ba sannan tace "mahaifinka fa kace?" Yace "eh Aysha, abinda ya kawo ni Kaduna kenan,ban gaya miki ba saboda ban tabbatar ba, amma yanzu na tabbatar, a gidan mu na kwana jiya Aysha, a cikin yanuwa na" muryar sa ta karye kamar zaiyi kuka yace "I have a family Aysha, and they love me so much".......... Sun jima suna magana da Aysha kafin ya baro garden din, shi sai yaji ma kamar ta fishi murna dan kamar zata shide masa a cikin wayar, yana jin Sultan yana tambayarta menene take kuka, tun kafin yayi mata zancen tahowa ita tafara yi masa kuma yadda yaji tana dokin abun ya tabbatar a yanzu haka ta fara hada musu kayan su ita da yara. Bayan sun gama ne kuma ya kira wayar abokinsa Sultan shima ya gaya masa abinda ya faru, shima kuma daga muryar sa ya san ba karamin dadi labarin yayi masa ba kuma nan take yace masa zai taho tare da iyalinsa zasu biya su dauko Aysha su taho tare, bayan sun gama wayar sai ya sake kiran Aysha yace ta shirya Sultan da Moon zasu dauko ta su taho tare. A palon Aunty ya samu uncle dinsa Hassan kamar yadda ya gaya masa ya same shi a can, ya gaishe da Aunty da kuma aunties dinsa da duk ya same su tare da auntyn, suna ta tsokanar sa wai sai ya fadi sunan kowa a a cikin su shi kuma duk ya gane fuskokin amma ba zai iya hada fuska da suna ba musanman saboda duk suna yanayi, sai ya juya yana waigen neman Amatullah, Hassan yace "bata nan ai interpreter din taka" sai yayi murmushi, Aunty tace "ina kallon ta ai tun jiya ita ce mai gaya masa sunan kowa da kuma alakar sa da kowa, fatan dai ta gaya maka cewa yar riko ce ita?" Amir yayi dariya "haba dai Aunty, ko makaho ne ya shafa fuskarta ya shafa tawa ai yasan kanwa ta ce" Aunty ta rike baki "la ha ila, zasu nuna min yanubanci ina a gaba na, har ina sakin sauran mazaje na saboda nayi sabo ashe sabon shima kasa zai watsa min a ido" duk suka yi dariya sannan Aunty tace "ina kishiyar ta wa?" Yace "munyi waya, nasan yanzu suna shirin tahowa in sha Allah" ya kalli Hassan yace "tare zasu taho da abokina Sultan" Hassan ya gyada kai yace "ya kyauta sosai, muma yanzu muke lissafin sanda ya kamata muje abujan dan ina so muje kafin mu tafi Dubai, kuma ina so muje dubai da wuri preparably cikin satin nan dan yadda labarin dawowar ka yake bazuwa a gari, duk da an fada wa duk yanuwan Fatima cewa karsu gaya mata so ake kawai akai mata kai, amma bana jin labarin zai rufu for long, bana so kuma taji a wani guri" yayi murmushi, "I just can't imagine yadda zata yi reacting idan ta ganka, it is unimaginable" Amir yayi murmushi, shima kansa ba zai iya imagining yadda zai yi reacting to ganin mahaifiyarsa ba. Jin sa yake yi kamar a mafarkin da har yanzu ya kasa farkawa daga cikin sa, bayan yayi wanka ya shirya ne cikin kayan Hussain sai suka fito suka yi breakfast gabakidayan su a gidan Aunty, sai a lokacin yaga Amatullah, ya jata gefe ya ce ta banbance masa sunayen aunties dinsu, tana ta yi masa dariya ta sake yi masa bayanin kowa da kuma yayanta, tana yi tana nuna su a boye, Khadijah ta hango su tace "duk dai mai gulma dai yasan matsayin sa, ballantana wanda yake gulmar iyayensa" sai suka yi dariya kawai amma basu daina hirar su ba har sai da Hassan ya taso ya kira Amir yace yazo ya raka shi waje, sai ya bishi suka fita su biyu, suka fita daga gate din gidan Aunty sannan suka tsaya a gaban wata bishiya suna facing gidajen Hassan da Hussain. Hassan yace "Hussain ne ya gina gidajen nan guda biyu" yayi murmushi yace "so yayi yayi su iri daya amma naki yarda, I can remember rigimar da muka yi dashi a lokacin yace zan bata masa tsari wai ba zasu yi kyau ba in akayi daban daban ni kuma nace bana son irin nasa" Amir yayi murmushi shima, Hassan ya cigaba "farko gate daya ne kuma babu katanga a tsakani, burinsa shine mu zauna tare da matayen mu a guri daya dan mu karfafa zumuncin tsakanin mu, so yayi ace yayan mu sun taso tare babu bambanci kamar yadda babu bambanci muma a tsakanin mu" ya danyi murmushi yace "it was even one of his dreams wai watarana yayanmu zasu yi aure da junansu" Amir yayi sauri ya kalle shi amma sai yaga shi hankalin sa bama ya tare dashi, it was deep in his thoughts, ya cigaba da cewa "kasan dan Adam da buri, amma duk kokarin ka na cika burikanka dole sai ka mutu cike da wasu burikan. Amma wannan duk da shine abinda na fito da kai nan in gaya maka ba, abinda na ke so in gaya maka shine wannan gidan a yanzu naka ne kamar yadda ya kasance na mahaifinka before you. Yana daga cikin abinda na gada daga gare shi, kuma tunda kana da rai hakan yana nufin bani da gadon sa kenan daga ni har yanuwana, dan haka dole zamu dawo maka da duk abinda muka gada daga gare shi as soon as possible dan mu guje wa cin dukiyar maraya. Ni abinda na gada shine gidan nan a kuma share a cikin H and H. Wadanda sune abinda na bawa Ruqayyah kamar yadda ta nema dan kar ta bata sunan mahaifin ka kamar yadda tayi iƙrarin yi. Dan haka a yanzu duk wani abu na dukiya da yake dauke da sunan Ruqayyah naka ne, ma'ana gidan nan da duk abinda yake cikinsa da kuma rabin H and H da kuma duk wasu kudi da suke account dinta. For the fast thirty five years babu abinda tayi sai gadin dukiya ita kuma dukiyar tayi ta ninkuwa tana habaka saboda Allah ya san cewa kana nan dawowa zuwa gare ta, ba tare da ita kuma Ruqayyah Allah ya bata ikon jin dadin dukiyar koda kuwa na rana daya ne ba" "Abu na gaba da zamu dawo maka dashi shine abinda yanuwana mata duka gada, wanda su kuma ni suka bawa nayi amfani dashi tare da sauran abubuwan da nake dashi a lokacin da kuma wasu abubuwan da Aunty ta bani wanda sune na hada na juya har suka zama abinda nake dashi a yanzu. Na san in na duba cikin tsofaffin takarduna ba zan rasa wancan tsohon lissafin ba, sai a zauna a fitar da percentage na abinda zai zama riba na kason da yake naka sai a hada a baka gabaki daya daga uwar har ribar" ya danyi murmushi "zaka iya tashi da estate guda koma fiye da haka" Amir da yake ta girgiza kai yace "kayi min afuwa Daddy amma ba zan iya karbar komai daga hannun ka ba, na yafe har abada. Abinda zan karba shine wanda yake hannun Ruqayyah saboda in cigaba da rike legacy din Hussain Aminu Abdullahi kamar yadda ka fada min cewa yana daga cikin biririkan sa cewa sunan sa ya jima a duniya bayan mutuwarsa. Zan cika masa wannan burin insha Allah, tare kuma da sauran wasu daga cikin burikansa" Hassan yace "to sai ka fara cika masa burin ta hanyar tarewa a gidan sa" yayi murmushi, "you have no idea how much yake son wannan gidan" ya fara tafiya zuwa cikin gidan yace "come, let me show you something" Amir ya bishi a baya da sauri yana tunanin abinda za'a nuna masa, the last time da aka ce masa "let me show you something" sai a aka nuna masa kabarin babansa. Cikin gidan Hussain, or rather gidan Amir suka shiga, sannan suka hau stairs suka yi sama sannan suka yi bangaren dama na inda stairs din suka rabu, sai Hassan ya dauko keys a hannunsa yana juyawa yace "na iya ajjiya, amma ban sani ba ko zasu bude kofar ma?" ya mikawa Amir "gwada mu gani" Amir ya karba ya saka a lock din ya dan yi fama for some seconds sai komar ta bude amma sai ya kasa shiga ya tsaya yana kallon katon palon da duk aka yi amfani da yadi aka rufe furnitures din ciki. Hassan ya wuce shi ya shiga yace "nan ne bangaren Hussain. Anan yayi rayuwar sa a gidan nan ta shekara biyu" Amir yabi gurin da duk yasha kura da yana da kallo, Hassan ya cigaba da cewa "na rufe shi tun sanda na barwa Ruqayyah gidan, saboda akwai abubuwa masu muhimmanci sosai a ciki wadanda ba zan so maci amana kamarta tayi amfani da su ba, na dauka zata yi kokarin balla kofar ta shigo ko something amma bata yi ba. Maybe ko dan dakunan gidan sunyi mata yawa ne already? Though ita kanta ma bata jima a saman ba ta koma kasa gabaki daya saboda Allah ya dauke kafar da zata hau benen da ita". Amir jinsa kawai yake yi amma hankalin sa yana kan kallon gurin, tun daga kan yanayin ginin zuwa hotunan da akayi wa gurin ado dasu. Sai Hassan ya wuce shi ya bude kofar da take can karshen palon, zuwa mintuna ya fito ya dawo ya tarar da Amir har yanzu a tsaye a inda ya barshi, sai ya bude hannun sa ya saka masa wani abu a ciki. Amir ya dawo da hankalin sa kanshi sannan ya kalli abinda aka saka masa a hannu, wani madaidaicin diary ne mai hardcover, ya maida idanunsa kan Hassan, sai Hassan yace "he spent almost a year writing this to you. Tun kafin ma a samu cikin ka. I almost burn it sanda na dauka ka mutu but cikin ikon Allah I kept it. Gashinan kuma yau na baka. Maybe zai debe maka kewar sa kadan" sai kuma ya bude daya hannun na Amir ya saka masa keys din gidan a motocin da suke cikin garage din gidan wadanda tun ranar da twins din Ruqayyah suka mutu ba wanda ya kuma amfani dasu. Yace "am telling you all of this and giving all this to you saboda kamar yadda mahaifinka yake yawan fada, today is what we have, tomorrow is never promised" Sai kuma ya juya zai bai gurin yana cewa "ba zan iya zagayawa da kai gidan nan ba, shekaru sun ja" Amir ya saka diary din a aljihun sa yana cewa "haka ne Daddy, Nagode sosai, hakan ma kayi kokari Allah ya kara lafiya. Bara in kira Amatullah sai mu zagaya tare" Hassan ya juyo yana kallon sa yace "Amatullah? Wannan mai shegen son jikin? In na fita zan turo maka Hussain da Abdulrahman sai su taya ka tsara komai. Duk abinda kake bukata zasu yi maka ko su hada ka da wanda zaiyi maka. Amaty babu abinda zata yi maka sai surutu da iyayi" yayi murmushi "halin su daya da baban ta" sai ya juya ya fita ya bar Amir a tsaye yana murmushi saboda ya san wanne baban yake nufi. Bayan fitar Hassan ne Amir ya cigaba da zagaye gurin da idonsa har idon ya sauka akan wata double door, ya tafi gurin da take ya saka hannu biyu ya murda handles din sannan ya tura su suka bude gabadaya yana jin fresh air tana wuce shi tana shiga palon. Ya lumshe idonsa ya bude yana dora hannun sa akan tudun diary din da aka bashi, his father's words written for him. Ya shiga cikin balcony din tare da zaro diary din ya bude, yana lura da yadda pages din suka manne da juna saboda dadewa, a page din farko yaga an rubuta Dear baby.. ..... Sai yayi murmushi, wai shine baby din. Motsiya ya hango daya dauki hankalin sa a waje, ya rufe diary din, this is not the time to read it sai ya samu nutsuwa tukunna. Ya mayar da shi cikin aljihun sa tare da kallon kasa dan ganin abinda yake faruwa. Sumayya ya gani tare da Hussain da Yusuf da Amatullah da Abdulrahim sun fito daga cikin gidan, Ruqayyah a rungume a kirjin Hussain yayi mata irin daukan jarirai. Yana kallo Yusuf ya tafi da sauri ya kunna mota sai suka bude baya suka saka ta sannan Hussain ya shiga gaba Sumayya kuma ta shiga baya kusa da Ruqayyah sannan wata mata mai kayan ma'aikatan asibiti ta shiga daya side din Ruqayyah suka tafi suka bar Amatullah da Abdulrahim. Yayi shiru yana tunani, yasan dauke ta suka yi daga gidan zadu chanja mata wani gurin zaman, sai kawai yaji zuciyarsa tana jin babu dadi saboda su, saboda su Hussain, they didn't choose her as a mother Allah ne ya basu ita, kaddarar su ce. Sai ya mike straight yana realising wani abu, between yesterday and today yayi loosing kansa, yayi mamakin yadda akayi jiya har ya shigo gidan da niyyar kashe Ruqayyah bayan kuma shi din shine kullum mai yiwa mutane preaching akan yadda da kaddara, shine mai gayawa mutane cewa is either suyi accepting destiny dinsu a yadda yazo suyi murma ko kuma su yi living a miserable life, amma shi ga shi lokaci daya bacin rai ya saka ya manta cewa destiny dinsa ne rayuwa for 35 years ba tare da iyayensa ba. Kamar yadda yake destiny din su Hussain ne su zama yayan mutum kamar Ruqayyah. Ya lunshe idonsa ya bude yana kallon su suna fita da ita daga gidan da tayi asarar komai saboda ta mallaka kuma mallakar tasa bata samar mata komai ba sai karin wasu asarorin masu yawa. Karar wayarsa ce ta katse masa tunanin sa, ya dauko ta yana ganin number din sultan ya dauka da sauri "ba dai har kun karaso ba" yace "yanzu dai zamu iso insha Allah, ka fito kan hanya sai ka tarye mu, matar nan taka ce ta bata mana lokaci tana ta hado maka kaya sai kace cewa akayi ba zaka dawo Abuja ba" Amir yayi murmushi, "kar ka takurawa sweetheart dina please, nasan haka zaka saka ta a gaba kayi ta tsokana har ku zo" yace "ba kula ni zata yi ba, tana ta faman dashe baki kamar gonar auduga" Amir yace "bata waya" Sultan yace "anki din, ai kana da number din ta kakira ta mana, ni mata basa karbar mim waya kar su goga fuskar su a inda na goga tawa. Kasan matata tana da kishi" Amir yayi tsaki. "Allah yasa dai nima ina da matar. Ballantana a yi min gori, kuma soon zan zo in wuce ka in ka tsaya wasa" ya kashe wayar yana dariyar mugunta sannan ya kira Aysha, yana sauraron yadda take ta murna, yana jin Maimoon tana tsokanar ta, suka yi sallama bayan ya gaya musu inda zasu tsaya in sun shigo gari. Ganin Amatullah da Abdulrahim sun fito daga gidan da kaya a hannun su ya saka ya juya ya fita da sauri yana hada stairs a uku uku har ya fita waje sannan ya gansu sun dauki hanyar gate sai yace "psss" suka juyo a tare da alamar damuwa a fuskarsu sai kuma yaga sun fara kokarin yi masa murmushi, ya karaso inda suke da key din mota a hannunsa yace "ina zuwa haka?" Abdulrahim yace "gida, kaya ne zamu bayar a shiga dasu ciki" ya gyada kai kawai yana so ya tambaye su inda za'a kai Ruqayyah amma sai yayi shiru, Amatullah tace "kai kuma fa? Na ganka da key" yace "mutanen Abuja ne suka kusa karasowa shine zanje hanya in taho dasu, ko zaki rakani?" Ta danyi shiru kamar zata ce a'a sai kuma tayi tunanin shima bako ne ba lallai ya san hanya sosai ba sai tace "Okay bara in dan gyara sai mu tafi" ya kalle ta sama da kasa yace "you look fine, great even. Me zaki gyara? Common let's go" ta dan bata fuska, Abdulrahim yace "yar gayu ce fa, bata fita sai tayi kwalliya, bara inzo muje" sai Amir ya harare shi ba tare da Amatullah ta gani ba, Abdulrahim a danyi dariya kadan yace "ohh na manta ana jira na zamuje wani guri yanzu. Kuje kawai sai kun dawo. Ya karbi jakar hannun Amaty yayi gaba da sauri. Bata motsa ba har Amir yaje ya dauko motarsa da tun daya gyara mata packing jiya bai kuma bi ta kanta ba, ya zo gaban Amaty ya tsaya sannan ya bude mata kofar kusa dashi ta zagaya ta shiga ta rufe suka tafi. Har yanzu yana ganin alamar damuwa a fuskarta sai ya tambaya "naga dazu an fita da........" Sai kuma ya kasa fadar sunan dan shi dai yaji a ransa ba zai iya ce mata aunty ba kuma ba zai iya kiranta da sunanta a gaban Amaty ba, sai ta hutacce shi tace "Aunty Ruqayyah. Eh an mayar da ita gidan yaya Yusuf zata cigaba da zama a can" ya danyi shiru yana jin sa lost, sannan yace "amma babu takura acan din? Ina nufin iyalin yaya Yusuf ba zasu gako an takura su ba?" Ta girgiza kai tace "babu, ai akwai maaikaciyar lafiyar da yaya Hussain ya dauka musamman saboda take kula da ita, to babu wani nauyi da za'a dora musu. Dama tun da aka sallamo ta daga asibiti yaya Aminu yace ta koma Abuja gurinsa mommy ce ta hana, sai yanxu kuma da kanta tace a mayar da ita gidan yaya Yusuf din tunda shi ba barin garin za'a yi ba. Ita bata so tayi nisa da ita ne kawai" ya gyada kai cikin fahimta, amma kuma bakinsa ya kasa furta komai. Suka cigaba da tafiya zuwa inda zasu hadu dasu Sultan cikin shiru sai dan nuna masa hanya da take yi. Sai ta dauko sunglasses ta saka a idonta dan boye damuwar ta har suka je i da zasu je duka yi packing ya kira su suka ce sun kusa karasowa suma. Sai ya fara kokarin kawar da tension din tsakanin su ta hanyar bata labarin family din shi, Aysha da yaran su, ita kuma tunda mai son yara ce sai ta fara murmushi tana jin dadin hirar. A haka har bakin suka karaso sukayi packing motocin su suna facing juna, driver yana tukawa Sultan a gaba sai Aysha da Maimoon a baya tare da little Sultan da Afnan a hannun Aysha, sai yace mata "akwai kyauta ta musamman in kika gane wacece matata a cikin matan can guda biyu tun kafin inje gurin" ta danyi murmushi tace "okay" amma kafin ya bata amsa sai yaga Sultan ya bude mota ya fito sannan ya bude wa Maimoon kofa yana cewa "gwara dai in fito da matata in rike hannun abata, kar wani yazo wucewa ya dauka ta mai rabo ce". Amatullah tayi dariya, Amir ya bita da kallo yana jin dadin ta saki jikinta tace "ta cikin motar wacee akayi abandoning ita ce matarka" ta mika masa hannu "a bani kyauta ta" yace "the bastard. Duk inda yake sai ya nuna halinsa, gashi nan ya tona min asiri. Bara nima inje gurin matata" ya fada yana bude kofa sannan ya leko yace "kina bina bashi". Bai kula Sultan ba ballantana Maimoon matarsa sai ya tafi da sauri ya budewa Aisha kofa ta fito ya rungume abarsa, tana ta murna, su kuma su Sultan da Amatullah da take cikin mota suna ta murmushin taya su murna dan tabbas abin murna ne ya same su ba karami ba. Sai daya gama jin dumin matarsa sannan ya juya kan abokin sa shima ya rungume shi duna tasu murnar, kowa ya gansu sai ya lira da kauna da kuma shakuwar da take tsakanin su. Amatullah ta fito cikin takunta mai kyau ta karaso inda suke tace "Assalamu alaikum. Sannunku da zuwa" suka juyo tare da amsa mata, ta dan rissina ta gaishe su, Maimoon tace "babu sauran tantama Amir, tabbas daga gida kake" ya nuna Amaty yace "she is my cousin" sai Sultan yace "babu bayani ma, she looks more like your sister ma ni a idona" Aysha kuma tana murmushi tace "ni kuma tafi yi min kama da little sultan ma" Amatullah ta kalli little sultan din da yake fitowa daga mota, daga alama sanda aka tsaya bacci yake yi sai yanzu ya tashi, ta mika masa hannu tana cewa "gaskiya ne Aunty Aysha munfi kama, musamman tunda bamu tara gashi a fuskar mu ba" duk suka yi dariya sun san tsokanar Amir take yi. Sai kuma Amir ya tambaye su yara, Maimoon tace "mun barsu gida saboda school. Suna gurin auntyn su Aisha" sai a lokacin ya kara godewa Allah da bai gaya wa Aysha yarinyar daya nema ba. Ta dauki Sultan ta daga shi sama tana tayi kissing cheeks dinsa tace "bara in dauki rabona na kisses din da zaka samu dan in muka je gida Aunty sai ta lashe ka tas" yace "wacece aunty? Wacece ke?" Ta zaunar dashi a bonet din motar tace "ni sunana Amatullah, ni auntyn ka ce. Aunty kuma kakar Abban ka ce" Sultan yace "har da kaka ka samu Amir" Amatullah tace "har da kaka mai ran karfe, da kuma tarin iyaye lodi lodi" Sai kuma Amatullah ta karasa kusa da Aysha tana cire sunglasses din idonta tare da saka su a jaka tace "kawo babyn, sai ki ji dadin rike mijin" duk suka yi dariya har Aysha data mika mata Afny da take bacci, sannan babu kunya ta kara rike mijin nata. Amaty tana kallon afnan tace "lah Yaya Amir, kasan babyn nan dawa take kama?" Ya juyo da sauri yana kallon ta yace "da wa?" Tace "aunty Fatimah wallahi. Ni dai da Aunty Fatimah naga tayi min kmaa" sai Amir yaji wani irin dadi a ransa.. Tun bayan da yayi aure ya kuma haifi Sultan, sai tunanin sa na problem din rashin Asalin sa ya tashi daga kan sa ya koma kan yayansa, wannan ne dalilin da yasa ya lallaba Aysha suka yi planning saboda yana tausayawa yaran dan yasan gorin ba a kansa kadai zai kare ba har sai ya dangana dasu da kuma yayansu. Amma ga yadda al'amurra suka juye masa, wai yau har yarsa ake cewa tayi kama da kakarta, mamansa. Sai kuma suka koma motocin su sannan suka karasa gidan. Tunda suka yi packing suka fito Sultan ya daga kai yana kallon gidan yace wow, sai Amir yace "hold your wow tukunna, zata yi maka amfani nan gaba". Gidan aunty aka fara shiga dasu, nan take Aunty ta rude ta rike Aysha ta rike little sultan ta ma rasa wanda zata tarya acikin su, ta kuma rasa da wanne baki zata yiwa Allah godiyar wannan kyauta da yayi mata. Wai yau ita ce ta ga ba ma dan Hussain kadai ba har ma da yayansa. Amatullah da take zaune akan hannun kujerar kusa da Aunty tace "aunty ki saki yaron nan Please, kar kije ki shafawa dan mu tsufa muzo mu rasa yadda zamuyi dashi in kin tafi, na sanki yanzu sai ki ce shima ya zama mijinki" Aunty ta harare ta "kinsan dai ni maxa har yawa suka yi min kullum sai na zaba na darje. Ke kuwa fa? Iyayi da kinibibi ya hana ki samun miji ko da guda daya ne. Ji wannan uban gilashi sai kace tsohuwar makauniya" Amatullah ta tura baki tare da mikewa. "Ni daya kwakwkwara zan samu ba irin mazajen ki ba taren yuyuyu" Sun jima nan gurin Aunty sannan kuma suka tafi gidan Hassan, anan suka samu tarya mai kyau da abinci iri iri ga kuma shimfidar fuska. Sultan karami kuwa dama gidan Aunty aka baro shi ya samu yara saaninsa ya shige cikin su suna ta wasa sai da Sumayya tayi waya tace a rako shi suma su ganshi sannan sai gashi an kawo shi. Hassan kuwa ya dauka ya rungume ya hana Sumayya tabawa ita kuma ta karbi afnan tace shima ba zai dauka ba. Aysha kuwada Maimoon suna dakin Amatullah nan sukayi sallah harda kwanciya akan gado suka huta, ita kuma Amaty ta zauna tana tayi musu hira tana kuma amsa wa Aysha tambayoyin ta akan family kamar yadda ta ringa amsawa Amir. Amma bata bata labarin komai in details ba tunda tana ganin hurumin mijin ta ne ya bata wannan. Sai bayan da Amir da Sultan suka ci abinci tare da Daddy da sauran mazan da suke gidan sannan Amir ya fita da Sultan zuwa gidan sa suka zauna acan su biyu kuma ya bashi labarin duk abinda ya sani game da yar da shi da akayi da kuma samo shi da akayi yanzu. Sultan ya taya shi murna sosai da sosai. Sai suka kira matan su suma suka zo suka ga gidan tare da rakiyar Amatullah. Suna nan har dare sannan suka koma gidan Daddy suka ci abincin dare shi kuma ya gama musu gobe gabaki daya zasu je Abuja suyi gaisuwa gurin mai martaba sarki kuma suyi godiya. "I can't wait to see his face idan yayi realising Amir dan abokin sa ne" Da dare Sumayya tace su Aysha da Maimoon su kwana anan gidan gurin Amatullah tunda godan Amir din sai anyi gyara sosai a ciki, amma su kuma mazan zasu iya kwana a ciki. Amatullah tana ta murna tana tsokanar su "yau kowa ta zama gwaurowa, sai ku kwanta inyi ta muku tatsuniya" Maimoon tayi murmushi tace "rike tatsuniyar ki, in dai mazan mu ne basu san bakunta ba ballantana alkunya. Muna nan dake zaki ga abinda zai faru" ai kuwa ba'a jima ba Amir ya kira Aysha a waya wai su fito ita da Maimoon suji wata magana mai abin mamaki" suka dauki mayafan su da sauri kamar dama jira suke yi suka lallaba suka fice suka bar Amatullah da citson yatsa, bata kuma ganinsu ba sai data farka da assuba ta gansu suna bacci, bata san kuma ta yadda suka shigo ba. Da safen kuwaaka shirya, iyaye da kuma manyan yaya, suka dauki hanyar Abuja bayan Sultan yayi waya ya sanar da zancen zuwansu da kuma abinda yake tafe dasu. Sanda suka sauka sai aka shigar da mazan gurin saukar baki na musamman da yake cikin gidan, matan kuma suka wuce cikin gida bisa jagorar Maimoon da Aysha, wadanda dama tare aka taho dasu. Suka wuce dasu direct gurin Ummee mahaifiyar Sultan, anan Sumayya taga balarabiyar da ake magana akanta. Sun samu sauka sosai a fadar Abuja abin dai sai san barka, Ummee da kanta take waya kowa da yasan Amir yazo yaga iyayensa gasu nan sunzo, haka aka yi ta zuwa ganin su kuma kowa yana ganinsu yake tabbatar wa cewa babu ja Amir dansu ne, sai kuma mutane suyi musu murna su kuma yiwa Aysha murna dan duk sun san sacrifice din da tayi ta auri Amir, sacrifice din da ba kowacce macece zata iya yin sa ba. Amma kuma yanzu gashi Allah yayi mata sakayya, dan ganin yanuwan Amir kadai ya isa ya nuna wa mutane cewa yan dangi ne kuma sun jiku da raina, da zarar an ambaci H and H kuwa sai abar mutane da sakakken baki. Mamakin kuma sai ya karu idan aka ambaci gidan sarautar kano a matsayin dangin sa na uwa. "Lallai Amir din mu dan gata ne gaba da baya. Shi yasa aka ce duk inda kaga mutum kar ka wulakanta shi dan baka san ko shi waye ba" A gurin maza ma haka ta kasance, hakiman gidan, yan'uwa da sauran bayi da barori kowa zancen yake yi "Amir dai wannan yaron abokin Sultan" "shine mai H and H din?" "Babansa ne, kuma uban ance ya mutu, kuma shi kadai ne dansa a duniya" "babarsa kuma yar marigayi sarkin kano ce, kanwa kuma ga sarkin kano na yanzu" "dan sarauta ne kenan?" "Sosai ma" "shi yasa ni tun farko naji ina son yaron nan, tun suna hatsabibancin su a gidan nan. Ashe babban mutum ne" Hmmmm Mai martaba sarki yayi murna matuka, ya kuma yi mamakin tare da alajabin kasancewar Amir da a gurin abokin sa Hussain. "Hussain mutumin kirki ne, yana kuma daga cikin abokai na wadanda har yau ba zan taba mantawa dasu ba dan nasan da yana raye da har yanzu abotar mu tana nan. Labarin rasuwar sa data matarsa mai dauke da cikin tilon dansa ta taba zuciyata sosai a lokacin, har naji duniya duk ta fita daga kaina. Amma sam ni bani da labarin ma cewa Fatima ta dawo gida bata mutu ba, ba kuma ni da labarin har anyi Shari'a ana neman dansa. Amma hakan ba abin mamaki bane ba saboda akwai abubuwa da dama, abubuwan da suke da tsananin muhimmanci a gare ni da wadanda ban basu muhimmancin daya kamata ace na basu ba. Tabbas Amir muna yi maka murna, kuma wannan ya saka ka kuma zama da a gareni sosai fiye da yadda kake a da saboda dan Hussain tabbas da na ne. Amma kuma muna jimamin rabuwa da kai a gidan nan, dan munsan dole zaka koma gurin mahaifan ka, sai dai kuma munsan zumunci a tsakanin mu yanzu ne ma aka fara shi insha Allah". Basu dawo Kaduna ba sai dare, kuma tun a hanya Hussain wanda shi Hassan ya dora wa bauyin shirye shiryen tafiya Dubai ya tabbatar musu da shirin yayi nisa tunda yasan wani a embassy wanda ya taimaka masa sosai gurin samar musu visas, siyan tickets kawai ya rage musu sai kuma shiri. Wannan ya sa washegari suka tashi da shiri, kowa yana haka kayansa manyansu da yaransu. Amir kam ji yaje kamar ya jawo jibi ta dawo gobe wanda shine ranar da jirgin su zai tashi. Ya kosa ya ga mahaifiyar sa, ya kuma kosa yaga Suna cikin shirye shiryen ne kuma sai mota guda na yanuwan Fatima daga kano dan tun ranar da Amir yazo gida aka gaya musu aka kuma roke su akan kar su gaya wa Fatima su bari yaje har can ya same ta. "Ba zamu iya jira ba, gwara mu zo mu ganshi dan ba lallai bane in Fatimah ta ganshi ta kuma barinsa ya dawo Nigeria" A ranar sake wuni akayi gidan a cike da mutane. Amir kuma ya wuni yana karbar gata ta ko'ina. Sai kuma Amir ya bawa kamfanin Moon Construction kwangilar renovating gidansa kafin ya dawo daga Dubai. Kwana biyu bayan nan suka tashi zuwa UAE bayan Hassan ya kira Adam ya ya masa cewa gasu nan zuwa surprise visit, har Adam din yake masa dariya cewa tunda ta riga ya fada kuma ai ya tashi daga surprise. Sai kuma ya gaya wa Fatima labarin zuwan bakin nasu, nan da nan ita da yammatan ta suka tashi suka fara shirin taryar baki. Sai kuma ga Fatiman Hussain ita ma tazo zasu yi aikin tare, amma fatima a jikinta sai take jin zuwan nasu Hassan yana da dangantaka da wayoyin da take ta receiving kwanan nan daga yanuwanta, kuma kowa sai ya tambaye ta sunyi waya da Hassan? Ko kuma dai wata tambaya data danganci yanuwan Hussain. Ita ji take ma kamar bata da lafiya, wani irin feeling mai wuyar fassara. A ranta sai take kwatanta feeling din da irin wanda taji ranar da Hussain ya tafi Abuja, ranar da tayi sallama dashi sallama kuma ta har abada, ranar da tayi sallama da abinda yake cikin ta. Duk da cewa duk tsahon shekarun nan bata mantawa da wannan ranar ba, bata taba kuma daina kokarin tunowa da abinda ya faru a ranar ba, amma abinda take ji a cikin kwana biyun nan yafi wanda take ji da, har ji take yi a kunnenta kamar ana kiranta a waje kuma da irin muryar Hussain sai ta duba sai taga babu kowa. Ga kuma Hussain karami daya tafi Nigeria yayi zamansa, ta lura kuma duk sanda suka yi waya kamar yana boye mata wani abu ne sannan kuma lokuta da dama takan ji shi kamar a cikin mutane, kamar ana hayaniya haka. Farko tayi tunanin ko jikin mahaifiyar sa ne yayi tsanani shi yasa yake zaune gurinta kuma bai gaya mata ba saboda basa maganar ta ita da shi, sai kuma daga baya ta lura babu damuwa a muryarsa, duk da tasan babu shakuwa tsakanin sa da mahaifiyar sa amma ta san ya damu da wellbeing dinta. Wannan, coupled with wayar da ake tayi mata daga gida ya saka ta zama kamar marar lafiya. Dan haka ranar ma kasa aikin tayi sai ta barwa su Islam suyi aikin ita kuma ta koma daki ta kwanta ta lulluba. A haka Adam ya shigo ya same ta, ya yaye rufar yana taba wuyanta yace "what's wrong?" Ta bude ido tana kallon sa tace "bana jin dadi" yace "menene yake damunki?" Tace "nima ban sani ba, kawai dai bana jin dadin jikina da kuma zuciyata" ya kama ta ya tayar da ita zaune, im da sabo ya saba da wadannan mood swings din nata kuma sam basa damunsa saboda shi yafi kowa sanin what she went through. Yace "kina so muje asibiti ne?" Ta girgiza kai tana jin kamar hawaye zai zubo mata. Yace "ko zuwan bakin nan ne ba kya so?" Ta sake girgiza kai duk da tasan abinda take ji din yana da dangantaka da zuwan nasu. Amma ta yaya zata ce bata son su zo gidanta bayan sun dauko hanya tun daga wata uwa duniya sun taho domin ita. Ta danyi murmushi, dole ta taushi zuciyarta ta karbe su ko da kuwa zuwan nasu zai tayar mata da tabon da yake cikin zuciyarta. Tace "inaso su zo mana, sosai. Zan dan kwanta ne kawai watakila kafin su karaso in danji dadin jikina sai in ji dadin karbar su" ya gyada kai yace "hakan yayi, ki kwanta ni sai mu tafi da Muhammad mu taho dasu". Sai da ya tabbatar babu sauran wani abu da ake bukata a gidan sannan airport tare da dan autan sa Muhammad wanda yake fifteen years a lokacin kuma yake carbon copy na babansa har gayun. Basu wani dade suna jira ba tunda yayi timing zuwan nasu sai gasu sun karaso. Sai da yaga suna fitowa daya bayan daya sannan ya tabbatar da gaske suke da yawansu suka taho dan family din Hassan gabakidaya Sumayya ce kadai babu sai matar Yusuf amma har matar Aminu da akwai da kuma yayansu duka. Sai kuma kuma kannen Hassan tun daga kan Hassana har kan Zulaihat, sai dai su duk basu taho da yara ba tunda yaran duk an girma. Babu Aunty kuma, girma ba zai barta tayi tafiya irin wannan ba. A take Adam ya fara mental calculation na gurin da zai sauke su dan yana ganin gidan sa yayi musu kadan, ya yanke shawarar sai dai ya kama musu hotel sai mazan su sauka a can matan kuma wasu gidan sa wasu kuma gidan Hussain. Saboda yawansu ya saka ya kasa fahimtar akwai bakuwar fuskar da bai sani ba, ya fara yin hannu da su daya bayan daya fuskarsa da faffadan murmushi da kuma Muhammad a gefen sa yana gaishe da duk wanda yaga babansa ya gaisar, har yazo kan Amir. Ya mika masa hannu sai Amir yaki bashi hannu ya rissina zai gaishe shi yana jin girmansa a zuciyarsa. Sai a lokacin Adam din ya kalli Amir sosai sannan yayi sauri ya dago kai suka hada ido da Hussain da yake kusa da Amir din da alamar tambaya a idon Adam, sai Hussain ya gyada masa kai yace "Amir sunansa. Abdullahi Hussain Aminu Abdullahi". Adam ya saki key din hannun sa harshen sa yana sarkewa, kwakwalwar sa ta dauke ballantana bakin sa ya samu kalmomin da zai furta dan ya rasa wacce kalma ce ta dace ya fada din, sai ya tuno da ubangiji, ya tuna cewa babu abinda ya gagare shi sai ya fahimci kalmar da zai yi amfani da ita ita ce tasbihi ga ubangiji dan iyawarsa ce kadai iyawa babu wani wanda ya iya sai dai shi ya iya wa mutum. "Subhanallah. Hasbiyallahu wa nieemal wakeel. Lallai tsarki ya tabbata ga Ubangiji mai yin yadda yaso a sanda yaso ga kuma wanda yaso" sai yanzu ya fahimci dalilin wannan ziyara da da ya dauka ta sada zumunci ce, ashe tsuntsu biyu ne aka jefa da dutse daya. "Amir!" Ya fada yana rike kafadunsa yana kallon fuskar sa. Bashi da tantama kamar yadda babu bukatar ta sake tambaya dan yasan wannan dan oga Hussain ne. Sai ya rungume shi yana tuno da mahaufinsa da kuma tarin kyautatawar sa gare shi, sai yaji kaunar da yake yiwa Hussain a duk shekarun can na baya ta dawo ta sauka akan dansa, sannan kuma ga matsayin sa na dan Fatima Zahra, tauraruwar da take haske zuciya da gangar jiki sa har yanzu bata dusashe ba. Ya sake shi ya juya yana kallon Muhammad yace "Muhammad kaga brother dinka, brother dinku da muka ce ba'a san inda yake ba shekara da shekaru ka ganshi ya dawo gare mu" ya fada yana hada hannyensu a guri daya. Amir yana kallon Muhammad kamar yadda shima yake kallon sa cike da shock, shi dai bai taba tunanin yana da kani ba, ballantana as cute as this one. Sai a lokacin Adam ya fahimci dalilin Hassan na boye maganar dawowar Amir ga Fatima, gar yanzu ba lafiya ce ta ishe ta ba da taji maganar da yanzu anxiety yayi mata yawa, da Allah kadai yasan yadda zata yi spending days din nan kafin suzo. Duk da haka sai ya nemi alfarmar Hassan cewa zasu yi gaba daga shi sai Amir, su kuma in sun gama karbar kaya sai su biyo su a baya tare da Hussain. Ya fi son sanda Fatima zata ga danta ya kasance babu hayaniya abin zai zo mata a nutse. Su biyu kadai suka shiga motar sa suna tafiya, yana ta so yayi wa Amir hira amma ya rasa abin cewa sai Amir yace " how is she?" Adam ya dan kalle shi yana concentrating a tukin sa yace "okay. She is okay. But she has never been her best tun ranar da aka rabata da kai. Har yanzu da akwai rami a zuciyarta wanda ni da yayana duk bamu iya mun cike mata shi ba" ya danyi shiru sannan ya cigaba da cewa "yanzu ma da zan fito a kwance na barta bata jin dadi kuma nasan zuwan su oga Hassan ne ya tayar mata da hankali ta san sai sun taso mata da mikin rashin ka a tare da ita. Har yau in dai tayi sallah sai tayi addu'ar in dai kana raye Allah ya nuna mata kai, kuma sai tayi addu'ar Allah ya saka muku akan wanda ya raba ku" sai Amir ta tuno da fuskar Ruqayyah. Tabbas addu'ar uwar da aka rabata da danta tsahon shekara talatin da biyar zata mayar da mutum haka ko ma fiye da haka. But with him back, yasan adduar mahaifiyarsa zata tsaya kuma hopefully suffering din Ruqayyah zai ragu. Sai yaji a ransa yana tunanin ko da akwai wamda ya taba zalunta? Tabbas in dai ka zalinci mutane kuma ba wai cikin rashin sami ba to kayi gaggawar zuwa neman yafiyar su dan ko basu daga hannu sunyi maka addu'a ba kamar yadda Fatima take yi to tabbas hakkin su yana nan yana binka har cikin kabarin ba. Har suka isa gida babu su Hassan babu labarin su, kuma Adam ya tabbatar zasu dauki lokaci a can din dan suna da yawa, kafin su gama hada kayan su ma aikine sannan sai sun nemi karin motocin da zasu kawo su gidan, but in ya gama da Fatima zai koma ya rago wadansu. Ya shigo da Amir har cikin palo, yana jin hayaniyar yan matan gidan a dining section amma baya son su zo suma suyi hayaniya. Sai ya dakatar da Amir a palo shi kuma ya shiga corridor din da zai sada ka da Bedroom dinsu. Zuciyarsa fal da farin ciki, yana jin dadi sosai daya kasance shine zai numa wa Fatima danta. A yadda ya barta a haka ya same ta. A bude rufar da tayi yana murmushi. Ta bude idonta a hankali tana jin bata ji dadin dawowarsu da wuri ba dan har yanzu bata jin dadi sai ma faduwar gabanta data karu. Sai dai yanayin da taga fuskarsa a saka ta mike zaune da sauri. Ya kama hannun ta ya mikar da ita tsaye yana murmushi mai hade da dariya yace "Fatima Zahra, gaya min, duk duniya menene burinki" taji hawaye yana bin fuskarta tace "ka sani ai, kafi kowa sanin burina a duniya. In dai yana da rai ina son ganinsa" sai ya ja ta kirjinsa ya rungume ta a hankali yace "Allah ya karbi addu'ar mu Zahra, ya dawo mana dashi" ta ture shi tana kallon sa dan bata tabbatar da abinda yake cewa ba, sai ya gyada mata kai yace "shi su Hassan suka taho kawo wa. Allah ya bayyana mana shi Zahra" Tayi sauri ta kalli hanyar waje, sai taji yace "he is waiting for you" Bata kuma jiran sauran wata magana ba, bata kuma san sanda ta fita daga dakin ta fita daga corridor din ba sai ganinta tayi a palo a tsaye tana mayar da numfashi da sauri tana zagaye palon da idonta. Sai idonta ya sauka a kansa, yana tsaye ya juya mata bayansa yana kallon family picture dinsu da yake rataye a palon, ita da Adam, Islam, Iman, Ilham da Muhammad. Yana yin tsayuwarsa sak na babansa, yanayin zubin bayansa sak na babansa sai tsaho da bai kai babansa ba. Bata san da wanne suna zata kira shi ya juyo ba saboda bata san sunan sa ba, a matsayin ta na mutum da yafi kowa kusanci da shi a duniya amma bata san sunanshi ba, sai kawai ta saki kukan da take ta rikewa, ya juyo da sauri yana sauke jan idonsa akanta. Ta tafi kamar zata fadi, "mother" ya fada da sauri tare da zuwa ya tare ta ta fado jikinsa sannan suka fada kan kujera tare, ta bude ido ta sauke a kansa tana kare wa fuskarsa kallo tace "you are here" yace "yes mother, I am here". Duk abinda Amir yayi ta mafarkin yadda haduwarsa da mahaifiyar sa zata kasance to abinda ya faru ya wuce nan saboda Fatima ta wuce duk yadda yake kwatanta mahaifiyarsa zata kasance. Haka beautiful beautiful sisters dinsa da little brother dinsa. Haka suka zagaye shi duka makalkale shi ta koina suka hana shi ko motsin kirki. Aysha kuwa da su Sultan nan da nan suka mayar dasu nasu ko ganin su ma bayayi, dan shi sai yaga ma Fatima kamar tafi son Aysha din ma akan sa dan suka zo tana daki a gurin ta shi kuma an barshi palo tare da sisters dinsa da suka hana kowa taba shi. Lissafin da Adam yayi na inda zasu zauna sai ya tashi a banza dan already tun kafin su taho Hussain ya kama musu wani apartment anan kusa da gidan sai yadda in suka hada da gidan sa ya ishe su, yayi hakan ne dan abar Amir yayi bonding da family dinsa ba tare da takurawa ba, kuma sai Adam ya amince da haka, dan haka gidan Amir kawai aka bari da family dinsa su kuma suka tafi can. Sanda bakin zasu tafi har da Amir a rakiya, ya dauki motar Fatima ya debi Amatullah, Suhaima matar Aminu yaranta da yaran Yusuf ya tafi dasu gidan Hussain bayan an saka masa address din a Google map, suna tafiya suna hirar kyawun garin har suka iso gidan a dai dai lokacin da sauran motocin ma suke karaso wa. Yana sane ya ja Amatullah da zance dan ya fahimci mai magana ce ita har saida sauran jama'ar motar suka fita sannan ta lura saura su kadai a gurin, ta fara neman jakarta zata fita sai ya dauke jakar ya dora akan cinyarsa. Ta bata rai "bani jaka ta" shima ya bata rai "sai kin tsaya na ga wani abu" tace "menene zaka gani a cikin jakar, ba'a bude jakar mata fa" ya danyi murmushi, "ba'a jakar ki zan gani ba, a fuskar ki zan gani" ta dan bata fuska cikin rashin fahimta tace "menene a fuskar tawa?" Yace "wai da gaske muna kama? Ni dai ba gani ba" tace "nima ban gani ba. Nafi ka kyau nesa ba kusa ba" yayi dariya tare da daga mata gira "Allah ko? To gaya min menene a fuska ta da bashi da kyau" sai ta juyo tana kare masa kallo har da karkata kai sannan tace "to ni dai ba gane kamannin ka nake sosai ba da wannan tarin gashin a fuska. Dama zaka aske ne watakila inga kamar tamu da ake fada. Ni a haka ma sai naga kana min kama da Davido" ya bude ido "what?" Sai ta kyalkyale da dariya, "wallahi kunyi kama sosai ma kuwa" sai ta bude motar da sauri ta fita sannan ta leko tayi masa gwalo. "Ka kaiwa matarka jakar na bar mata" Ya jima a zaune a motar yana murmushi sannan ya fita ya yi knocking gidan ya mika jakar ya koma mota ya koma gidan Adam. A palon ya tarar da Islam ya zunduma Sultan a cinya tana bashi abinci a baki, yace "wannan katon yaron kike dorawa a chinya? Sai ya ji miki ciwo?" Tace "aiya, nawa yake ja ganshi fa bai fi in saka zani in goya shi ba" yana kallon Sultan har da kara narkewa wai shi ana shagwaba shi. Amir yayi dariya yace "zaka yi bayani ne, kasan mamanka ba zata dauki wannan shirmen ba" sai ga maman nan kuwa ta fito tana masa murmushi ta zauna a hannun kujerar da yake zaune tana shafa cikinta tare da yin katuwar gyatsa. Yace "yayi miki kyau, wato an kaiki daki an cika miki ciki kin manta da mijinki ko" ta zagaye hannun ta a wuyansa tace "ni na isa in manta da mijina? Duk abinda naci na ajiye maka ai, ka taho muje in baka" ta mike tana jan hannunsa zuwa dining. Tana cikin serving dinsa abinci sai ga Adam da Fatima sun shigo, sai kuma taji kunya ta juya zata tafi amma sai Amir ya riko hannun ta ya dawo da ita ta zauna a kujerar kusa da shi. Adam ya zauna a gefensa Fatima tana zuba masa abinci tace "Aysha matar kirki ce, matar rufin asiri ce, tayi mana abinda ba zamu taba mantawa ba, tayi mana abinda mata da yawa ba zasu iya ba" Amir yayi murmushi yana jin dadin an yabi matarsa, ita kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannunta. Yace "hakane, she gave me a home, a family and stability when I needed them the most. And I will never forget that" Sai Adam yace "naji oga Hassan yayi mentioning abuja's palace, but bamu san abinda ya faru a can din ba. Zaka iya bamu labarin yadda abin ya kasance?" Sai Amir ya basu labarin, labarin wahalhalun da yasha da kuma dadin da yaji, labarin ups da downs din da yayi ta samu a rayuwa har karshe kamar yadda ya bawa Hassan tare da sauran yan'uwa. Fatima tana ta kuka "ba zan taba yafewa Ruqayyah ba. Ko na yafe mata halin da ta saka ni a ciki ba zan iya yafe mata halin da ta saka ka a ciki ba. And Hussain will never forgive her too." Sai Amir ya dawo kujerar kusa da ita yace "have you seen her lately?" Ta girgiza kanta "ban ganta ba kuma bana son in ganta. Bana buƙatar ganinta har abada." Sai kuma ta juya da sauri tana kallon sa tace "kar dai so kake ka ce min ka yafe mata?" Ya girgiza kai yace "ban sami ba, ban san ko na yafe mata ko kuma a'a ba. Na san dai cewa abinda ya faru dani, rayuwar da nayi a baya duk kaddara tace haka Allah ya rubuta zai kasance dani ko da ita ko babu ita kuma sai hakan ya same ni. Allah bai yi xan rayi a tare da iyaye na ba, ita din kawai sila ce ta kasance war hakan, kuma nasan ko da babu ita dole za'a haife ni a gurin kuma a barni, maybe wani ya tsince ni ya kaini gidan marayu, maybe kuma wani ne daban zai sace ni saboda wata a kida ta daban ya kaini can, maybe kuma in bata da kaina in na fara wayo a tsince ni a kaini can, whatever the case dole sai ya rayu a can, wannan shine kaddara ta. Kuma ni bana regretting rayuwar da nayi a baya mommy, saboda it is what made me who I am today. Badan nayi waccan rayuwar ba da ba lallai ne in hadu da amazing mutanen dana hadu dasu ba" ya karada yana kallon Aysha ita kuma ta sunkuyar da kanta kasa. Adam yace "amma naji dadin maganar ka Amir, tabbas you are your father's son dan kalaman ka sai naji tamkar shine yake furta su" Amir yayi murmushi yace "nagode" sai kuma ya juya gurin Fatima ya rike hannunta a cikin nasa yace "mommy, abinda ya faru dani kaddara ta ce, ke kuma a gurin ki jarabawa ce" sai ta dago kai da sauri tana kallon sa tare da tuna cewa Hussain ya taba fada mata magana exactly irin wannan. Sai kawai ta dora kanta a kafadar sa tana kuka. Ya fahimci ita saurin kuka ne da ita kuma ya fahimci cewa hakan yana da alaka da halin da ta shiga a baya, a saboda rashinsa da kuma rashin Mahaifin sa. Sai ya dora hannunsa a kafadar ta yace "it is over mommy. I am here". Sati daya Hassan da family suka yi a Dubai. Dama kuma duk sun shirya enjoying kansu a garin Dubai, mata sun ciko jakankunan su da niyyar shopping dan haka satin nan guda suna enjoying rayuwarsu sannan suka yi shirin komawa Nigeria amma Amir da family dinsa anan zasu bar su. A cikin satin kullum sai Amir ya dauki Aysha da kannensa sannan sun biya sun dauki Amatullah sai su tafi yawon bude ido. Islam ta tambaye shi dalilin da yasa suke zuwa daukan Amatullah bayan daga can ma suna fita sai yace "ita kadai ai ba zata ji dadin yawo a cikin maza ba" Iman tace "akwai mata ai, akwai aunties dinta da matan yayyenta" sai yace "sunyi mata girma" a dole suka rabu dashi. Kuma sai suka lura ita ma Amatullah din kamar tafi son fita dasu din tunda sune kusan sa'annin ta, sannan kuma gata yar gayu irin su da haa shopping interest dinsu yake zuwa kusan iri daya. Kullum kuma sai ta tsokani Amir akan gashin daya tara a fuskarsa. Har suma sisters din suka fara takura masa shi kuma yace tunda matarsa bata nuna ta damu ba ba zai aske ba. Sai ana gobe su Amatullah zasu koma Nigeria, sunzo gidan Fatimah gabakidaya zasu yi musu sallama sai ya dauke ta ita kadai yayi mata siyayya ta musamman yace tsaraba ce. Tayi godiya sai kuma yace "in zan taho me kike so in taho miki dashi kuma?" Tayi shiru tana kallon sa sannan tace "hmmm. Da dai zaka yi aski, maybe da ka burge ni" yayi murmushi, "shine abinda kike so kadai?" Tace "zaka yi ne?" Yace "in dai kina so zanyi" ta bude ido "Allah da gaske?" Yace "kin dauka wasa nake yi?" Tace "yaushe to zakayi?" Yace "yau. Gobe in nazo rakiyar ku zaki ga nayi" Sai kuma tace "babu ruwana, ban sani ba ko matar ka tafi son ganinka haka" yace "sai in aske rabi naki sai in bar mata rabi nata" sai suka yi dariya ta sake cewa "babu ruwana fa. Kayi zamanka da abinka" ta juya da sauri ta koma cikin gida gurin mutane. A ranar ne suna hira a cikin gidan Fatimah sai Safiyya take cewa "kamata yayi idan kun dawo Nigeria a shirya wata dinner haka ta musamman dan celebrating dawowar Amir" sai Adam yace "ni kuma sai nayi tunanin ba dinner ya kamata muyi ba, Umrah ya kamata mu shirya muje kamar yadda muka je lokacin rashin lafiyar oga Hussain muyi godiya ga Allah sannan kuma muyi wa Hussain addu'a kamar yadda muka yi masa a wancan lokacin" sai duk suka amince da wannan shawarar. Bayan sun tafi da dare sai Amir ya dauko diary din Hussain ya nunawa Fatima "kin tuna wannan?" Ta rufe baki da mamaki tana kallon diary din, a take kuma idonta ya kawo kwalla, ta karba tana jujjuya shi Amir kuma yana kallon ta yana murmushi, tace "yayi min alkawarin cewa zaka karanta min abinda yake ciki watarana" sai ya karba yace "to ga ranar tazo. Are you ready?" Sai sisters dinsa ma duk suka taho suka jeru, ya bude page din farko, wanda shine page din daya iya budewa har yau ya fara karantawa Dear baby.... Sai duk suka kwashe da dariya har da Aysha da Sultan saboda sun fahimci shine babyn, ya bata rai "an fasa karantawa ma tunda dariya zakuyi min" sai ya mayar da kayansa cikin aljihu, dama ba niyyar karanta wa yayi ba dan har yanzu he is not emotionally ready. Sai da suka gama dariyar sannan ya mike yace "mommy zan fita, zanje ayi min gyaran fuska" Ilham tace "ahh, finally". Fatima tace "da kafi kyau kuwa idan kayi" ya shafa fuskarsa yace "tunda kina so yanzu zanje inyi" ya juya ya fita Aysha kuma ta bishi da kallo. Sai da ya je gurin askin sannan ya kira Amatullah. "Duk gashin fuskar kike so a cire ko kuma kina so a gyara shine irin na 2pac?" Tayi dariya "a tambayi yaya Aysha, duk abinda take so shi zaka yi" yace "ai na gaya miki bari daya ne nata daya barin naki, yanzu side dinki nake tambayar me kike so ayi" sai tayi shiru kamar mai tunani sannan tace "duk sides biyun nata ne, ni dai babu ruwana" sai ta kashe wayarta. Sai kuma ya nemi number din Aysha ya kira "Finally dai burinki ya cika zanyi gyaran fuska" tace "burina ko burinta? Tun yaushe nayi ta nacin ka gyara kaki har na hakura na daina magana, sai yanzu kuma?" Yace "yanzun ai mommy ce tace....." Tace "babu ruwan mommy fa, dama kayi niyya tun kafin mommy tayi magana" sai ta kashe wayarta itama. Ya zauna hannu ruje da yawa ya rasa me zaiyi sai kuma yayi tsaki ya fita ya shiga shagon askin. Sanda ta fito ba zaka dauka shine wanda ya shiga ba, shi kansa yasan yayi kyau ba kadan ba. Compliments din kuma da ya samu daga mommyn sa da kannensa shi ya kara tabbatar masa da cewa yayi kyau, hatta Aysha da take fushi sai data sauko dan kanta kuma ta yaba tace yayi kyau har ta bashi tukuici a dakin da aka sauke shi. Washegari suka tafi rakiya. Kowa ya ganshi sai ya yaba da kyan da yayi amma Amatullah sai ta nuna kamar bata gani ba. Shi kuma ya kasa daurewa yayi ta binta wai sai tace yayi kyau ita kuma taki fada a karshe ma sai ta gudu ta buya inda ba zai ganta ba har sai da aka kira jirginsu, yana ta sallama da mutane yana tambayarsu ina Amaty, kusan kowa a gurin sai da ya fahimci halin da yake ciki yayin da ita kuma Amaty din ta rufe fuskarta ta shige cikin mutane ta wuce ba tare da ya ganta ba. Bayan sun tafi ya dauko Aysha suna dawowa gida yana ta kokarin yi mata hira ita kuma ta cika tayi fam. Sai da ya gaji da zance shi kadai sannan ya tambaye ta "wai sweetheart nayi wani laifin ne?" Ta juyo da sauri tana kallonsa "sweetheart? Kake cemin sweetheart?" Ya bude ido "miji ya cewa matarsa sweetheart kuma ya zama laifi yanzu?" Tayi banza ta rabu dashi sai kuma tace "menene tsakanin ka da Amatullah?" Ya bude ido "Amaty? Menene kuwa hadi na da Amaty?" Tace "shine abinda na tambayeka ai yanzu. Ai ni ba makauniya bace ba kuma ba kurma bace ba na san duk abinda kake yi. So nake kayi admitting da bakin ka ka gaya min ka daina wasu kame kame da hanya hanya" Sai taga yayi murmushi, ranta ya kara baci tace "au dariya ma na baka ko? Dariya ma kake yi min ko?" Sai ta fara kuka, ya sauke motar gefen titi tare da kokarin rike hannunta amma taki yarda "babu abinda zaka ce min Amir, kar ma kayi kokarin yi min dadin baki ko kokarin kare kanka. Kawai ka bani amsa direct ka gaya min menene a zuciyar ka" yace "I don't know. Okay. I am not sure menene a zuciyata ballantana in gaya miki. Kuma ni bansan ranki zai baci har haka har kiyi kuka akan abinda ni kaina ban tabbatar ba ballantana in tabbatar wa da wani. Ni ba son Amatullah nake yi ba idan haka kike tunani" Yayi shiru yana kallon gefen titi sannan yace "I thought zan iya cika daya daga cikin unfulfilled dreams na mahaifina. Yana daga cikin burinsa cewa watarana a samu auratayya tsakanin yayansa dana Daddy. Ni kuma ni kadai ne dansa, Amatullah ce kadai yar Daddy. I just thought maybe zanyi wani abu da idan da zai gani zaiji dadi. Ba wai burina inyi abinda zai bata miki rai ba ne. Kuma ko a haka din ma banyi niyyar yin maganar yanzu ba saboda ke, saboda bana son abinda zai bata ranki. Kuma ko da nan gaban ne banyi niyyar yi ba sai da iznin ki, sai kin amince tukuna idan baki amince ba it will just be one of his dreams da basu cika ba. And from your reaction nasan ba zaki yarda din ba dan haka it is over before it even begins". Ya fada yana stirring motar zuwa kan titi. Sun danyi tafiya kadan tace masa "ba sonta kake yi ba?" Ya girgiza kansa "uhm uhm" tace "ba baka ita suka yi a gida ba?" Ya sake girgiza kai "uhm uhm. Babu wanda yayi min zancenta" sai tayi shiru tana kallon gaban ta. It will be selfish idan taki amince masa, and from all indications watarana sai Amir ya kara aure ko tana so ko bata so kuma bata san wacce zai kuma jajibomata ba. Yes Amatullah yar uwarsa ce amma in dai har ba hada su akayi ba aurensu ba zai nufin cewa yanuwansa basa sonta ba. Kuma in tayi la'akari da yadda tarihi ya nuna yadda akayi auren ita kanta maman Amatullah din sai ta fahimci cewa suna da kara sosai. But ba zata bashi amsa ba har sai tayi addu'a akan lamarin. Tabbas itama tana bukatar zuwa Umrah tana bukatar ta gaya wa Allah kuma ta nemi zabinsa. Sati biyu bayan nan suka tafi Umrah kamar yadda suka shirya, su su Amir suka tafi daga Dubai su kuma yan Nigeria suka tafi daga can. Wannan ƙaron har da Sumayya tare da Jamila matar Yusuf, an mayar da Ruqayyah gidan Aminu kuma abin mamaki sai Sumayya ta asu labarin cewa Ruqayyah ta fara samun lafiya, tana iya motsawa yanzu kuma tana iya rubuta abinda take so ta fada. Sunyi adduoi sosai musamman ga Hussain, sannan kuma sunyi wa kawunan su adduoi. Aysha ma tayi nata adduoin. Tana kuma lura da yadda Amir ya koma gidan jiya tunda ya kuma haduwa da Amatullah a can, duk da ta lura yarinyar tana ta share shi kuma da alama utatake yiwa alkunya dan ta sha kama shi suna waya suna dariya amma in a gaban tane sai Amatullah tayi kamar bata san abinda Amir yake yi ba. Ta kuma lura da yauwan su duk sunsan halin da suke ciki amma ko maganar babu wanda yake yi ba kuma su taba ko da kwatanta gaya mata magana akan hakan ba. A haka har suka gama two weeks din da suka je da niyyar yi, daga nan kuma Nigeria zasu dawo gabaki dayan su. Ana gobe zasu dawo ne sai Amir yaga Sumayya tare da gabaki daya ƴaƴan ta har Amatullah sun shirya zadu fita, ya tambaye su inda zasu je sai suka gaya masa zasu je suyi wa Ruqayyah dawafi ne da niyyar nema mata lafiya. "Watakila in tana da rabo sai ta warke, harta samu damar neman gafarar ku da kanta" sai Amir yayi murmushi yace "na yafe mata ni ai. Da fatan Allah zai duba wannan ya yafe min nima tarin nawa zunuban, dan ina dasu da yawa" Yasan wannan zai faranta ransu amma bai dauka farin cikin su zai kai wanda yaga suna yi ba. And he felt soo good inside and outside. Suna komawa Nigeria suka tarar an gama renovating gidan Amir, farko ya kai Aysha Maiduguri ta ga danginta sun yi murnar abinda ya faru, sannan ya debi kudade masu yawa ya bata tayi shirin tariya a sabon gidan su duk kuwa da cewa an saka komai a gidan sai yan abinda ba'a rasa ba wadanda suke ra'ayin ta ne. Ita kuma saita shirya musu walimar tariya a sabon gidan su, inda ta gayyaci kowa da kowa dangin uwa da uban Amir, jama'ar gidan sarkin Abuja, abokan arzikin da aka zauna tare a abuja da kuma nata yanuwan. Kowa kuma yazo sai yayi san barka. A lokacin ne kuma Fatima tayi masa kyautar rabin share dinta na H and H, rabin kuma ta bawa kannensa. Ma'ana shi yana da kaso 75% kenan yanzu, sauran kuma na kanensa ne. Bayan an watse daga taron ne kuma taje har gida gurin Aunty ta shigar mata da maganar tana nemawa Amir auren Amatullah. Maganar da tashin farko Aunty tace bata yarda da ita ba, Hassan ma kuma ana fada masa yace a'a, wannan ai cin fuska ne, sai dai kuma dagewar da tayi akan taji ta gani ta amince, da kuma shima Amir din da ya nuna yana so, suka kuma iyayen dama ransu yana son abin sai suka karba. Cikin lokaci kadan aka tsayar da magana, aka kuma saka rana kusa ba tare da bata lokaci ba duk da Amaty taso a barta ta kammala masters dinta da take kokarin kammalawa yanzu. Aka sha biki babu bata lokaci amarya ta tare a gidan angonta tare da uwargidan ta. Mu dai namu sai muce Allah ya sanya alkhairi ya kuma kade fitina. *Two year Later* Tsakar gidan cike yake da yara yan makarantar allo kowa da allo a hannun sa yana biya karatun da aka dora masa, wasu kuma suna gefe suna yin rubutu a nasu allon yayinda a can kan barandar da take gaban falon da zaka shiga cikin gidan malamar su ce a zaune tana ɗorawa wasu daga cikin su karatun. Tana kuma yiwa wadanda suka kawo mata rubutun su gyara. A lokacin ne mazan su biyu suka shigo gidan tare da sallama. Ta dago kai tana kallon su tare da murmushi, ta fara kokarin mikewa tana neman crutches dinta. Aminu ya karasa da sauri ya taimaka mata ta mike tana cewa "mutanen Abuja, an shigo gari kenan" yace "dazu na shigo, nazo naga babyn Amaty" suka nufi cikin falon tana cewa "Sumayya ta gaya min haihuwar, yau nake shirin da dare in na sallami dalibai in kira Yusuf ya kaini in gani jaririyar" suka shiga falon Yusuf ya biyo su a baya, Aminu ya zaunar da ita a kujera sannan duk suka durkusa suka gaisheta, ta amsa tana gyara hearing aid dinta tare da saka musu albarka tana kuma tambayarsu lafiyar iyalan su. Mai aikin ta ta zo ta kawo musu lemo da ruwa. Suka sha suna yi mata hirar abinda ya shafi iyalan su tana da murmushi, lokaci zuwa lokaci masu daukan karatun sukan leko tayi mudu gyara akan karatun su koma su cigaba da biyawa. A haka har suka gama sai Aminu ya dauko kudi masu yawa ya ajiye mata a gefenta "ko za'a bukaci wani abu wanda babu a gidan" sai tayi saurin girgiza kanta tare da dawo masa da su tace "ina da duk abinda nake bukata, ni a yanzu babu abinda bana son gani a rayuwata irin kudi, kudi masifa ne kudi bala'i ne" Yusuf yace "kudi Mama, bala'i ne idan aka neme su ta haram, amma kuma alkhairi ne idan aka same su ta halak kuma aka kashe su ta halak. Wannan kudin albashinsa ne, gumin sa ne dan haka halal dinsa ne" Ta sake girgiza kai. "Duk da haka dai. Ni suna bani tsoro sosai. Bani da burin sake rike su. Burina a yanzu shine inci in sha yadda zan samu damar gabatar da ibada ta kuma in koyar da dalibai na sannan in cigaba da neman gafarar Allah data wadanda soyayya kudi ta saka ni na zalunta. Bani da damar zuwa inda Fatima take amma ba zan gaji da aika mata da yan aiken neman yafiya ba har sai ranar da na bar duniya ko kuma ita ta bari ko kuma ranar da ta furta cewa ta yafe min" Ta karasa tana share hawayen idonta da hannunta da yake a karkace. "Babban abinda zanyi muku nasiha dashi shine ku gode Allah, duk abinda ya baku ku karba ku gode masa saboda shi yafi ku sanin abinda yake shine mai alkhairi a gare ku, a kullum kuma kar ku kalli wanda yake sama daku dan hakan ne yake kawo rashin godiyar Allah. Kullum ku ringa duba wanda yake kasanku wannan shi zai kara muku godiyar Allah a zuciyoyin ku" "Duk wanda bai godewa Allah ba to kuwa tabbas zai godewa azabarsa" Ni shaida ce akan wannan *********************†********* A gidan Amir, yana zaune a palonsa da diary dinsa a hannun sa. Aysha ta shigo da yar jaririyar Amaty a hannun ta wadda take ta tsala kuka ta dora masa akan cinyarsa tace "kaima ka dana, duk munyi iyayin mu taki yin shiru, ya ajire diary din a gefe ya daga babyn, "Fatima Zahra, waye ya taba min ke duk garin nan yanzu mu mai ruwa rana ni da shi" Amatullah ta shigo hannun ta rike da afnan ta zauna a gefensa tana hamma "wa ya tabata kuwa in banda rikici?" Sultan ya shigo ya zauna a gaban babansa yace "a cigaba da karanta mana diary din grandfa" Amir yace "yauwa dan albarka, itama Fatima abinda take so kenan, tana son jin kalmomin mijinta yanzu zakuga tayi shiru" Aysha ta zauna itama a daya side din nasa tace "to a karanta mana muji" sai ya bude page din da yake ya cigaba da karanta wa daga inda ya tsaya. Dear baby Duk rubutun da zan yi maka daga yanzu zai iya zama abu na karshe da zan gaya maka. Rayuwa ta kadai ta isa nasiha a gare ka akan cewa babu wani abu da yake da tabbas, lokaci ne kawai yake da tabbas sai dai mu bamu da tabbas din kaiwa zuwa lokacin, an rigaan kayyade wa kowa iya kacin adadin seconds da zai yi a duniya kuma duk yawan kudin daka tara, duk kyawun fuskarka, duk yawan masoyanka da makiyanka, duk martabar ka, duk yawan ibadarka da rokon Allahn da zana yi akan ya kara maka kwanaki a duniya ba zaka wuce wadannan seconds din ba. Kowanne dan Adam yana tafiya ne akan nasa lokacin, dan wani yayi kudi da wuri ya sayi katon gida da manyan motoci ya auri kyakykyawar mace yar nasaba ba lallai ne shine successful man a duniya ba, maybe shi kwanaki kadan aka kayyade masa da kuma arziki da yawa, wannan shi yasa yayi arziki da wuri dan ya cinye arzikin sa kafin lokacin sa ya cika. Wani kuma sai yayi ta neman kudin da karfin sa da kwakwalwar sa amma sai ya dauki dogon lokaci bai samu ba kuma zata iya yiwuwa shi mai tsahon rai ne, dan haka yake cin arzikin sa kadan kadan. Wani kuma a wahala zai fara kuma a wahala zai kare saboda tasa kaddarar kenan. Babu wanda yake sauri babu kuma wanda yake lakaki, kowa yana tafiya ne akan lokacin sa. Shi arziki ba komai bane ba illa wata hanya da ubangiji yake jarabtar bayinsa, sai ya baka kudi yaga abinda zaka yi dashi ko kuma ya hana ka yaga abinda zaka yi. Ida har ka nemi kudi ka samu to Allah ne ya baka, idan kuma baka samu ba to shine ya hanaka. Idan ka samu dama ka nemi kudi ta hanyar halak, idan zaka kashe su ka kashe su ta halak. Idan kana dashi ka taimaka wa wanda bashi dashi, idan baka dashi ka nemi na kanka ta hanyar halak kar ka zama mai matacciyar zuciya ko mai roko a gurin mutane. A duk lokacin da dama ta same ka tayin wani abu to kayi shi a lokacin kar ka jira sai wani lokaci, dan ba kai kake da lokacin ba. Duk abinda kaji kana son yi to kayi abinka, as long as bai sabawa ubangijin ka ba kuma ba zai zamanto cutarwa ga wani abin halitta ba ba to kayi abinka kar ka damu da abinda mutane zasu ce dan su mutane ba'a taba iya musu, in kabi ta tasu ba zaka yi achieving komai ba. Ka zauna da clean heart, kar ka nufi kowa da sharri kar kuma ka rike kowa a ranka, always think positive dan shi negativity yana huda zuciya ne ya kuma hana ka ganin alkhairi ko da yana gabanka Bana tunanin halin da zan barka saboda nasan na barka da best mother in the world da kuma best father in the world. Na san ko ban bar maka ko kwandala ba Hassan zai iya yin dako ya ciyar da kai. Dan haka indai a kan wannan ne bani da damuwa" *Alhamdulillah* *Alhamdulillah* *Alhamdulillah* Anan na kawo karshen wannan littafin mai taken TAGWAYE. Alkharin da na rubuta Allah ya hada mu a ladan ni da ku bakiɗaya. Kurakuran da suke ciki Allah ya yafe min ni da na rubuta da kuma ku da kuka karanta. Godiya mai tarin yawa da masoyan rubutu na a duk inda suke. Musamman wadanda Allah ya bawa ikon siyan wannan littafin, it really means a lot to me, Allah ya bar kauna. Zuwa ga wadanda suka fara biyana da niyyar zasu karasa kafin in gama littafin, na yafe muku sauran. Zuwa ga wadanda suka karanta littafin tagwaye ba tare da sun biya ba, na yafe muku, amma ku sani wannan ba shine hanyar nuna kaunar ku gare ni ba. Like I always say, it is not about the money, it is about loyalty. Zuwa ga wadanda suka sayi littafin nan bisa amana kuma suka fitar dashi zuwa groups. Ku da Allah. Sai mun hadu a sabon littafi na mai suna *Jidda* in Allah ya kai mu da rai da lafiya. Nagode. Taku har kullum. *Maman Maama* Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020